Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels *GIDANTA NA GIRMA* *BY NANA: KHADEEJATU* _*UMMU IHSAN*_ *SADAUKAR WA GA:- DUKKANIN MASOYA NA NA BOYE DANA BAYYANE INA SONKU SOSAI SON FISABILILLAH* *YA ALLAH KAJIKAN MAHAIFINA KAYI MASA RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SA SHIDA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.* _*Bismillahir Rahmanin Rahim*_ 1~5 "Wayyo Allah Mamar mu kin tafi kin barmu cikin kuncin rayuwa wallahi sai na bikii... " Kawai bata 'karasa ba ta shed'e ko motsi babu, duk ilahir mutanen gidan gaisuwar nan akayo kan ta, ruwa aka fara zuba mata amman bata motsa ba. Rudewa yayar ta tayi, da gudu tafita kofar gidan tana ihu, mazan dake kofar gidan sukayo kanta da gudu, tambayar sukeyi miye yake faruwa amman ta kasa magana sai cikin gidan take muna masu, ai kuwa basuyi kasa a gwiwa ba suka shiga cikin gidan da gudun su. Hankalin su ne yayi mugun tashi ganin abunda ke faruwa, wani dattijo ne wanda daga gani kasan shine mahaifin su, dan sunyi matukar kammani dashi, ya duk kusa a kusa da yariyar wadda bazata wuce shekara Tara ba, ya duka ya d'auke ta idon sa cike da hawaye amman kuma hawayen ya'ki barin su, su zubo masa 'kofar gidan ya nufa da ita, wani mutume ne ya d'auke su a mota harda yayar tata, sai asibity. Taimakon gaggawa aka bata, su kuma duk suna waje a tsaye sai jeka dawo sukeyi. Doctor ne ya fito yace, "ga wannan takardar a nemo wannan maganin da sauri". Mutunen ne ya amsa ai kuwa sai gashi da magani da ruwa ya kai aka ansa, cikin ikon Allah, sai gashi ta falka da kuka. Allurar bacci yayi mata, ya fito, hannu ya baiwa mutanen yace, "ta falka amman nayi mata allurar bacci, saboda haka insha Allah data falka zata dawo cikin hayyacin ta". Sai doctor yace, "amman dan Allah miye ya firgita ta haka gashi zuciyar ta tafara kumbura dan gab take da kamuwa da ciwon zuciya mai tsananin gaske ". Sharce hawayen sa dattijon yayi, yace, "ai dole Husnah ta fir gita tayi kamar zata hauka ce, mutuwar uwa ai babban rashi ne, koda ciwo ballema mutuwar cotsom d'aya". Shi kamshi doctor ya tsorata sosai a take yaji tausayin yarinyar ya 'kara kama sa, Addu'a yayi masu tare da ta'aziyya. Godiya sukayi masa, ya wuce su. Zaman sukayi na d'an wani lokacin kafin dattijon ya tashi yazo gurin yar sa d'aya yace mata, "Zara ku sanya hakuri da juriya a cikin zuciyar ku ki zauna da yar uwar ki, lallashe ta, ki sanar da ita, mahaifiyar ku Addu'a take bu'kata ba kuka ba, zan je gurin ansar gaisuwar ne. Gyad`a masa kai takeyi hawaye na zubar mata a ido. Tafiya sukayi su biyu ita kuma ta zauna har sai da nurse tazo ta kirata sannan ta shiga cikin d'akin, gin cire yarinyar take a jikin gadon da Karin ruwa jone a hannun ta. Kujera taja ta zauna a kusa da ita tana kallon ta, tausayin kansu ne ya'kara kama ta. Tace, "Husnah muyi wa Mamar mu Addu'a ba kuka ba, nasani Mama duk da koda tana a raye bata iya hana a cutar damu kuma, duk azabtar war da akeyi muna tare da ita akeyi muna shi, uwa_uwa ce bare ma uwar da ta koyar damu hakuri da dan gana, ko kin manta da cewar, kullum sai tayi muna nasahar mu d'auki kaddara mai kyau ko marar kyau?, Husnah kin ga gashi doctor yace, kin kusa kamuwa da ciwon zuciya dan Allah ki rufa mani asiri kin san nice kawai zan shiga cikin wani halin idan kika samu wata matsalar". Hawaye sukeyi, babu mai lallashin su, sai mutanen dake gurin da yaran suka cika zuciyar su da tausayi, duk rashin tausayi irin na nurse amman sunji tausayin yaran. Daket Husnah tace, "Aunty Zarah shike nan Mama ta tafi ta barmu ko? Kuma sai da nace mata, kada ta tafi ta barmu gashi kuma Baban mu baya son mu, baya kulamu". Rufe mata baki Zarah tayi tace, "haba Husnah kada kice haka kiyi shirun ki kawai Baban mu yana son mu". Da sauri Husnah tace, "shine ya kawo mu nan ya gudu ya barmu ko? Kuma kice yana son mu, ko ya bar maki kud'in da, zaki siya muna abinci ne, nifa Mamar mu kawai zanbi". Kuka Aunty Zarah takeyi sosai, ganin hakane yasaka Husnah kuka itama sai tayi shiru da masifar ta. Tun 'karfe goma na safe suke asibityn nan har la'asar babu wani abunda ya shigo hannun su, ganin sun gala baita ne yasaka wata matar dake kusa dasu ta basu abinci da ruwa. Godiya sukayi mata, Zarah ce, take baiwa Husnah abincin a baki har sai da takoshi, sannan itama tace shinkafar jalof. Har dare babu Baban su babu labarin sa kuma babu wanda ya leko su, mutane sai ala waddai da irin wannan halin sukeyi. Mutanen gurin kowa basu abinci yakeyi da kayan mar mari iri daban_daban. Da safe 'karfe takwas da rabi, doctor ya duba Husnah yace, "zan sallame ta a yanzun dan Allah ku kula da maganin ta dan gab take da kamuwa da ciwon zuciya mai tsanani, amman idan an kula da damuwar ta da maganin ta Insha Allah komai zai zama dai dai kuma naga harda Olsar ke gareta dan Allah ku kula kunji ko? ". Gyad'a masa kai Zarah takeyi tace, "mun gode sosai". Sallama ya basu Husnah fad'ar takeyi, "Anty Zarah muyi zaman mu anan inda babu wanda yake takura muna kuma muna samun abinci mai yawa muna ci ko? ". Gir giza mata kai tayi tace mata, "dole ne mu koma gida mu zauna kawai dai musaka hakuri a lamarin mu". Wayau tayi mata, suka bar asibityn tare da wasu kud'in da wasu mutane suka basu, da murna Husnah ta anshi kud'in tana godiya tare da farin ciki, suna fita Husnah ta kwance zanen ta, ta nade kud'in ta kullesu a habar zanen ta, ita dai Zarah kallon ta kawai takeyi abun hawa suka hau suka sauka unguwar su. Mutane sai gaisuwa sukeyi masu, a take kuma mutuwar mahaifiyar su ta dawo masu sabuwa. 'kofar gidan su babu kowa duk mutane sun watse cikin gidan suka shiga wanda suke jin kamar kada su shiga cikin gidan. Addu'a d'auke a bakin su suka shiga cikin gidan sallama sukayi aka kyalesu ga mutane zazzaune kamar itace basu amsa Sallama. Baban sune zaune yana cin tuwo ya kallesu kallo d'aya, ya watsar, kawai cikin masifa wata mata tace, "to gan talali harda mutuwar uwar baisa kun natsu ba, sai da kukaje yawon karuwan cin, ai dama nasani tun jiya kuka baro asibityn sai yanzun kuka ga damar dawowa gidan nan ko!? ". Fashewa sukayi da kuka kamar ransu zai fita. Tace, "kukayi banza dani ko bada ku nake ba ne? " Cikin rawar baki Zarah tace, "kiyi hakuri Goggo wallahi daga asibity muka fito" cikin kuka take maganar. Tsawa ta daka masu tace, "kai..! Kada ku maida mu mahaukata ko kuma makafi mana! Dubi yanda kukayi mul mul abunku dubi yanda kuka dawo kamar ba masu jinya ba, anya ma kuwa kunji ciwon mutuwar uwar ku kuwa? ". Kukan makirci ta fashe dashi tanayi tana fad'ar, "Allah na tuba yaran nan zasu sakani bakin mutane bayan mutuwar uwar su, shine zasu fara biyar maza duka yau kwana d'aya da mutuwar uwar su, wai nikam yaya zanyi da y'ay'an Allah bani? ". Kukan takeyi tana fyace majina da habar zanen ta. Cikin 'bacin rai da masifa Baban ya jefo su da kwanon da yake cin tuwon sa yana fad'ar, "wallahi 'karya kukeyi ku saka ni kuka, tun kuna yaran ku, wato abun da uwar ku ta koyar daku ke nan ko? ". Da gudu suka shige cikin d'akin su suka rufe jikin su sai rawa yakeyi dan sun san yan zun nan za a had'a masu jini da majina. A bakin gado suka zauna sai rusa kuka sukeyi Zarah ce ta goge hawayen ta kwantadda Husnah akan kafafun ta, tana lallashi, dukan 'kofar yakeyi kamar zai 'karya ta yana fad'ar, "kuzo ku bud'e 'kofar nan kafin na balla ta na shigo ciki". `Kin bud`ewa, sukayi har sai da ya gaji yayi tafiyar sa. Basu fito ba sai bayan magrib suka bud'e sukayo alwala suka dawo d'akin sukayi sallah, suna zaune har 'karfe goma na dare babu abunda suka saka a bakin su, dabara ce ta fad'o masu, suka lallaba suka d'auki kwano, sukaje suka siyo tuwo suka dawo cikin ikon Allah babu wanda ya gansu. Tuwon sukaci, Zarah ta baiwa Husnah maganin ta suka kwanta. Sai kukan kewar mahaifiyar su sukeyi a haka bacci 'barawo ya sace su. Tun da asuba suka tashi, sukayi sallah sannan suka fita tsakar gida zaunar da Husnah Zarah tayi, ai kuwa a take tafara wanke_wanke da share_share sannan ta d'ora ruwan dafuwar kuko. Suna tafasa kawai ta dama kokon ta ajiye masu suka dawo cikin d'akin su. Fitowa uwar ikon tayi zata fara masifa sai hamma takeyi daga gani ko sallah batayi ba, gashi koda take ta zabga hamma babu Addu'a, abun da yabata mamaki shine duk aikin da take son taci masu mutumci idan basuyi ba, sunyi har sun gama, dube_dube ta somayi ko zataga wata matsalar ta daban amman bata gani ba. Tsaki tayi ta wuce ta d'auki buta, ta shiga cikin bayi ta fito ta wanke baki ta debi kokon tasha, ta zabga sugar sai da tayi biyu da robar koko san nan ta tashi ta fara `dauraye jikin ta ta shiga cikin d'akin ta sanyo hijab ta d'auko charbi ta shiga d'akin Baban su Husnah, ta gaishe shi sannan ta fito ta zuba masa kokon, ta kai masa, yaran ta ne suka fito su ukku mace biyu na miji d'aya babu sallah babu salati, kawai suka wanke baki suka zubo kokon suka 'koshi ragin da sukayi ne aka zuba wa su Zarah aka kira su suka zo suka d'auka, da sanyin sa suka sha. Misalin 'karfe sha d'aya gidan ya cika da ba'ki na ban mamaki. A take jikin su Goggo ya d'auki mazari sai ta samu guri d'aya tayi zaune ta rafka uban tagumi. Su Husnah kuwa farin ciki ne ya kamasu a take taje gurin mutanen ta shige cikin su. Bayan duk sun zazzauna ne, wani dattijo wanda yadara Baban su Husnah tsufa kadan kuma gashi kamar su d'aya, yace...... *Comment and share* _*Yin comment din ku da sharhin ku shine zai bani damar ci gaba da wannan labarin kuma shine zai bani tabbacin cewar kuna son labarin*_ *A GIDAN TA NA GIRMA* *BY NANA: KHADEEJATU* _*UMMU IHSAN*_ *SADAUKAR WA GA:- DUKKANIN MASOYA NA NA BOYE DANA BAYYANE INA SONKU SOSAI SON FISABILILLAH* *YA ALLAH KAJIKAN MAHAIFINA KAYI MASA RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SA SHIDA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.* _*Alhamdulillah Allah ya dawo dani lafiya na samu sau'kin jiki na ina godiya a gare ku masu kirana kuji ya na 'kara ji da jiki na Alhamdulillah Nasamu sau'ki sosai nagode da kulawar ku a kaina*_ _*Bismillahir Rahmanin Rahim*_ 6~10 Mutumen yace, "Allah ya jikan ki Hinde mutuniyar kirki a gaskiya anyi babban rashi a gaskiya mutuwar Hinde tabar gurbi mai wuyar cikewa ya Allah kayi mata rahma" Ya madaida kallon sa gurin Baban su Zahra yace, "zan dauki Zahra na had'ata da sauran yarana har zuwa lokacin Auren ta, Amina kuma tace itace zata dauki Husnah". Da kuru ruwa da har gowa delu tazo a gaban mutamen tana fad'ar, "dan Allah kada ku rabani da yarana wallahi ina son su zanyi masu ri'ko na amana da gaskiya" hawaye kawai take zubar wa tayi kwance ta rike 'kafar dattijon tana kuka. Kallon ta kowa yakeyi Zarah da Husnah kuwa sakin baki sukayi suna kallon salon makirci irin na marka. Girgiza kansa dattijon yayi yace, "nasani zaki iya ri'kesu a gurin ki bawai bazaki iya bane malka, ko dan ganin mahaifin su Amman gaskiya kiyi hakuri kuma ba yanzun zan dau'ke suba sai angama ansar gaisuwa duk da naga kamar angama ansar gaisuwar ace kwana d'aya har anwatse kamar daman an matsu mutum ya mutu? ". Babu wanda yace uffan daga cikin su Malka da Baban su Husnah. Yan uwan girgiza kansu kawai sukayi suna jin zafin wannan mugun halin na mutanen gidan nan, Malka kuwa tunda taji abunda wannan dattijon ya fada sai ta tashi zaune na matso hawaye dan yaji tausayin ta, amman ya dauke idon sa yana kallon su Zarah yana 'kara tausaya masu. Addu'a sukayi suka tashi tsaye dattijon yace, "Sa'idu kaji dai hukun cin dana yanke a matsayina na yayan ka kuma koda wasa kada naji kada nagani, Allah ya jikan ta da rahma Allah ya baku hakurin jure rashin ta". Kallon sa ya maida akan Zarah da Husnah yace, "to muntafi sai mun dawo ku kara hakuri kuma kuyita yiwa mahaifiyar ku addu'a kunji ko? Domin addu'ar ku tana isa a gareta ". Gyada masu kai sukayi. Rakiyar su, sukayi sai da suka ga tafiyar su suka dawo gida suka tarad da Malka ta balbale Baban su da fada tana fad'ar, "ai wannan tozarci ne wallahi dan mutum yana gaba dakai shine har yake da ikon zar tar da hukunci akanka da iyalan ka? Abu sai kace wanda ya haifeka ako dai koda wanda ya haifeka ne banyi zaton zaka kasa ce masa komai ba, wallahi malam ka bani kunya wallahi, yaran ka matane fa kasan irin abunda ya tsara a ransa kuwa a kansu ? nifa ban ma yarda da wannan salon nasa ba". Tashi mahaifin su Husnah yayi ya fita yabar mata gidan, dan ya kasa musawa Yayan nasa dan ko iya hada ido dashi bayayi ballema har takai ga yayi musu dashi. Da ido tabisa ta ri'ke ha'ba tace, "ikon Allah wato dai malam indai a kan zancen Yayan san nan ne bazai iya attaka komai ba, haka kawai mutum ya shanye kowa a cikin dan ginsa dan yafisu kud'i wallahi indai nice Malka sai na hana yaran nan jin dad'in rayuwar su". Kallon ta kawai su Husnah keyi kuma itama tana kallon su amman ta'ki daina fad'ar abunda take fad'a a gaban idon su. Bokiti kawai suka d'auka suka fita d'ebo ruwa, koda suka kawo masifar takeyi bata daina ba yaranta ne zaune sun d'aura kafa d'aya a kan d'aya suna zaman kashe wando. Ajiye ruwan sukayi suka hada kayan wanke_wanke Zarah ke wankawa Husnah na d'auraya, suna gamawa suka d'aura girki sukayi alwala suka nufi daki Malka cikin masifar ta tace, "munafukan banza uban waye kuke nunawa cewar ku musulmai ne , ita kanta uwar taku a lokacin karuwa ce sai da aka 'ka'kabawa Malam ita sannan ta daina a cewar ta amman bafa barin tayi ba, ina kallon yanda take fita zuwa yawon karuwan cin ta, asirin tane kawai bai tonu ba har ta mutu, kunga ke nan ku kan ku ba kuda ya'kinin cewar ku masu tsalki ne ko masu kazanta ne?". Wannan maganar kam ta shigesu musam man ma Zarah wadda take yar shekara sha biyar hawaye kawai ke zubo mata tana sharewa har suka gama sallar. Husnah tace, "Anty ki daina yiwa muguwar nan kuka wallahi idan nayi kud'i sai na rama muguntar da takeyi muna da zagin mahaifiyar mu harda su kazafi wallahi bamu yafe ba, ko kuma itama nayi mata Addu'a ta mutu kowa ma yafuta". Murmushi Zarah tayi tare da shafa fuskar kanwata, sai kuma ta tuno da itama Husnar an kusa rabasu, kawai ta sake sakin sabon kuka tana fad'ar, "mutuwa mai tonon asiri yau gashi rashin uwa zai saka a raba mu nida 'Kanwata ya Allah ka bamu hakuri ya Allah kabamu kariyar ka a duk inda muka tsinci kanmu ya Allah kada ka baiwa wani azzalumi cin nasara a kanmu ya Allah kasani yan zun bamuda wanda zai kwabemu idan muka aikata ba dai_dai ba,ya Allah ka d'ora marayun ka a kan dai_dai ya Allah kada kabarmu da dubarar mu!". Cikin kuka Husnah ke cewa,"amin ya Allah Anty ai kema ba mutuwa zakiyi ba kibarni ko? kamar yanda Mamar mu ta tafi tabar mu ". Kiran da akayi masu ne ya sakasu fita ni'kan gari suka kai sai kuma cefane, Husnah ce ke 'kul 'kule Zarah kuma ita ke girkin. Haka rayuwar su ke tafiya har akayi sati ukku da rasuwar mahaifiyar su . Du'ke Zarah take tana yiwa Malka da yaran ta wanki Husnah na zuwa d'ebo mata ruwa duk sun gaji, Baban nasu na zaune yana sauraren Radio yaran Malka ukku Ashiru da Nafi da indo suna zaune suna cin abinci dan basuda aiki sai wannan. Malka kuwa ta kasa ta tsare tana iya bakin 'karfin ta tana zabga bala'i, "wai wankin 'keta ne Zarah keyi masu bata murza kayan sufita". Sallamar da akayi aka shigo ne ya hanata ci gaba da masifar su Alhaji Audu ne wato Yayan malam Sa'idu shida wasu yan uwan sa harda mata a cikin su sun kai dai su biyar. Kallon su Zarah sukeyi da suketa zufa ga gajiyar wanki ga zafin rana ga yunwa, girgiza kan su sukeyi tare da kallon yaran Malka dake cin abinci a kusa da dan uwan su. 'Kara sowa sukayi cikin gidan Malka duk ta tsure karyar ta ta 'kare yau sai tayi mutuwar zaune dan batayi zaton cewar maganar daukar su Zarah tana nan ba dan har ta manta da wannan zan cen. Alhaji Audu ya kalli d'an uwan sa yace, "anyi walkiya mun gano komai Zarah had'o kayan ki mu tafi Amina kuma zata zo ta d'auki Husnah zuwa gobe". Wani kukan ne ya kama su Zarah da Husnah ai kuwa sunci kuka da ket aka raba su aka tafi da Zarah. Husnah sai ta dawo abar tausayi yanzun kam ta zama marainiya ga rashin uwa ga rashin Yayar ta kuma abun takaici babu mai janyo ta jikin sa yayi lallashin ta. Gabaki d'aya gidan zama yayi shiru saboda Malka yan zun han kalin ta yayi mugun tashi saboda taga alamar fa yaran nan za suyi gaba fa ita kuma ta d'auki alwashin wula'kan ta rayuwar su sai sun zama abun kwatance. Baban kuwa kamar baya gurin haka ya zama. Da dare Husnah batada abunda zataci abinci dole ta kwanta bacci ya kasa 'daukar ta gashi tsoro takeji babu mahaifiyar su babu Anty Zarah, sai yanzun takara yarda da cewar itama fa tafi kowa maraici kaka kawai takeyi ta dun kule guri daya, har bacci ya d'auke ta baccin wahala. Run sanyi aka kwalaya mata, a take jikin ta ya d'auki mazari da rawar sanyi. Malka ce a tsaye sai cika take tana batsewa ri'ke take da bokitin ta a hannun ta tana harar Husnah tace, "uwar kice zata fito ramin tazo ta hura wuta ta d'ora Abinci tayi mani shara da wanke_wanke Iye? " Girgiza mata kai kawai Husnah keyi, sai rawar sanyi takeyi Malka tace, "tsohuwar munafuka karuwa lalatacciya shegiya maza jeki kifara yi mani aiki tun kafin na kasheki da hannu na! ". Ai kuwa da gudu Husnah tabar d'akin taje ta had'o kayan wanke_wanke ta ajiye ta d'auki tsintsiya ta soma shara tana kuka ga iska na bugowa ga sanyi na shiga cikin jikin ta, tana 'karasa sharar cikin rashin kwarewa ta d'auki bokiti taje ta d'ebo mata ruwan sai da ta cika komai tafara kiciniyar d'ora girki gashi bata iya ba, ko itacen bata iya had'awa ba, Malka kuwa duk abunda takeyi akan idon tane, kuma tayi kamar bata ganta ba, ganin har tara tayi ne yasa kata zuwa gurin tasa hannu ta turata ta fad'i 'kasa, hannun ta ya daki dotsen murhun taji zafi sosai, da sauri ta tashi ta bata guri tayi gurin wanke_wanke tana gamawa taje tayo alwala ta shiga cikin d'akin nasu ta cire kayan jikin ta wanda ya soma bushe wa a jikin ta, ta tsane ruwan dake kwance a tsakiyar d'akin san nan tayi sallar asubahi. Har wucewar sha d'aya sannan aka kirata Malka tace, "dan uwar ki jeki ga ragin koko can 'kuda nabi ki d'auka kisha dan kawai naji ance babu kyau horo da yunwa dana haneki kokon nan. Allah sarki cikin rawar jiki da sauri Husnah ta d'auki kokon duk yayi 'kasa saboda iska gashi duk yayi kakka'bi abun dai zar tausayi haka ta zauna ta shanye kokon har tana sarkewa, harda sud'e kofin sai da Malka tace mata, "shegiya kada ki fasa mani kofi jeki kwaso sauran kayan ki wanke mani su kuma akwai kayan da Zarah bata 'karasa wankewa ba jiya yanzun ki 'karasa wanke su, dan uwarki dan baki sha kokon banza ba". Babu digon tausayi haka ta kwaso mata kayan nasu harda su zanen gado wanda akayiwa fitsarin kwance. Har Husnah ta d'uka zata fara wan kewa aka doko 'kofar gidan aka shigo ko sallama babu da ido kowa yake biyar su Baban ne ya fito daga cikin d'akin sa cike da mamaki yake kallon su, haka Malka da yaran ta duk sun saki baki da hanci suna kallon 'kofar gidan. Kallon kallo akeyi tsakanin Malka da Malam da yaran gidan Husnah kuwa kallo d'aya tayiwa gurin ta d'auke kan ta ta soma jika kayan dan kayan sunfi 'karfin ta bata iyawa dasu sai dai ji'ka_ji'ka. 'karaso mutanen biyu sukayi d'ayar tace, "bakwa bu'katar sallama da munyo maku, Am ba zamu 'bata lokaci ba, nasani sarai wannan gidan shine gidan Sa'idu kuma mijin mataciya da musaka, am batare da 'bata lokaci ba, munzo ne zamu d'auki "yar mataciya Husnah take ba? ". Malka tace, "uban waye ya turo kune yace kuzo kuyi wa mutane fitsara 'kana nan yara daku?". Kawai d'ayar tace, "ubanki ne ya turo mu kaji shegiyar mata ana magana da wanda yake matsayin uban yarinya shine zaki wani sakawa mutane baki? Kuma idan kika 'kara kwatantamu da 'kana nan yara sai mun nuna maki cewar munfi ma inda kike tuna nin kaimu". Malam yace, "waye ya turo kune gidan nan? ". Kai tsaye sukace, "Amina ce 'Kanwar ka ga photon ta, ansar photon yayi yace masu, "ga Husnah can ke kizo kibisu". Malka tayi tsalle ta dire tace masu, "babu inda zata, sai dai su d'auki Indo ko Nafi". Kallon inda takeyi masu nuni sukayi suka bushe da dariya, d'ayar wadda tun zuwan su batayi magana ba, tana dai kallon sune d'aya bayan d'aya tace, "Husnah muka zo d'auka kuma ita zamu d'auki dan haka kubamu Husnah ta bud'e jakar ta ta d'auko bandir din yan naira dari biyar biyar ta isa gaban Malka ta janyo hannun ta ta d'ora mata, ta wuce ta isa inda Husnah ta janyo hannun ta suka zo zasu fita Husnah da sauri ta kwace hannun ta tayi cikin d'akin su da gudu jakar da Zarah ta shirya mata jiya itace ta kama ta run gume, tayi zaune tana zabga kukan da tarasa na miye ma takeyi, saukar lafiyayyen mari taji wanda ya d'aga mata hankali ya rud'ata da sauri ta tashi tsaye Baban sune tsaye yana fuci kamar wani wanda yayi gamo da kumurcin maciji, ya janyo hannun ta da 'karfin gaske ya fito d'akin da ita ya dan kawa matan nan su biyu ita yace gata nan baiwar kuce duk irin hukunci da kuka ga damar yi mata kuyi mata shi saboda ta 'bata maku lokacin ku kuma ku sani ita din baiwar kuce duk irin hukunci da kuka ga damar yi mata koda laifi ko babu kuyi mata ai dai kun biya kud'in ta tunda kun bani dubu dari da goma kun baiwa Malka dubu hamsin yaran gidan nan kowa dubu ukku ukku". Dariya sukayi suka ja hannun Husnah wadda maganar da Baban yayi taka ma yi mata yawo a 'kwa'kwalwa sai kawai ta saki jikin ta tabisu babu wanda yayi yun 'kurin biyar bayan su babu wanda ya tambayi sunan su kawai dai sun sayar da marainiya ne. A cikin motar su suka saka ta suma suka shiga driver ne kejan taxi din, 'yan unguwar kuwa cike da mamaki yaran da suka labe lokacin da suka ga zuwan wannan mutanen duk sunji abunda ya faru ai kuwa suka sanar wa mutanen unguwar, ai kuwa mutanen na shiga motar har sun fara tafiya aka bisu da jifa. Da gudu suka bar unguwar suka d'auki hanya sai wani dajin a bakin titi suka tsaya, suka fito suka sallami mai taxi din suka shiga tasu motar suka d'auki hanya tun sha biyun rana sai 'karfe shida suka tsaya suka sayi abinci a wani hotel suka baiwa Husnah baiwar Allah Leda d'aya suka d'auki nasu suna tafe sunaci ita kuwa Husnah ta 'kasa wani dogon motsi dan ta tabbatar da wannan mutanen masu yanka kan mutane ne. Jin jikin ta na rawa, gashi har 'karfe tara na dare yayi ne ya sakata yin saduda ta bud'e ledar ta d'auko robar ciki ta lemo da naman kazar dake ciki ta soma ci, cin yuwa sai da ta 'koshi zuwa dare misalin 'karfe sha d'ayan dare suka 'karaso inda suka tsaya a bakin titi matar d'aya ta bud'e motar ta fito ta zago gurin Husnah ta bud'e motar ta janyo hannun ta daman Husnah ri'ke take da jakar ta, fitowa tayi sukayi sallama tace mata jirani na kawo maki naki kason, ai kuwa da murna matar ta sara mata, hannun Husnah ta ja suka tsallake titin a gurin wata 'katuwar mota fara suka tsaya ta janyo remote ta bud'e motar ta saka Husnah a kujerar mai zaman banza ta rufe, ita kuma ta zagayo ta bud'e motar ta d'auki wata jakar ta tsallaka titin ta kaiwa matar, aikuwa da farin ciki ta ansa ta bud'e jakar cike da kud'i, sukayi sallama suka rabu. Tana bud'e motar ta shiga kawai ta tayar da motar suka d'auki hanya tana tu'kin motar tana kallon Husnah ganin duk ta takure guri d'aya sanyi yayi mata yawa sai tayi dariya tace....... *Comment and share* *GIDAN TA NA GIRMA* *SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU SOSAI SON FISABILILLAH* *YA ALLAH KAJIKAN MAHAIFINA KAYI MASA RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SA SHIDA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.* *Alhamdulillah Allah muna godiya a gareka daka nuna muna sallah lafiya ya Allah ka karbi ibadun mu ka yafe muna kura kuren mu amin* *Ina yiwa kowa barka da sallah Allah ya mai_maita muna amin* *_Bismillahir Rahmanin Rahim_* 11~15 Tayi dariya tace, "idan ma zaki saki jikin ki yarinya to ki saki jikin ki dan duk duniyar nan babu wanda yasan wace ce ni kuma daga Ina nake sai Allah dan ko wannan matar ko sati d'aya ba muyi da haduwa da ita ba, ke ko sunana na gaskiya bata sani ba, ballema wata Amina gwaggon ki dan haka yariya sai kiyi mani biyayyah kamar yanda tsohon ki yace, idan kuma ba haka nan ba him! ". Ita dai Husnah da ido kawai take bin ta dan ba kowane irin zance take ganewa ba da manufar zancen saboda karancin shekarun ta da kuma uban baccin da takeji Amman kalmar ta da tafurta cewar, "gwaggo Amina bata santa ba ta bata tsoro matu'kar tsoro, tunanin ta ya bata saceta kawai akayi, sai kuka takeyi tana kiran Aunty Zarah. Wata uwar tsawa ta daka mata a take kukan ya bacewa Husnah sai ta kara firgita kamar kace mata ar ta gudu sai zarar ido takeyi, Abu da kuruciya idan an natsu guri daya sai bacci ai kuwa bacci ne ya dauketa mai cike da tsoro sai firgita takeyi acikin bacci, ita kuwa matar duk abunda Husnah keyi akan idon tane kuma tsab tayi kamar bata sanda ita ba hankalin ta na akan titi sai gab da asubahi suka iso cikin gari tayi tafiya sosai a cikin garin kafin ta 'karasa a wata unguwar wani katon gidane ta nufa tayi horn aka bude mata ta shiga da motar a cikin gidan a gaskiya duk da duhun asuba gidan kyawun sa yana nan daram bud'e motar tayi ta dauko Husnah tayi cikin gidan da ita a kujerar falo tree star ta kwantadda Husnar ita kuma ta haye up. Husnah sai 'karfe shidda ta samu falkawa ahan kali ta soma biyar falon da ido a figice kawai idon ta na 'karasa sauka akan katowar plasma kawai ta zun duma uban ihu wanda sai da duk wanda yake gidan ya firgita a tamanin duk suka karaso cikin falon harda matar da tazo da Husnar ganin iri yanda duk ta rudene bataji bata gani sai ihun takeyi ne gashi su basuga komai ba kawai da sauri matar ta karaso gurin Husnar ta riketa tana girgizawa tana fadar, "kee Husnah lafiyar ki kuwa uban miye kika gani wanda ya tsorata ki da har kike rafka wa mutane irin wannan ihun iye!? " A cikin masifa take zancen wanda ya kara firgita Husnah kawai tayi luuu ta some a take aikuwa duk mutanen dake gurin suka kara tsorata ganin karamar yariya a firgice gashi har ta kaita da somewa cikin zafin nama wasu maza masu uniform iri d'aya su biyu suka karaso da robar swan suka yayyafa mata ruwan a fuska da jiki atake ta sauke ajiyar zuciya ta dawo cikin hayyacin ta, ahankali ta soma bud'e idon ta. Da kallo take biyar su har idon ta yadawo a kan matar da tazo da ita hara rar da matar takeyi matane yasaka ta sauke idon a 'kasa. Matar tace, "zaku iya tafiya" tana nuna masu hanya, dukan su babu musu suka fita, kallon Husnah tayi tace, "bazan iya daukar maki kauyenci ba, kuma daga yau daga rana mai kamar ta yau kada na sake ganin kin tara mani mutane acikin falo kuma duk wani 'kauyenci naki ya 'kare daga yau saboda haka tashi ga kayanki nan ki dauka mushiga ciki na nuna maki masaukin ki koma nace muhallin ki, haka Husnah ta tashi jiki ba wani 'kwari suka shiga cikin d'a kunan dasuke acikin falon ta kaita wani d'akin mai dauke da gado madai_daici da way drop fentin d'akin purple ne da green akwai rowel na labulai ash color haka kayan d'akin ash color ne, nuna mata komai tayi da amfanin sa, sannan ta bud'e mata kofar toilet da take gurin ta 'karasa nuna mata da koyar da ita yanda zatayi amfani da komai dan bata son yawan tambaya, da gida danci tana gama koyar da Husnah komai sai ta fita tabarta a gurin wanka tayo da alwala cikin rashin iya amfani da komai sosai amman tayi 'kokari gaskiya, sauya kayan jikin ta tayi tayi sallah tayi zaune ta rafka uban tagumi kamar wata babbar mace, ahaka matar tashigo mata da abinci ta ajiye mata a gaban ta tace, "ga abinci nan kici idan kin 'karasa ki sameni a falo" bata jira amsar Husnah ba kawai tasaka kai ta fita. Da sauri Husnah ta soma shan tea mai kaurin gaske sai kamshin kayan yaji yakeyi har tana kone baki amman taki ajiye wa har sai da ta shanye coffin duka san na ta lura da wainar kwai aikuwa kamar an aikota kawai ta soma ci kamar wani zai kwace mata haka tazo akan arish amman ta kasa iya cin sa, loma d'aya tayi ta ajiye sa a gefe tana fadar, "wannan abun babu dad'i gaskiya dama nasani da banci ba na 'bata bakina, kuma fa na 'koshi sosai kamar zanyi amai wai Allah inda ma anty nanan ko mamar mu wai da sunci wannan dad'in wallahi amman ko yanzu ai nasha lama dan nakusa cinye komai bari dai naje na kai masu sauran kilama shike nan ni take jira na kawo mata sauran itama taci, kilama duk kurine irin na wannan aljanar matar ai wallahi tunda aka fara kawo mani dole ne naci yanda nakeso na rama irin yanda su Gwaggo marka da Baba da yaran su suke yi muna nida Anty Zarah da mamar mu". Haka dai Husnah tayi ta zabga shirme har sai da matar ta gaji da jiran ta tazo ta sakota a gaba tare da kwaso kayan da taci abincin, har kitchen ta raka Husnah takai kayan suka dawo cikin falon ta zaunar da Husnah a 'kasa ita kuma tana akan kujera ta d'ora 'kafa d'aya akan d'aya tana girgizawa tace, "Husnah ki bud'e kunnen ki, ki saurari abunda zan sanar maki, da kyau" "Husnah ban dauko ki dan narasa yar aiki ba, ban dauko ki dan bani da kanwa ba ko yan uwa ba aa kuma ban dauko kiba dan bazan iya haifuwa aa, kawai dai na d'auki kine, saboda wani dalili wanda bazan iya sanar dake ba ko wane irin dalili ne, amman zan iya sanar dake sunana da wasu abubuwa wanda babu wani mahalukin da yasan haka, tun bayan sauyuwar da nayi, Husnah Sunana Zubaidah Ashir mu hudu ne a gurin iyayen mu duk kannin mu matane nice ta ukku Asma'u ce babba sai Ruma sai ni sai kanwata Zulai, kowa daga cikin yan uwana yanada kamun kai nice kawai daban dasu, inada shekara sha hud'u na bata rayuwa ta iyayena sunyi kukan bakin ciki sunyi mani nasiha da lurar dani akan illar abun amman ni ban wani damu ba, sai itayen nawa suka rika sanya mani ido sam sun hanani fita, ko nan da kofar gida atakaice dai sun sanya ni kulle, nikuwa cikin dare nake tserewa tun basu gane ba har suka gane sunyi sunyi amman abun yacitura sai dai suka sanya mani ido tare da addu'ar shirya a lokacin inada girman jiki sosai babu wanda zai iya yarda da cewar Asma'u yayata ce, duk ganin akeyi nice babba, inada shekara sha biyar nasoma zubar da ciki tunda iyaye na suka fuskaci haka suka fara neman su auraddani ni kuwa na shammace su na gudu, akikacin inada shekara sha bakwai a gaskiya bariki tayi babu mai hanani babu mai takurani, bariki ta karbeni da bariki nayi kud'i natara manyan gidaje da motoci da manyan kadarori dan haka kema zan d'ora ki a wannan harkar idan kinason kiyi kud'i ki rama abunda matar Baban ku da Baban ku sukayi maku keda mamar ku da Antyn ki zan wayar dake fiye da tunanin mai tunani". "Nabaki wannan labarin ne Husnah dan nasan bakida wayau ballema 'kwa'kwal warki ta rike wannan sirrin nawa, ballema kisan duk abun da na aikata yanada kyau ko baida kyau dan bana bukatar zuwa gaba kiyi mani wata tambayar kwatan kwacin hakan". Ita dai Husnah kallon ta kawai takeyi amman sam bazara iya fahimtar miye jigon labarin nata ba itafa kawai kallon Zubaidah takeyi amman duk abunda take fad'a bata gane ba sai kud'in kawai da motoci sune kawai taji sun burgeta a labarin cikin farin cikin da an nushuwa Husnah tace, "dan Allah nima ina son nayi kud'i masu yawa da gani sai Anty Zarah kawai bada kowa ba". A cikin kuriciya Husnah take maganar ta amman kuma ita Zubaidah ta yarda har cikin zuciyar ta. Zubaidah tace, "Yauwa Husnah yanzun dai tunda kin yarda daman haka nake sonji ina son ki yarda da bariki dan bariki uwace, shiyasa na daukeki keda kike karamar yarinya kuma marainiya wadda batada uwa nasan bazan sha wata wahalar ba sosai, shiyasa na nafi yarda da na daukeki gaki kuma naga kwata_kwata bakida wayau koda zuwa girman kine sai na mayar dake babbar yar dana haifa da cikina". Dariya kawai Husnah keyi harda tsallen murna zatayi kud'i. Yinin ranar hidima kawai takeyiwa Husnah wanka ne kawai batayi mata, sai dai tace jiki kiyo wanka. Cikin wata biyu sosai Husnah ta sha'ku da Zubaidah wadda ta d'auki burin duniya ta d'ora akan Husnah kuma itama kullum cikin yawon ta takeyi. Kwanci tashi babu wahala a gurin Allah gashi Husnah ta shekara ukku gidan Zubaidah yanzun tana yar shekara sha ukku kenan sam idan kaga Husnah bazaka ta'ba gane taba dan ta zama kamar d'iyar turawa tayi fari da kiba abun sai sam barka kuma tana zuwa school tsadaddiyar gaske Husnah bata wasa da karatu turanci kuwa kamar wata baturiya ya zauna mata akan halshen ta, amman kuma sallah sai abun ya bugo mata takeyi idan tanayin sallar ma Zubaidah fad'a takeyi amman ita Husnah takasa dainawa saboda kullum tana kallon hoton su itada Anty Zarah, kuma tana mafalkin tada mamar su gashi kuma ta kasa sanar da Zubaidah. Husnah ce kwance tanayin Assignment Zubaidah ce ta shigo itada wani mutum saurayi sam Husnah bataga wani abun kallo a garesa ba amman shi kallon ta kawai yakeyi, kamar wani tsohon maye, hasala Husnah tayi, kawai tayi tsaki ta tashi ta kwashe kayan karatun ta, ai kuwa zata wuce, aka daka mata uban tsawa wadda sai da yan hanjin cikin Husnah suka katsa da sauri ta saki kayan hannun ta ta zaro ido waje, kawai...... To mizai samu Husnah? Kuma waye ya dakawa Husnah tsawa Zubaidah ko wannan mutumen? Shin Husnah zata biyewa yan bariki tayi bariki ko kuwa? Shin ina labarin Anty Zarah da kuma su baban su Husnah? Duk wannan amsar tana gurin Ummu ihsan, kudai kudai biyoni dan jin wannan amso shin, dan labarin ba'a fara komai ba daga cikin sa. *GIDANTA NA GIRMA* *BY NANA: KHADEEJATU* *_UMMU IHSAN_* *SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU SOSAI SON FISABILILLAH* *YA ALLAH KAJIKAN MAHAIFINA KAYI MASA RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SA SHIDA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.* *Alhamdulillah Allah muna godiya a gareka daka nuna muna sallah lafiya ya Allah ka karbi ibadun mu ka yafe muna kura kuren mu amin* *Ina yiwa kowa barka da sallah Allah ya mai_maita muna amin* *_Bismillahir Rahmanin Rahim_* 16~20 "Zaki rufewa mutane wannan shegun idon naki ko kuwa sai nayi maganin ki a gurin shegiya?" Wan nan gayen yace, "Him baby shiyasa nake tambayar ki wace ce ita wannan fitsa rarriyar yarinyar kika ki sanar dani ita din wace ce gashi raini 'karara a fuskar ta ya bayyana a kaina da alama idan ta 'kara girma sai tace ita d'in wata aba ce ni dama zaki bani ita na koya mata hankalin". Yana maganar yana lasar baki kamar wani tsohon maye. Wata uwar harar ce Husnah ke binsa da ita hawaye duk sun wanke mata fuska, sai shashshekar kukan ta kawai ake ji. Zubaidah cikin takaici da nuna bacin ranta a fili tace da Husnah "daga yau daga rana mai kamar ta yau na kashe wasa dake Husnah kuma na kashe maki kirana da Aunty sai dai mommy Ina ganin wannan shine 'karshen ranin da kike son yi mani tare da ba'ki na, kuma daga yau ko kallon banza dana arziki ban yarda su had'aki da duk wani bakona ba namiji ne ko mace, kuma yan zun nan nake son ki kwashe tarkacen ki kibar gurin nan kafin nafito maki ai nahin kala ta". Da hannu take nunawa Husnah ta bar gurin ai kuwa cikin hanzari Husnah ta kwashe kayan ta tabar gurin tana kuka. Bayan su Zubaidah sun zauna ne take baiwa mutumen hakuri take sanar masa da cewar Husnah yar Yayan tace aka bata halak malak. Acan cikin d'akin kuwa Husnah kuka kamar ranta zai fita, sai da tayi mai isar ta har bacci ya d'auke ta fuskar ta duk ta kumbura saboda kuka. Tun daga wannan ranar Zubaidah take d'aure wa Husnah fuska kuma Husnah girma sosai take bata mommy sama mommy 'kasa sam babu raini kamar wadda ta haifeta haka take baiwa Husnah umarni. Haka rayuwa take tafiya wata rana farin ciki wata rana akasin hakan gashi Husnah girma takeyi kyawun ta nafita amman sam Husnah bata san kimar kyawun taba ita dai gata macce har macce domin Husnah kam akwai daukar hankalin mai kallon ta mace ko namiji ita kanta Husnah kyawun nata har tsoro yake bata, sam Husnah bata san wani abu ba wai saka mayafi ajikin ta, kai ko dan kwali da hula Husnah tun da take a gurin Zubaidah bata ta'ba siya mata ba, duk cikin kayan Husnah daga riga da wando sai riga da skict na kanti kuma duk mafi aka sarin kayan Husnah mini ne takalmi kuwa hell sai mai tudu. Husnah ce tafe daga ita sai riga iyakar ta zuwa cibiyar ta sai wandon ta crazy kanta kuwa twisting ne a kanta kamar wata 'yar Baby ga wani no respect glass dake idon ta fuskar ta babu makeup sai with lips da ta d'an shafa, tafe take tana taku a hankali kamar mai tausayin 'kasa key ne a hannun ta tana kad'awa da d'aya hannun ta d'aya hannun kuwa littafai ne ta rugume, hara bar gidan ta nufo har ta iso a bakin wata jar mota tabud'e ta saka littafan zata shiga kawai daga bayan ta taji ance, "sannun ki Husnah wato kedai kullum cikin yin sakko zuwa makaran ta bayan ko karyawa bakiyi ba, duka_duka yanzun fa bakwai tayi na safiya, to nidai yanzun kam bazan lamunce maki ba muje maza ki karya kuma akwai maganar da zamuyi dake duk yanzun nake da wannan lokacin". Dan bata rai Husnah tayi tana doka kafa kamar wata karamar yarinya cikin shagwaba wadda bata san tanada ita ba, tace, " I'm so sorry mommy Wallahi bana son na makara ne, sabido akwai wanda suke da burin ganin nayi latti suyi mani fonishiment gashi mun kusa fara WAEC da NECO kin ga kuwa bazan so na fits da tabo ko d'aya baby dan ba girma na bane kuma ba ajina bane". Dariya marar tayi tace, "nikam dai yau sai kin bani lokaci dan wallahi idan kika tafi ba tare da munyi wannan maganar ba bazaki sameni a gidan nan ba dan zani dubai ne yau guy kawai nake jira, dan ma nice na dakatar da tafiyar da tun da asuba muka bar 'kasar nan". Tun lokacin da Zubaidah ta ambaci guy a cikin maganar ta, Husnah ta d'aure fuska ta rufe motar tabi bayan Zubaidah batare da kowace daga cikin su tasake cewa uffan ba, a babban falon gidan suka zauna inda aka jere abinci a cikin kuloli iri daban_daban tea kawai Husnah ta had'a tasha batare da kowa yayi wata magana ba, bayan Husnah ta ajiye coffi ne ta dawo da hankalin ta akan Zubaidah tace, "mommy na 'karasa". Zubaidah tace, "ok Husnah akwai kud'i masu yawa na tura maki ta account dan zanyi tafiya wannan lokacin mai dad'ewa kuma ni kaina ban san lokacin da zan dawo ba saboda tafiyar ba tawa bace, ta guy ce, so bana bukatar ki kawo kowa a gidan nan haka zalika ban yarda kije gidan uban kowa ba saboda akwai wani alkawarin a kaina kuma kin ga ni nasaba harka da manya masu kud'i dan haka bana harka da talauci kuma duk uban da kika baiwa kanki batare da sani naba sai na hallakar dake a 'kasar nan san nan kuma komai kudin mutum kada ki yarda suga damar ki har mutum yasamu kanki ba tare da yasha bakar wahala ba, kina ganin yanda mazaje masu naira suke gwaggori yon zuwa gidan nan dan haka idan kunne yaji jiki ya tsira". Tana kai aya Husnah data kafe ta da ido tun lokacin da Zubaidah tasoma maganar ta, ta nisa tace, "shike nan ko mommy? ". Zubaidah tace, "mai hali dai baya fasa halin sa kekam Husnah zan so naga naki mazajen". Tashi kawai Husnah tayi batare da tabata amsa ba ta saka kai zata fita har sai da ta kusa fita a bakin kofar sannan ta juyo ta kalli Zubaidah tace, "mommy sai kin dawo zanyi kewar ki duk da nasaba da hakan tun ba yau ba". Juyawa tayi, tayi tafiyar ta, taja mota ta fita da karfi kamar wadda zata tashi sama tana tafe tana duban a gogo karfe 7:30 har tayi ai kuwa ta karawa mota wuta. A can gidan kuwa tun lokacin da Husnah tayi wa Zubaidah magana ta fita kawai sai tayi murmushi tace, "nakusa zama miloniya nida nake da zan ka d'ed'iyar budurwa irin wannan gashi dai a zahirin ido idan ka ganta zaka dauka batajin hausa bama zakayi zaton cewar tasan kalma d'aya daga cikin hausa ba, Husnah ke nan yarinyar da zatayi gado na koma fiye dani da abunda nakeyi, Husnah kece jarina, yarinya 'yar shekara sha tara takwas yarinya mai lokaci ga natsuwa da aji a gaskiya dole ne na 'kara saka ido akan Husnah dan saura wata hud'u ta cike shekara sha tara, kuma a wannan ranar ne zan cika nufi na akanta". Wani makirin murmushi tayi kai da taga abun baiyi mata ba kawai ta tashi tafara taka rawa sai da tayi rawa mai isar ta sannan ta zauna ta d'auko waya takira wata number ta kara a kunne tayi wata magana ta kashe wayar, horn akayi mata kawai ta d'auki jakar ta da akwatin ta taja tayi waje, a dai_dai bakin get tasamu wata bakar mota tana zuwa aka bud'e mata tashiga suka tafi. Husnah kuwa a bakin get din wata makaranta, ta danna horn aka bud'e mata tashiga wow masha Allah wannan school din kamar ba a wannan 'kasar take ba, saboda tsabar girman ta da tsarin ta, a wani symbol aka, rubuta M.G. D. S. S millions GOLDEN DAY SECONDARY SCHOOL, a parking space ta tsaya AI kuwa haka matasa iron ta maza da Mata suke ta parking din motocin su, kamar a tare suka zo kowa yabude motar sa suka fito ai kuwa sun kai su goma sha biyar har gami da Husnah mazan su da Matan su haka suke tafiyar su cikin kwanciyar hankali kowa ne daga cikin su babu mai uniform kowa da irin shigar sa yanda yaga dama kamar ba secoundary ba. Tafe suke cikin isa har kowane ya kawo ajin da yake sam basuda wata damuwa, daga isar su cikin aji kowa ne daga cikin su shi d'aya ne akan kujerar sa kuma duk aji kujera goma ce acikin sa biyar mata biyar maza, wani class din ma maza bakwai mata ukku duk makarantar babu mutum d'aya mai shigar uniform ko shiga ta "ya"yan hausawa. Duk class din babu wanda yace da dan uwan sa uffan barema a gaisa kowa harkar gaban sa yakeyi, Husnah kuwa karatu takeyi, itada wasu daga cikin yan class din. Wata aunty ce ta shigo mai shigar kafurai kai cike da attace fuska babu annuri tayi karatu ta fita sai ga wani malamin idon sa tsab akan Husnah ai kuwa can 'kasa_'kasa wasu daga cikin yanda class din suka fara fad'ar, " shegen yazo mayen yazo". Ko kallon inda yake Husnah batayi ba, yayi karatu yazo dai_dai inda Husnah take, yafara yi mata tambaya akan karatun da yake yi masu, yaso ta kasa amma ina ta wuce da sanin sa, dole ne yasaka ya kyale ta yaje ga sauran "yan class d'in. A haka har suka tashi break babu ruwan kowa da kowa, wasu mazane 'yan gayu suka Sanya Husnah a tsakiyar su, su biyar suna tsokanar ta, murmushi kawai rayi masu suka sanya ihun murna suka bata hanya ta wuce. Haka Husnah take rayuwar makarantar sam bata da wata 'kawa ko kuma aboki, saboda makarantar babu ruwan wani da wani haka suke rayuwar su. Husnah ce zaune a tsakiyar falon su tana kallon series film na bolly wood tana jin dad'in yanda film d'in yake tafiya. Kawai ganin tayi mutum ya wuce ta yayi hanyar step zuwa d'akin Zubaidah takaici ne ya kama Husnah cikin ranta take wasu sa'ke_sa'ke bata 'karasa tunanin ba taga wul gawar sa yayi hanyar fita, tanajin tashin motar sa, kawai ta tashi ta kashe kallon tayi cikin d'akin ta, ta rufe, ta kunna kallon a can har bacci ya kwashe ta. Cikin ikon Allah ita dai Husnah karatu kawai takeyi bata ma san nawa bane kud'in exam ba dan babu wanda ya taba tambayar ta koda kud'in takarda ne amman dai tasan duk "ya"yan manya ne a makarantar mafi aka sarin su daga wanda ake kawowa a mota tare da bodyguard sai wanda suke zuwa da kansu da mortar su its kanta Husnah batama san yaushe a ka siya mata mota ba amman kullum motar ta mafi yawan dad'e warta wata shidda. Husnah ce kwance kawai tajiyo hayaniyar mutane maza da Mata cikin firgici ta fito dan bacci takeyi Turus tayi sai kallon kallo kawai akeyi a gurin Husnah kasa motsawa tayi sai jikin ta ke rawa...... To mike faruwa ne? *Bafa ayi komai ba dan yanzun ne za'a fara wasan* Kudai kara hakurin biyoni ๐Ÿšถ๐Ÿปโ€โ™€๏ธ๐Ÿšถ๐Ÿปโ€โ™€๏ธ๐Ÿšถ๐Ÿปโ€โ™€๏ธ๐Ÿšถ๐Ÿปโ€โ™€๏ธ? Manege place *Comment and share* *GIDANTA NA GIRMA* *BY NANA: KHADEEJATU* *_UMMU IHSAN_* *SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU SOSAI SON FISABILILLAH* *YA ALLAH KAJIKAN MAHAIFINA KAYI MASA RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SA SHIDA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.* *Alhamdulillah Allah muna godiya a gareka daka nuna muna sallah lafiya ya Allah ka karbi ibadun mu ka yafe muna kura kuren mu amin* *Ina yiwa kowa barka da sallah Allah ya mai_maita muna amin* *_Bismillahir Rahmanin Rahim_* 21~25 Ikon Allah kawai Husnah take kallo, zuwa can tace, "mommy miye ke faruwa ne? Shin su waye wannan mutanen shin miye ma yatara mutane haka maza da mata kamar wata club ga kwalabe duk a hannun su, kuma duk suna rungume da juna haka? " Husnah Cikin mamaki da jin haushin abunda tagani ne yakata mantawa da maganar da Zubaidah tayi mata tun shekaru biyar zuwa shidda akan kada ta koma saka mata ido akan duk abunda tagani. Coke da takaici Zubaidah ta daka wa Husnah tsawa tace, "shot up my friend ke Husnah har kin isa kiyi mani irin wannan tambayar dan kinga ina zura maki ido akan duk abunda kikeyi, to munyi d'in idan kin isa ki hanamu holewar mu, dan ubanki keda mukazo taya murnar cika shekara sha tara shine zaki samu damar wulakanta mu, wato kina nufin har kin fini kin wuce da sanina kin maidani sa'ar ki ko!? " Ga baki d'aya gurin duk suka sako masu ido ganin ya da uwa ana sa'in sa a tsakanin su, kamar wasu mayu mazan su da Matan su suke kallon Husnah. Ganin yanda idon kowa yake akan sune ya saka Husnah sauke ajiyar zuciya ta matsa a kusa da Zubaidah ta kama hannun ta, tajata ta zaunar da ita ta koma gurin frig ya dauko mata ruwa masu mugun sanyi ta bude robar ta d'auko coffi ta tsiyayo mata ta zauna a kusa da ita takafa mata coffin a bakin ta ai kuwa kamar Zubaidah jira takeyi da sauri ta shanye ruwan ganin Zubaidah ta shanye ruwan sai Husnah tayi shuru dukan su sai sukayi shuru kamar minti ukku babu wanda yace uffan a cikin su, ai kuwa mutanen gurin mamakin duniya ne ya kamasu zuwa can Zubaidah ta sauke ajiyar zuciya daga jin haka sai Husnah tayi saurin fad'ar, "I'm so sorry mommy nayi laifi kiyi Mani afuwa wannan ya zama kuskure dafatan kin fuce a yanzun" . sai ya kame kunnen ya fa hannu biyu. Sauke mata hannu Zubaidah tayi tace mata, "last to warning my Daughter yanzun kije ki shirya kinga kin bata muna shiri keda zamuyi wa suprise amman kin bata komai nadawo kasar nan kusan sati biyu da suka gabata inata shirya maki, wannan babbar ranar amman gashi kin so ki batawa tashi yi maza ki shiga cikin d'akina ki shirya komai naki na bukata yana ciki". Cikin sanyin jiki Husnah ta tashi tashiga cikin d'akin Zubaidah abun mamaki irin kayan turawan nan taci karo dasu na amare tsaki kawai Husnah tayi tashiga cikin bayi tayo wanka da had'in sabulai na musamman, tana fitowa, taje gurin kayan ta tsare su da ido sam hankalin Husnah bai kwanta da wannan shirin na Zubaidah ba, amman kuma sai Husnah tayi wani makirin murmushi ta d'auki kayan ta saka, farare da su tas doguwar riga ce mai tsayi a gefen dama, tun daga cinya aka tsage rigar har zuwa 'kasa rigar gurin rafar ta duk tattara ne da ita, gashi ta baje a 'kasa sai takalmi masu mugun tsini farare haka ta saka sai tayi jikin madubi tana duba kayan tana kwabe baki, mai kawai tashafa sai powder sai dan lips tic daman kanta a wanke yake gashin duk sai sheki yakeyi ya zubo mata har gadon baya sam Husnah ita bataga wani abun burgewa a wannan shigar ba illar takurawa,yar post kawai ta d'auka itama fara, tayi gaba abinta tana taku irin na 'kasaita daya bayan daya ta fita, Ta fara taka step kawai aka saki ihu da tafi, kawai aka saki wani uban kid'a wanda yasaka Husnah kasa karasowa samari da yan mata harda magidan ta, dake gurin jin sukeyi kamar su dauke Husnah su gudu da ita, karasowa gurin da Husnah take Zubaidah tayi, cikin wata muguwar shiga ta yan bariki duk jikin ta a matse kamar bata saka sutura ba. Cikin farin ciki da murmushi ta riko hannun Husnah suka fara sauka a hankali. Duk mutanen dake gurin suka tashi tsaye suna tafi suka matso dab dasu Husnah hannu kawai Zubaidah ta d'aga aka kashe kida suma mutanen sukayi shiru, gurin yayi kamar babu kowa a cikin gidan. Maclephone Zubaidah ta ansa tafara magana kamar haka, "to maza da mata yay dak kun ganewa idon ku cewar bana karya yau ga yata a gaban idon ku kun gani kuma wannan ranar ce da nake ta tanadin ta tun shekara shidda da suka gabata, Husnah "yatace danayi wa shiri na musamman yau kuma itace ranar handing over da zanyi wa wanda nayiwa alkawarin ita tun shekara shidda data wuce, dan haka, Alaji Tk gareka". Tafi aka sanya da ihu ita kuwa Husnah mutuwar tsaye tayi da jin furucin Zubaidah anya kuwa ba mafalki ne takeyi ba?. Bata 'karasa tunanin ba taji an rungume ta daga bayan ta, atake taji kamar ruwan zafine tafasashe aka kwalaya mata, ajiki, cikin zafin nama Husnah ta jiyo tasaka hannun ta ture sa har sai da yaja da baya yana matun fad'uwa 'kasa, harar sama da 'kasa ta fara aika masa, tare da kallon tsana, cikin yan sakanni Husnah tayi masa kallon tsab farine babu laifi kuma yanada kyau kamar bafilatani amman ba wani tsayi ne dashi ba, kuma ba saurayi bane, da alama yanada yara zasukai biyar, dauke idon ta tayi a kansa ta dawo da idon ta akan Zubaidah zatayi magana Zubaidah tayi saurin dakatar da ita tace, "Alaji Tk kada kadamu daman sai da na sanar dakai cewar ajiyar ka akwai aji bata kula kowa, kuma bata barin wasu su taba mata jiki ko nida nake mahaifiyar ta ba kasa fai muke zama a kusa da juna ba, ina fatan bazaka ji haushin abunda tayi maka ba, kaga abunda tayi maka shine ya baka shedar batayi maka wasa da dukiya ba". Tafi mutanen yasanya ya dawo a gefen Husnah ya tsaya yace, "your welcome baby gaskiya ajin nan naki ya burgeni dan haka yau zamuje cin amarcin mu a duk irin kasar da kika za'ba". Tsaki Husnah ta saki mai mugun tsayi tace, "mommy bayani nake nema". Murmushi kawai Zubaidah tayi tace, "Husnah wannan shine ya d'auki nauyin karatun ki tun kina yar shekara sha ukku shine mutamen da ya sauya maki school kuma shine ke biya maki kud'in makaranta dana duk kanin bukatun ki, motocin da kike hawa duk shine yake baki, ya zabi ya boye maki kansa ne saboda yana da bukatar ki mallaki hankalin ki kuma, duk abunda kikaga na baki na kayan sakawa dana buka tunki ci da sha duk shine yake yimaki shi saboda haka a madadin godiyar da zakiyi masa, ki bashi kanki shine tukwicin sa, kuma ki mallaka masa kanki a duk lokacin dayaso hakan daga gareki, kuma ki sani a yanzun kin wuce kuruciyar da zata hanaki aikata abunda yake ba wata illah ba". Tana kawo wa aya sai ta tsaya tana kallon Husnah tare da muta nen dake gurin. Shiru Husnah tayi tana nazari, zuwa can Husnah ta nisa tace, "sorry mommy gashi kuma ni nagaji da hayaniyar mutane da kallon da sukeyi mani, kinfi kowa sanin hali na dan kece kika koyar dani hakan". Dariya gurin ya d'auka da tafi da ihu dan gaskiya Husnah ta daban ce, duk abunda tayi burge mutane take. Tk yace, "haba baby ki dan bari ko cake din mu yanka mana nacika shekarar ki sha tara mana". Baki ta mere, tace, "zaku iya ajiyewa har zuwa karfe biyar da rabi dan nikam na gaji tuni, kawai ta juya tayi cikin d'akin ta ta rufe d'akin tayi jifa da post din da wayar ta ta fada saman katifa ta fara kuku wanda ta rasa kukan miye takeyi. A can cikin falon kuwa Zubaidah ce tayi tsalle ta rungume Tk tace, ", congratulation ma tayaka murna dan Husnah tayi na'am da bukatar ka, sai dai kasan ta da jan aji kamar wata sarauniya". Shima Tk 'kara rungume Zubaidah yayi, a jikin sa, yace, "wannan yar taki da alama zan sha wahala a gurin juyata amma duk abunda takeyi bana jin haushin ta, kuma dama haka nake son ganin cikkakkiyar macce mai aji da izza kamar wata sarauniya, kuma yau din nan zan angon ce da amarya ta duk da ba aure zamuyi ba, amman bazan bari wani namijin ya rabeta ba, haka zalika, zan siya mata gida a duk 'kasar da take son zama". Wani dake gurin da ya cika da takaicin rashin bashi Husnah da Zubaidah tayi, yace, "to kuma kana tare da uwa ai sai ka bar muna yar ko? ". Wani uban tsawa Tk ya dakawa mutamen, aikuwa rigima ta tashi a gurin har sai da wasu suka dam bata, ashe gurin mafi aka sarin su sun yaba da Husnah kuma duk suna cikin layin masoyan ta, Tk harda kujera aka doka masa a goshi sai da yayi jini, kai daket taron ya watse saboda bala'i. Ita kam Husnah batama san wainar da ake toyawa ba dan eyer phone ne ta saka a kunnen ta. Har dare Husnah bata sake jiyo motsin kowa ba acikin gidan, wanka tayo ta chanza shiga ta saka doguwar riga tree cotter, bata daura komai a manta ba, ta fito karo taci da Zubaidah da wani shuger baby suna manne da juna, rabasu tayi cikin jin zafin zuciya ta wuce su, ruwan tea kawai tasha, ta dawo zata shiga, cikin d'akin ta, sai ta jiyo muryar Zubaidah na fad'ar, "Husnah anwatse maki biki a yau amman ki shirya gobe tun larfe tara na safe zaku bar 'kasar nan". Batare da Husnah ta jiyo ba, ta wuce su, tayi cikin d'akin ta ta kwanta, sai takwas na safe falka, wanka tayo da alwala ta saka boyayyir hijab dinta tayi sallah raka biyu bakin ta sai motsin yakeyi ita kanta bata san mi take fad'a ba. Tashi tayi tsaye ta cire hijab d'in ta nad'e taje ta boye ta, dama ita bata kwalliya iya kacin ta lipstick sai yar powder kadan turare masu dadin kamshi ta saka ta dauki kaya ta saka riga ce mai karamin hannu da dogon wando ta saka sai ta tubke gashin kanta da ribom har zata fita sai ta dawo ta d'auko key din motar ta da post din ta, baka da takalmi baki suma, sai wani dan gyale da ta tsinto a cikin lokar ta wanda tama manta dashi dan kwali kai za'a iya kiran sa dashi amman ita sai taji duk a takure take, haka dai ta d'auki wayar ta, ta fito babu kowa a cikin falon kawai ta wuce parking space, ta d'auki motar ta tayi gaba abun ta. Ita kuwa Zubaidah cikin sauri ta fito zata hana Husnah fita amman inaaa ta makaro dan Husnah tayi nisa koda ta fito, wani uban tsaki ta doka, tana fad'ar, "kash oh my God a gaskiya Husnah kina da matsala taya zaki fita kibar gidan nan bayan kin san yau zaku bar 'kasar nan da karfe tara dai_dai". Tsaki ta koma saki wanda yayi dai_dai da isowar Tk. Da sauri ya karaso inda take yace, "Zubee yaya n? dafatan dai ta gama shirya wa, dan yanzu nake son mu wuce". Zubaidah tace a cikin takaici da dafe kai, "ina fa yarinyar nan son take ta bata muna lokaci dan yanzu ne taje neman abunda zata karya dashi". Tk yace, "what ! kina nufin bata gidan na?". Zubaidah tace, "to zanyi maka karya ne? Bayan duk kasan irin iskan ci da wulakanci irin na Husnah ? ". kiran wayar Husnah Zubaidah keyi amman tayi ringing har ta tsinke bata d'aga ba duk hankalin su a tashe yake sai kiran wayar sukeyi babu amsa. Husnah kuwa a cikin mota tabar phone din ta fito da post din ta, ta shiga wani restaurant hadden gaske, fura da kin dirmo kawai ta siyo ta fito ta d'auki hanya wata mata ta gani tana suyar 'kosai a gefen titi gashi wutar bata wani ci, duk haya'ki ya dameta, cikin sauri Husnah gan gara gefen titi taci gaba da kallon ta, yaran ta yan masu matsa kaicin shekaru kamar goma da takwas suna gefen ta sune suke kaiwa mutane mace da namiji. Husnah dai hankalin ta yana kan matar kawai taji tana sha'awar cin 'kosan ai kuwa da sauri ta d'auko jakar hannun ta, ta bude motar ta 'karasa gurin matar kawai yaran da mutanen dake gurin suka bita da ido a kusa da matar ta dan durkusa, cikin maganar ta ta sakuwa da yanga tace, "Umma abani wannan abun". Ta nuna kosan ai kuwa duk mamaki yakama mutanen gurin wai ace wannan balarabiyar ko baturiyar tana jin hausa har haka?. Da murmushi dauke a fuskar matar, jin Husnah ta kirata da sunan Umma, tace, "to "yata ai kuwa yan zun da kwai jira ko zaki dan 'kara hakuri ne ki koma a cikin motar ki kada wannan haya'kin ya dameki?". Murmushi itama Husnah tayi ta gir giza mata kai tayi zaman ta a gurin ai kuwa mutanen gurin sukace ki bata kawai maman bashari, mun yafe. Da murmushi maman bashari ta tambayi Husnah na nawa zata bata, amman Husnah tayi shiru dan ita kanta bai wuce taci ukku ko hud'u ba. Husnah tace, "ki bani hud'u naci, wallahi ban san ko nawa yake a yanzun ba, kinga akwai mutane da yawa suna da gurin zuwa kada na tauye su". Maman bashari kawai ta nemi leda ta zubawa Husnah na hamsin tace mata, "nasan idan kika ci wannan sai zuwa wani lokacin dan haka gashi aci lafiya". Amsa Husnah tayi tana godiya ta bata dari biyar aka bata chanji tace, "dan Allah yaran nan wani ya kai mani a mota" A cikin han zari yarinyar ta amsa tabi bayan Husnah wadda tayi wa Maman bashari sallama, a cikin motar Husnah ta shiga ta bude jakarta ta d'auko kud'i batama san ko nawa bane, ta baiwa yarinyar tace, ki kaiwa mahaifiyar ku ta saka ku makaranta kinji ko, kuma kuyi karatu shine zai zame maku fitila mai haskawa". Cikin farin ciki yarinyar ta amsa jin zancen karatu Husnah kuma ta amshi kosan tayi tafiyar ta. Maman bashari harda kukan ta da taga irin taimakon da Husnah tayi mata takeyi mutane sai kiran sukeyi ai aiki da zuciya yafi aiki da zahiri duk da yarinyar tayi shigar banza amman tanada hankali da natsuwa da alama wannan zatayi jin kan mutane Allah dai ya shirye ta". A dai dai kan hanyar Husnah ta zuwa gida ne taga motar wani mutume ta samu matsala kamar yayi hatsari dan ya bugi icce ne ai da sauri ta farka motar ta ta nufi gurin ai kuwa mutanen cikin matsanan cin hali ta ganshi ga jini a kansa yana zuba dattijo ne, sai wata yar karamar yarinyar da zata kai shekara hud'u a duniya a kansa tana fad'ar, "granny katashi kada ka mutu, mommy daddy, hajiya". Cikin zafin nama Husnah ta bude motar ta dawo gefen mutanen ta riko sa duk da karfin ta bai kai can ba, haka take ta kokari har ta fito dashi daga cikin motar tana hawaye yarinyar biye da ita bude motar ta tayi ta saka shi a baya tace da yarinyar ta shiga ciki ta rufe motar, a motar mutanen ta dawo ta fara bin cike har Allah yasa taga wayar mutanen ta d'auko ta rufe motar ta dawo motar ta d'auki hanya sai wata haddiyar asibity mai kyau, Husnah sai sannu takewa mutanen wanda yake cikin wani hali amman sam Husnah tana bashi mamaki. Da sauri tayi parking ta fito ta bude motar ta riko shi yarinyar ba biye da su, ai kuwa ma'aikatan asibityn da sauri suka zo suka anshe sa, sukayi ciki dashi ita kuwa Husnah ta riko hannun yarinyar suka mara masu baya. Emergency room aka shiga dashi, ita kuma Husnah wata nurse ce tazo ta kirata ta kaita gurin bude file da ansar katin asibity sam Husnah bata wani damu da yawan kud'in da suke chazar ta ba kawai dai ita fatan ta Allah yasa komai yazo da sau'ki cikin ikon Allah komai ya tafi dai_dai dan yasamu kula sosai duk da Husnah bata san waye shiba amman tace da ma'aikatan hospital din mahaifin tane dan yasamu kula sosai tace dasu sunan sa muhammad. Sai da doctor ya fito yasheda mata babu wata matsala anyi masa allurar bacci sannan ta tuno da wayar mutanen, a mota ta koma ta d'auko wayar ta baiwa yarinyar tace, "idan kin iya cire security ki cire mani nakira gida na shaida masu halin da ake ciki" Da sauri yarinyar ta bude mata security ta bata wayar duk wayar tayi dameji number ma babu wadda zaka iya gani, Husnah ta dafe goshi tace, "oh my God yaya zamuyi?" Zuwa can Husnah tace, "baby kina da number wani mutum ne a kanki? ". Shiru yarinyar tayi zuwa can yarinyar tace, "anty akwai number a wannan letter". Amsar takardar Husnah tayi aikuwa idon tane ya sauka akan number, cikin sauri ta d'auki number a wayar ta kira, sai da tayi kira ya kusa goma har ta hukura kawai aka d'auki wayar cikin masifa aka fara maganar, "uban waye ke damuna da kira wannan ai maitar banza ce haba waiku wannan yan matan haka zaku 'kare rayuwar ku a cikin biyar maza wanda sam mata basa gaban su". Sai da mai masifar ya kai aya Husnah tace, "dallah mallam ja can ka baiwa mai waya wayar sa zamuyi magana dashi, haka kawai kananan yara su raina manyan mu? ". Janye wayar mutanen yayi a kunnen sa yana mai 'kara duba wayar sa, cike da mamaki, matar dake kusa dashi da yaran mata da maza da suke gurin duk sukayi mutuwar zaune ko wane jikin sa sai rawa yakeyi matar kuwa dattijiwa da ita itace ta anshi wayar ta saka a Hans free Husnah kuwa sai masifa takeyi dariya matar tayi tace, "yata kwantar da hankalin ki Allah ya huci zuciyar ki, wace ce ke kuma waye kike nema n? ". cikin sauri mutanen yace, "haba mom miye na baiwa wannan kucakar yarinyar hakuri wallahi idan ta yarda mukayi ido biyu da ita sai nayi maganin ta". Samarin gurin da yan mata dariya kamar ta fito masu amman sun san sauran, Husnah daga can tace, "yauwa Ummy daga gani kece a gurin am daman, sai kuma tayi shiru tana nazarin abunda zata fad'a". Matar cikin jin dad'in lafazin Husnah sai tace, "fadi mana ina jinki". Husnah dai ta kasa magana dan ta gaji da magana yau tayi magana fiye da tunanin ta, zuwa can kuma Husnah tace, "Ummy idan a kwai wani babba ki hadani dashi muyi magana pleace". Da sauri matar ta baiwa wani mutane waya ba mai wayar ba, tace, " gashi" Husnah kuwa tace, yauwa yaya kana jina dan Allah kada ka sanar da Ummy wannan maganar dan kada a samu matsala" Yace, "ina jinki, fadi zan cenki". Husnah tace daman akan hanya tane naga anyi Accident Akan hanya kuma mutanen a lokacin baya hayyacin sa, yana ciki wani hali amman yanzun komai yazo da sauki yana king Yusuf special hospital, amman fa da sauki sosai". Tun lokacin da Husnah ta baci accident kuma face want mutum duk dakin suka rude harda abokin fad'an Husnah saboda basu cire wayar hans free ba a zaton su shirme ne zata fad'a . Har suna hada baki gurin fad'ar, "gamu nan zuwa! ". kashe wayar Husnah tayi taja hannun yarinyar suka dawo a kusa da d'akin da ala kwantar da mutumen, suka zauna akan kujerar gurin. Wayar Husnah ce ta d'auki ringing tana dubawa taga Zubaidah kawai tayi tsaki ta d'auka kafin Zubaidah tayi magana Husnah tace, "ina hospital ne banida lafiya kawai Husnah tayi shiru ta kashe wayar". Zuwa kamar awa d'aya, sai ga wani kiran kamar kar ta d'auka kuma sai ta d'auka tace, waye ne? Yace, " kuna wane gurin ne gamu mun iso". Husnah tace bari nazo da ku. Har ta tashi zata tafi nurse tazo tace, "kije inji marar lafiya". Da sauri Husnah tabi nurse d'in d'akin ta shiga, gurin mutanen Husnah da yarinyar ta nufa tace masa sannu daddy yaya jikin naka?. Cikin murmushi yace, "sannu nagode sosai". Yace ki zauna mana kinji "yata. Husnah tace, "zan taro mutane ne da sukeyi ta kiran" Yace, "ok babu damuwa kuma kada ki tafi har sai munyi sallama dake kinji ko? ". murmushi 'kawai Husnah tayi suka fita mutane ne ta hango kusan su goma a jikin motocin biyu suna dube_dube Husnah ta d'auki wayar ta takira ai kuwa aka da d'aga hannu ta d'aga masu cikin sauri suka iso inda take a tsaye tace masu, "muje ko? ". Bin bayan ta sukayi cikin hanzari amman kuma ita Husnah bata iya sauri ba, duk suka ka kagara su kai kawai abokin fadan Husnah yace, "dallah malama mu ki daina yi muna wannan tafiyar iskancin kawai dai Husnah tace, "malam zaka iya tafiyar ka ka tambayi wani". Har ya taso zaiyi masifa kawai aka dakatar dashi har kofar d'akin ta kaisu tayi tsayuwar ta sai da suka shige ita kuma Husnah ta jiyo ranta a bace tayi tafiyar ta ta d'auki motar ta tayi gida. Duk suna shiga wasu suka fashe da kuka, abokin fadan Husnah kuwa a bakin gadon ya zauna ya kama hannun mahaifin sa ya rike idon sa yayi ja sai jijiyar jikin sa ke halbawa. Hajiyar ma ido tsakiyar kai ta matso ta kama hannun sa tace, "ya jikin naka!?". Yace, " kada ku damu ai sai da na samu sau'ki sannan ta kiraku amman da alokacin ne kuka ga halin da nake ciki da ba zaku samu damar yin wannan maganar ba a ina kuka baro mani "yata ne? " Kallon kallo aka somayi a tsakiyar su kowa tunanin yakeyi ina take ne?. Yarinyar tace sai da nabi bayan ta cikin fushi ta shiga motar bata ma kalleni ba. Asha nasan ba aikin kowa bane face Husain nasan kaine baka jituwa da mutane, Husain dan Allah kada ka bar yarinyar da ta ceci mahaifin ka ta shiga cikin wani hali, dan baka san irin taimakon da tayi maka bane da an rutsa da karin kwana da tuni na mutu kun rasa ni, gashi ko sunan ta bata sanar dani ba. Duk kowa yaji yana bukatar ganin Husnah su zauna da ita ba kamar Hajiya. Haka d'akin yadawi cikin jimami ga mahaifin su yadamu da zan cen yarinyar da ta cece shi, gashi babu wanda yasan sunan ta. Husnah kuwa tana isa gidan tayi parking ta fito a falon gidan ta samu su Zubaidah kowa daga cikin su cike da damuwa sai a lokacin ne Husnah ta tuno da maganar tafiyar da zasuyi kawai Husnah ta fara matso hawayen karya ta soma din gishi ta dafe kai tace, "mommy Accident ne fa nayi gashi duk naji ciwo kuma gashi naga ranki a bace". Ganin jini a jikin Husnah duk sai suka yarda kawai da sauri sukayo kanta Husnah sai ta 'kara narkewa. A cikin d'akin ta Zubaidah ta rikata, ta rakata har toilet, Zubaidah na fita Husnah tayi murmushi tayo wanka ta d'auko wani bandeji da ta ta'ba ajiyewa ta nad'e gefen cikin ta dashi harda su shafa wani abu kamar jini haka tayi a kafar ta harda su dan jike bandejin alamar ruwan wanka ne ya taba gurin. Zuwa tayi ta zauna a bakin gado tana cije baki, shi kuwa Tk duk tausayin Husnah ya kamashi, Zubaidah sai tambayar ta takeyi miye sanadiyar wannan raunin. amman Husnah sai kukan karya takeyi masu cikin masifa Tk yace, "dan Allah ki barta har tasamu sau'ki sai muyi mata tambayar amman yan zun mu barta ta futa". Husnah kuwa suna fita tace......... *Comment and share* *A GIDANTA NA GIRMA* *BY NANA: KHADEEJATU* *_UMMU IHSAN_* *SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU SOSAI SON FISABILILLAH* *YA ALLAH KAJIKAN MAHAIFINA KAYI MASA RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SA SHIDA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.* *Alhamdulillah Allah muna godiya a gareka daka nuna muna sallah lafiya ya Allah ka karbi ibadun mu ka yafe muna kura kuren mu amin* *Ina yiwa kowa barka da sallah Allah ya mai_maita muna amin* *_Bismillahir Rahmanin Rahim_* 26~30 Husnah tace, "badai bariki ba? Ai wallahi nafiku iya bariki nida nataso nasamu kaina a cikin sa, muzuba zuwa nida ku" kawai tayi kyabci da biki kaji sautin nan 'kat... A can garin kuwa tun bayan barin su Husnah garin Marka ta shiga bokaye ita ala dole sai taga bayan su Husnah da Zarah. Amman kuma duk inda taje sukan sanar da ita cewar ai duk rayuwar yaran ta tarwatse duk kayan dakinta sun bata a gurin bokaye, Wannan farin cikin dashi take kwana dashi take tashi, abunda Marka bata sani ba shine "yarta indo biyar maza takeyi d'anta namiji kuwa duk unguwar kowa yasan halin sa da halin bera wato mugun 'barawo ne na agwagi da kaji da tumaki da awaki sam Marka bata san mike faruwa danata yaran ba, tana can gurin lalata rayuwar "ya"yan wasu. Dan ita basa nuna mata halin su idan kuma wani ya yarda ya sanar da ita halin su har suka gane sa to shi kam tashi ta samesa dan wallahi idan aka fara yiwa mutum sata harda coffin gidan sa bazai tsira ba, ballema mutum yayi tuwo a gidan sa, "yarta d'ayar kuwa gulma har ta siyarwa akwai a gurin ta sam itace uwar gulma ce a unguwar, fada har na mugun abu take had'awa, amman ita ko uwar ta bata ragawa ba ballema mahaifin su, a take ne, take haddasa masu fitina, gashi Marka sam bata yarda da maganar kowa sai ta yaran ta duk abunda suka fada dai daine a gurin ta. Baban su Husnah kuwa yau satin sa d'aya da zuwa garin su yayan sa wanda ya d'auki shekaru kusan ishirin rabon sa da garin, to a wannan lokacin ne dai yaji duk hankalin sa ya tafi gurin yan uwan sa amman kuma kash bakar wahala kawai ya shawo dan an sanar masa sunkai shekaru sha biyar rabon su da garin da suke saboda ma'akatan gwamnati ne kullum cikin sauya gurin aiki suke, gashi yanzun dai da alama sunyi ritaya, saboda tsufa sai dai yaran su, sai kuma yaji bakin cikin sa ya koma lunkuwa, ga rashin sanin inda zai samu dan uwan sa koda mutum d'aya ne, ballema ace ya samu ganin su Husnah dan yanzun yakai kusan shekaru biyar yana mafalki dasu da mahaifiyar su, yanzun ne yasamu damar fita nemo su, amman ya makara. Gidan sa ya dawo cikin damuwa, Marka kuwa babu ruwanta da damuwar ta ballema ta tambayesa shima baiyi gigin sanar da ita inda ya tafi ba. ita kuwa Zarah tun bayan rabuwar ta Husnah sam ts sake dawowa so silent magana bata wani damuwar ta, alokacin da goggo Amina tazo sanar dasu cewar taje gidan su Husnah ta d'auko ta, tun a gurin mutanen unguwar ta samu labarin ai itace ta aiko aka d'aukar mata Husnah, mutane na tambayar ta ya Husnah take, gidan wata 'kawar maman su Husnah taje ta bugo mata ciki tace, "ni kuwa Larai yaran nan da suka d'auki Husnah hauka ce suka zo maku da ita ko!? ". Larai tace, "yo hauka mana ke miyasa da zaki aiko da masu d'aukar Husnah baki aiko masu hankali ba ko kuma kizo da kanki ba? ". Anan ne Larai ta labartawa goggo duk abunda yafaru tabbas ta shiga kaduwa amman sai ta boye, haka data fito daga garin bata zarce ko ina ba sai gidan yayan su babba ta labar ta masu komai tana kuka duk idon ya kumbura, sosai hankalin kowa ya tashi a gurin shine aka yanke shawarar kada abari Zarah ra sani amman inaa sun makaro taji komai a yanzu hakama daskare take ta some. Hankalin su ne yayi munmunan tashi wanda tun daga wannan ranar Zarah ta daina wal wala. Sun tambayi gogg Amina akan cewar taya yaya akayi wasu suka d'auki Husnah da sunan ta?. Wannan shine damuwar ta itama dan har yan zun bata san ko su waye ba. Zarah kam ta zama wata irin mace miskila ta karshe idan kaji tana magana tofa abun babba ne, haka rayuwar ta ta dawo kullum tana d'auke da photon su ita da Husnah da maman ku gashi kullum tana mafalkin Husnah na miko mata hannu akan ta janyo ta a jikin ta amman kuma sunyi nesa da junan su sosai. A haka har kannen mahaifin su ya had'a Zarah da dan gidan ogan sa aure tunda duk wanda ya fito da sunan zai Aure ts, takan sanar da mutum cewar sai ranar da taga Husnah ko zata iya Aure ada sun saka mata ido amman kuma daga baya suka sauya shawara, badan Zarah tana son Auren ba aka had'a ta da dan gidan ogan su baffah Isah, kuma shima yana ganin Zarah yace tayi masa amman sai kannen sa ya ganta idan yace tayi tofa lallai ne ita yake so. Aikuwa kannen nasa ma baya 'kasar amman sai da yadawo yazo ganin Zarah, cikin ikon Allah a take yaji Zarah ta kwanta masa shi dai kawai ayi Auren da sauri ma, ita kuwa Zarah ta sanar dashi yayi hakuri amman sai ya dawo yana lallashin ta har suka sabu da juna ita da kannen nasa sam baya narin tayi zaune ita d'aya, sosai suke kula da ita dan sun san damuwar ta kuma mijin nata ya kwashe photon da yake saka ta damuwa tayi neman sa har ta gaji, wannan shawarar kannen sa ne. Haka dai rayuwar Zarah take tafiya har Allah ya bata haihuwar ya mace mijin kuwa ya saka mata sunan Husnah a gaskiya ba Zarah ba har su baffah sunji dad'in wannan karamchin, kuma aikin kannen mijin Zarah ne. Mundawo asibity tun suna sa ran Husnah ta dawo har suka cire tsammani ita kuwa Hajiyar har gurin ma'aikatan hospital din taje neman Husnah amman bata sameta ba, dole suka hakura har aka sallame su. Husain kuwa dad'in rashin ganin Husnah yayi, ta wani ban garen zuciyar sa, ta wani ban garen kuwa yaji haushin rashin ganin ta kodan da mahaifin sa da kuma rashin kunyar da tayi masa dan yadau alkawarin idan ya samu damar sake ganin ta sai ta yabawa aya za'kin ta. Husnah kuwa kwananta tara ta samu sau'ki a cewar ta, kuma babu wanda ya gano cewar karya takeyi. Zaune take tana buga game a wayar ta Zubaidah ce ta shigo ita da wasu maza suna rungume da juna, kallo d'aya Husnah tayi masu ta tashi zata bar gurin ta dawo cikin d'akin ta, mutanen d'aya yace, "ke ''yar mu zoki nemo mani abunda zanci dan mun kwaso yuwa da gajiya ga zafin rana". Yana gama fad'ar haka ya fad'a akan kujerar da Husnah ta tashi. Baki Husnah ta turo gaba ta juyo tana fad'ar, "a gaskiya gidan bamu dafa komai ba, kuma ni bance a dafa wani abun ba saboda a iya sani na mommy bata cin abinci idan ta dawo gida wannan shine 'ka idan ta, kaga kuwa ba zaku samu damar cin komai ba". Cike da masifa abokin tafiyar su yasoma fad'ar, "ke haka katuwar mace da ke gaki da sura son kowa amman ace baki iya dafa abinci ba, a gaskiya kinyi asara babba". Cike da tsanar mutanen Husnah tace, "yo kai miye naka ne a ciki tunda ba akan ka nake zaune ba,da har zaka wani damu da rashin iya abinci na, ai dai bamuda wata alaka da kai malam dan haka ka shafa mani lafi.... Kafin Husnah ta 'karasa lafiya tuni an wanke ta da mugun mari wanda a cikin sakan biyar ta tuno da irin sa, a lokacin da Zubaidah ta mareta irin wannan kuma a gaban saurayin ta har ta saka mata sharudda masu tsauri yau shine aka mai_maita. Zubaidah cikin hasala har jikin ta na mazari tace, "Husnah kanki d'aya kuwa? Kin san waye shi kuwa a garin nan? Rashin kunyar da na haneki ashe dai tana nan ko,? Babbar magana Husnah kin kusa d'ebo ruwan dafa kanki, tunda har zaki iya yiwa senator rashin kunya kuma a gidan nan babu mai rabaki dashi". Dafe kunci Husnah tayi, kawai ta fashe da kuka kamar ranta zai fita, saboda takaici. Daga can bayan su, suka jiyo muryar Tk yana fad'ar, "tabbas Zubaidah dan bariki baida amana da alkhawari tunda har zaki iya cin amanata ki d'auki budurwa ta ki baiwa wani bayan kin san tawa ce, kuma harda su dukan ta, dan kinga bana kusa daku to anyi walkiya na gano ki ". Kawai yazo har inda suke yasa hannun sa ya janye Husnah suka fita suka bar falon motar sa ya saka ta, ya figi motar sai wata park ya ajiye ta, ita dai Husnah har yanzun kukan takeyi dan yanzu kam ta mallaki hankalin kanta tasan tozarci. Kallon Husnah yakeyi ya saka hannun sa a aljihun rigar za, ya zaro wani dan akwati, ya bud'e ya d'auko zobe mai kyau ya kama hannun Husnah zai saka mata, da sauri Husnah tace, "wato kai burin ka ya cika ko? Ina cikin wannan halin ne zaka saka mani zobe bayan nasan cikin farin ciki ake saka zobe". Murmushi ya sakar mata wanda Husnah takejin kamar ta bushe da dariya saboda bai iyaba kamar wanda ya mere baki cikin fushi. Yace mata, "kiyi hakuri Baby daman dan na faran ta maki raine yasaka ni zan saka maki zoben badan wani abu ba". Kauda kai Husnah tayi tace, "kaina ciwo yakeyi kamar ya rabe biyu ka maidani gida in kwanta ko zai daina". Cikin rawar jikin da tsoro yace, "ashha tashi na kaiki hospital a duba mani ke". Tashi Husnah tayi suka nufi hospital sosai aka duba ta aka bata magani, ya d'auke ya kaita super market tayo siyayya, tace masa ita bata son komai, ai kuwa da kansa ya shiga ya kwaso mata kayan ma'kulashe gurare ya kaita yayo mata siyayya haka suka dawo gida shi be shiga ciki ba ita ce kawai ta shiga ciki da sauri Zubaidah tace, "ina fatan kin faran ta masa rai ko? Dan nasan halin Tk idan yayi fushi sai yaji macce a jikin sa, yake sauka". Husnah bata ce da ita komai ba tunda har yanzun wannan mazan su biyu suna nan zaune a kusa da ita. D'akin ta kawai ta wuce, masu aikin gidan ne suka soma shigo da kayan da Tk ya siyo wa Husnah, da sauri Zubaidah ta fara dubawa kayane masu yawa kamar bai san zafin kud'i ba, magani taci karo dashi cikin farin ciki Zubaidah tace, "wow Husnah an girma lallai dole Tk yayo maki uwar tsaraba tunda ya mallaki komai naki Husnah, a gaskiya bariki tayi tunda gashi Husnah abun bai sauya mata ba, har bayan barin budurcin ta a gareta". Mutanen yace, "ai kuwa da zaki bani ita nima da nayi mata tawa bajin tar tunda ita sabuwa ce ni ina so". Da sauri Zubaidah ta rufe masa baki tace, "Husnah bazata taba yarda ko inuwa d'aya ku had'a da ita ba, saboda ita bata kula kowa sai Tk koshi ba sosai take kulasa ba, barikin Husnah ya zarta tunanin mai tunani ku dai mu chanza zance kawai ". Husnah kuwa ta fito ke nan zata d'auki maganin ta saboda kanta ya matsa mata tajiyo duk abunda su Zubaidah suke fad'a kawai sai ta koma taci gaba da kukan ta, a haka Zubaidah ta sameta, aikuwa da ringa lallaba ta, taje bayi ta had'a mata ruwan zafi ta rakata har bayin ta fito wai ta gasa jikin ta. Husnah kuwa murmushi tayi wanda yafi kuka ciwo, haka tayi wanka, ta fito ta samu Zubaidah ta kawo mata ruwan tea, kin sha tayi maganin dai tasha ta koma ta kwanta. Tun daga wannan ranar Husnah ra sake zama wata irin shu'uma sam bata fira da Zubaidah kuma koda Zubaidah ta tambayi miye matsala takan ce mata akwai abunda ta hango gurin Tk shine take son amsa kuma abun mugun tsada ne dashi yace baya iya mallaka wa kowa abun nan kuma ita bata son yasan tana son abun dan yace zai iya rabuwa da kowa akan abun ". Zubaidah ta kasa gane inda zancen Husnah ya dosa amman tasan ko miye yanada muhimmanci sosai a rayuwa tunda Husnah taso hakan. Zubaidah tace, "Husnah kada ki d'auki abunda ya fi karfin ki kada ki yarda ki rabu da Tk batare da kin anshi abu mai mahimmaci a garesa ba tunda kinga yanzun ya anshi budurcin ki, sai kinyi da gaske dan kinaga tun ranar bai sake zuwa ba ko waya na kira sa baya d'aga wa daga karshe ma bana samun sa, yau kusan wata d'aya ke nan ". Murmushi Husnah tayi tana 'kara kallon Zubaidah tace, "mommy daman haka ne idan namijin bariki ya gama da maccen bariki sai ya juya mata baya, sai dai ya nemi wata, ko ita ta nemi wani? " Zubaidah tace, "itafa bariki haka take kamar wainar fulawa take lallaba ta akeyi, saboda idan mutum ya tafi da garaje zata lalace masa ne". Dariya Husnah tayi tace, "hum mommy na yarda da hakan nima zan afka sosai a cikin ta, saboda ina son ganin farin cikin ki mommy ". Da sauri Zubaidah ta rungume Husnah harda hawayen farin ciki Husnah zata cika mata burin ta, zuwa can Husnah tace, "amman bazan iya kula raga jabul ba dan inada aji nafi karfin irin wanda kike kulawa saboda haka koda wani yayi maki magana kice masa ya nemeni da kansa dan nice dai_dai da zancen" Sosai Zubaidah ke jin dad'in wannan maganar ta Husnah, Husnah tayi mata sallama taje ta kwanta, ta kama dariya harda rike ciki tace wayyo Allah biriki ashe dai Zubaidah mommy baki iya duniyan cin ba har nafiki iyawa nida na taso na sameki kinayi, shi kuma Tk taya zaki nemesa ki samu bayan nayi masa nasa tuggun na had'a sa da iyayen sa harda matar sa, kinga kuwa Husnah tafi mommy iya bariki". Husain dan Allah number da yarinyar nan ta kiraka ita zaka bamu. Da sauri Husain yace, "ya salaam kama tuno mani yaya ida zamu sameta ba karya ta, tunda tayi mani rashin kunya". Kai nifa ba masifar ka na nema ba ka duba yanda mahaifan mu suka damu da rashin ganin ta ko godiya muyi mata". Bin ciken wayar ya soma yi amman babu wata bakuwar number, shima yayan nasa ya ansa ya duba a hankali bai samu ba, duk sai sukayi shiru suka ajiye wayar suna nazarin yaya akayi number ta fita ne, tunda basa goge kiran da akayi masu?. Husain yace, "Anisah eh lallai Anisah babu ko shakka itace ke yawan d'aukar wayar mutum tayi waya idan baya kusa". Ai kuwa da sauri suka nufi cikin falon suna kwala kiran, "Anisah! Anisah!! Ai kuwa da kaduwa ta taso tazo gurin su ta durkusa, jikin ta na rawa, Husain cikin 'bacin Rai yace, "uban waye yasaka ki d'auki waya ta alokacin da muke jinyar Daddy!? ". Kuka Anisah ta fashe dashi jikin ta na rawa tace, "wallahi waya ta ce ban gani ba shine naga wayar ka na charge na d'auka na kira tawa, sai nagano ta, to ina gudun ka gani kayi fad'a sai na goge kiran da nayi nagoge harda kiran wasu numbobi da basuda suna Allah banyi zaton zaka gane ba amman dan Allah kayi hakuri ". wani uban shuri yayi da ita wanda sai da tayi mul mula ukku zuwa hud'u harda fitsari sai da ta saki bata sani ba, belt kawai ya ciro yayi ta lafta mata, da ket aka samu aka anshe ta, ita kuwa Hajiyar da Alhajin duk sai daga baya suka bada hakuri, yayan kuwa cewa yakeyi, "'kara mata munafukar banza" Sauran mutanen gurin duk suka sha jinin jikin su, Baby kuwa kuka takeyi da gudu tazo ta rungume Husain wanda ya saki belt din saboda ita" D'aukar ta yayi suka fita daga cikin gidan sukayi gurin yawo tun daga wannan ranar Husain bai sake wani farin ciki ba, shidai wannan yarinyar kawai yake son gani suyi fad'an masifa da ita. Yau kimanin wata bakwai ke nan rabon su da ganin dariyar Husain duk dashi ba ma'abuci fira bane, baya wani dariya a matsayin sa na Doctor Husain, zaune yake shi d'aya da wowar sa daga gurin aiki ke nan yayan sa ne ya samesa a gurin yayi zurfi cikin tunani kannen sa Shaheed Yana biye dashi rike da hannun Baby da jakar school din ta a hannun ta. Zama sukayi a gefen sa suka saka shi a tsakiyar su Baby kuwa saman jikin sa haye tace, "uncle yauwa maganar da nace idan ka dawo zan fad'a maka ko? " Sai alokacin ne ya dawo hayyacin sa, ya gaida yayan sa, Shaheed kuwa da Baby suka gaida shi sukayi masa ya aiki. Ya amsa masu, Baby tace "Uncle kana jina ko? " Shafa kanta yayi yace, "ina jikin yarinya ta". Sai da tayi gyaran murya tace, "Uncle kace kowa ya barin nayi magana" Dariya duk sukayi mata dukan su hardai yanda take gyaran murya. Tace, "Uncle wayar granny tana hannun anty? Anty wadda takai granny asibity? Kuma wayar tanayi amman iyakar wayar ta kawo haske bata komai duk tarar ratse". Wani irin farin ciki ne ya ziyar cesu da sauri Shaheed ya soma kira kafin kowa ya kira, sunyi kira ya kai sau goma babu amsa zuwa can Husain ya kira da wayar sa kamar almara wayar ta shiga duk suka saki baki suna kallon sa ga farin ciki ya baibaye su. Husnah kuwa tana fitowa daga cikin falon kawai ta wuce gurin way drop zata d'auki maganin ta saboda yau cikin ta ne ke ciwo wayar bawan Allah nan ne tayi tozali da ita kawai ta tuno da abunda ya faru a ranar shine ta kunna wayar ta 'kara bin cikawa ta gani ko zata samu number wani daga cikin iyalen sa, kawai wayar kamar abun jira ta soma ringing, cike da mamaki Husnah take kallon wayar. Sai da akayi kira biyar ta d'aga tace...... *Comment and share* *A GIDANTA NA GIRMA* *BY NANA: KHADEEJATU* *_UMMU IHSAN_* *SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU SOSAI SON FISABILILLAH* *YA ALLAH KAJIKAN MAHAIFINA KAYI MASA RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SA SHIDA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.* *Alhamdulillah Allah muna godiya a gareka daka nuna muna sallah lafiya ya Allah ka karbi ibadun mu ka yafe muna kura kuren mu amin* *Ina yiwa kowa barka da sallah Allah ya mai_maita muna amin* *_Bismillahir Rahmanin Rahim_* 31~35 Husnah tace, "wannan daga ji bakauye ne na karshe tunda daga bud'e waya har kayi kira biyar ba 'a daga ba ai kasan mutum yana wani aikin ne". Husain cikin fushi yace, "to barauniya ai sai ki dawowa mutane da wayar su tunda ba gadon ta gareki ba, shine kika wani za'kewa kina yiwa mutane fad'a kamar wanda kika haifa". Dariya Husnah tayi tace, "good job lallai ashe dai ta tabbata ina magana da mahaukaci ne to ka iya bakin ka ko kuma na yanke halshen ka". Husain yace, "nikuma sai yanzun ne nagane cewar babbar karya nake fad'a da ita, to kisani sai na yanke kafar ki kuma sai na zubar maki da hakori duka inga ta inda karya zatayi magana da kuma cizon mutane! ". Husnah tace, "ja jiki kanzo bani da ruwan ji'ka ka, ballema kayi ban kama". Husain yayi dariyar keta yace, "muzuba mugani ni dake kuma sai kin dawo da wayar da kika sace". Shaheed ne yayi saurin amsar wayar yace, "sorry yar uwata dan Allah ku dai na irin haka, ni suna na Shaheed munyi ta neman ki bamu sameki ba sai yau ga yayan mu babba kuyi magana dan Allah kiyi ha'kuri ki saurare mu" Husain yace, "miye na wani bata ha'kuri kawai kace mata ta dawo da wayar mutane kawai ". Husnah najin su sarai har tayi niyar kashe wayar sai kuma taji bazata iya wulakanta wanda yayi maganar ba wato Shaheed barema yace, ga yayan su babba. Husnah tace, "ok bashi wayar nasan duk ku masu hankali ne banda wani ". Da dariya Yayan nasu yayi mata sallama, Husnah cikin farin cikin jin ya mutun ta yayi mata sallama sai ta amsa. Yayan nasu yace, "kanwata ya kike ya bayan rabuwa? " Husnah tace, "lafiya lau ya mai jiki dafatan dai babu wata matsala atare dashi? ". Yayan yace, "Alhamdulillah yaji sau'ki tuni ma, amman yayi ta neman ki, gashi yace kinyi masa alkawarin ba zaki gudun masa ba". Sai alokacin ne Husnah ta tuno da alkawarin tace, "kash wallahi na manta ne, amman isha Allah zan nemi inda yake nazo gurin sa, ka sanar dashi ina gaida shi sosai da sosai". Yayan yace, "aa baza ayi hakan ba yanzun dai za'a kai masa wayar sai kuyi ta baki da baki kinga sai yafi farin ciki ko? ". Husnah tace, "ok babu damuwa amman dan Allah kada ku baiwa karen gidan ku wayar nan dan kar yadame ni da haushi, kuma idan zanzo gidan nan ku tabbatar da kun d'aure sa ko kuma kubar gidan dashi". Husain yayi saurin cewar, "idan kika kuskura kika zo gidan nan sai kinyi baya nine". Yayan nasu yace, "haba Husain miyasa kuke wannan rigimar takune bayan ba wani sanin juna kukayi ba, amman ba'kin fad'a kamar wasu kaji". Dariya Husnah tayi tace, " Yaya kai wa Daddy wayar muyi magana waima ina baby tane nasan yanzun ta girma sosai". Dariya duk sukayi banda Husain, da sauri Babyn tace, "gani Anty nayi kewar ki dan Allah kizo gidan mu kuma ku dai na fada da Uncle kinji kuma yaushe ne zaki zo? " Dariya duk sukayi Husnah tace, "to wace tambayar zan amsa maki, ina nan zuwa kinji ko? ". Yayan nasu yace, "Shaheed kaiwa Daddy wayar suyi magana ni kuma na tsaya akan wannan mai bakar zuciyar ". Tashi Shaheed yayi rike da wayar a hannun sa, yana yiwa Husnah firar bayan rabuwa da yanda Daddy da Hajiyar su, suka damu da rashin ganin ta, Husnah duk sai taji babu dad'i. Baby kuwa da gudu taje ta samu su Daddy zaune suna fira harda su Anisah, kawai ta fad'a akan jikin Hajiyar tana shashsheka alamar tasha gudu har ta gaji, Hajiyar tace, "wato dai sakar cin nan naki yana nan Allah yasa Uncle dinki ya ganki kici duka". Baby tace, "Daddy yau Uncle Shaheed yazo maka da wayar ka kuyi magana ". Dariya duk suka sanya mata dan basu fahim ci inda zancen ta ya dosa ba, Shaheed ne ya shigo da sallamar da wayar a kunnen sa, yaciro wayar ya saka hans free yace, "Daddy suprise gashi kaji muryar waye? ". Amsar wayar Daddy yayi, yayi sallama daga can Husnah tace, "Daddy ayi mani afuwa nayi laifi babba ". Ai kuwa cikin farin ciki, Daddy yaji muryar da bazai taba mantawa da itaba har ya mutu yace nikam nayi fushi sai kin zo da kanki zan hakura ". Husnah tace, " daman zan zo har gida da kaina amman Daddy Yaya akayi layin ka ba'a rufe saba akalla ansamu wattani da yawa" Dariya Daddy yayi yace, "ina son layin ne kuma dashi nake amfani duk wasu abubuwa nawa masu muhimmanci suna a cikin sa, sai kin zo zan baki labarin miyasa ba'a rufe saba". Husnah cikin damuwa tace, "zan zo ranar friday Daddy ". Daddy yace, "to kice Insha Allah nikuma Insha Allah nida iyalai na munayi maki barka da zuwa tun kafin kizo, ke zaki zo da kanki ne ko na aiko a d'auko kine". Shiru Husnah tayi zuwa can tace, "aa zanzo da kaina ne idan nazo sai a dawo dani ". Sallama sukayi suka kashe wayar da sauri Hajiyar tace, "tabbas koda baku bamu labari ba mun san cewar addu'ar mu ta 'karbu ne tun daga ganin farin cikin Alhaji dasu Shaheed dan haka yau sadaka zamuyi kuma Allah ya kawo ta lafiya ". Cikin farin ciki kowa yace, "amin " Ranar yini yan gidan sukayi cikin farin ciki ganin iyayen su sun samu abunda suka dad'e suna nema. Husnah kuwa ajiye wayar tayi ta mayar da ita inda ta ajiye ta, kwanta wa tayi tana tunanin wannan bayin Allah, da Allah ya had'a ta dasu. Zubaidah kuwa tuni tabar garin tayi gurin shashan cinta a can ta hud'u da wasu yan fafa kawai ta mike 'kafa taci gaba da abunda takeyi amman tana kiran "yarta taji wane abun takeyi. Yau friday gidan su Husain tashi sukayi sunata shirye shiryen tarbon bakuwar su Husnah , Husain kuwa sai hura hanci yakeyi kamar wani namijin zaki, sai cika yake yana batsewa shi ala dole kada bakuwar taga damar sa ta raina sa. Kowa da abundant yakeyi ma tarbon Husnah. Husnah kuwa sai karfe sha d'aya ta tashi tayo wanka tayi dan make up d'in ta, gurin saka kaya ne ta rasa wanne zata saka duk kayan sunyi mata 'kanana babu kayan mutumci, ai kuwa tunda Husnah take yaune kai ta taba takaicin rashin kayan mutumci a gareta, kawai ta fashe da kuka, tana kukan ne duk tabi kayan ta kaf ta saka tana cirewa, duk basuyi ba, kawai ta d'auko doguwar rigar ta ta sallah da hijab d'in ta saka ta goge fuskar ta, ta kalli madubi tace, "wannan shigar da ita zani gashi duk kayan sun tsufa ni yaya zanyi ne wai ni Husnah, kawai tayi zaman yan bori dir shan a 'kasa tayi tagumi. Tace, "nima fasa zuwa bari nakira wayar na sanar masu" kawai Husnah ta tashi ta d'auko wayar ta kunna to kuma wayar babu gurin kira baka ganin number ma kawai ta ajiye wayar. Kamar daman jira akeyi ta bude wayar kira ya shigo tana d'aga wa tayi sallama cikin sanyin murya aka amsa mata, aka ce, Anisah ce kanwar Yaya Shaheed muna ta jiran ki gashi har biyu tayi bamu jiki ba Daddy da Hajiyar mu duk sun damu suna cewa Allah yasa kada ki shuka su". Jikin Husnah ne yayi sanyi tace amso sorry kice masu yanzun zan fito amman kurika kirana kana yi mani kwatancen hanyar yanda zan gane" Cikin farin ciki kowa yace, to ranki ya dad'e" dariya Husnah tayi tace, ashe duk kuna jin abunda na fad'a to gani nan zuwa" tayi shiru sai ta tuno da maganar Daddy ranar yace tace, Insha Allah, kawai tace, "Insha Allah". Suka ce, " to Allah ya kawo ki lafiya " tace "amin" Husnah kuwa ta ajiye wayar, tace, "haka nan zan tafi sai dai suyi mani dariya ". Post da key kawai ta d'auka ta fito ke nan suka hud'u da Zubaidah suna shigowa, burki taja, amman ta dake cikin sauri Zubaidah ta fito cikin motar ta 'karasa inda Husnah take tanayi mata kallon sama da 'kasa da mamaki cike da fuskar ta. Murmushi Husnah tayi ta matsa inda Zubaidah take ta rungume ta, tayi mata rada a kunne, saboda ganin yanda abokan sha shancin ta maza da mata suke kallon ta tace, "mommy shigar ustazai ke nan nasamu labarin sa baya kula macce mai shiga irin tawa, sai ta ustazai kuma ko ustazai masu kamun kai, dan gidan mansir ne, haji mansir naira da kwabo dan sa wanda shine kawai ya gaji dukiyar sa, matar Aure yake nema ta kwarai bayan ya gama lalata rayuwar wasu, shine naje nabiya kud'i aka bani wannan kayan da yanda zanyi shigar da kuma yanada zanyi masa magana batare da gane wace ce niba". Wata irin ajiyar zuciya Zubaidah ta saki, Husnah kuwa murmushi kawai tayi, Husnah tace, "naso sanar dake da bakya nan amman sai na fasa saboda ban 'karasa iyawa ba yanzun ma zanje gurin koyon salon yanda zanyi masa makirci ne da iyayen 'karya". Zubaidah ta dawo da kanta saitin kunnen Husnah tace, "na jin jina maki amman zanyi shiru saboda wannan shegun zasu iya watsa maganar har zancen ya watse kin ga suyi muna ba'kin ciki, sai kin dawo ". Rabuwa sukayi Husnah ta bude motar ta shiga ta bata wuta, su kuwa "yan gulma duk sun so san miye Husnah ta sanar da Zubaidah amman kai tace masu, "ta samu ustaz ne irin na yan bari". Ta rufe wa kowa baki. Husnah kuwa tana tafe hankalin ta kwance, aka kira wayar ta sanar masu inda take, aikuwa tun daga wannan lokacin ne, suke waya a tsanin su, har tazo inda suke ta kwa tan ta mata, wata motar ce, dake gefen titi ta gani, mai motar ne ya fito yayi mata hannu tana zuwa gurin itama tayi parking 'karasowa inda take yayi yace, "kanwata muje nayi maki jagora, ni ina gaba ke kina biye". Dariya Husnah tayi tace, "ok Yayan mu muje kawai ". Haka suka jero shi bakar mota ita kuma ash har suka 'karaso wata unguwa mai manyan gidaje, a take Husnah taga ashe dai unguwar su kauye ce, bata gama tunani ba suka gangara wani titi hannun hagun su, kayataccin gidajen da Husnah ta gani ne suka so bata tsoro, batama 'kara sa rud'ewa ba sai da suka doshi wani 'katon gida wanda yafi ko wane gidan tsaruwa da had'uwa a unguwar, a take aka bud'e masu get suka shiga ciki get ukku ne a gurin duk babu na rainawa a ciki koda sukayi parking a wata rumfar alfarma a take Husnah ta fara raina suturar dake jikin ta ita ganin takeyi duk batayi kyau ba kuma ita ganin suturar dake jikin ta duk yawa ce, gashi zafi takeji duk rigar da hijab din sun takura mata. Kwan kwasa mata kofar akayi sai alokacin ne ta tuno da ita ake jira, fitowa Husnah tayi, ai kuwa tayi tozali da Hajiya wadda tana ganin Husnah sai taji duk son duniya tanayi mata shi, kamar ta goya ta , rungume Husnah tayi tace, " 'yata ina yi maki barka da zuwa nagode wa Allah da ya sake sada mu dake zo muje" hannun Husnah taja ta hana kowa yayi mata magana ko ya rungume ta. Husnah dai anzama ba kyauya sam idon ta na kallon tsarin gidan, ga kuma kaunar Hajiyar da taji ya darsu a zuciyar ta. A babban falon gidan suka yada zango kowa ka kalli fuskar sa zaka fahimci yaji dad'in ganin Husnah a kusa da Daddy Hajiyar ta ajiye Husnah, hannun Husnah Daddy ya rike guda biyu, yana murmushi yace, "your welcome my doughter Allah alhamdulillah da kasa ke nuna mani wannan baiwar taka, sannu da kokari kinji 'yata yau kin cika mani alkawarin da kikayi mani". A take idon Husnah ya cika da hawayen farin ciki tace, "nima naji dad'in shigowa ta a cikin ku, dan Allah Daddy nima nazama 'yarka man! ". Murmushi kowa yakeyi Anisah tace, " 'yar uwata kada kidamu yanzun haka kina cikin yan uwanki maza da mata, idan kun gama ganawa da yan iyayen ki, ki nemu a wan can d'akin suka nuna mata da hannun su". Murmushi Husnah tayi mata ta gyada mata kai dukan su suka tashi suka basu guri mazan dama tuni sun bar gurin. Wani irin farin ciki ne Husnah take cikin sa wanda batama san irin saba, duk sai ta saki jikin ta suna fira da Daddy da Hajiya sai kusan la'asar Daddy yace, "'yata har yanzun baki sanar da Hajiya sunan ki ba amman ki bari a dawo sallah sai ki sanar damu duka ". Dariya Husnah tayi ita da Hajiyar, Hajiyar tace, tashi ki samesu inda suka sanar dake tashi Husnah tayi ta nufi inda suka sanar da ita, tana zuwa a bakin kofar taji suna fad'ar..... *Comment and share* *A GIDANTA NA GIRMA* *BY NANA: KHADEEJATU* *_UMMU IHSAN_* *SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU SOSAI SON FISABILILLAH* *YA ALLAH KAJIKAN MAHAIFINA KAYI MASA RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SA SHIDA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.* *YA ALLAH KA BAIWA MAMA NA LAFIYA DA DUK KANNIN WANDA BASU DA LAFIYA NA GIDA DANA ASIBITI ALFARMAR ANNABI MUHAMMAD SALLALLAHU ALAIHI WA SALLAM AMIN* *_Bismillahir Rahmanin Rahim_* 36~40 Kawai Husnah taji suna fadar "a gaskiya wannan kam duk inda ta fito balarabiya ce ta asali wallahi" Ni kuwa wallahi Suhailat tafiyar ta kawai nake kallo cikin cikin 'kasaita da yanga nifa wallahi da zata koyar dani dana more wallahi. Kawai suka sanya dariya. Husnah kuwa tana a bakin kofar d'akin tana sauraren duk abunda suke fad'a akan ta, kawai ta soma duba shigar ta da 'kafar ta itafa ba taga wani abun burge waba a tattare da ita ba, kawai ta mere baki, ta tura 'kofar ta shiga, ai kuwa da gudu suka zo suka tarye ta, suna yi mata sannu da zuwa. Da murmushi Husnah take biyar su d'aya bayan d'aya, a bakin gadon suka yada zango . Anisah tace, "a gaskiya munyi farin ciki da zuwan ki gidan nan dan Allah wata rana kizo kiyi muna kod one week ne! " Dariyar da Husnah bata shirya bace ta kubce mata, ai kuwa duk suka tsare ta da ido sai da tayi dariyar ta mai isar ta, tace, "yo ku banda abun ku miye na han zari haka bayan duka_duka yau ne na fara zuwa, ai ina ganin kamar yan zun ku ne zaku zo gidan mu ko? ". Da sauri Anisah tace, "ai ko yan zun zamu iya biyar ki har gidan muyi maki wata koda biyu ne zuwa ukku ". Dariya sukeyi dukan su suna cikin dariyar ne Shaheed ya shigo hannun sa ri'ke dana Baby yace, "kai amman fa kun iya wayau wallahi shine zaku wani d'auke ta ku dawo cikin d'akin ku kuyi ta fira da dariya to ku taso muje falo muci abinci" Tashi sukayi suka fita daga cikin d'akin suna dariya a falo suka yada zango inda babban yayan su Husain yake zaune a kusa da 'kafar Hajiya shi kuwa Husain kwance yake akan kujerar da Alhajin yake zaune kansa a saman cinyar Alhajin yana duba husnul muslim hankalin sa ga baki d'aya yana a kan littafin, Husnah kuwa bata ma kula da waye a gurin ba, asalima Baby ta d'auke mata hankali shi kuwa kamar ance d'aga idon ka, ai kuwa Husnah ce yaga zata ratsa ta kusa da kujerar da suke shida Alhaji alamu sun nuna a kusa da Yayan nasa zata zauna, kawai yayi sauri ya tashi tsaye ya yayi kamar zai bar falon yasa hannun sa d'aya ya ture ta, kawai sai ganin Husnah sukayi inda Husain ya tashi a zaune kamar kace ar'''' ta gudu duk tsoro ya kamata da mamakin taya akayi hakan ta faru?. Husain kuwa kujerar nesa dasu ya dawo ya zauna kamar bai san abunda ya faru ba sai murmushi yakeyi ya daura littafin sa akan fuskar sa. Duka mutanen cikin d'akin sukayo akan Husnah Alhajin kuwa ashe shine ya tare Husnah da hannun sa saboda duk abunda akeyi akan idon sane wannan ne ya hana Husnah faduwa kwance. Sannu kowa yakeyi mata da Allah tsare gaba, gir giza kai kawai Alhajin yayi, Yayan su Husain kuwa cewa yayi, "haba Husain kowa yana jimamin fad'uwar ba'kuwar mu amman kai ko a jikin ka? haba Husain gaskiya baka kyautawa! " yi yayi kamar badashi ake ba Hajiya tace, "Husain ka gyara halin ka sai naga kamar da gayya ka ture yar mutane dan Allah yanda tazo gidan mu lafiya ka barba ta koma gidan su lafiya! ". Da sauri Husnah ta mai do da idon ta gurin Husain cikin zuciyar ta tace, "ashe dai inada shedun gani da ido him! Ba Husain kake ba ko husaina kake sai na rama dan naga ruwan marasa kunya ne da kai amman mu zuba ido baka san wace ce Husnah ba". Alhajin ne ya katsewa Husnah tunanin ta yace, "yata tashi kici abinci rabu da wannan mai zafin ran ". Hannun Husnah suka ri'ko suka je gurin da aka ajiye masu abinci Husnah ta zauna kowa ya zazzauna Hajiyar tace, "kai kuma sai ankira ka ko? " Tasowa Husain yayi ya zauna akan carpet nesa da Husnah Alhaji yace, "Husain ka dawo nan a kusa dani ". Gurin da Alhajin ya nuna masa ne ba Husain ba har Husnah Anisah dasu Shaheed sai da suka zaro ido ganin gurin da Husnah take zaune ne babu wata tazara mai yawa a tsakiyar su, Baby kuwa da murna tace, "yo sauri Uncle na tare maka gurin ka kada wani yazo ya zauna maka gurin ka". Ganin kallon da Alhajin da Hajiyar sukeyi masa ne yasaka Husain badan yaso ba yazo ya zauna a kusa da Husnah har da taka mata hannu aikuwa da sauri ta janyo hannun tace, "wash! Allah hannu na! " ta soma yarfa hannun. Babu wanda yaji abunda Husnah ta fad'a saboda kowa yasan Husnah da sanyin murya amman kowa yaga abunda ya faru kuwa babu wanda yace dasu uffan. Yana zama Husnah ta dan 'kara matsawa a nesa dashi amman duk da haka ba wani nesa da juna suke ba saboda gurin kowa ya zauna an zagaye abincin. Husnah aka fara zubawa sai daga baya aka zubawa kowa Husnah zata d'auki plate d'in ta ta soma ci Husain ya riga ta ya d'auke. Murmushin gefen baki Husnah tayi ta gir_giza kanta ta jin_jina kai ta janyo nasa plate din ta soma ci. Yayan zaiyi magana da sauri Alhajin da Hajiyar suka dora hannun su akan bakin su ai kuwa kowa yayi shiru kamar babu wanda yaga abunda yake faruwa a gurin. Husnah kawai ta tashi tsaye kamar wadda ta tuno wani abun ai kuwa ta samu sa'ar taka wa Husain yatsun 'kafar sa da wannan uban takalmin nata kuma harda mur zawa ai kuwa Husain da yaji wata uwar azaba kawai ya saki plate din hannun sa ya runtse ido zuwa can Husnah ta bar gurin tana dariyar 'keta 'kasa_'kasa Husain da sauri ya tashi yaja 'kafar sa yana d'in girsa 'kafar sa har ya iso inda kujera ya fad'a ya ri'ke 'kafar sa, ai kuwa 'kafar har tayi wani uban jaa kuma ta fara kumbura, Husnah dake tsaye a bayan sa ta dawo kusa dashi ta faki idon kowa tace masa, "kai dai ka daina ja dani baka san wace_ce Husnah ba Husnah bata d'aukar wulakanci a gurin kowa sai dai idan ita Husnar ce taso dan haka yaro sai ka ki yayi babbar Anty a gurin ka! ". Ta nuna masa yatsa tayi tafiyar ta. Zafin da Husain yakeji ne ya daina ji yadawo kallon karamar yarinyar a cewar sa, wadda yake ganin kamar Baby dan bai yarda ta kai shekara goma ba to koda ta kai shekara goma to shi ginin ta yakeyi kamar jiya_jiya ne aka yaye ta. Husnah kuwa da farin ciki ta koma cikin d'akin su Anisah tayi zaman ta, daman ita ba gwanar cin abinci bane shi yasa tayo masu wayau tabar gurin. Su Hajiya kuwa duk abunda akeyi akan idon sune sai dariya sukeyi Anisah harda hawaye da dafe ciki saboda dariya Samha tace, "Allah nagode maka yau gashi ina kallon Yaya Husain na biye wa yara tunda duk wata mace a duniya indai bata kai sa'an su Hajiya ba to yarinya ce a gurin sa". Yayan yace, "aikuwa ashe dana kubsa muna gurin kallon drama kai Allah na gode maka yau gurin Maman Baby zani na bata kyakykyawan labarin akan Husain". Kawai ya tashi yana dariya yabar gidan haka kowa ya dawo cikin babban falon ya zauna Husain kuma tuni yabar gurin. Husnah kuwa ganin kiran Zubaidah tayi bata d'aga ba sai da tayi kira ukku ana hud'u ne ta d'aga ta kara wayar a kunnen ta, tace, "mommy ya ya ne? ". Acan ban garen Zubaidah tace, "ki dawo gida haka nan idan har kin samu ganin sa, dan yanzu zan bar 'kasar nan tafiyar gaggawa ce ta sameni". Husnah tayi ajiyar zuciya dai_dai shigowar su Anisah tace, "duka duka yaushe ne kika dawo kuma yanzun kice zaki koma mommy kifa duba kad'aici ya dameni gaskiya amman kijira ni nadawo muyi magana dake! ". Cikin damuwa Husnah ta kashe wayar ta tashi zaune taga duk su Anisah sun baje ta da ido Husnah ta 'ka_'karo murmushi tace, "to wani satin ma zan dawo indai mommy bata tafi dani ba". Dariya kawai sukayi amman Anisah ta fahimci Husnah kamar ita d'aya ake bari a gidan kawai dai ita ma shiru tayi da bakin ta. Husnah kuwa kayan ta ta d'auka tace dasu , "mu tafi ko?". Jerawa sukayi suka nufi cikin falon Husnah tace, "Am Daddy Mommy zan koma gida kiran gaggawa akeyi mani ". Badan sun soba haka kowa ya raka Husnah harda su Shaheed, wani abu ne Daddy ya bata cikin leda ba'ka Haka mommy ma ta bata gashi Husnah bata san miye ba Shaheed kuwa tasa motar ya shiga ya bata wuta, ya tafi. Husnah taji dad'in wannan karamchin haka tayi masu godiya ta shiga motar ta ta nufi gida tare da kewar su Anisah. A parking space, ne ta ajiye motar ta ta fito kid'a ne kawai ke tashi, tsaki Husnah tayi ta d'auki kayan da aka bata ta shiga cikin falon duk ga maza da mata yan bariki wasu na rawa wasu kallon batsa wasu kuma run gume da juna, harda Zubaidah a cikin su babu wani mai shigar arziki a cikin su. Husnah kuwa bata bi takan kowa ba ta shige cikin d'akin ta, cike da takaici. Zubaidah ce ta shigo ita da wasu kawayen ta cikin takaici Husnah ta d'aure fuskar ta tace, "mommy kada ma kiyi mani wata tambayar har sai wannan mutanen sun bar mani cikin d'aki! " Sanin halin Husnah ne yasaka duk sukayi tsaki suka bar cikin d'akin, ita kuwa Zubaidah tace, "ba zanyi magana da gani sai ke ba, kizo da abunda kika samu ki same a falo". Kawai Zubaidah ta bar cikin d'akin cikin fushi. Tashi Husnah tayi, ta d'auki kayan ta nufi falon idon kowa akan ta kujera ta samu inda Zubaidah take a zaune ta zauna akan hannun kujerar ta bata kayan. Ansa Zubaidah tayi ta baiwa wata mata dake gefen kujerar ta ita kuwa cikin izzah da isa take bude ledar, wani kwali ne taci karo dashi ta bude, ai kuwa wani dan akwati ne ta gani mai mugun kyau ai kuwa da sauri matar ta daka tsalle ta rungume Zubaidah tace sweety lallai yarinyar nan da gaske take ba 'karya ba kamar yan da wasu daga cikin mu suka fad'a ba". Baiwa Zubaidah akwatin tayi aikuwa ita kanta Zubaidah sai da tayi ihu tace, "yauwa Husnah kin kyauta a gaskiya naji dad'in wannan fitar taki ki aje mani ita har zuwa sati ukku masu zuwa babbar rana a gurina ke nan " D'aya ledar kuwa ana bude wa turare ne masu kyau masu tsada ga kamshin gaske, har kala biyar, ba karamar murna sukeyi ba. Husnah kuwa bar masu kayan tayi ta koma cikin d'akin ta. Zubaidah kuwa cewa tayi, "ina fatan duk kun gama yi muna oder ankon namu da kayan amare da kayan diener dana kamu bana son asamu matsala koda ta gurin launin colour ne " Ihu suka sanya, ita kuwa Husnah da tazo zata d'auki wayar ta, kawai ta jiyo firar da suke yi da ihu cewa takeyi, "biki kuma? Kayan amare kamu kuma!? Nifa abun da mamaki dan ba'a taba bikin da mommy tace zata ba ko zatayi anko duk kuwa da irin alakar ta da mutum, to kodai mommyn ce zatayi Aure? ". kai inaa!!.......... Assalamu Alaikum yan uwa ga wanda bai san da maganar da nayi ba ta bada gudumuwa ta a gurin koyon sana'oi ba to wasu sun sani sune ma suka bada shawarar na ri'ka sakawa a 'karshen page d'ina dan wanda ba group dina yake ba shima ya koya. _*Abubuwan da zan ri'ka sakowa kuwa sune--:>*_ *koyon decoration koyon girki koyon kayan mata koyon wasu abubuwa da dai sauran su* dafatan bazaku raina aduk sanda na turk maku kuma zaku anshe sa da hannun biyu,. Bance dole mutum ya koya ba nayi ne dan wanda suke da ra'ayin koyon basu san yaya zasuyi ba. Dan haka duk wanda yake son koyo nabashi damar koyon abun sa. Bari dai mu fara abunda yake gaban mu. *Yau zamu fara ne da koyon decoration na bottle empty da zare rumy* _*kayan bukata*_ *1_Robar lemu Ko ruwa* *2_Zare Rumy* *3_Flower duk irin wadda mutum yake so* *4_Scissors da gum* Dafarko dai mutum zai samu kwalbar shi sai ya d'auko almakashi, ya yanke saman robar inda marfin, sai asamu gum ana shafawa ajikin rubar ana li'ka zaren Rumy har sai an zagaye ko ina, har a gama, sai ki saka fulawar ki duk irin wadda mutum yake so shike nan. zanci gaba insha Allah idan har akwai tambaya ko neman 'karin bayani ga WhatsApp number :- _08065348329_ Dan Allah banda kira. *Addu'a Kasai nake nema a gurin ku, kuyiwa mahaifiyata addu'a Allah ya bata lafiya Allah ya jikan mahaifina amin nagode* plc *Comment and share* *A GIDANTA NA GIRMA* *DAGA AL 'KALAMIN NANA: KHADEEJATU* *_UMMU IHSAN_* *SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU SOSAI SON FISABILILLAH* *YA ALLAH KAJIKAN MAHAIFINA KAYI MASA RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SA SHIDA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.* *YA ALLAH KA BAIWA MAMANA LAFIYA KA BAIWA DUK KANNIN WANDA BAIDA LFY NA GIDA DANA ASIBITI LAFIYA AMIN YA ALLAH* *_Bismillahir Rahmanin Rahim_* 41~45 "Kai inaaaa sam Mommy ba bu wani Aure a gaban ta Amman koma Auren waye zan gani da ido na dan sam ban yarda da wannan shirin na su Mommy ba, matar da ta tsani wani ya ce zaiyi Aure ballema ita tayi wani Auren!? Husnah" ke nan ta ke wannan zan cen cikin damuwa Haka Husnah ta kwana da tunanin wannan lamarin har yaso ya hana ta bacci. A can gidan su Husain kuwa. Fitowa Husain ya yi da niyar rama abun da Husnah tayi masa amman kuma kash ya makara, yana fitowa Husnah na barin gidan. Dafe goshin sa ya yi ya doko uban tsaki ya buga 'kafar sa ya juya a fusace ya dawo cikin d'akin sa, sai tsaki yake zubawa. Haka "Husain ya ya kwana da fushi da kowa na gidan dan a ganin sa sune suka saka Husnah ta raina sa da ya wa". Shirin biki kawai Zubaidah keyi ita da 'kawayenta amman Husnah ido ne na ta sai dai kuma wata sabuwar bidi'ar da Zubaidah ta zowa Husnah dashi wadda Husnah take kallon har "yan han jin Zubaidah shine kullum da safe sai ta kawo mata wasu kayan mata tana cewa sai Husnah tasha saboda sabon saurayin ta". yau ma kamar kullum Zubaidah ce tsare da Husnah tana bata kayan mata, ita kuwa Husnah kallon ta kawai takeyi ko 'kyafta ido babu har Zubaidah ta so ma tsar guwa, Zubaidah tace, "wannan kallon fa Husnah?. Dariya Husnah tayi tace, "ni kuwa zan so sanin wannan sirrin da ake shirya wa, da alama dai wannan Amaryar ba kowa bace face maku san ciya ta ce dan ina ji a jiki na kamar ke ce uwar Amaryar ni kuma ta kusa da Amaryar Mommy amman yau ba zan sha maku wannan abun ba kamar kullum domin kuwa kin san idan na karya da safe bana iya bu'katar komai a gaba na amman za ki iya ajiyewa har zuwa gobe indai ba bu wata damuwar". Mutuwar zaune Zubaidah tayi tun lokacin da Husnah ta soma baya nin ta, kawai Zubaidah tace, "Husnah waye ya sanar dake abun da muke shirin shirya wane?. Husnah kuwa yi tayi kamar bata gurin. Zubaidah ta ce, "Husnah zan yi maki Aure ne da wani mutum wanda baki ta'ba gani ba, kuma baki ta'ba jin labarin sa ba, shine ya za'bi Auren ki, fiye da kasan cewa dake na yan wasu shekaru, kuma Auren a can baya sati ukku na saka amman yanzun cikin wannan satin na biyu zamuyi bikin saboda zaku wuce America ne dan mafi yawan cin har kokin sa a can yake yin su mutamen bai da wata mata a tare dashi duk suna Kauyen su yaran sa sha biyar na Aure, bakwai wanda ya haifa ba tare da Aure ba kuma duk ana kular masa da su ba bu wanda yake cikin yunwa da talauci ". Sai da Zubaidah takai aya Husnah dake tsare da ita da idon ta, kawai ta tashi tsaye ba tare da tace da ita uffan ba ya shige cikin d'akin ta, zaunawa tayi a bakin gadon ta, tunanin komai ya 'bace mata kawai dai zaman tayi batare da tasan mike damun ta ba. Zubaidah kuwa wayar ta ta d'auka ta kira wata number ta ce, "hello Alhaji an yanka ta tashi domin kuwa Husnah ta gano komai, kuma naga alamar zata iya bijere muna badan komai ba sai dan naga bata ce dani komai ba, nafi kowa sanin halin Husnah domin Husnah 'yata ce". Daga can 'ban garen a kace da Zubaidah, "ku fara hidimar bikin tun yau san nan kuma zan aiko maku da duk abunda ku ke da bukatar sa, kuma kada abar ta zuwa ko nan da bakin get san nan kuma yara na zan turo su domin suyi mani sa ido akan ta da duk wani abun da take aika tawa kuma ba na bu'katar a takura mata kuma duk abun da take bu'katar sa ayi gaggawar kawo mata shi, kwata_kwata ba na bu'katar ta nemi abu ta rasa shi ki turo mani account number na ta zan turo mata da ishesh shen kud'i ". Cikin farin ciki Zubaidah ta ce, "to ranka ya dad'e angama". Ket ya kashe wayar. Husnah kam tashi tsaye tayi ta kama za ga yen cikin d'akin sai nazarin wannan shirmen ta ke yi har yan zun Husnah bata gamsu da wannan baya nin ba duk da ya fito ne daga bakin wadda bata yi mata 'karya. Haka Husnah takwana cikin matsa nan ciyar damuwa. "Zubaidah kuwa harkar gaban ta kawai takeyi ita da 'kawayen ta yau ma gidan kid'a ne kawai ke tashi har kamar kunnen mutum ya fashe, tsaki kawai Husnah keyi, wayar ta ce tayi alart kawai ta 'ki bi takan wayar dan yau ko karya wa bata yiba saboda Zubaidah hidimar gaban ta ta ishe ta, mutane maza da mata ne ke shar holiyar su, a gidan dan haka ne yasaka Zubaidah man tawa da Husnah bata ci abinci ba". "Husnah kuwa jakar ta kawata d'auka da wayar ta, tabar sai makulin motar ta, ta fito cikin falon gidan kallon mutanen gurin tayi, amman jin takeyi kamar ta samu bindiga ta halbesu kowa ma ta fu ta, kawai tayi gaba abinta, su kuwa sai kirarin amarya "yar 'kamshi sukeyi mata, zuciyar Husnah kamar ta fashe haka takeji saboda tsabar yan da wannan Sunan yake ta'ba zuciyar ta" Jikin motar ta ta 'karasa zata bud'e mota, kawai wasu gar dawa majiya 'karfi har su hud'u suka za gaye ta kowan nen su 'kirar yan rastalin ne dashi, duk sun had'e rai sun tur ni'ke fuska suna tambayar ta, d'ayan su yace, "Madam sai ina fa?. Cike da mamaki Husnah take kallon mutanen harda su ri'ke baki, tace, "to ko an saka kune ku hanani rawar hantsin gaba nane?. Duk suka zaro ido suna kallon ta, cike da mamaki ganin ko tsoron su ba ta ji ba, d'aya daga cikin su ya ce, "tabbas an saka mu duk inda kika saka 'kafar ki mu ma mu saka tamu 'kafar saboda tsaro, dan a yan zun haka kina da masu harin da suke da burin sace ki saboda wanda zaki Aura mutane da yawa ne suke neman sa cikin su kuwa harda jami'an tsaro ". Dariya Husnah tayi ta ce, "yo ni ina ruwa na a cikin lamarin sa, kai nifa ba bu uban da ya isa ya takurawa rayuwa ta, domin kuwa ni bance ina son sa ba, ballema nayi burin Auren sa, wai ma anya mutum ne ko aljani dan nifa nafa zargin sa?. Zaro ido sukayi waje suna kallon 'karamar yarinya marar tsoro amman suna ganin dan bata san waye zata Aura ba ne da ta shiga tai tayin ta da shi kuma ta kame bakin ta, da furta masa mummunar magana, amman zasuyi mata uzuri na rashin sani". Muryar Zubaidah ce ta jiyo tana fad'ar, "Husnah gidan uban waye zaki, baki ji nace kada ki yarda ki bar gidan nan ba ne!?. Ko kallon ta Husnah bata yi ba, tace, "yo da yunwar zan zauna ne, har 'karfe biyu da rabi ban karya ba, salon yunwa ta kashe ni, ni kam zan je neman abinci ne". Dafe kai Zubaidah tayi ta ce, "kiyi hakuri shaf na man tane, amman kije tare da wannan nasan zasu baki kulawa ta musamman". Husnah ta ce, "wallahi kowa ya kama gaban sa, kin dai san tun akan Tk halina bai sauya ba". Zubaidah ta ce, "wannan ya shafe Tk ya wuce sa kawai dai kiyi hakuri kuje tare". Husnah kuwa tsayuwar ta ta gyara a jikin motar alamar sai dai suyi ta tsayi a gurin, wayar Zubaidah ce tayi 'kara kawai ta d'auka cikin rawar jikin da kaud'in murya tace, "hello yallabai kayi hakuri Husnah rigimar ta tayi yawa, kabar ta, ta fita zata ciyo abinci ne kawai". Ta yi shiru, zuwa can ta ajiye wayar tace, "minti talatin na baki idan ki ka wuce hakan ni da ke ne". Murmushi Husnah tayi kawai taja motar ta tabar gidan sai da Zubaidah tayi ta kiran ta san nan ta koma gidan. Tun da safe Husnah kejin fad'uwar gaba amman bata san mike faruwa ba, kawai dai ta tashi jikin ta duk ba bu 'karfi, zuwa 'karfe ukku na rana Zubaidah ta shigo cikin d'akin wasu matan wanda Husnah bata san su ba biye da ita, hannun su cike da kaya har su biyar, kallon su kawai Husnah keyi, ajiye kayan sukayi a gaban Husnah duk sukayi tsaye suka run gume hannun su. Husnah kuwa kallon Ikon Allah kawai takeyi, Zubaidah cikin d'aure fuskar ta babu alamar wasa tace, da Husnah "Husnah yau kam nice uwar babu wani alamar d'aukar raini kuma yau ne ake kamun Amarya dan haka, ga masu shirya Amarya nan mijin da kansa ya turo su, sai ki tashi tsaye su shirya ki, idan an gama ku fito ga motoci can suna jiran Amarya". Kawai Zubaidah tabar d'akin, Husnah kuwa kallon Ikon Allah kawai takeyi sai da suka ce da ita, "tashi kiyo wanka " Husnah kuwa ta ce, "ni ba na wanka ku shirya ni a hakan ". Kallon_kallo aka shiga yi kowa cike da mamaki amman tunda Zubaidah ta sanar dasu halin Husnah kuma tace dasu duk abunda tace kada su biye mata sudai bita a sannu har su samu ta yarda ayi komai cikin sa'a da nasara" Haka dai suka dare sukayi yanda Husnah tace, suka gyara ta, Husnah sai dariya takeyi, su kuwa sun rasa dariyar miye takeyi, sai ma ta dawo tana burge su, kwalliya sosai sukayi mata ta Amarya Husnah tafito Amaryar ta tsab lallale ne kawai babu a ciki. Fito da Husnah sukayi kowa sai mamaki irin yanda Husnah ke takun ta suke gashi dai fuskar ta cike da annuri ita kanta Zubaidah sai da tayi mugun mamaki cikin ranta har wasi_wasi takeyi anya Husnar tace kuwa? Kodai_kodai a kwai abun da take shirya wa ne!?. "Kai ina sam Husnah bazata iya shirya komai ba dan Husnah rainon tace, kuma tasan daman Husnah ba za ta kunya tar da ita ba". Husnah kuwa ita ce a gaba gurin shiga motar Amarya wannan abun da Husnah tayi ya 'kara baiwa kowa tabbacin yar gidan Zubaidah ce. Husnah kuwa wani kallo take biyar duk mutane dake cikin motar ba kamar Zubaidah, wanda sai da Zubaidah ta tambaye ta, "Husnah ya ya dai? . Husnah ta ce, "zanyi kewar ki ne mommy shi yasa nake ta kallon ki". Wani irin dad'in gaske ne ya kama Zubaidah, wanda har sai da run gume Husnah a jikin ta, a haka suka 'karasa gurin kamun. A gaskiya gurin kam ya had'u iya had'uwa, kuma komai cikin tsari akayi sa, sai kusan 'karfe tara aka dawo gida ba bu sallah ba bu salati, Husnah kuwa tsaki kawai takeyi. Su na shigowa cikin gidan Husnah tayi cikin d'akin ta, tayo wanka tayi alwala, tayi sallah kamar yanda ta saba, cikin rashin iya wa. 'karfe goma na dare Husnah ce ta fito da wayar ta a hannun ta, tana waya, har ta bar cikin falon gidan tayo hara bar gidan, turus tayi ta fara zaro ido waje tana nuna wani gurin, cikin rawar baki ta ce......... _*Yau akan ta'ba ka lashe wato dai zamuyi girki ne yau.*_ *IRISH DA CHIKEN STRIPS* _*Abubuwan bu'kata*_ 1_Tattasai ja 2_Tattasai tsanwa 3_Albasa 4_Albasa Carrot 5_Thyme & Curry 6_mangyad'a ko man zaitun 7_Magi &Gishiri 8_Dankali Arish _*Yadda Ake Had'awa*_ "Yar uwa ki wanke naman ki na kazar ki mai kyau, sai ki d'ora a kan wuta, ki ta fasa shi, ki zuba gishirin ki kad'an da Magi star ki zuba curry da thyme da Albasa irin yan da kike so kid'an zuba ruwa kad'an ki barshi ya tana na idan ya fidda main sao ki kwashe kibar ruwan tafasar naman a cikin tukunya. Kidan Kara ruwa kadan sai kizuba Dankalin ki kika yanka yarda kike so sai ki zuba acikin tukunyar taki inda ruwan naman ki suke ki zuba magi da Gishiri ki bar Dankalin har ya kusa dafuwa sai a sauke tukunyar. "Yar uwa kisamu tasar suyar ki zuba man ki, ki saka Tattasan ki wanda kika yanka ja da tsanwa ki saka carrot da magi da Gishiri kad'an, ki barshi har na tsayin mintoci ki sauke tukunyar ki, ki maida tukunyar Dankalin ki ki juye soyayyen kayan miyan ki da naman ki wanda Kika kwashe, ki saka ludayi kijuya shi ya cure guri d'aya. "Yar uwa idan kin sauke a zuba wa mai gida da yaran albarka aci dad'i lafiya. *Daga Alkalamin Ummu Ihsan* _*Shawara ko karin bayani*_ 08065348329 *Comment and share* *A GIDANTA NA GIRMA* *BY NANA: KHADEEJATU* *_UMMU IHSAN_* *SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU SOSAI SON FISABILILLAH* *YA ALLAH KAJIKAN MAHAIFINA KAYI MASA RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SA SHIDA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.* *YA ALLAH KA BAIWA MAMANA LAFIYA KA BAIWA DUK KANNIN WANDA BAIDA LAFIYA NA GIDA DANA ASIBITI ALLAH KA BASHI LAFIYA AMIN YA ALLAH* *_Bismillahir Rahma Nin Rahim_* . 46~50 A cikin rawar jiki take nu na gurin da yatsan ta, ta saki wayar ta dad'i 'kasa ta ce, " Mo... Mommy.. Lafiyar ki kuwa.. Su.. Waye wannan suke shi... Shirin kashe mu... ta... ne... Ha.. Lam...!?. Dariyar 'keta Zubaidah ta sanya ta ce, "oh Husnah wai baki gane ko su waye bane? Duba da kyau dai ko zaki gane su! " Da sauri Husnah cike fa mamaki take kallon Zubaidah yau cike da mamaki ganin bindiga a hannun ta, kuma ta sai ta kan wani mutum wanda sam bata fahimci waye shi ba, su kuma wannan 'kat tin masu 'kirar "yan rastalin sun sai ta d'ayan da bindigogin hannun su, da alama sun kusa kashe ko su waye. Husnah kuwa ta ce, "Mommy yaushe ne kika zama yar bindiga ban sani ba halan? Duk zama na dake ban ta'ba koda jin zan ce maka mancin haka ba, Amman duk wani abun da kike aika tawa nasan dashi koma miye! ". Zubaidah ta ce, "Husnah ke nan ke a tunanin ki zan haife kine kizo kifini wayau, to bari kiji tun kina cikin zanen goyo nake wannan har kallar, kawai dai ina taka tsan tsan ne kawai dan bana son yawan surutu, kuma gashi ke duk abun da kika gani sai kinyi magana akai Husnah, ki sani koda nake karuwa ban 'boye maki ba dan nasan ka ruwanci shine cinki suturar ki kai komai ma naki kuma kema shine sana'ar dana d'ora ki akai, dan haka ba bu wani 'boyon da zanyi maki, yan zun dai ki duba wannan mutanen dan yan zun ne zan gwada maki ni kwarar riyya ce a gurin dan a gaban idon ki zan kashe su". Da sauri Husnah ta ce, "Mommy na ro'keki da kada ki aikata hakan duk da ban san ko su waye ba, bazan so ki aikata hakan akan su ba". Zubaidah ta ce," Husnah kidai duba da kyau kamar naga saboda ke suka zo gidan nan namu, da 'kararren kwana ". A hankali da sanyi jiki Husnah ta 'karasa gurin wanda tafi kusa dashi waye Husnah zata gani? Murza idon tane ta soma yi, cike da matu'kar mamaki, ta ce, "Shaheed kai ne kuwa!? Miye ya kawo ka gidan nan kuma waye ya sanar dakai wannan gidan nake? Kuma kai da waye!?. Bindigar dake sai ce a kan sa kusan biyar, taga ya kafe gurin Zubaidah da ido itama ta mayar da ido ta a gurin, turus ta yi, ta saka hannun ta, tana nu na wa, ta ce, "Yaya Husain harda kai, tana zarar ido, cikin tsoro da far gaba! ". Husain ya ce, "bindigar nan bata wani tsoratar dani ba, amman ke kam kin tso ratar dani, daman tun daga lokacin dana ganki na fahimci cewar ke ba mutuniyar kir_ki bace, dan haka ne yasaka na umarci Shaheed ya bin ciko muna wace ce ke?, sai gashi har ni na gane wa ido na komai ". Kuka Husnah ta sanya ta dur'kusa ta kama 'kafar Zubaidah ta ce, "mommy na ro'keki dan Allah kada ki aikata abun da kikayi niyar ai katawa, Mommy ki duba yanda na shirya yarda da umarnin ki, na Auren wanda ban sani ba, ban san waye shi ba, amman saboda naga hankalin ki yafi kar kata akan hakan, haka na jure ban musa maki ba, Mommy ki dubi wannan halarcin, ki kyalesu kada ki kashe su ! ". Zubaidah ta wani bushewa da kafurar dariya ta ce, "Husnah na fahimci kun sha'ku dasu fiye dani da nake Maman ki, tunda gashi yau kece kike kama 'kafar ta, harda kukan ki dan naji tausayin ki kada na kashe su, amman inaa! Tunda nafa himci shakuwar ku tafi tawa, ni kuma zan kashe su a yan zun nan". Da sauri Shaheed ya ce, "Husnah daman wannan ita ce, Maman ki? Daman kema karuwa ce? Daman gidan karuwai kike shine har kika shiga jikin mahaifin mu, ki ka zama kamar wata mutuniyar kwarai? Amman mi yasa kika shiga jikin mahaifin mu ko dan ku kashe shi ku kwashe dukiyar sa!? ". Husnah kuwa kallon Shaheed kawai takeyi cike da damuwa, ta ce, "Shaheed ba wan nan zan cen ba, ayi zancen ku'butar ku a hannun Mommy da wannan azzaluman mutanen! ". Husain ya ce, "ya Isah haka nan, na tsane ki tun kafin nasan ke wace ce , kuma ki sani idan na ku'buta sai na kashe ki da hannu na, muguwa azzaluma kuma mahaifin mu yafi karfin ki wallahi ta Allah ba taki ba, kuma sai na wulakanta rayuwar ki matsawar kika yarda na ku'buta sai kinyi dana sanin, sani "yan gidan mu! ". Matsanan cin kuka ne Husnah ta fashe dashi ta ce, "Mommy idan har kika yarda kika kashe su ko kuma kika illatar dasu, kisani kin rasa ni ke nan duk wani burin ki a kaina ya watse dan nima kashe kaina zanyi, sai na barki kiyi rayuwar ki yanda kike bu'katar ta! ". Dariya Zubaidah tayi ta ce, "Husnah dan na kashe su shine kema zaki kashe kanki, ai kuwa idan kika kashe kanki kinyi wa kanki, dan ko kin mutu kece kika mutu, baki ji wanda kike ya'kin a kan su ba, sunce zasu kashe ki, ba, ai gara kibar ni ni na fara gamawa dasu" kawai Zubaidah ta kira wayar ta ta ce, kuzo ina jiran ku". Ai kuwa sai ga 'kawayen Zubaidah ta basu umarnin su d'auke mata "yarta suyi cikin gidan da ita. Ai kuwa Husnah ta zille, ta janyo 'kafar Zubaidah da 'karfin da bata san ta dashi ba, ta wufce Bindigar dake hannun Zubaidah tayi saurin, ta'kawa duk wanda ya matso gurin ta da niyar ri'ke ta, Husain kuwa cikin zafin nama ya wafce Bindigar da Husnah ta fige, dan Husnah bata iya ri'kon Bindigar ba, kawai ya ta'ka Bindigar akan Husnah yace, "zan kashe wannan babbar karuwar, kowa ma ya futa, cikin rawar jiki Zubaidah da 'kawayen ta suka d'ora hannun su akai kamar zasu fasa ihu,. Husain ya ce, "ku d'auke Bindigar ku a kan dan uwana ko na kashe wannan annobar da naga kuna tsoron a kashe ta, cikin rawar jiki duk wannan gardawan suka, d'auke Bindigar su akan Shaheed. Shaheed kuwa yasan halin Husain zai iya halbe Husnah, saboda yanda yaga zallar kiyayyar Husnah a idon sa, da sauri Shaheed ya ce, "dan Allah kada ka aikata hakan akan Husnah wallahi bata da alaka da wannan aikin ". Husain ya ce, "mutuwar ta, ta zama wajibi yau sai na kashe ta da hannu na mun rage mugun iri a duniyar nan! ". Husnah kuwa kallon Husain kawai takeyi tasan yau mutuwar ta, tazo, tunda Husain daman ya tsane ta, yau kuma babu wanda ya isa ya hana shi kashe ta, zuwa can Husnah ta ce, "mutuwa kaine kake tsoron yin ta, ni kuwa daman na dad'e da mutuwa, dan haka barazana bata sakani wani tsoron mutuwa ka halbe ni kawai na futa da wannan 'kuncin rayuwar ! ". kawai Husain ya 'kara saita Bindigar sa akan Husnah Kawai sai sukaji ta lau anyi halbi, jin kake damm.......! *A GIDANTA NA GIRMA* *BY NANA: KHADEEJATU* *_UMMU IHSAN_* *SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU SOSAI SON FISABILILLAH* *YA ALLAH KAJIKAN MAHAIFINA KAYI MASA RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SA SHIDA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.* *YA ALLAH KA BAIWA MAMANA LAFIYA KA BAIWA DUK KANNIN WANDA BAIDA LAFIYA NA GIDA DANA ASIBITI ALLAH KA BASHI LAFIYA AMIN YA ALLAH* *_Bismillahir Rahmanin Rahim_* 51~55 Ga baki d'aya gurin duk sukayi mutuwar tsaye sai kallon_kallo a keyi Husnah kuwa tuni ka kame guri d'aya idon ta a rufe . Su Shaheed kuwa juyowar da zasuyi cike da mamaki sai ganin Alhajin su sukayi da su Hajiyar su dasu Anisah tare da jami'an tsaro harda Yayan su a ciki. Husnah na jiyowa idon ta ya sauka akan wani mutum kwance cikin jini ga Bindigar sa ta fad'i a 'kasa, ashe cikin duhu ya boye ya saita kan Husain zai halbe shi, wannan CID suka gansa suka halbe sa. Zubaidah kuwa ita a tunanin ta, Husnah ce, aka halbe, shine ta shiga cikin wani mugun shorct dan ita tunanin ta yanda zata sanar da yallabai. Husnah kuwa tana kallon su Shaheed da Husain taga babu abunda ya same su, kawai tabar gurin da gudun ta ta shige cikin gidan ta fad'a cikin d'akin ta, ta rufe, zaman dir shan tayi zaman yan bori, tana zubar da wasu uban hawaye masu a zabar zafin gaake. Ita kuwa Zubaidah ita da jama'ar ta suna ganin Husnah ta shige cikin gidan da gudu suma suka mara mata, baya. Jami'an tsaron kuwa kama wannan mutanen sukayi Suka anshi Bindigar dake hannun Husain suka bar gidan dasu, Hajiyar kuwa fad'ar takeyi, "ina fatan duk kuna lafiya, babu abun da ya same ku ko?. Duk suka rungume iyayen nasu, Shaheed ne kawai yake magana amman banda Husain. Alhajin kuwa cewa yakeyi, "Husain ka ri'ka aiki da hankalin ka, fiye da aiki da izgilanci, Husain dan Allah idan kasan fushin zuciya baya barin ka, aiki da ilimin da Allah ya baka to ka daina yin kutse a cikin lamarin da bai shafeka ba". Shiru Husain yayi Amman zuciyar sa jin ta takeyi kamar ta fashe saboda tsabar shiga cikin 'bacin rai. Hajiyar kuwa dafa ka fad'ar Husain tayi, ta ce, "Husain kada ka sake kwatan ta abun da ka aikata, badan komai ba, sai dan gudun dana sa ni amman kabi komai a sannu kaji yaro na? ". Jin jina mata kai yayi, haka suma suka jiyo zasu bar gidan Anisah ce, ta kula da wayar Husnah da sauri ta d'auki wayar tabi bayan su, da ita. Husain yanda taga rana haka taga dare sam bata runtsa ba, kuka kawai takeyi kanta wani irin mugun ciwo yakeyi mata kamar ya rabe biyu, idon ta kuwa duk sun kumba saboda kuka. Zubaidah kuwa yalla'bai ya kira ta yayi mata zagin kas, kanci kuma yace, idan ta bari aka batar masa da yaran sa, kuma ta yarda wani abun ya sami Husnah sai ya kashe ta, ita da duk wani wanda take tare dashi. Jin irin wannan furucin na yalla'bai ne ya 'kara fir gita Zubaidah dan tabbas tasan duk abunda ya fad'a zai iya aikata shi akan su ita da 'kawayen ta. Dukan su a zaune suka kwana, kuma yace Aure ba bu fashi a tsanin su. Husnah kuwa tana nan zaune idan kayi mata kallo d'aya ba zaka ce eh lallai Husnar nan bace, yar gayu, d'in nan ba, sai ka dad'e kana kallon ta. Ganin har 'karfe goma da rabi yan biki nata Shirin biki babu Amaryar babu labarin tane, yasaka mutane matsawa Zubaidah akan ta dibo Husnah indai bata samu wata matsalar ba, ko ta gudu, ba. Zubaidah jiki ba bu karfi ta matsa 'kofar Husnah ta ri'ka dokawa, Husnah na jin dukan 'kofar tasan ba kowa bace face Zubaidah, kawai Husnah ta share ta, har ta gaji da dukan 'kofar ta soma kiran, "Daughter na ki bud'e 'kofar nan fa ina son ganin farin cikin ki ne a wannan ranar da a ke da d'aurin Auren ki fa gashi ina ganin har yan zun ba ki ci abinci ba" Share ta Husnah tayi har ta gaji dan kan ta, ta bar gurin, sai kuma hankalin ta ya 'kara tashi dan tana tsoron abun da zai je ya dawo, makulli ta nemo, cikin zafin nama ta bud'e 'kofar, turus tayi ganin yan da Husnah ta dawo kamar wata ba'kuwa a gurin ta, 'karasa wa tayi gurin Husnah ta dur'kusa a kusa da ita. Ta ce, "haba Husy baby miye matsalar da har kika zauna ki ke wahalar da kanki a kan abun da ba wani abu ba". Ko kallon ta Husnah batayi ba, ballema tasa ran Husnar zata amsa mata ne. Zubaidah ta ce, "Ki tashi kiyo wanka kici abinci a zo ayi maki makeup, kin ga yau ke Amaryar ce, kuma Amarya da farin ciki aka san ta, kuma ba bu wanda ya kai ta farin ciki ". Ganin Husnah ta yi kamar ba bu ita a gurin ne, ya saka ta tambayar,Husnah ta ce, "Husnah ina wayar ki ne , naji yalla'bai ya ce, tun jiya ya turo maki kud'in hidimar biki kuma nasan kud'in da yawa, suke dan nasan baya maki 'karamar kyauta". Jin Zubaidah ta cika ta da surutu ne, yasaka Husnah tashi a gurin ta haye saman gado sai tayi kwanciyar ta, zuwa can Zubaidah ta tashi zata fita, Husnah ta ce, "a jiya nasan mommy kina cikin farin cikin ganin za'a kashe maki ni ki futa, to yau kuma farin cikin barin gidan kine kike yi da zanyi, ko miye ? dan ni ban fahimci komai ba har yan zun! " Da bur cewa Zubaidah tayi ta kama soshe_soshen rashin gaskiya, ta ce, "wato Husnah ni ba wai ina son kiyi nesa dani bane, a'a kawai dai ina son naga na aurad dake lafiya hankalin ki ya kwanta, kici naira ki taka naira ki wukanta na wulakan tawa". Husnah kuwa shiru kawai tayi mata, har ta fita cikin sauri. Husain kuwa kwance yake cikin d'akin sa, sai tsaki yake zubawa shi d'aya, zuwa can ya fita ya bar cikin d'akin sai d'akin Shaheed, shima Shaheed kwance, yake da alama tunani yake yi. Bai ma san da zuwan Husain ba, har sai da Husain ya ce, "Shaheed kai ma waccan ban zar yarinyar ta saka ka a damuwa ko? Yan zun ka fahimci cewar mutum ba abun yar da bane ko? Yan zun ka gane cewar ita d'in babbar karuwa ce ko!?. Wani irin kallo Shaheed yake bin sa dashi har sai da yaga ya tsaya Shaheed ya tashi tsaye ya rungume hannuwan sa, ya ce, "kai shine damuwar ka, kuma na fara fahimtar wani abun, wato kai dai kawai kace, karuwan cin ta, shine damuwar ka!?. Husain ya ce, "eh ni kam na tsani wannan ka ruwar wallahi kuma idan na sake had'uwa da ita sai na kashe ta, kowa ma ya futa". Jin_ jina kai Shaheed ya yi, kawai ya ce, "yan zun miye abun yi? Husain ya ce, "abun yi kawai kada mubari a d'aura wannan Auren domin ba'a Aure ba'ayi istimna'i ba, dan za suyi Auren ne, cikin zunubi". Shaheed wata irin dariya ce, ta zo masa, amman sai ya danne ta, amman duk da hakan sai da ya mur musa, ya ce, "a a mubar ta kawai tayi Auren ta yafi, wata kila ma ta shiryu, kaga sai ta rage wani lafin ko? ". cikin fushi Husain ya ce, "inji uban waye ya ce mu bari a d'aura mata Aure wallahi ba bu uban da zai Aure ta ko shi uban waye a garin nan kai bama a garin nan ba duk 'kasar nan, yarinyar da ko tausayin mutane bata ji! " Shaheed saboda dariya harda tarin karya wai dan kar Husain ya gane sa, amman a gaskiya ko shi baya goyon bayan Husnah tayi wani Aure dan ya fahimci yarinyar tana neman taimako dan akwai ayar tambaya a kai. Shaheed ya ce, "mu nemi wata mafita mana", haka suka zazzauna Shaheed sai dariya yake 'boyewa, . Anisah ce ta shigo cikin d'akin da gudu kamar wadda aka biyo tace, "Yaya Yusuf na kiran ka kazo ka gani wayar Husnah wallahi an zubo mata kud'i kuma, harda wayar da aka kira ta, munji cewar Auren dole ne za'ayi mat... ". Ganin yanda Husain yake kallon tane ya saka ta kasa 'karasa maganar, tsawa ya daka mata yace, "ke dan ubanki baki da hankali ne, uban waye ya ce ki d'auko mata waya, ke nama tuno, ta ya ya a kayi ma kuka gano gidan da muke? nasan ke ce ki ke da alhakin hakan dan haka muna saura renki kuma idan kika yi muna 'karya mu karya ki a gurin nan! " Yaya Yusuf ne ya biyo bayan ta, ganin bata dawo da wuri ba, shiru yayi shima yana sauraren ta. Anisah ta ce, "zan fad'a maku amman Husnah saura minti sha biyar a d'aura Auren ta! ". Ganin yanayin da take ciki kuma sun ji saura minti sha biyar, ai Husain ne a gaba gurin barin d'akin duk da suna cikin mamakin sa haka suka fita suna fita har ya tayar da motar, su Alhajin kuwa suma sun shiga cikin tasu motar dan duk abunda akeyi a kan kunnen su, mota biyu suka fita da ita. Husnah kuwa har 'karfe biyu dai_dai bata ci wani abun ba, Zubaidah tayi _tayi har ta gaji ta barta tace Aure babu fashi dan biyu da rabi ne za'a d'aura Auren. Biyu da kwata nayi Husnah ta tashi tayo wanka ta d'auko kayan ta na masu kyau da tsada ta saka ta fito sai 'kamshi take zubawa gashi taci uban takalmi masu tsayi, sai takun 'kasaita takeyi, a cikin babban falon gidan ta bayyana, ai kuwa duk koma ya tashi tsaye sake da baki harda su Zubaidah. Wani irin farin ciki ne ya mamaye zuciyar Zubaidah, Husnah kuwa dariyar gefen baki takeyi masu....... *Comment and share* *A GIDANTA NA GIRMA* *BY NANA: KHADEEJATU* *_UMMU IHSAN_* *SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU SOSAI SON FISABILILLAH* *YA ALLAH KAJIKAN MAHAIFINA KAYI MASA RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SA SHIDA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.* *YA ALLAH KA BAIWA MAMANA LAFIYA KA BAIWA DUK KANNIN WANDA BAIDA LAFIYA NA GIDA DANA ASIBITI ALLAH KA BASHI LAFIYA AMIN YA ALLAH* *_Bismillahir Rahmanin Rahim_* 56~60 Tana zuwa ta zauna a kusa da kujerar Zubaidah, ta sakar mata murmushi. Daskare wa Zubaidah tayi, tana cike da mamakin wan nan ba haguwar "yar ta_ta, ai kuwa kid'a aka sauya a take Zubaidah ta tashi ita da yan tawa gar ta suna rawa da gud'a, wasu na li'ka masu kad'in kari, Husnah kuwa da ido take bin su d'aya bayan d'aya, tana yi tana duba a godon jikin bango biyu da rabi dai_dai kawai Husnah ta tashi ta badalar dasu ta fito tabi ta bayan gidan su ta faki idon mutane, kawai ta durkusa, a jikin flower, ya dauki wata, karamar, trolley din ta, kawai tabi ta bayan motar ta, tabar gidan, da gudun ta, tana isowa bakin titi, motar su Husain na zuwa saura kad'an su taka ta, Allah ne ya kyauta. Husain da sauri ya taka burki, kamar wata guguwa haka ya fito, ya saka hannun sa, kawai ya jata, keeee... Kamar wata wadda yake gudu ta bata, duk su Hajiya da Alhajin fitowa sukayi daga cikin motar su, suka saki baki suna kallon Ikon Allah. Shaheed kuwa da gudu ya fito ya d'auke trolley d'in Husnah suka shiga suka tayar da motaci, suka bar unguwar. Husnah kuwa bata san ma su waye suka d'auke ta ba sai da suka iso gidan san nan hankalin ta ya dawo jikin ta, ta fara zaro ido kamar wadda tayi 'karya. Kallon Yaya Yusuf ta soma yi, ta dawo gurin Shaheed, har zatayi magana, ke nan Husain ya ce, "dallah karuwar banza rufe, muna biki, kin fito yawon karuwan cin naki shine zaki zo kiyi wa mutane iya yin banza da yofi! ". Husnah na ganin Husain ta ce, " karuwan ci mai dama ke yin sa, ni wallahi dama nasan kai ne da ban shiga ba'kar motar ka ba, ballema kazo, ka fad'a mani magana akan wannan kucakar motar taka". Baki ta mur gud'a masa, Husain cikin fushi ya juyo zai mareta, Yaya Yusuf da Shaheed suka tare sa, ita kuwa sake da baki take kallon sa, kwan_kwasa 'kofar motar akayi Shaheed ya bud'e daman 'kofar da Husnah take zaune ne, fita daga cikin motar tayi, tana had'a ido dasu Alhaji da Hajiyar sai ta du'kar da idon ta 'kasa ta kasa ko da dogon motsi, kafeta da ido sukayi, ganin yanda jikin ta, ya soma rawa ne, Hajiyar ta sauke ajiyar zuciya ta kamo, hannun Husnah suka tafi, Alhajin na biye dasu, har cikin falon suka zaunar da ita akan kujera, suma suka zazzauna. Suhailah ce, ta kawo wa Husnah ruwa mai sanyi a cofi, su Husain ma shigowa sukayi duk suka zazzauna, ruwan Husnah tasha ta fara sauke ajiyar zuciya gurin yayi tsit kamar babu kowa sai fankar dake aiki. Alhajin ne ya yi gyaran murya ya ce, "ada naso mubi komai a sannu a hankali amman na rasa mi yasa kwatsam wasu abubuwa suke faru, shin Husnah mike faruwa ne, kuma da kika gudo, ina zaki tafi ne?. Shiru Husnah tayi sai kawai ta saki kuka kamar ranta zai fi, shiru sukayi suna kallon ta, Husain ya ce, inafa zata tafi bayan sana'ar ta, ta karuwan ci! ". Cikin fushi, Daddy yace, "Husain!! " tare da daka masa tsawa, "kayi wa mutane shiru waye ya ce maka wasa muka zauna yi a gurin nan?. Shiru Husain yayi bai sake magana ba, Hajiyar tace, mubar ta har ta dawo cikin hayyacin ta, muyi magana da ita, cikin kwanciyar hankali ". Alhajin ya ce, "ok babu komai Anisah ku shiga da ita cikin d'akin ku, kuma ku barta sai ta futa, kada wanda ya dameta, oya tashi Husnah ku tafi ". Ri'ka hannun Husnah sukayi suka bar gurin da ita, bayan su Husnah sun bar gurin ne, Alhaji yace, "Husain ya kama ta ka iya bakin ka, ka daina ai banta yarinyar nan, kasan irin yanda nake son ta, dan haka na gar_gad'e ka akan ta kaji ko? ". Gyada kai Husain yayi ya tashi yabar gurin. Yaya Yusuf ya ce, "dan Allah Daddy nikam ina jin kamar Husnah jini nace, bana kaunar na ganta cikin damuwa, wallahi idan naga yanda take zubar da hawaye sai naga kamar zan tuno wani abun, amman kuma na rasa miye?". Daddy ya ce, "Yusuf kada ka damu muci gaba, da biyar komai a sannu Insha Allah komai zai dai_dai ta, sai dai nikam a tsanin Husain da Husnah na rasa miye Allah shine mafi sani, amman ni bana son ganin suna samun sa'bani" Hajiya ta ce, "ni wallahi idan na kalle su har wani abun yake dar suwa a raina amman ina tunda ina ganin yan zun da Auren wani a kan ta ". Shaheed ya ce, "Insha Allah babu Auren kowa a kan ta amman mubi komai a sannu ". Haka dai su Alhajin sukayi ta tattaunawa akai. Husnah kuwa bata dai na kuka ba, sai taga su Anisah duk sun fara taya ta kukan kawai sai ta bar nata kukan, ta dawo tana kallon su". Wayar ta ce tayi ringing sai kawai Husnah ta shiga cikin mamakin ya ya akayi wayar ta, tazo nan gidan, dariya Anisah tayi tace, "wayar ki tun jiya take hannu na, amman na rasa taya zan maida maki wayar ki a gurin ki ba, shi yasa na ajiye ta a guri na". 'karfe ukku da rabi nayi, Husnah ta anshi wayar ta, ta soma dan na wayar tana shafar wayar, suna labarin su, suna saka Husnah dariya, dan burin su Suhailah su saka Husnah cikin farin cikin. A can gidan su Zubaidah kuwa, suna ta chashe war su, ba bu ji ba bu gani, wasu dai sun ga fitar Husnah amman basu kawo komai a ran su ba, har sai da aka kira wayar Zubaidah, tana fita cikin mutane ta d'aga wayar tace, "hello yallabai an d'aura Auren kuwa? ". Daga can d'aya ban garen, yalla'bai d'in yace, "a a an kusa dai akwai wan da muke jira, manyan ba'kin mu, ina fatan dai Amaryar tawa, tana kusa, dan yau ina son jin muryar ta, ki bani ita muyi magana naji wannan zazza 'kar muryar ta ta, kamar yanda nasaba jin ta idan kuna waya da ita, yau nima nad'an d'ana mana kafin tazo gida na, ta zama ni d'aya zan ri'ka jin muryar ta". Dariya Zubaidah tayi ta ce, "to ranka ya dad'e bari na kira maka ita, na bata wayar ". Da wayar a hannun ta ta nufi cikin gidan bata ga Husnah gurin da ta bat taba, ta nufi d'akin Husnah nan ma babu labarin Husnah, haka tayi ta zaga gidan kamar da wasa abu ya zama gaske gidan kowa ya shiga cikin tashin hankalin neman Husnah wasu suce, sun ga fitar ta, wasu kuma suce basu ga kowa ba, ai kuwa gidan biki ya zama jaje da neman inda Husnah ta shiga. Shi kuwa yalla'bai d'in ya ce, "wallahi sai an nemo ta kuma wallahi kar wadda ta yarda tabar gidan namiji ne ko mace". Zubaidah ku ka kawai takeyi kukan gaskiya takeyi bana wasa ba, test message ne ya shigo a cikin wayar ta, ai kuwa cikin rawar jiki ta duba kawai ta tashi tsaye ta kurma uban ihu ta fad'i 'kasa babu rai a tattare da ita. To mike nan Zubaidah ko ta mutu ko tana raye! Shin wane sa'kon ne ya firgita Zubaidah har haka? Kudai ci gaba da bin Ummu IHSAN dan wal_wale maku wannan 'kullin *Comment and share* *Ummu Ihsan ce*๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน 8/25/21, 7:20 PM - Ummu Ihsan ce ๐ŸŒนโœ๐Ÿ?: ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ *ยฐโ€ขยฐA GIDANTA NA GIRMAยฐโ€ขย?* ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ *BY NANA: KHADEEJATU* *_UMMU IHSAN_* *SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU SOSAI SON FISABILILLAH* *YA ALLAH KAJIKAN MAHAIFINA KAYI MASA RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SA SHIDA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.* *YA ALLAH KA BAIWA MAMANA LAFIYA KA BAIWA DUK KANNIN WANDA BAIDA LAFIYA NA GIDA DANA ASIBITI ALLAH KA BASHI LAFIYA AMIN YA ALLAH* *Hahhhh wayyo ciki na wallahi duk kun bani dariya masoya, ita mommy Zubaidah kukeyi wannan mugun fatan? .* *Kai Djamila idan nice na turowa mommy Zubaidah sa'ko ai sai na sanar da ita inda kuka 'boye mata "ya.* Ina godiya sosai da Comment din ku da sharhin ku masoya. *Nafsy a gaskiya shar hinki na sakani farin ciki ina godiya sosai* *Kamar irin kowa da kowa duk ina godiya sosai da addu'ar ku* My takwara jin jina da ban girma a gareki* *A GIDANTA NA GIRMA* *_Bismillahir Rahmanin Rahim_* 61~65 Duk kan nin mutanen dake gurin sai sukayo a kan Zubaidah suna fad'ar, "Zuby! Zuby!! Zuby!! " suna gir giza ta amman inaa ko motsi Zubaidah batayi ba. Wani guy ne ya yi dabarar d'ebo ruwa ya yayyafa mata a take ta saki ajiyar zuciya, da 'karfi, ta kurma uban ihu, ta tashi tsaye tana dube_dube, ta ce, "na shiga ukku ni Zubaidah Husnah ta gudu ya ya zanyi da rayuwa ta ne? Gashi Husnah harda su turo mani sa'ko wai ita tabar ni, ni a daura Auren dani! " Yaya zanyi da rayuwa ne ni Zubaidah Husnah ta tona mani asiri a idon duniya, Husnah yan zun ne na kejin takai cin rashin hankalin da nayi, na yarda da fitowar ki, bayan nasan nayi, nayi ki tashi kiyi hakuri ki shirya tun waye war gari, amman kika 'ki yarda, sai yanzun ne, daga baya kika nuna mani kin fini iya bariki nida na haifeki da ciki na, amman kizo ki fini, kwarewa a gurin bariki, na d'auki alwashin duk inda kika shiga sai na gano ki! "Zubaidah" ke nan take magana a cikin fushi da nuna 'bacin rai, su kuwa mutanen dake gurin, duk sunyi zuru_zuru suna kallon ta, wayar tace, ta d'auki 'kara, bata ko duba mai kiran ba, ta d'auka ta saka hans free, kawai sukaji, muryar yallabai yana fad'ar, "Zuby kin raina mani da wayau dake da "yar ki da 'kawayen na baki to, kusani, dukan ku wanda yake cikin gidan da yar ki, da ke kanki, zanyi maganin ku, kuma ku saurari sharri na d'aya bayan d'aya kuma duk wani abu nawa wanda ki ku san cewar nawa ne, ni na baku ku dawo mani dashi, daga nan zuwa gobe, kuma kad'in da na turawa Husnah ko naira, ban yarda ba, ace ta 'bata, kuma kusani ba iya nan na tsaya ba, sai kunyi nadamar sa ni na a rayuwar ku, kuma na koreku aiki ga baki d'aya ". Tunda suka fara sauraren wayar, har aka gama wasu na kuka hawaye sha re_sha re a idon su, wasu kuma hannun su, suka d'aura a kai, dan kowa yasan waye yake magana kuma sun san zai aikata duk abunda ta fad'a, ba bu fashi. Tsine wa Husnah kawai sukeyi tare da Zubaidah tunda kowa sakacin Zubaidah yake gani, kowa ya manta da nasa laifin. Husnah kuwa hankalin ta, kwance, yake, har tama manta, da cewar ta baro fitina a gidan su. Tun lokacin da Husnah tazo gidan har dare bata fito cikin falon gidan ba, haka Husain, duk abun da Husnah take bu'katar sa, a take ake kawo mata shi, Husnah ta zama kamar wata yar gidan. Hankalin Husnah a kwance ta shari baccin ta, tun 'karfe tara na dare take bacci sai 'karfe goma na safe ta falka, su Anisah mamakin irin wannan baccin na Husnah sukeyi, amman ita hankali kwance take yin abin ta. Husnah na falkawa, ta shiga toilet, tun suna hakurin jiran ta, har sai da Suhailat, ta nufi bikin 'kafar bayin ta soma, kiran, "wallahi ki fito haka nan dubi mutum kamar wadda bacci ya d'auka a ciki" Husnah dake cikin bayin ta ce, "ke malama, son kikeyi na fito a ji jikina, na tsamin d'aud'a, haka kawai, kawai dai ki barni, idan na gama son rai na, sai na fito, zaki saka, ni na fito ban wanke wani gurin ba, ko na fito, wani gurin bai ma san anyi wasar ruwa ba". Ai kuwa ga baki d'aya suka, had'a baki gurin fad'ar, "Allahu akbar jaa muje muslima". Ai kuwa sai ganin Husnah sukayi ta fito d'aure da towel a jikin ta, sai dariya takeyi, kamar wata hauka sabon kamu harda hawayen ta, dan dariya. Kallon ta, kawai suka tsaya suna yi, Anisah ta kasa hakuri ta ce, "Anty Husnah lafiyar ki kuwa wan nan dariyar haka? " Husnah ta ce, "ku dan jira na gama shirya wa, zan baku amsa d'aya bayan d'aya". mai da hankalin su sukayi gurin Husnah suna kallon yanda take shirya wa komai cikin tsari kuma hankali kwance, trolley d'in ta, ta d'auko ta bud'e ta, mugun mamaki sukeyi ganin yanda duk kayan Husnah suke 'kananan kaya, babu atamfa ko d'aya a cikin kayan, ita kuwa hankalin ta a kwance ta saka riga da wando, rigar pink da kwalliyar yellow, sai wando, jeans blue, ta gyara gashin kanta, ta saka ribom pink da yellow, mai kawai ta shafa, da yar powder ta, sai turare kusan biyar sannan taje ta d'auki hijab ta saka, ta d'auki sallaya, ta shimfida ta, tayar da sallar Asubah. Duk suka rungume hannun su, suna kallon Husnah har ta kammala, bayan ta idar ta dad'e a zaune kafin ta, tashi, tayo gurin su, cikin murmushi Husnah ta ce, dasu, "antashi lafiya ya gidan? ". A tare suka amsa mata da, "Lafiya lau Alhamdulillah dafatan kin tashi lafiya ". Dariya kawai Husnah tayi bata amsa masu ba, suna dai ta bin Husnah da, ido ganin irin yanda kayan suka kama mata jiki, suna cikin kallon Husnah, kawai Husnah ta ce, dasu, "to muje kuci abinci ko? Dan nikam sai 'karfe sha biyu nake karyawa". Duk suka zaro mata ido, suna fad'ar "wane irin sha biyu? Mukam tun 'karfe tara munci abinci, ki dai chanza shawara, kije kici abinci kuma ku gaisa dasu Ummey". Husnah tace, muje kawai mu gaisa amman abinci ba yanzun ba". Haka suka kama hanya, amman su kunyar shigar da Husnah tayi sukeyi, amman kuma, abun mamaki Husnah harda takalmin ta, masu uban tsini ta saka, kuma hankalin ta, kwance take tafiyar ta. A falo suka sami su Hajiyar Husnah Kawai ta 'karasa gurin Hajiyar ta rungume ta, cikin so da kauna, Husnah tace, "ina kaunar ki Ummey, barka da safiya da fatan kin tashi lafiya ? ". ajiyar zuciya Hajiyar tayi, cikin tausayin Husnah wadda tun fitowar su, Hajiyar ta kafe su da ido, ita ma ta rungume ta, ta ce, "lafiya lau Alhamdulillah Husnah da fatan kin tashi lafiya, ya ba'kun ta, ya kika kwana ina fatan dai su Anisah basu takura maki ba? ". Dariya Husnah tayi ta ce, " a a ba suyi mani komai ba, sai tattalina, dai_dai da shigowar su Husain da Shaheed da Yaya Yusuf da Baby, ai kuwa Babyn tayo kan Husnah da gudun ta, ta rungume Husnah, itama Husnah cikin jin dad'in ganin Babyn kawai ta saki Ummey ta rungume Babyn suka sanya dariya, su Shaheed sakin baki sukayi suna kallon Ikon Allah. Husain kuwa cikin zafin zuciya ya ce, "kee! Uban waye ya baki damar da zaki ri'ka yiwa mutane wannan muguwar shigar, ta karuwai, ko an fad'a maki nan ma gidan karuwan ne!?. Ba Husnah ba, hatta Ummy da duk wani wanda yake gurin yaji ciwon wannan maganar da Husain yayi wa, Husnah wadda suka fahimci cewar ita bata da laifi, saboda abun da ta taso ta ga an koyar dai ta , to shine itama take amfani dashi, amman sun d'auki alkawarin taimakon ta, su maida ita tamkar yar gidan kowa. Ko kallon inda yake Husnah batayi ba, kawai taci gaba da, fad'ar "Baby nayi kewar ki, tun da nazo gidan nan ban gane ki ba, kawai dai yau ki kasan ce tare dani muyi firar mu ko? ". Yarinyar dakewa tayi dan tsawar da Husain ya doka wa Husnah, duk sun fir gita da ita. Husnah kuwa lura da kallon da Husain ke jifan ta da shine ya saka ta fad'ar, "nikam na tsani yawan shiga cikin mutane masu yawan surutu kawai aje a fasawa mutum dodon kunne a kaisa a baro, shi mutum idan yasan iska ya kad'a to mi zai saka shi shiga gurin mutane masu natsuwa? , ke Baby zo mubar gurin nan muje cikin d'akin can muyi firar mu". Tashi Husnah tayi, ta ja hannun Babyn suka bar gurin, ai kuwa kallon tsana kawai Husain ke jifan ta dashi gashi ta sakar masa magana Ummey ta galla masa harara, ta hana shi ya d'auki wani mataki, duk sai yaji ya 'kara tsanar Husnah. Yaya Yusuf ya ce, "dan Allah Husain kada ka hawa kanka raini a gurin yarinyar nan, kana jifa sai da ta rama abun da kayi mata ". Share sa Husain yayi sai cika yake yana batsewa, Shaheed ya ce, "Hajiya Auren nan fa ya fasu ba'ayi sa ba, acewar wani aboki na, amman kuma ita mahaifiyar Husnah tana kwance bata da lafiya dan yau tun safe aka kaita asibiti, hawan jinin ta ya taso, yan zun yaya ya kama ta ayi ne? " Ummey ta ce, "Ajiye wannan maganar Shaheed bari har Daddyn ku ya dawo, nasan zaiyi magana akai cikin hanciyar hankali, kai kuma Husain nadawo kanka, ka kiyaye ni fa! , kai wai ma, tun da ka gama ginin gidan ka, ka saka komai, tun shekaru biyu da suka wuce, to yaushe ne zaka kawo mani, matar da zaka Aura dan son nakeyi naga naka jikokin ga Shaheed nan cikin satin nan zamuje mu kai kud'in hidimar bikin sa, amman kai 'katon banza, kana nan kana ta kurawa 'kannen ka, to kasani, daga yanzun zan matsawa mahaifin ka, ayi gaggawar matsa maka ka fito da matar Aure haka nan! ". Zufa ce, take zubo wa Husain ta ko'ina, amman sai gun_guni yakeyi, zuwa can ya ce, "Ummey nifa har yanzun ban samu budurwa ba, duk yan matan yan zun basu da hankali ". Dariya kawai suka sanya masa, Hajiyar kuwa tace, "zakayi bayani ne Husain kwanan nan". Haka dai su yini Husnah sai 'karfe goma sha biyu tasha shayi da biredi tace shine kawai take ra'ayin ci. Daddy na dawo wa Hajiyar ta sanar dashi halin da ake ciki, a take ya kira Husnah yace, ta shirya yau zasu je gidan su. Zufa ce Husnah take zubo mata, sai yan zun ne ta tuno da Auren da aka shirya yi mata, to miyasa Daddy yace sai sunje gidan su cikin tsakiyar rana, ita kam taga ta kanta. Babu yan da Husnah ta iya haka ta shirya suka nufi gidan batare da tasan dalilin zuwan nasu ba. Suna shiga cikin gidan zuciyar Husnah kamar ta fashe saboda far gaba, suna yin parking suka fito dukan su, Husnah kuwa cikin sanyin jiki take takawa, har suka shiga cikin falon gidan suna rafka, sallama amman basu ji a anmsa masu ba, Husnah dai tana baya ita d'aya kuma tasan daman babu wanda zai iya amsawa, acikin tawagar Mommy, sannan kuma ai taga ba'kin motoci harda wanda ta sani, da wanda bata sani ba. Zazzaune suka sami mutane maza da mata dukan su babu mai shigar mutumci, a cikin su, Husain jin yakeyi kamar ya kashe su, saboda tsabar takaicin da yakeji nasu. Zubaidah ce kwance sai fifita akeyi mata, Husnah na d'aga idon ta, kawai ta hango Zubaidah a kwance duk ta rame tayi ba'ki kamar ba Mommy yar gayun nan ba. Da gudu Husnah tayi kanta tana kiran "mommy! Mommy!! Miya sameki ne, na shiga ukku na ni Husnah mike shirin faruwa dani ne Mommy please kada kiyi Mano haka, bani son ki mutu kibar ni, please mommy kiyi hakuri na tuba, nadawo gareki! ". Kawai Husnah ta fashe da kuka sai tattaba jikin Zubaidah takeyi da yayi mugun zafi, bud'e ido Zubaidah tayi a hankali idon ta ya sauka akan Husnah da take ta zubar da hawaye duk ta rud'e. Tashi zaune Zubaidah tayi da ket, ta ce, "Husnah kin bani mamaki Husnah yan zun nice zaki tonawa asiri, kin san kuwa irin halin da na shiga Husnah akan rashin ki a kusa dani!?, Husnah nayi zaton kamar yanda kika furta cewar kina son farin ciki na, fiye da naki, bazaki 'ki abun da nake so ba, kin fi kowa sanin bana bu'katar na ganki a cikin damuwa ballema a ce yau nice zan zabawa 'yata mugun miji, Husnah kiyi tu nani idan har kika fasa Auren nan yaya zanyi da kayan mutane ne Husnah!?. Su Daddy da Hajiya dasu Shaheed mamakin irin halin mahaifiyar Husnah sukeyi, wato ita ba ciwon rashin ganin Husnah takeyi ba, aa ciwon rashin samun biyan bu'katar ta, takeyi, amman Allah tir da iyaye masu irin wannan hali, haka suke ta sa'kawa, a ran su. Zubaidah ta ce, "Husnah hawan jini gare ni, zuciya ta, ta kumbura, dubi tarin yawan maganin da aka bani, bayan allurai, wanda ban san ada din su ba" maganin ta nunawa Husnah. Husnah ta ce, "mommy kiyi hakuri banza 'kara yin nesa dake ba, amman kuma ki sa ni bazan ta'ba Auren kowa ba, ke bama wannan mutanen ba, kowa bana bu'katar Aura a halin da ake ciki, sannan kuma ki sa ni, zan iya kula da lafiyar ki, fiye da tawa lafiyar amman kuma wannan bu'katar taki bata da ma sau'ki ko gurbi a zuciya ta" Wata uwar zabura Zubaidah tayi ta tashi tsaye cikin masifa har dasu rufe ido, jikin ta, sai rawa yakeyi, ta ce, "Husnah!!" Da 'karfin gaske wanda sai da Husnah ta zubura ta tashi tsaye cikin rawar jiki da kad'uwa. Zubaidah taci gaba da fad'ar, "Husnah ni zaki zubawa 'kasa a ido to wallahi baki isa ba, sai dai idan yau aka d'aura maki Aure da wannan yalla'bain ki fad'i 'kasa ki mutu, kuma Auren ku kamar anyi sa an gama ne". Cikin fushi da nu na rashin tsoro Husnah ta ce, "to Mommy kamar yanda kika damu akan cewar sai kin Aura masa ni to ke mi zai hanaki ki Aure san, mana, ko wani ya hana ki!?. Ba Zubaidah hatta Ummey da Daddy dasu Yaya Yusuf da Shaheed dasu Husain dasu, da mutanen dake gurin baki d'aya, sai da suka zaro ido suna kallon ta, cike da mamaki, Anisah harda murza ido. Zubaidah kuwa, murza idon ta takeyi tana fad'ar, "Husnah? Kin san abun da kike fad'a kuwa, anya ma kanki d'aya kuwa, kodai kin samu tabuwar hankali ne!. Cike da kaduwa Zubaidah ke maganar. Husnah kuwa ido tsakiyar kai tace, "kwarai kuwa Mommy ina cikin hayyaci na, akan miye zaki takurawa rayuwa ta, bayan kema ba Auren nan kikayi ba, ni kuma kice, dole sai kin yi mani Auren dole, akan miye akan wace hujjar!?. Saukar wani wawan mari taji a kuncin ta wanda sai da jin ta suka d'auke duka, sai da tayi kusan sakwan talatin sannan jin ta ya dawo, hankalin ta ya dawo jikin ta, ta d'aga ido kawai, idon ta ya sauka akan Husain wanda yake ta huci kamar wani kumurcin zaki. Yaya Yusuf ya ce, "nagode Husain kayi mani dai_dai ai nine nayi niyar ai kata hakan ka rigani, Husnah danan baki da kunya har hakan, dan baki da mutumci, mahaifiyar taki, kike fad'a wa irin wannan maganar!?. Daddy cikin matsanan cin fushi ya ce, "Husnah ta ba haka take ba, Husnah ta bata yiwa kowa rashin kunya ballema ace tayiwa mahaifiyar ta, dan haka kuzo mu juya, idan na samu Husnah ta, zuwa gaba, zan tarbi abuta, amman nikam wannan ba tawa bace, ku tafi muje". Dukan su juyawa sukayi, da gudu Husnah tabi bayan su tana fad'ar, Daddy dan Allah kada ku tafi ku barni, kada kuyi fushi dani, akan abun da baku sani, ba, amman ina sun sa kai kawai bar cikin falon gidan. Dariya mutanen gurin suka sanya harda tafawa, Zubaidah kuwa rawa ta fara takawa, Husnah kallon su kawai takeyi cike da mamaki ga fuskar ta, kumbura, saboda ta maru iya mari, har shatin yatsun Husain sai da ya fito, a fuskar ta,. Dariya Zubaidah tayi ta ce, "yaro_yaro ne Husnah ke a da a tunanin ki, kina nufin cewar zan saka maki ido ne ina kallon ki, haba Husnah ai ko wa ya riga ka bacci sai ya riga ka tashi, Husnah na lura kina son kiyi wasa da nine amman kuma ki sa ni nice uwar ki baki da wata uwa a duniya bayan ni, kuma Husnah na riga da na gano cewar kin samu wasu mutanen ne shi yasa kike son gudu na, amman Husnah yan zun nayi maki na babba da yaro". Zubaidah ta ci gaba da fad'ar "Husnah baki da wani za'bin sai na Auren yalla'bai kuma babu uban da zai hanaki Auren sa indai ina a duniyar nan, shi yasa nayi maki na yan duniya irin mu, goggagin yan bariki, kinga gashi sun tafi sun barni dake, yan zun baki da gurin zuwa ko? ". Hahhhh suka sanya dariya dukan su. Magana suka jiyo daga can bayan su, Hajiya ta ce, "Husnah daman nasan akwai wata a 'kasa dan ba halin ki bane wukanta babba, amman nayi mamakin haka, dan haka ne ni naji A zuciya ta ban yarda da wannan shirin Mommyn ta ki ba, muka dawo domin yi maki tambaya, Husnah mike faruwa ne". Kukan farin ciki Husnah ta fashe dashi ta ce, "Ummey daman nasan ku da fahim ta nadan bakwa yanke hukunci cikin fushi amman yanzun zakuji komai, amman Daddy sai kace ka yarda dana fad'a zan fad'a". Matsowa Daddy ya yi, ya ri'ko hannun Husnah yace, "ki fad'a 'yata na yarda da ke ". Murmushi Husnah tayi ta ce, "Mommy zan sanar da kowa dake gurin nan abun da bakiyi zaton nasani ba a taki wautar amman". Dariyar yan bariki Zubaidah tayi ta ce, "to fad'a mana waye ya hane ki iya? ". Murmushi Husnah tayi ta ce, "Daddy Ummey Yaya Yusuf da Shaheed Anisah Suhailah da duk wani wanda yake gurin nan, ku saurara da kyau kuji harda ke Mommy ". Duk gurin sukayi shiru suka zuba wa Husnah ido . Husnah tayi murmushi ta ce, " *A GIDANTA NA GIRMA!! * ". Ga baki d'aya gurin suka had'a baki tare da zaro ido wake da doka 'kirji gurin fad'ar, " *A GIDANTA NA GIRMA!!?* *(NIMA DAI NACE A GIDANTA NA GIRMA!!?)* to kufa masoya? *Comment and share* *A GIDANTA NA GIRMA* *BY NANA: KHADEEJATU* *_UMMU IHSAN_* *SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU SOSAI SON FISABILILLAH* *YA ALLAH KAJIKAN MAHAIFINA KAYI MASA RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SA SHIDA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.* *YA ALLAH KA BAIWA MAMANA LAFIYA KA BAIWA DUK KANNIN WANDA BAIDA LAFIYA NA GIDA DANA ASIBITI ALLAH KA BASHI LAFIYA AMIN YA ALLAH* *_Bismillahir Rahmanin Rahim_* 66~70 Husnah tayi murmushi tace, "Tabbas *A GIDANTA NA GIRMA!!* nasan zakuyi mamakin jin wannan maganar saga baki na, kwarai kuwa, mommy nasan zakiyi mamakin a ina naji wannan maganar toba a bakin kowa naji ba, kina gani na kamar 'kuruciya tayi mani na damuna, to abun ba haka yake ba" Mommy ina kiran ki da wannan su nan ne saboda ina son ki sani cewa ni yar halak ce ban ta'ba man tawa da cewar ke ce kika fitar dani daga cikin wahala ba, a lokacin ina cikin shan wahalar kishiyar uwa, dan haka ina son ki sani cewar, Husnah tasan komai tun daga mutuwar mama na, har zuwa wannan ranar, " Wata irin zufa ce, ke kwararo wa Zubaidah sai jikin ta da yake rawa, kamar mazari, abokan Zubaidah kuwa hannuwan su, suke tafawa cike da mamaki da zallar wautar Zubaidah suke gani. Daddy da su Hajiya kuwa cike suke da al'ajabi Husnah ta ci gaba da fad'ar, "tabbas ina yar shekara tara zuwa goma ne, kuka je kuka bada kud'i aka baku ni, kamar yanda naga tsabar rashin gaskiya a tattare da tafiyar da kukayo dani, na sauya motoci da barin taku motar a cikin jeji, da yanda kika baiwa abokiyar ki kud'in da ta taimaka maki kuka d'auko ni, tun daga ranar kika baro garin dani, ban sake ganin ta da ido na ba, kuma kema ko zan cen ta bakya yi" Mommy idan baki man tada wata rana ba, ranar da kika tasa ni a gaba kina bani labarin rayuwar ki, da yanda kike son na zama ba, tun a ranar nake tausayin rayuwa ta da taki rayuwar, Mommy ba zan sanar da kowa abun da kika sanar dani, daga cikin rayuwar kiba, domin yin hakan kamar ba tona wa kaina asiri ne, ko nace na sokawa ciki na wuka ne. Amman idan ke ce kika sanar da wani labarin da kika bani, to bani da damuwa. Mommy Husnar dai ce wadda kika zaba wa dadiro tun tana 'karamar ta, ita ce ta girma ta kori dadiron Mommy kin san waye kuwa?". Ganin Zubaidah na zubar da zufane yasaka Husnah fad'ar, "nasan zaki sha mamaki idan na sanar dake cewar nice, na had'a Tk da iyayen sa harda matar sa, kuma gashi ya shiryu, amman na nuna maki naji zafin abun". Mommy nice dai Husnah taki, na kori Tk a rayuwa ta, kuma kamar yanda kika hanani kula kowa a rayuwa ta, kika zabar mani rayuwar kad'aici to nima na za'bi na kori duk wanda kike son na kasan ce dashi domin duk abunda na aikata kece silah,kin koyar dani rashin ganin darajar kowa da girma ma kowa, da wulakanta kowa, amman ni bana son aikata hakan domin nasan da cewar a kwai ranar da zan nisan ce ki". Mommy ko anan kawai na tsaya na rufe babin da kike gani na ko ince kowa yake gani, na a matsayin yar da kika haifa, to kowa ya shaida Mommy ba ita ce, ta haife ni ba, *A GIDANTA NA GIRMA* kawai " Zubaidah cikin masifa ta ce, "Husnah yan zun duk kina nufin da wayon ki amman kuma baki ta'ba nuna mani ko da wasa ba, cewar kin san komai ba? Husnah daman kece kika kori Tk wanda yake taimakon rayuwar ki, tun kina cikin datti har kika zama mutum, shine ki ka basar,? Shin Husnah daman kin shirya tona mani asiri ne ko miye!?. Dariya Husnah tayi ta ce, "Mommy ke nan duk abunda kika ji na ambata babu 'karya ko d'aya a cikin ". Zubaidah ta ce, "Husnah idan har Tk ya bar maki abunda ya baki, to shi wannan ina yi maki albishir da cewar duk abunda ya kashe maki koda tsinke ne sai kin biya shi abun sa, kuma daga yau babu ni babu ke na koreki daga cikin gidan nan kuma nima badan duk hidimar kiba tun lokacin da nazo dake, Tk yake yinta ba da nace, sai kin biya ni abuna amman ina kin tsira Tk ne gatan ki yariya, kuma ki biya yalla'bai kafin ki bar cikin gidan nan kuma, kada na sake ganin 'kafar ki a gidan nan ". Dariya Husnah tayi ta ce, "mommy ai ni har yan zun ba zan dai na kiran ki da wannan su nan ba, amman ki sani ko kwabo na wannan kazamin mutumen banci ba, ga kud'in sa, bari yan zun zanyi maki transfer na kud'in nasa, Anisah bani wayar ". Anisah cikin kwarin gwiwa Husnah tayi mata transfer na kud'in da Alhajin ya turo mata, matar da wayar take hannun ta ta ce, "miliyan d'aya ta shigo, jama'a ku duba, ansar wayar mutane ke tayi suna gani, cike da mamaki, sannan Husnah ta ce Mommy na gode da ri'kon da kikayi mani bana bu'katar kayan cikin d'akin can naki nabar maki zan d'auki sauran ajiya ta, " Hayewa d'akin Husnah tayi ta d'auko tsofafin kayan ta, tace, "Mommy na barki lafiya yanda nake wa kaina fatan shiriya, kema ina yi maki fatan shiriya". Kawai Husnah tasa kai batayi wa kowa magana ba, tabar falon tayi waje gurin motar ta, ta nufa ta bud'e, zata shiga ciki Anisah ta tabiyo bayan ta, tace, Husnah kina nufin ba gidan mu zaki koma ba, tafiyar ki zakiyi, to ina zaki shiga ne a cikin duniyar nan?. Husnah kuwa ta ce, "Anisah zan shiga duniya ne, kin san duniya fad'i gare ta". Anisah tace, "subhanallah Husnah kina nufin kudurin ki na zaman hotel yana nan kina nufin zakiyi zaman kan ki ne!?. Husnah kuwa shiru kawai tayi, Husain kuwa cikin takaici ya janye Anisah da karfin, ta dawo gefe kawai yazo ya kama hannun Husnah ya murde, ya anshe makullin motar ya rufe, ya yi cikin gidan ya ce da Zubaidah, "ga makullin motar ku nan ku 'kara da ita". Kawai ya fito Husnah sai harar sa take ko kallon inda take baiyi ba kowa ya shiga cikin mota banda Husnah, har sun ta tar da mota Husain ya fito ya je ya janyo hannu Husnah tana tirjewa kawai ya jefa ta, a cikin motar shima ya shiga, Shaheed ya tayar da motar, suna dariya 'kasa_'kasa. gidan su suka dosa Husnah sai hura hanci takeyi tana gun guni, maganar dai bata fito fili ba, ballema aji abun da take fad'a, matsawa tayi can nesa dashi tana kallon window, har suka iso gidan. suna yin parking Husnah tace, "Yaya Yusuf nifa ba zan iya zama a gidan kowa ba, zan nemi sunan garin mu ne na koma, gida zaifi". Dariya suka saka Yaya Yusuf ya ce, "Husnah zo kiji wani labari, daga ni sai ke". Husnah dai kamar kada taje, sai kuma ta fito tayo gurin Yaya Yusuf suka jera suna tafiya, Yaya Yusuf ya ce, "Husnah kada kiyi gan_gan cin tafiya yan zun domin kin san halin Mommy ki baza barki ba, domin ba zatayi maki ri'kon banza ba, sai ta d'auki fansar tona mata asiri da kikayi a gaban idon mutane, kika karyata ta, gashi tayi karya baki san adadin mutanen da tayiwa 'karya ba, a kan ki ba". Ajiyar zuciya Husnah ta sauke ta shiga nazari, zuwa can ta ce, "tabbas nasan halin Mommy da wannan azzaluman mutanen da wannan mugun mutanen zasu d'auki mummunar fansa a kai na, babu inda zani ina gidan nan, amman wallahi kayiwa wan can mugun magana ya daina shiga har yata". Dariyar cin nasara Yaya Yusuf yayi, ya ce, "yauwa kanwata ta kaina". Haka suka shiga cikin falon gidan suka zazzauna Shaheed ya ce, "Husnah dan Allah ki zauna damu ina son ayi biki na tare da ke ". Dariya Husnah tayi ta ce, "na yarda za'ayi bikin ka dani Amman ba zan zauna ayi na ta zuru ba". Husain ya ce, "kam uban can ke wasa nake dake ne? ". Hajiya sunji dad'in yan da Husnah ta saki jikin da su, ta ce, "to kayi Auren mana sai a daina tsokanar ka". Tashi Husain yayi yabar gurin. tun daga wannan lokacin ne Husnah ta zama yar gidan sam Husnah ta dawo kamar ba ita ba, babu mai yi mata kallon da shi bane, kuma sam Husnah ta murje hankalin ta ya kwanta, sallah da karatun sallah da ambaton Allah shine suke koyar da ita, kowa tausayin Husnah yakeji musam man ma da sukaji cewar mahaifiyar ta rasu, kulawa sosai suke bata ". Ankai komai na bikin Shaheed Auren ma sati ukku aka saka, ai kuwa shirin biki kawai akeyi, Husnah sune kirjin biki, Husain ne ya shigo cikin gidan cikin uzuri ya sanar da Ummey da Daddy cewar matar da zai Aura iyayen ta, sun ce ya turo a had'a bikin sa dana Shaheed ". Kallon_kallo aka shiga yi tsakanin Daddy da Ummey, babu yanda suka iya, suka amsa masa, aka tura gidan su yarinyar aka bashi ita, aka maida bikin satin ukku daman saura kwana shidda. A ranar da aka sanar da su Anisah dasu Shaheed Auren Husain ne ya saka aka d'aga Auren duk sai suka bata fuska, Husnah kuma tsalle ta doka, cikin farin ciki tace ashe dai su mugu ana da budurwa Allah yasa a dawo da Auren a gobe ma, na dai na ganin mutum kullum ". Duk sai suka bita da ido jin sukeyi kamar su make ta, Shaheed ya ce, "dan Allah Husnah tashi ki koma cikin d'aki kina nufin ke farin ciki kike yi da wannan Auren ai wallahi kin bani kunya". Mere baki Husnah tayi tace, ni wallahi dama nasan yanda za'ayi da anfara yin nasa bikin ma, kowa ya futa". Dafe kai Shaheed ya yi, ya ce, "Husnah dan Allah ki.. Daddy ne yayi saurin cewar Shaheed kabar zan cen kawai, Allah ya tabbatar da alkhari. Duk suka ce, "amin " Tun da Husnah taje gurin kwanciya, bacci ya ce, bai san idon ta ba, ta rasa miye ya hana ta bacci, jure_juye kawai takeyi. Da ta gaji da kwanciya kawai sai ta d'auko wayar ta, ta kunna ta rasa, mi zata kalla, kawai Husnah ta rasa ita fa, yau mike damun tane, haka har asuba tayi, tana yin sallah, ta kwanta sai bacci, koda ta tashi bata da wata wal wala cikin damuwa take haka ta yini kowa dai yana mamakin miye ya sami Husnah? . haka Husnah ta dawo suku ku, har satin bikin duk wanda ya tambaye ta, mike damun ta, takan ce, Mommy take son gani, sai dai suyi ta lallashin ta, ana biki saura kwana biyu Husnah na zaune a baran dar gidan tana game da wayar ta, Husain da abokan sa, suka shigo sukayi parking, duk suka fito, Husain yana wai wayowa, kawai ya hango Husnah zaune tana wasa da wayar ta, harara ya ballama, duk da yasan Husnah bata gan sa ba. Cikin sauri yace da abokan sa kuje can ga key din d'akina ku tafi ina zuwa, duk basu lura da abunda yake nufi ba, har suka wuce, amman abokin sa d'aya murmushi kawai yayi ya gir giza kai. Sai da Husain yaga wucewar su, yayo inda Husnah take zaune hankalin ta, yana a kan wayar ta, da alama tana jin dad'in wannan game d'in, Husain na zuwa ya wafce wayar, ya duba game ne ya gani tana buga wa, ya maida wayar a cikin aljihun rigar sa, Husnah kuwa da bata san da zuwan Husain ba, yana wafce wayar ta tashi tsaye da sauri, zatayi magana taga Husain ne, kawai ta d'auke kai, Husain ya ce, "ki tashi ki baiwa mutane guri domin ina tare da bi'ki na, muna da bukatar gurin ki koma cikin gida ". Husnah kuwa ta ce, "malam nifa wallahi bana son takura kaje kaji da abunda yake gaban ka, ni game shine a gaba na, kaji ko? Waima dan Allah ba zaku sauya gurin da zakuyi taron ku ba ne? ". Husain ya ce, "malama ki dai kama gaban ki kawai, kiyi cikin gida, kuma ma Amarya ta tace, "kuzo gurin denier din da zai ayi yau da dare, ki sanar da "yan uwan ki". Mere baki Husnah tayi tace, "wallahi ba bu inda zani indai har zata su zasu je ba zan hana su ba amman nikam ba zani ba". Cikin jin haushi Husain ya ce, "dallah mallama, kada Allah yasa kije, kuma kafin na kirga biyar kin bar gurin nan ". Tafiyar ta kawai tayi, abokin Husain kuwa tace, "malam wayar ta fa? ". Galla masa harara Husain yayi ya juya suka koma gurin abokan su. Husnah na shiga cikin d'akin su tayi kwanciyar ta, kawai ta fashe da kuka sai da tayi kukan ta mai isar ta, sannan tayi bacci. Koda su Anisah suka dawo bacci takeyi gashi tare suke da maman Baby tunda basu ta'ba had'uwa ba, ganin tana bacci dole suka bar ta, suka sanar da Anty tasu,ita kuma ta koma gida saboda shirye_shiryen bikin Husain ita ce, komai. Husnah sai marece ta falka, anan ne take sanar dasu sa'kon Husain wanda har had'uwa sunyi dashi amman bai sanar dasu ba, sai Husnah ya sanar, cikin farin ciki suka ce da ita, "Husnah mu d'auki wanka muje" 'kawai Husnah ta sha mur da fuskar ta, ta ce, "sai kun dawo dama bikin Shaheed ne dana je ni kam". Dama sun san hakan ce zata faru, dole suka shirya suka nufi gurin denier din amman Husain na ganin basu zo da Husnah ba, ta ce, "maza suce shine yace ta zo kuma zuwan dole ne". Wayar Ummey suka kira dan sunyi ta kiran wayar Husnah tayi ringing babu amsa, Ummey ce ta kaiwa Husnah wayar tace, gashi inji Anisah, halan ina taki wayar ne Husnah? " Husnah ta ce, "Ummey ba wan can mugun bane ya anshe mani waya ba, bayan kuma game nake bugawa abu na, amman saboda tsabar mugun ta, sai da ya anshe mani waya ". Jin jina kai Ummey ta yi, ita fa mamaki Husnah da Husain suke bata a ce kullum mutane basa zama lafiya gashi duk sun ce, ba ruwan su da juna, Ummey ta ce, "him! Allah dai ya shirye ku, anshi wayar an sake kira". Husnah na amsar wayar ta saka hans free, ai kuwa Husain ne yake magana yace, " ke ban ce kuzo tare dasu gurin denier nan ba, wallahi kiyi maza ki shirya kizo kuma ki san motar da zaki shigo , aboki na yana nan gurin mai gadi yana jiran fitowar ki, saura kuma kiyi wan nan shegiyar shigar taki, kuma kada ki yarda kiyi magana dashi, ke dama kowa a gurin dan zan saka maki ido ne, saboda bana son kiyi abunda zai zubar da kimar gidan mu, tunda kowa yasan da cewar ke kanwata ce, kuma wallahi ki kula da kyau! ". Husnah kuwa ta buga uban tsaki ta ce, "to sannu uban Husnah ai dole ka saka ni aiki kuma kazo kana yi mani masifa, irin kai baban nan wanda bai d'aukar raini, to ba zan je d'in ba, ka jira idan ka dawo kayi mani dukan mutuwa, kaji baban Husnah". Ummey kuwa tun tana daurewa tana hana dariyar ta, fito wa fili har sai da dariyar ta fito fili, ta ce, "kai kuwa Husain ai lallashin ta zaka yi ba masifa ba, dan Husnah har tayi shirin bacci kaga kuwa bazan takurawa rayuwar "yata ba, a kan bikin ka, kuyi bikin ku kawai ita kam Husnah baccin ta kawai zatayi". Husain ya ce, "Ummey ki daina biye mata kice kawai tazo kinga duk gidan mu kowa yana gurin ban da ita, kinga idan tazo bikin zaifi yin armashi". Husnah kwanciyar ta tayi tace, "Ummey sai da safe ni kam ". Kashe wayar Husain yayi, Ummey kuwa tace, "Husnah da gaske ba zaki je ba? Idan har zaki iya zuwa kije mana tare da Auta, da wasu yan uwa mana dan gasu can zasu tafi ". Husnah ta ce, "Ummey nifa ba zani wani bikin nan ba, inda dai bikin Shaheed ne dana je". Ummey gir giza kai tayi ta tashi ta fita. Husnah kuwa kamar wadda aka tsun kula, ta tashi ta shirya tayi shigar doguwar riga purple mai adon stone, rigar nada ratsin ba'ki da pinki, sai dan kwalin rigar dama kan Husnah a kwance yake ta gyara gashin sai she'ki yakeyi, kawai ta banka turare sai 'kamshi ke tashi a bakin kujerar madubi ta zauna ta dayi light makeup, har ta tashi zata d'auki takalmin ta dawo ta zaun, ta fara bata, fuska tace, "wannan ma shegen bikin zanyi wa kwalliya? Bari dai naje naga shegiyar amaryar wadda ba yarinya ba, ni wallahi na tsani shegiyar amaryar nan, shi kuma sai shegen rawar 'kafa yakeyi akan ta, bari dai mugani da ido na". Tsani Husnah tayi ta d'auki uban takalmin ta masu mugun tsini ta saka kawai ta fito hannun ta ri'ke da dan kwalin, tana fita Ummey tayi murmushi ta ce, "daman nasan za'a ri na, wai an sace zanen mahaukaciya, Husnar ce, ko Husain d'in ". Husnah na zuwa gurin Ummey ta 'kwabe fuska tace, "Ummey gani na fito amman fa ba zan dad'e ba". Ummey tayi murmushi ta ce, " to ku tashi ku tafi, Tara nan ta fito ". Mutanen da Ummey tayi wa magana sai kallon Husnah sukeyi, ba kamar yanda ta fito kamar ba, bahaushiya ba, sai da Ummey ta anshi dan kwalin tayi mata rolling dashi, san nan suka ga ashe dai ita balarabiya ce, fita sukayi, sai kuma suka dawo kallon takun 'kasaitar da ta keyi, tana wani karai raya, sai uban tsinin takalmin ta, ita kuwa Husnah bata tasu ma takeyi ba, tafe take jin takeyi kamar kar taje gurin amman zuciyar ta, na son gane mata, abunda ke faruwa. Matar dire ban gidan nasu ta shiga tare da mutanen wasu kuma suka hau motar abokin Husain wanda yake jiran Husnah, kuma yaga Husnah ta gan sa amman tayi fuska ta hau motar gidan su, gir giza kai kawai yayi, yace, "Husnar Husain halin ku sai ku". Motocin na tashi, basu tsaye ko ina ba sai gurin da ake dinner din Husnah kuwa zaman ta tayi a cikin motar, kowa ya fita har direban amman ban da Husnah, kallon gurin kawai takeyi, mamakin cikar gurin takey, yan mata take kallo masu fira, wasu kuma na dance wa, su Anisah ta hango zaune sun takure guri d'aya ga Yaya Yusuf zaune a tare dasu, sai Kallon_kallo akeyi a tsakanin Anisah da Suhailah, suna 'bata fuska. Husnah saboda tsabar dariya motar ta fito sai dariya takeyi, dan tasan su Anisah sun tsara yanda zasu baje da rawa a gurin amman an takura su, gurin kawai Husnah ta dosa, babu ruwan ta da kowa amman idon maza da mata duk akan ta. Wasu jin sukeyi kamar suyi mata magana, har mamaki ta ina ta fito anya mutum ko aljan, ita kam Husnah na zuwa gurin su Anisah ta saka hannun ta, ta daki Anisah sai da Anisah ta zabura, tana ganin Husnah ce kawai itama ta tashi ta zago gurin Husnar ai kuwa Husnah na ganin hakan tayi saurin cewa, "Yaya Yusuf kace mata kada ta daki baiwar Allah ". Dariya yayi yace, "Allah dai ya shirye ku, to ku zana anan gaba na, dan ba zan barku ba ku d'aya kuyi, ta gogayya da samarin banza ba". Zama sukayi suka saka shi a tsakiyar su, sai suka soma yiwa Husnah dariya tunda tace ba zata zoba gashi anyi mata dole d'aure fuska Husnah tayi tace wallahi ra'ayi nane dai". Husain kuwa tun zuwan Husnah ya sauke ajiyar zuciya dan idon sa na akan ta, kuma zuwan ta yake jira, har Amaryar taso ta fahimci wani abun. Ganin irin shigar da Husnah tayi, gashi idon kowa a kanta, kawai sai yaji mugun haushi. Husnah kuwa kallon 'kasan ido tayi wa gurin dasu Husain suke tayi kallon tsab Husnah tayi wa Amaryar, wata dariya ce Husnah ta sanya wadda sai da su Anisah suka ce, lafiya dai Husnah wannan dariyar fa wallahi daga gani kin ga 'keta, dan nuna muna mu ma mu gani, wallahi Yaya Yusuf ya tsayar damu, gashi an soma wa'azin tun d'azu". Husnah kuwa tashi tsaye tayi zata bar gurin saboda dariya, Yaya Yusuf da Shaheed da isowar sa gurin ke nan, kawai yanye hannun Husnah ya zaunar, shima ya zauna ya ce, "Husnah ku kula da kyau kuji wallahi kin san akwai masu bibiyar ki, dan haka kada kiyi nesa da yan gidan ku". Zama Husnah tayi ta natsu, amman bata dai na dariya ba, har su Shaheed sakin baki sukayi suna kallon ta. Yau Husnah mamaki kawai take basu, zuwa can Husnah tace, "Yaya Yusuf dan Allah ka barmu muyi rawa ko sau d'aya ne mu taya dan uwan mu farin cikin wannan za'ben da yayi a gaskiya Amaryar ta had'u iya had'uwa" Tun da Husnah ta fad'i hakan sai kowa ya gane mi take yiwa dariya, su Shaheed kuwa suma dariyar suka sanya harda tafawa. Wasu samari ne masu ji da kyau da nera suka zo gurin da su Husnah suke sukayi, sallama kawai Husnah dasu Anisah sukayi shiru suka d'auke kai gefe. Hannu suka baiwa su Shaheed bayan sun gaisa, suka ce am dan Allah ko zaku iya bamu aron kannen ku? Dan wallahi da gaske nakeyi Auren su muke soyin indai kun bamu dama, cikin wata d'aya ne za'a d'aura Auren". Dariya Anisah ta sanya tace, "ikon Allah wallahi mu kam yau muna ganin abun dariya, to bari kuji nan duk da kuke ganin mu, muna da wanda zamu Aura nan da sati ukku, za'ayi wannan gagarumin bikin, muna gayyatar ku d'aurin Auren namu". cikin samarin d'aya ya d'aure fuska ya ce, "wallahi baki da wani mijin bayan ni! ". Husnah kuwa murmushi tayi bata ce uffan ba, Anisah tace, "Allah sarki to baban mu munji mun gode a sauka lafiya ". Yaya Yusuf da Shaheed kuwa ido kawai suka sanya masu, kawai sai ganin Husain sukayi, yana magana cikin 'bacin rai yace, "Anisah Suhailah Safiya da ke duk na sallame ku, ku tashi Shaheed ya kaiku gida nagode! ". Ganin yanayin fuskar Husain babu annuri ne ya saka kowa shiga tai tayin sa, Husnah kuwa ta basar dashi, tace, "kai kuma kai ne ke sona ko? To ka bani number wayar ka a rubuce, saboda bani da waya a hannu na, ko kuma ka bani wata wayar taka naje gida da ita, kaga ba zaka sha wata wahalar ba" Haushin Husnah ne ya turnu'ke Husain kawai ya saka hannun sa da karfin gaske ya janye hannun Husnah da gudu kamar zata kife 'kasa, amman Husain bai ma kula taba, sai cikin motar Shaheed ya saka Husnah ya maida 'kofar ya rufe, juyo kawai sai Amaryar sa ya gani tsaye a bayan sa sai fuci take kamar wadda ta had'iye maciji, duk abokan Husain suka matso gurin Yaya Yusuf da Shaheed su Anisah duk suna gurin cikin zafin nama suka iso gurin. Amaryar Husain cikin 'bacin rai ta ce, "wato yau ranar dinnier din mu shine zaka wani kama hannun mace a gaban ido na ko? To yau_yau d'in nan ko kuma ma nace yanzun _yanzun nan nake san sanin wace ce ita, miye alakar ka da ita! ? . Husain yace, "wannan ba muhallin ki bane, babu abunda ya shafe ki da wannan maganar, kuma ma ke miye naki a ciki? " Cikin fushi ta ce, "ni kuwa nake da muhallin son sani wace ce ita a gareka kuma miye alakar ka da ita, dan ko waye ya ganka a wannan lokacin sai ya zargi wani abun " Share ta yayi, Husnah kuwa tana samu ta bud'e 'kofar ta fito kawai sai jin sukayi muryar ta kamar yanda take magana ta ce, "him ke malama daman bai sanar dake cewar kece matar sa ta biyu ba? Ai kuwa dai gaskiya hubby baka kyauta ba, kana nufin kamar yanda ka yi mani haka kayi mata, tab lallai ma, yarinya to bari kiji tun ina karama ta, aka d'aura muna Aure dashi, kuma yau shekarar mu ukku da tarewa, gida d'aya, a 'kasar da yayi karatu ya baro ni nima na 'karasa nawa karatun, to kin san wani abu ku? ". Husnah tayi murmushi tace, "ya dawo ne nan ya ce, shi yana son ya auri tsohuwar mace wadda zatayi saurin haihuwa, wadda haihuwa d'aya zata tsufa shi kuma sai yafara yi mata wulakanci ya saketa ya d'auke muna dan ya kawo muna, kinga ba zamuyi saurin tsufa ba, shine yace nadawo gida ya samo matar da ta dace da aikin, nazo na gani za'ayi bikin cikin gaggawa, dan haka nazo bikin, to nikuma ina ganin ki sai naji tausayin ki shine nace zan sanar dake gaskiya amman shine yace ya rantse sai ya cika burin sa a kanki tunda har ya gano kin mutu a kansa shi kuma soyayyar 'karya ce yake yi maki dan haka babu wanda ya isa ya hana sa aikata hakan ". Husnah ta fashe da kuka kamar da gaske ta durkushe 'kasa tana kukan karya. Ba Husain ba hatta su Yaya Yusuf da Shaheed mutuwar tsaye sukayi, ganin Husnah harda hawaye a idon ta. Mutane kuwa cike suke da mamakin cewar wai Husain ne da wannan hadaddiyar matar amman shine zai koma wa, wata guzumar mata haka. Amaryar kuwa tace, "anyi walkiya Husain na gano ka kuma kowa ya gano ka, daga ganin yanda kake mazurai kowa yasan baka da gaskiya dan kowa yaga yanda idon ka ya rufe a lokacin da tazo gurin nan, dan haka malam na fasa Auren ka koda kuwa kaina kawai ka zama dan Autan maza a cikin duniyar nan". Kawai Husain sakin baki yayi ya kafe Husnah da ido ko kiftawa babu, su Yaya Yusuf da Shaheed kuwa cike suke da tsoron anya Husnar suce kuwa?. Anisah ce ta dawo gurin Husnah ta dafa ta ta shi tsaye suka bar gurin, suka shiga cikin motar su, babu wanda yace uffan har su Yaya Yusuf da Shaheed kuwa sai da suka je gida. Su Daddy ne suka riska a gidan Husnah na zuwa tayi ribas ta juya zata gudu cikin fushi Daddy yace, idan kika yarda kika bar gidan nan sai kin had'u da fushi na, zo muyi magana dake ". Dawo wa Husnah tayi cikin d'ari_d'ari ta dawo ta zauna gurin cike da mutane harda Husain da abokan sa, da yan uwan Daddy da abokan sa, da Ummey da yan uwan ta, da abokan ta. Su Anisah da kowa dai an zauna anyi shiru . Daddy yace, "miya sa husnah ta ta aikata wan nan dan yen aikin? ". Husnah ta fashe da kuka kamar wadda aka daka tace, "Daddy har wai kun manta da abunda ya yi mani a cikin taron mutane maka mantan haka wanda suka kasan ce, ba mutanen kwarai ba, ya wanke ni da mari abunda babu wani mahalukin da ya taba kwa tan ta hakan a a gareni, irin wannan to zarcin da yayi mani yana nufin zan iya kyalesa ke nan!? " Daddy tun kafin na aikata nasan miye zai biyo baya amman Daddy tunda rama irin yanda yayi mani to Alhamdulillah yaji abunda naji a rayuwa ta, dan haka duk hukuncin da kuka yanke a kaina zan rungume sa, hannu biyu, koda kuwa ya kasan ce zan bar maku gidan nan ne, nadai rama zuciya ta tayi fari fes, Daddy wasu saboda dariyar marin da yayi mani harda d'aukar photon abun sukayi, kuma harda gori a gaban idon kowa hakan ta faru". Shiru tayi sai shashshekar kukan ta kowa yakeji, shiru gurin yayi zuwa can Daddy yace, "Husnah tashi ki shiga ciki ki kwanta sai da safe zamuyi magana dake, san nan kuma kada na sake jin zan cen barin gidan ku, dan baki da gidan da yafi wannan". Tashi Husnah tayi cikin daddy ya yi murmushi ya dubi Husain ya ce, "Husain abun da naja maka kunne ke nan a kan sa, insha Allah yan zun ka fahimci abunda mukayi maka hange tun wancan lokacin, Husain Husnah ai kowa ma yasan a tsakanin ku, Sam babu ji ruwa, yan zun sai ka sami amaryar taka, ka bata hakuri ayi Auren kawai gone a futa, ni zan san mata kin da zan d'aukar wa wannan rashin jituwar naku" Daddy yace, to kowa dai yaji duk abunda ya faru dan haka sai kuyi masu fad'a su duka, sannan ku bani shawarar matakin da zan d'aukar masu zuwa da safe, ku tashi ku tafi ". Duk kowa fita yayi, Hajiyar kuma murmushi tayi kawai. Husnah tun da ta shiga cikin d'akin take farin ciki su Anisah dai kallon ta kawai suke yi. Haka suka kwana, Husain kuwa sai cizon baki yakeyi shi a dai haka ta kwana. Tun da safe su Yaya Yusuf da Shaheed abokan su dasu Anisah da yan uwan Daddy da Hajiya aka zazzauna a take kowa ya kawo tasa shawarar, ai kuwa Ummey da Daddy sai farin ciki sukeyi..... (Nima dai farin ciki nakeyi duk da ban san wace irin sharar bace) *Duk wanda ban amsawa Comment ba yayi hakuri ina godiya da soyayyar ku a gareni, na gode sosai Allah ya bar zumunci* *A GIDANTA NA GIRMA* *BY NANA: KHADEEJATU* *_UMMU IHSAN_* *SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU SOSAI SON FISABILILLAH* *YA ALLAH KAJIKAN MAHAIFINA KAYI MASA RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SA SHIDA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.* *YA ALLAH KA BAIWA MAMANA LAFIYA KA BAIWA DUK KANNIN WANDA BAIDA LAFIYA NA GIDA DANA ASIBITI ALLAH KA BASHI LAFIYA AMIN YA ALLAH* *_Bismillahir Rahmanin Rahim_* 71~75 Cikin farin ciki Daddy ya ce, "Shaheed kira mani Husain kace masa ina jiran sa da gaggawa yan zun nan, am kema Anisah nemo mani Husnah kice mata ina neman ta da gaggawa yan zun nan ". Ai kuwa cikin sauri su Shaheed suka cika umarnin Daddy, Husain ya ce, "wannan kiran na gaggawa Shaheed cikin fushi Daddy yake ko kuwa?". Shaheed ya ce, "to nima dai ban sa ni ba, amman dai kayi sauri gudun yin laifin". Jin abun da Shaheed ya fad'a ne, yasaka Husain tashi tsaye cikin sanyin jiki ya tafi kamar wani marar lafiya. Itama Husnah koda Anisah ta sanar da ita kiran Daddy ruwan da take sha ne ta fur zar kamar wata 'karamar yarinya ta zaro ido waje tace, "Anisah na shiga ukku na ni Husnah wane laifin ne kuma na sake ai katawa, ni shugabar marasa jin magana ta duniya! ?. Anisah ta ce, "kije da kanki kijiwa kunnen ki, dan nima ban sa ni ba amman dai kiyi saurin amsa sa'kon Daddy ". Tashi Husnah tayi cikin damuwa da rashin sanin laifin ta, tabi bayan Anisah kamar wadda 'kwai ya fashe wa a ciki haka take tafiya, a bakin kofar falon suka had'u wani ban zan kallo Husain ya aika wa Husnah, itama tayi saurin mayar masa harda mur gud'a masa baki, su Anisah kuwa wuce su sukayi suna dariya 'kasa_'kasa Husain yace, "yarinya kin taro wa kanki masifa dan yanda kina tozar tani a cikin taron mutane harda su kiran cewar ke mata ta ce ke a tunanin ki zan iya Auren karuwa ne? Yarinya kin yi 'karya ni nan Husain nafi karfin ki wallahi! " Tabe baki Husnah tayi ta ce, "ho ho shegiya 'karya, oh da kai har tunanin ka ya baka cewar ni Husnah zan iya Auren mum munan mutum kuma tsofo wanda ya zama tuzoru? Lallai tsohon nan kayi kus kure dan ni Husnah ta yaro ce mai jini a jiki, kuma kasani, ni ko mai sunan ka bana bu'katar hanya ta had'a ni dashi guri d'aya ballema ace Aure, kai tub da wannan yawun naka ma, ni idan aka bani damar tsayar da wanda nake son Aura ai Tk ne yafi kowa dace dana Aura ". Cikin zafin rai Husain zafin zuciya ya d'aga hannu zai kaiwa Husnah duka, Husnah tayi saurin fad'ar Allah ya baka ikon ai katawa, wallahi zan yi maka fiye da abun da ka aikata a gare ni!. Daddy ne ya matsa dab dasu yana kallon su, Husain ya d'aga hannu zai daki Husnah, ita kuma Husnah tana sakar masa magana ya ce, "wannan shine amsar kiran dana yi maku ko? Ashe dai har kun iso to ina godiya sosai da wannan amsa gayyatar da kukayi tawa". Juyawa ya yi ya dawo inda yake zaune su Yaya Yusuf da Shaheed dariya kawai sukeyi 'kasa_'kasa, kai gurin mamakin halin Husnah da Husain akeyi wannan rashin jituwa nasu yayi yawa. Da sauri suka dai na fad'an har suna rige_rigen zuwa, a gaban su Daddy suka dur'kusa kowa kai a 'kasa. Hajiya dariyar ta kasa 'boyewa tayi kawai ta ce, "Ikon Allah Husain kai da Husnah yau wani sabon kicihi kuka tsiro na jin kunyar had'a ido damu to kodai kun sa santa kan ku ne naga duk fuskar ku da annurin fuskar ku ya nuna hakan, to Alhaji Alhamdulillah tunda har su sasan ta kansu kawai sai ayi gaggawar d'aura Auren nasu yau ko? Ko ya ya kuka gani ne jama'a? ". Wata irin zabura sukayi su duka, Husain sai murza kunnen sa yakeyi da alama kamar kunnen nasa bai jiyo abunda Ummey ta fad'a ba sosai. Husnah kuwa zarar ido take yi kamar wadda tayi 'karya sai bin duk mutanen falon takeyi da ido d'aya bayan d'aya. Yaya Yusuf ya ce, "oh! Ikon Allah ashe dai shirya war tasu ba wani abu bane mai d'aukar lokaci da yawa ba, kai amman nikam nafi kowa farin cikin wannan sauyin da muka samu a gurin Husain da Husnah ". Dan uwan Daddy Alhaji Haruna ya ce, "to ai kuwa nine waliyin ango kai kuma Yaya nasan kaine uban Amarya sai muyi wa Annabi salati, Sallalahu alaihi wasallam". Duk aka amsa da, "Sallalahu alaihi wasallam ". Husnah fashewa tayi da kuka, zatayi magana ke nan wata dattijiya, tace, "ikon Allah Amaryar har ta fara kukan rabuwa da iyayen ta, zata je gidan abun son ta". 'kara fashe wa da kuka Husnah tayi, gashi tana son yin magana babu damar yi saboda mutane sun'ki su barta tayi magana, sai ta kaicin hakan ya 'kara yi mata yawa. Husain kuwa hankalin sa yayi munmunan tashi, Sai zufa ce ke karyo masa ta ko wane sa'ko da lungu na jikin sa, da ket ya bud'e bakin sa ya ce, "dan Allah Daddy kayi...... ". Da sauri Daddy ya dakatar dashi yace, "haba Husain miye na godiya kuwa ai Husnah kanwar kace kuyi zaman ku na gir ma ma junan ku ku ji ni ko?. Wani abokin Daddy Alhaji Isma'il ya ce, " a a ba haka yake nufi ba, nikam na fahimci abunda yake son fad'a ko Husain? . Da sauri Husain ya d'aga masa kai kamar wani dan 'kadan gare, ya ce, "eh Abba eh Abba ba hakan nake nufi ba". Cikin sauri sai Alhaji Isma'il ya ce, "yauwa Alhaji kun dai ji da kunnen ku ko? To abun da yake son fad'a shine yace dan Allah Daddy kayi hakuri ko Husain? " ya dubi Husain wanda har da murmushi ya saki da sauri ya ce, "eh eh Abba hakane kuma zan ce ". 'kara dakatar dashi Alhaji Isma'il yayi yace, "zan 'karasa maka mana yaro na". Da sauri Husain ya ce, "nagode Abba kai ne kawai ka fahimci nufi na". Dariya Alhaji Isma'il yayi yace, "to Husain dai yana mai baku hakuri ne akan irin yanda suke yawan fad'a a tsanin sa da kanwar sa Husnah amman ya dau alkawarin hakan ba zai sake faruwa ba matsawar kuka Aura masa ita, to kunji nufin yaro na dan albarka ". Ga baki d'aya gurin ya d'auki kai masha Allah abu ya yi kyau. Husain da Husnah kuwa hankalin su a tashe yake, Husnah kuka kawai takeyi babu 'ka'kkautawa, ganin take duk basa son ta, Husain kuwa saboda tsabar shiga cikin mamakin Abba, kawai ya kafe Daddy da ido, Daddy ya ce, "Husain kud'in da kake ajiyewa kace zakayi abu mai mahimmaci dasu, to na raba su hud'u na d'auki sadakin 'yata Husnah a cikin su kaga naira dubu dari biyar ke nan tunda baka dad'e da fara ajiyar ba, kuma cikin gida jen da ka kammala na d'aukar wa Husnah wannan gidan da ka gama kammala wa, a cikin shekarar nan gidan da yafi kowa ne gida bur geka da soyuwa ba zan hana ka kawo wannan matar taka ba, dan munje mun baiwa iyayen ta, hakuri sun janye maganar fasawar da aka ce a baya, amman kuma ka sani Auren Husnah zamu fara d'aura wa, kafin muje can a d'aura Auren ka da mardiyar, dan haka Auren mata biyu ya hau kanka a wannan ranar, kuma Husnah itace uwar gidan ka Husain, ku tashi nagama magana sai naga wanda bamu isa dashi ba a cikin ku, kuma sai naga wanda bai d'auke mu matsayin iyayen sa ba daga cikin ku". Daddy na gama magana ya sallami kowa, daga cikin yara amman banda abokan sa da yan uwan sa. Husnah har jiri ke dibar ta, har ta isa cikin d'akin su, ta fad'a a saman gado ta d'ora hannu a kai tace, "yau ni Husnah na shiga d'ari da talatin ace kamar ni Husnah zan Auri Husain tazuru, kuma tsofo, bama wannan ba, wai harda 'katuwar kishiya, ni yau Husnah nice haka, Allah na tuba ka yafe ni, idan laifin da nayi maka ne, ka hukun tani da Auren Husain! ". Su Anisah da Suhailah Safiya basu yin dariya ba, amman jin yanda Husnah ke shirme musam man ma yanda take kiran 'katuwar kishiya abun ya bala'in basu dariya wai Husnah ce yau da tsoron kishiya kishiyar ma wai matar Yaya Husain . Aikin da Husnah keyi ke nan su Anisah tun basu d'auki abun da gaske ba, har suka dawo sukaji tana bala'in basu tausayi, sai suka dawo lallashin ta. Husain kuwa cikin d'akin sa ya dawo ya rasa miye yake yi masa dad'i a rayuwa, shi dai kawai yasan ba zai iya sa'bawa umarnin su Daddy ba, amman ba zai iya Auren karuwa ba, da hankalin sa, kuma ma saboda tsabar an maida shi wani iri shine za'a ce karuwa itace uwar gidan sa, a gaskiya ba'a kyauta masa ba". Haka Husain ya zauna aikin komai baiyi ba, har abokan sa, suka shigo suna yi masa, kirarin mijin mace biyu a rana d'aya abun yayi kyau ya 'kayatar. Kyalesu ya yi, saboda duk haushin kowa yake ji, Daddy ne ya zo da kansa ya tasa shi a gaba sai da yaga Husain ya fito angon sa, tukuna kowa ya ga Husain a lokacin yaga ango sai dai matsalar d'aya ko kuma a abun ya zame masa ado wato rashin dariya, sai in ya lura da Daddy shi yake kallo sai yayi murmushi yayi yar fuska. A cikin gidan aka d'aura Auren Husain da Amaryar sa Husnah akan sadaki dubu d'ari biyar Ai kuwa gidan ya d'auki gud'a, da ihu su Anisah kawai suka saka kid'a sai dan cewa sukeyi harda kiran 'kawayen su a waya, Shaheed kuwa saboda murna sai ya tara nashi abokan yace a cikin ganin nasu ma zasuyi partyn su, na murnar Auren sa dana Husain da Husnah wannan shine ya 'kara cika gidan tako ina kabi mutane ne . Husnah kuwa duk tabi ta takurawa kanta ko wankan da ta saba yin sa yau batayi ba, Ummey ce da 'kawayen ta, akan Husnah sai da Husnah taga Ummey tayi fushi sanan tayi wankan gurin saka kayan da Ummey ta kawo mata ma, sai da taji Ummey ta ce, "Husnah idan baki saka kayan nan ba, to ba zan 'kara kulaki ba! ". Sannan Husnah ta saka materials d'in a gaskiya ya had'u iya had'uwa, gashi fari fes sai d'aukar hankali yakeyi makeup, aka ce ayi mata amman Husnah ta saka kuka dole Ummey ta ce, su kyaleta ita ce tayi mata da kanta, ai kuwa Husnah mamakin takeyi taya Ummey ma zatayi mata kwalliya, indai ba kwalliyar tsofafi ba? ". Husain ne ya shigo cikin d'akin neman Ummey dan Daddy ne ya aiko sa gurin ta, a nan ne tadda ana rigimar kwalliya, tsaki ya yi, yayi tsaye yana kallon yanda Ummey ta dage akan sai Husnah ta tsaya tayi mata kwalliya, amman Husnah ta 'ki , sai doka kafa takeyi. Duk takaicin Husnah ya 'kara kama shi, babu wanda ya kula da zuwan sa, sai Ummey amman tayi kamar bata san da zuwan sa ba. Husnah kuwa duk sai tsalle_tsalle takeyi da doka 'kafafun ta a 'kasa, Ummey tace, "Husnah ki zo ayi maki kwalliyar ko nayi maki da kaina ko kuma ki zauna kiyi wa kanki ". Husnah tace, "Ummey nifa wallahi ko d'aya kin san bana son 'bata fuska kuma tunda kin matsa mani nayi wanka na saka wannan kayan kibar ni haka mana". Dariya mutanen keyi, ganin wautar Husnah, sai da Ummey tasake 'bata fuska san nan Husnah ta zauna a ka fara yi mata kwalliya Ummey na fad'ar kuyiwa 'yata kwalliya banda 'bata mata fuska dan ana gamawa zasu je gurin partyn da Shaheed ya shirya masu, ta murnar Auren Husain da Husnah ta". A take Husnah ta 'kara d'aure fuska, tayi rau_rau da ido sai hawaye ai kuwa aka sanya mata gud'a ana yi mata kirarin Amaryar Husain ta soma kukan farin ciki kukan Allah ya nuna mata ta zama 'yar gatan ango Husain " ai kuwa ta saki kukan dole aka sakar mata fuska saboda ruwan hawayen da takeyi. Husain ya juya zai bar cikin d'akin Ummey ta ce dashi, "Husain angon Husnah ba gurin Amaryar taka ka zo bane? Kodai kunyar mutane kakeji shine ka juya, to ka jira ta a harabar gurin da ake taron". Cike da mamakin maganar Ummey Husain ya rasa ma mi zai fad'a kawai ya fita ya bar cikin d'akin. Da harara Husnah ta raka shi, Ummey dai tana kallon su tana dariya 'kasa_kasa, sai da aka dawo lallaba Husnah sannan ta yarda akayi mata makeup, d'in. Husain na fita ya nemeni Daddy ya rasa, Yaya Yusuf ne da Shaheed suka zo suka saka shi a gaba sai da suka zaunar dashi akan kujera, anan ne aka kawo Amaryar Husain wato Mardiyya, taci wanka iya wanka, Husain na ganin ta ya saki murmushi itama ta mayar masa, a kujerar kusa da Husain aka bata masauki wato shine tsakiya, kujerar hannu damar sa, aka ajiye flower, da wasu abubuwa, a kujerar hagun sa kuwa aka zaunar da Mardiyya. Shaheed da Amaryar sa su Anisah da 'kawayen su kai gurin dai ya cika masha Allah komai ya kammala amman ba a fara gaba tar da komai ba. Mardiyya ce ta ce, "mijina ba za'a fara gabatar da komai bane? Duba fa tun d'azun aka gama shirya komai to zaman miye mukeyi? ". Kallon ta kawai ya yi baice da ita uffan ba, kawai dai taga ya tsare guri d'aya da ido kuma ta juya haka taga kowa ya maida hankalin sa gurin, kawai itama ta juya, mi zata gani kawai sai ta tashi tsaye a firgice ta zaro ido waje ta daki kirji tana nuna inda mutane ke kallo...... *(Tofah shin miye Mardiyya ta gano??? kudai kawai ku biyo Ummu IHSAN )* *Comment and share* *A GIDANTA NA GIRMA* *BY NANA: KHADEEJATU* *_UMMU IHSAN_* *SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU SOSAI SON FISABILILLAH* *YA ALLAH KAJIKAN MAHAIFINA KAYI MASA RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SA SHIDA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.* *YA ALLAH KA BAIWA MAMANA LAFIYA KA BAIWA DUK KANNIN WANDA BAIDA LAFIYA NA GIDA DANA ASIBITI ALLAH KA BASHI LAFIYA AMIN YA ALLAH* *"Yan uwa barka da sallah da fatan kunyi sallah lafiya Allah ya mai_maita muna amin, Amman ni har yan zun banji wadda tace ta tuna da Ummu IHSAN ba ace Ummu IHSAN ga kafar gaba mai awaza da 'kafar baya ba, nidai nace kada ci ya rufe maku ido atoh* ๐Ÿ˜œ *_Bismillahir Rahmanin Rahim_* 76~80 Cike da tsabar rikicewa, take nuna gurin, hannun ta ta ri'ka d'aga wa tana dan dukan jikin Husain wanda ya kafe guri d'aya da ido, sai alokacin da Mardiyya ta dake sa ya sauke ajiyar zuciya a bayyane, san man kuma ya dawo da idon sa, gurin ta yace, "lafiya dai? Mardiyya cikin kidemewa ta ce, "a ina muka had'u da dangin aljannu kuma, nidai nasan duk a cikin dangi na da shige_shige na ban ta'ba had'uwa da su ba! ". Tsaki Husain ya doka ya ce, "dallah mallama ki zauna ki natsu, haka kawai kin wani dawo da hankalin mutane inda muke". Mardiyya ta ce, "kaga fa nan gurin suke nufowa fa nikam zan gudu dan na tseratar da rayuwa ta". Tsaki Husain ya 'kara dokawa,, ya saka hannun sa ya dawo da ita mazaunin ta ya ce, to ki saurari abunda dj yake fad'a a kan ki mana! " ya sake jan tsaki. Zama Mardiyar tayi, kawai ta jiyo muryar dj na fad'ar, "kai masha Allah uwar gida sarautar mata anfito ke ce taro, danki kowa ya taru daga zuwan ki, hankalin kowa ya dawo kanki domin kece fasa taro, uwar gidan Alhaji Husain Allah dai ya 'kara dan kon soyayya, kice fitila mai haskawa a cikin wannan taron daga zuwan ki, kowa ya sara maki, kai hatta Amaryar Husain ta tashi dan baiwa uwar gidan Husain girma, kai amman wannan uwar gidan kim d'aga tuta, ga ki kyakykyawar gaske, dake da mai gidan ana go gagga gurin kyau, kowa ya kalleki ya san da cewar za'bi da Husain yayi baiyi tumun dare ba, lallai Husain ka d'aga tuta". Wani irin 'kololon ba'kin ciki ne ya tukare wa Mardiyya zuciya har zuwa ma'koshin ta, sai huci takeyi, ta ce, da Husain cikin tsana nin 'bacin rai, "daman ka matsa mani nazo ne gidan ku gurin wannan tsi nannen partyn dan a wulakanta ni? To wallahi dana san cewar da gaske wannan ita ce za'bin rayuwar ka ba ni ba wallahi da tuni ban yarda da 'karyar da akayi mani ba, akan cewar babu Aure a tsanin ku, amman Yan zun iyayen ka sun had'a Auren na kune saboda wani alkawari tsohon ajiyewa to bari kaji tun daga yanda kake kallon ta na gane cewar duk 'karya ce, Auren so da kauna kukayi, kuma yan zun nan zan bar maku gidan ku, nafasa yin partyn! ". Mardiyya masifa kawai take zubawa ido rufe bata ma san da su Husnah sun iso gurin ba, har an zaunar da ita a gefen daman Husain. Husain kuwa haushin ganin irin yanda kowa yake kallon Husnah da irin yanda Dj yake ta kod'a irin kyaun ta, gashi idon kowa har yan zun akan Husnah ne, 'karin takaicin shi yanda Mardiyya take tayi masa hauka, a cikin mutane harda su 'kannen Ummey da Daddy da abokan Ummey wanda suka rako Husnah, abun haushi ma yan da Husnah keta yin murmushi kamar wata kyakykyawar gaske. Duk abun da Mardiyya keyi akan kunnen su Husnah kuma duk sunji abun da take fad'a. Murmushi Husnah tayi ta ce, "iska na wahalar da mai kayan kara, indan ta Husnah ne yarinya kama mijin ki dan bai gaba na, nifa yan zun jin kaina nakeyi kamar wata wadda take rayuwar ta ita d'aya, dan bazan takura kaina ba, a gidan wasu bana su Ummey da Daddy ba, eh". Cikin 'kara jin haushin Husnah Husain yace, "yarinya kin kawo kanki gidan yari, dan sai kin yabawa aya zakin ta" kallon su kawai akeyi ganin Husnah da Husain suna magana a tsanin su, ganin yanda kowa yake d'aukar su photo, waya da camera video, Kasai shims Husain sai ri'ka yin murmushi yana magana, "yarinya tun kafin aje ko ina kije ki cewa su Daddy kin fasa dan DUK kika yadda kika saka 'kafar ki cikin gida na sai nayi maganin ki". Dariya Husnah tayi ta ce, "Allah ko? Ni wallahi ba irin butulu bace mai mancewa da alkhari ba, Amman kai da kake da ja, kaje gurin su Daddy ko ka anshi abun maganar a hannun Dj sai ka sanar da kowa cewar ka fasa yin biyayyar, kaga ka futa da kallon idon su Daddy ko? ". Tsaki Husain ya ja ya ce, "to halan waye kike nufin kin fi sa son faran tawa su Daddy? Ke yarinya ni nan da kike gani indai akan farin cikin su, Ummey ne nafi kowa kaunar sa". Dariya Husnah tayi ta ce, "Allah sarki ni a yar gidan Zubaidah, wannan maganar da ban dariya take". Da sauri Husain ya ce, "wallahi idan kika sake kiran sunan wannan babbar karuwar a gaba na sai na sa'ba maki! ". A take Husnah ta ce, "sannu uban Husnah ai dole ka hana ni fad'ar sunan mommy wadda ta raine ni, tab lallai ma mikam wallahi.... ". Kasa 'karasa maganar Husnah tayi ganin abokiyar Ummey da kannen Daddy da Ummey, sai su Anisah wadda suke ta gimtse dariyar su. Goggo Aina'u tace, "to kaji iyayen fad'a ana can anata kiran ku, ku fito ku yanka cake, kira kusan biyar amman duk ba kuji ba, saboda tsabar masifa irin taku, ka duba Husain matar ka har gurin zama ta sauya saboda ita a tunanin ta, fira ce kukeyi, bata san masifa bace kukeyi iyayen masifa kawai, ni ku tashi muje, kuma Husain kaje ka lallashi Amaryar ka, ku same mu gurin da za'a yanka cake din ". Cikin fad'a da masifa take maganar ai kuwa da sauri suka dubi gurin da aka nuna masu Mardiyar ta koma, cike da mamaki suke kallon yanda take cika take batsewa sai hura hanci kawai takeyi. Hannun Husnah aka ja suka nufi gurin da za'a yanka cake din, Husain kuwa da mamaki cike a fuskar sa ya isa gurin Mardiyya wadda take tare da 'kawayen ta, suna 'kara fure mata kunne. Yana 'karasa wa, baiyi wa kowa magana ba, hannun ta kai ya janyo kawai ta ri'ke 'kawar ta, ta tirje, jiyowa Husain yayi, cike da mamaki, yake bin su da ido, Kawai ya tattare hannun rigar sa, kawai ya tallabe Mardiyya yayi sama da ita, ai kuwa mutanen gurin suka d'auki ihu da tafi, Husnah kuwa kallo d'aya tayi masu ta d'auke kanta gefe, tayi murmushin gefen baki, ta gyara tsayuwar ta, Husain na 'karasowa gurin ya ajiye Mardiyya wadda take kallon fuskar Husnah taga ko zata ga wani abun amman kuma Husnar sai murmushi takeyi, Husain ya tsaya a tsakiyar su Mardiyya jin takeyi kamar ta kashe Husnah, tunda ita har yan zun bata damuwa da abunda takeyi mata. Su Shaheed ne suka 'karasa gurin a kusa da Husnah ya tsaya ya dan matsa a kusa da ita kad'an ya ce, "gimbiyar Husain Daddy ya ce, a sanar dake kada ki basu kunya, ki nuna masa cewar ke yar sace, kinji kanwata?. Murmushi Husnah tayi ta ce, "ada nayi niyar bata wannan taron amman yan zun na fasa, wai nikam matar Yaya Yusuf har yan zun bamu ta'ba had'uwa da ita ba, duk da na fahimci cewar tafi kaunar Husain da wata ba niba, saboda ranar naji su Anisah suna maganar cewar duk abunda Husain yake so shi take so, wanda Husain baya kauna kuwa, tafi sa rashin kaunar abun nan, dan haka nasan ta tsaneni fiye da tunanin mai tunani! ". Kallon ta kawai Shaheed yake yi, Anisah tayi saurin fad'ar ai kema kin tsane ta ko? ". Kallon Anisah Husnah tayi tace,"taya zan tsani matar Yaya Yusuf bayan na d'auke sa kamar Yaya na wanda muka fito ciki d'aya dashi? " Shiru duk sukayi Suhailah ce ta ce, "Husnah kada ki damu tunda muna tare dake, ke tamuce, kuma Insha Allah komai zai zo maki da sau'ki nasan da cewar Husnah kina tunanin zamu iya juya maki baya kamar yanda kike tunanin Maman Baby tayi maki, aa mukam kece tamu kuma ba halin Maman Baby bane abunda kike tunani dan haka ki natsu guri d'aya kinji ko? Ki fitar da mu wannan kunyar ta mutanen dake gurin nan, kada ki yarda suje dake a bakin su, na wani mugun hali, kibar su, suyi ta ganin mutum cinki kinji yar uwar mu? ". Murmushi Husnah tayi ta ce, "kada ku damu ni kuma sai na baku mamaki sai kun san da cewar ni takuce Insha Allah ". Dariya duk sukayi suka gyara mata tsayuwar ta, Husain na had'a ido da su Shaheed ya watsa masu harara, su kuwa suka sanya masa dariya harda tafi, ai kuwa kowa ya d'auki tafi, ana kidaya daga d'aya zuwa ukku, aka basu umarnin su ri'ke wukar d'aya su yanka cake din. Kowa zuru_zuru kawai Husain yad'ora hannun sa a tsakiyar wu'kar kawai Mardiyya tayi saurin d'aura hannun ta a saman nasa, saura Husnah kowa ita yake kallo, kawai ta kalli su Anisah sukayi murmushi, suka 'kyafta mata ido kawai sai ta d'ora hannun ta akan tsin_tsiyar hannun Husain, ai kuwa aka d'auki ihu, Husain kuwa mutuwar tsaye yayi, ya jiyo yana kallon Husnah wadda tayi kamar ba ita ce tayi ba. Mardiyya kuwa ada tana murnar tayi wa Husnah tsiyar, kawai sai taga Husnah tayi fiye da mamakin ta. Ita fa hannun tane taga ta d'ora a wu'kar saman hannun Husain , haushin Husnah Kawai taji ya 'kara shigar ta taji ina ma zata samu damar kashe Husnah da babu wanda ya isa ya hana ta aikata hakan, amman ta lura da babu yanda zatayi da Husnah. Ana yanka cake din Husnah tayi saurin d'aukar cake din ta dur'kusa 'kasa ta d'aga hannu zata sakawa Husain a cikin bakin sa, amman bata kaiwa, aka d'auki ihu da tafi su Shaheed sai sara mata sukeyi, Amaryar Shaheed kuwa da sauri ta 'karasa gurin Husnah ta ri'ko hannun Husnah, Shaheed da Yaya Yusuf da abokan Husain sukayi saurin yiwa Husain rad'a a kunnen sa, kawai ya tsare Yaya Yusuf da ido, Yaya Yusuf kuwa yasha mur, kawai Husain yasaka hannun sa, ya d'ago Husnah ya kama hannun ta, ya saka cake din a cikin bakin sa har da had'awa, da hannun Husnah ya d'an ciza da sauri Husnah ta yi saurin kallon sa, ta janyo hannun ta, ta d'an cije baki, sakin Husnar yayi, itama Mardiyya cikin jin haushin Husnah ta d'auko ta saka masa a bakin sa, shima ya saka mata abaki sai ihu akeyi. Husnah kuwa tana kallon hannun Husain taga ya nufo inda take cikin sauri ta d'auki wayar Anisah da take hannun ta, ta kara a kunnen ta tana fad'ar, hello, hello zata bar gurin da sauri Husain ya ri'ko hannun Husnah wanda ba bu wayar a garesa, a take Husnah ta cije burki cike da mamaki Husain jiyowa yayi yana fuskan tar Husnah Kawai ya saka mata cake din babba a bakin ta, cikin jin haushin abunda Husain yayi mata tunda shi 'keta ce yayi mata, ai kuwa ta had'a da hannun sa ta girtsa masa uban cizo wanda sai da yace, "wash! " Dariya Husnah tayi bayan ta turo cake d'in dan yayi mata yawa sosai a bakin ta. Tafi kawai mutane ke yi har da ihun su, sudai Husnah tana bala'in burge su. Husnah kuwa gurin su Anisah ta nufa, cikin masifa tace, "wallahi nifa, na gaji da mugun tar da Husain yake yi mani ko ya daina ko nayi maganin sa" Dariya suka sakar mata Amaryar Shaheed ta ce, "kai Anty Husnah wallahi wannan dramar taku tana burge ni, ina ma ace zan ri'ka kasan cewa a tare da ku, wallahi da bani tare da hawan jinin dake damu na! " Duk sai suka juyo suna kallon Amaryar Shaheed wadda tayi magana cikin yanayin damuwa wadda har fuskar ta sai da ts nuna hakan. Cikin sauri Husnah ta ce, "ke kinga matar d'an uwa na kada ki 'bata muna wannan kwalliyar taki, kuma ma nida wan can tuzorun ai ba comedy bane mukeyi, rai na ni ne yayi da yawa, kin ga kuwa ba zan kyalesa ya ga da mata ba " Dariya suka sakar mata Anisah tace, "wallahi Husnah kin bani dariya wai tazuru? Dan Allah kuji fa, yo koda ace Yaya Husain tazuru ne, yau ai ya shafe wanda yake da mata, d'aya tun da gashi da mata biyu a rana d'aya kuma kece uwar gidan sa ko? ". Tsaki Husnah tayi, ta d'auke kanta, Amaryar Shaheed ta ce,"Anti Husnah dan Allah ki dai na kiran sa da wannan Sunan ba bu dad'in saurare". Ta'be baki Husnah tayi ta ce, "shida yake kira na da karuwa bakuga laifin sa ba, sai nida nake bare a cikin ku ko? ". A tare suka had'a baki gurin fad'ar, "Allah dai ya huci zuciyar ki Allah ya baki hakuri lallai duk kuna da laifi Husnah Husain ta bakin Ummey tace sai Allah ". Tashi taron akayi Husnah basu san ma lokacin da tabar gurin ba, tayi cikin gida mutane ta gani a cikin falon, ta raba su ta wuce gurin Ummey akan hannun kujerar da Ummey take ta zauna tare da fad'ar, "wash! Ummey nagaji sosai dan Allah gobe ki bar ni naje naga mommy na! ". Idon kowa akan su yake, Ummey tayi dariya ta ce, "Husnah manya keda kike da Auren wani a kanki shine kike zaton nice zan bar ki fita wani gurin, gashi naji Daddyn ku yana fad'ar yau ba zaki kwana a gidan nan ba sai d'akin ki, nida naso ya barki har mu shirya, amman shi yace, baya bu'katar hakan halin kune ya janyo maku". Zaro ido waje Husnah tayi cikin rawar murya tace, "yau ni... Husnah.. Na shiga d'ari da talatin ace kamar ni Husnah... Nice.. Nice.. wai zan... Zan... dawo gidan wan... Wan can tuzorun da zama , shike nan kuma hawan jinin sa zai 'karasa ni...". Kawai Husnah ta fashe da kuka iya 'karfin ta, tana fad'ar, "wallahi Ummey bazan iya zama dashi ba, dan Allah kada ki yarda a kaini gidan sa! ". Ai kuwa kowa sakin baki da hanci yayi yana kallon shirmen Husnah, ita kuwa Husnah kukan ta kawai takeyi tana doka kafa, sai aka sanya mata dariya da gud'a, ana yi mata kirarin Amaryar Husain wato ke kina nufin kishiyar ki kike son ta fara zuwa gidan nasa ta ri'ka juya ki kamar ra'kumi da akala? ". Husnah bata bi takan su ba, wata mata Ummey ne suka kama hannun ta suna lallashin ta Ummey ta ce, "Husnah share hawayen ki kinji ko? Zanyi masa magana nasan yanda yake ji dake zai iya ha'kurin d'aga maki 'kafa kinji Husnar Daddy? ". Gyad'a wa Ummey kai tayi matar cikin sanyin jiki ta ce, "Hajiya naji kin ce da ita Husnah daman kuna ri'kon yar d'an uwan kune? ". Kallon ta kawai Ummey tayi tace da ita, "Hajiya wannan yar muce, kuma yan zun matar d'an mu Husain ". Matar ta ce, "Allah sarki sannu Husnah ke kuwa kama ta ya yi kiyi farin ciki kin samu miji wanda yan mata suke rububin Auren sa, amman basu samu wannan damar ba sai ke, a gaskiya kinyi dace da mijin gogawa tsara". Cikin jin haushi Husnah ta ce, "yo ni ina ruwa na dashi ma kowa yayi mai fidda shi ni kuma ce maki akayi ba manyan mutane ne ba suka zo neman Aure na ba harda baiko na sai da akayi amman na'ki sa, shine zaki wani ce dani wai nayi dace, to wannan maganar taki ta wanda basu da masoya ne, ba ni Husnah ba! ". Kama baki matar tayi ta na kallon Husnah, cike da mamaki da al'ajab. Ummey kuwa dariya tayi ta ce, "Husnah ke nan iyayen rigima Hajiya ai sai dai kiyi hakuri bari kiga mutumen, naki wato Husain d'in " Ummey ta d'auki wayar ta ta kira Husain ta ce, "Husain kazo da hanzari ina jiran ka". Ummey na ajiye wayar tace, "sa ido kiyi kallo Hajiya ". Gyad'a wa Ummey kai kawai matar tayi. Husnah kuwa bata dai na kukan ba, kamar ma 'kara mata kaimin kukan akeyi. Husain ne ya shigo cikin d'akin da sauri yana kallon Ummey ya sauke ajiyar zuciya, matsowa yayi gurin Ummey ya ce, "Ummey gani ina fatan ba laifi nayi ba". Ummey tayi dariya ta ce "ga dai matar ka nan ka lallashi abar ka, wai ba zata yarda akaita gidan ka a yau ba, kuma gobe zata je gurin mommyn ta ". Husain kuwa ya kwa'be ya ce, "Ummey nifa bana son ganin mutum kullum baida hankali, shi yasa na ce bana son Auren yara, gashi antashi an had'a ni da jin jira, ni wallahi dama zaku barta gidan nan sai ranar da tayi hankali, kai Ummey wannan yarinyar kwata_kwata babu ranar da zatayi hankali, kuma ki rufewa mutane wannan bakin naki ko kuma yan zun nan na zane ki, dan bana son rashin kunya irin taki". D'aure fuska ya yi. Husnah kuwa cikin jin haushin sa, tace, "nifa Ummey ki daina saka tuzorun nan cikin lamari na, in dai ba son kikeyi ba mu sai da halin mu cikin ba'kin ki". Husnah na ajiye maganar Husain cikin 'bacin rai yace, "kan uban can uban waye tuzorun ne? ". Husnah ta murguda masa baki tace, "duk wanda ya tsargu dashi nake ". Duka Husain ya kawo mata Ummey tayi saurin tare sa, kafin Ummey ta dawo hannun ta tuni Husnah ta janyo ruwan sanyi ta bude robar zata zuba masa, wannan matar da mutanen gurin sukayi saurin anshe ruwan suka janyo hannun Husnah. Husain cike da fushi ya ce, "ai da kun barta tayi gan gancin ai kata wannan d'an yen aikin da yau anyi gaggawar kama maki gado a asibiti ". Husnah tace, "daman burin ka bai wuce kaga baya na ba, kuma ni nafi karfin ka wallah... Kafin Husnah ta rufe baki kawai taji saukar mari, wanda tunda Husnah take rayuwar ta da girman ta a iya sanin ta, shine mari na ukku da aka ta'ba yi mata, ba Husnah ba, hatta Husain da su Ummey sai da sukaji saukar marin. Daga ido sukayi suna kallon wanda yayi marin waye zasu gani?. Anisah dake zuwan ta ke nan ta zaro ido waje tace kai, Anty Husnar ce kika mara har hakan! ? . Ummey kuwa cewa tayi haba mi yasa kika aikata irin haka bayan kowa yasan ba halin ki ba ne?. Husnah kuwa rufe idon ta tayi sai kawai ruwan hawaye ke zuba, a take gurin yayi ja, shatin hannu ya bayyana, a fuskar ta. Kawai Husain ya ce, "haba Anty Z mi yasa kika aikata irin hakan bayan kin san kowa yana ganin girman ki da kawaicin ki, ga ilimin da Allah ya baki?. Cikin takaici ta fara magana, "haba Husain taya zaka bar 'karamar yarinya irin wannan tazo tana sa'in sa da kai bayan yanzun da, da can ba d'aya ba, yan zun fa kai ne a gaba da ita, kuma abun da take shirin aikawa aikin yan wuta ne, ya kamata a taka mata burki dan zuwa gaba zata ce, zaku ri'ka yin danbe ne ko a gaban uban kowa, tunda bata da kunya, shi yasa tun farko ban yarda da ka amince ka Aure ta ba! " Yaya Yusuf ne ya ce, "kin kyauta kamar yanda kike ganin Husain kane ne a gurin ki haka nima nake ta kamar cewar wannan yarinyar kanwata ce, kuma yanda baki son ganin an batawa wa Husain haka ita ma ta'ba ta tamkar ta'ba wani yanki ne na jiki na, dan haka, zaki iya zama anan gidan sai ranar da kanwata taji zata iya yafe maki ". Hannun Husnah ya ja suka bar gurin ya fita da ita daga cikin gidan suka shiga cikin motar sa, yaja suka tafi. Anty Z kuwa da su Husain da su Ummey zaman dirshan sukayi kowa sake da baki Husain ya ce, "Anty yau fa kin ta'bo wa kanki shi yasa ban so kika saka bakin ki ba tunda nasha sanar dake cewar nine kawai Yaya Yusuf yake iya d'aga wa 'kafa idan na ta'ba yarinyar nan, yan zun kin ga shedar ko? Kawai yan zun nasan yayi fushi dake dan haka kada ki yarda kuje tare dashi a gida d'aya wallahi zaiyi maki abunda bai ta'ba yi maki ba, amman yan zun nasan zai sauka idan Daddy yayi masa magana kinji Anty na? " Gyad'a masa kai kawai tayi cike da mamakin abun ita fa ada yanda take jin Yaya Yusuf yana fad'ar yanda yake jin yarinyar nan kuma Husain yana 'kara sanar da ita sha'ku war su ta d'auka duk da wasa ne amman Yan zun ta tabbatar". Husain ne ya kira Daddy yayi masa bayanin wani d'an sa'bani ne ya shiga tsakanin Husnah da Maman Baby gashi Yaya Yusuf yaji haushin abunda ya faru har ya ce da Maman Baby ta zauna a nan gidan ko kuma tayi gidan su". Daddy kuwa yace gashi nan zuwa. Haka Daddy ya shigo duk da cewar mata sun cika gidan amman ya d'aure ya shigo yana kallon Maman Baby yayi murmushi yace, "kinyi wauta 'yata ai tsakanin Husnah da Husain to kawai ki saka masu ido idan suna abun su, amman idan kika yi wasa kika saka biki su da kansu su Husain d'in zasu baki kunya ne, amman yanzun zan kira wayar Husnah sai na lallaba ta nasan halin zuciyar Yusuf idan yayi fushi ". Da sauri Husain ya ce, "Daddy bata da waya a hannu ta, wayar ta tana guri na tun kwanaki na anshe ta a gurin ta". Cike da tsabar mamaki suke kallon sa, Ummey kuwa ta ce, "ja iran ban za, yan zun daman wayar Husnah tana hannun ka shine ita bata fad'a ba kaima baka fad'a ba kukayi shiru? ". Murmushi Daddy ya yi ya ce, "ku jira zan kira wayar Yusuf d'in , ai kuwa Daddy na kiran wayar Husnah ce ta d'aga, Daddy ya saka hans free ya ce, "Husnah ya ya akayi kukayi fushi ne, kina son Yayan ki Yusuf ya rabu da matar sa, akan d'an wani abun? ". Husnah kuwa tace, "Daddy kawai sai ta dake ni dan kawai bata sona, tafi son wannan guzumar matar tashi, ai ni wallahi ba bu ruwa na da ita, amman kuma na riga da nayi wa ya Yaya Yusuf magana yayi hakuri ya bar ta tayi zaman ta a tare dashi amman nikam ba zani gidan ta ba, ko da ta haihu ne? Yaya Yusuf ne kawai Yaya na, amman ita kuwa tayi ta zama Yayar tuzorun nan da guzumar matar sa". Ba mutanen gurin ba hatta Daddy sai da yayi dariyar 'kuruciyar Husnah, tabbas daga jin yanda take maganar ta akwai yarinta a ciki. Husain kuwa cikin jin haushin Husnah yace, "zan kama ki ne da hannu na, sai kinyi dana sanin wannan kalaman naki ". Husnah kuwa tace, "kan ka akeji, wai mahaukaci ya fad'a rijiya". Dariya suka sakar masu, Daddy yace, "Husnah ku dawo gida kiga wani abun kuma kiji wani labari mai dad'in gaske da zan baki". Husnah najin hakan, cikin farin ciki tace wayyo Daddy daman mun dawo gamu nan a bakin kofar falon". kashe wayar Daddy ya yi yace, "kujira su 'karaso daga ciki". Husnah ce a gaba Yaya Yusuf na biye da ita d'aure da fuska, Maman Baby ce ta kafe Husnah da ido itama Husnah ta kafe Maman Baby da ido. Tashi tsaye Maman Baby tayi da alamun mamaki da far gaba. Husnah kuwa hawaye ta saki tana gir giza kai, ai kuwa kowa ya tashi tsaye yana kallon su, Maman Baby ta ce, "Huuuuuussssssnnnnnnaaaaashhhhhh......... *Comment and share* *A GIDANTA NA GIRMA* *BY NANA: KHADEEJATU* *_UMMU IHSAN_* *SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU SOSAI SON FISABILILLAH* *YA ALLAH KAJIKAN MAHAIFINA KAYI MASA RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SA SHIDA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.* *YA ALLAH KA BAIWA MAMANA LAFIYA KA BAIWA DUK KANNIN WANDA BAIDA LAFIYA NA GIDA DANA ASIBITI ALLAH KA BASHI LAFIYA AMIN YA ALLAH* *_Bismillahir Rahmanin Rahim_* 81~85 Tace, "Huuuuusssssnaaaaah"? Ta d'aga hannu tana nuna Husnah. Husnah kuwa gir giza mata kai kawai takeyi, tana ja da baya, kawai ta juya da gudu zata bar gurin, cikin zafin nama Husain ya tare ta, Yaya Yusuf ma 'karasowa gurin yayi ya kama hannun Husnah wadda take ta 'ko'karin 'kwace wa daga ri'kon da Husain yayi mata, tana ganin Yaya Yusuf ta fad'a jikin sa ta fashe da kuka, Husain kuwa damuwa ce cike da fuskar sa, kawai ya juya zai bar gurin Yaya Yusuf ya ri'ko hannun sa, ya janyo su shida Husnah sai a kusa da Ummey ya ajiye su, shima ya zauna ya fara magana. Ya ce Maman Baby zo nan ki zauna kema a kusa da Ummey ". Matsowa tayi a kusa da 'kafar Daddy ta zauna, tana kallon Husnah ita kukan takeyi. Bayan kowa yayi shiru ne sai shashshekar kukan Husnah da Anty Z kawai akeji, Daddy ne yayi gyaran murya ya ce, "Zarah da alama dai wannan ita ce, Husnar ki ko? ". Gyad'a wa Daddy kai tayi, Husnah tace, "ni Husnar ta ba ce, ni ban ma san taba! ". Murmushi kowa yakeyi dan gaskiya kam yan zun kowa yaga tsan_tsar kaman da sukeyi da junan su. Aunty Z ta ce, "Husnah wallahi ko da kin'ki ko kiso nice Anty Zarar ki wadda baki da wadda ta kai ta a fad'in duniyar nan, kuma koda kin furta cewar baki ma san ni ba, zan yar da, domin halin ki ko kwayar zaira ba zan iya man tawa dashi ba" Kallon ta Husnah tayi tace, "ni ban san ki ba na 'kara fad'a ni bani da kowa wanda zan kalla nace dashi nawa, sai Daddy da Ummey da Yaya Yusuf, amman duk wani wanda zan kalla daga bayan hakan to abokin had'uwa ne da rabuwa, dan haka kije can ki nemi "yar uwar ki ba ni ba ehe". Murmushi Anty Zarah tayi ta ce, "Allah sarki goggo Marka da Baban mu dasu Indo ko suna wace duniyar ne a yanzun? ". A take jikin Husnah ya d'auki rawa ta yi sauri ta tashi tsaye ta ce, "wallahi duk cikin wannan mutanen da kika ambata bana kaunar d'aya daga cikin su, kuma indai ina amsa Sunan Husnah wanda mahaifiya ta, ta za'bo ta rad'a mani wallahi sai na d'aukar wa mahaifiya ta fansa, kuma duk wanda yake da sa hannu a mutuwar ta, sai naga tashi mutuwar, kuma kamar yanda Baban su Indo ya nuna muna cewar baya son mu baya son mahaifiyar mu, nima bana son sa kuma bana kaunar sa, haka zalika Marka sai tayi mamakin abun da taso mu zama bamu zamo ba, sun sayar dani ita da mijin ta a gurin mutanen da basu san su waye su ba, dan kawai su halakar dani Allah bai soba, aka koyar dani miyagun dabi'u babu sallah babu salati babu ambaton Allah sai da nazo gidan nan, an kwashe duk wasu abubuwa nawa wanda zan ri'ka kallo ina tuna rayuwar da mukayi, ina kallon mahaifiya ta da yar uwa ta, wadda wani lokacin idan ina kallon photon nasu, nakan tuna da ibada nakayi duk da ban san ko mai ba, duk wannan Abubuwan sai na d'auki fansar su akan wanda yake da alhakin aikata hakan a kain! ". Tun lokacin da Husnah ta soma magana cikin tsana nin fushi da yanda take sakin magana wadda ya kama ta, a kwatse ta, sai Anty Zarah ta kama ri'kon a barta, tayi dan haka ne zai saka ta iya sauraren ta, ai kuwa kowa ya yi shiru, har ta gama. Anty Zarah ce ta tashi tsaye ta 'karasa gurin Husnah ta rungume ta ita ma Husnar run gume Antyn ta tayi, suka saki kuka a tare sai da sukeyi mai isar su, sannan Antyn Z ta ce, "Husnah daman kina a raye a kusa dani, aka sanar damu cewar masu satar mutane sun sace muna ke, Husnah kin san irin shiga tashin hankalin da nayi, a kan haka, ko Aure na ce ba zan yi ba, har sai ranar da na ganki, Husnah dan Allah kiyi hakuri ki saurare ni, nasan kanwata tayi farin cikin had'uwa dani sai dai fushin zuciya ne da kuma dukan da nayi maki wanda nasan ba zanyi nadamar sa ba, sai dai naci gaba da lallashin ki, Husnah ki zauna miyi magana ta fahimta kinji "yar kanwata? ". Sakin ta Husnah tayi ta dawo kusa da Yaya Yusuf ta jin gina da jikin sa tace Anty Zarah nayi farin cikin ganin ki amman kuma yan zun haushi kike bani, kin ma tuno mani ashe ke "yar adawa tace, kije can da naki kannen nima ga nawa Babban Yayan, ko Yaya na, yauwa Daddy gani wane albishir ne zaka bani? ". Kowa dariyar Husnah yakeyi ga hawaye tanayi, tana gogewa na farin ciki amman ita ala dole fushi takeyi. Daddy yace, Husnah ta, sun ta'ba mani "yatako? Rabu da su zan yi maki maganin su, yan zun dai mu dawo maganar farin cikin ganin yar uwar ki, Husnah kiyi hakuri kinji ko?, kuma Antyn ki duk abunda ta sanar dake gaskiya ne, nine da baffan ku muka matsa mata ta yarda ta Auri Yusuf amman tace ita fa sai ranar da kika dawo hannun ta, duk yan uwan ta sunyi Auren harda kannen ta, amman ita bata sa ranar Auren ba, ganin haka ne kuma na yaba da hankalin ta, shi yasa na matsa wa Baffan ku, shima yaatsa mata, duk da hakan sai da Husain ya baro 'kasar da yake karatu ya zauna da ita har ta yarda ta Aure sa, kuma koda akayi Auren kullum da photon ki take kwana dashi take tashi, kuma kullum cikin kuka take, sai da Yusuf ya d'auke photon ya 'boye san nan ta rage yawan kukan, kuma tun lokacin da na samu accident din nan na ganki Allah ya d'ora mani sonki, kuma lokacin da Yusuf ya ganki shida Shaheed tuni suka fahimci lallai akwai wata alakar dake tsakanin ki keda Zarah, kuma cikin ikon Allah har kika dawo gidan nan da zama baku ta'ba had'uwa da ita ba, mu kanmu muna mamakin irin wannan tsabanin had'uwar da kuke samu, dan haka Husnah ina taya ku murnar ganin junan ku". Sai kuma magana ta biyu shine Husnah ke da Husain mun gaji da ganin ku a cikin gidan nan yau d'in na zaki bi mijin ki, ku tafi gidan ku, kuma ni da kaina zan bi bayan ku dan naganar wa ido na, sashen da kika zaba, dan ko d'akin Husain ne kika ga kin fi so to a can zaki zauna, kunji ko? Kece uwar gidan sa sai gurin da kike da bu'katar zama zaki zauna, kuma akwai wasu kayan d'akin da na siya maki da wanda Yayan ku Yusuf ya siya maki, duk zamu saka a kawo maki abun ki a cikin sashen ki, masu d'aura wa zasu d'aura maki abun ki, zuwa da safe dan haka Husain idan gurin bai isa ba zaka 'kara mata da naka sashen ". Da sauri Husain da Husnah suka d'aga ido suna kallon Daddy wanda ya d'aure fuskar sa babu wata alamar wasa a cikin maganar sa, kawai Husnah taci gaba da kukan ta, Husain kuwa cewa yayi, "Daddy akwai kayan d'akin da na zuba a kowa ne sashen kuma kasan ni ba tarkace nake so ba, shi yasa na saka irin wanda nake so, kuma, ma Daddy ai bada ita na siya ba, amman kuma tunda gashi tayi shishshigi sai ta d'auki na can baya kawai, basai an kawo wasu kayan d'akin ba". Hararar sa Husnah takeyi ta ce, "kai Daddy dan Allah ku barni nayi zama na anan gidan dan ni ya fiye mani ko wane a kulki ne, irin na tuzoru Allah Daddy ". Anty Zarah ta ce, "Husnah wai ke miye yasaka kwata_kwata baki da hankali ne, mijin naki ne, kike kira da wannan Sunan? " Yaya Yusuf ne ya ce, "kin ga malama kibar su, mana suyi fad'an ban kwana dan nasan daga nan gidan an ajiye fad'a sai kuma soyayya da zasu 'kulla". Ummey kuwa cewa tayi, "Zarah dan Allah kibi komai a sannu indai Husnah da Husain ne sai dai ido kawai, ni kam zan raka "yata har gidan ta, yauwa Husnah ga goggo ki Hajiya Turai Matar baffah ki Isah ". Husnah kuwa 'bata fuska tayi tayi shiru bata kalle su ba, har sai da Ummey ta sake mai_maitawa , Husnah ta ce, "Ummey nifa bani da kowa kuma duk wanda yake fa alaka da rabani da Anty Zarah babu ruwa na dashi, kuma ni fa Ummey ki baiwa Daddy hakuri ya bar ni a yi zama na a kusa da ku ". Dariya Hajiyar tayi ta ce, "ni kuwa Husnah tun lokacin da na ganki nake da tabbacin cewar ke yar muce, ni nayi ma mamakin yanda akayi Husnah bata gane cewar ke kanwar ta bace, gaku a gida d'aya sai da naji wannan maganar na fahimci cewar ashe baku ta'ba had'uwa da juna ba, gashi kuma Husnah har nasanar da su baffan ki dasu goggon ki Amina nasan duk suna kan hanyar zuwa su ga "yarsu Husnah ". Husnah ture baki tayi, gaba, Ummey kuwa dariyar Husnah takeyi, zuwa can kuma Daddy yace, "Husain Husnah 'korafin ku bai 'karbu ba yan zun zaku tashi mu tafi, kuma tashin kawai ". Yaya Yusuf ne ya ri'ko hannun Husnah da Husain suka tashi tsaye yace, "to goggo dan Allah idan sun iso suyi hakuri bayan sati biyu zuwa ukku sai su ziyar cesu a gidan su ". Cikin dariya tace dashi, "ko kuma muje raka yar mu gidan mijin ta ba". Haka kuwa a kayi su baffah na zuwa aka shiga cikin motoci dan ko Husnar basu gani ba, suna zuwa duk an shiga motoci Husnah Anty Zarah Ummey Daddy motar su d'aya Anisah Suhailah Safiya Husain Yaya Yusuf Shaheed motar su d'aya . Yan rakiya ma sun shiga naso motocin suka d'auki hanya sai gidan Husain. Tun daga farkon unguwar, ake hango wani had'add'en gida, a gaskiya tsayawa fad'ar had'uwar gidan 'bata lokaci ne. Masu gadin gidan ne har mutum ukku suka bud'e 'katon get d'in shiga cikin gidan sukayi sunyi tafiya sosai suka 'kara riskar wani get din mutum biyu ne suka bud'e masu get din suka shiga sai harabar gidan flowers masu kyau da sheki da d'aukar ido wasu kuma masu fidda wuta, gida ne hadden gaske yanayin gidajen turawa, part ukku ne a gidan a jere, kuwa duk irin d'aya, gidan amman kuma duka 'kofar shiga cikin gidan d'aya ce, haka suka shiga ko ina glub glub ne masu haske wani babban falo ne suka tsaya suna kallon 'kofofi guda ukku, Daddy ne ya ce, "Husnah ki za'bi wanda kike, so a cikin ukkun nan". Husnah ta saka hannun ta ta nuna masa 'kofar dama, Daddy kawai ya kalli Husain kuwa cewa yayi, "Daddy ta dai shiga wan can na 'karshen ". Husnah kuwa tace yauwa Daddy duka biyun nake so, na tsakiyar da wan nan din na damar sa". Wani irin zabura Husain yayi ya ce, "a gaskiya Daddy ba zan yarda ba, sai dai ta d'auki wannan din na yarda amman banda wannan na tsakiyar nawa ne, kuma kasan na dad'e ina gyaran sa". Daddy yace, "bani keys din su biyun duka na d'aukar wa 'yata sai dai ka ro'keta ko aro ne ta baka. Ganin yanayin Daddy kawai sai Husain ya bada makullin yana harar Husnah ita kuwa murmushi ta sakar masa, Daddy ne ya bata makullin, ta bud'e na gefen damar suka shiga sudai yan rakiya dariyar su kawai suke kwasa, wannan Amaryar da angon sai kallon kawai a cikin lamarin su. Falone babba sai d'aki ukku acikin SA KO wane da bayi a cikin sa, gashi sunji gadajen alfarma da zannen gado GA labulai purple wani d'akin kuma lemon green d'aya d'akin shine mai red, a gaskiya abun sai sam barka. Kujerun ma abun kallo ne dan zaka rantse ba'a najeria kake ba, a yurai kake kai gidan dai komai yaji. Yan ganin d'akin na fita Ummey da Daddy suka zauna suka fara yi masu nasihar su zauna lafiya yan zun da da can ba d'aya bane Aure sukeyi a yanzun zo mu zauna zo mu sa'ba. Fad'an zaman Aure sosai akayi masu harda su Yaya Yusuf haka su baffah sunyi masu nasiha sannan aka kira wayar Daddy yace, "zan fita ansa kira idan kun gama ku jira ni, Hajiya zo kuga d'aya d'akin na Husnah ". Ummey tayi murmushi ita da su goggo kawai suka fita aka bar su Anisah dasu Yaya Yusuf. Yaya Yusuf ne yace kai kuje ku gano kuma kada a baku labari amman Husnah ki jira muyo maki video camera ki gani, haka su Anisah suka fita aka bar Anty Zarah da Shaheed da Yaya Yusuf da Husain. Wayar Yaya Yusuf ce tayi ringing kawai ya ce "ina ga sun kasa bud'e 'kofar ne Shaheed jeka ka bud'e masu" tashi Shaheed yayi ita ma Anty Zarah tace ni ba zani na gano ba, ai dole ne naje naga gidan 'kane na" Mere baki Husnah tayi ta d'auke kanta gefe Yaya Yusuf dariya kawai sukeyi shida su Shaheed lallai Husnah bata da wayo 'kuruciya ce zallar ta a kan ta, aka bar Yaya Yusuf kawai, Yaya Yusuf ya ce, "Husnah kin ga har yanzun basu dawo ba ko?, bari naje na gano miye ya tsayar da su? ". Husnah bata kawo komai a ranta ba tace, "ok". Fita yayi yana dariyar wautar Husnah, Husain kuwa cewa yayi "wallahi shi yaro duk inda yake sai anyi masa na babba da yaro, wai ke 'katuwar mace dake ace kamar ki za'ayi wa wayau a tafi a barki wallahi nikam dai an had'a nida jinjirar yariya shi yasa kika cika rashin kunya ko kuwa dai dan kin saba yawon karuwan cin naki shine zaki zo kiyi wa mutane shiru kamar baki fahimci miye suke nufi ba?. Husnah kuwa tana jin abunda Husain ya fad'a kawai ta fasa uban ihu ta tashi da gudu zata fita, kawai Husain ya riga ta a bakin kofar ya rufe ya yi tsaye yana dariyar 'keta, Husnah kuma jikin 'kofar tazo tana dokawa, shiko sai dariya yake yi, yace, "yarinya taya zaki zo kiyi wa mutane wasar kway_kwayo? Ni riga da na gano nufin ki yarinya dai na ma wahalar da hawayen ki" Husnah kuwa cikin kuka ta ce, "mugu kawai wallahi yau sai ka maidani gida ". Dariya kawai yakeyi tun lokacin da ya gano cewar Husnah kukan gaskiya takeyi bana wasa ba. Zauna tayi tun tana kuka ana jin muryar ta har takai ga muryar ta bata fita, Husain kuwa tun yana yi mata dariya har yazo ya zauna ya d'auko handkerchief ya ri'ke sa a hannun sa shima ya zauna yana kallon ta, har sai da yaga fuskar tayi ja, yace, dan sun tafi sun barki a gidan kine kika zo keda ma naji kin zabi har part biyu saboda tsabar zari irin naki". Husnah dai bata ce dashi komai ba har ya gaji da surutun sa yayi shiru abun sa yasaka handkerchief din yana goge mata hawayen idon ta yana dariyar yau fa abun yazo kamar Husnah mai shegen baki wadda bata barin ta kwana ita ce yau ta kyalesa yake cin karen sa babu babba ka. Suna nan zaune sunyi shiru har 'karfe sha d'aya na dare, yace, "yarinya kima tashi ki kwanta ko kuma kiyo wanka ki sauya kayan jikin ki, kuma kiyi sallar magriba da Isha'i nasan duk bakiyi su ba, saboda tun kayan da mukaje dinner ne a jikin ki, da alama ma rabon ki da kici abinci tun safe yarinya idan olsa ta kama ki ke kika sani, nikam bari ma ki gani". Tashi yayi ya bud'e 'kofar ya fita Husnah kuwa da harara take bin sa. Tashi tsaye tayi tana tan gad'i kamar wadda tayi shaye_shaye, a kan gado kawai ta fad'a tayi kwanciyar ta " Koda Husain ya shigo cike yake da mamakin Husnah, dan kwanciyar da tayi har tayi bacci. Ajiye kayan hannun sa yayi, ya dawo jikin gadon ya kama dukan filo har sai da Husnah ta tashi cikin jin haushin dariyar da Husain yakeyi mata yace, "bakiyi sallar ba ko? ". Kyalesa tayi ta tashi zaune cikin muryar ta wadda ta sha'ke tace, "wai miye ruwan ka dani ne, ka kyaleni mana". Ai wallahi ba zan kyaleki ba, haka kawai kizo ki saka Daddy da Ummey suyi fushi dani suce na barki da yunwa kuma ban kula da addinin ki ba?. cike da jin haushin sa Husnah ta tashi tsaye ta ce, "ina bayin yake ne saura kuma mutum yaci gaba da yi mani dariyar ". Dariya ya sakeyi yace, "ke jiki yarinyar nan wallahi dole ne kiyi sallah ". Nuna mata bayin yayi da hannun sa, kawai Husnah ta nufi bayin, har ta isa bakin kofar bayin ta jiyo tace, "sai shegen shishshigi kawai mutum ya iya". Ta shige warta cikin bayin ta rufe harda keys,. Dariya Husain yayi ya d'auki abunda ya zo dashi ya had'a tea ya kawo farfesun kayan ciki ya bud'e kaza biyu da hollondia dash exectic da dai sauran su, da kayan marmari iri daban_daban. Koda Husnah ta fito ko kallon sa batayi ba, ta soma neman hijab dan gyale ne tazo dashi, har ta gaji bata samu ba, gurin Husain ta dawo tace, "to ai sai ka kaini gidan Ummey na nemo hijab nayi sallah ". Kyaleta yayi ya tashi kawai ya bud'e waydrop kawai ya d'auko hijab d'aya ya bata, ta ansa ya shimfida mata sallaya, ta tayar da sallah, kallon ta kawai yakeyi, har ta 'karasa ta cire hijab d'in tazo zata kwanta yace, "malama baki gama ba, kizo ki ci abinci kafin ki kwanta " Kwanciyar ta tayi tace, "nifa wallahi idan mutum ya dameni, sai dai yaji haushin abunda zanyi dan nifa idan ina fushi da mutane da yawa kowa haushin sa nake ji". Shima kuwa yace, "indai nine dik abunda kika yi kanki bada ni ba saboda ni na riga da na saba da halayen mutane iri daban_daban musamman ma naki ". Shiru yaji koda ya duba har tayi bacci. Shi kam cin abincin sa yayi yana gamawa ya tashi ya fita, sai da Asubahi ya zo ya tayar da ita da ket ta tashi, tayi sallah ta koma sai 'karfe goma da rabi dai_dai ta tashi. Akwati ne dozin ta gani pink a gefen gadon ta, kawai ta tashi tayo wanka tazo ta bud'e babban atamfa ce duk an dinka su, riga da siket da riga da zani fisis tsaki kawai Husnah tayi ta bud'e wani, les ne da materials DUK an d'inka sa ta ajiye ta janyo kusan na takwas riga da wando ta gani irin_iri kawai Husnah ta d'auko tace, "haba yan zun dai naji magana " Saka kayan tayi ta rufe akwatin ta janyo wani akwatin na hud'u takalmi ta gani sai da ta za'ba ta darje ta saka taje gaban madubi ta gyara gashin kanta ta d'aure da ribom ta feshe jikin ta da turare tayi tafiyar 'kofar ta bud'e sannu a hankali taji ta bud'e ta sauke ajiyar zuciya kawai ta fito ta zaga ko ina, falo ta fito tv ta gani a kunne a kallon boll tsaki kawai tayi ta nufi gurin ta d'auki remote d'in ta dawo akan kujera ta sauya tasha ta dawo bollywood, Indian series akeyi tayi zaune tana kallo, kawai taji an anshe remote din kofa da duba Husain ne zaune a 'kasa yana kallon ta yace, "wallahi kin raina ni da yawa yarinyar nan nifa bana son raini". Husnah ta ce, "Allah ko? Wai ma nikam miye ya zaunar dakai cikin sashe nane? bayan ga naku sashen can, kwaya d'aya " Kallon kin ma raina mani da wayau yake yi mata yace, "wallahi kin ma ci uban rainin wayau wato dai ke kullum da abunda kike tsarawa ko? To bari anjima a kawo mani Amarya ta ki gani, wallahi sai kin nemeni kin rasa ina can ina shan soyayya ta da Amarya ta". Ta'be baki Husnah tayi tace, "oh ! dai wannan uwar guzumar matar mace mai kama da irin 'kattan nan da suka tashi kashe ka a gidan mu" Tsaki yayi ya tashi tsaye yace, "ga abincin ki nan da Ummey ta aiko maki dashi ni kinga tafiya ta, keda gani na sai ranar da muka fito shakatawa nida Amarya ta". Husnah kuwa tace "ayi dai mu gani in tusa na hura wuta". Dariya yayi ya fita Husnah kuwa tea kawai tasha, tayi kwanciyar ta, haka Husnah ta yinini ita d'aya daga kallo sai sallah sai bacci. Sai da safe Husnah na kwance a falo tana bacci, Husain ya shigo kallon ta yayi yace, "dube ta kamar ta kwarai ". Ina kanta yake, yake dokawa, bud'e idon ta tayi, tana ganin Husain kawai sai ta tashi zaune tace lafiya? Husain yace, "malama ki tashi muje ki bud'e mani sashe na muyi magana da ku ". Kamar ba zata tashi ba, kawai sai ta tashi tana zuwa d'akin ta ta d'auko makulin ta bashi tayi kwanciyar ta, shi kuma ya fita, har magriba bai ga Husnah ba, har akayi isha 'i har 'karfe goma da rabi kawai Husain ya sameta zaune ta buga uban tagumi, yana kallon ta yace, "mikike tunani ne kuma tun d'azun nake neman ki baki zoba tun safe har zuwa wannan lokacin ". Budar bakin Husnah keda wuya, tace, masa "ina waya ta" Ko kallon ta baiyi ba ya tashi tsaye yace, "tashi muje ke nake jira". Kin tashi tayi har ya gaji da jiran ta ya tafi. Satin Husnah ukku a gidan Husain Amman kullum cikin fad'a suke, Husain yayi_yayi akan Husnah tazo suyi magana da ita da Amaryar sa amman ta 'ki zuwa, yauma kamar kullum Husnah ce zaune tana yankan farce, Husain ya shigo kawai ya kara mata waya a kunne. Ummey ce tace, "Husnah ya kike ya na ba'kun ta?" shiru Husnah tayi, Ummey ta ce, "Husnah ki dai na fushi dani akwai dalilin da yasa kowa bai nemeki ba, saboda muna fatan ki daure ki zauna zaman Auren ki kamar yanda nima na nake zaune da nawa igiyar Auren, Husnah dan Allah kiyi hakuri kiyi biyayyar Aure, kuma na baki umarnin kije inda yake neman ki, zai had'a kanku ne keda matar sa, Husnah indai kin yarda da cewar nice maman ki ba Maman mijin ki ba tashi ki tafi". Tashi kawai Husnah tayi ba tare da tayi magana ba, shima tashi tsaye yayi yace, nsgode Ummey, suka kashe wayar. Tunda Husnah ta tashi ya shiga gaba tabi bayan sa, sai yau Husnah ta , ta'ba zuwa bakin 'kofar tun farkon zuwan ta gidan, d'akin na tsakiyar ya bud'e suka shiga a kwance suka same Mardiyya tana charting da wayar ta, Husain ne yayi sallama, Husnah kuwa kallon yanayi da tsarin gurin kawai takeyi. A kan kujera ta zauna ta d'ora 'kafa d'aya akan d'aya, Husain ya zauna bayan ya zauna ne yayi salatin Annabi muhammad Sallalahu alaihi wasallam, sannan yayi godiya ga Allah da ya nuna masu wannan ranar sannan yace da Husnah, "Husnah dake zan fara domin ke uwar gida duk da kasan cewar Mardiyya tana gaban ki nesa ba kusa ba, to ina son ku zauna lafiya ku fahimci junan ku bana son fad'a bana son raini ya shiga tsakanin ku" Mardiyya nadawo kanki kada ki ga cewar kin girmi Husnah yasa ki raina ta, aa ban yarda ba, itace gaba dake a gidan nan bana son ki raina ta bana son fad'a kuyi zaman ku na lafiya, Mardiyya zan koma jan hankalin ki, Husnah 'karamar yarinya ce, amman bata d'aukar raini da wulakanci idan kika zauna da Husnah zakiji dad'in zama da ita, amman idan aka samu sa'banin haka to wallahi, zan koma gefe ne nayi kallon ku, nidai a iya sani na, Husnah bata da daukar magana komai abun mutum indai ba shine ya tsokane ta ba, to babu ruwan ta da mutum, Husnah kada kiga kamar ina yabon kine a gaban ta aa iya gaskiya ta nake fad'a , ke kuma Mardiyya kada kiga kamar ina goyon bayan Husnah ne aa iya gaskiya ta nake fad'a nasan halin ta fiye da tunanin mai tunani nasan abunda zata iya aikata wa ko miye ". Shike nan sai kuma rabon kwana zaku iya za'ba wa kanku yanda kuke so. Husnah dai iya kacin ta bin su da ido, Mardiyya kuwa sai cika take tana batsewa sai hura hanci takeyi tana gun guni, Husain ya ce, ku nake saurare". Mardiyya ta ce, "wane rabon kwana kuma bayan wanda kayi kwana biyu_biyu to amman nifa gaskiya Husnar nan kada tace zata takani yanda take so, dan bazan d'auka ba, kuma ni wallahi ba bu wanda ya isa Ina tare da miji na yazo ya tsare ni da ido. Husnah kuwa murmushi tayi tace, "ka gama ko dan zan koma ne naci gaba da abunda nakeyi, bana son sai na tashi a dawo dani". Husain yace, "zaki iya tafiya". Tun daga wannan ranar Husain da Husnah basu 'kara had'uwa ba har sai ranar da Ummey suka zo da su Anty Zarah, Husain na zaune da Mardiyya su Anisah kuwa suna tare da Husnah suna labarin su, Husnah ta ce, "yauwa Daddy Ummey zan dawo wannan d'akin da zama na gaji da zama wan can sashen". Husain da Mardiyya cike suke da mamakin Husnah wadda ko kallon inda suke batayi ba. Daddy yayi dariya yace, to ai daman makulin nakine kuma suna hannun ki, ki dawo warki kiyi zaman ki" Husnah ta ce, "Daddy ya ari makulin bai dawo mani dashi ba". Daddy yace, "ka dawo mata da makulli ta yanzun nan". Bata makullin yayi, ba tare da yace uffan ba, Husnah kuwa murmushi tayi, haka suka yini sai dare suka bar gidan, Husnah kuwa rufe d'akin tayi ta rufe 'kofar shiga sashen ta, ta bud'e sashen Husain ta shiga, sai da ta za'bi d'akin da take so ta zauna. Husain kuwa tattara komai nasa yayi yabar mata sashen, har Auren su ya kai wata hud'u tsakanin Husnah da Husain babu wani ci gaba Mardiyya kuwa hankalin ta kwance Husain ya zama nata, sunje ganin gida yafi biyar kuma su Anisah na zuwa gidan. Yauma kamar kullum Husnah ce zaune tana kallo ga baki d'aya hankalin ta ya tafi akan film din bata ma ji shigowar su ba, sai daga baya ta lura da mutane zazzaune, Husnah yi tayi kamar bata gan suba, Husain ne ya shigo dai dai lokacin Mardiyya da abokan ta na fad'ar, "Husnah wallahi sai munyi maki d'an banzan duka a gidan nan, babu uban da zai iya kwatar ki a hannun mu, kuma Husnah ki sani sai kin bar wannan gidan da kike mulki a cikin sa". Murmushi Husnah tayi ta ce, "Husnah taje koyon sallama kuma yiwa Husnah duka a dai dai wannan lokacin tamkar yin kisan kaine a gaban kotu". Su shidda harda Mardiyya sunyo kanta ke nan Husain ya daka masu wata uwar tsawa ya sai ya d'aure su, har Mardiyar sai ta bar masa gida. Duk a razane suke kallon Husain cike da mamaki Mardiyya cikin rawar murya tace, masa, "yaushe ne ka dawo?". Ba tare da ya bata amsa ba kawai ya fita zuru_zuru sukayi, Husnah kuwa dariyar ta kawai takeyi tace, "indan Husain ne baku san halin sa ba, kema Mardiyya idan na fahimce ki to har yan zun baki san waye mijin ki ba, zaune ne kawai kike dashi har na tsayin wata hud'u zuwa biyar amman nikam halin Husain sai dai na bada labarin sa, da zakiyi mani biyayya da baki sha wahala ba gurin karantar halin sa ba, gashi dai yan zun zaki d'an dani station kiji dad'in ki Mardiyya matar Husain ". Kuka Mardiyya ta saki yan sanda ne mata suka shigo suka tasa 'keyar su a gaba suka bar gidan dasu. Shima fita yayi Husnah kuwa kamar bata gurin. Su Mardiyya sun sha matu'kar wahala a gurin yan sanda kuma Husain ya'ki zuwa belin su har sai da iyayen su suka je da kansu, Husain bai sake waiwayar Mardiyya ba, kuma baya d'aukar wayar ta, sai da iyayen ta suka je suka sanar dasu Daddy, ai kuwa Daddy yayi fad'a sosai da kansa yaje gidan ya d'auki Mardiyya da iyayen ta, sukaje gidan sosai Daddy ya tsare Husnah da Husain yayi ta zagin su, ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, ranar duk hankalin su ya tashi, kuma Daddy yace, Mardiyya ciki ne da ita wata hud'u idan kuka yarda cikin nan ya sami wata matsalar to sai kunyi na damar sani na a matsayin mahaifin ku! ". Tashi yayi ta fita ba tare da ya saurari d'aya daga cikin su ba. Iyayen Mardiyya kuwa Daddy ya burge su sai kuma suka dawo jin nauyin sa. Mardiyya kuwa cike take da mamakin irin yanda akayi Daddy yayi wa su Husain da Husnah haka bayan tasan irin son da yakeyi masu. Husnah kuwa murmushi tayi tace, "yau mun taro Daddy amman ni kam yau na tsani kaina ace Daddy yau nice na ta'bo sa ". Husain kuwa cewa yayi "hankalin ki ya kwanta, Mardiyya yau kin bar mani tarihi a rayuwa ta, kizo ki zauna kiyi yanda kike so bazan 'kara cewa dake komai ba". Shiru kawai Mardiyya tayi, tana kallon yanayin su, Husnah tashi tsaye tayi tace, "idan kina da bu'katar wani abun koda na cin mutumci nane zaki iya yi mani magana " kawai ta shige warta cikin d'akin ta. Haka suka bar ta cikin falon a zaune, tun daga wannan lokacin Mardiyya ta dawo sashen ta, bata sake zuwa gurin da zasu had'u da Husnah ba, Husain kuwa ya kanzo ya tambaye ta abunda take bu'kata ya kawo mata amman babu wani sakin fuska kuma har yan zun da ake maganar sati biyu da faruwar wannan abun Daddy baya d'aga wayar Husain kuma ko gidan yaje Daddy baya kula sa. Sai da akayi sati biyar Daddy ha'kura ya fara kula su, Mardiyya ce zaune tana kallo Husnah kuwa tana sanye da 'kanan kayan ta sai 'kamshi ke tashi kam badai 'kamshi ba, Husain kuwa fitowa yayi da kayan motsa jikin sa, yana zuwa kujerar da Husnah take zaune ya zauna akai, Husnah kuwa tashi, zaune tayi tace, "malam lafiyar ka kuwa? Zaka zo ka zauna mani akai na? ". Kyaleta Husain yayi, Mardiyya tayi dariya ta ce, "ni kuwa tun ban fahimci miye kuke ciki ba, har nazo na fahimci komai ace watan ku bakwai da Aure amman kullum cikin fad'a kuke, ya kamata ku zauna lafiya ". Husnah da Husain kuwa kamar basa gurin kawai Husnah ta tashi tsaye zata shiga cikin d'akin ta, ke nan sukaji saukar halbi tare da ihun Mardiyya, ai kuwa da gudu sukayo kanta sai jini ya fara zubar mata a gefen ciki, Husain da Husnah rud'ewa sukayi suna kiran Sunan ta, amman inah mutane ne kawai suka dirar masu, sanye da fuska ba'ka, da bindigogin su a hannun su, kawai suka ta'ka Bindigar su akan Husain da Husnah wadda ga baki d'aya suka shiga cikin tsananin tashin hankalin ganin yanda jikin Mardiyya ke jijjiga ga jini na zubar mata. Kawai aka saita kan Husain suka halba, jin kake darammmmmmmmmm....... *Comment and share* _Kada ku manta yau biyu ne... _ *A GIDANTA NA GIRMA* *BY NANA: KHADEEJATU* *_UMMU IHSAN_* *SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU SOSAI SON FISABILILLAH* *YA ALLAH KAJIKAN MAHAIFINA KAYI MASA RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SA SHIDA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.* *YA ALLAH KA BAIWA MAMANA LAFIYA KA BAIWA DUK KANNIN WANDA BAIDA LAFIYA NA GIDA DANA ASIBITI ALLAH KA BASHI LAFIYA AMIN YA ALLAH* *Godiya da jin jina a gareka masu comment da sharhi mai 'kara mani 'karfin gwiwa, kuyi hakuri kwana biyu ban samu amsa maku Comment din ku ba, amman na duba ina godiya sosai* *Djamila Ali* *NafseyAbraham* *Mommy na* *Halimatus sadiya* *Maman nana* *My takwara* *Maman hafsa* *Sarah* *Maman Muhammad* Da sauran mutanen gidan group din *A GIDANTA NA GIRMA* *_Bismillahir Rahmanin Rahim_* 86~90 "kawai kaji saukar alburushin bindiga saitin Husain darammmm, Husnah kuwa fad'uwa tazo zatayi 'kasa cikin zafin nama Husain ya taro ta yana ihun kiran sunan ta, "Husnah! Husnah!! Husnah!!!, miyasa kika aikata irin haka a gare ni bayan kin fi kowa sanin bana son abu koda kwayar zaira ne na cutarwa ya sameki, dan Allah kada ki mutu kibar ni, nine nafi da cewa dana kare lafiyar ki, ba keba, Husnah dan Allah kada kiyi mani haka, idan babu ke atare dani bana iya rayuwa Husnah! ". Husain kuka yakeyi harda hawayen sa yana gir giza Husnah wadda aka zo halbin Husain a kan sa, tayi saurin ture sa gefe saboda ita ce kawai ta lura da lokacin da za'ayi halbin kawai aka halbe ta a ka fad'ar ta, wanda yayi halbin kuwa cikin hanzari ya cire fuskar da yasaka, yana zarar ido, sauran ma duk suka cire abun, sukayo kansa suna fad'ar, " lallai jaga ka jawo wa kamka matsala waye yace maka ance ko rauni mubar ta tayi, bayan kasan da cewar aikata hakan a gareta tamkar rasa taka rayuwar ce". Cikin tsananin tsoro yace yan zun ku ba zaku iya taimako na ba ne?. Duk suka had'a baki gurin fad'ar, "to zamu iya taimakon ka Amman sai ka kashe wannan mutanen cewa da Husain wanda ya soma baiwa Husnah taimako gaggawa, suna juyowa a kan Husain suka ga yana 'ko'karin cire mata bulet din da yar askar dake hannun sa kawai suka zuba masa, ido. Da gudu ya tashi ya shiga cikin d'akin Husnah yaje ya watse lokar kayan Husnah ya d'auko akwatin sa na taimakon gaggawa, ya dawo a rud'e shifa har yama manta da wata Mardiyya kan Husnah ya yo su kuwa duk suna tsaye suna kallon sa, cikin ikon Allah yayi kokari ya cire mata bulet din ya saka mata magani ya wanke gurin ga jini duk yayi kaca_kaca dashi har a fuskar sa, sannan ya gyara mata gurin ya saka cotton fa plaster yana gawa ya kama Husnah ya rungume wadda ko motsin batayi. Mutanen ne sukayi ido a tsanin su, Husain ba tare da sanin saba suka daka masa bindiga a kan sa, a take jin sa da ganin sa suka d'auke sai jini, kawai ya fad'i 'kasa a some, su kuwa d'aukar Husnah sukayi suka tafi da ita. Kiran wayar Husain Yaya Yusuf yakeyi wanda suke a zazzaune kusa da Daddy wanda dukan su sun rasa mike faruwa ne, dasu suka rasa natsuwar su, duka Anty Zarah kuwa da fad'uwar gaba ta kwana sai wani irin zazzabi da ya rufe ta, Yaya Yusuf shima ya rasa miye yasaka baya cikin natsuwar sa, dole ne ya d'auko su Anty Zarah suka dawo gida gurin su Ummey, abun mamaki duk gidan haka suka tashi cikin wannan halin, Shaheed ne ya shigo ido tsakiyar kai ya ce, "Daddy nayi mummunan mafalki akan su Husnah da Husain kuma gashi ina ta kiran wayar su su duka ba'a d'aga wa". Ummey tace, "ni kaina nayi ta kiran wayar Husnah da Husain harda Mardiyya amman ba bu wanda ya d'aga daga cikin su, na rasa a ina suka shiga ne duk da wayar Husnah tana hannun Husain ya'ki bata Amman idan an kira yana bata tayi wayar ya tafi da wayar, Husain duk abun sa kira d'aya zai biyo ka yaji abunda ke faruwa, nikam dai hankali na ya kasa kwanciya". Daddy yace, "ba wannan ba ku tashi muje gidan mu ga abunda ke faruwa indai ba suna can ba suna aikata halin su, yara kamar masu zuciyar dutse kuyi wata bakwai a gida d'aya amman hali bai sauya ba". Babu mai wani 'karfi a cikin su haka suka nufi motocin su guda biyu suka shiga suka d'auki hanyar gidan su Husnah, tun a bakin get suka fara shiga far gaba saboda ganin get d'in a bud'e , tsayawa sukayi Daddy ya kira police, ai kuwa babu wani 'bata lokaci suka iso saboda sun san indai Daddy ne ya kira su kira mai mahimmaci ne, kuma harda CID ya kira duk suka iso, jami'an tsaron sune a gaba su Daddy na biye dasu, masu gadin gidan ne kwance jikin jini ai kuwa a take kowa ya saka salati Anisah kuwa tuni ta fad'i gurin a some, d'aukar ta Shaheed ya yi ya kaita gefen flower, ya kwantar ya ce, "Suhailah ku tsaya a tare da ita", gyada masa kai kawai sukeyi suna kuka. Haka get din na biyu babu kowa a gurin, cikin d'akin tsakiyar suka shiga wanda shine a bud'e kuma da alama akwai abunda ya faru saboda hanyar da bulet ya shiga, aikuwa atake suka 'kara shiga cikin rud'ewa, suna shiga ciki falon duk sukayi mutuwar tsaye jami'an ne kawai suka 'karasa gurin da sauri ai kuwa kiran motar asibiti sukayi kan kace kwabo har sun iso, su Yaya Yusuf da Shaheed da Zarah da Ummey kaka kawai sukeyi dan su kan yanda suka ga jini yana zuba a kan Husain sun san jinin sa ya 'kare yama mutu, haka suka ga yanda Mardiyya ta zama lallai kam duk an kashe su, kowa ya rud'e harda jami'an tsaron. Saboda tsabar rud'ewa duk sun manta da Husnah har sai da wani CID ya ce, "su biyu ne kawai a gidan ko akwai cikon na ukku? " Ummey ta ce, "Husnah? ". Atake hankalin kowa ya dawo to ina ita Husnar take ne?. A take jami'an suka ba zama bincike amman basu gano Husnah ba, wani jami'i ne ya ce, "kudubo nan da alama sun d'auke ta sun tafi da ita saboda kayan aikin da akayi amfani dasu kuma ku dubi jikin yaron ku, ku gani yayi mata aiki ne dan ga bulet din da ya cire mata nan, amman kuma suka bugesa suka d'auke ta bayan ya gama yi mata aikin gurin". Faduwa Anty Zarah tayi a jikin Yaya Yusuf wanda idon sa yayi jaa saboda tsananin tashin hankalin da suke cikin sa, d'aukar ta yayi suma su Husain aka d'auke su aka saka su, Ambulance su ukku aka nufi asibiti dasu, gidan kuwa bin cike aka shiga yi ansamu bulet biyu, da dai wasu abubuwan da jami'an tsaro ke nema. Taimakon gaggawa aka basu, tuni Anty Zarah ta falka, amman kuka kawai takeyi sai lallashin ta akeyi, da dai likita yaga zata jawo wa kanta wata matsalar musamman cikin dake jikin ta, kawai sukeyi mata, allurar bacci. Husain ma ya dawo hayyacin sa cikin sa'a sai dai kuma anyi masa allurar bacci shima, ita kuwa Mardiyya anyi asarar cikin dake jikin ta dan ya mutu cs ma sukayi mata suka cire d'an itama da ket aka samu ta samu kanta. Su Daddy da Ummey da Yaya Yusuf da Shaheed tunanin sukeyi taya akayi hakan ta faru ne, waye yayi masu wannan d'an yen aikin? Sun rasa gane wa, jami'an tsaron kuwa CID sune suke tsare da Husain. Can cikin dare Husain ya falka, cike da tsoro a zabure ya falka yana fad'ar mi miye mukayi maku ne? Husnah dan Allah kada ki mutu kibar ni, su Yaya Yusuf da CID nan su biyu sukayo kansa suna kallon sa, likita ne ya shigo da sauri saboda kiran da akayi masa, yana zuwa ya fara duba Husain, ya ce, dashi "ka kwantar da hankalin ka, kabi komai a sannu gudun bugawar zuciyar ka, am kana jin wani abun ne? Ko kuwa zakayi wata lalurar ne? ". Kallon su Husain yakeyi kamar wasu ba'kin halitta, zuwa can idon sa ya sauka akan Yaya Yusuf, Husain ya ce, "Yaya Yusuf sun kashe su ko!?. Gir giza masa kai yayi yace, "basu kashe kowa ba, duk suna a raye, amman kuma su waye su? ". Husain yace, "Yaya Yusuf ina ji a jiki na Husnah tana cikin wani hali dan Allah ka sanar dani tana ina ne? ". Yaya Yusuf ne zaiyi magana CID yace, ko zaka tashi kasha ruwan tea ne sai kayi sallah ko aboki na? ". Tunawa da bayi sallah ba shine ya saka Husain tashi suka raka shi har bayin yana tafe yana d'in girsa, jin yakeyi kamar kansa zai rabe biyu saboda tsabar buguwa. Tunda suka zai iya yin komai da kansa sai suka fito suka baro sa ya 'karasa. Zaune suke suna jiran Husain ya fito amman shiru, har kusan minti talatin kawai CID nan yace zaman yayi yawa ka dubu sa mana". Yaya Yusuf ne ya shiga ya dubu Husain amman babu Husain babu labarin sa si wani gurin, da yaga an fasa an shigo ko an fit, ai kuwa Yaya Yusuf ya kwatsa uban ihu sai ga bayi ya cika da jami'an tsaro da mutane, dur kushewa 'kasa yayi ya dafe kai ys rasa miye ma zai iya aikata wa a halin yan zun. Jami'an tsaron kuwa cikin tsananin tashin hankalin suka rufe asibitin babu shiga babu fita. Koda aka sanar dasu Daddy kuwa kasa cewa komai sukayi sai salati. Ummey kuwa dafe goshin ta tayi fa hannun ta, su Anisah sai kukan ya 'karu daman kukan rashin ganin Husnah sukeyi. Daddy yace, "ya Allah kaine mai iko akan komai ya Allah ka tona asirin wanda suka sace mani yara, ya Allah ka tsare mani yara na a duk inda suka tsinci kansu". Kowa yace, "amin" Neman duniya anyi wa su Husain Amman kuma labari, gidajen tv radio jaridu da mujjalu duk neman su ake ta internet, kasuwan ni asibitoci da dai sauran su amman kuma babu wani labari, Anty Zarah kuwa ta dawo kurma tun lokacin da taji labarin harda Husain an sace sa a asibiti sai ta dawo baci ba sha ba magana sai an matsa mata, su Shaheed da matar sa sun dawo gida, Mardiyya kuwa har yan zun tana asibiti gashi har anyi sati d'aya. Kowa ya rame yayi d'an wuya saboda babu kwanciyar hankali. Ko ina ka zaga gari da wajen gari neman su Husnah da Husain akeyi. Gidan Daddy ya dawo gidan ku rame kullum cikin sadaka da salloli da addu' oi suke. Kowa yayi zurfi cikin tunanin shin ina su Husain da Husnah suka shiga ne? Su waye suka sace su? Miye dalilin sace sun? kuma wane laifin ne suka aikata har hakan? ..... *Comment and share* *A GIDANTA NA GIRMA* *BY NANA: KHADEEJATU* *_UMMU IHSAN_* *SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU SOSAI SON FISABILILLAH* *YA ALLAH KAJIKAN MAHAIFINA KAYI MASA RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SA SHIDA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.* *YA ALLAH KA BAIWA MAMANA LAFIYA KA BAIWA DUK KANNIN WANDA BAIDA LAFIYA NA GIDA DANA ASIBITI ALLAH KA BASHI LAFIYA AMIN YA ALLAH* *_Bismillahir Rahmanin Rahim_* 91_95 Kawai Yaya Yusuf ya tashi tsaye da sauri ya ce, "Shaheed akwai gagarumar matsala sai yan zun na tuno da maganar da Zubaidah tayi akan Husnah cewar ta d'auki burika masu tarin yawa akan Husnah, haka kawai rana tsaka, tace zata guje mata? To wallahi sai ta tabbar mata da cewar ita tsohuwar yar bariki ce dan bata isa ta kunya tar da ita ba a cikin taron mutane ba, wanda basu san cewar 'karya takeyi masu ba akan cewar itace ta haifi Husnah da cikin ta, duk mutane sun yarda sai yanzun rana tsakiya ta zo ta yi mata wanan tonon asiri?" A take Shaheed ya ce, "tabbas kuwa babu ko shakka itace ta aikata hakan domin daga ganin Zubaidah komai zata iya aikata wa akan cikar burin ta". Daddy ya ce, "Tabbas ko shakka babu sai yanzun ne ma na tuno da cewar Husnah na cikin tarko, a baya mun d'auka abun ya wuce ashe ba haka bane, a gaskiya mun tabka babban kuskure, tunda muka bari Husnah tayi nesa da mu! " Ummey ta nisa tace, "humm to Alhaji ai ba sakacin mu bane saboda Husnah koda tana cikin gidan nan zasu iya zuwa su aikata abunda suka aikata yan zun tunda makamai ne dasu, ba haka suke ba". Kowa ya ce, "hakane kam gaskiya yan zun ta wace hanyar ne zamu bullowa wannan al'arin ne? ". Shaheed ya ce, "Daddy kamar yanda nayi bin cike a wan can lokacin har na gano gidan da Husnah take to ko a yan zun hakan ce zata sake faruwa kudai kawai ku taya ni addu'a Allah yasa mu gano su cikin 'koshin lafiya ". Shiru kowa ya yi suna nazarin wannan maganar ta Shaheed kafin Anisah ta ce, "Yaya Shaheed kai d'aya wannan aikin ba zaiyi dad'in yi ba, amman ni kuma zan shiga cikin aikin kodan, halaccin da Husnah tayi muna, duk yan da bata shiri da Yaya Husain Daddy ne kawai ya bata umarnin Auren sa, amman ko kukan tozarta maganar Daddy batayi ba, uwa uba ceton da tayi muna na ceto rayuwar Daddy, dan haka nima saboda Husnah zanyi wannan aikin a ma daina maganar Husain ace dan yana d'an uwa na ne". kallon ta kowa yakeyi, Daddy ya ce, "a a Anisah kiyi zaman ki, sai dai ko Yusuf ya taimaka wa Shaheed d'in ". Kuka Anisah ta sanya masu ai kuwa dole suka amince mata tare da addu'ar fatan nasara, Yaya Yusuf kuwa nasa shirin yakeyi Anty Zarah kuwa iya kacin ta dasu ido. Haka su Anisah suka fito tayi shigar ta, ta dau wanka sai 'kamshi takeyi ga jaka ta rataya, mota suka shiga su biyu Shaheed ne ke tu'ki sun sha addu'a sosai kafin su fita daga cikin gidan har suka bar gidan ana yi masu addu'a. Hanyar gidan su Zubaidah suka nufa a nesa da gidan sukayi parking a gefen titi, Shaheed ne ya fito yana duba mota ya bud'e gaban motar yana duddubawa, motoci da mashin sai wuce su sukeyi, Anisah ce ta fito ta rataya gyalen ta a kafad'a, sai gilas da ta saka a idon ta, no respect ta fito tazo a kusa da Shaheed ta dafa motar tace, "bro ina fatan ka lura da wata mota a bayan mu can nesa kad'an damu a anyi parking d'in ta da alama mu ake bibiya dan tun d'azun na lura da ita". Shaheed ya ce, "a ankare nake shi yasa nayi parking a dai_dai nan gurin na ga ko sune suke bibiyar mu". Murmushi Anisah tayi tace, "Yaya Shaheed ashe dai kana da target, amman ba wannan ba, yau nayi maka kama da Husnah kuwa? ". Tayi fari da ido, Shaheed ya bushe da dariya ya ce, "kai Anisah kin cire mani kewar yar kanwata 'yar gayu, kefa sai da mata ta ta ce sai na ri'ka barin ta, tana d'auko karatun gayu gurin Husnah, nine na hane ta, saboda nafi son sai sun dai na mugun halin su, tukuna mutane kamar wanda ba mutane ba, kamar dutse, ace mata da miji suyi wata bakwai amman babu wata sha'kuwa sai ta 'boye wadda sai mai hankali ne kawai zai iya gano cewar suna mugun son junan su da ga ba'kin kishin da sukeyi wa junan su amman shirme ya hana su gane komai ". Dariya duk sukayi Anisah ta bud'e baki zatayi magana ke nan, sukaji ance, "sannun dan Allah ko zan iya taimakon ku kuwa?". Da sauri suka jiyo suna kallon mai maganar, magidan cine kimanin d'an shekara arba'in da biyar, ba wani fari bane fes kuma ba ba'ki bane ba, wankan tarwad'a ne , daga ganin sa kasan cikin futu yake ba cikin wahala ba, duk cikin yan sakwanni suka 'kare masa kallo. Duk sai suka sha mur suka daina dariya, Anisah tace, "malam babu wata sallama zaka wani ce zaka taimakon mu, to mun gode masu taimakon mu sunje koyon sallama ". Kallon Anisah yake cike da mamakin tsiwar ta, Shaheed kuwa ya ce, "a'a mun gode ai har mun gyara yan zun zamu wuce, mun gode da kulawa". Murmushi mutanen yayi ya ce, "kuyi hakuri Assalamu Alaikum ya baiwa Shaheed hannu, Kallon_kallo aka shiga yi tsakanin Shaheed da Anisah, zuwa can Shaheed ya bashi hannu suka gaisa, bayan sun saki hannun juna ne, mutanen ya ce, "idan ba zaku damu ba, sai naga kamar ba saurayi da budurwa ba, kuma ba mata da miji ba, kamar dai Yaya da 'kanwar sa". Cike da tsabar mamaki suke kallon sa, Shaheed ya ce, "to kodai munyi maka wani laifin ne da har ya saka kake 'kare muna kallo? ". Gir giza masu kai yayi yana murmushi, Anisah tace, "to malam ba dai gayyatar ka mukayi ba, inma saurayin da budurwa ne ko mata da miji ko 'kanwa da Yaya miye naka a ciki? Nifa bana son rainin hankali irin na mutanen zamani". Murmushi ya sake yi, yace, "da alama sai naga kamar ke ce wadda zan Aura bayan rashin tawa masoyiyar wadda nake mugun 'kauna anshi waya ta saka mani number ki" wayar sace ya mi'kowa Anisah gashi wayar haddiyar gaske da ita. D'auke kai Anisah tayi daga baya kuma ta jiyo tayi murmushin takaici tace, "oh! Ada ka d'auka bani da masoya ko ya nufin ka, ko ka d'auka cewar ni irin matan nan ne makwad'aita? to indan wannan kallon kakeyi mani ka sauya, kuma sai anjima malam!" Ba mutanen ba hatta Shaheed sai da yayi dariya saboda yanda Anisah ta zage sai masifa takeyi daga maganar arziki. Mutanen yace, "da alama zakuje gidan Zubaidah neman Husnah ne ko? " Yayi maganar yana murmushi yana kallon yanayin fuskar su, Shaheed ya ce, "kamar ya kuma waye kai!? ". Anisah tace, "da alama wannan shine dalilin da yasa kake ta bibiyar mu tun lokacin da muka fito daga gida, to waye kai? ". Murmushi yayi yace, "zan taya ku neman Husnah amman kuma kafin nan, sunan da nasan wata kila kun san shi a gurin Husnah shine, Tk idan har kun ta'ba jin wannan Sunan a gurin Husnah to nine Tk ". Dukan su mutuwar tsaye sukayi, Shaheed ya ce, "kana nufin kaine wanda ya d'auki nauyin Husnah tun lokacin da aka zo da ita a garin nan? ". Dariya Tk yayi yace, "sosai ma kuwa kuma ni kaina Husnah tayi mani nata taimakon domin ita ce sanadiyar shiriya, nagano hakan ne tun lokacin da nayi bin ciken wanda ya aikata hakan a gareni domin na kyautata masa". Anisah kam yanzun tayi shiru bata sake cewa dasu uffan ba. Shaheed ya ce, "amman taya kasan muna neman Husnah ne? ". Tk ya ce, "saboda nasan irin son da kukeyi mata, tun kafin ta Auri Husain d'an uwan ku". Anisah tace, "amman kuma duk da kasan da cewar Husnah matar Yaya Husain ce, to Yaya akayi kake bibiyar rayuwar mu? " Murmushi yayi yace, "saboda Husnah ta zamo mani 'kanwata, tajini ne saboda nasan bata da kowa, kuma nasan halin Zubaidah zata iya aikata komai akan rashin Husnah a tare da ita saboda Husnah ita ce jarin Zubaidah, dan Zubaidah ta d'auki dogon buri akan Husnah, tun lokacin naso na d'auke ta na ceci rayuwar ta, amman kuma sai kuka zo kuka fini 'karfin a gurin Husnah, ni kuwa saboda yanda naga kuna bata kulawa sai na ji dad'i na zuba wa rayuwar gidan ku ido ". Tk yaci gaba da fad'ar, "sace Husnah da Husain kuwa a gari naji da jaridu da gidan redio, sai na fara bibiyar rayuwar ku saboda nasan ba zaku iya yin shiru ba, sai kun aikata wani abun shine yasaka nake bibiyar ku" Ajiyar zuciya suka sauke baki d'aya, Shaheed ya ce, "to yan zun ta yaya ne zamu samu shiga gidan Zubaidah neman Husnah da Husain? " Tk ya ce, "Zubaidah tana gidan ta, yanzun haka kuma nasan ba ita d'aya take ba, kawai ku zo mu tafi tare, nasan idan a tare muke ba zaku sha wata wahalar shiga cikin gidan ba". Haka kuwa akayi Shaheed da Tk sune gidan gaba, Anisah kuwa tana can baya bakin ta cike da addu'a. Suna isa 'kofar gidan Zubaidah masu gadin gidan ne suka zo koda suka duba Tk suka gani a take suka sara masa harda su kirari, kud'i ya d'auko batare da ya duba ko nawa bane ya basu, cikin farin ciki suka amsa sai godiya da murna da farin ciki addu'a kawai suke zuba masa, bud'e masu 'kofar akayi suka shiga cikin gidan, suna yin parking suka fito suka shiga cikin falon gidan kamar yanda Tk ya fad'a hakan ta faru kuwa, domin Zubaidah ce zaune ta rabka uban tagimi ga mutane maza da mata cike da falon kowa da abunda yake aikata wa. Zubaidah na ganin Tk tawani irin tashi tsaye ta daki kirji ta ce, "Tk...! Daman kana sane da gidan nan baka manta dashi ba?, kodai wani abun ne ya kawo ka, idan ma Husnah ce kazo nema, tofa lallai ne nida kai muhad'a 'karfin mu guri d'aya muje gidan da suka d'auke ta mu yankar masu sammaci domin kuwa naga sanawar sace tan da akayi har cikin gidan ta! ". Kallon_kallo aka shiga yi tsakanin mutum ukku Tk Shaheed Anisah, mutanen cikin falon kuwa kallon su kawai suke duk sun bar abunda sukeyi sun dawo da hankalin su akan su Tk. Shaheed kuwa ya ce, "kada ki rainawa mutane da wayau malama ko kin manta cewar Husnah ta ce, *A GIDANTA NA GIRMA* ba wai tana nufin cewar ke ce mahaifiyar ta ba, kuma idan ma ke ce kika saka aka sace Husnah da mijin ta Husain to kisani kin d'ebo ruwan dafa kanki! ". Da sauri Zubaidah tace, "eh lallai muna fukai tunda kun rabani da 'yata kun siyar da ita ai dole ne kuzo ku zargeni dan kada duniya ta zageku". Anisah tace, "wannan maganar da kikayi ita ce take bamu tabbacin cewar kina da sa hannu gurin sace Husnah da mijin Husain saboda tsabar ba'kin cikin da kike ciki na Husnah ta juya maki baya". Zubaidah tace, "ke kuwa uban waye ya saka bakin ki a cikin wannan maganar da dake ake yin ta ba? ". Anisah ta ce, "da dan kada na zageki wata rana na Husnah taji labarin hakan ba, ta d'an 'bata rai da kuwa kinga aiki da cikawa sai dai kash farin cikin Husnah shine namu farin cikin shi yasa zan iya d'aga maki 'kafa, da sai kin gane babban cin Husnah da Anisah!, Sannan kuma ki sani Husnah 'yar dangi ce gaba da baya, kodan kinga kunje gidan su kun sato ta, kike ganin kamar bata da kowa,? to idan ma haka kike tunani abun ba haka yake ba, Bari in sanar dake abun da baki sani ba, yan zun haka Baffan nin Husnah da goggo nin ta harda wadda kukayi 'karyar ta aiko ku, to duk muna tare dasu uwa uba ma, Yayar Husnah wato wadda ki kaji Husnah na kira da Anty Zarah, dukan su, idan ma har kin musan ta hakan, zaki iya bin cike ki gano gaskiyar, lamari dan haka ki ma dai na ala'kan ta Husnah da wannan kazan tacciyar rayuwar, Husnah yar halak ce mai cikakken hankali, addu'ar mahaifiyar tace ke tattare da ita shi yasa kike ganin bata yin irin abunda kike yi, dan haka malama tun kina da sauran dama, kije ki nemi yafiyar iyayen ki, da yafiyar Allah ki kasan ce, cikin tuba, kuma tuba ta gaskiya, ba tuban mazuru da kaza a bakin sa ba, San nan kuma magana ta 'karshen da zanyi maki, shine ki fito muna da "yan uwan mu, ko zaki ga dai_dai a rayuwar ki, ta duniya da lahira, ni kinji abun da kawai zan iya sanar dake! ". Ba Zubaidah ba hatta Shaheed Tk da mutanen dake gurin cike suke da mamakin 'karamar yarinya wadda bata wuce tsaran Husnah ba, ace itace ke irin wannan maganar ta masu hankali. Tk ya ce, "to malama Zubaidah kamar dai yanda kikaji Mata ta ta fad'a to haka abun yake ki tuba ki nemi yafiyar iyayen ki ki ajiye duk wasu alfasha da kike ina mai tabbar maki da cewar wallahi sai kinji dad'in sabuwar rayuwa, kuma Husnah da Husain idan kin san inda suke, ki sanar damu, idan kuma wani abun kike da bukata ko nawa ne to kiyi bayani kin sani ni mai iya baki ko nawa ne". Zubaidah tun lokacin da Anisah ta fara magana jikin ta yayi sanyi kuma ta yarda da cewar baffan nin Husnah suna nan da ran su harda antyn Husnah, to abun mamaki ma wai ace 'karamar yarinya ce keyi mata irin wannan kalaman masu shiga jiki, uwa uba ma Tk wanda yayi masifar bata mamaki. Anisah ta ce, "kai dubi mutum haka kawai zaka wani kira na da matar ka?, matar ka na gidan ka ka baro ehey". Shaheed ne yayi murmushin da bai shirya ba, ya ce, "Anisah dawa sa fa yake yi maki ". Murgud'a baki tayi Tk ya ce, "aboki da gaske na keyi ta bari na aika da kaud'in Auren ta, tace, "ba zata Aure nin ba". Anisah ta ce, "Allah ya sawa'ke nikam na Aure ka, ina da wanda nake so kuma shine za'bi na, ba wani can ba daga had'uwa rana d'aya ". Maganar Zubaidah ce ta katsewa Tk han zari, tace, "eh kam nasan da batan Husnah da mijin ta, amman babu hannu na a ciki, ada nayi farin cikin faruwar hakan, amman kuma yau, naji haushin faruwar hakan, nasan wanda ya sace Husnah da mijin ta, ku shirya makaman ya'ki dashi domin kuwa shi gagara ne ya gagari mutane da dama, har jami'an tsaro sun kasa iya wa dashi dan haka kodai muyi masu addu'ar fitowa lafiya daga gurin sa, ko kuma mu ja masu damu kanmu da yan uwan mu shiga cikin hatsari, domin mutum ne mai matu'kar hatsarin gaske". wata daga cikin 'kawayen Zubaidah ta ce dasu, "kuma dai yi hakuri domin yan zun nan daga cikin mu an samu in formers din sa sun sanar dashi cewar ana shirya yanda za'ayi a zo gurin sa a ya'ke sa cikin su kuwa harda Zubaidah, ga sa'kon da aka turowa muna nan cewar muma yan zun haka muna cikin hatsarin gaske ". ga baki d'aya gurin ya d'auki shiru, Anisah ta nisa tace, "koma dak waye shida Allah ne mun bar mutum da Allah, ya Allah duk wanda ya sanar da wannan azzalumin mutun abunda ke faruwa, Allah ka had'a shi da mugun ji da mugun gani, koda fushin wannan azzalumin mutumen ne! ". Zazzare ido aka farayi a gurin, a take wasu daga cikin gurin suka fara tashi suna fita daga gidan, cikin mutum sha bakwai sai da aka bar mutum biyar har gami da Zubaidah. Su Shaheed kuwa mamakin irin kalaman Anisah sukeyi a ina ta samo su. Anisah kuwa dariya tayi tace, "bro wannan aikin Husnah ne ita ce malamar mu nida Suhailah da Safiya, dan na fahimci kana cike da mamaki na". Ajiyar zuciya Shaheed ya sauke Zubaidah kuwa cewa tayi, "tuni na fahimci hakan daga gareki, yan zun ku tashi ku bar gidan nan, zan sameku a gidan ku zan zo da wasu bayane na wannan mutanen sannan sai kunyi hakuri dan zan dad'e ban zo ba, kudai kuci gaba da yi masu addu'a ". Amsa mata sukayi badan sun yarda da ita ba, suka koma gida suka sanar da kowa abunda ya faru har had'uwar su da Tk, su Daddy sun jin jina al'amarin, haka sukaci gaba da addu'a. A can wani gurin kuwa? Husnah na ce kwance jikin ta da bandeji kwance take akan wata jibgegiyar kujera mai kamar gado kuma ba gado bane sai laushi, ga sanyin A/c na ratsa ta tako ina gurin sai 'kamshi ke tashi. Motsawa ta soma yi ta saka hannun ta, ta dafe hannun ta, ta bud'e idon ta ta soma biyar ko ina da ido tashi zaune tayi a zabure, ganin gurin da take kwance a halin yan zun sai ta shiga cikin mummunan tashin hankalin saboda tsin tar kanta tayi a 'kasar da tasu ba, duk irin had'uwar gidan su sai taga ba komai bane, sauka tayi a 'kasa d'akin duk glass ne ta ko ina, hankalin Husnah ya kai matu'kar tashi, jin zugin da hannun ta yakeyi ne ya saka Husnah duba hannun a take ta tuno abunda ya faru kawai ta dur'kusa 'kasa ta fashe da kuka ". Husain kuwa bud'e idon sa ke da wuya ya soma ganin hazo_hazo jiri_jiri duhu_duhu fankar dake li'ke a sama ita ce ke juyawa, shi kuwa jin yakeyi kansa na juyawa dafe goshin sa yayi kansa na yi masa mugun ciwo kan nasa nad'e yake da bandeji, tashi zaune yayi gurin da ya tsinci kansa ne ya 'kara d'aure masa kai dube_dube ya farayi d'akin glass ne kuma inda yake zaune carfet ne tsanwa mai ruwan ciyayi, mamaki ne fal ransa, dafe kan nasa yayi da hannun sa duka biyun. Wata 'yar 'kara ce ya jiyo daga bayan sa kawai ya d'ago kansa a hankali ya juyo, mutane ne su biyu murtu'ke da fuska jibga_jibga dasu babu alamar tausayi ko nan da can, suna 'karasowa kawai suka saka hannuwan su suka tallabe Husain wanda yake ta kokarin su sauke shi 'kasa amman ina ko sauraren sa basuyi ba , sukayi waje dashi, gashi sunyi masa ri'kon bawa da maigida basu ajiye sa ko ina ba har sai da suka shiga wani katafaren hadden falo ma girman gaske, a gaban wani mutum ne suka sauke sa da 'karfin gaske har sai da yace wash!. Husnah kuwa tana cikin kukan ta, wata tsohowa ce ta ce, "yata taso muje kiga wani abu". Husnah na ganin wannan matar kawai ta tsare ta da ido dan ganin takeyi kamar mafalki takeyi, hannun Husnah ta kama ganin Husnar ta zama status da ita, cikin falon akayo da ita inda aka ajiye Husain a nan aka ajiye ta, a gaban wani mutum wanda bai d'aga fuskar sa ba amman mutanen daga ganin sa kasan babu imani a tattare dashi. Sun dad'e da zama babu um ba um_um, Husnah bata san da akwai mutane a gurin ba illah mutanen da tagani an ajiye ta a gaban sa sai kirjin ta ke dukan uku_uku. Husain kuwa tun isowar Husnah ya maida hankalin sa akan ta, har ta zauna yanda take kallon mutanen ne yasaka shi maida hankalin sa, a can gurin. Mutanen ne ya cire malfar da ya rufe fuskar sa da ita yana kallon su ya kalli Husnah ya kalli Husain, idon mutumen jawur dasu gashi ba'k'ki 'kirin dashi kamar bayan tukunya. Wata irin dariyar keta ce ya bushe da ita ba bu dad'in sauraren ta hahhhhh, yace, "Husnah yau gaki ga mijin ki wanda baki da wani mijin bayan sa, nine yalla'bai d'in da kikaji zuby na fad'a nine wanda na tashi Auren ki, a ranar kika gudu, gidan su saurayin ki wannan kika 'bata mani suna a gurin abokan hulda ta" ya nuna gurin da Husain yake da hannun sa. Gurin da yayi mata isharar ne ta maida hankalin ta, waye zata gani inba Husain ba, suna had'a ido dashi take suka d'auke idon su suka mayar akan mutanen. Mutanen yace ya naga kunyi kamar baku san junan ku ba? Bayan nasan tunda ku ka zauna a guri d'aya har tsayin wattani bakwai ai nasan kun murji anarci da kyau tunda gashi har yan zun baku tashi haihuwa ba, nida naso na ganki da ciki, sannan na d'auke ki tare da mijin na saka a ciro mani dan a gaban idon ku, na saka wu'ka ta na yanka jin jirin nasha jinin sa, nasa a kaiku kichin a gaban idon ku a dafa mani naman nacinye duka, akan idon ku, amman kash! Hakan bai samu ba, to yan zun zan yi maku hukun ci irin wanda ya dace, kai goga! Ka saita Bindigar nan ka kawo mani ita a nan! ". Da sauri wanda aka kira da goga ya cika aiki, ya kawo bindigogi guda biyu, ya ansa ya saita su ya halbi yaran sa guda biyu a hannun, ji kake darammm_darammm, su kuwa cewa sukayi washi, suka dafe gurin, sai jini ke zuba ido yayi kamar an watsa masu barkono. Husnah da Husain duk sai da suka zabura, mutanen da yaran sa cike da d'akin suka bushe da dariya harda doka 'kafa. Sai da sukayi dariyar su mai isar su, sannan mutanen yasha mur ya had'e rai yace, "Husnah keda wannan munafukin ku ri'ka kowa ya halbi dan uwan sa, gurin da yake so" Mika masu Bindigar yayi yana d'aure da fuska, kin amsar Bindigar sukayi, kawai ya ce, "to ni zan halbe ku da kaina ta inda naga yafi burgeni ". Mur yasha, ya saita Husnah a goshin ta, ya saita Bindigar d'aya a saiti da zuciyar Husain ya gyara zai halba da sauri suka anshi Bindigar suka tashi tsaye suna ri'ke da bindigogin a hannun su, tsawa ya daka masu wadda sai da Husnah ta zabura kamar zata fad'i 'kasa, daket ta saita kan ta, tayi tsaye, tsawar ya 'kara daka masu ya anso wata Bindigar zai halbesu, kawai sukayi saurin sai ta junan su da bindigogin Husain ya sai ta Bindigar sa a kan Husnah, itama Husnah ta saita Bindigar ta akan Husain, sai zufa ke zubo masu kawai Husain ya ce da Husnah, " daman nace sai na kashe ki da hannu na yau ga dama ta samu, kinga babu mai yi maki magiya ballema a hana ni aikata hakan " ya bushe da dariya. Husnah kuwa dariya ta bushe da ita, tace, "to kai ka manta yanda akayi har na yarda na zauna dakai? To ka sani daga yau sai nabar tarihi nice mace ta farko wadda ta fara kashe mijin da ya damu da ita" 'kara saita Bindigar sukayi a take suka halba, jin kake darammmmmmmmm_darammmmmmmmm..... Dai dai saiti da shigowar su Anisah Tk Zubaidah Yaya Yusuf, wata irin 'kara suka fasa, suka dafe kai....... *Comment and share* *A GIDANTA NA GIRMA* *BY NANA: KHADEEJATU* *_UMMU IHSAN_* *SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU SOSAI SON FISABILILLAH* *YA ALLAH KAJIKAN BABA NA DA MAMA NA KAYI MASU RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SU KA SANYA SU A ALJANNAR KA TA FIRDAUSI BIGAIRI HISAB SU DA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.* *AMIN YA ALLAH* *To Alhdulillah Allah ya nufeni da dawowa gashi zamuci gaba daga inda muka tsaya* *_Bismillahir Rahmanin Rahim_* 95~100 Wani irin uban ihu duk mutanen gurin sukayi, babu kamar yallabai wanda ya fad'i kwance 'kasa cikin jini yana zabga uban ihu hannun sa d'aya dafe da ka fadar sa, d'aya hannun kuma dafe da cinyar sa, sai jini ke zuba, mutanen gurin cike da mugun mamaki suke kallon Husnah da Husain da yallabai wanda ya fita cikin hayyacin sa, abunda ya 'kara baiwa mutanen mamaki shine ganin Husain da Husnah a tsaye ri'ke da bindigogin suna a jere da junan su, sun 'kara saita Bindigar akan yalla'bai kuma Husnah itace ta saita zuciyar yalla'bai Husain kuwa ya saita Bindigar sa akan yalla'bai, duk cikin jin haushin abunda su Husain da Husnah suka aikata wa ogan su, kawai suma suka d'auki bindigogin su suka saita su Husnah da su. Husain yace, "ashe dai ku duk kidahumai ne tunda har kukayi tunanin zamu iya kashe kan mu da kan mu mu aikata kusan kai, amman gaskiya na kara raina maku da wayau tunda har kukayi sakacin zama baku sha maganin bindiga ba, ai kuwa zamu 'karasa kashe mugun iri inyaso kuma sai ku kashe mu" Husnah tace, "yalla'bai kaga yaran nan naka basu damu da abunda muka aikata maka ba, tunda ka gan su nan kowa ya nemi Bindigar sa dan ya kare kansa kai kuma indan ta sune mu 'karasa kashe ka, ko suma sun gaji da goyon bayan ba, saboda haka kasan nayi fa, daga yau kayi ban kwana da wannan izzar taka da mulkin zalluncin al'uma". 'kara saita har sashen su Husnah da Husain sukayi zasu sake halbawa, cikin tsawa da rad'ad'in aza yalla'bai yace, "ku... da... Kata... Dan.... Allah, kada ku kashe.... Ni..... , ku fad'i abunda..... Kuke da bu'katar sa.... koma miye koda duka dukiyar... Dana tara ne.... ". Da sauri Husain ya ce, "dakata! An gaya maka cewar mu shasha sune da zaka bamu dukiyar haram mu ansa? To idan bacci ma kakeyi yanzun ka falka fansar a d'aya ce, ka basu umarnin su kawo bindigogin su anan su ajiye su a gaban mu kuma duk su durkusa 'kasa kai suma kwanta su rufe ido indai har suna bu'katar ganin ka a raye!, Kuma wannan yan uwan nawa da suka shigo a yanzun nan ka bada umarnin a maida su gida lafiya ba tare da wata damuwa ba" Cikin tsawa da a zabar da yalla'bai yake ji ya basu umarnin yanda Husain yake bukatar ai kuwa sukayi tsalle suka dire suka ce, "mufa sam bamu yarda da wannan maganar ta gamam min ha'kori ba kawai dai ka bar mu dasu mu kashe su dama kasan muna da haushin su a can baya lokacin da ka saka su goga gadin wannan masifar lokacin da suka suka saka muka rasa mutanen mu suka saka aka kaisu a gaban hukuma dan haka gara kabar mu mu kashe makiyan mu! " Husnah tace, yalla'bai kaga sun nuna maka shedar sun fi kowa farin ciki da ganin bayan ka, tunda sukeyi maka fatan barin duniyar nan". Cikin masifa yalla'bai yace, "idan kuka yarda suka sake aikata mani irin wannan raunin saboda gardamar ku, to ba kuba har dan ginku sai na 'karar dasu..." Tunda suka fahimci da gaske yalla'bai zai iya aikata fiye da abunda ya fad'a duk sai suka saduda sukayi yanda su Husain suka bada umarni aka fita dasu Yaya Yusuf ta wata hanya wadda Zubaidah ta nuna masu tace, "indai da gaske ne gidan zasu kaimu to nan ne kawai hanya mafi sau'kin bi". Anisah da Tk da Shaheed wanda suke cike da mamakin taya su Husain da Husnah suka koyi irin wannan aikin suda ba training din koyon halbi sukayi ba, daket suka ajiye tunanin suka ce, "kai gaskiya babu inda zamu saboda mutseratar da rayuwar mu, mubar ta yan uwan mu a cikin hatsari" Husain da Husnah cikin masifa sukace dallah ku tafi so kukeyi ayi mutuwar kasko anan ne? Iye? ". Tafiya sukayi badan sun soba sai dan ganin irin yanda su Husnah da Husain suka hasala, suna shiga hanyar kamar labule suka wuce zuwa wanda suka kaisu suka dawo suka nuna masu video sun kai su, murmushi su Husnah sukayi. Husain yace, "to ranka ya dad'e sun aikata yanda muke so, amman kuma wani hanzari ba gudu ba, nasan halin ka gaba da baya zaka iya idan mun barka a raye zaka iya biyar mu da dangin mu ka kashe kaga kuwa mun kashe wutsiyar maciji mun bar kai da gan_gar jiki, kaga kuwa da sauran Rina a kaba ke nan ". Husnah ta ce, "dan haka gara mu fara kashe ka kaida yaran ka, tun kafin ka kashe muna kowa namu, muma ka kashe mu". Cikin zabura wani yazo tashi ya d'auki Bindigar sa, Husnah ta dawo da Bindigar akan sa, tace, wato kaine kake son zama farkon mutuwar ko? ". Jin Bindiga a akan sane ya saka shi fasawa, cikin rawar jiki yaja baya Husnah tasa 'kafar ta, ta ri'ka tura bindigogin nesa dasu, sannan ta gyara tsayuwar ta ta ce, " yalla'bai ina da bukatar aron waya, dan ba zamu rabu da ku haka kawai kuji dad'in ganin bayan mu ba, dan haka gara musan nayi tun kafin lokaci ya 'kure muna ". Yalla'bai ya ce, "dan Allah kada ku had'a mu da hukuma d'an sun dad'e suna nema na basu ganni ba, amman ni ina ganin su, kuma koda sun ganni a lokacin ba zasu iya aikata komai a kaina ba, yau ita ce rana mafi muni a gareni domin kuwa tun kafin hakan ta faru masu yi mani duba sun sheda mani wata rana sai na d'auko wa kaina wanda zasu ga baya na, kuma duk tsafina baya aiki akan su, ni kuma shine na na saka akayi mani duba ga duk yara na, amman sam ba su bane wasu ne can na daban mace da namiji kuma babu wanda yake ganin fuskar su, shi yasa nake ta kashe duk wanda na d'auko koda kuwa a ce mace mai tsohon ciki ce, da mijin ta sai na kashe su, gudu ni su kashe ni". Kuka Husnah ta saka ta ce, "shi.. Ke.. Nan ka yarda da tsafin ka sabawa Allah kake kashe mutanen da baine ka kawo su duniyar nan ba, kuma shine kaso ka 'bata mani rayuwar ka Aure ni, ka kashe ni da raina..! " Kuka kawai Husnah keyi, "Husain cikin tsan_tsar tsana ya dubi mutanen gurin a wulance, yace, "tir da rayuwa irin wannan, wallahi kun daukar wa kanku kaya, kuma tunda har masu tsafin ku sun sheda maku cewar mune zamu kashe ku, mun fasa, idan kun so mu ku kashe mu, amman mu bamu yarda da tsafi ba, ballema mu zamo masu cika umarnin matsafa, kawai Husain ya jefawa yalla'bai Bindigar, ya juya gurin Husnah ya anshi Bindigar hannun ta ya ajiye sukayi zaune a 'kasa suna dafe da kai Husnah na kuka harda hawaye da majina Husain kuwa kukan zucci yakeyi idon sa yayi mugun ja, jijiyoyin kansa duk sun tashi saboda tsabar shiga cikin tashin hankalin. Su kuwa yaran yalla'bai suna ganin haka da sauri suka d'auki bindigogin su suka sai ta su Husain dasu, yalla'bai ne ya basu umarnin da su rabu dasu su kai sa d'akin sa, ayi masa aiki. Ya bada umarnin a fita dasu Husnah daga cikin gidan. Cika umarnin sa sukayi suka tasa Husnah da Husain a gaba suka fitar dasu daga gidan su Husnah na fita mutanen ya koma tanga menen gidan dan baiwa ogan su kulawa, sauran kattin dake harabar gidan ko kallon su Husnah basuyi ba, saboda suna lokacin da aka fito dasu duk da cike suke da mamakin wannan shine karon farkon da aka ta'ba shiga gidan da mutane kuma suka fito da ransu da kafafuwan su, har suka isa bakin get maigadin gidan suka bud'e masu get din cike da mamaki, su Husnah da Husain ba fita daga cikin gidan aka rufe get din kawai suka ga ashe ma cikin uban jeji suke kallon_kallo aka shiga yi, tsakanin Husnah da Husain, sai duba gurin da suke sukeyi. Rasa ma wace hanyar ce zasu kama, sukayi tunda gurin duk itace ne da shikko ki babu alamar gurin da mota ko mashin suke bi. Tsaye suke sun ri'ke 'kugu suna dube_dube, wata murya sukaji marar dad'in saurare daga bayan su ana fad'ar, tunda kuka ki kashe sa, to kusani ba zaku iya fita cikin jejin nan ba, idan kuma kuka dawo zaku shiga cikin gidan ku kashe shi da hannun su, to zaku sami hanyar fita daga cikin jejin nan cikin sau'ki". Husain ya ce, "mu ba jahillai bane kuma ba zamu cika umarnin wani banza ba, sha katafi, kuma mun dogara ga Allah shine zaiyi muna mafita! ". Husnah tace, "idan su kun samu damar batar dasu, to mu munyi imani da Allah kuma munyi imani da kaddara mai kyau ko marar kyau dan haka insha Allah yau a gida zamu kwana". Husnah harda su Murgud'a baki kamar irin taga mai maganar nan. Tafiya suka fara yi a jere duk sun gaji har suka bar kofar gidan kawai sukaji wani uban ihu da gir_giza sai kuma sukaji wani irin dammm kamar bom ya tashi sai hasken wuta suka gani ga iska mai 'karfi gaske ya taso da 'kura itacen gurin kamar su karye da wani irin 'karfin gaske Husain ya janyo Husnah ya rungume suka kama wani icce suka ri'ke sai addu'a sukeyi duk wadda tazo bakin su, aikuwa sannu a hankali har iskan ya daina jan su, kawai ma suka daina jin iskan a jikin su iskan yayi gaba, kawai sai zafin wuta ga hasken ta, kafin su Husnah su 'karasa mamaki sai kawai sukaga itace sun 'bace, gidan da suka baro ne keci da wuta bal_bal_bal cike da mamaki su Husnah da Husain suka saki baki da hanci suna kallon gidan wuta kawai yakeci da ita, juyawa Husnah tayi tace, "ikon Allah, Husain yace Allah mai iko da buwaya. Kawai suka fara jin motsin motoci a bayan su suna juyawa kawai suka gan su a kusa da titi, da sauri Husain yace, "mi hakan ke nufi!?. Husnah tace, "titin kusa da gidan da na girma ne, lallai kuwa nadawo gida" da gudu Husnah ta nufi gidan Zuby har ta kai bakin get Husain ya rigata ya tsare hanyar shiga cikin gidan yace, "kee! Kina nufin wannan kazamin gidan zaki shiga? To bari kiji bada umarni na ba, kuma na haram ta maki shigar sa, wannan karuwar matar zaki je gurin ta, wata kilama da saka hannun ta gurin kashe mani mata, kema taso kashe ki, to ba zaki shiga ba ciki ba". D'aure fuskar da Husnah taga Husain yayi ne ya sakata sakin uban kuka, tace, "haba haba wannan wane irin rashin adalci ne, ni wallahi uwata ce ita dan ni *A GIDANTA NA GIRMA*. Husain ya ce, koda kuwa *A GIDAN TA kika GIRMA* bata baki tarbiyya ba haka ilimin addini, dan haka wuce muje gida malama". Husnah kuwa kafewa tayi sai kuka takeyi zuwa can sukaji muryar Shaheed yana fad'ar, "haba Yaya Husain nifa a gani na tunda Allah ya kubutar daku kamata yayi ku samu gurin da zaku zauna ku futa, kuci abinci kuyi wanka, kuyi sallolin da ake biyar ku, sai sanar damu taya kuka ku"buto daga tarkon azzalumai ba wai fad'a ba". Cike da mamaki Husnah da Husain suke kallon Shaheed wanda yake tsaye da alama gidan Zubaidah ya fito, Anisah kuwa da gudu ta rungume Husnah harda kukan ta. Husain murza idon sa yakeyi cike da takaici yace, "mi kukeyi a nan gidan kema Anisah karuwancin ne kika soma? Shaheed dan kunga bana nan sai ku d'auki d'amarar zubar da mutumcin mu? " Yaya Yusuf ne ya dafa Husain ya ce, "zo muje cikin gidan zanyi maka bayanin komai" hannun Husain yaja wanda Husain a yan zun kam ya zama wani calendar dashi sai bin su yakeyi da ido. Husnah da gudu tayi cikin gidan itada Anisah a jikin Zubaidah Husnah ta fad'a ta fashe da kuka itama Zubaidah kukan ne takeyi ta ri'ke Husnah da kyau. Husain takaici ne ya kamasa ganin duk yan gidan su a cikin gidan Zubaidah jin yakeyi kamar yayi ta dukan kansa. Zuwa can Zubaidah tace, Husnah ki yafe mani nasan nice silar lalata rayuwar ki, dan Allah ki yafe mani nasan ko hakkin ki kawai ba zai bar ni ba, Husnah kiyi mani uzuri a lokacin ina cikin giyar 'bata ne da jahilci amman yanzun na dawo hanya madai_dai ciya Husnah yan zun ina jin ciwon lalata rayuwata da taki rayuwar da nayi da rayuwar wasu ma yayan mutane Husnah, yan zun na ajiye komai sai tuba da nakeyi da neman ya fiyar Allah makadaici, tabbas a yan zun haka ina jin kunyar yanda zan kalli cikin idon iyayen ki da nawa iyayen da iyayen mutane da dama, Husnah na tuba nabi Allah har nafa biyar iyayen yara ina neman yafiyar su wasu sun yafe wasu basu yafe ba, gashi nawa iyayen ban ma san duniyar da suke ciki ba, ko suna raye ko basa raye Allah shine mafi sani, amman wallahi ban san inda suke ba, sai a yan zun ne nake nadamar wulakanta iyaye na gashi na bari damar ta ku'buce mani, nayi wasa da dama! ". Kuka kawai Husnah da Zubaidah sukeyi Anisah cikin shashshekar kuka tace, "insha Allah suma duk inda suke suna nan suna yi maki fatan shiriya kuma da ace zasuga yanda kika shiryun nasani fushin su zai gushe ne su rungume yarsu, Anty Zubaidah har yanzun kina da sauran dama, da Allah yasoki da rahamar sa, shiyasa ya baki ikon tuba, fatan mu dai Allah ya kar'bi tubar ki". Anty Zarah ta ce, " Anty Zubaidah ba zan gushe ba nima ina taya ki addu'ar neman yafiya a gurin mahaliccin mu kuma Husnah ta yafe maki, dan Husnah bata da fatan da ya wuce ki shiryu tayi farin ciki ". Jin muryar Anty Zarah kawai Husnah ta koma jikin ta ta kwanta tana kuka tace Anty Zarah kece kikafi kowa sanin manufata ki 'kara sanar da ita cewar na yafe mata kuma burina ya cika wadda ta raine ne na *GIRMA A GIDANTA* yau ita ce zanyi alfari da ita, Alhamdulillah Allah kaine abun godiya ". Rungume ta Anty Zarah tayi, tace, Husnah kin san idan har zanyi farin ciki tofa lallai ne na fara ganin naki farin cikin dan haka Husnah ina godiya ga sarki Allah wanda ya bamu Ikon ganin wannan ranar ta farin cikin ki Husnah dan haka lokacin kuka ya 'kare yan zun lokacin dariya ne". Husnah gogoge hawayen ta , tayi tace, "bari nayo wanka na dawo zan baku labarin abunda ya faru " Da gudu Husnah ta haye sama ta shiga tsohon dakin ta, mamaki ne cike da Husnah ganin d'akin fes dashi babu alamar datti murmushi Husnah tayi, tayi shirin wanka ta shiga bayin ta rufe. Husain kuwa 'kara hasala yayi ya'ki cewa da kowa uffan Anty Zarah ce ta dawo a kusa dashi taja hannun su ya tashi sukayi waje can hara bar gidan suka nemi guri suka zauna Anty Zarah ta ce, "nafi kowa sanin halin Husain nasan Husain ya tsani gidan nan da matar gidan amman Husain kayi 'ko'karin yin afuwa da uzuri a gurin yan uwa musulmi baki d'aya, Husain Zubaidah ta tabka babban kuskure amman ta gane kuren ta, sai ka yafe mata, nasani zaka iya yafe mata dan haka Husain ka sassauta fushin ka a kan ta, dan tun kafin ka dawo tace, ba zata iya tun karar ka ba da sunan neman yafiya dan tasan da ta riga da tayi maka illa babba, Husain mu taru mu 'karfafa mata gwiwar ta dan kada ta sare, alhaki ya hau kanmu tunda ta tuba kuma muna yi mata fatan tubar gaskiya ". Ajiyar zuciya Husain ya saki yace, "nifa ba wai na ki yafe mata bane ni na dad'e da yafe mata kawai dai bana son ganin wan nan gidan ko kadan be, kuma itama idan ina kallon ta ada sai naji kamar na kashe ta amman yanzun yanda naga tana zubar da hawaye sai naji tana bani tausayi". Murmushi Anty Zarah tayi tace, to Alhamdulillah Husnah tazo mu koma gida, suna nan zaune har su Husnah suka fito aka shiga motoci suka nufi gida, suna isa a bakin get suka sami mutanen gidan suna jiran iso war su, cikin farin ciki Daddy ya rungume Husnah da Husain haka Hajiya su baffah ma cikin farin ciki suke a babban falon gidan suka yada zango Husnah na jikin Hajiya Husain kuma jikin Daddy, baffah ne ya bud'e taro da addu'a da nuna farin cikin sa ga Allah subhanahu wata ala da ya kubuto masu da yaran su, baiyi wani dogon bayani ba saboda ya sanar da cewar yaran na bu'katar yin salloli da cin abinci da futawa, haka aka tashi taron. Husnah d'akin su ta shiga Husain ma ya nufi tsohon d'akin sa, haka kowane daga cikin su ya gabatar da komai nasa, gashi magriba tayi basu fito ba abinci ma a d'akin aka kaiwa kowa, suna gama sallar isha'i suka kwana bacci sai sallar asuba kawai sukayi suka koma, sai 'karfe goma da rabi Husnah ta fito a cikin falon ta samu kowa a gurin harda Husain da fito 'karfe goma dai_dai. Gaisawa tayi dasu Daddy da Ummey da Yaya Yusuf da Anty Zarah da Yaya Shaheed da matar sa, sai su Anisah da suka tafa Amman ko kallon Husain batayi ba. Abinci aka bata taci ta koshi duk Husnah da rashin cin abincinta yau taci Indomie sosai, sai da ta 'koshi sannan kowa ya 'kara gyara zama nan Daddy yayi gyaran murya yake tambayar su abunda ya faru kuma taya aka zo aka d'auke Husain a asibiti, bayani dallah_dallah sukayi kowa sai da ya tsorata ga tsoron Allah daya 'kara ka masu, Husnah kuwa yan zun kuka takeyi sosai tace, "Daddy sai yanzun nake 'kara jin tashin hakali ace da hannu na ne na halbi mutum a 'kafar sa kai inaa!?. Share mata hawaye Ummey tayi tace, shida ya kashe mutanen da bai san adadin su ba fa ciki kuwa harda matar Husain wato Mardiyya da dan cikin ta da suka halbe a ciki, bayan sun dawo da ita d'akin futu sun cire mata d'an itama ta birkice tace ga garin ku nan". Tun daga Husnah har Husain tsaye suka tashi jikin su na rawa, Husnah wani uban kuka ta fasa, Husain kuwa fad'uwa yayi da'bas yayi zaman "yan bori, hakuri aka hau basu, da ket sukayi shiru yinin ranar basu da wani kuzari Husnah sai dramar su take tunowa, Husain kuwa ba'a cewa komai. Daddy ne yace su tashi suje suyi gaisuwa, haka suka tafi gidan su Mardiyya sai dare suka dawo gida. Haka suka zauna a gidan su Daddy kullum cikin damuwa har sai da sukayi sati d'aya sannan suka fara dawowa hayyacin su, sai da sukayi wata biyu sun murmuje Daddy ya tarasu yace, su dawo gidan kusa dashi cikin mutane dan ya gama gyara masu gidan ya saka masu komai dan haka zuwa dare zasu koma gidan su, idan yaso su dai_dai ta zaman Auren su ko kuma ya d'auki mataki akan su, tun da ya fahimci basu da hankali suna mata da miji ace ko magana basu ta'ba yi ba duk zaman su a gidan kuma a gaban idon su ma ke nan ina ga suna gidan su, cikin fushi Daddy da Ummey sukayi masu kaca_kaca, kuma suka 'kara jaddada masu ko su gyara ko kuma suga 'bacin ran su. Hakuri kawai suke badawa, Daddy ya ce, "ku tashi ku baiwa mutane guri sha_sha_shu kawai mutanen banza yofi! ". Tashi sukayi sum_sum suka bar gurin dare nayi Ummey tace, "kuzo ku tafi mun sallameku! " Cikin d'aure fuska Ummey ke magana dan haka suka bar gidan jikin su a sanyaye, driver ne ya jasu da mota ya kaisu gidan, ai kuwa gidan ba karya ya had'u kamar ma yaso yafi wanda suka baro had'uwa. Husnah na shiga cikin gidan kawai ta wuce d'aki d'aya haka Husain. Tunda suka shiga babu wanda ya fito Husnah fad'uwar d'akin ne ya saka ra kin fitowa Husain kuwa tsaki yakeyi an rabosa da gidan sa wanda yafi so da kauna. Babu wanda ya fito sai da safiya gidan har da masu girka masu abinci suke dasu kuma Kafin su fito angama gyara ko ina a gidan, Husain koda ya fito ya ga abinci a danie table kawai yaje ya duba tsaki yayi ya fita ba tare dayaci komai ba, Husnah najin fitar sa itama ta fito abincin ta duba, tace kan uban can uban waye ya da umarnin cewar adafa mani sakwara da miyar dage_dage, kai wai ma su waye a kitchen din? " Da sauri Husnah ta nufin hanyar da take jin kamshin girki a gurin. Yammata ne guda biyu sa'anta sai tsohuwa d'aya sai wata wadda zata kai sa an Zubaidah, kallon su kawai Husnah keyi, cike da mamaki a fuskar ta a hasale tace kai waye ya d'auke ku yin aiki a gidan nan kuma wai harda girk! ?. Duk shiru sukayi mata kawai Husnah ta juya a hasale zata fita, Husain ne suka ci Karl dashi kowa ya janye d'an uwan sa a hanya, cikin fushin Husain yace, "tunda kune kuka d'auki kanku aiki kuzo kubar gidan nan wallahi tunda ba gidan ku bane! ". Hanya Husain ya nuna masu, cirko_cirko sukayi suka tsare su da ido, Husnah tace, "kamar ana magana da ita ce? Dallah malamai kowa ce ta san inda dare yayi mata, bama bu'katar wasu yan aiki anan uwa uba wai masu abinci". Husain yace, "ko ku fita da arziki ko kuma ku fita da tsiya mayun mutane kawai ". Husnah ta bude baki zatayi magana sukaji magana daga bayan su, uban waye kuke kora ne? To nice na kawo maku su suyi maku aiki tunda ku bazaku iya tsara komai ba da kanku, shine nakawo maku masu kula da gidan dan gudun kada shima gidan ku koyar dashi ba'kin halin ku, kuma nice na sanar dasu indai ba nice na bada umarnin subar gidan nan ba, ko suyi wani aiki a gidan nan ba, to kada subi umarnin kowa ko waye a gidan nan kuma na basu wayar da zasu ri'ka kira na idan wani abun ya faru koda wata bakar magana kukayi masu! ". Jiki a sanyaye suke bin Ummey da kallo kawai ta juya tabar kichin d'in suma fita sukayi daga kichin d'in suna biye da Ummey kawai ta tace, "zan 'kara jan kunnen ku Husnah da Husain masu kunnen kashi, babu ku babu shiga sabgar masu aikin gidan nan tom na fad'a naku". Kawai Ummey tayi tafiyar ta, suna jin tashin motar ta, kowa ya kama gaban sa yayi cikin d'akin sa, Husnah kuka kawai takeyi tana fad'ar, "wan nan wace irin rayuwa ce, ni to miye laifi na? Mutumen da ya za'bi Auren wata a kaina shine zan shigewa yazo yana wulakanta ni, wallahi ba zaiyuyu ba haka kawai da ajina a gari nazo nayiwa wan can mutanen bauta Allah ya tsare! " Husain ma fad'ar yake, "haka kawai a shiga rayuwa ta dan anga nayi jihadin Auren karuwa kuma a zo ace sai abinda take so zanyi taji dad'in raina ni, ko dan anji nace ina son ta, ne to nayi ne kawai dan Anty Zarah kuma saboda farin cikin Anty Zarah amman badan haka ba da sai na wulakanta rayuwar ta, kuma wallahi sai na baiwa kowa mamaki dan ni kam ba zanyi zaman kunci ba, akan wata karuwa ba!. (Ni kuwa nace toh fa wannan wane irin ma'aurata ne haka a duniya ?) Abu kamar wasa Husnah da Husain ko kallon junan su basayi, Daddy, da Ummey sun hana kowa ziyar tar su kuma sun hana su zuwa gidan kowa, Husnah ba 'karamar takura take ciki ba, Husain kuwa daga gurin aiki sai hotel sa restored park shooping mail da dai sauran su amman Sam baya zuwa gidan kowa dan su Ummey sunyi rantsuwa akai, duk da haka yana cikin damuwa. A cikin yawon sane ya had'u da wata budurwa wadda ta li'ke masa tun baya kulata har ya soma kulata, soyayya suka 'kulla shida ita, har take shaida masa a gidan su ance ya turo iyayen sa, ai kuwa yayi farin ciki da hakan sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba koda ya sanar da Daddy abunda ke faruwa a waya Daddy ce masa yayi bada yawun sa ba, haka Ummey, Yaya Yusuf ma yana fara sanar dashi akan cewar yana neman Auren wata yarinya Zainab kuma ance ya turo manyan sa, Yaya Yusuf cewa yayi to ya tura manyan nasa mana dan shi yanada abun yi, Husain rikicewa yayi ya rasa waye zai saka baki har su Daddy su yarda? Kawai ya tuno da Anty Zarah, har ya fara farin ciki sai kuma ya tuno da cewar Husnah fa 'kanwar Anty Zarah ce, to amman kuma da kunya duk da Anty Zarah tafi kula da lamarin sa akan 'kanwar ta, kawai sai ya d'aure ya kira Anty Zarah cikin dabur cewa ya fara labar ta, mata, daga karshe yace su Daddy sunce babu ruwan su, Anty Zarah duk da taji babu dad'in amman kuma sani sakacin 'kanwar tane tunda tayi ta nuna mata illar abunda takeyi, ita ce mace ta zubar da komai ta rungume mijin ta, ta'ki jin magana yan zun sai ta Allah kam, lallashin sa tayi, kuma tayi masa alkawarin taimakon sa, yayi farin ciki sosai wanda ya kasa 'boyewa sai addu'a yake zuba mata, kashe wayar Anty Zarah tayi harda kukan ta. Kamar yanda Anty Zarah tayi alkawarin shawo kan su Daddy tayi nasara amman Ummey fad'a sosai tayi mata tunda tana goyon bayan yiwa Husnah kishiya, ita kuwa tace, "Ummey mukam yaran mu muke son gani ga matar Shaheed nan ta tsufa da yawa haihuwa yau ko gobe, kuma kowa yasan Husain na haihuwa dan kawai ankashe masa mata da yaro ne, da yan zun yaron ya fara wayau ita kuwa Husnah waye yasan halin da take ciki? ". Shiru Ummey tayi dan tasan Zarah akwai karamci ta bar yar uwar ta, ta goyi bayan kanen mijin ta, wanda sukafi sha'kuwa dashi tabar yar 'kanwar ta kuma jinin ta, wadda bata da ta biyun ta a duniya, Ummey taso butulcewa amman Anty Zarah ta dage har sai da suka yarda. Kiran Husain su Daddy sukayi fad'a sosai sukayi masa, har suke kiran sa da marar tunani yasaka Zarah a cikin lamarin sa, dan kawai ya kun tata mata, ta goyi bayan sa tabar gudan jinin ta har take kiran sa da mahaihuwa 'kanwarta kuma juya, sosai kunyar Anty Zarah ta kamasa har yaji baya iya had'a ido da ita. Haka aka tura aka kai sadaki da lefe koda aka saka biki wata biyu, Husnah duk bata san mike faruwa ba, har sai da Ummey tace tazo tana neman ta cikin d'oki Husnah taje gidan a lokacin bikin saura kwana biyar, Anty Zarah ce ta shirya haka. Ummey tace maraba lale mar haban da zuwan ki 'yata, ita dai Husnah cike take da mamakin wannan maraban da kowa yake yi mata, bata 'kara sa mamakin ba Ummey ta ja hannun ta suka shiga d'akin ta a bakin gadon ta ta zaunar da ita, Zubaidah ce ta shigo ita da Anty Zarah Yaya Yusuf gaban Husnah ne ya soma dukan ukku_ukku a take jikin ta ya bata akwai wani abu a 'kasa. Kusa da ita Ummey ta zauna su kuma duk suka zauna a 'kasa Ummey ce ta rasa ta ina zata fara, Anty Zarah kuwa tace, "Husnah! Husnah!! Husnah!!! Na kira sunan ki sau ukku dan ina son ki fahimci cewar ba mafalki ne kikeyi ba, Husain Auren sa yau saura kwana biyar, zaki zauna ne a nan gidan ayi himar biki dake matsayin ki na uwar gida, ga lefen ki nan saman gadon Ummey na fad'an kishiya duk da ni banga abun fad'a a nan ba, mijin da bakaso miye ma ba fad'a a kan sa?. kuma idan Allah yasa anyi wata tara cif da Auren sai kiga mun samu karuwar yara kinga Auren yayi albarka, an samu yan bari_bari a gidan, dama gida babu yaro ai babu dad'in zama gaskiya amman yan zun Husain yayi dabara wallahi ya burge ni" Husnah kallon bakin Anty Zarah kawai takeyi zuwa can tayi murmushi tace, Allah ya taimaka ai kuwa kunyi dubara kun kawo mafita, hakane Anty Zarah to ni miye zanyi da wasu kayan fad'an kishiya tunda ba ni akayi wa mutum kansa yayi wa, kuma ba akaina zata zauna ba, amman ku ri'ke kayan ku, ko kuma ku 'kara mata kawai zai fi". Murmushi Zubaidah tayi tace, "Husnah ki kwantar da hankalin ki, ki rungume mijinki da abokiyar zaman ki, sai kiga komai na tafiya yanda kike so nima nakusa Aure insha Allah ". Husnah tace, "kada ki damu mommy ni bani da wata matsala da Auren nan kuma bani da wata damuwa dashi, kinga sai dai ku baiwa wasu hakuri ba Husnah ba, Ummey na zan koma gida ina fatan kiran ke nan nazo na tayaku murna? " Shiru kowa ya yi Anty Zarah kuwa tace, "Husnah nan fa zaki zauna sai an gama hidimar bikin nan dan yau saura kwana biyar biki gidan amare tun ana saura sati d'aya suka fara shagalin biki". Tashi kawai Husnah tayi, tayi masu sallama ta baro d'akin, a falo ma bata kalli kowa ba, a harabar gidan ne ta had'u da Husain da abokan sa sun dawo gurin Amarya sai tsokanar sa, sukeyi, ta gefen su tabi zata wuce ke nan abokin Husain ya ce, "uwar gida sarautar mata an fito ke nan ko kina neman wani ne? ". Husnah kuwa ta wuce war ta, Tk ne da Anisah suna fira rabi fira rabi fad'a, Husnah tazo wuce wa Anisah tace, "haba yar uwa koda kowa yayi maki laifi ina ganin banda ni kuma laifin wani ba zai shafe ni ba". Kallo d'aya Husnah tayi masu ta d'auke kai tace Husnah fa bata da uwa a duniyar nan kunga kuwa Husnah rayuwar kadaici takeyi dan haka ni ban san ina da wani d'an uwa ba a duniyar nan Husnah juya a cewar wasu da kallon wasu mutanen ". Tk yace, Husnah ni nasan cewar jaruma ce a can da amman ban sanar wa yan zun ba". Husnah tace, "yan zun Husnah tasan maraici ba kamar can da ba, kawai ta wuce su ta kama tafiya da 'kafa har ta fita gidan, Husain kuwa idon sa na akan ta da duk wani motsin ta, kawai yabi bayan ta shima ya fita da 'kafar sa, da dan gudun sa ya cimmata ya jera da ita yace, "miya sa kika fito kika baro driver wanda zai kaiki gida? ". ko kallon sa Husnah batayi ba taci gaba da tafiya har suka isa bakin get d'in gidan su bata yi magana kwan_kwasa kofar tayi masu suka le'ko ganin masu gidan ne ya saka su bud'e masu suna basu girma, wuce su sukeyi har cikin falon ya rakota, kawai ta wuce cikin d'akin ta, shi kuma sai ya zauna a gurin ya kusan awa d'aya sai da abokan sa sukayi ta kiran sa, sannan ya tafi. Husnah kuwa jefar da mayafin ta tayi da jakar hannun ta, tayi kwance ta saki kuka, babu mai lallashin ta har ta gaji dan kanta Husnah tun daga wannan ranar bata sake d'aga kiran kowa ba kashe wayar ta tayi zaman d'akin ya dawo mata sabo ba dare ba rana ruwa kawai take sha duk tabi ta rame ta fita hayyacin ta. Koda aka kawo Amarya Husnah bata fito ba d'akin ta ma a kulle yake, Husain ma ya so ta fito ya had'a su yayi masu nasiha amman shuru_shuru kake ji ko ranar dasu Anty Zarah suka zo gidan Husnah na jin su suna doka mata 'kofa amman taki fitowa dole suka 'hakura. Tunda aka kawo Amarya sai da tayi sati d'aya Husnah ta bud'e d'akin ta, tadawo tayi kwanciyar ta, Husain ne ya shigo d'aure fuskar sa ya zauna a bakin gadon nata, ita kuwa daga ita sai yar shimi da wadon best d'in ta rufe rabin jikin ta da zanen gado tayi rub da ciki ta d'ora filo ta d'ora hannun ta duka a kai tana saka jan farce, ja. Husnah tana jin sa, shi kuwa ya bud'e bakin sa yace......... *Comment and share* *A GIDANTA NA GIRMA* *BY NANA: KHADEEJATU* *_UMMU IHSAN_* *SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU SOSAI SON FISABILILLAH* *YA ALLAH KAJIKAN BABA NA DA MAMA NA KAYI MASU RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SU KA SANYA SU A ALJANNAR KA TA FIRDAUSI BIGAIRI HISAB SU DA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.* *AMIN YA ALLAH* *To Alhdulillah Allah ya nufeni da dawowa gashi zamuci gaba daga inda muka tsaya* *_Bismillahir Rahmanin Rahim_* 1001~105 Cikin d'aure fuska yace, "Husnah kina nufin cewar haka da kika aika ta shine mafi ta? Ummey da kanta tazo gidan nan ta nemi alfarmar ki fito tayi mata dake amman kika ki fitowa kin kusan wace ce Ummey a guri na da matsayin ta kuwa?". Cikin d'aure fuska itama Husnah ta tashi zaune tace, "ban sani ba kasan ni ba'kuwa ce a gidan nakun ko? " Cike da jin haushin rainin da Husnah tayi masa ya d'auke ta da mari kuma ya 'kara d'auke ta da mari sai huci yakeyi wani irin uban ihu Husnah ta saka masa, sai da ya saka hannun sa duka biyun ya rufe kunnen sa, jan farcen Husnah zubewa yayi a jikin ta ihu kawai take rafkawa, da guda Amaryar sa ta shigo cikin d'akin babu ko sallama fuska taci bilicin sai uban atach da ta zubo, tana tafa hannu tana fad'ar, lafiya my honey? Mike faruwa ne? ". Husnah kuwa kukan ta kawai takeyi Husain kuma kukan Husnah ya damesa har cikin zuciyar sa yake jin sa, ita kuwa ta dage iya kar gaskiyar ta hawaye kawai take ambaliya, Amaryar Husain kuwa jikin Husain ta shige tana shafa shi sorry my honey kayi hakuri zo muje ka daina damuwa da rigimar mace bare masifaffen mutum wanda baya son mutane mai wulakanta kowa, kasan ni bana son fushinka dan ka zamo sadauki, oya muje na baka farin ciki kaji masoyina? " Shi bama kallon ta yakeyi ba, Husnah ce kawai ya kafe da ido wadda har fuskar ta tayi ja idon ta ya fara kum bura ga shatin hannun sa duk sun fito lafiya lau, kawai Husnah ta sauka a 'kasa ta soma tsalle daga nan taje ta janyo trolley d'in ta har biyu, ta nufi bakin koda dasu cikin zafin nama Husain ya tury Amaryar sa, yayi kan Husnah yasaka hannun sa biyu ya tallabe ta saboda tsoro dan bata sarar ba taji anyi sama da ita, sai ta saki trolley d'in shi kuma yayi kan gadon da ita ya kwatar, ai kuwa tayi wani zillo zata tashi ya danne ta, Amaryar Husain kuwa zuciyar ta kamar ta fashe ta saki uban tsaki tabar cikin d'akin harda bugo masu 'kofar da 'karfin gaske". Husnah kuwa duk da tana jin zafin marin sai da taji sanyi_sanyi a zuciyar ta, amman kuka kam yin sa takeyi ganin ya'ki barin ta, ta tashi tsaye ko zaune kawai tayi kamar ta ha'kura yana ganin ta saki jikin ta, sai ya koma gefe ya dafe kai, Ummey ce ta shigo cikin d'akin da saurin ta kamar zata tashi sama Husain da sauri kowa ya maida hankalin sa gurin Ummey, Husnah na ganin Ummey kawai ta saki wani uban kukan Anty Zarah da itama ta shigo cikin d'akin da saurin ta, sakin baki tayi tana kallon Husnah ta ta'be tace, "Husnah tace uban waye kike yiwa wannan iskan cin? Husain shine ka saka mata ido tana irin wannan iskan cin a gidan ka, bayan ta daki Amaryar ka, dan ka rama mata shine take wannan iskan cin kazo kana lallashin ta? ". Cike da takaicin abun da Anty Zarah takeyi mata, cikin kuka tace, "wallahi na fasa Auren dole mutum ya sakeni naje neman dan gina wallahi kuma na Auri wanda nake so, yake sona". Aikuwa da sauri Anty Zarah ta buge mata baki Husain kuwa jijiyoyin kansa har tashi sukeyi idon sa ya rufe cike da masifa yace, "sai mi dan na rabu dake ke kai ce mace ko kuwa ce maki akayi zama na karuwa son rai nane, dan kinga kowa yana goyon bayan ki, sai aka ce maki no sonki nakeyi ne!? ". Cike da ba'kin ciki Ummey ta fashe da kukan takaici duk sai iskan cin kowa ya tsaya tsab kamar anyi ruwa an d'auke babu wani mai magana kukan Ummey kawai ke tashi, tana fad'ar innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, allhuma afjirni fi musibati, wahalafni khairin min ha, kawai ta tashi buuuu kamar guguwa tabar d'akin kowa yana kiran Ummey Ummey amman inaaa Ummey tasa kai kuka kawai takeyi, tashi duk sukayi suka mara mata baya, Husnah kuwa kasa tashi tsaye tayi dan jiri ke d'ibar ta, kuka kawai takeyi, kanta jin takeyi kamar ya tarwatse saboda ciwo, Husnah daurewa tayi ta tashi a hankali ta nufi why drop dinta ta d'auki doguwar riga ta saka juwar da zatayi ta dawo bakin gado kawai jiri ya kwashe ta sai 'kasa wan wars, kwance Husnah take numfashin ta ya d'auke d'iba. Ummey kuwa haka tabi hanya tana kuka su Anty Zarah da Husain suna biye da ita suna kuka, basu tsaya ko ina ba sai cikin gidan duk wanda ya ga Ummey a lokacin sai tabbar da babu lafiya, a gidan mutane duk sun rud'e shi kan shi Daddy ya shiga cikin tashin hankalin dan yau shine farkon ganin kukan Ummey har tabiyo hanya a hakan yasan mummunan abune ya faru. Hannun Ummey Daddy yaja, suka zauna yace akawo mashi ruwa, da gudu Anisah ta kawo ruwan sanyi coffi ansa yayi ya zuba ruwan da hannun sa ya bata tasha, ya kawo mafefeci yanata fifita mata, yanayi yana tofa mata addu'a cikin Ikon Allah ta soma sauke ajiyar zuciya sai da yaga alamar natsuwa a tattare da ita ya kama hannun ta duka biyun yana murzawa yana kallon ta, zuwa can yace, "kin gano wa idon ki mugun zaman da sukeyi ko?" Naso na dakatar dake, amman kuma naga ya dace ki tabbar wa idon ki gaskiyar lamarin, Hajiya maganar gaskiya ita ce, Husnah da Husain ido ne kawai maganin su, duk ranar da suka ga damar gyara rayuwar Auren su, su gyara, ai idan ita Husnar shirme yayi mata yawa, shifa Husain baga matar Auren sa nan a gaban sa ba, miyasa ita ya d'auke ta a matsayin matar sa, kuma ita ma margayiya Mardiyya fa haka yake zaune da ita ne? , To dan Allah ki rabu dasu da iskan cin su, gir_giza kai Ummey tayi hawaye na zuba a idon ta, tace, "Alhaji na ri'keka da kasa baki a kawo karshe Auren nan da suke ikirarin ba zasu zauna da juna ba kowane a gaban idona ya bukaci a kashe Auren tunda basu kaunar junan su, Husnah da Husain Auren su zunubi ne kawai suke kwasa su dukan su biyun! " Gir_giza mata kai Daddy yayi yace, "ya ilahi tabbas kuwa zan d'auki mataki akan wannan kukan da suka saka mani mata tanayin sa, idan su basu san darajar Auren suba to ni nasan darajar nawa Auren, duk kuje ku bamu guri dukan ku bana bu'katar ganin mutum ko d'aya a gurin nan! ". Tashi kowa yayi kowa da kukan sa, Husain gida ya koma direct d'akin Husnah ya shiga halin da tsinci Husnah a cikin sa shine ya 'kara d'aga masa hankali koda ya ta'ba ta sam bata motsi, gaban sane ya fad'i cikin sauri ya kira Anty Zarah yasan ita ce kawai zata iya daukar wayar sa, cikin razana, yace "Anty Zarah Husnah ta mutu bata motsi". Kit ya kashe wayar. Anty Zarah kuwa wata uwar kalmata buga tace shike nan Husnah ta mutu, na shiga ukku ni Zarah da wani uban hanzari Yaya Yusuf yake kiran Husain Amman Husain ya kasa d'auka, kawai suka ja mota dan sai sunfi sauri suna isa 'kofar gidan suka taka burki suka fito da gudu Shaheed da Yaya Yusuf da Anty Zarah Anisah suka shiga cikin gidan d'akin Husnah suka nufa turus sukayi, suna murza ido, da ket su Yaya Yusuf da Shaheed suka 'karasa gurin Husnah suka fara dubawa Anisah tace shike nan Husnah ba'kin ciki ya kashe ki, wayyo Allah ni Anisah". Bin ciken Husnah sukeyi har suka gano cewar somewa tayi, ai kuwa d'aukar jin jira sukayi mata suka fita da ita sai mota suka nufi asibiti da ita, da sauri aka anshe ta taimakon gaggawa aka bata, bata falka ba har akayi awa ukku dole Yaya Yusuf ya kira Daddy ya sheda masa halin da ake ciki, da sauri Daddy ya sanar wa Ummey, ai kuwa ta 'kara rud'ewa, haka sukaje asibiti amman har zuwa lokacin bata falka ba, sosai suka shiga cikin tashin hankali, Husnah sai da cikin dare ta falka daga suman da tayi, kanta takejin yana sara mata kamar ya cire. Dafe goshi tayi a hankali ta juya sai akan idon Anisah wadda aka bari ita da Anty Zarah su Yaya Yusuf da Shaheed da Husain suna waje, da sauri Anisah tace, "Husnah sannu kin falka ne? " gyad'a mata kai Husnah tayi tana rufe da ido ta, haushin kowa takeji, Anty Zarah kuwa tun lokacin da taji Anisah ta ce Husnah ta falka ta soma ajiyar zuciya da godiyar ta kafe Husnah da ido. Fita Anisah tayi sai gata ta dawo dasu Yaya Yusuf da Doctor, sannu suke yiwa Husnah amman bata kalli kowa ba kuma bata amsa ba, Doctor ne ya ce, "ina fatan ba wata matsalar bace ta hanaki bud'e ido ba" Kai Husnah ta nuna masa wanda take jin kamar ya tarwatse saboda ciwo, sannu suke jero mata, Doctor yace, "ku bata koda ruwan tea ne ina son nayi mata allura ne da ruwa" Da sauri Anisah taje ta had'a mata ruwan tea sai da ya rage zafi sannan ta kawo mata, Anty Zarah ce tace, "Husnah bari na kamaki kisha tea ko? " Da sauri Husnah tace, "wallahi yau sai dai nayi ta zama da yunwa ta dana yarda ki bani wani abu da hannun ki! " Cikin muryar masa lafiya Husnah take wannan maganar, ai kuwa Anty Zarah taji babu dadi duk da tasan hakan zai iya faruwa, daman, Anisah ce ta kama Husnah ta tashi ta bata ruwan tea idon ta har yanzun a rufe suke, sai da ta dan sha san nan ta kauda kai gefe, dan lokaci Doctor ya bata kafin ya dubata, ya fita. Yaya Yusuf ne ya ce, "Husnah dan Allah ki ajiye komai ki samu lafiya sai muje gida muyi magana kinji? ". Ba tare da Husnah ta kalli inda yake ba kuma bata gyad'a masa kai ba, shiru tayi abun ta, kowa cike yake yau da mamakin irin wannan fushin na Husnah wanda ya shafi kowa. Allurar da Doctor yayi mata ne ta soma aiki, bacci har ya fara d'aukar ta Anisah ta tashi ta gyara mata kwanciya gudun wuyan ta yayi ciwo. Suna ganin ta koma bacci su Yaya Yusuf suka sauke ajiyar zuciya suka fita daga cikin d'akin suka nufi massallaci, su Anty Zarah kuwa a haka suka kwana, sai lokacin sallar asuba sukayi sallah da gari ya soma haske san nan sukayi shirin zuwa gida dai_dai lokacin ne su Ummey suka shigo bayan sun gaisa ne, Anisah take basu labarin farka war Husnah, hamdala Ummey ta sauke, ita da Daddy da Suhailah, Ummey kuwa tace, "kuje gida ku futa Zarah sai zuwa anjima sai ku dawo amman fa kuyi bacci kunji ko?". Amsawa sukayi suka tafi, tare dasu Yaya Yusuf suka tafi gida, Husnah kuwa tun lokacin zuwan su Ummey ta falka, ganin su Husain ne ya nata bud'e ido, sai fa da ta tabbar sun tafi sannan ta bud'e ido, murmushi Ummey tayi batare da ce Husnah uffan ba, rikata tayi, ta tashi zaune Suhailah ce ta, rikata suka nufi bayi, tayi brush, ta bata guri tayi lalurar ta sannan ta fito a bakin 'kofa suka had'u da Suhailah kawai ta ri'ko ta suka, dawo saman sallaya ta zauna, tayi sallolin da ake biyar ta, bayan ta gama ne Ummey ta bata breakfast da kanta, har sai da ta tabbatar da ta 'koshi Kawai doctor ya shigo koda ya duba ta yaga jikan ta yayi kyau yayi mata tambayar mike damun ta yanzun, ta sheda masa ciwon kai ne da ciwon ciki, allurai ya rubuta mata da magani ya basu sallama tare da sharuddan shan magani da cin abinci. Doctor na fita suka fara tattara komai nasu, Daddy ne ya shigo cikin farin ciki ya anshi takardar sallama da ta maganin yace, "ku fito mu tafi gida ko? ". Haka dai suka fito Husnah tana tafiya zaka fahimci cewar batada lafiya, saboda tanayi tana cije baki, har suka isa jikin motar Daddy suka shiga sai gidan Daddy, suna zuwa su Anty Zarah dasu Shaheed Yaya Yusuf suka fara murmushi tare da godiyar Allah, sannu suka hauwa Husnah amman kamar bada ita suke ba, d'aki kawai ta wuce abin ta. Dariya Daddy yayi yace, "Ikon Allah ni wannan fushin na Husnah dariya yake bani, ace kowa ya shiga ciki, To wai mukam miye laifin mu a ciki ne, Bayan abun a tsanin ta da mijin tane Husain?". Dariya duk sukayi Ummey tace, "yo ni wannan tam bayoyin naka a jere Alhaji ai duk bamu da amsar su, sai dai mu jira har ta samu sau'ki mu zaunar dasu zama na 'karshe akan wannan Auren nasu na jaraba". Haka dai akayi ta tattaunawa, Husnah kuwa bacci kawai takeyi bata magana da kowa, har aka kwana biyu ta samu sau'ki Alhamdulillah, Daddy ne ya tara kowa a gurin Ummey Yaya Yusuf Anty Zarah dasu Shaheed Anisah Suhailah Safiya sai iyayen gayyar wato Husain da Husnah, Daddy ne ya fara bud'e taro da addu'a fuskar shi sam babu wata walwala, ba dariya fuskar sa a d'aure. Yace, "duk kowa yasan abun da ya taramu anan to ba zanyi wani dogon bayani ba, Husnah Husain, miye kuka aikata a ranar da kuka saka Hajiya kuka abunda ya zo ya d'aga hankalin mu saboda munga ba'kon lamari a gurin wadda bama zaka iya fusata taba, sai gashi harda kukan ta da hawaye a idon ta, kuma ta biyo hanya a haka har gidan nan, ku muke saurare!? . Duk shiru gurin ya d'auka sai sautin kukan Husnah da shashshekar kukan ta ke tashi a gurin, cikin tsawa Daddy ya sake tambayar su wanda har sai da kowa ya shiga tai tayin sa. Husnah cike da dakewa ta soma magana tace, "Daddy zan sanar daku komai abunda ya faru a ranar kuwa shine, tun ranar dana bar gidan nan aka sanar dani cewar Husain zaiyi Aure saura kwana biyar to ina dawowa gida na rufe d'akina ban sake budewa ba sai ranar da wannan rigimar ta faru, duk da kuwa ana zuwa ana buga mani 'kofa amman bana bud'ewa, Daddy saboda wasu dalilai wanda nice nake hango su, kasan cewar bani da kowa ballema na sanar da abunda ke damuna kowa laifina yake gani, bayan naga Amarya tayi sati d'aya ne na bud'e 'kofa ta nadawo na kwanta ke nan Husain ya shigo wai Ummey tazo gidan mu har 'kofar daki na tayi ta kirana da dukan 'kofa ta naki bud'ewa, nasan darajar Ummey kuwa a gurin sa, nasan yaya yake jin Ummey maganganu dai ga sunan" haka Husnah ta labar ta masu komai bata boye, nata ko d'aya ba har zuwan Ummey da Anty Zarah har barin su gidan, tana zuwa gurin da fad'i, tayi shiru sai kuka sanban tace, "Daddy gashi nan duk wanda ya mutu shi ake yiwa 'karya idan na fad'i akasin abunda ya faru gashi nan da ransa kuma a gaban sa". Shuru gurin yayi Daddy yace, "Husain duk Hakane gaskiyar abunda ta fad'a ko da gyara? ". Husain ya ce, "duk gaskiya ne". Ummey ta ce, "Husain uban waye ya sanar dakai cewar nazo gidan ku, kuma nayi ta kiran Husnah taki bud'ewa har nayi fushi na tafiya ta!? " Cikin fushi Ummey ke wannan maganar, a take, Husain ya ce, "Ummey Allah ya huci zuciyar ki, wallahi Zee baby ce ta fad'a kuma wallahi har da kukan ta, har niyar nazo gurin ki na baki hakuri sai kuma tace ai da fushi kika fita ba zaki ko kalli inda nake ba". Cike da takaici Ummey tace, "Husain ban ta'ba sanin cewar kai wawa ne ba sai yau, kuma ban ta'ba sanin cewar kai baka san halin makircin mata ba, sai yau, kai har wai wata zata shirya maka 'karya a kaina kuma ka d'auka? Kai a tunanin ka kishin mata ban zane? In ma banda rashin tuni irin naka da mace ta maida kai wani soko taya zan kira Husnah kira d'aya biyu ta'ki amsa mani, da har kake fad'ar tasan irin yanda nake a gurin ka kuwa? To ita Husnar ya take ne a guri na? Ko kuma taya zan zo gidan ku ba tare da na nemi kuba kai da Husnar? To yan zun zan ja maka kunne ko dai kaja kunnen matar ka akan yi muna karya ko kuma musa 'kafar wando d'aya da kai da ita aikin banza da yofi kawai! ". Jikin Husain ne yayi mugun sanyi, dan shi kwata_kwata bai kawo tunanin halin kishi ba a gurin, yama manta da cewar itafa Husnah a gidan su take a gurin mahaifiyar sa ma. Daddy ya ce, "to amman Husain gaskiya ka sauya tunanin ka kuma ka gyara halin ka, ace mace ce zata haddasa maku har takai ga mahaifiyar ka ta zubar da hawayen idon ta? Kai da sa ke gaskiya, sannan magana ta biyu ita ce tunda bamu isa da kuba, bamu isa ku faran ta muna rai ba, ku raba wannan Auren da muka had'a ku saboda mu kam bamuga alamar zaku iya yi muna biyayya ba, Kuma kun wulakanta mu kunci zarafin yardar da mukayi daku, a yau ne muke baku umurnin rabuwa da wannan Auren da mukayi maku kowa yaje ta zauna da za'bin ransa za'bin da bamu mukayi maku shi ba, Husnah Husain yan zun nan nake son ganin cikar wannan umarnin namu na 'karshe wanda ba zamu 'kara saka maku baki a cikin lamarin kuba, sai kowa tasa ta fitar dashi! ". A zabure duk suka tashi tsaye, Ummey tace, "kwarai kuwa tunda daman mune mukayi wannan had'in da zaton zaku iya yi muna biyayya, sai kash shekara d'aya da wata ukku babu alamar hakan daga dare ku dan haka mun yanke hukunci na 'karshe dole ne ku wallawale wannan had'in da mukayi maku!. " Da sauri Husain ya dawo gaban Daddy da Ummey ya ri'ke 'kafar su su biyun ya duka yana zubar da hawaye yace, "Ummey Daddy dan Allah kada kuce haka wallahi mun anshi maganar ku kuma mu masu yi maku biyayya ne! ". Anty Zarah ta ce, "to Husnah hankalin ki ya kwanta ko? Mutanen da basu nuna muna wani ban baci ba da yaran da suka haifa yau sune kika kasa sakawa farin ciki ko? Dariyar takaici tayi taci gaba da cewar nasha zaunar dake na sanar dake cewar ke mace ce kece ya kamata kijawo mijinki a jikin ki, kuma kece ya kamata ki koya masa sonki amman kikayi kamar wata kurma ba kya sauraren duk wata nasiha tawa, to yan zun kina nufin idan har kuka rabu da Husain zaki dawo cikin gidan iyayen sa ki zauna ne ko miye kike nufi? ". Cikin fushi Husnah tace, "ya isa Anty Zarah haba! Komai Husain komai Husain, kuma komai laifin Husnah Husnah juya to duk naji kuma ki sani, da sani na nake kin yin abun da kike son nayi, kin ta'ba had'a mu nida shi kika tambaye mu mike faruwa a tsakanin mu, kiji laifin kowa kiyi muna fad'an tare? Sai dai kullum nice mai laifi nida bani da gata sai Allah!. Ummey Daddy yau zakuji miye yasa nake biyewa Husain bamu zaman Aure kamar yanda kuke so, Ummey ke uwa ce ta gari kuma ni a matsayin yarki nake, shin taya kike tunanin yarki zata yarda ta zauna da mijin da yake kiran ta da sunan karuwa! ? Ummey ada can bana damuwa da wannan kalmar dan ban san mi kalmar take nufi ba, saboda *A GIDANTA NA GIRMA* ita wannan kalmar amman kasun tuwa ta daku sai na fahinci cewar mummunar kalmar ce, ada ina d'aukar shirmen mune nida shi kafin muyi Aure amman ana d'aura muna Auren yaci gaba da kira na da wannan kalmar, har zuwa yau d'in nan! ". Kuka Husnah ta 'kara fashe wa dashi tace, "Ummey a yanda naji wani malami yana fad'ar zargin zina yana 'bata Aure dan haka nikam wallahi ba zan yarda na zauna da irin wannan mutanen b! ". Ummey ce ta tashi ta ri'ko Husnah ta kalli Husain tace, "ashe dai Husnah tafi ka sanin gaskiya, Husain ka bani mamaki sosai dan haka, a matsayina na mahafiyar Husnah na yanke wannan alakar taku, saboda 'yata ba karuwa bace kuma zargi daman yana 'bata Aure dan haka Auren ku ya 'bace, kaje gurin Amaryar ka wadda kake so ka kawo mani takardar 'yata da kuma sanar dani saki nawa kayi mata! " Ummey na kaiwa nan taja hannun Husnah zasu bar gurin, Anty Zarah ta ce, "Ummey dan Allah kiyi.... " Ummey tace, "kudai yi hakuri keda kanen ki wanda baku son gaskiya kuma ku koma islamiyya". Kawai Ummey tayi tafiyar ta da Husnah na jikin ta. Husain da ido yake bin Ummey har ta 'bace wa ganin sa, jiyowa yayi ya bud'e baki daker zaiyi magana da Daddy, Daddy ya ce, "kada kace dani komai malam dan haka hukunci yayi kyau ina goyon batan gaskiya na godewa Allah daya sa Husnah tafika ilimin addini ni kunga tafiya ta". Daddy tashi yayi yabar gurin Yaya Yusuf kuwa cewa yayi, "Zarah kinga abunda nake fad'a maki kirika bin cike ki daina ganin laifin Husnah ki bin ciki Husain amman kika rufe idon ki dan haka yan zun wa gari ya waya? ". Shima tafiyar sa yayi, Shaheed kuwa cewa yayi, nikam kunya ta kani ya tashi yayi tafiyar sa haka su Anisah suka bar gurin aka bar Husain da Anty Zarah kowa ya kasa furta kalma daya. *Comment and share* *A GIDANTA NA GIRMA* *BY NANA: KHADEEJATU* *_UMMU IHSAN_* *SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU SOSAI SON FISABILILLAH* *YA ALLAH KAJIKAN BABA NA DA MAMA NA KAYI MASU RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SU KA SANYA SU A ALJANNAR KA TA FIRDAUSI BIGAIRI HISAB SU DA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.* *AMIN YA ALLAH* *To Alhdulillah Allah ya nufeni da dawowa gashi zamuci gaba daga inda muka tsaya* *_Bismillahir Rahmanin Rahim_* 106~110 Anty Zarah ta dawo a kusa da Husain tayi 'kasa da muryar ta ta ce, "Husain shin da gaske ne kuwa abunda Husnah ta fad'a a yan zun? ". 'kasa yayi da kansa yana kallon Anty Zarah ya ce, "Anty Z kun yarki nakeji a yanzun tabbas ban kyautata maki ba, koda ace basu Daddy ne suka had'a wannan Auren ba, ai zanyi duba da irin yanda kike nuna mani soyayya da kulawa kamar wanda muka fito ciki d'aya, tabbas kuwa ni na zaman to butulu, wanda ya kasa saka farin ciki a cikin zuciyar ki, domin kuwa tun kafin ki yarda da Auren Yaya Yusuf nasan irin soyayyar da kike yiwa 'kanwar ki, kuma nine wanda yayi maki alkawarin nemo maki ita duk inda take tare da alkawarin bata kulawa ta musamman, amman kash! sai gashi na swaba wannan alkawarin nabi son zuciya ta, gashi Husnah zaman hakuri takeyi dani amman ke kullum cikin ganin laifin ta kikeyi a kaina, Anty Zarah ba zan boye maki ba ina jin haushin kaina da jin zafin kaina dan gane da kin faran ta maki Anty Zarah kiyi hakuri bazan iya zama guri d'aya dake ba a matsayin da nake ciki ba yan zun! ". Tashi yayi da sauri yabar gidan, Anty Zarah kuwa dafe kai kawai tayi ta kasa attaka komai. A can cikin d'akin Ummey kuwa lallashin Husnah takeyi tare da jaddada mata cewar zata amsar mata takardar ta sai ta Auri duk wanda take so, amman fa sai taga ta saki ranta ta cire damuwa a tattare da ita. Husnah dai kwanciyar ta kawai tayi, har sai da Ummey taga tayi bacci san nan ta sauka saman gadon ta fara zarya cikin d'akin ta maida hannuwan ta a baya ta soma zuwa gurin madubi ta dawo bakin 'kofa, tana ta aikin tunani. Husnah dake kallon Ummey sai duk taji ta bata tausayi, lallai Ummey takai Uwa har Uwa duk inda Uwa take Ummey takai can, haka Husnah tayi ta nata nazarin har tayi baccin gaskiya. Daddy ne da Ummey suke tattauna akan wannan lamarin, Daddy ya ce, "Hajiya ada naso ace Husnah a cikin mu ta rayu amman gashi Husain ya 'bata Auren nasu, ni na rasa ina tunanin Husain ya tafi ina gudun zuciyar sa suka tafi shin wai ma ina irin yanda yake yiwa Zarah alkawarin zai kular mata da amanar Husnah suke anya ma kuwa Husain kan sa d'aya kuwa? ". Ummey tace, "toh! Alhaji nifa wallahi Husain na kasa gane mike damun Husain ace kullum cikin kiran matar ka da karuwa kake, taya ma idan wata ce zata zauna da kai har ku kai irin wannan tsayin lokacin? " Suna cikin maganar ne Yaya Yusuf ya shigo cikin damuwa yace, "Daddy dan Allah kuyi hakuri tabbas nasan Husain bai kyauta amman ni nasan abunda, zan iya yin wani abu akai dan Allah Daddy kudai na maganar saki a tsakanin su, wallahi bana kaunar jin irin wannan maganar dan Allah Daddy Ummey ku janye ta kawai ku dai bani dama, kunji? " Shiru sukayi Daddy ya ce, "Husain son Husnah ne baya yi, ba komai ba". Ummey tace, "aa wallahi yana son ta sai dai bai san da hakan ba, har sai ranar daya tayi nesa dashi, irin nisan da zai iya zaman to masa, ga 'koshi ga kwanan yunwa". Dariya duk sukayi suka kitse maganar su, anan, Yaya Yusuf ya je ya duba Husnah wadda suke zaune dasu Anisah suna labari ita kuwa sai anzo gurin dariya take yin dariya amman bata saka masu baki ba a cikin labarin su ba. Tana ganin Yaya Yusuf ta saki fuskar ta tace, "Yaya Yusuf ina yini ina yara na, wallahi nayi kewar su ba kamar Baby na, amman babu komai itama yar tawa ta gujeni". Dariya Yaya Yusuf yayi yace, "lafiya lau Alhamdulillah Husnah ya jikin naki dafatar dai babu wata matsala? ". Husnah gyada masa kai, sannan yace, "masha Allah, yauwa to ke Husnah tunda baby taki zuwa gurin ki ke ki shirya ki kai mata ziyar bazata gashi kuwa yau juma'a da wuri suka dawo school kuma taje anyo mata kitso nasan yan zun dai tana gida". Mare masa baki Husnah tayi ta ce, "bazan je gidan ku ba, idan taso zata zo idan kuma bata zoba kanta dan gobe nake son zuwa gidan Mommy nayo mata wata d'aya ko sati ukku". Ba Yaya Yusuf ba, hatta su Anisah sai da suka zaro ido suna kallon ta, cike da mamaki. Da ket Yaya Yusuf ya saita kansa ya ce, "haba dai ina ma laifin kije kiyi mata kwana biyu ki dawo? " Dariya Husnah tayi ta ce, "Yaya Yusuf da gaske na keyi fa wata d'aya ko sati ukku zan yo". Anisah ce ta kasa daurewa tace, "kice dai zaki kwashe kayan ki ki koma gidan ta ko? ". Shiru Husnah tayi tana nazari zuwa can Husnah tace, ", toh Yaya Yusuf ni wallahi kadaici nake son yi ko kuma nayi tafiya wani gurin inda babu kowa". Shiru yayi yana kallon ta zuwa can yayi masu sallama yayi tafiyar sa ba tare da ya bata amsa ba. Suhailah tace, "Anty Husnah mi zai hana kije gidan Yaya Shaheed tunda kuna shiri dashi da matar sa, ki dan kwana biyu ina ga kamar zaki d'an futa a can ". Ajiyar zuciya Husnah ta saki ta ce, "ok to idan Shaheed din yazo zan bisa gidan nasan tun kun za'bi hakan kuna ganin kamar idan naje gidan Mommy yar gidan jiya za'a dawo ". Dariya kawai sukeyi mata har dare da Shaheed yazo Husnah ta sanar dashi zata je gidan sa gobe da safe tayi masu kwana biyu, dariya yayi yace, "sai dai ki tashi mu tafi yan zun saboda daman muna kewar ki tunda ba gurin kowa kike zuwa ba". Dariya Ummey tayi da yake ta san da maganar tafiya kuma farin ciki da jin gidan Shaheed din zata je ". Tashi Husnah tayi suka je gidan Shaheed matar sa na ganin Husnah ta rungume ta cike da farin ciki, taja hannun Husnah suka zauna sai fira, sai gurin sha biyu suka kwanta. Da safe ma tare suka had'a breakfast sosai Husnah taji dad'in zuwa gidan, satin Husnah d'aya tace zata dawo gida ai kuwa suka hana harda su 'boyewa Husnah trolley d'in ta, da ket dai Husnah ta zauna d'in. Husain ne ya shigo cikin gidan ya gaida Ummey da Daddy su Anisah suka gaida shi ya amsa yayi zaune yana kalle_kale ya kalli wan can ya kalli kofofin d'akin duka shiru_shiru, zuwa can ya maida hankalin sa gurin Ummey, ya fara sosa kai yace, "Ummey". Kallon sa Ummey tayi d'aure da fuskar ta, tace lafiya kuwa? ". Shiru yayi yana kallon Ummey yayi kamar tausayi ya 'bata fuskar sa, yace, Ummey yunwa nake ji ko zaku sam mani abinci? ". Kallon sa Ummey tayi tace, "babu shi ina abincin gidan ka, kuma ina yan aikin ku ina matar ka?. Shiru yayi kamar yayi kuka, Daddy yace, "abinci ya 'kare mun cinye amman ga 'kannen ka nan suje su dafa maka koda Indomie ce". Safiya ce ta tashi zataje ta dafo masa yace, "ki barshi kawai". Kallon Ummey, Ummey tace sai ki dawo ki zauna tunda ya fasa ko? ". Zama tayi, shi kuma a gidan ya yini sallah ce kawai yake fita yayi, kuma da ya gama sallar yake dawowa sai 'karfe goma da rabi ya koma gidan sa, tun daga wannan ranar kullum sai ya zo Ummey da Daddy kuwa da Yaya Yusuf da Shaheed duk suna kallace dashi. Sai da Husnah tayi sati ukku ranar ta saka masu rigimar dawowa gida dole suka kawo ta gida. Har dare suka koma gidan su A ranar kuwa Husain bai zo ba, da safe tun bakwai Husain yake zaune a cikin falon gidan nan yaci abincin safiya, Husnah sai 'karfe tara ta fito sanye take da riga da wando rigar iya cibi wando kuma ya kama ta sosai iya kwabrin 'kafar ta kanta kuma anyi mata kalaba ta, tana tafe hankalin ta a kwance, tazo ta wuce sa ta kawai tayi hanyar kitchen ta shige ta fara soya wainar fulawa. Husain a hasale kishi ya rufe sa idon sa ya rufe ya ce, "kan uban can uban waye ya saka yarinyar can zuwa wani gurin ba tare da izini na ba, kuma dan tsabar wulanci ku dubi irin shigar da takeyi wato dan ta ga nayi shiru shine har take wulanci son ranta har tazo ta ra'bani ta wuce, ba tare da ta ko kalli inda nake ba, wallahi sai nayi maganin wannan rashin kunyar taki! ". Tashi yayi fiiii ya nufi kitchen d'in ai kuwa kafin ya 'karasa Ummey ta dakatar dashi tace, "wallahi kada ka yarda kaje kitchen d'in nan saboda kai ba komai bane a gurin ta! ". Husain yaja burki ya jiyo yana kallon Ummey duk jijiyar jikin sa ta tashi, Ummey tace, "Husnah! Husnah!! Husnah!!! Sauri Husnah ta fito da wainar fulawa a hannun ta ta zubo tace, "Ummey gani kwad'ayi na tsaya yi, fa kinga abunda na soyo saboda tsabar kwad'ayi". Ummey tace, idan kika 'karasa zakuje gidan Alhaji Isma'il dan yaran sa sun dawo daga dubai dan Allah ki daure ayi wannan hidimar bikin tar bon su dake". Husnah ta ce, "yeeee Ummey daman ina son fita wallahi kuma naji dad'in wannan maganar taki.... Idon ta ne ya sauka akan Husain wanda ya kafe ta da ido, d'aure fuska tayi tace, "Ummey zan shiga ciki". Wuce Ummey tayi ta shige cikin d'akin su Anisah da sauri ta ajiye wainar fulawar ta haye saman gado ta dafe kirji tana sauke ajiyar zuciya kamar wadda tayi tsere da kura, duk ido suka zuba mata sai da ta dawo dai_dai sannan ta lura da kallon da sukeyi mata, Anisah tace, "lafiyar ki kuwa? ". Share zancen tayi kawai ta sauka ta d'auki wainar ta, ta soma ci suma duk suka shiga sahun ta, Anisah tace da alama kin had'u da twin d'in ki ko? ". Shareta Husnah tayi, Suhailah da Safiya suka saka dariya, Husnah ta share su. Koda suka gama Husnah kin fita tayi, harkar su tayi, suka ta yi mata shegan taka ta'ki kulasu tashi sukayi suka shirya harda Husnah sukayi anko suka saka doguwar riga sukayi rolling suka fito Ummey sukayi wa sallama suka fita Husain kuwa yana ganin sun fita ya faki idon Ummey yabi bayan su suna zuwa zasu shiga ke nan ya saka hannun sa ya janye Husnah ya ri'ke ta da karfin gaske tana ta son ta kubce ya kiya, yace, "zaku iya tafiya kuma wallahi duk kuka sanar da Ummey sai naci uban ku dukan ku". Babu yan da suka iya shiga motar sukayi suka ja suka wuce, Husnah kuwa duk haushi ya kama ta janta yayi ya shigar da ita cikin motar sa da sauri ya rufe da sauri tazo zata fito yayi saurin shiga yaja motar da 'karfi Husnah kuwa tace, wallahi duk abun mutum nafi karfin sa, kuma ba zan zauna dakai ba, kuma ko yan zun da ka sato ni, nafi karfin ka, dan ko 'kafar samarin da nake taraiyya dasu baka kai ba". Cike da zafin kishi Husain yaja motar sa ya bata wuta, wani irin horn ya danna wanda sai da mutane suka rud'e harda Husnah sai da ta tsorata da sauri ta rufe kunnen ta, masu gadin gidan ne suka bud'e 'kofar a tsorace, yaja ya fita da gudun sa, dai_dai fitowa Ummey da Daddy, cike da mamakin wannan uban horn d'in da ya doka, tambayar masu aikin tayi mi ya same sa, suka ce, matar sa ya d'auka suka fita. Kallon_kallo su Ummey suke yiwa junan su Daddy yace, "kin dai yarda da zan na ko? " Ummey ta ri'ke baki, tace, "ai dole na yarda wannan maganar kunyar yaron, ai naso ya 'kara horuwa ka dubi yanda ya dawo kamar wani sakarai yana neman inda take ya kasa magana dan yasan babu wanda zai bashi amsa, kuma fa harda ciwo yayi, mutanen da harda korar yan aikin sa yayi saboda ya gano cewar sune suka kira ni akan ana rigima shida Husnah ". Dariya Daddy yayi yace, "to Allah dai ya kaisu lafiya duk inda zasu amman wannan uban gudun haka? Nifa yarinyar tausayin ta nakeji wallahi" Hanya suka d'auka suka nufi wani uban gida hadden gaske horn yayi da sauri aka bud'e masu 'kofar gidan da 'karfin sa ya shiga gidan ya taka burki ji kake kiiiiii...., har 'kura na tashi, Ko kallon inda Husnah take bai kalla ba, bud'e 'kofar motar yayi yafita ya dawo ya bud'e wa Husnah 'kofar inda take ai kuwa ta d'auke nata kan tace, "babu inda zani nikam kama mai dani gida wallahi" . Ai kuwa kowa ya tattare hannun rigar sa ya dawo dai_dai jikin motar ya d'auke ta, ya d'ora a ka fad'ar sa ya rufe motar da 'kafar sa, ai kuwa tayi ta wutsil wutsil da 'kafar ta da hannu ta, shi kuwa ya share ta yaje ya bud'e 'kofar gidan ya shiga da ita yana zuwa akan kujera ya dire ta, ai kuwa ta kwasa da gudu, shi kuwa yayi saurin rufe d'akin da remote d'in dake hannun sa tana zuwa tayi_tayi ta bud'e ya'ki bud'e wa dole ta hakura tayi zaune a gurin ta fashe da kuka. Shigewar sa yayi ya barta a gurin tun 'karfe biyu har la'asar, sallah take son yi ta rasa yaya zatayi gashi har taji tashin motar sa, koda tashi tsaye taje jikin window shine ya fita cike da mamakin sa, tace, "mugu wallahi sai nabar wannan gidan, neman ruwan alwala, tayi ta kuwa sami fanfo tayi alwala, tazo tayi sallah har akayi isha'i bai dawo ba, tsoro ne ya kamata, da sauri ta nemi wani d'akin da tagani kusa da inda ya nufa gashi kanta ciwo yakeyi, gado ta gani aikuwa ta rufe d'akin tazo tayi kwanciyar ta gashi bata da waya a hannun ta sai ta 'kara jin wani sabon kukan a haka bacci ya d'auke ta. Can cikin bacci taji ana ta'ba ta ai kuwa a fir gice ta tashi zaune tana zarar ido mutum ta gani, ai kuwa ta fasa uban ihu da sauri ya rufe mata baki yace," ke nine fa matsoraciya kawai". Janye hannun sa tayi, ta matsa nesa dashi, dariya yayi yace,"kiji da zazzabin dake damun ki yarinya kafin nima na d'ora maki wani sabon ciwon dan naga alamar ba wani 'karfi ne dake ba kamar yan da kike cika baki, wai har ni kike kwatan tawa da 'kadan garun bariki wallahi yau sai kin gane da ban_ban ci". Tashi yayi ya dawo ya ajiye mata ledodi, yace Amarya ga kajin amarci nan da ango yake kawowa ranar farkon Auren su, ga kuma abinci nan nasan kina jin yunwa kuma ga magani nan nasan kina jin zazzabi". Tashi tsaye Husnah tayi tace, "wannan duk mafalki ne kakeyi dan haka tun wuri ka cire wannan maganar da ranka ni nafi karfin irin wannan shirmen naka, kuma ka sani nida kai sama tayi wa yaro nisa". Dariya yayi yace, "malama bisimillah ko ki kwantar da hankalin ki ko kuma ki tada hankalin ki labari ba zai chanza ba". Kallon sa Husnah takeyi cike da mamakin sa yau ya dawo mata sam ba Husain din da ta sani ba, har ma ta fara tsoron sa, lokaci d'aya, fita d'akin yayi ai kuwa da sauri taje ta rufe 'kofar ta dawo abinci taci taje tayo wanka ta dawo tana neman kayan da zata saka bata samu ba, da sauri ta nemi after dress din ta nan ma babu, zanen da ta d'ora ne kawai a jikin ta, da sauri taja da baya zata koma cikin bayin kawai taji anyi sama da ita, ihu tazo yi, yayi saurin rufe mata baki ya ajiye ta a bakin gadon ya d'auke hannun sa a bakin ta, yace, "shiiiii Amaryar Husain yau dai Husain yayi niyar mayar da matar sa Husnah ainahin matar sa ta sunna kinga kuwa yau babu wanda zai ce sai na rabu da mata ta, ke anaki tunanin kina nufin dan ina kiran ki da karuwa, abun ya kai zuciya tane, eh tabbas ina kiran ki da karuwa ne dan nine nake son ki zamo mani haka kuma a gareni kawai, kuma dan baki da wayau ne, da zaki tuno ranar dana mari Mardiyya akan ta kiraki da sunan da nine kawai nake kiran ki dashi, kuma a gaban ki nace idan ta 'kara furta wannan kalmar sai na koreta daga gida na, sai dai taje ta auri wani, to yan zun mu dawo maganar hakki na dan yau kam babu d'aga 'kafa ni ango ne" Husnah kam baki ya mutu, a take Husain ya........... *COMMENT AND SHARE* *UMMU IHSAN ce*๐ŸŒน:๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน 8/26/21, 12:41 PM - Ummu Ihsan ce ๐ŸŒนโœ๐Ÿ?: ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ *ยฐโ€ขยฐA GIDANTA NA GIRMAยฐโ€ขย?* ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ *BY NANA: KHADEEJATU* *_UMMU IHSAN_* *SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU SOSAI SON FISABILILLAH* *YA ALLAH KAJIKAN BABA NA DA MAMA NA KAYI MASU RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SU KA SANYA SU A ALJANNAR KA TA FIRDAUSI BIGAIRI HISAB SU DA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.* *AMIN YA ALLAH* *To Alhdulillah Allah ya nufeni da dawowa gashi zamuci gaba daga inda muka tsaya* *_Bismillahir Rahmanin Rahim_* ๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š 111~116 Yace, "malama kuma natsu kawai yau Misha soyayya, kai nima wannan hawaye da kikeyi tun zurani sukeyi dan bana jin tausayin ki yarinya, wai ma ni ina tsiwar taki take ita nake nema yau". Husnah dai ido ya raina fata, sai ta dawo kalar tausayi, yau harda su kiran Husnah da Yaya Husain dan Allah kayi hakuri wallahi na tuba nabi Allah na bika, amman inaa Husain kam sai da ya maida Husnah cikkakkiyar mace, abunda yayi ta bashi mamaki, bayan shi har photon Husnah ankawo masa ita da wani hotel wanda sai da yayi ciwo akan ganin wannan abun, amman duk da hakan baiji zai iya rabuwa da ita ba, lallai Husnah anji jiki, sai yaji tausayin ta duk ya kama shi ". Husnah kuwa tun da Asubahi take tsinewa Husain wanda ya yi zaune a kusa da ita ya aikin lallashin ta ita kuwa kukan ta kawai takeyi tana ja masa mugu wanda yake cutar marainiyar Allah, dariya yayi yace, "Allah Husnah idan kika sake koda furta kalma d'aya sai na kashe maki baki dan naga bai mutu ba, gashi ina na ganki d'auke da ciki na, kina tafiya daker". Tsit Husnah tayi sai shash shekarar kukan ta ke tashi, kama ta yayi ta tashi tana cije baki, ya kaita tayo wanka tayi alwala, ya dawo da ita, ko sallah da ket tayi ta, tana gawa ya kawo mata tea ta sha ya bata magani ta sha, sai bacci, d'aukar ta yayi ya maida ita saman gado, shima ya kwanta sai sha biyu suka tashi shine ya fara falkawa yayo wanka ya saka kayan sa ya fito ai nahin Angon sa, yazo ya fesa turare ya tsare Husnah da ido duk ta rame, murmushi yayi, yayi mata kiss ya fita, sai da Husnah taji tashin motar sa, sannan itama ta bud'e ido, a gaskiya Husnah kam anji maza ba wasa, duk ta zama wata iri. Daket ta tashi tayo wanka tana fitowa daga cikin bayin sai taga ya ajiye mata riga da siket mini, ba tare da damuwa ba Husnah ta saka kayan, sunyi mata cif rigar hannun d'aya na bireziya gareta, mai ta shafa ta sha powder da jan baki ta saka yan kunne da sarka, ta d'auki turare ta feshe jikin ta, sannan ta dawo bakin gadon ta zauna tace, "wash! Wallahi wannan mutanen mugu ne, 'karar waya taji a kusa da ita tana d'aukar wayar dake saman filo, Ummey ta gani kawai ta d'auka ta fashe da kuka, Ummey tace, "yi hakuri Husnah yan zun haka nace ya dawo mani dake gida, tunda sace ki, tun jiya ya kashe wayar sa, kuma taki wayar a kashe sai yanzu ya zo gidan ya bani wannan number yace wai ya sauya maki waya da layi haka ne Husnah? ". Husnah kuka dai take Ummey ke tambayar ta kodai wani abun ne, Husnah ta kasa cewa da Ummey komai sai kukan da takeyi, Ummey tace, "Husnah dukan ki yayi ne, ko yunwa kike ji ne? ". Husnah daket tace, "Ummey wallahi inda ma duka na yayi yafi mugun tar da yayi mani ". Murmushi Ummey tayi tace, "Husnah kibar ni dashi zanyi maganin sa ki kwantadda hankalin ki ki natsu zan lallaba sa ya dawo dake amman sai ki daina kukan nan gudun ciwon kai". Haka dai Ummey tayi ta lallashin Husnah ta daina kukan sukayi sallama, kwance Husnah take Husain ya shigo sai da gaban Husnah ya fad'i da sauri ta rufe idon ta dariya yayi yace, Husnah tashi kiji wani labari, kin tashi tayi, saman gadon ya hau da sauri Husnah ta tashi zaune, dariya yakeyi yace, wai Ummey na dawo mata dake gida nikam nace da ita ai kince ba zaki iya rayuwa babu niba". Kuka Husnah ta sanya masa tace, "wallahi nikam sai ka maida ni gida, dan kaga ka cucheni shine zaka hanani zuwa gida dan kar na kafad'a? " Dariya Husain yakeyi yace, "ke kina nufin zaki fallasa sirrin mijin kine da naki sirrin Allah ko tafiyar ki aka kalla ansan miye ya faru dan wallahi sai Ummey tafi kowa ganewa". Husnah kam yan zun taji ba zata iya yarda Ummey ta ganta a wannan yanayin ba kawai sai ta koma ta kwanta taci gaba da kuka, Husain kuwa ansamu abunda ake so Husnah ta daina maganar gida sai yaci gaba lallaba ta da ker ya samu taci kazar Amarcin ta, haka suka yini har dare inda Husnah tace, lallai yau ba zai kwana d'akin ba, yayi ta mata wayau har ta yarda, suka kwana a tare. Tun daga wannan ranar Husain bai sake yiwa Husnah komai ba sai da yaga ta soma sakin jiki dashi, Husnah kam tun ba'a saba ba har ta zama yar hannu, maganar komawa gida sai tasha kara, Husain yayi ta bata hakurin laifukan da yayi mata haka, ta hakura itama ta nemi yafiyar sa duk suka yafi juna, kawai suka dawo zallar masoya. Husnah ce kwance tasha ado, tana kallon series gidan 'kamshi kawai ke tashi hankalin ta ya tafi a film din, bata ji shigowar mutane ba sai dai kawai aka dafa ta, da sauri ta zabura, ai kuwa suka saka mata dariya. Husnah ganin masu dariyar Anty Zarah Anisah Suhailah Safiya da matar Shaheed kawai sai ta saki ihu ta rungume Anisah, Husain da tun d'azun yana tsaye yana kallon su yayi dariya ya 'karasa gurin shima, duk aka zazzauna Husnah da Anisah sai firar yaushe gamo suke, su Anty Zarah ne suka katse masu firar da fad'ar, "A Husnah haka akayi ko? An biyo miji batare da sanin muba ana nan ana shan soyayya". Dariya suka saka mata, Husnah tace, "kai Anty Zarah satoni fa yayi kuma ku ko kuzo nema na, ai babu komai, koda yake taya ma zaki zo nema ba bayan dan gaban goshin kine ya sato ni, gashi nasan baya laifi, gashi daga zuwan ki har kin nemo laifi na". Dariya sukeyi, Husain ya ce, "yau Anty Zarah dan Allah dubeta ki gani ai itace ta ce na sato ta ta gaji da zama gidan Ummey kuma tana jin kunyar tace wa Ummey zata biyo ni, shine na taimaka mata, ai kin san ni da taimako ko? " Da sauri Husnah ta ce, "wallahi mutum ya fad'i gaskiya ai dai naga yanda lokaci d'aya mutum ya dawo wani iri dashi ya rame yayi d'an wuya tunda na baro masa gidan sa, shine kullum cikin zama gidan Ummey ". Husain ya ce, "yauwa dan Allah halan wane gurin kika tafi, kika sa ina ta wahalar neman ki, gashi Ummey ta'ki bani damar da zan tambaye ta ko na tambayi wani, Anty Zarah dai nasan bata sani ba tunda inda ta sani da ta sanar dani dan kar na wahala da yawa kamar yanda nasha ba'kar wahalar neman gurin da kike, har gidan Anty Zubaidah naje da sunan nazo gaishe ta". Dariya duk aka sanya harda Husnah Anty Zarah ta ce, "wannan dariyar ta nuna muna cewar duk kun san inda take ko? ". Anisah ta ce, "kai ne baka kwantadda hankalin ka ba, amman da ka kwan tadda hankalin ka da ka gano inda take". Husnah tace, "nikam ina gidan Shaheed ina futawa ta". Husain ya ce, "Shaheed munafuki ashe kina gidan sa, shine yake ce mani nabashi number ki ko na sanar dashi inda kike? ". Dariya akeyi, Husain ya ce, "ina zuwa". Tashi yayi ya nufi d'akin sa, yana d'an dad'e kafin ya dawo, da wani babban littafi ya dorashi a jikin Husnah ya ce, "Baby na ki duba wannan littafin yau zakiji abunda baki ta'ba jiba keda yan uwa na, nabaku wannan damar ". Gefe ya koma Husnah sake da baki take kallon littafin wanda aka rubuta, sirrin zuciyar Husain, mijin Husnah. Duk sai suka sauka 'kasa suka ajiye littafin a tsakiyar su, Husnah ce ta fara bud'e littafin, kawai photon Husnah wanda takai Daddy asibiti ya bayya na, cike da mamaki Husnah ta d'aga idon ta tana kallon Husain gashi tana d'aukar photon taga rubutu kamar haka:-> _Wannan itace wadda tayi zarra acikin matan duniya muryar ta kawai naji, sai naji zuciya ta, ta amince da ita sai naji cewar kawai itace mata bugun numfashi na_ D'aga mata gira yayi, sai ta sake bud'e wani shafin shi kuma an rubuta, _ceton mahaifina tayi amman nikam nasan wannan ni aka aikowa da ita, domin na Aure ta, tabbas nikam Allah yayi mani gata, da ya had'a ni da wannan kyakykyawar yarinyar ajin farko, lallai nasamu babban rabo_ Wani shafin ta duba taga an rubuta, _"ya ilahi na shiga cikin mawuyacin halin 'batan masoyiya ta, na rasa mike damuna, farin ciki na ya gushe, Allah ya kawo mani wannan yar baiwa, wadda duk taku d'aya nata yake bugawa tare da zuciya ta!"_ Haka ta sake duba wani fejin, taga an rubuta, _Ciwon son wadda bata ma san dani ba a rayuwar ta zai kashe ni, ya Allah koda sau d'aya ne ka bayyana mani ita, damuwa ta Aure ni, nikam ya ya zanyi da rayuwa ta ne!?_ Haka dai sukayi ta dubawa duk na damuwa suke gani, suna zuwa tsakiyar sukaci karo da:- _Alhamdulillah Alhamdulillah yau Allah ya amshi addu'a ta, Baby Husnah 'yata ta kawo muna shawara munbi kuma gashi nayi nasarar samun jin muryar da ko a cikin mafalki na ba zata 'bace mani ba, ni Husain ina daga cikin masu rabo, abar kauna ta zata kawo kanta guri na.. Ina cikin farin ciki"_ Photon Husnah ne wanda take cikin motar ta tana driving ta sako kan motar ta a gidan su, da wanda ta bud'e motar da wanda ta zuro 'kafar ta, tana murmushi da wanda ta fito a jikin motar da wanda ta rungume Daddy da Ummey da wanda ta fara takawa kai har cikin falon gidan nasu da wanda tazo dai 'kofar d'akin su Anisah taji suna maganar ta, ta tsaya tana murmushi da wanda sukayi fad'a gurin cin abinci da wanda ta fito zata tafi gida har bayan motar sai da akayi masa photo. D'ago idon ta ta sakeyi tace, "amman taya duk ka d'auki wannan photon haka kuma duk ban san anyi su ba, kuma lokacin da zani koma gida baka nan". Murmushi yayi yace, "ki bari ki 'karasa mana". Murmushi Husnah tayi taci gaba da dubawa, photon da tagani ne wanda yafi bata mamaki shine ta fito 'kofar gidan Zubaidah da niyar zata 'boye trolley d'in ta, kafin ta gudo shine ta gani da sauri tace, "wannan ya bani tabbacin cewar kai ne ka sauya wa trolley d'ina gurin ajiya ko? ". Dariya ya yi babu amsa, tana duba wani shafin taga an rubuta, _guduwa guduwa guduwa, yan mata na ai guduwa indai ba a gida na ba ban ga gurin da zaki jeba, kiji dad'in sa, dole gida na ne mafakar ki domin nine suturar ki sirrin ki, kuma duk wan nan shirmen na had'in wannan Auren ba zaiyi amfani ba, saboda an ginawa zuciyar ki da tawa mafaka d'aya wato gidan Husain da Husnah zuciya d'aya"_ _Alhamdulillah ga Husain ga Husnah a gida d'aya zuciyoyi biyu a guri d'aya, a gaskiya ina jin dad'in yanda Husnah take biye mani muna fafata soyayya a dabai baye, ni ina nuna mata soyayya ba tare da sanin wani ba itama tana amsa, ba tare da sanin yanayi da girman soyayyar ba, kuma ina gamsu wa da yanda naga sa'kon yana isa a gareki masoyiya ta_ _"Tabbas soyayya tana dad'i musamman ma akanki Husnah, saboda akan kine nasan mine ne farin ciki mine ne ba'kin ciki_ _ya ilaihi wai nine za'a had'a Aure na da Husnah kuma harda su fad'ar sai kayi muna biyyaya dole, lallai ne nayi fice, Husnah ta yarda har zuciyar ta, amman kishi ya hanata bayyana, hakan, abun farin cikin anan kuwa shine, ta yanda Husnah taje gurin dinner din biki na ta soke abun tun alokacin ne na yarda da cewar komai 'boye soyayya wata rana sai ta bayyana tun da gashi, soyayya ta ta bayana akan idon ki Husnah da kuma gan_, gar jikin ki, tabbas ni mai nasara ne, Husnah saboda ki 'kara sona na yarda da cewar zan Auri Mardiyya amman sam ni ko son ganin fuskar ta bana yi_ _zaman Aure na da Husnah nine kawai nasan amfanin hakan kuma ni ba gangar jikin Husnah nake muradi ba ita kanta Husnah da zuciyar ta nake muradi banyi Auren sha'awa da Husnah ba, kuma nayi alkawarin sai idan ita ce naga tana bu'katar hakan amman ni kam nasan soyayyar Husnah halitta tace a hakan, ba zan takura mata ba duk kuwa da yanda nake bu'katar mata ta tabbas sai na tabbar da Husnah ta cika da sona ta yanda bani da wani aibu a gurin ta, sai soyayya zallar ta_ _Haa kashe ni aka zoyi Husnah ta kawo jikin ta, aka halbe ta, tun a wannan lokacin na fahimci cewar soyayya ta tayi tsiro a zuciyar ki Husnah, kasan cewar zuciyar mu d'aya shi yasa aka had'a dani dake aka d'auke wai har abamu bindiga ace na kashe kaina, toh idan na kashe Husnah ai kaina na kashe, haka Husnah idan ta kashe ni kanta ta kashe, to kasan cewar da zuciya d'aya muke amfani, da ido muka tsara komai da zuciyar mu sai gashi lokaci d'aya, mun kaiwa abokin tabar mu bari, kai amman yayan gata ne a soyayya ta da Husnah_ _Daddy kuci gaba da bamu hakuri amman duk da gan hanci muke abun mu, kasan cewar ina son na 'kara tan tance ya zurfin soyayya ta yake a yan zun a gurin Husnah shine na Auri Zee na Aura kuma nayi nadamar Auren nata dan taso ta kashe ni, ta rabani da ruhi na_ _Husnah ina son ki ina kaunar ki ina jiran ranar da kema zaki ce dani mijin ki soyayya ta har abada Allah ya azurta mu da zuri'a ta gari_ ajiye littafin Husnah tayi tace, "muna son 'karin baya nin ka" Husain ya ce, "Sai kuma abunda nine kawai nasan sirrin sa da fassarar sa shine wanda yake ci maku tuwo a kwarya Husnah shine ina kiranki da Karuwa ". Husnah tsakani da Allah ni dai wallahi tun lokacin da nafa ganin ki komai naki yana burgeni, amman dalilin da yasa nake cewa haka, shine idan na kiraki da wannan sunan idon ki na nuna mani wanni sirrin wanda na barwa kaina sani, kuma ba zan iya sanar da kowa ba, Husnah ke sheda ce ranar da naji Mardiyya ta ambaci sunan da nine kawai nake kiran ki dashi, na dake ta har na korata gidan su, Husnah wallahi ni har a zuciya ta bana zar gin ki da komai dan haka ni ban 'bata Aure na ba" "Husnah ina sonki ina sonki ina sonki ina sonki bana son ganin kukan ki ina kaunar ganin farin cikin ki ha 'karshen rayuwa ta dan Allah Husnah ki soni kada ki bani na rasa ki kada ki barni nayi kuka akan rasa soyayyar ki". Da gudu Husnah taje ta rungume mijin ta, tace, "ina sonka mijina". Tafi aka sanya masu kowa dad'i yake ji ganin yau su Husnah da Husain sun shirya a gaban su. Haka gidan ya kasan ce masu cikin farin ciki sai dare suka tafi, haka su Anisah suka sanar da Ummey sosai Ummey tayi farin cikin haka daddy, su Yaya Yusuf da Shaheed ma sunyi farin ciki sosai. Haka rayuwar su Husnah da Husain ta kasan ce cikin so da kaunar junan su da kulawa ta soyayya. Sai da sukayi wata ukku suka koma gidan su, Zee na ganin yanda suka dawo kawai ta tattara kayan ta tace ya zalunce ta ya muna funceta ashe dama yana can tare da Husnah yayi mata maganar wayau ya bata kud'i yaci gaba da zama da Husnah wallahi sai ya sake ta, Husnah tace, hubby kada ka yarda ka sake ta share ta kawa, ita ta manta cewar ita da kanta, tace ita tagaji da zaman ka kai da ita, kawai ka bata kud'i kayi tafiya mai nisa itama ta futa, to kanki kika yiwa". Cikin zafin nama ta kawo wa Husnah mari, amman kafin hannun ta ya sauka a kan fuskar Husnah tuni Husain ya ri'ke hannun yayi mata mari biyu masu kyau. Ya ce, "ban za kawai ke har kin isa ki mari mata ta bugun numfashi na a gaba na? " Hannun Husnah yaja sukayi d'akin Husnah, da 'kamshi kawai ke tashi, cikin mamaki Husnah tace, waye yayi wannan aikin? " Dariya Husain yayi yace, Suhailah ce, kuma idan kin futa kwana biyu, sai kije gidan Ummey kiyi sati biyu saboda bikin Anisah da Tk Suhailah da Muktar sai Safiya da Ahmad" Sosai Husnah taji dad'in wannan maganar. Haka kuwa kwanan su biyu da wowa suka nufi gidan Ummey, sosai Ummey tayi farin cikin ganin Husnah da Husain da sauyin da aka samu, jin takeyi kamar ta maida Husnah da Husain cikin ta, Daddy ma wani irin farin ciki yakeji, ganin wannan sauyin su Anty Zarah dasu Yaya Yusuf Shaheed matar Shaheed su Anisah kowa cikin farin ciki yake, tabbas Husnah da Husain sun dace da juna. Daddy ne yace su shirya yau zasuje ziya gidan baffah daga nan zasu je gurin baban su Husnah a take Husnah da Anty Zarah sukace su ba zasu ba, Husnah ma harda fad'ar, ai Baban mu ya dade da rasuwa ni ban ma san shi ba". Lallashin duniya sunce ba zasu ba, gidan baffah ma da akayi maganar cewa sukayi ba zasu ba, har sai da Daddy yace Yusuf Husain wannan aikin kune, dole a ranar aka fasa tafiyar. Husain ne ya zainar da Husnah yana lallaba ta amman ta'ki yarda, tun yana lallashin har ya hasala yayi fushi ya daina kulata ya koma gurin matar sa, har sati d'aya, ai kuwa Husnah ta 'kara hasala, tana fitowa daga cikin d'akin ta zata shiga kichen kawai Zee ta saka wa Husnah 'kafa dan ita sam saboda abunda Husain yayi mata tana cikin zafi ta share su shida matar sa ta daina shiga lamarin su, to bata kula da suna zaune a gurin ba kawai taji an tadiyeta, a take tayi luu zata fad'i cikin zafi nama Husain ya janyo ta, suka fad'a akan kujerar da yake zaune a kan ta, shine a 'kasa Husnah a saman sa, a take Husnah ta bud'e ido ganin ta kwance a jikin mutum kawai tayi yun kurin tashi, da sauri ya ri'ke ta, yace, "ina fatan baki samu rauni ba" D'aure fuskar ta tayi tace, "zan tashi ka kyaleni malam nayi abunda yake gaba na, kuma miye naka aciki koda raunin ne na samu ai dai naga ba jikin ka ba ko? " Dariya yayi yace, "Husnah nine fa kika yiwa laifi kamata yayi Husnah kizo ki bani hakuri ki lallasheni ko". Shiru tayi masa shi kuwa gyara mata kwanciya yayi a jikin sa, ita kuma ta daura kanta a jikin sa,. Wani wawan tsaki, Zee ta saka, tace bariki kawai, Husain ya daga idon sa, yace, oh tunda burin ki bai cika ba, ai ina kallon yanda kika saka mata kafa ni kuma kin san abunda ba zan d'auka ba ke nan, akan yar karuw... Da sauri Husnah ta rufe masa baki tace, "um umm nidai bana son wannan Sunan Allah". Cizon wasa yayi mata, ihu ta saka, cikin takaici Zee tabar gurin, anan gurin ya lallashi Husnah har ta yarda, da sauri yace to tashi muje gida tun yanzun dan da zafi_zafi akan daki 'karfe " Shiryawa sukayi suka bar gidan suna zuwa ashe daman su ake jira daman yayi niyar yau kam dole ya shawo kan Husnah. Hanya suka d'auka tare dasu baffah, shine ma ke nuna masu hanya cikin ikon Allah koda tara ba dare yayi sun kusa isa garin hotel suka kama suka kwana tun da safe suka d'auki hanyar shiga garin, zuwa 'karfe biyu na rana suka isa, ita dai Husnah da Anty Zarah cike suke da mamakin ganin gidajen guri duk sauya masu hanyar da suka sani ma taso 'bace masu, ko baffah sai da yayi tambayar gidan su Marka wanda aka tambaya yace, "kuce gidan barayin kauyen nan" ai kuwa a take aka nuna masu, hanyar tafe suke da mamakin barayin Kauyen, taro suka gani ana ta rafka bala'i mutane ne suka taru ko wane da makamin sa, a hannun ana dukan wasu mutane a gurin, Husnah kuwa bud'e motar tayi, ba tare da wata wata ba, a take Husain ya biyo ta yana kiran ta amman sai ture mutane takeyi tana shiga itama Anty Zarah da sauri ta shigo gurin, Husnah turus tayi ganin ana dukan matar da har ta mutu ba zata iya mantawa da ita ba, Anty Zarah ce ta dafa Husnah tace, "Husnah kin ga kuwa abun da nake gani da ido na kuwa? ". Husnah ce, tace Alhamdulillah duk sai mutane suka jiyo suna kallon baki duk sai aka matsa masu, akayi shiru Husnah tace, " *HAJIYA MARKA*!! ke nan to Alhamdulillah gamu da ran mu Allah ta nufa bamu mutu ba kuma bamu wukanta ba kamar yanda kikayi muna fatan gani, ki dubemu da kyau ki gani". Tun lokacin da Husnah ta ambaci sunan Marka kawai sa Marka ta saki ido da baki ita da wanda suke gurin suka zubawa su Husnah ido. Anty Zarah ta ce, "Marka ki duba da kyau ki gani ko idon ki daya zai iya gane mu, amman koda yake, bari abaki amsa, ta dubi Husnah. Husnah tace, "Anty Zarah ce da Husnah makinyanki mune nan a gaban ki, lafiya lau cikin kwanciyar hankalin amman ke dibeki keda "ya'yan ki "ya'yan so, kun dawo abun tausayi, yan mune zamu taima ke ku, Marka nazo da niyar d'aukar fansa amman Allah ya bi muna hakkin mu dan haka mun barki da halin da kike ciki". Anty Zarah ta ce, "hum Marka mune kikayi wa farar kasan cewa haka, a yanda kike a yanzun sai gashi kin ga, Ikon Allah wanda babu wani mahalukin da ya isa ya chanza kaddarar Allah da hukunci sa, dube ki dubi yanda wani mummunan wari yake fita daga jikin ki dubi yanda kika maiyar da yaran ki wata da ciki wani an toye masa rabin fuskar wata kuwa da Alama ba zata sake amfani da hauren bakin ta ba ko d'aya, Marka ina bokayen naki ina tsafin da kike takama da shi?, wanda mutuwar maman mu bata zame maki ishara ba, mahaifin mu da kika mai dashi jela, yan zun nasan kin 'karasa kashe shi ko? Him to Allah ya shiryi masu irin halin ki". Juyawa kawai baffah yace, "Marka ina kane na ko dai kin kashe sa ne?" Wani mutum ne yace, "ai malam ya dad'e baya tare da Marka yayi Auren sa mai gari ne ya bashi kanwar sa wadda yake ri'ko kuma makotan sa sun bashi gidan da yake zaune harda sana'ar sai da magi an bud'e masa kuzo muje gidan sa, ita wannan tar ta kwana biyar bata magana, kuma ido d'aya ne ke da ita, kuma warin nan dake tashi a jikin ta, bamu san na miye ba, yaran ta kuwa ta riga da ta gama da rayuwar su, dan sun raba jaha da mahaifin su, sun za'bi uwar su". Kaico kowa keyi da wannan rayuwar, tafiya sukayi gidan da baban su Husnah yake, da sallama su baffah suka shiga ita kuma Husnah kin shiga cikin gidan tayi duk sun d'auka Husnah tana tare dasu. Cike da matu'kar mamaki Baban Husnah yake kallon su baffah da sauri ya zo inda yake ya ri'ke sa ya fashe da kuka, haka gurin ya d'auki kuka, sai da baffah yayi magana akayi shiru, baffah yace, mun sameku lafiya? " Gaishe gaishe akayi wanda bayan an gama gaisawa, baffah yace, to ga ya'yan ka Zarah da Husnah, da sauri Zarah tace, ya'yan sa suna can tare da Marka mu ba ya'yan sa ba ne muda yake duka bayan mutuwar mahaifiyar mu, ma bai sauya ba sai karuwa, dan haka nikam". Baban su Husnah tashi yayi ya durkusa, a gaban Zarah zai fara magana da sauri Zarah ta tashi ta fad'a jikin sa tana kuka, Daddy ya ce Husain ina matar ka take ne? " Da sauri ya tashi ya ce, "him Daddy kadai san halin Husnah bari na shigo da ita ". Baban Husnah yace, "indai Husnah ce bazata shigo ba saboda Husnah tun tana 'karamar ta bata shiri dani, kuma idan tace ba zatayi abu ba tofa lallai ne bazata yisa ba, amman ni zan sameta da kaina ". Haka suka fita 'kofar gidan basu gan taba har hankalin Husain ya tashi Baban yace, indai Husnah kada ka damu zo muje, su Daddy ma biyo su sukayi cike da alhinin, rashin ganin Husnah, tshon gidan su ya shiga tare dasu da Daddy, d'akin su Husnah ne ya gani a bud'e yace, "Husnah kiyiwa Allah ki ajiye komai kibar ni na shigo cikin d'akin nan, wanda rabon da na shige sa tun kafin mutuwar mahaifiyar ku". Anty Zarah ce ta shiga cikin d'akin da gudu, Husnah ce ta isko ri'ke da sarka da yan kunnen da maman su take so sai har take sheda masu irin son da take yiwa yan kunnen, ai kuwa Anty Zarah da sauri itama ta d'auki kayan ta fashe da kuka kamar yan zun ne mutuwar mahaifiyar tasu, Daddy dake tsaye a waje duk mu shiga ciki ganin halin da suke ciki ne ya baiwa Yaya Yusuf da su Husain tausayin su, gurin su suka 'karasa Baban su Husnah ya matsa shima ya anshi kayan yace, "tunda ba addu'a zakuyi mata ba, ku kawo kayan na zubar" da sauri suka share hawayen idon su Husnah tace, bayan kayi farin cikin mutuwar mama na kwana d'aya akayi jimamin rashin ta, a gidan nan amman kuma, kuka ci gaba da jin dad'in ku, kuci abinci mu kuwa mu zauna da yunwa, kokon da mune muke damashi amman mune ake baiwa wanda kudaje suka bi wanda yayi datti dan dai kawai lokacin mutuwar tamu ba yi bane, shine yan zun kake cewa zaka rabamu da abu mai muhimmanci a rayuwar mu, baka zama damu baka sauraren mu, naira biyar taka baka bamu, zagi da duka ne tsakanin mu da kai, haba dai". Baban yace, "Husnah ki fad'i duk abunda yazo bakin ki nasan duk na aika ta shi amman dan Allah kiyi hakuri bada son raina na aikata maku hakan ba kuma kullum cikin kukan rashin matata nakeyi mace ta kwarai mai afuwa shin miya sa Husnah ba zaki gado da ita ba ne? ". Da sauri Husnah taje ta fad'a jikin sa tana kuka wanda kowa ya tausaya masu. Haka dai su Husnah suka yafi mahaifin su shima ya yafe masu, matar sa kamar itace ta haife su, da zasu tafi kamar kar su rabu. Koda suka koma garin su akayi bikin su Anisah aka kaisu gidajen su lafiya su Husnah kwana biyu suka dawo gidan su ba tare da sun sanar da dawowa war suba, sukayi mugun gani, dan Zee ce ta kwarto kwance a saman kujerar falo, zigidir haihuwar uwar su. Wani irin tsanar su Husain yaji a take ya d'auko wayar cabur yaci uban su ya saki Zee a gurin kuma yace ko tsinke bazata d'auka ba, a haka tabar gidan. Cikin kunci yake da ket Husnah ta samu ya sauka, tun daga wannan ranar ne suka dawo da soyayar su, watan Husnah d'aya da dawowa ta fara ciwo, sukaje asibiti aka sheda masu cikin Husnah boye, wa yayi yan zun ne ya fito watan sa hud'u, murna da farin ciki gurin su ba a magana, koda aka sanar dasu Ummey sunyi farin ciki sosai tare da fatan Allah ya raba lafiya. Bayan wasu watanni Husnah ce ke lebour, Husain duk ya rud'e kamar ba Doctor ba indai akan Husnah ne, mancewa ma yakeyi da cewar shi likitane. Nurse, ce ta fito tayi masu albishir da an samu baby boy, farin ciki harda sujada Husain yayi, da take lafiya ta haihu aka sallamesu suka dawo gida Ummey Zubaidah anyi Aure anyi hakali da ita ake Komai su Anisah kuwa ba 'acewa komai. Su Baban Husnah da matar sa sun zo anan ne matar Baban Husnah wadda suke kira da mama tace, "wai kun san kuwa a ranar da kuka baro garin a ranar ne Marka ta haukace tabi daji, a she yaran nan nata "ya'yan bokan tane yazo ya kwashe yaran tare da sanar da ita cewar ai tunda ta bari su Husnah suka zo garin ita kuwa sai bar garin kuma bada yaran sa ba, kuma fa a gaban kowa hakan ta faru, kowa Allah waddai da masu irin halin ta suke yi" Ai kuwa Husnah da Zarah suka ce Allah ya 'kara karemu da son zuciya" Atake kowa ya amsa da amin. Anyi biki lafiya Husnah kam an samu gudumawa a gurin yan uwa da abokan arziki, biki yayi biki, sai sam barka anyi taro lafiya an watse lafiya an samu Hanif Su Baban Husnah sun koma garin su tare da sha tara na arziki. Zubaidah ma tazo tayi barka ta zauna har akayi biki, mijin ta ya zo ya d'auke ta suka wuce. kwanan su sitting aka maida Husnah d'akin ta, suna kwance sun saka Hanif a tsakiyar su, Husain yace har dai na tuno da Husnah lokacin da kike cewa, suka had'a baki gurin fad'ar *A GIDANTA NA GIRMA* . *TO ALHAMDULILLAH NA GODEWA ALLAH DA YABANI IKON KAMMALA WANNAN LITTAFIN WANDA YA D'AUKI DOGON LOKACI BAN 'KARASA SABA SABODA RASHIN LAFIYAR MAHAIFIYAR FIYATA HAR ZUWA RASUWAR TA YA ALLAH KAJIKAN TA RAHMA KASA ALJANNA CE MAKOMAR TA ITA DA MAHAIFINA DA DUK KANNIN MUSULMI BAKI D'AYA* AMIN INA GODIYA DA HA'DIN KAN DA KUKA BANI MASOYA NA ALLAH YABAR 'KAUNA. AMIN *COMMENT AND SHARE* Sai mun had'u a wani sabon novel d'ina mai suna... *UMMU IHSAN CE* Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels