Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *😢DAREN AURENA💔* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *Daga alk'alamin 'yar mutanan zazzau Naanah M Sha'aban💖* _Labari mai tab'a zuciya😭_ _Wannan littafin sadaukarwa ne ga k'ungiyata da kuma jaruman cikinta💖_ *Wannan labarin k'irk'irarran labari ne ban yarda a juya min littafi na ta kowacce hanya ba😇* Shafi na 1 .............📖Kuka take tamkar ranta zai fita kwance take a kan d'an k'aramin gadon d'akin ta duk'unkune a cikin bargo ta rintse idonta zuciyarta nayi mata wani irin zafi da k'una cikin da sasshiyar muryarta ta fara magana "tabbas nayi dana sanin, sanin Jabir a rayuwata, ka cuceni, ka yaudareni bazan tab'a yafe maka ba har duniya ta nad'e, Insha...insha Allahu, Allah sai ya saka min abin da kayi min Kuma....." Sai Kuma ta kasa k'arasawa saboda irin kukan da ya shak'eta. Aunty Murja ce ta shigo d'akin da sallama d'auke a bakinta zuciyarta cike take da tausayin k'anwarta ta saboda Jabir yabar mata mugun tab'o Wanda bazan tab'a gogewa a cikin zuciyarta da ma rayuwarta gaba d'aya, yayi mata abinda ba za ta tab'a mantawa ba a daren aurensu. Zuwa tayi kusa da ita ta zauna tare da jawota jikinta suka k'ank'ame juna suna kuka, sun d'auki kusan mintuna biyar suna kukan Aunty Murja ta had'iye nata kukan domin ta samu ta rarrashi k'anwarta ta, Cikin muryar rarrashi ta fara magana "Khadijatullah nasan akwai zafi sosai a cikin zuciyarki, abin da Jabir yayi miki sai dai muce Allah ya saka miki domin kinsan mu ba wani arzik'i ne damu ba, barantana muce zamu kai shii k'ara kotu abi miki hakk'inki, Kuma ko min kai Jabir k'ara a zamanin nan na yanzu babu abinda za'ayi Masa saboda Yana da kud'i, Dan Allah Khadijatullah kiyi hakuri kinsan yawan kukan nan zai iya haifar miki da wata matsalar Ina tsoron kar in rasa ki kamar yadda muka rasa iyayanmu ke kad'ai nake kallo nake jin dad'i a cikin zuciyata" ta k'arasa maganar hawaye na zuba daga cikin idanuwanta. Khadijatullah ta d'auki kusan mintuna goma tana kok'arin tayi magana Amman kukan da take ya hanata tayi dakyar ta samu ta sassaita kanta ta fara magana cikin sark'ewar muryar "Aunty Murja nasan bakya son kina ganina a cikin irin wannan yanayin, Amman Aunty Murja Ina ga ba zan tab'a daina kuka ba, zuciyata ba zata tab'a daina min zafi ba, saboda yanzu mun d'aura k'awance da tashin hankali, Aunty Murja wallahi ina ga bak'in cikin Jabir ne zai kasheni" wani sabon kukan ne ya kwace Mata Aunty Murja ta k'ara rumgumeta sosai a jikinta, Khadijatullah ta d'auki kusan mintuna biyar tana kukan kafin ta cigaba da magana "Aunty Murja wallahi na tsani Aure kuma na tsani maza, wallahi da za'a bani dama da sai na kashe duk wani namijin da yake duniyar nan tabbas na yarda da maganar hausawa da suke cewa namiji ba d'an goyo bane duk yadda ka Kai ga goya shi wata rana sai yayi maka abin da ba kayi tunanin zai yi maka ba, Kuma idan kaga namiji a rana karka sake kace zaka jawosa inuwa idan kuwa ka jawosa wata rana kai zai tura cikin ranar, Aunty Murja namiji yayi min abinda har abada ba zan manta dashi ba a DAREN AURENA". Duk tana kuka take maganar zuciyarta na cigaba da yi mata zafi. Aunty Murja kuwa bata iya cewa komai ba, ta cigaba da rarrashin k'anwarta ta har ta samu baci b'arawo ya saceta hamdala Aunty Murja ta shiga yi a cikin zuciyarta domin ta samu yau Khadijatullah tayi bacci Wanda rabon da tayi bacci tun ranar DAREN AURENTA wanda yau kwana uku kenan. *'BANGAREN GIDANSU JABIR* Zaune yake a kan kujera wacce ake iya kwantar da ita a kwanta, a farfajiyar gidan ya saka shisha a gaba yana zuk'arta a hankali daga shi sai wani gajeran wando dan ko riga babu a jikinshi, fari ne tas wanda kana ganinshi za kasan balarabe ne, gashin kansa ya kwanta luf sai shek'i yake yi yana da manya_manyan idanuwa wad'anda farare ne tas, dogon hancinsa yayi matuk'ar dacewa da d'an k'aramin bakinsa, wayarsa wacce take gefensa ce ta shiga ruri hannunsa yasa ya d'auketa tare da duba screen d'in wayar ganin wanda yake kiran nashi *Teemarh namo* ya gani, wani gajeran murmushi yayi sannan cikin sanyayayyar muryarsa ya ce "yau akwai harka kenan" d'aga kiran yayi ba tare da ya ce komai ba, daga b'angaren Teemarh namo kuwa cikin shagwab'a ta fara yi magana "baby shine jiya ba ka zo club ba ina ta jiranka, kuma bayan kasan kwana biyu nayi missing d'inka sosai" ta k'arasa magana cikin nark'ar da murya, Jabir ya d'auki kusan mintuna biyar kafin ya ce "Am so sorry dear wallahi na d'an je wani guri ne kuma ban dawo da wuri ba". Cikin nuna tsantsar kishinta a fili ta ce "ina kaje? kodai kaje gurin wannan tsohuwar matar taka" wata iriyar dariya Jabir yayi wacce kana jii kasan ta tsantsar mugunta ce yana dariyar ya ce "haba dai ai wannan ta riga da tayi expired, please ki kwantar da hankalinki, ai yayinta ya riga da ya huce tuntuni" Murmushi teemarh namo tayi ta ce "to shikenan baby yanzu yau dai zaka zo ko? Kasan wallahi nayi missing d'inka sosai i miss your hug i miss you so so much" murmushi Jabir yayi ya ce "zan shigo da daddare yanzu ina d'an hutawa ne" yayi maganar kamar wanda ake yi masa dole "Ok to shikenan sai da daddaren ina nan ina jiranka" "Ok" yayi maganar a takaice. "i love you" "thanks you dear" Daga nan kowannan su ya ajiye wayarsa Jabir ya cigaba da zuk'ar shishar. *'BANGAREN KHADIJATULLAHI* Ta d'auki kusan awa d'aya tana bacci a jikin Aunty Murja dan ita ma har baccin ya d'auketa kamar an tsikareta ta farka a gigice, irin yadda ta farka ne yasa Aunty Murja ita ma ta tashi ta rikota "Khadijatullahi meya faru" Kallon Aunty Murja take hawaye na kok'arin zubowa daga idanuwanta "bakomai" tayi maganar cikin muryar kuka rumgumeta Aunty Murja tayi tana bubbuga mata bayanta tana cigaba da yi mata nasiha mai ratsa zuciya daga waje suka jii anyi sallama ana kok'arin shigowa d'akin "Assalamu alaikum" Mai shigowar ta fad'a tare da tura kofar d'akin ta shiga, Murmushi Aunty Murja ta sakar mata tare da amsa Mata sallamar "Wa'alaikissalam Amatullahi" "Ina wuni Aunty Murja" Amatullahi ta tsugunna har k'asa cikin ladabi tana gaisar da Aunty Murjan "Lafiya kalau ya kike" "Lafiya alhamdulillah" Sai kuma ta komar da dubanta kan Khadijatullah wacce tayi luf a jikin Aunty Murja. "K'awata ba dai har yanzu kuka kike yi ba, haba Khadijatullah dubi yadda fuskarki ta koma idanuwanki duk sunyi ciki_ciki saboda kuka ya kamata kisan cewa wannan k'addara ce Allah ubangiji ya d'ora Mana, Kuma dukkan musulmi ya kamata ya rumgumi duk iriyar k'addarar da tazo Masa Mai kyau ce ko akasin haka". Shuru kawai Khadijatullah tayi tana sauraronta tana sauke ajiyar zuciya idanuwanta na cigaba da zubar da hawaye, tabbas tasan su Aunty Murja ba zasu tab'a fahimtar irin tashin hankali, bala'i da masifar da take ciki ba, taya za'ayi a daketa Kuma a hanata kuka, bayan sun san irin cutar da Jabir yayi mata tana jin labarai a gidan t.v, kuma tana jin labarai iri_iri wad'anda maza suka yiwa matayensu na cin mutunci, Amman ita Bata tab'a jin labarin irin abin da Jabir yayi Mata a DAREN AURENSU ba, ta yaya za'ayi ta manta da wannan daren, wanda take kiransa da bak'in dare domin ita DAREN AURENTA ya kasance Daren bak'in cikinta, Wanda har yanzu take cikin bak'in ciki. Amatullahi ta saka hannunta a kan fuskar Khadijatullah tana goge Mata hawayenta,nan ita da Aunty Murja suka sakata a gaba suna yi Mata hira domin su samu ta hak'ura, ita dai kawai jinsu take Amman a wannan karon tayi kok'arin had'iye kukanta domin ta fahimci kukanta Yana jefa masoyannata guda biyu cikin tashin hankali, Aunty Murja ce ta tashi ta d'auko musu abincin da ta girka a wani d'an k'aramin kwanon silba, ta dawo gurin da take ta zauna tare da bud'e kwanon shimkafa da Mai da yaji ce, "Kash! na manta ban d'auko cokula ba" Amatullahi tayi murmushi "To Aunty Murja bari in d'auko miki" mik'ewa tayi ta nufi inda kwandon kwanukansu yake wanda babu wani kayan kirki a cikinsa, ta d'auko cokula guda biyu wad'anda kana ganinsu zaka san sunyi mugun dad'ewa domin har sun fara lank'washewa, zama tayi tare da mik'awa Aunty Murjan cokulan "Gashi Aunty Murja" cokali guda d'aya ta k'arb'a sannan ta ce "to matso sosai muci abincin" Da sauri Amatullahi ta girgiza kai domin abincin dake kwanon bama zai ishesu ita da Khadijatullah ba, saboda bashi da wani yawa "Kaii Aunty Murja Alhamdulillah wallahi sai da naci abinci sosai kafin in zo" sai kuma ta mik'awa Khadijatullah cokalin tana fad'ar "gashi nan kici abincin" girgiza kai ta shiga yi alamar bata cin abincin, cikin d'aurewar fuska Aunty Murja take magana "wato abin da kike son ki tsira kenan rashin cin abinci, ai shikenan tunda haka kika zab'ar wa kanki" sai kuma ta fashe da kuka, cikin tashin hankali Khadijatullah ta karb'i cokalin hannun Amatullahi "Aunty Murja Dan Allah ki dena kuka zan ci" ta fad'a tare da saka cokalin a cikin abincin, shuru Aunty Murja tayi ita ma ta shiga cin abincin loma biyar Khadijatullah tayi ta ajiye cokalin, ta zame ta kwanta a kan yaloluwar katifar da take kan gadon ta rufe Ido domin Bata so Aunty Murja ta k'ara takura Mata taci abinci, Aunty Murja ma Bata ce Mata komai ba, Amatullahi kuwa mik'ewa tayi tare da cewa "to Aunty Murja zan tafi". "Amatullahi yau tafiya da wuri haka" murmushi tayi ta ce "wallahi Aunty Murja zamu je Unguwa ne da Mama shine nace Bari inzo na ganku kafin mu tafi" Aunty Murja ta ce "Allah sarki Amatullahi to mun gode sosai" "Haba Aunty Murja bakomai ai" zagayawa tayi dai_dai saitin kan Khadijatullah ta shafa fuskar ta ta tana cewa "To k'awata sai na sake dawowa gobe idan yau min dawo da wuri zan k'ara dawowa na ganku" Kai kawai ta d'aga mata, Amatullahi ta k'ara yiwa Aunty Murja sai anjima sannan ta fita daga gidan da saurinta, Aunty Murja ta tashi ta shiga gyara d'akin daga nan ta dawo kan gadon ta kishim gid'a tana sauraron radio da ta kunna a wata matatciyar radio duk rayi raga_raga. *'BANGAREN GIDANSU JABIR* Shirye yake cikin wasu k'ananun kaya, kyau iya kyau ya gama yi, turarurrukan dake kan madubin d'akinsa wanda kamar shagon kanti saboda yawansu, ya shiga fasawa a duk jikinsa saboda duk yawan turaren nan sai da ya bisu d'aya bayan d'aya yana fesasu a jikinsa, wani d'an k'aramin kum ya d'auka k'irar dubai shi kanshi kum d'in abin tsayawa ka kalla ne, ya shiga taje kannasa da kum d'in a hankali tamkar wanda a kace dole sai ya taje kannasa, sai da ya d'auki kusan awa d'aya yana shiryawa, sannan ya nufi hanyar fita daga d'akin, ko kulle d'akin bai yi ba haka ya nufi b'angaren Mami Yana taku d'aya_d'aya kamar wanda yake tsoron tafiyar, a haka har ya isa part d'in Mami to sallama bai yi ba haka ya tura kai cikin falon nata a zaune ya tarar da ita tana kallon wani film a zee word, da sauri ya k'arasa kusa da ita ya rumgumeta tare da yi Mata kiss a kumatunta, Murmushi Mami tayi tare da shafa kansa "Wow my son you look so Masha Allah" Murmushi yayi tare da cewa "Thanks you Mum I really love you so much" Mami ta ce "Me too My son I love you so much" Mik'ewa tsaye yayi tare da cewa "Mami zan tafi club sai na dawo a chan zan kwana naga magriba tayi ana ta nema na akwai Abu Mai muhimmanci da zanyi me" yayi maganar cikin Yana yin shagwab'a "To sai ka dawo, Allah ya kaika lafiya, Amman goben ka dawo da wuri saboda Aliyu zai dawo daga dubai Kuma da wuri sai sauka" cikin yanayin farin ciki Jabir ya ce "Kaii d'an uwana Aliyu Ashe dai zan k'ara ganinsa kaii kamar ma kar inje club d'in saboda naga d'an uwana nayi ten year fa ban saka shi a idona ba". Murmushi Mami tayi "Ai sai gobe zai dawo kaga bai kamata kak'i zuwa club d'in ba saboda kace akwai abinda zakai Mai muhimmanci ai sai gobe zai dawo ai har ka dawo ma" cikin yanayin jin dad'i ya ce "please Mami karku je d'aukoshi har sai na dawo" wani k'ayatatcen murmushi tayi ta ce "karka damu zamu jiraka" wani irin tsalle yayi sannan ya nufi kofar fita daga falon Yana fad'ar "Yawwah Mami nagode sosai" da murmushi ta bishi sannan ta cigaba da kallonta hankalinta kwance, shi kuwa Jabir Yana fita kai tsaye wajen da aka tanada d'an ajiye motoci ya nufa, ya shiga sabuwar motar da Abbansu ya Aiko Masa da ita, Mai gadi ya bud'e Masa gate ya fita da gudu daga gidan bai zame ko ina ba sai club, ai kuwa Yana isa club d'in tun kafin ya fito daga mota aka saka Masa ihu, Yana fitowa daga cikin motar zee namo tazo da gudunta ta rumgumeshi tana yi Masa kiss ta ko ina a jikinsa, d'aukarta yayi cak dan Daman Shima a matse yake yazo club d'in ya huta da zee domin Yana jin dad'in yarinyar sosai hotel d'in club d'in ya nufa da ita, ana fa guri ya k'ara hau tsinewa da ihu, shi kuwa Jabir bai bii ta kansu ba domin burinsa kawai ya samu ya biya buk'atarsa da Zee d'in, d'akin da aka basa ya shiga, ya ajiye zee d'in a kan gado, ya cire mata kayan jikinta daman ba wani kayan k'irki bane a jikin nata rigar bacci ce wacce ko gwiwarta Bata Kai ba, Bata da hannu d'an haka ya zama duka rabin k'irjinta duk a waje suke, Anan ya shiga tsotsarta ta ko ina tamkar ya samu wata alewa, Zee abin nema ya samu dan haka ta sakar Masa dukkanin jikinta Yana tsotsarsa, Anan dai sukai ta shek'e ayarsu (ni kuwa 'yar mutanan zazzagawa nace Allah ya shiryeku Amin) sai wajen isha'i sannan ya sauka daga kan Zee d'in Amman ita Zee d'in sam Bata so haka ba, saboda bata gama dawowa dai_dai ba, toilet ya shiga da niyyar yin wanka, Zee ya mik'e ta shiga cikin toilet d'in, ta tarar da Jabir har ya fara yin wankan bayansa ta hau ta fara shafashi a hankali "Baby kasan fa baka gama dani ba, dan ni ban koshi ba". Jabir dai shuru yayi domin ya rasa masifa irin ta Zee kullum idan yayi sex da ita duk irin dad'ewar da zai yi a kanta sai tayi Masa korafin Bata koshi ba, janyota yayi ta dawo gabansa Yana kallonta tana kallonsa tana wurga Masa wani shu'umin murmushi. Jabir ya ce "Baby ki barni nayi wanka, zuwa anjima zamu had'u,karki manta fa muna tare yau gaba d'aya" yayi maganar cikin salonsa wanda yake rikita yammata, narke masa tayi a jikinsa ta lumshe ido bata k'ara magana ba, Jabir yayi² ta rabu dashi yayi wanka amman sam teemarh tak'i barinsa sai ma k'ara nanik'e masa da tayi, haka ya kyaleta ya shiga yin wankansa teemarh na jikinsa tamkar cingum ta mak'ale masa tana cigaba da shafa jikinsa. D'aga ta yayi suka fita daga cikin toilet d'in, a kan gado ya samu ya kwantar da ita, sannan ya shiga saka kayansa, ita dai teemarh da kallo take binsa idanuwanta sunyi jawur tana wani lumshesu tana lasar bakinta tamkar mayya tana k'ara zubawa surar jikin Jabir d'in ido, shi kuwa Jabir yana gama shiryawa ya dawo kan gadon yana shafa dukkanin jikin teemarh kuma ya tsotsarsa, haka dai sukai ta aikata Alfasha har kowannansu bacci yayi awan gaba dashi, basu suka tashi ba sai wajen k'arfe shida na safe, ko sallar asuba basuyi ba, haka suka tashi suka shiga wanka a tare, suka fito Jabir ya fara shiryawa da sauri saboda yana tsananin son ya ga d'an uwansa tunda Mami ta fad'a masa cewa yau d'in Aliyu zai dawo da kyar ya iya bacci saboda gani yake kamar idan yayi bacci bazai tashi da wuri ba, ita ma Teemarh shiryawa tayi cikin doguwar rigar baccinta, a tare suka fita daga d'akin Jabir ya rufe d'akin, suka nufi motar, A hanya ya sauke Teemarh domin kuwa baya son ya k'arasa wannan matatciyar unguwar tasu, ya ja motar da gudu bai tsaya a ko ina ba sai a gida, mai gadi ya wangale masa k'aton gate d'in gidan ya shiga da gudu har yana kok'arin yin ciki da mai gadin, Allah ya taimakeshi ya buga wani mugun tsalle sai da ya fad'i a k'asa har ya fasa goshi. Da saurinsa ya fito daga motar ya nufi hanyar da zata sadashi da tafkeken falon, yana shiga ya tarar su Mami da k'annansa guda biyu dukansu mata ne Shahida da Nihal, wad'anda baza su huce shakara sha bakwai ba, da gudu Nihal ta k'arasa gurinshi tana fad'ar "Yawwa bro daman kai muke ta jira yanzun nan Mami take kok'arin kiranka" murmushi yayi tare da rumgume k'anwar tasa "to darling sister ai gani nazo kawai mu juya muje mu d'aukoshi k'ar jirgin nasu ya sauka, bamu k'arasa ba" Mami tayi murmushi tare da cewa "Ai yau dai kam naga ana kok'arin mantawa dani, dukkanku kuna d'aukin ganin d'an uwanku" da sauri Jabir ya saki Nihal yaje ya rumgume Mamin "haba Maminmu taya zamu manta dake you are so speacial to us" haka su Nihal da Shahida ma duk suka rumgumeta, Murmushi take ta faman sakarwa 'ya'yannata, "Thanks you so much my darlings ina 'kaunarku sosai, yanzu dai muyi sauri mu k'arasa Airport kar Aliyu su sauka bamu k'arasa ba, tunda ya ce 7:00am zasu sauka, yanzu kuma 6:30am daga nan suka dunguma zuwa Airport mota d'aya kawai suka d'auka, k'arfe 7:00am suka isa filin jirgi dai-dai lokacin jirgin su Aliyu yana sauka, haka ya fito cikin takunsa na isa da k'asaita sai zuba kamshi yake yi, kaii masha Allah kyau iya kyau Aliyu yayi domin duk irin kyan Jabir, idan kaga Aliyu zaka san gaskiya Jabir ma mummuna ne, domin kuwa ya ninka Jabir a kyau sosai idan ka ganshi za ka yi tunanin wani balaraben ne, Nihal da Shahida suna ganinsa suka tafi da gudu suka rumgumeshi "We really miss you darling brother" Wani kayatatcen murmushinsa mai tsada ya sakar musu, cikin muryarsa wacce kamar wanda yake yin rad'a ya ce "Me too i really miss you" ana dai suka k'arasa gurin Mami ya rumgume ta tare da sumbatarta a kuncinta, "Mum i miss you so much", "me too i miss you my son" Jabir wanda yake tsaye ya hard'e hannunsa a kan k'irjinsa ya ce "Lallai yau ina ganin san kai" sai a sannan Aliyu ya lura ashe har da Jabir a kazo "Wayyo Allah na, Bro Jabir ashe har da kai aka zo" ya fad'a yana k'arasawa kusa dashi da niyyar ya rumgumeshi, Jabir yayi saurin ja da baya tare da hararar Aliyun "A'a banda ni aka zo saboda tsabar rainin hankali ma baka ganni ba, ni na kasa bacci ina ta son gari ya waye nazo na ganka shine zakai min izza" yayi maganar cikin jin haushin Aliyun "sorry brother kayi min afwa nayi laifi kasan fa kaii d'in jini na ne" Murmushi suka yi gaba d'aya tare da rumgume junansu daga nan suka shiga mota, domin tafiya gida. Suna zuwa Aliyu ya tarar da jerin abinci kala-kala a kan dining table, ai kuwa daman ya kwaso yanzu ya zauna, ya d'ebi fried rice wacce taji naman kaji ya shiga ci, suma duk suka zauna suna cin abincin suna yin hirarsu abin ban sha'awa. *BAYAN WATA BIYU* Amatullahi ce zaune a gaban Aunty Murja cikin nutsuwa Amatullah take magana "Aunty Murja daman nazo ne na nuna miki admission d'inmu na makarantar da muka samu" ta mik'a mata admission letter cikin nuna tsantsar farin cikinta mara misaltuwa Aunty Murja ta fara magana "Kai Alhamdulillahi masha Allah, Allah ubangiji ya tsareku ya baku sa'ar abin da zaku je nema" cikin jin dad'i Amatullahi ta amsa da "Amin ya rabbil'alamin" Aunty Murja ta ce "Amman wace makarantar ce? Kuma ke dawa kuka samu?" Wani kayatatcen murmushi Amatullahi tayi ta ce "Anan makarantar poly ta gadon k'aya, kuma ni da Khadijatullahi ne" ciki nuna mamaki Aunty Murja ta ce "wace Khadijatulla d'in?", Amatullahi ta nuna Khadijatullahi wacce take kwance tana jin duk abin da suka cewa, amman bata tanka musu ba, sai a wannan karon da taji k'awar ta ta, tazo musu da abin ban mamaki, da kyar ta samu ta mik'e idanuwanta na kan Amatullahi domin so take ta tabbatar da gaske take yi ko kuma wasa take musu, sannan ta ce "Aunty Murja wannan Khadijatullah d'in nake nufi, nayi hakan ne kuma domin na fahimci ta hakane kawai zamu samu ta rage tunani da koke-koken da tayi kullum ba dare ba rana, idan muna zuwa makaranta zata dinga samun sauk'in damuwarta" cikin zubar da hawaye Aunty Murja ta fara magana "Ni ban ma san da wane irin baki zan yi miki godiya ba, a gaskiya ke k'awa ce ta gari samun irin ki a wannan zamanin sai an tona domin zai yi wahala sosai mun gode mun gode sosai", hannu Amatullahi ta saka tana sharewa Aunty Murjan hawaye "Haba Aunty Murja menene na kuka ni na d'auke ku ne, tamkar 'yan uwana, dan haka komai nayi muku ku daina gode min dan Allah" Khadijatullahi ce ta rarrafo kusa da k'awar ta ta dakyar sannan ta kama hannayenta duka biyun tana kuka "nagode miki sosai, tabbas nasan kina sona sosai nagode sosai kuma....." aman da ya taho mata ne yasa ta kasa k'arasa maganar ta juya da niyyar ta shiga band'aki amman ina juyawarta kenan ta fara shek'a amai Aunty Murja da Amatullahi suka rik'eta, sai da ta gama shek'a aman sannan suka wanke mata jikinta inda ta b'ata suka kai ta kan gado ta kwanta, Amatullahi ta dawo ta gyara gurin da Khadijatullahin tayi aman sannan ta dawo ta zauna tana tambayar Aunty Murja "Aunty Murja bata da lafiya ne" Girgiza kai Aunty Murja tayi da alamun damuwa a kan fuskarta ta ce "Wallahi Amatullahi ban sani ba, dan bata ce min bata da lafiya ba" anan Amatullahi ta ce "to Aunty Murja mu tashi muje asibiti" da sauri Aunty Murja ta kalleta ta ce "haba Amatullahi ina nake da kud'in kai ta asibiti", "karki damu ni zan bada kud'in a dubata" haka suka samu suka d'aga ta da kyar akai sa'a kuwa suna fita suka sami mai adaidaita suka shiga sai asibitin nasarawa dake nan cikin garin kano, suna zuwa aka shigar da Khadijatullahi emargency domin duba lafiyarta sun d'auki kusan minti 40 suna jiran a fito a sanar dasu halin da Khadijatullah d'in take ciki, jin alamar da suka yi ana kok'arin bud'e kofar emargency room d'in ne yasa sukai saurin zuwa bakin kofar, doctor Halima ce ta fito tana ganinsu ta shiga sakar musu murmushi tare da cewa "ina tsananin taya ku murna, 'yar uwarku tana d'auke da ciki har tsawon wata biyu, kuma tana nan lafiya kalau dan yanzu na barta zaune tana hutawa, a yanzu ma zaku iya tafiya gida dan laulayi ne yasa tashiga cikin........" k'arar da suka ji an kwala ne ya katse doctor Halima k'arasa maganar da zata yi, juyawa sukai Khadijatullahi ce ta fad'i ta suma domin taji abinda doctor Halima ta fad'a Hankalinsu a tashe sukai kanta suna kiran sunanta "Khadijatullahi! Khadijatullahi!! Khadijatullahi" Amman ina bata ko motsi, haka doctor Halima ta shiga kiran nurses, suka zo da sauri suka ciccib'eta suka maida ita Emargency, Aunty Murja da Amatullahi suka koma gefe suka zabga tagumi fuskokinsu d'auke da tashin hankali mara misatuwa. Tun k'arfe hud'u da aka shigar da Khadijatullah Emargency room har k'arfe 8pm na dare, Babu Wanda ya fito daga Emargency d'in daga nurses d'in har doctor Halima,hakan yasa Aunty Murja da Amatullahi suka shiga cikin matsanancin tashin hankali suna tunanin kodai Khadijatullahi ta mutu ne. A b'angaren doctor Halima kuwa tunda suka shiga da Khadijatullahi suka shiga kok'arin ceto rayuwarta da ta d'an dake cikinta, yanayin Khadijatullahi ya tsananta domin numfashinta sai kok'arin d'aukewa yake yi, ga bugun zuciyarta sai bugawa yake da k'arfi tamkar ganga ake bugawa, gashi sai wata irin jijjiga take yi, sai da nurses kusan biyar suka rirrik'eta,hankalin doctor Halima ya tashi domin har ta fitar da ran rayuwar baiwar Allah, Anan take ta fara zubar da hawaye domin taga tashin hankali k'arara a fuskokin 'yan uwannata da suka kawota, yanzu idan aka ce ta mutu, ta san zasu shiga cikin mugun yanayi, anan take wani tunani yazo mata da sauri ta fita ta kofar baya office d'inta ta shiga taje ta had'o allurai ta dawo Emargency room d'in tayi mata, cikin ikon ubanjigi tana mata ko minti biyar ba'ayi ba, ta samu bacci, wata iriyar nannauyar ajiyar zuciya doctor Halima tayi tare da cewa "Alhamdulillahi Allah na gode maka" fita tayi domin ta koma office d'inta amman wannan karan ta kofar gaba ta fita, ai kuwa su Aunty Murja na ganinta sukai wajenta tare da wurga mata tambayoyi "doctor ya Khadijatullahi? Kodai ta mutu ne? Dan Allah ki sanar damu idan ta mutu" kamar had'in baki tambayoyin nasu suka zo dai-dai, "ku biyo ni office" tayi maganar a takaice, tare da yin gaba suka rufa mata baya da sauri, suna shiga doctor Halima ta huce kujerarta ta zauna, su kuma suka zauna a kujerar da ake ganin likita, bayan doctor Halima tayi d'an rubuce-rubucenta sannan ta d'ago tana yi musu bayani "A gaskiya 'yar uwarku tana cikin halin damuwa da kuma tsantsar tashin hankali, wanda a binciken da nayi na gano cewa ta dad'e a cikin wannan yanayin, kuma uwa uba wannan k'arar da ta suma ya k'ara sakata a cikin razana wanda har zuciyarta tana kok'arin bugawa, amman yanzu Allah ya taimaka mun shawo kan matsalar ta ta, amman in har zata cigaba da saka abu a ranta wanda har zai sakata ta dinga shiga damuwa to zata iya kamuwa da babbar matsala a zuciyarta kuma babyn cikinta zai iya samun matsala shima". Wata iriyar wahalalliyar ajiyar zuciya suka sauke, doin tunda doctor Halima ta fara magana suka kafeta da idanu sai da ta gama bayanin, Aunty Murja ce ta ce "to doctor mun gode sosai,Allah ya saka da alkhairi, kuma insha Allahu zamu yi iya bakin kok'arinmu ganin mun fitar da ita daga cikin halin damuwar da take ciki". Wata gajeriyar takadda ta mik'a musu Aunty Murja ta k'arb'a, doctor Halima ta ce "gashi nan magungunan da za'a siyo ne domin idan ta tashi sai a bata d'an ruwan tea ta sha ya d'an ratsata, sai ta sha maganin". Godiya suka k'ara yi mata sosai sannan suka tashi suka fita, Emargency room d'in suka nufa domin ganin yaya jikin Khadijatullah d'in, d'akin da aka kwantar da ita suka tambaya wata nurse ta nuna musu, suka shiga da sauri Amatullahi ta k'arasa kusa da ita ta kama hannuwanta sai ta fashe da kuka tana magana ciki tashin hankali mara misaltu "dan Allah Khadija ki tashi kin barni a cikin matsananci hali, Allah ya isa tsakanina da Jabir bazan taba yafe maka ba, kai ka jawo mana duk irin halin da muke ciki yanzu da muna cikin kwanciyar hankali amman yanzu ka tsarwatsa mana farin cikinmu insha Allah sai kayi mummunan k'arshe sai kayi mutuwar da ba za'a iya gane gawarka ba shege,d'an iska, azzalumi mara tausayi, mara imani" duk tana kuka take yin wad'annan maganganu, dafata Aunty Murja tayi ita ma tana hawayen "haba Amatullahi ki daina irin wad'annan furucin a kan Jabir, tabbas mun san ya zalinceta amman haka Allah ya riga ya k'addara mana kuma kin san komai muk'addari ne, kuma kowane bawa akwai irin tashi k'addarar ki yi hak'uri kinji k'anwata" ta k'arasa maganar tana bubbuga bayanta, Amatullahi kuwa ta riga ta gama kaiwa k'arshe tabbas da ace Jabir zai bayyana a yanzu zata iya k'asheshi domin ta ramawa k'awarta abin da yayi mata, kallon takardar hannun Aunty Murja tayi wacce doctor Halima ta bata ta magunguna "Aunty bani takardar nan zan siyo magungunan kafin Khadijatullah ta tashi tunda ance tana tashi a bata tea sai a bata maganin" babu musu Aunty Murja ta mik'a mata domin daman ta ba san indai zata samu kud'in siyo magungunan ba, tana kan tunanin ko taje ta ari kud'i sai kuma Amatullah ta ce ta bata zata siyo, tashi tayi daman hijabi ne har k'asa a jikinta ta ce "Aunty Murja sai na dawo" kafin Aunty Murjan ta bata amsa ta fita da sauri. Amatullahi kuwa tana fita bata zame ko ina ba sai bakin titi ta tari mai adaidaita tayi masa kwatancen inda zai kai ta, sun kai a kalla mintina 10 suna tafiya kafin su isa wani tafkeken gida, ta sauka ta biya mai adaidaitan kud'insa sannan ta d'auki wani k'aton dutse ta nufi gate d'in gidan cikin zafin nama take buga gate d'in gidan, cikin hanzari mai gadi ya nufo gate d'in yana jaraba yana bud'ewa Amatullahi ta bangajeshi ta shiga cikin gidan nan mai gadi ya biyota yana mata bala'i "ke baki da hankali ne kin shigo gidan mutanan kiyi maza ki fita ki yanzun nan nayi miki shegen duka" cikin zafin nama Amatullahi ta juyo ta d'auke mai gadin da wani wawan mari sannan ta cigaba da tafiya, duk da cewa bata san kan gidan ba, amman hakan bai bata damar tsayawa ba tayi tafiyar kusan mintuna 40 sannan ta hango wata kofar glass wacce da alama ita ce kofar shiga falon gidan nufar kofar tayi a kayi sa'a a bud'e take tana zuwa bakin kofar, ta bud'e da kanta, ta shiga ko sallama bata yi ba, hangosu tayi a chan falo gaba d'ayansu sun zauna suna kallon wani indian film, kawai taje ta tsaya a gurin tana yi musu wani irin wulak'antatcen kallo, su Mami da suke falo dukansu suka mik'e suna kallonta "ke kuma daga ina? Uban waye ya baki izinin shigowa har falon nan?" Nihal tayi maganar cikin jin tsiwa "Ubanki ne dan Uwanki" Amatullahi ta fad'a cikin zafin rai, sai kuma ta juya gurin Jabir "Dan ubanka, dan uwarka yarinyar sa ka wulak'anta ka tozarta yanzu tana da ciki dan haka ina fad'a maka da babbar murya kasan inda dare yayi maka domin kuma dole ka d'auki dawainiyarta" cikin mamaki da zafin jin zagin da tayi mata Jabir ya ce "ke kuma daga ina da har zaki zo har ciki gidanmu kina ci mana mutunci", "daga gurin uwarka" ta fad'a jikinta har rawa yake saboda bala'i Nihal ta nufota cikin tsiwa ta cakumeta, ai kuwa Amatullah ta cakumeta ita ma ta had'ata da bango, ta saki wata iriyar gigitatciyar k'ara, a rud'e Mami ta matso kusa da ita da niyyar ta cakumeta Aliyu ya rik'eta, sannan ya matsa kusa da Amatullahi wacce ta shak'e wuyan Nihal sai ihu take ya ce "ki yi hak'uri ki saketa muyi magana" sakinta tayi ta fad'i a k'asa tana rik'e da wuyanta, "ki zauna" Aliyu ya fad'a a takaice "ni ba zama ya kawo ni ba" ta bashi amsa fuskarta a murtuke, "na sani amman ki zauna domin muyi magana" zama tayi tare da hard'e hannayenta, Mami ta ce "kai Aliyu tayi mana irin wannan cin mutuncin amman ka dinga wani lallab'ata kamar kana jin tsoronta", "Mami dan Allah ki zauna, bai kamata ba hakan" yayi magana cikin sigar rarrashi zama suka yi gaba d'aya cike suke da jin haushin Aliyu, shima ya koma ya zauna sannan ya fara magana "baiwar Allah bai kamata ki shigo mana gida babu sanarwa kuma......." hannu Amatullahi ta d'aga masa tare da cewa "a fuskata kaga alamar nazo gidannan da niyyar mutunci, ai 'yan mutunci sune ake sanar dasu tun kafin azo gidansu, kuma wallahi ka ganni nan ba mutunci ne gareni ba, d'an uwanku ne ya sakani nazo har gidannan idan ba haka ba me zanzo nayi a wannan banzan gidan da har wani za'a ce sai na sanar, ina matuk'ar ganin mutuncinka da sai nayi maka abin da ba zaka tab'a mantawa dani ba", wani kayatatcen Murmushi Aliyu yayi ya ce "ki yi hak'uri amman ni ban gane me kike nufi ba, kin ce dan uwanmu ne ya saka ki, ki ka zo anan gidan me yayi miki haka", Amatullahi tayi masa wani matsiyacin kallo sannan ta ce"Ka tambayi d'an uwanka wannan Jabir d'in mai zumin shegu" ta fad'a tana nuna Jabir da yatsa, cikin rashin fahimta Aliyu ya ce "Bro me ya faru ne" domin shi Aliyu bai san Jabir yayi aure ba dan babu wanda ya fad'a masa, Jabir yayi wani gejeran murmushi sannan ya ce "ni da ban fahimci mai ya kawo ta gidannan ba, amman yanzu na fahimta wata yarinya ce wallahi da muka tab'a yin auren wucen gadi da ita a kan ta take magana", Amatullahi za ta yi magana Aliyu ya dakatar da ita ta hanyar cewa "dan Allah ki yi hak'uri duk da cewa ban san me ya faru a tsakaninku da Jabir ba, ina mai baki hak'uri ina zuwa" yayi maganar tare da tashi ya shiga d'akinsa bandir d'in kud'i ya d'auko tare da dawowa falon ya mik'a mata tare da cewa "gashi nan kuje kuyi amfani dashi", tashi tayi ta d'auki takardar da ta zurgawa Jabir a k'asa ta nufi kofar fita ko godiya ba tayi masa ba, haka tayi tafiya mai tsayi sannan ta kai bakin kofar gate d'in ta fita tayi sa'a kuwa tana fita sai ga mai adaidaita yana sauke wasu mata ta tsayar dashi ta shiga ta ce masa "Asibitin nasarawa zaka kai ni" mai adaidaita ya amsa mata da "to hajiya". A b'angaren Jabir kuwa Amatullahi na fita ya kalli Aliyu cikin jin haushinsa ya ce "Amman wallahi baka da hankali wato har da d'aukar kud'i ka bata" sai kuma ya ja tsaki, Mami kuwa mikewa tayi ta zabgawa Aliyu mari hagu da dama har sai da tayi masa sau bakwai sannan ta rufe shi da bala'i "Amman ban tab'a tunanin zaka iya yarda ayi wa 'yar uwarka rashin mutunci kana kallo ba tare da ka d'auki mataki ba kuma kana jii shashashar yarinyar nan har ni sai da ta zageni amman shine ka goyi da bayanta" Aliyu kuwa cikin jin haushin marin da Mamin tayi masa ya shige d'akinsa a fusace ba tare da ya ce komai ba, haka Mami ta matsa kusa da Nihal ta d'aga ta tare da cewa Shahida "Shahida dan Allah kamata ki kai ta d'akinta" ta ce "to Mami" haka ita ma Mami ta juya ta nufi d'akinta a ka bar Jabir shi kad'ai yana ta sake-sake a cikin zuciyarsa. Amatullahi kuwa suna isa Asibitin ta sallami mai adaidaita sannan ta nufi gurin da ake siyar da magunguna ta basu takardar suka mata total d'in kud'in magungunan gaba d'ayansu dubu ashirin 20k ta arga ta basu sannan ta nufi d'akin da aka kwantar da Khadijatullahi tana shiga ta tarar har ta tashi tana zaune, tayi sallama ta shiga, Aunty Murja ta amsa mata ta k'arasa ta zauna a bakin gadon tana yiwa Khadijatullahi sannu "sannu besty ya jikin naki" cikin muryar rad'a ta amsa mata "da sauk'i" Amatullahi ta bawa Aunty Murja ledar magungunan tare da ragowar kud'in, cike da mamaki Aunty Murja take kallo Amatullahi tare da wurga mata tambaya, "Amatullahi a ina kika samu wad'annan kud'ad'en masu yawa haka. Amatullahi ta ce. "Aunty Murja gidansu Jabir naje domin kuwa in sheda musu da cikin da ke jikin Khadijatullahi ba zai yi ace ga mari ga kuma tsinka jaka ba, dole su d'auki dawainiyyar babyn har ta haihu, anan ta fad'a musu duk yadda suka yi daga farko har k'arshe", Aunty Murja tayi shuru kawai tana kallon Amatullahi har ta gama yi musu bayani, sannan ta nisa ta ce "A gaskiya ban san da wane irin baki zan gode miki ba, ke d'in ta daban ce, amman daga yanzu karki k'ara zuwa gidan saboda kin san halin Jabir tantirin d'an iska ne, dan Allah kinji k'anwata k'arki k'ara zuwa tunda dai kin riga kin je kin sheda musu hakan ma yayi". "To Aunty Murja,ba zan sake zuwa gidan ba" tayi maganar cikin ladabi. kama hannun Khadijatullahi wacce hawaye sai ambaliya suke a fuskarta, ta shiga goge mata cikin muryar rarrashi ta fara magana "ki yi hak'uri kinji besty, bai kamata ki damu kan ki a kan wannan cikin ba, tunda dai ta hanyar aure kika same shi, nasan dai dole ki ji zafi da bak'in cikin samin cikin saboda irin abin da a kai miki A daren Aurenki". Da kallo kawai Khadijatullahi ta bi ta ba tare da ta ce mata komai ba, zamewa tayi ta kwanta a kan gadon ta rufe idonta zuciyarta na cigaba da k'una, Amatullahi ta kafeta da ido cike da tausayawa, har hawaye na kok'arin zubo mata, amman tayi saurin share hawayen dan kar Aunty Murja ta gani, jin Muryar Aunty Murja tayi tana cewa "Amatullahi ya kamata ki tafi gida tunda kin ga dare yayi k'arfe 9pm yanzu, in yaso gobe sai ki dawo" girgiza kai Amatullahi tayi tana cewa "A'a sam Aunty Murja ba zan iya tafiya gida ba, anan zan kwana dan Allah karki ce in tafi ko na tafi ba zan tab'a samun kwanciyar hankali ba", dafata Aunty Murja tayi cikin so da k'aunar yarinyar ta ce "Haba Amatullahi kina gani fa mun taho dake asibiti ba tare da kin je kin sanar a gida ba, kin ga bai kamata a ce kin kwana ba, kar hankalin iyayenki ya tashi basu san inda kike ba", "girgiza kai tayi a karo na biyu ta ce "waye zan damu idan bai ganni ba, Abbana ne kawai kuma baya gari yayi tafi ba yanzu zai dawo ba, kin san dai irin zaman da nake da step mother tunda Mamana ta mutu, ni yanzu ban da kowa daga Abbana sai kuma ku da nake ganinku tamkar 'yan uwana" ta k'arasa maganar cikin muryar kuka. Babu yadda Aunty Murja ta iya dole ta kyale Amatullahi domin ta kwana a gurinsu, Amatullahi ta zame ta kwanta, kanta na kusa da k'afafuwan Khadijatullahi ita kuma Aunty Murja daman tana zaune a kan kujerar roba dan haka ta k'ara gyara zamanta domin ta ji dad'in baccin, har sukai bacci idan Khadijatullahi biyu domin kuwa ita ba bacci take ba kawai rufe idonta tayi, tashi tayi zaune tare da d'aga hannayenta biyu sama hawaye na zuba daga idanuwanta ta fara jerowa Jabir mugayen Addu'o'i "ya Allah kaga abin da azzalumin bawanka yayi min, ya Allah na rok'eka kayi min muguwar sakayya, ya Allah kasa Jabir yayi mutuwar wulak'anci, ya Allah ka tarwatsa masa duk wani farin cikinsa ka maye gurin binsa da bakin ciki, bakin cikin da zai dauwama a cikinsa har izuwa ranar tashin alk'ima, ya Allah na rok'eka kafin Jabir ya mutu ka d'ora masa cutar da kowa zai dinga gurinsa ya zama abin k'yamata ga jama'a" sai kuma ta fashe da kuka mara sauti tare k'ank'ame jikinta guri d'aya, ta d'auki kusan mintina goma tana kuka bacci mai nauyi yayi awan gaba da ita. *B'ANGAREN GIDANSU JABIR* Kwance yayi a kan tafkeken gadonsa wanda mutane goma sha biyar ma zasu iya kwanciya ba tare da yayi musu kad'an ba, maganar da Amatullahi tayi masa ne ta tsaya masa take ta yawo a kunnansa "yarinyar da ka wulak'anka ka tozarta yanzu tana da ciki" bai san meyasa duk a maganganun da Amatullahi tayi masa ba wannan ta tsaye masa a rai, duk da cewa ba wai Khadijatullahi ce kawai ya tab'awa ciki ba, mata da yawa yayi musu ciki wad'anda ma bazai tab'a arga adadin su ba, amman wasu daga cikin matan su suke kawo kansu wasu kuma ta k'arfi yake yi musu, amman bai tab'a damuwa ba, amman gashi yau a kan cikin Khadijatullahi yayi matuk'ar damuwa har ya kasa yin bacci, wani dogon tsaki ya ja tare da cewa "koma dai menene bazan tab'a yarda cikina ne ba, domin ni bazan had'a zuri'a da 'yar gidan matsiyata ba" a haka dai ya rufe idanuwansa yana cigaba da saka abubuwa da yawa a ransa har bacci b'arawo yayi awan gaba dashi. *Wanene Jabir?* Jabir babban d'a ne ga Alhaji Mansur jikamshi wanda ya kasance shine minister mai fetur na k'asa nigeria, mahaifiyarsa hajiya Asiya 'yar wani malami ce wanda ya kasance yana koyar da almajirai karatu sun had'u ne ta sanadiyar mahaifinnata Malam kalla domin Alhaji Mansur idan ya samu lokaci yana shigowa unguwar tasu ya yiwa Malam kalla alheri da kuma almajiran da yake koyarwa, ranar nan yazo gurin Malam kalla sai ga Asiya ta fito daga cikin gidan sanye take da d'an k'aramin mayafi tsugunna har k'asa ta gaishesa cikin fara'a da sakin fuska ya amsa mata sannan ta fita zuwa aike da mahaifiyar ta tayi mata, haka ya tashi ya tafi gida tun daga ranar ya nemi nutsuwarsa ya rasa domin kuwa ya kamu da tsananin son Asiya da ya ga yana neman cutuwa dai haka ya shirya ya nufi unguwarsu Asiya domin ya sami babanta Malam kalla ya sheda masa abin da yake faruwa ya ji ko anyi mata miji. Yana isa kofar gidan Malam Kalla ya fito daga cikin motar kamar yadda ya saba yaje har cikin rumfar da Malam Kalla yake koyar da Almajirai karatu ya zauna bayan sun gaisa ne. Alhaji Mansur ya fara magana da cewa "daman Malam na ga 'yar wajen ka ce nace to bari in zo naji ko anyi mata miji ne, dan ni har ga Allah ina sonta da Aure ne a yanzu idan har ba'ayi mata miji ba ma zuwa nan da wata biyu ma nake son ayi biki" Alhaji Mansur yayi maganar cike da girmamawa, wani irin farin ciki ne ya kama Malam Kalla tabbas yayi matuk'ar farin cikin jin wannan furucin daga gurin Alhaji Mansur d'in domin kuwa Alhaji mansur mutum ne da kowane uba zai so ace 'yarsa ta aure sa" dan haka Malam Kalla ya fara magana cikin tsananin farin ciki "Alhamdulillahi Allah na gode maka a gaskiya Alhaji ba zan iya bayyana irin farin cikin da nake ciki ba domjn kuwa nasan kai d'in mutum ne na gari amman ban san wa ka gani ka ke so daga cikin yaran nawa ba?". Cikin jin dad'in yabon da Malam Kalla yayi masa ya ce "Wacce ta fito ranar da muke zaune ta gaisar da ni ta fita da mayafi", "Ohhhh Asiya kenan" Malam Kalla ya fad'a domin kuwa yasan kaf cikin 'ya'yansa ita kad'ai ce take saka mayafi sauran duka hijabi suke sakawa. "Eh ita nake nufi" Alhaji Mansur ya ce cikin Murmushin jin dad'i, Malam Kalla ya ce "A gaskiya Asiya ba'ayi mata miji ba, amman dai ban sani ba ko ita akwai wanda take so, ina son ka bani lokaci zuwa gobe domin in zauna da ita duk yadsa mukai da ita zaka ji insha Allahu". "To Malam insha Allahu goben zan dawo kamar dai-dai wannan lokacin", "To Allah ya kaimu" Malam Kalla ya fad'a da murmushi a kan fuskarsa, Alhaji Mansur bayan sun d'an yi hira sannan ya tashi ya ajiyewa Malam Kalla band'ir d'in kud'i ya rabawa almajirai kud'i sukai masa godiya ya tafi zuwa gidansa. Malam Kalla tunda Alhaji ya tafi ya zauna yayi shuru tabbas yayi matuk'ar farin ciki da har Alhaji Mansur ya ga d'iyarsa ya nuna yana sonta, Amman yaso ace daga d'aya daga cikin 'yan uwan Asiya ya gani ya ce yana so ba Asiya ba, domin Asiya sam bata dace da Alhaji Mansur ba, Macece mai girman kai da nuna isa bata ganin kowa da mutunci hatta shi da yake mahaifinta bata ganinsa da mutunci gashi uwa uba bata da kamun kai kwata-kwata, amman bazai so ace shi da kanshi ya aibata 'yarsa ta cikinsa ba, shiyasa bai nunawa Alhaji Mansur komai ba, kila idan Allah yayi ta sanadiyar Auren da zata yi ta shiryu ta dena duk abin da take yii, a haka dai ya yi ta tunane-tunanansa har a kai sallar magriba ya tashi ya nufi masallaci, anan idarwa ya dawo gida kai tsaye d'akin mahaifiyar Asiya ya nufa, zaune ya tarar da Asiya a kan 'yar yaloluwar taburmar d'akin tana taunar cingum tana danna waya, sallama yayi ya shiga d'akin amman Asiya ko d'agowa ta k'allesa ba tayi ba, baran tana ta amsa sallamar, sai mahaifiyar Asiyar ce wacce take tankad'an garin masara ta amsa sallamar tare da yi masa sannu da zuwa, ya amsa da yawwa sannan ya samu guri ya zauna, ya fara koro bayani. "Alhamdulillahi! Alhaji Mansur wanda yake zuwa gurina shine yau yazo min da maganar da ta sakani cikin farin ciki", cikin murna da farin ciki Inna ta ce "Wace magana ce wannan malam", "Wace yayi yana son Asiya zai aureta" ai kafin Malam Kalla ya k'arasa maganar Asiya ta mik'e tsaye cike da farin ciki, daman ta dad'e tana fatan Allah ubangiji ya mallaka mata Alhaji Mansur a matsayin mijinta domin kuwa tunda taga yana zuwa takanas yana yiwa mahaifinta alheri ta san ba k'aramin Attajiri bane shiyasa duk inda ta ganshi take tsugunawa har k'asa ta gaishe sa, gaba d'aya taji ta fara kyankyamin d'akin nasu ta fara magana cikin rashin girmamawa "Ai daman nasan zance yana sona domin na had'a dukkan abubuwan da ko shugaban k'asa ne ya ganni sai ya ce yana sona, daman na sha fad'a muku ni ba matar talakawa bace ai yanzu kun fara ganin gaskiyar al'amarin, kuma wannan gidan bai dace ace nii Asiya irin yadda nake da kyau ace ina zama a cikinsa ba, na de kusan na fita daga cikinsa na rabu da k'aya, ba zan sake gangancin k'ara shigowa ba". ta k'arasa maganar tare da fita daga gidan da sauri tana toshe hanci (ni kuwa 'yar mutanan zazzagawa nace daga baya kenan😂). Wani irin kuka Inna ta fara yi tana cewa "na shiga uku ni Indo ya ubangiji meyasa ka jarabceni da yarinyar da bata ganin mutuncinmu ni da mahaifinta", cikin muryar rarrashi Malam ya shiga bata hak'uri, har ya samu tayi shuru, Malam Kalla da Indo aure gida aka yi musu kasancewar iyayensu sun yaya da k'anine, tun daga ranar da ya aureta yake nuna mata soyayya har kawo yau da suka haifi 'ya'ya hud'u dashi kuma duka mata Asiya ce babba sai mai bi mata Hauwa,Hafsa, Hajara sai kuma k'aramarsu Na'ima, sam Malam Kalla baya k'aunar ganin bacin ran matar tashi ko kuma ganinta cikin damuwa shiyasa sam yake jin zafin 'yar tasu Asiya saboda kusan kullum sai ta saka Indo hawaye. 'bangaren Asiya kuwa tana fita kai tsaye bakin titi ta nufa ta tari mai adaidaita tayi masa kwatancen inda zai kai ta, a wani k'aton super market ya sauketa daman ta akwai ragowar kud'in da ta d'auka a jakar Inna naira 200 ta bashi ta nufi super market d'in, tana zuwa bakin kofar shiga super market d'in masu gadi suka hanata shiga, anan take ta k'ara jin haushin Mahaifiyarta da bata tsaya ta auri mai kud'i ba ta auri wannan matsiyacin Malamin, ta san yanzu da sun ganta da kaya mai tsada basu isa sun hanata shiga ba,amman kuma da ta tuna gurin wanda tazo kuma zata aura anan ba da dad'ewa ba, sai ta ji wani farin ciki ya lullub'eta, "Hmm da kun san wanda zan aura ba zaku tsayar dani,ku hanani shiga ba", d'aya daga cikin masu gadin ya ce "to mu ina ruwanmu da wanda zaki aura" Asiya ta bud'e baki zata yi magana kenan ta hango Alhaji Mansur ya nufo kofar fita daga super market d'in, cikin farin ciki da jin dad'in ganinshi ta shiga gyara mayafin dake jikinta, Alhaji Mansur yana fitowa idanuwansa suka sauka a kan masoyiyar tasa a nan take wani farin ciki ya lullub'esa "Asiya!" ya kirawo sunanta cikin wata iriyar murya,wacce take d'auke da wani irin salo, "Na'am Alhaji" tayi maganar cikin yauk'i da yanga, "Me kika zo yi anan" murmushi tayi tare da cewa "Bakomai" tayi maganar a takaice, "To shikenan muje in kai ki gida ko?" yayi maganar tare da yin gaba, ta bisa a baya kamar wata gela (ni kuwa 'yar mutanan zazzau naje Asiya ko kunya baki ji ba🤔). Bud'e mata gurin mai zaman banza yayi ta shiga da sauri sanyi A.C ya daki fuskarta ta lumshe ido, "Arzik'i dutse takashi ake ni dai kam na taka nawa" tayi maganar a cikin zuciyarta, Alhaji Mansur ya zagaya ya bud'e wajen driver ya shiga ya ja motar ya nufi gidansu Asiyan, sun d'an yi nisa sosai babu wanda ya kuma yin magana daga cikinsu, har sun kusan isa gidan Alhaji Mansur ya ce "Sarauniyar mata da fatan kin ji sakona gurin Malam" ta ce "Eh Alhaji na ji" tayi maganar tare da sunkuyar da kanta "to kin amince" wani kayatatcen murmushi tayi a zuciyarta ta ce "Anzo gurin, banda abin ka Alhaji wacce macen ce mai kud'i irin ka zai ce yana sonta ta k'i amincewa" a fili kuma ta gyad'a kai alamar "Eh". Alhaji Mansur ya ji dad'in amsar da ta bashi, suna isa gidan sun d'an dad'e suna hira sannan sukai sallama ta fito ta shige gidan cike da farin ciki fal zuciyarta. Tun daga ranar soyayya mai k'arfi ta shiga tsakanin Alhaji Mansur da Asiya, ko sati uku basu yi da fara soyayya ba ya turo iyayensa aka saka ranar aurensu, wulak'anci da rashin mutunci Asiya ta shiga yiwa 'yan uwanta da iyayenta, domin kuwa har cewa take idan ta auri Alhaji Mansur suka sake, sukace zasu zo gurinta wallahi sai ta saka anyi musu korar k'are, shiyasa sam basa shshshige mata suka barta take hada-hadar bikinta ita kad'ai kuma kowaccensu tayi alk'awarin ko talauci zai kashesu ba zasu je gurinta da niyyar taimako ba ko ziyara. Ana saura kwana uku d'aurin aure Asiya ta tattara kayanta wad'anda Alhaji Mansur ya bata kud'ad'e ta siyo su ta saka su a d'an k'aramin akwati ta fito kallonsu take yi d'add'e a wulak'ance tare da cewa "to sai anjimanku sai mun had'u a darussalam" ta fad'a tare da fita daga gidan Hajara cike da mamaki da tashin hankali ta ce "Innarmu wai Aunty Asiya yau ne bikin nata" cike da bak'in ciki Inna ta ce "Oho ita ta sani ai duniya ce ta isa kowa riga da wando wanda bai zo bama jiransa take" ina tak'arasa maganar tare da fashewa da kuka gaba d'ayansu sukai kanta suna rarrashinta da kalamai masu dad'i tabbas ta ji dad'i da ya kasance tana da wasu yaran dan da Asiya ce kad'ai 'yarta da bak'in ciki ya kasheta,Asiya kuwa tana fita gidan k'awarta Azima ta nufa daman har an ware mata d'akinta da zata zauna a ciki, Azima k'awar Asiya ce, ta gudo daga garinsu saboda auren dolen da iyayenta zasu yi mata tazo ta kama gida anan garin kano take zaune Alhazawa suna zuwa su d'auketa a tafi hutun yawon shak'atawada ita, wannan shine takaitatcen tarihin Azima k'awar Asiya, Anan gidan Asiya ta zauna har ranar d'aurin aure Azima ta gayyato k'awayenta 'yan bariki sukai ta shek'e ayarsu, har lokacin kai Amarya ya yi Alhaji Mansur ya turo motoci gidansu Asiya amman aka ce musu ba anan take ba, a kasa rakasu har gidan A ka fito da Amarya aka nufi makeken gidanta, suna zuwa suka kai ta har kan gadonta, sukai mata sallama domin suna da fita club yau akwai casun da za'ayi, suka tafi, Asiya ta yaye mayafin da aka lillib'eta ta shiga zata gidan lungu da sako tana dad'a godewa Allah, da ya mallaka mata Alhaji Mansur a matsayin mijinta, A babban falo ta ci karo da Alhaji Mansur murmushi suka sakarwa juna sannan Asiya ta koma d'akin da sauri shima ya rufa mata baya, daga nan suka shiga cin amarcin su har na tsawon kwana bakwai Alhaji Mansur yayi musu visa zuwa dubai, murna a gurin Asiya ba'a magana ta rasa inda zata tsoma ranta dan dad'i wai yau ita ake cewa zata je dubai,muryar Alhaji Mansur taji yana cewa "To gobe sai mu je ki yiwa su Malam da Mamata sallama tunda jibi zamu tafi" anan take Asiya ta b'ata rai ba tare da ta ce komai ba, domin kuwa tunda ta samu ta rabu da wad'annan iyayennata bata k'aunar sake ganinsu har abada, kuma uwar mijin nata ma bakyata tayi ba, domin akwai ranar da ta kira a waya ta ce ta bata su gaisa ta ce kunnanta ne yake ciwo ba zata iya amsa kira ba. Washe gari kuwa da duku-duku ta fara k'irk'irar rashin lafiyar k'arya domin karta je gurin iyayenta da kuma iyayen mijin nata,Alhaji Mansur hankalinsa yayi matuk'ar tashi jin matar tasa bata da lafiya, bayan ya bata abincin ya bata magani yaje shi kad'ai yayi musu sallama tare da basu uzurin Asiyan bata da lafiya ne shiyasa bata zo ba, shi dai Malam Kalla yana fad'a masa yasan k'arya take kawai bata son zuwa ne, washe gari da sassafe jirginsu ya d'aga zuwa dubai, watan su d'aya a dubai Asiya ta samu ciki zo kaga murna gurin masoyan biyu tamkar zasu had'iye junansu, haka sukai ta rainon cikin har ya kai watansa na haihuwa, a ranar wata labara ta haifi kyakkyawan d'anta mai kama da mahaifinsa, ranar suna a kasa saka masa suna Jabir a ranar da akai sunan da daddare Mahaifiyar Alhaji mansur ta kira a waya tayi ta masa fad'a a kan cewa yaje chan wata k'asa har matarsa ta haihu amman ba zan dawo a yi sunan a kano ba, hak'uri yayi ta bata ita kuwa Asiya tab'e baki tayi tare da jan ga gejeren tsaki, da yake suna da d'an tazara tsakaninsu Alhaji Mansur bai ji tsakin ba, haka ya katse wayar rayuwarsu ta cigaba da tafiya cikin farin ciki da walwala, Jabir ya taso cikin sangarci da gata daman ta yaya za'ai mara tarbiyya ace zata bawa wani tarbiyya dan haka Jabir ya debo gaba d'aya halayyar mahaifiyarsa a lokacin da Jabir yake shekara bakwai Asiya ta kuma samun ciki, suka dawo kano domin kuwa wannan cikin cewa Alhaji Mansur yayi a garin kano zata haifeshi kuma Jabir ya je ya ga kakanninsa domin ya sansu haka dai suka tahi ba dan ran Hajiya Asiya yaso ba, suna isa suka tarar har an gyara gidan haka aka zo ana tayi musu sannu da zuwa amman Asiya da ta gaji daga baya komawa tayi d'akinta ta kulle da mukulli, haka suka cigaba da rainon cikin har ya kai lokacin haihuwa ranar wata alhamis ta haifi d'anta namiji tun a asibitin jama'a sukai ta zuwa barka har aka sallamesu suka dawo gida, mutane suka cika gidan ai kuwa Hajiya Asiya ta d'aure fuska saboda ita sam bata son wani talaka ya rab'eta amman kuma taga a cikin dangin mijin nata har da talakawa, haka dai babu yadda ta iya kullum cikin zuwa barka ake a gidan har ranar suna yaro ya ci suna Aliyu, anyi shagalin suna sosai anci ansha sai wajen magriba kowa ya watse aka bar Hajiya Asiya daga ita sai yaranta sai kuma mijinta, haka suka cigaba da nunawa junansu da yaransu kulawa da soyayya Aliyu yana da shekara hud'u ta sami wani cikin amman wannan yayi matuk'ar bata wahala sosai dan haka Aliyu da Jabir aka kai su gurin Kakarsu ta wajen uba, ta rik'esu har sai da Asiya ta haifi yaranta 'yan biyu duk mata aka sakawa d'aya sunan mahaifiyar Alhaji Mansur Nafisa d'aya kuma sunan mahaifiyarta Aisha, Nafisa suke ce mata Nihal, Aisha kuma Shahida ranar da Asiya tayi arba'in aka kai mata su Jabir saboda irin matsawar da tayi a dawo mata da yaranta, suka cigaba da rayuwa cikin farin ciki da kwanciyar hankali. Wannan shine tarihin Jabir da Mahaifiyarsa. Aliyu ne kwance a kan gadon d'akinsa wanda tunda Mami ta mareshi ya shiga ya rufe kansa bai k'ara fitowa ba gashi har safiya tayi kusan k'arfe 10am na safe ko abincin dare bai ciki ba sai ruwa da ya bud'e fridge ya sha kad'an, maganar da d'an uwansa ya fad'a masa ce da yake tambayarsa jiya da yarinyar tazo gidan ta shiga dawo masa "wata yarinya ce da muka yi Auren wucen gadi da ita" shi abin da bai gane ba shine me Jabir yake nufi da auren wucen gadi, shin yayi aure ne ba'a fad'a masa ba kuma da duk alamu indai yayi auren da gaske to Abbansu ma bai san yayi ba, dan inda ya sani zai fad'a masa, da ya ga zai tak'ura kansa da tambayoyin da bashi da amsa ya watsar dashi,sannan ya tashi ya shige toilet wanka yayi sannan ya fito ya shirya cikin wata had'addiyar shadda marun colour, kyau iya kyau ya riga da yayi ya fesa turare sannan ya fita ta kofar baya domin kuwa baya k'aunar ganin kowa daga cikin 'yan uwan nasa da mahaifiyarsa,motarsa ya shiga mai gadi ya bud'e masa gate d'in gidan ya ja motar ya nufi gidan Abokinsa Musbahu. *'BANGAREN KHADIJATULLAH* Tun da ta tashi take kwarara amai daman gashi babu komai a cikin nata dan haka aman ma dakyar dake yinsa duk ta gama galabaita, Aunty Murja ce taje ta kirawo doctor Halima saboda ganin amai yak'i tsayawa, koda doctor Halima tazo ta ga yanayin da take, allura tayi mata wacce zata tsayar da aman ko minti 5 ba'ayi ba aman ya tsaya, kwantawa tayi tare da jero ajiyar zuciya, suna yi mata sannu tana amsa musu da kai doctor Halima ta ce "karku bata abinci yanzu ku bari sai wajen 12am sai a bata tea mai zafi tunda kun ga yanzu k'arfe 10:30am na safe" suka amsa da "to insha Allahu, zamu kiyaye" daga nan doctor Halima ta fita ta koma office d'inta, Amatullahi ta kalli Aunty Murja ta ce "Aunty Murja bari inje gida daga nan na taho mana da abincin da zamu ci" murmushi Aunty Murja tayi sannan ta ce "To Amatullahi" ta shi tayi sannan ta ce mata "Sai na dawo", "A dawo lafiya" Aunty Murja ta fad'a fuskarta d'auke da murmushi, fita Amatullahi tayi da saurinta tana fita daga asibitin ta dad'e a bakin titi duk mai adaidaitar da zata gani a cike yake da mutane, ta tafiya tayi domin ta ga idan ta tsaya ba zata samu masu adaidaita ba, Ai kuwa tayi sa'a ta hango wani mai adaidaita babu kowa a cikinsa da sauri ta tsayar dashi ta shiga tare da yi masa kwatancen gidansu, sai da mai adaidaitan ya kai ta har kofar gida sannan ta biyasa ta shiga gidan bakinta d'auke da sallama "Assalamu alaikum" Inna larai wacce take gaban murhu tana had'a wutar girki tayi mata wani irin kallon k'ask'anci ita ma Amatullahi ta mai dan mata da martanin kallon nata,ba tare da ta amsa sallamar ba ta ce "to 'yar gantali ina kika je kika kwana saboda tsabar rashin kamun kai irin naki da wannan shegiyar uwar taki bata koya miki tarbiyya ba har ki je ki kwana a wani wajen koda yake naji ance dangin nata gaba d'aya 'yan bariki ne anyi gadon tsiya" tayi maganar tana d'ora tukunyar ruwan kokon da zata yi, fusata iya fusata Amatullahi ta riga da tayi,tana raye a gabanta a zagi mahaifiyarta kuma har ace danginta 'yan bariki ne ace bata d'auki mataki ba "Lallai yau akwai bala'i" ta fad'a a cikin zuciyarta, wucewa d'akinta tayi wanka tayi ta chanza kayan jikinta sannan ta fito, lokacin har Inna larai ta gama dama kokon tana soya kosai, wani irin murmushin mugunta Amatullahi tayi sannan taje ta zauna a kan 'yar k'aramar kujerar k'arfe ta dora k'afa daya kan d'aya, cikin jin haushin Amatullahi Inna larai ta ce "Wai ke rashin tarbiyyar taki har ta kai ina aiki ba zaki zo ki k'arb'a ba, koda yake ba laifinki bane laifin wannan k'anjamamman uban naki ne, daga anyi magana sai ya ce ke marainiya ce to uban waye ba marayan ba" magana take cikin fushi, ita dai Amatullahi ba ce komai ba sai murmushi take domin kuwa yau zata koyawa Inna larai hankali "daga yau ba zaki sake bud'ar baki da niyyar zagin iyayena ba, sai nayi miki abin da zaki fi wata d'aya kina jinya baki warke ba" Amatullahi ta fad'a tana 'yar dariyar mugunta sai da ta gama soya kosan gaba d'aya Amatullahi ta tafi gadan-gadan ta hankad'a Inna larai ta fad'a kan wannan man da ta gama suyar kosai gaba d'aya man ya kelayo mata a fuskarta, Amatullahi ta d'auki wannan koko da kosan ta fita domin komawa asibitin tana fita ta bata samu mai adaidaita ba har sai da taje bakin titi ta shiga tace masa "Asibitin nasarawa zaka kai ni" mai adaidaitan ya amsa da "to hajiya" suna isa bakin asibitin nasarawa Amatullahi ta ga Aunty Murja ta fito daga cikin asibitin bayan ta sallami mai adaidaitan ta nufo gurin da Aunty Murjan take da sauri tana cewa "Aunty Murja ina zaki?" k'arb'ar bokitin kokon tayi tare da cewa "Liptom da sugar na fito na siya domin a had'awa Khadijatullahi ta sha, kamar yadda doctor tace naga sha biyun takusa, Amatullahi ta mik'awa Aunty Murja bokitin kosan sannan ta ce "Kawo naje na siyo, ki koma ciki Khadijatullahi tana buk'atar wani a kusa da ita bai kamata mu dinga tafiya muna barinta ita kad'ai ba, Aunty Murja ta k'arbi bokitin kosan sannan ta bata kud'in da fad'a mata abubuwan da suke buk'ata da zata siyo, Amatullahi ta nufi shagon da yake jikin asibitin domin siyo kayan da Aunty Murja ta fad'a mata, ita kuwa Aunty Murja ta koma cikin asibitin, Amatullahi tana gama siyayyar ta nufi cikin asibitin d'akin da aka kwantar da Khadijatullahi ta nufa ta shiga da sallama, suka amsa mata ta k'arasa ta bawa Aunty Murja siyayyar da tayi sannan ta koma gurin da Khadijatullahi take kwance ta d'agota ta taimaka mata ta zauna sannan ita ma ta zauna Aunty Murja ta had'a mata tea ta mik'owa Amatullahi ta ce "Gashi bata ta sha", k'arb'a Amatullahi tayi ta shiga bawa Khadijatullah tea d'in sai da ta koshi ta ture kofin daga bakinta Amatullahi ta ce "Kin koshi ne" kai ta gyad'a mata alamar "Eh" Amatullahi ta ajiye kofin a kan d'an k'aramin teburin da yake d'akin ta sauka k'asa domin ta zuba musu koko da kosan ita da Aunty Murja su ci, Aunty Murja sauka k'asan tayi ita ma tare da cewa "Kin ga tsaya muci a faranti d'aya ba sai kin raba ba" Amatullahi ta ce "to" suna ci suna hira har suka gama abin gwanin ban sha'awa. *'BANGAREN GIDANSU JABIR* Zaune suke a kan dinning table suna yin breakfast Mami ta kalli Jabir tare da cewa "Aliyu ya fito kuwa" tab'e baki Jabir yayi tare da cewa "tun jiya da ya shiga d'aki bai fito ba har yanzu" dafe k'irji Mami tayi tare da cewa "na shiga uku Aliyu na" da sauri ta nufi bangaren Aliyu har tana tuntub'e, rufa mata baya sukai gaba d'ayansu, Mami tana zuwa ta shiga bugun kofar tana kiran sunan Aliyu, "Aliyu! Aliyu!! Aliyu!!!" Amman shuru zub'ewa tayi a k'asa tare da fashewa da kuka "Wayyo Aliyu na ka bud'e kofar dan Allah kayi hak'uri" Shahida da Nihal suka zauna kusa da Mamin suna rarrashinta Jabir kuwa cikin zafin rai ya shiga buga kofar kamar zai k'arya "Aliyu ka bud'e kofar nan idan ka bari na k'arya kofar nan ba zaka ji da dad'i ba". "Aliyu ka bud'e kofar nan nace maka" Jabir ya d'auki kusan mintina 30 yana buga kofar tare da kiran sunan Aliyu amman shuru babu alamar za'a bud'e kofar kamar ance ya lek'a window sai ya ga kofar baya a bud'e take anan take ya ce "Mami kofar bayan d'akin Aliyu a bud'e take ko dai ya bar gidan nan ne" yayi maganar cike d tashin hankali, da sauri Mami ta mike ta zagaya suka bita a baya d'akin ta shiga ta shiga duba ko ina a d'akin amman babu Aliyu babu alamar sa, hakan yayi matuk'ar tayarwa da Hajiya Asiya hankali domin Aliyu bai tab'a fita ba tare da ya sanar da ita ba "to kodai Aliyu barin gidan yayi ya koma dubai" anan take ta zubai a kan gadon tare da dora hannu a kai, ta fashe da wani wahalallen kuka, Jabir kuwa wayarsa ya zaro a aljihu ya shiga kiran number Aliyu, amman a kashe, fita yayi da sauri bai zame ko ina ba sai wajen da aka tanada domin ajiye motoci, ya shiga d'aya daga cikin jerin motocin wacce ta kasance ta hajiya Asiya ce amman yaran nata suna d'aukar motar idan zasu fita, gidan kakarsu Hajiya Mama ya nufa domin duba Aliyun ko yana nan, yana zuwa ko sallama bai yi ba ya shiga kai tsaye, falon Hajiya Mama ya shiga ya tarar da ita tana kallo ta kishin gid'a a kan kujera, babu gaisuwa babu sallama Jabir ya ce "Hajiya Mama Aliyu yazo gidan nan kuwa" a zabure Hajiya Mama ta tashi har tana kok'arin fad'uwa, domin ko motsin shigowarsa bata ji ba, cike da bak'in cikin irin rashin tarbiyyar da Jabir bashi da ita ta rufe shi da fad'a "Kai wai meyasa baka da hankali ne kawai ka shigowa mutanan gidan zek'ek'e kamar wani bayahude, Aliyu da Shahida k'annanka ne amman sun fika hankali domin inda sune ba zasu tab'a shigowa ba tare da sunyi sallama ba, kuma suna shigowa kafin su fad'i abin da ya kawo su sai sun gaishe ni tukunna, daman wannan me kama da arnan bakin titin halinku d'aya" tana nufin Nihal domin haka take ce mata. Jabir ya ji haushin maganganun Hajiya Mama dan sunyi matuk'ar kona masa rai, koda ya ga alamar Aliyu baya gidan ya ja tsaki sannan ya fita daga gidan a fusace yana jin Hajiya Mama tana cewa "uwarka ka yiwa tsaki mara tarbiyya kawai". Haka ya shiga motarsa ya ja ta sa k'arfi sai huci yake kamar wanda yaje dambe, kai tsaye club ya nufa, yana zuwa bai shiga cikin club d'in ba ya huce hostel d'in d'akinsa ya huce ya bud'e ya shiga, fridge ya nufa ya bud'e ya d'auko giya ya balle murfinta cikin zafin nama ya shiga kwank'wad'arta har sai da ya shanye gaba d'aya, haka ya k'arasa kan gadon yana tangad'in ya fad'a gadon, yana kwanciya wani amai ya taho masa ya mik'e dakyar da niyyar ya shiga toilet ya zube a kan carpet ya shiga kwara wani irin bak'in amai, sai da ya gama sannan ya mik'e ya koma kan gadon bacci mai nauyi yayi awan gaba dashi. *'BANGAREN KHADIJATULLAHI* Alhamdulillahi jikinta yayi sauk'i dan har tana yin hira sama-sama dasu Aunty Murja, ganin yadda jikin nata yayi sauk'i ne doctor Halima ta rubuta musu takardar sallama, suka koma gida suka cigaba da lura da Khadijatullahi, b'angaren Inna larai kuwa tunda Amatullahi tayi mata wannan aika-aikar ta fita ta shiga kurma ihu da neman taimako tayi sa'a kuwa d'anta lado ya shigo gidan yaga yanayin da take ciki dan har fuskarta ta fara sabulewa, a gigice ya k'arasa gurin da take a bage yana tambayarta "Inna meyafara wa yayi miki wannan aika-aikan" cikin rawar muryar ta bud'e bakj dakyar ta ce "Ama....Amatullahi ce lado ka taimkeni ka kaini asibiti" lado kuwa ransa ya b'aci matuk'a "wato rashin mutunci Amatullahi har ya kai ga ta illatawa mahaifiyarsa fuska" ya fad'a a zuciyarsa a fili kuwa ya ce "Wallahi wallahi na rantse miki da girman Allah Inna kamar yadda Amatullahi ta kona miki fuska wallahi nima sai na kona mata", (Ni kuwa 'yar mutanan zazzau nace lado kayi sauri ka kai mahaifiyarka asibiti kar fuskar ta rub'e domin kuwa Amatullahi ba kanwar lasa bace dai-dai take da kai😂🤸🏽‍♀️). Haka Lado ya d'auki mahaifiyarsa a hannunsa ya nufi waje yayi sa'a yana fita ya tarar da abokinsa Tanimu a cikin motarsa da alama fita zai yi, Lado ya tsayar dashi da sauri, Tanimu ya tsaya Lado ya saka mahaifiyarsa sannan shima ya shiga, yana cewa "Tanimu dan Allah kaimu asibiti mafi kusa damu wallahi wannan shegiyar yarinyar ce ta hankad'a Inna cikin mai", cikin nuna damuwarsa Tanimu ya ce "Subhanallahi gari yaya haka ta faru" tsaki Lado ya ja cike da takaici ya ce "to wannan hatsabibiyar yarinyar ma har a tambaya garin yaya hakan ta faru, wallahi wannan yarinyar idan bata yi wasa ba siyar da ita zan yi kowa ya huta", dariya ce taso ta kwacewa Tanimu amman ya had'iye a zuciyarsa yana cewa "Kai banda abin ka Lado ai wannan yarinyar wallahi bata siyu ba dan duk wanda ya siyeta ya siyi jafa'i dan da kansa zai dawo da ita ya ce ya fasa". Abin da yasa Tanimu ya ce haka akwai wata rana da kanwarsa taje ta tsokani Amatullahi har gida Amatullahi taje ta zagesu gaba d'aya tare da cewa Innarsu "bata iya bada tarbiyya ba", Wani asibiti mai suna *BUBA SPEACIAL HOSPITAL* suka tsaya Lado ya fita da Innarsa ya shiga asibitin yana kiran "nurse! nurse!! nurse!!" Nurses kusan biyar ne suka fito suna tura gadon da ake dora marasa lafiya, Lado ya dora Innarsa ya taimakawa nurses d'in wajen tura innar sukai d'akin tiyata da ita (Allah sarki Inna larai anji bala😂😆). Haka su Tanimu suka zauna har tsawon awa d'aya babu wanda ya fito domin sanar dasu halin da Inna Laran take ciki, Tanimu ya kalli abokin nasa ya ce "Abokina zanje gurin Mama saboda zan kai ta unguwa kuma na barta tana ta jirana" Lado ya sauke ajiyar zuciya ya ce "to Abokina babu komai dan Allah ka mik'a min gaisuwata gurin Mama", "Insha Allahu" Tanimu ya fad'a tare da nufar kofar fita daga asibitin, Lado ya zabga tagumi zuciyarsa cike da tsanar Amatullahi, da kuma d'aukar fansar abin da tayi wa Innarsa. *'BANGAREN JABIR* Jabir bai tashi daga baccin ba sai wajen k'arfe uku, ya bud'e idanuwansa ya dorasu a kan wasu kyawawan yammata guda uku kowaccensu sanye take cikin kananun kaya riga da wando, wani kayatatcen murmushi yayi tare da kirawo sunansu "Leemsha, summy,Ammi" kowaccen su ta amsa da "Na'am sweety". Jawo su yayi jikinsa yana shafasu suma suna mai dar masa martani (Ni kuwa 'yar mutanan zazzau nace na shiga uku Jabir sai kace bursuru🙆🏼‍♀️),"Leemsha wacce ta kwanta a kan k'irjinsa tana tana kissing d'in lips d'insa ta ce "Sweetheart meyafaru da kai ne, dan naga kabar kofa a bud'e kuma nasan indai kazo kabar kofa a bud'e kana cikin damuwa ne" Cikin wata iriyar murya mai wani irin salo mai d'aukar hankali ya ce "Wallahi wata tsohuwar banza ce ta b'ata min rai", Leemsha kuwa bata k'ara cewa komai ba, suka shiga yin bad'alarsu. *'BANGAREN KHADIJATULLAHI* Yanzu Khadijatullahi ta fara sakin jikinta kuma ta rage yin koke-kokenta Amman kuma kullum ne babu ranar banza sai tayi wa Jabir mugayen addu'o'i tare da tsine masa, Amatullahi kuwa tunda ta koma gida taga babu kowa tayi wata shegiyar dariya tare da cewa "Yau asibiti yayi d'iba kenan, ai Inna Larai kad'an kika gani indai zaki dinga zagin iyayena zan cigaba da baki wahala wallahi". Yau kamar kullum suna zaune Amatullahi ta ce"Aunty Murja ya kamata mu fara shirye-shiryen makaranta domin nan da Sati d'aya insha Allahu zamu fara lecture" Khadijatullahi ta kalli Amatullahi domin kuwa ita har ta manta da sun sami admision ta ce "Amatullahi ni na hak'ura da zuwa makarantar kawai ke ki tafi" nan da nan hawaye ya fara zuba daga idon Amatullahi cikin muryar kuka ta fara magana da cewa "kina tunanin zan iya zuwa makaranta ba tare da ke ba, tun muna yara muke tare komai namu tare muke yinsa tun daga primary har zuwa yau babu abin da nake iyawa ba tare da ke ba yanzu kuma ina murna zamu fara zuwa makaranta zamu cigaba da kasancewa tare shine rana tsaka zaki ce min ba zaki je ba ai shikenan nagode sosai" tana gama fad'ar haka ta tashj ta fita daga gidan da saurinta tana kuka, hankalin Khadijatullahi ya tashi mik'ewa tayi ta d'auki hijabi ta saka duk sa cewa bata jin dad'in jikinnata haka ta bi Amatullahi domin ta bata hak'uri, Aunty Murja ta bisu da kallo tabbas k'awancen nasu yana matuk'ar burgeta "Allah ubangiji ya barku tare har abada". Ta fad'a a fili tana murmushi. Haka Khadijatullah ta bi bayan Amatullah tana kiran sunanta Amman Amatullah ta k'i tsayawa har sai da suka kusan isa gidansu Amatullah, Khadijatullah ta tsaya tana sauke numfashi domin cikin nata Yana tsananin bata wahala, wannan tafiyar ma da tayi ji take tamkar k'afafuwanta zasu fita daga jikinta, ganin Amatullahi tana kok'arin shigewa gidan yasa Khadijatullah ta fara tafiya a daddafe har ta Isa gidansu Amatullah, shiga gidan tayi bakinta d'auke da sallama, "Assalamu alaikum" jin ba'a amsa Mata ba tayi tunanin Babu kowa a gidan Amman tana shiga tsakar gidan ta ga Lado da wata Mata fuskarta nannad'e da band'egi, ta tsugunna ta gaisar da wannan matar Amman Bata amsa Mata ba, sai ma jan tsaki da taji matar tayi, Lado kuwa cike da jin haushi ya ce "to munafuka zaki tashi ki bar nan wajen ko sai na kwarfeki" Khadijatullah ba tare da ta cewa Lado komai ba ta tashi ta nufi d'akin Amatullahi, tayi sallama ta shiga d'akin zaune ta tarar da Amatullahi tana kuka a kan d'an k'aramin gadon d'akin nata, Tsugunnawa Khadijatullah tayi a gabanta ta rik'e hannunta ita ma tana kukan "ki yi hak'uri k'awata nasan nayi miki laifi Amman Dan Allah ki yafe min, na amince zan je makarantar in dai hakan zai saka ki cikin farin ciki, Dan Allah ki daina kukan nan haka ya isa, zan je wallahi da gaske nake" Amatullahi ta juyo fuskarta d'auke da murmushi ta ce "da gaske kike besty" Kai Khadijatullah ta gyad'a Mata alamar "Eh" Amatullah ta d'agota ta taimaka Mata ta zauna a kan gadon kusa da Amatullahi hannayensu suna had'e da juna, Amatullahi ta ce"kin ga yanzu kaya iri d'aya zamu dinga sakawa, kuma ya kamata muje kasuwa domin muyi siyayyar makarantar" Murmushin yake kawai Khadijatullah take yi dimples d'inta suna lotsawa,ba tare da ta ce komai ba. Haka Amatullahi tayi ta tsara musu yadda zasu dinga yin shiga idan zasu je makarantar ita dai Khadijatullah "Eh", "A'a shine kawai abin da take cewa, har wajen k'arfe 8:00am na dare Khadijatullah ta tashi ta ce "To besty zan tafi gida" Mik'ewa Amatullahi tayi tana cewa "Lallai kam yau Maman baby ta dad'e a gidan nan tun 5:00 na rana gashi yanzu karfe takwas na dare" harararta Khadijatullah tayi sannan ta ce"wacece Maman babyn?" Amatullahi ta saka duka hannuwanta a kunnuwanta alamun bada hak'uri ta ce "Am so sorry besty, ai nice Maman baby kin ga idan kika haihu ni zaki bawa babyn" Khadijatullah ta ce "Ai gwanda da kika gyara zancenki dan ni bazan tab'a son cikin nan ba" Amatullahi Bata ce komai ba suka gera suka fita daga cikin d'akin a tare, nufar kofar gida suka yi Khadijatullah ta juyo ta kalli Amatullahi dai-dai lokacin da ta saka k'afafuwanta zata fita daga gidan tare da cewa "Yau ban ga Inna ba ko Bata nan" Amatullahi cikin dariyar mugunta ta ce "kin ganta mana kamanninta ne suka chanza miki shiyasa baki ganeta ba" shuru Khadijatullah tayi Bata ce komai ba Amman zuciyarta ta cika da mamakin abin da Amatullahi ta fad'a, ta juya ta cigaba da tafiya ita ma Amatullahi ta bi ta a baya sai da suka kusan isa gidan sannan suka yi sallama da juna, Amatullahi ta koma gida ita Kuma Khadijatullah ta k'arasa gidan, tana zuwa ta tarar har Aunty Murja ta kwanta bacci ita ma ta kwanta a bayanta duk da cewa ba baccin take ji ba Amman ta lumshe idonta ta kusan awa a kwance bacci Mai nauyi yayi awon gaba da ita. *'BANGAREN GIDANSU JABIR* Hajiya Asiya ta gama rikicewa saboda rashin ganin d'an nata Aliyu har zazzab'i tayi ta kira Abbansu domin taji ko suna tare ya ce "basa tare" haka dai ta b'oye Masa Bata fad'a masa komai ba, saboda ta san in har ta fad'a masa to ta shiga uku a gurin Alhaji Mansur, gashi Shima Jabir tun ranar da ba'a ga Aliyu ba ya fita yau kwana uku Bata saka shi a idanuwanta ba, Amman shi Bata damu ba domin ta san ba zai huce yana club da yammatan shi ba, haka dai zata zauna tayi ta sam batunta duk da irin tsananin son da take yiwa Jabir Amman ranta yana matuk'ar k'aunar Aliyu, zaune suke ita da Shahida domin Nihal tun jiya da saurayinta yazo ya d'auketa suka fita bata dawo gidan ba, Hajiya Asiya ta zabga tagumi tana kuka Shahida ce ta matso kusa da ita tana ta rarrashinta, Jabir ne ya shigo falon daman bai shi bai san wata sallama ba, dan haka ya shigo falon ko sallama bai yi ba yana fi to, wani irin kallon yabi mahaifiyar tasa da 'yar uwarta dashi na rashin mutunci sannan yayi shigewarsa d'aki babu sannu da gida ba gaisuwa, (ni kuwa 'yar mutanan zazzau nace yau Jabir har Hajiya Asiyan baka kyale ba, lallai abin naka ya huce tunanina😂), Abin mamaki maimakon Hajiya Asiya ta damu da irin yadda d'annata yayi Mata, Amman ko kad'an Bata damu ba sai ma tashi da tayi ta bi sa 'bangarensa ta tarar dashi a falo ya bage a kan kujera ya d'ora 'kafarsa d'aya a kan center table d'in da ke falon yana jijjigata, k'arasawa kujerar da yake tayi tana yi Masa sannu da zuwa "My son sannu da zuwa" Kallon kan ki ake ji ya bita dashi sannan ya tab'e Baki tare da cewa "Ai nayi tunanin ba zaki zo kiyi min sannu da zuwa ba, sai wani kuka kike tun ranar da ba'a ga Aliyu ba, Amman ni kwanana uku bana gidan nan Amman ko ki kirani ki ji lafiya" Mami ta zauna a kusa dashi tare da cewa "My Son ai kai nasan kana club ne, shiyasa ban kira ka ba, saboda nasan baka son takura, Amman shi Aliyu bai dawo ba har yanzu kuma na kira Abbanku ya ce basa tare" ta k'arasa maganar tana kuka, duk da irin yadda Jabir yake jin haushin Mamin a kan rashin kiransa da ba tayi ba sai da yaji tausayinta kuma ya ji hankalinsa ya tashi,"Mami kina nufin har yanzu Aliyu bai dawo ba" kai ta gyad'a masa alamar "eh", Jabir ya bud'e kenan zai yi magana sai ga Aliyu ya shigo falon bakinsa d'auke da sallama "Assalamu alaikum" yayi sallamar cikin sanyayayyiyar muryarsa mai d'aukar hankalin mutane, babu wanda ya amsa sallamar gaba d'aya sukai gurin da yake tsaye a bakin kofar falon, rumgumeshi Mami tayi tana fad'ar "Yarona ina ka tafi ka bar ni, nasan ban kyauta maka ba amman bai kamata kayi tafiyarka ba,kasan ina sonka sosai" zame jikinsa yayi daga rumgumar da Mami tayi masa ya k'arasa gurin Jabir suna kallon kallo sunyi kusan minti biyar suna kallon juna Jabir da ya gaji ya ce "Menene kake wani kallona kamar wanda yayi maka wani mugun abu", Wani irin murmushi mai ciwo Aliyu yayi tare da cewa "ina kallonka ne saboda kayi abin da ya kamata a kalleka kuma a kiraka da mara tausayi mara imani, Jabir wallahi kaii ba mutum bane dabba ne" Mami tayi saurin zuwa gaban Aliyu tana cewa "Aliyu baka da hankali d'an uwan naka kake cewa dabba" kallon takaici ya bi Mami dashi daba dan ita d'in mahaifiyarsa ce ba da yau yayi mata abin da ba za ta tab'a mantawa dashi ba, amman kash! ta ci dajarar ita mahaifiyarsa ce, cikin muryar da take nuna alamu yana cikin tsantsar bakin ciki da jin haushinsu ya fara magana "Mami banyi tunanin haka daga gurinki ba, ta yaya zaki bada goyon baya aka zalinci baiwar Allah marainiya to ku sani duk abin da kuke b'oyewa yanzu nasan komai kuma zan fad'awa Abba, shiyasa kace wai Auren wucin gadi kuka yi da yarinya to kasani duk abin da kayi sai an yiwa k'anwarka ko kuma 'ya'yanka kuma idan an tashi yi musu sai anyi musu ninkin abin da kayi banza,dabba,dak'ik'i" yana gama fad'ar haka ya fita ya koma b'angarensa zuciyarsa cike da bak'in ciki, Jabir kuwa ransa ya gama b'aci sai huci yake kamar wank tsohon mayun wacin zaki, Mami ta kamashi suka je suka koma ta shiga rarrashinsa cikin hassala ya ce "dalla ni ki kyaleni kina kallon wannan yaron har ni zai zo gaba na ya ce min ni dabba, dak'ik'i, banza" ya mik'e ya fara zagaye d'akin Mami ta tashi zata matsa kusa dashi ya d'aga mata hannu cikin tsawa ya ce "Mami karki matso kusani ki fice min a d'aki kafin na sauke fushi na a kan ki" fita Mami tayi ba tare da ta ce masa komai ba, 'bangaren Aliyu taje tayi ta bubbuga kofar d'akin nasa amman yayi banza da ita sai da ta gaji dan kanta, ta koma b'angarenta bedroom d'inta ta nufa taje ta kwanta tana sake-sake a cikin ranta maganar Aliyu ce ta fad'o mata da yake cewa sai ya fad'awa Abbansu sauke nannauyan ajiyar zuciya tayi tare da cewa "duk yadda zanyi, zanyi Aliyu ba zan tab'a barin ka ka fad'awa Abbanku komai gamai da Auren wucin gadin da Jabir yayi ba" ta saka wannan ta saka wannan har bacci ya d'auketa. *B'ANGAREN AMATULLAHI DA KHADIJATULLAHI* Yau Lado ya shirya tsaf zai d'aukarwa mahaifiyarsa fansar abin da Amatullahi tayi mata, wajen k'arfe 9:00pm na dare Lado ya d'auki ruwan zafin da ya tafasa shi ya nufi d'akin Amatullahi dashi, yayi sa'a kuwa kofar d'akin a bud'e take dan haka ya kutsa kansa a kwance ya tarar da ita tayi lanfa dan ta ji shigowar Ladon Amman tayi kamar bacci take yi, "Lado kenan idan kasan wata ai baka san wata ba daman nasan duk daran dad'ewa zaka zo d'aukarwa mahaifiyarka fansar abin da nayi mata shiyasa kullum cike nake da shirin zuwanka" Zabagegiyar wuk'ar da take gafenta kasancewar Amatullahi ta kashe wutar d'akin shiyasa Lado bai ga wuk'ar ba idonsa ya riga da ya rufe kawai burinsa ya watsawa Amatullahi ruwan zafin a fuska, ya d'aga d'an k'aramin bokitin da ya d'ebo ruwan zafin zai shek'a mata ai kuwa sai jin saukar wuk'ar yayi a hannunsa ya saki bokitin a kasa ruwan zafin ya zuba a k'afafuwansa ya kwala wani irin jijitatcen ihuuuuuuuu....... Anan zan tsaya sai ku dakace ni a gobe idan Allah ya kaimu domin jin yaya zata kasance tsakanin Lado da Amatullahi shin Aliyu zai fad'awa Abba tak'adirancin da yake yi ko kuma Mami zata hanashi yaya rayuwar Jabir zata kasance anan gaba dashi da mahaifiyarsa da kuma k'anwarsa Nihal ku cigaba da biyo ni 'yar mutanan zazzau domin jin yadda zata kasance. Da gudu Lado ya fita daga d'akin Amatullahi yana zabga ihu kamar zai zauce, Amatullahi wacce take tsaye a kan gadonta ta shek'e da wata irinyar dariya tare da cewa "An gaya maka ni d'in ta wasa ce, da ka tsaya hannunnaka zan cire gaba d'aya d'an iskan banza". A tsakar gida Lado ya tarar da Inna larai tana jiran fitowarsa zuciyarta cike da farin cikin d'annata zai d'aukar mata fansa, jin ihun Lado da tayi ne yasa hankalinta ya tashi gashi kuma tana tsoron shiga d'akin Amatullahi saboda tana tsoron abin da zai biyo baya gashi daman bata gama jinyar fuskarta ba, da gudu Lado ya k'araso gabanta har yana ban gaje ta yana fad'ar "inna 'yar ta'adda ce Amatullahi 'yar daba ce" ya fad'a a rud'e hannunsa yana fitar da jini kamar da bakin k'warya, Inna a gigice ta ce "me tayi maka Lado?" Lado ya ce "Inna ta sare ni a hannuna, kalli ki gani" da kyar Inna ta iya bud'e idonta domin tun ranar da Amatullahi ta dannata a cikin kaskon mai ta dena gani sosai, kuka Inna larai ta saka tana magana cikin sarkewar murya "gaskiya yarinyar nan ta cika tantiriya,bari ubanta yazo wallahi bazan iya zama da ita ba, ko ni ko ita wallahi" ta k'arasa maganar tare da shigewa d'akinta tana kuka shi kuma Lado ya fita zuwa *BUBA SPEACIAL HOSPITAL* domin a duba shi. *Wace ce Amatullahi?* Mahaifin Amatullahi Malam Shu'aibu d'an asalin garin kano ne yana da rufin asirinsa dai-dai gwargwado mahaifiyar Amatullahi Asma'u 'yar abokin Malam Shu'aibu ce wanda shima ya kasance yana da rufin asirinsa, Malam Shu'aibu ya dad'e yana tsananin son Asma'u amman ya kasa fad'awa mahaifinta Malam Abbakar saboda a ganinsa kar ayi mata dole dan ya san indai ya fad'awa Malam Abbakar to zai amince ne kuma shi sam baya son ya auri Asma'u ba'a son ranta ba, haka dai ya cigaba da dakon soyayyar Asma'u a cikin zuciyarsa, ranar da bazai tab'a mantawa da ita ba domin a ranar ne burinsa ya cika na auran Asma'u, Malam Abbakar ne ya aiko har gida a kan yana nemansa a gidansa, cike da tashin hankali Malam Shu'aibu ya nufi gidan aminin nasa saboda shi a tunaninsa kodai wani abun ne ya faru a gidan, yana zuwa aka yi masa iso har cikin falon gidan da sallama ya k'arasa ya shiga falon, lokaci d'aya kuma ya shiga cikin matsanancin mamaki ganin gaba d'aya 'yan gidan a falon gidan ga kuma Malam liman da kuma mai unguwa Malam Tanko, bayan sun gaisa ne Malam Shu'aibu ya zauna a kan kujera, Malam Abbakar bayan yayi sallama tare da yin wasu addu'o'i sannan ya fara koro bayanin abin da yasa ya tara su gaba d'ayansu, "Malam liman da ranka ya dad'e mai unguwa abin da yasa na tara ku anan dan ku zame mana shaida nii Abubakar na bawa Abokina kuma aminina Malam Shu'aibu auren Asma'u, kuma ina so a yanzu ba sai anjima ba a d'aura musu aure, kuma nayi wannan shawarar ne tare da amincewar Asma'u ba wai dole nayi mata ba" wani irin farin ciki ne ya lullub'e Malam Shu'aibu ya dinga tunanin wai mafarki yake yi ne ko kuwa da idonsa biyu ashe akwai ranar da burina zai cika na auren muradina Asma'ul Husna, yana cikin tunanin ne ya ji muryar Malam liman yana yi masa Allah ya sanya alkhairi daga nan suka tashi shi da mai unguwa suka fita nan, Malam Abbakar ya tashi daga gurin da yake da dawo kusa da aminin nasa "Ina yi muku addu'ar Allah ya baku zaman lafiya ya ba ku zuri'a d'ayyiba, na san zaki yi mamakin abin da yasa na had'a auranka da Asma'u nayi hakane ba dan komai ba saboda bana son irin yadda kake zaune babu wacce zata dinga kula da kai, ina yi muku fatan Alkhairi zata iya d'aukar matarka ka tafi da ita domin ta ri ga da ta shirya", kallonsa Malam Shu'aibu yake cike da tsantsar son Malam Abbakar ya ce "ban san ma da wasu irin kalmomi zan yi amfani dasu ba wajen gode maka nagode sosai Allah ya saka da Alkhairi". Haka suka d'an tab'a hira Malam Shu'aibu ya tashi da niyyar tafi gida Malam Abbakar ya cewa Asma'u da ta tashi ta bishi, haka ta tashi tana kukan rabu da 'yan uwanta ta bi mijinta Malam Shu'aibu mahaifiyarta tana biye da ita da k'aton akwatin kayanta Allah sarki, motar Malam Abbakar suka shiga aka saka akwatin a boot driver ya ja su zuwa gidansu Malam Shu'aibu, suna zuwa driver ya shigar musu da akwatin sannan sukai sallama suka shiga gidan tare Asma'u ta rufe fuskarta da mayafi, suna shiga Inna Labara mahaifiyar Malam Shu'aibu ta tare su fuskarta d'auke da mamaki "Shu'aibu kai da wace?" cike da jin kunya ya ce "Inna Asma'u ce 'yar gidan Abbakar, nan Inna ta shiga fara'a ta ja Asma'u suka je suka zauna a kan taburma, shima ya d'auko taburma ya ajiye a kusa dasu Malam Shu'aibu ya fad'awa Inna duk abin da ya faru, wata iriyar gud'a inna tayi sannan ta shiga sakawa Malam Abbakar Albarka tashi tayi ta gyara musu wani d'an k'aramin ta d'auki akwatin Asma'u ta kai d'akin, abinci ta zubowa Asma'u ta ci sosai, tun daga ranar Malam Shu'aibu ya cigaba da nunawa Asma'u soyayya da tsantsar k'auna har Allah ya bata ciki wanda ba'a gane shi ba har sai da cikin ya kai wata hud'u murna gurin Malam Shu'aibu ba'a magana, haka ya cigaba da bata kyakkyawan kulawa ta musamman har Allah ya sauketa lafiya ta haifi 'yarta mace a gida a wata ranar litinin, ranar suna aka sakawa yarinya suna Amatullahi haka gidan ya cika damk'am da 'yan uwa da abokan arzik'i sai wajen k'arfe 10:00pm na dare sannan aka watse aka bar Asma'u daga ita sai Inna da yarinyarta Amatullahi, Amatullahi ta taso cikin gata saboda Malam Shu'aibu ya d'auki son duniya ya dorawa Amatullahi hatta yaye shi ya yayeta duk inda zai je da ita yake zuwa, Asma'u kuma bata k'ara samun ciki ba har sai da Amatullahi ta kai shekara 14 a duniya wannan cikin yazo mata da laulayi har yayi sanadiyar mutuwarta Allah sarki Malam Shu'aibu yayi kukan rashin matarsa mai ladabi da sanin ya kamata bashi kad'ai ba har Inna ma tayi kukan rashin Asma'u Malam Abbakar ne ya shiga rarrashin Malam Shu'aibu tare da yi masa nasiha mai ratsa zuciya, a ranar da Asma'u ta cika shekara d'aya da rasuwa, Inna Laraba Mahaifiyar Malam Shu'aibu ta koma ga Allah, tashin hankali ya k'ara aurar Malam Shu'aibu daman gashi bai gama fita daga cikin damuwar rashin matarsa ba, ya rasa abin da yake yi masa dad'i haka ya cigaba da rayuwa daga shi sai Amatullahi a gidan duk inda zashi tana nanik'e dashi, ranar da Inna tayi arba'in Malam Abbakar yazo masa da maganar auren wata bazawara 'yar abokinsa Larai, Malam Shu'aibu ya amince saboda daman yana buk'atar wacce zata dinga kular masa da Amatullahi, haka Malam Abbakar ya shige gaba aka d'aura auren Malam Shu'aibu da Larai, ya gyara gidan da suke zaune aka k'ara d'akuna, ka kawo Amarya Larai d'akinta tare da yaronta Lado, tun da Larai ta ga irin son da Malam Shu'aibu yake yiwa Amatullahi ta d'auki tsanar duniya ita da d'anta suka dorawa Amatullahi suka fara takura mata amman sai suka ga abin yafi k'arfin su saboda Amatullahi ba k'aramar 'yar bala'i ba ce dan komai sukai mata sai ta rama bata tab'a barinsu, Allah ya had'a Amatullahi da wata 'yar layin su Khadijatullahi suka kulla aminci kullum Amatullahi tana gidansu Khadijatullahi idan Khadijatullahi ta ga lokacin zuwa Amatullahi yayi bata zo ba haka zata d'auki hijabi taje gidan ta ga lafiya haka suka cigaba da rayuwa cikin so da k'aunar junansu, Inna Larai kuwa bakin ciki kamar zata yi hauka ganin tayi shekara biyar a gidan Malam Shu'aibu amman ko b'ari bata tab'a yi ba kuma tana tsananin jin bakin cikin irin yadda Malam Shu'aibu yake nuna damuwarsa a kan 'yar tasa kuma kullum cikin yi mata siyayyar tsire yake mata, shiyasa kullum ita ma take k'ara jin tsanar Amatullahi da kuma bakin cikin rashin samun cikin da bata yi ba. *Wannan shine takaitatcen tarihin Amatullahi, yanzu zan dora labarinmu* Yau ya kama su Amatullahi zasu fara zuwa makaranta, Amatullahi ta tattaro kayan da zata saka tazo gidan su Khadijatullahi domin ta shirya a gidan, kayan iri d'aya suka saka komai nasu iri d'aya sun yi kyau sosai, haka suka fita daga gidan zuciyoyinsu cike da farin ciki, Khadijatullahi ta tsinci kanta cikin wani irin farin ciki sosai mara misaltuwa, haka suka yiwa Aunty Murja sallama tayi musu addu'o'i ta samun nasara, suka kama hanyarsu ta zuwa poly, 'bangare d'aya suka cike gaba d'ayansu wato law, suna isa cikin makarantar suka tarar ana shirin shiga lecture bayan sun tambayi ina ne ajinsu aka nuna musu suka nufi ajin cikin farin ciki da annashuwa, suka shiga ajin bakinsu d'auke da sallama wasu daga cikin 'yan ajin suka amsa musu, suka nemi guri a gaba suka zauna suna yin hirarsu har Malami ya shigo kowa yayi shuru aka shiga lecture. *'BANGAREN GIDANSU JABIR* Jabir kuwa fitowa yayi daga d'akinsa a fusace ya nufi d'akin Aliyu ya shiga bugawa da k'arfinsa yana huci, Aliyu wanda yake kwance a kan d'aya daga cikin kujerun falon nasa yana ji yayi banza sai ma kunna t.v da yayi ya kai tashar Arewa 24 inda ya tarar suna film d'in *Rud'in zuciya* duk da kasancewar shi ba ma'abocin kallon indian film ba ne amman yau dan ya musgunawa Jabir ya k'unna, kiran layin Abba ya shiga yii ringing d'aya biyu Abba ya d'aga "Assalamu alaikum aminci Allah ya k'ara tabbata a gareka yarona" wani irin murmushi yayi wanda yake d'auke da tsantsar jin dadi "Wa'alakumussalam Abbana kai ma haka, ya dubai d'in Abba yaushe zaka dawo ina son yin magana da kai kuma gaskiya maganar ba zai yiyu muyi ta waya ba" ya k'arasa magana cikin wani irin yanayi na bakin ciki, Abba tunda ya ji Aliyu ya ce akwai maganar da zasu yi yasan maganar tana da matuk'ar muhimmanci dan haka bai yi niyyar dawowa kwanan nan ba amman ya cewa Aliyu "Insha Allahu zuwa jibi zan dawo, amman kowa lafiya dai ko" Aliyu ya kasa d'aurewa hawaye ne ya shiga zubo masa ya share da hannunsa cikin muryar kuka ya ce "Abba Jabir ne, Jabir yana zubar mana da mutunci Abba Jabir ya lalata rayuwar marainiyar Allah yarinyar da bata ji ba bata gani ba saboda son zuciyarsa shi da Mami, Abba labarin yana da tsayi Abba dan Allah ka dawo gobe gidan nan yana shirin tarwatsewa, Mami, Nihal da Jabir gaba d'aya sun had'u sun lalata rayuwar yarinya, Abba in takaice maka Nihal yanzu yau kwananta uku bata gidan nan wai saurayinta ne yazo ya d'auketa suka fita" ya k'arasa magana yana kuka mai tsima zuciyar mai sauraro, Abba kuwa sakin wayar yayi bayan ya gama jin duk bayanin Aliyu yanzu haka Asiya ta mayar masa da gida, ai kuwa babu shiri yasa aka yi masa visa zai biyo jirgin k'arfe biyar na yamma dan bazai ma bari ya kwana ba, Aliyu ya katse kiran sannan ya shiga kok'arin goge hawayensa. Masu karatu na san zaku so kuji shin a ina Aliyu yaji ta'asar da Jabir ya yi wa Khadijatullahi, ba'a gurin kowa ya ji ba Shahida ce ta fad'a masa komai, domin lokacin da ya shigo gidan ya tarar da ita tana kuka da sauri ya k'arasa kusa da ita yana tambayarta menene, anan take ta zai yana masa komai da komai ta dora da cewa "Yaya Aliyu ina tsoron abin da Yaya Jabir ya yi wa Khadijatullahi ya faru a kai na ko Nihal saboda kasan ance duk abin da ka yi wa d'an wani to kai ma sai an yi wa naka, Yaya Aliyu kuma abin takaicin Mami da sanin ta Yaya Jabir yake yin komai amman bata tab'a hanashi duk abin da yake yi ganin dai-dai take yi masa" kuka yake yi sosai amman haka ya dake ya shiga rarrashin k'anwar tasa da kalamai masu dad'i sannan ya nufi d'akin Jabir d'in. Jabir kuwa da ya ga Aliyu bashi da niyyar bud'e kofar ya koma nashi d'akin, ya zauna wayarsa ya zaro a aljihu ya kira number Teemarh kamar jiransa take ya kirawo ko ringing wayar bata yi ba Teemarh ta d'aga tare da cewa "Hello baby" Jabir cikin yanayin damuwa ya ce "Ina son kizo gida yanzun nan" ya fad'a tare da kashe wayar, murmushi Teemarh tayi sannan ta shiga wanka ta fito d'aure da d'an k'aramin towel ta shirya cikin wata 'yar yaloluwar rigar bacci wacce iya karta rabin cinyarta gaba d'aya rabin k'irjinta duk a bud'e yake shara-shara ce wacce ana iya ganin bra da pant d'in da ta saka wannan riga dai zan iya cewa da ita gwara babu, ko d'an kwali bata saka, ta baza gashin dokin da ta saka a kanta ya sauka har gadon bayanta, ta d'auki wata 'yar k'aramar jaka. Haka ta fito tana taku d'ay-d'ay ta nufi baki titi ta tari mai adaidaita tayi masa kwatancen gidansu Jabir suka d'auki hanya, suna isa ta sauka ta biya mai adaidaita kud'insa ta nufi gate d'in gidan ta shiga kwan'kwasawa mai gadi ya bud'e mata kofar 'yar k'aramar gate d'in dan daman Jabir ya sanar dashi zai yi bak'uwa, haka ta shiga gidan tana wani rangaji daman gidan ba yau ta saba zuwansa ba dan haka ta san ko ina a gidan, Babban falo ta shiga ta tarar babu kowa kai tsaye d'akin Jabir ta nufa tana tura kofar ta ga a bud'e take dan haka ta shiga tana girgiza ko ina na jikinta, a kan gado ta tarar dashi a kwance, ta nufi gadon tana zuwa ta hau kanshi tana sumbatarsa, duk da irin yadda yake cikin bak'in ciki sai da yaji zuciyarsa tayi wasai sabida yasan Teemarh zata bashi jin dadi, haka ya murgina Teemarh ta koma k'asa shi kuma ya hau kanta ya shiga kissing d'inta tare da zame rigar jikinta, ya shiga tsotsar ko ina na jikinta (ni kuma 'yar mutanan zazzau nace Allah ya kyauta Jabir anji kunya anyi asarar rayuwa) haka dai sukai ta shek'e ayar su. ***************************************************** *'BANGARENSU AMATULLAHI DA KHADIJATULLAHI* Kasancewar yau suka fara lecture basu wani dad'e a makarantar ba aka tashi wajen k'arfe 11:00am Amatullahi da Khadijatullahi suka fito daga ajin suna tafiya, Hafsa ce 'yar ajinsu ta nufosu da gudu tana cewa "Sisters! Sisters!! Sisters!!!" kasancewar bata san sunansu ba shiyasa ta kirasu da haka, gaba d'ayansu suka juya tare da tsayawa Hafsa ta k'araso tana murmushi ta mik'awa Amatullahi glass d'inta tare da cewa "kin yi mantuwa" murmushi Amatullahj tayi tare da cewa "nagode sosai" Hafsa ta ce "bakomai wallahi, amman meye sunan 'yan uwan nawa" Amatullahi ta ce "Ni dai sunana Amatullahi Shu'aibu mudassir" ta nuna Khadijatullahi ta ce "wannan kuma sunanta Khadijatullahi Abbakar mai yak'i" Murmushi Hafsa tayi tare da cewa "Am glad to meet you sisters (nayi farin cikin had'uwata da ku 'yan uwana)" Khadijatullahi wacce tun da suka fara magana ba ta ce komai ba sai yanzu saboda ta fuskanci Hafsa babu ruwanta tana da faran-faran "Mu ma munyi farin cikin had'uwa da ke, amman ke baki fad'a mana sunanki ba" Hafsa ta ce "Sunana Hafsa Alk'asim mai fata, amman idan babu damuwa zan iya zama k'awarku wallahi kawai ina ganinku naga kun shiga raina sosai", "ba damuwa" Amatullahi ta fad'a a takaice, haka suka nufi bakin gate d'in su uku Hafsa suna fita sai ga drivernta yazo d'aukanta, kallonsu tayi tare da cewa "Sisters kuzo mu rage mu rage muku hanya" babu musu suka nufi motar tare,domin kuwa sun san ko sun k'i yadda suka ga babu masu adaidaita a ta wajen dole sai anyi tafiya sosai kuma ga Khadijatullahi ba wata isasshiyar lafiya ce da ita ba, ba za ta iya tafiyar ba, Amatullahi ta ce tayi musu kwatancen unguwarta su har kofar gida, aka kai su suka sauka tare da yiwa Hafsa godiya Hafsa ta ce "Haba sisters menene na godiya ai mun zama d'aya" Amatullahi ta ce "Haka ne kam, sai mun had'u gobe" Hafsa ta ce "to shikenan" daga nan driver yayi wa motar key suka nufi gida, Amatullahi ta k'arb'i jakar Khadijatullahi suka nufi cikin gida, kai tsaye d'aki suka shiga bakinsu d'auke da sallama, Aunty Murja wacce take kan gado a kwance tana karanta wani littafi na *Na Hafsa Zubairu Sambo* me suna *Ikhlas* tashi tayi tana yi mush sannu da zuwa "Barkanku da dawowa 'yan k'annena" murmushi suka yi gaba d'aya Amatullahi ta zauna tana bawa Aunty Murja labarin Hafsa da kuma irin k'irkinta Aunty Murja ta ce "Ahhh gaskiya tana da kirki sosai Allah ya saka mata da mafificin alkhairi" suka amsa da "Amin" Khadijatullahi ta samu guri ta zauna a kan yaloluwar taburmar da take bage a d'akin wacce duk ta gama jin jiki ta yayyage, Aunty Murja ta shiga basu labarin littafin da take karantawa irin yadda Hilal yake wulak'anta Ikhlas wacce ta kasance tana mutuwar son shi kamar ranta, Amatullahi cike da jin haushi ta ce "Ai ni wallahi Aunty Murja babu ni babu maza shiyasa ni babu ruwana da saurayi namiji hmmm namiji kenan" Amatullahi ta k'arasa maganar cikin wani irin yanayi Khadijatullahi dai sun sosa mata inda yake mata ciwo hawaye suka shiga zubo mata shar-shar da sauri Amatullahi ta zo tana goge mata tana bata hak'uri "ki yi hak'uri besty kin ji komai zai wuce kuma insha Allahu Jabir sai yayi mummunar k'arshe" Khadijatullahi ta ce "Allah ya yarda ya ubangiji ka saka min" tayi maganar tare da k'ank'ame Amatullahi tana kuka ita ma Amatullahi kukan ta fashe dashi, Aunty Murja ce ta sauko daga kan gado tana rarrashinsu, har suka yi shuru abinci ta zubo musu suka d'an tab'ashi kad'an suka tureshi, rufe musu abincin tayi "gashi nan idan kun gama k'uncin tunda ku baku san k'addara ba sai ku ci" ta fad'a tare da juyawa ta koma kan gadon zuciyarta cike da tausayin k'anwar ta ta. ~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~ *'BANGAREN GIDANSU JABIR* Karfe biyar dai-dai goma dai-dai na dare girjin su Abba ya sauka a kano, Aliyu ya kira ya sheda masa ya sauka yana Airport haka Aliyu ya d'auki mukullin motarsa ya nufi Airport d'in ya d'auko Abba, a motar Aliyu ya shiga bawa Abba labarin duk abin da Jabir da mahaifiyarsu tare da Nihal suke aikatawa, kuma ya kwashe duk abin da Shahida ta fad'a masa a kan irin yadda Jabir d'in ya lalata rayuwar Khadijatullahi ya sana'ar dashi babu abin da ya boye masa, hankalin Abba ya tashi ransa kuma ya b'aci wato a gidansa za'a dinga yin irin wannan lalatar lallai zai d'auki mummunar mataki a kan Jabir, Nihal da mahaifiyarta su. A haka suka isa gidan kowan nan su zuciyarsa a jagule, Aliyu yayi parking a gurin da aka tanada dan ajiye motoci, Abbah ya fita daga motar ya nufi kofar da zata sadashi da babban falon gidan Aliyu na biye dashi, Abba yana tura kansa cikin falon ya hango wata yarinya daga ita sai wata arniyar riga wacce da ita da babu duk d'aya Jabir yana rumgume da ita yana shafa ko ina na jikinta ga Hajiya Asiya a zaune a falon tana kallonsu tana murmushi, gabansa yayi wani irin fad'uwa zuciyarsa ta fara kaiwa da komowa, cikin kakkausar murya Abba ya kira sunan Hajiya Asiya da k'arfi. "Asiya" Hajiya Asiya ta mik'e tsaye jikinta har rawa yake "shikenan yau ta faru ta k'are kashinta ya bushe" ta fad'a a zuciyarta Jabir kuwa da sauri ya ture Teemarh daga jikinshi jikinsa na b'ari, ita kuwa Teemarh ko a jikinta sai ma gyara jikinta da take yi, Abba kuwa yana zuwa ya d'auke Hajiya Asiya da wani wawan mari hagu da dama ji kake tas! tas!! tas!!! Sai da ya yi mata mari yafi goma sannan ya kama wuyanta ya shak'e shi sosai dan har ta fara kok'arin shid'ewa, Alhaji Mansur bashi da saurin fushi amman idan har ka sake yayi fushi to ka shiga uku domin bai iya fushi ba, Jabir cikin rawar murya ya ce "Abba karka kasheta Mami ce fa" ai bai san sanda yayi wurgi da Hajiya Asiya ba taje ta bugu da hannun kujera ta fad'i kasa sumammiya, Alhaji Mansur ya koma kan Jabir ya shiga dukanshi ta ko ina komai ya d'auka maka masa yake, Shahida ce ta fito daga d'akinta da gudu dan jin hayaniya a falon ganin Mami a k'asa Abba kuma yana d'aukar komai yazo masa a hannu yana makawa Jabir yasa ta kwalla wani irin ihu dai-dai lokacin Nihal ta shigo gidan cikin shigarta wacce sai ka rantse ba musulma ba ce, ai kuwa Aliyu yayi kanta da duka tana ihu ya gwara kanta a jikin bangon d'akin ta fad'i kasa kanta yana fitar da jini amman Aliyu bai kyaleta ba haka yayi ta dukanta kamar Allah ya aikoshi, Shahida ta rasa ya ya zata yi da ranta duk ta bi ta rud'e ruwa ta d'auko a fridge mai sanyi ta shek'awa Mami, ta farka a jijice tana kuka, Shahida ta koma gurin Abba tana rokonshi da ya dena dukan Jabir domin kuwa duk ya farfasa masa jiki ko ina na jikinsa jini yake fitarwa, da kyar ta samu Abba ya bar Jabir ta rik'eshi tana bashi hak'uri, Teemarh da taga gidan ya hargitse ta nufi hanyar fita da sauri domin kuwa tana tsoron kar kuma su juyo kanta, Abba cikin kakkausar murya ya tsayar da ita "Ke tsaya anan" tsayawa Teemarh tayi jikinta na rawa domin kuwa ta ji tsoron irin dukan da ya yiwa Jabir d'in, Shahida kuwa gurin Aliyu ta nufa "Yaya Aliyu dan Allah kayi hak'uri ka kyaleta please darling brother" tayi maganar cikin kuka, Aliyu ya je ya nufi kan kujera ya zauna zuciyarsa cike da bak'in ciki, da kyar Shahida ta iya d'aga Nihal dan kuwa Nihal ta gama galabaita bata iya tsotsi da jikinta numfashin ma dakyar take iya fitarwa, kusa da Mami ta zaunar da ita, ita ma ta zauna Abba kuwa yana tsaye cikin muryar da take nunawa yana tsantsar bakin cikin ya fara magana "nagode da irin yadda kuka mayar min da gida, gidan karuwai, amman ku sani daga yau ba zaku sake yin gangancin mayar min da gida na karuwai ba, ya nuna Jabir da yatsa sannan ya ce "nayi nadamar haihuwarka kuma nasan duk irin tarbiyyar da kake kai a yanzu uwarka ce ta dora ka a kai, dan haka nan da wata d'aya za'a d'aura aurenka da wannan yarinyar" ya nuna Teemarh da yatsa, wani irin farin ciki ne ya lillib'e Teemarh Jabir d'inta zai zama mallakinta, Jabir kuwa gabansa ne yayi mugun fad'uwar cikin muryar tashin hankali ya ce "Abbah dan Allah dan manzon Allah kayi hak'uri Teemarh ce fa, wallahi ba zan iya aurenta ba karuwa ce ta gama zubar da mutuncinta, duk wani d'an iska na garin nan babu wanda bai santa a mace ba, ni na yarda ka aura min duk wadda kaga dama amman dan Allah ban da Teemarh". Teemarh ta kalli Jabir tana cike da mamakin kalamansa yau Jabir ne yake kiranta karuwa kuma yake cewa ba zai aureta ba, bayan shine mutum na farko da ya fara saninta a 'ya mace cikin muryar kuka ta fara magana "Lallai Jabir tabbas na yarda da cewa kai d'in macuci ne mayaudari ne kai har kana da bakin da zaka kirani da karuwa bayan kai ne ka fara lalata min rayuwa Jabir wallahi kai ba mutum bane kai shad'an ne, ko shad'an ba zai tab'a aika irin wannan abin ba" cikin tsawa Abba ya dakatar da ita "Ke ya isa haka, kai kuma d'an uwarka aure kamar anyi an gama". Fita Teemarh tayi daga gidan tana kuka mai ban tausayi, Jabir ya nufi d'akinsa zuciyarsa cike da tashin hankali tabbas zai bi ko wacce iriyar hanya domin ya ga bai auri Teemarh ba, Abba ya juyo kan Nihal yana nunata da yatsa "kema d'an uwarki ki shirya aure zan miki domin ba zaki jawo min magana ba shegiya 'yar gidan gantalalliya" yana gama fad'ar haka ya juya ya nufi d'akinsa Aliyu da Shahida ma kowannan su ya koma d'akinsa aka bar Mami da Nihal, Nihal ta rumgume Mami tana kuka tana son tayi magana amman ta kasa, haka dai suka zauna su kad'ai a falon kowannan su cike yake da tsantsar damuwa da tashin hankali a cikin zuciyar. ~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~ *'BANGAREN KHADIJATULLAHI DA AMATULLAHI* Hankalin Khadijatullahi ya fara kwanciya kuma ta fara rage damuwa da tunanin da take yi, kullum a makaranta zaka gansu su uku ko a aji ma su uku suke zama a banci Hafsa tana matuk'ar jii dasu Khadijatullahi yau ma kamar kullum suna zaune a kujerun roba farfagiyar makarantar a k'asan wata bushiya, Hafsa ta kalli kayan jikinsu Khadijatullahi wanda ya kasance iri d'aya ta ce "Gaskiya fa bana jin dad'in abin da kuke min kuna ware ni a cikin ku" Amatullahi ta kalleta fuskarta d'auke da mamakin abin da Hafsa ta fad'a ta ce "Haba hafsiyy ya za'a yi mu ware ki a cikinmu bayan komai tare kuke yi da ke", Khadijatullahi ta ce "wai ma tsaya me muka yi miki da kika fad'i haka" Hafsa ta ce "gashi nan kuwa komai na ku tare kuke yi kama daga kaya, mayafi, hijabi, d'inki , takalmi, amman ni sai dai ku barni ni kad'ai kayana daban" murmushi suka yi gaba d'aya, Amatullahi ta bud'e baki zata yi magana wayar Hafsa ta hau ruri, Hafsa ta duba screen d'in wayar lokaci d'aya yanayin ta ya sauya hawaye suka fara ambaliya a fuskarta,l m hankalinsu Khadijatullahi yayi matuk'ar tashi cikin rawar murya Khadijatullahi ta ce "Hafsa me yafaru?" kallonsu tayi cikin tashin hankali ta fara magana "ina cikin tashin hankali sisters sabida irin muguwar yaudarar da namiji yayi min" Khadijatullahi da Amatullahi suka had'a ido gabansu yana fad'uwa, Amatullahi ta ce "Hafsa kenan kema kina nufin kin had'u da bakin cikin d'a namiji", Hafsa ta yi murmushi mai ciwo tare da cewa "Amatullahi kedai bari kawai", Khadijatullahi cikin sanyi murya ta ce "ke kuma me namiji yayi miki Hafsa" Ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa "Kamar yadda na fad'a muku sunana Hafsa Alk'asim mai fata kasancewar ni kad'ai ce a gurin iyayena suka d'auki son duniya suka d'ora min, na taso cikin gata babu abin da nake nema na rasa a lokacin da na kai shekara goma sha takwas, Yaya Safwan d'an k'anwar Abbana ya fara nunawa yana sona amman ni kuma ina basarwa, a hankali a hankali soyayyar Yaya Safwan ta ginu a cikin zuciyata har ina jin idan babu shi bazan tab'a iya rayuwa ba ko wuni nayi ban ganshi ba hankalina sai ya tashi inyi ta kuka har sai yazo na ganshi sannan zan sami nutsuwa, ganin irin tsantsar soyayyar da muke nunawa junanmu yasa su Abbana suka saka ranar aurenmu, kwatsam wata rana, ranar da bazan tab'a mantawa da ita a tarihin rayuwa ba Yaya Safwan yazo har gida ya sami Abbana ya fad'a masa wai bazai iya aurena ba, saboda ya gano cewa ni karuwa ce ina bin maza, kuma shi gaskiya bazai iya auren karuwa, lokacin da Abbana yazo ya fad'a mana abin da Yaya Safwan ya ce masa ban yarda ba hara sai da naje na sameshi har gida ya maimaita min irin abin da ya fad'awa Abbana, yayi min zagin cin mutunci nayi kuka nayi kuka har nagodewa Allah haka na kwaso k'afafuwana dakyar na dawo gida, Ummie mahaifiyar Yaya Safwan ta sako shi a gaba suka zo har gida amman Yaya Safwan ya ce shi ba zai tab'a aurena ba, amman in har aka tilasta masa ya aureni to tabbas a ranar da aka kai ni suzo su d'auki gawa ta dan wallahi kasheni zai yi, haka Ummie tayi ta kuka tana bani hak'uri Abbana ya ce mata babu komai suka tashi suka tafi, in takaice muku sisters har kwanciya nayi a asibiti ba na iya gane kowa,Allah ubangiji yasa dai akwai sauran kwana na a gaba, muka dawo gida Mommyna ta cigaba da rarrashina, ranar wata asabar sai ga mai gadin gidanmu ya shigo hannunsa rik'e da invitation card ya mik'awa Mommyna ya ce Yaya Safwan ne ya bada a kawo min nan da kwana uku masu zuwa za'a d'aura aurensa nayi kuka Mommyna tayi ta rarrashina, haka na k'arbi katin na yayyagashi nayi watsi dashi, na tashi na shige d'akina, bayan Auren Yaya Safwan da kusan wata hud'u shine aka samar min admission anan makarantar ana sauran kwana uku in fara zuwa makaranta ina zaune a cikin d'akina wayata ta shiga ruri ko dana duba sai naga number ce babu suna, na d'aga tare da yin sallama daga chan b'angaren ya amsa sallamar tare da kiran sunana gabana ne ya fad'i jin muryar Yaya Safwan da sauri na kashe wayar nayi wurgi da ita, na cigaba da yin harkokina a ranar sai ga Yaya Safwan yazo har gida, muna zaune a falo dani da Mommyna da Abbana muna hira yana zuwa gaban Abbana ya tsugunna yana kuka yana fad'ar wai ayi hak'uri da abin da yayi sharrin shaid'an ne, yasan yayi min sharri amman wallahi yana tsananin sona, takaici da bakin ciki ya lillib'e ni, ban san sanda na tashi nace ya tashi ya fitar mana daga gida, ya tashi zai k'araso gurin da nake na shiga d'akina da gudu tun daga ranar shine kullum sai ya kirani ni kuma bana d'agawa yanzu ma shine ya kirani" Hafsa ta k'arasa maganar tana kuka mai tsima zuciyar mai sauraro. Amatullahi ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya ita dai lamarin maza yana bata tsoro, kwata-kwata babu tausayi ko imani a zuciyarsu tashi tayi ta matsa kusa da Hafsa tana goge mata hawayen fuskarta tana rarrashinta, Khadijatullahi wacce fuskarta tayi sharkaf da hawaye ta ce "wai meyasa maza zazzalumai ne, gaba d'ayansu basu da imani macuta ne" tayi maganar tana sharce hawayen da suke ambaliya a fuskarta, Amatullahi ta ce "Hafsa ki yi hak'uri tabbas Yaya Safwan ya yaudareki kuma yayi miki k'azafi amman da zaki ji abin da Jabir ya yi wa Khadijatullahi zaki san abin da Yaya Safwan yayi miki ba komai ba ne" Hafsa cike da k'aguwar son jin abin da Jabir yayi wa Khadijatullahi ta ce "Sister Khadijatullahi kema kenan kin had'u da bak'in cikin namiji? Amman ke meya faru dake?" wani irin murmushin mai ciwo tayi sannan ta ce "Kamar yadda kika sani sunana Khadijatullahi Abbakar Mai yak'i iyayenmu mu biyu suka haifa daga ni sai Aunty Murja wacce ta kasance yayata kuma mahaifiyata, Mahaifina Abbakar mai yak'i yana da rufin asirinsa dai-dai gwargwado domin yana tafiye tafiye zuwa wasu garuruwar ya saro shanuwa ya dawo ya siyar dasu anan garin kano, wannan abin ne yasa gaba d'aya 'yan uwansa suka tsaneshi duk da cewa ciki d'aya suka fito da su, suke nuna mana tsana sosai har ya kasance bama zuwa gurinsu, mahaifiyar babbana da mahaifinsa sun rasu tun kafin babbana ya yi aure sakamakon gobarar da suka yi a gidan cikin dare gaba d'aya suka k'one, ranar wata lahadi ranar da bazan tab'a mantawa da ita babbana ya yi tafiya zuwa zaria domin saro shanuwa, sai gawarsa aka kawo mana ya rasu sakamakon hatsarin da suka yi motar da su babbana suke ciki wata gingimari ta daki motar babu wanda ya rayu dan har driver mutuwa ya yi, lokacin da innarmu ta ga gawar babbana ta yanke jiki ta fad'i ko da muka kai ta asibiti aka shiga da ita emergency room muna nan zaune sai aka fito da ita fuskarta a lillib'e da sauri na k'arasa gurin likitan jikina na rawa nake tambayarsa meyasa suka rufewa innata fuska, ku yi hak'uri domin Allah ya karb'i abinsa abin da likitan suka ce mana kenan, nan Aunty Murja ta fasa ihu ta zube a k'asa tana rusa kuka, nima naje kusa da ita na k'ank'ameta ina kuka, haka muka dawo gida mak'obtanmu suka shigo aka yiwa inna da babba wanka aka kai su makwancinsu na gaskiya, haka rayuwarmu ta cigaba da tafiya muna zaune a gidanmu daga ni sai Aunty Murja duk duniyar tayi mana zafi" A dai-dai nan Khadijatullahi ta tsaya saboda jin k'arar kad'ai k'ararrawar komawa aji "to bari in tsaya anan idan mun fito lokaci bai k'ure ba sai in cigaba idan kuma lokaci ya k'ure gobe idan Allah ya kaimu sai in k'arasa miki" Khadijatullahi tayi maganar cikin muryar kuka. Hafsa ta ce "Ko lokaci ya k'ure ma sai in bi ku har gida dan yau sai naji labarinki gaba d'aya sannan zan tafi gida" tayi maganar ita ma hawaye na kok'arin zubo mata share hawayen tayi sannan ta matsa kusa da Khadijatullahi ta kama hannunta ita da Amatullahi suka tashi suka nufi ajin zuciyoyinsu cike da bakin ciki. Wajen k'arfe shida suka tashi daga makarantar suka fito bakin gate Hafsa ta kirawo Mommy a waya ta ce mata yau ba zata samu dawowa da wuri da zata biya gidansu Khadijatullahi da yake Mommy ta san labarin su Khadijatullahi dan haka ta ce to shikenan bakomai, mai adaidaita suka tara ya kai su har kofar gida Hafsa ta biya kud'in, suka shiga gidansu Khadijatullahi amman abin mamaki basu tarar da Aunty Murja ba, Khadijatullahi ta ce "To ina Auntyna taje" Amatullahi ta ce "haba besty kila taje wani gurin ne" haka suka zazzauna a kan taburmar Hafsa ta ce "wallahi har na k'agu in k'arasa jin labarinki" wani murmushi mai ciwo Khadijatullahi tayi sannan ta ce "Yanzu kuwa zaki ji labarina gaba d'aya" Khadijatullahi ta fad'a cikin wani irin yanayi sannan ta fara magana. "ranar wata jumma'a muna zaune a tsakar gida ni da Aunty Murja lokacin kwanan su babbana hamsin da mutuwa sai ga Kawu Sani ya shigo gidan ko sallama babu mun yi mamaki sosai da ganinsa domin tunda su babbana suka mutu babu wanda yazo daga cikin 'yan uwansa wani matashin saurayi ne wanda kana kallonsa zaka san naira ta zauna wasu k'ananun kaya ne a jikinsa wanda ni a ganina dasu gwara babu, yake biye dashi a baya su Kawu lawan da Kawu Sanusi suna biye dashi a baya mik'ewa muka yi tsaye muna musu sannu da zuwa babu wanda ya amsa mana daga cikinsu sai ma kallon k'ask'anci da suke bin mu dashi, gaba d'aya na tsargu da irin kallon da wannan saurayin yake min, Aunty Murja ta nufi d'aki da niyyar d'auko taburma ta shimfid'a musu Kawu Sani ya dakatar da ita da cewa Ke Murja ina zaki je Aunty Murja ta ce taburma zan d'auko muku cikin tsawa ya ce ba zama ne ya kawo mu ba, mun zo ne mu sanar da ku cewar mun yiwa Khadijatullahi miji nan da sati d'aya za'a d'aura auren kuma ba kowane mijin ba sai wannan ya nuna wannan saurayi tare da cewa sunanshi Jabir ya ga Khadijatullahi yazo har gurinmu ya nuna yana son ya aureta, wani irin ihu na kwalla tare da cewa dan Allah Kawu kayi min rai wallahi bana son shi baka ganshi ba kalli kayan da ya saka fa, wani irin zafaffan mari Kawu Lawan ya wanke ni dashi wanda har sai da na rasa ganina na 'yan mintinue, da sauri Aunty Murja ta jawoni ta rumgumeni tare da dafe kan kuncina inda Kawu Lawan ya mareni, dan ubanki bakin ciki zaki yi mana shagiya mai mugun hali irin na ubanta, kai Jabir gata nan ko yau kake so a d'aura aure zan baka goyon baya d'ari bisa d'ari, wani irin shu'umin murmushi yayi sannan ya kalleni muka had'a ido ya kanne min ido d'aya, su Kawu Sani suka fita amman shi Jabir bai fita ba sai wani irin kallo da yake min wanda kana ganinsa zaka san na cikakkun 'yan bariki ne matsowa ya yi daf dani yana kok'arin kama min hannu nayi saurin komawa bayan Aunty Murja murmushi ya yi sannan ya ce dijarh kenan son kud'in wad'annan matsiyatan Kawun naki yayi yawa dan haka ki sani yanzu ina zuwa na sakar musu kud'i nace a yanzu nake son a d'aura mana aure da gudu zasu yarda kuma karki wani damu indai hannunki ne nan da sati d'aya zan yi duk abin da nake so a jikinki nasan dai kin san abin da nake nufi zan d'and'ani zumarki duk da cewa Auren wucin gadi zamu yi yana gama fad'ar haka ya fita daga gidan na rik'e Aunty Murja ina kuka sosai kamar raina zai fita, zaunar da ni tayi tare da rumgumeni a jikinta cikin muryar kuka nake ce mata Aunty Murja na shiga uku dan Allah ki yi duk yadda zaki yi kar in auri wannan d'an iskan, ita ma cikin kuka ta ce ba za ta iya hana auren nan ba saboda indai tayi yunkurin rama auren hakan zai iya jawo mana babbar matsala muna cikin wannan yanayin sai ga Amatullahi ta shigo nan na zai yana masa komai ita ma ta shiga yin kuka, haka dai muka kasance cikin tashin hankali har sati ya zagayo, da misalin k'arfe 10 na dare sai ga su Kawu Sani da Jabir kamar dai yadda suka zo ranar farko da yake lokacin zafi ne mun yi shimfid'a a tsakar gida muna shirin kwanciya da sauri na tashi ta koma bayan Aunty Murja jikina na rawa, Kawu Sani ya ce to kamar yadda muka zo muka sanar da ku satin da ya wuce za'a d'aura auren Khadijatullahi da Jabir to yau an d'aura kuma yanzu yazo tafiya da matar sa ne, kuka na saka mai had'e da ihu Amman haka Kawu Sani ya finciko ni daga bayan Aunty Murja ya tura ni gurin Jabir kamar jira yake ya kama hannuna ya rik'eshi sosai sannan ya nufi kofar fita, haka muka fita daga gidan ina tirjewa har muka isa gurin motarsa ya bud'e ya turani ya rufe motar ya koma mazaunin driver ya shiga ya ja motar mun yi tafiyar kusan awa biyu har muka isa wani babban gida gate mai gadi ya bud'e gidan a wajen da aka tana da dan yin parking yayi parking d'in motar ya bud'e motar ya fito ya zagayo inda nake a bayan motar ya bud'e ya jayo ni, yana jana ina tirjewa har muka isa wata kofa wacce ta sadamu da wani tafkeken falo kai tsaye wani babban bedroom ya nufa dani ya wurgani kan gadon sannan ya cire kayan jikinshi ya rage daga shi sai gajeran wando dakyar na iya tashi saboda yadda ya wurgani kan gadon sai da na bugu da bakin gadon haka Jabir yayo kai na ganin haka yasa na shiga kok'arin kare kai na ina d'aukar duk abin da yazo min hannuna ina wuraga mishi, tsayawa Jabir yayi cak ganin haka yasa na dena jifanshi ina nuna shi da yatsa ina cewa karka matso kusa dani, murmushi yayi tare da fad'awa kan gadon ya bage yana kallona, juyawar da zan yi in mayar da kwalbar da na d'auka kawai naji Jabir ya jawo ni na fad'a kan gado ya hau kai na yana murmushin mugunta yana cewa kinga ai kin shigo hannuna sai yadda nayi dake zan ci in more sosai yayi maganar yana kanne min ido, tureshi na shiga kok'arin yi ina kuka amman ina Jabir ya riga da ya sakar min nauyinsa gaba d'aya, Jabir bai d'aga ni ba har sai da ya rabani da budurcina, haka ya tashi ya shiga toilet yayi kusan mintune goma sannan ya fito d'aure da towel har sai da ya gama shiryawa sannan ya nufo gurin da nake kwance ya miko min wata farar takarda yana murmushi, zaki iya tafiya gidan ubanki, tashi nayi dakyar hawaye na bin kuncina na bud'e takardar _Ni Jabir Mansur jikamshi na sake ki saki uku_ abin da aka rubuta a takardar kenan wani irin kuka na saki ina kallonsa haka na saka kayana kamar jira yake in gama saka kayana ya dinga ja na har sai da muka fito farfajiyar gidan sannan ya ce bari in turo miki 'yan rakiya domin su rakaki har gida ko, ya zagaya bayan gida sai gashi da wasu karnuka sun kai guda biyar manya manya sai haushi suke nan karnukan nan suka nufo inda nake da mike dakyar domin tsiratar da kai na na shiga guda mai gadi ya bud'e min kofa da sauri na fita haka ina gudu karnukan nan suna bi na gashi dare yayi kowanne gida na huce a rufe ya ke babu kowa a unguwar daga ni sai wad'annan karnukan,har Allah ya kawo min wani mutum yazo wucewa a mashin ganin yadda nake gudu karnuka na bi na ya ce in hau mashin d'in haka na hau mashin d'in dakyar ya ja mashin d'in da gudu sai da muka yi nisa sannan yake tambayata daga ina nake? Ina kuka na sanar dashi komai ya tausaya min sosai dan haka sai da ya kai ni har kofar gida nayi masa godiya na k'arasa gidan, ina tura kofar na tarar a bud'e take na shiga gidan a inda muka bar Aunty Murja a nan na same ta na fad'a kanta ina kuka nan ta d'ago ni tana tambayata meyafaru cikin daren nan yanzu kusan k'arfe 2 kika dawo? na fad'a mata duk abin da Jabir yayi min ta rumgume ni tana kuka tana cewa ashe Auren wucin gadin da ya ce zaku yi wannan yake nufi Allah ya isa tsakaninmu dashi". Khadijatullahi ta kalli Hafsa wacce fuskarta tayi sharkaf da hawaye ta ce "Hafsa wannan shine labarin abin da Jabir yayi min, wanda ba zan tab'a mantawa dashi ba har abada" Hafsa cikin kuka ta ce "lallai Jabir ya cika zazzalumi,mugu,macuci kuma insha Allahu, Allah sai ya saka miki abin da suka yi shi da su Kawu Sani" Amatullahi wacce take kusa da Khadijatullahi tana kuka ta ce "Ai su Kawu Sani tun ranar da suka zo suka gama yin rashin mutunci Jabir ya tafi da Khadijatullahi suna fita suka had'u da 'yan fashi a hanya suka harbesu babu wanda ya rayu a cikinsu" Hafsa ta ce "Ai daman duk wanda ya zalinci wani Allah ba zai tab'a barin shi ba" sun jima suna zaune kowannan su zuciyarsa fal da bakin ciki had'i da tsanar duk wani namiji, a haka Aunty Murja tayi sallama ta shigo d'akin suka amsa mata Hafsa ta gaisheta "Ina wuni Aunty Murja" ta amsa mata cikin sakin fuska "Lafiya k'alau Hafsa ko?" Hafsa tayi murmushi ta ce "Eh" zama tayi a bakin gadon d'akin tana kallonsu "Hafsa wato saka ki suka yi a gaba suna kukan nasu da suka saba kenan" Murmushin yak'e kawai Hafsa tayi, kiran Mommy ya shigo wayarta tayi sallama Mommy ta amsa sannan ta ce "ga driver nan na turo shi zai zo gidansu Khadijatullahi ya d'auke ki" Hafsa ta ce "to Mommy" Daga nan suka kashe wayar wajen k'arfe 8:00 na dare driver ya aiko a kira Hafsa tayi wa Aunty Murja sallama su Khadijatullahi suka rakata wajen motar sannan suka dawo Amatullahi ita ma tayi wa Aunty Murja Sallama Khadijatullahi ta tashi zata rakata ta hanata ta ce "Haba besty bakomai kawai ki zauna ki huta" daga nan ta fita zuwa gida. ~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~ *'BANGAREN GIDANSU JABIR* Kwance yake a kan gadonsa yana ta juyi abin duniya ya taru yayi masa yawa yasan Abba sare baya tab'a yin magana biyu, anan take wata dabara ta fad'o masa, wani irin tsalle yayi tare da sakin wani irin shu'umin murmushi "tabbas wannan dabarar tayi kuma ita kad'ai ce zan yi nak'i auren Teemarh". Komawa yayi ya kwanta wani irin bacci mai dadi ya tafi dashi. *Washe gari🌸⚜️* Inna Larai ce zaune ita da Lado sun gama had'awa Amatullahi mak'irci gurin mahaifinta Malam Shu'aibu a kan cewa tana fita yawo kuma idan ta tafi makaranta ba ta dawowa sai chan dare wajen k'arfe goma za'a zo ayi parking d'in mota a sauketa a kofar gida, hankalin Malam Shu'aibu ya tashi dan haka ya buga sammako da dawo gidansa, ko da ya dawo ya tambaya ina Amatullahi suka ce tana cikin d'akinta, ya nufi d'akin yana kwad'a mata kira da sauri ta fito cikin wata doguwar rigar abaya plum colour ta yafa mayafin abayar rik'e da jakarta ta zuwa makaranta tayi kyau sosai sai kamshi take yi murmushi tayi ta tsugunna har k'asa ta gaisar da Abbanta, abin da ya bawa su Innah Larai mamaki sai suka ga Malam Shu'aibu yayi murmushi ya amsa gaisuwar da tayi yayi mata umarni da ta tashi tsaye ta mik'e, anan ya shiga tambayarta "Mamana meyasa idan kin je makaranta bakya dawowa da wuri sai goma na dare kuma ajiye ki ake yi a mota, kuma kika watsa Larai mai a fuska ita da Lado" cikin mamaki ta ce "Abbana ni kuma wallahi Abba kullum da wuri nake dawowa kuma ni da Khadijatullahi muke dawowa a adaidaita, kasan dai ba na kula kowane saurayi kai ma shaidata ne bare har in shiga motarsa wallahi zan iya dafa al'kur'ani ban tab'a shiga motar kowa ba kuma ban tab'a kai wa goma na dare a waje ba kuma Innah Larai da Lado sune suka ja duk abin da nayi musu anan ta fad'a masa duk abin da ya faru" ta k'arasa maganar tana kuka, anan Malam Shu'aibu ya shiga rarrashin 'yar tasa har tayi shuru ya kama hannunta suka yi hanyar waje, Amatullahi idanuwanta a kan su Inna Larai da fuskokinsu suka chanza saboda basu yi nasarar had'a uba da 'yar ba tasan tabbas sune suka had'a mata mak'ircin nan kuma wallahi ba za ta kyalesu ba sai ta rama (ni kuwa 'yar mutanan zazzau na ce su inna larai an taro match🤣) haka suka fita daga gidan mahaifinta na rik'e da hannunta a kofar gida suka tsaya mahaifina ta ya kalleta cike da so da k'auna "Mamana kiyi hak'uri nasan kina hak'uri zama dasu Larai daman nasan ni ba halinki ba ne, amman nasan yadda zan shawo kan abin" hannu ya zura a aljihu ta d'auko 2k (dubu biyu) ya mik'a mata sannan ya cigaba da magana "gashi nan kiyi amfani dashi dan ba lallai ki dawo ki same ni ba, zan koma chan companyn namu yanzu ma jirana ake yi" Amatullahi ta karb'a tare da yi masa godiya, ta nufi gidansu Khadijatullahi zuciyarta fal farin ciki domin kuwa taji dad'i da Abbana ta ya ce zai koma wannan zai bata damar had'a musu nata mak'irci amman kuma ita ba k'arya zata musu ba, a kan abin da suke aikatawa a gidan zata yi musu basu san dawa suke zancen ba ne, da wannan tunanin ta k'arasa gidansu Khadijatullahi ta tarar ita ma har ta gama shiryawa doguwar rigar abayar tasa komai iri d'aya haka suka yi wa Aunty Murja sallama suka nufi hanyar fita daga gidan. Suna fitowa suka yi sa'a ga wani mai adaidaita zai fita daga layin suka tsayar dashi suka shiga Amatullahi ta ce "Baba poly zaka kai mu ta gadon k'aya" kasancewar mai adaidaitar tsoho ne, shiyasa ta ce masa Baba, ya amsa mata da "to" suna isa Khadijatullahi ta bud'e jakarta ta d'auko naira d'ari biyar wacce ita kenan da ita zata mik'awa mai adaidatan Amatullahi ta dakatar da ita da cewa "to Hajiyata ai sai ki bari in biya ko?" ta fad'a tana mik'awa mai adaidatan naira d'ari biyar tunda daman a haka ake kawo su makarantar, suka shiga makarantar suna zuwa suka tarar da Hafsa har tazo abin da ya basu mamaki shine abayar da Hafsa ta saka komai iri d'aya da tasu babu abin da ya bambanta k'arasawa gurinta suka yi Amatullahi ta ce "Besty Hafseyy yau fa kinsa mun shiga mamaki sosai" murmushi tayi ta ce "Saboda kayan da nasa irin naku ko?" Khadijatullahi ta ce "Wallahi kuwa komai irin d'aya" Hafsa ta ce "ba abin mamaki ba ne ai, saboda tun jiya da muka je gidanku na ga abayar Khadijatullahi a kan gado kawai naji jikina ya bani ita zaku saka yau sai na k'are mata kallo Allah yasa naga kwalliyar jikin abayar duk da cewa ba duk na gani ba, shine muna tafiya na tsaya na saya a wani super market, murmushi suka yi gaba d'ayansu sannan suka nufi hanyar ajinsu domin an kusan fara lecture, basu dad'e da shiga ba Malam ya shigo suka fara lectures. •••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••• *'BANGAREN GIDANSU JABIR* Jabir ne tsaye a gaban madubi yana kallon kansa ya gama shirinsa tsaf cikin wasu kaya gajeren wando ne wanda ko guiwarsa bai kai ba sai wata farar riga wanda a bayanta an rubuta *JABIR D'AN TUWA* da manyan harafai gashin kansa ya kwanta luf sai shek'i yake yi, haka ya fito babban falo, babu kowa a falon dan haka ya nufi kofar fita daga falon, Jabir yana bud'e kofar falon Aliyu na fitowa daga d'akinsa kallo d'aya yayi masa ya d'auke kansa domin kuwa wani irin haushin Jabir d'in yake ji, shi kuwa Jabir bai ga Aliyu ba saboda ya riga ya fita daga falon, motarsa ya nufa ya shiga ya jaa ta da gudu mai gadi yayi saurin bud'e masa gate ya fita daga gidan wak'ar babban mawak'in yahudawa ya saka Ojoro wanda Omale yayi ya k'ure kid'an yana bin wak'ar a hankali, Club ya nufa yana isa farfagiyar club d'in ya tarar da wasu 'yammata su biyu a tsaye, fita yayi daga cikin motar ya nufi inda wad'annan 'yanmatan suke kai masha Allahu kyawawa ne ajin farko, sanye suke da wasu d'ammun riga da wando sun yafa wani d'an k'aramin mayafi, k'are musu kallo yayi bai tab'a ganinsu a club d'in ba "Yau akwai chilling kenan, wad'annan daga ganinsu sababbin hannu ne" ya fad'a a zuciyarsa a fili kuma ya ce "Hi bebs" cikin wata iriyar muryarsa ta shu'uman 'yan bariki, murmushi suka sannan suka ce Jabir d'an tuwa, bai yi mamakin jin sun fad'i sunansa ba domin kuwa Jabir yayi k'aurin suna gurin iskanci da shaye-shaye, murmushi yayi sannan ya ce "Sannunku bebs ya kamata ku fad'a min sunayenku domin nima nasani" d'aya daga ciki ta ce "sunana zulaihat amman zaka iya kirana da Zuly baby, sai ta nuna d'ayar ta ce wannan kuma sunanta Ummita" Jabir yayi kayatatcen murmushi sannan ya kama hannayensu yayi cikin hotel d'akinsa ya nufa ya bud'e sannan suka shiga gaba d'ayansu suka bage hajarsu a kan gado Jabir yana kwance a kan gadon su kuma sun kwanta a jikinsa suna shafa shi tare da kissing d'in jikinsa (tofa jama'a Jabir bai saduda ba, Allah dai ya kyauta) haka sukai ta aikata bad'ala har sai wajen k'arfen biyar da rabi sannan Jabir ya tashi daga kan su Zuly yayi wanka ya dawo ya fara kok'arin shiryawa Zuly da Ummita suka matso kusa dashi suka shiga shiryashi Jabir kuwa wani irin farin ciki ne ya kamashi tabbas wad'annan 'yammatan sun iya soyayya sai da suka gama tsaf sannan ya tashi ya bashi rabar 'yan dubu dubu ya fita daga d'akin Zuly da Ummita murna fal ciki dan tunda suke harkar bariki babu wanda ya tab'a basu dubu ashirin ma barantana har a basu rabar 'yan dubu dubu, shi kuwa Jabir ko cikin club d'in bai shiga ba ya shiga mota ya nufi layinsu Khadijatullahi. ~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~ *Poly🔱🏨* Wajen k'arfe shida dai-dai aka tashi daga makarantar, su Khadijatullahi suka fito daga aji Hafsa ta hango Yaya Safwan a jikin motarsa ya hard'e hannunsa a k'irjinsa yana ta baza idanuwana ya ga inda zai hango Hafsa gefensa wani kyakkyawan yaro ne wanda shekarunsa ba zai huce 6 ba,kamanninsa d'aya da yaron, Hafsa cike da mamaki had'i da bak'in ciki take nunawa su Amatullahi gurin da Yaya Safwan d'in yake ta ce "kun ga wanchan tsohon azzalumin yazo tare da d'ansa" Kallonsa suka yi sannan Amatullahi ta ce "gurinki ina ga ya zo" tsaki Hafsa ta ja sannan ta ce "wannan kuma shi ya sani" Yaya Safwan ya hango Hafsa tare da wasu yammata su biyu da sauri ya kamata hannun Khalid suka nufi gurin da suke, Hafsa ce a tsakiyarsu dan haka yana isa gurin yayi musu sallama "Assalamu alaikum" Khadijatullahi da Amatullahi ne suka amsa masa sallamar "Wa'alaikumussalam" suka yi gaba domin su basu damar yin magana, Hafsa ganin haka ita ma ta bi su da sauri Khalid ya kama hannun Hafsan yana cewa "Mommy ki tsaya Abbana zai yi magana dake dan Allah" kallon yaron tayi kamar ta ture yaron sai kuma ta tsaya Safwan ya k'araso inda suke ya dafa kan Khalid tare da cewa "Nagode yarona" Safwan ya bud'e baki zai yi mata magana ta dakatar dashi da cewa "yanzu ina tare da bestyna ka bari ka zo gida muyi magana" tayi maganar ba tare da ta kalleshi ba, tafiya ta fara yi Khalid yana biye da ita tsayawa tayi tana kallonsa ta bud'e baki zata yi masa magana Khalid ya rigata da cewa "Mommy zan biki dan Allah karki ce A'a" Hafsa ta ce "Ka tambayi Abbanka idan ya bar ka sai mu tafi" Safwan ya ce "Haba babyna ai kema Khalid kamar 'dan ki ne dan haka zaki iya tafiya dashi zan zo in d'aukeshi daga nan sai muyi maganar" kama hannu Khalid d'in tayi sannan ta nufi inda su Khadijatullahi suke d'an har sun fita daga cikin makarantar tana zuwa gurin da su Amatullahi suke ta watsa musu harara sannan ta ce "Shine zaku wani tafi ku bar ni" Murmushi Amatullahi tayi sannan ta ce "Ahh mun tsaya ai dole mu baku guri domin a ji dad'in bawa flower ruwa sosai". Khadijatullahi tayi dariya ganin irin yadda Hafsan take hararar Amatullahi fuskarta a murtuke, drivern Hafsa ne ya zo suka nufi motar gaba d'aya, haka suka nufi layin gidansu Khadijatullahi suna isa, tun kafin su fito daga motar Khadijatullahi take bin wata mota mai numfashi da ta gani a kofar gidansu mamaki ya cika zuciyarta, haka suka fito daga motar bayan sunyi sallama da Hafsa, Amatullahi ta kalli Khadijatullahi ta ce "besty yau bazan shiga gida ba ki cewa Aunty Murja zuwa anjima zan dawo akwai abu mai muhimmancin da zan yi ne" Khadijatullahi ta ce "to shikenan besty" Amatullahi ta nufi hanyar gidansu domin kuwa yau su Inna Larai sai ta tabbatar ta koya musu hankali, Khadijatullahi haka ta nufi kofar gidansu zuciyarta na buguwa, Jabir kuwa yana ganin Khadijatullahi ya bud'e motar ya fito idanuwansu suka had'u Jabir yana mata wannan Shu'umin murmushin nasa, Khadijatullahi tayi baya zuciyarta na bugawa idanuwanta suka firfito jikinta ya maka rawa tana nuna sa da yatsa tana kok'arin kiran sunan "jaa.....ja....jabir". Jabir ya nufi inda Khadijatullah take tsaye idanuwansa a kan cikinta "naji ance wai kina da ciki" sai Kuma yayi wani irin murmushin mugunta tare da ya mutse fuska sannan ya ce "Wayyo ni Jabir ina da k'arfin jini ace daga kwanci da mace sau d'aya har ta harbu ciki ya bayyana" cikin dakewa Khadijatullah ta fara magana "kaii tsinanne kayi gaggawar barin kofar gidan kafin na saka an jagaliya suyi min yaga-yaga da naman jikinka, shege d'an gidan shegiya" tayi maganar cikin zafin nama domin kuwa yau zata koyawa Jabir hankali zai san ita ma bawai k'anwar lasa ba ce Jabir ya kalleta sosai ya ga irin hucin da take kamar tsohuwar zakanya ya shek'e da wata iriyar dariya sannan ya ce "duk ki gama zagina karki ga nazo nan kofar wannan matsayacin gidan naku ki ce zaki yi min rashin mutunci ai kin san waye Jabir kuma kin san ba k'aramin aikina ba me wallahi yanzu a gaban kucakan 'yan layin naku nayi miki abin da ya faru ranar Asabar 26 ga wata march k'arfe 1 zuwa 2 na dare" wani irin a zababben mari ta wanke shi dashi hagu da dama sai da ta jera Masa sau biyar sannan fara magana "Eh tabbas nasan waye kai, Kai d'in ba kowa ba me in Banda dabba, Kuma ka sani idan a wanchan ranar kayi min ba yadda zan yi to yanzu baka Isa ba Jabir nima d'in nan da ka ke ganina ba k'aramar tantiriyar mara mutunci ba ce, wallahi Jabir na tsane ka na tsani duk wani Abu da ya dangance ka, Jabir idan baka bar nan kofar gidan ba zan iya kashe ka" magana take cikin wani irin yanayin bak'in ciki muryarta duk a shshshak'e, Jabir yaji matuk'ar jin zafin Marin da Khadijatullah tayi Masa domin kuwa tunda yake babu Wanda ya tab'a Marin shi, cikin zafin nama yake nuna Khadijatullah da yatsa Yana cewa "ba ni kika mara ba, wallahi ki jira zaki ga abin da zai biyo baya Kuma ki rubuta ki ajiye ni Jabir zan k'ara aurenki a Karo na biyu Kuma sai nayi miki abin da yafi Wanda nayi miki a baya" Yana fad'ar haka ya nufi motarsa ya bud'e zai shiga ya ji maganar Khadijatullah "Lallai Jabir sai yau na tabbatar Kai ka fi dabba ma, wa zaka aura?to Ina Mai tabbatar maka ni Khadijatullah na fi k'arfin ka, sai dai ka auri wannan shashashar uwar ta ka domin ita ce dai-dai kai, banza a jawo dak'ik'i Kuma insha Allahu sai kayi mutuwar da sai ana tattaro naman jikinka sai kayi mutuwar da ba za'a iya gane gawarka ba, na tsane ka na tsane shege Mai hali timakai" tana gama fad'ar haka ta shiga gida da gudu tana kuka, Jabir kuwa murmushi yayi domin kuwa yasan Yana zuwa gurin wad'annan kawun nata ya basu kud'i dole ko tana so ko Bata so a d'aura auren (ni kuwa 'yar mutanan zazzau nace Jabir ka makaro😂) Ya shiga motarsa ya ja ya nufi gidansu kawun Khadijatullah, ko da ya je ya ga gidannasu gaba d'aya an ruguje shi, Nan ya tambayi wani saurayi a kan meya faru aka ruguje gidan Kuma Ina mutanan gidan, nan saurayin ya fad'a Masa duk abin da ya faru sannan ya d'ora da cewa "yaran gidan Kuma tun ranar da aka kawo gawarsu Kawu Sani suka tattara suka bar garin babu Wanda yasan inda suka je" Yana gama sanar dashi ya juya yayi gaba Jabir ya daki motarsa yanzu shikenan sai ya auri Teemarh damar abin da yaso shine ya samu a mayar da aurensa da Khadijatullah hakan ne zai saka ba zai auri Teemarh ba, gashi duk Shirin da yayi Yana nema ya ruguje, haka ya shiga motarsa ya nufi gida zuciyarsa cike da tashin hankali, Yana zuwa gidan ya tarar gaba d'ayansu suna falo Abba sai zagaye yake a falon kallo d'aya zaka yi masa ka tabbatar Yana cikin fushi ga Hajiya Asiya a gefe sai kuka take yi ita da Nihal saboda yau Alhaji Mansur tunda ya tashi ya tambaya Ina Jabir? Aliyu yace ya ganshi ya fita nan ya saka Hajiya Asiya a gaba yana Mata bala'i a kan ita ta saka shi a kan wannan tarbiyyar, Kuma yake shaida musu cewa Aure zai k'ara domin ya samarwa 'ya'yansa uwa ta gari shine fa suke ta kuka ita da Nihal, (ni kuwa nace wallahi Alhaji Mansur ka min dai-dai👏😂) Shahida da Aliyu basu ji haushi ko bakin ciki ba domin kuwa sun San tabbas Abbansu Yana buk'atar macen da zata kula dashi saboda Mami Sam Bata damu da ta kula dashi ba ita dai kawai tana zaune dashi ne saboda Yana da kud'i. Jabir tunda yayi musu kallo d'aya ya watsar haka ya nufi d'akinsa yana cika yana batsewa kamar zai fashe, Abba ya k'are masa kallo daga sama har k'asa wai ace wannan d'ansa ne yake irin wannan shigar ya fita waje sai kace tsohon shaid'ani (ni kuwa nace Abba ai Jabir wallahi yafi shaid'an🤣) cikin zafin nama ya nufeshi gadan gadan ya jawoshi ya kifa masa mari wanda har sai da ya rasa ganinsa na tsawon dak'ik'a guda ya fad'a kan kujerar da take kusa da kujerar da Aliyu yake zaune, Abba ya ce "dan ubanka ina ka je tun safe sai yanzu ka dawo" Jabir ya d'ago ya kalli mahaifinnasa da rinannun idanuwansa ya ce "Club naje kuma......" Ai jin wani sabon marin da ya ji a fuskarsa yasa yayi shuru da maganar da zai k'arasa, haka Alhaji Mansur ya rufeshi, Aliyu ya tashi ya rik'e Abban yana bashi hak'uri shi kuwa Jabir tashi yayi sai da ya kusan shiga d'akinsa ya juyo ya kalli mahaifinnasa ya ja tsaki tare da tofar da yahu, nan fa Alhaji Mansur ya fusata yana kok'arin fusge rikon da Aliyu yayi masa, amman Aliyu ya riga ya rik'eshi sosai Jabir ya shiga d'akinsa ya saka mukulli, Abbah ya ce "to wallahi ka shirya goben nan za'a d'aura maka aure da wannan k'aruwar yarinyar shege gantalallan banza d'an iska mara kunya mara tarbiyya" Jabir duk yaji abin da mahaifinnasa ya ce dan da k'arfi yake magana, kwanciya yayi a kan gado yana tuna maganganun da Khadijatullahi ta fad'a masa "na tsaneka insha Allah sai kayi mutuwar sai ana tattaro naman jikinka sai kayi mutuwar da ba za'a iya gane gawarka ba" bai san meyasa ba wannan maganar ta tsaye masa a rai kuma ya ji son cikin da Khadijatullahi take dashi a zuciyarsa, tsaki ya ja tare da cewa "aikin banza" haka ya cigaba da sake-sake a cikin zuciyarsa. Abbah kuwa dakyar Aliyu da Shahida suka lallab'ashi ya shiga d'akinsa su ma suka shiga nasu d'akin, Mami da Nihal kuma abin duniya duk ya ishe su, haka dai suma suka nufi nash d'akin kowannan su zuciyarsa cike da bakin ciki da tashin hankali. •••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••• *'BANGAREN KHADIJATULLAHI* Tana shiga gidan da gudu tayi gurin da Aunty Murja take zaune tana tankad'an garin tuwo ta fad'a jikinta tana kuka cikin jijicewa Aunty Murja ta ce "Khadijatullahi meyafaru? Wani abun aka yi miki?" cikin kuka mai tsima zuciyar me sauraro ta fara magana "Aunty Jabir Jabir ne" zaro ido Aunty Murja tayi tare da cewa "A'uzubillahi minashshed'anir rajim Allah kayi mana tsari dashi, a ina kika ganshi" anan ta kwashe labarin duk yadda suka yi dashi ta fad'a mata, Aunty Murja ta ce "to aniyyarsa ta bi sa wallahi mun fi k'arfinsa, ki daina damuwa kin ji k'anwata ina tare dake ba zan tab'a bari ki wulak'anta ba" haka Khadijatullahi ta kwanta a jikin Aunty Murja, dakyar Aunty Murja ta iya k'arasa tankad'an sannan ta tureshi gefe d'aya, domin ji tayi ma ba za ta iya yin tuwon ba, daman akwai ragowar garin kwaki da sugar suka jik'a suka sha shi, suka shiga d'aki domin yin bacci haka suka kwanta kowanna su da abin da yake sak'awa a cikin ranshi. ```'BANGAREN HAFSA🥴``` Tunda ta shiga gida duk inda tayi Khalid yana biye da ita kamar jela, haka tai ta jiran Yaya Safwan domin ya zo ya d'auki Khalid su tafi gida amman har wajen k'arfe 10:30pm na dare babu alamar zuwan Yaya Safwan,ta kama hannunsa suka nufi b'angarenta domin suyi bacci, a kan k'aton gadonta suka kwanta Khalid ya rumgumeta sosai, yana tayi mata labarin makarantarsu "Mommyna kin ga a class d'inmu na fi kowa kok'ari, Abbana har keke ya siya min da nazo ta d'aya" Hafsa ta ce "Kai masha Allah yaron k'irki gaskiya dole Abbanka ya siya maka keke" murmushi Khalid yayi sannan ya ce "Mommy kinga an kusan fara exams idan nazo ta d'aya ke me zaki siya min?" Hafsa ta ce "Me kake so na siya maka?" Khalid ya ce "Ina son ki siya min waya na dinga yin games" Hafsa ta ce "to karka damu insha Allahu zan siya maka waya" cike da jin dad'i Khalid ya ce "da gaske Mommy" Hafsa ta ce "Eh mana, amman Khalid meyasa ka ke ce min Mommy?" Khalid ya ce "Abbana ne ya ce in dinga ce miki Mommy saboda kema Mommyna ce" shuru Hafsa tayi tana kallon yaron, "Lallai wato kitumurmurar da Yaya safwan yayi mata kenan, hmm Allah ya kyauta" tayi maganar a zuciyarta haka suka cigaba da yin hira har bacci ya kwashe su. ******************************************************* *'BANGAREN AMATULLAHI😂* Fans dole in dara anzo wajen fa🤣🤣Amatullahi iyayen bala'i bari muji yau da me zata jewa su Inna larai😂😂 Haka Amatullahi ta shiga gidan ta tura kai zata shiga tsakar gidan sai jin Inna Larai tayi tana cewa Lado "wannan yarinyar ba zamu tab'a barinta ba wallahi dole ne, mu kulla mata wata kitumurmurar da zata saka ubanta ya tsaneta" Lado ya ce "kamar me kenan?" Inna Larai ta shek'e da wata iriyar mahaukaciyar dariya sannan ta ce "za ka nuna cewa kana sonta zaka aureta, sai mu sanar da mahaifinta daga nan sai in fad'a maka shirinmu na gaba" Lado ya ce "Inna kin tabbatar wannan shirin naki zai saka mu rabasu" Inna Larai ta ce "rabuwa ta har abada kuwa". Amatullahi tayi wani gajeren murmushi sannan ta shiga gida da sallama sam bata nuna musu cewa taji abin da suka fad'a ba haka ta nufi d'akinta ta kwanta tana murmushi "Lado da Inna Larai kenan wallahi ni Amatullahi na fiku shaid'anci ina nan ina jiran ka furta ka na sona na yarda da soyayyarka daga nan wasan zai fara" Wayyo ni 'yar mutanan zazzau😂🤣😂Amatullahi da Lado za'a fara soyayya🤣🤣🤣ba zan iya daina dariya ba wayyo cicina😂😂😂Ummu Juwairiyya kina jin wata drama ko😅😅 *'BANGAREN GIDANSU JABIR* *WASHE GARI⚜️🔱* Misalin k'arfe sha d'aya na safe Abba ya fito daga d'akinsa ya shirya tsaf cikin wata tsadaddiyar shaddarsa teal blue ko minti biyu Abba bai yi da fitowa ba Aliyu ya fito daga d'akinsa shima shadda ya sa royal blue, Abbah ya ce "Aliyu yi da sauri mun makara fa, suna ta jiranmu" Aliyu ya amsa "to Abba" fita suka yi daga falon suka nufi wajen da aka tanada dan ajiye motoci, suka shiga kai tsaye suka nufi masallaci domin d'aura auren Jabir da Teemarh, masu karatu nasan zaku ce yaya aka yi Abba ya gano iyayen Teemarh har ya je musu da maganar d'aura auren yau, tun jiya da Abba ya shiga d'aki ya k'uduri aniyar d'aura auren Jabir gobe,Aliyu yana zaune Abba ya kirashi a waya ya ce "ya gano masa a ina yarinyar take? kuma su waye iyayenta?" Aliyu bai gane wace yarinyar Abba yake nufi ba sai da yayi masa bayani, sannan ya gane a daren Aliyu ya yi bincike suka yi sa'a kuwa gidansu Teemarh ba wani 'boyayyan gida ba ne, wani abokinsa mai suna Jafar da yake a layin yake shi ya nuna musu gidan, Aliyu ya kirasa a waya domin ya taimaka masa da binciken, da yake Jafar yana ganin Jabir yana zuwa kofar gidansu Teemarh anan yake sanar da Aliyu ai yasan yarinyar dan yana ganin Jabir d'in a gurinta kullum, a daren Abba da Aliyu suka je gurin Jafar ya rakasu har kofar gidansu Teemarh ko da mahaifin Teemarh ya fito Abba ya sanar dashi abin da ya kawosu Mahaifin Teemarh Alhaji Lamid'o yayi matuk'ar farin ciki domin daman bashi da wani buri a yanzu irin ya ga ya aurar da Teemarh domin wannan Harkar barikin da take yi yana matuk'ar kuntata zuciyarsa, haka suka yi sallama ya shiga gidan yake sanar musu Teemarh kuwa tayi farin ciki matuk'a kuma nan da kudiri niyyar sai ta kuntatawa Jabir sai ta gigita rayuwarsa zai san ita ya cewa karuwa haka tayi ta saka irin wahalar da zata bashi da kuma rashin mutuncin da zata dinga yi masa, wannan kenan. Taro yayi taro an d'aura auren Jabir da Teemarh a kan sadaki naira dubu d'ari haka su Abba suka biya ta gidan su Teemarh domin da ita zasu koma gidan, suna zuwa aka suka tarar har an shirya Teemarh cikin wani tsadaddan lace wanda Alhaji Mansur ne ya saka aka kawo mata kayan lefe akwati goma sha biyu, fuskarta a lillib'e da mayafi aka saka ta mota Aliyu wanda shi yake driving d'in ya ja motar suka nufi gida, suna isa mai gadi ya bud'e musu gate d'in tafkeken gidan suka shiga Aliyu yayi parking, Aliyu ya fito ya bud'ewa Teemarh motar ta fito fuskarta har lokacin a lillib'e take Abba na gaba suna fiye dashi a baya har suka shiga cikin babban falon gaba d'aya suna falon suna kallo Jabir ya dora k'afarsa a kan center table d'in falon, "Assalamu alaikum" suka yi sallama suka shigo, Shahida ce kad'ai ta amsa sallamar tare da yiwa musu sannu da zuwa, suka amsa mata da yawwa Jabir ya kallesu gaba d'aya sannan ya bi yarinyar da fuskarta take lillib'e da mayafi da kallon mamaki zuciyarsa cike da tambayoyi gabansa yana fad'uwa tsoro da firgici suka shigeshi mikewa tsaye yayi yana cigaba da kallon yarinyar, Mami ta kallesu sannan ta fara magana fuskarta kunshe da mamakin wacece wannan "Abban Jabir wacece wannan?" Wani irin kallo ya wurga mata domin gaba d'aya haushinta yake ji kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce "Matar Jabir ce Fatima" Jabir da ke tsaye cike da razana ya ce "Abba wace Fatima kake nufi, ba dai Teemarh kake son ka ce min ba" Abba yayi murmushi sannan ya kalli Teemarh ya ce " 'yata bud'e fuskarki domin su ganki" Teemarh kamar jira take ta yaye mayafin idanuwanta a kan Jabir tana yi masa wani irin kallon zaka gane kurinka, Jabir yayi baya jikinsa na rawa ashe daman jiya da Abba ya ce yau za'a d'aura auren da gaske yake shi gaba d'aya ya yi tunanin kawai fad'a yake yi, "Abba karka min haka dan la'ilaha illallahu ka ce min wasa ka ke min, Abba ba zan iya zama da karuwa ba" magana yake cikin yana yin tashin hankali, Abba bai bi ta k'ansa ba ya juya ya shige d'akinsa. Nihal kuwa gabanta ya shiga dukan uku uku domin kuwa tasan Abba zai waiwayo kanta dan baya tab'a furta magana ba tare da ya aikata ta ba, hawaye suka shiga zuba daga idanuwanta, ta k'ank'ame Shahida da ke kusa da ita tana cigaba da kuka, hankalin Shahida ya tashi ta shiga rarrashin 'yar uwar ta ta haka ta kama hannunta suka shige d'akin Nihal d'in, Mami ma jikinta a salub'e ta nufi d'akinta, Falon ya rage daga Aliyu sai Jabir sai kuma Amarya Teemarh. Aliyu ya kalli Teemarh tare da cewa "Aunty Fatima nikam zan huce Allah ya bada zaman lafiya, ina nan ina jiran babies da yawa nan da 'yan shekaru" murmushi Teemarh tayi sannan ta ce "To nagode Aliyu haidar" haka Aliyu ya huce yana kallon Jabir yana murmushin jin dad'i domin kuwa hakan ne ya kamace shi. Teemarh ta kalli Jabir sannan ta fara matsawa kusa dashi tana magana tana hurga masa harara ta had'e fuskarta kamar ba ita ce ta gama murmushi ba "Jabir d'an tuwa, kai k'aramin k'waro ne kuma zaka san nii Fatima Lamid'o ka cewa karuwa sai na gigita maka rayuwarka kai baka ji ma kunyar kirana da karuwa ba to kasan ni kai ne ka fara lalata ni dan haka dole ka zauna dani a matsayin matarka, kuma ina k'ara fad'a maka da babbar murya cewa idan ka k'ara kirana da karuwa to a wannan ranar zan nuna maka nii cikakkiyar karuwa ce zan bar maka mugun tab'o a rayuwarka" tana gama maganar ta shige d'akin Jabir d'in haka Jabir ya zauna dab'as a k'asa tabbas Abba ya auro masa masifa da bala'i amman kuma dole ya san matakin da zai d'auka dan ba zai tab'a zama da yarinyar da ya gama da ita ba, babu abin da bai sani ba a jikinta, haka dai ya d'auki key d'in motarsa ya fita daga gidan zuciyarsa cike da ba'kin ciki. *'BANGAREN KHADIJATULLAHI DA AMATULLAHI* Amatullahi ce ta fito daga d'akinta sanye da hijabi har k'asa kasancewar yau lahadi ne babu makaranta ta nufi hanyar fita Lado da ke zaune a tsakar gida shi kad'ai yana jiran fitowarta ya nufeta da sauri yana murmushi ya sha gabanta "K'anwata tun d'azu nake ta jiran ki fito, saboda akwai magana mai muhimmancin da nake so muyi da ke", "Lallai Lado anzo dai-dai gab'ar da nake so azo" ta yi maganar a zuciyarta a fili kuma ta d'an nuna alamun mamakia fuskarta kafin ta ce "Lado yau kuma da me ka zo?" Murmushi Lado yayi sannan ya ce "K'anwata babu da abin da nazo dashi sai alkhairi, domin a gaskiya ba zan iya b'oye miki ba tun ranar da kika gama secondary school d'inki naji soyayyarki ta shiga zuciyata amman ina tsoron in fitar miki dan karki k'i amincewa Amatullahi ina sonki sosai" Amatullahk tayi wani gajeren murmushi sannan ta ce "kana tunanin zan yarda da cewa kana sona? Bayan irin abubuwan da kake min hmmm Lado kenan" Lado ji yayi kamar ya kwad'a mata mari amman sai ya tuno indai yayi hakan shirinsu zai rushe dan haka sai ya da ke tare da cewa "Haba sweety da gaske nake yi ina sonki, idan kuma kina tunanin k'arya nake yi zan je in fad'awa Inna sai ta fad'awa Abba, ina ga hakan ne zai tabbatar miki da cewa da gaske na ke yi" Amatullahi ta ce "A'a ba sai ka yi hakan ba, zan je gidansu Khadijatullahi idan na dawo zamu yi magana" Lado ya ce "To shikenan, bari in taka miki" haka suka jera suna tafiya har sai da suka kusan zuwa gidansu Khadijatullahi sannan Lado ya koma gida zuciyarsa fal da farin ciki burinsu zai cika shi da Inna Larai, Amatullahi kuwa juyawa tayi tana kallon Lado tayi wata iriyar malalaciyar dariya sannan ta ce "Lado kenan ka ri ga ka fad'a tarkon Amatullahi, daga kai har uwar taka dai-dai nake da ku, d'an iska har da wani cewa sweety" ta ja wani tsaki tare da shiga gidansu Khadijatullahi, da sallama ta shiga d'akin "Assalamu alaikum" Hafsa da Khadijatullahi ta gani zaune a kan yaloluwar taburmar d'akin suka amsa mata sallamar a tare "Wa'alaikissalam" guri ta samu kusa da Khadijatullahi ta zauna tana tambayarsu "Ina Aunty Murja" Khadijatullahi ta ce "taje gidan Hajiya Mama" Amatullahi ta ce "Allah sarki Aunty Murjarmu tana kok'ari sosai wallahi" Hafsa ta ce "Wallahi kuwa sosai ma" Amatullahi ta ce "Besty ke kuma yaushe kika zo, ko kin yi tunanin yau akwai school" Hafsa ta ce "A'a wallahi besty kawai dai ba zan iya jira har sai gobe mu had'u ba shiyasa na zo" Murmushi Amatullahi tayi ta ce "Allah sarki besty mun ji dad'i kuwa" Khadijatullahi ta kallesu tana cewa "Ban baku labari ba jiya sai ga wannan d'an barikin Jabir ya zo gidan nan" Amatullahi ta wani daki bango tare da zaginsa sannan ta ce "uban me ya kawo shi gidan nan kuma shege dan gidan tambad'add'iya" Khadijatullahi ta kwashe duk yadda suka yi ta fad'a musu, Amatullahi ta ce "ai kuwa aniyarsa ta bi sa shege ai na gaba yayi gaba, wallahi da ace ban tafi ba had'u dashi sai na saka wallahi anyi mishi dukan tsiya na saka yara suyi ta jifanshi, nima ina nan muna shirya wata babbar drama a gidanmu" Hafsa ta ce "Wace iriyar drama kuma?" Nan Amatullahi ta kwashe duk komai ta fad'a musu bata b'oye komai ba ta d'ora da cewa "Sun yi tunanin zan iya fad'awa tarkonsu ne, ai yanzu wasan ya fara" Khadijatullahi da Hafsa ban da dariya babu abin da suke yi "Kai besty wallahi ke 'yar drama ce wato tsiyar da kika tafkawa Inna Larai shiyasa ranar kika ce wai na ganta amman ban gane ita ba ce" Khadijatullahi tayi maganar tana cigaba da dariya, Hafsa ta ce "Allah ya shiryeki besty kina zuba kamshi fa" Amatullahi ta ce "Wallahi ku tsaya ku ga yadda za'a buga wannan babban game d'in" Hafsa ta ce "besty muna biye da ke wallahi" Amatullahi ta ce "ya labarin yaya safwan kuwa?" Hafsa ta tab'a baki sannan ta ce "bai zo ba ya bar min yaronsa yau kuma da sassafe ya aiko masa da kayansa a akwati" Dariya suka saka sannan a tare suka ce "Mommy Hafsa" harararsu tayi sannan ta chanza hirar zuwa ta makaranta, sai wajen k'arfe 2pm na rana driver Hafsa ya zo ya d'auketa suka tafi gida, ko minti biyar Hafsa bata yi da tafiya ba sai ga Aunty Murja ta dawo suka yi mata sannu da zuwa ta zauna ta ajiye kwanon silban a k'asa sannan ta bud'e shi jollof d'in taliya ce da macaroni ga nama da yawa haka suka had'u suka cinye abinci, hira suka zauna suna yi abin gwanin ban sha'awa. *'BANGAREN JABIR ANGO DA AMARYARSA TEEMARH* Jabir kwata-kwata duk yadda yake tunanin Teemarh ta huce hakan domin gaba d'aya ta chanza masa, sam yanzu bata nuna masa soyayya kalaman soyayyar da take yi masa da yanzu bata yi idan ya shigo d'akin sai dai ta bi sa da wata muguwar harara kuma abin da yake bawa Jabir haushi shine Teemarh ta daina barin sa ya kwanta a kan gado sai dai a kan kujera ya ke kwana abinci kuwa idan an raba an basu bata ajiye masa sai dai ta ci iya cinta sauran ta kaiwa mai gadi, tana zaune a kan gado ta mik'e k'afa Jabir ya banko kofa ya shigo yana ta faman huci, Teemarh tayi masa wani wulak'antatcen kallo tare da cewa "Kai meye haka zaka shigo min d'aki kana wani huci kamar tsohon mahaukaci" Jabir ya gama fusata gaba d'aya jikinsa rawa yake yi ya ce. "Teemarh sai yau na tabbatar baki da mutunci, ashe ana baki abincina shine kike kai wa su wad'anchan matsiyatan, to wallahi baki isa ba tunda ba ubanki ne yake siyo abincin ba, shashasha 'yar gidan matsiyata" Jabir yayi magana yana cigaba da huci, Teemarh ta ce "To ai kai ne babban matsiyacin dan kuwa sun fika komai da komai wallahi, kuma da kake cewa ba mahaifina ne ya siya ba, na ji daman nace Abbana ne ya siya kuma haka nayi niyya su nake son na bawa abincin dan haka banga wanda ya isa ya hanani bawa su baba mai gadi abinci ba, kuma da kake ce min shashasha 'yar gidan matsiyata to sannu mai kud'i dan gidan k'aruna", Teemarh ta k'arasa maganar tana harararsa, Jabir ya gama fusata ya gama kaiwa k'arshe cikin zafin nama ya jayota yayi wurgi da ita kan kujera har sai da ta bugu da hannun kujerar goshinta ya fara zubar da jini, Jabir ya nufi kanta gadan-gadan Teemarh tayi saurin tashi tana nuna shi da yatsa "Jabir wallahi zaka san ni ka wurga kan kujera kuma...." bata k'arasa yin magana ba taji ya zabga mata mari har sau biyu hagu da dama ita ma kuwa tana d'agowa ta rama marin sai da ta jera masa sau hud'u sannan ta nufi hanyar fita da gudu tana kuka domin kuwa yau sai tayi wa Jabir sharrin da bazai tab'a mantawa da ita ba. A babban falo ta tarar da mutanan gidan gaba d'aya ta je gaban Abba ta zub'e tana k'ara saka sabon kukan, Abba ya kalleta ya ce "Fatima meya faru" cikin kuka ta ce "Abba na shiga uku Jabir zai kashe ni, wai kawai yana shigowa d'akin ya fara dukana ya gwara min kai na a bango" Jabir da ke tsaye yana jin duk abin da ta fad'a dan Teemarh tana fitowa shima ya biyo bayanta "Wallahi Abba k'arya take yi wai fa dan......"wani irin mari Abba ya d'aukeshi dashi yana fad'ar "Ok k'arya take yi wannan jinin da yake zuba daga goshinta fa, shima k'aryar ne ko kana nufin ita da kanta zata jiwa kanta ciwo" ya rasa abin cewa domin kuwa Teemarh tayi amfani da wannan ciwon wajen yi masa sharri, haka ya juya jikinsa a sanyaye ya nufi d'akinsa, Abba ya kalli inda Teemarh take durkushe ya ce "ki yi hak'uri kin ji Fateema, Aliyu kira doctor ya zo ya dubata" Aliyu ya Amsa da "to" haka ko minti d'aya Aliyu bai yi da kiran doctor d'in ba sai gashi yayi sallama ya shigo da yake a unguwar yake, bandegi ya saka ya had'e mata goshin sannan ya rubuta musu magungunan da zata dinga sha, yayi musu sallama ya koma gidan shi, Teemarh ta ce "Nagode Abba Allah ya saka da Alkhairi" Abba ya ce "Amin ya Allah" haka ta tashi ta bi bayan Jabir zaune ta tarar dashi a kan kujera ya zabga tagumi, Teemarh ta shek'e da wata iriyar mahaukaciyar dariya tare da tafa hannu tana cewa "Jabir kenan ai yanzu wasan ya fara tagumi yanzu ka fara yin shi, ai wallahi sai ka gane kurinka, banza kawai" Jabir yayi murmushi tare da cewa "Teemarh kenan nii Jabir d'an tuwa kika yi wa wannan abin ko? To wallahi zan nuna miki cewa nii babban d'an iska ne, karki ga wai ina tagumi kiyi tunanin wai tsoron ki nake ji, to wallahi ba'ayi macen da zan ji tsoronta ko kuma ta takura min ba, Teemarh ki rubuta ki ajiye Jabir yana nan sai ya rugu rayuwarki gaba d'aya" Teemarh ta zauna a kan kujera tana murmushi tare da cewa "Me kake cewa maimaita inyi hadda" tsaki ya ja ya fita daga d'akin kai tsaye gurin da aka tanada dan ajiye motoci ya nufa ya ja motar da gudu har yana kok'arin kwarfe mai gadin da motar Allah ya taimaka ya kauce masa (ni kuwa 'yar mutanan zazzau nace wai Jabir an had'u da k'arfen k'afa ko nace gaba da gabanta Aljani ya taka wuta😂). ~*BAYAN WATA DAYA*~ Cikin Khadijatullahi yana k'ara girma dan yanzu watansa hud'u, duk da cewa yanzu ta rage yawan damuwa sai dai idan abin da Jabir yayi mata ya fad'o mata ta shige b'and'aki tayi kukanta mai isarta ta wanke fuskarta ta fito, ga laulayi ya sakata a gaba duk abin da ta ci sai ya dawo shiyasa kwana biyu basa zuwa makaranta ita da Amatullahi saboda Amatullahi ba za ta tab'a iya zuwa makarantar ba tare da Khadijatullahi ba, Hafsa kuwa tayi matuk'ar damuwar rashin zuwa makarantar da basa yi, shiyasa ita ma ta daina zuwa ya zamana kullum ita da Khalid suna gidansu Khadijatullahi, Aunty Murja da ta ga abin nasu ba na k'are ba ne, ranar wata Asabar bayan sun zo suna ta hira ta zauna tare da fara yi musu fad'a "Gaskiya mun ba ni mamaki sosai, yanzu ace kun daina zuwa makaranta saboda Khadijatullahi bata da lafiya bata zuwa, to insha Allahu gobe kowannan ku ya shirya zaku koma makaranta dan na gaji da zaman da kuke kullum kuka kullum cikin damuwa kuke ba za ku iya d'aukar k'addara ba kenan" Amatullahi ta kalli Aunty Murja cikin yanayin damuwa ta ce "Aunty Murja ba zamu iya zuwa makaranta ba tare da Khadijatullahi ba" Hafsa ta ce "Wallahi Aunty Murja gaskiya Amatullahi ta fad'a ba zamu iya zuwa makaranta ba tare da besty ba" Aunty Murja ta ce "Ai shine nace ku shirya gobe har Khadijatullahi dukkanku makaranta zaku tafi" suka amsa da "to shikenan Aunty Murja". Haka kuwa aka yi washe gari kowannen su ya shirya suka fito su uku, kayansu iri d'aya motar Hafsa suka shiga drivernta ya ja su suka nufi makarantar, a makarantar ma haka Khadijatullahi tai-tayin Amai dan da har zasu dawo gida Khadijatullahi ta ce ba za ta koma gida ba har sai an tashi haka suka kyaleta har sai da aka tashi drivern Hafsa ya zo ya kai su har kofar gidan sannan ya nufi gidansu Hafsa, Amatullahi ta kama Khadijatullahi dan wani irin jiri take ji yana neman fad'ar da ita, suka shiga gidan kai tsaye d'aki suka nufa suka tarar da Aunty Murja tana share d'akin Amatullahi ta taimakawa Khadijatullahi ta kwanta a kan gadon, Amatullahi tayi wa Aunty Murja sannu da gida Aunty Murja ta amsa da "yawwa" Amatullahi ta ce "Aunty Murja zan koma gida zuwa anjima zan dawo naga jikin bestyna" Aunty Murja ta ce "to shikenan k'anwata sai kin dawo d'in" Amatullahi ta amsa da "yawwa" sannan ta fita zuwa gida. Tana zuwa gidan ta tarar da Lado a tsakar gida yana zaman jiranta domin kuwa yanzu soyayyar bogin da suke yi tayi nisa sosai,yana ganinta ya washe baki kamar da gaske sannan ya tashi ya nufeta yana cewa "Sweety shine yau kika yi tafiyarki baki fad'a min ba" Amatullahi ta kalleshi sosai A zuciyarta ta ce "ji shashasha,mahaukaci wallahi ina nan ina had'a muku tarko kai da wannan shakatafin uwar ta ka, za ku san dawa kuke zancen, kayi tunanin zan fad'a tarkonka ne" amman a fili sai tayi wani irin kayatatcen murmushi tare da cewa "Sorry my love wallahi hankalina gaba d'aya baya jikina su besty suna jirana shiyasa" Lado ya ce "Allah sarki to shikenan ba komai kin san bakya laifi a gurina" haka suka jera a kan taburma suka yada zango suna ta hira kamar wasu masoyan gaske (kai Allah ya kyauta miki Amatullahi). *'BANGAREN HAFSA* Suna isa gidan ta fito daga mota Khalid ya nufota da gudu yana cewa "Mommy oyoyo" rumgumeshi tayi tare da sumbatarshi a goshinsa kamar ance ta d'ago sai ganin Yaya Safwan yayi a kusa dasu ya rumgume hannuwansa a k'irji yana kallonsu yana murmushi, mik'ewa tayi sannan ta kama hannu Khalid dan har yanzu haushin Yaya Safwan d'in take ji sosai kuma bata tunanin zata iya k'ara soyayya dashi har abada, har sun fara tafiya Khalid ya ce "Mommy kin ga Abbana fa tun d'azu ya zo yana jiranki" Kallon Khalid tayi sannan ta ce "zaka zo mu shiga gidan ne ko kuma suturu zaka yi min" Khalid ganin yadda Hafsa ta chanza masa fuska lokaci d'aya har hawaye yana kok'arin zubowa daga idonta ya ce "Mommy kiyi hak'uri bana son kiyi kuka saboda ni, ki yafe min" Hafsa tayi murmushi sannan ta ce "To mu shiga ciki ko yaron k'irki" Duk abin da suke fad'a Yaya Safwan yana jin su, da sauri ya tsaya a gaban Hafsa tare da saka guiwoyinsa a k'asa cikin muryar tausayi ya fara magana "Hafsa nasan nayi miki abubuwa da dama na wulak'anta soyayyarki na muzguna miki, Hafsa gani a gabanki kiyi min duk hukuncin da kike so zan karb'eshi hannu bibbiyu amman dan Allah ki karb'i soyayyata a karo na biyu wallahi ina tsananin sonki sosai ina k'aunarki Hafsa dan Allah ki tausaya min, karki yi watsi dani dan manzon Allah Hafsa" wani irin kuka Hafsa ta saka tare da jan Khalid suka shige cikin gidan, kai tsaye b'angarenta suka shiga ta fad'a kan gado tana cigaba da kuka, Khalid da ke tsaye a bakin gadon ya zuba mata ido yana kallonta shima yana kukan (Allah sarki soyayya), shi kuwa Yaya Safwan tashi yayi ya shiga cikin motarsa dan ya dad'e da zuwa gidan ya fito zai tafi shine ya ga dawowar Hafsa, Mai gadin ya bud'e masa gate ya fita daga gidan zuciyarsa nayi masa zafi. *'BANGAREN GIDANSU JABIR* Yau aka d'aura auren Nihal da wani yaron Alhaji Mansur mai suna Salis, matarsa d'aya da d'ansa namiji sunansa Khamis, iyayen Salis talakawa ne kuma shi kad'ai ne suka haifa da yake Baban Salis yana gadi a ma'aikatar Alhaji Mansur shine ya nemi Alfarma da ya kawo d'ansa domin ya samu aikin yi shima Alhaji Mansur bai k'i ba ya amince aka d'auke shi aiki wannan shine takaitatcen tahirin Salis. Alhaji Mansur ya yaba da hankalin Salis shiyasa har ya bashi auren Nihal, lokacin da labari yazowa Nihal fad'uwa k'asa tayi sumammiya, Shahida ta d'auko ruwa mai sanyi ta watsa mata nan fa ta farfad'o ta rumgume Hajiya Asiya wacce take gefenta tana kuka, "Mami dan girman Allah ki cewa Abba zan dinga yi masa duk abin da yake so kuma ba zan sake fita daga gidan nan ba har sai idan shine ya bani umarni Amman dan Allah kice a fasa auren nan wallahi bana son shi" ta k'arasa maganar tana kuka kamar ranta zai fita, Teemarh take zaune tana kallonsu kawai ta ja tsaki ta kawar da kanta Abba ne yayi sallama ya shigo d'akin Aliyu da Ango Salis suna biye dashi a baya, Teemarh da Shahid suka amsa sallamar tare da yi musu sannu da zuwa zama suka yi suna amsa musu da "Yawwa" Salis kuwa tunda ya shigo yake kallon Nihal wacce take ta shan kuka zuciyarsa cike da farin ciki, Abba ya fara magana cike da farin ciki bayan yayi addu'o'i ya ce. "Nihal kamar yadda nasa aka shaida muku an d'aura aurenki yanzun nan to haka yake shiyasa ma nazo tare da mijinki domin ku tafi tare dashi" Amman yayi maganar cikin sanyayaryiyar muryarsa. Hajiya Asiya tana kuka ta ce "haba Abban Jabir a ina aka tab'a yin haka, ka aurar da yarinya ba tare da ka sanar da ita ba, kuma maimakon ka bari ta fito da zab'in ranta kawai sai ka aura mata wannan matsiyacin" Mami ta k'arasa maganar cike da bak'in cikin mijin nata. Alhaji Mansur ya ji matuk'ar zafin yadda ta ci mutuncin Salis d'in abin yayi matuk'ar k'ona masa rai amman ya da ke tare da cewa "Ai da ba'a san asalin balbala ba da sai ta ce daga madina take" yayi maganar yana harararta, Salis ma ya ji matuk'ar bak'in cikin yadda Hajiya Asiyan ta ce masa matsiyaci, amman zai tabbatar mata da cewa shi d'in matsiyaci ne a kan 'yarta, sai kuma yayi wani murmushi da ban san ma'anarshi ba. Hajiya Asiya kuwa mutuwar zaune tayi jin abin da mijin nata ya ce mata tun da take dashi bai tab'a yi mata gorin cewa ita 'yar talakawa ce ba sai yau, tsoronta d'aya kada yaranta su gane cewa ita 'yar talakawa ce dan kuwa idan suka gane ba za ta tab'a yafewa Alhaji Mansur ba, ganin babu wanda ya fahimci abin da Abba ya ke nufi yasa ta sauke ajiyar zuciya a b'oye, tare da godewa Allah. Muryar Alhaji Mansur ce ta dawo da Nihal daga dogon tunanin da take yi fuskarta shab'e-shab'e da hawaye, "Ke Nihal tashi taje ki shirya ki zo ku tafi domin k'afarki k'afar mijinki" haka Nihal ta mik'e jira na kok'arin d'ibanta ta fara tafiya tana dafa bango, Salis ya bi ta da kallo yana ra ya abubuwa da yawa a zuciyarsa, fuskarsa kuma har yanzu kunshe take da wannan murmushin nashi. Nihal tana shiga d'akinta tayi saurin shiryawa dan tasan halin Abbanta idan ta dad'e sai ya shigo har d'akin yayi mata dukan tsiya, cikin wata atamfa coffe brown ko mai bata shafa ba ta yafa mayafi ta fito, Salis ya mik'e suka yi sallama da Abba da Aliyu ya saka Nihal a gaba suka nufi gurin da yayi parking d'in motarsa, ya bud'e mata murfin motar ta shiga wajen mai zaman banza, sannan ya mayar ya rufe ya zagaya mazaunin driver sai da ya kalleta ya ga fuskar nan babu alamar murmushi ta had'e fuskar nan kamar bata tab'a murmushi a duniya ba. Salis yayi wani gajeran murmushi sannan ya ja motar mai gadi ya bud'e gate d'in gidan suka fita ya nufi gidansa gudu yake sosai a kan titin har suka isa gidansa, masha Allah gaskiya gidan ya had'u domin kuwa an zubda naira sosai wajen gina gidan, Nihal dai kallon gate d'in gidan take yi har mai gadi ya bud'e gate d'in gidan sannan suka shiga, a parking space yayi parking sannan ya fito ya bud'e mata murfin motar ta fito, hannunta ya kama da sauri ta shiga kok'arin kwacewa amman inaaa ta kasa saboda ya rik'e hannun nata sosai ta yadda ba za ta iya kwacewa ba, babu yadda ta iya haka ta barshi suka jera a tare suka shiga cikin madaidaicin falon, wata shirgegiyar mata ta gani a falon ga wani yaro shima k'ato gaba d'ayansu daga matar har yaron sun ba wa Nihal tsoro jikinta ya fara rawa. Talatu tana ganinsu ta mik'e dakyar fuskarta a murtuke ta fara magana cikin bala'i da masifa "to ma ci amana ka yaudareni wallahi Allah ya isa tsakanina da kai kuma wallahi sai na ga mai wannan shegiyar yarinyar ta fini dashi da har zaka aurota a matsayin matarka" nan ta nufo inda Nihal take gadan-gadan, Nihal kuwa ganin ta nufota ta k'ank'ame Salis tana cewa "Dan Allah kayi mata magana ni bana so" Salis ya rumgumeta sosai sannan ya kalli Talatu wacce ta kai hannunta zata jayo Nihal cikin tsawa ya ce "ke Talatu ki shiga hankalinki idan ba so kike yanzun nan nayi k'asa-k'asa da ke ba" yayi maganar yana nuna ta da yatsa. Talatu kuwa harara ta wurga masa tana gigiza ta kama k'ugunta da hannunta biyu, Salis ya nufi d'akinsa da Nihal a jikinsa Talatu tayi saurin zuwa ta tare kofar d'akin tana cewa "me zaka shiga kayi a ciki, wallahi baka isa ka kwanta da wannan yarinyar ba, dan ni ba zan had'a miji da wata shashasha ba, ni kad'ai zan zauna a gidan mijina" Salis yayi murmushi tare da cewa "Ai kin makaro, zaki ba mu hanya mu huce ko kuwa?" Talatu ta ce "baka ji mai nace ba" wani irin kallo Salis yayi mata sannan ya ce "to sannu uwata" ya bangajeta suka shige d'akin ya kullo ya saka key. Da sauri Nihal ta zame daga jikin Salis sannan ta zauna bakin gadon tare da dafe k'irji tana sauke ajiyar zuciya, Salis ya kalleta kamar zai yi dariya sai kuma ya had'iye tare da ce mata "menene? Kike faman sauke ajiyar zuciya sai ka ce wacce ta had'u da zaki", Nihal ta kalleshi ta ce "Wannan wacece Mamin ka ce?" ta tambayeshi tana kallonsa, bai yi niyyar yin dariya ba amman sai da maganarta ta bashi dariya zama yayi a kusa da ita yana cewa "Mamina kuma? Chabb wannan tayi miki kama da mahaifiyata, matata ce" zaro ido Nihal tayi tana kallonsa ido cikin ido, mamaki ya isheta "to shi wannan Salis d'in wane irin namiji ne da har zai auri wannan k'atuwar matar" ta fad'a a zuciyarta amman a fili ta tab'e baki tayi sannan ta ce "Amman lokacin da ka aureta tuwo ne ya mak'ale maka a ido ko?" harararta yayi sannan ya ce "A'a alkaki ne ya mak'ale min a ido ba tuwo ba" jawota yayi jikinsa tayi saurin zabura ta mik'e tsaye domin tayi wa kanta alk'awarin ba zata tab'a yarda Salis ya kusance ta ba saboda kwata-kwata baya cikin tsarin irin mijin da take so ta aura, dan Nihal halinta d'aya da Hajiya Asiya tana son ta auri mai kud'i kuma ta tsani talakawa. Salis ya gama fusata ganin irin yadda Nihal d'in ta zabura daman yana bin ta a hankali ne saboda mahaifinta amman ya ga ita so take ya bi ta ta kofar matsiyata, wata iriyar sha'awarta ce ta ta so masa ya fisgota da k'arfi ya kwantar da ita a kan gadon nan ta shiga dukanshi ya had'a hannayenta duka biyun ya rik'e ya sakar mata nauyinsa gaba d'aya, dakyar take iya numfashi saboda ya danneta sosai bata ma iya motsi, "daman ina so na nunawa mahaifiyarki ni cikakken matsiyaci ne" nan ya shiga cire mata kayan jikinta yana wurgi dasu, duk tsoro ya cika Nihal saboda abin da Salis ya ce "to me yake nufin zai yi mata?" tayi tambayar a zuciyarta, "Dan Allah yaya Salis kayi hak'uri ai ba ni bace nace maka matsiyacin ba, kuma da Mami ta ce ban......" bata iya k'arasawa ba ta kwalla ihu sabon wata iriyar azaba da tayi duk da cewa ita tana yawa maza da yawa sunyi sex da ita bata tab'a jin azaba irin ta hau ba, gaba d'aya jikinta ya shiga rad'ad'i, shi kuwa Salis ko a jikinsa bai san ma tana yi ba, ya cigaba da gana mata azaba iri-iri sai da yayi dan kansa ya gaji sannan ya tashi daga kanta a lokacin Nihal har ta kuma suma domin sumanta uku idan ta suma ya yayyafa mata ruwa. Wanka ya shiga ko da ya fito ya ganta kwance ya matsa kusa da ita ya tabbatar ta kuma suma yayi murmushi "kin farfad'o dan kanki ma, indai suma ne yanzu kika fara sumar ma" sannan ya shirya cikin k'ananun kaya, ya kunna t.v yana kallon sa hankalinsa kwance. *'BANGAREN YAYA SAFWAN* Yana isa gida matarsa ta taresa a bakin kofar shiga falon fuskarta cike da masifa take cewa "ina d'ana?" wani iri kallo yayi mata ji yake kamar ya zazzabga mata mari "bani guri in huce" yayi maganar fuskarsa babu alamar wasa, ganin haka yasa Safna matsawa ya huce har ya kusan shiga d'akinsa ya ji muryarta tana cewa "wallahi a yau d'in nan ba sai gobe ba zan je na d'auko yarona, dan ba zan bari wata shashasha wacce bata san ciwon haihuwa ba ta rik'e min yarona" Yaya Safwan cikin zafin nama yayo kanta, Safna ganin ya nufota gadan-gadan yasa ta fad'a d'akinta ta kulle, kofar d'akin ya nufa yana bubbugawa da k'arfi yana cewa "idan kika sake ki ka taka k'afarki ki ka fita daga gidan nan ta a bakin aurenki, idan kin d'auko yaron naki ki huce gidan ubanki dashi" yana gama fad'ar haka ya nufi d'akinsa ya shige, a kan gado ya kwanta zuciyarsa na cigaba da yi masa zafi. Safna kuwa kuka ta fashe dashi jin abin da mijin nata yake tana tsananin son Yaya Safwan tana kishinsa sosai, shiyasa ta ji duk duniyar nan babu wacce ta tsana irin Hafsa saboda ita ce take kok'arin rabata da farin cikinta, ta zabga tagumi tana cigaba da kuka mai tsima zuciya jinjina tayi da gadon tana saka-saka abubuwan da yawa a ranta har bacci ya d'ebeta. *'BANGAREN KHADIJATULLAHI DA AMATULLAHI* Kasancewar yau basu da lectures da yawa guda biyu ce dan haka suka dawo gida da wuri suna shiga gida suka tarar da Aunty Murja ta shirya zata je gidan da take yin aiki, Amatullahi ta ce "Aunty Murja zaki fita gidan Hajiya Mama ne?" Aunty Murja ta ce "Eh wallahi yau kun dawo da wuri lafiya dai ko?" Khadijatullahi ta kalli 'yar uwar ta ta cike da tausayawa sannan ta ce "Eh lafiya alhamdulillahi, yau bamu da lecture da yawa ne shiyasa" Aunty Murja ta ce "Allah sarki bari in je na dawo kar nayi ranar aiki" suka had'a baki wajen cewa "to sai kin dawo" fita tayi da sauri wasu hawaye ne suka gangarowa Khadijatullahi, Amatullahi tayi saurin dafata tana tambayarta "me yafaru" Khadijatullahi ta ce "besty ina tausayawa Aunty Murja sosai duk a kaina take ta wannan fad'i tashin duk ta hana kanta hutawa duk saboda ni ta k'arasa maganar tana kuka, Amatullahi ta rumgumeta tana bubbuga bayanta d'akin suka shiga a kan taburma suka zauna Amatullahi tana jan Khadijatullahi da hira har ta saki fuskarta. *'BANGAREN ANGO JABIR DA AMARYARSA* Teemarh ce zaune a kan kujera tana kallon wani film d'in hausa episode mai suna *So k'addarar zuciya* Jabir ne ya shigo d'akin har ya nufi hanyar shiga toilet sai ya dawo ya d'auki remote d'in t.v ya chanza tasha ya kai wata tashar wacce kawai sex ake yi da sauri Teemarh ta rintse ido tare da yin saurin juyowa tana kallon Jabir cike da takaici tana cewa "Wai kai wane irin mahaukaci ne" Kallonta yayi yana wani lumshe ido yana murmushi "menai miki kuma?", "ban sani ba" ta bashi amsa jikinta sai rawa yake yi saboda ganin abin da ake yi a tashar yayi matuk'ar motsa mata da sha'awarta. Jabir ya fara kok'arin jawo Teemarh jikinsa, ta tureshi da k'arfi Jabir nasan kayi haka ne domin ka tada min da sha'awa kuma wallahi ko zan mutu ba zan tab'a yarda na kwanta da kai ba har abada tayi maganar idanuwanta sun kad'a sun yi jajawur, Jabir wata iriyar mahaukaciyar dariya yayi sannan ya ce. "My Teemarh kawai ki bada kai bari ya hau, kar ki tsaya yanga nasan kin fi ni buk'atar hakan". Yayi maganar yana kashe mata ido d'aya, Teemarh kuwa harara ta watsa masa da idanuwanta da suka kad'a suka yi jajir "Allah kiyaye wallahi sai dai in mutu, amman ba zan tab'a yarda na kwanta da kai ba, da na kwanta da kai kwanta na kwanta da kare domin kuwa shi kare yasan abin da yake yi kai kuwa ba, abin da ka sani sai dabbanci". tayi maganar cikin wata iriyar murya mai rauni, Jabir kuwa ya gama fusata wato har Teemarh ta isa ta ce masa wai gwanda ta kwanta da kare da ta kwanta dashi, ai kuwa yanzun nan zai koya mata hankali yadda gobe ba za ta sake fad'ar wata mummunar kalma a kan shi ba, hannunta ya kama da niyyar ya ja a amman Teemarh ta kama hannun ta gantsara masa cizo ya saki hannun yana yar far da hannun, ta fita daga d'akin da sauri har tana tuntub'e. D'akin Shahida ta shiga jikinta sai rawa yake yi, Shahida tana kwance a kan gadonta wani irin mugun bacci ne yake kok'arin kwasheta, ta ji shigowar Teemarh da sauri ta tashi tana cewa "Aunty Fatima meyafaru? Ba ki da lafiya ne?" tayi maganar cike da tsantsar damuwa ganin yadda jikin Teemarh sai rawa yake "Shahida lafiyata 'kalau, ina son na shiga toilet d'inki" da sauri Shahida ta sauko daga kan gadon ta bud'e mata toilet d'in, Teemarh ta shiga sai da ta rage kayan jikinta sannan ta sakarwa kanta ruwan sanyi, a hankali ta fara samun nutsuwa, ta d'auki kusan rabin awa a cikin toilet d'in sannan ta mayar da kayan jikinta ta fito, in da ta sami Shahida a tsaye ta zabga tagumi, Teemarh tayi murmushi tare da dafata tana cewa "K'anwata lafiya kike kuwa?" Shahida ta ce "Aunty Fatima na ga kin shigo ne kamar ba'a cikin hayyacinki kike ba" Wani irin k'ayatatcen murmushi tayi tare da cewa "Haba kawai dai na d'an shiga cikin damuwana amman yanzu k'alau nake","To alhamdulillahi"Shahida ta fad'a tana murmushi, daga nan suka koma a kan kujera Teemarh ta cewa Shahida ta kunna mata tashar da ake So k'addarar zuciya domin ta cigaba da kallo, Shahida ta ce mata "to" sannan ta kai mata tashar ai kuwa tayi sa'a ba'a gama episode d'in ba dan haka suka zauna suna kallo. *'BANGAREN AMATULLAHI* Lado ne da Amatullahi zaune a kan taburma suna hirar su ta masoya, Amatullahi ta kalli Lado sannan ta ce "Baby wai kwana biyu na ga Innah tana d'aukar kajinka tana siyarwa,lafiya kuwa?" hankalin Lado yayi matuk'ar tashi domin kuwa haka Innah ta ce masa mutuwa kajin suke yi amman kuma yanzu Amatullahi ta ce siyarwa take yi, Amatullahi kuwa tana sa ne ta fad'a masa domin kuwa ta ji lokacin da Innar take ce masa kajin mutuwa suke yi, ita kuma ta k'uduri niyyar sai ta fad'a masa gaskiya domin ya san wacece uwarsa. Lado ya kalli Amatullahi ita ma shi take kallo ya ce "wai da gaske kike sweety Inna siyar min da kaji take yi?" Amatullahi ta ce "wallahi baby da gaske nake siyar da kajin take yi, amman ai nayi tunanin da sanin ka take siyarwa" hawaye ne ya fara zuba daga cikin idonsa yana fad'ar "Yanzu duk irin yadda nake yi wa Inna biyayya kuma nake nuna mata tsantsar soyayya, ina mata duk abin da take so dan ta ji dad'i amman tayi min haka ta yaudare ni" Amatullahi ta kawar da kan ta gefe tare da tab'e baki, zuciyarta fal farin ciki "wannan so min tab'i ne ma, yanzu aka fara wasan" ta fad'a a zuciyarta. Lado ya mik'e yayi waje zuciyarsa na k'una kamar garwashin wuta, ji yake kamar ya bi Inna gidan baffa Usmanu domin yau a chan ta wuni, "amman bakomai ai zata dawo ta same sa, dan kuwa ba zai yarda ba da wannan ha'incin ba" yayi maganar a zuciyarsa. Amatullahi kuwa Lado yana fita ta bi bayanshi da kallo tare da tintsirewa da wata iriyar mahaukaciyar dariya, "Kad'an ma ku ka fara gani wallahi, sai kun biya abin da ku kai min" ta fad'a a fili daga nan ta tashi tayi d'akinta ta kwanta tana rera wak'a zuciyarta fal da murna. *BAYAN SATI BIYU💥* Sauri sauri gudu gudu take ta isa gidan Hajiya Mama saboda yau ba ta samu ta fito da wuri ba, saboda jikin Khadijatullahi da yayi tsanani, tana isa gidan ta shiga da sallama d'auke a bakinta "Assalamu alaikum" Hajiya Mama da Alhaji Mansur suna zaune a tsakar gidan a kan taburma suna hirar su ta uwa da 'ya abin gwanin ban sha'awa suka amsa mata sallamar gaba d'ayansu "Wa'alaikumussalam" Aunty Murja ta k'arasa ta gaisar da su "Ina kwana Hajiya" Hajiya Mama ta amsa da "Lafiya k'alau Murjanatu yau kin dad'e nayi tunanin ba za ki zo ba ma" Aunty Murja ta ce "Wallahi Hajiya yau Khadijatullahi ce jikin nata yayi tsanani sosai shiyasa amman yanzu ta ji sauk'i", "Allah sarki, Allah ya bata lafiya" Hajiya Mama ta fad'a "Amin" Aunty Murja ta ce sannan ta kalli gurin da Alhaji Mansur ya ke zaune suka had'a ido shima gaisar da shi tayi sannan ta tashi ta shiga share gidan gaba d'aya sannan ta koma kitchen ta d'ebo kwanukan wanke-wanke sai da ta wanke su gaba d'aya suka fita tas, ta kife su gaba daya sannan ta dawo ta d'ora girki, wani littafi ta gani a kan window ta d'auke shi *Hajna* ta ga an rubutu da babba baki. Duba sunan marubuciyar tayi sai ta ga *Queen Nasmarh* wani irin farin ciki ne ya kamata domin kuwa tana neman littafin sosai, Hajiya Mama ta kalleta tana cewa "to sarkin karance-karance za'a fara kenan" sunkuyar da kanta Aunty Murja tayi sannan ta ajiye littafin ta shige d'akin Hajiya Mama, Alhaji Mansur ya bi ta da kallo yana sak'a abubuwa da yawa a cikin ransa. *'BANGAREN SAFWAN* Gaba d'aya Safna ta chanzawa Safwan ba ta yi masa girki ta daina kula dashi ta daina gyara gidan haka zata bar gidan kaca-kaca kamar babu mutane a cikinsa duk tana yin haka ne dan Safwan ya hak'ura da k'ara auran saboda ta san duk abubuwan da ta daina yi Safwan yana son su sosai musamman kulawa da tsafta domin Safwan mutum ne mai son kulawa kuma baya son k'azanta. Shi kuwa Safwan ya nuna mata kamar bai san abin da take yi ba duk da kuwa abubuwan da take yi suna matuk'ar k'ona masa rai, amman ya k'uduri niyyar sai ya koya mata hankali kuma aure ne zai k'ara shi babu fashi da zarar ya shawo kan Hafsa ta sauko, tunda daman Safna ce silar rabuwarsa da Hafsan, domin ta samu ta auri Safwan shine ta had'a baki da wani domin su b'ata Hafsan a gurin Safwan, daga k'arshe kuma Safwan ya gano gaskiyar. Zaune yake a d'akinsa yana kallon wani new a tashar *BBC Hausa* Safna ta banko kofar ta shigo tana huci kamar wata tsohuwar zakanya, Kallo d'aya Safwan yayi mata ya d'auke kansa ya cigaba da kallonsa, a kansa ta tsaya tana kiran sunansa "Safwan!Safwan!!Safwan da kai na ke magana fa" wani irin kallo yayi mata jin irin yadda take kiransa cike da gadara ji yake kamar ya tsinka mata mari amman kuma hakan ba halinsa ba ne dukan mace, "Safna ina matuk'ar hak'urin zama da ke, amman ina baki shawarar karki bari ki kai ni k'arshe domin kuwa komai zai iya faruwa", "Safwan ai baka nemi zaman lafiya ba tunda har ka na shirin auro wata shashasha, mai halin dabbobi, kuma..............." ai bata k'arasa ba sai ji tayi Safwan ya da ka mata wata iriyar tsawa wacce sai da ta jijita ta tayi baya da sauri jikinta har tsima yake yi. "Safna ki tausasa harshen ki, ka da ki sake ki zagi Hafsa domin kuwa yanzu nan zan yi miki abin da baki yi tunani ba, domin Hafsa rayuwata ce kuma zuciyata". Safna ta fita daga d'akin da gudu tana kuka, kai tsaye d'akinta ta huce ta fad'a a kan gado, maganar Safwan tana k'ara dawo mata a zuciya *Domin Hafsa rayuwata ce kuma zuciyata* tana kuka take cewa "wallahi Safwan ba ka isa ba ko ka k'i ko ka so da ni kad'ai zaka rayu". A haka dai bacci b'arawo ya sace ta. *'BANGAREN AMARYA NIHAL😂* Kwance take a kan gadonta hawaye yana zuba daga cikin idanuwanta ita dai lamarin Salis yana bata tsoro kullum idan ya kusanceta kafin ya gama sai ta suma kusan uku ko biyu, kuma gashi baya kusantarta sau d'aya sai dai sau uku safe, rana da kuma dare ko da kuwa ace yana d'akin uwar gidansa sai ya zo gurinta. Sallamar da aka yi ne ya dawo da ita daga dogon tunanin da ta shiga, a zabure ta mik'e jikinta ya fara rawa hawaye suka fara zuba daga idanuwanta "Dan Allah Yaya Salis yayi hak'uri wallahi ba na jin dad'i yau" murmushi yayi sannan ya ce "Menene na kuka babyna haba dan Allah ki daina kin ji" ba ta ce mata komai ba sai kukan da take yi, hawa kan gadon yayi sannan ta kai hannunsa wuyanta yana cewa "Me ke damunki zazzab'i ko kuma me?" Cikin rawam murya ta ce "Zazzab'i", "Wayyo Allah babyna sorry bari in d'auko miki magani ki sha, ko kuma tashi mu tafi asibiti" mik'ewa tayi da sauri ta d'auki mayafinta ta yafa, Salis ya tashi kenan sai suka ji a turo kofar da sauri Talatu ce tare da yaronta, fuskarta d'auke da fushi. "Munafikin Allah ta'ala shi ne kace min kana zuwa yanzu zaka dawo ashe gurin wannan shafaffiyar ka zo, bayan kuma kasan yau ba'a d'akinta ka ke ba", murmushi yayi sannan ya ce "Talatu kenan, to ai gurin matata na zo dan haka ba wani abu mugun abu na aikata ba", harara Talatu ta shiga wurga musu ji take kamar ta shak'e Nihal domin wani irin haushinta take ji, domin tun da ya aureta Salis ya rage yin sex da ita, wani lokacin ma ba'a son ransa yake kusantarta ba wanda a da ba haka yake mata ba, amman ta san maganinta zasu had'u da ita tana nan tana tara ta, Salis ta kalla sannan ta ce masa "Ka zo mu tafi to" Nihal ta kallesa sannan ta ce "Yaya Salis ka je kawai na ji sauk'i zan sha magani" ta fad'a sannan ta koma ta zauna a kan gadon, Salis ya fita daga d'akin tare da Talatu, Nihal tayi saurin zuwa ta kulle kofar ta saka key ta sauke ajiyar zuciya, tare da godewa Allah. Haka ta koma kan gadon farin ciki fal zuciyarta ji take kamar ta zuba ruwa a k'asa ta sha, yau dai ta huta da wannan jarababben namijin (ni kuwa nace nihal daga baya kenan wai anyi sadaka da karuwa🤣😂). *'BANGAREN ABBA* Tunda ya d'ora idanuwanshi a kan Aunty Murja ya ji gaba d'aya hankalinsa ya kwanta da yarinyar domin kuwa tana da saurin shiga ran mutane, yau kwana uku kenan amman kullum da tunaninta yake wuni a zuciyarsa, shiryawa yayi kyaf domin kuwa yau zai je ya fad'awa Hajiya Mama abin da ke cikin zuciyarsa ga me da Aunty Murja, motarsa ya shiga mai gadi ya bud'e masa gate d'in gidan ya fita daga gidan ya nufi gidan Hajiya Mama. Alhaji Mansur yana isa gidan Hajiya Mama yayi parking d'in motarsa ya shiga gidan bakinsa d'auke da sallama "Assalamu alaikum" babu kowa a tsakar gidan dan haka ya nufi d'akin Hajiya Mama ya shiga d'akin da sallama Aunty Murja ya gani zaune tana karatun wani littafi mai suna *Magajin masarauta* wanda *Murjanatu bintu Al'amin ce ta rubutashi* da sauri ta d'ago kanta suka had'a ido da ita zuciyar Alhaji Mansur ta shiga bugawa da k'arfi gaba d'aya ya shagala da kallo Aunty Murja ita kuma ganin irin kallon da yake mata duk gaba d'aya ta rikice ta kasa amsa sallamar da yayi sunkuyar da kanta k'asa tayi tana wasa da littafin da yake hannunta, Hajiya Mama ce ta fito daga bedroom d'inta ta tsaya tana kallon irin yadda d'an nata yake kallon Aunty Murja yana murmushi ko kifta idanuwansa ba ya yi, wani irin murmushin su na manya tayi tare da godewa Allah daman tana son ace d'an nata ya ga Aunty Murja ya ce yana sonta, kuma daman tana son ta yi masa magana a kan ya aureta, domin kuwa ta san zai more da mata kuma 'ya'yansa zasu taso cikin tarbiyya. Gyaran murya tayi Alhaji Mansur ya d'ago yana sosa kai tare da cewa "Hajiya ashe daman kina nan nayi tunanin ai bakya nan" harara ta watsa masa tare da cewa "To yau kuma da sabon salon da ka zo kenan, ka tab'a ganin ka zo gidan nan ba ka same ni ba" murmushi yayi tare da neman guri ya zauna yana cewa "A'a Hajiya ai nayi tunanin ko suna ki ka je", "A'a dambe na je ba suna ba" wannan maganar da Hajiya Mama ta yi ba k'aramar ba wa Aunty Murja dariya ta yi ba har ta kasa b'oye dariyar sai da ta yi ta a fili, Alhaji Mansur ya kalli yadda Aunty Murjan take dariya, ya k'ara jin ta shiga ransa domin ita kanta dariyar ta ta abin tsayawa a kalla ce "Murjanatu kema maganar Hajiya ta baki dariya kenan" ya fad'a yana kallonta, Aunty Murja ta yi mamaki domin jin Alhaji Mansur ya fad'i sunanta "to a ina yasan sunana?" ta fad'a a zuciyarta. Alhaji Mansur ranar da ya fara ganin Aunty Murja, ya ji Hajiya Mama ta kira ta da Murjanatu shikenan shima ya rik'e sunan, Kallonsa Aunty Murja ta yi sannan ta ce "Eh". Hajiya Mama ta samu guri ta zauna tana cewa "to ai sai kuyi ta dariyar, idan kun zare na kai ku dawanau" dariya Alhaji Mansur ya yi sannan ya ce "To mun dena Hajiya. yau fa zuwan nawa na musamman ne, na zo neman wani abu mai muhimmanci ne ban sani ba ko zan dace na same shi ya zama mallakina". Hajiya Mama duk da cewa ta san inda zancen sa ya dosa, amman sai ta nuna masa ba ta gane ma yake nufi ba ta ce "Wane irin abu ne wannan mai muhimmanci?" Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya kalli gurin da Aunty Murja take zaune suka had'a ido a karo na biyu, gabanta ne ta ji ya fad'i gaba d'aya ta ji zuciyarta tana bugawa da sauri, tashi ta yi sannan ta ce "Hajiya bari inje tsakar gida na k'arasa tankad'en na san yanzu ruwan ya tafasa" Hajiya ta ce "to shikenan" fita tayi da sauri ta zauna a tsakar gidan tana tankad'en, Alhaji Mansur kuwa Aunty Murja tana fita ya juyo yana kallon Hajiya Mama yana cewa "Hajiya Mama kin san dai irin zaman da nake da Asiya, gaba d'aya ta lalata min tarbiyyar yara Shahida da Aliyu ne kad'ai suka fita zakka, kuma uwa uba Asiya sam bata k'aunar 'yan uwana,Hajiya Mama ina buk'atar na k'ara aure tunda dai ina da halin da zan iya rik'e mace sama da d'aya, kuma ina son na auri Murjanatu idan ba'ayi mata miji ba domin na yaba da halayenta" Murmushi Hajiya Mama ta yi sannan ta ce "Alhamdulillahi daman ina da burin na ga ance yau kai ne zaka auri Murjanatu domin yarinyar tana da hankali sosai, kuma gaskiya ba na tunanin anyi mata miji saboda a yadda ta ba ni labari iyayensu sun mutu kuma ita kad'ai ce take kula da 'yan uwanta ita suke kallo a matsayin uwa kuma yayarsu" Alhaji Mansur ya ji matuk'ar dad'i ya ce "to yanzu Hajiya ya ya za'ai ina son nan da sati uku masu zuwa a d'aura auren saboda ba na son a ja wani dogon lokaci" Hajiya Mama ta ce "to ai sai ka bari muji ta bakinta ko?" Alhaji Mansur ya ce "Hakane kam Hajiya Mama" Hajiya Mama ta kira sunan Aunty Murja, ta amsa tare da ajiye tankad'en ta shigo d'akin har lokacin zuciyarta bata dena bugawa ba, zama ta yi a kujerar da ta tashi tare da sunkuyar da kanta tana cewa "Gani Hajiya" Hajiya Mama ta ce "Mansur ne ya zo min da wata magana wacce ta saka ni cikin tsananin farin ciki, da ina da dama da tun kafin ya rufe bakinsa zan basa abin da ya ke buk'ata amman ban da wannan damar shiyasa na ce bari in kirawo ki domin muji ta bakinki, Mansur yana so ya aureki kuma baya so a ja lokaci mai tsayi" Aunty Murja ta d'ago da sauri suka had'a ido da Alhaji Mansur wata iriyar kunya duk ta lillib'eta ta saka kanta a kan cinyarta tare da jan hijabinta ya rufe mata fuska, Hajiya da Alhaji Mansur murmushi kawai suka yi, Hajiya ta mik'e ta shiga bedroom domin ta basu guri su yi magana. Alhaji Mansur ya ce "Murjanatu ki d'ago domin ki ba ni amsa, kina sona? kuma zaki aure ni?" bata d'ago ba domin gaba d'aya ji ta yi kamar ta nitse a gurin saboda kunya "Dan Allah ki d'ago ki ba ni amsa kinji ki cire kunya domin in san in da na dosa" d'agowa ta yi kanta a k'asa dan ba za ta iya had'a ido da shi ba, murmushi yayi sannan ya ce "yawwa gimbiyata yanzu fad'a min na ji ra'ayinki" , "Eh zan iya auranka" abin da ta ce kenan sannan ta fita da sauri gidansu ta nufa wani irin farin ciki duk ya cika zuciyarta, Alhaji Mansur kuw murmushi yayi sannan ya shiga bedroom d'in Hajiya Mama yana cewa "to Hajiya Amaryata fa ta tafi, nima tafiya zan yi" ya fad'a yana zama kusa da ita. Hajiya Mama ta ce "Lallai Murjanatu wato tafiya babu sallama" Dariya sosai Alhaji Mansur yayi "haba Hajiya kiyi mata uzuri yau dan kuwa kunya ce ta sa ta tafi ba sallama" tashi yayi sannan ya ce "Hajiya nima zan huce", "to shikenan sai ka dawo". Fita yayi daga gidan ya shiga mota ya ja zuciyarsa cike da farin ciki, kai tsaye ma'aikatarsa ya huce. *'BANGAREN NIHAL* Zaune take a kan kujera tana chatting da Shahida tana mata korafin tunda ta zo gidan Salis d'in bata tab'a zuwa ba ko ta daina sonta ne?, Shahida ta shiga bata hak'uri da kawo mata uzurin yanzu tana zuwa aiki ne kuma bata dawowa da wuri shiyasa bata zo ba, amman zata kawo mata ziya nan zuwa wani satin insha Allahu Salis ne ya shigo ya ganta tana zaune tana chatting a bayanta ya tsaya, tare da rumgumota ta baya, a zabure ta mik'e ganin shi ne yasa ta sauke ajiyar zuciya, "kai Yaya Salis ka ba ni tsoro wallahi" murmushi yayi tare da cewa "Sorry baby nayi sallama ne na ji baki amsa ba, kin shagala da chatting", "Eh wallahi da Shahida na ke chatting shiyasa ban ji sallamar ba" matsawa kusa da ita yayi yana kok'arin jawo ta jikinshi, cikin muryar d take nuna alamar za ta yi kuka ta fara magana "Dan Allah Yaya Salis yau ka bar ni, dan manzon Allah", Kallonta yake ido cikin ido ya ce "wai me yasa kullum idan na zo gurinki domin ki biya min buk'ata ta sai kin wulak'anta ni" kuka ta fashe dashi tare da durkushewa tabbas tasan wannan duk alhakin Khadijatullahi ne yake bibiyarta Allah ya had'ata da Jarababben namiji, tsugunnawa yayi kusa da ita ya d'auketa cak be za me da ita ko ina ba sai kan gado, ya kwantar da ita domin shi ba zai iya jira wai ya bi ta ta lallami ba, haka ya fara tsotsar ko ina na jikinta ita kuma tana kuka, tabbas ta yarda alhak'i k'uikuyo ne gashi sun d'auki al'hakin baiwar Allah tun yanzu ita ta fara ganin sakamakon abin da Yayansu Jabir ya aikatawa baiwar Allah, haka Salis ya yi abin da ya kawosa ya d'agata ya shiga toilet ya yi wanka, ya fito d'aure da towel yana kallon inda Nihal d'in take sai wani irin nishi take ta yi matuk'ar ba sa tausayi, ta nufi inda take kwance ya d'agata ya d'auke ya kai ta toilet ya saka ta a cikin ruwan zafin da ya tara, ta kurma wani irin ihu tana kok'arin tashi zata fita daga cikin bahon wanka amman Salis ya rik'eta sosai kuma ya dannata cikin ruwan ta yadda ko ina na jikinta zai gasu sosai. Sai da Salis ya tabbatar ruwan zafin ya zama ruwan sanyi sannan ya fito da ita, a kan gado ya kwantar da ita yana mata murmushi, shiryawa ya yi cikin shadda kalar sararin samaniya sannan ya feshe jikinsa da turare ya yi mata sallam ya nufi ma'aikatarsu, Nihal kuwa ta ji dad'in ruwan zafin da Salis ya sakata domin yanzu ta ji jikinta yayi mata dad'i, doguwar riga kawai ta saka ta koma ta kwanta a kan gadon, ji tayi an banko kofar d'akin da sauri ta mik'e da kyar tana kallon wacce ta banko kofar Talatu ce ta shigo ,rik'e da wuk'a a hannunta sai shek'i take yi, Nihal ta tsorata sosai da ganin yadda Talatu ta shigo d'akin kuma da wuk'a, cikin rawar murya Nihal ta ce "Talatu mai za ki yi da wuk'a", "kashe ki zan yi kowa ya huta" Nihal jikinta ya kama rawa Talatu kuwa ta nufota Nihal ganin haka ya sa ta d'irgo daga kan gadon ta nufi kofar fita amman ta murd'a kofar ta k'i bud'uwa, wani irin ihu ta saka saboda yankan da Talatu tayi mata a baya har sai da doguwar rigar ta yage jini ya fara zuba kamar da bakin kwarya, a dai-dai lokacin Salis ya dawo saboda manta wata takadda da yayi yana shigowa ya ji ihun Nihal ya nufi d'akin da sauri sai jin muryar Talatu yayi tana cewa "wallahi yau ba zan bar ki ba sai na kashe ki" ya murd'a kofar ya ji a rufe take ya laluba jikinsa sosai yana da mukullin d'akin ya d'auko ya bud'e d'akin ya ga Talatu ta d'aga wannan wuk'ar tana kok'arin dab'awa Nihal da sauri ya finciko Talatu ta fad'i k'asa abin ka da mai k'iba sai ta fasa ihu,wani irin mahaukacin mari ya d'auketa dashi tare da janta ya fita da ita daga d'aki huci yake cike da jin haushinta ya fara magana "ki je gidanku domin ni ba zan iya zama da makashiya ba, na sake ki saki d'aya" Kuka Talatu ta fashe dashi, shi kuwa Salis ya juya d'akin Nihal, ya matsa kusa da ita yana kiran sunanta ba ta motsi sai yanzu ya ga irin yanka da Talatu tayi mata a hannunta da wuyanta d'aukanta yayi cak ya nufi motarsa da ita ya sakata a bayan mota ya kwantar da ita, ya ja motar mai gadi ya bud'e masa gate d'in gidan. Gudu yake a kan titin kamar zai tashi sama har ya isa wani katafaran asibitin Alhaji Mansur an rubuta *MANSUR SPEACIAL HOSPITAL* da manyan bak'i yana fitowa wasu nurses guda hud'u suka suka nufosa da gadon da ake d'aukar mara lafiya, ya bud'e bayan motar ya d'auko Nihal ya d'ora ta a kan gadon, nurses d'in suka tura gadon Salis yana biye da su a baya, Emergency room suka nufa da ita, Salis ya sami kujera ya zauna tare da zabga tagumi. *'BANGAREN HAFSA❤️* Hafsa zaune a kan gado tana shirya Khalid zai tafi makaranta, kallon yaron ta yi sosai tare da cewa "Wow sweetheart you look so cute" murmushi Khalid ya yi tare da cewa "Thanks Mommy i really appreciate" Hafsa ta ce "To yanzu mu je karka yi lating ko?" ta kama hannunsa suka fito falo, Mama suka tarar a zaune a falon tana breakfast suka gaisheta gaba d'ayansu, ta amsa cike da fara'a a fuskarta, zama suka yi domin yin breakfast, sai da suka gama sannan Hafsa ta kama hannun Khalid suka fita Ado driver ya bud'ewa Khalid d'in mota ya rufe ya shiga mazaunin driver ya ja motar, ita kuma ta koma falon ta zauna tana chatting kasancewar yau ba da wuri zasu shiga lectures ba. *'BANGAREN JABIR DA TEEMARH😹* Yau Jabir ya kudurce a zuciyar sai ya kwanta da Teemarh ko da kuma za ta mutu, duk da cewa yana zuwa club yana shek'e ayarsa da 'yanmatansa, zaune yake a kan kujera yana kallo ya kalli in da Teemarh take kwance saboda yau ta tashi da zazzab'i mai zafi tunda tayi sallar Asuba ta kwanta ba ta iya tashi ba, Jabir ya mik'e ya zo ya kwanta a kusa da ita idanuwanta a lumshe suke shiyasa ba ta san ya zo kusa da ita ba, hannunsa ya saka a kan wuyanta ya ji zafi rau kamar wuta ya kalleta tare da cewa. "Teemarh baki da lafiya ne?" Kai kawai ta gyad'a masa alamar "eh" dan ba za ta iya magana ba, murmushi Jabir yayi tare da cewa "wow abu yayi dad'i" Kayanta ya shiga cire mata, Teemarh kuwa dan k'arfin hali a haka ta shiga kok'arin tashi, amman inaaa ba za ta iya tashi da dan jikinta gaba d'aya babu kwari, tureshi ta shiga yi, amman Jabir ya hau kanta ya sakar mata nauyinsa gaba d'aya, a haka ya shiga tsotsarta har sai da burinsa ya cika a kan Teemarh sannan ya tashi ya shiga toilet domin yayi wanka, Teemarh kuwa kuka take yi mara sauti, tabbas sai yau ta sake yarda Jabir d'an akuya ne, bata da lafiyan ma ba zai kyaleta ba (ni kuwa nace amman Jabir ka cika mara imani, amman akwai ranar k'in dillanci). Haka Jabir ya fita ya kalli gurin da Teemarh take kwance tana kuka, ya saki wata iriyar mahaukaciyar dariya sannan ya nufi drower ya d'auko wata rigar ball da wani wando gajere ya saka sannan ya dawo gurin da Teemarh wanka ya shiga yayi mata da ruwan zafi sannan ya dawo ya shiryata cikin wata rigar bacci a kan gadon ya kwantar da ita ya kara bakinsa a dai-dai saitin kunnanta yana cewa "Teemarh 'yar gidan talakawa, sai ki je wannan matsiyacin uban naki ya kai ki, asibiti dan ni Jabir ba zan kai ki ba, dan an aura min ke ne domin na ji dad'ina, kuma kin ga wannan kurarin naki ya zama na banza kenan tunda gashi na kwanta da ke, wallahi ba zan tab'a kwantawa da kai ba, da na kwanta da kai gwanda na kwanta da kare" yayi maganar tare da fashewa da dariya, tashi yayi ya fita yana cigaba da dariya, Teemarh kuwa kuka ta fara yi, zuciyarta cike da bak'in ciki, wayarta ta samu ta lalubata ta ji ta a kusa da ita ta bud'e ido da kyar ta shiga kiran number Shahida. Sai da ta kirata kusan sau biyu amman taba d'auka ba, sai ana ukun ne, Shahida ta d'auka tare da yin sallama "Assalamu alaikum Aunty Fatima", "Shahida ki zo d'akina yanzu" abin da Teemarh ta iya cewa kenan dakyar, ko minti biyu ba'a yi ba sai ga Shahida ta shigo d'akin da Sallama d'auke a bakinta, ganin irin yanayin da Teemarh take ciki ne yasa tayi saurin fita falo gaba d'ayansu suna zaune suna hira har da Jabir, "Wayyo Mami Aunty Fatima bata da lafiya sai wani irin abu take yi" tsaki Mami ta ja tare da cewa "Shi ne ki ka taho duk a firgice kin razana ni kamar wacce aka yi mata mutuwa, to menene had'ina da ita, ta mutu mana ni ina ruwana" Abba ya bi Hajiya Asiya da wani irin mugun kallo ba tare da ya ce mata komai ba, sannan ya kalli Shahida tare da cewa "zaki iya kamata ki fito da ita" Shahida ta bud'e baki zata yi magana Jabir ya ce "Haba Abba wannan yarinyar fa munafika ce babu wani rashin lafiyan da take yi" Abba cikin fusata ya ce "Uwar ka ce munafikar, banza mara tausayi kawai" Shahida dai komawa d'akin Teemarh ta yi ta taimaka mata ta chanza kayan jikinta zuwa doguwar rigar atamfa, haka Shahida ta kamata suka fito falon Aliyu ne ya tashi domin ya kai su asibiti, Jabir ya bi Teemarh da kallo tabbas ta zame masa k'arfen k'afa amman dole ya rabu da ita dan ba zai iya zaman aure da k'aruwa ba, Shahida kuwa motar Aliyu suka nufa daman Aliyu ya ri ga ya bud'e musu murfin motar tun kafin su k'arasa dan haka duka shiga bayan motar gaba d'ayansu shi kuma ya shiga mazaunin driver ya ja su zuwa asibitin Abbansu, suna zuwa nurses suka zo da gadon d'aukar mara lafiya aka dora Teemarh suka shiga Emergency room da ita, Salis ne ya hango Aliyu da sauri ya nufeshi domin yanzu yake shirin kiran Abba ya sanar dashi abin da yake faruwa, Salis yana isa ya mik'awa Aliyu hannu suka yi musafaha, Shahida cikin jin dad'i take tambayar Salis d'in "Ango kasha kamshi, ina Amaryar take duk da cewa ni mai laifi ce a gurinta". Salis ya d'an yi murmushin ya ke sannan ya ce "Nihal ita ma tana nan asibitin" zaro ido Shahida tayi tare da cewa "Meya faru da Other half" anan ya basu labarin iya abin da ya sani, ya d'ora da cewa "yanzu nake shirin kiran Abba na sanar dashi sai ga ku kun zo" Hankalinsu ya tashi sosai Shahida ta shiga kuka tare da nufa inda Salis d'in ya nuna mata yake anan aka kwantar da Nihal, ta window d'akin ta lek'a nan ta hango likitoci kusan goma a kan ta suna kok'arin ceto rayuwarta, nan ta zub'e a k'asa tana fad'in "Meyasa za ki min haka Talatu ba ki kyauta min ba, me Other half tayi miki da zaki yi kok'arin kasheta". Aliyu ne ya k'araso inda take tare da d'aga ta yana rarrashinta da kalamai masu dad'i, Shi ma Salis d'in hak'uri yake bata haka dai tayi shuru, suka zazzauna a kan kujera Shahida ta d'auki wayarta zata kira Mami Aliyu ya ce karta kirata ta barta idan Nihal d'in ta farfad'o sai a kirasu a sanar dasu komai, kowannan su tagumi ya zabga zuciyoyinsu cike da damuwa. *'BANGAREN AMATULLAHI🤸🏽‍♀️😂* Inna Larai na dawowa daga gidan Baffa Usmanu ta tarar da Lado a kofar gida, ya ja ya tsaya sai huci yake yi kamar zai fashe, kallonsa tayi tana murmushi tare da cewa "jarumin d'ana ashe kana nan" Wani irin mugun kallo yayi mata tare da cewa "dole ki ce min jarumi tunda kina cuta ta, ai yanzu nasan komai kuma wallahi karki ga ke Innata ce sai kin biya ni, domin kuwa ban ga wanda zai ci min kud'i ya zauna lafiya ba" Inna Larai tayi masa kallon rashin fahimta tare da cewa "me ka ke fad'a ne, ban gane ba yi min bayanin yadda zan fahimta" Lado cikin hargagi da masifa ya ce "ina nufin kajin da kike zuwa kina siyar min, kina ce min mutuwa suke yi, to yanzu na san asalin gaskiyar" gaban Inna Larai neya fad'i "wa ya fad'awa Lado wannan maganar" ta fad'a a zuciyarta ba ta san maganar ta fito fili ba sai ji tayi ya ce "Amatullahi ce, ita ta fad'a min" Inna Larai ta kai kololuwa wajen k'ara tsanar Amatullahi "wato ita ce ta had'ata da gudan jininta, ai kuwa wallahi sai ta koya mata hankali" tayi maganar a zuciyarta. Huce Lado tayi ta shiga gida dan har mutane sun fara taru suna son jin ba'asin meya had'a 'da da uwar, shima Lado bin bayanta yayi da sauri yana cigaba da yin bala'i tun daga zaure Inna Larai take kwad'awa Amatullahi kira da sauri Amatullahi ta fito tana cewa "Waye wannan yake min wannan kiran mafarautan?", "Uban ki ne shegiya". Amatullahi ta mayar da fuskarta ta masu tausayi tare da cewa "Inna me nayi?" Inna Larai ta d'aga hannunta da niyyar marin Amatullahi, Lado yayi sauri ya rik'e hannunnata Yana cewa "Saboda ta fad'a min gaskiya shine zaki mareta, to wallahi karki kuskura" Amatullahi ta saka kuka tare da yin d'akinta tana shiga ta fashe da dariya "Kai Allah Mai yadda ya so, kad'an ma ku ka gani" hijabinta ta saka ta fito tsakar gida Babu kowa dan haka ta huce, ta fita daga gidan ta nufi gidansu Khadijatullah. Tana shiga ta tarar da Aunty Murja ta zabga tagumi tana ta murmushi, abin ya ba wa Amatullahi mamaki sosai, tayi sallama kusan sau biyar, Amman Aunty Murja ba ta ma san tana yi ba. K'arasawa tayi kusa da Khadijatullah wacce take zaune ita ma tana kallon Aunty Murja zuciyarta cike da tambayoyi domin ta ga kwana biyu Aunty Murja tana cikin farin ciki Amman da ta tambayeta sai ce Mata tayi bakomai, zama Amatullahi tayi kusa da ita suna kallon juna ta ce "bestyna meya faru da Aunty Murja ne, na ga na shigo Ina ta sallama ba ta amsa ba Kuma sai murmushi take yi" Khadijatullah ta ce "wallahi besty ban sani ba, nima yadda kika gan haka na ganta tun ranar da ta dawo daga gidan Hajiya Mama" Amatullahi tayi murmushi tare da cewa "to ko ta fad'a soyayya ne?","Ina tunanin haka gaskiya" Khadijatullah ta fad'a tare da kallon inda Aunty Murja take. Hannun Khadijatullah ta kama ta taimaka Mata ta tashi sannan suka k'arasa gurin da Aunty Murja take domin Amatullahi tana son tambayarta meke damunta zama suka kayi gaba d'ayansu kusa da ita, dafata Amatullahi tayi tare da Kiran sunanta "Aunty Murja" Firgita tayi ta d'anyi murmushi ta ce "Amatullahi yaushe kika zo","ban dad'e da shigowa ba, Aunty Murja me yake damunki?" Aunty Murja ta ce "me kika gani, bakomai","Dan Allah Aunty Murja ki fad'a mana kwana biyu Khadijatullah ta ce kina cikin farin ciki, Amman kin k'i fad'a mana mu ta ya ki farin cikin". Tabbas ba za ta iya b'oye musu ba, saboda su d'in jininta ne, Dan haka ta fara yi musu bayani "D'an Hajiya Mama ne, Alhaji Mansur ya ce Yana sona zai aure ni" wani irin tsalle Amatullahi tayi tare da furta "Alhamdulillah Allah Kai ne Allah, Auntynmu Ina ta ya ki farin ciki" ta fad'a tana rumgumeta sosai, Khadijatullah ma tayi farin ciki sosai a hankali ta furta "ina ta ya ki murna Auntynmu, Allah ya Baku zaman lafiya","Amin" Amatullahi ta fad'a haka sukai ta farin ciki dan ji suke kamar su zuba ruwa a k'asa su sha. *'BANGAREN SAFWAN DA HAFSA🥰* Tafiya take yana biye da ita a baya yana Kiran sunanta "Amrish Dan Allah ki tsaya, ki ba ni ko minti 1 ne nayi miki bayani" ba ta tsaya ba Kuma ba ta da niyyar tsayawa dan kwata-kwata ba ta k'aunar ganin Safwan a rayuwarta, wannan maganar da yake yi mata ji take kamar garwashin wuta ake watsa Masa a zuciya. To masu karatu nasan wasu zasu ce to menene Amrish d'in, to idan aka ce Amrish ana nufin masoyiya. Gabanta ya sha, hawaye suka fara zuba daga cikin idanuwansa, "Amrish" ya fad'a cikin wata iriyar murya, shuru tayi tare da kawar da kanta gefe, domin zuciyarta ta fara k'aryewa da ganin hawaye na zuba daga cikin idon Yaya Safwan d'in, ya cigaba da magana "Amrish wallahi ina sonki sosai, Ina k'aunarki, abin da ya faru a baya sharrin shaid'an ne da Kuma na matata. Da sauri Hafsa ta kallesa domin tabbatar da abin da ya ce, Kai ya gyad'a Mata alamar "Eh" sannan ya ba ta labarin duk irin mak'ircin da Safna tayi ta raba su "wallahi Amrish ban miki haka wai dan ba na sonki ba, Ina tsananin sonki sosai". Hawaye ne suka fara zuba daga idonta tare da cewa "Amman Yaya Safwan, nayi tunanin kafi kowa sani na, ka san ba zan iya yin irin wannan ba, ka ba ni mamaki ban yi tunanin haka daga gurinka ba", ta fad'a tana kuka Mai tsuma zuciya "na sani ban kyauta ba, ki yafe min insha Allahu hakan ba zai sake faruwa ba","Shikenan ya huce Yayana" wani irin farin ciki ne ya kama shi haka suka jera har wajen motarsa, sun dad'e suna hirarsu ta masoya daga k'arshe kuma suka yi sallama Hafsa ta koma gida zuciyarta cike da farin ciki, daman ta fito daga gidan ne saboda ba ta k'aunar su yi magana da Yaya Safwan d'in shine ya biyo ta, d'akinta ta shiga ta tarar Khalid ya kwanta Yana bacci fad'awa kan gadon tayi ta lula duniyar soyayya. *WASHE GARI☄️* Nihal ta farfad'o Shahida ta kira Hajiya Asiya ta fad'a mata babu shiri ta fito kamar wata korarriya tana zuwa Asibitin ta rumgume Nihal d'in tana kuka "yarinyata" Teemarh wacce take tsaye dan yanzu ta ji sauk'i tun da aka yi Mata allurai da k'arin ruwa ta Warware sosai, Baki ta tab'e Hajiya Asiya ta kudurce a zuciyarta Nihal ba za ta sake komawa gidan Salis ba sai ya saketa sai dai duk abin da zai faru ya faru. Alhaji Mansur ne yake tafiya cikin motarsa a nutse yake tukin gidan Hajiya Mama ya nufa domin shi bai San ma abin da ya faru da Nihal d'in ba, Yana zuwa ya tarar da Aunty Murja tana wanke-wanke yayi sallama tare da ja ya tsaya Yana kallonta, tabbas nan da sati mai zuwa zai yi kok'arin ganin an d'aura aurensu domin ba zai iya hak'ura ace har sai sati uku ba, Aunty Murja ta d'ago suka had'a ido dashi murmushi ya sakar Mata tare da cewa. "Amincin Allah ya k'ara tabbata a gareki ma'abociyar nutsuwa da hankali kyakkyawar Matata wacce nake saka ran a cikin wannan satin zan fara tunanin samun 'ya'yana daga gareki". Murmushi kawai tayi tare da sunkuyar da Kai, Amman kalmar da ta tsaya mata ita ce da Alhaji Mansur d'in ya ce a cikin wannan satin zai fara saka ran samun 'ya'ya, to shine ta rasa gane meyake nufi. 'yar k'aramar kujerar k'arfe ya d'auko ya ajiye kusa da ita ya zauna, da sauri ta kallesa domin kuwa gurin da rana sosai "ka tashi daga nan akwai rana sosai, karka sami matsala","A'a na k'i" ya fad'a yana mak'e kafad'a kamar wani k'aramin yaro, abin ya ba wa Aunty Murja dariya sosai, tsayawa yayi Yana kallonta tare da cewa "Murjanatu dariyarki tana saka ni nishad'i fi ye da yadda bakya tunani". Kallonsa ta yi sosai ta ce "Kai ne ai ka ke ba ni dariyar, nagode sosai Kuma......" Sai kuma tayi shuru tare da yin wasa da zoben hannunta, Alhaji Mansur ya k'ura Mata ido tare da cewa "Kuma me?","Bakomai"ta bashi amsa har lokacin tana wasa da zoben hannunta, "ba za ki fad'a min ba ko?", Kai ta girgiza Masa alamar "A'a". Mik'ewa yayi fuskarsa ta chanza zuwa yanayin fushi ya nufi hanyar waje, da sauri Aunty Murja ta bi bayansa a gabansa ta tsaya tana cewa "Dan Allah ka yi hak'uri","to fad'a min kuma me?" Aunty Murja ta ce "Daman godiya kawai zan maka" ta fad'a dan ba za ta iya fad'a masa abin da ke ranta ba, tana jin tsananin kunyarsa. "Shikenan nagode miki sosai, kuma nasan matsayina a gurinki tunda kin k'i fad'a min kin nuna min ban kai matsayin da zan san abin da ke ranki ba" Yana gama fad'ar haka ya huce ya fita motarsa ya shiga ya ja ya bar unguwar, Aunty Murja tsugunnawa tayi a k'asa tare da fashewa da kuka gaba d'aya haushin kanta take jii a kan meyasa ba ta fad'a masa ba, har ta bari yayi fushi da ita. Hajiya Mama kuwa duk abin da suka yi tana jin su, domin kuwa tana cikin toilet ne ta shiga kama ruwa kuma tsakanin toilet d'in da inda suke babu nisa, murmushi tayi sannan ta koma d'aki ba tare da ta bari Aunty Murjan ta ganta ba, a zuciyarta tana cewa "sai yanzu Mansur zaka san zakai aure". Ita kuwa Aunty Murja haka ta gama shan kukanta sannan ta tashi ta k'arasa wanke-wanken ta kifesu a kwanbo sannan ta shiga d'akin Hajiya Mama ta yi Mata sallama ta fito ta nufi gida zuciyarta a cunkushe. *POLY🚴🏽‍♀️🏦* Zaune suke su uku kamar kullum komai nasu iri d'aya abin gwanin ban sha'awa, Hafsa tana ba su labarin yadda suka yi da Yaya Safwan, Amatullahi tayi murmushi tare da cewa "Ahhh Lallai lovers ina ta ya ki murna k'awata, ki ce mun kusan shan biki" murmushi Hafsa tayi tare da cewa "insha Allahu" Khadijatullah ta ce "Nima ina ta ya ki murna k'awar arzik'i","Nagode muku sosai k'awayen arzik'i" Hafsa ta fad'a tana murmushin jin dad'i haka dai sukai ta hirarsu abin burgewa gaba d'aya makarantar suna burgesu dan wasu ma sunyi tunanin 'yan uku ne, babu wanda yayi tunanin ya iyayensu d'aya ba, sai da aka koma aji sannan suka tashi domin komawa ajinsu. Wajen k'arfe 6:00pm dai-dai aka tashi suka fito Yaya Safwan Hafsa ta hango ta saki wani irin murmushi sannan ta ce "yau fa, Yayana ne ya zo d'aukarmu" Murmushi Amatullahi tayi ta ce "gaskiya Yaya Safwan yana ji da Amaryarsa sosai" dariya Hafsa tayi sosai tare da cewa "ai dole ya ji da Amrish d'insa, ku taho mu tafi" Khadijatullahi ta ce "A'a zamu hau adaidaita Aunty Murja ta aikemu" babu yadda Hafsa ba tayi ba a kan su taho in ya so sai su biya wajen da Aunty Murja ta aikensu daga nan su kai su gida, amman Khadijatullahi ta kafe a kan Aunty Murja ta aikesu kuma gurin da nisa, haka Hafsa ta hak'ura ta tafi zuciyarta babu dad'i. Amatullahi kuwa mamaki ne ya isheta ita dai ta san babu inda Aunty Murja ta aikesu, amman kuma Khadijatullahi ta ce ta aikesu, haka dai suka fita suka nemi adaidaita suka shiga, Amatullahi ta kalli Khadijatullahi sosai sannan ta ce "ina Aunty Murja ta aikemu?" Khadijatullahi ta kalleta tare da cewa "ba ko ina" Amatullahi ta ce "to meyasa ki ka cewa Hafsa Aunty Murja ta aikemu","Saboda ba na son ko gaisuwa ta k'ara had'a ni da wani namijin, na tsani maza wallahi ji nake kamar na kashesu" shuru Amatullahi tayi daman ta san za'a rina, shi kuwa mai adaidaita tsoro ya kamashi "to anya wannan yarinyar lafiyarta k'alau kuwa" ya fad'a a zuciyarsa haka dai yayi ta mamaki har ya kai su kofar gida suka sauka Khadijatullahi tayi gaba Amatullahi ta tsaya domin biyansa kud'insa. Haka ta bi bayan Khadijatullahi suka shiga gidan da sallama Aunty Murja suka tarar kallo d'aya zakai mata kasan tana cikin damuwa zama suka yi kusa da ita suna tambayarta "me yake damunta" ta ce "bakomai" wannan karan basu takura mata ba domin kuwa kowannan su zuciyarsa cike take da damuwa. *'BANGAREN NIHAL😹🚴🏽‍♀️* Hajiya Asiya haka ta tattara Nihal ta nufi gida da itaba tare da Salis ya sani ba, Nihal ba ta san k'udurin Mamin ba dan duk a tunaninta sun fad'awa Salis d'in zata yi jinya a gida ne idan ta warke sai ta koma, dan da Alhaji Mansur ya dawo ya ga Nihal d'in yake tambayar meya sameta, Hajiya Asiya ta bashi labarin k'arya da gaskiya ta fad'a masa, da ya tambaya an fad'awa Salis d'in za'a taho da ita gida, Mami ta ce Eh an fad'a masa, Alhaji Mansur bai zurfafa bincike ba, domin duk ya d'auka da sanin Salis d'in. Kwanan Nihal biyar a gidansu sai ga Salis ya zo gidan domin jin shuru Nihal ba ta dawo ba, Nihal ta fito raka wasu k'awayenta ta hango Salis d'in da sauri ta k'arasa gurin da yake tana murmushi, shi kuma ya had'e fuska, Mamaki ta shiga yi "Yaya Salis me ya faru?" Harararta yayi sannan ya ce "ban sani ba, tunda ke kwata-kwata bakya tausayina","Ayya sorry Yayana, tuba nake ba zan sake ba" Salis ya ce "babu abin da zaki ce min tunda baki fad'a min zaki dawo gida ba, kuma gashi kwananki uku" ido Nihal ta zaro tare da cewa "wai daman Mami ba ta fad'a maka ba ta ce mana ta fad'a maka zan dawo gida har sai nayi wata d'aya zan koma" Mamaki ya kama Salis ya ce "ni d'in ne na fad'i haka, to wallahi Mami ba ta kirani ba" Shuru Nihal tayi na wani lokaci sannan ta ce "kayi hak'uri Yaya wallahi......" Dakatar da ita yayi yana murmishi "haba Sweetheart bakomai wallahi, yanzu ki je ki shirya ki zo mu tafi gida" ta ce "to shikenan" ta juya ta nufi gidan, d'akinta ta nufa ta hijabinta ta d'auka sannan ta fito kallonta suke cike da mamaki Shahida ta ce "Otherhalf ina zaki je?","Yaya Salis ne yake jirana zamu tafi" Mami ta mik'e cikin fushi tare da cewa "babu inda zaki je, kin dawo kenan" Abba ya kalleta cike da mamaki sannan ya ce "ba Salis d'in ya ce sai nan da wata d'aya ba fasawa yayi ne" Nihal ta ce "Abba Yaya Salis bashi da masaniya a kan wannan zance Mami ce ta fad'a yanzu yake fad'a min, wai na taho gida ba'a fad'a masa ba" Abba ya ce "daman baki fad'a masa ba Nihal" Nihal ta ce "Abba ba laifina ba ne Mami ce ta ce min ta fad'a masa kuma ta kwacen waya ni nayi tunanin d gaske take yi, ashe sharri tayi masa" Wani irin wawan mari Mami ta d'auke ta dashi tana cewa "Wani k'aton banza zaki fifita a kai na to wallahi ba zaki koma ba, shegiya wacce ba ta san ciwon kanta ba" Abba kuwa cikim fushi ya tashi ya nufi inda Mamin take ya zabga mata mari yana cewa "to sai mu gani, tunda ke baki da hankali, ke Nihal wuce ki bi mijinki ku tafi gida" Nihal ta ce "to Abba" ta fita da sauri tana kuka tana zuwa gurin Salis yake tambayarta "menene take kuka?" ta fad'a masa komai da komai nan ya shiga rarrashinta sannan ya bud'e mata mota ta shiga ya koma mazaunin driver ya ja mota suka bar gidan. *BAYAN KWANA BIYU* A yau ne aka d'aura auren Alhaji Mansur da Aunty Murja wanda aka biya sadaki naira dubu dari biyar kwata-kwata Aunty Murja ba ta da masaniya a kan auren ta zo gidan Hajiya Mama tana yi aiki ta gama wanke-wankr ta fara shara har ta kusan gama sharar sai ga Alhaji Mansur ya shigo gidan, da sauri Aunty Murja ta d'ago saboda jin kamshin turararsa wata iriyar nannanyan ajiuar zuciya ta sauke wani irin farin ciki ya ziyarci zuciyarta rabon da ta ganshi tayi kusan kwana biyar amman ji take kamar tayi shekara biyar ba ta ganshi ba a fili ta ce. "Sannu da zuwa, dan Allah ka yi hak'uri" tayi maganar kamar za ta yi kuka, k'arasawa kusa da ita yayi yana murmushi jikinsa ya jawota ya rumgumeta, da sauri ta fizge jikinta daga cikin nasa bakinta na rawa ta ce "Hakan bai da ce ba, saboda ni ba muharramarka ba ce, ba za ka samu damar min irin haka ba har sai an d'aura mana aure" Murmushi ya kuma yi a karo na biyu sannan ya ce "Ai kin san ban tab'a yi miki irin haka ba, saboda nasan ke ba muharramata ba ce, amman yanzu ina da damar yin komai a kan ki, dan haka karki haka ni". Shuru Aunty Murja tayi tana cewa "ban fahimci me kake nufi ba, dan Allah ka fahimtar da ni" jawota yayi jikinsa wannan karon bata yi yunk'urin hanashi ba,wayarsa ya d'auko ya kunna vedio da ya saka a ka yi a d'aurin aure ya ba ta a hannunta tana kalla, muryar liman ta ji yana cewa "An d'aura auren Alhaji Mansur jikamshi da Murjanatu Abbakar mai yak'i a kan sadaki naira dubu dari biyar" da sauri ta d'ago tana kallonsa tana cewa "wai da gaske ne, ba mafarki na ke ba an d'aura aurena da kai, idan har mafarki na ke yi zan so ace na dauwama cikin mafarkin nan ba tare da na farka ba" Sumbatarta yayi a goshi sannan ya ce "da gaske ne ba mafarki kike yi ba Amaryata, amman ni har yanzu ina fushi da ke sosai wallahi" idanuwanta suka ciko da kwalla ta ce "ka yi hak'uri","ni ba zan hak'ura ba, kawai ki fad'a min kuma me?" idanuwanta ta rufe a hankali ta ce "kuma ina sonka sosai" wani irin farin ciki ne ya kama shi ji yake kamar anyi masa albishir da gidan aljanna "nima ina sonki Murjanatu" ya fad'a cikin wani irin yanayin farin ciki. Muryar Hajiya Mama suka ji tana kiranta da sauri ta bud'e ido tana kok'arin zame jikinta domin zuwa kiran Hajiya Mama, amman Alhaji Mansur ya k'i barinta ta je domin ya rumgumeta sosai a jikinsa "Dan Allah ka bar ni naje kiran da Hajiya take min","idan kina so na cika ki,ki je to ki fad'a min wani suna zaki dinga fad'a min, dan na fuskanci bakya son kirana da kowane irin suna" Aunty Murja ta yi shuru cike da jin kunya a zuciyarta tana cewa "lallai wannan mutumin na fuskanci d'an soyayya ne, ga rigima iri-iri a cikinsa" Amman a fili ba ta iya cewa komai ba, jin alamar Hajiya Mama tana kok'arin fitowa daga d'akin ta ce "Yaya zan dinga cewa maka" tayi maganar da sauri tana juya bayanta tana kallon falon dan ba ta son Hajiya Mama ta fito ta gansu a haka. "To naji har a gaban kowa haka zaki dinga ce min?" Ta gyad'a kai alamar "eh" cika ta tayi dai-dai lokacin Hajiya Mama ta fito daga d'aki ganinsu a tsaye yasa tayi murmushi "Ashe Amaryar tana gurin Angonta shiyasa nayi ta kiranki na ji shuru" Aunty Murja kunya duk ta kama ta kamar ta nutse a k'asa, tsintsiyar ta tsugunna za ta d'auka domin ta cigaba da shara Hajiya Mama ta kira sunanta "Murjanatu ki bar sharar nan zan k'arasa ki zo ki shiga bayan gida ki yi wanka ki zo ki shirya anjima za'a yi walima","To" abin da Aunty Murja ta ce kenan sannan ta huce d'akin domin ta yi wanka kamar yadda Hajiya Mama ta ce mata. Shi kuwa Alhaji Mansur a tsakar gidan ya shimfid'a taburma suka zauna da Hajiya Mama suna hirarsu ta d'a da uwa, su Amatullahi da Khadijatullahi ne suka yi sallama domin yau sun ji Aunty Murjan ta dad'e sosai ba ta dawo ba shiyasa suka biyo bayanta "Lale da zuwa 'yan tagwaye wato yau kun ji auntyn ta ku shuru ba ta dawo ba ko?" Hajiya Mama tayi tunanin Amatullahi da Khadijatullahi 'yan biyu ne shiyasa take ce musu tagwaye"Eh Hajiya mun ga har yanzu k'arfe sha biyu na rana kuma idan ta koma tana dawowa k'arfe biyu shiyasa muka zo mu taimaka mata da aikin" Amatullahi ta fad'a sannan suka tsugunna suka gaishe da Hajiya Mama da Alhaji Mansur. Suka amsa fuskarsu cike da fara'a Hajiya Mama ta dora da cewa "Ai kuwa daga yau tare da ku zamu dinga zama domin kuwa Auntynku yau an d'aura mata aure anjima kad'an za'ayi walima tana d'aki wanka take yi" Khadijatullahi ta d'ago da sauri tana mamaki "An d'aura mata aure kuma?","Eh Khadija" Hajiya Mama ta bata amsa a takaice, Amatullahi kuwa murna ce ta isheta "Kai Hajiya Mama amman na ji dad'i ya kamata na yi miki kyautar goro" Amatullahi ta fad'a tana murmushi, duk da yanayin da Khadijatullahi take ciki domin tsoro take kar ayi wa Aunty Murjan abin da Jabir yayi mata a daren aurensu sai da maganar Amatullahi ta bata da dariya ta ce "Hajiya karki yarda so take ta mayar da ke tsohuwa kuma fa tasan kin fi ta jii da kuruciya" Alhaji Mansur dariya yayi sosai sannan ya ce "Lallai 'yan k'annan nan na wa sai na zane ku Hajiyan ku ke yi wa tsiya haka" Hajiya Mama ta ce "Kyalesu ai Allah ya kawo mu, zasu fara yi min tsiya" Gaba d'ayansu dariya suka yi sosai. Nan Hajiya Mama take fad'a musu cewa Alhaji Mansur shi ne ya auri Aunty Murja, sai a lokacin hankalin Khadijatullahi ya d'an kwanta domin ta fahimci Alhaji Mansur d'in ba zai tab'a iya aika irin abin da Jabir yayi mata ba, haka dai sukai ta wasa da dariya abin gwanin ban sha'awa. *'BANGAREN GIDANSU JABIR😂* Zaune suke a falo gaba d'ayansu suna kallon film d'in Tarkon k'auna a tasha arewa 24 Shahida da ke zaune a kan kujera one sitter ta d'auki remote ta chanza tasha zuwa Tauraruwa tv,Hajiya Asiya ta bud'e baki cike da masifa zata fara zazzagawa Shahida masifa sai ji tayi ana sanar da d'aurin auren Alhaji Mansur da Aunty Murja tare da katin Walimar da za'ayi a gidan Hajiya Mama da misalin k'arfe 2:00pm na rana. A zabure Hajiya Asiya da Jabir suka tashi bakin Hajiya Asiya na rawa ta fara cewa "me nake ji a cikin t.v Abban Jabir yayi aure" Fad'uwa tayi k'asa sumammiya, Jabir kuwa zage-zage ya shiga yii, Aliyu ne ya d'auko ruwan sanyi ya watsawa Hajiya Asiya a fuska nan ta farfad'o wani irin kuka ta fashe dashi "na shiga uku innalillahi wa inna'ilaihi raju'un Alhaji ya kashe min rayuwa ya lalata min duk wani burina wallahi duk wacce tayi gangancin zuwa gidan nan da sunan kishiyata sai na kasheta wallahi sai na illatata sai dai a fita da gawarta wannan gidan da kuma Abban Jabir nawa ne ni kad'ai babu wata shegiyar da ta isa na had'a miji da ita, kuma wannan munafikar uwarta sa wallahi sai na yi mata abin da ba za ta tab'a mantawa da ni ba" Tana kuka take maganar. Aliyu da Shahida kuwa tashi suka yi kowannan su ya nufi d'akinshi, Teemarh kuwa tashi tayi tare da fashewa da wata iriyar mahaukaciyar dariya "kai ya ubangiji yau ban san wane irin farin ciki na ke ciki ba, gaskiya zan je walima na ta ya Abba farin ciki, gwanda da yayi auren wannan shine abin da ya dace da jakar uwa irin ki" Tana gama fad'ar haka ta wuce d'akinta domin shiryawa zuwa walimar bikin Abba. Jabir ya ji haushin maganganun da Teemarh ta fad'awa Maminshi amman yanzu ba ta ita yake ba, domin kuwa suna cikin tashin hankali shi da mahaifiyarsa, haka dai suka zauna kowan ne daga cikinsu zuciyarsa kamar zata fashe saboda bak'in ciki musamman Hajiya Asiya. (ni kuwa nace Alhaji Mansur ka yi min dai-dai😂😂Hajiya Asiya Allah ya k'ara😹💃🏽💃🏽yau akwai shagali a gidan Hajiya Mama💃🏽💃🏽ina kuke Ummu juwairiyya djamila da dai sauransu ana gayyatar ku fa💃🏽💃🏽) *'BANGAREN LADO DA INNA LARAI😹* Lado ya tadawa Inna Larai hankali a kan sai ta biya shi kud'insa gaba d'aya ya chanza mata, kullum cikin bala'i yake mata ita kuma Inna Larai ba ta san inda zata samu kud'i ta biya shi ba domin kuwa akalla kud'in zai kai naira dubu goma sha biyu, Lado kuwa ko bacci ba ya iyawa dan har zazzab'i yayi saboda kud'insa dakyar Inna Larai ta lallab'ashi a kan zata ce Malam Shu'aibu ya turo mata da kud'i idan ya turo mata sai ta biya shi, Lado bai yarda ba har sai da Inna Larai ta je wajen masu kira, ta basu number Malam Shu'aibu suka kira shi ta fad'a masa cewa tana buk'atar kud'i naira dubu sha biyar domin katangar d'akinta ta fad'i ta kira masu gyara sun gyara amman kuma ba ta da kud'in da za ta biya su, Malam Shu'aibu ya ce zai turo mata da kud'in a cikin satin nan sai ta biya masu gyaran, sannan Lado ya hak'ura zuwa lokacin da Malam Shu'aibu zai turo kud'in. *'BANGAREN NIHAL🥳* Tun da suka koma gidan Nihal ta shiga nunawa Mijinta Salis soyayya a waje d'aya suke samun matsala idan zai kwanta da ita dan kullum sai sun yi fad'a da ita duk da cewa Salis d'in shima yana kok'arin ganin ya nunawa Nihal d'in soyayya amman shi yana da k'arfin sha'awa ba zai iya jurewa ba, yau ma kamar kullum tana kwance a kan gado tana bacci sai jin mutum ta yi a jikinta yana ta tsotsarta kuka ta saka ta fara rok'onsa "Dan Allah Yaya Salis kabarni haka na d'azu ma bai warke ba, wallahi zan iya mutuwa" Yau kam Salis ya zo da mutunci rarrashinta ya shiga yii cikin wata iriyar murya mai narkar da zuciya "Haba babyna ki yi hak'uri kinji ba zan miki da zafi ba, zan miki a hankali ba za ki ji zafi ba, kin san dai ina sonki ba na son abin da zai dinga saka ki kuka kema kuma na san kina sona ba za ki so ace na shiga wahala ba, ki taimaka min kinji babyna" ya k'arasa maganar cikin muryar tausayi. Nihal ta kalleshi sosai cikin sanyi murya ta ce "da gaske ba za ka min da zafi ba?" kai ya gyad'a mata alamar "eh" Nihal tayi murmushi sannan ta ce "Ok babyn baby go ahead" Murmushi yayi sosai tare da cewa "to babyn baby na gode da aka bani izini". Haka Salis yayi ta bin ta a hankali har sai da ya gama shan zumarta sannan ya sauka daga kanta tare suka yi wanka sun d'auki kusan awa guda suna wankan kamar ba zasu fito ba, bayan sun fito suka shirya cikin wasu riga da wando pink colour komai iri d'aya ne, sun yi kyau sosai zama suka yi a falo suna kallo, nan Salis yake shaida mata Abba yau ya k'ara aure abin ya girgizata sosai, amman kuma a wani b'angaren ta ta ya Abban farin ciki sabida ta san zaman hak'uri yake da ita. Talatu kuwa tunda ta koma gidansu ita da yaronta take ta kulla makirci iri-iri tana zuwa tana kai wa mahaifiyar Salis d'in labarai a kan Nihal d'in karuwa ce saboda an rasa waye zai aureta shiyasa a ka mak'alawa Salis aurenta tun Mama bata yarda har ta saka akai mata binkice a kan Nihal d'in aka tabbatar mata da cewa Nihal ta tab'a karuwanci dan saboda haka ne ma a ka yi mata aure, ran Mama ya b'aci sosai nan ta shirya ta nufi gidan Salis tana zuwa gidan ta shiga falon babu ko sallama a zaune ta tarar dasu suna kallo tashi suka yi suna mata sannu da zuwa. Wata uwar harara ta shiga hurgawa Nihal d'in cikin masifa ta shiga cewa "To munafuka tsohuwar kilaki asirinki ya tonu wato kin je kin gama yawon iskancinki shine zaki zo ki mak'alewa yarona to wallahi ba'a nan gidan ba dan yanzun nan ba sai anjima ba Salis zai sake ki ki je ki cigaba da yawon barikin na ki" tana gama fad'ar haka ta juyo kan Salis tana cewa "ka saketa ko kuma na tsine maka",Salis ya shiga tashin hankali ya shiga kok'arin rarrashin Mama amman sam ta tubure a kan ko ya saketa ko ta tsine masa. Nihal tana kuka ta kalli Salis tana cewa "Yaya Salis ka bi umarnin da Mama ta ba ka, ba na so na zama silar rabuwarka da mahaifiyarka ka sake ni kawai na sani kana sona sosai nima ina sonka amman ya zama dole mu rabu da juna" Salis ya rintse ido zuciyarsa nayi masa zafi cikin rawar murya ya ce "Nihal ki je gida" Luuuuuu ya fad'i k'asa sumamme Nihal ta saka kuka ta nufeshi amman Mama ta daka mata tsawa tare da cewa "ki tafi gidan ubanki, ba ya buk'atarki" Haka Nihal ta shiga d'aki ta had'a kayanta a akwati ta fito tana jan akwatin gidan Hajiya Mama ta nufa tana kuka, a zaune ta tarar da ita tare da Abbansu da wasu 'yanmata guda biyu a jikin Hajiya Mamar ta fad'a tare da fashewa da kuka tana fad'in. "Hajiya Mama na shiga uku dan Allah ki taimaka min" Tayi maganar tana k'ara sautin kukanta, Hajiya Mama ta ce "meya faru takwarata","Hajiya ta raba ni da Yaya Salis, Hajiya ta ce sai ya sake ni ba za ta yarda ya kuma zama da ni a matsayin matarsa ba" Kuka take yi sosai har sai da kan ta ya fara sara Mata, Hajiya Mama cike da tashin hankali ta ce "wacece wannan da d'anyen hukunci","Maminsa ce"Nihal ta bata amsa tana cigaba da kuka. Shuru Hajiya Mama tayi "tabbas abin da ka yi sai anyi wa naka, Jabir ya wulak'anta marainiya gashi ita ma k'anwarsa anyi mata" Tayi maganar cikin zuciyarta, Shi ma Alhaji Mansur Abin da yake fad'a a tasa zuciyar kenan, Hajiya Mama ta d'ago ta dai-dai lokacin Amatullahi ta kai fuskarta kan Nihal d'in a firgice take nuna Nihal tana cewa "ke ce daman" Da sauri Nihal ta juya tana kallon Amatullahi tabbas duk da tana cikin matsanancin tashin hankali Amman ba za ta, tab'a mantawa da wannan fuskar ba ita ma cike da mamaki ta ce "ke ce anan?". Sai kuma ta tashi ta nufi gurin da su Amatullah da Khadijatullah suke zaune ita ma ta zauna tana fuskantarsu hawaye na zuba daga cikin idanuwanta "ke ce Amaryar Abbanmu ko Kuma ke ce Khadijatullah" Khadijatullah ta kalli Nihal gabanta na fad'uwa "Wacece wannan? A Ina ta san sunana" Tambayar da take yi a zuciyarta kenan ba ta san ta fito fili ba, sai jin Nihal tai tana nuna ta tana cewa "ke ce Khadijatullah?"Kai ta gyad'a Mata alamar "Eh". Hannunta ta kama sosai ta k'ara fashewa da kuka "Ki yi hak'uri duk da cewa ni ban da laifi, amman nasan alhakinki ne yake ta bibiyata, na san Yaya Jabir bai kyauta miki....................." A zaburai Khadijatullahi ta mik'e dai-dai lokacin Aunty Murja ta fito ta ji duk abin da Nihal ta ce wato hakan na nufin mahaifin Jabir shi ne mijinta, kanta ne yayi matuk'ar sarawa ta shiga maimaita innalillahi wa'inna ilaihi raju'un a fili. Alhaji Mansur da Hajiya Maama sun yi matuk'ar jirjiga da jin wannan al'amarin "wato daman Khadija ita ce wacce wannan tsohon d'an iskan ya lalata rayuwarta" Hajiya Mama ta fad'a tana cigaba da jinjina lamarin, Khadijatullahi kuwa fita tayi da gudu Aunty Murja ta bi bayanta domin tsayar da ita, Nihal ma bin bayan su tayi ita kuma Amatullahi zama tayi tana cigaba da jin farin ciki domin kuma ta dad'e tana neman hanyar da zata addabawa Jabir sai gashi yau ta samu cikin sauk'i "ai kuwa sai na tabbatar na gasa maka aya a hannunka Jabir" Amatullahi ta fad'a a cikin zuciyarta. A zaure Aunty Murja ta rik'e Khadijatullahi ta rungume nan suka shiga kuka, Nihal ma zuwa tayi ta rungume su tana ita ma kukan take tana jin sonsu yana ratsa dukkannin zuciyarta, Shahida da Yaya Aliyu ne suka shigo gidan suka tarar da su sun rungume juna suna kuka, da sauri Shahida ta k'arasa kusa da su tana tambayar "meya faru? Ko mutuwa aka yi?" Nihal ce ta fad'a musu duk abin da yake faruwa, nan fa ita ma Shahida ta fashe da kuka har da kururuwa ta rumgumesu suna kukan tare. Aliyu ne ya shiga rarrashinsu da kalamai masu dad'i har ya samu kayi shuru haka suka koma cikin gidan Shahida da Nihal suna rik'e da hannun Khadijatullahi, zama suka yi jungum-jungum kamar gidan makoki, Amatullahi ce ta shiga jan su da hira domin kuwa ita kad'ai ta san abin da take shiryawa a kan Jabir domin kuwa sai ta tabbatar ta wulak'antasa sai ta saka shi a cikin bala'i da masifa sai ta hanashi kwanciyar hankali. (ni kuwa na ce Jabir ka shiga uku gurin Amatullahi iyayen fitina, ba'a tab'a ma yi take barantana an tab'o bestynta😂😂🥳) Haka kowa ya sake suka fara tab'a hira sama-sama, suka shiga gyara gidan da yin girke-girke duk da cewa Alhaji Mansur ya saka ayi musu order abincin bikin amman Hajiya Mama ta ce su ma ba za su zauna ba dole su k'ayin wasu abincin, shi kuwa Aliyu idanuwansa suna kan Khadijatullahi duk inda tayi sai ya bi ta da kallo tausayin yarinyar yake matuk'ar ji sosai sai kuma a yau ya k'ara tabbatarwa da cewa Jabir tabbas baya cikin jinsin mutane, sai dai aljanu domin kuwa ko wasu aljanun ma ba zasu iya aikata abin da yayi wa baiwar Allah salihar mace irin Khadijatullahi ba. Daman duk abin da aka sakawa lokaci dole sai ya zo tun kafin k'arfe 2:00pm 'yan uwa da abokan nan arzik'i suka cika gidan damkam har wajen gidan Teemarh ma ta zo, walimar tayi matuk'ar k'awatarwa domin kaf mutanan da suka cika gidan har da wajen gidan sai da suka samu abin ci wadatatce, shi kuwa Alhaji Mansur gidan ya tafi domin shirya tarbar Amaryarsa bayan sun keb'e shi da mahaifinyarsa sun tattauna a kan yadda zasu shawo kan matsalar Khadijatullahi, haka aka shiga yin walima sai wajen k'arfe 7:00pm sannan kowa ya watse aka shiga kuma shirye-shiryen kai Amarya, Hajiya Mama ta ce ita da kan ta zata kai Aunty Murja gidanta bata buk'atar kowa. Shahida ta ce "Wallahi daman Hajiya Mama ba na son komawa gidan nan, shiyasa na gudo nan, ba zan koma ba" Nihal ta ce "Hmm ai kuwa dai nima a nan zan zauna ba zan koma ba" Hajiya Mama ta ce "to su Khadija ma sai su zauna tare da ku nima ba zama zan yi ba ina kai ta zan dawo" suka amsa da "to a dawo lafiya" Haka suka fita daga gidan fuskar Aunty Murja a lillib'e take da mayafi, Aliyu yana biye da su domin shi ne zai kai su. Bud'e musu murfin bayan motar yayi sannan suka shiga ya rufe ya shiga mazaunin driver ya ja motar sai gidansu yana zuwa mai gadi ya wangale masa tafkeken gate d'in gidan ya shiga yayi parking sannan ya fito ya bud'e musu motar suka fito, babban falon gidan suka nufa Teemarh wacce bata dad'e da dawowa daga walimar ba tana ganin shigowar Aunty Murja da Hajiya Mama ta fara yin gud'a wacce hakan ta jawo hankalin Hajiya Asiya da Jabir suka fito ganin Hajiya Mama da wata wacce suke da tabbacin ita ce Amaryar hankalinsu ya tashi zuciyarsu ta shiga harbawa da k'arfi ita kuwa Teemarh gud'ar ta cigaba da yi kamar zata fasa musu dodon kunne, a kan kujera Hajiya Mama ta zaunar da Aunty Murja sannan ita ma ta zauna Aliyu kuwa yana shigowa d'akinsa ya shige tun kafin su Jabir su fito. Alhaji Mansur ne ya fito daga d'akinsa fuskarsa d'auke da murmushi yana yi musu sannu da zuwa, zama yayi Hajiya Asiya kuwa ta shiga zage-zage tana nuna Hajiya Mama da yatsa tana cewa "ke ce babbar munafukar da ki ka had'a auren nan ko to wallahi............" Ai bata k'arasa fad'ar abin da zata ce ba, sai jin saukar mari tayi a fuskarta Alhaji Mansur ne ya zabga mata mari yana cewa "tabbas yau kin k'ara nuna min cewa ke, babbar jahila ce, dak'ik'iya wacce kwata-kwata ba ta da tarbiyya dabba kawai" Jabir yayi matuk'ar fusata da jin abubuwan da mahaifinsu yayi wa Maminsa cikin hargagi ya fara cewa "Kai Abban nan wane irin mutum ne kwata-kwata zuciyarka kamar ta kare take ya kama......." Wani irin naushi Alhaji Mansur ya kai masa a biki domin cike yake da bakin cikinsa ai kuwa sai ga jini nan ya fara zuba kamar da bakin kwarya wani naushin ya k'ara kai masa a fuska, Hajiya Asiya ganin Alhaji Mansur yana ta yi musu rashin mutunci a gaban Amaryarsa da kuma sirikarta Teemarh Amman Hajiya Mama ba ta ce komai ba nan ta k'ara jin tsanar Hajiya Mama haka ta kama hannun Jabir suka shige d'akinta. Teemarh kuwa ita ma d'akinta ta shiga tana jin dad'in hukuncin da Abba yayi wa mijinnata da uwarsa, Alhaji Mansur kuwa zama yayi a kan kujera yana huci haka Hajiya Mama tayi musu nasiha a kan zaman aure da kuma yin hak'uri da juna, ta tashi ta fita ado driver ya bud'e mata mota ya shiga mazaunin driver ya ja motar domin ya kai ta gida. Aunty Murja ta tashi ta nufi gurin mijin nata ta zauna kusa dashi tare da cewa "Yaya ya kamata ka yi hak'uri ka tashi domin mu je mu kwanta nasan ka na jin bacci, b'acin rai bai chanchanta a wannan kyakkyawar fuskar ba" Duk da irin tsananin fushin da yake yi sai da yayi murmushi domin kuwa ko ba komai wannan daren bai kamata ace yana cikin bak'in ciki ba, ya kamata ace yana cikin farin ciki sosai, haka ya tashi suka shige cikin d'aki suka lula duniyar soyayya. *'BANGAREN HAFSA💓* Hafsa da Safwan kuwa wata iriyar tsatatatciyar soyayya suke yi wa junansu ji suke kamar zasu cinye junansu kullum a rana sai sunyi waya ta kai sau ashirin kuma kullum a gidan yake breakfast idan ya dawo daga office ma sai ya biyo Hafsa ta cika masa ciki da dad'ad'an abincinta sannan yake hucewa gida, Khalid kuwa yanzu sam har baya so ayi masa maganar komawa gurin Mommynsa saboda irin yadda Hafsa take kula dashi kullum suna manne da juna kamar cingum zaune take a kan kujerar d'akinta zuciyarta babu dad'i ganin hoton katin d'aurin auren Aunty Murja da tayi a t.v gashi har gidan su Khadijatullahi ta je amman a rufe yake "yanzu duk yadda muke dasu Khadijatullahi zasu iya ware ni, har ayi bikin Aunty Murja ba su fad'a min ba" Wani irin kuka ne ya zo mata, a haka Safwan ya shigo d'akin nata ya tarar da ita tana kuka da sauri ya zauna kusa da ita yana tambayarta "Amrish me ya faru?","Su Khadijatullahi ne" ta fad'a cikin kuka, a rud'e ya ce "meya samesu?","bakomai Yayana su Khadijatullahi ba su kyauta min ba, har ayi bikin Aunty Murja ba su fad'a min ba, me na yi musu ai ko menayi musu bai kamata ace sunyi min haka ba". Shuru Safwan yayi yana jin wani irin zafi ganin hawaye yana zuba daga fuskar Amrish d'insa nan ya shiga rarrashinta anan ne take fad'a masa sunan mijin Aunty Murjan da taje an fad'a a t.v "Laaa ai nasan gidan Hajiyarsa har gidansa ma na sani, saboda a ma'aikatarsa nake aiki". "Haba Yayana da gaske ka ke" Ta fad'a tana share hawayen fuskarta, "wallahi da gaske ki bari gobe zan zo da sassafe na kai ki gidan Hajiyarsa ina tunanin suna chan yanzu kin ga dare yayi k'arfe goma na dare babu damar fita" Ba'a san ranta ta yarda ba haka suka yi sallama ya tashi ya fita domin tafiya gida, ita ma Hafsan ta koma kan gadon domin tayi bacci zuciyarta a cunkushe. *'BANGAREN SALIS😣* Kwanan Salis uku a asibiti bai san wanda yake kansa ba hankalin Mama yayi matuk'ar tashi, ganin tilon d'an nata cikin yanayin rayuwa ko mutuwa, kuka take yi sosai kamar ranta zai fita ta kama hannun Salis d'in tana cewa "dan Allah tashi duk abin da kake so zan yi maka, kasan kai ne kad'ai yarona kai nake kallo na ji dad'i "Ai baki fara kuka ba, domin kuwa duk halin da Salis yake ciki ke kika jawo masa, ki ka je kika rabasa da matarsa ai gashi nan yanzu sai ki dafasa ki cinyesa" Mahaifin Salis ya fad'a cikin fushi, Mama bata iya tankawa ba, sai kuka shi kuwa takaici ma ya hanasa zama ya fita daga d'akin zuciyarsa cike da bak'in ciki. *'BANGAREN AMINAN JUNA AMKHAHAF😂💓* Kamar yadda Safwan ya ce mata zai zo da sassafe ya kai ta gidan Hajiya Mama haka kuwa aka yi yana zuwa ko yarda ya shiga gidan ba ta yi ba, ta taresa a farfagiyar gidan bai musa mata ba ya juya ya nufi motarsa ya bud'e mata gurin mai zaman banza ta shiga ya rufe ya zagaya gurin driver ya shiga ya ja motar ya nufi gidan Hajiya Mama yana zuwa ya nunawa Hafsan gidan ta fita suka yi sallama ya nufi ma'aikatarsu kasancewar su Hafsa yau lahadi babu makaranta. Ta shiga gidan da sallama a bakinta suna zazzaune a tsakar gida Amatullahi da Khadijatullahi suna ganinta suka tashi da sauri suka nufi gurinta suna murmushi rungumeta zasu yi tayi saurin dakatar da su cikin muryar fushi da cewa. "Ba na buk'atar jin komai daga bakinku nagode sosai, kun ji nasan irin zaman da zan yi da ku" Tana gama fad'ar haka ta juya zata fita Amatullahi ta rik'eta sosai tana cewa "Wallahi ba inda zaki je, nasan a kan bikin Aunty Murja da ba'a fad'a miki ba shiyasa kike fushi, to ki tsaya ki saurareni dan Allah Hafsa wallahi! wallahi!! wallahi!!! Kin ji na rantse miki ko, mu kan mu ba mu san da bikin ba, sai da muka zo gidan Hajiya Mama sannan" Fizge hannun Amatullahi tayi daga jikinta ranta a b'ace ta ce "daman baku yi niyyar na zo ba, tunda ranar ma a school babu yadda ban yi da ku ba, a kan ku shiga mota a kai ku gida ku ka k'i, kuma lokacin da ku ka hau adaidaita Yaya Safwan ya bi hanyar da ku ka bi, sai gani na yi kun bii hanyar gida anan na tabbatar kawai daman bakwa buk'atar cigaba da mu'amalarmu". Khadijatullahi jikinta yayi sanyi dan kuwa ta san bata kyautawa k'awarta ta ba domin ita ce da laifi Amatullahi babu ruwanta nan, rik'e hannun Hafsan tayi lokacin da ta juya zata fita, ta juyo da niyyar fizgewa sai ta ga Khadijatullahi ce kuma tana tsoron karta fizge ta je ta fad'i tunda cikinta yanzu ya tsufa sosai ya kai wata takwas, "me zaki ce min ke kuma?" Hafsa ta fad'a cike da masifa, "ki yi hak'uri dan Allah wallahi ba wai da niyya mu ka yi miki haka ba, kuma Amatullahi kwata-kwata ba ta da laifi ni ce nake da laifin dan mana k'aunar abin da zai sake had'a ni da wani namijin na tsane su, ba na son ganinsu, amman bikin Aunty Murja wallahi kamar yadda besty ta ce ba mu san dashi ba mu ma sai da muka zo ake fad'a mana, kuma lokacin ya ri ga ya k'ure shiyasa ki yi hak'uri". Hafsa tayi shuru tabbas ita ma ranar sai da ta raya wannan abin a zuciyarta cewa Khadijatullahi ba ta son ganin maza shiyasa ta k'i shiga motar "Shikenan ya huce" Hafsa ta fad'a tana murmushi, murmushin su ma suka yi gaba d'ayansu. Aliyu ne ya shigo gidan idanuwansa a kan Khadijatullahi duk ya ji abin da suka fad'a zuciyarsa ta shiga bugawa magana Khadijatullahi ta girgiza shi ba ma shi kad'ai ba har da su Hajiya Mama domin kuwa sun san Jabir shi ne silar da yasa Khadijatullahi ta tsani maza, "Assalamu alaikum" Ya fad'a har lokacin idanuwansa na kan Khadijatullahi, amman ita tun da ya shigo ta kawar da kanta domin kuwa wata iriyar muguwar tsanar Aliyun take ji saboda tsananin kamannin Jabir da take gani a fuskar Aliyun ji take kamar Jabir d'in ne. Suka amsa masa sallamar amman ban da Khadijatullahi d'akin Hajiya Maman ta shige tayi kwanciyarta, "ko me ya kawo shi nan, banza kawai" Tayi maganar zuciyarta kamar zata fashe saboda tsanar maza da tayi mata katutu a cikinta. Hafsa da Amatullahi kuwa k'arasa suka yi suka zauna Hafsa ta gaisar da Hajiya Mama cike da girmamawa Aliyu ma ya gaishe da ita ya zauna kusa da ita suna yin hirarsu irinta jika da kaka, Hafsa kuwa hira suka shiga yi su da Shahida,Nihal da Amatullahi, zuciyar Amatullahi ta karkata a kan ta je ta ga wace wainar ake toyawa a gidansu domin kuwa ba ta k'aunar ace Lado da Inna Larai sun shirya, tashi tayi tana cewa "Sisters zan je na dawo yanzun nan","ina zaki je besty" Hafsa ta tambayeta. "Ginin da na fara yi ne nake tsoron kada ya ruguje" Hafsa ta gane abin da Amatullahi take nufi dan haka ta fashe da dariya tana fad'i "gaskiya ne besty, gwanda ki je ki duba shi kar ya ruguje duk aikinki ya dawo baya" Khadijatullahi da take cikin d'aki tana jin su ita ma dariyar take yi sosai har suna iya jin dariyar Hafsa ta ce "Ahhh besty ke ma dole ki yi dariya, tana tsoron kar ya ruguje aikinta ya dawo ba, kin san fa besty akwai ta da iya tsara gini mai kyau","Ai kuwa dai kam" cewar Khadijatullahi. Wannan maganar ta su ta saka su Hajiya Mama a rud'ani har Amatullahi tayi musu sallama ta fita, da Hajiya Mama ta gaji ta tambayi Hafsa "me take nufi da kar gininta ya ruguje?" Nan Hafsa ta fad'a musu abin da take nufi da hakan, Nihal da Shahida dariya suka saka sosai har da hawaye "Ai daman na fuskanci sister ba k'aramar 'yar drama ba ce" Shahida ta fad'a "wallahi kuwa other half" Hajiya Mama dai girgiza kai kawai tayi Aliyu kuwa yana son yin dariya ya basar, suka cigaba da yin hirar ta su. *'BANGAREN INNA LARAI,LADO DA KUMA AMATULLAH* Cikin sauri sauri ta k'arasa gidan tana saka kanta a sauron gidan ta ji muryar Inna Larai tana cewa "dan Allah kayi hak'uri mana Lado tunda ya ce a wannan satin zai turo kud'in sai ka tsaya satin idan ya huce ka ga bai turo ba, sai ka fad'i duk abin da zaka ce, tunda dai kasan k'aryar da nayi masa cewar ginin d'akina ne ya fad'i na gyara ban bada kud'in ba, kai ma kasan zai turo kud'i" Amatullahi tayi wani irin murmushi "lallai kam da ace ban dawo ba, da tuni ginina zai ruguje, amman yanzu na dawo zan d'ora daga inda na tsaya" Tayi magana a zuciyarta. Shiga gidan tayi ko kad'an ba ta nuna ta ji abin da suke fad'a ba, ta saki wani irin murmushi tare da cewa "sannunku da hutawa Inna, my love nayi missing d'inka" Tayi maganar tana kallon Lado fuskarta tana nuna alamun tsantsar damuwa. Lado ya k'ak'alo murmushin dole ya wanzar a kan fuskarsa "nima haka my love" Ya fad'a tare da mikewa tsayi yana cewa "zan fita waje na d'an sha iska my love ki kula da kanki" Yana gama fad'ar haka ya fita ransa a b'ace shi sam baya k'aunar yi wa Amatullahi magana kuma duk Inna ce ta jaaa masa gashi ta zamar masa k'arfen k'afa. Ita kuwa Amatullahi d'akinta ta shiga tayi wanka, sannan ta fito wata doguwar ce a jikinta blue tayi mata matuk'ar kyau tamkar dan ita aka yi rigar, fita tayi daga gidan ta nufi gurin mai kiran waya ta biya shi kud'in sannan ya bata wayar ta saka number babanta sannan ta matsa chan nesa da mai kiran wayar domin kar ya ji abin da zata ce, ring d'aya biyu ya d'aga tare da yin sallama "Assalamu alaikum" ta amsa masa sallamar "Wa'alaikumussalam Babana Amatullahi ce","Allah sarki yarinyata nasan kinyi kewar babanki ko?" Yayi maganar cike da jin dad'in kiran da tayi masa "Eh babana nayi kewarka sosai da sosai kullum sai na ji dama nima ace na dawo gurinka mu dinga yin aikin tare","Allah sarki yarinyata karki damu na kusan dawowa insha Allahu na zo na ganki" Amatullahi ta ce "to Baba Allah ya dawo da kai lafiya","Aamin ya Allah" Sai kuma Amatullahi ta numfasa ta fara kora masa jawabi "Babana na ji wai Inna ta kira ka a kan cewa ginin d'akinta ya ruguje, ta kirawo mai gyara an gyara bata bada kud'in gyaran ba","Eh wallahi gobe ma nake shirin turo mata da kud'in dan ta biya shi kud'insa" Amatullahi ta ce "to wallahi Baba k'arya Inna take babu wani ginin da ya ruguje, so take ta damfare ka, kuma idan ka na tunanin ba gaskiya nake fad'a ba zaka iya zuwa ka duba ka gani da kanka" Shuru Malam Shu'aibu yayi domin a duniya babu abin da ya tsana irin kayi masa k'arya, gwanda ka fito fili ka fad'a masa gaskiyarka "Kin tabbatar babu ginin da ya ruguje","wallahi Baba da gaske nake yi maka" Amatullahi ta fad'a cikin fara'a, kashe wayar Malam Shu'aibu yayi ransa duk a b'ace kuma ya k'uduri niyyar ba zai bata kud'in ba kuma ko ta kirasa ba zai d'auka ba, Amatullahi kuwa mayarwa da kiran wayar tayi da wayarsa sannan ta shiga adaidaita ta nufi gidan Hajiya Mama. *'BANGAREN SAFNA* Tun ranar da ta ji labarin cewar Safwan da Hafsa sun shirya kuma yanzu soyayya suke yi, kuma ta fuskanci duk irin abubuwan da take yi a gidan dan ta kuntatawa Safwan d'in sam bai dameshi ba, nuna mata ma yake yi kamar bai san tana yi ba, hankalinta ya tashi zuciyarta ta shiga yi mata zafi, ta shiga neman hanyar da zata bi ta mallake Safwan d'in ita kad'ai kuma ta cusa masa tsanar Hafsa a cikin zuciyarsa amman kwata-kwata ta gaza samun hanyar, kullum cikin kuka gashi kuma kamar k'ara ruru mata wutar son Safwan d'in ake yi a zuciyarta, yau ma kamar kullum tana zaune a falo tana shan kukanta. Safwan ya shigo falon domin ya manta wata takardar wad'anda suka siya kaya kuma ake binsu bashi, kallon Safna yayi cike da tausayi tabbas shi kansa ya san Safna tana sonshi sosai, amman kuma Hafsa ita ma tana matuk'ar son shi bai san a cikinsu waya fi son shi ba wannan Allah ne kad'ai yasan hakan, har ya huce sai kuma ya dawo domin bai zai iya barinta cikin yanayin da take ciki ba a yanzu. Zama yayi a kusa da ita tare da kama hannunta yana murzawa, kamar jira take ta fad'a jikinsa tare da fashewa da wani irin kuka ta k'ank'ameshi kamar wanda aka ce mata idan ta cika shi guduwa zai yi, shi kuwa Safwan shafa gashin kanta ya shiga yi a hankali yana bubbuga bayanta "Yi shuru babyna ba na son kina yin wannan kukan, yana ta da min da hankali sosai","Ba ka so na yanzu, ka fi son Hafsa duk irin abin da nake maka baya burgeka shi ne zaka k'ara aure" Tayi maganar cikin kuka "Wa ya gaya miki cewar ba na sonki, na fi son Hafsa, kuma ke a tunaninki saboda na gaji da ke ne shine zan k'ara aure, ke sanin kanki ne, Hafsa tun kafin na aureki muke tare da ita 'yar uwata ce" Ya saka hannu ya d'agota yana share mata hawayen fuskarta sannan ya cigaba da cewa "Ina sonki sosai Amaryata","da gaske" Tayi maganar cikin farin ciki, kai ya gyad'a mata alamar "eh" sannan ya cigaba da cewa "ko da na auri Hafsa matsayinki ba zai tab'a chanzawa ba, saboda ke ce ruhina ita kuma ita ce rayuwata" Murmushi tayi tana mai jin farin ciki a zuciyarta. Yanzu kam ta fara samun sassauci a kan zafin da take ji a zuciyarta, sambatarta yayi a kuncinta yana fad'ar "Baby nayi mantuwa ne, shiyasa na dawo zo muje ki ta ya ni d'auko takardar","to" Ta fad'a tare da mik'ewa hannunsu yana rike da na juna suka shiga d'akin ya d'suki takardar sannan ta rakashi har bakin motarsa zai shiga motar ta rumgumeshi ta baya "Baby ka tafi da ni" Murmushi yayi sannan ya juyo ta dora kanta a kan k'irjinsa "Baby ina kishinki sosai ba zan iya tafiya da ke office ba, saboda akwai maza sosai" Murmushi tayi tare da janye jikinta daga na shi tana cewa "To shikenan baby yau da wuri zaka dawo amman ko?" Kai ya gyad'a mata alamar "eh" ta marairaice fuska cikin shagwab'a tace "to k'arfe nawa zaka dawo?","6:00pm dai dai" Nan ta fara kukan shagwab'a "gaskiya ni ban yarda ba, k'arfe 4:00pm na ke so ka dawo","to rigimammiyar matata yadda kike so haka za'ai zan dawo k'arfe 4:00pm insha Allah zan yi kok'arin ganin na gama aiki da wuri" Dariya tayi sosai tare da cewa "to a dawo lafiya" Mota Safwan ya shiga ya ja har ya fita daga gidan Safna tana d'aga masa hannu. Sai da mai gadin ya rufe kofar san ta nufi falon zama tayi a kan kujera ta lumshe ido tunda dai Safwan yace ita ce ruhinsa ai shikenan yanzu dai ta san ita ma tana da matsayi mai girma a gurinshi kuma ta san abubuwan da Safwan yake so da wanda baya so dan haka ta haka zata bi ta kwace mijinta ko da kuma Hafsan ta shigo ba ta isa ta fi ta a gurinshi ba dan ta san ba lallai ne ita ta san abubuwan da yake so da wanda baya so ba, murmushi tayi sannan ta tashi ta shiga gyara gidan wanda yayi kaca-kaca, nan gidan yayi kyau ta shiga kitchen nan ma ta gyara shi sannan ta dawo falon ta kwanta kafin k'arfe uku tayi ta dora girki ta san wajen hud'u ta gama sai ya dawo ya ci abincin da zafinsa. *'BANGAREN GIDANSU JABIR* Da sassafe Aunty Murja ta tashi dakyar tana dafa bango cikin sand'a take tafiyar dan kar ta tashi mijin nata daga bacci, shi kuwa Alhaji Mansur tun lokacin da ta tashi shi ma ya farka wani irin farin ciki ne ya kama shi tabbas tun kafin aje ko ina Murjanatu tana shayar da shi zumar soyayya wacce ya gaza samunta a gurin Hajiya Asiya kitchen ta shiga dan d'akin har da kitchen a cikinsa komai akwai a cikin kitchen d'in dan haka ta fere dankalin turawa ba tare da ta yanyanka shi ba, ta fasa kwai ta saka masa tattaruhu da albasa da su maggi da curry ta shiga tsoma wannan dankali tana soyashi har ta gama ta saka ta wani kwanon kas ta fito dashi ta ajiyeshi a kan teburin ta koma kitchen d'in ta dora ruwan tea ta saka masa citta,kanin fari da masoro sannan shima ta zuba a flask ta d'aukoshi ta ajiye kusa da wannan kwanon dankalin, toilet ta shiga tayi wanka sannan ta had'a masa ruwan wanka ta fito ta shirya cikin wata atamfa kofi colour d'inkin riga da siket tayi kyau sosai zama tayi kusa da Alhaji Mansur d'in dan ta tashe sa yayi wanka ya ci abinci kada ya makara gurin aikinsa. Kallonsa wata iriyar kunyarsa take ji tun jiya, murmushi tayi tare da shafar fuskarsa, idanuwansa ya bud'e ya zuba su kanta suka had'a ido tayi saurin saka hannuwanta ta rufe fuskarta tana dariya, tashi yayi zaune ya jawo ta jikinsa yana kok'arin cire hannuwanta daga fuskarta, Hajiya Asiya ta banko kofar d'akin da k'arfi idanuwanta suka sauka a kan su ganin Aunty Murja a kan cinyar Alhaji Mansur shi kuwa ya rumgumota jikinsa suna ta kokawa wani irin ihu ta kwalla. Babu wanda ya ji ihun domin kuwa kowa yana d'akinsa kuma akwai tazara mai yawa tsananin d'akin Abba da sauran d'akunan, Aunty Murja ta bud'e ido k'irjinta sai bugawa yake amman a fili ba ta nuna tsoro ko fargaba ba, ta shiga kok'arin tashi daga jikin Alhaji Mansur d'in amman bai ba ta izinin yin haka ba, ya rumgumeta sosai dan ko motsi ma bata iya yi, Hajiya Asiya zuciyarta kamar zata fashe "to tsohuwar 'yar bariki ke har kin isa har kina da matsayin da zaki zauna a jikin miji, to wallahi yau sai kin gammace da baki auri Mansur ba" Tayi maganar cikin yanayin tashin hankali. Juyo da fuskar Aunty Murja, Alhaji Mansur yayi suna kallon kallo wani irin murmushi yake sakar mata ita ma tana mayar masa da martani "meyasa ki ka je kika yi wanka ba tare da kin tashe ni mun yi tare ba" Abba yayi maganar yana kallon cikin idon Aunty Murja, ita kuwa duk sai ta ji kunya a wani b'angaren kuma ta ji babu dad'i domin Hajiya Asiya tana nan kuma ta san ta ji abin da ya ce mata. "Ka yi hak'uri ba zan sake yin makamancin irin haka ba, na ga ka na bacci ne shiyasa" Ta bashi amsa domin ta san inda tayi shuru zai ji haushi, kuma yayi fushi da ita,ita kuma a duniyar nan ta tsani Alhaji Mansur yayi fushi da ita, dan ba za ta iya jurewa ba. "To daga yanzu ba bacci ba ko mai kika ga ina yi indai zaki yi wanka ki tashe ni muyi tare","to insha Allahu zan yi yadda kace Yaya" A dai-dai kumatunta ya sumbaceta tare da k'ara rumgumeta. Hajiya Asiya kuwa ta ji duk abin da suka ce, cike da b'acin rai ta ce "dabba kawai abin da ka iya kenan shashasha kawai wanda bai san meyake ba, kuma wallahi ba ka isa ba" Nufarsu tayi gadan-gadan ta d'auki wannan kwanon dankali ta bugashi a k'asa ya tarwatse gaba d'aya a k'asa, cikin zafin nama Alhaji Mansur ya tashi da niyyar yayi mata dukan tsiya. Aunty Murja ta rik'oshi tana murmushi "dan Allah ka barta bai kamata daga tashinka ka fara da b'acin rai ba, kasan ba na son ranka ya dinga b'aci dan Allah ka kyaleta kaji Yaya" Wani irin mari Hajiya Asiya ta zabgawa Aunty Murja wanda sai da ta ji shi har tsakiyar kanta ai kuwa kafin ta sauke hannunta daga fuskar Aunty Murja ita ma ta ji saukar na ta marin a fuskarta wanda ya gigitata har sai da ta saki ihu, haka Alhaji Mansur ya finciketa har sai da suka isa bakin kofar ya hankad'ata ya mayar da kofar ya saka key. Dawowa yayi gurin Aunty Murja tare da dafe gurin da Hajiya Asiya ta mareta sumbatarta yayi a gurin sannan ya rumgume abarsa tare da zama a kan gadon, a kan k'irjinsa ta kwantar da kan ta tare da fashewa da kuka, hankalin Alhaji Mansur yayi matuk'ar tashi ya rasa inda zai tsoma ransa ya ji dad'i d'agota yayi idanuwansa sun kad'a sun yi jajahur "Haba Murjanatu dan Allah ki taimake ni ki yi shuru ki dena kukan nan kin san ina sonki sosai ba na son ganin zubar hawayenki" Goge mata hawayen ya shiga yi amman wasu na k'ara zubowa cikin muryar kuka Aunty Murja take cewa "ni Yaya ba wai marin da tayi min ne yasani kuka ba, irin abin da ta ce maka ne yasani kuka" Murmushi yayi tare da cewa "to ki daina kukan nan ya isa haka,ai idan ita ta fad'a min maganganu da ba su dace ba, ke na san zaki faranta min rai ki sa na manta da abin da ta ce min". Haka dai yayi ta rarrashin ta har tayi shuru ta raka shi ya shiga toilet dan yayi wanka ita kuma tana tsaye a bakin kofa tana jiranshi, yana fitowa ta tare shi da towel tana goge masa jiki dukka shima ya goge a cikin toilet d'in, ita ta zab'ar masa kayan da zai saka, sannan ta taimaka masa ya shirya ya fito a asalin angonshi ruwan tea d'in da ta had'e masa ta zuba masa ta bud'e fridge ta d'auko meatpie da cincin d'in da Hajiya Mama ta saka aka yi mata ta ajiye masa tare da cewa "ga wannan duk da nasan ba lallai ka koshi da shi ba","haba dai wannan kayan dad'in masu yawa ai sai kin taya ni ci ma dan yayi min yawa" Hannunta ya jawo ta zauna kusa dashi suka fara cin meatpie d'in hankalinsu a kwance sai da ta tabbatar ya koshi sannan ta kwashe plate d'in ta kai kitchen, haka suka jera a tare domin ta rakashi zuwa bakin mota ya tafi aiki, babu kowa a falon haka ta rakashi ya shiga mota har sai da ta ga ya fita daga gidan sannan ta koma ta shige d'akinta ta kulle da key. *'BANGAREN SALIS😣* Salis da taikamakon Allah likitoci suka samu suka yi nasara ya farfad'o amman duk da haka babu abin da yake iya cewa sai nishi da sauke ajiyar zuciya idan an ce masa ya jiki baya iya amsawa sai dai kawai ya gyad'a kai, bashi da wani tunani sai na babyn baby, kullum cikin addu'a yake Allah yasa tana cikin koshin lafiya, Allah ya bata kuwa juriyar rashin ganinsa da bata yi, yau kamar kullum yana kwance a kan gado Mama ta tafi gida domin dafa masa abinci babu kowa a d'akin. Doctor Sadiya ce ta shigo d'akin domin duba yanayin jikinshi,bayan ta duba sa ta ga jikin nasa da sauk'i ta juya zata fita Salis cikin rawar murya yana maganar a harhard'e ya ce "doctor dan Allah taimakona nake so ki yi" Juyowa tayi tana murmushi jin yayi magana dan duk da ya farfad'o bai yi magana ba, sai dai kawai ya dinga bin mutane da ido "Wane irin taimako kenan?","wayarki na ke so ki ara min zan kira babyna" Babu musu ta mik'a masa wayar sannan ta fita daga d'akin, shi kuwa Salis ya saka number Nihal a wayar sannan ya kara wayar a kunnansa ring d'aya biyu ta d'auka tare da yin sallama "Assalamu alaikum","Babyna" Salis ya fad'a cikin yanayin farin ciki, Nihal wacce take cikin su Shahida duk ta rud'e hawaye suka fara zuba daga idonta "Babyn baby kai ne, ya jikin naka, ko har yanzu ba ka ji sauk'i ba na ji muryarka wani iri" Da kyar ya iya cewa "Babyna duk rashin ki kusa da ni ne ya saka ni, cikin wannan yanayin wallahi ina sonki sosai" Nihal ta k'ara k'ank'ame wayar dan ji take kamar idan bata rik'e wayar sosai da hakan zai nisantata daga mijin na ta, cikin shash-shekar kuka ta ce "Nima ina sonka sosai, kullum da tunaninka na ke kwana ba na iya bacci, yanzu shikenan saki na zaka yi, ba zamu k'ara zama a matsayin ma'aurata ba?","ba zan tab's iya sakinki ba Nihal domin kin ri ga kin zama wani b'angare na jikina, idan har nayi gangancin rabuwa da ke to tabbas kamar nayi gangancin rabuwa da rayuwata saboda ke ce rayuwata" Kuka ta saka sosai, Khadijatullahi ta rik'eta tana ba ta hak'uri shima Salis d'in kukan yake kuma bai kashe wayar ba, rarrashinta ya shiga yi da kalamai masu dad'i har ya samu tayi shuru, haka dai yayi ta yi mata kalaman soyayya ita ma tana mayar masa har sai da kud'in wayar ya k'are sannan Nihal ta ajiye wayar. Shi kuma Salis a b'angarenshi ya samu sauk'in abin da yake ji a ranshi kuma ya samu nutsuwa doctor Sadiya ta shigo ya ba ta wayar tare da cewa "sai dai kuma mun k'arar miki da credit kuma gashi babu waya a hannuna da na saka miki","Laaa babu komai wallahi" Ta fad'a tare da fita waje, shi kuma ya kwanta wani irin bacci mai dad'i yayi awan gaba dashi. *'BANGAREN NIHAL💔😰* Shuru tayi tana jin wani irin sabon son Salis d'in yana k'ara ratsata, Shahida ta ce "to romeo sai ki daina kukan haka ko?" Amatullahi ta ce "Ahhh kin ji mu da wannan tsohuwar ba dole tayi kuka ba ana shirin rabata da kunun zak'in zuciyarta" Khadijatullhi ta ce "Allah ya shiryeki besty wallahi ke ko, meye wani kunun zak'in zuciya da yake duk salon magana kin san shi" Dariya sosai suka dinga yi dan kuwa maganar Khadijatullahi ta basu dariya Hafsa ta ce "wai besty ya kuwa ginin na ki?","Wallahi Allah ya taimake ni, yana daf da rugujewa na isa na samu na k'ara had'eshi da juna","Allah ya shiryeki to" Khadijatullahi tayi magana tana dariya haka dai sukai ta hirarsu abin ban sha'awa wajen k'arfe hud'u Safwan ya zo d'aukan Hafsa har bakin motar suka raka ta, Khadijatullahi ta so ta nok'e tak'i zuwa Hafsa ta b'ata rai shiyasa a dole ta bi su, suka gaisa da Yaya Safwan d'in sannan suka koma gida. Hajiya Mama wacce take zaune a kan kujera ita da Aliyi suna hira ta kallesu ganinsu reras ta ce "Ohhh ai kuwa idan na zo aurar da ku zan sha kud'i dan ma d'aya daga cikinku ita tana da aure" Tab'e baki Khadijatullahi tayi sannan ta shige d'aki dan ita ba ta son duk abin da ya danganci aure ko kuma namiji "to matar d'aki d'azu kin fito yanzu daga maganar aure shi ne zaki koma"Hajiya Mama ta fad'a tana bin bayan Khadijatullahi da kallo ma d'akin suka nufa Amatullahi ta ce Hajiya Mama "ai ke dai bari wallahi ni zan dinga tara miki kud'in ma, ki dinga shan farfesu" Ta yi maganar tare da shigewa d'akin. Hirarsu suka shiga yi daga k'arshe Nihal ta ce "ya kamata mu je gurin Aunty Murja yau kwananta d'aya kar ta ga ba mu je ba","hakane kam" Amatullahi ta fad'a "ku bari sai gobe kun ga yanzu yamma tayi sosai" Khadijatullahi ta fad'a "Allah ya kai mu goben lafiya" Shahida tayi maganar tana murmushi "Amin ya rabbi" suka amsa gaba d'ayansu. *'WASHE GARI💥🔱* Hankalin Safna a tashe yake gaba d'aya ta kasa tsaye ta kasa zaune, saboda tun da jiya da ruhinta ya fita bai dawo ba, kuma da dare yayi ta ga bai dawo ba ta shirya ta tafi gidan su Hafsa ta ga ko yana chan tana zuwa ta shiga gidan da sallama duk a firgice take dukansu suna falo har da Abbansu Hafsa tana rumgume da Khalid tana yi masa wasa, kai tsaye gurin Hafsa ta nufi tana tambayarta "Hafsa ina ruhina","wanene kuma ruhinki" Hafsa ta tambayeta dan gaba d'aya ta yi tunanin Khalid ta zo d'auka "to ya zaki tambayeki ki fito min da mijina" Sai a sannan Hafsa abin da Safna take nufi ta ce "ni tun jiya da ya kawo ni gidan wajen k'arfe hud'u ya ce gida zai tafi ban sake ganinshi ba","ki ka ce tun jiya ba ki ganshi ba?" Safna ta fad'a hawaye na zuba daga idanta Khalid ya matso kusa da ita yana cewa "Mommy ina Abbana","Ban san inda yake ba, tun jiya da ya dawo d'aukar wata takarda ban sake ganinshi ba" Safna ta fad'a tare da zubewa tana kuka, Khalid ma jikinta ya fad'a yana kuka yana kiran "Wayyo Abbana" Hafsa tun da ta ji abin da Safna ta ce hankalinta ya tashi, mikewa tsaye tayi ta nufi d'akinta da gudu tana kuka, Mama da Abba ne suka lallab'a Safna ta tashi da kyar tare da zaunar da Khalid d'in ta fita daga gidan, haka ta koma gidan zuciyarta babu dad'i, ba ta iya yin bacci ba, har gari ya waye yadda ta ga rana haka ta ga dare. "Ruhina ina ka tafi, kasan ba zan tab'a iya rayuwa ba tare da kai ba, idan har ban ganka ba rayuwata zata lalace, dan Allah ka dawo gareni" Haka tai tayin sambatu abin ban tausayi, t.v da ke manne a falon wacce tun jiya da yamma wajen k'arfe uku da Safna ta kunnata tana kallon bbc hausa ba ta kashe ta ba, ta ji abin da ya saka ta tashin hankali, sanarwa ta ji anyi a kan jiya da yamma anyi hatsari a wajen club road kuma ta san tanan Ruhinta yake bi kullum idan zai dawo gida. Anan fa aka shiga nuna gawarwakin mutanan da suka mutu hango motar Safwan tayi a gefen titin duk ta farfashe wata iriyar gigitatciyar k'ara ta kwalla tare da zubewa a k'asa sumammiya...................!😉💕 Hafsa ce ta shigo gidan a firgice saboda ita ma ta ga hatsarin da aka nuna a bbc hausa k'afafuwanta babu takalmi ko mayafi ba ta tsaya d'auka ba wata huta ce a kan ta, haka ta fito daga gidannasu tana gudu kamar wata mahaukaciya har ta iso gidan Safwan d'in. Kai tsaye falon ta nufa tana gudu, tana shiga ta ga Safna ta baje a k'asa, ta nufeta tana girgizata tana kiran sunanta Amman shuru, wata dabara ce ta fad'o mata da sauri ta nufi fridge ta d'auko ruwa Mai sanyi ta shek'awa Safna, ai kuwa sai gashi ko second d'aya Safna ba ta yi ba, ta farfad'o tare da rushewa da wani irin kuka, rumgumeta Hafsa tayi sukai ta rara kuka. Mama,Abba da Khalid ne suka danno cikin gidan daman gate d'in gidan a wangale yake domin kuwa, saboda dokar da Safwan ya sakawa mai gadin cewar idan lokacin dawowarsa yayi to ya dinga bud'e gate d'in dan baya son ya dawo gidan yayi tayin hon,shi kan shi mai gadi a gigice yake, tun da ya ji labarin hatsarin, a parking space sukai parking, kowanne daga cikinsu hankalinsa a tashe yake, sun fito kenan sun nufi hanyar da zata sadasu da falon gidan sai jin tsayawar mota suka yi a bayansu, ba su iya juyawa ba,sai ma cigaba da tafiya da suka yi sai jin muryar Alhaji Yahaya mahaifin Safwan yana kiran sunansa, da sauri suka tsaya tare da juyawa. K'arasowa suka yi gurin da suke, babu wanda ya cewa d'an uwansa komai suka rankaya suka shiga cikin gidan, ganin yanayin da suka sami su Hafsa yayi matuk'ar ta yar musu da hankali, zama suka yi gaba d'ayansu "ya kamata ku daina kukan nan domin kuwa, ina tunanin Safwan bai mutu ba, dan an duba min gawarwakin mutanan ba'a ga gawar Safwan ba, amman ance min an kai wad'ansu asibiti wad'anda ake tunanin basu kai ga mutuwa ba, na sa Hafiz ya je asibitin domin ya duba ko har da Safwan" A zabure suka tashi jin Abin da Alhaji Yahaya ya ce Safna ta tsugunna a gabansa tana kuka "Dan Allah Abbu ka min rai ka taimaka min ka fad'a min asibitin, na je na duba da kai na ka taimaka min dan manzon Allah" Ta k'arada maganar tana fashewa da kuka mai tsima zuciya. "Safna ki kwantar da hankalinki zuwan da nayi yanzu na zo ne domin, na kai ki asibitin kuma...............","Dan Allah Abbu ka tashi mu tafi to dan Allah dan Allah" Safna ta katse Abbu da maganar da yake shirin fad'a, tare da had'e hannayenta waje guda tana kuka sosai. Hafsa ma magiya ta shiga yi masa, haka Abbu ya tashi Mama da Abba su ma suka tashi, Hafsa ce ta kama hannun Khalid suka fita Hafsa,Safna da Khalid motar Abbu suka shiga, Mama da Abba kuma suka shiga motar da suka zo, Asibitin da aka ce ankai wad'anda sukai hatsarin suka nufi, suna zuwa kowanne daga cikinsu ya fito, gaskiya asibitin yayi matuk'ar had'uwa sosai tun daga farfagiyar asibitin zaka san tsadaddan asibiti ne a wani k'aton signboard an rubuta *JODA SPEACIAL HOSPITAL* Haka suka shiga cikin asibitin wata nurse ce ta nuna musu b'angaren da aka kai wad'anda sukai hatsarin, sukai mata godiya sannan suka nufi b'angaren suna shiga sai ga Hafiz yana shirin fitowa, da sauri Safna ta takumeshi tana tambayarsa "Ina ruhina?","Aunty Safna Yaya Safwan bai mutu ba, yana cikin wanchan d'akin likitoci suna kok'arin ceto rayuwarsa" Yayi maganar yana nuna d'akin da Safwan d'akin yake. Cika Hafiz tayi ta nufi d'akin da ya nuna mata da gudu tana shirin tura kofar wasu nurse suka yi saurin tare ta, cikin zafin nama ta shiga kok'arin ture nurses d'in Mama wad'annan nurses d'in ne suka rirrik'eta nan ta shiga kok'arin kwacewa tana kuka tana cewa "ku barni ina ganshi dan Allah wallahi sau d'aya zan ganshi, in fito ba zan zauna ba, na rokeku ku barni in ga ruhina" Gaba d'aya 'yan gurin ta basu tausayi, Hafsa kuwa gefe ta koma ta rumgume Khalid tana kuka tabbas a yau ta fahimci son da Safna take yiwa d'an uwan nata ba, na wasa ba ne, duk da cewa ita tana ganin ta fita sonshi. Da kyar aka samu aka fitar da Safna daga gurin domin kuwa likitocin asibitin ba sa son hayaniya saboda marasa lafiyan da suke b'angaren masu hatsarin, wajen asibitin Mama ta fito da Safna suka zauna a wasu kujeru tana rarrashinta da kalamai masu dad'i har Safna tayi shiru, a cikin awa d'aya 'yan uwa da abokanan arzik'i suka cika asibitin, suna yi musu jajan abin da ya faru da Safwan d'in har wajen k'arfe biyu sannan kowa ya fara watsewa, Khalid ne shi fito daga cikin asibitin da gudu ya nufo gurin da su Safna suke yana cewa "Mommy ki zo ki gani Abbana ya tashi ya min magana ma" Ai Safna ba ta jira Khalid ya k'arasa fad'ar maganar ba, ta nufi cikin asibitin da gudu Mama da Khalid suna biye da ita. D'akin da Safwan d'in yake ta nufa, ta tarar dashi yana zaune ya jingina da k'arfen jikin gadon idanuwansa suna kallon kofar shigowar an nannad'e masa goshinsa da bandage ga k'afafuwansa duka biyun nannad'e da alama karaya ya samu a duka k'afafuwan nasa, kuka ta fashe dashi lokacin da ta k'arasa kusa dashi. Hannunsa ya saka yana goge mata hawayen fuskarta yana murmushi "meya faru ne ruhina, ya kamata ki daina kukan nan haka, kin gani lafiyata k'alau babu abin da ya sameni","A'a ba gaskiya ba ne, gashi nan goshinka da k'afafuwanka nan sun samu karaya, zaka ce min ka na lafiya, ba gaskiya ba ne na shiga uku" Ta fad'a tana cigaba da kuka. "baki shiga uku ba Safna, saboda ruhinki yana lafiya zan iya yin tafiya sosai tun da kina kusa da ni,ke ce k'afafuwana na san ba za ki bari in ji cewa na samu karaya ba". Hafsa jin irin yadda Safwan d'in yake yi wa Safna ya ma manta da akwai wata Hafsan a d'akin ta nufi hanyar fita daga d'akin har ta bud'e kofar ta ji muryar Safwan kamar daga sama yana cewa "Ina zaki je kuma zuciyata? Dawo nan ina buk'atarki kusa da ni" Hafsa dawowa tayi ta zauna bakin gadon, Abbu,Abba da kuma Mama fita suka yi daga d'akin ganin Safwan d'in ya farfad'o hira sukai tayi abin ban sha'awa domin kuwa Safwan haka yake buk'ata ya had'a kansu tun kafin a d'aura musu aure da Hafsa. *'BANGAREN JABIR DA TEEMARH😂🚴🏽‍♀️* Fitowarta daga wanka kenan d'aure take da towel a k'irjinta wanda ko cinyarta bai k'arasa ba, Jabir ya turo kofar d'akin ya shigo yana rera wak'ar gwarzon mawak'insa Omale tsayawa yayi cak ya k'urawa Teemarh ido yana kallonta daga farko har k'arshe gaba d'aya ya ji wata iriyar muguwar sha'awarta lokaci d'aya rabon da ya kwanta da Teemarh tun ranar da bata da lafiya ya samu yayi mata ta k'arfi bai k'ara kusantarta ba. Teemarh kuwa bata ko kalli inda yake ba ta nufi drower tana tafiya jikinta yana rawa sai kayi tunanin tana sane take yin rawa da jikin nata amman ko d'aya ita bata ma san tana yi ba, wata doguwar riga ta d'auko blue colour. Juyowar nan da zata yi sai tayi ido biyu da Jabir ya k'ura mata ido haushi da takaici suka kamata "to kai kuma menene ka ke kallona kamar wani maye?" Murmushin su irin na cikakkun 'yan bariki yayi mata sannan ya ce "ina kallon kayan dad'i ne" Wata uwar harara tayi masa sannan ta ce "To ta Allah ba ta ka ba kuma nan gani nan bari sai dai kallo da ido, kara ma na saka kayana domin maye irinka sai ka saka min ciwon jiki". Wata iriyar mahaukaciyar dariya ya bushe da ita yana cewa "haba yarinya wallahi ba ki isa ba, yadda ki ka ta yar min da sha'awa wallahi yau sai kin biya min buk'atata","to sai mu gani, idan zaka min dole kuma wallahi Jabir ka kiyaye ni, baka isa ka min komai ba wallahi kwalelen kare da hantar kura" Tayi magana tare da kok'arin saka rigar, bata an kara ba ta ji ya fuzge riga yayi wurgi da ita, ya jawota jikinshi yana kok'arin cire mata towel d'in nan fa suka shiga kokawa tana kai masa duka da kok'arin kai masa cizo a kafad'a ya kama bakinta ya saka 'yanyatsunsa guda biyu ya matse bakin da k'arfi har sai da ta fasa k'ara, Allah ya taimaketa ta daddage ta kai wa k'irjinsa wani irin hauri da gwiwar hannunta yayi saurin cikata tare da dafe k'irjin, ta d'auki hijabin sallanta tana kok'arin sakawa ya fincike towel d'in tare da fizge hijabin yayi wurgi dashi ya rage babu komai a jikinta. Jawota yayi cikin zafin nama ya kwatar da ita a kan gadon ya kama lips d'inta yana tsotsa hawaye ne suka shiga zuba daga cikin idonta, da kyar ta samu ya saki bakinta yana kok'arin saka bakinta a k'irjinta ta shiga bashi hak'uri "dan Allah Jabir ka yi hak'uri ka kyale ba na sallah fa","Ai ko zakka ne bakya yi yau sai kin san wa kika tab'a","dan Allah wallahi na yi maka alk'awarin komai ka ke so zan yi maka dan Allah ka bar ni" Tsaki ya ja tare da cewa sai "kuma ki yi" Haka ya shiga tsotsarta ta ko ina har sai da biya buk'atarsa duk da cewa Teemarh ba ta sallah. (Chabb d'ijam amman Jabir ka cika dabba, ba ta sallan ma ba ka kyaleta ba😂🚴🏽‍♀️❤️) Haka ya shiga wanka ya fito ya shirya cikin wasu shegun riga da wando wad'anda da su gwara babu, ya fita zuwa club domin jiya yayi sababbin kamu, ita kuwa Teemarh haka ta tashi ta shiga wanka ta dago ta d'auki doguwar rigar ta saka, ta koma kan gadon ta kwanta tana k'ara jin haushin Jabir d'in tare da tsine masa har bacci ya d'auketa. *'BANGAREN GIDAN HAJIYA MAMA🔱🌸* Kamar yadda su Khadijatullahi suka ce zasu je gurin Aunty Murja sun gama shiryawa sai Hafsa ta kirawo Shahida tana fad'a musu cewa Yaya Safwan yayi hatsari kuma tana tunanin mutuwa yayi, wannan dalilin yasa suka d'aga zuwa gurin Aunty Murja domin ba za su iya tafiya ba, ba tare da Hafsa ba zama suka yi jugum-jugum suna ta ya 'yar uwar ta su bak'in cikin rashin masoyin nata, ba'a fi awa biyu ba sai ga Hafsa ta sake kiran Shahida tana fad'a musu Yaya Safwan d'in bai mutu ba yanzu haka ma suna asibiti amman da dukkan alamu ya samu mummunar rauni, sun ji dad'in da Safwan d'in bai mutu ba, haka suka barshi a zuwan idan Safwan d'in sun koma gida sai su je su dubashi. Nihal kuwa kwana yau da kewar mijinta ta tashi, dan haka da ta ji cewa Safwan bai mutu ba, haka ta faki idonsu Shahida ta shige bedroom d'in Hajiya Mama, ta kira number da Salis d'in ya kirawota jiya da ita ringing d'aya biyu doctor Maryam ta d'aga wayar tare da yin sallama, daman Salis ya fad'a mata cewa aran wayar doctor Sadiya yayi dan haka Nihal ta amsa mata sallamar tare da cewa "Ina wuni doctor","lafiya alhamdullahi da wa nake magana?" Murmushi Nihal tayi sannan ta ce "Nihal ce matar Salis, wanda ya ari wayarki jiya","Ohhhh nagane ya kike" Nihal cike da kosawa ta ce "Lafiya alhamdulillahi, dan Allah zaki iya had'a ni da babyn baby". Murmushi doctor Sadiya tayi tare da cewa "me zai hana babyn baby" Wani irin kayatatcen murmushi Nihal tayi tare da cewa "To nagode Amman idan Mama tana nan kawai ki san dabarar da zaki Dan Allah ko muryarsa ne, naji dan nasan ba za ta bari munyi waya ba" Tayi maganar Cikin muryar kuka hawaye na zubo Mata, nan doctor Sadiya ta san da akwai matsala tsakanin wad'annan ma'auratan duk da ta ga irin yadda kowannan su ya damu da d'an uwansa. "Meyasa bakya son Mama ta san kuna waya da mijinki","Saboda ta tsaneni, tana kok'arin rabani da babyna, Kuma saboda hakane Yaya Salis yake cikin wannan halin da yake a yanzu" Nan ta kwashe duk yadda suka yi ta fad'awa doctor Sadiya tana kuka tana ba ta labarin. Doctor Sadiya tayi matuk'ar tausaya musu dan haka ta d'auki Alk'awarin taimaka musu a zuciyarta, Amman a fili rarrashin Nihal tayi tare da cewa "ki yi hak'uri kinji insha Allahu komai zai yi dai-dai Kuma Mama da kanta zata zo gurinki rok'on ki koma gidan Salis Allah yasa mudace","Amin" Nihal ta fad'a "Yanzu gaskiya Mama tana nan, Amman kamar yadda kike so zan shiga d'akin a zuwan duba yanayin jikinsa na zo yi na d'anyi Masa tambayoyi idan yayi magana hakan zai saka ki farin ciki ko?","Eh doctor nagode nagode sosai" Doctor Sadiya ta ce "karki damu". Sannan ta nufi d'akin da aka kwantar da Salis d'in Bata kashe kiran ba, Amman ta cireta daga kunnanta,bata k'ara cewa komai ba ita ma Nihal d'in bata ce komai ba kawai dai ta rik'e wayar sosai a kunnanta. Da sallama doctor Sadiya ta shiga d'akin, Mama da Salis Wanda yake kwance a kan gado Yana hutawa gaba d'aya kewar Nihal ta hana shi sukuni, suka amsa Mata sallamar "Mama barka da hutawa","yawwa doctor" Doctor Sadiya ta nufi gurin Salis tare da cewa "Sannu Salis ya jikin","doctor jiki alhamdulillah" Karaf idanuwansa suka sauka a kan screen d'in wayar number babynsa ya gani wani irin farin ciki ya kama shi. Ya kalli Mama tare da cewa "Mama Ina son cin tuwo miyar busasshiyar kubewa","Wayyo yanzu Kuma Nafisa ta tafi gida, Amman Bari na je da kai na nayi na kawo maka" Murmushi Salis yayi tare da cewa "to Mama nagode" Fita Mama tayi daga Asibitin ta hau adaidaita ya suka nufi gidanta. Salis kuwa Mama tana fita yayi saurin k'arb'ar wayar yana cewa "Nagode sosai Doctor","bakomai babyn baby sai a Sha soyayya lafiya" Ta fad'a tana dariya sannan ta fita daga d'akin. "Babyna Ashe dai zai ji muryarka yau" Murmushi Salis yayi ya ce "Eh mana babyn baby, Ina cikin tsananin kewarki sai Kuma gashi nan zan samu kewarta ki ta d'an ragu dan kuwa waya ba zai saka ni na daina kewarki ba, babyna I really miss you badly, yaushe zaki zo ki duba babynki yau satina d'aya a asibiti Amman ace babyna ba ta zo ba","Ka yi hak'uri Ina tsoron Mama ne shiyasa Amman Ina son na zo gurinka, Kuma Nima nayi kewarka sosai" Salis ya ce "Ohh saboda Mama ne shine ba zaki zo ki duba babynki ba, ai shikenan" Yayi maganar tare da kashe wayar. Nihal ta kira wayar kusan sau goma Amman Salis bai d'aga ba, hankalinta yayi matuk'ar tashi ta rasa inda zata tsoma ranta, kuka ta zauna tai-tayi "haba babyn baby meyasa zaka min haka, kai ma kasan ina tsananin son na zo na ganka" Ji tayi an dafata da sauri ta juya tana kallon wacce ta dafata Khadijatullahi tana bin ta da kallon tausayi, zama tayi kusa da ita tare da cewa "Sister na san dole ki ji ranki babu dad'i, amman duk da nasan Mama ba ta son ki tare Salis, ya kamata ki je ki duba yadda jikinsa ya ke hakan zai saka shi cikin farin ciki","to ya ya zan duba shi Sister ko so kike na je ta wulak'antani" Murmushi Khadijatullahi tayi sannan ta ce "menene amfanin nik'af" Wani irin farin ciki ne ya kama Nihal ta ce "kai Sister na ji matuk'ar farin ciki da wannan shawarar","Amman ya kamata ki bari sai gobe, sai ki saka hijabi har k'asa ki saka nik'af babu mai gane ki","to shikenan Allah ya kaimu goben Auntyna" Dariya Khadijatullahi tayi sannan ta ce "Amin amman dai ki ce min Sister zan fi son haka","to shikenan Sister". Haka dai suka tashi suka fito zuwa falo inda su Amatullahi da Shahida suke zama suka yi suka shiga yin hirarsu ta duniya. *'BANGAREN INNA LARAI DA LADO😂* Lado ya gama d'agawa Inna Larai hankali gashi ko da ta je domin ta kirawo Malam Shu'aibu ta ji ya bai turo kud'in ba har yanzu, amman kiran duniya tayi masa ya k'i d'agawa, 'yar yaloluwar katifar d'akinta ta kira wata dillaliya ta shiyeta a dubu biyar, haka dai ta samu ta lallab'a Ladon ta bashi naira dubu biyar d'in bayan sun yi yarjejeniya a kan cewa idan ta d'auki adashinta wani satin zata cika masa kud'insa, ta ce masa ta yarda sannan ya karb'a, amman duk da haka kullum sai yayi mata masifa, haka dai take toshe kunnuwanta. Inna Larai ta cigaba da kok'arin kulluwa Amatullahi makirci saboda tana zargin cewa da hannunta wajen k'in turo da kud'in da Malam Shu'aibu yayi, saboda mai kiran wayar ya fad'a mata cewa Amatullahi ta zo gurinsa ta kira waya ammam bata yi magana a gabansa ba, sai da ta matsa nesa dashi, ai kuwa Inna Larai ta k'ara jin tsanar Amatullahi ta ji zata iya yin komai dan ta ga ta wulak'anta, gashi abin takaicin Lado yanzu baya sauraronta ya ce idan ta ga ya fara sauraronta to ta biya shi ragowar kud'insa, sannan sai su koma kamar da. (Lado uban son kud'i wayyo cikina🤣hawan ruwan Inna Larai zai tashi😂🚴🏽‍♀️) *'BANGAREN GIDANSU JABIR🤏🏾😎* Zaune take a cikin d'akinta wata doguwar riga ce a jikinta pink mai ratsin blue a jiki ta d'aura mayafin rigar a kanta hannunta rik'e da littafin hausa tana karantawa hankalinta kwance, fizge littafin da aka yi ne yasa ta juya bayanta da sauri Alhaji Mansur ne fuskarsa d'auke da murmushi "Wato mijinki ma ya dawo ba ki sani ba kina karatu ko?" Sunkuyar da kanta tayi tana wasa da 'yanyatsun hannunta tana cewa "ka yi hak'uri wallahi ban san ka shigo ba, kuma ban fara karatun ba har sai da na ga lokacin dawowarka yayi ba ka dawo ba". Mik'a mata littafin yayi yana cewa "to na hak'ura, kuma yau aikine yayi min yawa shiyasa ban dawo da wuri ba, na gaji sosai", Sannu ta shiga jera masa, zama yayi a kujerar da ta tashi sannan ya kamo hannunta ya jawota jikinsa yana wasa da ita cikin wani irin salo. Bugun kofar da ake yi ne kamar za'a k'aryata, yasa su dawowa daga duniyar soyayyar da suka lula, Aunty Murja ce ta tashi ta nufi kofar sannan ta bud'e Hajiya Asiya ce, tana ganin an bud'e kofar ta bangaje Aunty Murja sannan ta nufi gurin Alhaji Mansur gadan-gadan "Mansur" Ta kirawo sunansa da k'arfi kai ka ce uwarsa ce ita, wani irin mugun kallo ya watsa mata bai ce mata komai ba ya kawar da kansa gefe "ina fad'a maka da k'akkausar murya ka saki wannan karuwar yarinyar tun kafin nayi maka rashin mutuncin da ba za ka iya dashi ba","to sannu uwata Asiya ban tab'a tunanin ke dabba ba ce sai yau na k'ara tabbatarwa, ko ba rashin mutunci ba bismillah karki fasa yi min, kuma ina sake fad's miki idan kika sake ki a fusata ni to zaki koma inda kika fito shashasha mai shashashar zuciya jahilar banza jahilar wofi" Wasu irin hawaye ne suka zubo mata, lallai ma wato har Mansur ya isa ya gaya mata haka, ai kuwa sai ta tabbatar ya biya abin da yayi mata haka ta fita daga d'akin fuuuuuuuu kamar wata kububuwa, tashi yayi ya nufi kofar ya saka mata mukulli sannan ya kalli Aunty Murja wacce take tsaye kamar an dasata ta kasa ko da motsawa, hannunta ya kama suka nufi kan gadon domin kuwa yana buk'atar ya jita a jikinshi a halin yanzu. Aunty Murja ta bashi had'in kai domin kuwa ba ta da wani buri irin ta ga ta faranta ran mijinta, haka suka tsunduma duniyar soyayya. Hajiya Asiya kuwa tun da ta fita ta shiga d'akinta ta kasa tsaye ta kasa zaune, hankalinta duk a tashe gashi har 'yar wata rama tayi saboda halin da take ciki "ya zama dole na nemi mafita dan kuwa wannan gidan da kuma duk kadarorin Alhaji Mansur nawa ne ni da yarana" Wayarta ta d'auka ta shiga kiran number k'awarta Hajiya Suhaima amman a kashe take wani irin mugun tsaki ta ja sannan ta zauna ta tura mata text kamar haka _Shegiya sai ayi ta kiranki wayarki a kashe to idan kin kunna wayarki, ina son yin magana da ke domin akwai matsala, kuma wannan tsohon najadun ba zai bari in fito yanzu ba_ tana gama rubuta sakon ta tura mata tare da kishin gid'a zuciyarta nayi mata zafi, bacci b'arawo ne yayi awan gaba da ita. *'BANGAREN TALATU😂* Tun ranar da Talatu ta ji cewar Salis yana asibiti hankalinta a tashe yake amman tun da ta ji cewar wai saboda Mama ta je gidansu a kan ya saki Nihal shi ne ya fad'i aka kai shi asibiti ta ji wani irin kishi tare da jin haushin Salis d'in gaba d'aya tashin hankalin da take ciki gamai da rashin lafiyarsa ta nemeshi ta rasa, kuma ta shiga kulla sabon makirci domin kuwa ta rantse ba za ta barsu su k'ara kasancewa a matsayin ma'aurata ba kuma sai ta sakawa Salis d'in tsanar Nihal a cikin zuciyarsa, haka dai kullum cikin sak'a makirci take yi domin kuwa idanuwanta duk sun rufe hatta Salis ji take kamar ta kashe shi kowa ma ya huta. *'BANGAREN NIHAL🥰* Kamar yadda suka tsara ita da Khadijatullahi haka kuwa aka yi washe gari wajen k'arfe 4:00pm na yamma Nihal ta shirya cikin wata farar a atamfa da pupple sai shek'i take ta saka hijabinta har k'asa ta d'aura nik'af ta feshe jikinta da turarirrika kala kala masu kamshi sannan ta fito ta ce Hajiya Mama gida Mami zata je tunda ta dawo gida ba ta je ta ga Mamin ta ta ba, Hajiya Mama ta ce mata to sai ta dawo, saboda tasan idan ta fad'a mata gaskiyar in da zata je zata hanata zuwa, shiyasa ta ce mata hakan, ta fita kai tsaye asibitin da aka kwantar. Doctor Sadiya ta kirawo a waya ta zo ta nuna mata d'akin da Salis d'in yake tayi mata godiya sannan ta shiga cikin d'akin da sallama a bakinta, da sauri Salis ya mik'e jin muryar babynsa domin kuwa ko da ace daga bacci ya tashi zai iya gane muryar Nihal, zama yayi yana sakin murmushi, tsugunwa tayi ta gaishe da Mama har k'asa, Mama ta amsa tana murmushi sannan Nihal ta ke tambayarta ya jikin Mama ta ce da sauk'i, "Allah ya k'ara sauk'i" Nihal ta fad'a tare da zama kusa da Mama wacce take zaune a kan k'atuwar taburma "Amin" Maganar Mama ta dawo da Nihal daga kallon Salis d'in da ta shagala tana yi. Babu damar ta matsa kusa dashi, amman haka ma ta ji matuk'ar dad'i da ya kasance gata nan tana kallon babynta, mintuna ashirin Nihal tayi sannan ta tashi ta yi wa Mama sallama ta nufi gurin doctor Sadiya, Nihal tana fita Mama ta kalli Salis tana cewa "wannan yarinyar tana da hankali gashi ban san wacece ba","nima kam ban san ta ba Mama" Salis ya fad'a tare da komawa ya kwanta yana jin babu dad'i a zuciyarsa, saboda bai samu ya keb'e da babynsa ba. Nihal kuwa tana zuwa gurin doctor Sadiya ta ba ta wata takarda ta ce ta ba wa Salis d'in sannan ta yi mata godiya ta nufi gida zuciyarta fal da farin ciki. *Bayan wata d'aya* Cikin Khadijatullahi ya kai lokacin haihuwa ko yau ko gobe Hajiya Mama ta dena barinta ta fita ko ina Allah ya taimaka lokacin an bada hutun makaranta na first semister wato hutun farkon zango, kullum tana jikin Hajiya Mama, Aliyu kuwa a b'angarensa kullum sai ya zo gidan Hajiya Mama yanzu kuwa da ya ga cikin Khadijatullahi ya kai lokacin haihuwarsa ya tattaro kayansa ya dawo gidan Hajiya Mama domin kuwa a cewarsa Khadijatullahi tana buk'atar kulawarsa shima ba iya kulawar da su Hajiya Mama suke ba ta ba, wani irin tausayinta yake ji kuma bai san meyasa ba duk sanda ya kalli Khadijatullahi sai ya ji wani abu a cikin zuciyarsa. *BANGAREN GIDAN HAJIYA MAMA🌸* A yau ranar talata tun da asuba Khadijatullah ta fara jin wani irin sauyi a tare da ita, Amman ta daure ba tare da ta fad'awa kowa ba, gashi Hajiya Mama ta su Nihal sun fita gidan Kawu Bala matarsa ta haihu kuma baya garin, gidan ya rage daga ita sai Amatullahi sai Kuma Aliyu dan shi kam k'in bin su yayi domin kuwa yana tsoron ya fita kuma Khadijatullah ta tashi nak'uda baya kusa da ita. Wajen k'arfe 8:00am na safe Khadijatullah ta fito daga d'akin ta d'auki buta dan tana son ta kama ruwa, toilet ta nufa tana tafiya a hankali tana yi tana cije Baki a dai-dai kofar shiga toilet d'in ta saki buta tare da kwalla k'ara, a firgice Aliyu ya fito daga d'akinsa ya k'arasa kusa da ita tare da tambayarta "menene?","cikina ka taimaka min" Amatullahi ce ta fito daga d'aki da gudu har tana zabga tuntub'e kama Khadijatullah tayi tana cewa "besty haihuwar ce?" Aliyu ya ce "Amatullahi d'auko Mata hijabi ko mayafi mu tafi asibiti" Yana gama fad'ar haka ya shige d'akinsa ya d'auko mukullin mota Daman sanye yake da jallabiya fara ce sol kallo d'aya zakai mata kasan tsadaddiya ce sosai Yana fitowa ya tarar da Amatullahi har ta d'auko Mata mayafin, Amatullahi ba za ta iya kamata ba, dan haka Aliyu ya rumgumota suka fita har wajen da motarsa take, a bayan mota ya sakata sannan ya shiga mazaunin driver Amatullahi ta shiga bayan sannan ta rufe kofar motar Aliyu ya ja motar da k'arfi sai Asibitin Abbansu *MANSUR SPECIAL HOSPITAL*. Amatullah ta dinga raya abubuwa da yawa a ranta tana ji dama ace Aliyu shine mijin bestynta domin kuwa ta Yaba da hankalinsa shi Sam bashi da hali irin na wannan shashashan d'an uwana sa Wanda bai San ciwon kansa ba. Suna isa Asibitin sai ga wasu nurses da gadon d'aukar mara sa lafiya dan tun a hanya Aliyu ya kira waya a kan suna nan zuwa Asibitin, tare da nurses d'in aka fito da Khadijatullah wacce duk ta gama fita daga hayyacinta, haka aka dorata a kan gadon suka nufi Labour room da Khadijatullah, Aliyu ya so ya shiga Amman babu dama saboda shi ba likita ba ne, shi soja ne Jabir kuma engineer. Haka sukai ta yawo a filin gurin Amatullahi kuka take tana fad'in "Dan Allah besty karki mutu Ina sonki sosai" Zama tayi a kan wata kujera tana cigaba da kukanta, Aliyu ma ji yake kamar yayi kukan Amman wannan lokacin ba lokacin kuka ba ne, dan haka ya shiga yi mata addu'ar Allah ya sauketa lafiya. Sun d'auki kusan awa d'aya a haka Babu wani likita da ya fito, hankalinsu ya tashi, ji sukai tana kok'arin bud'e kofar labour room d'in da sauri suka nufi gurin kofar wata nurse ce ta fito rik'e da jariri a hannunta fuskarta d'auke da murmushi, "nurse ya jikin dija"Aliyu ya tambayeta a gaggauce "ta haihu lafiya an samu d'a namiji ga yaron ma" Ta yi maganar tare da mik'a Masa yaron k'arb'ar yaron yayi tare da k'ura Masa ido kamarsu d'aya sak da Jabir kamar an tsaga kara. Amatullahi kuwa cikin farin ciki mara iyaka ta ce "Alhamdulillah, nurse yanzu zamu iya ganinta?","Eh zaku iya" Nurse d'in tayi maganar tana kok'arin barin gurin Aliyu ya kirata ta dawo aljihunsa ya saka hannu ya d'auko kud'i naira dubu hamsin ya Bata, tayi Masa godiya sannan ta koma gurin aikinta. Shiga d'akin suka yi Khadijatullah suka tarar ita kad'ai tana kwance a kan gadon d'akin tana hawaye kwata-kwata bata k'aunar yaron, tun da ta samu ta haifeshi ta ji zuciyarta tayi mata haske domin kuwa ta rabu da k'aya. Zama suka yi a kan kujerun dake d'akin na roba sai a lokacin Aliyu ya tuna su Hajiya Mama ba su san Khadijatullah ta haihu ba, wayarsa ya d'auko a aljihunsa sannan ya shiga kiran layin Nihal tana d'agawa yake fad'a mata Khadijatullah ta haihu, ihun murna tare da godewa Allah ta shiga yi sannan ta kashe wayar ta fad'awa su Hajiya Mama ai kuwa babu shiri suka fito daga gidan Kawu Bala suka nufi Asibitin a hanya Shahida ta kirawo Aunty Murja take fad'a Mata da yake Abba yana gida dan haka suka shirya suka nufi asibitin, a harabar Asibitin suka tarar da adaidatan da ya d'auko su Hajiya Mama suka k'arasa gurin da suke bayan sunyi parking d'in motarta su suka tsugunnawa har k'asa Abba da Aunty Murja suka yi suna kwasar gaisuwa gurin Hajiya Mama, ta amsa musu cikin sakin fuska sannan suka nufi d'akin da Khadijatullah take duk inda suka huce sai ma'aikatan gurin da likitoci sun tsugunna suna ta kwasar gaisuwa suna shiga Amatullahi ta nufi gurin da Shahida da Nihal suke ta ce "kun kira besty kuwa?","A'a yanzu zan kirata" Shahida tayi maganar tare da d'auko wayarta Hafsa ta kira take fad'a mata Hafsa ta haihu,babu shiri ta fito ta Ado driver ya nufi da ita asibitin da yake asibitin ba wani boyayye ba ne, a cikin awa minti talatin asibitin ya cika damkam da jama'a Jabir,Teemarh da mahaifiyarsa Asiya kuwa ba su san abin da ke faruwa ba, kuma babu wanda yayi gangancin sanar dasu, domin a cewarsu ba yanzu ya kamata su san komai ba, akwai abin da Hajiya Mama da kuma Alhaji Mansur suke shiryawa wanda babu wanda suka sanar sun barshi a cikin zuciyarsu. *'BANGAREN SAFWAN DA SAFNA* Safna wata iriyar kulawa ta musamman take ba wa Safwan kullum tana manne dashi, ji take wannan karayar dama a k'afarta take ba a tasa ba, wani irin sonshi da k'aunarshi take ji suna k'ara ratsata domin kuwa Safwan kullum cikin kasheta yake da kalaman soyayya ita kuma sai k'ara narkuwa take a cikin kogin soyayyarta, yau ma kamar kullum tana zaune a kan kujera kusa dashi ta dora kanta a kan kafad'arsa idanuwanta a lumshe ta kama hannayensa duka biyun ta rike "Ruhina" Safwan ya kirata cikin wata iriyar murya mai rikita zuciya "Na'am Ruhina'' Safna ta amsa tana mai bud'e idanuwanta tare da d'ago kanta tana kallonsa ido cikin ido tana sakar masa wani irin murmushi. "Ruhina ban san meyasa ba kullum nake k'ara jin sonki da k'aunarki a cikin zuciyata, ina sonki sosai Ruhina tabbas na k'ara yarda cewa Safna ke ce Ruhina", Safwan yayi maganar yana kallonta cikin wani irin yanayin soyayya, "Hafsa kuma zuciyarka kuma Rayuwarka ko?" Tayi maganar hawaye na zuba daga cikin idanuwanta domin kuwa duk sanda ta tuno cewar Safwan zai auri Hafsa kuma daga ranar da ya aureta shikenan ya zama ba na ta ita kad'ai ba, kuma ita ma Hafsan haka zai dinga yi mata kalamai kuma gashi ma a gabanta ya ce Hafaa zuciyarsa ce kuma Rayuwarsa ita kuma kawai Ruhinsa ce kuma tana tunanin kawai dai dan ya ga tana son shi sosai ne shiyasa yake biye mata kuma uwa uba saboda d'ansu Khalid. Safwan cikin yanayin damuwa ya shiga share mata hawayenta yana cewa "Haba menene haka Safna matsayin da kike dashi daban haka ma, matsayin da Hafsa take dashi daban yake da naki, yanzu kenan ba ki yarda cewa ina tsananin sonki ba, haba Safna ka da kishi ya rufe miki ido mana, duk abubuwan da nake ce miki wallahi har cikin zuciyata nake fad'a". Ita dai ba ta iya cewa komai ba, sai shash-shekar kuka da take yi rumgumeta Safwan yayi yana bubbuga mata bayanta yana cigaba da yi mata kalaman soyayya har ya samu tayi shiru "Safna d'in ruhina ce kuma sarauniyar zuciyata, wallahi da gaske nake babyna ki kalli cikin idona zaki tabbatar da abin da nake fad'a miki" Safna ta d'ago tana murmushi dan kuwa yanzu burinta ya cika ita ma dai sun zama dai-dai da Hafsa, "Da gaske ni ce sarauniyar zuciyarka kuma ruhinka", Kai ya d'aga mata alamar eh, dariya ta fara yi tare da rumgumeshi tana cewa "na ji dad'i sosai ruhina". Murmushi yayi kuma sai yanzu ya fahimci a kan abin da Safna yasa take kuka saboda ya ce Hafsa ita zuciyarsa ce kuma rayuwarsa ita kuma ya ce ruhinsa ce kad'ai amman yanzu da ya ce ita ce sarauniyar zuciyarsa har ta sake ta fara dariya "hmmm Safna kenan wato bakya k'aunar ace Hafsa ta fiki ko kad'an a gurina" Yayi maganara zuciyarsa haka dai yayi ta lallab'ata har tayi bacci a jikinsa ya gyara mata kwanciyarta sannan ya kunna t.v yana kallon labarai. *'BANGAREN TEEMARH DA JABIR* Teemarh kam tun da Jabir kwanta da ita bata sallah anan ta tabbatar shi d'in cikakken jahili ne ko ita da take ganin cewar bata da ilimin addini sosai amman tabbas ta san abubuwa sosai da ya danganci musulunci, kuma tana ji ana cewa babu kyau a kwanta da macen da take yin jinin haila, to kuma gashi shi ya aikata harumun, shi kuwa Jabir abin nasa sai gaba gaba yake yi sai ya shafe wata biyu baya gidan yana club yana shek'e ayarsa ita kuwa Teemarh ko a jikinta dan kuwa yanzu ta fara jin son Jabir yana fita daga cikin ranta. Kwance take a kan kujera tana kallon episode d'in *Kwana casa'in a tashar arewa 24* gaba d'aya ta mai da hankalinta da tunaninta a kan t.v domin kuwa tana son Film d'in yana burgeta sosai, daga ita sai vest da wani dogon wando ya matseta sosai, tsaye yake ya k'ura mata ido rabonshi da ya ganta yau sati hud'u kenan, bai san meyasa ba yanzu wata iriyar Sha'awar Teemarh yake ji duk sanda ya dora idonsa a kan ta sai ya ji wata muguwar sha'awarta kamar zai mutu. D'aukarta yayi cak kamar wata jaririya, a gigice Teemarh ta shiga dukanshi tana cewa "Sauke ni, ka sauke ni na ce", Sai da ya zauna sannan ya ajiyeta yana yi mata wani murmushi "ki kwantar da hankalinki, ba zan k'ara yi miki abin da bakya so ba kinji babyna" Wata iriyar muguwar harara ta yi masa domin kuwa ita bata ga dad'in bakin da Jabir zai yi mata ba da har zata fad'a tarkonshi domin kuwa ta san wannan abin da yake yi mata akwai wata a k'asa kallonta ta cigaba da yi ta ba wa banza ajiyarsa, shi kuwa Jabir bai damu ba domin kuwa yasan idan ya lallab'a Teemarh yasan dole zata fad'a tarkonshi sai ya dinga biyan buk'atarsa da ita hankalinsa kwance dole sai ya ribace ta ya nuna mata cewar yana sonta sosai amman a zuciyarsa sha'awarta kawai yake yi. (to fa ko Teemarh zata amince ta fad'a tarkon nasa kuwa, ko kuma dai ba za ta amince ba, nima ban san amsar ba amman idan kun cigaba da biyoni zaku ji amsoshin tambayoyinku). Hajiya Asiya kuwa tana zaune jigum sai ga k'awarta Hajiya Suhaima ta shigo gidan kyakkyawa ce ajin farko kallon d'aya zakai mata kasan kud'in sun zauna sark'arta abin hannunta duka na gwal ne zama tayi kusa da Hajiya Asiya sannan ta dafata tare da cewa "K'awata meyasa ne ki haka ne" Ajiyar zuciya tayi sannan ta ce "Abin duniya sun taru sun min yawa k'awata" Nan ta kwashe duk abin da ke faruwa ta fad'a mata, Hajiya Suhaima ta shek'e da wata iriyar mahaukaciyar dariya tare da cewa. Hajiya Suhaima ta kalli Hajiya Asiya ta ce "Lallai k'awata kin yi babban sake da har ki ka bari aka auro miki wata a matsayin abokiyar zama,amman bakomai har yanzu lokaci bai k'ure mana ba, ki tashi ki je ki shirya zan kai ki wani guri in da za'a gama mana da ita ta bar duniyar ma baki d'aya kowa ma ya huta" Wani irin mugun Murmushi Hajiya Asiya tayi sannan ta ce "daman na san ke ce zaki fitar da ni daga cikin damuwar nan da nake cikinta a yanzu, dan haka na shirya yin komai dan na ga an kawar da wannan shegiyar 'yar matsiyata, kuma zance na je na shirya ai bai ta so ba,ni a shiryena na ke kawai tashi mu tafi" Wani mayafi ta d'auka ta yab'a a jikinta sannan suka fito zuwa farfagiyar gidan motar Hajiya Suhaima suka shiga tsadaddiyar mota ce mai numfashin gaske drivernta ya ja Hajiya Suhaima ta fad'a masa inda zai kai su daman ya san gurin dan kullum sai ya kai Hajiya Suhaima anan take kwana sai da safe yake zuwa ya d'auketa, sun yi tafiya mai nisa sannan suka isa wani babban daji ba gida gaba ba gida baya kofar wani gida suka tsaya sannan driver yayi parking d'in motar Hajiya Suhaima ta ce masa ya fita zasu yi magana,kafin ta rufe bakinta idris driver ya fita daga cikin motar ya tsaya nesa da motar. Hajiya Suhaima ta kalli Hajiya Asiya ta ce "K'awata ina son ki yi mini alk'awarin ba za ki ba ni kunya ba idan mun shiga gidan nan, domin kuwa a gidan nan bayan kin cika burinki na gamawa da kishiyarki, to zaki samu dukiya mai tarin yawa, ni kai na ta dalilin gidan nan na samu kud'in da nake dashi a yanzu kuma ba na tunanin akwai ranar da zasu k'are, na sanki sosai k'awata kina da matuk'ar son ace gashi yau ke ma kina da tarin dukiya" Murmushi Hajiya Asiya tayi ba tare da tayi tunanin komai ba, domin kuwa tana tsananin son kud'i wannan dalilin ne ma yasa take son yaranta su auri masu kud'i kuma wannan dalilin ne yasa ta auri Alhaji Mansur. ''Ni wallahi kin ba ni mamaki, ke kan ki kin sani a kan kud'i zan iya yin komai kuma zan iya hallaka kowa, in dai burika na zasu cika na samun kud'i da kuma gamawa da waccen munafikar 'yar matsiyatan" Hajiya Suhaima ta ce "to shikenan na ji dad'i" Haka suka fita daga cikin motar suka nufi cikin gidan, daman Hajiya Suhaima ta fad'awa Hajiya Asiya cewar ba'a sallama a gidan daman ita ma ba yin sallamar take ba, dan kuwa rabon da tayi sallama har ta manta, Wani dogon bene suka hau wanda matattakalarsa zasu iya kai wa d'ari, Hajiya Asiya har ta fara gajiya da hawa benen amman haka ta d'aure har suka gama hawa benen, wani babbar kofa ta ga Hajiya Suhaima ta nufa ita ma ta bi ta a baya, suna shiga d'akin Hajiya Asiya ta ci karo da abin da ya gigizata ta kurma wata iriyar k'ara tare da rintse ido tana ja da baya wasu mutane ta gani sanye suke da jajayen kaya suna zazzaune hannayensu rik'e da k'atuwar k'warya ga wani jan abu a ciki da alama jini ne, ga wata jaririya nan an yanka mata wuya da alama dai ita suka yanka kuma suke shan jininta, ta juya domin ta fita daga d'akin amman ta nemi kofar da suka shigo ta rasa. Gabanta ya shiga fad'uwa abin da take jin shi a radio yau ga shi ta ganshi da idanuwanta, kenan nan gidan 'yan mafiya ne masu shan jinin mutane, wannan yana nuna cewar Hajiya Suhaima ita ma tana cikin su kenan, ji tayi an dafata domin kuwa ta kasa juyowa ta kuma kallonsu, juyowa tayi da niyyar taa fusace domin a tunaninta Hajiya Suhaima ce amman sai ta ga akasin haka, wani kyakkyawan saurayi ne, son kowa k'in wanda ya rasa, kallonsa take cike da jin haushi shi kuma kallonta yake yana murmushi "Haba gimbiyar mata menene abin firgita anan dukanmu fa mutane ne, ko kin ga abin tsoro a jikinmu ne" Hajiya Asiya ta ce "Ku dawo da kofa ni zan fita domin kuwa duk rashin imani na ba zan iya abin da kuke aikatawa ba" Tayi maganar cikin wata iryar muryar tashin hankali. Wani murmushin ya k'ara sakar mata sannan ya ce "me muka yi na rashin imani, dan mun nemi duniyarmu shine zai zama rashin imani, kuma zancen ki fita ai bai ta so ba, domin duk wanda ya shigo nan d'akin to sai na tabbatar ya zama d'aya daga cikin 'yan k'ungiyarmu sannan zan bar sa ya fita","to ni ba na buk'ata ana dole ne?" Tayi maganar cikin bala'i da masifa, murmushi yayi sannan ya ce "ba'a dole amman kuma zaki yi danasani mara adadi, domin kuwa zamu kashe 'ya'yanki ga baki d'ayansu, Jabir, Aliyu, Shahida da kuma 'yar autarsu wacce kika fi so Nihal, idan kina son ki tsetar da yaranki to idan kuma bakya buk'ata to ga hanya zaki iya tafiya"Ya k'arasa maganar tare da nuna mata kofar fita daga d'akin hankalin Hajiya Asiya ya tashi tabbas ba ta son wani abu ya faru da yaranta kuma tunda wad'annan mutane suka iya shafe kofar ta b'ace babu abin da ba zasu iya yi ba kallon saurayin tayi sannan ta ce "na yarda zanyi abin da kuke so, karku tab'a min yarana" Murmushi yayi sannan ya ce "shikenan ai kin tseratar da yaranki, tunda kin yarda" Anan dai wannan saurayin ya ba wa Hajiya Asiya wasu abubuwan na asiri wanda zasu kek'ashe mata zuciya ta ji ba ta tsoron duk abin da zata yi ko suka sakata tayi. (tofa jama'a Hajiya Asiya ta shiga k'ungiyar masu asiri ya zata kaya kenan😎😳) *'BANGAREN SALIS* Jikin Salis ya dad'a rikicewa wanda a yanzu baya iya gane wanda ke kansa, babu abin da yake iya yi sai sunan Nihal da yake fad'a hankalin Mama yayi matuk'ar tashi ta rasa inda zata tsoma ranta, gashi doctor ya ce mata idan har ba'a ba sa abin da yake so ba to haka jikin nasa zai ta yi, ita kuma ta san Nihal yake son a dawo da masa da ita, dan haka babu shiri ta nufi gidan Hajiya Mama domin ta yi bikon Nihal. Tana shiga gidan ta tarar da Hajiya Mama a tsakar gida tana shan iska su Nihal kuwa suna gidan Kawu Bala babu kowa a gidan ita kad'ai ce, Mama ta tsugunna har k'asa ta gaisar da Hajiya Mama bayan ta yi sallama ta k'araso gurin da Hajiya Mama take zaune,Hajiya Mama ta amsa mata cikin sakin fuska tare da yi mata izinin da ta zauna, ta zauna sannan suka d'an tab'a hirarsu ta duniya sannan Mama ta fara fad'ar abin da ya kawota "Hajiya Mama daman nazo ne a kan ina so Nihal ta koma d'akinta, saboda zamanta haka ba son shi muke ba gaba d'ayanmu" Murmushi Hajiya Mama tayi sannan ta ce "Ai wannan tsakaninku ne uwa da y'arta, yanzu dai suna gidan Kawunsu amman zuwa anjima zasu dawo zan turo miki ita" Mama tayi murmushi sannan ta ce ''to shikenan Hajiya Mama nagode sosai" Daga nan suka cigaba da yin hirarsu sannan Mama tayi wa Hajiya Mama sallama ta tafi, Mama tana fita Hajiya Mama ta ce "Ohh ni yau na ji ikon Allah, wato d'anki yana kok'arin mutuwa shine zaki rarrafo wani biko, to ko zata koma ma ba yanzu ba, sai nan da sati uku" Anan Hajiya Mama tai-tayin fad'a ta inda ta shiga ba tanan take shiga ba. *'BANGAREN TEEMARH DA JABIR🤣* Jabir babu yadda bai yi ba a kan ya shawo kan Teemarh ta fad'a tarkonsa amman Teemarh ta gama sanin wanene Jabir da kuma shaid'ancinsa, ya dena fita ko ina kullum yana gida dan ya samu ya yaudari Teemarh tayi tunanin kamar ya dena abin da yake yi, amman a banza domin kuwa Teemarh sam magana ma bata barin ya shiga tsakaninsu, fitowarsa kenan daga toilet yana d'aure da towel ya kalli Teemarh da take zaune a kan kujera tana kallon wani series a Arewa 24 na indian *'kaddarar rayuwa* "darling ki zo ki taimaka min in shirya kinji" Yayi maganar yana marairaice murya, Teemarh tayi kamar ba ta ji mai yace ba, dan ko kallo bai isheta ba, har sai da ya k'ara maimaita maganar da yayi sau biyu sannan ta ce "indai ni zan taimaka maka ka shirya ai kuwa zaka dad'e baka saka kaya ba" Tayi maganar ba tare da ta kallesa ba. K'arasowa yayi har inda take sannan ya zauna kusa da ita suna fuskantar juna "darling" Ya fad'a tare da mayar da fuskarsa ta tausayi "menene?,wai Jabir me na tsare maka a duniya ka dameni?","babu komai kawai ina so na nuna miki irin yadda na ke sonki ne","hmmmm" Abin da Teemarh ta ce kenan, haka dai Jabir ya k'ara ci suturansa ya tashi ta je drower wasu kayan ball ya d'auko green colour a bayan rigar an rubuta Jabir d'in Teemarh, zama yayi kusa da ita suna yin kallon tare Teemarh dai kam ba ta da lokacin biye masa shiyasa tayi shuru ba ta ce masa komai ba. *'BANGAREN KHADIJATULLAHI* Zaune suke a falon Hajiya Mama dukansu sun sakata a gaba yau kwana uku kenan da Khadijatullahi ta haihu amman bata tab'a shayar da jaririn ba, da an zaunar mata da yaron ance ta shayar dashi sai ta saka kuka ta ce ita ba ta so, haka zasu yi su gama har su hak'ura Hajiya Mama ta kalli Khadijatullahi wacce sai kuka take yi sosai tare da cewa "Khadijatu yanzu haka ake rayuwa ace ba za ki shayar sa yaro ba, so kika ya mutu ne?" Ba ta ce komai ba sai ma k'ara sautin kukanta da tayi Aliyu wanda ya zuba mata ido yana kallonta ya ce. "Dija me jaririn nan yayi miki, dan manzon Allah karki hukuntashi a kan laifin da ba na saba, ki sani fa shi yaro ne k'arami bai san meyafaru a tsakaninki da Yaya Jabir ba, ida da ace yaron nan zai girma a bashi labarin irin abin da Yayana yayi miki to wallahi sai ya fi ki shiga damuwa, tunda an wulak'anta masa mahaifiyarsa, dan Allah Dija ki karb'eshi ki shayar dashi kar ya mutu". Ya k'arasa maganar cikin yanayin tashin hankali zuciyarsa cike da bak'in cikin Halin da Khadijatullahi take cikin yanzu musamman da ya ga hawaye na zubowa daga idonta duk sai ya ji ya tsani duniyar da abin da ke cikinta, domin kuwa ya tsani ya ga tana kuka. Karb'ar yaron yayi daga hannun Hajiya Mama ya mik'a mata, tare da cewa "Dan Allah ki tausaya masa ki bashi abinci kar ya mutu","ba na son shi" Amin da ace kenan tana kuka, "to na ji bakya sonshi, ina son ki shayar da yaron nan na wata bakwai ni kuma nayi miki alk'awarin ki fad'a min komai kike so zan yi miki shi" Kallonsa tayi tare da d'an tsagaitawa da kukan na ta "da gaske", kai ya gyad'a mata alamar "eh". "Ina son Jabir ya wulak'anta, ina son yayi mutuwar da ko gawarsa ba za'a iya ganewa ba, sai ana tattaro naman jikinsa saboda irin yadda ya ragargaje kuma..............." Saukar marin da Aunty Murja tayi mata ne, yasa ta rik'e gurin kuma ta kasa k'arasa abin da take son ta fad'a kuka ta saka tare da yunk'urin tashi Aunty Murja ta hankad'ata ta koma ta zauna ta karbi yaron daga hannun Aliyu ta dora mata a cinyarta "ga shi nan idan kin ga dama karki shayar dashi, tunda ke kwata-kwara baki da hankali ki je ki yi duk abin da zaki yi dan kin ga an zauna ana lallab'aki to dan manzon Allah karki shayar dashi ki barshi ya mutu shashasha kawai mara tunani" Tana gama fad'ar haka ta fita ta zauna a kan taburma a tsakar gida wani irin haushin Khadijatullahi take ji, saboda irin maganganun da tayi a gaban 'yan uwan Jabir d'in. Amatullahi ta kalleta tare da cewa "Ai kin huta tunda har kin sa Aunty Murja fushi saboda wannan bak'ar zuciyar ta ki ai sai ki yi ta yi, dan Annabi tsabar tsanar da kike yi wa Jabir ki kashe jaririn idan kin kashe shi, shi ba asararsa ba ce, tun da bai san ma kina yi ba kuma ko yau jariri ya mutu ko a jikinsa, amman ki yi abin da kika ga dama tun da haka kika zab'arwa kanki". Ita ma Amatullahi fita tayi kusa da Aunty Murja ta zauna tana raya abubuwa da yawa a ranta, tana son d'aukarwa bestyn ta ta fansar abin da Jabir yayi mata dan yanzu ma shirin da take yi kenan, amman yau bestyn ta ta taba ta haushi sosai, saboda Amatullahi ranta yana matuk'ar son jaririn dan har suna ta bashi Affan dan da haka take kiranshi. Khadijatullahi kuwa kukanta ya k'ara sauti tana kallon Aliyu shi ma d'in ita yake kallo, yana durkushe a gabanta, "ka ce musu zan shayar dasu su yi hak'uri ba zan k'ara ba","to idan kina son na fad'a musu to ki shayar dashi yanzun nan dan na fad'a musu, kuma na basu hak'uri, kin ga sai kuka yake yi" Aliyu ya fad'a idanuwansa na cikin na ta. Kallon jaririn take yi wanda sai tsala kuka yake yi ta saka shi a cikin hijabinta sannan ta shiga shayar dashi, shuru Affan yayi yana tsotsar abincinsa, Hajiya Mama,Nihal,Shahida da Aliyu ajiyar zuciya suka sauke tare da godewa Allah da Khadijatullahi yau ta shayar da Affan. Tashi Aliyu yayi gurinsu Aunty Murja yake basu hak'uri kuma ya fad'a musu Khadijatullahi yanzu haka tana shayar da Affan ne, sun ji dad'i sosai suka tashi suka shiga d'akin Khadijatullahi tana ganinsu ta saka kuka tana cewa "dan Allah ku yi hak'uri ku yafe min na dena" Zama Amatullahi tayi kusa da ita tare da rumgumeta ta ce "Ai yanzu komai ya huce indai zaki dinga kular mana da Affan d'inmu babu wanda zai dinga jin kanmu","Hakane kam indai kina so mu shirya to ki kula da Affan amman wallahi na k'ara jin kina tsangwamar yaron ko kina cewa bakya sonshi to wallahi idan na tafi ba za ki sake ganina ba" Aunty Murja ta fad'a fuskarta babu alamun wasa. "ba zan sake ba"Khadijatullahi ta fad'a muryarta na rawa dan tasan Aunty Murja tunda ta fad'i haka to zata aikata kuma ita bata son ace yau Aunty Murja tayi fushi da ita dan ita kad'ai ta rage mata a duniya, zama suka yi suna yin hira sama sama Khadijatullahi ta fito da Affan daga cikin hijabi baccinshi yake yi hankalinsa kwance, Nihal ce ta karb'eshi ta goyashi. *Bayan Sati d'aya* Inna Larai ce zaune ta zabga tagumi ta rasa abin da yake mata dad'i gashi ta je gurin Lantana mai adashi dan ta karb'i kud'in adashinta amman Lantana ta ce mata wai ta zo ta karb'a, ita maganar nan ta d'aure mata kai ta ya ya za'a ce ta karb'i kud'in adashinta bayan ita ta san bata karb'a ba, har police station sai da suka je a kan maganar amman Lantana ta kawo shaida har guda uku da ya suka tabbatarwa da 'yan sanda a gaban su Inna Larai ta shigo ta karb'i kud'in adashinta, wannan dalilin ne yasa 'yan sanda suka yiwa Inna Larai kaca-kaca, tare da yi mata jan kunne a kan idan ta k'ara kawo musu irin wannan maganar sai sun kamata tunda ita macuciya ce, Lado kuma gashi ya gama d'aga mata hankali dan kuwa har 'yan sanda ya kirawo mata bayan ta dawo daga police station ganin zasu tafi da ita ne, yasa ta ce musu su tsaya zata kira dillaliya ta zo ta siyi kayan d'akinta ta biya shi kud'insa. Lado ne ya tafi ya kira dillaliya ta siyi kayan d'akin naira dubu goma sha biyar a gurin ta ba wa Lado kud'insa sannan ta ce masa ya tafi gidan ubansa ba ta buk'atarsa, Lado bai damu ba ya tattara kayansa ya koma gidan mahaifinsa duk da cewa ba ya jin dad'in zamansa a gurin mahaifin nasa saboda irin yadda Matar mahaifinsa take yi masa wulak'anci ga tsangwama. Duk abin da yake faruwa tsakanin Lado da Inna Larai Amatullahi tana sani kuma kud'in adashin Inna Larai ranar da zata d'auki kud'in ita ce ta saka kayan Inna Larai ta je gidan Lantana mai adashi irin yadda tayi shigar kai zaka rantse Inna Larai ce, ta karb'i kud'in adashin, ta koma gidan Hajiya Mama. *(wayyo ni Amatullahi fa kin iya tsula tsiya😂😂wato ki kayi shigar inna larai kaii Amatullahi duniya🚴🏽‍♀️🚴🏽‍♀️😂)* *'BANGAREN TALATU😂* Babu irin bokayen da 'yan tsibun da bata bi ba, a kan su taimaka mata takoma gidan Salis kuma su sakawa Salis tsanar Nihal ya ji ko me, irin sunanta ya ji an ambata ya ji ya tsaneta, amman sai dai suyi ta karb'e mata kud'i amman har yau shuru babu alamar burinta zai cika dan haka ta d'auki d'amarar kashe Nihal ko ta halin ya ya dan a cewarta idan ta kashe Nihal dole Salis ya dawo gareta, shiri sosai ta shiga yi na ganin bayan Nihal har gidan Hajiya Mama sai da ta saka aka binciko mata. Ranta ya b'aci matuk'a da ta ji cewar Salis d'in jikinsa ya k'ara tsananta baya fad'ar sunan kowa sai na Nihal kuma labarin da ya k'ara girgizata shine da ta ji cewar Mama ta je bikon Nihal, a ranar sai da Talatu ta zama kamar mahaukaciya gaba d'aya ta gigita mutanan gidan sai kulleta aka yi a d'aki ta gama zage-zagenta da buge-buge dan Inna tayi tunanin ma haukacewa tayi dan har ta cewa 'yan uwan Talatun su kira motar asibiti dan su tafi da ita, Delu k'anwar Talatu ta ce mata "lafiyarta k'alau kawai zafin kishi ne Inna" Sai da tayi kusan kwana biyu a d'aki ba'a bud'eta ba, sai da Inna ta tabbatar da cewa Talatu ba ta haukace ba sannan ta yarda aka bud'eta. *'BANGAREN HAJIYA ASIYA👹* Hajiya Asiya ta zama cikakkiyar 'yar k'ungiyar Matsafa ko kad'an tsoron da take ji na shan jini da kuma yanka jarirai yanzu ya fita daga ranta ta zama cikakkiyar mara imani dan wataran ita take yanka musu jarirai su sha jininsu kud'i kam Hajiya Asiya yanzu ta samesu dan kullum cikin k'ara samun kud'ad'e take yi yau Hajiya Suhaima aka cewa ta kowa mahaifiyarta domin suna buk'atar su sha jininta babu musu Hajiya Suhaima ta amince a daren ranar ta kawo mahaifiyarta kuma ita da kanta ta yankata suka sha jininta, A ranar wannan saurayin da na lura cewa shine shugabansu ya nad'a Hajiya Suhaima a wakiliyarsa domin kuwa tayi abin da ya kamata a yaba mata, kwana sukai suna tsaface-tsafacensu sai da gari ya waye sannan kowa ya fito ya kama hanyar gidansa. Hajiya Asiya tana shiga motarta ta js da gudu ta bar gurin abin Hajiya Suhaima tayi yayi matuk'ar bata mamaki dan kuwa ta san irin yadda Hajiya Suhaima da mahaifiyarta suke matuk'ar son junansu kuma mahaifiyarta tana yi mata duk abin da take so kwata-kwata bata son b'acin ranta, amman ace ta yankata da hannunta kuma ba tare da ta nuna damuwarta ba. Da wannan tunanin ta k'arasa gida tana shiga ba ta tarar da kowa a falo ba dan haka ta huce d'akinta Alhaji Mansur ta gani zaune a bakin gadon d'akin ya k'urawa kofar shigowa ido, ko da suka had'a ido ta kawar da kanta gefe, Alhaji Mansur ya k'araso har inda take fuskarsa a murtuke kamar wanda bai tab'a yin murmushi ba "daga ina kike?" Kok'arin tureshi take ta huce amman ya rik'eta cikin tsawa yake cewa "ba tambayarki nake yi ba" Kuka ta fashe masa dashi tare da cewa "menene amfanin amsa maka tambayarka bayan baka damu da ni ba, kafi damuwa da wannan shegiyar matar ta ka, ka fifita ta fiye da ni, kullum kana ik'irarin kana sona to wannan shine soyayyar da ka ke yi min?","Asiya kome nake yi miki a yanzu ke kika jawowa kanki kin b'ata min tarbiyyar yara kin lalata musu rayuwarsu, kuma uwa uba baki d'auke ni a matsayin mijinki ba tunda har zaki iya saka k'afa ki fita har ki je wani gurin ki kwana baki fad'a min ba kai ni na fuskanci ma kwanannan bakya kwana a gida, ina kike zuwa?" Kukanta ya tsananta domin kuwa tasan haka shi zai saka Alhaji Mansur ya rabu da ita da tambayoyin da yake mata da bata da amsar da zata bashi, dan tasan a duniya babu abin da ya tsana irin ya ga matarsa tana kuka, ganin irin kukan da take yi ne yasa Alhaji Mansur ya rabu da ita ya fita daga d'akin zuciyarsa cike da tambayoyi a kan Hajiya Asiya dan kuwa ya d'auki alk'awari sai ya binciko abin da Asiya take b'oyewa domin kuwa zuciyarsa ta fara zarginta. *'BANGAREN SAFWAN,HAFSA DA SAFNA👨‍👩‍👦* Zaune suke a farfagiyar gidan suna hirarsu ta masoya Hafsa ta kalli Safwan ta ce "Ruhina" Tayi maganar cike da tsokanarsa, zaro Ido yayi tare da cewa "Lallai na ga alamar so kike Ruhina ta Zane ki, kin satar Mata suna" Dariya tayi sosai sannan ta ce "A'a fa Allah ya huci zuciyar Ruhin Ruhi" Shima dariyar yayi sannan ya ce "Awww haka ne kam fad'i ki k'ara fad'a, ke Kuma zuciyata ba","A'a nima Ruhinka ce na barwa Aunty Safna nawa Nima nasan zata bar min na ta" Tayi maganar cike da Shagwab'a. "Hakane kam" Safwan ya fad'a tare cigaba da kallonta, suka cigaba da yin hirarsu sai wajen k'arfe 4pm ya bar gidansu Hafsa ya nufi gidansa, da sallama ya shiga falon Amman abin da ya bashi mamaki bai ga Safna ba, domin ya Saba Yana shigowa da ita yake fara cin karo zata rumgumeshi tayi Masa sannu da zuwa. D'akinta ya shiga ya tarar da ita ta kifa kanta a kan guiyoyinta sai shash-shekar kukanta ka ke ji yana tashi da sauri ya k'arasa kusa da ita Yana cewa "Subhanallahi Ruhina me ya faru Baki da lafiya ne?" Yayi maganar Yana d'ago Mata kanta kallonsa take shima ita yake kallo cikin muryar kuka ta ce "Lafiya k'alau nake","to meya sa ki kuka?","bakomai" Safna ta yi maganar tare da fashewa da sabon kuka. Hankalin Safwan ya gama tashi ya jawo Safna gaba d'ayanta zuwa jikinsa Yana kissing d'inta har sai da ta yi shuru sannan ya cigaba da tambayarta "menene Ruhina?","bakomai Ruhina" Ta fad'a tana sauke ajiyar zuciya mai nauyi "ban kai matsayin da zan san damuwarki ba? Wato baki d'auke ni a matsayin Wanda zaki dinga fad'awa damuwarki ba ko?","A'a ba haka ba ne Ruhina kai d'in kana da matuk'ar muhimmanci a wajena"."To fad'a min me ya ke damunki?" D'agowa tayi tana kallonsa ta ce "Ruhina da gaske gobe za'a saka ranar aurenka?" Tayi maganar hawaye na kok'arin zubo Mata. Shuru yayi Yana kallonta na tsawon mintina sannan ya ce "haka ne" Hawayen da suke kok'arin zubo tana mayar dasu suka samu damar silalowa zuwa kan kuncinta, hannunsa ya saka Yana goge Mata hawayen fuskarsa ta nuna tsantsar damuwa Amman haka ya shiga b'oye damuwarsa Yana murmushi ya ce "Ruhina saboda haka shine kike yi min asarar hawayenki, to ba na son na k'ara ganin wannan kyakkyawar fuskar tana kuka, saboda tana da matuk'ar tsada da muhimmanci gurina, kin san ko da na auri Hafsa ba zan tab'a wulak'anta ki ba, karki manta fa ke ce Ruhina" haka dai Safwan yayi ta tsara Mata kalamai har ya samu ta sauko ta dena kuka, hirar soyayya suka shiga yi da nunawa junansu irin yadda suka damu da juna. *'BANGAREN TEEMARH DA JABIR😂* "Darling! Darling!! Darling!!!" Jabir ya shigo d'akin yana zabgawa Teemarh Kira, Teemarh kuwa tana jinsa tayi banza dashi sai ma tsaki da ta ja ta koma kan gado tayi kamar wacce take yin bacci, Jabir kuwa ya ga sanda Teemarh ta kwanta dan haka ya nufi kan gadon gadan-gadan yana yin wani shu'umin murmushi. Kwanta yayi kusa da ita tare da jan ta jikinsa da sauri ta tashi tana zabga Masa harara sauka tayi daga kan gado ta nufi kujerun d'akin ta zauna, biyota yayi ya zauna kusa da ita "darling wai me nayi miki ne, wallahi Ina sonki sosai sweetheart","to Jabir na ji Kuma nagode Amman Dan Allah ka kyaleni ba na sonka ni" duk da cewa ya ji haushin kalamanta, Amman Kuma ya zamar Masa dole ya kwantar da kansa ya samu abin da yake so gurin Teemarh. "To na ji Darling bakya sona kuma na san duk abin da kika yi min zuciyata ce ta jawo min tunda ta kasa dai na sonki" Yana gama fad'ar haka ya tashi ya futa daga d'akin, Teemarh ta bi bayansa da kallo sai kuma ta ji ba ta ji dad'in abin da tayi masa ba, zuciyarta ta k'arye ji take kamar ta bi sa ta ce masa ta hak'ura kuma tana sonshi amman kuma ta san Jabir farin sa ni ta ya ya zata yarda cewa ba yaudararta zai yi ba, kuma da gaske yana sonta, dole sai ta tabbatar da cewa yana sonta ba yaudararta zai yi ba sannan zata yarda dashi. Da wannan tunanin ta tattara ta koma kan gado ba'a fi minti d'aya da kwanciyarta ba wani irin bacci mai nauyi yayi awan gaba da ita. *'BANGAREN ABBA DA AUNTY MURJA* Tunda ya fito daga d'akin Hajiya Asiya ya shiga d'akin Aunty Murja kwance ya tarar da ita tana karatun littafi tana ganinsa ta ajiye littafin ta tashi ta zauna tana kallonsa fuskarsa ta nuna mata cewa yana cikin damuwa dan haka ita ma lokaci d'aya ta shiga tsananin damuwa, zama yayi kusa da ita tare da zabga tagumi, hannu ta saka ta cire masa tagumin tare da girgiza masa kai alamar "A'a" sannan ta ce "Yaya hankalina ya tashi zuciyata ta shiga tsananin damuwa saboda, sarkin da yake mulkarta yana cikin damuwa, shin ya zan yi da raina". Murmushi yayi sannan ya ce "to matata ki kwantar da hankalinki ina cikin koshin lafiya kawai dai lamarin Asiya ne yake ba ni tsoro kullum abin ta cigaba yake yi, kwata-kwata bata ba ni matsayina na mijinta" Ajiyar zuciya Aunty Murja tayi sannan ta ce "Addu'a ya kamata mu dinga yi mata, insha Allahu wata rana zata fahimci cewa kuskure take aikatawa kuma ina mai tabbatar maka da cewa zata gyara duk kuskurenta ka ji dan Allah karka saka wannan a ranka". Wani irin farin ciki ne ya kamasa tabbas yana matuk'ar alfahari da Murjanatu domin kuwa duk sanda ta ganshi cikin damuwa hankalinta ba ya kwanciya har sai ta ganshi yana cikin farin ciki, "Allah yayi miki albarka matata","Amin mijina" Ta fad'a tare da sakar mata murmushi, daga nan suka koma kan gado suka fad'a duniyar soyayya. *'BANGAREN SALIS* Mama hankalinta ya tashi matuk'ar tashi tun ranar da ta je gidan Hajiya Mama take ta faman jiran ganin Nihal amman gashi yau sati biyu babu Nihal babu alamarta, Salis kuwa jikin na shi kullum k'ara tsananta yake yayi bak'i ya rame sosai, Baffa mahaifin Salis ne ya shigo d'akin bakinsa d'auke da sallama da sauri Mama ta k'arasa gurinshi tare da fashewa da kuka tana cewa "Malam ka taimaka min ka je ka dawo masa da matarsa kar ya mutu dan Allah ba ni da wani d'a shi kad'ai ne gareni ina matuk'ar sonshi sosai dan Allah ka taimaka min Malam" Mama ta k'arasa maganar tare da had'e hannuwanta guri d'aya alamun rok'o. Murmushi Baffa yayi sannan ya ce "Sai yanzu kenan kika sauko kin ga yaronki yana kok'arin mutuwa ko? To ba da ni ba wannan abin kunyar gwanda............'' ,"Dan Allah Malam karka min haka ka taimaka min wallahi sharrin shaid'an ne da kuma matarsa Talatu da tazo ta fad'a min k'arya da gaskiya a kan Nihal ni kuma na zauna a kai, amman yanzu na gane gaskiya wallahi ba zan sake ba" Mama ta k'atse Baffa da maganar da yake son yi, Baffa ya ji tausayinta matuk'a dan haka ya kalleta sosai sannan ya ce "Zan je na bada hak'uri kuma zan yi kok'ari na ga na dawo da Nihal k'afata k'afarta amman sai kin yi min alk'awarin duk wanda ya sake kawo miki wata magana a kan Nihal k'arki ji ta, kuma ki yi masa kaca-kaca","Wallahi nayi maka alk'awarin zan doshe kunnuwana daga jin maganganun Talatu a kan Nihal". Jinjina kai yayi sannan ya ce "to shikenan zan je na dawo da ita zuwa gobe","Allah ya kaimu" Mama ta fad'a cike da farin ciki "Amin ya rabbil'almin"Baffa ya fad'a sannan ya mik'e saboda jin kiran sallar da yayi ya ce "bari na je nayi sallah","to a dawo Lafiya" Mama ta fad'a Baffa ya fita da sauri ya nufi masallaci. *'BANGAREN ALIYU❤️* Kwance yake a kan tafkeken gadon da ke d'akin nasa idanuwansa suna kallon saman d'akin gaba d'aya hankalinsa da tunaninsa suna kan Khadijatullahi wani irin abu yake ji duk sanda ya dora idanuwansa a kanta, ko da ace yana cikin bak'in ciki ne idan ya dora idonsa a kanta sai ya ji wani irin farin ciki yana ratsa zuciyarsa, idan kuwa ya wuni bai ganta ba baya tab'a samun nutsuwa har sai ya dawo yayi arba da kyakkyawar fuskarta, a hankali ya furta "Dija ta" tare da sakin wani irin murmushi wanda yake nuna tsantsar farin cikin da yake ciki "wai daman ashe haka so yake? ban tab'a tunanin haka so yake da dad'i ba sai da na fad'a sonki wanda ni kai na ban san lokacin da na fad'a cikin kogin soyayyarki ba sai ganina na yi a cikinsa Dija ta" Yayi maganar a fili tare da juyawa jikinsa "Dija ta na san cewa kin tsani maza sosai, amman insha Allahu ni zan cire miki wannan tsanar da ki kai wa maza, zan tabbatar nasa kin fahimci cewa ba duka maza ne suke da hali irin na Jabir ba ina sonki babyna". Khadijatullahi ta sauko daga iriyar muguwar k'iyayyar da take yiwa Affan har tana jin son yaron a cikin zuciyarta, Amatullahi kullum Affan yana gurinta ba ta ba wa Khadijatullahi shi har sai idan yana kuka alamar yana jin yunwa tana gama shayar dashi za ta karb'eshi tayi ta lallab'a yaron kamar wani kwai, Affan yafi sabawa da Amatullahi a kan Khadijatullahi, Nihal da Shahida kuwa ba'a magana dan kuwa kullum tare suke kwana dashi suna jin d'uminsa, ko kuka suka ga yana yi hankalinsu ya tashi har sai sun ga ya daina. Zaune suke a tsakar gida kamar yadda suka saba kullum da yamma zasu shimfid'a taburma su yi ta hirarsu ta duniya, Aliyu ne ya fito daga d'akinsa sanye yake cikin wani yadi tsadadde brown yayi kyau sosai tafiya yake a hankali kamar wani mai sand'a har ya k'araso inda suke ya tsugunna har k'asa yana gaisar da Hajiya Mama "Ina yini Hajiya","Lafiya alhamdulillahi" Hajiya Mama ta fad'a tana sakar masa murmushi, guri ya samu ya zauna yana satar kallon Khadijatullahi wacce tun zuwansa ta had'e fuska kamar wacce ba ta tab'a yin dariya ba, Nihal ta kalli Aliyu tana murmushi ta ce "Yaya Haidar wai kwana biyun nan na ga ka na d'aukar wanka da yamma, ko dai an samo mana Aunty ne" Harara ya wurga mata sannan cikin muryarsa mai jan hankali ya ce "To ke kuma uwar 'yan sa ido, meye ruwanki da ni ko kuma so kike ki ganni kace-kace kamar wata ke" Zaro ido Nihal tayi tare da dafe k'irji kamar wacce tai gano ta ce "na shiga uku Yaya Haidar ni ce 'yar sa ido, kuma k'azama" Tayi maganar cikin muryar shagwab'a. Shahida ta ce "Ai Other half wallahi Yaya Aliyu Haidar ya fad'a mai zurfin baki ga kwana biyun nan ba sai ki ga yana ta wani smiling shi kad'ai" Dariya su ka yi gaba d'ayansu amman ban da Khadijatullahi wacce har lokacin fuskarta babu alamar murmushi "Awww har da ke ko darling sister"Aliyu yayi maganar tare da satar kallon Khadijatullahi "Eh mana Yaya Aliyu Haidar ai ina kula da kai sosai yanzu fad'a mana wannan wace mai sa'a ce tayi sa'a sace zuciyar Yayanmu, zuciyar da take da matuk'ar tsada 'yan mata da yawa suna son su ga cewa wannan kyakkyawar zuciyar ta so su","hmmm! Shahida kenan kawai ku ta ya ni da addu'a kun ji, dan ina tsananin buk'atar haka a halin da nake ciki yanzu" Nihal ta kalli Aliyu sosai, ta fuskanci yana cikin tsananin damuwa "To Yaya Allah Ubangiji ya fitar da kai" Nihal ta fad'a tana cigaba da kallon d'an uwan na ta, Shahida ta ce "Amin ya rabbi". Amatullahi da ta fuskanci inda maganar Aliyu ta dosa dan ta fahimci cewa Aliyu yana tsananin son Khadijatullahi, saboda irin yadda yake nuna kulawarsa a kan ta, da kuma yadda yake sadaukar da abubuwa da yawa a kan ta, amman kuma tana tausaya masa saboda ta san cewa Khadijatullahi ba lallai ta yarda ta so shi ba, kuma ko da zata yarda gaskiya sai an kai ruwa rana "Yaya Aliyu Allah ya fitar da kai ya dora ka a kan wacce ka ke so, tayi maka son da ba ka tab'a tunani ba, ta so ka da dukkanin zuciyarta" Murmushin jin dad'in Addu'ar da Amatullahi tayi masa yayi sannan ya ce "Amin Allah ya sa sister nagode sosai","Amin" Suka amsa gaba d'ayansu. Hajiya Mama tana jefe tana jin su ita dai ba ta ce musu komai ba dan kuwa ita ma tuntuni ta fahimci cewar Aliyu yana son Khadijatullahi, ta ji dad'i sosai amman kuma ta wani b'angare na zuciyarta tana tausayawa Aliyun saboda Khadijatullahi ba lallai ta so shi ba, ta tsani maza bayan haka kuma ta tsani Jabir wanda hakan ya shafi Aliyu shi ma ta tsane shi, Aliyu ya tashi daman ya zo ne ya ga Khadijatullahi ya kalli Hajiya Mama tare da cewa "Hajiya zan je gidan Musaddik ba zan dad'e ba zan dawo","to A dawo lafiya" Aliyu ya ce "Allah yasa'' Sannan ya fita daga gidan motarsa ya shiga ya d'auki hanyarsa zuwa gidan Abokinsa Musaddik. Hajiya Mama suka cigaba da yin hirarsu har sai da aka kira sallar magriba sannan suka tashi kowannansu ya doro alwala suka gabatar da sallar magriba, ko da suka gama suka yi addu'o'in da ake yi bayan anyi sallah sannan suka dora hirarsu daga inda suka tsaya. *'BANGAREN TEEMARH DA JABIR💕🥀* Sanye take da wata doguwar riga tana share d'akin rigar tayi matuk'ar kamata sosai, ji tayi an bud'e kofar d'akin da sauri ta d'ago kai suka had'a ido da Jabir wanda yake tsaye a bakin kofar ya hard'e hannuwansa a k'irjinsa yana kallonta yana murmushi, a hankali kuma ya tako zuwa inda take "Love d'inta sannunki da aiki" Kallonsa tayi kamar ba za ta yi magana ba sai kuma ta ce "yawwa sannunka" Sannan ta cigaba da yin sharar sai da ta gama share d'akin gaba d'aya sannan ta zauna a ksn kujera ta kunna t.v, tashar Arewa 24 ta kai ta tarar ana yin episode d'in *k'addarar rayuwa* wani irin murmushi tayi dan tana bala'in son film d'in, Jabir yana kallonta dan yana tsaye a gurin da ta huce ta barshi ya k'i motsawa. Sai da aka gama episode d'in ta juya dan ta ga inda Jabir d'in yayi dan ta ga yau bai takura mata ba, dan tayi tunanin ma ko ya fita daga d'akin ne, mamaki ya kamata ganinshi a tsaye kamar wani soja a gurin da ta huce shi kuma idanuwansa yana kanta, abin har ya so ya ba ta dariya amman ta shanye tare da cewa "menene ka ke yi a tsaye ko dai soja ka dawo ne ban sani ba?" Zuwa yayi ya zauna kusa da ita "ba dole na zama sojan k'arfi da yaji ba Love d'ita tana fushi da ni, kuma na rasa yadda zan yi nasa ta fahimci cewa ina sonta, amman ita ta fifita kallon film fiye da mijinta" Murmushi tayi sannan ta ce "hmmm Jabir kenan yaudararka wacece ban sani ba kai kan ka kasani na sanka sosai fiye da yadda baka tunani, na san wannan nacin da kake min akwai buk'atar da kake so ka cimma a kai na, dan haka wallahi ni ba zan tab'a yarda da kai ba". Wata iriyar muguwar ajiyar zuciya ya sauke tabbas shi kansa yasan Teemarh ta san halinsa sosai, kuma yasan dole sai ya samu wannan k'alubalan wajen shawo kanta amman kuma dole sai ya tabbatar ya sa ta yarda da cewa yana sonta dan ya samu buk'atarsa a gurin Teemarh "Teemarh, nasan cewa ba za ki tab'a yarda da ni ba saboda irin abubuwan da nayi miki amman dan Allah ina so ki ba ni dama dan na tabbatar miki da cewa ina sonki","ko kuma kana son jikina ko?" Teemarh ta fad'a tana kallonsa ido cikin ido, Jabir ya rasa me zai ce mata kawai sai ya tashi ya fita wai shi a dole ya nuna mata yayi fushi, ita kuma Teemarh tab'e baki tayi sannan ta kwanta a kan kujera tana chatting, a haka har bacci ya kwasheta. *'BANGAREN BAFFAN SALIS🚴🏽‍♀️💕* Washe gari kamar yadda yayi wa Mama alk'awari da misalin k'arfe 2:00pm na yamma bayan yayi sallar azahar ya nufi gidan Alhaji Mansur, yana isa mai gadi yayi masa iso Alhaji Mansur ya cewa mai gadin ya kai shi falon bak'i gashi nan zuwa, haka ya fita ya shiga da Baffa falon bak'i, ba'a fi minti d'aya ba sai ga Alhaji Mansur ya shigo falon bakinsa d'auke da sallama "Assalamu alaikum" Da sauri Baffa ya tashi tsaye tare da amsa masa sallama "Wa'aikumussalam ranka ya dad'e" D'aure fuska Alhaji Mansur yayi tare da cewa "Amman ka ba ni mamaki sosai, ta ya za'ai ka na zaune ina shigowa ka tashi tsaye, raina yayi matuk'ar b'aci sosai" Baffa cikin girmamawa ya ce "Allah ya huci zuciyarka insha Allahu zan kiyaye gaba" Murmushi Alhaji Mansur yayi sannan ya ce "Allah ya sa, zaka iya zama" Ya fad'a yana nuna masa kujera". Zama yayi sannan suka gaisa Baffa ya fara fad'a masa abin da ya kawo shi "da farko dai Alhaji ina mai ba ku hak'uri a kan irin abin da Mahaifiyar Salis tayi muku na sa ni bata kyauta ba kuma na ji matuk'ar kunyarka saboda na san anyi muku ba dai-dai ba, amman ina mai neman alfarmar da Nihal ta dawo d'akinta" Alhaji Mansur ya gyara zamansa sannan ya ce "Haba dan Allah sirikina saboda haka ne daman ka zo har nan, ai na ga Salis ba sakinta yayi ba dan haka insha Allahu gobe zan dawo da ita har asibitin kuma dan Allah kayi wa Salis d'in ya jiki kafin na zo" Baffa yayi wa Abba godiya sosai sannan ya tashi ya tafi shima Abba ya koma d'akin Hajiya Asiya dan yau anan yake. *'BANGAREN ALIYU💃🏽💕* Dawowarsa kenan daga gidan Musaddik sai ga Nihal da Shahida sun shigo d'akin sun zauna kusa dashi, kallonsu yayi tare da sakar musu murmushi ya ce " 'yan biyu meya faru?" Nihal ta ce "Yaya Haidar gurinka muka zo" Kallonsu yayi sannan ya ce "To gani nan 'yan k'annai na" Shahida ta ce "Yaya Aliyu Haidar wa ka ke so?" Kallonta yayi kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce "Khadijatullahi" Waro ido Nihal tayi tare da fashewa da kukan tausayin d'an uwana ta tabbas daman ta so ta fahimci haka saboda irin yadda yake yi mata, amman ta ya ya Khadijatullahi zata karb'i soyayyarsa bayan ta tsani kowane namiji kuma tana ganin irin yadda Khadijatullahi take nuna tsantsar k'iyayyarta a kan Yayan na su. "Haba darling sister idan kina kukan nan sai zuciyata ta k'arye ai" Aliyu yayi maganar zuciyarsa nayi masa zafi, Shahida ta ce "Yaya Aliyu Haidar ai dole tayi kuka, kai ma kasan dai Khadijatullahi irin yadda ta tsaneka sosai ta ya za'a ta so ka, Yaya Aliyu Haidar wallahi ni............" Sai kuma ita ma ta saka kuka, hankalinsa yayi matuk'ar tashi shima yasan ya d'aukowa kan sa babban aiki amman kuma ba laifinsa ba ne laifin zuciyarsa ne, rarrashinsu ya shiga yi sannan ya samu su ka yi shiru, nan da suka d'aukar masa alk'awarin zasu taimaka masa har sai Khadijatullahi ta so shi, suka shiga kwantar masa da hankali ganin irin yadda ya damu sosai, Aliyu cikin raunanniyar muryarsa ya ce "Nagode muku sosai darling sisters, na san kun damu da ni kuma na san na d'aukowa kai na babban aiki, shiyasa na ce muku ku ta ya ni da addu'a","Insha Allah zamu ta ya ka kuma zamu taimaka maka wajen ganin Khadijatullahi ta so ka" Nan dai suka yi masa alk'awari kala-kala a kan Khadijatullahi sai sun san yadda su ka yi ta so shi. *'BANGAREN ASIYA👹* Yau ya kasance za'a fad'i wanda zai kawo musu wanda za'a sha jininshi bayan sun gama tsaface-tsafacensu Wannan saurayin da har yau ban san sunansa ba ya mik'e ya gama zagaye su sannan ya zo gaban Hajiya Asiya ya tsaya tare da mik'a mata wata laya ta karb'a sannan ya ce "me za ki kawo mana kishiyarki da kuma mijinki dan muna buk'atar shan jininsu" Hajiya Asiya tayi tare da cewa. "Alhaji kuma? Gaskiya ba zan iya ba da mijina ba" Ta yi maganar tana kallonshi ido cikin ido, ransa yayi matuk'ar b'aci cikin muryar da ta ke bayyanar da tsantsar b'acin rai ta ce "To idan kuwa ba za ki kawo shi mu sha jininsa ba to ki tabbatar da cewa lokacin mutuwarki yayiii dan kuwa za mu sha jininki, gobe da daddare mu ke buk'atar ki kawo su idan kuwa ba ki kawo su gaba d'aya ba to tabbas zan kasheki ne" Ya k'arasa maganar yana dora mata wata iriyar zagegiyar wuk'a a wuyanta, gabanta ne ya shiga fad'uwa, haka dai suka gama kowa ya fito dan tafiya gidansa, Hajiya Suhaima ce ta biyo bayan Hajiya Asiya wacce har ta bud'e motarta zata shiga kiran sunanta tayi da k'arfi "Asiya" Juyawa Hajiya Asiya tayi ranta a b'ace a halin yanzu wata iryar muguwar tsanar Hajiya Suhaima ta ke ji, domin kuwa ita ta ja mata ta kawota nan gidan, ita tayi tunanin ai gurin wani boka za su je ya gama musu da Aunty Murja. "Menene?" Ta yi maganar tana wurga mata wani irin kallo, wata iriyar dariya Hajiya Suhaima ta fashe da ita tana cewa "Ke daman kina tunanin cewa zaki sha jinin iyayen wasu, mazajen wasu, da kuma 'yaya da k'annan wasu ki ce wai ke ba za'a sha na mijinki ba, to wallahi ba ki isa ba, dole sai mun sha jinin mijinki, kuma ni ba haka na so ba, na so ace jinin wannan tambad'adden d'an naki a ka ce, amman mu je zuwa na san wata rana dole sai mun sha jinin d'an tsinanniya" Wani irin mahaukacin mari Hajiya Asiya ta zabgawa Suhaima hagu da dama sai da ta jera mata kusan sau biyar, sannan ta ce "To wawiya dabba ki sa ni burinki ba zai tab'a cika ba, dan kuwa ko Abban Jabir ba za ku sha jininsa ba ballantana yarona Jabir, ke ce tsohuwar mahaukaciya da har zaki iya ba da mahaifiyarki tabbas asara da tab'ewa su tabbata a gareki shashasha jaka mara tunani" Tana gama fad'ar haka ta shige motarta ta ja da k'arfi ta nufi gidanta. Wannan saurayin ya saki murmushi ya ce "Asiya kenan kina wasa da Jafar uban matsafa amman Allah ya kaimu gobe za ki ga aiki da cikawa, kar Allah ya sa ki kawo su ki ga abin da zai faru da ke" Yana gama fad'ar haka shi ma ya tafi gidansa, Hajiya Suhaima kuwa nan ta kuduri niyyar sai ta lalata Ahalin Asiya gaba d'aya, ta jima tana sake-sake sannan ta nufi motarta ta ja ta bar gurin, zuciyarta fal bak'in ciki. *'BANGAREN AMATULLAHI👰🏼‍♀* Tafiya ta ke yi cikin nutsuwa da kuma aji, a haka har ta isa club d'in da Jabir ya ke zuwa, nesa da club d'in ta tsaya,daga gurin da take ana iya hango cikin club d'in ta jima tana raba ido ta ga ta ina zata hango Jabir amman babu alamar Jabir a gurin ta shafe kusan awa d'aya tana tsaye sai chan ta hango Jabir ya fito daga hotel yana rumgume da wata budurwa da alama ta sha ta bugu sosai "Shege d'an gidan mahaukaciya, wallahi na juyo gareka sai ka gommace kid'a da karatu" Wani yaro ne ya zo hucewa ta yi saurin kiransa "kai yaro dan Allah zo" Zuwa yaron yayi tare da cewa "ga ni" Wata takadda ta ba shi, sannan ta nuna masa Jabir tare da cewa "Wanchan za ka kaiwa wannan takaddar dan Allah" karb'a yayi tare da cewa "to zan ba shi" Yaron ya nufi gurin da Jabir yake sai da Amatullahi ta tabbatar yaron ya ba wa Jabir wannan takaddar sannan ta juya ta nufi gidansu dan ta ga halin da 'yan gidan su ke. Amatullahi irin yadda take bibiyar Jabir ko mahaifiyarsa Hajiya Asiya ba ta yi masa, dan kuwa duk guraren da ya ke zuwa sai da ta bincikosu kuma duk motsin da yake yi tana sane dashi dan kuwa ya d'auki aniyyar d'aukarwa Khadijatullahi fansar abin da yayi mata sai ta tabbatar da wulak'antasa ta hana shi sukuni, tana shiga gidan ta tarar da abin da ya bata tsoro Inna Larai ta gani tare da Malam d'an ladi mai guga sun fito daga d'akin Inna Larai wani irin ihu ta fasa tare da fita waje ta tsaya dai-dai kofar gidan tana cigaba da kurma ihu, ai kuwa mutane su ka yi kanta suna tambayarta meya faru? "Inna Larai da Malam d'an Ladi mai guga na gani sun fito daga d'aki" Ta yi maganar tana kuka, ai kuwa nan jama'a su ka shiga gidan suka tarar da su Inna Larai da Malam d'an Ladi a tsaye duk sun rud'e dan sun san yau asirinsu ya gama tonuwa, dukan Malam d'an Ladi suka shiga yi ba ji ba gani, Inna Larai ta shige d'aki tare da kulle kofar tana kuka. Amatullahi kuwa wayar wani Adamu ta ara ta kira Mahaifinta ba fad'a masa komai ba bu abin da ta b'oye masa, hankalinsa ya tashi anan take ya ce ta ba wa Inna Larai ta ce ai ta shiga d'aki ta kulle ya ce to ki ce mata ta gaggauta fitar min daga gida na saketa saki uku, ba na buk'atar sa ke ganinta, a rayuwata yana gama fad'ar haka ya kashe wayar zuciyarsa na yi masa zafi, Adamu ta ba wa wayarsa tare da shiga gidan dan kuwa ba za ta bar Inna Larai ta k'ara ko da minti biyar ba a gidan, d'akinta ta nufa ta d'auko wani k'arfe mai tsini sannan ta nufi d'akin Inna Larai tana buga kofar d'akin da k'arfi tare da cewa "to tsinanniya tsohuwar 'yar bariki ki bud'e kofar nan ki bar mana gida dan Babana ya sake ki saki uku, sai ki je ki cigaba da yin karuwancin na ki a chan wani gurin amman ba'a gidan nan ba" Tana magana tana buga kofar kuma irin bugun da ta ke yi wa kofar ba na wasa ba ne, Inna Larai jin abin da Amatullahi ta ce ta fashe da kuka tare da saka kayanta a buhu ta bud'e kofar dan ta san halin Amatullahi ba ta k'i ta k'arya kofar ba kuma ta yi mata rashin mutunci. Hanyar fita daga gidan Inna Larai ta nufa tana jin kunyar kanta saboda irin mugayen maganganun da 'yan unguwar ta su suke fad'a mata Amatullahi ta bi ta a baya tana zungurarta da k'arfen tana cewa "Allah ya ra ka taki gona, sai a bi wani sarkin ba dai Yarima ba" Jama'a Unguwar kuwa bayan sun gama yi wa Malam d'an Ladi duka suka cukumeshi sau police station, Amatullahi ta ja kofar gidan ta mukulle da mukulli sannan ta nufi gidan Hajiya Mama ranta fas, dan kuma a rana d'aya ta jefi tsuntsu biyu da dutse d'aya. *'BANGAREN HAFSA, SAFWAN DA SAFNA😉* A yau aka saka ranar Safwan da Hafsa wata hud'u aka saka, ta kira Shahida ta fad'a mata sannan ta ce ta fad'awa su bestynta, Shahida ta yi mata murna tare da yi mata Allah ya sanya Alkhairin Hafsa ta amsa da Amin, daga nan suka kashe wayar, tana ajiye wayar ko minti biyar ba'a yi ba wayar ta shiga ruri da sauri ta d'auki wayar tare da kallom screen d'in wayar Hayatee ta gani murmushi tayi tare da d'aga wayar ta kara a kunne tare da cewa "Assalamu alaikum Yayana" Daga chan b'angaren Safwan wanda yake cikin office d'in ya ce "Wa'alaikumussalam Amaryata" Rufe fuskarta Hafsa ta yi kamar yana ganinta ba tare da ta ce komai ba, Safwan yayi ta tsokanarta, amman Hafsa yau kam ba ta biye masa ba, dan wata iriyar kunyarsa take ji dan har ba ta so ya zo dan ba za ta iya fita ba, a haka dai suka d'an d'auki d'an lokaci suna waya daga nan suka kashe wayar. A b'angaren Safna kuwa tun da safe take aikin kuka dan kuwa ta san rabuwarta da Safwan ta zo, saboda a cewarta idan ya auri Hafsa ya zama ba na ta ba, sai da ta ji kanta ya fara yi mata ciwo sannan ta kwanta a kan doguwar kujera wani irin bacci ne mai nauyi ya kwasheta dan kuwa daman rabonta da bacci tun shekarar jiya dan jiya yadda ta ga rana haka ta ga dare, sai wajen k'arfe 5:00pm na yamma ta farka wanka ta yi sannan ta saka wata doguwar riga pink wacce aka yi wa gaban rigar kwalliya da duwatsu manya manya, dawowa tayi ta kwanta dan kuwa bacci ne a idanuwanta baccin ne ya kwasheta. Safwan ne ya shigo falon da sallama, idanuwansa suka sauka a kan Safna wacce take bacci fuskarta ya k'urawa ido yana jin tausayin matarta sa ganin yadda fuskarta ta kumbura fuskarta tayi jajawur, k'arasa yayi kusa da ita tare da shafar fuskarta a hankali "Ruhina" Ya kira sunanta a hankali jin ba ta farka ba yasa ya d'auketa cak ya kai ta kan gado ya kwanta da ita, toilet ya shiga shi ma yayi wanka ya dawo ya kwanta a kusa da ita yana cigaba da shafata a haka shi ma bacci ya kwashe shi. *'BANGAREN SALIS🤗* Kamar yadda Abba ya ce zai kai Nihal Asibitin haka kuwa a ka yi da ya je yayi wa Hajiya Mama bayani ba ta k'i ba, dan kuwa yanzu ta san Mama ta yi nadamar abin da tayi wa Nihal d'in, haka Nihal su ka yi sallama da su Khadijatullahi, ta bi bayan Abba suka bar gidan tana jin kewar 'yan uwan na ta a cikin zuciyarta, su na isa asibitin Abba ya fito daga motar ita ma ta fito Abba ya huce gaba tana bin sa a baya har suka isa cikin d'akin, Baffa da Mama duk suna d'akin Nihal ta tsugunna har k'asa ta gaisar da su, sannan ta sami wajen kusa da Mama ta zauna, Mama da Abba suka gaisa da Abba cikin mutunta juna Abba yayi musu ya me jiki su ka amsa masa da cewa "Da sauk'i" Suka d'an tab'a hira daga nan Abba yayi musu sallama ya nufi hanyar fita daga asibitin Baffa sai da ya taka masa har gaban motarsa sannan ya dawo, ya tarar da Mama ta rumgume Nihal tana kuka tana ba ta hak'uri. Murmushi Nihal yayi tare da cewa "Haba Mama ai ke d'in kamar mahaifiyata ce dan haka, wallahi ni ban ji haushin abin da ki ka yi min ba, kuma ki daina ba ni hak'uri, dan ba na so kin ji Mamana" Ita ma murmushin ta yi sannan ta d'ago Nihal d'in tana murmushi tare da cewa "Nagode sosai yarinyata" Fita Mama da Baffa su ka yi daga d'akin dan su ba wa Nihal d'in damar ganin Mijin na ta, ai kuwa abin Mamaki Mama su na fita Salis ya mik'e zaune tare da kashewa Nihal ido yana murmushi "Babyn baby ya kika ga wannan drama" Zaro ido Nihal tayi tana k'arewa Salis d'in kallo zuciyarta fal mamaki "kenan Salis k'aryar rashin lafiya yayi dan ta dawo" Nihal dariya tayi tare da cewa "Gaskiya babyna wannan drama tana da abin burgewa amman kuma sauran kad'an zuciyata ta buga" Dirowa yayi daga kan gadon ya tako har gurin da take yana cewa "Ai kuwa gwanda da ba ta buga ba, domin babynki yana lafiya ya ji sauk'i fiye da yadda kike tunani kawai wannan wani wasan kwaikwayo na yi tare da taimakon su Dr Maryam dan ki dawo gareni" Janyo shi tayi tare da kissing d'insa a goshi tana cewa "gaskiya Baby ina sonka da yawa ba ka ji dad'in da na ji ba, da muka k'ara kasancewa tare da juna dan har na fitar da ran sake zama da kai darling" Ta k'arasa maganar hawaye na zuba daga idanuwanta. Goge mata ya shiga yi tare da gaya mata kalamai masu dad'i da kwanta da zuciya har ta yi shuru sai kuma ta kallesa tana murmushi ta ce "yanzu baby meye abu na gaba da za mu yi, dan gaskiya ya kamata ka warke haka" Tayi maganar tana dariya, dariyar yayi mishi sannan ya ce "zuwa gobe zan warke daga d'aya kuma za'a sallame mu kamar yadda mu ka tsara da su Dr Maryam, "Allah ya kaimu babyna" Ya amsa da "Amin" daga nan suka cigaba da hirar soyayyar su zuciyoyinsu cike da farin ciki. *'BANGAREN JABIR😂* Tun da wannan yaron ya ba shi takaddar ya saka a aljihu, bai sake tunawa da ita ba sai da ya gama shek'e ayarsa ya nufi hanyar gidan yana yin parking ya bud'e kofar zai fita sai ya tuna da takaddar da sauri ya saka hannunsa a aljihun ya zaro takaddar ya fara warwareta a hankali idanuwansa ya dora a kan takaddar ya fara karanta abin da aka rubuta a cikin takaddar a fili. "Kai daman baka chanchanci ayi maka sallama dan kuwa ba na saka ka a sahun mutane sai dai dabbobi, na rubuta maka wannan sak'on ne saboda na sanar da kai cewar nii Amatullahi sai na tabbatar na tarwatse rayuwarka, sai na saka ka yi nadamar haihuwarka da wannan tambad'add'iyar uwar ta ka ta yi, dabba kawai" Abin da aka rubuta a takaddar kenan, Jabir kuwa yana gama karantawa ya fashe da dariya tare da cewa "ke kuma irin na ki salon kenan, to koma wacece ina jin na ga ta inda za'a tarwatsa min rayuwar" Yana gama fad'ar haka ya fita daga motar ya nufi cikin hanyar da zata sadashi da babban falon yana cigaba da dariya kamar wani zararre takaddar tana hannunsa, sai da ya zo daf da kofar babban falon sannan ya gefar da takaddar a cikin bola, ya tusa kansa falon ba tare da yayi sallama ba, har ya nufi d'akinsa zai shiga sai kuma ya juya ya nufi d'akin Hajiya Asiya, ya kama hannun kofar kenan zai murd'a sai ya ji muryar Hajiya Asiya tana cewa "A gaskiya ni dai ba zan iya ba da mijina asha jininsa ba, da dai kun tsaya a kan wannan shashashar ne to, zan san yadda zan yi na kawo muku ita mu sha jininta tunda daman ban da wani burin irin na ga bayanta, Jabir kuma A'a gaskiya shima ba zan iya ba" Gaban Jabir ne ya buga yayi saurin ja da baya, jikinsa sai rawa yake yi, "me hakan ke nufi? Kenan Mami ta shiga k'ungiyar matsafa, suke son su sha jinin Abba, shine tak'i yarda suka dawo kai na, Lallai kuwa wallahi Mami baku isa ba chabb baki ma san da wa kike zancen ba" Wad'annan maganganun da Jabir ke yi duk a fili ya ke yi, kuma a kan kunnan Alhaji Mansur wanda fitowarsa kenan daga d'akinsa ya ji Jabir d'in yana magana, da sauri ya k'araso gurin da Jabir yake tsaye ya kama hannunsa su ka fita daga babban falon. Motar Alhaji Mansur suka shiga Jabir ya kalli mahaifin nasa tare da cewa "Abba wallahi ba zan tab'a yarda ba, babu wanda ya isa ya sha jinina, kashe su zan yi gaba d'ayansu kawai kowa ya huta" Dafasa Alhaji Mansur yayi yana d'an k'ak'alo murmushin yak'e ya ce "Jabir mu godewa Allah tunda Allah yasa ka ji mugun abin da mahaifiyarku take b'oyewa daman ni gaskiya ban yarda da ita ba, saboda irin abin da ta tsira idan ta fita daga gida da yamma sai da safe take dawowa, kuma na sha tambayarta ina take zuwa sai ta shiga yi min kuka, wata ran kuma ta ce min wai biki ta je, yanzu dai abin da na ke so da kai ka ja bakinka ka yi shuru karka fad'awa kowa game da abin da ka ji saboda idan ka fad'a har ya koma kunnanta komai zai lalace. Kallonsa Jabir yayi cike da tausayawa yau ne karo na farko da ya ji so da k'aunar mahaifin nasa suna ratsa cikin zuciyarsa "Abbana jininka fa suke son su sha kai da Step mother, kuma nima suna so su dawo kai na, ta ya zaka ce nayi shuru wallahi kashe su zan yi gaba d'ayansu kafin su, su kashemu","Jabir karka yi haka ka ji d'ana, a yau d'innan zamu shawo kan abin ba zan bari komai ya same mu ba" Ajiyar zuciya Jabir ya sauke sannan ya ce "to shikenan Abba, wallahi Abba ban tab'a jin tsanar Mami a cikin zuciyata ba sai yau wallahi na tsaneta sosai" Kallonsa kawai Alhaji Mansur yayi domin kuwa shi ma wata iriyar tsanar Asiya ce ta cika masa zuciya lokaci d'aya. Fita su ka yi daga cikin motar suka koma cikin gidan kowannansu ya shige d'akinsa zuciyarsu fal bak'in ciki, Jabir yana shiga ya tarar da Teemarh tana kwance idanuwanta a lumshe, kujerar da take fuskantarta ya zauna tare da zabga tagumi, Teemarh ta bud'e idonta ta zuba a kan Jabir tana nazarin yanayin da yake ciki tabbas ta san ba k'aramin abu ba ne zai saka Jabir cikin damuwa ba, dan kuwa da wuya ka ganshi yana cikin damuwa, ko da kuwa abin ya dameshi ba zai tab'a bari har ya nuna a fuskarsa ba, sai dai ya barshi a iya zuciyarsa. Tashi tayi ta k'arasa gurin da yake ta zauna tana cigaba da kallonsa "meke damunka?" Ta tambayesa tana kallonsa, d'agowa yayi yana kallonta sannan ya d'an sakar mata murmushi ya ce "ai ke ce damuwata, kin k'i yarda da soyayyata, Teemarh me zan miki ki yarda cewa ina sonki" Murmushi Teemarh tayi sannan ta ce "A kan wannan shine ka damu kan ka, to dan Allah ka dai na damun kan ka dan nima ina sonka, kuma kai kanka kasan da hakan" Jabir kawai murmushi yayi dan yanzu baya cikin yanayin da zai iya kula kowa dan gaba d'aya haushin duniyar ya ke ji, Teemarh ta kama hannunsa tana cewa "Darling anya kuma ba akwai abin da ka ke b'oye min ba?" Kallonta yayi sannan ya ce "Kina tunanin da akwai abin da zai iya b'oye miki karki manta fa ke d'in matata ce" Murmushin jin dad'i Teemarh tayi tare da kwantawa a kan k'irjinsa, Jabir ya jinjina da bayan kujerar ya lumshe idonsa yana jin wani irin zafi a cikin zuciyarsa. *'BANGAREN KHADIJATULLAHI♥️😢* Shahida da Amatullahi ne su kad'ai suna hirarsu ta duniya Shahida ta kalli Amatullahi tare da cewa "Sister ina son mu yi wata magana da ke dan nasan ke kad'aice za ki iya taimakon Yaya Aliyu Haidar" Amatullahi tayi shuru dan tunda Shahida ta kirawo sunan Aliyu ta san abin da zata ce mata "Ina jinki sister" Amatullahi ta fad'a tana kallon Shahida, Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi tare da cewa "Yaya Aliyu Haidar ne yake son Khadijatullahi, Sister nayi matuk'ar tausayawa Yayanmu dan nasan ba zan tab'a samun abin da yake so a gurin Khadijatullahi ba dan ta tsanesa sosai, duk da cewa ba shi ne ya aikata mata laifin ba, ya riga ya narku cikin soyayyarta yana tsananin buk'atar taimakonmu wanda ni kuma ban da halin taimaka masa","Inaaa wallahi ni ba zan tab'a sonshi ba, ina baki shawarar ki yi gaggawar basa shawarar ya daina sona, dan kuwa da nayi soyayya dashi gwanda na mutu, na tsaneshi saboda gaba d'aya maza halinsu d'aya ne" Khadijatullahi tayi maganar cikin zafin rai dan kuwa ta ji duk maganganun da Shahida ta ke yi wa Amatullahi. Hawaye Shahida ta shiga zubarwa ta tashi ta fita daga d'akin, falon saukar bak'i ta shiga ta zauna tana cigaba da rera kuka "Ya Allah kayayewa Yayana wannan masifar da take son tunkaroshi, tun kafin abin ya zo yafi k'arfinshi, Ya Allah ka taimaka masa kasan Yaya Aliyi Haidar yana da kyakkyawar zuciya karka dora masa abin da ba zai iya ba" Tana kuka take yin maganar abin gwanin ban tausayi. Aliyu ne ya shigo falon ya k'urawa k'anwar ta shi ido, shima hawayen ne suke zubo masa, "Darling Sister ki daina kuka na san wannan jarabawa ce Allah ya dora min ita kuma insha Allahu zan yi kok'ari na cinye Jarabawar da izinin Allah","Allah ya sa Yayana" Shahida ta fad'a tana goge hawayen idonta dan ba ta son ganin Yayan na ta cikin damuwa, zama yayi kusa da ita su ka yi jugum-jugum kamar masu zaman makoki. *(Allah sarki Aliyu Haidar ka had'u da babbar Jarabawa Allah ubangiji ka bamu ikon cinye ta mu jarabawar Amin👏🏽❤️)* *B'ANGAREN ABBA DA AUNTY MURJA💕* Zaune yake a kan kujera ya zabga uban tagumi hankalinsa gaba d'aya a tashe yake tunaninsa d'aya ya ya za'ayi ya shawo kan matsalar nan da ta kunno masa kai cikin gida daman ya gama yanke shawarar ba zai sake zama da ita ba dan yana gama warware wannan matsalar zai saketa takoma gidan ubanta, dan ya gaji da abubuwan da ta ke yi masa dan ya fuskanci wata ran idan har ya barta to tabbas sai gidansa ya kama da wuta, wata dabara ce ta fad'o masa a rai nan ya sauke nannauyar ajiyar zuciya tare da furta "Alhamdulillahi" a fili. Aunty Murja wacce ta ke zaune kusa dashi ta ce "Yayana wai me yake faruwa ne" Murmushi yayi ya ce "Wata matsala ce ta kunno min, amman yanzu na samu mafita, amman matata ina so ki dage da addu'a kuma karki dinga zama ba alwala kin ji, duk da nasan ke d'in ba daga nan ba indai wajen nan ne, amman ki cigaba da yi karki gaji" Murmushi ita tayi sannan ta ce "insha Allahu zan dage, kuma na ji dad'i da ka samu mafitar da zata fitar min da mijina daga cikin damuwa Alhamdulilah" Tayi maganar tana dora kanta a kan kafad'arsa, nan ya shiga shafa mata gashin kanta a hankali, yana zuba mata kalaman soyayya da kuma nuna mata irin yadda take da matuk'ar muhimmanci a gurinsa. (to ni 'yar mutanan zazzau nace Abba asha soyayya lafiya😂💕 nayi gidan su malam salis romeo🤣) *Washe gari☄️* Da sassafe Dr Sadiya ta ba wa su Salis sallama suka nufi gidansa kai tsaye, Mama da Baffa suna zuwa gidan ba su dad'e suka fito Tanimu driver ya bud'e musu motar suka shiga, ya shiga mazaunin driver ya ja motar sai da ya kai su har kofar gida, sannan ya nufi gidan. Salis kuwa su Mama na fita ya mike daga langwabewar da yayi ya jawo Nihal jikinsa yana cewa "Baby nayi matuk'ar missing d'inki haka na dawo tamkar wani mahaukaci saboda soyayyarki ta riga da ta samu babban gurbi a cikin zuciyata" Sai da tayi kissing d'insa a gefen kuncinsa sannan ta ce "nima haka Babyn baby, dan kuma sauran kad'an akai ni dawanau" Dariya yayi sosai sannan ya ce "to ai kuwa gwanda da ba'a kai ki ba dan kuwa da an kai ki nima da yanzu ina chan"."Yanzu dai ki tashi mu je mu kwanta kin san fa, na gaji ina buk'atar in huta tare da matata" Nihal ta ce "Na sani babyna tashi muje" Tayi maganar tare da tashi shima mik'ewa yayi suka shige bedroom ni kuwa 'yar mutan zazzau nace Malam Salis romeo wannan abin yafi k'arfi na nayi gidan Hajiya Mama dan naji yadda zata kasance da Aliyu. *'BANGAREN ALIYU😭♥️* Kullum soyayyar Khadijatullahi k'ara dad'uwa take a cikin zuciyar Aliyu gashi yanzu Khadijatullahi ba ta barin su had'u dashi kullum tana d'aki, wannan abin ba k'aramin tayarwa da Aliyu hankali yayi ba, yau gidan babu kowa daga Aliyu sai Hajiya Mama dan Amatullahi da Khadijatullahi sun koma makaranta yau sun shiga second semister Shahida kuma tana gurin aikinta, Aliyu yana zaune kusa da Hajiya Mama ya zabga tagumi Hajiya Mama sai magana ta ke yi masa amman shuru babu alamar zai amsa mata, tab'a shi tayi yayi wata iriyar zabura, Hajiya Mama ta ce "Wai meyake faruwa da kai ne Aliyu na ga kwana biyu, ka na cikin damuwa sosai" Nan ya k'ak'alo murmushi tare da cewa "babu komai Hajiya bari na koma d'akina akwai aikin da zan yi" Ya fad'a tare da tashi ya koma d'akinsa kwanciya yayi yana jin zuciyarsa nayi masa zafi "Allah na rokeka ka kawo min sassaucin wannan zazzafar soyayyar da na ke yi wa Khadijatullahi" Ya fad'a a fili. Wayarsa ya ji ta shiga ruri ya zura hannunsa ya d'aukota a cikin drower Big bro sunan da ta ga ya bayyana a kan screen d'in wayar kamar ba zai d'aga ba sai kuma ya d'aga tare da cewa "Assalamu alaikum" Jabir bai amsa ba ya fara zaiya na masa abin da ya sa ya kirawosa "Bro kasan me? Wallahi akwai gagarumar tashin hankali, gidannan yana kok'arin kamawa da wuta ga shi Mami ta zama matsafiya" Tashi Aliyu yayi zaune yana cewa "Ban gane Mami ta zama matsafiya ba? Kuma me zai saka gidan ya kama da wuta?" Anan ya kwashe duk abin da ya ji Asiya ta fad'a da kuma yadda su ka yi da Abba ya dora da cewa "Yanzu dai wallahi idan Abba bai d'auki mataki ba ni zan d'auka dan wallahi kashe su zan yi gaba d'ayansu" Hankalin Aliyu ya kuma tashi zuciyarsa kuma kamar zata fashe daman ga shi yana fama da ciwon son Khadijatullahi to ga shi kuma Maminsa ta zama matsafiya, Aliyu ya ce "to ita Mami tana ina?","hmmm d'akinta mana" Ajiyar zuciya Aliyu ya sauke tare da cewa "Insha Allahu burinsu ba zai tab'a cika ba, karka damu bro ka ji karka ce zaka kashe su ka barsu tunda Abba ya ce zai samu mafita na san zai samu a yau d'in nan","Allah ya sa" Aliyu ya amsa da "Amin" daga nan suka ajiye wayar, Aliyu ya komaya kwanta yana mamakin wannan lamarin. Kamar yadda suka saba kullum da yamma su ke tafiya gurin tsafinsu kuma a yau ake son Hajiya Asiya ta kai su Abba da Aunty Murja, Asiya ta ci kwalliya sosai kamar mai zuwa gidan biki tana fitowa ta tarar da Aunty Murja da Abba sun shirya cikin wata iriyar shadda kala d'aya Hajiya Asiya tayi murmushi tare da cewa "mu je ko?" Fita su ka yi suka shiga mota suka bar gidan Motar Hajiya Asiya ce a gaba sai ta Abba a baya. Na san masu karatu zaku ce to ya haka kuma? Hajiya Asiya ta had'awa su Aunty Murja k'aryar cewa yau ne ake dinner bikin 'yar k'anwarta Hajara da daddare tana son su je gurin tare wannan shine dalilin da yasa suka shirya domin zuwa dinner. Suna isa gidan matsafan Hajiya Asiya ta fito tare da nufo motarsu Alhaji Mansur cikin tafiyarta ta isa da k'asaita, bud'e motar su ka yi tare da fitowa Aunty Murja dai mamaki da tsoro ne suka kamata, amman ganin tana tare da Habibinta Alhaji Mansur yasa ta shiga b'oye tsoronta hannunta Alhaji Mansur ya kama tare da sakar mata wani lallausan murmushi, suka nufi cikin gidan. Suna zuwa kofar da za su shiga d'akin tsafin Hajiya Asiya ta juyo tana kallon Alhaji Mansur duk da cewa ita ba ta tab'a sonshi ba kawai tana zaune dashi ne saboda yana da kud'i amman ita kanta ta san yayi mata halacci ya nuna mata soyayya, murmushi tayi sannan ta komarda dubanta kan Aunty Murja "To ina so mu yi sallama da ku anan dan idan mu ka shiga wannan d'akin babu damar yin haka, idan kuma da wata wasiyya da ku ke so ku fad'a min ni kuma nayi muku alk'awarin zan isar muku da ita" Wani irin zafafan mari Alhaji Mansur ya shiga jera mata hagu da dama har sai da ta kai k'asa haka ya shiga tattakata yana ball da ita ya d'ago kanta ya gwara da gini har sai da kan nata ya fashe, amman Alhaji Mansur bai dai na gwara mata kai da gini ba har sai da Hajiya Asiya ta dena motsi, Aunty Murja ta shiga kok'arin janye Abba tana kuka, amman sam bai ma san tana yi ba dan idanuwansa sun gama rufewa. 'Yan sanda ne suka fito daga d'akin tsafin tare da su Hajiya Suhaima gaba d'ayansu an saka musu ankwa a hannunsu, Aunty Murja ta bi su da kallo ita gaba d'aya kanta ya gama d'aurewa, haka aka tisa k'eyar su Hajiya Suhaima 'yan sanda suka saka su a cikin motarsu aka nufi police station da su, suna isa police station aka saka su Hajiya Suhaima a cikin sell dukansu aka shiga yi ba ji ba gani har wasu daga cikinsu suka dai na motsi, Hajiya Suhaima kuwa duk ta gama jigata dan kuwa ta sha duka ba na wasa ba, har ba ta iya gane kowa idanuwanta suka shiga zubar da jini. *(ni kuwa nace ai kad'an ma ki ka gani Hajiya Suhaima, tunda har ki ka kashe mahaifiyarki da hannunki ai asara tabbata a gare😭)* Alhaji Mansur kuwa sai da ya gaji dan kansa sannan ya zube a k'asa yana huci, Aunty Murja ta zauna kusa dashi tana cewa "Yayana wai meyake faruwa ne?" Kallonta yayi sannan ya shiga bata labarin duk abin da yake faruwa, hankalinta yayi matuk'ar tashi ta ce "daman nan gidan matsafa ta kawo mu ta ce wai bikin 'yar k'anwarta za'ayi" Alhaji Mansur dai bai k'ara cewa komai ba ya tashi ya fara sauka daga benen ita ma Aunty Murja bin bayansa tayi, suka bar Hajiya Asiya a kwance jini ne kawai yake ambaliya a jikinta. *Wannan kenan😉karku manta fa yanzu aka fara kuma comments da sharhinku shi yake k'ara min k'warin guiwar yi muku typing more comments more typing* *'BANGAREN SAFWAN DA SAFNA😩😢* "Ruhina dan Allah ka tsaya ka saurareni wallahi ban yi haka dan in b'ata maka rai sai dan.............." D'aga mata hannu Safwan yayi fuskar nan ta sa babu alamar murmushi "Dakata nace ki dakata min Safna ina son ki bud'e kunnuwanki da kyau dan ki ji abin da zan fad'a miki daga yau karki k'ara kirana da wani ruhinki dan ni ba ruhinki ba ne, Shashasha kawai" Yana gama fad'ar haka ya fita daga falon da sauri zuciyarsa cike da tausayin Safna dan ya san maganar da ya fad'a mataa gaskiya za ta yi mata ciwo sosai, motarsa ya shiga tare da kallon kofar falon yana jin son Safna yana ratsa masa zuciya dan yasan duk saboda shi ne, ta ke yin haka "Ina sonki sosai Ruhina ya zama dole nayi miki haka domin ba na son ki dinga nunawa Hafsa k'iyayya, ba na son ya zama kanku a rabe ya ke, ina son ku zama tsintsiya d'aya mad'aurinki d'aya, ko dan saboda yaranmu ka da su taso su ga kanku a rabe su ma ya zama kansu ba a had'e yake ba, na san ba zan sami matsala daga gurin Hafsa ba, ke ce zaki ba ni matsala kuma na san hakan da nayi shi zai sa ki sauko daga masifaffan kishin da kika dorawa kan ki". Yana gama fad'ar haka ya ja motar mai gadi ya bud'e masa gate d'in gidan da gudu ya ja motar ya nufi ma'aikatarsu, Safna kuwa Safwan yana fita ta zube a kan kujera tana kuka, "meyasa ruhina za ka min haka saboda wata banza, haba ruhina kasan ina tsananin sonka sosai kuma dole nayi kishi a kanka" Haka tai-tayin surutai barkatai tana kuka tamkar ranta zai fita, kamar wacce aka tsikara ta tashi ta shige d'akin Safwan ba san me tayi a d'akin ba amman ta d'auki kusan mintina biyar a d'akin sannan na ganta ta fito ta shige na ta d'akin hmm ni kuwa nace Safna ki dai bi a hankali kishi ba hauka ba ne, daga nan na tarkata d'an komatsena na nufi gidan Hajiya Mama wajen Aliyu dan na ji ya zata kasance. *'BANGAREN ALIYU😭❤️🗝️* Da sassafe wajen k'arfe shida ya fito daga d'akinsa ya nemi kujera ya zauna tare da zabga tagumi idanuwansa suna kan k'ofar falo dan ba shi da wani buri a yanzu irin ya ga hasken idanuwansa Khadijatullahi, saboda ba zai tab'a iya jure rashin ganinta da bayayi ba, yana nan zaune sauro duk sun isheshi da kuka a kunne sai gani yayi ana kok'arin bud'e kofar falon nan ya shiga Addu'ar Allah yasa Khadijatullahi ce, ai kuwa ya yi babbar sa'a Khadijatullahi ta fito rik'e da Affan a hannunta shi kuma sai tsala kuka yake, Aliyu ya tashi ya nufi gurin da take fuskarsa d'auke da murmushin jin dad'in ganinta "ba ni shi na rik'e miki" Aliyu yayi magana yana mik'a hannunsa, had'e fuska Khadijatullahi tayi tare da kawar da kanta jefe tana jan tsaki. "Malam ka matsa min daga hanya zan huce" Tayi maganar cikin tsawa, "Haba Dija ta wai ni menene laifina, wallahi ni da gaske nake ina sonki kuma auren........." Saukar marin da ya ji ne yasa shi yin shuru bai k'arasa maganar ba, ya dafe gurin yana kallonta cike da mamaki, "Idan baka fita a harka ta ba, to wallahi kad'an ma ka gani, kuma idan ka cigaba da dorawa kanka soyayyata to tabbas za ka mutu ko kuma nace lokacin mutuwarka yayi, dan ni ba zan tab'a sonka ba na tsaneka kai ba ma kai kad'ai ba gaba d'aya mazan duniyar nan na tsanesu" Tana gama fad'ar haka ta wuce fuuuu ta shige falon saukar bak'i. Aliyu kuwa wasu zafafan hawaye ne suka shiga zubo masa ya d'auki kusan mintina talatin a tsaye har sai da ya ji k'afafuwansa suna rawa sannan ya samu ya lallab'a ya koma d'akinsa zuciyarsa kamar zata fashe ga wani irin zafi da ya ji zuciyar ta sa take yi masa, sai bugawa ta ke yi da k'arfi. Kwanciya yayi a kan gadonsa tare da runtse ido hawaye na cigaba da zuba daga idanuwansa babu abin da yake maimaitawa sai innalillahi wa inna ilaihi raju'un a haka har ya fara jin sauk'i a cikin zuciyarsa, wani irin bacci mai nauyi yayi awan gaba dashi, Allah sarki Aliyu ka ba ni tausayi Allah ya kawo maka sauk'i. *'BANGAREN JABIR😂* Tun da su Abba suka fita hankalinsa ya k'i kwanciya dan kuwa a kan idonsa suka fita gashi Abba yayi masa gargad'i a kan kar ya biyosu, wannan dalilin ne yasa bai bi bayansu ba, yana nan zaune a falo jugum yana jiran ganin Abba dan kuwa Jabir ya d'auki alk'awarin duk wanda ya sake ya sha jinin mahaifinsa to tabbas sai ya tabbatar ya kashe shi koma d'an gidan uban waye, Shigowar su Abba da Aunty Murja ne yasa Jabir mik'ewa da sauri yana sakin wata aijiyar zuciya tare da yin murmushi "Abbana kun dawo kai amman na ji dad'i sosai hankalina ya kasa kwanciya, dan ban san halin da ku ke ciki ba" Abba yayi murmushi tare da cewa "muna lafiya ya kamata ka je ka kwanta dare ya yi" Jabir ya ce "to Abba" Sannan ya shige d'akinsa Aunty Murja ta bi bayansa da kallon dan kuwa wani irin haushin Jabir d'in ta ke ji,duk san ta ganshi sai abin da yayi wa Khadijatullahi ya fad'o mata a rai, Alhaji Mansur ya kama hannunta suka shige d'aki, ni kuwa dijartyy nace ba sai na shiga d'akin ba, dan babu kyau shiga hurumin da ba na ka ba😂 Jabir yana shiga d'akinsa Teemarh ta rumgumeshi tare da kissing d'insa a kunci tana cewa "Darling shi ne ka tafi ka bar ni a d'aki" Tayi maganar cike da shagwab'a, Jabir ya ce "Ki yi hak'uri darling kin ji ki min uzuri yau d'in ne na shiga tension" Teemarh ta ce "Allah sarki darling sannu" Abin da ta ce kenan a kan kujera suka zauna Teemarh ta kwanrar da kanta a kan k'irjinsa tare da lumshe idonta shi kuma Jabir abin nema ya samu babu a kan haka ya shiga kissing d'inta har sai da ta kai su sun koma kan gado, ni kuma ina ganin sun nufi kan gado nayi saurin fitowa daga d'akin na koma gidan Hajiya Mama wajen Khadijatullahi. *'BANGAREN KHADIJATULLAHI🤔* Tana shiga d'akin ta ci karo da Amatullahi tana tsaye ranta ya gaba b'aci da lamarin Khadijatullahi nan ta shiga zazzaga mata masifa ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba "Wallahi kin ba ni mamaki k'warai da gaske yanzu har za ki iya d'aukar hannu ki mari Aliyu saboda kawai ya ce yana sonki, to insha Allahu wallahi tallahi zan je nayi magana da Aliyu ba zai sake tun kararki da maganar soyayya ba kuma sai na fad'awa Aunty Murja duk abubuwan da kike aikatawa, saboda anan kin ga Hajiya Mama da Shahida suna kyaleki shine har kika samu damar marin Aliyu wai me kike tak'ama dashi ne, kin tsani maza ko, to da ke da tsanar sai na had'a ku na zazzageku wanne ai wulk'anci ne da rashin sanin darajar d'an adam" Amatullahi ta k'arasa maganar tare da zama a kan kujera sai huci ta ke yi. Ita kuwa Khadijatullahi hawaye ne ya shiga zubo mata saboda maganganun Amatullahi sun yi matuk'ar tsaya mata a rai kuma sun bata haushi sosai ashe akwai ranar da za ta zo Amatullahi tayi mata irin wannan rashin mutuncin zaunawa tayi a k'asa tare da rumgume Affan tana kuka tare da cewa. "Besty meyasa ki ka yi min haka, saboda..........." Cikin masifa Amatullahi ta dakatar da ita da cewa "Ba na son ki ce min komai saboda ni ba na mu'amala da wacce ba ta san darajar d'an adam ba, kuma tabbas sai na tabbatar na fad'awa Aunty Murja duk abin da ki ke yi" Tayi maganar ba tare da ta kalli Khadijatullahi ba, "Dan Allah ki yi hak'uri ki fad'a min abin da zan yi dan na gyara kuskurena karki yi fushi da ni amman ni na yarda ki fad'awa Aunty Murja tayi min duk hukuncin da ya dace da ni amman dan Allah karki ce za ki dai na min magana dan hakan zai saka zuciyata cikin tsananin damuwa" Ta k'arasa maganar tana had'e hannayenta guri d'aya alamar rok'o tana cigaba da yin kukan. "To idan kina so kar inyi fushi da ke, ki je ki ba wa Yaya Aliyu hak'uri kuma ki karb'i soyayyarsa idan kuma ki ka k'i to babu ni babu ke har abada" Amatullahi tayi maganar fuskar nan ta ta a d'aure, Khadijatullahi cikin rawar murya ta ce "zan yadda ki ke so" Amatullahi ba ta k'ara ce mata komai ba ta d'auki Affan wanda ya ke kan cinyar Khadijatullahi ta shige bedroom ta bar Amatullahi zaune tana kuka, duk da cewar ta tsani Aliyu amman ya zame mata dole ta je ta nuna masa ta amince da soyayyarsa kuma ta bashi hak'uri saboda Amatullahi kar ta yi fushi da ita, dan haka ta barshi a zuwan idan gari ya waye sai ta je har d'akinsa suyi magana. Shahida duk abin da suke fad'a duk tana ji dan bata wani jima da tashi ba, tayi farin ciki sosai duk da cewar ita Khadijatullahi ba'a son ranta zata karb'i soyayyar Aliyu ba, amman ta san hakan zai faranta ran d'an uwan na ta kuma daga wannan lokacin Khadijatullahi za ta san ba duka maza ne suka taru suka zama d'aya ba kuma halin Jabir da Aliyu sam ba d'aya yake ba, shi Aliyu yana da kyakkyawar zuciya kuma ita gaskiya tunda suke dashi bai tab'a yin wata budurwa ba, dan 'yan mata ba sa gabanshi, a haka dai wani sabon baccin ya kwasheta wanda yake cike da mafarkai kala-kala a kan Khadijatullahi da Aliyu. Misalin k'arfe 7:30am na safe Khadijatullahi ta gama had'a musu breakfast ta shirya cikin wata shadda pink ta saka hijabinta har k'asa ta d'auki abincin Aliyu ta nufi d'akinsa a bakin kofar ta tsaya tare da kwankwasawa, Aliyu wanda yayi shirinsa na zuwa office amman saboda irin damuwar da yake ciki, ji yake duniyar tayi masa zafi dan a halin yanzu gaba d'aya baya cikin nutsuwarsa, jin ana kwankwasa kofar ne yasa ya zauna a kan kujera tare da cewa "Shigo" Dan shi a tunaninsa Shahida ce ta zo kawo masa breakfast d'insa. Khadijatullahi ta shiga d'auke da sallama a bakinta, da sauri Aliyu ya mik'e jin muryar zab'in zuciyarsa dan kuwa ko a mafarki ya ji wannan daddad'ar muryar to tabbas sai ya farka daga baccin nasa, "Dija ta" Aliyu ya fad'a tare da kafeta da manyan idanuwansa yana murmushi hawaye na kok'arin zubo masa, Khadijatullahi ba ta amsa ba har sai da ta ajiye masa abincin a kan table d'in da yake tsakiyar d'akin sannan ta dawo gurin da yake tsaye tasa guiwoyinta a k'asa tana cewa "Dan Allah Yaya Aliyu ka yi hak'uri da abin da nayi maka d'azu, ba zan sake ba" Wani irin farin ciki ne ya shiga ratsa zuciyar Aliyu ya k'ara fad'ad'a murmushinsa, shima ya tsugunna suna kallon juna ido cikin ido da sauri Khadijatullahi ta kawar da kanta dan jin wani irin abu da ya tsarga mata zuciya saboda Aliyu yana da matuk'ar kwarjini ba za ta iya jurewa su yi kallon ido cikin ido ba. "My Heartbeat yau ke ce da kanki ki ka zo ki ba ni hak'uri gaskiya na ji matuk'ar dad'i fiye da tunaninki ina sonki sosai dan haka tun lokacin da abin ya faru na mance dashi na d'aukeshi tamkar mafarki na yi muku na farka fatana shi ne ki karb'i soyayyata" Murmushin yak'e Khadijatullahi tayi "nagode sosai ni zan tafi besty tana jirana zamu tafi makaranta" Aliyu ya ce "to ai nima Office zan je, ai sai na sauke ku a makarantar","to shikenan" Abin da kawai Khadijatullahi ta fad'a sannan ta tashi tayi masa sallama ta fita. Aliyu kuwa ya rasa inda zai tsoma ransa ji yake tamkar anyi masa albishir da gidan Aljanna haka ya zauna ya bud'e abincin soyayyan dankalin turawa ne sai kuma kwai da aka soya shi daban ya ci sosai dan ji yayi kamar kar ya daina ci, "gaskiya matata ta iya girki" Yayi maganar a fili yana murmushi, jakarsa ya rataya a kafad'arsa sannan ya fita zuwa d'akin Hajiya Mama. A zazzaune ya tarar dasu sun gama shirin su da alama shi suke jira Shahida ta ce "kai Yaya Aliyu Haidar shi ne ka shanyamu sai mun yi lating" Harara ya wurga mata sannan ya k'arasa gaba Hajiya Mama ya tsugunna ya gaisheta ta amsa tana sakar masa murmushi sannan ya mik'e tare da juyawa nan suka had'a ido da Khadijatullahi tayi saurin sunkuyar da kanta k'asa murmushi yayi tare da cewa "to muje ko darling sisters karku makara" Sai da su ka yi wa Hajiya Mama sallama sannan suka fita Aliyu yana biye da su a baya, suna zuwa motar Amatullahi da Shahida suka shige bayan motar Khadijatullahi za ta shiga Amatullahi ta ce ta shiga gaban motar ranta ya b'aci sosai wato wulak'ancin da za su yi mata kenan Aliyu ne ya bud'e mata kofar gaban motar babu musu ta shiga ya rufe ya za ga ya mazaunin driver ya zauna sai da ya kalli Khadijatullahi sannan ya ja motar ya nufi makarantarsu Khadijatullahi sai da ya sauke su sannan ya kai Shahida gurin aikinta shima ya huce na shi gurin aikin. *Wannan kenan💃🏽* *'BANGAREN SALIS DA NIHAL🌹💍* Salis da Nihal wata iriyar sabuwar soyayya su ke nunawa junansu kamar su had'iye juna, kullum suna manne da juna kamar cingum, zuwa aiki ne kawai yake raba ta dashi nan ma idan zai tafi ta dinga yi masa kuka kenan ya tafi da ita, yau ma hakan take yayi shirinsa kyaf na zuwa aiki Nihal ita ma ta shirya ta saka hijabi har k'asa tana rataye da jakarsa a kafad'arta suna tafiya suna yin hirarsu ta masoya har suka iso gurin motar Salis Nihal tayi saurin shigewa gaban motar ta rufe, Salis ya saki murmushi dan kuwa ya fahimci kwana biyun nan wata iriyar sabuwar shagwab'a Nihal d'in ta ke ji. Bud'e motar yayi ya zura kansa yana kallonta ita kuma sai turo masa baki take idanuwanta sun cicciko da kwalla za ta yi kuka ta ce "Yau ma ba za ka je da ni ba ko?" Tayi maganar hawaye na gangarowa daga idanuwanta, hannunsa yasa yana goge mata hawayen fuskarsa ta chanza zuwa yanayin damuwa ya ce "Am sorry Babyna na saka ki kuka, kin san ina sonki da yawa ba na son kowane banza ya dinga kalle min fuskar kyakkyawar matata, ina matuk'ar kishinki sosai kin ga Ma'aikatarmu gaba d'ayanmu maza ne, babu mata wannan shine dalilin" Nihal ta ce "to na ji zan zauna a mota" Salis ya shiga motar dan kuwa yasan daman idan Nihal tayi irin wannan rigimar sai yayi da gaske yake shawo kanta "Ta ya ya zan bar gimbiyata a cikin mota ni kuma na tafi office kina tunanin zan iya barinki a cikin mota, to Wallahi Nafisa ba zan tab'a tafi na barki a cikin mota ko da kuma na minti d'aya ne barantana na awanni. Murmushi Nihal tayi jin ya fad'i sunata na gaskiya dan ba ta tab'a jin ya fad'a ba sai yau, irin yadda ya fad'i sunan nata cikin wani irin salo yayi matuk'ar sakata nishad'i kuma ta ji tana matuk'ar k'aunar sunan na ta, "to amman ni ina jin tsoron in zauna ni kad'ai a gidan nan" Murmushi yayi ya ce "to sai na ka na kai ki gidan Mama idan na dawo sai na biya na d'auke ki","Yawwa to shikenan" Fita Salis yayi ya koma mazaunin driver ya ja motar ya nufi gidan mahaifiyarsa, suna isa suka fita a tare suka shiga gidan, Mama tayi matuk'ar yin farin cikin ganinsu tare nan suka gaisheta sannan Salis ya tashi ya fita dan yayi lating ya shiga motarsa ya ja ya nufi ma'aikatarsu. *'BANGAREN HAJIYA ASIYA👹* Kwance take a gadon asibiti Alhaji Mukhtar wanda suke tare dashi a k'ungiyar matsafa yana zaune a kan kujera ya zabga tagumi yana kallonta, Alhaji Mukhtar jiya ya makara bai je gidan da wuri ba har bayan da Abba da Aunty Murja suka tafi sannan ya iso gidan yana shiga ya tarar da Hajiya Asiya kwance male-male cikin jini, bai tsaya yin wani tunani ba shine ya d'auketa ya sakata a mota ya kawota asibiti, wani irin sonta ne yake ji yana ratsa masa cikin jini daman ya dad'e yana son ya nuna mata yana tsananin sonta amman ya rasa yadda zai yi ya sanar da ita, amman abin da ya shige masa duhu shine meyafaru da gidan matsafan nasu ko da wani ne yayi musu lek'en asiri yayi musu shunan 'yan sanda? Amman bashi da me basa amsa dan haka ya watsar da tambayoyi ya shiga yin tunani a kan soyayyar da za su yi da Hajiya Asiya da zarar ta amince masa, shi kuma a shirye yake da yayi komai saboda ita. Haka dai har wajen k'arfe biyar babu alamar Hajiya Asiya zata farfad'o ko da yake daman likitan ya ce masa zata jima sosai kafin ta farfad'o dan kuma ba k'aramin duka a ka yi mata ba, dan da ba'a kawota asibitin da wuri ba da zata iya rasa ranta, Alhaji Mukhtar ya tashi ya fita domin ya samarwa kansa abin da zai saka a bakinsa wani babban shago ya shiga yayi musu siyayya kusan leda biyar manya-manyan ledoji ne kuma gaba d'aya kayan ciye-ciye ne, ya dawo d'akin da aka kwantar da Hajiya Asiya ya zauna yana jiran farfad'owarta. *POLY🏛️💕* Tafiya suka suna hirarsu ta k'awaye suna dariya har suka iso gurin da suke zama, kowaccen su ta samu guri ta zauna Hafsa ta kalli Khadijatullahi ta ce "Amaryar Yaya Aliyu ina gaisuwa" Harararta Khadijatullahi tayi kawai ba tare da ta ce komai ba, sai jijjiga Affan ta ke yi Amatullahi ta ce "Lallai kuwa dai gwanda kema ki fad'a mata ta gyara halinta, dan kuwa duk wanda ya ce yana sonka ai ya gama yi maka komai","Wannan haka yake besty tabbas Yaya Aliyu yana matuk'ar son Khadijatullahi amman ita ta tsaya yi masa shakara (yanga)" Dariya Amatullahi tayi ta ce "Ai kuwa gwanda ta dai na dan kuma Aliyu d'aya ne tamkar da dubu, ba irinsa ake yi wa yanga ba","tabbas"Hafsa tayi maganar tana kallon Khadijatullahi. Khadijatullahi ta ce " besty wai ba na ce miki shikenan ba"Tayi maganar cikin muryar kuka idanuwanta a kan Amatullahi, kallonta Amatullahi tayi ta ce "Ohh ni yau na ga abin da yafi k'arfina, ce miki nayi ki yi kuka" Khadijatullahi ta goge hawayen da suka zubo mata tare da sauke ajiyar zuciya, Hafsa ta dafata tana cewa "Besty wallahi Yaya Aliyu ba halinsu d'aya da wannan d'an iska kema iya zaman da ku ka yi dashi ya kamata ki fahimci hakan" Khadijatullahi ta kalli Hafsa ta ce "To shikenan Besty" Anan aka koma Aji suka tashi suka nufi ajin na su. *'BANGAREN TALATU😂* Lokacin da aka sanar da ita cewa Salis da Nihal sun koma gidansu kuma sun cigaba da yin rayuwarsu ta ma'aurata fad'uwa tayi ta suma har sai da aka kai ta asibiti haka tai-tayin zage-zage a asibitin nan da aka turasu asibitin mahaukata saboda irin yadda take dukan duk wanda ya matso kusa da ita, domin a cewarsu Talatun tana da matsala a kwakwalwarta. *'BANGAREN ALIYU💔💍* Da wuri ya dawo daga Office saboda ya d'auko su Khadijatullahi, ko gida bai je ba ya huce gurin da Shahida ta ke yin aiki ya kirata a waya ta ce masa yanzu zata fito ya jirata ta gama komai, ko minti d'aya ba'a yi ba sai ga Shahida ta fito gaban motar ta bud'e ta shiga, Aliyu ya ja motar ya huce makarantar su Khadijatullahi, ai kuwa yayi sa'a yana isa makarantar ana tashin su Khadijatullahi fitowa su ka yi daga motar suka jinjina a jikin motar, Khadijatullahi wacce tun fitowarta ta ga shigowar motar Aliyu gabanta yayi muguwae fad'uwa haka kawai ta ke jin wani irin abu a cikin zuciyarta, Amatullahi da Hafsa kuwa ba su gansu ba, sai da su ka zo daf dasu sannan Amatullahi ta gansu murmushi tayi tare da kallon Khadijatullahi "Besty ga mijinki ya zo d'aukarmu" Kallonta Khadijatullahi ta ce "Yaya Aliyu ai na ganshi tunda mu ka fito" Tayi maganar cikin wani irin yanayi dan ba ta son ran bestyn na ta ya b'aci. K'arasawa gurin da suke tsaya su ka yi Hafsa ta rumgume Shahida tana cewa "Oyoyo sister ina Sister Nafisa" Shahida tayi murmushi ta ce "Nihal tana chan gidanta, ta koma yau satinta uku kenan da komawa" Hafsa ta ce "Allah sarki zan kirata kuwa" Sai kuma ta kalli Aliyu ta ce "Yaya Aliyu ina yini" Murmushi yayi sannan ya ce "Lafiya alhamdulillahi, ya karatu?",mun gode Allah" Hafsa ta fad'a tana kallon motar Yaya Safwan wacce ya kunno hancin motar cikin makarantar yayi parking sannan ya fito ya nufo gurin da su Hafsa suke dan ya gansu tun shigowarsa, hannu ya mik'awa Aliyu su ka yi musafaha Hafsa ta ce "Yaya Safwan wannan shine Yaya Aliyun da nake baka labarin cewar shi zai auri bestyna Khadijatullahi" Murmushi Safwan yayi ya ce "Ai na sanshi Aliyu Mansur Jikamshi"Aliyu ya ce "Wato Hafsyy har kin ba shi wannan labarin kenan" Yayi maganar cike da jin dad'in maganar Hafsa sannan ya dora da cewar "Ai mun san juna ni da Safwan sosai" Hafsa ta ce "Au to ai shikenan ma" Haka su ka yi d'an hira da bata huce minti biyu ba, Hafsa tayi musu sallama suka jera ita da Safwan suka shiga mota Hafsa tana d'agowa su Khadijatullahi hannu har suka fita daga makarantar. Aliyu ya bud'ewa Khadijatullahi gaban motar ta shiga dan su Shahida tunda motar su Hafsa ta fita daga makarantar suka bud'e bayan motar suka shiga, suka bar Khadijatullahi a tsaye ita da Aliyu, shima zagayawa yayi ya zauna mazaunin driver ya ja motar suka nufi gida, Aliyu yana tuki yana satar kallon Khadijatullahi ita kuwa tana lura dashi dan tana kallonsa ta jefen idonta amman ta nuna kamar ba ta san abin da ya ke yi ba. Suna isa gidan Aliyu yayi parking sannan ya fito daga cikin motar cikin takunsa na isa da tak'ama ya zagayo ya bud'ewa Khadijatullahi motar ta fito su Shahida ma suka fito suka shige cikin gidan, Aliyu ya kalli Khadijatullahi ya ce "My heartbeat idan kin shiga gida kin huta ki zo falon bak'i ina son ganinki keda yarona","To Yaya Aliyu" Tayi maganar a sanyaye tare da nufar hanyar shiga gidan, shima ya bi bayanta zuciyarsa cike da farin ciki, ta huce zuwa falo, shi kuma Aliyu ya shige d'akinsa. Wajen k'arfe 8:00pm na dare sai ga Khadijatullah ta nufi falon bak'i tana rumgume da Affan a k'irjinta, ta shiga falon bakinta d'auke da sallama "Assalamu alaikum" Ido biyu ta yi da Aliyu yana zaune yana kallon bbc hausa "Wa'alaikissalam Matata" Ya amsa mata sallamar ciki muryarsa me jan hankalin mutane da kuma rud'a 'yammata. Khadijatullah ta shiga ta zauna a kan kujera tare da kwantar da Affan Wanda yake shan baccinsa hankalinsa kwance, Aliyu ya tashi daga gurin da yake ya koma kujerar da Khadijatullah take zaune, ya zauna da yake kujerar ta zaman mutum uku ce, Affan ya d'auka tare da sumbatarsa a kuncinsa, kallon Khadijatullah yayi ya ce "My wife to be, ya gajiya","ba gajiya" Ta ce a takaice. "Khadijatullah wallahi ina sonki sosai, Dan Allah ki karb'i soyayyata, nayi miki Alk'awarin ba zan tab'a bari ki tozarta ba, Kuma ba zan yi miki irin abin da Yaya Jabir yayi miki ba, saboda ni da shi ba halinmu d'aya dashi ba, zaki iya gwada ni ta kowacce hanya domin ki tabbatar da abin da nake fad'a miki". "Yaya Aliyu Ina tsoro kada.............." Sai ta fashe da kuka mai cin rai,hankalin Aliyu ya tashi "Final choice meyafaru?Dan Allah ki daina kukan nan haka" Shuru tayi tana sauke ajiyar zuciya ta ce "Yaya Aliyu kayi min Alk'awarin ba za ka tab'a cutar da ni ba, kuma idan munyi aure za ka rik'eni da amana" Murmushi yayi ya ce "Indai wannan ne matsalarki Matata kada ki damu, Kuma nayi miki Alk'awarin ba zan tab'a cutar da ke ba","To na amince da soyayyarka Yaya Aliyu". "Da gaske babyna" Khadijatullah ta gyad'a masa kai alamar eh, anan fa Aliyu ya shiga zuba mata kalaman soyayya, sai wajen k'arfe 8:45pm sannan Aliyu ya rakata har bakin kofar falo ya mik'a mata Affan sannan su ka yi sallama ya koma d'akinsa ita kuma ta shige falon, kai tsaye bedroom ta nufa ta kwanta, bacci Mai nauyi yayi awon gaba da ita. *'BANGAREN TEEMARH DA JABIR😂* Zaune suke a kan kujera suna kallon *so k'addarar zuciya* Arewa 24 Jabir ya janyo Teemarh jikinsa tana shafata, Yana sumbatar kuncinta kallonsa Teemarh tayi tare da cewa "Dan Allah darling ka bari mu gama yin kallon nan, sai mu yi abin da ya dace","A'a darling yanzu nake so please ki tafi mu kwanta". "Ya salam darling Dan Allah........." Toshe bakinta yayi sannan ya d'auketa cak ya kai ta kan gado, kayan jikinta ya shiga kok'arin cire Mata, Teemarh ta saka kuka tana cewa "Darling Wai meyasa ba ka son, farin cikina kawai Kai burinka ka samu abin da daga gareni" Jabir Wanda yake kok'arin zame Mata riga jin abin da Teemarh take fad'a yasa ya tashi daga kanta, kayansa ya mayar jikinsa ya fita daga d'akin a fusace, Teemarh ta saka kuka, ita ma ta mayar da kayanta ta bi bayansa da sauri, Amman Bata ga koda k'eyar Jabir ba, barantana shi, durk'ushewa tayi a k'asa tana kuka, ji tayi an d'agota da sauri ta juya tare da tashi tsaye tana ci gaba da yin kukan, Aunty Murja ta kalleta sosai sannan ta ce "Fatima meyafaru ki ke kuka?","Bakomai Mummy" Teemarh tayi maganar cikin shash-shekar kuka, "ba za ki iya fad'a min damuwarki ba Fatima" Kukan Teemarh ya tsananta ta ce "Darling ne" Tayi maganar tana goge hawayen fuskarta. Aunty Murja ta ce "koma Mai yayi miki bai kamata ace kin zo kina yin kuka ba, ya kamata ki zauna ki nutsu ki kirasa, sai ku tattauna a kan matsalarku, ta haka ne za ku fuskanci juna" Teemarh tayi murmushi ta ce "Nagode Mummy zan yi amfani da shawararki insha Allahu" Daga nan kowannan su ya koma d'akinsa, Teemarh ta d'auki wayarta ta shiga kiran layin Jabir Amman a kashe wayar take Dan haka ta zauna ta cigaba da yin kallonta Amman zuciyarta tana gurin Jabir. *'BANGAREN SAFNA😔👏🏽* Safna ta fito da gudu daga d'akinta tana murmushi suka had'a ido da Safwan ta matso kusa dashi zata rumgumeshi, yayi saurin tureta yana cewa "karki matso kusa da ni" Yayi maganar fuskarsa a d'aure, Safna ta ce "Ruhina ka yi hak'uri na tuba ba zan k'ara ba, Amman Dan Allah karka hukunta ta wannan hanyar ka yi min duk abin da ya dace da ni ka ji Ruhina" Kallonta yayi kamar ba zai yi magana ba sai Kuma ya ce "Akwai sharad'ai guda uku da zan fad'a miki, idan har ki ka amince dasu to shikenan komai zai huce" Safna ta ce "wad'anne sharad'ai ne?" Zama Safwan yayi ita kuma ta tsaya tana son jin wane sharad'i ne wannan "sharad'i na farko shine karki sa ke yin kishi a kan Hafsa ina son ki d'auketa tamkar Zahra k'anwarki wacce ku ka fito ciki d'aya, Sharad'i na biyu kuma karki sa ke yi min zancen yaushe Khalid zai dawo saboda ni nasan gurin da na kai shi babu abin da za'ayi masa na kuntatawa Sharad'i na uku kuma karki sa ke yi min maganar Hafsa idan muna tare da ke, idan kin yarda da su za ki iya zuwa" Safwan yayi maganar tare da bud'e hannayensa alamar Safnan ta zo jikinsa. Hawaye ne suka shiga gangaro mata a hankali ta fara tafiya kamar mai sand'a, ta fad'a jikinsa tare da rushewa da wani irin kuka, tana tsananin jin kewar yaronta amman kuma anyi mata katangar k'arfe dashi, tana ji tana gani ba ta da damar da za ta tambayi yaronta, sai ya zama laifi, "na amince da sharad'anka ruhina amman dan Allah ka kawo min yarona koda sau d'aya ne na ganshi, idan na ganshi ba zan sake cewa a kawo min shi ba nayi maka alk'awari" Tausayinta ya kamashi amman ya zama dole yayi haka, domin ya k'ara saka son Hafsa a cikin zuciyar Safna "to shikenan zan kawo miki shi gobe insha Allahu","to nagode" Safna ta fad'a cikin rawar murya, daga nan suka dora soyayyarsu daga inda suka tsaya. *Team Khadijatullahi where you😂😂yau fa ta gwangwaje ku da kalamai masu dad'i* *'BANGAREN HAJIYA ASIYA DA ALHAJI MUKHTAR🤔* Sai da Hajiya Asiya ta kwana biyu sannan ta farfad'o wajen k'arfe 8:00am na safe Alhaji Mukhtar yana zaune kusa da ita ya zuba mata ido yana kallonta cike da so da k'aunarta, a hankali ta fara bud'e idanuwanta ta zuba su a saman d'akin abubuwan da suka faru suka shiga fad'o mata hawaye na zuba daga idanuwanta, yanzu shikenan ta san gurin wad'annan wahalallun iyayen nata zata koma ta ci gaba da shan wahala, Alhaji Mukhtar ya saki murmushi tare da kiran sunanta "Asiya" A hankali ta juya ta kalli mai kiran na ta ganin Alhaji Mukhtar yayi matuk'ar ba ta mamaki tare da jefo masa tambayoyi "Ina ne nan? Me na zo yi nan? Waya kawo ni? Ina yarana? Ina Abban Jabir" Murmushi yayi mai cin rai jin ta ambaci sunan mijinta amman ya danne ya fara ba ta amsoshinta "kina asibiti ne, na je gidan tsafi ne na tarar da ke kwance cikin jini shine ya d'aukoki na kawoki, kuma tun da na kawoki babu wanda ya zo gurinki amman gaskiya nayi mamaki sosai yaranki ko mijinki babu wanda ya nemeki kenan hakan na nufin basa buk'atarki a rayuwarsu, ko kuma basu damu da ke ba?". Hawaye Hajiya Asiya tashi zubarwa tana cewa "A'a yarana suna sona sosai ba za su iya juya min baya ba kuma"............"To gashi sun juya miki kuwa tunda yau kusan kwananki goma babu wanda ya zo asibitin nan kuma har gidan na je amman su ka yi min rashin mutunci suka ce basa sonki a rayuwarsu" Alhaji Muhktar ya fad'a cikin yanayin damuwa dan kuwa ya fad'i haka ne kawai dan Hajiya Asiya ta ji haushi kar ta ce zata koma gidan mijin na ta, dan kuwa shi bai ma san ina ne gidan Hajiya Asiyan ba, kuma bai san waye mijin na ta ba. "Yanzu haka su Jabir za su yi min ban yi tunanin haka daga garesu ba kuma nima insha Allahu zan fita a rayuwarsu kamar yadda nima suka fita a rayuwata" Hajiya Asiya tayi magana tare da goge hawayen fuskarta, Alhaji Mukhtar kuwa murmushi yayi ganin cikin k'ank'anin lokaci yayi nasarar raba tsakanin Hajiya Asiya da mijinta da kuma yaranta yanzu shikenan dole yasan shi za ta bi ya kai ta gidansa ya samu ya biya buk'atarsa da ita dan a iya zaman da su ka yi da ita ya fuskanci cewar Hajiya Asiya macece mai shegen son kud'in tsiya, dan haka ya san da zarar yana sakar mata kud'i to bashi da wata damuwa,haka dai yayi ta rarrashinta tare da cusa mata tsanar yaranta da kuma mijinta. *'BANGAREN INNA LARAI DA LADO😂😣* Tun ranar da Inna Larai ta dawo gida, yaronta da iyayenta suka d'auki karan tsana suka dora mata domin sun ji labarin irin abin da ta aikata domin a cewarsu kaf danginsu babu mazinaci, dan haka suka cireta daga cikinsu wani d'an k'aramin d'aki suka ba ta wanda ake kiwon kaji a cikinsa, kaji ne gaba d'aya a cikin d'akin dan su kansu kajin ma d'akin yayi musu kad'an, a haka amman Inna Larai take rab'awa take zama duk a takure, ga shi sunyi mata gargad'in kar su sake su ga k'afarta a waje idan har ba su suka bata izinin ta fito ba, ba'a ba ta aminci sai kowa ya ci ragowar da aka rage shi za'a gefa mata a jikinta ya zube kajin su yo kanta su yi ta caccakarta sun cin abincin, wata ran kuwa ba za su bata ba haka zata wuni da kwana ba ta ci abinci ba. Lado kuwa duk irin abin da ake yi wa mahaifiyarsa ko a jikinsa dan wani abun ma shi yake tsara yadda za'ayi mata kuma shine ya hana a dinga bata abinci sai dai ragowar da aka ci aka rage, saboda a cewarsa wai ta haka za'a horata idan wani ya nemeta da niyyar yayi zina da ita ba za ta yarda ba, Yau kamar kullum Zaituna 'yar k'anwar Inna Larai Hafsatu ta d'auki kwanon abincin da aka tarkatawa Inna Larai abincin a aka ci aka rage ta nufi d'akin kajin "Ke! Ke Zaituna tsaya" Lado wanda ya fito daga d'akinsa ya dakatar da Zaituna daga shiga d'akin, juyowa tayi tare da cewa "Na'am Yaya" Karb'ar kwanon abincin yayi daga hannun Zaituna ya k'arasa d'akin kajin ta window ya jefawa Inna Larai abincin ai kuwa kaji suka yo kanta suna caccakarta suna cin abinci Lado ya saki dariya tare da cewa "Kaii wannan abin yana saka ni nishad'i sosai" Sai ya juya ya shige d'akinsa dan daman abin da ya fito dashi kenan. Zaituna kuwa hawaye ne suka shiga gangaro mata tana matuk'ar jin tausayin Inna Larai sosai kuma tana son ta taimaka mata amman bata da halin da za ta yi hakan dan kuwa ko ta ce zata taimaka mata Lado ba zai tab'a barin tayi ba, nan wata dabara ta fad'o mata tayi murmushi "Inna insha Allahu zan yi kok'arin na taimaka miki ta wannan hanyar, ba zan bari ki wulak'anta ba ai k'addara tana kan kowa" Tayi maganar a zuciyarta daga nan ta juya ta koma d'akinta. Inna Larai kuwa kuka take kamar ranta zai fita takaici da bak'in ciki had'e da nadama sun gama kasheta yanzu da bata biyewa D'an Ladi ba da tuni tana chan gidanta babu wanda ya isa yayi mata wannan wulak'anci, anan ta fara tunanin yadda za ta yi domin ta tsaratar da kanta daga wannan uk'ubar da ake yi mata amman ta rasa mafita tayi kuka har ta godewa Allah. Wajen k'arfe 9:00pm na dare bayan kowa ya kwanta Zaituna ta fito rik'e da kwanon abinci tana sand'a a haka har ta isa d'akin kajin ta shiga chan ta hango Inna Larai ta takure a jikin bango, k'arasawa tayi kusa da ita tare da kiran sunanta "Inna" Da sauri Inna Larai ta d'ago tare da cewa "Na'am Zaituna ke ce?","Eh Inna ni ce" Tayi maganar tare da zama kusa da ita ta bud'e mata kwanon da ta zo dashi Shinkafa da miya ce wacce ta ji kifi "Ga shi Inna ki ci, kuma Insha Allahu kullum da daddare bayan kowa yayi bacci zan dinga kawo miki abinci kina ci" Murmushi Inna Larai tayi hawaye suna bin kuncinta ta ce "Nagode sosai yarinyata, kowa ya guje ni amman kuma ke baki gujeni ba, nagode da kulawarki","bakomai Inna ki yi sauri ki cinye abincin kar wani ya fito" Haka Inna Larai ta karb'i kwanon ta dinga zabga loma daman wata iriyar bak'ar yunwa ta ke ji, gaba d'aya ta cinye abincin, sannan ta mik'awa Zaituna kwanon tare da cewa "nagode" Zaituna ta fita daga d'akin ta nufi na ta d'akin tana sand'a har ta shige ta ja kofar ta kulle, ta ajiye kwanon sannan ta koma kan gado ta kwanta tana jin wani irin dad'i a zuciyarta da ta samu ta taimakawa Inna Larai. *'BANGAREN ABBA DA AUNTY MURJA🥰💃🏽* Yau Aunty Murja ta tashi da rashin lafiya komai ta ci sai ta amayo shi, hankalin Abba ya tashi haka ya shiryata suka je asibiti likita yayi mata gwaje-gwaje anan ya gano cewar tana d'auke da d'an k'aramin ciki ne sati hud'u, farin ciki gurin Abba ba'a magana, haka ya rik'e Aunty Murja suka fito daga asibitin suka nufi gida, Aunty Murja gaba d'aya kunyar Abba ta ke ji kamar ta nitse a k'asa, Abba shima ya fuskanci haka, kuma ya ji ya k'ara jin son Aunty Murja a cikin zuciyarsa, suna isa gida ta fito ya zagaya ya bud'ewa Aunty Murja murfin motar ta fito kanta a k'asa tana shirin wucewa ta barshi ya rik'e hannunta "Menene haka kuma Murjanatu? Ba na so ki daina kinji" Kai ta gyad'a masa alamar eh "Yauwa ko kefa kin ga babu inda kika tab'a ganin ance wai mata tana jin kunyar mijinta, ko saboda kina da ciki yanzu shine zaki sauya min ki daina kula dani kamar yadda ki ke yi?","A'a ba zan sauya maka ba" Tayi maganar kanta a k'asa "To d'ago ki kalleni","ba zan iya ba, dan Allah kar ka ce dole sai na kalleka kuma karka yi fushi dani" Abba ya b'ata fuska sannan ya ce "Wato ban isa na ce ki yi abu ba ki yi ko?" Hawaye suka shiga zubo mata dan kuwa ba za ta iya kallonsa ba, gaba d'aya wata iriyar muguwar kunyarsa ta ke ji tun da likita ya sanar masu cewar tana da ciki "Kayi hak'uri dan Allah ba haka ba ne" Tayi maganar cikin muryar kuka. Abba zuciyarsa tayi matuk'ar shiga bak'in ciki saboda ganin zubar hawayen Aunty Murja amman kuma duk da haka dole ya san yadda zai yi ya cire mata wannan sabuwar kunyar da ta tsiro da ita yau, hannunta ya saki sannan ya nufi hanyar da zata sadashi da babban falon, Aunty Murja ta bi bayanshi tana kuka babu kowa a falon ko da yake babu kowa daman a gidan Teemarh ce sai Jabir shi kuma Jabir ba ya zama a gidan Teemarh kuma ba ko yaushe take fitowa babban falon ba kullum tana d'akinta, Suna shiga d'akin Aunty Murja ta sha gabansa tana kuka kuma har lokacin kanta na k'asa kok'arin tureta Abba yake amman ta rumgumeshi tare da k'ank'ameshi sosai tana kuka "Kayi hak'uri dan Allah zan kalleka wallahi da gaske na ke yi zan kalleka" D'agota Abba yayi yana murmushi "To kalleni" Yayi maganar tare da kafeta da ido, d'agowa tayi ta zuba idanuwanta a cikin na sa tana hawaye "Yauwa ko kefa Matata" Yayi maganar yana goge mata hawaye murmushi Aunty Murja tayi tare da cewa "ka hak'ura kenan Yaya?" Kai ya gyad'a mata alamar eh ta rumgumeshi ya kamata suka zauna a kan kujera yana fad'a mata kalamai masu dad'i. *Ni kuwa nace to Abba asha soyayya lafiya, amman ku yi a hankali karku kone nayi gidansu Safwan ni kam😂* *'BANGAREN SAFWAN DA SAFNA🤗❤️🌹* Kamar yadda yayi mata alk'awarin cewar zai kawo mata Khalid, haka kuwa a ka yi washe gari bayan ya dawo daga office ya biya gidansu Hafsa ya d'auki Khalid bayan ya cewa Hafsan gobe zai dawo dashi suka nufo gida tare dashi, Safna tana zauna tana kallo ta saka t.v a gaba kai sai kayi tunanim cewar kallon film d'in da ake yi ta ke yi saboda yadda ta kaf t.v da ido amman kwata-kwata hankalinta ma baya kan t.v yana kan yaronta da kuma mijinta dan ganin yau Safwan d'in ya dad'e ta san gurin Hafsa ya tafi kuma ga shi bata da damar tambaya sai ya ce tayi masa laifi. Ta share guntun hawayen da ya zubo mata, ji tayi an dafata tayi saurin d'agowa anan idanuwanta su ka yi tozali da yaronta Khalid cikin tsananin murna ta jawo shi jikinta tana cewa "Yarona kai ne","Eh Mommy ni ne nayi kewarki sosai" Safna ta ce "nima haka darling nayi kewarka sosai i miss you more" Safwan wanda ya hard'e hannuwansa a k'irji yana kallonsu ya had'a hannuwansa guri d'aya tare da yin tafi, da sauri Safna ta kalli gurin da yake sam tama manta dashi kallon Khalid tayi sannan ta ce "je ka d'akinka ka huta ko? Na san ka kwaso gajiya","Eh mommy bacci ma zanyi"Khalid ya ce tare da nufar d'akinsa bai jira jin abin da Safna za ta ce ba. Kallonta ta maida gurin Safwan wanda ya d'aure fuska kamar wanda aka aikowa da sakon mutuwa, tashi tayi ta matsa kusa dashi tana murmushi "Ruhina ka yi hak'uri kasan nayi missing d'in Khalid sosai, kuma".......... D'aga mata hannu yayi tare da cewa "yi shuru wannan shine dalilin da yasa nace zan bar yaron chan gurin Hafsa saboda ke kwata-kwata ida yana kusa da ke bakya damuwa da ni ko kuma menene damuwata bakya yin hira da ni gaba d'aya lokacinki yana k'arewa ne a gurin dan haka yanzun nan zan mayar dashi dan ba zai zo ya hana ni jin dad'ina ba" Safna ta kalleshi ta ce. *Eid Mubarak 💞✨ Fans Ina yi muku barka da sallah da fatan an ci nama lafiya, aci nama dai a hankali kar azo a dinga ce min Dijartyy a kawo filajin😂* "Ruhina wallahi ba haka ba ne kai ma kasan ka na da matuk'ar muhimmanci gurina ina sonka ina tsananin k'aunarka Amman tunda ka ce haka insha Allahu zan dinga ajiye duk abin da nake ina kula da kai" Safwan ya ce "To shikenan tunda kin ce haka Ruhina Ina sonki nima fiye da yadda ki ke sona" Murmushi Safna tayi sannan ta ce "To yanzu ka huce ko Ruhina" Kai ya gyad'a alamar eh, tayi kissing d'insa a kunci tare da cewa "Shiyasa nake sonka mijina, to yanzu tashi muje ka yi wanka" Harararta yayi ya ce "Kiyi min wanka dai" Safna ta ce "to shikenan tashi muje nayi maka wanka" Tashi yayi suka shiga d'akin Safwan d'in, toilet suka shiga tare su ka yi wanka sannan suka fito kayan bacci suka saka sannan suka kwanta bacci. _Yau fa kuyi hak'uri ba zan yi typing mai tsayi ba saboda zan je na ci naman sallah🤣_ *'BANGAREN KHADIJATULLAH DA ALIYU💔💃* Yau an tashi da ruwan saman tun asuba ake yi sai wajen k'arfe 11:00am na safe aka tsaya Khadijatullah ta fito tsakar gida ta tsaya bata da wani buri irin ta ga Aliyu ya fito ta kalleshi ta ji dad'i a zuciyarta, Amatullahi ce ta fito daga d'aki tana kallon Khadijatullah fuskarta kunshe da murmushi dafa Khadijatullah tayi ta ce "Dijan Yaya Aliyu meya faru?","Bakomai Bestyna me ki ka gani kike tambayata?" Amatullahi ta ce "Kawai dai na ga Mata ta fito tana jiran mijinta ya fito" Harararta Khadijatullah tayi sannan ta shige falon Dan ta San indai ta tsaya to Amatullahi sai ta k'ureta, Amatullahi ta bi bayanta tana yin dariya ciki². Aliyu kuwa bacci yayi tayi dan sai wajen 11:45am ya tashi ya shiga wanka ya shirya cikin wani yadi mai tsada green colour, ya fito ya nufi falo domin ya gaishe da Hajiya Mama kuma ya ga sahibarsa, Yana shiga ya tarar da Hajiya Mama zaune a kan kujera tana kallon labarai ita kad'ai ce "Assalamu alaikum" Hajiya Mama ta d'ago tana murmushi tare da amsa masa sallamar ta sa "Wa'alaikassalam" Zama yayi a k'asa wajen k'afafuwanta "Ina kwana Hajiyata","Lafiya k'alau d'an albarka ka tashi lafiya" Aliyu ya ce "Lafiya alhamdulillah Ina su Amatullahi ko sun tafi makaranta ne?" Hajiya Mama ta ce "A'a yau ai lahadi ba su je ba suna cikin d'akinsu" Aliyu ya ce "Ohh haka ne fa" Daga nan suka zaune suna yin hirarsu irin ta jika da Kaka. Khadijatullah wacce tunda Aliyu yayi sallama take son ta fito Amman ganin idanuwan Amatullahi a kanta yasa ta share rumgume take da Affan a hannunta gaba d'aya hankalinta Yana wajen Aliyu, mik'ewa tayi ta nufi hanyar da zata sadata da falon taji muryar Amatullahi tana cewa "Ina za ki je kuma bayan muna hira","Zan je gurin Hajiya Mama" Ba ta jira abin da za ta ce ba ta fita da sauri. Shahida tayi murmushi ta ce "Sister kin ga Allah ya amshi addu'armu sister ta fara son Yaya Aliyu Haidar" Amatullahi ta ce "Hakane kam dan d'azu ma jiransa ta fita yi a waje shine na je na fatattakota" Dariya Shahida tayi sosai sannan ta ce "Kaii Sister ki barta su soye abin su mana ke kuwa" ita ma dariyar tayi ta ce "To na barsu Sister Shahida" Daga nan suka cigaba da yin hirarsu ta duniya. Khadijatullah tana fita su ka yi ido biyu da Aliyu murmushi ya sakar mata, nan ta ji wani irin dad'i ya tsarga mata cikin jijiyoyin jikinta, zuciyarta kuwa ta cika da farin ciki, Zama tayi a kan kujera tare da sunkuyar da kanta "Sannu da hutawa Hajiya" Ta fad'a kanta a sunkuye "Yawwa Khadijatullah ya babana har yanzu bacci ya ke yi?","A'a ya tashi idonsa biyu" Hajiya Mama ta tashi tare da zuwa gurin da Khadijatullah take zaune ta karb'i Affan d'in sannan ta shige bedroom d'inta, Shuru falon ya d'auka na tsawon mintina 10 babu Wanda yayi magana a cikin su Aliyu ya kafeta da kyawawan idanuwansa Yana k'ara jin k'aunarta na shiga zuciyarsa, Khadijatullah ta ce "Ina kwana" Murmushi yayi sannan ya amsa "Lafiya alhamdulillah Gimbiyar Mata yau Kuma rowar kyakkyawar fuskar nan ake min ba'a d'ago a kalleni ba","A'a ba rowa nake maka ba" Tayi maganar cike da jin kunyarsa, Amatullahi da Shahida ne suka fito tare da zama kusa da Khadijatullah "Muma ba za'ayi ba mu ba, mun zo a koya mana soyayya" Amatullahi tayi maganar tana kallon Khadijatullah. Aliyu ya ce "Kun zo dai kawai ku takura mana, muna cikin soyayyarmu, idan soyayya ku ke son koya kowaccenku tayi zuciya ta samo saurayi mana gauraye kawai bamashinshini" Yayi maganar Yana dariya, Shahida ta ce "Laaa Yaya Aliyu Haidar mu ne gaurayen? Gaskiya ka taro match" Amatullahi ta ce "Fad'a masa dai dan kuwa ya taro babban match" Aliyu ya ce "Ahh abin na d'an sauk'i ni da nake da messi, please ku tashi ki bamu waje kun ji darling sisters" Tashi su ka yi Amatullahi ta ce"To zamu ba ku guri ku zanta Amman fa ba mu hak'ura ba" Aliyu ya ce "To na ji" Fita su ka yi tsakar gida suka zauna a kan taburma, Khadijatullah suna fita ta d'ago kai ta kalli Aliyu sannan ta ce "Kaii Yaya Aliyu Amatullahi rigimarta tayi yawa na san ita ta giggib'o Sister suka fito" Dariya yayi sosai sannan ya ce "Bar ni da su ai na fuskanci takura mana suke son su fara yi" Murmushi tayi ba tare da ta ce masa komai ba, nan Aliyu ya shiga kashe Khadijatullah da kalaman soyayya masu ratsa zuciya da jinin jiki. _Ni kuma na ce Bari na bar ku haka Masoya na rankaya gidan Nihal da Salis iyayen soyayya🤣💃_ *'BANGAREN SALIS DA NIHAL💕💖* Kwance take a jikinsa tana ta zuba masa shagwab'a iri-iri, shi kuma sai lallab'ata ya ke yi kamar wata kwai "Babyna ni gaskiya ba zan yarda ba, sai mun je tare Allah ba za ka bar ni a gida ba idan kuwa ka fita wallahi kuka zan tayi Kuma har ka dawo ba zan daina ba" Salis ya ce "Haba babyna so kike zuciyata ta buga, tunda haka ne to ni na hak'ura da fitar ma tunda daman yamma tayi" Murmushi Nihal tayi tare da cewa "Da gaske ka ke babyna" Salis ya ce "Eh mana Baby Nafisa kuma Baby Nihal Kuma Babyn baby" Dariya tayi sosai ta ce "Sweetheart duk ni kad'ai wannan sunan, to nagode sosai Babyn baby, can't love you less" D'aukarta yayi kamar wata jaririya suka shige bedroom suka rufe kofa. _ni kuma er sa ido na ce sai na bi su na ga me za su yi Amman kuma sun kulle kofar da key🤣sai na yanke shawarar kawai nayi gidan Teemarh da Jabir😂_ *'BANGAREN TEEMARH DA JABIR😂💖* Teemarh tana kwance tana jiran dawowar Jabir ganin har k'arfe 12pm na dare bai dawo ba, ta kifa kanta da guiyoyinta tana kuka kamar ranta zai fita, dan ta san Jabir yana chan yana shek'e ayarsa da yammata dan kuma hausawa sun ce Mai hali baya fasa halinsa, ji tayi an dafata da sauri ta d'ago rinannun idanuwanta ta zubawa Wanda ya dafatan Jabir ne da sauri ta ture hannunsa tare da juyar da fuskarta jefe ta cigaba da yin kukanta, Jabir kuwa duk da cewar baya son Teemarh Amman sai da ya ji hankalinsa ya tashi Dan ya San dalilin kukan na ta ba zai huce na rashin dawowarsa da wuri ba. Zama yayi kusa da ita tare da kok'arin jiyo da fuskarta, Amman tak'i yarda sai tureshi ta ke yi da ya gaji ya mik'e tsaye tare da d'aukarta cak sannan ya koma ya zauna a kan kujerar Yana rumgume da ita a jikinsa, Teemarh tai-tayi ta kwace Amman ta kasa tana kuka ta fara magana "Tunda ka nuna min ba ka k'aunata kuma ka tsaneni kawai ka rabu da ni ka sakeni na koma gidanmu" Tayi maganar tana cigaba da tureshi, Jabir ya k'ara k'ank'ameta sosai a jikinsa yana cewa "Haba Darling wane dak'ik'in ne ya fad'a miki na tsaneki kuma ba na sonki da har ki ke cewa na sakeki ai darling ni da ke mutukaraba babu mai rabamu dan ko mutuwa ma tare da za mutu da ke please ki tsaya ki saurareni kin ji","Me zan saurara daga bakinka na san club ka je gurin yammatanka ka fad'a min me na rageka dashi ko kuma me suka fini dashi, kyau ko kuma surar jikin ko Kuma......" Bakinta ya toshe mata "Ba su fiki da komai ba darling kuma wallahi ba Wai na je club Dan"........"Dakata Jabir ba na son jin komai daga bakinka". Da k'arfi ta fisge jikinta daga na shi ta fad'a kan gado tare da rushewa da wani irin kuka Mai cin rai, Jabir ya tashi ya koma kan gado Yana cewa "Darling ki daina kukan nan haka Dan Allah kinji babyn Jabir" Cikin zafin nama Teemarh ta mik'e daga kwancen da take tana cewa. "Karka k'ara cemin wani babyn Jabir dan ni ba babynka ba ce, babu ni babu kai ka ji na fad'a maka ka fita idona" Tayi maganar cikin kunar zuci, murmushi Jabir yayi ya ce "Ok am so sorry dear na dena, amman dan Allah ki daure ki saurareni ko da sau d'aya ne kinji baby boo" Teemarh tayi masa wani irin kallo "Ba ni da lokacin da zan saurareka, ka matsa daga kusa da ni dan manzon Allah","Hmmm!" Abin da Jabir ya iya cewa kenan sannan ya koma kan kujera ya zabga tagumi yana kallonta ta cigaba da kukan, wani irin haushin kansa ya fara ji saboda ya san Teemarh tana son shi sosai bai kamata yana yi mata abin da zuciyarta zata k'untata ba, kwantawa yayi a kan kujera a hankali bacci mai nauyi yayi awon gaba da shi, ita kuwa Teemarh sai da tayi kukanta mai isarta bacci 'barawo ya sace ta. ~*BAYAN WATA BIYU✨*~ A yau aka d'aura auren Alhaji Mukhtar da Hajiya Asiya bayan rigingimun da suka faru a tsakaninsu, dan da aka sallameta daga asibitin gidanta ya kai ta inda matarsa ta nuna ba za ta iya zama da ita ba tunda ba matarsa ba ce ta ya ya zai d'auko macen da ba muharramarsa ya kawo ta gidansa, nan suka huce suka bar ta tana ta 'ba'batu ya kai ta d'akinsa, kullum ya zamana ya na gurin Hajiya Asiya a cikin d'akin domin so ya ke ya shawo kanta ya gama da ita amman sam ta k'i yarda ta ce masa ita ba za ta yarda tayi zina ba sai dai ya aureta haka ya amince ba dan yaso ba, wannan shine dalilin da yasa a ka daura auren Hajiya Asiya. *Ya ku ke ganin wannan drama fans Alhaji Mukhtar ya auri Asiya domin ya cika burinsa a kan ta akwai cakwakiyoyi sosai🤣✨* Haka Alhaji Mukhtar ya dawo gida jikinsa na rawa dan yau burinsa zai cika, dole Asiya ta amince dashi yanzu ko ta k'i ko ta so, kai tsaye d'akinsa ya nufa inda ya tarar da Hajiya Asiya tana kwance a kan makeken gadon d'akin, hannunta rik'e da waya tana daddannawa, da kallo ta bi Alhaji Mukhtar har ya k'araso kusa da ita ya washe baki tare da cewa "Hajiyata an d'aura fa" Hajiya Asiya ta ya tsine fuska "To yayi" Tayi maganar tare da cigaba da danna wayar "To yanzu dai ai zancen 'boye-'boye babu shi, tunda kin zama mallakina" Ya k'arasa maganar tare da fad'awa kan gadon, a gigice Hajiya Asiya ta mik'e tana kallonsa tare da dafe k'irji tana cewa "Me zan gani, me ka ke shirin yi min, to karka so ma ka ji na fad'a maka ban shirya ba" Wani irin kallon kin raina min hankali Alhaji Mukhtar ya ke bin Asiya dashi "Lallai ma Asiya ba ki san ma wanene Mukhtar Sa'id Baba ba, ki je ki tambayi Sadiya za ta fad'a miki wanene ni, indai ina son abu to dole fa sai na same shi ko ta wane irin hali ne, wallahi Asiya tunda aka d'aura mana aure to a yanzun nan sai na samu abin da na ke so gwanda ki shafawa kan ki ruwan sanyi, ki amince tun kafin ki ga ba dai-dai ba" Wata iriyar mahaukaciyar dariya Hajiya Asiya tayi tare da cewa "Ka na tunanin zai amince ka kusance ni ne, to idan mafarki ka ke gwanda ka farka don kuwa ni Asiya wallahi na fi k'arfinka, ba zan iya amincewa d'an mafiya ya kusance ni ba, ko kuma nace matsafi" Ai tana k'arasa maganar ta ji ya d'auketa da wasu zafafan mari tun ina argawa har sai da na gaji na daina na ce Allah ya k'ara wallahi🤣. Har sai da ta fad'a kan gadon sannan ya cire kayan jikinsa ya kama doguwar rigar jikinta ya yaga ta "Yanzu za ki fahimci wanene ni ke har kin isa ki ce min matsafi to wallahi sai kinyi danasanin haihuwarki da uwarki tayi yau d'in nan" Tun Hajiya Asiya tana iya tureshi har ta fara gazawa haka tana ji tana gani Alhaji Mukhtar ya samu abin da ya ke so, ya tashi ya shiga toilet yayi wanka ya dawo ya shirya cikin tsadaddiyar shadda ya fita daga gidan. Hajiya Asiya kuwa tashi tayi ta shiga wanka zuciyarta babu alamar nadama wanka ita ma tayi sannan ta dawo ta shirya cikin atamfa blue colour doguwar riga ce, kwanciya tayi a kan gadon tare da lumshe idonta, har bacci ya fara d'aukarta ta ji saukar duka a jikinta, ta yunk'ura da niyyar tashi amman ta kasa sakamakon d'aure hannuwanta da k'afafuwanta da aka yi da sauri ta d'aga kai Alhaji Mukhtar ta gani a kan ta rik'e da wata dorina mai kauri, ta bud'e baki za ta yi magana ta ji saukar wata bulalar haka yayi ta jimgarta tun tana ihu har sai da ya zama ta kasa yin ihun sai dai hawaye da ya ke bin fuskarta, sai da ya gaji dan kansa sannan ya durgar da bulalar ya fita a fusace, kuka Hajiya Asiya ta ke yi mai tsima zuciya gaba d'aya jikinta rad'ad'i ya ke yi mata, fatar jikinta duk ta yi ja, tayi rud'u-rud'u. *'BANGAREN HAFSA✨* Yau sauran wata d'aya a d'aura auren Hafsa da Safwan wata iriyar soyayya suke nunawa junansu kamar su cinye juna kullum suna tare, yana zaune kusa da Safna ya d'auki wayarsa ya kira Hafsa ringing d'aya biyu Hafsa ta d'aga wayar tare da yin sallama "Assalamu alaikum Sweetheart" Murmushi Safwan yayi ya ce "Wa'alaikumussalam Ga ruhina za ku gaisa da ita" Yayi maganar tare da sakawa Safna wayar a kunne, Safna idanuwanta suka cicciko da k'alla tana kallonsa a hankali hawaye suka fara gangarowa, Safwan ya d'aure fuska tare da kawar da fuskarsa da kallonta ya fara kok'arin tashi ya bar ta, ganin haka yasa Safna dai-daita kanta "Assalamu alaikum Amarya" Hafsa tayi murmushi dan da taji shuru ta d'auka Safna ba za ta yi mata magana ba "Wa'alaikumussalam Aunty Safna ina yini" Safna ta ce "Lafiya alhamdullahi Ya shirye-shiryen biki","Alhamdullahi Aunty Safna" Safna ta ce "To Allah ya kaimu lokacin sai anjima" Bata jira mai Hafsa za ta ce ba ta ajiye wayar ta nufi d'akinta da gudu tana kuka. Safwan ya d'auki wayar su kayi sallama da Hafsa, ya bi bayan Safna yana shiga d'akin ya ganta kwance a kan gado tana kuka, ji ta ke zuciyarta kamar za ta fashe (Ni kam nace Safna kin yi namijin kok'ari wallahi ba za iya ba🤣) d'aukarta yayi gaba d'aya ya zauna a kan gado sannan ya dora a jikinsa yana rarrashinta dan kuwa yau Safna ta burgesa sosai ya san saboda kar yayi fushi da ita tayi haka "Ruhina ki yi shuru dan Allah ba na son ki na yin wannan kukan kin ji sarauniyata" Murmushi tayi mai ciwo ta ce "Ruhina dole nayi kuka, dan Allah ka bar ni idan nayi kukan zan ji dad'i a zuciyata, ina jin zuciyata kamar za ta fashe" Ta k'arasa maganar tana kuka, tausayinta ya kamasa "Babyna nasan kina tsananin kishina, amman za ki iya yi min wani alk'awari?" Safna ta d'ago idanuwanta tana kallonsa tare da cewa "Eh zan yi maka" Wayarsa ce ta hau ruri yayi sauri zarota daga aljihu tare da d'agawa yayi sallama ban ji mai wancan d'in ya ce ba sai ji nai ya ce "To insha Allahu ranka ya dad'e gani nan zuwa" Ya fad'a tare da kashe wayar kallon Safna yayi "Ruhin ki yi min afwa mai gidana yana kirana akwai lissafin da za mu yi dashi mun fara to ba mu k'arasa ba kuma uzuri ya kama shi, idan na dawo zamu kin ji Sarauniyata dan Allah ki yi min alk'awari ba za ki daina wannan kukan, zuciyata tana raya min cewar ni mara adalci ne indai na ganki ki na kuka" Yayi maganar cikin yanayin damuwa, murmushi tayi ta ce "Allah sarki ruhina kai ba mara adalci ba ne, kuma zan dai na kuka ka ji ka tafi kawai karka damu","Kinyi min alk'awarin za ki dai na kuka?" Kai ta d'aga masa alamar eh, haka ya tashi ya shirya Safna ta rakashi har gaban mota ya shiga, Safwan ya kafeta da ido yana kallonta ta ce "Allah ya dawo min da kai lafiya","Amin" Har ta juya ta fara tafiya Safwan ya kirawota "Ruhina" Da sauri ta juyo tana kallonsa tana murmushi "Na'am" Shima murmushin yayi mata sannan ya ce "Ina sonki sosai" Yana gama fad'ar haka ya rufe murfin motar ya ja mai gadi ya bud'e masa gate d'in gidan ya fita ya nufi hanyar ma'aikatarsu, Safna kuwa murmushi tai-tayi har ta koma cikin falon ta kwanta tare da kunna kallo. Sai wajen k'arfe 9:00pm na dare Safwan ya dawo da sauri Safna ta tashi daga kwanciyar da tayi tunda ya tafi tana yi masa sannu da zuwa murmushi yayi tayi zuciyarsa fas, rumgumeta yayi tare da cewa "Da fatan kin cika min alk'awarina ko?" Safna ta ce "Eh na cika ban yi kuka ba" Safwan ya ce "Yawwa er aljanna" Zama su ka yi a kan kujerar da ta tashi sannan ya ce "To yanzu za mu yi maganar alk'awarin da na ke so ki yi min" Safna ba ta ce komai ba sai dai gaba d'aya ta tattara hankalinta a kan sa da jin wane alk'awari kuma ya ke son tayi masa "Ina son ki yi min alk'awarin ba za ki sake yin kuka a kan auren nan da zan yi ba, dan idan na ganki ki na yin kuka ba na jin dad'i a cikin zuciyata dan Allah ruhina ki daure ki yi min alk'awarin nan ko na ji dad'i dan Allah ki daina yawan kukan nan kin ji dan Allah" Safna dai shuru tayi hawaye suna shirin zubowa, amman sai ta daure ta mayar dasu tana kallonsa "Yaya Safwan duk alk'awarin da ake cewa nayi maka, ina yi indai na ji bai fi k'arfina ba amman wannan ba zan iya ba dan ni kai na wani lokacin ban san lokacin da kukan ya ke zuwar min ba sai dai kawai na ji ina yi" Tayi maganar cikin muryar kuka, rumgumeta yayi sosai yana bubbuga bayanta tare da yi kalamai masu dad'i, daga nan suka tashi suka shiga d'aki. *'BANGAREN INNA LARAI🤦🏽‍♀️😩* Kullum Zaituna sai ta kawo mata abinci da daddare bayan kowa ya kwanta kuma babu wanda ya tab'a kamata, Zaune take a tsakar gida wajen k'arfe 5:00pm na yamma tana daka yaji sai ga Lado ya shigo ko sallama bai yi ba, Kallo d'aya Zaituna tayi masa ta kawar da kanta dan tunda ta ga irin wulak'anci da ya ke yi wa mahaifiyarsa ta ji ta tsaneshi kwata-kwata, shi kuma Lado yana ganin Zaituna ya saki murmushi tare da k'arasowa gurin da take, wata 'yar k'aramar kujerar k'arfe ya ja ya zauna tare da kiran sunanta "Zaituna" Bata amsa masa ba sai ma cigaba da aikinta da tayi, shi kuma bai damu ba ya cigaba da yin magana "Shine jiya na aiko a kira ki, ki ka k'i zuwa ko?","A'a ni babu wanda ya zo ya kira ni" Tayi maganar ba tare da ta kalleshi ba "kina nufi Idi bai zo ya kira ki ba?","Idi ya zo amman kuma ni bai ce min kirana ake yi ba" Nan Lado ya shiga zabgawa Idi kira "Idi kai idi kana ina?" Da sauri Idi ya fito daga d'akinsu tare da zuwa ya tsugunna kusa da Lado "Ga ni Yaya" Lado ya d'aure fuska tare da cewa "Jiya da nace ka je ka kira min Zaituna ashe da ka je ba ka kirata ba, ka zo ka ce min ka kirata ta ce tana zuwa" Idi ya zaro ido ya ce "Wallahi Yaya na kirata ai gata nan ka tambayeta na san Aunty Zaituna ba ta k'arya za ta fad'a maka gaskiya" Zaituna ta ce "Eh ya kirana ni kawai bai yi niyyar zuwa ba ne" Lado ya kalleta sororo kamar wanda aka dasa shi dai a saninsa Zaituna ba ta da rashin kunya amman yau gashi ta kalli cikin kwayar idonsa tana gaya masa magana mara dad'i ji yayi kamarya d'auketa da mari amman kuma da ya tuna cewar yana sonta sosai kuma hakan zai iya jawowa a k'i bashi aurenta ya sa ya fasa, ya fara magana cikin tsawa. "Ke Zaituna yaushe ki ka koyi raina na gaba da ke, wato wuyanki ya yi kaurin da har zan aika ki zo ina son ganinki ki k'i zuwa amman"........ "Ka ga Lado dan Allah dan annabi ka bar ni na sha iska, meye ruwanka da ni ko akwai abin da na tsare maka ne da har za ka ke fad'a min maganar da ka ga dama, ni ba zan tab'a yiwa wanda bai san darajar mahaifiyarsa biyayya ba, saboda haka zaka iya b'ace min da gani" Zaituna ta yi maganar cikin tsiwa tare da hurga masa harara, Lado ya tsaya sororo yana kallonta cike da mamaki, tunda suke da ita ba ta tab'a kallon cikin idonsa ta gaya masa maganar mara dad'i ba sai yau, kuma ba ta tab'a kiran sunansa ba sai dai ta ce masa Yaya amman yau gashi tana kiransa da asalin sunansa, "Zaituna ni ki ke gayawa wad'annan maganganun, kuma ki ke kirana da Lado" Ya yi maganar tare da tsare ta da ido zuciyarsa tana bugawa da k'arfi, wani irin kallon ta yi masa tare da cewa "Yo to menene sunanka idan ba Lado ba, kuma kai wanene da ba zan gaya maka gaskiya ba, ka je kayi wa mahaifiyarka biyayya ka bata hak'uri tun kafin dare ya yi maka" Tana gama fad'ar haka ta shige d'akinta da sauri tare da rufe kofa, shi kuwa Lado jikinsa a sanyaye ya mik'e ya nufa d'akinshi, zuciyarsa cike da bak'in ciki yana shiga d'akin ya zauna tare da zabga tagumi yana tunanin maganganun da Zaituna ta fad'a masa, ya d'auki kusan mintina talatin yana tunanin daga k'arshe ya kwanta a kan gadonsa tare da lumshe idanuwansa. *'BANGAREN JABIR DA TEEMARH☹️* Yau kusan kwana bakwai Jabir bai fito ko da falo ba, kullum yana d'aki yana kok'arin shawo kan Teemarh amman abin ya gagareshi, Teemarh ba ta da aiki sai dai ta zauna tai-ta yin kuka, fuskarta gaba d'aya ta kumbura tayi jajahur idanuwanta kuwa da kyar take iya bud'e su, saboda irin kukan da ta ke yi yasa su ka yi ciki-ciki, "Haba Daring ya kamata ki tsaya ki saurareni, wallahi akwai dalilin da yasa na je club ranar plss My Teemarh ki saurareni ba na son kina yin wannan koke-koken" Jabir wanda ya ke kusa da Teemarh a kan gado ya yi maganar fuskarsa tana nuna alamun damuwa, "Jabir na san baka so na dan Allah ka kyaleni" Teemarh wacce take kwance a kan gadon tana faman rera kuka tayi maganar cikin muryar kuka, "Wai wa ya ce miki ba na sonki, wallahi Teemarh ina sonki sosai dan Allah ki daina kukan nan, ki fad'a min abin da ki ke son nayi miki da zai saka ki yarda ina sonki" Teemarh ta d'ago fuskarta tare da zuba masa idanuwanta "Ka tabbatar duk abin da na fad'a maka za kai min" Jabir ya gyad'a kai tare da cewa "Indai hakan zai saka ki farin ciki, zan yi miki ko ma menene". "Darling ina son ka daina zuwa club, duk abin da ka ke so ni zan yi maka shi koma menene,amman dan Allah ka daina zuwa club ba dan ni ba, dan Allah na rok'eka da girman Allah" Jabir ya yi shuru kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya ce "Na amince darling indai hakan zai sa ki yarda cewar ina sonki" Teemarh ta yi murmushi "Da gaske ka ke Darling" Jabir ya yi murmushi "Eh mana, da gaske na ke, babyn Jabir" Ajiyar zuciya Teemarh ta sauke tare da cewa "To darling na yarda kuma na san ba za ka k'arya min alk'awarina ba, yawwah Darling dan Allah ina son na je gidan Hajiya Mama yau na dad'e ban je ba" Jabir ya jawo Teemarh jikinsa yana shafata "To darling da yaushe za ki je","Ni ko yanzu ma" Jabir ya ce "Nop ba yanzu ba dai sai anjima" Teemarh ta ce "Allah ya kaimu" Jabir ya ce "Amin ya Allah" Nan ya shiga shafe jikin daga nan suka tsunduma duniyar soyayya. _Habibaties ku yi min addu'a ba ni da lafiya cikina ke ciwo😭👏🏽_ *'BANGAREN AMATULLAHI🤣💃🏽* Amatullahi ta je gurin club d'in su Jabir amman abin mamakin har ta gaji da tsayuwa amman ba ta ga jibtawar Jabir ba, anan take tambayar wani mai shago Jabir ya daina zuwa ne?, da yake kaf unguwar babu wanda bai san shi ba, saboda irin shaharar da ya yi wajen lalata yaran mutane, ya ba ta amsa da cewa yau kusan sati guda Jabir bai zo club d'in nan ba, kuma gaskiya na ji labarin cewar matarsa ce take son ta hana shi zuwa, Amatullahi tayi masa godiya ta nufi gidan Hajiya Mama zuciyarta cike da mamakin wace 'yar kasada ce ta auri Jabir, kuma da wad'anne irin kalmai ta ja ra'ayin d'an iskan nan ya daina zuwa club, k'wafa ta yi tare da cewa "Koma wacece ita ta ga za ta iya" A haka ta k'arasa gidan Hajiya Mama, Falon saukar bak'i ta shiga tare da zama ta kunna t.v tashar arewa 24 ta kai anan ta tarar ana yin wani film d'in hausa, film d'in ya yi matuk'ar jan ra'ayinta sosai, gaba d'aya ta maida hankalinta wajen kallon film d'in. "Besty! Besty!! Besty!!!" Ta ji muryar Khadijatullahi tana kiranta, mik'ewa ta yi da sauri ta fita daga falon "Na'am Bestyna" Amatullahi ta yi maganar tana k'arasawa kusa da ita "Ina ki ka je? Tun d'azu ina ta faman nemanki" Murmushi Amatullahi ta yi "Yau Babana ya dawo ne, shine na je gurinshi" Khadijatullahi ta kafeta da ido, tabbas ta san Amatullahi ba gaskiya ta ke fad'a mata ba, dan tun suna k'anana indai Amatullahi ta yi magana tana iya gane cewar k'arya take fad'a ko kuma gaskiya "Yau kuma k'arya za ki yi min bestyna, ban yi tunanin za ki iya k'in fad'a min halin da ki ke ciki ba, na san ba gaskiya ki ke fad'a ba Baba bai dawo ba, dan in ya dawo zaki ce min na zo muje mu gaishe dashi" Da sauri Amatullahi ta kalli Khadijatullahi daman ta san zata iya gane cewar k'arya ta ke yi mata "Besty dan Allah ki fahimceni" Khadijatullahi ta ce "Ba na son ki ce min komai domin ba na gana da mak'aryaciya" Khadijatullahi tana gama fad'ar haka ta shige babban falon ta zauna a kan kujera tana kallon Aliyu tana sakar masa murmushi "Yaya Aliyu na bar ka kana ta jira na ko, dan Allah ka yi hak'uri" Aliyu ya bud'e baki zai yi magana Amatullahi ta shigo falon tare da zuwa gurin da Khadijatullahi ta ke zaune ta tsugunna "Haba besty kin san ban tab'a yi miki k'arya ba, wallahi bestyna gurin"....... Khadijatullahi ta dakatar da ita da hannu fuskarta a murtuk'e "Dan Allah ki tafi kawai ba na son ganinki". Hawaye ne suka shiga zubowa Amatullahi, ta mik'e tana goge hawayen na ta da gefen hijabinta "Ke Amatullahi dawo ki zauna" Aliyu ya yi maganar lokacin da Amatullahi take shirin fita daga falon, juyowa ta yi ta koma ta zauna dan ita sam ba ta ma kula da Aliyu yana falon ba, "Meya had'aku?" Ya yi maganar yana kallon Khadijatullahi wacce ita ma shi take kallo "Hmmm!" Abin da Khadijatullahi ta ce kenan "Yaya Aliyu ni ban tab'a yi mata k'arya ba, wallahi da gaske na ke yi maka" Amatullahi ta yi maganar tana kuka "Ai yau kuma kin yi min, kuma ni ba na mu'amala da mak'aryaci" Khadijatullhi ta yi maganar tana hararar Amatullahi, Aliyi ya ce "To ya isa haka, Amatullahi me ki ka yi mata?" Amatullahi ta ce "Ni Yaya Aliyu gurin Jabir na je" Wata iriyar zabura Khadijatullahi ta yi "Me ki ka je yi gurin wannan shegen d'an iskan" Nan Amatullahi ta bata labarin duk abin da take shirin yi wa Jabir d'in domin d'aukar mata fansa ta dora da cewa "Kuma duk zuwan da na ke yi sau d'aya na samu na fara isar masa da sakona, yau kuma da na je shine me shagon ya ke ce min ya daina zuwa club d'in saboda matarsa" Khadijatullahi ta matso kusa da Amatullahi ta rumgumeta tana kuka "Besty meyasa baki fad'a min ba, ki ka yi min shuru kin san wannan d'an iskan, kuma kin san halinsa, bai kamata kina saka kanki a tsari saboda ni ba, dan Allah ki daina saboda idan wani abu ya sameki ba zan tab'a iya yafewa kaina ba" Amatullahi ta d'agota tana goge mata hawayen fuskarta "Ki daina kuka ya isa haka, ka da kanki ya yi ciwo" Murmushi Khadijatullahi ta yi "To na dena dan Allah ki yi hak'uri da"..... Rufe mata baki Amatullahi ta yi "Dan Allah ki manta da komai ai ya wuce, bari na baku wajen ko kuna hirarku na katse ku, Yaya Aliyu a sha soyayya lafiya" Ta yi maganar tana dariya tare da fita daga falon. _Masu son daren aurena daga farko zuwa inda aka tsaya ya yi min magana ta wannan number 08122188717_ "My Heartbeat wallahi kun burgeni sosai, tunda na ke ban tab'a ganin k'awaye irin ku ba, kuna son junanku kuna tsananin k'aunar junanku, Allah ubangiji ya bar ku tare" Aliyu ya yi maganar yana murmushi "Amin Yayana" Khadijatullahi ta yi maganar ita ma tana sakar masa murmushi, nan suka shiga yin hirarsu irin ta masoya sun kai kusan rabin awa suna hira daga nan su ka yi sallama, Aliyu ya tafi gidan abokinsa musaddik. ⏰5pm K'arfe biyar na yamma dai-dai Teemarh ta isa gidan Hajiya Mama "Assalamu alaikum" Ta yi sallama tare da shiga cikin gidan, su ka yi ido biyu da Shahida "Laaa Aunty Fatima ke ce" Murmushi Teemarh ta yi tare da k'arasawa gurin da Hajiya Mama ta ke zaune ta tsugunna har k'asa tana gaisheta "Ina wuni Hajiya","Lafiya lau ina d'an duniyar mijin na ki?" Teemarh ta sunkuyar da kai tare da cewa " Yana gida" Tashi ta yi ta koma kusa da Shahida tana cewa "Hmm! Ai babu abin da za ki ce min" Dariya Shahida ta yi ta ce "Ki yi hak'uri Aunty Fatima akasi aka samu, kuma kin san gidan Hajiya Mama idan ka zo,to fa sai ka yi da gaske zaka iya fita" Teemarh ta ce "Gaskiya kam ga Aliyu ma ya k'i dawowa" Teemarh ta kalli su Khadijatullahi ta ce " Sannunku 'yan uwa ya ku ke" Murmushi su ka yi "Lafiya alhamdullahi" Suka amsa a tare "Wai Aunty Fati ina Yaya Jabir" Teemarh ta ce "Yana gida wallahi", "Wannan ita ce matar Jabir" Amatullahi ta yi tambayar tare da kafe Teemarh da ido, ita ma Teemarh jiyowa ta yi tana kallon Amatullahi tana murmushi, Shahida ta ce "Eh mana ita ce, sunanta Aunty Fatima" Amatullahi ta ce "Ohhh lallai kam, kin cika 'yar kasada" Ta yi maganar ciki-ciki, Teemarh ta ce "Sistoo magana ki ke yi ne?" Amatullahi ta yi murmushin yak'e tare da cewa "A'a fa, lazimi na ke yi" Khadijatullahi dariya ce ta kwace mata dan ta ji abin da Amatullahi ta ce, kuma ga maganar da ta fad'awa Teemarh "Tabbas Lazimi kike bestyna" Amatullahi ta kalleta tana murmushi "Bestyna abin k'aunata,me ya baki dariya kuma?" Khadijatullahi ta ce "No! Bakomai, kawai dai lazimin ki ne ya ba ni dariya, ya kamata ki nutsu sosai" Hararar wasa Amatullahi ta hurga mata, tare da d'auko wata hirar ta daban dan ta san indai ta biyewa Khadijatullahi to Teeamarh zata iya fahimtar inda zancensu ya nufa. Har wajen k'arfe 10pm na dare Teemarh tana gidan Hajiya Mama, Hajiya Mama da ta ga ba ta da niyyar tafiya ta ce "Yau Fatima kwana za ki yi ne?" Teemarh wacce take kwance a kan doguwar kujera ta ce "A'a Hajiya yau zan tafi" Hajiya Mama ta ce "To ikon Allah yaushe za ki tafi kenan, kin san k'arfe nawa yanzu kuwa?" Dariya Teemarh ta yi ta ce "Hajiya Mama na sani mana k'arfe goma har da 'yan mintina, ai Yaya Jabir ne ya ce zai zo ya d'auke ni" Tana rufe bakinta sai ga Jabir ya yi sallama ya shigo falon "Assalamu alaikum" Karaf su ka yi ido biyu da Khadijatullahi, duk da irin yadda ta chanza masa, amman ba zan tab'a mantawa da wannan fuskar ba "Khadijatullahi" Ya kira sunanta a gigice gumi yana k'aryo masa, Yaron da ke kan cinyar Khadijatullahi ya k'urawa ido, shima Affan kallonsa yake yana dariyarsu irin ta yara, yana gwarancinsa don yanzu watan Affan biyar "Kenan wannan yaron nawa ne" Yayi maganar a zuciyarsa, Teemarh ta mik'e ta k'araso gurin da yake tsaya ta ce "Darling lafiya kuwa? Ka santa ne?" Bai kalli inda Teemarh take ba, dan har lokacin idanuwansa suna kan Khadijatullahi da Affan, Amatullahi ta ce "Fatima kina son jin irin rashin mutuncin da mijinki yayi wa 'yar uwata ne?" Da sauri Teemarh ta juya tana kallon Amatullahi ta ce "Meya faru ni na rasa gane kan wannan abin" Amatullahi tayi gajeren murmushi tare da cewa "To yanzu zan warware miki komai, wannan shaid'anin mijin na ki ya auri 'yar uwata, bayan ya gama biyan buk'atarsa da ita ya saketa a cikin daren nan, bai tausaya mata ba, kuma wannan yaron da yake kan cinyarta, d'an wannan shaid'anin mijin na ki ne" Teemarh ta zaro ido domin ta san Jabir ya tab'a yin aure, amman ba ta tab'a yin tunanin ta tambayesa ina matarsa ba, "kina nufin Dijah matar Jabir ce" Cikin muryar b'acin rai Khadijatullahi ta ce "Karki k'ara ce min matarsa domin ni, ba matarsa ba ce Allah ubangiji ya kiyayeni na auri wannan tak'adirin d'an iskan, wancan lokacin da na aureshi akan babu yadda na iya ne" Jabir dai bai iya yin koda motsi daga inda yake ba, barantana har ya iya magana, Hajiya Mama wacce take zaune ta zuba musu idanuwa tana kallonsu ta ce "Kai Jabir shigowa za ka yi ne, ko kuma tsayuwar za ka yi ta yi ne kamar wani gunki" Dakyar Jabir ya fara tafiya gaba d'aya jikinsa a sanyaye yake, Zama ya yi kan kujera nadamar abin da ya yi wa Khadijatullahi ta shiga zuciyarsa, wani irin zafi yake ji a cikin zuciyarsa wanda bai san dalilin jin sa ba, "Hajiya Mama Dan Allah"...... Hajiya Mama ta yi saurin dakatar dashi da cewa "Jabir yanzu dare ya yi ka d'auki matarka ku tafi gida, gobe idan Allah ya kaimu sai mu yi magana" Jabir bai musa mata ba ya amsa mata da "to" Sannan ya mik'e ya nufi hanyar fita daga d'akin, ya juyo ya kalli gurin da Khadijatullahi take, sannan ya fita daga falon, Teemarh ta d'auki Jakarta da mayafinta ta bi bayansa, ita ma jikinta a sanyaye ya ke. Jabir yana zuwa wajen motar ya bud'e ya shiga, Teemarh ta shiga motar tare da kallonsa zuciyarta a cunkushe "Darling" Ta kira sunanshi muryarta a sanyaye, juyowa ya yi yana kallonta ba tare da ya ce komai ba, sai hawaye da yake zubowa daga cikin idanuwansa zuwa kan kuncinsa, hannunta ta saka tana goge masa hawayen tana yi masa murmushin yak'e "Ka daina kuka ka ji darling insha Allahu komai zai yi dai-dai" Jabir ya sauke ajiyar zuciya "Darling na san nayi wa Khadijatullahi abubuwan da basu dace ba, ban kyauta mata ba sam, idan har ba ta yake min ba tabbas ba zan tab'a yafewa kai na ba" Teemarh ta ce "Karka ce haka darling insha Allahu Dija zata yafe maka ka ji, yanzu tana cikin b'acin rai shiyasa,amman ka barta zuwa d'an wani lokaci kafin nan ta sauko" Murmushin jin dad'i ya yi tare da rumgume Teemarh "Nagode darling nagode sosai, da fatan zaki taimaka min wajen ganin Khadijatullahi ta yafe min","Insha Allahu" Teemarh tayi maganar tana murmushi, haka Jabir ya ja motar duk da cewar ba ya jin dad'in zuciyarsa, amman haka ya daure domin baya son ganin Teemarh cikin damuwa. *'BANGAREN HAJIYA ASIYA* Hajiya Asiya ta sha matuk'ar wahala a hannun Alhaji Mukhtar tun da ya samu abin da yake so daga gareta, ya ke nuna mata tsantsar tsana kullum cikin dukanta yake, gashi matarsa ma haka zatai mata rashin mutunci kuma ta sakata wankin kayanta dana yaranta, duk rashin mutuncin Hajiya Asiya sai da bakinta ya mutu, nadamar abin da tayi wa iyayenta da mijinta ta shiga zuciyarta, tunani ta shiga yi yadda zata samu ta rabu da auren Alhaji Mukhtar ta koma gurin mijinta ta nemi gafarsa kuma ta je gurin iyayenta duk da cewa ta san ba lallai su yafe mata ba, domin tayi masu rashin mutunci kala-kala, hawaye ne ya shiga zubo mata "Allah na tuba, Allah ya ubangiji ka yafe min kasa su Innata su yafe min, nasan na zalince su kuma abin da nayi musu ne yake bibiyata, tabbas hausawa sunyi gaskiya da suka ce abin da ka shuka shi zaka girba, yau gashi ina girban abin da na shuka" Ta k'arasa maganar tana kuka mai tab'a zuciya, ta d'auki kusan mintina talatin tana kukan nadamar abin da tayi daga k'arshe ta tashi ta shiga toilet, wanka tayi sannan ta dora alwala ta dawo falon ta shimfid'a dadduma tayi sallah raka'a biyu, ta dad'e tana rok'on Allah ya yafe mata, ta mik'e ta koma kan gado ta zabga tagumi. "Ke Asiya! Asiya dan ubanki kina ina ne?" A firgice Hajiya Asiya ta mik'e jikinta na rawa ta nufi kofar zata bud'e kamar ance ta lek'a ta window anan ta ga Alhaji Mukhtar ta wata sandar shan jini, gabanta ne ya fad'i, ta ja da baya, idanuwanta ne suka sauka akan wata 'yar k'aramar kofa da zata iya sadata da gate d'in da zata fita daga gidan, da sauri ta nufi wata drower ta d'auko key d'in kofar ta k'arasa gurin kofar ta bud'e ta fara gudu, Allah ya taimaketa gate d'in gidan a bud'e yake, tana fita ta ga wani mai adaidaita zai huce, ta tsayar dashi ta shiga tare da cewa masa "Ka yi sauri ka bar nan dan Allah zai kasheni" Mai adaidaitan ya ja da gudu sunyi nisa sosai, ya juyo yake tambayarta "Hajiya ina muka nufa?" Anan tayi masa kwatancen inda zai kai ta, suna k'arasowa, ta fita tare da ce masa "Ina zuwa yanzu zan shiga gidan, mai gadi zai kawo maka kud'inka" Mai adaidaitan ya ce "To shikenan babu damuwa" Juyawar da za ta yi suka had'a ido da Alhaji Mansur yana tsaye a bakin motarsa, da sauri ta k'arasa gurinshi tana kuka "Dan Allah Abban Jabir"........ "Ya isa Asiya ki yi min shuru, ba na buk'atar sake ganinki a rayuwata, tunda ke butulu ce baki san darajar d'an adam ba" Durk'ushewa tayi akan guiyoyinta tana kuka "Duk abin da ka fad'a min na san na chanchanci fiye da haka ma, zaka iya kirana da abin da ya fi butulu ma, Amman dan girman Allah Abban Jabir koda ace zaka yanke alak'ar da take tsakaninmu, ina rok'onka ka yafe min, na san nayi maka butulci ban kyauta maka ba, ka yafe min dan Manzon Allah" Alhaji Mansur jikinsa ne ya yi sanyi sosai, dan shi a rayuwarsa baya so ya ga matarsa tana kuk saboda shi "To na ji, ta shi tsaye" Mik'ewa tayi tana jin jiriri yana kok'arin kayar da ita, muryar Alhaji Mansur ta ji yana tambayarta "Wanchan fa, meya tsaya yi" Ya yi maganar yana nuna man adaidaita "Shi ya kawoni, kud'insa zan biya sa" Ta basa amsa kanta a sunkuye. Zuwa ya yi gurin da mai adaidaitan yake tsaye ya d'auko naira dubu biyar ya mik'a masa, nan fa ya shiga godiya ya ja adaidaitarsa ya yi gaba, shi kuma Alhaji Mansur ya dawo gurin da Hajiya Asiya take tsaya ya ce "Yanzu ai kin ga abin da son zuciyarki ya janyo miki, ni dai yanzu na yafe miki Allah ubangiji ya yafe mana gaba d'ayanmu" Godiya Hajiya Asiya ta shiga yi masa tana kuka, ya dakatar da ita da cewa "Ya isa haka, ni yanzu ina da gurin zuwa zaki iya yin tafiyarki" Hajiya Asiya ta ce "To zan tafi amman dan Allah ina neman wata alfarma a gurinka, ina so ka zo muje tare na nemi yafiyar su Innata dan na san indai na je ni kad'ai ba za su saurareni ba" Alhaji Mansur bai mu sa mata ba ya ce ta shiga mota su je, ta shiga gurin mai zaman banza ta rufe, shi kuma Alhaji Mansur ya ja motar ya nufi gidan su Asiya. To fa k'ak'ak'ara k'ak'a shin iyayen Hajiya Asiya zasu ya fe mata kuwa, ku biyoni dan jin yadda labarin zai kasance💃🏽. Suna isa gidan Hajiya Asiya ta ga gaba d'aya ya chanza mata ya koma irin na manyan masu kud'i ta san ko ba'a fad'a ba, Alhaji Mansur ne ya gyara gidan ya zama abin ban sha'awa, ta bud'e murfin motar ta fita amman me sai ta kasa motsawa daga gurin da take, wasu zafafan hawaye suna zubowa daga cikin idanuwanta yanzu da wane idon zata kalli iyayenata wanda rabon da ta saka su a idonta tun ranar aurenta da ta fita ta koma gidan k'awarta Aisha, Alhaji Mansur wanda har ya yi nisa ya juyo yana kallon Asiya, tabbas yasan tafi nadama amman ya kamata ya koya mata hankali sosai "Me ki ka tsaya yi anan? Kin kawo ni ne dan ki tsaya kina kuka" Tafiya ta fara yi inda Alhaji Mansur yayi gaba tana bin sa a baya, wani babban falo suka shiga inda nan take tayi ido biyu da iyayen nata, kuka ta saka tare da k'arasawa gabansu ta zube, magana take son yi amman ta kasa saboda irin kukan da ya ci k'arfinta, su kuwa Malam Kalla ido kawai suka zuba mata, "Dan Allah Inna da baffa ku yafe min abin da nayi muku, na san ban kyauta muku ba idan har baku yafe min ba, to tabbas haka rayuwata zata cigaba da tafiya cikin bak'in ciki da k'unci, ba zan tab'a ganin dai-dai ba, dan Allah ku yafe min na tuba" Alhaji Mansur ya ce "Baffa ku yi hak'uri ku yafewa Asiya tabbas tayi nadamar abin da tayi a baya, dan Allah ku yafe mata" Inna ta sauke ajiyar zuciya tare da cewa "Bakomai Mansur na yafe mata" Malam Kalla ya ce "Tabbas Asiya kin ci darajar Mansur yau da ke kad'ai ki ka zo gidan nan sai na b'alb'allaki, amman bakomai na yafe miki Allah ubangiji ya shiryeki" Nan Alhaji Mansur yayi musu godiya sannan ya mik'e tare da yi musu sallama, ya fita daga falon. Inna ta cewa Hajiya Asiya "Tashi na nuna miki d'akinki","To" Tayi maganar tare da mik'ewa ta bi bayan Innar, suna shiga d'akin Hajiya Asiya ta ce "Innata ina 'yan uwana","Gaba d'ayansu sun yi aure, amman Hajara tun tafiyarki da 'yan kwanaki aka nemeta aka rasa har yau ba'a ganta ba" Zaro ido Hajiya Asiya tayi ta ce "Inna na shiga uku ina Hajara ta je?" Inna ta ce "Wallahi bamu sani ba, ni na rasa ma ya zan yi"Ta k'arasa maganar tare da fashewa da kuka "Kiyi hak'uri Innata ai na dawo zan je zan nemo duk inda 'yar uwata ta je, zan dawo da ita gida" Hajiya Asiya tayi maganar tare da rumgume Innar tana rarrashinta, har tayi shuru haka dai Innar tayi ta ba wa Asiya labarin irin neman da su ka yi wajen neman Hajara amman ba su sameta ba, kuma basu ji labarin komai a kanta ba "Ina tunanin wani ne ya bata labarinta, shiyasa ta gudu" Hajiya Asiya ta juyo cike da rashin fahimtar inda maganar Innar ta nufa "Inna ban gane ba, labarinta kuma, wane irin labari ne?" Inna ta gyara zama tare da cewa "Hajara ba 'yarmu ba ce tsintota Baffanku ya yi, mun b'oye muku ne saboda ba ma son ku nuna mata wani abu da zai sa ta fahimci ba iyayenku d'aya ba, musamman ke dan nasan indai kika san hakan za ki yi mata gori ne" Hawaye ne ya shiga zubowa Asiya "Innata insha Allah zan nemota, duk inda taje ai bai kamata tayi mana haka ba, ko da ace wani ne ya fad'a mata asalinta ya kamata,ta fad'a muku domin mu ta ya ta nemo iyayenta, bai kamata ta gudu ba" Haka dai Hajiya Asiya tayi ta kwantarwa da mahaifiyar hankali abin gwanin ban sha'awa, ni kam 'yar mutan zazzau nace Hajiya Asiya ko ke fa🤣. *BAYAN WATA 'DAYA DA SATI BIYU🌼* Jabir hankalinsa ya gama tashi ko bacci ba ya iya yi saboda tunanin Khadijatullahi, zuwansa gidan Hajiya Mama yafi sau ashirin dan ya samu ya ga Khadijatullahi ya nemi yafiyarta amman kullum yaje baya samun damar ganinta, zaune yake a cikin office d'insa kasancewa Abba ya bashi jagorancin ma'aikatarsa wacce ake yin shainkafa, ya zabga tagumi wayarsa ce ta shiga ruri ya kalli wayar wacce take ajiye a kan taburin office d'in *Bro Aliyu* shine ya bayyana a kan screen d'in wayar, Jabir cike da jin haushin Aliyu gami da wani a zababban kishi da ya taso masa, ya katse kiran Aliyun tare da sakashi a blacklist dan Shahida ta bashi labarin Aliyu ne yake son Khadijatullahi dan har an kusa saka ranar aurensu, tarin takaddu ne a gabansa wad'anda ake jira ya saka hannu, amman ya kasa duba koda guda d'aya baren tana ya saka hannun. Mik'ewa ya yi da sauri ya d'auki wayarsa tare da mukullin motarsa, ya fita daga office d'in bayan ya kulleshi motarsa ya shiga yana tuk'i amman gaba d'aya hankalinsa baya kan titin ya lula tunanin Khadijatullahi da kuma yaronsa Affan, Jabir bai yi aune ba sai ji yayi ya daki wata k'atuwar mota, wanda haka ya yi sanadiyar motarsa ta fad'a cikin wani babban rami ta kama da wuta gaba d'aya motar ta cinye, Innalillahi wa inna'ilaihiraju'un mutanan gurin suke ta faman fad'a koda suka lek'a ramin basu ga alamar akwai mutum ba, dan kuwa komai a cikin motar ya k'one kurmus, da yake wasu a gurin sun san motar Jabir nan aka samu wanda yake da number wayar Alhaji Mansur nan suke fad'a masa Jabir ya yi hatsari kuma gaba d'aya motar ta k'one kuma yana cikin motar, Alhaji Mansur ana fad'a masa haka ya zube a k'asa tare da rushewa da kuka, Aunty Murja ta k'araso tana tambayarsa menene, ya kwashe duk abin aka fad'a masa ya fad'a mata yana kuka "Shikenan yanzu yarona ya mutu, ina tsananin son Jabir kamar raina amman yanzu ya mutu ya bar ni" Aunty Murja gaba d'aya hankalinta ya tashi, haka dai tai-ta rarrashin Alhaji Mansur har ya yi shuru, nan ya d'auki wayarsa ya kira Aliyu, Aliyu wanda yake zaune a falon Hajiya Mama suna hira ya ji wayarsa ta d'auki ruri ya yi tunanin Jabir ne, amman da ya kalli screen d'in wayar ya ga number Abba, ya d'aga jin muryar Abba a chan k'asa k'asa yasa Aliyu ya saka wayar a speaker don ya ji abin da Abban zai ce masa "Aliyu kazo yanzu, Allah ya yi wa d'an uwanka rasuwa a hanyarsa ta dawowa gida ya yi hatsari motar gaba d'aya ta k'one kuma yana cikin motar" Mik'ewa Aliyu ya yi jikinsa na rawa hawaye suka shiga zubo masa, nan da nan gumi ya dinga keto masa ya jik'ashi shark'af "A'a Abba d'an uwana bai mutu ba, yana raye ba zan yarda ba wallahi ba zan yarda ba" Aliyu ya yi maganar tare da yin jifa da wayar, Shahida kuwa hannu ta d'ora akai tare da kurma wani uban ihu "Mun shiga uku yayanmu ya mutu, innalillahi wa'inna ilaihi raju'un" Aliyu kuwa fita ya yi da sauri ya shiga motarsa ya nufi gurin da Jabir d'in ya yi hatsari. Ya na zuwa gurin nan ya nufi gurin rumin gadan-gadan, da yake akwai hanyar da ake bi a shiga cikin ramin Aliyu yana shiga ramin ya nufi gurin motar Jabir da ta k'one, yana kuka jikinsa ya yi sanyi domin ganin irin yadda motar ta k'one tabbas ya san ya rasa d'an uwansa dan gaba d'aya motar ta zama toka, nishin da ya ji a bayansa ne yasa ya juya da sauri, Aliyu ya mik'e ganin Jabir a kwance cikin jini rumgumeshi ya yi yana jin wani irin farin ciki yana shiga zuciyarsa, d'aukarsa ya yi cak suka fita daga cikin ramin a mota ya sakashi ya nufi asibitin Abbansu, suna isa asibitin Aliyu ya fito daga cikin motar, wasu nurses guda goma suka nufo shi suna tura gadon da ake d'aukar mara lafiya idan an kawoshi, Aliyu ya fito da Jabir ya d'ora shi a kan gadon, nurses d'in suka tura gadon Aliyu yana bin bayansu har aka shiga da Jabir emergency room, Sai a lokacin Aliyu ya dawo cikin hayyacinsa ya zaro 'yar k'aramar wayarsa ya kira Abba ya fad'a masa Jabir bai mutu ba yanzu ma suna asibiti dashi, sannan ya kira Shahida ita ma ya fad'a mata, ko minti goma ba'ayi ba sai ga su Hajiya Mama da Abba sun shigo cikin asibitin suka yo kan Aliyu suna tambayarsa "Ina Jabir d'in" Nan yake nuna musu d'akin da aka shiga da Jabir "Alhamdulillahi Allah mun gode maka, ya ubangiji ka tashi kafad'un wannan bawan na ka" Hajiya Mama ta yi maganar tana kuka, dukansu suka amsa da "Amin" Khadijatullahi ta ce "Yaya Aliyu ka tabbatar Jabir bai mutu ba" Ta yi maganar cikin yanayin damuwa "Eh Dija Mijinki bai mutu ba" Khadijatullahi ta kalli Aliyu cike da mamaki amman ba ta iya cewa komai ba, Teemarh ce ta rumgume Khadijatullahi tana kuka "Dan Allah Khadija ki taimakawa mijina ki yafe masa, ina da tabbacin sanadiyar tunaninki ne yasa ya yi hatsarin nan" Khadijatullahi gaba d'aya ta rud'e ta ma kasa magana, sai bin mutune da ta ke yi da ido, haka dai suka nemi guri kowa ya zauna, kowannansu ka kalli fuskarsa zaka ga tarin damuwa da tashin hankali mara misaltuwa. *'BANGAREN LADO DA INNA LARAI💃🏽💞* Durk'ushe yake a gaba mahaifiyar ta sa yana kuka yana neman gafararta "Dan Allah Innata ki yi hak'uri da duk abubuwan da nayi miki ki yafe min na san tabbas ban kyauta miki ba, na zalince ki ni ba d'a na gari ba ne" Inna Larai tayi murmushi ta ce "Bakomai Lado na yafe maka, abin da na shuka ne nake girbarsa" Lado ya ce "Nagode Innata Allah ya saka miki da alkhairi, ki tashi muje d'akina ni zan koma d'akinsu Lawal" Inna Larai ta mik'e Lado tana gaba Lado yana bin ta a baya, ta shiga d'akin Lado, kayansa ya shiga tattarawa yana kaiwa d'akinsu Lawal har ya gama ya zauna suka d'an yi hira da Innar ta sa, daga k'arshe ya yi mata sallama ya fita. Yana fita su ka yi kicibus da Zaituna, kallonsa tayi cike da girmamawa tana sakar masa murmushi "Yaya dan Allah kayi hak'uri ka yafe min, ban yi maka rashin kunya dan"............. "Yi shuru Zaituna meyasa ki ke ba ni hak'uri, ai gaskiya kika fad'a min kuma nagode da kika dawo da ni hanya madaidaiciya, kuma insha Allahu zan gyara kuskuren da nayi a baya" Murmushi Zaituna tayi ta ce "Indai kayi hakan ni kuma na amince zan aureka, domin kuwa kasan Ina tsananin son Inna" Zaituna tayi maganar tana rufe fuskarta, Lado ya ji matuk'ar dad'in kalaman Zaituna wani farin ciki ya shiga tsarga masa, ita kuma Zaituna ganin kallon da Ladon ya ke yi mata yasa ta shige d'akin da Inna Larai take da gudu tana dariya, shima ya nufi d'akin su Lawal yana jin dad'i a cikin zuciyarsa. *BAYAN KWANA BIYU✌🏽* Aka saka ranar auren Zaituna da Lado wata d'aya farin ciki gurin wad'annan masoyan ba'a magana, nan suka shiga nunawa junansu wata iriyar sabuwar k'auna kamar su cinye junansu, kullum suna tare Lado yana zuba mara ruwan kalaman soyayya, ni kuwa er mutan zazzau nace Lado ya za ka yi mana haka Amatullahi fa😅Karka manta ita ce tsohuwar zuma🤣. *BAYAN AWANNI GOMA SHA BIYAR🤧* Da taimakon Allah Likitoci su ka yi nasarar, ceto rayuwar Jabir bayan gwagwarmayar da suka sha, kafin su yi nasarar ceto rayuwarsa dan gaba d'aya likitocin jikinsu ya yi sanyi ganin irin yadda jini yake zuba kamar famfo daga jikin Jabir, dakyar suka samu suka yi masa aiki har jinin ya tsaya, Doctor Isham ne ya fito daga d'akin yana gyara rigar jikinsa da sauri Alhaji Mansur ya taresa yana tambayarsa "Ya jikin Jabir" Murmushi Doctor Isham yayi ya ce "Alhamdullahi da taimakon ubangiji mun yi nasarar ceto rayuwar Jabir, yanzu dai mun yi masa allurai nan da awa d'aya zai iya farfad'owa" Kowannansu ya shiga furta "Alhamdulillahi" Doctor Isham ya nufi office d'insa, Nihal ce ta shigo asibitin da gudu tana kuka dan Shahida ta kirata ta fad'a mata Jabir ya yi hatsari "Abbanmu ina Yaya Jabir d'in yake" Abba ya ce "Ki kwantar da hankalinki yana nan lafiya" Shiga d'akin su ka yi gaba d'ayansu, zama su ka yi a kan kujerun dake d'akin suna kallon yadda Jabir d'in ya ji raunika a jikinsa, masu kuka nayi masu tagumi da jimami nayi. Bayan awa d'aya Jabir ya fara motsi da 'yan yatsun hannunsa tare da kiran sunan Khadijatullahi, ras gaban Khadijatullahi ya yi mummunan bugu, duk da irin yadda ta tsani Jabir yanzu kam wani irin tausayinsa take ji saboda ganin irin yadda gaba d'aya kamanninsa suka chanza "Na'am" Ta amsa tana zubar da wasu zafafan hawaye, hannun Teemarh ta kama suka k'arasa gurin gadon zama su ka yi a kan gadon, Jabir a hankali ya bud'e idanuwansa ya dorasu a kan Teemarh "Zahra" Ya kira sunanta a hankali, duk da irin yadda Teemarh take cikin tashin hankali sai da tayi mamakin a ina Jabir yasan sunan da danginta ne kawai suke fad'a mata "Na'am" Cikin wata iriyar wahalalliyar murya ya ce "Ina Khadijatullahi?" Khadijatullahi ta ce "Gani nan" Ya juya a hankali dan Khadijatullahi ta zauna ta wajen kansa ita kuma Teemarh ta wajen k'afafuwansa, hannuwanta ya kama yana kok'arin fashewa da kuka "Dan Allah ki yafe min, nasan ban kyauta miki ba kuma"......... "Na yafe maka tuntuni Allah ya yafe mana ga baki d'aya" Khadijatullahi ta k'atseshi daga k'arasa maganar da zai yi "Nagode sosai, ina yarona?" Khadijatullahi ta karb'i Affan daga hannun Amatullahi ta ajiyeshi kusa da Jabir tana cewa "Gashi nan" Hannun Affan ya rik'e yana murmushi, gaba d'aya su Abba sun ji matuk'ar dad'in yadda Khadijatullahi tayi wa Jabir kuma sun san nan da 'yan lokaci kad'an burinsu zai cika, wasu kawar da k'iyayyar da Khadijatullahi ta ke yi wa Jabir. Bayan sati uku aka sallami Jabir suka daga gidan Hajiya Mama dan ya ji sauk'i sosai, yana iya tashi da kansa kuma raunikan da ya ji sun fara warkewa, kullum yana tare da Teemarh da Khadijatullahi a gefensa dan bai yarda d'aya daga cikinsu tayi nesa dashi ba, Affan kuwa kullum yana mak'ale dashi, a yau aka saka ranar auren Khadijatullahi da Jabir da kuma Amatullahi da Aliyu wanda babu wanda ya san da haka gaba d'ayansu, Shahida ce ta fad'o falon da gudu tana tsalle, kallonta su ka yi gaba d'ayansu Aliyu wanda yake zaune yana chatting da abokinsa ya ce "Lafiya kuwa kodai duk a cikin gwaurancin ne" Dariya Jabir ya yi ya ce "Wallahi kuwa bro wannan yarinyar ai sai ana yi mata uzuri" Amatullahi da Khadijatullahi suka fashe da dariya "Kaiii sister ce fa, ita ma ta kusan shiga daga ciki Ammar zai yi wuff da ita" Khadijatullahi tayi maganar tana kallon Shahida wacce ta had'e ranta jin ance Ammar "Allah Aunty kina yi min wulak'anci sosai ni fa ba na son wannan mutumin" Teemarh ta ce "Kin ga kyalesu me ki ka zo fad'a mana na san wannan bakin na ki akwai news da yawa" Shahida ta ce "Yawwah Aunty Fatima shiyasa nake sonki da yawa, A yau ne ranar laraba da misalin k'arfe hud'u da rabi na rana aka saka ranar auren Amatullahi da Yaya Aliyu sannan kuma aka saka ranar auren Khadijatullahi da Yaya Jabir inda za'ayi bikin nan da sati d'aya" Amatullahi a firgice ta ce "Ke! Sister dan Allah ba na son irin wannan wasa ki daina" Shahida ta bud'e baki zatai magana suka ji muryar Nihal tana cewa "Sannan kuma aka saka ranar Aisha Mansur jik'amshi wacce aka fi sani da Shahida da kuma angonta Ammar Muhammad wanda za'ayi bikin rana d'aya da su Yaya Aliyu" Duk da irin yadda Khadijatullahi da Amatullahi suka shiga cikin firgici amman da suka ji abin da Nihal ta ce suka fashe da dariya "Wayyo cicina" Khadijatullahi tayi maganar tana kallon Shahida wacce ta shiga zubar da hawaye, Teemarh ma dariyar ta ke yi "Kai wannan sanarwar tayi min dad'i sosai" Ta yi maganar tana kallon Shahida. "Nifa ba na son shi, wallahi ba zan au"........"Karki rantse Sister dukkanmu nan mun san bakya son shi, amman ya kamata ki yi hak'uri ki sani fa ai duk wanda yace yana sonka yafi wanda zai ce maka baya sonka Ammar yana sonki sosai to menene aibunsa da ke ba za ki so shi ba, me ya yi miki da kika d'auki tsanar duniya kika dora masa, ya kamata ki yi yak'i da shaid'anin da yake cikin zuciyarki yana kissa ki yi tsanar wanda bashi da wani aibu a rayuwarsa" Khadijatullahi tayi maganar tana kallon Shahida, Nihal ta ce "Dan Allah ki barta Aunty ai sai tai-tayi, tunda ita ma ta koyi wulak'anta mutane" Aliyi ya ce "Zo nan kinji k'anwata" Shahida ta k'arasa gurin da Aliyu yake ta zauna tana kuka "Yi shuru kin ji, karki yi kuka kan yi ya yi miki ciwo" Yayi maganar yana goge mata hawayen kan fuskarta "Yaya Aliyu ta ya zan iya zama dashi bayan ba na son shi" Aliyu ya ce "Shin Ammar akwai abin da ya tab'a yi miki ne? Ko kuma kun tab'a samum sab'ani dashi?" Ta girgiza kai alamar A'a "To meyasa bakya son shi" Shahida ta ce "Kawai Yaya Aliyu nima ban sani ba" Jabir ya ce "Kawai wulak'anci ne wallahi" Aliyu ya ce "Ina son ki yi min alk'awari guda d'aya" Shahida ta ce "Menene shi?","Ina son ki so Ammar kamar yadda yake sonki, idan kuma ki ka k'i to ba zan k'ara yi miki magana ba Yaya Jabir ma haka" Jabir ya ce "Ai ni tun yanzu babu ni babu ita, tunda wulak'anci take ji dashi" Shahida ta ce "Ku yi hak'uri zan aureshi" Aliyu ya ce "Yawwah ko ke fa" Daga nan suka d'an tab'a hirarsu abin sha'awa. Shirye-shirye bikin ake yi dan sauran kwana d'aya a d'aura aure, bikin yazo dai-dai dana Hafsa dan haka aka ce za'a had'a party aka kama babban guri dan komai yazo musu da sauk'i, Teemarh ita ce uwar biki dan ita ce take shirya yadda take son bikin ya kasance dan har gurin da aka kama ita ta ce aje nan ayi partyn sai yafi, yau da misalin k'arfe hud'u za'ayi partyn Teemaeh ta shirya cikin wani material tayi kyau sosai yadda kasan ita ce amaryar, ta zauna a falon Hajiya Mama ta zabga tagumi komai take tunani oho, Jabir ne ya shigo falon ya tarar da ita zama ya yi kusa da ita yana kiran sunanta amman sam bata ma san yana yi ba, dan tayi nisa sosai wajen tunaninta, hannunta ya kama ya sauke mata tagumin da tayi da sauri ta kalleshi tana murmushi "Darling ashe kai ne, ka ba ni tsoro sosai" Jabir ya ce "Babyna na san dole zaki ji babu dad'i saboda zan yi aure, amman ki yi hak'uri kema ina sonki sosai wallahi" Teemarh tayi murmushi tare da cewa "Haka nace maka saboda za ka yi aure ne, na tsorata karka damu ka ji kawai ka cigaba da shirye-shiryen bikinka, Allah ya bamu zaman lafiya" Tayi maganar tare da mik'ewa ta fita daga falon, Jabir ya bita da kallon yana jin babu dad'i a zuciyarsa. Wajen k'arfe hud'u aka kawo motoci sama da guda hamsin aka tafi gurin party, amaren gaba d'aya kowannansu kalar kayansa d'aya da angonta, sun yi kyau sosai Safna ita ma tazo bikin duk da cewa ba'a son ranta ta zo ba, Haka aka tashi daga party bayan anci an sha, suka koma gida kowannansu ya tafi d'akinsa dan ya yi bacci, Teemarh kuwa tun da ta shiga d'akin da aka bata take kuka wanda ni kai na ban san na menene ba, haka ta sha kukanta ta shiga toilet tayi alwala tayi sallah sannan ta koma kan gadonta ta kwanta a hankali bacci mai nauyi yayi awan gaba da ita. Washe gari da misalin k'arfe sha d'aya na safe aka d'aura auren Khadijatullahi da Jabir, Amatullahi da Aliyu da Hafsa da Safwan da kuma Shahida da Ammar, Baban Amatullahi ya samu halattar d'aurin auren 'yar ta sa, inda bayan sun dawo daga gurin d'aurin auren ya saka aka kirata yayi mata nasiha mai ratsa zuciya, daga nan yayi sallama da ita ta koma cikin gidan, shagalin bikin ake yi ba ji ba gani har lokacin kai amarya yayi Jabir ya shigo gidan inda yayi ido biyu da Maminsa duk da cewar yana tsananin fushi da ita sai da ya sakin mata murmushi, ya k'arasa gurin da take ya gaisheta, ta amsa masa tana mai maidar masa da martanin murmushin na sa "Ina Teemarh tun jiya ban ganta ba?" Jabir ya yi maganar yana waige-waige ko zai ga giftawa Teemarh "Yanzu nan ta shiga d'aki za ta yi wanka" Hajiya Mama ta bashi amsarsa, Jabir dai bai ce komai ba dan ya fahimci Teemarh tana cikin damuwa kuma ta k'i bari su had'u tun jiya yake son suyi magana da ita fita Jabir ya yi jikinsa a sanyaye. *7pm* Motocin kai amarya suka cika layin, haka aka cika motocin gaba d'aya aka nufi gidan amaren, gidan Khadijatullahi suka fara zuwa inda Jabir yayi katafaren gini aka kai ta har cikin bedroom d'inta suka zaunar da ita a kan gado tare da yi mata nasiha, sannan aka fito aka nufi gidan Amatullahi komai iri d'aya ne da na gidan Khadijatullahi, ita ma sukayi mata nasiha sannan suka huce gidan Shahida shima babban gida ne sosai nasihar ita ma sukayi mata sannan suka koma gida, Jabir yana shiga gidansa yayi sallama kai tsaye 'bangaren Teemarh ya shiga amman abin mamakin a kulle ya tarar dashi, "To ina Teemarh ta ke? Kodai tana gidan Hajiya Mama?" Duk tambayoyin nan a fili yake yin sa, haka ya nufi 'bangaren Khadijatullahi jikinsa a sanyaye k'arasawa kan gadon da take ya yi inda ya yaye mayafin da ta lillib'e fuskarta dashi "Sweetheart" Ya kira sunanta yana murmushi, Khadijatullahi bata iya amsawa ba dan wata iriyar kunyarsa take ji haka dai suka raya wannan daren wajen nunawa junansu soyayya. Hajiya Asiya ce zaune a d'akinta tana tunanin mijinta Innarta ce ta shigo bakinta d'auke da sallama "Assalamu alaikum" Hajiya Asiya ta amsa mata "Wa'alaikumussalam Inna barkanki da zuwa" Inna ta ce "Yawwah nagode sosai" Hira suka d'anyi sannan Inna ta fita ta koma d'akinta, Hajiya Asiya ta d'auki wayarta ta shiga kiran layin Labahani ringing d'aya biyu ya d'auka "Assalamu alaikum" Daga chan 'bangaren aka fad'a "Wa'alaikumussalam Labahani ya dai ka gano inda 'yar uwata take?" Labahani ya ce "Eh hajiya na dai gano inda yaranta suke amman ita ta dad'e da mutuwa, kuma na gano cewar 'yar uwarki 'yar asalin wani k'auye ne kantum sanadiyar gobarar da garin yayi ne yasa suka tattaro suka gudo a hanyarsu ta guduwa daga garin aka kashe mata iyayenta gaba d'ayansu" hawaye ne suka shiga zubowa Hajiya Asiya ta ce "To ina zan sami yaran na ta?","Murja da Khadijatullahi gaba d'aya sunyi aure, ita Murja ta auri Alhaji Mansur jikamshi ita kuma Khadijatullahi ta auri d'ansa" Da sauri Hajiya Asiya ta mik'e daga zaunan da take jikinta na rawa tare da sakin wayar dai-dai lokacin Inna ta k'ara dawowa d'akin "Lafiya Asiya","Inna ashe Murja da Khadijatullahi yaran Hajara ne" Nan ta kwashe duk abin da Labahani ya ce mata ta fad'a mata Inna ta ji matuk'ar dad'i, Hajiya Asiya ta d'auki mayafinta ta fita Inna ta bita da kallo, Hajiya Asiya tana fita ta tari mai adaidaita ta shiga tayi masa kwatancen gidan Alhaji Mansur, suna isa ta fito ta biyasa kud'insa tare da nufar kofar gidan tana bubbuga gate d'in mai gadi ya bud'e mata ta shiga kai tsaye falon ta nufa ta shiga bakinta d'auke da sallama Abba da Aunty Murja suna falon suna kallo, Alhaji Mansur ya kalleta cike da mamakin meya kawota gidan nan kuma "Ku yi hak'uri na shigo muku gida babu izini, Murja gurinki na zo ya ya sunan mamanki?" Aunty Murja ta mik'e tsaye tare da cewa "Mamana kuma sunanta Hajara" Hajiya Asiya ta ce "Kenan da gaske ke 'yar Hajara ce k'anwata" Zaro ido Aunty Murja tayi shima Alhaji Mansur ya mik'e tsaye yana mamakin wannan lamarin "Hajara kuma?" Ya tambayeta cike da tsananin mamaki "Eh Hajara k'anwata da aka nemeta aka rasa" Aunty Murja ta ce "Mami kenan ke Yayar Mamana ce, kune 'yan uwanmu" Hajiya Asiya ta fad'a mata komai game da Mamarta da har zuwa guduwar da Hajaran tayi aka nemeta aka rasa, Kuka Aunty Murja ta fara yi inda Mami ta juya ta fita daga falon, Alhaji Mansur ya biyo bayanta anan ya tarar har ta fita daga gidan, motarsa ya shiga ya ja mai gadi ya bud'e masa gate ya fita adaidaitar da ya ga Hajiya Asiya ta shiga ya bi bayanta a dai-dai kofar gidansu ta sauka ta biya mai adaidaitar kud'insa ya ja ya bar unguwar tana shirin shiga gidan ta ji muryar Alhaji Mansur yana kiranta "Hasiya" Juyawa tayi da sauri tana kallonsa k'arasowa ya yi gurin da take suka kallon juna "Ki shiga ki je ki yi sallama da Inna ki zo mu tafi gida" Alhaji Mansur ya yi maganar yana kallonta "A'a ka bari kawai","ban gane na bari ba" Yayi maganar cike da b'acin rai "Ka yi hak'uri ban yi hakan dan na b'ata maka rai ba" Alhaji Mansur ya ce "Ki shiga ki fito ina jiranki" Ta amsa masa da "To" Anan ta shiga take fad'awa Inna yadda su ka yi da Alhaji Mansur d'in Innar tayi mata nasiha sannan ta fito murfin motar ya bud'e mata ta shiga ya bud'e ya ja motar ya nufi gidansa yana jin wani irin farin ciki a cikin zuciyarsa. *'BANGAREN SAFNA😟🥰* Duk da irin tsananin bak'in ciki da zafin kishin da take ji a kan Hafsa amman tunda ta shigo ta ga irin yadda take kula da Khalid da kuma yadda take girmamata yasa ta zubar da makaman kishinta, ta rumgumi Hafsa a matsayin 'yar uwa, komai na su tare su ke yi sun had'a kansu sosai suna kula da mijinsu yadda ya kamata, Safwan shi kansa hankalinsa ya kwanta sosai har wata 'yar k'iba yayi. Teemarh ce zaune a kan gadonta ta zabga tagumi Jabir ya shigo d'akin ya k'ura mata ido, ya zauna a bakin gadon tare da hurgo mata tambaya "Yaushe kika dawo? Meyasa baki dawo jiya ba?" Teemarh ta ce "Jiyan na dawo" Ta bashi amsa tana kallonsa "Meyake damunki? Bana son ki yi min k'arya" Teemarh idanuwanta suka ciko da kwalla "Bakomai darling" Jabir cikin fushi ya ce "Ba za ki fad'a min ba" Teemarh ta ce "Ni ba zan haihu ba kenan" Tayi maganar hawaye na zuba daga idanuwanta, shuru Jabir ya yi yana kallonta wato kenan Teemarh saboda ba ta haihu ta shiga damuwa "Waya ce miki ba za ki haihu ba, zaki haihu mana ai kin san komai lokaci ne kema lokacinki yana nan zuwa","to Allah yasa" Jabir ya yi murmushi yana cewa "Ko kefa darling" Anan suka shiga yin hirarsu ta masoya har sai da Jabir ya tabbatar Teemarh ta fita daga cikin damuwar da take ciki. *'BAYAN WATA HUD'U🤙🏾* Gaba d'aya amaren suna zaune cikin farin ciki da kwanciyar hankali, Aunty Murja ta haifi 'yarta mace inda aka sha suna kamar ba gobe, dare ya yi kowa ya koma gidansa, a cikin watan kuma Amatullahi da Khadijatullahi suka shiga yin laulayi koda aka tabbatar musu da cewa suna da ciki Jabir ya yi murna amman da ya tuna irin damuwar da Teemarh take ciki akan rashin haihuwar da ba tayi ba, duk ya ji jikinsa ya yi sanyi ya san idan Teemarh ta ji Khadijatullahi tana da ciki to zata shiga damuwa fiye da wacce ta shiga a baya, amman ya san koda bai fad'a mata ba dole ta sani "Ya rahim" Ya fad'a tare da dafe kansa, haka dai ya shiga gidan nan Khadijatullahi ta huce 'bangarenta shi kuma ya huce gurin Teemarh yana shiga nan ya tarar da ita tana bacci ya k'arasa kusa da ita tare da shafa kanta yana murmushi, daga k'arshe ya fita ya koma gurin Khadijatullahi. Bayan wata biyu yau ya kama za'ayi bikin 'yar Kawu Bala haka kowannansu suka ta ho gidan Hajiya Mama,Nihal, Amatullahi, Shahida,Khadijatullahi da kuma Hafsa da yake ita ma ta zo gida shine ta biyo gidan Hajiya Mama da yake ta san su Amatullahi zasu zo gidan gaba d'ayansu suna da ciki har ya fito ma, Teemarh tana zaune wacce ita kad'ai ce ba ta da cikin hankalinta ya tashi ta ware kanta a gefe tana tunanin ita ma ya za'ayi ta samu cikin? Amman ta rasa mafita Jabir da Aliyu ne suka shigo Idanuwan Jabir ya sauka akan Teemarh wacce ta ware kanta "Zahra" Ya kira sunanta d'agowa tayi da sauri tana kallonsa bata iya amsawa ba saboda kukan da ya taho mata "Ki zo falon bak'i ina son ganinki" Yana gama fad'ar haka ya fita daga falon, Teemarh ta mik'e ta bi bayansa tana shiga falon bak'in ta zauna a kan kujera "Darling nayi mamaki sosai, wannan abin da ki ke yi fa kamar kina jaa da hukuncin ubangiji bai kamata kina damun kanki ba, haihuwa Allah ne mai badawa kuma ina da tabbacin kema zaki samu ciki ki daina damun kanki dan manzon Allah darling" Teemarh hawaye suka fara bin kuncinta "Shikenan badamuwa" Abin da ta ce kenan tana goge hawayen fuskarta haka dai yai-yi ta rarrashinta har tayi fara walwala daga nan suka fito tare dashi a gurin Hajiya Mama ta zauna a tsakar gida Jabir ya bita da kallo ya girgiza kai kawai ya shiga falon, haka aka yi bikin aka gama kowannansu ya koma gidansa. Khadijatullahi yau ne cikinta ya kai watan haihuwarta tun da safe Jabir ya kai ta Asibitin, inda anan suka tarar da Aliyu ya kawo Amatullahi har an shiga da ita labour room, ita ma Khadijatullahi ana shiga da Amatullahi ta fara labour nan ita ma aka an ta ya ta labour room, ni kam nace Amatullahi Allah ya sauke ku lafiya🥲. Wajen awanni biyu Jabir da Aliyu suna jiran su ga nurse ta fita ta shaida musu matarsu ta haihu amman shuru, chan sai ga nurses guda biyu d'aya ta fito daga cikin d'akin da aka shiga da Amatullahi d'aya kuma daga cikin d'akin da aka shiga da Khadijatullahi kowannansu fuskarta d'auke da murmushi "Congrats matarka ta haihu ta samu d'a namiji" Nurse d'in farko take fad'awa Aliyu d'ayar kuma ta ce Khadijatullahi ta haifi 'ya mace haka suka shiga d'akin suna farin ciki aka sallamesu suka dawo gida, nan 'yan barka suka cika gidan har aka rasa in ma za'aje gidan Amatullahi ko Khadijatullahi, ranar suna kuwa gidan Hajiya Mama suka ta ho gaba d'ayansu aka yi sunan a chan yarinyar Khadijatullahi ta ci sunan Mami (Asiya) Inda suke ce mata Mummy, d'an Amatullahi kuwa aka saka masa sunan Alhaji Mansur suke ce masa Pappy, inda a ranar sunan da daddare Nihal da Shahida suka haihu farin ciki gurin ahalin nan ba'a magana ji suke kamar su zuba ruwa a k'asa su sha, haka su ma ranar suna aka sha suna a gidan Hajiya Mama, Teemarh tana kwance kusa da Hajiya Mama duk ta rasa meke yi mata dad'i yau ta tashi da tsanancin ciwon kai ga kuma amai da ta ke yi komai ta ci sai ta amayoshi, gaba d'aya ta fita a hayyacinta Hajiya Mama ta ce mata ta tashi su je asibiti ta ce A'a ba sai sun je ba ta ji sauk'i, haka ta barta babu yadda ta iya da ita, Jabir ne ya yi sallama ya shigo falon Aliyu yana biye dashi a baya "Yawwah d'an nan zo ga matarka nan sai fama take da amai da ciwon kai amman ta k'i yarda akai ta asibiti" Jabir ya k'arasa gurin da Teemarh ta e kwance ya ce "Zahra tashi muje asibiti kin ta b'a ganin mutun bashi da lafiya ya zauna a gida","Ni fa na warke fa, kan ya daina min ciwo" Aliyu cie da tsokana ya ce "A'a fa Aunty Fatima kodai d'a muka samu ne" Teemarh ta kalleshi kawai bata ce masa komai ba, dan kuwa ita ta ma fitar da rai da samun haihuwa "Kin ga ni ki tashi ko kin warke ko baki warke ba mu je asibiti, idan kuma kika dage a kan ba za ki je ba hmmm!" Ya yi maganar yana d'aure fuska, haka Teemarh ta mik'e dak'yar ta yafa mayafi ta fita daga falon kamar wacce aka bugawa iska😅. Jabir ya bi bayanta suka shiga mota suna zuwa asibitin gwajin farko aka tabbatar musi da cewa Teemarh ciki gareta murna gurin Teemarh ba'a magana, ita ma ta samu ciki shikenan ita ma tana zata samu baby kamar dai su Shahida, haka suka dawo gida Khadijatullahi take tambayar Jabir meke damun Teemarh anan yake fad'a mata ciki ne da ita shine yake wujijjigata. *BAYAN WATA BIYAR😤* Cikin Teemarh ya girma sosai haihuwa ko yau ko gobe haka dai kullum tana jikin Jabir ta narke tana ta zuba masa shagwab'a iri-iri shi kuma yana biye mata anan yake tuna mata yadda ta shiga damuwa kafin ta samu ciki ta dinga yin dariya ta ce "Wallahi darling ba ka san yadda nake son na ga nima ina da baby ba ne shiyasa ka ke tsokanata" Jabir ya ce "Na sani mana tunda kin ta yar min da hankali lokacin, dan da ana siyan haihuwa da zan je na siyo miki ita na kawo miki dan hankalinki ya kwanta","Allah sarki darling ai yanzu komai ya huce" Cikinta ta ji yana murd'a mata mararta kuma ta d'aure da sauri ta rik'e Jabir tana cewa "Darling cikina" Da sauri ya mik'e ya samu ya taimaka mata suka shiga fita daga d'akin a mota ya sakata ya ja suka nufi asibiti, suna zuwa aka shiga da Teemarh labour room inda ko mintina hamsin ba ta yi ba ta haihu 'Yarta mace haka aka sallamesu suka dawo gida zuciyoyinsu cike da farin ciki, ranar suna anan gidan akayi suna anyi bidiri babu laifi an ci an sha, aka sakawa yarinya sunan Halima. Lado da Zaituna su ma sunyi aure inda yanzu suna da d'a mai suna Ahmad, Hafsa ma ta haihu ita ma d'a namiji sunansa Sabir, inda Inna Larai ta auri wani mai wanki da guga a layinsu, Malam Shu'aibu ma ya yi aure a chan gurin aikin na su ya had'u da wata mai kawo musu abinci inda ya yaba da hankalinta yasa ya aureta, Haka rayuwar bayin Allah suka cigaba da gudana cikin farin ciki da kwanciyar hankali, kowannan burinsa ya ga ya kyautatawa d'an uwansa, Inda 'yan uwan Mahaifinsu Khadijatullahi wad'anda suka gudu suka dawo garesu tare da neman yafiyarsu, suka koma gidan su Khadijatullahi da suka tashi daman babu abin da gidan ya yi. Zaune suke a falo suna hira Jabir ya kalli matan na sa da yaransa ya ce "A duk lokacin da na kalleku ina jin wani farin ciki a cikin zuciyata kuma ina godewa Allah, Alhamdulillahi ala kulli halin" Teemarh ta ce "Gaskiya kam darling dole ka godewa Allah" Khadijatullahi ta ce "Allah mun gode maka Alhamdulillahi😌" Nima anan zance Alhamdullahi rabbil'alamin, anan na kawo k'arshen wannan littafin mai suna daren aurena Allah ubangiji ya sa mu amfana da abin da na fad'akar, kuskuren da nayi Allah ubangiji ya yafe min🥲😣👏🏽 Nasan a cikin ku zaku ce, to ya akayi Jabir ya auri Khadijatullah bayan saki uku yayi Mata? Amman karku manta fa a addinance idan mutum ya saki matarsa saki uku a lokaci d'aya to wannan sakin guda d'aya ne. *'Yar mutan zazzau ce💃🏽💃🏽* Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels