Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels https://chat.whatsapp.com/IcgqoNAQ9V612x1JRXBMVS 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 WATA KISHIYAR 🥰👹 (Alkhairi CE KO SHARRI) 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 Na Maryamah_Mrs AM Page 1 Lagos Nigeria Cikin sauri nake har hada takaddun ina qara duba agogon hannuna dukda nasan dakyar idan bazan makara, qarfe Tara jirginmu ze tashi zuwa Kano dan halartar wani conference meeting da aka turani daga office din mu. Gaba daya befi saura 45 mins Taran tayi ba inda na dan samu kwanciyar hankali babu nisan tazara tsakanin unguwar tamu zuwa Airport din. Buda qofar dakina da akayi da dan qarfi ya sani cewa " not now please" azatona daya daga cikin yara nane sedai shirun da naji yasani waiwayawa, megidan ne da kansa wato ENGINEER BASHIR AHMAD da nake Kira da Baban Ali Yara kuma suna ce masa Abbi, Aliyu sunan babban Dana wanda Sunan Amininsa ne ya saka masa da ya rasu sati biyu kafin na haifi Aliyun. Fuskar sa a hade duk da kasancewarsa dama ba mutum bane me fara'a amma dai ai yanayimun nidai. Kallona yake kamar yanda nima nake kallonsa fuskata dauke da gajeran murmushi nace "Baban Ali ka ganni har yanzu ko? Wallahi Amna ce tayi mun shirme tun jiya da dare nace ta zubamun papers din nan a jaka ashe batayi ba (Amna Qanwata ce kuma Autar mu danake ruqo bayan rasuwar Mahaifin mu da Mahaifiyarmu ta sake aure). "Uhm" kawai yace mun yana nufar gaban mirror na, ban damuba na qarasa zuge jakata tareda ratayata na dauki wayata dake gefe kafin na nufi qofa da niyyar fita "Idan kin dawo zuwa end of the month ku fara shirya zaku koma Gombe" muryarsa ta doki kunnena, "To meya faru kuma? Bari dai in na dawo se muyi maganar a nutse" na sa kai na fice daga dakin. Already Emmanuel Driver office dinmu na waje yana jirana dan haka da sauri na fita ina amsa a dawo lafiyan da yara suka biyo ni suna yimun. Bayan na nutsu a bayan motar zuciyata ta tafi tunanin me zamujeyi a Gombe kodai wani abune ya faru a bangaren sa? To bangarensa mana dan nidai ko da safiyar nan nayi waya da yan uwana kuma ba abinda akacemun ya faru to ko Matar tasa ta haihu ne? Aa in haihuwa tayi ai kaitsaye zece Amira ta haihu bawai kawai zakuje Gombe ba. Haka dai naita tunane tunane har zuwa Sanda Jirgin mu ya tashi. A matuqar gajiye na shigo gida kusan qarfe 9 na dare, se yanzu nai dana sanin qin bari na kwana a Kanon dan jirgin 6 na biyo na dawo saboda ban gayawa yarana zan kwana ba nasan bazasuji dadi ba musamman da yake Gobe Saturday ne munsaba zama a gida. Bayan nayi sallar Magriba da Isha naci abincin da Aliyu ya kawo min, ina zaune tsakiyarsu kowa da hirar da yakeyi mun wani irin farin ciki yana cikamun zuciya. Tabbas yaya rahma ne, a duk sanda na kalli yara na ina jin tamkar bani da sauran wani damuwa a rayuwa se fatan Allah ya rayamun su. Amna qanwata dake matsayin babbar Yata a yanzu nada shekaru 15 tana SS2 se Aliyu shekaru 13 ya shiga SS1 saboda Jumping da makarantarsu suka masa dan Yaro Masha Allah yana da qoqari tamkar Mahaifinsa. Jafar ke bi masa se Farida, Abdallah, se yan biyu na masu shekaru 5 Ahamd da Muhammad su Shidan nan sune rayuwata ban kuma hadasu da komai ba. Har qarfe 11 muna zaune duk da irin gajiyar da nayi dan har wani ciwo kaina yakeyi, sauqin dana samu tun a kano na aika da report din komai Office dan haka Weekend din nan bacci zan shaqa. Sallamar Baban Ali ce ta katse ni na dago ina kallonsa da mamaki dan Duk hirar da muke a zatona yana Dakinsa dan shi dama be fiya zama ayi irin dogon hirar nan dashi ba, gaba daya muka masa sannu da zuwa ya Amsa yana nufar dakinsa. Se a sannan na tuna ko kirana beyi ba yaji ya na sauka, Se na miqe nima ganin kamar baya cikin yana yi me dadi dan in lafiya seya dan tsaya damu ko ze shige dakin ga kuma fita da yayi da daren nan, tashina yasa suma duk suka miqe mukayi exchanging Hugs kafin Mazan suka nufi dakinsu matan ma haka. A tsaye na same shi yana cire rigarsa na qara sa taya shi ina cewa "Ashe baka nan, na tambayi yara sukace kamar Zoom meeting kukeyi kana daki" "Uhm" ya kuma amsa mun. Nan da nan naji raina ya baci dan gaskiya ina da saurin Hasala amma fa ina da sauqin kai rainin hankali ne bana so, to rainin hankali mana ace wani inje kano in dawo a ranar ai ya tambayeni ya hanya koda yake dama duk satin nan tunda ya dawo Weekend naga yana wani fuzga ban kula shi ba nasan qiris yake jira ya sauke abinda ita yar Gwal din baze iya mata ba. A raina naja tsaki tareda cewa "Dan rainin hankali wato ga bolarka can Yarinya ta bato maka rai kazo ka juyemun to bazan tanka ba". Ganin ya shiga Toilet yasa na fita, dakinan yaran na shiga can na tarar da Ahmad da Moh suna kwasar Dambe abun haushi wai Jafar na musu waqa Su Casu bame rabasu, haka suke kamar Kaji kullum fada kamar ko yaushe kuma akan Gado ne saboda Bunk ne dasu Aliyu da Jafar se nasu Muhammad, Ahmad da Abdallah Babban gado suke kwana su ukun to wai se ace A gadon Yah Jafar za'a kwanta shine a sama dan haka yau in wannan ya kwana gobe wannan amma rigima irin ta Ahmad se yace sedai dan uwan ya bashi kwanansa. fada na musu kafin kwantar dasu dukka a gadonsu muka karanta Azkar din bacci naja musu qofa tareda kashe fitila. Amna da Farida tuni sunyi bacci suma Adduar na qarayi musu ma ja musu qofar na shiga dakina, jikina na qara gyarawa tareda daukar wayata na ja qofar na fita. Har Baban Ali ya kwanta ganin rigima yake nema yasakani kashe fitilar da ya bari a kunne nima na nemi wuri nesa dashi na aje muqamiqina wata gajiya na sake saukar mun. "Kufa fara Shiryawa Next week zaku koma Gombe" ya sake fada, sena gyara kwanciyata ina cewa "Allah ya kaimu dan wallahi na gaji bacci nake so inyi kuma na biye masa surutu zamuyi tayi dan dai yasan abinda yake fada bame yiwuwa bane tunda na fara aiki ai bama zuwa Gombe se lokacin hutu shima ba kowanne ba se yayi corresponding hutun Yara da nawa ko kuma da wani babban dalili amma rana tsaka ana tsakiyar Term yace wani tafiya ko yar Gwal din ce ta haihu wlh bazan bar aikina na tafi ba duk sanda nai hutu naje mata Barka. Ina wannan mitar bacci yai awon gaba dani da ban farka ba se Qarfe 7 harda Rabi na safe. Yau Baban Ali halin fulani ya motsa kenan ko ya tashe ni sallah dan gajiya ce ta danne ni banajin ko juyi nayi a baccin nan. A gurguje na dauro Alwala nai sallah bayanna idar da azkar dakyar na miqe dan bawai baccin ya sake ni bane na fito palour, Amna da Farida na zaune Se Ahmad dake bacci a kan Three sitter. A tare suka gaida ni na amsa ina tambayan ina Su Jafar Amna ce tace sun fita Jogging da Abbi "Kunyi karatun Asuba ne" na tambayesu suka amsamin da eh Mamaki ya qara kamani amma na dake na shiga kitchen Tea nake so nasha kafin na koma bacci. Kafin na fito sun koma dakin su har Ahmad sun dauke shi daga wurin dan haka na zauna kan Dining ina shan Tea ina tunanin meya ke damun Eng ne haka. Haka na qarasa na koma baccina wanda koda na sake farkawa 12 harta gota na rana. A dakin nai wanka na shirya kafin na fito ina jin gajiyar ta sake ni. Palour kamar Gidan biki saboda hayaniya Farida da Jafar na musu akan wani film da suka kalla. Da gudu Ahmad da Moh suka nufoni har suna neman kadani na riqe hannayensu muka qarasa cikin palour. "Ina Abbi" na tambayesu dan koda na farka ban ganshi a dakin ba kuma dai nasan Saturday Sunday yana gida seda babban Dalili yake fita kafin su bani amsa ya shigo da sallama ciki ciki, kallo daya yamun ya dauke kai tareda nufar kan Dining ya aje abunda ya shigo dashi, jin an fara kiran sallah yace su tashi suyi Alwala suka wuce masallaci da Mazan mu kuma muka tayar da tamu a Gida. Abun mamaki bayan sun dawo kuma se gashi ya zauna a palour tareda yaransa suna hira dan nidai kitchen na shiga na fara qoqarin dora mana abincin rana dan na dare a waje zamu je muci in yaga dama kenan. Da wuri na gama dan Garnished spaghetti na mana se na dumama Grill Fish din daya shigo dashi ko a ina ya samo da safen oho. Farida da Amna na kira suka jera komai akan Dining kafin muka zauna gaba daya banda Abbi dake amsa waya sena dakata har ya gama sannan na masa maganar Abincin. "Kifin kawai zaki kawomun da juice" ya fada. Ban kawo komai ba dan nasan spaghetti bata wani dame shi ba amma dai yana ci musamman irin wadda nayin, na hada abinda ya buqata na kai masa sannan na koma muka ci gaba da cin abincinmu. Koda muka gama wurinsa Twins suka koma da Abdallah Jafar da Aliyu suka kwashe kwanuka zuwa kitchen tareda wanke wa Amna da Farida kuma daki suka shiga Farida zata yiwa Amna tsifa. Nima palour na koma muka hadu muna yar hira sedai abinda na fahimta Baban Ali yaransa kadai yake amsawa dana saka baki se naji yayi shiru tsam na miqe Ahmad ya tashi shima ze bini dan haka yake indai muna gida da na dauke qafa ze aje tasa nace masa "koma ka zauna aiki zanyi" ban ma shiga dakinsa ba na shige nawa. Kwanciya nayi kan gadona ina replying whatsapp messages daga nan muka shiga hira da yayata Alawiyya da muke Uba daya, tamu tazo daya nan na shiga bata labarin abinda Baban Ali ya tsiro dashi kuma. Dariya tayi tana cewa "kedai da Engineer Miskili kafi mahaukaci ban haushi" nan muka ci gaba da firar mu ban san lokaci ya tafi ba seda naji ana kiran La'asar. A dakin nayi sallata ina idarwa na shiga wanka, daidai na fito naji Knocking nasan yaran ne basa shigomun daki sena basu izini koda kuwa Ahmad da Muhammmad da suke qanana. Bayan na amsa Abdallah ya shigo, sak kamanninsa da yanayin Miskilancinsa irin na Bashir ne sedai duk cikin yarana ya fisu haquri wannan kuma halin takwaransa wato mahaifina ya gado. Cikin sanyinsa Yace "Mami Wai Abbi yace kiyi masa text na abinda zamu taho miki dashi". Se naji wani dus kamar yaya na masa text? Ba tare zamu tafi ba? Har na bude baki da niyyar tambayarsa se kuma na fasa nace masa " Kacewa Abbi ya leqo ina son magana dashi". Da toh ya amsamin kafin ya fita ya barni da mamakin wannan sabon rainin hankalin. Abbi Lokacin da yaron ya gaya masa saqon har sun shiga mota ya ma kunnata, ganin idon su ya sahe cewa yana zuwa ya fito yana qara daure fuskar sa. Tana shafa wa santala santalan cinyoyinta mai ya sameta, yaso ya shagala da binta da kallo dan a duniya ASMA'U takai duk inda mace ake so takai, Asma'u mace ce guda harda Rabi wallahi ta ko ina ta hadu bakuma ze taba manta halaccinta a rayuwarsa ba shikansa ya kasa gane dalilin da yasa yake mata wasu abubuwan. Waiwayowan da tayi tana qoqarin sakin towel din jikinta dan sam bata ji motsinsa ba yau saurin juya fuskarsa dan a wannan bangaren baya taba iya tsallake tarkonta. Jikinta tamkar Magnet yake ga idonsa, a kullum gani yake kamar qara mata kyau da sura akeyi Ma'u bata tsufa. "Au Abbi ka shigo ashe, Ban gane me Babana yake fada ba yau kuma danwaken zagaye zakumin kenan" na fada ina cigaba da zura rigata dan nayi sauri na shirya nasan Bashir baya son jira sam a zatona ma dalilin daya sa zasu fita su barni kenan. "Nop banyi niyyar fita dake bane, kiyimun text din abinda zaki ci mu taho miki dashi in kuma beyi miki ba shikenan" kawai yasa kai ya fita. Se na raka bayan sa da kallo kawai kamar wata doluwa, " tofa Baban Ali kodai gamo yai da Aljanu ne" na tambayi kaina ina qara cika da tsabar mamaki. Share Share Share https://chat.whatsapp.com/IcgqoNAQ9V612x1JRXBMVS 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 WATA KISHIYAR 🥰👹 (ALKAHIRI CE KO SHARRI) 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 Na Maryamah_Mrs AM Page 2 WATA KISHIYA(ALKAHIRI CE KO SHARRI) Ni kadai tsuru kamar mayya a gida har qarfe 10pm ga gyangyadi inayi amma na kasa shiga daki na kwanta saboda tsoro gashi har sannan basu dawo ba. Tsayuwar motarsa da naji ta sani miqewa daidai lokacin da Ahmad ya kwaso da gudu yana kwallamun kira "Mami Mami" "Na'am Ahmad meya faru" na fada ina tare shi, labarin inda sukaje ya fara bani, gurin wasan da ya kaisu, Favorite restaurant dina sukaje suka ci abinci daga nan suka tsaya Cinema sukayi kallo abinda ya saka su yin dare kenan. Saboda gajiya kowa dakinsu suka nufa, dakaina nayiwa Twins wanka na shirya su kafin 11pm gida yayi tsit duk sunyi bacci sannan na shiga dakina raina yana suya, Tsabar bacin rai ko takan take away din da sukamun ban bi ba nima wankan na shiga ina sake danne zuciyata na shirya na nufi dakin Baban Ali. A kan gado na sameshi yayi daidai yana amsa waya fuskarsa dauke da wani shegen murmushin da bazan iya tuna rabonda yayi mun shi ba ko ba'a fada ba nasan da Amira yake waya dan Baban Ali bashida kwashe kwashen yammata, Ada ni kadai ce a rayuwarsa kafin ya kwaso min Alaqaqai. Wayar dana tarar yana yi ita ta qara bata mun rai saboda wannan ai wulaqanci ne ko? Nasan matar sa ce amma ya kamata nima ya mutuntani idan zeyi wayarsa se ya nemi kebantaccen wuri bawai cikin dakina akan Gado na ba, wannan sabuwar ta'asar da ya samu ta fara kaini bango dan haka ban san sanda na saki wani wawan tsaki ba ina janye ido na daga kansa bayan mun hada ido. "Ke dawa kike tsaki?" Ya tambayeni still wayar na kunnensa. "Ni da waye a dakin" na fada raina na qara quna. "Anty ce ko" na jiyo muryar Amira na tambayar sa daidai sanda na duqa kusa dashi dan na dauke Safar daya ajiye akan gadon sena daga sauti yanda nasan zata jiyo nace "Nice din yar iya ko kina da magana ne" "A ko yaushe ina gaya miki ki ringa jan girmanki ko? Amma shikenan" ya fada yana miqewa daga kan gadon ya nufi qofa. Wani baqin ciki ya tokare mun wuya, kawai na haye gadon na kwanta tareda fashe wa da kuka. Duk yanda nake daurewa se Bashir ya qure ni tunda ya auri yarinyar nan ban sakeyin sati ba tare da nayi kukan baqin ciki ba shikenan ni a haka zan qare? Bansan sandaya dawo dakin ba na dai farka cikin dare naji mutum ya kwaqumeni aiko na ingizashi da qarfi har seda ya farka na tashi daga gadon na shige toilet. Fitsari nayi na dauro Alwala, hijabina na zura na fara jero Salloli tare da dogayen Addua. Kamar kullum a duk sanda muka samu sabani na fara sallar dare nan haka ze zabga tagumi yana kallona in ya gaji shima ya to Alwalar ya tada Sallah (bawai dan banayi ba Aa nafi tsawaita Idan mun yi fada dan karna kwanta kusa dashi dan duk bala'i bama raba gado 😂😂) nasan me yake tunani qila qarar sa nake kaiwa gurin Allah ko 😂😂 wallahi ko daya duk abinda Bashir yake mun ban taba yi masa Allah ya isa ba sedai ma in roqi Allah daya yafe masa ya kuma bashi ikon Yin Adalci a tsakanin mu ya ci gaba da bashi yanda zeyi ya kula damu. Ko ba komai nasan Bashir yana sona nima kuma ina sonsa to ban rabu dashi a lokacin Matsi ba se yanzu da dadi ya samu se in tafi in barwa yar taka haye?? ina ba wannan magana. Ban sallame ba har seda aka kira sallar Asuba, ina kallonsa ya fita masallaci kafin nima na tashi nayi Raka'atanul fajir sannan na bada Farillah. Rashin samun bacci cikin dare yasa ina idarwa ko Azkar ban samu yi ba na koma bacci, sanda na farka goma harta gota dan haka anan dakin nayi wanka na shirya kafin na fito palour. Ko ina qalqal sun gyara dan ko kadan banyi wasa wurin koyawa yarana aikin gida ba komai nidasu mukeyi bani da me aiki tunda har kuma yanzu dana ke fita aiki da safe kafin mu fita mukeyin komai tunda kuma ba wuni muke a gidanba baya yin datti. Babu kowa a palor se Baban Ali yana aiki a system dinsa ya dago yai mun kallo daya tareda mai da kai ya cigaba se na qarasa kusa dashi ciki ciki nace masa ina kwana dan har yanzu haushin sa nake ji, se ya amsa ba tareda ya kalleni ba. A dakin Boys najiyo hayaniya da alama PS sukeyi tunda suna da Tv a dakin nan suke yin Game dukda lokaci da yawa yana dauketa saboda karsu shagala da wasa a qi karatu amma Weekend dama aikin kenan wani sa'in hardashi zasu hada anan palour suyi. Kitchen na nufa dan naga sun kwashe kayan kan dining, a roba na tarar da dankali ciki ruwa an yanka su, nasan Amnace ta ajiyemun tunda tasan nafison dankali da an kwashe daga wuta nan da nan na maida man da sukayi suya na zuba kafin na debo kwai guda uku na fasa tareda zuba abubuwan da nake da buqata a ciki, ina kwashe dankalin na maida wani pan din na soya kwai, scramble nayi dan ban fiya son me fefe ba na juye akan plate din chips na zuba Ketchup a gefe na fito. Ta gabansa na wuya ina juya jiki tareda baza masa qanshin turarukan dana fesa aikuwa naji yanda yaja numfashi da ajiyar zuciya ina kuma jin idanunsa akaina har na zauna a dining amma kafin na juyo ya dauke idonsa, girgiza kai nayi ina sake cika da mamakin Bashir a raina haka naja kayan tea na hada ina ci ina dan kallon drama da akeyi a Tv. Har na gama ci babu wanda ya leqo a yaran Gogan ma anata latsa laptop kamar besan Anyi digona a palour ba sena taso na dawo cikin palour na nemi 1 sitter dake facing nashi na karkace ina latsa wayata nima. Whatsapp na shiga group dinmu na Secondary na bude aikuwa na tarar da chats bila adadin, ban samu damar bi ba saboda wasu ne suke qara shigowa se kawai na fara bi daga nan. Ban karanta message din mutum hudu ba na fuskanci dalilin ubannin messages din dana gani ashe Labor zaayiwa kishiya (Labor prefect dinmu da muna school kuma abin dadin qanwar daya daga cikin yan ajin namu qawarta ta hannun dama zaa auro mata, tasan mijin zeyi aure amma bata san yarinyar ba se yau da taje karban lefen Qanwar Qawarta taga dangin Mijinta ne yan kawo lefen 🤣🤣😂😂🤣🤣😂) Wata muguwar dariya na sheqe da ita har ina kwarewa da ta saka Baban Ali dagowa ya zubamun ido, yasan Ma'u sarai tabbas mugunta ta gano shine dalilin wannan Dariyar. Be gama tunanin kuwa ba na fara voice note still ina dariyata nace "Alhamdulillahi layi ya fara ja ashe? To Allah ya qarawa mazajenmu budi suyi ta auran mana qannemu" na tura ina sake sheqewa da wata dariyar ganin yanda Safiya Sani Labor keta kumfar baki da daukan Alwashi kala da kala ita ma yayar Amarya Zulaiha Balarabe tana aiko da nata. Masifar da Safiya takeyi seta tunamun da lokacin da za'ayimun tawa kishiyar mun hadu gurin gate together dabanyi niyyar zuwa ba saboda a lokacin bana cikin nutsuwata. A kallo daya zaa gane damuwar da nake ciki duk na hargitse, na tuna yanda ta sakani a loko tana mun wa'azi. "Wallahi Asma'u kin bani mamaki kin kuma bata wayonki kamar wadda bata san Allah ba, duk ina karatun islamiyyar da kikayi? Kin karanta Alqur'ani tsaf kin haddace da fassara amma kina nema ki kasa aiki dashi. Karin auran nan kinsan umarnine na Ubangiji in har Namiji nada hali da biyu akace ya fara sedai ko in baze iya adalci ba ko kina so kice Bashir ba Adali bane?? Sannan ma ke ai kiji dadi koba komai kinsan wadda za'a auro miki ciki da bai baki da fargabar azo a tarwatsa miki gida tunda Ai Amirah kusan tarbiyyarki ce ma. Haka matar nan ta dage tanamun wa'azi har na sauketa kan layin gidanta mukayi sallama na wuce a raina ina Addu'ar insha Allahu itama se an mata taji in da dadi (Ni fa alokacin duk wanda ya bani haquri se na masa Addu'a Allah yasa shima a masa kuma Alhamdulillah gashi tana karbuwa kuwa 🤣🤣). Wani mulmulen ashar ta dannomun bayan taji voice dina nan kuwa na samu nayi na ci gaba da kunnata kafin kace me fada yabar kan Yayar Amarya ya dawo kaina harta na jcewa qila dani aka hada baki nace oho dai aikin gama ya gama biki saura 2 weeks , wannan nishadi ya mantar dani wanzuwar Baban Ali a gurin har wurin 12 sannan yara suka fito muka ci gaba da sabgogin mu. Gaba daya dai haka muka cinye weekend din ba dadi tsakanin mu Monday muka koma aiki. Office dinsa yafi kusa da makarantar yara dan haka kullum shi yake fita dasu ni kuma tunda ina rigashi tashi sena biya na debo su amma yau bayan mun fito gaba daya har Ahmad ya kama handle ze bude gaban mota ya dakatar dashu da cewa "kuje Maminku ce zata kaiku" Sororo nayi ina kallonsa araina nace meye haka toh sukuwa yara suka dauki Murna dan dama mitarsu kullum yawanci Friends dinsu Momys dinsu ke kawo su school dalilin ma daya sa na dawo ina dakkosu ke nan dan da duk shiyake hadawa. Tafiya ta qaru haka nayita sauri gudun makara na samu na ajiyesu amma dukda haka ni seda nayi latti dan school din tana gaba da office dina innaje sena dawo baya while shi kuma yana gaba da school din dole seya wuceta zeje nasa office din. Wuni nayi ina mamaki wato duk sati da sabon salon da ze bullo dashi? Allah dai ya kyauta. A daddafe muka cinye satin kullum kuwa sena makara dan kafin na kaisu na juyo traffic ya fara haduwa, abun takaicin wani sa'in zamu hadu a hanya har Horn ze mun in na tsaya ajiyesu ya wuce ni abin na qona mun rai ni kuma nayi alqawarin bazan masa magana ko na tambayi dalilin dayasa yake hakan ba nasan dai duk sare sarin neman fitina ne in tanka su samu nayi dani a dangi to an dena (Dangin fulani dangin magana 😎). Muna haka Weekend ya zagayo wannan karon ma yaransa ya diba suka fita yawonsu, abunda ya ragemun haushi ranar Saturday wuni nayi rama baccin gajiyar sati daban samu nayi ba danayi sannan Sunday fita mukayi nima da Matan layin mu dama muna haka once in a month zamu hada picnic muje beach a dan warware takaicin Namiji 😂😂 mu shaqi iskar duniya to wannan Lahadin ma can muka wuni dan a gida na fita na barsu ma muka dawo kusan lokaci daya. Yanda Bashir ya tsume haka nima na tsume na fita a sabgarsa sam tunda haka yake da buqata ina jinsa ze raba dare yana waya da Amaryarsa har inji yana ce mata tayi haquri ta kusa dawowa kusada shi ai, wani lokacin naji haushi wani sa'in nayi mamaki kai Namiji dai a barshi kawai. A da idan aka cemun Bashir ze sake kallon wata mace da sunan soyayya zance qarya ne amma daga sanda ya koyamun hankali ko ji nayi mace na shan Alwashi akan Namiji zan dakatar da ita dan tabbas Akan Bashir na sake yarda da akace Namiji Badan goyo bane (Inji Asma'u fa 😁). Ranar Laraba na tashi da ciwon kai da ya saukar mun da zazzabi, ina nade akan gado har Bashir ya fita masallaci, a zaune na iyayin sallah ina idarwa na koma kan gado na nade har ya dawo ya fara shirye shiryen fita office. Dukda ya ganni akwance which is unusual hakan be saka ya tambaye ni dalili ba abinda yai matuqar qona mun rai ace har mun kai matsayin haka kamar wasu maqiya to wai duk me yayi zafi ne? Seda ya gama shirinsa tsaf sannan ya kalleni "Yau bazaki je aiki ba kenan? Se ki tashi ki miqasu karsu makara" yasa kai ya fice daga dakin. Wasu hawayen baqin ciki ne suka fara tsere a fuskata, idan Bashir ya gaji da zama dani gara ya fito ya fada mun yafi wannan Kisan mummuqen da yakeyimun ai, shigowar Jafar ta sakani share hawayena, ya matso kusa da ni yana cewa "Mami mun shirya fa ko Abbi ne ze kaimu yau?" Cikin muryata da kuka ya fara dishewa nace mace "Kuje maza ku bishi Jafar bani da lafiya" Nan da nan fuskar yaron ta chanza zuwa tausayi yace "sorry Mami kinsha magani toh? Bari na hado miki breakfast to Abbi baze kaiki Asibiti ba?" Dole na qirqiro murmushin dole nace "it is not that serious Jafar Kaina ne yake ciwo nasan stress ne dana qara hutawa ze dena, maza kuje ku tafi and don't tell your brothers ku wuce Makaranta kawai Allah yai muku Albarka ya bada Ilimi me amfani" na qarasa ina dafa kansa se ya amsa da "Amin Mami Allah ya baki lafiya, Bye love you" ya mun peck a goshi ya fita da sauri dan su kansu kwana biyu ba wani gane kan Abbin suke ba. Yana fita na miqe dakyar na tsaya bakin window ina hangensu, Shiya gaya musu Abbi ne ze kaisu dan haka suka fita da sauri dan har ya gama Shan Tea ya fita yama kunna mota. Da ido ya bisu ganin sun jere masa a gaba, cike da baqin miskilancinsa yace " yadai kunzo kun mun layi a gaba?" "Abbi Mami ce tace kai zaka kaimu bata da lafiya" cewar Jafar. Seda gabansa ya fadi jin bata da lafiya dan ciwon Asma'u ba abune me sauqi ba, irin mutanen nan ce da suke dadewa basuyi ciwo ba amma in ya kwanatar dasu kamar bazasuyi ba. Harya niyyata daya koma yaji me yake damunta se wata zuciyar tace masa qila dan taja attention dinsa ne ya sakata kwanciya tace musu bata da lafiya dan Asma'u can pretend yasanta sarai dan haka ya qara gintse fuska tareda bude qofar sa ya shiga yana cewa "kuje ku ce mata tazo ta kaiku you are getting late" "Abbi kana jifa yace bata da lafiya base ka kaimu ba tunda hanyar zaka bi" Farida ta fada dan ita yar gaba gaba ce daman, be amsata ba yai wa motarsa key ya qara gaba se suka rakashi da idanu gaba daya kamar yanda nima Mamakin sa ya nemi kashe ni a tsaye BASHIR dai shine haka? BASHIR dana sani me jarabar son yaya da tattalinsu kamar kwai, to kodai shiga tsakanin mu akayi da BASHIR ne????? https://chat.whatsapp.com/IcgqoNAQ9V612x1JRXBMVS 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 WATA KISHIYAR 🥰👹 (Alkhairi CE KO SHARRI) 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 Na Maryamah_Mrs AM Page 3 A salube suka shigo gidan gaba daya suka zauna A palour banda Abdallah daya zarto dakin da nake, yana ganina ya wullar da school bag dinsa ya taho da gudu jikina se ya sa kuka, nasan kukan me yake Abdallah akwai son karatu indai ba ciwon gaske ba baya Missing school. Bubbuga bayansa nake da sigar rarrashi ina qoqarin hana nawa hawayen fitowa. “Mami kinga Abbi ya tafi ya barmu kuma Yah Jafar ya gaya masa bakida lafiya amma ya tafi” ya fada in between tears, se na jashi zuwa gefen gadon dan jin kaina yana dada sarawa ga zazzabin na sake ruruwa. “Ka dena kuka, sauri yakeyi yana da meeting ne shiyasa” “Mami bafa yanzu bane se 10 naji yana waya da Uncle Samuel ai” “Abdallah bana hana ka ba, idan babba ya fada maka magana ka dena jayayya” “Amma Mami...” “Shiii ya isa kirawo mun Amna se na kira muku Uber ya kaiku” na katse shi dan bana son aja maganar, fita yayi ba jimawa Amna ta shigo itama fuskarta da damuwa. “Ki dauko wayata kiyi muku order Uber bazan iya driving ba bana jin dadi” na fada mata ina kaiwa Kwance jin jiri na dibana. “Mami ko mun tafi ma kafin muje mun makara bazaa bude mana get ba sedai kiyi waya ki fada bazamu zo ba”. Agogo na kalla tabbas kafin a samu uber su tafi lokaci ya qure dan haka na miqa mata hannu ta bani wayar, Number da suka tanada dan wani uzuri nayi dialing dakyar ina ringing kadan suka amsa, cikin muryata dake nuna halin da nake ciki nayiwa receptionist din bayanin Bazasau samu zuwa ba bani da lafiya Abbinsu kuma yayi tafiya, fatan samun sauqi tayimun tareda cewa idan gobe ma babu me kawo ayi musu Registration na school bus tunda tana zuwa har nan estate din namu, shaf na manta da zancen ma school bus se yanzu dan haka ba bata lokaci nace tayi kawai. Har na gama Amna na tsaye bayan na aje wayar tace “Mami in kawo miki ko tea kisha se kisha Paracetamol kafin Abbi ya dawo kuje Asibiti?” Kai na daga mata ta fita ba dadewa se gata da try ta doro tea se toast bread da kuma paracetamol da ruwan roba. Da daddaya suka shigo suka mun sannu har sannan Amna na tsaye seda na shanye ta ballomun maganin nasha nakwanta sannan ta fita. Koda na farka bayan Azahar na danji dadin jikina dan zazzabin ya sauka sefa ciwon kan da sauran jiri da nake ji, wanka na lallaba nayi na dauro Alwala a raina ina qara mamakin Baban Ali da haryanzu ko waya beyo yaji sun tafi ko basu tafi ba. Agunda nai sallah na zauna naji anyi knocking, izinin shigowa na bada Aliyu ya shigo da Sallama hannunsa dauke da Babban try da suka dora abinci. “Mami kin tashi tun dazu muke leqowa kina bacci” “Na tashi Yaya (haka nake kiransa saboda qannensa su saba) ina su Ahmad naji shiru?” Na tambaye shi “Bacci suka kwanta bayan mun dawo daga masallaci, Maman Ruth ta shigo muka ce mata kina bacci(Maman Ruth maqociyarmu ce)” “Lallai an samu yanda ake so bacci yanzu, me kuka dafa ne” na fada ina jawo try din gabana. “Irish porridge Yah Amna ta miki mu kuma Rice and Beans muka ci da fish”. Kwanon na bude faten se tururi yake da qamshi kai kace Wata babbar chef ce tayi girkin. A plate na zuba wanda zanci muna dan hira da Aliyu har na gama ya kwashe kayan ya fita se nima na fito palour dukda dauriya kawai nakeyi amma kaina yana ciwo sosai, ban idasa zama akan kujera ba wani irin jiri ya kwashe ni daga nan ban sake gane komai ba nidai na farka kawai Na ganni kwance a gadon dana tabbata na Asibiti. BASHIR Tunda ya bar gidan hankalinsa ya kasa kwanciya, har ya kai get din estate din ya juyo da niyar daukansu se kuma Shedaniyar zuciyar da take ingizashi ta sake yi masa fanfo. Har ya kai office yana tunanin sun taho ko basu taho ba lokaci lokaci yana duba Mirrow koda ze hango su a bayansa amma shiru harya wuce makarantar tasu. Yana shiga Office be zauna ba ya kira layin makarantar ya tambaya ko sunzo nan matar ta sanar dashi Madam ta kira ta bada excuse ai haka ya aje wayar jiki a sanyaye jin dagaske dai ashe bata da lafiyar ba lambo tayi ba kaman yanda yayi tunani, duk haka ya shiga aiki sukuku babu kuzari har sanda ya shiga Meeting kafin su shigama yana Kallon kiran Amira amma yaqi dagawa dan se yaji yana jin haushin ta ita ce ummul Aba’isin ta komai da yake faruwa ai. Tun yana sallar Azahar da be samu yi ba se qarfe uku bayan sun fito daga dogon meeting din da suka share awoyi sunayi wayar sa take ta qara dan ya manta be sakata a silent ba, yana sallamewa wani kiran ya sake shigo wa ya zarota a fusace dan ya ayyana Amira ce kadai zata iya masa irin wannan kiran mahaukatan sedai ya cika da mamaki ganin Number Asma’u da yayi saving da MA’UNA akan screen. Be kai ga dagawa ba ta yanke kafin ya yi wani abu aka sake kira se yai saurin dannawa dan tabbas yasan ba lafiya ba. Muryar Aliyu ce cikin kuka yake ce masa “Abbi kazo Mami ta yanke jiki ta fadi tun dazu bata motsi” ai se yaji tamkar a saka guduma an bugi kwakwalwarsa Asma’u ta fadi meya sameta? Innalillahi. Ikon Allah ne ya kawo shi gidan kawai yana shiga ya tarar dasu a zagaye da ita suna kuka kamar wadanda aka cewa ta mutu se ya matsa da sauri ya dagota yana jijjigata “Asma’u Asma’u ya shiga kiran sunanta. Danshin da yaji a hannunsa daya tallafo qasan ta ya saka shi duba wurin Jini ya gani wanda duk basu lura ba se yanzu ai kuwa yaran suka sake rudewa da Kuka kamar me shikansa dauriya yayi ya dagata tareda cewa Amna da Aliyu su fito suje Asibitin sauran Yaran kuma yace su Shiga gidan Maman Ruth kafin su dawo dan Anty(Amaryar Ogan sa ta take flat din dake kallon nasu) ta tafi Zamfara garinsu bikin qanwarta. Bashi da Nutsuwar da ze ja mota dan haka yau Amna da kullum yaga Asma’u ta bata driving se yayi bala’i to gashi yau ta masa rana, ita kanta jikinta rawa yake cikin ikon Allah dai suka qarasa asibitin dan basu da nisa sosai. Emergency a ka karbe ta, bayan kusan Hour daya Dr Bolaji ya fito daga dakin da suka shiga da Asma’un. Alama yayi wa Bashir daya biyo shi office Se ya kalli Amna da Aliyu da fuskokinsu suka kode saboda kukan da suka sha, “Ku jirani a nan ina zuwa” ya fada tareda bin bayan Dr Bolaji. Bayan ya nutsu a office din Dr Bolaji ya kalle shi tareda turo masa takardar daya gama rubutu. “Strees da damuwa suka hadar mata har ya jawo jininta ya hau sosai shine kuma yai sanadiyyar fitar cikin jikinta, ga wannan kaje ka kai Pharmacy zasu baka bill na kayan da akayi amfani dasu se ka karbo wadannan magungunan kuma, Allah ya taqaita abun amma ku kiyaye faduwa irin wannan ko a gaba ze iya jawo mata Paralyze bama dai fatan hakan” Dr Bolaji ya fada cikin harsheb turanci yana maida kai ga takaddun dake gabansa, kamar kazar data sha ruwan zafi haka Bashir ya miqe ya nufi Pharmacy din dan karbo magunguna. Sanda ya dawo ya tarar da Nurse ta fito daga dakin da Bedsheet a hannunta daya baci da jini da kuma kayan jikin Asma’u da suka kawota dasu. Tambayan ta yanda zaayi da maganin yayi tace ya shiga dasu ya ajiye zata dawo yanzu seya tura qofar dakin a hankali ya shiga. A ciki ya tarar da Aliyu da Amna kowannensu na share hawaye nan da nan yaji shima hawaye da be zata ba sun sakko masa, shikenan ya rasa Babyn da be masan dashi ba. Allah ya dorawa Bashir jarabar son Yara a rayuwarsa, ya kance shi beqi ya haifi yara Ashirin bama in ya fadi haka Asma’u se tayi dariya tace “Haba se kace Akuya in dai ba kuma mata hudu zakayi ba”. A lokacin ya kan ce mata ke zaki zama Akuyar kuwa kiyi ta zubo su dan kinsan nidai babu gurbin wata mace bayan ke a cikin rayuwata. ko bayan data haifi Yan biyu Asma’un taso tayi planing acewarta yaran sun isa haka amma ya fitittike yace idan tayi koda be sani ba be yafe ba dan shi yana son yaga ya tara zuri’a masu yawa kuma Alhamdulillah yanzu Allah ya hore masa yana da yanda zeyi ya kula dasu, yasan bazatayi ba shi yasa dadewar da tayi bayan Yan biyu be dame shi ba yasan daga Allah ne bayan haka dama ance in shekaru suka fara ja haihuwar na ja baya ita ma kuma Asma’un na kusan shekaru 33 ne yanzu. A hankali ya ajiye ledar kan drawer dan Nurse tace karsuyi motsi me girma daze farkar da ita ya qarasa gefen gadon yana kallonta tayi wani fresh tana bacci kaman bame ciwo ba se ya rankwafa kanta tareda kissing goshinta, under his breath yace “get well soon my Ma’u, I’m sorry for hurting you”. Zaman kurame sukayi shida yaran kowa na tunanin abinda ya dame shi basu Ankara ba se jin kiran sallar Magriba sukayi se a sannan ya tuna ai ko La’asar beyi ba. Shida Aliyu suka tafi masallaci har suka dawo kuma bata farka ba dan haka cikin damuwa ya koma gurin likita yana gaya masa. “Babu damuwa mun mata Alluran bacci ne dan ta samu ta huta sosai jinin ya sauka zata farka amma se zuwa cikin dare, kaje kawai kayi settling bills babu buqatan me jinya Nurses din mu zasu kula da ita”. Jiki a sabule ya koma dakin, Gurin da Su Aliyu suke ya kalla yace su tashi su tafi gida “Abbi ni zan kwana a nan” cewar Amna “Aa baa barin me jinya mu tafi da safe kafin ku tafi school se mu biyo ku dubata”. Dakyar suka tafi har shi kansa ji yake kaman ya sake zama sedai tuna sun bar sauran yaran yasa dole suka tafi bayan ya biya kudin duk abinda ya kamata ace ya biya din. ASMA’U Basufi awa uku da tafiya ba na bude ido lokacin qarfe tara na dare harta dan gota, jinina yana da qarfi sosai ba kasafai Allurar bacci take daukata na dade ba. Sakayau na tashi kaman an zare mun qaya dukda bansan ainihin abinda ya same ni ba amma babu ciwon kan babu jiri se kawai kasala da nake ji da kuma bakina da sam ba dadi. Ina qoqarin miqewa Nurse ta shigo tana ganina ido biyu ta fada da fara’a tana cewa “Sannu patient har kin farka lallai kina da qarfin jini muda muke tunanin se kin kai gobe ma” “Murmushin na mayar mata cikin muryar marasa lafiya nace “gashi har na tashi kam amma naji dadin jikin ma sosai ai” “Karki tashi Bari na sake duba Bp na gani” ta fada ganin ina qoqarin miqewa daga gadon, zama na koma nayi ita kuma ta dauko Abun auna BP, seda ta gama ta kalleni still tana murmushin tace “kinga kuwa yayi normal bari na hada miki ruwa to ki wanke jikinki dukda naga bakiyi staining bama se kici abinci” Kallon rashin fahimta na bita dashi fahimtar haka ya sakata Dafani tace “I’m sorry kin samu miscarriage saboda faduwan da kikayi” “Miscarriage kuma? Cikine dani daman?” “Eh almost 3 months ma baki sani ba?” Ta jefin tata tambayan, se lokacin na gane a fili nayi magana. Sena qaqalo murmushin dole to ban ma san me zance ba dadi zanji ko rashin dadi ma oho nan ta barni ta shiga toilet din, mintina kadan ta fito bayan ta tara mun ruwan. Ita ta rakani har toilet din kafin ta baroni na fara wankan. Sosai naji dadin ruwan bayan na gama nayi brush da sabon tooth brush din data ajiye mun na saka pant da pad da duk a nan na gansu sannan na daura sabon towel babba na rufo kaina da qarami na fito ina jina wata sakayau a raina ina yaba tsarin Asibitin komai nasu tsaf kamar A Turai. Turus na tsaya kofar toilet din ganin Mutum a zaune bakin gadon dana tashi wanda da alama an kuma chanza bedsheet din kai, haka kawai na tsinci kaina da daure fuska abinda yai ma yara da safe yana dawomun se kawai na juya da niyyar komawa cikin toilet din yai zuruf ya miqe tare da biyo ni kafin na samu damar rufe qofar ya turo ta ya shigo ciki bani da zabi kawai na durqushe a qasa na fashe masa da kukan da ban san nima na menene ba. https://chat.whatsapp.com/IcgqoNAQ9V612x1JRXBMVS 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 WATA KISHIYAR 🥰👹 (Alkhairi CE KO SHARRI) 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 Na Maryamah_Mrs AM (Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah) Page 4 Zama yayi shima a qasan tareda janyoni jikinsa ya rungume yana bubbuga bayana a hankali, cikin qaramar murya yake cewa “I’m sorry Ma’una I’m sorry” ni kuwa kaman yana cemun ki qara volume ne. Kuka nake dagaske kukan takaicin daya dade yana shaqamun, qara tuno wasu abubuwan nake ina qarawa kukan nawa Armashi nasan Bashir baze hanani ba zebarni nayi iya yina ne a cewarsa kuka rahma ne idan yayi yawa ne yake zama matsala. A duk sanda irin haka ta faru ko yayi mun wani abu da har takaini da zubda hawaye dama shi ba Namiji bane me bada haquri duk kuwa girman laifin da yayi zedai saurare ki da kunne duk irin mita da qorafin da zakiyi se kinci babbar Sa’a ne zece miki “Uhmm” in ta kai maqura daya san shi yake da laifi shine ze rungume ni a jikinsa nayi kukan iya yina yana bubbuga baya na har nayi shiru dan kaina to yau an Auna arziqi har na samu arziqin sorry, Miskili kenan aka ce kafi mahaukaci ban haushi. Se ya tunamun da lokacin rasuwar mahaifin mu kamar haka ya riqeni nai kuka a jikinsa har seda naji wani kaso na radadin zuciyata ya ragu sannan ya rabu dani ya koma gurin karbar gaisuwa. Nurse ce ta dawo dakin, sheshshekar kukana da ta jiyo daga toilet ya sakata bude kofar da sauri a zatonta ko wani abun ne ya same ni amma se ta tarar damu “Haba Alhaji ya zaka barta tana kuka bayan kasan condition dinta please patient taso ki zo ki saka kaya a jikinki kar sanyi ya kamaki”. Fincikewa nayi daga jikinsa na fito ina ci gaba da sheqa kukana, kamar qaramar yarinya haka ina saka kayan baccin data ajiyemun ina kuka har na gama na dauki Mug din tea data hadamun na hausha ina kurba ina kuka kai abun ma abun dariya. Tsayawa tayi kawai tana kallon ikon Allah dan Bashir dai ba sabon abu bane a gurinsa indai Rigimar Ma’u ce, ganin dai dagaske nake ya saka Nurse fita ta kirawo Dr Bolaji. Tare suka shigo, kallona yayi ya nufi inda Bashir ya tsaya wanda kallo daya zaka masa ka hango tashin hankali da damuwar da fuskar sa ta kasa boyewa, ban san me yace masa ba naga sun fita waje se Nurse din ta juyo wurinata miqa mun magunguna data ballo tana cewa “kiyi shiru kishanye tunda ya tafi se ki kwanta na mayar miki da drip din” Shirun nayi ina jan majina da ajiyar zuciya hancina kuwa yayi jajir kamar me mura na hadiye kwayoyin tare da gyara kwanciyata raina Fes, a zuciyata nace “Wallahi kadan ka gani yanda zanyi kwanan Asibiti dalilinka kaima bazaka runtsa da dadi ba, ko minti goma ban qara ba bacci ya sure ni ga gajiyar kuka ga allurar baccin data qara a ruwan ko na samu na huta. Daga ita har Dr Bolaji daya dawo kallona kawai suke Dr yai murmushi ya nufi qofa yana cewa “This Madam na correct trouble maker” Nurse ta saka dariya kawai tabi bayansa dan dakko abubuwan da zata buqata ita zata kwana dani. BASHIR Tuqi kawai yake gaba daya baa nutse ba kansa in banda sarawa babu abinda yakeyi, a duniya babu abinda yake rudashi da hargitsashi irin Asma’u. Matar nan Tasan duk wani lungu da saqo da zata shiga ta tado masa da hankali (kuji fa) in banda fitina irin tata shi yanzu ai ta lafiyarta yake yi amma yaga alama ita neman tada zaune tsayene kawai a gabanta yanzu. Yana tafiya yana jin yadda wayarsa take ta faman vibrating Daidai ya faka motar kira ya sake shigo masa, a mugun fusace ya daga dan yasan Amira ce. Tun dazun ya gaya mata yana da uzuri idan ya gama ze kirata amma shine take zabga masa kira kamar ta na binsa bashi a qalla ta masa missed calls sunfi 100. Yana daga wayar ta fara magana cikin Son kwaikwayon salon da Asma’u take magana dashi tace “Yayana ina ta kiranka tun dazun baka answer ba kafasan duk yau banji muryar ka ba ga baby ma yana ta misss.....” tsabar takaici be bari ta qarasa ba ya daka mata tsawar da seda cikinta ya juya sannan ya cigaba “Ke wacce irin wawuya daqiqiyar yarinya ce, kin kirani nace in na gama abinda nake zan kira ki amma shi ne kika ci gaba da kira kamar kina bina bashi ko? Shiyasa Ma’u ta fiki dan ita bata da shishshigi da wannan mugun takurar, Stupid ki sake kiran wayata wallahi in bani na kiraki ba zakiga hukuncin da zan dauka akanki” qit ya kashe wayar. Wani huci yake fitarwa kaman kumurci, gaba daya yaji bala’in haushinta yake ji dan itace ummul aba’insin ta komai dayake faruwa. Dukda bata shigo rayuwarsa ba da bata juya masa daddadar rayuwar da suka gino me cike da so, qauna da sadaukarwa ba shida Ma’un sa. Yafi minti 30 a cikin motar yama rasa tunanin me zeyi se sannan yaran suka fado masa a rai ba shiri ya fito daga motar ya shiga gidan. Gaba daya suna zaune a palour sunyi zuru zuru alamun sun sha kuka sun qoshi har yan biyu basuyi bacci ba, suna ganinsa suka nufe shi gaba daya tareda sake fashe masa da sabon kuka daya sa gaba daya yaji dama shima yayi kukan ko zeji sauqin abinda yake ji a ransa. Dakyar ya samu sukayi shiru, Amna ya tambaya sunci abinci tace Aa, dare ya rigada yayi dan 12 harta gota dan haka yace ta hada musu cornflake kawai su sha. A qaton bowl ta hado shi suka hadu kowa da spoon suna sha yana kallonsu dan bayajin ko ruwa ze iya bita maqoshinsa. “Kai anya ze iya rayuwa babu Asma’u kuwa?” Ya tambayi kansa “Idan ta mutu fa” wata zuciyar ta qara tambayarsa “Kai ina insha Allahu ma sena rigata mutuwa” ya fada a fili ba tareda yasan a fili yake maganar ba da Alama Ma’u na dab da zarar dashi 😂😂 Bayan sun gama yace suje su kwanta amma qememe Suka qi yana tashi suka bishi Amna Farida da Aliyu ne kawai suka zauna a palour, ba yadda ya iya haka ya jera su akan gadon ya shiga toilet ya dauro alwala ya fara sallah dan yasan bama ze iya bacci ba yau, haka yai ta jera salloli in ya gaji ya huta har bacci barawo yai nasarar sace shi. HAJIA AMIRAH Sororo tabi wayar da kallo hawaye na kwace mata ta kalli Mamanta Adda Fatu da har tafi Amirah kidima dan a hands free ta saka wayar, ita dama bata so ta sake kiransa ba tunda yace ze kirata amma Adda Fatu ta sata a gaba dan a yau take so ya aikowa da Amirah kudaden da sukayi qaryar zatayi siyayya saboda tafiyarta Lagos amma wani uzurin daban take so tayi dasu. “Adda kin gani ko bamu samu biyan buqata ba yanzu mun ballo matsala Allah kadai yasan yanzu hukuncin da zeyi mun” ta fada tana share hawaye. “Ke dalla can ba abinda zeyi miki qarshe ma kiga ya kira ki yanzu ya baki haquri ta yuwu wani ya bata masa rai kika taka sahun barawo” bata qarasa rufe baki ba sukaji alamar shigowar message wayarta, baki washe Adda tace “kingani ko duba muga ko kudin ya sako” Ita dai Amirah jikinta be bata ba dan tasan waye Bashir a tsorace ta bude message din ashe MTN ne suke gaya mata zata iya aron kati dan nata ya kusa qarewa. Wata muguwar dariya Ummi qanwar ta ta sheqe da ita tana tashi zaune daga kwanciyar da tayi tace “Wai ke kin yarda Yaya Bashir ne ze kiraki ya baki haquri to sannu uwarsa, ai wallahi ki shirya ma Allah kadai yasan abunda ze biyo baya dan kinsan sarai fadansa kamar na kurma yake baya mutuwa” “To se kijie ki saka shi ya dauki matakin ai dan uwarki shegiya me baqar fuska” Amirah ta fada tana hayayyaqo mata “Gata nan a zaune ai uwar tawa baqar fuska kuma na gode keme farar ai gaki nan kin zama Bora a gurin miji, Allah dai ya rabamu da auran cin Amana” Ummin ta mayar mata dan itama ba baya bace gurin fitsara. Nanda nan fada ya kaure a tsakaninsu seda Adda Fatu ta zuzzunduma musu Ashar sannan suka yi shiru kowa tana harar yar uwarta. “Shegu kuda baku gudun abun magana a daren nan kunsan an kasa kunne a jiyo zancen mu a yada shine zaku min tijara kishiyoyi naji ni kubarni nayi tunanin mafita ma kun hanani” ta fada tana hararar su duka. Yunqurawa Amira tayi dan cikinta yayi girma sosai ta shiga daki har tana takewa Ummi qafa da gangan “Salon na taba ki wani abu ya same ki ko to bazan kula kiba aniyarki ta biki” Ummi ta fada. “Tashi ki shige kafin na rade ki yar kwal uba” Adda Fatu ta fada tana neman madoki, setayi saurin barin wurin dan tasan tsaf zata sha dukan kuwa. Tunani ta shiga yi ta yanda zata samu kudi kafin wayewar gari, bashi ne tun na lokacin Auran Amirah har yau bata gama biyaba kusan shekara biyu dan a zatonta zasu samu a hannun Bashir din ganin yanda Ma’u take wadaqa sedai tunda akayi auran ita dai bata ga kyautar dunkulalliyar dubu dari yayiwa Amiran ba, ze dai aje mata komai na buqata amma baze bata kudi ba. Ganin ba mafita kuma ta tabbatar kaman yanda matar tace da safe zata biyo kadin kudinta ko kudi ko kayan kudi tofa rashin mutunchi zata mata dole ta nemi mafita qarshe ta yanke shaqarar zuwa gidan su Bashir din gurin Nafi ai ita Uwarsa ce idan ta kira shi baze qi dagawa ba, da wannan shawara ta kwanta akan asubanci zatayi kafin matar tazo insha Allahu ta dawo. LAGOS Malam Bashir kuwa dakyar ya iya farkawa da Asuba kansa kaman an dora masa Dala tsabar ciwon da yake masa, basu iya fita masallaci ba a gida sukayi sallah suka hau shirin makaranta dan zasu fara biyawa Asibiti su duba Mami. Tea suka dafa suka soya kwai suka karya, basu daukar mata komai ba se kaya kala daya wanda zata saka idan An sallameta tunda Asibitin nada uniform na marasa lafiya baa buqatar kaya haka abinci ma a can ake basu.. A hankali ya tura qofar hadi da sallama, a nutse ta dago ta kalleshi tareda amsa sallmar, fuskarta dauke da wani kyakykyawan murmushi. Magana take yi da yaranta kowa na gaya mata yanda yayi missing nata. Qara shigowa yayi idanunsa akanta yana qarewa kyakykyawar fuskarta me cike da kalama kallo ganin yanda Omo blue din Uniform din Asibitin ya amshi fatar ta matuqa kamar wasu kayan kwalliya. Aliyu ne ya bashi kujerar da yake zaune akai still idanunsa akan ta yaja ya zauna dukda daqi sake dagowa ballantana ma su hada idanu da ita. Shigowar Nurse da taje kawo mata breakfast yasa ta daga kanta Yaran suka shiga gaida Nurse din tana amsa musu da kulawa, Dan gyaran murya yayi tareda kallon yaran yace “kuje mota ku jirani kar mu makara idan mun taso se mu sake biyowa aga Mami ko? Basu musa ba da daddaya suka fice bayan sun mata Addu’ar samun sauqi itama Nurse aje kayan tayi ta gaishe shi kafin tayi waje abunta. Cikin sanyi jiki ya miqe zuwa gefenta da tun kafin ya qaraso ta dauke fuskarta zuwa dayan side din, be haqura ba ya bita, can qasan maqoshinya furta “How are you feeling now? Ina ne yake miki ciwo?” “Oh really ka damu ne daman da lafiyata toh Alhamdulillah Yanda kaso be samu ba jinina ya sauka ya dawo dadai”. Be kula maganar taba ya sake matsarta yana cewa “Why? Me yasa baki gayamun that you are pregnant ba??” Ita se a yanzu ma ta gane dalilin wannan fake concern din wato saboda cikin da ya zube, murmushi tayi me kama da yaqe tana tashi zaune sosai tace “Baban Ai kenan, to ina ruwanka da ina da ciki ko bani da shi naga yanzu ai baka damu dani da yaya nane bako? Ko da yake dama ai bazaka damu ba tunda qaddarace tasaka kuka hada Zuri’a dani Yanzu ai gashi za’a haifar maka jininka yayan dangi na meye zaka damu akan wanda Allah ya taqaita samuwarsa bare yazo shima a barshi a titi a bula masa qura ko yaje makaranta ko kar yaje duk ba matsalar ka bace. Wallahi Baban Ali kayi nasarar doramun Hawan jini amma ina tabbatar maka bazan bari ka nakastamun rayuwa ba idan kuwa haka ta faru sedai muyi mutuwar Kasko”. Kaman wanda aka dasa haka ya bude ido da baki yana Kallon ta, kai wannan Mata wai ita bata yafiya ne a ko yaushe burinta ta ringa hukuntaka da kuskuren da ka aikata? To in ba haka ba meye na dawo da wadannan maganganun marasa dadi? Yana shirin maida mata da martani wayarsa ta dauki qara, hadiye bisashshan yawu yayi kafij ya zaro wayar yana tattara kalaman da ze bata amsa dasuba zuciyarsa. Sunan “DADA da ya gani ya saka shi saurin daga wayar ya kai kunnensa. Cikin harshen fulatanci ya shiga gaisheta ta Amsa tana tambayarsa Asma’u da yara. “Bashir Meya sami wayarka Amirah tace tun jiya tana kira baka dagawa” ta fada bayan sun gama gaisuwar. “Qarata ta kai kenan, ai kuwa seta gane bata da wayo” ya ayyana a ransa a fili kuwa se yace “Dada Ma’una ce bata da lafiya tayi Bari muna Asibiti tun jiyan” “Subhanallahi a garin yaya” ta tambaya muryarta na nuna Alhini se ya sake narkewa abin tausayi yace “Nima ban sani ba ina office aka kirani wai ta yanke jiki ta fadi ina zuwa muka hato Asibiti” ya yanko maganar da shi besan gaskiya ya fada ba ko qarya. Asma’u dai kallonsa kawai takeyi tana qara mamakin Bashir a ranta, miqo mata wayar yayi seta tsaya kamar bazata karba ba kome ta tuna kuma ta karba. Sama sama ta gaida Dadan tareda amsa ya jikin da take mata dan itakam ai sun shata ta warke abinda mutanen nan suka mata ta yaya zata manta dashi? Kallonta Bashir yake a ransa baya jin dadin yanda alaqar Dada da Ma’u ta lalace be kuma san ta yanda ze gyarata ba, yasan sun mata laifi amma Ma’u ma akwai ruqo da kafiya ai. Miqo masa wayar tayi ya karba sukayi sallama da Dadan sannan ya kashe. Hannu yaki ze riqe nata tayi saurin janyewa se ya girgiza kai kawai yace “Ki kwanta ki huta bari naje mun makara ma idan mun taso zan ga Dr ance be shigo ba yanzu naji yaushe zeyi discharging naki” Bata amsa ba shima be saka rai ba dan haka yaja qafafunsa ya fice yana sake kallon Wayarsa dan ganin da gaskw sun makara din. Asma’u kuwa da harara ta raka shi kafin ta zumburi baki tana qunquni tace “wato in dawo kaci gaba da Gallazamin ko toh ba inda zani se na tatike Aljihun ka qat na huta wallahi” Ita kadai tayi ta sababi har bacci ya dauketa sannan tayi shiru. Bashir kuwa sauri sauri ya kai yaran har an rufe get dakyar suka karbe su suna ta masa qorafin in suka sake makara bazasu karbe su ba shida ya ajiye su ya wuce nasa aikin da baya zaton ze amfani komai yau. Gaba daya shima ji yake kamar bashi da lafiya ga wani mugun bacci dayake jin idon sa yayi fici fici har wani yaji suke masa,haka ya lallaba ya qara sa office din. GOMBE Bayan da Dada ta ajiye wayar se ta maida hankalinta kan yayartata Adda fatu datayi kamar bata gane me Dada da Bashir din suka tattauna ba. “Ashe Ma’u ce bata da lafiya tayi bari suna Asibiti” Dadan ta fada. “Allah sarki Allah ya bada na aike” Adda Fatu ta amsata a ranta kuwa murna tayi gara ma da cikin ya zube ita duk wadannan yayan data zuba bazata haqura ta barwa Amirah itama ta samu rabonta ba ita dai fatan ta Allah yasa ba ita Amiran ta gado ba dan ta fara ganin sare sarin hakan, seta gyara zamanta tana cewa “Kinga daman maganar shirye shiryen tafiyarta lagos din nan ce lokaci nata tafiya yace ze turo mata kudi tayi siyya anan kafin ta tafi yanda kinga in lokacin haihuwa yayi ta howa kawai zatayi komai na jiranta a nan to kuma naga yana nema ya shiriran tar da maganar ga yarinya kuma ko baccin kirki wallahi bata iya yi to Allah ya hada ta da jarababben ciki gara dai yazo ya tattarata su tafi dan nikam na fara gajia gaskiya”. Kallonta kawai Dada tayi ita kam Adda Na bata mamaki da kunya wallahi in ba haka ba ina ita ina irin wannan magana ai tsakaninsu ne can ko amma ita babu ruwanta tana manta cewa Matsayin Suruka take a gurin Amira ba kowacce magana ya kamata ta ringa yi da ita b, dakyar ta bude baki tace “To Adda nake ga siyayya ai bawata matsala tunda in kayane ai can Lagos sun fimu in taje din se su siya acan su turo kuma ni da zaki ji ta tawa ma da tayi haquri ta yi zamanta a nan tunda yana zuwa sati biyu dan gaskiya abinda ake shirin yi ba Adalci bane. Yarinyar nan Asma’u mun mata abubuwa da yawa ni wallahi har kunyarta nake ji to yanzu kuma akace wannan gaskiya ya zama da daukar Alhaki kuma. https://chat.whatsapp.com/GBC9U1ddKHO94q4CSL2jZ8 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 WATA KISHIYAR 🥰👹 (Alkhairi CE KO SHARRI) 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 Na Maryamah_Mrs AM (Marubuciyar Rubutacciyar Qaddarah) Page 5 “Ban gane ba Nafi me kike nufi da ta haqura da binsa ko baki gane halin da yarinyar nan take ciki bane, yarinya na buqatar mijinta a kusa idan kuma ba halaka ake so ta fada ba se naji, nifa dama na gane take takenki kina so ki fifita bare akan yar uwarki ko Nafi. Kuma da kike zancen za’a shiga haqqin Asma’u ita Amirar daba uwace ta haifeta ba ai ba’a shiga nata haqqin bako” Adda Fatu ta fada cike da jin haushin Dada, se Dadar ta gyara zama tareda cewa “Ni ba haka nake nufi ba amma gani nayi ai tun farko tare suke a can, yanzu ko cewa akayi suringa yi idan wannan ta je ta kwana biyu se wannan taje kinga bame yiwuwa bane tunda Asma’u tana aiki a garin bakuma ze yuwu muce tabar aikin ta ba tunda idan Amira ce a matsayinta muma bazamu bari a mata ba ko? Ni dai a nawa ganin Adda ayi haqurin shi yafi a zauna lafiya tunda har komai ya daidaita tsakaninsu bana son wata rigima ta sake tasowa kindai san sharadin da Malam ya kafa mun dan Allah bana so ya sake ganin laifina akan lamarin gidan Bashir”. Se Adda Fatu ta miqe nan da nan ta fara sababi da fadan maganganu ta inda take shiga bata nan take fita ba, ga baqin cikin rashin samun biyan buqata a gurin Bashir gashi da Alamu wannan Karon Nafi na nema ta bata matsala amma ina bazata sabu ba wallahi dole tasan abinyi. Miqewa tayi still tana masifar ta nifi qofa, “Wato Nafi kina ganin yanzu kinkai matsayin da zaki qalubalance ni ko? Kin manta duk halaccin da nayi miki a rayuwa saboda qasa ta dade da cinye Naman Baffa da Inna dole ki watsar da maganar su tunda kina ganin yanzu kema Kin kawo qarfi. Na gode zan kuma tafi amma daga yau kisa a ranki baki da sauran wata yar uwa data rage miki a duniya tunda kin zabi Matar danki akaina da Yata shikenan Nafi na yafewa Duniya ke” ta qarasa tana rushewa Kukan munafunci wanda dashi take cin galaba akan Nafin. Ta kuwa samu yanda take so dan nan da nan hankalin Dada ya tashi ta shiga son nuna mata ita fa ba abinda take nufi ba kenan, “Idan har da gaske kike kuma kina so na haqura nida kawai kiyi yanda zakiyi Bashir ya dauki Amira ta koma kusa dashi, kuma baze yuwu yace Ze kwashe su su dukka ya kai can ba se dai ki saka shi ya dawo da daya ya dauki daya idan kikayi haka shine kadai Ze sa na haqura in ba haka ba wallahi ki saka a ranki baki da wata Yar uwa Fatu a raye” Ita dai Dada son su rabu lafiya ya saka ta amince mata, dole ta hado yan kudaden hannunta dubu 30 ta bata tace gashi nan ta kaiwa Amirar ta riqe kafin Bashir din yazo se a san yanda zaayi haka ta rakata har get Addan na sake jadda da mata fa akan tana nan tana jiran saka mako da haka suka rabu. Numfashi ta sauke bayan ta dawo cikin palour ta tazauna, gaba daya ta tasa ina zata kama akan wannan al’amarin. Har ga Allah bata so ta sake yin wani kuskuren akan na baya amma ya zatayi da Adda Fatu yar uwarta tilo a kaf fadin duniyar nan bata da kamarta. Addan tayi mata komai a rayuwa ya kamata ace ita ma ta saka mata da abinda ta mata. A zatonta Auran Bashir da Amira ya isa ga tukuicin kyautatawar amma se yanzu take dana sanin ma aikata hakan domin kamar ta bude wata qofa ce da Addan ta mayar da ita tamkar birin wasanta. Ko da yaushe cikin daga mata hankali take tunda akayi wannan auran da ita dai bata ga amfaninsa ba in banda bacin rayuka da ya janyo da yawa, shigowar Nazir Autan ta ya sakata dagowa ta kalle shi “Yanzu na hadu da fitinanniyar yayar ki a hanya seda tayi mun fashin 10k wallahi, gaskiya Dada ki ringa yiwa Adda fada abubuwan da takeyi basa dacewa. A yanzun fa ga kudi a hannunta amma ta tsaya suna fada da Dan Napep dan yace a 200 ze kaita gida” “Hmm Allah ya rufa asiri kawai Naziru amma ni lamarin Adda ya fara bani tsoro, yanzu ma fa kaji abinda ya kawo ta” tiryan tiryan ta labarta masa yanda sukayi. “Wallahi Dada ki kiyayi matar nan, ni dai ina ga Asiri take yi miki ma kike wasu abubuwan idan ba haka ba dan ta riqe ki ai ba baiwarta bace ke da kuma zata ringa juya ki yanda taso. Tun farko abinda muka guda a hadin wannan auran kenan amma kika rufe ido kika ce se anyi zumunchin ku ya qara qarfi ko ai gashi tun ba’aje ko ina ba kinzo kina dana sani. Shima Yayan banga qaddarar daya gani a jikin wannan mara mutunchin yarinyar ba daya yarda ya aure ta” “To Naziru yaya zanyi Adda yar uwata ce da bani da kamar ta ka sani kuma farincikin Yayanta shine nata idan banyi mata ba a rayuwa ta wa zan yiwa?” “Ai kuwa gashi nan, kafin da ki sake yanke wani hukuncin se ki tuna cewa Auranki kema yanzu lilo yake yi a garin faranta mata kuma baza muso ace Uwar mu ta shiga zawarci a wadan nan shekarun ba” ya fada ya miqewa dan ya fita dan dagaske Bala’in haushin Adda yake ji har ma da Dadan da yake ganin tana biye mata ne. “Allah ma baze sa ba Naziru zan lallabata insha Allahu babu abinda ze faru ma” Dada ta fada itama tana miqewa dan neman abinda zata ci, ko karyawa batayi ba Adda ta doko mata sammako. ADDA FATU Bayan barinta gidan Dada gaba ta qara dan kuwa bazata koma gida yanzu ba dan tuni Amira ta gaya mata matar tazo karbar kudinta gata nan a tsakar gida tana ta zuba Rashin mutunchi akan Adda ta fito ta bata kudin ta sunce mata bata nan amma taqi yarda, gara ta qara gaba ko Allah ze sa ta dace ta samo wani abun koda taimakon da zesa Bashir ya turo musu kudin ne. Gidan Aminiyarta Haj Balaraba ta wuce, ta sami Balaraban a qofar gida an kira mata me Napep zata fita unguwa. “Fatu daga ina da safiyar nan haka” ta fada tana qoqarin rufe gida. “Ke zan tambaya Balaraba keda nasan se ki kai 12 ma baki tashi ba” “Hmmm ta ina Kishiya na neman sabautani ina naga ta bacci, kinga yanzu ya akayi dan ni a tafe nake neman taimako zan tafi” Balaraba ta fada tana jefa muqulli a cikin jaka. “Ai kawai muje dan nima matsalar ce ta kawo ni ma tattauna a hanya” nan suka fada Napep Balaraba ta fada masa inda ze kaisu. Suna tafiya Adda Fatu na jerowa Hajia Balaraba matsalinta. “Ni na rasa wane irin shegen yaro ne Bashir wallahi naje gun malaman naje gun Yan Bori amma an kasa cin galaba akansa, ke har fa nafi ganin aikin kissa idan tayi masa akan na asirin nan wallahi dama Da Nafi nake samun yanda nake so a gurinsa to itama naga alamar tana so tayimun Bore. Ga shegiyar me kayan can da kika hadani da ita bashi kamar na masifa na kasa biyanta”. “Tab ai seda na gaya miki daman ita fa Indo in kaci bashin ta wallahi toshe maka hanyoyin samu yake kika ce bakomai shiyasa kika ni kudi hannu muke sabga da ita gata bata san sabo ba akan dubu daya seta keta miki rigar mutunchi” “Ai na gani kuwa yanzu haka fa tana can gidan tana ta tijara nidai na ce su Ummi su kulle qofa kar su bari ta shiga bare ta daukar kun wani abun, kudinta Dubu dari biyu yai saura da Mun samu kan Bashir zan tattara na biyata mun rabu kenan”. “To ai shi wannan yaron fa se kin dage masa gaskiya amma bari muje nan gurin, Maman lurwanu ta kwatantamun tace aikinsa sha yanzu ne dan shi yai mata aiki akan Isah ya saki Kishiyoyinta dukka biyun rana daya yanzu bakiga yanda take shanawa a cikin gidan nan ba ita kadai” cewar Balaraba “Kice Allah, ashe gara da nayo nan Allah yasa qarshen wahalata kenan (ko kuma farkon wahalar ki ba) in samu ina kafa Amira da kyau sannan in waiwayo kan nawa qananan kwarin ko da yake ni da zaman su da babu duk daya ai kin sani” haka suka ci gaba da tattauna wa har suka isa unguwar da aka mata kwatancen sedai ta kasa ganewa, sunyi tambaya kowa yace be san mutumin da suke nema ba kuma ta kira Number Maman Lurwanu a kashe. Kamar Adda zatayi kuka ta kalleta tace “yanzu Balaraba ya zamuyi dan Allah wallahi na gama saka ran waraka ta zo” kafin ta bata amsa Me Napep da tunda ya dakko su bece komai ba, tsaf ya gama nade hirar su ta hanyar voice note daya kunna tareda fahimtar matsalar ko waccen su se ya kashe mashin din yace musu bari ya kama ruwa kafin su gama yanke shawara. Can Nesa dasu yaje ya zaro wayarsa ya shiga kiran abokinsa aransa yana ayyana Banza ta fadi daga can bangaren aka daga wayar ana cewa “ungulu baka jewar banza da alama ta samu” Dariya yayi kafin yace “yi maza ka shirya area, ka duba whatsapp na tura maka saqo nan da minti Ashirin zan qaraso idan ta saitu” Dayan ya bushe da dariya yace”an gama kwaro kamar kasan wallahi dama ina ta lissafin ta inda zam samu kudin yiwa Latifa Anko gashi ta matsamin kwana biyu babu kasuwa, Allah dai yasa ta waru, se kun qara so toh” sukayi sallama. Gurinsu ya dawo harda karbar pure water a wani shago ya fasa ya zubda rabi ya taho yana wanke hannunsa, “To hajia ina muka nufa yanzu” ya tambaye su bayan ya kunna Mashin. “Maidamu inda ka dakko mu kawai” Balaraba da abun duniya ya ishe ta ta fada, se ya cilla suka dau hanya yana jin yanda suke ta jimami. Daidai wani gidan mai ya tsaya ya sha, seda ya dan bata lokaci sannan suka ci gaba ya gama shirya abinda ze gaya musu se yayi gyaran murya. “Am nace Hajia kuyi haquri fa dukda ban gane kan damuwar taku ba amma idan kuna so akwai wani guri da wancan satin nakai wasu passengers, can na jirasu suka gama gaskiya daga yanda naji sun fito nasan sun samu biyan buqatar data kai su, kun gama saqon daya daga cikin su daga Kano tazo ashe suka karbi Number dazu naje na karbo zan saka mata ta tasha akai mata” ya fada yana bude dan gurin da suke zuba kudi ya zaro baqar leda, basu san mene ne a ciki ba gadai shi harda suna da Number waya an rubuta ta wanda zaa turawa saqon. To wanda kwakwalwar sa ta toshe ai se a hankali ba tareda tunanin komai ba suka ce ya kai su, a ransa ya ayyana “Madallah” ya cilla kan mashin suka dau hanya dan yasan zuwa yanzu an kimtsa komai dukda haka seda ya sake yi masa text ya tabbatar masa komai is ready su taho. Tafiyar yan mintina takai su layin gidan har qofar gidan me dauke da shago se kuma soro na shiga cikin gidan. Wasu yan samari biyu ya gani daga gefe kan dakali yai musu sallama tareda tambayar su ko Malam yana nan “Ai kuwa ya fita amma nasan ba dadewa zeyi ba qilan ma yana hanya.. au ka ganshi ma muna maganar” daya daga ciki ya bashi amsa. Se ya nufi gurin Wizy abokinsa daya sha uwar babbar riga harda wani rawanin iskanci shi a dole ga malami ya miqa masa hannu suka kashe amma se ka zata musa baha sukayi. Cikin daga murya Yanda su Adda zasu jiyo su Wizy yace “Mal Kamar kaine ka karbi saqon hajia Larai dazu ko lafiya dai ko mantuwa kayi” “Eh wallahi Malam nine ba mantuwa nayi ba wasu iyayen daki na na rako ne” “Ah to to bismillah ku shigo ka barsu anan kuma kai Iliya me yasa baku bude musu shago sun shiga ba ko ka kaisu cikin gida gurin Maimuna kan nazo” ya fada yana hararar samarin da suke zaune. Seda Iliya yayi dagaske gurin riqe dariyar sa kafin yace “Malam ai ta fita gidan suna itama kuma ka tafi da muqullin shagon ai” “Anyi haka ya fada yana bude musu kofar suka shiga gaba daya, bayan sun zauna Me Napep yace bari yaje daga waje idan sun gama shima se yazo a bashi taimakon kasuwa. Malam ya jawo faranti me dauke da yashi ga kuma carbi me dubu ya hau ja yana muimui da baki nan kuma yana faman zane zane sannan ya dago ya kalle su “toh hajia dawa Zamu fara?” Ya tambaye su. Hajia Balaraba ce ta fara matsawa tace “Malam ni matsalar kaina ce a fara dani dama..” se ya dakatar da ita, “ki bari mu duba abunda bamu fahimtaba se kiyi mana bayani da kuma matakin da kike so a dauka. Tiryan tiryan ya ringa jera mata zance kamar me gani a film kai har abinda basu fada Me Napep yaji ba seda Wizy ya canka ya fada se kuwa tace kai Malam aikuwa hakane wallahi, yana ta tiqar dariya a qasan ransa to ai labarin duk daya ne dukma wadda tazo indai akan kishiya ne banbancin basu da yawa. Seda ya gama ratta ba mata zance Adda da me gefe ta gama yin Ammana sun zo inda zaa magance musu matsalar su harta gama Ayyano Yanda zasu juya Bashir kaman Tanda a waina. Tsaf Hajia Balaraba ta gama gaya masa yanda take so ayi nan kuwa ya yanka mata 50k babu neman ragi ba komai ta cake masa su to taji sauqi akan ubannin kudin data ke kashewa babu biyan buqata. Allonsa ya jawo da tawada ya hau rubuta abunda in zaka kashe shi be san menene ba ya gama ya miqa mata da kwano da ruwa yace ta wanke idan taje gida ta guntsi rabi ta fesa a kofar dakin kishiyar ko inda tasan zata taka rabin kuma ta kuskure baki ta zuba a miya kowa na gidan yaci to daga nan babu me jin maganar wani se tata. Wasu qullin Jan Maganin da kore ya sake dakkowa ya bata su kuma yace ta ringa jiqawa kwana 7 tana sha sannan ya qara mata da wani kuma a jarkoki guda biyu yace ta juye a bokiti ta qara musu ruwa ta ringa sha shima mijin ta san yanda zaayi yasha koda tea ne ta dafa masa dashi sauran aiki kuma karta damu zeyi daga nan shidai idan buqata ta biya kar a manta dashi (kuji dan banza 😂😂Koren Magani na sabara da Jan magani yake ba wa duk wadda tazo se na cikin jarka kuma maganin Basir ne ko banza ai ya temake so ko 😂😂😂😂😂😂). Adda ce ta matso aka buga mata nata duban se ya kalleta “Wace Mace ce haka gata nan dai Fara kyakykyawa kamar ma bata da lafiya tana gadon Asibiti” Ai caraf ta amshe “Asma’u ce ita ce kishiyar yar tawa” gyara zama yayi yana ayyano yanda ze tatsi matan nan yace “Kamar a kudu take fa wannan kai” se yai shiru kafin ya ci gaba “Tab di hajia akwai babban aiki a gabanki fa dan koma wacece wannan tasha kan shi wannan mutumin sosai dan kuwa Arnan kan dutse ne suke mata aiki an hada shi da gungun Aljanu suna gadinsa gaskiya wannan aiki yafi qarfina” “Ai Adda kamar zata rushe da kuka tace “haba Malam ba abinda ya fi karfinka ai (haba Adda Allah ne kadai keda maganin komai) ka duba ka taimakamun nidai a tarkato mana hankalinsa ai ko baya auran yata ni me tsayawa na nema masa taimako ce tunda dana ne ai dan yar uwata”. Zama ya gyara yace “abinda kamar wuya gaskiya kin san aiki da kafiran Aljanu akwai wahala amma in zaki saki kudi ayi musu yanka kinsan su jini suke so to wala Allah a dace” “Malam indai zaa samu biyan buqata ba matsaka yanzu kamar me zaa yanka?” “Gaskiya hajia a qalla za’a yanka musu raguna 20” seta dafe qirji tace Malam ina zan samu kudin nan yanzu fa nake maka bayanin na biyan bashi ma nake nema ni a fara rufemun bakin matar nan ma tukunna ta manta da zancen kudin”. “Wannan duk ba matsala bane kuma zaki iya ringa bayarwa a hankali ai in kin so ma kiringa yankan da kanki amma akwai kalar dabbobin da ake so da kuma abinda ake fada in za’ayi yankan in kina da wanda ze miki duk sena gaya miki ai” “Aa malam zaa mata komai anan” Hajia Balaraba ta fada “To ba matsala” “Kamar nawa kenan Malam” ta tambaya “To akwai qauyen dana ke siyo dabbobi ana samun qosashshen rago dai daga dubu Arba’in kinga a qalla guda koma dubu Dari hudu kenan amma zaki iya ringayi a sannu in so samu ne dai cikin wata biyu a kammala aikin”. Nan dai Adda ta zazzage masa dubu tamanin kudin data harhada zata rage biyan bashi tace in an kwana biyu zata kawo abinda ya samu, ita be bata komai ba se wani abu kamar goro yace idan matar tazo ta saka a bakinta ta ringa taunaqmwa tana mata magana kamar remote haka zata controlling nata aikin Bashir kuma Wannan Ze duqufa yai tayi itama Amira jin tana da ciki ya nemo wani garin Maganin zaqi dana sanyi da aka aike shi ya kaiwa Yayar sa da take da ciki ya bata yace ta kai mata tayi tasha zuwa sanda Bashir zezo daya kwanta da ita anci rabin aiki. Kamar wanda yai musu kyauta suka ringa zabga godiya ya basu Number wayar sa suka fito Me Napep har ya gaji bacci ya dauke shi fitowarsu ta farkar dashi, “Gaskiya kun dade hajia yau balance kawai zaku bani na maida Machine din nan na huta dan har na gama gajia” ya kunna suna shirin tafiya har sun ja Iliya ya tsaidasu akan Malam yace ya manta da taimakon kasuwar ne, se suka koma ya barsu a cikin mashin ya shiga. Be zauna ba 40% 60% suke raba duk abinda suka samu Wizy se dauki 50% ragowar 10 ya bawa su iliya da sauran masu yi musu cover a harkar, cas ya cake masa kudin sa tareda bashi wata qatuwar takadda da aka nade kamar laya yace zasuyi waya ya fito, ransa fes suka kama hanya bayan ya saqala Takaddar a gaban mashin wai ta kiran customers 😂😂 ikon Allah kuwa duk inda suka gifta se an tsaidashi yace drop ne har ya ajiye Hajia Balaraba ya wuce Da Adda Fatu dan tace gara taje ta kai mata ta fara sha tunda yau Alhamis a qa’ida gobe Juma’a ze zo To se muce Allah kauda tsautsayi da Asara 😂😂😂😂 https://chat.whatsapp.com/IcgqoNAQ9V612x1JRXBMVS 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 WATA KISHIYAR 🥰👹 (Alkhairi CE KO SHARRI) 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 Na Maryamah_Mrs AM (Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah) Page 6 Da Isar Adda gida bata ko zauna ba ta jiqawa Amirah maganin da aka bata tace gashi nan tayi tasha Zuwa goben sega yanda za’ayi. “Adda kin ganin ze zo ne ko kin manta yanda mukayi dashi jiya da daddare” Amirah ta fada cikin sanyin jiki. “Ke dallacan barshi ai idan be zo bama baze samu nutsuwa ba saboda sabon malamin nan da muka samu da zafin sa in gaya miki kedai kakarmu ta kusa yanke saqa, ai da lamarin ki sun gama daidaita zan juya kan wannan me baqin jinin itama ai taimaka a samo mata wani zaman ya isa haka” ta fada tana Kallon Ummi. Se Ummi tai zarab ta miqe tana cewa “Wa ni wallahi na yafe dadai irin Auran Amira kullum kina tafe ba biyan buqata gara in zauna banyi ba duk randa kika gaji kya barni na Auri Auwalu da nake so yake so na”. Mafice Adda ta cilla mata tana auna mata Ashar “Shegiya da bata gaji arziqi ba da dai wallahi ki auri wannan faqirin gara kiyi ta zama ina kallonki ba auran, duk yayan gidan nan wa kikaga ta auri ko Malamin Jami’a bare malamin makarantar primary” “Wato Fatu bazaki dena yin munanan kalamai akan Yaran nan ba ko? Amma ki ci gaba ai kina gani Idan Alkahiri kike shukawa kanki koma akasin haka” Alhaji Murtala da basuji shigowarsa ba ya fada, be ko qaraso ba ya juya kawai dan yasan wani qarin bacin ran ze jawa kansa. Tun kafin ya fito da safe ta bar gidan haka duk a kunnensa Indo Tazo tayi tijarar ta dakyar Yaran gidan Maza suka lallaba ta ta tafi dan shi qin fitowa yayi. Ya gaji da halin masufar da Fatu take jefashi a kullum shi be san Adadin bashin daya biya mata, idan baazo yau ba gobe se anzo to ya gaji. Yanzu ma maganar ya shigo ya mata akan ta nemi kudin matar ta bata idan ba haka ba tace gobe idan ta dawo da police zata zo to wallahi sedai su kulleta dan shi sisi baze sake biya mata ba ai badan ita kadai yake nema a rayuwarsa ba. Adda kuwa ko a jikinta ta cigaba da gayawa Amirah yanda sukayi da malami da kuma tabbacin da ya bata da an gama ai Bashir ze dawo hannunsu. “Amma fa Adda ni bana yarda idan akace wai Anty tana wa Yaya Bashir Asiri ke kanki Adda kin san ba haka bane” Hararar ta Adda tayi kafin tace “Ji banza, idan tanayi se tace miki zata fito fili a sani ne? Ko kuma ace da batayi to daman me zatawa Asirin bayan kusan ita ce Mijin shi Matar yanzu kuwa daya bunqasa ai bazatayi sanya wata tazo ta taya ta ci ba. Ni in zaki karbi abu kiyi kawai kiyi kafin ki fara saka wasiqasi ki bata mana aiki dama ni ina zargin bakyayin yanda akace shiyasa komai baya tafiyar mana daidai to ke kika sani wallahi kina ji kina gaji zata kado ki waje ki dawo mujere ana mana Dariya” da haka ta shige dakinta dan yin Sallar Azahar da La’asar da suka sameta a tafe ga Magriba an fara kira. Amirah ma jiki a sanyaye taja jug ta fara bankawa cikinta ruwan magani dukda qasan ranta bata jin Bashir zezo wannan satin amma dai gara tasha saboda tsaro se sannan ta tuna bata gayawa Adda yanda a ka qare da Indo me kaya ba, ta cicciba zuwa dakin Addan ta tarar tana sallah se itama ta wuce nasu dakin dan yin Sallar. WASHE GARI Qarfe bakwai a qofar gidan tayiwa Indo ta shiga biga gate baji ba gani dan ta rantse wallahi yau ko ita ko Fatu a garin nan ita zata rainawa hankali lallai bata san wacece Indo ba. Alhaji Murtala da fitowarsa kenan ze tafi wata Jana’iza ya qarasa ya cire sakata ta hankado qofar saura qiris ta bige shi tayi ciki abunta se kawai ya girgiza kai tareda juyawa ya kunna motarsa, Aminu daya daga yaran gidan ya qarasa bude masa gate yai ficewarsa dan bama ze tsaya yaga yanda zata kaya ba. Adda Fatu da tunda tajiyo bugun ta janyo abinda Malam Wizy ya bata ta bantara se taga kaman Namijin Goro amma kai bashi bane qila kama ce ita dai ta afa baki ta hau tauna harda guara zama akan kujera tana jiran shigowar Indo se kuwa gata kaman an jefota ta fado. “Fatu bani kudina kafin na yaga miki rigar rashin mutunchi a unguwar nan” ta fada tana huci, se Adda ta miqe tana qara bantarar magani ta tauni ta nufo Indo tana cewa “Ke Indo fita ki tafi karki sake dawo wa gidan nan ki manta da zancen bashi a tsakanin mu har abada idan ma da wasu kudin a jakarki yanzu cirosu ki bani” “Fatu hauka ne ya sameki ko to bari kuwa yanzu zan sauke miki shi wallahi ina batun ki bani kudina kina min wata maganar banza harda in qara miki wasu to bari kiga” Indo ta fada tana ja baya ganin Adda ta nufo ta tana sake maimaita kalamanta se zare ido takeyi ai bata yi aune ba se Ji tayi Indo ta dauke ta da wani gigitaccen mari daya sakata furzo da goron ba shiri ta kife gurin tana kururuwa dan ji tayi kunnenta, indo bata haqura ba ta sake kai mata Mahangurba a hanci aikuwa take ya fashe ya fara bulbulo da jini sannan ta bita ta turmushe ta hau duka, Adda ba hakin kwace wa se ihu take tana neman dauki. Kishiyoyinta uku duk suna tsaye a bakin kofa da yayan su mata ransu qal akan wannan abu se Ummi da Amira a gefe suna taya ta ihun ba damar kai mata dauki 😂. Se da tayi mata lilis sannan Samarin gidan suka kawo taimako dakyar aka kwaceta Indo na jaddada mata wallahi ko kudinta ko kuwa kullum seta zo ta nada mata na jaki dan ta bar maganar police ma da kanta zata kwaci kudinta sannan ta fice daga gidan. Adda fuska tayi luhu luhu se hawaye da ajiyar rai take ga hanci ya fashe a ranta Allah ya isa take jerawa Malam Wizy akan wannan abu daya bata gashi nan ba biyan buqata se bugu data sha a banza, bari Suga na Bashir idan taga ba nasara dole ta koma ya biyata kudinta dan bazata dauki asara biyu ba. Ita se yanzu ma taji wani tsautsayi ya kaisu yarda da Dan Napep din nan? Anya ma ba hadin baki bane shida Hajia Balaraba suka kaita a cinye mata kudi amma ai itama Balarabar ta bayar. Bari tayi ta kanta yanzu zata kirata taji yanda akayi. Ummi ce ta kamata ta kaita daki ta hada mata ruwan Me zafi a toilet ta shiga dan gasa jikinta, dakyar ta iya watsawa ta samu dai Habon ya tsaya ta dauro towel ta fito ta haye gado kan kace meye wannan zazzabi ya rafke ta se rawar sanyi take. (To Adda Allah ya qara lafiya ya kiyaye na gaba 😂😂😂😂). Kafin yamma dai jiki ya qi dadi dole suka kaita asibiti tasha Allurai suka dawo da magunguna gashi har sannan babu Bashir babu labarin sa kuma ta kira Dada ma wayarta a kashe, kukan baqin ciki ta fashe dashi da tsoron haduwarsu da Indo gobe. Mu koma Lagos Qiri qiri Asma’u ta qi bari a sallameta acewarta se tayi sati, Dr beqi ba tunda sabga ce ta kudi qaruwar su ce dan haka yace wa Bashir dole ta zauna suyi monitoring Bp nata na wani lokacin kafin a sallame ta. A kwana biyun nan idan kaga Bashir se ya baka tausayi yanda yayi wurjanjan dashi har a office an gane bashi da nutsuwa dole suka bashi leave na 1 week saboda ya samu ya kula da yaran kafin a sallami Asma’u, sauqin sa daya yaran sun rage kokekoken tunda kullum yanzu da safe ze kai su da daddare ma su koma. Shi ya ma manta da wata Amirah sam bare zancen zuwa Gombe yau ranar Sunday kaman yanda ya saba bayan ya kawo yaran, suna gurinta Abokinsa Abdurrahman da Matarsa suka zo dubata, su suka tafi da yaran gidan su akan da dare idan ya gama se yaje ya dauke su su tafi gida ya dan rage zirga zirga. Suna zaune kamar kurame bame cewa komai, ita tana chatting a wayarta shi kuma ya tasa ta a gaba yana kallo ganin yanda ta sake wani mugun fresh tayi kyau alamar ta samu hutu ba abinda yake damunta shi kuwa banda uwar rama da baqi da yayi to ga Damuwa ga babu abinci me kyau daya saba kwasa dan yanzu suma yaran mata yassara kawai suke ci dama Mami ce take tsayawa ayi abinci me kyau to bata nan dan haka baya iya ci ko sun dafa in yunwa ta dameshi ne ma zeci Indomie yasa tea in ba haka ba Snacks da lemo ne rabin abincin nasa. Dagowar da Asma’u tayi tana dan murmushi tareda tsare shi da ido tace “wannan week din bazakaje Gombe bane” Se a sannan manAmirah ta fado masa ya tuna rabonda suyi waya tun ran Laraba be kiratan ba yasan kuma itama bazatayi gigin kiransa ba tunda ya mata warning. Numfashi yaja kafin yace “Wallahi na ma manta shaf kuma ko waya banyi nace bazan shigo ba gashi har yau Sunday, ya kamata kam na kirata”. Kishi ne ya dan tsikareta ta wani fannin kuma tana yabawa Bashir dan ba laifi yana kaman ta Adalci wani Sa’ilin. A farko farko se sati biyu yake zuwarwa Amiran ze tafi Friday ya dawo Monday da safe to da aka samu qarin kudin jirgi dole ya chanza tsarin zuwa Qarshen wata, daga bayannan kuma bata san dalili ba wani Sa’in se ya jera sati uku hudu ma duk weekend se yaje duk kuwa da ayanzu kudin jirgin ma yafi da ita dai bata taba tambayarsa dalili ba haka nan ko tare sukaje Gombe ko kwana na wa zasuyi bata da Kwana a yanda suka tsarawa kansu shida Amaryar sa kuma da taimakon Adda to ita hakan be dame ta ba tunda daman idan taje ba zama take ba a lokacin take samun ziyartar yan uwa da sauran abubuwan da akayi bata nan. Tana kallonsa ya zaro waya ya shiga kiran Amiran ringing biyu kuwa ta daga tana fashe masa da Kuka, kallon Ma’u data juya baya ta kwanta yayi ya tabbatar ta jiyo kukan Amiran se ya miqe ya nufi qofa yana ce mata “kukan kuma Na mene kinsan bana so” Wani qululu ya tsayawa Asma’u, wato itace banza a wajensa da in zata mutu tana kuka baze ce ta bari ba kenan ashe ita ta zata so ne yasa yake barinta ta fitar da damuwarta ashe tsabar be damu bane kai Anya kuwa Bashir ya taba sonta a ransa?? Abubuwa da yawa da ada take daukar haka yaje se a yanzu take ganin banbance banbance ko kuma dama Haka Mazan suke ko wacce Mace da yanda halayyarsu taje a wajen ta? In kuwa haka ne Sun Amsa sunansu na Hawainiya. AMIRAH Sanda Bashir ya kirata suna zaune da Addah da har yau fuska bata daidaita ba ko jiya Indo ta dawo Allah ya taimaketa Alhaji na Nan, shi ya kashe rigimar cikin Kudinta da yake hannunsa yake juya musu da a qalla sun kai 2 Million yau ta kirbi dari gobe Hamsin a wayonta kudinsa take ci da yaga fa da gaske Fatu ba hankali ne da ita ba dole ya saka akayi rubutu kowacce cikin Matan da kudinta dake hannunsa ya kuma gaya musu duk wadda ta nemi kudi indai ba abinda ya zama dolensa ba to a cikin kudinsu suka ce sun yarda kowa ta saka hannu to ita Adda a nata baqin wayon da ganin tasha kansa bata dena ba ta ci gaba dacin kudinta hankali kwance ba tareda ta sani ba shi kuwa yana lissafe da komai ga kuma takaddu saboda Adar rai. To tun jiya daya fita ya yanke shawarar cikin 500 din data rage mata ze biya mata bashin nan dan ba ita kadai ba harda shi take zubarwa mutunci maqota kullum na jiyo an zo karbar bashi gidansa bayan Allah ya rufa masa asiri. Jiyan Indo na zuwa ya fito a gaban Fatu ya zaro kudi ya bata ta qirga su cif sun cika tace mata “Allah ya taimakeki wallahi da dukan yau se yafi na jiya kuma wallahi ko da wasa karki kuskura naga qafarki kinzo neman abu gida na dan ance ba kunya ce da ke ba se ki dawo” ita dai tayi muqus harda yiwa Alhaji godiya yace mata “Godiyar me zakimun a cikin kudinki na biya miki ai ba nawa ba tunda haka kika zaba se kiyi tayi wata ran idan ba kiyi hankali ba suturar da zaki daura se ta gagare ki indai baki dena cin bashi ba. Yana fita wayar Bashir na shigo wa Adda ta zabga Hamdala tace kin gani ko a sannu a sannu komai ze daidaita maza ki daga ki rushe da kuka duk kibi ki hargitsa shi ki samu yazo ko ya turo mana wani abun, haka akayi tana dagawa ta saka kukan. Seda ta tsagaita ta gaishe shi ya amsa yana tambayarta jikinta tace da sauqi. “I’m sorry Amirah ranar nayi miki ihu raina ne a bace Wlh ga Ma’una bata da lafiya a lokacin ke kuma kin dame ni da kira” “Ba komai Yayana ya wuce yanzu ya jikin Antyn? Ban sani ba ai dana kira na mata sannu dukda idan na kirata ma bata amsawa kaga yanzu kosu Aliyu ta hanani magana dasu” “Qorafi dai qorafi halin daya tsana da Amirah kenan a rayuwarsa” ya ayya a ransa a fili kuwa se yace “Ta samu sauqi, se zuwa Next week zan shigo insha Allah akwai abinda kike da bugata ne?” Se Adda ta zungureta tana rada mata tace kudi se tace “Uhm uhm Ba komai maganar siyayya ne kawai daman se kuma ni Yayana ina so in dawo kusa da kai gaskiya saboda....” “Amirah I’m looking forward to that ok maganar kudi kuma idan mun gama zan saka miki wani abun kafin End of the month saboda nayi hidimar Asibiti duk na kashe kudaden hannuna yanzu” “To shikenan amma dai gaskiya Yaya nidai ko wani gidan ne se ka samar min da zan zauna amma irin Na Anty nake so me kyau sannan fa yaya karka manta da zancen canjin kujerun irin natan” ta sake fada dan harga ranta fa ita tunda ta tashi burinta kawai shine ta kamo Asma’u ta ko ina. “Naji ki gaida su Adda” ya fada yana qoqarin kashe wayar jin tana so ta bata masa rai, “Bama ta da lafiya bari na bata kayi mata sannu” ta fada kafin ta miqa mata kuwa qit ya kashe wayarsa dan itama Addan haushin ta yake ji dan abu da yawa ita take dora Amiran akai, idan banda bata da tunani kwana nawa basuyi waya ba amma da abinda ya kamata ta tare shi kenan? Bayan haka yanzu fa yake gaya mata bashida kudi amma ita wannan baya gabanta buqatarta ce kawai a gaba. besan dalilin ta na gasa da Ma’u ba komai ta gani a gurinta yunqurinta se itama ta samu, tana mance cewa Asma’u na aiki tana da abin kanta abu dayawa ko beyi mata ba zatawa kanta. Gudun karta ishe shi ya saka shi yi mata transfer 100k saura 200k kenan kudin siyayyar kayan haihuwa dana fitar suna da tace ya bata, yace sun yi yawa ta ringa masa mita da qorafin bala’i dole ya yarda ze batan kota qyale shi. shi tunda Asma’u take haihuwa baya tunanin ya taba bata dunqulalliyar dubu Hamsin wai da sunan tayi siyayya shi bata ma taba tambayarsa ba, duk abinda ya dakko ya bata idan yana dashi karba take idan ma bashi dashi haqura take yan uwanta su mata harma ya samu Arziqin shaddar fitar suna shima. Baze taba manta Haihuwar Abdallah ba da tace ya saka mata sunan Babanta yace mata sedai ta se masa rago hakan kuwa akayi ta siyo raguna har biyu ta kuma cewa Yan uwanta da Nasa shi ya siya har yu har gobe ya kalli yaron se yaji wata kunya da Nauyin sa dana Uwarsa ya kamashi, shi wallahi a duniya in yai wani abun se yaga kamar dai shafar Aljanu yake samu su saka shi yayi abu daga baya yazo yana dana sani (Shafar Aljanu ko iskanci ba 😂😂) Dakin ya koma Ma’u najinsa tayi shiru kamar me bacci ya gaji da tsayuwa ya qaraso ya mata peck a goshi ya fita yanaso yaje gida ya dan yi bacci tunda yaran basa nan yau shima ya dan huta kafin gobe Monday. Su Addah kam Kudi na shigowa suka hau Murna “Ke yar nan kinga abu kaman wasa aikin malam ya fara kama Bashir to wannan aka gama aiki kuma ai ban san yanda zamu taka shi ba yanda muke so. Ita waccan shegiyar dama itama ba a zaune take ba dole nata yaqi tasiri amma tunda mun rabu lafiya shikenan, yanzu bari an jima zan kira Malam se ya nada account mu sake tura masa ko kudin biyu ne tunda na bada na biyu ayi a gama aikin nan mu fara shan romon damokaradiyya” “To Adda amma da mun bari dai akwana biyu a sake samun wani abun wannan mudan rage siyayyar mana” cewar Amira. “Ke dallacan ba gara a gama ba nasan ko million goma kika ce ya baki kawo wa zeyi” “Kuma fa haka ne, to ki kira se a tura masa din” “Allah dai ya kauda bacin rana” Ummi ta fada tana miqewa kafin ta karbi duka ko Ashar daga gurin Adda ai kuwa ta shiga aika mata dasu tana ce mata yar baqin ciki haka zata qare tana gani suna abin arziqi banda ita. Wai ya Hajia Balaraba ta qare da maganin Malam Wizy ne?? 😂😂😂 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 WATA KISHIYAR 🥰👹 (Alkhairi CE KO SHARRI) 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 Na Maryamah_Mrs AM (Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah) Page 7 A bangaren Hajia Balaraba kuwa cike da farin ciki ta bude gida ta shiga ganin har sannan Kishiyarta bata dawo daga gurin aiki ba, cikin sauri ta fito da rubutu ta huda leda tareda guntsa ta feshe kofar dakin Amarya tana cewa “Shegiya maza ki dawo ki taka ni Alhaji yaiyo waya daga kasuwar ma yace ya sake ki base ya jira ya dawo ba” ta qulle ragowar gudun kar ya zube ta qarasa qofar ta. Mayafinta kadai ta ajiye ta shiga kitchen ta hau kicikicin dora girki qarin farin cikinta ita ce da girki dama kai yau koda ba itace da girki ba ai dole tasan yanda za’ayi ta aiwatar da aikin nan tanayi tana tuna irin cin mitunchin da Alhaji yai mata dazu da safe kafin ya fita kuma ta tabbata duk Amarya ce ta zugoshi har yana iqirarin tabar ganin sun tara yaya da jikoki tsaf seya yanka mata tikitin zawarci. Itadai tunda Malam na kan Tudu ya kwanta dama kamar ya tafi da duk ayyukan da Tayi akan Alhaji ne komai ya karye shekara da shekaru tana cin duniyarta da tsinke se yanzu da tsufa ya kusa cin mata ne zata fara karbar taskun namiji ina bazeyuwu ba ai. Tsaf ta gama hada lafiyayyar Miyar taushenta kafin ta dakko qaramar tukunya ta sare wata wadda zata ci, nan da nan dakko ragowar rubutun Malam Wizy ta kurbe tas ta kuskuro dattin bakinta da komai ta watsa musu a miya ta sake kurbe ragowar ta zuba ta juyata dakyau ta rage wuta ranta fes dan gani take kamar ma aikin gama ya gama. Tana cikin malmala tuwan autarta me suna Ruqayya ta shigo ta dawo daga makaranta dan tana shekarar ta ta qarshe ne a GSU da mamaki ta kalli maman tata kafin tace “Hajia kece dakanki yau a kitchen ina Baba Zulai din” Bata ko dago ta kalleta ba tace “Taje gida Sa’adenta batada lafiya ina ga se gobe zata dawo” “Kai dukda haka da mamaki ace Hajia kina girki lallai yau zamu kwashi dabge bari nayi sauri nayi wanka nayi Sallah muzo mu kwashi ganima” “Zaki kwashi ganima dan uwarki duk zan kulle bakinku ai na ga ta inda zaki ringa kaiwa uban naki gulma idan na taba kudinsa” ta fada bayan Ruqayyan ta fita daga kitchen din Oho bata ma san tanayi ba dakin ta ta nufa a ranta tana ayyana tabbas akwai wata a qasa dan ita dai tafi shekara Goma rabonda taga Hajia tayi girki da kanta Baba Zulai ce take yi musu ko kuma ita idan taba gida. Ita zata iya cewa ma idan kaga Hajia a kitchen to an gama Abinci ne idan harda na Baban zatayi barbade daga baya ma daya gane yai Allah ya isa yama zo kuma ya dena cin abincin kwatakwata se baya bayan nan taga ya dawo yana ci. Ita kuwa Hajia tana sauke tuwo ruwan Tea ta mayar ta saka lipton dinta da kayan qanshi sannan ta zuba jiqon Wizy, bata matsa ko ina ba seda ta kammala tsaf ta hada komai ta kai kan Dining sannan tashi ga dakinta tai wanka ta fara jero Qara’in salloli. Seda akayi Isha Alhaji ya shigo, kai tsaye part din Amarya ya shiga dan akwai kayan daya manta da safe da ze tafi kasuwa yana so ya dauka kar gobe ya sake mantawa. da mamaki ya kalleta dan ya zata ta tafi aiki tunda tace masa Night Duty ne da ita. tana ganinsa ta miqe “Yawwa Alhaji dama kai nake jira tun dazu” “Lafiya Abida baki tafi aikin ba? Jiran me kike mun?” Ya fada yana kallonta. Seta miqa masa wayarta kawai ba tareda tace komai ba, karba yayi yana duba screen din sega video Hajia Balaraba tana kici kicin zuge jaka, baya jin me take cewa amma fes yaga sanda ta ciro leda ta guntsi rubutun ta feshe kofar dakin Amarya ta tafi” Se ya miqa mata wayar dason jin qarin bayani. “Wallahi Alhaji yanda ka gani dinnan kasan ka fita ka barni kaina yana ciwo dan haka sena kwanta dan ban ma samu zuwa Barkar Haula da nace maka zan fita ba, se bayan La’asar na ma idar da sallah na tashi zan leqa na karbo Kati se naji motsin a bude qofa, in duba ta window fa shine naga Maman Suhaila na wannan ta tsaya tana maganganu tareda bude jaka wayata na hannuna ni kuma shine na kunna video saboda kar a maimaita irin ta wancan karan data zuba magani akace qarya nakeyi yanzu dai ga Hujja ka gani da idonka, nidai ban fita ba koma na menene kai kadai ka tsallaka shi se kasan yanda zaayi azo a karya dan bazan yi ta zama a daki ba kona fita a sabautani a banza”. Wani irin tuquqin baqin cikine ya rufe Alhaji har huci yakeyi, wato duk Allah ya isar dayai wa matar nan bata daddara ba kenan? Shin wai se Yaushe Balaraba nutsu tasan Annabi ya faku ne ita dai duniya ce kawai a gabanta to kuwa Insha Allahu Allah baze sake bata ikon maidashi halin data jefa rayuwarsa a baya ba shi wallahi badan kar duniya ta zageshi ace ya saki matar sa auren shekara Arba’in ba da rabuwa zeyi da ita ya huta amma yanzu babu wand ze dubi abinda ta aikata masa shedai a dora masa laifi ace Ya wulaqanta Uwargidansa. Cikin fushin daya gaza boyewa ya fita, mintina kadan ya dawo tareda wani yaro ya shigo palour ya bar yaron a kofar dakin tareda nuna masa gurin yace ga inda zeyi fitsarin nan yaro kuwa ya tsula abunsa Alhaji ya fita ya nuna masa famfo ya taro ruwa suka sheqe a gurin nan da nan ya wuce daman tiles ne. Ciki ya dawo yace da Abida ta biyo shi yai gaba tana baya se palour Hajia Balaraba. Tana zaune ta hakimce akan kujera ta sheqa kwalliya ta garari ta kuwa yi kyau sosai dan Hajia Balaraba akwai kyan jiki da gayu kai bazakace tabawa Hamsin baya ba. Tana ganin Alhaji ta miqe da fara’a da nufin tarar sa sedai ganin Amarya a bayansa yasa ta gintse fuska a ranta tana tunanin meya faru kuma dan ita bata ma lura da yanayin fuskar Alhajin ba. “Balaraba me kika zuba a qofar dakin Abida?” Ya tambaye ta cikin kaushin murya. Qirjinta ne ya fara luguden daka zuciyarta kaman zatayi tsalle ta fito saboda razana, ya akayi ya sani to ko wani ya ganta ne? Ita dai a hasashenta babu kowa a gidan dan Tunda da zata fita seda ta saka muqulli ta kulle haka data dawo dakanta ta bude kofar, koma menene bazata bare a gano ta dole tasan yanda zata kare kanta. Qoqarin daidaita nutsuwarta tayi tana daure fuska tace “Bangane me kake nufi ba Alhaji wani sharrin kuma aka sake qullomin yau ma? Ni duk yau ma ban fita daga part dina ba bare har naje qofarta na zuba abu”. Kallon takaici da tsana yake binta dashi, se ya miqawa Abida hannu tayi saurin miqa masa wayarta. Video yayi playing ya miqawa Hajia Balaraba dake ta taraddadin me nene a cikin wayar Abidan, ai seda ta kusa Sakin fitsari a gurin saboda kidima nan danna zufa ta shiga keto mata. “Wane La’anannen ne ya dauki wannan video” ta fada bakinta yana rawa tsabar yanda ta rikice, zata sakw magana ya miqa mata hannu ta bashi wayar yana cewa “Kici gaba Balaraba sharri dan aikene ki sani duk nisan indai kika aika shi watarana seya dawo miki, tunda har kin raina Allah ya isar da nayi miki akan in kika sake yimun wani abu ko wani daga cikin iyalaina shikenan na barki da Allah kuma matakin qarshe dazan dauka shine wallahi Balaraba idan kika sake zuwa gidan wani malami kika aikata wani abun sihiri a cikin gidan nan kai na ko kan wani nawa, na sani ko ban sani ba to ki sani a bakin aurenki” Cikin tsananin razani ta dago ta kalle shi dan bata taba zaton tsaurin hukuncin ze kai haka ba, ta bude baki da niyyar neman sassauci yace “Karma kice komai dagaske nake kuma ba igiya daya ko biyu ba dukka ukun nake nufi idan kuma kika aikata a bayan idona ba tare da na sani ba muka ci gaba da zaman aure dake wannan kuma na barki da Allah shi ze bimin haqqin zaman zina da kika sa nayi ba tare da sani na ba” yana kaiwa nan ya shige dakin sa da yake a part din nata, Abida ma jiki a sanyaye ta juya ta fita aka bar Balaraba da dora hannu aka tama tasa kuka zatayi ko ihu? Wannan shi ake kira da An bata biyar goma bata gyaru ba (Dama ai duk wanda yace tukunyar wani bazata tafasa ba tabbas tashi ko dumi kuwa ba zatayi ba). Lagos Seda Ma’u ta cike satin nan daya raya cif aka sallameta, da safe bayan Bashir da yara sunzo sun tafi tacewa Dr ya sallameta haka. Da kanta ta karbi Discharging later ta hada yan kayanta kafim ta kira Uber ta cale gida (tsiyar garin da baka da dangi kenan). Koda ta isa gidan bata zauna ba seda ta gyara ko ina tsaf ya dawo mata yanda take so sannan ta shiga hidimar dora girki kuma, aikin ya jata da yawa dan har bayan La’asar sannan ta kammala komai ta jere akan Dining kafin ta koma dakinta kuma ta fada wanka. Tsaf ta shirya cikin wani hadadden cotton lace Army green da akayiwa dinkin Fitted gown datai bala’in yi mata kyau ta fito mata sauran quruciyarta. Indai gayune dole a cirewa Ma’u hula wannan ko a zamanin yammatancinta babu kamarta a kaf qawayenta tana da kyau ta kuma iya daukar wanka ga farin jini Allah ya mata abinda ya sa ta zama ta daban kenan da sauran. Daurin nan ta kawo shi gaban goshi bayan ta fake gashinta qasa qasa sannan ta saka cogenta ta qara feshe jikinta da turaruka ta shiga juyi a gaban mirrow dan ta burge kanta da kanta ballanta na Kuma Bashir ya ganta tasan duk yanda yake qyashin ya yaba kwalliyarta yau kam se idanunsa sun fado qasa qilan a garin kallo. Mint flavored chewing gum ta jefa a bakinta kafin ta fito palour ta samu kujerar dake facing kofar shigowa ta dora daya kan daya tana girgizasu tana danna waya ba koyi minti biyar da zama ba ta jiyo tsayuwar motarsu, seta qara gyara zaman ta dakyau tana sauraron shigowarsu. Aliyu ne a gaba dauke da Laptop bag din Bashir se school bag dinsa daya goya a baya se ga sauran a bayansa. Gaba daya suka nufe ta cike da murnar ganinta a gidan, Aliyu ne yace “Mami this house can never be complete without you Allah Mami da baki nan ji nake kamar a kango muke kwana amma yanzu tundaga qofa kawai naji it feels like home again ashe kece kika dawo ciki” Dukan wasa ta kai masa tana cewa “Oh Ali yammata kam se sun bani da dadin bakin nan naka Allah dai ya nuna mun lokacin” se ya rufe fuska wai shi kunya yana cewa “Kai Mami ki dena kunya nake ji” Gaba daya suka saka dariya, se a sannan ta daga kanta ta kalli inda Malam Bashir yaci burki tunda ya shigo, seta qara fadada murmushinta tana cewa “Aa Baban Ali yane ka tsaya ka shigo ka zauna mana ko ka qara sa ciki”. Bashir Numfashinsa ne ya dauke na wani lokaci sanda yai arba da fuskar Ma’u, tayi masa kyau matuqa gaya da har ya kasa iya cire idanunsa daga kanta. Maganar da tayi ce ta fargar dashi kamar dama me jiran umarninta kuwa se ya taho, kusa da ita inda Farida ke zaune ya daga Faridan cak ya zauna a gurin tareda dora ta a cinyarsa kafin ya maida kallonsa kan Asma’u yace “to naga ne hankalin ki yana kan yaranki kamar ma ni baki ganni ba” ya fada yana kafeta da kallon nan nasa me saka Yammata fadawa soyayyarsa ba tare da sun shirya ba. Irin kallon da shi ya ringa qara rura garwashin soyayyarsa a zuciyarta har ya tada gagarumar wuta da hauyau ba’a samu ruwa ko iskar da sukayi nasarar kashe ta ba. Seta tsura masa nata kyawawan idon tana hango abinda zuciyarta ce kadai take da tafsirinsa, a cikin idanun Bashir kadai take iya hango tsabtatacciyar qaunarta wadda babu Algus ko digo a ciki amma ginshiri da baqar izzar sa suke hana bakinsa iya furtawa. Har gara gangar jikinsa takan gaza bashi hadin kai gurin boye sirrin zuciyar tasa dan a duk sanda suka hadu gangar jikinsa na sarrafuwa ne kawai bisa umarnin zuciyarsa bawai kwakwalwarsa da take nan kamar wadda akeyiwa hayaqin wiwi ba, yanzu yai abin arziqi an jima ya tafka na tsiya. Ganin irin kallon qudar da Abbi da Mami sukewa junansu ya saka Amna kama hannun twins manyan kuma suka tashi gaba daya kowa suka shige dakinsu, miqewar Farida daga kan qafarsa ta ankarar dashi, seya janye idanunsa cikin son basarwa shima ya miqe yana ce mata “Zan samu abinci kuwa? Gaba daya yau coffee ne kadai a cikina” “Ai fa ga Kuku ta dawo dole ka nemi abinci babu tambayar ya akai na taho ni kadai ban kiraka ba balle jin ya jikina” ta ayyana a zuciyarta, a fili kuwa seta ce “kayi wanka first, ga abinci nan yana jiranku” se ta miqe ta nufi dakin su Amna. Se ya rakata da ido kuwa kamar zasu fado din, yanda take juya qugunta da ya fito sosai saboda yanda rigar ta bawa komai haqqinsa ga qarar takalmin qafarta da yake ji kamar qararrawa a cikin qwaqwalwarsa. Wasu busassun yawu ya hadiye tareda lasar lips dinsa da suka bushe kafin yace “Hmmm” (inji me ciwon haqori 😂😂😂) karaf a kuwa a kunnen Asma’u daidai sanda take tura qofar dakin su Faridan “Idan baka chanza hali ba Bashir wata rana sedai ka farka ka ganka a kabari Maganganun da kake dannewa sun shaqe maka wuya, ayi mutum bakin na son magana amma baqin rai ya hana shi Allah yai mana magani dai”. Guri ta nema ta zauna dan ba abunda zatayi a dakin dama ta tashi ne kawai dan ta bashi damar kallon kwalliyar tata da kyau. Ahmad daya fito daga toilet alamar wanka a ka masa ta shiga shafawa mai kafin Muhammmad ma ya fito, tsaf ta shirya su, kafin su gama an kira Sallar Magriba dan haka tace suje suyi Alwala ita ma ta fita dan zuwa tayi a bakin qofa suka kusa cin karo da Bashir wanda da alama shima wankan yayi ya chanza kayansa zuwa Jallabiyya Baqa da tayi bala’in masa kyau duk da kasancewarsa ba fari qal ba, Bashir nada kyau irin na Maza me sanyi daya hadu da kwarjinin da Allah ya bashi. “Kayi kyau Baban Ali” ta fada da zuciya daya dan ita bata iya munafunci irin nasa ba kuma rashin yabon kwalliyarta be taba sare mata guiwa akan ta denayi ba. Kallon ta yayi yana dan Murmushi kafin yace “Koh?” Seta amasa masa da sarar sa tace “Uhm” tana qoqarin kauce masa a ranta tana mita. A zaman shekara Goma sha shidda baza ta tuna ranar da a karan kan Bashir ya budi baki ya yabi kwalliyar ta ba tun tana qorafi idan tayi se ta tambayeshi tayi kyau sannan ze yaba har ta gaji ma ta dena, yanzu da yaranta suka girma kuwa indai tayi kwalliyarta se sunce Mami kinyi kyau shiyasa ma ta dena damuwa da yabawar Bashir dukda abun da zafi amma ya zakayi (Mazan hausawan Mu Allah ya shirye ku dai 🥺🥺). Wuce shi tayi ta shiga dakinta itama ta daura Alwala shi kuma ya hada kan yaran suka fita. Data idar da sallah zama tayi ta qara gyara fuskarta dakyau sannan ta fito, sun zauna a Dining da gani ita suke jira dan haka ta qarasa gurin. Seda tayi serving kowa sannan ta zauna suka fara cin abinci kowa na santi karma Bashir yaji labari dan kunnensa har motsi yake. Besan yawan abincin daya nada ba seda ya qara saka serving spoon ze debo abincin a karo na uku bayan wanda ta zuba masa yaji wayam aiko suka kwashe da dariya suna kallonsa. Seya bata fuska kamar yaro yace “To ai yunwa nake ji for almost a week fa bamu ci abincin Mami ba, please Mami karki kuma tafiya ki barmu, we are so sorry mun ji jiki wallahi, we missed you alot”. “Zobon da Asma’u ta kurba ne ya sarqe ta ba shiri ta watso shi tsabar yanda mamakin kalaman Bashir suka nemi kasheta a zaune. “Bashir dai data sani ne yake wannan maganar?” Kai ita kam badan ciwo ba dadi ba da tace ta ringayi duk wata ko Allah ze saito mata Bashir zuwa abinda ta dade tana fata. 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 WATA KISHIYAR 🥰👹 (Alkhairi CE KO SHARRI) 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 Na Maryamah_Mrs AM(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah) Page 8 To Aka ce mata da Miji se Allah dan kuwa Ma’u da Basharin ta suna qulewa a daki sukai muqus aka shiga sharafin soyayya dan dama an dade ba’a hadu ba qarshe har makara tashi bacci sukayi. Safiyar ranar duk su biyun da ka kallesu zaka san suna cikin walwala. Ta cancada kwalliyarta da skirt and blouse na Atamfa komai ya fito se juyi take tana saka kwakwalwar Bashir jijjiga. haka ta hada musu breakfast me rai da lafiya suka ci suka wuce makaranta dukda sam be so yau ta zama ranar aiki ba ya so ace suna gida yau yaci duniyar sa da tsinke ya more amma ba komai ai Gobe Friday zasu hadu. Suna fita Qarasa yan abubuwan da suka rage mata tayi kafin ta shiga dakin ta ta kwanta dan huce gajiyar da Bashir ya tara mata, “Bashir is too good” ta ayyana aranta. Wato yasan ta yanda duk ze wanke laifinsa ta wannan fanni gwanin malami neda ta tabbatar samun irinsa se an tona. Tana tsaka da tunanin shauqin daren jiyan ta jiyo qarar door bell da kuma ringing din wayarta. Wayar ta fara jawowa ta duba, Anty ce matar ogan Bashir dake Flat din da yake kallon nasu, seta miqe tareda daukan Qaramin mayafi dan dankwalin kanta ya zame. A palour suka zube tare da Anty da ta farayiwa Asma’un tsiya tun daga qofa” “Kai Ma’u kinga wani kyallin goshi da kike daga fitowa daga Asibiti har za’a maida wani kenan”. Daria Asma’u tayi tana cewa “Haba dai ai na gama nikam wadan nan ma sun isa Allah ya raya mana sisi na kwai zan ci gaba dayi” “Inafa kika gama kedai ki shirya dan qila wasu biyun ne a tafe” “Ba amin ba Anty” ta tare Antyn. Gaisawa sukayi kafin Antyn tace mata “Shekaran jiya na dawo wlh se dare ma nashigo Honey yake cemun Ai kina Asibiti ba lafiya, har zamu zo jiya da magriba kuma yace sun hadu da Baban Aliyu a Masallaci ya ce masa kin dawo gida” “Eh wallahi jiya da rana aka sallamoni ai gaskiya Anty kinsha gida kusan 3 weeks fa” Asma’u ta fada. “Ki bari kedai zama nayi na huta nayi gyara sosai dan anan ba wani lokaci kake samu ka baje yanda kake so ba mutum na saka maka ido” cewar Anty tana bawa Asma’u hannu suka kashe “Kai Anty a ringa tausayin Baba na dai karki qarasa mana tsohon mu” “Ke barni fa dole na kwaci kaina sarai kin san Uwargida na bata wasa da gyara dole nima na zage kar a raina ni. Hira suka shigayi Anty ta shiga fito da abubuwan da tayo wa Asma’u tsaraba tana cewa “Gashinan se a ci gaba da gashi ban ce ki raga masa ko na second daya ba atoh” suka tuntsure da dariya Asma’u tana cewa “Anty baki da dama”. Se wurin 12 sannan ta mata sallama ta tafi bayan ta rakata qofa ta dawo tana tattare kayan zuwa dakinta a ranta tana qara jin qaunar Antyn dan yanda ta dauketa take kula da ita kamar qanwarta da suka fito ciki daya. Anty Suwaiba matar Engineer Abdullahi Gusau ce ogan Bashir. Itace Matar sa ta biyu uwar gidan ta ma anan Lagos take da zama amma ba unguwarsu daya ba. Mace ce me tsananin kirki dukda ta dan girmi Asma’u amma yanda take mu’amalantarta kaman qawaye ko shaqiqan yaya da qanwa suke dan tunda suka fara haduwa jinin su ya hadu da Asma’un. Ita kanta Asma’u tana ji da Antyn dan Ita tunda suka hadu rabon da tace ta siyi wani abun gyara da kudinta, a koda yaushe Anty cikin yo musu aike kaya gangariya daga Zamfara garinsu take kuma duk sanda Asma’u ta tambayeta nawane ta biya seta nuna bacin ranta. Ta kance da Asma’un “Ni a qanwa na dauke ki, banida kowa a Lagos seke yanzu”. Wasu daga cikin kayan ta fitar ta fara amfani dasu a ranta tana hasaso haduwarsu da Malam Bash dan tasan yau kam se tafi jiya Armashi. Kafin ta gama an kira sallar Azahar dan haka tayi alwala tayi sallar sannan ta kwanta zuwa La’asar kafin tasan abinda zata dafa musu kuma. Couscous tayi musu da miyar hanta ganin lokaci ya qure, setayi marinating kifin da zata gasa musu su qara dashi zuwa can anjima kafin a kwanta. Yauma batayi wasa ba gurin cin kwalliya ta daukar magana dan har tafi ta Jiya. Wasu riga da skirt ta saka na kanti Oxblood da suka kama jikinta kamar tanayin nishi zasu yage. Bata daura dankwali ba ta faka dogon baqin gashinta daya sha gyara se qanshi yake yi kafin tabi kowanne lungu da saqo na jikinta ta shafe da hadaddun turarukanta da ita kadai tasan wadanda take mixing da duk bala’in kwakwkwafin mutum baze taba cankar wane turare bane. Abaya ta fitar Baqa tareda mayafinta ta ajiye a gefe saboda yaranta maza ne, dukda qanana ne tana takatsantsan da irin shigar da zata fita gabansu da ita. Qugin motarsa data jiyo ya sakata saurin dora abayar ta yafa qaramin veil dinta akanta tareda zura slippers din ta ta nufi waje dan ta taro su. Bashir Fitowarsa daga mota yayi kyakykyawan gani, Ma’un sa ce kamar wata yar budurwar Balarabiya, tundaga nesa ya fara shaqar qamshin da takeyi wanda be taba jin sa a jikin wata mace ba bayan ita. Tamasa kyau yanda tayi rolling mayafin ya zagaye kyakykyawar fuskarta tareda bayyar da gaban gashinta daya ke nan luf a kwance ya qara qawata kwalliyar tata. kallonta yake har besan sanda wayar hannunsa ta subuceba. Yana jin yanda yaran suke zuzuta kyan da tayi amma nasa bakin kamar wanda aka sakawa qaton kwado a ka kulle ya kasa koda budeshi se idanu daya zuba mata kawai. Qarasawa gaban sa tayi ta durqusa tareda dakko masa wayar da ya yar bata miqa masa ba se jinta yayi gaba daya ta rungumoshi, saitin kunnensa ta furta “Welcome home SH (sweet heart)”. Kamar wanda ta tsoma a ruwan qanqara haka ya daskare a gurin yana jin kamar ya shide saboda muryarta da kuma numfashinta daya sauka a cikin kunnensa. Hannunsa ta kama ta zura masa wayar kafin ta juya tabarshi da shaqar qamshinta, batayi ko taku biyar ba taji an janyota ta baya yai mata wata kyakykyawar runguma tareda sauke mata kiss a gefen wuyanta da mayafi be ida rufewa ba. Zaro ido tayi tana riqe hannunsa, “Baban Ali a waje fa muke” ta fada ganin gogan na neman kauce hanya 😂 se a sannan ya farga dan shifa a lokacin ita kadai yake gani se kuwa yaja hannunta qii suka shige cikin gidan dan tuni yaran suka kama gaban su. Mantawa yayi da batun wata yunwa da gajiya daya kwaso suka shige dakinsa kai tsaye , ai be ida birkicewa ba seda yai arba da ainihin kwalliyar Ma’unsa tuni labari ya chanza 🏃🏽‍♀️🏃🏽‍♀️. Basu fito ba se qarfe goman dare, Babu kowa a palour alamar yaran harsun kwanta. Ma’u da duk tayi laushi ta nemi kujera ta zauna Bashir kuwa Dining ya wuce dan se yanzu yake jinsa kamar ze fadi saboda yunwa. Ya manta sam rabonsa da abinci tun na safe. A Babban plate ya juyo dukka abincin ya sakko da shi inda take ya ajiye sannan ya koma ya dakko kwanon Fish din da Amna ta gasa. Yana ci yana bata a baki har suka cinye se wani tarairayarta yakeyi kamar kwai, yanda yake rawar jiki da ita se yake tuna mata da lokutan baya a sanda yana Bashir din Ma’u kafin zaman majalisa da sababbin abokai ya sauya mata shi zuwa wani mutum na daban. Tana tuna irin gata da tarairayar daya ringa nuna mata a shekarar farko ta aurensu. A lokacin ya kan sakata taji tamkar tafi kowacce mace dacen miji duk kuwa da bata samu yanda take so ta bangaren kayan more rayuwa ba amma soyayya da tattalinta da ya ringayi yafi mata komai dan dama ita ai dan soyayya ta aure shi bawai kudi ba. Suna gama cin abincin dakin suka koma, ta gaji tibis dan haka ta haye gado ta kwanta yana matsa mata jikinta. Wayarsa ce tayi qara, a tare suka duba sunan Amira da ta gani yana yawo yasa ta dauke kanta. Satar kallonta yayi karaf kuwa suka hada ido, haka kawai yaji wani abu kamar nauyin Asma’u ya kamashi cikin son basar wa ya dauke idonsa ba tareda ya amsa wayar ba. Kiran da ya yanke wani ya sake shigowa ya sakata cewa “ka daga mana ba kiranka akeyi ba” seya dauki wayar, be zauna anan ba ya fita falo. Da kallo ta bishi tana qoqarin hana shedan yin tasiri akanta “Itama matarsa ce matsayinmu daya da ita” ta fadawa kanta sejin hawaye kawai tayi suna bin fuskarta. Bata san randa zata dena jin zafin yankan bayan da suka mata ba. Da ace wata can Bashir ya aura koda cikin dangin nasa ne damuwarta bazata kai haka ba amma fa Amirah, Amirah data dauka tamkar Amna. Yarinyar da ta gama sanin sirrinta ciki da waje ita ya auro mata a matsayin kishiya se kawai ta rushe da kukan takaicin da duk sanda ta tuna yanda auran Bashir ya kasance seta yi shi. Babu wanda ze gane zafin da takeji se wadda aka kwatantawa irin abinda akai mata, se yanzu take ganin dalilin da yake saka wasu matan aikata abubuwa da dama akan kishiya ko ma mijin kansa dan wallahi in akayi maka wani abun in ba me qarfin imani da tawallaki ba se kaji kamar bazaka yarda ba se ka dauki mataki. Har bacci ya dauketa Bashir be shigo ba se Asuba ta farka ta ganshi a bayanta. Ko a fuska bata nuna masa komai tayi sallah a dakin sannan ta fita gurin yara dan jiya basu samu ko yin magana ba. Seda ta hada musu abinci suka shirya tareda zama suka fara breakfast sannan ta koma dakin ganin Baban Ali be fito ba. A tsaye ta ganshi yana zuge jakar da yake tafiya da ita Gombe, dauke kanta tayi kamar bata gani ba tana cewa”Sun shirya fa gasu can sun fara cin abinci basu jiraka ba” tayi gaba da niyyar shigewa toilet dan bata so yai mata maganar tafiyar sa sedai tun kafin ta shiga ta jiyo shi yana cewa “Ke zaki dauko su daga school yau zan wuce Gombe ne daga office bazan dawo ta nan ba” ba tareda ta juyo ba tace masa “Allah ya tsare ka gaishe su” tai shigewarta abinta. Bin kofar yayi da kallo kafin jiki a sanyaye ya dauki Laptop bag dinsa da jakar kayan ya fita, seda ya kaisu mota sannan ya dawo shima ya hau Dining din amma se ya kasa taba komai. Shiru yayi yana kallon yaran suna cin abincinsu har suka gama Ahmad ya kalleshi yace “Abbi ina Mami zamu tafi” “Kuje mu tafi wanka take yi” ya fada yana miqewa. Har sun fita ya juyo zuwa cikin gidan, Bayaso su rabu da bacin rai kodan albarkacin farin cikin data bashi a kwana biyun nan. Harya kama Handle din dakin shegiyar zuciyar da take masa famfo ta zugo shi “to me kayi da zaka ke bata haquri ma?” Zuciyar ta raya masa, Seya saki qofar ya juya kawai. Asma’u da ke zaune tana jiran tsammanin zuwan Bashir ya rarrasheta, ajiyar zuciya ta sauke jin an taba qofa harda qara narke fuska tana ayyana abinda zatayi ta gigitashi se taji shiru, the next thing ko se jin tashin motarsa tayi ta yaye window da sauri har sun wuce se qurar daya tayar, baki bude take kallon motar harya qule mata, “Hmmm” ta sauke numfashi kawai ta shiga shafa mai, bataso ta tuna abun ma bare ranta ya baci ita dai addu’arta idan Bashir nada rabon ganewa to Allah ya maido shi kan hanya. Gombe gidan Addah A daren ranar da Bashir ya turo musu da kudi tayi ta kiran Number da Malam Wizy ya basu bata samu ba, bata haqura ba tayita gwada Number har washe gari amma shiru gashi ta kira wayar Hajia Balaraba ma a kashe. Jikinta dabe gama warwarewa bane ya hanata fita ta bari akan zuwa talata tasan ta warke seta je gidan Hajia Balaraban ta dai ci gaba da kiran wayar tasa ko zata samu cikin Sa’a kuwa ranar Laraba da safe tana kira ta shiga. Ta gama ringing ba’a dauka ba seda ta sake kira aka daga. Muryar wata tsohuwa taji daga ji taji duniya har ta gaji tana cewa “kai ku duba nan waye ya bugo, Wizy da qaninsa Iliya suna zaune a dakin Kakarsu daidai lokacin sunzo gaishe ta, miqa wa Wizy wayar tsohuwa tayi tana sake cewa ya duba ga gani. Sallama Adda ta sakeyi, fes Wizy ya gane muryarta se yai saurin datse kiran ya miqe yana cewa Kaka yana zuwa. Can wani lungu ya buya yayi recharging wayar kaka ya dannanwa Adda kira. “Salamu alaikum malam ina wuni” ta fada cike da zumudi “Lafiya lau dawa nake magana” ya tambaya irin be gane ta din nan ba “Nice Malam wadda Sani ya kawo mu (sunan da Me Napep ya gaya musu kenan) “To to hajia ya gida naji ki shiru da alama buqata ta fara biya kenan” “Wallahi malam na danyi rashin lafiya ne kwana biyu kuma na kikkiraka ma wayar a kashe” Addah ta fada “Eh wallahi kwana biyu kam na kashe waya dan na shiga halwa ne inata ayyukan ku dafatan ana ganin haske ko” “Sosai kuwa Malam ya fara samuwa” “To haka ake so yanzu to ya akayi?” Ya sake tambayarta. “Dama na samu wasu kudin ne nace bari na turo a ci gaba da aikin mu sameshi gaba daya” “Kin kyauta kuwa ai ina tabbatar miki idan aiki ya kammala hajia nasan indai kin riqe amana har ni dinnan se kin mun kyautar kujerar hajji” Wizy ya fada yana tsallen murna jin wata banzar zata fado. “Insha Allahu kuwa malam yanzu dai ka bada akawun a tura kudin nan ayi a ci gaba” “Ba matsala da mun aje waya zan turo miki” sukayi sallama yana qara karanta mata qanzon kurege. Harya fara typing account details dinsa wani tunani ya kawo kansa, idan ta tashi fa za’a Iya tracing dinsa ta banki, se yai saurin gogewa ya danna mata kira. Tana dagawa yace “Hajia nace kudinnan ki cire su, akwai yaro da na aika qauye ya siyo ragunan wasu aiki bari naji in be tafi ba se ya biyo ya karba kawai ya wuce” da haka sukayi sallama. Minti kadan ya sake kiranta yace ze turo yaro, nan ta zayyana masa Address ashe ma basu da nisa ya ma gane gidan daya daga cikin yaran mijinta abokinsa ne. Isma’il me Napep ya dannawa waya suka tafi tareda wani qaninsa me suna Nasiru da yai shigar me zuwa kasuwar qauye. Ko kafin su Iso Adda ta aika Ummi an ciro mata 80k kudin rago biyu yaro na zuwa ya shiga har palour ta ta bashi kudi ya jefa a buhu ya fice. Gaba suka qara aka tsaya kowa aka bashi rabonsa ya zuba a Aljihu Malam Wizy ya zare sim din Kaka ya ballashi biyu ya zubar yana cewa “mun tatseta ya isa haka” suka sheqe da dariya. To Addah Allah ya maida Alkahiri ya kiyaye na gaba 🤷🏽‍♀️🤷🏽‍♀️ 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 WATA KISHIYAR 🥰👹 (Alkhairi CE KO SHARRI) 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 Na Maryamah_Mrs AM (Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah) Page 9 Gombe Ana kiran magriba Bashir ya shiga gidan sa na Gombe, tun qarfe hudu da rabi suka sauka tazarar tafiyar daga Akko zuwa Gombe ta kaishi Magriba. A qofar gidansa Me Taxi din daya dauko shata daga Airport ya sauke shi ya fito dakyar yana jan qafa ga yunwa ga gajia tiqis saboda yau yasha aiki a office ga kuma tafiya dukda a jirgine. Yana qoqarin bude get din a ransa yana ayya Allah yasa ma ta dawo gidan dan yana daga ciki rashin sanin ya kamatan Amirah a duk sanda zezo hankalin ta be taba gaya mata tazo ta gyara gida tayi girki dan tarbarsa ba se in ya tuna mata. Dama can tun tana yarinya yasan qazama ce ta gaske daga baya ne zama da Asma’u ya sa tadan chanza tareda koyar wasu abubuwan amma dukda haka tsaftar biri gareta. Zata yi wanka ta gyara jiki amma fa duk dattin guri haka zatayi zamanta. Yana jefa qafa busassun ganyayen bishiyar da suka zube ne suka masa Maraba. Compound din ya hada uwar qura dama ga shi an fara Sanyi da Hazo a garin. Takaici ya qume shi danya tabbata bata dawo ba kenan. Bangaren Asma’u ya nufa dan yasan yace zeje dakinsa na part din Amiran ma ransa ne ze qara baci. Seda ya kunna wutar bangaren sannan ya bude palour ya shiga da Bismillah. Komai na nan a kintse yanda ta barshi, cike da gajiya yake daga qafafunsa ya haye benen da ze kaishi dakinsa. Nan dinma fes dashi ya saka hannu ya yaye ledar da take shimfidawa akan Katifa bayan ta cire bedsheets din saboda qura sannan ya zube kayan daya shigo dasu. Toilet ya fada ya dan daurayeshi yayi wanka tareda dauro Alwala ya fito. Harya idar da sallah beji alamar waniya shigo gidan ba ransa ya qara baci amma seya danne kawai ya janyo wayarsa ya kira Qaninsa Naziru ya kawo masa motarsa dayake amfani da ita anan. Bayan ya kashe se yayi dialing number Asma’u, deep down yanajin kaman dazu da safe be kyauta mata ba. Har wayar ta qaraci ringing dinta bata daga ba, ya sake kira nan ma shiru se ya maida akalar kiran zuwa ga Amirah dan yaga alamar hankalinta ragaggene. Ai a qalla yaci ta kira taji yazo ko kuwa tunda tasan da zuwan nasa yau amma still itama bata dauki wayar ba. Ajiye wayar yayi a kan gado cikinsa na cigaba da qugin yunwa shikadai se sakin qwafa yakeyi da ayyana hukuncin da ze dauka akan Amirah. Kusan minti 20 Naziru ya kirashi ya iso, se ya dauki wallet dinsa da keys ya saka a Aljihu ya fita. Naziru na ganin sa ya fito daga motar da niyyar bude get ya shigar masa da ita Bashir din ya dakatar dashi da cewa “Muje ka kaini naci abinci yunwa nake ji”. Suna tafe babu me cewa qala kowa da kalar tunanin da yakeyi a zuciyarsa, Naziru ne ya datse shirun da tambayar Yayan nasa Su Aliyu yace suna lafiya. Wani restaurant ya kaishi be fita daga motar ba ya bawa Naziru ATM yace ya yiwo musu take away ya karba ya tafi a ransa yana mamakin meya faru Amira batayi masa girki ba, tunawa yayi da tana da ciki se yai zaton ko shi ya hanata girkin amma dai ko yaya ne mutum ya taho gari ya gari har Lagos ai ko Indomie ta daure ta girka masa shidai ya siyo abincin ya fito. Bashir kuwa bayan Fitar Naziru wayarsa ya zaro ya duba ko wata daga cikinsu ta biyo missed call dinsa amma yaga wayam. Na Ma’u be dame shi sosai ba dan yafi gasgata bata kusa da wayar ya santa sarai ko fada suke bata qin daukar wayar sa sedai ta daga tayi shiru amma ita wannan yarinyar fa? In tana da hankali ai ita ya kamata ta kirashi ko amma gashi haryanzu ana neman 8 na dare bata kira ba. Har qofar gida Naziru ya kaishi ya shiga da Motar kafin ya fito yai masa sallama da niyar wucewa ya tsaidashi yace su shiga ciki. Har saman ya kaishi yace ya gyara masa dakin dan baze iya kwanciya a ciki haka ba Bashir akwai tsafta koya datti yake a guri baya so abinda yake qara Masa son Ma’u kenan tsabtar ta ciki da waje ya jinjija mata ta wannan fannin sosai. Har palour seda Naziru ya gyara tsaf ya goge ransa fal mamaki dan ya tabbatar yanzu Amirah bata gida to ko bata san ya zo bane? Shidai ya gama tattara komai ya tsaya jiran yayan nasa daya shiga daki ya fito. Kudi ya bashi yace ya hau mota tareda ce masa idan yaje gida ya cewa Dada seda safe ze shigo ya bishi ya kulle qofar ya dawo. Yana shiga palour Asma’u ta kirashi se ya qarasa kan kujera ya zauna dakyau yana amsa wayar. Asma’u. Lokacin da Bashir ya kirata wayar ta na hannunta tana chatting da Umaima yayarta ce da suke Uba daya amma ita take bi a cikin gidansu. Akwai shaquwa sosai tsakaninsu dan kusan bata da Aminiya ma sama da ita. Hira suke yi tana gaya mata tafiyar Bashir din Gombe da yanda suka rabu. “Ma’u kenan nidai bazan gaji da ce miki ki qara haquri akan wanda kikeyi ba, zuwa yanzu inda sabo ma ai yaci ki saba da wannan mood swings din nasa, ki watsar lamarin sa idan yayi dariya kiyi in ya daure kema haka. Ki kuma ci gaba da addu’a idan ma wani ne yake shiga tsakaninki dashi Allah ya miki maganin sa” cewar Umaima. Tana cikin yi mata reply kiransa ya shigo tacewa Umaiman “kinga ma yana kira” “Ki daga kiji me zece” “Barshi kawai bazan daga ba se zuwa anjima sun kwanta zan kirashi” cewar Ma’u. Dariya Umaima tayi tana cewa “Haba ai kuma ba zaki biye mata ku taru ku zama daya ba tunda ke kinsan abinda ya kamata, ki daga kuma karki nuna masa wani bacin rai ko wani abu dukda nasan ki ma Ma’ulle akwai sanin ya kamata ai” tayi maganar cikin sigar tsokana. Da “toh” Asma’u ta amsa ta ta kashe Datan bawai dan zata amsa kiran ba dan ta qudurce a ranta seta koyawa yarinyar nan hankali taji idan abinda take mata da dadi yanda take kiransa duk sanda taga dama kamar ita kadai take dashi. Yanzu nema ta rage ada bata tashi kiransa wataran se sha biyun dare sun kwanta bacci, farkon wannan cikin nata ma lokacin tana laulayi akwai ranar da suna tsaka da soyayyarsu wurin 2 na dare ta kirashi wai ta kasa bacci se Amai take shine ta kira shima ta tashe shi. Baqin ciki kamar Asma’u ta fasa ihu har bata san sanda ta fizge wayar ta tuttura mata ashar ba kuma saboda rashin adalci irin na Bashir qarshe ita yaji haushi akan me zata zageta bata ga cewa lalura ce ta sakata kiransa ba ranar kwana tayi tana kukan baqin ciki ai kuwa seda tayi masa yajin kusan wata dakyar ya shawo kanta ta sakko. Sedata mula dan kanta ta gama komai sannan ta shiga daki ta kirashi, a yanda ta lissafa yanzu dole suna zaune ne suna hutawa dan haka tayi niyyar jan hirar har se illa masha Allahu harda loda kati a wayarta saboda tsaro (Sorry Ma’u wrong timing 😂😂😂😂). Lafewa ta sakeyi a cikin gado sanda ya amsa wayar ta gaishe shi da tambayar ya hanya ya amsa mata da lafiya lau. Rai rai ta saki jiki suka ringa hirar da sun manta rabon da suyi irinta, shi mamakin yanda ta sake kamar ba abinda ya faru ita mamakin yanda yake amsata sosai kamar ba Bashir ba yau ba Miskilancin nan babu baqin rai. Yanda take masa shagwaba kamar wata sweet sixteen yana biyeta gaba daya tagama narkar dashi a zaune, Hira tayi dadi tama manta da batun wai dan ta musgunawa kishiya yasa ta kirashi sema kwantowa kansu ruwa da sukayi gaba daya ta rudashi da salon da take masa magana shima ya rudata da masa salon, dakyar suka rabu a wayar lokacin 12 harta gota shima Asma’u ce ta kashe ganin yana neman sakata a uku to ai shi ga matar sa nan itafa sedai ta kama pillow batasan Gogan har ya fita shiga tashin hankali ba. Haka ta kwanta tana juyi Kafin bacci ya saceta ranta fes koba komai dai Ta qunsawa Amirah. Bashir Yana zaune bayan sun gama wayar se zufa yake sharewa duk da sanyin Ac daya karade palour dan gaba daya Asma’u ta warware masa notin kai. Dakyar ya miqe ya nufi fridge din daya kunna tun dazu ya dakko ruwan sanyi ya kwankwada yana sauke ajiyar zuciya Haushin Amirah na sake ninkuwa a Zuciyarsa har ya gama wayar nan beji shigowar kiranta ko message ba gashi yanzu dayan dare ta kusa idan banda bata da hankali ai yaci ta kira taji ko lafiya ya taho ko be taho ba amma ina da dai ya mata alqawarin kudi ne be cika ba da yanzu ta ishe shi da kira kamar yaci bashin ta. Kwafa yayi a ransa yana jin kaman gobe ya juya Lagos kawai tunda zuwan nasa beda muhimmanci tunda bata damu ba. Haka ya daddafa ya kwanta kafin ya samu bacci ya daukeshi. Gidan Addah Wuni Addah tayi tana bankawa Amira jiqe jiqen yan bori da magungunan mata ko tsoron halin da take ciki kar wani abu ya sami babyn basayi, bata haquraba seda Amiran ta fara sheqa Amai tukunna aka koma cushe cushe dana hayaqi. Bayan maganin gurin Wizy ta tura an sake karbo mata wasu duk ta banka mata a cewarta gara a hada hannu da yawa ayi maza buqata ta biya. Babu lissafin zuwa ta gyara gida bare aje ga batun yi masa girki sukayi zaman su na jira yazo da kansa yace su tafi tunda a kwanakin ta sami kansa suna abin arziqi dan kiran da tayi masa jiya da daddare ma kuka ta saka masa akan ita dai yazo tana missing nasa in ba haka ba zata hawo jirgi ta zo Lagos sedai Anty ta basu daki. A lokacin yasha mamakinta dan shidai Rashin kunyar Amirah na daure masa kai ko kadan bata jin nauyinsa wanda sam ba haka Asma’u take ba. Ma’u bata masa irin wadannan maganganun gatsal ta dai san signs da signals da take amfani dasu wanda suke bala’in burge shi da qawata zuciyarsa dan kullum cikin qara masa sabon ilimi take amma ita wannan se zance a baki ba abinda ta sani idan an zo wajen. Se bayan Magriba ta shirya taci uwar kwalliyarta dan tasan zuwa sannan ya sauka Gombe. Ita sam tunanin taje ta gyara gida be zo mata da daman duk sanda zezo shi yake tuna mata to jiya da be magana ba itama tunda tsaftar ba damunta tayi ba se bata je ba a ganinta ai befi sati uku da zuwansa na qarshe ba gidan beyi datti ba ai. Tana zaune Adda na qara karanta mata yanda za’a yi suna jiran zuwan Bashir shiru se ji sukayi ana rufe qofar gidan ta kalli agogo 12 saura. Seda gabanta ya fadi sanda taga missed call dinsa tun wurin bakwai ya kirata. A yanda ta lissafa sunyi waya sanda ze taso yace mata yanzu zasu taho kenan lokacin da ya sake kira yana Gombe ai ita yaci ta kira taji ya sauka. To yanzu ya zatayi ta kirashi ne ko Aa haka tayi ta wasi wasi bata ko iya tankawa Addah dake faman sababi naqin zuwan Bashir din ba har tana da safe zata je ta samu uwarsa taji dalili dan baze ja mata asara ba wallahi. Ita dai Amira daki ta shige ta chanza kaya dan Addah tace karta kuskura tayi wanka ance se ya kwanta da ita tukunna saboda abubuwan da ta sassaka, haka ta kwanta tana zullumin haduwarsu dan dai ta haqura bazata kirashi yau ba gara ta bari da safe se taji duk yanda ake ciki tasan dai ta kwafsa tabbas dama yaya ana lallabawa ne kuma yanzu ta sake ballo musu ruwa. Tunanin qaryar da zata yanka masa in sun hadu ta shigayi amma duk wadda ta hado seta ga ze dago ta qarshe ta fawwalawa Allah kawai ta kwanta duk yanda goben tayi shikenan. Washe gari Bashir tun qarfe takwas ya nufi gidansu, tun daga waje yake jiyo tashin muryar Addah data taso Amirah a gaba suka taho gurin Dada dan jin ina Bashir ya maqale dan ita bata magana a hankali. Bacin ransa ne ya nunku wato har sunada kwarin guiwar kawo qarar sa kenan ko? Se kawai ya juya dan bama ya so ya shiga yayi abunda ran kowa seya baci dan haka se kawai ya juya da niyyar fita, ya rigada ya makara dan tuni Addah ta hango shi ai kuwa ta shiga taratsin kiran sunan sa akan ya dawo bashida zabi ya juyo jin Dada ta saka baki fuskar nan a dinke kamar wanda yaga mutuwarsa ya nemi guri ya zauna yana muzurai. Kallo daya yai wa Amirah data duqar dakai kamar munafuka dan bata so suka hadu a gidan ba yanzu se yace ita ta kawo qarar bayan wallahi Addah ce, seda tace kar suzo amma taqi gashi yanzu ta ja matana jangwam. 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 WATA KISHIYAR 🥰👹 (ALKAHIRI CE KO SHARRI) 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 Na Maryamah_Mrs AM (Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah) Page 10 Kansa a duqe yana jin yanda Addah take surfa bala’i kamar wadda akayiwa wani abu magana daya biyu seta zagi Asma’u da ya rasa me ta tsare mata a rayuwa. Shifa Addah na bashi mamaki wallahi, idan ya tuna fuskar data zauna da Ma’u ada da kuma bayyananniyar fuskarta ta yanzu. Qiri qiri ta babbake ta hanashi magana bare ya yi nasa qirafin qarshe ma se suka dora masa laifin ai shi ya kamata ya biya ya dakkota tunda yasan halin da take ciki. Baqin ciki kamar ya fashe lokacin da yaji Dada tana cewa Amirah ta tashi ta bishi su tafi yanzu se ya miqe yai waje fuu yayi waje ba tareda ya shiga ya gaisa da Mahifinsa da kuma Abokiyar zaman Dadan ba. Har suka dauki hanya be ko kalli Amirah data takure saboda tsoron abinda ze mata ba, ita dai bata so akace ta biyo shi ba dan su basusan Bashir bane shiyasa. Tasan shirun sa ba Alkahiri bane dan haka ta saka ido tana jiran karbar hukunci har suka isa qofar gidan. A waje yai parking ya kashe motar ya fito yana gaba tana binsa a baya. Da key dinsa ya bude palour ta takaicin sa ya nunku ganin tarin datti a palour kamar wanda akayi biki dan robobin lemo ne da take away pack ko ina. Waiwayowa yayi ya kalli Amirah da jikinta ya fara rawa dan ita se yanzu ta tuno da bridal shower din bikin Qawar ta da sukayi sati biyu daya wuce a nan din, kuma koda suka gama bata gyara ba ta bari akan se ze zo tazo ta share aam kuma ta manta. Nan da nan ta fara inda inda tana tattaro rantsuwa dason yi masa bayani ya katse ta “Zan fita wallahi ko mutuwa zakiyi kafin na dawo ki tabbatar kin gyara gidan nan har compound ki fita ki share, in kin ga dama karkiyi ko kuma ki kira wani ya taya ki zaki gane wane ne Bashir shashasha da bata san ciwon kanta ba” yai maganar cikin fushin da har a muryar sa take ji kafin yasa kai ya fita. Ita kam indai iya hukuncin kenan ma ai tazo da sauqi, tasan Yaya Bashir da qazanta ko yaya yanzu za’a ji kanku kuma shi in kayi masa laifi yayi magana abun nada sauqi amma idan muskilancin nan ya motsa se yafi shekara yana azabtar dakai ba duka ba zagi to ita gara yai mata hargagin ya bata horo shikenan tasan ya wuce. Hijabin ta ayije ta debo kayan shara. 3 Bedroom ne a part dinta kowanne da toilet a ciki biyu nata se nasa daya, Madaidaicin palour,kitchen da store a ciki se Dining area. Nasa dakin ta fara gyarowa ta nutsu sosai dan gudun kuskure, ta share ko ina ta wanke toilet sannan tayi mopping. Bedsheet ta shimfida ta cire tsohon ta boye dan tasan ya gani se yayi magana ya hana ta barin Bedsheet a gado in bata nan amma taqi ji sedata kunna Ac ta tsaya tana maida numfashi, iya nan tayi amma harta gaji amma tasan idan batayi da kyau ba ma kanta ta jawa. Har zuciyarta tace tabar dakunanta ta gyara palour kawai da Kitchen wata zuciyar ta ce mata ko sama sama ne tayi tasan yanda yake a kusan nan tsaf ze leqa ko ina. Dakin baqi ta fara shiga Ba shara ba komai ta hau moping, toilet dinta ruwa ta watsa bata wanke ba taja ta rufe ta shiga Bedroom dinta. Yana nan a hargitsensa yanda ta tafi ta bari, kan gadon kayan gugar da aka kawo mata ne bata shiryasu a wardrobe ba, babu lokaci dan haka ta tattara ta watsasu duk gugar ta hargitse. Bedsheet din shima ta chanza ta hau moping bayan ta kwashe kufunan data sha wani lemo wani fura harda ledar balangun dataci ana gobe zata tafi ta manta bata dauke ba da sauran a ciki ya bushe. Tana bude toilet dinta kuwa zarni da warin kayan wankin data tara suka bugota dan ita fa a qasa take tsula fitsarinta ga Tiles da kama zarni, kaya kuwa nan take watsar dasu har kuwa da inner wears dinta seta tara ta rasa na sakawa sannan zata wanke. A farko tsabar wauta da rashin hankali ma harsu take hadawa a wanki se randa Allah yakai idon Bashir ya gani yai mata tatas tareda jan kunne me qarfi sannan ta fara wankewa daga baya kuma ya siyamata washing machine ta ringa wanke qananun abubuwa kayan sawa kuma suna da me wanki duk sati yake zuwa. Sau daya ya taba bata singlets da Boxers dinsa ta wanke masa a injin ta hadasu a ruwan dattin kayanta qarshe dai se zubar dasu yayi daga nan kuma be sake bama sedai ya wanke da kansa. Kayan ta tattara ta wanke bayin sama sama ta fito. Palour ma ta nutsu dai ta gyara kitchen kuwa da tasan ba shiga yake ba janyowa tayi ta kulle bayan ta kwashe kwanukan data bari da abinci a ciki duk sun rube kitchen din se doyin abinci yake seta watsasu a shara dan bazata iya wanke wa ba. Tana tsaka da sharar compound ya shigo hannunsa dauke da ledoji daga gani abinci ne a ciki, seda gabanta ya fadi Allah yasa karya shiga kitchen neman plate dan ruwa da lemo a kwai a fridge din Dining. kallo daya ya mata ya shige palour abinsa. Yafi babu sunan gyaran nata, centre table yaja ya dora abincin dan ko karyawa beyi ba ya fita dama ya zauna akan kujerun da suka fita hayyacin su kamar wanda suka shekara goma bayan ko cikakkiyar shekara beyi da chanza mata su ba lokacin waccen Haihuwar da tayi ne. Yana dab da kammala cin abincin ta shigo tana jan qafa tayi budu budu da qura dan da gaske ta gaji Kallonta yayi ya danji tausayinta kodan cikin dake jikinta se ya dan sassauta murya yace “kije kiyi wanka ga abinci kici”. Dan jim tayi, me ta tuna kuma tace “toh” ta shiga dakinta. Kwaskwarima tayi ta chanza kaya tareda fesa turare ta fito, ya tashi daga palour dan haka ta zauna taja abincin taci. Harta gama ta tattara gurin be fito ba dan haka ta bishi tasan yana dakinsa. Yana kwance akan gado jikinsa sanye da rigar wanka yana waya da su Jafar da Ma’u ta kira shi bayan sun gaisa ta basu. fuskarsa dauke murmushi saboda maganar da Jafar din yake gaya masa, beji ahigowarta ba se sautin tsakin ta daya ji kafin ta dora da fadin “Aikin banza saboda rashin Adalci ma baza’a bar mutum ya samu lokaci da mijinsa ba se an tauye shi” dan a zaton ta da Asma’u yake wannan murmushin. Mamaki ne ya kamashi, seya janye wayar daga kunnensa bayan yayi wa Jafar sallama yana kallonta, bata bari sun hada ido ba ta nufi qofa da niyyar fita ya tsayar da ita “Wace aikin banzan waye kuma mara Adalcin?” Ya tambayeta muryarsa a kausashe. Dukda a tsorace take amma seta dake dan Tayi amanna aikin su fa ya fara tasiri akan sa, murguda baki tayi gefe sannan tace “to in ba rashin Adalci ba nameye zata wani kiraka yanzu kuma...” bata samu qarasa ba saboda dukan daya kawowa bakinta Allah ya sota ta duge dukda haka ya same ta a goshi ta dafe gurin. “Fita ki bani guri kafin na illata ki wawuyar yarinya” ya fada cikin tsananin bacin rai ai tuni ta fice dan tasan fushinsa tabbas dukda sau daya ya taba marinta amma bata fata abinda ze sake sakashi sauke hannunsa a jikinta dan bataji da dadi ba. Tana fita ta kira Addah ta saka mata kuka tana gaya mata yanda sukayi, Addah data rasa abinda zatace ta danna mata Ashar kafin tace “kina zaton badan munje gaban uwarsa ba ze saurare ki da wuri ne? To wallahi in kika janyo mun asara bakiyi aiki da abinda yake jikinki ba ni dake ne” ta kashe wayar dan takaicin Amirah nema yake ya sa mata hawan jini. Ita komai se ance mata ga yanda zatayi in banda wauta har se an ce mata ta lallabashi ma yau din nan sannan zatayi kai wannan kayan takaici da yawa suke. Goge hawayen tayi ta shiga tunanin ya zatayi yanzu? A yanda ya fusatan nan tasan tabbas ze iya mata komai amma bazata yi asarar lokacin nan ba dan itama tana biqatar aikin nan yaci kodan ta fara zuba ikonta yanda take so, dole ganin ba mafita ta nufi dakin da taraddadin abinda zata tarar tasan dai baze daketa ba dan ba dabi’arsa bace dukan mace yanzu nema take tunzura shi harya kawo mata mari wani lokacin. Bashir Yana zaune a gefen gadon ya dafe kansa da hannu bibbiyu, shidai tunda ya auri yarinyar nan yai bankwana da farin ciki, idan ita bata baqan ta masa ba se taja Asma’u ta baqanta masa ta dalilin ta dama wai haka qarin auran yake ko kuka shine beyi dace data gari ba?? Yana jin sanda ta turo qofar dakin ta shigo, be dago ba dan besan kuma meze mata ba se jin saukar ihun kukanta yaji. Dagowa yayi ya kalleta tana zaune dirshen a qasa tana kuka reras ga hawaye da majina nabin fuskarta. Baqin ciki to uwar me yamata kuma ai shi ya kamata ma yayi kukan abubuwan datake qunsa masa ko. Yaso ya shareta amma cikin jikinta da gargadin likita suka saka shi fasa yin haka saboda hawan jini ne yai sanadin dan cikin ta ya mutu a wancan lokacin. Amirah nada ciwon hauhawar jini a lokacin da mace take da ciki wanda gado tayi a gurin Addah kuma likita ya tabbatar masa shine silar mutuwar jaririn data haifa dan ita ma Addan haka takeyi. Haihuwarta goma Amma Amira da Ummi ne kadai suka tsaya wasu tun a ciki suke mutuwa wasu data haifesu. Dukda haka seda ya barta tayi sannan cikin tsawa ya ce mata “wai kukan na uban menene? Me nayi miki?” Dan tsagaita kukan tayi tana jan dogayen ajiyar zuciya, seda yaja lokaci sannan ya waiwayo ya kalleta tareda miqa masa hannunsa alamar tazo da sauri kuwa ta miqe ta nufeshi gaba daya ta fada jikinsa seyai saurin dagota jin wani kamar qari qari takeyi kai harda qaurin hayaqi ma yaji,. kofar toilet ya nuna mata yana cewa “muje” ya tasata a gaba suka shiga. Yana tsaye ya saka ta salle jikinta sau uku har gashin kanta seda ta wanke wanda rashin gyara yake hanashi abin kirki dan itama Amirah tana da gashi sedai bekai na Ma’u ba. Seda ya tabbatar da ya duba duk wani lungu da saqon da datti ze buya yaga ya fita sannan ya sata a gaba tayi brush, shidai ko iya haka aka barshi ai sakayyar da Asma’u tace se Allah ya mata gata nan yana gani. Indai yana son kasancewa da ita ta kwanciyar hankali tofa se ya tasata tayi wanka a gabansa shi wai dama haka matan suke ne Asma’u ce daban a ciki be sani ba? Tunda yake be tabajin wani wari daga jikinta ba koda kuwa ta kwana batayi wanka ba. Ma’u me tsafta ce komai nata a tsaftace take yinsa ita kuwa wannan har fargabar cin abincinta yakeyi. To yarinyar da yanzu zata fito daga wanka amma kajita tana tsami, ashe da daya ke ganinta tsaf dan baya matsar tane daga nesa yake jiyo qanshin turare kawai. Fitowa sukayi ya nuna mata mai da turare yace ta saka ta shirya ranta a dagule shikenan sunyi asarar komai yanzu amma yata iya dole tayi yanda yake so. Daga nan dai suka shige daga ciki. Asma’u Jafar ne ya miqa mata wayar bayan da ya kashe “Har kun gama maganar shine ka kashe baka bani ba” ta fada tana qoqarin sake dialing dan tana so ta gaya masa zasu fita anjima se maganar Jafar din ta katseta “Shine ya kashe ai kaman Anty Amirah ce naji tana masa magana”. Kallon yaron tayi kaman shine Bashir din wani abu na sukan zuciyarta, wato ya kashe wayar saboda matar sa tana gurin ko? “Ai shikenan” ta fada a fili kafin ta tashi ta shige dakinta. Kwanciya tayi ta rufe idonta, tana so ta dena damuwa akan wasu abubuwan amma ta kasa. Yanzu ne take fahimtar ba rashin tawakkali yake saka mata suyi ta tashin hankali in an musu kishiya ba Aa abinda ake ci gaba da yi maka yau da kullum yafi zafin yin Kishiyar dan shi na lokaci daya ne ya wuce amma banbancin da za’a dawwama ana nuna maka shi yake hasala zuciya har wasu su kasa shanyewa ayita tashin hankali dasu.https://chat.whatsapp.com/DpZYwM6HCjs7WDTCBPkyj0 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 WATA KISHIYAR 🥰👹 (ALKAHIRI CE KO SHARRI) 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 Na Maryamah_Mrs AM (Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah) Page 11 Wannan karan dai Amirah ta samu yanda take so dan Har ranar Monday da safe da Bashir ze tafi basu sake samun sabani ba. Tayi iya qoqarinta wurin ganin ta tsaftace ko ina kaman yanda yake so shima ya sake da ita sosai ya mori weekend dinsa dukda dai a wannan bangare fa ya dade da cirewa Asma’u hula dan kuwa tayi zarra amma itama Amirah babu laifi yana samunta yanda yake so. A bangaren girki ne dai tunda yazo be ci abincinta ba gidan Dada yake tafiya yaci na rana na dare kuma ya siyo idan ze dawo saboda shi tun usuli dama baya cin abincin me ciki gani yake wannan Amai da tofe tofen da sukeyi har cikin abincin yana shiga. Ko Ma’u dakyar ya fara cin abincin ta lokacin da tana da cikin Aliyu shima seda ya ware lokaci ya tsaya akan ta ya tabbatar da ingancin yanda takeyin sannan ya saki zuciyarsa dukda ita bata fiya yin ciki me Amai ko tofe tofen miyau ba. To balle wannan da kullum tana tafe da Gwangwani wani Sa’in ma tana magana bakinta cike da yawu yana zubowa seda yai dagaske ta dena yace ta ringa samun wani abun ci tana sawa a bakin ze hana taruwar yawun sannan fa ya samu lafiya se kuma liqe liqen chewing gum din da ta koma ci wani lokacin har kan kujera ko kan carpet yarda shi takeyi ba abinda ya dame ta. Bashir Tun ranar Asabar dinnan basu sake waya da Asma’u ba, ita bata kira ba shima be kirata ba tadai yi masa text kan zasu fita ran Saturday da Sunday kaman yanda suka saba yace to tareda aika mata da kudi dukda bata tambayeshi ba. Ranar lahadi da yamma ya dauki Amirah sukaje gidansu, A nan ya barta suka fita da Amiru qaninsa daya zo daga Katsina a ranar can yake aiki yana zaune da iyalansa. Bayan isha ta idar da Sallah tana zaune Dakin Fainusa qanwar Bashir ce da take zawarci, Fainusan bata nan taje bikin qawarta Dada kuma tana dakin Baban su Bashir taje bashi maganin sa na dare. Bangaren shiru seda ta leqa ta tabbatar babu kowa sannan ta dannawa Addah kira dan kwatakwata bata samu sun tattauna komai ba dan Bashir na gida kusan ko yaushe in ya fita kafin tayi ayyukan ta gudun bala’insa kan ta gama ya dawo ita kuma Addah ba karatu ta iya ba bare suyi chatting Ummi ba shiri suke ba bare ta karantawa Dadan. Seda ta jera mata kira biyar sannan ta daga dan so take suyi shawarar abinda za’ayi kafin subar wurin Dada tunda itace makamin yaqin nasu. Addahn na dagawa babu gaisuwa ba komai tace“Addah gamu a gidan Dada fa kuma da safe ze tafi haryanzu beyi maganar tafiyar tawa ba” “Au nida naji ki muqus ai nazata komai ya kammala dama yanzu nake so nakira ki wato tunda kura tayi lafiya har kin manta dani”. “To dai ba lefi Addah, yanzu dai ya za’ayi kinga da safe fa ze tafi”. Motsin da ta jiyo ya saka ta saurin cewa Addah “nidai kishiga whatsapp dinki kiyimun voice na abinda zance mata dan wallahi muka bar nan kinsan dai ba iya magana zan masa ba” tayi maza ta kashe wayar. Fainusan ce ta dawo, gaisawa kawai sukayi ta shiga hidimominta batareda ta sake koda kallon Amira ba dan basa shiri. Ta girmewa Amiran amma tunda ta Auri Bashir ya zamana dan girman da take basu ma ta dena a cewarta yanzu matsayin Yaya take a gurinsu tunda tana auran Wan su dukda dama dai tun usuli ba Kunya ce da ita ba. Tana zaune tana duba waya kusan minti goma sega voice din Addah tayi maza ta kunna tareda saka wayar a kunne “Kinajina bude baki zakiyi ki mata magana kice befa ce miki ki shirya ba dan haka tayi masa magana dan gaskiya fa ke kina cutuwa bazaki zauna ba” qasa rayi da murya sosai kafin tayi mata reply tace “Addah anya kuwa Dada fa yanzu surukata ce nifa wallahi kunya nake ji” “To dan ubanki se ki zauna ai, kina dai jin abinda Jummai yar Bori ta fada tace indai ba kusa dashi kika koma ba babu aikin mu da zeyi tasiri to tun wuri kafin wannan din da muka dan samu yayi ya sake shi kiyi ta kanki” Addah ta fada cikin masifa. Shiru Amira tayi tana jimamin abun a ranta anya kuwa zata iya dosar Dadan dan duk wannan abun Addah ce takeyi mata yaqin amma fa yanzun ne kadai damar ta. Bata da burin daya wuce ta Mallaki Bashir ta same shi sama da yanda Anty Asma’u ta same shi. Ita ma yaringa yawo da ita a gaban mota duk inda ze shiga ya nuna ta a matsayin matarsa ya kuma ringa nuna yana sonta a gaban kowa. Tana zaune tana wasiqar jaki Dada ta leqo dakin, “Amirah kina zaune shiru ki fito palour kici abinci” Dadan ta fada Da “toh” ta amsa kafin ta yunqura tabi bayan Dadan Fainusa ta rakata da harara tareda tabe baki dan taji maganar Amiran batasan dai Me Addah ta fada ba ko akan me suke maganar. A palour kuwa Bayan Amira ta zubo abinci ta zauna tana tsakura Dada kuwa Ta maida hankalin ta kan Tv dan dama ita bame sakewa da mutane bace. Amirah ta dago yafi sau goma da niyyar yi mata magana seta kasa daga qarshe dai tayi qundumbala kamar an fuzgo maganar tace “Dada kiyiwa Yaya Bashir magana gashi har gobe ze koma beyi zancen tafiya ta ba kuma” ta qarasa tana sunkuyar dakai ganin yanda Dadan take kallonta. Shiru Dada tayi kamar bazata tanka ba se kuma ta sauke numfashi tace “Munyi magana da Addah na gaya mata ki zauna anan tunda tun farko da ya baku zabin jeka ka dawo ke kika qi kafin ma Asma’u ta fara aiki lokacin dan haka yanzu bana son wata fitina ta sake tasowa ki yi haquri ki zauna a inda ya ajiye ki ko dan lafiyar jikin ki ma yanzu kama ta yayi ki hada hankalin ki guri guda kiyi fatan Allah ya sauke ki lafiya”. Seda Amirah ta harari Dada qasa qasa wanda sarai tana ankare da ita kafin tace “Toh ai Dada lokacin ma shi yace nace na fi son zama anan din Anty ze bari acan kuma yanzu ma bani nake son komawa ba ai saboda Dan sa ne nake son zama a kusa dashi”. Ido bude Dada take kallonta har ta qarasa, bata iya ce mata komai ba illah “Allah ya rufa asiri” ta maida kai ga kallon da takeyi dan abin yafi qarfinta kuma. Amirah jin tayi shiru ta tabbatar da bazata sake cewa wani abu ba, se sannan ta gano wautar da tayi cikin salon son kare kai ta fara cewa “Dada ba abinda kike tunani bane wallahi ni kawai...” “Idan kin qoshi ki kai abincin kitchen zan koma gurin Alhaji in Bashir sun dawo ina can” Dada ta fada tana miqe wa jin da gaske so take ta baro wata maganar in ba haka ba menene kuma nayin bayani gaskiyar magana Addah ba tayiwa yarinyar nan goyon kirki ba ace yarinya bakinki babu control a gaban kowa ki fadi duk abinda yayi miki, Allah ya sawwaqa toh. Tana fita Amirah ta shiga kiran Addah a waya tana dagawa ta sakat mata kuka tana cewa “Addah kin gani ko nace miki bazan iya ba kince sena mata magana gashi yanzu na bata komai” “Dan ubanki me kika ce mata a garin yaya? Rashin hankalin naki kikayi ko ni wallahi na rasa wace Asararriyar yarinya ceke da komai baki iya siyaya da kissa ba se wauta da rashin hankali kika saka a gaba yanzu me kika ce da ita?” Tsaf ta gaya mata yanda sukayi da Dadan, Ajiyar zuciya Addah ta sauke kafin tace “Ni na zata ma wani babban abu ne rabu da ita na lura Nafi so take ta kware mana baya amma bata isa ba wallahi yanda ta saba tursasashi yayi abu yanzun ma haka za’ayi. Ki kwantar da hankalin ki ki rabu dasu muna zaune se ya dawo ya dauke ki wallahi in sun san wata basu san wata ba kedai yi qoqari ki amshi wani abu a hannunsa a turawa Malam a qarasa aikin nan Idan muka samu yanda muke so ko ita Nafin se mun so zata ganshi” fanfo ta cigaba dayi mata da bata dabarun yanda zata wanki Bashir din kafin sukayi Sallama. Gajia tayi da zamanta zame takwanta akan kujera bacci ya kwasheta, Bashir kuwa se qarfe goma ya dawo gidan, seda yaje sukayi sallama da iyayensa kafin ya shiga palour ya ganta harta fara bacci. Tashinta yayi suka tafi basu koyi sallama da Dada ba. Da suka isa gida ma kwanciya tayi dan baccin yaci qarfinta. Washe gari tun Kafin a kira Assalatu ya tashi Amirah, tana qunquni tana komai seda yasa ta gyara ko ina dukda beyi datti ba tunda kwana biyun tana kula da komai. Qarfe 6 suka sauketa a qofar gidan Addah, be shiga ba dan haushin Addan yakeji haryanzu dama basu sake haduwa ba tun waccen ranar dukda har kasuwa yaje ya gaida Baban Amiran kamar yanda yakeyi duk sanda ya shigo gari, duk yanda Amiran taso ya shiga wi yayi yace ta gaisheta kawai sauri yake qarfe 7 jirginsu ze tashi sannan ya kawo 50k ya bata sukayi sallama Naziru ya kaishi Airport ya juyo da motar. Murna gurin Addaha kaman wanda ya basu 50M. Shi dama bame kyautar kudi bane idan ze tafi dai komai ze ajiye mata na amfani sanda tana zama a gidanta Ummi taje ta tayata zama. Da ta koma tafiya gida ma be fasa ba duk qarshen wata ze sa akai Buhun shinkafa carton din taliya, macaroni da Indomie harda Mai da Maggi ga Kayan Tea sannan in ze tafi ya bata 10k kuma duk sati yana saka musu Katin waya na 1k ita da Asma’u Idan kuma zataje Asibiti Nazir ne ya ke kaita ya dawo da ita. “Yanzu cire Goma ki riqe a hannunki bari na kirawo Malam ya turo a karba in kuma A Akawun za’a saka masa toh. Nidai Alkahiri ya hada mu da Me Keken nan shekara da shekaru muna yawon rabar da kudin mu a banza babu biyan buqata kinga rana daya mun tsinci dami a akala” Addah ta fada tana qoqarin kiran wayar Malam Wizy, kira Daya biyu ana ce mata Switch off amma bata lura bama se sake kira takeyi, wayar ta miqawa Amirah tana cewa “Ke jimin me matar nan take cewa be wayar taqi shiga” “A kashe take Addah” Amirah ta fada bayan ta sake kira. “To bari mu saurara zuwa anjima na sake kira dan bazanyi wasa ba gara ayi wuta wuta a gama aikin nan bari ma Babanku ya fito inaga yau ze bamu ribar mu duk na hada a tura masa kawai a qarasa”. Ita dai Amirah neman guri tayi ta kwanta dan bacci ne fal idonta. Har kusan Magriba Addah na gwada layin wizy baya shiga, seta kalli Amirah dake cin Abinci a gefenta tace “Bari kiga na kira Hajia Balaraba itama tunda muka dawo ba waya da alama ta samu kan gidan se muji idan ta kama gobe mu koma kawai ko da abinda ze qara bamu ma” kai Amirah ta daga mata kawai nan ta maida akalar kiran kan Hajia Balaraba sedai itama kamar Wizy waya a kashe harta gaji ta bari akan Gobe idan Ummi ta dawo zata karbi Number Ruqayya a gurinta (Ummi tana gidan yayarsu da suke uba daya ta haihu). Gidan Hajia Balaraba Waccen ranar yanda suka watse suka barta ta dade a zaune a gurin tama rasa tunanin me zatayi, wai itace bata da Sa’a ne ko kuwa aikin Malam ne beyi ba? Tana zaune tana tunanin me zatayi, wannan hukuncin da Alhaji ya dauka yayi mata tsauri da yawa ta yaya ma za’ayi ta zauna bazata fita neman taimako ba? Dole da sake idan dama taqi se a kona hagu ai saqesaqen yanda zata wanke kanta ta farayi a zuciyarta har zuwa sanda taji Alhaji ya sake fitowa daga dakinsa. Cikin qarfafawa kai guiwa ta miqe tana cewa “Alhaji kayi haquri wallahi sam ba abinda kuke tunani bane, kafin gida ne na karbo mana ba kuma iya dakinta na saka ba wallahi kaga kwana biyu unguwar nan anan fama da sace sace shi....” kallon da yake binta dashi ya sakata hadiye sauran maganar ta. A tare suka juya Gurin Dining da Ruqayya ke qoqarin zuba tuwo abinta dan tana wanka bata ma san wainar da aka toya a gidan ba. “Mayar da miyar nan Ruqayya ki miqomin harda na shayun” ya fada murya a dake dan dukda be gani ba ya tabbatar ta saka wani abun aci ba kuma ze bar kowa yaci ba dan ba yau ta saba ba ita idan ta tashi abun tana ma ba kansa kadai yake tsaya wa ha kowa da kowa take hadawa na gidan. Karbar flask din yayi ya shige kitchen dasu Hajia Balaraba naji tana gani ya kwarara miyar a sink din ya bi da ruwan Tea kafin ya dauraye ya kora ruwa. Idon sa ne ya sauka kan wani flask daban a ajiye ya janyo ya bude, murmushin takaici yayi zargin sa ya tabbata duk sanda tayi irin haka seta ware nata daban be bata lokaci ba ya dauka tareda sabon plate da spoon se koma Dining. Tuwon sa ya diba ya zuba miyar ya miqawa Ruwayya ragowar yai shigewar sa daki ya bar Balaraba a tsaye da baqin ciki goma da ashirin, abincin ne sauran taqamarta taso ta lallashe shi yaci gashi yanzu ya zubar da miyar wadda ta ajiyewa kanta kuma ya kwashe duk wuyar da taci tayi girkin nan me kyau amma bata da rabo sena baqin ciki bata san sanda hawaye ya fara zubo mata ba kamar yarinya. Dakin ta ta shige tayi kukan ta me isarta ta share, ta kuma quduri niyyar ko bataje da kanta ba se tayi aike daga yanzu ma bazata qara karbar aikin da zatayi dakanta ba gara ta samu wanda ze yi mata komai da kansa bate ma har ta kuskure asake kamata. Washe gari tana zaune Alhaji ya shigo dakinta, wayar ta na hannunta tana shirin kiran Addah ta gaya mata yanda akayi su kuma yi shawara ya shigan. Hannu ya miqa mata ta bashi wayar cikin mamaki ta miqa masa tana tunanin to me kuma ya fatu yanzu? A gaban ta ya cire layin ya balla, kafin ya kalleta yace “Wallahi ko da wayar wani kika karba kikayi amfani da ita ki kira wani Boka Ban yafe ba” ya sa kai ya fice ya barta da baki a bude. Matakan tsaro na gaske ya saka mata ba waya ba fita ita ma kuma ya hana kowa zuwa gurinta har kuwa da Yayanta da suke gidan aure. Ruqayya kanta cewa yayi ta tattara ta koma Hostel haka me aikinta yace karta dawo ta zauna ta qara hutawa na wani lokaci duniya fa tayiwa Hajia Balaraba zafi Raba zafi inuwa quna gashi babu abokin shawara ita da Alhaji kuwa sedai tajiyo qarar bide qofarsa ko rufewa. Seda Addah ta jera kwana biyu tana kiran Hajia Balaraba da Wizy dukka bata samu ba, ranar Talata ta yanke shawarar zuwa gidan nata ta gano ko lafiya. Dakyar da sidin goshi Me gadi ya barta ta shiga shima seda tayi masa qaryar Ita Yar uwar Hajia Balaraba ce suna ta kiran wayarta ba’a samu shine tazo taji ko lafiya, be barta ba seda ya kira Alhaji ya shaida masa sannan yace ya qyaleta ta shiga. Halin da taga Aminiyar tata ya girgiza ta nan ta shiga tambayar ta meya faru, Hajia Balaraban na kuka ta shaidawa Addah komai harda sharadin da Alhaji ya gindaya mata. Addah tayi buqwi tana sauraronta kafin tace “Ikon Allah kinga dama akace magani dace ne to ni kuma kinga dai mun dace wallahi dan yanzu lafiya lau abubuwa suke tafiyar mana. Kema din nasan akasi aka samu wannan shegiyar ta ganki amma da abubuwan sun kammalu na tabbatar yanzu wani zancen ake ba wannan ba Allah dai yajiqan Malam na kan tufu shine Maganin Fitinannen Alhajin nan naki mtsw” taja tsaki kafin ta dora da cewa “Yanzu dai ai cewa yayi idan kika qara zuwa ko a sharadij nasa shikenan kiyi zamanki ni zan koma insha Allahu za’a gyaro komai base kinje ko kunyi waya ba” Cikin jin dama dama Hajia Balaraba tace “Yawwa Aminiyata shiyasa nake qaunar ki wallahi yanzu to zaki gane gurin? Dan Allah idan kinje ki gaya masa so nake ayi mun maganin Alhaji yafi da kamuwa yanda ko kara na ajiye ba ze tsallake ba ke ko magana in banace ya bude baki ba karya yi”. Da haka sukayi Sallama Addah ta kama hanyar zuwa Gurin Malam Wizy. Tiryan tiryan ta nunawa Me Adaidaita hanya har qofar gidan Malam dan Addah akwai gane hanya, da dan mamaki ta kalli shagon na Malam Wizy da ta gani cike da kayan provision ana siyar wa. Gaba tacewa Me Adaidaita ya qara ko basu zo gidan ba sedai har suka kai qarshen layin suka jiyo babu wani gida me kama dashi ma. Fitowa tayi ta tsaya dason tabbatar da nan din ne gama dakalin da suka ga yaran nan a zaune ranar, qarasawa tayi gurin me shagon suka gaisa kafin tace “Dan Allah tambaya nakeyi me shagon nan” “To hajia ai gani” “Aa ba kai ba Malam nake nufi” ta bashi amsa. “Malam kuma Malam wa?” Wata sabuwa inji yan caca ita ai se yanzu ta tuna da ko sunan sa bata sani ba, cikin ta ne ya bada qululu ta daure tareda korar abinda zuciyar ta take hasaso mata tace “Malam dai wanda yake zama a shagon nan Mijin Maimuna me wannan gidan” ta fada bayan ta tuno da sunan matar malam din. “Toh gaskiya hajia ban san wanda kike nema ba, hasalima nan shagona ne nafi shekaru goma ina saida kaya a ciki gida kuma da kike magana ba gida bane kangone da Almajiran waccen makarantar suke kwana zaki iya leqawa ki gani” me shago ya fada yana nuno mata makarantar daga nesa. Addah bata qi ta tashi ba ta leqa gidan, kamar yanda ya fada kuwa incomplete ne ta cikin ga kayan Almajirai nan tsubi tsubi, wata hajijiyace ta kwasheta jin zancen da wani saurayi da yazo siyya shagon yakeyi “Tab Malam Musa Allah dai yasa ba itama tafada komar Wizy bane dan a satin nan mata sunfi Goma da suka zo neman Malam” yana kaiwa nan ya karbi kayansa yayi gaba yana wa Addah dariya. Allah sarki Addan mu Allah maida Asara 😂😂😂 https://chat.whatsapp.com/DpZYwM6HCjs7WDTCBPkyj0 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 WATA KISHIYAR 🥰👹 (ALKAHIRI CE KO SHARRI) 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 Na Maryamah_Mrs AM (Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah) Page 12 Lagos Asma’u bata tsammaci dawowar Bashir a yau litinin ba ganin tun ranar Asabar din be ko sake bi ta kansu ba dan haka koda ta tashi aiki ta biya ta dakko yaranta suka wuto gida. Bayan Sallar Isha suna baje a palour, Dan wake sukayi abinsu sunaci suna kallo sukaji tsayuwar mota. Basu kawo shi bane dan baya haura 6pm a waje tsananin hold up ne ze riqeshi zuwa Magriba yanzu kuwa har 8 ta gota shiyasa ma suka fidda ran dawowar sa a yau dukda dai tasan akwai aiki to qila excuse ya dauka. Bude kofar da akayi ya saka su juyawa gaba daya , Bashir din ne hannunsa dauke da rigar coat din sa se waya a kunnensa. Da gudu yaran suka nufe shi suna murna, taso ta basar amma wata zuciyar tace “ki tura masa aniyar sa” se itama ta miqe tana gyara zaman hular kanta ta nufeshi. Side Hug ya mata tareda pecking goshinta bayan yaran dukka sun ruga mota debo kayan daya bari dan sun saba in dai ze dawo se yayiwo musu tsara ba ita kuma ta karbi rigar hannunsa tayi gaba ya rakata da ido bayan ya zauna a daya daga cikin kujerun palour ya ci gaba da amsa wayarsa. Ruwan wanka ta hada masa kafin ta fito masa da duk abinda ta san ze buqata. Sanda ta fito ya gama wayar yana tsakiyar yaran da suke zuba masa surutu se murmushi yakeyi Muhammad na kan cinyar sa yana cin Pizza. “Oh bama za’a jira ni ba kenan ko” ta fada tana daga Muhammmad din kafin ta ci gaba da cewa “Oya kowa ya kwashe nasa duk kunyi scattering palour,ga plates din nan ma ba’a kwashe ba”. ledojin suka shiga tattarewa kowa ya dauke tasa suka shige kitchen su ajiye seta juya ta kalleshi shima ita yake kallo. Murmushi me kyau tayi masa tace “Yallabai ai mun zata se gobe, ga ruwan wanka can na hada maka” “Jazakhillah” ya fada yana miqewa dan a gajiye yake sosai, tunda ya diro be huta ba aiki sosai yau yasha a office din ba. Sanda ya fito daga wanka tana zaune akan kujerar dake dakin sa. Ita ta taimaka masa ya shirya kafin ya tada Sallar isha ita kuma ta fita hado masa Tea da yace ta kawo masa. A babban Mug ta hada ta saka masa madara da Ovaltine sosai banda sugar se Cake din da tayi musu na makaranta ta zuba masa a bowl ta hado akan dan Try ta fito. Sun gama ciye ciyen an tafi yin Brush se Jafar kadai dake tsaye yana jiranta. “Ya akayi” ta tambayeshi “Gurin Abbi zani na tambaye shi abu” “Muje toh” ta fada tayi gaba yana binta a baya. Suna shiga dakin ta ajiye masa ta shiga toilet yin fitsari shi kuma Jafar ya zauna, ba abinda yake son ya tambaye shi ta sani qulafucin uba ne da Jafar dan gani takeyi yafi son Bashir akanta. Indai yana gida tofa yana nane dashi in ko tafiya yayi ya ringa kiransa a wayarta kenan shi kuma haka yake. A dakin ta barshi ta tafi nata tayi wanka, seda ta shirya sosai tabi dakunan yaran ta tabbatar sun kwanta har Jafar din ya dawo sannan ta kashe Fitilun palour ta tafi dakinsa. Yana zaune da waya a hannunsa yana juyawa Asma’u ta shigo, tunani yake ya kira Amirah ko yaya tunda ita Allah besa tayi hankalin jin ya ya sauka ba yauma. Yanayin walwalar da ya gani a fuskar Asma’u yasa ya fasa sema ya kashe wayar gaba daya ya ajiye kafin ya miqe ya fita. Seda ya leqa ko ina ya tabbatar da komai lafiya ya tofe ko wacce kusurwa da falaqi da nasi kafin ya koma Dakin har Ma’u ta kwanta taja bargo zuwa rabin jikinta. Kwanciya yayi shima yana jawota jikinsa, hannunsa ya tura cikin gashin kanta ya zame band din data daure shi dashi, Bashir nason Gashi sosai yana daga cikin abubuwan da suka sake jan sa akan Amirah yanda take kwalliya da gashi. “Madam ya akayi ne da alama ko missing dina bakiyi ba tunda na tafi bako waya”. Gajeran murmushi tayi tace “Qalau fa kawai dai mun barka ne ka huta sosai ka kula da Amarya, ya ka baro su suna lafiya ko?” “Lafiyar su qalau suna gaishe kuma” “Muna amsawa” daganan taja bakinta tayi shiru, shima shirun yayi tana jin sa yana jagwalgwala gashinta kafin bacci ya dauketa. Da Asuba ta rigashi farkawa, harta dauro Alwala be tashi ba dan haka ta shafa fuskarsa da sauran lemar ruwan hannunta jin ana qoqarin tada sallah. Kafin kuwa yayi Alwala an shiga, dole se a palour suka hadu da yaran dukka ya jasu sallar. Bayan sun idar ma bacci ya sake komawa tayi mamaki dan da wuya Bashir ya koma bacci da Asuba kai ko ba zashi aiki ba ze zauna yayi ta lazumi har se rana ta daga yayi walaha sannan yake komawa bacci. Tana wanka tana gulmarsa a ranta wato yaje ya gama kashe Arnansa ze zo yana baccin gajiya a nan ko. Tsaf suka shirya, tana jira taji shi ze tafi dasu ko kuwa ita zata ci gaba da jigilar har suka fita yaran suka shige motarsa taga ya kunna beyi magana ba , Hamdala tayi a zuciyarta kafin ta kunna tata motar suka hau hanya seda suka je junction din da suka saba rabuwa tayi musu horn ta shige kwanar office dinsu. Bayan tayi parking tana qoqarin Daukar jakarta da system Ilhama Abokiyar aikin ta ta qaraso gurin motar, “Aa Maman Farida yau da wuri haka” Ilhama ta fada bayan sunyi musabaha. “Wallahi fa Maman Khairi Allah ya ceto ni daga yawo kai yara makaranta” tare suka jera suna yar hira har suka isa 3rd floor inda anan office din Asma’u yake ita kuma Ilhama tana 4th floor ne. Tana isa office dinta ta tarar da takaddun da zatayi aiki a kansu kamar koda yaushe. Seda ta kintsa komai sannan ta fara duba su daya bayan daya kafin wani lokaci ta gama har ta shiga replaying mails da suke jiranta. Asma’u nada hazaqa sosai ta kuma qoqarin aiki gata Allah ya bata fasahar harshe, duk baqin abu Idan Asma’u ta tsara ka tace Fari ne bazaka san sanda zaka yarda ba dalilin da ya saka ta karantar Business Administration kenan dukda a farko taso ta karanci Law ne yanzu haka tana aiki ne da wanni babban company hadahaar ma’adanun qasa (Mineral resources) tana matsayin Sales Manager (manajan siye da siyarwa). Yanda take qoqari gurin janyo musu customers yasa take samun cigaba da Alkahiri sosai a kan aikin nata ga damammaki da suke shigo mata saboda yanayin aikin yana bata damar hulda da manyan mutane sosai masu siya ko wadan da suke kawo hajar su company ta siya. Tana tsaka da aiki Kiran Fainusa ya shigo mata “Tauraruwa me wutsiya” ta fada a fili dan ita dai duk kiran wayar Fainusa ba Alkahiri bane a gurinta, seda ya katse ta sake kira sannan ta dan dakata ta daga. Cikin sabuwar girmamawar da Fainusan takeyi mata tunda ta fara zaman gida suka gaisa Fainusan ta ke tambayarta yara tace suna makaranta itama ta tambaye ta ya Dada tace tana lafiya. Shiru ne ya biyo baya tana jiran taji dame tazo yau kuma can kuwa ta nisa kafin tace “Anty jiya har dare mutuniyarki suna nan gidan da yaya” “Uhm” kawai ta amsa mata, ita tarasa wannan abu kamar wadda take biya ta kawo mata rahoto kuma duk sanda ta tashi kawowar ba masu dadi bane. Fainusa kuwa bata damu ba taci gaba da cewa “wai fa in gaya miki ta samu Dada wai tayiwa Yaya Magana ya tafi da ita Lagos, to wai ke take so ki dawo nan ko kuma hadaku dukka ze yi anan?” Shiru Asma’u tayi tana so tayi tana sauraronta, jin tayi shiru alamar ta gama kenan yasa tace mata “Toh Nagode ina office ne ki gaida su Dada” taa kashe wayar. Duk yanda taso ta ci gaba da aikin seta kasa, ita sam ta manta da maganar da yai mata ta komawa Gombe se yanzu wato Amiran ce take Son dawowa nan kenan shine ita za’a tarkatata ta koma gida tunda tasan bazasu barshi ya debo su su dukka biyun ba dole ya bar daya acan Gombe. Lallai ma tayi yaya da aikinta toh? Bama wannan ba makarantar yaranta fa ko kuma yanzu Amiran ta shirya zama tayi mata rainon Yayan kamar yanda suka ce a lokacin da ya nemi su ringa karba karba A sannan Amiran ai cewa tayi kowa ta zauna a matsayin ta, dan baza tayi mata bautar Yaya ba, daga baya ma tace ita gara ta zauna cikin yan uwanta kuma ya yarda da hakan shine yanzu data juyo mata zata ce tana so ta dawo nan still kuma ya sake yarda wato ita ga sauna tana zaune se dai su juyata yanda suka so ko? To maji ma gani. Aikin ta taci gaba dayi a ranta tana shirya irin dibar Albarkar da zata masa duk ranar da ya sake tado da zancen ma wallahi se ta masa tatas, qaton sa dashi yazo yai tayi mata muzuran qarya se yaje yarinya qarama ta ringa controlling dinsa kawai. Data tashi kaitsaye ta biya ta dakko yara, sun dan bata lokaci a hanya dan ta tsaaya yin cefanen abubuwan da suka qare musu sam ta manta cikin weekend bata damu tayi ba dan haka kusan tare suka isa gidan dashi. Jakarta kadai ta ajiye ta shiga kitchen sauqinta daya tana da miya a Frizzer dan haka ta cirota ta dumama bayan ta dora white rice ta zuba kwan da zata hada salad dashi su dafu tare. Bata bar kitchen din ba seda ta kammala komai ta jere a Dining yana zaune a palour da yara suna kallo bayan sun dawo daga masallaci. Sannu suka yi mata yaran banda Oga daya bita da ido kawai Amna da Aliyu suka shiga kitchen din dan su jera kayan da suka siyo aikin su ne wannan. Seda tayi wanka da ruwa me zafin gaske tayi sallah sannan taji dan dama dama. Kai gaskiya mata na qoqari, kayi hidimar gida da yara kayi ta miji sannan in kana aiki ko Kasuwanci duk ka hada wallahi bataga laifin Cina zaune ba indai za’a basu komai na buqata dan aiki wahala ne amma dai ko yaya dai gara ka nemi na kanka kodan bacin rana. Kishingida tayi a gurin da tayi sallah kafin kace me baccin gajiya ya kwasheta se farkawa tayi taga Bashir a tsaye a kanta da alama tashinta yayi. Agogo ta kalla goma harta wuce, cikin dan baccin da be gama sakin ta ba tace “waifa na idar da sallah ina zaune ashe bacci nayi, wallahi yau din nan na gaji da yawa kullum work load dina qaruwa yakeyi maimakon ya ragu”. “Sannu, ki tashi kiyi sallar isha kici abinci ina jiranki” yasa kai ya fice daga dakin “Aifa Allah ya kawo mu” ta fada tana miqewa ta shiga toilet. Seda tayi sallar sannan ta fita neman abinda zata ci, kadan ta dibi abinci ta dora da fruit salad kafin ta tattare sauran ta gyara komai. Dakinta ta kima tayi brush ta chanza kayan ta sannan taja qofar ta tafi gurin Bashir. Yana kwance a kan gado ya zubawa pop dakin ido ta shigo, be motsa ba harta ajiye kayan da ta dakko su zata saka da safe tana zama akan gadon wayar sa dake kan mirror ta hau ringing. Bata motsa ba dan tasan me kiran shima kuma bece ta dakko masa ba dan haushin Amiran yake ji wato se yanzu ta raya mata ta kirashi kenan, jin kiran na yankewa wani na shigowa ya sakashi sakin tsaki ya tashi zaune tare da dakko wayar a fusa ce ya daga da niyyar balbaleta da fada amma kukan ta da kururuwar ta shiga uku da takeyi ya dakatar dashi. “Ki nutsu malama kimun magana meya faru” ya fada cike da gundura da kukan nata, Amira kuwa dakyar taja fasali ta tsagaita kukaj kafin ta shiga kora masa bayani tana cewa “Daman Addah ce tun da safe ta tafi gidan Umma Balaraba toh bata dawo ba se dazu bayan La’asar aka kira mu wai tana FMC wasu sun tsinceta a hanya a sume shine suka kaita can” Sabon kuka ta rushe dashi bayan data gama kora masa jawabin kafin qit ta kashe wayar kuma. Dafe kai yayi yana maimaita Innalillahi, a garin yaya toh meya sameta kuma? Asma’u data ga yanayin da ya shiga ce cikin damuwa ta shiga tambayarsa meya faru ya gaya mata ita hankalinta ya tashi sosai. Tasan baze wuce a garin shegen yawon qauyukan da take zuwa gurin malamai bane Allah dai yasa ba wani mugun abun ta hadu dashi ba. Haka suka hadu sukayita jimami bayan Bashir ya kira Naziru shima dai yace masa besan meya faru ba yana zaune Dada tace suje ya kaita Asibitin, kuma dai har yanzu suna zaune Addah bata farfado ba dukda Dr yace babu wata matsala sun dan mata allurar bacci ne ta huta kamar wani abu ne ya firgitata ta shiga tashin hankali. Sudai sunfi tunanin ko yan kwace ta hadu dasu suka zare mata wuqa tunda ba’a sameta da komai nata ba wayarta ma da aka kira aka fadi tana Asibitin ba’a san waye ya kira ba an kuma bi kiran wayar a kashe. Haka dai suka kwanta kowa rai babu dadi. Da safe ma tunda suka tashi yake bige bigen wayar jin yayi jikin nata, ance ta farka tun cikin dare se ihu take tana Allah ya isan kudinta abunda ya qara tabbatar musu da zargin kwace aka mata kenan todai seda aka sakeyi mata Allurar bacci kafin aka samu sa’ida. Be kira Amira ba seda ya isa office ya dan babbata baki kafin ya sukayi sallama yace ze turawa Naziru kudi koda zasu buqaci wani abun. Asma’u ma ta kira Dada tayi mata yame jiki ta kuma kira Ummi, shawarar ta kira Amirah ta shigayi da zuciyar ta ko karta kira dan ita ta manta rabon ma da suyi waya tana ga tun lokacin da Amiran kwanta a Asibiti bayan haihuwarta ta farko lokacin tana Adamawa taje gurin Goggonsu se a waya tayi mata sannu dan tacan ta wuto Lagos. Dama ta dade da blocking dinta a whatsapp saboda irin abubuwan rashin mutunchin da take dorawa a status dan Asma’u ta gani, yanke shawarar kiran tayi ko ba komai Ai rashin lafiya na gaba da komai. Seda wayar ta kusa tsinkewa sannan ta daga murya a dashe tace “Hello” tayi shiru, Ma’u tayi qarfin halin cewa “Amirah ina kwana yame jiki kuma?” Jin bata da niyyar magana. Seda na mula sannan kamar wadda akayiwa dole tace “Lafiya da sauqi kuma zata warware insha Allahu se an kammala abinda aka fara idan ma turen wani mugun abun akai mata sedai ya komawa mutum kansa ehe” ta ja tsaki tareda murguda baki kamar tana gaban Asma’un kafin ta kashe waya. Mamaki ne ya nemi kashe Asma’u a zaune, ita sam bata ma gane kan zancen da takeyi ba illah zallar rashin kunya da taji a muryar Amiran ga kuma kashe mata waya da tayi, daga abin arziqi shine zata mata wannan diban Albarkar? Koda yake ita ta kai kanta ai da bata kirata ba ai bazata mata ba gobe ma ta sake. 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 WATA KISHIYAR 🥰👹 (ALKAHIRI CE KO SHARRI) 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 Na Maryamah_Mrs AM (Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah) Page 13 Addah, abinda ya faru waccen ranar. Kuka riris Addah ta shigayi bayan data tabbatar da cewa Malamin nan dan damfarane, qarin tabbacin data samu tana tsaye wata da ta yankawa kanta kazar wahala ita ma ta zo neman malam Wizy anan suka samu daya daga cikin Almajiran ya fede musu abinda yake faruwa. Wato dama shi ance aikinsa kenan kuma takamaimai basu san dan wacce unguwa bane. Haka yakeyi duk sanda suka tashi zasu je inda ba’a sansu ba su kama guri idan sun gama cin kasuwarsu ta watse ba zaka san ina sukayi ba. Haka suka dauki hanya da me Adaidaita tana faman rusa masa kuka batayi aune ba taga yayi kwana da ita wata hanya daban, da taso tayi masa ihu ya zare mata wuqar dake boye a qugunsa dole Addah tayi shiru se yan idanu tana hawaye haka tana ji tana gani seda sukaje inda babu mutane ya kwace jakarta data zubo kudin raguna biyu ga kuma wadanda Hajia Balaraba ta bata na nata aikin duk ya kwamushe harda wayar ta sannan ya buga mata abu akai ta suma kafin ya kwasota ya kawota Asibiti ya tsere abinsa. Seda ta kwana 4 a Asibitin sannan aka samu kanta ta dena iface ifacen kudinta da takeyi shima se bayan da Alhaji Murtala yayi mata horror sannan ta dauki dangana a fili a zuciya kuwa baqin ciki kamar zeyi ajalinta. Abu goma da ashirin gashi babu damar ta raba baqin cikin da wani ayi mata Allah shi qara dan ko Amirah bata jin zata gayawa bare tsautsayi yasa wani yaji zancen. Amma fa wallahi an cuceta, Dubunta fa har dari da sittin dan iskan yaron nan ya lashe ga Hamsin din Balaraba. Wai ma wace toshewar basira ce ta same su kai wannan ibtila’i da yawa yake, amma bazata haqura ba wallahi insha Allahu seta nemo wanda ze mata aikin da Wizy ze kawo kansa da kansa ya biyata kudin ta (baki daddara ba ashe 😂😂). Haka dai tace a sallame ta ta warke suka koma gida taci gaba da jinyar zuciyarta. Dama damanta ma yanda Bashir yake ta rawar jiki akan ciwon nata, kamar yanda yace ya turowa da Naziru dubu dari yace ayi hidimar Asibiti dan ko babu auran Amirah ai Addah uwa take a gurinsa ze kula da ita kamar yanda zeyiwa Dadansa dan ma dai Addar se a hankali dai, already kuma Alhajin ya biya komai dan haka Nazirun ya danqawa Amirah kudin yace ko zasu buqaci wani abu inji Bashir. Wadan nan kudi ta qudure a ranta da taji dama dama zata kaisu a shaqo mata wuyan wizy kuma (Ai me rabon shan duka baya jin bari dama 😂). Ganin yanda Bashir din yake ta tasu dan kullum sau biyun nan Safe da Dare se ya kira yaji ya jikinta yasa taga dama ta samu na yadda zata tura Amirah gurinsa, (wai nikam dole ne 😂😂 Allah sa dai ba rabon wahala ke kiran Amirah ba itama). Tunda sun gwada wacceb hanyar bata yuwu ba dan haka suka sake wata. Sun san yanda Bashir yake da son yara ya kuka kwallafa rai akan cikin jikinta dan haka yanzu shine target dinsu, Addah batayi sanya ba ta karanta mata duk yanda zatayi, da Bashir din ya kira waya zata langwabe yau tace kanta anjima cikin ta, Aa jiri ne yake damu ta shidai se yace mata taje Asibiti ta kuma rage yawan zurga zurga saboda halin da take ciki. Ganin an kwashe sati biyu ana haka be ce ze zo ba ko ita ta tafin yasa suka shirya sabon plan. Ranar Juma’a data kama Sati biyu kenan rabonsa da Gombe da daddare suna cikin waya tace bari tayi fitsari, bata kashe wayar ba ta ajiyeta akan sink ta dauki hand shower tana tsiyayar da ruwa kaman me fitsari se kawai ta fasa ihu. Bashir da acan bangare yana riqe da waya yana jiran ta gama ya miqe a sukwane jin ihunta har yana tunkude cup din da Asma’u ta cika masa da Kunun Aya ya tuntsure a qasa take kuwa ya fashe. “Lafiya meya sameki” ya tambayeta a kidime, seta fashe masa da kukan qarya tana cewa “Jini, jini ne yake zubomun” ta ci gaba da kukan. Sosai hankalin Bashir ya tashi, idan be manta ba wancan karan da haka ta fara zubar da jini kafin Wani lokaci jaririn ya mutu a cikinta se inducing dinta sukayi ta haihu dan haka yake taka tsan tsan da abinda ze sake janyo faruwar hakan. “Subhanallahi a garin yaya toh ko kinyi wani abun ne daya fi qarfin jikinki?” Ya tambaye ta “Nima ban sani ba kuma ni banyi komai ba, dama ba tun yau ba ya fara kawai gaya maka ne banyi ba bana so hankalin ka ya tashi” Amirah ta fada tana sheshshekar kuka, a ranta Addu’a takeyi Allah yasa yace zezo dan wallahi qafarsa qafarta itama se taje an ci uwar da ake ci acan tare da ita. “Kin gane ki gyara bari na kira Naziru yazo ya kaiki Asibiti yanzu” maganar sa ta katse mata tunani, se ta dan diririce dan bata zaci zece aje Asibitin ba amma kuma idan taqi tasan wata matsalar zata kwantowa kanta in kuma sukaje akaga ba haka ba nan ma ba tsira zatayi ba, daurewa tayi tace masa “Aa karbar shi dare yayi yanzu kuma bada yawa bane ai da nayi tsarki ma ya dena zuwa, sannan Anty Ramle tana gida (Amaryar babansu Nurse ce) koda wani abu ya taso zata iya taimaka min kafin muje Asibiti”. Sallama sukayi ya kashe wayar Badan ya gamsu da maganarta ba dai ya qyaleta tunda yasan Anty Ramle tasan aikinta sosai zata kula da ita amma koma menene zuwa safiya dole taje Asibiti dan baze dauki ganganci ba, kai qila gobe ya tafi ma dakansa ya kaita gara in ma wani abune a shawo kan matsalar da wuri. Tsakin daya sakeyi a karo na ba adadi ya saka Ma’u daga kai ta kalleshi, tunda ya barar da kunun Ayan ta kwashe kwalaben tareda goge Gurin kawai ba tareda ta tankashi ba dan taji duk maganar da sukeyi. A ranta tadan tausayawa Amiran in da gaske takeyi dan dai duk mace tasan wahalar ciki da haihuwa dole in kaga wani dashi ka tausaya masa. Bata tambaye shi abinda ya faru ba shima kuma be gaya mata ba har sukaje kwanciya, juyi daya biyu ya saki tsaki kai har abin ya fara bawa Asma’u haushi amma ta jure bata tanka masa ba sema danna kanta da tayi cikin pillow ta tilastawa kanta yin bacci. Wai kuma ashe shirun data yi laifine se jinsa tayi yana cewa “Wai dan wulaqanci kina jina amma bazaki iya tambayata meya faru ba ko?” “Ikon Allah” ta fada a ranta, a fili kuwa daga kai tayi ta kalleshi sau daya ta juya ta rufe idonta ba tareda tace masa komai ba, ai bashi kadai ya iya miskilancin ba. Bashir kuwa jin ta masa shiru ya qara tunzurashi, kwafa yayi yana sake zabga tsaki kamar ze katse harshensa, ga damuwar halin da Amiran take ciki ga share shin da Ma’u tayi ta juya masa baya. Wayar sa ya dauka ya shiga duba jirgin Lagos to Gombe a gobe Asabar amma babu dolensa ya haqura, Haka yai ta juye juyensa har shima baccin ya dauke shi. Asubar fari ya dannawa Amirah kira, tana can tana sharar baccinta har wayar ta qaraci ringing bata ji ba, seda ya kira sau biyu ana uku ta daga cikin magagin bacci. A tsaitsaye suk gaisa ta tabbatar masa da komai lafiya babu abinda yake damunta yanzu sannan sukayi sallama yana jaddada mata ta shirya anjima Naziru ze zo ya kaita Asibiti ta amsa shi da toh bawai dan zata je din ba to me yake damunta ma. Suna gama wayar ya maida akalar kiran kan Naziru, gaya masa yayi yaje ya kaita Asibitin duk abinda ake ciki ya sanar dashi sukayi sallama. Asma’u tana kwance akan gado duk tana jinsa, mamaki take yanda gaba daya ya rikice, ganin yana neman ya hanata baccinta yasa ta miqe ta bar masa dakin ta koma nata ta kwanta. Har yamma bata san ya aka qare da jikin Amirah ba, ita bata tambayeshi ba shima be mata maganar ba dan wani shareta ma ya shiga yi a dole wai haushin ta yake ji ita abun ma se ya bata dariya. Da yamma ma kudi ya bawa Ahmad yace ya kai mata su fita su siyo abinda suke so shi bazashi ba ta kuwa karbe su ta zuba a jaka suka shige kitchen da yara suka hau yin shawarma suka gasa kaza da zasuci da daren se smoothy na Ayaba daya ji madara. Ta bayan kitchen dinsu akwai fili da suka gyara ya zama kaman wani garden wurin suka shirya abincinsu, kowa yayi wanka yasha kwalliya kamar masu zuwa wani guri suka haucin abincu ba tareda anyiwa Bashir daya hakince a palour tayi ba. Tunda suka fara gasa kazar qamshin ya fito dashi ya zauna yana jiran a gama a kawo masa amma yaga sun tattare sun tafi baya. Ganin da gaske fa zasu cinye yaja zaune yana jiyo dariyar su cikin nishadi se ya miqe ya tafi gurin ya tsaya a kansu yana muzurai. Gaba daya suka kwashe da dariya, sunsan dama ba ze iya dauke kai ba Bashir da Nama kamar kura in ya gani se ya ci haka kuwa ya zauna yana zare ido aka ci dashi tas suka dauka pictures kafin kiran magriba ya tayar dasu. Seda suka zo kwanciya Asma’u take tambayarsa yaya jikin Amiran yace mata da sauqi tayi masa fatan samun lafiya shikenan kuma fushin ya wuce aka shiga sabgogi. Lafiya lau suka cinye satin, yara sun fara exam ta third term zasu samu hutu me tsaho nan da sati biyu da wannan damar Asma’u take so tayi amfani ta dauki leave ita ma dan ta kwana biyu bata je Gombe ba, sannan tana son zuwa yola ta duba Maman ta da jikinta yake yawan motsawa kwana biyun nan. Ranar Wednesday daya rage saura kwana biyu kenan yaran suyi hutu, already ta rubuta takardar hutunta har anyi approving tana so ne a ranar friday su wuce Gombe dan babu jirgin Saturday. Da daddare bayan sun gama dinner suna zaune a palour ita da Bashir yaran na dakunan su suna Karatu Muhammmad da Ahmad kuwa sunyi bacci dan su sun gama tasu exam din. Kallon Bashir dake duba wasu takaddu tayi tace “Baban Ali kayi mana booking flight din kuwa mufa mun gama hada kayan mu” Ba tareda ya dago ba ya bata amsa da cewa “Waini saurin me kikeyi ku tafi ku barni ni kadai” Murmushi tayi kafin tace “ba haka bane, kaga na dade rabona da gida inaso mu dan kwana biyu na zaga dangi ga kuma tafiyar Yola ma gara mu je da wuri ai” “Hakane” ya fada ya ci gaba da aikin sa. Gombe Daga ciwon qarya Amirah ta fara na gaske, haka nan se taji kanta ya sara mata ko in tana tsaye ta fara jin dumm kamar jiri ze kayar da ita idonta ya ringa mata dundumi bata gani da kyau amma Saboda rashin sanin ciwon kai sam bata bawa abin muhimmanci ba ta cigaba da sabgoginta idan ta gayawa Bashir yace taje Asibiti ma bata zuwa Sedai ta karbi kudin a hannun Naziru ta kashe. A hankali kuma se ta fara kumburi, farko qafarta ce ta fara Se Addah tace mata alamu ne na ciki ya tsufa babu komai ta dai ringa dan tattakawa haka, sau biyu Antu Ramle na mata magana akan kumburin tace ta shirya suje Asibiti amma taqi qarshe ma tace ta dameta ita a rabu da ita ana haka kuwa ta ci gaba da hawa kafin kace me tayi himm ga ciki shima ya qara girma. Safiyar Friday dakyar dama ta tashi daga kan gado, Addah data shigo dakin take gayawa bata jin dadi tace mata ta daure tayi wanka ta shirya to se suje Asibiti haka ta yunqura ta shiga bayin, wai dan daurewar da jikinta yayi ya warware ta sakarwa kanta ruwa masu zafi gaba daya bayin ya turare kan kace me numfashinta ya fara sama sama yana neman daukewa ba shiri ta yunquro ta fito cikin tsautsayi tana fitowa ta yanke jiki ta fadi cikin tashin hankali suka kwasheta zuwa Asibitin da take Awo. Lagos Ranar Friday da zasu tafin yaran basu je makaranta ba dan babu abinda zasuyi takardar hutu kawai za’a basu kuma already an turo musu ta email daman, jirgin qarfe 6pm zasu bi zuwa Gombe amma tun kafin la’asar sun gama komai hatta jakunkunan su sun loda a mota. Se murna sukeyi kamar suyi tsuntsuwa su gansu a Gombe haka suke ji. Qarfe biyar sukaji tsayuwar motar Bashir dan daman yace ze dawo da wuri ya kaisu Airport sedai daga yanayin daya shigo gidan tasan ba lafiya ba. “Kuje Mota ina zuwa” ya fada yana shigewa dakinsa, yaran suka fita amma ita se tabi bayan sa. Sanda ta shiga yana waya gaba daya ya birkoto wata shelf daya ke ajiye files dinsa na office da alama wani abu yake nema. “Ayi duk abinda ya kamata kafin nazo yanzu zamu taho insha Allah” taji ya fada kafin ya kashe wayar ya shiga diban wasu daga cikin filea din daya zubar. Ita ya miqawa yace “Joseph na waje please ki bashi zamu yi waya” Karba tayi ta fita a ranta tana tunanin meyake faruwa ne toh, haka ta miqawa Joseph files din tana shirin kowa se gashi ya fito bayan ya kulle gidan gurin wutar gidan ya nufa ya kasheta gaba daya, seta kalleshi tana cewa “akwai kaya a freezer fa zasu lalace” “Please muje kawai” ya fada yana bude motar ya shiga itama seta bude gaban ta shiga kawai ya tayar suka tafi. A Airport din ya ajiye motar suka tashi zuwa Gombe gaba dayan su Asma’u nata mamakin wai me yake faruwa ne dan dai ba dashi suka shirya tafiyar ba yanayin data ganshi kuma bata zaton ze iya mata wani bayani, koma dai yaya ne Allah ya kaisu lafiya zasu gani Allah dai yasa Alkahiri ne. Gombe Daga Airport direct Asibitin da suke zuwa Naziru ya wuce da Bashir da Asma’u yaran kuma Sa’ad wanda Nazirun yake bi ne ya kwashe su a tasa motar suka wuce gidan Dada. “Hasbunallahu wani’imal wakeel” ta furta lokacin da tayi Arba da Amirah dake kwance tayi wani irin kumburi kamar zata fashe, cikin tashin hankali ta kalli Bashir da shima ganinta a hakan yai bala’in tayar masa da hankali. A yanda akayi masa waya beyi zaton abun yakai haka ba. Yana Office da Safe Isma’il yayanta da suke Uba daya ya kirashi wai Tana tsaye ta yanke jiki ta fadi dama dai tun Kwana biyu take yawan yi masa qorafin ciwon kai da jiri, ya cewa Naziru ya kaita Asibiti ya kuma je amma taqi zuwa Nazirun ya gaya masa. Beyi mata magana ba dan dama bashine karo na farko ba da zata ce bata da lafiyar in yace akai ta Asibiti taqi zuwa sedai ta karbe kudin ta kashe kawai yanzun barinta yayi se yazo sannan ze kora mata warning se kuma ga wannan abun ya faru. Da aka kawota Asibitin likitan yake gaya musu jininta ne ya hau sosai da sosai ga kuma alamun preeclampsia tare da ita (jijjiga) kuma daman tuntuni ya gaya mata duk sanda taji wani sauyi ko alama tazo a dubata tunda cikinta ya shiga wata na 7 toh awon ma seta ga dama take zuwa gashi yanzu abinda ba’aso ya faru se fatan Allah ya kawo sauqi kawai. Suna tsaye jungun jungun Bashir ya tafi office din Dr, acan yake gaya masa dole sedai suyi mata aiki in dai ana so a ceto rayuwar ta dan barin ta da cikin ze zamar mata hadari. “Toh Dr ai kuma cikin be isa haihuwa ba” Bashir ya fada a sanyaye “Wannan ba matsala bane Engineer idan an cire shi zamu sakashi a kwalba ne mu cigaba da kula dashi har sanda ze isa dauka amma yin aikin yanzu shine kadai maslahar mu, bansan wace irin yarinya bace ita da bata damu da lafiyar jikinta ba ta yaya ma akayi tana zaune har takai wannan stage din batazo Asibiti ba tunda ba abu ne da yake faruwa lokaci daya ba” Shidai Bashir bashi da ta cewa, takardar da likitn ya bashi yasa hannu, yace su kwantar da hankalin su babu komai insha Allah zasu ci gaba da monitoring nata su samu jinin ya sauka kafin a shiga da ita aiki suyi ta yi mata Addu’a kawai. A reception daya fito can lungu ya hango Addah ansha kuka an gode Allah se yan idanu kawai take kiftawa se sannan ya samu suka gaggaisa dasu kafin yacewa Asma’u da tuni jikinta ya mutu tabi Naziru ya kaita gida ta hutu jinawa ze taho. Fatan samun sauqi tayiwa Amiran ta bi Nazirun suka wuce gida. 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 WATA KISHIYAR 🥰👹 (ALKAHIRI CE KO SHARRI) 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 Na Maryamah_Mrs AM (Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah) Page 14 Seda Amirah ta kwana daya a daren rana ta biyu akayi mata aiki cikin ikon Allah aka ciro mata yar qaramar yarta bakwaini me tsananin kama da Farida, sosai Bashir yayi murnar samun mace sanda aka nuna masa babyn kafin aka sakata a kwalba, tun cikin daren kuwa ya ringa buga waya yana gayawa mutane haihuwar. Ya kira wayar Asma’u lokacin harta fara bacci dan basu dade daga dawowa daga Asibitin ba suna can ma aka shiga da ita aikin, ganin dare ya fara ga yara yasa ta tafi gida. “Masha Allah, Allah ya raya ita kuma ya bata lafiya, kace Farida tayi yar uwa Abokiyar shawara” ta fada bayan data daga wayar. “Wlh fa sema kinganta kamar su daya kamar sanda kika haifi Faridan girma kawai ta fita” Bashir ya fada cike da doki kafin sukayi sallama. Baccin ta ta koma dan dama tunda suka dawo ta rufe gida tasan ba dawowa zeyi ba dan jiya ma can ya kwana seda safe yazo yayi wanka ya chanza kaya bare yau da ya samu ya ai ba batun zuwa gida kuma. Washe gari da wuri ta tashi ta hau shirye shirye dan tana so taje gidan su yau ga zuwa Asibiti. seda tayi girki tayi musu farfesun Kaji ta soya doya sannan ta damawa Amirah kunun gyada dukda bata san ko zata faracin abinci yau din ba sannan ta dafa Tea suka shirya gaba daya ita da yaran suna ta murna data gaya musu sunyi qanwa. Se gurin goma sannan ta hada komai suka tafi. Dakin danqam da yan dubiya yan gidan su Bashir da kuma Dangin Amiran se hayaniya sukeyi dan ta farfado tun da Asuba. Ba yanda Likita beyi dasu ba subarta ta huta amma sunqi qarshe haushi yaji yai tafiyarsa ya barsu ya kuma gayawa Nurse kar wanda ya nemeshi in wani abu ya faru dan ya gaji da halinsu kuma. Aliyu da Jafar ne a gaba sunyi kama kaman kwandon da ta zubo Abincin su kuma suna binsu a baya suka shiga dakin da Sallama. Fuskarta dauke da Fara’a suka shiga gaisawa da mutanen dakin tayi musu barka kafin ta juya kam Amirah da tun shigowar Asma’un ta daure fuska tam taqi koda kallon sashin da take. “Amirah sannu ya jiki?” Ta tambaye ta idan ta amsa ta to ku da kuke karatu kun amsa abin yai bala’in bawa Aisha Babbar Yayar su Amirah da suke uba daya haushi har seda tayiwa Amiran magana tace “Kina ji tana miki magana saboda raini da wulaqanci bazaki amsa ba” Bata ko motsa ba kuwa sema cuna uban baki gaba da tayi dama fuska duk a kumbure tana qunquni. Asma’u kam ko a jikinta, yo ita bata ga abin da zesa Amirah tace bazata kulata ba idan kishin nema ai ita ya kamata tayi tunda aita aka aurewa miji, Allah ya raya ta sakeyi musu kafin ta juya da niyyar fita dan dama yaran tunda suka gaishe su sukayi waje abinsu, dab da zata fita ta jiyo muryar Addah na tambayar waya kawo abinci ashe tana bandaki seta juyo ta dawo cikin dakin. Har qasa ta durqusa ta gaisheta, fuskar Addah kuwa a washe ta amsa mata tana tambayarta ina Mazajen nata tace suna waje “Au shine suka fita ba su bani kudin cefane ba ai kuwa su dawo dan bazan yarda ba” Addah ta fada cikin sigar wasa. Murmushi kawai Asma’u tayi ta miqe tana musu sallama ta fice. Wato Yanda Addah ta wanke idanunta bata taba nuna wani abu akan auran Amirah da Bashir na bala’in daure mata kai, mutum, ka kalleshi kawai. A reception ta hadu da Bashir daya je gidansu ya dauko Dada dan Naziru yana makaranta yau, cikin mutuntawa ta gaisheta tareda yi musu barka Dada ta wuce ciki Bashir kuma yabi bayan Asma’un. “Har kun qaraso kenan, yanzu nake so dama na tafi gidan nayi wanka na huta wallahi duk na gaji” ya fada yana jingina da motar da tuni su Jafar suka shige bayan sun gaisa da Dada. “Ya kamata kam, abincinka na nan ma na ajiye maka nayi zaton kafin mu fito zaka dawo kuma naji shiru, mu zamu wuce Babban gida qila idan zamu dawo da dare mu sake shigowa mu duba su” Asma’u ta fada tana qoqarin bude motar, “Bazaki je kiga babyn ba?” Ya tambayeta “Ai bazasu bari ba ka sani ba komai Allah ya bata lafiya idan lokacin fito da ita yayi zamu ganta ai mu da zata dawo gidan mu da zama ma” “Eh kuma haka ne, bari na shiga na fito to nima na wuce ku gaida mutanen gidan ban samu na shiga ba wallahi Yanzu ma da zamu fito naga Kamar Alhaji Qarami dasu Yaya Mudassir a qofar gidan ashe yana gari” “Eh yazo daurin auran yarinyar Amininsa ne jiya saurin da nake tayi kenan ma mu tarar dashi ance yau ze koma” da haka sukayi sallama ya shige ciki ita kuma taja mota suka nufi gidansu. A can dakin kuwa bayan fitar Asma’u dayawan su sukayi wa Amirah caa akan abinda tayi bata kyauta ba, Addah ce ta tambayi meya faru Anty Aisha ta gaya mata. “Ai ni na rasa kalar wannan yarinyar dan barikin nan ma na mata bata iya shi ba ke se baqin kishi quru quru meye amfanin sa” “Wallahi fa Addah in nice ita yanda Anty Asma’u ta mayarda komai ba komai ba ake gaisawar mutunchi ai wallahi sake wa zanyi mu ci gaba da yanda muke amma kin zauna kina quntatawa kanki ita kuwa kina ganinta cikin walwala ji jikinta dan Allah wannan shegen Lashin nasan wlh yafi 100k ga zobuna a hannunta ji qanshin turare dan Allah har yanzu be bar gunnan ba” inji Samirah qanwar Bashir da suke Sa’anni da Amirah. Hirar su suka ci gaba dayi aka shiga da take qonawa Amirah rai dan duk yabon Asma’u sukeyi ga dabgen kaji suna ci abinsu a haka Dada ta shigo ta same su ta kuwa ji dadin Abincin da ta tarar Asma’un ta kawo dukda ita ma ta taho musu da abinci amma tasan ba lallai ya isa ba tunda kusan duk yaran suna nan. Asma’u kuwa hankali kwance suka isa gidansu wanda layi daya ne ya raba su da gidansu Bashir dan seka bi ta qofar gidan su Bashir din ma zaka shiga layin da gidansu yake da yake close. Cike da murna Seidu dan Baba Buzu daya daga cikin masu gadinsu tun na quruciya daya maye girbin Babansa yanzu ya wangale mata katafaren get din gidan na Alfarma ta shiga. Tabbas gidan ya amsa sunan sa na Babban gida domin kuwa layi guda ne gidan haka tun daga get da katangar gidan zaka san cewa ba qaramin gidan me Arziqi bane. Tana gama parking a inda aka tanadarwa motoci gasunan birjik da alama yau akwai mutane da yawa a gidan yaran suka fita da gudu saboda hango cousins dinsu yaran Yayye da qannen Asma’u da sukayi se lokacin ta tuna yau Sunday kusan dukka yan gidan da suke a cikin garin Gombe Mata da Maza suna zuwa gida yau da iyalan su su wuni tun zamanin da Mahifinsu yake raye har yau kuwa basu fasa ba. Seda ta gaisa da Samarin dake zaune a bakin get yawanci duk masu aikin gidan sannan ta shiga cikin gidan, part din Hajia Babba ta nufa dan a irin wannan lokacin tasan acan zata samu kusan kowa ai kuwa tana shiga katafaren palour nata fuskarta ta qara fadada da Murmushin ganin yan uwanta harma da wanda batayi zato ba. Kai tsaye inda Hajia Babban take ta nufa Farar Bafulatana da a qiyasi ta bawa Sittin Baya amma jin dadin da take ciki ya boye shekarunta “Maraba Maraba da mutanen Lagos” take fada sanda Asma’u ta nufota, seda ta zauna dab da qafafunta tana daukar wani Dan yaro daya ruqo mayafinta da bata san ko dan waye ba sannan ta shiga gaisheta. Cike da qaunar junan data ginu a tsakaninsu suka shiga gaisawa da sauran yan uwanta da suke a palour se tsiya suke mata wai ta qara kyau tayi wani haskee ta zama wanke ka taba ita dai se dariya kawai take musu. Suna cikin gaisawar Alhaji Qarami ya shigo Aliyu na take masa baya dan dama mutuminsa ne. Gaishe shi tayi ya amsa mata cike da kulawa yana tambayarta aiki babu dai wata matsala ko tace babu sannan yayi wa Hajia Babba Sallama bayan yayi musu gajeriyar nasiha da tunatarwa daya saba yi musu a duk sanda suka hadu da yawa irin haka akan su riqe zumunchin da Mahaifinsu yasha wahalar gina su akai, seda yabi duk wanda yake zaune da dubu biyar suda yayan su kaf sannan ya musu sallama Driver sa ya ja shi suka wuce Abuja inda yake zaune da iyalansa. Ance daman babban wa makwafin uba to tabbas sudai sunyi dace dan kuwa Alhaji qarami ya maye musu gurbin uban da suka rasa. A gaba ta saka yaran suka zaga saran part biyu na matan gidan suka gaisa Hajia Ummah da Hajia Anjin kafin suka wuce sabgarsu ita kuma ta koma part din Hajia Babba inda sauran yan committee suke jiranta a tattauna. “Ke ashe Kishiyar ki ta haihu, dazu naji Abbas yana gaya wa Hajia Babba” Ikilima yayarta ta fada, seda ta cire yafinta ta ajiye a gefe ta zame dankwalin yayi baya sannan tace “wallahi fa ta haihu an mata CS jiya da daddare an ciro mata baby girl” “Ayya CS ne Allah ya bata lafiya ya raya abinda aka samu” cewar Anty Hauwa matar yayansu Sunusi suka amsa da Amin gaba daya. “Kinje kenan?” “Naje mana daga can nake ma yanzu” “Cab kuma kika kwashi jiki kikaje nifa wallahi Yah Asma’u kina bani mamaki na rantse da Allah in nice kallon banza yarinyar nan bata ishe ni ba bare na arziqi wallahi bazan je dubata ba, bata da mutunchi kwatakwata baki san abinda ta mana ba ranar sunan Rufaida(qanwarsu ce itama tana auran Yayan Amirah da suke uba daya) wai saboda bata da kunya ta kalle mu muna zaune wai bamu gaisheta ba idan Bashir ne ai dole mu gaidashi tunda mijin yar mu ne dan haka matsayi daya take dashi a gunmu ita Kishiyar yayar muce , wallahi Anty Habi ce kadai ta hanamu nada mata dan iskan duka ranar amma da se mun koya mata hankali” cewar Amina daga yanda take maganr zaka gane zallar takaicin Amirah da take ji. Dariya Asma’u tayi tace “to ai se ku gaisheta meye a ciki zuwa dubiya kuma kema zakije dan ciwo na gaba da komai sannan ranar suna dole kuzo asha shagali daku” “Tab Allah ya rufa asiri” Aminan ta fada tana tura baki. Dariya suka saka mata dan dama indai aka fara wannan dramar Amina bata da dama a fili take nuna jij zafin Amiran harma dana Bashir din dan ita fa tunda yai auran nan ta dena gaishe shi. Tace yanda beji kunyar ciwa yar uwarta fuska ba itama bazata ji kunyar dauke kai idan ta ganshi ba taqi gaishe shi. Asma’u ta kance wai “Amina inda kece a matsayina ban san me zakiyi ba” ita kuma tace “Ai wallahi yah Asma’u da ko tsirena su Alhaji Qarami zasuyi na gama auran nan dan bazan koma ba”. Ranar wunin dadi sukayi suka sha hirar su kamar karsu rabu, se bayan isha suka fara watsewa bayan tayi musu Alqawarin zata bi kowacce gidanta su gaisa da kyau tunda zata kwana biyu a garin. Daga ita se Abdallah suka koma gida sauran yaran kowa ya kama gabansa dan daman idan suka zo indai ba tareda Bashir ba basa zaman gida in yana nan ne yake matsesu baya taba bari suje ko nan da can su kwana yanzun ma abinda yasa ta barsu yana cikin wannan digimi be zama lallai ma ya fuskanci basa gidan ba. Seda ta biya Asibiti ta sake dubasu, a can din dai ta kuma samun sa kuma suka barshi sukayi gida yace se ya taho har suka kwanta dai be dawo ba seda Asuba sannan taji motsinsa dan a dakinta suka kwanta ita da Abdallan. Washe gari Litinin Bashir yayi sammakon komawa aiki bayan yabar komai da zaa buqata hannun Naziru, ranar ma bata wuni gida ba, gidan Yaya Bilkisu taje da suke ciki daya kuma ita kadaice yanzu a Gombe Babbar Yayarsu Anty Suhaima tana America da mijinta se Junaidiyya da take Abuja sauran uku mazane biyun qannenta yan biyu Bilal da Nasir suna karatun masters a China se yayanta daya Muslim yayi aure tuni yana zaune a Rivers da matarsa da yaransu biyu da A Lagos yake shima akayi masa transfer. Sosai suka sha hira da Yayar tata har dare kamar karsu rabu, sun yi sallama akan Nan da kwana 7 zasu tafi Yola tare gurin maman su dukda ita Asma’u taso nan da kwana biyu ta wuce amma Yaya Bilki tace ta bari se anyi radin sunan yar Amirah idan yaso ko bata samu taron sunan ba babu matsala amma yanzu in ta tafi ze iya zama abin magana ai a kan hakan suka rabu. Haka taci gaba da zaga yan uwanta har ana i gobesunan Amirah bayan la’asar tana zaune ta jiyo hayaniya an bude get. Ta window palour ta ta leqa da mamaki take kallon su Addah dake fitowa daga mota da Amira tana takawa dakyar bata ga jaririyar ba tana asibitin ita har yanzu. Bangaren Amiran suka nufa seda suka shige sannan ta koma ta zauna tana mamaki tasan dai yau za’a sallameta dan ya gaya mata da tun Jiya daya dawo amma batayi zaton nan zata dawo ba kodan yanayin jikinta amma ita meye nata. Seda tayi sallar isha da dogon hijabin ta a jikinta ta nufi part din Amiran da kulolin da ta zuba tuwo da miyar kukar da ta saka Amna tayi. Seda tayi sallama uku sannan suka jiyota ta tura qofar ta shiga duk sukayi wani tsilli tsilli alamar basu da gaskiya da gulmarta sukeyi a lokacin ta shiga. Bayan sun gaisa ta sakeyi mata ya jiki yau dai ta amsa bata zauna ba tayi musu sallama ta koma gurinta. Washe gari suna da Asuba a masallacin unguwarsu aka radawa yarinya suna taci sunan Addah Fatu, Asma’u na daki Farida take gaya mata Amma Anty Ummi tace Iman zasu ringa kiranta, setayi Murmushi kawai ta tuna sunan Farida da tace nan ma ya saka mata Maryam sunan mamanta tunda yace ba sunan Dada ze saka ba ce mata yayi shi bashi da ra’ayin yiwa wani takwara, ko Aliyu daya saka raayin kansa ne badan Aliyu Abokinsa ba kamar yanda ake zato. Ana Abdallah kuwa cewa yayi ta siyi rago haka kuwa ta siya, haka aka yanka wa Baby Iman ragunanta biyu ba’ayi wani taro ba ranar tunda tana Asibiti har sannan sun dai qudurce a ransu fa se sunyi daga baya, dalilin ma daya sa suka dawo da ita gidanta kenan saboda duk abunda za’ayi ayi akan idon Asma’u dan Amirah tace shagali zatayi na kece raini. Washe gari Suka soye naman su ko hanji basu Aikawa Asma’u da bama su san asubancin barin garin tayi ba ita da yara zuwa yola, suka rabe abinsu tas dan Bashir ma ya tafi tun safe kuma har nasa rabon suka cinye. Toh maji ma gani dai. 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 WATA KISHIYAR 🥰👹 (ALKAHIRI CE KO SHARRI) 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 Na Maryamah_Mrs AM (Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah) Page 15 YOLA Su Asma’u sun isa yola lafiya sun kuma samu tarba me kyau daga mamansu da suke kira da Goggo da bakinta yaqi rufuwa ganin yayan nata da kuma jikokinta a gabanta ba qaramin faranta mata yayi ba. Se sannu da zuwa take musu tama rasa wanne zata kama ciki idan ta janyo wannan yaron se saki ta kamo wancan su Asma’u har seda sukayi kwallar kewar Mahaifiyar tasu. Seda suka nutsu sukayi sallolinsu sukaci abincin da Abokiyar zaman Goggon Innawuro ta kawo musu ga fura me sanyi da gardi sannan Goggo tayi musu jagora zuwa bangaren megidan su gaishe shi. Fari kyakykyawan bafulatanin me kamilalliyar fuska dake cike da haiba da hasken salati yana nan a yanda Asma’u ta sanshi tunda tayi wayo sedai a kwantar a tayar tun zamanin da suke zuwa Tareda Baffan su dubashi wanda kuma tun kafin a haife ta yake wannan ciwon kimanin shekarun sa Arba’in kenan a kwance yana wannan jinyar da har yau Allah ne yanke masa ba sedai fatan ta zamo masa kankarar zunubi. Seda sukayi dagaske gurin danne kukan tausayin bawan Allahn dake musu maraba daga kwancen ya miqa hannu ya kamo Abdallah yana cewa “Zo nan Abdullahi bawan Allah madallah da Amini na kwarai, Rahmar ubangiji ta dawwa ma tare da takwaranka a makwancinsa”. Akan shimfidar sa da take a gyare ya zaunar da Abdallah sannan ya janyo Arif din Yaya Bilki yana cewa “wannan kuma me idon yan Chinese dinfa wanene” seda sukayi dariya gaba daya Innawuro tace “Toh takwaranka ne Isma’il dan wajen Bilkisu” “Toh toh yi haquri ta kwara gajiyar hanya ce ta rufe idon ko nasan anjima zasu bude irin nawa”. Cikin mutuntaka suka gaisa ya tambayesu sauran Yan uwansu da kowa da kowa duk suka amsa lafiya daga nan ya shiga saka musu Albarkar da bakinsa baya gajiya da ita a kullum suka hadu ko suka gaisa a waya. Sun dan zauna kafin yace suje su huta haka suda suka sha hanya, a nan suka bar yaran suka koma Dakin Goggo jikinsu dukka a sanyaye. “Allah sarki Baffan Yola wannan jinya dai taqi ci taqi cinyewa Allah yasa kankarar zunubi ce” Asma’u ta fada tana kwanciya akan gado Goggo da Bilkisu suka Amsa da “Amin”. Basu ja wata hira ba suka kwanta aka barwa gobe dan sun gaji gaskiya. Washe gari bayan sun je sun gaisa da Innawuro da Baffa suna zaune a palour Goggo suna cin Wainar Gero da Kunu me kyau da Innawuron tayi musu dan tasan suna son sa sosai. Goggo dake zaune daga gefe ta kalli Asma’u tace “Ma’u ya Abokiyar zaman ki kuwa kuna dai zaune lafiya koh” Seda ta tsame hannunta kafin tace “Muna lafiya Goggo to ina muke ganin juna bare wani abu ya hada mu ina Lagos tana Gombe” “Haka ake so ai dama wani sa’in raba gidan yana da amfani idan har akwai wasu matsaloli amma dai ko zuwa gaba idan ta fara tara iyali itama dole ya hade ku saboda a samu daidaiton kawuna tsakanin su dan dai nasan baki tashi kinga ana yan ubanci a gidan ku ba kuma zaki kaishi gidan wani ba”. “Haka ne Goggo ai tama haihu fa shekaran jiya akayi suna” Yaya Bilkisu ta fada jin Asma’u tayi shiru bata ce komai ba. “Kai Masha Allah me aka samu? Kuma cikin satin da aka fita fa Bashir din ya kirani Allah yasa kuwa beji babu dadi ba banyi masa barka ba ban sani ba ai da har ita Dadan tasu da Fatu na kira na musu barka, miqo min wayata nan Bilki ki gani karma na sha’afa da batun”. Wayar Yaya Bilkisu ta bata ta kuwa shiga kiran Bashir sedai be Amsa ba saboda lokacin aiki ne seta maida kiran kan Dada ita ma seda ta kusa katsewa sannan ta daga. Cikin mutuntaka suka gaisa Dada ta tambayeta ya me jiki tace jiki gashinan se fatan Afuwa. “Ashe kuma an samu qaruwa wallahi ban sani ba se yanzu muke zancen dasu Asma’u nake ji” “Asma’u? Sunzo yola ne?” Dada ta tambaya dan bata sani ba Bashir din be gaya mata ba daman kuma tasan Ma’u ba Sallama zata mata ba yanzu. “Eh wallahi sunzo tun jiya ita da Bilki, Allah ya raya yayi Albarka, haduwa tayi wuya amma Insha Allahu ina sa ran zuwa Bikin Hashim (Qanin su Ma’u da suke uba daya) anyi abubuwa da yawa Gombe ban samu leqowa ba”Goggo ta fada, da haka sukayi sallama ta kashe wayar bata ajiye ba ta dannawa Addah Fatu kira. Itama lafiya lau suka gaisa tayi mata barka harta bawa Amirah waya suka gaisa da Goggo tayi mata sannu sannan ta kashe wayar ta maida hankalin ta kan Asma’u da tayi kinini da fuska dan tasan seta mata maganar qin gayawa Dada tafiyarta. “Wato Ma’u bazaki chanza ashe, wai ni shin Nafi ce tayi miki kishiya ko Bashir da zaki bi ki qullaci baiwar Allah ki ringa gaba da ita. Sehi wanda ya miki laifi kina zaune qalau dashi amma kina raina uwarsa” “Ni wallahi Goggo ban rainata ba me nake mata? Duk wani girma da ya kamata in bata ai ina bata to me ake so kuma nayi” “Oh kina ma da bakin mayar min kenan, yanzu ina bata masan kin taho nan ba kin kwaso mata jikoki har shida kin biyo wannan hanyar bata sani ba, ba fata ba idan wani mugun abu ya faru kuma fa sedai kawai suji sama”. “Toh ni yanzu Goggo ai ba haqqi na bane na gaya mata Danta ne ya kamata ya sanar da ita tunda ai ya sani da izininsa muka taho ai” “Haka ma zakice, to maza ki kirata yanzu a waya ki bata haquri kuma kodan gaba ki kiyaye kar irin haka ta sake faruwa” Goggon ta fada. “Dan Allah Goggo karki tilastani yin wani abun kuma dan kinsan bazan bijirewa umarninki ba, wane kalar haquri ne banayi, tunda Bashir yai aure sau daya na taba daga waya na kawo miki qarar sa akan yayi mun wani abu ai badan baya yimun din bane dan kince mun naje na shanye komai nayi haquri ne. Bazan iya ci gaba da alaqa dasu ba abinda ya zama dole zanyi amma wallahi na yanke duk wata alaqa ta baya da kika sani tsanina dasu ga yar uwarsu nan se tayi musu abinda suke ganin ni bazan iya ba”. Ta qarasa maganar hawaye na sakko mata Ta rasa me Goggo take so ta zama, a zatonta kowa irinta ne me tsananin hakuri, yakana da dauke kai akan komai? Ko kuwa duka maza kalar Mazajen data zauna dasu ne masu Adalci da sani ya kamata? Sannan kowane yayi dacen kishiyoyi na qwarai da dangin miji na gari. Sun fa qare tuni irinsu amma ita Goggo bazata gane wannan baudadden zamanin da muke ciki da ko cikin yayan da mutum ya haifa yake nuna banbanci dan daya yafi daya wadata, Namiji yake fifita buqatar wata mace akan wata saboda alaqar jini, sannan surukai suke zabar jinsu akan sauran surukai da suke baren su. Ita Dadan ai da bakinta tace mata Dama sun dade suna son dorar da zumunchinsu kuma ta hanyar hada auratayya ne kadai haka ze yiwu ko to gashinan sun hada ta kuma janye ta basu guri suyi yanda suke so se kuma ace seta cusa kanta cikinsu ina sam fa bame yuwuwa bane. “Toh yanzu menene na hawaye kuma daga magana” Goggo da jikinta yayi sanyi ta fada ai kamar Asma’u na jira kuwa ta fashe da kukan gaske harda sheshsheqa. Haka sukayi zukudi duk suna kallonta ranau babu dadi musamman Goggo, seta janyo Asma’un jikinta tana cewa “Kiyi Haquri nasani ba’a kyauta miki ba, ba’a miki daidai ba kuma badan nafi son su nake cewa kiyi haqurin ba Aa sedai ina so ki rabauta da ladan da Allah ya tanadarwa masu yinsa. Idan kika jure kikayi haqurin idan ma sun zalince ki ko anan ko acan se Allah ya saka miki amma kiyi shiru ki dena kuka dan Allah”. Dakyar ta tsagaita kukan tana ci gaba da share hawayen dai dai Innawuro ta shigo dakin. “Ashsha Maryam me yasa kike haka duk sanda yarinyar nan tazo se kin saka ta kuka dan Allah menee haka” Innawuro ta fada tana janye Ma’un gareta kafin taci gaba da cewa “Nasan zancen daya ne akan mijinki da danginsa, Duk abinda suka miki na cutuwa kar kiyi shiru Asma’u kiyi magana ki kwaci yan cinki, ki tsarkake zuciyarki kar ki nufi kowa da sharri kar kumaki bari su raina ki da sunan wai kina da haquri ko ita da take gaya miki hakan saboda Allah be jarabceta da irin wadannan fitintunun na zamani bane shiyasa take ganin kamar kowa irin zaman ta yake yi. Share hawayenki dan Allah karki ragawa duk wanda yace ze taka ki ki rama kinji Ma’u”. Dadi kalam Innawuro suka mata ai kuwa ta share hawayenta aka dauko wata hirar daban. Suna zaune Sauda da Maimuna Yaran Innawuro sukayi sallama sunzo wa su Ma’u sannu da zuwa nan suka shiga hirar yaushe gamo dan dama Saudah qawarta ce sosai. Se yamma suka fita tare dasu Saudah sukaje gidan Hamma Isah Babban Dan Innawuro matarsa ta haihu suna gidan a ka kira waya aka fada. Washe gari kuma suka fara zaga dangin Goggonsu ta ko ina sune har Mambila daman haka sukeyi, basu fiya samun damar zuwa ko yaushe ba amma duk sanda suka zo se sun zaga ko ina sun gaisa da dangi tareda kai musu abun arziqi hakan kuwa ba qaramin dadi yake yiwa yan uwan Goggon dadi dan ko basu kai musu komai ba zuwa a gaisa din kadai ya wadatar. Mu dawo Gombe 😂😂 Amirah na ci gaba da jinyar jikinta da kuma shirye shiryen shagalin sunan data rantse seta yi dukda haryanzu basuyi maganar da ogan ba amma jira takeyi da an sallamo baby Iman, ita kanta Addah wannan karon tace mata ta haqura gaba inda rabo se tayi kudin da ze bata se suyi wata hidimar dasu amma Amirah ta qeqashe qasa Allan fir se tayi. A cewarta haka kawai duk qawayenta tana gani in sun haihu yanda ake raqashewa kamar biki sannan ita ace kartayi wallahi ita ma se sunci uwar sabada kowa yazo ayi bushasha asan itama fa me kudinnan take aure se kuma Addah tace haka ne fa toh suyi kodan ma a maido musu da bikin gudummawar da sukayi. Ranar Talata da daddare lokacin data tabbatar yana gida ta danna masa waya dan tana so ya bata kudaden da zata siyi kaya ta bada dinki ga kuma shirye shiryen suna. Bashir na zaune a palour yana shan Tea da cake gaba daya dauriya yakeyi amma zaman kadaicin ya isheshi gidan ya masa wani wawakeke saboda babu Ma’u a ciki ji yakeyi kamar ya kirata yace ta dawo. Abinci kansa se kame kame yake in yunwa ta ci shine dole yake zuwa Restaurant yaci gaba daya besan me yasa wannan karon dan girke girken data saba masa ta saka a frizzer idan zatayi tafiya irin haka batayi ba, ya saba da sedai ya bude ya dauko yayi microwaving yaci to yanzu ko miya ce kadai itama ta qare dan Ma yayi dabarar sakawa a kunna wutar gidan bayan sun tafi wancan ranar daya tuna da abubuwan zasu baci gidan yayi wari dan haka ya saka aka karbo spare key na gidan a Estate Management Anty ta shiga ta qarasa kashe musu duk wani abu da ze iya kawo matsala aka bar frizzer. Yana cikin tura Cake din Wayar Amirah ta shigo ya harari wayar sannan ya daga a dake dan ya san labarin gizo baya wuce na qoqi, indai Amirah ta kira shi to ko tambayar kudi ko qorafi in yana son jin yanda suke sedai shi ya kirata. Bayan sun gaisa se duk sukayi shiru, yanayin dataji miryarsa ba walwala tasan dakyar in zata samu yanda take so amma haka ta daure taja numfashinta tace “Abban Iman dama naji shiru ne baka ce komai ba akan siyayyar kayan Iman da nawa kasan wancan da ka bani unisex muka siya na amfanin farko farko”. Seda ya mula sannan cikin dakewa dan karta kawo masa wani wargi yace “ke yanzu kayan me kuma kike magana kina fama da kanki?” “Kayan barka mana” ta fada itama tana dakewa. “Ni babu kudin wasu kayan barka da zan baki abinda nake dashi na bawa su Dada zasu hada da na gurinsu a siya wannan kayan Al’adar data ce na zata ma sun kawo muku” “Basu kawo ba inaga se gobe” ta fada a cukule dan ba haka taso ba yanzu ma sune zasu siyo kayan aka san irin wanda take so? Sannan itama nata duk se sun gama gane wa kenan kafin tayi kwalliyar gaskiya bazata yarda ba sedai ya bata ko kudin Lace daya ne da zatayi kwalliyar Suna dashi dan haka ta gyara zama tace “Toh shikenan amma dai se ka bani na siyi wanda zanyi fitar suna dashi danne kamata kowa ya gani ba sena saka”. “Suna wane sunan kuma” ya tambayeta da mamaki dan dai yasan ai shekaran jiya akayi radin suna ko? “Taron suna mana, idan an sallami Iman dole zamuyi tunda ai na farko ne kaga”. “Karki kuskura wallahi idan bakiji tausayin kanki da jikinki ba to kiyi ke kadai amma ko da wasa karki sako mun ya a ciki ke ko yan barka ki ka ringa bawa yata aka jagwalgwalata se ranki yayi mummunan baci wallahi bare har ki tara mata hayani ya akai. Ke yanzu ko lafiyarta qalau ma ai kya dagamun qafa kodan kashe kudin da nayi a Asibiti kice ba se kinyi wani taro ba bare yarinyar har yanzu kina ganin yanda take”. Seda ta tunzura baki kamar yana gaban ta tace “ to kowa ya haihu ana suna se ni ace baza’ayi nawa ba nidai se nayi gaskiya” “Allah ya baki sa’a” ya fada tareda kashe wayar, ya fuskanci so take ta qure shi seya saita mata kwakwalwar ta sannan zata dawo kan hanya. Allah ya bata ikon yin taron sunan tabbas seta gane waye Bashir kuwa. Amirah Hararar wayar tayi harda murguda baki tace “Dan rainin hankali wallahi se nayi kuma seka bada kudin, naga matar ka duk haihuwa ai setayi suna na Alfarma sanda ma baka dashi bare ni yanzu dole ma ka nemo su ka bani. Labarta wa Addah komai tayi tace ta rabu dashi ze bayar bari dai a sallamo yarinyar ai taji Likitan yace Alhamis ko Juma’a zasu iya sallamar su ko, haka sukaci gabada tsare tsaren su. Washe gari gurin goma na safe Suna zaune a palour tareda yan gidansu da suka sake zuwa dubata harda kishiyoyin Addah dukka biyun da matan yayyenta kamar aike sega Sallamr Dada ta shigo Naziru da Fainusa da Ihsan na biye da ita da akwatuna guda biyu ga kuka saitin baho da Qaramin gado me net. Nan suka shiga musu maraba suka zauna aka gaisa kafin Dada ta kalli Addah tana cewa “Addah ga kayan barka nan nace dai ya kamata a kawo tunda al’adace gashi munyi sa’a ma yan gidan nasu suna nan. Addah baki har kunne nan aka shiga zuge jakun kuna ga kaya nan tabarakallah komai yaji Babbar kayan jaririyane tsala tsalan riguna da sauran tarkacen kayan baby na yan gayu seta tsakiya kuma kayan Amirah Atamfofi guda biyu Madam Getzner daya se Laces masu kyau suma biyu kayan da gani kaf kasanba qanana bane harda mayafi kalar lace daya da jaka da takalminsa. Amirah na nade akan kujera Lace din da aka hadowa da takalmi da jaka ya tafi da ita amma kuma batajin zata saka tunda mutane sun gani. “Gasunan dana gurin Bashir da gudummawar yan uwansa dukka aka hada mukayo siyayyar” cewar Dada. “Kaya sunyi sosai Allah ya qara arziqi yasa lafiya ta kashe, Se ki fito da na gurin ku kema su gani ko Fatu” Inna Gaji dake faman daga kaya ta fada. “Fatu ai se ku fito dana ku ko tunda gasu su gani” ai Addah ji tayi kaman ta kwadawa Inna Gaji mari wannan tonon silili da take neman yi mata a gaban kishiyoyi sun kuwa zuba ido da kunnuwa suna jira suji me za’a ce dan Al’adar gidan su haka akeyi da an kawo kayan gidan miji suma zasu fito da masu a hada amma ita ko pant bata siya ba. Rasa ta cewa tayi dan haka ta shiga kame kame tana yaqe Dada ta taimaka ta kwaceta da cewa “kai se kace wani abun bare ai bamu raba daya biyu ba duk gasunan ai na dangin uwa dana miji kune dai zaku fito da naku yanzu dangin uba” tayi maganar cikin sigar wasa akabat Addah da sauke ajiyar zuciya da yaqen dole. Dada bata jima ba tayi musu sallama ta fita Addah tabi bayanta. “Kai Nafi kin ceceni wannan shegiyar Gajin dason qure mutum haihuwar data zo lokacin ta beyi ba ina naga ta siyan wasu kaya ga wannan lalura” “Hakane” Dada ta bata amsa. “Yauwa dama yau nake so nazo muyi maganar taron suna da za’ayi idan an sallamo yar, kin san yanzu se ya zama abin magana idanba’ayi ba fa” “Wace irin magana kuma Addah bayan kowa yasan halin da uwar da yar suke ciki, dan Allah kibar wannan magana Allah ya kaimu gaba ai ba gamawa tayi ba se ayi”. Cewar Dada “Kiji ki Nafi da wata magana to in kin manta bari na tuna miki Binta ba bakwainin kika haifeta ba(Babbar yarta) kuma haka muka shirya taron suna akayi”. “Amma Addah bazaki hada zamanin Binta dana wannan yarinyar ba, Binta a sannan ba ma waye da zuwa Asibiti ba qarewarta a gida na haifeta yanzu kuwa abu ko da anyi shi babu matsala tunda zamani yashiga cikin abubuwa koya kika kuskure se kiga an samu akasi azo ana dana sani nidai a shawara ku haqura nasan kuma shina Bashir din baze bari ayi ba”. Dada ta sake fada ranta fal takaicin Addah. “Wallahi se Anyi jikar tawa ta fari kuma takwarata kice bazanyi suna ma baqin ciki ma kikemun kenan ko” “Wane irin baqin ciki kuma Addah nima ai jikata ce ko ban haifi Bashir ba” “Toh in ma dai hada baki kukayi kedashi yace baza’ayi ba tun wuri ki gaya masa wallahi suna ba fashi ya lalo kudade ya bata da zatayi hidima in ba haka ba rai ya baci” tana gama fadar haka ta juya fuuu tayi ciki. “Dan Allah Dada muje wallahi ko Yaya ya yarda bazasuyi sunan ba ai dai ni zece nabada kudin ko zamu gani” Naziru ya fada yana huci, haka suka shiga motar suna tafe shida Fainusa suna debewa Addah albarka Dada dai bata iya ce musu komai ba gaba daya ta tafi tunanin meke damun Addah a rayuwa ne. Su yanzu inda hankali ko cewa akayi suyi ai sace Aa amma har tana rantsuwar ae sunyi, to wannan karon zata ja itama bazata takurawa Bashir ba kuma ko sunyi galaba akan sa ya yarda seta hana, zata nuna mata bafa tsoro yasa take mata biyayya ba. Allah dai ya mana maganin abinda yafi qarfin mu. 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 WATA KISHIYAR 🥰👹 (ALKAHIRI CE KO SHARRI) 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 Na Maryamah_Mrs AM (Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah) Page 16 Ranar Juma’a Bashir ya dawo Gombe kuma ranar aka sallamo baby Iman, Bashir da kansa ya dakkota bayan da ya dawo dan daman shi ya hana likitan sallamar su akan se yadawo saboda matsawar da Addah tai masa akan zancen shagalin suna. Amiran bata daddara ba washe garin randa sukayi maganar seda ta sake kira ya kuwa yi mata tatas dan dama sunyi waya da Dada ta gaya masa yanda suka kwashe da Addahn dan haka ya qara tabbatar mata da wallahi ko sisin sa baze bayar ayi wani suna ba idan bata gode rai da lafiyar da Allah ya basu ita da yar ba ta godewa Azabarsa. Ai kuwa itama Addah batayi sanya ba ta karbe waya ta masa wankan tsaf ta kuma sake tabbatar masa fa taron sun ba fashi. Shekara da shekaru tana rabar da kudin Barka da biki, haka auran Amiran kaman na munafukai basu barta tayi shagali ba yanzu ma a haifar mata jika suce Aa, to kuwa bazata sabu ba shidai ya mata shiru harta qaraci kumfar bakinta ta kashe ya kuwa rangadawa Amirah text din gargadi tunda ga ranar ma be sake kiranta ba idan ma ta kirashi baya dauka se yau Juma’a daya dawo garin suka hadu. Yaso ma da ya tafi ya karbo yarinyar shi kadai sedai kuma ya tuna Amiran na buqatar a karanta mata yanda zata kula da yarinyar yasa yace ta shirya su tafi se gata ita da Hajia Addah aka shige mota. Sau goma suka hada ido da Addah se sun jefi juna da harara ita da Bashir can dai da abin ya isheta tace “Bani kake harara ba Bashir Uwarka Nafi da Amadu su kake harara mara mutunchin kawai, kuma duk baqin cikinka suna ne se munyi se dai kayi bindiga ka mutu”. Kici kanki be ce mata ba har suka je Asibitin, sosai likita yaja kunnensu akan kula da Iman, Banda wanka a tsundumata a ruwa, suna tsaye ya saka Nurse ta kwatanta musu yanda za’a ringa wanke mata jikin shima ba kullum ba musamman yanayin garin sanyi ya kankama. Sannan ya dora musu da bayanin in so samu ne mamanta kadai zata ringa daukarta kar a jagwalgwalata su tabbatar kuma ko yaushe tana cikin dumi kar ake fitar da ita cikin iska ko sanyi a kula da kayan da za’a ringa saka mata kuma. Sallama sukayi suka tafi bayan ya basu ranar da zasu dawo ganin likita. Bashir be yadda ma an dauke ta a hannu ba cikin Baby carrier daya siyo tundaga lagos ya sakata ya dauka Addah ta hau salati da salallami wai ya saka ya a kwando to duk bala’in sa dai ko mayu ne su se ya basu yar in sunje gida tunda ba da ita ze ringa yawo ba, shida be tankata ba. Seda ya ajiyeta dakyau ya maqala belt din ko ina sannan ya shige ya tada mota har sukaje gida kuwa Addah bata saduda ba se sababi takeyi. A gidan ma suna zuwa da kansa ya bata feeder ta fara sha dan bottle feeding suke yi kafin ya bawa Amirah taci gaba da bata yana tsaye, seda ya tabbatar tasha yanda ya kamata ya dagata kamar kwan da baya so ya fashe ya sakata a kafada tayi gyatsa kafin ya kwantar da ita a dan gadonta. Seda ya dauketa hoto a wayar sa sannan ya juya. Kallo daya yayiwa Amirah dake doka uban Murmushi saboda ganin irin tattali da kulawar da yake nunawa yarinyar, ta san yanzu ko Albarkacin Iman seta qara matsayi a zuciyarsa shi kuwa gogan tsaki ya buga ya fice daga dakin dan haushinta yake ji. Yana fita Addah da jama’arta suka duru daki ganin Baby, kamar me tattaro kaya ta zura hannu zata cukumota Amirah kuwa tayi caraf ta riqe tana cewa “Haba Addah bakiji me likita yace bane shine zaki kawo mata wannan cafkar ai seki ballata”. Suka kwashi salati ita da jama’arta kafin ta fara masifa tana cewa “Eh lallai yanzu na yarda ba iya Bashir ne tanbadaddenba harda ke, yo in banda tanbada ni uwarki zaki hana na dauketa har ni zaki gayawa kar a karya miki ya, to da ban haihu ba yau se nayi kuka kiji da jinki seda na haifi Goma na binne takwas gaku nan biyu a raye harke ma kinyi yar kanki zaki nunamun sanabe da iyayi”. Inna Gaji ce ta ceci Amirah tace “Ba haka bane Fattu yanzu dai barta mu kalla daga haka dan Allah abunda in muna da tsahon rai watarana da qafarta zata taka ta hau jikin duk wanda take so” haka aka lallaba Addah kowa ya leqa yarinya dake baccinta masha Allah kyakykyawa da ita kowa se yace ta kwaso kaman nin yayan Ma’u. Addah dai bata haqura ba seda ta daukota Amirah na kumbura baki tana komai, “Oh ni Fatu wannan abu kamar yar kyanwa, kwanta karna manta Dan mutum ne nayi jifa dashi” ta fada tana maida yar cikin Gadonta kafin ta harari Amirah data cika baki da iska tayi qwafa ta fita daga dakin. Bashir kuwa yana fita Part din Ma’u ya bude ya shiga, ya zuqi qamshin da a gurinta kadai ya sanshi dan gidanta na nan dana Lagos qanshi su daya duk kuwa da bata ciki ya rigada ya kama Gurin se a sannan ya tuna dakin masu jegon ma daya shiga kodan Air freshener beji ba bare Turaren wuta. Wanka ya farayi ya yi sallar Isha da shafa’i da wuturi sannan ya shiga kitchen ko ze samu abinda ze ci tunda can basu bashi ba. ya yi sa’a kuwa cikin Freezer ya samu farfesun kayan ciki dama mutuminsa ne nan da nan ya dumma ya dauki bread ya hada tea ya fara ci. Seda ya kusa cinye wa naman suna ya fado masa a rai, kunsan mutuminku ko kura Albarka nan da nan ya qarasa cinyewa ya dauki waya ya dannawa Amirah kira dan baya so ya koma su hadu da Addah. Amirah na cikin waya da Tailor data bawa dinki dan tuni ta kai musanyen lace din da aka sako mata na barka ta karbo wani ta bada dinki da sauran kayan da zatayi amfani dasu a lokacin ma tailor yana gaya mata ya gama ne gobe ze kawo ya karbi bakance din kudinsa, ganin kiran Bashir yasa ta cewa Tailor tana zuwa ta amsa wayar da fatan Allah sa Zancen sunan ze mata. “Kizo ina son ganin ki, ki taho mun da nawa kason Naman” ya fada a taqaice. Seda cikinta ya bada qulululu dan bata taba zaton ze tambaya ba. Tas suka rabe naman nan ko gutsiren hanji beyi saura ba ita yanzu me zata ce masa? Ai kuwa beci ta manta ba aduk sanda Anty Asma’u ta haihu kasawa yake ya tsare se an cire masa nasa kason, tana kuma yawan jin Asma’un na qorafin daga baya se ya biyo wanda aka aje mata ya cinye ta rasa wane irin so Bashir yakewa Nama a rayuwarsa dukda gashi yanzu ita sun hada sun lamushe. Haka ta zari mayafin ta ta fita tana taraddadin me zata ce masa, a qofa taci karo da Addah ta dawo daga raka baqin ta. “Ke kuma ina zaki fita a daren nan da danyen jego” ta fada tana kallon ta ganin ta da mayafi. “Yaya Bashir ne yake kirana” “Oh to se kin dawo” Addah ta fada tana rabeta zata wuce se Amirah ta ruqota tana rartaba ido. “Ya akayi se wani qifta ido kike kamar an kama Kwarto?” “Addah wai cewa yayi in taho masa da kason naman sa na suna” cewar Amirah. “To se ki tafi ai” Addah ta fada tana son wucewa ciki. “Kin manta Addah ya qare fa babu ko diddiga yanzu me zan ce masa” “Ke dallah matsa ki ban guri se kice masa ya qare ko kice an hada an kaiwa Nafi bashi kenan ba”. “Addah wace Dadan kuma kin manta itama fa baki basu ba wanda aka ware musu bashi kikace a bawa su Hajia Salamatu ba da suka Zo barka kika ce ta rabawa yan group dinku?”. Se Addah tayi kasaqe tace “haka ne kuma fa, tab di amma fa mu ma munyi gwari wallahi to yanzu ya za’ayi?” “Nima ban sani ba” Amirah ta fada tana marairaicewa. Ta tabbatar laifin cinye nasa kadan ne akan idan yaji ko su Dada ba’a aikawa dashi ba. “Kinga yanzu kije kawai in ya tambaya kice kin manta, idan ya biyo sahu ni kuma zan ce masa Muzuru sun shigo sun cinye bamu sani ba se in nuna masa duddugar bashi kenan ba, shima ai yasan dangin ku da yawa ya wani se miki rago biyu ai yayi kadan” (😳) tana gama fada tayi ciki abinta, nama dai sun cinye ba kuma a isa ace su biya ba. Amirah kuwa jiki a mace ta shiga palour, ga abinda yake a gabanta amma ta bige da kallon qurilla taga me aka chanza a ciki i lai kuwa taga sabuwar Kantamemiyar Cinema Tv bango guda da Asma’un ta saka kana ganin muatanen ciki kamar zasu fito, sannan ta chanza Dining dinta ba na da bane ga wasu hadaddun Kwanuka akai shikansa Turkish Centre carpet din ba wancan bane kamar. Kallonta Bashir yake ba laifi ta sace amma bata gama dawowa daidai ba ga cikinta nan haryanzu da girman sa Allah dai yasa kar tayi tumbi dan a duniya ya tsani tumbi a jikin mace kuma da Allah ya taimakeshi Ma’un sa haihuwa Biyar amma har yau bata da tumbi ko dan tana kula da jikinta ne oho? yanda yaga Amiarn tana kalle kalle yasa ya girgiza kai kawai kafin yace “Malama ko zauna mana kin tsaya mun akai. Zama tayi kan Kujerun da suka dade da tsole mata ido ta kuma quduri niyya itama fa se ya mata irin su yanzu ko ga qarin Dining ma da TV duk irinsu take so itama a siya mata. Sake gaishe shi tayi ya amsa hankalin sa akan Tv, jin shiru bata miqo masa komai ba ya sakashi kallonta yace “Ina naman” dan fa shi har ya dakko a exotic drink coconut and pineapple dinsa da ze hada ya kora nama seta hau kame kame tana sosa kai tace “uhm uhm daman” Idonsa akanta yace “malama daman me kin tsaya kina wani kwana kwana in ma wani abu zaki tambayeni bani dashi ki bani namana ki tafi daman kiran da na miki kenan”. “Ai naman ne ya qare” ta zabi da ta fada masa gaskiya kawai komai ta fan jama fanjan. “Ya qare?” Ya tambaye ta, se daga masa kai alamar Eh dan ta kasa kuma bude bakinta saboda kallon da yake mata. Daurewa yayi ya danne bacin ransa kafin yace “ toh kun kai gidan Dada kun bawa Ma’una nata ko?” “Ai se tafi da rikicewa, kai ta juya masa alamar Aa cikin tsawar da seda ta zabura yace “Malama ki bude baki kiyi mun magana ko” Jiki na rawa tace “Ni wallahi ban sani ba kasan bani da lafiya su Addah ne suka raba ban san kota kai musu ba dan ni wallahi ko yanka daya banci naman ba”. Ya tabbatar basu bawa ko daya daga ciki ba kenan, dan haka kawai yace ta tashi taje kafin ya jawo wayarsa ya danna kiran Dada yana saita fushinsa. Bayan ta daga suka gaisa, tambayarta yayi an kai musu naman suna kuwa tace Aa. “Kar kace zakayi magana Bashir nama dai Allah na tuba kullum ai muna ci, ba wani Abu kasan yan gidan su nada yawa kowa ze so a qulla masa” Dada ta fada da son kwantar masa da hankali dan tasan Bashir da Nama. Seda yayi kokawa da bacin ransa kafin yace “Amma Dada raguna har biyu manya ne fa ba wai qanana ba su soya su cinye ko yanka daya su kasa kai wa uwata idan ni da na siya banda mutunchin da zasu bani sannan ga Ma’u da yara gaba daya suna cikin gidan a soya duk su kasa basu”. “Kadaiyi haquri” Dadan ta sake fada kafin su kayi sallama. Ransa a bace ya shiga dakinsa ya kwanta se kuma ya ja wayar ya kira Asma’u dan yau duk basuyi waya ba. “Ran Alhaji Bashir Baban Ali ya dade” ta fada cike da nishadi dan hirar sa suke yi da Yaya Bilki ya kira. Murmushin da beyi niyya bane ya kwace masa kamar wanda ake watsawa ruwan sanyi yaji zuciyar sa na huce wa, muryarta kadai ta wanke masa bacin ran Naman suna seya gyara kwanciya yana cewa “Ba wani nan bayan kunyi tafiyar ku ma kin manta dani inaga sena biyo ku sannan zaku dawo” “Haba dai kwatakwata fa kwanan mu biyar yau cikin weekend muke saka ran dawowa ai” Asma’u ta fada. “Shikenan ma kinga da kun dawo se mu wuce kawai, na gaji da zaman gwauranta kan nan”. Dariya tayi kafin tace “oh kana Gombe kenan” “Eh na shigo dazu, an sallamo Fatima yanzu tana gida”. “Masha Allah Allah ya raya mata ya bata lafiya, ashe Addah aka saka”. Da “Amin” ya amsa ya share tambayar ta ta. To me take so yace mata in dai ba son tada zaune tsaye kuma ba. Yaran ya tambayeta tace sunyi bacci suka dan taba hira kafin sukayi sallama bayan sun gaisa da Yaya Bilkisu. “Kinji mutuminki nace ashe Addah aka saka yayi kamar beji ba” Asma’u ta fada bayan ta ajiye wayar. “Kema da neman magana kike wallahi me kike so to yace miki?” Cewar Yaya Bilki “Me kuwa zece daman kinga ai ta ta uwar tafi tawa a gunsa shiyasa ya saka mata sunanta”. “To da be saka ba dama Addini ne yace dole ayi ko kuwa da ze zama laifi” cewar Goggo da shigowarta kenan. Muqus Asma’u tayi, dan tasan idan ta tofa wata fada ne zata sha ita kam se taga kamar Goggo tafi son Bashir a kanta ma wani lokacin, bargo taja ta rufe har kanta hankali tacewa Yaya Bilki “idan ta fita ki gaya mun” jin Goggo ta ci gaba da magana. Seda Goggon ta fita kuwa ta bude tana cewa “Ita Goggo bata san takaicin da ake qullawa mutum ba tayi ta rufeshi da fada, wai fa kinji ma cewa yake idan mun koma se mu bishi mu tafi ni nama fasa tafiya Sunday din sena tabbatar ya koma tukunna. Sati uku mukayi dashi munci biyu se na qarasa sati na wallahi dan har Bauchi nake so Naje wa Alawa sannan naje Jos ma”. “Ai kuwa da ba kwana zakiyi a Bauchin ba nima da naje Alawiyya har tayi mitar ta gaji ban taba zuwa ba” inji Yaya Bilkisu “Kai haba dai amma baki kyauta ba wallahi ina Gombe ina Bauch” cewar Asma’u “Ba haka bane kinsan yawan ci abin zuwan haihuwa ce to kusan tare muke haihuwa kota rigani kona rigata amma daya baya Arba’in to sedai mu hadu a gida”. “Eh to hakane”. Hira suka ci gaba dayi kafin sukayi bacci. A Gombe kuwa washe gari Bashir ga haushin cinye masa nama gana tambayar kudi da Amirah tazo ta fara masa da sassafe, buyagin gaske yai mata ya faffada mata maganganu son ransa qarshe ta fita tana kuka da dana sanin zuwan daman Qawarta Husna ce ta tsara mata yanda zataje ta same shi gashi babu biyan buqata se baqin ciki ta kwaso tana shiga dakin ta kuma ta tarar da Addah ta cika baho da ruwan zafi ta tube Iman tana shirin tsumbulata tai mata wanka. Da mugun gudu Amirah ta tare ta hannun ta ya shiga cikin ruwan da sauri ta cire jin zafin ruwan ta yayimi towel ta nade Iman tana kallon Addah data saki baki da Hanci tana kallonta itama. “Dan ubanki saboda zan mata wanka shine kika buga wannan tsallen kamar wata yar ball kika kwace ta? So kike a bar ya mace ba wanka kusan sati biyu da haihuwa tayi warin qashi To wallahi ba da ni ba dole a wanke mata dattin mahaifa”. Ita dai Amira bata kula ta ba, se jijjiga Iman da ke dan kukan da ko muryar ba’aji dakyau take dan ta firgita, jin Addah bazatayi shiri ba yasa tace “wai Addah baki ji me likita yace bane gaskiya idan ba zaki mata irin yanda yace ayi ba ki bar wankan kawai zan nunawa Inna Gaji ta ringa mata. Haka kawai idan wani abun ya sameta ai nice da Asara kuma ji ruwan da kika saka kamar wanda zaki fige kaza”. Salati Addah ta debo ta dire kafin ta shiga auno mata ashar tana cewa “kiji mun yar banza ni kike shatawa layi akan wannan magen dan bazance mutum ba to kinyi da yar halak in na sake taba ta kice shegiya nake” ta mike tana gyara zani tana ci gaba da banbaminta. Inna Gaji da shigowarta kenan ta tambayi ba’asi Amiran ta mayar mata seta dubi Addah tace “Wallahi Fatu kin fiya tada zaune tsaye in ba haka tunda ga abinda likita yace se kibi na dan lokaci ne ko cewa akayi zata dawwama ba wankan ne se ki mata yanda suka ce. Yanzu kizo ki zunduma musu ya a ruwa bayan naji ance tana da munoniya wani abu ya faru kinsan dai wannan sirikin naki manta komai zeyi wallahi har ni nan da babu ruwa na qila se yayi qarar mu ai wannan ruwan yayi yawa...kaii” maganar ta katse bayan data tsumbula hannu a ruwan, seta kalli Addah ido waje tace Fatu kice kisan kai kika shirya wannan ruwan ko uwarta bata wanka da me zafinsa shine zaki jefa wannan tatsitsiyar yar a ciki? To nidai inaga watan tafiyata gida ya kama dan bazan iya zuwa polisteshan bada sutotimen ba”. Addah da tayi tsilli tsilli dakyar tace “nifa ji nayi jikin ba kwari shine nake so na gasata jikinta ya hade amma tunda banyi abin kirki ba shikenan kuda kuka iya se ku mata” fuu tayi waje. Wunin ranar haka ta yini mita duk wanda yazo seta gaya masa abinda Amirah tayi mata kuma dai kowa ita yake bawa laifi. Ganin dai dagaske Bashir baze bada kudin taro ba Addah ta shiga ta fita da abinda Baban Amirah da yan uwanta suka hada da bashin Jama’a duk ta ganganda za’ayi bikin suna. Kayan abinci dama ba matsala bane sunyi akan na Store dinta za’a diba ayi komai. Kaji kawai zasu siya se ruwa da lemo da kayan snacks se kuma kayan rabo da Amirah ta nace se tayi dan har ta kira me hoto yazo ya dauki Baby wanda za’a saka ajikin Jaka da Memo. Duk shirin nan basu gayawa Dada ba tunda tace bada yawunta ba balle Bashir da ya rantse ya kuma rantsewa baza’ayi ba shiyasa ma suka tsaida ranar Laraba bayan ya tafi litinan sannan zasuyi sunan. Allah kaimu ranar suna lafiya 😂😂😂 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 WATA KISHIYAR 🥰👹 (ALKAHIRI CE KO SHARRI) 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 Na Maryamah_Mrs AM (Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah) Page 18 Taro yayi taro dan kafin la’asar gida ya cika ya batse da mata kala kala se an bulowa suke. Tuni mata sun zazzauna kan kujerun da aka shirya an wangale get duk inda ka duba qawayen Amirah ne yan gayu sunci kwalliya da kuma manyan Mata Qawayan Addah data gayyoto daga gefe DJ nata sakin duma wasu na tattakawa wasu kuma suna cin abinci dan tuni an fara rabo. Shinkafa gata nan kala kala, soyayyoyar taliya, dambu, Alala ga dabgen kaji da na naman Sa ga Fura me kyau da aka zuzzuba a kofuna Zobo dasu kunan Aya da lemon robobi dai kaya masha Allah an tanadi komai harda gurasa suka siyo daga kano akayi bandashe me kyau se rububinta kuwa akeyi. Wuraren Uku na tana su Ma’u na tsaka da Hira Jafar ya kwankwasa kofar palour da suke ciki, seda aka bashi izini sannan ya shiga ya tsaya daga bakin kofa yana cewa “Mami ana ta Knocking na tambayi waye wai Anty Aisha ce ta gidan su Anty Amirah shine nace bari nazo na gaya miki kafin na bude”. “Tam jeka ina zuwa” ta fada ya juya yai tafiyarsa. Kamar bazataje ba sedai kuma ta miqe dan Ko ba komai tana ganin girman Anty Aisha amma fa batajin yau akwai wanda zata bari ya shigo mata daki a cikinsu. Sun saba in ana hidima azo a yi mata kaca kaca da guri a tafi a barta da gyara to an dena bakuma za’a sake ba. Har kuwa ta sauka qasan Anty Aisha na tsaye a bakin qofar. Dan kadan Ma’u ta bude qofa taja ta tsaya Anty Aisha data taho da niyyar shigowa ganin ta tare qofar se jikinta yayi sanyi. Gaisawa sukayi ta tambayi Anty Aishan ya taro tace lafiya lau se sukayi shiru gaba daya kafin Aishan tayi qarfin halin cewa “Daman nace ne bari nazo ki bada abunda za’a zubo muku abincine” “Lah ai kubarshi ma wlh nayi abinci da yake ina da baqi”. Asma’u ta tareta kafin ta fara qoqarin juyawa tunda maganar kenan se Antyn ta katseta tana cewa “Am nace dan Allah in ba damuwa ko zamu dan kawo wasu baqin mu su dan zauna anan can din ya cika wallahi” “Ai haka taro yake daman se haquri ba lallai mutum ya samu yanda yake so ba, se suyi haquri su zauna tunda abun nadan lokaci ne” garam ta rufo qofarta tabar Anty Aisha da baki a bude. Data koma saman ma tambayarta sukayi ya akayi “Wai baqi zasu kawomun nan” “Kika ce me?” Suka hada baki gurin tambayarta, se tayi yar dariya kafin tace. “Me zance kuwa in banda karsu zo, nifa na yanke alaqa se wadda ta zama dole ba se an san cikin ka ba sannan za’a maka yankan bayan? To muje baya baya kowa yayi ya tasa dan ba qara”. Cewar Asma’un “Allah ya rufa asiri dai amma dangin mijin nan naku basuda kunya wlh” cewar Zahra. “Waa ai ni baza’a fara wannan wasan dani bama wallahi ni naga qoqarin Maman Aliyu da batai musu hauka dan order ba wallahi ai sam mutanen nan basu san mutunchi ba” Rahma ta fada, ita dai Ma’u shiru tayi bata ce musu komai ba. Bazasu gane ba duk yanda za’a musu bayani idan ba kansu ta fada ba. Hirar su suka ci gaba dayi har aka kira la’asar suka tashi dan yin sallah. Yan suna kuwa Qarfe hudu daidai Aka sanar da fitowar Me Jego Hajia Amirah da ta cancada kwalliya da wani dan ubansun Leshi Dark blue da adon light Blue din zare dayayi bala’in karbar farar fatarta. Tayi kyau harta gaji komai Hassadar mutum dole ya yaba anyi mata lafiyayyar Fitted gown dinki ya fita ko ina das. Ga Goggoron da aka daura mata ya zauna das ya qara qawata kyakykywar fuskarta hannu da qafa ya dau Ja da Baqin qunshi ga Danqareriyar sarqar gwal a wuyanta da zobuna harda awarwaro Allah kadai yasan ina suka samo su. Rungume take da yarta da akayiwa Kwalliya cikin daya daga cikin rigunan Ma’u fara harda shawl din dan shima farine ta nadeta a ciki Qawayen ta na take mata baya suka shigo filin tuni DJ ya ware wusu WARRR. Seda suka rakata har mazauninta aka dauki hotuna sannan kowa ya nemi gurin zama. Bayan kowa ya nutsa DJ Fele da takanas suka dakkoshi tun daga Kano ya nemi da wata ta fito ta bude taro da bayanin maraba, Hajiya Hassana daya daga qawayen Addah ce ta fita ta fara jawabi kamar haka. “Dafarko munawa kowa da kowa barka da zuwa wannan shagalin suna na Yar Gata yarinya haihuwar dangi, muna fatan yanda aka fara taro lafiya a tashi lafiya kowa kuma ya koma gidansa lafiya. Muna qarawa yiwa kowa barka da zuwa” aka dauki tafi raf raf. Can na hango Addah bakin nan kamar ze tsage saboda fara’a taci wanka ta saka wata Hadaddiyar Atamfa ta manyan mata ga dauri an cakare se maraba takeyiwa baqin ta ranta fes ganin yanda suka amsa gayyatarta suka zo mata taron da yawa dukda a qurarren lokaci tayi gayyatar. Suna ya kankama tuni a ka shiga shagali ka’in da na’in, duk yanda Amirah taso kwakwume yar haka seda ta bayar da ita Dangi da qawaye suka ringa daukanta ana ta hotuna. Ba daukan yarinyar yafi damunta ba, sanyi ya riga ya kankama musamman lokacin da yake La’asar sakaliya ga bishiyun tsakar gidan suna ta rangaji suna qara yawan isaka sannan Get ma a wangale yake saboda yawan Jama’a. A fili fara’a takeyi amma zuciyarta addua take ta ja Allah ya rufa mata asiri a tashi taron nan qalau batare da wani abu ya faru ba dan se a yanzu take jin kamar tayi wauta a lamarin. Haka ta daure zuciyarta ta zage suna ta kwasar rawa ana videon tiktok da qawayenta da kuma daukar hotuna wasuma live suke video amma fa rabin hankalin ta na kan duk inda akayi da yarinyar. Biki fa yayi baki mata an zage DJ Fele na kada musu ganga suna cin uwar sabada, daga can cikin gida bayan da Amirah ta gama shiryawa zata fito, harta zuwa key din dakin Bashir a jakarta ta tuna da kayan rabon da zasu sallami baqinsu yana ciki. Gudun kar azo a manta har a watse ba’a fito da kayan ba yasa ta danqawa Anty Aisha akan da taga an fara haramar tafiya ta fito da kaya a fara rabo. Haka kuwa akayi ganin magriba ta doso yasa ta bude daki ta fara fito da kayayyaki tana bawa wadanda suke zaune a palour basu fita gurin kida ba. Kunsan mutanen mu da souvenir nan da nan fa akayo mata caaa yan uwansu ganin kamar zabe take tana raba kayan aiko suka duru dakin Bashir duk yanda Su Ummi suka so su hana be yuwuba tun kuwa kafin aje da nisa a garin kwatar leda wata ta kaiwa Murfin wardrobe naushi, abunka da me qashi daya nan take gilashi ya tarwatse 😂😂😂 mata aka debi salati. Basu dawo daga wannan tashin hankali ba aka samu yaran biyu daga ciki da suna shiga su kan mirror sukayi ganin kayan wasa suka kuwa shiga watso tsadaddun turarukan Bashir suna fashewa Tush a qasa, babu me jiran a ce masa ya fita sum sum suka fara ficewa daga dakin dan sun san sun tsokalo tsuliyar dodo yau amma dukda haka seda aka samu was masu son zuciyar da suka saci turare suka fita dasu. Tsilli tsilli Ummi da Anty Aisha sukayi ko wacce ta kasa magana, “Yanzu Anty yaya zamuyi?” Ummi ta fada tana rarraba ido dan tasan Allah ne kadai ze kwaceta a hannun Yaya Bashir idan yaji harda ita a dakin. “Ummi nima tunanin da nakeyi kenan, amma kinga samo tsintiya mu tattare tunda me afkuwa ta afku maji da abinda ze biyo baya”. Tayi Na’am da maganar dan haka ta fita ta dakko tsintiya da abin shara suka shiga kwashe kwalabe da gilasan bayan sun gama suka hado kan kayan rabo tas suka dire a palour, dakin Amirah Anty Aisha ta shiga ta nemi guri me kyau da ba wanda ya gani ta ajiye mata muqullin da niyyar idan ta tambayeta ta gaya mata inda yake bata tsaya ba ta hada kan yayanta sukayi gida dan bata san yanda za’a qare ba. A can filin kida kuwa bayan yaran mata sun gama nasu, nan kuma Manyan mata qawayen Addah suka shiga suma su zubda nasu galangalan din. magriba tayi amma haka suka ci gaba da buga ganga mata na rawa. Addah da jikinta har tsuma yake ta shiga zuge jaka da niyyar fito da sababbin kudin data yiwo chanji daman saboda liqi sedai kudi sukace dauke mu inda kika ajiye. Hankali tashe take sake laluba jakar, da kudin liqi da da wayarta data Amirah data karba ta saka mata a jakar ga uban gudummawar da ta samu ta tabbatar da qila har chanji zasu samu bayan sun biya basussukan da suka ciyo se gashi gaba daya babu su babu alamarsu. Wata Ashar me maiqo ta janyo ta dire tana zazzare ido kamar ance zata ga kudin ne a qasa, wannan shi ake kira da tashin hankali ba’a saka masa rana. Amirah ta hango da wasu mutum biyu sun nufi cikin gida da sauri ta shiga kwala mata kira amma ina qarar kida bazata bari ta jiyota ba har suka shige se kawai ta nufi get afujajan ta shiga jansa ruf ta rufe gida. Kwadon yana jiki daman hatta da key din da suka bude basu cire ba tsabar rashin hankali ko kidane yai dadi oho Allah dai ya rufa asiri ba’a samu wani ya zare ba da wannan tayi amfani ta garqame gida tsaf ta jefa muqulli a riga ta nufi gurin gangar DJ gadan gadan tana zuwa kuwa batayi wata wata ba ta fizge wayar inji kida ya dauki dif. A fusace yaron DJ ya juya da niyyar ganin waye yai musu danyan aikin se ganin uwar biki yayi ta riqe qugu tana kumbura tana sace wa. “Zoka mayar amma ka kashe kidan ka bani abin magana” Addah ta fada, shikuwa beyi musu ba ya maida waya ya miqa mata lasifiqa ya tsaya yaga ikon Allah dan dai daga yanayinta yasan ba lafiya ba. Juyawa tayi ta kalli mata da suka qame suna kallonta da jiran jin wani wulaqanci ne yasa aka katse musu cashewa suna cikin Warwarewa. Addah na haki kamar wadda tayi gudu ta fara magana tana cewa “nidai bazan ja doguwar magana, idan kin san ke kika kwashe mun kudi a jaka kusan dubu dari biyu kika hada da wayata ta dubu saba’in data me jego Me kyamara uku ni ban san kudinta na to ki fito dasu yanzu ko kizo ga jakar can na ajiye kin sanya salin alin ki maidamun komai ciki idan ba haka na rantse da abinda ze kashe ni daga nan se police station dan se an fito mun da kudina ni ba taron farin ciki na tara ba dan azo a sabautani ni ba”. Hayaniya ce ta tashi a gurin mata suka shiga duka jakun kunan su ai se kuji an yanko salati kafin wata ta dire wata ta dauka kan kace me guri ya rikece da surutan mata da yawa an yashe musu jaka tas suna can basu ankara ba. Hajia Mariya daya daga cikin qawayen Addah ta zazzage jakarta tas a qasa komai na ciki ya zubo ga tsabar kudi nan da wayarta harda qaton zoban gwal data saka taji ya dame ta duk suna ciki amma babu muqullin motar da tazo da ita. Hannaye biyu ta dora a hannu ta fashe da kuka tana kururuwar ta shiga uku. “Ni Mariya na shiga uku yau in koma in cewa Alhaji me? Be san na fito ba da safiyar nan Fatu kika azazzaloni se nazo sunan nan na dauko sabuwar motarsa sau daya ya hauta kafin ya tafi Lagos gashi yanzu an dauke shikenan na kade har ganye na” Hajia Mariya ta sake rushewa da kuka. Ai se akayi tsilli tsilli, masu kukan wayoyinsu da yan kudade sunji wadda akayiwa dungurungun yo satar mota a zamanin nan motar ma ta miji besan ta dakko ba ai abin ayi mata jaje ne. Nan fa guri ya rikice, ita dai Addah duk wannanba matsalar ta bace jira take ace ga kayanta tunda ta rigada ta kulle Get kuma ta qudiri niyya bazata bude ba se an fito mata da kayanta. Ta kallon wasu suka nufi Get da niyyar su fita suka jishi a qarqame nan aka sakeyo wa cikin gida ana ci gaba da cece kuce Addah kuwa tayi qememe duk yanda Aminan nata suke mata maganar ta bude gidan su fita amma taqi. Tana tsaye a nan Inna Gaji ta kwaso da gudu daga palour Amirah ta dire a gaban Addah tana haki. “Yawwa Gaji gara da kika zo ki tayani ganin wannan bala’i wai duk kudin cikin jakar nan da wayata data Amirah an samu wata la’ananniyar ta yashe ni ko na kulle gida babu wanda ya isa ya fita wallahi se sun fito mun da kayana”. “Yanzu kibar batun wasu kudi Fatu ga bala’in da ya fi wannan can a cikin gida yana jiranki muje” ta shiga jan hannun Addah seta bita kamat raqumi da akala suka shiga dakin. Qulululu cikinta ya bada sauti tareda murdawa kamar zawo ze kece mata taji lokacin da tayi Arba da yar jaririyar da ke kwance idanunta na qaqqafewa kamar me suma ga qirjinta na sama da qasa da sauri har wani wahalallen tari take saki a shaqe ba’a maji sosai Amirah na gefenta tuni Goggoro yayi ta kansa kwalliya ta jagale tana rusar kuka hannu aka. Habiba Kishiyar Addah ce tayi qarfin halin cewa a dauki yarinyar a kai Asibiti mana se a sannan ma tunanin su ya kawo nan da nan Ummi ta shiga kiran wayar Naziru tunda shine wakilin Bashir din amma se aka ce mata call waiting, bata haqura ba taci gaba da kiran wayar amma be daga ba. LAGOS Nigeria Wato ranar bayan Bashir ya tashi daga aiki se yabi wani abokinsa gidan sa saboda koya dawo gidan baya masa dadi. Suna zaune suna cin abincin da sukayiwo take away a hanya dan shi abokin bashi da Aure suna yan hirarrakinsu. Bayan sun gama Bashir ya dauki remote yana chanza tasha kafin lokacin sallar Magriba yayi su fita shikuma abokin wayarsa ya dauka ya shiga Tiktok dan shi ma’abocin duba Tiktok ne. Bashir na daga gefe lokaci lokaci ya daga kai ya kalleshi jin yanda yake dariya shikadai, sedai ya girgiza kai kawai yana mamaki besan me mutane suke ji ko gani a wannan Tiktok dinba. Yana yawan ganin Abokanan sa suna shiga suyi kallace kallacensu har Ma’u ma yana ganin tana shiga ta kalli video Girke Girke amma shi a shirme yake daukansa. Dukda sunce akwai abubuwan amfani amma gani yake rashin Amfanin yafi amfanin yawa ai. “Mata da bidi’a abarsu kawai yanzu suna ma ya zama biki kenan ji wannan ai wallahi bama ko wanne biki ba” Abokin Bashir din Musa ya fada yana nunawa Bashir video bayan yayi joining Live din da wata friend dinsa takeyi. Kallo daya Bashir yayi musu “yace Allah ya sawwaqa” ganin mata nata tiqar rawa abinsu. “Masha Allah amma mejegon tayi kyau nima fa mutumina Gomben nan zanzo ka bani wata yar fara haka na aura wallahi” Musa ya sake fada. Haka kawai se ya samu kansa da juyawa ya sake kallon wayar karaf idonsa ya sauka kan mejego Amirah tana kwaso shoki. Murza idonsa ya sakeyi dan ya tabbatar ita dince ko kama ce ya miqa hannu ya karbi wayar daga hannun musan daidai Live Video ya katse. “Musa bude mun page din yarinyar nan na gani” Bashir din ya fada. Se Musa ya saka dariya yana cewa “Kai mutumina biyu ne fa dakai tsalatsala ka barmu dai mu zero mu nema amma banda kai” ya qarasa yana miqa masa bayan ya budo masa page din Nabila Dikko qawar Amirah. Videon farko da tayi uploading kadai ya kalla ransa yai qololuwar baci, videon da aka mata ne bayan an gama mata makeup da Baby Iman a hannunta. Wayar ya miqawa Musan kawai ya zaro tasa Musa kuma ya bishi da ido ganin yanda fuskarsa ta nuna bacin rai qarara. Number Naziru ya kira ringing biyu ya daga. “Naziru me yake faruwa a gidan nan?” Ya tambayeshi. Naziru da daman yake shirin kiran Yayan nasa dan dawowarsa daga makaranta kenan Dada take gaya masa ana can ana taron sunan, ze kira Bashir din kuma ta hana dan haka ya karkace ya fara jero masa yanda akayi “Wallahi yaya taron suna sukeyi gida ya cika da mata harda me kida suka dakko tun daga Kano wai Feli sunansa kowa nadai manta sunacan dai sunayi wallahi ga sanyi ya kankama a Gombe kuma.....” “Kanaji ko, kaje gidan ka kulle qofar ta waje kayi tafiyarka kawai kabarsu” Bashir din ya katse Naziru jin zancen nasa yaqi qarewa. “Yes” Nazirun ya fada ransa qal dan dama yasan Indai Bashir ne ya san takan Tsiya aikuwa Kwado ze siyo qundumeme ya garqame su kuma baze bude ba se irin sha biyun daren nan gobe ma su sake zuwa suna. Be fadawa Dada yanda sukayi ba haka be bi takan Kiran da Ummi takeyi masa ba dan daidai lokacin ne suna waya Bashir. Machine ya hau dan yafi sauri bayan ya siyi garqamemen kwadonsa kamar me kulle kurkuku ya nufi gidan. A gidan suna kuwa bangaren su Ma’u sun sha hirarsu sosai har Magrib sannan driver Zahra yazo, sallama sukayi kamar karsu rabu Sannan Ma’u da Rahma suka rakota kallon matan da sukayi cirko cirko a tsakar gidan sukayi dan duk budirin nan basu san me yake faruwa ba suna sama abinsu kuma da yake sun rufe windows yasa basa jin qarar kidan sosai koda aka kashe ma abun be dame su ba. Rabawa sukayi suka nufi Get dan bama wanda hankalin yakai kansu Asma’u ta saka key din hannunta ta budewa Zahra a ranta tana mamakin ganin an garqame qofa harda kwado Zahra na saka qafarta waje Naziru na dira ai harda gudu ya hado har yana tsorata su Zahra tayi Waje Ma’u tai ciki da sauri ganin yana neman datse mata hannu abinda ya ankarar da matan dake tsaye kenan suka yo Get din da gudu amma ina kafin suzo tuni ya danna Kwado ya bame. Baki bude Rahma da Ma’u suke kallonsu, “Kiyiwa Allah Hajia ki bude mana mu tafi dare yanayi haka kawai an kullemu kamar wasu barayi” wata mata ta fada. Kiran sunan Naziru Ma’u ta shigayi gaba daya kanta ya kulle se ya amsa mata yana cewa “Anty kije kawai zan kiraki a waya in miki bayani”. Seta juya ita da Rahma sunajin matan wasu na magiyar a bude wasu na zage zage. A palourn qasan suka zauna ta dannawa Naziru kira. “Baba Naziru wai ya akayi ne meya faru aka garqame mana gida” ta tambayeshi bayan ya daga wayar. Seda yai dariya san ransa dannan yace “Wallahi Anty ina zaune Yaya ya kirani yace na siyi kwado nazo na kulle gidan nan da duk jama’ar ciki inyi tafiyata ze kirani sanda ya kamata nazo na bude”. “Ikon Allah, me akayi toh” ta tambayeshi. “Oho inaga dai daman besan da zasuyi taron nan ba shine dalili qilan” cewar Nazirun. “Toh Allah ya rufa asiri nidai yayana suna waje daman yanzu nake shirin naje na dakko su tunda gaka taimaka ai kasan gidan Su Qawar Amna Amina ka debo munsu” “Ba case Anty Bari naje” sukayi sallama ta ajiye wayar. “Kinji me gidan ne yace a kulle masa gidansa” Ma’u ta gayawa Rahma. “Amma naji dadi dan fa sanda Abban Ilham ya kawoni yaga taron nan tambayata yakeyi meya faru nace nima ban sani ba nadai yi hasashen suna ake, yace aikuwa dakyar idan yaya bashir ya sani toh Allah dai yasa atashi lafiya nace Amin Yanzu kuwa naga alamar kamar ba lafiya ba dan banga iyayen bikin ba a gurin”. “Koma meye susuka sani dai, muje muyi Isha naji an fara kira” Asma’u ta fada suka miqe suka shiga dakinta na qasa dan yin sallar. Dakin Mejego kuwa kiran duniya Naziru be dauki waya ba haka suka tasa ya a gaba suna kuka ita se qaqqafewa take Su kuma suna aukij kuka Amirah kamar itama zata shide babu wanda fasahar kaita wani Asibitin tazo masa a cikinsu. “Ina Fatun, wallahi tun da sauran mutunta juna tsakaninmu kizo ki bude mu mu fita idan ba haka ba wallahi bazaki so abinda zan aikata a gidan nan ba” Hajia Mariya datafi kowa shiga tashin hankali dan kamar Mijin na jira ta gane an sace mota se gashi ya kirata akan yana Airport za’azo a karbi key din motar a dakko shi, seda wanda ya tura yaje aka ce masa bata nan ya kirashi gashi yanzu se kiranta yake yana Zazzage mata kwandon rashin mutunchi yace ta kuma tattaro dik inda take karya rigata zuwa gida in ma ita bata dawo ba to motarsa ta rigashi isa. Qaqawara qaqa 🤔🤔🤔🤔🤔🤔 Ayi qara haquri dai yanayin se a hankali 🙏🙏🙏 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 WATA KISHIYAR 🥰👹 (ALKAHIRI CE KO SHARRI) 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 Na Maryamah_Mrs AM (Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah) Page 17 Ranar Litinin Bashir ya tafi a ranar kuma Asma’u ta dawo dan ta tabbatar daman kafin su iso ya tafi. Da wuri suka taso dan haka sun sauka da wuri. Gaba daya ranar baccin gajiya sukayi har zuwa washe gari talata sannan suka wartsake. Da yamma ta shirya dan tana so ta fita harta kunna motar ta amma taqi tashi tayi duk abinda zata iya amma taqiyi dole ta haqura ta kira Naziru ya zo da bakanike suka dubata yace dole seya tafi da ita gareji haka suka lallaba suka tafi se fasa fitar tayi. Seda aka yi Sallar Isha tayi order Bolt, itada yaran suka fita, Shagonta na siyar da kayan yara sukaje dan tana so ta siyowa Baby Iman riguna, basu bata lokaci ba ta zabi masu kyau yan turkey guda uku se Shawl shima me kyau daya sannan tacewa yaran kowa ya dauki abu daya da ze kaiwa Baby Iman. A leda aka zuba musu kowa aka bashi nasa suka juyo zuwa gida, seda ta dakko Atamfar data ajiye da zata hada musu da ita ta saka da qaramar Barimar Gold da tun cikin su Ahmad ta siyeta da aka ce mata mace ce qarshe se gashi ta haifi yan Biyu duk Maza tama manta da ita se zuwan nan ta ganta shine ta dakko ta hada musu da ita. Yan uwan Amiran Suna zaune a palour sun baje kayan rabo ana zuzzubawa ita kuma tana daga gefe tana duba dinkunan ta ga gadon Iman a kusa da ita Asma’u sukayi sallama ita da yaran gaba daya. A sake suka amsa musu, Amirah ta ajiye Kayan hannunta tana kallonsu, hada ido sukayi da Ma’u, seda ta murguda baki ta juya ido sannan ta gaisheta ita ko Ma’u data na ankare da duk abinda takeyi murmushi tayi kawai ta amsa mata a ranta tace “zaki gane kurenki yarinya Allah sa kiyi kuskuren zagina wata rana”. Addah da tajiyo muryar Asma’u tai wuf ta fito daga daki, bakin kaman ze tsage saboda fara’a suka gaisa tana satar kallon Ledojin da suka shigo dasu. “Miqo musu Yar mana Amirah kina zaune” Addah ta fada tana yiwa Amiran signa da ido, se Amiran ta daga ido ta kalleta fuskarta na nuna alamun “kin san me kike cewa kuwa” Ma’u da duk tana kallonsu tayi saurin cewa”Aa barta ma kawai bari mu qaraso mu ganta kar a jagwalgwalata”. “Wane irin magana ne haka ke gafara da Allah ki gani se ayita wani saka ya a ke ji kamar kaza tunda tazo duniya ai dole a dauketa a haka zata saba” ta kwashe Net ta ciro Iman ta miqawa Ma’u. Bakinta dauke da Bismillah ta karbeta cike da taka tsan tsan, masha Allah kuwa ga kamannin Farida nan a Fuskarta koda yake ai duk yaran da Bashir suke kama saboda ita macece shiyasa kamar ta da Farida tafi fitowa. Tana hannunta duk yaran suka leqata har Ahmad yana kama dan hannunta ya riqe. “Mami muna son ta mu tafi da ita Lagos” ya fada yana wasa da hannun yarinyar, se Ma’u tayi murmushi kafin ta amsa shi Addah tayi caraf tace “Da ita zaku tafi ai Malam Amadu ko kuma in kunyi gaba zata biyo daga baya”. Sunyi kaman minti Goma Ma’u ta miqe ta kwantar musu da ita kafin ta turawa Amirah ledar kayan tace gasu nan babu yawa a sakawa Baby nan suma yaran kowa ya dire tasa duk kowa da abinda ya tsinto mata banda Aliyu da daman shi a qofar palour ya coge bema shiga ba. “An gode madallah” Addah da sauran Yan gurin suka fada, sukayi musu sallama ta tattara yaranta sukayi waje kamar suna jira suka shiga zazzage kayan a qasa. “Ke Amirah kinga rigar da nake gaya miki wallahi yar dubu Ashirin da biyar dinnan kin gani ga kudinta nan ma a jiki” Nusaiba Diyar Inna Gaji ta fada dan zancen rigar da za’a sakawa babyn lokacin Shagalin suka gama take gaya mata akwai wadda tagani ta fita kunya a gurin wata qawarta har sun fara shawarwarin yanda za’a samu kudi aje a siyo se gashi Allah ya kawo mata daga sama. Atamfar ta sake dagawa ta riqe baki tace “Amirah Embellished ce fa, bari dai muga ko qaramar ce” ta hau duba lambar Atamfa da fentin jiki seta dau sowa tana cewa “Wallahi babbar ce, ke harda dan kunnen Gwal kai lalai matar nan dagaske take Dama Allah ya bani kishiya irin haka ai na huce takaicina se in ta haihuwa duk shekara tana kawomun kayan arziqi” Nusaiban ta fada tana ta faman daga kayan. “Ke na taba ki da Arziqi, wannan uban kayan da kudinta ko na mijin aka siya?” Asiya yayar Amirah ta fada se Ummi da bata sa musu baki ba tayi caraf tace “Ce miki akayi itama cima zaune ce irinku kuna zaune kuna jira se abinda miji ya dakko ya baku, toh nema takeyi tana aiki tana kasuwanci ta kayan nan ma da kika gani a shagon ta take siyarwa ga ledar nan kina gani”. Ledar suka duba gashi nan kuwa “Asma’u Kiddies shop” a rubuce, se Nusaiba ta riqe baki tace “Lallai kice ta kama qasa irin wannan kaya yan order kodai ma shagon ne naji ana zancen sa an ce duk Gombe Albarka ko da yake wannan iwar dukiya da aka mutu aka bar musu dole suyi ta bude gurare, jifa Salon din Yayar ta Bilkisun nan ba abinda ba’ayi na gyaran mace a gurin” Inji Asiyar, daga nan kace nace ya kaure aka shiga fadar irin abubuwan da yan gidan su Ma’un suka kafa, kowa fadi yake suna birge shi yanda kansu yake a hade bazaka taba ganin wani abu wai shi yan ubanci a cikinsu ba. Ran Amirah in yayi duba ya baci jin yabon da suke wa Ma’un, ta rasa a duniya dalilin da yasa Asma’u keda farin jinin mutane, duk wanda ya budi baki sedai ya fadi Alkhairinta badai sharri ba. “Ke kanki shaida ce akan kyawawan halin Asma’u ai da mu’amarata me kyau” zuciyar ta ta raya mata. Seta ja tsaki tabbas ita sheda ce akan karamcin Anty Asma’u, tana da kyakykywar zuciya tabbas da mu’amala me kyau. Sannan sam abun hannunta be rufe mata ido ba gata da sauke kanta matuqa bazaka taba cewa ta fito daga gidan arziqi ba sedai idan ka dubi halayyarta kasan tabbas daga babban gida ta fito da suka tashi cikin Arziqi suka jiqu dashi dan haka basu dauke shi a matsayin wani abun dagawa ko da zesa suyi girman kai ba. Tsaki ta kuma ja ganin itama ta bige da yabon Ma’un a zuciyarta, tabbas tana kishi da Asma’u da duk wata halayya ta ta. Ta kan ji dama ita ce Asma’un, bata kasance yar Babban Attajiri kamar Baban Asma’u ba kuma wannan ne kadai tasan bazata samu ba amma baya ga haka tayi Alqawarin duk abinda Ma’u ta mallaka seta seta same shi. Tayi zurfi cikin tunaninta har bata san sun gama zuba kayan ba kowa ya fara neman makwancinsa se itama ta miqe ta dauki Iman suka shige daki suka kwanta saboda su samu tashi da wuri. A bangaren Ma’u ma suna komawa kowa ya nemi makwanci da wuri nan da nan bacci ya dauketa dan bata ma ji jerin missed calls din da Malam Bash ya ringa jera mata ba har bakwai seda Asuba data farka. Seda tayi sallah ta kirashi, qorafi ya hauyi mata akan rashin Amsa wayar ta samu ta bashi haquri akan bacci ne ya dauketa, basu jima ba sukayi sallama kafin ta sake komawa bacci. Qarfe goma na safe sautin kidan kwaryar da ake a filin gidan ya tasheta, da farko ta zata ko kunnenta ne beji daidai ba, seda ta kasa kunne sosai sannan ta tabbatar dagaske fa a cikin gidan ne dan ga hayaniyar Mata nan tana jiyowa. Miqewa tayi zuwa jikin window dan tana dakin ta na saman Bashir ne, labulen ta janye ta leqa da mamaki take kallon Mata masu kidan kwaryar da kuma wadanda suke juyi a fili suna watsa musu kudi. “Ikon Allah to me akeyi a gidan?”Ta fada a fili, ganin babu me bata amsa yasa ta saki labulen, gadon ta fara gyarawa kafin ta shige toilet tana ci gaba da mamakin abun. Wanka tayo ta shirya cikin wani danyen Lace Baqi da akayiwa kwalliya da Jan Zare ya karbi farar fatarta sosai da sosai ta kashe dauri tareda baza turarenta kafin ta dauki wayarta ta fito daga dakin takalmin qafarta na kwas kwas. Palour kasan qal dashi Aliyu da Amna na zaune akan Dining suna karyawa duk sunyi wankan su. Gaba daya suka gaisheta tana shirin tambayarsu sauran Ahmad ya bude qofa ya kwaso da gudu Muhammad na bayansa har yana neman faduwa ta tare shi “Ya haka bana hanaku guje gujen nan ba se kunji ma kanku ciwo ko” ta fada bayan ta tsaida Ahmad din. “Mami biki akeyi a waje zo ki gani harda masuyin kida da calabash irin na gidan Baba Sarki” Ahmad din ya fada. “Nima naji kidan tun ina sama ai me yake faruwa a gidan ne?” Tayi tambayar tana kallon Amna da Aliyu dan sune manya. “Wai suna waccen matar sukeyi” Aliyu ya fada ba tareda ya dago ya kalleta ba. “Wace matar“ ta tambaya tana tsare shi da ido dukda ta gabe wa yake nufi amma se yaqi ya dago bare ya kalleta kuma yaqi magana se ma kaida kansa gefe da yayi. “Yayi kyau matar Baban naka ce waccen matar ko Aliyu idan na sake ji se ranka ya baci tabbas” ta fada tana jan kujera ta zauna. Tea ta hada ta debi dankalin da suka soya dan da zafinsa ta hada ta fara ci a ranta tana ayyana kenan bikin suna sukeyi yau, sekace dole su kuwa ai da sun haqura sa hadu a wani karon amma to ita ina ruwanta ma. Tsaf suka gama cin abincin ta koma cikin palour ta zauna, wayarta ce ta shiga qara Amna dake kusa da ita ta miqa mata. Zahra ce take kiranta Qawarta ce tun ta yarinta tare suka tashi daman sunyi da ita yau din zata zo bayan sun gaisa kuwa take shaida mata tana nan tafe fa gurin qarfe biyu na rana sukayi sallama ta kashe wayar. A hankali hayaniya ta kaure gidan mata kuwa se shigowa suke kamar ana tunkudo su lokacin har sha biyu tayi ta dena jiyo kidan kwaryar da alama sun tashi ne sedai hayaniyar mata kawai. Saboda zuwan Zahra yasa ta shiga kitchen, fried rice ta dora ta window kitchen din da yake kallon tsakar gidan take kallon ikon Allah yanda Jama’a ke tururuwa a gidan nasu wasu na shiga wasu na fita. Bata tsinke da lamarinba seda ta ga an wangale get ana shigo da kujeru harda Wata rumfa da kayan decoration ba bata lokaci suka shiga har hadawa kuwa “Shagali kace abin nayi ne to Allah yasa a tashi lafiya” ta fada a fili tana hada salad dinta, kafin ta gama kuwa har sun gama sauke kaya sun hau shiryawa ga kayan DJ an ajiye daga gefe suma. Harabar gidan nasu nada dan girma ba laifi dan a qalla zataci mota biyar zuwa shida saboda filin gefen su da Bashir ya shigo dashi yayi ginin Bangaren Amirah ya ragu sosai shi ya qarawa gurin girma. Tsaf suka gyare ko ina aka jera kujeru can daga gefe ga High-table an shirya se zama kawai ya rage. Tsaf ta gama girkinta suka jere kayan akan Dining tana shirin shiga daki tayi sallah dan har biyu ta kusa a ka kwankwasa qofa, jafar tacewa yaje ya bude ta dan daka dan taga wanene. Sadiya da Afiya ne qannen Bashir se Suwaiba diyar qanwar Baban su suka shigo ko wacce da shirgin Jakar kaya a hannunta ga yara na biye dasu. Kada ran kada han take kallonsu har suka qaraso tsakiyar palour suka zube akan kujeru suna wash Allah jij sanyin Ac da qanshin turare na ratsa su. A kusan tare suka gaisheta, Asma’u da bata dara daga inda take ba ta amsa tana kallonsu da jiran ji da wacce suka zo kuma. “Ku tashi mu shirya lokaci ya na tafiya dan nasan yanzu zakuga shagali ya kankama fa kuma ni ko wanka ma banyi ba na fito daga gida” inji Sadiya “Ai bake kadai ba nima banyi wankan ba haka na fito” Suwaiba ta mara wa Sadiyan Baya suka miqe kowacce ta sabi jakarta suka doshi corridor da dakunan suke inda anan Ma’u ta coge. Seta qara gyara tsayuwarta ta yanda ta raba hanyar biyu ba ta yanda wani ze wuce fuskarta na nan a yanayin da bazaka iya fasaltawa ba. “Bari mu wuce Anty” Sadiyan ta fada “Zuwa ina?” Asma’u ta tambayeta, se suka kalleta duk su biyun da mamaki, Suwaiba ce tayi qarfin halin cewa “Wanka zamuyi”. “To yaushe gidan nan ya zama gidan wanka kuma bani da labari?” Ta fada tana gyara tsayuwarta da jinjinawa rainin hankalin wadannan yaran ta kuwa shirya nuna musu iyakarsu yau dan yanzu ba da bace. Kallon kallo aka shigayi tsakanin Suwaiba da Sadiya, still Sadiyar ce ta sake magana dan tafi sauran baki tace “ban gane ba Anty wanka fa mukace miki zamuyi anan kine zancen wani gidan wanka kuma ko bamu da damar da zamuyi wanka a gidan dan uwan mu ne?” “Allah sarki masu Dan uwa dama kuma babu ita kuna iya juyawa kuje wani Gurin tunda bani kadai bace a gidan ko? Ina ga ai kamar a kwai yar uwarku ma kuna iya zuwa gurinta”. Ba qaramin mamaki ne ya kama su ba da jin kalaman ta, Antyn da ada a dakinta suke duk wata dabdalarsu qarewar wanka har kayan sawa ta kama basu take idan ana wani taro ka zo da kayan da basu kamata ba seta dakko na fita taro ta baka ko yanzu ita Sadiya bata zo da mayafin da zata hada kayan da zata saka ba dan a safiyar nan suka samu labarin taron sunan suka kuma qudiri niyyar se sunzo duk kuwa da gargadin da Dada tayi musu amma sunce baza’ayi babu su ba wallahi. Sabon Leshinta ta dakko zata saka bata rigada ta siya masa mayafi ba dan ta tamawa bikin Qanwar mijinta ne zata saka saura sati biyu yanzu se kuma ga wannan taron ya taso shiyasa ta dakko tasan bazata rasa mayafi gurin Anty Asma’u ba tunda tana gari qila harda jaka ta samu amma shine take gaya musu wadannan magananganu haka. “Ku nake jira zan rufe qofata lokacin sallah ya kwace mun” suka ji muryarta ta dawo dasu daga suman mamakin da sukayi, har Suwaiba ta budi baki zatayi magana Afiya da tun farko bata ce komai ba ta dakatar dasu da cewa “Sadiya ku muje mana ko bakiji me tace bane” Dukyanda suka so su sake magana kuwa ta hanasu haka suka tattaru kayansu sukayi waje Sadiya da Suwaiba na kumfar bakin bazasu yarda ba su zata wulaqanta suda gidan dan uwansu ai se sun kira yayan suji idan shi ya bata sabon lasisin wulaqanta su. Oho bata ma san sunayi ba dan suna fita Jafar ya tura qofar ya rufe dan bata buduwa ta waje dole seta ciki suka ci gaba da kallonsu ita kuma ta shiga daki ta tada sallah. Tana dakin Jafar ya shiga da sallama “Mami ga Umman su Jawad tazo”(Zahra qawarta) “toh gani nan zuwa” ta fada ya juy ya fita. Daurin ta ta gyara da fuskar ta ta fito fuska a washe suka rungune juna ita da Zahran da murnar yaushe gamo dan an dade ba’a hadu ba kafin suka zube akan Two sitter ta shiga yiwa Zahra tsiyar qiba. “Kai matar nan gaskiya wayo kikewa Yah Sayyadi ji yanda kike narka qibar kamar wata Aisha Buhari 😂😂🤐” “To ya za’ayi barni nayi qibata kowa ya ganni yasan ina jin dadi tunda jikin yaqi zama irin naku jikin models” Zahra ta fada da sigar shaqiyanci suka kwashe da dariya tareda kashe wa, Sallamar da akayi ta katsew Ma’u maganar da tasoyi. Rahma ce matar Amiru qanin Bashir bayanta kuma Kamila ce itama qanwar su Bashir dince da me aikinta dauke da danta dagaje dagaje dashi ga ledar kaya a hannun Kamilan. Da sauri Kamilan ta shigo dan seda Rahma ta matsa gefe ta bata hanya ta dire ledar a kan centre Table ta na cewa Me aikinta “maza Usaina ki gyara masa jikinsa ga kaya nan ki saka masa nima yanzu zan zo na yi wanka na shirya” ta juya ta fice ita kuwa Usaina ta qaraso ciki tana gaishe su da niyyar ajiye yaron Asma’u tayi saurin dakatar da ita. “Dauki kayan maza ki bita” ta fada tana nuna mata hanya, ba musu kuwa Usaina ta kinkimi leda da yaron tayi waje harda ja musu qofa se sannan Rahma ta sama ma kanta gurin zama. “Keda mutanen naki kuma yau Maman Aliyu” Rahma ta fada tana dariya. “Da kenan Maman Nasir ai sun shani na warke kuma yanzu, kunga ku tashi kuje sama ina zuwa”. Zahra da Rahma suka miqe zuwa sama qaramin palour Ma’u da take sauke manyan baqinta. Kallon Jafar da Abdallah dake kallo tareda Jawad Dan Zahra tayi tace “ina su Ahmad?” Jafar ne ya amsa mata yace “Yaya ya fita, yah Amna da Farida ma sun tafi gidan su Amina Shehu sunce sun gaya miki tareda su Ahmad din” “Eh na tuna, kana jina duk bugub da za’ayi ko waye karka kuskura ka bude kofar nan”. “Tam Mami” ya amsa mata yana daukar Handle din Game din da suka kunna. Kitchen ta shiga ta hado ruwa da lemo da tarkacen kayan motsa baki a Babban Try Jawad ne ya karba dan yafi Jafar din girma ya kai saman ita kuma ta dibar musu Abinci da sauran kayan da zasu buqata duk ta basu suka kai, da kanta ta murzawa kofar key ta kuma sake jan kunnensu akan karsu bude mata qofa kafin ta haye saman suka hade da su Zahra aka shiga hirar duniya da abinda ze amfane su ba tareda sun koda taso da zancen Abinda ke faruwa a cikin gidan ba. A dakin me jego fa tuni abubuwa sun dauki Harami, tana zaune ta ci Ado da wata danyar shadda data sha aiki su Sadiya suka shiga palour suna kumfar Baki da zage zagen abinda Ma’u tayi musu, anan palour aka maida magana basu dasa Aya ba Me aikin Kamila Ma ta dawo tana miqawa Kamilar ledar kayansu. “Kan bala’i lallai matar nan au kema koroki tayi?” Kamilan ta fada. “Ta koromu ma bare wata me aikin ki ai wallahi bari a tashi taron nan bata ci banza ba se mun nuna mata nan gidan dan uwan mune muna da ikon yin yanda muka ga dama a ciki, ke Amirah bamu muqullin dakin Yaya naji kofar a kulle take”. Cewar Sadiya. “Nan fa daya yaya sadiya key din dakin mijin nawa zan baku kema kin san baze yuwu ba” Amirah ta fada tana yatsina fuska, tab waima ta basu key wallahi bazata bayar ba kuwa. “Oh kema diban Albarkar zaki mana dakin dan uwan mu fa mukace ki bude mana mu shiga mu shirya tunda kinga dai nan ko ina da mutane” Kamila ta karba se kuwa Amirah ta miqe tana sabar yarta da take ta nan nan da ita ga kuma key din a hannunta dan kayan da zata saka dana rabo duk suna ciki bata kuma yarda ta bawa kowa ba banda Ummi se Anty Aisha su kadai ta yarda suka shiga dakin. “Bafa zan bayar ba Yaya Kamila idan kun matsu da wankan ku shiga na dakin baqi dan na kulle toilet din dakina ma kar a batamin ko ga wani nan ai a kofar daki kuyi amfani dashi” ta shige dakin ta ta barsu sototo baki a bude tsabar mamaki. Mura ce take damuna wallahi kuyi manaji da wannan 🙏🙏🙏 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 WATA KISHIYAR 🥰👹 (ALKAHIRI CE KO SHARRI) 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 Na Maryamah_Mrs AM (Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah) Page 19 Tunda Bashir ya qulla tsiya ya kuma tabbatar Naziru ya kulle gidan dan sun sake yin waya ya gaya masa ya je dakko su Amna a gidan qawarsu a sannan ce masa yayi ya wuce ya kaisu gidan Bilkisu yayar Asma’u kawai dan idan yace gidan Dada zata zargi wani abu kuma baya so labarin ya isar mata da wuri. kashe wayarsa yayi dan karma wani dayake ganin mutunchi ya kirashi ya roqeshi. Beko qara minti goma a gidan Musa ba ya tafi yana tuqi a ransa yana wassafa irin hukuncin da ze dauka akan Amirah tunda har ta take dokarsa ta nuna bata jin maganarsa tabbas ze nuna mata shima ba kanwar lasa bane. Daya isa gida shikadai ya ringa safa da marwa a cikin palour yana kwafa tabbas se ya hukunta yarinyar nan hukunci me tsanani, tunanin halinda Baby Iman take ciki yake yana fatan Allah yasa yarinyar tana lafiya wani abu be sameta ba hakan ze dan rangwanta wa Amirah hukuncin da zeyi mata amma ya rantse tabbas wani abu ya sami yarinyar nan se kansa besan me ze mata ba. Yana so ya kira Ma’u amma bayaso ya kunna wayar wani kiran ya shiga qarshe haka ya haqura ya zauna jiran lokacin daya diba kafin ya sake kiran Naziru. Gidan suna kuwa gagarumin ruguntsumi ne ya sake tashi. Ana tsaka da dambaruwar yanda za’ayi a bude qofa, dangi da qawayen Addah sun taru suna mata tijara sun cika palour Amirah taf kaman an sakko daga Idi daidai da iska me kyau babu ta shaqa se kaya kaya akeyi. Amirah na durqushe se rasgar kuka take har sannan akan yarinyar da harta gaji da komawa da numfashinta ta kwanta laqwas kamar mara rai ita duk wannan hayaniyar ba ganewa take ba, buqatarta a samu me kai mata ya Asibiti dan ta dade da saddaqarwa yau kashi ta ya gama bushewa. Addah data gaji da tijara da cin mutunchin da Jama’a suke mata ta zaro Key ta cillawa Hajia Mariya datafi kowa hasala a cikin matan dan ita aka dira daka, so take kawai ta fita ta san nayi dan ko karan hauka ya cijeta bazata doshi gidan mijinta yanzu ba se da wannan mota da bata san uban da ya sace ba dan haka ta yanke shawarar daga nan office din Yan sanda zata ta bada report daga can kuma tayi gidansu dan tasan waye mijinta sarai haka kawai ma yayi bala’i bare yau da aka taboshi da lasisi. Cafkar key din tayi tana watsawa Addah kallon wulaqanci tace “da karki bayar wallahi da sena tubeki na dauki muqullin nan yau” ta fara kutsawa da niyyar zuwa bude qofa Hajia Hassana ta katseta tana cewa “Mariya wannan muqulli fa aikin banza ne dan ta waje wani hatsabibin yaro ya kullo mu wallahi. Kuna tsaka da hayaniya dazun nan Uwargidanta ta raka baquwa ta bude kofar tana fita yaron nan ya danno daga waje ya rufe jeki duba ma ki gani babu kwadon nan ta ciki”. Kafin ma ta qarasa dayawa sun dauki sabon kukan tashin hankalin rashin sanin wane kalar bala’in ne kuma yake tunkaro su, To bala’i mana in ba haka ba ta yaya za’a ce an kullo su ta waje ma bata ciki ba yanzu suyi yaya su fita dan dai wannan katangar gidan basu isa su tsallakata ba. Ummi ce da tuni itama ido sukayi mici mici saboda kuka ta sunkuci Iman tana ceda Amirah “nidai matsa ki gani wannan hayaniyar da hucin numfashin kadai sun isa su qarasata muje ko a Napep ne mu tare mu kaita Asibiti” ta nadeta a cikin shawl din ta kyau ta juya da niyyar fita kamar ana jiran ta kuwa dif wutar palour ta dauke duhu ya mamaye ko ina bame ganin wani a ciki. Gaba daya guri ya sake rikicewa da ihu dan kina tsaye sedai kiji an wafce miki jaka nan aka shiga turereniyar fita ana faduwa duk wadda kuwa ta fadi sunanta sorry dan taketa za’ayi ana neman hanyar tsira a garin haka aka dungure mata Tv ta fado qas tim Centre table kuwa daman tuni ya karbi rabonsa se fatan kar wani ya taka kwalba a garin gudu. Wata qara me kama da rugugin tsawa a ka fasa kafin sukaji faduwar abu tim a qasa, sabon gudu ne ya falle ga duhu ba wanda yasan takamaiman ina yake dosa aka ringa gwabza karo ana faduwa kuwa kafin kace me anyi wada wada da kayan palour Amirah, Seda aka kwashi a qallah minti goma se ga haske ya dawo ai kan kace kwabo wayam sun fice daga palour an dawo tsakar gida kowa tayi cirko cirko fuskokin mata jagejage da hawaye wannan Suna ko jaraba? Addah data ja qafa da niyyar gudu itama caraf aka riqeta cikin abinda befi sakan uku ba ta saki fitsarin tsoro ganin sunyi ido hudu da Hajia Mariya dake yashe a qasa da ko ba’a gaya mata ba tasan riqaqqun iskokanta ne suka tashi. Tun da tace an sace motar nan abinda take taraddadi kenan dan indai ranta ya baci se sunzo kuma Al’amarin bazeyiwa kowa kyau ba dan Aljanunta basu da mutunchi yanzu basuqi suyiwa kowa na gidan sunan nan bulala dari dari ba. Sake yunqurawa tayi da niyyar gudu Mariya ta miqe cikin muryar yara tace mata “Addah fatu muje washan goyo ja’ayi yau kowa seya goya ni in ba haka ba nayi masha buyayay goma ke zaki faya kuma” “Quuuu” cikin Addah ya bada qara, yo ai badanba gara bulalar akan tace a goyata. Ita kadai ma Hajia Mariya ba kadan bace qaruwar mace ce ta gaske bare idan wannan yar Aljanar tata tazo me son goyo seta Allah in kuma bakayi ba kaci na jaki. Addah naji tana gani ta tasata a gaba suka fito inda Jama’a sukayi cirko cirko ta dane bayanta kuwa. Zanso kuga idon Addah haka ta goya hajia Mariya tana nishi kamar zata mutu ta kaita ta dawo da ita amma taqi sauka tace se an sake haka ta kuma sahu daya da ita sukaje suka dawo sannan ta sauka. Zaba ta ringayi wanda ze goyata in ka tsaya gardama sedai kaji dundu kamar an buga maka guduma kuma in ta hau marasa qarfi suka fadi nan ma ta hau tamola da mutum aifa gida ya sakw zama kamar gidan Allura se kuka ake wannan jaraba har ina. Aliyu dake cikin dan dakin da Change over da Solar su ta gidan yake ya kwashe da dariya har yana kaiwa qasa. A kan idonsa komai yake gudana dama jira yake gari ya qara duhu ya kashe haske ya qara musu tension akan wanda suke ciki gashi kuwa yayi ga kuma sabon show an samu kai amma fa abu yayi kyau kuma yaji dadi, fitowa yayi ya wuce part dinsu, knocking biyu Jafar ya bude masa ya shiga yana Dariya. Asma’u dake zaune akan kujerar Dining suna waya da Yaya Bilkisu ta gayavmata su Farida suna can Naziru ya kaisu ta dago ta kalleshi, tun ma kafin tayi magana yace “Mami kinga yan suna kuwa ga wata can tana Aljanu tace se sun goyata kowa takalminta a hannu lipstick duk ya goge”. Duk yanda taso dakewa tayi masa fada kasawa tayi ta fashe da dariya dan tana hango harabar gidan dan tarwai yake da hasken fitulun da aka zagaye shi dasu, saboda ma taga komai dakyau yasa ta dage labulaye suka rage hasken fitulun palour duk drama da akeyi akan idonta ne tana ganin haske ya dauke kuwa jikinta ya bata Aliyu ne dan ta san aikinsa ne kashe wutakuma dazu ta ganshi a zaune a qofar power room din magana ce kawai bata masa ba ta wuce. “Allah ya shiryeka, kar naga ka sake fita in ba haka ba ranka ze baci” ta fada tana miqewa. “Sunan wani film waishi daga murna” ta fada tana shiga kitchen dariya fal ranta, Yogurt ta dauka da cups biyu ta koma dakinta inda ta bar Rahma tana sallar Isha tunda yaranta sun samu mafaka ai shikenan ita kam. Abuubuwa sun sake rikicewa Addah ido ya raina fata, data san haka ce zata faru kuma da bata kulle qofar ba gara tabar kowa ta tafi gidan ta idan yaso tayi Allah ya isa amma gashi yanzu an bata goma daya bata gyaru ba. Dakyar ta samu ta zillewa yar zulai Aljanar Hajia Mariya tayi bayan gidan gashi ta Rasa wanda ze kira mata Dada dan ita kadaice kuma madafarta a yanzu idan ma ba’a san wandaya kullo su ba ita zata iya nemo wanda ze zo ya buge kwadon amma wannan garqamewa da akayi musu idan wuta ta tashi fa Allah ya kiyaye subi ina su fita? To kuma kiran Dadar ma ba hali dan an sace waya kuma tasan babu me bata aron tasa idan ma an bata ita ba haddace Number ta tayi ba, dabara ce ta fado mata arai, bari taje gurin Ma’u ta kira mata Bashir ai shine me gida dukma tsiyar da za’ayi sudai a bude su tukunna jama’ar data tara su tafi wannan bala’in ya ragu dan dai kam taga suna yau ganin idonta bakuma ta fata Allah ya sake maimaita mata irin wannan taron. Sadadawa tayi ta faki ido ta zagaya ta kofar kitchen din Ma’u. Kamar zata balla qofa haka ta ringa doka musu bugu tanayi tana wai waye gudun kar wani ya ganita Har Jafar ze bude Aliyu ya riqo shi yana cewa “kai baka da hankali ko to jeka bude musu baka san me yake faruwa a gidan nan bane” se Jafar din ya fasa amma be zauna ba ya tafi ya gayawa Ma’u. Ta yar hudar jikin qofar ta hango Addah fuska tayi qozai qozai abunka da fara daurin da aka dandasa mata dazu yayi ta kansa ga kunnenta daya da dan kunne daya babu ta tabbatar bata ma lura da hakan ba. Bude mata qofar tayi tana shigowa kuwa takai qasa tana rushewa da kuka kamar qaramar yarinya. Kiyiwa Allah Asama’u ki kira Bashir azo a budewa mutanen nan qofa su fita kafin su kashe ni nidai nayi dana sanin wannan qaddararren taron suna ashe rabon wahala ne yasa muka nace se munyi” ta sake rushewa da kuka harda sheshsheqa. Ba qaramin dauriya Ma’u tayi ta riqe dariyarta ba amma dukda haka da Addah a hayyacinta take seta gane dariya take mata tace “toh Addah meya faru kuma ni da naji shiru an dena kida ma na zata kun tashi ne. Wayar Baban Aliyu kuwa a kashe take fa dan na kirashi tun dasu naji amma bari na same kira ko yanzu ya kunnata” ta fada tana danna wayar ta lalubi Number sa ta danna kira, kai kodan ta sake kunno musu shi idan be sani ba ai yasa ta kirashi sedai kamar dazu data kira ce mata akayi a kashe take. “Wallahi Addah a kashe take” ta fada tana janye wayar a kunnenta “Kiramun Nafi dan Allah ita ta samo mana wanda ze bude mu” Addah ta katseta seta maida akalar kiranta kan Dada itama seda ta mata kira biyu sannan ta daga ba tareda ta yi magana ba ta miqawa da Addah wayar ta karba tana rushewa da Dadan da kuka. “Nafi na shiga uku na hada taron masifa da Bala’i yau ki taimake ni yar uwata ki kawomun dauki” Addah ta fada cikin matsanancin kuka. Dada da harta kwanta dan cikin ikon babu wand aya kirata ya gaya mata wannan Al’amari dan yayanta da sukaje suna bayanda Asma’u da Amirah suka gwanya musu rashin M fushi sukayi suka bar gidan, ragowan dangin da suke can kuwa tunanin su kirata be zo musu ba koda yake rabi da kwatan yan suna an kwamushe musu waya wadanda suka tsira kuwa sunyiwa tasu boyo me kyau kafin a sane ta. “Addah lafiya, meya faru? A ina kuma? Dada ta tambayeta cikin damuwa da jin kukan nata tasan ba lafiya ba amma Number Asma’u data gani yasa hankali be tashi da yawa ba tasan koma mene ne da sauqi. Addah kukan ta taci gaba dayi, ganin da Asma’u tayi bata da niyyar ansawa Dada ya sakata karbar wayar ta danyi mata bayanin iya abinda ta fuskanta da lamarin. “Ashsha abu beyi kyau ba, yanzu waye ya kulle gidan? Shi Bashir din ya sani?” Dada ta tambaya se Asma’u tace mata “Muma bamu sani ba Ai, Baban Ali kuma ban sani ba gaskiya ko yasan maganar dan wayarsa a kashe take tundazu dana kira”. “Shikenan bari nayiwa Amiru magana gashi can yana cin abinci daman nan gidan naku ze taho ya dauki Rahma in yaso se suzo da Naziru yanzu Allah ya kiyaye gaba” Dadan ta fada zuciyarta sam babu dadi, yanzu wannan wane irin abune ai yanzu Allah kadai yasan inda maganar sunan nan zata tsaya sun jawo musu abun fada a gari. Fitowa tayi daga dakin ta ta tarar da Amirun a tsaye yana niyyar fita dan sunyi sallama ta shiga ciki. “Amiru ka nemi Naziru ku tafi tare gidan Yayan naku ba lafiya ba”. Da”Allah ya kyauta” ya amsa mata ya fita yana dannan kiran wayar Naziru dan shi duk a zatonsa be wuce a ce rigima ce tsakanin Ma’u da Amirah ba, a hanya ya dauki Naziru daya maze kamar besan me yake faruwa ba, gama wayarsu da Bashir kenan ya kirashi da wani layi yace masa duk me za’ayi karya kuskura ya bude gidan nan qasa da qarfe goma na dare yanzu kuwa har tara ta gota dan haka ya qara musu awa daya se sha biyu ze bude su kuwa. Kamar wata boarding school ranar hutu haka suka tarar da qofar gidan cike da motoci, yawanci mazajen wadanda Allah ya taimakesu suka tambaya kafin suka fito ne an kuma san inda suka tafi da sukaji shiru suka biyi sahunsu se wadanda yan uwansu suka kira su dauke su. “Kai lafiya kuwa gidan meyake faruwa haka” Amiru ya fada se Naziru ya marairaice kamar na Allah yace “Yanda ka gansu yaya nima haka na gani, mu qarasa mugani Allah yasa dai lafiya. Bakin get suka qarasa inda wasu suke qoqarin yanke kwado amma kamar na tsafi yaqi yankuwa wasu daga gefe kuma suna musu magana akan su bari, ta yaya zasu budewa mutum gida bada izininsa ba duk abinda yake ya dawo su tabbata yana kansu. “Wai meyake faruwa haka ne” Amiru ya tambayi masu yanke kwado dan shi tunaninsa ya tafi kodai gobara ko wani babban Al’amari ne kuma yake faruwa amma kuma hmga kwado ta waje ga kuma kururuwar mata suna jiyowa daga ciki suna ihun a taimaka musu. “Kagane Alhaji nima bansan me yake faruwa ba gaskiya Beb dita ce ta kirani tace nazo na dauketa a gidan nan tazo suna daman ni na kawota dazu se kuma tace na taho da me yankan kwado idan zan zo kaji iya abinda na sani nidai” shugaban masu kiciniya da kwado ya fada. Se Amiru ya kalle shi cikin masifa ce“wannan wane irin rashin hankali ne, meye a cikin gidan da har zaku zo ku budewa mutum ba tareda izininsa kona wanin sa ba idan wani abun nema ai se ku fara neman izinin me gidan tukunna”. “Megida ka ganmu nan dukka jiran a bude gidannan muke takamaimai babu wanda zeje maka yasan me yake faruwa dayawan mu munji shiru ne matan mu basu dawo ba muka biyo sawu wasu kuma kiransu sukayi a waya suzo su dauke su kaji yanda abin yake” wani mutum ya sake fada, se Amirun ya zaro wayarsa bayan yacewa Me Yankan ya tsaya ya dannawa Bashir kira cikin Sa’a kuwa ta shiga. Basu ko gaisa ba Bashir da yasan kiran ko na menene yace masa “Ni na saka Naziru ya kulle gidan kuma wallahi duk wanda ya budemun gida kafin sha biyu na dare se nayi sharia dashi” qit ya kashe wayarsa. Se Amirun ya juya yana kallon Naziru daya sha kunu “Bani key din Idan yaso se yayi shari’ar dani” ya fada fuska babu wasa. “Amma yaya kasan dai ni laifina ze gani ai kuma...” “Zaka bani ko bazaka bani ba, daman kasanabinda yake faruwa muka taho amma baka gayamun ba kayita biye masa kunawa mutane shirme. In ba haka ba matan auran zaku kulle har se sha biyun dare saboda shirme” fada sosai Amiru ya rufe Naziru dashi, wayarsa da ta shiga qara ce ta katse shi ya daga Ummi ce cikin kuka take gaya masa halin da ake ciki dan a zatonta yana Katsina shiyasa tun tuni bata kirashi ba. “Tundazu ina bakin Get din na rasa ta inda zan fita na kai yarinyar Asibiti Yaya tsoro nakeji karta mutu a hannuna” ta fada cikin kuka. Nan da nan hankali sa ya qara tashi, Naziru da yake kusa dashi duk yaji me take fada tun kafin ma ya masa magana ya zaro key ya bude gidan ba tareda ya saurari Mazan da sukayo masa caaa akan daman shi ya kulle amma ya barsu suna shan sanyi a tsaye. Yana bude qofar da Ummi yaci karo da azama ya karbi Babyn suka juya shida Amirun tabi bayansu suka shiga mota kafin Mata suka fara tseren fitowa kamar an sako kaji daga keji wata dankwali a hannu wata da takalmi qafa daya babu dai me cikakkiyar nutsuwa a cikinsu kowa tayi ta kanta. Suna dai kam da yawa sunce ko su suka haihu sun yafe bare a sake gayyatarsu suje. Cikin qasa da minti Goma sha biyar gida ya rage Me jego da Addah da Inna Gaji se wasu dangin su Addah da basu fi biyar ba ga Hajia Mariya data sha goyo Aljanar ta tafi har sannan shame shame bata farfado daga Iskokan data hau ba. Inna Gaji da ta rakube a lungu ce ta fito tana cewa “Allah na tuna Allah karka kuma hukuntani da irin wannan bala’i na tuba wallahi bazan sake zuwa taron suna ba” babu wanda ya kukata se ajiyar zuciya suke saukewa, dakyar Hajia Hassana ta numfasa tace “To Fatu se a san yanda zaayi da Mariya a kaita gida dan kinsan duk sanda tayi irin haka seta kwashi kwana biyu ko uku bata farfado ta dawo daidai ba nidai wannan suna naku ya shiga tarihi wallahi kar Allah ya sake maimaita mana...” Jiniyar Yan Sandan data karade gidan ta sakata yin shiru, toh fa wane bala’in ne kuma ya tunkaro??? Kuyi haquri qarfin hali kawai nakeyi abubuwa sun sha kaina 🙏🙏🙏🙏 A karanta da haquri banyi editing ba 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 WATA KISHIYAR 🥰👹 (ALKAHIRI CE KO SHARRI) 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 Na Maryamah_Mrs AM (Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah) Page 20 A kofar gida Alhaji Kabiru Dangaske ya faka motarsa data yan sandan dake tare dashi. Kofar gidan wayam kamar anyi ruwa an dauke kai bazakace gidan Engineer Bashir ne daka kwashi uwar Sabada dazu ba dan tuni ko wacce ta kama gabanta dan dare ya farayi musamman gashi garin sanyi daman. Mata biyu yan sanda doguwa da gajeriya da suka zo dasu ne suka shiga gidan dan qofar a bude take. Mamaki ne ya kamasu tsakar gidan ga kujeru Birjik wasu ma sun karye kamar wanda akayi wasan dambe a gurin ko ina dai kacakaca daidai da kayan DJ fa nan sukabarsu tunda suka samu hanya suka fece to ana ta kai wayake ta wasu Kayan kida 😂😂. “Naga part biyu ne ina zamu shiga” gajeriyar ciki tayi tambayar “Nima haka na gani mu koma gurinsu muji ina tracker ta tsaya” dayar ta bata amsa suka juya inda ragowar tawagarsu suke. “Oga mun shiga amma gidan part biyu ne wanne guri matar take?” Yar doguwar ta fada. “Inaga ku shiga tare kawai bana son bata lokaci nifa” Wani Dan baqi tsamurmurin mutum dayasa uwar babbar rigar shadda Getzner se maiqo take daga gani shine Alhaji Kabiru Dangaske ya fada. “Ai baze yuwu ba mu shiga gidan matan aure ba Alhaji sedai su matan da dai zamu samu ayi mana sallama da me gidan ne idan ya bada izini se mu shiga kuma kaga layin babu kowa, ku je na daga hannun hagu dai direction din yake nunawa”. Komawa sukayi kai tsaye kuwa suka nufi part din Amirah dan shine a hannun hagu din suka tsaya abakin qofa sukayi knocking. Bugun da suka jiyo anayi ya qara hargitsa musu ciki dan daman tunda suka jiyo jiniya kowa tasha jinin jikinta, Inna Gaji kuwa daman kuka ta saka tana tambayar wai wane tsautsayi nema ya tsayar dasu ne a gidan bayan wannan uban bala’in da aka sha yanzu idan wani abun nefa yazo ya sake rutsa dasu ta tafi ta kulle qofa ilai kuwa gashi ana bugu. Hajia Hassana ce tayi qarfin halin tambayar waye jin muryar mata ta dan sauqaqa musu tsoron har taje ta bude qofar sedai ganin mata da uniform yasakata ja da baya tana karanto wa’innahu sulaimanu dan itafa duk tashin hankali ayi shi amma aduniya tana tsoron Allah tana tsoron hukuma. Tsakiyar palour suka tsaya suna qarewa palour da akayi wa wada wada kallo, “Amm muna neman Hajia Mariya ne” yar gajerar ta fada tana qara tsuke fuska ganin yanda duk suka zuba musu ido ai kuwa a tare suka nuna musu Mariya dake kwance shame shame tana bacci”. “Meye haka ku tashe ta mana tana kwance cikin wannan tarkacen wai meya faru haka a gidan ne?” Doguwar ta fada kafin ma su amsata Gajetiyar ta katseta da cewa “Ba wannan ya kawo mu ba muyi aikin mu kawai” ta qarasa inda Hajia Mariya take kwance ta shiga tashinta amma shiru bata motsa ba. Dagowa tayi ta kalli su Addah da sukayi tsilli tsilli a gurin tace “Nauyin baccine da ita haka?” “Ranki ya dade yanzu ta sauka daga iskokai ne wani lefin tayi ake neman ta station?” Hajia Hassana ta tambaya. Ba tareda officer ta amsa mata ba ta juya tana cewa dayar “ina zuwa” ta fita. A qofar gidan tayi musu bayanin abinda aka fada musu, Alhaji Dangaske ya hau kumfar baki shifa a shiga a dakkota kawai haka takeyi duk sanda ta aikata wani abu seta hau iskokai To wallahi wannan karon ko bulukiya t hau se dai a kulle su ita da Aljanun nata. Inspecta da suke tarene yace taje tayi musu sallama da me gidan ta koma minti kadan ta dawo tace baya nan. “Wato ni za’ayiwa wasan kwaikwayo kuna tsaye kuma Naga alamar bazakuyi abinda ya dace ba ni bari na shiga dakaina na fito da ita dan wallahi wannan karon Mariya bata isa ba, ta saba salwantar mun da qananan abubuwa ko nata tace an sace to wannan karon bazan dauka ba ina gani ta sabautamun miliyan Ashirin a sama ba taci bulus seta biyani ko mota ta ko kudina fita kuma ba izinina da takeyi taje ita da Allah dan na gaji”. Ya tattare riga ya doshi Gate inspecta na tsayar dashi amma yaqi. Yana zura qafarsa Amiru na faka mota Suka fito da sauri ganin yan sanda, da sauri Naziru ya qaraso yana tambayarsu lafiya se Alhaji Kabiru ya dakata ya yo baya yana cewa “Yawwa Samari gidan kune ko? To shiga ka fitomun da Mariya qawar Fatu data zo suna gidannan ka gayamata wallahi idan bata fito ba tunda wadannan dana zo dasu basu da amfani mopol zanje na dakko ai tasan halina”. Amiru ne ya qaraso gurin shima Ummi daman wucewarta tayi bata ko kallesu ba tayi cikin gida. A taqaice Naziru yayiwa Amiru bayanin abinda ya fahimta cikeda takaici Amirun yacewa Alhaji Kabiru da Inpectta su biyo shi dan abin nasu Addah ya kaishi maqura. Yanzu haka Iman nacan a NICU sun barota wanda dakyar likitan ya karbeta yace tunda uwarta bata san ciwon kanta ba subarta kawai su koma gida idan ta mutu Allah yasa qarshen wahalar da zata sha kenan dan shidai be taba haduwa da Uwa da Ya marasa tunani irin Addah da Amirah ba, dakyar suka roqeshi suka karbeta yanzu dai sun baro an jona mata oxygen da sauran tarkacen wayoyi sedai su bita da Addu’ar samun lafiya dan su da kansu sun cire rai da yarinyar. Dirar mikiya sukayiwa Palour Amirah, Hajia Mariya da farfadowarta kenan tayi arangama da Alhaji Kabiru ai take qirjinta ya bada daram dam. “Gasunan ku duba wadda kuke nema ku tafi dare yayi ya kamata a rufe gida” Amiru ya fada yana qara hade rai. Ba bata lokaci Matan yan sanda sukayi ram da Mariya suka tisa qeyarta akayi waje Alhaji Kabiru na zuba tijara se muce Allah ya bada yanda za’ayi a biya Kabiru kudin motarsa 😂😂😂 suma basu tsaya ba suka fita, a qofar Asma’u ya tsaya ya kira Rahma da harta fara bacci ta fito suka tafi lokacin sha biyu harta gota, a gidan suka bar Naziru ya kwana saboda gudun abunda ka iya faruwa kuma, seda ya duba ko ina kafin ya kulle gidan ya kwanta a dakin Aliyu. Su Hajia Addah dai kamar masu kwanan keso haka suga safiya ido biyu kowa da abinda ya dameta Asubar fari kuwa wadanda suka kwana suka dade akabar Addah da Amirah se Ummi da itama tace gida zata tafi anjima bazata iya wannan masifa ba kafin takwas na safe kuwa se su biyu kawai ga uban barnar da akayi a dakin sun ma rasa ta ina zasu fara. Dakin Bashir Amirah ta nufa da niyyar tayi wanka saboda bala’in tsamin da jikinta yai mata kafin su san abinyi sedai ta tarar da qofar a rufe se a sannan ta tuna da Anty Aisha ta bawa key jiya kuma ita bata ma sake ganinta ba gashi babu waya bare ta kirata dole haka ta shiga dakinta ta binciko inda ta boye key din toilet data rufe dan kar a bata cikin Sa’a sega na Dakin Bashir a gurin da alama anan ta boye mata. Da murnarta ta dauki key din ta fita, Addah na zaune akan kujera ta rafka uban tagumi abin duniya ya taru ya mata yawa dare daya harta zabge tsabar Tashin Hankali yanzun ma tayi zurfi a tunanin yanda zasuyi su gyara gurin kafin azo tunanin neman kudin da za’a biya bashin da suka karbo bata maji fitowar Amirah ba se ihun salatinta data jiyo a dakin Bashir ba shiri ta miqe ta bita. “Na shiga uku Addah shikenan sun kashe ni wallahi Yaya Inaga yanka ni ne kuma kawai bazeyi ba” Amirah ta fada hannu aka tuni idonta ya fara tsiyayar da hawaye lokacin data ci karo da murfin Wardrobe din Bashir da aka fashe ga kan Mirrow dinsa wayam babu ko kwalli suma an kwashe wai iya abunda idonta ya gani kenan Allah kadai yasan dame dame aka dauka kuma. Ita kanta Addah seda hankali ta ya qara tashi dan duk a zatonsu tunda qofar na kulle bala’in be taba can ba basusan ta nan Al’amuran suka fara sauka bama 😂 “Dallah can ki mana shiru aikin gama dai ya riga ya gama duk ma abinda za’ayi daga baya ne me afkuwa ta afku ni dai yanzu ciro sarqar nan ki gani mu Adana su kafin suma bala’in ya dirar musu nidai wannan Ya dakika haifa kamar yar Allah bani ta jefa mu a masifa (babu ruwan Iman ku dai kuka jefa kanku uku ah to 😚😚). Wata sabuwa inji yan caca ai seda Amirah ta shafa wuyanta taji wayam sannan ta ankare babu wannan sarqa dama babu batun awarwaro tun tuni su ta ankare da sun zube amma a sannan bata su takeyi ba, yanda take rarraba ido ne yasa Addah a fusace cewa “bazaki ciro bane kike tsareni da ido ko kuma daman ta kice” ta wara idonta akan Amiran. “Shikenan ashe ba Mariya kadai ce take da rabon zuwa Birsin ba harda ni wayyo Allah na na shiga uku na lalace wannan wane irin bala’i ne suke bibiyata sahu sahu ni fatu?” Kuka riris Addah takeyi, sarqar da hayota tayi dakyar Hajiya Inna Qawarta tayi mata hanyarta a gurin wata qawarta. Seda ta bada dubu dari kudin Haya sannan ta bata takaddun gidanta dashi kadaine kadarar datayi mata saura a yanzu akan idan wani abu ya samu sarqarta sedai a siyar ta cire kudinta ta bata chanji to a qalla da sarqar da abin hannu sun kai na kusan miliyan biyu gashi babu ko daya se warin dan kunne daya ne a kunnen Amiran to ita kuwa yau ta shiga ina taga haske wannan Asara kan asara babu biyan buqata? Rasa me bawa wani haquri akayi cikinsu ita Amirah tana kukan haduwarsu da Bashir ita Addah tana na sarqa seda suka gaji dan kansu sannan sukayi shiru kowa tayi wanka suka shiga gyaran guri kafin kuma su san abinyi a gaba. Tsakar gida suka watso sharar Addah ta fita ta samo yara suka shiga sharar tsakar gida aka tattare kujeru masu lafiya aka ware karyayyu gefe suma kafin masu su suzo ayi lissafi haka suka tattaro kwanuka da kulolin abinci suka bayar yaran suka wanke komai bayan yaran sun gama ta biyasu suka koma ciki sukayi zugun zugun. Babu wanda yayi tunanin zuwa duba halin da Iman take ciki a cikinsu tunda dai Ummi ta gaya musu tana Asibiti shikenan daman ko wancan kwanciyar da tayi bayan an sallamota ba kullum take zuwa ba, da aka fara bata abincine taje zuwa tayi pumping Nonon da za’a bata daga baya ma a gida takeyi ta zuba a Container da suke bata akai shikenan. Seda sukaji Yunwa na neman hallaka su suka nemi abinci suka ci suka ci gaba da zaman jiran tsammani kuma. A bangaren Bashir kuwa Tun a daren Dr Ishaq ya kira yana zuba masa ruwan masifa kamar shine Amiran, bayan sun gama ya kira Naziru ya gaya masa yanda akayi harda qarin maggi da gishiri abinda ya qara tunzura zuciyar Bashir din kenan ya shiga kiran wayar Amirah amma Allah ya taimaketa wandaya sace ya kashe dan kuwa daya sameta a waya Allah kadai yasan yanda zasu kwashe a daren, Ganin be sameta seya maida akalar kiran kan Asma’u. Tana nade akan gadonta bayan ta gama shirin bacci har sannan Bata bar mamakin abubuwan da suka faru ba yau a gidan nasu kiransa ya shigo. Daga yanda ya amsa sallamarta tasan ba qalau ba se tayi shiru tana jin yanda yake magana ta inda yake shiga bata nan yake fita ba masifa yake mata akan me yasa tun farko bata gaya masa zasuyi taron sunan ba. Galala ta saki baki tana sauraronsa ganin fa ba shiru zeyi ba yasa ta katse shi da cewa “Dakata Malam wai ko baka san wa kakira bane To Asma’u ce ba Amirah ba”. Cike da masifa yace “oh maganar banza zaki gayamun kenan ce miki nayi bansan wanda na kira ba ai koma mene laifinki ne tunda kina gaba da ita ya kamata ki nuna mata abinda yake daidai da ba daidai ba data tace zatayi taron seki hanata tunda kinsan bana so”. “Ashema ni ce gaba da ita, meye darin gami na da ita da zatayi abu na hanata ko an saka ni a ciki ballantana kuma nima gani nayi anayi. Kuma da kake maganar daidai ko rashin sa qarewarta naga da sa hannun yan uwanku tayi komai danginku kaf babu wanda bezo gurin ba su a cikinsu babu wanda yasan daidai kenan, kuma naga ai ita da uwarta suka shirya kamai se kuma kazo kana gayamun wani qabali da ba’adi dan Allah in baka da abin fada ni bacci zanyi kabarni inji da hayaniyar da suka jazamana a gida har sha biyu sannan muka samu salama Allah yasa kar cikin dare kuma wata sabuwa ta taso”. Jin da yayi ta fitittike masa yasan halin Ma’u sarai itama ba baya bace seya sassauta muryarsa yana cewa “Kina nufin dangina ne basu san daidai ba kenan, kuma da kikaga za’ayi ai seki kirani ko a wayane tun da safen ki gayamun ni na tsaqatar amma fa kalli duk abinda akayi se a gari naji ke baki kirani da kanki kin gaya mun ba”. “Nidai ai kasan ban iya sa ido da munafunci ba bare kace duk abinda wata takeyi sena kwasa na gaya maka, bayan haka tsakanin ku can nasan koda yardar ka suke abunsu? Yanzu dai aikin gama yarigada ya gama mudai ka tiro azo a chanza mana keys din gidan nan kar muje wani ya sata shima muna zaman mu a ringa diro mana da daddare tunda yau gungun barayi aka hada a gidan”. Dagaske dai yaga alama Asma’u neman sa take ta magana tunda gashi shida ya kira yayi fada amma ta samu se gasa masa maganganu takeyi dan haka yace mata “Shikenan, da safe ki daure ki leqa Asibiti kiga jikin Iman koda wasa karki bari ta sake taba mun yarinya..” “Nan fa daya, zuwa dubata zanje da sassafe ma kuwa insha Allah amma batun kar uwarta ko wasu su tabata be taso ba ka nemi wani ka saka wannan aikin amma bani ba. Ba abinda yai mun zafi da lamarinsu ka sani” Asma’u tayi saurin katse shi. Se da yaja kwafa sannan yace mata seda safe suka ajiye wayar ta gyara kwanciya tana cewa “Haka kawai can ta qare muku kunfi kusa ni ai yar kallo ce irin haka kuma yanzu aka fara duk abinda ba’ayi shi dan Allah ba ai qarshen sa kuwa dana sani ne fal, Allah sarki sun jawa yarinya bata ji ba bata gani ba zanje na ganota da safe insha Allah badan halinsa ba” tana motar taja bargo tayi kwanciyarta bacci ya dauketa. Bashir kuwa yanda yaga rana haka yaga dare, ina ace gobe Friday ce ba Alhamis ba amma yanzu dole ya jira se goben ya tafi Gombe kafim nan yasan matakin da ze dauka akan daga Addan har Amiran. Su Addah dai wunin Alhamis ziri cikin rashin nutsuwa sukayishi, masu kujeru sunzo sun kwashe akayi lissafi kusan dubu Ashirin na wadanda aka lalata a drawer dakin Bashir Amirah ta lalubo aka biya DJ ma yazo ya kwashe sifikunsa yanzu ya rage me sarqa da kuma masu qananan bashi da basu biyo sahu ba. Har dare suna zaune suna saqawa da kwancewa babu wanda ya sake zuwar musu ko Dada da tayi zaton zatazo shiru har dare basu ganta ba gashi babu waya da alama ma su kafai suka wuni a gidan dan tun Azahar sunji fitar Ma’u itama bata leqa ko jaje tayi musu ba. Amirah shirun Bashir yafi daga mata hankali koda yake ta ina ze kirata ma tadai tabbatar gobe Juma’a ze zo Gombe Addua dai tayi tana kan yi ta Allah ya rufe bakinsa akan wannan Abu to bamu sani ba kota karbu Allah dai ya kaimu juma’ar mu gani. Washe gari kuwa qarfe hudu yana Gombe, kai tsaye Asibiti ya nufa a can ya tarar da Asma’u data sake komawa dan halin data ga yarinyar jiya ya tsaya mata arai matuqa. Ganin da Bashir yayi wa Baby Iman ya sanyaya masa jiki dan ya ma cire rai da yarinyar. Wani kalan numfashin wahala takeyi idan ta jashi kamar qirjinta ze burma, sanyi ya mugun shiga jikinta ga rashin kaita da wuri da sukayi. A hanya Asma’u ce tayi ta qarfafa masa guiwa ganin yanda yayi shiru damuwa qarara a fuskarsa, tasan Bashir yana son yaya amma wannan yarinyar ma dai daban take a zuciyarsa taga alama to amma ya zeyi abinda Allah ya qaddara dole ya faru. Suna isa gida ta shige part dinta shi kuma ya nufi na Amirah da tundaga qofa yake jiya hargagin muryoyin dabe tantance kona waye ba. Kallo daya yayi musu Addah, Amirah se mata biyu dabesan ko su waye ba ya dauke kansa kai tsaye ya wuce dakinsa yana jin Addah na cewa Alhamdulillahi ga me gidan ma yazo amma be tsaya ba, to ya tsaya yayi musu me tsaf dai ze iya hada su duk hudun ya nada musu na jaki ko ze rage wani abu daga baqin cikin da yake ji a cikin zuciyarsa. Murmushin takaici ya saki lokacin da idonsa ya sauka kan aika aikar da akayiwa dakin, kansa ya girgiza kawai ya juya ya fito daidai daya daga cikin matan tana cewa “Wallahi daga nan se kotu zan wuce dan bazan tsaya ma yansanda su batamun lokaci ba, ni zaki yaudara ki bani takaddun bogi? Seda na nemi Dillalai muka je suka ga gidan ayi masa kudi muji idan chanji zan baki ko ciko zaki mun aka ce na bada takaddu suna dubawa sukace mun na bogi ne da an riga an siyar aka gano ni se anyi qarata to wallahi kafin ki kaini prison ke zaki fara zuwa. Ni daman jikina seda ya bani tun zuwanku amma Innah tace mun babu matsala to kuwa ku zaku dauki Asara ki riqe warin dan kunnen ki siyar kya samu na daukar lawyer dan nidai kudina cis na sani gobe ma ku sake daukowa kanku abinda yafi qarfin ku kuce se kunyi”. Jin fitowarsa tasa Addah tun kuda Amirah tayi qasa da murya tace “ kiroqeshi yai mata magana in ba haka ba mun shiga uku wallahi banida sauran wani abu kuma”. Bata so ba amma ya zatayi seta tare gaban sa ta fashe masa da kukan da inda haka kawai ne kowa tayiwa shi seya tausaya mata dan kuka ne da kana jinsa kasan meyinsa yana cikin tashin hankali ne ta shiga cewa “Dan girman Allah yaya kasa baki matar nan tayi haquri ta bamu lokaci za’a biyata.....” “Dauuu” ya kwasheta da marin da kaf seda suka rufe fuska dan ji sukayi kamar su akayiwa bata dawo daga gigitar ba ya sake sauke mata wani a daya bangaren kafin ya hankadata gefen kafin ya nunata yace “Na rantse da Allah idan na sake shigowa na tarar dake a gidan nan sena illa taki, ya fice yana huci tabbas kuma idan ya sake tarar da ita se ya mata dukan mutuwa yau a gidan nan.🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 WATA KISHIYAR 🥰👹 (ALKAHIRI CE KO SHARRI) 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 Na Maryamah_Mrs AM (Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah) *INA MANYAN MATA NE* *INA MASUSON FARA SANA'A* *HANNUR COLLECTION tazo maku da alkairi domin qarin bayani kobiyo💥🔥💥*Munada amarya da uwargida package wannan package ya* *qunshi,abubuwa guda goma* *maganin sanyi da basur* *Nasha da madara* *Nasha da lipton* *Na dahuwar kaza* *Na tsarki* *Nasha da kankana* *Garin tsumi* *Hadadden tsumi* *Na matsi* *Nahadawa da zaitun* *Muna saida tahnia me gyaran aure* *Akwai kayan ORIFLAME* *Akwai kayan GHT* *Akwai kayan faforlife* *Akwai chocolate da coffee na mata* *Akwai turaruka,sabulai mayuka da duk wani kayan gyaran jiki da aure* *Munada dogayen riguna sari,yadin hijab materials,atamfofi,shadda,laces dss* *Albishirunku ina registration din ORIFLAME, GHT, FAFORLIFE ,Duk kayanmu farashin sarine,kuma muna aikawa kowanne gari cikin aminci* https://wa.me/message/3BCXWNGTI7ILC1 Page 21 Ihu Amirah ta fasa na zafi biyu ga mari ga maganar tafiya gida, me yake nufi badai sakin ta Bashir zeyi ba? Wannan tunani yasa bata san sanda ta bishi da gudun bala’i ba tana kiran sunan sa lokacin harya kai kan Balcony Ma’u ze shiga. “Na rantse da Allah kika qaraso nan Amirah sena karyaki, karayar da babu me iya gyara miki ita kuma karki bari na fito kina cikin gidan nan idan kuma so kike ki qure ni shikenan” ba Amirah da yai wa maganar ba hatta da Ma’u dake cikin palour seda ta tsorata, yanda yai maganar cikin tsananin masifa idanunsa sun kada sunyi jajir harwata qwallar bala’i ce ta taru a cikin su yasa ta kasa tunkararsa harya haye sama yana hada stair case bibbiyu. Amirah kuwa Kamar wanda ya sakawa pause haka ta bishi da kallo kafin ta juya zoqai zoqai ta koma part dinta tana toshe baki gudun kar ma sautin kukan ta ya fito ya dawo ya tattaka dan tayi bala’in tsorata da hanayinsa . A qofa suka hade dasu Hajia me gwal data bi Amiran da kallo kafin ta ja uban tsaki tana kallon Amiran tace “kadan ma kuka gani Allah yasa shima ba wata satar aka qunduma masa a daki ba, kinga Hajia muje nidai na gama magana in sammaci ya iso ma hadu a kotu kawai” ta yi waje abunta tana ci gaba da yada musu da magana. “Toh Fatu Allah fidda A’i daga rogo mun tafi” Hajiya Nuratu qawar Addah datayi musu hanyar sarqa ta fada dan ita kasa magana tayi ma tunda sukazo se ta juya tabi bayan Me gwal itama. Se Addah ta kalli Amirah data zube a qasa tana kecewa da sabon kuka. “Kukan me zaki zauna kiyi, shiga mu hada abinda zamu dauka muje kawai dan in kin zauna nasan ba mutunchi ne dashi ba ze miki abinda ya fada ne toh gara mu tafi gaban uwarsa duk abinda za’ayi akan idonta”. Dakin Amiran Addah ta shige tana sababi ta fara tattara komatsanta zuciyarta ko kamar tayi bindiga wannan bala’i har ina? Har Addah ta gama ta yafo gyalenta Amirah na zaune tana Kukan da bashi da Amfani. “Au kina zaune ko to shikenan ni kinga tafiyata se kiyi tayi idan kuka ze miki magani” Addan ta fada tana nufar qofa, se Amirah tayi saurin riqota cikin kuka tace “Addah idan na tafi ina zani? Kinsan dai idan na biki gida qila sena gwammace hukuncin Yaya akan na Baba to ina zanje” “Gidan uban sa mana, ni daman nace ki bini gida ne gaban Nafi zaki je ki zauna duk ma wacce za’ayi ayi da wanne zanji idan kin bini gidan da nawa tashin hankalin koda Masifar Ubanki”. Daki Amiran ta wuce ta shiga hada kaya a akwati tana kuka amma taji dama daman cewa gurin Dada zata tafi dan dai ko hauka tayi bazata je gidan su da sunan itace me laifi ba yanda Babansu yake a zuciye da lamarinta harda Addan ma tasan qiris yake jira wallahi ya samu dama akansu yaci musu mutunchi. Tare suka fice kowacce da jaka tana Ja Addah na gaba taba ta sababi ko tausayin Amiran da haryanzu jikinta bawai ya warke bane bataji ba bare ta karbar mata uwar akwatin da take ja ita dai masifarta kawai take, seda suka ci tafiya har bakin titi kafin suka samu Napep da ze kaisu gidan su Bashir. A qofar gidan Dada me Napep ya ajiye su, Amirah da tunda suka taho bata dena kukan nan ba kasa daukar jakarta tayi se me Napep din ne ya shigar mata da ita har tsakar gidansu Bashir din. Alhaji Ahmadu na zaune a tsakar gidan akan Kekensa Naziru da physiotherapist da yake dubashi suna tsaye a kansa bayan sun dorashi akan keken dan gama Exercise dinsa kenan suka shiga Addah na Masifa Amirah na kuka gaba daya suka juya suna kallonsu, wuce su Addah tayi bata ko kalli barin da suke ba itama Amiran ta rufa mata baya sallamar me Napep ce ta saka su Nazirun juyawa daga kallon su Addah. Akwatin Amirah ya dire musu ya kalli Naziru yana cewa “yi musu magana su bani kudina na wuce dan Allah” “Nawane kudin?” Naziru ya tambaye, bayan ya fada masa ya zaro daga aljihunsa ya bashi. Me Napep na fita shima Physiotherapist din yayi musu sallama ya tafi dan ya gama aikinsa, kama keken Naziru yayi da niyyar maidashi dakinsa ya dakatar dashi da cewa “Kaini daki Naziru” Alhaji Amadu ya fada dukda yaso ya zauna a tsakar gidan yasha iska amma zuwan Fatu baze barshi ba, yanzu haka yana jiyo bambaminta daga palour Dadan amma baze kula suba dama ya fada musu ai ayi dai su gani idan Tusa zata hura wuta kuma gashi da alama dai tun ba’aje ko ina ba da sun fara karbar sakamakon abinda suka aikata. A palour Dada kuwa Addah ce take sababi kamar zata hadiye harshenta, “Daga abin arziqi se ya zama na tsiya, yar nan naga kuma jikar kuce yanzu ta girma ace cikin yan uwanta kaf itace ba’ayiwa taron suna ba ai setace ba’a qaunarta. Ni kinga tafiyata gata nan ku qarata nima inje naji da masifar nawa mijin dan nasan su Binta munafukai sun kaimasa rahoto tun jiya” Addan ta fada tana kwasar jakarta data watsar tun shigowarsu, bata saurari Dada dake mata magana ba ta fice abinta ranta tana qissima duk abun Bashir be isa yayi a gaban Dadan ba tasan zata ta ka masa burki. Bayan Fitar Addahne Dada ta mayar da hankalinta kan Amirah dake durqushe har sannan tana kuka, “Amirah yanzu kina ganin biyewa Addah da kike kuna aikata duk abinda kuka ga dama daidai ne ko? Ke bazakiyi hankaliki zauna a gidan auranki lafiya ba se ki ringa biye mata kina saba umarnin mijinki to ki sani dai shi Allah babu ruwan sa, idan ya tashi ke kadai ze kama da laifin saba umarnin miji banda Addah tun wuri idan zakiyiwa kanki fada ki bi hanyar gaskiya kiyi dan nidai babu ruwana da duk wani shirginki yanzu” tana gama fadan haka ta miqe ta shige dakinta ta bar Amirah na cigaba da share hawaye. Sosai ranta ya baci da abinda ya faru a gidan Bashir din, ta rasa meyake damun yayarta ta har ji takeyi daman itace gaba da Addah qilan da ta ringa dorata akan hanya ta dena wadannan abubuwan zubda mutunchin da take yi amma ya zatayi sedai tayi ta binta da addua kawai. Wayar Bashir ta kira bayan ta shiga dakin, lokacin yana tsaye kan Asma’u yana zuba mata ruwan tijara kaman itace Addan ko Amirah. Yanda yake bambamin tasan ransa yakai qololuwar baci yasa bata tankashi ba ta sunkuyar dakai kawai tana jinsa saboda Bashir Miskiline, ko zeyi rashin mutunchi a ruwan sanyi yake dafa mutum. Auran Amirah nema taga yana neman ya mayar dashi mafadaci tunda yanzu yana iya bude baki yai fada idan an masa laifin sabanin da da ko laifi ta masa sedai ya dauki gaba da ita ko yayi ta gasa mata aya a hannu ta ruwan sanyi yanda ko qararsa ta kaiwa wani baza’a yarda ba dan babu shaida. Sau biyu wayar tana qara amma be kula ba se ana ukun ya zarota da niyyar kashewa dan a lokacin bayajin ze iya magana da kowa sedai ganin suna Dada yasakashi saurin dagawa bayan ya zauna akan kujera dan Uwa ba wasa ba, a magagin mutuwa ne kadai yakejin baze iya amsa kiranta ba amma inda yaji ya kuma gani ko halin yaya ne seya amsa idan yaso ya bata uzuri ya kira daga baya. Gaisheta yayi ta amsa tana karantar bacin rai a cikin muryarsa, kiran da tayi masa ta so ta tambayeshi ne shiya tura Amirah gida amma yanayinsa yasa ta fasa dan tasan qarshe wani laifin zata jangwalo mata yace ta kai qarar sa danhaka se tace cikin taushin murya “Bashari idan babu abinda kakeyi kazo gida yanzu mana ina son magana da kai” “To Dada gani nan zuwa” ya fada yana miqewa dan daman yana da niyyar zuwan a yanzun yaje ya gaya mata abinda Addah da Amiran sukayi dukda yasan ta sani amma dai gara yaje da kansa yaji ko harda sa hannunta a ciki. “Ku shirya gobe da safe zamu wuce kuma a mota zamu tafi” ya fada yana kallon Asma’u da kanta yake a sunkuye har sannan kafin ta dago harya kai qofa, kallonsa tayi tana zare ido a fili ta furta “kan bala’i Gombe to Lagos a mota” miqewa tayi ta bi bayansa da sauri dan baza’ayi wannan gangancin da ita ba, haka siddan Allah ya rufa musu asiri ya basu yanda zasuyi subi jirgi se yace a mota zasu tafi kamar ma itace tayi masa laifin kenan aikuwa wallahi bazata sabu ba shidai ya tafi su zasu jira Moday din su tafi dan daman already sun siyi tickets ta barsu a bude saboda bata san sanda zasu tafi ba. Ya kunna motar yana qoqarin bude get ta shige ta zauna, tana jin yanda yake kallonta a jikinta amma taqi daga kai bare su hada ido dan gara aje gaban Dadan itama ta saka baki a wannan al’amari kar goben tayi ma suzo suna wallahi tallahi. Tafiyar kamar ta kurame harsuka isa gidan Dada, ta rigashi shiga gidan dan sanda suka isa daidai ana kiran Magriba shi seya tsaya ya daura alwala ya shiga masallaci ita kuma ta shige gidan. Amirah na zaune har sannan a palour ta dena kukan dai se ajiyar zuciya take fuskarn nan ta kumbura tayi jajir abinka da Farar fata ansha kuka. Kallon kallo sukayi da Asma’un kafin ko wacce ta dauke kanta gefe Ma’u ta nemi kujera ta zauna tana zaro wayarta daga aljihun Diguwar rigar jikinta ta danna Number qaninta dan karya mayar da yara gida ba kowa da yake suna nan Babban gida tunda safe ta kawo su. Fitowar Dada da hijabi a hannunta da alama itama alwalar tayo ta kalli Amirah tace “au haryanzu kina zaune a qasa sanyi na shigarki da danyan jiki se ance ki tashi ko? Kiyita zama jikinki ne ai bana wani ba” ta fada tana zura hijabinta inda Abun sallarta yake ta nufa se a sannan ta ankare da Asma’un dake zaune seta sassauta fuskarta tana cewa “Aa Asma’u Yaushe kika shigo” “Yanzu na shigo Dada ina wuni” Ma’u ta fada tana zamowa daga kan kujerar, seta amsa mata tana cewa “Ki shiga kiyi sallah bari nima nayi gashi can har an yi raka’a daya” ta tayar da Sallah ita kuma Ma’u ta miqe ta shiga dakin Fainusa dukda ba sallar zatayi ba seta nemi gefen gado ta zauna tana duba wayarta. Batafi minti uku ba Amirah ta shigo tana jan akwati, kallo daya tayi mata ta ci gaba da dannan wayarta ita kuma ta jingine jakar tana dafe gefan kanta dayake sara mata ga wani jiri jirin yunwa dake son kayar da ita haka ta daddafa ta shige toilet dan wanka take son tayi. Da ruwan zafi sosai ta gasa jikinta dan yanzu base ance tayi ba tsamin jikin kadai yana sa ta shiga hankalinta ta gargasa jikin gashi taci sa’a jikinta me kyau ne tuni dinkin ya kame in banda ma kata’in da take jefa kanta aida ta fi haka warwarewa. Sanda ta fito har sannan Ma’u na nan ta sake bararrajewa akan gado da alama waya takeyi, a darare ta ja akwatinta ta ciro duguwar riga da undies ta sake komawa toilet din ta sako kayan ta dauro alwala ta fito daidai sanda Dada ta leqo tana kiran Asma’u, bayan ta idar tana zaune ita ba lazimi ba tayi zuru akan sallayar aka bude qofar. Dadan ce ta sake dawowa, cikin bacin rai tace mata “wai bazaki tashi kije kici abinci ba Amirah ko kin manta jego kikeyine idan kuma wani kike jira ya kawo miki se ki zauna”. Yunwa takeji ta gaske dan haka ta miqe salaf salaf ta fito palour inda take jiyo muryar Asma’u da Naziru da alama hira suke, a tsakiyar palour ta tarar dasu, Asma’u nacin tuwo da miyar kuka shi kuma yana mata hira, wuce su tayi ta nufi kitchen tana kaiwa daidai qofar Bashir ya shigo da sallama ciki ciki ai se kawai ta qame a gurin ta kasa gaba ta kasa baya, bata so su hadu ba, a yanda ta tsara in ta shige daki bazata sake fitowa ba abincinma idan an gaji a ringa binta dashi har seya bar garin gashi yanzu tun ba’aje ko ina ba sunyi kicibus. Shi kuwa Bashir bema lura da ita ba ya nemi guri kusada Asma’u ya zauna, Dada ce ta shigo itama daga Gurin Alhaji tan cewa Naziru yaje Alhajin na kiransa. Kallon Amirah dake tsaye kamar an dasa ta tayi tace “Ke kuma lafiya kike tsaye kin qi gaba kinqi baya” kidan duma zuciyar Amirah ta shigayi daidai sanda ta waiwayo idanunta suka hadu dana Bashir, wani mugun kallo ya aika mata dashi daya saka hanyar cikin ta kadawa bashiri ta shige kitchen din ta fara matsar kwalla. “Me yarinyar nan takeyi a gidan Dada oh danace ta tafi shine ta taho gidanmu saboda raini ko tam” ya fada yana sakin qwafa dagani yama rasa me zeyi kawai. Seda Dadan ta zauna tana kallonsa tace “Dalilin kiran dana maka kenan ai nima ina zaune sukazo ita da Addah sunce kace ta tafi gida” “Eh nace ta tafi gida Dada wannan yarinyar bata da mutunchi ta raina ni ban isa na bata umarni tabi ba se abinda ta rayawa kanta, seda na gargadeta nace baza’ayi taron sunan nan ba amma saboda ta nuna mun ban isa ba taje tayi” Bakiga dakina irin barnar da akayimun ba iya abinda na gani kenan ma Allah kadai yasan me aka dauka a ciki tunda ban duba ba, shikansa gidan karkiso kiga yanda suka maidashi. Ga Iman can a Asibiti babu tabbacin ta tashi sannan saboda ma sun raina mun hankali na dawo na tarar da wata mata ta biyo karbar bashinta wai ni suke cewa na roqar musu ita tayi haquri. Wallahi Dada Idan yarinyar bata kama gabanta ba ta bari hannuna ya sauka akanta sena mata dukan mutuwa wallahi....” “Babu inda zataje kar kuma ka fasa mata dukan mutuwar” Alhaji Amadu da Naziru ya turo akekensa ya katse wa Bashir Hanzari, se suka juya gaba daya suna kallonsa bayan da Nazirun ya kawo shi tsakiyar Palour. Kallon Bashir da yake ta qoqarin hadiye malolon daya tokare masa wuya Alhajin yayi ya girgiza kai kafin ya Kalli Dada yace “Ina Amiran take kirawo ta nan” Miqewa Dadan tayi ta shiga kitchen suka fito tareda Amirah dake risgar kuka kamar an ce mata Addah ta mutu ta nemi can gefe ta zube tana ci gaba da kukanta. Kallonsu Alhaji Amadu yayi daya bayan daya ya tsaida idonsa akan Asma’u da tunda ya shigo ta tsame hannunta daga cikin tuwon ta gyara lullubinta, se ya saki wani murmushi da bazaka tantance na mene ne ba ya kalli Bashir yace “A lokacin da zaka auri Amirah me nace maka” Sunkuyar da kai Bashir yayi yana cigaba da komawa da abinda yake taso masa idanunsa sun kada sunyi jajir, “Ba magana nake da kai ba” Alhaji Amadu ya katse shi cikin daka tsawa se Bashir din ya dago da sauri yana kallon mahaifin nasa, kalaman sa suna dawo masa daya da daya a kwakwalwa ranar dayazo yace masa ze qara aure ze auri Amirah diyar Addah tamkar a yanzu yake fada masa su. “Sharadi zan kafa maka Bashir, yanda ka dakko auran nan to ka tabbata Babu Yaji har qarshen rayuwarku. Ina raye ko bana raye idan ka rabu da yarinyar nan ban yafe maka Ba Bashir kaje ku zauna duk wuya duk dadin da zata zo maka dashi” “Kace babu Yaji babu saki” Bashir ya fada da kyar kamar me ciwon haqori. “Madallah, ka tashi ka dauki iyalan ka ku tafi aje ayita haquri, daman shi wanda ya siyi rariya ai yasan zata zubda ruwa”. “Asma’u ya gidan ya Mutane nawa dazu sun shigo Ina bacci kafin na yunqura kuma suka fice” Alhajin ya fada yana maida hankalinsa kan Asma’u. Seta sunkuyar da kanta tana dan murmushi tace “ lafiya lau Baba suna Babban gida ai yanzu zaka gansu ma tunda na fada musu ina nan”. “To masha Allah, yaushe zaku koma hutu ya qare ko?” “Eh Baba daman litinin muka shirya dazu kuma yace wai gobe zamu tafi amma a mota gashi bamu qarasa shirye shiryen mu ba” Asma’u ta fada tana janye fuskarta gefe dan karma su hada ido da Bashir. “Wane irin tafiyar mota kuma ana zaune lafiya, ko a zamanin da da muke tafiye tafiyen ai munji jiki bare ku yanzu da baku saba ba ga yara kuma, kudai jira litinin din dai kubi jirgin safe kamar yanda kuka saba, Allah yayi muku Albarka yaci gaba da ruqo da hannunku” Baban ya fada suka amsa gaba daya da Amin. Naziru na zaune kamar ya buga tsalle tsabar yanda da Al’amuran suka masa dadi, yanda aka tilasta Yayan nasa maida Amirah gida ya mugun masa dadi aransa fadi yake “Allah ya qara ai kadan ma ka gani in bakayi da gaske ba wataran se sun saka a kulleka kana zamanka da matar rufin asiri ka kwasowa kanka kaska. Baban ne ya katse shi yana cewa “zo Naziru ka maidani na kwanta kaji Dare ya farayi” yayi musu sallama Naziru ya maidashi. Kamar kurame haka sukayi jugum jugum a gurin, Amirah dai a tsorace take da hukuncin na Baba dan data bi shi su koma gara ta zauna agidan kai gara ko can gidan su ne ace ta tafi ita kuwa Ma’u ba abinda ya shalleta masifa ce dai tasan zeyi ya gama tunda dai an rushe zancen mota ai shikenan, shikuwa oga Bashir har wata zufa yake kamar wanda ya hadiyi kunama. Makwallaton wuyansa se sama yake yana qasa ya kasa furta komai se “hmmm” kawai. Miqewa yayi dakyar ya iya ce musu su tashi su tafi ya fice ko sallama be yiwa Dada ba, Asma’u ce ta fara miqewa tayiwa Dada seda safe tabi bayansa Amirah dai ko motsi ta kasayi. Kallonta Dada tayi tace “ki tashi ko so kike ki qara wani laifin a gurinsa” ai kamar tana jira ta sake fashewa Dadan da kuka tana cewa “Dan girman Allah Dada ki roqi Baba Ya barbi yau na kwana a gidan nan idan sun koma Lagos sena tafi wallahi idan na bishi yau kashe ni ne kawai Yaya bazeyi ba Dada dan baki san irin abubuwan da nayi masa bane” ta qarasa tana sake rushewa da kuka. Miqewa Dada tayi tana cewa “koma mene ai ke kika ja gara ki tashi ku tafi dan nima bazaki ja mun wani fadan a gun Alhaji ba kije kawai ba bu abinda zeyi miki” tayi shigewarta daki ta barta. Amirah tana kuka tana komai ta hado jakar Naziru ya daukar mata suka fita yana mata dariyar mugunta, dakyar ta bude bayan motar ta shiga dan tuni Asma’u ta kame a gaba abunta cikin ranta qal da wannan abubuwa da suke faruwa. Afuwan 🙏🙏🙏🙏qundumemen uzuri ne ya riqeni kwana biyu amma komai ya dawo daidai zaku ci gaba da jina insha Allah 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 WATA KISHIYAR 🥰👹 (ALKAHIRI CE KO SHARRI) 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 Na Maryamah_Mrs AM (Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah) Wattpad @MaryamahMrsAm Page 23 Ranar litinin kamar yanda muka saba tunda muka yi sallah muka hau wanka da shiri dan jirgin bakwai za mubi ga tazarar zuwa Airport Akko dago Gombe. Shida bata qarasa ba muna bakin Sienna da ake kwasar mu in munzo ko zamu tafi. Yaran sun gama shiga ina tsaye daga qofar ina jiran Bashir da yake qara dudduba cikin gidan kafin ya rufe ina murmushin hirar su Naziru da Ahmad yanda yake biye masa kamar wasu Abokai. Ba dade wa Bashir din ya fito yasha Suit kalar Dark Blue farar cikin nan har wani daukar ido haskenta yake, seda yayi Addu’a ya tofa kafin yaja qofar ya rufe se ya nufi part din Amirah yana cewa Nazirun “ka kunna motar mana ka tsaya kana surutu” ya shige nida Naziru muka rakashi da ido. Ashe tana gidan nayi zaton tun jiya ta wuce gida yanda ta saba ana washe gari mu tafi take farayin gaba. Cikin motar nima na shiga na zauna ina duba agogon wayata ganin shidan ta yi harda minti biyar. Bashir kuwa a daki ya tarar da Amirah hankali kwance tana baccinta, shurin qafarta yayi ta farka a firgice tana zare ido ganinsa yasa tayi saurin nutsuwa ta shiga gaishe shi. Be amsa ba ya cilla mata rafar 200 dubu Ashirin kenan yana cewa “Zamu tafi Naziru ze kawo miki kayan Abinci, wallahi koda wasa kika saka qafarki a qofar gidan nan ki tabbata kin fita kenan mtsw” ya ja tsaki ya juya dan har yanzu bala’in haushinta yake ji gashi an hanashi hukuntata. Harya kai qofa ta zaburo ta biyo shi da sauri dan kuma yanzu hankalin ta ya koma kan yarta, ga Nononta da suka dameta da ciwo saboda cika, saurin ce masa tayi “Dan Allah yaya zanje naga Iman” tayi maganan cikin rawar murya kaman kuwa yana jira ya jefa mata wani mugun kallo kafin yace “Ya zama kuskure na qarshe da zakiyi tunaninyi ki sake dora hannunki a kan yarinyar nan, da kina sonta kika jawo mata ciwo sannan tunda aka fita da ita daga gidan kin tambayi yanda take bare kije ki ganta? Idan ke bakya qaunarta ni inasonta dan haka nayi miki iyaka da ita kota warke bazan dawo miki da ita ba tunda bake kadai bace zan kaiwa wadda zata kular mun da ita” yana gamawa yasa kai ya fice ya barta tana rusa kuka. Abinda baze ma yiwu ba kenan taya ze raba ta da yarta ce masa akayi bata sonta? Ai tasan tana Asibiti kuma a kwanakin in ma tace zataje ba bari ta zeyi ba shi yasa amma wallahi bazata yarda ba dole ma ya barta ta fita kai ita bama zata iya zama a gidannan ba sedai ta tafi gidansu, ta yarda acan din bazata fita ko ina din ba amma badai a nan ba. Tana son magana da Addah amma babu hali, ita ba waya Addah ma haka dukda da tana da wayar samun Addah bazeyi wahala ba ko a wayar Ummi ne. Tunda suka rabu a gidan Dada basu sake magana ba bata san yaya Addah ta qare a nata gidan ba tilas kuwa tana buqatar magana da ita, ya dai tafin ko Nazirun in yazo anjima ta roqeshi ya siyo mata ko Key pad ce a cikin kudin da Bashir din ya bar mata. GIDAN ADDAH Ranar bayan Addah ta bar gidan su Bashir Napep ta hau ya kaita gidanta. Alhaji Murtala na tsaye a qofar gidan da wasu mutane su biyu Addah ta sallami me Napep zata shige ya dakatar da ita. “Yawwa ga Hajia Fatun ma ta dawo” ya fada yana nuna musu ita. Se Addah taci burki ta bisu da kallo daya da daya amma bata ga fuskar data sani ba dan haka se ta saka kai ciki kamar bataji maganar da Alhajin yayi ba harta tura get ya dakatar da ita dacewa “Wallahi kika shiga gidannan se ranki yayi mummunan baci Fatu” Alhajin ya fada cikin kakkausar murya. Se Addah taja da baya jiki a sanyaye, to su waye wadannan kuma? Wane jafa’in ne ya sameta. Takadda daya daga cikinsu ya miqo mata yana cewa “Hajia gashi sammacine daga kotu ana qararki akan laifin damfara”. “Damfara?” Addah ta fada da qarfi tana dafe qirji tareda zaro idanu waje “Ni Fatu wana damfara?” Ta sake tambayarsu hankalinta in yayi dubu ya tashi. “Akwai bayanin komai a ciki idan kunje kotu zakiji cikakken bayani kafin sannan kina iya neman lauya da ze tsaya miki” dayan mutumin ya fada, sallama sukayiwa Alhaji kafin suka hau mashin din da suka zo suka bar Gurin. Addah data gama jiqewa da zufar tashin hankali ce ta kalli Alhaji Murtala da yake jifanta da wani irin kallo data fassara dana tsana da takaici yace “Daman na fada miki Fatu tun kina dauko magana kina cin riba wata rana se kin dakko ta wanda yafi qarfin ki. Se kije ki san yanda zaki kare kanki ko kuma ki fara shirye shiryen tafiya gidan prison tunda halinki yaja miki” yana gama fada ya shige cikin gida Addah ta rufa masa baya tana kuka kamar yarinya. Bata tsaya ba har cikin uwar dakinsa inda ya shiga, Hajia Binta yar tsakiyarsu na cikin Toilet tana wankewa taji shigowarsu da kukan Addah seta leqo tana cewa “Aa Alhaji lafiya waye yake kuka... Au Addah kece lafiya dai waye ya mutu?” “Kiga mutuwa akanki munafuka kuma duk sharrin da kuka kitsa masa sedai ya koma kanku” Addah ta fada cikin hargagi, dariya Hajia Binta tayi harda tafawa tana cewa “Ikon Allah se kallo, da alama dai bana an kwaso me zafi” “Fita ki bamu wuri” Alhaji ya katseta, seta hade fuska tana cewa “kamar yaya Alhaji in baku guri bayan ni nake da aiki ko Alfarma za’a nema ai ba ta haka za a zomun ba” kafin yayi Magana Addah ta tareshi da cewa “Alhaji muje gurina Dan girman Allah”. Shiru yayi kamar baze amsa ba se kuma ya miqe yayi waje ta bishi a baya yana jin Hajia Binta na fadar maganganun an shiga haqqinta dan ba haka taso ba, dayace ta fita zata fitan in yaso ta labe inda zata ji kan zancen tas gashi yanzu ta jashi dakinta. Addah kuwa tiryan tiryan ta labartawa Alhajin duk abinda ya faru da basussukan jama’ar data ci da yanda sarqar Hajia me Gwal ta salwanta dama yanda suka rabu yanzu ga zancen sammaci”. Takaici ya gama qume shi, shidai Fatu qaddarar sa ce amma ba komai lokaci yayi daya kamata yayi maganinta ko yaya me taji a jikinta amma yanzu bari a gama wannan case din tukunna. “Wanda yaja ruwa ai shi ruwa ze doka, takaddun gidan original suna hannuna gobe se muje gidan matar aje da Dillalai suyi masa kudi a siyar a biya kowa kudinsa, Allah ya tsare gaba idan zaki gyaru” ya tashi ya fice ya barta tana ajiyar zuciya dan bata zaci abubuwan zasu zo da sauqi haka ba. Ita yanzu koma menen ai a siyar a biya wannan jarababbiyar matar, ita da tunda Allah ya halicceta ko Police station bata taba zuwa bare a ganta a gaban Alqali gara komeye a siyar a bata kudin su rabu lafiya. Da wannan ta samu sa’idah har ta iya kwantawa tayi baccin gajiyar da batayi ba. ASMA’U Gaba daya sukuku mukayi tafiyar babu wani kuzari har muka sauka Ikko, a Airpot din muka rabu Drivern Bashir ya kwashe mu shi kuma ya dauki Shatar Taxi ya wuce office daga nan. Yanda nayi tsammani gida na nan ya hada kari, bamu ko zauna ba na rabawa ko wa aikin da zeyi, Ahmad da Muhammad da suka fara mun rigimar wai Yunwa dukda munsha Tea kafin mu taho ga Cake da sukaci a jirgi se na turasu gidan Anty suna fita kuwa se gasu sun dawo wai Aliyu da Jafar suje inji Anty, Breakfast ne data shirya mana ta basu wanda ya zamar mata kamar dole duk sanda mukayi tafiya irin haka bata gajiya seta kawo mana. Nan da nan kafin wani lokaci mun qalqale ko ina har kayan da muka dawo dasu kowa ya jere nasa na amfani kuma an adana su a inda ya kamata. Bayan Azahar Muna zaune muna huce Gajiya Anty ta shigo su Ahmad na binta a baya da kulolin Abinci, bata gaji ba wai abincin rana ta kuma kawo mana, matar dai tana da kirki kwarai nayi sa’ar maqociya. Kan Dining suka koma Amna ta zubo nawa ta kawo mun cikin palour ina ci muna hira da Anty suna gamawa kuwa duk suka shige daki wai bacci se Anty ta miqe tana cewa bari ta barni nima na huta. Tsarabar Kindirmo me kyau da Dambun fura se Kuka da kayan qamshi na dakko mata daman na ware su daban na hada mata da wani turaren wuta da Alawiyya yayata take hadawa ta bani yana da kyau sosai mukayi sallama ta wuce gida. Na raka ta kenan David yaron da Bashir yake aikowa wani lokacin ya kawo saqo ya tsaya a qofar gidan, kayan amfani ya kawo su kayan miya, veggies, Nama, kifi, dankali, doya plantain duka dai kayan amfani da za’a nema ya siyo, qofar kitchen ta baya na bude masa suka shiga da kayan shida me Uber daya kawo shi. Dole na fasa kwanciyar na shiga ware komai ina saka shi gurinsa kafin na gama har uku tayi dan ban nemo yan tayi ba ganin sun gaji yasa na barsu su huta. Bayan na gama na shiga dakina, zama nayi akan gadon ina miqa Kafin na dan kishingida ina duba waya ganin da sauran kusan 30 mins kafin ayi la’asar yasa na kwanta wai in dan matse ban tashi farkawa ba kuwa se qarfe biyar harda rabi na yamma na miqe ina salati ganin irin baccin da nayi, anyi la’asar tun tuni ga Bashir nasan yana dab da gida yanzu kuma Azumi yake. Alwala na farayi nayi sallar bayan na idar na shiga wanka. Ban wani jima ba ina fitowa na shafa mai sama sama na goga yar hoda da kwalli se lip balm kafin na fesa turare, doguwar riga na saka ta wani plain material Silk Dark green an masa dinkin kamar Jallabiyar qirar Turkey babu adon komai a jiki se maballai da aka jera a jikin wuta zuwa qirji guda uku da kuma bakin hannu. Mayafin ta na yafa a kaina wanda be kai kalar rigar duhu ba na zura flat shoe baqi na fito da wayata a hannu ina tunanin me zan dora masa mara wahala da zan gama da wuri. “Mamina” Ahmad ya fada yana rungumeni, se na janye shi gefe ina cewa “Ina zuwa Ahmad Abbi ya kusa dawowa gashi ban masa abin buda baki ba” ai ban qarasa rufe bakina ba naji tsayuwar motar da nake da tabbacin tasa ce a qofar gida. Kitchen din na fada da sauri a rainaina cewa “shikenan yau an bani”dan Bashir baya wasa da abinci. Idan yayi azumi yafison kafin asha ruwa an gama jere masa komai a gabansa yanda bama ze jira komai ba. Da niyyar dafa masa tea in soya kwai na shiga in yaso kafin yaje sallah ya dawo ko couscous ne na turara masa, nasan dakyar idan yaran nan sun ci farfesun kayan cikin da Anty ta kawo dazun ba tunda ba son shi suke ba se in hada masa ya qarata, mita ce dai nasan sena sha ta yau dan babu ruwansa baze duba irin aikin da muka sha a gidan ko gajia ba tunda kawai nasan yana azumi dole na tanadar masa abincin. Amna da Farida na tarar Amna na kwashe dankali daga mai Ita kuma Faridan na yanka Fruits a bowl, suka kalleni a tare suna murmushi “Mami kinsha bacci, naga yamma tayi nace bari mu hadawa Abbi kayan shan ruwa” Amna ta fada tana kashe Gas din bayan ta qarasa kwashe dankalin. “Allah dai yayi muku albarka, na manta shaf ma kuna gida ai” na fada ina qarasawa kan Island inda suka ajiye kwanukan da aka zuzzuba abincin na bude na farkon. Farar shinkafa ce se ganyen parsley da aka yi garnishing na maida murfin ina cewa “Aa su Chef Amna harda wani ganye ganye aka zubawa Umfafar. Farida ta miqomun spoon tana cewa “Mami ci sauce din kiji ni nayi ko Yah Amna”. Na karba na bude kwanon miyar, sauce din hanta da qoda sukayi se qamshi take na kai baki dadin ya ratsani, se na ajiye spoon din, “dagaske ita tayi Amna” “Ita tayi Mami kawai gaya mata yanda zatayi nake se kuma na bata measurement na komai” Amnan ta fada. Lallai ashe mun samu sabuwar chef, Yayi dadi sosai amma karki fadawa Abbi ki bari se ya gama ci tukunna”. Ina rufe baki Bashir ya shigo kitchen din, Farida ta ajiye wuqar hannunta ta nufeshi tana masa oyoyo. “Me kike a Kitchen Farida da wuqa a hannunki bana hana ba” ya fada yana kallon fuskarta, ssannu da zuwa nayi masa ba tareda na amsa tambayar tasa ba dan dani yake ba Farida ba. Ledar hannunsa ya miqo Amna ta karba yace “ki sake warming nasa” ya juya suka fita yaja riqe da hannun Farida. Fruit Salad din na qara sa hadawa, muka fito da kayan dukka muka jera a Dining lokacin har an fara kiran sallah. Dabino na koma na dakko masa da ruwa mara sanyi na ajiye akan stool din gefen kujera sannan na zubo fruits din a dan qaramin bowl na ajiye daidai sanda ya fito daga dakinsa da alama alwala yayi. Ina kitchen ina hada kayan da zan soya masa kwai suka fita masallaci dan shi bazaki soya kwai ki ajiye masa ba ya fiso daga kasko se farantinsa. Kayan cikin na dumama na fito da Balangun da Amna ta saka a Oven shima na juye masa a bowl a raina ina jinjina qaunar Bashir da nama. Seda na soya kwan bayan sun dawo na ajiye masa komai sannan na shiga dakina na barshi da yaran suna tayashi shan ruwa. Dana idar da sallah ma ban fito ba, miqewa nayi ina chat da yan uwa da abokan arziqi har aka yi Isha. Ji nayi ana kwankwasa qofa. Aliyune, bayan ya shigo yace “Abbi yana kiranki” Da “toh” na amsa na miqe ya qara powder da turare na yafa mayafi na na fita. Suna zaune a kan kujerun Palour sun cika ko ina, “ikon Allah wai duk bataliyar nan yayan Ma’une” na raya a raina kawai na tuntsyre da dariya se suka juyo dukka suna kallona. “Lafiya kike dariya” Bashir ya tambayeni, seda na zauna a kusada shi kafin nace “ganin yaran nan nayi da yawa nake mamakin wai duk nawa ne”. “Da sauran wasu ma a gaba ai” ya fada yana kallona da wani kalar expression, kallonsa nayi nima har sannan fuskarsa bata koma daidai ba da sauran alamun damuwa da bacin rai akanta nace “Aa ni ai na gama, na barwa yan baya gashinan sun fara ai” harya bude baki zeyi magana wayarsa tayi qara, Dr Hadi ne pediatrist din da yake kula da Iman. Daga wayar yayi bayan ya miqe ya shige dakinsa nima sena tashi na qarasa kan Dining na debi abinci. Ina ci muna yar hira da yara, ina kammalawa suka kwashe komai aka kai Kitchen muka tattare palour qal dan kusan komai da dare mukeyinsa daman saboda fitar safiya muna gamawa nace suje su kwanta gobe akwai school. Dakina na koma na sake wanka na shirya tsaf na tafi dakin Bashir, yana kwance rabin jikinsa akan Gadon qafafunsa kuma a qasa ya harde hannu a qirji yana kallon sama da alama tunani yake. Banajin yaji shigata har seda na ajiye wayata da Zoben dana zare daga hannuna akan Bedside sukayi qara sannan ya dago a dan zabure. “Yadai?” Na tambayeshi se ya girgiza mun kai alamar babu komai kafin ya miqe ya shiga toilet. Ina shafa addua ta ya fito daga toilet din daure da towel a qugunsa, kallonsa nayi sam bazakace Bashir ya fara jiyo qamshin Hamsin ba saboda kyan jikinsa, a tsarin halitta befi ka bashi shekaru 35 zuwa 37 ba amma a zahiri shekarunsa 45 ne. Har ya shafa mai ya saka kayan bacci riga da wando light blue ina zaune ina kallon sa, yanda yake abubuwa a sabule kamar mara laka harya gama ya kashe fitilar tareda hawa kan Gadon ya janyoni jikinsa ya dora kansa akan qirjina mukayi shiru bakajin komai se qarar Ac a dakin, kusan minti goma a zatona ma bacci yayi naji ya riqo hannuna sosai yana cewa “bana so na rasa ta”. “Qum” naji kaman an jefeni da dutse dan a sukwane zuciyata Amirah ta kawo mun sedai kafin nayi magana naji ya sake cewa “bana son na rasa Iman Ma’u, ina son yarinyar kwatankwacin yanda nake son Farida, na dade inawa Farida fatan ta samu yar uwa se yanzu Allah ya bata gashi ina neman rasata”. Wato wani sanyi naji a raina, sena gyara kwanciya ta ina cewa “ba abinda ze faru da izinin Allah zata tashi, naga jikin ai da sauqi jiya da muka je koh?” “Eh da sauqi sosai, yanzu ma kiran da Dr yamun su naso su sallameta ne” ya fada yana tashi zaune sosai. “Kai masha Allah, Allah ya qara lafiya” na fada ina gyara kwanciya harda jan bargo a zatona maganar ta qare sejin Bashir nayi yana wani soki burutsu “Idan an sallamota ina so zan kawo ta nan” ya fada. Naji ba wai banji shi ba amma son na tabbatar da ma’anar maganar tasa yasa na dago na kalleshi kafin nace “Ban gane me kake nufi ba zaka kawo ta nan, Amiran nan zasu dawo ne ban sani ba?” “Aa ba Amirah ce zata dawo ba Iman nake nufi zan kawo miki ki riqeta na bar miki ita”. “Ikon Allah” na fada a fili kafin na tashi zaune sosai na ina kallonsa, “Ka kawota nan fa kace Baban Ali jaririyar da ko wata bata cika a duniya ba, me ya samu ita Amiran da bazata iya riqe yarta ba. To ai ko mutuwa tayi tunda tana da uwa a raye zata karbeta bare da ranta ace za’a raba ta da yar data sha wahala kafin ta sameta ah gaskiya kaima baka zo da maslaha ba”. Kallona yake har na kai qarshen maganar, nayi zaton ze balbaleni da masifa ne yace seya kawo yarinyar amma aka sin haka sema wani marairaicewa daya sakeyi ya kamo hannuna yana cewa “Kin fita cancanta daki tarbiyyantar mun da yaya, sam waccen yarinyar bata da tunanin da zata iya kula da kanta ma bare wani. Kina gani bataji tausayin yarinyar ba suka jaza mata wahala bana tunanin zata iya rainon yarinyar”. Sakato nayi ina ji da ganin ikon Allah rainin hankali da tsakar dare, ace ta haifi amma bazata iya kula da ita ba ni ga jakar Ÿaÿa shine za’a dakko wata bakwaini a kawo mun lallai zanga uban da ya isa kuwa. Fizge hannuna nayi na kwanta tareda juya masa baya nace “Ai Kowa ma be iya ba daga baya ya koya itama a hankali zata iya tunda babu wanda baya son dan sa” naja bargo na rufe har kaina. Shiru naji har kusan minti goma beyi magana ba be kwanta ba nima ban sake motsawa ba tun ina mita a raina har bacci yai gaba dani amma ahu daya na qudurce wallahi ko sama da qasa zata hade bazan zamar masa yar raino ba. Ban kuka ga uban daya isa ya saka na karbi yarinyar ba. 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 WATA KISHIYAR 🥰👹 (ALKAHIRI CE KO SHARRI) 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 Na Maryamah_Mrs AM (Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah) *INA MANYAN MATA NE* *INA MASUSON FARA SANA'A* *HANNUR COLLECTION tazo maku da alkairi domin qarin bayani kobiyo💥🔥💥*Munada amarya da uwargida package wannan package ya* *qunshi,abubuwa guda goma* *maganin sanyi da basur* *Nasha da madara* *Nasha da lipton* *Na dahuwar kaza* *Na tsarki* *Nasha da kankana* *Garin tsumi* *Hadadden tsumi* *Na matsi* *Nahadawa da zaitun* *Muna saida tahnia me gyaran aure* *Akwai kayan ORIFLAME* *Akwai kayan GHT* *Akwai kayan faforlife* *Akwai chocolate da coffee na mata* *Akwai turaruka,sabulai mayuka da duk wani kayan gyaran jiki da aure* *Munada dogayen riguna sari,yadin hijab materials,atamfofi,shadda,laces dss* *Albishirunku ina registration din ORIFLAME, GHT, FAFORLIFE ,Duk kayanmu farashin sarine,kuma muna aikawa kowanne gari cikin aminci* https://wa.me/message/3BCXWNGTI7ILC1 Page 22 Gudu ya ringa fellawa dasu kamar masu barin gari sanda ya tsayar da motar a bakin Get kuwa har qauri takeyi, a Get din ya watsar dasu yai gaba dan Amirah bata ko samu damar daukar Akwatinta ba Asma’u ta saka key din hannunta ta bude musu Get suka shiga. Yanda taga Amiran tana tafe tana layi se ta bata tausayi dan haka ta qarasa ta riqo kafadarta ai kamar me jiran majingini kawai ta fashe mata da kuka tana cewa”Dan Allah Anty ki bashi haquri, wallahi ba laifina bane Addah ce kema kin santa ita tace se anyi”. Asma’u bata tanka ta ba har suka shiga dakin Amiran ta zaunar da ita akan Kujera tana qarewa palour kallo baki bude saboda mamaki. Duk wani abu daya danganci glass an fasa harda Tv ba’a barta ba daidai da labulaye duk duk an sauke su qarafunan sun karyo. Ajiyar zuciya tayi kafin ta Kalli Amirah da har sannan kukan take tace “Kiyi shiru komai zai daidaita Insha Allah, ina zuwa”. Part dinta ta koma, Farfesun Tsokar rago ta ciro a freezer ta dumama kafin ta hada Shayi a qaton Mug ta dora su a kan Try hade da Bread ta dauka ta koma part din Amiran. Bayan ta ajiye su ta sake komawa ta debo mata tuwon semo da miyar danyar kubewa da tayiwa Bashir bema ci ba ta sake komawa part din Amiran. Tana zaune a qasa ta zamo daga kan kujerar riqe da cikinta tana murqususu, da sauri Asma’u ta ajiye try din ta nufeta tana “lafiya Amirah meya same ki?” Ita dai se juyi take tana malele kuwa akan Tiles saboda bala’in qullewar da cikin yayi mata. Dakyar ta nutsu ta kamata ta koma kan kujerar, Shayin ta fara bata a baki tana karba, kurba uku tayi Amai ya taso mata ko kafin ta miqe tayi shi a Gurin Asma’u na tsaye se sannu take mata. Bowl babba ta dakko ta debo ruwa a babban kofi da dawo gurin Amiran, ta zuba mata ta kurkure baki da dauraye fuskarta Ta koma yaraf ta kwanta tana sauke Numfashi. Abincin ta ajiye mata nan ta shiga ci kuwa dan Aman ya taimaka ya bude mata ciki ita kuma ta dauke robar ta tafi dakko mopper da packer, Duk Kyankyami irin na Asma’u haka ta daure ta kwashe aman tsaf ta zuba ruwan omo ta goge Gurin kafin ta sake saka ruwa ta goge tas ta nemi freshener amma bata samu ba sanda ta gama itama ma Amirah ta cinye farfesun tsaf ta shanye shayin se ajiyar numfashi takeyi. “Nagode Anty Allah ya biyaki” ta fada tana sunkuyar da kai, se Asma’u tayi murmushi kawai tace “bakomai, ki samu kisha magungunan ki se ki kwanta ki huta. Ga ragowar abincin nan koda zaki buqata anjima Allah ya qara kiyayewa” ta fada tana nufar qofa. Tashi tayi ta rakata tana sakeyi mata godiya ta kulle qofarta gam ta ciki karma ya dawo kenan ya shigo bata kwashe kwanukan ba ta haye kan kujera se baccin wuya ya kwashe ta. Asma’u ma tana komawa part dinta kulle qofar tayi idan Bashir ya dawo da akwai key a hannunsa dan sunyi waya yaran sunce a can zasu kwana ma bazasu dawo ba. Sama ta wuce ta shiga wanka, seda ta gyara jikinta tsaf lokacin har sha daya tayi ganin Bashir be shigo ba yasa tayi kwanciyarta kawai dan daman dai yau koya dawo tasan bazasu kwashe qalau ba. Bashir Yana sauke su kai tsaye tsohuwar unguwar da suka taso ya wuce gurin Bala, Abokinsa ne tun na yarinta tare suka tashi a unguwarsu su Hudu Bashir, Marigayi Aliyu, Bala da Sadiq yayan Asma’u su hudun Abokaine na rai da rai tun daga Primary ajinsu daya har jami’a sannan suka rabu kowa ya karanci course dinsa daban. A qofar gida ya tarar da Bala da yan majalisar sa kamar yanda yayi tunani, kashe motar yayi tareda jan kujerar baya sosai ya tokare qafarsa da stiyarin motar , zafafan numfashi yake saukewa a jere a jere zuciyarsa jinta yake tamkar ana soyata a mangyada. Me yasa meye dalili daya kasa samun nutsuwa tunda ya auri yarinyar nan? A shekara biyu an tafi ta uku da qara auransa be sakeyin sati daya na cikakken farinciki ba wai dama haka qarin auran yake ko kuma shine beyi dace ba. “Me yasa baka nemi wata ba me yasa se Amirah zaka aura Bashir? Yau da ace wata daban ka aura wallahi ko mata uku ka auro lokaci daya bazan damu kamar wannan auran da kayi ba amma shikenan haquri ko nayi haquri. Idan dan Allah kayi Bashir Allah ya bamu zaman lafiya ya bani ikon cinye jarabawar da yayi mun, idan kuma kayi ne dan kaci mutuncina to Allah baze bari na tozarta ba ba kuma zaka samu nutsuwar da kake iqirarin samu ba” kalaman Ma’u na qarshe wanda daga su bata sake tayar masa da hankali ko wata magana ba sanda ya auri Amirah. To wai alhakin nasa ne ko nawa shidai Allah ya sani beyi auran nan da wata manufa ba yayi ne kawai dan yana ra’ayi bakuma dan ya tozarta Matarsa ba kamar yanda take tunani amma gashi nan shi yake karbar sakamakon sa da Hannun hagu wai ta ina toh ya kuskure?” Glass din window da aka kwankwasa ya dawo dashi daga tunanin daya tafi, se ya dago yana gyara zamansa. Seda ya saita yanayinsa sannan ya bude qofar ya ziro dogayen qafafunsa yana sake kokawa da dacin ransa kafin ya fito gaba daya. “Kaga Na Ma’u Angon Amirah uban Aliyu ko dubu ta taru” Bala daya gaji da jiran fitowar Bashir din ya zo ya kwankwasa masa glass ya fada cikin sigar tsokana sedai yana yin fuskar Bashir din tasa ya gintse maganar tasa. “Lafiya kuwa Engineer kaga idanunka” Balan ya sake fada, se Bashir yaja tsakin da ya aure shi ya bude murfin motar ya koma ciki yana cewa Balan ya zagayo. Cikin zaquwa Bala ya shiga motar dason jin meya faru, dan Bala irin mutanen nan ne masu son bin kwakwkwafin duk wanda suke tare se sun san komai nasa. Shiru sukayi na kusan minti biyar, Bala da gulma take cinsa har ya gaji ya ceda Bashir din “Engineer wai yane kodai akan climax kake ne kaima ka fara busa eh yane” Wani mugun kallo Bashir ya jefe shi dashi kafin dakyar ya bude baki yace “Abinda banyi da quruciyata ba shi kake mun fatan yi yanzu insha Allahu har na mutu nida hayaqi sedai na murhu balle na kai ga shan wata kwaya kai dai da ka riga ka illata rayuwarka shikenan amma ka ringa tunawa Yaranka Mata ne kodan su ya kamata ka dena abinda kake yi”. Hade rai Bala yayi dan yasan dama qarshe seya jefe shi da maganar, tun suna secondary Bala ya fara bin wasu Sa’anninasu a unguwa har suka koya masa dabi’ar shaye shaye, babu yanda basuyi dashi ba akan ya dena amma ina qarshe har yaso koyawa Sadiq da taimakon Allah da jajircewar Iyaye beyi nisa ba ya bari amma shi Bala ya rigada yayi nisa dukda abun nasa harda daurin gindi daya samu gurin Babarsa dan shi kadai ne danta Namiji. Lokacin da aka ringa ankarar da ita akan ta ringa masa fada seta nuna an takura mata Da ba’a qaunar sa seda yayi nisan da baze ji kira ba sannan tazo tana kuka da idanunta akan dabi’ar tasa dan seda takai kayan maye har a cikin gida sha yake babu abinda baya ta’ammali dashi in banda Giya da Cocaine har kuwa ta mutu da wannan baqin cikin toh yanzu dai yayi sauqi saboda girma da iyali daya tara amma fa ko yanzu ba abin kunya bane a gurinsa ya murza wiwi yasha ko a gaban waye su kansu su Bashir dan dai babu yanda suka iyane suka ci gaba da zumunchi dashi musamman Bashir da Yake ganin Balan na bashi shawarwari daidai da ra’ayinsa. Shiru suka sakeyi kafin can Bashir ya mula dan yana buqatar abokin tattaunawa, idan so samune Sadiq ya kamata ya gayawa dan yafi Bala hankali amma tun auransa da Amirah alaqarsu taja baya dan a lokacin gani yake Sadiq din ya goyi bayan qanwarsa dan haka ya zage ya masa rashin kyautawa shi kuma da zuciya ya fita sabgarsa sam yanzu babu wata kwakwkwarar mu’amala tsakanin su daman ga banbancin gari yanzu ga aiki yasha kan kowa. Labarin duk abinda ya faru da hukuncin daya dauka da wanda Baba ya dauka shima ya bawa Balan, Bala dayai zuku di kamar gaske yana sauraronsa ya jinjiga kai yana cewa “kai Engineer kafa debo da zafi wallahi, nifa daman wannan Addan taku kasan yar bala’i ce tun duniya na kwance bazan manta sanda muke zuwa gidanta ba lokacin tana kiwon kajin nan in muka kwamusu daya haka zata biyo mu har layi tana sababi, amma ai ita Amiran tayi fa. Ka jure kawai tunda ka samu yarinya me kyau duk abinda ze zo ai daga baya ne”. Baki bude Bashir yake kallonsa, wai ma wannan ya gane kan matsalar sa kuwa yake masa wannan soki burutsun koda yake shima da laifin sa wani sa’ilin ina shi ina shawara da dan wiwi? Tsaki ya buga kawai tareda yaiwa motar key yace masa “Malam sauka seda safe” Bala ya kwashe da dariya yana cewa “ah da wuri haka kodayake gara kaje ka lallashi yar Babynka wallahi baka san wahala suke yanzu ba ko kodan kai Allah ya baka zuqa zuqa har biyu ka ajiye a gida baka san yanda kan gayu yake gwaruwa yanzu kafin su samu wadannan kalolin ba” “Bala sauka ko na tafi da kai” ya sake fada a fusace, se Bala ya balle murfin motar ya fita yana ci gaba da yi masa dariyar qeta yace “Haba Engineer ai daman ba’a samun abu biyu ka hada kyau da zaman lafiya ai baze yuwu ba mu dai da muka auri munanan ba gashi muna qalau ba wayake jin kanmu...” fizgar motar Bashir yayi Allah yasashi ya matsa gefe ya koma majalisarsu yana ci gaba da dariya a ransa yana cewa “Ai baka ga komai ba wallahi, yanda ban samu abinda nake so ba kai ka samu, a baya dai kaji dadi amma bazaka sake samun kwanciyar hankali ba”. Bayan Barin Bashir gurin yawo ya ci gaba dayi a mota dan baya so ya koma gida ko waccensu haushinta yake ji, seda sha biyu ta buga sannan ya kama hanyar gida bada ban ba ma Hotel zeje ya kama amma yanda duniyar nan take yanzu abu qalilan seya jefaka a masifa wani ya ganshi be san meya kaishi ba a canza masa manufa, gidan ya dawo masu gadin layinsu na zazzaune suna hira mutum biyu suka taso suka bude masa get bayan ya aje motar ya koma yayi musu dan ihi sani ya koma ciki. A tsakiyar part biyun ya tsaya ya riqe qugu yana balla musu harara kamar masu dakin ne a gabansa, fitilun palour Amirah a kunne suke, daga inda yake yana hango cikin palour tarwai ta window saboda babu labule kamar ya share sedai tunawa da Maganar chanza key da Asma’u tayi masa ya saka shi dosar gurin dan be san ko an sace din ba da gaske. Da key din hannunsa yayi amfani ya bude qofar tana kwance akan kujera ta duqubqune ya isa kanta ya tsaya ya, ganin yanda ta bar kwanuka ya sa ya fara kiran sunanta. Amirah kuwa Kamar a mafarki taji muryar Bashir yana kiranta, tana bude ido kuwa ta ganshi akanta ai ba shiri ta buga wani uban tsalle tayi gefe sedai kafin ta kai qasa yai azamar riqota dan shi kansa ya tsorata da yanda ta miqe din ba shiru suka zube qasa, a tare suka saki qara shi ta zafin buguwar rashin tsammani data same shi ita kuma ta azabar da taji cikinta ya dauka danji tayi kamar dinkin ze bare. Kuka riris ta saka gana tsoron abinda ze mata gana azaba abinda ya hadu ya qara qular da Bashir qoqari yake ta tsaya tabar mutsu mutsun amma ita se qara zillewa take tana ihun yayi haquri a zatonta dukanta zeyi, ganin tana bata masa lokaci yasa ya daka mata wata uwar tsawa yana ce wa “wallahi ko ki rufe mun baki kona make ki a gurin ki tsaya mu gani ko kinjiwa kanki ciwo”. Tsit tayi se shatato kwalla take hannu ta akan cikinta dayan kuma ta rufe baki, yanda take matsa cikin ya tabbatar masa da tana jin zafi ya saka shi cewa ta tashi ta biyo shi yayi gaba tana binsa a baya a dudduqe, seda ya kashe fitilun ya kulle qofa kafin suka shiga motarsa, wallahi badan yana tsoron kar wani abun ya sameta Allah ya kamashi ba da barinta zeyi jikinta ya gaya mata. Haka ya sake fita daya saura suka nufi Asibiti shi yana jera tsaki ita tana kuka qasa qasa. Basu bata lokaci ba dan an tabbatar musu babu komai motsawa gurin yayi amma dai ta kiyaye irin hakan, Allurar kashe zugi suka mata kafin suka kamo hanya kamar abokanan gaba har suka zo gida yana tsayawa ta wuce sedai tuna bata da key ya sakata rakubewa tana satar kallonsa. Har ze shige part din Asma’u shima ya tuna da bata dakko key dinba dan haka ya qarasa ya bude mata qofar be amsa Nagode din da take ce masa ba ya wuce abinsa. Kitchen ya fara tsaya wa ya dauki Yoghurt me sanyi kafin ya hau saman, beyi zaton samun Ma’u a dakin ba amma yana budewa qamshin Airfreshner dana turarukan baccinta suka masa sallama besan sanda ya fara sauke aji yar zuciya ba dan har ga Allah qanshin sun san yaya masa rai. Akan dan teburin da yake dakin ya ajiye yoghurt din da tarkacen keys dinsa da wayoyi kafin ya cire rigar sa ya shiga toilet. Wanka yayo da alwala, bayan ya fito ya shafa mai sama sama ya zura jallabiyya Ya fesa turare lokacin har biyu ta gota kafin ya kalli Gabas ya tada sallah. Raka’a biyu yayi a sujjadarsa ta qarshe ya dade yana yiwa Allah kirari kafin ya dora da istigfari tareda neman zabin Allah akan dukkan al’amuransa ya rufe da salatin Annabi kafin yayi tahiya ya sallame. Ya dan jima hana lazimin La’ilaha illah anta subhanaka inni kuntu minazzalimin har seda bacci ya fara fuzgarsa sannan ya tashi yana jin nutsuwa na saukar masa. Seda ya sha yoghurt din dan yunwa yake ji sannan ya kwanta ya juyawa Ma’u da bata san da dawowarsa ba baya. A kusan tare suka farka da Asuba, ya cuna baki Gabas ta cuna Yamma kafin ya miqe tayi wuf ta shige toilet tayo fitsari tareda chanza pad ta koma ta kwanta kafin ma ya gama shirin Masallaci bacci ya sake kwasheta. Da safe ma haka suka tashi, ya hada fuska tam yana zaune a palour yana kallon labarai ita kuma tana ta kaimawon hada masa breakfast, bayan ta gama ta masa magana daga “Toh” be sake ce mata komai ba kuma be motsa ba se itama ta share kawai dan dai fushin ai ba nata bane, idan kuma zancen komawa ne ai indai yar gaskiya za’abi batayi laifi ba. Dibar Abincinta tayi ta wuce dakinta taci, bayan ta gama ta fito sukayi kici bus ze shiga zata fito ta rabe masa ya wuce kafin ta fito. Abincin ta fara dubawa taga yaci da yawa ma tayi dariya a fili tace “na zata shima cikin fushi kake dashi ai” ta shiga tattarewa ta sauka qasa da kayan. Tana cikin dauraye kwanukan taji motsinsa ya bude qofa, ta window ta ga fitarsa tana ganin yanda yai diri diri a tsakanin parts din me kuma ya tuna ya wuce ya kunna motarsa ya bar gidan. Ragowan Abincin ta juye ta yafa mayafinta ta kaiwa Amirah. Tana zaune a palour tun jiyan a nan ta kwana sallah ma duk anan tayi kuma har lokacin bata kwashe kwanukan jiya ba ga plate din data sake cik tuwo bayan sun dawo shika a bushe. Ba qaramar kunya ce ta kamata ba ganin Asma’u, duk se taji ta muzanta saboda yanda Asma’un ta sheqa wanka da wata Atamfa doguwar riga se qanshi take ita kuwa tama zaune cikin kwanuka da kayan jiya a jikinta seta hau soshe soshen tana gaida Asma’u da tayi mirsisi kamar ma bata ga komai ba. Kayan ta dire mata tana cewa ta juye ta bata kwanukan kafin ta duqa ta kwashe na jiyan a ranta tana cewa “Na san darajarsu bari na kwashe abuna” bata ko saurari Amiran dake cewa ta barsu yanzu zata tashi ta wanke ba, ganin haka yasa ta tashi ta shiga kitchen ta juye ta daurayo kwanon da zallar ruwa ta kawo mata. Karba Ma’u tayi tana cewa “se ki nemi abinda zaki ci da rana tunda naga kin warware” tayi waje abinta. Wannan abincin taci tayi nak sannan ta tashi ta dan tattare gurin ta shiga dakin ta tana qarewa Hadadden Gadonta da aka rushe bedside din kallo. Ita dai yan sunan nan sun cuceta wallahi dan dai bata hango ranar da Yaya ze sake mata wasu kayan ba yanzu ma ta samu ya haqura ya sakko daga fushin nan ma kafin wani zance ya biyo baya. Wunin ranar zir Bashir a waje yayi shi, itama Ma’u bata zauna ba ta fita harhado sauran kayayyakin da take buqata da ba’a samu acan dan haka se yamma lis ta dawo bayan ta biya ta dakko yara. Koda suka dawo ma basu zauna ba kayansu suka hade tsaf dan gobe Sunday tanason suje su wanke kai da kitso Monday se Lagos. Sanda Bashir ya dawo yaran sun kwanta Amnah ce kadai idonta biyu tana karatu dan da sun koma sati biyu zasu fara SSCE, da niyya tijara idan basu dawo ba ya shigo gidan se Allah ya ceci Ma’u tana kitchen ta jiyo Amna na gaishe shi yana tambayarta yaushe suka dawo tace dazu. Kitchen din ya leqa suna hada ido ya wani qara shan kunu tayi masa sannu da zuwa ya daga kai ya fice ya haye sama qasan ransa yaji dadin ganinta. Seda suka zo kwanciya ta gama duk hidimominta taji muryarsa yana cewa “akwai abinda kuke buqata ne?” Seta dakata daga saka hular da takeyi ta kalle shi yana zaune a bakin gadon yanda yayi maganar yana fuskarta wani guri daban, kallo daya zaka masa kasan akwai abinda yake damunsa gaba daya yayi laushi. Kusa dashi ta koma ta zauna, seda ta shagwabe fuska sosai ta tara kwallar qarya a idonta kafin ta riqo hannunsa, waiwayowa yayi seda ta tabbatar ta saka kwayar idon ta cikin tasa yanda baze iya kaucewa ba sannan tafara magana tana cewa “Haba Baban Ali Haba Na Ma’u wai fushin ne haryanzu ina kake so na saka kaina naga haske bana ganin Murmushin ka? na tuba nabi Allah kayi haquri indai batun Tafiya a motane na yarda gobe muyi asubanci mu tafi idan kana tare damu nasan babu abinda ze same mu se ikon Allah”. Duk yanda yaso ya janye ya kasa dan riqon da tayi masa da kaifin idonta yayi tasiri a jikinsa, daman dauriya ce kawai amma yana buqatar ta, yana buqatar me kwantar masa da hankali kuma Ma’u ita kadaice duk damuwar daya shiga a duniya take iya magance masa ita har in yana tare da ita tana saka shi ya manta komai sedai daga baya ya tuna shi yasa duk sanda matsala take tsakaninsa da ita yake ji kamar ya zauce dan babu me masa magani. Fuzgota yayi jikinsa ya mata ruqo me tsauri tana jin yanda zuciyar sa take bugawa jikinsa har wani rawa rawa yake, cikin dasashshiyar murya yace “Badake bake fushi ba Ma’una, me yasa, meyasa ita bazata ji magana ta ba me yasa koda yaushe take sakani ciwon kai”. Seda Ma’u ta murguda baki ta harareshi dukda be gani ba a zuciyar ta tace “taya zan sanin maka ba kai ka kwasowa kanka ba” a fili kuwa seta qara riqeshi cikin kwantar da murya tace “Kayi haquri” . Yanda ta fadi haqurin yasa yaji tamkar ta watsa masa ruwan sanyi a zuciyar sa, kissing goshi ta yayi kafin yace “Na haqura Yar Aljanna”. Cikin tsananin farin ciki ta dago ta kalli kyakykywar fuskarsa tace “To Na kawo maka abinci, yau duk nasan baka ci komai ba ga fuskar ka nan ta nuna”. “Muje ki bani” ya fada yana daga ta gaba daya, seda suka sauka har qasa sannan ya ajiyeta Amnah da ta gama hada littattafanta zata shiga daki tayi saurin saka littafin a fuska tana tafiya da baya da baya. Rankwashi ya kai mata da wasa cikin harshen turanci wanda dashi yakewa yaran magan yace “gidan ku me kike yi anan baki kwanta ba haryanzu” Dariya tayi ta dan janye littafin tace “Abbi karatu Saura two Weeks mu fara WAEC fa” “Ok maza je ki kwanta karki manta kiyi Addu’a” ya fada yana zama akan kujera, seta juya tana cewa “Good night Abbi” “Good night Amna” ya fada daidai sanda Asma’u ta fito da plate din daya zubo masa dambun couscous se kunun aya a Jug. “Good nigh Mami” Amna ta sake fada, seda Ma’u ta ajiye kayan akan centre table kafin tace “Good night Amnan Abbi”. Dariya Bashir yayi yana cewa “fadi ki qara kam Amnan Abbi” murmushi kawai tayi, a ranta tana jin dadi yanda Bashir ya dauki qanwar tata tamkar yar da ya haifa a cikinsa dan gani take kamar yana mantawa ma ba yarsa bace, tunda riqon Amna ya dawo hannunta be taba sauya wa daga yanda ya karbi yarinyar ba ko a fuska, komai ya tashi yiwa yaran itace farko a matsayin first born dinsa. Cikin dadin rai yaci abincinsa ta tattara suka wuce Aza rum. 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 WATA KISHIYAR 🥰👹 (ALKAHIRI CE KO SHARRI) 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 Na Maryamah_Mrs AM (Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah) Page 24 Gombe Bayan Naziru ya kaimu Airport kai tsaye kasuwa ya wuce ya siyi duk abinda Bashir ya gaya masa ya kaiwa Amirah. Tana zaune a palour bayan ta gama kukan ta yai sallama ta amsa fuska a kumbure be kulata ba ya shiga kwaso kayan da taimakon Almajiran daya kira suka shigar mata da su Kitchen. Har ya gama bata ko sake kallonsa ba dan haushin sa takeji tasan shi yake qara zuga Bashir din ma akan komai, seda ya kai qofa ta tuna da zancen waya seta miqe da sauri tabi bayansa tana kwalla masa kira ya kuwa shareta kamar beji ba seda yaje gurin mota tana biye dashi. “Meye kike bina kamar naci miki Bashi” ya fada yana harararta, inda haka kawai ne seta rama amma tunda abu take nema seta karyar da kai tana cewa “Dan Allah Yaya Naziru waya zaka siyo mun da layi”. Seda ya harareta kafin yace “waya? Me zakiyi da waya ina taki?” “An sace” ta bashi amsa kai tsaye. “Toh ai shikenan gara da aka sace, kuma ni sa’an kine ko dan aikenki da zan siyo miki waya ke baki da qafa ko baki san inda ake siyarwa ba” Nazirun ya fada. Seta marairai ce tana cewa “Dan Allah ka taimaka mun Yaya”. Kwafa yayi kafin yace “Kawo kudin toh badan halin ki ba” “Nagode” ta fada kafin ta qirgo dubu biyar da dari biyar ta bashi, ya karba ya irga ya kalleta yace “Saboda a gidan ku ake qera wa ko waye ze siyar miki da wayar dubu biyar” “Yaya Tecno fa me keypad ai bata wuce haka ba” “To se kije ki siyo kin tsaya kina batamun lokaci” ya fada yana miqa mata kudin, setayi saurin dakatar dashi tana cewa “yi haquri dan Allah nawa ce se na ciki” “Dubu goma ce sannan ki bada dubu biyu kudin mai tunda babu siyo miki waya a lissafin da aka mun. Ba yanda ta iya tana ji tana gani ta zare dubu goma sha biyu da dari biyar ta bashi ya tafi, idan da abun nata da mutunchi tasan a kyauta ma siyo mata zeyi amma yanda tasan yana jin haushinta ma tayi mamakin da yayi saurin karbar aiken. Ciki ta koma ta tafasa ruwan zafi ta dakko kayan Tea a siyayyar da ya yo mata harda bread ta zauna ta karya, tana zaune a gurin ya dawo ya miqa mata leda da kwalin wayar a ciki da layi harda katin dubu daya ta karba tayi godiya harya juya ta kuma tsaida shi tana cewa “Dan girman Allah yaya ka roqar mun Yaya Bashir ya bari naje na ga Iman kaga fa tun da aka kaita Asibiti banje ba”. Wani banzan kallo ya mata kafin yace “karki rainamun hankali dan kin ga na biye miki malama, dacan baki san tana Asibitin ba se yau? To bari kiji ya gayamun sharadin daya gindaya miki kuma wallahi na baza CIDs a layin nan ki sake ki fita dan nasan ba tunani ne dake ba tsaf za’a iya zugaki ace ki fita ai be sani ba kinga kuwa auranki ya mutu” yana gama fada ya juya ya fice yabar Amirah da baqin ciki ya cika mata ciki kamar tayi bindiga. Dakinta ta shiga tana duba wani littafi da ta kwafe numbobinta a lokacin Ummi nata mata iskanci wai rashin aikin yi me sa hauka gashi yanzu ze mata rana. A garin neman littafin ta samo tsohon layin ta da ba sosai take amfani dashi ba, da murna ta saka tana Addu’a Allah yasa basu kulle shi ba ai kuwa tana gwada kira ya tafi amma babu kati seta loda katindaya siyo mata ranta fes ta samu numbobin harma da wasu masu amfani da bata dasu a wancan layin. Ummi ta kira ta hadata da Addah, tiryantiryan Addah ta bata labarin yanda akayi anje an siyar da gida miliyan uku da dubu dari shida, an biya me Gwal kudinta Miliyan Daya da dubu dari tawkas da Arba’in dan seda ta kawo resit din sarqar aka je da warin dan kunne gurin masu gwal suka fadi nawa gram din sa yake sannan aka buga lissafi a gurin aka siyar da warin ma aka bawa Addah kudin. Ragowar masu bashi ma tas seda Alhaji ya cire wa kowa aka biya dan abinda yai saura kuma ya riqe a hannun sa yace ze saka mata a kasuwa, ta qarasa tana cewa “Nayi baqin ciki amma dai hankali na ya kwanta da yanzu qila ina firzin, yanzu idan an kwana biyu kuma se muga yanda za’ayi ki maida abubuwan da aka lalata miki yanzu dai ki kwantar da kai ku shirya da Bashir dan a jikinsa zaki samu ni kuma zan nemo mana hanyar da zamu bi ta qarqashin qasa a samu komai daidai ba matsala”. Sallama sukayi Addah na gaya mata kartazo gida yanzu ta bari se an kwana biyu tukunna se a sannan ta gaya mata yanda sukayi da Bashir. “Ki rabu dashi, lambo zamu musu dagashi har uban naki zan nemo mana inda za’a tasar mana kansu dan shi kansa Alhajin shi ya siyi gidan sena san yanda na dawo da abuna amma yanzu muyi luf tukunna, zan turo miki Ummi seta taya ki zama. Waccen Magen yar kuma gara ki barta a Asibitin ma in aka dawo miki da ita qarin wahala ne” . Da haka sukayi sallama ta dan ji dama dama tunda an kashe waccen babbar wutar. LAGOS Kusan kwanan zaune Bashir yayi dan farkawata biyu ina ganinsa ido biyu yana faman tunanin da ban san koh na menene ba, yo ina dalili haka kawai ze saka kansa a damuwa akan abinda yasan bame yuwuwa bane ba ma. Ko masallaci basu fita ba a gida sukayi sallah yana idarwa kuma ya koma ya kwanta, ganin haka yasa na fita na fara hadawa yara abin kari su kuma suna shirin makaranta. Indomie na soya musu dan har na dakko doya Abdallah yace bazasu ci ba sauran ma suka amsa Aliyu daya baya cin soyayyar Indomin na soya masa kwai ya hada da Bread suka karya. Har suka gama ba Bashir ba labarin sa, se na miqe na shiga dakin dan in gaya masa sun shirya fa. Yana zaune a gefen gadon ya dafe kansa da hannu biyu na shiga. “Baban Ali lafiya dai baka shirya ba ga yara can suna jiranka” na fada ina zama a gefensa. Beyi magana ba ya tashi ya shiga Toilet minti kadan ya fito yana goge hannunsa da qaramin Towel, Rigar jikinsa ya cire ya dora Jallabiyya akan dogon wandon sannan ya dauki key da wayar sa ya fita yana cewa “kiyimun kunun gyada da kosai” ya sa kai ya fice. “Ko ba kunun gyada da qosai” na fada a fili ina hararar qofar daya fita, gadon na shiga gyarawa, babu dattin komai a dakin dan haka na dauke robobin ruwan da muka sha da dare na fita dasu. Seda na jiqa wake wanda daman bayarwa nake da yawa a gyara a surfa mun se a shanya shi ya bushe idan na tashi amfani kawai jiqawa nake na markada. Na debi gyada da farar shinkafa suma na jiqa. Palour na koma na gyara palour da Dining din tsaf na kunna turaren sannan na shiga wanka. Riga da Zani na saka na Atamfa na kashe dauri jelar kitson da aka mun two step sun zubo kan bayana. Juyi nayi a gaba mudubin nida kaina na burge kaina bare kuma Bashir ya ganni dukda ba cewa zeyi nayi kyau ba amma nasan har ransa ze yaba ai. Seda na markada gyada da shinkafar na saka danyar citta da kanumfari dan kadan dan kar yayi baqi sannan sake wanke blander na zuba waken na markada shi da attaruhu da Albasa se yar tafarnuwa. Kunun na fara damawa bayan yayi kauri na zuba ruwan lemon tsami yayi fari tas gwanin sha’awa na juye a Flask ragowar kuma na zuba a Wani qaramin flask din da niyyar na kaiwa Anty idan na gama. Ina ajiye Flask din kunun akan Dining Bashir ya shigo da sallama ciki ciki na amsa ina kallonsa tareda yi masa sannu da zuwa. “Yanzu zakaci na siya qosan?” Na tambaye shi, se ya girgiza mun kai yana cewa bari nayi wanka tukunna ya shiga daki na bi bayansa. Seda ya fara shafa mai bayan yayi wankan na fita na dora ma suya na yanka Albasa sannan na shiga buga qullina sosai bayan na saka kwai guda daya saboda ya qarawa qosan laushi, gishiri na saka da daskomiya dan kadan se Albasa dana yanka qanana na shiga suyar qosan, gaba daya kasko biyu da dan kadan nayi dan bashi da yawa, ina kwashe na qarshen na jiyo shi yana kira na sena kashe wutar na juye a Bowl na dakko na fita palour. Yana zaune a Dining din ya saka Jeans blue da Farar Short sleeve a gabanta an rubuta “HANDSOME” na kalleshi da murmushi nace “handsome indeed”. Murmushin ya mayar mun na ajiye kwanon na jawo Babban Mug na tsiyaya masa kunun na saka Sugar yace na saka masa Madara a raina nace “sarkin son dadi” na gama na tura masa komai gabansa harna zauna na tuna da kunun Anty sena miqe ina cewa “Bari na kaiwa Anty kunun nan”. A bakin qofa na miqa mata na juyo duk yanda ta keta magiyar na shiga amma naqi dan nasan in muka zauna qilan se Bashir ya biyo baya. Bayan na koma zama nayi nima na zuba kunun ina juyawa na kalle shi nace “Wai yau hutu ka samu ne bazaka office ba?” Seda ya cinye qosan bakinsa kafin yace “Eh zamuje fieldwork ne Delta so an banu kwana biyu mu shirya” “Toh Allah ya taimaka” na fada naja kununa da qosai na fara ci. Ya rigani tashi daga wurin nima ina qarasawa na kwashe komai naje Kitchen na ajiye dan na gaji gaskiya tun asuba idan na huta anjima na wanke su. Kan Three sitter na kwanta ina cewa “wash na gaji wallahi anya bazan nemi me aiki ba” Hankalin sa nakan Tv ya ce mun “idan da takura se ki nema din ai amma bame kwana ba” “Nima ai bana son me kwanan, abinda yasa ma ban damu dame aikin ba kaga ba wuni muke a gidan ba zaman gaba daya weekend ai” na fada ina gyara kwanciya ta yanda zan kalli TV dakyau. “Hakane” ya fada, se ya juyo yana kallona kuma yace “me kika yanke akan maganar mu?” Kallon rashin fahimta na masa, ya gane hakan se yace “maganar da mukayi jiya da daddare nake nufi kin gama shawara?” Na gano me yake nufi se nayi murmushi nace “Wai maganar Iman? To tunanin me zanyi ai tun jiya na gaya maka amsata ko” na fada ina kafe shi da ido kamar yanda yake kallo na shima, se ya sauke numfashi ya dan zamo gaba yana hade hannyensa guri daya yace “look Ma’u Alfarma zakiyi mun ki karbi yarinyar nan, kinsan uwarta sarai ba wai nutsuwa ce da ita ba bare har ta iya kulawa da wani halayenta duk se a hankali. Yarinyar nan mace ce karta tashi taga abinda takeyi ta dauka daidai ne, bana so ta tashi daban da yan uwanta ina so ta samu kula da tarbiyya irin daya....” “Anzo dai dai gurin” na raya a raina ina sheqa murmushi, tashi nayi dakyau na zauna kafin nace “Wai tsaya Baban Ali, da baka yarda da tarbiyyar ta ba ka aureta har ka hada zuri’a da ita”, se ya watsa hannu ya koma cikin kujerar sosai kafin ya juyar da kai gefe daya yace “ba haka nake nufi ba, beside Amirah ai tarbiyyar kice itama kawai.....” “To ai ka gama magana, tarbiyya tace kaga zata koyar da ita harda qari ma ko, sannan idan ma wani hali ne da ita na daban da baka so yarinyar ka ta dauka ai aikin gama ya gama tunda har ta dauki cikinta jininsu ya gauraya ta haifeta sannan tasha Nononta duk wani halayya kuma ai ta gama diba sedai ai fatan na kirkin su rinjayi na banza ko?” Zancen gaskiya ka bar mata yarta, nasan ma duk wannan maganar da kake bata sani ba dan bazata yarda ba itama. Babu uwar da tana ji tana gani za’a rabata da yarta hakanan ba wata gagarumar jinya ba ko mutuwa kai ko mahaukata se anyi da gaske ake iya raba su da Yayan su bare ita yar tilo haihuwar farko ko nicefa bazan baka ba. Idan Dan rashin lafiyar ta ne Allah ya hore maka ai ka barta a Asibiti suyi ta kula da ita har zuwa sanda suke ganin tayi kwarin da zata juri ko wanne kalar yana yi amma ba maganar ka bani ita, nawa ma idan za’a ragi wasu aciki bayarwa zanyi”. Shiru yai yana kallona harna dasa aya ina sake turo dankwalina gaban goshi, ajiyar zuciya yayi kafin yace “yanzu dai bazaki karba ba kenan?” “Allah me iko, da Hausa fa nayi maka jawabi dalla dallah amma kake sake tambaya ta kuma?” “Eh saboda kinsan ni bana son dogon surutu, amsa daya nake buqata Eh ko Aa kawai” ya fada a dan hasale alamar ya fara barin cool site dinsa ze koma Bashir dinsa na gaskiya, se kuwa na tura baki gaba nace “Toh a taqaice dai bazan karba ba”. “Shikenan, amma ina da ikon da zan kawota cikin gidan nan ko tunda gida nane” ya fada yana miqewa, nima sena miqe tsaye jin wani qundumemen rainin wayo, “Tabbas gidanka ne ka isa ka dakko kowa nene ka kawo shi ciki, zaka iya kawo ta tunda itama gidan ubanta ne ai se ka hado dame kular maka da ita, ko kuma kai zaka aje aikin ka ka zauna rainon duk ba matsala ta bace ni” na fada ina dauke kai gefe, ina jin yanda yake qare mun kallo kafin yaja tsaki tareda sakin kwafa ya shige daki na rakashi da harara ina cewa a fili “Wallahi ba tsaki ba kome zakayi sedai kayi, bazan karbi raino ba, rainon ma yar Amirah yarinyar da duk zamana da ita idan dana ze tsaga guri saboda kuka bazata dauke shi ba balle aje ga tsarkin kashi ko wanka shine ni ga jaka yanzu ta haifa za’a dakko a kawo mun in riqe mata toh ko daga turu aka kuntota qarewar rashin nutsuwa sedai duk handa za’ayi ayi”. Tsaf nasan yaji ni dan da qarfi nayi saboda yajin, na koma kan kujera na zauna, se kuma na miqe na dakko wayata na dokawa Dadar su kira dan fa karma inji wata magana daga baya. Ringing biyu ta dauki wayar, a taqaice na gaisheta ta amsa kafin na shiga koro mata jawabin yanda mukayi da Bashir, na rufe da cewa “Iya gaskiya ta na fada ko bana aiki bazan riqe mata ya ba kowa ya kula da nasa Allah ya taya masa, idan kuma Ya dage akan hakan to sedai na bar masa nawa nima ya nemo wadda zata riqe masa su ni intafi”. Shiru Dada tayi har na kai qarshe sannan ta numfasa tace “Ya kirani ya gayamun kuma na gaya masa wannan ba me yuwa bane, todai yanzu duk se hankalin ku ya kwanta tunda Allah ma ya raba muku gardamar ya karbi abarsa, se kowa yayi haquri ya maida wuqar” Dadan ta fada cikin sanyin murya, “Hasbunallahu wani’imal wakeel, ta rasu jikin ne ya sake tashi?” Na tambayeta a rude dan maganar ta dake ni dagaske, “ta rasu yanzu Likitan ya kira Naziru yake gaya masa lafiya lau dan yau sukayi niyyar sallamarta ma har an yi mata wanka ma sun bata madara tayi bacci to daga baccin ne kuma bata farka ba”. “Allah yasa me ceto ce, ya musanya mana da wadda tafi ta Alkahiri” Na fada a sanyaya tareda sauke wayar daga kunne na, ina dagowa muka hada ido da Bashir daya fito kamar wanda aka koro. “Se ki zuba ruwa a qasa kisha, da baki karbeta ba ta mutu” ya fada yana jifana da wani irin kallo kamar ni na kashe masa ita. Sena miqe na nufe shi ina cewa “karbarta ko akasin haka be isa ya chanza hukuncin Allah akanta ba tunda babu dayan mu daya halicceta ko kuma ranta yake hannunsa dan haka ko tana gidan nan tunda wa’adinta yayi dole ta mutu, in zuba ruwa a qasa nasha kuma bani zaka gayawa ba Uwarta da tai sanadinta can zakaje ka gayawa dan ita ta nuna a fili bata damu da ita ba” na wuce shi na shige dakina tareda banko qofa, in banda ma rainin hankali ji abinda fa yake cewa fa. Ina ciki naji tashin motarsa alamar fita yayi a raina nace a sauka Lafiya Allah ya gani qilan zamanta ze iya zama fitina shiyasa Allah ya karbi abarsa, Har qarfe biyar ina dakin fito ba, gaba daya zuciyata a jagule take ga alhinin rasuwar Iman ga soki burutsun Bashir na sake kiran Dada nayi musu ta’aziyya ta cikin wayar ina iya jiyo kururuwar Amirah da muryoyin mutane wasu na tausarta wasu kuma suna mata fada akan kukan da takeyi. Na tausaya mata harga Allah Kuka kam dole tayi shi wannan duka wani kan wani amma yata iya haka Allah ya tsara abinsa masu samari da yammata ma ake dauka bare ita jaririyar da ba dadewa tayi ba. Har na miqe da niyyar zuwana dora abinci wani tunani yazo mun, ta yuwu fa Bashir ya tafi Gombe be gayamun ba ga yara a makaranta lokacin tashin su tuni ya wuce, Hijabi na na dauka da wayata na fita, bari naje na ari motar Anty na dakko su dan tawa tana gurin Service ba’a dawo da ita ba, ina kulle qofar gidan motar sa na tsayawa da yaran ya dakko su se na bude na koma ciki ina jiransu. “Mami ina zakije” Abdallah ya fada bayan daya rungume ni, “Da zuwa zanyi na dakko ku na zata Abbi ya tafi Gombe” na fada ina kallon Bashir daya shigo a sanyaye kaman wanda aka sheqawa ruwan sanyi. “Abbi yace Baby Iman ta rasu wai Mami” Farida ta fada fuskarta kaman zatayi kuka, sena riqo hannunta ina cewa “ta rasu Farida” kaman tana jira kuwa ta saka kuka tanacewa “kenan banida sister mace yanzu har fa na fadawa friends dina yau a school step mum din mu ta haifo mun baby sis” “Dallah malama yi mana shiru, kina kallon yarinya kamar mage dama ai kinsan mutuwa zatayi kuma ai ma...” “Shut up You are very stupid Aliyu” Bashir da yake shan ruwa a dispenser ya katse Aliyu cikin tsawar da harni seda na tsorata amma ko gezau yaron nan beyi ba sema ido daya zubawa uban suna kallon kallo kamar wasu zakaru. “Zaka wuce daga nan ko sena zo na same ka wawan yaro har fada kake daman mutuwa zatayi kenan so kake ta mutu koh” Bashir din ya sake fada cikin bacin rai, se na saki hannun Farida da Abdallah na miqe da niyyar yin magana Aliyu ya rigani yana cewa “Toh ni Abbi me nace kawai dan na fadi gaskiya wayace su jagwalgwalata sannan su sakata a sanyi ai dole ta mutu....” be rufe bakinsa ba Bashir ya dauke shi da mari da har seda gefen bakin sa ya fashe kafin ya fizgo shi ya hau dukansa. Kuka yaran suka saka gaba daya ganin abinda be taba faruwa ba a gidan yau Bashir ne yake dukan Aliyu kamar wanda ya samu jaki, tsakiyar su na shiga ina qoqarin kwatar Aliyu da ko gezau sema cewa da yake yi “Ai daman seda nace miki ki koreta daga gidan mu muguwa ce kika qi seda ta aure shi, gashi nan yanzu yafi son su akan mu tunda ta haifi yarinyar nan kina kallo yanda hankalinsa ya koma kanta komai ita har comapany da ze bude da sunan Farida ma ya chanza na gani sunanta ya saka, shi yasa kullum nayi sallah sena yi Addu’a Allah yasa ta mutu dan akan Abbi ze iya yin komai gashinan kuma kina gani”. Bige bakinsa nayi ina fashewa da kukan nima dan na kasa tare dukan da Bashir yake masa shi kuma yaqiyin shiru nasan kalaman sa ne suke qara tunzurashi seda ya gaji dan kansa kafin ya kyale shi ya shige dakinsa ya banko qofar ya barmu muna rusa kuka kamar nan ne gidan mutuwar. Wannan wane irin bala’ine, ni na kashe yarinyar ko Yara na da ze huce akan mu? Ai kuwa wallahi da sake zan dauki komai amma banda irin wannan dukan da kalaman da basu dace ba akan yarana. 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 WATA KISHIYAR 🥰👹 (ALKAHIRI CE KO SHARRI) 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 Na Maryamah Farouk (Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah) Wattpad @MaryamahMrsAm Page 25 Ina kuka ina gasawa Aliyu fuskarsa da ta kumbura sosai saboda marin daya sha a hannun Bashir, tausayin sa ya cikani tabbas be kyauta ba amma ai dukan yayi yawa, Yanda ya zage ya ringa dukansa kamar wanda yake dambe da sa’ansa. Gaba daya yaran suna tsaye sunyi cirko cirko kowa fuska da hawaye kana kallonsu kasan a tsorace suke, bude qofar da Bashir yayi da qarfi yasa suka zabura kafin kace meye wannan sun maqalqaleni wani kan wani Jafar yana cewa “kice masa yayi haquri Mami dan Allah karya doke mu”. Tausayinsu da matuqar takaicin Bashir ya sake qume ni, na daga idanuwana da har sun qanqance saboda kuka na kalleshi yana tsaye shima mu yake kallo, fuskarsa a daure tam haka idanunsa sun kada sunyi jajir har wata jiniyace ta fito a goshinsa. Daga tsayen yace mun “Ina kika saka mun folder dana ajiye akan Gado”. Ayanda nake jina Banyi niyyar tanka masa ba amma saboda yaran da suke gurin bana so na bada qofar da zamu ringa raba hali a gabansu dan hakan ze shafi tarbiyyar su, “Ina zuwa” nace masa kafin na miqe na kama Aliyun da zuwa sannan jikinsa ya rufe da zazzabi me zafi amma saboda dakiya da taurin kai har sannan ko digon kwalla babu a idonsa. Dakinsu na rakashi, ina tsaye ya shiga ya watsa ruwa a jikinsa ya fito dakyar ya kwanta akan gadonsa. A cikin first Aid box dinsu na ciro masa Paracetamol na bashi yasha, ina zaune a gefen kansa nace “Aliyu kana babba kai kake so ka raba kan qannenka ko, irin abinda na koya muku kenan ka tsaya mahaifinka yana fada kana fada Aliyu?” Se a lokacin ya saka kuka yana cewa “Mami Abbi ya canza wallahi ya dena son mu, da bakwayin fada amma yanzu kullum se sukunyi kuma duk akan Anty Amirah ne. Mami yanzu fa da muna tahowa yana waya da Abokinsa Uncle Bala yana ce masa daman bakya son yarinyar yace ze kawo miki ita kinqi yanzu gashi ta mutu hankalinki seya kwanta ai”. Shiru nayi ina shafa kansa, wato a gabansu ma ya fadi haka kenan, tabbas shi ya bada qofar da yaran zasu ga baqin sa ko bayan haka yana sane Aliyu ai photocopy dinsa ne daman, duk wani hali daya ke taqama dashi Aliyun ya kwasa harda qari dan badan ma Irinta Allah ya bawa Aliyun a matsayin uwa ba da ba qaramin wuyarsa za’a sha ba. Numfashi naja kafin nace “koma menene karna sake gani, Abbinku yana sonku ka sani irin son da yakeyiwa Iman, ba fata ba yau ko daya daga cikin mu ya rasa irin damuwar da ze shiga kenan kasan halinsa kuma idan yana cikin damuwa Fada yakeyi da kowa. Dan haka ka kiyaye Aliyu karna sake jin wata magana irin haka kaine babba komai kayi qannenka suna koyi da kai ko so kake Allah yayi fushi daku kuna sabawa mahaifinku?” Girgiza kai yayi a sanyaye, na ci gaba da cewa “yawwa Haidar dina kar a sake, gobe kuma ka same ahi ka bashi haquri kaji ko dan yanzu dai be huce ba” “Insha Allah Mami bazan sake ba” ya fada. “Yauwa Allah yayi muku albarka ya kulamun da rayuwarku” “Amin Mami, I kove you” “I love you more” na fada tareda kissing goshinsa kafin na ja masa bargo na fita. Seda na lallaba sauran suka cire uniform na dora farar shinkafa dan ina da miya na barwa Amna ta duba sannan na tafi dakin nasa. Ina tura qofar yana sako kai ze fito, ya watsamun kallon banza na mayar masa da martani na shige se ya biyo ni yana cewa “Wato daman abinda kike gayawa yaran nan kenan kina koya musu mugun hali har Aliyu yana fadar na fi son Amirah akan su ko?” Banza na bawa ajiyarsa, na jawo drawer dana saka folder na dire masa akan gadon kafin na miqe na nufi qofa. “Ma’u” ya kira suna na kafin yaci gaba da cewa “Wato Ma’u kin rainani, saboda wulaqanci da rashin mutunchi ina miki magana shine kika sa kai zaki tafi bayan tara yayana da kike yi kina cusa musu tsana ta a zuciyar su ko?” Tsabar mamaki daskarewa nayi a guri daya na kasa gaba na kasa baya, wace kalar kwaya Bashir yasha ne? Ko kuma rasa Ÿa hauka ne ko a kansa aka fara, kai da alama dai kawai Bashir ya shirya ci mun mutunchi ne idan ba haka ba ya gama jibgar mun Da sannan ya kalleni yace wai ina masa wulaqanci da rashin mutunchi, waiwayawa nayi na gyara tsayuwata sosai ina kallonsa “Wulaqanci ko rashin mutunchi ba tarbiyyata bane dan da ace na iya da bamu kai shekara goma sha shida tare da kai ba, batun in tara yaran ka kuma in cusa musu tsanarka..” na dan dakata tareda qara taku biyu na dawo gabansa sosai, murmushi nayi me kama da yaqe kafin na ci gaba da cewa “Base na zugasu akan ka ba, yanda kyakykyawar mu’amalarka gare su ta sa suke sonka haka sababbin halayen daka tsiro dasu zasu bi su goge duk wannan so da shaquwar da kake gani a tsakanin ku, sannan kayi a hankali duk abinda yaro ya gani a gurin iyayensa tarbiyyar da ze tashi da ita kenan musamman kai me Ÿaya maza zasu tashi su zata abin kirki kake aikatawa kaga haka zasu tafi da matan da.....” “Ya isheki Asma’u” Bashir ya katse ni cikin hargagi tareda daga hannunsa ya nufoni da niyyar mari, sedai ko me ya tuna ya janye tareda kaiwa Bangon dayake bayan mu naushi sannan ya juya ya dafe kansa yana huci kamar wanda ya hadiyi kunama. Tabbas na tsorata, na kuma saddaqar sheya shararamun mari a yanda ya nufo ni amma taurin zuciya da dakiyar dana dorawa zuciya ta bata sa baki na ya mutu ba, kallonsa nayi da kallon da ni kaina bazan iya fassara shi ba, na tsana ne ko na takaici da baqin cikin abinda Bashir yakeyi mun nace “Nima dukana zakayi kamar yanda ka kusa illata danka gashi can kwance, to ka tabbata hakan shine abu na qarshe da kwakwalwarka zata raya maka akaina dan wallahi Bashir sekayi dana sanin dora hannunka a jikina da sunan duka, har Mahaifina ya koma ga Allah ban taba ganin ya dagawa daya daga cikin matansa murya ba ballantana har ya dake su se kai kake tunanin zaka daki yar sa? Toh bismillah” na fada ina zare masa ido kamar wani dana. Naga alamar se nayi masa haukan gaske sanann ze shiga hankalin sa, wata irin tsanar Amirah ce tayi mun dirar mikiya dan itace sila, ita ta janyo komai da yake faruwa da be aure ta ba da haryanzu muna cikin zaman lafiyar mu da qaunar juna amma tunda ta shigo rayuwar mu abubuwa suke rinchabe mana bamu taba rufa sati ba tareda munyi tashin hankali da Bashir ba. Shiru mukayi gaba daya, ni ina jiran ya sake wata magana ko yunqurin marin nawa dan wallahi sena gwada masa nima yar buyagi ce yau amma se yai shiru, kiran Sallar Magriba ya sakashi shigewa Toilet ya bugu qofar da qarfin gaske se na bishi da harara kafin na ja dogon tsaki na fice daga dakin. Seda na tashi Aliyu na sake bashi awa paracetamol bayan yaci abinci yayi sallah kafin bacci ya sake dauke shi, gaba dayan su basu da walwala haka na daure na ringa tausarsu har sukaci abinci sunayin sallar isha kuwa kowa ya nemi makwanci sa har yan biyu da suke qanana sun shiga nutsuwarsu dan Muhammad dayaga Bashir ya fito daga dakinsa ze shiga Kitchen ma kuka ya saka ya rirriqe Jafar. Ina kallon yanda yai turus yana kallon yaron, duk da fuskarsa bata nuna ba amma jikinsa yayi la’asar daga gani cike yake da nadamar abinda ya aikata amma izza irin tasa bazata barshi aga gazawarsa ba. Palour na dawo na zauna bayan duk sun shiga daki ina jiran kota kwana, jira nake naji ko Bashir zece na bashi abinci ko ya sake gayamun wata maganar banza a daren nannayi masa wankin babban bargo amma shiru har sha daya ina zaune ban sake jin motsinsa ba. Dakina na shige nayi wanka, Idona sun soye bana jin bacci dan haka nayi Alwala nayita jera salloli ina kaiwa Allah kukana har seda gabbaina suka gaji kafin na kwanta ina ci gaba da jan carbi. Nayi niyyar washe garin na kira Amirah da Addah nayi musu gaisuwa amma wallahi na fasa, na kuma shirya duk wanda ya sake bude baki ya gayamun zancen banza a gidan nan bazan daga qafa ba sena gaya masa na wofi. Da safe ban jira shi ba na shirya yara na kaisu Makaranta a motarsa daya bar Key akan Dining be dauke ba. Tare muka fita da Aliyu bayan na bada excuse din bashida lafiya na wuce dashi Asibiti aka sake duba shi suka rubuta masa magani muka dawo gida. Ina Kitchen ina dama masa wa Aliyu custard naji fitowar Bashir daga daki, sena dawo bakin qofar na leqa tareda kasa kunne ina jin Aliyun yana gaishe shi, se ya amsa harda tambayarsa yaya jikinsa yace da sauqi. “Abbi kayi haquri bazan sake ba” naji Aliyun yana fada, se Bashir yace “Ya wuce Aliyu kaima kayi haquri ina cikin fushi ne na dake ka gashi har naja maka ciwo, kaci abinci muje na kaika Asibiti a duba ka” Bashir ya fada, se Aliyun ya nuna masa ledar magungunan da muka siyo yace “Mami ta kaini yanzu ga magani ma an bani” “Ok Allah ya qara sauqi, ka huta sosai kaji bari naje office nakai papers din nan. “Yawwa yaron kirki ga shi tashi kasha” na fada ina ajiye masa. Nida Aliyu muka wuni a gidan ya warware har yana tayani aiki munata hirar mu, qarfe hudu har na kira Uber zan tafi dakko yara se gasu sun shigo wai Driver Office dinsu Abbi ne ya dakko su. Bashir ne dawo gidan ba se 9 na dare, muna zaune muna kallo ya shigo da sallama hannunsa dukka biyu da ledoji, Kallon cikin ido mukayiwa juna kafin na janye nawa ina tabe baki yara suka tashi suna masa sannu da zuwa ya amsa ya basu ledojin hannunsa manya guda biyu ya wuce da qaramar dakinsa. Be dade da shiga ba ya kwalawa Aliyu kira ya tashi ya tafi sauran suka bude ledojin, tarkace ne kowa Abinda yafi so ya siyo masa, indai yaudara ce ya kware daman, ya zuga rashin mutunchi sannan ya siye ka da abinda yasan kana so. Ina jinsu suna tsallen murna banbi takansu ba. Aliyu ne ya fito ya debi abinci a plate ya hada da ruwa da cup akan Try yaje ya kai masa ina kallonsa ban ce masa komai ba ya sake dawowa ya debi zobon dana hada ya kai masa. Da gudu ya fito daga dakin yana tsalle da ihun murna na waiwaya ina cewa “kai meye haka zaka zo kana mana ihu akai” “Kukalla ku kalla” ya fada yana daga kwalin wayoyi iphone X guda biyu, Amna ya jefawa daya kafin ya zauna cikin zumudi ya shiga bude ta hannunsa. “Yaya waya aka siya muku” Jafar ya fada yana komawa kusa dashi, “Wallahi Mamai waya ce, yeee munzama yan gayu muma Faree mun samu tayim snap” Amna ta fada tana daga wayar tata Fara ta Aliyu Baqa. Duk su biyun suka dawo kusa dani suna nuna mun, na karba ina cewa “iye yan gatan Abbi gaskiya kun gode Allah ya sanya Alkahiri ya sa lafiya ta kashe”. Gaba daya sun cika gurin da ihun murna, sun dade suna nacin a siya musu waya amma yaqi yace se sun gama secondary school idan zasu kira abokansu sedai su karbi tawa ko tasa kowannensu dai yana da Laptop itama dan dokar makarantar suce amma yanzu da yake neman shiri yake da yaran shine ya siyo musu da kansa, Bashir kenan. Ana tsaka da murnar ya fito da plate din abincin, Jafar ya tashi da gudu ya karbo yana cewa “Abbi mufa, se yaushe za’a siya mana?” “Ba yanzu ba Sheik baku isa riqe waya ba amma zan chanza muku PS 5 gobe kuma za’a kawo muku” ya fada yana zama akan kujerar da take kallon wadda nake kai. Sabon ihu suka dauka harda yan biyu dan suma sun koya musu Game, ba damar a samu zama a gida anyita buga PS sena gaji wani lokacin na dauke. Ina kallon yanda yake ta wani murmushi yana jin dadi ganin yaran na murna an shirya kenan, yana kallona na sake hade girar sama data qasa, sen miqe ma ina cewa Farida idan sun gama tura hotunan da sukeyi daga wayata ta miqomun na shige dakina a jikana ina jin yanda ya bini da kallo amma ban waiwaya ba. A dakin ma ban zauna ba, wanka na shiga nayi shirin bacci, sena dakko Backpack din da nake zuwa office da ita na fito da kayan ciki ina dubawa dan nima ranar Monday zan koma aiki in Allah ya kaimu, gajiya da jiran Farida nayi sena leqa dan ina so na kwanta har sannan suna zaune Bashir na nuna musu ko menene oho a wayarsa. “Farida bani wayata, bazaku tashi kuje ku kwanta ba ko gobe akwai school fa” na fada daga bakin qofa. Seta taso da gudu ta bani ta sake komawa, “Oh ina magana duk kunyi mun shiru ko” na sake fada, se Bashir ya dago yace “Babu aiki gobe Workers day” “Au toh, seda safen ku” na fada ina juyawa ciki. Harna kwanta naji message ya shigo wayata, kamar bazan duba ba sedai na janyota, Bashir ne “Ina son magana dake” ya rubuta. Guntun tsaki nayi na maida wayar na ajiye naja bargo na, Befi minti uku ba tsakani kira ya shigo, sauri nayi na sakata a silent, ina kallo seda yai kira uku nai likimo abuna dan bazan dauka ba, wato nice baze lallaba ba tunda ya shirya da yayansa shikenan ba ina cikin wannan tunanin naji an turo qofa. Luqus nayi harda wurga qafa gefe dan fitila a kashe take ni a dole bacci nakeyi, ina jinsa ya kunna hasken ya tsaya akaina yana kallona. “Ma’u Ma’u” ya fada yana bubbuga pillow da nake kai, senayi miqa tareda qantsarewa ina salati irin an tashen nin nan nayi mici mici da ido ina kallonsa nace “Lafiya zaka zo kana tashina a bacci”. Seda ya zauna gefen qafafuna ya wani kumbura baki yace “baki ga message dina ba da calls dina ba?” “A mafarki ka turomun halan” na fada ina tura baki gaba. Se da yayi kwafa sannan yace “saboda abinda ya faru yasa kika dauki fushi dani, naga wanda na doka din ma mun shirya se kece zaki ci gaba da gaba dani” “Ni kuma inyi fushi dakai ana me Baban Ali space dai na baka ka gama zaman makokin idan ka dangana kayi tawakkali se mu ci gaba da magana” na katse shi ina gyara kwanciya, gajeran tsaki yaja kafin yace “Oh banida tawakkali kenan” “Ni awa ince baka da tawakkali, hausa nayi maka bawai abinda nake nufi kenan ba” na fada ina danne dariyar dake neman kufce mun ganin yanda yai kinini da fuska yana jan iska. “Gobe da asuba zamu tafi Delta inaga zamuyi kwana biyar ko sati saboda tafiyar nema yasa ban tafi Gombe ba” “Allah ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya” na fada a qagare dan na fara jin baccin gaske, se ya miqe yana cewa “ta so muje can, ban hada kaya ba kuma ina so nayi bacci kinga fitar Asuba zamuyi”. “Yi gaba gani nan” na fada ina miqewa kamar zan shiga bandaki, yana fita na rufe qofar na murza key, a fili nace “Dan rainin wayo sedai ka tafi babu kayan kuwa” nai hayewata Gado na kwanta ina jinsa yana kiran suna na yana kwankwasa qofar a hankali nayi biris dashi harya gaji ya tafi, duk randa ya koyi karbar laifinsa, ya iaya bada haquri ma shirya. Da Asuba da muka hadu kamar kububuwa ya wuceni ya shiga kitchen, ya gama diri dirinsa ya fito daman nasan ba abinda ze iya tsinanawa mutumin da inaga ruwan zafi kadai yasan yanda ake dafawa. Amna ya kwalawa kira ta fito daga dakinsu yace maza ta soya masa kwai. Ina kallonsa ya shiga dakin ya fito yana doka uban tsaki ya kalli inda nake ya sake komawa seda ya shiga sau biyu ana ukun ne yace “Dan Allah Ma’u kizo ki hadamun kaya su Musa har sun kusa qarasowa” “Au wai baka hada kayan ba me kake jira toh” na fada ina tashi zaune akan kujera. “Kin sani ban iya ba ke kike hadamun, please Ma’u”. “Badan halinka ba muje” na fada ina miqewa. Kusan rabin wardrobe din ya watso su qasa, cikeda takaici na shiga hada masa kayan a qaramar akwati na gama ina zugewa ya shigo da kofin shayi a hannunsa ya ajiye akan mudubi yana cewa “har kin gama” Ban amsa ba na shiga kwashe na qasan ina mayarwa, horn da muka jiyo daga waje yasa na dakata na daukar masa Laptop bag dinsa shi kuma yaja akwatin muka fito, Jafar na tsaye a kofar dakin su ya gaishe shi yace “Abbi a kawo fa” “Za’a kawo Sheik ina sauran yan uwanka” “Sun koma bacci Abbi” “Ok idan sun tashi ka gaya musu na tafi Delta zamuyi waya idan na sauka” ya fada yana tafiya. “Allah ya tsare Abbi” Amna da Jafar suka fada. Daga bakin qofa na tsaya ya miqawa Driver Akwatin ya karbi jakar hannuna bayan na masa Adawo lafiya naja kofar na koma ciki. Seda na kwashe kayan da ya zubar tsaf ina mita “Abinda ko Su Muhammmad baza suyi mun ba shi yake yi, da yake buqatar kansa ce ai ya iya roqa a masa mtsw” naja tsaki. A dakin na kwanta na qarasa baccina. GOMBE Acan Gombe kuwa ranar talatar da safe Bashir sukayi waya da Naziru ya gaya masa yaje Asibiti ya karbi Iman daga nan ya wuce da ita gurin Dada kafin ya gama yanke abinda za’ayi. “Ni se nake ganin yaya da kayi haquri, be kamata ace ka raba Uwa da yarta ba idan kayi haka kamar ai bakayiwa Amirah da ita kanta Babyn Adalci ba. A yanayinta tana buqatar dumin uwa da kuma Nono ko dan ingancin lafiyarta” Naziru ya fada bayan da ya gama jin umarnin yayan nasa. Shiru Bashir yayi, Tabbas gaskiya Nazirun ya fada amma toh amma meye amfani mayar mata da ita ma yanzu bayan ta riga ta yaye ta kusan sati bata sha Nonon ba se madara ai dakyar ma idan zata karba yasan, kuma fa shi ya gama yanke hukuncin sa ta hakane kadai ze hukunta Amirah taji a jikinta yanda gobe bazata sake gwada yin abinda tayi ba. “Kaje kawai ayi yanda nace, na rigada munyi magana da Dadan, zuwa Next week idan na samu dama zanzo nan Lagos zan dawo da gurin Ma’u” “Anty kuma? Ita tace zata riqeta?” Naziru ya tambaya cikin mamaki. Se Bashir din yace “No, bata rigada ta amsa ba amma ai gida nane ina da ikon sawa da hanawa ko” “Hakane” Naziru ya fada sukayi sallama, a ransa yana mamakin wannan zallar rashin Adalci irin na dan uwan nasa. Tayaya zaka taba jaririya da uwarta ka dauka ka kaiwa wata wadda ita kanta tana da buqatar me taimaka mata. Ÿaÿa Bakwai nefa a gaban ta take kula dasu ga shi sannan kullum seta fita aiki ai wallahi ko ita kanta yanzu kamata yayi yace ta dakata da haihuwa ta ji da abinda yake a gabanta balle har ya dauki raino ana zaune lafiya ya kai mata. Daman lokacin daga wanka ya fito dan haka ya zura rigarsa ya cewa Dada bari yaje Asibitin ya karbo yarinyar “Amma fa Dada kiyi masa magana idan ba haka ba wallahi ze janyo abinda za’a zo ana samun sabani daga qarshe kuma ace za’a ga laifin Anty Ma’u” ya fada yana tsaye daga bakin qofa. “Ka rabu dashi Naziru, gurin uwarta za’a maida ta, shi a ina ma ya taba ganin anyi haka? Idan so yake ya kaita cikin yan uwanta se ya bari idan Allah ya rayata ta isa sakawa a makaranta a sannan yana da hujjar da ze iya dauketa ya maida ita can ko dan ta samu ilimi irin na sauran amma ba yanzu ba. Ni wallahi na rasa me yake damun Bashir, mutum tamkar wanda yake da wani motsi a kansa”. “Ba wani motsi wallahi Dada tsabar samun gurine tunda yaga duk sharar daya debo kina goya masa baya shiyasa”. “Yanzu dai jeka, idan ka dawo se muje tare can gidan nasa, dukda ya kamata na kirashi ma yabar yarinyar nan ta koma gida tayi jego ko ta dawo nan dole se an taimaka mata kafin ta saba ai” Dada ta fada, Naziru yayi mata sallama ya tafi Asibiti. Yana zuwa ya tarar da wannan tashin hankalin, bashida karfin guiwar kiran Bashir dan haka likitan ne ya kirashi shi kuma ya kirawo Dada ya gaya mata. Bayan an gama cike ciken takardu ya saka hannu aka bashi gawar, be iya tafiya ba seda Ya kira Sa’ad Yayansa da yake bi yazo suka tafi tare suna kaita gida Dada tace suje su dakko Amiran sannan ta kira Ummi a waya tace suzo ita da Addah yanzu. Fadar tashin hankalin da Amirah ta shiga bata baki ne dan sumanta uku ta ringa kururuwa tana ihu kamar wadda ta hau bori, se da Goggo Ladi qanwar Alhajin su Bashir tayi mata tatas sannan aka samu ta lafa da ihun amma fa bata dena kukan ba. Addah kanta tasha kuka fadi take daman yan baqin ciki basu so aka haifeta ba gashi yanzu anyi manaqisar da seda aka rabata da duniya su dai Allah ya isan su bazasu yafe ba. Babu wanda ya ko bi ta kanta, da dare yayi zata tafi da Amirah Alhajin su Bashir ya hana yace ta barta acan dan yasan idan sun tafi ma a maimakon ta taishe ta Allah kadai yasan abinda zata je ta kitsa mata kuma. A wayar Ummi Bashir sukayi magana da Amirah, yanda ta ringa ya bala’in daga masa hankali gaba daya tausayinta ya rufe shi. Allah ya sani yana son yara kuma wannan yarinyar haka kawai yaji duk cikin Ÿaÿan sa tafi shiga ransa kamar sanda aka haifi Farida sedai har nata ya zarce Faridan. Badan Assignment din da yake gabansa ba da a ranar yaso yaje amma ya mata Alqawari daya gama zezo Gombe, ya ringa rarrashinta yana gaya mata kalamai masu kwantar da hankali tareda Alqawarin kwanan nan zasu samu wata qilan ma yan biyu, da haka ya samu tayi shiru har tayi bacci sannan ya kashe wayar. Kunsan December watan hidima ne 😁😁 weddings everywhere To all the December brides Allah bada zaman lafiya 🙌🏼🙌🏼 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 WATA KISHIYAR 🥰👹 (ALKAHIRI CE KO SHARRI) 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 Na Maryamah Farouk (Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah) Wattpad @MaryamahMrsAm Page 26 Har Bashir ya gama kwanakin sa a Delta ba wani magana mukeyi ba, a ranar da ya tafi dai bayan sun sauka ya kirani haka washe gari da safe kafin su fita field munyi waya bayan nan kuwa har suka kwana hudu be sake kirana ba nima kuma ban kirashi ba. A tunani na ko aiki ne yayi masa yawa, dan daman yawan ci idan yana field bamu cika yin waya ba shine dai idan ya samu lokaci ze kira to wannan karon ma na dauka a hakan ne. Ranar Lahadin da suka kwana hudu da daddare muna zaune wayar Aliyu dake kusa da ni tayi qara, "Aliyu wato har ka rarrabawa Jama'a Number ka ni bani da ita koh, waye yake kiranka da daren nan?" Na daga wayar ina dubawa. "Super hero" naga an saka, na gane Number Bashir ce sena miqa masa ina cewa "uhm uhm su Bat Man ne ko Spider man naga an sa super hero". Gaba daya suka saka dariya, Aliyu ya daga wayar suka gaisa, ban san meya gaya masa ba nadai ji yace "toh ga Mamin ma ko na bata ka gaya mata?" "Tam Abbi bye" ya sake fada kafin ya kashe wayar yana kallona. "Mami, Abbi yace Mr Kunle ze zo yanzu ya kawo saqo, akwai kudi a bedside drawer dinsa ki bashi 20k". Kamar wata sokuwa haka nake kallon Aliyun harya gama. Abubuwan mamakin da yawa, ashe Bashir yana da lokacin kiran waya nice baze kira ba. Sannan yaushe muka fara haka da ze fadi abu ni baze kirani da kansa ya gaya mun ba sedai ya kira Aliyu? Wayata dake kan centre table na janyo na danna power button dan na tabbatar ko a kashe take be sameni ba ya kira Aliyun naga a kunne take. Ga network dina full to meye dalili? "Hmmmm" na fada a fili kawai na ci gaba da kallon da muke, ba'a jima ba kuwa aka danna Door Bell Jafar yaje ya bude se gashi da Babban Package da alama PS din da aka ishe ni da naci kamar nina ce zan siya aka kawo. "Mami yana jiran saqon wai" ya fada bayan ya zauna ya fara budewa Abdallah na taya shi. Se na waiwaya na kalli Aliyu nace "Kaje ka dakko masa baya gaya maka inda suke ba?" Seda yai dan jim kafin ya miqe ya shiga dakin nasa, be jima ba ya fito da kudin a hannunsa ya miqo mun yana cewa "Gashi na dakko". A hasale nace masa "zaka tashin mun akai ne ko yaya, ina kai ya gayawa saqon kuma kazo kana nunamun me zanyi dasu". Zugui zugui ya fice ya kaiwa Kunle kudin ya dawo. Ina kallon yanda yake satar kallona ganin na dora qafa daya kan daya ina girgizawa duk sanda suka ga ina haka to sun san zuciyata a kusa take, ina iya make su idan suka matsamun. Hayaniyar da Jafar da Aliyu suka fara suna qoqarin jona PS din da Tv tasa na daka mutsu tsawa ina cewa "ku bace mun a nan, ba gobe Monday ba shine a wannan lokacin kuke shirin dasa wata Game, ku tattara ko yanzu na fasata wallahi". Kama kansu sukayi sum sum gaba daya suka watse, ina zaune ina sakin tsaki, son na tabbatar da zargina sena janyo wayata na dokawa Bashir kira na kuwa taki sa'a akace call waiting. A da, indai na kira Bashir ko da wa yake waya se ya dakata ya amsa kirana, ba qaramar waya me muhimmanci bace zan kirashi ya kasa katseta amma yau har ta gama ringing ta yanke be daga ba. Na sake kira nan ma be daga ba, seda na jera masa kira hudu amma bawan Allahn nan ko a jikinsa kuma har sannan call waiting. Agogo na kalla, tara harda rabi tayi, nasan babu wani official call da ze ce yana yi yanzu, kuma na tabbata bada Dada yake waya ba dan sanin da na mata da Tayi Isha take kwanciya to da uwar wa yake waya da baze amsa tawa ba? "Amirah" zuciya ta ta raya mun, se ta yuwu kuwa din. A jiye wayar nayi ina jiran ya biyo baya amma har goma da rabi shiru ba kiran Bashir babu labarinsa, sena miqe jiki a sanyaye na shiga dakina. Tunani na shigayi ko na masa wani abu a wayar da mukayi qarshe, iya hasashena ban gano komai ba dan lafiya mukayi hira kamar ma be tafi muna fushi da juna ba. Haka na ringa juyi a gado ina tunane tunane to wane sabon shafin ne kuma ze bude mun, koma dai menene Allah ya bamu wuce wa lafiya da haka bacci yayi awon gaba dani. Daga mamaki mani abun na Bashir tsoro ya koma bani, dan fa washe gari be biyo kirana ba, da yake na koma aiki nima ranar na shiga busy ban wani nutsu ba se da daddare na duba wayar na tabbatar da be kira ba kuma qarin abun mamaki da magriba ma seda ya kira Aliyu ya bawa dukka yaran sukayi waya harda tambayar me ze taho musu dashi. Nidai ido na kawo na zubawa sarautar Allah, duk tsiya dai ze dawo gidan se inji me ya faru kuma. Na zata ranar Larabar ze dawo tunda itace cikar sati da tafiyar su daman kwana biyar yace ko sati to gashi har yau Talata dan haka na saddaqar se gobe ze dawo. Bayan na tashi aiki  na biya na dakko yara, dukda magriba ta kawo kai haka na biya wata yar kasuwa da ake siyar da Dangin su Kaji masu rai, Bashir yana son Danderun Zabi dan haka na siyi manya guda biyu aka yanka su aka fige kamun muka kamo hanyar gida Ba mu muka isa ba se ana shirin shiga sallar Isha saboda holdup. Jakata kawai na ajiye muka shiga Kitchen tareda Amna, seda na wanke Zabon tsaf yanda nake so kafin na saka a kwando su tsane na bar Amna ta hada kayan hadi dan tana fashin sallah ni kuma na tafi nayi magriba da Isha . Sanda na dawo ta hada komai na marinate dan tasan yanda nake so, seda na saka wuqa na huda jikinsu sosai yanda kayan hadin zasu shiga na shafe lungu da saqo na ko ina ya juqu sannan na nade a Foil paper ya nadu da kyau, Already ta kunna oven yayi zafi dan haka na dora su akan Baking try da aka zuba ruwa na kunna wuta sama da qasa na rufe. Ban san sanda ze dawo ba da safe ne koda daddare dan haka A daren nan seda na hada masa zobo irin wanda yake so na saka a fridge, na gyara zogale na yanka Albasar da zanyi masa Dambun shinkafa nice harda dakan gyada kamar aljana na turara tsakin shinkar  na saka komai a fridge yanda gobe kawai sedai na hada. Na gaji tiqis, haka na koma palour na kwanta ina yi ina duba naman dana saka ina qara ruwan dan karya qone nice har qarfe biyu, jin bacci na neman fin qarfina na kashe kawai tunda nasan zuwa yanzu yafi rabin dahuwa in Allah ya kaimu gobe na ci gaba. Dakyar na iya tashi sallar asuba dan ji nayi kamar ma ina kwanciya aka tashe ni. Haka ina yin sallah na koma kan aikin, ga shirin yan makaranta da ni kaina. Qarfe bakwai muna breakfast Bashir ya kirani. Rai a sake na amsa wayar duk da qasan zuciyata akwai haushin qin kirana da yayi amma na daure dan babu qarya nayi kewarsa sosai, rabon da mu kebe tun muna Gombe. A dake ya amsa gaisuwar da nayi masa, mukayi shiru gaba daya kafin ya nisa yace "Yau zamu dawo In sha Allah zuwa dare zan shigo gida". "Masha Allah, Allah ya dawo daku lafiya nayi kewarka da yawa". Na fada cikin shauqin da na kasa dakatar da kaina. Wani miskilin murmushi yayi kafin yace "Na sani ai" "Oh ka ma sani kenan" na fada adan shagwabe. "Zan kiraki anjima" ya fada, ko kafin na bashi amsa ya katsewa wayar, sena ajiye na ci gaba da kurbar Tea na rai fes. Seda nayi yar murya sannan aka bar yaran suka shiga makaranta saboda mun makara, School Bus nace su biyo idan an tashi kawai dan inaga idan Bashir ya dawo kawai zan masa magana su ringa bin school bus din kamar zefi sauqi. A office ma ban wani maida hankali ba, qarfe biyu na dauki excuse na tafi gida. Seda na gyare gidan qal na chanza Bedsheet din dakin Bashir na saka turaren wuta. Kayan harkar dana hada na shanye kafin na dakko wani hadin dilka da Anty ta bani na na mutstsike jikina tsaf na turara sannan na dauraye jikina na koma Kitchen. Na riga naci qarfin aikin tun jiya, Danderun na duba yayi luguf dan tun shigowata na ci gaba da bashi wuta gaba daya gidan ya dume da qamshinsa ga na turaren da nayi se suka hadu suka bada wani kalar qamshin yan gayu, nan da nan na hada Dambuna sannan na dora tuwon semo da miyar Danyar kubewa taji naman rago dan Bashir yana sonsa. Kafin Magriba munyi wanka nida yaran munyi kwalliya yanda kasan ranar sallah. Wata Atamfa na saka Batik Maroon da akayiwa dinkin A line me dogon hannu babu ado a jiki se aikin stones da aka mata se walwali takeyi na kashe daurina na baza qamshi duk inda na juya yara se sun ce "kai Mami kinyi kyau wallahi" ni kuwa se jin dadi nakeyi. Ina tahiyar qarshe a sallah naji waya ta tana qara kafin nayi sallama ta katse. Bayan na idar na janyota dan nasan Bashir ne, ilai kuwa wani kiran nasa ya sake shigowa. "Ranka ya dade Mijin Ma'u, ka iso nazo na bude maka qofa ne" na fada da yar dariya. Dariyar shima yayi cikin jin dadin sunan dana kira shi yace "Mun dawo amma ban qara so gida ba" "Masha Allah, sannunku da dawowa, muna jiranka nida yara mun shirya maka babbar tarba". "Dagaske, me kika tanadar mun?" Ya tambaye ni, seda na gyara zama kafin nace "Duk abinda kake so" na bashi Amsa. "Ke kadai nake So Ma'una" yayi maganar cikin wani salo da yayi mun dirar mikiya dan har seda naji kamar numfashina ya tsaya na dan lokaci, jikina ya karbi saqon sa dagaske, se na yi qasa da murya kamar me gudun wani yaji abinda zan fada nace "Na tana dar maka kaina, kai kadai nake jira Farin cikin Ma'u". Na fada sannan muka kashe waya. Cike da zumudi na tashi na mayar da dankali na na sake gyara fuskata sosai na qara turare. Palour na dawo muka zauna motsi kadan mu kalli qofa kowa ya qagara Abbi ya dawo har dai aka kira Isha Malam Bashir shiru. Tafi tafi fa har qarfe tara babu Bashir gashi yara har sun fara qorafin yunwa suke ji, se na tashi a sanyaye na dibar musu abincin bayan sun shimfida Table mat a qasa dan kar a bata gurin suka zauna suka ci. Muna zaune goma ta buga zuwa sannan hankalina ya fara tashi anya lafiya kuwa gashi na kira wayar sa har sau biyu bata shiga daga qarshe ma aka ce a kashe take. Muna tsaye tsuru nida Amna da Aliyu dan ragowar sun kwanta, Aliyu ya kalle ni yace "Mami ko naje na tambayi Baba Audu naga yana gida". Se a sannan ma tunanin yazo mun da mu gayawa Baban, na dago kai da niyyar bashi amsa wayata dake hannuna tayi qara alamar shigowar message. Number Bashir ce, sena bude da sauri na fara karantawa "I'm sorry Ma'una, na wuce Gombe" Abinda ya rubuta kenan. Wani duhu ne ya gifta idona na saki wayar a qasa nayi baya kamar zan fadi Amna da Aliyu suka riqe ni, "Mami meya faru? Wani abu ya samu Abbin?" Aliyu ya shiga tambayata a rikice, dakyar na iya cewa "Dauko mun Inhaler" se ya sake ni ya tafi da gudu dakina. Wayata Amna ta dauka ta bude, ina kallon ta bayan ta karanta message din ta goge daidai sanda Aliyu ya dawo yana bani Inhaler ya karbe wayar aga hannunta yana cewa "Na gani me aka turo" se ya bude ya kalle ta yace "Ni banga komai ba, Mami wai menene?". Seda naji numfashi na ya daidaita, Ina da Asthma kuma yawan ci baqin cikin Bashir ne yake motsamun ita dan ni da na shiga damuwa ko tashin hankali zanji numfashi shina yana sama sama. "Ku tashi kuje ku kwanta babu komai, ashe ma basu taho ba" na fada ina qoqarin miqewa. Se Aliyu ya zuba mun ido kamar be yadda da abinda na fada ba, seda na sake maimaitawa sannan suka miqe. Hannuna ya kama yace "Mami muje ki kwanta toh" "Aa Aliyu sena kwashe abincin nan karsu lalace" na fada cike da qarfin hali dan na matsu subar gurin ko zan samu damar fashewa da kukan daya tokare mun maqoshi. Qarfin hali kawai nayi muka kwashe kayan, ina shiga dakina na jingina da qofar na fashe da wani irin kuka na zallar baqin ciki da takaici, wannan wane irin wulaqanci ne, meyasa kwata kwata Bashir baya darajani? Meyasa ze yaudareni yace yana hanya sannan ya zagaye ya tafi gurin Kishiyata? Idan ya ce mun Gombe ze wuce ai bazan hana shi ba tunda itama matarsa ce amma wannan ai zalunci ne yasa na bata lokaci na na shirya tarar sa sannan ya zagaye ya tafi gurin wata. Haka na kwana ina kukan baqin ciki idona sunyi luhu luhu ga wani azababben ciwon kai daya kamani, sauqi daya dana samu Amna ba zataje makaranta ba saboda wani satin zasu fara WAEC ita ta shirya yaran ta basu abinci sannan tayi musu order Uber suka tafi. Ina zaune a gaban mudubi ina shafa mai bayan na samu nayi wanka dakyar ta shigo da Try ta dora Mug din shayi da plate din dankalinda kwai. Akan Coffee table ta ajiye kafin ta zauna akan daya daga cikin kujerun. "Mami" ta kira suna na, sena waiwayo nayi mata kallo daya na mayar da kaina. "Mami kiyi haquri dan Allah, wallahi ba laifin Abbi bane kin san su Anty Amirah har gidan bokaye suna zuwa qilan Asiri sukayi masa" ta fada muryarta na rawa alamar kuka zatayi. Sena juyo na kalleta ina murmushi nace "Kinsan menene Amna?" Seta girgiza kai alamar Aa, numfashi naja kafin naci gaba da cewa "Abbin ku be kyauta mun ba, inda ya fadamun ba yau ze dawo ba kinga da ban sha wahalar hada masa abinci ba. Kina kallo fa jiya ko baccin kirki banyi ba ina gasa masa zabo amma duk wannan wahalar ta tashi a banza kuma fa da magriba ma fa seda mukayi waya yace sun dawo yanzu ze taho gida". Na qarasa ina share hawayen daya zubo ta gefen ido na, gaya matan da nayi se yasa naji wani sanyi sanyi a zuciyata. "Haka ne Mami, nidai kiyi haquri ki dena damuwa daman abinda suke so kenan" "Na haqura Amna, kije ki kwanta ki huta toh nima idan na karya bacci zanyi" na fada ina miqewa na bude wardrobe na dakko Doguwar rigar Yadi me laushi na saka. Tura abincin kawai na ringayi dan bakina sam babu dadi. Bayan na gama na sha Paracetamol na kwanta. Dakyar ya yakice tunanin abinda Bashir yayi mun na samu bacci me nauyi ya dauke ni, gana jiya da banyi ba ga bashin na shekaran jiya. BASHIR Tun washe garin da ya sauka a Delta da daddare suna waya da Amirah tana ci gaba da yi masa kukan data ara ta dorawa kanta. Cikin kukan take cewa "Kowa ya kira ni yayi mun gaisuwa dangi na kusa da na nesa amma banda Anty, ai ko ba komai tsakanina da ita ya kamata ace tayi mun gaisuwa ko su Aliyu ma ai duk ya kamata su kirani ko banza qanwarsu ce" . "Ma'u bata kira ki ba?" Ya tambayeta da mamaki, "Bata kirani ba mana inda ta kira ai Zan gaya maka  indai kuma ba murna take da mutuwar Iman ba". Amiran ta bashi amsa. Wannan fushin cewa bata kira Amirah ta mata gaisuwa ba shi ya hana shi kiranta har tsahon kwanakin da yayin. Ko ranar data kirashi da Amiran suke waya, sanda kiran ya shiga harga Allah yaso ya daga dan yayi missing dinta amma daya gayawa Amirah nan da nan ta rikice ta fara masa kuka, basu kuma gama wayar ba se gurin sha biyu dan haka suna gamawa bacci ya kwashe shi. Gaba daya yanzu shi tausayin Amirah yake ji. Koshi me Ÿaÿa Shida rasuwar yarinyar nan ta tabashi sosai bare ita me guda daya sannan ga irin wahalar da tasha shiyasa yake biye mata ko zata samu sassaucin abinda take ji. Rabar laraban kuma da zumudin son ganin Asma'u ya taho, yasan be kyauta mata ba ya kuma bari ne se ya dawo sannan ya goge laifinsa, sanda ya kirata dagaske yana Lagos saukar su kenan amma suna ajiye waya Amirah ta kirashi tana kuka tamkar ranta ze fita. Akan gashi har anyi sati da rasuwar Iman amma beje ya ganta ba. "Ni daman nasan baka sona Yaya, baka qaunata farin cikin Anty da Ÿaÿan ta ne kawai matsalar ka baka damu da ni na rayu ko na mutu ba. Karinga tunawa nima matarka ce kamar ita, kuma ina da haqqi akan ka. kuma idan har ban yafe ba kasan Allah babu ruwan sa seya kama ka da haqqina". Tana gama fadar haka ta kashe wayar ta, bugun duniya kuma taqi dagawa. Gaba daya ji yayi hankalinsa ya tashi, shifa duk abinda za'ayi kar a saka batun Allah ya isa. Ya fito kenan ze taho gida suka hadu da daya daga cikin Directors dinsu shima dan Gombe ne suka gaisa se yake gaya masa Gombe ze tafi yanzu. "Sir Daman akwai jirgi yau ko a mota zaka tafi" Bashir din ya tambaye shi, se yayi murmushi yace "Haba Engineer mota kuma a daren nan ai kayi mun fada, a jirgine His excellency yazo wani taro, kasan Abokina ne, toh na samu alfarma za'a rabani Private Jet mu tafi. "Ai Sir ku manayan mutane ne da zan samu a rabani nima ai dana biku na dana" ya fada yana shafa kai, se Director yace "dagaske kake ko wasa se na kira Protocol naji idan ze samu". Beyi zaton za'a samu din ba kawai ya amsa, yana kiran protocol din kuwa yace su taho yanzu su akw jira. Babu damar yayi wa Director wasa da hankali dole ya bishi suka tafi dukda shi kansa yasan be aikata daidai ba, amma yasan Asma'u tana da Fahimta, gara ya fara gyarota da Amirah sannan ya dawo kan Ma'un sa dan yasan ita bazata taba yi masa Allah ya isa ba kome zeyi mata. A Flight mode ya saka wayarsa dan karma ta kirashi besan me zece mata ba, seda ya sauka a Gombe, yana kan hanyar zuwa gidan su ya tura mata da wannan Text din. Sanda ya isa har sun rufe gida seda ya kira Naziru ya bude masa tukkana. Da mamaki Nazirun yake kallonsa, ya karbar masa Jakar suka shiga ciki kai tsaye ya wuce dakinsu da Jakar shi kuma Bashir ya wuce Dakin Dada dan burinsa yanzu yaga Amirah yaga halin da take ciki. Palour babu kowa dan har sun kashe fitulu alamar sun kwanta, kai tsaye dakin Fainusa ya nufa inda yasba ze samu Amiran. Har ze tura qofar ya daka saboda tuna ba ita kadai bace a dakin baisan a yana yin da ze tarar dasu ba seya dakata. A hankali yayi knocking, seda ya buga sau uku sannan Fainusa ta taso ta bude qofar tana hamma a zaton ta ma Dada ce, seta yi saurin saita kanta ta shiga gaishe shi, a ranta tana mamakin daga ina da tsohon daren nan kuma. Fita tayi daga dakin ta koma palour shi kuma ya shiga. Abin mamaki matar da Tace bata iya bacci da ta kwanta mafarkin Iman takeyi se gata tana shaqar baccinta kashirban se a iya sace ta ma bata sani ba. Tashinta ya shiga yi amma ko motsi se wasu surutaj banza data ringa masa qarshe ya haqura ya koma dakin Naziru ya kwanta dan already Nazirun ya gyara masa Gadon sa shi kuma ya koma Dakin Sa'ad ya kwanta. Juyi ya ringa yi kawai ya kasa baccin, tunanin halin da Ma'u take ciki kawai yake. "Allah sarki Ma'una yar Aljanna nasan ke me haquri kuma zaki fahimce ni" ya fada a fili kamar yana gabanta. Dakyar ya samu yayi bacci ya qudurce a ransa dai In sha Allah gobe ko a mota ne seya tafi Lagos. 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 WATA KISHIYAR 🥰👹 (ALKAHIRI CE KO SHARRI) 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 Na Maryamah Farouk (Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah) Wattpad @MaryamahMrsAm Page 27 Amirah Da Asuba duk tashin da Fainusa ta ringa yiwa Amirah tayi sallah ko motsi batayi ba. Ba wai dan bata jin ta ba, A’a kawai ita ta tsani wannan tashin Asubar da sukeyi tun kafin ayi assalatu. Tana lafe akan gado ta jiyo Fainusa tana gayawa Dada zuwan Bashir din jiya da daddare, seta miqe zaune. “Kardai ya shigo ya ganni ina sharar bacci” ta fada tana zaro ido. “Wayyo ya zanyi yanzu” ta sake fada a fili tana tunanin mafita. Tunda akayi rasuwar take masa qaryar bata iya bacci da daddare shi yasa kullum suke raba dare suna waya se yayi dagaske take barinsa ta kwanta. Jiyan ma abinda yasa bata kirashi ba baccin taji da wuri, seta shirya a ranta da safe in sunyi waya se tace masa ai tasan ya koma gida ne bata so ta kirashi Anty taji haushi toh yanzu gashi qilan ya ganta wai ya ma akayi be gaya mata ze zo a jiyan ba. Yanzu ita wace qaryar zata zabga masa? Ganin ba mafita ya sakata tashi da niyyar ta yiwo alwala idonta ya sauka akan Maganin tari akan Mudubi. Nan take ta tuno ranar sadakar uku aka siyowa Yaron Anty Amina Babbar Yayar su Bashir da take aure a Bauchi, se akayi rashin sa’a aka karbo na manya dan haka bata bashi ba ta ajiye a dakin. Da sauri ta dauke shi, seda ta leqa ta jikin qofa ta hango Dada da Fainusa suna Nafila kafin ta bude kofar Toilet a hankali ta shiga ta tuttar da fin rabin maganin a rariya kafin ta koma ta kwanta bayan ta ajiye shi saitin kanta ta bar kwalbar a bude. Har qarfe shida tana kwance a gurin, Fainusa data gama Azkar dinta ta shiga dakin yin wanka dan zata fita gurin aiki tana koyarwa a makarantar secondary dake kusa dasu ta tarar da Amirah a bararraje tana bacci babu Alamar ta tashi tayi sallah. “Lallai yarinyar nan, daman baki tashi bama kikayi sallar nidai naga randa zakiyi hankali” ta fada bayan da ta danawa Amirah duka a cinya ta bude ido da sauri dan dukan ya shigeta. “Akan me zaki zo ki dakeni, Allah ya isana wallahi” ta fada tana sosa inda ta dake tan. “Ni kike yiwa Allah ya isa mara kunyar banza kawai” Fainusa ta hayayyaqo mata, Dada da tajiyo hayaniyar tasu ta shiga da sauri tana cewa “Bismillahi safiyar taku tayi zaku fara ba, kamar masu ganin hanjin juna yanzu kuma me akayi?” “Dada wai fa wannan mara kunyar tunda na tashe ta da Asuba ashe bata tashi tayi sallar ba, shine yanzu fa dana shigo na sake tashinta ta fara zagina tana mun Allah ya isa”. Bude baki Amirah tayi da niyyar magana ta hango Bashir ya turo qofa, se kawai ta fashe da kukan qarya harda sheshsheqa tana cewa “Wallahi Dada ba haka akayi ba, ni ban ji sanda ta tashi ni ba ban ma san safiya tayi ba kawai yanzu tana shigowa ta hau dana mun duka wai na kwanta ina bacci kamar wata kafura bayan tasan ko baccin bana iyayi, kuma ni maganin mura nasha shine bacci me nauyi ya kwashe ni” ta fara qoqarin miqewa, tana sane ta ture kwalbar maganin dan sauran na ciki ya zube ita kuma ta koma dabas ta zauna a dole jiri take gani. Sake yunqurawa tayi ta miqe se ta tafi kamar zata kife Bashir yai saurin tarota yana cewa “yi a hankali mana” nan idonsa ya saka akan kwalbar maganin, seda ya zaunar da ita kafin ya daga kwalbar yana kallonta yace “Amirah kina hauka ne, syrup kika sha saboda kin kasa bacci?” Kuka haiqan ta saka masa tana cewa “to ni yaya ake so nayi? Bana iya bacci ni kadai nasan damuwar da nake ciki babu wanda ya damu da ni har kai din ai baka zo ba bate kasan halin da nake ciki”. Seda ya yi qoqari ya hadiye bacin ransa, kafin ya sassauta murya yana cewa “shikenan, yanzu ki daure kiyo alwala kiyi sallah, lokaci yana qara ja” ya juya ya fita jin ana kiran wayar sa. Seta miqe tabi bango, dab da zata shiga bayin ta waiga tareda ballawa Fainusa harara ganin babu wanda yake kallonta ta shige ciki. Daga Dada ko har Fainu bude baki sukayi suna kallon wannan Drama, ita Dada mamakin yanda zata ce bata bacci kuma kowa babu me kula da ita, to wanne baccin ne batayi yarinyar da duk dare seta leqo su kuma ta ganta tana baccin ta qalau kai har na rana yi take, gaba daya fa jimamin na kwana biyu tayi ta ware se idan taga idon mutane ne zata wani koma kalar tausayi duk fa tana ankare da ita. Ita kuwa Fainu Murmushin takaici tayi ta nemi gefen gado ta zauna tana cewa “Allah ya kyauta” lallai Amirah ba qaramar makira bace, kullum tana jin yanda take kalallame shi a waya tana raina masa hankali to Yayan shima ba kirki ne dashi ba bare ka gaya masa gaskiya amma dai jiki magayi. Sanda ta fito Fainusa kawai ta tarar a dakin, bata so ba dan har wani kwararrabe fuska tayi a zatonta Bashir yana nan ganin Fainusan yasa ta saki tsaki ta dauki Hijabinta tana cewa “aikin banza mutum bashi da aiki se sa ido”. “Wai Amirah ni sa’ar kice? Ni kike gayawa wannan dan uwarki” Fainusa ta fada tana miqewa tsaye “Karki sake zagar mun uwa nidai” Amirah ta fada tana murguda baki, “Idan na zaga me zakiyi?” Cewar Fainusa tana qara matso Amiran, “Nidai karki sake zagina dai tam” Amiran ta fada kafin ta juya ta tada sallah, idan badan tsoron kar ko Bashir yana kusa ba da ramawa zatayi ai uwa bata fi uwa ba. Kwafa Fainusa tayi, taso ta fadi wani abun da be mata ba wallahi seta tsinkawa shegiya mari idan yaso duk abinda Yayan ze yi yayi. Ai daman saboda taga tana auranshi ne yasa ta raina uban kowa ko amma zatayi maganin ta wallahi. “Haka kawai dan mutum yana baqin cikin ana auran dan uwansa baze iya dauke kai yaga ana abin arziqi ba shine ze takurawa mutane, idan anji haushi mutum ya koma gidan mijinsa mana” Amirah ta fada daidai sanda Fainusa ta fito daga wanka. “Idan gidan uban ki nake zaune se kice an takura miki, sannan aure da kike magana kibi a sannu qaddarar zawarci bata wuce kan uban kowa ba” tana fadar haka ta qarasa gaban mirrow ta hau shiryawa, amma tabbas yau se yar iskar yarinyar nan ta bar mata daki. Ita Amirah zatayiwa gorin zawarci yarinyar da a shekaru ta girme mata da har shekara shida shine zata tsaya tana gaya mata wadannan maganganun dan kawai taqamarta tana auran yayanta? Tabbas dole tayi maganinta wallahi. Ita kuwa Amirah sum sum ta fice daga dakin ganin yanda fuskar Fainusan ta chanza tasan tsaf zata iya rufeta a daki ta nada mata mugun duka. Tayi tunanin zata taradda Bashir a Palour seta ga babu kowa, zama ta tayi tana jiyo motsin Dada a Kitchen din amma hankalin ta be bata ya kamata ta shiga ta taya ta aiki ba. Bayan Bashir ya gama amsa wayar, harya danno Number Asma’u ze kira se ya dakata. Wani nauyinta yake ji besan me ze ce mata ba idan ya kira. Seya karkata kiran zuwa Number Aliyu amma a kashe. Dadi ma yaji da ya sameta a kashe dan qilan ya zama yana tare da Ma’un hakan kuma ze zama qari akan laifinsa. Dakin Alhajinsu ya shiga ya same shi a zaune kan sallaya yana lazumi. Bayan sun gaisa da mamaki Baban yake tambayarsa yaushe yazo. Seya shiga shafa qeya yana cewa “jiya da dare Baba, Engineer Sha’aban na biyo zasu taho tareda His excellency bayan mun dawo daga Delta. “Kace ko gida ma baka je ba kayi yo nan” Baban Ya fada yana kallon fuskarsa, rasa abin cewa Bashir yayi dan haka yayi shiru kawai. “Ka kyauta, tashi kaje” Baban ya fada ya maida hankali ya ci gaba da jan carbinsa. Yana fitowa ya tare Naziru da ya fito daga Palour Dada da Kofin shayi a hannunsa. “Ji mana” ya dakatar da Nazirun kafin ya fara masa magana wayar sa tayi qara. Team leader sune yake gaya masa ranar Monday suna da presentation, dan haka yau idan sun huta gobe Friday zasu hadu a office dan su tattara reports din hannun kowa” bayan sun yi sallama Bashir ya kalli Naziru yace “Kayi mun booking morning flight gobe”. “Ai Yaya babu jirgi fa, an samu yar matsala sun dakatar da jirgin Gombe zuwa lagos till further notice. Sedai ka hau mota kaje Kano tukunna ka tafi ta can”. Kallon sa Bashir yayi kamar me son ganin gaskiyar maganar a fuskar sa, da hannu yayi masa alama da ya tafi, kafin ya lalubo Number Wani Agent da yake siya masa ticket ya kira. Irin bayanin da Nazirun yayi masa dai ya maimaita se ma qari daya masa akan Yau jirgin qarfe bakwai da rabi ne se na sha biyun rana, gobe kuma babu jirgin Safe se Shidan yamma. Godiya ya masa ya kashe wayar kafin ya shiga lissafin yanda zeyi, qarfe 10 na safe ake buqatarsa a office goben, dama babu zancen yau dan jirgin safe ya tafi yanzu kuwa qarfe takwas na safe ta gota, indai ba fiffike zeyi ba baya tunanin akwai ta yanda ze isa Kano kafin sha biyu na rana. Goben da yayi tunanin samu ance sena Magriba shida yake da Meeting qarfe goman safe to yanzu yaya zeyi?? Wai wane tsautsin ma ya saka shi tahowa yanzu gashi ya saka kansa a cakwakiya da hargitsin da yake jiransa a can gida, Mafita daya ce kawai Ya tafi a Mota in sha Allahu dai daga nan zuwa cikin dare ai ya isa. Da wannan shawara yayi Na’am dan haka ya juya ya shiga palour Dada. Amirah na kwance akan kujera ya shiga seta miqe ta zauna tana gaishe shi, kujerar dake kallonta ya zauna ya amsa dai dai sanda Dada ta fito daga Kitchen din ta try a hannunta. Fainusa ta kwalawa kira ta fito cikin shirin fita, Try din ta bata tace ta kaiwa Alhajin su sannan ta kalli Bashir tace “Yanzu zaka karya ne ko se an jima?” “Eh yanzu Dada, dana gama zan kama hanya ne ma”. Daga ita har Amirah kallonsa sukayi, “Da wuri haka?” Dadan ta tambayeshi, se ya miqe yana cewa “Wallahi Emergency ne ya taso mun a office, kinsan jiya muka dawo toh kuma ana buqatar wasu bayanai gobe gashi na taho dasu nan kuma babu jirgi dole mota zan bi”. “Tab amma kaima da ganganci kake, me yasa ka taho kasan kana da ayyuka a gabanka. Yanzu a yanda hanya take zaka bi mota har Lagos, to kana da tabbacin ma zaka isa kafin goben nan ina se dare motocin suke tafiya koh?” Dada ta fada tana riqe baki. “Addu’a za’a mana Dada In sha Allah zamu je lafiya, yanzu dana shirya zanje Tashar, Idan babu masu tafiya yanzu inaga Zan dauki Shatar mota ne kawai na tafi dan kinsan su office babu ruwan su dole na kai musu takaddun nan gobe qarfe goma” “Toh Allah ya rufa asiri, se kije ki hada masa abin karyawar ki kai masa tunda sauri yake” Dadan ta fada tana kallon Amirah data daskare a gurin. Dakyar ta yunqura ta tashi, lallai ma. Daga zuwansa jiya da daddare zece yau ze juya, wallahi qarya yake ta tabbata babu wani kiran office kawai Matarsa ce tace ya dawo shine ze fake da wani aiki ai kuwa bazata sabu ba wallahi. Kayanta hada ta kai masa Dakin Nazirun, sanda ta shiga yana wanka, seta nemi guri ta zauna tana jiran ya fito dan babu yanda za’ayi ta barshi ya tafi wallahi. Da gudun bala’i ta fada jikinsa tareda fashewa da kuka lokacin daya fito daga wankan, gaba daya yayi baya kamar zasu fadi Allah ya taimaka ya dafe bango dan a bazata ta fado masa se ya tureta daga jikinsa yana cewa “ke mahaukaciyar ina ce zaki fadowa mutum haka idan da na fadi naji ciwo kuma fa, mtsw” yaja tsaki yana hararar ta. “Yanzu dan Allah ko tausayina bazaka ji ba, daga zuwanka jiya ko zama bamuyi ba kaji damuwata ba yau zaka ce zaka tafi saboda wadda ka baro acan tafi ni, shi kenan kaje, amma sedai ka zaba ko ni ko ita wallahi dan na gaji da yanda kake nuna banbanci a tsakanin mu. Gara ka rabu dani kaje can ka zauna da matar so”. Kallonta ya ringayi har ta kai aya. Wai ya zaba ko ita ko Ma’u shi abun ma dariya ya bashi a ransa yace “idan zabi za’a bani dole sedai na zauna da daya yarinya aike zan saitawa hanya, na rabu da Ma’u nabi ina naga haske?? A fili kuma se ya saki murmushi ya janyo ta jikinsa yace “Allah ya huci zuciyarki haba Amaryata, yanzu kina kallo ko gida banje ba jiya na taho garin nan ko iya wannan be isa ya nuna miki yanda na damu dake ba. maganar na zaba a tsakaninku kuma ai bata taso ba kinfi kowa sanin Yanda Nake Son Ma’u, ban kuma ga abinda ze raba ni da ita ba se mutuwa sannan kema saboda ina sonki na aure ki dan haka ki dena kawo maganar rabuwata da daya daga cikin ku. And official call na samu dole na bar garin nan a yau, idan kuma so kike a kore ni daga aikin na rasa kudin siya muku abinci shikenan”. Qara lafewa tayi a jikinsa, taji haushin yanda ya wani fadi yana son ma’u amma ai ba qarya bane ita ma ta sani, ganin yana cikin yana yi me dadi yasa ta ce bari ta gwada sa’arta. Tana jikinsa suka qarasa kan gadon ya zaunar da ita ya dakko mai ya fara shafawa, taya shi ta shiga yi kafin cikin muryar shagwaba tace “Yayahh” Kallon ta yayi ba tareda ya amsa ba, ganin hankalin sa yana kanta taci gaba da cewa “Toh naji Yaya ka tafi amma da ka gama abinda zaka yi ina jiranka ka dai san alqawarin da kayi mun ni uku nake so ma ba biyu ba” ta fada tan rufe fuskarta da hannayenta. Murmushi yayi yace “karki damu, just be ready for me”. Murmushin ita ma tayi kafin ta ci gaba da cewa “Se kuma Yaya gaba daya kayan dakina an lalata su kuma...” ganin kallon da yake mata lokaci daya fuskar sa ta chanza ya sakata yin shiru, “Uhm ina jinki kuma me” ya tambaye ta yana saka rigar sa, seta girgiza kai tace “ babu komai” “Gara da ya zama babu komai din” ya fada yana zama ya jawo kayan abincin ya fara ci. Seda ya gama tsaf ya zuge jakarsa sannan ya kalleta yace “Karki sake kawo mun maganar kayan dakin ki ko wani abu, saboda banyi lissafin nawa damage din nace a biya ni ba ko? Zan tafi yanzu, zuwa gobe ki koma gida”. Seta marairaice fuska kamar zatayi kuka tace “Dan Allah yaya gidan yayi mun girma da yawa tsoro nake ji, ka barni na koma gidan Addah kaga in nace zanzauna anan ma kullum fada muke da Anty Fainusa”. Seda ya kalleta na dan wani lokaci kafin yace “ok ki koma din, shikenan ni zan tafi”. Ganin bata motsa daga gurin ba sema yan hawaye da take gogewa yasa yace mata “Come on babu ko goodbye” ya fada yana dagata tsaye, light kiss ya mata kafin ya saketa yayi gaba ta bishi a baya. A qofar dakin Alhajin su taci burki, harya saka qafa jij ta tsaya yasa ya waiwayo ya kalleta “Shigo mana” ya fada yana qarasawa ciki. Se Alhajin ya dago ya kalleshi yana murmushi yace “Amirah ce ko, ka barta kawai ban san menayi mata da bata iya zuwa mu gaisa ba”. “Hmmm” kawai ya iya cewa sukayi Sallama da Baban yayi masa fatan sauka lafiya ya fito. Shareta yayi ya shiga dakin Dada itama sukayi sallama kafin ya fito har Naziru ya saka masa jakar sa a mota. Tana bayansa kamar Jela suka fita, tunda yaji bata zuwa tana gaida Baban ransa ya sake baci, gaba daya dana sanin zuwa ma yake yi dan dai babu biyan buqata se kayan takaici daya kwasa kawai haka ya shige motar Naziru yaja tana tsaye kamar ta kurma ihu, yanda suka faro a dadin rai taso su qarashe haka ko ba komai ta samu kudin kashewa yanzu gashi ya tafi da sabon fushi. Sanda suka isa ya taki sa’ar samun qaramar mota sharon saura mutum biyu dan haka ya biya kudin mutum biyun kawai ya shiga suka dau hanya. Seda tafiya ta fara miqawa sannan ido ya raina fata. Rabon daya je Lagos a mota kusan Shekara Goma sha biyu kenan sanda ya taba samun wani aiki har aka kirashi interview daga qarshe aka ce wai ba’a dauke shi ba. Wannan aikin ko lokacin daya same shi da aka kirashi documentation harda ticket din jirgi Alhaji Qarami ya hada masa na zuwa da dawowa tundaga nan kuwa da Al’amura suka bude masa shida tafiyar mota sedai inda jirgi baya zuwa. Akace tafiya yankin Azaba tabbas Bashir ya kwashi Azabar tata. Wata irin tafiya yayi da a rayuwarsa ze iya cewa be tabayin me wahalarta ba. Haka suka kwana suna tafiya sau uku kacal suka tsaya shima sallah kawai sukeyi wasu su nemi abinda zasu ci sannan a qara wuta. Bashir dai Azumin dole yayi in banda ruwa babu abinda ya shiga cikinsa har suka Isa Lagos da Asubar Ranar Juma’a. Firkai firkai dashi kamar wanda ya qwato daga hannun Yan Kidmashin ya shiga kwankwasa gidan bayan da Shatar Taxi din daya dauko ta sauke shi. Lokacin Asma’u na kitchen sauran yaran kuma suna zaune a palour suna qarasa saka sport wear dinsu dan yau Juma’a. Da farko duk basu zaci gidan ake kwanwasawa ba tunda waye ze zo musu da sassafen nan shida ma yanzu tayi. Jin Basu bude ba yasa Bashir neman dutse ya hau buga qofar kamar an aiko shi dan a yanda yake ba shida qarfin da ze fara binciko keys a jakarsa, daga ciki Asma’u ta fito daga Kitchen din tana kallon yaran da sukayi cirko cirko tace “Waye wannan yake mana bugu kamar mara hankali” seta nufi gurin qofar. Seda ta leqa ta yar bular da ake ganin mutum, da mugun mamaki taja baya. Fuskar Bashir ce, tasan a kowanne yanayi bazata kasa gabe shi ba amma da seta ce wannan me kama da shi ne. Qofar ta bude da sauri tayi gefe ganin yana neman fado mata ya wuce ciki bayan ya watsar da kayan sa a bakin qofar, seta kwalawa Aliyu kira ya tafi da sauri ta nuna masa kayan tana cewa “shigar masa dasu dakinsa” ta juya ciki tana mamakin daga ina yake. Bashir kuwa Yana shiga ya zube akan kujera, yunwa, gajiya da bacci sun hadar masa gaba daya. Kallonsa yaran suka shigayi kamar sunga baqo kafin suka gaishe shi ya daga musu kai dan baze iya bude baki ba. Yanda Asma’u tayi kamar bata san da wanzuwarsa a gurin ba yayi bala’in bashi mamaki, shirinta ta ci gaba daya yi. Yana kallo suka qarasa cinye abin karin su yaran sukayi masa sallama suka fice gurin mota ita kuma ta shiga daki ta dakko jakar ta. Ina sane nayi tamkar na manta dashi a gurin, yana ganin nayi hanyar qofa yai saurin dakatar da ni da muryarsa a har dashewa tayi saboda yunwa yace “Ma’u baki ganni ba zaki tafi kuma”. Seta na dakata na kalle shi, da dan guntun murmushi a fuska ta nace “Na ganka Baban Ali ai nayi maka sannu da zuwa tunda ka shigo ko baka ji ba?” “Hmmm” ya fada kafin ya yunqura yana cewa “Nagaji wallahi a mota na taho, gashi qarfe goma ya kamata inje office ki taimaka mun da abinda zanci bari nayi wanka”. Se da na saki wata dariyar takaici, ina kada key din hannuna nace “wato ka rantse dai se ka biyo mota toh ai gashi dai kaji abinda ake ji. Abinci kuma akwai komai na buqata a Kitchen se ka nemawa kanka kaga mun makara ma se mun dawo” na juya nayi tafiyata ina jin yanda ya raka ni da kallo har na kulle qofar. Wato daga dan rainin hankali se Bashir, Allah ya qara. Abinci kuwa babu komai a Freezer mun cinye kwana biyun nan kuwa ban zauna ba bare nayi ko miya ce na ajiye. Malam Bashir kuwa dakyar ya iya miqewa ya shiga Kitchen din, ya zata ze samu ko ragowar abinda sukaci ne ya tarar da wayam, ya bude Freezer nan ma danyun nama ya tarar babu ko guntun abinci. Cike da takaici ya bude Fridge din shima babu komai se tarkacen ruwa da lemo se wani guntun nama ya samu a foil paper ya dauka da sanyin sa da komai ya cinye. Ganin fa babu mafita ga yunwa ga lokaci na sake qure masa yasa ya kunna Fanfon Kitchen din ya tari ruwan zafi, Madara da Milo ya zuba sosai ya dagawa daya ya kwankwade ya sake hada wani yasha rabi ya hango bread ya dauka ya hada, seda yaji cikin sa ya dan farfado sannan ya haqura yaja kafafuwansa ya tafi daki. Wayar s ya fara sakawa a chaji dan tun a hanya da dare ta mutu, Yau daya se be ji haushin abinda Ma’u ta masa ba, idan da haka kawai ne tayi masa wannan wulaqancin yasan me raba su se Allah amma yau daya tuna girman nasa laifin se yaga ai ba komai tayi masa ba. Kamar me maye haka yana layi yayi wo wanka ya fito, badan ba kwanciya zeyi ya dan rage bacci amma yasan tabbas ya kuskura ya kwanta a yanda yake jin baccin nan qila sedai ya farka yaga magriba tayi. Bayan ya saka kayan sa ya tattara abinda ze buqata kafin ya kunna wayarsa yayi order Bolt, se ya fito qofar gidan ya zauna kamar wani Almajiri, yunwa yake ji dan ba wai ya qoshi bene kawai haqura yayi idan ya fita se yaci abincin sannnan ga bacci har ji yake kamar zazzabi ze rufe shi, haka ya hau motar suka kama hanya. A cafeteria office din su yaci abinci, Patrick abokin aikin sa da suka shiga tare ya ringa kallonsa da mamaki ganin yanda yake lodar abinci kamar wanda ya shekara be ci ba, kasa daurewa yayi yace masa “Bash lafiya kuwa ji yanda kake cin abinci?” “Bazaka gane ba, rabo na da abinci tun shekaran jiya”. Dakyar ya iya kaiwa qarshen meeting din, suna gamawa suka fita sallar Juma’a. Bayan sun dawo Office din sa ya koma ya kwanta ya ringa bacci ba shi ya farka ba se qarfe bakwai shima Security da suke bi office office ne bayan an tashi suka ga fitilar sa a kunne dan haka sukaje su duba ko lafiya tunda be saba kaiwa dare a gurin ba. Haka ya tattara a gida ya wuce gida, da murnar sa ya shiga dan tun daga waje ya jiyo qanshin tuwo da miyar kuka harda man shanu abinka da me jin yunwa. Ya bude qofar ya shiga, fuska a sake Ma’u tayi masa sannu da zuwa harda tambayar ya akayi yau ya dade yace bacci ne ya kwashe shi. Da zumudinsa yai sallar magriba da Isha ya sako jallabiyya ya dawo palour aka kame akan kujera yana jira ayi masa tayij abinci ya kwashi gara amma har kusan minti goma da zaman sa yaji shiru sema harkar gaban su kawai suke. Gyaran murya yayi yana kallon Ma’u dake dannan waya yace “Akwai abinci ne yunwa nake ji” Seta dakata ta dago ta kalleshi da murmushi tace “ai kuwa babu dan ban san zaka dawo ba”. “Kamar ya baki san zan dawo ba ce miki nayi zan tafi wani gurin ko yaya, sannan nida gida na ayi abinci ace baza’a a jiye mun ba saboda me? Haka fa dazu da safe kika ce mun akwai abinci na duba ko ruwan zafi baku ajiye ba” ya fada a hasale, dan ya rigada ya gama saka rai da Tuwon. “Ko ajikina na sake gyara zama nace “Aa abin bana zafi bane bafa Baban Ali, gani nayi yanzu ai Idan zakayi tafiya baka fada seka isa inda zakaje toh gudun kar mu ringa asarar abincin yasa mukeyi dai dai cikin mu, idan kace zaka ci se a dafa dakai”. Abubuwa sun sha kaina, idan na samu sarari zaku jini gobe idan kuma ban samu dama ba se Monday In Sha Allah 🙏🙏🙏 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 WATA KISHIYAR 🥰👹 (ALKAHIRI CE KO SHARRI) 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 Na Maryamah Farouk (Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah) Wattpad @MaryamahMrsAm Page 28 Washe Gari Asabar tunda nayi sallar Asuba na koma bacci ban farka ba se goma na safe. Ko yaya Bashir ya qare jiya oho dan tunda na gaya masa babu abinci naji ya fara jan kwafa da tsaki na kwashi qafafuna na bar musu gurin, dan karma a biyo ni a dameni seda na murzawa qofata key sannan na kwanta. Tsaf na shirya cikin wani Material baqi doguwar riga bayan nayi wanka, tundaga dakin nake jiyo kaya kaya alamar Game suke ko ana musu akan wani abun ina bude qofata Yan biyu na suka taso da gudu suka riqe ni. “Kai ni yunwa nake ji karku kadani me kuka ci ne” na fada ina kama hannayensu, se Ahmad yace “Indomie Yah Amna tayi mana da Tea Abbi kuma gashi can yanzu aka soya masa Irish”. Kallon inda yake nuna mun nayi muka hada ido da Bashir daya watso mun wata harara kamar idonsa ze fado, duk yanda naso na basar seda dariya ta kufce mun dan haka na wayance ina nufar inda yake nace “Baban Ali barka da safiya, kace kaima yanzu ka tashi? Bari nazo muci dan Allah yunwa nake ji idan bamu qoshi ba se a qaro wani” nayi maganar ina jan kujerar da take kallonsa na zauna. Ban damu da shirun daya mun ba na fara hada Tea na ina masa surutun da na tabbatar sake qular dashi nakeyi, na gama naja kwanon dankalin, sena bude baki ina kallonsa nace “Kai Duk wannan da kai kadai zaka cinye shi?” Can qasa kaman an fuzgo maganar daga bakinsa naji yace “Banci abinci da daddare ba jiya da yunwa na tashi”. Kallonsa nayi, naji tausayinsa kadan dan nasan Bashir da abinci ci ne dashi kamar dan kwallo, cikin jimamai nace “Ayya meyasa ka kwanta da yunwa da ka saka Amna ko Spaghetti ce ta dafa maka ai”. Shiru ya sake yi mun, nima ban sake magana ba na fara cin abinci na, ya rigani gamawa, seya miqe ya shiga dakinsa ba dadewa ya fito ya chanza kaya ya saka Caftan na Yadi kansa babu hula. Key din motarsa ya dauka, be mun magana ba ya fice yara suna masa a dawo lafiya. Harya tada motar se gashi ya shigo, ko me ya tuna oho se ji nayi yana cewa “zan fita amma ba jimawa zanyi ba saura yauma karku ajiye mun lunch”. “Wa ya isa yaqi ajiye maka, jiyan ma aka si aka samu baka ce zaka dawo ba, amma yanzu tunda munsan kana nan ai zamu girka da kai” na fada ina dan murmushi. A raina nace “da bakayi magana ba wallahi yau ma dakaga Akuya sedai ka siyo ko kayi wunin yunwa. Jellop rice nayi da pepper soup din tarwada, sena yiwa Bashir pepper meat dan baya cin Tarwada shi se gasashshiya. Muna cikin yin lunch Amna ta kalleni tace “Mami idan mun gama muje gidan Baba?” “Za kuje ku dame su ko kunsan dai yau Weekend Baba yana nan zaku hana shi hutawa”. Bashir ne yace “Baya nan Ya tafi Zamfara tun jiya, idan kun gama kuje dama yau baza mu fita ba sedai ko gobe”. Muna gama cin abincin kuwa bayan sun tattare kwanukan suka tafi ita da Farida dasu Ahmad, Aliyu da sauran kuwa Ball suka dauka suka tafi Filin da suke bugawa gidan ya rage daga ni se Bashir. Qin zama nayi na shiga qaqale qaqalen ayyuka dukda na fahimci nufin Bashir, ganin da yayi bani da niyyar saurar sa, ina tsaye ina goge show glass din farantai a Gurin Dining kawai naji anyi sama dani, duk yanda naso nayi tawaye a dole fushi nake amma yaqi bani dama, daman abin be kai zuci ba kuma nima nayi kewar sa nan da nan nima na bada kai bori ya hau sosai kuwa na gigita Bashir. Ina zaune a gaban mirrow ina Busar da kaina bayan nayi wanka ya shigo dakin yana waya, ta cikin mudubin muka kalli juna murmushi me kyau da narkar da zuciya ya sakar mun kafin ya qaraso ta bayana yana taba Gashina yaci gaba da maganar sa be jima ba ya kammala seya ajiye wayar akan mirrow ya karbi Dryer yana cewa “Dama baki wahalar da kanki ba dan ba’a gama ba” “Wasa kenan” na fada ina zaro ido, saman da yai dani yasa sauran maganar suka maqale ban samu kaina a hannun sa ba seda aka kira Magriba. Ranar haka mukayi kwanan farin ciki duk fushin nan seda Bashir ya bi ya kore mun shi. Se wani nan nan yake dani ranar ba’ayi wata doguwar hira ba kowa ya tafi ya kwanta. Muna kwance a dakin sa nayi pillow da dantsen hannunsa yace “Dan Allah Ma’u karki sake horani da yunwa kinji” Dariya na sheqe kafin nace “wannan din ma bada gayya nayi ba, aka si kawai aka samu”. Lafiya qalau muka cinye Weekend din mu ranar Monday Amnah suka fara WAEC, da yake practical suka farayi sha biyu zasu fito dan haka nace mata ta taho gida kawai idan ta gama sauran idan sun tashi Zan dakko su yanda muka saba. Dawowar da Amnah takeyi da wuri ya sake ragemun abubuwa da yawa dan kafin mu dawo ta ci qarfin girki wani lokacin ma zata dafa musu nasu idan nazo sedai nayi wa Bashir kawai. ne da wuri. Har aka ci sati uku banji Bashir yayi zancen zuwa Gombe ba kuma da alama ko waya basayi da Amirah ban dai sani ba ko a cikin gidan ne bayayi se ya fita waje yake kiranta. Ranar wata Alhamis daya kama Sati hudu da dawowarsa da daddare muna kwance Text ya shigo wayarsa, Number Amirah ce dan da sunanta yayi saving, na fishi kusa da ita dan haka na miqa masa yana daga kwance se naga ya tashi zaune. Kamar wani mara gaskiya ya kalli wayar ya kalleni muka hada ido sena basar na gyara kwanciyata daidai sanda wayar ta shiga qara alamar kira se ya tashi daga kan Gadon ya fita waje. Tashi nayi nima na zauna, Kusan Awa daya yana wayar sa har sannan kuma bacci yaqi daukata, bawai na damu bane da kiran Aa harga Allah ina tsoron abinda ze iya zuwa ne kuma dan a duk sanda muke zaman lafiya kamar tauraruwa me wutsiya yarinyar nan seta wargazashi. yana bude qofa nayi luf kamar me bacci, ina jinsa ya tsaya akaina yana haskani da wayar dan fitilar dakin a kashe take kafin ya zagaya ya kwanta shima. Da Asuba yake ce mun daga Office Gombe ze wuce. “Ai ka kwana biyu daman baka je ba, ka gaishe mana su idan zaka dawo Dan Allah zata taho mun da saqo a gurin Maman Ayman (Bilkisu) saura kace ka manta” na fada ba tareda damuwar komai ba. Ni na hada masa dan abinda ze tafi dashi dan baya daukar kaya muka rabu salin Alin kowa ya tafi aikinsa, sanda jirginsu ze tashi ma seda ya kirani ya gayamun yanzu zasu tafi nayi masa fatan sauka lafiya mukayi sallama. Gombe A ranar da Bashir ya tafi itama ta koma gidan Addah cikin dacin rai. Naziru ne ya kaita bisa umarnin Dada, suna zuwa suka ci karo da Addah a qofar gida da alama fita zatayi. “Yawwa shiga da kayan ki fito muje” Addah ta fada tana kallon Amirah, seta wuce ciki ta ajiye jakarta ta fito, Nazirun ne ya rage musu hanya har zuwa gidan wata tsohuwar qawar Addan da tace wai mijin matar ne ya rasu zata je mata gaisuwa. Suna shiga basu zauna ba dan a shirye suka sameta itama tace su tafi. Amirah dai ranta fal mamaki toh ina zasuje haka dai ta bisu su ka hau Napep ya kaisu Tasha suka hau motar Dukku. Bayan sun isa can ma ashe ba iya tafiyar kenan ba, Babura suka hau daga tasha suka dauki hanyar wani surququn Jeji kafin su isa kuwa jikin su ya gaya musu da iska gashi lokacin sanyi da Hazo musamman Amira dan daman doguwar rigar Abaya ce a jikinta tayi rolling da mayafin rigar har wani kadawa taji haqoranta nayi tsabar sanyi. A wani dan qauye suka sauka da gaba daya bukkokin garin basufi shida ba, Masu Baburan suka tsayar kafin Hajia Maliya tayi musu jagora zuwa bukkar data fi kowacce girma. Sanda suka shiga ciki seda Amirah ta dawo da baya da son tabbatar da daidai take gani ko kuwa gizo idonta yake yi mata. Wato daga waje bukkace ta kara irin ta fulani amma abin mamaki idan ka shiga tamkar ka shiga dakin wani hanshaqin me kudi. Ciki da palour ce, palour Gaba daya a malale yake da Carfet Ja me shegen laushi har wani lumewa qafarsu take a ciki ga kujeru royal an zagaye gurin dasu, yanda gurin yai dumi ya tabbatar mata harda Room heater aka kunna. Zama sukayi ita da Addah se qarewa gurin kallo suke, Hajia Maliya kuwa da alama ta saba zuwa babu mamaki a fuskarta. Zubgurar ta Addah tayi tana cewa “Maliya ina kika kawo mu karfa muje gurin yankan kai ne”. Dariya Hajia Maliya tayi tace “ke fa Fatu shegen tsoro ne dake” daidai nan wani dan fari dogo siririn Bafulatani ya bude qofar uwar dakin ya fito. “Aa Hajia kune ashe tun dazu nake tsammanin zuwanku naji shiru saura kadan ma muyi sabani” ya fada yana zama a qasa inda aka qara shimfida wata darduma ga tarkacen kayan aikinsa akai. “Mune fa Malam kasan tafiyar mutane da yawa basu shiryo da wuri bane” Hajia Maliya ta fada. Gaisawa sukayi yana tambayar ta bayan rabuwa nan suka dan taba hirar aikin da yayi mata da irin yanda taji dadinsa su Addah dai anyi tsuru. “Wannan itace Fatu yar uwata da nayi maka baya ni wannan kuma Yarinyar tace Amirah” Hajia Maliya ta gabatar masa dasu Addah, seya gyara zama yana cewa toh toh bismillan a gurguje dan sauri nakeyi zan shiga garin ne nima zanje gidan Gomna. Matsawa Addah tayi gabansa tace “Allah gafarta yanzu dai matsalar wannan yarinyar itace a gabana dan tawa me sauqi ce” “Ki fadi taki kawai Hajia itama ai tana da baki zata fadi tata ko” malamin ya katseta. Se Addah ta gyara zama tace “Malam abubuwan da yawa gaskiya amma kadan daga ciki dai kaga Kishiyoyina uku nice ta fari. Da gaba daya gidan a hannuna yake daga Alhajin har su matan ni nake juya su ko kara na ajiye wa mutumin nan be isa ya tsallake ba amma yanzu Malam karka so kaga yanda yake mun wulaqanci a gaban kowa ci mun mutunchi yakeyi yanzu duk kishiyoyi sun rainani, gashi yayan su duk sunyi aure sun samu gidan hutu ni kuma biyu ne dani fa kacal na samu daya ta daga to gidan me mata ta fada dayar kuma yanda kasan wadda aka watsawa jinin baqar jaka ko tsayayyen an gagara samu se tarin matsiyata dake sintirin zuwa gurinta”. “Ya sunan me gidan naki da kishiyoyin?” ya tambayeta se tayi sauri tace “Alhaji Murtala, su kuma matsiyatan akwai Binta da Nasiba se Memuna”. Shiru malam yayi yana ta jan carbinsa daya shafe da turare Addah se zura ido take yana kallon bakinsa da yake motsi kamar tasan abinda yakeyi, minti biyu ya dago yana kallonta yace “Se haquri dai Hajia banajin wani aikin ki ze sake tasiri akan Mijin nan naki dan yanzu ya farka shima a tsaye yake da Addu’a da neman tsari, kishiyoyi kuma ai ke kike shiga harkar su kuma ni cikinsu banga wata da take jifanki ko wani abu ba”. Raurau tayi kamar yarinya tace “yanzu malam babu yanda za’ayi wallahi yanzu ko dan abinda nake samu a hannun Alhaji ya dena, kwanan nan da rigima ta hadani da wata mata akan kudi, gida na da na saka yan haya ya siye ya biyata kudin ni da so nake inda yanda za’ayi ma a dawo mun da gidan”. Dariya malam yayi yace “Hajia sama da shekara Arba’in fa kina yanda kika ga dama da bawan Allahn nan yanzu kuma Allah ya taimake shi ya kwace shi daga hannunki ki qyale shi mana. Ki godewa Allah ma daya ci gaba da zama dake dan yana sonki idan da zaki ajiye komai ki bishi zakiji dadin zama dashi sosai Allah na tuba kwana nawa ya rage muku gaba daya ma da kike tashin hankalinki? Gida kuma inda rabonki idan ya mutu se ki samu wanda ya fishi. Bismillah matso ke” ya qarasa maganar yana nuna Amirah. Addah zata sake magana Hajia Maliya ta riqe mata hannu tana girgiza mata kai, se tayi shiru kawai ranta gaba daya a dagule. Wannan wane irin abu ne? Yanda Maliyan ta zuzuta mata shi ta zata da tazo buqatarta ta gama biya amma tazo se wasu maganganu marasa kai aka gaya mata. Jiki a sanyaye Amirah ta matsa gabansa, ya dago ya kalleta yana murmushi yace Hajia ya akayi?” “Ni malam bani da wata matsala kawai so nake ya ringa so na yanda yake son matar sa” “Kunji Asararriya ba” Addah ta katseta kamar zata kai mata duka kafin taci gaba da cewa “Shiyasa nace ka barni nayi maka bayani malam dan wannan sallamammiya ce bata san ciwon kanta ba”. Seda Malam yayi dariya sannan yace “toh Hajia ina jinki”. Gyara zama Addah tayi ta shiga koro bayani “Kanaji malam, shi mijin nata Bashir Dan yar uwata ne. Da dabara muka samu har ya fara sonta ya aure ta. Toh munyi haka dan zumunchi sannan kuma ko ba komai dan na samu me taimakamun tunda ni kaga bani da Da namiji toh Amma yana da Mata. Ita Matar Asma’u sunanta ta riga tasha kansa gaba daya abinda ya mallaka akanta yake qararwa daga ita se yayanta, shekara biyu da auran nan amma ba uwar daya tsinana mana se rashin mutunchi salo salo daga wannan se wannan kuma ita matar tasa na can kusa dashi a Lagos ita kuma wannan ya barmun ita anan se sanda yaga dama yake leqo ta nayi nayi ya maida ita can amma abin yaci tura”. “Toh ita matar shekarar su nawa a tare kuma yayan su nawa” Malam ya tambayi Addah yana murmushi dan matar dariya ma take Bashi, se Addah ta karkace tace “Inaga ta sha bakwai suke yanzu, haihuwar ta biyar harda tagwaye da anyi magana se ace ai ita tare suka sha talauci”. Seda Malam yayi dariyar qarfin halin Addah kafin yaja qasarsa ya baza yana cewa “Toh yanzu Hajia in banda qin Allah irin naki ta yaya kike so ya fifita matar daya aura shekara biyu akan wadda suka shafe shekara goma sha bakwai tare Ai koda Arziqinsa ya aure su dukka su biyun bazaki taba hada shaquwar shekaru goma sha data kwananna ba sannan ga zuri’a har shida a tsakani”. “Toh nidai malam ko ma menene dai ina so Amirah ta zama mowa a gidan sannan ya ringa sakar mata hannu yana mana bushasha idan so samu ne ma ni banqi Ma’u tabar gidan ba dan indai tana nan be zama kallai mu samu yanda muke so ba”. Addah ta fada tana hura hanci, se Malam ya dago ya kalle ta yace “Hajia ribar musulmi ya mutu ya shiga Aljanna ni bana kashe aure sedai na qulla qilan Hajia bata gaya miki ba kinganni nan bana aiki in cutar da wani sedai nayi maka kai ka samu mafita sauran zunubai na ma sun ishe ni bazanyi dakon haqqi ba”. Seda ya gama irga carbinsa kafin ya mayar da hankalin sa kan Amirah yace “Ita uwar gidan naki ma tana dab da fita, sannan mijinki duk kalar asirin da zakiyi masa tasirinsa qalilan ne akan sa baze dade ba ze karye. Ko ita da kuke ganin ta mallakeshi bada Asiri bane kawai ta iya zama dashi ne amma bawai dan tana jin dadi yanda kuke zato ba. Shawarar da zan baki itace kije ki gyara kanki ki gyara zaman ki kawai shi me son kyalekyale ne tun farko abinda ya ribace shi harya aure ki kenan kuma itama matar sa da abinda take galaba akan sa kenan amma batun ya so ki sama da ita babu shi, dan ko mutuwa tayi ba na jin akwai wadda zata iya maye masa gurbin son da yake yi mata”. “Toh malam na gode, se kuma matsalata malam haihuwa biyu kenan nayi ta farkon bezo da raina ba ta biyun kuma sati uku da haihuwar ta koma daman bakwaini ce” Amirah ta fada a sanyaye, “Wannan Kuma daga Allah ne itama mahaifiyarki ai haka tayi ko, randa yaso se ya baki rayayyen” ya fada yana miqewa. Kamar anyiwa Addah Bushara da aljanna baki har kunne tace “Malam kace zata fita yaushe kenan amma bazata dawo ba ko?” Banza yayi mata ya shiga dakin daya fito minti kadan ya dawo da daurin wata saiwa da kuma garin magani a leda ya miqawa Amirah yace “ki tafasa ki ringa sha ze gyara miki jiki wannan kumburin ya sabe tunda bakiyi wanka ba wannan kuma kisha da madara ko Kunu Allah ya qara rufa asiri amma a shawarce dai da kin nutsu dan kalar mijinki ko kinyi asiri idan baki san yanda zaki tafiyar dashi ba wahalar banza zakiyi”. Godiya tayi masa ta miqe, Addah ta kalleta tace ina zaki je kuma?” “Shikenan ai ko Hajia na sallame ku koda wata magana” ya fada yana kallon Hajia Maliya se Addah tayi caraftace “malam baka ce komai akan daya yar uwar tata ba batun aure babu tsayayye”. “Shidai malamin Primary da kika qi shine mijin idan kuma kika daga za’ayi dayan biyu ko ki mutu ayi ko kuma a haife miki shege a gida” ya fada ba tareda ya kalle ta ba, se Addah ta dage qirji tace “na shiga uku Malam na mutu fa kace?” “Hajia Da wani abu ne ko shikenan” ya sake fada yana kallon Hajia Maliya, seta miqe tana cewa “Aa babu komai malam daman yau rakiya nayo ni ai al’amura se godiya kawai, Fatu bada abin sadaka mu tafi”. Kallonta Addah tayi da niyyar Magana Malamin ya rigata da cewa “Kuje tayi mun sadaka da kudin Allah ya yafe mun zunubaina” daga haka sukayi masa sallama suka tafi. Seda masu babur suka sauke su a Tashar Dukku har sun shiga mota Hajia Maliya ta kalli Addah tace “Fatu bakiyi sadakar bafa ko se munje cikin gari?” “Ke dallah rabani da dan rainin wayo, aikin me yayi mun da zanyi masa sadaka wani Allah ya yafe masa ashe yasan abinda yake babu kyau kenan” Addah ta fada a fusace dan sam ita ba abinda taso ba kenan, dukda wani sashe na ranta yayi fari da aka ce Ma’u zata fita amma ita so tayi ayi mata abinda idan ta fitan bazata dawo ba. “Ai aikin gama ya gama tunda har kika taka kikaje gurinsa kema kin debo naki kason zunubin kuma dole ki bada kudin nan kinsan dai ba’acin kudin malamai a zauna lafiya” itama Hajia Maliya ta hayayyaqo mata. “Gashinan nidai Allah ya saka mun” Addah ta gada tana cilla mata yan dubu dubu guda biyar, se Hajia Maliya ta cafe ta fita daga motar tana cewa “Ya saka mun dai nida na kawo ki ke da ba’a miki abun arziqi, Yara Almajirai ta samu ta bawa kudin kafin ta koma motar mintina kadan ta cika suka dauko hanya. Da suka sauka a tasha ma sama sama sukayi sallama kowa ta kama gabanta, suna zuwa gida kuwa Amirah ta tafasa saiwar nan ta fara sha dan tafi mata magungunan da Addah ta karbo kwana ki tana ji Addan nata bala’i waya sani ko shima hadin bakine da Maliya irin nasu Wizy ita dai bata kula ba harta gaji tayi shiru dan kanta. Suna dan yin waya da Bashir lokaci zuwa lokaci badai kamar da ba kuma yawanci da rana ne idan yana gurin aiki da ya shiga gida kota kira baya dagawa ta rasa abinda yasa. Randa ta yi masa qorafi ma seda suka samu sabani har yayi mata yaji kusan kwana hudu be kirata ba toh da yake neman shir takeyi tana so ta karbi kudi a hannunsa ta danyi wasu abubuwan shi yasa ta kira ta bashi haquri. Kwananta uku da dawowa sukayi baquwa, Amaryace da aka kawo gidan da yake kallon nasu daman matar gidan ta rasu tun tuni se yanzu mijin ya sake aure. Amarya Sa’ada da kadan ta girmi Amirah amma bazawarace auranta daya tana da yaya biyu ma suka rabu da mijinta cikin dan lokaci sabo sosai ya shiga tsakaninsu da Amiran da yake mijinta ba mazauni bane kusan kullum in ta gama ayyukanta se ta shiga gidansu Amirah kota kira ta ita taje suyi hira a haka har ta karanci Amiran ta gane irin zaman da sukeyi da Bashir har ma da kishiyarta. “Amma kedai anyi mara wayo wallahi, yarinyar ki dake kin maida kanki baya ita me haihuwa biyar itace star a gurin miji kina zaune. Inda kinsan kanki wallahi da tuni sanda ze tattarota ya dawo da ita nan ke ki bishi bama ze sani ba” Sa’ada ta fada ranar da Amiran take mata qorafin Bashir yaqi kaita inda yake aiki. Kwananta Arba’in da biyar da Haihuwa Sosai kuma taji dadin maganin da Malamin nan ya bata dan duk sauran kunburin nan bata fi sati tana sha ba ta neme su ta rasa jikinta ya dawo dai dai rashin kwarin da takeji ma duk ya ragu daman kuma aikinta tuni ya kame yayi kyau dan haka ta fara shirye shiryen tarbar Bashir. Tunda ya tafin nan be sake ce mata ze zo ba itama kuma ganin bata gama shirya wa ba ya saka bata ce masa yau she zezo dinba amma yanzu da take jinta garau dole ta nemo shi dan haka ta chanza salon hirar su yanzu, babu ruwanta ko yana offfice ta kirashi seta san yanda tayi ta rikitashi da salo kala kala da ta koya a gurin sabuwar qawarta Sa’ada. Wayar da sukayi ta qarshe ma wani Text Sa’ada ta rubuta mata tace ta tura masa, duk bala’in taurin kansa se ya sauke ya taho gurinta idan kuwa taga bezo ba to ta sallama kawai Asma’u tasha gabanta har gaban abada Bashir baya Sha’awar wata Mace idanba ita ba ilai kuwa tana tura masan ta kirashi ta sake gigitashi da kalamai masu kashe jiki se ji tayi yace gobe zezo Gombe, da tayi masa qorafin ba,a share gida bama cewa yayi babu komai ta shirya daya zo se suje Hotel kawai ai kuwa kamar tayi me dan murna tun a Daren ta fara shirya kaya da abubuwan da zatayi amfani dasu ji takeyi kamar ta janyo safiyar tayi. Bashir ya sauka Gombe lafiya kamar yanda suka tsara da Amirah yana sauka ya kirata dan da Naziru ya dakko shima a hanya ya sauke Nazirun ya karbi motar ya wuce gidan Addah yana zuwa ta fito suka tafi. Babban Daki me kyau ya kama musu, su Amirah se rawar kai ake itama yau an fita yawan shanawa da miji, dan hoton nan da akeyi mata da miji anje chilling ita sedai ta gani a gurin qawayenta saboda duk sanda zezo gurinta a Gomben seta jangwalo tsiyar da zasuyi in ma an shirya fitar ta rushe shiyasa take shaqar takaici idan taga hotonsu da Ma’u Fitar Asabar da Lahadin nan da sukeyi toh itama wannan karon in sha Allahu zata dage babu abinda ze bata mata wannan lokacin hotuna kuwa sedai zuciyar wasu ta buga dan haushi. Sosai sukaji dadin zama a hotel din nan an murji Amraci an more, washe gari Asbar da safe yaje gidan su Ya gaida su Dada be dade ba ya koma, sun sha yawon su kuwa Joint joint ta dinga janshi ansha hotuna sosai ya kuma yi mata shopping sosai. A yar Keypad dinta ta tura hotunan saboda me memory ce, ta daure ta cije batayi masa zancen waya ba ta bari ta gani zuwa ya tafi tukunna karta ballo wata tsiyar. Seta tuna maganar malamin nan daya ce idan ta kwantar da hankali zata ji dadin Bashir Asiri ba wani tasiri zeyi akan sa ba gashi kuwa ta gani dan cikin lumana ya amince ze chanza mata Tv da Set din Tv stand da Centre table harya bada kudin Tv da deposite din su Centre table din duk da dai Tv ba irin ta Asma’u bace amma itama babba aka siya mata 53’ ina laifi? Randa ze tafi kuwa harda ita suka kaishi Airport tana narke masa kamar karsu rabu suna dawowa gida Naziru ya ajiye ta ba’a rufa awa biyu ba se gashi da sabuwar IPhone 11 pro inji Bashir a kawo mata harda layi me Data. Murna kamar Amirah tayi me ta ringa kwasar Shoki tana tsalle nan da nan ta kirashi tayi masa godiya “Indai zaki chanza ki dawo irin haka babu abinda bazanyi miki ba Meerah” Bashir ya fada. Cike da sabon jin dadi sukayi sallama ta kashe wayar nan da nan ta hada ta ta dora layi ta shiga downloading WhatsApp, a wayar Ummi ta saka Memoryn ta ta tura hotunan zuwa sabuwar wayar ta tana cewa “yau akwai fafatawa kenan, dole nawatsa hotuna a Internet kowa ya gani” (An kuma ashe tuban muzuru kikayi toh Allah sa a wanye qalau dai 😂😂) Biki mukeyi se Monday In Sha Allah zaku ji ni 🙏🙏🙏🙏 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 WATA KISHIYAR 🥰👹 (ALKAHIRI CE KO SHARRI) 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 Na Maryamah Farouk (Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah) Wattpad @MaryamahMrsAm Page 29 Asma’u Alhamdulillah shine abinda zance dan yanda komai yake tafiyar mun lafiya lau ba tareda wata matsala ba. Dukda aikina na office ya dan qaru dan yanzu har tafiye tafiye zuwa sauran states na Nigeria nake yi amma saboda goyon baya dana samu daga Bashir se abin yazo mun da sauqi musamman da tafiyar tawa bata wuce kwana daya a mun dade ne mu kwana biyu. Tuni Amna sun gama sun gama SSCE tana zaune a gida se jiran sakamako kuma abinda ya qara sauqaqamun abubuwa kenan dan kona dade a waje bani da tunanin na dawo gida na tarar da wani aiki. Baban Ali da Amaryarsa kuwa se sam barka dan naga wani shiri sukeyi yanzu bini bini yana hanya an tafi Gombe, ina yawan kama shi yana waya da daddare dukda yanzu ya denayi a daki sedai ya fita ko kuma naga Text dinta idan ta turo har mamaki da dariya abin ya ke bani na tabbatar wannan ba dabarar ta bace ta samu wani da yake dorata a hanya ne. Ni kuwa sosai hakan yayi mun dadi ko babu komai hankalin na ya kwanta yanzu ne zamuyi kishi na hankali kowa ta iya Allonta ta wanke dan haka bana wasa babu daga qafa idan ya tafi kafin ya dawo nayiwa kaina Gyara gangariya yanda zan kwance masa kai na shafe duk wani gigi daya taho dashi. Sannu sannu rayuwa na shudawa kusan wata biyar kenan rabon mu da Gombe, tuni akayiwa Yara register da School Bus zata dauke su ta dawo dasu abinda ya sake sauqaqamun zirga zirga ma kenan tunda idan Bashir ya kaisu ni nake dawo wa dasu toh yanzu kuwa suna rigani dawowa ma tunda daman kullum se sunyi jira bayan an tashi kafin a dauko su. Jikin Goggon mu ne ya sake tashi da har seda aka kawo ta nan Lagos Asibiti wanda Alhaji Qarami Babban Yayan mu ne ya dauki nauyi dukda yanda muka so ya barmu muyi amma yaqi harya nuna bacin ransa akan mun banbanta tsakani kenan. Satin ta hudu a Lagos shima dakyar dan kwananta uku a Asibitin aka sallameta amma zata ci gaba da zuwa ganin likita na tsahon sati hudu dakyar da ban baki ta yarda zata zauna a gida na wai ita bazata je godai godai ta zaunawa siriki a gida ba seda Bashir din yasa baki sannan fa ai kuwa ranar zuwanta na qarshe washe gari ta koma Yola tareda Amnah da Faridah zasu yi kwana biyu dan su Faridan sunyi hutun Term. Tafiyarsu da kwana biyu Bashir ya tsiromun da wani sabon hali, a da duk dadewa baya wuce sallar Magriba a waje shima se ta qure kenan ko da zeje wani guri seya dawo gidan dai ya shirya sannan ya tafi amma a kwanakin nan se ya kai Tara Goma be shigo gida ba. Ranar farko qarfe Tara ya dawo a gajiye na tare shi, seda yayi wanka na kai masa abinci yana ci nake cewa “yau kayi dare Baban Ali ina ta kiran wayar ka kuma bata shiga ba”. “Eh aiki ne yayi mun yawa shiyasa na tsaya na dan rage wasu abubuwan” ya fada yana ci gaba da cin abincinsa. Har ga Allah na yarda saboda ya samu qarin girma kwananan dan haka nasan ayyukan zasu fi nada dalilin daya saka washe gari ma daya kai goma ban damu ba da yake ma ina dan fama da ciwon kai ka fin ya shigo nayi bacci seda Asuba Aliyu ya ke cemin jiya se 10 Abbi ya dawo. Abinda ya fara jan hankalina da dadewar tasa yanda abin ya zamar masa jiki dan seda ya jera kwana hudu kullum kuma a maimakon ya rage lokaci qarawa yakeyi, a ranar na hudun data kama Asabar, tun Daya na rana yayi wanka ya fice wai zeje gurin Musa abokinsa akwai wani aiki da sukeyi tare beyi awa biyu da fita ba nayi baquwa. Maman Shukra maqociyar muce a Estate din da muka fara zama kafin mu dawo nan rabon da mu hadu har na manta ma ina zaune se gata. Bayan na gabatar mata da kayan ciye ciye na zauna ina sake yi mata sannu da zuwa. Yanda take kallona tunda ta shigo ya tabbatar mun bakinta akwai magana dan Maman Shukra akwai gulma sedai na tabbatar da bata qarya, duk labarin data fada maka to kodai ba gaba daya bane idan kabi diddigi seka gano gaskiyar. Kallonta nayi da yar dariya nace “Maman Shukra wace jarida muka samu dan tunda kika shigo naga bakin nan naki yana motsi”. Seda ta kora ruwa me sanyi kafin ta kalleni tace Maman Farida Engineer yana gida kuwa?” Ina dan murmushi nace “ai kuwa kunyi sabani danba dadewa ya fita yaje gurin abokin aikinsa suna wani aiki ne”. “Aiki, lallai aiki kuwa” ta fada tana kama baki. Sena maida hankalina gaba daya kanta na kalleta da son jin qarin bayani. Qasa tayi da murya kafin ta fara cewa “Nidai ba zan fada miki dan na hada ki husuma da mijinki ba sedan kawai ki tashi tsaye ki dauki matani tunda wuri kina dai kallon halin da nake ciki kullum cikin fargabar kar kana zaune a zo a shafa maka alaqaqai”. Wato tunda ta fara magana qirjina ya shiga kidan Mandiri, ko bata fayyace mun komai ba na rigada na gano inda maganar ta ta dosa dan Mijinta ba qaramin dan Akuya bane, saboda tantiranci har gida yake kai mata mata seda tayi da gaske da taimakon Allah sannan ya rage ba wai ya dena dukka ba. Jin da tayi nayi shiru ina kallonta yasa taci gaba da cewa “Baban Shukra ne yazo mun da soki burutsun sa wai Mijin qawar tawa da kike qara zugani ina masa rashin mutunchi ashe duk kanwar ja ce shi da shi yau sun hade a Jungle ya dakko wata Babe me zafi, banyarda ba tunda nasan halin sa ba sanin me yakeyi bama yake wani lokacin se washe gari wallahi Maman Farida mun fita da daddare za’a siyowa su Hisham Icecream mukayi kicibus da su a gurin, Saboda Baban Shukra ya tabbatar mun seda muka jira su suka gama abinda zasuyi suka fita yabi bayan su har Hotel din da take mukaje kafin muka tafi gida. Washe gari ma ya sake cemun ya ganshi kamar ma daki ya kamawa yarinyar a gurin yake zuwa yana tafiya in taqaice miki jiya gurin 11 ma video call ya kirani ya nuna mun su a Gurin swimming pool kin ga har hoto ya musu kiga evidence fuskarta ce daibata fito ba”. Idan da Maman shukrah tasan yanda maganganunta suka jefani da ta dade dayinshiru amma seta miqomun wayarta tana cewa “kin gani karma kice qarya nake”. Duk yanda naso na hana ido na kalla abin ya gagara, a fili na furta “Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un” ina dafe qirjina jin kamar zuciya ta zata bullo ta fito, dagaske Bashir ne ga fuskarsa nan yana murmushi ya rungume wadda bansan ko wacece ba ta juya baya dan haka ba’a ganin fuskarta. Har Maman Shukra ta qaraci surutanta ta tafi ban sake gane komai ba, dakyar nayi sallar Magriba da Isha na nemi guri a palour na zauna ina jiran naga ta inda Bashir ze bullo. Gaba daya ido na sun soye kaina ya qulle na ma rasa ta ina zan faro tunani kalmar “Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un” kawai nake maimaitawa wadda ta taimakamun wajen zama cikin hayyacina. Ina zaune a palour har qarfe sha biyu na dare ina jiransa ga wayarsa na kira yafi sau nawa amma se ace not reachable har Musan na kira shi kuma wayarsa a kashe. Hankali na a tashe ina ta zagaya Palour ina kuma sake gwada wayar sa cikin Sa’a ta shiga daidai sanda naji tsayuwar motarsa a waje se na kashe na tsaya jiran shigowarsa. Yanda yaci burki yana kallona ya tabbatar mun be so ya tarar dani ido biyun ba amma saboda iya duniyanci irin na Namiji se ya wani chanza fuska zuwa kalar gajiya ya fara sakin wasu guntayen tsaki yana langwabewa, zuciyata na dukan uku uku na nufe shi, a raina Addu’a nakeyi Allah yasa abinda Maman Shukrah ta fada ba gaskiya bane sedai ina qarasawa dab da shi Qamshin Turaren Humrah da kuma shatin Jambaki daya fito radau a gefen kumatunsa da wuyansa suka yi mun sallama, Dum naji a kaina kamar wadda aka kwadawa guduma, Ban yarda daidai idona ya gani ba dan haka da saurin gaske na riqo fuskarsa na kunna torch light din wayata na haska da kyau se ya janye yana cewa “Ma’u lafiyarki kuwa, me kike nema a fuskata kuma?” “Kai zan tambaya Bashir daga ina kake? Turaren waye a jikinka sannan ga shatin Lips din mace nan a Fuskar ka Bashir daman zaman da kakeyi a waje abinda kake yi kenan to yau Allah ya toni asirinka?” Na fada cikin tashin hankali ina ja da baya, se yayi saurin riqoni ganin ina neman fadawa kan Centre table ta baya na fizge cikin faga murya nace “karka kuskura ka tabani, daman an gaya mun ana ganinka da mace amma saboda yardar da nayi dakai yasa ban taba kawo wa raina zakaci amanata ba, kana da Mata har biyu dame muka rage ka Bashir zaka fita waje kana zubar mana da mutunchi? Wace yar iska ce ka ajiye a Hotel kake zuwa Gurin ta har mutane suke ganinka ana daukar hotonku?” A zabure ya kwalalo ido waje yana kallona yace “Hotona Ma’u? Waye ya dauke mu?” “Oh ta tabbata kenan ka aikata, kana zaton Asirinka ze rufune? Toh Allah ya tona ka na gani kuma mutanen duniya ma sun sani duk me maka kallon mutumij kirki ka zubarwa da kanka mutunchi a gurinsu” na fada wasu hawaye masu zafin gaske suna zubo mun, Se ya sake matsowa yana qoqarin riqe ni yace “Ya isa Ma’u karki tayar da yara a bacci ki bari muje daki zan gaya miki komai ba abinda kike zargi bane wallahi”. Wani banzan kallo na watsa masa kafin nace “Dawa zakaje dakin? Idan kaga na dara daga nan toh ka gayamun wace yar iska ka ajiye a hotel yara kuma ai bakayi tunanin su ba kaje kana zubar musu da qima kana raba musu abin gori a gari”. Duk yanda Bashir yaso dana sassauta na zauna muyi maganar qi nayi, gani nake yama raina mun hankali tunda alama ya nuna maganar Gaskiya ce dan da nace naga hotonsa ai be musa ba abinda ya qara dagamun hankali kenan na shiga rusa kuka ina cewa “Ka cuce ni Bashir ka cuce ni idan har mugun halinka ya shafi yayana bazan taba yafe maka ba”. “Wallahi Asma’u ba abinda kike tunani bane ta yaya tun da quruciyata ban nemi matan banza ba se yanzu da girma ya fara kamani na tara iyali? Ku biyu fa nake da ku wace ni’ima ce Allah beyi muku ba da zan fita waje na nema?” “Ita waccen din da ka ajiye qanwar uwarka ce kenan” na fada a mugun fusace nayi kansa dan rainin hankalin nasa kuma ya fara yawa, ganin da yayi na taho gadan gadan se ya matsa yana cewa “ba wata bace Ma’u Amirah ce, wallahi Amirah ce tazo nasan bazaki yarda ki sauketa a gidan nan ba shiyasa na kaita Hotel”. Wani burki naci tareda qamewa a inda nake ina rarraba ido tsakanin idonsa da bakinsa, so nake na tabbatar da abinda kunnena yaji ko kuwa ba daidai bane, se ya matsoni yana sake cewa “Amirah ce tazo wallahi tun last week Sunday, nima ban sanda zuwanta ba seda ta sauka tace mun gata a Lagos, ban san yanda zaki dauki maganar ba shi yasa na kasa fada miki wallahi amma gobe ma zata tafi”. “Bashir dakai da ita kuje Allah yayi muku yanda kuke mini” na fada cikin wani irin sanyi kafin na juya na shige dakina kfain ma ya biyoni na sakawa qofar key. Kan gadon na fada na fashe da kukan da ko mutuwar Mahaifina banyi irinsa ba. Kuka ne na zallar baqin ciki da takaici wannan wane irin abu ne? Anya Bashir yana da hankali da tunani kuwa, yana lissafi kafin ya aikata wani abun? Idan ya gayamun Amirah zata zo me zanyi, kai ko be fadamun ba ina zaune ta shigo gidan na ya zanyi da ita ai gidan sa ne kuma ko bata auran Bashir ita me iya zuwa gidansa ta zauna ce amma shine ze dauketa ya kaita Hotel ya ringa satar hanya yana zuwa mutane suna ganinsa yanzu Allah kadai yasan mutum nawa suke masa kallon Fasiqi ya ajiye farka a Hotel. Inajinsa yana buga qofar yana magiya na bude amma nayi banza dashi na tashi nayiwo alwala nayi na tada sallah ina yi ina kuka ban idar ba seda aka fara kiraye kirayen Asuba, ina idar da Sallar Asuba kuwa wani wahalallen bacci ya kwashe ni da ban farka ba se sha biyun rana shima qiqi qiqin da ake da qofa ne yasa na bude ido na. Ina dafe da kaina dayayimun nauyi na nufi qofar jin surutan mutane kamar ma ballata ake so ayi se na murza key din naja baya ganin yanda Bashir ya fado kamar an cillo shi, a bazata ya rungumoni ban yi wata wata ba kuwa na hankadashi da dukkan qarfina yai baya Allah ya taimake shi bango ya tare shi, ina kallon securities din daya gayya toh suka juya suka tafi. Be daddara ba ya sake nufo ni yana cewa “Ma’u lafiya kike tun jiya kin kulle qofa babu irin bugun da banyi ba gaba daya kin tayar mana da hankali ga yara can se kuka sukeyi”. Tsaki nayi na juya na cire Hijabina na shige bandaki na bar shi a tsaye a gurin, sanda na fito baya nan, riga kawai na zura dan banida nutsuwar da zan saka komai a jikina, bakina har wani daci yake mun saboda bacin. Lokacin da na fito Suna zaune shida Matarsa da ban san sanda tazo ba sunyi tsuru kamar masu jiran Sadaka. Kallo daya nayi musu na wuce Kitchen inajinsa ya taso ya biyo baya na seda muka shiga ciki sannan na waiwaya na kalle shi nace “kasan Allah ko ka fita ko kuma ka kalli nan (na nuna masa bangaren da wuqaqe suke) gasu nan kala kala in ka qureni se nayi maka aika aika na huta da takaici” ai kafin na qarasa fit ya fice daga Kitchen din duk yanayin bacin ran da nake ciki seda nayi dariya sosai dan dagaske ya tsorata. “Allah ya tsare ni da irin wannan zuciyar” na fada a fili kafin na zuba ruwa a kettle na kunna kafin ya tafasa na hada kayan shayi a babban kofin dan bazan bari baqin cikin Miji da kishiya su naka sani ba. Shayina me kauri na hado na zubo dambun nama a bowl na dakko ledar biredi, kamar bansan da tsurom mutane ba haka na nemi kujera na hakince sannan na kunna Tv ina shan shayina ina kallo. “Ma’u ga Amirah kin ganta wallahi ita ce ba wata daban ba na yarda nayi kuskure tun farko da ban sanar miki da zuwanta ba amma kiyi haquri”. Yanda yai maganar kamar wanda yayi wa babarsa wani qundumemen laifi yazo bata haquri harda wani zamowa qasa saboda tsabar iya sharri ga muryar sa har rawa take yasa na kalle shi, seda na cinye biredin dana tura a bakina na kora shayi sannan cikin dan murmushi nace “Oh wannan be ishe ka ba kenan seka qulla mun sharri a sake tafiya dani a baki ace na mallake ka har durqusamun kake ba? Ni tunda nake dakai ma ka taba bani haquri ne amma da yake yau kana so ka qaramun baqin jini shine kake duqawa ai shikenan, ni na gama magana ta tun jiya duk abinda mutum yayi mun na barshi da Allah” daga nan na ci gaba da cin abincina ina jinsa ya qaraci naci da magiyar sa amma tafi ka mutu bance masa ba. Amirah da ta shaqa tayi tam daman ga takaicin dakko ta dayayi tun da sassafe ya ringa surfa mata ruwan masifa ga abinda ta janyo masa nan ana yawo dashi a gari an ce ya ajiye karuwa ya taso ta a gaba wai tazo su bawa Ma’u haquri tun bakwan safe take zaune se yanzun dana fito ga wannan Dramar da yakeyi kuma har wata kwallar takaici ce ta taru a idonta. Cikin muryar bacin rai tace “Ni Yaya ka dakko ni tun safe ko wanka banyi ba bare naci abinci gashi yanzu Azahar tayi gaskiya ni yunwa nake ji”. “Waya hana ki kici abincin ai gaki ka Kitchen nan duk bake kika jawowa mutane ba” ya hayayyaqo mata, seta miqe zata tafi Kitchen din nayi sauri tare ta da cewa “Ji mana, karki shigar mun Kitchen malama ku koma can inda ya aje ki ki nemi abinci ba’a nan ba” ban qarasa cinye biredi na ba na daure ledar kawai na kwankwade shayin na tashi. Seda na kullo qofar Kitchen din da mukulli na zare kafin na shige dakin su Aliyu na bar Bashir da Amirah baki sake suna bina da kallo. Aliyu da Jafar na zaune da alama duk suna jin abinda yake faruwa se nayi murmushi na zauna ina cewa “me kuka bawa yan biyuna har yanzu basu tashi ba?” “Game sukayi tayi Mami basu kwanta da wuri ba jiya dakyar suka tashi dazu suka ci abinci ma” Jafar ya fada. Whatsapp na bude a wayata ina shiga message din Maman Shukra ya fado nayi murmushi na bude “Maman Farida ina fatan dai bada tashin hankali kika tunkare shi ba ko, kinsan fa irin wannan abun se a hankali da Addu’a kuma in ba haka ba a maimakon a samu sauqi se ka qara tunzura mutum” ta rubuta, se na mayar mata da cewa “Ai baki sani ba, ashe Amaryar sa ce tazo sh ya sauke ta acan kin gansu tun dazu ya dakko ta tana nan”. “Tab amma se abar Engineer, to ke me kakace yanzu?” “Me zance kuwa, gasu can na barsu a palour ni ina daki ma bacci zanyi se anjim mayi magana” na fada dan na datse hirar. Alawiyya yayata na duba naga bata online, fita nayi daga dakin na koma nawa dan ina so na l kirata, sanda na fito palour Bashir kadai na tarar har na wuce na yi kwana na shiga dakinsa. Addu’a nake Allah yasa tana ciki yau na gwada musu danyan kai daga shi har ita se Allah ya temaketa babu kowa har Toilet na duba bata ciki na kullo qofar na fito se ya tare ni yana cewa “Ta tafi gidan Ghali daga can gobe seta wuce Gombe” (Ghali dan wan Baban su Bashir ne). Wunin ranar zir haka yayi shi a palour daya ji motsina ze taso yana so yayi mun magana amma naqi bashi fuska sam da daddare ina jinsa suna waya yana ta masifa nidai qala bance masa, daya biyo ni dakina ma abinda tun tsahon zaman mu a gidan nan be taba kwana a ciki ba yana kwanciya na juya mukayi kai da qafa yana fita sallar Asuba kuma na saka Key. Haka muka cinye satin, har zuciyata na huce kodan irin ban haqurin da ya ringa yi mun amma ban nuna masa ba, yanzu dai ina dafa abinci dashi kuma in yayi mun magana ina amsawa sakin fuska ne dai babu na kuma dena shiga sabgarsa sannan na koma dakina da kwana kullum kuwa se ya bini. Bansan ya suka qare da Amirah ba nasan dai ta tafi, dukda abinda ya aikata ai ba laifi bane ko babu komai ai matarsa ce daman ai yana da ikon kaita ko ina amma yanda ya biyo da abun ne babu tsari a ciki. Dan haka fushin kwana biyu na qara kafin na ware muka koma daidai kamar bamu samu wani saba ni ba. Amirah Da baqin ciki da takaicin Ma’u da Bashir ta koma Gombe, har kuka tayi sanda take labartawa Addah abinda ya faru. “Se kinga yanda ya rikice Addah harda durqusawa yana bata haquri a gaba na ita kuma se yankwana shi takeyi saboda ta nunamun ta isa dashi. Saboda wulaqnaci fa gidan Ghali ya turani na qarasa kwana sannan da zan taho ma Taxi yasa ta kaini Airport se a waya mukayi sallama”. “Tab lallai Asma’u ta gawurta yanzu Bashir din ne ya duqa mata, lallai dole mu sake tashi tsaye. Ni ina ganin komai yayi lafiya yanda kwana biyun nan aketa abin arziqi ashe da sauran rina a kaba” Addah ta fada tana kama baki. “Ai wallahi bata ci bulus ba, yanda ta rusa mun tsarina nima sena rama” Amirah ta fada, daga nan suka shiga qulle qullen yanda zasuyi su rama abinda Ma’u tayi mata. Lagos Ranar Juma’a data kama litinin a koma makaranta Amna da Farida suka dawo, ban gayawa Bashir ba na saka Naziru ya siya musu Tickets dan daga Yola Gombe aka kaisu se ganinsu kawai yayi ai kuwa ya ringa masifa akan me zan doro masa yara a jirgi su kadai me yasa ba’a gaya masa yau zasu dawo ba yaje ya taho dasu ko shi Nazirun ya rako su nidai nayi banza dashi tunda sun dawo ai magana ta qare. Monday qalau muka rabu kowa ya tafi aikinsa ranar na dan jima a office saboda shirin Tafiya Abuja da mukeyi wani conferees se bayan Magriba na shigo gida. Seda mukaje kwanciya sannan nake gayawa Bashir dan saura sati daya tafiyar. “Lallai Big woman anya nima bazan zo a dan sama mun guri ba naga fa kuna kwasa da yawa a office din nan naku” ya fada da dan murmushi yana danne danne a wayarsa, sena gyara zama ina cewa “Kaidai bari wallahi yanzu ma fa package din tafiyar nan naji Accountant yana cewa kusan 700 huns za’a bamu each kudin TP da accommodation ni daman gidan Alhaji Qarami zan sauka kaga sena soke kudina, Goggo nake so ma na biyawa Umarar Azumin su tafi tareda Maman Ayman”. “Hakan yayi kyau, nima idan na samu yanda nake so se mu tafi da ke ita kuma Amirah se taje Hajji”. “Allah ya yarda toh” na fada sannan muka ci gaba da hira har bacci ya dauke mu. Weekend din daya kama satin da za’a shiga zanyi tafiyar ranar Asabar da daddare na sake gaya masa zancen tafiyar base ranar Monday ya ganni da jaka ba. Yana zaune na kawo masa coffees da yace yana so nake masa zancen ina cewa “Allah ma ya taimake ni Amna na gida yanzu da bansan yanda zanyi tafiya harta sati guda ba”. Shiru ya mun yaci gaba da shan coffee dinsa nima se na mayar da hankali na kan Tv seda ya mula dan kansa se cewa yayi “wai dole ne se kinyi tafiyar nan?” Ban waiwayo ba na bashi amsa “Kaji Baban Ali da wata magana, tun fa last week na gaya maka, me ze kaini toh idan ba dole ba”. Tsakin daya ja ne ya saka ni waiwayawa na kalle shi, fuskar nan a mugun hade seda gaba na ya fadi dan rabon da nagan shi a irin haka an kwana biyu. “Lafiya” na fada ina gyara zama na fuskan ce shi da kyau, se ya miqe kawai ya shige dakinsa nima na rufa masa baya. “Kibar tafiyar nan kawai dan bazan iya zama har sati guda ni kadai ba” ya fada yana cire rigar jikinsa da alama wanka ze shiga. Sena marairaice cikin lumana ina cewa “Haba Engineer satin fa kamar yaune qilan ma baza mu kai haka ba, kayi haquri ka daure In Sha Allah gaba idan haka ta taso zan nemi a chanza wani dani amma yanzu lokaci ya qure kaga jibi ne fa tafiyar” A maimakon ya sakko se nagama kamat fetur na qarawa wutar dan hargagi ya shiga yi mun yana cewa “nidai na gaya miki kawai, ke ni aikin nan ma gaba daya bana sonsa daman idan mace taga tana samun kudi gani takeyi kanku daya tunda babu abinda zata nema a gurinka, kai ta yaya ma za’ayi mutum yana da mata amma ta tafi wani guri tayi har sati daya meye marabar sa da gwauro” bam ya shige Bandaki ya bugo qofar sena rakashi da ido kawai ina karanta Hasbunallahu wani’imal wakeel a zuciyata. Abin ya motsa kenan, haka naja jiki a sabule na fice na koma dakina. Rasa wanda zan kira na gayawa wannan abu nayi ina zaune sega kiran Babbar yayar mu a dakin mu Anty Suhaima da take America ta kirani. Bayan mun gaisa mukayi shiru dan babu sabo sosai tsakanin mu saboda ita da wuri tayi aure ta auri dan Abokin Baffan mu yan Kano ne a lokacin Baban sa shine Ambassador na Nigeria a America dan haka tunda tayi aure can aka kaita kusan shekara Ashirin da biyar yanzu. Jin shirun naw yayi yawa ya sakata cewa “Ma’u lafiya kuwa kamar akwai abinda yake damun ki” haka kawai naji kuka ya taho mun ba kuwa ta hanani ba ta barni na yi abuna seda nayi shiru dan kaina kafin na gaya mata yanda mukayi da Bashir. “Daman baya son aikin naki tun farko ne ko yaya” ta tambaye ni, “Wallahi Anty be taba nuna baya so ba, tun ma ba yanzu ba kinsani kafin wannan nayi wau qananun ayyukan kuma be taba hanawa ba a koda yaushe yana bani goyon baya, yanzun mafa ya yarda yau ne kawai dana sake gaya masa zancen tafiyar shine kuma ya bullo da wannan maganar”. “Shikenan, ki rabu dashi ki ci gaba da Addu’a zuwa goben ku sake maganar idan be yarda ba ki haqura karki tafi ba tareda izinin sa ba idan yaso ki gayawa Alhaji qarami se aji me yake nufi da aikin naki daman ai zaman aure dole akwai qalubale Ma’u Allah dai ya sa mu dace kawai” nasiha taci gaba da yi mun kafin mu ka gaisa da yaranta dukka su hudu sannan mukayi sallama bayan na tura musu da Number Aliyu da Amna da suka ce. Ban koma dakin Bashir ba a zato na kuma ze biyo sahu amma har dare ya tsala naji shiru. Da safe na sake tun kararsa da maganar se kuwa cewa yayi “In dai izinina kike nema toh ban yarda ba” ya sa kai ya fice daga gidan. Yana fita na dannawa Dadan su kira dan kuwa bazata sabu ba, tas na gaya mata yanda mukayi tace na kwantar da hankali na zata masa magana, ilai kuwa da daddare ina zaune se gashi fuskarsa nan kamar Hadari yace “Wato qarata kika kai Gurin Dada ko? Shikenan kije amma ki tabbata sena dauki hukunci akan hakan”. “Tunda dai ka barni ai zance ya qare” na fada bayan daya fice daga dakin, washe gari na cale zuwa Abuja bayan na barwa yara komai da zasu buqata karma ya huce haushi na akansu. Amirah Sosai ta kunnowa Bashir wuta tunda ta fuskanci shi mutum ne me son a girmama shi ba kuma yason raini se tayi amfani da wannan damar gurin nuna masa ai Asma’u ta raina shi kuma abinda take nuna wa mutane kenan cewa tafi qarfinsa. Da Samirah qanwar sa suka shirya komai dukda ita Samiran bata san amfani da ita Amirah tayi ba. Tana zaune ta kirata take bata labarin abinda ya faru ai Bashir ya durqusaw Ma’u, Smairah kuma irin masu dan banzan surutun nan ne idan taji abu kamar dukka dangi kowa yaji ne dan haka kafin kace me wannan Labari ya karade kowa kamar wutar Daji cikin haka maganar ta koma kunnen Bashir. Amma saboda rashin Adalci irin nasa a maimakon ya ji haushin Amirah data fada tunda a gabanta akayi se laifin ya koma kan Ma’u a cewarsa da batayi masa boren da tayi ba ai da be durqusa matan ba har Amiran ta samu abin yayatawa ba wannan fushin ya qudure a ransa. Kwana biyu tsakani har ya huce tayi masa zancen biyawa Goggonsu Umarah se akayi dace washe gari Bala ya kirashi, suna cikin waya yake ce masa “Mutumina ashe Ma’u ta siyi gida nan kusa damu, jiya mun zagaya ta gurin naga gidan hadadde nake tambayar na waye akace na matar ka ne kamar ma guda biyu ne fa ko Su Aliyu ta siyawa ne”. “Anya kuwa Ma’u ta siyi gida ba tare da na sani ba me zatayi dashi, ina ga dai ba nata bane sedai wata daga cikin yan gidan su ko” Bashir ya fada. “Lallai Bashir baka san mata ba, ka manta lokacin baya kenan yanda yan uwanta suka tinga zugata akan karta doraka akan dukiyarta. Yanda take karbar kudin Hayar gidajenta ga Albashi me tsoka ai dole ta ringa siyan kadarori tana boyewa baka sani ba, nifa wallahi nama ga baikenka kana zaune na tabbatar yanzu ta ninkaka sau uku a arziqi wallahi in bakayi wasa ba kwanan nan zaka zama mijin Hajia se yanda tayi dakai tunda tafi qarfin komai babu abinda zata nema a gurinka. Da zaka ji ta tawa ma kasa ta ajiye aikin nan wallahi dan tana dab da finka Albashi bashi ne taqamarka ba”. Wadannan maganganun na Bala dana Amirah su suka yi tasiri a ransa dan yana ganin abinda Balan ya fada gaskiya ne. Tunani ya shigayi Rabon da ya dauki kudi ya bata ma shi harya manta daidai da kudin sati na man mota da yake bata yafi wata shida be bayar ba kuma bata tambaye shi ba. Daman cefane baya yankewa a gidan kusan zece buhun huna kadai yasan yana siya amma sauran abubuwa tunda daman ita yake bawa kudin tayi mantawa yake kuma bata tambayarsa haka zega komai a ajiye. Yanzu a satin daya wuce ta ce masa Bilal ya turo mata wasu motoci idan yana so ita ma zata chanza tata ko School Fees din makaranta na wannan term din ita ta biya se daga baya ya mayar mata da kudinta gashi kuma a kullum cikin yin suturu na alfarma take daga ita har Yaranta har shi tana siya masa takalma da Agogo ga turaruka. Wadannan abubuwan daya hasaso a shirmensa su yake ganin zasu sa tafi qarfinsa har ya kasa juyata gashi kuma sauran mutane ma sun fahimci cewa Asma’u tafi qarfinsa a ganinsa babbar gazawa ce kamar shi ace matar sa tafi qarfinsa dan haka dole ya dauki mata ki akai. Kunsan December ansha Bukun kuna Allah ya bawa Amaren mu zaman lafiya ya kawo na yan baya 🙏🙏🙏 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 WATA KISHIYAR 🥰👹 (ALKAHIRI CE KO SHARRI) 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 Na Maryamah Farouk (Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah) Wattpad @MaryamahMrsAm Page 30 ASMA’U Cikin kwanaki biyar muka gama abinda ya kaimu, ada naso na yi weekend na huta ne har nadan zaga dangi amma saboda yanayin rabuwar mu da Bashir yasa na fasa daga gidan Alhaji qarami ko gidan Yayata Junaidiyya da mijinta yayi Accident, naso naje na dubashi amma gudun kar sauran suce banje musu ba yasa kawai na haqura. A ranar Juma’ar da muka gama na bi jirgin dare zuwa Lagos. Kadaran kadahan Bashir ya karbe ni, ban damu ba na shiga sabgogina ina dai ta qoqarin ganin komai ya daidaita a tsakanin mu amma yaqi bada hadin kai sam. Ranar Talata da daddare bayan mun gama cin abinci Bashir da Aliyu suka fita siyo Biredi sauran yaran kuma duk suka koma cikin palour ni kuma na zauna a Gurin Dining din ina danna waya, kiran Muslim Yaya nane ya shigo wayata, mun dan jima muna magana kafin mukayi sallama yana kashewa Khadija qanwata ta kirani. Abdallah ne ya taso ya kawo mun littafinsa na quantitative reasoning ya kakare a wani guri daman ina jinsu da yayyan yanata su koya masa kowa yaqi dan haka na saka wayar a speaker muna hirar ina nuna masa. Hirar wata faccalarta takeyi mun, babansu yana da kudi kamar su kashe shi amma irin matsolon nan ne ba’a cin kudin sa se akayi dace data tashi aure ta auri me kwadayi dan shi dalilin auranta ma saboda kudin baban nata ne. Tofa tunda akayi aure yaga babu lashi se rashin mutunchin yau daban na gobe daban qarshe ya yiwo mata kishiya ma shine yanzu ba’a dade ba baban nasu ya rasu anyi musu rabon Gado ta samu kudi sosai se kuma ya dawo kamar yaron ta se yanda take so yakeyi har Kishiyar ma yanzu ya mayar mata da ita kamar me aiki kome take so shi za’ayi a gidan nan. “Wallahi Anty se kin ganshi jiya da mukaje sabon gidan da tayi yana tsaye yanda kika san dan aiki daga tayi motsi ze zaburo yace Hajia me kike so Hajia me za’ayi, ni ban taba ganin meson zuciya irin Rabi’u ba wallahi” Khadija ta fada. Dariya nayi ina cewa “kudi ake gaya miki huce takaici kenan, ai idan mace ta gawurta zakiga har mijin ma wani shakkar ta yakeyi balle kuma kishiya. Shiyasa kika ga mun dage muna neman su maganin wulaqanci” na fada dai dai sanda Bashir da Aliyu suka shigo, wani kallo dana kasa fassara ma’anarsa ya yimun kafin yasa kai ya shige dakin sa. Hirar mu muka ci gaba sannan mukayi sallama lokacin na gamawa Abdallah Homework din se na tashi daga gurin nima na shiga dakin Bashir. Qarar ruwa da naji yasa na gane yana Toilet, sena zauna a gefen gado ina jiransa ya fito. Kudi nake so na ara a gurinsa ina so na qarasa mana siyayyar kayan sallah dan haka nakeyi kafin lokacin yazo na siyi komai idan ya bani kudin se nayi wasu hidimar dasu yanzu kudaden hannuna duk na tattara na bada kudin Umarar Goggo daman Kudin Hayar da zan karba na saka rai dasu to su kuma tun kafin suzo ma na bada Aron su. Seda na barshi ya gama shiryawa ya zauna sannan nace “Baban Ali Aron kudi nake so dan Allah”. Shiru yamun ban damu ba na cigaba da cewa “Kasan na gaya maka zancen tafiyar Goggo to na bada kudin, wadanda kuma nake saka rai na hayar gidajen nan wallahi Yaya Abubakar ya rance wai ya cikawa su Bilal sun tada ginin gidajen su bayan Babbar Sallah nan muke saka ran bikinsu”. A maimakon ya amsa ze bani ko baze bayar ba se ji nayi yace “Lallai Ma’u karanki ya isa tsaiko. Wato ban isa ki tambayeni kudi ba sedai kice na ara miki ko? To bari kiji ni ba sakaran namiji bane da har kike tunanin dan kina riqe wasu yan kudade zaki fi qarfina, inaji har fada kikeyi kudi maganin wulaqanci idan mace ta gawurta miji zeyi shakkarta to bari kiji ko kin fi Dangwote kudi ina nan a matsayin mijin ki kuma baki isa na biki ba. Daman tunda kika fara aikin nan naga halayenki da yawa sun chanza, saboda zan fita nema kema ki fita kina ganin kanmu daya ba? to ya zama dole zan dauki mataki, ki fara shirin ajiye aikin nan”. Kamar sokuwa haka na ringa binsa da kallo har ya gama magana. Dan Allah meye laifina anan? Daga neman rancen kudi shine ze tado wadannan maganganun haka. Sena sake matsawa kusa dashi ina cewa “Yanzu saboda Allah Baban Ali rashin tambayar ka kudi da nakeyi ashe nan ma laifi nake ada da nake tambayar ka kuma cewa kayi ai na ishe ka da bani bani kai bakaga amfanin Kasuwancin da nake yi ba wai dan Allah me yasa ba’a maka gwaninta ne?? Kuma ni a yaushe kaji nace nafi qarfin ka ko ina so ka bini idan dai ba neman tada zaune tsaye ba daga ji mutum yana waya se kace dakai ake baka san hawa ba baka san sauka ba. Maganar aiki ko kuma wani kudin daban da nake samu kasan idan da tarawa nakeyi da yanzu na kai inda nakai wallahi amma ko na samu jikinka suke komawa tunda kafin na amfani kaina da biyar na amfana wa yaranka da dari. Yaushe rabon da ka dauki sisinka ka bani da sunan wata hidima tawa kota yaran nan? Siyowar da kakeyi da kanka ma tunda kaga idan ya qare inayi ka sakar mun se sanda ta raya maka sannan zaka siyo ko ka bada kudi a siyayyar. Idan ba sallah ba na manta rabonda yau Baban Ali ka kawo dankunne kace gashi wannan naki ne kuma kullum kana ganina da sabon abu amma baka taba tambayata a ina na samu ba duk ba sauqin ka bane, idan da bani da abinyi ai duk nauyin a kanka suke”. “Oh gori zakiyi mun kenan daman ni nace ki ringayi ko ke kika dorawa kanki? To ki dena, daga yau karki sake saka silenki a hidimar gidana kota yayana ki gani idan bazan iya ba” Ya fada a fusace. Haka kawai naji zuciyata ta karye wani kuka yana neman taho mun, wai me zanyi na burge Bashir a rayuwa ne? Duk abinda nayi aje a dawo wata rana se ya zama abin fitina, seda na dauke hawayen daya zubo mun akan fuskata kafin nace “Ko baka fada ba nima bazan sakeyi ba idan yaso seka gani in abin kirki nake maka ko akasin haka” daga haka naja bakina nayi shiru ina goge hawayen da suke zuba daga ido na dan na kasa hana su fitowa. Meyasa maza ba’a iya musu a rayuwa ne? Idan kika zauna baki nemi na kanki ba a goranta miki idan kin tashi kin nema shima baki tsira ba to ya ake so kayi? Wayar sa ce ta katse mana shirun da mukayi se ya daga yace “zan kiraki” kafin ya kashe. Ina lura da yanda yake satar kallona yana zuba tsaki se na dena goge hawayen na barsu kawai suna shata se ya miqe gaba daya ya bar mun dakin yana fita kuwa na fashe da kuka me sauti harda sheshsheqa. Bashir Gaba daya jikinsa yai sanyi da ganin hawayen nata, shi da kansa yasan be kyauta sam Asma’u bata cancanci wani abu a gurinsa ba bayan kulawa da tattali amma dole tasa kashi yin koma menene dan a nasa ganin an fara dakko sare sarin da zata fi qarfin nasa saboda sam ada ai ba haka take ba. Idan ya gaya mata magana tana ji amma yanzu abinda tasa a gaban ta kawai shi takeyi. Bata yij shawara dashi sedai kawai ta gaya masa zatayi abu kaza in aka ci gaba da haka ai wataran ma se tayi sannan ze sani dan haka ya quduri niyyar kawai ta aje aikin nan tunda shi yake sake bude mata ido tana hulda da manyab mutabe tana ganin rayuwa kala kala. Kwana biyu a tsakanin gaba daya na dauke masa wuta na fita a sabgarsa na kuma qudurce a raina yar biyar dita Bashir baze sake ci ba. Dakansa ya sakko ya ringa neman shiri dayaga yanda na watsar dashi seda na gara shi kuwa sannan na haqura amma fa ba wai na chanza ra’ayi ba jira kawai nake wata yayi na fara tatike Aljihun Bashir. Sati biyu tsakani wata ya qare kuma a satin nasan zeje Gombe, ina sane na zauna na rubuta uban list kai harda abinda muke dasu seda na rubuta na hada total dina kusan dubu dari da Ashirin, ana gobe ze tafi ina jinsa yana mitar an qara kudin jirgi seda ya gama na miqa masa takardar ina cewa “Ga wannan karna manta ka tafi, na manta Gas din mu ya qare shima qaramar cylinder da tayi saura ita aka saka jiya sannan lemon yan makaranta da Biscuits suma babu na manta ban rubuta”. Takardar ya karba ya duba se ya dago ya kalleni yace “Wannan kudin duk na menene haka kusan dubu dari da Ashirin?” “Shi yasa fa na rubuta maka komai dalla dalla da kudinsa karma kace qari nayi maka ko wani abu” na fada ba tareda na kalle shi ba, seda yaja wata qwafa kafin naji yace “Yanzu kudin zan baki kenan?” “Ka siyo da kanka ma duk daya ne ai” nayi saurin katse shi. Beyi magana ba mintina kadan naji wayata tayi qara alamar shigowar message na jawo na duba Alert ne na dubu dari da Hamsin daga Bashir nayi murmushi nace “Sun shigo harda qari ma muka samu toh mungode Allah ya qara budi”. Washe gari ya tafi Gombe. Weekend din a daddafe nayi shi dan gaba daya bana jin dadi, zazzabin dare ne yake damuna safiya nayi kuma naji garau na bari akan Monday idan be dena ba zanje Asibiti. GOMBE Wato wata Irin ladabi da biyyaya Amirah ta ara ta yafawa kanta wanda duk hudubar Sa’ada ce. Jikinta na bari Daman yanzu da yace zezo zataje ta qalqale gida a gyara ko ina dukda dai da taimakon Ummi harda Sa’adan ma suke zuwa wani lokacin sannan idan yazo tana iya qoqari tayi tsafta harya tafi a bangaren girki ne dai har yanzu da saura yana ci yana qorafi dan baya masa kamar na Ma’u. Wannan zuwan da yayi sosai yaji dadinsa ga tarairaya yana samu da kula kamar wani jariri babu aikin office babu hayaniyar yara. Butulci irin na dan Adam a yanzu se yake ganin Yafi samun yanda yake so a gurin Amirah musamman da yanzu ta dena masa qorafin da tambaye tambayen kudin da takeyi gashi a karan kanta ta canza sosai komai tana yi yanda yake so. Suna zauna ana gobe ze tafi tana bare masa Ayaba yana ci ya kalleta yace “kina son zuwa Lagos?” Sam Amirah bata kawo da ita yake ba dan a bazata maganar tazo mata har seda ya sake maimaitawa kafin tace “Meze hana mana Yaya ai kowacce mace zata so ta zauna kusada mijinta daman, wani gidan zaka samar min kenan”ta fada tana danne zumudin ta, lallai ta yarda kissa tafi Asiri tunda gashi yanzu hankali kwance tana samun abubuwan da suka wahala suka kashe kudinsu a banza akansu. “Aa ina ganin zaku ringa karba karba ne dan baze yuwu na ajiye ku gaba daya acan ba”. “Toh Anty fa ya zatayi da aikinta” ta fada tana gyara zama a ranta tana Addu’ar Allah yasa matsala suka samu daman ta lura tunda yazo bata ga sunyi waya ba. Seda Bashir yasha ruwa kafin yace “Ina ganin zata ajiye aikin ne kawai idan yaso ta cigaba da kasuwancinta kema ya kamata ki samu wani abinyi zaman haka ya isa”. Tamkar Amirah ta taka rawa haka taji amma ta dake, cikin kisisina tace “Toh yaran kuma fa su acan za’a barsu ko suma nan zasu dawo?” “No su zasu zauna can saboda School” “Amma Yaya indai makaranta ce anan ma fa akwai ko wacce iri kake so, ni ba wannan ba ma abinda yafi damuna Tarbiyyar su kasan fa yaran da suka tashi a Kudun nan duk zaka gansu se a hankali ko a gida ana musu tarbiyya tunda kullum suna fita su cakudu da yara kala kala se kaga anayi tana warwarewa. Ni da zakaji shawarata ka dawo dasu nan ga makarantu nan na kudi masu kyau a saka su”. Shiru Bashir yayi yana tunani, baza’a hadama karantun boko nacan da na nan ba amma maganar tarbiyya tabbas tayi gaskiya abinda yasa ya hana Amna yin Jamb wannan shekarar kenan yace ta bari se next year saboda kafin nan ta dan qara girma da wayo yana tsoron turata Jami’a cikin Yayan Arnan nan. Su kansu su Aliyun yasan badan Ma’un ma Jajirtacciya bace irin yaran da suke cakude dasu a makaranta da sun debi dabi’un da ba nasu ba. “Haka ne kuma, shikenan zanyi magana da Ma’un se muga yanda za’ayi”. Litinin ya koma Lagos da wannan qudurin a ransa. A daren ranar suna cin abinci bayan ya gama ya kalli Asma’u da tunda suka zauna ta kasa cin komai yace “Inason magana dake idan kun gama” ya wuce dakin sa. ASMA’U Yana tashi nima nabi bayansa gaba daya jikina baya mun dadi dan haka ina shiga na kwanta akan gado ina jiransa ya fito daga yin Brush. “Daga Next month Amirah zata fara zuwa nan”. “Wata sabuwa” na fada a raina, sena miqe zaune ina kallonsa nace “toh ni mene ne nawa a ciki idan Amirah zata zo ko a nan gidan zata sauka ne?” “Ina nufin ke zaki tafi Gombe idan zata zo, then se ku tsara yanda kuke ganin lokacin da kowacce zata ringayi a nan din”. Ya fada yana zama a gefena. Yanzu kam na gane inda ya nufa, wato tsohuwar magana ce ta taso kenan yaje ta sake masa fanfo akan tanaso ta dawo nan. Zaune na tashi na jingina bayana da Allon gadon nace “Toh Baban Ali ya zanyi da aiki na kuma? Sannan Yara suma ya za’ayi dasu?” “Maganar aiki na gaya miki zaki ajiye daman yara kuma dasu zaku tafi duk wadda take Gombe se su zauna a gurinta”. “Kan uban nan lallai ma” na fada ina kallonsa kafin naci gaba da cewa “Yanzu saboda matarka tana so ta dawo nan shine zakace na ajiye aiki na amma kasan sam wannan ba adalci bane ko?” “Ke zaki koyamun yanda zanyi adalci kenan, toh ki dauka duk yanda yayi miki amma na gama magana dole ki ajiye aikin ki Ma’u ki koma Gombe tunda haka na tsara” ya fada yana kallona. Seda na qare masa kallo dan na tabbatar da gaskiyar abinda yake fada kafin na sassauta muryata ganin dagaske neman rigima yake nace “Haba Baban Ali, ka manta wuyar dana sha kafin na samu aiki nan, mutum nawa ne suke nema Allah ya zabe ni akan su ya bani amma yanzu lokaci daya kace na ajiye. Da ace muna da Branch a Gombe da babu musu zan nemi transfer in koma can amma yanzu kawai dan kana so ka kawo wata ni kuma seka tauyeni kace na bar aiki na ai bakayi mun daidai ba. Ni bani da matsala zaka iya dawo da ita ko a cikin gidan nan ne ka bata daki amma dan Allah kabar maganar aikina ina son sa ban kuma shirya barinsa a yanzu ba”. “Shikenan tunda kina son aiki ki, seki zaba ko shi aikin ko kuma umarnina” yana fadar haka yaja bargo ya rufe har kansa nima sena fice nabar masa dakin. Sam abin ma dariya ya bani lallai akwai match me zafi a gidan nan to Allah ya bawa me rabo sa’a. Washe gari tsaf na shirya zan fita aiki, ina tsaye ina barwa Amna sallahun abinda zata girka ya fito muka kalli juna se cewa yayi “Kiyi mun tuwo da miyar Kubewa da rana za’a zo a karba” “Naman rago zaki sakawa Miyar Akwai soyayye ma a Freezer seki diba” na fada ina zuge jaka ta dan duk a zatona da Amna yake seda naji yace “Dake nake ba ita ba, daga yau ma karta sake yimun girki kuma kullum za’a ringa kaimun lunch office” yana gama fada yasa kai ya fita na bishi da saurin. Sanda na fito yana tsaye a jikin motarsa. “Ban fahimci abinda kake nufi da nayi maka lunch ba ka manta zanje aiki ne” na fada ina kallonsa, idan ya amsa ni to motar sa ma tayi magana, ya kunna mota ya bata wuta, harya taka ya leqo ta window yace “Banyarda ki dara qofar gidan nan ba” ya qarawa motarsa wuta ya barni a tsaye. Kamar mara laka haka naja qafafuna na koma cikin gidan, akan kujera na zube ina sauke numfashi, dagaske dai Bashir yake ya na so ya rabani da aikina kenan. Badan ina tsoron Allah da fita zanyi sedai duk abinda ze faru ya faru amma yau zan haqura idan yaso ya dawo naji me yake nufi dani tukunna. Anty Suhaima na kira ina kuka na shaida mata komai tunda daman da ita muka fara maganar ai, haquri ta bani tace yanzu zata kira Alhaji qarami ta gaya masa duk yanda mukayi zanji ba’a rufa awa guda ba kuwa sega kiran Alhaji Qaramin. Shima din nasiha yayi mun akan na kwantar da hankali na shedan ne kar mu bashi qofar da ze farraqamu ya tabbatar mun kuma ze kira Bashir din yayi masa magana. Ban san yaya sukayi ba dan daya dawo be kulani ba fuskar nan dai kamar ta shanu haka muka kwana kamar abokan gaba. Washe gari dan na gwada Sa’a ta na shirya kuma akayi dace tafi kuma mutu be ce dani ba hakan yayi mun dadi alamu sun nuna sunyi magana da Alhaji Qarami kenan kuma ya barni naci gaba da zuwa aiki. Haka muka cinye sati biyu cir ana wannan yanayin duk iyakar qoqari inayi gurin kyautata masa dayi masa duk abinda nasan yana so amma kallon banza ban ishi Bashir ba bare na arziqi haka idan zan kwana ina masa magana baze daga kai ya kalleni ba ko wani abin yake so sedai ya kira daya daga cikin yaran yayi masa. Abinda na lura dashi shine harda zugar mutane a cikin abun nasa kuma daman na san Bashir halinsa ne daukar shawarar wasu indai ka gaya masa abinda yayi daidai da ra’ayinsa tofa shikenan. Haka dai nake lallabawa ina taka tsantsan da duk abinda ze qara mun laifi a gurinsa ga zazzabin da yake damuna kullum qaruwa yake ga kuma sabuwar damuwar Bashir gaba daya na susuce har wata rama nayi, A bakin Aliyu naji cewar Monday zuwa Laraba su Bashir bazasu yi aiki ba an basu hutu, nan da nan nima na rubuta letter akan bani da lafiya naci sa’a akayi mun approving da wuri dan daman duk wanda ya ganni yaga mara lafiya. Nan da nan na shiga shirye shiryen yanda zamu gyarota da Bashir dan wannan zaman doya da manjan da mukeyi bayamun dadi kuma a zahiri na fishi cutuwa sedai nima qudurce a raina indai yana tunanin abinda yakeyi ne zesa na sakko na bi ra’ayin sa na ajiye aiki na na koma Gombe ya dakko wata Mata ya kawo nan to kuwa bazan chanza ba. Idan da ace wani uzuri can na daban yasa ya yanke hakan zan iya karba amma wallahi indai akan Amirah ne a wannan gabar na shirya karbar komai.🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 WATA KISHIYAR 🥰👹 (Alkhairi CE KO SHARRI) 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 Na Maryamah_MrsAM TALLAH TALLAH TALLAH "ASMA'U Baban Ali ya kirayeni da ainihin suna na wanda ko a lokacin Auransa da AMIRA da muke kan ganiyar zuba rashin Mutunchi ba haka yake kirana ba "MA'UNA" shine sunana a bakinsa kuma a gaban kowa duk kuwa da baqin miskilanci irin nasa, a gaban wanda yake matuqar kunya ne yake kirana da "HUSNA". "ASMA'U ASMA'U ASMA'U sau nawa nawa na kira sunanki".. tun be kai ga qarasa ba nace "Sau uku ENGINEER BASHIR AHMAD" dan nidin fa ba baya bace a fagen iya fitsara kawai dai shekaru suka sa na farayin sanyi amma a wannan gabar dole na fito masa a ainihin MA'U ta wadda ya sani shekaru goma sha shida da suka gabata bawai ASMA'U uwar Aliyu, Jafar, Farida, Abdallah, Ahmad da Muhammmad ba. Qara gyara tsayuwata nayi ina kallonsa ganin yanda yake bina da kallon dana tabbatar na zallar mamaki ne jin sunansa a bakina Gatsal bako Sakayawa, lallai ya manta dawa yake magana, a zatonsa nayi tibis be san haryau da saurana ba sedai baa tabo ni ba. Kansa ya girgiza yana qoqarin kokawa da hukuncin da zuciyarsa take ayyana masa, wani sashe na ingizashi akan  yayi inda dayan ke kwabarsa da nuna masa zafa ta iya kwabewa amma idan ya ja da baya ai ma zata raina shi kuma yabi abinda take so kenan. Kai ba wannan ba raini biyu ma tunda itama ma AMIRAN zata qara tabbatarwa duniya be isa da ASMA'U ba tunda gashi ya bata umarni taqi tabi. Se ya gyara tsayuwarsa tareda qara tsuke fuskarsa da dama can bata da fara'a sam, wani kallo yake jifanta dashi da yasan yana ladabtar da koma waye amma banda wannan kangararriyar Matar. Cikin kaushin murya yace "For the last time ASMA'U ina baki umarnin kiyi resigning daga aikin ki ki tattara yara ku koma Gombe d....." "Na gaya maka bazan bar aiki na na koma Gombe ba saboda zaka kawo Matarka Lagos" nayi saurin katse shi. "Se ki zaba ko auranki ko kuma aikinki" ya fada cikin sautin dake nuna zallar bacin ransa. Qara jinjina qarfin hali da rainin wayonsa nayi a raina, yau na shirya ganin qarshen rainin hankalin Bashir dan haka nace "Idan har saboda matar ka kake so nabar aikina to na zabe shi BASHIR" "Haka kika ce" "Eh" "Kije na SAKE KI SAKI DAYA idan yaso se ki zauna da aikin naki". Wani irin dum naji kunnena ya dauka, wallahi wannan kalmar itace mafi muni ji a rayuwata gaba daya, wannan rana tafi kowacce duhu a tarihin rayuwata. "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Bashir dagaske kake" na fada cikin yanayin da ni kaina bazan iya fasaltawa ba "Oh baki yarda ba? To kije na qara miki DAYA badan babu kyau ba ma sena cike miki ukun ki kinga se kiji dadin yin aikin ki dakyau" ya fada daidai sanda yake shirin ficewa daga dakin. Wani jari ne ya kwashe ni ya yar akan gadon dake bayana, Allah ne ya rufa min asiri, a yanda nake na tabbata in a qasa na fadi babu abinda ze hana barin jikina shanyewa. "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Allahumma ajirnifimusinati wa'allifni khairan minha" cikin ikon Allah kalaman da bakina ya shiga maimaitawa kenan. Duk yanda naso kwakwalwa ta tayi tunani na kasa tamkar kan saka super glue an liqeta haka naji nanda nan kaina yai dum kafin kace meye numfashina ya fara sama sama ba shiri na fara laluben inda Inhaler ta take wadda sabuwa ce na shigo daukowa dan ta cikin jakata ta qare. Seda na zuqa sosai sannan numfashina ya fara dawowa daidai amma fa kwakwalwar na nan a toshe. Kai ido na fa ya soye bama alamar Hawaye zasu fito, to kukan maganin me ma zeyi mun? Ni Ni Asma'u yau Bashir ya saka? Wallahi ko a mafarki naga Bashir ya sake ni nasan shedan ne amma gashi kamar a zahiri hakan ta faru. Ina cikin wannan yanayin naji an turo qofar dakin, nasan yarana dukka suna makarnata kuma lokacin tashinsu beyi ba. Nima rabon ganin wannan baqar rana ya saka ni daukar Excuse din rashin lafiya wai dan na huta na zauna da Habibina mu sasanta sabanin da muketa samu a dan tsakanin nan ashe ashe.... "Zaman me kikeyi? Ki tashi kisan inda dare ya miki dan gobe nake so azo a sakawa AMIRAH sabon kaya Zuwa Weekend zata dawo dan haka na baki grace of today ki hada ya naki ya naki kinga yanzu komawa Gombe dole" kalaman Bashir kenan da suka fi dafin maciji a wurina haka ya juya yabarni ni bame rai ba ni ba sumammiya ba. Dakyar na miqe na rarumi hijabi na, dole na nemi inda zan tsugunna kafin qarewar yau nida yayana. To tunda BASHIR ya iya sakina Allah na tuba watsi dani akan titi kuma ai shi yafi komai sauqi. Kofar gidan na fito ina tunanin ina zan nufa? Flat din da yake jikin namu ido na ya fada, idan ban manta ba Abokin aikin Bashir ne a ciki wanda tsautsayi ya fada masa a ka koreshi daga aiki dole ya saki gidan tunda dama Office ne suke basu dan haka yanzu babu kowa a ciki. Gidan dake kallon namu na nufa nan kuma Ogan Bashir ne a ciki da nake kira da Baba saboda sunan Mahaifina ne dashi dukda be haifeni ba amma kadan ya rage, nasan yana gida kaman yanda Bashir yake nan yau suna hutune company su dan haka na shiga danna door bell ba saurarawa. Banyi zaton nayi sallama ba lokacin da Anty Matar sa ta biyu ta budemun qofa haka na nausa kai dan fa bazan iya cewa wallahi ga abinda nakeyi ba ni kaina cikin Sa'a kuwa Baba na zaune a palour yana Kallon News na isa gabansa na durqusa. "Hajia Ma'un Bashir" haka suke tsokanata kai kowa na Estate din ma haka yake kirana kadan suka sanni da Maman Aliyu wasu Maman twins. "Meya faru" ya fada dan se sannan ya lura da yanayin fuskata. Banyi kuka ba amma kallo daya zakamun ka hango zallar tashin hankalin da nake ciki se kawai na tsinci kaina da cewa "Baba Flat din Maman Boda zakamun hanya a bani haya na shiga yau dan Allah". "Bangane ba? Me ya samu gidan naku? Ina Bashir din?" Duk ya jero mun wadan nan tambayoyi da daya kadai nake jin zan iya amsawa dan haka na bude baki dakyar nace masa "Baba BASHIR ya SA KE NI SAKI BIYU kuma yace na tattara kayana a yau nabar masa gida kafin ya dawo" na qarasa ina Rushewa da kukan da se yanzu na samu damar yinsa. Kuka nake tamkar raina ze fita inda Baba da Anty keta faman zabga salati suna qarwa. "Asma'u ya sake ki fa kika ce? Me kikayi masa har haka??" Wace ce ASMA'U? Wanene BASHIR? Me ASMA'U tayiwa BASHIR da har ta cancanci wannan hukunci haka??? Amsar ku tana cikin Sabon littafi na Me suna WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI) Wannan salon na daban ne na kuma tabbatar muku bazan baku kunya ba kuma ina fatan kar ku bani kunya. I to tell 10 10 to tell Ozers 🤣🤣 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 WATA KISHIYAR 🥰👹 (ALKAHIRI CE KO SHARRI) 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 Na Maryamah Farouk (Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah) Wattpad @MaryamahMrsAm Page 32 Tareda Anty muka koma, Bashir na zaune a palour muka wuce dakina. Wayata dana gani ta tunamun da gida, wazan kira na gayawa wannan mummunan labarin?? “Alhaji Qarami” zuciyata ta raya mun, nan da nan na danna masa kira cikin sa’a ringing biyu ya daga yana cewa “wato a kwanakin nan dai Ma’u tana yi dani irin wannan kira akai akai haka”. Kuka na fashe masa dashi sosai ya shiga tambayata ya akayi, dakyar na iya tsagaitawa na gaya masa cewa Bashir ya sake ni. Seda yayi salati ya sanar da ubangiji kafin yayi shiru na wani lokaci yace “Ma’u kowa da kalar qaddarar sa a rayuwa kiyi haquri ki dauka jarabawa ce daga ubangiji idan kika jure se ki samu saka mako me kyau. Yanzu kina ina?” Alhaji Qarami ya fada cikin jimami, seda Naja sheshsheqa kafin nace “Yace ya bani iya yau na kwashe kayana na bar masa gidan sa Yaya yanzu ina gidan kayan nake hadawa”. “Shike nan, ki hada iya abinda ya samu, bari na kira Abubakar dan yace mun yau ze shigo nan din idan yaso ko hotel ne se ku zauna kafin gobe a duba miki gida zuwa muga yanda hali ze yi, ki dena kuka sannan karki kira kowa a gida ki gaya masa kinji ko”. “Toh Yaya Nagode Allah ya saka da Alkahiri “ na fada kafin mukayi Sallama naci gaba da taya Anty hada kayan dan tuni ta sauke kayan wardrobe dina tsaf tana ta durasu a akwatuna. Seda muka kwashe komai dan seda muka Hada da manyan Jakunkunan Bakko da muke zubo abubuwa daga Gombe daman in na cire kayan ciki sena ninkesu na ajiye da rabon zasu min rana ashe. Har kayana na dakin Bashir seda ta kwaso komai bayan da tayi masa watsa watsa da nasa a qasa. Da muka gama da nawa kayan dakin yaran muka koma, lokacin Bashir ya bar gidan suma muka shiga hada musu kaya kowa a akwati kafin wani lokaci mun gama Anty ta fita ta samo samari suka ringa dauka suna kaiwa gidanta. Mun fito da akwatin qarshe kenan Yaya Abubakar ya tsaya da motarsa a qofar gidan, rabon da yazo tunda Bashir ya auri Amirah suka samu sabani sedai mu hadu dashi a gida idan naje Gombe ko muyi waya. Kai tsaye na fada jikinsa na fashe da kukan dana samu dakyar ya tsaya mun dazu yana bubbuga baya na yace “kiyi shiru Ma’ulle abinda yake so kenan yaga gazawarki bayan shi yayi asara bake ba”. Tare dashi muka shiga gidan Antyn muka tarar da Baba ya dawo, cikin mutun taka suka gaisa Baba ya shiga bashi haquri akan abinda ya faru kamar shi yayi laifin sannan ya gaya mana ya samu approval an bani gidan kuma harda 50% discount akan kudin hayar ma suka bayar kuma ya biya yanzu ze kira kamfani masu wankin gida suzo su gyara yanzu se muje mu ga gurin ga Key nan an bashi. A tare muka fita gaba daya, gidan lafiyar sa qalau dan daman ba’a dade da renovating nasa ba qura kawai yayi se yana saboda babu mutane a ciki, muna tsaye ma sega kamfanin daya kira sunzo da kayan aiki cikin qasa da awa daya suka wanke gidan tas har bangwaye seda suka wanke ko ina ya dauki kyalli. Bansani ba Ashe tunda muka shiga Yaya Abubakar ya kira Alhaji Qarami ya gaya masa maganar gidan, se ganin motar kayan furnitures nayi sunzo da saitin gado da kujera harda labulaye da carpet kamar wasu kayan Amarya nan da nan suka shiga daurawa. Muna fito wajen gidan motar makaranta ta sauke su Aliyu, da mamaki suka tsaya suna kallon gidan Farida tace “Mami gida zamu chanza naga ana saka sabon kaya a nan” Gaba daya kasa kallonsu nayi dan ji nayi wata sabuwar karaya tana zuwar mun, yaya zasu ji idan suka gane mun rabu da mahaifinsu? Fitowar da Yaya Abubakar yayi daga cikin gidan ta ceceni daga tambayoyinsu suka nufeshi da murna nan take na sulale na shige gidan Anty ban san Aliyu yana baya na ba seda naji ya ruqo hannuna yana cewa “Mami meya faru, kukan me kikeyi?” Aliyu ya wuce shekarun da zance zanyi masa wayo, kai tsaye ina hawaye nace masa “Aliyu mun rabu da Abbinku, kuje ku duba idan akwai sauran abinda ban dauko muku ba a dakin ku wan can gidan zamu koma”. Gaba daya se yaron ya kasa magana ya tsaya yana kallona, a sanyaye ya saki hannuna ya juya ya fita daidai sanda Itama Aman ta shigo ina jinsa yace mata suje waje na raka su da ido har suka fice daga gidan. Rayuwa kenan, dan Adam yana tafe besan abinda ze same shi a mintunan da suke gabansa ba, dazu da safe na tashi da yaqinin gyaruwar Al’amura a tsakanina da Bashir, ga labarin abin farin cikin daya same mu bansan mummunar qaddara na tafe tana shirin shafe duk wani farin ciki da nake shiryawa ba. Shafa cikina nayi, Allah sarki shi kuma tasa qaddarar kenan baze tashi a tsakanin iyayensa ba. Da taimakon yaran kafin sallar Magriba mun shirya gidan nan tsaf yayin da muka yiwa gidan Bashir qat dan kaida fata Anty ta kafe sena dauke duk abinda yake nawa ne a cikin gidan nan haka kuwa akayi yara suka ringa jidar kaya qananan se murna suke wai mun chanza gida. kayan Kitchen dina tsaf Gas da qaramar Freezer da muke zuba nama kadai aka bari dan sune nasa babbar me qofa Biyu Yaya Muslim ne ya bani ita da suka tashi daga gidan su na Lagos ya koma Rivers, haka kayan amfani ko ko cokaci Anty bata bari ba harda su spices seda ta tattare. Haka palour Kujeru da Da Tv se Dining kadai ya tsira dasu sefa gadon dakinsa dan na dakina ma da kudina na siya, wanda ya saka mun shi na cire na sakawa Farida da Amna a dakinsu dan haka masu daurin Gado na gama hada sabon Anty tasa suka hau kwanto nawa tace ko baze hadu a yau ha su kwance a ajiye gobe su dawo su hada. Har bayan Isha muna jigilar kaya daga tsohon gida zuwa sabo, mungama tattaro komai wanda ze saku a lokacin muka saka ragowar muka barwa gobe idan Allah ya kaimu se a qarasa. Na fito raka Yaya Abubakar ze tafi masaukinsa daidai lokacin Bashir ya dawo, tundaga waje ya fahimci aika aikar da akayiwa gidan dan ga winduna nan hanhai babu labule ana hango ciki, a sukwane ya shiga gidan, kai tsaye dakin yaran ya leqa ya kuwa yi sa’a se katakwayen gadajen su ya tarar dan mun kwashe katifun saboda bacci a zuwan gobe suma se a dakko su. Cikin tsananin Bala’i kamar zeyi aman wuta ya tunkaro inda muke “Ke kadai nace ki tafi bance ki daukar mun yaro ko daya ba” ya fada yana kallona. Seda na watsa masa wani banzan kallo kafin nace “Wannan ne kuma kayi kadan Wallahi Bashir, saki dai na saku kuma kamar yanda kace na barmaka gida kafin gobe gashi nan ka gani Allah be hanani inda zan zauna ba amma maganar yara baka isa in bar maka yarana a hannunka ba”. Sosai rigima ta barke tsakanin mu shi yana rantsuwar sena bashi yaransa ni ma ina ta bazan bayar ba, Yaya Abubakar ne ya katse mu da cewa “Ya ishe ku haka, wane irin shirme ne zaku zo kuna neman tarawa kanku mutane a titi ga yara duk suna kallon ku akan abinda be wuce ku zauna ku sasanta ba. Ki shiga Gida Ma’u zamuyi magana” Sena juya ina cewa “ka gaya masa bazan bayar ba idan ya takura kuma seadi kotu ta raba mu” nayi shige wata gida. A waje kuwa Asma’u na wuce kafin ma Abubakar ya fara magana Bashir din ya katse shi da cewa “Ka gani cikin lallama ka gaya mata ta bani yarana dan wallahi bazan bar mata su ba ballantana ta koya musu dabi’ar raini da kafiya irin tata”. Seda Abubakar ya qare masa kallo kafin yaja qwafa, ba qaramin danne zuciyarsa yayi ba yace “Naji, zata baka amma kayi haquri kabarsu yau. Nayi maka Alqawari gobe za’a baka yayan ka”. Shiru Bashir yayi kamar me tunani se yace “Shikenan, Amma wallahi goben idan ba’a bani ba se anyi tashin hankali” “Babu da wanda zakayi tashin hankali Bashir dan babu wanda yake da lokacin ka, kuma kayi a hankali idan ba haka ba seka rufta kanka a inda duk ihun ka bazaka iya fitowa ba” yana gama fada masa haka ya shige motarsa ya bar Bashir da cizon yatsa. BASHIR Ko kusa beyi nadamar abinda ya aikata ba dan a ganinsa yayi irin abin nan na ya tauna tsakuwa dan Aya taji tsoro. A tunaninsa dole Asma’u zata bishi ta roqe shi ya maida ita dakinta, shi kuma ya qudurce se ya gama wanata son ransa tukunna ta gane muhimmancin sa sannan se ya mayar da ita. A lokacin yasan ta biyu ta yanda ko kara ya ajiye mata bazata tsallake ba. Be damu da kwashe kayan ma da tayi ba, sema guri daya samu a palour ya dora kafa daya kan daya, a cikin kudin da yayi niyyar biya musu umara shida itan ya yi order sabon gadon da za’a saka a dakin da ta cire nata da kuma labulaye kai kujerun ma chanza su ze kawai idan yaso kayan Kitchen in Amirah tazo se ta siyo da kanta tunda shi be san abinda ake buqata ba. Koda ya shiga dakinsa ma yaga kaya a watse be wani damu ba yasan duk cikin haushin sakin ne yasa tayi haka, se kawai ya tattare ya watsa su kan gado yayi shigewarsa Toilet yayi wanka kafin yayi shirin bacci ya zauna akan kujera da wayarsa a hannu. Cikin sa da yayi qara ne ya tuna masa da yau fa be ci komai ba, se ya miqe ya fito palour kai tsaye ya wuce gurin Dining sedai kafin ma ya qarasa ya hango shi wayam daga teburi se kujeru, yar Show gilas din kwanukan da ta qawata gurin ma an dauke bare yasa ran samun wani guntun abinci. Dolensa ya sake fita ya siyo abincin a waje a ransa yana cewa “Dole yarinyar nan ta dawo a satin nan dan bazan iya sintirin zuwa siyen abinci ba, yana gama ci ya ahige daki yayi kwanciyarsa abinsa. ASMA’U Qarfe 11 na dare ina zaune akan abin sallah tun bayan da nayi sallar Isha ban tashi ba, gaba daya hankali na yayi nisa da inda nake na yi nutso a cikin kogin tunanin abubuwan da suka faru dani tun daga haduwata da Bashir har zuwa yau daya yanke alaqar da take tsakanin mu. Tiryen tiryen komai ya ringa dawo mun lokutan da suka kasan ce masu dadi a cikin rayuwar mu da wadanda suke aka sin haka, haduwar mu ta farko da Bashir wadda har muka qulla soyayya a tsakanin mu nake tunawa. ASMA’U ABDULLAHI TUKUR shine cikakken sunana. Baffan mu Alhaji Abdullahi haifaffen Kumo ne ta Jahar Gombe. Yana da matan aure guda hudu Hajia Babba da Hajia Umma rana daya aka saka musu lalle se Hajia Anjim kafin ya auro Goggon mu Maryam daga qarshe. Ita Goggon mu yar Asalin Numan ce kuma Babanta shine limamin garin a lokacin. A yanda aka gaya mana asali ba Baffan mu Goggon zata aura ba, Baffa Sama’ila Amininsa ne saurayinta wanda har an saka musu rana cikin tsautsayi a ranar da za’a daura auran ya gamu da mummunan hatsari akan hanyar su ta zuwa Numan daga Yola wanda yayi sanadiyyar tabuwar lakar bayansa dalilin da yake kwance kenan har yau yana jinya. A lokacin su Baffan mu sun riga su isa garin, bayan da aka samu wannan mummunan labari hankalin kowa ya tashi har aka watse daga taron daurin aure seda Baffa Sama’ila ya bar wasiyyar akan Baffan mu ya auri Maryam dan beyi zaton ze tashi ba, haka kuwa akayi se kawai gani sauran matansa sukayi yazo da Maryam da suka je bikin Amininsa a matsayin kishiyarsu babu kuma wata jayayya ko tashin hankali suka karbeta tamkar yar uwa. Zaman gidan mu zama ne me tsafta tsakanin matan guda hudu wanda suke kishi gurin kyautatawa mijinsu da qoqarin ganin ko wacce ta zama ta gaban go shi bata hanyar cutar da yar uwarta ko tashin hankali ba. Allah ya azurta Alhaji Abdullahi ta kowanne bangare domin ya masa arziqin Dukiya, mata da kuma Yaya saboda seda ya haifi Yara 42 inda biyu suka mutu tun kafin a haife ni yanzu haka mu 40 cif muna raye Maza 24 mata 16. Mu 8 ne a dakin mu, maza uku mata biyar. Zan iya cewa kusan nice mafi soyuwar ya a gurin mahaifina kodan ina da sunan mahaifiyar sane amma dai kowa ya shaida nidin yar gata ce ta gaske, Baffan mu yayi matuqar qoqari gurin bamu tarbiyya tareda hada kanmu dan bamu san wani abu wai shi yan ubanci a gidan mu ba mun tashi tamkar tsintsiya baka taba banbance yan wannan daki dan kowa inda yake so yake warkajamin sa. Dukda kasancewar Baffa beyi boko ba amma yayansa ya bamu damar yin ilimi iya yanda kaso kuma mata da mazan mu, baya tsawwalawa, dukda anayiwa mata auran wuri a lokacin sam shi babu ruwansa idan yayyen mu mata sun gama secondary school yana basu zabin aure ko makaranta wanda kika dauka shi zakiyi dan tun duniya na kwance Baffa yake fitar da yayansa mata qasashen waje suyi karatu, idan ma kuma kina karatun kika fitar da miji dukka ze miki auranki. Nice ya ta Ashirin da bakwai a gidan mu, Ma’u kwalisa shine laqabin da akeyi mun a makaranta saboda yanda Allah yayi ni dason gayu abin ya hade mun da irin qirar halittar da nake da ita dan haka nake bawa gayu haqqinsa yanda ya kamata. Tun muna SS1 na qudurce a raina nifa dana gama secondary aure zanyi duk kuwa da yanda nake da qoqari sosai a makaranta nidai kawai aure nake so abinda ze baku dariya shine ko saurayin bani dashi dan bana kulasu, ni a lokacin ma duk wanda yace yana sona tofa ya zama abokin gaba ta har tsokanata yan gidan mu sukeyi indai kana so muyi rigima dakai to ka nuna wani kace saurayi nane. Ranar da muka fara haduwa da Bashir wata rana ce mun taso daga islamiyya da yamma, muna hanya wani da Ake kira Ibbah saurayine dan layin mu daya nace shi ala dole sona yake yi mun taho a hanya kawai ya tare mu. Ibbah girman Ingila ne acan aka haife su dan basufi shekara biyar da dawowa Nigeria ba dan haka gaba daya dabi’unsa na turawa ne abinda yasa nake qara tsanarsa kenan muna tafe muna hirar mu se ganin sa kawai mukayi a gaban mu ya kalleni yana murmushi yace “Hey pretty yau na kamaki bazaki gudu ba, tsaki nayi masa na murguda baki kafin na kauce ina cewa “Aikin banza mutum kamar maye yayi ta bin mutane, se kayi tayi ai dan wahala” nayi gaba abina se ji nayi caraf ya riqomun hannu banyi wata wata ba kuwa na kwashe shi da mari kafin na hau zazzaga masa tsiwa ina zaginsa. Tahowar da Yaya Abubakar din gidan mu da Abokanan sa uku yasa na dakata ina hararar Ibbah dayayi mutuwar tsaye yana kallona, Yayan ne ya tambayi meya faru Alawiyya tayi caraf tace masa “Ma’uce ta Mari Ibbah saurayinta” tun kafin ta gama na juya kanta da masifa ina cewa “Ta ina ya zama saurayina wallahi karki sake hadani dashi niba saurayina bane” kawai na saka kuka kawai se suka samun dariya dan yanda nayi abun seka rantse wani mugun abu aka jinginani dashi. Daya daga cikin Abokan Yaya Abubakar wanda ban sanshi ba, cikin taushin murya yace mun “waya gaya miki mekyau tana yin kuka rabu dasu ba saurayin ki bane ki share hawayenki”. Haka kawai naji ya burgeni, na saka hannuna na goge fuskata tsaf kuwa fuu nayi gaba na barsu suna ci gaba da yi mun dariyar ina jin Yaya Abubakar na bawa Ibban haquri kafin ya taso su Alawiyya a gaba suka biyo bayana. “Ma’u danja Ma’u rigima daga ance mutum saurayinki kawai ki kama kuka ke wai baki san kin girma ba” Bala daya daga cikin Abokan nasu ya shiga taokana tun kafin ma na bude baki Yaya Aliyu da duk yafi sauran abokan su kirki ya tareshi da cewa “Zaka fara ko Bala, Ma’u kyaleshi yi shigewar ki gida” seda n harari Bala na murguda masa baki kafin na shige dan sam bana son Balan nan saboda yana shan Taba nasha ganinsa yanayi ni ban ma san me yasa su Yaya suke kula shi ba. Da Daddare muna zaune a palour Baffa muna hira yanda muka saba nake bashi labarin abun da ya faru “Wani sabon abokin Yaya Abubakar ne yace na dena kuka amma su da duk se dariya ma sukeyi mun” na fada cikin shagwabar da idan ina gaban Baffana jina nakeyi kamar wata yar jaririya zuba tabara nake son raina idan akayi sa’a Goggo na kusa ta make ni. “Banda dai tsiwa irin ta Mamana ya zaki mari mutum kawai dan yace yana sonki, ki kiyaye kar a sake kuma gobe kuje har gida dasu Alawiyya ki bawa Ibrahim din haquri kinji ko” Baffan ya fada. Sena marairai ce nace “toh Baffa bazan kuma ba. Washe Gari Alhamis kuwa bayan mun taso boko da yamma babu Islamiyya mukaje har gidan su Ibbah na bashi haquri, da yake yana da sauqin kai yace shi harya manta ma Maman sa se nan nan take dani wai yarinya me kyau da hausarta wata iri ta hado mana kayan dadi muka tafi muna gulmarta wai su a dole turawa. Muna zuwa qofar gidan mu muka ci karo dasu Yaya Abubakar yau ma su na zaune, gaishe mukayi ina ta satar kallon na jiyan nan daya maida hankali yana danna waya so nake naga ko zeyi mun magana amma har muka shige gida be ko dago ya kalle mu ba. Baki na tunzura nayi wucewata dakinmu, inajin su Alawa suna cewa nazo mu raba kayan da Maman au Ibbah ta bamu nace bana ci nayi kwanciyata ina jin haushin da ban san koma mene ne ba. Da daddare Yaya Abu yace na dafa musu Indomie, ina gamawa na juye a flask na bawa Khadija ta kai musu ina zaune a palour Hajia Umma se gata wai naje inji Yayan yana kirana. Suna zaune a tsakar gida daga gefen inda akayi kujeru na sumunti da tebura, su hudun dai kamar kullum ga kular Indomin a tsakiya an cinye tas Yaya Aliyu ya kalleni yana cewa “wai Bashir ne yace ne yadda ke kikayi girkin nan ba shine muka kiraki ki gaya masa da kanki” “Wai daman Yaya Bashir kaine” na fada da mamaki ina kallon wanda aka kira da Bashir din. Se yanzu kuma nagane fuskarsa Bashir din gidan Baba me Mota ne, rabon dana ganshi har na manta tunda su ka fara zuwa Jami’a shi aka ce A Zaria ban sake ganinsa ba kusan shekara shida yanzu. “Daman Fainusa tace Yayansu ya zama dan gayu ashe dagaske take “na fada ina zama a gefen Yaya Abubakar, se Bashir ya dago ya kalle ni yana murmushi yace “dagaske? Har nakai ki gayu?” Rufe fuska nayi da mayafina irin naji kunyar nan, sosai na ringayi masa tambayoyi meyasa na dena ganinsa yace makaranta ce tasa saboda nisa baya zuwa gida se qarshen shekara, duk sanda yake zuwa mu kuma bama nan munyi tafiya. Haka na shantake seda Goggo ta aiko kirana sannan na tafi. Tundaga wannan ranar kullum da daddare idan na dafa musu indomi zanje na zauna ina taya su hira kuma duk saboda Bashir dan haka kawai nake jin ina son yin magana dashi, haka ko a cikin gida banida labari se na Bashir yayi Bashir yace kaza ana haka muka fara shirin qualifying exam daga ita zamu shiga SS3. Bashir ne yake tayani karatu yana ganar dani inda ya shige mun duhu, wannan kusancin da muka qara samu ya saka Shaquwa sosai ta shiga tsakaninmu dan idan na wuni ban ganshi ha har ji nakeyi kamar bani da lafiya gashi lokacin sun fara Service dan ma anan Gombe yakeyin nasa. Banfarga cewa nayi nisa a soyayyar Bashir ba saboda ban ma san menene so ba, abu daya dana yarda Ya zama wani bangare na jikina haka ina bala’in jin haushin na ganshi yana magana da wata mace ranar haka zan wuni ina qunci. Yaya Bilkisu ce ta fara haska mun cewa son Bashir nakeyi, nayi futu futu nace qaryane ni ba wani so kawai dai Allah ne ya hada jinin mu amma a qasan raina ina jin dama hakan ta kasance yace yana sona dana ji dadina kuwa. Mun shiga SS3 kamar anyiwa Samari bushara da zuwa gurina sukayi mun caaa saboda yanda kyau da surata suka sake bayyana sosai, ban kuma canza hali ba ina nan ina tatawa duk wanda yace yana sona rashin mutunchi a qasan raina kuma ina cike da damuwa da takaicin me yasa shi Yaya Bashir baze ce yana sona ba se wannan banzan Balan ne ranar ya wani ce wai yana so na se kace nayi masa kalar budurwar yan shaye shaye. Muna second term aka fara Registration na Jamb, duk su Alawiyya sunyi ni kuwa ranar da za’a kaisu siyi qin zuwa nayi nace banida lafiya, washe gari da yamma Su Yaya sun shigo gida ake hirar, Ina ji Bashir na tambayar kowa course din daya cike nayi banza dasu sanda yazo kaina har seda Junaidiyya ta tabo ni sena tura baki nace “Ni ba zanyi ba”. Kafe ni yayi da idanunsa masu sakani a wani irin yanayi da bansan na menene ba yace “Me yasa bazakiyi ba?” “Haka kawai” na fada ba tareda na kalleshi ba, se ya miqe yace na biyo shi muka fita can tsakar gida inda muke zama muna hira. Idonsa akaina na sunkuyar da kai ina wasa da yatsun hannuna yace mun “me yasa bazakiyi Jamb ba” “Ni babu komai kawai bana so nayi” na fada ba tareda na kalle shi ba. “Toh aure kike so kenan?” Sena dago da sauri na kalleshi, ganin ni yake kallo se na sauke idona ina tura baki nace “Ni ban ce haka ba”. “Toh idan ba aure kike so ba me yasa bazaki ci gaba da karatu ba bayan ma ko saurayin baki dashi wa zaki aura ma”. Harara qasan ido nayi masa kafin nace “Allah ze kawo ne Idan lokacin yayi” “Idan kuma yanzu ya kawo fa” ya fada cikin qasa da murya, se na daga kai na kalleshi. “Allah kasa yace yana sona” na fada a raina tamkar kuwa Bashir yaji ni se ji nayi yace “Idan kuma ni ne mijin naki fa Ma’una zaki aure ni?” Abunku da ba kwaila tsabar murna se kawai na tashi nabar gurin da gudu ina dariya ina jinsa shima yana mun dariya abinda ba kasafai ya fiya yi ba. Kan gado na na hau na ringa tsalle ina ihun murna, Yaya Fati Dake kwance akan Nata gadon ban sani ba ta tashi ta rufeni da fadan wane irin shirme ne zanzo ina wa mutane tsalle a gado kamar wata yarinya. Sena fada kanta ina cewa “Tsallen murna ne Yah Fati ki barni nayi”. “Murnar me kikeyi” ta tambayeni bayan data daga ni daga jikinta. “Bazaki gane ba Yah Fati kawai kedai se lokaci yayi” tashi nayi na shige Toilet nayo alwala, inajinta tana cewa Allah ya shirye ni nidai na tayar na ringa jero sallolin godiya ga Allah daya sa Bashir yace yana sona. Washe gari dakansa ya tasani a gaba mukaje nayi register Jamb, Law na ciki muka gama komai muka koma gida. A hankali soyayyar mu ta bayyan kusan kowa yasan abinda yake tsakanina da Bashir. Da yawa gani sukeyi kawai shirme nane haka shima a bangaren Bashir lokacin daya gayawa Aliyu halin da muke ciki se yace masa “Anya Bashir kana ganin abin nan me yuwuwane?” “Me yasa kace haka Aliyu” Bashir din ya tambaye shi, se ya ci gaba da cewa “Kawai gani nayi kamar akwai tazara me yawa tsakanin mu dasu, ka ture abotar mu da Abubakar wannan ba wani abu bane amma ka fahimceni da wuya kaga mace ta fito daga gidan Attajiri ta auri na qasa da ita sedai shi namiji me kudi ya auri diyar talaka, sannan idan ka dubi irin mazajen da yaran gidan su suke auri babu qaramin mutum a ciki ita kanta Ma’u a kalar da Allah yayi mata Bashir ko a gidan talauci ta fito ba matar qaramin mutum me fafutukar neman abinda ze rufawa kansa asiri irin mu bace ba”. Shiru Bashir yayi dan tabbas Aliyun yayi gaskiya. Shidin ba dan kowa bane Babansa me rufin asiri ne kawai Ma’aikacin gwamnati me da yake dab dayin ritaya kuma ba wani babbaba kusan yanzu shi ake saka ran ya zama jigo a cikin gidan su tunda shine Namiji Babba yayar sa daya da qanne biyar, a yanzu ne ma ya gama makaranta yake bautar qasa kafin ya fara fafutukar neman aikin yi kuma. Amma tabbas yana son Asma’u kuma itama ya yarda tana sonsa ba kuma ya fatan ace ya rasa ta. “Haka ne Aliyu, ka taya ni da Addu’a Allah ya zaba mana abinda yafi Alkahiri toh” “In sha Allahu, Allah ya sadamu da akhairan mu” Aliyun ya fada. Wannan maganar da sukayi da Aliyu seta sa ya dan fara ja baya da Ma’u musamman yanda a yanzu kullum yaje gidan ze tarar da zaratan samari yayan masu qunbar susa a manyan motoci sunzo gurin Ma’un duk da bata fitowa amma hakan se yake ganin kamar wata rana zata iya chanza ra’ayi ta zabi wani daya fishi dan haka se yayi baya da zuwa gidan. Da yake itama suna shirin fara SSCE se bata damu ba dukda indai sun hadu se tayi masa qorafin me yasa yanzu baya zuwa gidan sosai se yace mata aiki ne ya masa yawa dan yanzu ya samu temporary aiki a wani company yana zuwa. Cikin dan lokaci su Ma’u suka gama Jarabawar su, kamar kuma yanda Alhaji ya saba a shekarar ya kaisu gaba daya suka sauke Farali tafiyar da sukayi kusan rabi da kwatan tsarabar da tayiwo ta Bashir ce harda yan gidansu. Randa suka dawo bata jira yazo ba ta hada akwati guda ta kai masa har gida tayi sa’a ta same su gaba daya yan gidan suna nan harda Alhajinsu dan haka bata zauna ba suna gaisawa ta tafi. Bayan tafiyarta Su Fainusa suka bude akwatin suna zaro kayan ciki, sosai mamaki ya kama su ganin uban tsarabar se Dada ta kasa haquri tana kallonsa tace “Bashir ni meke tsakanin ka da yarinyar nan haka irin wannan uwar tsaraba data kawo mana?” Fainusa ce tayi caraf tace “Dada soyayya sukeyi, ina jin a Islamiyya ma Ma’un Bashir ake ce mata”. Se Bashir ya harareta yace “ke waya tambaye ki? Tashi a nan kona mammake ki”. “Ikon Allah, Anya bata fi qarfinka ba Bashir kaida zaka dauko daidai” “Daman mace tana fin qarfin namiji ne Nafi?” Alhaji Amadu ya katseta, seta girgiza kai tace “Gani nayi Alhaji idan ka kallemu ka duba gidan data fito kar ace son zuciya ne yasa ya nemi auranta”. “To ai Annabi ma yace ana auran mace dan Asali da kuma dukiyarta kinga in hakan yayi ma ba laifi bane ballantana nasan ma ba hakan bane, idan matarsa cea se kiga Allah ya qulla abun, kiyi masa fatan Alkahiri kawai” cewar Alhaji Amadu. “Hakane Allah ya tabbatar da Alkahiri toh ai Asma’u yarinyar kirki ce”. Daga haka suka ci gana da hirarrakin su. 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 WATA KISHIYAR 🥰👹 (ALKAHIRI CE KO SHARRI) 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 Na Maryamah Farouk (Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah) Wattpad @MaryamahMrsAm Page 35 ASMA’U Muna cikin wata takwas da aure me kamfanin da Bashir yake aiki ya rasu dan haka akayi rabon gado yayansa suka saka kamfanin a kasuwa abinda ya tilasta wa ma’aikata barin aikinsu. Wannan dalili yasaka Bashir dawowa zaman gida a koda yaushe saboda har sannan babu wani aiki daya samu ya dai rarraba CV amma babu inda aka kirashi. Da farko abin yazo mana da sauqi saboda Alhamdulillah kusan komai na buqata muna dashi a gida dan abinda ba’a rasa ba muke siya irin su kayan miya ko ganye da dai sauran masarrafi dan haka idan na fita makaranta se nayi amfani da kudaden da suke hannuna na siyo mana komai yanda zamu dan kwana biyu tunda kudi basa yanke mun. Duk sati Baffa yake bani kudin makaranta dan shi yake dauke da nauyin karatuna ga kuma na man mota da ake hadamun dashi yanzu. Ta inda matsala ta dan bullo mana rashin lafiyar da Baban su Bashir ya fara, bayan kaishi Asibiti suka tabbatar da cewa yana da Suga da hawan jini ne suka taso masa lokaci daya seda yaci kudi sosai kafin lafiyarsa ta samu sannan aka dorashi akan magani abinda ya turgude dan jarin kasuwancin da yake yi kenan dan da kudin akayi duk hidimar Asibitin sa. Ganin da nayi rayuwa ta fara yi musu matsi, kuma Baban da yake fita ya nema musu na cefane gashi a gida babu wadatacciyar lafiya. Bashir baya aiki a yanzu Amiru yana shekarar qarshe a Jami’a, Afiya tana Level 1 se Fainusa da Sadiya da suke secondary daga Sa’ad,Samirah har Naziru lokacin a primary suke. Akwai ranar da mukaje duba Baban da da yamma, abinda ya daga mun hankali muna zuwa na tarar da Dada tana yi musu kwadon garin kwaki harda Baban da yake fama da Siga a sannan shi aka zuba masa yaci. Abun ya bala’in daga mun hankali. Bayan mun koma gida washe gari banyi shawara da Bashir ba na dauki Buhun shinkafa biyu, taliya, macaroni, semovita komai biyu ga pastar mai hatta Maggi seda na diba na hada sannan na tsaya a hanya na siyi kayan Shayi da kayan miya na tafi gidan. Yara na samu a qofar gidan suka shigar da kayan, motar Aliyu dana gani ya tabbatar mun da Bashir yana gidan dan daman tun safe yau ya fita dan haka ban shiga ba kawai na wuce gidan mu. A can na tarar da Junaidiyya wai ta zo gida haihuwa ga Yah Bilki ma tazo da tsohon cikinta haka Yah Fati Alawiyya ce dai nata be isa haihuwa ba ni se a sannan ma tunani na ya tafi ga rashin samun cikin da banyi ba. Dukda ina son yara amma hakan besa na taba damun kaina da sena samu ciki dole dole ba kuma shima Bashir ko sau daya be taba mun maganar ko nuna wani abu akan hakan ba gaba daya mun barwa Allah shi ke bayarwa idan lokaci yayi nasan zamu samu namu muna. A gidan na wuni har dare dan ina son naga Baffa, se bayan Isha ya shigo gida ashe Yola yaje daurin auren Yar Baffa Sama’ila. “Mamana ya akayi ne har yanzu baki tafi gida ba” ya fada bayan dana gaishe shi, sena marairaice fuska nace “Baffa Kasan Alhajin su Bashir bashida lafiya ko” “Na sani wallahi ai na dubashi ma sanda yana Asibiti sannan bayan sun dawo ma na sake leqa gidan, ciwo ne babu dadi yanzu kuma abinda ake ta fama dashi kenan wannan Siga Allah ya tsare mu dai”. “Amin Baffa, daman wata Alfarma nake nema idan babu damuwa” na fada ina gyara zamana. Se ya kalleni yace “Gidan ku Ma’u ni zaki kalla kice kina neman Alfarma a gurina, idan banyi muku abu ba wa kuke dashi a fadin duniyar nan daya fini? Kar na sake jin haka, ki tambayeni kai tsaye abinda kike so ko menene shi a duniyar nan zanyi miki dan duk abinda na mallaka domin na inganta rayuwar ku ne” Baffa ya fada cikin dakewa alamar babu wasa a maganar sa. Sena saki murmushi. So da qaunar Baffan nawa tana qara ratsani nace “Wallahi Baffa gani nayi gaba daya rashin lafiyar nan ta saka sun shiga wani hali, kaga yanzu baya iya fita kasuwa ga Bashir kuma aikin da yakeyi ma an siyar da kamfanin shine nace ban sani ba ko akwai abinda zaka iya yi akai”. “Ash sha yanzu shi Bashir din baya aiki kenan, kinga ko jiya seda mukayi maganar da Muhammadu (Alhaji Qarami) yace mun yana iyakar qoqarinsa akan maganar aikin, kinsan qasar tamu ne yanzu da lamarin aiki ko kana da hanya fa idan wanda yafi ka yazo se kiga an samu tangarda. Sannan yace daman su masu kwalin Irin nasa me martaba ta daya (first class) suna wahalar samun aiki a ma’aikatun mu na cikin qasa saboda yawanci manyan gurin suna ganin kamar in suka dauke su zasu fisu sedai a ma’aikatu mallakin qasashen waje su daman sunfi buqatar irinsu din ze ci gaba da bada takaddun in Allah yaso za’a dace. Shiyasa ni nafi ganewa kasuwanci amma ku yaran yanzu gaba daya kun ta’allaqa akan aikin gwamnatin nan da gaba daya abinda kuke samu a wata se kiga Dan kasuwa ya same shi a sati daya wani ma cikin yini, yanzu dai ki turomun shi, idab yana da sha’awa yazo kasuwa idan Allah yasa yana da nasibi a ciki se ki gani. Maganar Alhaji Amadu kuma zan duba abinda za’ayi, kama daga kan rashin lafiyar tasa har zuwa matsalar iyalin se muga abinda Allah zeyi”. Sosai na ringa zubawa Baffa Godiya da Addu’oin fatan Alkahiri, har na tashi zan tafi ya tsaidani da cewa “Yawwa na tuna kuwa Jiya Manager Bankin da nake ajiya munyi magana naji yace zasu dauki Ma’aikata, shi bangaren nasa ze iya aiki a banki ne?” Cikin farin ciki na koma ina cewa “Eh Baffa, shi aikin banki indai ka iya kwanfuta da kana da lissafi a takardun ka zasu dauke ka, kuma duk yana dasu” “Toh bari na kirashi yanzu naji idan da hali se ya fara wannan din kafin sanda Allah ze kawo wani”. Ina tsaye ya kira Manager ya kuma amsa tareda cewa ze turowa Baffan Email yanzu a tura da CV din, sannan ranar Litinan yaje Bankin ya same shi da hardcopy na takaddun. Haka na koma gida raina qal na tarar da Bashir ya rigani komawa yana zaune yana shan Shayi. “Se yanzu” ya faaa yana kallona, seda na ajiye jaka da mayafina na zauna kusa dashi tareda rungumo shi nace “Canki” “Kinsan ban iya cankar abu ba ko” ya fada yana kallon fuskata, sena dakko wata ta na bude inda na rubuta Email din na miqa masa ina cewa “Gashi yanzu kaje Cafe ka tura da Soft copy na CV dinka sannan ranar Monday zaka kai hard copy din”. Kallona yayi da rashin fahimta, nan da nan na gaya masa yanda mukayi da Baffa na rufe da cewa “Idan kuma kafi son kasuwar yace kaje ka same shi, ni da zaka hada dukka ma kana aikin kana taba kasuwancin se ya fi yanda su Yaya sukeyi. A zatona zanga farin ciki a fuskar Bashir irin wanda nake ciki amma se naga akasin haka, cikin daure fuska ya kalleni yace “Yanzu Ma’u har kin fara gajiya ne yasa kika tafi nemar mun taimako a gidan ku, daman dazun ina gida an kai kaya yaran suka ce kece kika kawo yanzu kuma kinzo da wannan”. Tsabar mamaki ma kasa rufe baki nayi na tsaya ina kallon Bashir, a zatona abun kirki nayi ashe shi a nasa girman kan gani yake baya yaci kenan na nema masa taimako a gidan, se kawai na miqe na kwashi gyalena da jaka na ajiye masa Key din motar ina cewa “Ban shigo da ita ba tana waje naga ka datse get din da kwado” nayi shigewata daki. Yanzu fisabilillahi da ace na samar masa aiki da kuma na zama ni nake dauke da dawainiyar mu wanne yafi? A zatona tunda ya fadi hakan baze yi ba se gashi washe gari yana ce mun ya tura ranar litinin din kuma yaje ya kai Takaddun cikin ikon Allah ba’a rufa sati ba sega shi sun tura masa da takarda sun daukeshi aikin wani satin ma ze fara zuwa. Haka muka cigaba da tafiya zuwa yanzu duniya tayi mana daidai, Baffa ya dauke nauyin makarantar Sa’ad, Samirah da Naziru ya saka su cikin foundation din sa da yake biyawa Marayu da wadanda iyayensu basu da qarfi makaranta, shikansa Alhajin ya saka Ahmad Yayan mu da yake likita ne yana aiki da Asibitin Malam Aminu Kano su acan ana samun tallafi daga qungiyoyi dan haka ana daukar nauyin magungunan masu lalurori ansamar wa Alhajin kyauta yanzu ake bashi magani ga ganin likita duk sanda ya tashi har kanon yake zuwa tunda sunfi mu kwararrun likitoci se gashi a dan lokaci ya dawo hayyacin sa ramar da yayi duk ta cike ya koma fita kasuwarsa yanzu sannan ga Kayan Abinci da ake rabawa maqota yanzu suma duk wata se an kai musu Albarkacin surukuta nasu rabon ma daban yake. Dan haka yanzu dan abinda Bashir zeyi musu be wuce na neman Albarka da duk da yakewa iyayensa ba idan yana da hali ni kaina yanzu se sambarka dan babu abinda Bashir ya rageni dashi ya karbi ragamar gidan sa komai yana yi yanzu har kudin makaranta yake bani daman tuni na bashi mota ta saboda zuwa aiki wanda dakyar ya karba acewarsa Wanda ya siyamun bazeji dadi ba, be karba bama seda na kira Alhaji Yasir din a gabansa na gaya masa Bashir ya samu aiki dan haka na bashi motata saboda sauqin zirga zirga tunda ni ina dab da kammala karatun Jarabawa zamu fara, “Babu komai ai taki ce kina da damar yin duk yanda kika so, daman saboda bana so naga kina hawa motar haya ne ko ki ringa neman lift yasa tunda mijinki ne kinga ze kaiki ko ina kuma ya dakko ki, Allah yaci gaba da baku zaman lafiya mu shine fatan mu kawai” Alhaji Yasir din ya fada. “Wallahi Ma’u rayuwar gidan mu tana burgeni, yayunku nada mutunchi sun kuma riqe girmansu ba tareda nuna banbanci ba ko yau Baffan ku ya mutu bashida damuwa yasan kanzuri’arsa a hade take ba kamar yanda yake faruwa a yawancin gidajen masu kudi ba da zaki ga kowa yan dakinsu ya sani kuma burinsu ace sune a gaba sun fi sauran” Bashir ya fada bayan da muka gama wayar, se nayi murmushi nace “Idan Namiji ya zama tsayayye a gidan sa tabbas kan zuri’arsa zata hadu, amma daga inda ka nuna banbanci tsakanin matanka shikenan kayiwa zaman lafiya gibi a gidan ka dan yayan ko wacce zasu tashi wasu na ganin an fi son uwarsu sune yan gata sauran kuma zaau qullace ka na ganin kana wulaqanta uwarsu ka banbantata da dayar kaga baza’a taba samun zaman lafiya ba. Kaima idan ka tashi qara aure kayi koyi da halin Baffan mu wallahi zakaji dadin rayuwarka” “Ni ai dan ke kadai aka halicceni Ma’u babu sauran gurbin da wata zata sake samu a cikin zuciyata” ya fada yana janyo ni jikinsa. Haka rayuwa taci gaba da shudawa. Nagama Diploma ta har sakamakon mu ya fito Bashir ya siya mun DE form dukda ban so ba yace gara naci gaba na gama lokaci daya na huta kawai. Zaman gida da nake yanzu yasa Amirah ta dawo da zuwa, ba laifi yanzu ta dan saitu tunda ta qara girma ga makaranta da take zuwa kuma nima ba kamar da ba da bana saurara mata yanda zan tarbiyyan tar da Dan dana haka haka nake kula da ita dukda wani sa’in in ta koma taja gayawa Addah haka zata qaraci mitar ta nidai bazan kukata ba. Indai har zata ci gaba da turomun ita to kuwa dole na saita ta yanda nake so. Yanzu kusan kullum a nan take wuni dan Addah bata zama, tun safe in zata fice qantalinta zata kawo mun Uniform din Islamiyyar Amiran da farko har Ummi ta fara Bari Bashir ya hana kai tsaye yace mata karta sake barinta dan matarsa ba me raino bace ai kuwa munga ruwan masifa dan har Dada seda ta karbi rabonta haka dai aka dena se Amiran ake barmun. Wani lokacin ma har kwana takeyi idan Addah tayi dare bata dawo ba ko Bashir yace ta tafi ta zauna a gun Sauran Matan gidan se nace Yabarta kawai dan har ga Allah ina son yarinyar daman rashin jin ta ne ya ke hadamu nima kuma zuwa yanzu na fara sha’awar ajiye nawa Dan dan duk su Alawiyya sun haihu shekarar mu daya da kusan wata takwas yanzu da aure amma ni shiru. Akwai ranar da na taba yiwa Bashir maganar nace masa ko zamuje Asibiti yace muna Aa “Komai lokacine kuma bamuyi dadewar a har zamu ce zamu Asibiti ba, mu qara haquri Allah yasa jinkirin ya zama Alkahiri” ya fada dole na haqura. Da zaman haka da nakeyi akwai wata makaranta a qasan layin mu nacewa Bashir zan nemi koyarwa acan be hana ni ba kuwa dan da kansa ma yaje ya tambayarmun suka ce naje ai kuwa aka sauke ni zan ringa koyarda yan JS1-3 Computer Science, qarfe 8 nake shiga 12 na gama classes dina in tafi gida kuma sosai nake jin dadin aikina haka yaran suna ganewa dan Allah yayi mun baiwa ta iya magana, sannan yanda nake da Sakin fuska yasa muka saba sosai da dalibaina. Cikin hukuncin Allah se gashi na samu ciki wanda sam ban san dashi ba seda ya kai kusan wata uku a jikina sannan naje Asibiti saboda rashin ganin Al’adata na tsahon lokaci se gashi gwajin farko an tabbatar mun ina da ciki bayan an yi scanning aka gayamun watanninsa. Tun ina Asibitin na kira Bashir na gaya masa, sosai kuwa ya nuna murnar sa yace na tafi gida na huta kafin ya dawo haka muka kwana ranar cikin farin ciki kamar mu ciro dan haka muka ringa kallon hoton scanning din da ba ganinsa ake yi sosai bama. Kamar kuwa cikin nan na jiran a san dashi se Laulayi ya taso ni gab, kuma wani abu safiya nayi idan Bashir ya fita haka zan wuni da zazzabi da ciwon kai amma duk inda La’asar tayi kafin ya shigo gida na ware dan haka ko nayi masa qorafin baya yarda musamman idan ya dawo banyi girki ba ya ringa mita kenan in ce bani da lafiya kuma yace shi be gani ba. A daidai lokacin kuma Admission dina ya fito, wannan karon na samu daman Business Administration na nema sun bani Level two haka na fara jigilar zuwa makaranta ga ciki ga karatu dan ma farkon semester ne, randa naji ba kanta kwanciyata nakeyi a gida naqi zuwa, haka muka ci rabin zangon, an tafi hutun Midsemeater aka tsunduma yajin aikin da ba qaramin dadi abun ya mun ba na ringa Addua Allah yasa kar a koma sena haihu. Haka mukayi ta lallabawa, ina rainon cikina, Addah kullum tana tafe da kayan kwalamar da tasan zan so amma fa idan tazo ita ma haka zata koma da niqi niqin tsaraba dan duk abinda idonta ya kai se ta dauka ni kuma bana hanawa sedai Bashir yayi ta fada idan ya gani ko ya tambayi abu nace babu dan yasan ita kadai ce take zuwa ta dauka. A lokacin su Fainusa sunyi candy dan haka suna zuwar mun sosai wata ran ma ni zan kirasu idan naga kwana biyu basu zoba haka zasu wuni suyi warkaja min su son rai, kayan sawata da duk suka mun kadan saboda ciki haka zan tattara in basu, kayan kwalliya turare duk zuwa da abinda zan basu har seda ta kai ta kawo ko bikin qawaye zasuje gurina za’ayi aron su takalmi, jaka sarqa wani lokacin in suka karba nace su barshi. Lokaci daya maganar auran qannen Bashir Mata su ukun ta taso. dafarko auran Afiya aka saka, wane tudu wane gangare se ji nayi a bakin Addah wai ai gaba dayansu za’a hada”. “Ni nacewa Nafi a hada yaran nan dukka kawai lokaci daya a huta to me za’a jira tunda duk da tsayayyun maneman su gasu da garin jiki ai bata jerasu a gaba su zamar mata kamar wasu kishiyoyi ba. Tana wani ya za’ayi hidima zatayi yawa bayan ga Bashir Allah ya rufa masa asiri aikin Banki fa yakeyi har a tsaya ana wani zancen kudi” Addahn take gaya mun. Niko banda “Allah ya sanya Alkahiri” ban ce mata komai ba dan mamaki take bani yanda take ji da aikin Bankin nan na Bashir seka rantse wani babban Manaja ne a CBN idan ba haka ba ta yaya za’a tattago auran yaya mata har uku kuma a dan qurarren lokaci kwata kwata wata hudu fa suka saka rana. Ai ko bashi da nasa hidindumun a bashi isashshen lokaci ya shirya balle ga hidimar haihuwa a gabansa dan kusan lokaci daya bikin ze kama da haihuwata. Haka Bashir ya ringa mita kullum ya zauna saurin me akeyi da za’ace su uku za’a hada ina laifin Afiya da Sadiya dan duka duka Fainusa bata cike sha shida ba kawai girman jikine yasa aka mata tsallake a makaranta suka gama tareda Sadiyan. Haka naci gaba da rainon ciki na a can kuma suna ta shirin biki, Alhajin su yayi iya qoqarin sa ya bada kudin gadajen Amaren kowa daya harda katifa dan shi kansa ba’a san ransa aka saka auran duka ba amma bala’in nacin Addah da har ta zuge Dadan itama ta hau ta zauna dole yasa musu ido sannan ya kira Bashir ya gaya masa karya kuskura ya takura kansa su saka shi yin hidimar data fi qarfinsa akai kowacce da abinda Allah ya hore tunda sun nace se anyi. Dan haka gaba daya dan Albashin nasa da duk wani saving dinsa ya basu akayi musu kujeru gudummawar da aka samu daga sauran yan uwa da abokan arziqi suka harhada aka yi abunda ya samu. Ido kawai na zubawa Bashir ganin har cikina ya kusa fita daga wata na takwas amma ko pant din jariri be siyo ba ko ya bani kudi yace na siya se hidimar auran qannensa yake yi. Raina ya sosu da abin har na kasa haqura wata rana nayi masa magana se ce mun yayi “Ma’u kenan saurin me kike yi ki bari a haihu mana ko bakiga hidimar data ke a gaba na bane duk qoqarin da nayi kina kallo kullum da sabon abunda zasu ce akai ni gaba daya ma na gaji Allah Allah nake ayi bikin nan kowa ya huta”. Sosai naji zafin maganar sa a lokacin, cikin bacin rai nace masa “Amma shima wannan abu me muhimmanci ne kuma kasan dai kaine meyi sannan ba yau kasan ina da ciki zan haihu ba tun ma kafin maganar bikin ta taso cikin ne a gaba yanzu kake cewa a bari a haihu tukunna cikin da ko a yanzu za a iya haife shi amma ko rigar da za’a saka masa bamu tana da ba ai shikenan” na tashi na bar masa gurin. Nakuma qudurce a raina bazan sake masa magana ba dan daman tuni na sissiyi wasu wasu kaya unisex dana gani suka mun kyau se kawai na hada akwatina ta zuwa Asibiti na jingine in yaso naga iya gudun ruwan Bashir. Wannan Abun yasa gudummawar danayi niyyar bayarwa ma na maida abata tunda a take takensa nasan ba abin arziqi zeyi mun idan na haihu ba nayi amfani da kudin na toshe wata kafar, Addah tayi shaguben harta gaji akan biki nata matsowa wai matar babban Yaya bance komai ba, ai ni ma ina da wayona ni na iya bauta musu amma abinda yake doke ayi mun saboda tasu buqatar tafi tawa ana nema a tauye ni sannan na kwashi gudummawa na bayar lallai ma se kawai nayi dariya nace mata “Ai babban yayan ya wakilce ni yayi komai sedai mu jira Allah ya kaimu musha biki”. Ana saura sati daya bikin Matan gidan nu suka aika wa Dadan da saitin Kuloli manya guda uku, a ranar ta kirani a wata tana ta godiya wai an kawo kula masu kyau da tsada daman suna ta yanda za’ayi a qara musu duk wanda suka siya ba wasu na arziqi bane yanzu gashi an samu sun gode sosai. Haka kawai kuma se naji nauyin qin bayar da komai din da nayi, dan haka washe gari naje Awo da yake da mota na fita dan Asabar ce Bashir yana gida sena Biya na siyi wasu kulolij masu kyau guda uku da zannuwan gado manya masu abun rufa suka uku na wuce gidan Dadan na kai mata. Taringa zubamun godiya amma qiriqiri Addah dana tarar ta nuna sunyi kadan, har tana cewa “Yanzu a matsayin ki guda a nuna wadannan kayan ace ke kika kawo ai se a raina ki ni dana ga wadanda akace an kawo daga gidan ku inji su hudun duka se naji wani iri nida na dauka mota za’a sauke mana” da wasa da dariya tayi maganar amma duk me hankali ai yasan me take nufi. Dan haka nima cikin wasan na mayar mata da martani nace “Yo Addah kin manta ance taqamar mace gidan mijinta kudin uba ai ado ne kawai, kuma a iya qarfin mijina nayi wannan ai kuwa na kai a yabamun su kuwa da suka bayar fa kara suka mun bawai dole ya zamar musu fa se sunyi ba” Washe garin ranar muka tashi da Alhinin Rasuwar Aliyu Abokin su Bashir, mutuwar ta dake ni kwarai dan A jiya bayan na dawo a gidan na tarar dasu shi da Bashir harda Bala suna hira, yana ta tsokana ta wai bana jin nauyin jikina nake iya tuqi nace masa ai Laifin abokinsa ne da be kai ni ba, na wuce ciki na barsu yana ta faman yi mun Addu’ar sauka lafiya ashe rabuwar kenan da safe se kiran Bashir akayi wai ya rasu da Asuba anji shi shiru be fita Masallaci ba Qaninsa ya duba shi aka tarar babu rai. Mutuwar Matashi akwai firgitarwa musamman ta mutun irin Aliyu me mutunchi da mutunta Jama’a ya samu shaida ta kwarai sosai, haka muka tafi Jana’iza Allah sarki Mamansa se Kuka takeyi su biyu ne Yayanta daga shi se qaninsa haka budurwar da ze aura da suka zo Abin tausayi gaba daya se jikina ya sake yin sanyi da lamarin duniya. Tunda akayi rasuwar Bashir ya zama wani iri, ranar kwana uku, ranar kwana uku da daddare muna zaune shiru yake cewa “Allah sarki Aliyu, ranar kafin ki shigo yake cewa mun Wallahi Bashir kayi dacen mata Allah yasa mu a danshin ka dan Allah ka riqe yarinyar nan da kyau dan Alkahiri ce a rayuwarka kuma matar rufin Asiri ce. Kaga dai a yana yin da kukayi aure gashi a hankali abubuwa suna ta warwarewa bata nuna gazawarta ba ni kuwa kana kallo yarinyar nan Momy ba yar kowa ba amma ta dauki buri ta dorawa kanta wai fa dana kaita taga gida na rainawa tayi wai ban dora bene ba, ta shiga kawo mun wasu tsare tsaren banzanta, Ni fa in ba’ayi wasa ba auran ma fasawa zanyi. Idan da rabo nayi a Aljanna, ashe bamu sani ba tafiyar ma tazo gangara” se ga hawaye ya zubo ta gefen idonsa. Jikina ya qara macewa dakyar na iya cewa “ Allah ya sa muyi kyakykyawan qarshe, waya sani ko nika mutuwar zanyi” “Karki sake fadan haka In sha Allahu lafiya lau zaki haihu” ya fada yana kama hannuna. Wannan rasuwar ta rage kaifin shagalin bikin su Fainusa dan duk wani makusancin Bashir yasan Su su hudun nan tare suka tashi, Ranar Asabar data kama kwana shida da rasuwar Aliyi aka daura auran a ranar kuma kowa aka kaita gidanta. Daman Banje kai Amare ba dan gidan mu ma na tafi da hayaniyar yan biki ta fara yawa se dare Bashir yaje muka tafi gida. Kamar ciwo na jira kuwa yana yin parking nayi wani ciwon baya da mara lokaci daya sunyi mun sallama, se Bashir ya shiga ya dakko mun Akwatina muka kama hanyar Asibiti. Tsabar takaici ina cikin azabar ciwon da nakehi kamar haihuwar ta taho gab ne wai Bashir tambayata yakeyi yanzu ya za’ayi idan haihuwa ce bamu siyi kayan Baby ba bansan sanda na qunduma masa zagi shiga kayan babyn ba nace ya mun shiru ko ya sauka a motar, Haka muka qarasa aka shiga filin daga, zo kuga idon Ma’u a labor room ashe aka ce wasa Farin girki wannan ciwo sallama ne, haka dai akayi ta gumurzu har Asuba, cikin ikon Allah Ana kwada kiran Assalatu na santalo qaton Baby na me kama da Bashir sak kamar an tsaga kara hasken Fata ta kawai ya dakko. Murna a gurin Bashir kamar ya taka rawa, kafin Gari ya gama haske Asibiti ya fara cika da dangi na harda nasa, Hajia Babba da Hajia Umma ne suka zo, a kunne na radawa Hajia Umman akan tace gida zasu wuce dani dan tun farko farko danayiwa Bashir maganar wankan gida yace ba wannan maganar ban sake ba. zuwa rana kuwa da likita ya tabbatar babu wata matsala aka bamu sallama Hajia Umma tace gida aka yi dani, ze musa Addah ta tace muje babu komai daman sunyi niyyar kawo nin, saboda haushi ko sallama Bashir beyi mana ba ya kama hanya ya tafi. Oho nidai muma mukayi tafiyar mu gida, daman na dade da hada kayan tafiya wankan muna zuwa aka tura su Khadija gidan suka dakko mun ina ta Addu’ar Allah yasa kar a tambayi ina kayan wanka da sauran abubuwan da ake siya ilai kuwa kafin ma mu qaraso Hajia Anjin saka su Baba Jummai sun shirya mun dakin da zan zauna duk wani abun buqata na zaman jego an tana da. Seda muka kwana muka wuni sannan Bashir yazo shi ala dole fushi yake yi, ko a jikina jegona kawai nakeyi ingantacce haka yarona Aliyu da tun a Asibiti yayi masa Huduba shima yana samun kula sosai. Kwanan mu biyar aka kawo kayan barka daga gidan su Bashir tareda ragon suna. Yan rigunan su ba laifi da turamen Atamfa uku nawa, haka aka taresu cikin karamci suka tafi yan barkar da suka tarar yan uwan mu nata yan qananan maganganu dan kowa yayi zaton yanda yanzu ya samu budi babu laifi zeyi abinda yafi haka ni kuwa ko a jikina dan dama ba jiran abinda zasu kawo nake ba, ko sanda na masa magana kawai dan haqqinsa ne ya kamata yayi. Ranar suna munsha shagalin mu, na ringa shiga ina fita ta Alfarma. Amirah da tun kwana biyar da suka zo tana gurina da yake anyi hutun makaranta daman nayi mata dinku na duk inda na shiga tana nan yan gidan mu suyita tsokanarta ana yar Anty tayi dariya. Zaryar da Bashir ya ringayi ta saka aka tattara ni satin mu uku muka koma se na tafi tareda Baba Jummai da zata qarasa mun Arba’in. 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 WATA KISHIYAR 🥰👹 (ALKAHIRI CE KO SHARRI) 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 Na Maryamah Farouk (Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah) Wattpad @MaryamahMrsAm Page 31 BASHIR Ransa fes ya bar gidan ranar dan ya tabbatar da Ma’u bazata fita batareda izininsa ba. Zuciyarsa ta kasu biyu, wata tana gaya masa abinda yayi daidai ne inda wata take nuna masa kuskuren abinda yake shirin aikatawa kuma kamar rashin Adalci ne. Shikansa ya tabbatar da aikin Ma’u rufin asirinsa ne kamar yanda ta fada kudin jikinsa yake komawa shida yayansa. Haka yayita juya abun a ransa har ya isa office, Lokacin da suka fita break kiran Alhaji Qarami ya shiga wayarsa, yayi matuqar mamaki amma daya tuna abinda ake ciki seya goge mamakin. A mutunce suka gaisa sannan Alhajin ya fara cewa “Engineer yanzu Suhaima take gaya mun wata magana wai ko ka hana Ma’u zuwa aiki ne ko menene dai, nasan halinsu qilan wani laifin tayi maka koh?” Kame kame Bashir ya shiga yi yama rasa abinda zece masa, se Alhajin yayi murmushi irin na manya. Yana sane yayi masa haka tunda Suhaimah ta fada masa komai harda dalilin daya saka yace tabar aikin amma yana so ne yaji gaskiyar komai a bakinsa hakan da yayi ya tabbatar masa da son kaine kawai irin nasu na maza ya saka shi aikata hakan. Seda yayi gyaran murya kafin yaci ga da cewa “Koma mene dai yanzu ina roqa mata arziqin a barta taci gaba da aikinta, kuma koda gaba wani abu ya sake tasowa nine uban Asma’u ni ya kamata ka gayawa zan dauki mataki akai” daga haka dukayi sallama ya kashe wayar. Sam hakan be yiwa Bashir dadi ba, akan me zata kai qarar sa gurin sa saboda tasan Alhaji Qarami yafi qarfin yayi jayayya dashi ko ya nemi alfarma a gurin sa yaqiyi, yanzu gashi saboda qanwar sa ya sauke kai yana roqonsa bayan ko shi aikin nasa da yake taqama dashi bazar Alhaji Qaramin ce. Yana hanyar komawa gida suna waya da Amirah Yake gaya mata abinda ya faru “Amma wallahi Yaya sun ma raina maka wayo, kaida gidanka amma ace dan ka yanke hukunci wani yazo ya warware shi kawai dan suna da kudi se su ringa zuba iko a duk inda suka ga dama, gaskiya seka tashi tsaye koda yake aikin gama ya gama ai tunda har ka bada qofar da zasu ringa yanke maka hukunci a gida kaga gaba baka isa ka sa ko ka hana ba se a kai qarar ka inda akasan bazaka musa ba” Amiran ta fada kafin taci gaba da yi masa fanfo Da yake abinda yake so ne nan kuwa ya hau kai yayi daram akayi sa’a akayi Sa’a daya tuntubi Bala da maganar shima, da yake duk kanwar ja ce duk irin Abinda Amiran ta fada ya dora nasa akai, wannan dalili da hujjojin da suka kafa masa na cewa daga inda wasu suka fara shiga cikin hukuncinsa tsakaninsa da Ma’u toh raini yazo dan tasan duk sanda ya fada mata abinda be mata ba tana da inda zata kai a tilasta shi ya chanza, wannan yasa shi ya kasa ganin kyautatawa da duk qoqarin da Ma’u ta ringa yi na son ganin ta wanke kanta. Se yake ganin duk ihu ne bayan hari, ta rigada tayi abinda tayi dan tayi ta nuna wa duniya be isa ba shi kuwa yayi Alqawarin bazata ga gazawarsa ba dan haka su zuba su gani da kanta zata haqura tace ta bar aikin nan dan babu gudu babu ja da baya. ASMA’U Ranar Litinin da wuri na tafi Asibiti dan daren jiya kasa bacci nayi ga zazzabi ga wani ciwon mara dakyar naga safiya. Ina zuwa bayan likita tayi mun tambayoyi kai tsaye ta turani lab inda suka dauki jini na da fitsari suka ce na jira a waje. Minti 30 tsakani Nurse ta kirani dan har an kaiwa Dr result. Ba qaramin mamaki nayi ba jin wai ciki ne dani dan ko kadan ban kawo hakan ba har likitan tana tsokana ta wai haihuwa Biyar amma na kasa gane alamun ciki. Seda tayi mun scanning, cikin sati 9, magunguna ta rubutamun da zasu taimaka mun da zazzabi da kasalar da nake fama dasu na karba a pharmacy kafin na wuce gida raina qal kamar an mun bushara da Aljanna. Ada na ce na gama amma yanzu damun cikin nan naji dadinsa sosai dan nasan shine ze zama silar daidata tsakanina da Bashir. Sanda na koma gidan ya fita daman Amnah yareda sauran yara suka fita taje makarantar ana neman su dan suna shirye shiryen yi musu graduation party. Ban zauna ba saboda murna duk se naji na warke ma, dakin Bashir na shiga na gyaro shi tsaf na wanke Toilet na saka qamshi, kafin na nemi guri me kyau na ajiye takardar test din Asibitin inda nasan hankalinsa ze kai. Dakina na koma nima na sake wanka na sheqa kwalliya sosai dana san dole na burge Bashir, Dumamen tuwon da mukayi jiya naci da baqin tea kafin na sakeyin brush na dawo palour na zauna zaman jiransa. Se gurin sha biyun rana ya shigo, na miqe fuskata dauke da murmushi na nufe shi amma kafin na qarasa ya dakatar dani ta hanyar daga mun hannu se na tsaya din kuwa ina kallonsa ya wuce ni ya zauna akan kujera. Jiki a sanyaye nima na koma na zauna, idonsa akaina yace “Weekend din nan zaki Tafi Ita kuma Amirah tazo”. “Wai dan Allah Baban Ali me yasa kake da son tada zaune tsaye? Ina mun gama da wannan maganar ko. Nagaya maka ni bani da matsala da zaman Amirah amma banga dalilin da zesa ni a takurani ace na koma wani waje ba saboda ita, tazo mana kowa ba zaman ta zatayi ba namene se an shiga haqqina wai” na fada ina yatsina fuska dan harga Allah na gaji da maimaita abu guda. Kullum daga ya zauna zancen kenan Amirah zata zo toh ko Addah ce tazo mana ina ruwan wani. “Oh hakane, wato kina ganin kin isa kenan a zaton ki dan kin kai qarata ze sa na chanza ra’ayina ne? Ni ba irin namijin da ze zauna yan uwan matarsa suna tsara masa yanda zeyi bane kin kuma fi kowa sanin idan nayi niyyar yin abu babu uban da ya isa ya saka ni ko ya hanani”. Bashir ya fada yana kallon cikin ido na, sena miqe tsaye nima ina kallon sa nace “Duk abinda zakayi ya tsaya kaina ni kadai karka ce zaka zagar mun Yaya dan ni nasan mutunchinsa kuma ko banza wallahi Alhaji Qarami yafi qarfin raini a gurin ka dan yayi maka abinda duk duniya babu wanda yayi maka shi, ko gani kayi za’a zage shi kamata yayi ace se inda qarfin ka ya qare” “Ni kike gayawa haka Ma’u ni kike gorantawa cewa Yayanki yayi mun abinda babu wanda yayi mun shi ko?” Shiru nayi masa dan idan na bude baki nasan bazan fadi abu me dadi ba dan gaskiya Bashir ya qure ni na tabbatar so yake sena zazzage masa galan din rashin mutunchi daga nan se ya juya duk wani laifi zuwa kaina tunda daman neman sanadi yakeyi, ina jinsa yana ci gaba da fadar maganganu son ransa ban tanka shi ba qarshe ma nayi wucewa ta dakina na ina shiga ya biyo baya na yana cewa “Wato ga mahaukaci ina miki magana kin tafi kin barni a tsaye ko lallai Ma’u kina so kiga asalin kala ta kenan”. A fusace na juya nace “wace kalar taka ce tayi saura da ban gani ba Bashir, ai duk wata fuska ta ka ka rigada ka gama bayyana mun ita na gani na kuma san da wanda nake zaune dan tsahon shekarun da mukayi a baya Kura ce da fatar Akuya nake zaune da kai. Daman mutane sunyi gaskiya da suka ce baka tantance halin namiji se randa ya qara aure. Wallahi ka bani mamaki Bashir ban taba tsammanin ka a cikin layin maza masuyiwa matansu butulci ba a lokacin da suka samu wasu. Dame na rage ka, ta ina na gaza? Dame ita wacce kake fifitawar ta fini? kullum hanqorona na burge ka nayi maka abinda zaka ji dadi amma a koda yaushe sakamakona baya zama me kyau anya ka taba sona kuwa? Karkasa na yarda da cewa ka aure ni ne kawai dan biyan buqatar kanka yanzu da kake ganin ka samu yanda kake so kake neman ka mayar dani bolar da zaka juye sharar ka duk a sanda ka debo ta idan ba haka ba meye laifi na? Ko kuma ni ban cika mace ba nata matancin yafi nawa da yasa kake take nawa haqqoqin dan biyan tata buqatar. Wallahi Bashir idan baka yi a hankali ba zaka tashi cikin jerin mazan da zasu je lahira da shanyayyen jiki saboda ka gaza Adalci a tsakanin matanka, idan ma kana tunanin idan kayi mun abu zan yafe ko ban kaiwa Allah qarar ka ba Bashir yana kallo kuma se yayi mana hisabi nida ku” nayi maganar cikin muryar da take nuna qololuwar bacin raina dan gaskiya nakai bango na kuma shirya tarar ko menene tunda naga alamar Bashir ya fara daukar kawaicina a matsayin sakarci shiyasa yake kawo mun duk shirmen da yaga dama. “Ni kikewa fatan na tashi da shanyayyen jiki Ma’u saboda nabaki umarni a matsayina na mijinki kinqi bi?” ya fada muryarsa na rawa idonsa ya kada yayi jajir har wasu jijiyoyine suka fito a cikinsu, banji ko dar ba a raina ba na gyara tsayuwata ina kallonsa ido cikin ido. Se ya girgiza kai yayi kwafa kafin yace "ASMA'U, ASMA'U, ASMA'U sau nawa nawa na kira sunanki? Dukda yanda Asma’un daya kirani ya dake ni dan na manta rabon da Bashir ya kira ainihin sunana amma se na dake, hannu biyu na saka na riqe quguna nace "Sau uku ENGINEER BASHIR AHMAD" dan ni ma fa ba baya bace a fagen iya fitsara, kawai dai shekaru da yanayin rayuwa suka sa nayi sanyi amma a wannan gabar dole na fito masa a ainihin MA'UN BAFFAH ta wadda ya sani shekaru goma sha shida da suka gabata bawai ASMA'U matar Bashir uwar Aliyu, Jafar, Farida, Abdallah, Ahmad da Muhammmad ba. Qara gyara tsayuwata nayi ina kallonsa ganin yanda yake bina da kallon dana tabbatar na zallar mamaki ne jin yanda ni na kira nasa sunan gaba daya ma Gatsal bako Sakayawa, Sena saki wani guntun murmushin takaici, lallai Bashir ya manta dawa yake magana, a zatonsa nayi tibis ne ko? be san har yau da saurana ba sedai ba’a tabo ni ba. Kansa ya girgiza yana qoqarin kokawa da hukuncin da zuciyarsa take ayyana masa, wani sashe na ingizashi akan  yayi inda dayan ke kwabarsa da nuna masa zafa ta iya kwabewa amma idan ya ja da baya ai ma zata raina shi kuma yabi abinda take so kenan. Kai ba wannan ba raini biyu ma tunda itama ma AMIRAN zata qara tabbatar wa duniya be isa da ASMA'U ba tunda gashi ya bata umarni taqi tabi. Se ya gyara tsayuwarsa tareda qara tsuke fuskarsa da dama can bata da fara'a sam, wani kallo yake jifanta dashi da yasan yana ladabtar da koma waye amma banda wannan kangararriyar Matar. Cikin kaushin murya yace "For the last time ASMA'U ina baki umarnin kiyi resigning daga aikin ki ki tattara yara ku koma Gombe d....." "Na gaya maka wallahi Bashir bazan bar aiki na na koma Gombe ba saboda zaka kawo Matarka Lagos" nayi saurin katse shi. "Shikenan, Se ki zaba ko auranki ko kuma aikinki" ya fada cikin sautin dake nuna qololuwar bacin rai yana harde hannu biyu a qirji yana bina da kallo, daga inda nake ina iya jin yanda yake sauke numfashi kamar wanda ya hadiyi kunama. Qara jinjina qarfin hali da rainin wayon Bashir nayi a raina, wato ni nice rumfa sha shirgi ko ga Uwar garke wai na tattara yara mu koma Gombe, to kuwa yau na shirya ganin qarshen rainin hankali da duk abinda Bashir yake taqama dashi dan haka nace "Idan har saboda MATAR KA kake so nabar aikina to na zabe shi BASHIR". "Haka kika ce" "Eh Haka na fada”. Seda ya hadiye wasu qulalai da suka tokare masa maqogaro, kaso tamanin na zuciyarsa yana kwabarsa amma kashi Ashirin ya rinjayi harshen sa "Kije na SAKE KI SAKI DAYA idan yaso se ki zauna da aikin naki". Wani irin dummm naji kunnena ya dauka, wallahi wannan kalmar itace mafi munin ji a rayuwata gaba daya, wannan rana tafi kowacce duhu a tarihin rayuwata. "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Bashir kasan me ka fada kuwa? dagaske kake" na fada cikin yanayin da ni kaina bazan iya fasaltawa ba "Oh baki yarda ba? To kije na qara miki DAYA, badan babu kyau ba Asma’u da sena cike miki ukun ki kinga se kiji dadin yin aikin ki dakyau ba tareda nayi miki rashin Adalci ba" ya fada daidai sanda yake ficewa daga dakin. Wani jari ne ya kwashe ni ya yar akan dake, Allah ne ya rufa min asiri na fada kan gadon da yake baya na. A yanda nake na tabbata in a qasa na fadi babu abinda ze hana barin jikina shanyewa. "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Allahumma ajirnifimusinati wa'allifni khairan minha" cikin ikon Allah kalaman da bakina ya shiga maimaitawa kenan jikina yana wani irin rawa tamkar wadda aka jona mun shocking. Duk yanda naso kwakwalwa ta tayi tunani na kasa dan ji nayi tamkar an saka super glue an liqeta, se zufa ce take ketomun ta ko ina kaina yai dum kafin kace meye numfashina ya fara sama sama ba shiri na fara laluben inda Inhaler ta take wadda sabuwa ce daman dazu dana fita na siyo, dakyar na samota bayan dana zazzage jakar dana fita da ita a qasa saboda yanda nake a rikice jikina yana rawa. Seda na zuqa sosai sannan numfashina ya fara dawowa daidai amma fa kwakwalwar na nan a toshe. Kai ido na fa ya soye bama alamar Hawaye zasu fito, to kukan maganin me ma zeyi mun? Ni? ni Asma'u yau Bashir ya saka? Wallahi ko a mafarki naga Bashir ya sake ni nasan shedan ne amma gashi kamar a zahiri hakan ta faru. Ina cikin wannan yanayin aka sake turo qofar dakin, nasan yarana dukka suna makaranta kuma lokacin tashinsu beyi ba. Nima dai rabon ganin wannan baqar rana ya saka ni daukar Excuse din rashin lafiya wai dan na huta na zauna da Habibina mu sasanta sabanin da muketa samu a dan tsakanin nan ashe ashe.... "Zaman me kikeyi? Ki tashi kisan inda dare ya miki dan gobe nake so azo a sakawa AMIRAH sabon kaya Zuwa Weekend ita dana isa da ita zata dawo dan haka na baki grace of today ki hada ya naki ya naki kinga yanzu komawa Gombe dole" kalaman Bashir kenan da suka fi dafin maciji a wurina haka ya juyawa yabarni ni bame rai ba ni ba sumammiya ba. Dakyar na iya miqewa na rarumi hijabi na, dole na nemi inda zan tsugunna kafin qarewar yau nida yarana. To tunda BASHIR ya iya sakina Allah na tuba watsi dani akan titi kuma ai shi yafi komai sauqi a waje sa. Kofar gidan na fito ina tunanin ina zan nufa? Flat din da yake jikin namu ido na ya fada, idan ban manta ba Abokin aikin Bashir ne a ciki wanda tsautsayi ya fada masa a ka koreshi daga aiki dole ya saki gidan tunda dama Office ne suke basu dan haka yanzu babu kowa a ciki. Gidan Baba na shiga dan nasan yana gida kaman yanda Bashir yake nan tunda Office dinsu daya, haka na ringa danna door bell ba saurarawa. Banyi zaton nayi sallama ba lokacin da Anty ta budemun qofa na nausa kai ciki kawai dan fa bazan iya cewa wallahi ga abinda nakeyi ba ni kaina cikin Sa'a kuwa na tarar da Baban na zaune a palour yana Kallon News, se kawai na isa gabansa na durqusa. "Hajia Ma'un Bashir" ya fada yana murmushi. haka suke tsokanata kai kowa na Estate din ma haka yake kirana kadan suka sanni da Maman Aliyu wasu kuma suce Maman twins. "Meya faru" Baban ya sake fada dan se sannan ya lura da yanayin fuskata. Banyi kuka ba amma kallo daya zakamun ka hango zallar tashin hankalin da nake ciki, se kawai na tsinci kaina da cewa "Baba Flat din Maman Boda zakamun hanya a bani haya na shiga yau dan Allah". "Bangane ba? Me ya samu gidan naku? Ina Bashir din?" Duk ya jero mun wadan nan tambayoyi da daya kadai nake jin zan iya amsawa dan haka na bude baki dakyar nace masa "Baba BASHIR ya SA KE NI SAKI BIYU kuma yace na tattara kaya na a yau nabar masa gida kafin ya dawo" na qarasa ina Rushewa da kukan da se yanzu na samu damar yinsa. Kuka nake tamkar raina ze fita inda Baba da Anty keta faman zabga salati suna qarwa. "Asma'u ya sake ki fa kika ce? Me kikayi masa har haka?” Baba Ya fada bayan daya tashi tsaye ya goya hannunsa a baya, sena dago cikin matsanan cin kukan da nake dan har kamar zan shide nace “Wallahi Baba banyi masa komai ba, kawai saboda yace na ajiye aiki na saboda Amirah nace bazanyi ba shikenan yace se naje na zauna da aikin nawa”. “Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un, meya ke damun Bashir da ze yanke wannan danyan hukuncin ba tare da shawara ba? Wacece ma Amiran?” Baban ya fada yana kallon Anty da tayi mutuwar tsaye jin musabbabin sakin, cikin tsananin bacin rai tace “Amma Wallahi Bashir ya isa Asararre yanzu akan wannan tanbadaddiyar yarinyar me zubin Aljanu ya sake ki lallai Namiji se a barshi”. “Wai wace yarinya ce ina tambayarki” Cewar Baba, se Anty ta kalle shi tace “Wacece kuwa idan banda wannan yar iskar maci Amanar yarinyar da yayi mata kishiya da ita, shine cin Amanar be ishe su ba yanzu seda suka raba ta da auranta. In sha Allahu se Allah ya saka miki kima dena kuka Alfarmar Annabi se yayi nadamar da bazata amfane shi ba a rayuwa tunda dai shi wawa ne”. “Ya isa haka Halima wannan wace irin magana ce, ka mata kuje ciki bari naje na ga Bashir din ni” Baba ya katse ta, se ya dauki Glass dinsa na qara qarfin gani da wayar sa ya fita Anty ta zauna akan kujera tana sake tsinewa Bashir da Amirah nidai in banda aikin kuka babu abinda nakeyi. Sanda Baba ya fita rashin ganin motar Badhir ya tabbatar masa yafita dan haka ya kirashi a waya itama seda ta kusa katsewa sannan ya daga. “Bashir kana ina ne nazo gida baka nan” Baba ya fada bayan da Badhir ya daga wayar. “Na dan fita ne” Bashir ya fada murya a cunkushe kamar wanda aka yiwa duren dusa. “Idan ka dawo kazo ina son ganinka” Baban ya sake fada kafin ya kashe wayar ya koma cikin gida. A inda ya bar mu nan ya tarar damu ina ci gaba da rusa kuka Anty na faman debewa Bashir Albarka. “Yanzu Halima a maimakon ki tausheta shine zaki zauna kina fadar maganganu kina sake daga mata hankali ko kin kyauta, ki samo mata ruwa tasha, Asma’u kiyi shiru haka, na kira Bashir din yanzu ze zo”. Baba ya fada bayan daya zauna akan kujera. Sassauta kukan nayi na shiga jan rai ina ajiyar numfashi kamar zan shide, dakyar na dan zuqi ruwan da Anty ta bani dan jinsu nayi sun min daci a baki, na hade kai da guiwa ina ci gaba da hawayen da na kasa tsaida su, wai ni yau aka saka? Ni Bashir ya saka saboda Amirah. Kusan mintina 30 aka buga gidan, Anty Baban ya kalla kafin ma yayi magana tace “wallahi yallabai bazan bude masa ba, ni gara ka fita can ka same shi a waje dan idan ya shigo zan iya duddura masa Ashar ma”. Se Baban ya girgiza kai kafin ya miqe yaje ya bude qofar da kansa. Tare suka shigo da Bashir da kallo daya zaka masa kasan ba’a cikakken hayyacinaa yake ba. Idanunsa sunyi jajir sun koma ciki ga jijiyoyin kansa sun fito rudu rudu. Guri ya samu ya zauna ba tareda ya kalli ko gefen da nake ba, nima sau daya na kalle shi na mayar dakai ina ci gaba da share hawaye na dukkan mu munyi shiru se Baba ya katse shirun da cewa “Bashir me ya hada ka da Asma’u har ta kai ga yanke irin wannan hukunci mara dadi, koda yake abinda ya faru ya faru dawo dashi bashida amfani dan haka koma menene haquri shine maganinsa dakai da ita duk kuyi haquri ka maida ita dakinta tunda da sauran zama bama se wani ya san Abinda ya faru ba” Luguden duka qirjina ya shigayi na dago na kalli Bashir ina jiran naji amsar da ze bawa Baban, ina ma ace yace daman wasa yake yimun ba dagaske bane ba. “Daman ana saki da wasa ne” zuciyata ta raya mun, sena sun kuyar da kaina qasa ina jin wani abu me tauri ya taso ya tokaremun maqogaro daidai sanda Bashir yake cewa “Ayi haquri kawai Baba amma ko zan maida ita ba yanzu ba, taje kawai lokacin data san muhimmanci na idan da rabo se mu koma”. “Kai dai za’a gayawa haka Bashir kaine zaka san Muhimmancin Asma’u a lokacin da ta rigada tayi maka nisa, se kayi kuka da idon ka kayi nadamar da bazata amfane ka ba wallahi tunda baka godewa Ni’imar ubangiji ba ka shirya godewa Azabar sa” Anty ta fada cikin Masifa kamar zata rufe Bashir da duka kafin ta juyo kaina inda nake durqushe ina kuka tace “Ke kuma kukan me zakiyi kanki aka fara sakin mace ko yaya idan wani yaqi ka da yini wani da shekara ma ze soka har zaki damu dan wani Bashir da dama can ba ajin auranki bane ya sake ki, in sha Allahu akan idonsa zakiyi auran da se ya gigita shi tashi muje” ta fincikeni muka shige dakin ta. Bansan me suka tattauna da Baba ba ya shigo ransa a matuqar bace yana cewa “Lallai yaron nan bashida mutunchi Halima, yanzu ka saki mace da yaya shida har kana iqirarin ta bar maka gida a yau zaka kawo wata se yanzu na fuskanci kan abun daman akan ze dawo da kishiyarta nan ya saketa kenan, babu komai duk wanda ya cuci wani a cikinsu Allah ya saka mas. kuje ki tayata ta hada kayanta zanje Management office yanzu naji yanda za’ayi su bada gidan”. 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 WATA KISHIYAR 🥰👹 (ALKAHIRI CE KO SHARRI) 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 Na Maryamah Farouk (Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah) Wattpad @MaryamahMrsAm Page 34 Ranar Juma'a aka daura aure na da Bashir, Juma'ar data shiga cikin jerin rana kun tarihin rayuwata na farin ciki da bazan taba mantawa da su ba. A qa'ida ranar da aka daura aure a gidan mu ake kai Amare amma mu ba'ayi haka ba saboda Dinner da manyan Yayyenmu suka shirya zasuyi a daren ranar sauran Yayyen mu mata se tsiya sukeyi wai an fi son mu su kuwa kamar ana jira da an daura ake kwashe su. Da yake tun ana sati daya da biki muka san da shirin Dinner, nasan dole sauran Angwaye zasu gwangwaje suyi shiga ta alfarma tunda suna dashi dukda Bashir ma nasan ze yi iya qoqarinsa amma baze iya kamo su ba saboda tattalin arziqinsu ba daya bane su duk masu dashi ne. Haka na samu Baffan mu na tasa shi da naci seda ya bani shadda yadi goma cikin irin wadanda yake dinkawa ni kaina bansan kudinta ba kawai dai nasan suna da kyau kuma ko cikin Mutane ina dadewa banga wanda ya saka irinta ba sefa manyan irinsa. A gurin Yah Mustapha  na samu hula harda takalmi daya siya dan daurin aure saboda duk gidan mu ya fisu gayu, dakyar ya bani wai order su yayiwo takanas seda mukayi ma zan biya kudin rabi nidai dana samu suka zo hannuna nace a gudunmawar sa, yana ji yana gani na masa fin qarfinsu se na bawa Yah Abubakar shaddar nace ya kaiwa Bashir dinki tunda abokinsa ne yasan Size dinsa na roqeshi dan Allah karya gaya masa ina so na bashi mamaki ne. "Ma'u kenan, yanda kike son Bashir kike tattalin sa Allah yasa kar wata rana yayi miki halin mu na maza" abinda Yah Abubakar ya gaya mun kenan a lokacin da se naji jikina yayi sanyi. Gaba daya daman na lura dashi kamar hadi na da Bashir beyi masa ba na rasa dalili dan har tambayarsa na tabayi yace mun babu komai, da yake daman shi ba mutum ne me yawan magana ba se na bar maganar kawai nasan idan da Bashir nada wani mugun abu baze barni na aure shi ba. Tsaf na hade kayan nan bayan an dawo daga daurin aure angwaye sun shigo aka dauki hotuna, masha Allah gaba dayan mu munyi kyau kuma ko wacce ta dace da zabin ta se fatan Alkahiri dangi da abokan arziqi suke yi mana. Suna shirin ta fiya nayiwa Sadiya qawata rada dan daman ita na bawa ajiyar Kayan tayi maza taje ta dakko su, seda suka fita tabi bayan Bashir din ta bashi. Muna zaune a bangaren da qawayen mu anan ta hira irin wadda ko wanne qawayen Amarya sukeyi idan ana biki, hayani ya na tashi wayata dake hannuna tayi qara, Bashir ne daman zaman jiran kiransa nakeyi sena miqe da sauri na shige bandaki na kullo qofar ko naji maganar sa dakyau. "Ma'una kayan menene wadannan, ina kika samo shadda me bala'in tsada haka?" ya tambayeni bayan dana gaishe shi. "Kamanta an jima akwai Dinner da za'ayi, kalar kayan da zan saka ne zamuyi Anko". "Ina sane har ma nayi dinki nima, mantawa nayi sam ban ma gaya miki kalar nawa kayan ba ai" ya fada daga daya bangaren, sena marairaice nace "Se ka ajiye su gobe ka saka idan za'ayi budar kai nidai yau wannan nake so na gani a jikinka". "Shikenan an gama Amaryata, na tabbatar yau ke kadai ce zaki fini yin kyau a gurin nan" "Haka nake so Angona yafi na kowa, se anjiman idan kunzo, kar dai ku bata lokaci qarfe takwas zuwa Goma Baffa yace za'a tashi" daga haka mukayi sallama na kashe wayar. A filin tsakar gidan mu aka shirya za'ayi dinner, tun la'asar masu decorashan din da aka dakko suka katange iya inda suke buqata suka fara aikin su, kafin magriba sun gyara guri tsaf se ka rantse wani babban dakin taro ne. Seda mukayi sallar magriba sannan aka fara shirya amare, munyi kyau har mun gaji cikin dinkin riga da skirt na wani hadadden material da akayi mana kowa da kalar nata da ze dace da shigar Angonta, munsha daurin goggoron mu me kyau dan fa fashion designer guda aka dakko ta shirya mu dukda a sannan ba'a fara kwalliya me fente fenten nan ba amma ta tsatso mana kyau da iya abinda ake amfani dasu a sannan. Har mun saka kayan sarqoqin mu Hajia Umma tace mu cire, saitin sarqa, awarwaro da zubuna ta kawo mana na gwal qirar dubai wanda sallama ce Baffa yake bawa Iyayen mu mata kudi su siya mana idan za'a kaiki dakin ki saka shi ta bawa kowacce nata ta saka nan da nan kwalliyar mu ta qara qawatuwa se walwali mukeyi ta ko ina. Seda mukayi sallar Isha'i sannan muka fita babban palour inda kafatanin yan gidan mu mu a lokacin mu talatin da tara ne muka hallara ga Baffa da Matansa Hudu aka shiga daukar hotunan family. Lokaci daya hawaye suka balle mun kamar sauran na jira kuwa muka dauki kuka wiwi wanda nasan na zallar murna ne Baffa kansa seda ya kauda kai gefe ya goge kwalla ganin irin wannan arziqi da ubangiji yayi masa. A ko da yaushe kalmar godiya ga Allah bata taba barin bakinsa, ya bashi lafiya, ya bashi arziqin mata, dukiya da Tarin Yaya ya kuma shirya masa su, sannan be jarabce shi da wani babban Alkaba'i daya dame shi a rayuwa ba banda qananun abubuwan da kowanne mumuni ba'a gaza jarabtar su dashi to shi kuwa me zeyi idan be godewa Allah ba da kuma Addu'ar neman cikawa da Imani dan abinda ya rage masa kenan a yanzu. Bayan mun gama hoto da yan gida Angwaye ma suka shigo, kowa yayi kyau amma wallahi Bashir dina ya fisu dan se ya zama tamkar wani wata a cikin taurari kamar yanda na zama Zara cikin yan uwa na, haka muka sha hotuna musamman da iyaye da manyan yayye suka fita aka bamu guri nan muka baje kojin mu aka dauki hotuna kala kala kafin muka dunguma zuwa gurin dinner. Taro ne akayi shi a tsare harda Baffa duk fulatancinsa seda Yayyen mu suka tilasta shi ya dan zauna a teburin da aka shirya masa da Aminan sa da be ma san an gayyato su ba, ganin su ya sa ya saki jiki haka iyayen mu mata Goggo ce dai seda aka kai ruwa rana dan seda muka yi mata hawaye nida Yah Bilki sannan ta fito se wani jan mayafi take tana rufe fuska yanda kasan ita kadai ce bafulatana a gurin. Cikin Awa biyun nan akayi komai aka tashi, anci an sha abinci na alfarma qarshen dai yan gayun Yan Abujan ma sun yaba gashi komai a tsare babu kida balle ayi rawa irin slow music din nan aka saka kawai aka ci abinci aka dauki hotunan tarihi seda aka fara watse wa nema qannen mu suka dage se an saka musu kida ai kuwa waqa biyu aka saka Baffa na hango yanda aka hade mata da Maza ana rawa yace a kashe kowa ya tafi haka muka kwana ana ta hirar taron nan dan babu qarya munji dadin sa. Washe gari da wuri aka miqa mu. Munsha kukan rabuwa, Junaidiyya aka fara tafiya da ita dan jirgi sukabi qarfe goman safe suna tafiya yan Bauchi ma suka dauki Amaryar su, kafin qarfe biyu an tafi kai Yah Bilki da Yah Fati ni kadai nayi saura tunda kusa da gida ne. Seda aka dawo daga kai su aka baro wadanda zasu tsaya musu budar kai kamar yabda kowa yasan Al'adar mu ta Gombawa, anayin sallar La'asar nima aka kwashe ni se gidan su BShir inda za'ayi budar kai na. Seda aka damqani a hannunsu, ga kayan garar da kashi biyu akayiwa ko waccen mu, ta gidan su miji daban tamu daman tun da akai jere kowa an kai mata gidan ta sannan ga turame da kwanuka harda Saitin Gado da akeyiwa Uwar miji seda akayiwa kowacce babban Gado dan Dubai haka aka kai musu. Bayan sun biya kudin budar kai da Turmin zani da tabarma nan qanne da abokan wasan Bashir suka fara zuwa kowa ta ajiye kudinta se ta fadi sunan da ta sakamun, wannan yar farar yarinyar da muka gani randa muka zo gurin Bashir ta taho da gudunta da naira goma a hannunta. A inda taga ana ajiye kudin ta ajiye kafin ta kama mayafina cike da rashin ji har tana neman ture mun daurin dankwali ta bude fuskata tana cewa "Na saka mata ANTY" mata suka dauki guda kowa ya yaba da ganin kyakykyawar Amaryar Bashir, hannunta na kama na zaunar da ita nace "Yaya sunanki?" "AMIRAH" ta fada tana yar dariyar yarinta, nan da nan naji ta shiga raina saboda ina da son yara daman gata yar fara kyakykyawa da ita. Anyi Budar kai lafiya seda aka kira sallah aka tashi, yan uwana sun mun kara dan ba qaramin kudi suka zuba mun ba haka dangin Bashir ma ba laifi sun mun liqi sosai bayan an gama qawayena suka tattare mana kudin mu muka koma dakin Bashir inda nan aka gyara aka sauke mu. Anan muka kwana se washe gari muka tafi gidan mu daga ni se Bashir dan daman ba'a raka amarya mu iya kacin su gidan su miji se ku qarasa keda shi kawai. Soyayya me tsafta suka shimfida a cikin gidan auran mu, ban qara tabbatar da Bashir yana qaunata ba se a yanzu dan a aikace yake nuna mun duk abinda bakinsa baya iya furtawa. Cikin sati daya da mukayi wata irin shaquwa me qarfi ta sake shiga tsakanin mu dan kullum muna manne da juna babu inda yake zuwa se masallaci da yayi sallah kuma ze dawo gida kuma har zuwa sannan babu wanda yazo mana kullum gidan mu a kulle muna ciki muna kashe juna da soyayya. Matsalata daya da Bashir dan irin taya aikin nan da naji ana cewa Angwaye na taya Amaren su shi bayayi, yana zaune zanyi komai na sedai na kawo masa idan muka ci abinci yana zaune zan tattare kwanuka naje na wanke qarqari ya zo Kitchen din ya tsaya ina aiki muna dan hira idan yan maganar na kansa kenan dan Bashir be fiya magana ba, miskiline seta raya masa sannan ni kuma gani da dan banzan surutu dole da qarfi da yaji tasa yake biye mun wani lokacin kuma na qaraci maganata idan na ishe shi ya jani ya kashe bakin maganar da Zazzafan Kiss shikenan. Seda muka kwana goma sannan muka fita, da yamma Aliyu yazo da yar motarsa one door daya siya dan shima ya samu aiki tuni kuma da yake bashida wani nauyi akansa shiyasa har ya iya siyan mota. Muna tafe yana tsokanata wai me nake bawa Bashir a dan lokaci haka yayi kumatu ya yi haske shima ze zo a ringa samma sa miyar Amarya ko ze dan farfado nidai murmushi kawai nakeyi irin najin kunyar nan har muka je gidan su Bashir. Cikin farin ciki Dada ta karbe mu harda Anty Amina Babbar yayarsu da bata koma Bauchi ba tunda tazo biki. Haka sukayi ta jana dan saki jiki nidai ina ta sunkuyar da kai, da Dada taga haka se ta tashi ta barmu ai kuwa na dan sake dasu dan basu da duhun kai nan da nan muka saba mukayita hira. Dab da Magriba Alhajin su ya dawo, seda sukayi sallah kafin Anty Amina ta rakani muka gaisa se saka mun Albarka yakeyi. A gidan mukaci abincin dare sannan Aliyu ya dawo muka tafi bayan na ajiye musu tsarabar da na kawo na manta ta a motar Aliyun ina jin Dada na Tambayar Bashir mun shiga gidan su Addah kuwa yace Aa, tace yayi qoqari ya kaini mugaisa. Da muka fita a zatona zamu shiga gidan mu dan tun tuni a qagare nake, saura qiris ma na dauki Fainusa dazu muje amma dai na danne . Ganin da nayi Mun dau hanya har mun wuce gidan yasa na tabo Bashir nace "Baza muje mu gaida su Baffa bane naga mun wuce gidan?" Be tareda ya waiwayo ya kalleni ba yace "Ai ni munje dasu Aliyu ranar nan mun gaishe su, ke kuma ba yanzu ba. Se kinyi wata sannan zamuje" ya maida kai suka ci gaba da maganar su da Aliyu. Tsabar takaici bansan sanda kuka yazo mun ba. Muzo har unguwar ina kallon kofar gidan na mu yace wani bazan shiga ba se nayi wata amma ai shi munje nasu gidan idan Adalci ne me yasa be bari duk maje lokaci daya ba. Sakin kuka na nayi ya fito fili, Yah Aliyu ya shiga bani haquri yana cewa Bashir "muje mana ko a tsaitsayene ta gansu" amma mutumin nan mirsisi yaqi magana har muka isa gida Aliyu ya ajiye mu na shige na barsu a waje yana wa Bashir din mitar be kyauta ba. Ranar haka na share shi, bayan mun kwanta ina jinsa yana wani shafani nai masa banza qarshe yaja tsaki ya juya ya kwanta nima na gyara kwanciyata a raina nace "kaima kaji yanda naji idan da dadi ai". Haka na tashi washe gari babu walwala, nayi duk abinda na saba na koma daki na kwanta, ina kallonsa se zarya yakeyi yana kallona amma dan baqin hali ya gagara bude baki yayi mun magana haka muka wani har dare dadai yaga abin nawa bana qare bane se jinsa nayi a cunkushe yana cewa "Dan bamu shiga gida jiya bane wai kike ta wannan Fushin to shikenan wani satin se kije" nayi masa banza kuwa tunda shi baze iya bani haquri ya rarrashe ni ba ai shikenan. Dakyar ya samu na sakko shima seda ya yarda randa na cika sati biyu ze kai ni nan da kwana uku kenan sannan na haqura, washe garin ranar da yamma yace na shirya zamu je gidan Addah ashe ma unguwar mu daya suna ta bayan layin mu ne. Sam Addah ta kasa zaune ta kasa tsaye sanda mukaje, haka ta ringa kawo mun Abubuwa se sannu da zuwa take mun kamar wadda tazo daga China ina kallon Bashir se hada fuska yake da gani abin be masa ba yaran Abokanan zamanta da yaransu suka ringa shigowa muna gaisawa da yake akwai yammata da yawa Sa'annina a cikinsu dama wadanda suka girme ni nan da nan muka saba. A nan Bashir ya tafi ya barni yace ze dawo da magriba, Amirah na naniqe dani qaramar Ummi ce me dan qyuya bata sakewa da mutane  Addah kuwa ta ringa bani labarai kala kala anan nake jin ashe su kadai ita da Dada iyayensu suka haifa anyiwa Addah aure ba dadewa suka rasu dan haka Nafi(Dada ta koma gurinta har tayi mata aure). Na zata tana da wasu yayan bayan su Amirah a cikin hirar da muke  naji su kadai ne yayanta tace dai ta haihu duk basu tsaya ba dan Babban Danta ma ya girmi Amina yayar Bashir. Da zamu tafi haka ta hada mun kayan yaji su citta da kanumfari da daddawa dasu kuka harda Barkono se kuma tace bari abarshi a daka se a kawo mun daga baya, Amirah harda kukanta da zan tafi wai seta bimu seda Bashir yayi mata jan ido sannan ta koma muka rabu da alqawarin zasu zo daman sun barmu mu dan huta ne tukunna. Kwana biyu naje gidan mu, wannan tun safe na tafi ai kuwa nasha Fada gurin Goggo kamar tayi me wai tunda nake wa na taba gani tazo gida sati biyu da aure sena tattara na tafi bazan zauna ba aikuwa na ringa kuka dakyar Baffa ya bata baki ta haqura na kuwa bar mata dakin ta na koma gurin Hajia Babba har dare seda zan tafi naje mukayi sallama tana sake buga mun warning din karta sake ganin qafata idan ba wani abu ake a gidan ba, a hanya Bashir yayi ta tsokana ta wai gashinan, da yace bazan zo ba ai harda daukar fushi dashi yanzu gashi naje din an koroni. Haka rayuwa taci gaba da mirginawa. Su Addah da kishiyoyinta uku masu kirki suma duk sunzo haka yaran gidan suna zuwar mun musamman da yanzu Bashir ya koma aiki in ya fita se gidan duk kadaici ya isheni in suka zo musha hirar mu kafin ya dawo sun tafi. Tunda Amirah taga hanya kullum seta zo, abinda na lura shekara shida amma ba'a sakata a makaranta ba kuma duk sauran sa'anninta na gidansu suna zuwa. Dana tambayi Addah dalili tana dariya take cemun "An kaita fa in gaya miki se tayi ta kuka wai bata son makaranta, ni kuma nace ina dalili tunda bata so yanzu a barta, in ta qara wayo dakanta ma zata ce a sakata". Mamaki ya kashe ni, wai shekara shida se wani lokaci zatayi wayo ta zauna a makaranta? Abinda na lura dashi daman sam Addah ta sangarta yarinyar nan yanda kasan goyon gwarawa babu kwaba gata da shegiyar rashin kunya ga barna duk abinda ta gani seta lalata abinda yake hadani da ita kenan ma na fara gajiya da zuwan naya dan kullum tazo seta bata mun wani abun. Akwai randa tazo inada wata yar Aku ta roba me magana, ina son Akun nan tun banfi shekara goma Hajjin su Anty Suhaima ta siyomun ita. A lokacin tace a kantin ita kadai ce tayi saura har Goggo tace baza'a siya ba dan rigima kawai zata zo ta hada a gida idan sauran suka gani amma Baffa yace se an siyowa Mamansa suka kuma yita nema ba'a samu wasu ba. Tun sannan nake ta boyonta ko wasa bana fitowa da ita ayi kai in kana so kayi wasa da ita sedai mu shiga daki kuma ka biya ni kudi shekararta Tara yanzu na qudure har Yayana se sunyi wasa da ita. Da yake babu wuta lokacin ni kuma ina Kitchen ina girki sena dakko mata na saka mata batir wai ta samu abin wasa. Ina Kitchen ina jinta tana magana Akun na maimaitawa, se ji nayi tana qundumawa Akun zagi ita kuwa Aku ta maimaita. "Yada wasan zagi Amirah ki dena babu kyau" na fada daga cikin Kitchen, se tace "Anty ita ce komai na fada se ita ma ta fadi irinsa" tana gamawa Akuma Ta maimaita. "Bazaki dena kwaikwayata ba ko" Amiran ta fada caraf Aku ta sake fada itama, se abin ma ya bani dariya, ina shirin in leqo na gaya mata rikodin Akun takeyi duk abinda mutum ya fada itama seta maimaita se ji nayi Amiran nacewa "Shegiya mahaukaciya wallahi kika sake kwaikwayona sena cire miki kai" ba kuwa ta rufe baki ba Aku ta dauka sena leqo ina cewa "Ke Amirah bana hana ki zagi ba in banda shirmenki batiri ne da ita tana rikodin...." maganata ta maqale daidai sanda tayi wurgi da Akun nan da qarfin gaske ta daki bango take ta tarwatse komai ya kama gabansa. Tsabar takaici kasa ko motsi nayi, yanzu Akun da har nagama tawa yarinyar ko kwarzane be sameta ba shine yanzu zata rada mun ita da qasa? A fusace na qarasa inda take na miqar da ita tsaye ina zare mata ido nace "Amirah bakida hankali me yasa zaki fasa?" Se kuwa ta wani murguda baki cike da fitsara tace "Na fasa din, ai seda na gaya mata ta dena kwaikwayona harda fa zagina take yi yanzu dana fasa se naga yanda zatayi". Saboda haushi ban san sanda na kai mata ranqwashi ba, kamar zanyi haqaye nace "kin san shekarun Akun nan kuwa ta ma girmeki amma saboda shegen rashin jinki shine zaki fasa mun ai kuwa sena zane ki yau a gidan gobe ma ki sake yimun barna". Fincikewa tayi ta nufi gurin Akun, injinta da shima ya cire ta hau tattakewa tana cewa "kika ranqwashe ni  toh na fasa na fasa din ayi koma menene". Lallai rashin kunyar yarinyar nan ta isa dole na koya mata tarbiyya tunda bata da ita ai kuwa na jata Kitchen na zari tsintiya na shiga tsula mata a jiki daman rigar ta me kamar Bea ce bata da hannu ai kuwa dukan ya shigeta tana tsalle tana ihu ina tsula mata ina cewa "Gobe ki sake yiwa wani rashin kunya tunda ke fitsararriya ce". Seda na mata lilis kafin na saketa, ta kwasa da gudu tana kuka ko ta kan Takalminta da Hijab bata bi ba ta bar gidan ni kuwa ko a jikina na tattare fasashshiyar Akuna idona ya ciko da kwallar takaici ganin babu ta yanda za'ayi ta hadu, a kan Centre table na ajiye jin abincina na kamawa a Kitchen. Ina kwashe abincin Bashir ya dawo, yasan yanda nake son Akun nan da mamaki ya kalli pisis din da suke ajiye ya kwalo mun kira na fito ina masa sannu da zuwa. "Meya samu Akun taki? waya fasa ta haka?" ya tambayeni yana kallona, se ji nayi hawaye ya silalomin na bude baki da niyyar magana hargagin Addah ya katse ni. A sukwane ta fado dakin tareda Amirah a bayanta da har sannan bata dena kuka ba tayi tumu tumu da ita qasa har cikin gashinta da naci wuya jiya na gyara mata shi tsaf da niyyar yau zamuyi kitso da gani birgima tayi a qasa. Ke Asma'u me Amirah tayi miki zaki kama ta kiyi mata wannan dukan kamar kin samu jaka" Ta fada tana hura hanci. "Ni ba abinda nayi mata Addah kawai dan na fasa waccen shegiyar Akun shine ta kama ta dokeni da zabori" Amirah ta fada cikin kuka kafin Addah tayi wani abu se ji mukayi "Fuu" Bashir daya fi kusa da Amiran ya dauketa da mari ta kuwa kwala ihu dan marin ya shigeta da gaske. "Zaki wuce daga nan ko sena tattakaki fitsararriyar banza da wofi, wato ke kika fasa har kina sake fada kuma an hukuntaki shine zakije ki kai qara toh zuwa kukayi a rama miki ko me" ya hayayyaqo mata kamar ze sake rufe ta da duka tayi bayan Addah tana hadiyar zuciya dan tuni kukan nata ya tsaya. "Idan ita ba'a rama bata ba ai kai seka zo ka dakeni dan ubanka se insan ka isa ka tarewa matar ka fada" Addah ta fada kafin ta juyo kaina tace "Ke kuma wannan ya zama na qarshe da zaki sake dukar mun Yarinyar idan ma ba cin zali ba akan ta fasa abin wasa kawai ki hau dukan ta to wallahi karki sake" ta juya fuu suka fice ni kuwa na rakata da ido. "Maganin ki kenan ai da kike jawo yarinyar kece baki san halin ta ba amma Yanzu gashi ta fara nuna miki, mtsw" ya ja tsaki ya shige dakinsa ya barni a tsaye. Daga wannan abu naja baya gaba daya da Addah dan ba'a fi kwana uku ba se gata da Amiran ta kawo su harda Ummi wai zataje unguwa akayi sa'a Bashir yana nan yace mata muma fita zamuyi ta ringa mita kuwa nidai suna fita na sakawa qofa muqulli to ina dalili yaro yayi maka ba daidai ba in ka hukuntashi a zo har gida a gabansa a ci maka mutunchi to ni banga ana haka a gidan mu ba. Bata haqura ba dan ba'a rufa sati ba ta kuma zuwa wai tazo duba mu kamar ma ba'ayi komai ba, ranar nayi Farfesun kaji akan da daddare se na soya mana doya muci dashi. Bayan na kawo mata ruwa da lemo na koma Kitchen din, har ga Allah banyi niyyar zuba mata ba dan kadan nayi. Ina da dambun nama harda kilishi su nayi niyyar na kawo musu se ji nayi tana cewa "Asma'u zubo mana farfesun mana idan da biredi ki hado mun". Se nayi tsam a Kitchen, a raina nace "ikon Allah" na dai samu dan bowl na saka mata cinya daya da rabin qirji dan fa be kai gudar kaza bama wanda nayi nasan Bashir kadai se ya tashi dashi ma. Ina ajiye mata ta kalli kwanon, se cewa tayi "meye wannan kika zubo haka, a gidan dan nawa a kawo mun wani abu kamar na roqa, matsa nan ki gani" ta miqe se gani nayi ta shige Kitchen abinta, ina tsaye ta dawo da kular naman dukka da biredin dana manta ban dakko mata ba ta zauna ta hau ci ta nayi mun hira. Abinda yafi qarfin ka aka ce seka mayar dashi wasa, haka na zauna ina kallon ikon Allah ta cinye tas har tana cewa wai tayar mata da kwadayi kawai yayi. Da zata tafi babu kunya tace idan muna da danyan nama na bata, na shiga Kitchen zan debo mata se gata ta biyo bayana, ta debi kwai, taga kayan miya suma ta diba nidai na saka mata kaza daya a leda daga yanda ta karba nagane kamar ta raina ne nayi saurin tare ta da cewa "Daga gidan gonar Baffan mu aka kawo mun, kinsan idan ya fitar da kaji yana rarraba mana da kwai" se tayi wata yar dariya tace "Au uhm kunji dadin ku kuwa" mukayi sallama ta tafi. Ina sane na mata haka dan karma tayi zaton dan nata da take iqirari ne yake siyowa bare har tayi iko dasu, daga gidan mu aka akawomun dan har yau kayan miya kadai Bashir yake siyowa sedai idan munyi sha'awar jan nama ya siyo danye ko gasashshe saboda tunda muna da komai na cefane kamar ma bama taba kayan garar nan, sannan kaji basa yanke mun da kwai. Idan na aika a siyomun a gidan gona Baba Idi Manager kyauta yake bani ko a bani ninkin na kudin dana bayar. Da naci da komai Amirah ta dawo zuwa tun Bashir yana fada shima har ya haqura sauqin ta daya mun koma makaranta dan haka bana zama Asabar da lahadi ne kawai take zuwa shima daga baya na takurawa Bashir akan yaje ya samu babanta yayi masa magana akaita makaranta haka akayi kuwa aka sakata har Islamiyya ma shikenan muka samu sauqin abun. Watan mu shida da aure ranar da safe ina zaune Yah Bilki ta kirani take cemun wai Goggo ta haihu, a kwance nake amma seda na miqe zaune nace "kinsan me kike fada kuwa haihuwa fa kika ce wace irin haihuwa ana zaune lafiya yaushe ma ta samu ciki?" "Wallahi dagaske, ni kaina bakiji yanda nayi mamaki ba amma kuka fa nayi zargin haka dan zuwan da nayi na qarshe nidai naga cikin amma se nayi zaton ido nane wallahi yanzu Su Bilal suka zo suke gaya mun munyi Auta" "Ikon Allah amma yanzu dan Allah wace irin haihuwa ce haka yaya nayi suma suyi gaskiya daga wannan an gama" na fada se Yah Bilki tasa dariya tace "Se ki gayawa Baffan ki ai bani ba, nidai gobe zanje naga Baby kefa?" "Nima in na taso makaranta inaga in biya goben yanzu dai ai bazata kori mutane ba ko daman abinda bata so a gani kenan yasa take kora ta in naje" na fada ina dariya, se tayi dariya itama tace "Yo ai sanin hali, yanzu da kin sani har na America tuni da labari ya tarar dasu, shikenan se mun hadu goben" mukayi sallama. Bashir na dawowa na gaya masa ina ta mita dan me Goggo zata haihu shida cikanki be qara ce mun ba tunda yace Allah ya raya. Washe gari kuwa daga makaranta gida na wuce, abin Allah ina ganin yarinyar naji ta shiga raina, haka na tasa Goggo a gaba kamar wata kakata da zolaya data gaji ma daki ta shige ta barmu Baffa kuwa se nan nan yake da Yar Babyn me kyau da akayiwa Huduba da Aminatu muka yi mata laqabi da Amna. Ranar a gidan muka wuni da yawa munje ga matan yayyen mu maza da muka tashi tafiya kowa ta kama hanyarta a motarta muka fito tareda Yaya Fati ina cewa "Bari na biki ki sauke ni a gida toh tunda kece yar hanyar mu" daidai mun qaraso inda Yayan mu na biyu a gidan Alhaji Yasir yake tsaye yana waya. Muka gaishe shi har mun gota ya tsayar dani sena dawo. Seda ya gama wayar ya kalleni yace "ke dawa zaki tafi" "Yah Fati ce zata sauke ni a gida" na fada ina dan wasa da hannuna dan yafi Alhaji Qarami zafi daukar sa muke kamar shine babban Yayan, "Ta tafi, kije Bello ya kaiki gida, ga wannan" ya fada yana miqo mun kudi da ban san ko nawa bane, sena karba nayi masa godiya na juya inda Yah Fati take jirana nace mata "Ki tafi Kawai, Baban Sharifa yace naje Bello direbansa ya kaini, kinga har kudi nasa mu ma se jibin zaku zo dai ko?" "wallahi kina sharafin ki yarinyar nan komai aka tashi ace ke wani tausayin ki ake ji a gidan nan bayan babu abinda kika rasa ta wani fannin ma kin fimu jin dadi dan dai ana ganin mu a qaton gida ne kawai, shikenan bari naje dare yana qarayi" muka yi sallama muka rabu. Kwana biyu dayin haka da daddare muna zaune aka buga get, Bashir ne ya fita ya bude se gashi ya dawo wai gurina aka zo sena zura hijabi nabi bayansa. Ina zuwa na ga Bello ne direban Alhaji Yasir daya dawo dani ranar nan da wata dalleliyar mota Toyota qirar shekarar baqa dukda dareni amma kana ganin yanda take qyalli. Gaisawa mukayi nace da Bashir "Bello ne direban Alhaji Yasir fa" se yace "oh ai ban san shi ba. Key da takaddu Bellon ya miqo mun yana cewa "Gashi Alhaji yace a kawo miki, tun jiya ma naso kawowa wallahi takaddun ne basu kammala ba se dazu, mota fa tayi kyau Hajia Allah ya sanya Alkahiri ya tsare ki da sharrin qarfe". Tsabar murna bansan sanda na dane Bashir ina dariya ba nace "wayyo dadi munyi mota muma munyi mota" shima dariyar yake ya riqeni ganin muna neman faduwa Bello ya juya ze tafi irin yaji kunyar nan na tsayar dashi na shiga gida da gudu cikin kudin da Alhaji Yasir din ya bani ranar nan na qirgo dubu biyar na bashi ya ringa kuwa zuba mun godiya ya tafi. A daren na kira Alhaji Yasir  nayi masa godiya "Ba komai, ki tabbatar idan kina buqatar wani abu ki ringa gaya mana" ya fada kawai ya kashe wayar. Na kira Baffa na gaya masa shima yace "Inye yar gatan Yayanta kice se munzo dani" nayi dariya. Haka na ringa kiran yan gidan mu ina fada musu abin arziqi kowa ya taya ni murna, badan dare yayi ba ma ba abinda ze hana ni ta fiya gida yanzu na nuna musu, haka nayi bacci da ido daya, bini bini na daga labule na leqa motar nan Bashir se dariya yake mun. 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 WATA KISHIYAR 🥰👹 (ALKAHIRI CE KO SHARRI) 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 Na Maryamah Farouk (Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah) Wattpad @MaryamahMrsAm Page 36 Shekarar Aliyu daya na samu cikin Jafar, nasha kuka sosai saboda ba qaramar wuyar raino nake ci da karatu ba sannan yanzu kuma ga wani sabon cikin har rigima se da mukayi da Bashir ya kuma tabbatar mun se ya bata mun rai in har wani abu ya samu cikin nan bisa gangancina. Haka na hada ciki da raino ga karatu da lokacin ina Level 3 ga hidimar gida idan na fita makaranta duk yammar da zanyi haka zan dawo nayi girki da abubuwan dana fita banyi ba kuma Bashir babu ruwansa ko yaya na kuskure ya ringa mita kenan. Ganin Aliyun yana cin abinci sosai yasa na tambayi Bashir ko zan ringa barinsa a gurin Addah idan zanje makaranta, da farko qi yayi seda na tasa shi da kuka sannan ya yarda washe gari kuwa da zan fita na hada masa duk abinda nasan ze buqata na kaishi gidan. Faran faran ta karbe shi musamman daman na hada dan ihisani na kaimata, na tafi makaranta ta hankali kwance tunda nasan za’a kulamun dashi. Ranar qarfe biyu na taso, tun daga Get din gidan nake jiyo kukan Aliyu gabana ya yanke ya fadi na qara sauri ina shiga na tarar dasu a tsatstsaye akan Aliyu da yayi faca faca da ruwan kwata yana ta tsanyara kuka abin tausayi. Da sauri na qarasa na daga shi, a bakin Mama Binta Kishiyar Addah nake ji wai Amirah ce ta dauke shi suka fita waje wasa shine wai ta ajiye shi ya tsallaka kwata ya fada ciki, ita Addah bama ta gidan tuni ta fice, haka na dauke shi muka tafi gida raina duk a bace. Idan ba wulaqanci ba taya za’a barta ta fita dashi har ya fada kwata. Seda ina masa wanka naga inda ya kuje a jikinsa, haka na lallabashi yayi shiru bayan na bashi abinci da paracetamol na ruwa dan jikinsa yayi duki kafin na goya shi na shiga aiki ina tunano irin tijarar da Bashir zeyi mun idan ya samu labari. Ilai kuwa yana dawowa ya fara dudduba yaron kamar yasan me ya faru se ji nayi yana kwala mun kira, haka muka kwana yana masifa ya kuma ce karna sake kai masa yaro ko ina nima din daman ba sake kai shi zanyi ba. Haka na ci gaba da karatu da raino cikina wanda yana wata takwas Bashir ya sake rasa aikinsa sakamakon korar ma’aikata da Banki sukayi haka suddan kuma ta rutsa har dashi. Sosai muka shiga tashin hankali musamman yanda korar tazo musu ba tareda tsammani ba gashi a lokacin shekara ta qare lokacin biyan kudin Hayar mu yayi ga shirin haihuwa ta shi kansa Bashir din a sannan ya koma Mesters kuma kowa yasan yanda Masters yake da cin kudi. Haka nayi ta qoqarin kwantar masa da hankali da nuna masa In Allah ya yarda komai ze zo da sauqi mu ci gaba da Addu’a kawai Allah ze kawo mafita. Hidimar yanzu data farkon Auran mu ba daya ba, a wancan lokacin muna da ajiyayyun kayan abinci wanda sune jigo sannan sauran buqatun mu ba wasu masu yawa bane yanzu kuwa shi yake siyan kayan abinci ga qaruwar Yaro da shima akwai nasa buqatun na yau da kullum da dole suna buqatar kudi chanjin rayuwar da muka samu se nan da nan ta nuna a jikina musamman saboda yanayin da nake ciki ga tsohon ciki ga karatu da yazo mana gangara. Haka muka ci gaba da malejin rayuwa kullum cikin saka ran samun budi daga qofofin ubangiji, da dan abinda nake samu daga kasuwancin da nakeyi nake riqe damu dan sam Bashir beyi wani tanadi ba ba kuma zan dorawa yan uwana nauyin da Allah ya sauke musu ba dan iya zumunchi sunyi mun ya kamata ace yanzu kuma shima ya jajirce ya riqe gidan sa. A sanda yana aikin Babu yanda banyi da Bashir ba akan ya ringa cire wani abu a Albashin sa duk wata yana saving amma yaqi. Shi irin mutanen nan ne da a rayuwarsa idan ya samu kudi kawai a biya buqatar da take a lokacin baya ajiyewa saboda buqatar kota kwana. Nayi nacin har na gaji akan bayan aikin yaje ya samu Baffa suyi maganar kasuwar ya ringa gwada wata sana’ar ko babu komai ya zama mutum yana da wata madafar bayan albashi saboda gudun bacin rana akwai sanda har magana ya gaya mun wai ko fata nake masa ya rasa aiki ya ringa fushi yana jin haushi na daga nan nace bazan sake masa magana akan yin wata sana’a ba. Abinda na lura dashi wannan a halin mazan Bauchi da Gombe yake sunbada amanna da aikin Gomnati, kadan daga ciki ne suka yarda da kasuwa, Nidai dana tashi gidan mu naga ba’a zaman banza zan ci gaba da saida saidena dan bazan dogara da se abinda miji ya dakko ya bani ba. A wannan yanayin na haifi Jafar, wannan karon a gida na na zauna daman kuma ban saka rai da samun komai a gurin Bashir ba kodan halin da muke ciki ma da yaya ya biya kudin haya haka dai akayi suna na kuma samu Alkahiri sosai daga yan uwana. Bayan haihuwar Jafar abubuwan da suka faru ba masu dadi bane dan sosai muka shiga matsin rayuwa, tun muna iya siyan kayan abincin wata a ajiye har seda takai mun koma awo a kullum na abinda za’a dafa kuma duk nice qarfin riqon gidan a abinda nake samu zan bashi yayi a haka har seda muka cinye jarin nawa duk ma abinda zan samu a haka yake qarewa tunda komai da shi mukeyi babu wani abu da yake shigowa Bashir daidai da ci gaban karatunsa da tallafi na yake yi seda takai har mota ta na siyar na bashi kudin akan ya kama wata sana’ar sedai wane tudu wani gangare kudin suka narke, Bala ya bawa akan ze saro masa kaya daga Lagos wai yan Fashi suka tare su suka karbe sukayi masa dukan tsiya dan seda yayi kusan wata a kwance yana jinya. Haka muka ci gaba kullum ina hanyar zuwa gida karbar kudi seda ta kai ni da kaina na fara jin kunyar hakan na dena zuwa, aiki kuwa kullum ina tafe, ina Teaching ga wasu training centers dana ke koyarwa suma duk dan dai mu rufawa kan mu asiri seda ya zama wata rana idan mun samu abinda zamu ci da rana sedai ni dashi mu haqura da na dare yara suci nakan kwana ina kuka wani lokacin idan na tuna yanzu fa akwai wadanda tunda suka somi rayuwa cikin irin wannan qunci da matsin suka tashi ko? Idan kaga yanda na koma sena baka tausayi yanda kasan nice Mijin ba Bashir ba dan shi yana zaune a gida zan fita aiki na dawo kuma na dafa abinda ya samu muci wannan abun yana bala’in baqanta ran yan uwana kuma yana daga dalilin daya sa duk suka zuba mun ido suga gudun ruwana ni kuwa ko a jikina, Ina son Bashir bana jin duk abinda zanyi masa na fadi kuma ko banyi dan shi ba zanyi dan yayana dan haka ban taba jin haushin kaina akan abinda nake yi ba. Abin takaici daya lokacin qannen sa da sukayi aure Allah ya taimake su gaba daya sun samu gidan hutu dan haka yanzu gidan su basu da wata matsala ko wacce na iya qoqarin ta se kuma ya zamana sun ware Bashir domin ko gidana yanzu babu wadda take zuwa tunda bani da abinda zan basu. Ita kanta Dadan yanzu wani gani gani takeyi mun idan munje gidan babu wannan sakin Fuskar irin nada wanda duk cikin zugar Addah ne, a cewarta baqin ciki da kyashi ne ya hana nasa a bawa Bashir kudi a gidan mu na gwammace mu zauna cikin talauchi ni da shi din saboda wai ina baqin cikin yana wahaltawa yan uwansa sama dani, a raina nace ashe sun san da yana da shi din ma su ya ringa wahaltawa bani ba dan kafin ya mun abu daya ya musu goma sannan wane baqin ciki zanyi da har zan zabi zama cikin Daidai da Addah se in manta rabonda na sakata a ido ko su Aliyu na kai gidan ba’a minti Ashirin se a dawo mun dasu tace fita zatayi, Amirah kanta yanzu ta rage zuwa idan nace mata me yasa se tace Addah ce take hana ta rayuwa kenan se kana dashi mutane suke yi da kai a duniya. Ana cikin haka wata rana Bashir ya shigo gida cikin tsananin murna yake nuna mun saqon gayyatar da wani wani kamfani suka aiko masa daga Lagos, a cikin ayyukan da Alhaji Qarami ya ke ta fafutukar nema masa se yanzu Allah yasa daya suka gayyace shi, a yanda yake gaya mun mutum biyu za’a dauka kuma su biyar aka gayyata Jarabawar gwajin nan da kwana uku ze tafi. Tun daga ranar na fara Azumi ina Yiwa Bashir Addu’ar nema sa’a. Gogan kuwa se shiri yake ya binciko tsofaffin littattafan sa yana ta karatu. Ana gobe ze tafi da daddare har wurin daya yaha zaune yana fama da takaddu na kalleshi nace “Baban Ali da ka ajiye karatun nan haka ka huta Addu’a ya kamata muyi tayi dan a irij wannan abun fa sa’a ake nema ba wai karatu ba”. “Ma’u kenan, a irin karatun da nayi na tabbatar da duk tambayar da sukayi mun sena amsata sannan duk wata kwarewar aiki da zasu nema ina da ita, kedai kawai ki fara shiri dan har na hango mu a Lagos” ya fada yana ci gaba da bude littafinsa, se na ja numfashi na gyara kwanciyata nace “Toh Allah ya tabbatar da Alkahiri”. Washe gari ya hau mota se Lagos, kwanan sa biyu ya juyo bayan sunyi Jarabawar ya dawo da tabbacin kamar ma ya samu aikin dan har yana ce mun “ko mutum daya zasu dauka nasan nine, bakiga yanda su kansu masu Jarabawar suka ringa jinjina qoqari na ba” Ni kuwa nace masa “Kadai ce In sha Allahu, kuma muci gaba da Addu’a idan rabo ne za’a samu”. Sati daya sakamakon ya fito amma babu sunan Bashir wasu mutum biyu daban ne dan daya ma babu shi a wadanda sukayi Jarabawar tare, ina jin abokin da yayi yana gaya masa wai dan wani Minister ne aka aiko da sunan sa dole aka cire mutum daya aka saka shi. Haka Bashir ya ringa qunci da bacin rai akan rashin samuwar aikin, duk yanda naso na nuna masa komai na rayuwa rabo ne idan Allah be tsaga da naka ba duk wuya haka zaka haqura bazaka samu ba amma yaqi fahimta qarshe ma abin ya zamar mana rigima har yana gaya mun magana akan niyyar samar masa aiki ne kawai ba’a yi ba aka wahalar dashi idan ba haka ba duk hanyar da muke da ita ace an rasa ta inda za’a samar masa aiki me yasa su yan gidan mu mata da maza da sun gama makaranta suke samun aiki ga Abubakar tuni ya samu chanjin aiki daga inda yake a Kano zuwa NNPC. Ganin fa yana neman ya raina mun hankali yasa nima na horance masa, nayi masa tatas na gaya masa ai ba haqqi na bane na samar masa aiki dan haka idan ze tashi ya nema tun wuri ya nema kuma na cire hannuna daga duk abinda ya shafi sabgarsa, idan har ya aureni ne saboda ya samu kudi toh ya sawwaqe mun kawai. Wannan abun ya bala’in dagawa Bashir hankali se gashi har yana bina yana bani haquri akan sharrin shaidan ne shi ba abinda yake nufi kenan ba, haka muka ci gaba da jalan ta rayuwa yau fari gobe baqi a haka na kammala karatuna na fara hidimar qasa. Ranar wata Talata da bazan manta da ita ba, muna zaune da yamma nida Jafar dan a lokacin Aliyu ya fara zuwa Islamiyyar da take cikin layin mu. Shekarun sa uku a sannan tuni bakinsa ya bude sosai dan haka nake hadashi da Amirah suna tafiya kuma sosai yake karatun dan in aka dawo ya ringa tilawa Bacci kadai yake saka shi yayi shiru. Lokacin zafine kuma babu wuta dan haka na shimfida mana tabarma a tsakar gidan muka zauna Jafar nata wasa da Yar motarsa me Batiri ni kuma ina duba takaddun Test da nayiwa dalibai na a makaranta Aka bugo Get, Hijab na na saka na leqa, Alhaji Buba ne me gidan da muke haya shida wani mutum da wani saurayi me kama dashi daga gani dan sa ne. Seda gabana ya fadi da ganinsu dan nasan zancen baze wuce na kudin haya ba amma ai da sauran kusan wata biyu nan gaba haka muka gaisa nace musu Bashir din baya nan. “Eh ba wurinsa muka zo ba munzo ne mu duba gidan daman mun riga mun gama magana dashi” Alhaji Buban ya fada. Sena kalleshi da mamaki dan ban gane su duba gida ba, “Wani abu aka ce ya samu gidan Alhaji” na fada ina kallonsa, se ya girgiza kai yace “Shi Bashir din Beyi miki bayani ba? Hidima ce ta taso mun yaro na zeyi aure dan haka ina buqatar gidan nan ze zauna a ciki, dalilin zuwan mu kenan yanzu ma dan ya duba ya gani ko akwai wani abu da za’a chanza kafin lokacin bikin” Alhajin ya fada ba tareda damuwar komai ba. “Amma kuma Alhaji muna da sauran lokaci kafin kudin hayar mu ya qare ko ba wannan ba ma ya kamata ka bamu notice da wuri domin mu nemi inda zamu koma ko?” “Ta yuwu kece baki da masani domin shi mun dade dayin magana dashi daga lokacin kuma zuwa yanzu ya kamata ace ya nemi wani gurin daban, maganar ragowar kudi kuma ba matsala bane zan mayar muku da abinda yayi saura a kudin hayar ku dan haka se ku fara shiri zuwa nan da sati daya nake da buqatar gurin”. Seda na hadiye abinda ya tokare mun maqoshi kafin nace “Shikenan, zamu tashi in Allah ya yarda amma yanzu babu yanda za’ayi ki shigar mun daki se ku jira idan mun kwashe kayan mu daga baya ku duba” ina fadar haka na mayar da qofar na rufe. Bansan hawaye nake ba seda naji Jafar yana goge mun fuska se kawai na saki kuka ganin haka yasa shima yaron ya fashe da kukan. Kuka ne na zallar baqin ciki da takaicin nake yi, yanzu saboda Allah ace an bamu notice mu tashi daga gida Bashir ba ze gaya mun ba kenan da se ranar da aka bashi ta cika zece na fita ko kuma se masu gidan sun watsar mana da kayan mu tukunna. Kwata kwata ni banga Lefin Ahaji Buba ba tunda gidansa ne yana da damar da ze buqace shi a duk sanda yaso sannan ya gayawa Bashir din tuni nice beyi niyyar gaya mun ba to yanzu ina zamu dosa wane tanadi yayi mana? Da dare yana dawowa na tare shi da maganar “Na sani kuma ina ta qoqarin ganin an samu wani gurin har yanzu dai babu, samun gidajen yayi wahala sannan kuma sun qara kudi” Abinda ya gaya mun kenan yaja bakinsa yayi shiru. Nayi masifar nayi bala’in amma ko kallo ban ishi Bashir ba qarshe na fashe da kuka haka na kwana ina tunanin mafita a raina, idan nace zan jira naga abinda zeyi bana tunanin samun mafita daga gareshi dan ko an samu gidan nasan bashi da kudin da ze biya dan chanjin da za’a bashi ba isa zeyi ba qarshe dai ni din ni zanyi fafutukar yanda za’ayi. Kafin safiya na yanke zuwa gurin Baffa na, shi kadai nake dashi da ze share mun hawaye masan kuma baze kasa sama mun mafita ba dan ko kusa ban hasaso rabuwa da Bashir ba akan wannan dalilin, gari na waye wa kuwa na shirya yara muka tafi gidan mu saboda haushi ko Bashir ma ban gayawa inda zani ba shima be tambayeni ba. Kuka na fashewa Baffa daya zuba mun ido yana kallon yanda na lalace na fita hayyacine kamar wata matar qauye. Seda na gama lissafa masa matsalolina yana ji, murmushi yayi kafin yace “Ko wanne aure da kalar qalubalensa Ma’u ayi ta haquri zan duba naga yanda za’ayi kafin lokacin da suka dibar mukun, tashi ko shiga cikin gida ku karya kin debo yara ga Sheik Jafar nan da gani bacci be ishe shi ba”. Haka na wuni a gida ranar ina jin kamar kar na tafi duk yanda Na ringa shan zagi a gurin yan uwana kowa na fadar ni na jawa kaina. “Ba kalar mutanen arziqin da basu zo kanki ba Ma’u amma kika nace se wannan Bashir din da ba mutunchi ne dashi ba. Ki ajiye maganar bashi da shi a gefe dan mu ba itace matsalar mu ba Aa girman kansa da yake hana shi fita ya nema shi ya jefa ku a duk halin da kuke ciki shi se aikin office zeyi ko ke ce yar wahala yana zaune ki fita ki nemo masa. Se kije kiyi tayi, ina dai jiye miki ranar da dadi ze zo ya dakko miki yar tayin cin arziqi ta hanaki zaman lafiya idan ma be yar dake a sannan ba tunda kin gama masa aiki” Anty Zubaida Yayar mu ta biyu a Mata dana tarar a gidan ta gayamun. Haka suka ringa gayamun maganganu kala kala wanda ko dar banji a raina akan Bashir ba, abinda na yarda na kuma amincewa zuciyata Bashir yana so na ba kuma ze taba juya mun baya ba dan haka zan taimakeshi da iya qarfina in har ni ina dashi. Da zan tafi Goggo ta sake yi mun nasiha akan nayi haquri na zauna lafiya da mijina kar na yarda da abinda yan uwana suke gayamun. Allah sarki ita kadai ce take qaunar Bashir a gidan mu se ko Baffa da bazance ga bangaren da yake ba. Haka na koma gida ba tareda na cewa Bashir komai ba. Kwana biyu a tsakani Baffa yace naje gida, a gaban Yayyena dukda suke gari da Iyayen mu ya mallaka mun takardun gida wanda aka siya da sunana sannan ya bani kudi naira miliyan biyu a sannan yace naja jari. “Ku zama shaida nayiwa Asma’u kyautar wannan gidan sannan ga kudi nan taje suja jari ita da mijinta su riqe kansu”. Haka na tattaro na dawo gida cikin dimbin farin ciki bayan Yah Abubakar ya karbe kudin daga hannuna yace naje nayi tunanin abinda zanyi dasu. Godiya sosai na ringa zuba wa na kuma qudurce a raina in sha Allahu bazan sake komawa gida da niyyar neman wani taimako ba. Zanyi tunanin abinda zanyi da kudin ba kuma zan gayawa Bashir batun su ba gida dai gashi nan muje mu zauna a ciki. Da na nuna masa takardun gidan ma kada ran kada han fuskarsa, washe gari mukaje muka ga gidan. Sabon gida ne me kyau ginin zamani a cikin GRA Flat me dauke da Qaton palour da Dining se dakuna bibbiyu a cikin corridor hagu da dama ko wanne da bandakinsa a ciki ga qaton kitchen da store tsakar gidan kansa a qalla zeci mota uku zuwa hudu sannan ga dakin me gadi. Ni kadai na ringa tsalle ina murnata Allah sarki Baffana Allah ya biyashi da Aljanna, tun a ranar muka fara kwashe kaya, a kwana na uku muka tare bayan da yan uwana da Abokanan Arziqi suka rakani kowa se yaba guri yakeyi yanda yayi kyau dan har kujeru da labulaye na sake. Satin mu daya a unguwar na fahimci matsalar masu kantina da take damun gurin duk abinda kake nema seka fita can babban titi ko kaje kasuwa. Ni da nake neman abinyi se na yanke shawarar bude provision store kawai dana gayawa Yah Abubakar shima yayi na’am da maganar nan da nan yasa aka fashe dakin me gadi aka sake ciyo filin cikin gidan aka yi babban shago a gurin. Lokacin da nakeyiwa Bashir zancen muna zaune se yake cemun “ai kuwa hakan yayi dan kinga ko ni ma se na ringa zama a gurin kafin na samu wani abinyin”. A lokacin ba qaramin dadi naji ba, dan daman tunanina kenan amma ina tsoron na gaya masa ya fassara maganar da wata manufa ko yace na rainashi shi yasa na yanke kawai zan sa a nemo min yaro da ze ringa zama tunda ga qofa anyi ta cikin gida na ringa leqawa naga yanda abubuwan suke tafiya. Cikin dan lokaci aka hada shago sosai aka shaqe shi da kayan masarufi harda su ruwa da Lemo duk muka zuba cikin ikon Allah kuma ya samu karbuwa dan sosai ake ciniki kafin cikar wata biyu seda ya zamana har buhun huna muke siyarwa na kayan abinci da muka ga ana yawan tambaya. Bashir ne yake zama se wani yaro Shafi’u dayazo yace ze ringa taya shi. A dan qasan mu yake maraya ne ake ruqonsa a gidan qanin Babansa sedai beyi sa’ar mariqiya ba ai kuwa na riqe shi sosai gashi da amana. Shekarar mu daya a gidan na sake haihuwa yar mace da se naga kamar Bashir yafi yin murna akan ta sama da sauran haihuwar da nayi har na ringa tsokanar sa wai saboda an samu Dada ne yasa yake murna amma yace Aa shi ba sunanta ze saka ba. A raina har na dauka ko ni zeyiwa kara ya saka Goggona se ji nayi ya mata huduba wai da Aisha Farida. “Ni na zata Dada ko Goggo zaka saka ai” na fada bayan daya gaya mun sunan, se ya kalleni yace “Bani da ra’ayin yiwa wani takwara, ko Aliyu da kuke zaton sunan marigayi Aliyu ne kawai ra’ayin kainane”. Haka naci gaba da rainon Faridata dan tuni an saka Aliyu da Jafar Makarantar Boko da Islamiyya. Nisan da mukayi dasu Addah be sa Amirah ta dena zuwa ba dan yawanci duk Juma’a se sunzo musamman tunda na haifi Farida wani lokacin ta kwana daya ko biyu wani sa’in ma ni zan kira Addah nace ta turo mun ita tayi mana kwana biyu dan yanzu ta fara zama yammata ta rage fitsara da rashin kunya abu daya yake hadani da ita qazanta da rashin son aiki dan in tazo se nayi da gaske take kama mun ayyuka ga bata guri haka zasu ci abinci su bata ko ina idan bani nace a kwashe ba sedai su zauna a cikin dattin. Daman batayi mun raino qarqari ta in zanyi wani abun na ajiye mata Faridar ta kula da ita amma fa ko zata kwana tana kuka Amirah bazata goya mun ita ba bare naci arziqin tayi mun wankin yara ko yi musu wanka ba tayi to kanta ma se nayi dagaske take wankan bare tayiwa wani. Watannin Farida Shida Allah ya karbi rayuwar Baffan mu sanadiyyar ciwon ciki da yayi na kwana daya har seda aka kaishi Asibiti inda acan ya rasu. Fadar irin tashin hankalin da muka shiga ma bata lokaci ne, munyi kukan rashin Baffa babban bango ya fadi se dai mu bishi da fatan Alkahiransa da halinsa na gari su bishi. Rasuwar Baffa da kwana Arba’in aka yi mana rabon gado kamar yanda ya bar wasiyya bayan an gama tattara komai kowa aka bashi kason sa. Wannan karon ma ba’a bani komai nawa a hannuna ba dan ana gama rabon Yah Muslim ya danqawa Alhaji qarami nawa dana Amna. Bansan dalilin da yasa sukeyi mun haka ba, amma koma menene banyi magana tunda nasan baza su cutar dani ba. Seda Alhaji qarami ya gama tsara duk yanda yake ganin yayi sannan ya sameni har gida wata rana yake gaya mun, mota biyu ya kawo mun cikin rabona yace gashi nan se na dauki daya na bawa Mijina daya. Na samu gonaki manya har biyu yace za’a ci gaba da noma su kamar yanda akeyi dabbobi na suma ze zuba mun su a gidan gonarsa. Akwai fili manya guda biyu dana samu se ya bani shawarar tunda mun samu wani gida me flat takwas a Abuja aka raba mana ni biyu, Junaidiyya biyu se nasa guda hudu idan na yarda ayiwa kowanne kudi muyi musanye ya karbi filayen ya bani gida itama idan tana so ayi haka mu ringa karbar kudin hayar duk shekara dan a cikin gari suke nan take na amince na kuma bar masa duk sauran abubuwa a hannunsa yaci gaba da kular mana dasu kafin ya tafi ya turamun zunzurutun miliyoyin kudade na a account da seda jikina yayi sanyi da ganinsu. Rayuwa kenan, shi wanda ya tara su yanzu tasa ta qare muma da muka samu wata rana haka zamu tafi mu barsu, shawara muka yanke akan gidan mu kar a tabashi, abar shi a yanda yake tunda kowa sun san kason su kowa mahaifiyarsu tana ciki sannan muka samu Qaton fili muka siya akayi Babbar Makarantar Islamiyya da masallaci Muka kuma bude foundation ta tallafawa Marayu da mabuqata me sunan ABDULLAHI TUKUR KUMO FOUNDATION ladan Allah ya kaiwa Baffan mu. Duniya sabuwa tuni al’amura suka daidai tar mana. Na bawa Bashir mota daya sannan na hada masa da kudade masu nauyi, Alkahiri babu wanda na manta dashi dan hatta su Fainusa da suka yanke alaqa dani yanzu sun dawo kuma ban qisu ba na karbe su da hannu biyu ba wai dan bani da wayo ko ban san me nake yi ba, Aa shi wanda kafi a rayuwa har abada ka fishi arziqi kuma kashi ne kowa yazo ya dangwala. Har sannan Bashir na zama a shago amma ba na qofar gidan mu ba dan a cikin kudi na na bude babban super market acan kan titi shine manager muka dauki ma’aikata tsohon kuma na barshi a hannun Shafi’u da sabon yaron daya samo yake tayashi saboda na mayar dashi makaranta se da yamma yake zama a Gurin. Bayan fitar Su Goggo takaba kawai ta taso da wata maganar wai zata koma Yola ta daura aure da Baffa Sama’ila. Qiri qiri muka nuna qin Amincewar mu gaba daya seda Alhaji Qarami ya tsawatar mana sosai akan me yasa mu zamu haramta abinda Allah ya halasta, babu wanda ya isa ya hana mahaifiyarsa qara aure a cikin mu gaba daya ko da kuwa cewa sukayi zasu kawo mazan cikin gidan mu tunda dai suka da kason su. Haka muna ji muna gani aka daura musu aure da Baffa Sama’ilan ta shirya komawa Yola nan na tada sabuwar rigimar sedai ta bar Amna bazata tafi da ita ba a wannan karon dai na samu goyon baya se kuma rigima ta koma tsakanin manyan cikin mu mu Ashirin da bakwai a sannan maza da mata masu aure kowa yace shi ze riqeta daga qarshe dai nayi nasara riqon Amna ya dawo hannuna wanda Bashir da kansa ya goya mun baya aka bani ita. Riqon Amna da na karba wane tudu wane gangare se ganin Amirah nayi da faggon kaya Addah ta kawo ta wai Addahn zasuyi tafiya zata je Niger, daga tafiyar sati biyu taji dadi da su Addan suka dawo se cewa tayi bazata tafi ba, Bashir zeyi fada nace ya barta ta zauna zan riqe dan har ga Allah ina son yarinyar kuma ina so naga tarbiyyarta ta inganta dan duk in tazo mun sena ga abinda beyi mun ba a cikin halayyarta wannan shine mafarin dawowar Amirah hannuna. Sosai Allah ya sanya Albarka a cikin kasuwancin mu, kudin da na bawa Bashir a cikin super market din shima ya saka ake juyawa, wata dabara da nayi masa muka zauna akayi rubutu kudinsa da yake ciki nace masa ya cigaba da juya su duk ribar daya samu ya barta a ciki karya cire sannan za’a ringa biyansa a matsayinsa na manager kamar sauran ma’aikata, da Allah ya sakawa abin Albarka se gashi muna neman yin kankan kan dashi a mallakin shares na super market din. Salin Alin muke zaune rana daya Bala da rabon dana ji duriyar sa har na manta yazo mana ziyara. Faran faran muka gaisa na basu guri shida Bashir na koma ciki, bansan me suka tattauna ba bayan tafiyarsa na fara ganin chanjin fuska a gurin Bashir. Kwanaki biyu a tsakani ya dena fita super market, a rana ta uku ne nayi masa magana se ce mun yayi “Akwai sauran Ma’aikata nasan zasu kula da komai” “Amma baban Ali kasan dai yanda mutane suke yanzu idan babu idon ka zasu iyayin yanda suka ga dama, ka manta rungon lissafin da suka ringa yi mana kwanaki ko” daga wannan maganar da banga abin zafi a cikinta ba se Bashir ya hau fada yana cewa “Ni na gaji naga alama kin mayar dani wani yaronki kina zaune ina miki neman kudi ko? wato kina so na saka ido a Shago dan kar a cuceki amma kika kasa aminta ki damqamin gadonki a hannuna na kula miki dashi. Daga yau na dena zuwa, kinemo wanda ze ci gaba da kular miki da gurin” haka yai ta fadar maganganun sa ni dai na tsaya kawai ina Jin ikon Allah. Kusan sati baya fitar dan haka na nemi Nasir qani na ya maye gurbinsa a gurin sannan ga Naziru qaninsa da daman yana zuwa na kwashe shi shida duk tsiyatakun da yake ji dasu na watsar dan ni yanzu hidimomin gabana sun ishe ni. Beci gaba da zuwan ba amma dai ya dawo yana neman shiri dani, nima ban nuna masa komai ba muka ci gaba da sabgogi cikin hukuncin Allah se gashi ya sake samun aiki a Ma’aikatar haraji ta qasa reshen Gombe. Aikin da Bashir ya sake samu ya tabbatar mun da cewa idan har yana dashi babu abinda baze yi ba, rayuwar mu se sambarka idan ka cire sabanin irin na yau da kullum da a kowanne gidan aure anan samun irinsa bani da wata matsala da Bashir. Albashin sa nada tsoka dan haka a wannan karon na bashi shawara daya siyi gidan da muke ciki ya zama nasa, kai tsaye ya amince yace ze ringa biyana duk wata na yarda, da na gayawa Yah Abubakar a take ya karbe takaddun yace kuma A ringa tura kudin ta account dinsa har zuwa sanda ze biya sannan a chanza suna ya koma nasa abun nan kuwa ya qona ran Bashir ya ringa mita yana masifa nidai bance masa komai ba cikin qanwanin lokaci kuwa ya biya kudin tsaf aka chanza takaddu aka bashi ni kuma Yayan ya siyar mun da shagunansa guda biyu a wata babar plaza dan ina so na fara siyar da kayan yara Anty Suhaima zata ringa turomun su daga UK. Bayan Farida na haifi na sakw haihuwar Da Namiji, kai da fata a wannan karon na kafe se Bashir ya sakamun sunan Baffana, dan gaske kuwa ya murzawa idon sa toka yace sedai na siyi ragon suna, dukda naji zafin abun amma haka na siyi manya manyan raguna guda biyu harda Bijimin Sa na qauri aka yankawa Abdallah na. TUSHEN MATSALATA Shigar Amirah Ajin Babbar Sakandire yazo mata da wani sabon tashen fitsara da rashin mutunchi. Amirah Kyakykyawar Yarinya ce Fara tas me gabaren girma a shekaru sha hudu qugunta ya bude qirjinta ya cika tazama budurwa sosai da bazaka yarda ba idan aka fada maka shekarunta. Abinda ya fara hadani da ita shegen rawar kai da kule kulen samarinta dan har ta kai an fara zuwa sallama da ita. Zuwan saurayin na farko da kaina na fita na kora masa jawabin karya sake zuwa, hakan da akayi kuwa saboda rashin kunya har gurin Addah takai qarata wai ka korar mata saurayi. A sannan da Addahn tayi magana na ce mata “Tunda kika bani ita ta zama yata dan haka zan lura da ita ne a matsayin uwarta idan kuma ba haka ba sedai ta dawo nan se tayi duk yanda take so amma muddin tana gabana Ba yanzu Amirah zata fara kula samari ba, se ta gama makaranta idan bata da burin ci gaba a sannan na yarda zamuyi mata aure”. Jin da tayi nace ta koma ya sa ta haqura har da yiwa Amiran fadan da be kai zuci ba muka koma gida ashe bata deba ba, idan suka tafi Islamiyya seta tura sauran yara ta tafi warkajamin ta se lokacin tashi yayi su dawo wata rana Allah ya dawo da Bashir da wuri gida ya kamata a can farkon layi a motar saurayi suna zance har yana bata Ice cream a baki, ina Kitchen suka shigo tun daga get yana tamola da ita ashe an dade ana kai masa gulmar a unguwa yau Allah yasa ya gani har da daddare tana satar hanya ta fita hira ban sani ba. A wannan karon ma dagewa yayi yace seta koma gida taje can kome zatayi a gaban Addahn amma zata lalace a nan ba ace a gidan sa ne, seda nayi ta bashi baki sannan itama naja mata kunne dakyau kafin ta shiga hankalinta. Gashinan na yau dana gobe 😂😂 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 WATA KISHIYAR 🥰👹 (ALKAHIRI CE KO SHARRI) 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 Na Maryamah Farouk (Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah) Wattpad @MaryamahMrsAm Page 37 Takun kumi Bashir ya sakawa Amirah na daga gida se makaranta hakan ya taqaita duk wata firirita data fara dan yanzu ba inda take zuwa ba kuma wanda yake zuwa gurinta ban dai sani ba ko idan ta tafi gidansu tana yin hirar a can. wata rana nayi baquwa, maqociyata ce Maman Ahmad ta shigo muna zaune su Amirah suka shigo daga makaranta. Uniform dinsu irin me guntun skirt din nan me da riga me dogon hannu se doguwar safa da dan qaramin hijabi dan haka sosai kayan suka bayyana qirar jikinta musamman ga wata tafiya data samu a kwanakin nan takeyi tana gantsaro qirji. “Maman Aliyu wai qanwar kice wannan ma” Ta tambaye ni bayan da suka wuce ciki, se na kalleta ina murmushi nace “Eh, qanwata ce me kika gani?” “Qanwarki ciki daya ko kuma ta dangi?” Ta sake tambayata ba tareda ta bani amsa ba, “”Gaskiya ba qanwata bace,qanwar Baban Ali ce diyar yayar mahaifiyarsa” “Lallai Maman Aliyu se a barki, yanzu duk yayan danginsu qanana ki rasa wa zaki dakko se wannan qatuwar budurwar zaki ajiye a gida wai cousin din mijinki kina kallon Yarinya wanda be sani ba in ya kalleku ma se yace kishiyoyine wallahi nidai bazan iya ba, kema kuma tun dare ne miki ba kisan abinyi tam” Maman Ahmad din ta fada. Se nayi murmushi nace “Girman jiki ne fa kawai Maman Ahmad ko sha shida bata cika ba ina ga idan ma Bashir kike tunani nasan babu abinda zeyi da ita ko aure zeyi baze nemi qaramar yarinya ba balle wannan da sam ba tsarar sa bace” “Ai wallahi ta wuce kice mata yarinya dan duk abinda mace take taqama dashi gashi nan a jikinta dadin da dawa ga quruciya meze dami namiji da qananun shekarunta bayan kina kallo yanzu yayin yan sha shidan sukeyi, shiyasa randa kika aiko su da Amna ko palour ban bari sun shiga ba dan Abban Huzaifa yana nan shi daman ido a farar fata, tun wuri kisan nayi wallahi kafin kiji kidan Janaral a sama”. A lokacin jin Maman Ahmad kawai nayi bawai na dauki abinda take fada da muhimmanci bane dan na yarda a zuciyata Bashir baze taba kallon Amirah a matsayin mace ba balle har yayi sha’awar auranta. Yarinyar da banda kyara da tsangwama babu komai tsakaninsa da ita har haushi nakeji idan yayi mata wani abun, barar magi na bawa Amirah idan har na kuskura Bashir ya sani to ranar baze ci abincin ba saboda yanda yayi mata tambarin qazanta balle har takai ace ze aureta na tabbatar wannan ko a mafarki ba abu ne me yuwuwa ba. Shigarta SS3 yasa ta qaro wani sabon tsagwaron rashin kunya da fitsara. Ganin ta takeyi kai daya dani dan yanzu idan na gaya mata magana ma se ta ga dama zata aikata, fita kuwa ko Bashir ze kasheta idan ta dawo setaje daman tuni ta sallama Islamiyya ta dena zuwa qarin daurin gindin data samu a gurin Addah harma da Dada kanta dan sunce data kammala makaranta aure zasuyi mata dan haka dole a barta ta fara tsayuwa da samari ta samu wanda zasu daidai ta a ciki. Nima banqi ta tasu ba tunda har aure za’ayi mata ya kamata a barta ta farayin zancen dan haka koda Bashir yace sedai tabar masa gida ko kuma in zatayi zancen ta ta tafi gidan su se nace masa baza’ayi haka ba. Dakyar na lallashe shi ya yarda sedai ya kafa mata sharadan kar ta kuskura ta mayar masa da gida centre tara samari duk randa ya ga sama da mutum biyu suna zuwa gurinta se ya mugun saba mata daga nan ta fitar da wanda take so a ciki ta sallami daya amma da yake me kunnen qashi ce kullum da wanda zata gayyato yazo gidan. A cikin samarinta akwai wani Yaro Sadam, irin fitinannun yaran masu kudin nan ne. Tana bala’in sonsa musamman yanda yake mata barin kudi duk sanda zezo haka ze ciko ledoji niqi niqi da kayayyaki ya kawo mata sannan haka zebi su Aliyu da kudi idan sukaje suka gaida shi wani sa’in harni yake shiga ya gaisar, yana da kirki amma idonsa a bude yake na kuma tabbatar ita kanta Amiran ba dagaske yake son ta ba duk yanda kuma naso na nisar da ita qarshe dukda ba kai tsaye ta fada ba se jin ta nayi tana cewa duk baqin cikin mutane seta auri Sadam da kowa ze ringa wani ce mata ba auranta zeyi ba, daga ranar na cire bakina a sabgar samarinta, Allah Allah nake ma ta qarasa makarantar ayi mata auran kowa ya huta. Bazan taba manta wata rana da mukaje gidan Dada ba, akwai wani Lace me kyau da tsada da nayi mana nida Amiran da Amna harda Farida da sallah shi muka saka ranar mukaje. Muna zaune kamar an matsi bakin Addah se cewa tayi “Baku ganku ba wallahi Abin sha’awa kamar wasu Uwar gida da Amarya”. Ban kawo komai ba a raina nayi murmushi muka yi hirar mu muka gama, har mun tashi zamu tafi Addah take cemun “Ni kuwa wata shawara nake nema Asma’u, kinga nida Nafi mu kenan shaqiqai da iyayen mu suka haifa, gara ita ma Allah ya bata yaya da yawa ni kuwa kin gansu nan biyu kamar kunnuwa. Shine nayi wani tunani ina so ko bayan ranmu zumunchin Yarana da nata ya dore kinga ta hanyar Auratayya ne kadai hakan ze tabbata. Toh yanzu ina so na gabatatar mata da maganar cikin yaranta maza daya ya nemi Amirah ko ya kika gani?” “Kai Amma kuwa kinyi tunani me kyau Addah idan abin ya yiwu kuma zakuji dadi wallahi Allah ya tabbatar da Alkahiri yasa zamu ga lokaci” na fada sak da zuciya daya dan dagaske naga kyan tunanin ta, Auran zumunchi yana da dadi idan yayi kyau. A lokacin tunanina gaba daya kan Amiru ya tafi dan shine me shirin aure a sannan amma kuma sam basa shan inuwa daya da Amirah saboda rawar kanta. “Idan Allah ya qulla abun haka zasu shirya su zauna tare” na raya a raina. A haka muka ci gaba da lallabawa har Amirah ta fara rubuta Jarabawar fita daga sakandire lokacin ina da tsohon cikin yan biyuna. Daman iya WAEC tayi, dan haka suna gamawa ta tattara kayan ta ta koma gidan Addah haka kawai ba tareda wani abu ba, nima ban takurata ba, nadai tambayeta ko wani abu aka yi mata tace Aa daga nan na barta ta tafi. Ranar da na haifi yan biyu ranar Bashir ya samu aiki a wani Babban Oil company a Lagos. A tsakanin watanni uku Alhaji Qarami ya tura masa da Advert dinsu yace ya cike, yana rashin mutunchi da fadar maganganun sa dai ya cike din cikin ikon Allah kuma da yake se a sannan rabon sa ya tsaga se gashi suka gayyace shi Interview shine yanzu kwasam muna Asibitin sun aika masa da Email cewa sun dauke shi aiki. Fadar irin farin ciki da murnar da muka shiga ma bata baki ce, Allah kenan me kyauta da qari a kuma sanda yaso. Lokaci daya ya bashi kyautar yara har biyu sannan ya qara masa da tukuicin Aiki me gwabi irin wanda ya dade yana fatan samu se gashi ya same shi a sanda be taba zato ba. “Albarkar yan biyu kenan, yanzu Legas din zaka koma kenan? Daman ina so naje legas nima naga yanda take yanzu tunda dana zeje kaga na samu gidan zuwa” Addah ta fada cikin murna kamar ta taka rawa musamman jin yanda su Amiru suke ta zuzuta irin aikin da Bashir din ya samu da kuma Albashin da ze ringa kwasa a wata. A ranar aka sallamo ni na koma gida, da Daddare Bashir ya shigo dakina, fuskarsa dauke da murmushin da na dade banga irinsa ba. Seda ya dakko yan biyu daga cikin gadonsu kafin ya dawo kusa dani ya zauna yana kallona yace “Wane suna kike so a saka musu” Se da na kama baki ina yar dariya nace “Tofa, yaushe aka fara haka? To bana dai bani da kudin siyan raguna har hudu dan haka ka saka musu duk abinda kaga yayi maka”. “Kina so ki ringa dawo da abinda ya rigada ya wuce, dagaske nakeyi, ki zabar musu sunan da kike so kin cancanci fiye da haka ai” ya fada yana kallona. “Toh Daya dai a saka masa sunan Baba dayan kuma na bar maka zabi” Da daddaya yayi musu huduba, seda ya gama ya miqo mun Hassan yace “Ga Ahmad” sannan ya bani Hussain shima yace “Muhammad Tukur”. Sosai naji dadin karar da Bashir yayi mun ta saka sunan Alhaji Qarami dan kuwa ya cancanci sama da haka a gurin mu. Wannan haihuwar dai nayita da qafar dama dan sosai Bashir yayi bajinta ya gwangwaje ni da zadaddun sururu na fitar suna haka yaran ma akwatunan su tsaf aka ciko da kaya, ga kuma kayan takwara da Alhaji Qarami ya jido mana abin dai se sam barka haka shagalin sunan da mukayi kansa bazakace haihuwa ta biyar bace tamkar sunan Aliyu da akayi shi lokacin ina cikin gata na a gidan wannan kuwa ya samu qarin tagomashin cigaban zamani. Tuni Bashir ya kama aiki a Lagos bayan da ya dauki leave a tsohon gurin aikin sa a matsayin ze tafi qaro karatu saboda baka barin aiki kai tsaye har sekaga kamun ludayin wanda ka samu tukunna. Shi kadai ya tafi Lagos duk qarshen wata yake zuwa Gombe. A cikin shekara daya da fara aikin Bashir rayuwa ta qara sauya mana sauyi irin na Alkahiri, ba qananun kudi yake karba a Albashin sa ba sannan ga Kasuwancin mu da Allah ya sakawa abin Albarka tuni mun sake bude branches guda biyu bayan na farkon a wasu unguwannin ga kuma harkar siyar da baqin mai daya kafa bayan daya fara sabon aikinsa ya zamana yana supplying daga kamfanin zuwa gombe ya rabawa yan sari abin dai se godiyar Allah kawai. A shekarar ya biyawa Dada da Alhajin su Aikin Hajji suka tafi tare da shi kansa bayan sun dawo ya sake biyawa Addah da Anty Amina Babbar yayarsu harda Amiru sukaje Unarar Mauludi. Bayan dawowar su Addah da sati daya sega Amirah ta dawo mun harda jakar kayanta bayan kusan shekara guda da barinta gidan, yanda sanda zata tafi ban hanata ba haka yanzu ma data dawo ban tambayeta dalili ba ban kuma chanza mata ba muka ci gaba da zaman mu kamar baya. Abun daya fara hadamu bayan ta dawo wasu halayen data tsiro dasu, Duk lokacin da Bashir zezo gari yanda zanyi shiri nayi kitso dasu lalle haka Amirah ma zatayi tamkar matar gidan taci kwalliya itama ranar da ze dawo ta kame a palour. Sannan a da idan har Bashir yana gida indai bashi ya zaunar dasu ba da daddare daga mun gama cin abinci zasu shige dakinsu tunda ko wanne daki na saka musu Tv idan ma kallo ne zasuyi acan wannan karon kuwa tun dawowar ta idan muna zaune itama zata nemi guri ta zauna ne babu ruwanta. A ranar farko data fara zaman dakansa ya mata magana ta tashi hakan be hana washe gari ta sake zama ba har tana tsoka baki a cikin hirar da mukeyi nan ma yayi mata kaca kaca kafin aka samu sa’ida har ya tafi basu sake haduwa guri daya ba. Wani rainin hankali data samu ma se ina waya da Bashir din zata zauna ta tasa ni a gaba tana kallo, idan nayi mata magana se tace mun wai “Wallahi Anty soyayyar ku da Yaya tana bala’in burgeni shi yasa nake zama nayi kwas, Kai Allah nima ya bani miji irin yaya mu kwashi romon soyayya”. Wani lokacin kuka tace “Dan Allah Anty ki ringa koyamun yanda zan mallake zuciyar mijin da zan aura nima na zama kamar ke a gurinsa ya ringa riritani irin yanda Yaya yake miki” idan ta fadi haka se nayi dariya nace “Nidin har wani riritani Baban Ali yakeyi kenan, miji kuma ai banga kin dakko hanyar samun sa bama dan ni rabon da naga kinyi waya da wani a gidan nan ko anzo gurinki har na manta man Amirah anya lafiya?” “Lafiya lau Anty, kedai ki taya ni da Addu’a kowa se yayi mammakin mijin da zan aura”. Hutun da Bashir ya sake dawowa ta bullo da sabon salo, wannan karon se dare ya tsala irin 10-12 nan kawai zata sako qananun kaya wando skin tight ko Pencil skirt daze fito mata da surarta ta kai babu dankwali ta saki dogon gashin ta ta bazo turare ta fito tana miqe miqen iskanci irin ala dole daga bacci ta tashi har kuma ta kalle mu tace wani “Au har yanzu Anty bakuyi bacci ba? Ruwa na tashi zan sha mun manta bamu shiga dashi dakin ba” sannan ta tafi tana rangwada ta bata lokaci a Kitchen kafin ta koma daki. Na daya na biyu ranar a daren na same ta naci mata mutunchi musamman abinda ya qara tunzurani ganin yanda Bashir ya ringa binta da kallo har yana cemun wai me yasa na dena saka irin kayan nan, ban kuwa yi qasa a guiwa ba na bi bayanta nayi mata tatas tareda kashedin kar na qara ganinta a gaban Bashir ba tareda hijabi ba. Washe gari da safe yace su shirya ya kaisu gidan Dada gaba daya harda Yan Biyu zasu tafi, muna tsaye a palour suna jiran Amirah se gata ta fito da wata fitted gown ta Atamfa ta kamata tsam kamar zata yage idan tayi numfashi me kyau se dan mayafi data rataya a kafada. Ina kallon yanda Bashir yakalleta kafin ta qaraso inda muke nace ta juya ta canzo kaya ina jiran naji ya dora nasa fadan se cewa yayi ta wuce su tafi baya son bata lokaci ya tasa su gaba yana baya suka barni tsaye kamar bishiyar da aka dasa. Haka na kusan wuni ina saka da warwara ni kadai akan sababbin halayen na Amirah da na kasa fassara ma’anarsu, shin da wata manufa takeyinsu ko kuwa haka kawai? Idan ma yin kanta ne kawai shi kuma Bashir fa da baya ganin laifin abinda take aikatawar fa? Gaskiya bazan zuba ido ba saboda zuciya bata da qashi, kodan gudun afmuwar barna dole na taka mata birki tunda Bashir ba muharramin ta bane shedan yana iya qawata masa ita ya kuma tunzura zuciyarsa ga aikata abinda be kamata dukda na yarda da Bashir ba kuma na masa tunanin wani abu makamancin haka amma fa zuciya bata da qashi. Allah sarki ni a sannan sam zancen ace wata aba me kama da soyayya tsakanin Bashir da Amirah be taba zuwar mun ba kawai ina daukar abin da takeyi a matsayin tashen fitsarar dake kanta daga irin kalamanta a yanzu kuka nake ganin kamar aure take so dukda ina mamakin dalilin da kwata kwata yanzu samarinta babu me zuwa ko waya ta dena yi dasu se na mayar da hankali na cikin yayyena marasa aure na fara qoqarin samo mata wanda zasu daidaita dashi. Abinda ya raba mana gari da Amirah kwata kwata na sallama ta ta barmun gida gaba daya a wani zuwa da Bashir yayi mana, a lokacin dama na fara gajiya da hakayenta saboda kullum sabon salon da zata bullo mun dashi. Gaba daya ta gama raina ni dana rasa menene musabbabin rainin dan har takai Amirah ta shiga dakina ta bude cikin kayana ta dauki abinda take so ba tareda ta tambayeni ba sedai kawai na ga abu a jikinta duk fada da masifar da zanyi mata kuwa baze hana gobe ta sakw yi ba dukda haka naci gaba da haquri nake zaune da ita saboda a yanzu idan nayiwa Bashir qorafi baya cewa komai sabanin da da qiris yake jira tayi abu ya samu nayi. Abinda ya faru da yasa na tilasta mata barin gidan kuwa shine zuwan da Bashir yayi qarshen wata. Fasalin ginin gidan mu corridor ne guda biyu hagu da dama ko wanne da dakuna biyu daya na kallon daya a ciki dan haka na dauki daya nawa dana Bashir dayan kuma ya zama dakin su Amirah, Amna da Farida daya kuma na yara maza. Bayan da Bashir ya gama weekend dinsa ranar litinin ya koma Lagos a ranar saboda tsabar gajiyar dana kwasa a hannunsa Se Amirah ce ta hadawa yara abin tafiya makaranta suka bi Amiru da ze kai Bashir Airport ya sauke su a makarantar. Da misalin sha biyu na rana na fito daga dakin Bashir bayan na gama ramuwar bacci gidan shiru se Amirah kadai a zaune a palour tana sana’arta ta kallon Indian series yan biyu suna gidan Dada an kaisu yaye kusan sati biyu kenan ba’a dawo dasu ba. Dagowa tayi da murmushi tana kallona tace “Sannu Anty se yanzu kika tashi” “Yawwa Amirah sannu da gida, me kuka rage yunwa nakeji wallahi” na fada ina zama a gefenta. “Na dai feraye miki dankali bari na soya” ta fada tana miqewa, mintina kadan ta soyo dankalin harda kwai ta kawo mun nasa ta hado mun shayi na zauna na fara ci”. “Ai dole kisha Baccin Gajiya Anty irin wannan gurza da kika sha a hannun Yaya jiya kai, gaskiya Anty dole ki shirya ni idan zanyi aure yanda nima zan rikita shi ya ringa sambatu irin na Yaya...” Kwarewar da nayi da shayin dana kurba tsabar kidimar jin magangan ta suka sa tayi shiru ta miqo mun ruwa tana yi mun sannu. Kallonta kawai na ringayi zuciyata tana luguden duka a raina ina ta maimaita “Hasbunallahu wani’imal wakeel”. “Dagaske Amirah taji mu’amalar mu da Bashir? Tun yaushe hakan ya fara sannan ita kadaice ko har sauran yaran ma duk suna ji?” Tambayoyin da nayiwa kaina kenan dana rasa me bani amsar su, tabbas wannan dalilin shine silar rainin da naga Amirah tayi mun shi a yanzu har ma da Bashir din kansa ashe a banza take kallon mu amma ta ina ko ta yaya taji? Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un. Ganin da tayi na dena tarin ba tareda damuwa ko tunanin komai ba taci gaba da magana tana cewa “Wallahi Anty kum....” “Rufe mun baki Amirah” na fada cikin tsananin bacin ran da fuskata da muryata suka nuna kafin na ci gaba da cewa “Ashe baki da hankali ban sani ba? Saboda tsabar rashin mutunchi da rashin kunya har ki iya tsayawa kina maimaita wadannan maganganun a gaba na sa’arki na zama, wallahi se na yi mugun saba miki” na qarasa ina huci bayan dana ture kayan abincin gaba na dan gaba daya komai ya fice daga raina ita kuma sum sum ta tashi daga gurin ta shige dakinsu. Wannan abun kunya har ina, tabbas Bashir irin mazan da basa iya rufe bakinsu ne a lokacin da yake mu’amalar aure amma ban dauka ihun nasa har yana karade gida da Amirah zata iya jiyo wa ba musamman idan ka duba tazarar da ke tsakanin dakin sa da inda nasu dakin yake dama dai a dakina ne ana jiyo duk motsin da akeyi a dakin Bashir. Haka na wuni cikin rashin sukunin zuciya dan Amirah tuni ta fice ta tafi gidan Addah ina nan sukuku har yara suka taso daga makaranta su kansu seda suka gane bana jin dadi. Da magriba muna Kitchen da Amna ina girki tana dan tayani da wasu abubuwan, tun tuni nake saqawa a zuciyata na tuntubeta da dabara naji ko suma suna jin wani abun ina ta fargabar amsar da zan samu tunda dai daki daya suke kwana, me nauyin bacci ma taji bare amma da sam bata da nauyin bacci amma kuma ya zama dole na tambayeta kodan nasan matakin da zan dauka saboda tarbiyyar su, ina ta hiqilo akai kar naje tufka nakeyi ta baya tana warwarewa. Gundumbala nayi nace “Amnah, ni kuwa jiya kinji wani motsi ko maganganu a gidan nan da daddare?” Seta dago daga yankan Albasar da takeyi tace “motsi kuma Mami gaskiya ban ji komai ba in banda karatun da kika kunna a Mp gurin qarfe uku ma dana tashi zanyi fitsari shine naji ya mutu na fito na duba ashe chaji ne ya qare na jona kuma dai banji komai ba wallahi”. Ajiyar zuciya na sauke me qarfi kafin na sake cewa “Ni kuwa se na ringa jin kamar ana hayaniya da daddare bama iya jiya ba, duk sanda Abin ku yake gari ina ji ta windon dakinsa kuma dana tambayi Amirah ma se tace mun itama tana ji”. “Toh Mami qila daga qidan su Faisal ne (maqotan mu ta gefen da dakin Bashir yake) kin san suna da yawa kuma Raliya tace suna kaiwa har qarfe uku wataran basuyi bacci ba suna kallo musamman weekend, Anty Amirah kuma daman ai a dakin ki take kwana itama kinga zata ringa ji”. “A dakina take kwana kuma?” Na tambayi Amna da mamaki, seta daga kai Alamar da gaske tace “Eh mana Mami bake kika ce ta ringa kwana a can ba duk sanda Abbi yake gari wai kince idan ana barin daki babu kowa Aljanu suna kwana a ciki shiyasa duk sanda zaki kwana a dakin Abbi to ita kuma a dakin ki take kwana se da Asuba take dawowa nan”. “Lallai watan cin kutumar uban Amirah ya kama” na raya a zuciyata. Ban taba sanin yar is kar yarinya bace mara mutunchi se yau, daman dakina take zuwa ta kwanta tayi mana labe kenan saboda taji abinda muke tabbas kuwa a yau ba se gobe ba seta bar gidan nan wallahi. Muna cin abinci ta shigo gidan sadaf sadaf kamar munafuka se tayi turus da ganina a zaune dan nasan hasashenta ina daki saboda idan na idar da sallar Isha se nayi shafa’i da wutri na danyi lazumi na kafin nake futuwa palour yau din kuma da magribar nan Period yazo mun. Kallonta nayi daga sama har qasa a fili na ce “kan uban nan” ina miqewa tsaye sosai na qare mata kallo, Kayana ne a jikinta, Wata Atamface falle biyu na siya saboda kyan da tayi mun akayi mun fitted straight gown dikin yaqi shigata saboda ya matse, tunda ta gani take nacin na bar mata ni kuma naqi saboda ina son Atamfar kuma na nema tsaf an rasa samun wata se plain yadi tailor ya siya yace ze gyara mun dinkin shine taje ta dauka ban sani ba dan da zata fita ma Hijabi ta saka har qasa ban ga kayan jikin ta ba. Irin kallon da nake jifan ta dashi ya sakata qarasowa tana cewa “Dan girman Allah Mami kiyi haquri wallahi dan Allah...” tas na kwasheta da Mari kafin na nuna mata qofar dakin su cikin kaushin murya nace “Minti goma na baki ki shiga ki cire mun kaya ki kuma tattara yanaki ki wuce gida yanzun nan dan bazan sake zama dake ba tunda baki da tarbiyya”. Kuka ta saka mun tana tambayata wai me tayi dan Allah nayi haquri na sake jaddada mata wallahi seta bar gidan nan a yau, tunda har take yi mana labe wata rana kuma ai leqa mu zatayi idan ba’ayi sa’a ba haka ta tattara a daren ta wuce gida tana fita muka kulle gida na kuma kashe wayata dan na tabbatar idan Addah bata biyo sahu ba toh kuwa zata kira waya. Washe gari kuwa qarfe bakwai da rabi A gidan tayiwa Addah, mun fito zan kai yara makaranta naji ana dukan Get, Musbahu yaron shagona yaje ya bude se gata kamar an wullota ta hau tijara da diban Albarka akan me zan korar mata ya ita da gidan dan uwanta. “Gata nan ai a gaban ki ki tambayeta me tayi mun” na fada ina kunna mota, ina ji tana ta zuba rashin darajar ta nayi banza dasu na zuba yara a mota, dai dai zan fita naji tana cewa “Wallahi baki isa ba Asma’u, baki isa kice me kadai zaki mallake Bashir da dukiyarsa ba se Amirah ta dawo cikin gidan nan kuma a lokacin baki isa ke koreta ba” nidai nayi zooming na fice na barta a tsaye tana kumfar baki. Dariya ma ta bani wai na mallake Bashir da dukiyarsa nayi me dasu, su kudi suka dama da har suke ganin ya tara wata tsiya dab dai ni har yanzu ina masa Kallon Bashir din dana sani me tun bashi da komai, idan ma ba haka ba babu wanda ya tayani shan wahalar sa a cikin su idan ma nace zan mallake shi ni kadai ai banyi laifi ba ko. 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 WATA KISHIYAR 🥰👹 (ALKAHIRI CE KO SHARRI) 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 Na Maryamah Farouk (Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah) Wattpad @MaryamahMrsAm Page 38 Se bayan dana kai yaran na dawo sannan na kunna wayata, kiran Dada ne ya fara shigowa na daga na gaishe ta daga yanda ta amsa nasan labari ya isarmata kenan. "Akan me zaki kori Amirah daga gidan Bashir Ma'u" ta fada bayan da muka gaisa. Lallai wato gidan Bashir tana gaya mun ba gidana bane kenan, murmushi nayi, babu kunya tiryan tiryan na karanta mata abinda ya faru da duk abinda Amiran ta fada mun dama sauran abubuwan da takeyi a cikin gidantsaf seda na tsara mata. Seda tayi jum da na tabbatar na kunya ne kafin tace "To ai koma menene be kamata ki koreta ba haka da se kija mata kunne ko ki kawo mana qararta mu se mu tsawatar mata, yanzu dai se kuyi haquri ta dawo kuci gaba da zama Allah ya kiyaye gaba". "Wallahi Dada bazan sake zama da Amirah a gidan nan ba, ta koma gidansu idan auranta ya tashi bazan fasa yi mata duk abinda idan a hannuna take zanyi ba amma fa ba dai gidan nan ba" na fada kai tsaye dan ganin ana nema ayi mun fin qarfi, ita bataga illar abinda tayi ba kenan har ake cewa nayi haquri ta dawo to kuwa baze sabu ba. Muna gama waya na kira Bashir na kora masa jawabi dan tun a jiya da daren nake ta neman wayar sa ban samu ba se text message na bar masa. Yanzun kuwa yana amsawa na kora masa abinda yasa nace ta tafin, zuwan Addah harma da wayar da mukayi da Dada. "Wallahi bazan sake zama da yarinyar nan ba kama gaya musu" "Daman ai ke kika gayyato ta gidan tun farko ai ni meye nawa a ciki?" Bashir ya fada. Bansan dai ya suka qarke ba a batun Amirah kwanaki kadan tsakani ya tayar da maganar komawar mu Lagos dan ya samu gida babba da ze wadace mu. Nayi zaton za'a samu matsala dasu Dada saboda kes din Amiraj da mukayi amma se naji shiru haka muka fara shirye shiryen dan a lokacin ana Third term ne har yara sun fara shirin jarabawa, daga sun gama zamu tafi se a saka su sabuwar makaranta su koma sabon session. Lokacin da zamu tafi gida gida nabi duk nayiwa kowa Sallama har gidan Addah naje muka rabu faran faran tana cewa se sunzo dan tana son zuwa Lagos in muka nutsu zata zo tayi mana sati har bakin ruwa se an kaita nace Allah ya nuna mana lokacin ta hada mana tsarabar kayan qamshi da su daddawa harda man Shanu ga dambun nama da tayiwa Jafar dan shine mutumin ta. Haka muka tattara muka koma Ikko, gidan da Bashir ya samu babban gida ne me kyau yana cikin rukunin gidajen manyan ma'aikatan su. Flat ne me dauke da manyan dakuna guda biyu se madaidaita suma biyu ko wanne kuma da Bandaki a cikin sa, ga qaton palour da Gurin Dining, Kitchen, store sannan ta bayan gidan da akwai babban fili da akayiwa  shuke shuke daga gefe akayi garden. Gida dai masha Allah kuma Bashir ya saka komai na buqata a ciki. Se da nayi dagaske kafin na iya daure kewar gida na saba da garin, dan ma nayi sa'ar maqociya wadda take matar Ogan Bashir ce Anty Halima mutuniyar kirki, ita ta qara wayar mun kai da zaman Lagos na gane kan kasuwa ya zaman ina sarar kaya na turo dasu ko ina kake so a fadin Nigeria. Kamar wasa naga tallan daukar ma'aikata na wani kamfani da suke hadahadar ma'adanan qasa anan Lagos, a lokacin na cewa Bashir zan cike ya kuma bani goyon baya na nemi aiki cikin ikon Allah se kuwa na samu suka daukeni matsayin meyi musu tallace tallace. Na kama aiki ba dadewa wata rana kwasam muka samu baquncin Addah, Dada harda Amirah. Sosai mukaji dadin zuwan su dan baka gane dadin gida se randa kayi nesa da yan uwanka kwanan su hudu Addah da Dada suka juya aka bar Amirah da alokacin wai an saka ranar auranta da wani yaro Bashir shima sunansa dan Abokin babban su Bayan sallahr Azumi da sati daya. Dalilin kawota kuwa saboda acewarsu na koya mata yan abubuwan da ya kamata ta iya, nayi dariya kuwa nace duk abinda bata koya ba a zaman kusan shekara goma da mukayi tare banajin zata iyashi a watanni biyu kacal, haka dai suka tafi suka barmu na kuwa dage tsakani na da Allah ina dora yarinyar nan akan hanya ta hanyar nusar da ita komai. Tunda tazo sau daya Saurayin nata Bashir yazo da yake anan Lagos shima yake zama, nidai itin yanda naga yana ta dari dari da ita bayan ya tafi na kasa shiru seda nayi mata magana nace "Wai ni Amirah hada ku akayi da Bashir ne?" "Aa Me kika gani Anty?" "Gani nayi yanda yaqi sakewa dazu da yazo musamman tunda Baban Ali ya dawo jikinsa fa har wani rawa ya ringayi". Dariya tayi tace "haka fa yake Anty ni wallahi har tunanin yanda ma zamu zauna dashi nakeyi, nida nake son na samu miji mu sha soyayya irin taku da Yaya shi yasa fa na samo me irin sunan sa ma. Nidai ki taimaka mun Anty ki koya mun duk irin abubuwan da kikeyi nima na zama star". Hade rai nayi, na fuskanci Amirah dai se gyaran Allah sauqin ta dai za'a mata auran taje ta qarata in huta, haka muka ci gaba da zama ina koya mata duk wasu abubuwa daya kamata macen data san kanta ta iya su. Bilhaqqi nake bata sirrika da kuma gyara tamkar yanda zanwa qanwata ciki daya kafin cikar wata daya kuwa ta fara hawa saiti dayake ita ta saka kanta hatta girki yanzu tana qoqari sosai dama abun nata harda qyuiya da qyashi suke hanata tayi a lokacin baya yanzu da yake a rajin kanta ne wani lokacin kafin na taso daga aiki ma ta gama abinci, gyaran gidane dai se a slow, zata ci kwalliya amma gurin da zata zauna be dameta ba. Tsakanin ta da Bashir dai bana ce komai ba dan daga gaisuwa wata magana bata qara hadasu idan yana zaune ma bata fitowa tana daki tana chatting din daya zamar musu dabi'a yanzu daga ita har Bashir dan shima yanzu muna zaune bini bini yana danne dannen waya wani lokacin kuma se naga ya zauna yayi shiru kawai kamar akwai abin da yake damun sa dan inbanyi qarya ba se nace har rama yayi amma se na ta'allaqa hakan qila da yanayin aiki, a haka muka shiga watan Azumi wanda ya rage saura sati biyar bikin Amirah kenan. Ranar da aka kai Azumi na uku bayan ansha ruwa Addah ta kirani take gayamun sunje ganin gidan Amirah. "Gidan yar taki yayi kyau Ma'u sena kin gani daki uku mijin ya bata da palour se ku yunquro dan kinsan gidan kishiya ne dole ki gwangwaje yar taki". "Gidan kishiya kuma Addah dama Bashir din ya taba aure ne" na fada da mamakin maganar tata, se ta shiga in da in da tana cewa "Au Faccala nake so nace miki, gidan su daya da matar wansa wannan kishin ai har yafi na kishiyoyi zafi, zan saka a turo miki da kudaden da Babanta ya bayar a siyi gado dana gurina da za'ayi mata kayan Kitchen tunda ai kece uwarta". "Hakane kuwa to Allah ya sanya Alkahiri ya nuna mana lokaci babu damuwa, a turo din kinsan daman kaya anan sunfi kyau da Sauqi se mu siya a kawo kawai" daga haka mukayi sallama Allah a raina naji dadin karamcin da akayi mun aka dorani akan har kar bikin. Haka na tasa Bashir da nacin se ya siya mata gado daya se a hada da na gurin Babanta biyu kenan daki dayan in mijin yaso se ya gyara abinsa amma Bashir ya dage akan shi bazeyi ba bashida kudi saboda a sannan gini yakeyi, ya rushe gidan mu na Gombe ya siyi filin kusada mu an qara ana mana sabon gini kuma daga yanayin plan din nasan dole zeci kudi. Dana takurashi daga qashe yace dubu dari yayi niyar bada gudummawa nace sunyi kadan gadon nan fa dole shi ze siya mata haka dai ya haqura daga qarshe ya yarda yace na ranta masa kudin muka siya mata gado me kyau dan dubai a sannan ma dubu dari hudu muka siye shi irin nawa dana siya na chanza na dakina na mayar da na ciki dakin su Amna. Hidimar da nayi ta kayan auran Amirah ko bikin Farida nake yi se haka dan wallahi bazan iya lissafa nawa na kashe mata ba a kayan Kitchen Anty Halima har fada ta ringa yi mun tace dangin miji nakeyiwa wannan hidimar a maimakon nayi musu gwaninta qarshe baki zan janyowa kaina suce da kudin dan uwansu nake wadaqa amma na toshe kunnena nayi mata. Haka na tattara kaya rankatakaf aka kwasa a mota aka kai Gombe sannan muka ci gaba da gyaran Amarya kuma da shirin biki dan har dinkunan ta duk nan aka kawo na bawa sabon tailor da nayi ya yi mata dinkuna na daukar magana biki kawai muke jira. Randa aka kai azumi na Ashirin da biyu Bashir yazo mun da Albishir din ya biya mana Umarah nida Yara Gaba daya kuma wai a gobe zamu tashi abin ne da kamar baze yuwu ba shiyasa be gayamun ba se yau da safe sannan komai ya kammala. Nayi murna kuma banyi ba. Murnar da nayi ta tafiya Umarar ce da kuma yarana dukka gaba daya abinda na dade ina mafarkin yi inda naji rashin dadi kuma ba tare da Bashir zamu tafi ba dukda sati biyu zamuyi dakyar idan tarar da bikin Amirah qila ranar da aka gama zamu dawo amma. Haka muka tashi hada kaya a daren dan ma tashin namu bana safe bane, ta waya na kira gida mukayi musu sallama washe gari tun safe Amirah ta fara tafiya Gombe, harda kukanta wai bana nan za'ayi biki gaskiya zataje ta cewa su Addah a qara sati se na dawo haka na rarrasheta ta tafi, mun samu delay najirgi dan haka se qarfe 7 na Magriba muma muka tashi zuwa qasa me tsarki muka bar Bashir shi kadai yana ta daga mana hannu. Mun sauka qasar madina lafiya, sosai na kama ibadah ta dan ko kusa ban bari hidimar yara ta hanani ribatar goman qarshe da muka shiga ba. Kwanan mu biyar muka tafi Makka muka dauki Haramin umarar mu, bayan mun sauke nan ma a kullum ina Masallaci ina ibaduna, kwanan mu biyu aka sallace banyi sanya ba na duqufa sosai ina ta kaiwa Allah kokena. Adduata duk akan Iyayena, Yarana da Mijina tareda sauran Al'umar musulmi baki daya. Ranar Juma'a data kama Lahadi zamu dawo Nigeria da yamma mun fita kasuwa da yara wayata dake cikin jaka ta ringa qara, seda muka shiga shagon nacewa Amna zu zagaya su dauki abubuwan da suke so kafin na dakko wayar na duba, Rahma ce Amaryar Amiru da mamaki nake kallon tarin missed calls dinta gida shida se na fara qoqarin kiran ta dan tabbas nasan ba lafiya ba irin wannan kiran nayi sa'a kuwa ringing biyu ta amsa wayar. "Maman Aliyu wane labari naji dan Allah kice mun ba gaskiya bane" ta fada ba tareda ta bari ko gaisawa munyi ba. Se naji gaba na ya fadi, daman dauriya nakeyi, a kwanakin kullum cikin faduwar gaba nake da quncin zuciya na rasa me yake damuna shiyasa ko da yaushe ina cikin Harami ina sallah ko karatun qur'ani su kadai suke sanyayamun zuciya na kuma fawwalawa Allah ya iya mun koma menene yake tun karo ni dan a duk sanda naji irin wannan yanayin to tabbas wani mummunan abu ne yake shirin samuna. "Maman Aliyu bakya jina ne kin yi shiru k baki samu labarin abinda yake faruwa bane" Rahma ta sake fada abinda ya fito dani daga duniyar tunanin dana luluqa. "Wani abun ne ya faru Rahma ban sani ba wallahi Allah dai yasa lafiya" na fada a sanyaye, se tayi shiru kafin cikin wani yanayi tace "Tunda baki sani ba bazakiji a bakina ba Maman Aliyu amma ki kira Yaya Bashir yanzu base anjimaba kiji komai" kafin nace wani abu ta yanke wayar. Seda na kira Bashir sau uku amma be daga ba, ganin magriba ta kusa sena haqura muka qarasa siyayyar mu muka koma masauki akan zuwa bayan Isha se na sake kiransa idan na dawo daga masallaci amma sam na kasa samun nutsuwar zuciya. Kira na ringa doka masa abinda ya bani mamaki ko ince ya fara bani tsoro ganin na kira yafi sau Ashirin wayar tana qara amma ba'a daga ba sena mayar da akalar kiran nawa kan Amiru dan na sake kiran Rahman itama bata amsa ba. Kira biyu ana ukun Amiru ya daga. Cikin sanyinsa muka gaisa se mukayi shiru gaba daya ni ina jira naji yace wani abu ne ya samu Bashir shima yana jiran jin dalilin kiran, ni na katse shirun da cewa "Baba Amiru Bashir kunyi waya da Bashir kuwa yau" "Eh mun yi waya bamu dade da rabuwa bama na barshi a gida yanzu na fita" "Oh yana Gombe ashe, nayita kiran wayarsa ne amma ban samu ba shine nace bari na kiraka naji ko kunyi magana yau shikenan se an jima" na kashe wayar. Daga yanayin sa sam banji cewa wani abu ya faru ba to me yasa Rahma zata kira ta daga mun hankali?? Qoqari nayi na yakice tunanin daga zuciyata muka shirya muka tafi masallaci, ina cikin yin shafa'i da wutri wayata da sam na manta ban saka ta a Silet ba ta dauki qara lokaci daya gaba ya yanke ya fadi da har seda na dafe qirji na shiga nanata Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un a zuciyata. Ina sallamewa na jawo wayar na duba, Alawiyya ce ta kirani, sena miqe kawai ina shirin bin bayanta wani kiran ya shigo sena yi saurin daga wa na saka wayar a kunnena. "Ma'u bansan daga ke har mijinki yan kutumar uba bane se yau, anya ba asirce ki yayi ba kike zaune dashi ya kulle miki baki? yanzu ace za'ayi miki kishiya duk duniya ki kasa gayawa kowa sema ki tsallake kibar qasar wai kin tafi Umara sedai kawai muji a gari, shikenan ai Bashir ko gaki gashi nan tun ba'aje ko ina ba kin fara karbar saka makon ki a hannunsa". A duk maganganun Alawiyya babu abinda na tsinta banda kalmar kishiya data fada, seda na da dage piller masallaci jin jiri yana neman kadani. "Lallai wato ga mahaukaciya tana magana kin yi mun shiru ko Ma'u, shikenan amma ki tabbata kin nemi wata yar uwar da zaki raba baqin cikin Bashir da ita dan wallahi bazaki dora mun hawan jini da takaicin mijinki ba, mtsw" taja tsaki. Seda nayi da gaske na iya bude baki nace "Alawa ni duk ban gane abinda kike nifi bane waya gaya miki Bashir yayi aure?" "Kina nufin baki sani ba to maza shiga whatsapp yanzu na tura  miki hotuna kigani se ki tabbatar wa idon ki" tafada kafin ta kashe wayar. Wata wawuyar Ajiyar zuciya na sauke lokacin da naga hotunan da Alawiyya ta tura mun. Hotunan Bashir ne da Amirah tareda sauran yan uwan su wanda na tabbatar na daurin auran Amiran ne amma ai na zata se gobe Asabar aka saka a katin data tura mun kuwa. Da daddaya na ringa binsu da kallo Bashir yaci uwar Babbar riga fara gasu Addah nan baki ya gonar Auduga an washe shi ina shirin bude na qarshe da naga kamar kati ne kiranta ya sake shigowa. "Yanzu kin yarda ko kuwa dai kina tantama" ta fada". "Haba Alawa haka kawai kin saka hawan jinin dare daya ya nemi kamani a marrar nan kike mun zancen kishiya. Amirah cefa kin manta da bikinta akeyi hotunan daurin auren nefa duk kika bi kika kidima kanki". "Allah ya yafe miki Asma'u ya nuna miki hanyar daidai, shikenan tunda ni na kidima kaina ba lefi idan kika dawo hayyacin ki se muyi magana dan naga alamar kwakwalwarki ta juye Ma'u kina buqatar saiti amma ki nutsu ki sake kallon hotunan dakyau ga wasu can ma na qara tura miki" Alawiyya ta fada sannan ta yanke waya. Hotunan na sake bi da sababbin Videos din data turo mun na Amirah data sha kwalliya tayi kyau suna ta shaqiyanci, akan katin dazu na sake tsayawa na bude shi na fara karanta abinda aka rubuta. "DAURIN AURAN ENGINEER BASHIR AHMAD DA AMIRAH MURTALA" Abinda na gani an rubuta kenan, daga Bashir din har Amirah ko daga bacci na farka naga sunansu na san sune ballantana wannan ga gurin daura auran nan masallacin dake layin gidan Addah ne hakan ya sake tabbatar mun da gaske dai Nawa Bashir din ake nufi bawai wani na daban ba. Wayar hannuna ce ta dauki qara, ban san ya akayi na daga kiran ba nidai naji muryar Anty Halima tana cewa "Asma'u dagaske ne ko wasa yanzu a duniya Bashir ya rasa irin cin Amanar da ze yi miki se ya tura ki wata qasa sannan ya daura da yarinyar da kika riqe?" Iya abinda naji kenan lokaci daya tsikar jina suka zuba  kaina yayi mun dum kamar wadda aka kwadawa guduma daga nan ban sake sanin inda nake ba se farkawa nayi na ganni a gadon Asibiti. Waya ta da nagani a gefena na jawo na sake budo hutunan dazu dan in tabbatar gaskiya ne ko qarya. Ina kunna Data kuwa kamar ana jira messages rututu suka fara shigo mun alamar dai magana ta baza gari ga status din yan gidan su   Se a sannan ma naga status din Jama'a ashe an yi posting hotunan sosai hankali na nae bekai kai ba. Tun yaushe aka shirya hakan? Daman Bahsir da Amirah suna soyayya ina zaune dasu ban taba ganin wata alama ba? Wai ma me nayi wa Bashir a rayuwa dana cancanci irin wannan sakayyar bayan tarin dumbin sadaukarwa da Alkhairan da ni da yan uwana muka yi masa. Wane irin mugun hali ne dani da har ya kasa gayamun zeyi aure sedai naji a duniya bayan daya rigada ya daura me nayi masa dan Allah? Sannan Ace duk matan duniya manya da yara farare da baqar fata Bashir ya rasa wadda ze aura se Amirah yarinyar dana gama bautawa tun tana qanqanuwarta har girma yanzu ace da ita zanyi zaman kishi yarinyar data  san sirrina, na bude mata duk wasu sirrika da nake taqama dasu saboda yanda na dauketa tamkar qanwata na gyarata saboda ta samu daraja a gurin mijin da zata aura yanzu ashe duk mijina nayiwa wannan tanadin? Ni za'a yaqa dasu? "Yah ubangiji kaika halicceni, kai ka tsara mun rayuwata tun kafin wanzuwa ta a doron duniya Allah kasan zan iya shi yasa ka dora mun na roqeka nayi tawassali da sunayen ka tsarkaka nayi tawassali da Annabin ka Muhammad SAW Allah in har sunyi dan su cutar dani na roqeka karka basu ikon ganin gazawa ta, ka sanya min juriya da dakiyar tun karar duk wani qalubale da zan fuskanta a rayuwa. Ubangiji ka sauqaqa mun dau wani ka bani zuciyar da zan iya dauka" na fada a fili ina fashewa da wani irin kukan baqin ciki. Wallahi ko kadan banji haushin auran da Bashir yayi ba, da ace wata ce daban zan shanye na danne bazan taba nuna masa komai ba har in ga iya gudun ruwan sa amma Amirah fa Amiran Addah me yasa se Ita? Da ace Ummi qanwarta ya aura nasan bazan ji baqin ciki irin wanda nake ji yanzu akan auran Amirah da yayi ba. "Amirah zata dawo gidan nan kuma a sannan baki isa ki koreta ba" kalaman Addah suka dawo mun a kwakwalwa ranar da na kori Amirah daga gidana a Gombe. Ashe abinda suka shirya yi mun kenan daga ita har Dadan suka dakko kishiyata suka kawo mun da nufin na gyarata su kuwa wasu irin mutane masu saka Alkahiri da sharri ta ina na kuskure musu a rayuwa da suka zabi hukunta ni ta irin wannan hanyar? Kuka na ringayi wanda tun likitocin da suka dubani suna bani haquri har suka haqura sukayi shiru, bana buqatar sauran bata lokaci a qasar tunda daman ba dan Allah ya turani ba dan ya aiwatar da nufin sa ne to yaci galaba amma nima dole na koma Nigeria muyi wacce zamuyi da Bashir dan bazan taba hada miji da Amirah ba. Yana da damar ya auro mun mata uku mu zauna amma ba Amirah yarinyar da nakewa Kallon Yata ita ce ze hadani kishi da ita baze sabu ba. Sanda na koma Hotel din da muke na tarar da yara zuru zuru dan da aka kaini Asibiti can suka koma saboda a qa'idar su ba'a barin dan jinya. "Ku hada kayan ku yau zamu tafi" na fada ina hargitso duk abinda hannuna ya kai kansa ina sakawa a jaka. Seda na gama sannan na tuna da ai Passport dinmu ma baya hannunmu yana gurin Agent din da Bashir ya hadamu dashi, wayata na dauka na shiga kiran nayi sa'a tana shiga ya daga. "Malam Isah kayi mana booking jirgi idan da akwai Yau ka, ka fada mun kudin ko nawane zan biya wani abu ya taso mun bazan iya jira har se gobe ba" na fada ba tareda na amsa gaisuwar daya fara mun ba. "Amma Hajia me ya faru haka, bayan haka kuma ai Ticket din ku bana komawa Nigeria bane Dubai zaku wuce daga nan na zata ai Engineer ya gaya miki ma" "Isah dakai da Dubai din da Engineer kunci abu ta kazan ubanku" na lailayo wata Ashar me maiqo da ni kaina bansan na iya ta ba na kora masa kafin na ci gaba da cewa "Ka kawo mun passport din mu nan da Awa daya idan ba haka ba wallahi se nayi qarar ka nace safarar mu kayi, kasan ina da duk wasu bayanai naka da zan bayar ka kuskure lokacin baka zoba ka gani". "Kiyi haquri hajia ku shirya yanzu zan turo mota da zata kaiku Jiddah ni ina can yanzu haka akwai jirgin da ze tashi yau da daddare bari na bincika idan da akwai guri se a siya" Isah ya fada jin abin yafi qarfinsa. A dakin muka bar kusan rabin kayan mu dan bana buqatar abinda ze bata mun lokaci bate har aje ana maganar wani awon kaya ko wani abu muka hau mota se Jiddah gaba daya ma gani nayi motar bata sauri, ina ma ace zan iya rufe ido na ganni a Nigeria, ina buqatar naje naga da wadanne idanu Bashir da danginsa zasu kalleni. Mun samu jirgi amma se munyi jiran Awa goma sha biyu kafin tashinsa, haka Isah ya nema mana hotel gaba daya ya rasa meya faru haka gashi kiran duniya Bashir yaqi dagawa daga qarshe ma ya kashe wayar gaba daya Asma'u kuwa bega fuskar da ze mata tambayar abinda yake faruwa ba ma dan haka yaja Aliyu yana tambayarsa ko mutuwa akayi "Nima ban sani ba, kawai daga Masallaci aka kaita Asibiti kuma data dawo mun kasa tambayarta abinda ya faru idan mukaje gida koma menene se mu gani" Aliyun ya bashi amsa. Haka muka hawo jirgi se Nigeria ya sauke mu a Kano,Asuba ranar lahadi muka sauka tun a AirPort na samu shatar mota ta kwashe mu kafin Goman safe mun sauka a Gombe muka ci burki a qofar gidan su Bashir cikin Sa'a nayi kyakykyawan gamo da Ango Bashir da tun daren Alhamis rabon da ya sake daga wayata. 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 WATA KISHIYAR 🥰👹 (ALKAHIRI CE KO SHARRI) 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 Na Maryamah Farouk (Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah) Wattpad @MaryamahMrsAm Page 39 A qofar gidan motar mu ta tsaya, idona akan Bashir da suke tsaye tareda wasu mutum biyu da ban gabe su waye ba. “Ku jirani karku fito” na fadawa yaran, seda na yi kokawa da duk wani rauni da karayar zuciyar daya taso mun kafin na bude motar na fito ina gyara mayafin kaina gaba daya mutanen gurin suka bini da kallo banda Bashir da tunda muka hada ido ya maida kansa qasa kaman wanda aka kama yayi qarya. Kai tsaye cikin gidan na shiga, nayi sallama ina jiyo hayaniyar su daga cikin dakin Dada amma ba’a Amsa ba dan haka na nufi can din, har na kai bakin qofar naji an kira sunana, sena waiwaya. Alhajin su Bashir ne yana tsaye daga qofar dakinsa ya yafito ni da hannu sena juya na koma gurinsa. Ina durqushe a gabansa kusan minti biyu kafin yaja numfashi yace dani “Asma’u kiyi haquri nasan an cutar dake amma zan roqeki Arziqi kar kice musu komai yanzu, ki barsu akwai ranar da su da kansu zasu maidawa junan su martanin abinda sukayi miki. Na sani Qarin aure ba haramun bane amma ta yanda aka shirya naki sam be kamata ba. Ya zama zamba cikin aminci. Ki sani Ita Amana daya ce kuma wanda yacita baya taba zama lafiya, idan har Bashir da uwarsa sun qulla wannan aure dan su ci mutunchin ki Asma’u in Allah ya yarda muna raye ko mun mutu se sunga sakayyar cin Amanar da sukayi miki. Ina qara roqonki da kiyi haquri, ki qara akan wanda kike yi in sha Allahu bazaki tabe ba, duk me neman gazawarki akan idonsa zakiyita ci gaba da yardar Allah”. Kuka nakeyi dagaske a raina ina hasaso irin tarin qaunar da na nunawa Bashir da Ahalinsa, a tsahon zamana dashi kusan shekara goma sha uku yanzu bazan iya cewa taka maimai ga wani abun laifi daya taba hadani da wata daga cikin su ba, a kullum cikin kyautata musu nake iya qarfina kuma duk albarkacin so da qaunar da nakeyi wa Bashir din ce ta shafi su amma ace a gurinsu basu da abokin hamayya seni. Sosai nasha kuka na ba tareda Baba ya hanani ba in banda “kiyi haquri Asma’u” babu abinda yake cewa. “Naji zan haqura Baba bazan tanka musu ba amma kayi haquri bana jin zan iya ci gaba da zama da Bashir. Bazan iya ci gaba da zama cikin Ahalin da basa qaunata ba Baba. Sannan Baba Amirah fa, yarinyar dana raina da hannuna ita zan hada miji da ita wallahi bazan iya ba. “Zan bi umarnin ka a yanzu zan koma ba tareda na cewa kowa cikin su komai ba amma Baba karka roqeni ci gaba da zama da Bashir saboda ina girmamaka bazan iya tsallake unarninka ba amma tabbas zan cutu. Zuciyata zata iya bugawa a dalilin haka muddin zan zauna inuwa daya da Amirah a matsayin kishiyata” na fada cikin sheshsheqa me qarfi. Se Baba yayi murmushi wanda da ganinsa na takaici ne kafij yace “Asma’u ke Yarinyar kirki ce sannan abar Alfaharin duk Miji me hankali da yayi katarin samun irin ki sannan ko wanne uba zeyi alfaharin zamtowarki Suruka a gare shi. Bazan so na rasa nagartacciyar suruka irin ki a cikin zuria’ata ba domin ke din mayafi ce da kika lullube Bashir duk kuma ranar da wannan mayafin ya yaye ba baki nayiwa Bashir ba tabbas se rayuwar sa ta shiga cikin gararin rayuwa. Idan har ki ka ce bazaki ci gaba da zama da Bashir ba ni me tsaya miki ne in tayaki kwatar yancin kanki amma yanzu kije ki samu nutsuwar zuciya, karki yanke hukunci cikin fushi idan kika nutsu duk abinda kika yankewa zuciyarki ki dawo ni ki gaya mun in Allah ya yarda zan baki goyon baya dari bisa dari ki share hawayenki yanzu”. “Baba bana tunanin ina da buqatar yin wani dogon nazari ka taimakeni kawai kasa Bashir ya sawwaqe mun dan ina da yaqinin ko ba yanzu ba watarana se sunyi nasarar fiddani daga dakina” na fada cikin kuka, se ya tare ni da cewa “Haba Asma’u ke da na sanki jaruma ya zaki karaya tun yanzu ki bada qofar da za’a ci galaba akanki? Maganar su fitar dake daga dakinki kuka babu wanda ya isa yayi Abinda Allah beyi ba, kije gida ki huta ki bawa zuciyarki haquri idan kuma kinga bazaki iya karbar Al’amarin ba ki dawo zan tsaya miki”. “Shikenan Nagode Baba Allah ya qara girma” “Nima na gode Asma’u Allah yayi miki albarka keda zuri’arki gaba daya”. Haka mukayi sallama da Baba seda yasakani na share hawayena tas yace naje na dauraye fuskata a bayin da yake cikin palour sa kafin na fito. Ina fitowa naci karo da Dada da yayanta sun fito daga dakinta, Yanda kasan anyi ruwan sama an dauke haka sukayi shiru gaba daya suka zubo mun idanu kamar wanda sukaga wata sabuwar Halitta nayi musu kudin goro gaba dayabna watsar na nufi qofar fita. Sanda Na fita ban tarar da Bashir a waje ba se Naziru suna tsaye a jikin motar da muka zo tareda yara. Kallo daya nayi masa na kama murfin motar na bude se ya riqe yana cewa “Wallahi Anty babu sa hannuna basu gayamun ba se ana gobe za’a daura, da nace zan gaya miki Dada tace duk wanda ya kuskura ya sanar dake wallahi se tayi masa baki shiyasa ko Yaya Amiru da kika kira jiya ya kasa gaya miki komai” ban bi takansa ba na cewa me motar muje na nuna masa hanya ya qara sa damu gidan mu gidan Baffana. A waje na barsu ana sauke kayan mu bayan na sallame shi na wuce ciki. A yanzu babu abinda nake buqata sama da na kebe ni kadai a inda zan sha kukana kar wani ya rarraahe ni. Dakin Hajia Babba nayi masauki na haye can qarshen gadonta na saka kaina a cinya na ringa rirgar kukan da wadda akayi wa irin abinda akayi mun ce kawai zata fahimce ni, tambayar kaina nakeyi me nayiwa Bashir a rayuwa daya qullaceni yaga ta haka kadai ya kamata ya rama. Ina jin matan gidan mu suka ringa shigowa suna bani baki amma na toshe kunnena, nasha kukana seda naji Numfashi shina yana barazanar daukewa kafin na bawa kaina haquri na koma sauke ajiyar zuciya kawai ga wani masufaffen ciwon kai daya dirar mun maqogarona kuwa kamar ze tsage saboda bushewa dan in ban manta ba rabonda ko ruwa ya wuce ta cikinsa tun kafin na samu wannan baqin labarin. Har dare ina cikin dakin sallah kadai na tashi nayi na koma na kwanta ba tareda na ko kalli kayan abincin da Hajiyar ta kawo mun ba. Haka ta zauna akaina tana ta faman yi mun nasiha dana gaji da jinta sena sa mata kuka dole ta tashi ta bani guri, qarin abinda yake damuna ganin har zuwa sannan banji komai daga Bashir ba, be zo ba be kuma kirani a waya ba haka na kwana kafin safiya jikina ya rijice dole se da aka danganani da Asibiti. Gwajij farko likita ya tabbar mun da jini na ne ya hau sosai abinda ya saukar mun da mugun ciwon kai kenan ga kuma zazzabi me zafi, shawara ya bani da koma menen yake damuna nayi haquri na kuma fawwalawa Allah domin lafiyata tana gaba da komai, duk wani al’amari na rayuwa baze tafiyar mun daidai ba idan babu lafiya daga nan yayi mun Allurai da zasu taimaka mun zafin jikin ya ragu da ciwon kan ya bani magunguna muka tafi gida. Seda akayi mun wuqa wuqa sannan naci abinci nasha maganin ban dade ba bacci ya dauke ni seda na shafe awanni ina yi kafin na tashi. A yammacin ranar Alhaji Qarami yazo, bashi kadai ba kusan yayyena dukka seda suka zo gida aka taru masu tsinewa Bashir nayi masu bani baki sunayi. A bakin su nakeji wai ashe jiya da daddare ma yazo gidan ma, nidai ina kwance ina jinyar zuciyata. Seda muka kwana biyu da dawowa a daren ranar da daddare ina kwance a daki da carbi a hannuna ina ja Jafar ya shigo yace wai naje inji Dadyn Abuja. Da dogon Hijabi na har qasa nayi sallama a Palour Hajia Babba kaina a qasa seda na kai tsakiya sannan ido na ya sauka akan Bashir da Bala se Abdulkarim Dan Qanin Baban su ne, ba tareda na qara ko taku daya ba na juya da niyyar fita Alhaji Qarami ya dakatar dani dole na koma na samu can gefe kusada qofa na zauna ina jin zuciyata kamar an watsa fetur an cinna mata wuta. “Asma’u mijinki ne yazo bada haquri shine nace a kiraki tunda ke akayiwa laifi ke ya cancanci abawa haquri ko” Alhajin ya fada yana kallona, kafin ya miqe yana sake cewa”ki matsa ciki kin zauna a bakin qofa ga dare idan kun gama ki same ni gurin Hajia Umma ina son ganinki”. naji shi sarai amma ban dago ba ban kuma matsa daga inda nake ba ya tsallakeni ya fice daga palour, be san jira kawai nakeyi ma na samu wata dama na fice na bar musu gurin dan bazan iya musa masa ba tun farko dalilin da ya sa na zauna ma kenan. “Gamu munzo guiwoyin mu a qasa Asma’u munsan ba’a kyauta miki ba ni kaina wallahi bansan abinda ya faru ba kenan se daga baya amma ki dubi girman Allah kiyi haquri, kuskure dai an rigada anyi shi sedai muyi fatan Allah ya kiyaye na gama amma yanzu kiyi haquri ku karbi qaddara a yanda tazo muku” Abdulkari ya fada, se na daga kai na kallesu ina shirin buda baki nayi magana Bala ya rigani da cewa “Allah ya huci ran uwar gida sarautar mata, kinsan fa kinsha kan mutumin bala’in tsoronki yakeyi shiyasa ya kasa gaya miki zancen auran nan. Kuma ma ni gani nayi ai ba wani abu a ciki tunda qanwarki ce daman da aje a dakko miki Bare wadda baki san halin ta ba Uwargida ai gara ta gida ko, easy kawai ki shanye a koma a ci gaba da gashi” “Sedai a koma a ci gaba da gasa ubanka Bala” na fada a fusace ina miqewa tsaye kafin na nuna Bashir da yai tsamo tsamo kamar kazar data sha dukan ruwa ya zate ido yana aikawa Bala da mugun kallon katobarar dayayi nace “Kai kuma tun da sauran burbudin mutunta juna a tsakanin mu ka rubuta takaddata ka aiko mun da ita dan wallahi Bashir kayi kadan ka wulaqanta ni kayi mun kishiya ta rashin mutunchi, idan kuma kaqi tabbas kotu ce zata raba auran mu da kai” ina fadar haka na juya amma kafin na kai waje Bashir da bansan tasowarsa ya riqe ni kamar dansanda da Barawo yana cewa “Bazan iya ba Ma’u, na sani nayi kuskure amma wallahi rashin sanin ta inda zan fara gaya miki maganar yasa na aikata haka. Basan a ya zaki kalleni ba Ma’u idan nace miki zan qara aure. Ni kaina na rasa ta yanda Al’amura suka juya har na fara son Amirah na yarda kiyi mun duk irin hukuncin da kikaga ya dace komai tsananinsa zan dauka amma bazan taba iya rabuwa da ke ba Ma’u” Wani tuquqi ne ya taso mun, yanzu har Bashir ya iya kallon tsabar idona yace dani wai yana son Amirah lallai na yarda In da ranka zaka sha kallo. Hannayensa daya riqeni na banbare daga jikina ina cewa “Tunda kana sonta seka je ka zauna da ita amma ni dai wallahi na gama zaman aure dakai ko kaine autan maza Bashir kaje ka zauna da matar so tunda na gamayi maka rana” “Kiyi haquri dan girman Allah Ma’u ki yafe mun ki bani dama na wanke kaina nayi miki Alqawarin babu abinda ze chanza a tsakanina dake saboda wannan auran, Ina sonki ina qaunar ki ki dauka wannan abun yana cikin qaddadarar mu daga ni har ke” ya fada yana qoqarin sake kama hannuna nayi baya ina cewa “Qaddarar ka dai kai kadai kuma ka matsa karka sake rabar jikina idan ba haka ba Bashir sena kwada maka mari wallahi”. Sosai na birkice nayi masa tijara yanda ne taba tsammani ba a rayuwar sa, na hada da Balan da Abdulkarimun nayi musu zagi na tsamar nama kafin na jadda da masa akan ya kawo mun takaddata dan wallahi na gama zama da Bashir na yarda su Addahn suci galaba a kaina. Dana hada miji da Amirah gara na fita na bar mata gidan ta zauna dashi ita kadai. Bangaren Hajia Umma na wuce gurin Alhaji Qarami, banko bashi dama yayi magana ba na fashe masa da kuka ina rantsuwar bazan komawa Bashir ba ya saka shi ya kawo mun takaddata na tsane shi na tsani zama dashi. Haka yayita bani haquri ya kuma tabbatar mun da cewa tilas Bashir ya sake ni tunda har na nemi hakan amma yanzu na kwantar da hankalina kodan jinina da akace ya hau a samu ya sauka kar kuma na sake janyo wa kaina wata matsalar. Haka na kwashe sati biyu cif a gida muna kan wannan danbaruwar, kullum Bashir se ya zo kamar maye haka ze durqusa yana bani haquri nima kuma ban fasa ci masa mutunchi da jaddada masa cewa ya bani takaddata ba tunda ba’a aure dole nace na gama. Gashi makarantar yara kullum se kiran waya sukeyi an koma tuni lafiya basu dawo ba nace musu mun bar gari ne za’a zo a fada officially a cire su haka gurin aikina ma da suka tuntubeni tunda hutun sati uku na dauka gashi na haura kawai se nanemi takaddar hutu ba tareda biyan Albashi ba, dan bazan bar aiki na ba saboda a yanzu ne nafi buqatar sa Idan Bashir ya sake ina da buqatar neman hanyoyin da zan ruqe kaina da Yayana dasu. Bazan manta ranar da Dada da Addah suka wanko qafarsu wai sunzo biko na ba, na yaba da tsantsar rashin kunya irinta mutanen nan. A ranar nayi musu abunda Bahaushw yake cewa idan Malam beji kunyar hawa Jaki ba to shima Jakin baze ji kunyar kada shi ba. Na fito musu a yar zamani na wanke su tas da soso da sabulu na kuma sake jaddada musu da idan sunji haushi su saka Dan su ya sake ni su gani tsakanij ni dashi waya rasa na raka su da Allah ya isar abinda sukayi mun kuma in sha Allahu nan kusa zasu ga sakayyar yaudarata da sukayi haka suka kwashi kafafu a sanyaye dan ba Dada ba Addah kanta da bata raina abin kunya tayi mamakin yanda na sakawa idona toka nayi musu tas. Daukata sukeyi a duk yanda suka takani zan biyune shiyasa ma yanzun suka zo saboda horon da Bashir yaje yayi musu akan kodai suje su bani haquri na koma dakina ko kuma ya saki Amirah tunda ita ce duk musabbabin tashin hankalin da akeyi. Wai mutane saboda qin Allah se kaga sun kirani da sunan wai ban kyauta ba abinda nayi wa iyayen Bashir tunda auren daya qara ai ba haramci bane da zance ni bazan zauna da kishiya ba. Har da wadda take cemun ilimina be amfana mun komai ba ina Karatun islamiyyar da nayi ina Bokon nawa zan zauna ina ja ina jayayya da abinda Allah ya halasta, ban dagawa ko wace yar iska qafa ba na kuma roqi Allah duk wadda tace nayi Haquri Allah yasa ayi mata abinda yafi nawa muni idan yaso se taji in ma rashin tawakkalin me ya sakani yin haka ko yaya. A cikin wannan yana yi wata rana muka samu baquncin Goggo da tunda aka fara wannan abun sau daya mukayi magana da ita shima ni na kirata kuma tace mun nayi haquri daga haka bata qara komai ba. Ina kwance a daki aka kirani a lokacin idan ka ganni se na baka tausayi, na rame na fige fuskata babu komai daga ido se dogon hanci ina shiga palour idona ya sauka akan Bashir daje zaune a qasa, ban lura da sauran mutanen da suke ciki ba na hau kansa da masifa ina cewa “Wallahi ko maye ne kai Bashir haka zaka ganni ka kyale tunda nace banayi banga wanda ya isa ya tilastani ci gaba da zama da kai ba, ka tashi ka tafi tun kafin nasa azo a fitar dakai mara zuciya kawai” “Idan baki saka an fita dashi ba baki isa fitsararriya mara mutunchi ba Asma’u” muryar Goggo da ban san da zuwan ta ba ta katse ni kafin ta ci gaba da cewa “Ashe duk rashin mutunchi da diban Albarkar da akace kinayi dagaske ne kuma a gaban ku Hajiya kuna kallo aka rasa wanda ze tsawatar mata. Saboda bakida mutunchi Mijin naki kike sakawa a gaba kina fada masa irin wadannan maganganun ku to bari kiji shi Allah babu ruwansa ze hukuntaki ne akan laifin ki na sabawa miji da ci masa mutunci babu ruwan Allah da cewar Bashir ya auro miki wadda bakya so anyi miki ba daidai ba dan haka tun wuri ki dawo cikin hankalinki kafin ki kanki wuta da qafafunki. Sannan saboda kin zama yar kanki se abinda kika tsarawa ranki zakiyi shine kike iqirarin zaki kashe auranki saboda kanki farau kishiya ko kuma kece ta qarshe da za’ayiwa ko? Ki idan kina da hankali ma ya kamata ki tashi jiniyoyij wuya akan za’a miki kishiya, gidan mu mata nawa Ubanki ya aura gamu nan mu Hudu ya mutu ya bari kin taba gabin wata tayi tashin hankali da yar uwarta a cikin gidan nan?” “Amma Goggon su bazaki hada mu dasu ba, ko bayan haka hanyar da Bashir yabi tayin qarin auransa ce bata dace ba kuma ko wacce mace akayiwa irin haka dole ranta ya baci ai” Hajia Anjin ta tare Goggo jin yanda take ta surfa fada, se Goggon ta kalleta tace “Saboda ya auri yar uwarsa ne take tashin hankali dan ba’a gaya mata ba, ai ba kansa aka fara ba tunda ubanta ma a sanda ya auro ni ai baku sani ba tafiya yayi bikin abokinsa ya dawo muku da ni a matsayin kishiya me yasa a sannan ku baku yi tashin hankali kunce bazaku yarda ba?” “Aa Maryam Allah ya jiqan Alhaji bazaki taba hadashi da wannan yaron ba domin Alhaji Adali ne gamu nan dukka bari kiji kafin A daura auran ku da Alhaji seda ya kira mu a wayar landilayin da daddaya ko waccen mu seda ya gaya mana abinda ya faru ya kuma sanar mana da cewa ze aureki bisa wasiyyar Sama’ila dan haka da yardar mu da Amincewar mu Alhaji ya auro ki, sannan tunda tace bazata koma ba ai Asma’u ta wuce yarinta bare ace za’a zabar mata abinda zatayi” Hajia Babba ta fada sauran suka amsa da “kwarai haka aka yi. “To shikenan tunda kun daure mata gindin tayi duk rashin mutunchin da take so kun bata goyon baya ni baza’a hada kai dani ba, Ke Asma’u idan na isa dake ki tattara ya naki ya naki yanzu ki bi mijinki, kuma diban Albarkar da kikayiwa uwarsa da yayarta kije ki basu haquri, dan cikin matan yayyen ki kaf babu wadda ta taba duban idon mu ta gaya mana maganar banza balle mu yayanmu suje suyiwa na wasu”. Tunda suka fara mahawarar na durqushe a gurin ina Kuka, wato qarata Bashir ya kai gurin Goggo ita kuma ta goya masa baya. Da sauri na daga kai na kalleta hankali tashe jin irin umarnin data bani, se nayi saurin matsawa kusada ita ina cewa “Amma Goggo...” “Karki ce mun komai sedai kuman idan kin shirya nuna mun ban isa dake din ba shikenan” ta yi saurin katse ni, se na mayar da kaina qasa na ci gaba da kuka me ciwo, ya zalunce ni kuma ha hadani da mahaifiyata Bashir wane irin mugun mutum ne a rayuwa. Haka naja qaqafuna na koma daki na shiga tattara kayana ina kuka yarana da suka biyoni suna tayani. Ina cikin hada kayan Hajia Babba ta shigo dakin, “Ki bar shirin yanzu Asma’u tace ku bari zuwa jibi se ki koma. Kiyi haquri ita rayuwar Ya mace daman haka da qalubale wata rana komai ze zama tarihi in sha Allahu” haka tayi ta bani baki har seda naji zuciyata tayi sanyi na kwanta a kan Gado ina saka da cin alwashin irin gashin qumar da zanyiwa Bashir idan har na koma gidan sa. Shi da sake jin dadin zama dani har abada. Washe gari Goggo ta koma bayan ta sake yi mun kakkausan gargadi akan idan na sake ta sake jin wani abu se tayi mummunan saba mun, na koma gidana na zauna kuma duk abinda zan gani naje nayi haquri karna kuskura na dauki dabi’ar kai qara ko na ce zan sake yin yaji. “Asma’u badan bana sonki yasa nayi miki haka ba, nasan ba’a kyauta miki ba amma hakan baze zama silar da zaki bar uban yayanki ba idan kin rabu da Bashir saboda kishiya qarshe dai wata zaki je ki tarar a duk inda zaki fada to menene amfanin haka” Goggo ta fada cikin lallama bayan da ta gama yimun fadan kuma, sena share hawayena tunda yanzu ta sakko se muyi magana ta fahimta nace “Wallahi Goggo ni ba qarin auran sa ko rashin gayamun da beyi bane ya dame ni amma me yasa ze auri Amirah?” “Saboda yana sonta kuma ita Allah ya zaba masa kin san dai duk yanda mutum yaso da son kasancewar abu idan Allah be hukunta hakan ba baze faru ba ko, haka duk yanda ka kai ga qin abu idan Allah ya qaddara faruwar sa babu abinda ya isa ya tsayar da hakan to kar kiyi jayayya da hukuncin Allah Asma’u, ki dauka daman tun kafin wanzuwar duniya yanda Ubangiji ya qaddara ke matar Bashir ce haka itama aka rubuto matar sa ce dan haka dole se ya aure ku. Maganar munafunci ko yaudarar ki da sukayi wannan ki barwa Allah komai kina zaune se kiga ya saka miki a ruwan sanyi kinji ko kiyi haquri kar kuma wannan dalilin yasa kice zaki quntata zamanki da mijinki, a yanzu ne ya kamata kija shi a jiki dakyau ki bashi dukkan kulawa da soyayyar data kamata saboda ba ke kadai bace, duk abinda ya rasa a gurinki ze same shi a wani gurin daga nan kuma se hankalin sa ya fi karkata can saboda zuciya ai tana son me kyautata mata ke kuma daga qarshe se kiga kamar dan ya samu wata ne ya watsar dake bayan ke kika bada damar hakan. Dan haka bani da damuwa akan ki Ma’uta nasan zaki riqe kanbun nan naki na Uwargida sarautar mata dakyau ina so ki nuna musu cewa ke din fa badai mutum ba se Allah, Allah yayi miki Albarka ya ci gaba da kareki a duk inda kike”. Kalaman Goggo sunyi tasiri sosai a zuciyata dan gaskiya ta fada da ace wata daban aka auro mun davkuwa tabbas na nuna mata cewa kishi da MA’U ba wasa bane se ta shirya amma a duk sanda na tuna wa Bashir ya aura se naji bazan iya amfani da ko daya daga cikin abinda ta fada din ba. Haka ta koma Yola washe garin ranar nima yan uwana suka raka ni gidan mu na Gombe bayan da suka hadu suka sake yi mun nasiha da rarrashi, banje na bawa su Dada haquri ba itama kuma Goggon bata tsananta ba tunda na yarda zan koma din ta rabu dani. Gini yayi kyau sosai kuma an saka komai na amfani sabo daga yanayin kyau da tsaruwar kayan na tabbatar da aikin Yan gidan mu ne sunyi zumunchi sosai suka hada mun gida kamar na wata sabuwar Amarya ko tsohon lokaci nada ba’a saka a gidan ba. Yanda kowa ya ringa yabawa ni kuwa baqin sa nake gani dan da gidan da mamallakinsa a yanzu basa gabana ko kadan biyayyar iyaye ce ta dawo dani cikinsa. Bayan kowa ya watse Bashir ya shigo yanda kasan wasu Baqin da basu taba haduwa ba haka muka zama, shi yana kaffa kaffa dani karya yi abinda ze zama laifi ni kuma na baiwa Banza ajiyarsa ina ta sabgogina se shi da yaransa yake ta magana yana tambayarsu abubuwan da suke buqata wanda sarai nasan dani yake naji dadi da suka ce masa babu. Su kansu yaran daga kan Amna zuwa Farida ba wani sakewa sukayi dashi ba Abdallah da yan biyu ne babu abinda ya sha musu kai suke ta murna sunyi kewar Abbi. Aliyu daman yafi kowa daukar zafi, kuka ya ringayi da gaske lokacin da yaji maganar auran ya kuma dauki fushi da uban ko yau din da muka dawo ina kallon yanda yake cika yana batsewa. Da daddare gurin qarfe tara muna zaune a palourn qasa muna hira muka ga an bude qofa, da yake irin wadda bata buduwa ta wajen nan ce nasan Bashir ne shine yake da key dan haka ban ko kalli qofar ba na sake hada rai na zubawa TV ido. Da sallama a bakinsa ya shigo, takun qarar takalmin da naji bayan muryarsa ya saka na waiwaya da mamakin naga shi da waye haka karaf idona ya sauka cikin na Amirah data sha Kwalliya da wani Material Cotton baqi me Pink din flowers dinkin riga da skirt sun kamata dam se wani dan yalolon gyale data yafo a kafada. Cikin abinda be wuce second biyar ba na qare mata kallo na mayar da kaina zuwa ga TV ina nanata “La’ilaha illah anta subhanaka inni kuntu minzzalimin” a zuciyata saboda jin wani abu yana tasomun kamar zanyi aman zuciyata har wata zufa naji tana tsatstsafo mun. Ta gefen ido nake kallon sanda suka zauna akan kujera, ina jin qamshin turaren data saka ya baza gurin irin turaren da nake amfani dasu ne na Maryam collection ta zauna a kusa da Bashir sosai kamar zata shige jikinsa shi kuma se turata yake yi abin ma se ya bani dariya na dan yi murmushi a raina nace “yaro yaro ne” amma ban ko juya na kalle su ba. Ina jin yaran suka hada baki suka gaishe shi ya amsa a zatona zasu gaida Amirah se naji dif sun ma mayar da hankali akan film din da muke kallo Bashir da qarfin hali naji yana cewa wai “Baku ga Antyn ku ba baku gaisheta ba” “Wacece tana ina ai mu kai kadai muka gani Abbi se Amirah” Aliyu ya fada yana kafe uban da kallo wanda mamaki ne nasan ya hana Bashir din magana. Yanda kasan bana gurin haka nayi musu dayake film din yazo qarshe ana gamawa yaran suka miqe dan daman abinda ya zaunar da mu kenan nima se na shiga qoqarin miqewa Bashir ya dakatar da ni da cewa “Ma’u ina kuma zaki je gurinki fa muka zo” sena koma na zauna na waiwaya ina kallon sa da murmushi akan fuskata wanda a badini kuka nakeyi cikin zuciyata amma nayi Alqawarin wannan yarinyar bata isa taga gazawata ba, se a yanzu nima na dawo hayyacina tabbas idan na bar mata gidan ta ci galaba akaina dan haka zan zauna kuma ba zaman dadi ba kowa se yaji a jikinsa. “Amirah baki gaida Antyn ki ba “ ya fada bayan dana zauna, Amirah da ta hada fuska bakin nan kamar ze tabo POP tace “Nima ai yayanta basu gaishe ni ba, kana ji fa wannan marakunyar Aliyun cewa yayi ma be ganni ba kuma baka ce komai ba”. Dukda qasa qasa tayi maganar amma tsaf naji ta a raina nace “zanci uwarki ne yarinya mu dai ke zuwa”. Kamar me jira kuwa l Bashir ya hau masifa yana fada mata maganganu, abin haushi abin dariya dramar tasu ganin abin bana qare bane na miqe nace masa “Ka rufe mana qofar idan kun fita” ban ko saurara ba na haye sama na barsu a gurin. Har na kwanta Bashir ya shigo dakin, da saurin gaske ya nufoni kafin ya qaraso na dire daga gadon ban yi wata wata ba na izge Fitilar gefeb gadona daga soket na daga ta na nuna masa ina cewa “Wallahi ka kuskura hannunka ya tabani sena yi maka rotse da wannan, badai ka hadani da Goggo ta tilastani dawowa gidan ka ba, ka tabbatar da ka kaiwa tashin hankali katin gayyata da hannunka”. Yanda nayin ya tabbatar masa dagaske idan ya matsa zan iya kwada masan, daga nesa ya ringa yi mun magiya da nayi haquri na saurare shi amma nayi masa banza haka ya qaraci nacinsa ya fita ya bar mun dakin. Haka muka ci gaba da rayuwa a gidan tsakanina da Bashir daga kallo se harara shi kuma kullum yana nan a lalace gurin roqona da bani haquri amma nayi kunnen uwar shegu dashi dukda qasan raina na fara hucewa bafa wai dan na manta da abinda yayi mun ba Aa sedai kawai na yarda cewa komai muqaddari ne a rayuwa daman tun a lauhul mahfuz an rubuta faruwar wannan al’amari a rayuwar mu. Kusan sati biyu ranar ya same ni da batun komawa Lagos saboda hutun daya dauka ya qare, a lokacin bani da zabi kodan aikina da makarantar yara da suke zaune a gida ya kamata na koma sannan hakan ze dada nisan tani da Amirah dukda ko a yanzun ma tun ranar farkon suka shigo bamu sake haduwa ba. Haka muka fara shirye shiryen tafiya, ana i gobe zamu tafi ban san meya shigar da Ahmad bangaren ta ba se kukan sa muka jiyo a waje Amna ta tafi da gudu ta dakko shi ina duba fuskar yaro naga shatin yatsu da alamar marinsa akayi. Cikin tsananin bacin rai na tambayeshi waya mare shi, yana kuka da maganar sa da bata gama fita ba yace “Anty Amirah ce, da safe Abbi ya nuna masa gurin yace tana ciki shine yaje suyi wasa (Sun saba tana wasa dasu) saboda na zubar da Tea ban sani ba ta mare ni”. Zan dauki komai amma banda taba mun yara musamman ma ya zamana da cin zali amma tayi kadan dana taka gurinta nayi mata kashe di dan haka zan jira wanda ya ajiyeta yazo shine daidai yina. Da yamma Bashir ya dawo, yana shigowa Ahmad din ya tafi gurinsa da gudu ya fashe da sabon kuka yana gaya masa abinda ya faru. “Ka ja mata kunne karta kuskura ta sake taba mun yara idan ba haka ba zan dauki mataki” na fada ba tareda na kalle shi ba. Se ya juya da Ahmad din a hannunsa suka fita ban san me yace mata ba dab da magriba dan har nayi alwala naji ana buga qofa. Farida nacewa taje ta bude, tana budewa kuwa ta turo qofar da qarfi dan qiris ya tage ta buge Faridan, seda ta qaraso tsakiyar Palour ta wani tsaya ta kama qugu tace “Saboda munafunci shine za’a hadani da Mijina dan na daki yaro, ai barna yayi mun kuma ko yanzu wani ya sake zuwa yayi mun wani abu se na daka yaro sedai duk abinda za’ayi ayi, mtsw aikin banza kawai...” ban bari ta kai qarshen rashin kunyar tata ba na kai mata wani bahagon mari cikin sa’a na sameta dakyau na doke bakin fitsarar take kuwa leben ta ya fashe kafin ta gama gane abinda ya faru na sake kai mata wani ta dama ta fasa qara ta dafe kunci dama da hagu tana ihu daidai lokacin Bashir ya shigo. Ban damu da shigowarsa ba ko ihun da takeyi na nunata nace “wannan gargadi nayi miki duk ranar da kika sake tako qafar ki gurin nan ki qaddara ma gaisuwa ce ta kawoki ba wai kinzo yimun fitsara da rashin kunya ba wallahi se nayi miki dukan da zaki kasa tashi, wawiya mata hankali kawai” na juya na haye sama Bashit yabi bayana muka barta a gurin tana zunduma ihu. “Ma’u meya faru” ya fada bayan daya tarar dani” “Kaja mata kunne tafi kowa sanin ni ha sa’arta bace idan tana ji da rashin kunya da fitsararta ni daidai nake da ita zan koya mata hankalin da bata dashi” na juya na tayar da sallah ta na barshi a tsaye. Washe garin ranar muka koma Lagos, Sanda muka je na tarar Bashir ya sake gyara mana palour an chanza komai na ciki, sannan ga sabuwar mota me kyau model din shekarar a ajiye a inda nake saka mota ta, lambar jikin tsohuwar tawa dana gani a jiki ya tabbatar mun da tawa ce. Haka ya ringa yi mun abubuwa har makaranta ya chanzawa yara ya mayar da su wata da tun farko naso a saka su yace tayi tsada abubuwa dai kala kala wanda duk na neman shiri ne, daga qarshe dai bayan dogon jan rai da ban haquri dana sha kala kala daga gurin Bashir na haqura na sakko muka dawo zaman mu lafiya badan na manta abinda yayi mun ba sedan ban isa na jada hukuncin Allah ba. Iya horon da zan yi masa nayi ya kuma sauke kai ya bani haquri da tarin alqawarurruka kala kala Albarkacin son da nake masa da dattijantakar mahaifinsa ga kuma Alfarmar Mahaifiyata daya shiga na cire komai daga zuciyata ta na nemi muqulli na kulle wancan baqin littafin na rayuwar mu muka bude sabon babin rayuwa me cike da qauna da Aminci, haka rayuwa taci gaba da gara mana yau fari gobe baqi har kawo wannan lokacin da me afkuwa ta afku, Bashir ya yanke igiyoyin auran mu a lokacin dana gama ammana da bashi rayuwata. CiGaBaN LaBaRi Afuwan Uzuri ya riqeni kuyi manaji da wannan 🙏🙏 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 WATA KISHIYAR 🥰👹 (ALKAHIRI CE KO SHARRI) 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 Na Maryamah Farouk (Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah) Wattpad @MaryamahMrsAm Page 40 Mau ta kwalla ihu tadauki wuka ta nufi adda tace dan kutumar ubanki uwar bashir da dada yau sekun tafi lahira ta caka ma adda a duwawu tsiii kKeji jini nafita ta wanka ma dada mari tayi tsalle ta naushi bshir ta kwaso amira ta hau ruwan cikanta...tsiiii 😂😂😂😅😅😅🤪🤪🤪🤪sekuma kuyi nice nan shugaban en bati Har Bashir ya gama kwanakin sa a Delta ba wani magana mukeyi ba, a ranar da ya tafi dai bayan sun sauka ya kirani haka washe gari da safe kafin su fita field munyi waya bayan nan kuwa har suka kwana hudu be sake kirana ba nima kuma ban kirashi ba. A tunani na ko aiki ne yayi masa yawa, dan daman yawan ci idan yana field bamu cika yin waya ba shine dai idan ya samu lokaci ze kira to wannan karon ma na dauka a hakan ne. Ranar Lahadin da suka kwana hudu da daddare muna zaune wayar Aliyu dake kusa da ni tayi qara, "Aliyu wato har ka rarrabawa Jama'a Number ka ni bani da ita koh, waye yake kiranka da daren nan?" Na daga wayar ina dubawa. "Super hero" naga an saka, na gane Number Bashir ce sena miqa masa ina cewa "uhm uhm su Bat Man ne ko Spider man naga an sa super hero". Gaba daya suka saka dariya, Aliyu ya daga wayar suka gaisa, ban san meya gaya masa ba nadai ji yace "toh ga Mamin ma ko na bata ka gaya mata?" "Tam Abbi bye" ya sake fada kafin ya kashe wayar yana kallona. "Mami, Abbi yace Mr Kunle ze zo yanzu ya kawo saqo, akwai kudi a bedside drawer dinsa ki bashi 20k". Kamar wata sokuwa haka nake kallon Aliyun harya gama. Abubuwan mamakin da yawa, ashe Bashir yana da lokacin kiran waya nice baze kira ba. Sannan yaushe muka fara haka da ze fadi abu ni baze kirani da kansa ya gaya mun ba sedai ya kira Aliyu? Wayata dake kan centre table na janyo na danna power button dan na tabbatar ko a kashe take be sameni ba ya kira Aliyun naga a kunne take. Ga network dina full to meye dalili? "Hmmmm" na fada a fili kawai na ci gaba da kallon da muke, ba'a jima ba kuwa aka danna Door Bell Jafar yaje ya bude se gashi da Babban Package da alama PS din da aka ishe ni da naci kamar nina ce zan siya aka kawo. "Mami yana jiran saqon wai" ya fada bayan ya zauna ya fara budewa Abdallah na taya shi. Se na waiwaya na kalli Aliyu nace "Kaje ka dakko masa baya gaya maka inda suke ba?" Seda yai dan jim kafin ya miqe ya shiga dakin nasa, be jima ba ya fito da kudin a hannunsa ya miqo mun yana cewa "Gashi na dakko". A hasale nace masa "zaka tashin mun akai ne ko yaya, ina kai ya gayawa saqon kuma kazo kana nunamun me zanyi dasu". Zugui zugui ya fice ya kaiwa Kunle kudin ya dawo. Ina kallon yanda yake satar kallona ganin na dora qafa daya kan daya ina girgizawa duk sanda suka ga ina haka to sun san zuciyata a kusa take, ina iya make su idan suka matsamun. Hayaniyar da Jafar da Aliyu suka fara suna qoqarin jona PS din da Tv tasa na daka mutsu tsawa ina cewa "ku bace mun a nan, ba gobe Monday ba shine a wannan lokacin kuke shirin dasa wata Game, ku tattara ko yanzu na fasata wallahi". Kama kansu sukayi sum sum gaba daya suka watse, ina zaune ina sakin tsaki, son na tabbatar da zargina sena janyo wayata na dokawa Bashir kira na kuwa taki sa'a akace call waiting. A da, indai na kira Bashir ko da wa yake waya se ya dakata ya amsa kirana, ba qaramar waya me muhimmanci bace zan kirashi ya kasa katseta amma yau har ta gama ringing ta yanke be daga ba. Na sake kira nan ma be daga ba, seda na jera masa kira hudu amma bawan Allahn nan ko a jikinsa kuma har sannan call waiting. Agogo na kalla, tara harda rabi tayi, nasan babu wani official call da ze ce yana yi yanzu, kuma na tabbata bada Dada yake waya ba dan sanin da na mata da Tayi Isha take kwanciya to da uwar wa yake waya da baze amsa tawa ba? "Amirah" zuciya ta ta raya mun, se ta yuwu kuwa din. A jiye wayar nayi ina jiran ya biyo baya amma har goma da rabi shiru ba kiran Bashir babu labarinsa, sena miqe jiki a sanyaye na shiga dakina. Tunani na shigayi ko na masa wani abu a wayar da mukayi qarshe, iya hasashena ban gano komai ba dan lafiya mukayi hira kamar ma be tafi muna fushi da juna ba. Haka na ringa juyi a gado ina tunane tunane to wane sabon shafin ne kuma ze bude mun, koma dai menene Allah ya bamu wuce wa lafiya da haka bacci yayi awon gaba dani. Daga mamaki mani abun na Bashir tsoro ya koma bani, dan fa washe gari be biyo kirana ba, da yake na koma aiki nima ranar na shiga busy ban wani nutsu ba se da daddare na duba wayar na tabbatar da be kira ba kuma qarin abun mamaki da magriba ma seda ya kira Aliyu ya bawa dukka yaran sukayi waya harda tambayar me ze taho musu dashi. Nidai ido na kawo na zubawa sarautar Allah, duk tsiya dai ze dawo gidan se inji me ya faru kuma. Na zata ranar Larabar ze dawo tunda itace cikar sati da tafiyar su daman kwana biyar yace ko sati to gashi har yau Talata dan haka na saddaqar se gobe ze dawo. Bayan na tashi aiki  na biya na dakko yara, dukda magriba ta kawo kai haka na biya wata yar kasuwa da ake siyar da Dangin su Kaji masu rai, Bashir yana son Danderun Zabi dan haka na siyi manya guda biyu aka yanka su aka fige kamun muka kamo hanyar gida Ba mu muka isa ba se ana shirin shiga sallar Isha saboda holdup. Jakata kawai na ajiye muka shiga Kitchen tareda Amna, seda na wanke Zabon tsaf yanda nake so kafin na saka a kwando su tsane na bar Amna ta hada kayan hadi dan tana fashin sallah ni kuma na tafi nayi magriba da Isha . Sanda na dawo ta hada komai na marinate dan tasan yanda nake so, seda na saka wuqa na huda jikinsu sosai yanda kayan hadin zasu shiga na shafe lungu da saqo na ko ina ya juqu sannan na nade a Foil paper ya nadu da kyau, Already ta kunna oven yayi zafi dan haka na dora su akan Baking try da aka zuba ruwa na kunna wuta sama da qasa na rufe. Ban san sanda ze dawo ba da safe ne koda daddare dan haka A daren nan seda na hada masa zobo irin wanda yake so na saka a fridge, na gyara zogale na yanka Albasar da zanyi masa Dambun shinkafa nice harda dakan gyada kamar aljana na turara tsakin shinkar  na saka komai a fridge yanda gobe kawai sedai na hada. Na gaji tiqis, haka na koma palour na kwanta ina yi ina duba naman dana saka ina qara ruwan dan karya qone nice har qarfe biyu, jin bacci na neman fin qarfina na kashe kawai tunda nasan zuwa yanzu yafi rabin dahuwa in Allah ya kaimu gobe na ci gaba. Dakyar na iya tashi sallar asuba dan ji nayi kamar ma ina kwanciya aka tashe ni. Haka ina yin sallah na koma kan aikin, ga shirin yan makaranta da ni kaina. Qarfe bakwai muna breakfast Bashir ya kirani. Rai a sake na amsa wayar duk da qasan zuciyata akwai haushin qin kirana da yayi amma na daure dan babu qarya nayi kewarsa sosai, rabon da mu kebe tun muna Gombe. A dake ya amsa gaisuwar da nayi masa, mukayi shiru gaba daya kafin ya nisa yace "Yau zamu dawo In sha Allah zuwa dare zan shigo gida". "Masha Allah, Allah ya dawo daku lafiya nayi kewarka da yawa". Na fada cikin shauqin da na kasa dakatar da kaina. Wani miskilin murmushi yayi kafin yace "Na sani ai" "Oh ka ma sani kenan" na fada adan shagwabe. "Zan kiraki anjima" ya fada, ko kafin na bashi amsa ya katsewa wayar, sena ajiye na ci gaba da kurbar Tea na rai fes. Seda nayi yar murya sannan aka bar yaran suka shiga makaranta saboda mun makara, School Bus nace su biyo idan an tashi kawai dan inaga idan Bashir ya dawo kawai zan masa magana su ringa bin school bus din kamar zefi sauqi. A office ma ban wani maida hankali ba, qarfe biyu na dauki excuse na tafi gida. Seda na gyare gidan qal na chanza Bedsheet din dakin Bashir na saka turaren wuta. Kayan harkar dana hada na shanye kafin na dakko wani hadin dilka da Anty ta bani na na mutstsike jikina tsaf na turara sannan na dauraye jikina na koma Kitchen. Na riga naci qarfin aikin tun jiya, Danderun na duba yayi luguf dan tun shigowata na ci gaba da bashi wuta gaba daya gidan ya dume da qamshinsa ga na turaren da nayi se suka hadu suka bada wani kalar qamshin yan gayu, nan da nan na hada Dambuna sannan na dora tuwon semo da miyar Danyar kubewa taji naman rago dan Bashir yana sonsa. Kafin Magriba munyi wanka nida yaran munyi kwalliya yanda kasan ranar sallah. Wata Atamfa na saka Batik Maroon da akayiwa dinkin A line me dogon hannu babu ado a jiki se aikin stones da aka mata se walwali takeyi na kashe daurina na baza qamshi duk inda na juya yara se sun ce "kai Mami kinyi kyau wallahi" ni kuwa se jin dadi nakeyi. Ina tahiyar qarshe a sallah naji waya ta tana qara kafin nayi sallama ta katse. Bayan na idar na janyota dan nasan Bashir ne, ilai kuwa wani kiran nasa ya sake shigowa. "Ranka ya dade Mijin Ma'u, ka iso nazo na bude maka qofa ne" na fada da yar dariya. Dariyar shima yayi cikin jin dadin sunan dana kira shi yace "Mun dawo amma ban qara so gida ba" "Masha Allah, sannunku da dawowa, muna jiranka nida yara mun shirya maka babbar tarba". "Dagaske, me kika tanadar mun?" Ya tambaye ni, seda na gyara zama kafin nace "Duk abinda kake so" na bashi Amsa. "Ke kadai nake So Ma'una" yayi maganar cikin wani salo da yayi mun dirar mikiya dan har seda naji kamar numfashina ya tsaya na dan lokaci, jikina ya karbi saqon sa dagaske, se na yi qasa da murya kamar me gudun wani yaji abinda zan fada nace "Na tana dar maka kaina, kai kadai nake jira Farin cikin Ma'u". Na fada sannan muka kashe waya. Cike da zumudi na tashi na mayar da dankali na na sake gyara fuskata sosai na qara turare. Palour na dawo muka zauna motsi kadan mu kalli qofa kowa ya qagara Abbi ya 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 WATA KISHIYAR 🥰👹 (ALKAHIRI CE KO SHARRI) 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟 Na Maryamah Farouk (Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah) Wattpad @MaryamahMrsAm Page 41 Addah tana cin abincinta tana sake gayawa Dada da tayi zugudi yanda za'ayi. Da tasan halin da Dadan take ciki a sannan ma da tayi shiru tuntuni. Seda ta kwashe abincinta tas tayi gyasa kafinta dauraye hannunta tana cewa "Kinga kirashi muji zancen sakin nan da kunnen mu karma qarya shegiyar yarinyar can takeyi kinsan fa daman ta iya ta, qilan dan fada sukayi kar mu gama murna muji sabon labari". "Nidai Addah da kin tashi kinje gida kawai daga baya mayi magana" Dada ta fada tana waiwayen dakin Alhajin su Bashir daidai lokacin kuwa ya turo kekensa ya fito daga dakin. Fuskarsa ba yabo ba fallasa suka gaisa da Addah, ba tareda ya ko kalli inda Dada take ba ya kira Naziru daya kafe a guri daya kaman gunki yace ya kaishi waje. A qofar gidan kuwa bayan Naziru ya ajiye a gurin da yake zama suyi hira da mutanen sa se ya kalli Nazirun yana murmushi yace "Kaji abinda uwarku da yar uwarta suka aikata ko? Ni sam ba wannan Nafisan na aura ba ban kuma san lokacin data zama me son kanta da son zuciya irin haka ba. Amma shikenan, suma ai sun haifa". "Kayi haquri Baba" Naziru ya fada, "Kai zan bawa haquri ai Naziru ku da Allah ya jarraba da uwa mara tunani, kuyita Addu'a Allah ya tsare ku da fadawa hali irin wanda dan uwanku yake ciki dukda shi da kansa ya jefa kansa ba wani ya aike shi ba, idan kuwa harta tabbata Bashir ya rabu da yarinyar nan, hmmm Allah dai ya rufa asiri" Baba ya fada yana zaro kudi a aljihunsa ya miqawa Naziru yace "Karbomin katin Mtn na kirashi naji, wayata babu kudi". "Bari na tura maka ta Banki Baba" Naziru ya fada sannan yayi masa transfer katin ya danna wayar Bashir. BASHIR Se da gabansa ya fadi da yaga kiran Alhajin su dan muddin ba abu me matuqar muhimmanci ba Alhajin baya kiransa sedai shi Bashir din ya kirashi. Yasan kiran baze rasa nasaba da maganar sa da Ma'u ba labari yaje musu kuma wannan yarinyar ce zata fada dan se daga baya ma ya shiga dana sanin me yasa ya gaya mata? Dukda ko ba yanzu ba ai dole zasuji amma qila se kafin sannan ya gama daidaita komai. Be daga ba seda wayar ta katse yabi bayan kiran a ransa yana shirya abinda ze fada masa. "Barka da Rana Baba" Bashir ya fada bayan da Alhajin ya daga wayar, se ya mayar masa da cewa "Barka dai Muhammadu ya aikin ya iyali?" "Duk suna lafiya Baba, muna cikin aiki ne ma yanzu idan ba damuwa zuwa anjima idan muka fita sallah sena kira" Bashir ya fada yana goge zufar da tafin hannunsa yayi a jikin rigarsa, Allah yasa ba wannan maganar Baban ya bugo suyi ba dan besan me zece masa ba "Ai maganar tawa gajeriya ce tambaya daya ce zan maka seka ci gaba da aikinka, shin dagaske ne ka saki Asma'u?" Maganar Baban tayi masa dirar mikiya nan da nan ya fara in ina kamar wani sabon kurma duk yabi ya rude, dakatar dashi Baban yayi da cewa "Nutsu mana Malam Bashari tambaya ce fa me amsa da Eh ko Aa amma duk ka rikice kamar wanda Alqali ya titsiye, kaga aiki kakeyi ka amsamin na kashe wayata shikenan". Yanda yayi maganar a dake ya tabbatar wa da Bashir ba a cikin lokacin wasa yake ba, dan haka dole ya kama kansa kamar qaramin yaro yace "Eh Amma..." "Riqe bayaninka ai ka amsamin, yanzu dai ina so naji ka tuna rabar daka zo mun da zancen zaka auri yar gurin Fattu abinda na gaya maka?" Shiru Bashir yayi ya rasa ma wani abu ne ya dabaibayeshi, "Dakai nake magana kayi shiru fa Bashir" Baban ya daka masa tsawar data sakashi magana babu shiri yace "Na tuna Baba" "Me nace maka?" "Ka tambayeni dole akayi mun nace maka Aa ra'ayin kaina ne, sannan ka sake tambayata me Asma'u tayi mun nace maka babu komai" "Daga nan kuma fa?" "Ka gayamun cewa Asma'u matar rufin Asirice kuma mayafi ce data lullube ni, idan kishiya zan yi mata naje na nemo yar gidan mutunchi wadda tasan qimar kanta na hadasu amma na kafe nace ni Amirah nake so". "Ba shakka kafiya tayi amfani. Tun ba'aje ko ina ba ta rabaka da uwar gidanka uwar yayanka shida ko, to ka dai bi a sannu Bashir idan bakayi sa'a ba duniya da kanta zata koya maka karatun da ka kasa ganewa, seka zubda hawaye a lokacin da babu amfanin da zasuyi maka, ita matar fari komai mugun halin ta tana cin wannan darajar ta kasancewarta tushiya bare kai da Allah ya datar dakai da samu mace ta gari yar gidan mutunchi shine kaga ta wannan hanyar zaka gode masa ba madallah, gaka ga Fattu nan da yarta sun isheka bada misali a gaba" yana gama fadar haka ya kashe wayarsa. Sosai yake jin baqin ciki da takaicin abinda Bashir ya aikata, me yasa tun a lokacin da Asma'u ta nuna bazata zauna dashi ba be goya mata baya ta barshi tun a sannan ba? Daya san haka zata faru a gaba da koda qarfin tuwa se Bashir ya bata takardarta a lokacin da ita da kanta ta buqata amma ba'a tara sani da ikon Allah, shi yanzu da wane ido ze kalli yarinyar da Ahalinta. Wayarsa ya shiga lalubawa ya shiga neman Number Alhaji Qarami dan a yanzu shine matsayin uban Asma'u, cikin Sa'a ya samita kuwa ya dannan masa kira. Cikin mutun taka suka gaisa kafin suka shiga jimamin abinda ya faru kafin yace ya turo masa da Number Goggo ze kirata da kansa tunda Alhajin yace bata sani ba. Suna gama wayar kuwa ya tura masa dan shikansa yana ta taraddadin ta yanda ze sanar mata da wannan labari a irin yanda ta daukaki Bashir kamar dan data haifa. Cikin sa'a Alhaji Amadu yana kiran Goggo ta daga wayar, bata da lambar ya sani dan haka yayi mata bayanin shine nan suka sake gaisawa tana tambayarsa jiki da su Dada ya amsa da duka lafiya kafin suka yi shiru. "Hajia abu ne mara dadi ya faru amma ina so dukka muyarda da komai muka gani a rayuwa muqaddari ne daga ubangiji ya na yin abinda yaso a kuma sanda yaso" Alhaji Amadu ya fada bayan daya katse masu shirun. Goggo cikin rashin fahimtar inda zancen sa ya dosa dukda tasan dai baze wuce akan Asma'u ba dan haka tace masa "Amma Alhaji meya faru ne ban gane maganar da kake yi ba". "Kiyi haquri Hajia kuma ki fahimceni, magana ce akan Asma'u da Bashir, kinsan da aure da mutuwa da haihuwa lokaci ne dasu kuma idan Allah ya saukar dasu babu wani abu da ya isa ya canza faruwar hakan to a wannan gabar ma Allah ya saukar da ikonsa ya kawo qashen wa'adin zama tsakanin Asma'u da Bashir". Salati Goggo ta kwaso ta dire, cike da jimami tace "Yanzu yarinyar nan seda ta kashe auran hankalin ta ya kwanta wai me Asma'u take nema ne a rayuwa? Yarinya ace zuciyarta babu salama shekaru kusan uku da yin abun nan na zata ta haqura komai ya wuce ashe ita akwai abinda take qulla kai Jama'a wadannan yara namu Allah dai kayi musu Albarka". "Sam wallahi Hajia ba laifin Asma'u bane, bama tun yanzu ba tun tuni duk abinda ya faru ita akayiwa laifi kuma aka danneta aka sakata yin biyayyar dole saboda ita an isa da ita. Shi Bashir din ne dai daman gaban kansa yake yi a komai to yanzu ma ya sake nuna mana ya isa da kansa ya isa yanke hukunci babu shawarar kowa yayi saki ba tareda sanin mu ba be kuma gaya mun ba se matar sa ya gayawa yanzu na tsinci zancen a bakin yar uwar tasa na kirashi kuma a waya ya tabbatar mun da haka akayi, Dan girman Allah kiyi haquri, munyi magana da Alhaji Tukur yace mun baki sani ba saboda sun rasa ta yanda zasu gaya miki wannan al'amari shiyasa nace ni bari na kiraki da kaina na sanar dake Bashir be kyauta mana ba be kuma kyuatawa kansa ba. Idan Bashir yana da hankali ko dan irin qaunar da kika nuna masa kika fifita farincikin sa akan na yar da kika haifa wallahi ko zaginsa Asma'u takeyi yaci ace taci wannan darajar ya daga mata qafa ballantana na tabbatar da ko kallon banza bazatayi masa ba". "Karka yi saurin yanke hukunci cewa laifinsa ne Alhaji ita kanta Ma'u yarinya ce me naci da kafiya, wanda yake zaune da ita ne kadai yake gane halin ta tsakanin mace da mijinta kuma se Allah, Allah kadai yasan irin quntatawa da baqin halin da take masa" Goggo ta katse shi a sanyaye dan abin ya dake ta kwarai, Me Ma'u tayi wa Bashir har haka da yayi zafi ya sake ta. "Allah yasa hakan shi yafi Alkahiri" Goggo ta fada bayan dogon ban haquri da Alhajin ya sake yi mata, haka suka ajiye waya jikinta gaba daya ya mutu, "Allah sarki Ma'u ita kuma tata Jarabawar kenan akan abinda take so". Alhaji Amadu kuwa bayan ya gama wayar sa yasa wani saurayi Abokin Naziru da ya zo wucewa ya turashi zuwa cikin gida, har sannan suna zaune a tsakar gidan Addah na zuba masifa da besan ko akan me takeyi ba, haka ya gungura kekensa ya shige daki ko a fuska be nuna musu yasan me akayi ba ya kuma qudurce baze taba yiwa Nafi maganar ba koda kuwa ita ta kawo kanta da kanta, ze ci gaba da Addu'a Allah ya raya shi ya kai lokacin da zasu girbi abinda suka shuka, a rabar ne ze silleta tas ya yada mata da maganganun da suka dade suna ci masa zuciya. BASHIR Suna ajiye waya da gaba daya ji yayi rasa me yake yi masa dadi a rayuwa. Har a yanzu shi bega abinda yayi ba ya kuma san babu me fahimtarsa adan an tashi kowa bayan Ma'u zebi baza'a duba martabarsa ta matsayin mijinta da ita take takewa ba. Babu abinda yafi daga masa hankali da a kullum Alhaji yake maimaita masa watarana se yayi kuka da idonsa akan Amirah wannan ai baki yake yi masa kawai kuma ita Amiran nan fa ba irin wadda ya sani a baya bace yanzu ta chanza ta gyara duk wasu halayenta marasa kyau da ake gani a baya ita kuma Ma'un da akewa kallon ta kirki yanzu ita ce take masa abinda baya so. koma dai menene aikin gama ya gama saki dai ya rigada ya furta dukda yanzu dai yaga yayi zari da yayi mata saki har biyu dan daya ya kamata yayi na gargadi amma dai ba matsala, ze cigaba da lissafi se ya rage wata daya ta gama Iddah sannan ze ce ya mayar da ita, Dukda yasan tabbas zeji jiki na rashin Ma'u a kusa dashi abinda be taba koda mafarkin faruwarsa a rayuwar su ba amma ita ta janyo musu haka, daga ita har shi dole su shiga gararin rayuwa kafin komai ya daidaita dan ta wannan hanyar ce kadai ze horata ta yanda gaba ko ance ta sake musa masa magana bazatayi ba bare har ya bata unarni taqi bi. Haka ya ringa saqa da warwara har lokacin tashinsa aiki yayi, yasan yanzu yara sun koma gida, ze barsu daga nan zuwa Jibi Amirah tazo dan ko ya dakko su yanzu baze iya musu hidimar da suke da buqata ba dole se mace dan haka dai ze ci gaba da ja har zuwa sannan dan idan yayi shiru kar ta dauka ze bar mata yaran ne. ASMA'U Ganin har magriba tayi Bashir bezo da wani tashin hankali ba yasa hankalin tavya dan kwanta tayi tunanin ko ya haqura ya sakar mata ragamar yaran ne tunda taji sunce ya dawo harma su Ahmad sunje gidan ya basu Chocolate. Bayan Isha tana zaune wayarta tayi qara, shareta tayi dan ta gaji da amsa waya. kamar wutar daji labarin mutuwar auranta ya karade Gombe se kiranta akeyi ana mata jaje ta rasa ta bakin wa maganar ta fita amma bata raba daya biyu Bashir ya gayawa matarsa, ko yan uwansa su kuma suka kwaza a duniya daman mutane kuma masu jiran qiris nan da nan labari ya zagaya. Har wayar ta qaraci qararta bata ko duba ba can sega Amna ta fito daga daki da wayarta a hannu ta miqa mata tana cewa "Goggo ce tace ta kiraki baki dauka ba". Karbar wayar tayi ta saka a kunnenta kawai dan ta tabbatar labari ya rigada ya isar mata yanzu. Cikin sanyin daya aureta yanzu ta gaida Goggon kafin tayi shiru tana jira taji ta inda zata rufeta da fada amma ga mamakinta se ji tayi tace "Ma'u kiyi haquri, shi aure raine dashi Idan lokacin mutuwarsa yayi koda dalili ko babu se an rabu, sannan kowa da kika gani da irin qaddarar sa a rayuwa, mutuwar aure bata da dadi amma kar hakan ya sa ki dauka gazawarki ce ta janyo ko kuma wani ne silar hakan Aa babu wanda ya isa ya qulla aure ko ya kashe shi se Allah dan haka ki dauka cewar wa'adin da Allah ya dibarwa zamanki da Bashir ne ya qare kawai. Kar kuka ki ce zaki saka kanki a damuwa ko wani abu kinji kiyi Addu'a Allah yasa hakan shi yafi Alkahiri, saki nawa ne?" Cikin karyewar murya nace mata "Wallahi Goggo ma Banyi masa komai ba, kawai saboda yace se ba bar aikina saboda Amirah Shikenan abinda ya faru" "Na sani Suhaima ta gaya mun komai kiyi haquri yanzu dai saki nawa ne?" Ta sake tambayata, seda naja Majina dan ta tuno mun da kukan da na bari nace mata "Saki biyu ne kuma nayi bari dazu da safe". "Subhanallahi Bari kuma a garin yaya daman kina da ciki ne" Goggo ta tambaye ni muryarta cike da Alhini, seda na tsagaita kukan nace mata "Nima ban sani ba se shekaran jiya naje Asibiti na dawo ban ma kai ga sanar masa ba ya sake ni". "Yanzu be san da maganar cikin bama bare barin kenan, ai kuwa ya kamata tun wuri a gaya masa tunda kinga kenan kin gama Iddah kar yaje yayi ta lissafin Bogi tunda da sauran igiya a tsakanin ku" Goggon ta fada, da mugun mamakin maganar ta nace "Yanzu Goggo har kina zaton cigaban zama tsakanina da Bashir, ai Goggo ko shine autan Maza na haqura dashi. Sakina fa yayi sakin wulaqanci akan kishiya wallahi sedai ya zauna da ita wadda yake so har qarshen rayuwarsa ko ze mutu dan nagama auransa, dan Allah a wannan karon kar kice zaki tilastani komawa gidan Bashir in dai ba so kike zuciyata ta buga na mutu kowa ya rasa ba" na fada ina qara fashewa da Kuka. Qarshen abinda Goggo zata sakeyi mun a yanzu ta maida ni gidan Bashir, ba dan na dena son Bashir ba wannan nasan wani abu ne da har na mutu yana raina amma na tsani zama dashi ba kuma na fatan Allah ya kawo dalilin da ze maidani gidan sa. Duk da yana yin da take ciki seda tayi yar dariya kafin tace "Ni ban ce ki koma gidan Bashir ba amma idan zama be qare a tsakanin ku ba haka zaku gama duk abinda zakuyi kuma ku koma ku ci gaba da zama dan haka duk abinda zakiyi karki tsananta ko dan Albarkar zuri'ar da take tsakanina ku. Sannan maganar yara idan har ya matsa ki bashi yayansa kar kice zaki tsaya ja in ja dashi tunda yana da me riqe masa shikenan, ke kuma zamanki a nan baze yuwu ba zuwa safiya zan kira Alhaji Qaramin kodai ki nemi transfer ki koma can Abujan gabansa ko ki aje aikin ki dawo gidan ku ki zauna amma bazaki zauna ke kadai anan ba". A gaba daya tsarikan na Goggo babu wanda naji yayi mun, bana jin zan iya bawa Bashir yarana maganar Transfer kuma ko barin aiki ta manta aikin akansa aka sake ni sannan na barshi ai kuwa na tashi a tutar babu, amma yanzu bazan musa mata ba zan barta tayi magana da Alhaji Qaramin na tabbatar shi baze bari a rabani da yayana ba ko aikina. Haka mukayi sallama tana sakeyi mun nasiha na kuwa ji dadin magana da ita sosai muka rabu tana jaddada mun dana sanar da Bashir maganar ciki da kuma Barin da nayi dan gudun abinda kaje ka dawo, haka na kwana da niyyar gobe idan yazo kai yara makaranta zan gaya masa tunda da alama bega takardar dana ajiye masa ba. BASHIR Yauma dai a hanya ya siyo abincin sa haka ya dawo gidan na nan a yanda ya barshi sema qarin datti da yayi saboda qurar qasan gado da suka watso masa palour dazu. Haka ya shiga dakinsa yayi wanka gaba daya gurin ya hargitse masa ya rasa ta yanda ze fara mayar da kayansa cikin wardrobe tunda ya saba da an kawo masa guga Ma'u ce take jera komai a inda ya dace. Haka ya zura jallabiyya ya dawo palour ya kade kujera ya zauna ya bude abincin, loma uku yayi ya ture gaba daya abincin ya fice masa daga rai dan bakinsa ya saba dame dadi, dukda wannan din ma me dadin ne amma dandanok girkin Ma'unsa ya banbanta dana kowa shikadai ne abincin da ko iya qamshinsa yana rage masa yunwa dan shi fa abinci indai ba nata ba ko yaci baya jin ya qoshi sedai kawai cikinsa ya cika maganin yunwa amma ba wai dan ya gamsu da cewa abinci yaci ba. Yana zaune yana dannan waya su Ahmad suka shiga gidan da gudunsu, Ganin sune ya debe masa kewa har aka kira sallah suka tafi masallaci tare, yana kallon Aliyu ko inda yaje yaron be kalla ba yayi murmushi kawai da suka dawo zaau tafi ya dakko Chocolate ya basu harda ta sauran kafin ya raka su har qofar gidan suka shiga, yana jiyo qamshin abinci da alama girki sukeyi. Badan kar mutunchinsa ya zube ba babu abinda ze hana ya shiga yaci amma ya qudurce a ransa dole ya koyawa Ma'u hankali ta yanda da kanta zata bishi ta bashi haquri, a qalla se tayi kusan kwana dari da wani abu kafin cikar Iddarta dan watan ta me kwana talatin da shida ne kafin sannan kuwa ta biyu liqis ta yanda ko kara ya ajiye bazata sake tsallakawa ba. Haka yaja jiki ya wucw yana hadiyar yawu, qarshe se se shayi yasha da wani guntun cake da Allah yasa basu dauke ba ya hada da dambun nama shima a irin wanda take masa ne ya ajiye a office ya tuna yana mota ya dakko shi. Seda yaje kwanciya idonsa ya kai kan farar takardar da tun jiya ya ganta amma be duba ba, daga kwancan ya janyota ya bude yana mamakin ko tasa ce ma ya manta sedai tambarin Asibiti da sunan Ma'u daya gani yasa ya qara hasken fitila dan ya gani da kyau. "Kai Allah na gode maka, Wallahi Allah yana sona" ya fada a fili cikin farin ciki, wannan wata dama ya samu ya tabbatar se Asma'u ta kawo kanta da kanta musamman da yawancin cikinta suna qara mata buqata yana zaune zata zo har inda yake ta bashi haquri kai wannan abu ya masa dadi. Hotonsu dashi da ita da yake akan bedside drawer ya dakko yana shafa fuskar ta, ranar Anniversary dinsu na shekara Goma suka duke shi daga shi har ita suna dariya ya manta dariyar me sukeyi a lokacin. Sumbatar fuskarta yayi kafin yace "Kiyi haquri Ma'una, nasan sena fiki azabtuwa da rashin ki a kusa dani amma ke kika jawo mana, taurin kanki da kafiya ya saka komai ya faru amma yanzu ga dalilin da ze dawo mun dake cikin ruwan sanyi na samu, Ina son ki Ma'una". Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels