Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels . *************************⬇********************** ************* Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ ************************** [7/10, 10:34 PM] Bintu: *'YAR BANGAR SIYASA!!* 🌺 romantic love story🌺 *NA:* *BINTA UMAR ABBALE 🍒* *🌍Manazarta Writes asso* _'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_ ~~~~~~~~ *NA KUDI NE.......!* _Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176 sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko orange_ _*'KIRKIRARRAN LABARI NE, BA'AYI DAN ACI ZARAFIN WANI KO WATA BA WANDA YAGA YAYI DAI-DAI DA YANAYI NA RAYUWARSA TO A RASHIN SANI NE!*_ ~~~~~~~ _Pegen farko naki ne_ *_Ummi 'yar bare bari na gaisheki kanuri kina 'kamshi ina binki da humra 'yar dakina Allah ya bar 'kauna ta dan Allah!_* ~~~~~~~~ _Bisimillahi_ Free Pege *1* *'DORAYI* Wani rugujajan gida na hango na jar 'kasa duk katangar gidan ta zaizaye ta dur'kushe ta zama 'yar 'karama saboda tsabar wahala 'kofar gidan hanhai!! yake masu wucewa ma suna kallon cikin gidan .....Wani tattararran buhu na hango wata budurwa ta saki tana fad'in"Haba wannan wace irin masifa ce ace kullum gida a bud'e saboda tsabar mutunci duk kuna zaune a rasa wanda zai sakaya 'kofar ko kishin kanku ba kwayi meye amfanin talauci Allah ubangiji kayi mana katangar 'karfe dashi." "A'a aunty Wasila kyalemu mu sake mu sha iska yo wannan gidan in ba abude shi ba me za'ayi masa gida a ru'be da jar 'kasa ai wallahi ko ta halin 'Kaka sai nayi kudi in huce takaici nayi dakace dana fito ta tsatson babanmu duk shine ya cuce mu aikin banza kawai." Ta 'karasa maganar tana jan dogon tsaki! Uwani dake sunkuye a bakin rijiya tana wanki tace"Kya fad'a Rashida ni kaina da kace nakeyi da auran babanku gashi ya mutu ya barni da wahala da 'kailulu kafin zuwansa gidanmu akwai manyan mutanan da suka fito zasu aureni nace shi nake so saboda naga fari kyakkyawa sai da tafiya tayi nisa a tsakaninmu na gane kyau bashi bane kawai ka auri mai kudi ka huce bakin cikin duniya." Rashi da turo daurin dankwali gaba tace"Ai wallahi Uwani nayi alkawarin sai nayi auran kece raini dan ba zan auri 'karamin mutun ba sai na za'ba na durje sannan dan wannan kyawun nawa ba zai tashi a banza ba." Uwani tace"Yawwa 'yar gari kiyi komai ba komai nice Uwarku nice Ubanku babu shegen da ya isa ya sanya ido a kanku tunda babu wanda yake taimaka mana to kuwa banga dalilin da zai sanya ace dole sai kunyi aure ba ko wacce tayi abunda take so kwalliya kuwa ko wace iri ce kuyi ku futa ku samo manyan maza masu abun hannu ni kaina wannan kyawun da Allah ya baku bana so ya tashi a banza a wofi." Wasila dake tsaye tana sauraransu tace"Yanzu dai Uwani idan na fahimce ki kina so kice mu tafi yawon karuwanci ko."? Uwani tace"To meye idan karuwanci kukayi? ai halak dinku kuke nema da kuje ku dauki na wani gwara ku mika jikinku a biya bukata sai me waye zai gani abunda ba fitowa yake a saman goshi ba." Wasila tace"To sai dai in Rashida amma ni na fad'i miki kome zakiyi wallahi bazan zubda daraja ta da mutunci na ba, na yarda zanyi ko wace irin sana'a ce amma banda karuwanci." Uwani tace"Kece babba kuma kece mara wayo yo mara wayo mana duk wata sana'ar da zakiyi a yanzu ba takai ta karuwanci ba itace yanzu yanzu zaki mi'ka kiji dumus! a hannunki yanzu sai kiga kina murza sitiyarin mota yanda kike da zubi ai nasan manyan mutane da sarai ne za suyi karakaina a kanki." Wasila ta harari mahaifiyar tata tace"Wallahi Uwani kinji kunya kwarai komai hud'ubarki ba zanyi wannan sana'a ba ina da ilimi dai-dai gwargwado sannan kuma ni babu abunda na tsana a duniya irin iskanci, wallahi da in mi'ka kaina gurin wani gardi gwara na kwana banci ba, Sana'a kam nace zanyi ko wace iri ce banda karuwanci." Rashida tace"Wallahi aunty Wasila baki da wayo kin fini fa zubin jiki mai kyau da daukar hankali wallahi kina fad'awa wannan harkar maza zasuyi caaaa! a kanki shikkenan mu da talauci munyi hannun riga." Ashar! ta lailaya mata tace''Kika sake mun irin wannan maganar sai ranki ya 'baci! kema bana fata kiyi wannan sana'a in dai kudi ne ku bari ku gani ku dai ku taya ni da addua." Uwani na shanya kayan wankau din mutane tace"To shikkenan muna zuba ido mu gani a 'kasa uwar tsari yau ki shigo mana da gassasun kaji da lemo nan zamu gane kin zama "yar kasuwa." Wasila tace"Uwani dan girman Allah da Annabi kar kuje yawon bin gidajan jama'a sannan kar ki tura Rashida tayi wannan sana'a wallahi bata dace damu ba a matsayinki na mahaifiyarmu ki kare mana martabarmu insha Allahu yau zan fita a sa'a za'a dace." Uwani tace"To tunda kince haka shikkenan Cin mu da shan mu duk ya rataya a wuyan ki." Tace"Eh naji insha Allahu Allah zai bani ikon d'aukar nauyinku." Har ta d'aga buhun zata futa sai ta dawo tana kallon mahaifiyar tasu tace"Ko na futa dan Allah karku daga buhun nan ku barshi a haka yafi mutunci." Uwani tace"Shikkenan Allah yq bada sa'a." Wasila ta amsa da "ameeen" tasa kai ta fice daga gidan. _Muje zuwa_ *BINTA UMAR ABBALE* [7/10, 11:29 PM] Bintu: *'YAR BANGAR SIYASA!!* 🌺 romantic love story🌺 *NA:* *BINTA UMAR ABBALE 🍒* *🌍Manazarta Writes asso* _'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_ ~~~~~~~~ *NA KUDI NE.......!* _Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176 sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko orange_ *Free Pege2* Wasila na fita ta nufi gidansu Hadiza 'Yar camas! 'kawarta ce sosai amma kuma halinsu ya bambamta! Camas! tana bin maza kuma tana d'an ta'ba shaye shaye sa'banin Wasila da bata shan komai na maye sannan kuma bata bin maza kawai dai ku barta da tsiwa da rashin kunyarta. Camas! na zauna a tsakar gidansu suna hira jefi jefi da mamanta Wasila tayi sallama ta shiga gidan Mahaifiyar Camas mai suna Asabe ta amsa tana fad'in"Wasila kece a gidan." ? Tace"E wallahi ina wuni." Suka gaisa a mutunce har Asabe na tambayarta Uwani tace"Tana nan lafiya. Camas! Tace"Ke 'yar iska ina zuwa kuma nagan ki da mayafi yau ina hijab din."? Wasila tace"Dauko mayafinki muje." Camas ta mike a hanzarce ta shiga dakinta ta dauko wani karamin mayafi ta yafa suka fita Asabe ta bisu da kallo tana girgiza kai al'amarin na 'yar tata sai addua dan a zahiri ma gwara Wasila kanta komai ma Hadiza ya lalace har karatu duk ta watsar gwara Wasila nayin asha ruwan tsintsaye gurin zuwa makarantar. Sai da suka kusa futa daga layin sannan Wasila tace"Ke Camas! yau fa a shirye nake wallahi! Gidan gwammanti zamu je yanzu." Camas! tace"Kai! Wasila me zamuyi a gidan gwamnati kuma."? Wasila tace"Muje kawai ina so in fara harkar Siyasa ne." Camas! tace"Harkar Siyasa kuma lallai Wasila kina so ki jefa rayuwarki a rud'ani Siyasa masifa ce duk ga sana'oi nan da zakiyi ki rufawa kanki asiri sai kice siyasa za kiyi."! "Kinga Camas! idan zakije to ni bana son wata doguwar magana anan gurin harkar Siyasar ma idan ta kar'beka sai kaga ka samu kudi sannan kuma duniya ta san da zamanka." Camas! tace"Kuma fa hakane wallahi hausawa nacewa matsoraci baya zama gwani kawai mu afka ba'asan inda rana zata fad'i ba.'' Wasila tace"Ashe kin gane 'kawata." Bakin titi suka fito suka samu a dai-dai ta sahu kai tsaye sukace ya kaisu gidan gwamna. Mai d'an sahu ya kallesu da mamaki sosai a tare dashi gidan gwamnati to me zai kai wad'annan yaran can? bashi da mai bashi amsa kawai ya ja babur din sukayi gaba.....Yanda suke hirar ne ya fahimci inda suka dosa yace''Yaya na ni dai shawarar da zan baku shine ko zakuyi wannan harkar dan Allah ku tsare mutuncin ku kar ku ku watsar da martabar da Allah yayi muku." Wasila tace"Insha Allahu baba zamu kiyaye." Yace."To nagode da kuka dauki magana ta." Ana kiran sallahr magariba ya sauke su a bakin titi Wasila ta ciro dari biyu a bayan condem din wayarta ta bashi yace."Ai saura dari dari uku ne kudin." "Haba Baba kayi hakuri da wannan d'in ita kenan muka baka ka gani ko na dawowa ma bamu dashi." Yace"Shikkenan." Babur din yaja ya barsu a gurin. Camas tace"Shiyasa sam bana son shiga babur! din dattijai duk 'yan buri ne gwara in shiga na samari masu tara suma su kunna maka kad'e kad'e in ta kama ma suce ka bar kudinki." Wasila hankalinta na kan wata mota dake kokarin shiga rukunin gidan gwamna tace"Wallahi haka maganarki take Yawwa kinga wata mota zata shiga bari na tsayar da ita sai ta hau d'agawa mai motar hannu. A hankali motar ta tsaya inda take kana gilashin motar ya sauka a hankali mamalakin motar ya bayyana.....Wani 'kosashen mutun ne bayan motar a hakimce kana ganinsa kasan yaci ya tada kai da nera yana hada ido da Wasila ya had'iya wani yawu zuba mata ido yayi har suka 'karaso gurin.........Manya manyan idanunta ta juya kana ta dafa motar da hannunta guda ta lankwasar da mirya ta tace"Barka da wuni yallabai ya gida ya fama da jama'a."? Alhaji Ma'aruf ya amsa yana washe baki sosai yace."Lafiya 'yan mata jama'a kuma ku za'a tambaye." Ta saki wani shu'umin murmushi tace"Yallabai kenan, Dama muna neman wata alfarma ne." Yace."Ko wace alfarma ce ku fad'eta mutukar ta shafi gidan gwamnati to zanyi kokarin ganin kun sameta." "Yawwa Yallabai muna so mu fara harkar siyasa ne shiyasa muka dacewar muzo muyi tambaya akai." Alhaji Ma'aruf yayi mirmushi hade da shafa sajensa ya dan tura hular sa 'keya yace"To ai kaya ne suka tsinke a gindin kaba, babu matsala ku shigo mota muje zan shiga gurin mai girma Governor idan na fito sai muje daku guest hause dina in yaso sai muyi maganar. Ba tare da wata fargaba ba suka bude mota suka shiga suka zauna dravar yaja motar suka bar gurin. _Muje zuwa_ *BINTA UMAR ABBALE* [7/11, 12:37 AM] Bintu: *'YAR BANGAR SIYASA!!* 🌺 romantic love story🌺 *NA:* *BINTA UMAR ABBALE 🍒* *🌍Manazarta Writes asso* _'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_ ~~~~~~~~ *NA KUDI NE.......!* _Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176 sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko orange_ *Free Pege3* Kunnanshi ma'kale da waya ya fito daga bedroom din shi ya zauna daya daga cikin shirga shirga kujerun dake palon ya wani d'ora kafa d'aya kan d'aya yana masifa!....."Khalifa wad'annan mutanan fa babu Allah a tare dasu ni wallahi tuntuni na dawo daga rakiyarsu shin wai mulki hauka ne!? duk wannan kashe kashen da akeyi da sace sacen yara kananun mun san daga ina ne kawai saboda ana jin tsoronsu sai ayi shiru to wallahi daga yau na shirya d'amarar ya'ki! dasu mulki suke so nima shi nake so Allah ya bawa mai rabo sa'a haba! wannan al'amarin ya ishi talakawa wuya tayi wuya mutane sai mutuwa sukeyi gobe ka fito da wuri zamu fara yawon kamfen insha Allah." Khalifa dake daya bangaran yace."Insha Allahu zan fito da wuri amma yana da kyau ka tanadi matakan tsaro kafin fitar tamu.'' Yace."Kar ka damu da wannan insha Allah Allah zai karemu tunda domunshi muke." Sallama sukayi da juna ya kashe wayar tare da ajiyeta saman tevur din dake gabanshi.....Zuba masa ido nayi ina kallo wai! Allah yayi hallita a gurin kyakkyawa ne ajin farko fari gaggausa yana da dogon hanci da manya ido da gashin gira kewayayyiyar fuskarsa na dauke da sisirin sajensa wanda yasha gyara ya zauna das ya kawata fuskar tashi......Ya wuce ka kirashi yaro gaskiyar magana kenan domin idan ka tsaya ka kalleshi da kyau zaka fahimci shekaru sun d'an tura masa a 'kalla yanzu shekarunsa ar'bain da biyu zuwa da uku........ *Ahamad Musa (Ba iya ka!)* ainin sunansa kenan Matashin saurayi mai jini a jiki mai tashen kudi wanda bai san iya adadinsu ba, shi ya sanya jama'ar gari suke kiranshi da wannan suna *Ba Iya ka!* shima ya samo shi gurin mahaifinsa *Alhaji Musa (Ba iya ka)* wanda ya shahara yayi shura a zamaninsa Allah ka ji'kan maza. Ahamad kawai ya haifa shima kuma kafin ya haifeshi din sai da ya futar da rai! da haihuwa lokacin duk girma ya baibayeshi ya auri wata 'yar filani ashe rabon a jikinta yake haduwarta ta farko ta dauki ciki.......Farin cikin da ya shiga a lokacin Allah yayi yawa dashi ya dinga sadake sadake yana kai mutane saudiya suyi wa matarshi addua Allah ya sauketa lafiya. Allah babu yanda baya tsara lamarinsa gurin haihuwar Ahamad mahaifyarsa ta rasu sosai iyalin Alhaji Musa sukaji mutuwar daga bisani suka barwa Allah lamarinsa.....Sai suka dawo kan Ahamad suka dinga nuna masa so da kulawa mussaman mahaifinshi Allah ya jarrabeshi da kaunar yaron nashi ashe ba zasu dade da juna ba Allah ya dauki rayuwar Alhaji Musa....Mutuwar da ta girgixa zu'katan al'ummar gari suka dinga kuka da fadin"Bango majin ginar talakawa ya fad'i!! Jama'a sukayi dafifi a harabar gidan suna masa addua da fatan Allah ya kai rahama kabarinsa. Tunda Ahamad ya taso yaga yanda mahaifin shi ke taimakon al'umma sai ya dora a inda ya tsaya tun yana dan shekara ashirin a duniya sunanshi ya 'bace a gari mutukar baka kira *(Ba iya ka)* ba to babu in zaka kwana kana kiran Ahamad babu wanda zai gane wanda kake nufi.... Ahamad jama'ar gari ne suka kwadaita masa sha'awar mulki da sam ba tsarinsa bane ya fiso yayi harkokinsa to shima kuma da ya zauna yayi nazarin yanda al'amuran siyasar ya ta'bar'bare sai kawai yayi sha'awar fantsama kansa a harkar domin ya taimaki al'ummar da suke galabaita a jahar mussaman talakawa sune dama abun tausayi. Kallo guda za kayi masa ka gane yana da fuskar Salihai! a zahirinsa kenan a bad'insa kuwa mutum ne shi mara hakuri kuma sam baya barin ta kwana kamar zawo yake mutukar kayi masa abu idan bai rama ba sam baya jin dad'i....bayan wannan halin nasa bai da wani mummunar hali dama ance adan adam tara yake bai cika goma ba Ahamad nada tausayi da taimako sai nace muku ma duk rabin neman kudinsa yanayi ne kan jama'ar gari marasa galihu da na kasassu gami da marayu.......Dalili kuwa bashi da nauyin kowa a kanshi tunda shi ba aurene dashi ba ballanta ayi maganar yara, Jama'ar gari duk sun dauka yana da aure da iyali shiyasa duk adduarsu a kan iyalinsa take 'karewa sai dai kawai amsa da "ameeen" Nasan zakuyi mamakin namiji kamar Ahamad mai jini a jika sannan uwa uba kudi! ga kyau da kwarjini da haiba da yake dasu amma me yasa bai aure ba? Yana zaune hakane ba wai dan bashi da lafiya ba ko kuma rashin matar aure akwai 'yan mata bila adadin dan ba zasu lissafu ba, kawai duk cikinsu bai ga wacce ta kwanta masa a ransa bane ya ajiye maganar aure a gefe saboda yasan cewa lokaci ne idan Allah ya kawo masa matar lokaci guda za'ayi a gama. 'Daya daga cikin masu tsaronshi ne ya shigo palon....Ya d'aga kanshi yana kallonshi A nutse yace."Ya akayi."? Garba yace."Kana da bakuwa tana dakin 'baki mun sauketa." Jim! yayi yana nazari wace 'bakuwa yayi kuma yanzu karfe goma na dare! Ko da yake ai tunda ya fara wannan harkar kuma yayi ta ganin jama'a ya mike a nutse Garba ya bashi hanya ya wuce kana ya take bayanshi. _Muje Zuwa_ *BINTA UMAR ABBALE* [7/11, 9:41 PM] Bintu: *'YAR BANGAR SIYASA!!* 🌺 romantic love story🌺 *NA:* *BINTA UMAR ABBALE 🍒* *🌍Manazarta Writes asso* _'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_ ~~~~~~~~ *NA KUDI NE.......!* _Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176 sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko orange_ *Free pege4* Cikin takun girma gami da 'kasaita ya shiga d'akin, lokaci guda 'kamshin turaransa ya karad'e hancinta, ta d'ago shanyayyun idananunta ta zubasu a kansa, tun kafin ya 'karaso inda take zaune ya 'kare mata kalau black beauty mara tsayi sosai da cikar kirji dauke kansa yayi daga kanta ya had'e fuska sosai wannan bakuwar tashi ba ta arziki bace duba da yanayin suturar dake cikinta. Tana sanye da wata matsatstsiyar t_shart da dogon wandon jins wanda ya fitar mata da zahirin hallitarta ta sanya karamin hijab wanda ko kirjinta bai rufe ba tsakiyar kanta yayi tozo da tsayi da alama tana da gashi sosai tunda ga alamunsa nan ya nuna saman goshinta. Hannunsa cikin aljuhu ya isa inda take, ta mike tsaye da sauri tana marmar da shegun idanunta masu rikita lissafin da namiji......Ya kura ma jikinta kallo tayi sosai dan bai hango makusa a tattare da ita ba ta cika har ta batse kuma tana da abubuwan da yake bala'in so a jikin 'ya mace sai dai kash! ba wannan ne a gabansa ba abunda ke gabansa a halin yanzu shine ya za'ayi talakawa su samu walwala da farin ciki. Fuskarshi ya sake tamkewa tamau! yace."Baiwar Allah daga ina? ance dani nayi bakuwa na dauka ta arziki ce sai a ka samu akasi." Wasila taji ciwon maganarshi kasancewar ta macen da bata daukar raini mussaman ga da namiji basarwa tayi ta matsa kusa dashi cikin salon janye hankali tace"Daga duniya na fito nazo ne in d'ebe maka kewa nasan namiji lafiyayye kamar ka na bukatar lafiyayyar mace ka mata. Tsawa ya buga mata yana nuna ta da hannu"Ke! cikin gidana kika shigo kina min wannan maganar? ashe dama zargin da nake miki gaske ne okey get out from my house. "! Maimakon ta fita sai ta durfafeshi tana so ta rungumeshi, ya kai mata wani wawan mari! yana ya tsine fuska sai karkad'e jikinsa yake kamar wanda ya ra'bi motar daukar kashi.....Ya mutsa fuska yake yana korar shaid'an, yace." Za kici Ubanki yanzu yanzu zan sanya a xane miki jiki har gida zaki shigo ki kawo min iskanci ni ba'irinku bane." Fita yayi yana 'kwalawa Garba kira. Wasila ta dauke hannunta dake fuskarta gaskiya yana da taurin kai ta lura ba zai bari ha'kansu ya cimma ba ruwa ba d'an iska kawai tayi irin wannan shigar ya dinga kauda kai yana ya tsine fuska anya ma kuwa lafiyayye ne? bata da mai bata amsa sai tayi maxa ta dauki jakarta zata futa suka buga karo dashi yazo zai shigo kirjinta ya daki kirjinsa yayi saurin ja gefe guda yana kallonta sai wani gumi yake kamar wanda yayi tsere. A ya tsine ta kalleshi tace"Na d'auka ai lafiyayyan namiji ne ashe hotiho ne har kana zagina 'kato da kai baka kunyar zagi anzo a jiyar da kai dad'i kana gudu Allah ya kyauta kaje ka nemi magani." Wata sha'ka ya kai mata ya matse ta a jikin bango (garo) ta dinga kakari idanunta sunyi jajawur!!! Cikin kaushin murya yace."Idan za'a had'a min iri-irin irinki guda dari duk zan gama musu aiki ba tare da nagaji ba, 'karyar iskanci kike yarinya da ina da bukatar mace a yanzu dana fatattaka ki kuma in kwana lafiya 'yar iska mara galihu." Hannu tasa tana 'kokarin 'bam'bare hannunsa dake sha'ke da wuyanta duk ta muzanta sai kyarmar jiki take tana cizan le'banta.....Sai da ya gama galabaitar da isa sannan ya saketa aikuwa ba tayi wata-wata ba ta kai hanni gabanshi zata d'amka! yayi gaggawar ri'ke hannunta yana kallonta da mamaki a tare dashi. Sun jima suna kallon juna ita dashi mugun mamakin 'karfin halin yarinyar yake wato shammatarsa take so tayi ta nakasta shi....Ido jawur! tace"Sake min hannuna."! Ya 'kara rike hannun tamau! yana sakin wani killer smile yace"Kina so ki ta'ba ne."? Wasila tayi tsuru-tsuru tana kallonsa sam ba tayi tsammanin guy zai samu galaba a kanta ba. "Wannan kayan aikin da kike gani yafi 'karfin irinku 'yan iska! na kamilar mace ne mai addani ba irinki mai yawon ta zubar ba." A fusace! ta fuzge! hannunta ta watsa masa kallon raini fuuuuu!! ta kama hanyar fita......Taku uku yayi ya cimmata tare kofa yayi yana me bin jikinta da wani shu'umin kallo. "Sosai kikayi babu wata makusa a jikinki duk inda 'yan mace ta kai kin kai yarinya sai dai sam baki burgeni ba idan ma turo ki akayi to sai kije ki sake sabon shiri ki sani Ahamad ya wuce tunaninki." Yana 'kare maganarshi ya 'kwalawa Garba kira. Ya shigo da sauri yana fadin "Yalla'bai! gani.'' Yace." Maza rakata da bulala idan tayi gardama ka zane 'kafafunta." Garba Ya kalleta, "Wuce muje." Yafada cikin bin umarnin Ubangidansa. Wasila kamar ta hadiye zuciya ta mace tunda take a rayuwa ba'a ta'ba tozarta irin yau ba lallai guy bashi da mutunci amma babu komai sun d'aura idan kere na yawo zabo na yawo watarana za'a had'u. Kallon uku shaura kwata tayi masa kana ta gyada kai ta wuce shi.....Garba ya bita a baya da zabgegiyar bulalarsa....Harbar gidan ya fito ya tsanya tare da zuba hannuwansa cikin aljuhu yana kallo Garba ya tasa 'keyarta har bakin gate yanayi yana caud'a bulala a 'kasa kamar zai daketa hakan ya sake kular da ita ta sake 'kullatar guy girgiza kai kurrum take tabbas maganar da chamas! tayi gaskiya ne babu abunda yake cikin harkar Siyasa sai tozarci da wulakanci, Garba na ganin tayi nisa da layin sai ya juya ya koma cikin gidan. _Muje Zuwa_ *BINTA UMAR ABBALE* [7/12, 8:39 AM] Bintu: *'YAR BANGAR SIYASA!!* 🌺 romantic love story🌺 *NA:* *BINTA UMAR ABBALE 🍒* *🌍Manazarta Writes asso* _'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_ ~~~~~~~~ *NA KUDI NE.......!* _Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176 sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko orange_ *Free Pege5* Yana tsaye a inda yake Garba ya shigo ya sanya masa ido har ya 'karaso inda yake tsaye.....Kai a 'kasa Garba yace."Sir tayi nisa da layi sosai amma fa ina zargin wani dan gane da wannan yarinyar." Ido ya sanya masa a nutse yace."Kamar name kenan." Garba ya 'kara risinar da kanshi a kasa yace."Anya kuwa ba turo ta akayi ba kuwa kasan fa mutanan babu abunda ba zasu iya ba." Murmushi yayi yace."Garba idan ma turo ta sukayi tayi min sharri ko abu makancin wannan to insha Allahu ba zasu samu nasara ba ni nafi karfinsu tunda bana nufin su da sharri sai alkairi harkata ta siyasa kuma yanzu na fara babu gudu babu ja da baya ni dasu Allah ya bawa mai rabo sa'a." Garba yace."Ka gama magana Yallabai Allah ya baka nasara kan dukanin abunda kasa a gaba." Ya amsa da "ameeen.'' Ya juya cikin yanayin tafiyarshi ta gwazan maza, Garba ya take masa baya. Wasila na fita daga Estate din ta hango motar Alhaji Ma'aruf a can tsallake a fake.....ranta duk a bace ta karasa bakin motar.....'Dan kwankwasa jikin motar tayi Camas! da Alhaji Ma'aruf suka firgita sukayi saurin sakin junansu suna gyarawa Ido jawur! ya bude mata motar yana fad'in" Ya akayi *'Yar gaske* Allah yasa kin aiwatar da komai." Rai a 'bace tace" Wallahi ya'ki bada had'in kai d'an iska kawai yasa na fitar da tsaraicina amma kallo ban isheshi ba." Alhaji Ma'aruf yace."Kai! wannan d'an iskan mutumin taurin kanshi yayi yawa wallahi yanzu duk cikar ki da batsewar ki bai sanya yaji sha'awarki ba? anya ma kuwa yana da lafiya? duk mutum mai lafiya dai ya ganki sai yaji sha'awa ta kamashi." Ya 'karashe maganar yana bin jikinta da kallo. Wasila ganin yana mata kallon iskanci yasa ta dan ja tsaki kadan ta mika hannu tana jan hijab dinta wanda Camas! take kwance a kai! Kallo guda tayi mata ta gane abunda ke faruwa wato bayan futar ta ayarsu suka she'ke! Allah ya kyauta. Hijab dinta ta sanya tace"Alhaji kaimu gida dare nayi sai dai kuma mu sauya wata dubarar na gane guy sai an bude masa wuta dan a tsaye yake kuma wallahi kuka bari ya hau kan kujerar mulki sai kashin ku ya bushe duk sai ya kame ku. Alhaji Ma'aruf ya kunna motarshi yana goge gumi yace."Maganar ki gaskiya ce *'Yar gaske* shiyasa muke 'kokarin muga mun kassarashi tun kafin ya cimmana amma babu damuwa zamu shirya masa wani sharrin." Suna tafiya suna zan can Ahamad dashi da taurinka kansa Alhaji Ma'aruf na fada musu yanda suke dauki ba dad'i a kan suga bayanshi amma abun yaci tura yace shi har jinin kad'angare ya sha duk saboda yaga bayan Ahamd amma asirin bai kar'beshi ba a lokacin ma so yayi ya dawo kansa sai da bokan da ya kulla asirin ya warware tukkuna ya samu lafiya. Wasila tace"Ka rabu dashi Alhaji duk ku daina wahalar da kanku da kudinku da yawon bin malamai a kanshi sharrina ma kad'ai ya isheshi sai nayi fata-fata da rayuwarshi." Alhaji Ma'aruf yaji dadi maganar ta yace.''Mu kuma munyi miki alkawarin baki dadin duniya *Yar gaske* zaki fantama sosai da kudi sai dai ki bawa wasu." Da jin wannan magana tashi sai Wasila ta sake daukar aniyar babu gudu babu ja da baya a kan Ahmadu Musa *(Ba iyak ka)* har sai taga abunda ya turewa buzu nadi. 'Karfe goma sha biyu saura na dare ya ajiyesu a kofar gidansu Ledoji cike da kayan dadi ya bawa Wasila rafar kudi ta dubu dari camas ya bata dubu hamsin sukayi sallama da juna kan cewar zasu fito da wurwuri domi zuwa yawon kamfen........ 'Yar 'kofar da suke karawa Wasila ta tura firgigit Uwani ta mike zaune dama ba baccin take ba tana zaune tana dakon dawowar 'yar tata. Wasila ta mayar da 'kofar ta kare gidan kana ta saki buhun dake sakale suka shiga cikin gidan suna ihu! kamar ba dare ba. Uwani da Rashida suka fito a guje! Wasila ta farke rafar kudin dake hannunta ta soma mannawa Uwani a saman goshi.....Uwani na ganin Sabbin 'yan dubu-dubu na watsi a a tsakar gida sai ta fasa ihu! ta rungume! 'yar tata suka kama rawa wata lafiyayyar gud'a ta dinga rangadawa tana sakarwa 'yar tata kirari......Ita kuwa Rashida kudin take bi tana tsince tana ta faman kyalkyala Dariya sai kace mahaukaciya. Sai da suka gama murnarsu sannan suka dauki ledojinsu suka shige ru'babbiyar rumfarsu da ta kusa ruftawa Rasida ta samo katon faranti suka baje wasu 'kosassan kaji guda shida wanda komai zulamar mutum bai iya cinye guda saboda girmansu ga had'ddaun lemuka masu sanyi nan suka baje suka dinga yagar kaza suna yi mata cin ala tsine uwar me karya, wai! yaushe rabon duniya da ayya raye."!! Uwani ta fada tana shigowa dakin bayan taje ta wanko hannunta........Wasila tace"Yanzu dai mu kwanta muyi bacci dare yayi sai gobe in yaso sai kuji labarin abunda yake faruwa. Uwani tace"Ki d'an gutsira min wani abu mana na kwana dasu a karkashin filona anya ma kuwa yau zan iya bacci oh! duniya kenan." Wasila tace"Uwani kwanta kiyi bacci harda munsharri ai insha Allahu mu da talauci munyi hannun riga." Uwani ta dinga wata mahaukaciyar dariya tana fad'in"Ai dama ni nasan jari na haifa ke ba 'karamar mace bace idan ba'aso ki dan komai ba a so ki dan 'kirar jikinki ita kuma Rashida wannan farar fatar tata itace jarina." Wasila tace"Uwani nifa ba karuwanci naje nayi ba sana'a muka fita mukayi ko ba haka ba Camas!." Tafada tana kallon Camas! dake irga kudinta. Camas tace"Kwarai kuwa sana'ar mukaje mukayi ta siyasa gobe zamu fita da wurwuri shiyasa ma ban wuce gida ba." Uwani tace"Kai amma wannan sana'a ta karbeku wallahi Allah ya bada sa'a ya taimake ku." Suka amsa da "ameen." Sannan ko wacce ta gyara shimfida ta yada ha'karkari ta kwanta ana jira kuma gari ya waye a fita *Sana'a* _Muje Zuwa_ *BINTA UMAR ABBALE* [7/13, 1:07 AM] Bintu: *'YAR BANGAR SIYASA!!* 🌺 romantic love story🌺 *NA:* *BINTA UMAR ABBALE 🍒* *🌍Manazarta Writes asso* _'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_ ~~~~~~~~ *NA KUDI NE.......!* _Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176 sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko orange *Free Pege6* Da safe suka tashi da wurwuri sukayi wanka tsaf suka shirya tuni Uwani ta ta fasa musu shayi Rashida ta siyo su madara da milo da bread har da su kwai Uwani ta soya musu yau karin kullamo sukayi rigijib suka karasa cinye sauran kajinsu na jiya....Wasila ta kalli Camas! dake gyara daurin dankwali tace"Ya kamata kije gida mamanku ta ganki kafin mu tafi ko." Camas! tace"Ke kin san idan na shiga gida yanzu babanmu nanan ba zai bari na sake fita ba kawai ki kyalesu idan na dawo ma had'u." Tace"Shikkenan ke Rashida zan bada dubu talatin ayi aikin gidanan a sanya kokafi data waje data bandaki saboda bana so in doso layin nan wallahi in hango ku kamar tumaki a akurki wai sunan kuna cikin gida a zaune amma jama'ar dake waje na ganinku wannan gidan ai sunansa kango ba gida ba. Uwani tace"Naji kinyi maganar dubu talatin duk a aikin gidan anya kuwa basuyi yawa ba." Tace"Na fiso ayi komai da inganci a sa kofofi masu kyau insha Allah yau ma idan mun fita zamu samo kudi.' Uwani tace"To Allah yasa." Wasila ta irga dubu talatin da biyar ta bawasu Uwani talatin na gyaran gida biyar kuma tace su dan auno kwanan shinkafa suyi cefane kafin ta dawo.......Haka sukayi musu sallama suka kama hanya suka tafi can guest house din Alhaji Ma'aruf dake a can yace su had'u. Suna shiga harabar gurin suka wasu gugun matasa rukuni rukuni! amma 'yan daba da shaye-shaye sunfi yawa.....Alhaji Ma'aruf da wani mutumi suna tsaye a kansu suna magana dasu. Kai tsaye can suka nufa Alhaji Ma'aruf na ganinsu ya washe baki ya kalli Alhaji Tasi'u "Yawwa kaga 'yan halak! ko yanzu yanzu mu ka gama zancensu ashe suna tafe. Wasila tace" Aikuwa dai muna hanya wallahi kun san matsalar abun hawa sai a hankali." Alhaji Tasi'u ya kalli abokinsa yana nuna Wasila da bakinsa yace"Ko baka fada mun ba na gane wannan ce *Wasila 'Yar gaske!"* Yace."Kwarai kuwa Alhaji kayi mamakin ganinta 'yar karama ko." Yace."Dai-dai kenan duk da kankantar ta nasan zata bamu gudumawar da muke bukata daga gareta Wasila naji kina maganar abun hawa da sauransu ki kwantar da hankalinki zan siya miki mota ta kece raini ke dai kawai ki bamu goyon baya domin zamuyi amfani dake domin cimma manufarmu.'' A dake! tace"Kar ka damu Alhaji a shirye nake wallahi domin harkar na shigo gadan gadan duk inda nasan zan samu nan zan nufa in zaku sakar min kudi magana ta 'kare." Alhaji Ma'aruf da Alhaji Tasi'u suka fashe da dariya suna tafawa, Sai bayan sun tsaigata da dariyar ne Alhaji Tasi'u yace."Kunga wad'ancan mutanan dake zazzaune ko."? Suka ce."Eh." yace."To zaku fita dasu yawon kamfen saboda mun samu labarin *Ahamadu (Ba iya ka)* zai fita zagaye gari domin yad'a munufarsa a kan talakawa to muna so duk inda suka shiga suna yad'a manufarsu su shi ku soke! ku watsa jama'a akwai kayan aiki a tare dasu Lauje karkuji komai kuyi aiki sosai mune muke da mulki a hannunmu babu wani abu da zai same ku." Wasila tace"Kar ka damu alhaji nayi maka al'kawari bakin rai bakin fama." Alhaji Ma'aruf ya kalli Camas yana lumshe mata ido yace."Kefa baki ce komai ba." Tace"Haba karfa ku damu nima na dauki alkawari insha Allah sai mun rusa shirin *Ba iya ka."* Alhaji Tasiu ya nunawa matasan nan su Wasila yace sune abokanan tafiyarsu su kula dasu a matsayinsu na mata, har bakin mota suka rakasu suka shishhiga a'kalla sai da suka cika motaci hud'u irin na haya saboda yawansu sun kai su ashirin da wani abun....Kai tsaye suka dauki titin da zai futar da mutun cikin gari. Cikin shadda fara kal ya fito yana daura agogon silvar a hannunshi hularshi ya kar'ba daga hannun Garba ya d'ora a kanshi *Ba kano* zallah yayi kyau har ya gaji ya zaune gefan gujera yana sanya safa Garba ya gama goge masa takalminsa sawu ciki ya mika masa ya sanya a kafafunsa yana mikewa Khalifa babban amininsa ya shigo shima yana sanya da manyan kaya shi harda babbar riga cikin kamala da mutumta juna suka gaisa kai kana ganin mu'amularsu zaka gane masu ilimi ne suna kuma aiki dashi........suna fita harabar gidan suka tadda matasa sun kai su goma duk suna jiran fitowarsa....Aikuwa ya dinga amsa gaisuwarsu yana daga musu hannu su kuma sun rud'e da fad'in" Sai kayi Ko garin ba kowa mu muna tare da kai kane za'bin talakawa, Kano sai *Dan Musa."* Ahamad ya d'aga dukanin hannuwasa biyu sama da 'karfi yace." *CPC."!* Suka amsa da *"Sa'a!!!"* Yace."Sa'a ta mai rabo ce." Sukace "Kaine kake da Sa'a mai Sa'a." Ya saki murmushi da fad'in "Allah ya bawa mai rabo Sa'a." Suka amsa da "ameeen."!!!" Da sauri Garba ya bude masa bayan wata had'addiyar mota ya shiga Khalifa yabi bayanshi Garba da Dan uwanshi Hadi suka shiga sai direba ya shiga mazauninsa.....Kafin kice kwabo kin nemi jama'ar gurin nan kin rasa duk sun shisshige motocin dake fake a gurin domin su raka dan takararsu yad'a munufarshi.....Kai tsaye titin da zai sadaka da wata unguwa a cikin gari suka nufa mai suna *Jakara* nan yake so ya fara zuwa saboda yanda yake jin labarin unguwar babu kyau ga ta'bar'barewar al'amura da yawa tarbiyar yara matasa ta lalace babu sana'ar yi sai jagaliya da harkar gwan-gwan da sauransu yana so ya fara zuwa unguwar ya yad'a munfarashi kafin ya shiga sauran unguwanni. A kan idonsu motocinsu suka dinga parking, dake duk rabin unguwar Jakara kasuwa ce kafin kice kwabo guri ya hargitse da kaya-kaya jin cewar ga d'an takarar gwamna nan yazo yad'a munufarshi masoya *Ahamdu Musa Ba Iya ka* suka dinga turereniya domin suje su daga masa hannu.....Matasan nan suka fito da tarin pastocinsa suka fara aikin mannawa a bango da shagunan mutane gefan titi suka dinga bi suna mannawa guri ya cika ma'kil! Khalifa ya bude masa samar mota ya fito da jikinsa ya daga hannuwansa biyu yana fad'in" *CPC."!* Sai gurin ya rud'e! da fad'in" *Sa'a!!!!!* Su Wasila suka keto gurin da motocinsu a guje!!!! A take mutane suka watse kowa na ceton ransa.....Parking din motocin sukayi suka fito a fusace! ko wanne da makami a hannunsa.....A sai guri ya hargitse ihu!! kawai kakaji da gudu radadada!!!!! Hankalin Ahamad ya tashi sosai gashi Police guda biyu kacal ya dauka kuma suma al'amarin yafi 'karfinsu domin 'yan daban gidan gwamnati suna da muggan makamai!! Ya ware murya sosai yana fad'in"Kowa yayi takansa ya tsira da rashi."!!!! Wani *Dan daba* ya 'bullo daga wata hanya dake da maraba da wata katuwar kwata hannunsa rike da wata shar'be'biyar addah! sai kartar ta yake a 'kas! yana sakin wani uban ihu! da fad'in" *Sai kayi ko garin ba kowa."* Eh! yane! mu za'a kawo wa raini a unguwar tamu! ashe yau sai an zubar da jini wallah!!!! Huhhhhhh! ya kurma wani uban ihu! yayi kan 'Yan daban Gidan gwamnati yana sararsu ta ko'ina!!! Wasila dake can aikin Ya'bawa Fastocin Ahamad kwata da 'bakin mai!! ta hango abunda ke faruwa Abokanan tafiyar ta sun suna shigewa mota saboda *'Kumd'um!* dan daban nan ya soma fitarwa da wasu jini sai suka razana suka soma shiga mota.....Da gudu tazo shiga mota *'Kumdum'* ya fuzgo hijab din jikinta ta dawo baya 'Kara ta 'kwallara! ganin yana 'kokarin kai mata sara da 'katuwar addar dake hannunsa ta rintse ido gabanta na buguwa fat! fat! fat! shikkenan ta mutu!!! Shiru taji gurin yayi ta bude idonta a hankali tana bin mutanan gurin da kallo......Shi ta gani tsaye a gabanta hannuwansa cikin aljihu yana mata wani mummunan kallo still ga *'Kumdum* rike da shar'bebiyar addarsa a hannu.!! Kallon juna suke ita dashi! tsaf! ya gane yarinyar nan ce da shigo masa gida jiya tabbas ga maganar Garba ta fito ashe da wata manufa ta ziyarceshi ya gode Allah da bai sanya masa kwad'ayin mata ba da badan hakaba da tuni bukatarsu ta biya a kansa. Ya kalli 'Kumdum dake zare ido yana ciccije baki!!! Yace."Rabu da ita kar kayi mata rauni ko ka zubar mata da jini! taci albarkacin sunan mace da ta amsa mace duk inda akasanta mai daraja ce da kame kai Astagafurullah wannan yarinyar ta 'batawa mata sunansu idan ka daketa ko ka zubar mata da jini duk a banza tunda na lura da akwai bakin iyaye a kanta so ka kyaleta taji da abunda ke damunta zamu dai cigaba da yi mata addua idan mai shiryuwa ce kuma insha Allahu muka samu mulki a hannunmu duk zamu tattara ire irensu mu samu mu had'asu da mazaje dai-dai dasu muyi musu aure babu shakka za'a samu sassaucin wasu abubuwan." 'Kumdum! ya saki hijab d'in Wasila dake damke! a hannunsa yana fad'in"Eh! Yanda kace haka zakayi mahadi mai dogon xamani insha Allahu kano ta kace ko ana ha! maza ha! mata sai ka tuge! wancan wawan! da bai iya komai ba sai hauka.''!!!!!! Jama'ar dake gurin suka sa ihu! da fadin""Maganarka haka take 'Kumdum Kano ta d'an Musa ce ko ana so ko ba'a so sai yayi."""!!! Wannan damar da Wasila ta samu ya sanya tayi wuf! ta bar gurin can inda motocinsu suke ta nufa ta tarar duk an ragargaza gilashin motocin Camas! ta bude motar ta shiga da sauri wani matashi ya daki motar da kafarsa yana musu ihu!!! Sai da suka yi nisa da gurin sai suka saki wa'kar gwamnan dake ci a yanzu Mai taken *Munyi muku fintinkau!!!!!! Kano sai kallo daga nesa mai raba gardama yazo Enginer Lawan Rabo, duk wanda zai ja dakai shine wawa!!!!!* Wasila ta fito da jikinta ta saman mota tana watsawa Ahamad da'kuwa! da dukanin hannunta tana sake fad'id" *Wanda zai ja da Engener Lawan Rabo shine wawa!!* Ahamad yana kallon sanda take watsa masa hannayenta da sunan da'kuwa! *{Zagi!}* ransa ya 'baci sosai lallai yarinyar nan bata da kirki ya lura yar adawa ce mutuka dole ne ya sanya ayi masa bunkice akanta domin abun nata ya wuce gona da iri. Mota ya shiga tare da jama'arshi jama'ar gurin sai daga masa hannu suke suna masa fatan alkairi yana amsa musu cikin sakin fuska amma in zaka tona zuciyarsa a lokacin zaka tarar tayi ba'kikkirin sakamakon zagin da Wasila tayi masa wanda ba kowa ne zai fahinta ba sai shi wanda akayi dominsa. _Muje Zuwa_ *BINTA UMAR ABBALE* [7/13, 4:15 PM] Bintu: *'YAR BANGAR SIYASA!!* 🌺 romantic love story🌺 *NA:* *BINTA UMAR ABBALE 🍒* *🌍Manazarta Writes asso* _'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_ ~~~~~~~~ *NA KUDI NE.......!* _Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176 sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko Orange_ *Free Pege7* Wani irin gudu motocinsu sukeyi kan kwalta, suna sakin ihu!Wa'kar injiniya Lawan Rabo ta tashi a motocinsu jama'ar gari suma suka dinga ihu! da fad'in "Ba mayi!!! insha Allahu kano ta d'an Musa ce! su dinga jifan motocinsu da duwatsu suna ihu!!! Su Wasila da kyar suka sha amma dai hakan yayi musu dadi tunda dai sun rusa shirin *Ahamadu* sun hanashi aiwatar da nufinsa wannan ya nuna musu suke da nasara a kanshi. Khalifa ya kalli fuskarshi ya ganta a murtuke! yasan ranshi a 'bace yake gyaran murya yayi yace." Wai wannan cin maganin da kakeyi na menene dole fa ka fuskanci irin wannan 'kalubalan al'amarin siyasa sai addua komai mutuncinka sai ya zube kauda kanka kawai zakayi. Ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya d'an gyara zamanshi yace."Khalifa sam abunda mutanan suka turo ayi mun bai dameni ba saboda nasan sunyi abunda yafi wannan......Shin wai baka ganin zagin da yarinyar tayi min ne."!? Khalifa ya dan gyara zaman hularshi yana sakin murmushi a hankali yace."Duk akan idona al'amarin ya faru sosai nayi mamakin tsaurin idonta na fahimci kuma harkar takeyi da gaske so kar ka damu da wannan Siyasa ce a gabanka ma sai a zage ka a jefe ka kai dai tunda kace za kayi to sai ka daura d'amara! "No!!! Karya ne wallahi." Yafada a zafafe! ya kalli Khalifan da jajayen idanunsa da suka rine da 'bacin rai! yace."Khalifa Siyasa ba hauka bace kamar ni wannan yarinyar gantafalfala ta zageni! kai kanka kasan halina bana ya fiya mutukar mutum ya shiga gonata ban hanata tayi min komai ba na yarda siyasar 'kasa ce amma banda zagi sai na ci mutuncinta wallahi."!!! "Clm dwon mana ka nutsu fa ba'a saurin yankw hukunci da gaggawa ka kyaleta kawai idan ta sake sai ka dauki mataki a kanta amma yanzu kana yi mata wani abu zasu 'kulla maka wani sharrin kasan halin su dai." Ya rintse ido yana sake hango lokacin da take watsa masa hannuwanta da sunan zagi! Ya bude ido yana sauke numfashi idan fa bai rama abunda yarinyar tayi masa zuciyarsa zata iya tarwatsewa mutum ne shi mai bala'in kishin kansa da 'kaunar iyayensa ya tsani na 'kasa dashi ya raina shi ko ya zageshi baya daukar irin wannan rainin shiyasa yanzu hankalinsa ya tashi mutuka duba da yanda yarinya 'kankanuwa wacce bata wuce 'yar cikinsa ba ta zageshi dole yayi bunkice a kanta. Khalifa ya dinga tausarsa da kalamai masu sanyi yana nuna masa haka lamarin siyasa yake dole fa sai ya kauda kansa ga dukanin abunda 'yan adawa zasuyi masa idan ba hakaba kuwa zai 'bata rawarsa da tsalle kawai ya share yarinyar ya bari kawai duk sanda ta sake to suma baza su kyale ba. Garba Da Hadi suka ce "Sir da ka bari wannan 'dan daban ya koya mata hankali wallahi yarinyar bata da mutunci ko kadan muma munga abunda tayi maka wallahi munyi rantsuwar duk sanda ta sake maimaita abunda tayi sai munyi mata tsirara sai mun tujara ta a gari karyar iskanci takeyi. Ajiyar zuciya ya sauke ya dan ji sanyi cikin ranshi Yace." Na rabu da ita saboda maganganunku ammafa ku sani duk sanda ta sake kwatanta zagina wallahi ranar sai ta raina kanta sai tayi nadamar zuwanta duniya babu ruwana." Khalifa yace."Yawwa mai girma Governor haka ake son shugaba da daukar shawara insha Allahu kai ke da nasara a kansu" Hannu ya bashi suka rike suna sakin dariya Ahamadu yace." *CPC."* gabad'anyansu suka amsa da *"Sa'a!* Ya sake fadin." *CPC."* Suka amsa da *"Sa'a."!* Yace." Mulki na Allah ne."! suka amsa da fad'in "Insha Allahu kai Allah zai bawa." Ya amsa da "Allah ya bamu Sa'a." Suma suka amsa da "ameen." Wasu Wasila kuwa kai tsaye gidan Governor suka nufa domin su alhaji Ma'aruf nacan gidan suna meeting sai sukace su samesu a can, suka samu wata katuwar rumfa suka zazzauna kamar wasu almajirai suna jiran fitowarsu.....Can sai gasu sun fito daga wani dakin wanda yake nuna alamun dakin taro ne sun kai su goma wannan yana wane wannan sun sha lafiyayyun shaddodi sai motsi takeyi tana she'ki masu Cot a cikinsu kad'an ne......Kai tsaye rumfar dasu Wasilar suke suka nufa ta ganinsu sun doso gurinsu sai ta mike da saurin gaske ganin harda Governor ya sanya ta fara masa kirari da bambad'anci! dama Wasila akwai shegen za'kin murya tsiya Governor tun kafin su karaso yake murmushi babu shakka wannan yarinyar za'aje da ita irin wannan washi haka!!!! Gabadayansu suka mike tsaye ganin sun iso gurin Lauje dake jin haushin abunda Wasila takeyi ya buga mata tsawa da fad'in"Ai sai ki saurara haka domin mai girma governor ya iso ki bamu damar magana." Wasila tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya. Gaisuwa suka mike garesu suka amsa sosai Alhaji Ma'aruf ya kalli Lauje yace."Kaine wakilin tafiyar ya akayi alamu na nuna mana cewa akwai nasara a tafiyar." Kafin Lauje yace komai Wasila tayi karaf! tace"Alhamdullihi muke da nasara insha Allah domin tun zuwanmu gurin muka watsa shirinsu muka tashi hankalinsa dana jama'arsa ni da kaina na dinga bin pastes dinsa da suke mannawa ina yagewa ina watsa masa ruwan kwata da bakin mai! da 'kyar! nasha a hannun wani d'an daba."! Governor Ya kallesu yana fad'in"Da gaske maganar haka take."? Duk suka amsa da "Hakane ranka ya dad'e."! Lauje yaji tamkar yaje ya sha'ke wuyan Wasila shin wai me take nufi ne? yarinyar fa ta za'ke da yawa anya ba sai ya taka mata burki ba kuwa." Governor Ya kalli Wasila yana murmushi Yace."Dama tun kafin na ganki na samu labarinki gurinsu Alhaji Ma'aruf gaskiya ne *'Yar gaske!* kin cancanci ayi miki komai zamu zauna dake insha Allahu ki fada mun dukanin bukatunki." Wasila aka saki murmushi ana gyara tsayuwa farin ciki duk ya isheta tace"Godiya nake mahadi mai dogon zamani governor da ba ta'bayin irinshi ba ba za'ayi ba insha Allah." tana gama maganarta Ta koma ta zauna inda take kana ganinta zaka gane tana cikin farin ciki babu shakka bukatarta ta kusa biya sun kusa yin hannun riga da talauci. Alhaji Tasi'u ya kalli Lauje dake faman cin kunu babu shakka katsalandan din da Wasila ke masa akan harkarsa ya isa har yaushe ta shigo harkar da zata dinga za'kewa da za'kalewa kan komai kafin zuwanta shine yake jagoranta al'amura da suka shafi harkar jagaliya amma ya lura yarinyar idanunta kar suke zata iya komai bayan haka kuma macace dole tafi shi samu power a kanshi Yace."Duk wasu bayanai munji su daga bakin *'Yar gaske!* kuma kun tabbatar da maganarta babu shakka munji dadin kasancewarta a wannan tafiya tamu, domin ta nuna mana ita jaruma ce kuma mai alkawari zata iya fansar da ranta a kan wannan harkar Kai Lauje daga yau Wasila *'Yar gaske* itace shugaba a wannan tafiya taku abunda tace muku shi zakuyi kai kuma in yaso sai ka zama mai take mata baya. Lauje wani irin gumi! ya shiga yanko masa kai!!! 'Karya ma kenan! wannan afiruwar yarinyar itace za'ace zata jagorance shi aikuwa da sake!!! wallahi ba zai yarda ba. Cikin ranshi yake wannan zantukan amma a fili sai yace."Gaskiya ne Yallabai dukaninmu mun yaba bajintar yarinyar dan haka zamu bata hadin kai dari bisa dari mu dai fatanmu mulki ya cigaba da dawwama a hannunmu." Governor Ya kalli Alhaji Ma'aruf yace."Ayiwa *'Yar gaske* kyauta ta mussaman Kafin mu zauna da ita.....Lauje da sauran yara suma ayi musu kyauta dai-dai gwargwado ai sun faranta min rai mutuka." Aikuwa Alhaji Ma'aruf ya d'auko daurarrun kudi 'yan dubu dubu sabbi fil fil ya mikawa Wasila dauri hud'u....Kana ya mikawa su Lauje dauri hud'u kwatankwacin na Wasilan Ita kuma Camas aka bata dauri d'aya.....Wannan al'amari yayi masifar 'batawa su Lauje rai!! lokaci guda sukaji sunyi masifar tsanar Wasila daga zuwanta zata zo ta kar'be musu fada lallai da sake sai sun dauki 'kwakkwaran mataki a kanta. Wannan karon da wuri suka koma gida wajejan karfe biyar da rabi tunda suka doso layin Wasila ke sakin murmushi ta hango gidansu da 'kofa lafiyayya sannan an d'an kwaskware wasu guraran da suka ruguje hakan yayi mata dadi sosai babu abunda ta tsana irin taga ana hango mahaifiyarta da kanwarta a waje.....Gidan sai 'kamshi yakeyi Uwani an dage ana ta soya miyar dage dage Rashida kuma na gefe tana yanka salak gefe guda kifi ne manya manya (sukunbiya) an soya cikin kwalanda za'a sa a miya....Uwani ta amsa sallamarsu tana washe baki Rashida ta gyara tabarmar da take zaune tana fadin "Aunty Wasila yau da wuri kuka dawo Allah yasa dai an samo wasu kudin.....Wasila ta cire hijab din jikinta ta ta shiga zazzage kudin da suke cikin jakarta......Uwani ta razana! ganin uban kudi gaban Wasila sun tassama dubu dari biyar! Sai kawai ta dora hannunta a saman hancinta ta dinga rangwada bud'a yi takeyi kamar zata tsine hancinta. Sai da tayi mai isarta sannan ta iso inda suke zaune Rashida sai faman irga kudin take tana ihu!! " Kai jama'a! ashe dai zanga wannan rana ni Uwani, ashe idona zai ta'ba ganin irin wadannan uban kudade masu yawa lallai wannan sana'a tafi irin wacce nakw cewa kiyi 'yata Wasila ina alfaharin haifarki Allah yayi miki albarka Wasila." Uwani ta gigice sai sambatu takeyi Camas da Rashida sai dariya suke mata....Wasila kam mikewa tayi jikinta duk ya mutu duk sanda ta tuni artabunsu da *'Kumdum!* sai gabanta ya yanke ya fad'i shikkenan fa idan da da tsautsayi da karar kwana da tuni ta zama tarihi domin ta lura babu imani a cikin zuciyar dan daban ta wani gefan kuma guy nan ya taimake ta dan sai yanzu take nadamar zagin da tayi masa kuma ta lura ya gani ya kuma ji rashin dad'i, sosai abun yake dan ta'ba zuciyarta babban mutum ne da shekarunsa suka wuce tayi masa haka domin zuwanta gidanshi na farko bata tantance kamaninsa da shekarunsa ba sai ganin da tayi masa a dazu.....Ganin zuciyarta na damunta ya sanya ta tattara ta watsar da al'amarin babu wani abunda zai faru dan ta zageshi ai Siyasar 'kasa ce kowa yana da 'yancin yin abunda yake so ga wanda baya so....Wanka tayi ta fito ta tarar Camas ta tafi gida ta kalli Rashida dake zuba musu abinci tace"Idan anjima zamuje Sto muyi siyayya dukanin abunda bamu dashi walau naci dana sha da daurawa." Rashida tace"Shikkenan bari nima nayi wankan sai muci abinci mu tafi." Uwani kam sai faman juya miya takeyi tana murmushi Ah!! Allah maiyin yanda akeso dare daya Allah kanyi bature Arziki ya sakko musu lallai babu abunda yafi haihuwa rana a duniya shiyasa masu karin magana ke cewa ko kana gudu haifi ka jefar ita dai gashi haihuwa tayi mata rana. _Muje Zuwa_ *BINTA UMAR ABBALE* [7/13, 10:52 PM] Bintu: *'YAR BANGAR SIYASA!!* 🌺 romantic love story🌺 *NA:* *BINTA UMAR ABBALE 🍒* *🌍Manazarta Writes asso* _'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_ ~~~~~~~~ *NA KUDI NE.......!* _Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176 sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko orange_ *Free Pege 8* Suna idar da sallahr magariba suka fito har Uwani domin tace itama zata bisu kasuwar suka sanyawa kofar gidan katon kwado kana suka fito titi domin samun abun hawa, suna tsayawa wani mai d'an sahu ya tsaya gabansu Wasila tace" Al'Ikilas zaka kaimu." Yace."An gama hajiya nawa zaku bayar."? A ya tsine tace"Muje dan Allah bana son harkar fatara ko nawa ne kudinka zan baka." Me dan sahu yace."A'a hajiya daga magana karfa ki zageni dan wallahi kika zageni ba yarda zanyi ba." Rashida tace"Kai dan Allah muje kana jan duguwar magana ai laifinka ne meye na tambayar nawa zamu bayar mu ba mutsiyata bane." Yace."Bana son in dauke ku ne bamu daddale daku ba sai kunzo sauka ku kawo min kauli da ba'adi shiyasa nake so naji nawa ne kudina." Wasila taja tsaki! tana kokarin shiga babur dole ne ta siyi sutturu masu tsada saboda ta lura suma 'yan a dai-da ta basu da kirki daga sunga mace da kod'addiyar atamfa sai su hau wulakanci in kuwa suka ga mace da dankareran lesi da gwala gwalai har rubibin daukarta sukeyi saboda sun san ko nawa sukace ta basu zata basu. Wasila har waya take so ta sauya sai dai kuma abun yayi yawa dole gobe ma su sake fita dan yau kayan kwalliya zasu siyo da atampopi da mayafai da takalma, har bakin super Sto din ya ajiyasu ta dauko dubu daya dal ta mika masa baiyi tsammanin haka daga gareta ba ya dauka zaiga ta fito da dukukkunanniyar dari biyu canji yake kokarin dauko mata tace''Rike na barka maka." Ya sako baki yana kallonsu sun juya suna tafiya, kai! ammafa yayi mamakin lamarin nan ashe arziki ne yake binsa yana basarwa duka kudinsa dari uku ne gashi ya tashi da dari bakwai sun isheshi karin kummalo da safe dan haka sai kawai ya nufi gida ya tashi daga aiki sai kuma gobe. Su Wasila kuwa zagaye Store din suke suna so suga iyakarsa sun kasa babban store ne da sai wane da wane ke zuwa gurin duk abunda ke cikin gurin ba na yarwa komai kudi ne Wasila suka dauki atampopi kusan kala bakwai suka d'ibi lesuka da mayafai sannan suka nufi gurin kayan make up nan ma ta dinga hada kayan kwalliya so take ta dawo babbar mace ta dinga cin kwalliya dama can ita bata yarda da karamar shiga ba, Can bagaran turirrika ta nufa su Uwani da Rashida suka tsaya gurin gwala-gwala sai 'kyauyanci sukeyi..........Yana kai hannunsa kan wani kwallin turare itama ta kai nata hannun ya sauka akan nashi. Da sauri ta dauke hannunta tana kallon zatinsa gaggausa mutum ta gani tsaye a kanta yayi mata rumfa kasancewar ta mace mara tsayi sosai.....Sai ta daga kanta tana kallon fuskarta a lokaci guda taji wani irin miyau! ya tsinke mata a baki ganin wanda yake tsaye kusa da ita. *Ahamdu* Da sauri tayi 'kasa da kanta tana adduar Allah yasa bai gane ta....'Kokarin wucewa takeyi taji yo muryarshi na fad'in"Zo ki dauki turaranki na samu wani." Gaba tayi ba tare da ta amsa masa ba, suka hadu da Garba wanda yake kokarin isa inda ubangidansa ke tsaye.....Sarai! Garba ya ganeta sosai dan har waiwayenta yakeyi Ahamdu yace."Kai! kula dallah! kallon me kakeyi ne." Da sauri yacs."Sir baka gane waccan yarinyar ba."? Tsaki yaja yana d'an ya tsine fuska yace."Meye ya dame ni da ita da zan tsaya tantance wacece."? Garba yace."Sorry sir yarinyar nan ce fa ta d'azu." Ya zare gilashin dake fuskarshi yana kallon Garba da mamaki yace."Da gaske."? Garba yace."Wallahi itace sir wai baka gane yanayinta bane ai naga a furgice ta bar gurin nan." Murmushi yayi kawai ya mai da gilashinsa, ashe ita ta ganeshi shiyasa tayi gaggawar barin gurin yanzu ya gane Jagaliyarta ta 'karya ce tunda bata iya tsayuwa a gabanshi ta mai da masa da martani.... Suna tsaye a gurin biyan kud'i ya 'karaso gurin sai taga ana bashi girma duk ma'aikatan gurin na kiranshi da Sir tayi 'kasa da kanta tana jinsa na magana cikin had'addan turancinsa da babu tangarda a ciki duk sai ta raina kanta gaskiya ilimi yayi addua takeyi Allah yasa kar ya waiwayo ya kallesu..........Ya kalli Manager gurin da Hausa yace."Cikin wannan satin Salim zaije saudia wani na'uin turare da babu a gurin nan sa ka rubuta masa gudun mantuwa.'' Yace."Insha Allahu." Wucewa yayi ba tare da yayi kuskuran kallon inda suke tsaye ba, suna fita Uwani tace"Oh wannan turanci sai kace wani ba amuruke da alama dai shine shugaban gurin.....Manager da ba hausa yake ji sosai ba ya d'aga mata kai alamar Eh......Rashida tace"Gaskiya aunty Wasila mutumin nan yayi wallahi kun dace dake dashi dama yace yana sonki." Wata harara ta watsa mata "Dallah kwaso kayayyakin mu wuce kin tsaya kina shashanci dare yayi." Rashida ta dauki manya manya ledoji guda biyu Uwani ma ta dauka itama ta dauka haka suka fita hannunsu ni'ki ni'ki da kaya su ba mota ba, sai da suka fito ne ma suka fahimci dare yayi sosai dan goma ma ta gota.....Da kyar! suka samu mai babur ganinsu da kaya ya sanya ya lafta musu kudi wai dubu biyu Wasila tace"Muje zan baka." aikuwa da sauri yaja babur din suka dauki hanya. Sai da suka zo dai-dai titin makarantar legal tayar a dai-dai tar tayi faci!!! Tofa ga dare gashi babu masu faci a kurkusa ga gurin tsit! sai kukan tsintsaye....Uwani ta fito tana salati da sallami motocin gida jefi jefi ne suke wucewa suma kuma da gudu suke wucewa saboda sun samu arhar titi babu go solow, Wasila ta fito daga babur din tana fad'in"Yanzu ya za'ayi? kai innalilihi gaskiya banji dad'i ba wallahi." Mai babur yace."Ni wallahi na rasa ma ya zanyi dana sani nake wallahi dan idan ban samu wanda zaiyi min faci ba dole in bar babur din a gurin.......Wasila tace"To mu kuma muyi yaya kenan."? Yace."Hajiya dan Allah ki kyaleni naji da abunda ya dame ni ai kuna da kafafu ku karasa mana a kafa." Rashida tace"Ka duba tazarar dake tsakanin nan da dorayi fa akwai sauran tafiya gaskiya mu dai kasan yanda zakayi damu." Haushi yasa mai babur din fad'in"Ai sai ku kwana a gurin ni kunga tafiya ta." Ya zare key dinsa daga jikin babur din ya dauki hanya ya barsu a tsaye a gurin.......Sai da suka daina hangoshi sannan suka tabbatar da cewar da gaske ya tafi din Wasila tace"Ai sai ku dauki kayan muma mu daura damarar tafiya da kafafunmu dan babu wani alamun babur a kan titin nan." Suka d'addauki ledoji suka saici hanya suna tafiya fakam fakam! ga nauyin kaya ga gajiya sunyi masifar galabaita......Sunyi nisa d a tafiya sosai suka hango ana haske su da touch Dukaninsu sun razana! ganin wasu tsagerun matasa sun durfafo inda suke "Kai! matanan daga ina kuke ne."? Uwani tace" Ku bamu hanya mu wuce munyi dare zamu koma gid.....ai kafin ta rufe bakinta na kusa da ita ya wafci ledar hannunta yana zazzagewa.....Wasila tace"Kai meye haka kuk.....Ita taji ya fizgo jakarta dake rataye a kafad'a ya zazzage a kasa uban kudi suka watse a gurin....Ihu!! suka zumduma! suna fad'in Kai!! ashe yau mun fito a sa'a Kwashe mana su mana jeka bunciki jikinsu kaga ko da akwai sauran wasu idan da gold a jikinsu ka ciro." Babban cikinsu ne ke wannan maganar....."Kar ka kuskura ka ta'bani wallahi hannunka ya sauka a jikina sai nayi maka illah."!! kamar mahaukaciya take maganar....babban cikinsu ya taso yana haskata da touch "Wow!! yafada yana lasar le'be." Baby wannan jikinki naki ai bana banza bane ke kanki kin san sai an mora da har kike maganar zakiyi wa yarona illah to kafin kiyi masa ni bari nayi fara miki." Yana kai hannunsa jikinta ta gaura masa wani lafiyyan mari!!!! Ya kurma wani ihu! "Ni kika mara!? kanta yayi ta goce a guje tayi kan titi yabi ta hijab dinta ya take da kafafunsa tayi dubarar zare hijab din ta mike a sukwane ta sake ranta a na kare gashin kanta duk ya warware ya zubo mata a fuska da kafada......... tana tsallaka titi taga haske fitilar mota ta doso, tun kafin ta karaso take daga hannunta sama......Yace." Garba rage gudun motar nan babu lafiya waccan kamar yarinya mace Allah yasa ba fyade za'ayi mata ba." Garba yace."Ai kuwa sir ga dukanin alamu hakad'in n.... ai kafin Garba ya rufe baki Goga ya iske inda Wasila take suka hargitse da kokawa......Da sauri yace."Subahannahi Garba kashe mota." Garba ya kashe mota da sauri ya bude motar ya fito wanda yayi dai-dai da lokacin da Wasila ta samu nasarar kwatar kanta daga Hannun Goga, a jigace! ta iske! inda yake tsaye ta afka kansa ba tare da ta sani ba, yayi saurin dafe bayanta da hannunshi guda yana kallon Goga ya dumfaro gurin......Yana isowa ya kai masa 'kwakkwaran naushi! da hannunsa guda ba tare da 'bata lokaci ba Goga ya zube a gurin hancinsa na zubar da jini _Muje Zuwa_ *BINTA UMAR ABBALE* [7/14, 3:04 PM] Bintu: *'YAR BANGAR SIYASA!!* 🌺 romantic love story🌺 *NA:* *BINTA UMAR ABBALE 🍒* *🌍Manazarta Writes asso* _'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_ ~~~~~~~~ *NA KUDI NE.......!* _Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176 sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko orange_ *Free Pege 9* Yaran Goga na hango ogansu a kwance a 'kas yana matagugu! sai suka ranta a ana kare ko wannesu na neman mafaka a tunaninsu jami'an tsaro ne sukayi basaja, a gurin......Uwani da Rashida suka iso gurin hankalinsu a tashe Uwani fadi take"Shegu tsinannu 'yan iska kawai mu samu kudinmu da 'kyar! su biyo dare su 'kwace ai gaskiya 'barawo baiyi ba." Ahamad ya d'an ja jikinsa kadan ganin ta daina rawar jikin da takeyi ya dan tsira mata ido fuskatara na kallon 'kasa ta kasa dago kanta har yanzu da akwai furgice a tare da ita sosai ta tsorata da goga a duniya babu abunda takeji dashi kamar budurcinta Rashida ta 'karaso inda take tsaye tana mika mata hijab dinta ta kar'ba ta zura Uwani tace"Amma dai babu abunda yayi miki ko." Daga kai kawai tayi tana goge fuskarta 'kamshin turaran da mutumin yake yi shine ya dabbeta tana ji kuma kamar tasan me irinshi Muryarsa ce ta daki dodon kunnata wanda yasa tayi saurin dagowa sai taga ya juya yana tafiya bayanshi kawai ta kalla ta gane shi! *Ahamdu* ne Garba yace."Yallabai yace."Ku shigo motar sai mu aje ku a gida amma yana da kyau ku daina tafiya irin wannan ku kai dare kasancewarku mata akwai 'bata gari a ko ina zasu cutar daku." Wasila ta dago kanta tana kallon Garba ya kalleta da mamaki! sai yanzu ya ganesu sune ashe!? to anya ma kuwa Yallabai din ya gane su.....Uwani ta hau daukar kaya ta nufi motar Garba yace."dan dakata tukkuna." Motar ya nufa ya tarar dashi a kishingide idanunsa a lumshe wata iriyar kasala ce ta dabaibaye shi sakamakon rungumar da yarinyar tayi masa duk ta gwaggoga nasa nonowanta a kirjinsa tsigar jikinsa sai wani irin mikewa takeyi sanyi sanyi ma yake ji burinsa ya isa gida ya kwanta ko samu sauki......"Sir." Garba ya kira sunanshi yana runkufar da kansa ya bude lumsassun idanunsa yana kallonsa yace." Shin ka gane ta kuwa? naji kace su shigo mota yarinyar nan ce fa mara kunya wacce ta zage ka dazu gurin kamfen." Ya tsirawa Garba ido yana kallonshi da mamaki a tare dashi.....Garba yace."ai da kana gurin kasa dago fuska tayi saboda itama tasan bata kyauta sai bayan ka bar gurin ne ta dago fuskarta nan na ganeta.......Jim! na minti biyu kafin yace."Kyaleta kawai shigo dasu muje dare nayi taci albarkacin abokanan tafiyarta." Garba baiyi tsammanin hakaba saboda yasan halin Ogan nashi baya barin bashi babu shakka yarinyar nan na samu dama a gurinshi..........Wasila kam masifa ta hau yiwa su Uwani wai lallai sai sun shiga motar tunda Allah yasa zai tamaike su ita kuma kunya tasa tace dole su dauki kayansu su karasa da kafa ai sun kusa isa gida babu yanda zasuyi da ita suka dauki ledojin suka hau tafiya fakam! fakam!!! Garba ya cimmusu yana fad'in"Yallabai yace."Ku shigo muje ku kawo kayan." Ya hau kar'bar na hannun Rashida ta sakar masa dan dama ita ta riga ta gaji tsoron masifar wasila takeji Uwani ta kalli Wasila dake cigaba da tafiya tace"Haba Wasila ki tsaya mana a taimaka mana kinsan fa kafin muje gida mun galabaita gashi kin san inada ciwon kirji idan ya tayar min kamar zan mutu. Tace"Tunda dai kun nace sai mun shiga muje amma meye saura anan mun kusa zuwa 'yan babura fa." Rashida tace"Eh duk da haka dai aunty Wasila ai ragi ragi ne." Shiru tayi musu suka kawai tabi bayansu a zahirin gaskiya bata son shiga motar dan dai kawai sun nace ne! Yana hango zuwansu gurin ya fito daga bayan motar ya bude gaban motar ya zauna gilashinsa ya gyara, ya tamke fuskarsa yayi dakacen hada jiki da ita ko da yake ai itace ta rungumeshi........Yana da tausayi sosai mussaman kan 'yaya mata shine dalilin ma da ya sanya ya tsaya amma da yasan yarinyar nan ce mara kunya babu abinda zai sanya ya tsaya ya 'bata lokacinsa Hanyar biri daban ta mota daban. Suna shiga motar sanyi Ac da kamshi ya bakunce su, Uwani ce a farko sai Rashida Wasila ta zama karshen shiga motar sai dauke kai takeyi bata so su hada ido dashi gashi sun zauna a site daya tana kallon fuskarshi ta mirror ya hade rai! sai itama ta hade nata ran! tayi kasa da kanta, ita sam wannan taimakon baiyi mata ba saboda babban abun kunya ne guy nan yaje yaga makwancinta duk da haka dai ba zata bari su shiga ciki ba a bakin titi zasu sauka. Jin surutun da su Rashida yayi yawa yana nema ya karasa wata damuwar bayan wacce yake ciki......Sai ya sanya hannunshi ya kunna redio karatun alkur'ani ya soma a tashi daga bakin *Ahamd Sulaiman* Duk da haka dai su Uwani basuyi shiru ba sai surutu suke suna ta zancan 'barayin da suka tare su. Gyaran murya yayi sai suka yi shiru suna kallonsa....Wasila ta dan ja tsaki kadan tace"Dan Allah kuyi shiru idan munje gida kwayi maganar haba." Shiru sukayi basu sake cewa komai ba motar ta cigaba da tafiya. A hankali ya dago idanunsa dake sakaye da gilas yana kare mata kallo ko da wasa baza kace ita yake kallo ba saboda yanda yake wani basarwa.......Yarinyar nada kyau! sosai sai dai bata da kunya ko kad'an! shi kuwa baya shiri da mara kunya marasa ganin girman na gaba dashi. Dai-dai bakin titin 'yan babura Wasila tace"Ajiye mu anan ba sai ka shiga damu zamu karasa da kafafunmu. Uwani tace"Haba 'yar nan ki bari mana a karasa damu mana mutumin nan fa taimakon yake yi kar ki katse masa hanzari." Dan Allah aunty Wasila ki bari a karasa damu." Rashida ta fadi maganar tana karyar da kai.....Sai magiya take mata kamar zatayi kuka." Yace."Garba shiga da motar nan ka kaisu har kofar gidansu kar ka dakata maganar ta." Yace."Angama Yallaba.'! Uwani tace"Mungode sosai Allah yayi albarka alhaji Allah yasa a gama lafiya, Allah ya raya zuria." Ya amsa da "ameen." yana duba wayarshi....Wasila kam! sai shan kunu takeyi sam bata so haka ba dan dai kawai sunfi karfinta ne. Wani tsukakken layin suka shiga motar ta dinga gwajab gwajab!! tana cijewa......Ya dan gyara zamanshi yana duba yanayin ungywar kai da gani kasan unguwace ta marasa galihu gidaje kananu babu tsayin katangar arziki ga kwatoci duk sunbi hanya abun babu kyan gani sam unguwar bata yi masa ba, bai shiga mamaki ba sai da yaji muryata na fad'in"Tsaya anan ga gidanan ai." Yabi gidan da kallo yana mamaki! wai sunan angyara ansa kofa da lokacin buhu ne abun sai ya bashi mamaki dan adam ke rayuwa cikin wannan gidan rubabbe lokacin damuna mutum na cike da fargaba da alhini kar ya rikito masa amma su haka suke kwanciya hankalinsu kwance......Tausayi suka bashi yanzu ya gane abunda ya sanya yarinyar famtsama harkar Jagaliya talauci masifa ne! da'alama kuma su kadai suke rayuwa a gidan.....Tunaninsa ne ya katse lokacin da ya hangota tana bude gidan...Uwani da Rashida sai faman godiya suke masa, Ya bude wani guri a cikin motar kudi ya dauko a daure a kyaure! ya mika ma Uwani ta karba hannunta na rawa gwiwa kasa ta zube tana godiya yace."Tashi dan Allah kamar hakan bai dace ba nayi niyya ne na baku amma akwai 'yar shawarar da zan baku idan babu damuwa." Tace"To Alhaji Yace."Ki hana 'kanwarki harkar Jagaliya sam bai dace da 'ya mace ba ni zan taimake ku sannan idan kun samu mijin aure kuyi aure ni zan dauki nauyin komai naku." Sai Uwani ta fashe da kuka tana fadin "Alhaji labarinmu mai tsayi ne Wasila kuma ba kanwata bace babbar 'yata ce sai Rashida su kadai na haifa marayu ne babansu ya mutu tun kafin suyi wayon haka sannan duk dangi sun guje mu saboda bamu dashi mune muke ciyar da kanmu kaga kuwa har jagajiya ai sana'a ce bazan iya hanata ba tunda gashi ta rufa mana asiri." Yayi shiru yana sauraronta tausayinta yaji ashe itace mahaifiyar yaran shi ya dauka yarsu ce, Ganinta tana kuka ya sanya yace." amma al'amarin akwai hadari a ciki tunda kun daukeshi a matsayin sana'a Allah ya taimaka." Uwani ta amsa da "ameen tana sake godiyar kudin da ya basu....Ahamad ya bawa Garba Umarnin tafiya Garba yaja motar suka bar gurin Wasila kuwa ta jima da shiga gida sai haushin tsayuwar su Uwani takeyi a waje Allah yasa dai ba ro'konsa suka tsayi ba tasan halin masifar kwadayi da roko na mahaifiyar tata. _Muje Zuwa_ *BINTA UMAR ABBALE* [7/15, 12:15 PM] Bintu: *'YAR BANGAR SIYASA!!* 🌺 romantic love story🌺 *NA:* *BINTA UMAR ABBALE 🍒* *🌍Manazarta Writes asso* _'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_ ~~~~~~~~ *NA KUDI NE.......!* _Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176 sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko oragne_ *Free Pege10* Suna shiga cikin gidan Wasila ta rufe su da masifa,"Haba Uwani nifa bana son 'karanta bisabillahi yanzu minti na nawa da shigowa cikin gidanan kuna can kuna maula da zubda mutunci dama tunda naji shiru nace to kun tsaya roko wane irin rayuwa ce ban saka kaina ba a akanku amma duk da haka sai kun watsa min kasa a ido idan kuka ce haka zaku dinga yi to wallahi zan barku da halinku ko na samu kudi in boye kaya na." "Haba 'Yar nan, mutumin nan ya cancani a tsaya ayi masa godiya ba don komai ba sai dan taimakon da yayi mana a wannan zamanin ba ko wane mai kudi ne zai tsaya ya taimaki talaka ba yanzu idan da badan yazo gurin ba da me kike tunani zai faru tsakanin da 'barayin nan nasan wallahi sai sunyi mana tas! wannan budurcin naki da kike tattalawa su keta shi da wagari ya waya ai dole a tsaya ayi masa godiya ba abunda kike tunani ne ya tsayar damu a gurinsa shine dai yayi niyya ya bamu kudi kingasu ma." Ta mika mata daurarrun kudin dake hannunta, Wani banzan kallo tayi wa kudin kafin tace"Yanda ya baku kudin to ku ajiye ko lissafawa bance ayi ba ni ina da a'kida idan ina son mutum a siyasance ina sonsa idan bana son mutum bana sonsa dan haka banga abunda kudinsa zasuyi min ba tunda dai ina dasu." Uwani da Rashida suka saki baki suna kallonta da mamaki! wannan kudin masu tarin yawa zasu aje to akan me? ai su ba 'yan siyasa bane kuma ai ba ita ya bawa kudin ba su ya baiwa ballanta tace. Wasila tace"Ko kuna so dai inyi muku bayani dalla dallah akan mutumin nan domin naga kudinsa duk ya furgitaku." Uwani tace"To ai kece naji kina wata magana a wannan zamanin ayi maka kyautar kudi ka mayar gaskiya abin da kamar wahala." "Uwani wannan guy fa shine dan takarar Governor a yanzu dashi suke fafatawa da Governor mai ci a yanzu kuma duk kudin da kikaga na samu ta bangaran harkar siyasar nan to ta dalilinsa ne dan akanshi muke jagaliyarmu saboda haka duk ranar da mai girma governor yasan da cewar ina bangare biyu a wannan harkar to yan kudin da nake samu zai hanani dazu fa cewa yayi zai zauna dani na fada masa dukanin bukatuna sannan kuma ya sauke mukamin wani a dora ni a kai nan gaba kadan ina ganin zan zama 'kusa a harkar dan haka banga amfanin da wad'annan 'yan kudin zasuyi mana gobe insha Allah kafin mu isa government house zan kai masa kudinsa har gida bama bukata." Uwani tace"Kuma fa hakane maganarki Wasila duk ranar da governor ya gane baki da a'kida to kashinmu ya bushe gwara ki tsaya a bigire guda mussaman yanzu sune ludayin su yake kan dawo zamu kwashi roman da mukarad'iya gwara mu tsaya da kafafunmu kafin ya sauka. Wasila tace"Ashe kin gane abunda nake nufi dan haka bani kudin na ajiyesu taimakon da yayi mana kuwa shine yayi niyya 'yan kudinsa baza su sanya ni na sauka daga a'kida ta ba." Uwani ta mika mata kudin ba dan ranta yaso ba sai dan ba yarda zatayi da 'yar tata. ****** Tunda suka doso layin suke ganin cincirindon mutane wasu na shiga wasu na fita ga 'katon gate din da ya zama security ga estate din a bude jama'a sunja dogon layi sai kar'bar tallafi sukeyi layin mata daban na maza daban.....Camas! tace"Kawata me yake faruwa ne naga mutane sunja layi." Wasila ta gyara ni'kab din dake sakeye da fuskarta tace"Zai wuce kamfen yake domin yaudarar al'umma amma dai bari mu tambayi wannan matar." "Baiwar Allah dan Allah me akeyi anan gurin."? Matar ta tsaya tana washe baki tace" Tallafi mai girma Governor mu na gobe yake raba mana mata dubu goma maza dubu ashirin." Wasila tace"Ke kin samu kenan."? Cike da farin ciki matar tace"Na samu mana gasu ma nasa a cikin jakata, zuwa zanyi na siyo gyada buhu biyu mu dinga soyawa da yara na kafin muga abunda Allah Zaiyi." Wasila tayi murmushi tana jan tsaki tace"Kin san wani abu."? matar ta girgiza kai...."Zan baki baki dubu ashirin yanzu kije ki watsa masa kudinsa kice baki so kudinsa basu isa su siyi 'kuri'arki ba mulki kuma sai dai yaga anayi." Matar tabi Wasila da kallon mamaki.! Wasila tace"Ko dai kudin da na fada sunyi miki kadan ne to na kara miki talatin akai sun zama hamsin nasan dai zasu isheki kija jarin ko wace sana'a ce." Matar tace"Bana son roman baka yarinya in fara gani a'kas! tukkuna." Wasila ta zaro jakarta dake rataye a kafada ta lissafa kudi dubu hamsin cif tace kin gansu a hannuna kina aiwatar da aikin dana saki zan baki su. Laraba na ganin kudi dumus a hannun Wasila sai ta gigice! tace"To yanzu ya za'ayi na shiga gurinan akwai 'yan sanda sosai a gurin kuma suna ganin shige da ficen jama'a kana suna gane wanda ya fita da wanda ya shiga kuma kina ganin idan na aikata hakan ba za'ayi min komai ba." Wasila tace"Karki damu malama muje tare zamu sanyaki a tsakiya ba zasu gane ki ba." Laraba tace."To ku muje." Kai tsaye suka durfafi kofar shiga gurin jami'an tsaron dake tsaye a gurin sukace su tsaya wani abu suka kara a jikinsu minti biyu sukace su wuce ciki.......Wasila da Camas! suka kama layi kamar gaske! Laraba kuma ta mike hanya dan isa inda yake tsaye..........Tana zuwa ta watsa masa kudinsa a jikinsa da karfi tace." *Bama so bama yi! wa 'yan nan 'yan kud'in naka basu isa su siyi kuri'armu bamu ba!.* Ai sai gurin ya kaure da hayaniya Garba da Hadi sukayo kan laraba Ahamad dake tsaye cikin dumbun mamaki ya hanasu dukanta, su kansu Police din dake tsaye a gurin Sunyi mamakin matar amma ya hana a ta'bata komeye dalili oho." Ya Kalli Garba a nutse yace."Zo ka tsaya ka cigaba da raba musu." Garba ya tsaya inda yake shi kuma ya kalli Laraba dake tsaye jikinta yayi sanyi kalau yace."Baiwar Allah bance dole ki za'be ni a matsayin d'antakarar ki ba wannan kudin da nake raba muku duk karshen wata inayi ne saboda Allah ba da wata manufa fa ra'ayinki ne ki za'be ni ko ki za'bi abokin gamayya ta ni nasan ba zai iya siyan 'yanci ki ba nafi so duk wanda zai za'beni ya za'beni saboda Allah da kishin kansa da kuma 'kasarsa...." Laraba ta fashe da kuka tana fad'in"Kagafarce ni yallabai! wallahi bayin kaina bane roman baka akayi min wata yarinya ce yanzu tayi min alkawarin zata bani dubu hamsin idan na aikata maka haka yanzu kuma wad'annan maganganun da kayi sunyi bala'in kashe min jiki don girman Allah ka gafarce ni." Ahamd ya sauke ajiyar zuciya shi sam baiji zafin matar ta saboda yasan irinsu siyansu ake da 'yan kud'i kad'an! saboda an san shi talaka bukatarshi kudi ko ta halilin kakane zai iya siyar da 'yanci akan sabulu ko omo ko sukari. Yace."Yanzu zaki iya nuna min inda yarinyar take."? tace"Kwarai kuwa Yallabai ai gatacan ma ta kama layi." Ahamd ya goya hannunsa a baya suka mike dogon layin dake jere da mata har suka inda su Wasila suke....."Gata nan Yallabai."! Laraba ta nuna Wasila dake tsaye fuskarta da ni'kabi.....Zatin ta kawai ya kalla ya gane ta ya d'an tsirawa idanunta kallo dake ni'kab itama ta sama ido suna kallon juna.....Ya d'an juya a nutse ya kira police yana karaso yace."Zura mata ankwa ka kai min ita cikin gida." Camas! tace"Innallihi wa'ina ilahi raji'un! Jama'a me mukayi baiwar Allah me tayi miki zakice itace haka kawai dan sharri! Yalla'bai wallahi ba ita bace hasali ma mu yanzu muka shigo gurin kuma ai ba ita kadai ce mai niqab ba a gurin." Ahamdu ko sauraranta baiyi ba ya bar gurin. Camas! ta dinga ihu! tana zagin Laraba Wasila ta dinga turjewa tana fad'in''Me nayi muku wannan sharri tayi min bani bace wallahi Police din yace."Wallahi idan bakiyi shiru ba zan fuxge wannan niqab din dake fuskarki in yaso kowa ya ganki munafuka kawai." Jin abinda Police din yace ne sai ta daina turjewa saboda bata so ya cire mata niqab jama'a su ganta akwai tozarci sai kawai ta hau fuffukar 'karya da fad'in"Ai gaskiya daya ce kuma wanda ya zalinci wani Allah yana gani haka kawai saboda rashin adalci za'a sanya min ankwa sai kace 'barauniya ko kuma wacce tayi kisan kai!! kuma a haka ake cewa za' a iya mulki wannan ba adalci bane wallahi duk wanda ya shiga hurima na barshi da Allah."!!! Dan sanda kuwa ya tasa 'keyar ta tana tafiya tana surutai da farfad'ar bakake maganganu masu harshen damo wanda wanda ake dominsa ya sani masu hankali ma a gurin sun gane da wanda takeyi....Angizata yayi cikin gate din yayi ya mayar da 'kofa ya rufe......Ta waiwaya bayanta babu kowa har masu gadi duk suna waje gefen bainci masu gadi ta zauna gabanta na fad'uwa sai yanzu jikinta yayi sanyi da al'amarin, dole ta cire tsoro da shakku a kan abunda zai faru ita dashi tayi al'kawarin ba zai ta'ba samun nasara a kanta ba.......Can ta hango shi ya fito daga wata iriyar kofa ta gilas ya durfafo inda take zaune gabanta ya dinga duka yana daka! mussaman ganin yanda fuskarsa take had'e tamkar hadarin da ya daf da zubar da ruwa. _Muje Zuwa_ *BINTA UMAR ABBALE* [7/15, 3:19 PM] Bintu: *'YAR BANGAR SIYASA!!* 🌺 romantic love story🌺 *NA:* *BINTA UMAR ABBALE 🍒* *🌍Manazarta Writes asso* _'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_ ~~~~~~~~ *NA KUDI NE.......!* _Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176 sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko orange_ _*Babu mahalu'kin da ya isa yayiwa mutum abunda Allah bai masa ba, bama nema gurin kowa! gurin Allah muke nema Allah ka yi mana ba dan mu ba*👏🏻_ ~~~~~~~~~~~~~~ *Page d'in naku ne* _HAUWA S ZARIA_ *(Mmn Uswan)*🌺 _MAMAN MAMY_ *(Shalele)*🌺 *Free Pege11* Ganin ya kusa isowa inda takene ya sanya tayi maza ta yi 'kasa da kanta gani tayi ya kara wani kwarjini da kamala adduar neman rinjaye ta soma sai dai duk wacce ta dauka sai ta subce ta kamo waccen ma ta subce duk sakamakon tsayuwarshi a kanta ga masifar kamshinsa ya rikirkita mata lissafi. "Cire wannan ba'kin abun na fuskarki." Yafad'a cikin wata iriyar murya.....Ta dago kanta tana kallonshi, "Kamar yaya na cir.....Kafin ta 'karasa ya fuzge niqab! din ya jefar, tayi saurin kauda kanta gefe. Hannu ya mika yayi kamar zai juyo da fuskarta sai ya fasa yace." Juyo ki kalleni ina son muyi magana dake." Sai da ta dai-dai ta nutsuwarta tukkuna ta juyo tana kallonshi........Sun kai kimanin minti uku suna kallon juna kafin ta dauke kanta tana wani ya mutse fuska. Gyaran mirya yayi a nutse yace."Ina so ki fad'amin nawa aka biya ki kika tsunduma kanki a wannan harka ta jagaliya ki fada mun ko nawa suka baki ni nayi miki al'kawari zan nin ka miki abunda suka baki ko sukayi miki alkawarin mutukar zaki dawo kiyi harkar ta siyasa mai kyau, da tsari! Ta mike tana karkad'e hijab d'inta ta kalleshi ido da ido tace"Ni! bana jagaliya siyasa nake tsaftacciya kuma kai baka da kudin da zaka iya biya na kan wannan harkar." Murmushi ya saki yace."Kina bani tausayi yarinya baki san waye Ahamdu ba ko."? Tace"Saninka ba zai amfana min da komai ba tunda nasan anayi siyasa ne da ra'ayi ni bana ra'ayinka kuma baka isa kasa ni na sauka daga a'kida ta ba.'' "God."! yafada yana tafa hannunsa ya kalleta da kwantaccen murmushi a fuskarshi yace." Gaskiya kin burgeni yarinya kuma ana siyance ana son mutum mai a'kida ni kaina idan da zan samu abokin tafiya irinki da naji dadin harkar ammafa ni yanda na dauka kin tsunduma kanki wannan harka ne domin cimma wata manufa taki. "Kwarai kuwa akwai manufofi da nake dasu akan wannan harkar wanda ni kadai na barwa kaina su ina so kuma Allah ya cika min burika na." "Masha Allah shin meye sane kuka daura tuntuninku akaina kuka tsawwala min sai kace ni kadai ne dan takarar Governor dake takara da governor ku me yasa duk inda nake kuna bibiyata da al'amurana saboda tsabar bin diddigi irin naki har gida kike biyo ni kina kokarin ci min mutunci shin wai me kuka dauki wannan harkar ne."!? Wasila tayi shiru yace." Siyasa ba hauka bace! wad'anda suka san abunda sukeyi sunayi ne kan tsari amma ke naga kina so ki wuce gona da iri saboda talauci yayi miki katutu shiyasa kike ganin zaki iya zagin mutum kamar ni wanda yake da shekarun da suka nunka naki sau uku, okey nasan babu abunda ke damunki sai jahilci da rashin mafad'i to wannan shine lest winning na 'karshe kada! na sake ganin wad'annan kafafun naki a gidana duk ranar da kika sake kuskuran shigo min gida to a ranar ki kwana da shirin wad'anann kafafun naki ba naki bane dan sai na sanya an ragargaje su! in yaso sai naga kafafun yawon *Banga* ban hanaki ki zageni ba ko ki jefe ni kije kiyi tayi idan kin cimma burinki nasan zaki bari gidana dai ban lamunce in sake ganin kafafunki a ciki ba." Maganganunsa sunyi mata zafi sosai! ta kalleshi tana girgiza kai *"Jagaliya da Banga* yanzu na fara." Tana fadin wannan magana sai tw zuge jakarta ta zaro kudinshi na jiya ta jefa masa "Wannan kudin da ka bawa Mamana da kanwata basu ishemu kallo ba saboda aban bamu wanda yaf.......... Taji saukar Wani bahagon mari a kumatunta! A razane! ta dafe fuska idanunta yayi jawur! Ya dam'ki! wuyanta ya sha'ke cikin hijab.....Ta dinga kyarma! tana kyafta ido!! Ganin idanunta sun soma shagid'ewa ne ya sanya ya saketa sai ta fad'i a gurin ragwajab! tana kakari! tare da rike ma'kogwaronta! kanta 'kas!! ya tsugana dai-d'ai kafafunta, A kausashe yace." Har yanzu baki san waye Ahamadu ba ko! ni zaki jefa da kudi! ke! wai shin ma dame kike takama ne.''!!! Wasila tayi shiru bakinta ya mutu har yanzu ma'kogwaronta suya yake mata wai! sauran kadan ta bakunci lahira......"Wallahi wallahi duk ranar da kika sake gangancin aikata min abu makamancin wannan sai kin raina kanki in yaso su wad'anda suke daure miki gindi su same ni da kansu ni bana tsoron kowa kije ki fada musu basu isa nayi dake ba su zasu zo da kansu mu fafata! mahaukata kawai wadanda suka dauki mulki wata tsiya kije ki fad'a musu ni *Ahamadu* ina jiransu suzo da kansu sa'ko na baki duk ranar da suka sake turo ki to zan huce fushina a kanki Tausayi da jin kai ya sanya nake kyaleki kina min abunda kike so kuma ina baki damarki a siyance okey tunda ke d'in dabbace! mara kishin kanta zan fara cin ubanki idan kin soma ji a jikinki sai kije ki gyara *BANGAR SIYASAR KI* Tashi! maza ki kwashe min wannan kudin da kika watsar a kas! dubban mutane nacan suna nema ke kin samu kina zubarwa saboda kina da masu baki....Ki shirya min kudina tsaf! a cikin kyaure kamar yanda suke tunda bakwa so akwai dubunku masu so." Wasila ta yunkura ta tashi tsaye idanunta yayi jawur!!! Gefan hijab dinta tasa ta goge gomin goshinta ta ratse shi zata wuce!!! Tare ta yayi da kirjinsa ta dannata a jikin bango (garo) Sai ya zamana ma nuffashi da kyar take futarwa Gaggausan mutum irin wannan ya sanya mata nauyinsa ai sai Allah...."Ni zaki nunawa zafin kai ko."!? Yafada yana sake matse ta a jikin bango.....Kanta tasa ta daki kirjinsa dashi Yace."Idan kukan jini zakiyi anan gurin sai dai kiyi sai naga karshen tashen balagarki kiyi abinda nace kawai shine mafitarki." Cikin 'kunar rai! tace"Ka matsa daga jikina ka matseni a bango domin ka cimma wata manufa taka akaina to Allah ya isa kudi kuma zan tsince dan karan kaina ba dan wani ba." Ya matsa daga jikinta yana ya mutse fuska.......Bani da wata manufa da zan cimma akanki saboda na had'u mata iri iri wad'anda suks fiki komai kazama dake mai zanji a jikinki da kike wannan maganar." Shiru tayi masa ba tace komai ba ta hade masa kudinsa ya sanya hannu ya karba da hannu ya nuna mata 'kofa "Fice min a gida wannan shine karo na biyu idan kika kuskura kika sake shigo min gida to kin san abunda zai biyo baya." Hijab! d'inta ta buge! tayi masa wani irin kallo mai nuna alamun akwai sauran kalubale tayi kwafa ta juya tana tafiya da sauri sauri!!! Hannuwa ya zuba cikin aljihu yana kallo ta tsaya ta daura niqab dinta kana ta murda kofa zata futa......Dake a kulle take daga waje, Hadi yazo da sauri ya bude mata ta fice da sauri tamkar zata tureshi.....Can ta hango Camas tsaye jikin wata bishiya ta nufe ta da saurin gaske sam! bata damu da kallon da mutanan dake gurin suke mata ba, saboda babbar dama ce ta samu domin cimma manufofinta a kansa.....Suna fita suka samu babur kai tsaye government house suka nufa. _Muje Zuwa_ *BINTA UMAR ABBALE* [7/16, 10:09 AM] Bintu: *'YAR BANGAR SIYASA!!* 🌺 romantic love story🌺 *NA:* *BINTA UMAR ABBALE 🍒* *🌍Manazarta Writes asso* _'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_ ~~~~~~~~ *NA KUDI NE.......!* _Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176 sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko orange_ *Free Pege12* Sai da sukayi nisa sosai Wasila ta cire niqab din fuskarta tana goge fuska Camas tace"Ammafa matar nan taso ta saka ki a bala'i wallahi dan naga guy ranshi ya 'baci sosai ni na dauka ma zan ga kin fito da fasashen baki! wallahi." Ajiyar zuciya ta sauke tace"Bai fasa min baki ba amma ya mareni ya sha'ke min ma'kogwaro har na soma jiyo 'kamshin mutuwa! ammafa bai daki banza sai na kulla masa sharri nifa naji dadi da hakan ta faru wani plan zan shirya a kanshi ke dai kawai mu bar maganar sai munje gida tukkuna." Camas tace"Shiyasa naga kin fito a furgice! gaskiya Wasila akwai ki da jarumta wallahi da nice da tuni na karaya da wannan harkar akwai hadari a cikinta......"Camas idan kinga na daina banga to na cimma manufofina ne kawai ke dai ki cigaba da take mun baya insha Allahu wannan plan din da zan shirya shine zai janyo min arziki na har abadah." Camas tace"Allah yasa kawata kice dai mun kusa daina yawo a babur din haya zamu mallaki motar kanmu." Murmushi tayi har fararan hakoranta suka bayyana tace"Ke dai lokaci Camas! Allah dai ya taimake mu." Camas! ta amsa da "ameen" kana suka cigaba da wata hirar. Koda suka isa government house din Governor da sauran mukarrabansa suna dakin meeting sai da sukayi xaman awa biyu tukkuna suka fito lokacin har magariba tayi duhu ya shigo a gurguje suka gaisa kana Wasila ta fada musu abunda ya faru a gidan Ahamadu tace....Wannan damar tamu itace zata rusa duk wani shirinsa a gaban bainar jama'a al'amarin ya faru saboda haka da kaina zan shiga gidan redio in watsa maganar nasan wad'anda abun ya faru a gabansu zasu gazgata kaga da kanan shikkenan magana ta kare." Governor Lawan Rabo yace."Mutukar wannan magana taki ta rusa shirin Ahamdu to ni Lawan Rabo nayi miki al'kawarin baki kud'in da zasu gigitaki! zan baki mamaki 'Yar gaske in har wannan plan din da kika shirya kan Ahamdu ya sanya ya janye kudirinsa na zama dan takarar governor a jam'iyyar *CPC."* "Kar ka damu mai girma governor insha Allahu magana ta 'kare kujerar mulki kam kaine zaka cigaba da zama a kanta." Tafada cikin karfafawa kanta gwiwa kuma tana sanya ran insha Allah bukatarta zata biya. Basu dawo gida ba sai kusan karfe goma na dare dan daukarsu sukayi a mota suka nufi wani kayataccen hotel sukayi ciye ciye kana sukayo guzirin wasu, har bakin layi Alhaji Tasiu ya kawo su yana so ya fadawa Wasila munufarshi a kanta ya kasa wani irin kwarjini take masa shiyasa har ya yanzu ya kasa tunkararta yana kallon yanda abokansa ke shakawata da mata sam baya sha'awa amma yanzu ganin Wasila ya sanya yaji yana sha'awarta kuma ya daura aniya a kanta insha Allahu sai ya dandani zumarta yaji ya take....Dama tuntuni Alhaji ma'aruf ke kwadaita masa harkar yana basarwa sai yanzu kuma yaji yana sha'awar yi da Wasila *'Yar gaske!* **** Bayan mako biyu da faruwan al'amarin Ahamd ya sake fita kamfen dashi da mutanansa alhamdullahi anyi an kare lafiya dan har gidajen redio sai da suka sanyo muryarsa yanda take jawabi da irin ayukan da zaiyi idan Allah ya bashi gwamnati a hannunsa.....Ahamdu yaga masoya ta ko wane bangare dan gurin cika yayi ma'kil! da jama'a 'yan nahiyar birget da kwana hudu, babban abunda zai baka mamaki! shine yanda mata da maza manya da yara suke fitowa suna turmutsutsu da fad'in "Se jam'iyar *CPC* sauyi muke so da *Ahamdu dan Musa* insha Allahu kano takace." Wasila na zaune kan tabarma anci kwalliya da wani uban les kunnanta da wuyanta gold ne sai sheki yake yi kawai taji muryarsa na jawabi yanda zai kula da gari da ayyukan da zaiyi mutukar Allah ya bashi iko, ta karo murya tana sauraran jawabin nasa da ba'aji sosai sakamakon hayaniyar da tayi yawa, mamaki take ya akayi har ya fita yayi wannan kamfen din basu sani ba.....Cizan lebe tayi ta dauki tafkekiyar wayarta mai tsadar gaske, Alhaji Tasiu ta kira ya daga wayar da sauri tace"Yallabai ka kunna redio kaji abunda ke faruwa mutuminka ya fita kamfen sai alkawarin karya yakeyi jama'ar gari na yi masa ihu.'' Alhaji Tasiu ya kunna redion wayarshi yana saurara......Kiranta ya sakeyi a waya bayan ya gama saurara yace."Yanzu meye matakin dauka." Kwafa tayi tace"Bari bayan sallahr isha'i kazo ka dauke mu muje gidan redion *Salama* zan musu magana idan Allah ya kaimu gobe su sanar da cewar za'a hira dani *Wasila 'Yar gaske* a filin mu Siyasa." Yace." Hakan yayi dai-dai 'Yar gaske insha Allahu zan shigo da wuri sai muje ammafa nima ina da wata bukata da nake nema a tare da ke." Yafada yana wani kashe murya.....Tuntuni ta riga ta gama gane inda ya dosa kawai tana basar dashi ta fahimci yanda yake kulafucinta bai san me cin wannan budurcin nata ba sai ya shirya ji takeyi dashi domin tasan shine darajarta ta gama yawace yawacen ta dawo tilas tasan zatayi aure kuma shine mutuncinta shiyasa take tattala abinta domin ta mika shi ga namijin da yayi nasarar auranta......Amsa masa tayi kawai da shikkenan sai kazo d'in." Alhaji Tasiu ya kashe waya yana me cike da nishadi zai biya bukatarshi gurin Wasila.....A waya ta kira Camas! tace bayan sallahar isha'i ta fito zasuje inguwa. Aikuwa Camas! na idar da sallah tayi kwalliya tayiwa mahaifiyata sallama ta nufi gidan su Wasila mahaifinta na zaune kan tabarma yana shan iska yana kallon fitarta baice komai ba wanda inda dane da tuni ya korata gida amma dake yanzu ta toshe masa baki da kudi shiru kakeji wai malam yaci shirwa. Cikin wata dan'kareriyar mota Alhaji Tasi'u yazo daukarsu Wasila matasan unguwa suka dinga zind'en Wasila da Camas! cewar ba harkar siyasa kadai suka tsaya ba harda karuwanci ganin irin manya motocin dake zuwa daukarsu, ganin irin shigar da Wasila tayi ta fito dashi ya sanya suka sake gazgata zatonsu a kanta tana sanye da wani material roba roba anyi mata wani irin dinki riga da siket ne sun matseta ga wuyan rigar daga baya a fafake! daga gaba kuma anfutar da gidan nono ya matseta sosai Wasila akwai hips da brest duk sun fito sun das duk lafiyayyan namijn da ya kalleta a lokacin sai ya d'arsa wani abun a ranshi gashi ta kawo wani siririn mayafi ta rataya a kafadarta hannunta sakale da jakarta mahadin takalminta kana kallonta zaka gane ta soma wankuwa idanunta sun bude tar! tar! sai taunar cingum takeyi.....Alhaji Tasiu yaji jijiyarsa ta mike ganin tsarin jikin Wasila ashe cika da 'kasaitar yarinyar ya kai haka babu shakka dole xaiyi mata kwance kwance ya dandana zumarta. Gaban mota ta shiga ta zauna camas ta zauna a baya Kana Alhaji Tasi'u As na gomna ya tuka motar suka fuce daga layin yara na jifan motar da fad'in"Ba mayi! Kano ta d'an Musa ce wallahi.....Alhaji Tasiu yace."Na lura jama'ar unguwar nan taku basayin wannan gwamnatin tamu shin bakya musu hasafi ne kin san fa dole ki sake musu kudi sosai saboda ranar za'be! su fito su mara miki baya. Wasila ta sauke ajiyar zuciya tace"Na rasa abunda mutumin nan yake bawa mutanan jahar nan wallahi in kaga yanda jama'a ke sonsa sai ka rike baki ni kaina wani sa'in idan na fito jifana sukeyi sai nayi da gaske tukkuna." Alhaji Tasiu yace."Ai yana da masoya gaskiya dalili kenan da muke so mu dakusar da duk wani shirinsa muna so mu kashe masa gwiwa kan harkar yaji kwata kwata ta fita daga ranshi." Wasila tace."Kar ka damu insha Allahu bukatarmu zata biya a kanshi. Alhaji Tasiu ya biya tashar redio *Salama* kudi masu kauri yace."Tun yanzu su soma watsa wa cewar zasuyi hira da *Wasila 'Yar gaske* Yar partyn Lawan Rabo governor mai ci a yanzu." aikuwa kafin ma su bar cikin gidan redion sun soma sanarwa kan zasu hira da Wasila 'Yar gaske a filinsu na Siyasarmu da misalin karfe takwas na dare." Tun a cikin mota Alhaji Tasiu ke yi mata wani irin kallo yana lumshe ido tana hankalce dashi kawai tana basarwa ne babu zato taji saukar hannunsa kan cinyarta....kici kici tayi da fuska tace"Meye haka kuma kar ka kara kuskuran ta'ba jikina duk mutumcin da muke da kai naga zaka keta min martaba ta mutuntaka to zamu raba hanya." As ya soma yake yana sosa kai yace."Har yanzu baki gane inda na dosa ba kenan *Yar gaske* ki taimaka min rana daya ki mallaka min kanki." Ta watsa masa wani irin kallo, kankance ido tayi tace"As ina ganin girmanka da mutuncinka muyi harkar data hadamu da kai wato siyasa ni ba yar iska bace bana kuma shiri da mazinaci saboda haka kada ka kara yi min magana irin wannan duk ranar da ka sake to kam zan fadawa mai girma governor yayi min tsakani dakai ka kyaleni nayi sana'a ta kaje ka nemi 'yar iska kuyi iskancinku amma ni ba wannan na fito ba." As yaji ciwon magangunta Wasila butuluce meye bai yi mata ba a rayuwa da girmansa da komai take fada masa irin wannan maganar.....Shiru yayi bai sake tankawa ba Ita taci kunu tana tauna cingum dinta jefi jefi tana amsa waya Camas na baya da tata wayar a hannu tana chating duk tana jin abunda sukeyi tana ganin idan da itace Wasila da gudu zata amince wallahi ai duk sana'a ce a wannan zamanin samun irinsu As zaiyi wuya kuma ta fahimci mutumin bashi da mugunta iya kudi yana sakar musu ya kaisu su dungo siyayya harda ta banza ya biya kudin kuma ya basu wasu ita kam idan ya nemeta zata amince masa da gudu. **** Washe gari gidan redion *Salama* suna bude tasharsu da abunda suka fara kenan "Jama'ar gari da misalin karfe takwas da rabi na dare zamuyi hira da Hajiya Wasila 'Yar gaske a filinmu na Siyasa kowa ya kasance da redionsa a kusa dashi a dai-dai wannan lokaci domin yaji abunda yake tafe da wannan shahararriyar 'yar siyasar." Gari ya dauka kowa na jiran lokaci......Labari ya iske Ahamdu ta bakin abokinshi Khalifa wanda yake mara masa baya ga dukanin harkokinsa tare sukeyi kuma shine a matsayin mataimakin shi idan Allah ya basu mulki a hannunsu.........Sam bai wani damu ba da jin wai zai ai hira da yarinyar a tashar redio ta *Salama* yasan dai zancan gizo baya wuce na 'koki shirme ne zasuyi tayi har su gaji su daina, Khalifa kuwa yasha jinin jikinsa jiran lokaci kawai yake yi. *** Karfe takwas da rabi an soma gudanar da shirin *Siyasarmu* Jama'ar gari na makale da redionsu da wayoyinsu. Mai gabatarwa ya fara magana kamar haka.... "Jama'a yau filin namu na da babbar bakuwa Hajiya Wasila 'Yar gaske wanda tun kafin zuwan wannan lokacin muke ta sanar daku cewar zata shigo cikin shirin Siyasarmu domin ta warware mana zare da a bawa kan wata kullalan kulli dake faruwa a wannan jahar wanda jama'ar gari basu sanshi ba yau dai tace bari ta shigo wannan fili ta fasa 'kwan! kowa yaji ya san abunda ke faruwa 'yan takarkarin da suke gwabzawa guda biyu, masha Allah *'Yar gaske!* filin Siyasarmu ya shirya tsaf hakanan masu sauraro suma sun shirya suna sauraranki." _Muje Zuwa_ *BINTA UMAR ABBALE* [7/16, 10:37 PM] Bintu: *'YAR BANGAR SIYASA!!* 🌺 romantic love story🌺 *NA:* *BINTA UMAR ABBALE 🍒* *🌍Manazarta Writes asso* _'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_ ~~~~~~~~ *NA KUDI NE.......!* _Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176 sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko orange_ *YABON GWANI YA ZAMA DOLE* 🕺🕺🕺🕺🕺🕺🕺 *PEGE DIN YAU KACOKAN! NAKI NE UWAR ARZIKI MACE MAI FARAR ANIYA DA FARAR ZUCIYA KINYI MIN KINA KAN YI MOMYNA FATIMA MUSA NIJAR ALHERIN ALLAH YAZO INDA KIKE DAKE DA ZURIARKI BANTA'BA MU'AMULA DA MUTUM IRINKI BA BANI DA BAKIN GODIYA A GURINKI MOMY ADDUA CE A TSAKANINA DAKE UBANGIJI ALLAH YA DUBA 'KARSHEN KI YASA KI GAMA LAFIYA ALLAH ABUNDA KIKEYI MIN ALLAH YAYI MIKI MOMY BAZAN TA'BA MANTAWA DAKE BA DOMIN KINYI MIN ABUNDA BAZAN MANTA DASHI BA NAGODE NAGODE NAGODE ALLAH YA AMFANI ZURIA👏🏻* ~~~~~~~~~~~~~ *Free Pege13* Cikin zazza'kar muryata tayi sallama har da addua kamar wacce za tayi abun arziki...."Bisimillahi rahamanir rahim rabi sharali sadari wayasirli amri wa'alal u'kudatun millisani yaf'kahu 'kauli ameen ya Allah, to jama'a assalamu alaikum warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu kamar yanda mai gabatarwa ya fada musu suna hakane nice Wasila 'Yar gaske 'yar partyn mai girma Governor Lawan Rabo governor da ba za'a ta'bayin irinshi ba insha Allah to a yau dai na shigo wannan filin ne domin nayi tankade da rairaye kana kuma na fed'e muku biri har hutsiyarsa, to jama'a hausawa nacewa yabon gwani ya zama dole dan haka kafin in fara cewa komai zan yabi maigirma Governor na saboda ya cancanta a yabe shi duba da irin dumbin ayyukan da yake a wannan jahar tamu......*A dad'e anayi sai gaskiya Engineer Turmi kake sha sassaka! Gugan 'karfe sha kwarafniya! kayi mun gani jama'ar gari sun gani sun shaida! mun shaida! A daka a bari dole uwar na'ki! ayi ayi a hakura kai d'in dai kaine duk inda akaje aka dawo sai kai!!! Engineer ma'kiyan ka! sai da su mutu domin ka riga kayi musu nisa sai dai kallo daga nesa! mu dai kaine gwaninmu kai muka za'ba jama'ar gari kai suka za'ba kawai dai 'yan adawa nayi musu romon baka da kuma al'kawaririkan 'karya! tare basu tsohiyar hanci domin a siyi kuri'arsu mu mun yarda da kanmu ba sai munyi kamfen ba insha Allahu babu canji da yardar Allah sai mun maimaita 4+4 Ba sauyi insha Allahu." Ta kare maganar tana sauke nuffashi, Mai gabatarwa yace."Hajiya Wasila wannan yabon da kikeyi fa ni sai nake gani kamar kune kukeyi irinshi dan tuntuni jama'ar wannan jahar tamu suka dawo da rakiyar wannan gwamnati a cewarsu har yanxu basu gani a 'kas ba ance za'ayi mugudanar ruwa kana za'a saki wutar lantarki za'a biyawa yara kudin makaranta za'a gina sabbin makaranta da asibitoci da dai duk ayyukan da mai girma governor ya fada zaiyi kafin hawansa kujerar mulki shuru kakeji malam yaci shirwa wasu ayyukan idan an fara gadan gadan sai ajiye a shiga wata sabagar gashi yanzu har kunci shekaru uku akan wannan kujera babu wani sauyi da suka gani shiyasa suke ganin gwara su nemawa kansu mafita tun kafin dare yayi musu." Wata siririyar dariya ta saki tace"Haba d'an jarida kasa kunne kaji da kyau!! Wallahi wannan gwamnatin ayyukanta daban suke dana sauran gomnonin da suka gabata haba Alaji ka duba babbar gadar da mukayi wacce ta fara tun daga farkon titi gwaron dutse bata tsaya ba sai da takai unguwar na'ibawa, wannan katuwar kwatar ta jakara mun rufe ta ruf! idan ana ruwa mutane hankalinsu akwance duk wannan fargabar da suke a da sun daina sai ka fada min wace gwamnati ce tayi wannan aiki."? ''To ai ba anan take ba 'Yar gaske sufa jama'ar gari suna magane akan al'kawarrikan da kuka dauka baku cika ko daya ba ba wai gada da aikin katuwar kwata ne ya damesu ba burinsu kawai suga ruwa da wuta kana kuma 'yayansu su samu ingantaccan ilimi har yanzu fa akwai makarantun da suke zama kan buhu babu banci da sauran abubuwan amfani kuma kafin hawanku wannan kujera kunyi alkawarin kan zaku inganta ilimin yara kana kuma kuyi karin albashi ga ma'aikata." "Humm! ai kaji gareje irin na mutane jama'a basa tsayawa suyi aiki da lura wannan gwamnati fa kafin hawanmu akwai abubuwan da muka tarar akai akwai tarin bashishshika da gwamna na baya ya bari bai biya ba tilas! mu muka biya wanda har yanzu ba'a karasa ba haba jama'ar gari ku kwantar da hankalinku kamar tsumma a randa insha Allahu dukanin abunda mai girma gwamna ya ambata zaiyi to zaiyi ku dai kawai ku mara masa baya a za'be na gaba ya maimaita insha Allahu zakuyi mamakin aikin da zaiyi muku kano zata koma tamkar kasar waje saboda yanda za'a gyarata da titina da makarantu da asibitoci da sauransu." " 'Yar gaske na tabbata jama'ar gari na sauraranki da duk bayanai da kikeyi to amma inda gizo ke sakar anan shine! sufa a halin yanzu duk wata magana da zaku fito ku fad'a a yanzu ba zasu dauketa da muhimanci ba saboda zuciyarsu ta riga ta gama makancewa da kaunar wannan d'an tahalikin mutumin wato *Ahamadu Musu* wanda suke masa inkiya da *(Ba'iya ka!)* shine nima nake ganin gwara kawai ku hakura ku bar masa tunda a zahiri kamar yafi ku mutane a wannan tafiyar." Dariya ta saki harda tafa hannu "Oh! mutane kenan!? Ni wallahi ma abun mamaki yake bani idan naji suna kiran wannan mutumi da sunan dan takarar gwamna banta'ba jin inda *Gwauro* yayi mulki ba babban mutumin dan kimanin shekaru ar'abain da biyar yana zaune banu aure ai dole a bunkice shi.....To jama'a yau dai bari na fad'a muku abunda baku sani ba akan wannnan mutumi da kuka nace ya zama shugabanku.....Ahamdu dai tunda yake bai ta'ba aure ba duk wani mai shakku yaje yayi bunkice akai, yana zaune a gidanshi yaci karansa babu babbaka ya kawo duk macen da yake so yayi mu'amula da ita tamakar matarshi....Jama'a ni Wasilatu 'Yar gaske zancen dai da nake muku nima ya auna ni a gidanshi Allah ne ya tseratar dani nasan mutanan da suka je gidanshi kar'bar tallafin da yakeyi duk karshen wata sun gani lokacin da ya sanya aka daura min ankwa babu ji babu gani ya sanya aka shiga dani ciki gidanshi a kulle da kwado..... dan jaridar ya katseta da fadin" To Yar gaske ya akayi kikeje gidanshi bayan kowa yasan ke ba 'yar bangaranshi bace shin ko zaki fadawa masu sauraranki dalili."? Shiri fa ya dauki zafi!! Zama ta gyara tace"Eh tabbas jama'a zasu zargi haka to abunda ya kaine gidanshi shine sati biyu da suka wuce yazo har kofar gidanmu da niyyar yaudarar kanwata sai ni kuma Allah ya nuna min shi ya dauki makudan kudi ya bata nice nan na hanata ta'ba kudin washe gari na nufi gidanshi domin na bashi kayanshi sai na tarar yana rabawa jama'ar gari kudi......Kafin nayi aune! kawai na ganshi tare da wata mata a kaina tana nuna masa ni wai nice! 'kawata Camas! da muke tafiya tare ta shiga rudani a gaban mutane ba tare da yayi wani bunkice ba ya kira police yasa aka buga min ankwa aka tasa 'keya ta cikin gidanshi a kulle to wannan damar ya samu yaso ya biya bukatarshi a kaina sai Allah ya kare ni." Dan Jaridar maganar tasha masa kai sosai.....Ashe bashi kadai ba harda jama'ar gari dake sauran shirin kafin kice kwabo zantuka sun soma tashi a garin wanda tun kafin a rufe shirin gari ya hargitse da hayaniya kowa na fadin albarkacin bakinsa kan Ahamdu ashe dama bashi da aure Gaskiya magana ta fito kan zargin da mutane ke masa gurin bada kudin da yake a cikin gidansa yana lalata da 'yayan mutane, sai wad'anda akayi abun a gabansu suka fara gazgatawa har suna bada larabi zance fa yayi tsanani a gari anata kace!kace! masu tsinewa Ahamadu sunfi yawa kan wadanda suka karyata maganar. Wani irin gumi yake tsiyayarwa a jikinsa ita kanta rigar dake jikinsa sai da ta jike saboda tsananin tashin hankali ashe dama alkairi yana zama sharri! bai ta'ba nadamar zamanshi a haka ba sai yanzu shin wai yama akayi yarinyar nan tasan bashi da aure.....Shine taje ta kwancewa zani a kasuwa tilas masu karamin tunani su gazgata maganarta, Innalilihi wa'ina ilaihi raji'un! bai ta'ba tunanin al'amarin siyasa ya kai hakaba amma kuma wannan siyasar da sukeyi kamar ta sa'bawa dokar 'kasa 'kazafi! babu shi a siyance. *Humm! Ahamdu kenan har yanzu baka san meye Siyasa ba.!* Garba da Hadi suka fusata sosai Suka mike cikin zafin nama zasu fita Khalifa ya dakatar dasu da fad'in"Ina zakuje a wannan halin."? Garba Yace."Yallabai yarinyar nan yau sai tayi nadamar uwarta bata haifeta ba mu za tayiwa 'kazafi! banta'ba ganin butulu irinta ba, wallahi da ba don Yallabai yace tun farko a kyaleta da yanzu na zubar mata da hakora da tuni tana kwance tana jinyar kanta dan sai nayi mugun sa'ba mata kammani."! Khalifa yace."Ku dawo ku zauna ku samu nutsuwa." Suka koma suka zauna suna huci! yanda suka fusata niyyarsu subi Wasila gidan redion tana fitowa suci ubanta sai kuma aka katse musu hanzari.....Khalifa yaje ya zauna kusa dashi ya sanya hannu ya dafa kafad'arshi a hankali yace."Siyasa ce f........! katse shi yayi ta hanyar d'aga masa hannu Khalifa ya tsira masa ido ganin yanda duk ya wani burkice har yanzu yana digar da gumi kamar dakin babu Ac 'yan ya tsunsa biyu ya d'ora saman fatar le'bunansa ya tsurawa guri daya ido yana girgid'a kansa. _Muje Zuwa_ *BINTA UMAR ABBALE* [7/17, 10:05 AM] Bintu: *'YAR BANGAR SIYASA!!* 🌺 romantic love story🌺 *NA:* *BINTA UMAR ABBALE 🍒* *🌍Manazarta Writes asso* _'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_ ~~~~~~~~ *NA KUDI NE.......!* _Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176 sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko orange_ _*Allah dan tsarkin mulkin ka, Allah dan 'karfin ikon ka, Allah da buwayar ka, Allah dan jin'kan ka, ka azurta wannan baiwa ta ka Hauwwa'u da sanyi idaniya👏🏻 Ya Allah munyi tawassali da Annabi Muhammadu SAW kayi mana dominsa Allah ka azurta Hauwwa da 'yaya masu albarka👏🏻 Allah ka yaye mana hijaban da suke lullube ka biya mana dukkanin bukatanmu na alkairi👏🏻*_ ~~~~~~~~~~~~~~~ *Free Pege13* Khalifa ya dafa kadarshi a karo na biyu yace."Duk abun fa ba na tashin hankali bane naga kamar ka dauki al'amarin da zafi tuntuni na fada maka dama siyasa ta gaji haka dole ne kafin mutum ya kai gaci yayi ta fuskantar kalubale iri-iri amma a zahirin gaskiya abunda su kayi basu kyauta ba ai abun ya shigo da cin zarafi kuma ni banga laifin yarinyar ba domin sanya ta sukayi su biya ta shiyasa na hana su Garba daukar mataki a kanta, ka kyalesu kawai kar ka tofa wata magana shiru ma magana ce, surutu kam da kace nace na jama'ar gari ka dauke kanka a kai idan sun gaji zasu bari amma kuma munanan kan bakanmu babu gudu babu ja da baya.....Ya dago jajayen idanunsa yana kallonshi yace."Wane irin mataki zan dauka kan yarinyar."? Khalifa yace."Kawai ka kyal....." Wasa ma kenan!!." yayi saurin katse shi ya cigaba da cewa"Wancan karon ta zage ni! kace in kyaleta wannan karon tayi min 'kazafi na zina abunda na tsana a rayuwa ta kace na kyaleta No! kai kanka kasan 'karya ne wallahi ba'a haka dani da farko na tausaya mata a matsayinta na 'ya mace kankanuwa yasa na rabu da ita na kuma bata damarta a siyance tayi abunda take so amma abun ya wuce gona da iri da gaske takeyi yarinyar kana maganar sata sukayi ko basu sata ba za tayi tunda bata kaunata yana da kyau in nuna mata asalin waye ni."!! Khalifa ya sauke ajiyar zuciya yace."To yanzu kai me zakayi mata kake wannan maganar."? Kai tsaye yace."Auranta zanyi." Khalifa ya kalleshi da mamaki a fuskarsa....."Aure."!? yafada yana jimantawa....."Kwarai kuwa wannan ce hanyar da zanbi inci mutuncinta yanda raina ke so."Khalifa ya jinjina kai yana mamakin al'amarin yanzu duk tsayuwar ka da tsantseninka da bin diddiginka sai ka kare kan wannan yarinyar da bata da tarbiya." wani irin murmushi yayi kana ganinsa kasan na mugunta ne yace."Wai Khalifa ka mance waye Ahamdu ne? kai kana tunanin auran zanyi shine da manufa mai kyau! No! zan aureta ne kawai dan in nuna mata iyakarta." Khalifa yace."Sai nake ganin da ka sauya wata shawarar wannan ba tayi ba bana so ka auri yarinyar nan ka keta mata haddi sannan kuma ka saketa daga baya." Wani irin kallo yayi masa yace."Baka so na keta mata haddi ita ta keta nawa! kai kana tunanin wannan yarinya zaka sameta da wani Haddi a kanta tana daukar sunan budurwa ne kawai amma bata da maraba da bazawara so kar ka wani damu da wannan matakin da zan dauka zan aureta ne dan in cimma munufata a kanta harkar siyasa kuma babu gudu babu ja da baya da kaina zan dauketa in kaita tashar da taje ta gabatar da sharrin nata ta warware musu ku'lalliyar data 'kulla." Khalifa yace."To ai shikkenan shawarar tayi ma'ana dan gaskiya nima yarinyar tayi mugun bani haushi na lura ta dauki lamarin da zafi kuma akwai kuruciya a tare da ita." Girgiza kai yayi yace."Koma meye a tare da ita ni zanyi maganinta sai 'kura ta lafa tukkuna zan sanya su Hadi suyi min bunkice a kanta dan na lura zaman kansu suke da mahaifiyarsu....duk inda iyayenta maza suke zan sanya a buncika min su." Kira ya shigo wayarshi dake gefe guda a ajiye ya mika hannu ya dauka a nutse..."Hajiya Babba ce matar mahaifinsa ta farko Cikin girmamawa ya gaisheta ta amsa babu walwala sosai yanda yaji muryarta a cunkushe yasan ta samu labarin abunda ke faruwa yace."Hajiya kunanan lafiya ko."? Ta amsa lafiya lau idan ka samu dama kazo gobe idan Allah ya kaimu zamuyi magana da kai." Yace."Shikkenan Hajiya Allah ya kaimu lafiya." Ta amsa da "ameen." Sallama sukayi ya kashe wayar yana kallon Khalifa yace."Zancan dai daya ne hajiya ta samu labari ko da yake ma'abociyar sauraran redio ce taji da kunnanta na riga nasan maganar da za tayi min kenan maganar aure wanda saboda maganar yasa na dauke kafata da zuwa gidanta duk zuwan da zanyi sai ta kawo min tallan mace wanda hakan ba ra'ayi na bane ni nafi so inga mace da kaina na aura ba sai an kawo min ba, magana dai duk ta 'kare gobe insha Allahu zan sanar mata da cewar na tsayar da matar da zan aura kalas."! Khalifa yace."Shikkenan kuma maganar Zainab ta tashi kenan dama kuma mune muke ta naci kana wulakanta mu." Yace."Khalifa ina jin kunyar Hafsa ne wallahi shiyasa ma zaka ga sau tari bana son zuwa gidanka saboda bana so ta dinga kallona da wata manufa tayi min alkairi na 'ki kar'ba, Zeey bata da makusa ta ko wanne bangare tayi kawai bana so in auri abunda baiyi min ba gudun shiga hakki ka basu hakuri da ita da kanwarta." Khalifa ya mike yana fadin"Ni zan wuce gida sai yadda ta yiwu mu bari gari yayi lafiya tukkuna sai muyi magana kan kazafin da akai mana." Ya mike yana fadin"Eh wannan ce shawara mai kyau.!!!! To a ranar da al'amarin ya faru Wasila bata kwana a gidansu ba, domin mai girma gwamna najin irin 'baram'baramar da tayi sai kawai ya sanya security suzo su dauketa saboda yasan idan ta fito za'a iya ragargaza mata kai!! aikuwa hakan ce ta kasance da mabiya Ahamadu dan sun shirya tsaf sunyi dafifi a farkob titi suna jiran fitowar 'yar gaske da 'yan rakiyarta irinsu Camas! suyi musu tsirara su dake su...... da kyar Jami'an tsaro suka sha dasu Wasila ita kanta ta furgita da al'amarin.....Sai salati takeyi ganin yanda take hango jama'a da shar'ba! shar'ban makamai da bulalai! a hannunsu suna hayaniya da kiran sunanta wai duk ita suke nema wai!! tasan da sun ritsata kuma sai buzunta. A daran mai girma governor yayi mata wanka ta 'yantu a siyance ta tashi daga 'yar banga ta koma cikkakiyar 'yar siyasa mai lasisi mai al'bashi kamar ma'aikaciya ya sanya mata miliyan hamsin a account dinta kana ya damka mata mukullin mota yar yayi ya bata dankareren gidansa dake tishama, gida na gani na fad'a cikin GRA babu abunda babu a ciki na more rayuwa........Mai girma governor yace ba zata koma gida ba tukkuna sai nan da sati biyu kura ta lafa tukkuna sai ta koma sabon gidanta tunda jama'ar gari basu sani ba hakan zaifi kwanciyar hankali itama sai taji wannan shawarar tayi mata saboda tana jin tsoro ta koma gida azo a kasheta da daddare sai ta kira Rashida a waya ta sanar mata da halin da ake ciki tace ta fadawa mahaifiyarsu ta kwanta da hankalinta duk wani alkairi da jin dadi na duniya sun samu." Da jin wannan magana da wasila tayi sai duk suka kwantar da hankalinsu ya tsumma a randa suka cigaba da rayuwarsu a hankali kwance.....Wasila da Camas! suka cigaba da zama a government house alhazawa nayi musu facaka da kudi Camas! sai tsikarar duniyarta takeyi da tsine babu abinda ya dameta Ita kuma Wasila sai kaf-kaf take da budurcinta duk 'kwakwar mai 'kwakwa dole ya hakura. *** "Wai Bitan! Malam mai allo yasan abunda ke faruwa kuwa da zuriar d'an uwanshi Habibu wannan rayuwar dasu Uwani sukeyi ba rayuwa bace yarinya 'kankanuwa ta zama karuwar karfi da yaji gari ya dauka da maganar Wasila har wani kirari ake mata da *'Yar gaske!* yarinya karama ta fantsama kanta har siyasa yau ta zagi wancan gobe ta shiga redio ta zagi wancan tayi shigar banza ta fita a gari tana zubda mutunci ni ganauce ba jiyau ba sati uku da suka wuce na ganta tare da wani hamshakin mai kudi a mota yarinyar nan yi tayi kamar ma bata sanni ba ta dauke kanta." Matar da aka kira da suna Bitan! ta gama gyara itacen dake cikin murhu ta karaso kan tabarmar da kanwarta ke zaune tace."Wallahi Kattime bamu san abunda ke faruwa ba kinga mu nan muna cikin karkara gashi sai muyi sati bamu kunna redio ba ballanta muji abunda ke faruwa a gari kune mutanan cikin gari kunfi mu sanin abunda ke faruwa amma bari malam din ya shigo sai ki fad'a masa abunda ke faruwa inyaso tin kafin abu yayi nisa yayiwa tufkar hanci." Haraja tace."Aikuwa ba zan tafi ba har sai naga shigowar malam gidanan na fad'a masa abunda yake faruwa dan wallahi ina jin tsoron yarinyar nan ta haifo d'a mara ido." Bitan! tace"Ai yamma tayi yanzu yanzu zakiga ya shigo kin san yamma nayi yake tashin al'majiransa su tafi bara sai kuma takwas na dare su sake zama." To kafin ma ta rufe bakinta sai gashi yayi sallama ya shigo cikin gidan.....Yana sanye da farin yadi babbar riga da 'yar ciki kanshi nan nad'e da koran rawani hannunsa rike da carbi fari tas! Bitan! tayi saurin mikewa tsaye tana masa barka da zuwa da sauri ta dauko masa buta wacce ke cike da ruwa ta mika masa asuwaki ya fita waje domin daura alwala lokacin sallahr magariba ya gabato dalili shine limamin babban massalacin dake 'karamar hukamar Garko. _Muje Zuwa_ *BINTA UMAR ABBALE* [7/17, 9:28 PM] Bintu: *'YAR BANGAR SIYASA!!* 🌺 romantic love story🌺 *NA:* *BINTA UMAR ABBALE 🍒* *🌍Manazarta Writes asso* _'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_ ~~~~~~~~ *NA KUDI NE.......!* _Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176 sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko orange_ *PEGE DIN NAKU NE* 👨‍👨‍👧 *MYSON, NAJIB SA'ID* Tare da kai da *LAWAN RANO* Nagode kwarai da kulawar ku akan wannan book din Allah ya 'kara kauna ya baku mata na gari👏🏻 ~~~~~~~~~~~~~~~~ *Free Pege14* To ganin Malam mai allo ya nufi masallaci yasa suma suka daura alwala domin gabatar da tasu sallahar kafin ya shigo gidan su tattauna abunda yake faruwa, suna zaune kan tabarma ya shigo bakinsa da sallama kamilin mutum ne wanda karatun al'kur'ani ya ratsa shi fari tas dashi kana ganinshi kaga bafulatani usul......Bitan! ta gyara masa tabarma ya zauna yana fad'in"Ashe bakuwa mukayi a gidan Hajara kece kike tafe."? Ta amsa da "Eh wallahi malam tun kusan azuhur nake gidanan Bitan tace min kana tsangaya tare da yan makaranta malam ya gida ya damuna dafatan duk mun same ku lafiya."? Ya aje carbin hannunsa a gefe ya amsa da fadin" Lafiya lau Haraja ya yara ya mai gidan naki."? Duk sunan lafiya kalau wallahi ai yace ma a gaishe ku da kyau."! To masha Allah muna amsawa amma dai za kiyi mana kwana biyu kafin ki koma." Murmushi tayi "A'a malam gobe nake sanya ran komawa dama muhimaniyar maganace ta taso wanda shi mai gidan nawa ne ma yace lallai nazo na shaida maka abunda ke da akwai." To Allah yasa alkairi Hajara ina sauranki." Malam mai allo ya gyara zamanshi yana fuskantar Hajara wacce ta soma warware masa abunda ke faruwa ga iyalin Dan uwanshi Yahuza mai rasuwa.........Ta kara da cewa"Malam yana da kyau ku sanya ido sosai kan wannan yarinyar domin a gaskiyar magana abun da takeyi ya soma wuce gona da iri watarana zata dauko muku abin kunya ko kuma taje ta zagi wani babban mutumin da zai daureku gabadaya yau da al'amarin ma a kanta zai tsaya da sauki wani abun idan ta dauko to ku da bakuji ba baku gani ba sai ta shafeku wannan shine dalilin da ya sanya nace to bari nazo na fada muku halin da ake ciki." Malam mai allo yayi shiru yana jimanta al'amarin, to har yausha hakan ta faru basu sani basu sani ba ko da yake hakan zata iya kasancewa tunda bayan rasuwar Yahuza rigima suka dinga tafkawa da Uwani mahaifiyar yaran kan dole sai an raba gado an bata na yaranta shi kuma yace ko za'a raba gado to ba za'a bata na yara saboda ita mace ce su kuma yaran lokacin suna yara kananu za dai a siyar da gona a raba kudi kaso biyu shi ya dauki kashi daya sauran kuma ya zama magada wato Wasila da Rashida kenan in yaso ita sai a fitar da ita na tuminin takaba kamar yanda addini ya shara'anta.....Nan ma sai ta tada ballin masifa taje 'yan uwanta suka zugota tazo tana yiwa su malam rashin kunya wanda hakan ya janyo sukayi mata fatata fatata! sannan suka kwace su Wasila daga hannunta, kwana biyu da faruwan lamarin Wasila dake tana da wayo a lokacin ta kai kimanin shekaru goma sha biyu sai ta fakaici malam din ya tafi tsangaya ra rike hannun kanwarta suka gudu da malam ya dawo ya samu labari yace."Suje idan shine sai sun tako da kafafunsa sun neme shi, to hakance ta kasance koda su Wasila suka koma gaban mahaifiyarsu sai wahala tayi tsanani a garesu da kyar suke ci daya a rana Wasila itace yawon bin gidajen amare tana musu wanke wanke da raino da share share su bata kudi da abinci ita kuma Uwani itace aikin wankau da dakau da sauransu.....Wasila ta yanke shawarar tun karar wan mahaifin nasu domin su bashi hakuri suka shirya tsaf suka nufi Garin nasu Garko!! Malam ya dinga musu fad'a sosai yace."Duk tsiya dai nine mahaifinku tunda babu ubanku kuna bin shawarar mahaifiyarku kuna bijere ma dangin ubanku to ko auranku ake nema gurinmu zaku zo gwara ku nutsu kuyi hankali ku zauna tare damu zaman ku cikin wannan gida ku kadai bai dace ba saboda haka na yanke shawarar zan baku daki daga ku zauna har Allah yasa ku samu mijin aure ita kuma Uwani ta tafi gidansu itama bata wuce aure ba idan ta samu miji tayi aure....Da jin wannan magana ta malam mai allo sai su Wasila suka yanke sgawarar guduwa domin a ganinsu yanda suka saba da zaman birni zasu cutu a kauye....Washe gari Uwani ta tasa kan 'Yayanta da asuba suka gudu....Wannan abu da sukayi ya batawa malam mai allo rai tun daga lokacin ya dauke hannunsa daga kansu idan ma sauran 'yan uwa suka kawo masa maganarsu sai ya koresu yace kar wanda ya sake kawo masa maganar wadannan yaran marasa kunya suje duniya ce zata koya musu hankali. *Wannan kenan* Malam mai allo ya kalli Hajara yana girgiza kansa yace."Hakika naji dadi da kukayi gaggawa zuwa ku sanar dani wannan al'amari dake faruwa, wannan rashin tarbiyar ne yasa tuntuni na hana Yahuza tafiya maraya da zama saboda nasan tilas a haifi da mara ido a lokacin ya rufe ido yaki sauraran kowa shi dai kawai ya tafi burni ya nemi kudi karin abun kuma ya hadu da mata mara kamun kai ya aure ai asalin lalacewar yaran daga mahaifiyarsu ne da ta basu tarbiya da duk haka bata faruwa ba mu kanmu Uwani bata ganin girmanmu ballanta tana nuna musu muhimancimu a gurinmu, amma babu komai insha Allahu gobe tare zamu tafi kome za'ayi kafata kafar yaran nan dan bazan bari su lalace ba ace muna kallo nan zan kawo su duk in aurar dasu kowa ya huta." Hajara tace"Wannan shawara taka itace abun dubawa Allah ya tabbatar mana da alkairi." suka amsa da "ameen" gaba d'ayansu. To kamar dai yanda malam mai allo ya fad'a hakane ya kasance da wurwuri yayi sallama da 'yan uwa ya fad'a musu abunda ke faruwa suma suka bada goyon bayan kan hukumcin da ya yanke, kana suka hadawa Haraja sha tara ta arziki suka bita da godiya da fatan sauka gida lafiya. Uwani da Rashida kadai ne a gidan sunci kwalliya har sun gaji kamar wanda zasuje gidan buki ga cefane nan kayan miya da nama cikin takarda za'ayi miya gida sai kamshi yake yi....Amina na kwance a tabarma tana danna katuwar waya Uwani na kicin tana aiki Malam mai allo yayi sallama a kofar gidan.....Gaba d'ayansu sai da gabansu ya fadi! Uwani ta fito daga kicin da ludayi a hannunta tana fad'in"Ke Rashida muryar wa nakeji kamar ta wannan masifaffan tsohon."! Rashida tace"Wallahi nima irib muryarshi naj......Kafin ta karasa muryarsa ta sake karad'e gidan "Salamu alaikum."!! Uwani ta amsa da karfi tana fad'in" Waye wai yake rangwada mana sallama kamar munci bashi." Malam mai allo ya girgiza kansa jin muryar Uwani radau! yasan zata aika tunda dama ba kunya gareta ba......"Nine malam mai allo na Garko."! Yafada yana dafe kyauran kofar gidan. "Ayyo koda naji wannan sallama haka to ana zuwa." Uwani tafada tana jan karamin tsaki." Ta kalli Hajara "Ai sai ki tashi kije kece tilas dinsa ni kuwa yace zai min wannan wa'azin sai dai mu kwashi 'yan kallo ni dashi a unguwar nan." Jiki a sanyaye Rashida ta mike ta dauki yalolon mayafinta dake kan igiya ta yafa, duk rashin kunyarsu suna shakkar malam mai allo dan baya musu da sauki.........Tana fitowa ta durkusa tana gaisheshi bai amsa ba sai kare mata kallo yake ganin irin dinki dake jikinta atamfa ce duk an kacalcalata saman nonowanta duk a waje......Girgiza kansa yayi yace"Rashida kece kika dawo kamar ba d'iyan musulmai ba wannan shigar ta jikinki ta sabawa sharia meye abun burgewa anan.? to babu komai duk magana ta kare kiyi maza ki kirawo min daya marakunyar yanzu yanzu zan tasa ku a gaba mu wuce garko saboda na samu labarin ashararanci da kukeyi a gari mahaifiyarku na daure muku gindi kuna yiwa manya mutane rashin kunya wai Wasila ce take siyasa tana gogayya da maza saboda kasa ta rufe idon ubanku shiyasa annabi yace ka zabawa 'yayanka mace tagari duk dan gudun faruwar irin wannan, mu ba'a son ranmu dan uwanmu ya auri mahaifiyarku ba saboda sam bata da tarbiya gashi kuma kun dauko irin nata halin to kome zakuyi sai da kuyi amma tilas ku koma can Garko da zama idan Allah ya kawo muku miji kuyi aur......"Babu wanda ya isa ya rabani da 'yayana wallahi akan wannan sai in maka mutum a kotu."!!!!Uwani ce ke fadar wannan maganar ashe tana la'be tana jinsu......"Haka kawai zaka zo har gida kana zagina malam ka rike mutuncinka da girman ka ada can ma ban yarda ba ballanta yanzu da nasan ina da 'kumbar susa a hannuna dan haka ni banga wanda ya isa ya rabani da 'yayana ba." Malam mai allo yace."Uwani rashin kunya za kiyi min."? Wannan ba rashin kunya bace gaskiya ce, sai da yarana suka girma suka zama mutane inacin ganiyarsu sannan za'a lalla'bo kawai saboda an samu labarin mun faso gari ace ga zance ga magana kafad'i idan kana bukatae wani abu yanzu yanzu sai na kira Wasila tayi maka hasafi ba wai kace zaka tafar min da 'yaya kauye ba." Malam mai allo 'kwalla ta taru a kwarmin idonsa yace."Baku da kudin da zaku bani Uwani kuma kinyi min abunda yafi haka dan kin zageni a yanzu ba wani abun bane ni dai na gama yanke hukunci ke Rashida idan na isa daku maza jeki had'o kayanku muka kama hanya mu tafi.". Rashida ta mike ta shiga cikin gidan tana kuka wayarta ta dauka ta kira Wasila ta fada mata abunda ke faruwa.....Wasila tace''Kome zaiyi kar ku sake ku bishi ku kyaleshi a soro idan ya gaji da tsayuwa ya gaji ya tafi masifaffan tsoho kawai." Uwani kuwa taja tunga ta tare bakin kofa ta rantse babu inda zai tafar mata da 'yaya......Suka dinga tafka rigima da Malam mai allo Uwani ta dinga yi masa rashin kunya kamar ba wan mijinta ba har hankulan mutane ya fara dawowa kansu mutane suka fara taruwa a'lamarin yayi wa malam ciwo a ranshi sai ya fito waje ya tsaya yana tsumayin fitowar Rashida ganin ya fita daga gidan sau kawai Uwani ta rufe kofar gidan ta zura sakata ta koma ciki tana surutai "Idan ka kaji da tsayuwa ka tafi tsoho mai nacin tsiya kawai..........Garba dake can gefe suna magana da wani mutumi ya nuna masa malam mai allo dake bin kofar gidan da kallo yana mamakin rashin kirkin Uwani wato shi suka rufewa kofa, sai ya sanya gefan babbar rigarsa yana goge gumin saman goshinsa.....Garba ya karaso inda yake hannu ya mika masa suka gaisa yace." Aramma idan ba zaka damu ba ina so mu tattauna wata magana da kai." Malam mai allo dake neman wanda zai rarrashe shi kan abunda su Uwani sukayi masa yace."Babu komai yaro ina sauraranka." Garba yace."Muje mota arrama." Malam mai allo baiyi shakkun bin Garba ba saboda lokaci guda yaji ya aminta dashi suka nufi inda yayi parking din motar a tare. _Muje Zuwa_ *BINTA UMAR ABBALE* [7/18, 2:01 PM] Bintu: *'YAR BANGAR SIYASA!!* 🌺 romantic love story🌺 *NA:* *BINTA UMAR ABBALE 🍒* *🌍Manazarta Writes asso* _'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_ ~~~~~~~~ *NA KUDI NE.......!* _Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176 sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko orange_ *PEGE 'DIN YAU NAKI NE* *Real Eshaa🌺* Marubuciyar book d'in. *NAGA RAYUWA* Fatan alkairi har karshen rayuwa aysha Allah ya kawo miji nagari wanda zai rike min ke tsakani da Allah👏🏻 ~~~~~~~ *Free Pege15* Cikin nutsuwa Garba yace."Aramma alamu sun nuna kamar kana da ala'ka da masu wancan gidan, dan Allah idan babu damuwa ina so in san wani abu dangane da wata yarinya a gidan mai suna Wasila." Malam mai allo yace."Ni a matsayin mahaifi nake a gurin Wasila da kanwarta Rashida Yahuza mahaifin yaran kanina ne ciki daya muka fito kuma mu 'yan asalin garin garko ne Yahuza yazo kano neman kudi tun yana saurayi sai ya sai gida yayi aure tare da wannan matar wacce ta kasance a matsayin mahaifiyar su Wasila da Rashida......Garba ya katse shi ta hanyar fadin"Alhamdullhi dama abunda nake so naji kenan ashe faduwa tazo dai-dai da zama malam idan babu damuwa zamuje can gidan ubangidana wanda shine ya sanya ni nayi masa bunkice akan asalin iyayen yarinyar to kuma sai nayi katarin had'uwa da kai, kar kadamu arrama idan mun isa sai kayi masa cikakken bayani akan yarinyar." Malam yace."Yaro ina fata dai ba laifi yarinyar tayi ba domin nima abunda ya taso ni kenan saboda na samu labarin cewar tana cin mutuncin manyan mutane a gari tana fakaicewa da siyasa wannan shine dalilin zuwa na garin." Garba yace."Kar ka damu arrama alheri ne insha Allahu muje koma meye zakaji daga bakin mai gidana." Malam yayi shiru yana nazari yana tsoro kar daga zuwan sa ya shiga masifar yarinyar nan tasa a daure shi baiji ba bai gani ba....Girgiza kai yayi yace."Babu damuwa samari muje kawai Allah yasa alheri ne." Garba ya kunna motar yaja suka futa daga cikin unguwar. Suna tare da Khalifa a harbar gidanshi suna hutawa motar su Garba ta shigo cikin gidan.....Can parking spece ya nufa yayi parking din motar ya fito ya budewa malam mota yana fitowa Idanun Ahamdu suka sauka a kanshi A fuzge yaga suna kama da yarinyar babu tamtama wani nata ne amma babu shakka Garba ya iya aiki bai dauka futa ta farko za'a samu nasara ba to amma yanda yaga kamilin mutum sai yasha jinin jikinsa anya wannan kudi zasu rud'ashi ko dai ya sauya wata hanyar ne dan baiga alamar zalama ta kudi a idon dattijon ba......A nutse ya mike yana masa barka da zuwa dake suna zaune a wata rumfa wacce aka kewaye ta da wasu kujeru masu kyau tsakiyar kujerun katon teble ne da lemuka akai kana ganin gurin kasan na hutawa ne....Malam mai allo ya zauna nutse suka gaisa cikin girmama juna......Garba yace."Yallabai Allah ya takaita mana wahala ina zuwa unguwar nayi katari da wannan bawan Allahn shine yake shaida min shi din shine mahaifin Wasila shima zuwanshi kenan garin to anan na nemi alfarma a gurinshi kan yazo kana son magana dashi." Cikin girmamawa Ahamadu yace."Alhamdullahi naji dadi da hakan ta faru dama ni nafi so nayi magana baki da baki da mahaifin yarinyar dan haka Garba kana iya tafiya babu damuwa." Garba ya bar gurin yana godiya....Ahamadu ya sake mikewa Malam hannu suka sake gaisawa Yace."Malam kan maganar wannan yarinya ne Wasila.'' Malam mai allo ya kalli Ahamadu ganin nutsuwa da kuma a kamala a tattare dashi ya sanya hankalinsa ya kwanta yace."Alhaji ina fatan dai yarinyar nan ba wani laifi tayi muku ba dan wallahi dukkanin abunda takeyi bamu sani ba tunda bama tare dasu labarin abunda takeyi ne ya iskemu hakan ya sanya hankalinmu tashi, muka yanke shawarar zuwa domun mu tattara su mu koma can inda muke da zama dama kuma zamansu hakan bai dace ba a matsayinsu na 'yaya mata komeye zai iya faruwa da rayuwarsu. Khalifa yace."Kwarai kuwa malam muma abunda muka hango kenan ya sanya muka sa ayi mana bunkice akan asalin yarinyar sai kuma Allah ya takaita mana lokaci guda kazo gari ashe ma ba a kurkusa kuke ba." Malam yace." Mu 'yan karamar hukumar Garko ne Yahuza mahaifin yaran ciki daya muke dashi mu hudu iyayenmu suka haifa ni ne babba sai Habibu sai shi Yahuza sannan kanwarmu Kattime To shi kadai ne ya tsalle a cikin mu ya tawo nan yake sana'oinsa har Allah yasa ya samu sana'a ya siyi gida kana yayi aure ya hayayyafa yanzu shekaranshi Takwas da rasuwa bayan karamar jinyar da yayi wanda muma sai labarin mutuwarsa mukaji......Dalili kenan da ya sanya nazo da kaina na dauke yaran har da ita mahaifiyar tasu na tafi dasu can garin namu ko sati daya ba suyi ba suka gudo........Tiryan tiryan Malam ya zayyane musu rayuwar dasu Wasila suka dinga yi tun farkon mutuwar mahaifinsu da irin rashin kunyar da mahaifiyarsu ke sawa suyi musu da yanda shi kuma yayi zuciya ya zare hannunsa daga kansu....Sai wannan karon da yaga abun yayi tsamari ya sanya yace bari ya dauki mataki na karshe kan abunda sukeyi. Ahamadu yace."Arrama yanzu idan ka tafi dasu can Garkon kana da wanda zaka bawa auransu ne."? Malam yace."Ba za'a rasa ba Alhaji kasan shi auran karkara ba'a tsawwala da yawa insha Allahu sati biyu ba zasuyi a gida ba zab daura musu aure." Yace."To idan babu damuwa ni ina son abani auran babbar kuma bana so a ja dogon lokaci idan da hali wannan juma'ar mai kamawa nake so a daure aure." Malam yace."Alhaji da dai 'karamar ka dauka dan sai naga kamar tafi babbar hankali hankalin ka zaifi kwanciya da ita karamar." Yace."Kar ka damu malam shi aure ni'ima gareshi watakila ta sanadiyar auran namu sai kaga tayi hankali fiye da tunani mai tunani idan da hali a amince mun in bada sadaki na yanzu." Malam yace."To to ai babu damuwa nima zanfi jin dadin hakan kaga sai in koma gida da karfin gwiwa ta kuma in sanar da 'yan uwa abunda ke faruwa." Ahamadu yace."Kwarai naji dadin yanda ka yarda dani ka amince min auran yarinyar da wuri ba tare da kaga waliyai na ba insha Allahu ranar juma'a zamu zo tare da kanin mahaifina Wanda shi kadai ne ya rage min a halin yanzu kasancewar nima tun ban kai matsayin wannan shekarun ba mahaifina ya rasu na rayu tare da yan uwansa wannan kuma da kake gani a zaune kusa dani abokina ne sha'kikina tare mukayi karatu kuma muke harkokinmu a tare insha Allahu tare zamu zo dashi ranar juma'a." Malam yace."To masha Allah Alhaji ai ni ganin farko da nayi maka naji hankalina ya kwanta da kai wallahi babu d'ar! zan baka auran Wasila koda banga Waliyinka ba nasan zaka rike mun ita da kyau da amana, babu abunda zance sai dai ince Allah ya saka da alkairi saboda ka gama min komai tunda har ka yarda zaka auri wannan yarinya." Ahamdu yace."Babu damuwa malam, ai an riga an zama daya kuma Allah dai ya kara girma." Mikew yayi ya nufi cikin gidan..........mintuna goma yayi a ciki ya fito hannunsa rike da wata doguwar takarda dake cike da kudi." Ya mikawa malam na fad'in"Wannan shine sadakin Wasila malam." Malam ya kalli uban kudin da ya mika masa sai ya girgiza kai a nutse yace."Ashe baka so auran yayi albarka ba Alhaji Annabi Muhammdu SAW yace."Mafi albarkar aure shine karamin sadaki wannan da yayi yawa duk da ban lissafa na gani ba amma idona ya gane min kudi ne masu yawa, saboda haka dubu biyar kacal zaka biya sadakin wannan yarinya." Ahamadu yace."Malam ka ka'rba don Allah ai ba wani kudi masu yawa ba dubu dari ne kacal kuma kasan dai yanda kudin mu suke basu sa wani daraja kar damu insha Allahu aure zaiyi albarka." Malam yace."Shi dai ba zai kar'bi wannan zunzurutun kudin ba a matsayin sadakin Wasila ya fiso idan yayi mata aure ta zauna mutuwa ce zata raba.....Ahamadu da Malam suka dinga ta'kardama da jayayya shi ya dage sai ya 'karba shi kuma yace ba zai kar'bi dubu dari ba dubu biyar zai 'karba....Khalifa ne ya raba gardama ya ciro kudi daga jikinsa dubu goma ne ya irga dubu biyar ya mikawa Malam yace."Ga sadakin Wasila daga Ahamadu." Malam ya sanya hannu biyu ya kar'ba yana fadin"Ubangiji Allah ya tabbatar da alkairi Allah ya basu zuria mai albarka." Khalifa ya amsa da "ameen rabbi malam muna godiya da karamci." Ahamdu yaji haushin abunda khalifa yayi masa amma bai nuna ba sai ya aje takardar kudin kan teble din gabansa dauki wayarshi ya kira Garba......Garba na zuwa yace maza ya fito da mota ta zuba kayan abinci komai da koma yazo ya dauki malam ya kaishi har Garko Garba ya wuce da sauri domin aiwatar da aikin da aka sa shi. Ahamadu yace."Malam yanzu Garba zai kai gida maganar su Wasila kuma da kaina zan sanya a kai maka su har inda kake daga gobe jibi insha Allahu." Yace."To Alhaji Allah ya saka da alkairi ya biya dukanin bukatu na alkairi." Bayan tafiyar Malam mai allo Khalifa ya kalli Ahmadu yace."Na lura wannan dattijon na arziki ne wallahi sai duk naji jikina yayi sanyi musamman yanda naga ya tsaya kai da fata akan ba zai kar'bi wannan kudin da ka bashi a matsayin kudin sadaki na fahimci yana so auranku da yarinyar yayi albarka wanda kai ba haka abun yake ba a zuciyarka, dan Allah ka kar ka watsa wa mutumin 'kasa a ido ka rike yarinyar nan amana ko dan saboda karamcinsa kamar yanda ka fad'a masa watakila ta sanadiyar auran sai kaga tayi hankali duk abubuwan da suka faru a baya su wuce kamar ba'ayi ba." Shiru yayi yana nazarin maganar khalifa din yace."Nima jikina yayi sanyi lokacin da naga mutumin sam! ban dauka zanga kamilin mutum daga bangaran yarinyar ba ashe ta fito daga tsatso mai kyau gaskiya wannan mutumin ba duniya ce a gabanshi ba ka duba ka gani kudi a wannan zamanin sam basu gabansa wasu iyayen da suke so in kaje neman auran 'yayansu ka sakar musu kudi a gurinsu hakan burgewa ce, shi kuma na lura albarka kawai yake nema." Khalifa yace."Shine ai shawarar da nake baka rike masa yarinyar shine zai sanya ya tabbatar da cewa kai d'in mutumin kirki ne."" Murmushi yayi yace.''Kai nifa ina nan kan bakana wallahi! sai naci uban yarinyar nan wallahi in keta ta kuma in saketa." Khalifa yace."Subahanallahi! wai me yasa kake hakane? ka sani kake takewa yanzu meye amfanin hakan da za kayi."? Sosa kanshi yayi yace."Ai kai dama ba za kaga amfani ba saboda ba kai akayi wa auran nan da zanyi zanyi shine da manufofi da dama kaga na farko zan tashi daga sunan Gwauro kamar yanda ta fad'a zata zame min garkuwata a siyance na biyu zan dawwamar da rayuwarta a cikin 'kunci da ba'kin ciki in takure ta guri guda in muzguna mata har sai ta durkusa gwiwa bibbiyu tana bani hakuri na uku kuma na taimake ta daga wannan yawace yawacen banzan da takeyi a gari tana zubda mutuncinta na killace ta a guri guda....Na hudu kuma auranta zai wanke ni daga zargin da tasa jama'ar gari suke min....Ita ta nufe ni da sharri ni na saka mata da alkairi kaga anan jama'ar suka ji labarin na aureta za tasha tofin ala tsine da zagi sannan ita da harkar Siyasa har abadah! na biyar bukatata ta biya na raba abokanan adawata da ita tunda yanxu kamar itace a matsayin yarinyar su wacce suke sanyawa nayi musu abu ba tare da shakkar kowa ba, nasan kafin su samu 'yar siyasa mai mutukar a'kida irinta za'a sha wuya, kasancewar siyasarmu ta yanzu ta zama sai a hankali duk inda mutum yasan zai samu nan zaije hakanan za kagansu yau su zagi wancan gobe su zagi wanannan sam basu da gwani mutum in dai zaka bashi na 'batarwa shikkenan magana ta kare, amma ita yarinyar ns fahimci ba wannan ke gabanta ta tsaya bangaransu su kadai shiyasa suka riketa hannu bibbiyu saboda sun lura abokiyar tafiya ce....Kuma kasan ba zasu ta'ba bari tayi aure ba zasuyi ta bata kudi tana shirme a gari rayuwarta ta lalace a banxa a wofi.''''' Khalifa yace."Kayi tunani me kyau gaskiya amma dai duk da haka don Allah ka sassauta mata idan ta shigo. Murmishi ya saki mai dauke da manufofi da dama ta'be bakinsa yayi yace."Kana 'bata bakin ka ne khalifa yanda yarinyar nan tasa ni 'bacin rai itama ranta sai ya 'baci." _Muje Zuwa_ *BINTA UMAR ABBALE* [7/18, 10:18 PM] Bintu: *'YAR BANGAR SIYASA!!* 🌺 romantic love story🌺 *NA:* *BINTA UMAR ABBALE 🍒* *🌍Manazarta Writes asso* _'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_ ~~~~~~~~ *NA KUDI NE.......!* _Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176 sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko orange_ *Free Pege16* Uwani ta fito daga kicin tana fad'in"Da alama dai mutumin nan ya gaji da tsayuwa ya tafi haba! jama'a wai babu dama aga Allah ya rufawa mutun asiri sai a dinga bakin ciki! kiga mutum da rigima haka kawai ka ni'ko gari gari ya gari kazo kace zaka dauke min 'yaya saboda munafurci nasan magulamata ne suka kai masa gulma shine shi kuma ya bazamo babbar riga yazo har gidana ya nuna min iko to ni babu wanda ya isa yace zaiyi min iko da 'yayana 'yan uwana ma ban d'agawa 'kafa ballanta wani saboda haka ke Rashida maza maza ki kira Wasila a waya kice tazo yau d'in nan ta dauke mu a mota mu bar nan tunda har wannan tsohon ya soma zuwa shikkenan kuma zai ta daga mana hankali gwara kawai a nemu mu a rasa a unguwar." Rashida tace"Ni wallahi tausayinsa nakeji gaskiya Uwani banji dadin abunda kikayi masa ba Kamar uba yake a gurinmu kin tozarta shi a unguwa." '' Ayyo kina so ki nuna min kinfi kaunarsa a kaina ni dana tsuguna na haifeki naci kashinki da fitsarin ki shine zaki butulce min shi me ya ta'ba tsinana miki a rayuwa." Rashida tace"Wallahi kafin babanmu ya mutu ya fada min lokacin da aka haifeni da ya rasa yanda zaiyi da hakika can kauye ya nufa gurin Malam mai allo din ya bashi katuwar tinkiya aka rada min suna da ita." Uwani tayi kasake tana kallon 'yar tata ashe kafin mijin nata ya mutu sai da ya fada musu abubuwan da suka faru a baya....."To ai hakika dama dole ce a wuyansu take idan basuyi ba ai sai a kira ki da shegiya gwara ma ki daina wannan magana dan bayan ya bada tinkiya anyi miki rad'in suna babu abunda ya kuma tsinana miki." Rashida tace."Gaskiya dai ki daina ci masa mutunci." Uwani ta fashe da kuka tana fadin"Sai ki zageni Rashida ki fito fili kawai ki zageni yau naga matsayina a gurin ki shiyasa ni Wasila tafi min ke sau dubu duk abunda tasan za tayi ta faranta min rai shi takeyi duk abunda nace tayi tana yi min babu musu ke kuwa fa sai dai ta nemo kudi kina daga kwance kice, to duk rashin mutuncin da kikeyi min sai na fada mata." Tana gama maganarta ta shige daki tana matse hawaye.....Wayarta ta dauka da Wasilan ta siya mata ta hau kiranta....Lokacin suna tare da mai girma governor suna meeting Wasila taga kiran amma bata dauka ba sai bayan sun fito daga dakin meeting din ta kira ta....Uwani na daga wayar ta fashe da kuka "Wasila maza ki zo gida Rashida na nan tana min rashin mutunci duka na ne kawai ba tayi saboda zuwan Malam mai allo." Rai a 'bace! ta kashe wayar ta nemi numbar Rashidar.....Rashida ta daga wayar tana zumbura baki "Wallahi Rashida ki shiga hankalin ki! dan Kutumar ubanki me malam mai allon ya tsinana miki da har kikewa mahaifiyarki rashin kunya har kin manta irin wahalar da tasha akanmu ashe dama kika bawa malam din yaci mata mutunci kamar yanda ya saba to wallahi sai ranki yayi mugun 'baci! kan hakan." ''Aunty Wasila ki saurara kiji abunda yake faruwa." Rashida ce ke ta magana amma taki sauraranta sai zaginta take cikin jin haushi ta kashe wayar....Wasila ta tsaya tana mamaki! lallai Rashida bata da mutunci ta gama wahala da ita amma ta kashe mata waya....Mahaifiyar tasu ta kira tace"Kinga Uwani na soma zargin yarinyar nan wallahi harda hadin bakinta gurin zuwan Mai allo gidanan dan haka hankalina ba zai kwanta ba komai dare zan shigo unguwar in daukeku ku zauna cikin shiri." Uwani tace"Nima dama shawarar dana yanke kenan dan tunda malam din yazo nasan sauran ma suna tafe haka kawai su rusa mana rayuwa waye zai koma kauye ya zauna? sai dai duk abunda zasuyi suyi." Duk dai magana ta kare ku zauna cikin shiri." Uwani tace "To shikkenan sai kinzo." kashe wayar tayi ta iske inda Camas take zaune tana kallonta. Har kusan karfe goma da rabi na dare Garba na layin su Wasila cikin matasa yayi basaja so yake yaga ta inda Wasila zata 'bullo, shiru asalima tunda ya zauna ko kare bai gani ba a bakin kofar gidan nasu.....Yananan zaune mutane suka fara raguwa saboda dare kowa na tafiya gida shima sai ya yanke shawarar tafiya dama a Mashin yazo roba roba ya sanya mukuli zai kunna kenan ya hango tawowarsu Wasila jikinta sai walwali ya keyi kasancewar material din dake jikinta mai kyalline wani bala'in kamshin turare ya bakunci hancinsa lokacin data giftashi ta suka shige ita da Camas! wace ta nufi gidansu ita kuma ta hau buga kofar gidan......Matasan dake kusa dashi ne suka fara magana kasa kasa..."Shegiya karuwa kawai ina su Mado nanan da sunci ubanta ta gama guje gujen ta dawo karuwar banza da wofi! ai sai munci ubanta wallahi." Zaginta sukeyi suna kwashe mata albarka garba na jinsu bai ce komai ba yana nan zaune yaga sun fito ita da sauran mutanan gidan.....Gidan suka kulle suka wuce simi simi kamar munafuka...nan yaji matasan dake kusa dashi na fad'in"Ai babu matsiyaciyar uwa sama sa wannan matar duk itace ta sanya ta take wannan rashin mutuncin dazu fa wan mahaifinsu ne yazo suka rufe masa kofa ai wallahi mun kusa tashin su daga unguwar nan." "Kai kasan me zamuyi ma yanzu."? girgiza kai yayi yace." Kone gidan zamuyi dan uwarsu in sun dawo su kwana a waje." Kai wannan shawara tayi kyau abokina." Tafawa sukayi suka mike tare.....Garba ganin sun bar gurin sai shima ya hau mashin dinsa yabi bayan su Wasila can ya hangosu tsallaken titi inda tayi parking din motarta suka shiga a take ya bi bayansu amma yanda yake binsu a hankali ba zasu dauka su yake bi ba. Dake unguwar masu hannu da shuni ce ko ina haske babu duhu da tarin kazanta daga can bakin titi Garba ya tsaya ya kafe mashin dinsa a hankali yabi bayan motar inda yaga ta nufi wani estete wanda manya manya mutane ke zaune a ciki Garba yayi mamaki sosai babu shakka yarinyar samu kudi ganin motar ta tsaya a bakin gate din wani tangamemen gida ginin zamani, yana kallo mai gadi ya bude gate din ta shigar da motar ciki, sai ya juya da sauri ganin sucurity na nufowa inda yake, da sauri ya tashi mashin dinsa ya bar gurin a guje......A daran ya shaidawa Ahamdu unguwar da Wasila take sam baiyi mamaki ba saboda yasan zasu iya yi mata abunda yafi haka, kudi ne gasu nan a banzace ayi abunda ya dace an'kiyi ana watsar dasu a banza a wofi jirgin sama ma zasu iya siya mata mutukar bukatarsu zata biya. Uwani da Rashida suka gigice ganin ubangidan da Allah ya mallakawa Wasila suka dinga shige da fice a gidan suna ta'be ta'ben abubuwa Uwani dai kusan zautuwa tayi saboda ta masifar rudewar da tayi taga uwar daula da duniyar da 'yarta ta cikinta ta samu.....Wasila tace "Ko wanne ya dauki daki daya ya ishe shi bukatar rayuwarsa Uwani kinga Abunda Allah yayi mana ko? da kina cewa muje muyi karuwanci shine zamuyi kudi da gaggawa to wannan sana'a da nakeyi mutukar ta karbe ka nan take zakayi arziki yanzu ina da kudi cikin account dina da ban san a dadin su ba kullum 'yan fadar mai girma governor tura min kudi suke bamu da matsalar komai a halin yanzu Allah ya yaye mana kuncin talauci ba tare da mun aikata sa'bo ba. Uwani tace" Sai yanzu kuma na gane abunda kike nufi Wasila wallahi ni a daukata yanzu babu abunda ke saurin kawo kudi da gaggawa kamar karuwanci ashe akwai sana'ar da tafi wannan to Allah nagode maka da bai sa kun dauki gurguwar shawarar da nake baku ba." To a ranar dai da kyar su Uwani sukayi bacci dan Wasila dakinta ta shige tayi wanka tayi kwanciyarta bacci mai dadi ya dauketa........A furgice! ta bude idonta tana salati! ta sanya hannu ta kunna fitilar gefan dago tana bin dakin da kallo kamar me neman wani abu....Kafafunta ta zuro kasa suka sauka kan kafet, ta jima a haka kafin ta mike ta nufi toilet fitsari kawai tayi ta dawo ta kwanta ta rufe jikinta da bargo amma banda fuskarta ta kasa kashe fitilar dakin tayi domin gani take kamar zai iya mamayarta kamar yanda ya mamaye ta cikin mafarkinta na yanzu, Tun da take a duniya ba ta'ba ta'ba mafarki wani d'a namiji ba sai yau! shin wai wannan mafarkin me yake nufi ne? meye ala'karta da wannan guy? ita dai tasan ba'kar gaba ce tsakaninsu to mai zai sanya yazo mata a mafarki yana mata murmushi saboda kuma tsabar wuce gona da iri har ya rungumeta yana tatta'ba mata sassan jikinta....Tayi sauri ta sanya hannunta a ramin cibiyarta sai taji tamkar hannunsa ne a gurin a lokacin da yake shafa mata cikin mafarkinta, jin tsigar jikinta ns tashi ya sanya tayi gaggawar cire hannunta daga gurin.....Rufin dakin ta tsurawa ido, itafa wannan mafarkin ya bata tsoro har yanzu tana hango fuskarsa da tattausan murmushi, shin wai abunda tayi masa bai dame shi bane da har zai zo yana mata murmushi, ita ta dauka zasu kulla gaba ne ita dashi wacce tafi ta da tsanani!!!!!!! Juyawa tayi ta rungume pillow tana lumshe ido....."Subahanallahi." Hannunsa taji a jikinsa ta mike a zabure! tana dube dube a dakin........Yau satin ta daya a gidanan amma bata ta'ba shiga tsoro da farga ba irin na yau! mikewa tayi ta zura hijab! ta bude dakin ta futa....Dakin da su Uwani suke nan ta nufa, gani take kamar in ta zauna a dakin ita kadai mafarkinta zai iya tabbata.....Duk suna tare dake bed din babbane su Rashida da Uwani anji Ac sai bacci akeyi, ta samu ta ra'be gefensu ta kwanta had'e da takure jikinta guri guda.......Ta jima a haka kafin bacci ya dauketa. *** Cikin Shiri ya fito daga bedroom dinshi, Garba da Hadi na zaune a katafaran palon nashi suna ganin fitowarshi suka mike a tare gaisuwa suka mika amsa yana mika musu hannu sukayi musabaha da juna Ahamadu bashi da girman kai da d'agawa........Yana mutumta dan adam!! Garba ya isa inda yake yana gyara masa babbar rigarshi da yake yau shigar manya kaya yayi dakarkiyar galila ce a jikinshi green color wuyan babbar rigar anyi masa aiki na manya mutune wanda mafi aka sari masu sarauta keyi, yana gyara links dinshi Garba ya miko mishi hula zanna bukar 'yar gasken ya d'ora saman kanshi a sai ya sake wankuwa da kyau gyaran fuskarshi yayi dai-dai da tsarin askin dake kanshi saisaye yake yi bai fiye tara suma ba amma baya kwal kwabo ana masa saidaye ne agyara masa fuskarsa dai-dai da zamani....Duk wanda ya kalleshi sai ya sake kallo babu wanda zaice ya kai matakin shekurun da yake kai a yanzu.....tare suka futa dasu Garba mutukar ba nisa zaiyi ba baya tafiya da securities su Garba kadai yake dauka su raka shi, Garba ya bude masa bayan mota ya shiga ya zauna Hadi ya zauna kusa dashi ya mayar da murfin motar ya rufe.....Da sauri Garba ya zauna maxaunin direba tun kafin su iso bakin gate din mai gadi ya bude gate din.....Securities din dake zaune a bakin gate suka dinga daga masa hannu da fadin "A sauka lafiya Allah ya tsare a dawo lafiya." Shima hannunsa ya daga musu yana amsawa da "ameen." Har suka futa daga gidan......Sai da suka hau kwalta tukkuna Garba ya tambayi inda suka nufa, ya shaida masa inda zai suje gidan Hajiya Babba dake Zooroad. Garba ya dauki hanya kamar yanda aka umarce shi. _Muje Zuwa_ *BINTA UMAR ABBALE* [7/19, 10:35 AM] Bintu: *'YAR BANGAR SIYASA!!* 🌺 romantic love story🌺 *NA:* *BINTA UMAR ABBALE 🍒* *🌍Manazarta Writes asso* _'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_ ~~~~~~~~ *NA KUDI NE.......!* _Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176 sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko orange_ *Free Pege17* Hajiya Babbah na xaune a palonta tare da wasu 'yan mata guda biyu Suhairat da Salimat 'Yayan mutun d'aya ne wato Hajiya Maryam wacce ta kasance 'kanwa ga Hajiya Babbah! kasancewar Allah bai bata haihuwa ba har mijinta ya rasu.mutane ke ta nani'ka mata 'yayansu mussaman 'yan uwanta waccan ta turo 'yarta gobe waccan ma ta turo 'yayanta jibi duk dan ganin daular dake tattare da gidan....Suhairat ce mai nacin zuwa gidan saboda kawai tayi katari da Ahamdu mutumin da ta kwallafa ranta a kanshi take masifar sonsa shi kuma bai san tana yi ba sai tayi zuwa goma gidan ba ganshi ba dan bai fiye zuwa da safe ko da yamma ba sai dare yake zuwa gaisheta, to yau dai sunji dadi jin Hajiya tace sunyiwa waya dashi yace zai shigo da wuri Suhairat ta sake gyara fuskarsa ta fesa turare ta 'kame! a kan mujera Salimat kuwa sai dariya takeyi mata tana fad'in"Allah yasa dai ya kyasa dan na lura kinyi masifar matowa a kan mutumin nan." Suhairat tace"Ke dai bari 'yar uwa ni wallahi da zai aureni da gudu zan yarda ina masifar sonsa komai nashi yana burgeni mutum kamili ga nutsuwa kamshin turaransa ma abin alfahari ne." Salimat ta dinga 'kyalkyala dariya tana tsokanar yar uwar tata......Cikin nutsuwa da kamala ya shigo palon bakinsa dauke da sallama. Dukaninsu suka mike tsaye suna masa barka da zuwa, kamshin turaransa ne ya cika musu hanci Suhairat sai murmushi takeyi tana gyara masa gurin zama....Ya zaune a nutse yana fadin" Suhairat kune yau gidan? ina Hajiyata." Wani fari tayi da ido tace"Wallahi kuwa Mune yau a gidan Hajiya na daki bari na kirata." Ta juya tana tafiya cikin wata iriyar siga.....Oho bai san tanayi ba dan idanunsa na kasan kafet, Tare suka fito da Hajiya babbah tana masa barka da zuwa ya amsa yana tambayar ta gida.....Suhairat ta dauko mishi lemo da ruwa ta tsiyaya masa ta mika mishi.....Ba tare da ya kar'ba yace."Bana jin zansha komai yanzu nagode Suhairat." Jiki a sanyaye ta ajiye cup din ta nemi guri ta zauna kusa da Hajiya......Yace."Ina ta son zuwa Allah bai nufa abubuwa sunyi yawa hajiya a gafarce ni." Tace."Ai babu komai Ahamdu dole ne ayi muku uziri saboda yanayin harkar taku ta jama'a bayan nan kuma nasan akwai hidimomi da yawa Allah dai ya taimaka." Ya amsa da "ameen." Palon yayi shiru Yana so yayi mata maganar dake tafe dashi amma zaman su Suhairat a gurin ya hanashi shi mutum ne mai sirri yafi son komai nashi a cikin tsari dan ya lura da yarinyar kanta rawa yake yasan dai zancen gizo baya wuce na koki ga yanayin yanda take masa kwarkwarsa za tace itama sonsa takeyi. Gyaran mirya yayi a nutse yace."Hajiya muhimiyar magana ce take tafe dani dan daga nan ma idan na tashi can gidan Kawu Almu zan nufa." Hajiya Babba tace "To babu laifi Ahamadu Allah dai yasa maganar dake tafe da kai irin wacce take bakina ce da nayi mutukar jin dadi." Murmushi ya saki wanda yasa Suhairat shagala gurin kallonsa Yace."Yana da kyau yaran nan su dan bamu guri." Hajiya ta kalli su Suhairat da suka kasa kunne suna so suji maganar ko kunya babu tace."Suhairat ku shiga ciki mana." Simi simi suka mike sam basu so hakan ba mussaman Suhairat tafi so ya fadin maganar a gabanta da jikinta na bata wani abu. "Hajiya na samu matar aure insha Allahu ranar juma'a ta jibi za'a daura aure." Maganar data fito daga bakinsa kenan.....Fuskarta da yalwataccan murmushi tace"Alhamdullihi Ahamdu baka ta'ba zuwa da labarin da yayi min dadi kamar wannan ba masha Allahu to amma kuma al'amarin baiyi sauri ba kuwa ko bazawara ce ne."? Ya girgiza kai "Budurwace Hajiya." Tace."To to masha Allah amma kuma abun yazo min bagatatan banyi shirin komai ba ko da yake dama haka aure yake dashi da mutuwa ba'a shirya musu in lokaci yayi sai anyi, shin yarinyar 'yar wace unguwa ce kuma." Yace." Yar wata karamar hukama ce a wannan jahar sunan garin nasu Garko amma anan tayi rayuwarta Unguwar dorayi daurin auran dai Can Garko zamuje ayi." Tace."To Ubangiji Allah yasa za'ayi damu ya tabbatar mana da alkairi." Ya amsa da "ameen Hajiyata, ni zan wuce can gidan Kawu Almu babu wani abu da kike bukata ko."? Tace." Alhamdullahi Ahamdu bana bukatar komai ka wadatani da duk abun bukata kafin wani ya kare kasa an kawo wani babu abunda zance sai da nace Allah ya saka maka da alkairi ya jikan iyayenka." Yace."ameen Hajiyata Ubangiji Allah ya barmin ke na dinga ganinki ina jin dadi." Tayi dariya da fadin"Wace ni Ahamdu ai mutuwa rigar kowa ce zan mutu kaima zaka mutu." Ya mike yana kallon a gogon dake daure a hannunsa yace."Duk da haka dai Hajjah ina fatan kiyi rayuwa mai tsayi a duniya tace."To Allah yasa Ahamdu Allah yayi maka albarka ya baka 'yaya masu albarka." ya amsa da ameen yana mata sallama har bakin kofa ta rakoshi tana sanya masa albarka Suhairat dake la'be bakin kofa ta silale 'kasan daki ta fashe da kuka "Shikkenan na mutu ni suhairat shikkenan karyata ta kare zaiyi aure ina zaune duk na kori masu sona saboda dashi bai san inayi ba na shiga uku na lalace." Kuka take sosai Salimat na bata hakuri Hajjah ta shigo dakin. Tace"Ke suhairat lafiya kike wannan kukan." Rungumeta tayi tana shashsheka take fada mata tsayin shekarun da tayi tana jiran Ahamdu amma yanzu yazo yace zai auri wata. Hajjah tace"Inda Ahamdu zai aureki da tuni ya aure ki Suhairat ni da kaina nace ki hakura dashi ki zabi miji cikin manema auranki ki aura kikaji ni ba zanyi masa tilas ba, saboda yaron ya daukeni a matsayin uwa yana min biyayya komai nake so yanayi min ban haihu ba amma an haifar min addua ce tsakanina dashi ni dai shawarar da zan baki shine ki hakura dashi ki fito da miji cikin ma nema auranki ki aura magana ta wuce." Suhairat ta mike daga jin hajjah tana kuka mayafinta ta figa ta dauki handbang dinta ta fice....Salimat ce kawai tayi wa Hajjah sallama tana bata hakuri kan abunda Suhairat din tayi mata.....Tana fitowa harabar gidan taga Suhairat ta figi mota a guje ta fice daga gidan....Girgiza kai kurrum tayi ta sanya direba ya dauketa domin kaita gida.....' Yan asalin unguwar galadanci ne. **** Wasila ta tashi da wata iriyar kasala da mutuwar jiki, dan ta jima ma a daki kafin ta fito cikin kayatacciyar kwalliya gold kamar yayi magana a jikinta har yatsun 'kafafunta gold ne tana sanye da legos less dan gasken tayi daurin ture kaga tsiya gashinta ta daure shi da katon ribbon ya kwanta a kafadarta idan ka kalleta sai ka dauka irin masu shegen karatun nan ce saboda yanda takeyin mu'amula cikin jan aji da isa......Uwani da Rashida sai girki suke su sauke su dora suci wannan su sha wannan duniya ta samu. Tunda ta kunna wayarta sa'konni ke shigo mafi yawanci daga abokanan harkarta ne maza sunfi yawa babu wanda ta duba a cikin messages din wayar dai kawai take latsawa tana ya mutse fuska, ita kadai tasan me takeji a jikinta har yanzu gabanta bai daina faduwa ba mutukar zata tuna da mafarkinta na jiya.....Kiran As ne ya shigo wayar ta sai da ta kusa katsewa sannan ta dauka suka gaisa yace anya zaki fito yau kuwa? Ya mutsa fuska tayi tace"Yau dai zan huta a gida Gaskiya sai dai gobe." Yace."To babu laifi ko nazo na taya ki hira ne."? a ya tsine tace"Ina da abokanan hira ka huta kawai." Mara zuciya sai ya sake cewa "Okey anjima zan shigo zamuje musha iska." Tace."Ba damuwa sai ka shigo amma dai ka bari sai bayan sallahar isha'i." Yace."Haka za'ayi gimbiya." Hira suka dan ta'ba tayi masa sallama da fad'in zata kwanta bacci ba dan yaso ba ya hakura. Kashe wayar tayi tana tsaki....Camas! tayi sallama ta shigo palon....Taci uwar kwalliya da material mai uban tsada wani shegen dinki akayi mata mai fitar da tsaraici gashi bata sa mayafin kirki ba Camas an samu duniya har mota ce da ita sannan itama Alhaji Ma'aruf yayi mata alkawarin mallaka mata gida cikin gidajensa da yake ginawa.....Tace."Kawata ya yau dai duk na ganki babu kuzari ne na jima da zuwa government house ina jiran zuwanki sai yanzu As yace yau ba zaki fito ba sai gobe." "Camas yau hutawa zanyi wallahi na gaji kullum kana cikin maza shegu suyi ta kare maka kallo wani ma yana sane zai zo ya gogi jikinka wai bai sani ba, na kusa daina wannan harkar tunda bukatata ta biya." Camas tace"Wallahi karki soma shin me na kasa yace ballanta ya bawa na sama me kika mallaka me kika ajiye a account dinki karfa ki manta yanzu lokacin da zaki sake zage damtse ki tatsi abunda kika tatsa wanda ko bayan mulki ya bar hannunsu kin samu kasonki me tsoka ai wallahi ni yanzu na fara har sai naga abunda ya turewa buzu nadi." Ajiyar zuciya ta saki a hankali tace" Duk da haka dai zan dinga daga kafa ba kullum zan dunga zuwa government house din ba, kina sane dai da kallon da jama'ar gari ke mana ko wasu fa karuwau suke daukarmu, na tsani ace min karuwa wallahi." Camas! tace" Sun dade basu kirani da karuwa ba abunda ya damesu ne idan kace zaka daka ta mutane sai su cuce ka.'' Shiru kawai tayi tana girgixa kai ta tsani a kirata da karuwa gwara Camas idan sun kirata da karuwa babu laifi tunda tana ta'bawa amma ita ba taji ba bata gani ba ana kiranta da kalmar da tafi tsana a rayuwarta. **** *RANAR JUMA'A* Su shida ne kacal a cikin motar Ahamdu Kawu Almu da abokinshi sai Khalifa da mahaifinshi Alhaji Iliyasu sai Garba dake gaban mota yana draving, kasancewar shine yasan gidan ya sanya zai jagoronce su.....Ahamdu da Khalifa suna sanye da kaya iri daya farar shadda ce kal dinki babbae riga da yar ciki hula iri daya agogo iri takalamsu iri daya hattata da links dinsu iri daya ne sosai idan ba fada akayi ba ba zaka bambance waye angon ba a cikinsu. Can bangaran su Malam mai allo kuwa sun shirya tsaf dan tuntuni malam ya shaidawa limamin dake sallahar juma'a a babban massalacin dake garin cewar bayan an idar da sallah akwai daurin auren da za'a gabatar.......To lokacin da suka sauka garin ana ta shirye shiryen tafiya massalaci dan haka a gurguje suka daura alwala suka bi ayarin mutane ya zuwa masjid d'in. Bayan liman ya gabatar da hud'uba kamar yanda addini ya tanada sai aka tayar da sallah........An idar da Allah anyi addua kana kuma aka shiga daurin aure.............Ana shafa fatiha Garba da Khalifa suka soma rabon alawa da goro gami da dabino cikin bakar leda za'a bawa mutum goro da alawa daurin aure yayi albarka jama'a sai addua suke gami da fatan xaman lafiya ga amarya da ango. _Muje Zuwa_ *BINTA UMAR ABBALE* [7/19, 10:49 PM] Bintu: *'YAR BANGAR SIYASA!!* 🌺 romantic love story🌺 *NA:* *BINTA UMAR ABBALE 🍒* *🌍Manazarta Writes asso* _'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_ ~~~~~~~~ *NA KUDI NE.......!* _Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176 sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko orange_ *Free Pege18* Su Kawu Almu suka rufawa Ahamdu baya zuwa gidan Malam mai allo dake cike taf da dangi, katuwar tabarmar dake shimfide a tsakar gidan suka zazzauna aka shiga gaishe gaishe 'yan uwa sai tambaya sukeyo waye angon ne tsakanin Ahamdu da Khalifa.....Ahmadu yayi kasa da kanshi a lokacin sai ya tsinci kanshi da jin kunya duk da a zuciyarsa auran yayi shine da wata siga ta daban amma sai yaji kunyar mutanan mussaman malam mai allo dake ta kai kawo yana hidima da mutane kana ganinshi kasan yana cike da farin ciki....Khalifa ne ya dinga nuna shi yana fad'in"Gashi nan wannan ne angon bani ba.'' Tsoffin ciki suka soma yi masa d'an biki suna tsokanarshi da fad'in ya tsinci dami akala tunda ya samu nasarar auran Wasila saboda haka ya riketa da kyau dan ba karamar mace bace." Shi dai jinsu kawai yake yi yanayin yanda suke mu'amular su ya bashi sha'awa mutuka kuma ya lura suna masifar son su Wasilar halinsu kawai suke gudu, magana cikin magana suke masa hannunka mai sanda kan yarinyar kan yayi hakuri da halinta da dai sauraransu, sai ya kara jin jikinsa yayi sanyi da al'amarin auran yanzu kuma ya soma da ya sani tunda shi har cikin zuciyarsa ba da manufa me kyau ya auri yarinyar ba amma kuma darajar iyayenta na nema ta sauya masa tunani. Lafiyayyan towon shika da miyar taushe aka kawo musu miyar taji manshanu gefe guda kuma ga soyayyan naman zabi nan fal katuwar silba......Babu wanda yayi wasa a cikinsu duka suka zage suka ci abincin dan tsabarta da kayatuwarsa tamkar a restaurant babu wata alama da zai nuna abincin karkara ne kwanika sabbi aka zubo musu dalili kenan da ya sanya suka saki jiki suka ci suka koshi suka kora ruwa mai sanyi irin na randa. Bayan sun kammala sai suka shirya tafiya gida,Malam mai allo ya ke'be da Ahamdu yana masa maganar kan ya za'ayi da tariyar Wasilar Yace." Ya bar komai a hannunshi.'' Malam mai allo yace."Nida nafi so yau yau yarinyar nan ta kasance a dakinta bana so mu shiga hurumin ubangiji ya kasance muna wasa da aure, tunda an daura auranan to ta tare a dakinta barin ta haka sasakai zai janyo matsala babba tunda dai ita bata san halin da ake ciki ba.'' Yace."Tabbas maganar haka take malam babu damuwa insha Allah yau zata tare a dakinta kamar yanda ka bukata din." Malam yace."To bari in baka sadakin a hannuka ka mika mata da kanka tunda dai mu ba ganinta Zamuyi ba." Yace."babu damuwa Malam." ya ciro dubu biyar din ya mika masa ya sanya hannu biyu ya kar'ba, kana ya shiga yi masa godiya sukayi sallama cikin mutunci da mutuntawa.....Har bakin mota suka rakosu sai da motarsu ta 'bacewa ganinsu sannan suka juya cike da farin ciki sun auran da Wasila saura Rashida zuciyarsu wasai mussaman malam mai allo yana fatan d'orewar zaman lafiya ga Ahamdu da Wasila. Cikin mota tunani kawai yake yi kan al'amarin duk ya rasa wane matsayi zai aje wannan auran nashi zuciyarsa na kawo masa shawarwari iri iri tabbas ko A lahira wani nacin albarkacin wani babu shakka yarinyar taci albakarcin dattijo malam mai allo a gurinsa, da ya dauki mummunar aniya a kanta albarkacin mutumin ya rage kashi tamanin daga cikin abunda ya tanadar mata amma dai duk da haka zai ba zai kyaleta ba sai ta gane bata da wayo......Haka suka isa gida tunani duk ya addabe shi yanzu ya za'ayi ma ya tunkari inda yarinyar nan take dame zai fara ne." ? Khalifa yace."Naga ka shiga tunani da yawa ka bari muje gida mu dan huta tunani ya dawo tukkuna nasan abunda ke damunka a yanzu amma aka bi komai a hankali mai sauki ne." Ajiyar zuciya ya sauke ya dan gyara zamanshi ya sake mai da idonsa ya rufe ba tare da yace komai ba. Cikin wata lafiyayyiyar lifaya ta fito Tana baza kamshi turarruka masu tsada da sanyin kamshi, Tayi ado da gold 'kirar dubai masu jajayen stones a jiki shi kanshi gyaran gashin da tayi wa kanta abun kallo ne tamkar wata balarabiya haka ta zama babu shakka kudi na iya canza mutum nan take Wasila ya zanzu dai da zata shiga cikin labarawan Itopia sai ta saje dasu saboda yanda fatarta ta goge ta 'kara fitar da kalarta chocolate color dama can haka kalar fatarta take Rashida ce fara itace ta d'ebo haske babansu Uwani kuwa ba za'a kirata fara ba kuma ba za'a kirata baka ba kusan kalar fatarsu daya da Wasilan amma dai yanzu ta Wasilar tafi kyau da gogewa, takalmi mai tsayi ta sanya kasancewar ba ta fiye tsayi sosai tana tsaka tsaki dai! Hannunta rike da pose da key na motar ta take takawa sannu a hankali.....Camas dake zaune na latsa waya ta kalleta "Wow! Kinga yanda kikayi kyau kawata, gaskiya lifayar nan ta miki kyau wallahi ke kin jima bakiyi kyau irin na yau ba tamkar wata amarya lalle ne kawai babu a hannunki da kafafunki.'' Murumsi tayi tace" Haka kawai yau nace bari nayi shigar bare bari ashe nayi kyau."? Camas! ta kwalawa Rashida kira ta fito daga kicin....Ganin Wasila ya sanya ta rude! "Aunty Wasila kece dan Allah nima ina son lifayar nan ki siyamin wallahi kinyi kyau! sai kallonta takeyi tana dariya Camas tace " Wai tambaya takeyi tayi kyau shine na kira ki ki fada mata." Rashida ta hau kod'ata "Wallahi aunty Wasila ko makaho ne yazo kusa dake ya tsaya sai ya kiyayi kansa babu wanda zaice kin hada jinsi da bahaushen mutum kamar wata balarabiya." Ganin yanda suke sambatu ya sanya ta dinga musu dariya...Uwani ma ta fito daga daki ta dinga nata shirma da zasu fita ta dinga yiwa 'yar tata kirari sai kace wata maro'kiya ita Wasila ma dariya suka bata tace"aikuwa dai tunda shigar lifaya nayi min kyau zan dawo yin irinta.... Suna shiga motar kiran As ya shigo wayarta ta dauki wayar tana dan ya mutsa fuskarta.....A nutse tayi sallama da sauri ya amsa yana fad'in "Gani a bakin gate din gidanki ki fito kawai muje mu dawo dan ma dai nayi alkawari ne da sai nace mu bari sai gobe ma futa yanzu aka kirani a waya karfe goma dai-dai muna da metting da shugaban 'kasa kin san tun safe ya shigo gari yanzu haka suna tare da mai girma governor." Tace."To mai zai hana mu bari sai gobe." Da sauri yace." Ai ni kuma ba zan fuskanci komai ba gurin metting din nan mutukar banyi tozali da kyakkyawar fuskar nan taki ba." Murmushi tayi ta kashe wayar ta kalli camas tace"Ga d'an anace nan ya iso kawai ina zama na wai na shirya muje shan iska komai abunsa dole ya hakura dani wallahi wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa Camas tace"Tunda dai yaki hakura ba sai kiyi kwance kwance ki kwashi rabonki ba." Ke dai kawai fito muje dare nayi kudi kam ai kamar mahaukaci haka yake samun a account. " Camas taji inama itace dan a zahiri As yafi Alhaji Ma'aruf sakin hannu shiyasa taso ace As din ne ke mu'amula da ita tasan da tuni ta wuce gurin........Kamshi turaranta shine ya buwaye shi, yana draving yana kallonta idanunsa sun kada sunyi jawur babu shakka yau Wasila ta kaishi makura ga bukatuwa da ita yana ganin koda bai shiga wannan ramin ba a'kalla dai ta bashi dama ya d'an rage zafi a jikinta....Da kyar suka isa 'katon gurin hutawar wanda sai wanda ya amsa sunansa ke zuwa gurin......gurin tamkar rana ko ina haske tar tar jama'a nata shigowa da motacinsu da yawa daga ciki tare suke da mata wasu karuwansu wasu matayen su kowa harkar gabanshi yake.........As yayi kwance a gabanta yana lumshe mata shegun idanunsa da suke cike taf da sha'awarta duk sun kankace saboda jaraba, ganin yana matsowa jikinta ne yasa tayi saurin matsawa tana 'bata fuska.....Yace."Yana da kyau yau daya ki bani dama ko yaya ne na ra'bi jikinki babu shakka zuciyata na azabtuwa da so da kaunarki ki bari na rungume ki ko zanji dadi a jikina" Ranta a bace ta kalleshi "Haba As wai yaushe ne zaka daina yi min irin wannan maganar? na sha fada maka ni ba 'yar iska bace amma ka kasa fahimta ko dan kana ganin Camas! kawata ce shine nima kake zargin halinmu daya da ita, Wallahi da zanyi karuwanci da tuni nayi amma ni ba layina bane kaje ka nemi karuwa ta debe maka kewa bani ba, idan kudin da kake turo min da wannan niyyar ne to dan Allah daga yau kar ka sake kuma tunda ka kasa daukata a matsayin abokiyarka to ka goge numbarta dake wayarka bana bukatar wata mu'amula ta sake shiga tsakanina da kai. Mikewa yayi zaune yana marairace fuska yana so ya kama hannayenta ta fuzge da karfi ta mike tsaye da sauri jikinta na rawa...Camas na can tare da wani alaji suna zance ta iskesu rai a 'bace tace" Ni zan wuce gida Kya biyo bayana." Mutumin yace."A bari nazo na kaiku mana." Ko sauraransa ba tayi ba tayi hanyar futa....Ita ko Camas! ganin alhajin nada kumbar susa a tare dashi sai tace"Rabu da ita Alhajina idan da wata bukata da kake nema a gurina yi min magana kawai kar kaji shakka." Ya shafa fuska yana lumshe mata ido yace."Muje mu kama daki zuwa gobe da safe sai na sallame ki." Ba tare da wata doguwar jayayya ba tabi bayanshi. As yabi bayan Wasila yana nema neman duniya bai ganta ba guri ne babba ga jama'a na shiga suna fita ya fita bakin titi ya jima a tsaye yana waige waige bai ganta ba, haka ya koma ciki domin daukar motarshi anan kira ya shigo wayarshi kan lokaci ya kusa da zasu zauna metting dole ya nufi government house din ba dan ransa yaso ba yaso ko yaya ne ya rage zafi da Wasila amma ya dauki alkawarin komai tsantsaninta sai ya rusa shirinta. Tana ganin futar motarsa ta fito daga inda ta 'buya babu shakka As so yake ya yaudareta ya rabata da budurcinta wanda da ta jima tana tattalinsa, tabbas zata janye jikinta dashi da lamuransa tunda ta lura shi baya abu dan Allah. Koda ta fito titin tsif! babu abun hawa na haya dama kuma ba kasafai a dai-dai ta sahu ke shigowa gurin ba saboda babban titi ne na masu hannu da shuni yawanci motocin gida sunfi karakaina a kan titin.....Tsoro yasa ta kasa tsaida motar kowa sai ta kama hanya ta dingi tafiya ga cokalelen takalmi a kafafunta. Tana daf da futa babban titi motar ta fito daga wani babban layi mai dauke da dogwayen gina gine, dole tasa ta ratse a gefe domin ta bawa mai motar hanya, haushi da takaici ya turnuke ta ganin yanda mai motar ke dallare mata fuska da hasken fitilar motar....Ta sanya hannunta ta kare fuskarta tana jan tsaki!!! Ahamdu dake gaban motar gabanshi ya fad'i Allah yasa dai idonshi ba gizo yake masa ba, sai da suka zo daf da ita ya tabbatar da zarginsa Itace! ma'kale a jikin bango tana jira su wuce! sai ya shiga tambayar kansa, Yarinyar nan daga ina take a cikin wannan daran? shin ita da waye? kuma meye ya fito da ita daga gida. Bashi da me bashi amsa dole sai ita, da sauri ya sanya Garba ya tsayar da motar ya bude motar da zama ya fito ya iske inda take ma'kure! _Muje Zuwa_ *BINTA UMAR ABBALE* [7/20, 6:48 PM] Bintu: *'YAR BANGAR SIYASA!!* 🌺 romantic love story🌺 *NA:* *BINTA UMAR ABBALE 🍒* *🌍Manazarta Writes asso* _'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_ ~~~~~~~~ *NA KUDI NE.......!* _Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176 sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko orange_ *Free Pege19* Saboda yanayin hasken gurun ya sanya tun kafin ya karaso kusa da ita ta ganeshi gabanta ne yayi wata mummanar faduwa da azama! tayi kokarin barin gurin.....Taku biyu yayi ya cafki hannunta guda.....Cak! taja ta tsaya tana mai da nuffashi domin ganinsa ya sanya jikinta kyarma wanda shi kanshi sai da yaji a jikinsa sakamakon rike hannunta da yayi, Sai da ta dan samu nutsuwa sannan ta juyo fuska a had'e! Suka hada ido dashi yana tsaye shima tashi fuskar babu alamun wasa....Kafin tace"Komai ya mangantu.....'Karfe goma sha biyu na dare kina waje a matsayinki na 'ya mace mai daraja kin watsar da wannan 'kimar da Allah ya baki kin mai da kanki tamkar tunkiya kiyi nan kiyi can cikin dare saboda rashin sannin ciwon kai kin mai da kanki tamkar namiji namijin ma irin wanda bai san darajar kanshi ba." murmushi tayi mai ciwo tace." Idan hakane kai ma Ashe kana d'aya daga cikin jinsin irin mazan da ka fad'a yanzu, Kai ma me ya fito da kai da daddare idan ka yarda da kanka? kana kirana tinkiya kai kuma sai ka kira kanka da bunsur......! kamar ya sanan sunan da zata kirashi dashi yayi saurin kife ta da mari! jikinsa na kyarma! yace."Ahir!! d'inki ki kirani da wannan suna! na kira da tinkiya din domin sunan da ya dace a kira ki dashi kenan, dube ki don Allah wai ke kinyi kwalliya kina yawo sa'ko da loko kina rabawa jama'a jikinki a banza job wane wawa ya jaki ya jaki ki bishi saboda rashin martaba kai ya jama'a ba zasu kira ki da sunanan tinkinya ba."!? Wasu zafafan hawaye ne suka shiga zubo mata a kumatu idan ta fahimci maganarsa anan shima yanayi mata kallon karuwa kenan? wai shin mai yasa mutane basa yi mata adalci ne a duniya ta tsani a kira ta da wannan suna, sunan tinkiya na nufin mace mara hankali mara ilimi mara nutsuwa da kamun kai....Tunda suke karawa da guy din bai ta'ba 'kona mata rai irin yau! ba su kansu hawayen dake zuba a fuskarta ta bata san sanda suka zuba ba, da budurcinta da komai yake kiranta da tunkiya.....Hannunta da cikin nasa ta fuxge! ta bar gurin a gaggauce!!! bayanta yabi ya sake ruke hannunta ta sanya karfi ta tureshi kuka take hai'kan! tsabar kalmar daya kira ta da ita tayi mata ciwo tana ji ma tamkar ta hadiyi zuciya ta mutu.......Yayi saurin tatar gabanta rai a bace yace."Idan baki tsaya ba wallahi yanzu a gurin nan zan tu'be ki na kwashi rabona duk da hakan ba halayyata bace zanyi miki hakane dan in nunawa duniya halinki....Gwara kawai ki tsaya ki daina sauri." Hawayen fuskarta ta goge tace"Kai baka isa ka tu'be ni ba wallahi sai dai na tu'beka! kuma sai nayi maka sintir! zaka san wanda ka mara." murmushi ya saki hakika dauriya da jarumatar yarinyar na burgeshi, yace."Idan kin isa ke mara kunya ce ki 'kara taku d'aya anan gurin wallahi sai na baki mamaki! sai na tu'beki! kuma na gudu da kayanki ki 'kara taku daya ki gani." Wasila ta kalli fuskarsa taga babu alamun wasa a ciki sai gabanta ya fadi tabbas zai aikata abunda ya fada bari kawai ta lallabashi su rabu lafiya amma sai ra rama abunda yayi mata. Tsayuwa ta gyara tace"Wai shin yanzu da ka tare min hanya me kake nufi dani.'" Yace."Abubuwan da nake nufi dake suna daya wa saboda haka shige muje ki shiga mota muje." Ta kalleshi she'keke! tana gyada kai! "Ko da kudi ba zan shiga motarka ba nasan idan na futa babban titi ba zan rasa abun hawa ba kawai ka fada mun dalilin da ya sanya ka tsare min hanya." "Kin san ke mai laifi ce a gurina ko? so bana son jayayya kiyi abunda nace dake idan ba hakaba zan kira Yarana a waya so zu su baki mamaki! duk yawansu sai sun kwanta dake sunyi miki fata fata!!!!!! Tsorata tayi dajin maganarsa mussaman da taga yayi kici kici da fuska yana kokarin dauko wayarsa,, sai ta sassauta murya a hankali tace" Dan Allah kar ka kira su muje motar nayi alkawarin kome kake so zanyi maka amma kar ka kira yaranka su wulakanta ni." Yace."Wuce muje." Gaba tayi da cokalalen takalminta har tana gord'ewa sai waiwaye take ko zata samu mafakar da zata arce babu gida gaba babu gida a baya.....Da kanshi ya bude mata mota ta shiga ya zauna kusa da ita fukarsa babu wasa, gabanta sai masifar faduwa yake shikkenan yau ta fada komar Ahamdu sai Allah kuma tsinewa babu irin wacce ba tayi wa As ba shine silar fitowarta da wannan daran da bai fito ba da tuni ta gida tare da mahaifiyarta da 'yar uwarta. 'Kasa tayi da kanta hawaye na d'iga ta dinga sanya gefan lifayar tana gogewa sam! ba taso ya ga gazawarta a kansa amma inaa ta kasa tsayar da hawayen dake zubar mata mutukar ta tuna kalmar da ya kira ta da ita sai taji zuciyarta ta karye *Tinkiya* wannan kalma tayi masifar ragargaxa mata jikinta da duk wani kuzarinta da kwanjinta a kanshi....... Gani tayi mai gadi na bude tangameman gate din gidanshi, tayi saurin dagowa tana kallonshi taga yayi masifar 'bata fuska, yana magana da securities din dake bakin gate din....Tsumu! tayi hankalinta a tashe kar dai guy nan ya kawo ta gidanshi ne domin ya keta mata haddi innalilihi wa ina ilahi raji'un! yanzu meye mafita.... Taga ya bude mota ya fita sai tayi yunkurin fitowa itama, da sauri ya mayar da murfin motar ya rufe da karfi dan har yana had'awa da hannunta, cije baki tayi tana duba ya tsanta, tunaninta kaf yanzu ya ta'alla'ka ne akan yanda za'ayi ta ku'butar da kanta daga hannunsa. Can ta hango sun nufi bakin gate tayi saurin mikewa kan site tana le'kansa taga yana magana da securities akwai ta zata sosai parking spece da kuma bakin gate din ba tajin abunda yake cewa amma yanda ta lura da fuskarsa babu wasa yana musu magana mai muhimanci.....Juyowa tayi ta fara kokarin bude motar gam! take da mukulli ko wane murfi a rufe.....Hawaye ya tsinke mata, Innalillhi wa'ina ilaihi raji'un! Sake mikewa tayi tana le'kensa, Can ta hangoshi ya durfafo inda take tayi saurin zaunawa! jikinta na kyarma, yana bud'e motar hankalinta a kai tayi wuf!! ta fito fit! har sai da ta tureshi yayi saurin tsayuwa cikin zafin nama ya cafki 'kugunta ya rike tam! ya had'e bayanta da 'kirjinsa! Jini hannunsa kan kirjinta ya sanya tayi masa wata wawar bangaza ta sanya tsinin takalminta ta daki gwiwarsa guda! yayi gaggawar juyo da ita mari ya kifa mata!!!!! ya rike fuskarta da hannuwansa suka tsirawa juna ido.....Numfashi take saukewa mai zafi !! tana hura hanci! ga idanunta yayi jawur! Tsananin tashin hankali da fargaba ya gani cikin 'kwayar idonta, Ya gyada kanshi cikin jajurcewa yace."Ki shiga taitayinki ki kuma nutsu wannan haukan da kikeyi babu inda zai kai ki a gurina muje ciki in fad'a miki wani abun al'ajabi."!! "Ba zan shiga gidanka saboda ni ba 'yar iska bace ka daukoni ne dan ka biya bukatarka ni nafi karfin ka idan kuma ka tsananta to za'ayi mutuwar kasko dani da kai a gidanan, dan nayi rantsuwa da Allah babu wani d'an iska da ya isa ya rabani da budurcina akan hakan zan iya aikata komai." Ya jima yana kallonta kafin yace."Ke! kina nufin kina sa budurci a yanzu, da har kike wani tada jijiyar wuya! okey to kar ki damu ba wannan bane manufata a kanki kawai dai yanzu na baki umarni kan ki nutsu kana kuma muje ciki na sanar miki da abun al'ajabin da ya faru dake." Taji wani irin shocking ya kama jikinta shin wai wannan wane irin abun al'ajabi yake so ya fad'a mata ne? Ji tayi wata jarumta tazo mata a take tace"Muje amma akwai sharad'i idan ka kusance ni sai nayi maka illah." Yace."Na yarda." Gaba tayi tana gurd'ewa ga lifayar tsabar wahala duk ta warware sai silmiyowa takeyi tana gyarawa gashin kanta duk ya baje a kafadarta ribbon din ya fad'i a bakin mota......Bayanta yake bi cikin nutsuwa yake 'kare mata kallo warwarewar lifayar ya sanya ya fahimci kayan dake jikinta t_shart ce mai karami hannu sai dogon wando na jins amma ya da'me ta d'am-d'am! ya fito mata da mazaunai tamkar suyi magana....Dauke kanshi kawai tayi yai saurin wuce ta yaje ya bud'e kofar palon....Yana tsaye ta 'karaso da hannu yayi mata alama ta shiga ta tsuguna tana kwance takalminta dake mai igiya ne... Nan ma kasa tsayuwa yayi saboda yanda ya hango brest dinta sun bullotso ta saman d'amammiyar rigar dake jikinta sai ya shige palon ya tsaya...Ta shiga ya mai da kofa ya rufe da key. Had'uwar palon da 'kayatuwarsa sam! bashi ne a gabanta ba burinta kawai ya fad'a mata abun al'ajabin ko ya nuna mata ta zuba masa furgitattun idanunta Cikin wani irin taku iske inda take tsaye ya zura hannunsa cikin aljihu dubu biyar d'in sadakinta ya zaro ya kama hannunta ya sanya mata kana ya kalleta ido da ido yace."Ri'ke sadakin auranki da kyau!! Yau! ni *Ahamdu Musa* na cika d'an halak na tashi daga sunan gwauro na 'yantu na cika cikakken namiji inda nayi tattaki 'kafa da 'kafa na iske har Garkin Gargo na d'aura aure da Wasilatu 'Yar gaske Kawunki Malam mai allo yace na baki sadakin ki a hannunki ki lissafa su dubu biyar ne."! Yana gama maganarshi ya sakar mata hannunta kud'in suka watse a kasan palon.....Bai damu ba ya nufi bedroom dinshi hankalinsa kwance.......Da wani irin mamaki take kallonsa har ya bude dakinsa ya shiga tana kallonsa tana jinn sautin miryarsa na amsa kuwwa a kunnanta *"Wannan shine sadakin auraki Ni Ahamdu Musa nayi tattaki kafa da kafa na iske garin Garko na daura aure da Wasilatu 'yar gaske na tashi daga sunan gwauro na 'yantu Kawun ki Malam mai allo yace na baki sadakin ki da hannuna."* Wannan maganganun kawai takeji a cikin kunnanta kamar yanzu yake fada mata idanunta tsaye a kofar dakinshi.......Kimanin minti goma tana tsaye a gurin tana jajanta maganar gani take ma kamar mafarki take sai da ta kai idanunta kan kudin da suke watse kasan kafet, sannan gabanta ta sake faduwa ta tsuguna kamar wacce kwai ya fashewa a ciki ta dinga daukar kudin tana hadawa guri guda tsaf! ta lissafa su dubu biyar....... *"Ni Wasilatu ni aka daurawa aure da sadaki dubu biyar sai kace bazawara!! Bazawarar ma mara gata da galihu tir'kashi!!!! A fusace! ta mike! ''Karye ne wallahi! Ni Wasilatu nafi karfin ayi min wannan wulakancin Ni za'a daurawa aure ban sani ba Wallahi wannan auran dashi da babu duk d'aya a gurina."!!! Sai ta nufi kofar dakin nasa gadan gadan!! hannunta rike da 'kudin sadakin auran na ta."* _Muje Zuwa_ *BINTA UMAR ABBALE* [7/21, 9:47 AM] Bintu: *'YAR BANGAR SIYASA!!* 🌺 romantic love story🌺 *NA:* *BINTA UMAR ABBALE 🍒* *🌍Manazarta Writes asso* _'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_ ~~~~~~~~ *NA KUDI NE.......!* _Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176 sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko orange_ *NA SADAUKAR MUKU DA WANNAN PEGE 'DIN* Rahima Aliyu Hauwwa Saudia H.Rabi 'kofar bai Fatima Yakubu Nafisat Ahamad Zahra Kaduna Fatima Binta Jamila Abubukar Mum Basma Maimuna bichi Ummu Yusif Atou Tabalak Anty Zeey Kazaure Zainan Khabir Ishak Jamila Yusha'u JiddatulKhairi _*Kuna da yawa sosai masoya wanda baiji sunanshi ba afuwa zamu hadu a gaba ina mutukar alfahari daku masoya Ubangiji Allah ya 'kara 'kauna ta gaskiya*_ ~~~~~~~~~~~~~ *Free Pege20* Lest Free Pege A fusace! ta buga 'kofar d'akin ta shiga, yayi hanzarin juyowa jikinsa sanye da rigar wanka da alama yayi shiri tsaf wanka zai shiga dan yana daf da bakin toilet din....Idanunta a rufe ta durfafo inda yake tsaye yana kallonta ga mamakin sa sai yaga ta d'aga hannunta dake ri'ke da kud'in zata watsa masa yayi hanzarin ri'ke hannun! suka tsaya suna kallon junansu.....Sai yanzu ta lura da irin kayan dake jikinsa, rigar wanka ce mai bud'ad'addan gaba kuma bai daure ba ya sake ta faffad'an kirjinsa mai cike da yalwar gashi yana a bayyane kuma karamin wando ne a jikinsa wanda da ya d'ameshi. da sauri ta sunkuyar da kanta 'kas! gabanta na masifar fad'uwa Ganin yanda wandon jikinsa ya masifar matse shi ba ta ta'ba ganin zahirin namiji ba sai yau! Har yanzu hannunsa na rike da nata wanda kudin ke ciki yana watsa mata wani irin kallo yace."Kar ki kuskura kiyi min watsi da kudi a d'aki idan kikayi sai ranki ya 'baci! hakkin ki ne kije dasu duk wanda ki kaga damar bawa ki bashi wannan bai dami kowa ba." Hannunta ya saki ya kama hanya zai shiga toilet d'in! aikuwa ta watsar da kud'in kasan dakin tana fadin "Wallahi wannnan auran dashi da babu duk daya suke a gurina ka kwashi kudin sadakin ka bana sonka bana ra'ayin auran mutum irinka da har zakaje har mahaifata kasa a dauro maka aure dani to yanzu ba gobe ba sai ka sake ni dan wannan budurcin nawa na mai rabo ne." Da jarumta take maganarta kuma tsakaninta da Allah take....Ya juyo cikin wani irin yanayi yana bin kudin da ta watsar a 'kas! wato dai sai da ta watsar masa da kudi a d'aki saboda taurin kai!! Nufar ta yayi cikin tsanani na 'bacin rai!! Sosai ta tsorata! da ganin yanayinsa sai ta soma ja da baya yana sake tunkarar ta tana sake matsawa gabanta sai duka yake yana daka haka suka dinga yi har sai da suka dangane da jikin bango. (Garu) d'aga hannu yayi kamar zai mareta! sai tayi saurin kauda fuskarta ta sanya dukanin hannunwanta ta kare tana sakin 'karamin ihu!! Shiru taji ta bud'e idonta a hankali tana kallonshi ta kafar hannunta yana tsaye daf da ita ya dafa hannunsa guda a jikin bango ya tokare ta sannan faffadan kirjinsa dake bud'e yana gogar hannayenta, 'Das!d'as gabanta yake fad'uwa lokaci guda ta rasa miyau! a bakinta ya bushe kamas!!! Sai zare ido takeyi wani irin tsoronsa ne ya shige ta mussaman yanda taga zahirin hallitarshi sai ta ganta wata 'yar ficika a tsakaninsa ya za tayi idan wannan 'katon mutumin ya hau ta duka. "Ashe rashin kunyarki ta banza ce! tunda har kika razana tin kafin nayi miki hukunci." Shiru ya dan yi yana kallonta yanda take kyarma! sai uban gumi take hadawa Murmushi ya saki mara sauti ya girgiza kansa kana yace." karki kuskura nayi sabo da dukan ki ko marin ki zaki sha wahala, aure ni nayi ra'ayin na aureki saboda na karya al'kadarinki kin shiga gidan redio kin zageni kin aibatani kinyi min kazafin na zina kawai saboda ki bata min suna a idon mutune to bukatarku bata biya har yanzu da mutuncina a idon mutane na aureki da mummunar niya ba zan munafurce ki ba amma kuma mutunci da 'kimar wannan dattijon ya sanya na janye kudirina a kanki! karyi tunanin ko zanyi wata mu'amular aure dake domin naji baki da wani zance da magana sai na budurci ki sani da budurcinki da babu duk daya suke a gurina domin bashi ne a gabana ba, zan killace a cikin gidana ne domin na taimake ki da wannan yawace yawacen da kikeyi kinga ke idan 'yar halak ce godiya ce zata biyo baya a tsakaninmu dalili kuwa na 'yan taki na aureki tare da killace ki guri guda, magana ta karshe da zanyi miki itace maza ki kwashe kudinki da kika watsar min 'kasan d'aki! ruwanki ne kiyi amfani dashi da kanki ruwanki ne ki bayar sadaka bai dami Ahamdu ba." Bakinta mutuwa yayi murus! sai dai Ubab hawayen dake ambaliya a fuskarta, tayi tayi ta d'ago fuskarta ta kasa saboda yanda taji duk wani alkadari nata ya karye amma Ahamdu yayi mata wulakancin da ba zata ta'ba mantawa dashi ba....Cikin tsawa yace."Kin kwashe kudin ko kuwa."! Hucin maganarshi ya daki fuskarta tunda har yanzu yana kusa da ita ta ina zata wuce ya babbake hanya.....Idonta ta zuba masa tana motsa baki! Ko kusa ko alama bata bashi tausayi ba sai ma wani irin tsanarta da yake ji, ya kauce daga jikinta yana nuna mata kudin da hannunsa.....Tsugunawa tayi ta dinga binsu daya bayan daya tana tsincewa tana sha'kar hanci ta gama ta mike tsaye ba tare da ta juyo ba......Tsaki yaja mai sauti ya wuce toilet abinsa. Yana shigewa toliet din ta fara dube dube a dakin kan mirror dinshi ta nufa ta hau duddubawa key take nema ba ta ganshi ba tayi d'age sosai tana lalube saman wardrobe dinshi, ganin tana wahala sai tayi nufin dauko drowar guda itama ta'ki daukuwa saboda yanayin katakon ba na wasa bane.....Da sauri ta bude wardrobe din tana dube dube can ta hango rigarshi da ya cire a rataye ta ciro tana zazzage ta babu komai a ciki sao gilashinsa da kuma carbinsa mai ma dannai.....Ta mayar da rigar a gaggauce! ta bude drowars ta fara dubawa nan taga tarin mukulai ba tare da 'bata lokaci ba ta d'aukesu ko rufe drowars din ba tayi ba ta fice daga dakin...Yaji lokacin da ta bude dakin ta futa sai jikinsa ya bashi a gaggauce ya cigaba da watsa ruwa a jikinsa ya dauro towel ya fito, nan yaga dakin a hargitse duk ta baza masa kaya....Ya fito palo da sauri, a take yaga kofar palo a bude bayan yasan ya rufe ta da key! Shaf ya manta towel ne a jikinsa da takalmin wanka ya fita a haka can ya hangota suna dambarwa da Masu gadi......Sosai ranshi yayi masifar 'baci! ganin yanda ta zakalkale tana musu masifa har da marin daya daga cikin yaranshi sai dungure masa kai take wai dole sai sun bude mata kofa ta fita!! Taku biyu yayi da niyar zuwa gurin towel dake kugunsa ya kwance nan ya tuna ashe daga wanka ya fito a gurguje ya koma ciki ya zura jallabiya ya fito, sai dai me!? 'Karamar 'kofa ya gani a bude Wasila ta shammace su ta fita.....Wasu daga cikinsu sun bi bayanta, Sauransu ya dinga zabgawa masifa kamar ya yari baki sai bashi hakuri sukeyi suna fadin"Wallahi shamtarsu tayi ta bude karamar kofa ta fita......Hadi ne ya paka mota a inda yake ya kar'bi key din motar rai a 'bace! ya shiga da gudu ya fice daga gidan.......Can ya hangota ta kusa fita daga Estate din tana wani irin gudu Su Garba na binta a baya....Yaji duk lamarin yarinyar ya fuce masa da kai wannnan zubda mutunci dame yayi kama, da ya sani ya shiga yi ace wannan ce matar auranka tana gudu maza na binta. Wani wawan burki! yaci a gabanta! Tsabar wuya da galabaita ya sanya ta zubewa a gurin tana mai da nuffashi!! Ya bude mota ya fito rai a 'bace! sai ta yunkura cikin zafin nama zata sake arcewa da azama! ya sanya mata kafarsa guda a tsakanin tata sai tayo kanshi zata fad'a! yayi saurin matsawa ta kirjinta ya daki jikin motar....Ta dago kafadunta tare da juyo da ita ba tare da 'bata lokaci ba ya kife ta da wani wawan mari! wanda sai da taga gilmawar taurari ta dinga jin dum!! dum!! a kunnenta....Luuuu!! tayi zata sake kifawa a jikinsa ya kauce! ta sake dukan motar a zabure!! ta bude idonta ta dinga ganin zatinsa dishi dishi a cikin idonta.....Kawai sai wasu lafiyayyun hawaye suka wanke mata fuska.....Motar ya bude ya tankad'ata ciki ya mayar da murfin ya rufe kana ya zagaya mazauninsa ya shiga yaja motar, Su Garba kuwa dama tuni sun juya..........Gate din a bude yake dan haka kawai sai ya shiga da motar duk suna tsaye ciro cirko ya tsai da motar ya tsaya yana musu fada da gargadi kan duk wanda yayi kuskuran sake barin ta ta futa daga gidan to a bakin aikinsa." Dukaninsu suka shiga bashi hakuri tsabar haushi bai ma tsaya ya sauraresu ba ya fuzgi motar a guje ya wuce. Yanayin parking ya fito hade da bude kofar da take tana kwance ruf da ciki kan site gashinta ya wargaje yayi buyaya lifayar ma ta cire dan saura kadan ta rabu da jikinta, Tsawa ya buga mata kan ta fito masa daga mota! shiru yayi ya sake kwatsa mata wata tsawar yaji shiru, sai da yayi magana sau biyar ba ta amsa ba, ya zura jikinsa cikin motar ya burkitota fuskarta ya tsirawa ido yana kallo....Idanunta a rufe ruf! dai-dai da gashin idon baya motsi! yaji faduwar gaba kadan ta kamashi Hannunsa ya dora a kirjinta minti biyu ya dauke! da sauri! ya kara hannunsa saitin hancinta nan ma yayi minti biyu babu alamun nuffashi a tare da ita....Babu shiri ya tattaro ta jikinsa ya taraiyaye ta daukar jarirai yayi mata ko motar bai rufe ba ya nufi cikin gidan da ita, hankalinsa a tashe. *_TO JAMA'A NAN NA KAWO 'KARSHEN FREE PEGE NA WANNAN LITTAFIN GA DUK MAI BUKATAR CIGABA DA KARANTAWA SAI YA DUBA BAYANAN DA NAYI A SAMA KAZO KA BIYA KUDINKA KA KARANTA DOMIN KAR AYI BABU KAI WANNAN LABARI DAI YANZU MA AKA FARA AKWAI TAFIYA A GABA WANNAN D'ANDANAN GISHIRI NE..........HAR KULLUM INA FAD'A CEWA KUD'IN KARATU KIKA BIYA BA NA MALLAKA BA IDAN KIN YARDA KIZO KI BIYA KI KARANTA IDAN BAKI YARDA DA WANNAN TSARIN BA TO DAN ALLAH KAR KIZO KI BIYA KI FUTAR MIN DA BOOK KI RUSA NI KIYI ZAMANKI NAGODE SANNAN DUK MAI BUKATAR KARANTA NOVLS DINA AKWAI COMPLETED KAN FARASHI MAI SAU'KI KAR KU MANTA DAI HAUSAWA NACEWA SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA_* 'WADANNAN SUNE LITTAFAN NAWA *NANA KHADIJA* *YARO DA KUDI* *GIMBIYA BALARABA* *TSANTSAR BUTULCI* *BABBAN YARO* *LADIDI KWADAGA* *MASHAHURI* *SADAUKI OMAR* *RUWAN DARE* *NI DA YAYA SADAM* *'YAR BANGAR SIYASA* Kar ku manta da cewar ni Binta Umar Abbale nice mamalakiyar wad'annan novels din.....Saboda haka ga duk wani mai bukatar ya karanta completed dinsu sai ya nemi numbar ta ya biya ya karanta hankali kwance, Ina kara tunasar daku cewar kada kuje ku biya wani ko wata kudin wannan novels din dana jera muku 'karya yake 'karya take zasu siyar muku da hakkin da bana su ba kumai ba zama lallai su baku complete ba shikkenan sunci kudinku a banza, hanya mafi sauki anan ita ce ku tuntu'be ta wannan numbars din nawa *08089965176* *07084653262* Masha Allah masoya sai naji ku🙋🏻‍♀️ *BINTA UMAR ABBALE* . *************************⬇********************** ************* Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ ************************** Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels