Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels ο»Ώ[7/28, 8:20 AM] Nana BMB: πŸ’πŸ’–πŸ’πŸ’– RABON KWADO.... BOOK 2 NA NANA BMB BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM. page 1-2 Inty hawayen dadi kawae Take nafarin ciki sosae mujaheed ya kwakumeta kamar wadda za ah kwace masa ita duk nisan tafiyan dasuke bayajin ta sosae ya kagu sukae titi kamar zeyi kuka yace pls sameer muyi sauri numfashinta daukewa zeyi,dakyar inty take tafiya saboda azabar gajiyar datayi ahaka suka kae bakin motan nasu yashimfideta abaya sannan yazauna yadora kanta akan cinyarsa su inty suna gaba sameer yasoma jan motan a sukwane, mujaheed yazuba mata idanu yana shafa mata kanta cikin yanayin tausayi kamar zesa kuka haka itama kallonshi takeyi ahankali tana lumshe idanunta wadanda sukayi jajir, sunkuyawa yayi cikin sanyin murya yana cewa sorry my dear meenal babu abinda zesameki insha allah yanzu zamu karasa hospital kinji sosae yarike mata hannu harsuka karasa asibitin jiki nabari kuwa yadaukota suka shiga ciki batare da bata lokaciba aka amsheta aka soma bata temakon gaggawa, Mujaheed hankalinshi bakaramin tashi yayiba donseda suka shiga cikin haske sosae suka kara ganin yadda jikinta yayi sameer yadafashi yace kayi hakuri mujaheed insha allah babu abunda yafaru da meenal babu abinda zesameta ka kwantar da hankalinka kajee,muryarsa tana rawa yace sameer allah ne kadae yasan mesukae mata kadubi yadda takomafa, shiru yayi don inya cigaba da magana kuka ma zeyi,inty ma kukan take ganin yadda meenal takoma ko ince MIMI,sosae tadafe kanta saboda yadda yake sara mata ga nukurkusan dajikinta yakeyi tana gani juwa na ibarta dukansu bawanda yakula da halinda take ciki ko mujaheed dayake gefenta be kulaba, shikuwa sameer yana waya da mom ne yanasanar musu anganta,munaheed jiyay kawae inty tafado kanshi bata numfashi hankalimshi yakara tashi yasoma jijjigata yana kiran sunanta amma shiru,cikin daga murya kuwa yake kwalawa nurses kira akazo itama aka soma bata temako sunyi jigum jigum sameer yasan wahalane kawae da inty tasha dayawa natafiya, bayan wasu mintuna su mom suka iso hospital din dasu sakina tashin hankali goma da ishirin sunji itama inty tana gadon asibiti, sunyi zugum suduka kowa da abinda yake sakawa, abinda yadaure musu kaene shine jawabin da nurse tazo tanamusu cewar mara lafiyarsu tana cikin mawucin hali meya sameta hakane tayi kwanaki babu abinci olcer yana shirin yimata illah, cikin firgici kowa yake kallonta galala mom tace nurse duka ko yini bamuyiba damuka rasata kuma gashi munganta, rasa abincemusu tayima don mamaki mujaheed yace nurse meke faruwa da itane gyaran murya tayi sannan tace tawahala dayawa sannan raunikan jikantama banayau bane olcer dinda yake shirin mata illah akallah za ah kara mata jini leda uku ruwa leda biyar saboda sosae sukayi karanci ajikinta,haba mom tarike tace gaskiya wannan abun bagaskiya bane yarinyarda seda sukaci abincifa suka fita daga gida dazunnan fa muka rasata taya hakan zekasance, nurse ganin basu bawa maganarta muhimmaci bane yasata kin karasa musu bayanin daya kawota ta tafi tabarsu ko maganar inty batayiba, cikeda tausayi sameer yace gaskiya lamarin daban mamaki mom sema kinga yadda meenal takomane dole kiyadda da abinda nurse tafada tamkar wadda tayi sati awahale gaba daya tacanza haka,dakyar nurse din tabarsu suka shiga room da su meenal suke wayyo sosae kaga MIMI zata baka tausayi jikinta mujaheed kawae yakebi da kallo sosae yaga tama kara girma meenal din tashi kowa da mamakin dayakeyi suka fito su sakina dole aka bari agurinsu domin dukansu ance musu sewashe garima zasu farfado dakyar mujaheed ya iya tausan zuciyansa suka tafi zuciyansa fal da mamaki yana kuma gode allah dabasu ketawa meenal haddin taba.... TAKU A KULLUM NANA BMB. [7/28, 8:20 AM] Nana BMB: πŸ’πŸ’–πŸ’πŸ’– RABON KWADO.... BOOK 2 NA NANA BMB page 3-4 Washe gari inty ce tafara farkawa taji dadin jikinta sosae tarage jin ciwon jikin saedae jikin ba kwari kam, bare kuma mimi da nurse sunce farkawanta se bayan azhar, koda su mujaheed suka iso asibitin dasu mom jikin kowa seya karayin sanyi anyi jigum harsu inty dinma duka suna gunta,mom tace yanzu mujaheed yazamuyi da iyayenku shin ka kirasu kuwa kada kace basusan halinda ake cikiba haryanzu,murmushin karfin hali yay yace mom ay banasonma su sani saboda kinsan hankalinsu zasu tasa ga gidansu bauchi tasosu suma zamuyi sunajin hali da take ciki tunda allah ya takaeta abin base an gaya musuba ana gama biki takara murmurewa semu tafi gida, sameer yace to kace kuma mummy zatazo yinin biki yakenan inbata gantaba, girgiza masa kae yayi yace ay bazan bari tazoba dama zamuyi magana da ita, cikin damuwa mom tace oh yarinya allah yabaki lpy wannan yarinya yini daya tasa kamanninki sun canza kae allah ka kara shiga tsakanin nagari da mugu, itakadae tsautsayin yake kanta ita kadae suka dauka kuma cikin sauri inty tace wlh mom nima abin yana damuna meyasa se ita zasu dauka, katseta sameer yay dacewa tunda dae allah yadawo mana da ita alhmdlh sefatan tasami lpy kuma,cikin yanayjn tausayi mom tace ni wlh daza ah daga bikin nan se 'ya'yana sun sami lpy,da mamaki mujaheed yace no mom gaskiya baza ayi musu hakaba sunacan sunata shirin biki dangin amarya gashi muma mun hada taro a ah gaskiya aykoda ba ah ga meenal ba baha ah fasa wannan bikiba da yaddar allah gara mutafi mom mufara shirye shirye n biki tunda farkawanta bayanzuba ga mutane munfara ay baze yiwu mubarsu hakaba,cikin yanayi mara dadi inty tace pls ya mujaheed kabari muga yanayin jikin meenal tukunna kana ganin duk yadda tasauya,girgiza mata kae yayi yace idan mukayi haka bedaceba tunda bata farkaba ay pls mom gara mutafi kawae maraeraece mata yayi kamar zeyi kuka, sanan jikinta yay sanyi mom tace tom shikenan tana farkawa kasanarmin kajiko yanzu ga zara nan tazauna agurinta toh, murmushi yayi yace insha allah tana farkawa za ah sanar miki, suduka suka tafi kuwa sukabar mata zara tana kwance batasan meke faruwaba, Da la asar kuwa zara ta idar da sallah tana addu ah taji motsinta tayi saurin juyawa sosae taga tana kankame hannaye da alamu mafarki take, saurin tasowa tayi tarike mata hannu tana kiran sunanta ahankali harta bude ido sukae 2 eyes kuwa allah mungode maka sannu meenal kinji kin tashi dama nurse tace kina farkawa nakirata,jajayen idanun mimi kawae tazuba mata domin bata taba ganintaba, harta bar dakin babu jumawa kuwa segata da nurse din sunshigo tambayoyin take mata dakyar take iya buda baki tanabada amsa, seda tagama abinda zatayi mata sannan tacewa zara abata tea tasha kafin tafara cin komae,tana fita zara mujaheed tafara kira tasanar masa sanan su mom,mimi tunani kawae take tana kukan zuci oh ya allah ka kubutar musu da 'yar su ya allah kafiddamu cikin wani hali meyake shirin faruwa dani ni mimi yanzu sabuwar rayuwa zan fara kuma gaskiya bazan iyaba yazanyi da iyayena yanzu idan suka kashe musu itafa dole nayi hakuri nazauna amatsayin ita tunda ta dalilina ta bata baiwar allah nasata amasifa, mafarkinta danayi yakara sawa jikina yay sanyi, shin wacece wannan damuke kama haka,sosae tashiga tunanin mujaheed jiya da kalamansa wanda take ganin kamar amafarki da daukan dayayi mata, seda taji zara ta girgizata sannan tadago tana kallonta ashe hawayene yaketa shatata a fuskanta cikin kaduwa zara tace wlh meenal seyanzu dana kare miki kallo hankalina yakara tashi mesukayi mikine wadan can azzaluman harkaya naga kin canza, yamutse fuska tayi tace babu abinda sukayimin wahalan dana shane dagudu a cikin ciyayi duka sune suka jimin ciwo,kallonta dae zara kawae take saboda setakejin muryan kamar bata meenal dinbama sauke ajiyan heart tayi tace allah yabaki lpy, basu wani juma azuneba sega su mom din sun karaso cikin farin ciki kuwa ganin mimi dasukayi azaune bare kuma mujaheed kallon kowa take cikin rashin sani, kusada ita mujaheed yakarasa murya asanyaye yace meenal sannu koh, koda tadago idanunta sarkewa sukayi danashi tabbas taganesa jiya shine take tunani bugu zuciyanta take sosae haka shima tashi takasance sabida irin kallonda mimi ta kafeshi dashi,karfin hali yayi yace yakikejin jikin naki yanzu to,dasauki kawae tace ta sunkuyar dakanta, pls meenal kiyi hkr da abinda yafaru kada kice zaki tafi gida kiyi hkr kisamu sauki tukunna semu tafi kinji,kallon su mom take azuciyanta tana tunanin tosuwaye wadan nan toh? daga masa kae kawae tayi alamun toh, suduka suke mata sannu tana amsawa kamar bataso,zara ce tahada mata tea zata shane tace mata setayi brush tukunna koda tamike tsaye taji kwarin jikinta mimi sosae dakafarta suka shiga toilet din tamatsa mata maclean din a sabon brush tamika mata tayi,sannan tace wanka girgiza mata kae tayi tace a ah kibari nurse tace sekinci abinci zatazo tayi miki saboda raunikan jikinki haka suka fito duk batajin dadin jikinta,tea din tasha sosae sannan mujaheed yasoma bata abinci suduka kuwa da mamaki suke kallon irin cin datakeyi tas seda tacinye abincin harda kamo masa hannuwa alamun yay sauri.... TAKU A KULLUM NANA BMB. 08147110349 [7/28, 8:20 AM] Nana BMB: πŸ’πŸ’–πŸ’πŸ’– RABON KWADO.... BOOK 2 NA NANA BMB page 5-6 Ruwa yabata ta kwankwala abinta iyason ranta sannan tafara sauke ajiyan heart kasa magana mujaheed yay saboda mamaki kallonta kawae yake sameer yace meenal ko akaro miki abincin,girgiza masa kae tayi alamun a ah,wata nutsuwace take ratsata harwani lumshe idanunta take saboda taji daedae acikinta, zuwa inty tayi gefenta tarike mata hannu tana hawaye tace pls meenal duk nice silar saki awannan hali kiyi hkr kiyafemin kinji nakasa samun nutsuwa inna tuna duka nice nasaki a wannan yanayin, kallon inty mimi take sosae taji tabata tausayi tana kuma kara tsinkewa da lamarin nan naganeta dasuka gazayi cikin sanyin muryarta tace kada kidamu don allah niban rikeki azuciyanaba komae kikaga yasamu bawa daga ubangine so pls kada kidamu kinji,ba nujaheed ba hatta duka 'yan dakin seda suka sau baki suna kallon yadda take magana, cikin yauki dawani dalo kaman batason magana maganar babu hayaniya, dukda hakan sunji dadin maganar tana dagowa suke hada ido da mujaheed tasunkuyar dakae se inty takalla tacewa pls inason nayi wanka nayi sallah, mikewa zara tayi tace tom bari nakira nurse din tace dama idan kinci abincin nakirata, sudukansu mikewa sukae domin tafiya subasu guri mom tace meenal allah yakara sauki kinji bari muje yanzu mujaheed zedawo miki da kayanki jinjina mata kae tayi suka fita, Ba bata lokaci nurse din tazo tahada ruwan wankan suka shiga rabin wankan da towel akeyinsa saboda 'yan kukkujewan jikinta aka wanke daudan data nake mata agashi yay fes sunjima sosae abayin sannan nurse din tafito abinta bajumawa itama tafito daure da towel tana takawa ahankali tazauna gefen bed din magun guna nurse din takawo mata tasha dana shafawa tafita tabasu guri, zara itace tashafa mata gananin duka agurin ciwokan nata sannan tashiga wankan itama,tana zaune ta lula duniyar tunanin meenal ya allah ka kubutar musu da yarinyarsu kamar yadda natsira nima taya zangaya musu gaskiya hankalinsu tashi zeyi natabbatar dakyar yanzuma intana raye, bazan taba iya yimusu hakaba dole nahakura da rayuwata nazame musu tasu tunda nice silar batan yarinyarsu sam bataji shigowan mujaheed bah shikuwa harya karaso yazauna kusada ita yana kallonta kamar zeyi kuka yana mamakin jikinta yadda yakara girma haka ga raunikan dayaketa gani ajikinta, Seji tayi kawae yakarkato da ita tasauke idanunta akansa saboda mamaki tamantama taga ita se towel kamar zeyi kuka yace sorry my dear haka suka wahalanmin dake wlh allah ya isa tsakanin mu dasu, sunkuyar dakanta tayi tasoma hawayen itama domin tuno mata da abinda yafaru yay,jin yayi shirune kamar bayagun yasata dagowa, sosae zuciyanta take bugu dasauri ganin ba ita yake kalloba yakurawa kirjinta idanu seyanzu ta tuna dan towel din dake jikinta wani irin yawo tahadiye raurau idanunta yakawo ruwa sam bazata iya tashiba ahaka yaganta,kamar zata tsala ihu dayakae hannunsa gurin saurin rintse idanunta tayi,shikuwa yatsa daya yasa yadan shafa inda takurge a dan sam breast dinta da yatsa dayan yadan yi kasa da towel din gurin donganin ciwon dakyau, takuma karce balaifi agurin dayatsan nashidae yake dan shafa gurun slowly murya asarke kamar zeyi kuka yace my dear taya kikaji ciwo ana gurin, kodae wadan can azzaluman sunmiki wani abune tell me pls, idonta gam arufe yake tama kasa masa magana sehawaye dake bin fuskanta, koda yadago yaga halinda take ciki yay saurin dauke hannunshi yaja mata towel din, sannan yace ina saurarenki, haryanzu bata bude idoba bakinma dakyar ta iya budewa tace basuyimn komaeba gudune danayi ina faduwa anan nakarce agurin,sosae yakejin zafi azuciyansa ga tausanda take bashi, mikewa kawae yay yace tom shikenan ga kayanan wanda zakuyi amfani dasu kafin asallameki a hospital din, ina zaran take? yatambayeta, tana wanka shine abinda tace masa ba bata lokaci k yace tom shikenan kushirya juwa anjima zamu dawo insha allah,bude kofan yay yafita abinsa tabisa da idanu kawae, tanajin wani abu yanamata yawo azuci sam batason taga yamatsa akusa da ita amma takasa nuna masa hakan, Meenal tana kwance awani room seyanzu tafarka don tun amota suka shaka mata wani abu dayasata sumewa don kartaga inda sukakaeta ma,juye juye take tana bin tadakin da ido cike da tsoro mikewa tayi ahanzarcenta data hangi kofa sedae tana budewa kuwa taga ashe toilet ne sosae tashiga daki to a ina take itakuwa inane nan babu kofa dakin takebi dakallo ko tsinke babu sae ita kadae duk wani kayan alatu nadaki babushi ko kadan, azuci tace toko mutuwa nayine, komae daya faru da ita yashiga dawo mata takuwa saki kuka meban tausayi ta zuve agurin tana cewa wayyo allah ka kawomin nauki nashiga ukuna ni meenal wlh bani bace mimi kuyarda dani meyasa kuka kasa ganeni ya muhammad nashigesu ya mujaheed kana ina ka kawomin dauki auntie kina ina wayyo nana zasu kasheni haka taita kiraye kirayen neman dauki,sosae taci kukanta takoshi harta gode allah kanta yasoma sarawa idanunta sunyi nauyi haka ta rarrafa tashiga toilet din takwankwali ruwa tadauro alwala tafito tana tunanin yanzun ranace ko dare oho allah masani dakin dako agogo babu haka tayi dakakenta tayo sallolinta da dan dankwalinta data rufa akan harta idar takwanta tarufa dankwalin afuskarta tae lamo yunwa nakwakwular ta haka baccin wahala yadauketa, cikin mafarkanta kuwa taji anma kafanta wani taku tasaki wata gigitattar kara don atunaninta kafan yacire afirgice tamike zaune daya daga cikin samudawan mutanen ne yake kallonta da jajayen idanunsa bedauke kafansa akanta yadae sassauta takun daya matane wayace yamiko mata tasau baki tana kallonsa yakuwa kare danne mata kafan tasoma kuka harda ihunta hannunta narawa ta anshi wayan takara akunne kuka kawae take, cikin wayar taji wani mutumi yana cewa mimi mimi dagaji cikin tashin hankali yake kiran sunanta tana jinshi sedae takasa magana saboda azaban datakeji akafarta yaki dagata tana juyakan da azaba tace don allah kazo katemakeni zekasheni cikin muryar tausayi yace kiyi hkr insha allah kinkusa kubuta ahannunsu mahaifiyarki jikinta yay tsanani takwanta a asibiti sabida rashinki jikinta yay tsanan..... bekarasa maganaba mutumin yawarce wayar, cikin gardiyar muryarsa yake cewa matsalar kace wannan tunda kaji muryanta sekayi abinda yakamata kuskure daya zakayi na aikoma da gawarta..... TAKU A KULLUM NANA BMB. 08147110349 [7/28, 8:20 AM] Nana BMB: πŸ’πŸ’–πŸ’πŸ’– RABON KWADO.... BOOK 2 NA NANA BMB page 7-8 Yana gama fadin haka yakashe wayansa yadaga mata kafa takuwa sa hannu biyu tarike kafan tana matse inda yataketa, da razanannar voice dinsa yasunkuyo yafara cewa saura kadan ubanki yayi abinda mukeso daganan zan turaki kiyama natura masa da gawarki kada sam kisa aranki zaki zaki fita darae a dakin nan sam bazaki kubuta ahannunaba bantaba sace mutumin daya bani wahalaba kece wadda kikafara samun daman guduwa keme wayau hukuncin abinda kikayi kuwa dama mutuwa kuma daga yanzu bake babu cin wani abu harzuwa lokacinda zan harbeki, Tuni meenal tamanta ma dawani ciwon kafa jin kalamansa gaba daya tafice ahankalinta cimimiyo masa riga tayi tana cewa nashiga ukuna don girman allah kayi min rae kayarda dani wlh bani bace wadda kuke nema karka kasheni ni sunana meenal ba mimi ba,sosae yakara kufula ganin irin raenin hankalinda zatayi masa garikon datayi masa yadda tadimaucema seta bashi dry koyaushe tasoma tsoron mutuwa haka,cireta kawae yayi awuyansa hannu biyu yasa yadamki wuyanta cikin karaji dazare idanu yace idan kika sake cemin bake bace mimi sena markadaki digi digi zanyi dake yarinya babu abinda nafi tsana sama darainin hankali to amma kigwada kigani yarinya idan zaki kuma kwana aduniya kinji menace ay,saurin daga masa kae tayi tana numfarfashin suma,sakinta yay tazuve agurin tasoma tari kaman zata mutu ido yay tulu tulu,abinda yadaure mata kae shine ganin bango datayi yabude wannan mutumin yafita yakuma dawowa yakoma ganin hakanne yakara sawa jikinta yin sanyi datsinkewa da wannan al amarin duk addu ar datazo bakinta yitakeyi tama kasa kukan sabida tashin hankali tana cewa meyake shirin faruwa danine ya allah, BAYAN KWANA 2 Takama ranar daurin auren sameer kenan mom tazama busy sosae saudaya take samu tazo hospital shima seda daddare kullum dabakin dake zuwa haka suma su sameer din sae sun dage suke zuwa asibitin sau biyu,sunata saukan bakinsu suma jikin mimi yayi sauki sosae se 'yan raunikanta dabasu gama warkewaba wannan dalilinne yasa mujaheed sakewa sosae ana shagalin biki banda zara da mimi suna asibiti abinsu zara hartama saba darashin maganar mimi yanzu don semagana takamata dole takeyinta,suna zaune sunacin abinci ko ince zara kadae tunda ita mimi juya spoon din hannunta kawae takeyi bataci,kallonta tayi tace wae meenal meyasa yanzu bakyason magana sedae kiyi shiru kowani abun yana damunkine gaba daya kin canza,mimi tae murmushi tace zara bakomae maganarne banajin yinta kawae,jinjina kae tayi tace tom shikenan kici abincin koh kidena juya spoon din din haka,ajeshima tayi tamike takoma kan bed tana cewa no nama koshifa,damamaki zara tace mekikaci dazakicemin kinkoshi kinga kisauko kici abinci sarae kinajin abinda nurses suka ce akanki koh kidena zama da yunwa yanzu cikinki zefara zafi kada kizauna jiran ya mujaheed domin yau busy dinsu yafi nakullum balallae suzo da ranaba sezuwa dare nasan zezo seya baki nadaren kici abinda kikeso dae kenan koh, donhaka kisauko yanzu kona kira miki mom nasanar mata, Turo baki kawae mimi tayi jin zara ta ramfota ga haushinda yacikata sam bataga mujaheed ba yau dukse takejin haushi,kamar tayi kuka tace nifa nakoshi kawae nidae ki kiraminshi awaya,sakin baki zara tayi tana kallonta sannan tace wlh bazan kirashi yanzuba suna tsaka da tarbar mutane sedae nakira miki mom barima kigani wayanta tadauka tayi kiran ganin dagaske take yasata saukowa tasoma tsakuran abincin tana hararan zara takasan ido, ita drym tabata ana daga wayan tayi sallama takuwa marae raece fuska tace pls zara bagashi inaciba kada kigayamata,murmushi tayi mata tacigaba da maganarta tace sis yataron biki andaura aure yanzu koh,inty tashaida mata andaura komae lpy, to masha allah yasanya alkhairi yabasu zaman lpy ya albarkaci rayuwar aurensu,tace ameen Zara ina mutuniyata i hope dae tanajin sauki sosae zara tasaki murmushi mesauti takalli mimi tanata juya spoon din hannunta alan dole ita abinci takeci,sannan tace inty mutuniyarki lafiya tananan tanata zuban rigima harda harara naki kira mata mutumin,kinsan yau basu zoba,dariya inty tayi sosae tace kema laifinkine waya gayamiki ana shiga tsakaninsu zaki iya ganinshi yanzun nan kuma kiji kunya,haba zara tarike tace wlh sister naga alama domin mitanen nakifa ana zazou segodiyan allah,murmushi tayi tace wlh ni wlh burgeni sukeyi sosae meenal da ya mujaheed suka dace dajuna inason meenal dayawa jinake dama inbiyoku hospital dinma,murmushi maryam tayi tace a ah kitaho kuma kiyi yaya dabakin namu bari dae nabaki ita kuyi magana,mika mata wayan tayi ta ansa tana tura baki suka gaisa yacca take mata maganarma suduka setabasu dariya,inty tace meenal kada kidamu kinji yanzu zannemo miki ya mujaheed dinki yazo gareki kokyadena fushin nan ay kuwa mimi tasaki murmushi tace to nagode tamikawa zara wayan sukae sallama suna dry. Suna zaune tayi jugum shi kawae takeson gani duk haushi yacikata saboda yaki zuwa itakuwa zara charting take abinta suna haka,yaturo kofan yashigo da sallamarsa tayi saurin daga kanta kuwa suna hada ido tasauke ajiyan zuciya because yayi kyau matuka yasha kananun kaya abinshi bakake tuni yacire manyan kayan na dauren aure saboda zafi hannunshi dauke da juice dayan hannun kuma wayanshice yarike murmushi kawae yake zuba mata harya karaso yazauna gefen bed dinnata, sam beji sallamar da zara take amsa masaba ma,ko ina kamshinsa yagauraye room din sosae farin ciki yallubeta naganinshi datayi, amma seta turo baki itafa anbata mata rae se atime din yajuya suka gaisa da zara tacigaba da danna wayanta haka shima ya aje juice din yana danna tashi wayan, habawa takaeci kuwa yacikata tasa musu kuka, Hanzarta ajiye wayar yayi yakamo hannunta yana cewa sorry my dear meyay zafine haka nazo ko kulani ma kinkiyi,kara tunzura baki tayi tace to bakae bane kaki zuwa inda nake kuma kazo shine kashareni,hadiye dariyarsa yayi is ok sorry kinji kinsan yadda aiki yamana yawa yau yanzuma nikadae ne bazan iya jurewaba na aje komae nataho sameer yanacan yacedae namiki sannu, ina fata dae kinci avinci baki zauna dayunwaba? Shiru tayi masa, zara tace inafa kaema kasan bazata ciba tunda baka zoba tundazu nake fama da ita takici wae saina kiraka, saboda nakine tundazu aketa antayamin hararan kasan ido,wani farin cikine yaziyarci zuciyansa yasaki lallausan smile yace aida kinkirani zara don meenal tafi min komae agurina ay, murmushin jin dadi kuwa mimi tayi har beauty point dinta suka lotsa wanda sam bekae na meenal ba ita intana magana har bayyana suke,amma sam bawanda ya ankara acikinsu gwalo tajuya taewa maryam alamun an gwaleta, bani abincin zara yanzu zataci kuwa takoshi mikewa tayi tadauko abincin tabashi tafita abinta domin answer waya,bata abincin yake cikin nutsuwa tana karba harta kusan cinye abinci tashagala da kallonsa hankalinshi yanakan abincin koda yadago zemata magana yaga yadda takafeshi da ido shima kanshi yana mamakin yadda meenal kemasa irin wannan kallon haka murmushi yaymata ya hura mata iska a fuskanta yace yadae,murmushin kawae tayi tasunkuyar dakanta,meenal yanzu kinacin abinci sosae nagode allah sosae su mummy nasan zasuji dadin hakan seda takoshi kadan yarage abincin,sannan yasoma bata lemun daya shigo dashi tanasha wayarsace tafara ruri alamun ana kira kallon wayan yayi besaniba yasheka mata ajikinta jin saukan ajiyan heart dinta yayi lemun dasanyi gashi yana ratsata,dafe goshinsa yayi yace sorry meenal tissue yaciro yasoma goge mata lemun dadan sauri sauri yakeyi don kiran yakara shigowa besaniba yagoga maga kan kirjinta gurin ciwonta tasaki siririyar kara, koda yakkalleta yaga idonta tafda kwalla yamutse fuska yay cikin tausayi yace ya allah wlh namanta kinada ciwo duk muhammad dinkine yarudani kwana biyu yahanani sakat sena hadaku awaya so banason kowa yasan abinda yafaru shiyasa banbashi ke kunyi maganaba, yanzuma ina rokonki idan kunyi magana kada kigaya masa kinji kisaki jikinki sosae kada yagane,ay mimi cikinta wani kadawa yayi tana masa kallon rashin fahimta zuciyanta nabugu to waye kuma muhammad.... TAKU A KULLUM NANA BMB. 08147110349 [7/28, 8:20 AM] Nana BMB: πŸ’πŸ’–πŸ’πŸ’– RABON KWADO.... BOOK 2 NA NANA BMB page 9 -10 Koda yadago yana kallonta yaga yadda tazuba masa idanu cikeda tsoro setaso bashi dry ma hannunta daya matsane yasata dawowa cikin tunaninta,murmushin karfin hali tamasa yace yadae kada nakirashine kasa bashi amsa tayi tanadan kallonshi kamar mara gaskiya tambaya yajeho mata wae ina kikasa wayankine agidansu inty koda ita kika tafine tafadi ahanya, yace yanata kiran wayanki akashe haka su aunty suma,dan saisaeta kanta tayi tadukanda kanta don tarasa bakin magana,yana sauke idanunshi kan kirjinta yaga dan jini yabata mata saman rigarta kadan dake milk ce cikin damuwa yace hasbinallah meenal haryanzu baki warkeba agurinnan kallonshi tae taga meyake magana akae taga yana kallon kirjinta tayi ssurin maida kanta kasa kuwa, bazato ba tsammani taga yakae hannu kan kirjin nata gefen rigar yadan janye yana kallon karcewar da tayi yana yamutsa fuska kanar zeyi kuka yanzunma dayatsansa daya yadan shafi gurin yace ina maganin dakike shafawa agurin?lumsassun idanunta tabude tayi masa nuni da inda inda suke a ajiye yadauko yazauna kuwa dakanshi yasa tissue yagoge mata gurin yashafa mata maganin harya gama idanunta yana lumshe, gyara zamansa yayi sannan yakira muhammad koda yakara waya akunne yace sorry muhammad gata ay yanzu nashigo ne,mika mata wayan yayi ta ansa hannunta narawa tamkar anmata dole tace hello! cikin fada kuwa yace wae baza ah bawa meenal wayanba ne bae rufe bakiba yaji tace ina wuni,bae amsataba kawae yace bawa mujaheed wayan mika masa wayan tayi jikinta asanyaye,tsaki yay ya anshi wayan yace to meye kuma,mujaheed nizaka rainawa hankali ina meenal take,da mamaki mujaheed yace bangane ba ayni haka raenawa hankalin bagata tanama maganaba kace tabani gata ni cikin haushin yamika mata wayan,koda takara wayan akunne sunan daya kirata dashine yasa zuciyarta rudani sweety yakara kiran sunanta, cikin sanyin muryanta tace na am dan shiru yayi sannan yace meyake damunkine kifadamin gaskiya,babu komae babu abinda yake damuna dama yamata tambayarne donyakarajin muryanta,bashi wayan shine kawae abinda yafurta tabashi wayan kuwa ta lula duniyar tunani shin towaye wannan kwalla taf a idanunta,yankewa tunaninta yayi jin mujaheed yayi sama da ita abakin kofa yasauketa yasaurin zura mata hijab dinta na sallah yakama hannunta suka fita harcikin mota yasakata sannan yakuma kiran muhammad amma vidio call ya aje mata wayan kan cinyarta yazauna gefe shima yazuba mata ido, ya allah koda suka hada ido tacikin waya kasa kuma kallonsa tayi dagashi se gajeren wando iya gwiwa,dakyar ta iya kakalo murmushi tace sannu yaya kana lpy baima jitaba saboda irin kallonda yake mata,cikin tuhuma yace ina wayanki kika kaeta?tayi shiru cikin jin haushin hakan yace badake nake maganaba ne, yaya bansan inda takeba wlh,yayi kyau bakisan inda takeba sam babu abinda yadameki saboda kinsamu freedom na yawo ko bakidamu da halinda zamu shigaba kullum zuciyata cikin fargaba take da tunani marasa dadi akanki daddy yakikkira kinki daga wayan karshe wayannaki akashe su nana harsun gaji dakiranki ma, ko awayan mujaheed base ki kiramuba wani irin haline kikeson daukane yanzu? Kayi hkr yaya bazan sakeba tayi maganar idonta tafda kwallah zatayi kuka har mujaheed seda yayi mamakin yadda takewa muhammad magana,MEENAL! yakira sunanta zuciyarshi tabda tambayoyi kala kala, meyake damunki?yanzunma bata dagoba tace bakomae,sosae tabashi haushi kawae yakashe wayanshi ma, Da mamaki mujaheed yace meenal meyasa zakiyi masa magana ahaka ne sokike yagane bakida lpy,tagirgiza masa kanta,to kada kikuma amsashi awannan mood din pls kisaki jikinki,yanzunma kae kawae tadaga masa yakama hannunta suka koma cikin hospital din se kallon ko ina take harda wae waye saboda time dinda aka shigo da ita cikin asibitin bata hayyacinta sun shiga room din datake zara tana zaune tayi tagumi tana ganinsu kuwa tasaki murmushi tace ya mujaheed ina kukajene ina nan har tsoro yasoma kamani,murmushin yamata shima yace nakaeta motane tayi waya da yayanta kinsan basusan abinda yafaruba bawanj guri tajeba ay, wae zara kinsan inda wayan meenal takene,tagirgiza masa kae alamun a ah, bewani zaunaba yay musu sallama yatafi don jiranshi su sameer sukeyi, Tana kwance duk ta rame tabushe dakyar take bude idonta haka zama ma gagararta yakeyi saboda yunwa ta dagazata ruwane kawae take iya samu tasha abayi,numfashintama dakyar yake fita bata kara ganin mutuminba tundaga ranar hawayene kawae yakebimata fuska data lumshe idanunta lapiyayyaen abinci take hangowa tana hadiyar yawo,cikin wahalalliyar muryarta take cewa ya allah kadauki raena kozan huta dawannan ukubar sun tafi sun barni da yunwa ko kukama kasawa tayi,baccin wahale yadauketa kamar amafarki kuwa taji shigowan mutumin tabude ido ahankali taba wanan gardin mutumin shine dae yadawo hannunsa daukeda bindiga dakuma cup tayi saurin tashi zaune cikin tashin hankali take kallonsa harya karaso ya tsugunna agabanta, batare dayayi maganaba yamika mata cup din hannunsa, bamusu kuwa ta ansa fresh milk ce aciki batajira meze ceba takafa baki tas tashanyeta dataga hakan bematabama tasa hannu tana lashe kofin, yadda takeyi nema tabashi dry yay murmushi,cup din ya anshe yamika mata waya takuwa ansa takara akunne dukda hankalinta yanakan bindigar dayake nunata da ita,hello! tacikin wayan kuwa taji kukan wata mata tana cewa mimi ina fata dae basuyi miki komaeba nakasa bacci diyata narasa inda zan tsoma rayuwa, shiru meenal tayi saboda yadda kukan matan yake taba mata zuciya basuyimin komaeba tacewa matan, to nagode allah mimi kiyi hkr kinji allah ze kubutar dake kullum cikin addu ah muke yimiki, kasancewa meenal ba itabace mimi yasa hawaye zubuwa daga idanunta masu zafi kafin tayi magana kuwa ya anshe wayan yakashe tasoma binsa da kallon tsana,da murmushi yamike yace madarar dakikashace tasaki jin kwarin gwiwar yimin rashin kunya kiyi kome kikeso duka kwana nawane yarage miki aduniya,ficewa yayi abinsa,tabishi da harara sam tadena tsoron mutuwar ma ko kadan muryan matarne kawae yake mata yawo ajiki, mikewa tayi tayo alwala tazo tasona sallah abinta don ayanzu itace mafita agareta, tana idarwa tasoma rero karatun Alkur ani, washe gari Su sadiyane sukazo yiwa meenal sallama zasu tafi gida domin biki yakare jiya anmika ango dakinsa,duka dasu mom akazo da inty, gashi harda zara za ah tafi hakanne yasata samusu kuka wlh ita se ansallameta, mujaheed azuciyansa yace daman nasan za ah rina haka, lallabata yasomayi cewan tabari tadan sami sauki,mom tace a ah mujaheed kira doctor dole amata abinda takeso aitamayi har aka gama biki tana asibiti,zara tayi dry tace kinji mom itama banata bikin takeyi anan bah suduka sukasa dry kuwa banda mujaheed dayayi murmushi kawae yana kallonta ta tura baki gaba tana hararan zara,sunsha hira sosae sanan doctor yasallamesu suka tafi gida da murnarta se kallon gari take abinta. ... TAKU A KULLUM NANA BMB. 08147110349 [7/28, 8:20 AM] Nana BMB: πŸ’πŸ’–πŸ’πŸ’– RABON KWADO.... BOOK 2 NA NANA BMB page 11 -12 Koda suka karasa gidan kowa yanata shirin tafiya gida abinsa ita kuwa mimi tayi lamo tanata kallon gidan don yau ta taba zuwansa seda su zara suka gama shirinsu sannan tazauna gefen meenal tace to meenal zamu tafi sae allah yakaemu naki bikin muzo musha shagali,murmushi mimi tay batareda tadagoba tace hmmm,inty ma murmushin tayi tana kallonta,sosae tafiyar su zara tasa sukaji babu dadi ga mimi bata wani magana sedae kallo kawae gidan yayi shiru bakaman jiyaba wayar meenal inty tadauko tace meenal gawayanki koda naga miss calls dayawa sena kashe miki wayan tunda ya mujaheed yace bayason asan bakida lpy,murmushin karfin hali tayi mata ta ansa tana godiya tasoma juya wayan ahannunta yinin ranar inty tafuskanci meenal tacanza sam batason magana ko ana hira sedae tai murmushi, kasa jurewa tayi tace pls meenal menene yake damunkine sam bakyason magana yanzu murmushi tamata tace wlh babu abinda yake damuna, to ko inkira miki ya mujaheed?setabawa mimi dry tagirgiza mata kae tace a ah, tom shikenan muje mukwanta kikara hutawa anjima gidan ya sameer zamuje ku gaisa da amarya don shima yace gobe zaku wuce gida, tunda mimi ta anshi wayan meenal takeson ganin abinda yake cikin wayan amma da security awayan dole takashe wayan ta ajiyeta,bayan ishah su inty suka tafi gidan sameer mujaheed yana driving dinsu mimi nagefenshi se inty abaya suna ta fira har suka karasa bakarya kam gidan sameer yahadu haka auntie salma matarsa tanada kirki sosae se nan nan take dasu tanatama mimi sannu don sameer yabata labarin komae koda yatambayi salma ina sameer tashaida masa ay yana bedroom dinsa, kae tsaye yawuce dakin nasa sukuma ancikasu dakayan ciye ciye, Akwance yasamu sameer yana danna laptop dagashi se boxer murmushi yayi kawae yazauna kusa dashi yakae masa duka abaya kamar yasani kuwa yazille, yajuyo yazuba masa uwar harara,dry mujaheed yay donya fahimci abinda sameer yake nufi,hannunshi yahade guri daya yarike baki yace oh ni mujaheed shin sameer duka yaushe kasan zakin amarcin nan ne dazaka dinga turomin baki harda hararata munzo mun katsema jin dadi koh inkayi hakuri dagayau bazaka sake ganinaba dakudi seka nemeni, murmushi sameer yay mesauti yagyara kwanciyarsa yajuyo yana kallonsa yaharde hannayensa abayan kansa yace mujaheed bazaka ganeba ne yau nakeson fara cin amarcina amma don iskanci irinnaka karasa sanda zaka kawomin su inty seda daddare don mugunta irintaka duka sameer yakae masa saboda dariyar dayakeyi masa dan iska ainasan dama dabiyu kaimin haka,saeda nujaheed yay dariyarsa son ransa sanaan ya tsagaita yace kace amarya wanaka takeyi shiyasa naganka duk ba adaidaeba,kallon kafafun sameer yasomayi har zuwa sama,yakuwasa hannu yature masa fuka yace munafiki mekakeson kallone juyawa yay yakifa akwance abinsa yana dariya shima, Jinjina kae mujaheed yayi yace tabdijan babbabar magana dole ka kasa fitowa kagaisa dasu inty wlh amarya tarufawa kanta asiri tabada kae bori yahau,mintsininshi sameer yafara yana cewa allah yashiryaka mujaheed bansan sanda ka kara zama hakaba duk jarabata ay ban kaekaba tundani bana rawar sanyi dashan magani ehe! kamakalewa 'yar yarinya ai meenal zatae fama da ..... Saurin toshe masa baki mujaheed yayi yace to mara mutumci naji bari nabarma dakin kasan yacca zakayi wlh kafito don bayanzu zamu tafiba, cije baki sameer yay yana girgiza kae yace habawa mujaheed zan ramane, Mujaheed yana fitowa yasamu salma takunna musu TV sunata kallo abinsu inty tana ganinshi tace kae ya mujaheed harka fito badae tunyanzu zamu tafibah, girgiza mata kansa yayi alamun a ah yana murmushi haka salma itama murmushin jin dadi tayi jin bayanzu zasu tafiba mujaheed na ankare da ita azuciyansa yana cewa habawa yarinya zakiyi bayani ne,fitowansa da dan jumawa sameer yafito shima yazumbula babbar rigarsa ta daurin aure se muzurae yake yazauna kujeranda mujaheed kezaune wanda yaketa faman dry kasa kasa, gaisawa sukayi yanata ma mimi sannu da jiki yalura da dariyar da mujaheed kemasa matsawa yafarayi kusa dashi mujaheed namatsawa shima yana kara matsawa harya kureshi akarshen kujeran seya seya mike yay waje yana murmushi yasan yanzu ze iya kunyatashi gaban kannensa, Duka hankalinsu nakan TV basusan mesukeyiba sameer yay dry yamike yabi bayanshi yana cewa karamin dan iska dakatsaya kaga meze faru,haka kawae kazomin gida kahanani sakewa, Awaje suka cigaba dahirarsu gwanin burgewa har lokaci yajama basu saniba intyce tafito tanata kwala musu kira takuwa hangosu zaune saman mota kiran da take musune yasa dukansu suka zuba mata idanu tayi tace ya mujaheed mom ce tace mutaho gida dare yayi, Cikin masifa sameer yace wani irin shashancine wannan zaki dinga yimana irin wanan kiran ni nazacima wani abune yafaru wlh sim sim itadae takoma ciki, murmushi mujaheed yay yazo dafda kunnensa yace kwantarda hankalinka aibacazatai dakae wani abu yasamu amaryaba daze hanaka cin amarcinka yau bare kasauke mata kwandon masifa yana gama fadin hakan yay saurin dirowa akan motan yay ciki tunkan sameer yay magana, kwafa yayi kuwa yabishi abaya kayan azziki salma tahadawa su inty suna shirin tafiya sameer yace wae meenal meke damunkine naga kinyi shiru kawae abinki, caraf inty tace ay tunda tadawo haka take bamagana gida takeso ay,kallon inty tayi tace allah sis bagida nakesoba kawae maganan ne baya kaena,sameer yay murmushi yacewa mujaheed to inkun koma yaushe zaka maidata gidannasu kenan,ay mimi tanajin haka taji cikinta yabada wani kara jin ashema ba agidansu ya mujaheed takeba, tabdijan babbar magana! Maganar mujaheed dinne ya katse mata tunani yana cewa muna komawa bawani jumawa zamu tafi ay hutun nasu yakusa karewa sunkusa komawa school don muhammad ma yanata azalzalata,lebe sameer yarike a ah kaji masu kanwa fah jarababbe yanzu dae munji sit abinmu tunda yabar kasar saura shekara nawa yadawone,mujaheed yay dariya yace kaidae bari masifaffen bah saura shekara daya da rabi yadawo, time dinda yashekara biyu ba irin faman dabanyi dashiba yadawo gida yay hutu amma yaki yace wae inya dawo baze kuma komawa ba,sameer yace to kada yakoma mana shifa yayiwa kanshi ay muma hutunmune sosae magan ganunsu suke daurewa mimi kae, ahaka sukayi sallama suka tafi gida zuciyanta cikeda tunani kala kala.... TAKU AKULLUM NANA BMB. 08147110349 [7/28, 8:20 AM] Nana BMB: πŸ’πŸ’–πŸ’πŸ’– RABON KWADO.... BOOK 2 NA NANA BMB page 15-16 Messeges dinda suke shigowa cikin wayanne yadawo da ita tunanin datakeyi tanason duba me ake turowa haka amma babu hali haka ta aje wayan ta tashi tayi alwala tazo tayi nafilfilinta da addu o ei tana nan zaune taji wayanta yasoma ruri tamike dahanzarinta ta dauki wayan sunan data ganine kan screen yasata kasa daga wayan anyi serving number din da"hearty" har wayan ya tsinke bata dagaba se akaro nabiyune tadaga wayan azuciyanta tana cewa ko muhammad dinne to, daga cikin wayan tajiyo muryar yousef kamar zeyi kuka muryanshi harrawa yake yace my baby sosae zuciyanta yatsananta bugawa jin muryan nashi dasunan daya kirata dashi,shirun da tayine yasashi cewa shin meyasa kekuwa kika azabtar dani haka why inaji ina gani bacci yagagareni ina cikin tashin hankali meenal menene yake faruwa haka kullum cikin mafarkinki nake marasa dadi meya samekine, pls talk to me mana kozan sami nutsuwa,cikin inda inda tace wayana ne yasami matsala shiyasa kajini shiru but am so sorry,sosae taji sauke ajiyan zuciyansa yace yaushe zaki dawone banyi tsammanin zaki iya tafiya wani guri ki dade baki nemeniba,mimi tace bahaka bane nakusa dawowa ay kada kadamu kajee yanzu bacci zanyi zamuyi waya gobe batareda tajee meze ceba takashe wayan tanata zaro idanu harda guminta kamar wadda tayiwa sarki karya,koda meenal tafado mata arae se hawaye shar allah sarki meenal masoyinki yana bidarki amma sedae kinyi masa nisa allah ya tseratar dake kidawo cikin 'yan uwanki namiki alkawari zan riritamiki soyayyarki harzuwa sanda zaki dawo,jikinta asanyaye tahau kan bed takwanta zuciyanta fal da tunani kala kala, Washe gari Tunda tayi sallan asuba takwanta bata kuma sanin inda kanta yakeba tayi nisa abaccinta aunty saratu harta gama shirya musu breakfast amma shiru bata fitoba tayi mamaki tunda kullum tare suke girkin tunda tazo amma yau ko motsinta hakanne yasata shiga dakin nata taganta akwance tanata sharar baccinta ganin haka yasata yin murmushi tajuya tace lallae meenal anshawo gajiyar biki,har mujaheed yafito bata tashiba don haka sukayi breakfast dinsu sukadae, wajan karfe 12 rurin wayanta yatasheta takuwa lalubeta cikin bacci tadaga wayan batasan kowayeba jin muryan inty datayi yasata watstsakewa tamike zaune balaifi sundan taba hira sannan tashiga bathroom koda tafito seda tagama shirinta tsaf tafito parlour aunty saratu nazaune taganta tasoma murmushi tace meenal seyanzu allah yanufa kenan antashi gaisawa sukayi tanemi guri tazaun, a ah yazaki zauna kije kisamawa kanki abin kari koh,inda allah yatemaki mimi tayi mata nuni da dahannu inda kitchen din yake, Indomie kawae tadora tahada tea tana tazauna a kitchen din tana dan kurban tea din,talula tunaninda tasaba taji anmata doss akumatu,tayi saurin juyowa kuwa suka hada idanu taga ashe mujaheed ne yamata kiss a kumatu lallausan murmushi yasakar mata itama tamayar masa tace yayana ina kajene zama yayi gefenta yace ayke zanwa tambayar ina kikaje haka ina baccinki yakaekine bata cemasa komaeba sema murmushi datayi masa,ruwan indomie dinda tadorane yatafasa kamshi kuwa yacika kitchen din harda hadiyan yawunsa yace my dear mekike girka mana haka me dadi dariya tadanyi tace indomie cefa bawani abu bane jinjina kae yayi yace masha allah matata ta iya girki kenan maganarshi seta bata kunya tasunkuyar dakae tana murmishi,koda yaga seya gyara zama yace meenal arayuwata inason matata ta iya girki inaso sosae kuwa,to yayana allah yabaka wadda tafini hadawa mah,saurin girgiza mata kanshi yayi yace no ina bazan taba samun wacca tafiki agurinaba babu ita bazan gantaba kaf 'yan matan duniyar nan kekadaece wadda nake kauna kike zaune azuciyata tsawon lokaci bazan iya jure tashinki bah ayanzu meenal ina matukan kaunarki kuma inason yin rayuwa dake tahar abada muzauna matsayin miji da mata,kawae dae fatana shine bazaki kiniba meenal inason sanarwa iyayena amma inajin fargaba bansan meye azuciyanki bah bakuma nason ayimiki dole arayuwa indae bakya sona kada kikee fadamin kada kiji nauyina asoyayya babujin nauyi meenal nibazanyi miki doleba zan hakura koda kuwa hakan zezama ajalina, burina dae kullum kikasance cikin farin ciki, Sauke ajiyan heart yayi yace dukda kinada yarinta meenal amma hakan bashine zahanaki sanin so bah inason jin furicin ki abindake cikin zuciyanki kigayaminshi yanzu meenal,duk maganan dayake kan mimi yana kasa idanunta nata zuban hawaye tanaji wani irin zafi azuciyanta jitake kamar takwala ihu duk wanan kalaman nasa bada ita yakeba da meenal yake,ita kuma tun randa tafara ganinshi zuciyanta takamu dakaunarsa,sedae shikuma meenal yakeso, wata ziciyan tace mata kada kiga laefinsa tunda meenal yasani bakeba, hearty ne yafado mata arae wato yousep sosae kanta yadaure to ayga wanda meenal takeso ma bashiba, oh ya allah katemakeni wlh nakamu da kaunarsa matuka har inaji zafi idan yana furta kalaman kauna yana kiran sunan meenal yazanyine idan na amince mishi meenal tadawofa, kodae nafada mishi gaskiya ina baze yiwuba gaskiya bazan iya jure rashinkaba mujaheed koda meenal tadawo bazan iya rabuwa dakaeba, rintse idanunta tayi hawaye nafita, ya allah kaine kadai kasan nufinka na kawoni cikin wadan nan mutane allah kasa hakan shiyafi alkhairi agaremu, Hannunda tarike cup din tea dinne taji yarike danashi hannun cikin yanayin tausayi yace pls say something meenal,hawayenta tashare datago suna kallon juna tace ina kaunarka yayana ina tabbatar maka sonda nake maka yafi wanda kake yimin ina hawayen farin cikine ayanzu dajin kalamanka,kayimin alkawari koda anan gaba bazaka taba juyamin bayaba komenene zefaru anan gaba kada ka kini bazan iya jure rashinkaba arayuwata tana magana tana masa kuka,hakan kuwa bakaramin tafiya da mujaheed yay wani irin sanyi yana ratsa masa zuciya jinshi yake kamar yafi kowa sa ah,yana zuba murmushi yasa hannu yana share mata hawaye yamatsa daf da kunnenta yana cewa i promise u my dear komin wahala bazan taba barinkiba meenal kece farin cikina zan zame miki bango jigo a rayuwarki so pls stop cry am always with u,sam mimi tarasa farin ciki take ciki ko bakin ciki batajin dadi idan yana ambaton meenal,tanajin yadda yake ambatun meenal yana mata kalami masu dadi, Jiki babu kwari tamike tasoma juye indomie dinta a plate shikuma yafita zuciyanshi kal da farinciki tabare egg dinta guda uku tafito jiki babu kwari,suka zauna tare sukaci indomie din mommy di nakallonsu duk abinda suke tana ankare dasu farin ciki sosae ya lullubeta.... TAKU A KULLUM NANA BMB. 08147110349 [7/28, 8:20 AM] Nana BMB: πŸ’πŸ’–πŸ’πŸ’– RABON KWADO.... BOOK 2 NA NANA BMB page 13-14 Mujaheed yana ankare da mimi gaba daya yanzu tasauya komae nata dasanyi takeyinshi bata wani surutu sedae murmushi inta kama to bewani damuba yana tunanin duk sabida abinda yasametane takoma haka, Koda suka kwanta bacci inty tanata latsa wayanta abinta itakuwa mimi seta juya mata kada taga hawayenda takeyi abin duniya ya isheta kamar tasoma tsala ihu,cikin zuciyanta tana cewa mekikeyi ne haka mimi kinkuwa kyautawa diyar mutane, wato "meenal" allah ne kadae yasan halinda take ciki inma tana raye kekuma gashi kina amfani da farin cikinta,rintse idanunta tayi tana dafe zuciyanta,yanzu yazanyi da rayuwata ni mimi ina komawa gidanmu meenal zasu kwashe idan tana raye sanan sudawo kaena komawata gida sam ba alheri bane gashi inason ganin mahaifiyata,zuciyata takamu da kaunar mujaheed matuka bazan iya barinshi cikin tashin hankaliba da kowama na meenal ina tausaya musu sosae dole nahakura da rayuwata nazauna inda allah yakawoni kuma shikadae yasan nufinshi nayin hakan,ya ubangiji ka kubutar da ita domin tadawo garesu nima nakoma nawa family din,tanata magana azuciyanta bacci yasaceta batare da tasaniba, WASHE GARI Tunda suka tashi inty kamar zatayi kuka duka 'yan biki suntafi se sukadae itada mimi itama kuma gashi yanzu zata tafi dawuri sameer yazo donyi sallama da aminin nashi mom tanata rarrashin inty itama mimi na nata jimamin azuci batasan wani kalar gidaba kuma yanzu zasu jitake dama suyita zamansu anan kayan azziki suka hada mata su mom sosae sannan suka tafi,suna hanyane yake cewa meenal ina wayanki ne?hankalinta nakan hanya tace tana cikin jakana,to meyasa kika kasheta meyasa kikeson rufe wayankine yanzu kowa yayta kiran wayanki akashe laifina suke gani jiya auntie ba irin fadan dabatayi minba awaya akan kin rufe wayanki kindena nemansu why?har daddyn ku tace bakya kiransa cikin damuwa take kallonsa harya gama sannan tace am sorry yayana banasonne sufahimci wani abu yasamenine amma yanzu tunda naji sauki muna zuwa zan kunna wayannawa murmushi yayi dajinjina kansa jefi jefi suna hira harsuka karasa gidan sedae mamakine yacika mimi ganin tsoffi datayi tanata tunani tasandae wadannan sunyi tsufa bazeyiwu ace iyayensabane inna tana salla se baba agefe yana lazimi yana ganinsu kuwa yasoma tafa hannuwa yana cewa oyoyo oyoyo 'yan jikokina sundawo gida sannaunku dazuwa,sosae mujaheed yaji dadin ganin kakannin nasa dayayi,yazauna gefen baba yana cewa tsoho meran karfe kaci zamaninka kanacin nawasu yana dariya yay naganar shima baban hakan yace fadi ka kara yaro naci zamanina inacin naku cakwas dani yaranka kaga nafika tsadadden jiki koh dakaene kakae shekaruna ina zaka ganu,mujaheed yay murmushi yace haba baba jifa jikin naka ai ina tunanin munkusa fara dakan gumba agidan nan,baba yay murmushi yadamki damtsen mujaheed yace tokumu gwadane innuna maka tsohon kashi ba irinna yarintaba,zafinda yajine yasashi cewa wlh naji baba nayarda amin afuwa, yakuwa sakeshi yana fara ah yace ja irin yaro allah yashiryaka mujaheed,dubansa yakae kan mimi tana zaune tanata sake sakenta yace meenal meke damunki ne kikayi shiru haka kamar ruwa yacinyeki koduk gajiyan bikinne,murmushi tayi tace a ah baba,girgiza kae yayi yace a ah dakwae abinda kedamunki ayda kalau kike dayanzu gidan nan bama jishi shiruba, zuciyan mimi kuwa tawani harba dajin furucinshi ita mezatace musune sam batasan surutu ko kadan hawan mata kaema yake inyayi yawa,kallon mujaheed baba yayi yace meke damun jikalletane se kallonta yake yana mata alamu da ido amma kanta yana kasa,dan yake yayi yace gida takeson komawa ne,se ayanzun tadago takalleshi tana yana mata inkiyi da idonshi tagane nufinshi kada tabari agane tashiga matsala,baban yace to koyau zaka maidatane ya girgiza kae yace a ah haba bayauba dae hakuri zatayi, koda inna ta idar da sallah mimi tahubawa idanu tana murmushi alamu taji ana kallonta koda tadago kuwa suka hada idanu tayi saurin sunkuyar dakanta tace ina wuni sororo da mamaki ta amsa mata wanda inda dane datuni taje ahaye mata cinya,inna tace sabon salo lallae meenal gida akeso kaga yadda tayi wani ladaf kamar wadda akayiwa mutuwa keda kikace bazaki komaba kinzo kenan sedae suyi hakuri ashe kinfasa zama gurin saratun kenan,to ay setazo takwashi kunyarta taji abinda kikeso yanzu,sosae suke hira avinsu cikin jin dadi wanda mimi nata murmushi ne kwae har tsokanarta inna takeyi sedae tayi murmushi sosae taji tsofaffin sunshiga ranta,sunkuwa yi mamakin yin shirunta kuwa haka su mummy suka karaso itama taga mimi cikin wannan yanayin nashiru mujaheed yanata zuba tabararsa yaga yadda mummy kezuba masa harara yarasa meye dalilin yin hakan, daga karshema hannun mimi takama shiga daki suka zauna tace meenal fadamun abinda yake damunki kada ki kuskura kiyimin karya meyasa kikeson komawa gida kada ki boyemin idan mujaheed yay miki wani abune just tell me duka gaba daya kincanza jikinki yayi sanyi haka zaki koma musu gidan,murmushi mimi tayi tace wlh mummy babu abinda yayimin kuma gida nakeson tafiyaba, banason maganane dayawa haka nakeyi dama indae ina menstruation gashi yace auntie ma takirashi, Seyanzu tasauke ajiyan zuciyan da harseda mimi taji tace ok yanzu nafahimci damuwan keda auntienki ne ko hakuri zakiyi meenal watarsna se labari kita mata addu ah itadae mimi amsawa take azuci kuma tana fargaban tome auntn takewa meenal?komawa parlour din sukayi aka cigaba da hira dob tayi tunanin kodae wata ayka aykar dannata yaywa 'yar mutane donba ah shedar dan yanzu,sedare suka tattara suka tafi koda suka isa dukda darene hakan behana mimi gane gidan part biyu bane ga tsaruwa iya tsaruwa gidan yatsaru kayanta da mujaheed yaketa kaewa daki yasata gane acan masaukinta yake bawanda yazauna hira sabida dare yayi kowa yanufi makwanci,ita kuwa seda takarewa dakin kallon tsaf sannan tadauko wayan meenal takunnata tazauna kan bed tazubawa wayan idanu.... TAKU A KULLUM NANA BMB. 08147110349 [7/28, 8:20 AM] Nana BMB: πŸ’πŸ’–πŸ’πŸ’– RABON KWADO.... BOOK 2 NA NANA BMB page 19-20 Tana tafiya cikin sanda harta isa inda yake tasa hannu tarufe masa idanu tana bayanshi sedae mujaheed bakaramar tsorata yayiba addu ah yasomayi ba kakkautawa ita kuma jin yadda yake jero addu o ei yasata fashewa da dariya tajanye hannayenta dariya harda tafa hannu tana nunashi koda yabude idanunshi suman zaune yayi yana kare mata kallo ay yau ganiyay tamafi koyaushe kyau yadda take dariya kamar sakarae yake kallonta seda takare dariyar tata tace kae yayana haka kake da tsoro dama sam bemaji metake cewaba saeda takae hannu ta dungure masa kae sannan ya lumshe idanunsa tana murmushi tace kunya kakeji nabaka tsoroko, Bude idanunsa yayi dasuka soma sauyawa wayarshi yadauka yaga time har kusan biyu saurama ya jinjina kae ya aje wayan bazato taji yajawo hannunta yana daga zaune tana tsaye harseda ta dsngane daga jikinshi kirjinta yasauka akan fuskarsa yasauke ajiyan zuciya dakyar ya iya furta my dear kinbani tsoro over mekikeyi anan bakiyi bacciba shirun datayi masane yasashi dagowa yana kallonta suka hada idanu yadda nashi yacanzane bazata iya jurewa kallonshiba ta sunkuyar dakanta kasa tace nayi bacci farkawa nayi,sukayi shiru nadan lokaci sannaa taji numfashinsa awuyanta yana cewa nimafa sena rama tsoron dakika bani kishirya jinsa yanzu ato,bata fahimci meyake nufiba sema rintse idanunta datayi tana murmushi hakanne yabashi damar karewa kirjinta kallo gaba daya rigan ta zanzare dan kadan tarufe mata kirji bakin cikine yakamashi ganin karcewar datayi haryanzu akwae shatinta,hannu yasa yadan shafi gurin,habawa aykuwa kamar an tsikareta tabude idanunta tana kokarin kawcewa seyanzun ta tuna ayadda tafitoma don manni irinna mimi takasa kwacewa don riko mekyau yamata kuma yaki dena abinda yakeyi mata haushi sosae yatiketa takae baki tacizar masa hannun dole yasaketa tajuya dasauri zatabar gun tabdi tana juyowa taga yama cimmata saboda tsoro takife agurin ido kawae take kwalowa tana bashi hakuri cikin shan kunu yace tonima wayace ki tsoratani,ganin abin nashi gabama yakeyine yasata sakin kuka tana ture hannunshi tana cewa nika kyaleni banaso kukan tane yasashi tattaro hankalinshi yacire hannunshi cikin rigarta tamike asukwane kuwa tanufi cikin gida tana hawaye masu zafi koda tashiga dakin nata tasake fashewa da kuka tafada kan bed tana jin zafin mujaheed sosae azuciyanta donme zetaba mata jiki ita ba matar saba kuma ba ita yakesoba meenal yakeso ziyi mata haka, shima mujaheed kayanshi yatattara yakoma daki yanajin haushin kansa abinda yayiwa mimi,seda taci kukanta takoshi sannan bacci yadauketa, WASHE GARI Da wuri mimi ta tashi tayi wanka tashirya ta tasa kayan meenal agaba tanata kallo natafiya tana tunowa da muryar auntie takejin zuciyanta na harbawa tanajin fargaba dukda batasan gidanba amma zuciyanta bata kaunar tafiya gidan,tare sukayi breakfast dasu auntie saratu banda mujaheed donbe shigoba kallo daya sukayi mata sukasan tayi kuka sekuma basarwa take don karsu gane wani abu, daddy yana shirin fita aikine nujaheed yashigo yana waya seda yakammala sanan yagaida iyayen nashi mimi nagefe tanata zumburar baki ita ala dole anmata badae dae bah beko kulataba dasu mummy kawae yake hira har suka fita zata raka daddy din bakin gate suna fits yatashi yaje yazauna a dining yasoma breakfast dinsa beko kalli inda mimi takeba,seda daddy yashiga motan yarufe kofan sannan mummy taruza kanta tana masa magana cewar kajawa danka kunne yafaja girmansa meenal yarinyace tsaf zata rainashi kana ganidae yau kogaisawa basuyiba zuba mata ido daddy yay yana murmushi harta kare maganarta,sannan yace niba abinda zancewa dana kema idan kika gaya masa ay yayi,mujaheed yasan abinda yakeyi saedae ita meenal daganin wannan yarinya zeyi fama da ita itazakiyiwa fada kada ta lalatamin yaro,hade rae tayi tace kaedama indae akan mujaheed ne kada sonkanka dayawa goyon bayanshima kake kamar batare dakae muganshiba jiya a garden yanama 'yar mutane ayka aika,kace zata lalata wancan katon yaron duka nawa take metasani mah katseta yayi dacewa aydama ku mata haka kuke kuyi tsokana kuma kuce anmuku ba dae daeba inbanda jiya kintaba ganinsa yamata wani abu nifa bazanga laefin danaba wani kinibibinne yafito da ita daga dakinta cikin wannan dare tasameshi har inda yake kuma babu shiga ta mutumci itacefa takae kanta don dana ba dutse nahaifa bani,so kigaya mata taringa suturta jikinta harsuyi aure kada kada ta lalatamin tarbiyarr yaro da ace dakinta yabita ne wannan to zega abinda zefaru kuwa to amma yanzu laifi na 'yarkine,duka meenal matasani arayuwarta dazata iya wannan aikin,dariya yayi sosae sannan yace ki kyale zanceb kankanta duk inda mace take to macen ce so kidena yimata kallon karama aynazu akama 'yar can aure seta zauna harda murnarta kike abinki keni koyanzu my son keson yin aure yimasa zanyi donnaga 'yar takima kila setafiki iya rike miji! dama yatada motansa kafin takuma magana yaja motansa yana dariya yana cewa sekun dawo matafiya agaidasu Dr maryam sun saba mummy da daddy irin wannan drama din soyake dama yakunnota kan yafita, Seda yagama breakfast dinsa sannan yadawo kusads ita yazauna zumbur kuwa tamike cikin fushi yarike hannunta tajuyo cikin tsiwa suna hada ido tayi lakwas da ita rae abace yace baki iya gaisuwa ba koh cikin tura baki tace ina kwana yadda tayi masa maganar ne yasa ranshi yakuma baci kawae yasaki hannun nata yamike yafice daga parlour din tabishi da harara harda murguda masa baki,yana fita mummy tashigo tace meenal kingama hada kayankidae koh anjima zamu tafi kamar tayi kuma ta daga mata kae seda tazauna tace meyake damunkine kika shiga damuwa tundazu bakomae mummy, tomeya hadaki dayayanki nanma shiru batace komaeba, mummy tasauke ajiyan zuciya tace aduk sanda zakiji gurin yayanki kiringa suturta jikinki kafin kije kinga ba aure kukayiba saboda gujewa hudubar shedan, ay zuciyar mimi tsinkewa tayi tana kwalo idanu kardae mummy tagansu jiya dakyar ta iya daga mata kae alamun to don takasa dagowa, yawwa meenal allah yayi miki albarka kije kirasa kimtsa kayanki koh, tamike jiki asanyaye tanufi dakin abin duniya yaymata yawa tarasa abinda yake mata dadi tanajin wayar meenal tanata ringing amma taki kulata sotake taga mujaheed amma ko motsinshi batajiba har karfe biyu tayi narana sosae take kuka tunda tafito awanka tamakasa shirin daga ita towel tana haka taji ance kukan me kikeyi?tayi saurin dagowa suka hada ido kunyace takamata tasunkuyar dakanta kasa cikin tura baki tace to ay bakuka nakeyiba kaenane yake ciwo,betankataba yajuya zefita yace kitashi kishrya kifito mutafi kemuke jira zamu gidansu inna dagacan muwuce rintse idanunta tayi don sam tamace batasa kayaba ga towel din dukya tattare ganin zefice ne sayata saurin saukowa tazura hijab tace yayana cikin sanyinta, ay zuciyar mujaheed tawani harba jin muryar meenal dayayi tacanza wanda bakowane zefahimci hakanba takowa tayi har inda yake tazagayo tatsaya agabansa idonta tafda kwallah tace sokakeyi natafi nabarka nifa banason tafiyar nan kagayawa mummy tabarni banason tafiya nabarka nafison kasancewa dakae koda yaushe bazanyi farin cikiba indae kayarda aka maedani gida kuma sena dena yima magana, tana kuka tamatsa ta dora kanta kan kirjinshi tana kuka tana cewa pls yayana pls.... TAKU A KULLUM NANA BMB. 08147110349 [7/28, 8:20 AM] Nana BMB: πŸ’πŸ’–πŸ’πŸ’– RABON KWADO.... BOOK 2 NA NANA BMB page 17-18 Yinin ranar tare suka kasance cikin nishadi sae bayan la asar suka tafi gidansu innah basu suka dawoba se bayan ishah suka sami auntie saratu tana zaune a parlour fuskanta daukeda damuwa suduka suka zauna gefenta kan carpet mujaheed yace menene yafaru mummy naganki cikin damuwa tayi murmushin karfin hali tasa hannu ta shafi kansa tace babu komae my son dubanta takae ga mimi wacca tazuba musu idanu tace meenal kishirya gobe insha allah nida mujaheed zamu rakaki gida Damuwa karara tabayyana afuskan mujaheed kamar yay kuka yace haba mummy abari hutun natama yakarasa karewa mana kamar mungaji da ita nasan wlh auntie ce zata kiraki tabata maki rae, batabi takan zancen nashiba tace kamantane bayan boko tana zuwa islamiyya ne gobe insha allah zamu tafi takalli mimi wadda kirjinta ke dukan uku uku tace kije kishirya kayanki kinji meenal kada karatu yadinga wuceki,kamar zatayi kuka kuwa tace don allah mummy kubarni anan nibanason komawa gidan,girgiza mata kae tayi tace kiyi hakuri meenal mahaifiyarki kebidarki shin ina kika aje wayankine seyanzunma mimi ta tuna da wata waya tunda safe dasukayi waya da inty bata karabi takan wayanba,tana daki shine abinda tace to tashi kije ki kirata jikinta asanyaye tamike tashige dakin shima mujaheed yanufi nashi guri cike da bakin ciki,aunty saratu itama tahaye sama abinta ran kowa babu dadi,koda mimi tashiga ciki jitake kamar tasa kuka itafa wlh tagaji da anje wannan gida ace za ah tafi nan gashi wannan auntien dagani bakin hali gareta tanata masifarta ita kadae tajiyo karar wayan harseda takusa tsinkewa sannan taje tana gani tasan auntien ke kira yadda meenal tayi serving number din picking call din tayi sedae tunkan tafara magana tasoma jin ruwan bala ei wlh meenal kiji tsoron haduwata dake tunda kinzama mara mutumci yanzu 'yan uwanki basuda mahimmanci agareki da iyayenki kira nawa nayi miki seyanzu zakiga daman dagamin waya sabida kinsamu guriko! sati daya mukace kiyi kidawo gida shine kika zauna dake suma basusan darajar karatun da kikeyiba gajiya dasauraren ihun mimi takatseta dacewa pls auntie kiyi hakuri bagobe zandawoba,kadama kidawo kiyi zamanki kinji duktsiya dae ay sekin dawo garemu mimi bata iya jure fadan don haka tayanke kiran ta aje wayanma tashige toilet abinta, Meenal ce akwance kotashi bata iyayi dakyar take bude idonta duk jikinta yay yaushi tawani kojale sae kace ba itaba azuci kawae take iya ambaton allah haka tayini ahaka sedare taji anshigo dakin ko daga kae takasa motsi kawae take iyaji nawanda yashigo daga bisani taji ankuma fita,sam yanzu tafidda rae da rayuwa addu ah take allah yasa intamutu anan to tamutu 'yar aljannah tadena tunanin kubuta mutuwa kawae take hange don ta sallama rayuwarta ayanzu, Wani irin kara kara takeji akunnenta kasa kasa mamakinta bekareba seda aka kuma shigowa kara take kuma shiga kunnenta tsawa da hargagi kawae take jiyowa takasa mikeww zaune donhaka tarintse adanunta tasadakar yauce ranarta takarshe aduniya, Bazato tajee an dan dora mata wani abu awuyan tsoro kuwa yakara rufar mata ta daskare akeance wata murya tajee ance yanaga kamar bata numfashi, daga kusada ita tajee ance bata mutuba numfashinnedae yake barazanar daukewa,se awannan karon tayi karfin halin bude idanunta tazubasu kan mutumin ga hasken fitilinsu duk da haka dishi dishi take gani ashe yatsunsane yasa awuyanta kuma kakin sojane ajikinshi,ba bata lokaci yadauketa cak yanufi waje da ita karar datake jine yake gigita mata kunne haryanzu batayi tunanin karar bindiga takejiba duk tafiyan dataji anayi da ita taki bude idonta sam seda taji wata san sanyan iska naratsata yasata saurin bude ido sedae duhu tagani ako ina hakan ya tabbatar mata anfito waje,seda ya isa bakin motansu sannan yashimfideta yadauko goran ruwa yabata tasoma kwankwala seda takoshi sannan tasoma maida numfashi bazato taji karar data firgitata tasaki dan guntun fitsarinta tasulale kasa saumamma! Mimi cikin baccinta taketa mutsu mutsu da alamu mafarki take firgigit kuwa tafarka tana sauke numfashi siraran hawayene ke bimata fuska tana murmushi tadaga hannayenta tana mika godiya ga ubangiji ya allah kaene abin godiya allah kasa mafarkina yazamo gaskiya meenal dinsu takuta daga hannan azzaliman cen,kasancewar tana menstruation ne yasata batayi sallaba tamike tamaida hular kanta tafito palour domin shan ruwa rigar baccine ajikinta 'yar yaloluwa gata shara shara komae breast dina kana gani saboda batasa bra bah, fridge tabude tadauki ruwan tasha abinta tanemi guri tazauna se sauke ajiyan zuciya takeyi sosae takejinta wani wasae da ita gajiya tayi dazaman parlour din ita kadae yasata mikewa sam bacci yakauracewa idanunta takuwa bude kofa tafita abinta kofan daze sadaka da dayan part din nagidan tazubawa idanu" da alamu wanan mimi din batada tsoro kamar meenal" tafiya take harta dangane da garden sedae abinda yabata mamaki shine ganin mujaheed datayi zaune kan daya daga cikin kujerun garden din yanata danna laptop dinsa duka hankalinshi nakanta sam bejitaba dagashi se gajeran wando,wani irin farin cikine ya lullubeta ganin masoyin nata datayi itakanta tarasa dalilin farin cikin dakeji tunda tafarka abacci sanda tafara ahankali tana nufar inda yake," waeshin mimi tamanta suturar dake jikintane"? TAKU A KULLUM NANA BMB. 08147110349 [7/28, 8:20 AM] Nana BMB: πŸ’πŸ’–πŸ’πŸ’– RABON KWADO.... BOOK 2 NA NANA BMB page 21-22 Sam mujaheed besanda sanda yamata kyakkyawan rumguma yanadan yasunkuya saitin kunnenta yana cewa am sorry my dear zanyi kewanki matuka but iyayenki ne suke bukatanki kusadasu bamuda iko akanki nidake seyadda sukayi damu kwaedae meenal in dae kina sona kina kaunata dayawa kina gama secondary school kibari amana aure hakan shine ze bamu damar rayuwa atare harzuwa karshen rayuwarmu,bugun zuciyartane yakaru tana tunanin taya zatayi aure bada sanin iyayentaba? Dan matsatan dayayine yadawo da ita tunanin data lula tayi saurin janye jikinta takoma bakin kofa tace to yayana nayarda kafita nashirya sedae gani tayi yakara matsota sosae harsunajin numfashin juna yace kinutsu meenal bawani abu zanyi mikiba bazan kara aikata abinda nayimiki a garden bah nasan ban kyautaba kiyi hakuri kawae yajanyeta gefe yabude kofan yafita suna paulour suduka suna jiranta sauri sauri tashirya takwaso kayanta tafito suka kaemata mota suka nufi gidansu su innan sukayi musu sallama sannan suka dauki hanya kuma mimi ansami abinyi abinda take so kallon duniya idanunta nakan hanya, GOMBE Meenal ce kwance kan gadon asibiti gefenta kuma wata matace azaune tazuba mata ido ba tsammani taga meenal din tasoma bude idanunta tanadan motsi harta bude idanunta tangaran matar kuwa tadurkusa ta rungume meenal tana kukan dadi tasoma magana sedae me? sam bahausa matar takeyiba fulatanci take yarawa tana mika godiyarta ga ubangiji daya tashi kafadun yarinyarta,tamkar zuciyar meenal zata fito waje haka takeji duk abinda yafarune yashiga dawo mata sedae tunaninta yatsayane atime din da mutuminnan yake bata ruwa sedae tafarka taganta anan yanzu matar tana dagata tajuya suka hada idanu komae na na tunaninta yatsaya saboda tsorata ita kanta matar seda tafuskanci hakan karkashin zuciyan meenal addu ah take sosae saboda wannan matar tarike fuskanta itace take yawon zuwa mata a mafarki tana kuka tana mika mata hannuwa rintse idanunta tayi tana cewa dama mutuwa nayi kenan gashi naga wannan matar shikenan nabar gidamu har abada tana wannan tunanin ne muryar wata yarinya tadoki kunnenta wadda tashigo yanzu bazata wuce shekara shadaya da rabiba sewasu twins yara maza dasuka biyota abaya kyawawa dasu masha allah sukuma bazasu wuce shekara 7 bah zuwa 8 yarinyar tana cewa UMMI! wae haryanzu yayarmu bata farkaba jin yarinyar tayi hausa yasa meenal saurin bude idanu tana kallonsu ganin hakanne yasa yarinyar farin ciki mara misaltuwa taje takwanta akanta tana murna kamar me yaryarmu munyi kewanki kullum cikin kuka muke munrasa inda zamu tsoma rayuwarmu ina fata babu abinda azzulam can sukayi miki koh, shiru meenal tayi musu taki tankawa kowa sedae ido kawae datake binsu dashi jikinta asabule tamike tsaye tana kallon yayar tasu kamar tayi kuka takalli matar tace UMMI meyasamu yayar mune bata magana hannunta tariko tace hasana kiyiwa yayarku uzuri bata gama dawowa dae daeba bata juma da farkawaba twins suna gefe sunzuba mata idanu suma, idonta tafda kwalla tace allah sarki yayarmu allah yasaka miki yabaki lpy kokarin mikewa zaune take ummin ta temaka mata ta tashi tasa mata pillow abayanta tazuba mata idanu ko kiftawa batayi hasana takalla tace kira abbanku kisanar masa yayarku ta tashi bamusu kuwa tadauko waya cikin jaka, ummin mamaki take yadda meenal take kallonta haka hannunta tariko sosae tana cewa kiyi hakuri MIMI kinji kinriga kindawo gida kiwantar da hankalinki babu abinda zesameki,wata faduwar gabace tasami meenal jin an ambaci mimi seyanzu komae yadawo mata tuni tafara ambaliyan hawaye tana girgizawa matan kae ita yanzu taya zata ganar dasu ba ita bace mimi seyanzu ta tuna itace matar datakejin kukanta awaya yanzunkam mamakinta yakare ta tabbatarda ba mutuwa tayiba to amma wacece wannan matar rarrashinta ummin tasu tashigayi dakalami da dada masu kwantar da hankali itama hassana gefenta tazo tazauna tace sorry kinjee yayarmu nakira abbanmu yanzu zezo kidena kuka kinji tasa hannu tana share mata hawaye haka twins kafafunta suka rike suna cewa pls yayarmu karkiyi kuka, tunda meenal take bata tabajin nutsuwar zuciya da farinciki irin wannan bah ganin ita kadae sukema wannan rarrashin ga nuna kauna da kalawa hakanne yasa hawayenta kin tyayawa duksetake ganin abin wani iri yau ana mata irin wannan rarrashin bandaki tace musu zata shiga don haka ummin tasu ta rakata bakin bayan tatsaya daga kofa tana jiranta, Tana cikin bandakin abban nasu yashigo da sallamarsa kana ganinshi kasan yana cikin farin ciki suduka sukayi kanshi cikin fillacin yasoma magana shima cayake ina mimin take ummin tanadaga bakin bayin tayi masa nuni da hannu alamun tana ciki hasana tace abbanmu yayarmu ay bata magana,itama fulatancin tayi masa magana,meenal tana daga cikin bayin tana jiyo yadda suke magana sedae sam ko kalma daya bazatace ga abinda suke tattaunawaba don sun juye harshensu tuni idanunta yadinga tsiyayar hawaye tagama abinda takeyi amma takasa fitowa kamar tasa kuka catake ya allah wani irin mutanene wadan dan ka kawoni cikinsu bansan mesuke cewaba ganin batada mafitane yasata dole bude kofa tafito, ummin takamota har kan gadon tazaunar da ita, sannan tayi mata hausa tace mimi inane yakemiki ciwo yanzu,girgiza mata kae tayi alamun bakomae, abban nasu yace to alhmdlh 'yata tadawo gida lpy makiya kuma sedae suji kunya ankusa kama wadanda sukeda sa hannu a saceki mimi alkawari nayi bazan taba kyale kosuwa sukayi mana hakaba wlh, kuma tunda allah yanufa kin farka ayau zamu koma gida bazaki kara kwanan hospital dinnan bah duka gaba daya gari yadauka 'ya ta tadawo so nan babu wani tsaro gara mutafi gida acan hankalina zefi kwanciya sam umminsu batayi masa musuba yana maganar tana hadawa meenal tea mekauri a cup tabata tasha takoshi sosae taji kwarin jikinta dama ga drip ansa mata ba iyaka, GARIN KANO koda suka isa janbulo gidan alhj abubakar horn biyu gateman yabude musu gate suka shiga gidan bayan sungaisa da megadin, nana tana kwance tadora kanta akan cinyar auntien tasu ita kuma auntien tana karatun jarida,koda suka shiga parlour din nana tamike cike da mamaki tana kallonsu sunshigo bawani hayaniya, aduk sanda meenal tayi dawowa irin wannan tunkan motansu ta tsaya zata fita aguje tayi ciki tana kwala musu kira sallamar dasukayima kasa amsawa nana tayi saboda mamaki se auntie ce ta aje jaridar ta amsa musu,koda suka hada idanu da mimi zuciyar tace tawani irin jarbawa saboda yadda tayi mata kwarjini ga girman dataga takara dakuma cika ido babu fuskar data fado mata seta safiyya,hakadae ta daure aka gaggaisa mujaheed yana dariya yace nana yadae meenal din taki tacanza mikine kikayi poster haka kina kallonta da mamaki nana tace sosae makuwa tacanza ya mujaheed wannan ba halin meenal bane akwaedae wani abu ganima nake kamar ba itaba shida mummy sukasa dariya kana yace lallae nana abinnaki aziminne toke meenal kinji mimi nazaune tadanyi guntun murmushi don ita tunda suka shigo tajee mutanen basuyi mataba duk zuciyanta acunkushe yake mussam irin kallonda dataga auntien nayimata, nandanan aka cikasu dakayan ciye ciye mimi ruwa kawae ta iyasha saboda bata yanayi me dadi nana kuwa takasa dena kallon mimi saboda mamaki auntie duk wannan baragadar babu komae kasa jurewa nana tayi tace waike meenal lafiyanki kalau kuwa suduka kallo seya koma kanta murmushi tayi mata again tace lafiya kalau fah ba abunda kedamuna tafiyan nance tasa kaina yana ciwo ko magana banasonyi amma bawani abu mekika gani,wlh ban yardaba shine abinda nana tace kawae, sosae auntie take mamaki yadda mimi take magana da aji cikin yauki amma saboda abindake cimata zuciya ko kulata takiyi hirarsu suke da mummy ita kuma nana sunayi da mujaheed hakanne yasa mimi juyawa takwanta akan kujera ta lullube fuskanta da mayafinta, Suna cikin fira munaheed yakira muhammad vidio call yana shaida masa aysun iso aje wayan yayi yadda zega kowa suna gaisawa mummy ce tafara tsokanarshi tana cewa kadae zama dan can can ho dae ko muhammad kememe kodan hotunma kaki zuwa kamana,mujaheed yana dariya yace lallae mummy ina zedawo bakisan yadda kasar nan take gara masabane kilama acan zesamo muku sirika yajuya ya kannewa muhammad ido yana dariya,mummy tace a ah wlh allah karya biye bakinka bakada kirki allah yatsaremu duka takae masa yagoce, auntie ma tayi dariya tace tomeye aciki kae muhammad kataho tasu inyaso shima mujaheed kataho masa datasa kuyi anko bashikenanba, yakuwa gimtse dariyarsa yace haba auntie wlh allah yakiyaye ni inada wadda zan aura,ay nana kamar an mintseleta tamike tazauna gefenshi tana cewa wow ya mujaheed wacece wannan fadeta naji don allah,hararnta yayi yace to uwar gulma bangayawa su mummy bah seke muhammad yace aikin banza to kada kafada mana,mummy tace shakuriminka muhammad aynama santa ko ince munma santa, dasauri mujaheed yace pls mummy kiyi shiru mana, muhammad yace aishikenan kuma munma dena damun kanmu tunda munsanta abinda zamu ganta meye nadamuwa kada kafada kila bata azziki bace kake hana musani mudae indae batayi manaba dole acanza, dariya sosae mujaheed yayi yace bakasan kowaceceba zaka fara yimata rashin ta ido inda kuma kanwar kacefa? nepar kan muhammad ne yadauke haka itama auntie dakyar yatattaro nutsuwarsa muhammad yace banganeba, Zaka gane nan gaba kadan cewar mujaheed. Tambayarsa yayi yace ina meenal ne nibanjita tunda muka fara waya, tana kwance mimi tana kunshe dariyarta don bakaramin dadi hirar tasu takeyimataba, kallonta mujaheed yay yana murmushi yace kaganta tana hutawa takwaso gajiya murmushi muhammad yay metarin ma ano ni dayawa yace to nunamin ita nagani waca irin gajiyace haka dazatasata shareni, Wayan yadauka ya isa inda take kwance tanajinshi tarufe idanunta ya yaye mayafin fuskanta tabayyana kafansa yadora kan tata yada yatsansa babbashi yana mata susa a tafin kafan nata tanata mamar mamar da idanunta kana gani kasan ba bacci takeyiba dariya take shirinyi saboda abinda yakeyi mata tasaki murmushi har dan dimple dinta ya lotsa abinda muhammad yakeson tabbatarwa dama kenan wani irin gumine yake tsatstsafo mishi mikewa tayi tari kafan nashi tace kae yayana kaga katasheni ina bacci tayi maganar cikin shagwaba shikuma yarankwafo saetin kunnenta yace baki gaisheda yayankiba yay maganar harda dan cizar mata kunne muhammad ya lumshe idanunsa time din tadago tace yaya ina wuni, bekara bari yaji mezata ceba yakashe wayan.... TAKU A KULLUM NANA BMB. 08147110349 [7/28, 8:20 AM] Nana BMB: πŸ’πŸ’–πŸ’πŸ’– RABON KWADO.... BOOK 2 NA NANA BMB page 23-24 Muhammad jiyayi karatun yafice mishi a rayuwa gida kawae yakeson komawa domin tabbatar da raenin hankalin da wannan mimi din keshirin yimasa shin ya akayi meenal zata koma haka tabbas ba ita bace to ina takaemin meenal dita ya akayi koea yakasa ganewane kodae nine bana gani dakyau kae ina baze yiwuba sam kasa nutsuwa yayi yanata zagaye a room dinsa zuciyarsa na azalzalarsa yakoma Nigeria,koda yakashe wayan mimi kallon mujaheed tayi da mamaki shikuma yadan tabe baki yace yayi fushi seki kirashi kibashi hakuri,duk abinda sukeyi auntie nakallonsu tagefen ido rabin hankalinta nagun mummy rabi nagunsu mimi, nana ma matsawa tayi kusa dashi tace wae ya mujaheed son meenal kakeyine shiyasa tayi wannan nutsuwar dabata taba yiba,murmushi yayi yadungure mata kae yace ina ruwanki ne,mummy tace kyaleshi nana intayi tsami fah kowa seyaji rabi dasu abinki,wani irin tukukine yake tasowa auntie amma tana dannewa hab da magrib shima daddy yadawo gida ko sama behauba sabuwar hira tasake barkewa sedae kasan zuciyanshi fal take da mamaki ganin mimi shiru shiru tunda suka gaisa bata kara maganaba ga girman dayaga takara, inda taga dazu sunshiga dominyin alwala itada nana yasata ganewa nanne dakinsu sunata zuba ta silale tanufi dakin tana tafiya kamar bataso jitake kamar za a cemata ina zaki, Koda tashiga tatsaya tanata bin dakin dakallo kana ganin tsarin dakin zakasan na mutum biyune kae tsaya wanka tashiga tayo koda tafito setarasa wacce ce wardrob din meenal koda tabude ta tan taci karo da teddy guda manya daga kasa wannan ne ya tabbatar mata itace ta meenal kuma ga rubutun dataga anyiyyi an manne a wardrob din duka tabisu tana karanta tana murmushi rabin rubutun akan ya muhammad dintane se nana seyanzun tasoma fahimtar irin shakuwar dake tsakaninsu da muhammad simple kaya bacci tadauko tadan murza mae da dan turare tasa kayan seda tagama zagayenta adakin sannan takwanta bacci, Sedare Dr yasallami meenal suka fito dakanta take iya takawa abban nasu yarike mata hannu abinda yabawa meenal mamaki shine ganin motaci datayi birjik abakin hospital din ga bodyguards sun zagayesu kallo daya zaka musu kasan nera na aiki gurin motocinnan biyu ta bodyguard sebiyu tasu atsakiya sekuma biyu again abaya ta guards din aka bude musu suka shiga ummin tasu da mimi dakuma abban nasu su hassana kuma suka shiga tagaba motan guards din suka antaya motocin suka soma tafiya nan danan meenal tatsure ganin tsaron da ake musu meenal azuciyanta cewa take ya allah waca irin rayuwace wannan kuma allah sarki iyayena yanzu nayi muku nisa taya zan kubuta a hannun mutanen nan dole nagaya musu gaskiya life dinta kawae take tunani tabaya yadda taketa ikirarin intabar kano bazata dawoba ashe tayi maganar bakin bakin mala iku shiyasa allah yacanza mata rayuwa,lumshe idanunta tayi tanadan cizar lips dinta nakasa don kuka keshirin kwace mata jitayi ummin tarungumota jikinta tana da da rarrashinta don taga halinda tashiga taji dadin hakan sosae meenal shiyasa takara shige mata koda suka isa gidan ko ince estate seda meenal tamike daga jikin umman tasu securities ne tako ina daga sama an kafe wani symbol an rubuta WELCOME TO GIDAN FULANI! se walwalin haske rubutun yake abin kayatarwa, wangamemen gate din securities suka bude musu suka shiga tunda meenal take bata taba ganin gida irin wannanba anshiga gidan amma haryanzu tafiya ake ga bene wani kan wani hakanne yasata rintse hannayenta zuciyanta na tsananta bugawa kodae gidan 'yan yankan kae allah yakawoni ne? tunani take kala kala harsuka isa parking space sukayi parking suka fito ko ina haske take gani tunda suka shigo amma sedae inda suke tunkarane babu haske ko kadan kam kuwa takara rike hannun ummin tasu tanata raba idanu koda suka inda duhun yake kamar walkiya taga haske yakawo jama ar gurinne yasata firgicewa tana shirin guduwa rikon da ummin tasu tamata yasata kasa matsawa daga inda take,duka jama ar gurin suka dauka da tafi suna fillaci cikin nishadi da farin ciki daya bayan daya kowa yake zuwa yana welcoming dinta ido kawae take bin kowannensu dashi mutanen abin burgewa kana gani base angaya makaba kasan family dayane hardasu ummin da abban nasu sukayi welcoming dinta baki saro take kallonsu sunata mata murna da dawowa mutanen sun burgeta matuka har smile takeyi sedae sam batajin abinda suke cewa, haka ummim tasu takama hannunta suka nufi part dinsu 'yar kauye meenal tazama ganin haduwan gidan nasu mimi sekace a London tsarin gidan nasu har dakin mimi takaeta tace zauna na hada miki ruwa kigasa jikinki sosae gefen makeken bed din mimi tazauna wani sanyin kamshi nadukan hancinta dakin ya tsaru komae nadakin peach colour ne da butter milk tasau baki tanata kallon dakin ummi tafito daga bathroom din tatsaya tana karantarta seda takare mata kallo sannan tace meenal kitashi kishaga wankan koh saurin juyowa tayi ganin irin kallonda takeyi matane yasata sunkuyar dakanta tace to, fita daga dakin tayi tace kiyi kishirya kikwanta kisamu isasshen bacci don kinsan gobe hardare baki bakarewa zasuyiba, da kallon mamaki meenal tarakata harta fice taja mata kofan koda tashiga wankan tajuma acikin kwamin wankan don sosae tajee dadin ruwan sannan tafito kods tabide wardrob din tsarin kayan yaburgeta ga kamshin dake tashi tadauki sleeping dressed tasaka kana tayi sallah gurin aje sallayama zamanshi yake seda tagama addu inta sannan taje tamurza lotion me kamshi takwanta tunani kala kala ne a zuciyanta tagaza yaddanma kanta ita meenal itace awannan life din wani irin sanyin ni imane yake ratsata har bargon jikinta tana wannan tunanin bacci yadauketa, WASHE GARI Su mimi suna kwance kana gani zakasan baccin baya wani yimata dadi saboda ta takure gure daya haka auntie tashigo tasamesu da asuba akayi sa ah kuwa fuskar mimi itace awaje takarasa harda sandarta kuwa tazabga mata mari ta tashi firgigit tana kallon auntien hawaye na ambaliya a idonta don bakaramin zafi tajiba,nana ma afirgicen ta tashi ganin abinda yafarune yasa cewa haba auntie metayi miki kuma daga dawowarta cikin fushi tace zaku tashi kuyi sallah ko yaya tayi maganar tana huci suduka shiru sukayi tafita tanata masifa ita kadae abin sosae yadaurewa mimi kae tomeyasa tamareta haka? TAKU A KULLUM NANA BMB. 08147110349 [7/28, 8:20 AM] Nana BMB: πŸ’πŸ’–πŸ’πŸ’– RABON KWADO.... BOOK 2 NA NANA BMB page 25-26 Tunda meenal tayi sallah asuba bata koma bacci bah tanata azkar har gari yasoma yin haske sannan tashafa tamike tacire hijab din tazauna gefen bed tana ganin komae yazame mata nadaban a arayuwarta iskace taketa daga labulaye ga sanyin asuba daya ratsa bedroom din hakanne yasata mikewa tabude labulayen haske ya gauraye dakin cike da annushuwa tabude kofan bayan inda aka aje furanni masu kyau dasuka zagaye gurin abin sha awa iska nata fificeta tana sauke ajiyan zuciya se daga mata gashi take seda tagama kallon furannin sannan tasoma kallon tsarin gidan tana hangen ragowar benayen abin sha awa komae cikin tsari tana murmushi tace ya allah wani irin gidane haka ka kawoni me abin me abin birgewa da mamaki tashagalta da kalle kalle taji ana jifanta da wani abu hakanne yasata saurin kallon kasa domin ganin menene taga wasu furannin ne ake jifanta dashi peach colour da alamu dae kalan da mimi kekauna kenan ganin hakanne yasata saurin karasawa tarike glasses dinda yazagaye gurin tahangi wani saurayi kuwa yana kan mota atsaye yana rikeda wani dogon basket dayake zuba furannin yana watsa matasu dukda tazararsu hakan behanata ganin haduwar guy dinba black beauty sunkuyawa tayi tana kwasar furannin tana shaka kamshinsu sosae yaymata dadi, Muryarshice takatseta dataji yana WELL COME BACK MY SWEET MEEMS! dakarfi yake maganar yadda zata jiyoshi aykuwa se yashe baki take tanan tsaye taji anriko mata hannu dasauri tajuya taga ashe ummi ce zuwa tayi ta leka tawatsawa saurayin dakuwa tace anshi naka "BASSAM" hannun nata tarike tace muje kishirya nazaci zanganki kinshirya kinbiyewa bassam, cikin jin kunya tagaisheta ta amsa tace kishiga kiyi wanka kishirya kinji koh, batare da musuba tace to ummi, seda tashiga wankan sannan tabude wardrob dinta tadauko mata wani tsadadden less fari tass dashi se shekin kyau yake sannan ta ajiye mata akan bed tafita, bawani bata time tafito tazauna gaban dressing mirror kayan shafan kawae take kallo nagurin da turaruka tama rasa wadda zatayi amfani dasu su " su meenal an zama 'yan kauye hhhhh" tajuma tana shafe shafenta sannan tasoma fesa spray kala kala tasaka kayan na mimi sedae rigan bata kamata yadda ake soba taso tayi mata yawa, tana gama saka kayan taji anayi mata knorking seda tazauna tabada izinin shigowa, hassana ce tashigo hannunta dauke da tray nakayan breakfast murmushinta ta fadada tace hasana kece, cikin jin dadi takaraso ta aje tray din gefe tace morning my besty, morning my love sis ykk ina twins, zama hasana tayi gefenta tace wow yayarmu kinga yadda kike walwali nakyau kuwa gaskiya kinfi dakyau tabdi kinganki kamar amarya tubar kallah, lallae suya bassam akwae zuba shirme yau dama najishi yafara ay, kiyi kiyi break din yayanmu yanzu yaya zara zata hawo yimiki kwalliya fah! meenal haka tafara tunanin waca irin kwalliya kuma za ayi mata abinda tunda take arayuwarta ba ah taba yimataba hannu takae tafara daukan kofin tea hasana tarike hannunta tace a ah kifara shanye madarar shanun cikin dayan cup din tukun da dumintama tunkan tayi saunyi dama ummi tace bazaki kula madarar bah kifara da ita tukunna, bansan meyasa bakisan shan madarar nan yayarmu?galala meenal takebin glass cup din madarar da kallo batace kalaba tadauka tashanyeta,kadan taci abin karin shima tea din iya rabi tasha cup din ta ajiye da mamaki hasana tace badai koshi kikaeba, meenal tace haba hasana aynamaci dayawa bakiganiba, Hasana tayi dariya tace kae yayarmu ahakane kikaci dayawa kallifa ko rabi bakiyi bah, itadae meenal kishigida tayi akan pillow tana kallon hasana tana zuba mata murmushi najin dadi tanason hasana sosae wani farin cikine takejin ya mamayeta ganin irin gatanta tan dasukeyi abin yana mata dadi, itakuwa hasana mamakine yakamata ganin yadda yayar tasu tacanza semagana take mata cikin faran faran da fara ah sabanin da dako magana ma batasonyi, Tasauke ajiyan zuciya tace to yayarmu bari nafita da abinci sena turo miki yaya zarah din nasan ketake jira tamike tadau tray din tafita tanamejin dadin sauyawar yayar tasu tana fita meenal tayi wani irin birgima a kan bed din tana cewa ya allah wani irin gatane wannan nake gani arayuwata nagode maka daka sauyimin rayuwa me dadi " to me karatu lamarin meenal aziminne tamantama da yayanta da masoyinta" koda hasana tasoma saukowa daga steps din benen tana fara ah, hango bassam datayine yasata daure fuska yana zaune a parlour yaharde kafa sunata hira da yaya zara, Tunda tasoma saukowa daga steps din yake kallonta tana sanye da jeans blue yakamata se riganta pink tazo mata gwiwa tayi kyau sosae tadan kamata rigan hakanne yasa dan kirjinta daya soma tasawa bayyana ga hulan kanta ma pink tayi kyau sosae tana tafiya cikin takamarta da nutsuwa ita alan dole kada a raenata jiyake kamar yaje yarufeta da duka batasanma yanayiba seda ta ane tray din kan dining sannan ta dawo tazauna itama taharde kafa zara da bassam hira suke cikin fulatanci gefe gefe suke saka turanci sam basa hausarma, cikin shan kamshi tace yaya zara yayarmu tagama, ta amsa mata da to seda suka gama tattaunawarsu tadauki jakarta tahaura saman, ita kuwa hasana batasan ma me akeba buga game dinta take a tap dinta kawae sejin tsawar data razanata tayi dasauri tamike zata gudu kuwa yace lallae yarinyar baki iya gaisuwaba koh? jin hakanne yasata dawowa cikin tura baki tace ina kwana kawae yaja tsaki yace stupid girl dallani kawomin breakfast tunkan nazo na anshi wayan na faffasata inga ta maitar game, idonta tafda kwalla ta aje wayan nata tanamejin haushin zaginta dayayi taje kan dining din tadauko masa ragowan da meenal tarage tazo ta aje masa tunkan takarasa mikewa yakuma zuba mata wata tsawar ashema kin raenani har haka nizaki kawowa saura nayi miki kama damecin saura almajiri kika maidani kome, Cikin zucuciyar hasana tana cewa ba almajiri bane kae kuma wlh sekaci, arazane takarasa dagowa tana kallonshi alamun maganar tasa ta tsorata ta ta dafe kirji tace ya bassam yanzu ragowan yayarmune bazakaciba kyamarta kakeyi kenan to wlh sena gaya mata galala bassam yake kallon makirci irinna hasana tajuya dasauri tasoma hawa steps din,dagudu yakarasa yafisgota saura kadan tafadi yariketa ya wancakalata kan kujera yana cewa uban wayace miki nace bazan ciba,da hannu ya nunata yace wlh kika haura samannan sena lahira yafikijin dadi, yajuya cikin takaeci yazauna yasoma tura abin karin yana nadamar sata takawo mata abin kari dayayi ga tea din ya huce kuma gashi rabi haka yashanye hasana zuciyanta kal dafarin ciki ta kuntata masa kuma taki tafiya saboda kada yatashi yagudu yakici hka ya cuccusa yanamejin zafinta a zuciyanshi yadauki wayoyinsa yafice daga gidan hasana don dariya harda kifawa da tsallen murnarta tanufi dakin twins donyi musu wanka tasan yanzu sun tashi suna zuba rashinji.... TAKU A KULLUM NANA BMB. 08147110349 KUYI HAKURI MUTANE NAH KUNJINI SHIRU KWANA BIYU INA BUSY DAYAWA NE. [7/28, 8:20 AM] Nana BMB: πŸ’πŸ’–πŸ’πŸ’– RABON KWADO.... BOOK 2 NA NANA BMB page 27-28 Fitowar mimi daga wanka kenan wayarta tasoma ruri ita tamantama dawata waya a jaka batabi takan wayarba tazauna kan sofa tana fuskantar mirror kome ta tuna kuma tamime taje ta dauka wayan a time din ma kiran yayanke kawae taje tajonata a charged nana binta da idanu kawae take cikin mamaki tace waya kirakine? mimi bata tanka mataba illah zubawa fuskanta idanu datayi cikin mirror tana shafa inda auntie tamareta haryanzu abin mamaki yake bata,tana nan zaune wayar tata takuma ringing nana nazaune tayi fushi dama saboda taimata magana taimata banza,tahanzarta zuwa tadauki wayar don ganin mekira nana ganin mekiranne yasata tasau baki tace yanzu nadiyace take kiranki dama shine kikaki daga wayan itadae mimi kallonta kawae take ta mirror harta daga wayan suka gaisa taji tana cewa jiya sukazo ay wlh nadiya ba wayanku kadae tadena dagawaba harda tamu hatta ya muhammad yayi fushi da ita sabida bata kiransa ay gata dae bari nabata wayan, nana takaraso tamika mata wayan ta kara akunne tace hello! haba my auntie meyay zafi akasamu a site kwata kwata anmanta damu cikin sanyinta mimi tace am sorry nadiya wayanane yasami matsala shiyasa kika jini shiru, Nadiya tace kuma ko ki kirani ashe tunjiya kika dawo ga ya yousep nan saboda rashin kiranshi dakike bashida lpy yana kwance, zuciyar mimi tawani harba don ita harga allah tamanta dashi cikin tausayi tace pls kiyi masa sannu kinji, aww inyi masa sannu ba kikirashiba, zan kirashi mana nadaice kiyi masane yanzu, tom ay anjima zamuzo yimiki sannu dazuwa ma, wae kinshirya komawa school kuwa saura 3 days fah akoma donnaji bauchi ya ansheki hutu yazauna miki irin wannan magana haka kamar bakyaso hatta voice dinki tacanza, Mimi tae murmushin karfin hali tace kae nadiya kinada abin dariya sekunzo dae din kawae tayanke kiran ta aje tana tunanin wani school kuma zata fara zuwa itakenan zamanta awannan gidan katse mata tunani nana tayi dacewa meenal waye bashida lpy jin yadda tayi maganar ne yasa mimi dagowa taga kamar zatasa kuka cikin nazar tarta tace ya yousep ne bashida lpy, nana tadan cije tace allah yabashi lpy, wata tambayar takuma cillo mata meenal ina fata dae bawanda yasan kina soyayya dashi a can ko, da mamaki mimi take kallonta tace banganeba?cikin jin haushi nana tace uwar baki ganeba yanzu duk gargadin danayi miki kinmanta kenan ko sun tashi abanza kinsan allah maganar nan tafaso banga abinda ze hana daddy yimiki aureba garama ki hankalta, Kuma meye tsakaninki da ya mujaheed ko kina nufin tun kina 'yar mitsitsiyarki dake zaki fara tara samari,baki sake mimi take kallonta seyanzun ta tabbatar da abinda take tunani wato tanason yousep kenan shiyasa take hakikancewa, dauke kanta tayi tacigaba da murza manta ajiki seda tadau lokaci sannan tace babu abinda yake tsakanina da ya mujaheed inbanda my love dina ya yousep, dogon tsaki nana taja kawae tamike tabar dakin, itakuma harta gama shirinta tana tunanin wani irin gidane wannan allah yakawota koda tafita tasamesu harma sun fara breakfast kallo daya mummy tamata tasan tana cikin damuwa amma batace komaeba shikuwa daddy kasa hakuri yayi yace wae meenak meyake damunkine tunjiya bakida walwala kujerar kusada mujaheed taja tazauna kanta akasa tace daddy babu komae, kallon mummy yayi yace saratu menene yake damunta, itama mimin take kallo tace nidae bansan wani abu yana damuntaba lpy kalau muka dawo bansaniba ko akwae abinda batason asanine, caraf auntie tace babu abinda yake damunta donda da akwae wani abu meenal dae bazata iya shiruba seta fada, kallon tuhuma daddy yasoma binta dashi amma seta dauke kantama tacigaba dacin abin karinta,mimi bata zuba nata abin karin bah tasomaci tareda ya mujaheed abin yabawa daddy mamaki yana ankare dasu da irin wasannin dasukeyi kasa jurewa yayi cikin tsawa yace MEENAL! jikinta nabari kuwa tadago a tsorace cikin fada daddy yace wani irin shashancine wannan kikeye haba mujaheed dagirmanka meenal zata baka abinci abaki to daga rana irinta tayau karnaji kar nasake gani don batsari bane wannan,da mamaki mummy tace yaya shin menene yanzu don meenal tabashi abinci abaki idonta tafda kwalla tayi maganar jin sabon al amari datayi gurin yayan nata, kallonta yayi yace to kada su sake dagayau banason nasake gani komenene ma daga yanzu inyana bukata yasaka nana tayi masa amma banda meenal, kallon mujaheed yayi yace kaji dae nagaya maka, jiki asanyaye yace to daddy,bejira komaeba daddy yawuce dakinshi nana tabudi baki zatayi magana auntie tabuge mata bakin dole tayi shiru mummy madae mikewa tayi tanufi masaukinta taname mamakin yayan nata dayake shirin sauyawa lokaci daya, Zuciyar auntie kal da farin ciki don sosae taji dadin abinda yafaru tace to mujaheed kadaeji seka kiyaye don kaga kabatawa kawunka rae,kamar yay kuka yace shin auntie meye laefina anan haramunne donnayi mu amala da meenal, azuciyarta catake yaro dama kadena kame kame kadena tunanin shegiyar yarinyar nan don batada azzikin shigomana cikin family, afuskanta kuwa seta nuna alamun tausayi kayi hakuri kabarni dashi zanyi masa magana inji meye damuwan, jikinshi asanyaye yatashi yanufi garden itama mimi da zuciyarta take cikin rudani tamike tabi bayanshi, auntie tabita da harara azuci tana cewa bakiga komae bana yarinya, Nana tace insha allahu ya mujaheed son meenal yakeyi nidazaewa daddy magana komae zezo dasauki donnasan rashin fahimtace tasa daddy yay masa ha.....Tasss nana taji saukan mari tadago kuwa dasauri tana kallonta zatayi kuka wlh nana nakumajin maganar nan takuma fitowa abakinki sena sabamiki tunda nafuskanci bakida hankali bakiji abinda daddynki yafada bah keda mujaheed din yake ambato amma zakizo kinamin shirme, ay nana mantawa ma tayi damarin da aka mata tamike cikin tashin hankali wae kina nufin inso ya mujaheed wlh bazan iyaba bazan taba sonsaba shima kuma baya sona meenal yakeso meyasa zakuyimin haka bazan iya auren ya mujaheed ba wlh sama tahaura itama tana kuka, takaecin duniya ya ishe auntie tana zaune tana tunanin wani rin haukane yake damun nana.... TAKU A KULLUM NANA BMB. 08147110349 [7/28, 8:20 AM] Nana BMB: πŸ’πŸ’–πŸ’πŸ’– RABON KWADO.... BOOK 2 page 29-30 Har cikin garden mimi tabishi tazauna a gefenshi murya kamar zatayi kuka tace yayana kayi hakuri nasan daddy yabata maka rae ina tunanin be fahimci menene a tsakanin mubane shiyasa yamaka haka, mujaheed idanuwansa dake lumshe yabude yazubasu akanta yace my dear nayi tunanin haka so abinda yadaure min kae meyasa yace sedae nana tamin abinda nakeso bakeba, hawayen da mimi take makalewane yazubo mata murya a raunane tace wlh yayana inajin tsoron kar daddy yace nana zebaka ka aura baniba,saurin toshe mata baki yayi dahannunsa yana girgiza mata kae yace no impossible kada ki kara furta wannan sabon abinda baze yiwu bane kike fada meenal insha allah nine mijinki nahar abada lokaci kadan nake jira nabaiyana komae hawayenta yasa hannu yana sharewa dayan hannun nasa kuma yarike nata hannun yana murzawa ahankali yana kwantar mata da hankali don yaga tafishi rudewa ma, Duk abinda akeyi nana tana daga room dinsu tana hangensu ta window zuciyar za kal da farin ciki tana tunanin masoyinta yousep takusa mallakarsa, Kwalliya auntie zara ta tsarawa meenal ta nada mata hadadden dauri masha allah bakarya meenal tayi kyau sosae zara tasau baki take kallonta tana mamakin irin wannan kyau data kara haka ita kanta data kalli kanta a mirror seda tasaki smile najin dadi ganin yadda kwalliyan yamata kyau turaruka takara fesa mata ta dauko mata daya daga cikin sarkokinta na gold tasaka mata saboda taga bata saba tafito doss da ita kamar amarya zara takamo mata hannu suka fito 'yan biyu naganinta sukae gunta cike da murna haka itama takarasa garesu tana fara ah tace twins seyanzu nake ganinku tadan turo masu baki tace ni nayi fushima tunda bakuje inda nakeba,murnushin jin dadi sukayi sukace am sorry yayar mu minyi missing dinki fah sosae ummi ce tace bazamu gunkiba sekin huta tana murmushi tace to ay nahuta yanzu kutaho guna takama hannunsu suka gefenta, hasana nazaune mamaki yacikata wae yau yayarsu ce take tattalin kannenta haka ita kuwa umminsu mamakine yacikata ganin wani kyau da diyar tata takara tanata hira da twins abbansu yasauko shima cikin kayansa na alfarma waya yake harya zauna amma hankalinshi nakan meenal yazuba mata ido yana murmushi, yana ida wayar kuwa tunkan yay magana ta zanzaro kasa cikin ladabi tace abbanmu ina kwana mamakine yakamasu ganin sabon ladabi gurin meenal wanda ada daga sama ake mika masa gaisuwa twins naganin haka suka sauko suma suka kwashi gaisuwa hasanama dole tasauko tayi ladabin da yayarta tayi, cikin jin dadi kuwa ya amsa yaname cewa kae diyata irin wannan kyau haka masha allah sekace amarya kamar ba jinya kika tashiba kamar irin anzo miki fadan nan za ah tafi dakin miji suduka sukasa dariya baki yarike yace lallae yau bassam akwae shirme kenan inyaga amaryar tasa aikuwa kada kubari yaga kwalliyar nan seya biya zara kudin kwalliyarta, ita meenal tunda taji ankirata da amaryar bassam se nepa din kanta yadauke azuci tace to tunda bani bace meye nawa nadamuwa tasaki ranta kuwa, abbansu yana cikin yin maganar bassam suka jiyo muryanshi yashigo yana waya ya tunkaro parlour din koda isowarsa sukayi 4 eyes da meenal dama hanyar tazubawa idanu besan sanda yasaki wayan hannun nashiba daga tsaye ta tarwatse daskarewa yayi atsaye yana kallonta dakyar ya iya furta my precious,yanda yay maganar yana dafe heart dinshi suduka sukasa dariya harda ita wanda dariyar tatace takara dulmiyar dashi, ahankali ya iya taka kafafunsa yazauna gefenta yana kallonta kamar yacinyeta ganin hakanne hasana tace haba ya bassam kallon yayi haka mana karage mana wanda zamu kalla muma, nan danan annurin fuskarsa yadauke cikin jin haushi yace ke kikiyayeni fah karki kara shiga tsakanina da matata nida abata kice inragewa wasu kenanma batada matsayi agareni keda bakyason kiga narabeta saboda bakya sona kominyi aure dama kada naga kafarki agidanmu, ummi da abban nasudae dariya suke yana cewa to tom an jerry zaku fara cikin tura baki hasana tace dama meze kaeni duk iya kiran dazakumin kuwa kuma yayarmu fushi take dakae tunda bakazo welcoming dintaba seyanzu,meenal kamar jira take kuwa ta tura baki gaba tace eh mana ni baruwana dakae tunda nadawo seyanzu nake ganinka inacan najiyo kamshin lahira kana nan ko missing dinama bakayiba, kowa sakin baki yayi yana kallon meenal jin abinda basu tabajiba agareta duk bawanda yay tsammanin wannan furucin abakinta saboda duk irin fara ar da mimi takeyi bassam yana zuwa gurin tabarta bata kara tsanarshiba seda akayi musu baiko an bashi ita tana gama school se aure sam mimi bata kaunar bassam ko kadan kuwa biyayyane kawae takewa mahaifinta,cikin zuciyan bassam jiyake kamar yazagi hasana kozeji sanyi tawani fannin kuwa wani sanyin ni imane na farin ciki yake ratsashj jin furucin meenal saukowa yayi yay zaman dirshan agabanta kamar zeyi kuka yace my meems am so sorry sam bansan kindawo bah inacan rashinki yasani larura ki tambayima abbah kiji, kusan tsorone yakama meenal ganin wannan katon a gabanta yana magana kamar ze kuka abinda bata taba ganiba shiyasa takasa cewa komae, Murmushin jin dadi abbansu kawae yake yaname addu ah azuciyanshi allah yasa mimi tafarason bassam ne donshi yanason bassam sosae yana kaunar ganinsu cikin sahu namasoya kullum yana addu ar allah ya daedata tsakaninsu hakan kuma kullum ya gagara kusan shekara nawa ana abu daya zuwa yanzu takusa kare karatunta afara shirin aure abinda kullum yake dagawa mimi hankali kenan, kaf cikin family dinsu bawanda besan irin sonda bassam kewa mimiba ita kuma akasin haka har magana ake gaya masa akanta amma yana shanyewa,abban yace ayya mimi shalele aymasa afuwa bashida lpy murmushi meenal tasaki na mugunta sannan tace.... TAKU A KULLUM NANA BMB. 08147110349 [7/28, 8:20 AM] Nana BMB: πŸ’πŸ’–πŸ’πŸ’– RABONKWADO.... BOOK 2 NA NANA BMB page 31-32 Ya bassam anjima indae kayimin abinda nakeso to shikenan mun shirya cikin zakuwa yace aikuwa komenene fadeshi zanyi mikishi insha allah takara sakin murmushi tace tom shikenan sezuwa anjima zan gaya maka yanzu kaga gurin baki zamu cikin jin dadi bassam ya amsa mata yanajin kamar yafi kowa sa ah aduniya hasana kuwa tunani take me yayarsu zatasa ya bassam yayi anjima allah yasa wahala zata bashi,suduka suka tafi masaukin bakin mutanen abbansu nata zuwa yimasa murnar dawowar mimi ko ince meenal koda meenal taga irin manyan mutanen dake halartarsu se abin yabata mamaki tasoma tunanin shin wani matsayine haka da abbansu mimi ne seda azhar abban nasu yasamu yafita da masu tsaronsa, Hakanne yasa umminnsu cewa su tashi sushiga gurin hajiya suna tafe bassam da meenal cikin tsari abinnsu ummi tanata kallonnsu tanajin dadi har suka isa fadar hajiya matattarar jama ah bah tundaga kofa zakana jiyo maganar mutane itadae meenal nata ido se baza idanu take kamar me, koda shigarsu cikin parlour dinnan yadauki shewa suna cewa yayi mrs bassam dama sune agaba suka fara shiga tsayawa tayi kaf takarewa 'yan dakin kallo kama daga kan manyan har zuwa matasan 'yan mata da samarin cikin murmushinta tace yes kufada ku kara mrs bassam,se kowa kuma yay galala yana kallonta cikeda mamaki hasana take kallonta kodae yayarsu tasoma son ya bassam ne? bassam farin ciki yarasa inda zetsoma ranshi ma sewani isa yake yana basarwa yana kallon kowa dae dae irin yayi winning dinna,sabanin da dayake komawa abin tausayi, nandanan kuwa kowa yasoma tofa albarkacin bakinsa umminsuce tafara tsugunnawa tagaida hajiya cikin fulatanci sannan tazauna gefenta ita kuwa meenal tana zuwa tayi rashe rashe kan cinyarta tace kakus how are u? hajiya tarike baki tace mimi wato kakus nakoma kuma yanzu to nabi are u din dagudu,cikin dariya hasana tace ay hajiya da sabon salo yayar tamu tadawo,ummi tace salon iya shege uwattawa zata kira da kakus bama kaka bah, Wata dattijiwar matace gefensu zaune wanda sam meenal bata kula da ita bama tadaega anata gaisawa da 'yan dakin seda tagama gyara kallabinta taharde kafa cikin rashin mutumci tace wato mimi yayi kyau hajiya kawae kika sani tunda itace tahaifi uwarki nida nahaifi ubanki ba ah bakin komae nakeba koh! jiyowa ummi tayi wanda tinda suma gaisawa hankalinta yakarkata gurin malama suna hira tace kiyi hakuri yaya babba ashe baku gaisaba bawae don wani abu bane,cikin kallon rainin hankali tace sumaya kema bansa dakeba meye naki aciki batada bakin magana ne seku tokarna kumajin bakinki da mimi nake magana yanzu, dakin yadauki shiru wannnan yatabe baki wannan yay tsaki haka suka dingayi cikin kasa da murya bassam yace to wannan bala e wannan tsohuwa zata fara jikin meenal asanyaye tamike tazauna agabanta tana kallonta tanata regewa ummi albarka,meenal kamar me shirin aikata abin azziki ta karkace tasoma fanyara uban kuka da ihu tamkar waddaa ake duka wayyo nashiga ukuna jama ah ashe yaya babba bata sona bata kaunata ansaceni nakusa mutuwa amma nadawo tana zagina ashe dama bata sona bataso nadawo gidannan bah abbanmu kadawo kaji abinda yaya babba ta aikata sotake dama taji ance namutu,duka 'yan dakin mamakine yadaskarar dasu suka kasa cewa uffan haka yaya babba tasau baki kamar sauna tana kallon ikon allah, meenal ganin babu wanda yatankata yasata mikewa takara azamarr kukantaa harda sheshsheka tana bubbuga kafafu, hakanne yajawo hankalin gwaggo dake daki akwance tatakarkaro tayo waje tana tafiya dakyar saboda tsufa jin kukan meenal datake karayine yasata magana kae kae meyake faruwane? wanene yake kuka ay meenal da gudu takarasa gunta tariketa tana cewa kitemakeni ashe yaya babba bata sona ansaceni nakusa mutuwa amma ina daga dawowata tana gani na tasoma zagina,jikin gwaggo har karkarwa yake tajata har zuwa gaban yaya babbar tana cewa kin kyauta halimatu allah yawadaran wannan hali naki shin kekuwa seyaushe zakisan kin girma? yanzu daga dawowar yarinya zaki fara zaginta saboda bakida mutumci duk hakuri irinna safiyya gashi yau seda kika kureta to wlh bari ubanta yadawo sena gaya masa kiyayyar dakikewa 'yar tasa inbanda hauka irin naki halimatu keda jikarki saboda banzan riko irinnaki kindau abu kinsawa zuciya haryanzu yaki wucewa agurinki sumaya da mahaifiyarta kullum cikin hakuri suke dake to ki kiyayeni kinji nagaya miki bari kuma mijin naki yadawo shima, kowa jikinshi yayi sanyi don abin yagirme kan kowa dake cikin dakin, To itama yaya babba abin yasha kanta wae yau mimice da wannan makircin yarinyar da ko magana batasonyi yau itace harda ihu da kururuwa da hada makirci cikin jimami tace don allah gwaggo kiyi hakuri wlh banufina kenanba babu wani bakin nufi azuciyata ay abinda yawuce yariga yawuce gani nayi kawae tashigo ne tazauna amma bata kulaniba nayi mata maga na yaya babba tana magana tana matsar kwallah, caraf meenal tace gwaggo ay nadago zangaisheta naga tana hararata, salati gwaggon tafara tana sanar da ubangiji yaya babba kamar tayi kuka tace wlh karya take min gwaggo,zaki aikata wlh halimatu zaki aikata abinda yafi hakama bakin halinki kuma wannene bansaniba to wlh ki kiyayeni tunkan musa kafar wando daya dake itadae yaya babba juya kae kawae take tana bawa gwaggo hakuri har hajiya tasa baki amma abanza seda takarewa yaya babba cin mutumci takoma dakinta, yaya babba cikin zubar hawaye tariko hannun meenal tace don allah mimi kiyi hakuri wlh inasonki kije kibawa gwaggo hakuri kada tafadawa kakanki inya dawo kinsan fushinsa shiga uku zanyi wlh, Wani murmushin mugunta meenal tasaki tashare hawayenta tace lah yaya babba bakomae sonake dama kawae aramawa ummi cin mutumcin dakikae mata ay nasan kina sona wace kakace zataki jikarta koba hakaba yaya babba, itadae majina tasharce tana jinjina kae tace ni haryanzu nagaza yaddarwa kaina wae jikatace kemin wannan ibar albarkar, daga gefe wani saurayi yamike yace kae impossible wannan ba mimi bace gaskiya, jin wannan furucinne yasa 'yan hanjin meenal juyawa kawae takuma saka kuka hajiya tace sadiq ka kiyayeni saboda yarinya tacanza zakace ba ita bace kan tarufe bakinta kuwa meenal tasoma kwarawa gwaggo kira jiki nabari kuwa yace allah yabaki hakuri wlh kingama nafita yay waje dasauri, ragowan 'yan dakin dariya suke amma banda bassam mamakin meenal ya dabae bayeshi kallonta kawae yake yana haka kanwarsa tashigo parlour din tazauna donjin abinda kefaruwa amma seta fara mika sakonta ga bassam tace ya bassam mama ce tace nakiraka takira wayanka akashe,saurin dafe goshi bassam yayi donshi wlh yamantama wayarshi ta tarwatse gidansu mimi, kawae yamike yafita kaf kowa ranshi kal abinda meenal tasa akawa yaya babba dama ta gallabi kowa,kowa cayake yaushe mimi takoma haka kuma daga dawowarta da abinda tadawo kenan itadae bin bakunan kowa take da ido bawanda tasani ma shiyasa bata tankasu sedae karantarsu datakeyi. Misalin karfe biyar na yamma motar yousep ta tsaya a kofar gidansu nana nadiyace tafara fitowa tasha kwalliya tanata zuba kamshi tashiga gidan bayan tayi knocking anbude mata kujeran baya yousep yakoma yakwanta ya lumshe idanunsa yanajiran abar kaunarsa meenal ita kawae yakeda burin gani ayanzu.... TAKU A KULLUM NANA BMB. 08147110349 [7/28, 8:20 AM] Nana BMB: πŸ’πŸ’–πŸ’πŸ’– RABON KWADO.... BOOK 2 NA NANA BMB page 35-36 Zuwa yanzu su meenal anzama 'yan gari a gidan fulani koya yanzu yasaba da surutun meenal kuma ana magana akan canzawarta lamarinta kamar asiri yanzu ta dawo saurarar bassam wanda hakan bakaramin farantawa abbansu rae yayba ummi kuwa yau lpy gobe babu kullum cikin ciwo take tunanin 'yar uwarta take akowani time makarantar da aka canzawa mimi yanzu babu wanda yasan inda takoma saboda tsaro daga ummi se abbansu kadae suka sani saura 'yan watanni tayi candy, To su nana suma yau sukusa watanni uku danyin cabdyn su itada mardy damuwan nana takaro saboda rashin ganin yousep abin kaunarta wannan dalilinne yasa yanzu nana kullum setabi driver dauko mimi a school shikuwa yousep yana zuwane don babyn shi meenal sam auntie batasan cakwakiyar dake faruwaba mardy ma dae hakan take kullum cikin ddamuwa saboda mimi tacanza mara tanata zarya gidansu amma abanza dama nana bata shiga sabgarsu, Yau friday takama yau daddy yadawo daga dubai se dare ya tattara iyalan nashi a parlour seda yayi gyaran murya tukunna yace shin nana kinada saurayi tsayayye ne wanda kikeso bata taba tsammanin tambayarba cikinta kuwa yabada wani kara mimi kuwa addu ah tafara azuci allah yasa kada nana tace tanason yousep suduka ita suka zubawa idanu seda daddy yakuma maimaita tambayar sannan tafara i nda inda takasa magana ma auntie tace wani irin shirmene wannan nana ana miki magana kina kame kame hannu yadaga mata daddy yace kyaleta ay abin bana fada bane idan batadashi ayba matsala bane karatu zatayi dama kada natauye mata hakkine ko aure takeso yanzu shiru takumayi auntien takuma cewa kinaji to kinyi shiru kanta a sunkuye tace zancigaba da karatun daddy inada wanda nakeso yatafi karatune shima bedawoba cikin gamsuwa daddy yace to allah yasa haka shiyafi alkhairi, sosae auntie takewa nana kallon mamaki shin wanene nana takeso batasaniba? kallon mimi yayi yace ke kuma meenal inaso kimaida hankalinki kan karatunki kawae banason shashanci kiyi iya abinda yake gabanki kawae kanta asunkuye tace insha allah daddy, idan mimi tana magana cikin sanyinta daddy seyay ta mamaki yadda meenal tasauya haka, sanya musu albarka yayi suka tashi suka nufi makwanci zuciyar nana cikeda fargaba tana tunanin yadda zata bullowa lamarin kota wani haline kuwa setasan yadda taraba meenal da yousep tunkan asan suna soyayya, GIDAN FULANI Zaune suke a parlour suduka hasana tana koyawa twins homework ita kuma meenal tana kishingide tana karatu a book dinta don saura 3 days takoma school ummi nadaga gefensu tayi zurfi cikin tunaninta meenal tana kulada yanayinta tanason tambayarta damuwarta amma bahali meenal yanzu angirma anzama cikakkun 'yan mata takara girma kamar ba itaba tazama 'yar gayu kullum kara kyau take makeri nakara kerowa fata natasheki tajee hutu,itama tunanin talula na yadda zata koma gida amma tarasa taya zata fara kullum intayi yunkurin yin maganar seta kasa saboda tsananin tausayin ummi datakeji kamar tayi kuka intana ganinta cikin damuwannan shiyasa takasa tabuka komae amma zuwa yanzu ruhinta yayi gida mussam dataji tanayin candy bajumawa za ah musu aure itada bassam iya yanzu kuma tasan ya muhammad dinta yakusa yadawo wa gida bawan allah kowani hali yake ciki tana cikin wannan tunaninne taji twins sunfado kanta suna kikkifta mata idanu alamun tabasu satar amsa sam batasan mesukeyi bama mikewa hasana tayi tana cewa wlh yaya tagaya muku kunfadi murmushi tasaki don ganin irin kallonda twins suke mata se suka bata dariyama kiri kiri kuma hasana tahanata magana suna cikin wannan drama din abbansu yadawo yauma fuskarsa dauke da tashin hankali yayi sama batareda bata lokaci ba kuwa ummi tabishi, sosae ta girgiza dajin kalamin bakinsa cewar jami ay sungano cewar harda sa hannun 'yan gidansu a sace mimi da akayi yanzu su ake lalube zaha gano kusuwaye sunjima suna tattaunawa kozasu san suwaye amma tunaninsu be basu kowaba har lokacin sallan ishah yayi yafito suka tafi masallaci shida twins itama umman tasu fitowa tayi sukayi sallah taredasu meenal koda suka idar sukayi addu ah suka shafa sannan ummi tariko hannunsu dukansu tajawota kusada ita sannan tace yaku diyae na yau zan sanar daku abinda kullum kuke burin kusani akan abinda yahaifarmin da ciwo mimi kullum kina tambayata damuwata amma ina miki shiru to yau zancireku aduhu baki dayanku, TUSHEN LABARIN TAKU A KULLUM NANA BMB. 08147110349 [7/28, 8:20 AM] Nana BMB: πŸ’πŸ’–πŸ’πŸ’– RABON KWADO.... BOOK 2 NA NANA BMB page 33-34 Zamanta kenan a parlour takira mimi awaya tashaida mata sun iso gata a parlour mimi jitae kamar tasa kuka haka ta daura dankwalinta tafito tana rike da wayarta tana saukowa daga steps idanunta nakan nadiya haka itama da mamaki take kallon mimi zama tayi gefenta tana mata murmushi cikin sanyinta tace sannu dazuwa sam mamaki yahana nadiya magana kallon jikinta tayi taga me nadiya take kallone haka amma bataga komaeba zuciyanta ce tasoma shiga rudani daganin kallonda nadiya take mata, Ahankali takae hannunta tarike nata cikin mamaki tace auntie wow haka kika koma masha allah mimi tayi murmushi tace keda ya yousep dinne kukazo nadiya tadaga mata kae tace kuma baki kirashiba auntie bayan gawayan ahannunki yana cikin wani hali sabodake ke naga babu abinda yadameki kodae kindena yinsa yanzu kinyi new catch ne wayar nadiya ta ansa tace bari naga abinda yasami wayan, ga mamakin mimi kawae segani tayi tacire pin din wayar nandanan dadi yakamata ganin numbers dinda tadanna,messeges dinda nadiya taganine bata budeba tace yanzu auntie meyahanaki bude sakon yayana haka nifa amma bari dae nabude sakon naga meya kunsa, saurin fisge wayar mimi tayi tana fara ah tace meyasa zaki ganemin sirri, nadiya tace sokike nagani dama tunda kika ki budewa nibasena bude mikiba, wai ina yayane? kanta rufe baki taga nana n nasaukowa daga steps tana mata fara ah har takaraso tazauna taname cewa nadiya kun iso kenan,eh yaya munsameku lpy? nana tace lpy kakau yajikin yayan naki, dasauki yaya kinga yanzuma ina mata maganarshi tana shareni nana takalli mimi wadda tayi zurfi cikin duba sakonnin wayar duka na yousep ne sena nana guda daya se sakon muhammad daya daga mata hankali se miss calls data gani ciki harda sunayen mutanen dabata saniba wato su mardiyya dube dubenta kawae take awayan tamantama da nadiya gurinta tazo koda tayi arba da hoton meenal zuciyanta bugawa kawae take tana matukar mamaki dole baza ah ganetaba kuwa, Tuni ran nadiya yabaci ganin irin wulakancin da mimi ke mata abinda bata taba yimata bah da nana kawae suke hira harta gaji tace wae auntie wani irin wulakancine haka kikemin tunda kika zaune kike basar min kamar bakisa dani agunba meyake faruwane, mimi ta aje wayan tace sorry nadiya kinji bawulakanci nayi mikiba naga kuna magana da yayane, nadiya tana shan juice dinda aka kawo mata tace to ya yousep fah ke yake jira tunda nashigo bazaki gunnashiba harsena yi magana shirunda tajine yasata dagowa taga ashe mimi tacigaba da danne dannenta awaya bakin ciki ya isheta kawae tamike tadauki jakarta tace yayarmu bari natafi bazan iya jure wannan wulakancinba gaskiya allah yabamu alheri zuciyar nana kal da farin ciki tace tsaya nadiya nazo nawa yayan naki sannu nana tamike tabi bayanta, Dole mimi batasoba ta aje wayan tabi bayansu har tashige gaban motanma yousep yana hango mimi yasauke ajiyan heart sedae fuskarsa babu fara ah ganin nana dayayi daga cikin zuciyanta mimi tace kaene ya yousep din kahadu babu karya dole meenal tasoka seda takarasa gaban motan tarusuna tace ya yousep ina wuni cikin sanyin muryanta shikuwa kasa magana mah yayi yazuba mata idanu nana kuwa jitake kamar ta galla mata mari don ganin irin kallonda yousep kemata jin baze amsataba yasata kallon nadiya tace sorry sis love banyi haka donna bata miki raeba, caraf yousep yace no nadiya tanada gaskiya baby dole tayi fushi yanzu kin watsar damu baruwanki damu, cikin marae raece fuska tace ya yousep bahaka bane kufahinceni kajee sauke ajiyan heart yayi yace baby indae kinason nafahimceki toki bari iyayenmu sushiga lamarinmu, koda nana taji haka batasan sanda tafisgi hannun mimiba sukayi ciki tana cewa sorry kwayi waya ya mujaheed ne yake kiranmu idonta tafda kwalla tayi maganar yanzu da biyu dama yousep yay maganar seguwa gashi yaga abinda yake tunani kuna zuciyarshi tashigayi yana tunanin mezewa nana yahuce shikuwa haka yafigi motan yay gaba nadiya na mamaki, Yinin ranar gidan fulani sunyishine cikeda mamakin sauyawar mimi surutu kamar aku kowa bashi labarin irin azabar datasha take ko ina agidan yadauka abinda meenal tayiwa yaya babba kowa yaji dadi sam meenal takasa tantance iya adadin al ummar dake wannan gida dataga wannan taji sunansu zata kuma ganin wasu har zuwa dare suka koma bangarensu shikuwa bassam mahaifinsa yay masa kiran gaggawa bedawoba har wanna lokaci ummi sama tahaura donyin wanka sukuwa su meenal suna parlour sunata hira dadi yacika su hasana yau yayarsu tabasu lokacinta, Suna cikin hira se ganin abbansu sukae kamar daga sama dukansu kuwa suka tsorata da ganin fuskan abban nasu babu alamar annuri atare da ita ciki ciki ya amsa musu sannu dazuwan dasuke masa ko twins be kallaba ya haura sama, yana shiga bedroom din ummi tafito daga wanka tana daure da towel ganin yanayinshine yasata tsayawa tace lafiya kuwa, dogon tsaki yaja jikinshi har rawa yake yake saboda bacin rae yasoma cire rigan jikinshi yana cewa sumaya bansan mezanwa imam inhuceba arayuwar nan, cikin firgici ta dafe kirjinta tace wani imam kake nufi?cikin cije baki yace imam dae mijina safiyya, habawa tuni takaraso kamar zararra tarikeshi hannuwanta na kerma hawaye wani nabin wani tace ina 'yar uwata take ina yakaemin ita meyake faruwa da ita? Iska yafitar dags bakinshi mezafi sannan yajawota jikinshi yarumgumeta yaname cewa am so sorry sumaya imam yaci amanar mu ya yaudaremu yasaki safiyya ahalin yanzuma besan inda takeba harma yaje yayi wani auren se ayau da dubunshi tacika allah ya hadani dashi yanacan nasa a kullemin shi sakin jikin dayaji tayi masane ajikinsa ya tabbatar da tariga tasume cikin kidima kuwa yadagota amma ina sam bata numfashi jijjigata yake yana kiran sunanta amma ina hankalinshi atashe yakwantar da ita kan bed yadauki wayanshi dakyar ya iya lalubo number din doctor yakirashi bugu daya yadaga wayan bejira komaeba yace jikin sumaya yatashi doctor nan da mintina biyar tayimaka a cikin gidannan ya yanke waya, yadebo ruwa a bowl yanata shafa mata ajiki kozataja numfashi amma abanza dole jiki asanyaye yadauko kaya yasaka mata, yasoma sintiri adakin, bajimawa doctor yakirasa yabasa umarnin shigowa ayyada su meenal suka ganshi sumasan ba lafiyaba yasharbe da gumi sosae dagani bakaramin azababben sauri yashaba yawucesu, To numfashin ummi be daedaetaba harzuwa 11 sedae koda ta tashi kara daga musu hankali tayi kuka take tamkar ranta zefita tana kiran sunan safiyya seda doctor yamata alluran bacci tukunna aka sami salama,su hasana suna parlour hankalinsu yamatukar tashi tasan jikin umminsune yamotsa tunda sukaga shigan doctor, se bayan tafiyan sane abban yake shaidamusu suyi hakuri suje su kwanta jikin ummine ya motsa amma dasauki ranar dae suduka gurin meenal suka kwana suna cikin jimami, Tome karatu haka rayuwa tacigaba da gudana tsakanin gidansu mimi da gidansu meenal wani irin kauna meenal takewa su ummi dakuma tausayinsu da kulawanda suke bata hakanne yasa takasa bayyana musu gaskiya tana jin tausayin ummi batasan halinda dazata shigaba kullum tana tunanin ina mimin take shin mafarkinta da takeyi tana ganin auntie nadukan mimi gaskiya tana gidansu a matsayinta, idan suna tare da bassam masoyinta take tunawa yousep haka zataci kukanta takoshi sam batada mafita ayanzu sosae meenal take mamakin rayuwarta itadae kullum cikin addu ah take allah yakawo mata mafita a rayuwarta tana tunanin 'yan uwanta wani hali suke ciki ayanzu tawani bangaren tana mamakin yadda ummi take kamata da wasu alamomi amma tayi kamar bata ganiba, tasha yimata fulatanci amma takasa maida mata martani haka idan da fulatanci suka hadu suna hira sedae tayi shiru tana saurarensu, To mimi kuwa harkawo iyanzu sunkasa daedaeta kansu da nadiya kullum cikin mita take mata yanzu shareta takeyi batason yimata magana haka suke kullum a school zuwa yanzu ta diga ayar tambaya akan auntie tana tantama akan ba itace tahaifi meenal bah saboda irin muguntar da takeyi mata abu kadan tahau sharara mata mari kuma tashanye don acewarta allah ne yakawota wannan rayuwa shiyasa tayi tawakkali garesa take jure duk wata wahala tawani bangaren kuma soyayyar mujaheed tagama kasheta hartanajin bazata iya komawa gida batare data aureshiba don tasan mezataje ta tarar soyayya suke zubawa abinsu haka yousep ma don acewarta meenal take riritawa soyayyarta, NI NANA NINAGA ABINDA YAGIRMI KAENA WANNAN KWADON BAKA KENAN, mimi tanason sanin halinda mahaifiyarta take ciki amma bahali tasaba da kowa agidan haka suma sunsaba da shiru shurunta yanzu magana seta gadama tana waya dakowa harda mardy sedae ita sosae taga canji hakan kuma beyk mata dadiba ko maganar muhammad mimi batason tayi mata shiyasa abin yake damunta sosae bata iya kiran muhammad mugun jin tsoronshi take ko sunanshi suka ambata se heart dinta taharba bare yakira awaya abata jikinta har bari yake saboda kallon da yake mata me tarin ma a noni dayawa komae ya ajeshi agefe seya dawo tukunna don saura 5 mount yadawo kenan kullum mimi cikin addu ah take allah yabaiyyana meenal tabar gidannan kafin yadawo cikinsa.... TAKU A KULLUM NANA BMB. KUYI HAKURI DA RASHIN TYPING DINA SOSAE AIKI NE YAKEMIN YAWA. 08147110349 [7/28, 8:20 AM] Nana BMB: πŸ’πŸ’–πŸ’πŸ’– RABON KWADO.... BOOK 2 NA NANA BMB page 37-38 TUSHEN LABARIN UMMI tace yaku 'ya 'yana kunsani kaf cikin yola babu wanda besan dazaman gidan fulaniba sedae bare gidane na family gaba daya dukanmu kanmu ahade yake gida me cikeda farin ciki dakuma tarin ni imomi gamida nishadi dukwanda yazo gidanmu seyayi marmarin dawowa sabida yadda muke gudanar da rayuwarmu,bangaren gidanmu kuwa mahaifina su ukune mahaifiyarsu tahaifa hashim shine nafarko se osman sae autanta abdullahi shine mahaifinmu nida 'yar uwata kishiyar mahaifiyar su babanmu wato gwaggo itama tanada danta kuda daya sulaiman shikadaene tahaifa, to kunsani dae 'ya'yan abbah hashim 6 ne matansa biyu inna hafsatu da inna maimuna,se abbah osman shikuma kunsan matarsa dayace dama halimatu wato yaya babba kenan isarta da ikontane yasa taci wannan suna yaya babba 'yan biyu tahaifa abdul halim shine hasan allah yajikanka da rahama marigayi se abdul hamid shine usain wato mahaifinku, yaya babba tana matukar kaunar hasan sosae marigayi ko ayanzu duk wanda yazauna da ita seta bada labarinshi, to sena ukunsu abdullahi kasancewar beyi aure da wuriba yagama karatunsa tukunna wannanne yasa duk 'yan uwanmu nawajan uba suka girmemu mahaifiyarmu amina wato hajiya duk cikinsu halimatu itace take haddasa bala i batason zaman lapiya sedae hajiya kullum cikin hakuri take da ita wannan dalilinne yada suke zama inuwa daya sabanin ragowan matan nasu lokacinda hajiya tahaifemu 'yan biyu annuna manaso kamar me mukadae allah yabata 'yar uwata itace babba safiyya wasu nakiranta da hasana haka nima wasu kan kirani da usaina duk da bakowane yake ganemubama mahaifinmu yanaji damu sosae gata ba irin wanda baya nuna mana, to se dan gwaggo sulaiman lokacinda yatashi aure anshiga matsala agidannan saboda ze auro kado ba ah cikin family dinmu takeba balaraba kanwar abokin mahaifinkuce ya aura seda akayi tashin tashina kafin abarshi ya aureta sedae ansami akasin abinda manya suke gudu sam balaraba batada kirki ga girman kae bawanda take gani da mutumci hatta mahaifinku dayake aminin yayanta da tasanadiyyarshi ma tashigo cikinmu bata ganin hakan 'yar ta daya itama tahaifa wato asiya duka halayyar babarta seda takwashe taso tafi uwarta wulakancima sosae balaraban taso abbah sulaiman yabar asiya tafita kasar waje tayi karatu ammah yahana saboda dokane haka tsarinmu yake sosae take lalata asiya kome tayi bata ganin laifinta ganin tana shirin lalata masa tarbiyyar yarinyane yasashi yimata aure tunkan tagama karatuba, To alokacinda manyan gidanmu suka tsunduma harkar siyasa lokacin kuma farin cikinmu yasoma tangarda saboda tashin hankalinda muka shiga kullum cikin kawoma hari ake mussam dani da 'yar uwata wannan dalilinne yasa aka zuba matakan tsaro agidanmu ake bamu tsaro dama islamiyyanmu tana cikin gidanmu sedae karatun bokone muke fita yowa alokacinda mukayi saukar alkur ani megirmane mahaifinmu yayimana kyautar gwal saitinsa kuwa daban yasa aka kera masa su donya bamu asaukarmu iri dayane masu kyau munyi matukar farin ciki sosae mahaifinmu yana dasawa da safiyya sosae saboda hakurinta sam batada hayaniya sabanin nida nake 'yar hayaniya nima banida hakuri kome akae mana sena narama mana koda kuwa mahaifiyata akawa wannan dalilinne yasa bama shiri sosae dashi, tunda muka taso muka zama 'yan mata kowa a family yasoma samari suka yinkuro domin aurenmu to abudul halim marigayi dukya buge ragowan masoyan na safiyya saboda yana mata wani irin so naban mamaki tamkar ze mutu akanta sedae kash ita kuma 'yar uwata bata sonsa ko kadan nayi nayi alokacin tafadamin wanda takeso amma taki abu kamar wasa har lokacinda muka gama makaranta mahaifinmu yatashi aurar damu dama yariga yazaba mana mazajen aure wato 'yan biyun yaya babba sedae sam alokacin 'yar uwata tayi abinda yabawa kowa mamaki don tace batason zabin mahaifinnamu dukda beji abinda abinda tayiba yace to shikenan tafadi wanda takeso acikin family din shi ze aura mata nanmadae taki magana harseda ran mahaifinmu yabaci tukunna tukunna tace ai ba ah cikin family yakeba aranar babanmu yataba dukan safiyya saboda takaishi karshe yakumace maganar biki babu fashi abdul halim zata aura mari gayi seda kuma yatitseyeta tafadi wanda takeso tashaida masa cewar imam takeso babban drivern gidanmu kowani gari mukasiyi kaya imam ke kawo mana allah yazubawa imam kyaune naban mamaki shiyasa 'yar uwata tamutu akan sonsa sunkwashi shekaru suna soyayya amma bawanda yasani sewannan lokaci data bayyana, abin yamatukar tunzura mahaifinmu aranar yakira imam yaymasa zagin cinmutumci ya muzan tashi sannan yakore daga aiki, ranar haukane 'yar uwata kawae batayiba kullum cikin kuka muke nida ita ina bata hakuri ina nusar da ita tayi hakuri taiwa iyayenta biyayya ta auri abdul halim din tunda yana matukar kaunarta mahaifiyarmu tayi rarrashin harta gaji sam idanun 'yar uwata sun rufe taki saurarar kowa tadena cidasha sedai kuka gashi anata shirin biki wata rana da asuba tasoma aman jini cikin gaggawa aka kira doctor dinmu yazo yadubata asanan yashaidawa mahaifinmu cewar abawa safiyya abinda takeso inba hakaba zuciyarta nabarazanar bugawa bada jumawaba don tana cikin matsala ran mahaifinmu yay matukar baci yakule yace sedae to ta mutu kuwa amma baze fasa aurenba To mahaifiyarsuce tace sam baza ah yi hakaba yakashe 'yarsa dakansa tunda baharamun bane to yabata wanda takeso dolenshi kuwa ya ilahi mahaifinmu yazuciya iya zuciya aranar yakira imamu da mahaifiyarsa aka daura auren da imam din yasa aka debo komae nata yaci to tabi mijinta daga wanaan rana yacireta acikin family din mu ita ba yarsa bace mahaifiyar imamu itace uwarta itace ubbanta, koda abdul halim yasamu labarin abinda yake faruwa yabazamo cikin tashin hankali yazo cikin kuka yatsugunna agaban safiyya yana rokonta tayi hakuri awarware auren ya aureta inba hakaba wlh mutuwa zeyi ta temaka masa yana matukar kaunarta kada tayi masa haka 'yar uwata sam taki saurarar sa tariga tayi nisa banifa kaf 'yan gidanmu ranar seda mukaji haushinta agaban kowa agidan yake mata magiya amma ko kallonsa takiyi haka dan uwansa mahaifinku yazo yanata yimata magiya amma sam taki saurarar kowa dama mahaifiyarmh ko fitowaba bataiba tana ciki tana nata kukan itama hannunta yadamka ahannun mahaifiyar imam yace gatanan yasallama musu ita dagayau sosae yakara ciwa imam mutumci dacin zarafi saboda aganinshi shine ya hirewa 'yarsa kunne bayan kuma yarigada yasan dokar gidan ba ah taba shiga tashin hankalimda muka shigaba awannan rana don 'yar uwata suna tafiya abdul halim ya yanke jiki yafadi ya babba kuka take tana sambatu tana tsinewa safiyya tana mata mugun fata bayan kwana hudu ta tafiyar su safiyya allah yaywa abdul halim cikawa ya rasu saida yaya babba tazauce malamae aka kira suka tsaya akanta tanata kururuwan setaje takashe takashe safiyya itama itama tabar duniya daga masu zagin safiyya se masu yimata fatan tsiya haka gidan fulani yadauka harseda wannan abun yashafi shiyasar mahaifinmu anata yamadidi agari cewar 'yarsa tagudu tai aure mahaifiyar su babanmu inno sam bata iya jure tashin hankali yanzu zata rude bare wannan babban al alamari ranar ukun abdul halim ita inno taraso, kowa yashiga tashin hankali mahaifinmu kuka yake kamar karamin yaro abinda yakara bawa kowa mamaki sam ba safiyya babu alamunta.... TAKU A KULLUM NANA BMB. 08147110349 [7/28, 8:20 AM] Nana BMB: πŸ’πŸ’–πŸ’πŸ’– RABON KWADO.... BOOK 2 NA NANA BMB page 39 Se aranar addu ar bakwae sega 'yar uwata kamar anjehota ko hijab babu cikin tashin hankali ashe batasan abinda yake faruwaba shiyasa bata zoba koda mahaifinmu yay arba da ita aranar seda yay mata duka gami da mugun fata sosae yake furuci marasa dadi akanta saboda tsananin fushin da yakeyi da ita muna ciki muna zaman jugum jugum ajikina naji 'yar uwata ta iso nabazama nafito naga halinda take ciki hankalina yay matukar tashi mahaifinmu yakuma janyeni yahanani zuwa inda take inaji inagani natafi nabarta yasa aka fita da ita daga gidan yakuma ce koda wasa securities suka kuma barinta tashigo to seya koresu a aiki, Tundaga wannan rana haka muka cigaba da rayuwa farin cikinmu yayi karanci musamma ma madaeni ga gulmar marmu da akeyi agidan na abinda 'yar uwata tayi kullum cikin zubar hawaye nake bayan rasuwarsu akayi bikina nida mahaifinku anyi taro naban mamaki alokacinne 'yar uwata takuma zuwa sedae koda muka ganta seda muka tsorata yadda takoma tarame ta kojale nida mahaifiyata munyi kuka mahaifinmu ko gezau yahana abarta tashigo cikin gidannan sede hange daga nesa haka ta tafi tana kuka mecin rae tundaga wannan tafiyar tata rayuwata tashiga matsala narasa farin ciki da walwala ahaka nacigaba da rayuwata dukda mahaifiyarmu itama tana damuwa da 'yar uwata sedae bayadda zatayi awata rana 'yar uwata takuma dawowa nanma dae aka hanata shiga gidan tayi musu magiyan harta gaji tana kuka haka takoma sebayan kwana uku tadawo da letters tace abamu, Koda aka kaewa mahaifinmu wasikar cayay baze amsaba se mahaifiyarmuce ta ansa takaranta abinda takunsa dukanmu seda zuciyarmu ta raunana harda mahaifinmu damukaji halinda take ciki tayi bari har sau biyu kuma ahalin yanzu mijinta zetafi da ita legos abinda tayi mana kuma mutemaka muyafe mata koda inta mutu tasami rahama ta ubangiji awanan lokacin hawan jini yakamani shine naketa fama dashi haryanzu nakasa samun sauki alokacin yayi tsanani hartakae ina kasa tabuka komae dakaena Dr yace amagance damuwata itace samun lpyta mahaifina yatambayine shin menake so? nashaida musu cewar 'yar uwata sutemaka su dawo da ita gida inringa ganinta barin farin cikinace ita sutemaka suyafe mata haka tunda tagane kuskurenta kowama yana kuskure ayafe masa jikin abbanmu alokacin yay sanyi alokacinne shine governor nagarinnan hajiyama taringa lallaminsa daban hakuri sannan yasa aka tafi legos neman safiyya sedae kuma babu ita ba dalilinta anyi neman iya nema basacan koda aka tambayi mahaifiyar imam itama tace suna legos tunda suka tafi basuzo gidaba haka akaci nemansu har gaji haka nacigaba darayuwa yau da lpy gobe babu har allah ya azurzani da haihuwarku kullum da tunanin 'yar uwata nake kwana nake yini bamu sake jin labarinta har kawo i wannan lokaci da ciwona yamotsa abbanku yahadu da imamu ashe yasaki 'yar uwata besan inda takeba shima cikin kuka ummi takarashe maganar haka su meenal suma sun kankameta suna kuka dakyar tayi jarumtar rarrashinsu sosae meenal tashiga kogin tunani wanda batasan randa ze kareba dolane ayanzu tafito tafadi gaskiya koma meze faru yafaru, CI GABAN LABARI Tome karatu yau friday takama kuma ranar dawowar muhammad daga China mujaheed da su mummy dasu inna duka sunzo domin tarbar shalelen nasu.... TAKU A KULLUM NANA BMB 08147110349 [7/28, 8:20 AM] Nana BMB: πŸ’πŸ’–πŸ’πŸ’– RABON KWADO.... BOOK 2 NA NANA BMB page 40 Tunda gari yawaye ake girki da soye soye kala kala su mardy dama sammakon zuwa akayi don tarbar masoyi πŸ˜„harda nadiya sedae mimi tayi lake da ita kamar wadda akacewa yaune ranar mutuwarki sam batada kuzari ganin yanayinne nata yasa daddy cewa meenal meke damunkine naga baka murna sam da dawowar yayan naki mummy tace nima dae abinda nagani kenan shiyanacan yana allah allah yadawo yaganta ita ko ajikinta itadae mimi murmushine nata daddy yana kulada yadda mimi take shigewa mujaheed haka shima yake mata to sedae yana daurewane baya nunawa,daddy da daddyn mujaheed ne suka tafi airport din se mujaheed dake driven dinsu, Koda sukayi harba da muhammad suduka se suka sau baki suna kallon shi kamar shashashu harya karaso garesu cikin tafiyarsa nakasaeta sumar kannan nasa tanata zuba kyalli skin dinshi kamar zaka taba jini yafito yaji hutu yay kubul bul dashi dariya sosae yaringayi harda rike ciki ganin irin kallonda suke masa sannan yace tunda babu wanda zeyi welcoming dina mutafi gida se a time din mujaheed yasaki ihu harda tsallensa ya rungumesa yana zuba masa shakiyancinsa dagowa yayi yanadan yamutsa fuska yace yana gannka kae kadae ina sirikar tamu muhammad yakaemasa duka yazille shige mota yana dariya gaisawa sukayi dasu daddy suma sunata zolayansa suka shiga mota yabankawa mujaheed harara yace kada kadamu indae sirikace zamuje kataho da ita baseka damemuba, shidae mujaheed yay murmushi yaja motan sukatafi gida azuciyanshi yana cewa yau zakaji komae sha kuruminka, Cikin tsananin farin ciki nana tafara tarbar yayan nata ta rungume tana cewa wayyo allah ha ya muhammad haka ka dawo sam hankalinshi baya kanta mimi kawae yazubawa idanu wadda tayi masa sannu dazuwa cikin sanyinta, tuni auntie ta hassala tace kinata zumudinshi bayanshi batake yake bama se alaokacin yadagota yana fara ah yace nana enyee girma yakaru haka aka zama manya dafatan nasameku lpy cikin jin kunya nana tasunkuyar dakanta yagaishe da auntie da mummy su mardy anata kwarkwasa da iyayi aka gaisa harda wani gift donneman suna gurin kakannin nasu yakarasa cikin jin dadi yana cewa oh baba ashe darabon zandawo nasameka nazaci zaka karasa ay kafin nadawo baba yace allah kahadamu da jikokin zamani se du ah ei to mujaheed ma yayi yakyaleni kaema saura kae muhammad yace hajiya inna kedama ay tamuce ba abinda zamuce sedae allah yaja kwana, daddy yace to seme donkayiwa inna ita kadae 'yan amin sun ansa hardashi kuma kakiyayeni shida mujaheed sukasa dariya baba yace barni dasu nine daedae dasu wlh mimi nagefe tazuba musu ido ta lula duniyar tunani daddy yace meenal zonan, jiki asanyaye tamike ta isa inda yake ta tsugunna yace menene yahadaki da yayanki?shiru ba amsa seda yakuma maemaita mata tambayar sannan tace babu komae dadd y kaenane yake saramin shiyasa sam muhammad bekara kallon inda takeba tunda tazauna seyanzu da daddy yake mata magana meenal nazaci idan muhammad yadawo zaki warware to sekuma naga kinfi takurama kifadamin gaskiyar abinda ke damunki, muhammad ne yace daddy ka kyaleta kawae ay bataso dawowata gidanba se alokacin tadago tana zubar hawaye koda taga irin hararan dayake zuba mata seta maida kanta kasa mujaheed yazo zekama mata hannu daddy cikin fada yace menene haka mujaheed koma gurinka kazauna shima jiki a sanyaye yakoma yazauna yana karayin mamakin daddy tafi daki meenal ki kwanta kihuta kinji tunda bakyason hayaniya ay zuciyan mimi kal da farin ciki tamike dasaurinta tahaura sama muhammad yabita da kallo yana murmushin mugunta bajuma sega yayan auntie shima da iyalansa 'ya'yansa 'yan mata sewani yauki ake ana yanga gurinsu muhammad hakan bakaramin bakanta ran mardy yayba suduka sukaci abinci aka koshi akayi hira nayaushe gamo, koda suka dawo daga sallan la asar mujaheed yajashi daki shikuma yasoma cirewa kayanshi ze shiga wanka mujaheed yace muhammad daddy inyay min wani abu kan meenal inayin mamaki sam bayason narabeta kuma gashi itace abar kaunata adum duniyar nan ita kadaece macen danakeso kuma nakefatan rayuwa da ita har abada tsayawa muhammad yay da daure towel dinda yake a kugu jin kalaman namujaheed yake suna dukan kunnensa.... TAKU A KULLUM NANA BMB. 08147110349 [7/28, 8:20 AM] Nana BMB: πŸ’πŸ’–πŸ’πŸ’– RABON KWADO.... BOOK 2 NA NANA BMB page 41- 42 Tsaiwa ce ta gagari muhammad yanemi gefen bed yazauna yana kallon mujaheed yace shin mujaheed meenal tasan kana sontane?wani kallo mujaheed yay masa yana murmushi tunyaushe nawuce gurin soyayyafa mukeda meenal fiyeda yadda kake tsammani, cikin mamaki muhammad yace shin mujaheed yaushe duk akae hakan bansaniba meenal koda wasa bata taba gayaminba, mujaheed yace mun boye soyayyarmune ga kowa sekadawo zamu baiyanata sabida mahimmancin da kake dashi agurin meenal, muhammad ya jinjina kae yace muhammad baka ganin yanzu meenal bata daukeni abakin komaeba yanzu, gyara zama mujaheed yay yace inason ka gayamin dama pls muhammad meyasa kakewa meenal hakane yanzu? mikewa yay yashiga bathroom yana cewa ita zaka tambaya tabaka amsa yarufo kofa abinsa mujaheed yabisa da kallo, Sakarwa kansa ruwa muhammad yay yadafa bango sosae ya lula duniyar tunani tabbas jin furucin mujaheed dayayi yanzu yakara tabbatarwa dakansa ba meenal bace wannan shin meyake faruwane haka wacece wannan ne? tabbas akwae babban al amarin dake faruwa shin ina meenal dinshi takene yasan baze yaudari zuciyansaba yana tsananin kaunar meenal amma dole yaboye nashi son saboda yadda ta daukeshi uwa daya uba daya yayanta dukda idan yayi shiru yasan ze cuci zuciyansa, yajima a ciki yana nemarwa kansa mafita dason gano gaskiya amma abin ya gagareshi haka yafito sam yarasa walwala dukda abokansu dasuka hallara sam hankalinshi baya gunsu, Koda daddare bayan sallan ishah suna bedroom yanajin mujaheed yadda suke waya da mimi yashaida masa cewar su hadu da garden yana zaune mujaheed din yay wanka yashirya yafita, muhammad yanata zagaye dakin yarasa nutsuwa tunda mujaheed din yafita, kasa jurewa yayi shima yanufi garden din kallo daya yamusu yasan sunyi nisa a love amma kuma mimi tana hangoshi annurin fuskarta yadauke zujiyanta tafara lugude, yana karasowa yazauna gefenta yana kallonta yay smile yace mujaheed pls dan bamu guri muyi magana ta fahimta nida,mujaheed be kawo komaeba sema dadi dayaji don bayason abinda muhammad kewa mimi, fitsarine kawae mimi bataiba don tsoro wani irin gumine yasoma tsatstsafo mata mujaheed yana mikewa ta mike itama zata bishi ya rike mata hannu yadawo da ita mazauninta kuma yaki sakar mata hannu kanta akasa shima yana yimata kallon kurrillah yana nazartarta, meenal yakira sunanta, tayi masa shiru yakara kiran sunan nata muryanta narawa tace na am, dago ki kalleni mana mimi daurewa tayi tayi tamaza tadago sedae takasa kallon kwayar idanunsa menene a tsakaninki da mujaheed?tayi masa shiru, badake nakeba, yana sonane, ke kumafa?kanta a sunkuye tace inasonshi nima ina kaunarsa dayawa, muhammad ya jinjina kae yace good, ina ajiyata dana baki bafin natafi China?sosae yake ganin gumi yadda yake fimata wuya daga cikin gashinta saboda yadda yake magana ba alamun wasa afuskarsa, idanunta nazubar hawaye tace tananan,koda yaji haka seya saki murmushin mugunta yace maganar dakikace zaki gayaminfa sena idan nadawo ina saurarenki yanzu,mimi tadanyi shiru sannan tace dama maganar ya mujaheed ne zangaya maka muna soyayyane,ok yanzu ke kin iya soyayyane kinsan yadda take? dukda halinda mimi take ciki furucinsa seda yasa tasaki murmushi hakan kuwa yawa muhammad dadi yakara ganin wata shedar,batae tsammaniba taji yarike mata hannuwa yana murzawa cikin nashi cikin jin tsoro tadago tana kallonsa se sannan yaji yadda jikinta yake rawa, kasa jurewa kallonsa tayi tasunkuyar dakae tana hawaye, yasauke ajiyan zuciya yakara matse hannunta cikin kakkausar murya yace banason raininin hanakli zaki iya rainawa kowa hankali amma bandani kafin kowa yafahimci wacece ke inason yanzu kifadamin asalinki kifadamin abinda yake faruwa kuma shin ina kika kaemin meenal ditane kamar kowa yamakance kowa yaki fahimtar bake bace meenal banason muyi rigima dake yanzu kifadamin ko waceceke,mimi ji take kamar kasa tabude tashige ciki, murya tana rawa tace nice meen..... yatsansa yadora akan bakinta yace karmuyi haka kada kiyimin gaddama wannan al amarin yadauremin kae, zakiyimin bayani tasauki ko kuwa,kukan da mimi takerikewa ne yakufce mata tamike zata ruga ya kuma fincikota ta dawo tazauna cikin shashhseka tace wae meyasa yaya kakemin haka kawae saboda nacanza kace bani bace mimi banason haka karabu dani, sosae muhammad ransa yabaci daganin raenin hankalinda ake shirin yimasa, kafansa yasa yatake mata yatsun kafarta tasaki kara cikin zare idanu yace shut off malama kifadamin gaskiya konayi miki abinda yafi haka, cikin dakiya mimi tashare hawayenta tace nice meenal! muhammad yay murmushi yace ok tunda kece meenal inason gobe kafin su daddy mujaheed sutafi agaban kowa ki shaida musu cewar kinason mujaheed da aure idan dae kina sonsa tokiyi haka gobe, cikin sauri taga masa ya jinjina kae gud gal tashi kishiga ciki semun hadu goben koh! da gudunta nabara mimi tae cikin gida yabita da kallon mamaki al amarin nan yana matukar daure masa kae zuciyansa a cunkushe yarasa meyasa kowa yaki fahimtar abinda yake faruwa ne.... TAKU A KULLUM NANA BMB. 08147110349 [7/28, 8:20 AM] Nana BMB: πŸ’πŸ’–πŸ’πŸ’– RABON KWADO.... BOOK 2 NA NANA BMB. page 45 Abinda muhammad yace tayine tasa mujaheed yayi cewar yasanarwa su daddy yana sonta se aureta,mujaheed yayi mamaki dajin wannan furucin daga bakinta haka da wuri beyi mata musuba ya amsa mata zeyi domin baya shakkar tunkarar kowa indae akantane, to haka yadawo parlour yanata tunani yakasa aiwatarwa don kalamin yamasa nauyi kusada muhammad yakarasa yazauna yafada masa abinda mimi tace yakuwa saki kayatatccen murmushi yana kallon mujaheed yaname kara mamakin yadda idanuwan mujaheed suka rufe haka daya kasa fahimtar abinda yake faruwa koda yake kauna dole yamasa uzuri tarufe masa idanuwa, gyaran murya yay yace tome kazauna jira kaje ka aiwatarmana time yana tafiya,mujaheed yarike hannunsa yace pls muje karakani nagaya masa cikin shan kunu yace indae sedani ne to kafasa bama son abin kakeyi bah kenan,mujaheed gajiya yayi yatashi yanufi gurinsu daddy suna zaune da nashi daddyn sunata fira tunda ya tashi muhammad yake kallon ikon allah sosae yakejin zuciyansa tana dancing, koda ya karasa yazauna agabansu kamar me neman gafara yasunkuyar dakansa kasa zuciyansa tana wani irin bugu haka meenal shikawae tazubawa idanu,haka suma su daddy shi suka gubawa idanu ganin irin usmanda yayi agabansu cikin ladabk yace daddy dama inada maganane, kallon juna sukayi su daddy don basu san cikinsu dawa yakeba dagowa yay yakalli daddy sannan yakuma sunkuyar dakansa hakanne yasa yatabbar dashi yake,seya gyara zamansa yace to mujaheed ina saurarenka kaf dakin yadauki shiru kuwa aka zubawa mujaheed idanu, Dama maganace....Mujaheed yay shiru secan yakuma cewa dama maganace akan meenal daddy, tunda yaji ya ambaci meenal yarintse idanunsa cikin wani irin yanayi don yasan meze furta ayanzu, Dama ina sontane daddy kuma itama tana sona iname rokonka daddy kabani auren meenal tazememin abokiyar rayuwa ta har abada, Wani krin takaecine yacikawa auntie zuciya jitake kamar ta harbe mujaheed kallon kuma seya koma kan daddy ana tsumayin hukuncin daze zartar, muhammad jiyay kamaryashige huciyan daddy yaga wani hukunci zeyanke ne?bude idanunsa yayi sannan yay gyaran murya yace Mujaheed! Na am daddy Mujaheed inason kasani yadda nadauki muhammad haka kake agurina babu bambamci komene ne kakeso agareni indae dayiwuwarsa to bashakka sena yimaka, to amma batu akan meenal inason daga yauma kasoma kokarin cireta azucinka saboda abinda kukeda muradi bame yiwuwa bane.... TO ME KARATU MUHADU A BOOK 3 INME DUKA YAKAEMU DONJIN YADDA ZATA KASANCE! SHIN MEYASA DADDY YAHANA MUJAHEED AUREN MEENAL? TAKU A KULLUM NANA BMB. MASOYANA INA MIKA DUNBIN GAISUWATA AGAREKU DA GODIYA TA MUSAMMAN. 08147110349 [7/28, 8:20 AM] Nana BMB: πŸ’πŸ’–πŸ’πŸ’– RABON KWADO.... BOOK 2 NA NANA BMB page 43-44 Meenal ce kwance a kan bed tayi lamo inbanda tunani babu abinda takeyi abin duniya gaba daya ya isheta tarasa mafita kullum cikin damuwa take harta soma ramewa, tayj zurfi cikin tunaninta tajee ana knocking seda ta gyara kwanciyarta sannan tabada izinin shigowa, hasana tashigo dauke da cup ahannanunta tana murmushi tazauna gefenta tana cewa yayarmu tunda kika gama school damuwanki takaru kullum bakida sukuni kuma ummanmu tace ki kwantar da hankalinki akan aurennan naku keda ya bassam nasan bakya sonsa kawae kinawa abbanmu biyayyane kuma baze taba canza maganaba kinsani so kiyi hakuri kada kisa damuwa aranki tadameki ko bakomae ya bassam yana matukar kaunarki zakiji dadin zama dashi kema kuma nan gaba zaki soshi, Hawaye meenal tafara don yanzu ba abinda tafi tsana samada ai mata maganar aurennan danasani kullum tanayinta dabata yimusu bayani tunfarko kota wani hali kuwa bazata bari ta auri ya bassam be kome zefaru sedae yafaru yayanta kawae yake fado mata arae tasan yanzu yadawo gida saboda bata taba bata a lissafintaba tunda yatafi,hannun hasana tariko tace hasana ina cikin wani hali bazaki ganeba nasa yadda zanyi da rayuwata, jikin hasana a sanyaye tace kiyi hakuri yayarmu ki fawwalawa allah komae tamika mata cup din tace gashi ummi tace kisha akae mata cup din,ran meenal yakara baci saboda bata kaunar irin abubuwan nan da ummi take bata tunda aurensu yakusa fuska adaure ta anshi abin cikin cup din tshanye tabata cup din, hasans tafito cike da tausayin yayar tasu kods tasauko tasami bassam azaune suna hira da twins da ummi cikin cukurkude fuska tanemi gu tazauna cikin ko in kula yace ke jeki kiramin yayarku, hasana ta tabe baki itama tace yayarmu tayi bacci, Bai kukalataba yadauka wayansa yacilla mata yace jeki kaemata inason muyi magana ne nakira ta ta wayan akashe cikin tura baki tadauki wayan kuwa takoma gun yayar tasu sam itama bataji dadin kawo wayanba don sabodashi takashe wayanta seda suka gama wayan tabawa hasana wayar tamayar masa koda tasauko twins kawae tasamu a apalour din ummi tana dakinta shikuma yafita answer waya da dayan wayan nashi hakanne yabata damar zama tasoma bincieke awayan tana shiga inda ranta yamata tana cikin kallon pictures a wayan taganowa kanta abinda yadaga mata hankali tamike dasauri tashige dakinta tacigaba da kallon hotunan jikinta har bari yake saboda tsoro duk rabin hotunan bassam ne shida mata fitsararru babu kayan mutumci ajikinsu wanda dasuma gara babu wasu sun makale masa ajiki hawaye kawae taji yana bimata ido, Koda bassam yadawo yace wae twins hakasan bata sauko bane haryanzu suduka sukace tasauko mana tundazu tashige bedroom, jiyay wani daram kirjinshi yaharba inibin dayake shirin kaewa baki ya saki tsam yamike ya nufi daki, kallonta kawae take tana hawaye tana cewa allah ya isa ya bassam wlh yau allah ya toni asirinka bazaka taba auren yayarmuba ashe kae dan iskane dama tokuwa sena kaimata taga abinda kake aikatawa yaudararta kakeyi tanata masa ibar albarka, tadagowar dazatayi taganshi jingine a kofanta yana kallonta saboda firgita tamike batasanma tasaki wayanba tasaka kuka tana cewa kuma wlh kome zakayimin sena gayawa yayarmu don bazan bari ta auri dan iskaba hakanne yasa yasoma nufuta ahankali tanaja baya fuskarsa babu alamar rahamar annuri atare da ita seyanzu yake danasanin bawa hasana wayarshi dayay don yamanta ba security, harseda tadangane da jikin bango yazo dafda ita ya nunata da yatsa yace kewacece dazaki hanani auren my meems yarinya duk duniyar nan babushi sannan kuma wayace kiyimin bincike awaya?cikin zafin rae tadago btace saboda allah yatoni asirinka wayanka tazo hannuna yau tasss bassam yadauketa damari tasa hannu biyu kuwa tadafe fuskannata tana kuka cikin bakin ciki yace ke wace irin dakikiyace saboda kinganni da mata zaki kirani dan iska saboda bakida kwakwalwa mekyau kisake gangancin cemin dan iska kiga abinda zanwa shegen bakinnan naki mara kunya, hasana takuma kulewa cikin rashin tsoro tadago tace ayba karya naiba anfada din yayarmuce kuma daga yau kasa aranka bakae ba ita donsena tonama asiri katafi can kasamo matarka amma ba ah gidanmuba, Cikeda mamaki bassam yake kallon hasana yarasa meyasa hasana batajin tsoronsa koda kuwa meze mata bata shakkar yimasa rashin kunya tunani yayi tabbas yakyale yarinyar nsn wlh seta ballo masa ruwa yanagani burinshi yakusa cika so dole yadauki mataki, murmushi keta yasaki sanan yakara matseta abango yay mata rumfa ko kyallinta ba ah hange yarufeta seda suka kwashi mintina ahaka ba umm ba um umm sannan yadago fuskarsa daukeda kaya tatccen murmushi yajuya yadauki wayanshi data yar yatafi seda yabude kofa zefita yajuyo yace no problem ayanzu zaki iya fadin abinda kikeso nima nasami nawa abin fadan so ki gwada kiga meze faru, yay ficewarsa yabarta ajiki bango hawaye shabe shabe zuciyarsa kuna kawae takeyi tafada kan bed tasoma kuka me cin rae, WASHE GARI Tunda su mummy suka tashi suka soma shirin tafiya mimi kuwa tunda ta tashi tarasa sukuni har sukae breakfast mujaheed yana kula da halinda take ciki sam muhammad ko inda takema be kallaba hakanne yakara tabbatarwa daddy da akwae matsala bayan gamawarsune suna parlour nana ta dafata tace meenal wae meyake damunkine nigaba daya natasa gane kanki yanzu wlh, zuciyan mimi bugawa kawae take tarasa ta ina zata fara tana cikin tsaka me wuya tanason mujaheed matuka kuma ayanzu idan tafurta to nana tasmmu abinyi zata kwacewa meenal youseep "NIKUWA NACE HMMMM" ganin tarasa mafitane yasata hayewa sama takira mujaheed koda yaga haka yasan akwae magana mikewa yay yabar palour din don answer wayan muhammad nakula dasu yana murmushi kawae soyake kafinsu daddynshi sutafi ayi komae yau ayita takare yau zefadima kowa yasan cewa wanann ba ita bace meenal.... TAKU A KULLUM NANA BMB. 08147110349 Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels