Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels ๏ปฟ[7/23, 10:28 AM] Ummi Tandama: ๐Ÿ“ฟ *KUYANGA...* ๐Ÿ“ฟ *_๐ŸŒˆKAINUWA WRITERS ASSOCIATION_* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *Nabilancy Luv* ๐Ÿ’˜ (Auntyn S&S) 1-5 Sarki Abdallah Adalin Sarki ne mutum me kamala da Son talakawansa Wanda yake da mata Uku sai yara biyu matarsa ta farko uwar gidan itace Hauwa,u Anace mata *UMMAH* Mebi mata itace Saratu *MAMAH* sai ta Uku amaryar sarki itace Fatima Amma *FATU* akece mata UMMAH macece me tsananin kishin gaske Tanada gadara da iko ita din yar gidan Sarautace tana buga ikonta agidan sarki domin sarki Abdallah yanaji da ita don haka take buga sha,aninta ackn gidan kowa shakkarta yakeyi tundaga fadawa,Bayi maxa da Kuyangin gidan da duk wanda ke cin gidan har kishiyoyinta D'anta Daya jal Yarima Anwar Wanda aka shagwaba shi da Gata Awaje yayi karatunsa Tundaga Sakandare har tagaba da Sakandaren wanda ba karamar tabarbarewar tarbiyya zamansa acan yaja masa ba don tun daya gama karatunsa yaki dawowa Yasamu guri xan babu kwaba babu harara Har saida labarin abinda yakeyi yadawo kunnan me martaba yai masa aike takakkiya aka taho dashi Yayi masa fada sosai har kurari yaimasa yace inhar baidaina ba zai yi masa Aure ackn dangi zai laluba yadaura masa Aure da koma wacece Aikin Anwar acan neman matan banza turawan nan sun sassanshi haka abokan banza yake mu,amula dasu basu da aikin komai saibin club club ana lolewa da mata anashan Giya ana raye raye Amma yafi Ronce da wata baturiya data nace masa mesuna RIHANNA wacce duk wulakancinsa takan shanye Abu daya yasa yake d'anshan mintinta tasan takan iya kulawa da d'a namiji duk luggar yaudara da iya Romance ta kware Inda tayi musu zarra kenan gata da kishin tsiya tasha zane mata masu kawo masa hari Amma ahakan yake yakiceta yaje yashana da wacce yakeso danma tana shakkarsa da bazata bari yasakeba Anwar yanada isa da jinkai jinsa yake tamkar sarkin wani zubin to kullum azuciyarsa yana jin kome zaiyi babu wanda ya isa yakawo masa cikas tunda shi din dan sarkine me jiran gado Mahaifiyarsa ke kara sakawa yaji izxa aransa akullum takan nusarsa cewar shine sarkin gobe duk da shi bawani son yazama sarki yakeyiba tunda yasan inya zama sarki dole yazauna guri guda kuma yabar duk abinda yakeyi knn. Sarki Abdallah akullum cikin bakin cikin Abinda dansa Anwar yakeyi yakeji aransa wanda yarasa yadda zaiyi dashi don yakintsu tunda shine babban dansa wanda wataran dole shine sarki agarin Yasan da cewar Mahaifiyarsa ke xugashi tunda yahaneshi da zaman turai tace abarshi yahuta acan kafin wani lokaci bata son abinda zai bata masa rai Sauran matan Sarki su idone nasu domin ta tsakiya MAMAH bata taba haihuwa ba itako Amaryar sarki FATU ta haifi Danta namiji tsiransu shekara biyar da Anwar yaron sunansa LAMIDO Ummah bata kaunar FATU da D'anta sbd Fatun bata dade da zuwa gidanba ta samu ciki Ko MAMAH data rigata xuwa bata qullaci fatun ba domin MAMAH macece me tawakkali duniya bata dametaba Kowane d'a daga cikinsu tadaukeshi tamkar ita ta haifeshi Amma tun tasowarsu da suka girma sai tafi kaunar Lamido domin shi yarone me hankali magana ma bata dameshiba a Nigeria yayi karatunsa Lokacin daya isa shiga jami,a alokacin Sarki yaso turashi Turai shima Amma sai FATU taki amincewa sbd a ganinnta xaman turai ga yaro ba uwa ba uba na bata yaro da canza masa halinsa mekyau zuwa mara kyau tunda shima Anwar dayaje ba haka yakeba ada daga baya yakoyo wasu dabi'un Sarki bai bata rai akn hknba domin takawo masa kwararan hujjojinta akan rashin son zuwan nata Turai yakuma gamsu MAMAH ma bataga laifin taba domin tasan komai kuma kansu ahade yake su biyun Sautari UMMAH takance wai sun hade mata kai Sukuwa shakkarta da sukeyine yasa basa shiga Sabgarta ****** Tun Dawowar da Anwar yayi Nigeria kusan wata biyar yaji yagaji da zaman atakure yake baya futa club balle korawa da neman mata sbd babu dama duk inda yayi ido akansa suke inma yayi awajen gari Sarki zai iyaji azo ace yabatawa gidan suna shiyasa yafison yafita away Rihanna tayi ta damunsa akan inhar bai dawo Turai ba zata hado kayanta ta biyoshi ta nemi inda yake Hankalinsa yadaga dan yasan zata iya shiko yasan inhar tazo kashinsa yagama bushewa ackn gidan Ba shiri yahau hada kayan dazai tafi dasu domin yai mata Alqawarin zaitaho cikin Satin domin ma kwana biyu yabata zaitafin Da tunanin yanda zaishawo kan Sarki yabarshi yatafin yashiga cikin gidan Bangaren Mahaifiyarsa domin yafara kai mata zancen su samo mafita tukun Yana tafe afarfajiyar gidan yana tafiyar Jinkai da wani shankamshi da Rangaji ackn Shigar Alfarma ta sarauta Bayi maza Da kuyangu mata nata aiyuka suna wuceshi tareda durkusawa suna kai gaisuwarsu ga Yarima sarkin gobe Wata *KUYANGA* Yakurawa idanu dayaga tanata sharar gurin ajiye dawakai kanta ba dankwali dan gyalen data yane kanta ya xame bata saniba Farace shar gata da hips ga nashanu suncika mata kirji Ta dago zata bar gurin yakwalla mata kira Aguje takaraso gareshi da biyayya ta durkusa tana gaidashi Yakara kallonta na sakanni kana yace ckn shanqamshi "me kikeyi acan? Da rawar murya tace "ina..,ina yin..,Shara nakeyi... Yace "Dama Sharar gurin Dawakai nakune mata kona Bayi Maza? Tayi kasa da kai tace ckn rage murya "Allah yataimaki Yarima tuba nakeyi ba aikina bane MAHBUB nake tayawa yatafi wani uzurin. Yace "MAHBUB!wanene kuma *MAHBUB?* Tahau kame kame tazaci ko laifi tayi Tace "Abokin shawaratane tamu tazo daya.shima yana tayani Aiki shiyasa nake tayashi Ayanda take maganar yabashi Sha,awa bakinta me kama da anzana heart yatsurawa idanu yaga tana motsashi ahankali Koda tayi shiru shima shirun yayi yana kallonta kawai Wani abu yaringa ayyanawa aransa Dataji shi shiru saita dago kanta dasauri tayi tsammanin yatafine saitaga ashe yana gun Tayi saurin yin kas da kanta don gudun kada suhada idanu Yace mata "meye sunanki? Tace " sunana *KUYANGA* !! Yace "ke Sunanki nace zaki fadamin na gaskiy KUYANGA ba suna bane aguna wannan kalmar larabcine abangaren hausa kuma ace Baiwa. Tace "Sunana *ZEENATU* Ya gyada kai kawai yawuceta yana kara ayyana abubuwa ackn ransa Koda yashiga cikin Dakin Mahaifiyar tasa tararta yayi hadimanta na mata hidima daga me matsa mata kafa ana mata tausa sai meyi mata furfita saikuma masu bare mata ayaba tana karba tanaci Yana shiga hadiman suka miko tasu gaisuwar xuwa gareshi Ya amsa da ka Ta nuna musu kofa tareda alamun sufuta subasu guri Saida suka futa kana yagyara zama yace "UMMAH Barkanki da warhaka Tayi murmushi " Yawwa barkanka Abin faharina yarima Mejiran gado sarkin gobe da yardar Allah. Yayi murmushi yace "Uwata maganin kukana yauma gani gabanki nakawo kukana nasan banda matsala tabangarenki zaki sharen hawaye Mai martaba kawai nakeji Tace "fadi ko meyeshi zanmaka zankuma saka ayi maka Yace "Ummah inaso inkoma Turai nagaji da zaman Nigeria niba aiki nake futaba kusan kullum nake gida bana motsa jiki kewa ta dameni kitaimakamin kisa baki me martaba yabarni intafi. Tayi murmushi "Angama Yarima yaushe kake son katafin? Yace "Jibi nashirya tafiyar Tace "Jibi jibin nan? Amma baiyi kusaba kuwa nikaina bason kayi nesa dani nakeba gashi kaida akeso kahaye karaga wataran yaxa,ayi aga baka xama abaka. Yace "kada kidamu da Wannan Ummah na wataran ai dole inxauna din nidai yanzu kiyimin kokari intafi Tace "kada kadamu kamar katafi kagama zanyiwa TAKAWA maganar ayau. Yayi murmushi yace "Yawwa nagode Ummah saidai kuma.โ€ฆโ€ฆ yai shiru yana sosa keya Tace "ehe!fadi mana yakai shiru kafadi komeye in akwai bazai gagara ba zanmaka. Yace ckn rage murya "Saidai naga wata yarinya awaje ackn KUYANGU zanso mutafi da ita tayimin Rakiya domin ta hidimta mini acan. Murmushi tayi tace "bakada wannan matsalar kowannensu akarkashinka suke kanada ikon kowanne bawa agidannan ko kuyangu dan haka kasa aranka kamar ka tafi da ita kagama yatake yarinyar? Take yahau kwatantata Tagano ko wa yake nufi domin KUYANGA Zeenatu tafi kaf kuyangun gidan Nutsuwa dakyawun yanayi tanada kyau nagani afurta Jin mahaifiyar tasa ta Amince masa yasa yaita xuba mata godiya Shiyasa yake matuqar son mahaifiyar tasa baitaba neman abu ta bangarenta yarasaba tana son akullum tafaranta masa bata son laifinsa Koda yafuto farfajiyar gidan baza ido yaitayi ko zai sake ganinta Amma baiyi sa.ar ganin kome kamartaba Tsaki yaja Aransa yace "to meye nawa nadamuwa da son ganinta Alhalin ita zata zamo gadon baccina ita xata xamo jin dadina ita zata zamo komai nawa sai yadda nayi da ita..โ€ฆโ€ฆ _Tabdijan muje zuwa_ [7/23, 10:28 AM] Ummi Tandama: ๐Ÿ“ฟ *KUYANGA....* ๐Ÿ“ฟ *_๐ŸŒˆKAINUWA WRITERS ASSOCIATION_* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *Nabilancy Luv*๐Ÿ’˜ (Auntyn S&S) 5-10 mai Martaba Sarki Abdallah yayi shiru bayan gama jin Bayanan da Ummah Tazo masa dashi natafiyar Anwar Turai Yakalleta yana murmushi yace "Naga alamar yaronnan inmuka ta tashi bazai gyara halin saba Nikam bana sonsa da zaman wajen nan nafisonsa akusa damu domin Aure nake so yayi tunda yakai munzalin Aure ko Lamido yanzun ya isa Aure barantana shi Ummah tace " Aure ai nufin Allah ne baisamu wacce tayi masa bane shiyasa saimu tayashi da Addu,a kada mutakura masa Tunda can din yafi jindadi gara kabarshin yaje aidebe kewa yakeso yayi "Kina baiwa yaronnan gudummawa naga alamar bakya son yagyaru shiyasa kike daure masa gindi Ta dafe kirji tacanza fuska "Kamar yaya? Nikam walh babu wani daure masa gindi danakeyi kawai bana son yashiga takurane da damuwa Tunda shi bayaro bane da hankalinsa ai ko yana nesa damu bazai lalace ba shiriya fa ta Allah ce Addu.a kawai yadace muringa binsa dashi. Mai martaba yace "Amma dai kinsan bazaki hada halinsa dana Lamido bako? Lamido yafishi nutsuwa da hankali harma biyayya da ace Lamidon ne babba dana more.... Ta katseshi tana kuka "Kawai dai kace kafison Lamido akan shi nikam walh banajin Dadi sai inga kamar kana nunan banbancine kuma komai lalacewar Yarima ai dai shine babba kuma dole shizai zama sarki acan gaba.... Yakatseta dacewa "Saurara Fulani kinsan dacewa Adalin Sarki me kamun kai shike cancanta da yin sarauta akowace masarauta dan haka dole sai inyarima yakasance da hakan sannan zai mulki garin nan inko bai canzaba to Al,umma bazasu soshiba Tunda ko a yanzun sunfara farga da banbancin halayyarsu Tace "To walh koma meye Nikam Bazan taba barin Wani bayan Yarima ya mulki garinnan ba inba shiba dan haka koma meye za,a yi masa shine dai gaba Yadaga mata hannu "ya isa meye na tada hankali da kuka indai wannan maganar mulki ce Allah ketsara komai bamu zamu tsara ba tafiya turai kuma Yaje yaita tafiya Nadaina hanashi tunda bakya so inhana din duk randa yagaji da zuwa yadaina Amma kusan da sani zanbashi mata nan ba dadewa ba Har zatayi magana kuma saita fasa tunda bazata ari bakin yariman ba tasan halinsa sarai shima bazai so Auran hadiba. Ta mike tafuce batareda ta gaya masa cewar da "yar rakiya zai tafiba wannan tafiyar tasan Sarkin bazai bariba ***** Ana gobe zai tafin Ummah tasa aka kira mata *KUYANGA* Koda tazo ckn biyayya ta durkusa gabanta tana jiran umarni domin tayi tsammanin aiki aka kirata tayi Ummah tace mata "Kuyanga Zeenatu ko? Ta daga kai sama "To kifara shiri daga yau gobe zaku tafi turai keda yarima zakijene domin kiringa hidimta masa komai nashi kece basai yace ba indai aikin wahalane kada kibari yayi Har sai ranar da yaga damar dawowa zaku dawo tashi kije. *KUYANGA* Tace "Angama Ranki yadade. Ta mike tafuce daga dakin fulanin Koda takoma sashinsu zama tayi a inda suke zama da MAHBUB Ta zabga tagumi tashiga tunanin wai itace zataje turai tabdijan lallai zataji dadin Rayuwa zata canza tawaye tunda tashigo gidan sarki tun tana karama bata taba futa wajen gari ba sai gashi abin farin ciki zata keta hazo TO ABIN BAKIN CIKIN FA? wata xuciyar ta tambayeta tare dayi mata tunin abinda zatajeyi turai dakuma tuni da wanda zataje din Take fuskarta tacanza daga walwala zuwa Damuwa Zuciyarta tahau bugawa to shin wane irin zama zasuyi Alhalin halinsa bame kyau bane?ance yana shan giya ance yana neman mata zance ya yadu agidan dan dai ana boyewane kada aji abakin mutum a hukuntashi. Jitayi antabata afurgice tadago kanta saitaga ashe MAHBUB ne abokinta abokin sha,awararta Takalleshi kawai yau babu dariyar datakeyi masa Yazauna kusa da ita yafahimci akwai damuwa yau kenan Yacire mata tagumin da tayi yace " *ZEENAH*! Haka yake ce mata Takalleshi akaro na biyu tasunkui dakai Yace mata "meya faru naganki ckn damuwa anyi miki wani abin ne bayan nabarki anan din? Ta dago ahankali tace "Bayan barinka nan gurin aka aiko kirana daga Fulani Koda naje kiran saitake gayamin wai infara shiri gobe Yarima zaiyi koma Turai dani xai tafi domin hidimta masa da koma kuma inmun tafi ba ranar dawowa harsai inyagaji yadawo dankansa MAHBUB yadafe kirjinsa tareda Rintse idanu yana kiran sunan Allah Tabbas yashiga tashin hankali domin ayau yashiga halin dabai taba shiga ba arayuwarsa tunda yazo duniya Yana bude idonsa kwalla nabiyo baya yace mata "ZEENAH tafiyarki Turai tana daidai da tafiyar farin cikina nackn gidannan Domin kece me deban kewa akoyaushe kuma ke nake kallo nake jin dadi koda ina ckn jin Yunwa ke nake kallo naji nakoshi kinsan da cewa Nadade ina son..... Yayi shiru yana goge kwallar datake gudu akuncinsa Yakalleta ido da ido yace "ZEENAH bantaba gaya miki Sirrin zuciyata ba saiyau, yauma dole ce zata saka domin naga zakiyi nisa dani Walh ZEENAH zaman da nake dake bana abokantaka bace Na SO Ne zallah dan Allah kisoni koda bazamui Aure ba kice kema kina sona ko naringa tuno kalmar inajin Dadi *KUYANGA* Taji wani yarrr!ajikinta taringajin shigar wani abu tundaga tafin kafarta har zuwa kwanyarta tabbas Tafahimci wannan abun dayake shigarta bakomai bane illah Son MAHBUB ada itakam tadaukeshi aboki amini amma ayau saitaji yanayin yajuye mata da So Tabbas tana sonsa itama bayama data tuno zasuyiwa juna nisa saitaji xcyrta ta karye hawayen da basu zubo ba saigashi sunxubo ganin nasa ma sunzubo din Tace ahankali " MAHBUB meyasa baka gaya min tuntuniba meyasa kaboye sai yau da muka makarowa juna zaka fada yanzu gashi zanyi maka nisa Yace "Duk nisan da zakiyi indai kina sona to tamkar muna tare ne kedai kitaimaka ki furta min ko naji dadi. Takalleshi tayi murmushi tasadda kanta akasa tace "INA SONKA MAHBUB."! yai ajiyar zuciya tareda yin hamdala ga Allah yace "nagode naji dadi ki rikemin Alkawari ki rike amana kikuma kula inkun tafi bamu da ikon kanmu ZEENATU akarkashin ikon Sarki da Matansa da "YA"YANSA muke bamu isa muyi musu da Umarninsu ba sai yadda sukayi damu amma kada kiyi biyayya da aikin zalinci kada kisake acuceki kikasance me addu,a aduk inda kike kikuma zamo me kamun kai aduk inda kika tsinci kanki domin kada ayi miki cutar da zata karya miki Lagon Rayuwarki. Taja ajiyar zuciyar Zuciyar xuciya tace "Naji na amince nakuma gode da Shawararka ya masoyina . . Ya mike yace mata "maza tashi kije kifara shiri indare yayi kizo muhadu anan dan muyi sallamar karshe Tayi murmushi tace " sallamar karshe kamar wanda xan mutu inmunje can Yayi murmushi yace " ba haka nake nufiba, nasan wataqila da sassafe zaku tafi kinga ai zaifi kyau mukadaita mu dade tare mukara yin wata hirar soyayyar ko? Tagyada kai tana dariya Ya daga mata gira tareda kanne ido yana kallonta Harya tafi yabar gun bata daina kallon saba tabbas MAHBUB yahadu rashin gata ne da yanayi yasa cikar kamalarsa bata fito ba harsai ankura ido ake hanga atattare dashi Ta girgiza kai kawai takara gaba tabar gun tayi dakinsu Tana shiga Taga Aminiyarta ZULAI Zulaihat tace "Hhhmmm inata nemanki ai saikuma nahangoki acan lambun soyayya. *KUYANGA* Tayi dariya tareda dukan kafadar Zulai tace "harkin sakawa gurin zaman namu lambun soyayya lallai Zulaihat ke "yar sa ido ce. "Ba wani sa,ido gaskiyace ba lambun soyayyar bane? "Eh bashi bane, to ai ba soyayyar akeba. Cewar *KUYANGA* Tana dariya Zulaihat tace "kifadawa keya yarinya kowa yafahimceku ingaya miki duk wanda yaga yanda kuke tabbas zaigano ckn mintina batareda yasha wuya ba. "Hhhmmm to inma soyayyar akeyi saime? Ko bamu daceba. Zulai takama baki tace "ho! Ni na isa ince baku daceba aji haushina to walh bari kiji kundace da MAHBUB tamkar danjunanku akayoku ina kuma Son tarayyarku. Zama *KUYANGA* Tayi kusa da ita tace " Zulai gobe zanketa hazo fa. Da sauri Zulaihat takalleta da alamar tambaya tace "hazo kuma?kamar yaya? Nan Ta zayyano mata komai nagame da Rakiyar da Zatai wa Yarima Turai Zulaihat tace "wayyo Allah na inama ni aka zaba. *KUYANGA* Tace "tabdijan !kenan har wani son tarayya kike yi da Yarima?mutumin dakowa yasan halinsa marasa kyau. To walh ni ckn bakin ciki nake ahalin yanzu da har aka zabeni Zulai tace "Dan dai zakiyiwa MAHBUB nisa ne amma aikinsan zaki huta zakuma kisami hutu da Aikin gidannan ZEENATU kifa tuna mubayine bayinma kaskantattu wadanda ba,a san inda iyayanmu sukeba ko suna raye?ko sun mace Allah shiyasani mudai muntsinci kanmune agidan nan Dan Allah kikwantar da hankalinki inkinje domin Allah ne yazabeki domin kihuta kedai kiyi biyayya dama ke me biyayyarce kowa yasani bakida surutu magana bata dame kiba inba sabo kikayi da mutum ba basawa ba hanawa dan haka ki ajiye soyayyar MAHBUB anan zuwa sanda zaki dawo kwacigaba *KUYANGA* Tace "to inma ban ajiyeba yazanyi bayan askiyazo gaban goshi gobe nefa zantafin dole inyi hkr da komai dama saiyau yabayyana min abinda ke ransa Zulai tace "hhhmmm keda bakida gano abu da wuri aisaiyau kika ji kika gane amma ai kowa yagane manufarku tabbas muna muku fatan Alkairi kedashi. *KUYANGA* Tace "mungode. Nan *KUYANGA* Tahau shirya kayanta ckn wani Dan akwatin karfe me kyau dashi tana Ninka kaya tana sakawa tana ayyanota A turai shin ko wane Zama zasuyi insunjeโ€ฆโ€ฆโ€ฆ ??? *muje zuwa fans* [7/23, 10:28 AM] Ummi Tandama: ๐Ÿ“ฟ *KUYANGA* ๐Ÿ“ฟ *_๐ŸŒˆKAINUWA WRITERS ASSOCIATION_* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *Dis Page i Dedicated to My Best friend Hauwa,u* *(UMMU ALEESHA wa WALEED)* *Nabilancy Luv* ๐Ÿ’˜ (Auntyn S&S) 10-15 Da Sassafe tagama kintsawa misalin Bakwai na safiya Aka aiko kiranta daga Fulani Tana shiga Sashin Fulanin ta tararta atsaye Yarima na kusa da ita da akwatinsa babba guda daya da alamar zai dade din domin fam yacika akwatin da duk abinda yasan zai bukata duk da acan gidan nasa akwai kayansa na sawa UMMAH Ta daka masa Yaji ta sa anyo masa dambun nama ta soya masa gyada me gishiri duk abinda tasan dai yana matuqar So ta tanadar masa taxuba masa ckn Akwatin Yana ganin *KUYANGA* Da akwatin yahau kallonta fuska ba fara,a yace "ke wannan akwatin irin na mutanen da kumafa? Kina nufin dashi zaki bini? Kinsan kuwa Turai ?Bafa Me dile bace, maza jeki canzoshi kokuma kitafi ba kaya inmunje xan nasiya miki wasu kawai UMMAH tayi murmushi tace "Yi mata hakuri Yarima ta canzo kasan sai ahankali kayi mata uzuri taje ta canzo kayan kokuma inshiga innema mata cikin akwatina na Yahau girgiza kai yana duba agogon hannunsa "Barshi UMMAH saura mintina Jirginmu yatashi saima munyi wuta ahanyar zuwa Airport din don karmu makara Yakalli *KUYANGA* Yace "ke ajiye kayanki anan muje da najikinki inmunje zansai miki wasu kiringa sanyawa. Ckn ladabi tace "to shikenan. Ta ajiye akwatin karfen nata agefe tabi bayansa UMMAH tana musu Addu,u,a da fatan Alkairi Wasu bayi maza ne suka kai masa akwatin nasa har ckn mota aka zura a boot *KUYANGA* Ta shige gidan baya Motar natafiya zata fuce agidan Sarautar saitaji wani iri aranta tabbas zatayi kewar MAHBUB yau ranar zata zamo mata ranar bakin ciki tunda ta taso kullum suna tare gashi yau zasuyiwa juna nisa kamar ance ta dago kanta kuwa tana dagowa takalli bayanta saita hangoshi ta glass yana dago mata hannu Ta zura hannunta tahau daga masa itama Ashe Yarima yana hangosu ta mirro amma baiyi maganaba yai shiru a Airport kuwa da sukaje Dakyar ta iya daga kafa tahau matattakalar jirgi saida ta rintse idonta Jirine ma yaso kadata Allah yaso ya kula yai saurin rikota tayo luuu jikinsa yatarota yamannata ajikinsa yahau da ita ahankali Yasan arina tunda yasan ba taba hawa tayiba Koda suka shiga ckn jirgi akusa da juna suka zauna Kujerarsa na kusa da tata Idonta akasa bata iya hada ido dashi don kunyar abinda yafaru da kuma biyayya Yakalleta yadauke kai yana so yai mata magana amma yarasa me zaice mata don baya son tana jin kunyar nan tasa shikam tana burgeshi amma baya son kunya shi faranse ne wayyayye Gani yake duk kauyancin nan da zatayi masa bazasu shiryaba domin saiya wayarta kada tabashi kunya irin nayau Da aka kawo musu abinsha kin dauka tayi saida yadaka mata tsawa "Ke Dauki mana meye na kunyar! Tasa hannu ahankali tadauki lemon taja ta rike takasa budewa Yana kallonta tagefe taki budewa kanta akas! Saida yashanye kana yakalleta yace "kawo inbude miki. Ta mika masa ahankali Yabude mata na gongwanine me gas Taringasha ahankali kusan awa guda kafin tagama Anyi rabin tafiya Tafara bacci takwanto da kanta kan hannun kujera yatsura mata idanu yana kallon kyakykyawar fuskarta da dan bakinta yaji kamar yakai hannunsa yashafata saidai yana gudun kada tafarka Can bacci yai mata dadi saiga kanta ajikinsa Yarasa yazaiyi da ita saboda mutane nakusa dasu suna kallonsu Haka yabasar bai motsaba gudun kada ta farka takasa komawa ******* Koda suka Sauka a England Kaitsaye suka hau mota ta haya har gidansa Tamfatsetsen gidane da maimartaba yasiya don kawai insunzo karatu suzo suzauna ackn sa Daki guda mekyau da tsari yakaita yace mata nanne inda zata ringa kwana Dayake kayan jikinta riga da zanine tasanya hijabinta hannunta rike da carbi Tazauna zagwade abakin gado tana so tayi sallah gashi bata san yazatayiba nafarko bata san inane gabas ba gashi Bandakin yawuce tunaninta batasan yanda zata sarrafa ruwa yazubo ba gashi ba agogo adakin Data gaji da zama saita futo falon domin tambayarsa Ta dade afalon azaune bayanan yana ciki tajiyoshi yafito daga wanka Tananan zaune harya kintsa yafito Yakalleta yace "Ya kika baro dakin kika dawo nananan Qalau ko? Tace "Dama, Alwala zanyi inyi Sallah to bansan yazanyi ruwa yaxubo ba kuma bansan ina zan kalla ba gashi lokaci nakeson gani Ya koma ciki yadauko mata agogon bango yadawo yace mata "Taho muje. Ta biyoshi abaya har dakin da yace natane Suna shiga ya ajiye mata agogon Akan mirro me lado ladone xata gane shi Yashige bandakin yana kiranta Tabi bayansa yaringa nuna mata yanda zata kunna komai takashe ckn Sauki Da yanda zatayi wanka da shaya dakuma yanda intayi kashi zatayi fuloshin da duk abinda yasan dai zai gagareta Saida ya tabbatar tagane komai kana suka dawo dakin yanuna mata Gabas sannan yace mata inta idar ta jirashi xaije yasiyo musu abinci yadawo Kafin yadawo kuwa tagama komai don har wanka itama ta sallo ta maida kayan jikinta taxauna ta takure agado tana jiransa don yunwa takeji Daya dawo yashigo yakawo mata abincin na take away sannan yabata wata ledar kaya yace "Ga kayan sawa nan kala biyar na Siyo miki kafin nakaro miki wasu gaba Takarba da biyayya tana godiya Daya fita yabarta tacinye abincin tas tana santi kunnanta kamar yacire Tayi mamakin ma data iya cin wannan kalar abinci domin a ido dai yaburgeta dama gashi abaka ma gwanin dadi bata taba ganin irinsa ko a hoto ba Ta wanko hannun tasha ruwa sannan tazo ga Ledar ta zaxxage kayan tana daddagasu daya bayan daya tana mamaki da yatsina fuska domin kayan basuyi mataba Asalima tayi tsammanin ko canzan leda sukayi da wani domin kayan bana sawar "yar musulmi bane Itakam ko da kudi bazata taba sasu ba rigunan "yan bigil suke kanana wanda in an saka zasu damewa mutum jiki Ga Wanduna pensil ga "yan gajerun wanduna sai siket masu roba iya cinya da riguna marasa hannun harda bes tashan iska kayan sunyi kyau Ga masu sawa Amma๐Ÿ˜‰๐Ÿ˜Š Ta maidasu cikin ledarsu tana mamakin wannan kaya ai baxata taba iya sasuba haba aiko batada kunya wannan kayan sai a gidan mijinta yaushe Sai bayan wasu awanni yashigo mata don ganin ko qalau take Yana zuwa yaga kayan akusa da ita yahau tambayarta "Baki bude kayan bane?nakine fa nasiyo mk yakamata kigwada ma ingani don inga wanda sukafi miki daidai sbd xankoma siya miki irinsu nan gaba. Tace aranta "Aiki game k'areka. Afili tace "kayi hkr nagansu baxan iya Sawa bane sunyi kanana dayawa. Yahade rai baya son kauyanci da Raini fa Yace "akan wane dalili tokisani nanba gida bane baxakiyi kauyan cinnan nakiba dolene kisaka su don awannan garin baruwan wani da wata dankin saka bame kallonki balle yaga laifinki kuma bazaki taba samini wadannan riga da zanin naku nagargajiya ba dan haka maza kisaka su ingani nabaki minti biyar ina jiranki afalo Yana gama fadin hakan yajuya yafuce Wani qululun bakin cikine yatsaye axcyr *KUYANGA* TABBAS tun daga yau tafara nadamar xuwa Turai lallai inko haka zata ringa shigar kayan arna gara bataxoba Gara kuma taita zama dana jikinta Tasaka kayan agaba tana kallonsu data kalli agogo taga saura minti biyu lokacin daya bata yacika saitayi saurin tashi ta janyo ledar taciro wata riga me karamin hannu tacire ta jikinta tasaka dakyar Sannan ta sille zanin tasaka wani dogon wando Bata iya cire dankwalin kayan ba tabarshi akan nata don kada yaga gashinta Takalli kanta a madubi Ai dasauri ta rintse idonta tana fadin "innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Yanzu haka xanje gaban namiji?yanzu haka zanje gareshi yagannin nashig uku yau naga takaina ๐Ÿ™†๐Ÿผ meye mafita โ€ฆโ€ฆโ€ฆโ€ฆโ€ฆโ€ฆ? *Fans kugaya mata mafita* ๐Ÿ˜‚ *Auntyn Sayyada da Shahida ce* ๐Ÿ‘Œ๐Ÿผ [7/23, 10:28 AM] Ummi Tandama: ๐Ÿ“ฟ *KUYANGA...* ๐Ÿ“ฟ *_๐ŸŒˆKAINUWA WRITERS ASSOCIATION_* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *Dis Page i dedicated to my lovely Sister *NABILA RABI'U LADY* a writer of *BANI BANE* Always i solute you my Namesake. oh my Lord! bless her and help her everythings *Nabilancy Luv* ๐Ÿ’˜ (Auntyn S&S) 15-20 *KUYANGA* Tak'ara kallon kanta a madubi taga agaskiya bazata iya futa gaban Yarima ahakaba ai taxama mara kunya kenan inhar yaganta ahakan..."bashi yabaki umarni daki sakaba " bashi yakawo miki don ki sakaba? Wata zuciyarta tace mata Azancen gaskiya kayan sun mata kyau domin wandon yamatseta tsam !dam! Yafito mata da shap sosai abin gwanin burgewa dai Ga rigar ta kamata tamkar ajikinta aka kirkireta dama ita ba ma,abociyar saka bra ba saiga nonuwa tsaye tsar ! Me sifar kan tasa ga nipple nan tsir ya nuna kansa Ita kanta abin bai mata tsari ba balle kyangani domin sifarta tafito tamkar komai awaje yake To yata iya inhar taki futa taje gun nasa zaizamo hakan tamkar ta bujirewa maganar sane sannan umarni yabata ba zab'i ba Kuma ita din akan bin umarninsa take zaune sannan babu musu ko k'iwa atsakaninsu akullum ita din baiwa ce makaskanciya agunsa *KUYANGA* me hidimta masa Ta tuno kalaman mahaifiyarsa da take ce mata "DUK ABINDA YA UMARCEKI DAKIYI KIYI MASA DONKI FARANTA MASA KECE MEYI MASA KOMAI ME KULA DA KOMAI NASA Saikuma ta tuno da kalaman masoyinta MAHBUB da yake ce mata "KADA KIBARI AZALINCEKI KADA KIBARI ACUCEKI SBD KINA AMATSAYIN BAIWA KADA KIYI ABINDA BAI DACEBA ACKN BIYAYYA. ta rintse idanu tana kwalla tana fadin "MAHBUB kayi hkr gashi anfara, zankuma karya maka doka Zanyi biyayya ga abinda bai daceba zanbi umarnin uban dakina. Tana gama fadin hakan tafuce gurinsa Yana zaune afalon yadora kafa daya kan daya yana latsa waya Tun daga nesa yakura mata idanu itako kanta na kasa Saida ta isa dab dashi tadago kanta taga ashe shid'in ita yake kallo saiTaji wata kunya ta mamayeta Yai saurin kawar da ganinsa daga kanta yace "Very nice sunyi mk kayan daga yau sune Kayan sawarki kada nakara ganinki da zani domin nanba kauye bane ina mu,amula da wayayyu bazanso suga dawa nake tareba inhar ba kin kile ba tunda duk bakon danayi saikinzo kinyi masa hidima Ta gyada kai kawai Yace "oya muje kicin na nunnuna miki kayan amfanin da zaki ringayi akullum. Ya wuce gaba tabi bayansa ad'arare Yaringa nuna mata abubuwa komai har gas yanuna mata yanda zatayi amfani dashi domin acan gidan sarauta Manyan bayi ke girki ba yaransuba Balle su iya komai su k'ananan Bayi saisun kai munzalin Aure ake fara Trenasu Saida yaga ta kwashe akwanyarta na wasu abubuwan kana yace suje su zaga gidan domin can ma akwai abinda zai nunnuna matan Tana gaba yana bayanta yana karewa mazaunanta kallo Yawu yake had'iya kawai domin yasha Mamaki aransa yarinyar ta da ita amma komai yaji ๐Ÿ˜‹๐Ÿฅด Yakaita gurin shukoki don yace ita yakeso taringa basu ruwa kana yakaita gaiding nanma yace hurumin tane Cai !! ๐Ÿ™†๐Ÿผ ashe zaki wahala *KUYANGA* Yakaita yanunata ga mai gadinsa domin su san juna sosai tunda ita zata dawo girkin gidan zata ringa bashi shima Au ainaxaci gadinma ita zatayi ๐Ÿ˜‰๐Ÿ™„ Kwanan *KUYANGA* Biyar agidan takwashe komai akwakwalwarta ta iya kunna gas tayi masa sassaukan girki takan mikawa me gadi intayi Girkinsa bai wuce indomie Cuscus da suyar dankali da doya da kwai sai sauran abubuwan da basuda nauyi masu Saukin yi D'an wahala shiyasa bakada k'iba ๐Ÿ˜ iyakarta dakinta in yana falo bata yarda tafito inba abinci zata kai masaba shima a kunyace take zuwa sbd kare mata kallo yakeyi duk kayan kuma data sanya saiya furta cewar sun mata kyau Magana me tsayi bata hada su to me zatace masa ? Bayaga ina kwana ina wuni sai tambayar wani abun kuma ******* Cikin Sati biyu yazamto tafara sabo da komai hatta kayan datake sawa matsatstsu yazame mata jiki tasaba dasu tunda yakaro mata wasu yakawo mata dayawa Tun tana kunya inta sakasu harta daina Yakawo mata manshawa masu kyau da man wanke kai da sabulai nagyaran fata dai Tana tsafta sosai tana gyara kanta dayake tanada tsahon gashi da cika saidai kullum yasha gyara ko tayi masa manyan kalba ta bazo jelar kalbar baya aiko takanyi balain kyau dama ga fuska kamar ba india sosai kyanta yanata bayyana don hutu yanata shigarta ba koina take zuwa ba kullum bacci daga dakinta sai kicin sai falo Sai intafuta kaiwa me gadi abinci ko aikin farfajiya Zaman gidan yafara damunta to amma bayanda zatayi tunda baice tazo tafuta wajenba aibaxata iya futa batare da izinin saba Yakan futa tun dare sai tsakar dare yadawo tarasa wane aikine haka kamar na barayi Hhhh bakisan club yake zuwa ba kenan to zauna wataran zaki sani๐Ÿ˜… wata ranar Lahadi tana Daki akwance tayi rub daciki tanata tunanin masoyinta MAHBUB Tasan akoina yake yanzun hakan yananan da kewarta Kawai taji yashigo mata ba sallama Ta tashi da sauri tace "Sannu dashigowa akwai abinda kake bukatane? Yaja yatsaya yaruke murkar kofa yace "kitaso maza kidafa abinci ga bakina nan zuwa gidannan "yan Nigeriane amma anan suke karatu Abokina ne sosai Shi d'in Jinin Sarautane kitsaya kinitsu kiyi abinci me dadi bawai bamuda inda zamu ciyo bane akwai hotels kawai dai yafison abincin gidane nasan sa sarai Ckn ladabi kai akasa tace "to angama. Yajuya yafuta yana karewa "yar shimin dake jikinta kallo wanda agaban rigar aka rubuta *HOT KISS!* Da manyan Harufa adaidai lokacin da bak'in nasa sukazo adaidai lokacin Allah yabata sa,a tagama komai Har juice ta hada na mango da Banana da kayan fruit dai dayake yakawo komai yasaka afurji Itako akwai basirar iya yin komai wani abunma ba koya tayiba datayi nazari aranta tsaf zata hada *Tab kaga KUYANGA "YAR Baiwa* ho Allah yabamu yataki zeenatu ๐Ÿ‘ Tayi musu sallama falon yarimane sai bak'in su biyu kawai kallo suke suna hira Bakin suka bita da kallo Ta dire akan table tareda durkusawa tagaidasu Yarima yana kallon yanda suketa kallonta Saida takoma ciki Yarima yakaiwa nakusa dashi duka yana fadin "kai SAHABI kashiga hankalinka wannan kallo haka na miyene? Wanda aka kira da SAHABIN yakyalkyale da dariya yace "yo mutumina ai abu nagani kamar Zinare agidanka tabbas inhar zai dauku saina daukeshi. Yarima yasake kai masa bugu "dan ubanka wannan ba kalar taku bace kafi karfinta *KUYANGA* Ce fa da ita nataho ita tadabance ackn BAYIN ma SAHABI yace "kai anya kuwa zanyarda da batunka ace wannan *KUYANGA* CE tabbas ackn kuyangun ma ta dabance kaga halitta fa ga kyau ga cikar halitta Ga kumaโ€ฆโ€ฆโ€ฆ Yarima yarufe masa baki yana fadin "basaika karasaba abar maganar akoma wata wannan munwuce ajinta. SAHABI YACE "kaga yarima kabarni nikam wannan tayimin ta furgitani dayawa domin ko ackn KUYANGIN gidanmu bantaba ganin mekyau irinta ba ASHRAF da sukazo tare ya bushe da dariya yace "Kai SAHABI kadai tafi dayawane Plz cool your mine kada kafara ma you are handsome and gentle fa karike girmanka dai. Yarima yace "yama fara mana nikam dai bazan yardaba badani a wannan abin kunyarba domin yafi karfin ajinta shima yasani SAHABI YACE "Kai! yarima bangane bafa kodai dama kaine aciki.? Yarima yaja wani mugun tsaki yace "Allah yakiyaye niko mezan da wannan kamanta nine? ko a mata cikakku ba kowacce nake kulawa ba balle ackn Bayin gidanmu haba Abokina Me Yarima irina zaiyi da *KUYANGA* Yahau bude abincin Duk Dan abar maganar yana fadin "Kufara cin abinci tukunna dai. Anyi haka da kwana guda yacimmata har daki yace mata "Ke Daga yau inhar kinjini da baki kidaina Saka kananun kayan dana kawo miki Tace "to, amma babu wasu dazansaka sai wanda mukazo dasu kuma sun tsufa Yace "bakomai kisasu ahakan inzaki fito gun bak'ina kafin asan abinyi Ckn ladabi ta gyada kanta alamun xatabi umarnin Ammafa ta dade tana tambayar kanta shin ko meyasa yace mata hakan? Toko tayi ba daidaiba ko sunyi maganar dasu akanbai dace bane ? Dayake dai batada Amsar tambayar sai muje zuwa โ€ฆโ€ฆโ€ฆโ€ฆ *Auntyn Sayyada da Shahida ce* ๐Ÿ‘Œ๐Ÿผ [7/24, 8:15 PM] Ummi Tandama: ๐Ÿ“ฟ *KUYANGA...* ๐Ÿ“ฟ *_๐ŸŒˆKAINUWA WRITERS ASSOCIATION_* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *NABILANCY LUV* ๐Ÿ’˜ (Auntyn S&S) 20-25 Ranar wata lahadi Tana mopping a falo daga ita sai 3quater da body hug me karamin hannu kanta da kallabi bata taba yarda tabar kanta abude ba sbd akullum lokacin tana gida sai MAHBUB Yahaneta da hakan Wakarta takeyi ahankali tana Dan motsa kafada *SAI WATARANA MASOYI ZANBARKA SAI WATA RANA INA MAKA BANKWANA* _bankwana_ ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ *ASHE SABO YANADA DADI* ๓พ ผ๓ฝฐพ๑   *AMMA IN ZA.AI RABO DA ZAFI* ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ *MAHBUB NATAFI NABARKA...BANSAN HALIN DA KASHIGE CIKI BA.* _Bankwana_ ๐ŸŽป๐ŸŽง๐ŸŽบ๐ŸŽธ ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ tahau goge hawaye domin wata kewar MAHBUB ce tazo mata shiyasa take masa waqa Ashe duk abinda takeyi Yarima yashigo yana bayanta yajingina da bango yana kare mata kallo ga muryarta ta masa dadi ga shigar da tayi ta fusgeshi domin wata sha,awarta ne yashigeshi lokaci guda Saida tagama tajuyo zata bar gurin da tsumma da mofa ahannunta kawai taja tunga kanta akasa tana masa barka da shigowa wata kunyace ta lullubeta domin tasan yaji irin waqar da takeyi Yayi gyaran murya bayan amsa mata da yayi yace mata "kishirya anjima zaki rakani wata unguwa. Ta gyada kai tana amsawa da "to. Tagama shirinta ckin wata doguwar riga daya hado mata dasu ckn kaya da siririn mayafi Tayi kyau ainun tamkar balarabiya tafuto sak Yaleko yace ta futo sutafi Takwas ta wuce alokacin wani Store suka fara zuwa *ROYAL STAR* Yajibgo kaya aleda yabata tarike suka fito Yakarbi kayan yasaka a boot Tashiga gidan gaba Yaleka fuska ba fara.a yace mata futo kishiga gaba niba Drivern ki bane. Ta futo sum sum tashige gaba domin itakam kunyar rabarsa takeji tanajin nauyinsa tafi son bayan domin tana shiga takura takuma fi son taringa nesanta dashi Suna tafe suna saurarar wakar Nancy Ajram ackn motar daya kunna yana son wakokinta sosai Yakatse shirun da watso mata tambaya "Zeenatu! Wanene MAHBUB ne? Kuma meye alakarki dashi? Tahau sinne kai ahannunta tana in inar magana yace mata "alamu sun nuna masoyin kine kenan.? tayi masa shiru fuskarta dauke da murmushi Yace "Amatsayinki na *KUYANGA* Meye ribarki in kika Auri *BAWA* ? ranta taji ba dadi kalmar batayi mata dadiba tunda aiduk mutanene kuma Allah ne yayo *KUYANGA* yayi *BAWAN* Dayaga batada niyyar magana saiyaci gaba "Wato nafuskanci kina cikin soyayya kuma kina ckn kewarsa ko? Inban mantaba naganki aranar da zamu baro gida kina daga masa hannu. Anyi hakan? Ta daga kanta Ya d'aga kafad'a yace "Well Zancire miki kewarsa domin kiji farin ciki ayau. Itakam bata ce kanzil ba domin bata fahimce shiba sam Kaji sokuwa hhhmmm muko fans mungane ๐Ÿ˜… dayaga taki cewa komai saiyace "Zan baki farin cikin da Saurayin naki yake baki domin farin cikinki....Ta dago da sauri tasadda kanta akasa ckn mintina kwakwalwarta tahau aiki to me yake nufi kenan soyayya zaiyi da ita? "Bawai zamuyi soyayyar da kukeyi dashi bane zandai ringa debe miki kewarsa da baki jin dadi Gabanta yaringa bugawa ina sam.!bazata iya ba yana ubangidan nata?ba da itaba Dayaga batada niyyar magana dai saiyakyaleta yaci gaba da tukinsa yana kallon waje yana kiyasta tayanda zaibi da ita don da alamar zatayi duhun kai awannan harkar Saida yabiya da ita ta club dinsu Ya ajiyeta agefe yace tajirashi Taita kallon mata da maza anata cakud'ed'eniya ana ta shan giya da masu shan sigari Saikaga mace acinyar namiji suna manne ana tsotse tsotse ba ruwan wani da wani acan gefe guda wasu sunata rawarsuanne ajikin samarinsu wasu acan kan filo ana dance Abin mamaki yabata duk da kasar masu jan kunnece akwai musulmai bakake agun kuma har dasu ake wannan harka Daga nesa ta hangoshi da wata mace yana mata kiss agoshi sannan ta rumgumeshi suka rabu tana dago masa hannu Kafin yakaraso gunta saiga wani bature duf!agabanta ya tsaya dab da ita yana mata magana da harshen turanci To dayake bawani ji take sosai ba don kadan kadan takejin turanci tsintar binda ba.a rasaba takeyi daman tunda ana musu daraci da islamiyya da bangaren koyarda harshen turancin duk ackn gidan Sarkin Ta juyar da kanta Aiko dai wannan bature yai gangancin kama hannunta yana mata fara.a Yarima na zuwa ya fuske hannun nata sannan ya wanke baturen da mari A furgice baturen ya ranta ana kare domin yai tunanin ko mijin tane yadawo gunta Tashige motar da sauri gabanta na dukan uku .uku Saida suka fara tafiya sannan yace mata "ke bakida hankali zaki kulashi dahar zai rike miki hannu. Tace ahankali "bansan yaxo gunba walh kuma kafin inyi masa magana yarikoni. Yaja tsaki kawai ransa na msa quna baisan daliliba Amaimaikon yawuce gida saiya nufi wani makeken hotel da ita Saida yakama daki sannan yace ta biyoshi Yabude dakin da key wanda ke a saman hawa na biyu Dakin babbane daya jal amma ahakan VIP ne domin yakawatu yaji kayan alatu ga komai nan daka danna wata tarho ma,aikata zasu iso maka da gaggawa Gadone makeke da mayan kujeru adakin duk sunciye ga furji da toilet ack Ya kwanta akan gadon yana nishi waishinan yagama gajiya Ta zauna akan kujera tana kallonsa Yakalleta da ido guda yace Zoki daddanna min jikina Ta mike ahankali ta tsaya akansa Yacire kayan jikinsa dagashi sai gajeran wando da bes Hankalinta yadaga ganinsa ahaka tunda take bata taba ganin halittar namiji abayyane ba saiyau domin yar bes dinma cireta yayi Tayi kas da kanta gabanta na faduwa domin jikin yarima na dabanne akwai gargasa ga kwanji ga cikar halitta Ya janyota kan gadon yana fadin Matso sosai kiyi min tausa bacci xanyi Batace komaiba tahau yi masa cikin biyayya ba musu Yalumshe idonsa wani magana disu na shigarsa Tabbas abubuwa sun gama motsa masa babu abinda zai hanashi jin dadi ayau dama tun dawowarsa Kasar sau daya yayi da wata baby Rihanna tayi tafiya karuwar tasa Tuni yabirkitota jikinsa yana neman zille mata rigar jikinta Gabantane yaci gaba da bugawa tana addu.a ckn ranta domin dai tasan tashiga hannu babu me kwatarta sai Allah sannan bata isa tayi masa musun komai ba ayau sai alokacin ta tuno kalamansa na ckn mota wato nufinsa zaisha mintinta amma ba soyayya zaiyi da ita ba To ai ita gara suyi soyayyar yabar mata mutuncinta Hawaye taji zai taho mata tayi saurin mayar dasu don kada yagani yazaci zata bujire masane Itako kanta take tausayi ayau tasan batada mafita sai Allah....โ€ฆโ€ฆ ๐Ÿค” tabdijan Fans akawo mata taimako [7/24, 8:16 PM] Ummi Tandama: ๐Ÿ“ฟ *KUYANGA* ๐Ÿ“ฟ *_๐ŸŒˆKAINUWA WRITERS ASSOCIATION_* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *Wannan Page Sadaukarwane kyauta sukutum ga Takwara takaina wato NABILA DIKKO* marubuciyar *DANGIN MIJI* _ina jinjina miki inayinki irin Sosai dinnan Alherin Allah yakai inda kike yakuma kawo mana Daukaka da tsari mu 4 Stars Writers_ *Nabilancy Luv* ๐Ÿ’˜ (Auntyn S&S) 25-30 Tanajinsa ya hau sille mata kaya tareda shafata ahankali salo salo Yahau shinshinarta kamar wani kare ko mage Itako tayi lakwas ranta baya so amma takasa motsawa don gudun bata masa Yaringa wasa da sassasan jikinta axuciyarta addu,a kawai takeyi akan Allah yakawo mata dauki Harya cire wandan jikinsa kuma sai yaji wata Izza tashigeshi yaji aikwata kwata bai dace yakusanci baiwarsaba domin hakan zai iya kawo masa ragin Aji Ya turarta gefe tareda tashi da sauri yahau zira kaya yana fadin "maza tashi kisaka kayanki mutafi Ckn Sanyin jiki ta mike ta fara maida kayanta ajiki tana godiy ga Allah daya kubutarta Koda suka baro hotel dinnan kai tsaye gida yamayarta Da dare saida yadawo Club yasami mata yazaba ciki tareda diddikar giya son ransa yasha yayi tatil sannan yakebe da mata Bai dawo gidanba saida tasakeshi giyar Wajen 4 na asuba yadawo Duk bidirin da yakeyi nafutar dare da yawon dare bata ramfo abinda yake fita yiba Duk azatonta ko wani aikin yake futayi tunda bata sanin lokacin dawowarsa ******* Da Safiyar wata juma,a Yarisketa akicin tana kokarin dora masa abin kari Yayi gyaran murya tayi saurin juyowa Ta durkusa ta gaidashi ya amsa fuskarsa ba fara,a Yace mata "kishiga kigayara min dakina Kitabbatar kingyara minshi tsaf domin yayi kura goge koina Domin Bakuwa zanyi Ta gyada kai tana fadin "angama Ranka yadade. Yafuce yabarta tana ci gaba da abinda takeyi Aranar ta wuni aikin gyaran dakin nasa bata taba shiga ba sai ranar Duk yanda yake kwalliya da kwalisa da izza da d'agawa irin na Jinin Sarauta amma dakinsa cikin datti yake gado kawai yake hayewa yakwanta tun xuwansu duk da satinsu biyu baisa ta shareba saiyau Damasu maza aisai a slow sungaji hakan ๐Ÿ˜… Saita hau tunanin ko wacece hakan da zatazo lallai tanada babban matsayi agunsa tunda har asbd ita akeyin gyaran dakin Ta goge koina ta gyara dakin tsaf tafeshi da Air freshner me dadin kamshin Splash Harta juya zata futa kuma saitayi tunanin mezaisa bazata bude d'an furjin data gani adakinba ko shima cknsa zaibukaci gyara Tadawo da baya ta budeshi Aiko wani wari yabugi hancinta Tayi saurin toshe hanci Kwalabe tagani wanda bata fahimci kona meye ba Saida tahau fito dasu tana dubawa tafara gano kona meye A iya fahimtarta kwalaben giyane taga anrubuta *WISKY* da manyan harufa sai wasu datagani sunfi yawa agun anrubuta *ORIGINAL ALCOHOL* Tahau gyada kai tabbas giyace! Ta maidasu inda suke ashiryensu Takama baki tana mamaki da zancen xuci "Yanzu dama giyar da aketa cewa yana sha da gaskene? Lallai wannan ya iya takunsa Allah yashiryaka. Ta mike tsam tafuta abinta Sai dare yadawo gidan amma bashi kadai tajiyoshiba Ta fito da sanda tarabe a wata siririyar hanyar dazata sadaka da falo ta hanyar dakinta tana hangensa yashigo shida wata siririyar baturiya da kananun kaya ajikinta sunshige dakinsa Ta tsaya kem agun tana Allah wadaransa Aranta domin yarima dai ba hali ga bin mata ga shan giya tabbas Duk wacce ta Aureshi batayi dace da uban "ya"yaba Sarkinsu adali me kyan hali Allah yajarabcesu da D'a mara kyakykawar zuciya Takoma daki abinta tana tuno masoyinta MAHBUB ko yaushe Allah zaiyi komawarsu gida taganshi!? ****** Da safe tagama abin kari takai musu daining table Dankalin turawa ta soya da kwai sai shayi dayasha kayan hadi data dafa taxuba a flask Takoma daki abinta Basu fitoba sai karfe 11 daya suka fito tana rike dashi ajikinta Tare suka ciyar da juna tana bashi abaki yana bata Rihannah kyakykyawar baturiyace wacce itace mace kadai dayafi so tafi kuma gamsar dashi Tasan salo salo da luggar gamsar da namiji Macece me tsananin kishin tsiya saita kashe mutum akan kishi Tunda suka fuce basu dawo ba sai dare daga yawon su Yatarta da *KUYANGA* adakinta tana bacci Yabubbuga mata kafa ta farka afurgice ta tashizaune tana mitstsika idanu Yace mata "nazone don inja miki kunne akan kada ki sake kiringa futowa alokacin da kikasan bakuwata na nan banason taganki zamu iya samun matsala da ita. Tayi saurin gyada masa kai Yajuya yafuta yana waiwayenta domin tayi masa kyau ga surarta tar wacce yake tsananin kwadayi ckn wasu kananan kaya ****** Duk yadda yake gudun RIHANNAH kada taga kuyanga saida aka sami akasi taganta domin kwananta uku agidan akai kicibus a falo Tafito tabaroshi adakin xatayi kallo ita kuma *KUYANGA* Tafito Zata dauki Abinta akicin kuma dole saita sada kanta ta falon tunda dakinta atsakiyar falon yake yana kallon nashi Kallon kallo aka hauyi Ita *KUYANGA* Ba damar yin magana gashi gabanta na dukan uku uku tana ganin tasab'a doka gashi Ba turanci take jiba balle tagaidata ckn harshen turancin RIHANNAH Tayo kanta tana fadin " _hey girl what Are you Doing here_ *KUYANGA* Tasadda kanta kasa jikinta na kyarma RIHANNAH takarewa kuyanga kallo taga yanda yarinyar tahadu ga kayan jikinta ya amsheta wandone pensil da riga b'igil me siririm hannu ajikinta kanta ba kallabi gashinta yakwanto agadan bayanta RIHANNAH Ta fuxgota Tana ihu kamar zata cinyeta don kishi " _When are you coming This house_? *KUYANGA* takara furgita ta kankame jikinta takasa magana tunda bata fuskanci mema takece mataba balle tabata amsa RIHANNAH ta gaura mata mari tana fadin " _are you mad_? _If you talk me Rubbish i will kill you now_ ganin *KUYANGA* Batada niyyar magana yasa taga kamar raina mata hankali takeyi Tashakota ta hadata da bango Ihu da kakarin da *KUYANGA* Keyi yasa YARIMA dake can dakinsa kwance yasa yafito aguje Yana ganin abinda ke faruwa yayo kansu aguje yakwaci *KUYANGA* Ahannun RIHANNAH yatura *KUYANGA* Gefe yana fadin taje maza dakinta RIHANNAH ta cakumeshi tana masa ihu akan saiya gaya mata wacece tagani agidansa Yazabga mata mari saida taga taurari Agigice ta sakeshi tana rike da gurin taji marin har kwanyarta tahau kuka tana tumami agurin Yawuce ta afusace yayi dakinsa Ta tashi tabishi tana cewa saiya kori yarinyar kokuma ita tabar masa gidan Tasan yana sonta sosai shiyasa take fadin hakan Amma agun yarima wannan ba abune dazai yiyuba yama xa.ai yakori *KUYANGA* To inya ma koreta ina zataje itada batasan kowa akasar ba shine dalilin xuwanta ai inhar yabiyewa son zcyr yabi zabinta tabbas zai aikata kure domin sai ya fuskanci bacin rai gun mahaifinsa inyaji toko mahaifiyarsa da bata son bacin ransa itanma ai baxata barshi ba Dayagaji da hargowar tata saiya zare belt yaringa dukanta ko ta kyaleshi Ranta yabaci da irin hukuncin da yayi mata wanda bata xataba Kwana tayi tana faranta masa rai domin sau biyar yahauta kafin wayewar gari domin ita din jurauce itace tayi masa sabo da ZAZU ๐Ÿ˜… "Oh!SU Rihanna yau ga karshenki sai akara gaba ๐Ÿ˜› Itadai *KUYANGA* tana jiyo ihunta ana dukanta saita kara cika da tsoro taji kuma baiburgeta ba domin shine yajawa kansa dabaya dauko mata da bazasuzo suyi masa hauka agidaba. RIHANNAH bata kwana agidanba tuni ta fuce da ita da komatsanta tayi fushi dashi sukayi baran baran aranar โ€ฆโ€ฆโ€ฆ *Hhhhh muje zuwa* Auntyn Sayyada da Shahida ce๐Ÿ‘Œ๐Ÿผ [7/25, 3:33 PM] Ummi Tandama: ๐Ÿ“ฟ *KUYANGA* ๐Ÿ“ฟ *_๐ŸŒˆKAINUWA WRITERS ASSOCIATION_* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *SHARHI*.... *ZUWA GAREKU MAKARANTAN LITTAFIN KUYANGA INASO INYI MUKU WANI DAN TSOKACI MUSAMMAN MASU YAWAN KAWO NASU RA,AYIN AKAN KUYANGA TOKU SANI BAWAI INA KUSHE GA BATUNKU BA INASO KUBARNI DA NAWA RA,AYIN NAYANDA NA DAUKO ABUNA, AKWAI MASU CEWA KIYI KAZA GURI KAZA!KADA KIBARI YAYI MATA KAZA!KYANTA DAMA KISAKA TAYI KAZA KO YAZAMO MEYIN KAZA!!! TO DUK INASO KUZUBA IDO KUGA KARSHENSA WANDA YAGA ABIN HAUSHI MA YACE ABIN BAI MASA BA ZAIDAINA KARANTAWA INBAN YI KAZABA DON BAI DACE BA TO FALILLAHI HAMDI NI DAMA BANYI DAN INMUKU DOLE BA DOMIN INHAR NABI TA BAKIN WASU TO LITTAFINA ZAIYI KWANA NE YATAFI LABARIN WATA MARUBUCIYAR TONIKUMA BANA FATAN INYI SATAR FASAHA YANDA NA DAUKO LABARINA ABARMIN AHAKA DOMIN DIRECTOCIN INDIA DANA KASAR MU NIGERIA DA SUKE HAUSA FILM BA DAYA SUKE DANA INDIYA BA AKWAI BAMBANCIN FASAHA KARYAR MUTUM YAGANO YANDA FILM DIN INDIYA ZAI KASANCE AKARSHE TO NIMA KADA ACANXAN RA,AYI INA KARA FADA WACCE TAGA NOVEL DINA YABATA HAUSHI AKAN STAR MACE KO NAMIJI ANYI ABINDA RANTA BAISOBA TABAR ABIN ARANTA BASAITA FURTA MARA DAD'IBA INA K'ARA JADDADA MUKU BABU FA DOLE.DOMIN KUYANGA YASAMI DAUKAKAR DA BAZAI FADUBA, KALAS*!!!! _tank you fans inayinku yanda kuke yina Allah yabar kauna_๐Ÿ’‹๐Ÿ’˜ *Nabilancy Luv*๐Ÿ’˜ (Auntyn S&S) 30-35 Da daddare *KUYANGA* Tana kwance taji shigowarsa dakin nata Tayi saurin tashi tana masa Barka da dawowa Ya xauna bakin gadon nata yana mata murmushi tare da Amsawa Tayi mamaki domin bata xaci zataga fara,arsa ba ma tunda tasan ta karya masa doka tafuta alokacin dayace kada tasake tafuto in RIHANNAR tana nana gashi harsun sami sabani adalilinta tsorone ma yadarsu aranta tana tsammanin ko fada yazo yi mata Ta takure jikinta agefen gadon Daya fahimci atsorace take dashi sai yasha mur yace "meye kike wani matse jikinki wato kina ganin ko wani abu nazo miki ne? Ko a hotel kyaleki nayi bawai hkr nayiba yanzu kuma ba zuwa nayi na taba kiba tunda kinyi sanadin barin me debe min kewa gidan dole yazamo kece zakici gaba da deben kewar tunda dama dan hakan nataho dake bawai donki dafan girki koki gyaramin daki nake zaune dakeba don inji dadin rayuwa ta dakene dan haka kizama cikin shiri zuwa daren gobe yau ba,a gidan xan kwana ba inada Dinner din wani abokina till down kwana zamuyi acan. Yana gama fadar hakan ya mike yafuce yabarta da fargaba aranta Zancensa ke mata yawo akwanya tome yake nufi? Nufinsa kenan zai maidata farkarsa innalillahi wainnailaihirrajiin Allah kayimin tsari da aikata zina. Tarintse idonta wasu zafafan hawaye suka hau mata xarya akuncinta MAHBUB ne yafado mata aranta domin akullum insun zauna a inda suka saba zama aikinsa ne yi mata Nasiha da wa,azi akan kamun kai ga mace dakuma tsare mutuncinta Yanzu kenan yana nufin agoben zai santa a "ya mace ? Batada tsumi bata da dabara domin ita baiwace agareshi dolene tayi masa biyayya fatanta dai Allah yatseratar mata da mutuncinta kawai kada yayi sa.ar abinda yake da kuduri akanta Da safiyar Allah Ta tashi da Zazzabi fargaba ce da tsoron abinda xai faru da ita yasanya mata zazzabin Bata iya futowaba sai shadaya na safe ta mike dakyar ta nufi kicin don neman abinda zatasaka abakinta Dafe take da kanta bari guda na mata ciwo ga jikinta zafi rau kashinta kamar ana kwankwatsarsu Wani jiri ne yakwasheta ya yarda ita afalon bata san inda kanta yakeba ashe suma tayi ma ๐Ÿ˜ณ๐Ÿ™„ Allah cikin ikonsa sai ga SAHABI abokin Yarima yazo nemansa gidan Yana shigowa falon yai kicibus da ita ayashe ba nunmfashi Ya isa gareta da sauri Yana tabata yana fadin "ke lafiya kuwa? Meya sameki Yataba kirjinta yaji bata numfashi ga jikinta zafi rau Ai ba shiri ya kinkimeta yai waje da ita yasata amota sai asibiti Shidai megadi yaga shigowarsa kuma yaga futarsa batareda SAHABIN yagaya masa dalilinsa na futa da *KUYANGAR* magashiyan yafito da ita ahannunsa yasata amotar Me gadi yacika da mamaki don dai yawayi SAHABIne sosai yasan matsayinsa ga Yariman da Bazai barshi yafuta da itaba Amma kuma awani barin na zcyrsa yana zaton ko batada lafiya ne zaitaimaka mata tunda yasan dai yarima Baikwana gidanba ****** Dayake Babban Asibitine na kwararru akasar ma sai wane da wane anbata taimakon Gaggawa tasamu kanta tafarko nan akai mata allurar bacci dontasami hutun ko ciwon kan yaragar mata Saida tayi awa uku sannan tafarka ckn ikon Allah kuma bata farka da ciwon kan ba normal tajita Zazzabinma yarage mata amma still dai jikin da zafi kwankwatsar kashin ma yarage SAHABI yasiyo magunguna anbata tasha Yakawo mata abinci Dakyar takeci don yatakura matane Ita tambayar kanta ma tahau yi ya akai wannan mutumin yakawota asibiti?taya suka hadun?bata manta fuskar saba Tagane abokin yarima ne duk da gani daya tayi masa agidan Amma taji yaburgeta yana da kirki matuqa yakuma ceci rayuwarta bazata manta Alkairinsa ba Yakura mata idanu yana hango tsantsar kyan da Allah yabata Tabbas ayau yaji zogin sonta yakara addabarsa Bazai bar wannan damar da Allah yabashiba zai bayyana mata Soyayyarsa gareta tunda dama wancan karan Yarimane yakawo masa tsaiko da dalilinsa mara amfani Tana gama cin abincin yakawo mata ruwa takarba tana godiya Yace "Niya kamata ingode miki. Tayi murmushi tace "ana me zaka goden kaifa kataimakeni ahalin da nake rai ko mutuwa bazan manta da wannan Alherin nakaba nagode sosai. Yayi murmushi yace "ai yiwa kaine yaya sunanki? Ahankali tace " *ZEENATU*! Amma amatsayina na baiwa zaka iya kirana da *KUYANGA* Ya hau girgiza kansa yana fadin "Zeenatu yadace nakiraki domin sunanki me dadine me kuma amfani yanada matuqar ma,ana a musulunci kinganni nan Allah yajarabceni da sonki tyn aranar da Allah yasa naganki agidan yarima yakuma gayamin ke baiwace agareshi shiyasa yahanani inbaiyama miki domin acewarsa matsayina yawuce naso baiwa tunda nidin Dan sarkin Garin Daurane Tayi murmushi tace "Dacewar hakan dayagani yasa yai saurin yi maka Togaciya don kada asalinka ya da ajinka yaragwanta Nima kuma ina me baka shawara akan kacire sona Don bazai maka amfani ba tunda bamu dace ba kaidin da "yar sarki ka dace Yayi murmushi tareda zama agefen gadon yace "ZEENATU nine D'a na uku agun mahaifina SARKI ADAMU wanda kaf cikin "yayansa nine Namiji yafi sona ackn su Ankuma bani mata Amma nace bana so "yar sarkice tana sona banida Ra,ayin in Auri yar mulki ko Sarauta Nafi son in Auri "Yar marasa shi atsarina ma yar talakawa nake so in Aura... Tagyara zama don hira dashi yamata dadi yakuma kara burgeta Tawatso masa tambaya akaro nabiyu "kaiko meyasa hakan? Yace "Zaki sani anan gaba inna Aureki. ๐Ÿ˜ณ tazare ido aranta tace "tab kayi nisa lallai ashe dagasle yake abin naka babbane badaniba. Tace "Dan Allah kacire wannan maganar ma tun wuri kafin yarima yafuskanta zanmayarka yaya agareni abokin shawara inka yarda Yace "To zandau hakan abayyane don kada yarima yagane tunda naga bazai bani goyon bayaba amma azahiri azcy kinanan awacce nakeso nima inaso kidaukeni amasoyinki nagaske azcy kada kinuna amma azahiri mununa mu Abokaine kinji. Ta daga kanta kawai ta gamsu da hakan Wayar sace tahau ruri Yana dubawa yaga Yarima ne Yai picking yana fadin "abokina kana ina haka? Yarima yahau masa fada "Meya kawoka gidana alokacin da kasan bananan wato shiyasa kaki zuwa Dinner din dankazo kadauki Zeenatu kuje yawo ko?bansan zaka nuna halinka ga baiwata ba to walh kasani baxan xuba ido inga kana aikata... "Dakata mallam angaya maka ni irin kane? Yarima yadaga murya kamar zai cinye SAHABIN ta waya "Bazan dakataba harsaika dawo da ita gida nan da minti biyar inba hakaba.... SAHABI Yace" Zan dawo da ita amma harsai likita yasallameta... "What! Meya sameta mekayi mata? Cewar yarima agigice yake tambayar sahabin dan axaune yake sai gashi baisan yamikeba SAHABI Yace "Kai zancewa me kayi mata domin asume nazo nasameta afalon gidanka bata hayyacinta Ni taimakonta nayi nakawota asibiti inzakazo kadauketa saika taho asibitin da muke da file acan wanda familyn mu kezuwa nasan kasanshi tunda kataba xuwa kaima. SAHABI yana kaiwa nan amaganarsa yakatse wayar Yariman yana tsaki Itadai sakato tayi tana jinsu tana kuma mamaki aranta Duk yanda suke amma Yarima saida ya zargeshi toko dai halinsu daya ne? Hhhmmm Allah dai yasa ba kalmar Abokin Barawo barawone ne zaiyi tasiri akan suba...๐Ÿ™„ Sallama SAHABI yayi mata yabar Asibitin domin Yarima yabata masa rai bazaima bari yazo yatarar saba don haushin kalamansa daya gaya masa Koda yariman yazo yanemi Dakin da aka kwantarta Yana ganinta yahau tambayarta meya faru da ita? Ta gaya masa abinda tasani tareda nuna masa SAHABI ne yataimaketa alokacin da take ahalin neman taimakon Yarima yace "toke meya haddasa miki shiga wannan halin.? Tayi shiru Yasake mata tambayar again Tace "babu komai Daga Allah ne. Yace "to yanzun yajikin naki? Tace "naji sauki Alhamdulillah. Yace "Ok zanje su sallameki ban iya xaman Asibitiba. Yafuce zuwa mintina yadawo yace "Anbasu sallama yanzu likita zaizo yaganta su wuce. ******* Koda suka dawo gida Taga canji agunsa don wani tattalinta yakeyi yana nuna mata kulawa ga cima kala kala dayake kawo mata Har manta matsayinsa gareta yakeyi Bawai zama yake yayi hira da itaba kawai dai kulawa yake bata saikuma aikin dazatayi masa yakeyi dakansa harma yayi matan Bawai Son ta yakeba tsananin dabara yake yi mata don ta saki jiki dashi yasha romonta Ranar karshe da baxata taba mantawa ba atarihinta shine ranar da yaraba dare adakinta bayan yabata magani tasha Yarabata da jikinsa yaringa mata wasu launikan wasanni yana romance da ita waiduk aganinsa debw kewa ne hakan Saida yakashe mata jiki likis kana ya sille mata kaya yacire nashi yahaye ruwan cikinta Yahau aikin kokarin shigarda abin arxikinsa Wato dai yahau kokarin zira guga arijiya don debe ruwa ๐Ÿคฆ๐Ÿผโ€โ™€ kuyi hkr fans haka tsarin yk sai agaba zaku gane ma,anar hakan zakuma kuga cancantar hakan. Ahankali yaringa bi da ita har yacimma burinsa Aiko dai yakidime yashiga halin firgici alokacin dayaji cakwai yaji banbancinta da sauran matan daya saba lasa. Tabbas yaji *KUYANGA* ta daban take ackn mata Domin Dadinta Daban yake Anya kuwa Yarima ba mutuwa yayi ba don Dadi da shiga jazaba Don daya gama kasa motsi yayi kamar yadda itama takasa motsawa amma hawaye ne kawai kefitowa a idonta *Yarima Suma yayi fans ku kawo ruwa mana* ๐Ÿ˜… HHHH muje zuwa [7/26, 3:44 PM] Ummi Tandama: ๐Ÿ“ฟ *KUYANGA* ๐Ÿ“ฟ *_๐ŸŒˆKAINUWA WRITERS ASSOCIATION_* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *WANNAN PAGE DIN SADAUKARWACE GA AUNTY FAUZA JAGORA UWAR TAFIYAR KAINUWA WRITERS ASS.* _TARE DA D'AUKACIN ELDAS AND MEMBOBIN CKN QUNGIYA ME ALBARKA NAN KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_ *Nabilancy luv* ๐Ÿ’˜ (Auntyn S&S) 35-40 YARIMA yana gama Abinda zaiyi da *KUYANGA* Yasauko daga gadon yazira kayansa yafuce yabarta kwance lakwas tana zibarda hawaye Hawayan bakin ciki takeyi domin yarima ya cuceta ya karya mata lagonta data shiryashi ga MAHBUB tabbas ta tausayawa kanta takuma Tausayawa MAHBUB Domin insunyi Aure bazai samu abinda ake samu ga Cikakkiyar mace budurwa ba tabbas dolen ta koka Dakyar ta iya mikewa tashiga tayi wanka da ruwan dumi tashiga cikin ruwan kana tafuto ta dawo takwanta ta shiga tunani Tundaga wannan Rana da Yarima yadandanata bai sake bi takantaba ko ganinsa batayi a idonta Ita hakanma dadi yai mata domin bata kaunarsa ko kusa ko kadan tunda bai zama me tausayin mace ba yanada son kansa ita yanzun ji take gara Allah yadau ranta akan dai ta zama farkarsa ******** Ranar wata Lahadi ta Dade tana bacci tun ana sallar ishsha,i takwanta bacci me dadi mecike da mafarkin masoyinta Mafarki takeyi wai takoma gida gata nan ita dashi alambu suna Tadi suna cikin Annashuwa Kayan sarauta ne ajikinsu ita dashi anata hidimta musu Abinda kuma yabata mamaki cikin mafarkin sai aka musanya mata da LAMIDO amadadin MAHBUB da suke zaune kunsan dai mafarki yanda yake saitaga LAMIDO sunata shan Soyayya kamar karsu rabu ga bayi sunata kawo musu gaisuwa kafin su wuce Shigowar yarima dakin nata da matsananciyar Sha,awarta shiya katse mata Daddad'an mafarkin Kai tsaye yahaye gadon tareda kwantawa abayanta yahau shinshinata kamar wani kare Yazira hannayensa cikin shimin jikinta ya kamo Breast dinta yahau matsasu cikin wani azababben salon Sanyawa ashide Matsasu yakeyi yana futarda nishi sama sama kana yahau mirzar kan nonon nata yana wani fadin ""wash!Ashhh!! Tafarka azabure tareda fadin "wayyo Allah na waye ?? Tayi zaton ko Aljanine saitahau addu,a cikin ranta Can kuma taji ya murginota zuwa jikinsa yamannata da jikinsa yana kokarin yakai bakinsa ga nata Kafin taganeshi ta fuska ta kamshin turarensa taganeshi Yarima yana cutar da ita domin adole take amincewa dashi badan tasoba gashi ba damar ta bujire ba damar ta hanashi to ta inama Alhalin Ya iya kashewa mace jikinta murus Ai walahi koke da kike karantawa inkikaji yanayin saikin langwame ajikinsa ๐Ÿ˜… Tokoni danake Rubutawa ji nake inama yarima mijinane kawai dan yajiyarni yanayin ๐Ÿ˜›๐Ÿ˜‹๐Ÿ˜…๐Ÿ˜‚๐Ÿคฃ aradu karkuga laifina irin mazajen da ake so asamu kenan wanda zakiso WeekEnd ta riskeki dashi zakuma kiso kik'i fita unguwa dan shi uuhhhuuhmm Bari dai inyi shiru haka kada intunzuro wasu ko aga rashin kunyata kuyimin uzuri tsohon hannu ce ๐Ÿ˜…๐Ÿ˜Š Saida yagama luguiguita ta jikinta yai sharkaf da narkewa wajen Relarx Gashi tagama jikewa dan *KUYANGA* Lafiyayya ce me tarin Ni,ima irin yadda mata akeso dai sukance domin Maza nason hakan ga mace Batada tsumi batada dabara saina mika kai bori yahau Yau abin haushi sau biyu yanayi Saida yagama gamsuwa kana yatsallaketa yabarta anan Sam bayama damuwa yaga shin itan ta gamsun ko tana bukatar taimako Kai!!! Yarima mamuguncine kai Aradu bakada hali ๐Ÿ˜ก kubarni dashi fans kada kufuto da jin haushinku ma wani yaji zanyi maganinsa yasin saiya kwashi kashinsa ahannu Alkur.an dan tusa kawai Yauma haka ta tashi taje tayo wankan janaba kamar yadda MAHBUB ya koyarta dayake shidin me ilimin addinine dan har dan gemu yatsayar wasuma Uztaz suke kiran MAHBUB Yakan koyar da makarantar dare ga yara da manya na BAYIN gida maza ko mata Saida yajera kwana uku ajere yana zuwar mata tun tana masa shiru tana kyaleshi har wata rana taki bashi hadin kai Ta matse jikinta tana kuka tana ce masa itakam yakyaleta haka bata so Tagaji kuma yamayarta gida Haushin kalamanta yaji wato tarainashi kenan tunda akan yana neman abinda yakeso ajikinta amatsayinta na baiwarsa hartanada bakin magana lallai xaiyi maganinta Daya ga da gaske takeyi saiya zuciya ya wanketa da mari saida ta dafe gurin Yace "kije kirike kayanki inada wadanda suka fiki komai taimaka miki nakeyi tunda naga ackn kewar masoyinki kike kuma kinkai munzali sannan inban nemekiba wazan nema kokinsan dan hakan nataho dake to walahi bari kiji indai gidane bazan koma yanzuba harsai lokacin danaga dama dan kaina Yana gama fadin haka yasauka daga gadon bayan yasaka kayansa Haryaje kofar futa zaifuta kuma saiya dawo da baya yatsaya akanta yanunata "Kisani bawai Sonki nake yiba balle inga wulakanci indai nine bazaki karajin na kusancekiba zankawo kowace mace gidannan inada iko saidai kisani inhar kika kara karyan doka irin wancan to xaki fuskanci hukunci fin wancen Me zanyi da *KUYANGA* makaskanciya irinki.mmttss yaja tsaki yafuce Tarushe da kuka tareda dafe kai *"YA ALLAH KAJI ABINDA BAWANKA YAKE FADAMIN ALLAH KA "YAN TAR DANI KASA INADA RABON FARIN CIKI ADUNIYA*! Aranar wuni tayi tana kuka kanta har ciwo yafara taji inama zataga SAHABI ko zata fada masa kadan daga cikin damuwarta ko taji sanyi ckn ranta ko hakan zaisa ya maidata shi Nigeria Aiko Dan halak sai gashi Allah yajehoshi gidan kawai domin yaganta don sun bata da yarima tun asilar daya kaita asibiti SAHABIN ne yayi fushi da yariman ganin irin faassarar da yafara masa Dayaga bata falon saiya saka kansa ckn dakin nata yana rafka sallama jikinsa nabashi ko batada lfy Yana shiga yahangeta karshen gado dake da kanta tanata kuka Ai da sauri ya isa gareta yana tambayarta ko lfy Tadago da sauri ganin shine yasa takara sautin kukan tana fadin "DAN Allah kataimaka ka kaini Gida kamayar dani Nigeria walh nagaji da Abinda yarima yakemin. SAHABI arude yace mata "me yake miki?Zeenatu wane irin zalinci yake miki? Bata boye masa ba don kada ta cuci kanta ta zayyane masa komai Ya dafe kansa yana jin quna ackn ransa Yakasa magana don takaici Yace "kinada laifi kinxamo me biyayya wacce batada amfani awannan bangaren yarima bai dace yai mk hakaba tabbas sainayi maganinsa saiyasan cewar ya aikata ba daidai b maza taso hado kayanki daga yau kinbar zaman gidansa har Abada Jin hakan yasa taji dan sanyi aranta Da karfin guiwa ta sauko daga gadon Aranta tanajin inhar zai mayarta gida toko inane ma zata bishi Da sauri Sauri tahau hada kayanta a dan akwatin daya bata Duk kayan kananun kayane shedanun kaya ma kuwa irin fitinannun da bazata iya shiga ckn mutane dasuba don rashin mutuncinsu Doguwar riga dayace ackn kayan sai kayan da tazo dasu riga da zani Hijab ta zura tunda riga da siket din jikinta sunkamata Yarike mata akwatin ta mara mas baya har ckn motarsa dake farfajiyar gidan Akan idon me gadi suka futa don har dagawa juna hannu sukayi Yasan cewar inhar Yarima yadawo zai fada masa yafuta da ita toshiko bai damuba tunda gyara xanyi Ackn motar yaita rarrashinta don tadaina kukan fadi yake "saikin fita daga damuwa sannan zanmaidaki gida Nig. Yanzu dai gidana zanfara kaiki kafin innema miki Bisa โ€ฆโ€ฆโ€ฆโ€ฆ A,a fa SAHABI muna gudun fadawa gidan jiya munfiso kafidda A'i daga rogo bawai kadora daga inda aka tsaya ba ๐Ÿ™„ To kodayake dai ance โ€ฆโ€ฆโ€ฆโ€ฆ Kubiyo Antun Sayyada da Shahida donjin meke gaba [7/27, 4:35 PM] Ummi Tandama: ๐Ÿ“ฟ *KUYANGA...* ๐Ÿ“ฟ *_๐ŸŒˆKAINUWA WRITERS ASSOCIATION_* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *JINJINA GAREKU KAWAYEN ARZIKI SA'ADATU HUSSAIN AMINCI RADIO TAREDA SHAMSIYYA BAHUR MAMAN SADIQ R/K QUATERS* *Nabilancy Luv* ๐Ÿ’˜ (Auntyn S&S) 40-45 Gidan da SAHABI Yake tamfatsetsene Dan yafi na Yarima komai da komai Sashe biyune agidan kowanne daki kashiga bazakaso kafita ba kayan alatu tamkar kadauki new decoration kagudu dashi abubuwan kawata daki ba magana Wani daki yakai *KUYANGA* wanda yake dauke da babban gado da kayan kallo acknsa da toilet da kujeru ack girman dakin yakai fili rabin filoti Yanuna mata kujera yace "Zauna anan ki huta inxakiyi wanka ga toilet nan inkuma xaki kwanta ga gado nan Kayanki kaf bayardasu xanyi bazaki kara sakasuba domin kwata kwata babu na arxiki ack Yanzu zanfita zansayo miki Dogayen riguna kala uku natabbatar baxa,a dara kwana uku biza bata samuba sannan zantaho miki da magani sbd ciwon kan naki zantaho miki da abinci ma kada kisawa kanki damuwa baxan cutar kiba ba halin na daya da yarima ba domin ni ina zuwa kasar nan ne don hutawa ba wai don lalata da mata ko yin mummunar dabi,a ba dai kiyi hkr da abinda yayi miki haka kaddarar ki take kijure kixama me tawakkali Zeenatu watarana sai labari zanje baxan dadeba Tace ahankali "Nagode Yace "ba damuwa kigodewa Allanki. Yajuya xaitafi kenan tace masa "Dan Allah kada kanuna masa muna tare ina tsoron abinda xai faru tunda shike da iko da ni da kuma.โ€ฆ SAHABI yakatseta da Cewa "kwantar da hankalinki nasan kina cikin tsoro kuma kina neman taimako bazan bari yasan kina guna ba zankoma gidan ma yanzun gun me gadi inja masa kunne akan kada yagaya masa Tayi ajiyar zcy tareda kakaro murmushi tace "To saika dawo. Yasa kai yafice Kai tsaye Gidan Abinci ya wuce yasiyo mata me tsadar gaske Kana yashiga pharmacy yasiya mata magunguna hardana ciwon jiki dana zazzabi da ciwon kan Sannan yawuce gidan Yarima yai sa,ar kuwa Baidawoba Yakebe da Me gadin yabayyana masa komai tareda bashi kudi cinhanci Me gadin musulmine dan kasar cameroon ne yanajin hausa sosai Yahau gyada kai yace "bazan fadaba insha Allahu domin natausaya mata yarinyar tanada kirki tun zuwanta nadaina zama da yunwa wannan Yaro bashida kirki sam, baya ganin karama ce Amma dai kaima kayi taimako Allah yabiyaka. SAHABI yaji dadi yayi murmushi yace "Amin ngd.suka karayin musabiha yatafi ****** Abangare guda da YARIMA ANwar yadawo gidan bai neme inda takeba ko kusa ko alama domin cikin fushi yake da ita Kwana yayi yana tuna yanda takasance atsakaninsu domin ta bashi haushi sosai wato don yana jin dadi ajikinta shine tasami hanyar rainashi har tana iya musanta masa da sa,insa dashi lallai dolene yayi maganinta domin bazai zauna da *KUYANGAR* Da bata ganin darajar saba zai gyara mata zama Abu daya yake masa yawo akwanyarsa Baiwarta da YANDA take wajen ni,ima tabbas awannan fage yasan ta ciri tuta ba karya yarinyar tacika mace baitabajin macen daya kusanta yajita zam -zam kamar taba Aikoda zaiyi fushi da ita na lokaci kalilan ne bazai iya rabuwa da itaba tunda ya dan daneta yaji wani abu aransa akanta yazaune masa kamar super glu aransa Yakwana yana tuno Dadin dayaji ajikin *KUYANGA* Da Gari yawaye sai yashirya zaifuta gidan wani abokinsa zasu je wani shoping har ya futa kuma yai tunanin yacancanta yaganota tunda baiji motsin taba ko batada lafiya Yana kuma son dai yaganta domin shap dinta na burgeshi da cikar kirjinta Yana shiga abin mamaki baiganta ba baikuma ji motsinta a toilet ba har lekawa yayi Saiyaja yatsaya a tsakiyar dakin yana tambayar kansa "to shin ina wannan yarinyar taje ne? Yai sauri yafuta yaleka kicin namma bata nan Yazaga bayan gidan shine har lambu yagama zagayensa yana neme nemensa amma shiru ba bayaninta balle ma wata alamar ko tana gidan Nan kuma jikinsa yafara sanyi kada dai guduwa tayi? Yatambayi kansa Gabansa yafadi alokaci guda Domin yasan inhar ta gudu ba iya kai kanta gida xatayiba tunda batada kudin jirgi balle wata hanya agarin da xata iya guduwa gida Yatafi da saurinsa yatambayi me gadi yace masa shin ko yaga fitowar Zeenatun? Me gadin yahau girgixa kai yana nuna tu,ajjibinsa azahiri yana fadin "bangantaba tun jiya rabona da insata a ido Yarima yace "azamanka nayau aget kamatsa na awa nawa ko minti nawa? Me gadi yahau sosa keya yace "Eh to dayake dai yau natashi da bacewar ciki inata shiga toilet shiyasa bana ce ko sau nawa ma nabar get ba kuma nakan dade kafin nadawo. Yarima yadafe kai yace "Shikenan ta gudu! Nashiga uku. Me gadi yazabura yace "ta gudu? Zeenatun innalillahi wa innailaihirrajiun. To yanzu ina za.aje aganta wata sani a kasar nan? Yarima yaharareshi yace "koma wata sani ko bata sanin ba ai kana da hannu aciki tunda kana wasa da aikinka baka rufe gidan yadda yakamata. Yajuya yabar Megadi da atsaye saroro Aifa aranar yarima yarasa tsugum yanata Faman xaryar gun jami,an tsaron garin yana basu bayanin B'atan *KUYANGA* waiko Allah zaisa aganta ahanya Kwana biyu sukai suna checking akanta amma shiru dole yahakura yakira gida yana tambayar mahaifiyarsa Koda UMMAH taji abinda yake faruwa daga bakinsa ta kidime tahau yi masa fada "Yarima kodai akwai abinda kake matane?ko takura mata kayi da ayyuka da fadanka? Yarima yace "To UMMAH inma nayi mata fadan saita gudu? Banida ikon dazan matane?kawai dai yawon bude ido nakejin ta tafi tunda idonta yabude dama bakiga yanda take shigar kananan kayaba tana son tafuta gari nahanata ashe dai xata shammaceni tagudu Jin Hakan yasa UMMAH ta yarda tahau fada tana cewa "to ai da ba guduwa yakamata tayiba saita fada maka maza take bukata saika dawo da ita gida ayi mata Aure yanzu kaga hakan ai sharri zata jawo maka ace kai ka koreta ko cutarta kakeyi yasa ta gudu gani da mahassada ackn gida (kishiyoyi) Kuma dole kasan TAKAWA zaiyi fada amma kabarni dashi zansan mezan fada masa Yarima yahau godiya yanajin dadi aransa ****** Akwana na ukunta agidan SAHABI bizarta ta samu itadashi Suka kamo hanyar dawowa Nigeria Dayake tasaki jikinta dashi tunda taga ba cutarta xaiyiba sai suketa hirarsu ajirgi tana ta masa godiya da nuna masa farin cikinta azahiri Shikam bakomai yake ce mata ba sai "nikam bazan daina gaya miki ina sonkiba kirike alkawari Ta lumshe idanunta tabbas inda wanda zataso to abayan SAHABI yake amma ina yau data nufi kasarta ji take wata kaunar MAHBUB ta dawo mata sabuwa Dayaga tashiga tunani saiyace mata "Zeenatu kada fa kisawa kanki damuwa kicire komai aranki domin ni da Aure nake sonki kuma bazan ringa miki kallon abinda yarima yai miki ba kimance da komai yadda nima zanmanta da komai haka kuma kija bakinki kiyi tsit kada kifadawa kowa abinda yasa kika dawo ko abinda yarima ke miki kimarki zata ragu agun mutane sannan za,aita yawo da maganar agidan. Tagyada kanta tagamsu itanma ai zataso asirinta yarufu domin kada masoyinta yaji bazaiji dadiba sannan ga "yan uwanta KUYANGU abin xai iya zama abin surutu ayi mata wani kallo Da dare suka diro kasar Nigeria bayan Ishsha'i Har gidan sarki Abdallah yarima yadauki shatar mota aka kaisu amma shi bai bari anganshiba Ita kadai aka sauke akodar gidan sarki aka tafi dashi zuwa hotel din dazai kama yakwana ingari yawaye ya wuce Daura garinsu Kafin su rabu tun amota yabata waya karama kirar Tecno domin yace yana son yaringa jin muryarta akoyaushe sannan in tanada Damuwa ta sanar masa zai mata maganin damuwar Tabbas SAHABI yagama mata komai Shigarta gidan tun daga kofa aka fara mamakin dawowarta tunda ansan da Ita da yarima suka tafi kuma basuda labarin dawowar yariman Kai tsaye bangarensu ta zarce bata bari kowa yagabta ba Adakinsu mutum biyune basuyi bacci ba Zulaihat idonta biyu kawarta Da zulaihat taganta kirji ta dafe tana fadin "wa nk gani kamar Zeenatu? Dama yau kuna tafe amma banji sanarwar ackn gidan ba *KUYANGA* Tazauna tana fadin "wash !barni na huta tukunna zulaihat saiki watson tambayar Zulaihat ta janyo jakar da Zeenatun tashigo da ita takaya tace "lallai kyan tafiya dawowa ina yariman ko batare kuka dawo ba? "Idan tare muka dawo zaki ganmu atarene? Zulaihat Tahau murmushi tana fadin "inafa kawai dai tambayace *KUYANGA* tace '"to batni nahuta tukunna sannan kibani labari akan MAHBUB dina. Zulaihat tayi dariya tace "MAHBUB dinki yananan qalau. "To masha Allahu. ****** Gari na wayewa aka aiko kiran *KUYANGA* labari yakaiwa UMMAH anga Zeenatu ta dawo gdn da daddare Saida UMMAH ta tabbatar da lallai Zeenatun ce tunda tazo da gaggawa kiran tadurkusa agabanta UMMAH tace "Meya dawo dake Gida yarima baisaniba? Gaban *KUYANGA* Yafadi take dabara tazo mata "Fita nayi don ganin gari shine na bace har wasu suka tsinceni suka tambayeni inda nake nikuma namanta inda zance musu bansan kwatancen mazaunin yarima shiyasa dasukace zasu dawo dani Nigeria ban musa musuba UMMAH nagama ji tace "kodai yawon iskanci kika tafi Allah yakamaki aka dawo dake gidan?. Da sauri tahau girgixa kai tana hawaye tabudi baki tace "walh ba haka bane waccen maganar danayi ce gaskiya. UMMAH Tace ta tashi tabata guri tayiwa kanta rayuwar jin dadi wasu ma nema suke Tana futa UMMAH takira Yarima tagaya masa komai Yarima yasha mamakin dahar ta iya dawowa ita kadai yacewa UMMAN yana tunanin akwai wanda yataimaka mata ta gudo zaiyi bincike UMMAH Tace "nidai kawai kadawo Yarima domin nafi son zamanka akusa da mahaifinka don inyana ganinka akusa dashi zaifi shakuwa dakai sannan Hakan ne zaisa sarauta ta dawo hannunka ta sauki tunda wancen Sahoramin yatafi Sudan karatu bazai dawo yanzuba Yarima yace "Nima bana jin Zandawo Yanzun UMMAH saikamar nanda wata guda. Tace "To kayi kokarin kadawo awata gudan kada ka kara fa. Yace "angama UMMAH Na baxan karaba. Sukai sallama Saida Labari yakai kunnan sarki wai *KUYANGA* Dasuka tafi Turai da Yarima ta gudo itakadai Mamaki ya ishi sarki domin baisan anyi tafiya da mace ba da bazai bariba balle har ya yarda yabar yarima yatafi da mace Aranar yasaka UMMAH agaba yace ban kanki in aske Yaita mata fada harsaida tayi hawaye Tana fadin "Ayi hkr Takawa ai anrigada anyi kure dahar aka tafi ba.a gaya makanba baza.a karaba Ita kuwa *KUYANGA* tasake ackn "yan'uwanta Bayi bata nuna wata damuwa ba ko Wani abun Haka suma basu gano komai ba saima yabon canxawarta dasuke tayi wai tayi kyau fatarta tayi kyau acan Shiko MAHBUB kallonta yai tayi yana fara,a dajin dadi yana fadin '" kincanza dayawa Zeenah kinyi matuqar kyau fatarki sai sheki takeyi lallai kin huta acan kinbarmu ckn aikin wahal Inafa Hutu tambayemu kasha labarin komai ๐Ÿ˜… tayi fari ๐Ÿ™„ tace kaima ka kara kyau anya kayi kewata kamar yadda nayi taka kuwa? Yace "sosai kuwa ko nan gurin damuke xama zaishedi hakan dafatan dai soyayyata batayi gibi ba tananan yanda nasanta da yawa? Gibi kai๐Ÿ˜‰๐Ÿ˜„ Amma injini ita cewa tayi "Saima karuwa tayi ai aduk inda nake dana tafi ina tare da sonka da kaunarka Yace "naji dadi soaai. Dayake wayar da yarima yabata Boyeta tayi sam bazata bari MAHBUB yagani ba balle yayi mata fassara gara Zulaihat ta nuna mata amma tace kada tafada wa kowa Zulaihat hartana tsokanart dacewa "Toko dai SAHABIN nan zaki Aurane komai kice SAHABI mudai kada kiyi mana sakiyar daba ruwa *KUYANGA* tace "Banga abinda zaisa nabar MAHBUB ba kima bar wannan maganar SAHABI abokin shawara ne abokan taka ce atsakaninmu Dariya kawai Zulaihat tayi tare dajan bakinta tayi gum ***** Watan *KUYANGA* D'aya da dawowa yanayinta yacanxa domin wani laulayi taringayi ga yawan Zazzabin dare Da ciwon Ciki da bacci da kasala da kwadayi da take yawan yi Zulaihat itace tajikinta ita tasan matsalarta na rashin lfyr saita samo mata magunguna taita bata na gargajiya tana jikawa tana bata tana sha Kwana biyu tayi akwance MAHBUB yatada hankalinsa ganin ciwo yaki lafawa Kullum cikin Aikawa da Rubutu yake Aranar data gama shanye jikon da Zulaihat tayi mata aranar tayita malelekuwa atsakar daki mararta na ciwo kamar ta mutu Tana ihu tana kiran sunan Allah Jini ne yaringa xuba ajikinta ta kasanta me yawa Zulaihat ta tsorata ainun Da gudu tagayowa manyansu tsoffin Bayin gidan Da sukazo kanta sukaga ikon Allah abin yafi karfinsu sai suka baxama cikin gidan gun matan Sarki aka gayo musu Mamah ta tsakiya da Amaryar Sarki Faatu mahaifiyar Lamido sune suka fara zuwa gunta kafin UMMAH Tazo Likitansu na ckn gidan aka kira macece *DOCTOR HALIMA WASAI* da kayan aikinta tazo taxaci abin karamine Saida tazo taganta tace musu ai bari zatayi da alamar cikine da ita maza atafi da ita asibiti don inya bare ayo mata wankin cikin Hankalin kowa na gidan yatashi ba,a bari sarki yajiba UMMAH taringa fadin "shegiyar yarinya Me sifar munafukai ashe abinda tayo akasar ta gudo kenan lallai asirinki yatonu Yarima bashida Alhaki shiyasa baima saniba ta munafurceshi. MAMAH tace "ai irin wannan ba,a aibunta mutum kuma bamu tabbatar ba likitanma zato takeyi dan haka muyi mata fatan Alkairi tunda D'a nakowane UMMAH ta harari MAMAH dama haushinta takeji ganin ta rungumi FAATU sunhade mata kai UMMAH ta watsowa MAMAH magana me zafi dan taji haushi tace "TO IN D'A NAKOWANE WANI MA YAYI D'AN MANA NAZACI TUN ZUWANKI GIDANNAN KATON KASHI KAWAI KIKEYI KOKIN TABA YIN BARIN MA? MAMAH jarumar mace me tawakkali tayi murmushi tace "Bantabayi ba Amma nagodewa Allah yabani Taqwa da Sanin yakamta kuma ina dada gode masa nasn kuma bai manta daniba, na tabbatar kuma inhar yabani agaba inda yawan rai xanfiki iya yiwa yara tarbiyya....FAATU ce taja hannun MAMAH tana fadin "kibar maganar haka kiyi shiru ga mutane fa bayinku agun baikamata ba. MAMAH da FAATU suka bar gurin Ita UMMAH Data gwaba me zafi aka mayar mata tafi MAMAHn jin xafin maganar ma Yawwa ai gara hakan dama inbaki yafadi son rai aibaisan me za,a mayar masa ba. *Muje zuwa dai Auntyn Sayyadah da Shahidah* ๐Ÿ˜…๐Ÿ˜‚๐Ÿคฃ๐Ÿ˜€๐Ÿ˜ƒ๐Ÿ˜„๐Ÿ˜†๐Ÿ˜‡๐Ÿ˜‰โ˜บ๐Ÿ˜Š [7/28, 9:09 PM] Ummi Tandama: ๐Ÿ“ฟ *KUYANGA* ๐Ÿ“ฟ *_๐ŸŒˆKAINUWA WRITERS ASSOCIATION_* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *WANNAN PAGE DIN SADAUKARWA CE GA KAWATA TAKAINA REAL UMMEEY ZEEY Marubuciyar "YAMMATA ALKAIRIN ALLAH YAKAI INDA KIKE INA FANS DINA KUNEMI BUK DIN "YAMMATA KADA KUBARI ABAKU LABARI* *Nabilancy Luv* ๐Ÿ’˜ (Auntyn S&S) 45-50 ACAN Asibiti Likitoci sunata iya bakin kokarinsu domin Suga jinin dake zuba daga jikinta yatsaya don tafuta ahayyacinta Saida Allah yataimaka jinin yatsaya kana sukai mata allurar bacci sannan aka nemi "yan uwanta domin suzo adebi jininsu akara mata Likitocin kansu sunyi zaton cikin dake jikinta yazube to ajiyar Allah baifita ba sai wuya datasha Iya Yabi wata tsohuwa cikin wadanda suka kawota tace musu su taimaka su karasa fitar da cikin ba Aurene da itaba Abin kunya taja musu Dr Halima tace mata "Gaskiya bama zubda ciki domin inmunyi hakan tamkar munyiwa ubangiji shishshigine domin bamusan nufinsa dayasa tasamu cikin ba alokacin da bai dace tasamu ba Iya tace "Amma dai da kuntaimaka sbd idan labarin yaje kunnan sarki baxataji ta dadiba dan korarta ma zaiyi agidan kuma gashi bamusan cikin wayeba gata marainiya Dr halima tace "koma dai meye ne iya saidai kuyi hkr mufa bama Abotion a asibitinnan sannan kusani wannan ciki bame futa bane inhar kuma kukayi kokarin yi masa dole to tabbas zaku iya rasa ranta awajen zubarwa Iya Yabi ta tsorata matuqa gaya jiki na rawa tace "to abar maganar Allah yabata lfy yarufa Asiri Acan gida Da labarin neman jini yazowa kowa sai akaita nokewa MAHBUB kuwa da rawar jiki yanufi asibitin sbd yabada jininsa ga masoyiyarsa Shi atunaninsa ko wata lalaurar ce tadaban take wahalar da ita ********* Dayake aranar LAMIDO yadawo yanufi daga SUDAN yagama karatunsa wanda yayi na shekara 5 Rangadi suka futa shida maimartaba domin Sarki yana son LAMIDO kwarai. can bayan gari yajashi wai suyi hirar yaushe gamo anitse kada atakura musu LAMIDO yaji dadin wannan zaman da mahaifin nasa domin sunsa hira tun da sukazo wajen sha daya nasafe sai yamma suka fara haramar komawa gida dayake dirar sassafe yayi Nigeriyar Jakadiya tana gaban UMMAH tana fadin "Ranki yadade naje cikin azama fada domin insanarwa sarki labarin irin abin kunyar da *KUYANGA* ta hada mana ayau sainatarar bayanan natambayi Dogari wai yafuta shida LAMIDO dakuma fadawa Rangadi Lallai nayarda Sarki yana son LAMIDO domin namanta rabon dana ganshi yafuta ran gadi balle bai taba zuwa da YARIMA ba anya kuwa ranki yadade ba asiri Matar can tayiwa Sarki da Yarima ba kuwa? UMMAH ta hau gyada kai ckn takaici tana fadin "Ai walh jakadiya matar can burinta ackn gidan nan baxai taba cikaba domin D'ana shine sarkin gobe da yardar Allah kuma Duk me binsa Da sharri sai nayi maganinsa muxuba mugani Har dare da Sarki yadawo shida LAMIDO labari baije kunnan saba Sai da Sassafe Jakadiya ta bazama taje takai gaisuwa tagurfana agabansa don takware a munafurci da gulma Saida tagama banbadan cinta dayi masa kirari kana ta zayyano masa komai duk abinda tasani daya faru Sarki yayi Shiru kirjinsa na dukan uku uku dan fargaba Yanzu cikin KUYANGUNsa akaiwa 1 ciki?me hankalin ciki da yasanta farin sani sbd yawan Ayyukanta ackn gidanba da ladabinta Yadafe kai yai tsahon minti biyar ahakan kana yadago ya kalli jakadiya yace "maza kije ki kira min matan gidannan su ukun Su UMMAH Da FAATU Da MAMAH yake nufi Dakin fulani tafara isa tagaya mata kana tawuce dakin MAMAH Bayan tasanarta kiran sarki saita wuce Dakin FAATU Tana shiga ta tararta da LAMIDO Suna hira tadurkusa takai gaisuwarta garesu kana ta isar da sako tafuta Koda suka hadu gaban Sarki UMMAH tafisu faduwar gaba sbd tasan kaf dinsu itace me laifi tunda itace silar samuwar cikin *KUYANGA* dan dabata turata kasar wajeba da yarimanba da batasa samuba Bayan Shiru na wasu mintina Sarki yayi gyaran murya kana yakallesu d'aya bayan d'aya yace "Kunada masaniyar Abinda yake faruwa agidannan? Suka hau gyada kai Yace "to ya akai har hakan tafaru ?ya akai *KUYANGA* Tasami ciki a ina akai hakan meyasa kukai wannan saken...? MAMAH ta budi baki ahankali ckn ladabi tace "Ranka yadade Takawa banida laifi ciki FATUU ma tace "Nima dai banida laifiโ€ฆ UMMAH ckn jin haushinsu tace "to tunda bakuda laifi ciki saiku gaya masa me laifin naga alamar dai so kuke kununa masa karara nice da laifi ack Mai martaba yadaga mata hannu yace "ya isa bana son daga murya domin zcy ta tafasa takeyi raina abace yake tambaya kawai nayi ba neman jin fitina ba ya akai hakan tafaru agayamin. MAMAH Tace "Ranka yadade cikin nanfa tun daga turai aka sameshi domin da alamar dashi ta dawo domin YARIMAN ma da suka tafi dashi can tabaroshi baisaniba ta dawo. Sarki Abdallah ya furgita da jin wannan maganar yace "TURAI!? ya akai har *KUYANGA* taje turai batareda sanina ba meyasa yarima yatafi da ita ba,a gayamin ba tabbas FULANI kece da laifi tunda kinsan da tafiyar tasu kika boyemin kinkuma san halina akan in aka munafurceni a abu UMMAH tayi kasa da kanta Yaci gaba da cewa "To shi yariman ne yayi mata cikin ko wa? Da sauri tadago tana fadin "ba cikin yarima bane baima san ta taho ba Yace min ta dade bata gidansa tun zuwanta kasar idonta yabude take bin maza farkan natane yasata ajirgi ta taho ahalin yanzuma yarima baisan tanada cikiba Mai Martaba yace "Koma dai menene laifin na yarima ne ko ba cikinsa bane to kune sila sannan Alhakin yana kanku meyasa Da hankalinki xaki hada mace da namiji suje su zauna agida daya ba matar saba bakomai ba Alhalin kinsan halayyar d'anKi munada masaniyar yana bin matan turawan nan acan Maimartaba yaja ajiyar zuciya yace "Yarima baidauko halin kirki na gidan sarauta ba domin babu me munin halinsa adangina banyi fasikanci ba banyi shaye shaye ba amma gashi Allah yajarabceni da yaron dakeyi Allah nagode maka Allah kashirya minshi UMMAH tahau zubda hawaye tana fadin "Amma dai kasan akwai mahassada na agun baidace karinga aibunta min Da suna gunba., Tsawa yadaka mata "yimin shiru fulani ko ranki yabaci banasan zancen banza wadannan abokan zaman kine ba mahassadan kiba Kuma ki gaggauta kiran yarima awaya kigaya masa maza injini yadawo gida Tahau gyada kai tana goge hawaye Yace duk sutashi sutafi Sun mike kenan zasu futa saiga Jakadiya ta shigo da sauri tadurkusa tace "Anzo da babban batu daga asibitin da aka kwantar da *KUYANGA* Ana bukatar jini ackn gidannan za,a kara mata domin tana cikin wani hali. UMMAH taharari Jakadiya Yayinda FAATU taji wani tausayin *KUYANGAR* Yashigeta tace da jakadiya "Maza Ki kiramin Ladimo A bangarensa kisanar masa yafito yaje asibitin adebi nasa.โ€ฆ Mai martaba najin tafadi hakan yai mata magana "akan wane dalili zaki bashi wannan umarnin Alhalin jiya-jiya yadawo baigama hutawa ba zaki sashi wahala babu nasiyane da baxamu siyaba.? FAATU tace "Ranka yadade dazu muna hira dashi yagama fadamin an auna jininsa anga Group O" ne yace kuma yana son yaga yabaiwa mai bukata domin yasami lada natabbata kuma inyaji ackn gidannan ne zaije da gaggawa Mai martaba yagyada kansa yace "To ace masa yabayar din nima na Amince tunda ladan yake nema. Jakadiya tace "angama zanje yanzu ko ingaya masa. Duka suka fucedaga Turakar Sarkin Koda jakadiya tajewa da Lamido wannan magana ta umarnin yaje yabadajini inji mahaifiyarsa bashiri yahau shiryawa zuwa Asibitin Direbansa na gidan da aka ware masa yanema yace maza yakaishi Asibitin da suke ganin likitansu Zuwansu keda wuya suka tarar ana Auna jinin MAHBUB Likitan daya gama awon jinin yadawo yatarar dasu duka azaune yace "jinin MAHBUB baiyiba damar diba shima yana bukata sannan yanada Typhoid Nan LAMIDO yamike yace da likitan shi aje a debi nasa yanada tabbacin nasa zaiyi tunda group O ' Ne dashi zai iya baiwa kowa jini Likitan daya Auna yagani yatabbatar saiyace da LAMIDO "jininka yayi saidai ba leda daya take bukata ba adebi biyun ba matsala ko adebi daya su sai dayan? LAMIDO yace "Debi biyun na amince lada nake nema bawani abuba Take yakwanta aka debi leda biyu Saida yahuta agadon sannan yafuta daga asibitin ko *KUYANGAR* bai nemi inda takeba don hankalinsa ba,a gunta yakeba bukatarsa dai ta biya yataimaka mata don baiwaye taba ma. Koda yakoma gida mahaifiyarsa taringa masa godiya da addu,a gareshi takuma bashi labarin yarinyar da abinda yafaru da ita LAMIDO yadade yanajin ciwon abin aransa meyasa akaiwa baiwar Allah haka meyasa don anga batada gata aka danne mata hakki? Dayake shi mutum ne mejinkai da tausan bayi sannan gashi da ilimin Addinin domin acan din dayaje karatu Islamic yakaranta yanada sani sosai Yadago da kansa ckn Qunar rai yace da Mahaifiyarsa "Amma sam abinda yarima yakeyi baya kyautawa kodayake UMMAH ta daure masa gindi kuma inada tabbacin shine ma zaiyi cikin Sharri kawai za.ayi mata FAATU tace "Muma tunanin mu kenan Amma dai koma meye ai dole asiri zai tonu tunda Inta futo daga Asibitin zata fadi ko cikin waye kuma Takawa yace agayawa yarima yadawo da gaggawa LAMIDO Yace "Insha Allahu saina taimaka mata Da jikina da abin hannuna. FAATU tayi murmushi tace "Allah yabaka iko D'an Albarka ACAN asibiti kuwa MAHBUB ne Shida Zulaihat suka kebe yana tambayarta shin abinda yaji ackn gidan sarki gaskene? Zulaihat tarintse ido tana futarda kwallah tace "MAHBUB duk abinda kaji gaskiyane Likitocin sun tabbatar Zeenatu cikine da ita na Daya da satittika wanda yaso ya bare Allah baiyiba rabon dai ta wahala ne Nayi kuka sosai danaji hakan dama kuma nafara fahimtar hakan kafin rashin lfyr tata. MAHBUB yarintse idanuwa yana hawaye kirjinsa zafi yake masa meyasa Zeenatu taci amanarsa?meyasa Zeenatu tacanza hali? Meyasa tabiyewa sharrin Shaidan da Namiji ta Amince da wani Alhalin Sunyi Alkawarin Aure โ€ฆโ€ฆ? Muje zuwa fans [7/30, 2:25 PM] Ummi Tandama: ๐Ÿ“ฟ *KUYANGA...* ๐Ÿ“ฟ *_๐ŸŒˆKAINUWA WRITERS ASSOCIATION_* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *Nabilancy Luv* ๐Ÿ’˜ (Auntyn S&S) 50-55 Jakadiya ce Zaune agaban UMMAH tagama kawo mata tsegumin Matan Sarki wai da alamar sun hade mata kai sunaso asirinta yatonu agidan abata mata d'a UMMAH ta furzar da iska abakinta kana tace "jakadiya nadade da sanin abinda suke ciki nasan basa sona dani da yarima Kuma walh sainayi maganinsu agidan nan daya bayan daya cikinsu Jakadiya tace " nibakomai nakeji ba sai *KUYANGA* Kada tacewa sarki cikin na Yarima ne domin zata iya k'ak'aba masa don tagaji abin arxiki na gdn Sarauta UMMAH ta quta kana tace "zankuwayi maganinta domin nagama yanke shawarar abinda zansaka kiyi mata Wanda inhar kikayi zanbaki makudan kudi da zinare da gida agefen gari ckn gidajen Yarima Jakadiya tahau murmushi tace " fadi ko meye kikeso inyi zanyishi uwar dakina "yr sarki jikar sarki me babban daki uwar gidan Sarki Fulani uwar Yarima Wanda zaihaye karaga da yardar Allah UMMAH tayi murmushi najin Dadin kambamawa tace " So nake dazarar ansallamo *KUYANGA* daga asibiti yazamo tadawo karkashin kulawarki koda ace ta fadi ckn Yarima ne ko bama nashin bane yazama tana tare dake kullum zansa ta dawo dakinki inyaso kafin ta haihu kisa mata guba a abinci ko kishaqeta da filo ta mutu kawai Zabura jakadiya tayi kana tace "Ranki ya Dade bazai yiyu akasheta da gaggawa ba za.a fassara mu kokuma azo ayi nadama gara dai inta haihu inbi dare inkashe abinda ta Haifa UMMAH tayi murmushi tace " Dakyau jakadiya kinada hangen nesa tabbas zama dake akwai riba hakan ma da kika tsara yayi don haka kizama ckn shiri Koda jakadiya ta futa daga dakin UMMAH saita nufi Dakin MAMAH domin kai mata tsegumin UMMAN tayi sa,a kuwa ta tarar da FAATU atare da MAMAHn suna hira Jakadiya takai gaisuwa garesu kana ta xauna gefe bakinta na motsawa irin na munafukai sunso tsegumin MAMAH tace "ya akai jakadiya akwai wani abun ne? Jakadiya tahau shafa hab'a tana fadin 'Dama wani Abu najiyo dayake damuna tunda naji nakasa fada muku FAATU tace 'ikon Allah mene wannan Abu fadi muji shi Jakadiya tayi kasa da murya tace " Ranki ya Dade Gimbiya FAATU zancen ma dai akan d'an kine domin FULANI tananan tana hakon tayi masa mugun Abu domin kada yagaji sarautar mahaifinsa kada ma yaji yanaso aransa sannan inada tabbacin Yarima ne yayiwa *KUYANGA* cikin nan amma naga tanaso adanne mata hakkinta don haka yakamata kuyi wani Abu akai MAMAH Da FAATU suka kama baki suna mamaki domin kuwa basu zataba duk da sun Dora zarginsu akai MAMAH tace "lallai jakadiya mungode munyarda ke me kaunarmuce don haka munbaki izini akan kiringa bibiyar lamarin don kar hakanta yacimma ruwa Jakadiya tace " Angama ranki ya Dade Amaryar Sarki Dangwale shalele agun maimartaba Uwar Lamido me jiran gado Koda jakadiya tafuta sai FAATU tacewa MAMAH "Nifa shiyasa bantabajin inason LAMIDO yahau kankaragar nan ba in maimartaba yayi murabus haka shima LAMIDON bashida ra,ayi Sam mulkin baya gabansa balle yadorawa ransa MAAMAH tace " to duk da hakan dai saiki tashi tsaye kiringa addu.a ba dare ba rana kirage bacci kigayawa Allah akan yakawo muku agaji kada aje a cutar miki dashi Nan dai MAMAH tayita bata addu,o,in na kariya domin sunfurgita da zancen da sukaji abakin Jakadiya ********** A can Asibiti kuwa anbaiwa *KUYANGA* kulawa daidai gwargwado harta samu kanta Zulaihat CE agunta kafin arubuta musu sallama Domin sai data kwana daya a asibitin kana aka bata sallama Suka dawo gida Zulai ita ta gaya mata duk abinda yafaru da ita tunda a sume aka debeta xuwa asibiti batasan me akai mata ba tundaga Karin jini da daukar jininta aka auna aka gano tanada shigar cikin Hannu ta Dora aka taringa kuka tana fadin "Nashiga uku na cuci kaina da tun farko na aminta dakai ban bujire makaba.biyayya batayimin ranaba wayyo Rayuwata ta gurbata Allah kadauki Raina kona hu.... Zulaihat tayi saurin toshe mata baki " kada kice haka Zeenatu Allah yajarabceki da hakan babu tsimi babu dabara sannan Ni bana zarginki sai tausayinki "Inke bakya zargina Zulaihat MAHBUB fa ? Nasan kome zance baxai yardaba Allah ne kadai zaifutar ni ko a gidannan. Zulaihat tace " Waye yayi miki cikin? *KUYANGA* Tace "wakuwa zaimin inba Yarima ba cikin sane bantaba sanin wani namiji ba inba shiba harta dole yakemin....nan tahau baiwa zulaihat labarin yanda rayuwarta ta gudana a Turai tareda Yarima bata rage mata komai ba har taimakonta Da SAHABI yayi Zulaihat tashare hawayen tausayin zeenatu tace " Zeenatu Yarima yacuce ki domin ayanda nafuskanci MAHBUB yaji ciwon abun yakuma zaci ko kinyi cikinne abisa sonki har kuka yayi yace yayi nadamar fara kaunarki yace kincuceshi yayi kuka sosai a asibiti Kuka takara fashewa dashi jin yanda MAHBUB yadauki lamarin Shikenan tafaru ta kare tasan ko a agidan bakowa zai yarda ba sai Wanda yasan halayyar Yariman Zulaihat ita tayi ta dannarta tana bata baki Dan kwantar mata da zcy Kwana tayi kuka duk tafuta hayyacinta ta rame Ko futa dainawa tayi saidai Zulaihat ta karbo mata abincinta in an gama abangaren nasu dayake dakinsu daya da zulaihat din Tayi zaton ko MAHBUB zaizo yadubata amma saitajishi shiru na wasu kwanaki baizoba Sannan takara tabbatarwa lallai yadau zafi da ita Sati Daya da maganar cikin da *KUYANGA* Tazo dashi daga turai YARIMA yadawo Magana ta yada ko ina na cikin gidan sarki Wasu suna yarda na yarimane wasu kuma suna ganin bazai zama nashiba tunda ance yawonta take da maza dataje turan KARSHEN TIKA TIKI TIK!! Dawowar yYarima yasa kowa agidan yashiga murna domin ansan tunda yadawo kasar za,a samo matsaya akan cikin *KUYANGA* Tana Zaune adaki tana tunanin data sabayi Zulaihat ta shigo da Sauri tace mata "Zeenatu yi sauri kidauko hijabi muje an aiko sanarwa daga Fada Sarki nabukatarki agun Yarima yana can fadar da Kaf Ahalin Gidan za,ayi Zubeben kwarya... Gabantane yafadi tareda dafe kirji take hawaye suka hau zarya akuncinta Zulaihat tajata jiki tace mata "daina kuka kwantar da hankalinki me gaskiya yana tare da Allah Abinda kika Sani shi zaki fada kada kiji tsoro kada kuma kirage komai *KUYANGA* Tahau gyada kanta taredajin karfin guiwa ajikinta Zulaihat tace " muje inrakaki fadar...... ๐Ÿƒ๐Ÿผโ€โ™€๐Ÿƒ๐Ÿผ๐Ÿ‘ญ๐Ÿšถ๐Ÿผโ€โ™€๐Ÿšถ๐Ÿผ๐Ÿ•ด๐Ÿฝ๐Ÿ‘ช๐Ÿ‘ฉโ€โคโ€๐Ÿ’‹โ€๐Ÿ‘ฉ๐Ÿ‘จโ€โคโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โคโ€๐Ÿ‘ฉ fans kutaho rakiya mana Duk masoyin *KUYANGA* kada yasake abarshi abaya ataho arakata Fadar *SARKI ABDALLAH* MUJE ZUWA FANS๐Ÿ˜… [7/31, 11:29 AM] Ummi Tandama: ๐Ÿ“ฟ *KUYANGA...* ๐Ÿ“ฟ *_๐ŸŒˆKAINUWA WRITERS ASSOCIATION_* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *Nabilancy Luv* ๐Ÿ’˜ (Auntyn S&S) 55-60 CARBI ne ahannun *KUYANGA* datake ja ackn burmemen hijabin dayake jikinta Addua kawai takeyi Akan Allah yabata Nasara yashige mata gaba yakuma dorata akan maimartaba Gaban tane yafadi ganin yanda fada ta cika da ahalin gidan daga matansa da yaransa YARIMA da LAMIDO da kuma fadawa da Galadima da sauran masu mukaman gidan Bayi ne kawai basa gurin Kowa ita yake kallo itako kanta akasa tasami guri anesa dasu tazauna Zulaihat ma ta xauna kusa da ita Maimartaba yana ganin shigowarta yayi Gyaran murya ganin tazauna nesa da mutane duk aka nutsu ana kallonsa Yace " *KUYANGA ZEENATU* Ke muke jira kuma adalilinki muka taru anan Dan haka kidawo tsakiyar mutane kizauna domin ki amsa tambayoyi daga bakina Tayi saurin tashi tabi umarni takoma tsakiyarsu inda fadawa suka bata guri akusa da Yarima dayake kusada Sarki LAMIDO na gefen yariman Wanda tunshigowar *KUYANGA* Yazuba mata idanu yana kare mata kallo Bayan ta zauna Mai martaba yawatso mata tambayar data rikita mata kwanya "Dawa kike tarayyar fasikanci a kasar waje ??? Ahankali tace " Bakowa, Yace "To waye yayi miki ciki? Hawaye na zuba a idonta tace " cikin jikina bana kowa bane illah na YARIMA! fadawa suka hau salati Yayinda Sarki ya rintse idanu jin yasami jika Dan gaba da fatiha a ckn gida Suko matan kirji suka dafe alamun mamaki Yarima kuwa fuskar sace ta nuna bacin rai tsababa ji yake tamkar yashaqeta ta mutu akan wannan tonon sililin datayi masa LAMIDO kuwa girgiza kai kawai yk yi na al,ajab sannan yana mamakin yayan nasa da wannan hali UMMAH mahaifiyar Yarima Ta dakawa *KUYANGA* Tsawa "karya takeyi munafuka saikin nemo Wanda yayi miki inma ackn turawan da kika barosu kika gudo Sarki ne yatsawatar mata akan tayi shiru Yajuya kan Yarima yace masa " YARIMA ya abin yake? kanada tabbacin naka ne ko ba nakaba? Yarima yaji sassanyar Tambaya sai yahau gyada kai yana fadin "Ranka ya Dade bansan da maganar ba baninayi mata cikiba Sarki yace " to wanene? Yarima yayi shiru Jin yayi masa shiru yasa yaci gaba da tambayarsa "Sau nawa kataba Kusantar ta? Nan ma yayi shiru kansa akasa yahau fidda xufa Ganin haka sarki yace " tun anan alamu sun nuna cikin kane Dan haka bazaka wulakanta Rayuwar yarinya kaci riba ita ta wulakantaba Dolene ka Aureta.... "bazai yiyuba! Cewar UMMAH tafada ranta abace " don ci baya sai D'ana ya Auri KUYANGA gaskiya da sake Mai marmataba yanunata da yatsa "kishiga taitayinki Fulani idan Dan kine nima nawane nama fiki iko dashi danhaka magana dole abita in anason zaman lfy dani YARIMA yadukar dakansa yana magana ahankali " Ina Neman Alfarma ayimin rai walh bana sonta akwai wacce nakeso mun mayi alkawarin yin Aure atsakaninmu ayimin kowanne irin hukunci amma banda wannan Galadima yayi Gyaran murya yace "kwantar da hankalinka Yarima Munanan ma baza.ai hakaba kaidai katsaya da gaskiyarka inhar bakai kayi cikin nan ba Ai jini zai nuna dazarar ta haihu za a auna jininka da abinda ta haifan agani Galadima yadubi *KUYANGA* duk don yakamata da laifi sbd yana goyon bayan Yarima yace mata " Ke Wanene shaidarki akan wannan lamari? Tadago dakai ahankali tana tace "SAHABI shine Shaidata domin shine yadawo dani daga kasar waje YARIMA yazaro idanu yana mamakin lafazinta wato Ashe SAHABI munafukin Sane? Galadima yace mata " wanene kuma SAHABI? Tace "Abokin Yarima tun acan yasan wasu abubuwan Nan tahau bada labari tiryan tiryan Har takai karshe tana fidda kwalla a idonta Kowa agun yaji labarin KUYANGA me taba zuciya Wanda masu tausayi agun harda hawayensu irinsu MAMAH da FAATU Haka LAMIDO yacika da tausayinta zufa taringaa karyo masa agoshi yana gogewa Sarki yakalli Yarima daya sunkui dakai alamun rashin gaskiya yace masa "Maza kira SAHABI awayarka kasaka handsfree kowa Jiki asanyaye yakira wayar SAHABI yabarta a bude sunajin tana ring Saida takusa katsewa kana Sahabin yadaga Sarkine dakansa yahau masa magana SAhABI yanutsu awaya jin martabane dakansa Duk yanda ake ciki dai da mai martaba yazayyane masa kana yakara da koro masa Tambaya SAHABI yakadu dajin hakan tabbas yasan abin babbane Nan yagyara zama yafede masa biri hr wutsiya bai rage masa komai ba na abinda yasani duk domin yaga yafutar da *KUYANGA* Yarima yaita mamakin SAHABI nayanda yake zayyano bayanai Da sarki yagamaji yaiwa SAHABI godiya yakashe wayar Ran sarki yagama baci akan musantawar da Yarima keyi Yarima yahau sose sosen kai jin Sarki yace masa " kaji abinda abokinka yace anyi hakan? Yagyada kansa Sarki yace "Kasan da saninka Inta haihu zan daura muku Aure da ita sannan ayanzu Alhakin kulawarta yadawo kanta sbd abinda ke jikinta YARIMA bai yi maganaba UMMAH Ranta yabaci sosai da jin sannan hukunci Take Sarki yasallami kowa aka watse Kwana biyu da faruwar hakan YARIMA yabar gidan batareda Sanin kowaba ckn dare yagudu ko UMMAH bata saniba Yahada kayansa yasilale cikin dare yatafi inda yafito Da labarin yashiga ckn gidan ba karamin tashin hankali mahaifiyarsa tashiga ba Don hartahau zargin waiko Asiri akai masa dahar yabar gida Abu kamar da wasa saida yakwana hudu labari ya isa fada Tabbas Sarki ya guntsi bakin ciki awannan ranar yasan Yarima yanason yakun yatashine kawai tun aranar yakara tabbatarwa kansa cewar Yarima bai cancanci yaxama sarki ba Tuni aka hadu kowa da kowa afadar Sarki domin shi yakira taron Inda yabayyana musu bakin cikin dayake ciki Yace da *KUYANGA* dafarko inaso kizama me daukar kaddararki haka Allah yatsara miki naso inga yarima ya aureki domin Asirinki yarufu kedashi dinma To gashi Allah baiba yanunan ban isaba yawatsan kasa a ido yagudu yabar kasar Dan haka inaso kikwantar da hankalinki da zarar kinhaihu zan karbi abinda kika Haifa hannu bibbiyu nayi miki Alqawarin baxaku wulakantaba ke dashi Dan haka wanene kike so ackn gidananna fadawa ko ckn BAYI xan muku Aure domin inwanke miki zuciya *KUYANGA* tayi shiru kanta nakasa Ayayinda MAHBUB dake ckn mutane nesa da ita yadago dakanta yana kallonta gashi dai har ynzu yana sonta to amma wani Abu ma sukar ransa inya tuna ta yaudareshi duk da azaman farko da akayi babushi ankawo masa Rahoton cewa Ba da saninta komai yawakamaba Yarimane ya cuceta Yana so yafurta kalma abakinsa ya gagara jiyayi mai martaba yayi masa kwarjini bakinsa yayi masa nauyi Yaso yafurta shine maaoyinta na asali na gaskiya da akai musu kutse arayuwa aka rushe musu farin ciki Allah cikin ikonsa MAHBUB saiya kasa magana Allah yanufi LAMIDO Da maganar data furgita kowa harni Hannu LAMIDON ya daga yana fadin "Ranka ya Dade ka Amince min Na Aureta domin inraya sunnar manzan Allah nakuma shiryi taimaka mata kota halin kaka domin naji zuciyata ta kwanta da ita.... Kallon kallo UMMAH suka hauyi da Jakadiya hakama MAMAH takalli FAATU yayinda FAATUN takalli Mai martaba domin jiran Abinda zai yanke akai.... To muma fans da writers sai mubi layi afada domin jiran tacewar Sarki Abdallah ๐Ÿ™‡๐Ÿ™‡๐Ÿผโ€โ™€๐Ÿง–๐Ÿผโ€โ™‚๐Ÿ‘ฉโ€โคโ€๐Ÿ’‹โ€๐Ÿ‘ฉ๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฆโ€๐Ÿ‘ฆ๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ง Muje zuwa [8/1, 3:17 PM] Ummi Tandama: ๐Ÿ“ฟ *KUYANGA...* ๐Ÿ“ฟ *_๐ŸŒˆKAINUWA WRITERS ASSOCIATION_* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *Nabilancy Luv* ๐Ÿ’˜ (Auntyn S&S) 60-65 AFIRGICE *KUYANGA* ta dago dakanta takai kallonta ga LAMIDO daya furta wannan kalami wanda azatonto ko karya kunnenta yajiye mata saitaga da gasken ne jin Abinda Mai martaba yace "LAMIDO da gaske zaka Aureta? Har zuciyarka ka Amince? LAMIDO da fuskarsa ke cike da Murmushi da Annuri yace "Na Amince har ckn raina babu wasa ko yaudara zan Auri *KUYANGA ZEENATU* ko domin inga asirin gidannam bai buduba kuma don itama inrufa mata Asirin Amma inhar kaida mahaifiyata kun Amince Mai martaba yayi murmushi yace "Nidai na amince nakuma yi farin ciki kafitarni kunya domin banzamo me kyamatar talaka ba ko bawa na duk daya muke mu dasu gun ubangiji Saidai ko mahaifiyarka xamuso muji ta bakinta domin bata hakkinta. FAATU tayi murmushi tace "Tunda har ka amince TAKAWA ainima dole in amince akullum Allah nakewa Godiya akan yanda mukai dace da samun D'a nagari wanda akullum burinsa shine yaga ya kyautata mana ya kuma bi sahun masu bin tafarkin ubangiji burinsa akullum yasami lada arayuwarsa kaga dole muzamo masu bashi goyon baya Allah yasa hakan yazamo Alkairi arayuwarsa *"AMINNNN*" Kaf Al,ummar gurin suka furta banda mutum biyu MAHBUB da xcyrsa ta cika da kishi Da kuma UMMAH da hakan bai mata dadiba Mai martaba yadubi *KUYANGA* yace mata "Dazarar kin haihu za,a daura muku Aure da LAMIDO kigodewa Allah sannan duk abinda kika haifa mace ko namiji zamu karba da hannu bibbiyu Zansoshi kamar yadda nake son iyalaina tunda jinina ne za.a bashi kulawa sosai bakuma nafatan yataso cikin tsangwama ko bayan raina dan hakan ki Kizama me mika lamuranki ga Allah *KUYANGA* Ta ckn ladabi ta Amsa tana godiya Sarki yadubi LAMIDO yace "Asakamakon Wannan farantawar da kaimin ina me yi maka Albishir da cewa kaine zaka haye kan karagar Sarauta idan nayi murabus nan ba da dadewa ba Halayanka sunnuna kaine zaka iya rike masarautar nan ko bayan raina kacancnta babu haufi kaine adalin Mutumin da akullum ake nunamin amafarki wanda zai zamo sarkin garinnan Kadauko halayen kwarai na iyaye da kakanninmu kwarai ina godiya da Allah daya bani kai amatsayin D'a Yadubi Tarin jama.ar da suka cika fadar maza da mata na gidan yaci gaba dacewa "Inaso kusheda daga yau LAMIDO Shine wanda zaizama jagoranku nan bada dadewa ba LAMIDO shine xai xama sarkin gobe da yardar Allah. Take Gurin yahautsine da sowa da murna fadawa Suka hau Kabbara Bayi mata tsoffin da manyan suka gau guda Yayinda MAMAH ta rafka guda tareda cewa sarki "TAKAWA Allah Yaja da ranka muna taya LAMIDO murna kuma muna tayashi yin Godiya da wannan kyauta Maimartaba yagyada kai yana murmushi Dayake anyi tsit ana sauraren maganr MAMAH Saijin kukan UMMAH Akayi ta dora hannu aka tana fadin "Shikenan burinku yacika kun raba D'ana da gidan ubansa kunyi kutunguilar da D'anku zai zama sarki kuma walh baku isaba Sarki yadaka mata tsawa Amaimakon tayi shiru saita mike tana fadin "walh baza,a dakeni ahanani kukaba. Tafuce fuuu tana kukan bakin ciki LAMIDON da kansa yanuna godiyarsa ga sarki Maimartaba yahau shafa kan LAMIDON yana fadin "Kacancnci hakan LAMIDO fatana harkullum Abinda kayi min na Farantawa to ubangiji Allah yafaranta maka kaima LAMIDO ya amsa da "Amin, Aminn Saida Sarki yabada umarnin tafiya sannan kowa yatashi yayi nasa guri Jakadiya har sashin FAATU tabisu tana Rangada guda Tareda fara yi masa kirari na sarakai Saida tafaranta musu rai Da kalamanta garesu masu dadin saurare sannan tafuta Jakadiya Tana barin Bangaren FAATU ta wuce sashin UMMAH Domin tayata Jimami da Alhini tunda tafi kowa sanin yanda UMMAH take da burin taga Yariman yazamo sarki Ta tarar UMMAH tana waya da Yarima tana bashi labarin komai daya faru sannan Tabashi ixinin akan yadawo Gida maza maza akwai abinda take shirya masa akai Yarima ya amsa da to zaidawo nanda kwana uku ko biyu Kai UMMAH ta hada da guiwa tareda dayin shiru na minti Talatin Jakadiya na gefe taa jiran tafara kawo gulma da soki burutsin karya Data saba donta sami fada agun Fulanin UMMAH tadago takalleta tace mata "Jakadiya jeki kya dawo anjima ayanzu baxan iya maganaba ina ckn wani hali banda lokacin zanta wata magana kibari nahutawa bakin cikin dana dauko afada Sum sum jakadiya ta tashi tafuce guiwa asage Itako *KUYANGA* Kwana tayi ba ci basha Sai dakyar Akwana na biyu da Yin abun sannan Zulaihat data matsa mata taci abinci kadan duk tasaka damuwa ackn ranta Zulaihat tace mata "walh kigodewa Allah ma ayanzu ji nake dama nice ke kuma nasan bani kadai ke wannan tunanin ackn bayin gidan nanba domin kin xama "yar baiwa tunda gashi Allah yakusa "yantaki Zaki zamo matar sarki Surukar Sarki.โ€ฆโ€ฆ "Uwar Shege ko Shegiya kuma ba. Cewar Zeenatun tana matsar kwallah Zulaihat tace "kibar fadin hakan domin inma shegene ko shegiya duk kafin yafito duniya ne ko tafito duniya domin Kinji ta bakin Sarki yakarba kuma za,a bashi kulawa zai zamo tamkar d'a ko "ya me "yanci to balle LAMIDO natare dake kinyi matsayin da bakowacce zata iya takashiba ackn mu *KUYANGIN* Gidan kema kinsan hakan Zeenatu tace "hhhmmm ke kike ta wannan tunanin ni tunani na yatafi ga masoyina MAHBUN tausayinsa nakeji yanzu shikenan โ€ฆโ€ฆ Zulaihat ta daga mata hannu "saurara niarki dameni da xancensa domin banga yayi hobbasa yanuna soyayyar da yake mikiba agun dan da,a ce sonda yake miki har zucine da kafin LAMIDO yace wani abu akai tuni shizaice Dan Allah kicireshi aranki tunda yanzu bake kadai bace ba,bafa ason me ciki da shiga damuwa balle kuma abinda zaki haifa me matsayine agidan Zeeatu tace "Zulaihat da alama bakisan radadin soyayya a zuciba Ni LAMIDO baya gabana Mulkin gidannan baya gabana ko arzikinsu kawai Matsayina nake tunawa ayanzu Zulaihat tace "ke nifa Allah nagodewa da bai nufi MAHBUB da magana akan kiba agun natabbata da tuni LAMIDO baice komai b.โ€ฆโ€ฆ Sallamar Wata yar matashiyar yarinya ce cikin bayi tashigo dakin nasu takatseta tashigo musu da ladabi tagaidasu Zulaihat tace "Laminde ya akai akwai wani abune? Laminde tace "Ustaz ne yace Zeenatu taje yana waje. Da sauri Zeenatun tace mata "kije maza kice masa ina zuwa Ta xira hijab tabi bayan Laminde data futa da mintina uku Yau ya canxa gurin tsayuwa can gefen hanya yaja tunga yatsaya yana jiranta Tun daga nesa yakura mata idanu yana kallonta tayi haske fuskarta taxamo yar kuyas tayi kyau saidaita rame Takasara gareshi da sallama tagaidashi Ya amsa yana kallon yana fadin "ZEENAH ina sonki amma dole inbarki, yanzu kinmin nisa kinfi karfina.โ€ฆโ€ฆ takatseshi dacewa "kadaina fadin haka komai nufin Allah ne matar mutum kabarinsa saikaga muna tamune Allah na nasa zai iya kuma canza lamarin aduk sanda yaso bamu zataba kaifa malamine kasan hakan kazama me tawakkali mana kana fa da Sani.... Yace "Duk na susuce Zeenatu ayanxune akwanakin nan biyu da faruwar lamarin naji kaunarki ta karu araina tamkar ana kara rura wutarta ma Kokinsan YARIMA yadawo Gida adaren jiya labarin yakarade gidan nan. Sarki ko kallonsa baiyiba haryanzu yayi fushi dashi kuma duk akan ne "yar baiwa Duk da gabanta yafadi jin ya ambaci sunan yarima sai bata nunaba a fuska ta dake tareda kawar da maganar ma tace masa "Ko awane hali nake bazan manta dakaiba bakuma zan daina son kaba kaine kadai wanda naso a afarko da karshe ackn Duniyar nan โ€ฆโ€ฆ Adaidai lokacin da *KUYANGA* Ke furtawa MAHBUB wannan daddad'an kalma ar daidai lokacinne Allah yakawo yarima yazo xai girfta ta gun yahangosu yabiyo ta jikin katangar da suke tsaye kunnansa yadebo masa wannan kalami da muryarta yawatso akunnansa Yaja da sauri yatsaya baya so su ganshi domin dan ita kawai yabiyo ta gurin Rintse idanunsa yayi wani abu yaji yana masa yawo akirjinsa Tabbas yau yakara aminta da zargin dayake mata na soyayya da MAHBUB duk da ta taba tabbatar masa amma kalaminta na yau yakara bashi haske Ya dafe kansa domin Wani hali yashiga Akanta yadawo adalilinta tun daya hada kayansa yabr kasr yakoma turai yakas sakat Allah yajarabceahi da azababbiyar kaunarta dayaji batun da mahaifiyarsa ta gaya masa na LAMIDO zai Aureta bakaramin tashin hankali yashiga ba domin yasan shirinsa yagama baci Nemanta yakeyi ido arufe ruwa ajallo Donsu keb'e yanuna mata nadamarsa ya amshi cikin nasa domin ta yarda dashi yakuma roki alfarmar tarakashi gun Sarki Ta tayashi neman yafiya Yasan ita din me hkr ce da biyayya bazaisha wahalar taba Waishin ma tawace hanyar zaisamu hakan? Anya bai makaro ba kuwa hhhhhh fans kufito ku gaya masa ๐Ÿ˜†๐Ÿ˜…๐Ÿ˜‚๐Ÿคฃ Muje zuwa [8/2, 5:04 PM] Ummi Tandama: ๐Ÿ“ฟ *KUYANGA..* ๐Ÿ“ฟ ๐ŸŒˆ *KAINUWA WRITER'S ASSOCIATION* {United We Stand and succeed;Our Ambition is to entertain & motivate the mind of reader's} *Nabilancy Luv* ๐Ÿ’˜ (Auntyn S&S) *KAFIN AYI NISA KAI TSAYE INA MIKO GAISUWA DA GODIYA GA D'AUKACIN "YAN CIKIN GIDAN NABILA'S ONLY 4 STARS WRITERS MA,ABOTA KARANTA KUYANGA MUSAMMAN MASU COMMENT* 65-70 A SANYAYE Yarima yajuya da baya don gara yakoma kada wani cikinsu yaganshi su rainashi Yakoma sashen mahaifiyarsa ya tararta tana Safa da marwa atsakar dakinta tana buga hannunta daya cikin daya tana kwafa da alamar har yanzun ranta abace yake tana kuma ckn halin damuwa Tana ganinsa tahau fadin "Ya Akai yarima kasame tane? Yazauna akan kushin yana fadin "Bansami ganawa da itaba UMMAH natarta ne da wani Kazamin bawa da take so..,UMMAH Takatse shi da sauri "Au dama ackn gidan nanma akwai wanda take soyayya dashi ? Ashe haka tazama yarinyar to da alama ma cikin agida tayishi kenan Yarima yadago da sauri yadubi mahaifiyarsa da jajayen ido yace "A,a UMMAH tunjiya Dana dawo nagaya miki cewar Wannan cikin fa nawa ne kada ki kakabawa wani makaskanci mana jini na karba.... " Dakata! Ta dakatar dashi da daga murya ranta abace "Wai bazaka daina kiran cikin jikin *KUYANGA* da sunan mallakin kaba,walh inkai ka karba to ni ban karb'aba domin bazan yarda da shege ace shine jikanaba jikanma ajikin baiwa Allah yakiyaye dama ajikin wata baturiyar ne ko " yar sarauta da sauki Yarima yace " Amma ai u UMMAH shi .mahaifina yakarba ballantana ke da kike mace kikafi sona. Tace "Dan babanka yakarba be dameniba domin yakarbane da wata manufa aransa tunda bayason azageshi bakuma yaso Dan daza,a haifa yatashi yarasa madafa amma nasan ba har zuci yakarba " kidaina fadar haka UMMAH. "Saina fada din kaida bakasan inda yake mk ciwo ba baka ma damu da kyautar kujerar sarauta da Aka baiwa LAMIDO ba Yarima yace "Ni wannan kam baya gabana fatana dai ayanzu *KUYANGA* zeenatu ta Amince da abinda nazo dashi sbd Allah yajabceni da kaunarta UMMAH kitaimaka kiyi wani Abun walh sonta nakeyi sosai har cikin raina UMMAH ta maka masa wata harara tace "Shima LAMIDOn daya Amsa yana sonta zai Auretan nasan badan Allah yayiba a to. Yarima ya shiga tunani Kai Yadafe don kan nasa ke bugawa dolene yasamo mafita akan MAHBUB Domin irin kalamin dayaji tana watsa masa na soyayya tabbas su yake muradin yaji wataran tagaya masa Toshin ta wace hanyar? Ta Yaya? Yakasa samo amsar tambayar domin kansa yakulle Dole saiya nutsu UMMAH bacin ran abinda Yarima yaxo mata dashi baisa tasami nutsuwa ckn rantaba tabbas dolene tasami mafita akai rana zafi inuwa quna knn domin wannan shine ana wata ga wata can Hukuncin da sarki ya yanke nabaiwa LAMIDO sarauta nacinta arai saigashi Yarima yazo mata da wani batu wai yana son *KUYANGA* to tawace hanyar ma zaisameta Alhalin LAMIDO yakarba kowa yashaida hakan lokaci kawai ake jira Yarima yadago dakansa yaga mahaifiyarsa ta hada kai da guiwa .yasauko kasa Yakama kafafunta yana fadin "UMMAH kitaimaka mini kije ga mai martaba kinemamin yafiya sannan kifada masa batuna na karbar cikin *KUYANGA* da zanyi kice nayi nadama sharrin shaidanne inasonta yadaina fushi dani Wani dunqulelen abune yatsayewa UMMAH a maqoshi na takaici da bakin ciki Taki jinin jin Kalmar nan dayake furtawa na son *KUYANGA* dayake fada mata yanayi domin ita ji takeyi tana kara tsanarta ma tunda itace tazamo silar rushewar Burinta ayau,tayi nadamar amincewa da tayi tun farko daya yatafi da ita kasar waje tasan da bata yarda sun tafin ba da tuni hakan bata faruba tunda gashi akan Yariman yak'ita yaki cikin ne LAMIDO yashirya manaqisa yakarba don abashi sarauta kuma anbashin kamar yadda sukeso kuma bazata taba bari suji Dadin yin mulkinba indai daranta saita zame musu masifa a ckn gidan Wannan tunanin tane UMMAH dai taga Yarima da Gaske yakeyi domin shirin kuka yake mata akan bukatarsa Dabara ce tafado mata tace masa "kwantar da hankalinka shalele zansan abinyi agun Takawa Yace " to agun ZEENATUN fa? Tahade rai Yamarairaice mata Taga dai da Gaske ne lamarin nasa saitahau tunanin anya kuwa ba Wani abun akaiwa D'an nataba mutumin dayaqi Abu futuk kuma cikin "yan kwanaki saiya haukace akai Lamarin Allah nefa UMMAH ๐Ÿ˜ƒAllah yakara inji fans ๐Ÿ˜‚ Takama hannayensa itama ckn marairaita tace masa "YARIMA kai D'ane D'an fari abin so aduk wani gidan sarauta baikamata ka lanjare a son BAIWA ba kafi karfin Auren *KUYANGA* ajinka da kimarka da izzarka na Dan sarki zai ragu inhar ka Auri *KUYANGA* inaso kayi hakuri kabarta ni dakaina zansamo maka ko ackn gidan sarautar mune akwai mata masu kyau adangina mahaifina kafin ya mutu yayi sarki yanzu babban yayana shine sarkin garinmu kasan da haka Babbar masarautace datafi wannan munada mata kyawawa yan boko wayayyu sai wacce kazaba babu me kinka walh kanada cikar da namiji kaidin gwarzone me tattare da mazan taka gaka kyakkyawa kafi LAMIDO kyau da kwarjini Meye naka na damuwa da Baiwa Alhalin kafi karfinta shi din dayace abashi ita ya Aura kabarsu dama da ita yadace Yarima yakyabe fuska yace " UMMAH bazaki ganebane Tace "tayakuwa zangane kaki amsar batuna Dayaga da Gaske takeyi baxata sakkoba saiya rushe mata da kuka yasan lagontane bata son damuwarsa balle ganin hawayensa Nan take kuwa ta rude tace masa yayi shiru zata duba lamarin yaje zuwa gobe kafin tasan abinyi Yana Fita ta aika aka nemo mata jakadiya Jakadiya na zuwa tagurfana gabanta " gaisuwa nakeyi Uwar dakina barka da warhaka gani ckn ladabi mezan miki ?nasan bukatace babba tasa kk kirani UMMAH tagyada kai tace "tabbas kuwa jakadiya domin Yarima yaxo min da banzan zance wai yanzu shi *KUYANGA* yakeso kuma ya amince da cikin jikinta nasane Jakadiya tadafe kirji tace " wannan Abu bai Dadin jiba kamar Wanda akai masa surkulle UMMAH TACE "Maza kije kishirya kije min gurin GOGAL matsafiya kice inaso acire masa son yarinyar ckn kwana daya Da sauri jakadiya tace " angama uwar dakina. UMMAH takawo kudi tabata jakadiya tafuce da sauri Amma kafin ta tafi gurin matsafiyar tasu dake bayan gari saida tafaki ido tashige Sashin MAMAH Takai musu Gulmar wai ga Yarima can yarikicewa Mahaifiyarsa waishikam yanzun *KUYANGA* Yakeso kuma ya amince cikin jikinta nasane FAATU DA MAMAH sunyi mamakin wannan Abu sunkuma Daukeshi arainin hankali yariman yazo dashi sunsan kuma TAKAWA bazai daukaba Yo muma ba dauka zamuyi ba ๐Ÿ˜ก Muje zuwa [8/3, 11:13 AM] Ummi Tandama: ๐Ÿ“ฟ *KUYANGA* ๐Ÿ“ฟ *_๐ŸŒˆKAINUWA WRITERSโœ๐Ÿป ASSOCIATION_*๐Ÿค๐Ÿป ```{United we stand and succeed;Our ambition is entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *Nabilancy Luv* ๐Ÿ’˜ (Auntyn S&S) *wannan shafin Sadaukarwace ga Binta kabir Auntyn Yasmin Mrs ibrahim R/k quarters* ๐Ÿ‘๐Ÿผ๐Ÿ‘๐Ÿผ Kawata inayinki Ina godiya da tayani posting a grps 70-75 JAKADIYA tana isa cikin Dajin tayita shiga cikin Ko tsoro babu atare da ita haka har tazo gindin wani tsauni ta haye daf !daf!!daf!!! Ta nufi wata babbar bishiyar Kuka dake kan katon Dutsen Tana isa ga bishiyar saita cire takalmanta ta tsaya gaban bishiyar tana fadin "Gafaranku dai manya da kanana na fadar GOGAL ga jaririya tazo tazo Neman taimako da cin Albarkaci ayi min iso gurin Hakima mandiya shugabar matsafa Wani kuka taji yana tashi na muryoyin yara daga ckn bishiyar taitaji harna tsahon minti talatin can kuma taji shiru sai kuma ga amsa kuwwar Babbar murya tana fadin " SANNUNKI DA ZUWA HATSABIBIYAR JAKADIYA GAMANDI ME HADA WANDA TASO Jakadiya ta hadiyi yawu domin kirarin nan bai mataba tasaba yi matashi ,"Barkanki da isowa GOGAL Cewar Jakadiya GOGAL da ba,a ganinta saijin muryarta ta jikin bishiyar tace da jakadiya "NAji zuwanki angayamin tunkina afarkon daji nasan meke tafe Uwar Dakinki ta aikoki akan Acirewa D'anta son da yakewa *KUYANGA* Daga zuciyar sa ko? Jakadiya tace " E kwarai hakan yake. Jakadiya taci gaba da cewa "Hakan data tsara nikuma incanza salon abun yazamo amaimakon ancire masa son yarinyar saidai ma akara masa don ya axabtu sosai Yakasa sakat yashiga damuwa akanta sakamakon yanda yasaka yarinyar adamuwa Wata bunsurar dariya aka sheke da ita dg jikin bishiyar kukar Daga can kuma akace da jakadiya " ko baki fadaba hakan za,ayi domin Baxan iya cire wannan soyayyar dake ransaba na duba naga ajiyar Allah ce ban isa in girgizata ba Dan haka zankara da Dora aikinki da kika bukata domin nima ayaune zanrama abinda YARIMA yataba yiwa Jikana yafita rangadi suka hadu ahanya YARIMA yabuge minshi da doki yafadi ko kulaminshi YARIMA baiyiba harya suma agun Jakadiya tahau gyada kanta Tana mamakin jin wannan labari na GOGAL duk da tasan zai aikata din Jakadiya tahau godiya tareda ajiye kudin da uwar dakinta tabata agindin bishiyar ta mike da niyyar tafiya Sai taji ana mata magana da muryar tsohuwa ta jikin bishiyar "Kema kibi lamuranki na gidan nan a sannu domin a irin zaqewar da kikeyi wataran zaki girbi kashinki ahannu domin akwai abinda zaki aikata zaija miki babban aiki da kuma danasani HAHAHAHA Aka rufe da katuwar dariya Jakadiya na kyarma tace " Ataimaka agayamin ko mene wannan Abu da zaijamin danasani don inkiyaye Dariyar dai akaci gaba dayi mata babu wani Karin bayani Tana kallo kudin data ajiye yabace sundauke Difff! Taji anmata tasan bakuma xasu karace mata kanxil ba shiyasa ta tafi da baya kamar yadda ta saba ******* Yarima Yana kwance akan makeken Gadonsa yanata juyi yakasa controlling din kansa akan soyayyar *KUYANGA* Da take azabtar dashi arai Hotonta ke masa gixo alokacin dayake kanta a time din suna Turai Tabbas Yanda takeda tarin baiwa bazai iya barin taba saiyayi yanda yayi ya mallaketa baxai taba barin LAMIDO ya Aure taba Can kuma saiya mike da sauri ayau saiya ganta kota halin kakane koda zai karya billensa yashiga ckn gidan bayin bazaiji wani Abu aransaba Sontane yaja Yazira kaya ajikinsa dama dagashi sai gajeran wando da singilet Yafito farfajiyar gidan yatsaya yana karewa kowa dake wucewa kallo duk Wanda zai wuce ta kusa dashi saiya kawo masa gaisuwa Da ka kawai yake amsawa Sarkin gida ya hango agurin ajiyar dokuna yana baiwa wani farin doki da LAMIDO kefuta dashi abinci Matsawa yayi kusa da Sarkin gidan tareda kwalla masa kira Da sauri yabar abinda yakeyi yataho gurin Yariman Ya mika gaisuwa tareda tsayawa ckn ladabi agefen yarima yanajiran abinda zaice masa Yarima yace "Sarkin gida Inaso kaje ka kiramin *KUYANGA* Zeenatu Sarkin gida yace " Tana tareda MAHBUB acan bayan Gamji da suka saba zama Yarima yadaka masa tsawa yace "To intana tareda wani bazatazo ba ko Yaya?shi wanin yafinine ?mijin tane ko waye dinta? Sarkin gida yahau fadin " kayi hkr ba nufina kenan ba sanar maka nayi dai bata gida agarceni bari aje can akirata Yatafi da sauri inda yasan zaisametan Yarima yahau cizar yatsa jin wai tana can tareda MAHBUB tabbas dole yadau mataki akan wannan Bawan dazai kawo masa tsaiko Yananan har lokacin da Sarkin gida yadawo tareda ita tana biye dashi sanye take da zurmemen hijab harkasa Yaringa kare mata kallo na yanda take tafiya anutse kanta akasa Gabantane yake faduwa domin batasan dame yazo mataba Tana ZUWA gareshi tagaidashi tareda tsayawa gefe kanta akasa Yana murmushi yace "Zeenatu dago kai kikalleni gani agabanki da kokon barata Nazo Neman yafiyar kine Akan laifin dana aikata miki nayi nadama nakuma karbi cikin jikinki domin tabbas D'ana ne ko "yata zaki Haifa jininane inason abuna ki kwantar da hankalinki kisaki kowa ki kamani domin rufuwar asirinki Ta dago da sauri takalleshi ido cikin ido ayau Allah yadauke mata shakkarsa tace masa " Ai asirina yagama rufuwa atun lokacin daka budeshi Allah yanufi Dan uwanka da rufeshi kuma abinda yaimin bazan taba mantawa dashiba bakuma zankishiba na aminta shi zan Aura....dasauri yakatseta "Kina nufin kice Kinason LAMIDO? Ta girgiza kanta " zan Auri LAMIDO sbd halaccinsa agareni da muhimmancinsa aguna da gun abinda zan Haifa sannan bazan bijireba INA ganin kima da daraja ta me martaba amma SO d'aya tak! MAHBUB nabaiwa shi Kamar ta watsa masa wuta amakoshi yaji jinta Ambaci MAHBUB take so Tabbas Zeenatu tacanxa yaushe tayi baki haka yaushe tasan tagaya masa magana tsararo babu taunawa tabbas babu musu MAHBUB ne zai kintsa mata komai akansa tunda suna tare yasan gunsa ta taho kuma saiyayi maganinsa Yadubeta duba na tsanaki yace "Nayi alqawarin saina raba zuciyarki da soyayyar bawa Mara amfani Tace " agunkane baida amfani amma aguna yana da amfani Tana gama fadin haka tajuya tatafi abinta Ayanxu ji take komai zata iya gaya masa tunda yazubda mutuncinsa agunta Yadade tsaye yana kallonta harta qule zancenta na masa yawo azuci kamar tadaba masa wuqa haka yaji tabbas ayau ba sai gobe zaiyi maganin MAHBUB shine sila nakomai datayi masa ayau Kafin yabar gurin saida ya yanke shawarar abinda zaiyiwa MAHBUB wasu fadawa Yasamu guda biyu dasuke girmamashi ya yafito su suka taho da sauri suna zuwa yace musu "Wani aiki zanbaku me tattare da hatsari amma zaku samu abin alheri me tsoka Sukai farat sukace " indai zamu samu matsayi agunka da kuma abin duniya kowane irine zamuyi Yarima yaji dadi yagyara tsaiwa yace "nasan zaku iya daganinku anga jarumai Wani bawa nakeso kukashe adaren yau... Yayi shiru yana so yaga wane action zasuyi ko zasu firgita saiyaga sabanin hakan ko gezau basuyiba da alamun zasu iya abinda yafi hakanma dama da ganinsu tantiraine Yaci gaba dafadin " dazarar kunkasheshi zanbaku gida ackn gari zanbaku kudi har naira Miliyan daya duk kuraba amma kuxama masu sirri so nake dasafe atashi da kukan mutuwarsa Sukace atare "angama ranka yadade. Yace " kutafi kujira zuwa dare da zaku aikata hakan saikunyi natabbatar zanbaku abinda na alqawarta muku Sukace "to shikenan Ranka yadade. Suka tafi shima yajuya yashige ciki Itama Jakadiya dataji komai akan kunnenta tajuya koma inda tafuto tana gyada kai mamakin abin fal ranta lallai Yarima yazama Takaddari acikin gidan Sarki...... To fans mujira zuwa safe muga ikon Allah mukasa mutsare mujira Auntyn Sayyada da Shahida CE ๐Ÿ‘Œ๐Ÿป [8/4, 11:18 AM] Ummi Tandama: ๐Ÿ“ฟ *KUYANGA...* ๐Ÿ“ฟ *_๐ŸŒˆKAINUWA WRITERSโœ๐Ÿป ASSOCIATION_*๐Ÿค๐Ÿป ```{United we stand and succeed;Our ambition is entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *Nabilancy Luv* ๐Ÿ’˜ (Auntyn S&S) 75-80 Kwana Jakadiya tayi tana Tunanin abinda kunnenta yajiye mata akan Abinda YARIMA yasa ayiwa MAHBUB tabbas indai suka aikata hakan Sai ta tona asirinsu Da gaggawa wata zuciyar ta kwabeta "Ke kinsan ko abinda kk fada?yariman zaki tonawa asiri toki tabbatar indai kika fada sunanki matacciya kema kokuma korarriya a gidan Sarki domin yarima da mahaifiyarsa babarinki zasuyiba Ta tuno yanda mahaifiyarsa keji dashi da sangartashi da gudun Bacin ransa Ta tuno rashin mutuncin Yariman Sannan ta tuno Yanda za.aita bibiyarta ana Neman cikakkiyar sheda daga gareta dazarar ta tona asiri domin dolene saita kawo shaida inko bata kawoba za,a hukunta akuma koreta agidan dama UMMAH ce ta daukaketa agidan Dataga jan bakinta tayi shiru yafiye mata alkairi saitaja komai tasa agefe Dan yafiye mata kwanciyar hankali ******** Tashin hankali Wanda ba,asa masa rana domin abangaren bayi suntashi dashi *KUYANGA* Da zulaihat suna kwance da Sassafe ihun da suka ringa jiyowa da koke koke agidan shiya tashesu afurgice Zulaihat tace da ita " munshiga uku wannan ihun kuwa na lafiyane. *KUYANGA* Tace "Ba lafiyaba gaskiya tashi muleko Suna futowa bakin kofarsu sai suka hango dandazon mutane Asashin maza Suntaru gefensu kuma mata ne tsoffi da yaran mata sunata kuka Zulaihat ta yafito wata yarinya Laminde da batafi shekara gomaba yar Aiken Uztaz MAHBUB Laminde tana goge hawaye ta iso garesu Zulaihat tace mata " Ke laminde meyake faruwa agidanne? Cikin kuka laminde tace "Tashi kawai akayi akaga wai UZTAZ ya mutu kuma ance kasheshi akayi da fullo.... " me!? Afirgice *KUYANGA* ta riketa tana tambayarta "waye yakashemin MAHBUB wayyo nashiga uku in Zeenatu Ta Dora hannu aka tana kuka Zulaihat da jikinta yayi sanyi takamo Zeenatu ajikinta tana fadin " kada kidaga hankalinki muje mutabbatar dai Tajata suka karasa gurin tsoffin Lantana wata sa,arsu ta matso da sauri garesu tana kuka tana fadin "shikenan Ankashe uztaz Ya mutu ancucemu munyi rashin mallam Zulaihat ta kara yadda sai kuka itama Wata tsohuwa Iya Sha,awa mutuniyar Kirki tana son *KUYANGAR* ta maso da sauri gunsu ta janyo *KUYANGA* da taketa rufza kuka hannu aka tace mata " yi shiru Zeenatu kiyi masa addu,a Wanda kuma duk yayi wannan Abun Allah yatoni asirinsa Zulaihat tace "wai iya me akayi masane? Iya sha,awa tace " antashi dai anganshi yana kwance ayashe akasan katifarsa ga filo akan fuskarsa Awuyansa da alamar shaqeshi akayi yajigata ma kafin sukasheshin ba,a gano kosuwaye suka aikataba Kuka sosai suka ringayi dagama jin wannan mummunan labarin Kaf kafatanin gidan sarki sun shiga tu,ajjibun abun Banda wadanda suka aikata da yarima Itako jakadiya ackn bakin ciki ta wuni Gashidai tasan kosu waye amma badamar bayyanawa tana tsoro Taji mutuwar MAHBUB sosai har kuka tayi itama Yo muma munji mutuwarsa ๐Ÿ˜ญ fans kutaho muje gaisuwa gidan sarki Matan Sarki kaf sun halacci bangaren Bayi domin yi musu gaisuwa Mai martaba yazo gun ansallaci mamaci amma sai yakoma fada akaci gaba da karbar gaisuwa acan Suma bangaren bayi mata a bangaren Tsoffin gidan suka taru ake zaman makokin *KUYANGA* Tafi kowa agun damuwa domin jiyan sun Dade tare suna hira me dadi yana bata shawara na yanda zata zauna da rayuwarta tayi kyau inta Auri LAMIDO sosai yaita kwantar mata da hankali yana gaya mata irin son da yake mata Ko zuwa kiran da yariman yai mata suna taren shiya takura mata saida taje ajiyan Kwana tayi baci basha saida iya sha,awa ta takura mata Sai aranar sadakar ukun MAHBUB sannan LAMIDO yazo bangaren Bayi ya aika tazo domin yai mata gaisuwa Ta iso cikin hijab har kasa kanta akasa Tagaidashi ckn sanyin murya Idonsa akan fuskarta yana murmushi ya amsa tareda yi mata gaisuwa Ta amsa tana yi masa godiya Yace "Allah yajikansa yabaku hakuri da juriyar rashinsa Ta dago da kanta takalleshi tace " Amin ngd Yana murmushi yace "bakomai yiwa Kaine bari nakoma. Yakawo kudi masu yawa yamika mata " gashi kibada Sadaka Takarba tana fadin "Allah yakarba. Tajuya ta tafi tana zancen zuci " wato shi wannan nafahimci yana matuqar son yaga ya aikata aikin lada. Tayi murmushi "yanada hali me kyau ga yawan fara,a ๐Ÿ˜†๐Ÿ˜ฎ๐Ÿ™„๐Ÿ™„ *KUYANGA* kodai kin yaba ne...?? ********* Sai ranar sadakar bakwai Yarima yazo mata shikuma Gaisuwa Fuskarta babu annuri tafuto gurinsa tagaidashi tayi shiru agefe guda kanta akasa Yace mata " nasan kina cikin damuwa na rashin masoyi to amma yakamata ace kinsa hkr aranki domin Allah yafimu sonsa shiyasa yakarbi kayansa Tayi masa banza don ba burgeta kalaminsa yayiba Yaci gaba da fadin "duk kinrame Zeenatu Saikace Wanda mijinta yarasu Bata dago takalleshiba balle tabashi amsa Dayaga batada niyyar magana saiyayi mata sallama yatafi kawai yanajin farin ciki aransa Yasan gaba dole zata soshi inta zama mallakinsa domin Saiya kauda LAMIDO shima inyaso ahakura abashi ita don bazai juri yaga tazama mallakin waniba alhalin ayanzu yana mata mugun so Bayan wata biyar Cikin *KUYANGA* yana wata Takwas alokacin Yarima yazo mata da Kudi wai tayi sayayya na kayan jarirai Taso taki karba saikuma taga dacewar karbar dazatayi domin Allah ma take godewa da har Ya karkato da hankalin yariman kan cikin tunda wasu sunshiga zarginta afarko tunda yariman yace bacikinsa bane ake tunanin cikin wani ne YARIMA yazo da Sati biyu *KUYANGA* ta haihu ta haifo D'anta Zankadede kyakykyawa Wanda tsananin kyansa yasa aketa zuzutashi agidan tamkar balarabe Saidai kuma yadauko wasu abubuwan na yarima afuskarsa kamar kwayar idonsa da habarsa sannan wani ikon Allah saiga cindo ahannunsa na hagu Haka yarima yanada wannan cindo ahannun hagu Wannan shiya kara tabbatarwa Al,ummar gidan lallai wannan yaro mallakin Yariman jinin sane ba haufi Mai martaba ya Dade yana kallon Yaron Yatabbatar da wasu abubuwan na yarima ajikin Yaron saiyaga tamkar yarima yana Yaro Wata kaunar yaronce taringa shigar Sarki yaji inama tahanyar sunna aka haifoshi Koda yakebe shikadai kuka yaringayi waiyau shine da jikan dayazo bata hanyar Aureba yarima yacuceshi yabata masa suna Yarima baidauko halinsa ba baiyi shashanci ba yana saurayi Komai nasa da nutsuwa da kamun kai yayishi harsaida yayi Aure yasan mace to amma gashi Allah yajarabceshi da abubuwan tir agidansa Munjajanta maka Sarki Abdallah ๐Ÿ˜ญ Abin arxiki FAATU da MAMAH suka hada sosai na kayan jariri aka kaiwa *KUYANGA* Jakadiya tabazama ta gayowa UMMAH Fulani tahau gyada kai tana fadin "munafukai nagama ganosu sunayine badan Allah ba saidon Neman suna da kuma Neman duniya agun Sarki Kinaji ko Jakadiya nima zanhada kayan inbaki kikai badan Allah zanyiba saidan wadancan munafukan Dan aga banyiba sukayi tunda za.ace niya kamata nayi ko To zan yi nima Wanda yafi nasuma yawa sannan ke zanbawa kikai harkudi zandora amma inaso kiyawaita kai kafa don hidimtawa mejego dakuma duba yaro inaso kinuna musu soyayya tayanda inkin kashe Yaron baza,a zargekiba Jakadiya tahau gyada kai " angama ranki Dade. Jakadiya nafuta ta wuce sashen su FAATU dontakai musu tsegumin abinda UMMAH tace na kayan da zata hada itama Amma dai wannan jakadiya duk randa aka karya miki kafar dama baxamuzo cetoba kuma ko jaje bamuzuwa๐Ÿ™„๐Ÿ˜† Muje zuwa [8/5, 11:13 AM] Ummi Tandama: ๐Ÿ“ฟ *KUYANGA...* ๐Ÿ“ฟ *_๐ŸŒˆKAINUWA WRITERSโœ๐Ÿป ASSOCIATION_*๐Ÿค๐Ÿป ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *Nabilancy Luv* ๐Ÿ’˜ (Auntyn S&S) 80-85 YAU jakadiya bata samu damar yin tsegumin ba tana shiga sashen nasu ta tararsu Da Baki ga LAMIDO yana nan Dole tayi kwana takoma da baya *KUYANGA* Tasa jaririn agaba tana kallo Abu biyu takeji akansa na farko Tsanarsa adalilin Haushin Ubansa da ta hanyar da akasameshi tunda takasa manta yanda YARIMA yaringa mata karfa karfa akan saiya Santa a "Ya mace Ashe duk rabone Ke kira tabbas Banda ba,a Tara Sani ga Allah da tanada masaniyar samun ciki dashi da saita bujire masa bazatayi masa biyayya ba koda zai kasheta ko yaumata korar kare Awani bangaren kuma tanajin Tausayin Yaron ta irin hanyar da yazo Yanzu da ace ta hanyar sunna yazo da tuni gidan yacika da yan zaryar yiwa mutan gidan barka na xuwan jikan fari garesu Wani makokon bakin cikine yatsaye mata ganin Yaron yana kama da yarima futuk yanda tatsani yarima bataso zata ringa kallon photography dinsa akusa da itaba Kafin rasuwar MAHBUB ta tsara idan ta haihu in namiji ta haifa tasakawa Yaron SAHABI ta dalilin taimakon da yayi mata arayuwa takasa mantawa dashi akullum saita tunoshi inama zata Ganshi Amma yanzu data haihu babu MAHBUB aduniya saita canza tunani inhar za,a bata dama sunansa zatasaka Tasan dakyar in yarima zaiyarda tunda tasan ba kaunar sa yakeba Da SAHABIN nema ya iya bari tunda Abokin sane Ta goge wasu hawaye masu zafi akuncinta Adaidai lokacin da Zulaihat tashigo dakinta da Leda ahannunta Zulaihat tazauna kusa da ita kan katifar tareda ajiye ledar tana fadin "Kintisa yaro agaba sai kallo kike ko kunya bakyaji na D'an fari Yanzu idansu iya Sha,awa sukashigo suka ganki kina masa qurillar nan aikin kade da magana bayama inna Dije taji labari uwar karadi da gyani bakyalewa cewa zasuyi Ma kinata masa wasa *KUYANGA* Tayi gajeran murmushi tace " hhmmm Zulaihat walh banajin kaunar Yaron nan araina ko kusa dakinsan tsanar Dana masa da bazakice komai akai ba adole nake bashi NoNo nasan inban bashiba baida abinda xaisha kuma hakkin ne akaina kuma madara ba dauwwama zatayi gunsaba ba za tayi masa amfani kamar nononba sannan Za,a tuhumeni ackn gidan nan Zulaihat tace "hhhuuimm Zeenatu kenan kifa godewa Allah ma da kaddararki tazo da sauki gashi Allah yasa kinyi arxikin da yaro yasami gata ackn gidan kowafa sonsa yakeyi Nifa ji nakeyi inama niceke inama nice na haihun nan... " amma dai Zulaihat kina da son duniya shiyasa kike wannan tunanin meye abin so ga haihuwa irin wannan nifa bana kwadayin sarauta ballantana arxiki kenifa da ayanzu LAMIDO zaidawo yace yafasa Aurena ko ajikina tunda dama bansaka akaba Kuma da kike cewa yaron nan Dan gatana ta INA yazama Dan gatana tunda har yanzu Wanda yake amatsayin mahaifinsa baileko shiba balle mahaifiyarsa da bata kaunar Yaron Zulaihat tace "barfadin haka kadama suzo din aikowa dai yasan nasune kuma ko tasoshi ko kada tasoshi yarodai jinintane kowa yashaida tunda d'anta yadawo yafadi gaskiya anji Sannan inbasu so shiba dubunsu agidan sunsoshi koina fa kikayi zancen kyan yaron nan akeyi da kamarsa da ubansa ni tunani ma ko kunyace ta hanashi zuwa suda uwar HhhhmM " kawai *KUYANGA* Tace tana fadin "me kika kawo aledar ne ? " magungunan da akasiyo mk ne gashinan hardana Karin jini aciki Tahau budewa tana nunnuna mata ********* Da daddare bayan Sallar ishsha 'i saiga sakon kiran *KUYANGA* daga fada sarki ya aika mata Zulaihat ce "yar Rakiya tadauki jaririn ta goya abayanta Koda sukaje bayan sungaida mai martaba yace mata " kiyi hakuri Zeenatu natasoki da dare ga jego Kanta akasa tana murmusawa tace "Bakomai " Yaci gaba "To dalilin kiran dama akan sunan da za,a sakawa Yaron ne daga bakinki nakeso ba daga bakin yarima ba domin bai isa komai ba aguna kenafiso kixaba domin ranar suna arada masa Sai taji inama ta hanyar sunna aka samoshi da kawai cewa xatayi SUNANKA ME MARTABA To amma yata iya daidai ruwa daidai tsaki takada baki tace " sunan margayi MAHBUB nakeso asaka masa Ranka yadade Ya gyada kai yagamsu yaga kuma kyautawar ta duk da baisan tsakanin suba amma dai yasan Dan UWA yake gareta kamar yadda yake matsayin bawa haka take itama Sarki yace "to jeki abinki za,a saka masa akwai wani Abu da kike bukatane? Ta girgiza kai tace " Babu. Yabasu umarnin tafiya tunda babu Suka mike suka futa ko Dan. Bai Tambaya ba (amma bawai Dan baya son saba shikansa yanajin ba dadi inya tuna yanada jikan da aka haifa ba Aure ack) Bayan kwana biyu ana gobe Za,a rada masa sunan saiga kaya daga UMMAH akwati guda kayan jarirai manya masu tsada ga kudi ackin akwatin dubu hamsin (Dan ma mekawowar jakadiya ta dauke hamsin din kai yarima me yasako dama) Iya Sha,awa da inna Dije da sauran tsaoffin gidan nasu *KUYANGA* Sukaita murna ana guda Jakadiya ta dauki Dan tana yabashi azahiri azuci kuwa kiyasta yanda zata kasheshi takeyi Tun daganan jakadiya take kawo musu kafa sashen nasu duk don su saki jiki da ita tana nuna soyyyarta ga jaririn Aranar ma agunsu ta wuni harda tayasu yiwa yaro wanka Da dare ana gobe suna saiga Yarima yazo shima ganin yaro domin yanada labarin yanda aketa fadin kyansa da kamar da sukayi shiyasa yazo dai yaganewa idonsa yakuma gaya mata sunan dayakeso yasakawa Yaron ๐Ÿ˜๐Ÿ˜‡ka makaro Ajikin katangar dakin *KUYANGA* yaja yatsaya ta farfajiyar tsakar gidan bai shigaba Ta aika aka kai masa farar kujera ta roba Ta aika masa da Yaron duk Zulaihat CE yar Aiken Yakurawa Yaron idon akwai hasken tsakar gida nafitilu Yaji kaunar yaron tashigeshi tabbas ko bai Aure taba zai karbi kayansa inyayi Aure yarike kayansa Tafito gurinsa tana taku ahankali Ya amsa sallamar da tayi Bayan tagaidashi tanemi ta juya takoma Yace mata "Dakata tukunna daga zuwa saiki tafi banga kyakykyawar fuskar kiba sannan banyi miki godiyar Haifar me kama dani da kikai ba Tayi masa banza Yace " Zeenatu INA matuqar sonki nasan kingane hakan walh nakasa sakat araina INA so tunda kin haihu lfy inkinyi arba,in Adaura mana Aure... Tadago da sauri takalleshi "anya yarima ba kwaya yashaba kuwa tunda tasan yana korawa To ita kuwa me zatayi dashi ga LAMIDO mutumin Kirki Allah yai mata tsari aiko babu LAMIDO bazata Aureshiba Yakatseta da cewa " kin amince ? Ta girgiza kai tace "LAMIDO shine mijin da zan Aura ayanzu haka ina ganin Allah ne yadubi abinda kayimin shiyasa yabani shi amatsayin miji dan hakama kacire batun wai zamuyi Aure dakai Yace mata " kina nufin bakya sona? Tace "babu sonka araina kam! Waima kamanta wata rana daka so kwanciya dani naki kacimin zarafi kace mezakayi dani bawai sona kakeba me zakayi da BAIWA maqasqanciya... Yadaga mata hannu don borin kunya yace " ya isa bance kiyimin tuniba yadade da wucewa yanzu dai gonb suna na zabi insaka masa SAFWAN Tayi murmushi tace "to saikaje kasanar dame martaba yacanza Wanda zaisaka Yace " me kike nufi? Yaxabi wanine bansaniba? Tace "tun jiyama yakirani fada yabukaci zabina akai nagaya masa MAHBUB nakeso asaka Yaxabura yakusa yarda Yaron don furgici Tayi saurin taro D'an ta Eyeeee๐Ÿ˜…๐Ÿ™„๐Ÿ™„๐Ÿ˜ณ๐Ÿ˜ณZeenatu Ashe dama kina sonsa Yanunata da yatsa " Baki isaba wannan suna baiminba niya cancanta inzaba bake ba Nike da iko danhaka maza kikoma kice SAFWAN za,a saka masa ba Wani sunan BAWA ba Tayi murmushi tace masa "aika makaro aikin gama yagama mai martaba yakarba tuni Dan haka banzamo meraina nagaba daniba da zanje masa da canxa magana Tana gama fadin hakan ta juya ta tafi abinta Yabita da kallo yana kwafa Da bakin ciki yakwana Tirkeken ragon daya ware zaikai don ayankawa jaririn saiya fasa bayarwa domin ba sunan dayakeso za,a sakaba bazai iya xuwar wa sarki da canjin sunan ba domin kallon arxiki ma baya samu inyaje gaidashi Yanajin wata irin kaunar jaririn domin sonta ma yafara raguwa yadawo kan Yaron kyan Yaron yatafi dashi tabbas zaiyi fashion dashi agun abokai Da Sassafe gida yakacame da taron suna dama tun asuba a masallaci da suka idar da sallah aka radawa yaro suna da MAHBUB Raguna biyu manya mai martaba ya aika fadawa suka kai bangaren Bayi aka yanka amatsayin Hakika Tabbas kowa ya aminta agidan yaro dan gatan sarkine tunda gashi sunga abubuwa da dama na soyayya daga sarkin Ita kanta *KUYANGA* taji Dadin hakan saikuma tasake akoina tunda da ace Dan bai karbuba agidan da tuni anata tsangwamarsu Aranar kwana tayi rumgume da d'anta tanajin wata kaunarsa na shigarta ayau da yaron ya amsa sunan Masoyinta taji kaunarsa tashiga jikinta tabbas tana masa so sosai Albarkacin son da tayiwa margayi MAHBUB A Bangaren UMMAH Jakadiya takawo mata tsegumin yanda Sarki yakai abin yanka manya manya na hakika UMMAH ta quta cikin Takaici tace "Lallai Ashe har soyayya aka shiryi nunawa Dan shege kenan nifa har yanzun jakadiya banyarda da jaririn nan Jinina bane tabbas akwai meshi awaje Jakadiya kamar ta furta " Duk kamar da sukai ๐Ÿ™„๐Ÿ˜† Saitaja bakinta tayi tsit sbd tsaro kada UMMAH Taji haushinta UMMAH tace mata "kinajina ko agobe nakeso aikinki yafara akowane lokaci kika sami dama ki shaqe min Yaron yamutu shine kadai burina da farin cikina mutuwarsa inhar kika aikata hakan Alkawarukanki sunanan zanbakisu Jakadiya tace " angama uwar dakina yanzuma can zantafi inshiga cikinsu inzauna ayi komai dani kafin gobe in aikata aikinki........ Tofa muje zuwa fans Auntyn Sayyada da Shahida ce ๐Ÿ‘Œ๐Ÿป [8/8, 10:02 AM] Ummi Tandama: ๐Ÿ“ฟ *KUYANGA...* ๐Ÿ“ฟ *_๐ŸŒˆKAINUWA WRITERSโœ๐Ÿป ASSOCIATION_*๐Ÿค๐Ÿป ```{United we stand and succeed;Our ambition is entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *Nabilancy Luv* ๐Ÿ’˜ (Auntyn S&S) 85-90 *KUYANGA* takurawa junior MAHBUB idanu tana karewa irin kyan Da Allah yabashi sai ayau taji ta kara kaunar Yaron dayaci sunan MAHBUB Ta rumgumeshi sosai ajikinta tamkar Wanda za,a kwace matashi tana Adduar Allah yasa yagado hali da ilimi na me sunan sa Yanata baccinsa dama yarone me hakuri inyasha nonon dare baya farkawa saisafiya Sallar ishsha,i akayi inba,aci sa'a ba shida tashima sai safiyar Zulaihat bata dakin nata taje sashen Inna Dije takarbo abincinta Kafin ta dawo bacci yafara daukanta tana rungume dashi akan kirjinta Can ta motsa da sauri da taji motsi ana shigowa tayi tsammanin ko zulaihat CE Saitaji sanda can kuma taji tsit Da taji dai shiru ba,a shigo dakinba saita dire junior tafuto tana kiran zulaihat saitaga bakowa atsakar gidan Ta dau buta tashige bandaki abinta dama fitsari takeji ga cikinta yana murdawa tunsafe dama take Dan shiga toilet din tana ba haya Acan waje kofar gida Yarimane yazo gunta yanata Neman Wanda zai aika yaji shiru tsit babu gilmin mutane sbd whether ta sanyice da wuri ake shigewa akwanta Yananan tsaye dai dayaga zai tsayu agun saiyayi kokarin yacusa kansa kawai domin dama sallama yazo yi mata yaga dansa kafin gobe yatafi Turai abinsa Adaidai sadda yazo saka kai cikin gidan alokacin ne Yaga fitowar mace aguje tayo waje daga ciki afurgije ba gaskiya atare da ita ta bangajeshi tazura da gudu Baiyi kasa aguiwaba yabi bayanta yazage karfinsa yacimmata acan nesa da gidan yadamqeta Wa zai gani inba Jakadiya ba Tana ganinsa tasan yaganta sai jikinta yayi sanyi tunda tasan asirinta yagama tonuwa ayau Yace mata "jakadiya kece dama?meya kaiki bangaren bayi awannan Daren meyasaki uban gudunnan ? Take tarasa ta cewa ta diririce tafara kuka tana fadin " karufamin asiri kamar yadda narufa maka Yanuna kansa "kika rufa min kamar Yaya? Tace " Eh Ai inada wani sirrinka da bakowa yasaniba sai ni da mutanenka dakasa aikin Yarima ya mamakantu da maganar jakadiya ya nuna kansa yace "Sirri kuma?ni nasaka aiki ?to akan me nayi aikin dahar kika Sani? Tayi wata dariya kana tace " kasani cewa akan kunne na naji kabada Umarnin aje akashe Bawa MAHBUN kawai don son rai da kishin da kake dashi nasan komai yarima ayanzuma daka ganni nima akan aiki nake Yace "wanne aiki kikaje gidansu Zeenatu awannan Daren ? Jakadiya tace " aikin kisan kai... Dasauri yawatsa mata Tambaya "wa kika kashe ?kada dai Zeenatun? Ta girgiza kai babu tsoro atare da ita don tasan me ta taka " Dan Zeenatu nakashe amma mahaifiyar kace tasani hakan Yadafe kansa "wa,iyaxubillah D'an nawa kika kashe? Tace " kayi hkr banida laifi Yaharxuko kanta "Kinfi kowa laifi kuma saina hukuntaki bazan kyale kiba Tace " idan har katonamin asiri tokamar mahaifiyarka katonawa sannan nima saina tona naka asirin nabaya Tana gama fadin haka ta tawuce abinta tabarshi da tarin bakin ciki Kai yadafe yana fidda hawaye Jakadiya ta cuceshi yana matuqar son Yaron nan SBD shi yazo gidan tabbas mahaifiyarsa ce taja masa komai Ashe dama ba kaunar jininsa takeba Ihu da hargowa yajiyo ta cikin gidan Su Zeenatu itada Zulaihat ne suke kuka da karfi da neman dauki ganin anzo ankashe yaro hargida Dayake ta bayan gidan yake tuni yai saurin barin gurin kada wani yaganshi yashiga zargi ****** Kuka sosai sukeyi gidan yacika da mutane anata jajanta mata narasuwar jaririn ta Wanda akashigo hargida aka kasheshi Kowa mamakin wannan Abu yakeyi anata fadin lallai duk yanda akai makashin yana ckn gidan kafin tashiga bandakin haka bayan makashin yafito zulaihat ta shigo gidan Da filo akai amfani wajen danne shi harya mutu Saida safe aka sallaceshi aka kaishi Da yarima aka kashi aka binne yanaji yana gani dole yai shiru bai iya bayyana wacce takashe yaronsa abin sonsaba Ranar dama fushi yayi da mahaifiyarsa bayan adaren yaje yai mata bore da kuka akan ta aika ankashe abin sonsa jinin jikin sa Mai martaba ma yaji mutuwar Yaron dakansa yataka yaje yaiwa *KUYANGA* Ta,aziyya domin yana son Yarinyar aransa domin Nutsuwarta Kwana tayi tana kuka tana tuno fuskar yaronta Aranta kuwa tanajin bazata taba yafewa Wanda yai mata wannan abuba don ancuceta saida akaga tafara kaunar yaron aka rabata dashi UMMAH kuwa ranta fes ta cikawa jakadiya alkawarinta na abubuwan datace zata bata Ammafa agun yarima bata jin ta dadi shiga daya shiga biyu saiya gaya mata magana tamkar ba mahaifiyarsa ba "Kinji dadi kinraba Dan tahaliki da duniya kunji Dadin hakan Kuda Allah kuncuceni kunrabani da farincikina. ๐Ÿ˜kunjishifa kaika manta daka sa aka raba bawan Allah da duniya Ashe abun ba dadi Kwana uku da faruwar hakan LAMIDO yazo yi mata gaisuwa Tafito cikin hijab har kasa Yakura mata ido harta iso gareshi tagaidashi ckn ladabi Ya amsa yana kallon Dan karamin bakinta mekamada alawar lollipop Yace " ZEENATU ya hakuri kuma? Ckn sanyin muryarta tace "Da Godiya Yace " Allah yajikansa yabaki hakurin rashinsa Ahankali tace "Amin nagode" Yaso yafurta mata wata kalma saikuma yafasa Yaimata sallama yatafi Yauma binshi tayi da kallo Yanda yake takunsa na kasaita da iya tafiya ta sarakai abin birgewane kokusa Yarima baikamoshi akomai ba Tabbas LAMIDO na daban ne Ayau tayiwa Allah godiya dayasa zata zamo mallakinsa donta farajin wani Abu akansa Abin mamaki ma da dare kasa bacci tayi tayita juyi akatifa tana tuno irin yanda yake maganarsa da tsari da tausasawa ga iya kallo kodon idanunsa Sexy eyes ne gashi da kyau da tausayi Tabbas Samun Namiji irin LAMIDO sai antona Tooo๐Ÿ™„๐Ÿ˜ณfans *KUYANGA* me kuka fuskanta ne a Heart din KUYANGA To kodai ta kamu ne ??? Muje zuwa [8/8, 8:11 PM] Ummi Tandama: ๐Ÿ“ฟ *KUYANGA...* ๐Ÿ“ฟ *_๐ŸŒˆKAINUWA WRITERSโœ๐Ÿป ASSOCIATION_*๐Ÿค๐Ÿป ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *Nabilancy Luv* ๐Ÿ’˜ (Auntyn S&S) 90-95 FAATU ce A zaune aturakar mai martaba bayan yagama cin abinci yadubeta yace "Kince kinada magana inajinki meke tafe dake akwai damuwane? Ta gyara zama tace "Dama maganar LAMIDO ne Naga tunda har anyi sadakar arbain din jaririn Zeenatu nace to me zai hana atsaida ranar Auransu da LAMIDON ba tunda har ya amince kuma naga kamar yafara sonta Murmushi Sarki yayi yace "To babu komai sai a tsaida Wata daya mai zuwa sai adaura Auran nasu bamusan me Allah ya ajiyeba kuma Inaso aranar da za,a daura Auran ayi bikin dorashi Kan karagar mulki natsufa yakamata nayi murabus nadorashi akai duk abinda nakeyi wanda yakamata yake kaina zai iya sannan ya cancanta don haka zansa ayi shela agari kowa yasanda wannan rana FAATU tace "To amma Takawa kana ganin wannan abun dakayi bazai kawo rabuwar kai atsakaninsa da Dan,uwansa yarima ba mahaifiyar safa ta kudurci dantane zai zama sarki natabbata zataji ba dadi koma tayi bore Sarki yace "Nike da iko da komai daga kan mutan gari da bayi da ku kanku iyalaina da dukuma Sarautar kanta Dan haka babu me canzamin zabin da nayiwa Garina Ckn biyayya FAATU tace " angama ranka ya Dade Allah yaja kwana yakara lfy Yace "Amin Fatima. Inkin futa kituromin LAMIDO tace "To. Bayan futarta tazarce Dakin MAMAH domin takai mata wannan batu sbd duk abinda take ciki saita sanarta kuma bata zartar da komai saida izininta Jakadiya na zaune kusa da MAMAH tana mata hira Shigowar FAATU yasa ta tsahirta tareda gaisata FAATU ta amsa tareda zama kusada MAMAH Ta zayyanewa MAMAH komai na abinda Mai martaba yatsara na bikin LAMIDO da *KUYANGA* Da kuma bikin nada LAMIDO Sarki da za,ayi Jakadiya na qunsa tafuce da rawar jiki ta nufi dakin UMMAH Donkai mata Rahoto UMMAH taga shigowar Jakadiya hankali atashe Ranta yai matuqar baci dajin wannan kalami daga bakin Jakadiya kamar ta Dora hannu aka tayi kuka taji Inama tana da damar da zata hana wannan Nadi Jakadiya tace "Kibar komai ahannuna domin nima bazanso adora Lamido INA gani ba zanso ace Yarima ne zaizama sarkinmu UMMAH ta gyada kanta tana fadin "Nagode jakadiya nasan ke me qaunata CE Jakadiya taxo futa adakin kenan sukai kicibus da Yarima shima yashigo dakin UMMAH Kallon kallo sukaiwa juna ko gaidashi Jakadiya ba tayiba kowa aransa akwai abinda yake ayyanawa akansu Yaxauna akan kushin yana fadin "UMMAH naxo gaya mikine zantafi turai nan da kwana biyu nagaji da zama agarinnan babu masu sona Tace "Kamar yaya babu masu sonka baya gamu nida mahaifinka Yace "Hhhmmm adane kike sona amma ayanzu kam dagake har TAKAWA babu me kaunata kinrabani da gudan jinina kinkuma ki sanyawa Takawa ya yafemin yafaina fushi dani Tace "YARIMA kai kake janyo komai gashi yanzuma zaka tafi kuma kasan bason tafiyarka yakeyiba Danhaka tafiyarka daidai take da karin wani laifin kanka sannan kuma abinda nayi daidaine agunmu nidakai domin inhar Yaron ya girma xai iya tasowa ackn wani yanaya na mugayen halayya ko kuma muzama abin kwatance Inaso kacireshi aranka kafuskanci abinda ke shirin Kasantomu na Nadin Sarauta da mai martaba zaiyi akan kaninka LAMIDO Yarima ya gyara zama da firgici akan fuskarsa yace "Da gaske UMMAH yanzu haka Takawa zaimini SBD yabakanta min rai. Tabbas saina dauki mataki sosai akai Waye ya kawo miki wannan labarin? Tace "JAKADIYA CE yace "shikenan. Yafuta yanufi Dakinsa yadebo kudi masu yawa aljihunsa yafito yanufi sashin da Jakadiya take Cikin ikon Allah Yatararta Ita kadai kuwa Tanaganinsa gabanta yafadi ganin irin kallon da yayi mata dazu tana ganin ko akwai manufarsa ta hakan Yakalleta ba fara,a afuskarsa ya mika mata kudi ahannunsa yace "Karbi wannan ! Jiki na tsuma ta karba Tace "na menene wannan? Yace "Nakine aiki zansaki Tace '"aikin meye hakan? Wannan uban kudi yafi karfina Yace "Yanda kika zama makisiya shine nakeso ki kashemin wani nima Ta zabura "Baxan iya ba walh Yadaka mata tsawa "zaki iya !! Waishinma kinji kowaye? Tace "waxan kashe? Kaitsaye yace mata "LAMIDO!! taji dirar Kalmar akunnenta tadira gefe tana miko masa kudin "karbi kudinka bazan iya kashe LAMIDO ba ka kaiwa wadanda sukai maka aiki akan MAHBUB suyi walh bazan iyaba Yadaka mata harara yace "babu Wanda zansa yayi saike don haka kisani k'in yinki yana daidai da tonuwar asirinki Yana gama fadin haka yajuya yabar ta tsaye atsorace take da wannan lamari ina ita ina iya kashe LAMIDO to yanzu yazatayi gashi tana bukatar kudin sbd yawansu yakai ace tagina kanta da rayuwarta na wasu shekaru toshin yanzu Yaya zatayi ? Rana zafi inuwa Quna!! Mafita ce tazo mata arai gara taraba kudin biyu taje tasami Fadawan da taga yasa su kashe MAHBUB tabasu sutayata aikin ****** Abin Duniya yadami Yarima gashi da gasken Gaske Mai martaba yajuya masa baya ko gaisuwarsa baya amsa masa don hakan ma ya qudiri niyyar kawar da LAMIDO domin yazamo dolen sarki yanad'ashi agaba yakuma Auri *KUYANGA* Shawara ya yanke natafiya Turai tun agobe domin in aka kashe LAMIDO kada adora zargi akansa gara ayi bayanan Da safiyar Lahadi ya daga ko sallama da Mahaifinsa baije yayiba yabarwa UMMAH sallahun tagaya masa Itako dama ranta baiso ba Da kuwa taje ga sarki tagaya masa ko uffan baice mataba shiru yayi mata dole tabar maganar yariman ta tafi Amma ta qudurci yin aikin Asiri atsakaninsu domin janyo soyayyar yariman azuciyar sarkin Yarima Yana dira akasar waje Allah yahadashi da wata bakar fata Ta nuna tana muradinsa azahiri bama tasan shidin Dan sarki bane saida taga alamomi a Dan zaman da sukayi na mintina a Airport Hindu "Yar Minister ce a jahar Kaduna mahaifinta me kudine sananne Alh Khalid Baffanyo "Yar boko ce gata da jijji da kai da dagawa Amma yau sai Allah ya damketa duk yanda take wulakanta samari a garinsu sai gashi ayau Allah yasa mata Soyayyar Saurayin da batasan asalin saba tashi guda Dayake yariman ma na mamajo ne tuni ya afka cikin sonta shima taringa kanainaya da kissa don yasota takuma yi sa,a Har rakiyarta yanema gidansa takuma bishi Saidataje gidansa ta tabbatar shidin Dan babban gidane ta gane dawa take tare Domin tafahimci da alamar Dan gatane kamar yadda take yar gatan babanta Saida suka kadaita sannan yahau tambayarta meya kawota England ? Tace masa tazo Hutu ne gun kawunta Wanda shiya riketa alokacin datayi karatunta acan Takuma gaya masa asalinta da matsayin data taka na aiki domin tana aiki da Ministry of Health itace Director asashen kula da Asibitocin Shiyyar Su Ya jinjina kai yace " Ina sonki zaki Aureni? Da zakuwa tace "Kwarai kuwa inhar da Gaske kake na amince maka amma kada ka yaudareni bani da dadi Yayi dariya yace " nima ba Dadin gareniba. Tayi dariya kawai Aranar ta tayashi kwana agidan sunyi romance amma basu zarta nan ba don ya ayyana aransa ita zai aura takwanta masa Aranar sun tsaida magana zaizo nanda sati biyu Kaduna yagaida iyayanta zai kuma tura magabatansa Tunda suka tsaida magana da Hindu shikenan soyayya ta dinke atsakaninsu akullum suna tare awaya ba dare ba rana Shaquwa sukai sosai in basuji muryar juna ba basajin dadi Tana daga Kaduna amma kowa nata yasan da Fara soyayyarta da yarima Iyayanta harsun San da sunansa domin ta gaya musu tuni Dama ita kadai suka Haifa itace shalele sunaji da ita basa son bacin ranta Yarima yakasa sakat tuni yahado kayansa sai Nigeria Amaimakon yadiro Kano saiya zarce Kaduna Kai tsaye yabi kwatancen d tayi masa Ta aika da mota aka daukoshi aka kaishi gidan Yaji Dadin tarbar da tayi masa da yan gidan Yai mamakin ganin shankwamen gidansu kamar gidan Gwamna ga tarin motoci kamar ana saidasu Akaita kawo masa gaisuwa ma,aikatan gidan aka cika gabansa da kayan ciye ciye A main falour aka saukeshi Mahaifiyarta taje takuma yaba da zabin diyar tata Saida yajira mahaifinta Alh baffanyo yadawo suka gaisa ckn mutunci Dayake mutumne wayyaye tuni yace yabashi ita yakuma bashi sati yaturo magabatansa Yarima yai na,am Sunyi soyayya kafin yatafi da yamma yai mata sallama yabi jirgi yataho Kano Yaringajin kamar karsu rabu tamkar Wanda tayi masa asiri yaringaji Ransa Dari qal yasami Matar Aure yasan yanzu dole maimartaba zai sauko inyaji zaiyi Aure Muje zuwa fans [8/12, 10:51 AM] Ummi Tandama: ๐Ÿ“ฟ *KUYANGA* ๐Ÿ“ฟ *_๐ŸŒˆKAINUWA WRITERSโœ๐Ÿป ASSOCIATION_*๐Ÿค๐Ÿป ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *HAPPY SALLAH* Eidโ -Mubarak to all the muslims all around the world. May Allah SWT grant us the ability to make the most of this years. *Nabilancy Luv* ๐Ÿ’˜ (Auntyn S&S) 95-100 Da Isar yarima gida kai tsaye gun mahaifiyarsa ya nufa Tayi mamakin zuwansa bai sanar mata ba Yana murmushi yace "UMMAH dawowar gaggawace tasameni adalilin Matar Aure dana gamu da ita UMMAH da mamaki tace " Matar Aure kuma yarima ?a INA? Yagyara zama yazayyane mata komai Tahau gyada kai tana jin farin ciki aranta domin jin yarinyar yar masu dashine kuma hakan yayi mata arai tafiso shima yariman yayi Aure kamar yadda LAMIDO zaiyi domin Aure yana karawa mutum martaba da kima a idon Al,umma abin tinkahon tane ace tayi suruka Yar babban gida ba "yar Bayi ba dama Tasawa abin albarka tareda karfafa masa guiwa " na amince maka kayi Aure adaidai wannan lokaci Yarima domin makiya suji kunyar abinda ake shirin maka tunda nasan duk don abakanta maka aka shiryi Auren su balle anga kafito da maitarka karara ka watsar dasu zuwa gaba mushirya kutunguila akansu inhar Aka nada LAMIDO sarautar domin baxamu barsuba Ya gyada kai yace "Nima akwai shirin Dana shirya akan LAMIDON, UMMAH saidai zan ajiye komai agefe sai bayan nayi Auren tukunna amma kiyi kokari Takawa ya karbi abin da muhimmanci ahada ayi tareda na LAMIDON domin iyayan yarinyar da Gaske suke asatinnan zasu Zuba idon ganina UMMAH tace " kada kaji komai Aure fa kamar anyi Angama ****** Koda UMMAH tajewa da Mai martaba wannan zance Murna ma yayi domin yasan yin Auren Yariman kamar wata hanyace zatazo masa ta shiriya don haka saiya nuna amincewarsa da gaggawa tareda tsayar mata da maganar zai tura aje akai kudin Aure tareda tsaida musu rana daidai Dana LAMIDO Taji dadi tayi masa godiya takoma yiwa Yariman Albishir Da farin ciki yakwana jin antsaida masa ranar Aure sati uku masu zuwa Yaiwa Amarya Hindu albishir Ai ihu taringayi Dan dadi da farin cikin data tsinci kanta aciki Tuni ta gayawa iyayanta tamkar suma sungaji da itan saigashi suma suna murnar Ackn Satin kuwa Mai martaba ya Aiko batun nan Aure Galadima ne da Liman Amintattun Sarki sukaje kai kudin Aure Dubu Dari biyar Da kwatance suka sami gidan domin mahaifin Hindu fitaccene babu Wanda baisan Gidan Minista ba a A T/wada Kaduna Anbasu an amince musu nanda sati ukun Dayake kanin mahaifinsa ne da Yayan mahaifin nata da Amininsa suka karbesu agidan Ministan Anbasu tukuici me tsoka tareda karramawa domin da tsaraba aka rakosu da zasu koma Kaji da cake da lemuka da turarika da shaddoji haka aka zubasu a but din motarsu Koda suka koma suka rattabasa sarki abinda suka gano cewar iyayan yarintafa Sunada mutumci da Halin girma Sarki yaji dadi yasawa abin Albarka Zancen Auren yarima da LAMIDO yazagaya gari anata irgen kwanakin dasuka rage sbd irin shagulgulan da aka shiryi yi sbd nad'in da za,aiwa LAMIDO na zama sarki da zaiyi Lefe ma yarima A England yatafi yahado Shiko LAMIDO dayaje gun *KUYANGA* tambayarta yayi "Gimbiya! Takalleshi da murmushi kan fuskarta tana murza zoben hannunta da MAHBUB yabata kafin yarasu Tace ahankali " Harna zama gimbiyar ?ai naga Gimbiya Matar Sarkice wacce yakeso kuma Yayi murmushi dama shidin ma,abocin murmushine yace "Zeenatu kenan ai kamar kinzamane Tunda saura kwanaki daga lokacin da Aka daura mana Aure nima naxama Sarki Kema kinzama Gimbiya tunda aranar za,ai Nadi Ta gyada kai tanajin annashuwa aranta da kuma sonshi ackn zcyrta Shima hakan yakeji aransa agame da itan Yakatse shirun nata dacewa " Awace kasa kikeso ahado miki lefe? Takama baki "Ni na isa? Wacece ni tab ahado anan Yasha mur! Yace " keko kika isa kuma ke me matsayice da kima don haka daga yau kidaina ma daukar kanki maqasqanciya agidannan domin kintashi daga *KUYANGA* kindawo *GIMBIYA ZEENATU* Tayi murmushi ita kanta sunan yayi mata dadi Yaci gaba da fadin"kinaji ko zamuje Sudan ko Dubai inhado miki komai acan nida Abokina Safwan tare mukai karatu dashi acan mahaifinsa ne liman na gidannan tare TAKAWA ya biya mana zaizo kugaisa Takawa yana sonki Zeenatu ki godewa Allah jarabtar da Allah yayi mk arayuwa tazame miki riba da ci gaba domin ayau yakirani yakaramin kudi akan Wanda yabamu na siyayya nida yarima yace ke tadabance inyi miki siyayya mekyau Yakarasa maganar yana kallon kyakykyawar fuskarta yana murmushi Itama murmushin takeyi tana fadin "Naji dadi nagode ayiwa takawa godiya Yace " To ni zankoma Tayi masa yar rakiya da baifi taku biyar ba ta koma tana waigensa LAMIDO ya burgeta tabbas yanada aji ga iya magana da kalami duk macen dayace yanaso dole ta amsa domin shi din abin sone Tana shiga Daki tafada akan gado tana fara,a Zulaihat tabita da kallo tana fadin "Yarinya tashiga kogin soyayya tafito Dafatan kinyo iyo kinkamo kifi? *KUYANGA* tayi murmushi tareda tashi tazauna tana fadin "Zulaihat kifaye ma nakamo ba kifiba tabbas LAMIDO yatafi dani kamar yadda nima natafi dashi Allah nake godewa da yabani wannan baiwar ta zama matarsa gashi Yace Takawa yana sona yakara masa kudi akan Wanda yabasu da yarima na soyayyar lefe Mahaifiyarsa kawai nakeji bansaniba ko itama tana sona kamar yadda Sarkin ke sona? Zulaihat tace "Hhhhmm Zeenatu kenan aike abar soce itama banajin zataki sonki tunda ta tako har gidannan tazo miki barka da gaisuwa Dan haka kigodewa Allah kawai " Allah nagode maka.cewar *KUYANGA* Zulaihat tace "Ga magunguna can inji Iya Sha,awa tace kada kiyi sake da kowanne masu kyaune akwai nasha da nono dakuma nasha da Zuma anjima zata kawo miki na tsugunno *KUYANGA* takama baki " oh maganin mata kuma tun yanzun? Zulaihat tace "Eh aishine daidai hakan kinga abin xaifi kamaki Sosai " Hhhmmm Allah dai yasa ba daci Zulaita tace "koma me gareshi haka zakisha tunda kinsan Halin tsoffin nan insuka bada Abu ba,ashaba fada zasuyi suce suna mana gata muna gocewa *KUYANGA* Tayi murmushi tadauki magungunan tafara hada wa xatasha ****** Yarima yadauki wayarsa yalalubo nambar abokinsa SAHABI da suka Dade basuyi wayaba Acan bangaren SAHABI yana ganin kiran Yariman yayi murmushi yadaga yana fadin" Dama kana da nambata kamance dani Yarima yace "inada ita mana fushi nayi dakai na abinda kayimin amma yanzu na huce Dan haka Ina gayyatarka Aurena karshen wata SAHABI yayi murmushi yace " Allah yasanya Alkairi nima Auren zanyi nanda sati mezuwa kafin nakama Yarima yace "Shegen kaya wato banda nakira bazanjiba kenan ?lallai na yarda karikeni aranka SAHABI SAHABI yace " ba haka bane yarima Aurenne ba Wanda nakeso ba Hadani akai da yarinyar diyar kanin mahaifina ce ita ke sona Dariya yarima yabushe masa yace "sunmin daidai walh domin insun kyaleka " yar talakawa zaka dauko musu banza me sakaran ra,ayi Sahabi yace "kai " yar INA zaka aura? Yarima yabashi labarin Hindu da yanda suka hadu a Airport a England SAHABI yace "Hhhmmm to bagiringirin ba dai tayi mai Yarima yace " oho dai nafika tunda ni Auran Soyayya zamuyi "Nima bawai kinta nakeba tunda yar 'uwa tace Ina Zeenatu naji ance abinda ta Haifa yarasu Yarima yace " Eh, Sunkusa Aure da LAMIDO... SAHABI yakatseshi da sauri "ya akai hakan dama soyayya sukeyi? Nan yarima yazayyane masa komai SAHABI yace " Gud ammafa naji dadi LAMIDO yaburgeni Allah yasanya Alheri Yarima baikulaba yai masa sallama Acan kasan ransa soyayyar Zeenatu na nan baxai mantawa ****** Anata shirye shiryen biki akowane bangaren Shi yarima agidansa na cikin gari zai zauna baiyda ra,ayin zama acikin gidansu wai kada atakura masa shida amaryarsa Shiko LAMIDO sashi guda aka gyara masa agidan me dauke da dakuna agidan gidan yasha gyara babbane dama ba kowa ciki Aka zuba komai na alfarma agidan Lefe yazo daga Dubai akwatuna goma Sha biyu cike fal da kaya tsadaddu Komai dozinne ciki koina acikin gidan da wajen gidan zancen kayan lefensa akeyi domin sunhadu sunburge kowa Saida aka kaiwa takawa yagani yace sunyi yasa albarka kana mata suka hadu suka dauka bayan Su MAMAH DA FAATU sun gani aka kaiwa KUYANGA Tsoffinsu sunsaka albarka sunyaba Angyagije Zeenatu anfiddata kunya dukda sunsan arina Shiko Yarima karya yahada ackn kayan duk don ace nashi sunfi na LAMIDO Harda key din mota yasaka akan lefen mahaifiyarsa ta saka takardun gida duk akan lefen gudummawarta duk don mutane suga na LAMIDO lami ne sannan su burge mutan Kaduna Amarya anata rawar kai anatashan magungunan karin Ni,IMA da tsukewa sbd gurin anshigeshi Tun fara karatunta a Abroad tayi soyayya da wani Anwar yamaisheta tamkar mata ta amince masa daga baya ya yaudareta yana gama karatu yakoma kasarsu yamance da ita Shiyasa data hadu da yarima takasa ta tsare saida taga natsaida lokacin Aure sannan hankalinta yakwanta Duk kashe kudin da akai alefenta baisa sunyi rawar jiki ko an yababa tunda su ba farin shigar komai bane ita kanta motocinta biyu na hawa tanada gidaje kuma Aiko dai yan kawo kaya suka koma jiki asanyaye danma anbasu tukuici me tsoka Rana bata karya saidai uwar diya taji kunya Allah yakawomu wannan rana Ranar Asabar takama ranar daurin Auren da nadin sarautar Ancika agdn sarki anata kade kade da bushe Bushe da algaita LAMIDO yasha kwalliyar sarakai Yayinda yarima yai tashi ta angwaye daidai misali ba yabo ba fallasa yasha tsadaddiyar shadda babbar Riga d yar ciki Saida akayi nadi LAMIDO yazama sarki sannan aka daura auransa da KUYANGA kana akayi shagulgula sannan wasu suka dunguma da angoma Yarima suka tafi daurin Aurensa Kaduna Andauro Aure antaho da Amarya a ranar domin sai dare suka iso aka ajiyeta a gidansa dake GRA Itako KUYANGA data tashi daga wannan suna daga yau ta tare ackn gidan sarkin A gidan mijinta LAMIDO daya zamo sarki ayau To fans saimu Tara a page din gaba *GIMBIYA ZEENATU* Cigaban KUYANGA Wanda zakuji badaqala da cakwakiya ackn Wanda nake muku zaton yafi wannan Dan haka kada kubari abaku labari Taku har kullum Auntyn Sayyada da Shahida Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels