Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels ๏ปฟ๐Ÿ’™๐Ÿ’™ RABON KWADO.. ๐Ÿ’™๐Ÿ’™ Tare da Khayratie Er Mutan Ungogo..๐Ÿ’‹ Ina roqon Allah S.W.A yadda ya bani ikon farawa ya bani ikon ganin na kammala wannan littafi. Wannan littafi qirqirarren labari ne,wanda nake fata ya fadakar,wa'axantar,Ilimantar da kuma nishadantar da masu karatu. A matsayi na yar kowo wanda wannan shine littafi na na farko ina son idan anga kuskure ko gyara ayi gaggawar sanar dani. Na sadaukar ga wannan littafi ga Qawata,Aminiyata kuma yaruwa mafi soyuwa agareni wato RUQAYYA RABI'U MUSA(RUKY NICE)Allah yabar qauna. Bismillahirrahmanirrahim๐Ÿ™ ๐Ÿ…ฟ1-๐Ÿ…ฟ5 Kamar kullum yauma kwance nake akan makeken gadona ina sana'ar tawa wato kuka,wanda ya zamar min jiki duk daren duniya sai nayi shi tunda na tsinci kaena a sabuwar rayuwa.Jin Alamar bude qofa yasa na fara qiqarin hadiye kukana dan ko kadan banason yara na suxo su ganni a wannan hali. Iman ce ta qaraso ta fara tashi na don a zatonta bacci nake. "Aunty!Aunty!ki tashi daddy yace kiyi mana shirin bacci mu kwanta gobe akwai school" Saida na qarasa goge hawayena da hijabin dake jikina kafin na fara sakkowa daka bed din. Wanka nayi mata na shiryata cikin nighty dinta pink sannan na hade mata qashinta da band. "Kije ki kira ya shahida itama tazo tayi bacci"nace ina mai nuna mata qofa dan surutunta ya fara haddasan ciwon kai ga kuma kukan da nasha. A tare suka shigo da yoghurt dinsu a hannu. "Aunty kinga daddy ya siyo mana kuma harda coculate ita mun shanyeta a falin daddy"shahida tace tana nuna min jarkar dake hannunta. Murmushi nayi tare da cewa"gsky daddy ya kyauta,kunce masa kun gode koh? "Mu mun fada amma ya shahid bai fada ba"shahida ta kuma fada. "Wai da gaske babyna?"na tambayi iman ina shafa kanta ganin alamun bacci ta fara ji. Cak na dauketa kasancewa suma basu da jiki kamar ni na dorata bisa gado,kafin na kama dayar akun tawa nayi mata wanka. Saida nayi musu addu'a na tabbatar sunyi bacci kafin na fara shirin nawa wanka. Shirina na gama cikin nawa kayan baccin milk calour kafin na feshe jikina da turare kasancewa ta ma'abociyar son qamshi. Kaina na qurawa ido ta jikin mirrow,basai an fada min ba nasan ni kaena na rame,to ba dole na rame ba?kullum cikin aiki da walahar yara ga kuma kuka da yawan tunani. Allah sarki Amminah gsky ina kewarta amma ita da abbi naga alamar sun manta dani tunda ko kiransu nayi a waya bata ma shiga bare nasa ran jin muryarsu.zaman kadaecin nan ya fara damuna tunda idan su iman suka tapi school tun safe sai yamma,shi kuwa mai gidan sai nayi kwana biyar,shida kai har sati daya ma ni banganshi ba. Kana naka Allah na nasa,wai ni khadija Autar Amminta nice rayuwatah ta dawo haka?Ba haka na tsara rayuwar aure na ba amma ga a yanda taxo min.Amma a hakanma cikin godiyar Allah nake kuma na yarda da qaddara. Nasan mai karatu yana cikin zaquwa da sonjin cikakken tarihi na,to ga asalin wacece ni๐Ÿ‘‡ FLASHBACK. Cikakken sunana shine khadija isah muhd,mu cikakkun hausawa ne maxauna garin kano unguwar karkasa. Mahaifinmu ma'aikacin gwamnati ne ba wani mai kudi ba,muna rayuwa cikin rufin asiri da kuma qoqarin farantawa juna. Amminmu mu biyar ta haifa duka mata,hakan yasa dangin mahaifinmu suka dora mata karan tsana acewarsu uwar mata ce taqi haifar da namiji,ko a xatansu mutun shike xabarwa kansa abinda zai haifa?oho. Rashin jituwar dake xakanin Ammi da dangin abbi yasa ko kadan bamu qaunar zuwa wani abu daya dangancesu,tun abbi yana fada har ya gaji ya qyale mu,sbd ko munje ma ranmu a bace yake dawowa. Yaya Aisha itace babba a gidanmu,sai Ya Ruqayya,ya Fatima,sai kuma yaya zainab wadda daga ita Ammita qara haifar wata amma babu rai,tun daga lokacin haihuwar ta tsaya sai bayan shekara 3 sannan ta samu cikina wanda kowa ya cire tsammani dashi,hakan yasa kowa ya dora soyayyarsa kan cikin tare da fatan sauka lafiya. Bayan wata tare Ammi ta haifeni,wanda kowa yake cewa kyawun yan gidanmu aka tattaramin,a cewarsu nafi kowa kyau tun ina jaririya. Haka na taso cikin gata da kulawar iyaye na da yayyena abin alfarina,dan kowacce ji take dani komai aka samo to na autar ammi ne,haka abbi duk fitar da zaiyi to sai da tsarabar auta zai dawo. Ina primary 5 akayi bikin yaya Aisha inda aka kaita unguwar sharada. Munyi kewarta sosae duk da a lokacin ba wani wayo ne dani ba amma nasan shaquwar dake tsakaninmu,dan so da dama muna sharing problems ayi a gama ammi batasan anyi ba,duk da lokacin ba wani fahimtar abinda suke mgn nake ba hakan bayasa su ware ni muna tare koda yaushe school ce kawai take raba mu,hakan yasa bani da wasu qawaye bayan yayyena sai Nusaiba da muke class daya kuma a farkon layinmu gidansu yake shiyasa muke tafiya tare mu dawo tare. Tafiyar yaya aisha yasa gidan ya fara shiru dan ya ruqayya ba xama take ba tana schooling a CAS kano. Ya fatima tayi candy tana waiting result yanxu koda yaushe tana gida,amma kasancewarta bamai yawan mgn ba yasa bama wani hira sosai,to ni dimma ba wata gwanar surutu bace,barni da da shagwaba da son jiki,koda yaushe ina jikin ammina ko su yaya fatima. Ya zainab yanxu tana Ss1,mu kuma muna shirye shiryen common interest. Cikin ikon allah mukai Exam,inda rana tsaka abbi yazo da mgnr data tayarwa da duk yan gidan hankali,wai xa'a kai autar ammi bording school.saida aka kai ruwa rana kafin aka shayo kan ammi ta yarda akaini ni kuwa banda kuka babu abinda nakeyi. Ammi dasu yaya fatima kullum cikin rarrashi,nice a siyon wannan a siyon wancan har ranar tafiya mkrnt tazo aka kaini makarantar yan mata ta DALA. Fadin irin kukan dasha bata lkc ne dan harta abbi nasan kawai dauriya yake amma su yaya zainab suma sunsha kuka. Bansha wani wahala ba kasancewa ta kyakkyawa kuma mai tsafta yasa seniors suka ringa nan nan dani nidae a daddafe mukae first term,sbd ni irin mutanennance masu maqon uwa bare tawa uwar da muka shaqu sosai. Ranar da muka samu hutu kuwa murna biki har baka๐Ÿ˜ฌ. Abbi ne yaxo ya daukeni a machine dinsa.muna xuwa gida kuwa duk yanuwana sun hallara,abinci kuwa kala kala kamar ana jiran dalibi daga malesia๐Ÿ˜œ. Ranar nayi yinin farin ciki,inda nake maqale da jaririyar yaya Aisha mai suna muhibba.Anan nakejin zancen sa ranar ya ruqayya amma abin takaicin ina school xa'ayi. Tun daga lkcn na fara kukan shagwaba ina buga qafata a qasa ni a dole yar auta๐Ÿ˜„ "Kinga ni miqon 'yata karki fadarmin da ita"ya aisha ta fada tana karbar muhibba. "Dan allah ya ruqayya kice a daga bikin sai na nawo"na fada ina zama akan cinyarta. "To Ammi haka za'ayi"tace tana ture ni daga jikinta. Dukansu dariya suka saka hakan ya bani haushi nayi dakunmu da gudu kamar xanyi kuka. Ina jiyosu suna hira akan yawan shagwaba da son jikina Ammina tana shigarmin. Sai dare mijin ya aisha yaxo ya dauketa,ba mgnr da bata min ba naqi kulata dan har lkcn fushi nake dasu hakan yasa ko dakin ban kwana ba na tafi gadon ammi na kwanta. Washe gari gidansu Nusaiba na yini inata bata labarin bording ita kuma allah da yayita tana sha'awar bording school.Sai wajen magriba na dawo. Haka har hutunmu ya qare babu yadda ya aisha batai ba naxo gidanta hutu naqi,nace ni ban gaji da gani abbi da ammi ba.haka dai na tattara na koma inata kumbure kumbure na. ๐ŸฅฐKhayratie Er mutan Ungogo๐Ÿ˜˜ ๐Ÿ’™๐Ÿ’™ RABON KWADO... ๐Ÿ’™๐Ÿ’™ ๐Ÿ’‹ Er mutan Ungogo๐Ÿ’‹ ๐Ÿ…ฟ6-๐Ÿ…ฟ10 Haka rayuwa ta cigaba da tapiya,inda akayi bikin ya ruqayya da mijinta abbas aka kaita gidanta dake tarauni. Ya fatima ta samu gurbin karatu a polytechnich dake nan kano. Yau satinmu daya da dawowa daga mkrnt,sosai nake jindadin holyday din dan nakaiwa yanuwa na xiyara nida ya zainab kasancewar ya fatima lectures sun mata zafi. Yau Lahadi na tashi da shirin xuwa gidansu qawata Nusaiba dan ammi tace xuwanta biyu bama nan,kuma nayo mata guxurin labarurruka kala kala na mkrntrmu. Ammi nayiwa sallama na dauki sabon hijab din data siyamin ina mkrnt na saka na fice abuna kicin nutsuwa. Sallama naita kwadawa a qofar falon kafin daga bisani najiyo alamar tafiya. Dogon saurayi ne mai cikar halitta sai saje da qasunba da sukayiwa dogon hancinsa qawanya,duk da a lokacin shekaruna 13 ba wani kyakkyawa na sani ba amma xan iya cewa wannan kyakkyawa ne.ko ba'a fadan ba nasan wannan yayan nusaiba ne duk da ban taba ganinsa ba amma kamanninsu ya nuna hakan. Kamar yadda ya zuba masa ido haka shima ya zuba min nasa idanun.bazan iya tantance iya lokutan da muka dauka a haka ba kowa da abinda yake kissimawa a ransa. Sallamar Nusaiba ce ta katse mana kallon da mukewa juna na qurrilla.Duk sai naji kunya ta kamani amma shi gogannaka falon ya koma ba tare da yace komai ba. Da gudu nusaiba taxo ta rungume ni tana dariya. "Ai naxata baxaki xo ba harki koma" "haba dae xanxo mana,Ammi ma tace zuwanki biyu bama nan" "Eh mn,ai na qagu nasha lbrn bording,daxu ma fa har umma na tmby da xata fita nace xanxo gidanku shine ya sadiq ya hanani" "Au dama wannan shine ya sadiq din?"nace ina rage muryar kamar ina tsoron karya jini. "Eh shine,shima shekaran jiya ya dawo,ni banso dawowarsa ba gashi sai aiki yake saka mutan....."bata qarasa ba mukajuyo muryarsa mai sanyi yana cewa"Nusaiba!! A tare muka xaro ido dan a xatonmu yaji mgnr da mukeyi. Da sauri ta shiga falon. Bata dade ba ta fito tana tura baki gaba. "kinga ni koh?wai chemist zanje na siyo masa mgnin mura,kuma fa idan umma nanan ba'a aikena titi" "To muje na raka ki dan nima yau yawo nakeso" Tafiya muke ina bata labarin bording,mun kusa tsallakawa titi kawai naji kamar an watsamin ruwa a jiki.Mexan gani?kwata a jikin hijabi na sabo?? Bin motar nayi da ido dataketa sharara gudu ba alamar zata tsaya ma. Nusaiba na kalla dan tuni idanuna suka ciko da kwalla ganin yadda mutane suke kallo na wasu har dariya suke min. "Kiyi hqr bari naje na siyo na dawo,shi kuma shida allah"nusaiba tace tana yin gaba da sauri. Bazan iya tsayawa a gurin ba,ga zuciyata dake zafi hakan yasa nayi tafiyata. Ina shigo layinmu na hango motar dazu a kusa da uncompleted building din dake layinmu,ban san lokacin da zuciya ta tiqoni ba na nufi motar dan ni kaina bansan idan naje mexanyi ba. Ina xuwa nayi knocking glass din dan ba'a ganin na ciki.Nafi munti biyu a tsaye dan harna fara tunanin mai motar baya ciki kafin naga an fara sauke glass din qasa. Saida na fara galla masa harara kafin na fara mgn da fada dan ya kaini bango. Kai makaho ne da kana ganin ka fallatsawa mutum kwata bazaka iya tsayawa ka bashi hqr ba?ko an fada maka kudi haukane?aikin banxa kawai."nace tare da jan tsaki nayi hanyar gida. Ina shiga soron gidanmu na fashe da kuka sannan na shiga.da ya fatima naci karo taci kwalliya xata fita ta riqeni. "Me akai miki auta?fadawa kwata kikayi?" Duk tmbyoyin da tamin ban amsa ba saima qara sautin kukan da nayi dan Ammina ta jiyo. Ai kuwa saeda ta fito nayi mgn. "Ba wani ne a mota ya fallatsamin kwata ba" "Allah sarki yi hqr qila ma bai sani ba"ya fatima tace tana ciren hijabin. Jin Ammi taqi mgn yasa na kuma fashewa da kuka๐Ÿ˜ฉ. Itadai ya fatima gaba tayi dan tasan halina sai Ammi ta rarrasheni xanyi shiru. Dakinmu na shiga ya zainab sai bacci take,kanta na fada na cigaba da kukana har bacci ya dauke ni. Sai magriba na tashi sannan Abbi ya dawo dan haka yana bani tsaraba na ware aka cigaba da hira dani. Washegari nusaiba tazo itama daqar na kulata dan haka nace itace ta jamin aka zuban kwata.da yake tana da hqr har hqr ta vani sannan muka cigaba da hira. Ana gobe xamu kama mkrnt na fito raka nusaiba naci karo da ya fatima da wannan mutumin da nayiwa rashin kunya ranar daya xuban kwata a hijabi. Inaji nusaiba ta gaida shi ni kuwa na maka masa harara nayi gaba abina. "Kai khadija meyasa baki gaida saurayin ya fatima ba?kinga baxata ji dadi ba"Nusaeba tace. "Bazan gaida shi dinba,kuma insha allah bazata aureshi ba mugu kawai๐Ÿ˜" Kinsanshi ne?" "Eh mn shine ya xuba min kwata ranar,bakiga na taho ba?zuwa nayi nayi masa rashin kunya" Zaro ido nusaiba tayi"a ina kika ganshi? A...mgnr ce ta maqale sakamakon hango yayan nusaiba da nayi yana nufo inda muke. kallo na yake yana tahowa nima kuma na kasa dauke ido daga kansa ko meyasa?oho Saida ya qaraso sannan na iya dauke idona daga kansa.Qasa nayi da idon ina wasa da azurfar dake hannuna. "Yaya har kun dawo?"nusaiba tace da alama ba'asan ta fito ba. "Kika qaramin mgn saina bigeki,wuce gida kafin ka Karya ki" ya sadiq yace. Sumsum nusaeba ta wuce ko sallamar da muka sabayi idan xan koma mkrnt yau ba muyi ba. "Ke kuma baki iya gaisuwa ba koh?"najiyo muryarsa. Har lkcn na kasa dago ido. Ina yini?"na fada a hankali "Bazan amsa tunda saida na roqa" Murmushi kawai nayi dan wata kunyarsa nakeji ban san dalili ba. Gobe sai scul ko?"naji yace Daga masa kai kawai nayi alamar eh dan duk a takure nake kodan ban taba tsayuwa da wani haka ba,kuma ga kallona da yake yi duk da ina kallon qasa amma a jikina inajin kallona yake. "To kimin alqawari xakiyi krt kuma kece Xakiyi first position wannan term din" Bansan lkcn dana daga idona ba na kalleshi.gyada min kansa yayi alamar haka yake nufi. "Nayi maka alqawari"nace "Tom kije gida kinga anfara kiran magriba." To nagode"nace tare da juyawa na nufi gida. Ina idar da sallah ya fatima ta kama kunnena na dama. "Dama jira nake ki idar yarinya,shine dazu kina ganin Abdul kikaqi gaidashi koh?har nusaiba ta gaidashi amma ke kikayi kaga koh?" "To wai ba shine ya zubamin kwata ranar ba"na fada kamar xanyi kuka sbd har lkcn bata sakar min kunne ba. "Sbd ya zuba miki kwata sai kiqi gaida shi koh?so kike yace yan gidannan bamu da tarbiyya?" Aa kiyi hqr zan gaidashi gobe๐Ÿ™"na fada danta sakarmin kunne na. Daya fi miki yarinya"tace kafin ta sake ni. Da dare kwatakwata bacci ya qaurace min,in banda tunanin yan maganganun da mukayi da ya sadiq ba abinda nake.To me hakan ke nufi? Daqar bacci barawo ya dauke ni. Washegari da safe Abbi ya lula dani mkrnt cike da kewar yan gida da kuma........ Guess who? Duk wadda ta fada dai dai Mari uku ๐Ÿ’™๐Ÿ’™ RABON KWADO..๐Ÿ’™๐Ÿ’™ Na Er mutan ungogo๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ Luv u oll Readersโคโคโค ๐Ÿ…ฟ11-๐Ÿ…ฟ15 Haka na mayar da hankalina akan krt domin ina son na cika alqawarin dana daukarwa ya sadiq duk da damacan ina mai da hankali dan ana sakani sani farko farko a class dinmu,amma wannan term din saina qara jajircewa dan ganin na bawa kowa rata a class dinmu. Da lokacin visiting tazo naji dadin ranar domin duka yanuwa sunxo wani abin dadinma harda nusaiba. Haka mukaita zaga mkrnt ina nuna mata abubuwa da kuma mutanen da nake bata lbrnsu. Da lokacin tapiyarsu yayi kuwa rasa inda xansa kaina nayi dan saida ya aisha taji haushina wai na fiya fitina indai ban nutsuba bazasu qara zuwa ba. Dan dole na nutsu na goge hawayena amma xuciyata suya kawai takeyi. Nusaiba ce ta kama hannu na mukai inda ba mutane sosai ta bani wata qaramar leda wai inji ya sadiq๐Ÿ˜€ Dama yananan?"nace da ita ina murmushi. "Eh to da ina zaije?kullum ya dameni wai saina bashi lbrnki,yanxu bakiga shirin da mukeyi da shi ba" "Allah sarki,kice ina gaidashi" Hararar wasa tayi min"ni yar aikenki ce?" To shikenan karki fada din"nace ina yin gaba. Saida muka koma hostel na nutsu sannan na bude ledar. Kayan zaqi ne akai wrapping a wata leda mai gyalli sai zobe mai kyau da qaramar takarda. Takardar na bude ina murmushi. Harna gama karantawa ban fahimci komai ba,kawai dai nasan akwai tunin alqawarin dana daukar masa. To meyasa ya damu nayi krt?tmbyr danayi tayiwa kaina kenan amma ban samu amsa ba. Kodai sona yake?Aa bazan yaudari kaina ba nasan ni ba mate dinsa bace,dan nasan bazai rasa budurwa ba.mutumin da ya gama service Yana neman aiki me xaiyi da Er Js 3. Haka dai na gama tunani na na tattara kayan na ajiye. Jiya muka dawo daga mkrnt amma allah allah nake naje gidansu nusaeba,abinda da sae ammi tayi ta mita banason fita kullum ni kenan a gida kamar daddawa amma yau nice washegarin da na dawo xan fita. Dana tambayi ammi xanje gidansu nusaiba saida ta tmby me ake a gidan?nace kawai dai na gaji da zama ne xanje muyi hira.Dama su ya fatima tunda na dawo basa xama wai shirin bikinta ita da wannan mutumin. A jiyanma dana dawo saida mukai da ita nace mata"wai ya fatima ki rasa wa xaki aura sai wannan mutumin? Janyo ni tayi"wai dan allah me abdul yai miki kika tsaneshi haka?" "Kawai mugu ne shiyasa,kuma dan yaga yana da kyau da mota shine yake wulaqanta mutane" Bata cemin komai ba ta sake ni. Dan haka ni ba wani shirin bikin da nakeyi dan a zuciyata haka nace dama muna mkrnt xa'ayi,dan yanxu har ya fatiman ma haushinta nakeji. Na dade a bakin get din gidansu nusaeba na kasa shiga,ni kaina bansan dalili ba. Ganin qaninta haidar yasa nace yaje yace mata taxo ina kiranta. Bai dade ba ya dawo wai ya sadiq yace idan bazan shigo ba na koma. Murmushi kawai nayi na samu wani dutse a qofar gidan na zauna dan na koma gida tmbyoyi xansha a wajen ammi. Wasa nake da qasa ina rubutu ina gogewa naji tsayuwar mutum a kaina. Ya sadiq ne tsaye ya xuban mayatattun idanunsa,ba shiri na maida kaina qasa dan gani nayi ya qara wani kyau. "Gidan surukanki ne shiyasa kk kasa shiga koh?" Ban dago ba saima qara boye fuskata da nayi cikin hijab. "Ki tashi ki shiga ciki kinga kowa yazo wucewa saiya kallemin ke" Maganganun nasa naita juyawa a kwakwalwata "a kalle masa ni?" Maganarsa ce ta katsen tunani. "Tunda bazaki shigo ba ki tafi gida"ya tada yana shigewa gida. A hankali naja qafafuna nayi gida dan ji nake kamar ban kyauta masa ba. Haka naje gida sukuku nacewa ammi nusaeban batanan. Washegari inata zuba idon ganin nusaeba shiru har dare. Tsahon kwana biyu ba nusaiba duk sai naji ba dadi dan nasan haka kawai bazata qi zuwa ba,dazu ammi har tmbyta tayi wai nusaeba nanan kuwa. "Auta xo ga cingam din biki ki kae gidansu nusaiba"ammi tace tana lissafa cingam. "Wlh dan gidansu nusaeba ne da bazan kai cingam din bikin mugu ba" na fada ina kallon qofar dakinmu dan nasan ya fatima ta jiyo ni. Ai kuwa fitowa tayi nawo hanyar waje da gudu ina dariya. "Ammi ki rabani da yarinyar nan wlh xan zane ta"ya fatima tace. "Ke yanxu akan saurayin kike wannan abun?ke kuma bansan sakarci xo kije inda na aike ki"ammi tace. "To Ammi kiyi mata mgn karta dake ni" Jin anyi min shiru yasa na shigo ina rabe rabe. Wullo min ledar cingam din tayi na dauka na fice,dama hanyar xuwa gidan nake nema,dan inaso naga nusaeba(nasan wata sai tace na fadi gsk๐Ÿคฃ). Ganin ya sadiq danayi da abokinsa yasa nayi sauri na shige gidan duk a zatona bai ganni ba. Nusaeba na tarar dana wanke wanke ai kuwa tana ganina ta dafe ni. "Ke kam nusaeba bakya girma,yanzu sae kin kayar da ita."najiyo muryar umma. Har qasa na tsugunna na gaida ita na bata saqon kafin mu shige daki nida nusaeba. "Wai ranar kikazo kikaqi shigowa" "Ke sauri nake ammi tace karna dade" "Ba wani nan,gashi kinja yaya yace ya qara ganin qafata a qofar gidanku saeya karya ni" "Dan allah da gsk?"Nace jikina a sanyaye. "to da baki ganni a gidan ba washe gari?kindai sanni da son labari" "To meyasa ya hanaki zuwa? "Oho masa,ni kinga na qagu ma ya fara aiki yayi aure yabar mana gidan" Rass!!!naji gaba na ya fadi,amma na qaqalo wani murmushi kawai. "Kinga tapiya zanyi kinga munata shirin biki"Nace ina miqewa. "Kai dan allah yanxu baxaki bani lbrn ba" "Zan baki idan kinxo gida"nace ina fita daga dakin. Har bakin get ta rakoni,ai kuwa muka ci karo da ya sadiq dina๐Ÿ™Š๐Ÿ™ˆ. Da gudu nusaeba ta koma ni kuwa nayi kasaqe. Khadija!!"naji yace a hankali Daqar na samu kalmar Na'am ta fito a bakina. ๐ŸฅฐKhayratie Er mutan Ungogo๐Ÿ˜˜ ๐Ÿ’™๐Ÿ’™ RABON KWADO...๐Ÿ’™๐Ÿ’™ NA ER MUTAN UNGOGO๐Ÿฅฐ ๐Ÿ…ฟ16-๐Ÿ…ฟ20 "Meyasa bakyajin mgn? Dagowa nayi na kalleshi dan bansan rashin jin da nayi ba. Banaso nasa mutum abu ya qiyi kinji?daga yau idan nace kiyi abu ki ringa yi,ko kinaso muyi fada? Girgixa kai kawai nayi ina tuna me yasa ni banyi ba. "Jiya banji dadin abinda kikai min ba,nace ki shigo kk qi" "Kayi hqr"nace ina satar kallonsa. "Ni dama banyi fishi ba,kinsan meyasa?" Qara girgixa kai nayi. "Sbd bazan iya fishi dake ba" Shuru nayi dan gaba daya na kasa gano ma'anar mgnr. "Idan kin gama school me kk son xama?"ua katsen tunani. "Inason zama zama doctor" "Aa khadija ba doctor xaki zama ba,kinsan me nakeson ki xama?" Girgixa kai nayi. "Inaso ki zama lawyer,nayi miki alqawarin baki gudummawa da goyon vaya da aljihuna da lokacina indai kikai min alqawari zaki maida hankali kiyi krt" Juya maganganunsa kawai nake dan naji yana mgn kamar wani abbinah. "Koda yake gana abbi aure yake muku koh"naji ya fada "Indai nace inason krt zai barni" "To ki maida hankali indai kinaso mu shiryaa" "Tom" "Kije gida kar ammi taga kin dade" Mamaki nake yadda sunan ammi da abbi yake radau a bakinsa. "Ko akwai wani abu"yace dan ganin na tsaya. "Eh,dan allah kabar nusaeba ta runga zuwa gidanmu" "Murmushi yayi"kema zaki ringa zuwa nan gidan?" Eh" To zan barta ta ringa zuwa" "Ngd"nace ina wucewa. Ranar asabar aka daura auren ya fatima da wannan mutumin,lahadi aka kaita gidanta dake rijiyar zaki. Sosai gidan ya daina yimin dadi sbd daga ni sai ammi dan ya zee ma ta fara zuwa wata computer school. Hakanne yasa kusan kullum muna tare da nusaeba,idan batazo ba ni zanje.A hankali muka fara shaquwa nida ya sadiq,har takai indai a rana banganshi ba sai inji duk na damu๐Ÿ™. Hakan yasa na bashi no.din ammi duk dare muna waya ba tare data sani ba. Ana gobe xan koma school kuwa kuka ne kawai banyi masa ba amma shagwaba ba'a mgn. Daqar ya lallasheni mukai sallama dan saida ya nunamin indai ban maida hankali nayi krt yadda anan gaba zaiyi alfahari dani ba zai daina kulani. Haka washegaru na tashi sukuku har abbi saida ya tmby ni koh lpy?nace masa kaina yana min ciwo. AFTER 3YEARS Abubawa da yawa sun faru a cikin shekaru uku,ciki kuwa harda kammala krtna na secondry,inda na dawo gida cikin dokin ganin iyayena,yanuwa,aminiyata da kuma masoyana a haqiqa wato ya sadiq. Zuwa wannan lkc soyayya mai qarfi ta qullu a tsakanina da ya sadiq amma a gidanmu ya zainab ce kawai tasan tsakaninmu. Ya aisha yanxu yaranta 4 biyu maza biyu mata,ya ruqayya itama yaranta 4 duk maza,sai ya fatima da take da yara 3 namiji sai mata guda biyu,ya zainab yarta daya amma allah yayi mata rasuwa,sai yanxu da take dauke da wani cikin. Sosai nakeson yaran yanuwana kamar yadda iyayensu suke sona,amma wani abinda zai bawa mai krt mamaki har yanxu bama ga maciji da mijin yaya fatima,shiyasa da wuya idan nazo hutu naje gidanta,tun tana fishi dani harta bari ganin abin nawa bana qarewa bane.Ammi har abbi ta fadawa shima yayi min nasiha akan riqo nidai na bishi da to amma banajin wata ma'amala xata shiga tsakaninmu dashi. Gama mkrnt ta yasa ya aisha ta siyamin waya mai kyau da tsada,ya ruqayya ta bada kudi a saka ni a mkrntr koyan girki da kuma kwalliya,ya fatima baiwar allah dinkuna tayimin wajen kala bakwai,Inda ya zainab ta siyamin kayan kwalliya dana shafa. Gsky ni yar gata ce shiyasa a kowani lkc nake alfahari da yanuwana duk da kasancewarsu mata amma suna qoqarin yimin abinda koda yanuwa maza gare ni ba lallai suyi min haka ba. Zuwa yanxu tsantsar kyauna ya qara fitowa,duk da kasancewata baqa amma inada wani kyau na ban mamaki,inada gashina dai dai na zaman falo,sannan ni bamai qiba bace,doguwace ni mai dogon hanci sannan inada beauty point a kumatuna,kai na taqaice muku dai ni mai kyau ce kawai๐Ÿ˜‰. Wayar da nayi yasa muka bude sabon babin soyayya nida ya sadiq,abinda yake qara min qaunar ya sadiq shine yadda yake bani kwarin gwiwa akan karatu,ya damu da krt na sosai dan lkcn da zamu fara SSCE kamar shi zaiyi exam din duk ya damu,kullum cikin nasiha da qarfafa gwiwa,dan yace sai yaga na fara krt a university sannan zai kai mgnr mu gaban abbi. Cikin ikon allah na mayar da hankali na akan koyan kwalliya da girki dan naga yanxu sune mace duk wadda bata iyasu ba ita ce baya. Yauma kwance nake a kan katifar dakinmu ina waya da ya sadiq ammi ta dago labule. "Sannu daddawar daka,ni bansan yaushe kk koyi zaman daki ba mutum ma ya rasa abinda kikeyi a daki" Janye wayar nayi a kunne na kafin nace. "kaii ammi ni maixan qulla baki sani va" Kya dai ji dashi idan tayi wari ai xamuji,ki tashi ki damawa abbinku fura nasan yanxu yana hanya" Da to na bita,saeda ta fita mukai sallama dashi na tafi yin aikin. Kwana biyu abbi yayi tpy qauyensu ziyara,kadaici ya isheni na shirya na tafi gidan ya Aisha. Sosai muke hira inda yaranta suka baibaye ni kamar su maidani ciki. Babbar itace muhibba yanxu shekararsa 6,sai Ammar,hanif sai kuma Hudallahi. "Wai bazaku qyaleta ta huta bane ba muhibba?kuyita damun mutane kamar xaku shige cikinsa"ya aisha tace ganin yadda suka tarusuna sukuwa a kaina. "Qyalesu yaya ai nama fasa kwana tunda basa jin mgn" Da sauri suka sauka kowa ya nutsu dan anaso na kwana. Kwana biyu nayi niyyar yi amma washegari nace ni gida zan tafi na baro ammina ita kadai. "Ai dayake wani abune xai cinyeta ko kuma ke inkinje wani abu xatayi miki"ya aisha tace "Yaya baxaki gane ba,ita uwa dadine da ita,jina nake kamar na shekara bama tare duk da dazu munyi waya,kuma nusaiba tace tanason gani na da lbr" "Oho kudai kuka sani,dan ba tun yau ba nasan akwai abinda kuke qullawa dake da nusaiban" "Wlh ba abinda muke qullawa sai alkhairi"nace ina ninke kayan dana cire xan shiga wanka. "Oho dae idan tayi wani maji"tace tana fita a dakin. Sai yamma na baro unguwar,kamar kullum saida muka sha dabi da yaran sannan na taho,wai kowa sai ya bini,wayyo ni uwar yara๐Ÿ˜œ. Tun dana sauka a titi wani yake bina a baya,ina sane dashi,qara sauri kawai nayi dan banaso ya biyoni cikin layinmu dan yau juma'a nasan yanxu ya sadiq yana gida kar ya jamin fishin sahibil qalb๐Ÿ˜. Assalamu alaikum"najiyo sallamarsa a baya na. Saida na runtse idona kafin na amsa sallamar,dan banso ya min mgn ba dan mun kusa da gidansu ya sadiq. "Baiwar allah idan baxaki damuba ba ki bani mintina biyu muyi mgn" Banyi mgn ba dan sallamarma nasan muhummancinta shiyasa ba amsa,gashi hankalina yana kan qofar gidansu ya sadiq dan ban manta marin da nasha shekaru biyu da suka wuce ba agunsa,akan wasusun biyomu nida nusaiba munje gidan wata qawarmu. A lkcn harna koma mkrnt ban qara ganin dariyar ya sadiq ba,a lkcn muka fara ganowa sona yake dan alamu duk sun bayyana. Ganin har lkcn mutumin nan bina yake yasa na tsaya dan neman maslaha. "Dan allah bawan allah kayi hqr,wlh an kusa bikina kuma babanmu idan ya ganni dakai dukana zaiyi" "To shikenan yanmata na gode,yaushe ne bikin sai nazo idan an gayyace ni" Murmushi kawai nayi wanda yayi dai dai ta qarasowar ya sadiq inda muke tsaye,kallon da yayimin kawai yasa nasha jinin jikina.Wucewa yayi dama akan lifan dinsa yake da dukkan alamu daga wajen aiki yake dan a gidan radio yake aiki kasancewarshi dan jarida. Ban kuma bita kan wannan mutumin ba nayi gaba dan duk shiya jamin nasan halin ya sadiq da kishi amma saiya wayence wai karatu karatu,wai na daena kula kowa inba haka ba zan samu rauni a krt na kuma daga baya yaxo ya kasheni da kalaman soyayya๐Ÿ˜„. Daga lkcn xuwa dare nayi masa missed calls sunyi goma,hakan ya bani tabbacin na taro march. Da wuri nayi bacci dan yau ba abokin hirar.nusaiba na kira itama swich off dan haka baccin takaici ne ya daukeni. ๐Ÿ’™๐Ÿ’™ RABON KWADO..๐Ÿ’™๐Ÿ’™ Na Er mutan ungogo๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ Luv u oll Readersโคโคโค ๐Ÿ’™๐Ÿ’™RABON KWADO...๐Ÿ’™๐Ÿ’™๐Ÿ’™ ๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹Er mutan ungogo๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ ๐Ÿ…ฟ21-๐Ÿ…ฟ25 Washegari ma haka naita kiran ya sadiq wayar a kashe,duk sai naji ba dadi duk da allah ya sani ba laifina bane. Wayar nusaiba na kira dan samun mafita kasancewarta abar shawaratah. Hello sis"najiyo muryarta daga can bangaren. Naam sis kin tashi lpy?" Lpy lau,yadae najiki haka?" Sis ya sadiq ne ke wahalar da zuciyata" Hhhh,me kuma ya faru?" Labarin abinda ya faru na shiga bata. Tab!ashe kece kk jamin yau akaqi amsa gaisuwata" Dan allah da gsk?wayyo ni ya zanyi?" Kawai ki shareshi malama idan ya gama fishin nasa ya sauko,mutum yaita wani abu sai kace mijinki?" Aa sis kar miyi haka dake,kishi pa halak ne,nasan nice mai laifi dan haka dole sai na bashi hqr" Kedai kk sani" Au haka ma xakice koh?" Allah kuwa sis wani lokacin kamar a dakeki,ki qyaleshi dan allah kepa mace ce allurar cikin ruwa mai rabo ka dauka" Kinga ni shawara na kiraki ki bani ba wani qarin bayani ba,in kuma baxan samu ba nayi gaba" Maida wuqar to,yanxu ya kk so ayi" Inaso ki tayani bawa ya sadiq hqr har mu shawo kansa" Tom xan gwada na gani" Haka mukai sallama na ajiye wayar na shiga aikin gida,amma xuciyata duk a jagule. Har dare ba wani canji dan ya kunna wayar amma yaqi amsa kiran. Dan dole na hqr,amma xuwa yanxu na fara fusata akan lamarin,Taya zanta kiransa yaqi dagawa,dole nabi shawarar nusaiba na qyaleshi har lkcn da xai sakko. Haka na cigaba da harkokina dukda xuciyata ta kasa jure rashin ya sadiq amma haka naita dauriya,qarshe dai na yanke shawarar barin unguwar gaba daya. Inason xuwa gidan ya fatima amma wannan mijinnata mai baqar zcy shine banson gani.dan hk gidan ya ruqayya nace zanje. Da azahar na shirya na tafi tarauni dan nusaiba ma text nayi mata nace na tapi. ya ruqayya taji dadin zuwana sosai haka itama muka sha hira,yan samarinta haka suka dameni kowa da irin tasa fitinar. Munif ne babba,sai mufid shine mai sunan abbi,affan da kuma qaramin mubin. Qaunarsu nakeji har cikin raina,amma abinda zai bawa kowa mamaki shine duk yaran yayyena nafi qaunar yaran ya fatima,duk da rashin jin shahid amma ina qaunarsa.yaron fitinanne ne yafi kowa rigima a cikinsu hakan yasa nake cewa halin babansa yayo,itadai ya fatima murmushi ne kawai nata. Yaran ya fatima shahid ne babba,sai shahida sannan iman ita yanxu shekarta daya da rabi. Da dare haka mukaita tatsuniya munashan dariya,itadai ya ruqayya gurin mijinta ta tafi ta barmu anan. Bacci sukayi suka barni ina zuba,qarshe dai da dai daya na kaisu makwancinsu kafin nima na nemi nawa. Tunda na taho na kashe wayata,sai yanxu da kadaici ya isheni na kunna,dan da a gidane yanxu ina kwance kan qafar abbi munashan hira. Kamar jira ake kiran nusaiba ya shigo. Haba sis tun dazu inata kiranki a kashe" Wlh sis kashe wayar nayi" To ai kin kyauta,naga text wai kin bar unguwar?" Eh wlh unguwar ce ta daina min dadi" Eh lallai,dama ya sadiq ne ya tmby ni wai mene ya samu wayarki ya kira a kashe" Dan allah da gsk? Eh mn,dama bana fada miki ba,shi kanshi bazai iya jurewa ba,amma duk kibi ki damu kanki" Uhmm sis baxaki gane matsayin ya sadiq a zcytah bane,baki san zafin so ba da fushin masoyi shiyasa kk fadar haka" Sannu wadanda suka yankewa soyayya cibiya,ni kinga yaushe zaki dawo?" Ki tmby ya sadiq,dan sai ranar daya daina fishi dani xan dawo" Dif!naji ta kashe wayar ko ba'a fadan ba nasa haushin mgn ta taji.oh nusaiba danger,ita gani take banida aikin yi idan ina irin wadannan maganganun batasa ita kadai nake iya fallasawa sirrin zuciyata ba,dan koshi ya sadiq din cikin qorafi yake wai banasonshi. Jin danayi nusaiba tace ya sadiq ya tmbyta ni ya tabbatar min ya sauko daga fushin da yayi,kuma a kowani lkc xai iya kirana,amma inason ya dandana abinda naji dan haka nayi addu'a tare da kashe wayar nabi lpyr gado. Washegari ma saida muka gama aikace aikace nida ya ruqayya,nayi wanka nayi breakfast sannan na dauko wayar dan yaran gidan duk sun tafi mkrnt,mubin ne kawai tunda shi bai isa xuwa mkrnt ba kuma shi ba wata hira xamuyi da shi ba. Data na kunna dan ganin me duniya take ciki,dan ni ban damu da hawa online sosai ba(ba kamar Er baby ba da kullum ana online๐Ÿ˜œ). Sosai nake jin dadin chatting din kiran ya sadiq ya shigo.har ta katse ban dauka ba saboda nidin mai ajice๐Ÿ˜„,duk da dunbin qaunarsa da kewarsa da nake hakan bazai sa na zubarda ajina na 'ya mace ba. Daya qara kira ma saida ta kusa katsewa na dauka.vanyi mgn ba shima kuma baiyi ma.munkai tsahon 5mnts a haka dan da niyyata na kashe wayar tunda bashida abin fada. "Khadija ni kk wulaqantawa koh?"najiyo muryarsa data fi kama data marasa lpy. Nipa ba wulaqanta ka nake ba" To mene wannan inba wulaqanci ba?ko kuma raini ne dan kinga ina wasa dake?" Aa kayi hqr"nace dan jin ya fara mgn da fada fada. Waye wanda na ganki dashi jiya?" Saida nayi murmushin mugunta kafin nace. "wani ne wai sona yake,shine ya biyoni yaga gidanmu wai zai turo a tmbyr masa izini" Wani dan iska ne kuma a ina yake?baki fada masa ba yanxu xakiyi aure ba?ko kuma baki fada masa akwai wanda yake jiranki ba?wlh wlh khadija ki gaggauta sallamarsa idan ba haka ba kuma.." Dif!ya kashe wayar.ni dariya ma wallahi ya bani,wannan tmbayiyi kamar yana mini interview? Sai daga baya tausayinsa ya kamani,gsky ya sadiq masoyi ne na gsky,tun bansan kaina ba yake dakon soyayyata,kuma ya haqura da aure badan wai baya buqata ba Aa sai dan gani ya ingantan rayuwa ta ta hanyar ganin na fara karatu,dan yanxu karatun shine mutum. Ya sadiq yana taka matsayi kala kala a gurina,wani lkc yazo min a matsayin yaya wanda yakeji da qanwarsa wanda nakan ji dadin hakan koba komai nima naji abinda masa yayye maza sukeji,wani lkcn yakanxo a matsayin masoyi yaita kasheni da kalaman soyayya dan a wannan bangaren gwani ne,wani lkcn yakanxo a matsayin yayana wanda zaimin fada tare da bani umarni shima nakanji dadin hakan dan nasan wani fada da nasihar da yakemin ko nusaiba da take qanwarsa ta haqiqa bayayi mata. Hakan kan qara masa matsayi da qima a idona,shiyasa ko yaya naga ransa ya baci sai na shiga damuwa musamman ma idan nice silar bacin ran nasa,dan shima ko kadan bayason yaga bacin raina.ya sadiq ko budurwa yayi saiya fada min,nakan tmbyshi ki meyasa yake fadan shine yace shi bayaso zargi ya shigo cikin lamarinmu shiyasa tun kafin naji yake fadamin da bakinsa kuma da sigar da zan fahimci inda ya dosa. Kai ya sadiq mutum ne wanda ko wace mace take fatan ya xama abokin rayuwarta amma ni qaddarar rayuwa ta nisanta ni dashi,tayi mana katangar a tsakaninmu mai wahalar rushewa๐Ÿ˜ญ๐Ÿ’™๐Ÿ’™RABON KWADO....๐Ÿ’™๐Ÿ’™ Na Er mutan ungogo๐Ÿ’‹๐Ÿ’–๐Ÿ’‹ ๐Ÿ…ฟ26-๐Ÿ…ฟ30. A gurguje Haka rayuwa ta cigaba da tapiya inda result dinmu ya fito muka zana jamb nida nusaiba dan alhmdllh result dinmu yayi kyau. Cikin ikon allah muka nasarar samun admission da taimakon abban su nusaiba,inda zan karanci bangaren law nusaiba kuma bio/chem. Farin ciki wajen yaya sadiq ba'a mgn nasiha da shawarwari kuwa na shasu kamar shine abbi na. Cikin nasara muka fara gudanar da lectures dinmu a jami'ar bayero,inda mukayi da ya sadiq xaije wani course na 6months daya dawo xa'akai mgnr aurenmu wajen abba asa rana duk a lkcn dan yace bayaso asa sama da wata biyar. Haka mukai sallama dashi da tarin nasihohinsa gareni ya tafi ya barni da kewarsa dan har kuka saida nayi. Sosai lectures suka fara daukan dimi,inda muka maida hankali kan krt ba wasa. Ya fatima ce ta kirani wai nazo gidanta mijinta yayi tafiya ga dawainiyar yara ga kuma cikin da take dauke dashi. Haka na tattara na tafi dama kuma gidanta yafi kusa da scul din tunda ita tana rijiyar xaki. Duk wata dawainiyar yaranta nice nake musu kafin na tapi scuk duk da suma idan suka tafi tun safe sai yamma,amma fitinar shahid sai abinda ta qaru. Yauma haka yaje ya zazzagen handbag dina a qasa ya dauko handouts dina ya yi min zane a jiki. Naji haushin abinnan naje tana barandar gidan tana shan iska. "Yaya kinga yadda shahid ya wuqanta min handout dan allah" Kinga auta kuje can ku qarata na gaji da shirginku keda shahid,tsoronsa kk ji da baxaki hukunta shi ba?ko kuma idan danki ne haka zaki biye masa kina kai qararsa?" "Amma yaya kina ganin yadda ya rainani ban isa nayi abuba sai yayi mgn kamar wata sa'arsa" "Dan allah ni kuje ku gyaleni naji da kaina"tace tana kwanciya. "Wlh mai rabani da yaron nan sai allah"nace ina komawa cikin gidan. Bansan fitinar shahid takai haka ba saida naga muna dambe dashi kamar wani sa'a na,ai kuwa zuciya ta deboni na samu nasarar warbar dashi a qasa aka samu akasi goshinsa ya fashe ya kwalla qara,wadda tayi dai dai da qarasowar daddynsa da ya fatima wanda da dukkan alamu dawowarsa kenan,amma da nasan yau xai dawo da daga mkrnt na wuce gidanmu bare na kwashi wannan kayan takaicin. ko kadan banyi nadamar abinda nayi ba sai danaga jinin da yake fitowa daga goshinsa. "Hayaty bari muje asibiti ko zamu sami jinin ya tsaya"daddyn nasu ya fada yana wani cin magani. Ni kuwa nace idanma dan ya ganni a gidansa ko dan najiwa dansa ciwo yake wannan abin to gobe da safe ma xan kama gaba na,yanxunma dan dare yayi ne amma da ba abinda xai hanani tafiya. Daki na shige dan gaba daya gidan haushi yake bani. Ban dade da kwanciya ba ya fatima ta shigo. "Auta badai bacci ba bakici abinci ba?" Ni na qoshi" Haba autar ammi ki taso kici ko kadanne,ko kinason ammi tace bana baki abinci?" Girgixa kai nayi. "Yawwa to tashi muje kici,sai ki dauko su iman daga falo ki kyautar dasu" Kadan naci abinci na daukosu dama tunda naxo tare muke kwana,bacci nayi bansan lkcn da yan asibiti suka dawo ba๐Ÿ™ Washegari tun asuba nayi wanka dan inason barin gidan tun kafin mai gidan ya farka daga bacci. Da yake weekend ne har 9 ina xaman jiran yaya tazo dan tana bangaren mijinta.da yake gidan babba ne gsky kuma an kashe masa kudi iya kudi,dan duk gidan ya fatima yafi na sauran haduwa. Kiran wayarta nayi a kashe dan haka tea kawai na hada na rubuta letter na ajiye mata a gado nace mata kirana akayi muna da text 10 shiyasa na tafi kuma daga can xan wuce gida. Daqar na samu abin hawa kasancewar safiya ce kuma unguwar shuru kowa yana cikin gida dan saida nayo tpy mai nisa kafin na samu amma duk ban damuba sbd sa kai ance yafi bauta ciwo. Ammi batai mamakin ganina ba dan tasan halina,kuma tasan bama jituwa da gidan ya fatima,abbi ne dai yake ta tmby ko lpy na dawo yanxu kamar an koro ni? "Abbina mafarkinka nayi shine yau da safe nace ni saina xo na ganka"na fada a shagwabe. Dariya yayi "Khadijatu bakya gajiya da shirme,kin baro su lpy dai koh?" Amsa masa nayi na shige daki. Da ya fatima ta kira kuwa nasha fada wajen ammi nidai bance komai ba tunda nazo gida. A kwana a tashi babu wuya a wajen allah. Yau muke saka ran dawowar ya sadiq,amma bansan mai yasa ba yau din banajin dadin jikina ga gabana da yaketa faman faduwa. Haka na fara shirin xuwa scul ina karanta du addu'ar data xo bakina. A scul ba haka na yini sukuku,da muka fito a lecture na fara kiran number din ya sadiq dan jin ko wani abu ne ya sameshi. Hello yanmatanah"naji ya fada hakan ya tabbatar min yau a masoyi yake mgn,dan naga ko jiya da mukai waya sai wani rawar qafa yake waishi angon wata5 ne. Yaya kun sauka ne?" Eh mun sauka heartbeat tun dazu amma office na wuce dan akwai wani record da nakeson bayarwa" Tom saika qarasa gidan nima yanxu tapiya xanyi" Har kun gama lecture dinne?" Aa kawai inason xuwa gida ne dan tun safe gaba na yake faduwa" Subhanallah!kina addu'a dai koh?" Eh nayi" To kije gidan anjima zamiyi waya" Sallama mukayi na kamo hanyar gida. Ina shigowa layinmu na hango motoci biyu a qofar gidanmu,ga wasu mutane a tsaye dana hango a gefe. Gaba nane ya tsananta faduwa,tunani kala kala da zullumi sun cika min xuciya. Banbi takan mazan da suke qofar gidan ba na fada gidan a sukwane. Mutum na fara cin karo dashi a kwance an lullubeshi da farin gyalle,abbi a tsugunne a gefe yana sharar kwalla sai ya ruqayya itama da take rusar kuka. Gabana ne ya cigaba da bugawa kamar xai fado,ya ruqayya na nufa ina tmbyrta ina amminah dan banason gargina ya tabbata. Nuni tayi min da daki ba shiri na fada dan tabbatarwa. Ammi na zaune akan sallaya tana jan carbi,lokaci lokaci tana share kwalla. Ammi meya faru?waje ya mutu?"Na tmby ta rarrauniyar xuciya. "Sai hqr auta yayarku fatima ta rigamu gidan gsky" Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!!ya fatima?ya fatima kuma?ya fatimanmu ce ta rasu?? Cak!nunfashina ya tsaya Inda duhu ya fara mamaye idanuna wanda daga lkcn banqara sani meya faru ba kawai dai na bude ido na ganni a gadon asibiti. Ya zainab ce zaune a gefe na,kana ganinsa xaka gane tarin damuwar dake tare da ita. A hankali abubuwa suka fara dawo min inda wani kuka yazo min bai daci. Ya zee da gsk ne?da gsky ya fatima ta rasu?da gsk ta tafi ta barmu baxamu qara ganinta ba?yanxu shikenan...." Ya xainab ce ta saka hannu ta rufen baki. Ya isa haka,baki ga halin da kk ciki ba?bakiga tsahon kwana biyun da kk dauka ba numfashi a tare dake ba?ki inason ki qara janyo mana wata damuwar?"kuka ne yaci qarfinta dan dole tayi shiru.nima kukan nake ina jadadda cewa wai ya fatima ta rasu. Auta yaya ta rasu,yaya ta tafi baxata qara dawowa ba,mutuwa ba qarya bace fatanmu allah ya jiqanta da rahma,duk da tayi mutuwar shahada dan bata kai ga haihuwa ba allah ya karbi abinsa" Haka muka hadu mukaita rabxar kuka. "Yaya inasu ammi?"na tmby da dasasshiyar muryata. "Dukkansu suna gida karbar gaisiwa kinsan yau sadakar uku,amma duk dare suna zuwa duba ki" Allah mai iko ashe dai da gsk nayi kwana biyun ba motsi,allah kenan mai rayuwa da mutuwa. Turo qofar da akayi ne yasa muka tsagaita da kukan.nusaiba ce da ya sadiq,wanda shima kallo daya xakayi ka gano yar ramar da yayi. Da gudu nusaiba tazo ta rungume ni tare da sakin kuka.haka muka hadu ba mai rarrashin wani shidai ya sadiq fita yayi sai gashi sun dawo da doctor. Dubani yayi tare da rubuta magunguna sannan yayiwa ya sadiq bayanin xasu riqeni xuwa gobe idan sunga jikin da sauqi xasu sallame ni. Godiya ya sadiq ya masa kafin ya sadiq din ya xauna ya fara mana nasiha mai shiga xuciya.sosai nasiharsa tayi tasiri a xuciyoyinmu,saida ya tabbatar mun samu nutsuwa kafin su bar asibitin. Da dare su abi sukaxo da su ya aisha amma wai babu ya fatima,allah mai iko.nan ma wani sabon kukan mukasha,Daqar abbi ya shawo kanmu da nasihar yadda da qaddara don hatta ammi ma kukan take. Sai can dare suka tafi.ya zee ta samu bacci amma ni tunanim rayuwa kawai nake.haka fa rayuwar take yau kananan gobe baka nan. Tuno ranar da dukkansu sukazo gida muka hadu akaita wasa da raha da kuma shirye shiryen suna idan ta haihu,ashe bama zata haihun ba bare ayi sunan. A ranar da zasu tafi mijinta yazo daukanta,na rakata ina dauke da iman datayi bacci dansu ya aisha tun yamma suka tafi ita kuma ta zauna tace sai mijinta ya dawo daga aiki xaixo ya daukesu,har na saka iman a mota ina musu bye bye ta jawo kunne na. Wato kina ganin daddyn shahid bazaki gaida shi ba koh?kewai a rayuwarki bakya yafiya ne?" Turo baki nayi nace"to bana gaidashi ba" Baki gaida shi ba na sani kawai dai kin fada ne,kuma zanyi maganinki tunda bakyajin mgn"Tace tana sakin kunne na. Kiyi hqr kinji sweet yaya"nace ina kamo hannunta. Idan kinason na hqr sai kin yafewa mijina" Ganin mijin ya shiga mota yasa banyi mgn ba na tafi ina mata waving da hannu ashe na bankwana nayi mata๐Ÿ˜ญ. Haka naita tunanin abubuwan da suka faru tare da ita,bansan lkcin da bacci barayo ya sace ni ba. ๐Ÿ’™๐Ÿ’™RABON KWADO...๐Ÿ’™๐Ÿ’™๐Ÿ’™ Tare da Er mutan ungogo๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ Gaisuwa da jinjina gareku masoya abin kaunata,musamman yan khayratie's hausa novels allah ya bar xumunci.๐Ÿค๐Ÿค ๐Ÿ…ฟ31-๐Ÿ…ฟ35 Washegari wajan 11 na safe ya sadiq ya dawo asibitin,inda yaje ya karbo takardar discharge kafin ya shigo. Ina kwana"nace ina satar kallonsa ganin ya tsaya yana kallo na. Lpy lou,ya jikin?" Da sauqi" Ya haqurinmu?"ya kuma tmby. Kwal kwal idona ya ciko da kwalla. Kinga ni ba kuka nace kimin ba,ina ya zee din?" Yanxu ta fita bansan ina taje ba" Shine take barmin princess dina salon azo a sace min ita?" Murmushi nayi kawai ina qara satar kallonsa dan ramar dana ga yayi. Ya sadiq naga ka rame?" Ba dole ba nernah?kina gadon asibiti rabi rayuwa rabi mutuwa" Allah sarki ya sadiq,allah ya bani ikon faranta maka tsahon eayuwata"na fada a xcytah dan bana iya sakewa dashi indai mu kadai ne a guri,duk da dadai nasan bazai cutar dani ba,amma idan muna tare da nusaiba hira mukesha sosai. Khadija kinga yadda allah yake al'amarinsa koh?a yadda na tsara washegarin dana dawo zan tura wajen abbi amma sai wannan rashin ya samemu,kinga dole a jinkirta zuwa lkcn da komai xai dai dai ta" Allah ya kaimu"nace cikin jin kunya. Wa yaga khadijan abbi amarya"ya fada da sigar wasa. Haka yaita jana da hira har ya zee ta dawo muka tattaro muka dawo gida. Har lkcn muna samun masu xuwa gaisuwa duk da abbi ya hana zaman makoki. Ina maqale dasu iman dan tausayin yaran nakeji yana ratsa zuciyatah,Allah ka haskaka kabarin ya fatima amiin๐Ÿ˜ญ. Bayan kwana biyu kowa ya watse dan abbi haka yace su ya aisha su koma gidajensu xaman ya isa haka ita dai ta riga ta tafi ba dawowa zatayi ba. Tafiyarsu ta karamin kadaici dan su shahida ma wai anxo an daukesu daga gidan kakarsu. Tsahon sati biyu bana zuwa scul,hakan yasa abbi ya ringa fada dan dole na na shirya na tafi dama nasan ba'a son ran ya sadiq naqi xuwa ba dan bayasan takura ni ne kawai,ga exams da muka kusa farawa. Yau satin ya fatima 3 da rasuwa. Ina kwance a daki ina karatun text naji an daga labule,duk a zato na ammi ce amma ga mamaki na naga abbi. Saurin tashi nayi xaune ina gyara dankwalin kaina tare da yiwa abbi sannu da xuwa ganin yana niyyar shigowa dakin. Ban gama mamaki ba sai danaga yana zama a gefen gadon. Abbi ashe ka dawo?daxu na tmby Ammi tace ka fita" Eh khadijatu na dawo"yace yana kama hannu na. A hankali na zame na kwanta akan qafarsa kasancewata mai son jiki๐Ÿ˜Š. Khadija wannan zuwan dan ke nayi shi,ina neman wata alharma ne a wajenki shiyasa na tako da kaina a matsayina na mai nema" Abbi alfarma kuma?har inada abinda zaka nema a wajena?"Nace ina wasa da yatsun hannunshi. Eh,fitarnan da nayi naje can wajen sirikan marigayiya fatima ne,kuma a zaman da mukayi mun yanke shawarar ranar asabar mai xuwan nan za'a mayar da auren fatima kanki" Wata zabura da nayi bansan lkcn da na fado a kan gadon ba. Abbi kamar ya?ban fahimci me kace ba"Nace duk a rude. Kinga inaso ki kwantar da hankalinki,muma bawai mun yanke hukunci ne haka kawai ba.bayan fatima ke kadai ce wadda zata iya riqe yaranta da gsky,kuma xaki riqesu kamar kece kk haifesu,koba danni ba khadija ki tausayawa rayuwar yaran nan ki maye musu gurbin mahaifiyarsu" Wayyo allah na,Allah yasa mafarki nake akan wannan batu,kai ko mafarki nake nasan to yau mummunan mafarki nayi. Khadija ki min mgn mana,bawai kuka nace kiyi mini ba"na jiyo maganar abbi. Kuka?dama kuka nakeyi?Wayyo wlh ina ganin na haukace. Abbi dan Allah ka taimaki rayuwata karka hadini aure da mijin ya fatima,abbi akwai wanda yake sona tsakani da allah dan allah ku tausaya masa"nace ina ja da baya. A hankali abbi ya kamo ni ya kwantar dani akan qafarsa,bai kuma mgn ba sai daya ga na fara samun nutsuwa. Khadija kk ce akwai wanda kk so?" Eh Abbi,wlh ya sadiq yana qaunatah,Mutuwar nan ce ta hana a aiko manya daga gidansu" Shiru yayi na tsahon lkc kafin ya kira sunana. Khadija yanxu a matsayi na mahaifinki ashe baxan iya baki umarni kibi ba?a dazu naxo miki a matsayin mai neman alfarma a yanxu kuma ina mai baki umarni ne,inaso ki saka a ranki zuwa ranar asabar zaki bar gidan nan da sunan aure"bai tsaya bi takaina ba ya tureni daga jikinsa ya fice daga dakin. Daga inda ya tureni nidai haka na kasance a kwance,ban sani ba suma nayi?kai ba suma bace qila mutuwa nayi tunda ance idan mutum ya mutu yana jin abinda mutane suke cewa kamar yadda nima ina iya juyo wayar da abbi yakeyi da mutane cewar ranar asabar akwai daurin auren yar wajensa. To wai har gani mutum yanayi idan ya mutu??na tmby kaina ganin ammi ta shigo dakin ta riqoni fuskarta da alamar tausayawa daqar nema idan ba kuka tayi ba. Khadija kiyi hqr kinji?ki yiwa abbinku biyayya insha allah zakiga ribar hakan" Wai ammi batasan na mutu bane take tayimin mgn?bari dai nayi mata bayanin na mutu suje kawai su binne ni. Ammi" Naam khadija kiyi hqr kinji,kiyita addu'a allah yasa haka shiyafi alkhairi" Wayyo masu karatu wlh na haukace,nashiga uku da gsk na hauka ce....... Wait a moment....๐Ÿ˜Š๐Ÿ’™๐Ÿ’™RABON KWADO...๐Ÿ’™๐Ÿ’™ It's me Er mutan ungogo๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ ๐Ÿ’™๐Ÿ’™RABON KWADO...๐Ÿ’™๐Ÿ’™ Er mutan ungogo๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ ๐Ÿ…ฟ46-๐Ÿ…ฟ50 wai auta yaushe zaki bar wahalar da kanki kibar asarar hawayenki?Abinda kk yiwa kuka ya riga da ya faru,to y not ki samawa zcyrki sauqi ki dauki qaddara"ya aisha tashe ganin na samu damar kuka. Banyi mgn ba domin nasan duk abinda zan fada mata bazata fahimta ba kunga maganar bata da amfani. Da yamma ina kwance ina saqa da warwara ya aisha tazo ta zauna a kusa dani. Ki tashi kije kiyi wanka" Banyi musu ba na tashi dan ni kaina nasan ina buqatar wanka. Dana fito kaya na tarar akan gadon sababbi ne na dauka na saka dan banida lkcn tsayawa tambaya. Ga kayan kwallaya nan kiyi"naji ya aisha tace. Kallonta kawai nayi. Banajin zan iya shafa wani abu"nace ina niyyar kwanciya. Ko kwalli baxaki sakawa wannan kodadden idon ba?" Ya ilahi!!banasan damuwa.Daukan kwalli nayi na saka tare da daukan hijabin dana cire. Ki bude jakar can akwai hijabi,bakya ganin wannan yayi datti?" Jakar na nufa kawai dan naga abin bana qarewa bane.jin an fara kiran magriba yasa na fasa kwanciyar na tada sallah dan nayi alwala danaje wanka. Dana idar ma zama nayi ina azkar din yammaci.sai danayi issha kafin na tashi akan sallayar.kamar jira take ta wani biqon plat din abinci. Karba kawai nayi na fara dannawa badan inajin dadin abincin ba. Kiyi hqr kinji auta?insha allah zakiyi alfahari da wannan auren,kinsan dai abbi yana sonki bazaiyi abinda yasan zai cutar dake ba.maganar sadiq kuma ki ajiye gefe ki rungumi mijinki da 'yay'an yaruwarki" Surutanta taita yi dan maganarta bata min rai take.wai zanyi alfahari da wannan qaddararran auren?na rungumi mijinah?uban waye yace mijina ne?wlh na kusa fara dura ashariya tunda baza'a barni na huta ba. Turo qofar akayi tare da sallama.Abbi ne da mijin ya fatima yana binsa a baya kamar tsohon munafiki. Da gudu shahida da iman suka zo suka dafe ni,su kansu yaran yanxu haushinsu nakeji. Turesu nayi a jikuna ina tsugunnawa ina gaida abbi. Sama sama ya amsa min kafin ya fara yiwa ya aisha mgn. Kin karbo takardar sallamar ne?" Eh abbi na karbo" To ita ta gama shiryawa dai koh?" Eh ta gama" To khadija ga mijinki nan zaku tafi,kya qarasa jinyar acan dakinki,Allah ya qara sauqi ya bada zaman lpy"yace yana kallo na. Tirqashi!!wato ni ko irin gatan da masu gata suke dashi na sallama da mahaifiya da karbar nasiha a wajenta ni bazan samu ba?bani da gatan da za'aje gida a dauko ni sai a asibiti?wannan ua alama ce ta an gaji dani,taya ma mijin zaiga daraja ta bare kuma miji irin wannan?" Tunani nane ya tsaya danjin ya aisha ta kama hannuna ta nufi hanyar waje dani. A wata muta ta sakani kafin tace. Auta kiyi hqr,nasan akwai abubawa da dama daba haka ya dace ayi ba,amma inaso ki cire komai a raki kuma ki ringa tuna waye abbi da kuma matsayinsa a wajenki.Akwai wata akwati zaku gani duk kayanki ne na buqata,sauran suna cikin wardrob,Ammi tace tana miki fatan alkhairi" Kifa kaina nayi a cikin cinyoyi na dan ganin abbi yazo bakin motar,inaji sukai sallama dashi suka shigo cikin motar. Dukansu a gaba suka zauna saini a baya,inajin tashin motar na sawa raina nayi bankwana ta walwala,kuma nayi dammarar karbar ko wani matsayi ne a gidan tunda hakan aka zabar min. Shiru motar tayi sai surutun su iman da suke tayi ba qaqqautawa,shidai da eh ko a'a yake binsu dashi. Jin motar ta tsaya yasa na tabbata ta faru ta qare.inaji duk suka fita a motar amma ban dago ba. Malama ki fito kona janyo ki wlhnajiyo muryarsa a gefe na. A hankali na dago kaina dan nasan zai iya aikatamin abinda yafi haka. Saurin kare fuskata nayi dan ganin hasken daya dalle min fuska.a hankali na zuro qafata wadda na tabbatar ba gidan ya fatima muka zoba,to inane nan?Allah yasa gidan yankan kai ya kawo ni su yankani na huta. Ganin yayi gaba ya fara tpy yasa nabi bayansa.Ganin girman gidan da qofofin da muke wucewa yasa na gasgata zargina. Ki jirani anan"yace ba tare da ya juyo ba ya cigaba da tafiya. Guri na samu na zauna ina tunanin inda kuma su iman sukayi dan dana fito banfansu ba. Ganin ya dade bai dawo ba yasa nace qila ciniki ne bai fada ba. ๐Ÿ’™๐Ÿ’™RABON KWADO...๐Ÿ’™๐Ÿ’™ Written by:Er mutan ungogo๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ ๐Ÿ…ฟ41-๐Ÿ…ฟ45 Dana koma daki ma wani sabon kukan na dasa. Da gsk na rasa ya sadiq?da gsk ya sadiq ba RABONA bane ba?lallai duk wadda ta samu ya sadiq tafi kowa sa'a a duniya,ni kuma dana rasa shi pa?ni kuma nafi kowa rashin sa'a. Da dai daya yayyena suka fara zuwa,inda kowacce tazo tausata take da bani hqr,abin takaicin ba wadda ta bani goyon baya a cikinsu,nidai a ganina zuwan nasu bashida wani amfani. Haka suka tattara suka tafi ba wani cigaba,dan har lkcn naqi cin abinci kuma ban bar yin kuka ba. A jiya zuwa yanxu harna rame,fuskata kuwa kamar an hura baloom sbd kumbura,muyarta kanta zuwa yanxu ta dashe,hawayena ne dai basu kai da qafewa ba. Ina a kwance sallah ce kawai take tayar dani,ga wani azababben ciwon kai dake damuna. Wayata ce ta fara neman agaji amma banyi niyyar dauka ba,dan tun rana ake ta faman kirana nasan bazata wuce yan scul dinmu ba ace banxo test ba. Jin qarar wayar ta fara damuna yasa dole na miqe na dauko dan da alama mai kira bashida niyyar dainawa. "Heartbeat"shine sunan da yaketa reto a saman wayar,banda niyyar daukar wayar saima tasata a gaba da nayi ina rusa kuka. Mai zai kira ya fada min bayan yasan na rasa shi?kodai ya yarda da qudirina na guduwa ne? Da sauri na daga wayar.Daga can naji yace"khadija!! Naam"nace da dasasshiyar muryata. Har yanxu bazaki bar yin kuka ba koh" Bafa kuka nake ba" To naji,inason qara baki hqr ne,khadija bawai dan mun rasa juna shikenan mun daina rayuwar farin ciki ba,dan allah ki saki ranki,ki bada hadinkai ayi abinnan lpy kinji?dan allah kada kiyi wani abu dazai badawa abbi rai,kindai san fishin iyaye akan yayansu" Kuka nake kawai,dan yanxu na tabbatar na rasa shi,wlh da gsk na rasashi๐Ÿ˜ญ. Kinci abinci kuwa?" Naji yace. Eh" Bakici ba nasani,kuma idan kinason mu shirya ki tashi ki dauko abinci kici,idan ba haka ba kafin gobe zakiji lbrn nabar garinnan" Dan allah karka tafi,wlh xanci"na fada ina qara sautin kuka. Baiyi mgn ba sai tari da yake tayi tun inayi masa sannu har nayi shiru ina kuka. Ya sadiq ka gani koh?kaga zamu cutar da kanmu sbd farin cikin wasu koh?"na fada danjin tarin ya lafa. Dif!!ya kashe bawar ba tare da yayi mgn ba,haka naita bin number din amma bata shiga. **-**-**-**-**-*-* Yau ta kama Alhamis,wanda a lissafinsu abbi saura kwana biyu daurin aurenah,zuwa lkcn duk wanda ya gani saiya tausaya min,sbd na lalace kamar ba khadija yar gayu ma'abociyar san ado da kwalliya ba. Ina zaune a tsakiyar yayyena da suketa yimin magiyar naci abinci,amma ni duk hankalina ba'a kansu yake ba,tunanin nusaiba da ya sadiq nake,dan tun ranar da mukai wayar nan banqara samunshi a waya ba,nusaiba ita kanta na kasa samunta,gashi har lkcn ban qara ganin qeyarta a gidan ba. Khadija!khadija!!ko khadijan bata nan ne"najiyo muryar abbi na kwalan kira. Saida gabanah ya fadi danni yanxu tsoron kiran abbi nake. Ya ruqayya ce ta miqon hijabi tare da cewa "maza kisaka kije kiranki yake" saka hijab din nayi na fito tsakar gidan wanda na kusa kwana 4 ban tako shi ba. Abbi yana tsaye a qofar dakinsa naje na zube ina gaisheshi da kodaddiyar muryata. Ki shiga ciki Abdurrahman yananan"yace yana nunan dakinsa. Abdurrahman?waye kuma haka? Ganin ya tsaya yana kallonah yasa na miqe na danna kaina dakin ba tare da nasan mai kiran ba. Rass!Gabana ya fadi dan ganin mijin ya fatima a zaune kan sallaya ya tankwashe kafa yana latse latse a wayarsa. Ba shiri na tsugunna dan jin wani jiri danayi yana qoqarin kayar dani. Mun dauki tsahon lkc a haka inata saqa da warwara na jiyo takunshi yana qarasowa inda nake. Zama yayi daf dani wanda yasa bugun xcy tah qaruwa da sauri. Sai daya gama qaremin kallo danni koya aka kalleni inaji a jikina. Dubeki dan Allah,ke a dole xaki aure mijin yayarki saboda cin amana koh?to inason ki sani,zaki aure ni kamar yadda kike buqata,amma ki sani na karbi wannan qaddararran auren nakine sbd yarana suna buqatar 'yar aiki..." Inaso kisa a ranki ba gidan aure zakije ba gidan aiki xakije,dan nasan kinsan nafi qarfinki tun ba yau ba" Sannan naji kamar ance wai kina zuwa jami'a koh?to inaso daga yanzu ki saka hakan a tarihin rayuwarki,domin zakina zama a gida ne kinamin gadin gida na.wannan shine saqon idan kin kiyaye kanki" Innalillahi wa inna ilaihirraji'un!! Wai meyake faruwa da nine?me yasa rayuwa zata juya min baya irin haka?bayan hanashi aurena da akayi burin nashi ma baza'a bari na cika masa ba? Bansan lkcn da ya fita a dakin ba,sai muryar abbi dana jiyo yana cewa. "me kuma kk jira har yanxu baki shiga ciki ba" A hankali na furta"Abbi ku taimaka min na cigaba da karatu na koda zaku aura minshi dan allah" Guri ya samu ya zauna kafin yace"khadija inaso kisan cewa abdurrahman a yanxu kamar mijinki yake,zan iya cewa yafini iko dake,kamar yadda ya buqata baya son kici gaba da xuwa mkrnt dole ki hqr da hakan.ki duba dukka yanuwanki akwai wadda take gidan miji take karatu?fasa rayuwa sukayi a haka?to ki cire wannan a ranki ki tashi ki bani waje" A hankali na miqe na fara barin dakin,wanda a lokacin juya ta dibeni ta zubar a wajen. Ina farkawa na ganni kwance akan gadon asibiti. Meyasa ma aka kawoni?aida an barni a gida na mutu kawai na hutu da wannan baqin cikin. A hankali na miqe zaune dan inajin qarfin jikina.zare allurar qarin ruwan nayi na wurgar domin bana buqatar hakan. Tashi nayi na shiga toilet nayi fitsari tare da dauro alwala dan nasan ana bina sallah tunda yanxun naga kamar safiya ce. Ina fitowa naga ya aisha a zaune.Riqoni tayi tanamin sannu,nidai daka na amsa na dauki hijabin dana gani na saka. Yaya yau wace rana?"nace ina kallonta. Yau friday" Au ai nazata wannan karon sati nayi a asibiti ba numfashi,amma duk da haka langwabewa zantayi har abbi ya gaji ace an fasa auren,tunda ina asibiti dai ba'a dauran aure ba. Saida na idar da sallah nayi wanka naci abinci na kwanta muna dan taba hira da ya aisha dan da alama taji dadin ganin nadan saki raina. Da dare inajin muryarsu abbi na rufe ido haka suka gama maganganunsu suka tafi. Washe gari nida ya aisha muka yini a asibitin dan bayan ita ba wanda ya leqo,da dare ma haka. Ranar lahadi ina zaune na jingina da bango ina sana'ar tunani,ya aisha kuma taje gida,naji an turo qofar dakin tare da sallama. Nusaiba ce,dan haka da gudu na tashi naje na rungumeta. Kuka ta fara min,ni kuwa naje na zaunar da ita a kan gado ina kallonta,domin ni sha'awa take bani yadda take kukan dan ji nake dama nice na samu damar zubar da hawaye. Ganin batada alamar tsayawa da kukan yasa na fara rarrashinta. Daqar tayi shiru tana sauke ajiyar xuciya. Sis ina kk shiga inata nemanki,kuma kinsan a halin danake ciku ina buqatarki a kusa dani?"nace ina qarasa goge mata hawayen fuskarta. Kiyi hqr sis,bama nan ne sai dazu muka dawo,kuma danaje gidan ammi tace kuna asibiti" Eh muna nan tun ranar alhamis,amma ina kukaje?" Muna asibiti ne ya sadiq bashida lpy,wai ciwon zcy ne ya kamashi,yanata aman jini,shine uncle dinmu yace kawai a fitar dashi abroad,to jiya da dare suka tashi mukuma yau da safe muka taho" Ciwon zcy?nusaiba ciwon zcy fa?meyasa ni bai kamani ba sai ya sadiq?Nusaiba dan allah ki kaini wajenshi naganshi"nace ina girgizata. A yanxu sis ya sadiq ya mana nisa,yana buqatar nisanta da duk wani abu dazai daga masa hankali,kuma a matsayinki na matar wani a yanxu inaso mubar mgnr wani daban" Matar wani?waye ya fada miki ni matar wani ce a yanxu?" Naje gida mana ammi tace jiya da safe an daura aurenki,ko kina nufin baki sani ba?? Shiru nayi dan bani da abin cewa. Yanxu ina gadon asibitinma baza'a hqr da wannan qaddararran auren ba?wai me nayiwa abbi da zafi haka harya tsane ni? Amminma cewa tayi Abbin yace anjima za'a kaiki wai kya qarasa jinyar acan,shiyasa ma na taho dan muyi sallama" Anjima za'a kaini?Lallai abin na abbi ya girmama. Sannan ya sadiq yace na fada miki dan allah ki maida hankali akan krtnki danki cika masa burinsa,a lkcn baya iya mgn sai a paper ya samu ya rubuta min"nusaiba ta kuma cewa. Wayyo nusaiba ina akeso na saka kaina?krtnma an hanani birinsu na mutu kawai.ni dama nasan na rasa komai tunda na rasa ya sadiq" Kibar fadar haka khadija,dama allah yayi bazaki cika masa burin ba" Amma nusaiba rashin adalcin.... Ya isa dan allah khadija,ba kowani mgn ake fada a irin wannan al'amarin ba,bamusan abinda allah ya boye ba" Haka nusaiba taita tausata da dadadan kalamai har lkcn da ya aisha ta dawo,bata wani jima ba ta tafi wanda sai lkcn na samu hawaye suka zubomin. ๐Ÿ…ฟ36-๐Ÿ…ฟ40 "Auta inaso ki kwantar da hankalinki,komai yayi farko zaiyi qarshe,ba tun yau ba zainab ta fadamin tsakaninku dashi Sadiq din hakan yasa na fadawa abbinku,a lkcn ya nuna goyon baya amma bansan dalilinsa na canja shawara akan hakan ba.inaso khadija kiyiwa mahaifinki biyayya duk wuya duk rintsi nasan bazai zabar miki abinda zai citar dake ba" Cuta?cuta ta wuce a raba ka da masoyinka na gsky?ta yaya wai ake tunanin xan iya rayuwa da wannan mutumin?kawai dama can anyi niyyar kashe ni da raina. Nidai nasan ammi mgn take amma baxan iya tantance abinda take cewa ba,daga qarshe ta tashi ta fita,nidai ina kwance amma na kasa tunanin komai,ko kwakwalwata ce tahi expire oho. Nadau tsahon lkc a haka ina kwance,kafin Ammi ta dawo da ita da nusaiba. Auta ki tashi kiyi sallah kafin ki daure ki danci wani abun"ammi tace tana ajiye kwanan abinci. Zama nusaiba tayi daf dani kafin tace Wai sis meyake faruwa?ammi ta aika a kirani kuma naxo batace min komai ba" A hankali na tashi zauna na jingina da bango. Sis dan allah ki taimaka kije ki fadawa abbi bazan iya rayuwa da wani ba ya sadiq ba,ki fada masa dimbin qaunar da mukewa juna.ki sanar dashi bazan iya rayuwar aure a gidan ya fatima da kuma mijinta ba,dan allah ki sanar dashi kafin zuciyata ta buga"nace ina girgiza kafadarta. Wai me kk son fada ne khadija"tace tana riqo ni. Nusaiba abbi zai dauramin aure nan da kwana shida da mutumim da ya tsaneni,zai mayar da auren ya fatima kaina" Innalillahi wa inna ilaihirraji'un"tace kawai ba tare da tace komai ba tsahon lkc. Sis ba shiru xakiyi ba ki fada min mafita dan allah" In baki shawara a matsayina na qawa kuma yaruwa wadda baza kiyi dana sani ba?" Saurin daga mata kai nayi. Khadija abinda yafi kawai kiyiwa su abbi biyyaya,kada kiyi la'akari da wanda zaki aura,matsayinsa ko kuma alaqarku ta baya,kisa a ranki kin aureshi ne dan tallafawa rayuwar yaransa marayu,kuma..." Ya isa haka nusaiba,dama baki da hankali?ina kk son nasa soyayyar da nake yiwa ya sadiq?meyasa baza kiyiwa zuciyoyinmu adalci ba?ko kowa zai fadi haka ke bai kamata ki fada ba sbd kinsan komai game da soyayyarmu,kuma idan kinsan irin wannan mgnr xaki ringa fada min ki tashi ki tafi bana son ganinki"nace ina nuna mata hanya. Bazan tafi ba khadija sbd bakece kk kirani ba,kuma gsky bazan fasa fada miki ba,ruwanki ne ki dauka ruwanki ne kiqi" Ganin ta fusata yasa na kamo hannunta. Sis dan allah ki fahimce ni,zuciyata zata fito wlh dan allah ki taimaka min"nace ina fashewa da kuka. Itama kukan takeyi,sbd tafi kowa sanin halin da ya sadiq zai shiga idan yaji wannan mgnr,kawai dai ta fada mini gsky ba dan son xuciyarta ba. Daqar nayi shiru,sannan mukayi sallah,amma ba yadda nusaiba batayi ba naci abinci naqi. Sis yanxu ina ya sadiq yake"? Ya fita aiki tun safe" Allah sarki bawan allah,allah ka kawo mana mafita akan wannan al'amari. Sai magriba nusaiba ta tafi,inda na dauki tsahon dare ina saqa da warwara amma ban samu mafita ba,dan dole na tattara komai na barwa gobe dan bawa kwakwalwa da zuciya hutu. Da safe ma ba yadda ammi batayi naci abinci ba naqi,danaga ranta ya baci ne nadan sha tea. Yau inada test amma banajin xan iya zuwa mkrnt,kai koda naje bazanyi abinda ya kamata ba,hkn yasa Na haqura. Misalin qarfe goma na safe saqon kiran abbi ya riskeni.Addu'a kawai nake allah yasa yace ya janye gudirinsa. Saida nayi sallama aka bani umarni sannan na shiga. Abbine a zaune akan kujera,sai a sadiq a qasa kansa a qasa dan banga fuskarsa ba amma ina ganinsa nasan shine. Qirjina ne ya tsananta bugu tare da fargabar abinda xanji. Can gefe na samu waje na zauna kafin abbi ya fara mgn. Khadija kamar yadda jiya mukai mgn dake kika kawomin xancen Abubakar shiyasa yau na nemeshi da yazo inason mgn dashi,to Alhmdllh yazo kuma mun tattauna dashi kuma ya fahimceni.a gsky na yaba da hankalinsa dan da ace babu wannan mgnr a qasa ba abinda zai hanani bayar dake gashi,to amma allah ya riga da ya shirya al'amarinsa,shine nace kixo ko akwai abinda xaku iya tattaunawa"Abbi yace yana tashi ya fita. Ya fahimce shi kamar yaya? A hankali na rarrafa zuwa gaban ya sadiq da har yanxu kanshi a qasa yake. Ya sadiq dan allah kacewa abbi karya bawa kowa ni idan ba kai ba,ya sadiq wlg mutuwa zanyi" Dago jajayen idanuwansa yayi kafin yace. Nernah kiyi hqr,abbi mahaifinmu ne kuma yana da damar dazai iya aurar dake ga duk wanda yaso,mu qadda cewa allah yayi damacan baza muyi aure ba" Dan allah ya sadiq karka min haka,wlh bazan iya rayuwa da wani a matsayin miji ba bayan kai,ta yaya kake ganin zan ita zama da mijin ya fatima a matsayin miji?ya sadiq a shirye nake dana bika ko ina ne dan gujewa wannan aure" Ashe baki da hankali khadija?kinsan abinda kk fada kuwa?guduwa fa?"ya fada a fusace. Eh guduwar ya sadiq,bazan iya wannan auren ma,idan ma baka yarda mun gudu ba nixan gudu"nace da fada nima. Shiru yayi ni kuma naci gaba da kukana. Daf dani ya dawo tare da riqo hannuna abinda bai taba yimin ba kenan,kai bama shiba ba wani namijin da ya taba riqemin hannu bayan abbi,Au na tuno shahid ya riqe hannuna da mukai fada๐Ÿ˜œ. Haba qanwata,bai kamata irin wadannan maganar suna fitowa a bakinki ba,tun muna yara iyayenmu suke dawainiya damu,sai yanxu dan sunxo da buqatar da batafi qarfinmu ba mu juya musu baya?banason qarajin kin kirawo zancen guduwa kinji koh?" Amma ya sadiq meyasa za'a raba mu,na dauka ko kowa yaqi fahimta ta kai zaka fahimci abinda nakeji?" Ba wanda ya isa ya rabamu nernah,ko ban aureki ba ba hakan yana nufin mun rabu ba,ni yayanki ne koda ban aureki ba,amma khadija dan allah ki maida hankali akan krt,kar kiga bama tare kisa wasa a krtnki,ki cika min burina sbd inaso kixama lawyer mai xaman kanta,ta yadda xaki taimaki yan uwanki mata,ki rage musu radadin cin zarafi da yawan fyade,na roqeki kiyiwa su abbi biyayya kinji?" Yanxu shikenan kana nufin ya sadiq mun rabu?soyayyar da kk min ta gsky ce da har xaka bada lasisi akan aure na da wani?" Saida ya goge kwallar data zubo masa duk a zatonsa ban gani ba,kafin ya qaqalo wani murmushi. Inaso ki cire duk wannan a ranki,wannan shine so na haqiqa bawai goyon baya akan son ran xuciya ba,kisa a ranki cewa damacan keba RABONA bace,ki tashi ki shiga ciki nima tafiya zanyi anjima za muyi waya" Dan dole na tashi,amma shi kansa kana kallonsa kasan dauriya kawai yake kuma yayi haka ne dan qara min qarfin gwiwa. Allah ka barmu da masoyanmu na gaskiya Luv u oll ma fams๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’™๐Ÿ’™RABON KWADO...๐Ÿ’™๐Ÿ’™ Er mutan ungogo๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ ๐Ÿ…ฟ46-๐Ÿ…ฟ50 wai auta yaushe zaki bar wahalar da kanki kibar asarar hawayenki?Abinda kk yiwa kuka ya riga da ya faru,to y not ki samawa zcyrki sauqi ki dauki qaddara"ya aisha tashe ganin na samu damar kuka. Banyi mgn ba domin nasan duk abinda zan fada mata bazata fahimta ba kunga maganar bata da amfani. Da yamma ina kwance ina saqa da warwara ya aisha tazo ta zauna a kusa dani. Ki tashi kije kiyi wanka" Banyi musu ba na tashi dan ni kaina nasan ina buqatar wanka. Dana fito kaya na tarar akan gadon sababbi ne na dauka na saka dan banida lkcn tsayawa tambaya. Ga kayan kwallaya nan kiyi"naji ya aisha tace. Kallonta kawai nayi. Banajin zan iya shafa wani abu"nace ina niyyar kwanciya. Ko kwalli baxaki sakawa wannan kodadden idon ba?" Ya ilahi!!banasan damuwa.Daukan kwalli nayi na saka tare da daukan hijabin dana cire. Ki bude jakar can akwai hijabi,bakya ganin wannan yayi datti?" Jakar na nufa kawai dan naga abin bana qarewa bane.jin an fara kiran magriba yasa na fasa kwanciyar na tada sallah dan nayi alwala danaje wanka. Dana idar ma zama nayi ina azkar din yammaci.sai danayi issha kafin na tashi akan sallayar.kamar jira take ta wani biqon plat din abinci. Karba kawai nayi na fara dannawa badan inajin dadin abincin ba. Kiyi hqr kinji auta?insha allah zakiyi alfahari da wannan auren,kinsan dai abbi yana sonki bazaiyi abinda yasan zai cutar dake ba.maganar sadiq kuma ki ajiye gefe ki rungumi mijinki da 'yay'an yaruwarki" Surutanta taita yi dan maganarta bata min rai take.wai zanyi alfahari da wannan qaddararran auren?na rungumi mijinah?uban waye yace mijina ne?wlh na kusa fara dura ashariya tunda baza'a barni na huta ba. Turo qofar akayi tare da sallama.Abbi ne da mijin ya fatima yana binsa a baya kamar tsohon munafiki. Da gudu shahida da iman suka zo suka dafe ni,su kansu yaran yanxu haushinsu nakeji. Turesu nayi a jikuna ina tsugunnawa ina gaida abbi. Sama sama ya amsa min kafin ya fara yiwa ya aisha mgn. Kin karbo takardar sallamar ne?" Eh abbi na karbo" To ita ta gama shiryawa dai koh?" Eh ta gama" To khadija ga mijinki nan zaku tafi,kya qarasa jinyar acan dakinki,Allah ya qara sauqi ya bada zaman lpy"yace yana kallo na. Tirqashi!!wato ni ko irin gatan da masu gata suke dashi na sallama da mahaifiya da karbar nasiha a wajenta ni bazan samu ba?bani da gatan da za'aje gida a dauko ni sai a asibiti?wannan ua alama ce ta an gaji dani,taya ma mijin zaiga daraja ta bare kuma miji irin wannan?" Tunani nane ya tsaya danjin ya aisha ta kama hannuna ta nufi hanyar waje dani. A wata muta ta sakani kafin tace. Auta kiyi hqr,nasan akwai abubawa da dama daba haka ya dace ayi ba,amma inaso ki cire komai a raki kuma ki ringa tuna waye abbi da kuma matsayinsa a wajenki.Akwai wata akwati zaku gani duk kayanki ne na buqata,sauran suna cikin wardrob,Ammi tace tana miki fatan alkhairi" Kifa kaina nayi a cikin cinyoyi na dan ganin abbi yazo bakin motar,inaji sukai sallama dashi suka shigo cikin motar. Dukansu a gaba suka zauna saini a baya,inajin tashin motar na sawa raina nayi bankwana ta walwala,kuma nayi dammarar karbar ko wani matsayi ne a gidan tunda hakan aka zabar min. Shiru motar tayi sai surutun su iman da suke tayi ba qaqqautawa,shidai da eh ko a'a yake binsu dashi. Jin motar ta tsaya yasa na tabbata ta faru ta qare.inaji duk suka fita a motar amma ban dago ba. Malama ki fito kona janyo ki wlhnajiyo muryarsa a gefe na. A hankali na dago kaina dan nasan zai iya aikatamin abinda yafi haka. Saurin kare fuskata nayi dan ganin hasken daya dalle min fuska.a hankali na zuro qafata wadda na tabbatar ba gidan ya fatima muka zoba,to inane nan?Allah yasa gidan yankan kai ya kawo ni su yankani na huta. Ganin yayi gaba ya fara tpy yasa nabi bayansa.Ganin girman gidan da qofofin da muke wucewa yasa na gasgata zargina. Ki jirani anan"yace ba tare da ya juyo ba ya cigaba da tafiya. Guri na samu na zauna ina tunanin inda kuma su iman sukayi dan dana fito banfansu ba. Ganin ya dade bai dawo ba yasa nace qila ciniki ne bai fada ba. ๐Ÿ’™๐Ÿ’™RABON KWADO...๐Ÿ’™๐Ÿ’™ Written by:Er mutan ungogo๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ ๐Ÿ…ฟ41-๐Ÿ…ฟ45 Dana koma daki ma wani sabon kukan na dasa. Da gsk na rasa ya sadiq?da gsk ya sadiq ba RABONA bane ba?lallai duk wadda ta samu ya sadiq tafi kowa sa'a a duniya,ni kuma dana rasa shi pa?ni kuma nafi kowa rashin sa'a. Da dai daya yayyena suka fara zuwa,inda kowacce tazo tausata take da bani hqr,abin takaicin ba wadda ta bani goyon baya a cikinsu,nidai a ganina zuwan nasu bashida wani amfani. Haka suka tattara suka tafi ba wani cigaba,dan har lkcn naqi cin abinci kuma ban bar yin kuka ba. A jiya zuwa yanxu harna rame,fuskata kuwa kamar an hura baloom sbd kumbura,muyarta kanta zuwa yanxu ta dashe,hawayena ne dai basu kai da qafewa ba. Ina a kwance sallah ce kawai take tayar dani,ga wani azababben ciwon kai dake damuna. Wayata ce ta fara neman agaji amma banyi niyyar dauka ba,dan tun rana ake ta faman kirana nasan bazata wuce yan scul dinmu ba ace banxo test ba. Jin qarar wayar ta fara damuna yasa dole na miqe na dauko dan da alama mai kira bashida niyyar dainawa. "Heartbeat"shine sunan da yaketa reto a saman wayar,banda niyyar daukar wayar saima tasata a gaba da nayi ina rusa kuka. Mai zai kira ya fada min bayan yasan na rasa shi?kodai ya yarda da qudirina na guduwa ne? Da sauri na daga wayar.Daga can naji yace"khadija!! Naam"nace da dasasshiyar muryata. Har yanxu bazaki bar yin kuka ba koh" Bafa kuka nake ba" To naji,inason qara baki hqr ne,khadija bawai dan mun rasa juna shikenan mun daina rayuwar farin ciki ba,dan allah ki saki ranki,ki bada hadinkai ayi abinnan lpy kinji?dan allah kada kiyi wani abu dazai badawa abbi rai,kindai san fishin iyaye akan yayansu" Kuka nake kawai,dan yanxu na tabbatar na rasa shi,wlh da gsk na rasashi๐Ÿ˜ญ. Kinci abinci kuwa?" Naji yace. Eh" Bakici ba nasani,kuma idan kinason mu shirya ki tashi ki dauko abinci kici,idan ba haka ba kafin gobe zakiji lbrn nabar garinnan" Dan allah karka tafi,wlh xanci"na fada ina qara sautin kuka. Baiyi mgn ba sai tari da yake tayi tun inayi masa sannu har nayi shiru ina kuka. Ya sadiq ka gani koh?kaga zamu cutar da kanmu sbd farin cikin wasu koh?"na fada danjin tarin ya lafa. Dif!!ya kashe bawar ba tare da yayi mgn ba,haka naita bin number din amma bata shiga. **-**-**-**-**-*-* Yau ta kama Alhamis,wanda a lissafinsu abbi saura kwana biyu daurin aurenah,zuwa lkcn duk wanda ya gani saiya tausaya min,sbd na lalace kamar ba khadija yar gayu ma'abociyar san ado da kwalliya ba. Ina zaune a tsakiyar yayyena da suketa yimin magiyar naci abinci,amma ni duk hankalina ba'a kansu yake ba,tunanin nusaiba da ya sadiq nake,dan tun ranar da mukai wayar nan banqara samunshi a waya ba,nusaiba ita kanta na kasa samunta,gashi har lkcn ban qara ganin qeyarta a gidan ba. Khadija!khadija!!ko khadijan bata nan ne"najiyo muryar abbi na kwalan kira. Saida gabanah ya fadi danni yanxu tsoron kiran abbi nake. Ya ruqayya ce ta miqon hijabi tare da cewa "maza kisaka kije kiranki yake" saka hijab din nayi na fito tsakar gidan wanda na kusa kwana 4 ban tako shi ba. Abbi yana tsaye a qofar dakinsa naje na zube ina gaisheshi da kodaddiyar muryata. Ki shiga ciki Abdurrahman yananan"yace yana nunan dakinsa. Abdurrahman?waye kuma haka? Ganin ya tsaya yana kallonah yasa na miqe na danna kaina dakin ba tare da nasan mai kiran ba. Rass!Gabana ya fadi dan ganin mijin ya fatima a zaune kan sallaya ya tankwashe kafa yana latse latse a wayarsa. Ba shiri na tsugunna dan jin wani jiri danayi yana qoqarin kayar dani. Mun dauki tsahon lkc a haka inata saqa da warwara na jiyo takunshi yana qarasowa inda nake. Zama yayi daf dani wanda yasa bugun xcy tah qaruwa da sauri. Sai daya gama qaremin kallo danni koya aka kalleni inaji a jikina. Dubeki dan Allah,ke a dole xaki aure mijin yayarki saboda cin amana koh?to inason ki sani,zaki aure ni kamar yadda kike buqata,amma ki sani na karbi wannan qaddararran auren nakine sbd yarana suna buqatar 'yar aiki..." Inaso kisa a ranki ba gidan aure zakije ba gidan aiki xakije,dan nasan kinsan nafi qarfinki tun ba yau ba" Sannan naji kamar ance wai kina zuwa jami'a koh?to inaso daga yanzu ki saka hakan a tarihin rayuwarki,domin zakina zama a gida ne kinamin gadin gida na.wannan shine saqon idan kin kiyaye kanki" Innalillahi wa inna ilaihirraji'un!! Wai meyake faruwa da nine?me yasa rayuwa zata juya min baya irin haka?bayan hanashi aurena da akayi burin nashi ma baza'a bari na cika masa ba? Bansan lkcn da ya fita a dakin ba,sai muryar abbi dana jiyo yana cewa. "me kuma kk jira har yanxu baki shiga ciki ba" A hankali na furta"Abbi ku taimaka min na cigaba da karatu na koda zaku aura minshi dan allah" Guri ya samu ya zauna kafin yace"khadija inaso kisan cewa abdurrahman a yanxu kamar mijinki yake,zan iya cewa yafini iko dake,kamar yadda ya buqata baya son kici gaba da xuwa mkrnt dole ki hqr da hakan.ki duba dukka yanuwanki akwai wadda take gidan miji take karatu?fasa rayuwa sukayi a haka?to ki cire wannan a ranki ki tashi ki bani waje" A hankali na miqe na fara barin dakin,wanda a lokacin juya ta dibeni ta zubar a wajen. Ina farkawa na ganni kwance akan gadon asibiti. Meyasa ma aka kawoni?aida an barni a gida na mutu kawai na hutu da wannan baqin cikin. A hankali na miqe zaune dan inajin qarfin jikina.zare allurar qarin ruwan nayi na wurgar domin bana buqatar hakan. Tashi nayi na shiga toilet nayi fitsari tare da dauro alwala dan nasan ana bina sallah tunda yanxun naga kamar safiya ce. Ina fitowa naga ya aisha a zaune.Riqoni tayi tanamin sannu,nidai daka na amsa na dauki hijabin dana gani na saka. Yaya yau wace rana?"nace ina kallonta. Yau friday" Au ai nazata wannan karon sati nayi a asibiti ba numfashi,amma duk da haka langwabewa zantayi har abbi ya gaji ace an fasa auren,tunda ina asibiti dai ba'a dauran aure ba. Saida na idar da sallah nayi wanka naci abinci na kwanta muna dan taba hira da ya aisha dan da alama taji dadin ganin nadan saki raina. Da dare inajin muryarsu abbi na rufe ido haka suka gama maganganunsu suka tafi. Washe gari nida ya aisha muka yini a asibitin dan bayan ita ba wanda ya leqo,da dare ma haka. Ranar lahadi ina zaune na jingina da bango ina sana'ar tunani,ya aisha kuma taje gida,naji an turo qofar dakin tare da sallama. Nusaiba ce,dan haka da gudu na tashi naje na rungumeta. Kuka ta fara min,ni kuwa naje na zaunar da ita a kan gado ina kallonta,domin ni sha'awa take bani yadda take kukan dan ji nake dama nice na samu damar zubar da hawaye. Ganin batada alamar tsayawa da kukan yasa na fara rarrashinta. Daqar tayi shiru tana sauke ajiyar xuciya. Sis ina kk shiga inata nemanki,kuma kinsan a halin danake ciku ina buqatarki a kusa dani?"nace ina qarasa goge mata hawayen fuskarta. Kiyi hqr sis,bama nan ne sai dazu muka dawo,kuma danaje gidan ammi tace kuna asibiti" Eh muna nan tun ranar alhamis,amma ina kukaje?" Muna asibiti ne ya sadiq bashida lpy,wai ciwon zcy ne ya kamashi,yanata aman jini,shine uncle dinmu yace kawai a fitar dashi abroad,to jiya da dare suka tashi mukuma yau da safe muka taho" Ciwon zcy?nusaiba ciwon zcy fa?meyasa ni bai kamani ba sai ya sadiq?Nusaiba dan allah ki kaini wajenshi naganshi"nace ina girgizata. A yanxu sis ya sadiq ya mana nisa,yana buqatar nisanta da duk wani abu dazai daga masa hankali,kuma a matsayinki na matar wani a yanxu inaso mubar mgnr wani daban" Matar wani?waye ya fada miki ni matar wani ce a yanxu?" Naje gida mana ammi tace jiya da safe an daura aurenki,ko kina nufin baki sani ba?? Shiru nayi dan bani da abin cewa. Yanxu ina gadon asibitinma baza'a hqr da wannan qaddararran auren ba?wai me nayiwa abbi da zafi haka harya tsane ni? Amminma cewa tayi Abbin yace anjima za'a kaiki wai kya qarasa jinyar acan,shiyasa ma na taho dan muyi sallama" Anjima za'a kaini?Lallai abin na abbi ya girmama. Sannan ya sadiq yace na fada miki dan allah ki maida hankali akan krtnki danki cika masa burinsa,a lkcn baya iya mgn sai a paper ya samu ya rubuta min"nusaiba ta kuma cewa. Wayyo nusaiba ina akeso na saka kaina?krtnma an hanani birinsu na mutu kawai.ni dama nasan na rasa komai tunda na rasa ya sadiq" Kibar fadar haka khadija,dama allah yayi bazaki cika masa burin ba" Amma nusaiba rashin adalcin.... Ya isa dan allah khadija,ba kowani mgn ake fada a irin wannan al'amarin ba,bamusan abinda allah ya boye ba" Haka nusaiba taita tausata da dadadan kalamai har lkcn da ya aisha ta dawo,bata wani jima ba ta tafi wanda sai lkcn na samu hawaye suka zubomin. ๐Ÿ’™๐Ÿ’™RABON KWADO....๐Ÿ’™๐Ÿ’™๐Ÿ’™ Er mutan ungogo๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ ๐Ÿ…ฟ51-๐Ÿ…ฟ55 Nayi nisa a tunani naji alamun tafiya.ban dago ba dan bana buqatar ganin ko waye. Sannunki da zuwa 'yata,ya kuma kk zauna a qasa kamar wata baquwa?" Saurin dagowa nayi dan jin muryar mace. Kallo daya zakayi mata ka gano tsantsar kamar da sukeyi da mijin ya fatima๐Ÿ™. Kana ganinta kaga cikakkiyar mace mai kamala,wadda ta jiqu da naira. Katse tunanin nayi na fara gaisheta ganin tana ta sakarmin murmushi. Lpy lou,ya jikin naki?" Da sauqi"nace ina tunanin ina tasan banida lpy. Ai inata son xuwa dubaki to allah bai nufa ba,ya hqrinmu na rashin fatima?" Alhmdllh"nace idona na kayo ruwa. Da gudu shahida tazo ta hau kaina. Aunty wai grandy tace tare zamuje gidanmu dake,kina dafa mana abinci,ki shirya mu mu tafi scul kamar yadda momy take mana?" Daga mata kai kawai nayi. Amma ke bazaki tafi ba kamar yadda momy ta tafi koh?"nan ma daga mata kai nayi. Zata kuma watson wata tmbyr matar tace da ita. Ya isa haka,kibarta ta huta bakiga bata da lpy ba?" Tashi tayi ta koma can gefe ita a dole taji haushi. Sai lkcn daddyn nasu ya fito yana riqe da hannun iman sai shahid a bayansa.neman guri sukayi suka zauna inda iman tazo ta hau kaina ta zauna. Kai bakaga auntynku ba bazaka gaida ita ba"tace tana kallon shahid dake game abinsa. Baiyi mgn ba saima tashi da yayi ya koma inda ya fito. Tasamu a gaba tayi taita nasiha,nidai inaji ne kawai amma hankali yanaga yadda zan fara rayuwa a gidan ya fatima a matsayin matar mijinta,da kuma yadda zan rayu da mutumin da natsana ya tsaneni.Ammi zanyi qoqari wajen ganin nayi duk abinda nasan baza'a samu matsala a wajena na. To ummi xamu wuce dare yanayi"ya fada yana miqewa tare da duba agogon dake tsintsiyar hannunsa. Ka daiji abinda na fada maka koh babanah?banason wani abu ya fara daga gareka dan nasanka sarai" Insha allah ummi bari muje"yace yanayin gaba. To 'yata Allah ya tsare hanya ya qara sauqi.Ki kula sosai kinji?su kuma yaran za'a barsu anan zuwa wani satin kafin nan kin qara warwarewa" Wayyo allah!!yanxu mu kadai zamu tafi salonma ya kasheni a hanya?yanxu taya zan fara rayuwa daga ni sai shi a cikin gida? Miqon ledar datayi yasa na dago tare da qaqalo murmushi. Nagode ummi saida safe" Har harabar gidan ta rakoni inda shi tuni ya shige mota. Ganin a backseat nazo hakan yasa yanxuma na bude nayi zama na a ciki. Munfi mintuna biyar a wajen bamu tafi ba,nidai bansan dalili ba. Wlh idan baki dawo gaba ba zaki fitar min a mota sai dai ki taho da kanki"najiyo muryarsa. Ikon allah!shi matar tasa ta mutu ma bazai saduda ba? Budewa nayi na shiga gaban batare dana kalleshi ba,dan ko kallonsa banason yi. Kin zata kin kai matsayin da zan zama driver dinki ne?to kisani ko a mafarki hakan bazata kasance ba,idiot kawai" Kalmar idiot din ce kawai ta bani haushi amma sauran maganganun ko a jikina,dama ni bana kai kaina inda allah bai kaini ba. Haka na cigaba da tunani har na fara bacci.har mukaje ban sani ba,dan mugunta maimakon ya tasheni shine ya bugamin kai da jikin motar. A firgice na tashi dan naji zafi sosai,shi kuwa ficewarsa yayi ya barni. Haka na fito ina sosa gurin ina binsa a baya. Bangarensa ya shige ya barni a nan,ganin tsayuwa bazata yimin ba yasa na nufi bangaren ya fatima. Falon yananan kamar yadda nasanshi sai dai wasu canje canje da ba'a rasa ba kamarsu labulaye da sauransu. Kai tsaye bedroom din na shige dan sosai nake a gajiye. Danayi shirin baccin kuma sai na kasa na shiga tunanin rayuwa. Allah sarki ya sadiq ko yanxu a wani hali yake?Tuni idanuna suka ciko da kwalla. Ya allah ka bawa bawan nan naka lpy,ka bashi sauki da kuma hqrn rashina. Saukowa nayi daga bed din na nufi akwatin da naga ni dan ina tunanin itace wadda ya aisha take fada. Wayata na shiga dubawa dan inason jin muryar ammina. Amma abin mamaki ba waya ba dalilinta.harna hqr xan koma na kwanta sai kuma na bude aljihun akwatin. Wata qaramar wayace wadda ake mata laqabi da keypad sabuwa dal. Kunna wayar nayi amma ba contact ko daya,dana qara dubawa ma sai naga ba sim card dina bane wani sabone. Allah sarki ni!!haka akeso na cigaba da rayuwa ba tareda farin ciki ba. Number din ammi nasa da yake na hadda ce amma bata shiga ba,dole na hqr na fara dannawa ya sadiq kira duk da an sanar dani baya ma qasar. Ba yadda banyi na tuno number din nusaiba ba amma na kasa dole na sawa zcytah hqr na koma nayi lamo kamar wata marainiya. Ganin kwanciya bazata min ba yasa na tashi naje na dauro alwala dan kai kukana wajen ubangiji. Sai uku saura na tashi daga sallaya dan jin barci ya fara doko sallama. Tun daga ranar ban kuma ganin ko quda a tare dani ba,koda yaushe ni kadai kamar mayya. Hakan yasa na qagu sati yazo dansu shahida su dawo koba komai sa runga debemin kewa kafin su tafi scul. Tun inajin tsoron girman gidan ni kadai har na hqr na fara sabawa da zaman shiru da tunani. ๐Ÿ’™๐Ÿ’™RABON KWADO...๐Ÿ’™๐Ÿ’™ Er mutan ungogo๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ So much luv u my fans๐Ÿ’ž๐Ÿ’žAllah ya bar qauna๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ ๐Ÿ…ฟ56-๐Ÿ…ฟ60 A daddafe nayi sati daya a gidan nan,jina nake kamar a prison,to ko a can ai ba kai kadai kk zama ba. Yau sati na daya a gidan amma jina nake kamar nayi shekaru,to ai koba komai mutum ma rahma ne,bareni da bansaba zaman shirun ba. Tunda safe na tashi da dokin yau su iman zasu dawo dan haka nayi wanka na shafa mai wanda rabona dashi tun kafin rasuwar ya fatima. wata atampa na saka sabuwa,Don naga sababbin kaya a cikin wadrob nasan aikin ammina ne ko yanuwana. Kitchen na shiga na fara dora ruwan shinkafa wanda tunda nazo tea kawai nakesha idan naji yunwa zata halaka ni,rana daya ce nasan na dafa indomie. Shinkafa da miya nayi lafiyayyiya wadda miyar taji kaji dan ba laifi komai na amfanin gida akwai a kitchen din kai harta kayan lambu(vegetables)friege dinsu daban,kaji ma haka. Coslow nayi sannan na hada pineapple juice.Dinning nakai na jefe sannan na zauna zaman jiran tsammani wanda yafi kama dana gawon shanu,domin har la'asar basu ba dalilinsu. Bedroom din na koma na dauko wannan akwalar wayar wadda tafi kama da calculator,dan ganinta ma bata min rai yake tunda batada wani amfani.Ba contact bare memory shiyasa tun a ranar na kashe na jefa akwatin.sai yau dana dauko na kunna gidan radion da ya sadiq yake ko xanji wani abu game dashi. Dakinsu shahida na shiga na gyara kafin na dibo wasu kayan nasu na kayo cikin wadrob din bedroom din ya fatima,dan idan suka dawo bazan bari suna kwana su kadai ba,koba komai nima na riqa jin motsin mutum a kusa dani. Tsaf na gyara dakin tare da saka room freshner sannan na rufo. Dakin oga shahid na shida dan duka dakunan a jere suke sai qaton falo a tsakiya tare da dinning area.irin dai wanda ake cewa mu hadu a falo. Dakin kaca kaca yake da takardu ga kayansa da suke bar baje a qasa.haka nabi na tattara na gyara sannan na fito nayi alwala dan magriba tayi. Har akayi issha babu su hakan yasa na cire raina a yau zasu dawo. Har na fara gyangyadi akan sallaya naji an fado kaina. Momy au aunty mun dawo" Ai nayi fishi tun dazu inata jiranku bakuxo ba"nace ina juya baya. To ba daddy ne yaqi zuwa da wuri ba muma mukaita jiransa"Shahida tace. To naji ya ummin take?" Lpy lou,tace wai mu gaida ke kuma duk abinda kk ce muyi mu ringa yi kema momynmu ce.wai haka aunty?" Eh mn kuda baku sani ba?ba kuga da momynku tana nan ba idan kukace ayi muku abu tana cewa ga babarku can kuje gurinta?" Eh haka ne"suka hada baki. Yauwa,yanxu kunyi sallah?" Aa" To ku shiga toilet kuyi alwala sai kuxo kuci abinci" To amma zaki kunna mana catoon koh?tunda momy ma tana kunna mana" Eh zan kunna muku"nace ina tura qeyarsu. Aunty ni ban iya alwalar ba"iman tace tana kallona. To muje nayi miki"na fada tare da miqewa. Saida sukai sallar kafin muka fito falo da taimakonsu na kunna qatuwar plazma din domin kunsan babu a house๐Ÿ˜œ. Abinci na zubo musu na zauna ina basu a baki muna kallo. Shahid ne ya fito a dakinsa ya wani rakube kamar na allah. Kazo kaima kaci abinci"nace ina kallonsa. Ni bazanci dasu ba" To kaje kitchen ka dauko plat a zuba maka" Haka muka zauna suna cin abinci muna hira,naji dadi sosai dan mutum rahma ne,kuma duk sainaji qunci da damuwar danake ciki kashi 50 babu ita. A hankali ya turo qofar kafin ya qaraso cikin falon da wannan tafiyar tasa ta taqama.sallamar ma ciki ciki yayi ta inda yaran dukansu sukaje suka dane shi. Iman ya daqa sama kafin ya ajiyeta sunata dariya. Dama yana dariya haka?ban taba ganin ko murmushinsa ba tunda nake.zuba masa ido nayi inda muna hada ido ya watsomin wata harara. Ba shiri nayi qasa da kaina. inaji sunata surutansu nidai nakai plats din kitchen kafin nayi hanyar daki dan naga sun manta da rayuwa a wajen. Ke zonan"najiyo muryarsa. Ke?baisan sunana ba daxai kirani da ke? Tsayawa kawai nayi ba tare dana juyo ba. Ko ni nazo?"naji ya kuma fada. A hankali na dawo na nemi guri na zauna. Shahid kuje zamuyi magana da auntynku"yacewa yaran. Tafiyarsu tasa falon yin shiru sai qarar tv,inda ya dauki remote ya rage qarar. Ina fatan kina sane da dalilinki na zuwa gidan nan?idan ma kin manta to ki tuna kinxo gidannan ne a matsayin yar aiki.dan haka yanzu zan kafa miki dokoki kanar yadda ake kafawa duk wata mai aiki idan tazo,haka kuma idan kin saba zan hukunta ki kamar yadda ake hukunta yan aiki." Inaso kisan cewa gobe monday yarana suna da scul,dan haka kafin 7:30 ki tabbata kin gama shirya su,kin hada breakfast dinsu sannan kinyi musu abinda zasu tafi dashi wani daban ba wanda sukai b/fast ba.ina fata kin gane abinda nake nufi?" Banyi mgn ba kuma bani da niyyar yi dan bansan mezance masa ba. Tashi yayi ya kashe tv tare da fita ya rufo qofar. Nima tashi nayi naje nayi musu wanka inda muka sha tataburza da mutumun shi wlh bazan masa wanka ba,nidai qyaleshi niyi naja suiman muka tafi bedroom dimmu.wannan wayar na dauko dan da alamar yau zatayi amfani,Alarm na saita na 4:30am dan banason wata matsala ta hadoni da wannan mutumin dan naga qiris yake jira ya qaddamar mini. Ana Tare๐Ÿค๐Ÿค๐Ÿ’™๐Ÿ’™RABON KWADO...๐Ÿ’™๐Ÿ’™ Khayraty Er mutan ungogo๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ ๐Ÿ…ฟ61-๐Ÿ…ฟ65 Qarfe 4:30 na asuba alarm ya tashe ni da yake bani da nauyin bacci. Alwala nayo na gabatar da raka'atanul fajr kafin na dauko qur'ani na fara karantawa. Saida akai kiran assalatu kafin na kayo sallar asubahi. Kitchen na nufa dan fara gabatar da aikace aikace na. Doya na fara ferayewa sannan na feraye dankali bayan na dora ruwan tea akan cooker. Soyayyan dankayi da kwai nayi a matsayin breakfast,inda nayi feten doya wanda yaji hanta a matsayin wanda xasu tafi dashi. 7:09 na kammala komai hakan yasa na koma daki na shiga tashinsu. Da rigima da komai na samu na kallama shiryasu cikin uniform dinsu,inda na nufi dakin oga shahid dan taimaka masa ya shirya dan lkc ya tafi gashi ko breakfast basuyi ba. Haka muka fafata dashi,ko dan yaga ina cewa yai sauri ya ringa abubuwa kamar mara laka,nidai danaga ya fito a wanka na fito na qyaleshi. Dinning mukaje na fara hadawa su shahida b/fast din dan 7:30 din harta dan gota. Kamar kullum da tpyrsa ta taqama da isa ya shigo falon inda sai a lkcn ma nasan akwai kofa da zaka iya shiga bangarensa ta nan falon. Tashi sukayi sukaje suka rungumeshi,kafin ya sakarwa kowa kiss a kumatu. Good mrng my angels"naji yace yana shafa fuskokinsu. Shahid ne ya fito nidai na hada masa nasa abincin,inda nake saqe saqe na gaisheshi ko kuwa? Kar naje na gaidashi ya yarfa ni,kuma sai nake ganin kamar idan ban gaida shi ba ban kyauta ba. ina kwana"nace ba tare dana kalleshi ba. Bai amsa ba hakan yasa nayi dana sanin biyewa dayar xcyta data saka na aikata haka,gashi ya shareni kamar baisan inayi ba. Shahid sauri fa zakayi kaga driver yana jiranku kar kuyi late"yace yana zama akan kujerar falon. Saida shahid din ya gama suka dauko lunch-box dinsu dan tafiya,a inda shahid din ya bude dan ganin mene a ciki. Kai kai kai!Daddy kaga abinda tayi mana,wlh ni baxanje da wannan abin ba yan class dinmu suyi min dariya"yace yana ajiye basket din nasa a gaban daddyn nasu. Sai lkcn ya kalleni,nidai ina tsaye da plat din da suka gama cin abinci mamaki ya cika ni. Dan yaje da faten doya shine za'ayi masa dariya?faten da na baje basirata akanshi shine akeyi masa haka? Kuje wajen motar ganinan,duk ku ajiye baskets din"yacewa yaran. Aikuwa ba musu suka dire suka fice. Wato bakiji gargadin danayi miki akan kulamin da yara ba koh?to ki sani kamar yadda na fada indai kk yi laifi zan hukuntaki kamar yadda ake hukunta masu laifi to zan aiwatar da hakan,ki jira purnishment dinki kafin dare,hakan xaisa ki ringa kiyaye duk wani abu daya dangance ni da kuma yara na" Yana gama fada yayi ficewarsa abinsa. Guri na samu na zauna inda wasu hawayen takaici suka zubo min.Wato duk qoqarin da nayi na hana kaina bacci nayi abinda yace badan komai ba sai dan banason matsala ta fara daga bangare na amma hakan bai samu ba.Bai yaba abinda nayi musu ba duk da dama ba dan ya yaba nayi ba,amma shine zaice wani zai hukuntani. Banga laifi na ko kadan ba,sbd bai fada min kalar abinda zanyi ba,bansan wani irin abu suke tafiya dashi ba amma da yake ya tsaneni shine zai dora laifin akaina. Daki na koma na kwanta ina kuka,dan bacci da gajiya ke damuna amma nasan bazan iya baccin ba. Haka na wuni sur ni daya a daki saida naji yunwa na neman kasheni na rarrafo na dauki faten da suka bari na fara ci. Wai wannan abincin ne za'ace baza'aje scul da shi ba?to ko shugaban qasa ya samu wannan abincin ci zaiyi bare su daba yayan kowa ba. Bayan la'asar zaman dakin ya isheni,ina fitowa falo na ganshi a kishingide. Wlh na tsorata sosai dan banyi tunanin da mutun a gidan bama duka. Zo nan"najiyo muryarsa cike da isa. Can gefe na zauna ba tare dana kalleshi ba. Kamar yadda na fada miki dazu zan hukuntaki akan lefin da kk yi,yanxu ina so kiyi abinci kala hudu da juice kala biyu,ko wanne ya kasance dai dai cin mutum goma ne,na baki nan da awa biyu idan kk wuce haka ki tabbatar gobe xakiyi wanda ya ninka hakan." Komai na amfani akwai a kitchen,idan kuma kina buqatar wani abu zaki iya fada in babu sai a siyo." Tofa!wata daban,da gsk aikin nazoyi kenan? Ta inama zan fara wannan aikin har kala 4 a cikin awa biyu?kuma ma wai dai dai cin mutum goma. Ko a gida bantaba yin girkin da mutum goma suka ci ba,amma gashi an kawo ni inda zanyi,allah sarki ni. Kina batawa kanki lkc ne"na jiyo muryarsa. Daki nayi ina zuwa na fada kan gado na rushe da kuka. Abbi why?Abbi meyasa zaka kawoni inda ba'a qaunata?Abbi meyasa zaka daina sona ka hadani aure da mugu mara tausayi? Ya sadiq kazo gareni dan allah,ina buqatarka a kusa dani,nasan da kana kusa bazaka bari a cutar dani ba....haka na ringa kuka ina surutai,saida nayi mai isata kafin na bawa zcyta hqr na yanke shawarar zuwa nayi girkin. Tashi nayi na nufi kitchen tare da tunanin abubuwan da zan dafa masu sauqi wadanda baza su ja lokaci ba,dan yanxu ma na kusa cinye awa daya. Haka na raba hankali na,inda na dora coconut rice akan electric,fried rice a kan cooker,sai kuma blander din kayan miya dana jona a socket,ga blander din fruit itama tana markada min abinda zanyi juice dashi. Juice din na fara gamawa,inda nayi lemon mangwaro,sai kuma pineapple and coconut juice. Saida na gama coconut rice din sannan na dora macaroni armlet a electric din. Da taimakon allah na samu na gama girkin amma kala uku nayi dan bazan iyayin na hudun ba tunda ba fadar allah bace,wannan dimma da nayi nayi qoqari dan sosai na gaji danma abincimasu sauqi nayi sannan na samu kayan aiki masu sauri. A coolers na zuba abinci,yayin da na zuba juice din a jugs naje na jera a dinning,ni har mamaki nake yadda zaiyi da wadannan abinci masu yawa haka. A falo na wucesu nayi ciki abina dan tun dazu ina jiyo dawowarsu dan yanxu har an idar da sallar magriba,inacan ina aikin daba godi bare na gode. Shahida ce ta biyoni. Aunty wai meyasa bakya zama tare damu da daddy muna hira kamar yadda momy takeyi kafin ta tafi?" Kamo hannunta nayi muka zauna a gefen gado. "kinga shahida banason surutu kinji koh?idan kuma kinaso mu bata shikenan" To na daina" Yawwa babyna,kije kuyi hira dasu ya shahid kinga na gaji wanka nakeso nayi gashi banyi sallah ba" Dana shiga toilet haka naita gasa jikina da ruwan dumi sbd rashin sabo,dan yau na aikatu ba kadan ba. ๐Ÿ’™๐Ÿ’™RABON KWADO...๐Ÿ’™๐Ÿ’™ Khayraty Er mutan ungogo๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ ๐Ÿ…ฟ61-๐Ÿ…ฟ65 Qarfe 4:30 na asuba alarm ya tashe ni da yake bani da nauyin bacci. Alwala nayo na gabatar da raka'atanul fajr kafin na dauko qur'ani na fara karantawa. Saida akai kiran assalatu kafin na kawo sallar asubahi. Kitchen na nufa dan fara gabatar da aikace aikace na. Doya na fara ferayewa sannan na feraye dankali bayan na dora ruwan tea akan cooker. Soyayyan dankali da kwai nayi a matsayin breakfast,inda nayi faten doya wanda yaji hanta a matsayin wanda xasu tafi dashi scul. 7:09 na kammala komai hakan yasa na koma daki na shiga tashinsu. Da rigima da komai na samu na kallama shiryasu cikin uniform dinsu,inda na nufi dakin oga shahid dan taimaka masa ya shirya dan lkc ya tafi gashi ko breakfast basuyi ba. Haka muka fafata dashi,ko dan yaga ina cewa yai sauri ya ringa abubuwa kamar mara laka,nidai danaga ya fito a wanka na fito na qyaleshi. Dinning mukaje na fara hadawa su shahida b/fast din dan 7:30 din harta dan gota. Kamar kullum da tpyrsa ta taqama da isa ya shigo falon inda sai a lkcn ma nasan akwai kofa da zaka iya shiga bangarensa ta nan falon. Tashi sukayi sukaje suka rungumeshi,kafin ya sakarwa kowa kiss a kumatu. Good mrng my angels"naji yace yana shafa fuskokinsu. Shahid ne ya fito nidai na hada masa nasa abincin,inda nake saqe saqe na gaisheshi ko kuwa? Kar naje na gaidashi ya yarfa ni,kuma sai nake ganin kamar idan ban gaida shi ba ban kyauta ba. ina kwana"nace ba tare dana kalleshi ba. Bai amsa ba hakan yasa nayi dana sanin biyewa dayar xcyta data saka na aikata haka,gashi ya shareni kamar baisan inayi ba. Shahid sauri fa zakayi kaga driver yana jiranku kar kuyi late"yace yana zama akan kujerar falon. Saida shahid din ya gama suka dauko lunch-box dinsu dan tafiya,a inda shahid din ya bude dan ganin mene a ciki. Kai kai kai!Daddy kaga abinda tayi mana,wlh ni baxanje da wannan abin ba yan class dinmu suyi min dariya"yace yana ajiye basket din nasa a gaban daddyn nasu. Sai lkcn ya kalleni,nidai ina tsaye da plat din da suka gama cin abinci mamaki ya cika ni. Dan yaje da faten doya shine za'ayi masa dariya?faten da na baje basirata akanshi shine akeyi masa haka? Kuje wajen motar ganinan,duk ku ajiye baskets din"yacewa yaran. Aikuwa ba musu suka dire suka fice. Wato bakiji gargadin danayi miki akan kulamin da yara ba koh?to ki sani kamar yadda na fada indai kk yi laifi zan hukuntaki kamar yadda ake hukunta masu laifi to zan aiwatar da hakan,ki jira purnishment dinki kafin dare,hakan xaisa ki ringa kiyaye duk wani abu daya dangance ni da kuma yara na" Yana gama fada yayi ficewarsa abinsa. Guri na samu na zauna inda wasu hawayen takaici suka zubo min.Wato duk qoqarin da nayi na hana kaina bacci nayi abinda yace badan komai ba sai dan banason matsala ta fara daga bangare na amma hakan bai samu ba.Bai yaba abinda nayi musu ba duk da dama ba dan ya yaba nayi ba,amma shine zaice wani zai hukuntani. Banga laifi na ko kadan ba,sbd bai fada min kalar abinda zanyi ba,bansan wani irin abu suke tafiya dashi ba amma da yake ya tsaneni shine zai dora laifin akaina. Daki na koma na kwanta ina kuka,dan bacci da gajiya ke damuna amma nasan bazan iya baccin ba. Haka na wuni sur ni daya a daki saida naji yunwa na neman kasheni na rarrafo na dauki faten da suka bari na fara ci. Wai wannan abincin ne za'ace baza'aje scul da shi ba?to ko shugaban qasa ya samu wannan abincin ci zaiyi bare su daba yayan kowa ba. Bayan la'asar zaman dakin ya isheni,ina fitowa falo na ganshi a kishingide. Wlh na tsorata sosai dan banyi tunanin da mutun a gidan bama duka. Zo nan"najiyo muryarsa cike da isa. Can gefe na zauna ba tare dana kalleshi ba. Kamar yadda na fada miki dazu zan hukuntaki akan lefin da kk yi,yanxu ina so kiyi abinci kala hudu da juice kala biyu,ko wanne ya kasance dai dai cin mutum goma ne,na baki nan da awa biyu idan kk wuce haka ki tabbatar gobe xakiyi wanda ya ninka hakan." Komai na amfani akwai a kitchen,idan kuma kina buqatar wani abu zaki iya fada in babu sai a siyo." Tofa!wata daban,da gsk aikin nazoyi kenan? Ta inama zan fara wannan aikin har kala 4 a cikin awa biyu?kuma ma wai dai dai cin mutum goma. Ko a gida bantaba yin girkin da mutum goma suka ci ba,amma gashi an kawo ni inda zanyi,allah sarki ni. Kina batawa kanki lkc ne"na jiyo muryarsa. Daki nayi ina zuwa na fada kan gado na rushe da kuka. Abbi why?Abbi meyasa zaka kawoni inda ba'a qaunata?Abbi meyasa zaka daina sona ka hadani aure da mugu mara tausayi? Ya sadiq kazo gareni dan allah,ina buqatarka a kusa dani,nasan da kana kusa bazaka bari a cutar dani ba....haka na ringa kuka ina surutai,saida nayi mai isata kafin na bawa zcyta hqr na yanke shawarar zuwa nayi girkin. Tashi nayi na nufi kitchen tare da tunanin abubuwan da zan dafa masu sauqi wadanda baza su ja lokaci ba,dan yanxu ma na kusa cinye awa daya. Haka na raba hankali na,inda na dora coconut rice akan electric,fried rice a kan cooker,sai kuma blander din kayan miya dana jona a socket,ga blander din fruit itama tana markada min abinda zanyi juice dashi. Juice din na fara gamawa,inda nayi lemon mangwaro,sai kuma pineapple and coconut juice. Saida na gama coconut rice din sannan na dora macaroni armlet a electric din. Da taimakon allah na samu na gama girkin amma kala uku nayi dan bazan iyayin na hudun ba tunda ba fadar allah bace,wannan dimma da nayi nayi qoqari dan sosai na gaji danma abincimasu sauqi nayi sannan na samu kayan aiki masu sauri. A coolers na zuba abinci,yayin da na zuba juice din a jugs naje na jera a dinning,ni har mamaki nake yadda zaiyi da wadannan abinci masu yawa haka. A falo na wucesu nayi ciki abina dan tun dazu ina jiyo dawowarsu dan yanxu har an idar da sallar magriba,inacan ina aikin daba godi bare na gode. Shahida ce ta biyoni. Aunty wai meyasa bakya zama tare damu da daddy muna hira kamar yadda momy takeyi kafin ta tafi?" Kamo hannunta nayi muka zauna a gefen gado. "kinga shahida banason surutu kinji koh?idan kuma kinaso mu bata shikenan" To na daina" Yawwa babyna,kije kuyi hira dasu ya shahid kinga na gaji wanka nakeso nayi gashi banyi sallah ba" Dana shiga toilet haka naita gasa jikina da ruwan dumi sbd rashin sabo,dan yau na aikatu ba kadan ba. ๐Ÿ’™๐Ÿ’™RABON KWADO...๐Ÿ’™๐Ÿ’™ Er mutan ungogo๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ ๐ŸคStill ana tare๐Ÿค ๐Ÿ…ฟ66-๐Ÿ…ฟ70 Ina fitowa a wanka sallah nayi na kwanta a wajen dan wani irin ciwo da jikina yake min kamar ana sassarawa. Wai kixo inji daddy"shahid yace yana juyawa. Zo nan"nace dan naga rainin ya fara yawa. Can bakin qofar ya tsaya yana turo maki. Nan nace kazo"na fada ina miqewa. Qarasowa yayi ya tsaya a kaina. Hannunshi na kamo na zaunar dashi inda ya shiga kokawar qwace hannun. Naga alamar raini ya shiga tsakaninmu koh?to wlh ina qyaleka ne sbd inajin tausayinka,amma duk ranar daka kaini bango zaka gane baka da wayo,mara kunya kawai" Sakinsa nayi na tashi na fice dan zuwa naji me kuma zanyi masa dayake kira na? Suna baje a falon kowa da robar ice cream irin manyan nan,sai ledoji wadanda nafi tunanin nama suka gama ci a ciki. Dinning na kalla naga wayam ba coolers din. To ina ya kaisu? Nace kiyi abinci cikin 2hours shine bakiga dama ba sai sanda kikayi ra'ayi koh?to gobe zakiyi dai dai cin mutane 15 sannan banasan ki kumayin kalar wanda kikayi yau,kuma zaki qarasa ragowar nayau guda daya da bakiyi ba kinga kala biyar kenan. Ina baki shawara kiyi abinda nace idan ba haka ba kullum zaki ringa yi kuma yawansu zai rinqa qaruwa. Kuma bawai dan kkina wannan aikin zaki qyalemin yara ba,suma nasu dawainiyar tana nan,idan kika kuma wani kuskuren shima wani hukuncin ne zai hau kanki" Jin yayi shiru yasa na gane ya gama,dan haka naja qafata na koma inda na fito. Yanxu shikenan ni haka rayuwata xata cigaba?koda yake banga laifinsa ba,iyayen da suka haifeni suma banxatar dani sukai bare shi. Ko Ammi bata nemeni ba sbd wani dalili su ya aisha fa?ko sadakata aka bayar ai yaci ace ko ba'axo inda nake ba a kira aji lpytah.Amma ba komai rayuwa ce. Aunty wai gashi inji daddy"iman ta dawo dani daga tunani. Inason yarinyar da yawa,dan duk itace mai kama da yan gidanmu,amma sauran duk can sukayi,dadin dadawa kuma sunan amminah aka saka mata wato maryam. Karbar ledar nayi na duba. Wannan ice cream dince da nama a qunshe a irin takardar nan mai kyalli. Dacan ba'ayi niyyar bani ba sai da akaga na gani sannan,to bazanci ba. Ungo kice masa na qoshi"nace ina danqa mata ledar a hannu. Har ta juya sai kuma wani tunani ya fadomin,ai raba arne da makami ibadah ne. Kawo nan iman,kixo nayi miki wanka kinga gobe da scul koh?" Batai musu ba da dawo,Ajiye ledar nayi,kafin nayi mata wanka inda mukayi sallar issha tare sannan,na dauko naci naman na dora da ice cream. Kadan nasha dan a qoshe nake kawai dai rabar arne nayi da makami. Kayan bacci na saka kamar yadda na sakawa iman dan da wuri nakeso muyi bicci dan nasan gobe ma da wuri zan tashi. Harna kwanta na tuno da shahida dake can falo. hijabi na dora akan kayan baccin jikina tare da daukan ragowar naman da ice cream sannan na fita. Surutu take ta zuba masa inda ya tasa laptop a gaba yana latsawa. A friege din falon na saka ledar kafin na qarasa can kusa dasu. Baby taso muje kiyi bacci,gobe da scul"nace ina kallon game din da shahid yake bugawa a tv. Kaima shahid tashi kaje ka kwanta game din ya isa haka"daddynsu yace yana cigaba da latse latsensa. Nidai kama shahida nayi muka tafi dan burina kawai na kwanta na huta. Ina dubo mata sleeping dress bayan nayi mata wanka naci karo da ledar da Ummi ta bani da mukaje gidan. Ni gaba daya ma mantawa nayi da ita,dan ina zuwa na bude wardrob na saka ta. Turaruka ne masu qamshi da tsada,na fesawa da kuma na wuta. Gsky naji dadin kyautar nan,dan ni mutumce mai son qamshi shiyasa nake qara qaunar ya sadiq dan shima akwai shi da fesa turaruka masu sanyi da qamshi. Allah sarki,ko yanxu a wani hali yake?Allah shi kadai ya sani. Aunty wai yaushe zamuje gidan Ammi ne?ke tunda kk zo bakya kira mana Abbi muna gaisawa"shahida tace. Uhmm shahida magana,ke wai bakya gajiya da surutu ne?" Ai daddy yace surutu na yana da kyau,kuma journalist zan zama" Haka dai,shi yana son cigaban yayansa amma bayasan na yayan wasu.gashi qiri qiri yasa mafarkina ya rushe inaji ina kallo an hanani zuwa scul din. Mutane nawa ne suke neman shiga mkrntr basa samu,amma ni na samu anyimin buqulu. Makwanci na nema bayan na tofe mu da addu'o'in kwanciya bacci,inda yaran suka sakani a tsakiya. kwanciyata ba dadewa bacci yai gaba dani dan gajiya. **-**-**-***-***-* Washegari daqar na miqe dan baccin bai isheni ba.Amma dana tuno ayyuka da nauyin dake kaina dan dole na hqr da baccin na tashi. Kamar jiya,yauma saida nayi asuba kafin na shiga kitchen. kosan doya nayi da kuma sandwich tunda naga su yan gayu ne,kuma ni ai baza'a nunan ire iren wadannan girke girken ba. Kai Allah ya sakawa ya rukayya da alkhairi data kawo shawarar sakani a mkrntr koyan kwalliya da girki,dan gashi yanxu na fara ganin amfaninta.Dan da ace ban iya ba da nasha takaici a wannan gidan. To ko dan ya qureni yake bani purnishmeny din girki?tunanina zai iya zama gsky tunda jiya yace kar nayi irin abincin da nayi na sake wasu kalolin. 7:35 suka gama suka fita dan har lkcn daddyn nasu bai zoba. Tunda suka tafi na gyara ko ina na baza turaren da ummi ta bani dan qamshinsa yayi min sosai. Ko ina kuwa ya dau qamshi da qyalli dan saida nayi mopping din ko ina. Wanka nayi na fara aikin abincin da zanyi dan sonake daga yau na dena wannan azabar naji data yaran su kadai. Cikin ikon allah kafin la'asar na kammala.sai dai gajiya dake nuqurqusa ta dan nasan dole nayi jiyyar kaina. Dambun cous cous nayi,sai jelop din rice and beans,coconut juice,zobo drink,sakwara,Dan wske,da kuma faten dankali. A falon na zube ina mayar da numfashi kamar wadda tayi tseren gudu. Knocking naji a qofar falon,daqar na tashi ina addu'ar allah yasa baqi mukayi dan xaman haka ba dadi. Wani dogon saurayi ne a tsaye.Sai kwanukan jiya dana zuba abincin da nayi a hannunsa. Sannu hajiya,dama alhaji ne yace nazo na karbi abincin da akayi"saurayin yace. Ciki na koma na fara dauko masa abincin,saida na gama na karbi kwanukan na dawo na kwanta dan bayana ji nake kamar ya cire. Ko ina za'a kai abincin oho"nace a zcytah. Da yaran suka dawo kawai qarfin hali nayi nai musu wanka na saka musu kaya. Dambun cous cous din dana diba a cikin wanda nayi na zuba musu. Aunty gobe ma zakiyi mana irin abinda kk mana yau?wlh akwai dadi ko iman?"Aku shahida tace tana zuba lomar dambu. Ai wani abin xan kuma yi muku mai dadi wanda yafi na yau dadi"nace ina dry,dan da alama maggi ne ya kama kunnenta take wannan batu. Da dare har muka kwanta daddynsu bai xo ba,in taqaice muku tun daga ranar saida yayi sati bamu ganshi ba.ni dadi ma naji dan koba komai na hutu da fi'ilinsa. Yaran ne dai suke isata da tmby dan shahid ma saida ya tmby ni,nidai ce musu nayi yayi tpy kawai tunda bansan me xance ba. Haka rayuwa ta cigaba da gudana yau da sauqi gobe ba dadi.dan yanxu ma kwata kwata ya daina shigowa bangaren sai dai da dare idan ya dawo su yaran su bishi can falonsa dake sashinsa,saidai na zauna kwalam hakan ke bani damar kukana son raina,dan har xuwa yanxu da nake baku lbrn nan 4months kenan da kawo ni gidannan amma ko quda ban taba gani ba kamar banida dangi,gashi rayuwar gidan bata sauya ba kullum jiya i yau,dan ma bana ganinshi sosai dan sai tashi ta kawoshi yake shigowa bangaren. Wannan shine asalin labari na. Ku biyo ni dan jin yadda zata kaya har zuwa qarshen lbrn. Taku har kullum KHAERATY Er mutan ungogo๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ [07-23, 20:40] Sistoh: ๐Ÿ’™๐Ÿ’™RABON KWADO...๐Ÿ’™๐Ÿ’™ Er mutan ungogo๐Ÿ’‹๐Ÿ’–๐Ÿ’‹๐Ÿ’–๐Ÿ’‹ ๐Ÿ…ฟ71-๐Ÿ…ฟ75 Ban tashi dawowa daga tunanin ba sai 12:39pm. Ba shiri nayi Addu'a na kwanta,ina fatan Allah ya bani ikon tashi da wuri dan sallamar yarana. A hankali nake bude idanuwa na wadanda suka sauka akan qaton agogon dake mannne a bangon daki. Da sauri na duro daga gadon dan idan ba idanuna bane 6:31am na gani agogon ya nuna. Alwala nayo cikin hanxari kafin na gabatar da sallah.Yau ko krtn qur'anin dana saba banyi ba haka na miqe ina tunanin ta ina zan fara. Indomie zan dafa duk wanda yaga bazai ci ba ya batta dan na fara gajiya da wannan tsirfar,ko haka suke yi da ya fatima tananan?ko kuma nice da aka mayar baiwa ake min wannan iskancin. Cikin muntuna da basu haura 20 ba na kammala indomie sannan na soya kwai. Kwan na qara fasawa Dan yin alalar kwai(awarar kwai)ko kuma kwai cikin kwai naji wasu na kiransa. Qullawa nayi a farar leda bayan nasa kayan dandano dana qamshi. Nan ma ban dau lkc ba na kammala na fito.Amma da yake ban farka da wuri ba dana duba agogo 7:27. A hanzarce nayi musu wanka tare da saka musu uniform,yau ko shafa musu powder din dana saba banyi ba. Wajen oga shahid naje inda saida na dakeshi sannan ya maida hankali ya shirya na taso qeyarshi gaba. Yana zaune a daya daga cikin luntsuma luntsuman kujerun falon yayi crossing din legs yana girgizasu a hankali,ga dukkan alamu mulki da rashin mutunci yake ji dashi. Kamar ko yaushe wucewa nayi dan Zuba musu breakfast ba tare dana gaidashi ba,dan tun ranar dana gaisheshi yaqi amsawa ban qara gigin gaidashi ba. Gsky ni baxanci indomie ba"naji shahid ya fada. Kada Allah yasa kaci,ai kana da hannu zaka iya shiga kitchen ka dafa abinda ranka yake so"na fada a qufule dan yaron ya fara kaini bango. Jin abinda shahid din yace yasa suma duk suka daina cin abinci,shidai yana zaune baice mana komai ba saima wayarsa da yake latsawa. Malamai idan bazaku ci ba zan tashi dan ina da abinyi"nace cikin fada dan zuciyata kamar ta fito. Haba ai abin ya isa hk kullum nice cikin aiki sannan uba yayi min yara su yimin?wlh ina raga musu ne sbd maraicinsu,kuma abinda nasan bazan yiwa yaran dana haifa ba wlh bazan iyayi musu ba,Amma da sbd halin ubansu ne wlh ko kallo basu isheni ba. A barni da ciwon rabuwa da masoyina mana,a bari naji da kadaici da kewar su ammi dake damuna mana,A barni da baqin ciki da takaicin dake raina na banzatar dani da kowa nawa yayi,a bari naji da aiyuka da dawainiyar da nake kullum mana. Amma bayan wadannan sai anxo ana min wani fi'ili? Kawai na sakawa zcytah hqr ne,amma har a gayamin seniority nida nayi bording scul. Tashi kawai nayi na nufi daki dan idan na cigaba da zama a wajen takaicin zai min yawa. Bansan lkcn da suka tafi ba nadai kwanciya nayi ina hawayen takaici. Tunda na shiga dakin ban kuma fitowa ba,dan ko girkin da nakeyi kafin su dawo banyi ba.ni kaina yunwa ce take nuqurqusata tunda ko breakfast banyi ba,wanka kawai nayi dama ina fashin sallah. Tashi nayi na taimakawa kaina na bude friege na dauki fresh milk na kwankwada sannan na fara dawowa dai dai. Harabar gidan na fito wanda tunda nazo gidan leqe ma saida dalili. To nagaji da wannan rayuwar takura kan,fitowa zan ringayi ina shaqar ni'imar ubangiji. Zagaya gidan nayi tayi harda inda ban taba zuwa ba yau saida naje.Tsarin gidan ya burgeni amma da ace nida ya sadiq za muyi rayuwa a ciki da abin yafi qayatarwa. Iskar yammar data fara kadawa yasa na qara shagaltuwa dan sosai yanayin yayi min dadi. Duk wata damuwa saita ragu a zcytah,dan na dade banji irin wannan nishadin ba. Allah sarki nusaiba,itama tanason iskar yamma,dan ita har ware hannuwa take kiga tanata sakin murmushi. Zama kawai nake naita mata dariya. Takance min"Khadija bazaki gane abinda nakeji game da yanayin nan ba,ina imaging abubuwa da dama wadanda bazasu lissafu ba.Amma kuma kinsan masoya sunfi more irin wannan yanayin musamman ma idan suna tare" Allah sarki sis itama ta manta dani,koda yake kowama bayan su ya zee yake,nidai Allah ya kawo ranar da zan fita a gidan nan naga gari. Sai wajen magriba sannan na farga da lkcn dana bata a wajen,aikuwa na samu gurin dibe kewa na raya a zcytah. Iman na fara karo da ita tana rusa kuka. Babynah menene kk kuka"nace ina tsugunnawa a gabanta. Ba tpy kikayi kika barmu ba"tace tana shassheqar kuka Srry kinji iman dina?bazan kuma tpy na barku ba ina tare daku kinji?"nace ina share mata hawaye. Daukanta nayina saba a kafada dan basa min wahalar dauka,har shahida idan ta rayomin har goyata nake. Ya fatima taita yimin fada wai nice nake qara sangarta yaran nan shiyasa suke tabara son ransu. Nidai dariya kawai nake nace"ba dai a shiga tsakanin uwa da yaya ehe" Sai kiyi tayi ai,ni dai idan mutum ya fara ciwon qirji sannu da dura madara ne kawai nawa" Allah ka jiqan baiwarnan taka amin. ina su ya shahidan suke?"na tmby iman. Tana daki wai abinci xata ci" Wanka nayi musu kafin suma na basu fresh milk din suka sha dan har lkcn ban huce ba bare na dora abinci. Ni yunwa nakeji"shahid dake tsaye a bakin qofa ya fada. Ko kallon inda yake banyi ba,tunda baisan sunana ba kuma bazai iya shigowa ba. A qasan carpet din dakin muka baje ina koya musu karatun qur'ani kafin daga bisani suka dauko jakunkunan su sukai bitar abinda aka koya musu. Saida daddynsu ya dawo sannan muka gama,suka tafi wajenshi ni kuma na hau gyaran wadrob. Aunty wai daddynmu yace kixo"iman tace tana darewa baya na. Wash baby,lukutar nan dake zaki ringa dare min baya saikin karya ni" Dariya mukasa dukanmu. Saida na dade kamar bazaje ba kafin na tashi muka tafi kiran. Zama nayi ina dora iman akan cinya ta. Da hikima duk ya kori yaran kafin ya juyo kaina. "Wato harkin samu damar da zaki ringa yiwa yarana tsawa a gabanah koh?Da kinsan bazaki iya jure duk wata dawainiya tasuba kika ce zaki aure ni" Saurin dagowa nayi na kalleshi,wato nice ma nace zan aure shi?ko a tunaninsa da son raina akai auren?. To inaso ki sani idan har bazaki iya jurewa ba kiyi musu duk abinda suke so to wlh yanxu muka saka qafar wando dake.Sannan ki fadan dalilin da kika hana shahid abinci,dama ba tun yau ba na fahimci banbancin da kike nunawa akansu,to wlh baki isa ki raba min kan 'ya'ya ba dan duk daya suke ba bambamci." Sannan akwai purnishment da kika saka yaranah sukai late a scul,purnishment din kuma shine Zaki girka traditional food kala uku da kuma juice suma kala uku,zaki iya tashi ki bani guri" Kayi hqr,amma gsky bazan iya wannan girkin ba,dan duk lkcn da nayi sai nayi jinyar kaina.Kuma bada sani na sukai late ba nima makara nayi a bacci"na fada dan wlh bazanyi girkin nan ba wanda nayi dai a baya allah ya bani lada. Ni kike fadawa bazaki iya abinda na sakaki ba koh?"ya fada yana kallona. Shiru nayi amma duk abinda za'ayi na riga na fada bazanyi ba dan ba yar aiki aka kawo masa ba. Banyi zato ba na ganshi a gaba na,zcytah kawai bugawa take amma idan ka ganni a zahira zakai tunanin irin jarumar nan ce. Dan kinga bana shiga harkarki shine raini zai shiga tsakanin mu?ina daga miki qafa sbd darajar fatima wlh" Nima ai sbd itan nake daga maka qafa"nace tare da kama hanyar daki da gudu. Inajinsa yace "mara kunyar qarya kawai" nidai nace oho dai.๐Ÿ˜œ [07-23, 20:47] Sistoh: ๐Ÿ’™๐Ÿ’™RABON KWADO...๐Ÿ’™๐Ÿ’™ Er mutan ungogo๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ ๐Ÿ…ฟ76-๐Ÿ…ฟ80 Washegari ta kama asabar,muna falo a zaune ina tsefewa shahida kai,domin duka gashin namu yayi datti musammanma ni,domin su nayi musu kalba sati biyu da suka wuce. Duk rashin son kitsona amma yanxu duk gashin ya isheni,a gida kuwa kar kuso kuga yadda Ammi takeyi dani akan kitso amma yanxu nema nake ido rufe ayimin ko kalbar ce. Baby a ina akeyi muku kitso?"na tmby shahida ina cigaba dayi mata tsifar. Da momy tana nan daddy ne yake kaimu salon ayi mana,idan kuma bayanan driver ne yake kaimu" Kuma Aunty kinsan matar ta iya sosai idan muka dawo ma har daddy yana cewa munyi kyau" To naji fadi ba'a tmbyki ba,idan daddynku ya dawo kice ya kaiku ayi muku kinga har gashinku ya fara lalacewa,ko kunasu ku zama kwakwido๐Ÿ˜‡?" Aa nidai banaso"Iman tace. Muna gama mgnr yana shigowa,inda sukaje sukayi hugging dinsa. Ko zama baiyi ba akun ta fara sharhi. Daddy,wai Aunty tace ka kaimu ayi mana kitso kar muzama kwakwido" Dafe kaina kawai nayi dan ta kwafsa min,sbd me zata ce nace? To kuje ku shirya akaiku kaima shahid kana buqatar aski sai kazo kaima muje"yace yana zama. Da gudu suka nufi daki sunata murna. Dafatan kin gama girkin dana saka ki"naji ya fada. Ni sam na manta da wani girki wlh,koda ina sanen ma bayi zanyi ba,sbd niba yar aiki bace๐Ÿ˜. Ganin banyi mgn ba yasa ya nufi dinning area domin duba wa. Koda baiga komai ba baiyi mgn ba yaran suka fito suka bar gidan. Allah sarki,dama ni ina za'aje dani?Ai ya fatima itace matar so shiyasa ake zuwa da ita. Wanke gashina naje nayi nazo nayi masa kalba duk da ba wani kamuwa tayi ba amma naji sakayau. Yau ma a lambu na wuni saida magriba ta kawo kai sannan na koma kuma har lkcn basu dawo ba. Wasa wasa har nayi sallar magriba ga gidan ya fara duhu sbd yau hasken bai kawo ba,amma da anayin magriba haske yake gauraye gidan bansani ba solar ce ko inji oho. Fitila na shiga dubawa wanda tsahon zama na a gidan ban taba nemanta ba. Haka nasha duba har na gaji dan daqar nake ganin hanyar danake takawa. Abun takaici ga wannan calculartor din taqi kawowa tunda ban taba saka ta a caji ba. A hankali tsoro ya fara kamani dan ga duhu gashi banaji motsin kowa. Haka na cigaba da zama a duhun har issha ina tsammanin dawowarsu amma shiru. Ban qara tsorata ba sai da na fara jiyo kukan mage ta window wanda a rayuwata bana qaunar mage. Tun ina daurawa ina addu'a har dai naga kamar kukan qaruwa yake na fashe da kuka tare da darewa gado na lullebe a bargo. Jin kukan bana mage daya bane yasa na firgice na fara qwalla qara ko zan samu agaji amma inaa. Tun ina toshe kunnena da hannu har na gaji na saddaqar mutuwa zanyi domin jin kukan nake kamar a kusa dani. Haka na bata tsahon dare ina kuka wanda yasa muryata dashewa sbd ihun dana sha. Sai wajen asuba na daina jin kukan magen,kamar hadin baki sai ga haske ya bayyana. Kuka na na cigaba dayi wanda baka iya jiyo kukan sbd dashewar murya. A daren dai banyi bacci ba,koda asuba daqar na tashi nayi sallah sbd wani zazzafan zazzabi da nakeji. Daqar na samu bacci ya daukeni wanda daka kalleni kasan bana dadi nakeyi ba. Sai 12pm na farka kuma har lkcn akwai zazzabin a tare dani amma dai ba kamar na dazu ba. Lallabawa nayi na samu nayi wanka tare da yin brush kafin nazo na zira wata doguwar riga. Fita nayi kitchen dan samarwa kaina abinda zanci. Fried indomie nayi na dawo falon ina cusawa dan ba wani dadin abincin nakeji ba. Da sallama ya turo qofar dake sadashi da bangarensa ya qaraso. A ciki ciki na amsa ba tare dana kalli inda yake ba. Ban kula ba kawai na ganshi kusa dani ya zauna. "Sannu fa Mai tsoron mage"yace da murmushi a fuskarsa. Da mamakina kalkeshi.Dama shine ya shirya min wannan muguntar?koda yake bai kamata nayi mamaki ba domin dama can mugu ne. Kamar yadda bakya yafiya haka nima ba nayi,kuma na tanadi hanyoyin ladabtarwa kala kala domin sbd ke๐Ÿ‘‰,Amma duk ranar da kika shirya yafiya nima a shirye nake da ajiye makamai na.Bawai ina buqatar hakan bane domin bani da matsala ta wannan fannin,kuma ko gobe kk qara wani lefin ko na baki purnishment ki qiyi wlh ba daga qafa" Bai jira abinda zan fada ba ya koma inda ya fito duk da ni dinma ba abin fadar gare ba. Kuka na kuma dasawa wanda tasa jikina qara zafi sosai,daqar na rarrafa na koma daki na lullube da bargo dan wani sanyi nake ji. Saida nakai tsahon kwana biyu kafin zazzabin ya sakeni kuma har zuwa lkc ban kuma saka kowa a idona ba. To dama wa zan gani?waye ya damu dani bare yazo ya duba ni? Da ace da ne nayi wannan zazzabin nasan gata sai na rasa inda zan saka kaina. Sannu,sannu auta,yanxu ina yake miki ciwo?me kikeso a dafa miki?me kike son ci a siyo miki? Ire iren wadannan tmbyoyi haka nake shansu,amma yanxu ko sannu ban samu ba. Hk na ringa dauriya ina qarfafa jiki na ,dan gaba daya gidan yayi datti,hk na shiga gyarawa dan qarfafa jikina. Da yamma ina zaune ina game mai miciji a calculator ta dan ba shiri na zirata a caji dan naga ranar ta. Tun ban iya ba har nazo na fara iyawa dan koba komai ta ringa debemin kewa da rage kuka da tunani. Da gudu suka shigo suka rungume ni suna dariya kowa yana cewa"na riga" Nidai a sakeni kar a qarasani"nace murmushi dauke a fuskata. Aunty wai Grandy tace tana gaidake"iman tace. Ina amsawa" Aunty kinga yau bamuje scul ba munacan gidan grandy...kuma" Kefa matsalarki kenan shahida,idan bakyanan mutum yaita kewa,amma kina dawowa ki ishi mutum da mgn"Nace ina kwanciya. Sum sum tabar wajen da alama fishi tayi. Dole naje nayi rarrashi kafin ta hqr muka dawo nml. Da dare kamar yadda suka saba da daddynsu ya dawo suka tafi wajensa,ganin na fara tunane tunane yace na tashi na nufi kitchen dan rage aikin da zanyi gobe Da safe. Haka ya zanto kullum idan suka tafi nakan shiga na rage aiki,idan abin doya zanyi da safe saina feraye tun dare sannan na dafa tea na zuma a flask.hakan da nakeyi yana taimaka min sosai wajen gama shiryasu da wuri dan hk yanxu baya samun damar dazai min mugunta. A haka har azumi ya shigo inda na duqufa kai kukana ga mahallicina akan sauyin rayuwat dana samu,da kuma nemawa ya sadiq dani kaina sauqi a cikin zcyiyinmu. Cikin ikon Allah abubuwa suka fara raguwa a zcytah,inda na maida hankali wajen kula da yaranah da kuma koya musu karatu. Yanxu tare muke shiga kitchen da shahida dan yanxu tana 9years ne,sosao take taimakamin kuma take gane abubuwa sbd kasancewarta mai tmby komai ta gani saita magantu. To alhmdllh yanzu shima shahid yana shigowa cikinmu ayi krtn dan shima ina saka shi cikin addu'atah Kuyi hqr da wannan bansamu lkc bane amma next zanyi mai yawa insha Allah.Ngd๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ [07-23, 20:47] Sistoh: ๐Ÿ’™๐Ÿ’™RABON KWADO...๐Ÿ’™๐Ÿ’™ Er mutan ungogo๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ ๐Ÿ…ฟ81-๐Ÿ…ฟ85 Cikin ikon Allah yau idan mun kai azumi 27. Dama rayuwar haka take kana naka allah na nasa,sai dai muyi fatan cikawa da imani. Muna zaune a falon bayan shan ruwa,iman tana danna min qafafuwa na sbd gajiyar da nayi na haka kayan shan ruwa,domin duk cikinmu iman ce kawai batayi. Sosai nake jan yaran a jiki ina koya musu abubuwa wadanda nasan zasu amfane su,hakan yasa muka zama abokai dasu dan har shahid yanxu shiri mukeyi dashi. Ta qofar waje ya shigo da alama yanxu ma ya shigo a gidan. Kamar ko yaushe suka tashi suka rungume shi suna masa welcome. Tashi nayi na nufi daki dan irin haka idan ya dawo daki nake tpy na barshi da yaransa. Har bacci ya fara daukata najiyo muryar shahid. Aunty khadija ki tashi kiga kayan sallarmu da daddy ya siyo mana" Dan dole na miqe dan yadda suke jijjigani kowa yanaso na tashi naga nasa kayan. Masha Allah kawai nake maimaitawa dan kayan sunyi kyau sosai,dan ba sai an fada maka ba kasan an kashe kudi masu yawa wajen siyansu. Kowa kala 4 ne kayan sai takalma kala 2. Gsk daddyn nan yanaji daku"na fada ina qara daga kayan dan sun tafi dani. Aunty ai yace ba suke nan ba,gobe za'a karbo sauran a wajen dinki"shahida tace. To kun dai ce kun gode koh" Aunty wai ke ina naki kayan sallar?"iman ta jefon tmby. Nawa suna nan da safe zan nuna muku"nace ina yaqe. Aunty kema daddy ne ya siya miki?"ta qara tmby. Aa ammina ce ta siya min"nace ina miqewa dan adana kayan domin nasan idan na zauna qara tmbyta zatayi ba kamar shahida. **-**-**-**-***-** Da safe muna zaune a falo ina yanke musu farce ya shigo yana wani ciccin mgn. Ummina ku shirya na kaiku kitso kar yamma lkc ya qure"yace yana kallon shahida don sunan umminsa gareta. Daddy ni fa?"shahid yace. Kaima ka shirya zan kaika aski"yace yana zama. Da suka dawo cikin hikima ya korasu wajen mota kafin ya juyo kaina. Ina shirin miqewa najiyo murtarsa. Anjima za'a kawo kaya,dan gobe friends dina zasu zo kuma za'a kaiwa ummi da gidan Abbi abinci"yace yana ciccijewa kamar wanda aka yiwa dole. Kamar yadda ya fada bai dade da fita ba aka kayo kayan. Kaji ne da kayan miya sai sauran abubuwan amfani. Ba bata lkc na fara aiki dan naga aikin mai yawa ne. Sosai na rage aikin dan sinasir nake sonyi goben da miyar kaji๐Ÿ˜‹sai wasu kajin dana ware dan soyawa. Sai wajen 11pm suka dawo dan har na fara cire ran dawowarsu. Ai kuwa sunsha jan lalle wanda yayi maroon sbd kamu,sai twisting da akayi musu shima ba'a cewa komai. Shahid kuwa aski da gyaran fuska yasha. Nan fa akaita bani labarin abubuwa,nidai gado na haye dan ganin basu da shirin kwanciya dan kowa ya dauko kayansa da suka shigo dasu suna gwadawa. Leshi ne mai kyau da tsada,sai wata dakakkiyar shadda da akayi musu iri daya dukansu. Da wuri na shiga kitchen washe gari,dan saqon na shiryasu da wuri zasuje idi tuni ya riskeni. Saida na gama suyar kajin na dora miya bayan na hada qullin sinasir din sannan naje dan shiryasu. Zama nayi na tsara musu kwalliya tare da musu daurin dan kwali da yake wai yace shaddar zasu saka. Ras yaran suka fito dan idan ka gansu kamar ka sace su ka gudu. Fitowarmu tayi dai dai da fitowarsa,inda shima yake sanye da shadda irin tasu sai zuba qamshi yake kamar wani ango๐Ÿ˜„ Ganin sun manta dani sunata kwasar selfie dinsu tasa naja jiki na koma kitchen dan cigaba da aiki na. Allah sarki ni,kowa yana tafiya idi ni ina kitchen ina aiki,nima da a gidane da yanxu mun tafi nida abbi koda nusaiba. Gashi ace sallah guda bani da kayan sallah?duk da ba rasa sababbin kaya nayi ba amma ai kayan sallah daban yake. Ace sallah guda ba kitso bare lalle? Haka na raya a raina ina sauke idanuna da suka cika da kwalla akan hannayena wadanda yanxu suka fi kama dana maza sbd ko digon lalle babu a farce na. Saida na kusa kammalawa suka dawo. Zuba musu abincin nayi bayan na cire musu kayan dan karsu bata. Daki naje na kwanta dan sosai jikina yake amsawa. Inaji shahida na fada min ga abokan dadynsu nan,nidai ban motsa ba tunda na gama jera musu komai a dinning. Bansan lkcn da bacci yayi gaba dani ba wanda ban farka ba sai azahar. Da hanxari naje nayi wanka tare dayin simple make up wanda tunda nazo gidan cream ma saita raya min nake shafawa. Haka na saka wani light purple din leshina nayi daurin zamani,dan yau haka kawai naji ina sha'awar hakan kodan ranar farin ciki ce? Fita nayi don samawa cikina haqqinsa,inda na samesu suna buga game da shahid da daddynsu,yayinda su iman suke ta ihu da alama kowa da wanda yakeson yayi winning. Har na gama cin abincin basu kula dani ba,don hk dana gama ma daki na koma na kunna calculator ta ina sauraron waqoqin da ake sakawa a gidajen radio. Aunty wai daddy yace kisa mana kayanmu sannan ki zuba abincinsu grandy ki fito mu tafi"shahid yace. Tashi nayi naje na zuba abincin a cooler kafin na qara gyara musu kwalliyar na koma na kwanta. Nayi zaton sun dade da tafiya kawai naga iman wai nazo inji daddy. Barinmu kk yi muna zaman jiranki ko kuwa ajiyemu kk yi?wlh kk wuce 2mnt zaki sha mamaki"yace yana jan hannun iman. Kaji mutum ni nasan dani za'a tafi ne? Da sauri na koma daki dan dokin yau zan fita har naje naga amminah. Kiyi hqr da wannan nayi typing mai yawa zan turo bansani ba nayi delete. Ku buyoni. [07-23, 20:47] Sistoh: ๐Ÿ’™๐Ÿ’™RABON KWADO....๐Ÿ’™๐Ÿ’™ Er mutan ungogo๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ ๐Ÿ…ฟ86-๐Ÿ…ฟ90 Da sauri sauri na dauko mayafina wanda zai shiga da kayan jikina,na zira takalmi nayo waje. Yauma a front sit na samesu sai shahida dake baya. Shiga nayi ba bata lkc mukayo waje. Wayyo zo kuga farin ciki kwance a fuska ta.inaji suna hira jefi jefi nidai Allah Allah nake na ganni a cinyar ammi dan nayi missing sosai.๐Ÿ˜œ Kwantar da kaina nayi inashan AC tare da zubawa titi ido ina ganin abinda yake wakana. Can gidansu muka fara zuwa dake unguwar kuntau. Sosai gidan ya tsaru kaida gani kasan na masu abun ne๐Ÿ˜„. Ban gama shan kallo ba saida muka doshi sassan gidan,kai na taqaice muku kamar yar qauye na zama. Ganin sun danyi min nisa yasa na saita kaina tare da qara sauri kar naje na rasa qofar da suka shiga. Da sallama na qarasa shiga falon inda duk hankalinsu ya dawo kaina. Zubewa nayi a gaban ummi ina kwasar gaisuwa wadda tun shigowata murmushi yake wanxuwa a fuskarta. Mata ne guda uku wadanda suke cikin shigar alfarma,duk da nima kayana ba marasa kyau bane amma duk sainaji na takura. Nidai inajinsu suna jana da hira kawai murmushi nake musu dan burina inganni a dakin ammina. Sama sama nakejin hirar tasu inda Nake satar kallonsu cikin dabara. Kana ganinsu kasan yayan ummi ne,dan duk kamar danake ganin daddynsu shahid nayi da Ummi sai naga ashema nafila ne. sinasir din da mukazo dashi Suka baje a qaton plat sukaita jana har saida na sako muka fara ci tare. Broz haka Auntyn tamu ta qware a girki?shiyasa har wata qiba kk ta musamman"babbar cikinsu ta fada dan da alama itace sakuwarshi,dan sauran biyun kansu daya kamar yadda komai da suka saka iri daya,saidai daya tafi daya fari amma duk daddynsu shahida ya fisu fari dan kamar ba dan nigeria ba๐Ÿ˜„ Har suka gama shaqiyancinsu bai kulasu ba don inaga muskilanci sana'arshi ce. Tuni yaran suka watse kowa ya shiga wasa,nidai duk a takure nake dan ko ido bana iya dagowa. Mubinah kinga kuje dakinku da khadija naga ta kasa sakewa damu"Ummi tace Wadda aka kira da mubinah dince ta kama hannuna mukai saman benen gidan. Allah sarki malam talaka"na fada a raina ganun irin aljannar duniyar dake kan benen. Wani daki muka shiga wanda aka tsara komai da kalar red,dan dole na saita kaina dan karta fahimci halin danake ciki. Haba matar broz dan allah ki saki jikinki,kinga nan ma gida ne dan duka an xama daya"tace tana zaunar dani akan gadon dakin. Murmushi nayi kawai. Kinga mu kamar yar uwa haka muka daukeki dan Allah ki saki jikinki"ya kuma fada. Dai dai nan dayar ta shigo dan nafi tunanin twins ne. Sakani a gaba sukai suna taban lbr dan dole na saki jikina,dama ni banason nayi shisshigine nida ba yar kowa ba,amma da naga ba wannan a ransu tuni na saki jiki munata hirar scool. Kasancewarsu masu surutu yasa cikin lokaci kadan mukai kamar dama can mun san juna. A shekaru zamu iya sa'anni dasu koma su girmeni dan yanzu suna level 200 ne a wata private university dake nan kano. Sosae nake jin dadin hirar dan rabona da samun wanda zamuyi hira irin hk har na manta. Iman ce ta shigo da gudunta tana kwalan kira. Aunty!Aunty wai daddy yace ki fito zamuje gidan Ammi" Kafin nayi mgn mubina ta riqota. Aunty kuma iman?ba mummy ba?daga yau mummy zaki ringa cewa kinji darling?"tace tana kama habarta. Kai kawai iman din ta daga mata. Kinji broz wai har zai dauke mana ke,shifa haka yake da takura"mufida ta fada. Har bakin mota suka rakoni bayan munyi sallama dasu ummi. Ganin da sukayi su shahid a front sit yasa suka fito dasu suka sakani a front sit din. Nidai yaqe kawai nakeyi dan banason yazo ya bata min rai dan shi yana can gefe yana waya. Yanxu sai yaushe zaku xo dan allah"nace ina kallonsu. Kafin aunty anisa ta koma zamuxo insha allah kinsan ita a Abuja take aure jiya sukazo da mijinta da yaranta biyu,basu dade da fita ba kuma kikazo wai ya tafi kaisu park ne"mubina tace dan da alama shahida ita ta gado dan itama surutu ne da ita kamar parrot. Saida ya gama wayar kafin mukai sallama suka koma mukuma muka bar harabar gidan. Farin cikina ne ya qaru lkcn danaga mun dosh shiga layinmu.wayyo duk wanda yabar gida gida ya barshi. Tunanina ya tsaya cak lkcn da mukazo dai dai gidansu ya sadiq. Ko yanxu yana ina oho?ko yaji sauki allah ne masani.Ko ina nusaiba tayi saurin mantawa dani haka oho. Bansan mun qaraso qofar gidanmu ba sai da naji an buga murfin mota da qarfi. Ba shir na dawo hankali na inda naga ba kowa a mota saini kadai. Da hanxari na bude na fito inda tuni yaran sunyi cikin gida sai gogan naku a tsaye jikin mota. Banbi ta kansa ba da gudu na shige gida ina dokin ganin Ammina. Gidan cike yake da yaya da jikoki dan gaba daya su ya aisha da yaransu sunanan. Duk da farin cikin ganinsu da nakeyi amma inajin haushi akan mantawa dani da sukayi,dan haka direct wajen ammi nayi na rungumeta tare da fashewa da kuka. [07-23, 20:47] Sistoh: ๐Ÿ’™๐Ÿ’™RABON KWADO...๐Ÿ’™๐Ÿ’™ Er mutan ungogo๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ ๐Ÿ…ฟ91-๐Ÿ…ฟ96 Ke kuma lapiyarki daga shigowa sai kuka?idan kinsan kuka zakimin ki tashi ki bani guri"Ammi tace dan taga kukan bana qarewa bane,dan su ya zee sunyi mgnr duniya banyi musu mgn ba. Saida nayi mai isata kafin na share hawayena. Ammi har kema kin daina sona koh?korata ma kikeyi sbd bakiso ki ganni koh?"nace hawaye na qara zubomin. Haba auta,taya zaki ringa fadar haka bayan kinsan kaf cikinmu Ammi tafi ji dake"ya zee ta fada. A baya dai idan aka fadi haka zan gasgata,amma yanxu wlh bakwasona"nace cikin kuka. Kinga ni wannan dramar ta isheni haka,keda kika dade bamu ganki bs maimakon kizo ki faranta mana rai sai kizo kina mana kuka"ya ruqayya ta fada. Tashi kawai nayi na shiga dakin Ammi na fada gado tare da cigaba da kuka na. Allah sarki uwa!Ammi ce ta zauna kusa dani tare da dora kaina akan cinyarta tana gogen hawayen fuskata. Ya isa haka kinji auta?kar kije kanki yayi ciwo.kiyi hqr nasan ba'a kyauta miki ba,kullum da zancenki nake tashi a raina,amma ina mgn Abbinku zai fara fada,ko yanuwanku ba yadda basuyi zasuje ganinki ba ya hana,a cewarsa a barki zuwa wani lkcn sai aje" Amma kuma Ammi..." Dan allah ya isah haka auta,ki tashi kije cikin yanuwanku kamar yadda kuka saba,Abbinku ya fita shima yana dawowa kije ku gaisa" Dan dole na tashi na fito fallon,inda sukayo kaina caaa. Waikina nufin har yanxu baki cire komai a ranki ba khadija?kalli yadda kk rame dan allah"ya aisha tace. Nidai kawai kallonsu nakeyi daya bayan daya,dan basu san halin da nake ciki ba,kuma na daukarwa kaina alqawari ko naman jikina ake gutsira a gidan nan bazan taba fada ba,idan na mutu dai sai suje su dauki gawata. Ganin Ammi tana kallona yasa na saki jiki idan anyi abin dariya nayi dan hira da raha akeyi kamar yadda al'adar gidanmu take indai muna tare to fara'a bata barin fuskokinmu. Ana haka Abbi ya shigo,inda ya zauna shima aka taba hirar dashi kafin ya tashi. Zumbur na miqe. Ammi bari naje gidansu nusaiba" Kin tambayi mijinki zaki wani wajene bayan nan?"ammi tace tana kallona. Komawa kawai nayi na zauna dan bani da amsar bayarwa. Ke kuwa auta sallah guda ko lalle baza kiyi ba"ya ruqayya tace. Ya ruqayya kenan,a wannan anguwar ina zanga mai lalle?ni kinga kaina nema ya damenu ba kitso,kiyi mun ko kalba ce"nace tare da cire dan kwalin kaina. Ke wai yaushe kika zama qazama ne,ga kanta Ammi dan allah"ya zee tace tana tamin kai. Ammi dai bata ce komai ba,sai ya ruqayya data miqe tsaye. Ina wayarki take"tace tana kallona. Ni nama manta inada waya dan can na barta a kan gado. Wayar ammi ta karba ta fara kira,bansan wazata kira ba,nadai naji tace wai dan allah zamu fita tare. Jin tace na tashi muje naji fita yasa na zira mayafi mukai waye. Can wajen salon din bakin titin layinmu mukaje. Mun dan sha zama kafin kazo kanmu. Sosai nakeji iska na shiga kaina bayan an wanke min relaxer ana gyaran kan. Tsaf aka gyaranshi yanata qyalli da gamsu,ya ruky ta biya kudi muka fito. Gidan mai lalle mukaje duk da yamma ta fara haka muka samu daqar tayi min hadadden jan lalle na son kowa qin wanda ya rasa๐Ÿ˜‰ Cikin qanqanin lkc na dawo mace sai dai rama da duhun dana qarayi. Ana kiran sallar magriba muka dawo gida. Kowa yaita yaba lallen,kafin suka fara shirye shiryn tafiya. Yaya yanxu yaushe zakuxo"na fada kamar nayi kuka. Munason zuwa auta amma abbi ya hana mu kuma bamusan dalilinsa nayin hakan ba,kedai ki cigaba da haquri zakici riba insha allah" Haka ina gani suka tafi,na dawo muna hirar yaushe gamo da ammi dan su shahida suna wajen abbi. Ammi dan allah ki barni naje gidansu nusaiba"na fada a shagwabe. Ba hanaki nayi ba auta,mijinki shike da ikon barinki fita bani ba. Cikin hikima ta ringa min nasiha tare da nusar dani akan muhimmancin haquri dayiwa iyaye biyayya. Har bayan issha muna jiran dan milkin baixo ba,ni kuwa addu'a nake allah yasa ma yaqi zuwa mu kwana. Zuwan almajirin ammi yasa na rubuta gajeren saqo a paper nace yakai gidansu nusaiba. Ai kuwa cikin qanqanin lkc sai gata ta bayyana a gidanmu. Daku muka qule bayan mun gama ihun ganin juna. Lallai nusaiba manyan qasa,ai banyi tunanin xaki xo ba" Kinji ki maizai hana ni zuwa nida nake son ganinki" Ba wani da kinason gani na ai xakixo inda nake" Wlh ki tambayi ammi ina zuwa nace ayimun kwatancan gidan,ammin ce tace wai abbi ya hana kowa zuwa dan dole na hqr" Nima haka dazu tace,nusaiba na rasa gane dalilin dayasa abbi yayi haka" Ke bafa komai,kawai dai ya fison ki nutsu ne,sbd idan kina ganin yan gida xakiyita tada hankalinki ne" Uhmm,ni kuwa ina ya sadiq dina?" Wata muguwar harara ta kwada min kafin tace. "badai kina nufin har yanxu kina wahalar da kanki akan abinda kk san bazaki samu ba?" Kamar ya?" Kamar yadda wanda kk wahala a kanshi,kk kasa nutsar da hankalinki ki rungumi mijinki sbd shi,shi kuma yaje yayi aure tuni ya manta dake dan yanzu matarsa nada qaramin ciki๐Ÿคฐ. ๐Ÿ™Š๐Ÿ™Š๐Ÿ™‰๐Ÿ™†๐Ÿ™†๐Ÿ™†๐Ÿ™†๐Ÿ™† Manage it plss. [07-23, 20:47] Sistoh: ๐Ÿ’™๐Ÿ’™RABON KWADO...๐Ÿ’™๐Ÿ’™ Er mutan ungogo๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ ๐Ÿ…ฟ96-๐Ÿ…ฟ100 Karya ne,wlh karya kk nusaiba kice ya sadiq zai manta ni hakakuma qarya ne kice zai auri wata bayan ni"na fada ina riqo wuyan hijab din jikinta. Kallona kawai ta tsaya tana yi. Khadija wai yaushe zaki dawo hankalinki ki daina abubuwa irin na jahilai?da aurenki kk dakon soyayyar wani?to gsky ce bazan fasa fada miki ba kuma zan qara maimatawa ya sadiq yayi aure ya manta dake"tace tana fizgewa daga riqon da nayi mata tare da ficewa a dakin. Kifa kaina nayi a katifa ina maimaita maganganun nusaiba. Ya sadiq why?meyasa xakayimin haka?da gsk ka manta dani?ka manta dumbin soyayyar danake maka?wayyoo... Jin an zauna a kusa dani yasa nayi saurin dagowa. Ammi ce take bina da kallon tuhuma. Kukan me kk?"ta jefomim tmby. Shiru nayi ina qoqarin tsayar da kukan dan bansan amsar da zan bata ba,gashi banga alamar wasa ko sassauci a fuskarta ba. Meya hadaku da nusaiba najiyo hayaniyarku?"ta kuma tmby. Nan ma shirun nayi tare da qasa da ido dan ko hauka nake bazan iya cewa ammi sbd ya sadiq yayi aure nake kuka ba. Khadija! Da sauri na dago dan na manta rabon ammi da kirana da wannan sunan. Saboda Abubakar yayi aure kike kuka?ko kinason ki fada min har yanxu baki cireshi a ranki kin manta dashi ba?" Nan ma banyi magana ba. Kin dauka yadda baki da hankali da tunani haka shima yake da zaita dakon soyayyarki kina matar wani?ko kuwa so kike yayiwa iyayensa butulci kamar yadda kika yiwa naki iyayen kika kasa xama da mijinki lpy?kin zata tunda ya rasa ki shikenan bazaiyi aure ba?ko zaman jiranki xaiyi ki kaso naki auren kixo ya aure ki?" Wlh,wlh,wlh khadija idan baki gyara rayuwar aurenki kin xauna da mijinki lpy ba xaki sha mamaki na.shashasha kawai,ki tashi ki ficemin anan mijinki nacan na jiranki." jikina ba qarfi na miqe dan gsky ran ammi ya baci sosai dan bantaba ganinta a wannan yanayin ba. Mayafina na dauka kafin na nufi dakinta,dan tuni ta fito ta barni anan. tana zaune a gefen gadon naje na tsugunna a gabanta. Ammi dan allah kiyi hqr"nace cikin kuka. Ke zan bawa haquri khadija,kije ki gyara rayuwar aurenki wannan ne kawai zaisa na sakko.ki tashi kin barsu suna jira. Haka na fito ina kuka inda Abbi ma yayi min fada nidai kuka kawai nake na shiga mota muka tafi. Shiru motar sai shassheqar kukan da nakeyi. Aunty me akayi miki kikeyin kuka?"shahida dake gefena tace. Jin banyi mgn ba yasa ta mayar da tmbyr ga daddynsu. Daddy me akayiwa Aunty take kuka?" Ummina gata nan ki tmbyta nima bansani ba"yace yana cigaba da driving dinsa. Tun daga nan ba wanda ya kuma cewa komai har mukaje. Dan tuni iman ma tayi bacci. Jin munxo yasa na fita ban jira kowa bai nayi gaba abina. Sosai na raya daren da kuka,tare da roqar allah ya ciremin son ya sadiq daga raina,dan nasan yanxu yayi min nisa,son maso wani kawai nake. Washegari ma ko falo ban iya fitowa ba,sbd kaina da yakemin axababben ciwo. Aunty ki shiryamu inji daddy zamuje park"Iman tace tana jijjigani. Baby bazan iya ba kaina yana ciwo kinji?" Daga kai tayi ta fita a dakin. Nidai ina kwance kawai ihun shahid na jiyo. Bansan lkcn da na tashi da gudu nayi kitchen inda ihun yake fitowa ba. Inannalillahi! Na fada na riqo shahid dayake ta tsalle yana riqe da hannu,da dukkan alamu qonewa yayi da ruwan zafi,sbd ga cattle nan da ruwa a yashe a qasa. Shahid meya kawoka kitchen? dama kuna zuwa kitchen?"na fada a rude dan ganin yadda yake kuka,amma ba wata qonewa bace mai yawa. Cak!na tsaya dan ganin daddynsu tsaye a bakin qofar kitchen din da sauran yaran. Riqo hannun shahid din yayi tare da tmbyrsa garin yaya ya qone? Wanka zanyi kuma ba ruwan zafi a heater din toilet dina shine nazo na diba anan shine na qone"na fada yana kuka. Kallona yayi wanda bazan iya fassara ko wani irin kallo bane yaja yaransa sukai gaba. Nima jan jiki nayi na koma daki ina tunanin to kallon na menene?nidai bani nace yaje ya dibi ruwan zafi ba,asalima bansan zaiyi wankan ba. Sbd mugunta shine kikeso ki kashemin da ko?to na gaji da wannan abun naki bazan iya ba"daddynsu shahid ya fada yana figoni daga kwancen da nake. Nima na gaji,wlh na gaji da wannan abin naka,ko anfada maka baiwa aka kawo maka?"nima na fada a fusace dan da gsk na gaji da wannan rayuwar rashin yancin. Ni kike fadawa haka koh?sbd.... Aaaaa,karka fara,karka fara dabi'ar daba taka ba babanah,dukan mace?" Da sauri na bude ido dan jin muryar ummi,domin na shirya kawai saukar mari nake jira. Aunty anisa ce ta kamani tana sharen hawayen fuskata wadanda bansan ma suna zuba ba. Inda ummi ta ja shi suka fita yana wani huci. Khadija me kk yi masa haka har ya fusata yake qoqarin kai miki hannu"?aunty anisan ta fada. Kukan da yazo min ya hanani mgn,inda suka rufu akaina sunata rarrashi na,dan gaba dayansu sukazo. Kafin wani lkc zazzabi mai zafi ya rufeni. Daqar naci wani abun mubina ta bani magani nasha na kwanta. Sosai naji relief bayan na farka,inda suka shiga nan nan dani dan har lkcn suna gidan. Bayan na idar da sallah aunty anisa ta zauna tana fuskanta ta,domin a lkcn mu kadai ne a dakin dan su mufida sun fita. Khadija! Naaam"na amsa da dasasshiyar muryata. Inaso ki dauka cewa yanxu kina tare da fatima zaki ita fada min duk abinda na tmbyki,domin nima ina miki kallo matsayi daya danasu mufida" Nafi kowa sanin halin broz,kuma nafi kowa sanin wayeshi.Na fahimci akwai matsala a zamantakewarku tun jiya da kukaje gidan ummi,Dan nayiwa broz sanin da kallo yayi nasan abinda yake nufi,kuma lkcn fatima tananan ba haka ya saba yiba dan muka hadu,hakan yasa nace muzo yau dan inason nayi wani abu akan abin kafin na koma" Dan haka yanxu ki fada min mene ya hadaku dazu?" Banyi mgn ba sai hawayen da suka zubomin" Kinga ba kuka nace kimin ba,idan kuma baki yarda dani ba bazaki iya fadan damuwar ki ba shikenan" Tabbas zan fada mata kodan na samu sauqi a cikin xcyta,duk da akwai wadanda sukafi cancanta na fadawa damuwata kafin ita amma yanxu sun min nisa,ammi danake tunanin zata fahimceni itama fushi take dani. Dama can ya tsaneni tun ba yau ba,kuma akazo aka hadani aure dashi.ya fadamin tun kafin nazo gidan nan xan zauna ne a matsayin yar aiki...... Haka na bata lbrn abubuwan da sukafi damuna dan nasan bazasu fadu duka ba. Mundau tsahon lkc ba wanda yayi mgn kafin ta kalleni. Kina nufin tsahon lkcn nan zaman da kuke kenan?" Daga mata kai kawai nayi. Kuma ba wani mataki da kike shirin dauka a kai?kinsan dai rayuwa bazata cigaba a haka ba,kuma idan na fahimceki kina nufin ko abincinki bai taba ci ba,bare aje ga sauke haqqin aure" Shiru nayi. Shikenan,insha allah zanyi iya qoqarina kamar yadda idan su mubina ne a irin wannan conditon din sai inda qarfi na ya qare haka kema dan duk daya kuke a wajena,dan haka inason ki bani hadin kai,Domin dole saida hadin kanki komai xai tafi dai dai" Broz irin mutanen nan ne masu wahalar sha'ani,amma kina fahimtar halayensa kin gama dashi,sbd hk saikin jure" Tom ngd" Banason gdy,yanxu ina wayarki?" Tashi nayi na dauko mata calculator dita. Karba tayi tana jujjuyata kafin taja tsaki ta miqe ta fita. Ganin shiru bata dawo ba yasa na koma na kwanta,domin sai naji zcyta sakayau kamar na sauke wani nauyi a kaina,ko ba komai na amayar da damuwata. Mubina ce ta shigo. Sannu sis" Murmuhi kawai nayi. Kixo ummi na kiranki" Hijabi na nasaka kafin na fita. Can gefe na zauna dan ummin ce da aunty anisa sai daddynsu shahid. Fada ta shiga yi mana sosai tare da nuna rashin jin dadinta akan abinda tazo ta gani. Haduwa sukai suna bata hqr nidai kaina a qasa.saidata gama kafin ta tashi ta fita ya bita yana qara bata hqr. Anjima zan bayar da saqo a kawo miki kinji?ki qara hqr kinsan irin wannan abun sai mutum ya jure dan inaso ki shirya yaqin janyo hankalinsa da mallakar zcyarsa.zuwa gobe nake tunanin zamu koma,amma idan bamu tafi ba zan dawo" Daga mata kai nayi ina qara jaddada qoqari irin nata,tare da samar mata matsayi a zcyta dan ko ba komai ta nuna qauna da damuwa akan lamarina. [07-23, 20:47] Sistoh: ๐Ÿ’™๐Ÿ’™RABON KWADO....๐Ÿ’™๐Ÿ’™ Er mutan ungogo๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ ๐Ÿ…ฟ111-๐Ÿ…ฟ115 Har dare ni kadaice a gidan dan yaranma bansan inda ya kaisu ba,ko su ummin suka bi oho. Wani nishadi nakeji danasan yana da nasaba da amayar da abinda yake zuciya. Sosai lamarin auren ya sadiq idan na tuno yake bani mamaki,amma a kalaman ammi sai nake ganin kamar tilasta masa iyayensa sukayi. Koma yayane nidai na dau aniyar cireshi a raina koda ta qarfin tuwo ne. Ina kwance shiru bayan nayi shirin bacci,dan yar calculator din ma dana ke sauraran radio ko nayi game mai miciji itama babu,dan da ita nake tunanin aunty anisa ta tafi. Da sallama ya danno kai cikin bed room din,wanda nayi saurin miqewa daga kwanciyar da nake domin tsahon zamana a gidan bai taba takowa koda bakin qofar dakin bane. Fuskarsa ba yabo ba fallasa ba kamar yadda na saba ganinta ba koda yaushe a hade. Ganin ya nemi gefen bed din ya zauna yasa na qara matsawa can qarshen gadon duk da girman daya ke dashi. Saida ya gama shan qanshinsa da danne dannen wayar data zama kamar ibada sannan ya kalloni. Ganin yadda na takure yasa ya tabe baki kafin yayi mgn. Ga saqo nan anisa ta bayar a kawo miki,kuma daga yau ba wani zakina tmby wani abu idan kina buqata ba,ni dana ajiyeki niya kamata ki tmby"ya fada tare da ajiye qatuwar ledar hannunsa ya fita. Har yakai bakin qofa ya juyo. Tace ki hada wayar yanxu akwai sim card a ciki zata kiraki"yace ba tare daya juyo ba. Jin zancen waya yasa nayi saurin durowa tare da bude ledar cikin gaggawa. Kayan bacci ne masu kyau da tsada kusan kala biyar sai turaruka da banbi takansu ba na dauki kwalin wayar na budeta. Masha allah!na fada cikin zaquwa tare da raya cewa wannan wai wayata ce?Ipone 7 pa,wayyo dadi ashe nima inada rabon riqe irin wannan wayar. Jikina har rawa yake na kunna wayar tare da fara processing. Sosai nake murna da jaddada kalmar nan ta mahaqurci mawadaci. Banyi mintina da kunna wayar ba kira ya shigo wanda nafi tunanin na aunty anisa ne. Assalamu alaikum"naji an fada wanda ko ba'a fada ba na gane muryarta ce. Wa'alaikissalam aunty anisa" Naam aunty khadija ashe ya kawo saqon?" Cike da jin nauyin auntyn data kirani dashi nace. Eh ya kawo na gode sosai" Nafa fada miki banason godiya.yanxu abinda nakeso dake gobe da safe idan allah ya kaimu kwalliya zakiyi ta kece raini,sannan ki shiga kitchen ki shirya masa kunun gyada da qosai,kafin kije ki kirashi kice yazo yayi b/fast.ki cire wani abu a ranki ko wata kunya kiyi abinda nace,wannan shine matakin farko da zaki fara dauka,dan inason kafin a dawo da yaran ace wannan bangaren mun gama dashi kingane koh?" Eh"nace ina jinjina irin wannan aiki data sakani mai wahalar aikatuwa. Kamar yadda na fada sai kinyi hqr kin jure,bawai kinayi so daya ya disgaki zakiyi zcy kice bazaki kuma yi ba,Aa haka zakita jurewa har allah ya karkato miki da hankalinsa.bana tunanin zaiqi cin abincinma dan jiya sosai ummi tayi masa fada kuma naga alamar fada ya shigeshi.Nidai fatana khadija karki bani kunya,kiyi duk abinda nace miki kinji?na taqaitaccen lkc ne insha allah" Tom aunty anisa insha allah zan qoqarta" Yawwa qanwata,yanxu kiyi bacci ta yadda zaki tashi da wuri kiyi abinda ya dace,goben zamuyi waya" Tim saida safe"nace ina zare wayar daga kunnena,tare da fargabar yadda zan tunkari wannan babban al'amari. washegari kamar yadda Aunty anisa ta sakani haka nayi nayi kwalliya na cakare wanda ni kaina inada tabbacin nayi.zakifi tunanin gasar sarauniyar kyau zani. Iphone dita na dauko na shiga daukan pictures,inda suka fita yadda ya kamata musammanma da kyan camera ya hadu da good background๐Ÿ˜Š. Abinka da an dade ba'a haduba haka na bata lkc na wajen daukar picx din kafin na shiga gyara wadrop dan shirya kayansu iman da aka kawo wanki tun shekaran jiya. Saida na tabbatar na gyara kayansu kafin na fara gyara nawa dan shiryasu yadda ya kamata. Ledar jiya na dauko tareda zazzage kayan akan bed. Kayan na fara dagawa wanda nayi saurin cikwikwiyesu na saka a wadrop dan kunya ma kayan suka bani๐Ÿ™ˆ Turarukan ma sunmin qamshi sosai,inda ba bata lkc na fara turara gidan da turarukan. Haka na cigaba da aiki na cikin nishadi ina shaqar qamshin turaren. Ba bada lkc na gama komai dan gidan ba dattine dashi ba. Kitchen na fada na shirya kunun gyadar tare dayin qosan naje na jera a dinning ina sake saken ta ina zan fara tunkarar sashensa?to idan najema mezance? Ganin banida wani zabi daya wuce yadda aunty anisa tace yasa nayi qundunbala tare da qunar baqin wake na nufi sashen duk kuwa da fargabar yadda zai karbi baqon al'amarin daya cika min zcy. Tofa! nafi mintuna 30 a bakin qofar ina tunanin ta yadda zan fara knocking qofar. Jin an bude qofar yasa naja da baya da sauri tare da diriricewa kamar mara gsky,bayan luguden da zcyta takeyi ganin mamaki kwance a fuskarsa.nasan mamakin bai wuce na ganina da yayi a qofar sashin sa ba. Ganin ya tsaya riqe da qofa yana kallona yasa nayi qoqarin aro nutsuwa da dauriya na yafa. Dama inaso na fada maka na gama b/fast ne"na fada cikin dauriya. Nace ina buqatar abinci ne"ya fada yana qara gyara tsayuwa. Shiru nayi ina kuma jin takaici a raina. Tunda bance ina buqata ba zaki iya bace min anan gurin,idiot kawai"yace tare da banko qofar. A hankali na zame a wajen na zauna dan nasa qafafuna bazasu iya kaini daki ba. Idiot?nice idiot?meyasa yakeson kira na da wannan sunan?idan zan iya tunawa wannan shine karo na uku daya kirani da wannan sunan.Amma yanxu banga laifinshi ba,da banzo inda yake ba da bazai fada min haka ba. Why aunty anisa?meyasa kike tunanin zan iya mallakar mutumin dayafi kowa tsanata?meyasa kikeson na cusa kaina inda nakeda tabbacin bazan samu shiga ba? A hankali na miqe ina goge hawayen fuskata,dan banaso ya kuma fitowa ya sameni a bakin qofarsa,dan bansan me zai kuma fada min ba. Ina shiga dakin na fizge dankwalin kaina tare da wullar dashi,sannan na kifa na cigaba da kuka dan samun sauqin zcy. Inaji wayar ta fara qara naqi dagawa,tunowa da ba mai kira sai aunty anisa yasa na share hawayena tare da daga wayar. Matar broz yaya dai?inata zumudin kira naji bayani dan nasan yanxu broz ya dade da tashi a bacci" Qaqalo murmushi nayi tare da cewa "ina kwana aunty anisa" Shiru naji tayi kafin tace"an samu matsala koh khadija?" Aa"nace da muryata da take rawa dan kukane ya tahomin. Kiyi hqr kinji?dama na fada miki sai kin jure" Aa aunty anisa,kiyi hqr wlh bazan iya ba,daddyn shahid da irin mutanen da suke saurin sarrafuwa bane,kuma na sanar dake tun farko baya sona,bai bata min kallon mutunci ina qanwar matarsa ba bare yanxu da nake amsa sunan matarsa" Haba khadija,bai kamata kiyi saurin karaya haka ba,nasan halin ya abdul sosai shiyasa naje so kema ki gane halinsa kiyi hqr dashi har zuwa lkcn da zaku fahimci juna" Banason yi mata musu ko gardama a qoqarinta na ganin ta saita min rayuwar aure,hakan yasa nayi shiru kawai ina kuka. Khadija! Naam" So nawa ne abu ya sameki kikayi kuka ya warkar miki da matsala ko damuwa?kuka ba shine mafita ba,banaso duk abinda broz zai miki ki yarda ya gano fishinki ko gazawarki" Aunty anisa ki gane,daddyn shahid nice bayaso,da yake yanason ya fatima kin taba ganin wani abu ya hadasu?" Naji baya sonki,shine yanxu nakeson yasoki fiye da yadda yaso duk wata mace daya taba so.idan kin yarda dani kinsan bazan cutar dake ba khadija kawai ki yarda kuma ki amince da duk abinda na fada miki.Ya abdul ba dutse bane bare kiyi tunanin bazai lanqwasu ba.inaso ki share hawayenki yanxu kiji wani matakine wanda zamu shirya na gaba" Dan dole na share hawayena ina sauraron duk abinda take fada ba tareda na ayyana zan iya aiwatar da hakan a raina ba. Sosai take tausata da qarfafamin gwiwa har saida taga na yarda na dauki duk wasu shawarwarinta. Da yamma ma wanka nayi na kumayin kwalliyar,badan wai koxai yaba ba saidan kawai nabi shawarar aunty anisa,kuma koba komai gyara yana da dadi nima naji dadi a raina. Tuwon semo nayi da miyar kubewa kamar yadda aunty anisa ta sakani,bayan na cinye qosan danayi da safe dan dama kadan nayi. Haka shima na jere a dinning kafin na zauna a falo inayin game dita mai aji๐Ÿ˜„ [07-23, 20:48] Sistoh: ๐Ÿ’™๐Ÿ’™RABON KWADO.....๐Ÿ’™๐Ÿ’™ Er mutan ungogo๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ ๐Ÿ…ฟ106-๐Ÿ…ฟ110 sai wajen 9pm ya shigo kamar kullum fuskarnan a hade kamar hadari. Sannu da dawowa"na fada cikin fargabar abinda zai biyo baya. Ko inda nake bai kalla ba bare nasa ran zai amsa. Bin bayansa nayi da kallo kafin na koma mazaunina Ina jinjina hali irin nasa.Amma a yadda aunty anisa take fada wai yana da sauqin kai,ko ina sauqin kan yake anan oho. Kiran aunty anisan ne ya katsemin tunani. Ita dai baiwar Allan nan ta damu da lamarina. Khadija broz ya dawo koh?"ta fada. Ni lamarinta har mamaki yake bani,tana abuja amma tasan duk wani motsi nasa da duk lokutan dayake gabatar da abubuwa? Kiyi qoqari kiyi abubuwan dana fada miki kinji?" Aunty anisa yanxu ma fa ko sannu da zuwana bai amsa ba" Nasan bazai amsa ba dama khadija,yanxu ki bari zai fito kallon News falon saiki gabatar masa da abincin,insha allah indai yaga abincin zaici dan yana matuqar son cimar" Da To naita binta har mukayi sallama. Inanan zaune kuwa sai gashi ya fito,nan ma ko inda nake bai kalla ba ya fara kunna tv. Ganin ya kishingida ya fara kallon labaransa yasa na tashi na shiryo masa abincin a babban faranti na kawo na ajiye a center table. Flat na dauka na zuba abinci,kafin na zuba masa tataccen inibi a cup. Ga abinci"nace ina kallonsa. Wani mugun kallo ya watsa min nida abinci kafin yayi mgn. Is better for u ki bar wahalar da kanki,ki daina bata lkcnki kina yaudarar zcyrki.Bakida abinda zaki burgeni dashi,zaifi miki ki cigaba da zama a matsayin yar aiki kamar yadda na shawarce ki tun farko"ya juya ya cigaba da kallonsa kamar bashine yayi mgnr ba. Gwiwa a sace na fara tattare kayan abincin zcytah na zafi. Kitchen nakai kafin na koma daki.kashe wayar nayi na sakata a drower,dan nasan dole aunty anisa ta kira. Bazan qara kunna wayar bama bare ta kuma fadan wani abu dazan jawa kaina raini. Tsahon kwana uku ban kuma yarda mun hadu dashi ba,dan yunwa ce kawai take fito dani daga daki.wayar ma tun a ranar ban kuma waiwayarta ba,dan zamana haka ya fiye min alkhairi da nakai kaina a wulaqanta ni. Dauke nake da cup na fito daga kitchen ina shirin komawa daki naji ance. Zo nan" Saura qiris cup din ya fadi dan na tsorata sosai,banyi zaton da mutum a falon ba sai yanxu. Falon na qarasa na nemi guri can nesa na zauna na fara shan custard din dake cikin kofin. Tashi naga yayi,ga mamakina naga yazo kusa dani ya zauna. Daxu munyi waya da ummi ta fadan Mubina gobe zatazo holyday,kuma nasan ummi zata turota ne C.I.D,dan haka zakiga abubuwa na faruwa karki dauka wani abun ne.sannan Me anisa zata fada miki ta dameni da kira?" Nidai banyi mgn ba,hasalima ni ba wani fuskantar abinda yake cewa nake ba. Kunnena ya kama yaja da qarfi wanda yasa dole na saki qara. Banaso ina yiwa mutum mgn yayi min shiru" Nidai Allah ya isa nake ja a zcyta dan ba qaramin ja yayiwa kunnen ba. Sum sum na tashi na bar gurin ina qara jajjada allah ya isa. Sosai naji dadin xuwan mubina,inda muka baje munata shan hira kasancewarta gwanar surutu,dama kadaici ya isheni. Tare mukayi girki muka jere a dinning kafin mukayi wanka. Das!na fito a cikin wata maroon din shaddata datasha aiki.duk da banyi wata kwalliya ba nayi kyau ba qarya. Wannan duk kwalliyar yayan namu ce?kice haka ake kasheshi da wanka"ta fada da sigar wasa. Murmushi kawai nayi ina feshe jikina da turare. Nipa qamshin abincin nan duk ya hargitsani,nidai ci zanyi nasan ke saikin jira mijinki"tace. Falo na dawo na kwanta ina kallon pictures a wayarta inda ta dawo falon tanacin abinci tana min bayanin hotunan daki daki. Da sallama ya shiga hannunsa dauke da qaramar leda. Fuskarsa dauke da murmushi ya qaraso yana amsa sannu da zuwan da mukayi masa a tare. Nidai kallon mamaki kawai nake masa.ban gama mamaki ba sai danaga yaxo Daf dani ya zauna tare da dora kansa akan kafadata yana kallon wayar. Nernah yau na gaji sosai wlh"yace da wata murya da bansanshi da ita ba. Tuni na daskare a wajen,dan numfashima daqar nakeja. Sosai abin ya bani mamaki dan gani nake kamar a film. Mubina me kk yiwa matata taqi yimin mgn?"yace yana kallon mubina. Ai kunfi kusa yaya,gatanan ka tmbytah,maybe dan baka dawo da wuri bane tanata jiranka ku ci abinci"tace tana cigaba da cin abincinta hankali kwance. Wayyo allah!๐Ÿ™†๐Ÿ™† Gyara kwanciya ya qarayi a jikina yana wani lumshe ido. I'm sorry nernah,Dauko mana plat ga abin dadi na kawo miki"yace yana janyo ledar daya ajiye. Nernah"na maimaita a zcyta.ya sadiq kadai ke kirana da wannan sunan,sai shi yanxu dan munafinci zai rada min?A iya tunanina duk tsahon zamanmu ko sunana bai taba ambata ba. Wata dabara ce ya fado min,bashi ya iya bariki ba?hmmm Ba fushi nake ba,kasan kaima bazan iya fishi dakai ba"nace ina sakar masa wani killer smyl. Kallona yake da alama na mamaki ne,sai kuma yayi saurin dauke idonsa daga kaina. To maza dauko plat din"yace. Gafa abinci can yana jiranka,kuma kasan sbd kai nayi"na fada a shagwabe. To duk zanci a kawomin"ya fada still yana kallona. Ina barin falon na jingina da bango ina maida numfashi dan ba qaramin qoqari nayi ba. A trey na jero abincin na kawo inda muka zauna qasan carpet din ya wani bude qaramin bakinsa shi a dole saina bashi abinci. Yadda yake langwabewa yana zuba min shagwaba kamar wani qaramin yaro shi zaifi baku mamaki,ita kuwa mubina in banda dariya ba abinda takeyi. Idan ka ganshi yanxu bazata taba tunanin daddynsu shahid bane wanda ka sani,dan yadda yake shagwaba ko iman batayin irinta. Nima duk shagwabata saida na sara masa dan wannan har PHD yayi akan shagwaba๐Ÿ˜„ Shagwabar ma tafi cin abincin yawa,nidai biye masa nakeyi dan na qagu a gama cin wannan abincin. Dan dole na bude nawa bakin yana zubamin loma.haka dai muka gama shirin film din na tattare kwanuka nakai kitchen. Daga nan ban dawo falon ba nayi daki. Wanka na sake nayi shirin bacci dan nace bazan koma falon ba,dan bazan iya wannan shutting din ba. Wayatah na dauko na kunna na dannawa aunty anisa kira,dan nasan ban kyauta mata ba,kuma inaso ta bani shawara akan wannan rikitaccen al'amarin. Sannu khadija kin kyauta"tace bayan ta amsa sallamar. Amin afuwa auntynah"nace ina murmushi. Ba wani aunynkikin samu miji shine kk manta dani"tace tana dariya Aunty ba haka bane wlh" To yanxu ya ake ciki?" Lbr na bata duka kafin tayi shiru kamar bazatai mgn ba. Kinsan me khadija?wannan ma wata hanyace mai sauqi Allah ya kawo mana,dan haka zagewa zakiyi kiyi duk wani abu daya kamata,akwai abubuwa masu tarin yawa anan gaba,dan haka sai mun qara shiri sosai" Amma aunty..... Khadija banason kina karaya haka,zaki iya kiyi kawai" To Aunty nagode" Yanxu ina mubinan?" Na barsu a falo" To maza ki koma ayi hirar dake,kuma duk abinda yayi ki biye masa,zamuyi mgn da mubinan itama" Tom aunty saida safe" Na dade zaune a gefen gado ina tunanin wannan baqon al'amari kafin daga bisani na zira hijabi akan kayan baccin duk da kasancewarsu masu kauri na fita. Mubina ce kawai a falon tana waya naje kusa da ita na zauna. Wai yau baza muyi bacci bane?"nace ina kallon agogo ganin 11 harta wuce. Saida ta kashe wayar kafin itama ta kalli agogon. Kinsan in mutum yana tare da masoyi baya sanin lkc yayi"tace tana dariya. Qarasowarshi yasa na fasa mgn,inda yake sanye da farar riga mai qaramin hannu sai wando baqi ina gwiwa. Laptop din hannunsa ya bude bayan ya zauna can wata kujera. Yaya ana shirin bacci kana shirin aiki?"mubina tace. Idan banyi yanxu ba mubina gobe bani da lkc"ya fada yana kallon abinda yakeyi. Tom nidai saida safe"tace tana miqewa. Bayanta nabi dan ni kaina baccin nakeji. Wanka ta shiga inda ni kuma na nemi maqwanci. Wai mene haka kin wani bar mijinki a can kinzo nan"tace bayan ta fito daga wankan. Shiru nayi mata kamar banji ta ba. Hawa gadon tayi tana jan blanket din dana rufa. Wlh ki tashi ki tafi gurin mijinki babu ruwa na" Dan allah mubina ki kyaleni,ni anan nake kwana'"nace inajan blanket din daga hannunta. Kafa min idanu tayi kamar zata cinye ni. Amma wlh khadija bakida wayo,to mijin naki wa kk barwa?" Ke na barwa kije ki tayashi hira"nace ina dariya. Ke wlh baki isa ba sai kin tashi kin tafi"tace tana jana. Kaji mata da qarfin hali,dan allah ki barn..." Sallamarshi ce tasa nayi shiru ina qara jan blanket tare da rufe jikina. Tashi mu tafi"yace yana wani tsare gida kamar ba shagwababben nan ba๐Ÿ˜œ. Ganin ba alamar wasa a fuskarshi yasa na miqe ina turo baki. Hannu ya miqomin ba musu na kama ya riqoni muka fita๐Ÿค Muna fita ya juyo. Daga yau banaso na qara zuwa nace ki tashi mu tafi,idan kunne yaji...."yace tare da sakin hannuna yayi gaba. To meye hakan?yana nufin a part dinsa zan ringa kwana?Wayyo ni hadiza naga ta kaina๐Ÿ™† Masu bibiyar littafin RABON KWADO..๐Ÿ’™๐Ÿ’™ Muna gdy,da fata za'ayi mana afuwa na rashin yin typing na kwanaki,hakan ya faru sakamakon rashin lkc da bana samu,amma insha allah zan ringa qoqari inayi ko da babu yawa.ngd Sannan akwai mistake na page number da nayi zansa 101-105 nasa 111-115 ina fatan za'amin afuwa. Er mutan ungogon ce dai๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ [07-23, 20:48] Sistoh: ๐Ÿ’™๐Ÿ’™RABON KWADO...๐Ÿ’™๐Ÿ’™ 11:02] ๐ŸญRukiey๐Ÿญ: ๐Ÿ’™๐Ÿ’™RABON KWADO๐Ÿ’™๐Ÿ’™ Er mutan ungogo๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ ๐Ÿ…ฟ111-๐Ÿ…ฟ115 Ganin tsayuwar bazata amfaneni ba yasa naja qafafuwa na nabi bayanshi,duk da shi tuni ya shige abinsa. Hannuwana na rawa na dorasu akan handle din qofar. Kamar barauniya nake sanda a makeken falon,wanda haduwarsa ma baki bazai iya fada ba. Duk wani abu dake cikin falon white and pink ne.kasancewar yaune ranar dana fara shigowa bangaren sai na rasa inda zan dosa. Qofofine guda biyu suna fuskantar juna,nidai gudun kar nayi laifi yasa na nemi daya daga cikin kujerun falon na kwanta. Ban dauki lkc ba bacci yayi gaba dani. Jin sanyi na shigata ta ko ina yasa na bude idona. Duhu ne sosai har bana iya ganin komai,hkn yasa na shiga lalube ko zan samu abinda zan lullube jikina dan jin sauqin sanyin. Jin abu mai laushi wanda nafi tunanin bargo ne hakan yasa banyi tunanin komai ba na shiga ciki tare da komawa bacci dan sosai naji sanyin ya ragu. A firgice na tashi jin an ja minin gashi kamar za'a cire shi. Duk da zafin da nakeji hakan bai hanani tsorata ba dan ganina kwance jikin daddyn shahid. Qara jan gashin yayi wanda na saki qara tare da hawayen azaba dan da mugunta yake jan gashin.gashi ya hanani sauka daga kanshi. Kuka nake sosai dan azaba jinake kamar kaina zai cire dan jan gashin yake kamar yanajan igiya. Tun ina kuka mai sauti har wahala tasa bana iya qara sai dai hawayen dake zuba kamar fanfo. Inaso kisan bakin rijiya ba wajen wasan yara bane,sbd nace kixo dakina ki kwana har hakan zaisa qaramar kwakwalwarki tayi miki wani gurbatatten tunani?To ki canja tunani kuma ki saka a ranki nafi qarfinki har abada,useless kawai"ya fada tareda ture ni ya tashi. Ruf da ciki nayi inajin zafi da zugin da kaina yakeyi. Ba bata lkc zazzabi ya rufeni wanda ko hannuna bana iya dagawa. Cikin ikon Allah zazzabin ya sauka sai dai kan ne da har lkcn yake sarawa. Agogon dake bedside drower na kalla wanda ya nuna 12:04 Lallabawa nayi na kashi dan ko sallar asuba ban samu nayi ba. To nida na kwanta a kujera waye ya kawoni gado?tunanin da nakeyi kenan ina fitowa daga bedroom din. Yana zaune a qasan rugs yana danna computer tare da kurbar wani abu a kofi. Kallo daya nayi masa na dauke kaina dan babu riga a jikinsa,daga shi sai sai gajeren wando. Wani haushi da tsanarsa ce ta qara huruwa a raina,dan ba makawa tsanar da yakemin ta ninka wanda nake masa. Zo nan" Yi nayi kamar banjishi ba nayi ficewata. Mubina har lkcn bacci take,dan haka wanka nayo da brush,kafin na gabatar da sallah. Akan sallayar na kwanta cikin qanqanin lkc bacci ya daukeni. Sai 2 na harka inda nayi alwala na gabatar da sallar azahar don lkcn mubina bata dakin. Gadon na hau ina shirin kwanciya ta shigo. Sannu matar broh ashe kin tashi"tace tana qarasowa inda nake. Ya jikin?"tace tana dafa goshina. Waya fada mk banda lpy?"nace ina kallonta. Hararar wasa tayi min. Tun dazu ai mijinki yazo ya tasheni,wai na hada breakfast baki da lpy,to tun dazu na gama yace karna tasheki na bari ki tashi da kanki wai baki samu kinyi bacci da dare ba" Munafikin Allah ta'ala! Na fada ina qara jaddada kwarewarsa wajen iya Tsara zance. Ki tashi muje kiyi breakfast don amanarki ya bani yace inda hali ko quda karna bari ya tabaki,baki gani ba duk ya damu daqar ya fita ma" Takaici bai barni nayi mgn ba.jin ya fita yasa natashi muka fita nayi b/fast din. Magani ta kwaso wai yace idan na tashi ta bani nasha.haka na karba nasha dan nasan ni kaina ina buqatar mgnin. Falon muka fita inda ta dauki wayata wai tana buden watsap. Nida ba contact ba ai bazanji dadin watsap din ba"nace ina dora kaina a kan cinyarta. Yanxu kuwa zakiyi contact yammata,dan har grp zan sakaki na matan aure,kinsan muma mun kusa shiga daga ciki sai kana leqa irin wadannan grps din kana koyon abubuwa,harna hausa novels ma" To ni inaga lkcn karatun novels mubina?" Duk da haka dai zan sakaki,idan kin sallami mijinki da yaranki ai saiki ringa karantawa" Nidai shiru nayi mata. Wai naga number din aunty anisa ce kawai a ciki kota ya abdul babu"tace tana kallona. Sabon sim ne,wancen daddynsu shahid ya kwace tun farkon xuwa na"nayi mata qarya don bansan mezance mata ba,dan ko number iyayena da yayyena ai a gani a wayar. Wlh ya burgeni,shiyasa nake qarason broh sbd ya iya tattalin mace,muma allah yasa mazajenmu irinshi ne" Murmushi nayi kawai. Wai har yanxu daddyn shahid kk fada masa?gsky ya kamata ki canja masa suna kinsan yayan namu dan soyayya ne,bakiga har wani jan sunanki yake ba wai nernahh" Dariya kawai nayi. Allah da gsk khadija kidan samo masa irin sunan soyayyar nan,bakiji aunty fatima hayaty take ce masa ba?koni da bamuyi aure da fahad ba Baby nake ce masa" Sosai ta bani dariya. Wai yaushe ne wannan bikin ne?"nace ina dariya. Saura 2 months" Kice zamusha biki" Sosai ma" Duka muka dago muna amsa sallamarsa. A hankali na koma na kwanta inda mubina tace. Broh mantuwa kayi ne?" Aa mubina,kawai dai na kasa nutsuwa ne kinsan nabar nernah ba lpy shiyasa na haqura da meeting din kawai"yace yana tsugunnawa tare da dafa goshi na. Nernahna ya jikin naki?"yace yana langwabar da kai kamar qaramin yaro. Mai karatu idan ke ce wace irin amsa zaki bashiโ“โ“ A kafta! Yawan comment yawan posting๐Ÿ˜‰ : ๐Ÿ’™๐Ÿ’™RABON KWADO๐Ÿ’™๐Ÿ’™ Er mutan ungogo๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ ๐Ÿ…ฟ116-๐Ÿ…ฟ120 Shiru kawai nayi batare dana ce komai ba. Mubina taci abincin kuwa?"yace yana kallon mubina har lkcn hannunsa na goshina. Taci amma kadan,har magani na bata" That's gud"yace yana dawo da kallonsa kaina. Kimin mgn mana soulmate kona samu na koma office,aiki ne dani sosai na baroshi na dawo duk sbd ke,amma ko swt voice din ma baza'a barni naji ba?"yace kamar abin tausayi. Hada ido mukayi da mubina inda tayi min mgn da ido,duk da ban gane mai tace ba nasan tanaso nayi mgn ne. Nifa naji sauqi kawai dai banajin qarfin jikina ne"nace ina qasa da idona dan ya zubamin idonunsa masu kama dana mage. To ko asibiti zamuje?nifa wannan zazzabin daren ya fara damuna nernah,gashi sai wata rama kikeyi wani sai yayi zaton bana baki kulawa ne"yace yana satar kallon mubina. Wlh munafiki ma wutarshi daban take"na ayyana a raina. Gsky yaya kawai kuje asibitin,ka sani ma ko za'a yiwa su iman qani ne?"tace tana dariya. A tare muka kalli juna inda nayi saurin dauke idona. Wai ita wannan bakinta baya tantance mgnr da zai ringa fada ne?ko duk cikin shirin aunty anisa ne dan tace zasuyi waya da mubina? Wai haka nernah?"yace yana shafan kumatu. Yaqe kawai nayi. Hhhh ai yaya ita ta sani akwai kawai dai bazata fada bane,barima na kira ummi dan na riga kowa samun gift wlh"tace tanayin dakina da gudu. Nashi uku๐Ÿ™†๐Ÿป๐Ÿ™†๐Ÿปmubina nada hankali kuwa? Hancina daya ja yasa nayi saurin dagowa. Fuskarsa a hade ya zubamin ido. idan ma keci kk sanar da ita wannan shirmen ki gaggauta fada mata ba haka bane,idan kuwa kika bari ummi taji zaki gane kuskuran da kk aikata" Nifa ba abinda na fada mata"nace kaina a qasa. Kedai kk..... Eh wlh ummi gata ma"muka jiyo muryar mubina tana qarasowa. A kunne ta kara min wayar inda najiyo amon muryar ummi. Cikin ladabi na gaida ita,ta amsa cikin sakin fuska. Yanxu nakejin abin farin ciki wajen mubina,to allah ya raba lpy kuma ki kula sosai kinji?,da zuwa gobe nace za'a dawo da yaran amma za'a barsu zuwa wani lkc kafin ki qara warwarewa" Tom ummi ngd"na fada kaina a daure ga wani kallo da daddynsu shahid yake jipana dashi. Ina baban nawa mubina tace kuna tare?"ummi tace. Eh ummi gashi nace ina miqa masa wayar. Tashi yayi ya nufi bangarenshi,suna mgn da ummin. Maida kallona nayi kan mubina. Yanxu dan allah ke waya fada miki ciki ne dani da zaki fara yadawa mutane?to ko cikin ne dani sai ki fara buga waya kina fada?"nace ina hade rai. Hhhh lallai ma ke dinnan,to ki rantse ba cikine dake ba.ni kinga burina ya cika ummi tace naje company na zabi mota dama abinda nakeso kenan dan na qagu na fara driving da kaina dama mijinki ne ya hana mu"tace tana tsallen murna ita ko a jikinta. Takaici yasa ya tashi nayi daki dan wani qululu nakeji a zcytah,gashi shi wancan mutumin ya dauka ko sanshi nake dazanje na fadawa wani ciki ne dani.allah ma ya rabani da daukan cikinsa๐Ÿ˜”. Shiga ta daki yayi dai dai da qarar wayata dake ajiye akan mirrow. "Sis mufyderh" naga yana yawo akan screen din,wanda ba makawa na gano mufida ce dan nafi zaton mubina ce tasa min number din. Hello momyn twins"najiyo muryarta. Wayyo allah wlh mubina ta gama cuta ta. Ko cikinne ya fara hanaki mgn?"na qara jiyota,keda kinji kinsan cikin nishadi take mgn. Wai waya fada miki ciki ne dani" Hhh radio mai jinin gidanki mana,ni kinga ma hada kaya nake dan nima tahowa zanyi ayi rainon cikin nan dani kafin hutun semester ya qare" To allah ya kawo ki"nace ina ajiye wayar dan da alama qaramin ciwon kan xasuyi idan suka hadu. "Aunty anisa" Shine sunan daya qara shigowa cikin wayar. Jikina a salube na daga tare da sallama. Aunty khadija manyan qasa"tace bayan ta amsa sallamar. Aunty kinga mubina sai yadani take wai ciki gareni"nace kamar zanyi kuka. Dariya ta saka. Ai ni wlh ta burgeni,wannan ma wata hanya ce mai kyau" Kenan aunty da hadin bakinki?"nace da mamaki. Ko kadan khadija,kindai sai halin mubina ni bama muyi wannan xancen da ita ba" To ki fadawa ummi wlh qarya take kinsan dai ba'a shan ciki a ruwa" Hhhhh naqi din,ni yanxu ma jinake kamar nayi tsuntsuwa nazo,dan ummi bata dauki zancen cikin nan da wasa ba,yadda kikasan bata taba jika ba,dan ko cikin shahid bancen tayi irin wannan murnar ba dan nima itace ta kirani ta fada min yanxu" Wayyo ni,to yanxu aunty ya za'ayi?" Ki bari zuwa next week insha allah zanzo dama akwai wasu shirye shirye da nakeyi miki" Tom aunty Allah ya kawoki" [07-26, 11:04] Cwt-besty: ๐Ÿ’™๐Ÿ’™RABON KWADO....๐Ÿ’™๐Ÿ’™ Er mutan ungogo๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ ๐Ÿ…ฟ121-๐Ÿ…ฟ125 Duk yadda mubina tayi dani qin fita falon nayi duk da ta tabbatar min ya koma office. Tasani tayi a gaba da tsokana kala kala,nidai gyaleta nayi dan naga abin nata ba mai qarewa bane. Sai yamma mufidat tazo,inda suka hadu suka maida ni kamar wata kakarsu. Dan allah ku qyaleni,wlh qaramun ciwon kai kuke yi"nace cikin qosawa. Kinga sis qyaleta kar wannan mijin nata ya dawo ta hadamu dashi"mubina ta fada. To na bari dan yadda yake dokin cikin nan zai iya yin komai a kanshi" Wai ciki.su sai zuzuta abinda babu shi sukeyi,kuma babu ranar samunshi. Mai ciki me kk so mu dafa miki kar broh ya dawo yace mun barki da yunwa"mubina tace. Ni ki barni idan zanci zanje da kaina na dafa" Ai tunda kika samu ciki ko tsinke bazaki kuma daukewa ba bare shiga kitchen.yanxu ki kwanta ki huta kafin muyi miki farfesun kifi kici ko?"tace tana jan kumatuna. Ni banajin bacci"nace ina turo baki. Hhh kema mijin naki ya koya miki shagwabar kenan?ke mufida bakiga soyayya a gidan nan ba,ai daukar course kawai nake,dan bakiga yadda yaya yake wani narke mata ba yadda kikasan qaramin yaro,ashe duk shagwabar da yakeyiwa ummi nafila ce"mubina tace. Wayyo kice kallo ya barni" Ai kuwa dai" Ganin bazasu barni ba yasa na kwanta na rufe ido kamar bacci nakeyi har suka gaji kowa ya kama gabansa. Yau maigidan bai dawo da wuri ba dan har 10 bai shigo ba. Dan hk abinci muka ci dukanmu a flat daya kafin muka dawo falo ko wacce ta dauki waya tana chat.nidai a kwance nake kawai,dan har lkc kaina yana dan min ciwo. Kawai mafita nake nema dan banaso na kuma kwana a part dinshi,amma bansan wace hanya zan bi na kaucewa hakan ba.gashi yau harda mufida nasan banida hanyar dazan kare kaina. Vibrating din da wayata takeyi yasa na janyota,ganin aunty anisa yasa nayi picking mukasha hira. Aunty anisa akwai mgn fa,kuma ga yan biyun ummi sun tasani a gaba"nace ina dry dan ganin duk sun kalloni. Sai ki tafi daki ai,badai mgnr matan aure ce ba?muma dai mun kusa shigowa daga ciki ehe"mubina tace Ina dariya na tashi nayi daki dan duk abinda tace anty anisa na jiyota dan itama dariyar takeyi. Inajinki khadija ya akai?" Aunty mgnr cikin nan ce dai,ni wlh banaso anayinta kuma kinga har ummi ta dauka da gsk ne"nace ina kwanciya a kan gadon. Kinga kibar mgnr nan plzz,shi broh din ma dazu na kirashi domin nayi masa congrts dan banaso ya fahimci nasan wani abu game daku. To shine yake fada min ummi ta baki mota shi kuma yace mata ta barta tunda ba wani guri kk zuwa ba,kuma idan zaku fita akwai driver,idan ma kina buqatar motar zai baki qarama,amma ummi taqi wai wannan kyautarta ce" Haka ne gsky a yanxu bana buqatar mota aunty"nace ina qara lafewa a kan gadon. Duk da haka nace a karbo miki tunda kyautar surukarki ce sbd samar mata jika da akayi"tace tana dry. Kema tsokanar tawa zaki yi?"nace a shagwabe. Dariya ta cigaba. Yawwa aunty,kinga Jiya da mubina tazo a part dinshi na kwana,kuma ni yau banaso na kwana a can" Sbd me?" Aunty Allah bayaso na kuma...." Ya isa khadija,wannan tsakaninki da mijinki ne ba komai zakina fada min ba kinji?hk zaki daure ki ringa zuwa kina kwana,hakan zai qara muku kusanci da kuma sabawa da juna.ki tashi kiyi shirin bacci,akwai wata farar sleeping dress a cikin kayan nan ki sakata kije wajen mijinki,bayasonki ba hujja bace ba" Aunty allah bazan iya ba"na fada kamar nayi kuka,dan da gsk bazan iya din ba,domin da rigarnan gwara babu.kuma shi zai fassarani da wani abu tunda jiya yace min bakin rijiya ba wajen wasan yara bane,ko yana tunanin wani abu naje nema oho,bare ya ganni da wannan shigar saiyafi wulaqanta ni. To shikenan khadija,kita fadar bazaki iya ba kinji?"tace tare da kashe wayar. Fishi tayi kenan?wai meyasa kowa ya gaza fahimta tane?ita danake samun dan sassauci a gareta yau dinma ta gaza fuskanta ta. Allah kasan halin danake ciki ka sassauta min. Tunane tunane na shigayi,wanda tsahon lkc ban samu wata mafita ba. Mufida ce tazo ta tabani. Matar broh wai bacci kikeyi?" Dagowa nayi"Aa nadai kwanta ne. Kije wajen broh dan yana cikin damuwa sosai"tace itama da damuwa kwance a fuskarta. Damuwa kuma?ya dawo dama?"na jera mata tmbyoyi. Tun dazu ya shigo,kukama naga kamar yanayi,kuma nasan bazai rasa nasaba da company din motors dinmu ba,nasan shi kadai yake iya karya zcyr ya abdul,dan family din Abbanmu sun sakawa company din nan ido khadija,kuma wlh dashi kawai muka tsira"nace tare da fashewa da kuka. Rasa wani tunani xanyi don haka na shiga rarrashinta tare da bata baki,don a kalamanta na fara gano wasu abubuwa. Daqar tayi shiru inda muka fito falon jikina duk yayi sanyi. Kwance yake a qasan rug inda yayi matashi da cinyar mubina. Nidai gefe nayi na zauna ina nazarinsu daya bayan daya danshi idanunsa a lumshe suke. To yanxu broh ka sanarwa da ummi?"mubina tace. Banason ummi taji wannan mgnr kwata kwata,kunsan ummi da saka abu a ranta nasan zatafi kowa shiga damuwa" Amma yaya haka zamu zuba musu ido suna ja mana asara a company?"mufida tace. Ganin da nayi mgnr kamar tasuce suda family dinsu hakan yasa na miqe domin basu waje. Ina zakije?"na tsinkayo muryarsa. Cak na tsaya dan bansan amsar dazan bashi ba. Mufida kuje ku kwanta dare yayi,tea din nernarh ta dafa min"ya fada yana tashi zaune. Saida safe sukai masa kafin suka wuce amma kana kallonsu kasan da akwai damuwa a ransu. Lkc daya naji tausayinsu ya kamani duk da bansan gundarin damuwarsu ba amma na fuskanta daga bangaren mahaifinsu ne. To wai duk dangin mahaifine haka?tunda gashi muma bama ga maciji da namu dangin mahaifin.to su ina nasu mahaifinma? A yimin afuwa na rashin jina kwana biyu.Ngd [07-26, 15:28] Cwt-besty: ๐Ÿ’™๐Ÿ’™RABON KWADO...๐Ÿ’™๐Ÿ’™ Er mutan ungogo๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ ๐Ÿ…ฟ126-๐Ÿ…ฟ130 Ina tsaye kamar an dasa ni naji an kama hannuna. Juyowa nayi ina binshi da kallo. Baiyi mgn ba illa jan hannuna da yayi zuwa part dinshi. Binshi kawai nake kamar jela tare da faduwar gaba dan bansan abinda kuma zaiyi min ba. Zama nayi kamar yadda naga ya zauna a daya daga cikin kujerun falon kaina a qasa. Inda na zubawa hannuwanmu da har lkcn suna hade ido inda farar fatar hannunshi da baqin gashi yayi mata qawanya ta hadu da tawa baqar fatar. Zan iya samun koda tea ne dan tun safe banci komai ba"yace yana shafa cikinsa da daya hannun. Saida na kalleshi dan tabbatar da cewa shine yayi mgn,domin ban zaci hakan ba dan da wata tattausar murya yayi min mgn. Ganin ya zuban ido yasa nayi qoqarin tashi amma still yana riqe da hannuna. Da naga bashi da niyyar sakina yasa na fara qoqarin kwace hannun sannan ya sakeni. Kitchen din naje na hado masa tea dan iyayi na harda soya masa kwai dan naji yace tun safe baici komai ba kuma nasan tea kawai bazai daukeshi ba. Yana zaune inda na barshi,sai dai yanxu ya cire rigar jikinsa inda ya jingina da bayan kujera tare da lumshe ido. Tausayinsa naji yana shiga ta,don nasan ba qaramin abune zai sakashi yin la'asar haka ba,tunda gashi nima naci albarkacin hakan. Dora qaramin plat din hannuna nayi a qaramin glass din dake gefen kujerar. Ga tea din"nace ina satar kallonshi,don duk sai naji ni a takure sbd cire rigar da yayi. Tnks"ya fada tare da daukan cup din ya fara kurba. Har na shiga yiwa kaina allah ya qara ganin bai kula soyayyan kwan ba,sai kuma naga ya fara ci. Kije ki kwanta dare yayi fa"yace yana qara gutsirar kwan. Tashi nayi na nufi waje dan nasan zuwa yanxu su mubina sunyi bacci saina kwanta acan gashi kuma banyi wanka ba bare na saka kayan bacci. Ina kuma zakije?" Tsayawa nayi ina harhado amsar da zan bashi. Zan zanje nayi wanka ne"nace ba tare dana juyo ba. Bathroom din nan baiyi miki bane?"yace. Aa babu...uhmm ban dauko kaya bane"nace muryata na shaking. Zoki wuce kiyi anan" Da sauri na juyo na kalleshi,amma abin mamaki shi abincinsa yake ci kamar ba dashi nayi mgn ba. Ban iya musu ba,dan haka na wuce ina tunanin wani daki zan shiga. Juyowa nayi ko zai ganni a tsaye ya nunamin amma naga shi hankalinsa ma baya kaina. Qofar hannuna na dama na nufa tare da budewa na shiga. Tabbas wannan ba dakin dana kwana jiya bane amma ya hadu shima sosai kuma zai iya amsa sunan bedroom tunda akwai gado a ciki. Ganin ba dakinshi na shigo ba hakan yasa na saki jiki.na shiga wanka na hankali kwance. Saurin komawa nayi dan ganinshi zaune akan sofa yana danna waya. Na dade a tsaye a bandakin kafin na qara leqowa amma naga wayam. Ko meya kawoshi nan bacin ga dakinsa can?"nace ina turo baki kamar yana ganina. Zaman dirshan nayi akan kujerar mirrow ina shafa cream din dana gani jere akan mirrow din. Saida na kammala kafin na bi duk turarukan kan mirrow din na fesa a jikina tare da sakin murmushi,dan inason qamshi sosai. Hannu nakai kan kayan dana gani a kan gadon. Jiga da wando ne kalar red masu laushi.Ai kuwa na zira tare da kashe light nabi lpyr bed. A hankali na bude idona inda suka sauka a kanshi,yana sanye da milk din jallabiya mai qaramin hannu. Idan zakiyi sallah ki tashi"yace yana jan bargon dana rufa. Idan zanyi sallah?kodai ya gane bana sallah ne?wayyo allah. Miqewa nayi ba shiri ina tattare dan gashina daya barbazu dan jiya ba shiri na tsefe kan sbd ciwo. Toilet din na shige na barshi a wajen.dana fito baya dakin dan haka na qara kwanciya dan naji dadi daya fita. Aunty!Aunty ki tashi mun dawo"kamar a mafarki naji ana fada ina bude ido naga iman. Oyoyo"nace ina bude mata hannu inda ta fado jikina tana dariya. Aunty tun dazu muka zo daddy yace kina bacci,shine grandy tace wai zaki haifa mana baby mai kyau koh?" Murmushi nayi. Ita grandy dince tace hk?" Eh kuma dama frndz dina a scul duk suna da baby a gidansu" To ai kece babynmu anan gidan" shigowarsa yasa ta tashi da gudu tayi hugging dinsa. Daddy wai aunty tace zata haifa mana baby mai kyau,nima nacewa frndx dina muna da baby a gidanmu" Riqe hannunta yayi kafin su qaraso. Kice mun kusa yin baby koh amminah?"yace yana zama a gefen gado. [07-26, 19:42] Cwt-besty: ๐Ÿ’™๐Ÿ’™RABON KWADO...๐Ÿ’™๐Ÿ’™ Er mutanen ungogo๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ ๐Ÿ…ฟ131-๐Ÿ…ฟ135 Eh daddy kuma zan ringa goyata kullum koh?" To idan Amminah bata goyata ba waye zai goyata?"yace yana jan habarta. Murna take sosai inda ya dawo da kallonsa kaina. Kiyi qoqarin kawo baby nan sbd kowa ya huta,domin ga kakarsa can ma ta doko sammako dan taga lpyr jikanta" Lallai ma mutumin nan.na fada a raina. Hade rai nayi na ciri mayafin kan iman na daura a kaina kafin na tashi na bar musu dakin. inaji suka biyoni a baya nidai na fito inda na samu ummi dasu mufida duka a falon. Shahida ce ta taso da gudu inda shahid ya tsaya yana murmushi. Aunty ina babyn da zaki haifa mana?" Duka suka saka dariya,nidai janyeta nayi daga jikina na qarasa na kwashi gaisuwa a wajen ummi. Sai kika gammu da sassafe,wlh fitinar yaran nan yawa ne da ita ko b/fast ba'ayi ba aka dameni baby baby nidai nace a zo muje a ga wannan baby a huta" Murmushi kawai nayi. Ganin anata hira yasa na tashi naje nayi wanka na shirya kafin na fito mu fara shirin abun karyawa duk da lkc 11 ta wuce. A saman dinning aka hadu kowa da kowa ana cin abinci,inda gogan naku ya kafa ya tsare sai wani nan nan yake dani kamar gsk,nidai kunyar ummi da yaransa duk ta cikani,dan danayi sakema abinci a baki zai bani. Duk na takura sai wani shigemin yake yana kashe min murya. Saida ummi ta kammala ta tashi kafin nadan fara sakewa. To surukar taki ta tashi sai ki bude baki kice abinci"yace yana kawon kofin tea wajen bakina. Nifa na qoshi"nace kamar na fasa ihu. Broh kawai ka barta kasan su masu ciki ba komai sukeson ci ba,kawai ka tmbyta avinda take son ci"mubina uwar tsari tace. Shikenan me kk so kici?"yace yana riqoni Ni babu komai"nace ina tashi daga wajen. Parlou din na koma na zauna muna dan taba hira da ummi. Shiya fara dawowa falon inda ba kunya yaje ya kwanta a jikin ummi. Tashi fa zakayi babanah dan mu tfy zamuyi,kana girma wannan dabi'ar ta son jiki taqi tabarka" Ummi idan banyi miki ba wai wazanje nayiwa?kuma kinsan kedin kawai nake iya yiwa"yace yana qara kwanciya. Naji tattaromin yaran nan mu wuce rana tana qatayi." Mudai bazamu biki ba gsky"shahid yace yana kwabe baki wanda qarasowarshi kenan. Ai kuwa saikun bini dan bazaku takuramin yarinya ba" Ummi kawai ki barsu ai naji sauqi"nace kaina a qasa. Kuma ummi gasu mufida zasu ringa kulawa dasu"ya fada. To ai shikenan tunda yaranku kukeso nima sauqina ne naji shiru kwana biyu"tace tana tureshi tare da miqewa. Duka mukayi mata rakayi har bakin mota,saida driver ya fitar dasu kafin mu dawo ciki. Mgn ce dai guda daya akan cikin da babushi sukai tayi shi kuwa sai biye musu yakeyi,idan yasan ya fadi abinda ba haka bane saiya kalloni tare da kashen ido. Sosai a jiya zuwa yau lamuransa suke bani mamaki dan idan yayi wani abun kamar ba shi ba.Gashi duk wannan budirin da ake yana maqale dani kamar za'a kwace masa ni.๐Ÿ’™๐Ÿ’™RABON KWADO....๐Ÿ’™๐Ÿ’™ Er mutan ungogo๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ˜Š๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ ๐Ÿ…ฟ136-๐Ÿ…ฟ140 Ta qarfin tsiya su mufida suka hana su shahid kirana da aunty sai dai mommy. Tun inajin kunya da nauyin amsawa har nazo ina amsawa,shi kanshi gogan naku ya goyi bayan haka. Wata irin kulawa nake samu ta musamman daga gareshi wadda na kasa tantance ta gsky ce ko kuwa shirin film ne. Yanxu ko mu kadai ne a guri wannan kulawar tananan,yaita wani nan nan dani,ni kuwa na samu waje sai shagwaba,muyita narkewa juna dan shi kanshi zakusha mamakin yadda yake sakin jiki yaita shagwaba,ni wani lkcn ma dariya yake bani wlh. Tun inajin nauyi idan yanayi a gaban yaransa har na fahimci su basa daukar haka a wani abu maybe sun saba ganinshi yanayi ne. Ta bangaren aunty anisa ma sosai take bani gudummawa sai dai abubawa da dama bana iya aikatawa dan banason na wuce gona da iri ko yaga gajen hqr na. Yau tun yamma ciwon mara yake damuna dan hk walwalata qalilance,kawai dai ina daurewa ne domin idan ya tayar min baya min da sauqi. shahida sai dira suke a kaina,tun ina juriya har take na turo su dama akan 3seater nake a kwance da tsautsayi iman da bige baki da jikin kujera bakinta ya fara jini. Sosai na shiga damuwa muka hadu dasu mubina muna aikin rarrashi tunda shi tun safe ya fita wai yayi baqi a company din motar su. Ganin taqi shiru yasa na goyata duk da azabar ciwon dake damuna har na samu tayi bacci. Kafin ta tashi kuwa baki ya kumbura,shi kuma yana dawowa shahida ta sanar masa na fasawa iman baki. Haka ya rufe ido ya dawo asalin daddyn shahid dinsa. Tun su mubina suna bashi hqr har suka gaji sukai shiru domin kadan ne ya rage bai mari mufida ba da tana mayar masa da abinda ya faru. Nidai banda kuka ba abinda nakeyi,dan haka yace so nake na kashe masa yara tunda na qona shahid yanxu kuma na fasawa iman baki. Saida yayi mai isarsa kafin yaja yaransa zukayi part dinsa. Rarrashina su mubina suka shigayi nidai kukana na cigaba.saida na gaji dan kaina nayi shiru. Tsit gidan yayi kamar ba wasu halittu a ciki,dan har lkc suna part dinshi su kuma su mufida sun tasani a gaba sunyi jugum jugum. Sister ki tashi mu fara shirya kayanmu dan gobe zamu tafi,dan yaga munxo gidanshi shine zai ringa yi mana fada"mubina tace tana nufar inda kayansu yake. A hankali na miqe ina roqonsu da karsu tafi amma mubina tahauni da fada. "Ai duk laifinki ne da kk bari yana miki duk abinda yaga dama,ni wlh miji bai isa duk shirginsa ya kwaso ya doramin ba,bacin kema yaran nan nakine,ki gama wahala dasu sai dan rana daya an samu matsala za'a nuna miki iyakarki" Haka taita bambami kamar ta ari baki mudai kallonta kawai muke. Har washegari mita takeyi,daqar ta yadda muka hada b/fast dan tana idar da sallah tayi wanka tayi shirin tpy. Muna zaune akan dinning ya fito da yaransa biye dashi. Mufida ce kawai ta gaidashi ita daya kusa marin ma,amma mubina kicin kicin tayi ko kallonsu batai ba. Nima kallo daya nayi musu naci gaba da jujjuya abincina dan tun dazu na gagara ci. Tun safe nake jina wata inconculusive jina nake kamar ina missing wani abu amma na rasa ko menene shi. Ciki ciki ya amsa gaisuwar yace taje ta canja musu kaya dan inaga da kanshi yayi musu wanka.ni dama haka yakeyi daya ragemin wata wahalar. Falo ya koma tare da kwalawa mubina kira. Qasa qasa yake mgn dan hk banajin abinda yake cewa kuma nima ban damu da naji din ba tunda ba abinda ya shafeni bane. Tattare kwanikan na farayi dan na kasa cin abinci tea din dai na dan kurba. Tare suka fito da mufida inda ta tarkato kansu sukazo suka tsaya a kusa dani. Mommy kiyi hqr"suka fada a tare. Murmushi kawai nayi. Ai bakuyimin laifi ba yaya shahid,zo nan baby naga bakin"nace ina miqawa iman hannu. Mommy yanxuma ya daina min zafi,daddy ya sakamin mgn"tace tana riqeni. Nima bari nayi miki addu'a sai ya kuma warkewa ko?" Daga kai tayi,sannan nayi mata addu'a. Hada musu abincin nayi ina basu a baki muna hirarmu kamar ba abinda ya faru. Sis ki kaiwa yaya abincin mana"mufida ta fada. Wlh baza'a kai masa ba,yayi mata laifi sannan itace zata bishi,kar kiyi masa mgn indai baiyi miki ba"mubina tace tana zama. Nidai cigaba da abinda nakeyi nayi,duk da inaso na kaimasa abincin dan nasan yanxu yanajin yunwa๐Ÿ™ Idan baki tashi tsaye ba wlh abinda zaiyi miki nan gaba saiya fi haka,dan yaja miki raini ma a gaban yara zai ringa yi miki fada"mubina ta cigaba. Ganin yaran suna kallonta yasa nayi mata alama da ido tayi shiru. Sannan ta juya akalar zancen. Wai sister kinji roqona yake karmu tafi yau sbd ummi zata dauka wani abun ne tunda tasan ba yanxu zamu koma ba"tace tana kallon mufida. Dama ba kece ba wai dole sai mun tafi ni dama ban shirya komawa da wuri haka ba,dan horo nake bawa Abbas" ai mazan ne saida horo"tace tana tabe baki. Mubina kenan mutuniyata,wai kece babba ne"nace ina dariya. Wlh nice babba amma idan tanamin wani abu saiki dauka haifata tayi"mufida tace. Ai kin fita sauqin kai da hqr"na kuma fada. Mantawa kikayi ni fetir ce" Hk muka cigaba da hira munashan dry amma rabin hankalina duk yana kan duk wani motsinsa,duk da ba gano fuskarsa nakeyi sosai ba. Da wannan leqen ai da wajenshi kk je"mubina data gama ganoni ta rada min a kunne. Murmushi nayi dan da gsk inason zuwa wajenshi amma bansan mezan fada masa ba๐Ÿ™ Mufida ya kuma kwalawa kira. Allah sarki wlh yunwa yakeji wai dan allah na samar masa tea"mufida tace bayan ta dawo. Tausayinsa naji a raina,to wai dacan a ina yake cin abinci? Wlh karki biyewa mubina taita zugaki kiqi yiwa mijinki biyayya,ki tashi kije ki kula dashi"mufida tace. Nidai tea din na hada na barsu sunata yi kamar zasu cinye juna. A hankali na samu gefensa na zauna tare da sallama a baki na. Ciki ciki ya amsa dan dabadan bakinsa danake kallo ba bazansan ya amsa ba. Ya abdul ga tea din"na tsinci kaina da fada. Ture laptop din gabanshi yayi kafin ya kalleni. Nace inaso ki kawon tea ne?"yace still yana kallo na. Shiru nayi jikina duk yayi sanyi. Nernah" Har raina naji sunan,har hakan tasa na kasa amsawa sai kallonshi da nayi kamar yadda yake kallona. Miqon hannu yayi,ba musu naje tare da shigewa jikinsa. A tare muka sauke ajiyar zcy,na qara lafewa a jikinsa. Bazaki iya ba koh?bazaki iya kulawa dani da yarana ba na kawo wata koh?" Da sauri na bude ido dan da na lumshesu sbd rada yakemin a kunne. Nasan bazaki iya ba dama,sbd kinyi qanqanta da yawa,kawai dai bazan iya qin jinin fatima bane,kuma kinsan wani abu?" A hankali na girgiza kai. Wasu lokutan kina min kama da fatima.lokuta da dama kuma idan na tuno alaqarku da ita sai naga kamar naci amanarta,har yanxu fatima kawai nakeso nernah,duk da nasan bazata dawo gareni ba" Shiru dukkan mu mukayi inda numfashinsa a hankali yake sauka cikin kunne na. Ni kuwa babu kalmar dakemin tawo sai"har yanxu fatima kawai nake so!!" Fatima ta dabance na sani,shiyasa na bata kaina da zcytah,amma allah daya fini sonta ya karbi abarsa"ya cigaba. Fatima...... Bansan lkcn da na fizge daga riqon da yayi min ba,ban jira komai ba nayi daki da gudu,na kifa kai tare da saka kuka. To kukan me nakeyi?mai zaisa na damu dan yana yabon matarsa? bacin nasan dama can yana sonta? Ku biyu ni sannu a hankali dan samun cikakkiyar amsar tmbyoyin. Khayratie๐Ÿ’‹๐Ÿ’™๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’™๐Ÿ’™RABON KWADO....๐Ÿ’™๐Ÿ’™ Er mutan ungogo๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ ๐Ÿ…ฟ141-๐Ÿ…ฟ145. Kuka nake sosai wanda zaka iya dauka dukana akayi ko wani abun daban. Ni kaina bansan dalilin kukan ba,kawai dai nasan raina ya baci da jin kalamansa. To meyasa raina zai baci?tmbyr da nake yiwa kaina kenan.Daidai lkcn naji an zauna a gefe na. Koda ban dago ba qamshinsa ya tabbatar min shine. Zuwa yanxu ya kamata mu sabarwa kanmu da rashin fatima,duk da nima duk dare nakanyi kukan rashinta.Na sani fatima tana da kirkin da za'a dauki lkc kafin mutum ya manta da ita,kuma banyi zaton wannan mgnr zata saka ki dawo da mutuwar fatima sabuwa ba" Ya ilahi!!๐Ÿคฆ๐Ÿปโ€โ™€Fatima!Fatima!!Fatima!!komai fatima?Waya fada masa mutuwa ce yanxu tasa nake kuka?to idan ba mutuwar ba mezaisa nayi kuka?mutuwarce ma kawai ta sakani kukan.Na raya a raina. Dukkansu suka shigo suka tsaya mufida na tmbyr me akayimin don ina tunanin sunga lkcn danayo daki da gudu. Kuje kawai ba abinda ya sameta kawai rigima ce irinta nernah"ya fada yana janyoni jikinsa. A hankali yake busa min iska cikin kunne na,hakan yasa nayi shiru ina sauke ajiyar zcy Har bansan lkcn da bacci ya daukeni ba. Dana farka ni kadaice a bedroom din,don haka wanka nayi na shirya cikin wata doguwar rigar atamfa. Mai kawai na murza dan har lkcn banajin dadin jikina kuma bazance taqamaimai ga abinda ke damuna ba. Mubina ce da iman kawai wai sauran sun fita zasuyo shopping sbd gobe zasuyi resuming school. Wayata na dauka nahau watsap inda na fara krtnta wani novel a wani grp,duk da ba wani fahimta nake ba amma novel din da alama zaiyi dadi da ma'ana. Sai daf da magriba suka dawo,saida kowa ya gabatar da sallah sannan aka baje kayan da suka siyo suna duddubawa. Nidai ina maqele da hannunshi tun lkcn da suka dawo a masallaci shi da shahid ya riqoni. Yaya ya kamata pa a fara siyan kayan baby tun yanxu"mubina tace. Nidai kishingida nayi a jikinsa inajin yadda yake murza hannuna a hankali. Waya fada miki anan zamu sayi kayan baby?zuwa end of dis month nake saka ran tpy Dubai,acan zan fara hado kayan" Inajinsu sunata hira akan tpyr tasa nidai bance komai ba hasalima idona a lumshe yake dan haka kawai sai naji banaso ya tafi. Yaya gaskiya babyn nan yana wahalar da sister,ni gani nakema rama yake sakata"mufida tace. Banji yayi mgn ba sai jin hannunsa nayi akan fuskata. Karkiyi bacci mana bakici abinci ba"ya fada bayan na bude ido. Yaya ko Lunch din da mukayi ma bata ci ba wlh"inji mubina. Aa banason rashin cin abinci kin sani,tashi muje kici abinci" A baki ya ringa bani ina amshewa,nidai satar kallonsa nake inajin wasu abubuwa game dashi,dan kwana biyun nan bana gajiya da kallonsa,duk da banayi ta yadda zaisan shi nake kallo. Kwana biyu kin rage walwala nernah kuma kowa cewa yake kin rame,ki fada min damuwarki,kinga ni yayanki ne kuma amanarki Abbi ya bani,banaso ace na gaza wajen kulawa dake" Qaramin bakinsa kawai na zubawa ido ta yadda yake shiryo zance. Da can mantawa yayi da amanar yake gasa min aya a hannu? Ki fadamin mana kinji nernarhnah" Inason ganinsu ammi ne"na fada dan kawar da zargi. Murmushi yayi"kinga kuwa indai mukayi waya sai tace na gaishe da auta kawai fada miki ne banayi dan nasan rigimarki" Ya abdul da gsk?dan allah ka kiramin ita yanxu"nace ina miqewa. Sai kina cin abinci kuma kinyi qiba sannan,har gida zan kai ki sannan muje gidansu ya aisha" Haka ya ringa ja min rai har nayi zcy nayi tapiyata daki. Shirin bacci nayi duk da ba bacci nakeji ba. Wayata na janyo tare da dannawa aunty anisa kira. Hira mukasha inda take fada min suma sun kusa tahowa dan fara shirin bikinsu mufida. Sai da muka gaisa da yaranta tukunna mukayi sallama,kafin na cigaba da karatun novel dina. Da sallama a bakinsa ya shigo cikin wata shadda sai gyalli yakeyi,nidai har ya qaraso idona a kansa,Domin zan iya irga lokutan dana ganshi cikin manyan kaya gashi sai zuba qamshi yake. Wayar hannuna ya karba ya ajiye gefe. Shine kk gudo kk barmu ko?kinga ni fita ma zanyi zanje zance ne,baki ce nayi kyau ba"yace murmushi kwance a fuskarsa. Saida na rintse idona dan takaici kafin na qaqalo murmushi. Kayi kyau sosai,saika dawo" Haka ina kallo ya fita,sakin kuka nayi na tausayawa rayuwata,dan a yanzu na tabbatarwa kaina na fada tarkon sonshi,dan da gsk kishinsa nake. Wayyo allahnah,zuciya baki min adalci ba,sbd me zakimin hk?why?why? Kuka nasha na godewa allah kafin nayi addu'a na gyara kwanciyata,dan yau bazan kwana a part dinsa ba,ya zama dole na nisanta kaina dashi tunda kusancin da muke dashi ne duk ya jayo min hk. Amma kuma sai me?duk yadda naso bacci ya daukeni abin yaqi yiwuwa,ga wani zafi da zcytah takeyi idan na tuno inda mijina ya tafi. Ta wani bangaren banga laifin zcytah data kamu da son daddyn shahid ba,domin ya cancanta a soshin. Amma kuma ta wani bangaren nasan yafi qarfina,abinda yake qara sagar min da gwiwa kuma bai wuce kalamansa ba da yasha fadamin su lokutan da suka wuce amma idan na tuno daddyn shahid din da dana yanxu ba daya bane sai naji sassauci kadan. Haka na ringa juyi a kan gado tare da neman mafita amma ban samu ba. ๐Ÿ’™๐Ÿ’™RABON KWADO....๐Ÿ’™๐Ÿ’™๐Ÿ’™ Na Er mutan ungogo๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ Ina alfahari daku Rabon kwado fans,ina gdy da fatan alkhairinku game da exam din da nayi. Da yardar Allah zan fara subirbido muku rabon kwado. ๐Ÿ…ฟ145-๐Ÿ…ฟ150 Har su mubina suka gama kallo suka dawo daki kusan 11 na dare ba daddyn shahid ba alamarsa. Gsky zance yayi dadi.. Wai ina yaya yaje ne naga har yanxu bai dawo ba?"mubina tace. Zance ya tafi inaga acan zai kwana"na fada a qufule ina daukan iman datai bacci don mayar da ita dakinsu. Dana dawo dukkansu ido suka zubamin,nidai kuma daukar shahida nayi na fice na barsu. Ina komawa na nemi gado na hau tare da jan bargo. Bacci fa bai kamaki ba sister"mufida tace. Idan batai bacci ba fita zatayi ta nemo shi ko kuma ita tace yaje yakai daren?wlh dama nice ke khadija wlh dasai yau mutum ya gane kurensa,sbd rainin hankali da matarka zaka tafi wani zance?" Ni mgnrma qara bata min rai takeyi,haka mubina ta cigaba da mita,jin dirar mota yasa dukansu suka nufi bakin window tare da daga labule. Zaiga zance wlh da ummi zan hada shi"mubina tace tana sakin labulen tare da dawowa. Yadda nakejin zcytah kamar zata fito yasa nayi saurin dafe qirjina kozan samu sauqi. Nasani dama son maso wani shi zai kasheni tunda nasan yadda na fada tarkonshi bazai taba sona ba. Namiji kenan!kamar ba shine dazu ya gama yabo da koda ya fatima ba amma 6month da mutuwarta har ya fara neman wata,Allah sarki wanda ya mutu ai ya mutu,nida nake rayenma watana 4 da aure akace ya sadiq yayi aure bare ya fatima da yasan bazata dawo ba. Sallamarsa cikin dakin yasa zcytah qara gudu wajen harbawa,dan dole na kuma dafe dai dai inda nake tunanin anan zcyr take. Mufida ce ta amsa sallamar dan mubina rufe ido tayi kamar mai bacci,ni kuwa dama har kaina yana cikin bargo duk da ba sanyi akeyi ba. Mufida badai har sunyi bacci ba?"yace Eh mn yaya bakaga qarfe nawa ba?"mufida tace. Mtw wlh ni kaina bansan dare yayi haka ba,dan taba min nernah ta taso mu tafi daki"naji yace. Inaji mufida na tashina nayi mata banza harta gaji ta qyaleni. Barta tunda bazata tashi ba,saina dauketa dan nasan tana jina" Cak!naji an daga ni tare da janye bargon. Qoqarin kwace kaina na farayi,ganin haka yasa ya qara rungumeni a jikinsa ya nufi hanyar waje. kuka na farayi a hankali har saida naji ya saukeni akan gadon. Dagoni yayi har lkcn idona a rufe yake sai hawaye da yake zuba dan kukan bamai sauti bane. To menene kuma na kukan bagashi na dawo ba?ki daina banason kuka kinji?"yace tare da saka hannu yana sharen hawayena. Jin ya daina goge hawayen yasa na bude idanuwa na. Caraf muka hada ido nayi saurin kauda kai. Saida naji ya tashi kafin nayi addu'a na gyara kwanciya duk da na fahimci a bedroom dinshi nake ba wanda na saba kwanciya ba. Da taimakon Allah da addu'ar danake yasa na fara jin sauqi a cikin zuciyata.Gskyr batureda yace"Struggle Never End"ni kuma qaddarata kenan dakon soyayya,na gama ta ya sadiq yanxu na fada ta wani. Ganin dakin ya dauki duhu yasa na qanqame jikina tare da fargabar allah yasa ba irinta ranar bane,to ai yau banyi masa laifi ba. Jin an riqoni yasa na kuma firgita tareda qwala qara. Qara riqoni yayi bayan ya kunna Lamp dake gefen gadon inda haske ya fara kawowa kala daban daban. Ki rage tsoro kinji nernerh?"yace yana qara shiga jikina kamar mai jin sanyi. Nernah inason yin aure amma wata zuciyar na rayamin idan nayi haka kamar ban kyautawa fatima ba,ki bani shawara dan allah"" Shiru nayi ina jujjuya maganganunshi,wato shi baya ma daukata a matsayin mata?Eh mana ai dama ya jiga ya sanar dani a mai yiwa yaransa hidima zan zauna nice dai na zaqe gashi na janyowa kaina na fada tarkon sonshi. Ki fada min yadda zanyi nernah,inaso ne a hada bikin dana su mubina amma bansan yadda mutane zasu dauki mgnr ba,musamman ma ummi plzz ki fadamin mafita" Tirqashi!! Idan kece khadija wace iriyar shawara zaki bashi?shin xaki bashi shawara yayi auren ne ko kuwa? Khayratie er mutan ungogo๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ Ya Abdul kayi aurenka kawai?ya fatima ta riga ta tafi bazata dawo ba,mgnr mutane kuwa ka toshe kunnuwanka domin Allah ne halarta muku auren mace fiye da daya idan har zakuyi adalci,bare ya fatima bata raye.Ka sanarda ummi insha Allah zata amince"nace muryata a rauna ne. Jin yayi shiru bashi da alamar mgn yasa na janyeshi a jikina na fara sauka a gadon. Ina kuma zakije?"najiyo shi. Ban jiyo ba illa qoqarin mayar da kwallar data taru a idona da nayi. Zanje na kwanta ne dare yayi"nace cikin dauriya domin kadan ya rage na fasa ihu. Kizo ki kwanta anan mana?" Banyi mgn ba sai ma hanyar fita dana nufi da sauri jin kukan takaici ya taho. Ya bari idan yayi aurn ya samu hakan daga matarsa,dama yace bazan iya daukar dawainiyarsu shida yaransa ba,dan hk daga yau na daina yarda ko hannuna ya taba,kamar yadda yace shi yayana ne zanzauna a matsayin qanwarsa,soyayyarsa kuwa zanyi ta dakonta har lkcn da allah zai yayemin ya bani mafita. Haka na raya daren da kuka da addu'ar neman sassauci,saida naji zcytah wasai kafin na nemi makwanci cike da qissima abubuwa iri iri. [09-07, 12:55 PM] Cwt-besty: ๐Ÿ’™๐Ÿ’™๐Ÿ’™RABON KWADO....๐Ÿ’™๐Ÿ’™๐Ÿ’™ Er mutan ungogo๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ ๐Ÿ…ฟ191-๐Ÿ…ฟ195 Bugun get din na shigayi ba tare da tunanin wani abu ba,hkn yasa su ummi nufo inda nake cikin hanzari. Jin wata tsawa ta cikin gidan yasa na tsaya da bugun da nakewa get din. Wani murdadden soja ne ya fito kakkaura mai jini a jika,siffarshi ma kanta abar tsoro ce. Masifa yake da gurbatacciyar hausarsa.ganin yaya sun qaraso yasa na harareshi tare da murguda baki๐Ÿ™„๐Ÿ˜ Yaya ne ya shiga bashi hqr tare dayi masa bayanin gurin masu gidan mukazo. Hajia yasan da zuwanku?"itace kalmar data kuma batamin rai da sojan ya fada. Wai yaushe mutanen nan sukai arziqin da ganinsu ma sai an nemi izini? Kince mini ke yaronsu ne,bari na kira hajia a waya,idan yace abarku ku shigo to"sojan ya fada yana shigewa ciki. Lallai ma mutanen nan wato Duniya sabuwa suka samu suke cin karensu babu babbaka"na fada cikin takaici. Malama kiyi mana shiru"yaya yace ganin yanayin ummi. Su mubina ne suka tattaro yaran suka biyomu don ganin mu a tsaye. Leqowa sojan yayi tare da yafito mu don hk muka shiga qatuwar farfajiyar wadda ta qunshi bangarori guda shida.yanayi da tsarin gidajen duk iri daya ne kamar yadda suke a jere bibbiyu bibbiyu. Daga gefe wajen ajiye motoci ne da kuma qaramin masallaci. Hajia yace a shiga daku,daya dauka masu neman taimako ne sai da nace a mota kukazo,kinsan hajia bayason talaka"sojan yasa yana murmushi. Mu duka ba wanda ya kulashi,bayansa mukabi ganin ya nufi daya daga cikin gidajen. Knocking yayi wata matashiyar yarinya ta bude,inda yayi mata bayanin mune baqin hajia sannan tayi mana iso. Qaton falon nabi da kallo ina qissima kudin da aka kashe masa,gsky mutanen nan sun sami duniya,kardai ace wannan rubabbiyar tsohuwarce a ciki? Zama mukayi akan kujerun ni harda miqe qafa. Hajia na hutawa,amma nan da 1hour zata fito"yarinyar ta fada tana komawa inda ta fito. Shiru mukayi kowa da tunanin da yake ganin yaran kamar sun takura yasa na janyo remote control din dana gani kan centre tble na kunna t.v. Hararata ummi tayi nayi murmushi kawai. Wai me wannan tsohuwar take nufi ne?sai kace munxo neman wani abu,ko kuma bamu da aikinyi ne?"yaya ya fada cikin bacin rai ganin mun haura awa daya a zaune. Ayyah babanah,ka qara hqr mana har lkcn da zata fito,idan muka abinda ya kawomu ba shikenan ba" dama sabon shigar arziqi ai sai ya nuna kansa,bare wadanda suka samu sama ta ka"na fada ina qara bararrajewa kamar ina falon ummi๐Ÿ˜Š. Anisa na qarajin bakinki ranki zai baci"ummi tace. Jin alamar bude qofa yasa duk hankalinmu yayi wajen. Dariya ce ta kusa subucemin ganin baba shatu a while chair,kai da ganinta sakasan taci duniya,kamata yayi zuwa yanxu tana ta istighfari domin mutuwa ko yau ko gobe,amma sbd budurwar zcy sanye take da rantsattsen less don masifa harda kafa wani dauri a goshi. Harara ummi ta gallamin hakan yasa na gintse dariyata ina kallon ikon allah don yan mata biyu ke turota. Bangama shan mamaki ba saida naga sun shimfida mata wani rug sun shimfideta akai tare dayi mata matashi sa cushion,ta wani kishingida kamar wata sarauniya. Saida ta kuma dai daita zaman glass din fuskarta kafin ta fara binmu da kallo daya bayan daya. Gaisheta muka shiga yi,kafin ummi tayi mata bayanin mu suwaye da kuma abinda ya kawo mu. Shuru tayi tana qara binmu da kallo kamar tanason gano wani abu,kafin daga bisani tayi murmushi. Dama nasan wannan ranar zata zo,dama kuma wannan ranar nake jira,domin nasan dole akwai ranar da zaku nememu,kuma na godewa allah da ina raye wannan rana tazo,ranar da ahalin abubakar suke durqushe a gabana suna neman wani abu gareni nida ahalina" Kallon kallo muka farayi danjin abinda ta fada,ita ta dauka abu mukazo nema a gurunsu?ai duk lalacewar goma tafi biyar albarka. Mannira!mannira!Ta shiga kwala kira.wata budurwace ta fito tana wani yauqi. Nifa shiyasa banason zuwa bangarenki hajia,kita batawa mutum suna kuma kullum sai na fada miki munirat sunanah" Kedai kika sani 'yar nema,maza kirawon iyayenki kice inason ganinsu yanxu yanxu" Ficewa tai batare datayi mana mgn ba,muma ko kallo bata ishemu ba. Muna nan zaune raina in banda suya ba abinda yakeyi,sbd yadda baba shatu take zuba mulki saika rantse jinin sarauta ce. Su mufida kallo daya zaka musu ka gano bacin ran da suke ciki musamman ma mubina,bare kuma oga kwata kwata daya hade fuska yana danne danne awaya.Ummi ma dauriya ce kawai ta lullube damuwarta. Uncle sani ne ya fara shigowa kafin sauran suka fara zuwa daya bayan daya.Bayan gaisuwa ba wanda yake qara mgn. Ni dariya suke bani ganin yadda suna shaidamu sai kowa ya fara cin magani da shan qamshi. Kamar yadda kuke gani wadannanahalin danuwanku abubakar ne,mahaifiyarsu tamin bayini sunxo ne akan mgnr auren wadancan yaran guda biyu.To yanxu dai niba dolensu bace,kune dolensu,don hk idan da akwai abinda zaku iya taimaka musu dashi sai ku basu" Gsky hajia ta bangarena babu wani abu dazan iya,ban sani ba ko sani"uncle auwal ya fada yana ciccin magani. Har yaya zaiyi mgn ummi ta hanashi,don hk nima dole na hadiye mgnr da nayi niyyar yi. Banda abin hjy ai kinsan yanxu bamuda wasu ajiyayyun kudi da zamu iya dauka muyi kyauta dasu,muda muke shirin saka hannun jari a qasashen waje ai muma abin a bamu taimako ne" Murmushi baba shatu ko nake hajia shatu mai jan kai tayi,kafin ta kalli su aunty hafsatu. Ku kuma fa iyayen amare ko akwai wata gudummawa?" Abinda maza suka kasa ai mu mata ba'a sako mu a ciki ba,Allah dai ya bada zaman lpy,ya bada yadda za'ayi"aunty zuwaira ta fada. To asiya kin daiji daga bakin iyayen nasu,don hk ayi gaba ko za'a dace,ko kuma a fitowa yara da haqqinsu da sunusi ya washe ya kai qasar waje"inji baba shatu. Allah ya huci ran hajia,dama ba munxo neman wani abu bane,domin alhmdllh bamu nemi komai mun rasa ba ba,tunda har wasu suna samu daga qarqashinmu Suna ci,sannan ta sanadiyyar abinda muke dashi har wasu sunaji kamar sunfi kowa arziqi a duniya.munxo ne domin sanar dasu iyayen nasu domin fita haqqinsu,don koba komai su dangin mahaifinsu ne suna da haqqi akai" Ke asiya,karki kuskura kizo har cikin gida kice zaki zage mu,idan ba maular ba mezai kayoku inda muke?to wlh salin alin ki tattara kan watsattsun yaranki kuyi gaba tun kafin nasa a wulaqanta ku"aunty hafsatu ta fada tana miqewa kamar zatayi dambe. Hafsatu kenan,ai watsattsun yara sune wadanda aka ciyar dasu da haram,aka shayar dasu da haram kuma suka rayuwa cikin haram,kuma sanin kanki ne ahalin abubakar sunfi qarfin wulaqanci daga wulaqantattu wadanda suke taqama da dukiyar marayu" uncle sani ne ya miqe yana huci kamar zai daki ummi. Barta sani ai idan bata zagemu ba bazamusa zafin talauci ya ratsata ba"baba shatu tace. A fusace yaya ya miqe yaja hannun ummi suka fice,don haka muma muka kwaso yaran muka fito muka barsu sunata zage zage. Ni kuwa raina fes,don ummi ta gama min komai data fada musu wadannan maganganun. Daqar muka samu ummi ta dawo hankalin ta,don hawan jininta saida ya tashi,satinmu daya a asibiti aka sallamo mu,uncle kuwa fada yaitayi akan zuwan namu.shine dashi da wasu daga cikin abokan abba sukai komai daya shafi mgnr aurensu mubina. Baba shatu da ahalinta kuwa bamu qarajin duriyarsu ba,amma lkc lkc akan yi barna a company,amma zuwa yanxu ni na daina zargin su baba shatu,nafi tunanin ta wani bangare ne muka qara samu maqiya. Cigaban lbr๐Ÿ‘Œ [09-07, 12:55 PM] Cwt-besty: ๐Ÿ’™๐Ÿ’™๐Ÿ’™RABON KWADO๐Ÿ’™๐Ÿ’™๐Ÿ’™ Er mutan ungogo๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ ๐Ÿ…ฟ186-๐Ÿ…ฟ190 Sosai hankulanmu suke a tashe don iya buncike anyi amma ba'a gano musabbabin zurarewar kudin ba,hakan ya bamu tabbacin na jiki jiki wanda yasan sirrin abbanmu shike aikata hakan. Addu'ar da muka yawaita yasa asirinsu ya fara tonuwa. Inna ladi itace shugabar masuyi mana hidima a gidannan,komai idan suna buqata ta hannunta ake basu,hatta albashi ita ake bawa tana basu.kasancewarta dattijuwa yasa muke girmamata,ba kamar ummi data dauki dukkan yarda ta bata. Azal ce ta ciyota da kanta tazo tana kuka da neman gafara akan duk abinda ake ciki tanada masaniya,domin ita aunty hafsatu(yayar abba)ta bawa wani abu a leda tace ta tabbatar da zuba a abincin abba.washegarin da yaci abincin shine wannan ciwon ya kama abba. Kuka nasha sosai dan ummi sam taqi amincewa na nada mata dukan da zata daina numfashi. Da uncle ma yaji shida yaya cewa sukai zasu kai qara kotu ta haka ne za'a gano duk wani mai laifi.Amma fir ummi taqi amincewa acewarta abin kunya ne mu tsaya shari'a da yanuwan mahaifinmu,kuma koshi yana raye tasan bazai goyi da bayan hakan ba don hk mu barsu da allah ai shi ba azzalumin sarki bane. Badan uncle yaso ba yabar mgnr,amma yasa aka kori duk wasu masu hidimar gidan don yace da hadin bakinsu komai ke faruwa. Daqar ya yarda aka samo sabon get man,mai bawa shukoki ruwa sai kuma wadda zata ringa taimakawa ummi da abinda ba'a rasa ba,amma itama bata shigowa part din gidan tanacan part din da aka tanada domin masu aiki,kuma idanma ta kama zata shigo to iyakacinta falon qasa. Durqushewar A.A motors yasa aka siyar da sauran Kadarorinsa domin farfado da company din. Tunda yanuwan abba suka samu abinda sukeso suka dauke qafa daga garemu,akasin da da kullum suna tafe a hanyar gidanmu.hakan ya qara tabbatar mana da cewa komai daga garesu ne.Kamar yadda basu qara neman mu ba muma sai muka manta dasu. Tasowar bikinsu mufida yasa ummi ta matsanta sai munje wajensu mun sanar dasu domin a yanxu bamuda wasu dangin mahaifa da suka wucesu. badan raina yaso ba na tattaro yara muka zo domin zuwa wajen dangin mahaifinmu. Gaba dayanmu kwanmu da kwarkwatarmu muka tafi tsohuwar unguwar da suke zaune.Munsha wahala sosai don har mun fadda tsammani zamu koma gida domin duk yadda ummi take musu kwatance kowa muka tmby sai yace baisan wadanda muke nema ba. Wani mai kanti mukai sa'a ya gano kwatancen da muke dan kusan shekara 8 kenan rabonmu dasu. Hajia ai idan kwana kuna tambayar auwalu da qaninsa sani bazaki sani ba,nima dan dai na dade a unguwar ne yasana gano wadanda kuke mgn akai,mgnr gsky yanxu duk ahalinsu sun tashi daga wannan unguwa.Akwai wata sabuwar unguwa da ake kira sabuwar abuja can suka koma wajen shekaru 4 da suka wuce.yanxu hakazan muku kwatancen unguwa kuna zuwa ku tmby kigan hajia shatu mai jan kai na tabbata duk wanda kuka tmby zai nuna muku" Duk cikinmu ba wanda ya iya mgn saboda mamaki da al'ajabi ni kuma mamaki nake har yanxu baba shatu na raye. Yaya ne ya miqa masa hannu suka qara musabaha,mudai mota muka koma muka barshi yanawa yaya kwatancen unguwar da zamu nufa. Har muka dauki hanya ba wanda ya iya cewa komai. Kamar yadda dattijon yayiwa yaya bayani hk muka isa unguwarmai qarancin jama'a da zirga zirgar ababan hawa. Yayane ya fara parking don dama motarmu ce a gaba inda yake tuqamu sai ni a gefensa sai shahid,zaid,zarah da shahida a back seat. Dayar motar kuma driver ne sai ummi,mufida,mubina da kuma iman. Mun dade a cikin mota kafin yaya ya samu wanda zai tmby inda aka kwatanta mana. Dawowa yayi muka qara gaban wani qaton gida wanda za'a kira da estate. Yaya ba'a samu gidan bane?"nace ganin ya tsaya kuma baice komai ba. Nan dai wanda natmby ya nuna min,amma ina tunanin gsky banan bane"yace yana nuna estate din. Wangale daya daga cikin manya manyan get din estate din yasa muka maida hankali ga rantsattsiyar motardata sako kai waje. Da hanzari yaya ya fita don gani motar na shirin wucewa,gashi na waje baya iya hango na cikin motar. Ganin mamallakin motar ya sauke glass suna mgn da yaya yasa na fito kamar yadda naga ummi ma ta nufi wajen. Kafin mu qarasa mai motar ya maida glass din tare da bawa motar wuta yayi gaba tare da budemu da hayaqin motar,kana gani kasan da gayya akai hakan. Saida hayaqin ya lafa kafin muka samu qarasowa ida yaya yake a qame kamar an dasa shi. Ba gidan bane ba koh?"muka fada a tare nida ummi. Gidan ne,don fu'ad ne ya fita a mota yanxu"yace yanason boye damuwarsa. Fu'ad?fu'ad fa kace"muka sake tmby kamar hadin baki. Eh shine,kawai mu koma gida don ya sanar dani babu mai sauraronmu tunda ba'asan da zuwanmu ba"ya fada yana tpy dan komawa mota. Eh lallai,shi fu'ad din har yaushe yayi baki da arziqin da zai fada mana haka?sbd rashin mutunci harda budemu da hayaqi,to wallah yau komin bala'i sai mun shiga gidan nan koda shugaban qasa ne a ciki"na fada na nufar get din da aka rufe baba dadewa. Muje zuwa don jin yadda zata kaya.shin suna nasarar shiga gidan ko kuwa?idan sun shiga wace iriyar tarba zasu samu wajen masu gidan? Er mutan ungogo๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ [09-11, 7:57 PM] Cwt-besty: ๐Ÿ’™๐Ÿ’™๐Ÿ’™RABON KWADO....๐Ÿ’™๐Ÿ’™๐Ÿ’™ Er mutan ungogo๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ ๐Ÿ…ฟ196-๐Ÿ…ฟ200 Gaba daya jikina yayi sanyi da jin lbrnsu,inda tausayinsu ya mamaye min xcy. Sosai na jinjinawa qoqarinsu don idan bakaji lbrnsu ba bazaka taba tunanin sunada wata matsala ba. Amma khadija bayan abinda kk fadamin dazu akan fadanku da broh babu wani abu daban"ta tmby ni. A iya sani na babu komai aunty anisa,koshi yace nayi masa wani abu?"nace ina kallonta. Kamar zatayi mgn kuma sai tayi shiru. Shikenan dai kiyi bacci yanxu kinga dare yayi sosai" Haka na kwanta inata jujjuya lbrn a zcytah,na dade banyi bacci ba kafin sarkin barayi ya sace ni. Banyan munyi sallar asuba ma banyi wani bacci mai yawa ba sbd rashin sabo,dan hk qur'ani mai girma na shiga karantawa. Dana gama ma na qara kwanciya amma baccin yaqi zuwa,don hk na shiga nayi wanka. Dakinsu mufida naje sunata sharar bacci,dan haka na dauki kayana na sakatare da kafa dauri duk da banyi kwalliya a fuskata ba. A hankali nake takawa ina qarewa falon saman kallo,kafin na fara saukowa daga stairs din. Can saman kujera na hango ummi da littafin azkar da alama karantawa takeyi. Qarasawa nayi na zube kan rug ina gaisheta. Kamar ko yaushe ta asma cikin kulawa kafin tayimin nuna dana koma kan kajera,murmushi kawai nayi ba tare dana koma ba. Hk muka kasance tsahon lkc,ganin ta gama azkar din yasa nayi mgn. Ummi akwai wani abu daza'a taimaka dashi?" Aa diyatah yi zamanki,akwai mai aiki zata gudanar da komai,zuwa yanxu ma nasan ta kusa kammalawa.Su wadancan kasoshin har yanxu baccin suke?" Murmushi nayi ina qara qasada kaina. Bude qofar falon da akai yasa muka kalli gurin a tare. Sanye yake cikin suit ash colour,fuskarnan tashi kamar kullum,amma kana ganinsa zakasan akwai abinda ke damunsa,dan tafiya yake kamar yana tausayin qasa,akasin da da yake tafiya cikin kuzari,qasaita da tafin jarumta. A cikin sakwanni da basu wuce 10 ba na gama karantar yanayinsa,kafin na dauke kai kamar ban damu da sanin wanda ya shigo din ba. A dan nesa dani ya zauna tare da lankwasa qafa sannan ya shiga gaida ummi. Fuskarta ba yabo ba fallasa ta amsa a taqaice ba tare data kalleshi ba,hakan zai tabbatar da akwai wani abu a qasa. Nima gaidashi nayi kamar anyi mini dole,shima a taqaice ya amsa yana satar kallon ummi da alama bashida gsky. Su shahid sun tafi school ne?"yace. Aa kai ake jira kazo sai ka shiryasu ka kaisu"ummi ta fada still bata kalli inda yake ba. Tsam ya miqe ya isa inda take ya zauna tare da riqo hannunta. I'm so sorry umminah,wlh indai a kan mgnr jiya ce na janye tunda bakya so,kinsan dai banason ganin wannan yanayin a fuskarki" Batai masa mgn ba don hk ya cigaba. Ummi jiya kwata kwata kasa bacci nayi,rabona da abinci tun jiya da safe,plzz ki tausamin,kuma bazan qara mgnr ba tunda bakyaso" Rashin bacci ko cin abinci duk kaine ka jawowa kanka,tunda kana zaman zamanka zaka jajibowa kanka wani aure,kuma inhar kanaso mu shirya dakai karna qarajin makamanciyar wannan maganar daga gareka" Allah sarki ummi ashe duk akan mgnr aure take wannan fushin,data amince yayi aurensa kawai maybe yana buqatar hakanne. Sama sama suke mgn akan abinda ya shafi company,kafin ya sanar mata cewa a satinnan yakeson zuwa dubai wajen wasu abokan kasuwancinsu daganan zaije US dan ganawa da uncle. Tashi ummi tayi domin samo masa abinda zaici nidai har lkcn kaina a qasa don bazakayi zaton ina falon ba ma. Jiya su Ammi na gaidake"najiyo shi. Ina amsawa"na fada a qasan maqoshi ba tare dana dago ba. Gashi ta bani saqo wai inji qawarki" Da sauri na dago dan nasan bani da wata qawa sama da nusaiba,don sosai nake missing dinta kawai dai daurewa nake,bama ita ba duka family dina,musamman ma su muhibba,sauqinta ma ina ganinsu shahida inajin dadi. Ina dagowa naganshi yana danna waya kamar bashine yayi mgnr ba. Ganin ummi ta taho yasa banyi mgn ba. Madaidaicin farantin hannunta ta ajiye.Ganin zata fara hada tea yasa nayi saurin tashi don karba domin bai kamata tana aiki ina zaune ba. Batai musu ba ta bani na shiga hada tea din ita kuma ta zauna tana ganin kayan da yak nuna mata a waya ko za'a siyawa su mubina. Ina gama hadawa naje ta gefensa na miqa masa,banyi aune ba naji ya kama harda hannu na kuma yaqi saki ya wani basar ya cigaba dayi mata bayani batare daya kalleni ba bare yasan yanayin danake ciki. Duk a firgice nake dan banaso ummi ta dago taganmu a haka,amma shi bashida niyyar saki na. Sunyi kyau sosai,bari na tasosu su gani,idan sunyi musu sai kowacce ta zabi colour"ummi tace tana miqewa,amma inada tabbacin zata ganmu shiyasa ma nayi qasa da idona. Tana dan nisa kamar jira yake ya hanyoni har tea din na zuba akan hannu na. Qara na qwalla kadan sbd zafin danaji,inda shi kuma ya rude ya ajiye tea din a centre table ya shiga fifitamin hannu da iskar bakinsa. Ba qonewa nayi ba don kadan tea din ya zuba a hannun amma ganin ya rude yasa na qara langwabewa ni a dole zafi nakeji. Fahimtar da yayi kukan na shaqiyanci ne yasa yayi smiling tare da janyoni jiknsa. Nernah rigima"ya radamin a kunne da sexy voice dinsa hakan yasa naji yani yarrrrr. Plzz ka sakeni kar ummi ta dawo"nace muryata na rawa jin numfashinsa akan wuyana. Zan sakeki idan kin fadan dalilinku na gudowa kuda yara kuka barni ni kadai,nernah jiya kwata kwata kasa bacci nayi sbd ummi fushi take dani dan nace zanyi miki kishiya,ummi bata taba fushi dani irin haka ba" Kishiya kuma?ai matarka zakace zaka yiwa kishiya kuma ta rasu,ni ai a matsayin qanwarka nake ko ka manta?"nace ina nuna halin ko in kula. Nasan kallona yake don hk naqi dagowa na kalleshi. Plss kar wani yazo ya ganmu a haka yayi tunanin wani abu"nace ina ture hannunshi dayayi min qawanya. Da alama yana cikin shok dan bansha wahala wajen tureshi na tashi ba. Ga abincin nan kaci karyayi sanyi"nace ina barin falon da dan gudu na. Turus naja na tsaya don ganin aunty anisa tsaye akan stair ta rungume hannu a qirji tana murmushi,da alama ta dade a wajen,duk da nasan bazata jiyo abinda muke cewa ba amma da alama taji dadin ganinmu a haka. A kunyace na tsaya inda ta qarasa saukowa. Hk dama akace miki ana kula da miji?maza muje ki bashi abincin kinga fita zaiyi"tace tana riqo hannu na Allah aunty zaici da kansa"nace ina turjewa. Idan kinje saman mezakiyi?"tace tana qara jana. A gefensa ta zaunar dani kafin itama ta zauna a daya gefen nasa. Gud mrng broh" Tace tana murmushi. Mrng angel,how was ur nyt"yace cikin kumawa. Its cool,but yaya yanayinka yana nuna kamar jiya baka samu bacci ba"tace tana binsa da kallo. uhmm Kinsan na tafi ummi tana fushi"yace Ai kasan kaima dole ummi tayi fushi yaya" Koma dai me nene yanxu na janye tunda kunfi qarfina baby"yace yana smiling. Harka tunomin mum dakace baby"tace itama cikin nishidi,hakan ya qara tabbatarmin da shaquwar dake tsakaninsu ganin yadda ya ware yake zuba tare da bata dukkan hankalinsa. ni kaina naYi missing nasu over,amma a satin nan nakeso naje don qarasa tattaunawa akan bikinsu twins. Ni dauka zuwa yanzu mum tazo dan tace ita zata gyara amare " Sai dai naje sai muje yaushe zasu taho din" Wai ba kaine mai co mplain kanajin yunwa ba,amma ka tasa abinci gaba kana surutu kamar ba office zakaje ba"ummi tace tana nufar qofar da take sadamutum da kitchen. Ummi kefa nake jira kiyi feeding dina"yace a shagwabe. Ka bari idan kaje wa jen iyayenka da suka sangartaka sai suyi maka haka"tace tana shigewa. Kallonsa ya dawo dashi kan aunty anisa"Yanxu ummi ta daina ji dani"yace kamar wani dan 7years. Yanxu tana aiki ne bari ni na baka"tace kamar tana lallaba yaro qarami. Um um ni wannan nakeso ta bani"yace yana poiting dina. Yarda yayi yasa na kasa riqe dariyata na shiga yi,itama aunty anisa dariyar take. Shi kuwa tsayawa yayi yana kallona da alama bai tava ganina ina dariya irin haka ba. Khayratie ce!!๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ [09-17, 9:28 PM] ๐Ÿ˜˜rukiey๐Ÿ˜˜: ๐Ÿ’™๐Ÿ’™๐Ÿ’™RABON KWADO......๐Ÿ’™๐Ÿ’™๐Ÿ’™ 17, 9:28 PM] ๐Ÿ˜˜rukiey๐Ÿ˜˜: ๐Ÿ’™๐Ÿ’™๐Ÿ’™RABON KWADO......๐Ÿ’™๐Ÿ’™๐Ÿ’™ ๐Ÿ…ฟ206-๐Ÿ…ฟ210 Sakkowar su mubina yasa na fara tsagaitawa da dariyar da nake. Ita kuma wannan ita da wa?"mubina tace tana samun wajen zama. Ita da mijinta?"Aunty anisa ta bata amsa. Miji manya muma dai mun....."bata qarasa ba saboda mugun kallon daya watsa mata. Ai kadan kaji indai mubina ce wlh"aunty anisa ta fada. Uncle mrng"zarah tace masa. Mrng queen"yace yana maida kallonsa gareni. Sarai na fahimci mgn yakemin da ido,kawai na basar kamar ban gane me yake nufi ba. Broh ummi tace zaka nuna mana furnitures mu zaba"mubina tace. Bazan nuna ba"yace a hasale kamar anyi masa laifi. Shiru falon yayi sai mubina dake kumbure kumbure. Miqewa yayi ya dauki car keys dinsa dake center table. Neesa bari na wuce nabar saddam da aiki,Gashi zuwa anjima muna da baqi"yace yana wani shan mur tare da fara tpy. Ba yunwar dama kakeji ba,inbanda haka mai jin yunwa ne zai tsaya yace dole sai an bashi abinci a baki?nifa shirmen nan naka ya fara isata babanah"ummi data fito a kitchen take fada. Ummi yace rabonsa da abinci tun jiya,bai kamata ya kuma fita baici komai ba,kuma kinsan yaya ba wani tsayawa yaci zaiyi ba idan ya fita"Aunty anisa tace cikin damuwa kamar cikinta zai kaiwa. Kada allah yasa yaci ai jiki magayi na fada a raina. To anisa shi qaramin yaro ne da sai an tasa shi gaba yaci abinci?kullum girma yake yana tara iyali amma bazai nutsu ya ringa cin abinci ba?Almost 35years ace sai an zauna ana feeding dinsa?"fada take sosai da alama ba rashin cin abincin bane kawai laifin da yayi,shidai tuni ya fice hakan yasa aunty anisa bin bayansa da sauri. Ta dade bata dawo ba hakan yasa ummi tace muje dinning area mu fara cin abinci ita kuma ta zauna a falon tana nazarin wata newspaper. Ummi kinga ya tafi bai nuna mana ba"mubina tace kamar zatai kuka. Ummi dai batai mgn ba sai aunty anisa data bi da ido da take shigowa. Kitchen ta shiga kafin ta fito da basket ta nufi waje da alama mutumin naku zata kaiwa. Aunty anisa ta yaya"mufida tace tana dariya. Saji dashi,suje can su qarata"ummi tace da alama ta jiyo abinda mufidan tace. Aunty wai yaushe ne bikin naku?momma tace bikinku za'ayi pa"zarah tace. Ki kwantar da hankalinki darling an kusa saura kadan"mubina tace tana fifita mata tea. Dawowar aunty anisa yasa kowa yayi shiru,inda ta nufi wajen ummi ta zauna. Ummi wai yaya ya kuma wani laifinne?plzz kiyi hqr tunda yace ya fasa zuwa yanxu saiki daina fushi dashi,wlh duk ya shiga damuwa" Ki tashi ki bani guri kafin na dawo kanki,meyasashi baki tmbyshi abinda yayi min ba?harni zai fadawa ya fasa bacin sun gama mgn da uncle dinku cewa za'a hada bikin dana 'yan biyu,ni kenan ban isa na nuna banason abu a qiyi ba" Kiyi hqr,Amma koni haka yace min ya fasa amma zamu kuma mgnr" Ni ba aure ne banaso yayi ba anisa,amma fisabillahi wani kallo yakeso mutane suyi mana?kofa shekara ba'ayi ba da rasuwar matarsa,bayan haka duk irin halarcin da iyayenta sukai mana na bashi auren qanwara sai kuma yanxu suji zai qara aure?shima babban yayan ya gayo da bayansa sbd shi bayaso ace yayi laifi" Dukansu kallon tausayi suke min,nima kawai dai ina daurewa ne,domin zuwa yanxu kowa ya fahimci ni din ce bayaso,kuma nima insha allah zan cireshi a raina. Ganin mufida ta tashi yasa nima na tashi don banaso suyi zaton sbd mgnr ne zan tashi,kuma har lkcnsu ummi mgn suke sai dai yanxu bama iya juyo abinda suke cewa ba. Da sauri na nufi sama domin kadan ya rage kuka ya kwace min.Dakin aunty anisa na shiga inda na fada gado tare da rushewa da kuka mai ban tausayi. A saboda qaddararren aurensa na rasa kowa nawa da komai nawa,akan wannan auren nasa burina na zama lawyer ya tarwatse,saboda shi kowa ya gujeni amma wannan itace sakayyar da zaimin. Ta wani bangaren bashi da laifi tunda ba sona yake ba aka qaqaba masa ni,kuma an gina auren akan cewa zan kula masa da yara ne bawai zaman aure ba. Jin kamar za'a bude qofar yasa na fara share hawayen fuskata ba tare dana juy ba don na juyawa qofar baya. Aunty khadija"tace tana dafa ni. Ban amsa b sai yaqen da natimata duk a qoqari na na boye halin da nake ciki. Kuka"?tace tana mini kallon tausayi. Saurin girgiza mata kai nayi don ina mgn kuka ne zai taho. Bata ce komai ba sai rungumoni da tayi,hakan ya bani damar sakin wani kukan don dama ina buqatar mai rarrashi. Yaushe kika fara sonshi" Rasss!gabana ya fadi,badai kowa ya gano inasonshi ba? Khadija meyasa zaki fara sonshi tun yanxu?"tace tana dagoni. Kiyi hqr nima bansan yaushe hakan ta faru ba,ki fadan yadda zan cireshi a raina don allah aunty" Kuka na cigaba dayi sosai. Ki daina wannan kukan plxx,zamuyi nasara insha allah"tace tana sharemin hawayen fuskata Badan na aminta da maganarta na tsagaita da kukan,don nasan wannan mafarkin nata bazai tabbata ba,amma kasancewarta wadda ta damu da damuwata Da dukkan al'amura na dole nayi abinda takeso. Labarai ta shiga bani na dramar zaid da zarah duka qoqarinta na ganun na saki raina na manta komai. Har yamma muna tare da ita,duk abinda tasan zanji dadinsa shi takemin,Hakan yasa na saki jiki mukaita hira tana bani lbn zamansu a U.S. Mubina ce tashigo ita da iman da alama basu dade da dawowa a scul ba don 5pm ta wuce. Da gudu ta kwace hannunta tazo ta rungume ni,hakan yasa aunty anisa sakarmin gashin da take tajemin da hand dryer bayan ta wankemin da shampoo masu qamshi. Gsky kin shagwaba yarinyar nan da yawa,bakiga yadda akaita rarrashinta ba ummihar goyata tayi amma kamar bata sammu ba ita dole wajen mommy zata"tace tana dungure mata kai. Qara rungumeta nayi a jikina"Ai yanxu gashi tazo kuka ya qare"nace ina kallonta ta lumshe ido sai ajiyar zcy take da alama tasha kuka. Shigowa mubina tayi"wai me ake qullawa ne tun safe aka qule a daki?" Zoki zauna kiji me ake fada?"aunty neesa tace. Aa fita zamuyi zanyiwa ummi rakiya karkasara,sis kinga motarki kuwa?gsky tayi kyau nima allah yasa a bani irinta" Har ya kawo motar ne"aunty anisa tace. Eh tana Can waje arsh color broh ya zabar mata,nidai ku fito ku gni tafiya zamuyi har su zarah duka"tace tana ficewa. Mu gani ta window kawai don saukarma aiki ce"tace tana yaye curtain din window. Arsh color ce sabuwa dal don banda qyallinta ba abinda kake hangowa. Wai wannan motarce da sunan tawa?ni ko a mafarki bana kawo zanyi mota bare a irin wannan qananan shekarun nawa.Abbi kawai zance ya ringa hawa donni ba abinda zanyi da ita. Tsaf tagyaramin kaina sai sheqi yake da qamshi,ni kaina nishadi nake dan sakayau nakeji na. Tare muka Shiga kitchen inda muka gabatar da sakwara da miyar agushi. Basu dawo da wuri ba sai wajen 9 inda muka baje ana hira tare da cin gyadar Da amminah ta basu. Sailkcn na tuno da saqon da daddyn shahid yace ammi ta bashi,don haka na matsu ya shigo gidan don na karba,amma abin takaicin har muka koma upstair don kwanciiya bai dawo ba.Washe gari ma kwata kwata bai shigo gidan ba,naji dai aunty anisa tayi maganar rashin zuwanshi ummi taita fada tana cewa kada yazo din ai itama ba nemanshi take ba. Allah sarki ita dai ummi har lkcn fushi take da babannata. Er mutan un gogo๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ ๐Ÿ˜˜: ๐Ÿ’™๐Ÿ’™๐Ÿ’™RABON KWADO.....๐Ÿ’™๐Ÿ’™๐Ÿ’™ Er mutan ungogo๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ Ina neman afuwarku readers akan rashin jina tsahon kwanaki,hakan ya faru ne sakamakon rashin Nepa da aka fama dashi ina fata za'ayi min afuwa. Sannan akwai mistake na page number da nayi,last page zai kama 201-205 yanxu zamu tashi 206-210.Ngd. ๐Ÿ˜๐Ÿ˜Wannan page sadaukarwa ne ga tsofaffin daliban G.G.S.S kwah 2015 musamman B Class. Khadija isah muhd Ruqayya musa Ummahani adam Hauwa musa bello Rabi Aminu sulaiman dungurawa. Bashariyya abdulhamid Khadija Bala muhd Jamila ibrahim(jam jam) Aisha usaini yarkanya Asma'u Aliyu ungogo. Kuna raina bazan manta daku ba tsahon rayuwa๐Ÿ˜๐Ÿ˜ ๐Ÿ…ฟ206-๐Ÿ…ฟ210 Tun daga ranar bai qara zuwa gidan ba,kuma in aka kira numbr dinsa batashiga kamar yadda naji aunty anisa ta fada. Sosai suka shiga damuwa idan ka cire ummi da kullum cikin mita take,yaransa kansu sun faratmby ina daddy dinsu,nidai ko a jikina dan nasan ta hanyar daina ganinshi ne kawai zanyi nasarar cireshi a zcytah. Jin dadin gidan nake sosai,dan kowa ji yakeyi dani ba kamar ummi da take min kamar ta goyani ko yaya taga nayi shiru xata shiga tmbytah ko ina buqatar wani abu. Samunsu aunty anisa da mufida yasa na daina damuwa akan rashin yanuwana. Shirye shiryen biki sukeyi sosai,ba kamar mubina da take ji kamar ta janyo ranar bikin. Cikin ikon allah na fara nasarar cire daddyn shahid a zcytah domin shidin bai cancanci a so shi din ba.idan na tuno da matsayinshi na mijin ya fatima sai naga butulci ne ace na fada tarkon sonshi. Ana saura 1month bikin mutanen U.S suka diro ciki kuwa harda mutumin naku. Sosai matar da suke kira da mum take da fara'a da jan mutum a jiki,tun inajin nauyinta har nazo na sake da ita kamar yadda naga yan gidan sunayi. Uncle din kuwa kallo daya zakayi ka gano tsantsar kamar da sukeyi da cwt daddyn shahid๐Ÿ˜œ da kuma ummi,shim na samu karbuwa a gurinsa. Kwanarsu biyu da zuwa aka fara gyara amare ciki kuwa harda ni,ba yadda na iya dole nake tsayawa duk abinda akayi musu ayi min don mum da aunty anisa sun tsaya kai da fata ai nima amaryar ce. Cikin kwanaki kadan muka fara canjawa asalin kyawunmu yana bayyana,don abune akeyinsa kamar cin kwan makauniya,safe rana da kuma dare duk da su mum din ba anan suke kwana ba kullum da safe suke xuwa ayi break fast dasu sai idan uncle sun dawo daga company da dare bayan dinner sai su wuce masauki. Das qamshi ya zauna ajikinmu duk inda muka zauna muka tashi sai mun bar qamshi don hatta wanka da ruwan turare mukeyinsa. Daddyn shahid kuwa bama haduwa dashi don downstair dinma bama Sauka komai biyomu akeyi dashi. Duk yadda sukai kyau amma sai suyita zuzita kyauna,nidai kawai jinsu nake dan su da suke farare ai sune zasufi yin kyau. Yau ta kama saura 3weeks biki,Kamar kullum yau ma abin da mum ta saba dama mana aka dama nidai kwata kwata bana jin dadinsa don haka kowa saiya shanye a barni a baya wataran mum har dura takemin. Ganin mum ta fata yasa na ajiyeshi a bedside drawer nayi kwanciyata. Ashe da rabon yau ma ayiwa wata dura"mufita tace. Sis bazaki gane menake ji idan inashan abin nan ba,kwata kwata babu dadi ko pa suger babu"nace ina gyara kwanciya. Kowa ma ai babu suger din yakesa,wlh ki tashi kisha dan mum tace yana da matuqar amfani"mubina amarya tace. A wajenku amare ba"nace ina dariyar mugunta. Eh koma dai mezaki ce ki tashi ki shanye ko naje na kira aunty anisa"tace tana harara ta. Wlh har tausaya miki nakeyi mubina,wannan gigin da rawar kan da kikeyi duk a sati daya za'a sauke miki shi"mufida tace muna ci gaba da dariya. Pillows ta dauka tana dukanmu dasu muna cigaba da dariya. Zuwan zaid yasa muka dakata da dariyar sai mubina daketa harare harare. Mommyn shahid wai gashi inji uncle saqonki ne sai yanxu ya tuno dashi"ya fada yana bani wata leda. Bude ledar na shigayi batare dana tuno da ko wani saqo bane. Inner wears ne masu kyau,sai pictures din nusaiba dakuma wanda mukayi tare a waya aka wanko,sai kwalin chewing gum da sweet sai kuma letter. Letter din na hau karantawa don daga note din nagane daga nusaiba take. Slm sistr Ina fata kina lpy kamar yadda nake duk da kewa da rashinki a kusa har zuwa wannan lkcn ya kasa bari na nayi rayuwa kamar ko wani dan adam. Baxan iya kwatanta yadda nakeji a kullum idan na tuno irin rabuwar da mukayi ba,amma hakan ba yana nufin canja miki matsayin a gurina ba. Wani albishir kuma shine on 7 may bikin sistr dinki,rashin halartarki yana nufin rashin gudanar da biki cikin walwala. Luv u so much sistr. Yau nawa ga wata"na tmbyi su mubina ina share hawaye ba tare dana kula irin kallon da suke min ba. Five"mufida tace. Tsalle na daka sbd murnar lkc bai wuce ba zanje bikin nusaiba. Lpy sis"suka fada a tare. Bikin besty dina za'ayi jibi ai zaku je koh?"na fada ina murna. Sosai m dama zaman gidan ya isheni,gashi an karbe mana phone kamar wasu prisoners"mubina tace Amma ummi xata bari?"na tmby Zata bari insha allah"mufida tace Ai kuwa muna tmby ta bari harda bada wani purple din material mai kyau wai a dinka mana muje bikin dashi. Ban gama m amaki ba saida naga washe gari da yamma an kawo dinkin,dinkin doguwar riga ce qasanta ya bude sosai.Da yake su mubina sun dan fini qiba siririyar ciki na dauka ina gwadawa kuwa dai dai ni,sai lkcn mufida take fadamin aunty anisa ta dauki measurement dina don tuni an kai mana dinkunan biki. Tun safe na fara shiri sbd zumudi,ga murnar ganin amminah da kuma nusaiba. Daqar na bari mukai azahar kafin mu shirya mu tafi tare da driver,fadin irin kyau din da mukayi kuwa bata baki ne,kamar wasu triple haka muka fito. Tun shigowarmu layi nake tuno abubuwa da dama da suka faru tun daga yarinta ta har zuwa lkcn da akai min auren rashin gata๐Ÿ˜“ A qofar gidanmu m.sabo yayi,jikina a sanyaye na bude murfin na fito don lkc daya fargaba ta shigeni dana tuno yadda mukayi da Ammi a wannan can xuwan. Tun daga soron gidan zakasan an samu cigaba,dan haka sallama dauke a bakunan mu muka shiga gidan inda nake bin gidan da kallo kamar wata baquwa. Ammi ce ke qoqarin amsa sallamar tana fitowa daga kitchen. Banyi sanya ba na tafi da gudu na riqeta tare da sakin marayan kuka. Aa yau manyan baqi ne a gidannamu"tace tana fara'a. Ke kuma daga zuwa sai kuka"ta kuma fada tana dago ni a jikinta. Falo muka shiga har Lkcn inamatsar kwalla,su kuwa su mufida suna min dariya. Shima falon kamar bashi ba dan komai bana dabane a ciki an gyarashi kamar na yan gayu. Gaisuwa aka shigayi nidai ina maqale jikn Ammi kamar wani zai kwace min ita. Ki tashi ki samo muku abinsha kafin abincin ya qarasa,suma su ruqayya sunce zasu xo,ita zainab ma dake kusa kuma ita ba yara ba amma har yanxu shiru" Ammi suma zasu xo"nace ina mai jindadi. Eh haka aisha ta fada min jiya da mukayi waya" Fridge Dana gani a falon na nufa don samo abin sha.kunun aya ne da zobo juice dan haka na dauko mana kafin naje kitchen dauko cups. Shi kanshi kitchen din kamar na wata amarya Ko yaushe aka samu wannan cigaban oho. Ammi abbinah pa?Nasan dai yau ba aiki"nace ina tsiyayawa su mubina juice. Tun daida suka shigo bayan daurin aure suka fita amma duk inda yake yana kusa da gida don a qasa ya fita"tace tanashiga ciki. Sallamar ya zee dana jiyo yasa na dire jug din na fita a million.Kamar wata baby haka na dafeta har muna qoqarin faduwa. Oh my lil sis har yanxu kinanan a yadda kk,kwata kwata gudu da tsalle bayayi miki walaha" nayi missing dinki ne pa"nace a shagwabe. jin kamar goyo a bayanta yasa nayi saurin sakinta. Baby boy ne kwance a bayanta yanata sharar bacci. Ya zee dama kin haihu shine ko a sanar dani"nace hawaye na taruwa a idona. Kiyi hqr auta wlh munso sanar miki amma...." Amma abbi ya hana koh?shikenan tunda an cireni cikin family dinnan"nace ina shigewa daki. kuka na shigayi suka hadu suna lallashina,sai da ammi tasa baki kafin nayi shiru na dauki yaron mai suna muhammad Aameen. muka shiga hira,suma su mubina warewa sukayi mukaita labaran duniya,harsu ya aisha sukaxo bamu sani ba sai dai kamai mukaga muhibba.rungume juna mukai muna murnar ganin juna falo muka fito Na rasa Gurin wanda zan nufa Kaawai na Fashe da kukan murna.Dama inada wannan bataliyar amma da nake rayuwar kadaici? Haba auta keda zakiyi murnar ganinmu saiki buge da kuka?common share hawayenki"ya aisha tace tana ruqoni Tare da share min hawaye. Duka yaran nawa sukayo kaina kowa yanaso Na daukeshi.haka naita dagasu sama muna nishadi abinmu. Ranar jinta nake kamar sallah danagamun hadu dukanmu muna kwasar dambun ammi,sai naji haushi da bamu taho dasu iman ba da suma sunga yanuwansu ai. Kwata kwata na manta biki mukazo sai da aka fara kiran la'asar kafin ammi ta fara fadan mu tashi mu shiga gidan bikin. wajen da muka ci abinci Na shiga gyarawa su kuma suna sallah da yake ni ina off. ๐Ÿ’™๐Ÿ’™๐Ÿ’™RABON KWADO๐Ÿ’™๐Ÿ’™๐Ÿ’™ Er mutan ungogo๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ Rabon kwado fans ina yinku irin totally dinnan,fatana a koda yaushe mu kasance daku domin da yabo da kwarin gwiwarku komai ke gudana. Ana mugun tare๐Ÿค ๐Ÿ…ฟ211-๐Ÿ…ฟ215 Bayan idar da sallar qarayin wata kwalliyar su mubina sukayi,nidai gyara fuska kawai nayi nayi yafen mayafina kamar yadda naga suma sunyi. Har tym din ammi tana cikin dakinta hakan yasa naje domin sanar mata zamu wuce. Oh wlh nayi missing gadon nan naki ammi,kai duka gidanma nayi missing,amma ku sam baku damu dani ba kamar an cire ni daga cikin yaran gidan nan"na fada muryata na rawa alamar kuka. Waya ce miki mun manta dake auta?wlh kullum a gidan nan sai anyi mgnrki,bama ni ba ko abbinku koda yaushe maganarsa ke ce,tayaya za'ayi mu haifi 'ya mu manta da ita?"Ammi tace cikin rarrashi. To amma Ammi meyasa kowa yayi avoiding dina kamar bani da dangi" Ai yanxu komai ya wuce auta kuma sai yanxu na gamsu da hukuncin da abbinku ya dauka,gashi yanxu kin kwantar da hankalinki kina zaune da mijinki da yanuwansa lpy.Hajiya asiya ta fadan kwanaki bakiji dadi ba ranar da suka kawo mota,dama Abbinku yace zamuje mu duba jikinnaki hajiyar tace kin warware kunacan gidan nasu ba.kuma mgnr motar yace zai ajiye duk ranar da kikazo sai ayi mgnr yadda za'ayi da ita" Ammi ni na barwa Abbi motar ya jiqa hawa" Dama hakan shine ya dace,amma dama inake ina hawa wannan motar khadija?sai ki qara mana gdy wayan shi mai gidan naki don duk qarshen wata baya gajiya da hidima,tun abbinku baya karba har yazo yana karba,yaron dan mutunci ne ba ruwanshi" Ammi naga an samu canja canja a gidannan ya koma kamar na wata sabuwar amarya"nace ina dariya don son kawar da waccan maganar. Abbinku ne ya samu qarin matsayi a wurin aiki shine yaketa gyara" Ai gwara ya gyara amarya tazo ta ganshi da kyanshi"na fada da zolaya. Ke ni banson shaqiyanci kinxo kenan zakimayar dani kamar kakarki,ga wannan sai ki kaiwa nusaiban gudummawa"tace tana zaro qaton kwali daga qasan gado. Kai ammi angoda"nace ina bude set din kulolin masu kyau. Tashi nayi ina gyara zaman mayafina"Ammi bari muje suna jirana,zan turo su mufid su dauki gudunmawar"nace ina neman hanyar fita. Zo nan auta,badai a haka zaki fita ba sbd sakarci,maza ki gyara lullubinki kafin na saba miki,ince dai har yanxu kina nan da shiriritarki,ace kina matar aure bazaki lullube jiki ba" Ware mayafin nayi na dora a kai ina turo baki,domin ni kwata kwata mantawa nake ni matar aure ce๐Ÿ˜ Gidan cike yake kamar ko wani gidan biki anata hidima da kai komo da dangin abinci kala kala,Umman tasu ma bamu samu ganinta ba muka shige dakinsu nusaiba kamar yadda aka sanar mana sunacan ita da tawagarta. Ganinmu yasa ta saki ihun murna tare da tasowa muka rungume juna.A tare muka saki kuka domin a lokutan baya aka fada mana zamu kai wannan lkc bamuga juna ba tsaf zamu qaryata. Sis dama zaki xa?wlh tun shekaran jiya da aka fara event nake saka ran zuwanki ganin har yau maki zo ba yasa na fitar da rai"Nusy tace bayan mun tsagaita da kukan. Zanzo mana sis,idan banxo ba ai naci amanar aminta" Qara rungume juna mukayi,inda ilahirin yan dakin suka mana kallon tausayi musamman wadanda sukasan yadda muke a lkcn baya. Wato kinxo da muta ne kin manta dasu ko?To mu bari mu shiga muyiwa umma allah ya sanya alkhairi daganan zamu koma gida sai kun taho"ya ruqayya tace kafin suka fita. Sorry sisters,yau ina farin cikin ganin besty ne shiyasa,amma karku damu ana tare"nace ina zaunar dasu a kan katafar dakin. Qara jiqo nusaiba nayi,itama ta riqeni gam kamar za'a kwace mata ni. Amma sis yau da za'a kaini shine ranar da zakixo?bafa kano zan zauna ba can kd ne"tace tana matsar kwalla. Gsky baiwar allah ki saketa haka,lpy lou muke za'ayi mata kwalliya amma daga zuwanki kin sakata kuka" Juyowa nayi don ganin meyin wannan furucin na fada mata mgn dai dai da wacca tayi min,amma me kallon mamaki muka bi juna dashi domin tabbas wannan classmate dina ce a G.G.C Dala. Khadija isah!!.. Hauwa musa!!.. Muka fada a tare domin tabbatarwa. Duk da cikin dake jikinta batai qasa a gwiwa ba tazo ta rungume ni. Hirar yaushe gamo data school muka shigayi ba qaqqautawa hakan yasa kiwa a dakin yayi shiru yana saurarenmu kunsan dai yan bording suka hadu ba sauqi ni,bare mu da muke class daya tun j.s 1. Hauwa musa bani numbrs din yan mate dinmu dama inata nema don nayi missing contact"Na fada ina zaro wayata daga hand bag. ki kwantar da hankalinki har DOGAS zansa a sakaki,Dama yan grp dinku sai cigiyarki suke" Allah sarki yan biyar nasan zasu neme ni sosai musamman ummulkhair A. ungogo,Ruqayya musa da kuma ummahany adam" Ai kuwa muna waya da ruqayya musa bari na baki number dinta sauran kuwa ko a grp kwa hade" Wai sis damakunsan juna ne"nusaiba da aka fara yiwa kwalliya ta tmby. Eh tare mukayi Dala da ita"nace ina kwashe number din ruqayya musa a wayata. Yawwa saiki saka min taki,zanyi miki mgn ta watsap sai kiyi adding din nawa" tana saka mn number din wata yarinya ta shigo. Aunty jidda wai kizo inji ya sadiq yana falon baqi" Ambatar sunan ya sadiq yasa na zuba ido dan gani wadda zata tashi domun tabbas sunan matarsa jidda kamar yadda ya fada da muka hadu a Mall. Ga mamakina naga hauwa musa ta miqe. Khadija isah ina zuwa mijinah yana kira kinsan ba'a sanya da kiran mai house" Harta fita ban samu zarafin amsa mata ba,kallo na mayar kan nusaiba domin samun amsa tmbyoyina.Akaci sa'a itama ni take kallo don hk ta daga min kai alamar eh" Eh itace matar ya sadiq?Eh hauwa musa itace mace mai sa'ar data samu ya sadiq?Eh cikin jikinta na ya sadiq ne? Ganin kamar mutane zasu fahimci wani abu yasa nayi qoqarin saita kaina inajansu mufida da hira. Da aka kawo abinci ma mufida ce kawai taci alala din dukkanmu bama tare da yunwa. A lkcn su mufid suka kawo kayan suka tafi. Rade radin da aka fara anxo daukar amarya yasa nusaiba zuwa ta qanqameni. Dan allah sis kice min dake za'aje kaini,wlh ke kadai zan gani na ringa jin sanyi a raina,kin sani munyi missing juna,And we have a lot of thing to talk,gashi kinxo a qurarren lkc"ta fada kwalla na zubowa. Plzz sis karki bata kwalliyarki mana,banzo da shirin zuwa kd ba amma da babu abinda zai hanani kai cwthrt dina dakin mijinta,kuma kinga tare nake da baqi,qannen daddyn shahid ne kuma shima ban sanar dashi tpyr ba,Amma insha Allah ko banxo ba akwai waya kuma zamu ringa haduwa indai kinxo"nace cikin dauriya don qarfafa mata gwiwa. Ga wayar ki saka min number din,ga wannan kayan inji Ammi tace a baki,bari muje mu gaisa da umma sai mu wuce,sai munyi waya" Har lkcn kuka take bata samu damar mgn ba.Zuwan wata mata kirantaza'ayi mata fada ya qara sakawa da riqeni,don haka kwallar da nake riqewa da zubo ba tare dana shirya ba,daqar ta sakeni suka fita da ita ni kuma ina cigaba da sharar kwalla. A tsaitsaye m uka gaisa da umma muka fito don tana busy sosai haka mukai mata allah ya sanya alkhairi muka fito. Rassss!Gabana ya fadi don hangosu suna tahowa fuskokinsu dauke da farin ciki,Da inada halin canja hanya da nayi domin banso muka hadu dasu ba,ita kanta hauwa musan na bari kawai mu hadu a chat kawai mu ringa gaisawa. Badai har kun fito ba"na tsinkayo muryarta. Eh zamu wuce can gidane kinga yan daukar amarya sunxo"na fada da yaqe domin banason ta fahimci wani abu don ko inda mijinta yake ban kalla ba. Amma duk yadda kuke da amaryar bazaki tsaya akai ta da ke ba?"ta kuma fada Wlh naso hakan amma ina tare da baqi shiyasa"na fada cikin qosawa da tsayuwar wajen domin kamar akan wuta haka nakeji na. Mijin jidda ga qawata khadija,Maybe kunsan juna don naga qawar Nusy ce"tace tana kallonshi. Wai nernah?Ai keya kamata nayi introducing a wajenta"yace yana sakin killer smiling. Kamar na rusa ihu haka naji. Nernah?kana nufin wannan ce nernan da kullum kake damun mutane da zancenta"ta fada tana nuna ni da yatsa tare da qanqance ido kamar bata taba sani na ba. Yp ko bata cancanta bane?"yace yana harde hannu a qirji. Dogon tsaki taja kafin ta bangajeni ta wuce tanata huce kamar wata zakanya. Da kallon mamaki muka bita dukanmu ba kamar su mubina da sukaga hirar da mukasha dazu dazun nan. Yana qoqarin yimin mgn nayi saurin jan hannun mufida muka bar gurin don hankulan mutane ya fara dawowa kammu. Wlh Allah ya taimaketa ciki ne a jikinta amma da taga qarshen rashin m"mubina ta fada. Barta zafin kishi ke dawainiya da ita,Amma a tunani na ko miji muka hada da hauwa bazatai min wannan wulaqancin ba bare yanxu data auri Ex dina"na fada ina share hawaye. Dama wasu matan haka suke,ko yaya kuke dasu qaddara ta hadaku miji daya ko saurayi sai kasha mamaki"mufida tace. Murmushin takaici kawai nayi don idan akace hauwa zata min abinda tamin yanzu tsaf zan qaryata. Har muka qarasa gidan za ncen sukeyi nidaiban kuma cewa komai ba. Badai har kun dawo Ba"Ammi dake kishingide ta fada Eh yan daukar am arya ne sukazo shiya muka taho"nace Allah sarki Allah ya b asu zaman lpy,ai nusai ba akwai hankali ko bayan da bakyanan bata bar zuwa muna gaisawa ba,duk da a lkcn mahaifiyarta fishi take dani gani take kamar da gayya aka hana danta aurenki,shine tayi masa auren huce haushi da yar aminiyarta"Ammi tace Ashe dai da gaske ya sadiq yake daya ce ba aure yayi ba aure akai masa,Amma hakan bai hanashi yin biyayya ga iyayenshi ba ya zauna da matarsa lpy gashi cikin qanqanin lkc ya samu Riba ga matarsa dauke da juna biyu. Su mubina suka shiga bawa su ya aisha lbrn yadda mukayi da hauwa musa.Gajiya nayi da zancen na shige daki na kwanta kafin nayi dialing number din ruqayya musa,Allah ma yaso na karbi ta tan don nasan yanxu kam hauwa musa bazata saurareni ba bare ta sakani wani grp.Allah ya taimaka itama ruqayyan Admin ce tace zata sakani a grps din. Daf da magriba mukaje raka ya zee don zataje tayi girki a gida,a dawowa muka hadu da Abbi,duk da layi ne banji kunya ba naje na daneshi. Aa khadijatu karki qarasa abbin naki mana"Yace yana dariya. Abbi nayi kewarka ne pa"Na fada cikin shagwaba. Daga shi harsu mufida dariya sukemin har muka koma gida. Dawowarmu Abbi ya fatattaki su ya ruqayya akan su tafi gidajensu,sunaja kumburi wai don yau ya samu auta shiyasa yake korarsu. Ana wannan dramar mijin ya aisha yazo,don haka suka tattara duka bayan na karbi numbers dinsu inda zasu raqewa su ya ruqayya hanya. Kamar yadda na saba lkcn ina gida yauma haka ina kwance cinyar abbinah,su mufida na gefe munashan hira gaba daya. Yan biyu ince dai kwana biy u akazo yi mana,don naji abdurrahman yace kuma gaf ake dayin naku bikin"Abbi yace. Aa abbi m.sabo muke jira idan yazo zamu wuce"mubina tace. To allah ya tabbatar da alkhairi ya jiqan mahaifinku" Saida mukaci tuwon dare kafin m.sabo yazo,zan fara kukan shagwaba Ammi tace zasuxo dukansu bikinsu mufida.ba shiri na fara goge hawayen. Dakinmu na shiga na kwashi sauran tarkace na danake buqatamuka tattara muka wuce. Khaeraty ce!! Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels