Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels [10/25, 7:34 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️ RUBUTAWA DAGA HAFSAT MAGAJI DABO(RUHAZ) SADAUKARWA GA MY DAUGHTER SABEEHA BILKISU Z.YA'U (🅱️K) AISHA MAGAJI DABO(AMA) Page 1 Tana zaune a wani d'aki mai kyau na gaske riga da wando ne a jikin ta masu kyau black jeans ne sai white T-shirt kanta a sunkuye ta tallafe fuskar ta da duk hannayen ta sai zubar da hawaye take yi kamar an bud'e fanfo. Kyakkyawa ce ta gaske doguwa brown skin ke gare ta Mai haske fatar ta har shek'i take yi ga idanun ta masu matuk'ar d'aukar hankali manya da su hancin ta har baka tare da wani irin lips red ga wata siririyar wushirya da ta k'awata tsakiyar kananan hak'oran ta gashin kanta ya zuba har gadon bayan ta na gaban goshin ta kuma ya kwanta luf a gefe da gefen fuskar ta kasancewar ba d'ankwali a kanta. Sosai take hawaye ba k'akk'autawa har shesshek'a take yi. Wasu 'yammata ne su biyu suka shiga d'akin suma sanye cikin irin shigar ta sak sai dai su da k'ananan veil a kansu. Ganin 'yar uwar su na kuka da gudu suka k'arasa sai lokacin na lura ashe da su biyun da suka shiga da wacce ke kukan dukan su kamannin su d'aya kamar an tsaga kara danko babu bambamcin komai tsakanin su daga kamannin su har zuwa tsayin su. Gefe da gefen ta suka zauna suka sata a tsakiya d'aya a cikin su cikin sassanyar muryar ta ta ce "Haba sabeeha meya faru kike kuka?" Ba tare da mai kukan ta amsa ba ta d'ayan gefen ta ce "Sabeeha sister fad'a mun duk d'an iskan da ya tab'a ki a gidan nan dan wallahi za a hau sama dani," har lokacin Sabeehan bata yi magana ba d'ayar ta Kuma cewa "Haba Sabreen karki kasance mai tayar da rigima mana kinsan dai duk neman maganar ki da tsokanar ki Sabeeha ta fiki amma kinga yau kuka take yi Kuma kinsan da na d'aukar mataki ne da tuni ta d'auka ba tare da mun saniba kamata ya yi mu tsaya muji damuwar ta," ta fad'a tana shirin fara kukan itama. Wata ce ta tura k'ofar d'akin ta ce "Sameeha kizo yanzu inji yallab'ai," da sauri Sameeha ta tashi ta fice jikin ta na rawa. Sabreen ta kalli sabeeha ta ce "Haba Sabeeha dear ki fad'a mun mana damuwar ki," sai lokacin Sabeeha ta kalli Sabreen da jajayen idanun ta ta ce "Sabreena wallahi gaba d'aya damuwata ta yanzu akan Sameeha ne ki duba fa abinda waccan wawan yake yi mata ina jin ciwon hakan bansan wanne mataki zan d'auka a kan shi ba ranar nan fa har d'akin nan yazo ya zane ta duk dan muna aiki a k'ark'ashin su ba wai yana nufin duk abinda suka ga dama su yi mana ba Kuma may be bayan hakan aikwai abubuwan da yake yi mata sai dai kinsan ta da zurfin ciki," Sabreen ta ce "gaskiya kam sister Nima na dad'e ina tunanin hakan Amma ko tambayar ta muka yi kinsan ba lallai ta fad'a mana," jinjina kai Sabeeha ta yi ta ce "Dear damuwata ta biyu bai wuce Abbba ba ki duba fa mun baro shi ba lafiya sannan shi kad'ai ne bamu san halin da yake ciki ba Sabreen dear nifa na yanke shawarar kawai gara mu tattara kayan mu mu gudu," zare ido Sabreen ta yi ta ce "me?mu gudu fa kika ce Sabeeha wato so kike muje d'in Kawu ya kashe mu d'in kamar yadda ya fad'a ko Kuma ya yi mana auren da ya ambata?" Tsaki Sabeeha ta ja ta ce "Nifa damuwata akan mahaifin mu ne ba akan Kawu ba," shiru Sabreen ta yi sannan ta ce "Nagane Amma mu bar maganar zuwa nan da kwana biyu kinji?" Gyad'a kai Sabeeha ta yi sannan ta ce "Yanzu dai muje mu ga wanne kira yake yiwa Sameeha," tashi suka yi Sabeeha ta d'auki veil d'in ta irin nasu ta yafa suka fice daga d'akin. Babban falon gidan suka fita turus suka tsaya ganin Sameeha ta yi kneeling gaban yallab'ai Kamis Wanda suke wa aiki kuka sosai Sameeha take yi tana cewa "Yallab'ai Dan Allah kayi hak'uri bazan sake ba," shi Kuma yana zaune akan kujera ya d'ora k'afa d'aya kan d'aya sai karkad'awa yake yi ga Kuma wata zabgegiyar dorina a hannun sa. A zuciye Sabeeha ta yi niyyar yin wajen Sabreen ta yi saurin damk'e hannun ta tana girgiza mata kai tare da janye ta gefe. Fisge hannun ta Sabeeha ta yi cikin masifa ta ce "Sabreen Wai haka zamu tsaya muna kallon kamis yana yi mana abun da duk ya ga dama yanzu Kuma me ta yi masa?" Cikin tsananin damuwa Sabreen ta ce "Wai fa matar sa ce ta aika waccan tsinanniyar Rashida d'in ta kira Sameeha shine baka gaya mata ba ta koma ta ce da matar yallab'ai wai ta ce baza ta zo ba shine fa d'azu ina cikin yin wanke wanke shine matar yallab'ai ta sameni ta k'are mun zagi Wai ta aika a kirani nace bazan zoba dan haka na shirya karb'an hukunci idan mijin ta ya dawo a tunanin ta Sameeha ce na so ni aka yiwa hukuncin Amma wacce d'azu ta je ta kira ta ganin mu mu ukun Kuma bazata iya gane mu ta ido ba shine kawai ta yi amfani da suna ta kira ta," jinjina kai Sabeeha ta yi ta ce "kinsan Allah sister tun daga kan waccan Rashidan zan fara har zuwa kan Farida sannan na dawo kan Kamis duk kafin na bar gidan nan saina nuna musu kuskuren su," saurin rufe bakin Sabeeha Sabreen ta yi ta ce "Sabeeha dear ki rufa mana asiri kar wani ya ji kinsan fa 'yan aikin gidan nan dukan su munafukai ne," Mtswww Sabeeha ta ja dogon tsaki ta ce "Ai ni zanso a fad'a musu ma yanzu fa tuhumar Sameeha ake yi akan laifin da bata san da shi ba kinga wallahi sai na je," tana gama fad'in haka ta juya da sauri Sabreen na Kiran ta amma ko waigawa bata yi ba. Babban falon ta koma ta ganshi zagaye da 'yan aikin gidan maza da mata domin dama indai yallab'ai Kamis zai yi hukunci sai ya tara duk 'yan aikin gidan ya yi a gabansu saboda wasu su kiyaye. Ba tare da tsoro ko wani d'ar ba Sabeeha ta nufi wajen gaba d'aya wajen da kallo aka bita har ta k'arasa gaban Yallab'ai itama ta yi kneeling kamar yadda Sameeha ta yi ta ce "Yallab'ai ba ita ce bace nice mai laifin ita ba tasan komai ba," kallon Sabeeha Sameeha ta yi ta girgiza kai ta ce "Wallahi ba ita bace nice," daga bayan su Sabreen ta ce "Yallab'ai dukan su k'arya suke yi nice nayi laifin," Nan fa wannan tace ita ce wannan tace ita ce. Tsawa Yallab'ai ya yi musu tuni suka yi shiru cikin bud'add'iyar muryar sa ya ce "Karku ce zaku raina mun wayo dan kunga bana wa wanda bai yi laifi hukunci ba wacece mai laifi a cikin ku?" A tare suka ce "Ni ce Yallab'ai," tsaye ya mik'e rik'e da dorinar sa kamar ta dukan jakai yana kallon su. Sannan ya kalli 'yan aikin gidan ya ce "Waye yake iya bambamce su?" Dukan su ba girgiza kai suka yi domin ba mai iya banbance su. Saukowa Farida ta fara yi daga stairs tana nufo falon tasha bleaching ta k'oshi sai wani yanga take gaba d'aya 'yan aikin suka durk'usa dan girmamata kallon banza ta yi musu sannan ta zauna kan kujerar da Kamis ya tashi sannan ta kalli 'yan uku ta yatsina fuska tare da jan tsaki. Sannan cikin muryar ta kamar ta mijin ta ta ce "Rashida," Rashida dake gefe ta matso gaba ta ce "na'am ranki ya dad'e," "Wacce na aike ki Kiran ta?" Kallon 'yan uku Rashida ta yi ta ga gaba d'aya kamannin su ba bambamci a zuciyar ta ta ce "ka ji banza ta ya zan iya gane su," a fili Kuma ta ce "Gaskiya ranki ya dad'e bansan wacce bace a cikin su," jinjina kai Farida ta yi sannan ta mai da kallon ta gun su Sabeeha ta ce "Ku dan uwar ku wacece Sameeha a cikin ku," da sauri Sabeeha ta ce "nice Ranki ya dad'e," Sameeha ta ce "k'arya take yi ni ce," Sabreen ta ce "ba haka bace Ni ce Sameeha," Tsaki Kamis ya ja ya ce "Duk ku tashi ku bar nan kafin naci uwar ku," da gudu su Sabeeha suka bar wajen. Sannan ya mai da kallon sa kan ragowar 'yan aikin ai tun kafin ya yi magana kowa ya watse. A zuciye Farida ta tashi zata bar wajen ya yi saurin rik'e hannun ta ya ce "Haba sarauniya ta ina Kuma zaki?" Banzan kallo ta yi masa "Meyasa baka had'a dukan su ka zane su ba?" Girgiza kai ya yi ya ce "Sanin kanki ne bana yiwa mara laifi hukun ci," "Amma ai kasan yaran nan ba yau suka saba yi mana irin haka ba muna kyale su ba dama d'aya ta yi laifi sai su taho dukan su su ce sune a rasa mai laifin a ciki to daga yau dukan su nake so a hukun ta," ya ce "An gama ranki ya dad'e ai sai abinda kika ce," Su Sabeeha kuwa suna barin wajen kowacce ta kama aikin ta Sabeeha ta nufi kitchen domin yiwa Kamis da Farida girki Sameeha Kuma ta tafi shara da mooping Sabreen Kuma wanke wanke. Da daddare Sabeeha duk ta riga su gama aikin ta ta nufi d'akin su wanka ta yi tare da sallar isha sannan ta haye saman gado ta kwanta bata dad'e da kwanciya ba Sabreen ta shiga itama wanka ta yi da sallah sannan itama ta kwanta kusa da Sabeeha kowacce da abinda take tunani can Sabreen ta ce "Sabeeha dear nima fa na fara tunanin barin gidan nan dan gaskiya na gaji da wannan wulak'ancin," Sabeeha ta ce "Sabreen sister ni hankalina ya dad'e da karkata kan Abba gaskiya," Sameeha ce ta shiga d'akin cire kayan jikin ta ta cire ta shige toilet wanka ta yi tare da yin sallah sannan ta shirya cikin kayan bacci irin nasu sannan ta zauna gefen gadon ta ce "Gaskiya bana son yadda ku ke sa kanku a matsala saboda ni yanzu fa Farida ta gayawa yallab'ai daga yau duk ranar da muka sake yin irin haka dukan mu za a had'a ayi mana hukunci," Sabreen ta yi juyi sannan ta d'ora kanta a jikin Sameeha ta ce "Sameeha dear ki dena damuwa akan hakan baza mu tab'a bari wani abu ya same ki ba," murmushi Sameeha ta yi ta ce "Amma Sabreen sister nifa nayi laifin ba ku ba," tab'e baki Sabreen ta yi ta ce "Kema ai baki yi komai ba domin kama ki akayi da laifin da baki da masaniya a kansa," "Amma dear wannan karo na goma kenan fa da irin hakan na faruwa gashi yanzu sunce idan muka sake dukan mu zasu had'a dan Allah kar ku sake gara ayiwa d'aya kawai," mtswwww Sabeeha ta ja wani dogon tsaki tare da tashi zaune ta kalli Sameeha ta ce "Kar su fasa d'aukar matakin sannan Kuma dole ne mubar gidan nan da zarar sun bamu salary d'in mu Kuma wallahi kafin nan saina had'a musu fitinar da basu tab'a tunani ba," a tsorace Sameeha ta ce "Amma dai Sabeeha wasa ki ke wallahi gara masifar gidan nan da ta Kawu Ni dai ban yadda da hakan ba kinsani muna komawa aure zai yi mana Kuma kinsani dole sai ya d'aura miki aure da Sadam d'in da bakya so sannan ya aurawa Sabreen aure da d'an mai gari ni Kuma ya bawa dansa faruk," "To kar Allah yasa ya fasa gidan nan dole mu barshi Kuma kaf cikin mu ba wacce ya isa ya yiwa auren dole," ajiyar zuciya Sameeha ta yi ta ce "Amma kinsan tunda ya fad'a sai ya aikata Kuma kinsan wannan ne gida na takwas da Kawu ya kawomu Kuma ya ce idan muka sake guduwa aure zai yi mana Kuma kema kinsan yadda Sadam ke kashewa Kawu damu kanmu kud'i ba yadda za ayi kice baza ki aure shi ba duk da cewar bakya son sa," wani tsakin Sabeeha ta ja ta ce "kud'i yanzu ya fara kashe mana ni da Kuma ku tunda ba rok'on sa muka yi ba Amma wallahi bazan tab'a auren sa ba," haka suka dinga tattauna matsalolin su har tsakiyar dare sannan suka yi bacci. Washe gari tun safe suka tashi suka sake shiryawa cikin bak'ak'en dogayen riguna iri d'aya suka fita suka fara ayyukan su. Sameeha na cikin sharar falon Farida Rashida ta shiga falon ture Sameeha ta yi ta wuce ko kallon ta Sameeha bata yi ba saboda hak'uri ne da ita sosai ita kuwa Rashida a zuciyar ta ta ce shegu sai kyau shiyasa na tsane su domin bana so nan gaba idan yallab'ai zai k'ara aure ya auri d'aya a cikin su domin na dad'e ina dakon soyayyar sa a zuciyata. A fili Kuma ta ce "banza ye kawai," har lokacin Sameeha bata kalle ta ba ganin Sameehan tak'i kulata kawai sai ta je har gaban ta ta tsinka mata mari dafe kunci Sameeha ta yi sannan itama ta d'aga hannu ta rama daidai lokacin Farida ta fito wata uwar tsawa ta daka musu wacce tasa kowaccen su nutsuwa. Tana k'arasawa ta ce "Mahaukatan ina ne ku rasa inda zaku yi fad'a sai a falona?" Rashida ta ce "Kiyi hak'uri ranki ya dad'e na sameta ne tana shara shine nace ta gyara yadda take shara baya fita shine ta mare ni," kallon Rashida kawai Sameeha ke yi cikin mamakin k'aryar da ta shirga. Farida ta kalli Sameeha cikin b'acin rai da kuma jin haushin ta ta ce "Ke dan uwarki baki san cewa ko a cikin 'yan aiki Rashida ta daban ce a wajen ba da zaki mare ta?" Bud'e bakin da Sameeha ta yi da niyyar yin magana Farida ta zabga mata mari ta ce "karki kuskura kice wani Abu anan," dafe kunci Sameeha ta yi hawaye na bin fuskar ta. Tsaki Farida ta ja ta kalli Rashida ta ce maza rama marin da ta yi miki ba tare da tausayi ba Rashida ta dinga zabgawa Sameeha mari har sau uku. Farida ta ce "b'ace mun da gani shashasha," da gudu Sameeha tabar falon tana kuka ga kuncin ta sai zafi yake yi domin hannun Rashida tafkeke ne. Da gudu Sameeha ta shige kitchen tana kuka Sabreen dake wanke wanke ta mik'e da sauri ta tare da tana cewa "Sameeha dear maiya faru?" Sai lokacin Sabeeha ta waiga tana kallon yadda Sameeha ta rungume Sabreen tana kuka. Ajiye ludayin hannun ta ta yi ta k'arasa tana kallon Sameeha damuwa fal fuskar ta sannan cikin b'acin rai ta ce "Sameeha dear waye ya mare ki?" Sai lokacin Sabreen ta lura da shatin yatsun dake fuskar Sameeha. Girgiza kai Sameeha ta yi ta ce "bakowa," k'ara hasala Sabeeha ta yi ta ce "Kamar ya bakowa ga shatin yatsu nan a fuskar ki waye ya mare ki?" Cikin kuka Sameeha ta zayyane musu abinda ya faru. Sabreen ta ce "Wai meyasa Rashida ke miki irin haka ne?" "Nima bansan me nayi mata ba," Sabeeha ta ce "Barta Wallahi kwanan nan zasu raina kansu a gidan nan," Sameeha ta k'arasa gaban Sabeeha ta ce "Sabeeha sister na yadda mubar gidan nan Wallahi na gaji da abinda ake mun kullum cikin yi mun sharri ake," ajiyar zuciya Sabeeha ta yi ta ce "karki damu dear zamu bar gidan nan Amma Wallahi saina fara gyara musu zama," shiru Sameeha ta yi bata yi tunanin hana Sabeeha ba saboda abinda ake mata ya fara isar ta. Da daddare bayan Sabeeha ta gama abinda take yi ta nufi d'akin su tafiya take yi tana rera wak'ar ta "wata rana sai labari ka zamo mai aikata kairi...," Dif ta yi shiru saboda muryar Rashida ta jiyo daga cikin d'akin su tana cewa "Wallahi Dije ina mutuwar son yallab'ai kullum k'ara son shi nake yi," Dije ta ce "A'a fa Rashida ki rufawa kanki asiri dan wallahi idan Farida ta sani kin shiga uku," Rashida ta ce "Ita d'in banza ke nifa dama duk shige matan da nake yi dan kawai na k'ara samun kusanci da ita ne sannan abinda baki saniba duk wata kulawar da take ba yallab'ai ba wacce ban saniba so nake na gama karantar ta yadda idan na aure shi zan bashi kulawar da ta ninka wacce yake samu wajen waccan banzar damuwata d'aya shine idan har yallab'ai baya sona to Wallahi akwai matsala shiyasa har yanzu ban gayamasa ina son shi ba saboda idan har ya ce baya sona daga ranar korata k'auye zasu yi saboda nasan dole zai fad'awa Farida Amma idan yana sona sai dai kawai ta ji maganar aure daga sama ina shiga Kuma naci uwar ta," dariya suka yi har da tafawa. Sabeeha dake jinsu ta yi dariyar mugunta a zuciyar ta tace shikenan dama ta samu sannan ta wuce zuwa d'akin su da farin ciki ta shiga d'akin ta yi sallama Sameeha da Sabreen da tun dazu suka gama aikin su suka amsa mata sallamar. Towel ta d'aura ta shige toilet ta yi wanka sannan ta fito ta yi sallah ta haye gadon ta ce ku tashi kuji wani labari a tare suka tashi suna tambayar ta wane labari bata b'oye musu ba ta basu labarin abinda ya faru dariya suka kama yi Sabreen ta ce "Ni Wallahi banga abin so a wajen yallab'ai ba ku dube shi fa kamar kwad'o," suka Kuma tuntsirewa da dariya Sameeha ta ce "A'a may be k'atuwar muryar ce ta ja ra ayinta," Sabeeha tsagaitawa da dariyar ta ta yi ta ce "Ku barni da su zasu gane basu da wayo," ranar ma haka suka raba dare fira sannan suka yi bacci. KADUNA Wasu motocine wajen guda ashirin suka jero gudu suke yi a kan titi na fitar hankali ga jiniya na tashi gaba d'aya motocin hilux ne da sojoji rik'e da bindigu a hannun su gud'a d'aya BMW army colour sai shek'i take yi wata area suka shiga sai da aka bud'e musu gate sannan suka bi wani titi dake tsakiyar layin Wanda bishiyu suka yiwa titin runfa. Wani had'adden gida ne unguwa guda a wajen suna k'arasawa sojojin dake tsaron gate d'in suka bud'e musu gate suka shiga basu tsaya ba sai da suka kai wajen wani dogon bene Mai kyawun gaske sannan suka yi parking. Sojojin suka diddiro daga motar gaba d'ayan su suka zagaye army green d'in. D'aya daga cikin sojojin ne ya bud'e bayan motar sannan ya ja gefe ya k'ame. Mutumin dake cikin motar ya ziro k'afar sa mai d'auke da wani takalmi Mai matuk'ar kyau irin nasu na sojoji sannan a hankali ya fito. Wayyo kuzo ku ga kyau iya kyau a wajen guy d'in nan kamar balarabe dogone sosai fari sol da shi har yellow yake yi gashin kansa kamar na indiyawa gashi bak'i wuluk yana shek'i sannan askin dake kansa ma abin kallo ne Yana da dogon siririn hanci ga pink lips abinda zaifi d'aukar hankalin mutum shine idanun sa farare ne kar k'wayar idon Kuma bak'i wuluk kamar yadda gashin kansa yake da Kuma gashin girarsa da ta kasance siririya mai shape kamar zata had'e ga zara-zaran eye lashes kamar mace. Guy d'in ya had'u iya had'uwa kana kallon sa ka ga k'akk'arfan namiji Yana sanye cikin kak'in su na sojoji Wanda kamar dan shi kad'ai aka d'inka su saboda yadda suka yi masa matuk'ar kyau kamar ka sace shi ka gudu. Wani b'angare ya kalla ya saki wani sassanyan murmushin da ya bayyana dimples d'insa dake gefe da gefen fuskar sa da Kuma fararen jerarrun hak'oran sa. Sannan cikin k'asaita ya fara tafiya kan jan carpet d'in da aka shimfid'a masa Wanda a jiki aka rubuta da manyan bak'i WELCOME BACK TO HOME OUR HAPPINESS MG ABDUL MALEEK. Wata kyakkyawar mata ce a tsaye tasha kyau cikin wani tsadadden less orange colour wuyan ta sanye da sark'ar gold da d'an kunne haka ma zobunan hannunta da warwaron ta duk na gold ne fara ce sol sannan suna kama sosai da MG wato major general. Gefe da gefen ta wata budurwa ce da Kuma saurayi kyawawa kamar larabawa. Yana k'arasawa budurwar ta ce "Welcome ya Maleek," cikin dakakkiyar muryar sa mai dad'in sauraro ya ce "Thank you Rinaz," saurayin Kuma ya yi huging d'insa ya ce "Sannu da zuwa ya Maleek," Nan ma ya ce "Thank you Fauwaz," daga haka ya nufi wajen mahaifiyar su wacce tun fitowar sa daga mota take sakin murmushi. Yana k'arasa ya rungume ta ya ce "I really miss you Ummina," ta ce "mee too I miss you much more my son," sannan ta bashi kiss a goshi ta ja hannunsa zuwa cikin falon. Falon ya tsaru iya tsaruwa babban falone na gaske Yana d'auke da kujera set uku ga wata tafkekiyar plasma a falon da home speakers ga wani lallausan carpet da wasu fulawoyi da aka k'awata falon da su ta kowacce kusurwa ga wasu show glass na jikin bango dake cike da kayan k'amshi da wata red da blue d'in haske a ciki can gefe kuma had'adden daining ne mai kujeru birjik da Kuma ba babban kitchen tsayawa fad'in had'uwar falon ma b'ata lokaci ne. Zama suka yi dukan su a falon Ummi ta ce "Son ya hanya?" Ya ce "Ummi hanya lafiya," sannan ya mik'e ya ce "Ummi zanje part d'ina I want to have some rest," ta ce "Ok ga abinci yana jiran ka," yatsina fuska ya yi ya ce "Amma Ummi kinsan ni bazan ci abinci 'yan aikin ki ba?" Murmushi Ummi ta yi ta ce "ai yau da kaina na girka maka saboda ban fita office ba amma kasan dole sune zasu dinga yin girki a gidan nan," shagwab'e fuska ya yi ya ce "Amma Ummi duka fa basu iya komai ba?" Ummi ta ce "ka ga ya isa zan canja ma Mai yi ma girki yanzu kaje idan ka shirya kazo dan Daddyn ka ya bayar da sak'o a fad'a maka sannan ka tabbatar kaje ka gaida Umman ku," tab'e baki ya yi sannan ya yi hanyar fita Yana cewa "To," yana fita Salman ya biyo bayan sa Wanda Salman ya kasance soja ne sannan amintaccen Maleek Kuma d'a a wajen k'awar Ummi. Kai tsaye part d'insa ya nufa duk inda ka kalla 'yan aiki ne a gidan suna ta hidima duk wacce ta ganshi sai ta gaishe shi tun Yana amsawa har ya dena dan ya gaji da magana. Tun kafin ya k'arasa sojojin dake wajen suka bud'e masa k'ofa ya shige falone na gani na fad'a ya yi kyau matuk'a komai na d'akin fari ne yasha ado kamar d'akin amarya stairs ya haye nan ma wani falon ne mai kyawun gaske bedroom d'in sa ya shige sannan ya fad'a bathroom sai da ya d'au lokaci sannan ya fito yana tsane sumar kansa da towel cikin k'ank'anin lokaci ya shirya cikin black jeans da red riga sai k'amshi yake zabgawa juyawa ya yi ya fita daga part d'in. Ko da ya fito sojojin sa suka biyo bayan sa d'aga musu hannu ya yi suka tsaya shikuma ya cigaba da tafiya abinsa har sai da ya je wani b'angare shiga ya yi da sallama a bakinsa wata mata ce kashingid'e a kan carpet ga fruits a gaban ta 'yan aiki zagaye da ita wasu na yanka fruits wasu na mata tausa k'arasawa ya yi ya zauna ya ce "barka da rana Umma," kallon sa ta yi ba yabo ba fallasa ta ce "yawwa," shi kuma ganin yadda take amsa masa ne ya b'ata masa rai ya mik'e tare da fad'in na barki lafiya ya juya zai fita har ya kai k'ofa ya jiyo muryar ta tana cemasa "Ya zaka Tafi baka tambayi Nasreen ba?" Ko kallon ta bai juya ya yi ba ya fice. [10/25, 7:34 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️ RUBUTAWA DAGA HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ) SADAUKARWA GA MY DAUGHTER SABEEHA BILKISU Z.YA'U (🅱️K) AISHA MAGAJI DABO (AMA) Page 2 Maleek na fita daga part d'in na Ummi ya nufa a garden ya hangi Nasrin zaune kan wata kujera sai zabgawa wata 'yar aiki mari take yi kamar wata uwar ta tsaki ya ja kamar Nasrin tasan Yana tsaye a wajen ta waiga suna had'a ido ta tashi da gudu ta nufe shi rungume shi tayi niyyar yi ya tsayar da ita ya ce "Meye haka?" Ya fad'a a d'an tsawa ce had'e fuska ta yi ta ce "Haba ya Maleek murnar ganin ka ce fa sannan kasan wani Abu kuwa jiya Daddy yazo sannan anyi maganar auren mu," kallon banza Maleek ya yi mata ya ce "Bangane me ki ke son fad'a ba kinga idan ma kina wasa ne ki dena nifa ban tab'a cewa ina sonki ba kinga maganar aure it is impossible thing," "Haba MG bangane auren mu bazai yiwu ba Amma aini ina sonka Kuma wallahi ko baka sona sai ka aureni," wani murmushi Maleek ya yi ya ce "Idan kin gama zaki iya barin nan wajen if not Wallahi saina buge ki stupid kawai," da gudu ta yi part d'in Umma tana kuka shi Kuma ya ja tsaki ya tafi. Bud'e masa k'ofar falon sojan sa ya yi ya shige ya samu su Ummi zaune a falo suna kallo zama ya yi ba tare da ya yi magana ba Ummi ta ce "Muje kaci abinci son," duka daining suka nufa suka fara cin abinci sai dai shi Sam ba wani cin abincin yake ba tashi ya yi kawai yabar daining d'in ya koma falo ya zauna fuskar sa babu alamun wasa. Ba Wanda ya yi masa magana har suka gama cin abincin sannan suka koma falon dukansu shafa kansa Ummi ta yi ta ce "My son meye matsalar?" Kallon ta ya yi ya ce "Ummi dagaske ne maganar da Nasreen ta fad'amun wai za ayi mana aure ni da ita?" Jiki a sanyaye Ummi ta ce "Hak'uri zaka yi son kasan halin yayan Daddyn ku Sam bashi da hak'uri jiya haka yazo nan ya dinga fad'ar maganganu har Daddyn ku ya kira dole ya baro Landon yazo aka yi maganar auren yanzu haka one month aka sa bikin shiyasa mahaifin ku ya kira ka ya ce lallai ka dawo a yau," cije leb'e MG ya yi sannan ya ce "Yanzu Ummi ina Daddy yake?" "Ya koma Landon yau da safe," jinjina kai Maleek ya yi sannan ya ce "Ummi Sam bansan meyasa Uncle yake son ganina a cikin damuwa ba sannan ni fa ba sonta nake ba," Ummi ta ce "nasani son amma kayi hak'uri wata rana sai labari," gyad'a kai ya yi ya mik'e ya fice. Part d'in sa ya koma ya kwanta bacci ne ya d'auke shi. Nasreen Kuma da kuka ta shiga falon ta fad'a jikin Umma a rikice Umman ta ce "Lafiya Nasreen mai ya faru?" Cikin kuka ta ce "Umma Wai kinji baya sona," tsaki Umman ta ja ta ce "kyale banza duk da baya sonki aure ke da shi babu fashi ya yi duk abinda ya ga dama amma sai ya aure ki Kuma mun kwashe dukiyar d'an iska," Nan dai Umma tai ta rarrashin ta. B'angaren 'yan uku kuwa Sabeeha ce a kitchen tana yin girki Rashida ta shiga sai wani shan k'amshi take tana yatsina ko kallo bata ishi Sabeeha ba fridge ta bud'e ta d'auki ruwa ta juya zata fita Sabeeha ta ce "Rashida baki ji ba," waigawa Rashida ta yi ta ce "Lafiya kuwa?" K'arasawa gaban ta Sabeeha ta yi ta ce "Akwai maganar da nake son fad'a miki amma sirri ce bana so wani yaji," "Ina jinki," cewar Rashida murmushin mugunta Sabeeha ta yi sannan ta ce "Wai kuwa kinsan yallab'ai yana mutuwar sonki kuwa?" Zare ido Rashida ta yi kamar gaske ta ce "nidin Kuma?" Gyad'a kai Sabeeha ta yi ta ce "sosai ma domin jiya naji yana waya Yana sanarwa da abokin sa shi duk duniya ke yake so," tsalle Rashida ta yi ta ce "Nagodewa Allah dama Wallahi ina mutuwar son shi kamar raina amma dan Allah ki tayani rufe sirrina bana so Farida ta sani dan gaskiya ina tsoron hukuncin da zata yanke mun," tsaki Sabeeha ta yi ta ce "karki damu ni nan zan taimake ki karki damu tunda ai shima Yana son ki kinji?" Gyad'a kai Rashida ta yi cike da gamsuwa sannan ta ce "Amma aike d'in bangane ki ba a cikin 'yan ukun?" Tab'e baki Sabeeha ta yi ta ce "Manta kawai ni dai burina na taimake ki dan haka karki damu kanki wajen sanin wacece ni cikin 'yan uku," tana gama fad'in haka ta juya ta cigaba da abinda take yi Rashida Kuma ta fita zuciyar ta fal farin ciki. Haka Sabeeha tai ta jan Rashida tana zugata akan cewar Yallab'ai na mahaukacin sonta ya yinda shi baima san wainar da ake toyawa ba. Zaune Yallab'ai yake shida wani gabjejen abokinsa suna fira yallab'ai ya kalli abokin sa cikin k'atuwar muryar sa ya ce "Gaskiya Habibu ina mutuwar son yarinyar nan dake yi mana girki a cikin gidan mu saboda gata doguwa kyakkyawa ga iya girki dan tunda nake a rayuwata ban tab'a cin girki mai dad'in na ta ba," jinjina kai Habibu ya yi ya ce "Yanzu kana nufin auren ta zaka yi ko me?" Gyad'a kai Yallab'ai ya yi ya ce "Sosai ma kuwa kawai abinda nake so da kai shine kai nake son aikawa wajen ta," Habibu ya ce "Haba dai ai gara kaje da kanka ka gaya mata," girgiza kai Yallab'ai Kamis ya yi ya ce "A'a gaskiya kamar ni da matsayina naje wajen ta bayan 'yar aikina ce," Habibu ya ce "Shikenan yanzu yaushe zan same ta d'in?" "Ka bari zanyi ma magana kawai," Habibu ya ce "To Shikenan an gama," haka firar ta su ta tashi. Sabeeha ce ita da Rashida a kitchen suna fira idan ka kalle su zaka d'auka k'awaye ne domin fira suke suna dariya kamar gaske Rashida ta ce "Yanzu kina ganin anjima ya yi daidai dana fad'a masa abinda ke zuciya ta?" Gyad'a kai Sabeeha ta yi ta ce "Sosai ma kuwa d'azu ya kirani yake ce mun Wai Yana son ki ya lura kwana biyu munfi kusa ni da ke shiyasa ya fad'a mun sannan anjima Yana neman ki a falon Farida," d'an zare ido Rashida ta yi ta ce "Amma kina ganin ba matsala?" "Bawani matsala gani nake yi ya yi hakan ne dan ba k'aramun so yake Miki ba kuma son naki ne yasa yace kije har falon Farida dan da alama so yake ya nunawa Farida kalar son da yake Miki," wani wawan tsalle Rashida ta yi ta ce "Wayyo dad'i Amma nagode sosai," cikin murmushi Sabeeha ta ce "Karki damu," haka suka gama hirar su Sabeeha ta tafi tabar Rashida a kitchen domin dama kawai fira ce ta kai su kitchen d'in. Da yamma Yallab'ai Kamis da Farida na zaune a falon Farida suna yin fira sai Sabeeha ta shiga falon d'auke da tray a hannunta da fruits a ciki har k'asa ta tsugunna ta gaishe su Yallab'ai Kamis ne kawai ya amsa yayin da Farida ta galla mata harara dan ita bata son ganin wacce ta fita kyau musamman idan mijin ta na wajen. Sabeeha kuwa tana ajiyewa ta mik'e ta fita tana fita ta kalli Rashida dake tsaye tasha kwalliya ta ce "Yace ki shiga," cikin farin ciki Rashida tasa kai cikin falon ya yinda Sabeeha ta mak'ale tana lek'e tana dariyar mugunta. Da sallama Rashida ta shiga sai wani yanga take tana lankw'asa jiki da kallon Mamaki suka bita ba tare da wani tunani ba Rashida ta k'arasa ta zauna d'ayan gefen Yallab'ai Kamis ta ce "Barka da hutawa masoyina a gaskiya naji dad'in cewar da kayi kana sona dama Kuma na dad'e ina mahaukacin sonka dama damuwata ka ce baka sona Amma tunda ka furta hakan da bakin ka cewar kana sona naji dad'i sosai sannan ina so asa bikin babu yawa saboda bana so abin ya yi nisa nafi so asa nan kusa domin na baka kulawar da ta dace ba irin ta wawiyar matar ka ba," duk abinda take da kallo suka bita sai da ta kai k'arshe sannan Yallab'ai ya mik'e ransa a matuk'ar b'ace saboda ba wacce ma bata kwanta masa a rai cikin 'yan aikin gidan ba kamar Rashida dan dai kawai Farida na sonta ne yasa bai kad'a keyar ta gidan su ba. Ya ware zabgegen hannunsa ya zabgawa Rashida Marin da sai da ta fad'o daga kujera tana ganin stars bata gama wartsakewa ba ya Kuma k'ara mata wani Marin ya yi ball da ita har sai da ta buge da jikin kujera goshin ta ya fashe kuka ta fashe da shi tana ihu. Cikin k'atuwar muryar sa ya ce "Ke dan uwar ki ni sa'an ki ne da zaki zo kice kina sona shegiya munafuka so kike ki had'ani da sarauniya ta ko?" Farida ma cikin b'acin rai ta mik'e ta ce "Dama duk abinda ki ke yi dan ki aure mun mijine aikuwa Wallahi yau sai kinci uban ki a gidan nan sannan daga yau sai kinbar gidan nan munafuka kawai," duka suka rufe Rashida da shi sai ihu take yi gashi babu Mai ceto. Sabeeha tana daga waje har rik'e ciki take yi saboda dariya sannan ta nufi d'akin su da gudu tana k'wala Kiran "Sabreen sister Sameeha dear kuzo ku yi kallo," da gudu suka fito suka bita ragowar 'yan aikin gidan jin ihun da 'yan uku ke yi suma suka fito suka nufi falon su ma. Kowa tsayawa ya yi Yana kallon yadda Farida ke yawo Rashida daga bene sunyi mata jinajina sai ihu take yi tana bada hak'uri Amma ko sauraron ta basa yi har tsakiyar falon suka jawo ta suka yi wurgi da ita zabgegiyar dorinar hukunci Yallab'ai ya karb'a ya fara zabga mata sai ihu take yi har sai da ta kasa motsi sannan ya kyale ta ya koma gefe ya zauna. Sabeeha kuwa har lokacin dariya take yi harda rik'e ciki wani farin ciki take yi Sabreen ma sai taya ta dariyar take yi Sameeha kuwa tun tana dariyar har ta koma kuka tsabar tausayin Rashida galala su Sabeeha suke kallon yadda take hawaye sannan suka cigaba da dariyar su. Farida ta ce "Dan uban ki ki dena yi mana ihu a falo ki tashi ki bar mana gida ko insa a fitar dake daga cikin gidan nan," mik'ewa Rashida ta yi dakyar tana tafiya har wani layi take yi suna had'a ido da 'yan uku Sabeeha ta kashe mata ido d'aya. Juyawa Rashida ta yi ta fita daga gidan ya yinda kowa ya watse. Da murna su Sabeeha suka shiga d'akin su sai taka rawa suke yi ita da Sabreen ya yinda Sameeha ta zauna gefen gado tana kallon su. Sabreen ta d'ebo shoky tana cewa "Sabeeha dear saura Kuma Farida itama ta gane kuren ta," Sabeeha rawa take yi kamar wata macijiya ta ce "Ai yanzu aka fara wasan," Sameeha ta ce "Ni dai please Sabeeha sister ki dena abun nan," ko kallon ta basu yi ba suka cigaba da rawar su sai da suka yi Mai isar su sannan ko wacce ta tafi wajen aikin ta. Zaune Maleek yake a falon sa wasu takaddu yake dubawa wani soja ya shiga falon ya Sara masa sannan ya ce "Ranka ya dad'e kana da bak'o," sai da ya ajiye takardar hannun sa sannan ya kalli sojan ya ce "waye?" Cikin ladabi sojan ya ce "Umar ne ranka ya dad'e," cikin Mamaki Maleek ke kallon sojan sannan ya ce "Ok ya shigo mana," sanna ya cigaba da abinda yake yi. Umar ne ya shiga falon ya k'arasa gaban Maleek ya Sara masa hararar sa MG yayi sannan ya ce "Yau Kuma me ka ke ji da sai an nema maka izinin ganina?" Zama gefen sa Umar ya yi ya ce "Wallahi Maleek baka da kirki yanzu ka shigo gari Amma ba labari yanzu ma fa sai da na je wajen Ummi ne Rinaz ke fad'amun ka dawo shiyasa ma yanzu nace a nema mun izini kar nazo a harbe ni tunda haushina ake ji," kad'an Maleek ya yi murmushin gefen baki sannan ya kalli Umar idanun sa sunyi jajur ya ce "Umar kasan auren dole?" Dariya Umar ya yi ya ce "Yeah I know it but for what reason ka tambaye ni?" Tab'e baki Maleek ya yi ya ce "To shi za ayi mun," Ware ido Umar ya yi ya ce "Kai haba dai amma you are joking?" Mtswww Maleek ya ja tsaki ya ce "Umar I'm not joking I'm serious Wai ko ka manta halin Uncle ne yanzu haka fa bikin bai fi 3 weeks ba," jinjina kai Umar ya yi tare da cewa "Kenan mu fara shiri?" Tsaki Maleek ya ja ya tashi ya fice. Bin bayan sa Umar ya yi dan yasan haushi ya ji da sauri ya tarar da Maleek dake tafiya shi da Salman ya ce "Sorry MG amma dai ba Nasreen ba ce ko?" Ba tare da Maleek ya kalle shi ba ya ce "Ita mana," daga haka ya wuce ya yafi part d'in Ummi. Salman ya kalli Umar ya ce "Amma Umar abinda ake yiwa MG Sam ba a kyauta masa Dan ma dai mai biyayya ne shiyasa," Umar ya dafa kafad'ar Salman ya ce "Captain Nima abin na damuna Wallahi Amma kawai mu taya shi da addu'a kawai," haka suka cigaba da tattaunawa akan matsalar dake faruwa a gidan. Da Sallama Maleek ya shiga falon Ummin sa ya zauna akan kujera ya jingina a jikin kujerar Yana tunanin damuwar da yake ciki ji yayi falon ya d'auka da "Fauwaz is open the door," har lokacin bai ko bud'e idanunsa ba. Fauwaz ne ya shiga falon kunnen sa manne da ear piece yana rera wak'ar fire boy ta like I do har wani kad'a kai yake yi Yana bin wak'ar "e-sure for you baby I'm going no where your love is true I know you always be there no one can take my place bad energy stay fa...," Tsawar da Maleek ya yi masa ne yasa shi saurin cire ear piece d'in jikin sa har d'an rawa yake yi dan tsoro. "Zo nan," Maleek ya ce Yana k'ara had'e fuska kamar bai tab'a dariya ba k'arasawa Fauwaz ya yi ya zauna k'asan carpet Dan yau ya ga ba wasa kallon sa Maleek ya yi ya ce "Kai Wai meyasa baka jin magana ka shigo waje babu ko sallama," Fauwaz ya ce "Sorry ya Maleek bazan sake ba," d'aga kafad'a Maleek ya yi ya ce "Is left for you," Rinaz ce ta k'arasa falon tana yiwa Fauwaz dariya k'asa k'asa. Hararar ta Fauwaz ya yi sannan ya cije baki ya kalli Maleek ya ce "Yaya kasan kuwa me Rinaz ta yi da baka nan?" Duk da yana cikin damuwa sai da ya girgiza kai domin yana so ya ji halin da k'annen nasa ke ciki domin rayuwar yanzu sai a hankali musamman shi da ya san baya rasa mak'iya. Fauwaz ya ce "Last week fa Rinaz ta fita unguwa tun around 5:00pm bata dawo ba sai wajen 10 Wai ta tafi birthday party d'in friend d'in ta," jinjina kai Maleek ya yi tare da kallon Rinaz da ta yi tsilli tsilli da ido ya ce "Haka ne?" Cikin rawar murya ta ce "Sorry ya...," Tsawa ya daka mata ya ce "Don't sorry me I just ask you haka ne!" Noding kanta ta yi sannan ta ce "Kuma wallahi yaya shima fa bro kullum sai cikin dare yake dawowa kuma kullum sai Ummi ta yi masa fad'a," Girgiza kai Maleek ya yi Yana binsu da ido sannan ya ce "Ok yanzu nagane wato duk ranar da bana nan duk abinda kuka ga dama shi kuke aikawata ko?" A tare suka girgiza kai kwafa ya yi ya ce "You really know bazan ce ku dena ba dan Allah ku cigaba da duk abinda ku ka ga dama," yana gama fad'in hakan ya ce "Kun isheni da zama da anan," da sauri suka bar wajen suna hararar juna. Falon ne ya d'auka da "Ummi is open the door," k'ofar Nabil ya kalla sannan ya mik'e ya nufi inda take rungume ta ya yi ta yi masa kiss a for head d'insa ya ce "Sannu da dawowa Ummi," ya fad'a tare da karb'ar hand bag d'inta suka k'arasa falon ta zauna a gajiye tare da cire farin glass d'in dake idanun ta. Ya ce "Ummi Sannu shiyasa nace ki hak'ura da aikin nan Ni Sam banga amfanin hakan ba," hararar wasa ta yi masa ta ce "Yanzu kai taimakon al'umma ne bai da amfani bayan kaima abinda ka ke yi kenan," murmusawa ya yi ya ce "Amma Ummi ai ni daban zuwa yanzu kamata ya yi ki zauna ki huta a gida zuwa asibitin ya isa haka," banza ta yi da shi ta k'wala Kiran "Hadiza," wata budurwa ce ta fito daga kitchen d'auke da wani had'adden tray mai d'auke da ruwa da drinks da glass cups ta ajiye akan center table ta ce "Sannu da dawowa Ummi," cikin fara'a Ummi ta ce "Yawwa Hadiza da fatan komai lafiya," Hadiza tana satar kallon Maleek ta ce "Lafiya lau Ummi," "Ok kun gama girki ne?" Cikin ladabi ta ce "Eh mun gama," gyad'a kai Ummi ta yi ta ce "Me ku ka girka?" Murya na rawa Hadiza ta ce "fried rice with coslow and papper chicken then white rice with fish soup and fruits salad an...," Tsakin da Maleek ya ja ne ya hanata k'arasa fad'in abinda zata fad'a dan mugun tsoron sa take ji gashi da kwarjini. Kallon sa Ummi ta yi ta ce "Son me za a kawo ma?" Kallar tausayi ya yi ya ce "Ummi fa ni naki nake so dukan su ba abinda suka iya," girgiza kai Ummi ta yi ta ce "Ni yanzu Son na gaji amma ka fad'i wacce kake so ta yi ma girki cikin Hadiza,Salma,Halima,Yasira,Zainab,Hajara ko fati?" Kamar zai yi kuka ya ce "Ummi duka basu iya ba," D'aukar waya Ummi ta yi kira ana d'agawa ta yi sallama suka gaisa sannan ta ce "Yawwa Fulani ina so ki samo mun 'yan aiki wad'an da suka iya girki," tana gama fad'in haka ta kashe wayar tana yiwa MG hararar wasa ta ce "Wallahi na gaji da rigimar ka," tana gama fad'in haka ta yi stairs shi Kuma ya kalli Hadiza ya ce "kina jiran meye ne?" Da sauri tabar wajen har tana tuntub'e. Sabeeha ce kwance a d'akin su da yamma wata 'yar aiki ta yi sallama ta ce "Kece Sabeeha?" Gyad'a kai Sabeeha ta yi. "Ki zo inji Yallab'ai," ba tare da tsoro ba ta ce "Gani nan," ta tashi sanye da dogon hijabin ta ta fita a hanya suka had'u da Sabreen dake komawa d'aki. "Sabeeha dear ina zaki?" Tab'e baki Sabeeha ta yi ta ce "Wai Kamis ke kirana," zare ido Sabreen ta yi ta ce "Dafatan dai lafiya?" "Nima bansani ba amma kije yanzu zan dawo," tana fad'in haka ta tafi Sabreen ta bita da kallo Dan gani take yi kamar za ace laifi Sabeehan ta yi. A falo ta samu Yallab'ai shi da Habibu tana zuwa Kamis yabar wajen Yana binta da wani irin kallo ita kuma tana hararar sa. Habibu ya ce "k'araso mana 'yan mata," k'arasawa ta yi ta zauna k'asan carpet ta ce "Gani," Nan fa Habibu ya zayyane mata dalilin kiran ta wani murmushin mugunta Sabeeha ta yi ta ce "Kace masa na amince zan aure shi," shi kansa Habibu ya yi mamakin saurin amsawar da ta yi Amma ya fuske ya ce "To ba damuwa mun gode," sannan ya d'auko kud'i wajen dubu hamsin ya bata karb'a ta yi har da godiya ta tafi. Ko da Kamis ya ji yadda suka yi ba k'aramun dad'i ya ji ba Dan ranar har kyauta ya yiwa 'yan aikin gidan abinda bai tab'a ba su kansu mamaki suke yi. Nan fa kusan kullum sai ya aika an kira ta sunyi fira ba tare da Farida ta saniba. A haka aka yi sati d'aya Sabeeha da Kamis suna kwasar soyayya kamar gaske. Yau ma firar suka gama ta nufi d'akin su tana farin ciki da sallama ta shiga d'akin Sabreen ta tare ta tana cewa "Ka ga ta Yallab'ai," dariya suka yi harda tafawa ta ce "Mu zauna Sabreen dear akwai labari," zama suka yi ta ce "kinsan mene yau nace da Kamis ya sanar da matar sa yana sona Kuma aurena zai yi," Sameeha ta ce "Shikenan mun shiga uku yanzu Sabeeha dear abinda ki ka jawo mana kenan," Sabreen ma a tsorace ta ce "Amma sister kina ganin hakan bazai jawo mana matsala ba?" Sabeeha ko a jikin ta ta tab'e baki ta ce "Manta ba abinda zai faru ba dai saura kwana hud'u ayi salary ba ranar zamu bar gidan nan sannan zuwa lokacin ku zuba ido ku ga abinda zai faru," "Son gobe nake so na tafi Dubai ni da Asiya da karimatu Amma ba dad'ewa zamu yi ba bai fi muyi 3 to 4 days ba," Maleek dake gefe yasha kyau cikin jajayen k'ananun kaya ya ce "Me zaku yi a can?" Ummi ta ce "ka manta bikin ka bai ma kai 2 weeks ba zamu je had'o lefe mana," take ya had'e rai kamar bai tab'a dariya ba. "Haba yaron Ummi dan Allah ka saki ranka kasan auren nan ba fashi kayi hak'uri ayi a gama lafiya ka cigaba da yiwa mahaifin ka biyayya kaji?" Noding kansa ya yi cikin damuwa sannan ya ce "To Ammi maganar abinci fa?" Dariya ta yi ta ce "Yadda ka ke damuwa da maganar abinci da haka ka ke cinsa da kafi haka girma to ban da rigima irin taka Kai da zaka yi aure ai matar ka ce zata dinga girka ma," shiru kawai ya yi ba magana. Washe gari Ummi da Maman Umar da Umman Salman suka tafi Dubai had'o lefen auren Maleeek. B'angaren amarya Nasreen kuwa shiri suke yi ita da friends d'in ta sai shirya events take yi bata damu da yadda Maleek baya ko kiranta ta waya ba hidimar ta kawai take yi tana cin uwar kud'i kamar central bank a gidan yake sai rawar Kai take yi zata auri kyakkyawan jarumin namiji Mai dukiya ya yinda friends d'inta kowa burin sa ya ga MG Maleek. Shi kuwa a nasa b'angaren ko a jikinsa har mantawa yake yi Wai aure zai yi idan ba zancen aka yi masa ba. Kwanan su Ummi hud'u a Dubai suka koma tare da kayan lefe akwatuna ashirin da hud'u Maleek da kansa tare da sojojinsa da Kuma Salman da Umar suka je suka tari iyayen nasu. Ko da suka koma gida ana nunawa Maleek kayan ko kallon basu ishe shi ba daga k'arshe ma tashi ya yi yabar wajen su Umar suka bi bayansa Dan suma jinin su bai had'u da amaryar ba Dan bata da kirki kwata kwata ga wulak'anci da girman kai da rashin girmama na gaba da ita. A haka akai ta shagali ya yinda Rinaz itama Sam bata son Nasreen Dan tunda aka fara Shirin bikin bata wunin gidan. Ballantana Fauwaz da ko kallo Nasreen bata ishe shi ba Dan da Yana da hali yayan sa bazai aure ta ba dan Sam bata da kamun Kai. A b'angaren uwar amarya Umma shiri take yi sosai na aurar da tilon 'yar ta. A haka aka fara gabatar da events ba tare da ango ya lek'a ko nan da can ba amarya ma bata damu ba domin gayyar maza abokan ta ta yi suka dinga shek'e ayar su duk abinda ke faruwa Maleek Yana sane sai dai shi ko a jikin sa. Wuni yake yi a part d'in sa dan ko part d'in Ummi baya zuwa saboda yasan cike yake da bak'i kullum Yana tare da Umar da Salman idan ba a fad'a ma ba bazaka ce bikin sa ake yi ba dan uzurin gaban sa kawai yake yi. A gobe d'aurin aure Daddy da Uncle suka dira a Nigeria. Maleek ya fito kenan cikin Shirin masallaci kasancewar juma'a ce ya ga motocin su Daddy na shigowa gidan kallo d'aya ya yiwa motocin ya d'auke Kai ya kalli Salman ya ce "Salman muje ko?" Mota suka shiga suka tafi masallaci. Daddy kuwa motocin su gama parking guards d'in su suka bud'e musu k'ofa suka fito manyan mutanene sannan kana kallon su kaga ya da k'ani saboda kamar da suke yi. Sannan Daddy ya wuce part d'insa haka ma Uncle ya wuce part d'insa. Da daddare Maleek na zaune a falon sa yana kallon news Nasreen ta shiga falon sai wani karairaya take yi tana iyayi kallo d'aya ya yi mata ya d'auke Kai domin tsoro ma ta bashi tayi wani fau kamar aljana dama fara ce ita sai Kuma ta k'ara da mai sai dai bata wani kyau ga ta da k'ananun idanu kamar 'yar China. K'arasawa ta yi ta zauna a gefen sa ta ce "Sannu da hutawa husby," bai kalle ta ba ya ce "Kece da sannu ba Maleek ba," basarwa ta yi ta ce "yawwa Ya Maleek dama cewa nayi mai zai hana na zauna a nan part d'in ni bana son waccan part d'in," kallon banza ya you mata sannan ya ce "koh?" Wayar sa ce ta yi ringing d'auka ya yi ya ce "Ok gani nan zuwa," yana fad'ar haka ya yi hanyar fita ta ce "Yaya Maleek ina Kuma zaka muna magana?" Ba tare da ya juya ba ya ce "Kiran da ya fi naki muhimmanci zani Kuma a can zaki zauna kya iya fitar mun a part," Yana fad'ar haka yasa Kai ya fice itama ranta a b'ace ta fita. [10/25, 7:34 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️ RUBUTAWA DAGA HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ) SADAUKARWA GA MY DAUGHTER SABEEHA BILKISU Z.YA'U (🅱️K) AISHA MAGAJI DABO (AMA) Page 3 Yana fita Kai tsaye part d'in Uncle ya shiga da sallama a bakin sa amsawa sukayi suna zaune akan kujera k'arsawa ya yi ya zauna k'asan carpet ya ce "Daddy uncle sannun ku da hutawa da fatan Kun dawo lafiya?" Daddyn say ya ce "Lafiya lau Son," Uncle baban Nasreen kallon banza ya yi masa ba tare da ya amsa ba shima Maleek bai sa akan sa ba ya kalli mahaifin sa ya ce "Daddy gani," "Son dafatan ka sanar da auren ka ga abokan ka da Kuma wajen aikin ka ko Dan naji har yanzu banji wata sanarwa daga radio ko jarida ko gidan televisions ba," ya ce "Daddy gaskiya ban sanar ba," kafin Daddy ya yi magana Uncle ya fara zazzaga masifa "Ai dama Kai baka da tarbiyya baka daraja iyayen ka wato kai ba a isa da Kai ba ko to wallahi ka kiyayeni wawan yaro kawai wato saboda tsanar da ka yiwa daughter ne yasa baza ka sanar da auren ba kenan?" Shiru Maleek ya yi zuciyar sa na tafasa dan ji yake kamar ya shak'e Uncle ya kaisa har lahira Amma ba dama saboda wan mahaifinsa ne. Kallo d'aya zaka yi masa kasan Yana cikin b'acin rai saboda idanunsa sunyi jajur kamar Wanda aka watsawa barkono a idanun jijiyoyin dantsen sa duk sun tashi dan a lokacin duk Wanda ya damk'a sai dai wani ba shi ba. Daddy dai ko uffan be ce ba mik'ewa Maleek ya yi yayi hanyar waje Uncle na cewa "Ka gani ko Hamza ka ga rashin tarbiyyar ko ina magana Amma saboda ya rainani ya tashi zai fita wato ga mahaukaci na magana," har lokacin Daddy bai yi magana ba dan yasan idan har Maleek ya tsaya a wajen zai iya aikata abinda ba a tab'a tunani ba domin yana da zuciya sosai. Haka Maleek ya fita yabar Daddy Sai Masifa yake yi Daddy dai bai ce komai ba shiru ya yi Yana sauraron yadda yayan sa ke k'arewa d'ansa zagi da tsine masa a gaban sa. Maleek kuwa ko da ya fita part d'in sa ya wuce ya kwanta saman lallausan gadon sa sai sauke ajiyar zuciya yake yi kamar Wanda ya yi kuka ya k'oshi da abun ya dame shi ya tashi ya yi ta sallah ya yi karatun Qur'an sannan ya ji zuciyar sa ta yi sanyi. Washe gari aka d'aura auren Fatima Aminu mai dala da MG Abdul-maleek Hamza mai dala akan sadaki dubu d'ari biyu d'aurin auren ya samu halartar abokan Daddy da Uncle daga k'asashe daban daban sai dai ango ba tawagar sa dan bai yi gayyata ba. Ana gama d'aurin auren ya nufi gida part d'in sa ya nufa ya watsa ruwa ya kwanta bayan ya ba sojojin sa umarnin kar su bar kowa ya shiga inda yake. A firgice su Sabeeha suka tashi daga baccin da suke yi sakamakon bugun da akewa k'ofar d'akin su gaba d'aya sun gama tsorata especially ma Sameeha Dan har ta fara hawaye ta b'oye a bayan Sabreen da itama jikin ta rawa yake yi Sabeeha kuwa tsaki ta ja tare da nufar k'ofar ta bud'e. Farida ce ta shiga d'akin tare da cin kwalar Sabeeha ta ce "Ke har wacece ke da zaki aure mun miji to wallahi yau sai kin bar gidan nan tunda bana uban ki bane," yatsina fuska Sabeeha ta yi ta ce "Wanne mijin naki ki ke magana Wai?" Dak'uwa Farida ta yi mata ta ce "Dan uwar ki miji nawa gareni to wallahi daga ke har 'yan uwanki sai kun bar gidan nan shegu aljanu," k'arfi Sabeeha tasa ta fisge rigar ta ta ce "Dalla can malama cikani muje wajen mijin naki shine yace Miki akwai alak'a tsakanina da shi to bari kiji ko maza sun k'are bazan auri wannan wawan ba kawai dama danna had'a ku ne Kuma ko yanzu alhamdulillahi burina ya cika," Sabreen da Sameeha sakar ido suka yi suna kallon ikon Allah basu tab'a tunanin k'arfin halin Sabeeha ya kai haka ba. Juyawa Farida ta yi ta fita tana cewa "Gara da ki ka tonawa kanki asiri," tana fita Sabeeha ta kyalkyale da dariya ta ce "Sabreen dear Sameeha sister ya ku ka ga wannan," to ku biyo ni ku ga wani salon ta d'auki hijabi ta d'ora saman hijabin jikin ta ta fita suma binta suka yi suma. Falo suka fita suka samu Kamis zaune kan kujera Farida kuma na tsaye a kansa sai zabga masifa take yi kamar zata tsaga gidan saboda d'aga murya "To Wallahi sai dai idan ka sake ni ka rasa wacce zaka aura sai waccan yarinyar wacce ba son Allah da annabi take ma ba so take kawai ta ga ta rabamu," Sabeeha na zuwa falon ta fashe da kukan munafurci har da k'ak'alo hawayen k'arya tuni Kamis ya rikice ya yi wajen ta kamar zai rungume ta ya ce "Subhanallah maiya faru?" Cikin kukan k'arya Sabeeha ta ce "Ni kawai bar maka gidan ka zanyi saboda bazan iya da masifar matar ka ba yanzu fa zuwa ta yi ta hauni da duka ina cikin bacci ni kawai tafiya zamu yi bazan iya ba tun yanzu ta fara dukana ina ga munyi aure?" A fusace Kamis ya kalli Farida ya nuna ta da yatsa ya ce "Wallahi Farida ki kiyayeni idan ba haka akan yarinyar nan yanzu zan sake ki ki tafi," zazzaga masifa yake yi kamar Wanda aka yiwa asiri ita kanta Farida mamaki take yi. Sabeeha ta ce "A'a my love ka kyale ta kawai indai nice na hak'ura amma ka ja mata kunne ba ruwan ta dani," aikuwa nan ya fara bugawa Farida warning har ma 'yan aikin gidan akan duk abinda Sabeeha ta ce ayi ayi shi ba b'ata lokaci sannan ya sallami kowa. Su Sabeeha ma suka koma d'aki suna tik'ar rawa ko a jikin su wannan karon har da Sameeha a rawar. Tun daga ranar ko aiki denawa suka yi a gidan Farida kuwa makirci kala kala tana shansa wajen Sabeeha wataran har duka Kamis kewa Farida akan Sabeeha. B'angaren amarya Nasreen kuwa a ranar da aka d'aura aure aka Kai ta part d'in ta dake gidan yasha kaya gida guda ne harda gate a gidan upstairs ne ya sha kyau har ya gaji ga sojoji ta ko ina a gidan sai dai har aka kaita bata ga ango ba yana can yana bacci abinsa. Amarya kuwa har k'arfe sha d'aya ba ango ba labarin sa har k'awayen ta duk sun watse amma babu shi wayar ta ta d'auka ta kira Uncle tana kuka kamar wacce aka yiwa mutuwa yana d'agawa ta sake fashewa da kuka daga can uncle a rikice ya ce "Mamana ya akayi ne mai ya faru?" Cikin kuka ta ce "Daddy ka ga fa har yanzu ya Maleek bai zo ba," Uncle ya ce "kwantar da hankalin ki ina zuwa yanzu zaki ga ya zo," bai jira cewar ta ba ya kashe wayar ya fara neman layinkan MG amma duk a rufe shi kuwa rufe wayoyin sa yayi saboda kar ma a neme sa. K'wafa Uncle ya yi sannan Kai tsaye ya nufi part d'in Ummi babu ko sallama ya shiga falon sai hura hanci yake yi Fauwaz ne zaune yana charting yana cin fruits ko kallon inda Uncle d'in yake bai yi ba sai ma rera wak'a da yake yi ta joeboy "oh my baby I'm getting jealous already," "Kai Fauwaz!!" Uncle ya daka masa tsawa kallon sa Fauwaz ya yi yana yamutsa fuska alamun tsawar ta dame shi sannan ya ce "Na'am," jinjina kai Uncle ya yi ya ce "Dan uwar ka baka ganni bane da bazaka gaishe ni ba ko da yake ba ta kai nake yi ba uban ka nake nema kira mun shi," mik'ewa Fauwaz ya yi ba tare da ya kalli inda Uncle yake ba ya bud'e wata k'ofa ya shige da alama d'akin sa ne. Sakin ido Uncle ya yi yana kallon ikon Allah lallai wannan yaron ya zama dole na koya masa hankali Yana nan tsaye Rinaz ta sauko daga stairs hannun ta rik'e da glass cup sarai ta ga Uncle amma ta nuna kamar ba mutum a falon ta nufi kitchen ta ajiye cup d'in hannunta ta fito. Har zata fara hawa stairs ta ji Uncle ya ce "To 'yar gidan marasa tarbiyya baki iya gaisuwa ba?" Sai lokacin Rinaz ta kalle shi ta ce "Sannu Uncle tarbiyya Kuma ai babu ita a nan tunda ni goyon Nasreen ce," tana fad'ar haka ta tafi ta barshi Yana danna ashar. A falon sama ta had'u da Ummi k'ofar d'akin ta ta bud'e zata shiga Ummi ta ce "Mamana ke da waye naji kamar kina magana da wani a down stairs?" Murza ido Rinaz ta yi ta ce "Eh to naga wani kamar Uncle sai dai idanuna basu tantance ba saboda daga bacci na tashi," tana fad'ar haka ta shige d'aki tasa key. Girgiza kai Ummi ta yi saboda sarai tasan Uncle d'in ne sai dai tasan halin su Rinaz rashin kunya suke masa sab'anin Maleek da ya kasance mai girmama shi sai dai shi uncle d'in baya gani su Kuma su Rinaz ganin irin rashin mutuncin da Uncle d'in kewa yayan nasu ne harma da Ummi yasa su Kuma basa ragawa Uncle duk da basa yi a gaban Maleek saboda sun san tsab zai iya zane su. K'asan Ummi ta sauka ta ce "Laa Yaya kaine sannu da zuwa ai bansan da shigowar ka ba," tsaki ya ja ya ce "Ai dama baza ki saniba tunda kin fini iko da k'anina tun d'azu na shigo amma kin hana shi fitowa sai yara mara tarbiyya da ki ka haifa," k'asa Ummi ta yi da kanta bata ce komai ba domin idan da sabo ta saba da halin wan mijin nata. Daddy ne ya sauko yana cewa "Sannu da zuwa yaya ai bamusan ka shigo ba," harara ya aikawa Daddy ya ce "ta ya zakasan na shigo bayan gimbiyar ka uwar mata ta hanaka fitowa," girgiza kai Daddy ya yi ya ce "A'a Wallahi yaya ba laifin Aysha," d'aga masa hannu Uncle ya yi ya ce "Ba abinda ya kawoni kenan ba nazo ne akan waccan d'an naku ni zai rainawa hankali na d'auki 'yata na ba shi amma kamar an kai masa abu mara amfani to wallahi duk inda yake ku kira shi ya tafi wajen amaryar sa," Yana fad'ar haka ya kad'a babbar rigar sa ya fice da kallo suka bi shi har ya fita. Daddy ya kalli Ummi ya ce "Aysha kinga halin d'an ki ko Sam baya gudun b'acin ranmu da nashi gaba d'aya ki kalli abinda ya ja to yanzu ki kira shi ya tafi wajen matar sa," shima Yana fad'ar haka yabar falon. Ajiyar zuciya Ummi ta sauke sannan ta d'auki wayar ta ta kira wayar Maleek lokacin kunna wayar kenan wayar Ummi ya shiga d'agawa ya yi ya ce "Hello Ummina," ta ce "Son ina ka shiga ne yau fa kwana wajen biyar ban ganka ba?" Ya ce "lafiya qalau nake Ummi," ta ce "Masha Allah amma dan Allah son ka dena jamun magana yanzu Yaya yabar nan wai baka je wajen amaryar ka ba dan Allah ka tafi yanzu," daga can ya sauke numfashi ya ce "To Ummi bari naje," ta ce "Yawwa d'ana Allah ya yi maka albarka," ya ce "Ameen Ummina goodnight I love you," ta ce "I love you more," daga haka ya ajiye wayar ya tashi ya fad'a bathroom ya yi wanka. Yana fitowa ya zura jallabiyya tare da fesa turare ya d'auki wayoyin sa ya fice daga d'akin. Yana fita motar sa ya hau ya nufi gidan ko da ya yi parking aka bud'e masa k'ofa ya fita ya shiga falon ya nemi waje ya zauna a falon ya jingina a kujera ji yake dama bai dawo k'asar ba gaba d'aya bai da wani kwanciyar hankali ya dad'e yana tunani sannan ya mik'e ya haye stairs. Tura k'ofar d'akin ya yi ya shiga da sauri Nasreen ta kalli k'ofar idanunta sunyi jajir saboda kukan da tasha sai kuma ta ba shi tausayi Dan ko ba komai 'yar uwar sa ce bai kamata ya barta tana kuka haka ba ai laifin mahaifin ta bai kamata ya shafe ta ba tunda ita mai son shi ce halin ta ne kawai bai so. Bai gama tunanin da yake ba Nasreen ta tashi da gudu ta rungume shi tana kuka bai shiru ya yi yana jin yadda take kuka sannan a hankali ya janye ta daga jikin sa ya zaunar da ita gefen gado Yana kallon ta sannan ya ce "Kukan na meye?" Ba k'aramun dad'i ta ji ba saboda kulata da ya yi ta ce "Tun d'azu nake jiran ka baka zo ba," d'an tab'e baki ya yi ya tashi tsaye ya ce "Kinci abinci?" Girgiza kai tayi ya juya ya je kitchen ya ebo mata snacks da kaza da drinks ya Kai mata ya ce "Ki daina zama da yunwa," noding kanta ta yi sannan ta fara ci sai da ta gama ci ta koma ta kwanta ya ce "Wait kinyi sallah ma kuwa?" Shiru ta yi dan rabon ta da Sallah tun kafin a fara bikin su shirun da ta yi ne ya tabbatar masa da bata yi ba ya ce "Please tashi ki yi kar asa mun gida ya kama da wuta," ya fad'a kamar ba shi ya fad'i maganar ba. Tashi ta yi tai wanka lokacin da ta fito bata same shi a d'akin ba sallar ta yi sannan ta fita zuwa falo can ta same shi ya rufe ido kamar mai yin bacci ta zauna gefen sa ta ce "Ya Maleek," a hankali ya bud'e ido ya kalle ta ta ce "Nayi sallar," ya ce "Good," daga haka bai Kuma cewa komai ba ta ce "Ya Maleek muje mu kwanta," bece komai ya mik'e yana gaba tana binsa a baya har d'akin ta kwanciya ya yi ya ce "Bismillah kwanta," ya fad'a yana nuna mata gefen sa hayewa ta yi ta kwanta. Maleek ya kasance mutum mai hak'uri da Kuma tausayi hakan ne yasa yake mata hakan sannan zai yi k'ok'ari wajen sauke duk wani nauyi nata da ya hau kansa yana cikin wannan tunanin ya ji ta rungume shi ta baya ji ya yi kamar namiji ne ya tab'a shi saboda bai da wani feeling a kanta. Juyawa wajen ta ya yi Yana kallon ta itama kyakkyawar fuskar sa ta tsurawa ido kamar zata had'iye shi a hankali ya lumshe idanunsa mai d'auke da zara-zaran eye lashes bai ankara ba ya ji ta had'e bakinsa da nata ta fara kissing da sauri ya bud'e idanunsa Yana kallon yadda take tsotse masa baki kamar mayya. Tun baya biye mata har ta bashi tausayi ganin yadda ta fita hayyacin ta ya fara k'ok'arin faranta mata sai dai abinda ya ji ne ya sa shi saurin tashi ya shige toilet wanka ya yi ya fito ya nemi gefen gadon ya zauna ba tare da ya kalle ta ba. Ita kuwa a nata b'angaren Addu'a yake Allah yasa bai gane ita ba virgin bace bata gama tunanin ba ta ji ya ce "Ya akayi hakan ta faru?" Kuka ta fara yi tsawar da ya daka mata ne yasa ta yi shiru ya ce "Tambayar ki nake yi!!" Cikin kuka ta ce "Dan Allah Yaya kayi hak'uri dama Arfat ne ya gama sanina," jinjina kai Maleek ya yi ya ce "D'an gidan waye?" Tana hawaye ta ce "D'an gidan Alhaji Hamisu kwangila," a d'an razane Maleek ya kalle ta ya ce "Tabbas baki da hankali Nasreen ke yanzu har iskancin ki ya Kai Nan ko da yake ba laifin ki bane na Uncle ne Amma kisani daga yau karki kuskura kice zaki k'ara tab'ani stupid kawai," kuka kawai take yi tana bashi hak'uri ya ce "kukan da kike ba abinda zai amfana Miki ni dai bazan tona Miki asiri ba saboda bani da riba amma idan kin tona kanki I don't care," yana fad'ar haka ya tashi yabar mata d'akin sai aikin kuka take yi. Sabeeha ce zaune a d'akin su ita da 'yan uwan ta wata 'yar aiki ta shiga hannunta rik'e da envelope har k'asa ta tsugunna ta ba Sabeeha ta ce "Ranki ya dad'e gashi inji Yallab'ai ya ce a kawo muku salary d'in ku ne," karb'a ta yi ta ji da nauyi ko ba a fad'a ba tasan kud'in sunfi k'arfin iya na salary d'in su. 'yar aikin na fita ta kalli su Sameeha ta ce "Sabreen dear ku fara had'a mana kaya yau ba sai gobe ba zamu bar gidan nan," aikuwa suka fara had'a kayan su. Da daddare suka d'auki trolleys d'in su suka fito suna tafe suna sand'a a falo suka hangi Farida zaune ta zabga uban tagumi sai kuka take yi fuskar ta ta kumbura tsabar dukan da take sha gun Kamis ko kula dasu bata yi ba har suka fice bata sani ba. Turus suka tsaya ganin Mai gadi a bakin k'ofa da Kuma Mai bawa flowarers ruwa Sameeha ta ce "Sabeeha dear yanzu ya zamuyi?" Jan hannun Sameeha ta yi a hankali suka bi ta baya kasancewar katangar bayan babu wani tsayi suka d'ane suka haure suna haurawa suka fara gudu har sai da suka fita titi kasancewar ba wani dare ne ya yi ba suka samu mota suka shiga sai k'auyen su. [10/25, 7:35 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️ RUBUTAWA DAGA HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ) SADAUKARWA GA MY DAUGHTER SABEEHA BILKISU Z.YA'U (🅱️K) AISHA MAGAJI DABO (AMA) Page 4 Ba su suka je k'auyen su ba sai tsakar dare tafiya suke a tsorace saboda dare ne Kuma garin su duk daji da haka suka k'arasa gidan su da ko k'ofa babu Kai tsaye suka shiga gidan da sallama amma gidan tsitt kamar babu kowa cikin sa. Kad'an suka hango haske a d'akin Abban su d'akin suka nufa Sameeha ta bubbuga k'ofar d'akin daga ciki Abban su ya ce "Waye?" Sabeeha ta ce "Mune Abba, jin muryar 'ya'yan sa ne yasa ya bud'e k'ofar Yana bud'e musu k'ofa suka rungume shi suna murnar ganinsa shima tsabar farin cikin ganin su har hawaye ya yi. Sannan suka zauna Abba ya ce "Aminaina k'ara goduwa ku ka yi?" Sabeeha ta ce "Eh mana mun gaji," Sameeha ta ce "Eh Wallahi Abba mutanen gidan basu da mutunci kullum wulak'anci ake yi mana," Sabreen ta cigaba da cewa "Kuma fa Abba wataran ma har dukan mu suke yi," kallon tausayi Abba ya yi musu sannan ya ce "Aminaina rayuwa fa dole sai kunyi hak'uri da ita yanzu dawowar nan da ku ka yi Allah kad'ai ne yasan abinda zai faru idan yaya ya sani kunsan bata d'aga muku k'afa har dukan kunsan yi muku shi yake yi," shiru suka yi saboda sarai suma sunsan halin wan mahaifin nasu. Sabeeha ta ce "Abba kaci abinci kuwa?" Girgiza kai ya yi ya ce "Yarinyar Abba ai yau ba ranar abinci bace Ni Kuma babu lafiyar da zan fita na nema," tausayin mahaifin nasu ne ya kama su suka bud'e trolleys d'in su suka fito da snacks da lemo suka ci dama suma suna jin yunwar sai da suka k'oshi Abba ya ce "Yanzu ku kwanta a nan tunda d'akin ku ba a gyare yake ba gobe sai ku gyara," suka ce "Toh Abba," Kwanciya suka yi dama kafin su baro gidan Kamis sai da suka yi sallah haka suka yi bacci cikin farin ciki haka ma Abba shima bacci ya yi cikin farin cikin dawowar 'yan ukun sa. Washe gari tun asuba da suka tashi basu koma bacci ba suka fita k'aton tsakar gidan su suka fara gyara shi sai da suka fara gyara d'akin su mai d'auke da k'atuwar katifa da ledar tsakar d'aki da labulaje masu kyau haka ma bedsheet d'in Mai kyau ne har da rishow a d'akin Wanda duk abinda ke d'akin Sadam ne ya shiya musu dan ma wasu abubuwan Kawu Bala Yana k'wacewa shi da matar sa. Tsaf suka gama gyara d'akin sannan suka tsafta ce ko ina a gidan tsakar gidan su ya yi fess duk da ba suminti bane amma ya yi kyau. Suna gamawa suka yi wanka suka shirya cikin 'yan kati riga da skirt dama 'yan uku akwai tsafta Sabeeha da Sabreen suka d'auki Hijabi sannan Sabeeha ta kalli Sameeha ta ce "Sameeha dear na ga akwai kananzir a cikin rishow d'in mu ki d'ora mana ruwan shayi bari muje shagon shazali mu siyo kayan had'awa," Sameeha ta ce "To sai kun dawo," suka fita. Tunda suka fita ake kallon su kowa da abinda yake cewa domin d'auka ya yi 'yan uku sun tafi yawon karuwanci Kai tsaye shagon suka je suka siyi kayan shayi suka tafi gida ba tare da sun lura da kallon da mutanen k'auyeb ke yi musu ba saboda su dama ko k'awaye ba su da su rayuwar su kawai suke yi su uku abinsu. Da sallama suka shiga gidan Abba da Sameeha suka amsa musu k'arasawa wajen Abba dake zaune kan tabarma k'ark'ashin bishiya suka yi suka gaishe shi tare da yi masa ya jiki ya amsa cikin fara'a sannan suka je suka had'awa Abba tea d'in suka Kai masa ya ce "Allah ya yi muku albarka," suka ce "Ameen Abba," sannan suma kowacce ta had'a nata suka sha bayan sun gama suna zaune wajen Abba suna fira kawai sai tsintar kawu Bala suka yi a kansu sai huci yake yi da alama a zuciye yake. Gaishe shi suka yi ya musu kallon banza sanna cikin masifa ya ce "Wato Dan uwar ku shine ku ka sake gudowa to bari kuji na fad'a muku nan da sati d'aya zan aurar da ku shegu 'yan iska," shiru suka yi har Abba ba Wanda ya ce uffan. Mtswww ya ja tsaki sannan ya ce "Ina kud'in da ku ka zo da su ku bani nan," Sabeeha ce ta yi k'arfin halin cewa "Mu bamu zo da kud'i ba," "Dalla can rufe mun baki dama ai ke kinfi kowa rashin kunya to wallahi bari kuji kafin naje na dawo ku fito mun da su idan ba haka ba na lahira sai ya fi ku jin dad'i," Yana gama fad'in haka ya fice yana masifa. Bai dad'e da fita ba 'yar sa Zainabu ta shiga tasha kwalliyar irin tasu ta k'auyawa ko kallon Abba bata yi ba balle ta gaishe shi ta ce "Karuwai ashe yawon iskan cin babu riba kenan tunda har gashi an dawo Wallahi anji kunya Uban ma da yake kamar mai hankali Amma ya kasa hana ku," tashi Sabeeha ta yi ta je gaban Zainabu ta ce "Au Wai kina nufin naki uban bai gaya Miki inda muka tafi ba to ai shine kawalin mu," Zainabu ta ce "Ki ka zageni?" "An zage ki d'in ki yi abinda zaki yi," duka Zainabu ta kaiwa Sabeeha dama haka Sabeehan take so aikuwa ta kama Zainabu da duka sai ihu take yi. Dakyar Abba da Sameeha suka raba fad'an ya yinda Sabreen ke gefe tana kallon su dan bata so aka raba ba so tayi Sabeeha ta yiwa Zainabu jinajina duk abinda zai faru ya faru. Zainabu kuwa fita ta yi tana kuka kamar wacce Uwar ta ta mutu tana zuwa zauren gidan su ta k'ara volume d'in kukan ta. Lantana matar Kawu Bala tana jiyo kukan Zainabu ta mik'e tana karkad'e zani ta d'urma ashar ta ce "Wane d'an shegiyar ne ya tab'a mun 'yata Wallahi yau sai an hau sama dani," Zainabu ta ce "Lantana kinga 'yan uku ko daga zuwa gidan su suka hauni da duka har ma da Uban su," mayafi Lantana ta d'auka tana cewa "Muje gidan yau zanga uban da ya tsaya musu har suka dokar mun 'ya," haka tasa Zainabu a gaba suna tafe tana masifa. A hanya suka ci karo da Kawu Bala shima yana jin abinda Zainabu ta fad'a ya bisu shima Yana balbala kalar tasa masifar. Suna zuwa suka samu 'yan uku zaune a kan tabarma kawai suka rufe su da duka su Sabeeha kawai ji suka yi an rufe su da duka tako ina gashi Abba ya fita baya nan tab'arya Zainabu ta d'auka ta nufi Sameeha dan duk a tunaninta Sabeeha ce Aikuwa ta rafka mata a goshi. Wata k'ara Sameeha ta saki ta fad'i sumammiya hankali tashe Sabeeha da Sabreen suka yi kanta suna kuka jijjiga ta Sabeeha ta fara yi tana cewa "Sameeha dear please ki tashi karki mutu ki bar mu a wannan halin please," ganin da su Kawu Bala suka yi Sameeha bata yin ko motsi aikuwa suka fice a tsorace. Sabeeha da Sabreen kuwa sai kuka suke yi suka d'ebo ruwa suka zuba mata ajiyar zuciya Mai nauyi ta sauke sai dai har lokacin jini sai zuba yake yi daga goshin ta a rikice Sabeeha ta fita ta nemo mai machine suka kai Sameeha chemist treating d'in wajen aka yi mata tare da magunguna sannan suka tafi gida. Ko da suka koma gida ruwan wanka suka d'ora mata ta ta yi wanka ta kwanta sannan suka dafa taliya da manja suka ci Saneeha tasha magani ta kwanta saboda ji take yi kanta kamar zai tsage domin ba k'aramun ciwo yake mata ba. Da Abba ya dawo hankalin sa ba k'aramun tashi ya yi ba ganin kan Sameeha nannad'e da Bandage ko da su Sabeeha suka fad'a masa abinda ya faru hak'uri kawai ya iya basu. Kawu Bala sai da ya yi kwana biyu bai je gidan ba a b'angaren su Sabeeha kuwa ba k'aramun dad'in hakan suka ji ba sai dai duk da haka hankalin su ba a kwance yake ba saboda ciwon kan Sameeha kullum k'aruwa yake yi wataran har kuka suke tasa ta a gaba su yi tayi saboda gani suke yi kamar mutuwa zata yi ta barsu shi kansa Abba hankalin sa ba a kwance yake ba. Wata rana da yamma Sabeeha ta fita zuwa shagon shazali ta siyo maggi suka ci karo da Zainabu itama an aike ta shagon kallon banza Zainabu ta yi mata ta ce "Ina mara kunyar gidan ku ai nasan yanzu ta shiga taitayin ta banzaye Karuwai ashe gado ku ka yi ashe haka uwar ku ma ta tafi yawon karuwanci sai dai ita nata yawon yayi riba tunda gashi har yanzu bata dawo ba tun kuna yara," wani irin juyawa kan Sabeeha ya fara yi juyawa kawai ta yi ta nufi gida tana jin kanta ya yi mata wani mugun nauyi. Da gudu ta k'arasa shiga gidan Abba da Sabreen ne zaune a kan tabarma sai Sameeha dake gefe a kwance da sauri ta k'arasa ta zauna gaban Abba hawaye na fita a idanunta ta ce "Abba Dan Allah kaji tausayin mu ka fad'a mana ina maman mu take Abba ashe dama maman mu na raye bata mutu ba," Sabreen a rikice ta ce "Sabeeha dear waye ya fad'a miki maman mu na raye?" Cikin kuka ta ce "Yanzu Zainabu ta fad'amun wai maman mu yawon karuwanci ta tafi ta barmu Abba meyasa meyasa mama zata yi mana haka?" Dukan su kuka suke yi har Abba Wanda aka tab'o masa inda ke masa ciwo ya ce "Ku gafarce ni yarana maman ku na raye Amma ba yawon karuwanci ta tafi ba hakan ba halin Maryam bane," share hawaye Abba ya yi ya cigaba da cewa "Tun ina yaro mahaifana suka rasu daga ni sai Yaya Bala mu kad'ai iyayen mu suka haifa sai dai tun muna yara Yaya Bala ya d'auki tsanar duniya ya d'ora mun saboda a cewar sa iyayen mu sunfi sona kuma bakomai ne yaja hakan ba sai dan nafi jin maganar su nafi yi musu biyayya shi kuwa babu Wanda ya isa ya sa shi ballantana ya hana shi tunda iyayen mu suka rasu Kuma na rasa gata domin Yaya Bala baya duba maraicin mu haka zai tara abokan sa suyi mun duka haka rayuwata ta cigaba da kasancewa daga baya da naga rayuwa na yi mun wuya saina fara neman aiki saboda mu bamu yi makaranta ba Kuma iyayen mu 'yan gudun hijarane bamu san kowa a garin nan ba haka nayi ta bin shaguna ina neman aiki har na had'u da malam Haruna Wanda yanzu ya rasu Allah sarki mutumin kirki shine ya d'auke ni a matsayin yaron shagonsa ina zama idan mun tashi ya sallame ni Ni Kuma idan ya bani bana kashewa duka nake yin tari sannan duk sanda kaya ya k'are mana muke shiga cikin kaduna muyo sarri a haka har muka saba da Wanda muke zuwa sari wajen sa a birni har ya tambayi Malam Haruna ni d'ansa ne malam Haruna bai b'oye masa komai ba ya fad'a masa ni maraya ne mutumin ya tausaya mun sosai sai kawai ya xe da malam Haruna dan Allah a bashi ni na zama yaron sa koda malam Haruna ya tambayeni nace na yadda saboda mutumin Yana da kirki sosai haka na koma kaduna da zama sannan idan aka tashi Yana bani kud'i da yawa hakan ne yasa na koma makarantar islamiyya," Shiru Abba ya yi sannan ya cigaba da cewa "haka na cigaba da zama a wajen Malam Usman har na girma a lokacin ne kuma cuta ta kama malam Usman har ya rasu bayan ya mallaka mun shagon kyauta saboda ya sanar dani shi ba d'an kaduna bane sannan bai da kowa nayi kukan rashin sa haka na cigaba da zama da shi har na kai shekara talatin da biyu a lokacin ne na had'u da Maryam kyakkyawa ce sosai sannan iyayen ta masu kud'i ne kuma hakan bai sa ta kasance mai girman Kai ba tana da mutunci bata da wulak'anta talakawa ko kad'an kusan kullum tana zuwa shagona siyayya ba Dan komai ba sai dan jinin mu ya had'u da ita abu kamar wasa na fara jin soyayyar ta a zuciyata tun ina b'oyewa har sai da na fad'a mata ga mamakina sai na ga ta kamu da matuk'ar farin ciki ashe itama ta dad'e tana sona sai dai lokacin da iyayen ta suka ji ba irin wulak'ancin da bangani ba saboda sun tsane ni kasancewa ta ba mai kud'i ba har duka mahaifinta yasa aka yi mun akan na rabu da ita dan bazai bani auren tilon 'yar sa ba Amma kamar k'ara sonta nake yi haka itama a nata b'angaren ta zab'i zama dani iyayen ta suka ce to indai ta nace sai ni babu su ba ita tace ta yadda haka aka d'aura auren mu na tafi da ita garin mu dama Ina da gadon wannan gidan a ciki muka zauna lokacin Kuma Yaya Bala ya yi aure ya auri Lantana zama muke Ni da Maryam zaman lafiya sai dai Kawu Bala yana d'ora idanunsa akan Maryam ya ji ya tsane ta ba dan komai ba sai dan ita ta kasance mai ilimi domin a k'asar waje ta yi karatu gata kyakkyawa sab'anin matar sa masifaffiya ce sannan ba ilimin boko bana Arabic kamar yadda shima yayan ya kasance hakan ne yasa suke mata hassada k'iyayyar da Yaya ke mun saita shafi Maryam ba irin wulak'ancin da ba ayi mata ba amma ta shanye Dan tana da hak'uri da kawaici a haka har matar Yaya Bala ta haifi d'anta na fari Faruk lokacin ne Kuma aka farke shagona dana dawo da shi nan k'auyen aka kwashe min komai na ciki da Kuma cinikin dake shagon daga lokacin na koma ba cin yau babu na gobe Maryam kuwa iyayen ta suka watsar da ita har kaduna ta je ta nemi gafarar ta suka yafe mata lokacin tana d'auke da cikin ku haka muka cigaba da rayuwa saboda iyayen ta sun bani wani jarin a haka har aka haife ku kyakkyawa da ku sannan kuna kama da Maryam sai dai ita ta fiku haske sosai haka muka cigaba da rainon ku inda muka sa muku sunana mahaifiyar Maryam wato Rukayya ke kenan Sabeeha sai Sadiya sunan mahaifiya ta wato Sabreen Sameeha Kuma sunan kakar Maryam Hajara kuna da shekara uku wata rana na fita shago ina dawowa na tarar Maryam bata nan har dare bata dawo ba hankalina ya tashi sosai a haka har akayi sati d'aya kawai saina shirya naje kaduna Amma da naje sai na samu labarin mutuwar iyayen Maryam da suka yi hatsarin jikin sama sannan an tabbatar mun Maryam ta je garin sai dai tunda iyayen ta suka rasu ta siyar da gidan tabar unguwar ba neman da banyi mata ba Amma ban ganta ba haka na hak'ura na dawo sai dai ina dawowa na tarar an Kuma farke shagona an sace komai sannan ku kuma naje na tarar matar Yaya ta yi muku duka harta fasawa Sabeeha baki haka na d'auke ku zuwa gida na cigaba da kula da ku na koma wajen Malam Haruna sai dai shima lokacin Yana kwance ba lafiya 'ya'yan sa ke zama a shagon haka nai ta dako ina ciyar da ku har kuka kawo wannan lokacin akwai wata rana da akayi bak'i a k'auyen nan anan Sadam ya ga Sabeeha ya ce Yana rik'o ni sam ban yadda dashi ba saboda Sam bai da isasshiyar tarbiyya Amma Yaya Bala yayi caraf yace ya bashi ke ya saku a makaranta haka yake aiko driver Yana Kai ku Yana d'auko ku inda naji dad'i Yaya bai nuna baya so ba saboda yana tsoron Sadam haka ya cigaba da d'awainiya da ku komai ya siyo Miki sai kik'i k'arb'a kice sai ya kawowa 'yan uwanki tun daga ranar komai zai siyo miki guda uku yake siyowa wannan ne labarin mu Amma Wallahi Maryam ba yawon banza ta tafi ba sai dai bansani ba ko tana raye ba ko ta mutu sannan bansan meyasa ta tafi ta barmu ba," kuka sosai su Sabeeha ke yi gwanin tausayi har shesshek'a suke yi dakyar Abba ya yi k'arfin halin rarrashin su. Tun daga lokacin su Sabeeha su ka fara addu'ar Allah ya bayyana musu maman su. B'angaren Maleek kuwa tun washe garin da aka Kai Nasreen ya dena shiga harkar ta har kallo bata ishe shi ba idan ta gaishe shi zai amsa daga haka ba ruwan sa da ita. A haka har aka yi sati d'aya ranar yana part d'in Ummi kasancewar ranar week end ne Ummi bata fita office ba da kanta ta yi masa girki fira su Ummin ke yi ita da su Fauwaz shi dai Maleek bai ce Komai ba. Ummi ta ce "Rinaz gobe ki shirya kije gidan Doctor Maryam Dan ta damu kije Wai kwana biyu bakya zuwan mata," Rinaz ta ce "Nima Ummi ai nayi missing d'in ta Allah sarki mamana Wallahi Ummi ina son Mama sosai tana da kirki sosai," Fauwaz ya ce "Gaskiya dai akwai kirki nima tana burgeni," Murmushi Ummi ta yi ta ce "Ku ma kenan Ni kaina ina son Doctor Maryam k'awa ce ta gari ko a asibiti kowa yabon halin ta yake," "Son," Ummi ta kira shi kallon ta Maleek ya yi sannan ya ce "Na'am Ummi," "Ka ga daga yau fa ba k'ara yi maka girki zanyi ba," zare ido ya yi ya ce "Why Ummi?" "Saboda gobe matar ka zata fara yi maka girki," langab'ar da Kai ya yi ya ce "Allah Ummi ba ta iya ba," dariya Ummi ta yi ta ce "Ta ya kasan bata iya ba bayan ba tab'a cin abincin ta kayi kaji ba?" Ya ce "Ai shiyasa nace bata iya ba ban fa tab'a gani ta yi ba," Rinaz ta ce "Wallahi kuwa Ummi bata iya ba akwai sanda na tab'a ci Kai abin kamar ayi amai ko a ido," pillown kujera Ummi ta jeri Rinaz da shi ta ce "Kinga Mamana ki kiyaye ni," tura baki Rinaz ta yi ta ce "Allah Ummi dagaske," shi dai shiru ya yi bai Kuma magana ba haka ma Fauwaz da ko maganar Nasreen baya so ayi. Washe gari kuwa 'yan aiki ne suka yiwa Nasrin girki kamar gaske tasa a ka jera mata komai a daining a waya ta kira Maleek ta sanar masa an gama abinci yace Yana zuwa. Dama lokacin Yana waccan part d'in nasa wanka ya yi ya shirya cikin black trouser pencil tare da white T-shirt sannan ya d'ora bottles one a sama tare da black tunber loon takalmi a kafarsa sai zabga k'amshi yake yi kan nan yasha had'adden aski sai shek'i yake yi yana fitowa sojojin sa suka bud'e masa k'ofa aka jashi zuwa d'ayan part d'in da Nasreen ke ciki duk da ba nisa Amma abin ku da Mai mulki da gata sai a mota yake zuwa suna zuwa soldier's suka bud'e musu gate suka shiga aka bud'e masa k'ofa ya fita. Da Sallama ya shiga falon Nasrin na zaune ta hakimce a kujera tasha kyau ba laifi cikin doguwar rigar material ga 'yan aiki zagaye da ita. Tunda ya shigo take binsa da ido domin ba k'aramun kyau ya yi ba tafiya yake yi cikin k'asaita ji take yi kamar ta je ta rungume shi a jikin ta sai dai ba fuska. A hankali ta tashi ta nufi inda yake ta ce "Sannu da zuwa ya Maleek," ya ce "Yawwa," daga haka suka nufi daining yana jin haushin kallon da 'yan aikin ke binsa da shi sannan ga haushin Nasreen da yake ji ita sam ba ruwanta bata cewa 'yan aikin su basu guri indai yaje part d'in ko magana zata fad'a masa bata cewa su bar wajen. Kujera ta ja masa ya zauna sannan ta fara sarving d'insa abinci kallon abincin yake Yana yatsina fuska domin ko a ido bai da kyan gani sai dai da gani tasha uban curry shinkafar Wai nan a dole anyi jallop sai dai naman da akasa kamar zai yi magana zama tayi tana wani fari da ido ita a dole ta yiwa miji girki. Kad'an ya d'iba a spoon ya kai bakinsa da sauri ya fesar Yana aikawa Farida harara domin 'yan aikin Ummi ma sunfi nasu iyawa sau dubu balle shi da ya saba cin na Ummi. Sink d'in dake daining d'in ya je ya kuskure bakin sa sannan ya koma ya zauna ya zuba ruwa yana sha Yana hararar Nasrin. Ta ce "Ya Maleek lafiya maiya faru?" Sai da ya yatsina fuska sannan ya ce "Who cook for me?" Ta ce "Maid's," ya ce "Maid's Ni kika bawa 'yan aiki suka ma girki to bari kiji daga yau ban yadda wata a cikin su ta yi mun girki ba dan haka tashi ki je ki dafo mun wani," Yana fad'ar haka ya nufi cikin falon ya kalli 'yan aikin ya ce "Kubar mun nan," da gudu suka fice shi Kuma ya zauna Yana kallon diamond watch d'in hannunsa sannan ya kalli Nasreen ya ce "Ki wuce ina jiran ki," wucewa ta yi tana k'unk'uni shi Kuma ya yi k'wafa Yana danna wayar sa. Ta dad'e sosai a kitchen d'in kace wani wahalallen girki take yi shi Kuma Yana sane yasa ta dan so yake ya gwada ta ya gani ta iya ko bata iya ba sai da ta yi wajen awa biyu sannan ta fito hannunta rik'e da plate ashe duk dad'ewar da tayi jallop d'in taliya take girkawa. Har zata wuce daining ya ce "No need kawo mun nan," ya fad'a yana nuna mata center table ajiyewa ta yi zata zauna ya ce "Kawo mun ruwa," tashi ta yi ta kawo masa ruwa da cup har da lemo sai lokacin ya kalli abinci a zuciyar sa ya ce duk dai d'aya. A tsorace ya Kai abincin bakin sa Yana addu'ar Allah yasa kar ya yi amai ai da gudu ya tashi daga wajen yaje ya zubar ya fara aikin kuskure baki kamar Wanda yaci d'anyen nama idanunsa sunyi jajur. Komawa ya yi ya kalle ta yace "D'auke abincin ki," d'auka ta yi tabar wajen ta Kai kitchen sannan ta dawo saboda ji ya yi taliyar kanta bata dahu ba ga uban ya ji gashi an cika maggi ga curry an zabga har k'anin maggi taliyar ke yi ya ce "Zauna," ta zauna ya ce "Ba ki iya girki ba?" Ta ce "Uhm ni ban tab'a yi ba," jinjina kai ya yi ya ce "Good ki shirya gobe Rinaz zata zo ta koya miki," zata yi magana ya ce "Karki kuskura Wallahi," shiru ta yi shi Kuma ya fice. Kamar zai yi kuka ya je yana bawa Ummi labari itama Ummi ta tausaya masa tashi ta yi da kanta ta girka masa tana tunanin ya zama dole ta samowa Maleek wacce ta iya girki dan bazata barshi ya dinga zama da yunwa ba gashi ya ce Rinaz ma da kad'an nata ya fi na 'yan aikin. Washe gari Nasreen ta je koyawa Nasreen girki sai dai ita Nasreen mugun son girma ne da ita Wai lallai sai dai Rinaz ta je kitchen ta yi girki sannan ta kaiwa Nasreen d'in taci sannan Kuma ta fad'a mata yadda ta yi ta girka da kuma abubuwan da tasa aikuwa Rinaz ta yi tsalle ta dire ta ce wallahi bazata yi ba sai dai su shiga kitchen d'in tare a yi a gabanta ta gani aikuwa nan Nasreen ta fara zage-zage. Ganin haka Rinaz ta d'auki mayafinta tabar gidan. Ko da Rinaz ta fad'awa Maleek jinjina kai ya yi ya ce "kyale ta tayima kanta idan ma ta iya kanta idan ma akasin haka kanta," tun daga ranar bai sake magana akan girkin ba haka ma Nasreen Rinaz ma tafiyar ta gidan k'awar Ummi doctor Maryam ta yi. Kwana biyu a tsakani Maleek ya shirya tare da sojojin sa suka tafi duba wata masana'anta a wani k'auye sanye yake cikin uniform d'in su na sojoji ya yi kyau sosai motoci suka shiga suka d'auki hanya. Sabeeha da Sabreen ne zaune a tsakar gida sun sa Sameeha a gaba sai kuka suke yi ganin yadda take jin jiki saboda kanta dake matuk'ar yi mata ciwo duk ta rame Abba ne ya yi Sallama da sauri Sabeeha ta tare shi ta ce "Abba an samo mai motar?" Ya ce "Eh yana waje ku yake jira ku taso mu tafi," Sabreen ta ce "A'a Abba ka zauna a gida kaima baka da lafiya Ni da Sabeeha dear mun isa," Sabeeha ta ce "Eh Abba ka zauna," haka ya zauna su Kuma suka kama Sameeha zuwa mota suka tafi gashi tunda ranar da su Kawu Bala suka dake su basu k'ara zuwa gidan ba. Tunda suka hau titi Sabeeha ke lure da wasu garada machine biyu suna binsu bata damu ba sannan bata gayawa Sabreen ba har suka je wani k'aramun asibiti dake garin dake gaba da nasu shima k'auye ne garin sai dai yafi nasu samun ci gba. Emergency room aka Kai Sameeha likita ya fara dubata yayin da su Sabeeha ke waje suna jiran fitowar likita sai gab da magriba sannan likita ya fito da sauri da takarda a hannunsa ya mik'awa Sabeeha ya ce "Ki sauri yanzu ki fita wajen asibiti ki siyo wannan maganin dan bamuda shi a nan," Sabeeha ta ce "To doctor," ya ce "Ki hanzar ta dan yanzu ake buk'atar sa da gaggawa," ta ce "Toh," ta kalli Sabreen ta ce "Sabreen dear ki zauna a nan bari naje na dawo," tana fad'ar haka ta fice da sauri ga hadari ya had'o sosai a garin tana fita harabar asibitin ta ga wad'an nan na machine d'in da suka biyo su tun daga k'auye bata damu da kallon da suke mata ba ta k'ara sauri burin ta kawai ta je ta siyo maganin ta koma. Sai dai abinda ta lura da shi shine suma binta suke yi k'ara sauri ta yi har tana had'awa da d'an gudu. Tafiya motocin MG ke yi bana wasa ba jiniya kawai ke tashi shi kuwa yana bayan wata benz Army green sai kallon Rolex watch d'in hannunsa yake yi domin ya matsu su isa gida sai dai Yana kallon agogon ya ga time d'in sallar magrib ya yi a hankali kamar mai koyon magana ya ce "Salman idan an samu masallaci gaba mu tsaya time d'in sallah ya kusa," Salman dake zaune a gaban mota ya ce "Ok," motocin gaba ya sanarwa umarnin ogan nasu aikuwa basu dad'e suna tafiya ba suka tarar da masallaci. Waigawa Salman ya yi ya ce "An samu masallaci sai dai a k'auye ne Kuma masallacin ba wani Mai kyau bane," kad'an Maleek ya murmusa har dimples d'in sa suka lotsa sannan ya ce "Salman kenan ibada ai ba sai a waje Mai kyau ba kuma suma masu yi a ciki ai mutanene kamar ni kuma nasan babu najasa a wajen domin na tabbata baza su yi sallah a wajen da yake da najasa ba dan haka muje kawai," Yana gama fad'in haka bai jira an bud'e masa k'ofa ba ya bud'e ya fice. Salman kuwa k'imar Maleek ce ta k'aru a idanunsa domin shi mutum ne mai son jama'a ba ya kyankyamun talakawa sam balle kuma wulak'anci shi kowa nasa ne. Sabeeha kuwa ganin sun biyo ta ne yasa ta d'iba da gudu suma suka bita gudu take yi sosai suma haka d'aya a cikin su ya ce "Mu tabbatar mu kama ta saboda biyan mu Rashida ta yi sannan bayan ita mu nemo ragowar," jin haka yasa Sabeeha k'ara gudu har ta fita titi gashi tunda ta fito bata ga jama'a ba ko d'aya. A can nesa ta hangi wasu Manya Manyan sababbun motoci sunyi guda goma Sha biyar da Kuma sojoji a tsaitsaye da bindigu da gudu ta d'iba ta yi wajen daidai lokacin Maleek ya gama alwala ya mik'e kenan ta wuce ta gaban sojojin kamar walk'iya ta rungume shi ta baya tsam tana b'uya a bayan sa wani irin shock Maleek ya ji a jikin sa k'ok'arin juyawa yake yi ya ga waye ya rik'e shi haka Amma ba dama saboda yadda ta k'ank'ame shi cikin daddad'ar muryar ta ta ce "please help me zasu kamani Kuma Sameeha dear na buk'atar magani yanzu," sojojin sa ne suka yo wajen sa a zafafe domin zuwa su hukunta yarinyar da ta tab'a musu ogan su da sauri ya d'aga musu hannu suka tsaya sannan ya kalli 'yan daban da suka biyo ta sun tsaya cirko cirko suna ganin kallon da yake musu suka fara ja da baya Maleek ya kalli sojojin sa ya ce "Yanzu nake buk'atar ku zo mun da su," sai lokacin Sabeeha ta sassauta rik'on da ta yi masa amma idanunta a runtse suke waigawa ya yi a hankali Yana kallon ta yadda ta rintse idanune yaso bashi dariya. Wai gawa wajen da Sojojin sa suke ya yi ya ga suk basa nan sun tafi bin umarnin sa ajiyar zuciya kad'an ya sauke tare da kallon agogon sa sannan a hankali ya juya wajen yarinyar sai dai Yana juyawa ya ga wayam ba kowa gefe da gefen sa ya kalla nan ma ya ga ba kowa a zuciyar sa ya ce "To Ina kuma ta yi?" Ita kuwa Sabeeha kunyar rungume shi da ta yi ne yasa ta zanzare bai saniba ta gudu chemist d'in taje ta siya maganin sannan ta nufi asibitin tana mamakin dama Rashida 'yar daba ce da wannan tunanin ta k'arasa asibitin. Da gudu ta k'arasa Emergency ta samu Sabreen a tsaye Sabreen d'in na ganinta ta tare ta ta ce "Sabeeha dear a Ina ki ka tsaya haka?" "Akwai abinda ya tsayar dani sister ina zuwa," bakin k'ofar d'akin ta tsaya ta k'wank'wasa likitan ya fita ya amsa ya juya ya koma ita Kuma ta koma kusa da Sabreen ta zauna tana sauke ajiyar zuciya. Kad'an Sabreen ta kalle ta ta ce "Sis wannan daddad'an k'amshin turaren fa da kike yi?" Kad'an Sabeeha ta yi dariya tare da tuna aika aikar da ta yiwa Wanda bata san waye ba. Cikin dariya ta bawa Sabreen labarin abinda ya faru sannan ta ce "Sister da gani babba ne a sojojin ma ke Kinga matsu tsaron sa da bindigogin su kuwa hmm ai Wallahi na d'auka zan sha harbi," dariya Sabreen ta yi ta ce "Dear dama haka Rashida ta koma ni Wallahi tsoro nake ji kar su dawo Kinga fa abinda Rashida ta aikata to ko me su Yallab'ai zasu yi Kuma oho," Sabeeha ta ce "Dalla can rabu da su," Nan sukai ta fira. Maleek kuwa Yana tsaye a wajen bai motsa ko ina ba. 'yan garin kuwa tsoro ne ya kama su ganin babban soja kamar Maleek tsaye a k'ofar masallacin su domin da yawa a cikin su masu karanta jarida sunsan sa addu'a suke yi Allah yasa ba laifi suka aikata ba Kuma ga motoci nan birjik a wajen. Duk cikin su an rasa mai k'arfin halin zuwa wajen da yake ballantana su yi tunanin shiga masallacin su yi Sallah. Maleek kuwa agogon hannunsa ya kalla ya ga k'arfe bakwai saura kad'an tsaki ya ja Yana tunanin anya kuwa masallacin nan ana yin sallah cikin sa gashi har yanzu sojojin sa basu dawo ba bai gama tunanin ba sai gasu sun dawo tare da 'yan daban har gaban sa suka gurfanar da su k'are musu kallo ya yi. Sannan ya juya ya ga mutane a bayan sa Kuma alamun su ya nuna a tsorace suke kallon sa ya mayar kan sojojin jin nasa wad'an da ba musulmai ba ya ce "Michel,jamsyn,Monday daniel,mesharck stay with them," sannan ya k'arasa gaban mutanen ya yi murmushi ya ce "Muje mu yi sallah lokaci yana k'urewa," sai lokacin mutanen suka saki jikin su suka shiga masallacin suna mamakin lallai wannan yaron ya basu mamaki duk muk'a munsa Amma a wannan masallacin zaiyi sallah. Liman kuwa gani yake yi idan ya ja sallah Maleek zaice bai iyaba Dan haka yak'i jan Sallar Maleek ganin time na k'urewa kawai ya je ya ja su sallar cikin had'add'iyar muryar sa da Kuma k'ira'arsa Mai matuk'ar dad'i su kansu jama'ar k'auyen kowa mamaki yake yi wannan Kuma waye haka kamar sheikh sudais. Sabreen ta tab'a Sabeeha ta ce "Wayyo sister kinji wata murya na jan sallah Wallahi tunda nake ban tab'a jin murya mai dad'in ta ba kinji a hankali yake yi ga muryar tasa mai shiga k'wak'walwa nasan a kaf garin nan baza a samu mai wanna muryar ba sai dai ko bak'o," kallon Sabreen kawai Sabeeha ke yi kamar za ta yi dariya ta ce "Allah ya shirye ki Sabreen ni tashi muje muyi alwala," fita suka yi suka yo alwala sannan suka yi sallah. Maleek kuwa bayan ya idar da sallar tare da kwararo addu'oi ya tashi ya fita har mota 'yan k'auyen suka yi masa rakiya ya shiga sannan ya kalli Salman ya ce "Me wad'an can abubuwan suka ce?" Salman ya ce "Wai biyan su aka yi su kamo yarinyar," jinjina kai Maleek ya yi ya ce "Good a kaini wajen Wanda ya turo su," ba b'ata lokaci aka sanarwa da motocin gaba Wanda 'yan daban ke cikin d'aya daga ciki. Sai da suka yi tafiya Mai nisa sannan suka isa inda gidan su Rashida yake ko fita daga motar Maleek bai yi ba ya ce "Salman jeka kayi masa warning idan yak'i ku nuna masa kuskuren sa," abinda Maleek bai saniba ai ba Wanda ya isa ya ga wannan zugar sojojin da bindigu bai tsure ba. Fita Salman ya yi d'aya daga cikin Wanda Rashida ta aika d'aya ya kirata a waya ba b'ata lokaci ta fita sai dai ganinsu tare da sojoji sai da ta fara fitsari a wando Maleek kuwa mamaki yake yi mace ce ma wai da wannan karf'in halin shi kansa Salman ya yi mamaki amma ya dake ya koma yanayin sa na jaruma sojoji ya buga mata warning wanda Rashida har kuka take tana basu hak'uri sannan Salman ya tafi ya bata waje ya koma mota suka kama hanya bayan sun sauke mata 'yan daban ta. Gudu suke yi sosai a hanya yayinda Maleek ya lumshe idanunsa ya jingina da kujera ga mamakin sa tunda ya lumshe ido hoton fuskar ta kawai yake hangowa saurin bud'e idanunsa ya yi Yana mamakin kansa basarwa ya yi ya sake rufe idanunsa sai dai nan ma ya sake hango fuskar ta tsaki ya ja sannan ya bud'e idanunsa ya d'auki wayar sa dake ringing. Ya d'aga tare da yin sallama daga can Ummi ta amsa ta ce "Son ya hanya?" Ya ce "lafiya lau Ummina," ta ce "Masha Allah dama Kiran ka nayi naji lafiyar ka," cikin son mahaifiyar tasa ya ce "Ina lafiya Ummina mun kusa sauka insha Allah," ta ce "Tom Allah ya tsare hanya," ya amsa da "Ameen," daga haka ya katse kiran sai da dare sosai sannan suka Kai gida. Rashida kuwa ta yi da ta sani yakai sau million gani take yi kamar zasu iya dawowa. Su Sabeeha kuwa sai da suka kwana bakwai a asibiti sannan aka yi discharging d'in su. Jikin Sameeha ya yi sauk'i sosai domin dama rashin samun kulawar da bata dace bane yasa ta ciwon kan tafiya suke yi su uku suna fira abinsu suna dariya inda Sabreen ke ba Sameeha labarin abinda Rashida ta so aikawata Sameeha ta ce "Tabdijan lallai ma Rashida ni tsorona kar su Kuma dawowa," daga bayan su suka ji wasu samari na cewa "Wallahi yau sati d'aya kenan da MG Abdul-maleek ya zo garin nan Kuma shi ya ja sallah a wancan masallacin," d'aya ya ce "Anya kuwa da gaske MG Abdul ne domin abun da mamaki Mai matsayi kamar sa mai ji da kyau ilimi kud'i da Kuma muk'ami ya rasa inda zai tsaya ya yi sallah sai a garin nan domin ko a saudia yaso ya yi sallah zai je ya yi ya dawo," waccan ya Kuma cewa "Abokina kenan MG ba kamar sauran jama'a bane Wanda na tabbata ko D.P.O na garin nan ba zai yi sallah a can masallacin ba amma MG ba bu ruwan sa kowa nasa ne ballantana ya nuna k'yama kai fak'at ma bari na nuna maka hotan sa," nan ya nunawa abokin sa hoton Maleek. "Kai gaskiya ina yin sojan nan sosai ko dan taimakon sa ga talakawa," Sabreen ta kalli Sabeeha ta ce "Wallahi Sabeeha dear shine Wanda ki ka bani labari bari naje na gansa," saurin rik'o ta Sabeeha ta yi ta ce "Ke meye haka so ki ke su rainaki zo mu tafi," ta ja hannun Sabreen suka yi gaba Sabreen ta ce "Tunda kin hanani na gansa bani labari ya kamannin sa yake?" Sabeeha ta ce "Wow," ta yi gaba tana kallon wata k'aramar mage da ta d'auki hankalin ta fara ce magen sai bak'i-bak'i kad'an a jikin ta nufar magen ta yi tana cewa "Wow pretty," d'aukar magen ta yi tana shafa jikin ta. Da kallo su Sameeha suka bita da shi Dan duk a tunanin su da Sabeeha ta ce wow labarin kyawun MG zata fara zayyana musu ashe mage take cewa wow d'in. Wani mata shine ya k'arasa wajen Sabeeha ya ce "Mage tace," mik'a masa Sabeeha ta yi tana jin dama ya bar mata ya ce "Dama zan bayar da ita ne ko kina so?" Da sauri ta ce "Eh Wallahi ina so ta shiga raina," ya ce "Tom na baki amma ki kula da ita sosai," ta ce "Tom zan kula da ita nagode," tana fad'ar haka ta waiga wajen su Sabreen ta ce "Ku zo mu tafi mana," k'arasawa wajen ta suka yi suna kallon magen su ma ta yi musu kyau. Sabreen ta ce "Ban manta ba fa dear ya sojan yake?" Tsaki Sabeeha ta ja ta ce "Ni fa bansani ba abinda nasani kawai dogo ne sannan yana dadda'an k'amshi kamar yadda ki ka ji k'amshin ranar domin ni banga fuskar sa ba ko kad'an kawai dai nasan babban mutum ne saboda yawan sojojin dake tsaron sa wajen mota ashirin sai dai ni ana bani mamaki ki kalla yadda wad'an can samarin ke firar sa Kai shiyasa fa duk inda d'an k'auye yake sai ya nuna k'auyen ci nasan yanzu ya ma manta ya zo nan amma kalli tsahon sati d'aya kenan Amma ba a dena firar sa ba," tana fad'ar haka ta yi gaba abinta abinda Sabeeha bata saniba shine ko a birni ma rububin ganinsa ake yi. B'angaren su Yallab'ai Kamis kuwa tunda aka nemi su Sabeeha aka rasa ya kwanta rashin lafiya saboda shi dagaske sonta yake yi har sai da ya kwanta a asibiti gashi baisan garin su ba Rashida ce kawai tasani Kuma itama bata gidan gashi Farida tak'i fad'a masa garin su Rashida bare su je su tambaye ta haka yai ta jinya har ya ji sauk'i ya warware amma son Sabeeha na nan a ransa. Maleek kuwa tun daga ranar kullum tuna ta yake yi ko bacci yake yi mafarkin ta yake yi gaba d'aya ya canja sai ya zauna kawai Yana tunanin ta shi kansa har mamakin kansa yake yi domin bai tab'a jin hakan akan wata mace ba sai ita. Yau ma zaune yake a falon sa ya zurfafa a tunanin ta kamar kullum ya tashi kawai ya fita zuwa part d'in Ummi. Yana shiga ya samu waje ya zauna yana danna wayar sa Ummi ce ta sauko daga stairs gefen sa ta zauna ta shafa kansa ta ce "Son," ya ce "Na'am Sannu da fitowa Ummi," ta ce "Yawwa ni kuwa kwana biyu mai yake damunka ne naga kamar kullum cikin tunani kake ko Kai da matarka ne?" Girgiza kai ya yi ya ce "A'a Ummi ba da ita bane," sannan ya bawa Ummi labarin komai. Murmushi ta yi ta ce "Son kenan you're fall in love with her right?" Shiru ya yi yana tunanin jin soyayya kenan to indai kuwa haka ne to kuwa ya fad'a son ta Ummi ce ta katse shi da cewa "Har naji ina sonta me sunanta?" Kallar tausayi ya yi ya ce "I don't know Ummi Anya kuwa ba aljana bace Ina juyawa fa na ga bata nan," dariya Ummi ta yi saboda wani lokacin idan Maleek ya yi wani abun kamar yaro ta ce "Son kenan mutum ce mana saboda kasan wad'an da suka biyo ta baza su biyo aljana ba ko suma aljanun ne?" Dariya ya yi ya ce "A'a mutane ne fa," "Nima dai abinda nagani kenan amma son yanzu idan kasan gidan su Mai zai faru?" Shiru ya yi alamun tunani sannan ya ce "Uhmm kawai Auren ta zanyi," kallon sa Ummi ta yi tana jin farin cikin hakan domin ko ba komai tasan idan ya k'ara aure da Kuma wacce yake so hankalin sa zai fi kwanciya sai dai tana tsoron abinda zai je ya dawo. Falon ne ya d'auka Rinaz is open the door da gudu Rinaz ta shiga falon ta yiwa Ummi side hug ta ce "Ummina na dawo Kuma fa tare muke da Mama," kafin Ummi ta yi magana Doctor Maryam ta shiga falon tasha gayu cikin doguwar rigar shadda maroon ta yi kyau sosai hannun ta rik'e da hand bag da key d'in mota sai k'amshi take yi. Tashi Ummi ta yi tana murnar ganinta sai da suka d'an rungumi juna sannan suka k'arasa falon cikin girmamawa Maleek ya gaida doctor Maryam ta amsa cikin fara'a sau biyu kenan suka tab'a ganin juna amma doctor Maryam ta ji yaron k'awar ta ta ya shiga ranta saboda biyayyar sa da Kuma girmama manya. Suna gaisawa ya mik'e ya ce "Ummi bari naje," Ummi ta ce "To ka fa binciko mun inda yarinyata take," ya yi murmushin da ya bayyana dimples d'insa ya ce "Toh Ummi," ya fice Doctor Maryam ta ce "Wacce yarinya Kuma?" Ummi ta ce "Wata yarinya ya had'u da ita yake so," murmushi Doctor Maryam ta yi ta ce "Masha Allah yarinya ta yi dacen miji kam," Rinaz kuwa murna take yi domin idan abun ya tabbata ba k'aramun budiri zata had'a ba. Maleek kuwa yana fita ya ga Nasreen cikin motar ta ta figo ta da gudu kallo d'aya ya yiwa motar ya d'auke Kai yana yiwa Salman magana. Gurin ta k'arasa ta ce "Ya Maleek," waigawa ya yi ya kalle ta tasha kwalliya cikin wata doguwar riga Mai k'aramun mayafi ta wani d'aura shi a ka sai kace ba matar aure ba yatsina fuska kawai ya yi ta ce "Dama bikin friend d'ita ce ko zamu je tare?" Kallon Mamaki ya yi mata domin bai ma san zata fitan ba ya ce "No jeki abinki," ta juya ta tafi tana wani karairaya shi kuwa ko kula da abinda take ma bai yi ba dan hankalin sa na gun Salman Yana fad'in "Ina so ku bincika mun garin ina so nasan komai a kanta," Salman ya ce "angama ranka ya dad'e," shi Kuma ya wuce part d'insa Salman kuwa mota ya shiga tare da wasu sojoji suka bar gidan. [10/25, 7:35 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️ RUBUTAWA DAGA HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ) SADAUKARWA GA MY DAUGHTER SABEEHA BILKISU Z.YA'U (🅱️K) AISHA MAGAJI DABO (AMA) Page 5 Sabeeha kuwa mota suka samu suka tafi gida suna sauka a bakin titi suka tafi a k'afa har zuwa k'auyen su hango mota suka yi a k'ofar gidan su Sabeeha ta da fa goshi ta ce "Na shiga uku waccan mayen ya zo kenan?" Sameeha ta ce "Anya ba wani abu Kawu ke k'ullawa ba?" Zare ido Sabreen ta yi ta ce "Kai kunga fa mai gari can har ma da d'ansa waccan Mai k'aton Kai lallai akwai abinda kawu ke k'ullawa," tunawa da wani Abu da Sabeeha ta yi ne yasa ta ja da baya su ka ce "Meya faru?" Sabeeha ta ce "Kun manta da maganar kawu ne da ya ce nan da sati d'aya zai yi mana aure?" Ai take dukan su suka tsure Sabreen ta ce "Anya kuwa ma je gida kuwa dear Dan Wallahi aka aura mun Dauda mutuwa zanyi," Sameeha ta dafe k'irji ta ce "Wallahi da na auri faruk gara na mutu banyi aure ba," Sabeeha ta ce "Ku kwantar da hankalin ku ba Wanda zamu aura cikin su ku zo ku ji wata magana," rad'a tayi musu aikuwa suka shek'e da dariya suka nufi gidan kamar basu da wata damuwa. Da sallama suka shiga gidan turus suka tsaya ganin akwatuna da cofee guda shida sai bak'ake guda biyu. K'arfin hali Sabeeha ta yi ta k'arasa tana kallon Sadam dake zaune kan tabarma sai wani hura hanci yake yi yana wani karkad'e jiki da hanky shi lallai ga d'an gayu gashi bak'i k'irin da shi da jajayen idanu gefen sa kuma Kawu ne shi da D'ansa faruk wanda Sam shi ba halinsa d'aya da Kawu ba kawai dai Sameeha bata son shi da aure ne amma shi ba ruwan sa da takura musu. Daga d'aya gefen Kuma Mai gari ne tare da Dauda d'ansa daga can Kuma Abba ne ya yi jugum kamar Wanda aka yiwa mutuwa yana kallon ikon Allah Wai a matsayin sa na mahaifi sai dai kawai ya ga an kawo kayan lefen 'ya'yan sa ba tare da ko izinin zance ba Wanda ya zo ya nema wajensa. Sabeeha na k'arasawa ta d'urk'usa ta gaishe su tana washe bakin da iyakar sa bakinta amsawa suka yi banda Kawu Bala da ya aika mata harara bata damu ba ta mik'e sannan ta kalli su Sabreen da suka yi mutuwar tsaye ta kanne musu ido d'aya take suma suka baje hak'ora suka k'arasa suka kwashi gaisuwa. Kawu ya ce "Naji dad'i da ku ka zo domin ayi komai a gaban ku wad'an nan akwatunan da ku ka gani naku ne," ya nuna guda shida ya ce "wannan sune naki ki godewa Allah ki samu mai dukiya," ya fad'a yana nuna Sabeeha sannan ya ce "ku Kuma ko wacce d'ai d'ai," Mai makon ya ga sun had'e rai ko su tubure kawai sai ya ga suna ta washe baki Sabeeha ta ce "Wayyo murna yau nice da kayan aure har haka amma naji dad'i yanzu yaushe ne auren?" Shi kansa Abba mamakin su yake yi Sabreen ta ce "Nima murna nake yi," Kawu Bala kuwa had'e rai ya yi domin ba haka yaso ba domin shi burinsa ya k'untata musu amma sai ya ga sai rawar Kai suke yi ya ce "Jibi ne d'aurin auren," Sabeeha ta ce "Dan Allah Kawu a k'ara mana ko kwana biyu ne saboda mu shirya," har Kawu zai yi magana Sadam ya ce "A k'ara musu," Kawu ya ce "Shikenan nan da kwana hud'u za a d'aura auren," ana haka Lantana da Zainabu suka shiga gidan kayan suka fara bud'ewa suna kallo sai da suka gama sannan suka kalli su Sabeeha suka yi dariya suka ce "Amaren kwana hud'u," ga mamakin su suka ji 'yan uku sunce "Na'am," had'e rai Lantana ta yi bata Kuma magana ba. Kud'i Sadam ya zaro sun Kai dubu goma ya ajiyewa Sabeeha a gaba ya ce "Ga wannan kiyi amfani dasu a shagalin biki gobe zan dawo," Sabeeha ta yi far da ido ta ce "To sai ka dawo my love," ya fita yana dashare baki. Haka ma Dauda ya ajiyewa Sabreen dubu biyar tai ta godiya har da raka shi zaure sannan ta dawo Sameeha ma Faruk ya bata tana ta fara'a wanda faruk bai tab'a ganin ta yi ba. Ta tafi raka shi sai da ta raka shi waje har zata koma cikin gida ya ce "Sameeha," tsayawa ta yi ya k'arasa har inda take ya ce "ki yi hak'uri nasan bakya sona nayi duk yadda zanyi Baba ya janye maganar auren nan amma yak'i," ta ce "Ya faruk kenan karka damu da kanmu zamu d'au mataki," jinjina kai ya yi ya ce "Nasan kuna hak'uri da Baba amma ku cigaba da hak'uri wata rana sai labari amma yanzu me ku ka yanke yi?" Kasancewar sun yadda da shi Sameeha ta fad'a masa ya ce "Hakan yayi yanzu bari na baku number ta duk sanda ku ke buk'atar taimakona ku samu waya ku kirani domin ni gobe zan koma makaranta," number d'insa ya bata sannan ya tafi. Dama shi ba mazaunin k'auyen bane karatu yake yi a birni. Komawa cikin gidan Sameeha ta yi tana shiga ta samu su Kawu sun mik'e suka fice suna fita Zainabu ta sa kuka ta ce "Baba sai da nace karka bari Waccan ta Auri Sadam ni zai aura amma kak'i yadda wallahi Kuma ni shi nake so," Kawu Bala ya ce "Haba 'yar lelena ki kwantar da hankalin ki zaki aure shi domin na riga na gama shirya hakan so nake yi sai anyi auren sannan zan k'ulla mata tugun da sai ya sake ta daga nan kuma saina ba shi auren ki Kuma Kinga munci riba biyu saboda ko ba komai kin auri Mai kud'i ita Kuma mun mayar da ita bazawara," Lantana ta ce "Gaskiya Malam kana da basira Wallahi aida na d'auka haka zaka zuba ido ta Auri mai kud'i 'yar mu kuwa ko oho," Kawu ya ce "Kema kinsan hakan bazai yuwu ba kawai yanzu lallama shi nake yi saboda yanzu naga ya gama makancewa akan waccan d'in," Haka suka yi ta kitsa yadda zasu mayar da Sabeeha bazawara. Su kuwa bayan su Kawu sun tafi su Sabeeha suka bubbud'e kayan suka gani suna dariyar da su kad'ai suka san ma'anar ta Abba kuwa kallon su kawai yake yi ba tare da ya ce musu komai ba suma Kuma basu ce komai ba suka had'a kud'aden da aka basu suka had'a da kud'in salary d'insu da aka basu Wanda ko rabi basu tab'a ba ga kuma dubu hamsin d'in da Habibu abokin kamis ya bata. Shigar da akwatunan d'aki suka yi sannan suka d'ora girki suka ci suka k'oshi. Da daddare suka samu Abban su a d'aki ya yi jugum zama suka yi a gaban sa Abba ya ce "Aminaina yadda ku ka nuna farin cikin kawu lefen ku hakan ya nuna kuna son auren ko?" Sabeeha ta ce "A'a Abba dama mun yanke wata shawara ne," ya ce "Ta me?" Sabreen ta ce "Abba gaskiya ba ma son auren nan shiyasa muka yanke shawarar mubar garin har sai komai ya nitsa," Sabeeha ta ce "Eh Abba dan wallahi na tsani Sadam," Sabreen ta ce "Ai gara ke Sabeeha Wallahi," hararar wasa Sabeeha ta yi mata ta ce "Ai Wallahi da na auri Sadam gara na auri Kamis," Sameeha ta ce "Ai ni kuwa bani da case domin ya Faruk ya hak'ura," Abba ya ce "Ni yanzu damuwata ina zaku je?" Sabeeha ta ce "Abba ka kwantar da hankalin ka zamu kula da kanmu," ya ce "Na yadda daku sai dai Dan Allah karku wuce Kaduna saboda tafi kowacce state kusa damu sannan ku rik'e mutuncin ku kula da kanku," Suka ce "To Abba insha Allah," "To yanzu yaushe zaku tafi?" Sameeha ta ce "Zuwa jibi Abba," ya ce "Allah ya kaimu Allah ya yi muku albarka," suka amsa da "Ameen Abba," Washe gari da yamma suka shirya duka su Uku suka fita Kai tsaye gidan wata Mai abinci a unguwar su bayan sun gaisa suka bata dubu ashirin suka ce ta ajiye a wajen ta kullum ta dinga aikawa da Abban su abinci tunda da safe tana yi tayi da rana da daddare ma tayi. Rok'on ta suka yi akan karta fad'awa Kawu matar ta ce "Kar ku damu zan b'oye muku sirrin ku ko dan mahaifiyar ku saboda mutuniyar kirki ce," godiya suka yi mata sannan suka tafi. Suna fita kuwa tasha suka je suka samu mai wata mota golf suka yi magana akan gobe da asubar fari zai je ya d'auke su ya kaisu har kaduna domin basa so wani ya ga sanda zasu bar garin balle a kaiwa Kawu Bala munafunci. Sai yamma lik'is suka koma gida girki suka yi sannan suka shiga d'akin su suka harhad'a kayansu tass suka ajiye. Tun dare suka yi wanka suka ajiye kayan da zasu sa ranar raba dare suka yi suna fira da Abban su sannan suka sanar da shi duk abinda suka yi da suka fita yai ta sa musu albarka sannan suka tafi d'akin su suka kwanta. Da asuba kuwa suna yin sallah suka zira dogayen rigunan su blue iri d'aya sannan suka fita waje suka samu mai motar zuwan sa kenan trolleys d'in su suka d'auka suka fita da su akasa a mota sannan suka shiga gidan d'akin Abban su suka nufa yana zaune akan sallaya yana addu'a gefen sa suka zauna suka shafa tare sannan cikin tausayin yaran nasa ya ce "Kun gama shiryawa mai motar ya zo?" Suka ce "Eh Abba," Nan ya fara yi musu Nasiha kuka kawai suke yi domin gani suke yi idan suka tafi bazasu dawo ba shima Abban hawaye yake yi ya ce "Ku tashi kuje Allah ya yi muku albarka ku yi ta addu'a nima zan taya ku Allah ya karemun ku ya d'aukaka ku," suna kuka suka ce "Ameen Abba," sannan suka rungume shi suna kuka har wajen ya raka su sannan ya ce "Ku tafi kar wani ya ganku Allah ya kiyaye," suka amsa da "Ameen," sannan Suka shiga mota Sabeeha na gaba da magen ta a hannunta Sameeha da Sabreen na bayan mota. Haka suka tafi suna d'agawa Abba hannu kowaccen su na sharar hawaye. Lokacin da suka isa Kaduna karfe Goma na safe tunda driver ya ajiye su suka rasa inda zasu yi ga yunwa na damunsu magen Sabeeha ma kukan yunwa take yi kifi ta siya mata ta bata taci ta k'oshi Sameeha ta ce "Sabeeha dear nifa yunwa nake ji," Sabreen ta ce "Nima haka wallahi," tashi Sabeeha ta yi ta tari Mai keke napep ya ce "Ina za a kaiku?" Sabeeha ta ce "Wallahi yayana mu ba 'yan gari bane dan Allah so muke ka kaimu wajen cin abinci mafi kusa," ya ce "To ba damuwa ku shigo," trolleys d'insu suka d'auka suka shiga ya jasu suna tafe suna fira kasancewar Mai napep d'in akwai surutu sai mamakin kamar su yake yi su Kuma suna amsa masa sama-sama saboda yunwar dake damun su. Ya ce "Yawwa 'yan uku ga wani wajen cin abinci gaban mu kad'an sai dai na hajiyoyi ne domin wajen akwai tsadar abinci sai dai sun iya girki," Sabeeha ta ce "Bakomai mu tsaya a nan d'in," suna k'arasawa ya tsaya suka biya shi kud'in sa suka shige wajen janye da trolleys d'in su Sameeha na rik'e da magen Sabeeha wacce suke kira da pretty. Motoci ne da yawa a harabar wajen suna shiga kuwa kallo ya dawo kansu saboda ganinsu janye da trolleys su kuwa basu damu da kallon da ake yi musu ba saboda damuwar su bata wuce cikin su ya d'auka ba guri suka samu can nesa da mutane suka zauna saboda ba sabawa da cin abinci suka yi cikin mutane ba. Waiter ce ta je wajen ta ce "Me za a kawo muku?" Kallon Sameeha Sabeeha ta yi ta ce "Sameeha dear me za a kawo miki?" Sameeha ta ce "Jallop rice please with mirinda," Sabreen Kuma ta ce "Nima jallop rice amma da hollandia Mai sanyi," Sabeeha ta ce "Ni kuma fried rice with coslow sai maltina," juyawa waiter d'in ta yi ta tafi ba dad'ewa ta dawo ita da 'yar uwar ta d'ayar ta ce "Wow identical triple," murmushi kawai Sabeeha ta yi ta ce "Sunana Aysha," Sabreen ta ce "Nice name I'm Sabreen and here is my sister's Sabeeha and Sameeha," Aysha ta ce "Nice names nice to meet you," cikin gajiya da surutun ta Sabeeha ta ce "Nice to meet you too," tana fad'ar haka suka fara cin abincin. Aysha ganin sun fara cin abinci ta tafi tana waigen su hakan ne ya janyo hankalin yawancin mutanen kansu sai kallon su ake yi saboda ganin su su uku iri d'aya. Su kuwa sai cin abincin su suke yi Sabeeha ta ce "Kusan wani abu?" Sabreen ta ce "Meya faru?" Dariya Sabeeha ta yi ta ce "Da alama wata zata daku a wajen nan," Sameeha ta ce "Wato Sabeeha dear kin fara ko ni na rasa irin ki yanzu sai ki fad'i magana kuma sai ta tabbata wai to meyasa hakan?" Murmushi Sabeeha ta yi ta ce "Bansani ba nima amma Ni kaina Ina mamakin kaina haka kawai zanji wai abu kaza zai faru kuma ya faru wani bana ganin alamun abun zai faru amma wani lokacin kuma ina ganin alamun faruwar hakan kamar dai yanzu ku kalli waccan guy d'in Mai siffar 'yan daba magana yake yiwa waccan siririn abokin nasa tare da nuna masa waccan budurwar mai shan ice cream kuma alamu sun nuna magana yake cikin fushi har k'wafa yake yi," ta fad'a tana nunawa su Sabreen mutum da Kuma yarinyar. Tunani suke yi anya Sabeeha bata da aljanu kuwa domin tunda suka taso take hakan sai dai ta dad'e hakan bai faru ba sai yau ko dan basa shiga mutanene oho basu gama tunani ba suka ga guy d'in ya shiga wajen direct ya yi wajen budurwar itama tana ganinsa ta mik'e tana zare ido Yana zuwa bai jira wata-wata ba ya fara zabgawa budurwar mari ita kuma tana zaginsa har mutane sun fara taruwa. Mik'ewa Sabreen ta yi ta ce "Lallai ma waccan guy d'in d'an iska ne bari naje tsabar baisan darajar mata ba shine zai wani kama Marin ta?" Rik'e ta Sabeeha ta yi ta ce "Karki je babu ruwan ki domin ita ce bata da gaskiya," a tare su Sabreen suka had'a baki wajen cewa "Ta ya kika sani?" Dariya Sabeeha ta yi ta ce "Da kan ku ya kamata ku gane hakan ku duba lokacin da guy d'in ya shigo nan a firgice ta mik'e tsaye Kinga da alamau akwai abinda ya had'asu sannan ki duba mulki irin na mace da shine ya yi mata laifi baza ku ga ta tsure haka ba," aikuwa nan suka ji yo guy d'in na cewa "Ke dan kin raina mun hankali saboda bana kula ki shine zaki je har gurin mom d'ina kice kina d'auke da cikina to Wallahi kotu ce zata raba mu," duk mutanen dake wajen domin raba fad'an suka tafi jin maganar ta fi k'arfin su. Sabreen ma zama ta yi tana cewa "Ahhab ai gara da yaci uban shegiya," Sabeeha kuwa waiter ta yafito da hannu zuwa waiter d'in ta yi Sabeeha ta ce "How much your money?" Ta ce "Six thousands eight hundred," bud'e jaka Sabeeha ta yi ta fito da kud'in ta biya. Aysha ce ta k'arasa wajen ta ce "Sai tafiya?" Sabeeha ta ce "Eh," "A wanne unguwa ku ke ku bani address d'in ku wataran nazo," Sabeeha ta ce "Mu ba 'yan gari bane Kuma bamu san kowa nan ba yanzu ma zamu je mu nemi masauki ne," jinjina kai Aysha ta yi ta ce "Zan iya taimakon ku?" Sameeha ta ce "Haba Aysha waye yak'i taimako," Aysha ta ce "Kun ga rayuwar garin nan Yana da tsada mai zai hana ku zauna a nan ku dinga aiki," Sabreen ta yi caraf ta ce "Eh Kuma Sabeeha dear ta iya girki sosai," ta fad'a tana nuna Sabeeha. Aysha ta ce "Ok ba damuwa bari naje wajen madam naji," tana fad'ar haka ta juya ta shige wani d'aki da alama Office ne. Tana shiga ta samu ogar tasu a zaune kan kujera da glass fari manne a fuskar ta durk'usawa Aysha ta yi ta ce "Madam dama wasu bak'i ne a garin nan suka zo nan cin abinci sunce mun basu da masauki shine nayi musu tayin aikin mu tunda naji kina neman ma'aikata shine nazo na sanar Miki sannan d'aya a cikin su ta iya girki sosai," jinjina kai madam ta yi ta ce "Zo mun dasu," fita Aysha ta yi suka koma tare. Kallon su Madam ta yi bayan sun gaisa ta ce "Amma 'yan uku ne ko?" Suka amsa mata da "Eh," ta ce "Masha Allah meye sunan ku?" Nan suka fad'a mata sunayen su ta jinjina kai sannan ta ce"Zan d'auke ku aiki sai dai naji ance akwai wacce ta iya girki sosai a cikin ku Kuma akwai wata Hajiya da ta bani cigiyar wacce ta iya girki sosai saboda yaron ta da duk Mai aikin da aka tura masa idan ya ci girkin ta sai yace bata iya ba bansani ba idan na turaki zai ji dad'in girkin ki ba domin idan na turaki mutum goma kenan dana tura musu ya ce abincin su ba dad'i wad'an da anan har santin girkin su ake yi Amma yanzu zaki yi anan muci muji kafin ki je can su Kuma 'yan uwanki zasu zauna anan tare da mu," a tare su Sabeeha suka kalli juna domin tunda suka tashi ko ina tare suke zuwa Sabeeha ta ce "To nagode amma gaskiya madam kiyi hak'uri bazan iya rabuwa da su Sameeha ba kawai zan zauna anan tare da su," Madam ta ce "No karki damu zan sanar da Hajiya idan ta yadda sai ku tafi dukan ku amma yanzu je ki Aysha ta raka ki kitchen white rice with fish soup nake so ki girka," gyad'a kai Sabeeha ta yi sannan ta tashi tabi bayan Aysha. Kitchen suka tafi Aysha na tsaye na taya ta fira ita kuma tana girkin ta cikin k'arewa har ta gama sannan ta zuba a plate ta zuba miyar a k'aramun bowl sannan ta zuba salat d'in da tayiwa k'ananan yanka a gefen shinkafar yasha kayan had'i ta ajiye cokali a gefe ta d'auka suka tafi. Fira ta samu su Sabreen nayi da Madam suna dariya saman table d'in Sabeeha ta ajiye abincin ta ce "Gashi na gama," Madam ta yi dariya ta ce "Iya saurin gamawar da ki kayi na yaba," murmushi Sabeeha ta yi. Jan plate d'in gaban ta madam ta yi tai Bismillah ta kai one spoon bakin ta lumshe ido ta yi tana jinjina kai har wani kad'a kai take yi ta ce "Wow gaskiya kin iya girki ba dan kar nayi k'arya ba sai nace ban tab'a cin abinci Mai dad'in naki ba," gaba d'aya mutanen wajen suka sa dariya. Aysha ta ce "Madam ba d'and'ane ne?" Madam ta ce "Kai Anya kuwa ko da yake zo kici one spoon kawai," k'arasawa Aysha ta yi ta ci cokali d'aya ta ce "Wallahi madam ban tab'a cin abinci Mai dad'in wannan ba gaskiya Sabeeha zanzo ki koyamin," dariya su Sabeeha ke yi ga mamakin su kuwa daga lauma d'ayan nan Madam bata k'ara bari Aysha ta ci ba. D'aukar wayar ta ta yi ta kira Ummi tasa wayar a handsfree tana d'agawa bayan sun gaisa Madam ta ce "Yawwa Hajiya ansamu mai girkin sannan Wallahi ta iya girki sosai," daga can Ummi ta ce "Masha Allah Fulani yadda ki ke fad'an nan ta iya girki Allah yasa son ya so girkin ta," madam ta ce "Gaskiya Hajiya da wuya girkin ta yak'i burge shi saboda ta iya sosai na yaba sosai da girkin ta sai dai ba ita kad'ai bace 'yan uku ne Kuma tace idan ba tare da 'yan uwan ta zasu zo ba bazata ba da alama ba k'aramar shak'uwa ce tsakanin su ba," Ummi ta yi dariya ta ce "Banda abin Fulani ina ke Ina raba 'yan uku Wanda suka taso tare abinda za 'ayi gobe zan aiko driver ya d'auko su kawai," Fulani ta ce "To hajiya," daga haka suka yi Sallama. [10/25, 7:37 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️ RUBUTAWA DAGA HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ) SADAUKARWA GA MY DAUGHTER SABEEHA BILKISU Z.YA'U (🅱️K) AISHA MAGAJI DABO (AMA) Page 6 Bayan Fulani ta ajiye waya ta kalli su Sabeeha ta ce "kun dai ji yadda muka yi da Hajiya da kunnen ku ni dai abinda nake so da ku shine ku tsaya kuyi abinda ya Kai ku babu ruwan ku da harkar da ba taku ba duk abinda aka saku kuyi sannan ku dage da tsafta duk da dama da ganin ku ba sai an fad'a ba kuna da tsafta sai dai ina so ku ninka wacce ku ke yi yanzu idan kunje can saboda Hajiya macece mai son gayu tana tsafta sosai sannan tana son duk wani mai tsafta bata da matsala da kowa na tabbata zata kula da ku sosai kamar yadda zata kula da 'ya'yan cikin ta ke dai Sabeeha abinda nake so dake shine ki dage sosai wajen yin aikin ki yadda ta kamata saboda ta d'auke ki ne saboda yaron ta shine babban d'anta Kuma babban soja ne kamar yadda na fad'a muku na kai 'yan aiki gidan da dama amma sai yace basu iya girki ba hatta k'anwar sa bai cin girkin ta sai dai idan mahaifiyar sa ce ta girka masa har mata ce da shi amma bai cin girkin ta domin Sam ita bama ta iya abincin ba kasancewar ta 'yar hutu," kallon juna su Sabeeha suka yi Fulani ta ce "kuna mamakin ta ya nasan matar sa bata iya girki ba ko?" Sabeeha ta ce "A'a saboda da ta iya ai baza a nemi Mai yi masa ba," jinjina kai Fulani ta yi ta ce "Good girl kin fad'i gaskiya sannan abinda nake so daku shine gidan wani irin gida ne dole sai kunyi hak'uri sannan duk masu aikin gidan suna da uniform Kuma nasan idan ku ka je za a baku zancen kud'in albashi Kuma baku da matsalar sa saboda suna da kud'i sosai haka kawai ma kyauta suke yi balle anyi musu aiki dan haka ku kula sosai," suka ce "Insha Allahu," suna tunanin lallai wannan gidan daga ji sun fi Yallab'ai Kamis kud'i. Fulani ta ce "Aysha ki kaisu su d'akin ku su yi wanka su huta kafin gobe dan nasan da safe driver zai zo d'aukar su," Aysha ta ce "To," sannan suka fice. Har d'akin ta kaisu suka ajiye kayan su sannan suka yi wanka suka yi sallah bayan sun idar ne suka yi shiru suna tunanin gidan da zasu aiki Sabreen ta ce "Wallahi daga jin gidan bana wasa bane Sabeeha dear Dan Allah ki nutsu gobe ki yi masa girki Mai matuk'ar dad'i wanda baki tab'a mai dad'in sa ba," hararar wasa Sabeeha ta yiwa Sabreen ta ce "Allah ya shirye ki," Sameeha ta ce "Ni dai fatana Allah yasa 'yan gidan basu da wulak'anci saboda bana son wannan karon mu sake guduwa," ita dai Sabeeha bata ce komai ba ta yi shiru tana sauraron su haka sukai ta fira abinsu sai tsakar dare suka yi bacci Aysha na jin kamar ta bisu goben. Washe gari bayan sunyi Sallah basu koma bacci ba suka yi aika ce aikace sai wajen k'arfe goma sannan Madam ta je wajen ta shiga d'akin da suke ta ce "Ya kamata ku shirya yanzu," suka amsa da "toh," wanka sukayi sannan suka fara tunanin kayan da zasu sa saboda ce musu da akayi Hajiya na son mai tsafta. Sameeha ta d'ago wata amfar su iri d'aya ta ce "Kun ga musa wannan mana," kallon kayan suka yi Sabreen ta ce "A'a gaskiya gara musa wad'an nan rigunan,"ta fad'a tana nuna wasu dark pink d'in dogayen rigunan su. Sameeha ta ce "Sabeeha dear ke wanne ne zab'in ki?" Girgiza kai Sabeeha ta yi ta ce "Karku damu duk Wanda ya yi muku shi zamu sa," Sameeha ta ce "To mu sa rigunan kawai," dogunayen rigun nan suka sa har turare suka fesa duk da su basa kwalliya amma sunyi kyau sosai kamar ka sace su ka gudu sai shek'i suke yi. D'akin Fulani ta shiga ta ce "To driver yazo ku fito," trolleys d'in su suka d'auka suka nufi waje Aysha ta karb'i trolley d'in Sabeeha ita Kuma ta d'auki pretty d'in ta suka fita wajen. Tsayawa kallon motar da tazo d'aukar su suka yi saboda motar ta yi kyau bak'ar BMW ce sannan tinted windows ne da ita sai shek'i take yi driver cikin uniform d'insu na drivers fari. Trolleys d'insu yasa a boot gaisawa suka yi da Fulani su Sabeeha ma suka gaishe shi ya ce "Lafiya lau 'yan uku," Dan ko ba a fad'a ba kana ganinsu ka ga 'yan uku. Fulani ta ce "To Allah ya kiyaye baku da waya ko?" Suka ce "Eh," ta ce "Karku damu zamu dinga gaisawa a wayar Hajiya Allah ya kiyaye," gaban mota Sabeeha ta shiga su Sameeha a baya driver ya ja mota suna d'agawa su Aysha da Fulani hannu. Suna tafe driver mai Suna Alasan yana jansu da fira aikuwa nan sukai ta fira abinsu kamar sunsan juna ya ce "Wannan magen ki ce?" Gyad'a kai Sabeeha ta yi sai lokacin ta yi tunanin kar dai akwai Wanda bai son mage a gidan take sai ta ji jikin ta ya yi sanyi domin ba k'aramun so takewa pretty ba. Tunanin ta ne ya katse ganin layin da suka shiga nan suka fara raba idanu suna kallon ikon Allah domin ko a mafarki basu tab'a tunanin zasu gansu a irin wannan gidan ba suna zuwa gate sojojin dake gate d'in suka bud'e musu suka wuce ba tare da wani bincike ba domin ansan motar ta gidan ce nan su Sabeeha suka dinga kalle kalle ganin ko ina sojojine birjik kamar a barrack sannan ko ina a gidan shuke shuken fulawoyi ne kala kala da suka k'awata gidan sai da suka yi tafiya mai d'an Nisa suka isa wani gate d'in ana bud'e musu suka hango wani had'adden gini duk glass ne a jikin ginin ga sojoji ta ko ina parking lot Kuma cike da motoci na gani na fad'a ga wasu parts d'in a gidan sannan ga 'yan aiki mata da maza ko wannen su cikin uniform maza coffee mata blue d'in riga da skirt har da hijabi k'arami. Tunanin su ne ya tsaya lokacin da suka tsaya gaban part d'in Ummi a hankali suka fita suna k'arewa gidan kallo. Alasan ya ce "Nan zaku shiga bari a shigar muku da kayan ku," Hadiza ce da Yasira suka fito daga part d'in Alasan ya ce "Yawwa Hadiza ku shigar musu da kayan su bak'in Hajiya ne," d'aukar kayan su Hadiza suka yi suna yi musu Sannu da zuwa basu tab'a tunanin 'yan aiki bane saboda basu yi kama da 'yan aiki ba. Bin bayan su Hadiza suka yi har zuwa cikin falon nan suka k'ara tabbatar da cewar masu gidan manya ne na gaske ta b'angaren kud'i gani suke yi kamar a mafarki can suka hangi Ummi zaune tasha gayu cikin wani less ash Mai matuk'ar kyau falon banda k'amshi ba abinda yake yi k'arasawa suka yi lokacin suka ji Ummi na cewa "Eh gasu sun k'araso ok sai anjima," Ummi ta katse kiran tare da kallon su Sabeeha ta yi murmushi ta ce "Sannun ku da zuwa ku k'araso mana," a k'asan carpet suka zauna suka ce "Hajiya Ina wuni?" Cikin fara'a Ummi ta ce "Lafiya qlau," sannan ta kalli su Hadiza ta ce "kuje," tafiya suka yi suna cewa "Wallahi 'yan uku ne ikon Allah kama sak ba banbanci," Ummi ta ce "Sannun ku da hanya 'yan uku," haka kawai Ummi ta ji son yaran har cikin ranta murmushi kawai suka yi Ummi ta ce "meye sunayen ku?" Sabreen ta ce "ni sunana Sabreen," Sameeha ta ce"Ni Kuma Sameeha," "Ni Kuma Sabeeha," cewar Sabeeha Ummi ta ce "Masha Allah," Zainab ta fito daga kitchen ta cika gaban su Sabeeha da abinci da drinks. Ummi ta ce "Wacece ta iya girkin a cikin ku?" Sabeeha da ta zuba lemo a cup zata sha ta ce "Ni ce Hajiya," Ummi ta ce "A'a ni bana son Hajiya ku kirani Ummi ku d'auke ni kamar mahaifiyar ku," suka ce "Toh Ummi," "Sabeeha ke ce daga yau zaki dinga yiwa yarona girki tun daga safe har dare gobe zaki fara sannan ku Kuma zaku dinga yi mun abinda ba a rasa ba saboda ina da masu yi mun komai sannan muna da uniform da 'yan aikin gidan nan ke sawa amma ku banda ku saboda ina jinku kamar 'ya'yana sannan naga kayan ku iri d'aya ku ke amfani da shi sannan za a dinga biyan ku dubu d'ari duk wata," a razane suka kalli Ummi jin nannauyan kud'in da za a dinga basu duk wata ba tare da sunyi wani nannauyan aiki ba dan ko a gidan Yallab'ai da suke aiki kamar bayi dubu goma ne a wata. Ummi ta ce "Ko kud'in sunyi muku kad'an sai a k'ara muku," da sauri har suna had'a baki suka ce "A'a wallahi Ummi mungode Allah ya saka da alkhairi," ta ce "Ba damuwa ai hakk'in ku ne," Sabeeha ta ce "Ummi dama wannan magen ba matsala bansaniba ko wani baya so a nan gidan," Ummi ta ce "A'a ki bar abar ki," wani sanyi suka ji a ransu. Rinaz ce ke saukowa daga stairs da alama daga bacci ta tashi riga da wando ne a jikin ta kusa da Ummi ta zauna sai lokacin ta lura da su Sabeeha zare ido ta yi tana kallon ikon Allah kasa yin shiru ta yi ta ce "Oh my God Ummi Kinga kama kamar mutum d'aya?" Dariya Ummi ta yi ta ce "Allah ya shirye ki to ga k'awaye Nan nayi miki," Nasreen ta ce "Na karb'a Wallahi Ummi," Nan ta tambaye su sunayen su suka fad'a mata itama ta fad'a musu sannan Ummi ta ce "Yanzu kuje d'akin ki su huta zuwa gobe zansa a gyara musu dakunan su," kallon juna suka yi Sabreen ta ce "Ummi idan da hali dan Allah a barmu a dak'i d'aya dukan mu," Ummi ta ce "To ba damuwa kuje ku huta," bin bayan Rinaz suka yi suka haura stairs suna kallon aljannar duniya. D'akin Rinaz d'in suka shiga wayyo kyau komai na d'akin pink ne gwanin sha'awa Rinaz ta ce "feel free ku d'auka a gidan ku ku ke kunaji dai Ummi ta had'a mu k'awance," murmushi suka yi zama suka yi Nan Rinaz taita yi musu surutu domin so take su saki jiki da ita. A haka har lokacin sallar azahar ya yi suka yi alwala suka yi sallah sannan Sabeeha ta haye saman gadon Rinaz ta kwanta bacci ne ya d'auke ta yayin da tabar su Sabreen na fira. Maleek ne kwance saman gadon sa 3Quater ne a jikin sa black da white t-shirt ruf da ciki ya kwanta yana danna laptop d'in sa sai dai gaba d'aya hankalin sa baya kan aikin da yake yi gaba d'aya tunanin sa yana wajen yarinyar hannunsa ya zura cikin lallausar sumar sa ya hargitsa tare da rufe laptop d'in ya lumshe idanunsa yana jin wani iri a jikinsa ji yake tun yanzu son yarinyar na neman yi masa illa gashi yasa an bincika masa k'auyen da ya ga yarinyar amma ba bu labarin ta. Saurin bud'e idanunsa ya yi jin an kwanta masa a jiki Nasreen ce sai wani narke masa a jiki take yi a hankali ya janye ta a jikin sa sannan a hankali ya ce "Please Nasreen ki kyaleni sanin kanki ne na hanaki hawar mun jiki," tura baki ta yi ta tashi ta fice fuu da kallo ya bita har ta fita ya koma ya kwanta. Sai bayan la'asar Sabeeha ta tashi daga baccin da take yi ta samu su Sabreen basa d'akin kayan ta ta gani akan gadon tashi ta yi ta fad'a toilet ta yi wanka ko da fito Mai kawai ta shafa tasa riga da skirt na atamfa tayi sallah ta gyara d'akin tsaf sannan ta fita falon dake saman basa nan down stairs ta sauka anan ta samu Ummi na zaune tana shan fruits Fauwaz na gefen ta yana danna waya wajen ta k'arasa ta ce "Sannu da hutawa Ummi," kallon ta Ummi ta yi ta ce "Yawwa yarinyata," ta kalli Fauwaz ta ce "Ina wuni?" Sai lokacin ya d'aga Kai ya kalle ta domin Fauwaz halin sa daban yake yana da d'an girman Kai da miskilanci a hankali ya ce "Lafiya lau Ummi Wai ita ce d'ayar?" Ummi ta ce "Eh ita ce," a zuciyar sa ya ce Masha Allah. "Ummi ina su Sabreen fa?" Ummi ta ce "sun fita zaga gida su da Rinaz," jinjina kai ta yi sannan ta tashi ta nufi inda take tunanin kitchen ne aikuwa kitchen ne Wanda ya gaji da had'uwa yasha kaya sosai ko fridge sun Kai biyar su Hadiza ta samu zasu d'ora abinci gaisawa suka yi sannan ta fara taya su aikin tana yi suna fira kad'an-kad'an zobon da ta ga zasu had'a tace a bar mata ta had'a aikuwa suka bar mata can cikin kitchen d'in ta shige kasancewar kitchen d'in ciki da falo ne. Ta d'ora zob'on a saman wuta sannan ta d'an daka ginger tasa a ciki sai da ya tafasa sosai sannan ta sauke shi ta tace shi a wata roba Mai kyau sannan ta d'auko water melon a fridge ta yanka ta cire b'awon ta yankata k'anana ta cire k'wallayen ta zuba a blander sannan ta d'auki cucumber ta feraye itama ta yankata ta had'a da water melon d'in ta yi blanding d'insu ta tace ta zuba cikin zob'on sannan ta zuba tiara mai watermelon sannan tasa kayan k'amshi da color sannan ta samu wani jug a cikin d'in ta juye a ciki tasa a fridge sannan ta cigaba da ta ya su Hadiza aiki har suka gama suka jera komai a daining. Ko da su Sabreen suka dawo a falon suka zauna suna ta fira abinsu. Da daddare suka hallara a daining su Sabeeha duk suna jinsu daban a hakan ma sai da Ummi ta nuna musu fushin ta sannan suka zauna zasu ci abinci tare sai dai sun kasa sakewa zob'on Ummi da Fauwaz suka zuba suka sha Fauwaz ya ce "Wow Ummi amma ya yi dad'i sosai," itama Ummi ya yi mata dad'i sosai ta kalli Sabeeha ta ce "Ke kika had'a ko?" Noding kanta ta yi Ummi ta ce "Ko da naji ni nasan basu Hadiza bane suka had'a," Rinaz ta ce "Wayyo dad'i Wallahi Ummi," dariya suka yi mata a haka suka gama cin abincin sannan suka kwashe komai suka haye stairs dan zuwa su yi sallah. Tunda suka yi sallah suka zauna zaman fira. Maleek ne zaune a falonsa dawowar sa kenan daga masallaci ya yi wanka amma yana zaune ya zurfafa a aikin nasa ji yake kamar a daren nan ya tafi k'auyen ya duba da kansa wani Abu ya tsaya masa a k'irji yak'i tafiya. Wayar sa ce ta katse masa tunani hannu yakai ya d'auka ya kara a kunne daga can Ummi ta ce "Son kazo yanzu zamu yi magana," a hankali ya ce "To Ummi," ta ce "Lafiya kuwa na jika haka?" "Ummi sai dai nazo," yana fad'ar haka ya kashe Kiran ya mik'e ya fita daga part d'in mota ya hau har part d'in Ummi. Da sallama ya shiga falon ya zauna kusa da Ummi ya ce "Gani Ummi," ya fad'a yana kallon yadda Ummi ke ta faman sha zob'o ta ce "Yawwa dama magana ne akan Mai yima girki," take ya had'e rai baice komai ba Ummi ta cigaba da cewa "Yarinya ce mai hankali sannan da alama ta iya girki bari na kira ma ita ka ganta," girgiza kai ya yi yace "No Ummi kyaleta kawai dai ki samun zan Sha abinda ki ke sha," matsawa kusa dashi ta yi ta Kai masa cup d'in bakinsa ya sha lumshe ido ya yi saboda ba k'aramun dad'i ya yi masa ba k'ok'arin janye cup d'in daga bakin sa Ummi ta yi amma ya rik'e hannunta gam Yana girgiza kai kamar k'aramun yaron da uwar sa zata janye masa abincinsa. Sai da ya shanye tass sannan ya ce "Ummi wannan abun ya yi dad'i waye ya yi?" Hararar wasa ta yi masa ta ce "Mai girkin ka mana," jinjina kai ya yi ya ce "Da alama ta iya ko da yake bari gobe naji kar naje wannan abun kawai ta iya," ya fad'a ko a jikinsa Ummi ta ce "Wai ni kuwa Mai yake damun ka?" Langab'ar da Kai ya yi ya ce "Ummi Wallahi Ina sonta kullum tunaninta nake yi har mafarkin ta nake yi na rasa yadda zanyi Ummi Wallahi Ina sonta a Ina zan ganta," ajiyar zuciya Ummi ta sauke cikin tausayin d'an nata ta ce "karka damu yarona insha Allahu zaka same ta okay? Gyad'a kai ya yi yana jin sabon tunanin yarinyar dako sunanta bai saniba na zuwar masa haka sukai ta fira da Ummi sannan ya yi mata sallama ya tafi. Washe gari tunda safe da su Sabeeha suka tashi basu koma bacci ba gyaran gidan suka fara suka gyara ko ina fess sannan suka yi wanka suka shirya cikin dogayen riguna na material red sunyi kyau sannan Sabeeha ta nufi kitchen ta fara tunanin mai zata girka masa ne domin bata saniba ko wanne kalar abinci yafi so ba. Wata zuciyar ta ce Kinga gidan ba abinci kala d'aya suke yi ba ki yi masa biyu dole idan wani bai yi masa ba wani zai yi masa. Feraye doya tayi ta yi doya da kwai da tasha attaruhu da kayan had'i sannan ta yi kunun gyad'ar da yasha madara ta zuba a plask sannan Kuma ta yi wata k'warya-k'wayar white rice da miyar hanta sannan ta dafa ruwan tea da ya sha kayan k'amshi sannan ta yi chips. Tana gamawa ta Kai komai daining sannan ta je ta gyara kitchen d'in sannan ta fita falo lokacin har su Ummi sun fito saboda Ummi zata fita office har k'asa ta tsugunna ta gaida Ummi ta amsa cikin fara'a tare da yi mata Sannu da aiki. Ummi ta ce "Ai daga jin k'amshin girkin ki nasan son zai yaba bari na kira shi yazo ya yi breakfast d'in," ranar kam breakfast d'insu daban dan d'akin Rinaz suka tafi Ummi bata hanasu ba saboda ganin jiya basu wani sake ba. Suna tafiya Maleek ya yi sallama a falon yasha kyau cikin shadda light blue ya yi kyau sosai kamar a sace shi a gudu gaida Ammi ya yi su Rinaz suka gaida shi sannan suka tafi daining tare da Rinaz da Fauwaz. Tunda Rinaz ta bud'e warmers d'in wani daddad'an k'amshin girkin ya daki hancinsa har sai da ya lumshe ido aikuwa ana zuba masa ya ja plate d'in gaban sa ya fara cin doyar lumshe ido ya yi ya bud'e ya ga su Ummi na kallon sa domin jin Mai zai ce. Bai yi magana ba ya yi sipping kunun gyad'ar nan ma ya ji dad'i kallon Ummi ya yi ya ce "Ummi ta iya girki sosai ba Dan kar nayi k'arya ba sai nace ta fiki iyawa," Rinaz ta ce "Eh Wallahi Yaya Sabeeha ta iya girki," a zuciyar sa ya maimaita sunan domin ya yi masa dad'i sosai. Ranar kuwa ya ci abinci sosai Ummi ta ce "Bari a kirama ita ku gaisa," ya ce "A'a Ummi ki rabu da ita," ta ce "Shikenan ni bari na tafi office Rinaz ku kula sosai sannan an gyarawa 'yan uku d'akin su zasu iya komawa," ta ce "Tom Ummi," Maleek ya ce "Ummi ni fa yau binki office zanyi," ta ce "To taho mu tafi," tashi ya yi ya bita suka fita. Da kansa ya ja Ummin tasa yayinda soldier's d'insa suka sa motar su a tsakiya jiniya kawai ke tashi. A haka suka k'arasa tafkeken asibitin suka nufi office yayinda sojojin sa ke biye da su suka tsaya k'ofar office d'in su Kuma suka shiga kujera ya samu ya zauna ya tafi sana'ar tasa wato tunanin Sabeeha yayin da Ummi ke aikin ta. Tare suka koma gida da Ummi ya wuce part d'in sa ya yi wanka ya d'an kwanta sai dare sannan ya nufi part d'in Ummi ya ci Abinci Wanda ji ya yi yama fi na safiyar dad'i har santi ya ringa yi Ummi na masa dariya. A k'auye kuwa Kawu bai je gidan ba sai ana gobe d'aurin aure amma sai ya ga wayam ba kowa sai Abba Nan ya tambaye shi 'yan uku Abba ya ce shima baisan inda suka tafi ba aikuwa ranar Abba ya ga ruwan bala'i domin daga yaran har shi sun sha zagi shi dai Abba shiru ya yi baice komai ba har Kawu ya gama masifar sa ya kad'a riga ya tafi bai dad'e da tafiya ba aka je aka kwashi akwatin Dauda Dana faruk ya yinda aka bar na Sadam domin Kawu so yake idan sadam d'in ya je su rarrashe shi ya auri Zainabu sai dai tunda suka gayamasa buk'atar su ya ce shi Sam bai yadda ba hakan yasa Lantana ta je wajen boka aka yi mata asiri har Sadam ya dawo duk duniya Zainabu kawai yake so ya ce shi a satin a d'aura musu aure amma kawu yak'i amincewa wai sai nan da wata d'aya zuwa lokacin sun shirya haka sadam ya hak'ura. [10/25, 7:37 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️ RUBUTAWA DAGA HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ) SADAUKARWA GA MY DAUGHTER SABEEHA BILKISU Z.YA'U (🅱️K) AISHA MAGAJI DABO (AMA) Page 7 Sabeeha ce a kitchen tana girkin dare ya yinda tabaro Sabreen da Sameeha a d'akin su kasancewar su ba wani aiki da suke yi a gidan gashi Sabeeha ta ce bata so su bita su hanata aikin ta yadda ta kamata. Falo ta fita lokacin Shigar Nasreen falon kenan zama ta yi sannan ta aikawa da Sabeeha wani banzan kallo ta ce "Ke zonan," Sabeeha a zuciyar ta ta ce wannan fa daga Ina tab'e baki Sabeeha ta yi ta k'arasa gaban Farida ta ce "Gani," harara Nasreen ta aika mata ta ce "Baki iya gaisuwa bane?" Banza Sabeeha ta yi kamar bata ji me Nasreen ta fad'a ba. Jinjina kai Nasreen ta yi ta ce "Dan uwar ki ba magana nake miki ba?" Sai lokacin Sabeeha ta yi mata wani kallon karki k'ara sannan ta yi k'wafa kawai. Cikin fushi Nasreen ta ce "Ke!! Kece mai yiwa mijina girki?" Sai lokacin Sabeeha ta ce "Waye mijin naki?" D'an cije baki Nasreen ta yi ta ce "Ya Maleek," Shiru Sabeeha ta yi kamar mai tunani sannan ta ce "Waye Maleek a gidan nan?" Bata ankara ba ta ji an zabga mata mari dafe wajen Sabeeha ta yi domin jin bak'on abu a fuskar ta tuni ta ji wani bak'in ciki a zuciyar ta saboda a rayuwar ta ta tsani a mare ta aikuwa tana d'aga kanta itama ta tsinkawa Nasreen mari. A idon su Sabreen komai ya faru da sauri suka k'arasa Sameeha ta ce "Subhanallah Sabeeha dear Mai ya faru?" Ko kallon su bata yi ba ta yi wucewar ta kitchen tabar suna bawa Nasreen hak'uri ita Kuma tana cewa "To Wallahi yau sai kunbar gidan nan tunda bana Uban ku bane Kuma sai kinyi regretting marina da kikayi banza ye kawai daga ke har wad'an da suka kawo ki gidan nan," Rinaz dake gefe ta ce "Ke Wallahi karki kuskura ki zagar mun mahaifiya idan ba haka ba sai kin gane kuren ki Wallahi an gaya Miki kowa irin ki ne da baisan darajar iyayensa ba?" K'wafa Nasreen ta yi ta fita. Sabreen ta ce "Rinaz waccan d'in wacece?" K'wafa Rinaz ta yi ta ce "Matar Yaya ce," zare ido suka yi suna kallon ta ganin yadda ta yiwa matar yayan nata ita kuwa ko a jikin ta ta haye stairs su Kuma suka nufi kitchen suka samu Sabeeha sai aikin ta take yi amma lokaci zuwa lokaci ta yi k'wafa. Kallon su Sabreen ta yi ta ce "Meye ku ke ta wani kallona ku yi tambayar ku mana," aikuwa har suna had'a baki wajen tambayar ta Mai ya had'a ta da Nasreen bata b'oye musu komai ba ta fad'a musu ta ce "Kuma wallahi sai tasan ta taroni fad'a," Sameeha ta ce "Sabeeha dear Dan Allah karki fara kinga ba dad'ewa a gidan nan muka yi ba kar a fara haka damu Kuma matar fa Wanda kika zo gidan nan domin sa ce," "To sai me dan matar sa ce to ko shine ya yi mun ba rabuwa zanyi da shi ba balle wata matar sa danni bazan d'auki iskan ci ba Wallahi," Nasreen kuwa tana fita direct part d'in Maleek ta nufa yana zaune akan kujera Yana waya da Umar ta shiga falon tana kuka ta zauna gefen sa tana sharar hawaye kallon ta ya yi sannan ya ce "Umar Ina zuwa," daga haka ya katse kiran ya ce "Lafiya maiya faru?" Cikin kuka ta ce "Ya Maleek part d'in Ummi naje shine na samu wata Wai ita mai yi ma girki dan kawai na tambaye ta ita ce mai yima girki da ka fad'a mun shikenan Nasreen ta fara yimun gori wai ban iya girki ba ita kuma yarinyar hadda marina," ya ce "What mari fa ki ka ce?" Matsawa kusa da shi ta yi tana nuna masa wajen aikuwa ya ga shatin yatsun Sabeeha domin ba k'aramun mari tasha ba. Take ran Maleek ya b'aci akan me wata can 'yar aiki ta zo har gida Kuma harta marar masa mata jinjina kai ya yi ya ce "Shikenan kwantar da hankalin ki zan d'auki mataki a kansu," wayar sa ya d'auka ya kira number d'in Rinaz tana d'agawa ya ce "Ku zo yanzu Ina son ganin ku ke da wacce ta mari Nasreen," Yana fad'in haka ya katse kiran bin wayar da kallo Rinaz ta yi sannan ta sauka down stairs ta samu Sabeeha na jera abinci a daining ta ce "Mata Sabeeha zo muje," Sabeeha kuwa warware mayafin blue black d'in doguwar rigar jikin ta ta yi ta yafa shi sannan ta ce "Muje," Sabreen ta ce "Au abin ba gayyata?" Rinaz ta ce "No ku zauna nasan yanzu Ummi zata dawo," suka "Ok," su Kuma suka fita. Suna tafiya Sabeeha ta ce "Nasan k'ara aka kaimu ko?" Dariya Rinaz ta yi ta ce "Eh mana yaya ke neman mu," Daram gaban Sabeeha ya fad'i amma ta dake bata ce komai ba. Sojoji suka tarar a bakin k'ofar sai dai basu hanasu shiga ba Rinaz na gaba Sabeeha na binta a baya a kwance suka same shi idanunsa a lumshe hoton fuskar yarinyar kawai yake gani sanye yake cikin red t-shirt da red 3Quater gefe Kuma Nasreen ce zaune idanunta sun yi jajir ko kallon ta basu yi ba Rinaz ta ce "Yaya gamu," ba tare da ya bud'e idanunsa ba ya ce "Ku zauna a nan," Zaman suka yi Sabeeha ta b'uya a bayan Rinaz domin kallo d'aya ta yi wa Maleek ta ji gaban ta na fad'uwa take ta ji tsoron sa ya kamata gashi kamar aljani saboda kyau ga jajayen kayan sunyi masa kyau sosai ga wani k'amshi da ya daki hancin ta Wanda bazata tab'a manta shi ba. Tashi zaune ya yi fuskar sa a matuk'ar had'e ya kalli Rinaz ya fara balbale ta da fad'a "Dama baki da hankali bansani ba ashe bakya amfani da ilimin ki to tsaya ke iya abincin ki kayi da har zaki dinga yi mata gori akan bata iya abinci ba," Rinaz ta bud'e baki da niyyar yin magana ya ce "Wallahi karki kuskura kice zaki yi mun magana a nan to ita mai marin na ta sai tabar gidan nan na hak'ura da cin girkin nata," magana yake you hankali yana yatsina. Sannan ya ce "A yau kuma a yanzu subar gidan nan saboda bazan lamunci wulak'anci ba domin ita matata ce," ku tashi kubar nan Rinaz na hawaye ta ce "Dan Allah Yaya kayi hak'uri Wallahi ba laifin Sabeeha bane," kallon da ya watsawa Rinaz d'in ne yasa ta yin shiru Sabeeha kuwa a zuciyar ta ta ce Lallai ne mai mata mu ai bamu da mai kare mu amma ko ba komai ka ji me ya had'a mu da ita. Ai take ran Sabeeha ya b'aci ta mik'e ba juya ta yi hanyar fita daga falon tana tunanin ai yanzu yanzu zasu bar gidan dama ai ba yanzu aka saba korar su a gidan aiki ba akwai gidan ma da ranar da aka kaisu suka barsa ballantana wannan sunyi sati d'aya. Tana fita part d'in Ummi ta nufa tana shiga su Sabreen suka tare ta suna tambayar ta maiya faru ta ce "Ku had'a kayan ku yanzu mu tafi," Sameeha ta ce "What ina zamu je?" Tsawa Sabeeha ta daka musu ta ce "Mu tafi nace!!," Ba b'ata lokaci suka had'a nasu ya nasu suka fita daidai lokacin Rinaz zata shiga part d'in domin gudu ma ta yi Dan kar su tafi ganinsu janye da akwatunan su ta ce "Dan Allah karku tafi ku zauna," Sabeeha ta ce "Kiyi hak'uri Rinaz amma dole mu tafi saboda yace lallai a yau mubar gidan nan," Rinaz ta share hawaye ta ce "Naji amma ina ne gidan ku?" Sabeeha ta ce "Mu ba a garin nan muke ba zamu koma garin mu ne dama k'addara ce ta rabo mu da mahaifin mu mahaifiyar mu dama tun muna yara aka nemeta aka rasa yanzu ma mun baro gidane saboda auren dolen da Kawu zai yi mana munzo ne domin idan komai ya lafa mu koma wajen mahaifin mu da yanzu bamu san halin da yake ciki ba iya haka mun gode da taimakon ku idan Ummi ta dawo kice mata mun tafi," kuka Rinaz ta fashe da shi ta ce "Dan Allah kuyi hak'uri yanzu idan Kun tafi Ina zaku," Sameeha Mai saurin yin kuka tuni ta fara ta ce "mu ma bamu saniba," k'arasawa gaban su ta yi ta ce "Akwai wata k'awata iyayen ta suna k'asar waje ita Kuma tana gidan auntyn ta Dan Allah kuje can kunga yanzu dare ya fara gobe sai ku tafi zan sa a kaiku can zanyi mata waya," girgiza kai Sabeeha ta yi ta ce "A'a Rinaz kar mu sake jawo Miki wata matsalar," daga haka ta ja trolley d'in ta dakyar Rinaz ta lallab'a su suka yadda tasa driver ta ce ya kai su gidan su dija. Sai da suka tafi sannan ta kira dija a waya ta sanar mata sannan ta shiga gidan ta zauna a kan kujera ta saka kuka domin wani tausayin 'yan uku ne ya kamata ga wata shak'uwa da suka yi kamar sun shekara biyar tare tana wannan halin falon ya d'auka Fauwaz is open the door. Yana shiga ya samu Rinaz sai kuka take yi ya k'arasa da sauri ya ce "Rinaz lafiya me aka yi Miki?" Wani kukan ta fashe da shi ta ce "Bro yaya ne ya kori 'yan uku," a razane ya kalle ta ya ce "Ya kore su fa kika ce?" Ta gyad'a kai. Shiru Fauwaz ya yi Yana jin ba dad'i har cikin zuciyar sa basu ji shigowar Ummi ba kawai sai ji suka yi ta ce "Lafiya kuwa mamana?" Rungume Ummi Rinaz ta yi ta ce "Ummi yaya ya kori su Sabeeha," take gaban Ummi ya fad'i domin ji tayi kamar an raba ta da wani abu nata Mai matuk'ar muhimmanci ta ce "What! Yanzu Ina suka tafi," shiru Rinaz ta yi zama Ummi ta yi tare da zaro wayar ta daga hand bag d'in ta ta kira wayar Maleek yana d'agawa ta ce "Yanzu kazo Ina son ganinka," tana fad'ar haka ta katse kiran. Tashi ya yi ya tafi Kiran Ummin tunda ya shiga falon Ummi ke binsa da wani irin kallo gefen ta ya zauna ya ce "Ummi gani," ta ce "Meyasa ka kori su Sabeeha?" Fad'a musu abinda Nasreen ta fad'a masa ya yi. Ummi ta kalli Rinaz ta ce "Meya faru mamana nasan ba haka abin yake ba haka kawai Sabeeha bazata mari Nasreen ba," Rinaz na hawaye ta ce "Ummi Nasreen ce ta shigo bakya nan sai Sabeeha shine tace mata Wai dan uwar ta bata iya gaisuwa ba sai Sabeeha ta yi shiru shine Nasreen ta ce Wai ita ce mai yiwa mijin ta girki shine Sabeeha ta ce Waye mijin nata kusan ita bama ta tab'a ganin Yaya ba shine fa Nasreen ta mare ta ku duba lamarin ba fa abinda akayi mata shine itama Sabeeha ta rama shine muka rabasu shine Nasreen tace sai su sabeeha sunbar gidan nan shine ta ce musu banzaye dasu da Wanda ya kawosu Ni Kuma nace karta sake tasa Ummi ciki shikenan fa tace ta fad'awa yaya k'arya da gaskiya," dafe Kai Maleek ya yi a hankali ya furta ya "Ya ilahi," Yana jin dama bai kore ta ba ya fara jin Mai ya had'asu sai dai shatin yatsun da ya gani a fuskar Nasreen ne ya tunzura shi. Ummi ta ce "Son ka ga irin ta ko Wallahi yaran nan babu ruwan su suna da girmama na gaba da su basu da raini," Fauwaz ya ce "Wallahi kuwa Ummi ni kaina suna burgeni," Ummi ta kalli Rinaz da har lokacin kuka take ta ce "Yanzu Ina suke?" Nan ta basu labarin abinda Sabeeha ta fad'a mata dangane da rayuwar su. Ummi har hawaye ta yi gaba d'aya tausayin su ya kama su Maleek kuwa tunda Rinaz ta fara magana yake kallon ta saboda ya tausaya musu jin za ayi musu auren dole a zuciyar sa yace kamar dai ni da Uncle ya yi mun amma nasu daban ne domin ko uwar da zata rarrashe su bata kusa. A hankali ya ce "Ummi dan Allah kuyi hak'uri duk bansan da haka ba amma insha Allah zansa a nemo su Ina son hoton su," Ummi ta ce "Mamana akwai hoton su?" D'aukar wayar ta ta yi ta ce "Eh akwai video d'in da nayiwa Sabeeha tana yin girki," ta fad'a tana mik'awa Maleek wayar. Karb'a ya yi ya Kai idanunsa kan wayar saurin mik'ewa ya yi Yana k'urawa wayar ido gani yake ko dai gizo idanunsa ke masa murza idon ya yi Yana kallon ta tana girki tana murmushi saurin juyawa ya yi da sauri yabar falon da kallo su Ummi suka bishi har ya fice. Yana fita ya k'walawa Salman kira yana zuwa ya ce "Ku kawo motoci," motocin aka kawo aka bud'e masa ya shiga sannan suka bar gidan sai jiniya ke tashi wajen mota ashirin suka fita neman 'yan uku. Ya yinda Maleek ta lumshe idanunsa hoton fuskar ta kawai yake gani yana jin meyasa ya aikata hakan ashe dama ita ce a gidan su take masa daddad'an girki bai saniba bud'e idanunsa ya yi Yana k'ara kallon videon sannan ya nunawa Salman ya ce "ita zamu nemo," Nan suka fara zagaye garin kaduna suna duba inda zasu hango su Sabeeha amma shiru babu su ba alamun su. Basu suka koma gida ba sai dare a gajiye Maleek ya shiga falon Ummi domin tunanin ta da yake yi ne ya saukar masa da wani irin ciwon kai Wanda bai tab'a tunaninsa ba domin Maleek yana d'aya daga cikin masu barin abu a rai abu kad'an sai ya hana shi sukuni. Yana shiga falon Rinaz ta mik'e da sauri ta ce "Yaya an same su?" Girgiza Kai ya yi sannan ya zauna kusa da Ummi gaba d'aya ya rasa nutsuwar sa ganin halin da ya shiga Ummi ta ce "Son lafiya kuwa?" Kallon Ummi ya yi da idanuwan sa da suka yi jajir ya ce "Ummi bamu same ta ba Ummi ita ce ita ce Wacce zuciya ta take so ita ce Wacce tunanin ta ya hanani sakewa," ya fad'a kamar zai yi kuka. Ummi ta ce "Ita ce wa?" Ya ce "Ummi ita ce Wacce nagani waccan lokacin a waccan k'auyen yanzu a Ina zan ganta sonta ya yi mun kamun da ban tab'a tunani ba," cikin Mamaki da tausayin d'an nata ta shafa kansa ta ce "Nasan kana sonta tunda har ka iya furtamun domin nafi kowa sanin yarona idan har ya furta Yana son abu to ba k'aramun so yake wa abun ba dan haka ka kwantar da hankalin ka har zuwa lokacin da za a gansu," noding kansa ya yi yana jin idan ba a ganta ba zai shiga wani hali. Har Rinaz ta bud'e baki da niyyar fad'in inda suke sai Kuma ta yi shiru a zuciyar ta tana fad'in ashe dama ita Yaya ke matuk'ar so aikuwa sai na wana shi kafin yasan inda suke. Karb'ar wayar ta ta yi ta haye stairs ta kira dija a waya daga can Dija ta ce "Beb yane nagode da kyautar k'awaye masu shiga rai," dariya Rinaz ta yi ta ce "Ya suke to?" Dija ta ce "Normal ga Sabeeha a nan Sabreen da Sameeha na tare da aunty a kitchen," jinjina kai Rinaz ta yi ta ce "Yawwa ba Sabeeha wayar," karb'a Sabeeha ta yi ta ce "Hello Rinaz dear," Rinaz ta ce "Yes kina jina ba Ummi ta dawo taji mai Yaya ya yi sannan bata ji dad'i ba haka ma yaya Fauwaz amma kinsan me sharri Nasreen ta yi mana wajen yaya sannan na fad'a masa abinda ya faru yanzu haka baki ga damuwar da ya shiga ba bai dad'e da dawowa daga neman ku ba amma ban sanar da kowa nasan inda ku ke ba Dan haka ku zauna a nan har saina wana Yaya," murmushi Sabeeha ta yi ta ce "To ba damuwa ya Ummi fa?" Rinaz ta ce "Tana lafiya sai dai tana cikin damuwar rashin ku," murmushi Sabeeha ta yi tabbas tasan Ummi Mai k'aunar su ce. Da haka suka yi sallama Rinaz kuwa ba ta fad'a wa Sabeeha komai akan budurwar da yake so ba saboda tasan zuciyar Sabeeha cike take da haushin Maleek idan ta fad'a mata ma ba lallai su koma gidan domin zata iya tunanin dan yana sonta ne shiyasa ya matsu su koma sannan Kuma ba ta da tabbacin Sabeeha ya gani a k'auyen may be Sabreen ce ko Sameeha domin tasan Yaya Maleek bai tab'a ganin ko d'aya a cikin su ba. Ranar Ummi da Fauwaz basu rintsa ba balle Kuma oga Maleek domin tunda ya yi wanka ya yi sallah ya kwanta saman gadon sa ya fad'a tunanin yanzu idan ba a ganta ba ya zai yi haka ya yi ta tunani gashi Nasreen ta dame shi da kira Amma ya k'i d'agawa domin wani mugun haushin ta yake ji domin duk ita ta ja komai ranar dai inda ya ga rana haka ya ga dare ko da Asuba da ya yi Sallah bai iya yin baccin ba addu'a kawai yake yi Allah ya bayyana ta sai dai zuwa lokacin shima ya fara karaya akan idan ma ta dawo dakyar ta so shi saboda yasan cewar yanzu haka haushin sa take ji. Yana zaune har gari ya yi haske wanka kawai ya yi suka k'ara fita neman su ba tare da ya ko yi breakfast ba ranar ma haka suka wuni neman su Sabeeha amma basu ba labarin su domin Ummi har Fulani ta kira ta tambaya Amma aka ce basu je ba. Haka ranar ma Maleek ya komawa Ummi kamar zai yi mata kuka dakyar ta rarrashe shi amma duk yadda taso ya ci Abinci k'in ci ya yi ranar ma haka ya kwana bacin abinci ga rashin bacci. Sabeeha ce kwance da daddare haka kawai taji bacci ya k'auracewa idanunta sai juyi take yi Sabreen ta yi juyi ta ce "Sabeeha dear lafiya kuwa? A hankali ta ce "Bansaniba dear banjin bacci ne kawai amma kina ganin mu koma gidan nan kuwa?" Sabreen ta ce "Eh mu koma mana idan bamu koma ba Ina zamu je?" Sameeha dake jinsu ta ce "Nima ji nake kamar kar mu koma saboda kar suyi tunanin saboda dukiyar su zamu koma," Sabeeha ta ce "Nima abinda nake tunani kenan sannan Wallahi yayan Rinaz bai da kirki akan Matar sa ita Kuma da gani makira ce tunda har ta nuna bata son mu nasan kad'an muka fara gani a cikin makircin ta Ni nasan tabbas akwai abinda zai faru gaba," Sabreen ta ce "Haka ne Kuma dear yanzu meye mafita?" Sabeeha ta ce "Kawai gobe mubar gidan nan," haka suka tsayar da shawarar gobe zasu bar gidan gara ko k'auye ne su koma abinda basu saniba shine duk firar su Dija na jinsu sannan sun burge ta ta wani b'angaren sai dai bata ji dad'in tafiyar da suka ce zasu yi ba domin har ta saba da au gasu da shiga rai sannan tasan indai ta b'angaren su Ummi ne basu da matsala sai dai Nasreen domin bata da kirki ko kad'an. Washe gari da wani zazzafan zazzab'i Maleek ya tashi domin tun daren jiya ya rufe shi gashi yak'i ya sanarwa kowa Yana kwance lullub'e da blanket fuskar sa ta yi jajir da kyar ya iya tashi ya yi sallah ya yi wanka ya koma ya kwanta gashi bai ci komai ba balle ayi maganar magani hatta soldier's d'insa dake tsaron sa basu san baida lafiya ba gashi har lokacin Nasreen bata dena Kiran sa ba. Kasa jurewa Nasreen ta yi ta shirya ta nufi part d'in nasa tura k'ofar d'akin nasa ta yi ta shiga can ta hango shi duk'un k'une a blanket da sauri ta k'arasa ta ce "Ya Maleek baka da lafiya ne?" Saurin runtse idanunsa ya yi domin baya son ganinta domin ita ce silar faruwar komai ganin yayi mata banza ne yasa ta zari wayar sa d'aya dake bedside drower ta lalubi number d'in Ummi ta kira lokacin Ummi zata tafi office ta kalli Rinaz ta ce "Mamana zan tafi office daga nan zan je na bayar da cigiyar su Sabeeha na damu da rashin ganinsu gari ko garin su bamu saniba gashi son ya damu sosai," jinjina kai Rinaz ta yi. Wayar Ummi ce ta d'auki k'ara ta d'auka sai Kuma ta ce "Subhanallah gani nan zuwa," tana fad'ar haka ta nufi k'ofa hankalin ta a tashe domin sanin kanta ne Maleek Yana da ciwon zuciya Wanda tun yana yaro yake da shi Kuma bai fiya tashi ba sai ya shiga damuwa. Ganin Ummi ta fita hankalin ta a tashe yasa Rinaz binta da gudu tana tambayar ta lafiya ba abinda Ummi ta iya furtawa mota kawai suka shiga zuwa part d'in Maleek. Da sauri suka shiga d'akin suka same sa kwance a cikin blanket da sauri Ummi ta k'arasa ta ce "Son," sai lokacin ya bud'e idanun sa da suka yi jajir ya kalli Ummi ba tare da yace komai ba dafa goshin sa ta yi taji zafi zau ta ce "Son tashi mu tafi hospital," janye masa blanket d'in ta yi ya mik'e duk da bai da lafiya jarumtar sa na nan domin mik'ewa ya yi tsaf Ummi ta rik'e hannunsa suka fita Rinaz na biye da su ita da Nasreen. Suna fita Ummi ta bada umarnin a kawo motoci ba tare da b'ata lokaci ba aka jera motoci suka shiga sojojin suka ja motar suka bar gidan Rinaz na gaban mota Ummi na back seat Maleek ya d'ora kansa a kafad'ar ta Yana tunanin wane hali yarinyar sa take ciki. A haka suka k'arasa asibitin suka yi parking aka bud'e musu k'ofa Ummi ta fita hannun ta rik'e da na Maleek direct office d'in ta suka nufa su Salman na biye da su har sai da suka shiga office d'in sannan suka tsaya daga waje domin tsaron ogan nasu yayinda su Ummi suka shige ciki tare da su Nasreen. Suna shiga Ummi ta zaunar da shi kan kujerar ta ta fara yi masa gwaje gwaje nan ta gane zazzab'i ke damunsa wanda tunanin da yake yi ne ya kawo masa shi d'akin dake office d'in ta ja shi tasa masa drip sannan ta zauna gefen gadon yayin da Rinaz ke gefe a tsaye Nasreen Kuma zaune kan wata hadadd"iyar kujera ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya sun dad'e a haka kawai suna kallon sa Ummi ko ba a fad'a mata ba tasan akan Sabeeha ne itama Rinaz tunanin da take yi kenan Nasreen Kuma tunani take yi Mai ya kawowa Maleek wannan zazzab'in cikin k'ank'anin lokaci. Ummi ta kalli Rinaz ta ce "Rinaz ku je da Salman ki had'o abinci ki kawo mun," Rinaz ta ce "To Ummi," ta fad'a tare da juyawa da niyyar fita wayar ta ta fara ringing tana dubawa ta ga Dija ce ta ji dad'in Kiran dama so take ta kira ta domin ta aika a dawo da su Sabeeha sai dai tana d'agawa ta ji Dija na cewa "Beb akwai matsala fa jiya da dare naji su Sabeeha na shawarar barin gidan mu domin baza su dawo gidan ku ba domin gudun abinda zai je ya dawo gashi yanzu sun fita ba yadda banyi da su ba sun k'i zama," a rud'e Rinaz ta ce "Kina nufin su Sabeeha sunbar gidan ku to Ina suka tafi?" Dija ta ce "Nasan baza su wuce tasha ba domin gida suka ce zasu koma," Rinaz ta ce "Bari naje tashar," Maleek na jin haka ya yi saurin tashi zaune ya fisge drip d'in da aka sa masa ya mik'e ya yi hanyar waje tare da cewa Rinaz "muje," bin bayan sa ta yi suka fita daga office ya ce "Salman muje," bin bayan sa soldier's d'insa suka yi. Ummi kuwa kasa magana ma ta yi tana kallon ikon Allah mara lafiya da tafiya neman Sabeeha lallai ba k'aramun so yake mata ba. Nasreen kuwa wani bak'in ciki ne ya mamaye mata zuciya ganin Wai ya tafi tasha neman su Sabeeha lallai dole ne ta d'au mataki a kansu. [10/25, 7:37 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️ RUBUTAWA DAGA HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ) SADAUKARWA GA MY DAUGHTER SABEEHA BILKISU Z.YA'U (🅱️K) AISHA MAGAJI DABO (AMA) Page 8 Maleek yana fita aka bud'e masa mota ya shige yana jin wani farin ciki a zuciyar sa gudu sosai soldier's d'insa ke zabgawa a hanyar ga jiniya na tashi duk inda suka wuce sai an kalle su. Rinaz na gaban motar da Maleek ke ciki a hankali ta juya ta kalle shi suna had'a ido ya zabga mata harara ya ce "Wallahi zaki gane kurenki wato dasa hannunki a rashin lafiya ta ko?" Ya yi k'wafa ta ce "Sorry Yaya ita ce fa tace baza ta koma ba Kuma ai kaine baka tsaya kaji meya had'a mu ba," ya ce "Hmm baza ki gane baki da wayo ba sai idan bamu ga yarinyar nan ba," ya fad'a Yana k'ara aika mata harara ita kuwa Rinaz shiru ta yi tana addu'ar Allah yasa ma a gansu d'in. Shi kuwa Maleek lokaci zuwa lokaci yake kallon agogon hannunsa domin gani yake duk wasu mintunan dake wucewa suna nufin tafiyar su Sabeeha. Kai tsaye ya ce a shiga har cikin tashar aikuwa suka shiga cikin tashar Nan fa kallo ya koma kan motocin sa domin ko ba a fad'a ba ansan shine a ciki kowa mamaki yake yi to me ya kawo MG Maleek tasha yake yi ya yinda shi kuwa MG bai damu da kallon da akewa motocin sa ba. Cewa ya yi su yi parking aikuwa suna yi bai jira an bud'e masa k'ofa ba ya bud'e ya fita Rinaz ma ta fita haka ma sauran soldier's d'insa suka fito suka tsaya a bayan sa kowannen su rik'e da bingiga. Kai tsaye ya nufi inda motocin tashar suke yayinda mutanen dake tashar kowa yabar abinda yake yi ya tafi kallon MG Maleek wasu sun sanshi a TV wasu a jarida domin ba Wanda ya tab'a ganinsa a araha haka wani ma sai dai ya ga wucewar motocin sa amma yau gashi har cikin tasha. Mata kuwa har ma da mazan sai nuna shi suke yi domin ganin tsananin kyawunsa sanye yake cikin army green d'in trouser da farar t-shirt sai Kuma army green shirt a sama takalmin k'afar sa ma army green ne sumar kansa sai shek'i take yi gashi ta sha wani had'adden aski sai k'amshi ke tashi Nan fa matasan suka fara "Allah ya kare mana MG," hannu kawai ya d'aga musu yana sakin murmushi Wanda ya k'ara faranta ran masoyan nasa domin Yana da masoya sosai saboda bai da girman kai Yana da son al'umma. Sabreen ta kalli Sameeha dake kusa da ita ta ce"Sameeha dear kalli fa gab'a d'aya 'yan cikin tashar nan sun taru waje d'aya lafiya kuwa?" Sameeha ta ce "Nima dai abinda na gani kenan gashi Kuma Sabeeha dear har yanzu bata dawo ba," Sabeeha kuwa cikin wani shago ta je siyo ibon sweet ta dawo ta ga gaba d'aya tashar ta wani rikice kowa ka kalla fuskar sa tabb farin ciki a fili ta tab'e baki sannan ta nufi wajen mutanen tana fad'i a zuciyar ta Kai nima bari naje na ga Mai ake kallo haka da a bani labari gara na bayar. Lokacin da ta nufi wajen Maleek ya fara tafiya shi da Rinaz domin duba ta aikuwa mutanen gaban su na matsawa domin basa hanya ya wuce ita Kuma na k'ara kutsa kanta aikuwa sai tsintar ta ta yi gaban su cak ya tsaya yana binta da ido kamar bai tab'a ganin ta ba sai ranar Sabeeha kuwa kallo d'aya ta yi masa ta kauda fuskar ta ba Wai dan ta gaji da kallon sa ba a'a kawai dan tana d'an jin haushin sa ne ga kuma wani hamshak'in kyau da ta ga ya k'ara. Rinaz kuwa da gudu ta k'arasa wajen Sabeeha ta rungume ta tana murnar ganin ta ita kuwa Sabeeha murmushin yak'e ta yi tana satar kallon Maleek Wanda ya kafeta da idanuwa Rinaz ta ce "Yanzu Sabeeha dear da tafiya zaku yi ku barni?" Kad'an Sabeeha ta yi dariyar da iyakar ta fuskar ta saboda ita har ga Allah taso sun tafi. "Sameeha dear muje mu gani me yake wakana a can wajen muma," cewar Sabreen ta bud'e k'ofar motar ta fice itama Sameeha ta fita suka nufi wajen mutanen. Suna zuwa suka tarar da Sabeeha tare da Rinaz su Sam basu kula da Maleek ba da yake gefe a tsaye ya hard'e hannayen sa a k'irji yana kallon Sabeeha. Rinaz ta ce da Sabeeha "Ina su Sabreen fa?" Sai lokacin ta hangi su Sabreen suna tsaye ai da sauri suka k'arasa suka rungume juna da Rinaz suna farin ciki sai lokacin idanun Maleek ya sauka a kan su Sabreen da Sameeha zare ido ya yi cikin Mamaki Yana kallon su sannan ya kalli Sabeeha ya sake kallon su ya kalli Sabeeha shi a dole yana son ya nemo banbancin su amma ba bambamci a zuciyar sa ya ce "Tofah MG kana ruwa yanzu wacce nagani that time," su Sabreen ma sai lokacin suka kula da Maleek kallon sa suka tsaya yi kamar guma ka gani suke yi kamar a mafarki ne suke kallon wannan balaraben yadda ya tsaya kallon su su d'in ma haka suka tsaya kallon sa shi Yana mamakin kamar su su ukun su Kuma suna mamakin kyansa. Su kansu mutanen tashar tsayawa kallon 'yan uku suka yi ganin tsananin kamar dake tsakanin su juyawa kawai Maleek ya yi ya nufi motar sa ana bud'e masa ya shiga ya yinda Rinaz da su Sabeeha suka shiga motar dake bayan tasa suka bar tashar. Kai tsaye gida suka nufa Rinaz ta kira Ummi a waya ta ce "Ummi mun wuce gida tare da Yaya da kuma su sabeeha," cikin jin dad'i Ummi ta ce "To shikenan sai na dawo," daga haka suka ajiye wayar. Kallon Sabreen Rinaz ta yi ta ce "Ke kuwa lafiya kike irin wannan sakin baki haka?" Sabreen ta ce "Hmm ke idan ana sallah ba a magana wato Rinaz dama akwai irin yayan ki a Nigeria Wallahi ni ko a tv banga Mai kyansa ba tabdijan yaseen na d'auka a mafarki ne ba dan da mutane ba sai na tab'a shi nagani shin dagaske ne ko mafarki," dariya suka shek'e da ita ban da Sabeeha da ta yi kicin kicin da fuska Sameeha ta ce "Wallahi Nima dai haka Sabreen ban tab'a ganin Mai kyan sa ba," Jinjina kai Rinaz ta yi domin ita kanta tasan yayan nata ya gaji da had'uwa a wani gefen Kuma tana tunanin kenan indai Sameeha da Sabreen basu tab'a ganin ya Maleek ba kenan hakan na nufin Sabeeha ce Wacce suka had'u wancan lokacin. A haka suka k'arasa har gida suna gani aka bud'e masa mota ya fita ya nufi part d'in Ummi su ma fita suka yi zuwa part d'in Ummin. Suna shiga suka same shi zaune a falo ya jingina da jikin kujera ya lumshe idanunsa mai d'auke da zara-zaran eyelashes hannunsa d'aya akan lallausar sumar sa har lokacin bai dena mamakin kamar da ke tsakanin su ba. Har zasu wuce suka ji muryar sa mai dad'in sauraro ta ce "Kuzo nan," ba musu suka juya suka nufi wajen sa suka zauna k'asan carpet suna kallon sa a hankali ya bud'e idanunsa ya kallesu a zuciyar sa ya ce "Ikon Allah," a fili Kuma ya gyara zaman sa tare da gyaran murya ya ce "Da farko dai kuyi hak'uri akan abinda ya faru," ai Sabreen ba ta jira ya k'arasa fad'a ba da sauri ta ce "Bakomai Wallahi komai ya wuce," harara Sabeeha ta zabga mata duk Yana kallon ta Sameeha ta ce "Wallahi kuwa komai ya wuce dama misunderstanding aka samu," Sabeeha kuwa tab'e baki ta yi bata ce komai ba shi kuwa ita yake kallo domin jin abinda zata ce amma shiru a zuciyar sa ya ce to kodai ita ne wacce ke yin girki kallon Rinaz ya yi ya ce "Yunwa nake ji wacece ke dafa mun abincin?" Rinaz ta ce "Sabeeha kinji Yaya na jin yunwa ki dafa masa abinci," ta fad'a tana kallon Sabeeha shima ita ya kalla ba tare da ta ce komi ba ta mik'e ta nufi kitchen shi Kuma yana binta da ido har ta shige kitchen d'in haka kawai ya ji zuciyar sa tafi karkata akan ita ya gani waccan lokacin. Ya kalli su Sabreen ya ce "Sunayen ku fa?" Sabreen ta ce "Ni Sabreen ga Kuma Sameeha," ta fad'a tana nuna Sameeha kallon Sameehan ya yi sannan ya jinjina kai sannan ya tashi ya kalli Rinaz ya ce "Idan ta gama ta kai mun part d'ina," yana fad'ar haka ya juya yabar falon. Ko da ya koma part d'insa zama ya yi kan kujera ya lumshe idanunsa Yana tunanin shin wacece sahibar tasa ne a cikin su shi dai zuciyar sa tafi karkata ga Mai yi masa girki sai dai ba shi da tabbacin ita ce saboda duk irin su d'aya saurin bud'e idanunsa ya yi domin tunawa da wani Abu da ya yi tunawa ya yi lokacin da ya ganta ta kira wani suna da ta fad'a mayar da idanunsa ya yi ya lumshe fuskar ta ya gani sannan ya ji muryar ta ta ce "Please help me zasu kamani kuma Sameeha dear na buk'atar magani yanzu," a hankali ya bud'e idanunsa sannan a fili ya ce "Kenan ba Sameeha ce na gani ba a cikin Sabreen da Sabeeha ne naga d'aya," bud'e k'ofar falon nasa aka yi aka shiga a hankali ya Kai duban sa wajen ya ga Umar tsaye kamar gunki Yana sara masa harara ya aikawa Umar d'in sannan ya ce "Ka fara ba?" Dariya Umar d'in ya yi sannan ya k'arasa ya zauna ya ce "MG yane?" "Kamar ya fa?" Maleek ya tambaya Umar ya ce "Nifa aure nake so gaskiya dan harna fad'awa mommy," dariya Maleek ya yi har da rik'e ciki sannan ya ce "Kai amma dai anyi d'an iska yanzu Kai ko kunya baka ji?" D'aga kafad'a Umar ya yi ya ce "Wallahi ni banji kunya ba Kai dan kaga kana da taka matar Kai nifa har yanzu bani da budurwa," jinjina Kai Maleek ya yi ya ce "Lallai sannu babban ango ba budurwa ake zancen aure lallai na jinjinawa iskancin ka," "Ni yanzu MG mata nake nema Mai hankali a Ina zan samu?" Sai da Maleek ya harare shi sannan ya ce "Tofah shi Maleek ta ya zai sani bayan sanin kanka ne ba shiga harkar su nake ba," ya fad'a yana danna wayar sa. Nasreen ce ta shiga falon ta tsaya gaban Maleek ta rik'e k'ugu bai d'aga Kai ya kalle ta ba balle Umar da ya gyara zaman sa ya kama yin chart hakan ne ya k'ara k'ular da ita ta ce "Gurin ka fa nazo," har lokacin ba Wanda ya kalle ta cikin k'ulewa ta ce "Ya Maleek," sai lokacin ya kalle ta bata jira ya amsa ba ta ce "Wallahi bazai yiwu ba su Sabeehan ya kuke da su da har zaka tafi neman su ko Kuma akwai wacce kake so cikin su ne?" Mik'ewa ya yi tsaye tare da cire rigar sa shirt d'in dake sama sannan ya ce "Wow gaskiya kina ja yanzu har kin gano ina son d'aya cikin su kin fad'i gaskiya sannan ki tayani da addu'a Allah yasa tana Sona kamar yadda nake sonta," Yana fad'ar haka ya nufi stairs ta ce "To kuwa Wallahi bazai yiwu ba Kuma baka siyi zaman lafiya ba domin zan iya jure komai daga gareka amma Wallahi banda kishiya zanga shegiyar da zata aurar mun miji cikin su," bai ko waiga ba ta nufi stairs d'in itama sai lokacin ya ce "Kinsan Allah idan kika zo kina mun hayaniya a nan zanyi miki dukan da bakya tunani," yana fad'ar haka ya shige d'akin. Fuuu ta fice cikin jin haushi Umar kuwa dariya ya kyalkyale da ita yana tafa hannu ya ce "D'an iska MG ashe wata zaka k'aro?" Banza Maleek ya yi da shi ya shige wanka abinsa. Sabeeha kuwa girki tayi masa kamar yadda ya buk'ata tana gamawa ta fice ta k'ofar kitchen d'in zuwa d'akin su ta yi wanka ta shirya ta koma tana shiga falon Rinaz ta ce "Na manta Sabeeha dear Yaya ya ce ki kai masa abincin part d'insa," bata ce komai ba ta je ta zuba komai a basket ta nufi part d'in nasa tana cewa a zuciyar ta Allah yasa ba wani cin mutuncin za ayi mun ba tana zuwa ta ga soldier's wajen biyar a k'ofar sai Kuma taja ta tsaya dan tsoron su take yi sai Kuma ta gyara nutsuwar ta ta nufe su ta ce "Dan Allah Yana ciki dama zan Kai masa abincin sa ne," basu ce mata komai ba d'aya ya shiga falon ya samu Umar zaune a falon ya ce "Oga fa dama wata ce tazo Wai za a kawo masa abinci ne," Umar ya ce "Ok ta shigo mana," juyawa sojan ya yi ya fita sannan ya kalli Sabeeha ya ce "Shiga," Kai tsaye ta shiga had'adden falon da sallama a bakin ta Umar ya amsa tare da binta da kallo k'asa ta yi ta kanta. Daidai lokacin Maleek ke saukowa stairs yasha kyau cikin wasu k'ananan kaya dark blue sai k'amshi yake yi tun daga nesa ya k'ure ta da ido Yana kallon ta yana k'arasawa ya zauna k'amshin da ya daki hancin ta ne yasa ta lumshe ido sannan ta ce "Ga abincin," ya ce "Ok zuba mun," babu musu ta zuba masa ta ajiye kan center table d'in dake gaban sa sannan ta ajiye jug d'in d'in zob'on da ta had'a masa da glass cup domin dama Ummi ta fad'a mata yaji dad'in zob'on ta dinga yi masa tana gamawa ta mik'e zata tafi ya ce "dawo ki zauna," tura baki tayi dan ita har ga Allah a takure take shi kuwa yadda yadda ta tura bakin sai ya bashi dariya dan ganinta ya yi kamar 'yar baby zama tayi har da tank'washe k'afa tana kallon sa. Shi kuwa abincin sa ya d'auka yana ci a hankali Umar kuwa tunda ya kyalla ido ya ga zob'o ya fara gyara baki dan Yana son sa aikuwa ya zuba ya fara sha. Kallon sa kawai Sabeeha ke yi yadda yake cin abincin a nutse yana yi yana kallon ta sannan ya ajiye spoon d'in ya fara shan zob'on da ya yi masa dad'i sosai a zuciyar ta ta ce kai ba dai har ya k'oshi ba sai ji ta yi ya ce "Yes na k'oshi," ashe a fili tayi maganar k'asa tayi da kanta dan kunya ta ji sai da ya gama shan zob'on sa sannan ya daidai ta nutsuwar sa a kanta ya ce "Na tambaye ki mana?" Gyad'a kai ta yi ya ce "3 weeks back I think it's Thursday around 6:35pm kina ina wannan lokacin?" Shiru Sabeeha ta yi tana tunanin tambayar tasa inda ta dosa ta tuna tabbas wannan ranar suna asibiti tare da Sameeha Kuma a wannan lokacin ta fita siyan magani Kuma lokacin 'yan daban Rashida suka bita har ta rungume wani soja zare ido tayi domin wata zuciyar ta ce tace tabbas wannan ne sojan duk da banga fuskar sa ba Amma ai na ji k'amshin turaren sa irin na wannan ne sannan motocin waccan lokacin na sojojin sa irin na sojojin wannan ne tabbas ma shine tunda har ya yi mun maganar tunda idan ba shi bane ta ya yasan naje waccan k'auyen sannan har ma da lokacin tabbas shine. Maleek kuwa tsayawa kallon ta ya yi yadda ta zurfafa a tunanani har wani tallafe kumatun ta take yi a nata b'angaren kuwa ji ta yi kamar lokacin ta rungume shi dan wata kunya ce ta rufe ta sai Kuma wata zuciyar yace ai baisan ke bace ko bake bace kawai ki zabga masa k'arya aikuwa ta gyara zaman ta ta ce "Dama waccan lokacin muna asibiti ne tare da Sameeha dear," ya ce "Kina nufin baki fita ko ina ba?" Gyad'a kanta ta yi ta ce "Ni kam ba inda naje," ajiyar zuciya ya d'an sauke ya ce "Ok shikenan zaki iya tafiya," zumbur ta mik'e dan dama ta matsu tabar wajen ta d'ebi kayan da yaci abinci ta fice da sauri da kallo ya bita har ta fita. Sannan a zuciyar sa ya ce may be d'ayar ce zan tambaye ta itama kuwa Umar ne ya katse masa tunani da cewa "Kai wannan tambayoyin fa ko dai ka Santa ne?" "Ni kuwa nasan ta domin tun 3 weeks ago na tab'a ganinta a wani k'auye," nan ya labartawa Umar komai sannan ya ce "Abinda ban saniba ashe triple's ne hmm na shiga rud'u Umar dukan su fa iri d'aya suke ba different na rasa ta yadda zan gano tawa a ciki amma na cire Sameeha ciki domin time d'in itane a hospital kaga kenan ita bata fita ba hakan na nufin cikin su biyu ne kenan tunda ita wannan tace ba ita bace dole zai kasance d'ayar ce to tunanin da nake yi kar waccan ma tace ba ita bace Kuma fa dole hakan zai iya kasancewa waccan d'in ma tace ba ita bace sai dai I don't know why zuciyata tafi believing cewa wannan ce saboda yadda ta tafi dogon tunani ka ga da ita ce kai tsaye zata ce Ita ce amma sai ta tafi wani tunanin daban ba sai dai bansan mai take tunani ba amma soon zan gane shin ita d'in ce ko a'a," yana gama fad'in haka ya d'auki zob'on yana sha Umar kuwa sakin baki ya yi yana kallon Maleek domin tunanin sa ya zurfafa akan yarinyar har da ya iya gano wani abu Wanda yake tunanin tana b'oyewa Maleek ne ta katse masa tunani da cewa "Kai karka b'atawa kanka lokaci wajen mamakin magana ta ko ka manta matsayina ta hanyar binciken masu laifi?" Girgiza Kai Umar ya yi kamar dolo ya ce "Lallai kam na Sara maka Amma kana nufin irin wannan wacce ta fita biyu ne duk da ita uku?" Gyad'a kai Maleek ya yi. "Amma MG Wai auren ta zaka yi?" Nan ma gyad'a kai Maleek ya yi Umar ya ce "Amma Ina hango damuwa a harkar auren," "Me kenan?" Cewar Maleek dake kallon Umar. "Gani nayi kwata kwata yaushe ne aka yi bikin ku da Nasreen sannan yanzu kace zaka k'ara aure?" Kad'an Maleek ya yi murmushin da ya bayyana dimples d'insa ya ce "Manta kawai nikam a kanta ba abinda bazan iya ba," yana fad'ar haka ya haye stairs. Sabeeha Kuma tafiya take yi tana tunani a zuciyar ta yanzu mai zai faru da na fad'a masa nice ta waccan ranar shin ko laifi nayi masa yake nemana to amma indai ya kasance mai tunani irin nawa ne a iya haka zai gane nice wacce ya gani sannan bazan sanar da Sabreen firar mu da shi ba wata zuciyar ta ce amma kice da Sabreen ko ya tambaye ta tace ba ita bace itama wata zuciyar tace idan har Sabreen ta ce ba ita bace to dole kece saboda cikin ku ya ga d'aya domin dole bazai sa Sameeha a lissafi ba. Tab'e baki ta yi ta ce zan gani ai shan gabanta da akayi ne yasa ta tsayawa cak tana kallon Nasreen dake tsaye a gabanta tana huci cikin d'aga murya Nasreen ta ce "Uban me kika je yi wajen mijina?" Kallon banza Sabeeha ta yi mata domin ta yanke hukuncin bazata d'auki wulak'ancin Nasreen ba domin idan ta ga tana raga mata to rashin mutunci Wanda ta gani a banzan ce Sabeeha ta ce "Na kai masa abinci mana," huci kawai Nasreen ke yi ta ce "Ke nifa dukan ki ban yadda dake ba sannan baki yi mun ba haka kawai naji na tsane ki," kad'an Sabeeha ta yi dariya ta ce "Nagode da tsana ta zancen yi Kuma ba lallai sai nayi Miki ba idan har nayi wa Yallab'ai," tana gama fad'in haka ta tafi tabar banza a wajen. Binta da kallo Nasreen ta yi tana tunanin to waye yallab'an da take magana daga bayan ta ta ji Sabeeha ta ce "Bari na rage Miki aiki ba sai kin yi tunani kan wa nake magana akai ba simply ina magana ne akan Wanda aka kawoni gidan nan domin sa," tana fad'ar haka ta tafi tana dariya dan tasan dole ta kunna Nasreen. [10/25, 7:37 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️ RUBUTAWA DAGA HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ) SADAUKARWA GA MY DAUGHTER SABEEHA BILKISU Z.YA'U (🅱️K) AISHA MAGAJI DABO (AMA) Page 9 Nasreen kai tsaye part d'in mahaifiyar ta ta wuce tana shiga ta samu Umma zaune 'yan aiki zagaye da ita fad'awa jikin ta Nasreen ta yi ta saka kuka mahaifiyar tata cikin rud'ewa ta ce "Lafiya maiya faru?" Cikin kuka ta ce "Wallahi Umma na gaji da abinda ya Maleek ke yi mun," kallon 'yan aikin dake wajen Hajiya Asiya tayi tuni suka bar wajen sannan ta ce "To maiya faru?" Cikin kuka Nasreen ta labarta mata abinda ke faruwa tun daga ranar da tasa 'yan aiki suka yiwa Maleek girki da kuma tura mata Rinaz da yayi ta koya mata girki har izuwa abinda ya faru tsakanin ta da Sabeeha sannan ta fad'a mata abinda Sabeehan tayi mata yanzu sai dai bata fad'a mata abinda ya faru ba ranar da aka kaita gidan ba sai dai tace wai baya bata hakk'in ta. Cikin masifa Umma ta ce "Ke yanzu akan wata Mai aiki zaki zo kina yimun kuka to Wallahi basu isa ba me akayi akai Abdul-maleek ballantana wata banzar'yar aiki to wallahi sai sun gane kuren su kema kinsan halina sannan zancen hakk'i Kuma karna sake jinsa a bakin ki saboda dama bana buk'atar ki samu haihuwa da shi saboda dama ba zama ne ya Kai ki gidan sa ba so nake mu kwashe duk wata dukiya tashi saboda Sam ni na tsani yaron ita kuma yarinyar ki barni da ita," shiri Nasreen ta yi tana tunanin ita dai gaskiya tana son mijin nata domin irin namijin da take so ne kuma ba ma ita ba ba macen da zata ga Maleek bata ji yayi mata ba ga kyau ga ilimi ga kyau ga kud'i uwa uba bashi da wulak'anci akwai daraja mutane. Umma ta ce "Ni tashi ki bani waje kin gama bani kunya Wai kizo kina mun kuka akan wata 'yar aiki kamar bani na haife ki ba da bazaki gyara mata zaman ta ba," tashi Nasreen ta yi ta fice tana tunanin lallai ne ta koyawa Sabeeha hankali domin akan mijin ta ba abinda baza ta iya ba. Sabeeha kuwa tana shiga falon ta samu Ummi ta dawo daga office k'arasawa ta yi ta zauna k'asan carpet inda su Sameeha suke gaisar da Ummi ta amsa cikin fara'a sannan ta ce "Sabeeha daga Ina haka?" K'asa da kanta ta yi ta ce "Dama naje na kai abinci ne," jinjina kai Ummi ta yi sannan ta ce "Ina k'ara baku hak'uri akan abinda ya faru shima Son sai daga baya yaji gaskiyar abinda ya faru Kuma bai ji dad'i ba Yana da son mutane kawai rashin fahimta aka samu," Sabeeha ta ce "Wallahi Ummi bakomai," Nan suka cigaba da fira suna dariya a haka Fauwaz ya shiga ya samesu ya ji dad'in dawowar su shima zama ya yi ya aka cigaba da firar da shi ana dariya Fauwaz duk miskilancin sa yaba son 'yan uku domin suna burgesa gasu da shiga rai musamman ma Sabreen domin tana burge shi akwai ta da barkwanci da surutun tsiya. Washe gari Ummi ce ta fito cikin shirin zuwa office ta samu Sabeeha tana jera breakfast a daining har k'asa Sabeeha ta durk'usa ta gaida ita Ummi ta amsa cikin fara'a ta ce "Ni zan fita office," Sabeeha ta ce "Amma ai Ummi baki yi breakfast ba," kallon diamond watch d'in hannunta Ummi ta yi ta ce "Wallahi na kusa late ne Kuma akwai patient d'in da zan duba nayi breakfast d'in a office kawai," Maleek ne ya shiga falon yasha kyau cikin black d'in shadda yayi matuk'ar kyau kansa ba hula sai sumar sa da tasha gyara sai kyalli take yi yana zabga k'amshi. Yana k'arasawa ya ce "Good morning Ummi," ta ce "Morning Son," ya ce "Amma ba fita zaki yi yanzu ba?" Ta ce "Fita zanyi har zanyi late ma Sabeeha ki bashi abinci yaci sai na dawo," tana fad'ar haka ta yi hanyar fita zama ya yi a kan sofa ya ce "Nima Ummi zan biyo ki yanzu," ta ce "Alright sai ka iso," Sabeeha ta ce "Allah ya kiyaye hanya," "Ameen," Ummi ta amsa tare da ficewa juyawa Sabeeha ta yi zata koma kitchen d'in ya ce "Ki kawo mun breakfast d'in," ba musu ta had'a masa ta nufi inda yake ta ajiye masa komai kan center table ya ce "Baki iya gaisuwa ba ko?" Kunya ce ta kama ta ta ce "Ina kwana," banza ya yi kamar bai jita ba ta Kuma cewa "Ina kwana," ya ce "Ina fa jinki amsawa ne bazan yi ba saboda rok'a nayi," shiru ta yi tare da barin wajen. Su Sameeha ne suka shiga falon ita da Sabreen da Kuma Rinaz har k'asa suka gaishe shi ya amsa cikin fara'a Sabreen ta yi magana saitin kunnen Sameeha ta ce "Wow Sameeha dear kalli dimples Wallahi kyakkyawa ne," dariya kad'an Sameeha tayi sannan suka haye stairs zuwa d'akin Rinaz. Maleek kuwa yana gama breakfast d'in ya fice ya hau mota zuwa hospital lokacin da sojojin sa suka yi parking ya yi daidai da zuwan doctor Maryam tana gama parking ta fita daga motar tasha gayu sai k'amshi take yi lokacin Maleek ya fito daga mota har wajen ta ya k'arasa har k'asa ya tsugunna ya gaishe ta ta amsa cikin fara'a ta ce "Yaron Ummi an biyo ta kenan?" So sa Kai ya fara yi sannan ya nufi cikin asibitin yana tunanin kamar yasan Wanda ke kama da Doctor Maryam amma bazai iya tunawa ba da wannan tunanin ya shiga office d'in Ummi. A kujerar da patient ke zama ya zauna ya ce "Doctor nazo a dubani ne?" Kallon sa Ummi ta yi ta girgiza kai ta ce "Me yake damunka?" Ya ce "Ciwon nan yake yi kuma sanadin wata yarinya," ya fad'a yana nuna saitin zuciyar sa zare ido Ummi ta yi ta ce "Dagaske kake yi yana yima ciwo muje na duba ka," ta fad'a a d'an rikice dan ta d'auka dagaske yake yi. Murmushi ya yi ya ce "A'a fa doctor wasa nake yi," ajiyar zuciya Ummi ta yi sannan ta rik'o kunnen sa ta ce "Wato ka mayar dani k'awar tsokanar ka ko?" rik'e hannun Ummin ya yi ya ce "Ouch Ummi da zafi," dariya ta yi ta ce "Kai sai kace ba soja ba," shima dariyar ya yi ya ce "Ummi kinsan wani abu?" Girgiza kai ta yi ya langab'ar da kai ya ce "Banfa san wacece nagani ba waccan lokacin ashe dama su uku ne nasani dai ba Sameeha bace," dariya Ummi ta yi ta ce "Kuma ni ba ruwana ba Kai da kake gano masu laifi wannan ma ka gane da kanka," shiru ya yi ya ce "Shikenan Ummi zan gano ta da kaina," Nan suka yi ta fira abinsu. Da yamma Sabeeha ce a kitchen tana girki Sabreen na taya ta tana yi tana cin popcorn Fauwaz ne ya shiga kitchen d'in ya samu Sabreen ta zauna kan kujera tana cin popcorn d'in ta gurin ta ya nufa yakai hannu ya d'ibi popcorn d'in ya ce "yane parrot me ki ke yi a nan dan nasan ba wani iya abinci kika yi ba?" Hararar wasa ta yi masa ta ce "Ya Fauwaz nice Wai ban iya girkin ba aikuwa na iya idan nayi ma girki kaci sai kunnen ka d'aya ya tsinke," dariya ya yi ya ce "Tabd'ijan ban yadda ba wai Sabeeha haka ne?" Ya fad'a yana k'arasawa inda Sabeeha ke yi aiki murmushi ta yi ta ce "Ta iya mana," ya ce "Aikuwa zan gani wataran yanzu dai parrot tashi kije ki shirya ki rakani unguwa," tsalle Sabreen ta yi kamar 'yar baby ta ce "Yawwa ya Fauwaz kamar kasan yawo nake so wallahi bari naje na shirya karfa ka tafi ka barni," ya ce "Ok Ina jiranki a falo," ya fad'a tare da fita daga kitchen d'in itama ta fice zuwa d'akin su a can ta samu Sameeha kwance tana bacci. Hadiza ce ta shiga kitchen d'in ta kalli Sabeeha ta ce "Ya akayi naga Sabreen da gudu haka?" Dariya Sabeeha ta yi ta ce "Wai zata raka Ya Fauwaz unguwa ne shine take murna," Hadiza ta ce "Lallai jinin su yazo d'aya sosai dukan ku ma naga har dariya yake yi muku kuyi ta wasa da dariya," Sabeeha ta ce "Hmm ai haka yake," Hadiza ta ce "Tab Wallahi ba haka yake ba miskili ne duk 'yan aikin gidan nan ba ruwan sa da kowacce iya kaci mu kai masa abinci yaci bai da sakin fuska ga kowa sai yayan sa da sauran 'yan gidan nan amma yayan sa yana da fara'a babu ruwan sa duk da shima bai da shiga harkar mutane amma yana da kirki shi dai idan Kinga ya canja mana fuska to sai dai idan abinci aka Kai masa domin shi bai cin girkin mu amma Oga Fauwaz ya tab'a korar wata 'yar aiki dan kawai tace tana son sa," dariya Sabeeha ta yi ta ce "Ikon Allah," Nan dai suka yi ta fira har Sabreen ta shigo kitchen d'in tasha kyau cikin maroon d'in doguwar riga ta ce "Sabeeha dear nayi kyau kuwa?" Kallon ta Sabeeha ta yi ta ce "Sosai ma dear sai Kun dawo," ficewa Sabreen ta yi ta samu Fauwaz a falo yana jiran ta ta k'arasa ta ce "Ya fauwaz na shirya," ya ce "Wow kinyi kyau muje," suka fita a kitchen Sabeeha ta ce "Ni kuwa na rasa sanda shak'uwa ta shiga tsakanin su Wallahi," Hadiza ta ce "Au Wai baki saniba ni kuwa Ina ganin su a garden suna fira suna dariya," jinjina kai Sabeeha ta yi ta ce "Ok idan kuwa bata nan tana cemun tana garden," Nan dai sukai ta fira abinsu. Sabeeha na gama aikin ta takai komai daining ta jera sannan ta koma d'akin su tayi wanka har lokacin Sameeha na bacci sannan Rinaz ma bata nan dan haka tana gama Shirin ta ta fice daga part ta fara yawo cikin gidan tana kalle kalle abinta. Nasreen ce da Umma suka fito zasu unguwa ya yinda 'yan aiki uku ke binsu a baya d'aya na rik'e da hand bag d'in Umma tafiya suke suna fira abinsu Nasreen ce ta fara hangar Sabeeha ta ce "Umma kin ganta can duk da ba lallai idan ita ce amma zo muje," Umma ta ce "sa aninta ne mu da zamu je wajen ta?" ta kalli d'aya 'yan aikin ta ta ce "Ke Huwaila je ki kira mun waccan yarinyar," ta fad'a tana nuna mata Sabeeha. Huwaila taje ta fad'a mata waigawa Sabeeha ta yi ta kalle ta sannan ta nufi wajen tana zuwa ta kalli Umma ta ce "Ina wuni?" Kallon banza daga Umman har Nasreen suka bita da shi ganin hakan Sabeeha ta ce a ranta ashe irin su d'aya. Umma ta ce "Ke meye sunan ki?" Ko kallon ta Sabeeha bata yi ba ta ce "Sabeeha nake," jinjina kai Umma ta yi ta ce "To abinda nake so dake tun kafin na shiga maganar ki raba kanki da mijin 'yata sannan ki tsaya a matsayin ki na baiwa," "Waye mijin 'yar taki da kike magana Wai?" Nasreen ta ce "Umma Kinga halin ta ko kawai ki bari na kira Daddy na fad'a masa," Umma ta ce "Ki kyale ta ba sai baban ki ya ji ba ni nan zanyi maganin ta," Sabeeha kuwa juyawa kawai ta yi ta tafi tabar banzaye a wajen. Tafiya suka yi su ma kowaccen su na ayyana abinda zata yi mata ita kuwa Sabeeha ta dad'e tana zaga gidan sannan ta nufi part d'in Ummi tana shiga ta samu Ummi ta dawo tana zaune a falo yayin da Maleek ke tsaye ya ce "Ummi bari naje sai na dawo," ya fad'a Yana yin hanyar fita Ummi ta ce "Tom son," kallon Sabeeha ya yi kamar zai yi magana sai Kuma ya yi shiru ya wuce ta a wajen ya fice. K'arasawa ta yi ta ce "Sannu da dawowa Ummi," Ummi ta ce "Yawwa ya gidan?" Ta ce "Lafiya Ummi," tashi Ummi ta yi ta ce "Bari naje na d'an watsa ruwa," Sabeeha ta ce "To Ummi," Da dadare Sabeeha ce Zaune a gefen k'aton gadon su Sameeha kuma tana kan sallaya ta idar da sallah magrib Sabreen ta siga d'akin ta ajiye ledar hannunta ta kwanta a kan gadon Sameeha ta ce "Sabreen Wai Ina kika je ne haka?" Sabreen ta ce "Wallahi yawo muka je da ya Fauwaz munje wajen cin abinci munje munsha ice cream Kai munyi yawo sosai ga naku nan ma a leda," d'auka suka yi suna sha Sabeeha ta ce "Wai Sabreen dear meye sirrin ne?" "Na me fa?" Cewar Sabreen Sameeha ta ce "kamar ya tsakanin ki da ya Fauwaz mana," dariya ta yi ta ce "Bakomai kawai jinin mu yazo d'aya ne," shiru kawai suka yi basu k'ara cewa komai ba. Bayan sati d'aya shak'uwa ce mai k'arfi ta shiga tsakanin Fauwaz da Sabreen kullum cikin yawo suke haka Kuma sun saki jikin su a gidan suna harkokin su kamar gidan su. Maleek ne ya yi parking a k'ofar part d'in Ummi sai dai tun kafin ya shiga falon yake jin kid'a na tashi mamaki ya fara to waye da wannan aikin shiga kawai ya samu bakowa a falon sai wak'ar dake tashi a falon girgiza Kai ya yi bai kashe ba ya nemi can gefe ya zauna Yana danna wayar sa. Sabeeha ce ta fito daga kitchen hannunta rik'e da glass cup da zob'o a ciki sanye take cikin pink d'in doguwar riga Mai dogon hannu tana fita falon ta fara bin wak'ar Hamisu breaker da ta cika falon "Duk tsanani ya zam mini sauk'i da cikar samun d'an kirki ka d'orani a mulki tilas ne na tsananta kula kai mini uzuri shi nake maula zana had'a maka daula a guna kaiwa maza zarce domin kullum kai nake zance shigar ka irin ta daban ce Mai sona annurina Kuma angona ni rok'on da nake maka sirrin mu rik'e shi ta damk'e," ta fad'a tana yin juyi tare da d'ebo shoky da hannun ta d'aya. Maleek dake gefe sai kallon ta yake yi yana dariya ita kuwa batasan Yana wajen ba sai rawar ta take yi ta canja wak'ar zuwa wak'ar Mandydollz ft-selebobo (jealousy) tik'ar rawa kawai take yi. Juyawa ta yi da niyyar ajiye cup d'in hannun ta kan center table kawai suka had'a ido da Maleek da ke tayiwa rawar tata dariya cak ta tsaya ga wata kunya ta rufe ta kamar ta nutse. Har ya tashi bata motsa ba ta gaban ta ya wuce ya kashe kayan kid'an sannan ya kalle ta tuni tayi k'asa da kanta sannan a hankali ta juya ta nufi stairs ya ce "Baki ji ba" tsayawa ta yi ba tare da ta waiga ba ya ce "Kece Sabeeha right?" Saurin girgiza kai tayi alamun a'a. Dariya ya yi ya ce "Hakan na nuna kece Sabeeha saboda haka turomun Sabreen," ya fad'a tare da zaunawa ita Kuma ta haye stairs d'akin Rinaz ta shiga ta zauna kan kujera Rinaz da ta fito daga wanka ta ce "Sabeeha dear yane naji kin kashe kid'an?" D'an sosa goshi ta yi ta ce "Ammm dama yayan ki ne ya shigo shine fa ya samu ina rawa," dariya suka shek'e da ita tare da su Sameeha. Had'e rai Sabeeha ta yi ta ce "Sabreen kije inji sa," zare ido Sabreen ta yi ta ce "Ni kuma maiya faru?" D'aga kafad'a Sabeeha ta yi ta ce "Oho kije dai," tashi Sabreen ta yi ta fice a zaune ta same shi yana danna waya tace "Ina wuni ya Maleek," ajiye wayar ya yi ya ce "Lafiya zauna mana," zama ta yi k'asan carpet ya ce "Daman zan tambaye ki ne," ta gyad'a kai ya ce "Wani lokaci baya Kun kai Sameeha asibiti right?" Ta ce "Laa aikuwa haka ne ya akayi kasani?" D'an kallon ta ya yi ya ce "Manta kawai cikin ke da Sabeeha waye ya fita siyan magani?" "Bani bace Sabeeha dear ce ai har wasu 'yan daba suka bita dakyar ta had'u da wani soja shine ya taimake ta ma kasan wani abu ita fa bata sanshi ba Kuma ko fuskar sa bata gani ba amma 'yan garin sunce babban soja ne Kuma sunansa MG Malee...," Shiru ta yi tana kallon sa sai Kuma ta ce "ko dai kaine?" Murmushi ya yi a zuciyar sa ya ce Na jinjinawa surutun ki a fili Kuma ya ce "Eh nine yanzu kira mun ita Sabeehan," tashi Sabreen ta yi ta nufi stairs. Da gudu ta shiga d'akin ta ce "Sabeeha dear Wallahi shine," "Shi wa?" Dukan su suka had'a baki wajen tambayar ta ta ce "Shine sojan da ku ka had'u a waccan ranar sanda Sameeha sister ke asibiti," Sameeha ta ce "Dagaske Wai?" Sabreen ta ce "Wallahi kuwa," Rinaz ta ce "Dama ai ke nake tunani tun lokacin Yaya fa ke ba Ummi labarin ki Wai ya kamu da son ki," Sabreen ta buga tsalle ta ce "Wow love at first sight," Nan Rinaz ta cigaba da basu Labari Sabreen ta ce "Wayyo k'auna Sister kije fa yace," mik'ewa kawai Sabeeha ta yi ta fice tana tunanin wannan abu ba mai yuwuwa bane saboda a haka ma ya suka k'are da Nasreen balle idan ya ce Yana sonta. Tana fita ta samu waje ta zauna ta ce "Gani," kallon ta ya yi tare da sakin ajiyar zuciya ya ce "Dama zuciya ta tafi aminta da kece wacce nagani amma meyasa waccan lokacin kika tafi?" Tura baki ta yi ta ce "Saboda sauri nake yi," murmushi ya yi ya ce "Sai yanzu na yadda da ba aljana na gani ba domin tun lokacin tunaninki kawai nake yi ban iya cikakken bacci saboda ke ina son ki," kallon sa ta yi sannan ta mik'e ta ce "Ka ga ka dena ma saboda soyayya ni da Kai babu ita," a razane ya kalle ta ya ce "meyasa?" "Saboda ban shirya karb'an cin mutunci daga wajen matar ka ba ni bana son tashin hankali," tana gama fad'in haka tabar wajen. Wani Abu Maleek ya ji ya daki zuciyar sa rintse ido ya yi Sam bai ji dad'in maganar ta ba duk da bata ce bata son sa ba. Tashi ya yi yabar part d'in direct part d'in sa ya wuce ya kwanta akan bed d'insa yana jin wani iri yanzu idan tace bata sona fa wata zuciyar ta ce Insha Allahu bazata fad'a ba haka ya yi ta tunani. Sabeeha kuwa d'akin su ta wuce ta kwanta akan bed tana tunani anya ya kamata na sanar da shi haka kuwa wata zuciyar ta ce wannan shine kawai mafita domin Nasreen bata da kirki sam musamman akan mijin ta. Itama tunani taita yi yayinda su Sabreen ke can suna rawar murna Ummi na komawa suka bata labari itama ta yi murna sosai haka ma Fauwaz a nan gaban Ummi ya ce shima yana matuk'ar son Sabreen nan falon ya d'auki ihun murna har da Sabreen saboda itama ba kunya ta cika ba Ummi kuwa murnar da tayi ba a magana. Da daddare suna komawa d'aki suka samu Sabeeha kwance zama suka yi Sameeha ta ce "Lafiya kuwa sister ya ku kayi da ya Maleek d'in?" "Wai fa cewa ya yi yana sona Kuma ya dad'e yana sona," Sabreen ta ce "Ke Kuma ki ka ce me?" Tab'e baki ta yi ta ce "Ni kawai nace ya dena ma saboda bazan iya da Nasreen ba," tsaki Sabreen ta ja ta ce "Haba dear ya zaki ce masa haka karki manta ba fa auren soyayya suka yi ba beside ma tunda yana sonki ina ruwan ki da wata banzar matar sa?" Sabeeha ta ce "Hmmm Sabreen kenan akwai matsala a duk sanda na amsa ina son shi domin tunanina na bani akwai abubuwan da zasu faru idan har na amsa buk'atar sa kawai dai ku tayani da addu'a Allah ya zab'a mini mafi alkhairi," suka ce "Ameen," domin jikin su ya yi sanyi sosai. Maleek kuwa kwana ya yi ba bacci washe gari kuwa har office ya bi Ummi ya fad'a mata yadda suka yi da Sabeeha kamar zai yi mata kuka ajiyar zuciya Ummi ta yi ta ce "Son ka kwantar da hankalin ka tabbas Gaskiya ne abinda ta fad'a akwai rikici a wannan lamarin Kai kanka kasani musamman idan Uncle d'in ku ya samu labari Kuma nasan tsoro take ji akan abinda zai je ya dawo domin bayan hakan ba wani dalili," rik'e hannun Ummi ya yi ya ce "Please Ummi ki taimaka mun Wallahi Ina sonta so mara misaltuwa Wallahi a kanta ba abinda bazan iya ba Kuma na shirya d'aukar ko wanne hukunci daga wajen uncle," shafa kansa ta yi ta ce "Ka kwantar da hankalin ka insha Allah zata amince ka ji ni dai karka sa damuwa a ranka please," bud'e k'ofar aka yi aka shiga Doctor Maryam ce ta ce "Uwa da d'a kuna tattaunawa ne?" K'asa da Kai Maleek ya yi Ummi ta ce "Wallahi kam kin ganshi nan soyayya ce damuwar sa," zama Doctor Maryam ta yi ta ce "To meye damuwar," kaf Ummi ta zayyane mata abinda ke faruwa. Jinjina kai ta yi ta ce "Tofah ni nasan ka Kai namijin da za a so sannan Mai wuyar samu abinda za a yi kawai ku turo min ita gidana zanyi magana da ita," Ummi ta ce "To ba damuwa zata zo," Nan dai suka cigaba da tattaunawa akan maganar. Tun ranar Ummi ta sanarwa da Rinaz akan su shirya nan da kwana biyu su je gidan Doctor Maryam Rinaz ta ce "Toh Ummi," tun lokacin ta je ta sanarwa da Sabeeha akan zasu gidan k'awar Ummi Sabeeha ta tambaye ta me zasu yi Rinaz ta sanar mata akan maganar ta ne da Yaya sai kawai ta ce "Ok bakomai Allah ya kaimu," Ko da ranar tayi kwanciya Sabeeha ta yi ta ce Wai bata da lafiya ita ba inda zata Ummi ta ce Kawai tunda bata da lafiya a kyale zuwan haka aka bar zuwan Sabeeha kuwa k'arya take yi duk Dan karta je ne tayi k'aryar cuta dan wasan b'uya suka fara yi da Maleek bata bari suna had'uwa shi kuwa hakan na damunsa sosai domin idan ya ganta Yana jin farin ciki amma rashin ganin nata ne ya fara sa shi a damuwa. Yau ma kwance yake a falon sa yana tunanin ta bai San shigowar Nasreen ba kawai sai ganinta ya yi a kansa tana girgiza domin yanzu sabon salon iskanci ta tsiro da shi akan lallai sai ya kori su Sabeeha daga gidan. Tashi zaune ya yi yana kallon ta baice da ita komai ba ta ce "Wallahi bazai yuwu ba sai yaran nan sunbar gidan nan tunda bana uban su bane ko Kuma wallahi zan iya illata yarinya," kallon banza ya yi mata ya ce "Ke ki kore su mana tunda ke gidan naki uban ne ke kyale kin da nake yi fa bawai tsoron ki nake yi ba kawai ina raga Miki ne Kuma bari kiji ko kina so ko bakya so ba inda yaran nan zasu Kuma ki shirya karb'ar Sabeeha a matsayin abokiyar zama," "Kutmar uba aikuwa Wallahi baka isa ba Kai d'in banza Kai d'in wofi Kuma sannan karka kuskura kace zaka yiwa Daddy na gorin gida Kuma wallahi idan har ka auri yarinyar nan saina kashe ta," Marin da taji a fuskar ta ne ya hamata k'arasa fad'ar abinda ta yi niyya ya nuna ta da yatsa ya ce "Wallahi Ina tausaya Miki a duk sanda ki ka yi k'ok'arin tab'a Sabeeha domin ita ce rayuwata ita nake so sanin kanki ne ke ba zab'i na bace saboda haka baki isa ki hanani auren wacce nake so ba," cikin kuka ta ce "Eh tabbas laifina ne da na aure ka to bari kaji idan har ka auri yarinyar nan sai kayi Dana sanin rayuwar ka Wallahi," barin Mata wajen ya yi yana jin wani b'acin rai a zuciyar sa. Ita kuwa Kai tsaye wajen Umma ta wuce ta je tana kuka ta fad'a mata yadda suka yi da Maleek cikin masifa Umma ta ce "Mari fa kika ce shiyasa nace ki fita harkar wannan yaron domin bashi da mutunci abinda nake so dake shine ki manta da soyayyar da kike masa domin akwai yaron k'awata da nake so ki aura yanzu haka yana London yafi Maleek komai kyau da ilimi da Kuma dukiya," da sauri Nasreen ta ce "Dagaske Umma?" Ta ce "K'warai da gaske," Nasreen ta ce "Na yadda Umma a d'auki mataki a kansa sannan da Ina gani ya auri wata gara kawai a kashe shi kowa ma ya huta," Dariya Umma ta yi ta ce "An gama dama abinda nake son ji kenan sannan Shirin zai biyo ta 'yan uwan Sabeeha domin dole ne d'aya ta dawo tana mun aiki domin Shirin mu yabi ta kanta yadda ana ganewa nasan Aysha da kanta zata kore su kora irin ta karnuka domin nasan tana matuk'ar son yaron ta so mai tsanani," Nasreen dake zaune ta ce "wannan haka yake Umma," haka suka yi ta kitsa makirci kala kala. [10/25, 7:40 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️ RUBUTAWA DAGA HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ) SADAUKARWA GA MY DAUGHTER SABEEHA BILKISU Z.YA'U (🅱️K) AISHA MAGAJI DABO (AMA) Page 10 Sabeeha ce zaune a kan gadon su sai pretty dake gefen ta a kwance gyara farcen ta take yi Rinaz ta shiga d'akin da waya a hannun ta ta mik'a mata ta ce "Ga yaya," kallon wayar Sabeeha ta yi sannan ta karb'a Rinaz kuma ta juya ta fice. Kara wayar tayi a kunnen ta tare da yin sallama daga can had'add'iyar muryar Maleek ta amsa mata sallama sai kuma dukan su suka yi shiru Maleek ya d'an yi gyaran murya ya ce "Ina wuni?" D'an zare ido ta yi sannan cikin jin kunya ta ce "Ina wuni kana lafiya?" daga can ya ce "Ba lafiya," d'an kallon wayar Sabeeha ta yi sannan tasa wayar a handsfree ta ajiye ta cigaba da gyara farcen ta da nail cutter ta ce "Maiya faru?" Marairai ce murya Maleek ya yi ya ce "Please kizo part d'ina Ina so zanyi magana dake ne," jim ta yi kamar bazata yi magana ba sai Kuma ta ce "Ok gani nan," tana fad'ar haka ta katse kiran. Tana k'arasawa ta mik'e ta bud'e drower ta d'auko k'aton hijabi maroon har k'asa ta d'ora saman riga da wandon jikin tayi kyau sosai ta fice. Tafiya take yi tana tunanin to lafiya yake kirana ko dai wani abun ne a haka ta k'arasa k'ofar part d'in Kai tsaye ta shiga falon ba kowa a ciki sai sanyin Ac dake falon da Kuma wani daddad'an k'amshi da falon ke yi kujera ta samu ta zauna tana tunanin to ta ya zai san nazo gashi ban taho da wayar Rinaz ba tana cikin tunanin ne ta ji tafiya a stairs. A hankali ta kai duban ta wajen karaf suka had'a ido da Maleek dake saukowa stairs ya yi kyau sosai cikin coffee color d'in jallabiyya kallon Sabeeha kawai yake yi domin ba k'aramun kyau maroon hijabin ya yi mata ba. K'asa ta yi da kanta har ya k'arasa cikin falon ya zauna akan kujerar dake facing Wacce take kai yana cigaba da kallon ta yayin da ita kuma take wasa da yatsun ta. Kad'an ya yi ajiyar zuciya sannan a hankali ya ce "Sabeeha," saurin d'aga Kai ta yi ta kalle shi domin ji ta yi yafi kowa iya fad'in sunan ta sunan ya yi dad'i sosai a bakin sa a hankali ta ce "Na'am," tashi ya yi daga inda yake ya nufi inda take ya zauna k'asan k'afafun ta sannan ya d'aga Kai ya kalle ta ya ce "Sabiha kiyi hak'uri bani da niyyar cutar dake ki tausaya mun ina son ki i really love you with all my heart with every breath I take," shiru ya yi sannan ya ce "Ashe dama haka so yake hankali na a tashe yake saboda rashin sanin matsayina a wajen ki ko da yaushe soyayyar ki k'aruwa yake a zuciya ta ina jin zuciyata tana yi mun zafi a duk sanda na tuna bansan wanne matsayi ki ka ajiyeni ba a zuciyar ki ni ban tab'a soyayya ba ban tab'a jin son wata a raina ba sai ke ki tausayawa zuciyar da batasan komai ba sai k'aunar ki Sabeeha zuciya ta ba kowacce irin zuciya bace ban iya saka abu a raina ba komai k'ank'antar sa sai ya hanani sukuni," a hankali ya kai lallausan hannun sa ya rik'o nata hannun saurin rintse idanu ta yi domin wani shock da ta ji sannan wannan ne karo na farko da namiji ya rik'e mata hannu. Ya kalle ta ya ce "ki tausaya mun soyayyar da nake miki mai girma ce ki daure ki sanar dani matsayina a wajen ki domin na samu sauk'in abinda nake ji a zuciyata," ya fad'a yana langab'ar da Kai irin ta tausaya masa. Kallon sa Sabeeha ta yi tabbas ya bata tausayi sosai a hankali ta janye hannun ta daga cikin lallausan hannun sa ta mik'e tsaye ta kalle shi ta ce "Kayi hak'uri bana son ka bazan iya auren ka ba ka nemi wata," tana fad'ar haka ta juya ta fice da gudu tana zubar da hawaye domin ita har ga Allah tana son Maleek sai dai tana tsoron abinda zai je ya dawo a haka ma ba a kyale ta ba balle ta had'a kanta da Maleek ga halin Nasreen da mahaifiyar ta baza ta iya da su ba saboda ita ba 'yar kowa ba a illata ta a banza da sauk'i ma idan abun iya kanta zai tsaya domin tana matuk'ar jin tsoron wani Abu ya faru da 'yan uwan ta. Tafiya take yi tana zubar da hawayen tausayin Maleek domin ta tabbatar yana son ta so ba Kuma na wasa ba Kuma itama tana son shi sai dai zama lafiya yafi zama d'an sarki. Da gudu ta wuce Ummi a falo ta wuce d'akin su tana kuka mik'ewa Ummi ta yi tabi Sabeeha da kallo tana tunanin to idan har ga Sabeeha na kuka to wane hali Maleek ke ciki?? KU YI MANAGE DA WANNAN SANNAN KUYI HAK'URI DA JINA SHIRU DA KU KA YI AN SAMU WATA MATSALA NE AMMA INSHA ALLAHU ZAN CIGABA DA POSTING KULLUM KAMAR YADDA NA SABA NA GODE DA KULAWAR KU A GARENI DOMIN NAGA MASOYAN NOVEL DIN NAN SOSAI DA MASU KIRANA DA MASU YI MUN TEXT DA KUMA MASU YI MUN MAGANA TA ONLINE DUK NA GODE ALLAH YABAR ZUMUNCI. [10/25, 7:40 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️ RUBUTAWA DAGA HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ) SADAUKARWA GA MY DAUGHTER SABEEHA BILKISU Z.YA'U (🅱️K) AISHA MAGAJI DABO (AMA) Page 11 Hanyar fita Ummi ta yi hannunta rik'e da key d'in mota tana fita ta hau motar ta zuwa part d'in Maleek. Tana zuwa ta shiga falon sai ta tarar ba kowa ta wuce stairs ta tura k'ofar d'akin Maleek ta shiga da Sallama. Zaune a gefen gado ta samu Maleek a hankali ya juya ya kalli Ummi abinda Ummi ta gani shi ya yi matuk'ar razana ta hawaye ne ke zuba daga idanun Maleek gashi sunyi jajir kamar Wanda aka watsawa barkono a cikin idanun. Saurin k'arasawa Ummi ta yi ta zauna a gefen sa ta ce "Subhanallahi son lafiya me yake faruwa ne?" A hankali ya share hawayen fuskar sa ya ce "Ummi tace bata sona bazata aure ni ba," ya fad'a wasu hawayen nabin fuskar sa cikin tausayin yaron nata ta jawo shi jikin ta ta rungume shi tana shafa bayan sa ta ce "Son kayi hak'uri kaji?" "Ummi ni laifin me nayi mata da bata sona meyasa baza ta gane son da nake mata ba k'arami bane Ummi na rasa ta bansan inda rayuwata zata kasance ba Ummi ki taimaka mun," dakewa kawai Ummi ke yi amma ji take yi kamar ta yi kuka domin tausayin d'an nata gaba domin tasan son da yake wa Sabeeha bana wasa bane tunda har gashi yana kuka ta sanadin ta. Shafa sumar kansa Ummi ta yi ta ce "Son kayi hak'uri haka Allah ya k'addaro maka ka cigaba da addu'a Allah yasa hakan shi yafi alkhairi sannan dan Allah karka bar abin nan a ranka kasan baka da cikakkiyar lafiya please," a hankali ya yi noding kansa. Ummi ta ce "Yawwa soja na kayi k'ok'ari ka cire soyayyar ta a zuciyar ka kaji kayi ta addu'a," Nan ma gyad'a kai kawai ya yi domin yasan da soyayyar Sabeeha zai mutu domin baza ta tab'a fita a ransa ba. Nan dai Ummi tai ta lallab'a shi sai dai duk da haka take zazzab'i ya rufe shi dakyar ya yi wanka Ummi ta bashi tea yasha tare da magani sannan ya kwanta. Sabeeha tana shiga d'akin su kan gado ta fad'a tana rera kuka kamar ranta zai fita sai da ta yi Mai isar ta sannan bacci ya kwashe ta. Ko da su Sabreen suka ji abinda Sabeeha ta aikata basu ji dad'i ba dan kunyar Ummi suka ji ta kama su saboda yadda ta rik'e su Kuma take son su kamar ita ta haife su amma Sabeeha ba kunya tace bata son d'an da Ummi ta haifa Kuma wanda take matuk'ar k'auna. Ita kanta Sabeeha kunyar Ummi take ji sosai sai dai gani take yi hakan shine mafitar ta domin ta fuskanci Nasreen da mahaifiyar ta babu imani a zuciyar su ita damuwar ta ba a kanta bane akan 'yan uwan ta ne. Ummi kuwa bata canja musu fuska ba sai ma ninka kulawar ta da tayi a gare su. Maleek kuwa rashin lafiya yake yi sosai domin ciwon sa ne ya tayar masa gaba d'aya damuwa tayi masa yawa Ummi ce kad'ai ke kula da shi ko office dena fita ta yi tana gida tana bashi kulawa sannan tana kwantar masa da hankali tana masa nasiha Kuma Alhamdulillah yana rage damuwa domin ko da yaushe yana kai kukan sa wajen ubangiji akan Allah ya sassauta masa soyayyar Sabeeha a zuciyar sa domin soyayyar ta kullum k'aruwa take yi a zuciyar sa kuma gani yake yi idan har soyayyar ta tafi yadda yake jinta yanzu a ransa to ita ce ajalin sa. Haka Ummi ta dage wajen ba Maleek kulawa har ya warware amma Nasreen ko da wasa bata je wajen sa ba bata ma san bai da lafiya ba saboda ta yanke shawarar rabuwa da shi domin ta samu Wanda ya fi shi a cewar mahaifiyar ta. A haka har akayi sati biyu Sabeeha duk tabi ta damu kanta saboda ita kanta tasan bata kyauta ba yanzu ma kwance take a d'aki domin yanzu tafi yin wunin d'aki tunda wannan abun ya faru sannan ta lura tun lokacin Maleek bai k'ara shiga part d'in ba sannan tun ranar bata k'ara sa shi a idanunta ba wanda ita hakan shi ya dameta domin itama batasan son da take masa ya kai haka ba sai da ta dena ganin kyakkyawar fuskar sa abinci ma sai dai a Kai masa part d'insa. Tana nan a kwance Sameeha da Sabreen suka shiga d'akin zama suka yi Sameeha ta ce "Sabeeha dear lafiya tunanin me ki ke yi haka?" Kallon ta Sabeeha ta yi ta ce "Sameeha tunanin Abba nake yi tunda muka taho ba musan halin da yake ciki ba sannan da zamu taho dubu ashirin kawai muka ba zuwaira mai abinci ina so gobe naje naga halin da yake ciki," Sabreen ta ce "Sabeeha sister zanje nima please," girgiza kai Sabeeha ta yi ta ce "A'a dear ni kad'ai zani saboda bana so kawu yasan naje kuma ba kwana zanyi ba," suka ce "Allah ya kaimu," ta amsa da "Ameen," Washe gari tunda Sabeeha tayi sallar asuba bata koma bacci ba ta shiga kitchen ta fara had'a breakfast tana gamawa ta jera komai a daining sannan ta nufi d'akin Ummi. Da sallama ta shiga d'akin ta samu Ummi zaune akan sallaya tana karatun Qur'an sai da takai aya sannan ta juya tare da amsa sallamar ta ce "K'araso mana daughter," k'arasawa ta yi ta zauna ta ce "Ummi Ina kwana?" Cikin fara'a Ummi ta ce "Lafiya k'alau har kin tashi kenan?" "Eh Ummi dama Ina so ne anjima naje na duba Abba," Ummi ta ce "Lafiya dai ko?" "Lafiya Ummi kawai dai ina so naje na duba shi ne," Ummi ta ce "To shikenan ba damuwa ku shirya zansa driver ya Kai ku," Sabeeha ta ce "A'a Ummi ai ni kad'ai zanje kuma ba kwana zanyi ba saboda bana so Kawu yasan naje," jinjina kai Ummi ta yi ta ce "Ok to ki shirya sai Alasan ya Kai ki tasha," ta ce "To Ummi," daga haka ta koma d'akin su ta fara shiri. K'arfe 9 su Sameeha Sabreen da Rinaz suka yiwa Sabeeha wajen mota tana sanye da k'aton hijabi har k'asa har da nik'af a hannun ta saboda rana ta d'anyi idan taje zata d'aura saboda gudun Kar a ganta a kaiwa kawu Bala labari. Rungume juna suka yi su Sameeha suna jin ba dad'i domin gani suke yi kamar idan ta tafi bazata dawo ba Sabreen ta ce "Dear kice muna gaida Abba," ta ce "Zaiji kuma wataran zaku je ai," K'amshin had'adden turaren Maleek da ya ziyarci hancin ta ne yasa ta saurin waigawa ta kalli inda part d'insa yake domin mugun son ganin sa take yi sai dai bata gansa ba sai su Salman dake k'ofar part d'in cikin kakin su na sojoji. Kalle-kalle take yi ko zata ganshi amma har lokacin bai fito ba sai k'amshin sa da ya cika compound d'in gidan kallon su Sabreen ta yi ta ce "Saina dawo," Rinaz ta ce "Sai kin dawo ki gaida Abban," a sanyaye ta ce "To," sannan ta shige motar suka tafi su Sabreen na d'aga mata hannu. Juyawa suka yi har zasu shige part d'in Ummi wayar Rinaz ta fara ringing ta tsaya su kuma suka shige. Maleek ne ya fito daga part d'in sa ya yi wani fitinannen kyau cikin uniform d'insa ya k'ara haske sosai kansa yasha wani aski Mai matuk'ar kyau duk da ya rame amma kyau ba a magana kamar shi sace shi ka gudu da kallo Rinaz ta bi shi domin itama tasan yayan nata mak'ura ne wajen kyau da wanka har ya gaji da had'uwa. Yana zuwa ya ce "Ina kuma zata?" "Zata k'auyen su ne duba Abban su," ya ce "Baya da lafiya ne?" Rinaz ta ce "Eh to gaskiya bansani ba," d'an jinjina Kai ya yi ya ce "Alasan zai kaita kenan?" "A'a zai kaita tasha ne," kallon agogon hannun sa Maleek ya yi ya ce "Ok kice da Ummi naje NDA ba dad'ewa zan dawo," Rinaz ta ce "To a dawo lafiya," ya ce "Ameen," sannan ya juya ya nufi motar sa. Har zai shiga ya kalli Salman ya ce "Salman ku bi su Alasan har tasha sannan har garin Ina so nasan duk wani information akan ta," Salman ya ce "Ok sir," d'an hararar sa Maleek ya yi ya ce "Don't sir me I'm Maleek," yana fad'ar haka ya shige motar Salman ya rufe yana murmushi domin ogan nasa kuma abokinsa na burge shi. Jan motocin aka yi suka tafi sannan Salman ma tare da wasu daga cikin sojojin suka shiga mota suka bi su Sabeeha zuwa tasha tun a hanya suka same su Saboda a hankali Alasan ke tafiya suna tafe suna fira sojojin Maleek kuwa duk inda zaka gansu da gudu suke driving. Har tasha suka bisu kamar yadda aka umarce su suna mota a zaune har motar ta cika driver ya shiga suka tafi su Salman na biye da su. Maleek kuwa suna zuwa aka bud'e masa mota ya fita direct wani office ya shiga ya samu duk wani babban soja na wajen kowa cikin kakin sa wani soja dake tsaye ne ya ja masa kujera ya zauna sannan ya Kai duban sa wajen shugaban rundunar sojoji dake zaune kujerar dake tsakiya. Ba b'ata lokaci shugaban sojoji ya ce "Dalilin da yasa aka shirya wannan taron gaggawar wato magana ce akan the most criminal person wato Alhaji Sammani so kamar yadda ku ka sani babu Wanda a cikin mu yasan shi wanene wannan Alhaji Sammani a fuska domin ko yaushe b'oye fuskar sa yake yi yana aikata ta addanci sannan yana kashe bayin Allah da basu ji ba basu gani ba da hanyar magungunan da ake sai da su ba tare da k'a ida ba da kuma shigo da makamai suma ba bisa k'a ida ba saboda shi ya mayar da hakan sana'ar sa to wannan karon yana shirin shigo da cocaine k'asar nan tare da makamai kimanin guda dubu d'aya da d'ari biyu da hamsin Wanda mun samu wannan information d'in ne daga jami'in mu da muka tura dubai domin bincike sannan wad'an nan makamai da hodar iblis za'a turo su ne ta jirgin ruwa kamar yadda ku ka sani Alhaji Sammani yana da mataimaka wad'anda bamu san suwaye ba amma muna bincike bakin k'ok'arin mu domin gano su kuma mu d'auki mataki a kansu," Wani cikin sojojin ya ce "But sir ta ya zamu gano su bayan komai a b'oye suke yi?" "Zamu iya gano su amma idan har anyi nasarar kama wad'an nan kaya da kuma wad'an da suka d'auko kayan," Wani daban cikin sojojin ya sake cewa "Sir yanzu wanne mataki za a d'auka?" "Kusan baza mu tab'a bari a cigaba da kashe al'ummar mu ba saboda haka kamar yadda ku ka sani kuma ku ka shaida sannan ku ka yadda da k'warewa da kuma gogewar rundunar MG Abdul-maleek akan aikin su da kuma jajircewar su saboda mun samu nasarori da dama ta sanadin su saboda haka wannan lokacin ma su kasance cikin shiri domin zamu turasu duk wata hanya da mukasan wad'an nan kaya zasu shigo," Gyad'a kai kawai Maleek ya yi domin yasan rundunar sa na musamman ne sun samu horo na musamman suna da k'warewa sosai akan aikin su. Nan suka cigaba da tattauna ta yadda aikin zai kasance kowa na bada tasa shawarar. Su Sabeeha kuwa suna zuwa ta sauka a mota ta nufi gidan su su Salman na biye da ita ta d'aura nik'af sannan ta shige gidan su. Faruk dake zaune akan benci Salman ya ba hannu suka gaisa Faruk d'in nayi musu kallon tsoro ganin su sanye da uniform d'in sojoji. Salman ya ce "Dan Allah muna tambaya ne," Faruk ya ce "To Allah yasa nasani," Salman ya zauna gefen sa ya tare da nuna masa gidan da Sabeeha ta shiga ya ce "Kasan wata yarinya a gidan can mai suna Sabeeha?" Gyad'a kai Faruk ya yi ya ce "Eh nasan ta k'anwata ce Allah dai yasa ba laifi ta yi ba," murmushi Salman ya yi ya ce "Ba laifi ta yi ba amma ita da su waye a gidan?" Faruk ya ce "Ita da 'yan uwan ta ne Sameeha da Sabreen amma yanzu dukan su basa nan sunyi tafiya sai Mahaifin su kad'ai a gidan," jinjina Kai Salman ya yi ya ce "Amma mamar su fa?" Ajiyar zuciya Faruk ya sauke ya ce "Mamar mu bata nan gaskiya," Nan Faruk ya labarta musu labarin b'atan Mamar su Sabeeha. Salman ya ce "Mun gode sai anjima," daga haka suka yi sallama suka juya suka tafi. Sabeeha kuwa da sallama ta shiga gidan su ta samu Abban su zaune akan tabarma yana jan carbi zare nik'af d'in fuskar ta ta yi Abba yana ganin ta yaji wani farin ciki a zuciyar sa domin tun tafiyar su kullum tunanin sa a kansu yake yana tunanin wanne hali suke ciki shin suna lafiya ko a'a sunci abinci ko a'a wataran har kuka yake yi saboda ba mahaifin da zai so 'yan'yan sa suyi nesa da shi bayan ba aure suka yi ba kuma 'ya'ya mata ba maza ba dole hankalin sa bazai kwanta ba. Itama Sabeeha tsayawa kallon mahaifin nata ta tsaya yi cikin tausayin sa ganin ya rame sosai. Bayan ta Abba ke lek'awa domin ganin ta ita kad'ai k'arasawa ta yi ta zauna gefen sa ta ce "Abbana Ina wuni?" cikin murmushi ya ce "Lafiya qalau Ina sauran aminan nawa?" Dariya ta yi ta ce "Abba ba tare muke ba suna gida sunce na gaida Kai sosai kuma suma ai zasu zo wataran," ya ce "suna lafiya dai ko?" "Lafiya k'alau Abba dama bamu zo tare bane saboda Kar Kawu ya samu labari," shiru Abba ya yi sannan ya ce "Amma me ku ke yi a can d'in hankalina yak'i kwanciya," murmushi ta yi ta ce "Abba ka kwantar da hankalin ka aiki muke yi a wani gida Abba mutanen kirki ne sosai suna kula damu sosai Wallahi Abba matar kamar ita ta haife mu," Abba yaji dad'in hakan sosai ya ce "Alhamdulillah ko dai a can za a samo mun surukan nawa?" Dariya Sabeeha ta yi ta ce "Aikuwa Abba Sabreen dear saurayin ta a gidan yake," Abba ya ce "Masha Allah," nan suka cigaba da fira Sabeeha ta ce "Yawwa Abba ya aka yi da Sadam kuwa?" Abba ya ce "Yaya ne ya zo har gida yaci mun mutunci sannan daga baya ya aurawa Zainabu shi," tab'e baki ta yi ta ce "Allah ya basu zaman lafiya," Abba ya ce "Ameen," tashi Sabeeha ta yi ta fara kiciniyar d'ora girki domin tasan Abban nasu ba abinda yaci. Tana girki suna fira har ta gama ta zuba musu tare suka ci suka k'oshi sannan suka yi sallar azahar. Su Salman kuwa suna komawa NDA suka wuce direct office d'in Maleek suka wuce suna shiga suka samu yana duba wasu files d'aga kai ya yi ya kalli Salman ya ce "Salman zauna mana," zama Salman d'in ya yi Maleek ya ce "Me yake tafiya?" Salman ya ce "Mun je kamar yadda ka sani 'yan uku ne sannan su kad'ai ne wajen iyayen su sannan a meyere suke sannan su da mahaifin su kad'ai ne a gidan su," "Mamar su fa?" Maleek ya tambaya yana kallon Salman. Salman ya ce "Gaskiya nemar ta aka yi aka rasa ba asan inda take ba kuma tun suna 'yan 3years," tsayawa da abinda yake yi Maleek ya yi yana kallon Salman sannan ya ce "Ina da abubuwa da yawa amma jibi zamu je k'auyen," Salman ya ce "Angama," daga haka Maleek ya tashi suka nufi gida. [10/25, 7:42 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️ RUBUTAWA DAGA HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ) SADAUKARWA GA MY DAUGHTER SABEEHA BILKISU Z.YA'U (🅱️K) AISHA MAGAJI DABO (AMA) Page 12 Sabeeha kuwa sai yamma sannan ta yiwa Abban su sallama ta tafi bayan ta ba shi kud'i mai yawan gaske da Ummi ta bata a bashi sannan taje gidan zuwaira mai abinci ta k'ara mata wasu kud'ad'en. Abba kuwa sai godiya yake yi yana sa mata albarka haka ta tafi tana jin ba dad'i haka ma Abba ji ya yi kamar kada ta tafi domin ya ji dad'in zuwan ta sosai ranar ya ji shi cikin farin ciki. Sai dare sannan ta isa Kaduna mai keke napep ta samu ta shiga zuwa gida. Maleek ne tsaye a compound d'in gidan sai kai da komawa yake yi sannan lokaci zuwa lokaci yana kallon agogon hannunsa ji yake yi kamar ya bita k'auyen meyasa zata yi dare haka? Salman ne ya k'arasa wajen sa ya ce "Ranka ya dad'e da alama fa ta iso sai dai tana gate d'in farko domin bincike," k'aramun tsaki Maleek ya ja sannan ya ce "Kira mun Adam a waya," Kiran sa Salman ya yi sannan ya mik'awa Maleek wayar. Maleek ya ce "Adam ka barsu su shigo kasan dai abinda ya dace," Adam jin muryar boss d'in su jiki na rawa ya ce "Ok sir," katse wayar Maleek ya yi. Adam jiki na rawa ya hau mota har wajen Sabeeha ya bud'e mata ta shiga ya ja motar. Sarai tasan wannan umarnin Maleek ne dan haka sai zuba ido take yi ta ga ta inda zata ganshi amma babu shi sai k'amshin turaren sa da ya cika wajen Adam na tsayar da motar ta bud'e ta fice tunanin fal zuciyar ta domin zuciyar ta fad'a mata take yi Maleek ya hak'ura da ita tunda gashi ko son ganin ta baya yi. Abinda bata saniba kuwa Maleek baya son su had'u ne saboda ya tabbata idan ya ganta sabuwar soyayyar ta ce zata k'aru a ransa sai dai baya buk'atar hakan tunda har ita bata son shi. Da sallama ta shiga falon su Sabreen da gudu suka rungume ta suna yi Mata sannu da zuwa har k'asa ta tsugunna ta gaida Ummi cikin fara'a ta amsa tare da tambayar ta hanya da kuma Abban su tace "Lafiya lau Ummi yace na gaida ki," Ummi ta ce "Masha Allah Ina amsawa yanzu kije ki watsa ruwa kici abinci ki huta," ta ce "To Ummi," ta fad'a tare da mik'ewa ta nufi d'akin su. Bin bayan ta su Sameeha suka yi tana shiga d'akin ta cire hijabin jikinta ta ajiye gefen gado sannan ta cire bak'ar doguwar rigar jikin ta ta d'aura towel. Su Sabreen ne suka shiga d'akin har suna had'a baki wajen cewa "Abba yana lafiya dai ko?" Murmushi ta yi ta ce "Lafiya k'alau yake yace yana gaishe ku," a tare suka sauke ajiyar zuciya Sameeha ta ce "Ya b'angaren su Kawu fa?" Kallo mai kamar harara Sabeeha ta yi mata sannan ta ja tsaki ta ce "Oho bansani ba amma dai ya aurawa Sadam Zainabu," tsalle Sabreen ta buga ta ce "Wayyo dad'i gaskiya kan Kawu naja irin wannan had'i haka dama yana da wata macen sai ya aurawa Dauda," dariya Sameeha ta yi ta ce "Allah ya shirye ki ai Dauda yana nan yana jiran ki 'yammata," wata uwar harara Sabreen ta makawa Sameeha ta ce "Ya ishe ki malama," juyawa Sabeeha ta yi ta shige toilet tana dariya ganin yadda Sabreen ta yi kicin-kicin da fuska. Itama Sabreen juyawa ta yi ta nufi k'ofa tana cewa "Kuma yaseen ki ka yi wasa sai na fad'awa ya Fauwaz domin yasan zaman da zai yi dake," da sauri Sameeha ta rik'o hannun ta ta ce "Haba sister mie kinsan fa ni dake ba fad'a tsakanin mu Dan Allah karki fad'a masa harna fara jin kunyar sa tun kafin ki gaya masa ai Sabreen sister sai ya Fauwaz Wallahi ke da shi ba rabuwa wallahi ke da shi ba rabuwa bazar kowa bazar kowa da bazar sa ke kike taka rawa da bazar sa ke ki ke taka rawa," aikuwa Sabreen ta fara taka rawa domin wak'ar Sameeha ta faranta mata sosai. Dariya Sameeha ta yi ta fice tabar Sabreen ta tik'ar rawa ita kad'ai. Washe gari Ummi na zaune a falo tana yin waya aka bud'e k'ofar falon aka shiga falon da sallama kallon wajen Ummi ta yi mamaki ne k'arara ya bayyana akan fuskar Ummi domin ganin Umman Nasreen a part d'in ta domin rabon ta da part d'in an dad'e kuma idan har an ganta a b'angaren to ba alkhairi ne ya Kai ta ba, katse wayar ta yi tare da amsa sallamar. K'arasawa cikin falon Umman Nasreen ta yi ta zauna gefen Ummi ta ce "Aysha Ina wuni," ta fad'a tana washe baki kamar gaske Ummi ta ce "Lafiya k'alau ya yara?" Umman Nasreen ta ce "Wallahi lafiya k'alau ya su Abdul-maleek?" Nan ma da kallon mamaki Ummi ta bita domin wannan tambayar tafi komai bata mamaki domin tana da tabbacin duk duniya ba wanda Asiya ta tsana kamar Maleek amma yau ita ce ke tambayar lafiyar sa abinda bata tab'a ba kenan tun kuwa Maleek d'in na jariri. Kawar da tunanin Ummi ta yi ta ce "Yana lafiya," "Masha Allah," cewar Umman Nasreen sannan ta cigaba da cewa "Aysha dama zuwa nayi na k'ara baki hak'uri akan abubuwan da suka faru a baya nayi nadama Dan Allah kiyi hak'uri," cikin farin ciki Ummi ta ce "Haba Asiya komai ya wuce," Ummi ta fad'a zuciyar ta fal farin ciki domin dama bata da burin da ya wuce su had'a kansu ba ma tun yanzu ba dan dai kawai ita Umman Nasreen ta nuna ba hakan a ranta ne. Rinaz da Sameeha tare da Sabreen ne suka yi sallama a falon gaishe da Umman Nasreen suka yi suka wuce banda Rinaz da ta d'auke kai kamar bata ganta ba duk da hararar da Ummi ke aika mata suka haura stairs. Umman Nasreen ta ce "Aysha wad'an nan tagwayen fa?" Murmushi Ummi ta yi ta ce "Ai 'yan uku ne," nan Ummi ta bata kad'an daga cikin labarin su Umman Nasreen ta ce "Allah sarki ko zaki bani aron d'aya ta dinga zuwa tana yi mun aiki dama Huwaila taje unguwa?" D'an jim Ummi ta yi tana tunani sai kuma ta yi tunanin kar ta hana Umman Nasreen ta yi tunanin wani abu sai kawai ta ce "Shikenan sai Sameeha ta dinga zuwa tana yi miki," Umman Nasreen ta ce "To bakomai nagode," murmushi Ummi ta yi ta ce "Bakomai wallahi," daga haka Umman Nasreen ta yiwa Ummi sallama ta tafi. Bayan tafiyar ta ne Ummi ta kira Sameeha ta fad'a mata cewar zata dinga zuwa part d'in Umman Nasreen tana ta ya su wasu ayyukan kafin Huwaila ta dawo duk da akwai wasu 'yan aikin Sameeha ta ce "To Ummi," Da daddare Sameeha ta samu su Sabeeha a d'aki ta fad'a musu cewar ita fa zata fara zuwa part d'in su Nasreen domin yiwa Umman su Nasreen aiki a d'an razane Sabeeha ta kalle ta saboda tasan dole akwai abinda Nasreen da mahaifiyar ta ke k'ullawa a kansu amma sai bata nunawa su Sameeha ba ta ce "Allah ya kaimu amma sun fad'a miki sanda zaki fara zuwa?" Sameeha ta ce "A'a," Sabreen ta ce "Kai nifa ba abinda Umman Nasreen d'in nan tayi mun amma duk na tsane ta Wallahi," Sabeeha dai bata ce komai ba. Washe gari da wuri Maleek ya shirya domin zuwa k'auyen su Sabeeha k'arfe 9 ya fito daga part d'in sa ya matuk'ar yin kyau cikin light blue shadda kansa da bak'ar hula yayi kyau iya kyau kullum kamar k'ara masa kyau ake yi wayar sa ya zaro k'irar iPhone 12 pro max ya yi kira. Sabeeha na kitchen tana k'arasa had'a breakfast Rinaz ta lek'o ta saman bene ta ce "Ummi Yaya yace na fad'a miki zai je unguwa ya k'ira wayan ki bai samu ba," Ummi ta ce "Ooh ni son mai part d'ina ya yi masa da bai son zuwa Allah ya dawo mun da shi lafiya," Rinaz ta ce "Ameen," Sabeeha na jin haka ta fice ta k'ofar baya dake kitchen d'in da gudu domin bala'in son ganin sa take yi rabon da ta gansa har ta manta sai dai tana fita lokacin an bud'e masa mota zai shiga bata ga fuskar sa ba sai bayan sa ta hango Salman ya bud'e masa k'ofa ya shiga an rufe sun ja motocin da gudu. Had'adden k'amshin sa ne ya daki hancin ta da ya sata lumshe ido wanda hakan yaba hawayen da ya taru a idanunta damar zubowa a ranta tace shikenan na rasa shi na tabbata yanzu ba soyayya ta a zuciyar sa haka ta juya ta koma direct d'akin su ta wuce ta sha kukan ta ba tare da kowa ya saniba. Tana cikin kukan ne bacci ya d'auke ta ta dad'e tana baccin sannan ta farka Sabreen ce ta shiga d'akin tasha kyau sosai cikin riga da skirt na less maroon mai adon flowers silver color ta kalli Sabeeha ta ce "Sabeeha dear kin tashi dama zamu fita ne da my love," jinjina Kai Sabeeha ta yi sannan a hankali ta ce "Sai Kun dawo," kallon ta Sabreen ta tsaya yi sannan ta ce "Dear mai yake damun ki?" Girgiza Kai Sabeeha ta yi ta ce "No bakomai," Sabreen ta ce "Kinsan nasan ki nasan yanayin ki Dan Allah ki dena saka komai a ranki idan har kina son farin cikin mu," Murmushi Sabeeha ta yi ta ce "Bakomai fa kawai kaina ke mun ciwo," Sabreen ta ce "To ki sha magani ni na tafi," Sabeeha ta ce "Ok," fita Sabreen ta yi zuwa falo ta samu Fauwaz zaune ya ci ado ba k'arya ta ce "My love muje ko," tashi ya yi ya ce "Ok let's go my heart Ummi sai mun dawo," hararar su Ummi ta yi ta ce "To marasa kunya," dariya suka yi dukan su har Sameeha dake zaune kan kujera tana buga game a wayar Rinaz. Wayar Ummi ce ta fara ringing ta d'aga tana gama wayar ta mik'e ta kalli Sameeha ta ce "Daughter d'auko mun d'aya a cikin key's d'in motana a bed side drower zani hospital ne Ina da patient," Mik'ewa Sameeha ta yi ta ce "To Ummi," ta nufi stairs bata dad'e ba ta dawo sannan ta d'auki hand bag d'in Ummi ta ce "Ummi muje na raka ki motor," Ummi ta ce "To muje," har mota Sameeha ta raka ta sannan ta koma direct stairs ta nufa d'akin Rinaz. Tana haurawa stairs Sabeeha ta fito daga kitchen daidai lokacin d'aya daga cikin 'yan aikin Umman Nasreen ta yi sallama. Amsawa Sabeeha ta yi sannan 'yar aikin ta ce "Dama Hajiya ce ta aikoni ta ce gashi a bawa Sameeha lokutan da zata dinga zuwa aiki ne," tab'e baki Sabeeha ta yi sannan ta karb'a ita Kuma 'yar aikin ta fice. B'angaren su Maleek kuwa suna zuwa k'auyen sojojin sa suka diddiro daga motocin su suka nufi motar da yake ciki suka zagaye ta Salman ne ya bud'e masa mota ya fito. Gani ya yi 'yan garin sun taru suna kallon sa har da masu lek'e ta katanga sai dai ana cewa kett zasu gudu saboda kallo d'aya zaka yi musu kasan a matuk'ar tsora ce suke. Kallon Salman ya yi ya ce "Kayi mun sallama dame gidan," zauren gidan Salman ya shiga ya yi sallama Abba dake zaune bisa tabarma ya amsa sallamar sannan ya ce "Bismillah shigo," Shiga suka yi da Sallama Abba ya amsa tare da nuna musu tabarmar da yake zaune ya ce "Ku K'araso ga guri," zama suka yi sannan suka gaida shi ya amsa cikin fara'a sannan ya ce "Sai dai bangane ku ba?" Maleek ya ce "Abba ni sunana MG Abdul-maleek Hamza mai dala wannan Kuma Salman," a tsorace Abba ya ce "Lafiya dai ko?" Domin Abba yasan MG a radio k'arara mamakin ganinsa a gidan sa ya bayyana a fuskar Abba. Maleek ya ce "Lafiya lau Abba yaran ka 'yan uku a gidan mu suke ai," nan Maleek ya ba shi labarin tsananin soyayyar da yake yiwa Sabeeha da kuma k'in amincewar da ta yi sannan ya cigaba da cewa "Nayi bincike ne nagane a nan suke Kuma kaine mahaifin su sai dai Abba mamar su fa?" Kallon tausayawa Abba ya yiwa Maleek domin ba k'aramun so Maleek ke yiwa Sabeeha ba sannan Abba ba tare da tunanin komai ba ya bawa Maleek labarin auren sa da mamar su Sabeeha har zuwa b'atan ta domin haka kawai yaji ya yadda da Maleek ba ma haka ba duk Wanda yasan MG yasan yana da halaye masu kyau ga taimako. Jinjina Kai Maleek ya yi sannan ya ce "Abba ko zan samu hoton ta a wajen ka?" Shiru Abba ya yi kamar mai tunani sannan ya ce "Eh akwai bari na d'auko ma," tashi Abba ya yi ya shiga d'aki. Kawu Bala na zaune a k'asan wata bishiya kan tabarma labari ya same shi cewar ga sojoji can da bindigu a gidan k'anin sa take Kawu ya rikice ya ce "Tabdijan wacce masifa Habu ya kirawa kansa to Dan Allah karku ce ni yayan sa ne bari ma na tashi nabar nan shi kad'ai ya Kira masifar sa dan haka a kansa zata k'are," yana fad'ar haka ya kad'e babbar rigar sa ya mik'e ya zura takalman sa ya nufi bayan gari da sauri har yana had'awa da gudu. Fitowa Abba ya yi hannun sa rik'e da hoto ya k'arasa ya zauna sannan ya mik'awa Maleek hoton ya ce "Wannan shine hoton Maryam tare da k'awar ta," Karb'a Maleek ya yi ya kalli hoton a hankali ya ce "Ummina kuma?" Ya fad'a yana kallon hoton Ummin sa ce tare da doctor Maryam. Abba ya kalle shi ya ce "Kana nufin kai yaron Aysha ne?" Gyad'a kai Maleek ya yi ya ce "Eh tabbas wannan Ummina ce tare da Doctor Maryam," a zuciyar sa kuwa yana mamakin dama k'awancen Ummin sa da Doctor Maryam ya dad'e haka. Abba ya ce "Yanzu Ina Maryam take tana lafiya dai ko?" Gyad'a kai Maleek ya yi ya ce "Abba ka kwantar da hankalin ka tana lafiya Kuma nayi maka alk'awarin had'a ka da ita dama yaran ku gaba d'aya," wani farin ciki ne ya mamaye zuciyar Abba domin tun b'atan Maryam bai k'ara jin labarin ta ba sai yau domin da yana ko kwanton shin tana raye ko ta mutu amma da ya ji tana lafiya hakan ba k'aramun faranta ran Abba ya yi ba. Nan Abba ya fara zubawa Maleek Addu'a Yana sa masa albarka Maleek dai da "Ameen," kawai yake amsawa sannan ya mik'e ya ce "Abba sai ka ji daga gare ni," Abba ya ce "To Abdul ka gaida mun da Aysha sosai," murmushi Maleek ya yi ya ce "To Abba," daga haka ya ajiyewa Abba mak'udan kud'in da baisan adadin su ba ya fice Abba na yi masa godiya. Suna fita suka samu k'ofar gidan cike famm da jama'a har da wad'an da suka zo daga makwaftan garin jin labarin MG Abdul-maleek yazo sai dai ko wannen su a tsorace yake. Ana bud'e masa mota ya shige yana mamakin to meyasa Doctor Maryam bata neman mijin ta ballantana mijin ta shin meye dalilin ta kuma bayan suna raye ba mutuwa suka yi ba dole ne ya je wajen doctor Maryam ya ji daga gare ta har ma da Ummin sa da wannan tunanin suka tafi. [10/25, 7:42 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️ RUBUTAWA DAGA HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ) SADAUKARWA GA MY DAUGHTER SABEEHA BILKISU Z.YA'U (🅱️K) AISHA MAGAJI DABO (AMA) Page 13 Su Sabreen da Fauwaz kuwa yawon su suka sha sannan ya wuce wajen sai da wayoyi iPhone 11 + ya siya guda uku sannan ya biya kud'in suka nufi gida. Suna zuwa a falo suka ya da zango wayoyin Fauwaz ya mik'a mata ya ce "Wannan naku ne tare da su Sameeha," wani uban tsalle Sabreen ta buga ta ce "Wow dagaske My love," bata jira amsar sa ba ta fara k'wala kiran "Sabeeha dear Sameeha sister ku fito," yadda ta kira su ne yasa su fitowa da sauri. Rungume Sabeeha ta yi ta ce "Dear kalla my love ya siya mana waya," ta fad'a tana mik'a musu wayar karb'a suka yi suna yi masa godiya. Rinaz ce ta fito itama tana taya su murna wayoyin irin ta ta ne itama ta taya su yiwa Fauwaz godiya. Maleek kuwa sai dare suka koma gida saboda ya biya NDA a masallacin dake gidan suka tsaya suka yi sallah sannan ya k'arasa part d'insa wanka ya yi ya kwanta gaba d'aya shi kansa a d'aure yake akan lamarin Doctor Maryam meyasa zata bar yaranta mata kamar haka ko waiwayen su bata yi ko meye dalilin ta nayi hakan? Ganin babu Mai basa amsa ne yasa shi barin tunanin amma gobe zaije har hospital zai je ya sameta akan maganar. Sabeeha tare da su Sameeha ne a d'aki ta d'auko takarda ta mik'awa Sameeha ta ce "Dear gashi d'azu aka aiko miki takarda ce mai d'auke da lokutan da zaki dinga zuwa aiki part d'in Umman Nasreen," karb'a Sameeha ta yi tana dubawa. Sabeeha ta ce "Amma please sister sai kin kula sosai ko da yake nasan ke baki da shiga sabgar da ba taki ba da dai wannan ce," ta fad'a tana nuna Sabreen. Dariya Sabreen ta yi ta ce "Ai wallahi a hakan ma Umman Nasreen sai ta ga iskanci," dariya suka yi dukan su Sabeeha ta ce "Kinga Sameeha dear rabu da wannan marar aikin yin ke dai baccin wuri ne ya kamace ke saboda kinsan gobe ne zaki fara fita," Sameeha ta ce "Wallahi kuwa dear gaskiyar ki dan idan na biyewa Sabreen sister sai mu kwana nan bata dena zuba ba," ta fad'a tana kwanciya. Washe gari da wuri Sabeeha ta tashi ta shiga kitchen ta had'a breakfast sannan ta nufi d'akin su a k'ofa suka yi kacib'us da Sameeha. "Dear daga Ina haka da safiyar nan," Sameeha ta tambaya tana kallon Sabeeha wacce kallo d'aya zaka yi Mata kasan a gajiye take Sabeeha ta ce "Daga kitchen mana kinga ki je aikin ki kada kiyi latti," tana fad'ar haka ta shige cikin d'akin Sameeha Kuma ta fice zuwa part d'in Umman Nasreen. Tun kafin Sameeha ta shiga falon ta fara jiyo muryar Umman Nasreen na narka zagi daram dam gaban Sameeha ya fad'i dakewa ta yi ta shiga falon da sallama ko amsa mata sallamar ba a yi ba sai marin wata 'yar aiki da Umman Nasreen ke yi. K'arasawa wajen Sameeha ta yi ta tsugunna ta ce "Hajiya ina kwana?" Wata uwar harara Umman Nasreen ta aikawa Sameeha sannan ta ce "Wannan Kuma wani salon iskancin ne sau nawa Kuma zaki gaishe ni ko ni sa'ar wasan kice?" Girgiza kai Sameeha ta yi tana tunanin to yaushe tazo part d'in ma da har ta gaishe ta. Bud'e baki Sameeha ta yi a hankali ta ce "Yi hak'uri Hajiya yanzu wanne aikin zanyi?" Cikin masifa Umman Nasreen ta ce "Bayan aikin da ki ka gama yi yanzu amma tunda neman aikin ki ke yi jeki ki gyaramun store yanzu," mik'ewa ta yi sannan ta ce "To Ina ne kitchen d'in?" Wani uban zagi Umman Nasreen ta yiwa Sameeha ta ce "To uwar ki ma ta yi kad'an ta raina mun hankali balle ke yanzu ki yi wanke-wanke kibar kitchen d'in amma yanzu ki zo kina tambaya ta kitchen zaki wuce ko sai nayi ball dake?" Saurin matsawa Sameeha ta yi ta nufi inda take tunanin kitchen ne zuciyar ta fal tunanin anya kuwa Umman Nasreen bata ci Kai ba kuwa. Tana shiga ta ga kitchen d'in ne kuwa zama ta yi kan wata kujera ta zabga tagumi hawaye ne ya fito daga idanunta ita dai duk inda zata aiki sai ta fuskanci wannan matsalar. Share hawayen ta ta yi ta fara aikin da aka sata kamar ance ta kalli window ta hangi Sabreen tana yarfe hannu da alamu ta yi aikin ruwa take maganar Sabreen ta jiya da daddare ta fad'o mata da take cewa a hakan ma sai Umman Nasreen ta ga iskanci. Murmushi Sameeha ta yi sannan ta cigaba da aikin ta har ta gama sannan ta fito daga kitchen d'in ta samu Umman Nasreen zaune akan kujera ta ce "Hajiya na gama," kallon banza Hajiya Asiya ta watsa mata sannan ta ce "B'ace mun da gani," juyawa Sameeha ta yi da sauri tabar falon. Maleek ne ya fito tsaf cikin Shirin sa na zuwa hospital wajen Doctor Maryam Sabeeha na kitchen Hadiza ta shiga kitchen d'in hannun ta rik'e da breakfast d'in Maleek da ta tafi kai masa ajiyewa ta yi kallon ta Sabeeha ta yi ta ce "Lafiya ki ka dawo da breakfast d'in?" Hadiza ta ce "Cewa ya yi a dawo da shi ya k'oshi," shiru Sabeeha ta yi tana jin zuciyar ta ba dad'i tunani take yi ba dai har girkin nata ya dena ci ba? Ummi ta jiyo tana cewa "Son na lura da kai kwana biyu sam baka son cin abinci ballantana ka sha drugs d'in ka," muryar Maleek ta jiyo yana cewa "Sorry Ummina Ina da abubuwa da yawa yanzu fita zanyi," da gudu Sabeeha ta nufi k'ofar barin kitchen d'in zuwa falo sai dai kafin ta fita Maleek ya fice. Yana fita mota ya shiga sai hospital wajen Doctor Maryam jiniya ke tashi a garin Kaduna a duk inda motocin MG suka gifta. Suna zuwa asibitin sojojin sa suka zagaye motar da yake ciki Salman ne ya bud'e masa k'ofa ya fito sannan suka nufi cikin asibitin direct office d'in Doctor Maryam suka nufa knocking Salman ya yi daga ciki Doctor Maryam ta ce "Yes come in," tura k'ofar suka yi suka shiga da Sallama. Cikin fara'a Doctor Maryam ta amsa musu sallamar tare da cewa "m "Maraba da yaron Ummi ku zauna," zama suka yi tare da gaishe ta ta amsa cikin murmushi sannan ta ce "Yaron Ummi yau Ina Ummin fa fatan tana lafiya?" K'asa Maleek ya yi da kansa yana sosa kai ya ce "Tana lafiya tana gida," Doctor Maryam ta ce "Masha Allah," ta fad'a tana gyara zaman farin glass d'in dake idanta. Maleek ya ce "Mama dama wata magana ke tafe dani," ajiye biron hannunta Doctor ta yi ta ce "Tom Ina jinka," "Mama ko kinsan wani malam Abubakar a k'auyen meyere?" Maleek ya fad'a yana kallon ta hawaye ne ya zubo daga idanun Doctor Maryam sannan kamar an tsikare ta ta mik'e tsaye tana kallon Maleek ta ce "Wallahi nasan shi yana ina? Wanne hali yake ciki Ina yarana?" Ganin duk ta rud'e ne Maleek ya ce "Mama ki kwantar da hankalin ki please zauna," komawa ta yi ta zauna ta ce "Son please yana ina?" Ajiyar zuciya Maleek ya sauke ya ce "Come down Mama yana nan lafiya amma Mama meyasa duk tsawon lokacin nan baki neme sa ba?" Share hawaye ta yi ta ce "Bansani ba amma duk lokacin da nayi niyyar zuwa na duba lafiyar su sai wani abun ya d'auke mun hankali na rasa meyasa hakan ke faruwa dani bansan wanne hali yake ciki ba bansan halin da yarana ke ciki ba bazan iya jurewa ba yanzu zan tafi naje na ga halin da suke ciki," Maleek ya ce "A'a Mama ki kwantar da hankalin ki nayi miki alk'awarin had'a ki da mijin ki da kuma yaran ki duka," Nan dai Maleek ya yi ta kwantar mata da hankali har ta hak'ura. Sabeeha na zaune a d'akin su Sameeha ta shiga d'akin ta zauna sannan ta kalli Sabeeha ta ce "Sabeeha sister kinsan me?" Girgiza Kai Sabeeha ta yi. "Kinsan Sabreen sister ita taje ta yi mun aiki kafin naje a part d'in Umman Nasreen," nan dai ta bawa Sabeeha labari dariya Sabeeha ta yi ta ce "Kyale ta karki nuna mata kinsani ki barta ta cigaba da taya ki dama ita ce mara aikin yi ai," Sameeha ta ce "Wallahi kuwa amma fa naji tsoron Umman Nasreen saboda zagin da tayi mun," Sabeeha ta ce "Ki kyale ta wannan ita da mahaliccin ta," daga haka ta mik'e tabar d'akin. Maleek kuwa ya dad'e a asibitin suna magana da Doctor Maryam sannan ya yi mata sallama suna fitowa daga office d'in aka kira shi a waya daga wajen aikin su dan haka direct NDA ya wuce daga can kuma JAJI barrack ya wuce bashi ya koma gida ba sai yamma wanka kawai ya yi ya kwanta domin hutawa saboda ya gaji da yawa domin zuwa ya yi ya had'a tawagar sa da zasu tura domin aiwatar da aikin tsayar da shigo da cocaine cikin k'asar nan dan haka bai samu damar ganawa da Ummi ba kamar yadda yaso domin ya yi waya da Rinaz ta kuma tabbatar masa dukan su suna falo shi kuwa bai son zuwa ya ga Sabeeha beside ma ga gajiyar dake damun sa. Washe gari Maleek ya nufi part d'in Ummi bai samu kowa a falo ba ya haura stairs ya tura k'ofar falon dake saman a can ya hangi Ummi zaune saman kujera gama wayar ta kenan da Daddy. K'arasawa Maleek ya yi ya zauna gefen Ummi ya ce "Sannu da hutawa Ummina," shafa kansa Ummi ta yi ta ce "Yawwa son," d'an gyara zaman sa ya yi sannan ya ce "Ummi Wai dama k'awancen ki da Doctor Maryam ya dad'e haka?" Murmushi Ummi ta yi ta ce "Eh mana ai tare muka yi karatu da ita a malesia lokacin da muka dawo hutu ne ni ban koma ba nayi aure ita Kuma ta koma har lokacin da na haife ka tana can kuma dalilin da yasa baka santa ba a lokacin saboda baka k'asar kana Dubai," gyad'a kai Maleek ya yi sannan ya ce "Ummi ashe dama tana da miji a k'auyen meyere?" Nan fa Maleek ya bata labarin zuwan sa wajen Abba dama zuwa wajen Doctor Maryam da ya yi. Farin cikin Ummi kasa b'oyuwa ya yi domin kuwa har hawayen farin ciki ta yi ta ce "Yanzu son kana nufin su Sabeeha yaran Maryam ne?" Noding kansa Maleek ya yi sannan ya ce "Ummi ni mamakina meyasa duk tsawon lokacin nan bata je k'auyen ba bata damu da ta duba lafiyar mijin ta da yaran ta ba wanda tun suna 3 years rabon ta da su?" "Son kenan Maryam mutuniyar kirki ce kowa yana yaba halin ta ko sanda muna malesia kamar yadda na fad'a ma tare muka yi karatu da ita sai dai ni muna zuwa hutu ban koma ba nayi aure ita Kuma ta koma har ta gama lokacin Kuma na haife ka lokacin kana Dubai sanda ta dawo ne iyayen ta suka ce ta fito da mijin aure amma ita Sam a maneman ta bata samu Wanda take so ba har iyayen ta suka fara tunanin ko aljanu ne suka aure ta domin lokacin kai ka gama primary school d'in ka kwatsam ta bani labarin ta had'u da wanda take so naji dad'in hakan sosai domin nima lokacin burina shine ta yi aure sai dai sam iyayen ta suka nuna basa son Abubakar saboda ita kad'ai iyayen ta suka haifa sannan suna da dukiya hakan ne yasa su basa so 'yar su ta auri talaka nasan Abubakar sosai saboda wasu lokutan har nan gidan suke zuwa su yi fira saboda basu da damar yin fira a gidan su Maryam saboda tsananin mahaifin ta akan Abubakar," shiru Ummi ta yi sannan ta cigaba da cewa "Har duka mahaifin Maryam yasa aka yiwa Abubakar akan ya rabu da Maryam amma hakan baisa ya ji a ransa zai rabu da Maryam ba daga k'arshe ma iyayen Maryam suka ce idan har ta nace sai ta auri Abubakar to basu ba ita haka ta amince aka yi auren su ya tafi da ita meyere sai daga baya ta samu daidaitawa da iyayen ta sai dai ta fuskanci matsaloli sosai daga matar yayan Abubakar Bala dama shi kansa balan kullum musguna mata suke yi sai dai Maryam macece mai hak'uri bata nunawa a hakan ta samu cikin 'yan uku harta haife su kwatsam watarana Maryam ta dawo gida ba a cikin hayyacin ta ba abun kamar shafar aljanu hakan ne yasa k'anin mahaifin ta Kawu Bashir tsayawa tsayin daka wajen nema mata magani harta samu sauk'i sai dai idan aka tambaye ta mijin ta da yaran ta bazata ce komai ba abu kamar wasa Maryam bata maganar su ni da kaina naje k'auyen sau da yawa amma sai dai Bala ya ce mun shima rabon sa da Abubakar ya manta har na gaji na dena zuwa," ajiyar zuciya Maleek ya yi ya ce "Ummi duk abinda yake faruwa da alamu akwai hannun wan mahaifin su amma bincike ne zai tabbatar da hakan," Nan suka cigaba da tattaunawa akan lamarin. Hankali a matuk'ar tashe Sabeeha ta shiga d'akin su ta fad'a saman gadon su ta saka kuka a hankali ta fara magana "Meyasa zata aikata hakan shin wanne irin laifi muka aikata mata?" Jin za a bud'e k'ofar d'akin ne yasa ta daidai ta nutsuwar ta Sameeha ce ta shiga d'akin ta zauna ta ce "Sabeeha dear kinsan yau ma Sabreen sister ita taje ta yi aiki a madadina," murmushin da iyakar sa fuskar ta Sabeeha ta yi ta ce "Kyale ta idan ta gaji zata dena dan kanta," Sabreen ce ta shiga d'akin tana rik'e da pretty a hannunta ta kalli Sabeeha ta ce "Sabeeha dear da alama fa pretty bata da lafiya gaba d'aya tak'i taci abinci bari mu kaita asibiti ni da my one," "Ayyah sorry pretty," Sameeha ta fad'a sannan ta kalli Sabreen ta ce "Sister nagode da aiki fa," kallon rashin fahimta Sabreen ta yi mata Sabeeha ta yi saurin cewa "Sabreen dear please ku tafi Kinga pretty sai kuka take yi," juyawa Sabreen ta yi ta fita tana cewa "sai mun dawo," ta fice. K'ara matsawa kusa da Sabeeha Sameeha ta yi ta ce "please dear duba mun forehead d'ina kiga naji ciwo," Sabeeha ta ce "Mai ya same ki a wajen?" D'an tura baki Sameeha ta yi ta ce "Munyi karo da wani ne?" "Wanene," cewar Sabeeha "Nima bansan shi ba amma ya tambaye ni ko nice Sabeeha nace mishi a'a," Sameeha ta fad'a tana shafa goshin ta Sabeeha ta ce "Ayyah sorry dear," Sabreen na fita falon daidai lokacin Maleek ke saukowa stairs gaishe shi suka yi ita da Fauwaz ya amsa da "Lafiya," ya fad'a yana kallon pretty sannan ya ce "Wannan magen fa?" Sabreen ta ce "zamu kaita asibiti ne ni da my one bata da lafiya ta Sabeeha dear ce," baice komai ba Fauwaz ya ce "My heart mu tafi ko," hararar sa Maleek ya yi a zuciyar sa ya ce na jinjinawa rashin kunyar ku daga haka ya fice. Part d'insa ya nufa yana shiga falon ya tsaya yana kallon Umar dake kwance saman kujera sai murmushi yake saki shi kad'ai aikuwa ya kyalkyale da dariya har da rik'e ciki domin duk Wanda ya ga Umar sai ya dara. K'arasawa Maleek ya yi ya ce "Lafiya kake kuwa," wani Murmushin Umar ya yi ya ce "MG wallahi nayi matar aure a gidan nan kana kallon ta kasan hankali nutsuwa tarbiyya sun samu a wajen ta," "Wacece," Maleek ya tambaya yana zama gefen Umar. "Gaskiya bansani ba amma suna kama da Sabeeha na tambaye ta ko ita ce ta ce A'a," shiru Maleek ya yi ya ce "Idan kuwa ba Sabeeha bace to kuwa Sameeha ce," Umar ya ce "Wallahi ina son ta please ka taimaka mun ta wannan b'angaren," D'an hararar sa Maleek ya yi ya ce "To bud'e zuciyar ta zanyi nasa mata sonka idan har dagaske kake to kaje da kanka ka same ta," ya fad'a yana nufar stairs Umar ya ce "Amma dai kasan ban tab'a yaudarar d'iyar kowa ba ko?" Maleek ya ce "Ta ya zan sani bayan ban dad'e da dawowa k'asar ba," yana fad'ar haka ya shige bedroom d'in sa. [10/25, 7:43 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️ RUBUTAWA DAGA HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ) SADAUKARWA GA MY DAUGHTER SABEEHA BILKISU Z.YA'U (🅱️K) AISHA MAGAJI DABO (AMA) Page 14 Bayan kwana biyu Sabeeha ce kwance akan gado tana buga game a wayar ta sai pretty dake gefen ta a kwance. Tashi zaune ta yi ta tankwashe k'afar ta sannan ta ajiye wayar tana shafa jikin pretty. Da gudu su Rinaz suka shiga d'akin suka fad'a kan gadon suna ihu saurin sa hannuwanta Sabeeha ta yi ta toshe kunnuwan ta sannan ta ce "Lafiya ku ke kuwa?" "Dear jibi birthday d'in ku fa," cewar Rinaz itama Sabeeha ihun murna ta saki ta fara tsalle akan gadon Sameeha ta ce "Wayyo harna matsu ranar tayi akwai shagali," Sabreen da ta kwaso shoky ta ce "Ke dai bari sister ai akwai kodumo," Rinaz ta kalli Sabeeha ta ce "Ummi ta ce mu Kira ki ne fa," tsayawa da rawar da take yi tayi sannan ta ce "Muje to," Tare suka fita falon Rinaz ta ce "Ummi Ina Kuma yayan ya tafi?" Ummi ta ce "Cewa ya yi zai fita may be akwai inda zashi ko da wata matsala ce?" Girgiza kai Rinaz ta yi ta ce "Naso dai yana nan zamu yi tsare-tsaren celebrating d'in," tana rufe baki wayar ta tayi k'ara alamar shigowar sak'o. Tana dubawa ta buga tsalle ta ce "Wow Ummi yayane ya turo mana 2 million muje shopping," murmushi Ummi ta yi ta ce "Ya kyauta kuwa sannan dalilin kiran ku shine ina ga zaku Kai birthday party d'in ku gidan Doctor Maryam saboda ranar ina da bak'i," Rinaz ta ce "To Ummi bari muje gidan Maman," Ummi ta ce "No ba sai kunje ba zansa ayi komai," Umar ne ya shiga falon sai tura baki yake yi kusa da Ummi ya zauna sai cika yake yana batsewa shafa kansa Ummi ta yi ta ce "Son lafiya?" Tura baki ya yi ya ce "Ummi ni da Maleek ne tun shekaran jiya nake masa magana akan yarinyar da nake so ya taimakamun amma sai yace wai bud'e zuciyar ta zai yi yasa mata sona naje da kaina idan kuma bata sona na hak'ura tunda ba a so dole," Dariya Rinaz da Sabreen ke yi har ma da Ummi. Sabeeha kuwa gaban ta ne ya yi mummunar fad'uwa jin abinda Umar ya fad'a kenan hakan yana nufin itama ya hak'ura da ita kenan take ta ji wasu hawaye na neman zubo mata saurin mayar da shi ta yi. Ummi ta ce "Manta da Son kasan halin sa ni nan zan taimaka maka fad'a min wacece yarinyar," matsawa kusa da Ummi Umar ya k'ara yi ya ce "Zo kiji Ummi," rad'a ya yi mata yana kallon Sameeha. Murmushi Ummi ta yi sannan ta ce "Kai ku bamu guri," tashi suka yi dukan su Ummi ta ce "No banda ke Sameeha zauna," komawa Sameeha ta yi tana kallon Umar sarai ta gane shi shine wanda suka yi karo. Kallon ta Ummi ta yi ta ce "Daughter kina da saurayi kuwa?" Kallon ta Umar ya tsaya yi dan jin me zata ce. Girgiza Kai ta yi ta ce "A'a Ummi," saurin sauke ajiyar zuciya Umar ya yi ya ce "Yawwa Ummi kinji bata da shi," hararar wasa Ummi ta yi masa ta ce "Babu ruwan ka a maganar mu if not zan fasa taimakon," jan bakin sa ya yi yayi shiru Dan kar Ummi ta fasa. Mayar da kallon ta Ummi tayi kan Sameeha ta ce "Daughter tunda baki da saurayi to ni nayi miki yaro ne mai hankali da sanin ya kamata sannan zai baki kulawa sosai dan haka ki rik'e shi gam haka zalika nasan shima zai rik'e ki sosai da kulawa domin samun irin ki a yanzu abu ne mai wuya," ajiyar zuciya Ummi ta yi sannan ta cigaba da cewa "Idan ya yi miki laifi ki fad'a mun dan bazan lamunci rabuwa a soyayyar dana had'a ba sannan daughter karfa ki yi tunanin ba wai shi yace Yana son ki ba A'a da kansa ya ganki yake sonki," d'an tsayawa Ummi ta yi sannan ta ce "Kaga ni bakina ya gaji da magana ka cigaba da kanka," tana fad'ar haka ta mik'e hannun ta rik'e da wayar ta ta nufi stairs. Kallon Sameeha ya yi sannan ya ce "Kin dai ji abinda Ummi tace ki rik'e ni gam domin idan ki ka rasani baza ki tab'a samun sumulmulin saurayi kamata ba," dariya maganar tasa ta bawa Sameeha sai ta ce "Idan nace bana yi fa karfa ka manta ban amsawa Ummi cewar ina sonka ba," d'an zare ido Umar ya yi ya ce "A'a Dan Allah karki ce haka Kuma ai nasan baza ki k'ibin zab'in Ummi ba," ya fad'a yana yin kalar tausayi. Murmushi Sameeha ta yi domin dariya Umar ke ba ta Yana da barkwanci d'aga ido ta yi ta kalle shi ya langab'ar da kai ya ce "Ki tausaya mun Kinga ni maraya ne," dariya Sameeha ta yi ta ce "Bayan lokacin da ka bugeni a kai ko hak'uri baka bani ba," ta fad'a tana tura baki. "Ayyah lokacin k'ararrawar zuciya ta kad'awa take yi a kanki dan tun lokacin ki ka tafi da imanin Umar," k'ara tura baki Sameeha ta yi ta ce "To bani hak'uri," Saurin saukowa daga kujera Umar ya yi ya ce "Wannan shi yafi komai sauk'i," rik'e kunnuwan sa ya yi ya ce "Kiyi hak'uri zuciyar Umar," Su Sabeeha dake lek'e ta saman bene Sabeeha ta ce "Ah lallai Sameeha dear irin wannan kwasar love haka," Sabreen ta buga tsalle ta ce "Shegiya Sameeha dear ashe dama haka ta iya love gaskiya za a kwashi love da ruwa ruwansa yaseen wayyo Allah," Sabeeha ta ce "Dear ku kalla gashi sun dace sosai gaskiya na taya ta murna sosai samun miji irin ya Umar abu ne mai wuya," Sai lokacin Rinaz ta ce "Gaskiya kam hakane sai dai wata ta samu Wanda ya fi shi amma tace bata yi," Sabreen ta ce "Wallahi kuwa Rinaz habibty," shiru Sabeeha ta yi domin tasan gaskiya suka fad'a a zuciyar ta ta ce hmm baza ku gane ba 'yammata. Diamond watch d'in hannun ta Rinaz ta kalla sannan ta ce "Sister's time na tafiya fa ya kamata mu tafi shopping yanzu," down stairs suka nufa suka samu Sameeha da Umar sai fira suke abinsu suna dariya. Suna zuwa Rinaz ta ce "Sameeha dear ki taso mu tafi time na tafiya," kallon ta Umar ya yi ya ce "Ina zaku kuma?" Sabreen ta yi caraf ta ce "Zamu je shopping ne jibi ne birthday d'in mu," hararar ta Sabeeha ta yi kamar ita aka tambaya. Umar ya ce "Amma abin ba gayyata?" Sabreen ta ce "Karka damu ai indai Sameeha sister na wajen to kaima kana nan," hanyar fita Sabeeha ta yi a zuciyar ta ta ce na jinjinawa surutun ki Sabreen. Kallon Sabeeha Umar ya yi ya ce "Ita ce Sabeehan Maleek ko?" Rinaz ta ce "Eh ita ce," Mik'ewa Umar ya yi ya ce "To muje nayi muku rakiya zuwa shopping d'in," suka fita a waje suka samu Sabeeha ta tsirawa k'ofar part d'in Maleek idanu domin burin ta bai wuce ganinsa ba. Mota suka shiga su uku a back seat Sameeha a front seat. Suna zuwa suka fara jidar kaya mayafai leases jakunkuna sarka agogo dogayen riguna kayan make up da sauran kayayyaki suna gamawa Umar ya biya kud'in sannan suka nufi gida. Godiya suka yi masa sannan suka shige gida suka barshi tare da Sameeha suka yi sallama sannan ya tafi yana jin wata zazzafar soyayyar Sameeha a zuciyar sa. Ko da suka shiga gida Ummi suka nunawa kayayyakin itama ta yaba kyansu domin kayane masu matuk'ar tsada ga kyau ta ce "An godewa son," daga haka suka tafi d'akin su. Washe gari suka fita zuwa saloon bayan an gama musu suka ce da Alasan ya kaisu gidan abincin Hajiya fulani. Da gudu Aysha ta rungume su Sabeeha tana murnar ganin su suma haka Office d'in Hajiya Fulani suka shiga suka gaishe ta ta amsa cikin fara'a suka ce dama sunzo su fad'awa Aysha birthday celebration d'in su ne da za a yi gobe. Fulani ta ce "Masha Allah,Allah ya k'aro shekaru masu albarka," suka amsa da "Ameen," sun jima suna fira sannan suka yiwa Fulani sallama suka fita. Rakiya wajen motor Aysha ta yi musu Rinaz ta kalle ta ta ce "Please goben kizo da wuri banda African time," Aysha ta ce "To ba damuwa sai goben," suka yi sallama suka tafi. Daga nan gidan su Dija suka wuce da sallama suka shiga k'aton falon Dija dake zaune ta tare su cikin farin ciki suka rungume juna sannan suka zauna. Sabreen ta ce "Ina Aunty fa?" Dija ta ce "Tana bedroom d'in ta," Rinaz ta ce "Beb me zaki kawo mana ne yunwa nake ji," Dija ta ce "Meye na tambayana bayan kinsan hanyar kitchen," tashi Rinaz ta yi ta shiga kitchen ta d'ebo snacks da lemuka ta kawo musu suka fara ci. Aunty ce ta sauko daga stairs tana cewa "Muryar suwa nake ji kamar 'yan uku?" Suka ce "Mune aunty," suka gaishe ta ta amsa cikin fara'a sannan suka cigaba da firar yadda birthday celebration d'in zai kasance. Sai yamma sannan suka yi musu Sallama suka tafi gida daidai lokacin da suka shiga gidan lokacin motocin Maleek ke fita bin motar da Maleek ke ciki Sabeeha ta yi da kallo duk da tinted windows ne ji take kamar ta tsayar da su dan kawai ta ganshi. "Su waye a motar can?" Maleek ya fad'a yana kallon Salman. "Sir Ina ga su Rinaz ne domin naji d'azu tana cema Alasan zai kai su saloon," shiru Maleek ya yi baice komai ba. Washe gari tunda Wuri Sabeeha ta tashi ta gama had'a breakfast tana zaune gefen gado Rinaz ta shiga d'akin cikin wasu pink d'in sleeping dress da earpiece a kunnen ta da alama waya take amsawa. Zama ta yi gefen Sabeeha tare da fad'in "Wow sweetheart da gaske to Allah ya dawo da Kai lafiya," daga haka ta katse Kiran Sabeeha ta ce "Man d'in ne?" Dariya Rinaz ta yi ta ce "Shine kam," sannan ta ce "Ina Sameeha dear ne?" "Tana part d'in Umman Nasreen," cewar Sabeeha kallon Sabreen dake sharar bacci Rinaz ta yi ta ce "Ah lallai dole kiyi bacci jiya fa har 12 suna tare da ya Fauwaz," Sabeeha ta ce "Aikuwa dai bari na yi wanka," tana fad'ar haka ta cire kayan jikin ta ta d'aura towel ta shige wanka. Tana fitowa ta samu Rinaz ma ta yi kwanciyar ta gefen Sabreen tana bacci. Sameeha ce ta shiga d'akin da Sallama kana kallon ta kasan ta gaji zama ta yi tare da fad'in "Wash!" Sabeeha ta ce "Sorry dear," "Dear dama haka Sabreen ke shan aiki yau da bata je ba Baki ga aikin da nasha ba," Sameeha ta fad'a tare da nufar inda Sabreen ke kwance ta bata light kiss a goshin ta ta ce "Nagode dear," Murmushi Sabeeha ta yi ta ce "Nikam yunwa nake ji zan fita naci abinci," towel Sameeha ta zara ta ce "Nima Bari nayi wanka na biyo ki nima yunwa nake ji," daga haka ta shige toilet Sabeeha kuma ta k'arasa Shirin ta ta fice. Kitchen ta shiga ta had'a tea d'in ta mai kauri sannan ta d'ebi chips a plate ta nufi falo ta zauna taci ta k'oshi sannan ta Kai kayan kitchen ta fito can gefen falon wajen wasu set d'in kujeru ta je ta kwanta sai bacci. Da yamma suka fara Shirin su takanas Ummi tasa aka d'auko musu make over ta shek'e musu fuskokin su sunyi kyau har sun gaji dogayen rigunan dark blue d'in material suka sa duka su hud'un anyi musu d'aurin da red abu kamar ka sace su ka gudu musamman su Sabeeha dan baza ka iya banbance su ba sun zama su uku iri d'aya. Falo suka fita Ummi ta kalle su ta ce "Masha Allah yarana kunyi kyau," suka had'a baki wajen cewa "Thank you Ummi," sannan suka zazzauna. Wayar ta Sabreen ta d'auka tare da dialing number d'in Fauwaz yana d'agawa ta ce "Hello my one kana ta Ina ne haka?" Daga can ya ce "Sorry cwt gani nan fitowa," Daga haka ya katse Kiran. K'ofar part d'in Fauwaz d'in aka bud'e ya shigo ya yi matuk'ar kyau cikin k'ananun kaya sai k'amshi yake zabgawa domin Fauwaz akwai kyau da d'aukar wanka tunda ya shiga falon yake kallon su shi a dole yana so ya gano Sabreen a cikin su. Zama ya yi a kujerar da take facing Wacce suke kai yana kallon su d'aya bayan d'aya sannan ya kalli Ummi ya ce "Nikam Ummi Ina Sabreen cikin su?" Dariya falon ya d'auka Sabreen ta ce "Ashe dama my one baza ka iya gane ni ba?" Ya ce "No zan iya mana baby amma idan bakwa tare kamar haka," k'ofar falon aka bud'e aka shiga Dija ce tasha kyau cikin doguwar riga da murna suka tare ta ita kuwa sai yaba kyan da suka yi take yi. Suna zaune nan Umar ya shiga falon yasha wanka cikin dark blue d'in k'ananan kaya ya yi kyau ba k'arya yana shiga yabi su Sabeeha da ido domin sunyi kyau har zai yi magana Ummi ta ce "Son ya kamata ku tafi time na k'urewa," kallon Rolex watch d'in hannunsa ya yi ya ce "Ummi daga wajen Maleek nake akan yazo mu tafi sai ya ce Kawai muje zai zo daga baya," Ummi ta ce "Shikenan kuje kawai," hanyar fita suka yi Sabeeha ta ce "To Ummi kefa sai yaushe?" "Karku damu zamu zo tare da son," cewar Ummi su Kuma suka fita. A waje suka ci karo da Aysha da ta dad'e da zuwa amma tun a gate d'in farko aka tare ta dan bincike sai da Salman ya yi magana sannan aka barta ta shiga itama ta yi kyau ba k'arya cikin doguwar riga pich color. Ba b'ata lokaci suka shiga mota suka tafi mota biyu suka yi. B'angaren Kawu Bala da Abba kuwa sai da labari ya samu Kawu Bala cewar sojojin da suka zo gidan Abba sun tafi sannan ya nufi gidan a zaune ya samu Abban kan tabarma kallo d'aya zaka yi masa kasan yana cikin farin ciki. Kawu Bala ya ce "Kai habu na samu labarin sojoji sunzo gidan ka hala cikin yaran ka ne d'aya ta jawo maka masifa ko?" Cikin farin ciki Abba ya kalli yayan nasa ya ce "A'a yaya yau na samu labarin inda Maryam take Abba anga Maryam d'inta," daram dam gaban Kawu Bala ya fad'i maimakon ya yi farin ciki da ganin matar k'aninsa da aka yi sai ma wata uwar zufa da ya had'a yasa Kai ya fice kawai. Tafiya kawu Bala yake kamar zai kifa tsabar sauri tun daga zaure yake k'wala kiran "Lantana! lantana!!" "Haba malam wanne irin kira ne wannan kamar naci bashi lafiya dai ko?" Yarce gumi Kawu ya yi sannan ya ce "Ina fa lafiya Lantana Maryam zata dawo yanzu Habu ke fad'a mun ya samu labarin ta," take itama Lantana ta rud'e ta ce "Shikenan mun shiga uku malam bamu ga ta zama ba mu tafi wajen bokanya kawai," gyalen ta ta yayi ba akan igiyar shanya suka fice suna zuba uban sauri. Har titi suka fita suka hau mota tafiyar da suka yi ba wata mai nisa bace sannan aka ajiye su suka hau machine sai da suka yi tafiya mai nisa sannan suka sauka suka fara tafiyar k'afa wani daji suka nufa mai sauk'in bishiyu sai da suka yi tafiya mai nisan gaske sannan suka isa wata bukka. Tun kafin su k'arasa wajen bukkar wata murya mai ban tsoro ta ce "Ku dakata dama sai da na fad'a muku idan har ku ka yi kuskuren k'in barbad'a wannan maganin na kwana d'aya a k'ofar gidan to tabbas zata dawo kuma sannan kamar yadda ku ka hana Habu yin arziki zai yi arziki sannan ku kuma zaku d'and'ana talauci mai zafi ku je ku tafi ku jira dawowar ta domin tabbas zata dawo ba abinda zamu iya," take jikin su Kawu ya mutu suka juya a sanyaye suka nufi gida. Tun a hanya Kawu Bala ke fad'a "Wallahi Lantana ke dai ba mutuniyar arzik'i bace akan meyasa baki barbad'a maganin na kwana d'aya ba?" Lantana ta share gumi ta ce "Wallahi Malam mantawa nayi ranar gidan Zainabu na wuni shiyasa," tsaki Kawu ya ja ya ce "Ai shikenan sai muje muyi ta fama tunda kin dai ji abinda bokanya ta fad'a aikin banza aikin wofi," yana fad'ar haka ya yi gaba abinsa. B'angaren su Sabeeha kuwa wani dank'areren gida suka ga an nufa gidan ya tsaru iya tsaruwa upstairs ne sannan bai da wani girma amma ya had'u matuk'a da. Ana bud'e musu gate suka shiga da motocin su suka yi parking sannan suka shiga cikin falon gidan da shima ya had'u sosai 'yan aiki ne ke kai da komo a falon zama suka yi akan kujeru Rinaz ta kalli d'aya daga cikin 'yan aikin ta ce "Halima mama fa?" Wacce aka yiwa maganar ta ce "Tana bedroom d'inta," tashi Rinaz ta yi ta nufi d'akin Doctor Maryam tana shiga ta samu tana wanka falon ta koma ta zauna suka cigaba da fira. Bayan wajen minti talatin motocin Maleek suka yi parking a compound d'in gidan Doctor Maryam fitowa sojojin sa suka yi suka zagaye wacce yake ciki. Salman ne ya bud'e masa mota a hankali ya ziro k'afar sa sannan ya fito gaba d'ayan sa wayyo ya had'u iya had'uwa har ya gaji da yin kyau shadda yasa blue black sai shek'i da kyalli take yi color d'in ta matuk'ar yi masa kyau tare da fito da hasken farar fatar sa da kullum k'ara kyau take yi kansa ba hula sai bak'in gashin kansa daya sha gyara bana wasa ba askin kan nasa ma abin kallo ne sai kyalli yake yi kamar a tab'a saboda d'aukar hankali. Bak'in tsadadden agogon dake hannunsa ya kalla ya lumshe manyan idanunsa mai d'auke da zara-zaran eye lashes sannan ya kalli Salman ya ce "Kira mun Umar a waya," yana d'agawa Maleek ya ce "Yane na iso," daga haka ya katse kiran. Daga can Umar ya mik'e ya ce "Mu k'arasa ciki," wata k'ofa suka nufa suna shiga a tare dukan su suka furta "Wow," domin wajen ya had'u sosai yasha decoration ko ina sai walwali da kyalli yake yi ga wasu fitilu masu color da suke haska gurin wajen sai tashin k'amshin wani d'addan turare yake yi ga k'amshin snacks da kajin dake wajen ga kuma k'amshin turaren su da Kuma sanyin Ac ga kuma wani music dake tashi a wajen mai kwantar da hankali. Tuni Sabreen da Fauwaz suka fara falla hoto hakama Sameeha da Umar su Rinaz da su Aysha ma lalacewa suka yi wajen d'aukar hoto. Murmushi Sabeeha ta yi tana tunanin da tuni itama tana nan suna nasu hoton da MG tsayawa ta yi tana kallon su har sai da su Sabreen suka jata sannan aka cigaba da hoton da ita. Sai da suka gama hotuna sannan su Sabeeha suka nufi inda aka tanada domin su suka zauna cake kuwa yafi kala ashirin a wajen wannan yana wane wannan wannan yana wane wannan wajen kyau da tsaruwa. Tura k'ofar wajen aka yi aka shiga da sauri Sabeeha ta kalli k'ofar saboda k'amshin turaren sa da taji ya cika falon aikuwa tana kallon wajen suka had'a idanu. Kallo d'aya ya yi mata ya gane ta saurin kawar da idanunsa ya yi ba dan komai ba sai dan fad'uwa da gaban sa ya yi domin wata soyayyar ta ce ta k'ara dasuwa a zuciyar sa. Sabeeha kuwa a zuciyar ta ta ce Yanzu kam na gama yadda ya hak'ura dani saboda ko san ganina baya yi sake kallon sa ta yi a zuciyar ta ta ce Masha Allah irin wannan azababben kyau haka gaskiya Allah ya yi halitta a wajen nan. Kallo ne ya koma kansa saboda had'uwar da ya yi duk da wajen ba wani wadataccen haske Salman dake bayan sa ne ya ja masa kujera ya zauna ya fara danna wayar sa sai basarwa yake yi domin bai cika son kallo ba. Umar ne ya fara gabatarwa tare da yi musu birthday wishes Fauwaz ya yi Rinaz ma ta yi haka ma su Dija da Aysha suka taya su murna cikin had'adden turancin su wanda ba gargada domin 'yan boko masu ji da aji da ilimi aka had'a a wajen. Kallo ne ya koma kan Maleek domin shima ya taso ya yi musu wishing amma bai ko motsa ba sai ma danna wayar sa da yake yi Umar ya ce "MG gare ka we are waiting," "For what?" Maleek ya fad'a ba tare da ya kalli inda Umar yake ba. Umar ya ce "U have to say something," hararar Umar d'in ya yi ya ce "No need," har Fauwaz ya bud'e baki da niyyar magana Maleek ya d'aga masa hannu saurin jan bakin sa ya yi ya tsuke. Sabeeha kuwa bata san sanda ta saki murmushi ba saboda ganin hararar da ya watsawa Umar a hankali ba tare da kowa ya ji ba ta ce "komai ya yi kyau yake masa," Murmushi Umar ya yi sannan ya fito da gift d'insa wasu diamond rings ne da diamond watch masu matuk'ar kyau da tsada ya d'auko a cikin wasu akwati ya bawa kowa d'aya sai dai akwai banbanci a zoben Sameeha domin nata anyi masa ado da shape d'in heart. Godiya suka yi sannan Fauwaz shima ya gabatar da nasa gift d'in shima rings ne sai agogunan gold masu kyan gaske nan ma suka yi godiya Rinaz ma ta yi musu kyautar rings Dija ma da Aysha duk suka basu gifts. Suna gamawa kowa ya mai da hankalin sa kan Maleek sarai yasan kallon sa suke yi mik'ewa ya yi tare da zaro wasu k'ana nan akwati masu kyau guda biyu daga aljihun sa ya nufi gaban table d'in. Kowa mamaki yake yi ya kits d'in guda biyu yana zuwa ya ajiye d'aya gaban Sameeha d'ayar kuma gaban Sabreen. Kowa na wajen tambayar kansa yake yi to Ina na sabeeha fa Sabeeha kuwa k'asa ta yi da kanta ita kanta tasan bata cancanci kyauta daga Maleek ba sai dai lokaci d'aya ta d'aga kanta jin tsayuwar sa a gaban ta. Hannun sa ya mik'awa Salman dake bayan sa wani had'adden kwali Salman ya mik'a masa shi kansa kwalin abun kallo ne farine tas sai adon Red flowers a jiki sai tashin k'amshi yake yi ya ajiye gaban Sabeeha sannan ya juya ya kalli mutanen wajen ya ce "Kyauta na ta gaba na zuwa," ya kalli Salman dake tsaye. Hanyar fita Salman ya yi domin ya gane ma'anar kallon. Kowa zuba ido yake yi domin ganin kyautar Maleek ta gaba. [10/25, 7:43 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️ RUBUTAWA DAGA HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ) SADAUKARWA GA MY DAUGHTER SABEEHA BILKISU Z.YA'U (🅱️K) AISHA MAGAJI DABO (AMA) Page 16 Bayan fitar Nasreen zama su Sabeeha suka yi akan kujera kowa zuciyar sa fal mamakin abinda su Nasreen suka so aikatawa Maleek. Sameeha kuwa har lokacin hawaye take yi ta ce "Wai dama har yanzu akwai masu irin wannan zuciyar a duniya?" Rinaz ta ce "Hmm gasu ma sai dai mu yi addu'ar Allah ya tsare mu daga sharrin su," suka amsa da "Ameen," Sabreen ta ce "Ai dama da ganin wannan rafkeken kai na Nasreen bazai yi ja ba," duk da suna cikin jimami sai da suka dara Fauwaz ya ce "Wallahi kuwa my love munsani ma dake muka kyale su," Sabreen ta ce "Wallahi kuwa da wani k'ananun idanun ta kamar na 'yan china," nan ma dariya suka yi banda Sabeeha da take zaune har lokacin bata ce komai ba can ta mik'e tabar falon. Direct part d'in Maleek ta nufa ko d'aya a cikin sojojin dake tsaron k'ofar ba Wanda ya hana ta shiga domin Salman ya sanar da su matsayin ta a wajen Maleek har Sara mata suka yi ita kuwa shigewa kawai ta yi. Tana shiga ta hangi Maleek kwance saman kujera idanunsa a lumshe kamar mai yin bacci k'arasawa ta yi sannan ta zauna k'asan lallausan carpet d'in dake malale a wajen tana kallon sa. A hankali ya bud'e idanunsa ya sauke su a fuskar Sabeeha sannan ya tashi zaune yana mai cigaba da kallon ta ita kuwa ta yi k'asa da kanta tana wasa da yatsun ta. "Say it out kamar da magana a bakin ki," Maleek ya fad'a yana k'ura mata ido a hankali ta d'aga kanta suka had'a ido a hankali ta ce "Dama tambayar ka zanyi meyasa su Umman Nasreen suke son kashe ka?" D'an murmushi ya yi ya ce "Bansan ainahin dalilin ba amma dai nasan Umman Nasreen ta tsane ni tun ina jariri," Zare ido Sabeeha ta yi ta ce "Jariri fa to meyasa hakan?" Ajiyar zuciya Maleek ya sauke ya ce "Sunan kaka na Alhaji Muhammad Mai dala wato wanda ya haifi Daddy kenan yana da mata biyu Hajiya Sadiya da Hajiya Hauwa'u suna zaune zaman lafiya da kwanciyar tare da yaran su Uncle da Daddy shi Uncle d'ane ga Hajiya Hauwa'u Daddy Kuma yaron Sadiya amma idan kaje gidan baza ka iya bambance hakan ba domin suna son junan su da yaran su suna basu kulawa sosai suna gatata su sosai," d'an shiru Maleek ya yi sannan ya cigaba da cewa "A inda aka fara samun matsala shine a duk sanda aka zo ba da result a makaranta Daddy ne ke d'aukar first class saboda yana da k'ok'ari sosai sab'anin Uncle da yake d'aukar kusan na k'arshe duk da ba ajin su d'aya da Daddy ba kuma sosai Uncle yana zuwa makaranta kuma yana Mai da hankalin sa sosai sai dai shi haka Allah ya yi shi kwakwalwar tasa bata d'auka a duk sanda aka raba result suka kaiwa mahaifin su sai ya yiwa Daddy kyauta duk dan saboda Uncle ya k'ara dagewa amma ba wani canji abun sai ya damu Uncle sosai tun yana yin kuka har ya dena ya dawo tsangwamar Daddy da nuna masa tsana shi kuwa Daddy baya damuwa domin sau da yawa ko mahaifin su ya ba Daddy kyauta sai ya barwa Uncle abu kamar wasa Uncle ke nunawa Daddy k'iyayya da mahaifin su ya lura da hakan sai ya fara k'ok'arin daidaita tsakanin su amma abu yaci tura tun yana Nasiha ya dawo fad'a daga k'arshe har duka amma ba abinda ya canja haka iyayen suka zuba musu ido lokacin da Uncle ya gama secondary School d'insa sai aka tura shi k'asar waje karatu yayin da Daddy ke secondary ko da shima ya gama sai aka tura shi Dubai karatu yayinda Uncle ke London mahaifin su ne ya yanke shawarar k'in had'a su karatu a k'asa d'aya domin rashin jituwar dake tsakanin su a haka uncle ya gama karatun sa ya samu aiki a can Landon d'in wani hutu ne da Daddy ya je gida ya samu mahaifin su baida lafiya bayan gajeriyar jinyar da ya yi Allah ya yi masa rasuwa sunyi kukan rashin sa sosai haka ma matan sa haka Daddy ya cigaba da karatun sa yana gamawa ya fito da result mai kyau sai rububin d'aukar sa aiki ake yi a k'asashe daban daban kasancewar sa architecture ne a wani campany a Dubai d'in Daddy ya fara aiki yayin da bak'i ciki yake fal zuciyar Uncle domin ganin babban matsayin da Daddy ya samu a campany ga salary d'in Daddy yafi nasa a haka rayuwar su ta cigaba Daddy na zuwa Nigeria sosai domin duba lafiyar mahaifiyar sa ga Kuma kud'ad'e dake shigowa tako Ina domin zuwa lokacin Daddy Yana da campanies nasa har guda biyar a lokacin ne kuma rashin lafiya ya kama mahaifiyar sa har k'asar waje Daddy ya fitar da ita amma satin ta d'aya ta rasu Daddy ya yi kuka sosai haka ma hajiya Hauwa'u domin sunyi zaman lafiya da Sadiya a haka Daddy ya koma bakin aikin sa wata rana Daddy ya je malesia domin duba wani campany nasa dake can a nan ne ya had'u da Ummi suka k'ulla soyayya har Ummi ta bashi dama ya tafi Nigeria ya samu iyayen Ummi aka gama magana domin Mahaifin Ummi yasan mahaifin Daddy hakan ne yasa da Ummi tazo hutu bata koma ba ta yi aure Daddy ya d'auke ta suka koma Dubai da zama arzik'in Daddy kullum k'aruwa yake yi domin yanzu Campanies d'in sa goma ne kowa yasan shi a haka har maganar auren Uncle ta tashi amma Uncle bai ko fad'awa Daddy ba amma hakan bai hana Daddy d'aukar Ummi su zo bikin ba sai dai basu samu kallon arzik'i wajen Uncle ba sai ma yana d'ora idanunsa kan Ummi ya ji ya mugun tsanar ta domin tafi amaryar sa kyau da ilimi hakan ne yasa uncle ya ji kamae ya fasa auren domin shi baya so a komai Daddy ya fi shi haka aka gama shagalin biki Uncle ya tafi da amaryar sa Landon su Daddy ma suka koma Dubai," shiru Maleek ya yi Sabeeha ta ce "Cigaba please," kallon ta Maleek ya yi ya ce "Bakina ya gaji," Langab'ar da Kai ta yi ta ce "Please," d'an shiru ya yi sannan ya cigaba "Bayan auren Uncle ba dad'ewa Hajiya Hauwa'u ta auri wani d'an kasuwa mai suna Alhaji sammani sai dai auren bai dad'e ba itama ta rasu lokacin bayan wata biyu da faruwar hakan aka kori Uncle daga wajen aiki saboda kama shi da laifin cin amana da aka yi haka ya d'auki hajiya Asiya suka koma Nigeria duk wasu kud'ad'e da Uncle ke da shi haka suka saka a gaba suka cinye shi da Hajiya Asiya daga nan ne fa suka fara rayuwar talauci wata rana labari ya jewa Daddy cewar d'an uwan sa na cikin wani hali ko da Daddy ya ji labari sai da ya yi kuka domin jin halin da d'an uwan sa da bai da kamar sa ke ciki Wai ace d'an uwan sa ne ke cikin halin talauci bayan shi gashi baisan adadin dukiyar sa ba ba Wanda baisan shi ba babu shiri Daddy ya tafi Nigeria lokacin Ummi tana da ciki lokacin da yazo Nigeria ya ga halin da Uncle yake ciki sosai Daddy ya yi kuka yana cewa idan laifi ya yiwa d'an uwan nasa ya yafe masa domin bai cancanci haka daga gare shi ba ace d'an uwan sa yana cikin wannan hali amma sai dai ya ji a gari shi Kuma yana can da dukiya me zai yi da ita idan bai taimakawa d'an uwan sa ba duk kukan da Daddy ke yi k'in sauraron sa Uncle ya yi sai da Daddy ya yi sati guda yana rarrashin Uncle akan ya yi hak'uri su bishi zuwa Dubai amma Sam Uncle yak'i yadda haka Daddy ya fara Shirin komawa Dubai domin ya baro Ummi ita d'aya a daren ranar ne Hajiya Asiya ta ba Uncle shawara akan cewar ya ce da Daddy idan har da gaske Yana son taimakon sa to ya dawo Nigeria da zama su zauna tare Kuma a gida d'aya domin so take su cinye duk abinda Daddy ya mallaka take Uncle ya yadda da shawarar ta domin itama Hajiya Asiya halin su d'aya da mijin nata wajen bak'in ciki da hassada ko da Uncle ya samu Daddy da maganar sosai Daddy ya yi farin ciki Kuma ya yadda da hakan domin ko ba komai ya samu hanyar kyautatawa d'an uwan sa ko da Daddy ya fad'awa Ummi itama ta yi farin ciki ko ba komai itama zata baro Dubai domin ta ishe ta gashi idan tana kusa da gida zata fi jin dad'i saboda iyayen Ummi suna Abuja tana da yayye biyu maza sai k'anwar ta mace itama a Abuja ta yi aure," cikin gajiya da magana Maleek ya kalli Sabeeha da ta yi shiru tana sauraron sa ya ce "Zan k'arasa miki wataran yanzu na gaji," mak'e kafad'a ta yi ta ce "Ni dai uhm uhm yanzu nake so," D'an girgiza kai ya yi ya ce "Ok kina ji ba cikin k'ank'anin lokaci Daddy yasa aka gina musu wannan gidan shi da Uncle suka dawo sai dai Ummi sam bata jin dad'in zaman gidan saboda Daddy baya samun zama sannan b'angaren zaman ta da Hajiya Asiya kuma ba dad'i domin wani irin kishi Hajiya Asiya ke nunawa Ummi kamar kishiyar ta ga rashin mutunci na yau daban na gobe daban Ummi kuwa ko da wasa bata tab'a gayawa Daddy ba domin tana son a zauna lafiya a haka har aka haifeni Daddy ya yi farin ciki sosai ya yinda Uncle k'iri-k'iri ya nuna bai ji dad'in hakan ba shi da matar sa saboda basu so Daddy ta samu d'a namiji ba domin gani suke yi nan gaba wannan yaron zai kawo musu tsaiko a lamuran su a haka na tashi cikin kulawar Daddy da Kuma Ummina idan naje part d'in Uncle kuwa da kuka nake barin sa hakan ne yasa na dena zuwa domin tsana suke mun ta musamman kamar ma wacce suke mun tafi tsanar da suke yiwa iyayena gashi na yo kamar Ummina hakan ba k'aramar k'iyayya ya k'ara ja mun ba wajen Umman Nasreen Ummi ma hakan ne yasa ta yanke shawarar ta bawa Daddy ni ya tafi dani can Dubai nayi primary da secondary d'ina a can haka muka tafi da Daddy can nayi primary da secondary school d'ina daga nan ne na sanarwa da Daddy nikam soja nake son zama Daddy kuwa ya amince mun da haka lokacin muka zo Nigeria a nan ne na ga wata yarinya a gidan Ummi ke fad'a mun yarinyar Uncle ce wacce namiji suka so haifa ba mace ba ni kuwa ko kallon yarinyar banyi saboda tun tana k'aramar ta bata da kunya ga rashin girmama na gaba da ita ban dad'e a Nigeria ba Daddy ya turani Russia ni da Salman d'a a wajen k'awar Ummi a bayan zuwan mu Russia munyi shekaru da dama inda aka yi passing out ya yinda na fito da wannan matsayin na MG inda ake ji dani sosai a aikin wanda aikina zai kasance a office ne sai dai ni bani da sha'awar zaman office na fi so duk wani aiki na fita ayi shi dani domin taimakon k'asa ta tunda na dawo daga Russia Nasreen ta nuna cewar tana sona amma ni sam bana son ta domin bata d'aya daga cikin irin matan da nake so sai dai ko da Uncle ya fad'awa Daddy maganar haka Daddy ya dage dan dole aka yi auren a yanzu sai abinda Uncle ya ce da Daddy shi ake yi a gidan nan Wanda na rasa dalilin hakan yayinda ni tsanata ke k'aruwa a wajen su Uncle domin sun san bazan tab'a bari su cuci Daddy na ba Ina tunanin hakan ne yasa Umman Nasreen ta yanke hukuncin kashe ni Wanda ita kanta Nasreen ba tasan ainahin dalilin da yasa Umman ta ta yadda da batun a kashe ni ba Sabeeha gidan nan ana yin wata iriyar rayuwa duk wani kud'i da motoci da Uncle ke da shi duk na Daddy ne Uncle na iya iko da komai na Daddy amma sam baya son jinin Daddy abun na d'aure mun kai na samu labarin Uncle na yin wata sana'a amma har yanzu bansan meye ba na dai sa ayi mun bincike wannan shine tarihin gidan nan," Wani tausayin Maleek da Daddy ne ya kama Sabeeha har hawaye ta goge jin yadda Daddy ke k'aunar d'an uwan sa amma shi Uncle ba wanda ya tsana kamar Daddy da matar sa dama yaran su duka. Mik'ewa Maleek ya yi ya nufi stairs shan gaban sa Sabeeha ta yi ta ce "Tambaya d'aya," cikin gajiyawa da magana Maleek ya kalle ta ya ce "Kiyi mun afuwa malama Sabeeha questioner yanzu kam na gaji ma had'u next time," girgiza Kai ta yi ta ce "Please wannan ne na k'arshe," noding kansa ya yi. Ta ce "To maganar cutar da naji kuna yi da Ummi fa wane ciwo ke damun ka?" D'an murmushi ya yi ya ce "Ciwon zuciya ne Wanda haka na taso na ganni da shi amma yana dad'ewa bai tashi ba saina shiga damuwa," yana fad'ar haka ya ya wuce. K'ara shan gaban sa ta yi ta yi k'asa da kanta lumshe ido ya yi ya bud'e a kanta ya ce "Yanzu kuma mene?" Murmushi ta yi ta ce "Dama wata tambaya ce d'aya ta rage shine nace bari na tambaya karna manta," dariya taso ba shi ya dake ya ce "Uhm Ina jinki," "Daman cewa nayi yaushe rabon da ciwon ya tashi?" D'an shiru ya yi sannan ya k'ara matsawa gaban ta ya ce "Tun sanda ki ka ce baki sona har yanzu Ina kan shan magani," k'asa ta yi da kanta sannan ta d'aga Kai ta kalle shi ta saki murmushi ta ce "To daga yanzu sai ka dena sha," "Meyasa hakan?" Ya tambaye ta tare da k'ura mata ido juya idanun ta ta yi ta ce "Saboda yanzu Ina son ka," wani farin ciki Maleek ya ji a ransa ya ce "To meyasa da d'in baki Sona?" dariya ta yi ta ce "Waye ya fad'a maka ai ko da d'in ina son ka kawai dai akwai abinda nake tsoro ne," murmushin da ya bayyana dimples d'insa ya yi ya ce "Yanzu fa?" D'an kara matsawa gaban sa ta yi ta d'aga idanunta ta kalle shi ta ce "Sai dai idan a mutu a kanka," tana fad'ar haka ta juya da gudu tabar falon dariya ya yi ya haye stairs yana jin yanzu bai da wata sauran damuwa. Nasreen kuwa da kuka ta shiga part d'in su ta baje akan carpet tana rusa kuka domin sai yanzu da Maleek ya sake ta ta gane ba k'aramun so take yi masa ba da sauri Hajiya Asiya ta sauko daga stairs tana cewa "Mamana lafiya ko har ya mutun?" Banza Nasreen ta yi da ita sai ma k'ara volume da ta yi. Hajiya Asiya ta ce "Ko baki fad'a ba nasan ya mutu yanzu Ina gawar tasa take?" Kallon ta Nasreen ta yi ta ce "Na shiga uku Umma ya Maleek ya sake ni," "Bangane ya sake ki ba yana gawar ya sake ki ko me?" Hajiya Asiya ta fad'a tana son sanin Mai ya faru cikin Kuka Nasreen ta ce "Umma bai mutu ba yana raye gaba d'aya waccan yarinyar ta lalata mana shiri," Nan Nasreen ta zayyane abinda ya faru. Ba tare da alamun nadama ba Hajiya Asiya ta ce "Kutmar uba shi Abdul-maleek har waye shi da zaici mana mutunci to wallahi duk sai sun gane kuren su," "Ni dai wallahi Umma mijina nake so kawai ni ki mayar dani," Nasreen ta fad'a tare da hayewa stairs da ido Hajiya Asiya ta bita har ta b'acewa ganinta. Su Sabeeha kuwa tana zuwa part d'in Ummi basu dad'e ba Fauwaz ya tafi mayar da su gidan Mama. Maleek kuwa yana shiga d'akin sa wanka ya yi ya fito cikin bak'ak'en k'ananun kaya ya yi kyau ba k'arya Kai tsaye part d'in Ummi ya nufa. Yana shiga falon ya samu ba kowa sai ya wuce stairs nan ma ba kowa bedroom ya tura ya shiga da sallama Ummi dake zaune gefen gado ta amsa masa sallamar tare da juyawa ta kalle shi a lokaci guda kuma hawaye na fitowa daga idanunta ga idanun nata sunyi ja sosai. Da sauri Maleek ya k'arasa ya tsugunna akan lallausan carpet d'in d'akin ya rik'o hannun Ummi ya ce "Ummina lafiya maiya faru?" Cikin hawaye Ummi ta ce "Meyasa Abdul me kayi musu da suke son raba ka da duniya wannan wacce iriyar k'iyayya ce?" Ummi ta fad'a tana hawaye d'an murmushi Maleek ya yi domin yasan hakane yasa Ummi kuka ya ce "Ki kwantar da hankalin ki Ummi su basu isa su yi mun abinda Allah bai mun ba kuma duk abinda suke yi Allah na ganin su," jinjina Kai Ummi ta yi ta ce "Allah ya yi maka albarka ya k'ara karemun Kai a duk inda kake," ya ce "Ameen Ummina addu'ar ki mai tasiri ce a gare ni," ya fad'a yana share mata hawaye. Tashi Ummi ta yi rik'e da hannun sa ta ce "Taso muje na yima abinci nasan baka ci komai ba," mik'ewa ya yi suka sauka down stairs har kitchen ya bi Ummi wai lallai sai ya taya ta girkin. Tare kuwa suka shiga tana yi tana cewa ya mik'a mata wani abun har suka gama suka fita falo a daining suka zauna Ummi da kanta ta bashi abincin har ya k'oshi ta kalle shi ta yi murmushi ta ce "To yanzu fad'a mun kana farin ciki da amsa soyayyar ka da daughter ta yi?" Shiru ya yi ya kalli had'adden p.o.p celling d'in falon alamar tunani sannan ya kalli Ummi ya ce "Eh Ummina I'm very happy har na matsu ranar auren ta yi," dungure masa kai Ummi ta yi ta ce "Marar kunya a gaban nawa," rik'o hannun Ummin ya yi yayi masa kiss yana dariya itama Ummin tana dariya ya ce "To Ummi bayan ma Sabeehan ta yi tafiyar ta gidan Mama," Ummi ta ce "To ai tace zata dinga zuwa yima abinci," murmushi ya yi. Sai da suka d'an yi fira sannan ya yiwa Ummi sallama ya koma part d'insa ya yi sallah ya kwanta bacci zuciyar sa fal farin ciki. Da daddare Sabeeha na kwance akan gadon su wayar ta ta fara ringing d'aukar wayar ta yi tana kallon ta cikin mamaki domin ita har mantawa take yi tana da waya tunda ba Kiran ta ake yi ba d'agawa ta yi tare da yin sallama daga can had'add'iyar muryar Maleek ta amsa mata sallamar zare ido ta yi kamar yana gaban ta ta ce "Ya Maleek are you amma a Ina ka samu number nah?" Murmushi ya yi ya ce "A radio," had'e fuska Sabeeha ta yi cikin shagwab'a ta ce "Yanzu number d'in nawa ake raba ta radio?" Dariya Maleek ya yi ya ce "Sorry wasa nake yi amma kinsan number d'in ki bazai yi mun wuya ba beside ma kinyi mun text da ita that time," ta ce "Ooh hakane fa na manta," Sameeha ce ta shiga d'akin tasha kyau cikin doguwar rigar shadda pich color ta ce "Sabeeha dear naje wajen ya Umar," Sabeeha ta ce "Ok my regard to him," Sameeha ta ce "Ok tare da ficewa," Sabeeha ta ce "Hello ya Maleek," daga can ya ce "Hi Sabee na," dariya ta yi ta ce "Yawwa wai ka fasa yin tafiyar ne?" Ta fad'a tana rungumar pillow. Zumbur Maleek ya tashi zaune daga kwancen da yake yasa hannunsa cikin sumar kansa sannan ya dafe goshi ya ce "Ayyah nikam Sam na manta da batun tafiya and zuwana Dubai yana da muhimmanci sosai amma Ina tunanin next week zanje," ta ce "Allah ya kaimu," ya amsa da "Ameen," sannan ya ce "Sabee na ya batun abinci fa Ummi ta ce Wai kince zaki na zuwa kina yi mun," ta ce "Eh mana," ya ce "Shikenan wataran ma zan dinga zuwa naci a nan," "Da gaske wai?" Sabeeha ta tambaya ya ce "Sosai fa," nan suka cigaba da fira abinsu sannan suka yi sallama. Washe gari da Sabeeha ta tashi daga bacci wanka ta yi ta shirya cikin riga da skirt na wata red d'in atamfa ta yi kyau sosai kamar ka sace ta ka gudu sai k'amshi take yi abinta d'akin Mama ta nufa ta je ta gaishe su ita da Abba sannan ta yi musu Sallama ta fita driver ya kaita gidan su Maleek. Tana shiga ta samu Ummi na saukowa stairs har k'asa ta tsugunna ta gaishe da Ummi cikin murmushi Ummi ta amsa ta ce "Daughter kenan sannu da k'ok'ari har kin fito?" Ta ce "Eh Ummi office zaki fita ne?" Ummi ta ce "Eh zan fita office ne ina da patient ki shiga su Hadiza na ciki sai na dawo," ta ce "To Ummi sai kin dawo," Ummi ta fita ita kuma ta nufi kitchen ta had'awa Maleek breakfast ta bawa Hadiza ta kai part d'insa ita Kuma ta koma gidan Mama. Da sallama ta shiga falon ta samu ba kowa kitchen ta wuce kitchen inda take jiyo hayaniyar su Rinaz da sallama ta shiga kitchen d'in suka amsa mata kallon fuskar Sabreen ta yi ta kyalkyale da dariya ganin yadda fuskar tata ta yi kaca-kaca da flour ita a lallai tana yin cake. Su Rinaz ma dariyar suke yi Sabeeha ta ce "Sannu dear da aiki," Sabreen ta ce "Yawwa sister wallahi kuwa girki da wuya," jinjina kai Sabeeha ta yi ta ce "Aikuwa idan ma zaki zage ki zage domin ba zamu Kai ki ki dinga yiwa ya Fauwaz jagwalgwalo ba," Dariya Rinaz ta yi ta ce "Wallahi kuwa fad'a mata habibty dan tsab zamu k'aro mata wata," ai tuni Sabreen ta yi kicin-kicin da fuska dan ita ba dai kishi ba ta ce "Aikuwa Wallahi baku isa ba ko ban iya ba haka zai ci kuma zaku yi yadda cake d'ina zai yi wuta bari ma na Kira my one d'in," ta fad'a tana dialing number d'in Fauwaz Rinaz ta ce "Aikuwa sai dai kici kwab'ar ki ke d'aya banda Rinaz," ta fad'a tana dariya. Sabeeha ta kalli Rinaz ta ce "Sameeha dear fa?" Rinaz ta ce "Suna tare da ya Umar a wancan falon," jinjina Kai Sabeeha ta yi. Fauwaz na d'aga wayar Sabreen bata jira ya ce komai ba ta ce "My love Wai kaji zaka yi mun kishiya," zare ido Fauwaz ya yi kamar Sabreen na gaban sa ya ce "Inji waye?" "Inji su Sabeeha dear mana Rinaz habibty har da cewa Wai jagwalgwalo na iya baza su ci cake d'ina ba," kasancewar wayar a handsfree take ya ce "Ke Rinaz ki kiyayeni rabu da su baby gani nan shigowa gidan," daga haka ya katse Kiran su Sabeeha Kuma suka fita suna dariya. Suna zama babu dad'ewa Fauwaz ya yi sallama a falon yasha gayu cikin wasu k'ananan kaya masu matuk'ar kyau kalar fari da blue sai k'amshi yake yi ga wasu sark'ok'i a wuyan sa sai walwali suke yi kana kallon su kasan masu tsada ne sosai ya yi kyau dama Kuma Fauwaz akwai kyau. Gaishe shi su Sabeeha suka yi ya amsa cikin fara'a da gudu Sabreen ta fito daga kitchen jin shigowar sa waigawa Fauwaz ya yi ya kalle ta dariya ce ta sub'uce masa ganin yadda fuskar ta tasha kwalliyar flour su Sabeeha na taya shi dariyar. Tura baki Sabreen ta yi tare da juyawa ta shige ta koma kitchen d'in binta Fauwaz ya yi yana cewa "Baby baby," Amma bata ko waiga ba sai da suka shiga kitchen d'in sannan ta tsaya dakyar ya rarrashe ta ta sauko ya taya ta suna yi tana yi masa surutu shi kuwa sai biye mata yake yi. A haka suka gama suka fito daga kitchen d'in Fauwaz sai goge fuska da hanky yake yi shi a lallai ya yi aiki sannan ya kalli Sabreen ya ce "My love bari naje na dawo," ta ce "Ok my heart sai ka dawo," daga haka ya fice itama ta haura sama domin yin wanka. Can Fauwaz ya dawo ya canjo wani wankan ya yi kyau abinsa zama ya yi suka sha fira da Sabreen suna cin cake d'in abinsu. Bayan tafiyar Fauwaz Mama da Abba suka dawo daga asibiti dan tun fitar Sabeeha suka tafi. Kitchen su Sabeeha suka shiga tare da 'yan aikin Mama suka shirya abinci mai rai da lafiya sai da suka yi wanka suka yi sallah sannan suka nufi daining suka ci abinci bayan sun gama sannan suka koma falo suka zauna suna fira Sabreen ta zubo cake d'in ta a plate tana ci kallon cake d'in Sabeeha ta yi gwanin sha'awa ta ce "Sabreen dear d'an sammun mana," hararar ta Sabreen ta yi ta ce "Gaskiya bazan iya ba," had'iye yawu Rinaz ta yi ta ce "Ni fa dear," Sabreen ta ce "Rinaz habibty sai dai kiyi hak'uri amma zan cinye kwab'a ta ni kad'ai babu mai ci sai Sameeha dear," ta fad'a tana ajiye plate d'in kan center table ta d'auki d'aya ta nufi bakin Sameeha ta ce "Yawwa sweetheart bud'e bakin," Sabeeha ganin Sabreen ta juyawa plate d'in baya ta yi wuff ta d'auki d'aya ta mik'e. Sabreen ta ce "Sabeeha dear ni kawai ki bani abina," k'in bata Sabeeha ta yi nan suka fara zagaye falon Sabeeha ta ce "Mama kina jinta ko?" Sabreen ta ce "Abba kace ta bani," dariya su maman ke yi musu da su Rinaz Sabeeha ta nufi stairs da gudu ta shige d'akin su tasa key. Sabreen ta koma falo sai tura baki take ta tarar Rinaz ma ta d'auka tana ci bin Rinaz d'in ta yi tana cewa "Ni dai gaskiya kizo ki bani abina," ficewa Rinaz ta yi da gudu itama tura baki Sabreen ta yi ta ce "Mama kina dai ganin su ko?" Dariya Mama ta yi sannan ta k'wala kiran "Halima!halima," daga kitchen Halima ta amsa sannan ta fito da sauri ta ce "Mama gani," "Halima Ina so yanzu ke da su abasiyya ku yi mana yanzu cake a gidan nan," Halima ta ce "To Mama," ta fad'a tare da komawa kitchen d'in Mama Kuma ta kalli Sabreen ta ce "Gashi nan za a yi muku wani shikenan ko?" Gyad'a kai Sabreen ta yi Mama da Abba Kuma suka nufi d'aki. Sabeeha kuwa wayar ta ce ta fara ringing d'agawa ta yi tare da fad'awa kan gado ta ce "Washh," "Lafiya kuwa Sabee na?" Maleek ya tambaya cikin shagwab'a ta ce "To ba Sabreen dear bace ta biyo ni da gudu ba," "Lalala me ki ka yi mata haka?" Ya tambaya cikin kulawa k'ara shagwab'e fuska ta yi ta ce "Wai fa dan na d'aukar mata cake," murmushi ya yi ya ce "To banda abun Sabee na meyasa ki ka d'aukar mata abinta?" "To shikenan na ma fasa ci," Maleek ya ce "A'a wasa nake miki ci ki kyale ta," ci ta fara yi sannan ta ce "Ya Maleek zaka ci?" Girgiza Kai ya yi ya ce "No kici da nawa," ta ce "To," nan suka cigaba da fira suna dariya. Haka rayuwa ta cigaba Sabeeha da Maleek na soyayya cikin bawa juna kulawa da soyayya ta musamman har gidan yake zuwa ya ci girkin ta ya tafi wataran yasa mata rigimar ta bashi a baki. B'angaren Kawu Bala kuwa a zaune yake abun duniya ya yi masa zafi saboda tun kafin Maryam ta d'ora k'afar ta a k'auyen amma talauci yasa shi a gaba tun ranar da sojojin Maleek ma suka zo suka tafi da Abba labari ya Kai masa cewa ya yi shi ina ruwan sa wata k'ila cikin yaran sa ne wata ta jawo masa masifa dan haka ba ruwan sa shima ya ji da masifar dake tunkaro shi. Tashi ya yi ya nufi gida tun daga zaure yake k'wala kiran "Lantana! Lantana," fitowa daga d'aki lantana ta yi da d'ankwali a hannu ga kannan ya yi datti ko tsagar kitson kan ba a gani ta ce "Wai Bala lafiya ka ke mun irin wannan Kira kamar na cima bashi ko wata tsiyar zaka bani," kusan Wanda talauci ke ci abu kad'an ke tunzura shi aikuwa ya fara masifa "Wallahi Lantana ki fita daga idanuna na rufe idan ba haka ba wallahi saina mangare ki," dariyar rainin hankali Lantana ta yi ta ce "Ah lallai ne Bala ka mangare ni kaji," "Wallahi Lantana ki fita a idanuna na rufe idan ba haka ba sai kinga bala'i na," ta ce "Dan Allah Bala naga bala'i da wallahi yau sai kasan ka tab'o lantana Wallahi sai nayi maka abinda baza ka tab'a mantawa dani ba," jinjina kai Kawu Bala ya yi ya ce "Lantana karki fasa nace lantana idan kin fasa Allah ya tsinewa dangin ku shegiya mai farar k'afa," aikuwa nan lantana ta fara sababi tana zage-zage aikuwa Kawu Bala ya zabga mata mari. Dafe kunci ta yi ta ce "Bala nika mara?" "An mare ki d'in ki rama mana," Kawu ya fad'a yana nufar hanyar fita Lantana ta ce "Bazan rama ba amma Wallahi sai nayi ma abinda baka tab'a tunani ba matsiyaci kawai wallahi Bala da kai gara garin kwaki na ashirin," ficewa Kawu Bala ya yi yana k'wafa. Bayan fitar Kawu lantana ta yi k'wafa ta ce "Zaka ga me zanyi," ta cije baki sannan ta tsaya tunanin me zata yiwa Kawu Bala can ta shige d'aki sai gata ta fito da kayan sawar Kawu Bala da almakashi ta zauna ta yayyanka su gutsi-gutsi ta kai shara ta watsar ta ce "Ka dawo naga uban da zaka yi," Kawu Bala kuwa yana fita k'ark'ashin wata bishiya ya je ya zauna yana sababi shi kad'ai malam saleh ne yazo wucewa ya ce "Malam Bala kaine zaune a nan?" Kawu ya ce "Eh wallahi ni ne malam saleh ina zuwa haka ka ke sauri?" Malam Saleh ya washe baki ya ce "Wallahi aski zani kasan yau ake auren yar wajena ta inna da k'arfe uku dafatan zaka zo," Kawu Bala ya ce "Zan zo," daga haka Malam Saleh ya wuce. Kawu Bala a zuciyar sa ya ce "Ai ko dan naje na cika cikina naje wallahi," kallon kayan jikin sa ya yi farin jadi ne amma duk ya zama milk saboda datti hammatar duk ta yage haka ma gwiwoyin duk sun ya ge. A hankali ya ce "Na tuna akwai kayana na shiga jama'a basu fi wanki aahirin ba bari na tashi naje na fara shiri," daga haka Kawu Bala ya tashi ya nufi gida. [10/25, 7:43 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️ RUBUTAWA DAGA HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ) SADAUKARWA GA MY DAUGHTER SABEEHA BILKISU Z.YA'U (🅱️K) AISHA MAGAJI DABO (AMA) Page 15 Bud'e k'ofar aka yi Salman ne ya shigo tare da mutum biyu a bayan sa. Zare ido Sabeeha ta yi gani take yi kamar a mafarki haka ma Sameeha da ta sake murza idanunta ko sune suke yi mata gizo Sabreen kuwa ko motsi ta kasa domin gani take yi kamar mafarki take yi. Can dai Sabreen ta yi k'arfin halin mik'ewa tsaye ta ce "Abba kaine?" Gyad'a kai Abba ya yi da gudu Sabreen ta yi wajen sa ta rungume shi tana murnar ganinsa gashi ya canja kamar ba shi ba. Daga bayan Sabreen suka ji Sameeha ta ce "Abba wacece wannan?" Ta fad'a tana kallon Doctor Maryam da zuwa lokacin harta fara hawayen farin ciki tana mamakin girman 'yan ukun ta. Abba ya ce "Maman ku ce Allah ya dawo mana da ita ta sanadin Abdul-maleek," rungume Doctor Maryam Sabreen da Sameeha suka yi suna murnar ganinta tare da hawayen farin ciki haka ma Doctor hawayen take yi. Sabeeha kuwa har lokacin bata motsa ba ta tsaya kallon ikon Allah haka ma Rinaz da take tunanin dama maman ta ce Mahaifiyar su Sabeeha haka ma su Umar suka tsaya kallon su. Sabreen ta ce "Mama dama kina raye ashe dama zamu ganki?" Share hawaye Doctor ta yi ta ce "Ku gafarceni yarana ba laifina bane a ko wanne lokaci kuna raina ku gafarce ni," Sameeha dake rungume jikin Doctor ta ce "Mama baki yi mana komai ba mun yafe miki," Sabreen kuwa sai gyad'a kai take yi. Doctor ta kalli Maleek dake tsaye ta ce "Abdul-maleek nagode sosai domin ta sanadin ka na samu farin cikin dana fidda rai da samun sa Allah ya saka mata da mafificin alkhairi Allah ya faranta maka kamar yadda ka faranta mana Allah ya cigaba da kare mana Kai a duk inda kake," a hankali ya amsa da "Ameen Mama," su Sabreen ma suka amsa da "Ameen," domin wani girma da mutuncin Maleek ne ya k'aru a idanun su sosai suka k'ara ganin mutuncin sa godiya suka yi masa sai kawai ya yi musu murmushi. Kallon inda Sabeeha take Doctor Maryam ta yi a hankali ta nufi wajen ta ta tsaya a gaban ta ta ce "Nasan na aikata muku ba daidai ba yarinya ta amma ki gafarceni banyi hakan da son raina ba nasan ban cancanci yafiya a wajen ku ba," fad'awa jikin Doctor Sabeeha ta yi ta saka kuka ta ce "A'a Mama mu baki aikata mana komai ba mun yafe miki," Sabeeha ta fad'a tana hawaye itama doctor Maryam hawayen take yi. A hankali Sabeeha ta waiga inda Maleek yake amma sai ta ga wayam baya nan wani sabon hawayen ne ya zubo mata domin wata sabuwar soyayyar sa ce taji ta d'arsu a zuciyar ta duk da cewa da tayi bata son sa ta k'ona masa zuciya ta hana shi farin ciki har cuta sai da ya yi amma shi hakan bai sa ya tsane ta ba sai ma nema mata nata farin cikin da ya yi tabbas Maleek na daban ne zuciyar sa kyakkywar zuciya ce take ta ji mutuncin sa da soyayyar sa sun k'aru a zuciyar ta. Ummi ce ta k'arasa wajen su wacce zuwan ta kenan rungume ta Doctor Maryam ta yi ta ce "Nagode Aysha nagode da kulawar da kika bawa 'yan uku Allah ya saka da alkhairi," Ummi ta ce "Haba Maryam ai tsakanina dake ba godiya nima ai 'ya'yana ne," rungume Ummi su Sabeeha suka yi cikin farin ciki daga nan aka cigaba da gudanar da celebration aka yanka cakes aka ci aka sha su Sabeeha sai godiya suke wa Ummi bisa k'ok'arin ta. Anan suke jin ai duk abinda suka gani a birthday d'insu duk Maleek ne ya yi musu nan ma Maleek ya k'ara samun rank a zuciyar 'yan uku. Bayan an gama ne suka koma falo Doctor Maryam ta basu labarin abinda ya faru tun auren su da Abba da kuma barin su da ta yi bayan Ummi tasa driver ya kai Aysha da Dija gida. Tausayin Mahaifiyar tasu ne ya kama su har ma da Abban su. Tashi Ummi ta yi ta ce "Nikam bari na tafi," a tare Rinaz da 'yan uku suka tashi kallon su Ummi ta yi ta ce "Ina kuma zaku?" Sabeeha ta ce "Ummi binki zamu yi," girgiza Kai Ummi ta yi ta ce "A'a ban yadda da hakan ba ku zauna tare da Mamar ku kunji?" Doctor Maryam ta ce "Aysha ku je mana," Ummi ta ce "Ai da nan da can duk d'aya ne kuma zasu je duk sanda suke so sai dai banda yau domin Ina so ku samu zama," ta kalli su Sabeeha ta ce "Ku zauna," zama suka yi. Doctor kuwa taji dad'in abinda su Sabeeha suka yi saboda ganinta da suka yi hakan baisa sunji sunfi buk'atar ta fiye da wacce ta rik'e su na wani lokaci ba duk da kuwa dad'ewar da suka yi ba tare da ita ba. Rakiya suka yiwa Ummi har mota sannan suka koma cikin gidan tare da Rinaz domin tace duk inda 'yan uku suke to tana nan. Wanka suka yi da sallah sannan suka fita falo suka ci abinci su sabeeha suka gyara wajen sannan suka koma falo suka fara fira suna dariya gwanin sha'awa sai dai banda Sabeeha da duk hankalin ta ya yi wajen Maleek tunani take yi gobe waye zai had'a masa breakfast. Doctor ta kalli Abba ta ce "Ni kuwa Abban 'yan uku bangane rigimammiya ta ba a cikin su," Rinaz dake kwance cinyar Doctor Maryam ta ce "Mama wacece?" Doctor ta ce "Kullum fa sai ta hanamun bacci da kukan ta haka zata yi ta kuka har sai ta tashi 'yan uwan ta," Abba ya kalli Sabeeha ya ce "To aminiyata kinji fa," dariya falon ya d'auka su Sabreen sai tsokanar ta suke yi suna ce mata "Rigimammiyar Mama," ita kuwa sai hararar su take yi sannan ta tashi ta haye stairs. Wani had'adden d'aki ta shiga komai na d'akin pink ne d'akin ya had'u ba k'arya zama ta yi gefen gadon ta fad'a tunanin Maleek. Su Sameeha ne suka shiga d'akin Sabreen ta d'auko kyautar da Maleek ya yi musu ta bud'e a tare ita da su Sameeha suka ce "Woww amma fa ya yi kyau," kallo itama Sabeeha ta yi wata siririyar sark'ar diamond ce sai kyalli da walwali take yi tayi kyau over haka ma d'an kunnen ya yi kyau. Sameeha ta ce "Gaskiya ya yi kyau sosai nima bari na duba nawa," bud'ewa ta yi sak irin ta Sabreen ba banbanci Rinaz ta ce "Sabeeha sister ke ina naki kyautan," bed side drower ta nuna mata. D'aukowa Rinaz ta yi ta nufi su Sabreen suka bud'e k'amshin da ya daki hancin Sabeeha ne yasa ta lumshe idanunta sai dai lokaci guda ta bud'e su jin ihun da su Rinaz suka saki suna fad'in "Wallahi ya yi kyau sosai dear zo ki gani," sark'a ce irin tasu Sabreen sai dai ita da wani ring mai d'aukar hankali na diamond da Kuma wani diamond watch harma da wani fashion designer d'in abun hannu ga wani tsadadden turare Mai dad'in k'amshi. "Wow," kawai Sabeeha ta iya furtawa domin ganin key d'in mota su Sabreen kuwa ihun murna suka saki tare da ficewa da gudu suka nufi falo domin nunawa Abba da Doctor Maryam. Sabeeha kuwa kwanciyar ta ta yi sai lokacin idanunta ya Kai kan wata farar takarda dake wajen d'auka ta yi ta bud'e take idanunta suka yi mata tozali da wani kyakkyawan rubutu mai kyan gaske Wanda bata tab'a ganin mai yanayin sa ba ma tsabar kyau da tsaruwa fara karantawa ta yi cikin nutsuwa. "Assalamu Alaiki sarauniyar kyawawa Ina fatan kina lafiya hak'ika naso wannan sarauniyar kyan ta kasance mallakina sai dai hakan ba mai yuwuwa bane saboda wannan sarauniyar da zuciya ta ta makance a k'aunar ta ya kasance ni bana d'aya daga cikin tsarin ta Ina addu'ar Allah yasa hakan shine mafi alkhairi ga k'aramar kyautata nan a gareki karki yi tunanin nayi miki ne domin ki soni a'a nayi miki ne a matsayin wacce zuciyata taso kasancewa tare da ita sai dai hakan bai samu ba Sabeeha na hak'ura dake kuma ba Wai dan bani sonki ba sai dan kawai na baki dama ki zab'i wanda ki ke son yin rayuwa da shi fatana shine ki kasance cikin farin ciki a k'arshe ina yi miki fatan alkhairi Allah ya zab'a Miki mafi alkhairi na barki lafiya," tun kafin ta gama karantawa hawaye ya wanke mata fuska. Kifa kanta jikin pillows ta yi ta saka kuka mai ban tausayi a hankali ta fara magana "Why Maleek meyasa zaka yi mun haka wallahi Ina sonka please karka rabu dani," ta fad'a tana k'ara sakin wani sabon kukan. Shiga d'akin su Sabreen suka yi tare da su Abba da Doctor domin su taya ta murna sai suka tsaya turus domin ganin yadda Sabeeha ta kifa kanta jikin pillows sai kuka take yi kamar wacce aka yiwa mutuwa. A hankali Doctor Maryam ta k'arasa gefen ta ta zauna tare da dafa kafad'ar ta d'aga jajayen idanuwan ta Sabeeha ta yi tana ganin Doctor ce ta fad'a jikin ta ta cigaba da rera kukan ta. Shafa bayan ta Doctor ke yi tare da gashin ta ta ce "Meya faru ne?" Shiru ba magana sai kuka. Sabreen da Sameeha ma harsun fara nasu kukan matsawa gaban Sabeeha Sabreen ta yi tana kuka ta ce "Please dear ki fad'a mana meye yake damunki bamu tab'a ganin ki cikin irin wannan yanayin ba dan Allah kiyi hak'uri hakan na cutar damu," jin muryar Sabreen na kuka ne yasa Sabeeha rage volume d'in kukan ta. Sameeha itama tana hawaye ta ce "Sister damuwar ki tamu ce bazamu iya jurar ganinki a irin wannan yanayin ba please kiyi hak'uri," shiru Sabeeha ta yi sai ajiyar zuciyar da take saukewa domin a duniya idan akwai abinda ta tsana to damuwar su Sameeha ce. Abba ne ya k'arasa tare da rik'o hannun Sabeeha ya ce "Zo nan kinji aminiyata zo muje ki fad'a mun meye damuwar," ya fad'a tare da janta suka bar d'akin binsu Doctor Maryam ta yi zuwa falo. Zama Abba ya yi tare da zaunar da Sabeeha kusa da shi Doctor Maryam kuwa fridge ta nufa ta zubo ruwa a cikin wani glass cup mai matuk'ar kyau ta k'arasa inda suke ta mik'awa Sabeeha karb'a ta yi ta sha sannan ta ajiye cup d'in akan center table a hankali take sauke ajiyar zuciya. Abba ya ce "Aminiya ta muna jinki ki fad'a mana meye damuwar ki domin ba wanda ya kamata ki fad'awa damuwar ki fiye da mu kinji?" Gyad'a kai ta yi sannan ta fara basu labarin had'uwar su tunta farko da Maleek da kuma cewar da ta yi bata son sa da Kuma dalilin ta sannan ta d'ora da basu labarin letter d'in da ta gama karantawa yanzu. Bayan hannun ta tasa tana goge hawayen da ya b'ata mata fuska jinjina kai Abba ya yi sannan ya ce "Gaskiya ne aminiya ta ni shaida ne akan son da Abdul-maleek ke miki domin bai ko ji kunya ta ba ya bani labari kamar yadda ki ka fad'a yanzu aminiya ta Abdul-maleek ya cancanci ya samu soyayya a duk inda ya je neman ta domin duk wata nagarta da ake nema a wajen mijin aure to ya had'a su na kuma ba inda za a hana shi aure yana da kyawawan halaye sosai abinda nake so dake shine kiyi ta addu'a kinji aminiyata?" Noding kanta ta yi. Doctor ta ce "Abinda Abban ki ya fad'a gaskiya ne Sabeeha Maleek mutumin kirki ne fiye da tunanin ki ya kai a so shi ya kuma cancanci samun aure a duk inda ya nema na tabbata idan har kika aure shi zai baki kulawa sosai ko wad'an ne iyaye fatan su Allah ya had'a 'ya'yayen su da mazaje na gari Sabeeha idan har wannan ne kin samu duk da na fuskanci dalilin ki kuma baki yi kuskure akan hakan ba domin duk Wanda yasan Nasreen da Mahaifiyar ta ba wanda zai yi marmarin wata alak'a ko da ta gaisuwa ce ta shiga tsakanin sa da su Sabeeha wata iriyar rayuwa ake yi a cikin gidan nan domin mutum d'aya ke juya gidan sai abinda ya ce kuma wannan shine mahaifin Nasreen kamar yadda Abban ki ya fad'a kiyi ta addu'a Allah ya zab'a miki abinda yafi alkhairi mu ma zamu taya ki," A hankali Sabeeha ta ce "To Mamana," domin iya fad'a musu damuwar ta da ta yi taji sanyi sosai a zuciyar ta nan kuwa su Abba suka dinga janta da fira harta saki jikin ta sai dariya take yi. Farin ciki fal ranta ta mik'e ta ce "Abba Mama sai da safe," sannan ta haye stairs tana shiga d'akin su ta tsaya kallon su Sameeha da suka yi jugum-jugum murmushi ta yi sannan ta k'arasa ta haye saman gadon ta zauna tsakiyar su ta ce "Sisters ku kwantar da hankalin ku dama fa damuwata akan Yaya Maleek ne," bud'e baki Rinaz ta yi ta ce "Ooh ke da ki ka ce bakya yi kuma?" Hararar ta Sabeeha ta yi ta ce "Sanin da kika yi babe ni bani number d'insa ma," bata Rinaz ta yi sai tsokanar ta suke yi ita dai banza ta yi da su ta turawa Maleek text. Suna zaune tare da Salman a falon sa wayar sa ta yi k'ara jin a special number d'insa ne yasa shi dubawa ya ga an rubuta "Thank for everything," d'an shiru ya yi yana kallon text d'in sannan ya ajiye wayar ya kalli Salman ya ce "Salman kaje ka gama mana booking gobe domin jibi nake so nabar k'asar nan," Salman ya ce "Ok sir," banza Maleek ya yi masa sai ma hararar sa da ya yi ya tashi ya haura stairs. Tashi Salman ya yi ya fice yana murmushi domin yasan dalilin hararar dan kawai ya Kira shi da sir ne. Sabeeha kuwa wanka suka yi suka kwanta bacci bayan sun raba dare suna fira. Washe gari sai 8:00 Sabeeha ta tashi kallon agogon dake d'akin ta yi saurin sauka daga gadon ta yi ta fad'a toilet ta yi wanka dama ta yi sallah tun asuba. Gaban mirrow ta nufa ta shafa mai cikin sauri powder da lipstick kawai tasa sai kwalli sannan tasa doguwar rigar atamfa mai red and yellow sai ratsin blue d'auri ta yi mai kyau akan ta sannan ta yafa blue mayafi da plat shoes blue ta rataya jaka itama blue ta feshe jikin ta da turare ba k'aramun kyau ta yi ba wayar ta ta d'auka ta fice. Tun kafin ta sauka down stairs take jiyo hayaniyar su Sabreen a kitchen murmushi ta yi sannan ta nufi kitchen d'in. Tana Sameeha ta ce "Sabeeha sister sai ina haka?" D'aukar yam boll gud'a d'aya Sabeeha ta yi takai bakinta ta ce "Wa ki ke tunanin zai yiwa ya Maleek breakfast?" Rinaz ta ce "Amma ai ke yanzu ba 'yar aiki bace," hararar ta Sabeeha ta yi ta ce "Naji yanzu zanyi masa ne a matsayina na k'anwar sa kafin na zama matar sa," dariya Sabreen ta yi ta ce "Wow gaskiya ne Sabeeha dear ashe haka kika yi nisa," kanne mata ido d'aya Sabeeha ta yi. Rinaz ta ce "Sabeeha habibty zan raka ki muje tare," Sabeeha ta ce "Ok Ina jiran ki amma karki dad'e," tare suka fita da Rinaz ita ta wuce d'akin Doctor. Knocking ta yi a k'ofar Doctor ta ce "Yes come in," shiga Sabeeha ta yi da Sallama a bakin ta Doctor dake zaune gefen gado tana rubuce-rubuce ta amsa mata sallamar. Tsugunnawa Sabeeha ta yi ta ce "Mamana barka da safiya kin tashi lafiya?" Murmushi Doctor ta yi ta ce "Lafiya k'alau rigimammiya ta tun d'azu naga'yammata na sun fito amma banda ke fatan dai lafiya ko da yake naga kinsha gayu sai ina haka?" Sunkuyar da Kai Sabeeha ta yi ta ce "Lafiya lau Mama uhm da..da..dama," sai Kuma ta yi shiru. "Uhmm say it out," cewar Doctor Sabeeha ta ce "Mama dama zanje na yiwa ya Maleek breakfast ne," ta fad'a tana wani rintse idanu. Dariya Doctor ta yi ta ce "To shikenan sai kin dawo driver na waje zai kai ki," ta ce "To Mama saina dawo," ta fad'a tare da ficewa. A falo suka had'u da Rinaz tare da su Sabreen tare suka fita compound d'in gidan wata had'add'iyar farar BMW suka gani a wajen motar ta yi kyau sosai kamar ka sace ka gudu wajen motar suka nufa suna yaba kyanta sai kyalli take yi ko ba a fad'a musu ba sunsan ta Sabeeha ce wacce tun jiyan Maleek yasa aka kawo ta. Sai da suka gama shafa motar sannan suka tafi su Sabreen kuma suka koma cikin gidan suna santin motar. Su Sabeeha kuwa suna isa gidan suka samu falon babu kowa direct stairs suka nufa suka yi knocking d'akin Ummi. Ummi ta ce "Yes shigo," tura k'ofar suka yi suka shiga suka samu Ummi zaune tana danna laptop har k'asa suka gaishe ta cikin fara'a ta amsa sannan ta ce "Yana ganku ku kad'ai ina ragowar 'yammatan nawa?" Rinaz ta ce "Suna gida Ummi muma zuwa muka yi rigimammiyar Ummi zata yiwa Yaya abinci," kallon Sabeeha da ta yi k'asa da kai Ummi ta yi ta ce "Ayyah daughter meyasa ki ka taho baki kwanta kin huta ba aike yanzu kin dena yi masa girki zansa a nemo masa wata," saurin girgiza kai Sabeeha ta yi ta ce "A'a Ummi dan Allah karki samo wata Allah zanyi," Murmushi Ummi ta yi Wanda ya bayyana dimples d'in ta sai a lokacin Sabeeha ta lura ashe wajen Ummi Maleek ya kwaso dimples hatta kamannin sa ma na Ummi ne sai dai dimples d'in sa yafi na Ummi lotsawa sosai. Ummi ta ce "Banda rigima irin taki daughter har yaushe ki ka baro can kika zo nan yin girki," ta ce "Allah Ummi zan iya," ta fad'a tana mik'ewa ta fice zuwa kitchen. Tana shiga kitchen d'in Hadiza ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Mun godewa Allah da baki zo ba ba musan ya zamu yi ba tun d'azu yallab'ai ya ce a shirya masa breakfast amma mun rasa me zamu shirya masa wanda zai burge shi," dariya Sabeeha ta yi ta ce "To shikenan kuje abinku bari nayi masa," ta fad'a tare da shigewa can cikin kitchen d'in su Hadiza kuwa suka fita suna hamdala. Cikin lokaci k'alilan ta gama had'a breakfast d'in ta gama ta nufi d'akin su na gidan. Da sauri Maleek ke saukowa daga stairs yasha kyau sosai cikin black trouser da farar t-shirt sai shirt bottles one black da ya d'ora a sama sai k'amshi yake zabgawa kallon breakfast d'in dake falon ya yi sai lokacin ya tuna ashe fa Sabeeha bata gidan k'aramun tsaki ya ja sannan ya nufi k'ofar fita. Har zai fita sai ya tuna yanzu fa idan ya fita baisan lokacin dawowar sa ba gashi yanzu yana jin yunwa sannan shi ba gwanin cin abincin Restaurant ba juyawa kawai ya yi ya koma falon ya zauna ya bud'e abincin. Wani daddad'an k'amshin girkin ne ya daki hancin sa ko ba a fad'a masa ba yasan Sabeeha ce ta yi girkin domin k'amshin girkin ta ya fita daban zubawa ya yi yaci ya k'oshi sannan ya koma d'akin sa ya yi brush ya fita zuwa part d'in Ummi. Hankali a tashe Sabeeha ta shiga d'akin su ta fad'a saman gado ta saki wani kuka mai ban tausayi a hankali ta furta "Meyasa Wai meyasa hakan ne me ya yi muku ku ke k'ok'arin raba shi da rayuwar sa," zumbur ta mik'e tsaye ta ce "Bazan tab'a bari ku yi nasara a kansa ba ko da kuwa hakan na nufin rasa tawa rayuwar," tana fad'ar haka ta goge hawayen ta ta yi hanyar fita. Direct upstairs ta nufa har ta kai hannu zata murd'a handle ta jiyo muryar Ummi tana cewa "Son wai meyasa baka son shan magani ne kasan fa ciwon dake damunka ba ciwon da za a dinga wasa da magani bane duk da naga ya yi sauk'i sosai," murmushi Maleek ya yi ya ce "Ummina ki kwantar da hankalin ki naji sauk'i sannan Ummi gobe nake son tafiya Dubai," kallon sa Ummi ta yi ta ce "Saboda me ko ka hak'ura da Sabeeha ne?" Girgiza Kai ya yi ya ce "A'a Ummi har gobe Ina sonta so bana wasa ba amma Ummi tunda ita bata sona bai kamata a takura mata ba Ummi ni yanzu damuwa ta yi mun yawa ga rashin wacce nake so ga matsalar Nasreen a gefe kuma ga wajen aikina shiyasa zan tafi ko dan tsira da lafiya ta kuma bazan dawo nan kusa ba," cikin tausayin d'an nata Ummi ta ce "Ka cigaba da addu'a kaji son sannan ka tafi da matar ka kaji?" Noding kansa ya yi. Ganin yanayin Ummi ya canja yasa Maleek yin murmushin da ya bayyana dimples d'insa dake k'ara masa kyau ya ce "Ummi ki ka sanima ko daga nan nayo miki suruka dama akwai wata balarabiya mai suna Surayya dake sona kyakkyawar gaske ce nasan zata kula miki dani sosai," dariya Ummi ta yi ta dungure masa kai ta ce "Marar kunya," suka yi dariya gaba d'ayan su. Daram dam gaban Sabeeha ke fad'uwa lokaci guda hawaye ya wanke mata fuska a zuciyar ta take fad'in shikenan na rasa shi yanzu gobe zai bar k'asar sannan bazai dawo nan kusa ba gashi kuma zai auro balarabiya fasa shiga Sabeeha ta yi ta nufi d'akin su tana kuka. Kwanciya ta yi saman gadon su tana kukan rasa Maleek tura k'ofar d'akin Rinaz ta yi ta shiga da Sallama. Saurin goge fuskar ta Sabeeha ta yi tare da amsa sallamar kallon ta Rinaz ta yi ta ce "Lafiya ki ke kuwa meyasa idanun ki suka yi red haka?" Murmushin yak'e Sabeeha ta yi ta ce "Bakomai Habibty kawai baccin da ya fara d'auka ta ne yasa hakan," shiru Rinaz ta yi ba don ta yadda ba ta tab'e baki ta ce "Shikenan tunda baza ki fad'a mun ba anyway ki tashi mu tafi yamma ya fara yi," girgiza kai Sabeeha ta yi ta ce "Ni anan zan kwana Rinaz please kema ki bari sai gobe Habibty," "Saboda me zamu kwana a nan d'in to?" Rinaz ta tambaya Sabeeha ta ce "Kawai nafi so mu kwana a nan," jinjina kai Rinaz ta yi ta ce "Ok ba damuwa Allah ya kaimu goben," Sabeeha ta amsa da "Ameen," fita Rinaz ta yi. Sabeeha Kuma ta shiga wanka ko da ta fito doguwar riga ta zura ta yi sallah sannan ta kwanta tana shafa jikin pretty dake kusa da ita tunani fal zuciyar ta a haka bacci ya d'auke ta. Sai yamma sosai ta tashi toilet ta fad'a ta yi alwalar sallar la'asar da bata yi ba gashi lokaci na tafiya tana idar da sallar ta nufi kitchen ta d'ora girki. Tana gamawa ta jera komai a daining sannan ta koma d'akin su ta zabga uban tagumi gaba d'aya ita tama rasa dame zata ji hawayen dake zubo mata ta goge sannan ta tashi ta yi sallar magrib ta nufi d'akin Rinaz. Akan sallaya ta samu Rinaz ta idar da sallah zama ta yi gefen gado ba tare da ta ce komai ba kallon ta Rinaz ta yi ta girgiza Kai bata ce komai ba tasan dole akwai abinda ke damun Sabeeha amma tak'i fad'a gashi lokaci d'aya duk ta fita hayyacin ta fuskar ta ta kasa b'oye damuwar ta. Ko da Rinaz ta buk'aci su je su ci abinci cewa ta yi ta k'oshi Rinaz ta ce "Haba dear wai me yake damun ki ne yau fa banga kinci abinci ba sannan naga kina cikin damuwa sannan yanzu kink'i kici abinci Wai me yake faruwa ne?" Ganin Rinaz ta damu tana neman yin kuka yasa Sabeeha nemo k'aryar da zata yi mata. Ta ce "Rinaz habibty karki damu kaina ke mun ciwo tun d'azu shiyasa," Rinaz ta ce "Ayyah sorry sister tashi muje asibiti," zare ido Sabeeha ta yi ta ce "Asibiti fa dear kaina fa nace yana ciwo," Rinaz ta ce "Eh mana Ooh na manta bari na sanarwa Ummi," ta fad'a tana yin hanyar fita Sabeeha na kiran ta amma ko waigawa bata yi ba. Can sai gasu tare da Ummi kallon ta Ummi ta yi ta ce "Sannu Daughter me yake damun ki?" Murmushi Sabeeha ta yi ta ce "Ummi kaina fa ke ciwo kuma bada yawa ba," ajiyar zuciya Ummi ta sauke ta ce "Bari na kawo miki magani," ta fad'a tare da fita daga d'akin. Dawowa Ummi ta yi da Abinci a plate tasa Sabeeha a gaba ta bata da kanta sannan ta bata magani tasha ta ce "Ki kwanta ki huta kinji daughter?" Gyad'a kai Sabeeha ta yi sannan Ummi ta fita Rinaz tabi bayan ta domin zuwa ta ci abinci. Tashi Sabeeha ta yi ta d'auro alwala ta yi sallah sannan ta koma ta kwanta duk da tasan ba wani bacci da zata iya tana nan kwance Rinaz ta shiga d'akin tana waya tana gamawa ta shiga bathroom ta yi wanka sannan ta shirya cikin kayan bacci ta kwanta ba tayi tunanin tashin Sabeeha ba domin a tunanin ta bacci take yi ta fara bacci abinta. Sabeeha kuwa yadda ta ga rana haka ta ga dare domin ita bata tab'a had'uwa da abinda ya hargitsa kwakwalwar ta ba kamar wannan lamarin. Alwala ta yi ta fara nafila tana rok'on Allah da ya kare su daga sharrin mutum dana aljan tana zaune har asuba ta yi sallah ta yi sannan ta tashi Rinaz itama ta yi. Gari yana d'an fara haske Rinaz ta koma bacci ita kuma Sabeeha ta yi wanka ta shirya cikin dark purple d'in doguwar riga ba kwalliya a fuskar ta amma tayi kyau sosai kitchen ta nufa ta fara had'a breakfast tana gamawa ta kai daining ta ajiye. Maleek ne zaune akan gadon sa Nasreen ta shiga d'akin kallo d'aya ya yi mata ya d'auke idanun sa shi har ya manta rabon da ya ganta k'arasawa ta yi ta zauna gefen sa tana kallon sa domin gani ta yi ya k'ara yi mata kyau sosai suna had'a ido ya harare ta wanda hakan da ya yi ita gani ta yi ya k'ara kyau ta ce "Ina kwana ya Maleek," d'an kallon ta ya yi ya ce "Wai ke bakya jin kunyar zuwa waje babu sallama ne?" Ta ce "Sorry ya Maleek," baiko kalle ta ba ya ce "Sorry for yourself," daga haka ya mik'e ya nufi bathroom. Ta ce "Ya Maleek ina Kuma zaka je zuwa fa nayi muyi fira," ya ce "Ina da abun yi kema ki tabbatar kafin na fito kin shirya domin zamu yi tafiya," zumbur ta mik'e ta ce "Tafiya kuma ina zamu je?" Kallon mamaki ya bita da shi ganin yadda ta rikice daga fad'in zasu yi tafiya ya ce "Yadai?" Murmushi ta yi ta ce "No bakomai," tab'e baki ya yi ya ce "To aje a shirya," daga haka ya shige bathroom ita Kuma ta fita da sauri. Part d'in ta ta fara zuwa ta had'a kayan ta sannan ta nufi part d'in mahaifiyar ta a zaune ta samu Hajiya Asiya tana yin breakfast ko gaishe ta bata yi ba ta ce "Umma kinji wai Ya Maleek ya ce na shirya yanzu zamu yi tafiya," kallon ta Umma ta yi ta ce "To meye naki da damuwa ki shirya sai dai kafin ku tafi ki tabbatar ya yi breakfast," Murmushi Nasreen ta yi ta ce "To Umma,"daga haka tabar part d'in. A falo ta ajiye trolley d'in ta sannan ta haura stairs ta shiga bedroom d'in Maleek ta zauna tana nan zaune ya fito daga dressing room d'insa ya yi matuk'ar shan kyau cikin uniform d'insa Wanda ke yi masa kyau a duk sanda yasa k'amshi kawai ke fita a jikin sa da kallo Nasreen ta bi shi a zuciyar ta tana fad'in Anya kuwa Umma dagaske take yi akwai Wanda yafi Ya Maleek had'uwa. "Wannan kallon fa?" Maleek ya fad'a cikin had'e rai ta ce "Kayi kyau sosai," banza ya yi mata sannan ya ce "Muje," saurin cewa ta yi "Amma sai kayi breakfast zamu tafi?" Kallon ta ya yi ya ce "Kina da damuwa da hakan ne?" Murmushin yak'e ta yi ta ce "A'a gani nayi bai kamata na bari ka tafi da yunwa ba," kallon tsaf Maleek ya yi mata ya ce "Kina da damuwa da hakan ne har yaushe ki ka fara damuwa da naci abinci?" Shiru ta yi tare da yin k'asa da kanta wuce ta ya yi tare da fad'in "Muje ko," daga haka ya fice. Da gudu Sabeeha ta shiga kitchen ta kalli inda ta ajiye breakfast d'in Maleek sai ta ga wayam babu shi hankali tashe ta fito daga kitchen d'in da gudu ta kalli Hadiza dake goge-goge ta ce "Hadiza ina breakfast d'in ya Maleek ko kin kai masa ne?" Girgiza Kai Hadiza ta yi ta ce "A'a yau bani na kai masa ba Fati ce ta tafi kai masa," ai Sabeeha bata bari fati ta k'arasa fad'a mata ba ta fice da gudu. A k'ofa taci karo da su Sabreen amma ko ta kansu bata yi ba ta yi hanyar part d'in Maleek da gudu ganin a yanayin da take ciki ne yasa su Sabreen binta a baya da gudu suna Kiran ta amma ko waigawa bata yi ba ko Kiran nasu ma bata ji. Sai da ta kai k'ofar falon sannan ta tsaya har zata bud'e taji muryar Maleek na cewa "Ki kai mun abincin part d'in Ummi a can zanci," kad'an Sabeeha ta yi ajiyar zuciya sannan ta ja hannun su Sabreen suka bar wajen da sauri. Suna shiga falon suka samu Ummi zaune akan kujera sai Rinaz da Fauwaz dake daining suna breakfast. Rinaz ce ta ce "A'a sisters saukar yaushe?" Ganin su kamar a cikin damuwa Rinaz ta ce "Lafiya kuwa?" Kallon Sabeeha suka yi kallon Sabeeha da idanunta suke tab da k'walla k'iris take jira ta fara kuka Ummi ta yi sannan ta ce "Daughter zo nan ki fad'amun meye damuwar?" A hankali ta taka zuwa wajen Ummi sannan ta zauna gefen Ummi. Ummi ta ce "Fad'a mun meye matsalar ko ciwon Kai d'in ne?" Girgiza kai Sabeeha ta yi "Ummi ta ce to fad'a mun meye," har ta bud'e baki zata yi magana Fati ta yi sallama a falon ta kalli Ummi ta ce "Ummi dama Yallab'ai ne yace a kawo masa abincin sa nan," Ummi ta ce "Ok ajiye a can," Ummi ta fad'a tana nunawa Fati can gefe wajen wasu had'addun kujeru. Ajiyewa saman center table Fati ta yi sannan ta fita mayar da kallon ta wajen Sabeeha Ummi ta yi ta ce "Yanzu fad'a mun Daughter meke faruwa?" Hawaye ne ya zubo daga idanun Sabeeha har ta bud'e baki zata yi magana Maleek ya shiga falon Nasreen na biye da shi. Kallo d'aya ya yiwa Sabeeha yasan tana cikin damuwa itama da kallo ta bi shi domin gani ta yi kamar kullum k'ara masa kyau ake yi ko dan ranar birthday d'insu bata ga kyan sa haka ba ko dan ranar bata gansa a mai haske sosai bane. K'arasawa wajen Ummi ya yi ya ce "Good morning Ummina," ta ce "Morning Son," d'aga ido ya yi ya zabgawa Nasreen wata uwar harara da sauri ta durk'usa ta ce "Ummi ina kwana?" Cikin fara'a Ummi ta amsa. Mik'ewa Maleek ya yi ya kalli su Rinaz da suka yi tsilli-tsilli d'aga mata gira d'aya ya yi da idanunta ta yi masa nuni da Sabeeha kallon Sabeehan ya yi da tasa bayan hannun ta tana goge hawaye sannan ya kalli Ummi Rolex watch d'in hannunsa ya ce "Ummi mu zamu tafi," da sauri Sabeeha ta kalle shi. Fauwaz ya ce "Ya sai tafiya?" Gyad'a kai Maleek ya yi tare da juyawa ya nufi hanyar fita saurin Shan gaban sa Nasreen ta yi ta ce "Ya Maleek ga breakfast d'in can fa," ta fad'a tana nuna masa. Wajen ya nufa ya zauna Nasreen d'in ta zuba masa chips d'in a plate ta ajiye masa. Fork yasa ya d'ebo chips d'in ya kai bakinsa ji ya yi an fisge cokalin anyi jifa da shi zumbur Nasreen ta mik'e ta ce "Mahaukaciyar dabbar ina ce ke da zaki hana mijina cin abinci," tsawa Maleek ya bugawa Nasreen ya ce "Kina haukane zaki yi mata irin wannan zagin?" Ya kalli Sabeeha baice komai ba. Kowa mamakin abinda Sabeeha ta yi yake yi Ummi ta ce "Daughter Mai ya faru ne meyasa zaki hana son cin abinci?" Gyad'a kai Maleek ya yi alamar tambaye ta dai Ummi hawaye ne ya zubo a idanun Sabeeha ta ce "Dan Allah karka ci abincin nan," kallon mamaki ya yi mata meyasa zata ce Kar yaci abincin da ita da kanta ta dafa ya ce "Nikam saina ci domin yunwa nake ji," ya fad'a yana d'auko cup d'in kunun gyad'a ya kai baki saurin rik'e hannun sa Sabeeha ta yi ta ce "Karka sha Dan Allah," Ummi ta ce "Meyasa Daughter?" Da gudu Sabeeha ta isa wajen Ummi ta rik'e hannun ta ta ce "Please Ummi kice kar ya sha idan yaci abincin idan ya ci mutuwa zai yi," wannan karon kowa mamakin maganar da Sabeeha ta fad'a yake yi banda Maleek da ya gyara zaman sa akan kujera. Nasreen kuwa lokaci guda ta jik'e da zufa duk da Ac dake falon Ummi kuwa kasa magana ta yi Fauwaz ya ce "Amma ta ya kika san hakan?" "Ya Fauwaz ka yadda dani akwai poison a cikin abincin," a zafafe Fauwaz ya ce "Poison fa waye yasa masa poison a abinci?" "Nasreen ce tare da mahaifiyar ta kuma sun dad'e suna shirya hakan nasani cewar Nasreen da mahaifiyar ta basa sona sun tsaneni hakan ne yasa suke ta shirin yadda Zan bar gidan nan duk da nayi iya k'ok'arina wajen ganin ba wata hanya da ta had'ani da su amma su hakan bai yi musu ba hakan ne yasa suka shirya cewar Sameeha ta je can domin yin aiki yadda zasu yi amfani da ita wajen sa poison a cikin abincin ya Maleek ni kuma lokacin da aka kawo takardar dake d'auke da lokutan da Sameeha zata dinga zuwa aikin na canja lokutan nake zuwa ba tare da sun gane ni ce nake zuwa ba ta nan ne nake jin Shirin su a duk lokacin da naji Shirin su hankalina yana matuk'ar tashi dan dai kawai bana shiga mutane lokacin ne sai dai kawai a fuskanci Ina cikin damuwa jiya ne naji Shirin su akan cewar zasu zuba masa poison a abinci wanda sunsan idan har yaci ya mutu to dole ne nabar gidan nan domin ba Wanda za a zarga sama dani tunda nice na girka shine suka sa Fati domin ta yi musu aikin Ummi bansan meyasa suke son kashe shi ba Ummi Ina son shi bana so mu rasa shi Ummi rasa shi na nufin rasa tawa rayuwar," Sabeeha ta fad'a tana sakin kuka. Ummi kanta hawaye take yi domin bata yi tunanin tsanar da Hajiya Asiya ta yiwa Maleek ya kai harta iya raba shi da ransa ba Sameeha Rinaz da Sabreen ma hawayen tausayin Maleek dama kansu gaba d'aya suke yi domin sunsan da Maleek ya ci abincin nan basu da mafita. Maleek kuwa murmushi kawai saki domin jin maganar Sabeeha ta k'arshe shi yanzu ba maganar kashe shi ce ta tsaya masa a ransa ba kunnuwan sa ke maimaita masa "Ummi Ina son shi bana so mu rasa shi rasa shi na nufin rasa tawa rayuwar," Fauwaz kuwa take idanunsa suka yi jajir tsabar b'acin rai direct wajen Nasreen da tayi mutuwar tsaye ya yi ya d'aga hannu ya zabga wasu zafafan maruka guda biyu Wanda yasa ta ganin stars ya Kuma d'aga hannu da niyyar k'ara mata Ummi ta ce "Rabu da ita duk abinda suka yi dan kansu amma duk sanda ku ka cutar mun da yaro bazan tab'a yafe muku ba," Ummi ta fad'a tana share hawaye. Hanyar fita Fauwaz ya yi rai b'ace domin yaso anbar sa ya sauyawa Nasreen kamanni bai dad'e da fita ba ya dawo tare da yo wurgi da Fati a tsakiyar falon harta buge da centre table fuska ba alamar rahama Fauwaz ya ce "Dan uban ki me aka baki kisawa yayana a abinci," Fati na kuka ta ce "Dan Allah kuyi hak'uri cewa suka yi idan na aikata hakan zasu bani kud'ad'e sannan idan ban aikata hakan ba zasu koreni nabar gidan nan," "Aikuwa gidan nan dole kibar sa tunda bana ubanki bane," Rinaz ta wurgawa Fati wani matsiyacin kallo ta ce "Zaki tashi kibar mana gida ko sai nasa an canjawa fuskar ki kamanni?" Da gudu Fati ta tashi. Wata k'aramar k'walba ce ta fad'o daga gefen zanin Fati d'auka Fauwaz ya yi ya gani tabbas poison ne quick action ma kuwa. Mik'ewa tsaye Maleek ya yi ya kalli Nasreen da tayi tsilli-tsilli da idanuwa ya ce "Bayan yadda da auren ki da nayi bayan bana son ki wanne laifin na aikata muku da ku ke son ganin nabar duniyar?" Shiru Nasreen ta yi wata uwar tsawa Maleek ya daka mata wacce tasa kowa na falon razana. Nasreen kuwa wacce aka yi tsawar domin ta tuni ta kai k'asa ta ce "Dan Allah kayi hak'uri ganin irin soyayyar da kake yiwa Sabeeha ne wacce ni ko kwatar ta bansamu daga gare ka bane yasa nace gara kawai mu rasa gaba d'aya saboda ina son ka bazan juri ganin wata a matsayin matar ka ba Kuma Umma ce ta ce akwai wani yaron k'awar ta dake sona ya fika dukiya da kyau shiyasa amma dan Allah kayi hak'uri," kallon da ya watsa mata ne yasa ta shiga hankalin ta ya ce "Allah kuwa ya tsinewa so idan har haka yake ki sani na da ki ke gani na wuce duk inda ki ke tunani tabbas nasan akwai abinda aka zuba a cikin abincin tun lokacin da kika zo part d'ina har kina mun magana akan breakfast abinda bakya yi amma dan kina mahaukaciya kiyi tunanin ni bazan zargi akwai abinda kike k'ullawa ba tun shigowa ta falon nan naga tashin hankali a idanun Sabeeha baya ga haka kuma a d'azu nasan sanda ta je k'ofar part d'ina Wanda nasan haka kawai baza ta je ba idan har bani na Kira ta ba ki sani ni bazan cigaba da zama dake a matsayin matata ba ba dan ina tsoron karki sake tunanin cutar dani ba kin dad'e baki cutar dani ba na tsallake mutuwa daga wajen mak'iyana da dama wad'an da suka fi ki had'ari kallo d'aya na yiwa abincin nasan anyi poisoning d'in sa da wani k'aramun poison saboda haka na sake ki saki biyu domin bana tunanin sake kallon ki a matsayin matata," kuka Nasreen tasa ta ce "Dan Allah kayi hak'uri," wata uwar harara Maleek ya wurga mata ya ce "Wallahi karki kuskura idan kuwa ba haka ba saina yi miki dukan da saina sauyawa fuskar ki kamanni da iyayen ki ma baza su iya gane ki ba," Juyawa Ummi ta yi ta haura stairs tana hawaye. Maleek kuwa hanyar fita ya yi Fauwaz ya kalli Nasreen ya ce "Ni dama na dad'e da tsanar ki ban tab'a kallon ki a matsayin 'yar uwa ta ba saboda ko isasshiyar tarbiyya baki da ita zaki tashi kibar mana falo ko saina yi mummunan duka sannan ki sanar da uwar taki cewar plan d'in ku bai yi aiki ba," Rinaz ta ce "Dalla can malama tashi ki fita me ki ke jira sannan itama uwar taki ki sanar da ita nan gaba ko ciwon Kai yayana ya sake yi sai kun gane naku wasa ne," da gudu Nasreen tabar falon domin ganin kallon da Fauwaz ke mata tsab zai iya yi mata mummunan dukan da ya ambata. [10/25, 8:43 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️ RUBUTAWA DAGA HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ) SADAUKARWA GA MY DAUGHTER SABEEHA BILKISU Z.YA'U (🅱️K) AISHA MAGAJI DABO (AMA) Page 18 Haka Lantana da Zainabu suka tafi gida ko wannen su zuciyar sa ba dad'i ko da suka je gidan ko kallon arzik'i basu samu daga Kawu Bala ba. Da gudu Sabeeha ta shiga d'akin su ta kalli Sabreen dake gaban mirrow ta ce "Haba Sabreen dear please kiyi sauri time na tafiya fa," tana rufe baki wayar ta ta fara ringing d'auka ta yi tare da karawa a kunne ta ce "Sorry Sweetheart gani nan tahowa fa," shiru ta yi tana sauraron abinda Maleek ke ce mata sannan ta ce "A'a ba sai kazo ba gani nan," daga haka ta katse Kiran sannan ta yi hanyar fita daga d'akin Sabreen na biye da ita sun sha kyau ba k'arya. Suna sauka down stairs suka samu Mama zaune tana danna laptop Sabeeha ta ce "Mama mun tafi sai mun dawo," d'aga musu hannu ta yi ta ce "Ok bye take care," suka ce "Ok," daga haka suka fice a wajen mota suka samu Sameeha da Rinaz na jiran su sannan suka shige driver ya jasu zuwa gidan Ummi. Suna shiga gidan suka samu motocin sojojin Maleek a jere a k'ofar part d'in Ummi suna fitowa daga mota daidai lokacin Ummi ke fitowa daga part d'in ta tana rik'e da hannun Maleek ya sha kyau har ya gaji cikin maroon trouser da white T-shirt sai shirt bottles one a sama maroon da maroon p-cap sai wani farin takalmi sai k'amshi yake zabgawa. Tunda suka fito idanunsa yake akan Sabeeha haka itama kallon sa take yi kamar basu tab'a ganin juna ba ido d'aya ya kanne mata ita Kuma ta aika masa da murmushi Ummi ta ce "yammata na saukar yaushe?" Sameeha ta ce "Yanzu Ummi," har k'asa suka gaishe ta sannan suka gaida Maleek ya amsa cikin fara'a. Kallon agogon hannunsa Maleek ya yi sannan ya kalli Ummi ya ce "Ummi lokaci na tafiya ni zan wuce," murmushi Ummi ta yi sannan ta manna masa kiss a goshin sa ta ce "Allah ya kiyaye ya bada sa'a son," rungume Ummi ya yi ya ce "Ameen sweet mom," kallon su su Sabeeha ke yi cikin birgewa har ya saki Ummi ya juya ya ce "Auu Ummina bari kiji wata magana," saitin kunnen ta ya rad'a mata "Ummi Ina dawowa fa za ayi maganar auren mu da Sabee na," murmushi Ummi ta yi shi Kuma kai tsaye ya nufi inda Sabeeha ke tsaye tana kallon sa a gaban ta ya tsaya ya ce "Muje ko my Queen," tare suka jera zuwa motar sa inda take zagaye da sojoji a k'ame kamar gumaka. Tura baki Rinaz ta yi ta ce "To Yaya mu fa?" D'an waigawa ya yi ya ce "Ooh ku idan kunga dama ku kwana nan," dariya Sabeeha ke yi k'asa-k'asa tana yi musu gwalo Sabreen kuwa k'wafa ta yi tana cije baki. Bud'e musu mota aka yi suka shiga su Rinaz ma suka shiga wata motar suka bi bayan tasu motar sai Airport. Suna zuwa bayan an tsayar da motocin Maleek ya waiga ya kalle ta itama kallon sa take yi ya ce "Kin shirya?" "Dame kenan?" Ta tambaye shi murmushi ya yi ya ce "Da auren mu mana da zarar na dawo," d'an juya idanu ta yi ta ce "Eh na shirya fa," ya ce "Good girl," "Yawwa ya Maleek wai yaushe zaka dawo," shiru ya yi kamar mai yin tunani sannan ya ce "Ba dad'ewa zan dawo six months kawai zanyi," zare ido Sabeeha ta yi ta ce "Six months fa ni dai gaskiya ban yadda ba," ta fad'a cike da shagwab'a. 'yar dariya ya yi ya ce "To naji yanzu kwana nawa ki ka bani?" Shiru ta yi tana tunani sannan ta ce "Sweetheart ka dai ga k'asar nan ba tamu bace karka je ka zaunar musu a gari su zo suna yi maka gori saboda haka karka dad'e kayi kwana kad'an ka dawo," dariya Maleek ya yi ya girgiza Kai ya ce "Ok na fahimta baby nima bazan so su yi mun gori ba ai one week ya yi ba?" Ta ce "Yawwa ya yi," Kallon agogon sa ya yi ya ce "Ni zan wuce sai munyi waya ki kulamun da kanki sosai," ta ce "Toh Allah ya kiyaye," ya ce "Ameen," bud'e murfin motar ya yi zai fita itama ta bud'e tana cewa "Bari na raka ka mana," ya yi saurin cewa "No baby nan wajen da mutane bana so a kallar mun ke," ya kalli driver ya ce "Adam ka mayar mun da ita gida," cikin girmamawa Adam ya ce "Ok sir," daga haka Maleek ya juya suka tafi. Su Sabeeha ma direct gidan Doctor Maryam suka nufa bayan Adam ya yi parking motar ya fito ya bud'e mata motar tare da Sara mata tana fitowa ta ga su Rinaz su ma suna fitowa daga mota amma ko waccen su fuska a had'e dariya Sabeeha ke k'unshewa Sabreen da ta zo wucewa ta gaban ta ta ce "Zaki sani yaseen," daga haka suka wuce suka barta sai dariya take yi sai da ta gama dariyar sannan ta bisu a baya. Da sallama ta shiga falon Mama ce ta amsa banda su Sabreen da kowacce ta d'auke kai murmushi Sabeeha ta yi Doctor Maryam ta ce "Ni kam me yake faruwa ne ku ke ta had'e fuska tunda ku ka shigo?" Tashi Sameeha ta yi ta nufi fridge ta zubo ruwa a cup ta juyo tana fad'in "Hmm Mama ai yau mu muka ga love," Sabreen ta d'ora da cewa "Dube ni fa Mama yadda na d'auki kwalliya duk domin zani Airport amma kinsan me Sabeeha sister da ya MG suka yi mana kuwa?" Girgiza Kai Mama ta yi tana murmushi. Sabreen ta ce "Hmm Wai fa Mama muna tsaye muna jiran ya MG ya shiga mota mu tafi amma Sabeeha dear kad'ai ya yiwa magana suka tafi mota tare mu aka barmu," Sabreen ta girgiza kai irin na takaicin nan sannan ta ce "Har fa zanyi magana Rinaz habibty ta rigani cewa ya MG mu fa kawai sai cewa ya yi ai ya zata nan zamu kwana hmm Mama bakina k'in rufuwa ya yi," Rinaz ta ce "Ni Mama abinda yafi tafasani Wai Sabeeha sister ke yi mana dariya har da gwalo," "Wallahi kuwa habibty nima ta kunnani kuma Mama wai da muka je airport d'in kawai suka yi zaman su a mota ko me suke cewa oho Mama na tak'aice miki zance ni dai banga amfanin zuwan mu ba Dan ko a dawo lafiya bamu samu damar cewa Ya MG ba Mama Anya aka yi bikin Sabeeha sister zata ga 'yan k'afafuna a gidan ta kuwa?" Dariya Mama kawai ke yi Sabeeha dake bakin k'ofar falo kuwa sai da ta gama sauraron Sabreen sannan ta nufi cikin falon ta zauna ta ce "Mama kinsan me muke tattaunawa da shi kuwa?" Girgiza Kai Mama ta yi Sabeeha ba kunya ta yi tsalle ta ce "Wallahi Mama cewa ya yi yana dawowa za a yi maganar auren mu," ihu falon ya d'auka Sabreen ta rungume Sabeeha ta ce "Wayyo dad'i kice mun kusa warwasawa ai dear da bikin ki akwai kodumo," Rinaz ta ce "Ya kamata mu fito da anko mai kyawun gaske," Sameeha ta ce "Wanne color ne zai fi kyau," Sabreen ta ce "Pich ya yi," Rinaz ta ce "A'a sea green yafi," Sameeha ta ce "No sai dai red zai fi ko light blue," tab'e baki Sabeeha ta yi ta ce da Sabreen "Kinga malama cikani Karki karyamun wani gurin," sakin ta Sabreen ta yi tana hararar ta. Wucewa stairs Sabeeha ta yi tana dariya Mama ma dariya ta yi ta mik'e tana cewa "Ummi's girls Allah ya shirye ku," ta fad'a tare da shigewa bedroom d'in ta. Maleek kuwa jirgin su yana landing motocin sojojin sa na nan suka zo d'aukar sa jiniya kad'ai ke tashi ana bud'e masa mota ya shige sojojin suka ja motocin da gudun gaske zuwa gidan Maleek. Suna zuwa aka bud'e masa mota ya fita kallon su ya yi sun kai su ashirin ya ce "Ku biyo ni ciki," yana fad'ar haka ya yi gaba suna binsa a baya had'adden falon suka shiga su suka tsaya a falon shi kuma ya haura stairs. Wanka ya yi ya shirya sannan ya sauko down stairs suna nan a tsaye yadda ya barsu zama ya yi kan sofa sannan ya ce "Ku zauna," cikin bin umarnin sa suka zazzauna kallon Salman dake gefe a zaune ya yi sannan ya fara magana "Salman Ina son cikin sirri ba tare da sanin da motsin ku ba a Dubai ku je kuzo mun da Ahmad," Salman ya ce "Ok sir," daga haka suka fita domin cika umarnin ogan nasu. Kallon agogon hannun sa ya yi sannan ya kalli daining an jera masa komai tashi ya yi ya nufi daining d'in ya zauna ya fara cin abincin kamar mai cin magani sai yamutsa fuska yake ture plate d'in ya yi tare da jan tsaki daddad'an abincin Sabeeha ya tuna domin ji ya yi wannan ba wani teste duk da da yana jin dad'in abincin wata zuciyar ta ce aika saba dana Sabeeha ne shiyasa kaji wannan ba dad'i. D'aukar wayar sa ya yi ya Kira Sabeeha lokacin da yake Kira Sabeeha na wanka har Kiran ya katse sake Kira ya yi lokacin fitowar ta kenan k'arasawa inda wayar take ta yi ta d'aga ko ba a fad'a mata ba tasan Maleek ne domin ganin number d'in bata Nigeria bace a hankali ta ce "Hello sweetheart," ajiyar zuciya ya sauke sannan murya can k'asa ya ce "Baby kina lafiya?" Ta ce "lafiya but just missing you," murmushi ya yi ya ce "Same here," ya fad'a tare da mik'ewa daga kan kujerar daining d'in ya koma falon ya zauna ya ce "Nayi missing girkin ki naci abincin Juliet but ba dad'i," kamar tana gaban sa ta had'e fuska ta ce "Waye Juliet?" Sai da ya tab'e baki sannan ya ce "Wata mai yi min abinci ce," hmm kawai Sabeeha tace domin wani kishi ne ya tokare mata k'irji. Maleek ya gane hakan ya ce "Karki damu baby ni sam ban ma tab'a ganinta ba iya kacina kawai naci abincin ta," cikin shagwab'a ta ce "To ita wannan Surayya d'in fa ai ita kana ganin ta," d'an zare ido ya yi cikin mamakin a Ina tasan Surayya ya ce "Ina ki kasan batun Surayya?" "Ni dai kawai ka fad'a mun," dariya ya yi ya ce "Baby rigima ai Surayya ba tasan nazo ba kuma ai ina da ke ba abinda zai had'a ni da ita ki kwantar da hankalin ki kinji?" Noding kanta ta yi kamar yana ganinta. Su Salman ne suka shiga falon cikin wata iriyar shiga bak'ak'en riguna ne a jikin ta sai army green d'in wanduna sarawa Maleek suka yi jinjina musu kai kawai ya yi sannan ya ce da Sabeeha "Sabee na I will call you back later," ta ce "Ok bye," daga haka ya yi hanging up na wayar ya ajiye saman center table ya kalli Salman ya ce "Ina Ahmad?" Bud'e k'ofar falon Salman ya yi Ahmad ya shiga cikin shiga irin tasu Salman. Sarawa Maleek Ahmad ya yi "Zauna," Maleek ya fad'a yana nuna masa sofa zama Ahmad ya yi ragowar Sojojin suka juya domin barin falon Maleek ya ce "No ku zauna ya yi bayani kuna ji," komawa suka yi suka zazzauna. Kallon Ahmad ya yi ya ce "Meke tafiya?" Ahmad ya cire farin glass d'in idan sa ya ce "A bincinken da nayi akan safarar miyagun kwayoyi da makaman da za ayi a zaman su na k'arshe da suka yi suna shiri ne akan zasu shigar da kayan ne nan da 2 months sakamakon shugaban su da ya yi tafiya zuwa Egypt saboda haka suka bar maganar har sai ya dawo but sir gaskiya mutanen suna da had'ari na gaske akwai gang guda da suka shirya domin su shigar da kayan suna yin shiri sosai," jinjina kai Maleek ya yi sannan ya ce "Ba sunan ko da mutum d'aya daka samu a cikin su?" "Gaskiya har yanzu ba wani bayani game da hakan amma zan cigaba da bincika hakan," cewar Ahmad kallon sojojin Maleek ya yi ya ce "kunji dai abinda ke tafiya saboda haka ku kasance cikin shiri," suka amsa da "Ok sir," tashi Maleek ya yi ya nufi stairs su kuma suka fita daga falon. Tunda Maleek ya je Dubai baya samun zama domin shima bincike yake fita da kansa sai dai kullum da dare sai sunyi waya da Sabeeha. B'angaren su Kawu Bala kuwa rayuwa ta yi musu zafi zuwa yanzu sun fara nadamar abinda suka aikata domin ruwan sha wuya yake yi musu duk sun fita daga hayyacin su musamman Zainabu da take da tsohon ciki idan ka ganta kamar almajira. Kawu Bala ne ke tafiya yana tangad'i saboda yunwar da ta addabi cikin sa kayan jikin sa duk a yage kamar mahaukaci ya yi bak'i ya rame da ya gaji da tafiyar ne ya samu waje ya zauna a hankali hawaye ke malalowa a idanun sa duk Wanda ya gansa sai ya tausaya masa domin ko ka sanshi ba daga kallo d'aya zaka gane shi ba domin hatta kamannin sa sun sauya a hankali ya fara magana "Habu kana Ina Dan Allah ka dawo ka gafarceni tun kafin mutuwa ta riskeni na zalince ka Kai da matar ka harma da 'yan uku," kuka ya fashe da shi duk Wanda yazo wucewa sai ya kalli Kawu Bala cikin tausayawa. Doctor Maryam ce zaune a falon ta ita da Abba tana taya shi lissafin wasu kud'ad'e domin yanzu Abba ya zama babban d'an kasuwa super market ne da shi manya manya wad'an da akasan da su kullum dukiya k'aruwa take yi Sameeha ce ta yi sallama a falon suka amsa Abba ya ce "K'araso mana aminiya ta," k'arasawa ta yi ta zauna akan carpet ta yi k'asa da kanta ta yi shiru. Murmushi Doctor ta yi ta ce "Ya aka yi ne uhm?" A hankali ta ce "Mama dama uhm momyn Ya Umar ce tace tana so naje ta ganni shine nace bari na sanar muku zamu je tare da su Sabeeha dear," murmushi Doctor ta yi ta ce "To shikenan ba damuwa sai kun dawo," ta ce "To Mama," sannan ta tashi ta fita. Kitchen ta nufa Sabeeha ta samu tana yin abincin rana tare da su Halima ta ce "Dear ku shirya da yamma zamu je gaida mommyn Ya Umar na sanarwa Mama," Sabeeha ta ce "Ok ba damuwa," Sallama suka ji a falo da gudu suka fita domin jin muryar Ummi. Aikuwa ita ce rungume ta suka yi suna murnar ganin ta karb'ar jakar hannun ta Sameeha ta yi suka k'arasa cikin falon suna yi mata sannu da zuwa zama Ummi ta yi suka tsugunna har k'asa suka gaishe ta ta amsa cikin fara'a domin yaran kullum k'ara shiga ranta suke yi saboda ladabin su shiyasa take jin dad'i domin zasu zama surukan ta. Sabreen ce ke saukowa daga stairs itama da gudu ta k'arasa ta ce "Laa Ummi sannu da zuwa," Ummi ta ce "Yawwa daughter," bayan ta gaishe ta ne ta ce "Bari na Kira Mama," Sabreen ta tafi domin Kiran doctor Sabeeha Kuma ta nufi fridge ta kawowa Ummi ruwa da lemo. Doctor ce ta fito tare da Sabreen sai da Ummi da Doctor suka rungume juna sannan suka zauna Ummi ta ce "Kwana biyu naji yarana shiru shiyasa daga hospital na taho nan domin na gansu gaba d'aya gidan babu dad'i duk sun tafi sun barni," Mama ta yi dariya ta ce "Haka nima na gama fad'a musu jiya sai Sabeeha ta ce ai yau zasu je," Ummi ta ce "Wallahi kuwa da naji dad'i," Rinaz ce ke saukowa daga stairs da alama daga bacci take yi sai dai kallo d'aya zaka yi mata kasan ranta a b'ace yake. Da kallo suka bita da gudu ta k'arasa falon ta fad'a jikin Ummi ta saki kuka hankali tashe 'yan uku suka fara tambayar ta lafiya Doctor ta ce "Daughter lafiya maiya faru?" Cikin kuka ta ce "Mama Daddy wai na shirya next week zan tafi India karatu Ummi ni wallahi ki fad'a masa bazan je ba," Doctor ta ce "To meye damuwar daughter ko karatun ne baki so?" Girgiza Kai ta yi ta ce "A'a Mama ni bana so na tafi nabar 'yan uku ne," Sameeha mai saurin ku ka har ta fara hawaye su Sabeeha ma sunji ba dad'i sai dai ba yadda suka iya Ummi ta shafa bayan ta ta ce "Shikenan ya isa mamana zanyi magana da shi," sai lokacin Rinaz ta ji sanyi a ranta sannan ta zauna anata fira banda ita domin gaba d'aya jikin ta ya yi sanyi haka ma 'yan uku. Sai da suka ci abinci sannan Ummi ta tafi har mota suka raka Ummi sannan suka koma cikin gidan jikin su a sanyaye domin jin batun tafiyar Rinaz India. Da yamma suka shirya cikin shigar su ta alfarma sun sha kyau ba k'arya musamman Sameeha da suka nutsu wajen shirya ta wani milk less mai flowers coffee color riga da skirt suka yi mata simple make up tasa mayafi coffee color haka ma jaka da takalmin k'afar ta sai zabga k'amshi suke yi sallama suka yiwa Doctor sannan suka fita inda umar kw jiran su a waje. Suna fita suka shiga mota suka tafi tun daga nesa suke kallon gidan domin ya had'u ba k'arya horn ya yi gate man ya bud'e musu gate suka shiga parking ya yi sannan ya fita da kansa ya bud'ewa Sameeha mota ta fita su Sabeeha ma suka fita suka nufi cikin gidan Umar na gaba suna binsa a baya. Da sallama suka shiga babban falon gidan da ya gaji da had'uwa Umar yana k'wala kiran "Mummy! Mummy!!" Saukowa stairs mommy ke yi ta ce "Ka fa kiyayeni Faruk irin wannan Kira haka," dariya Umar ya yi ya ce "Mummy gamu munzo," ya fad'a yana nuna mata su Sameeha. Cikin fara'a Mummy ta ce "Sannun ku da zuwa," tun kafin su yi magana Umar ya ce "Yawwa," hararar sa Mummy ta yi ta ce "Da Kai nake," sannan ta kalli su Sabeeha ta ce Ku K'araso yarana. Har k'asa suka gaisheta sannan suka zauna Umar na zaune a gefen Mummy bakin sa yak'i rufuwa Sameeha kuwa sarkin 'yan kunya kanta na k'asa ta kasa had'a ido da Mummy Mai aiki Mummy ta kira take aka cika musu gaba da abinci kala kala da lemuka. Sannan mummy ta kalli Rinaz ta ce "Daughter ya Ummin ki fa?" A hankali ta ce "Tana lafiya tana gaida ki," ta ce "Masha Allah Ina amsawa," Lemo Rinaz ta zuzzuba musu a cups ta d'auka tana sha haka ma Sabreen. "Amma dai 'yan uku ne ko?" Umar ya ce "Eh Ummi ga Sabeeha wacce Maleek zai aura wannan Sabreen ita kuma ta Fauwaz then ga sarauniya ta masoyiya ta matata da yardar Mai sama Sameeha," ya fad'a yana nuna Sameeha da ta yi k'asa da kai saboda duk ya bata kunya. Mummy ta ce "Masha Allah kace duk yarana ne anan zo nan kinji d'iyata," a hankali Sameeha ta tashi ta k'arasa ta zauna k'asan carpet mummy ta ce "Sameeha," a hankali Sameeha ta d'aga kanta ta kalli maman Umar. A hankali Mummy ta ce "Masha Allah,Allah ya yi muku albarka Allah ya kaimu lokacin bikin ku yarinyata da gani kina da nutsuwa gaskiya naji dad'i sosai na Kuma yi murnar kasancewar ki suruka a gareni domin kullum addu'ata Allah ya had'a faruk da mata ta gari sai gashi Allah ya amshi addu'a ta amma fa sai kinyi hak'uri da wannan fitinannen," k'asa da Kai Sameeha ta yi tana murmushi tura baki Umar ya yi ya ce "Kai mummy so ki ke ta rainani Kuma ai bata manta ba Ummi ta ce ta rik'e ni gam domin karta rasani," dariya kowa na falon ya yi har da Mummy. Sun d'an jima a gidan sannan suka yiwa mummy sallama bayan ta cika su da abin arzik'i su turaruka kayan make up da sark'ok'i da agoguna masu tsadar gaske suna ta godiya sannan suka tafi. Direct gidan Ummi Umar ya Kai su da sallama suka shiga falon Fauwaz suka samu kwance akan kujera yana waya yana cewa "Kai haba ki kwantar da hankalin ki zan zo insha Allah," ai tuni Sabreen ta had'e girar sama da ta k'asa sai ka rantse bata tab'a dariya ba tunda take. A zafafe ta nufi inda Fauwaz ke kwance ta fisge wayar ta kara a kunne muryar budurwar ta ji tana cewa "Please karka k'i zuwa I'm waiting for you," "To munafuka bazai zo ba Wallahi indai Sabreen na raye sai dai idan mutuwa nayi ke yanzu ko kunya bakya ji kinsa mijin wata a gaba kina cewa yazo wajen ki to Wallahi ki kiyayeni marar aji kawai," fisge wayar Fauwaz ya yi ya kashe ya ce "Haba my Love wannan fa friend d'ita ce tare muka yi school da ita a Landon," hararar sa Sabreen ta yi sannan ta zauna a inda ya tashi ta zabga tagumi sai hawaye. Ummi dake kallon su ta saman bene ta yi murmushi ta koma d'aki abinta. Hankali tashe Fauwaz ya zauna gefen Sabreen yasa hannunsa ya cire mata tagumin harara ta zabga masa sannan ta cigaba da kukan ta ya ce "Please dear calm down," cikin muryar kuka ta ce "Ank'i ai calm down d'in kuma wallahi Allah ya isa tsakanina da ita iya muryar ka da taji," ta fad'a tana sakin wani kukan shi dariya ma ta bashi ya dake ya ce "Please mana ki fahimce ni," murgud'a Baki ta yi. Sabeeha kuwa dariya ta yi ta girgiza Kai sannan ta haye stairs. Su Sameeha kuwa tsayawa suka yi ganin drama tashi Sabreen ta yi zata bar falon tashi shima Fauwaz ya yi ya janyo mata hannu abinka da mara k'arfi tafiya gaba d'aya ta yi zata fad'i yayi saurin rik'o abar sa ta fad'a a jikin sa. Ai tuni su Sameeha suka zanzare sukabar falon Sabreen kuwa ba k'aramun tsorata ta yi ba ta fara k'ok'arin janye jikin ta amma Fauwaz ya hanata ta ce "Ni kawai ka cikani na tafi," ya ce "Please don't be upset with me try to understand me dear," ta ce "To ni cikani," sakin ta ya yi ta d'anja baya sannan ta kwasa da gudu ta yi stairs tana cewa "Ank'i a tsaya d'in," zama kan kujera Fauwaz ya yi ya dafe Kai ya ce "Tofah meerah kin jawo min ruwa ya zanyi da rigimar Sabreen," Sabreen kuwa da gudu ta shiga d'akin Rinaz a nan ta same su dariya Sameeha ta yi ta ce "Dear wannan gudun fa?" "Bakomai," Sabreen ta fad'a tana zama Sameeha ta ce "Amma sister ya kamata ki tsaya ki saurari abinda zai fad'a miki," shiru Sabreen ta yi ba magana Rinaz ta ce "Ya Fauwaz na falon?" Gyad'a kai Sabreen ta yi ficewa Rinaz ta yi. A falo ta samu Fauwaz a zaune da kallo ya bita har ta k'arasa kusa da shi ta zauna kallo d'aya ya yi mata yasan tana da damuwa ya ce "K'anwa ya aka yi ne?" Hawaye ta share ta ce "Ya Fauwaz kaji wai Daddy India zai turani karatu kuma ni wallahi bana so na tafi nabar 'yan uku sai dai mu tafi tare," zare ido Fauwaz ya yi ya ce "K'anwa kenan maganar ku tafi tare babu ita domin kwanan nan zamu yi wuff da su amma ki gayawa Ummi ta yi masa magana may be ya janye," "Na fad'a mata tace zata yi masa magana amma kana ganin zai hak'ura kasan halin dad indai magana akan karatu ne Kuma fa next week yace zan tafi," jinjina Kai Fauwaz ya yi ya share mata hawaye ya ce "Ki kwantar da hankalin ki insha Allah zai barki kiyi a nan kinji?" Noding kanta ta yi sannan ta tashi ta nufi stairs. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya satin su d'aya a gidan Ummi suka koma gidan Mama inda a sati d'ayan nan Sabreen bata bari suna had'uwa da Fauwaz ko wayar sa dena d'agawa ta yi duk ya damu ya fad'awa Ummi ita Kuma ta ce ba ruwan ta sunfi kusa. Sabeeha kuwa tana lissafe da ranar da Maleek ya ce Mata zai dawo ya wuce yana sati na biyu amma bai yi mata maganar zai dawo ba itama kuma bata yi masa ba saboda tasan yanayin aikin nasu. Kawu Bala ne zaune a tsakar gidan sa ya zabga uban tagumi kamar ko yaushe Lantana na gefe itama duk ta fita hayyacin ta saboda yunwa Zainabu na gefe a kwance kan tabarma haihuwa ko yau ko gobe kallon ta Kawu ya yi ya kalli Lantana ya ce "Lantana mun cuci kan mu ki duba halin da muka jefa kanmu a ciki nayi nadamar abinda na yiwa d'an uwana da iyalan sa ki duba abinda zamu ci ma babu duk wani abu namu na amfani duk mun siyar gidan nan kad'ai ya rage mun bansan me Kuma zai faru ba duk sanda Maryam ta taka k'afar ta a garin nan ba nayi nadama Wallahi," ya fad'a yana share hawaye. Lantana ta ce "Tabbas mun tafka babban kuskure a rayuwar mu mun aikata laifi babba banga amfanin hassada ba a rayuwata nima nayi dana sani gashi Sadam tunda ya koro yarinyar nan har yau bai ko lek'o ganin lafiyar ta ba tir da halin mu," Zainabu na gefe sai hawaye take sharewa domin zuwa yanzu tasan meye rayuwa. Motoci ne wajen guda goma suka yi parking a gidan su Maleek guards ne suka bud'ewa Uncle mota ya fito fuskar sa a had'e can wata motar aka bud'ewa Daddy mota ya fito fuskar sa fal farin ciki domin zai ga farin cikin sa kallon sa Uncle ya yi ya ja tsaki ya wuce fuuu zuwa part d'in Hajiya Asiya Daddy ma ya nufi part d'in Ummi. Da sallama Daddy ya shiga falon Ummi dake saukowa stairs ta tsaya tana kallon sa domin bai sanar da ita da zuwan sa ba murmushi Daddy ya yi tare da bud'ewa Ummi hannu a hankali ta taka har inda yake ta fad'a jikin sa ya rungume ta a tare suka saki ajiyar zuciya domin sun dad'e rabon su da juna a hankali Ummi ta ce "Sannu da dawowa," d'ago fuskar ta ya yi ya kalle ta sannan ya ce "Yawwa Aysha Ina zuwa haka?" Murmushi ta yi ta ce "Hospital amma na fasa," ta fad'a tana jan hannun Daddy zuwa upstairs ruwan wanka ta had'a masa sannan ta sauko k'asa ta nufi kitchen ta fara yi masa simple food bata bar kitchen d'in ba sai da ta gama ta jera komai a daining sannan ta koma bedroom d'in ta wanka ta sake yi ta shirya cikin maroon less ta gaji da yin kyau sai k'amshi take yi ta juya ta kalli Daddy da ya tsaya kallon ta ta ce "Mu je kaci abinci," tare suka je daining d'in Ummi tayi sarving d'insa suka fara cin abincin. Suna gamawa suka koma falo suka zauna Fauwaz ne ya fito daga part d'in sa ganin mahaifin nasu ya k'arasa falon ya ce "Ina kwana Daddy ka dawo lafiya?" Daddy ya ce "Lafiya lau Abbana Ina zuwa haka?" Kallon agogon sa ya yi ya ce "Daddy zani office ne," murmushi Daddy ya yi cikin son yaron nasa ya ce "To a dawo lafiya," cikin jin dad'in addu'ar Fauwaz ya ce "Ameen Daddy Ummi na tafi," itama ta yi masa addu'a sannan ya fita. Kallon Ummi ya yi ya ce "Abbana kenan ya zama cikakken mutum saura aure," murmushi Ummi ta yi ta ce "Aikuwa dai amma wannan zuwa naka haka dafatan dai lafiya?" Ajiyar zuciya Daddy ya yi ya ce "To nima bana ce ba Aysha ina tsaka da aiki Yaya ya kirani yana ta yi mun fad'a ni gaba d'aya ban fahimci akan meye ba sannan ya ce lallai na shirya yau muzo gida shine dalili," gaban Ummi ne ya fad'i domin tasan dole akan Maleek ne bata so a karo na ba adadi Uncle ya rusawa yaron ta farin cikin sa. "Aysha lafiya kuwa?" Girgiza Kai Ummi ta yi cikin murmushi ta ce "Bakomai muje ka huta nasan ka gaji," stairs suka nufa Daddy ya ce "Banga Rinaz ba tana Ina?" Ummi ta ce "Tana gidan Maryam," gyad'a kai Daddy ya yi. Uncle kuwa yana shiga falon ya tsaya turus jin muryar Nasreen na cewa "Wallahi Umma kin gama dani ashe Dan ki kashe mun aure ne ki ka shirya min wannan k'aryar kika had'ani da yaron k'awar ki dake wata k'asar can tare da matar sa harma da yaran sa hud'u yana yaron shago mummuna da shi ashe biyan sa ki ka yi ya yaudare ni ni kika rabani da mijina Wanda ya fisa komai," shiru Hajiya Asiya ta yi ba magana Uncle ya k'arasa falon Nasreen na ganinsa ta fad'a jikin sa ta saki kuka ta ce "Daddy Umma bata sona ni kawai ka mayar dani gidan mijina ta biya wani ya yaudare ni nima Kuma na biya shi ya fad'amun gaskiya," shafa bayan ta Uncle ya yi ya ce "ki kwantar da hankalin ki nima abinda ya dawo dani kenan na mayar dake d'akin ki kinji?" Noding kanta ta yi tana jin wani farin ciki a ranta. Sabeeha ce kwance akan gado a d'akin Doctor waya take yi ta ce "Amma sweetheart tahowa zaka yi yanzu meyasa hakan?" Daga can Maleek dake sauka stairs ya ce "My choice Ina tunanin akwai wata damuwar ce tun jiya Uncle ke kirana akan lallai yau nazo gida na sanar da shi akwai abinda nake yi a nan mai muhimmanci bazan samu damar zuwa ba shine yanzu Daddy ya kirani yana ta yi mun fad'a tare da bani umarnin yanzu na taho bansan me Uncle ya sanar da shi ba shiyasa nasa aka shirya mun flight d'ina yanzu zan taho amma ki kwantar da hankalin ki," Maleek ya fad'a tare da shiga mota. Sabeeha kuwa tunda aka ambaci Uncle gaban ta ya fad'i dakewa kawai ta yi ta ce "Tom Allah ya kawo ka lafiya," ya amsa da "Ameen," sannan ya katse kiran. Rinaz dake tsaye a bakin k'ofa ta kalli Sabeeha ta ce "Dear lafiya naga kamar kina cikin damuwa?" Kallon Rinaz ta yi ta ce "Bakomai kawai dai Daddy ya dawo tare da Uncle," shiru Rinaz ta yi domin tasan zuwan Uncle ba alkhairi bane gashi har da Daddy Kuma suna neman Ya Maleek kallon Sabeeha ta yi ta ce "Gaskiya Dear akwai wata matsalar amma ki kwantar da hankalin ki bari nazo naje gidan duk yadda ake ciki zan sanar miki," Sabeeha ta ce "Toh saina jiki," tafiya Rinaz ta yi. Daddy kuwa yana gama Kiran Maleek ya kalli Ummi ya ce "Aysha duk yadda aka yi zuwan nan akan Maleek ne tunda kullum shike yawo mana matsala shine ma tunda gashi Yaya ya kirani akan na Kira shi lallai ya dawo Mai ya aikata?" Tab'e baki Ummi ta yi ta ce "Ba abinda ya aikata wanda yake ba daidai ba mu dai jira muji," Ummi na fad'in haka tabar d'akin. Rinaz kuwa tana zuwa gida direct d'akin Ummi ta nufa a zaune ta samu Ummi ta k'arasa ta zauna ta ce "Ummi lafiya Uncle ya zo tare da Daddy a wannan ranar tunda ba ranar zuwan su bace kuma meyasa zasu ce Yaya yazo?" Numfashi Ummi ta sauke ta ce "Mamana kema kinsani bazai wuce akan Nasreen ba so suke su hargitsawa yarona farin cikin sa su burin su kullum su ganshi a damuwa," Ummi ta fad'a kamar zata yi kuka Rinaz ta ce "Ummi mu taya Yaya da addu'a kawai insha Allah abun su kansu zai koma," sun dad'e suna tattaunawa akan lamarin sannan Ummi ta yi alwala ta tayar da sallah Rinaz ma ta wuce d'akin ta ta yi wanka tayi alwala. A sanyaye Sabeeha ta shiga d'akin su ta yi wanka Sabreen dake kwance ta kalle ta ta ce "Lafiya kuwa sister?" "Eh lafiya," Sabeeha ta fad'a tare da nufar wadrobe ta d'auko kaya ta saka ta tayar da sallah kyale ta kawai Sabreen ta yi amma tasan tana da damuwa. Ummi da Daddy da Rinaz na zaune a falo Uncle ya shiga falon Nasreen a bayan sa tare da Hajiya Asiya ko sallama basu yi ba suka samu waje suka zauna Ummi ta kalli uncle ta ce "Yaya Ina wuni anzo lafiya," banza Uncle ya yi da ita Ummi bata damu ba ta kalli Hajiya Asiya ta ce "Asiya Ina wuni?" Tsaki Hajiya Asiya ta ja Ummi kuwa ta ja bakin ta ta yi shiru Rinaz kuwa ganin da Daddy a wajen ta gaishe da Uncle amma ko kallon ta bai yi ba bare ya amsa shiru falon ya d'auka Tsayuwar motoci suka ji a k'ofar part d'in Maleek ne ya yi sallama a falon Ummi Daddy ne da Rinaz kad'ai suka amsa Nasreen kuwa da kallo ta bi shi kamar ta had'iye shi saboda tsabar kyan da ta ga ya k'ara shi kuwa waje ya samu ya zauna sannan ya ce "Daddy Ina wuni ka dawo lafiya?" A ciki-ciki Daddy ya ce "Lafiya," saboda haushin Maleek yake ji saboda yana basa matsala shi da yayan sa. Maleek kuwa kallon Ummi ya yi abun tausayi saboda bai ji dad'in yadda Daddy ya amsa masa gaisuwa ba ya ce "Ummina Ina wuni?" Ta ce "Lafiya lau son ka iso lafiya?" Ya ce "Lafiya lau Ummina," Rinaz ta gaishe shi ya amsa. Saboda iyayi Nasreen ta ce "Ina wuni ya Maleek ka dawo lafiya?" Banza ya yi mata Uncle ya ce "Au baza ka amsa ba ana gaishe ka?" Shiru Maleek ya yi kamar bada shi ake magana ba sai ma cewa ya yi "Uncle Ina wuni," Uncle bai ko amsa ba ya fara balbala fad'a "To bari kaji daka amsa gaisuwar daughter da karka amsa dole ne ka mayar da ita wato saboda bamu isa da kai ba shine zamu aura ma yarinya ka sake ta har saki biyu saboda baka da tarbiyya?" "Saki fa?" Daddy ya maimaita yana kallon Maleek Uncle ya ce "Eh saki har biyu saboda shi mahaukaci ne kuma sakin ma akan budurwa," shiru Maleek ya yi kansa a k'asa idanunsa sunyi jajir saboda b'acin rai ga zagi ana k'are masa. Daddy shima ransa a b'ace ya ce "Saki Abdul-maleek ka saki 'yar uwar ka har saki biyu to akan wane dalili," kafin Maleek ya yi magana Uncle ya yi caraf ya ce "Ba shi da wani dalili wanda ya wuce a kan budurwar da yake so wannan ne dalili idan Kuma ni baka yadda dani ba nayi k'arya to ka cigaba da tambayar sa," Uncle ya fad'a duk Dan kar aba Maleek damar magana saboda yasan duk abinda Nasreen da mahaifiyar ta suka aikata. Daddy kuwa jin abinda Uncle ya fad'ane yasa shi yin shiru Ummi ta ce "Son bai sake ta ba dalili ba..," d'aga mata hannu Uncle ya yi ya ce "To masu d'a kare shi Zaki yi kenan ai dama naji ance budurwar tasa 'yar gidan aminiyar ki ce dole ki so a saki Nasreen domin ya aure ta domin naji labarin a gaban ki aka yi sakin amma baki tsawatar masa ba kece ma ki kasa ya yi sakin," kallon Ummi Daddy ya yi girgiza masa Kai Ummi ta yi alamun ba bata da hannu domin jin Uncle na neman had'a mata sharri wajen mijin ta. Sai lokacin Maleek ya d'aga Kai ya kalli Daddy domin baya son abinda zai had'a tsakanin Ummin sa da Daddy ya ce "Ba ruwan Ummina dan ra'ayin kaina na sake ta domin bana so na cigaba da zama da ita," "Ato Hamisu ka dai ji da bakin ka ko ya sake ta ne dan ya tozar ta mu," Fauwaz ne ya yi sallama a falon waje ya samu kusa da Maleek ya zauna baice komai ba. Ucle ya ce "To baka isa ba tunda ba Kai ka haifemu ba yanzu sai ka mayar da ita Kuma babu saki tsakanin ka da ita Kuma wannan yarinyar dole ne ka rabu da ita," a razane Maleek ya kalli Uncle idanunsa kamar an watsa masa jajjagaggen attaruhu Uncle ya ce "Kalle ni dakyau yarinya tun yanzu tasa ka saki 'yar uwar ka ai bata arzik'i bace saboda haka ba kai ba ita Kuma yanzu yanzu ka mayar da daughter," Zumbur Fauwaz ya mik'e tsaye ya ce "Saboda me Yaya zai mayar da Nasreen bayan ba k'aunar sa take yi ba mahaukaciya ce ita dabba wacce taso ta ga bayan...," Kasa k'arasa maganar Fauwaz ya yi saboda marin da Daddy ya zabga masa ya ce "Ashe dama baka da hankali bansani ba idan ka Kuma magana anan saina b'ata maka rai Kuma lallai ka fito da mata kayi aure kabar gidan nan tunda baka da amfani a gidan kai kuma umarni ne wannan ba shawara ba yanzu ka mayar da matar ka," Daddy ya fad'a ransa a b'ace. Hannu Maleek yasa ya rik'o na Fauwaz ya zaunar da shi zama Fauwaz ya yi dafe da kunci domin Daddy bai tab'a sa hannu ya daki d'ansa ba sai ranar Rinaz dake gefe sai hawaye take yi Ummi ma hawaye ta goge idanunta na kan Maleek domin ganin yanayin sa ya canja sosai jikin sa har rawa yake yi sannan ga gumi Yana yi duk da Ac dake falon shiru kawai ta yi. "Kai muke jira," Daddy ya fad'a cikin had'e fuska yana kallon Maleek. A hankali Maleek ya bud'e baki murya na rawa ya ce "Na mayar da ita," ya fad'a hawaye na zuba a idanunsa sannan ya ce "Daddy bazan yi saki ba tare da wani dalili ba amma na mayar da ita duk abinda ta yi mun Allah yana ganin ta amma Daddy Ina so na k'ara aure," kafin Daddy ya yi magana Uncle ya yi caraf ya ce "Baza ka k'ara auren ba saboda yarinyar bata da tarbiyya tun tana waje tasa ka saki matar ka ina ga ta shigo sannan saboda ba son daughter ka ke ba ita ke son ka idan ka auri waccan baza ka yiwa daughter adalci ba saboda haka baza ka yi auren ba," Daddy jin bayanin Uncle ya ce "Haka ne baza ka yi adalci ba saboda haka karna k'ara jin batun aure a bakin ka," zuwa yanzu kukan Ummi Mai sauti take yi domin tausayin yaron ta. Maleek kuwa lokaci guda zuciyar sa ta yi wani irin bugawa da sauri ya mik'e tsaye ya yi hanyar fita sai dai kafin ya fita sai ji suka yi timm ya fad'i a wajen. Da gudu Ummi Fauwaz Rinaz Daddy dama Nasreen suka yi wajen sa suna Kiran sunan sa amma ko motsawa bai yi ba. A rikice Ummi ta ce "Fauwaz mu kai shi asibiti," da gudu Fauwaz ya fita ya Kira Salman suka kama Maleek zuwa mota Ummi da Daddy suka bisu a baya Rinaz ma zata bisu Daddy ya ce ta zauna a gida su kuma suka tafi. Uncle kuwa tab'e baki ya yi ya fice shi da Hajiya Asiya. Rinaz kuwa Kuka ta saki ta kwanta taita kuka Sabeeha kuwa hankalin ta kasa kwanciya ya yi ko abinci kasa ci ta yi duk ta damu jiran Kiran Rinaz kawai take yi gashi har yanzu magrib shiru sannan Maleek ma shiru bai kirata ba kasa hak'uri ta yi ta Kira wayar Rinaz. Rinaz dake kwance zazzab'i ya rufe ta ta d'auki wayar ta ce "Hello," Sabeeha ta ce "Please Dear maike faruwa?" Hawaye ne ya fito daga idanun Rinaz ta ce "ki hau WhatsApp yanzu," "Bani da WhatsApp lafiya ki ke kuwa?" Sabeeha ta tambaya a rikice jin muryar Rinaz wani iri Rinaz ta ce "Ki karb'i ta Sabreen zan tura miki sak'o yanzu," Sabeeha ta ce "Ok turamun," Sabeeha ta fad'a tare da kashe wayar ta nufi down stairs da sauri. A zaune ta samu Mama da Abba da su Sameeha a falo ta kalli Sabreen ta ce "Sabreen dear bani wayar ki," mik'a mata Sabreen ta yi ta karb'a tare da komawa d'aki da kallo suka bita ganin ta kamar a d'an hargitse sai dai ba Wanda ya kawo komai a ransa. Tana shiga d'aki ta kunna da ta kasancewar ba chart da mutane sosai Sabreen ke yi ba dan da nan message d'in Rinaz ya shigo jiki na rawa Sabeeha ta bud'e recording ne Rinaz ta tura mata wanda ta yi shi tun shigar su Uncle part d'in Ummi. Zama ta yi gefen gado tana sauraro tass take jin abinda ke faruwa da maganar Uncle da ta Daddy duk abinda aka tattauna tana ji wasu hawaye ne masu zafi suka zubo mata jin abinda Uncle ke fad'i a kanta Wai bata da tarbiyya tausayin kanta da Maleek ne ya kamata kuka Mai sauti ta fara tana yinsa kamar ranta zai fita bata ji k'arar fad'uwar Maleek ba sai dai ji da ta yi hankali take su Ummi na Kiran sunan sa daga nan recording d'in ya k'are. Hankali tashe ta tashi zaune gaban ta na fad'uwa jiki na rawa ta d'auki wayar ganin da voice a k'asa ta yi saurin bud'ewa ta kara a kunnen ta. Muryar Rinaz na kuka ta ji tana cewa "Sabeeha Yaya yanke jiki ya yi ya fad'i tun lokacin har yanzu suna asibiti tare da su Ummi tun lokacin likitoci suke a kansa amma har yanzu bai farfad'o ba," Sabeeha na jin haka ta mik'e zumbur gaban ta na fad'uwa idanunta kuwa sai ambaliyar hawaye suke yi. Kamar mahaukaciya ta fara magana a fili "Ya fad'i likitoci na kansa ko dai ya mutu ne Rinaz ta b'oye mun A'a bai mutu ba to meyasa bai tashi ba har yanzu?" Wata zuciyar ce ta bata amsa da kin manta yana da ciwon zuciya ko dai ya tashi ne. Ai da gudu Sabeeha ta nufi down stairs yana kuka ko kallon inda su Mama suke bata yi ba ta yi hanyar fita ganin ta a hakane suma ya razana su da sauri Sameeha ta rik'o ta ta ce "sister Ina Zaki je lafiya kuwa?" Tana kuka ta ce "Cikani Sameeha ki cikani naje naga halin da yake ciki," wajen Mama da Abba suka yi ganin yadda Sabeeha ta koma kamar mai aljanu Sabreen ta ce "Dear lafiya?" Cikin kuka Sabeeha ta ce "Sister mutuwa zanyi kinsan me Rinaz ta fad'a mun kuwa?" Jin haka Sabreen ta nufi stairs domin d'auko wayar ta ta kira Rinaz ta ji meke faruwa. Doctor ta rik'o hannun Sabeeha ta ce "Lafiya maiya faru Ina Zaki?" Abba ma ya ce "Aminiya ta maiya faru ne?" Kuka ta fashe da shi ta ce "Mama na shiga uku," tana fad'ar haka ta fad'a jikin Mama a sume. A rikice suka fara Kiran sunanta Amma ko motsi bata yi ba. [10/25, 8:43 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️ RUBUTAWA DAGA HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ) SADAUKARWA GA MY DAUGHTER SABEEHA BILKISU Z.YA'U (🅱️K) AISHA MAGAJI DABO (AMA) Page 17 Da sallama Kawu Bala ya shiga gidan sa ransa fess domin so yake idan ya je d'aurin auren yarinyar malam saleh ya bawa abinci mamaki. Lantana ya k'walawa kira ta fito tana hura hanci tab'e baki Kawu ya yi ya ce "Je ki ki d'auko mun wannan kayan nawa babbar riga zani d'aurin aure," hanyar zaure Lantana ta nufa Kawu ya ce "Baki ji me nace bane kayana nace ki kawo mun fa," ba tare da ta waiga ba ta je har sharar da ta zuba kayan ta d'ebo su ta je ta zubar a gaban Kawu Bala. Ba tare da ya kalli Kayan ba ya ce "Wai ni kuwa Lantana baki samu tab'in hankali ba taya Ina yi miki maganar kayana zaki d'ebo mun bola?" Kyalkyalewa da dariya Lantana ta yi ta ce "Kalli dai dakyau Bala kayan naka ne ai," saurin kallon gaban sa Kawu ya yi aikuwa idanunsa suka yi masa tozali da kayan sa da Lantana ta yiwa gutsi-gutsi. Saurin mik'ewa Kawu ya yi ya nuna Lantana ya ce "Me nake gani haka?" "Kayan ka mana ai nasan bayan su baka da komai shiyasa na huce haushin marin da kayi min a kansu Kuma wallahi kad'an ka gani daga aikin Lantana," jinjina kai Kawu ya yi zuciyar sa fal takaici da jin haushin abinda ta yi masa ya ce "Eh lallai ne naga aikin ki Lantana yanzu kuma zaki ga na Bala," ya fad'a yana d'aukar wani itace dake gefe. Kamar wasa Lantana ta ji saukar itaccen a goshin ta wani uban ihu ta saki dan lokaci d'aya ta ji kanta ya yi mata mugun nauyi da gudu ta nufi d'aki sai dai kafin ta rufe har Kawu Bala ya shige yana shiga yasa sakata a k'ofar ya fara jibgar ta. Ihu Lantana ke zabgawa tana cewa "Na tuba wallahi na tuba bazan k'araba shikenan zai kashe ni wayyo Allah hancina," haka lanatana tai ta ihu tana neman taimako amma Kawu bai dena nad'arta ba fad'i ya ke yi "Yau ai banga mai ceton ki ba a gidan nan dan Wallahi sai nayi Miki mummunan duka shegiya mai bak'in hali," Nasreen ce kwance saman gadon ta sai kuka take yi a fili ta ce "Wallahi Allah ya isa Umma da kika rabani da mijina," ta fad'a tana k'ara fashewa da wani sabon kukan sannan ta d'auki wayar ta ta kira wayar Uncle yana d'agawa ba tare da ta gaishe shi ba ta fashe da kuka har cewa ta shiga uku. A rikice Uncle ya ce "Daughter lafiya maiya faru?" Cikin kuka ta ce "Daddy ya Maleek ya sakeni," "What!?" Daddy ya tambaya tare da cewa "Ki kwantar da hankalin ki ki dena kuka next week zan zo k'asar zanji dalilin da yasa hakan dan uban sa tunda shi ba a isa da shi ba yaro sai rashin tarbiyya to zamu dawo tare da uban nasa naji ko shine yasa shi ya sakar mun ke," ya fad'a tare da katse Kiran. B'angaren Lantana kuwa sai da Kawu Bala ya gaji dan kansa sannan ya kyale ta ya fito daga d'akin ya fice yana masifa. Lantana kuwa da dafa bango ta fito daga d'akin ga wani jiri dake d'ibar ta mayafin ta ta zara dake kan igiya ta fita tana tangad'i ko da ta fita bata ga Kawu Bala ba ta zari hanya ta tari mai machine ta fad'a masa inda zai Kai ta tana suna zuwa ta nuna masa wani gida mai koren fenti ya tsaya. Sauka ta yi a hankali sannan ta kalli mai machine d'in irin d'an yau d'in nan ne Kuma daga ganinsa yana shaye shaye ga gashin nan an tsayar da shi a tsakiyar kai yayi buzu-buzu Lantana ta ce "D'ana yi hak'uri bari na shiga cikin gidan nan na karb'o maka kud'in ka," kallon banza ya yi Mata ya ce "Bangane d'anki ba Kinga malama bana son rainin hankali kawai ki ba mutum kud'in sa ya ware," a zuciyar ta Lantana ta ce "Na shiga uku ni Lantana gashi bani da ko sisi bari naje na samo masa kud'in sa idan ba haka ba tsaf na lura wannan zai d'ora wani dukan kan na Bala," "Kinga iya muna jira fa haba kinsan Baki da kud'i har da wani hawa babur," shiru Lantana ta yi ta juya tare da nufar k'ofar gidan. Sadam ne ya fito daga gidan fuu kamar an jefo sa ajiyar zuciya Lantana ta sauke domin ba k'aramun jin dad'in ganin sa ta yi ba yana zuwa ko kallon Lantana bai yi ba ya kalli mai machine d'in ya ce "Kai yane zaka juya ne?" Mai acab'ar ya ce "Gaskiyar ka fad'a," Sadam ya ce "To muje," mai acab'a ya ce "To ke iya jira nake yi fa dan ba kwana nazo yi a nan ba ki bani kud'ina mana ke dan fa kece wallahi da tuni na bazar dake a nan," ya fad'a cikin wata k'atuwar murya Lantana ta kalli Sadam cikin bada umarni ta ce "Kai Sadam bawa wannan yaron kud'in sa," Wani kallon banza Sadam ya yi mata kamar ya ga kashi ya ce "A matsayin ki nawa a wajena zan baki kud'i kinga malama ki ba shi kud'in sa kawai ni wallahi mutane suna bani mamaki ace baka da kud'in kaza kace sai kayi haba," ya fad'a yana jan wani dogon tsaki. Cikin gidan Lantana ta nufa tana fad'a a zuciyar ta shikenan komai ya lalace asirin da muka yiwa Sadam ma ya lalace. Da sallama ta shiga gidan turus ta tsaya ganin Zainabu zaune ta rafka uban tagumi tana hawaye ga ciki duk ta rame ta k'anjale tayi bak'i har Lantana ta je ta d'auki naira hamsin d'in dake gabanta ta fice bata saniba sai da ta dawo sannan ta zauna gefen Zainabu tare da dafe goshin ta da ya yi wata uwar kumbura gashi har jini yake yi. Dafata Lantana ta yi ta ce "Zainabu ta lafiya Mai ya faru?" Firgigit Zainabu ta yi tare da kallon Lantana tana ganin ita ce ta rushe da kuka ta fad'a jikin ta ta ce "Na shiga uku Lantana Dan Allah ki tafi dani gida Wallahi kashe ni zai yi idan ki ka barni a nan," a rud'e lantana ta ce "Zainabu baki da lafiya ne ki ka zama haka kamar mai ciwon k'anjamau?," "Lantana ni dai ki tafi dani kullum dukana yake yi baya bani isasshen abinci gashi baya barina fita Lantana asirin jikin sa ya barsa cewa yake yi uban meyasa aka aura masa ni ai shi bani ya ke so ba Sabeeha yake so sannan an kore shi daga wajen aikin su yanzu abincin da zamu ci ma gagarar mu yake yi," hawayen tausayin Zainabu ne ya fito daga idanun Lantana ta ce "Mu dai kam munga ta kanmu yanzu haka ma Bala ne ya yi min duka na taho nan gashi yunwa nake ji Zainabu bani abinci naci," Girgiza Kai Zainabu ta yi ta ce "Lantana kenan ai ko ruwan sha bamu da shi a gidan nan wannan hamsin d'in da ki ke gani ita ya bani na nemi abinda zanci na k'oshi," ta fad'a tana kallon gaban ta inda ta ajiye hamsin d'in ta ga wayam dube-dube ta fara yi ganin babu hamsin d'in inda ta ajiye ta. Lantana ta ce "Ai hamsin d'in ita na d'auka na biya Mai acab'a da ita," Zainabu ta mik'e tana karkad'e daddaud'an zanin ta ta ce "Lantana tashi mu tafi," mik'ewa Lantana ta yi ta ce "Shawarata Zainabu ki zauna a gidan mijin ki domin idan ki ka bini sai kin dawo domin Bala yanzu banda talauci ba abinda yake fama da shi gara ma a nan kina samun hamsin d'in amma a can garin k'waki na ashirin babu me baki," kuka Zainabu ta fashe da shi tana rik'e wuyan hijabin ta da ya yage ta ce "Wallahi baki isa ba lantana saina biki," ta fad'a tana nufar k'ofar fita turus ta tsaya ganin Sadam a k'ofar take jikin ta ya fara rawa kamar ta ga mala'ikan mutuwa. K'ok'arin bud'e baki take yi ta bashi hak'uri ya ce "Saurin me ki ke yi to ki tattara ki bi uwar ki," yana fad'in haka ya juya ya fice. Kuyi hak'uri da wannan bani da caji ne amma insha Allahu zuwa dare zaku jini😂 [10/25, 8:43 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️ RUBUTAWA DAGA HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ) SADAUKARWA GA MY DAUGHTER SABEEHA BILKISU Z.YA'U (🅱️K) AISHA MAGAJI DABO (AMA) Page 19 A matuk'ar rud'e Sameeha ta nufi fridge ta d'auko ruwa suka yayyafa mata a hankali ta sauke ajiyar zuciya sai dai ko idanunta tak'i bud'ewa haka ta kwanta shiru a jikin Doctor. Sabreen ce ta sauko daga stairs idanunta taf hawaye domin tana zuwa d'aukar wayar ta samu Sabeeha bata fita daga cikin app na WhatsApp ba da suke yi da Rinaz kunna voice d'in tayi ta ji duk abinda ke faruwa. Tana zubar da hawaye ta k'arasa da gudu ganin su Mama duk a wajen Sabeeha domin ita bata san ma Sabeehan suma ta yi ba tana zuwa ta fad'a jikin Sabeeha ta fashe da kuka. Abba kuwa gaba d'aya ya gama rud'ewa ya yi domin shi dai kam bai tab'a ganin yaran nasa cikin irin wannan yanayin ba shi yama rasa abin yi kallon Sameeha ya yi ya ga yadda ta had'a Kai da gwiwa itama tana nata kukan Doctor kuwa tagumi ta yi domin itama bata cikin nutsuwar ta ballantana su. Abba ne ya ce "Haba aminaina me yake faruwa ne haka gaba d'aya hankalin mu yak'i kwanciya ku fad'a mana menene silar damuwar ku ne?" Dakyar Sabreen ta iya d'aga Kai ta kalli Doctor da idanunta da suka yi jajir ta mik'a mata wayar ta ba tare da tace komai ba. Karb'a Doctor ta yi ta kalli screen d'in wayar ta yi Rinaz habibty ta ga ansa daga k'asa kuma sak'on k'arshe na Rinaz ta kalla ba tare da wani tunani ba ta kunna tare da k'ara volume yadda Abba zai ji suka fara sauraro shiru falon ya d'auka sai sheshshek'ar kukan Sabreen da Sameeha domin gaba d'aya ji ta yi kanta ya yi mata wani mugun nauyi sai hawaye kad'ai ke fita a idanunta. A tare Abba da Doctor suka kalli Sabeeha cikin tausayawa sannan Doctor a hankali ta janye Sabeeha a jikin ta ta mik'e ta ja hannun Abba suka koma cikin falon suka zauna suna cigaba da sauraron abinda ke faruwa har k'arshe. A hankali Sabeeha ta yunk'ura ta mik'e ta nufi inda doctor take a gaban ta ta tsugunna ta rik'o hannun ta cikin zubar da hawaye ta ce "Mamana dan Allah ki barni naje na ganshi please Mama," "Meyasa ki kayi sanadin raba shi da matar sa Rukayya?" A razane Sabeeha ta d'aga Kai ta kalli Doctor a hankali ta fara girgiza mata kai sai lokacin sabeeha ta tuna ashe fa duk abinda ya faru basu gayawa Mama ba. Tsawa Doctor ta daka mata wacce tasa ta razana "Ba dake nake magana ba meye dalilin ki na shiga tsakanin miji da mata shin ina ruwan ki da matar sa kin kuwa san halin mahaifin ta gashi dai kinji da kunnuwan ki yadda yake zayyana wasu halaye wad'an da yarinyata bata da su amma yake danganta ki da su meyasa Sabeeha akan me zaki shiga lamarin nan?" Sabeeha gaba d'aya ta kasa magana tunanin ta Ina ma zata fara tayi. Saneeha ce ta k'arasa gaban Doctor ganin yadda ta d'auki zafi zata yi magana Doctor ta yi Mata wata uwar tsawa da ta k'ara firgita 'yan uku ta ce "Matsa mun a nan Sadiya tun kafin raina ya b'aci a kanki bake nake tambaya ba," Sameeha wajen Abba ta nufa ta rik'e hannayen sa tana hawaye ta ce "Abba ka saurare ni wallahi Sabeeha dear bata da laifi," Sabeeha kuwa gaba d'aya tunanin ta baya tare da ita damuwar ta kawai shine tasan halin da Maleek ke ciki a hankali ta tashi domin ficewa daga falon. Wani wawan mari Doctor ta zabga mata cikin d'aga muryar da basu tab'a ji ta yi ba ta ce "Kina hauka ne kin raba aure sannan ki ke k'ok'arin zuwa wajen?" Jin k'arar marin ne yasa Sabreen yin wajen Doctor da gudu ta rungume ta ta fashe da kuka ta ce "Please Mama ki dena dukan Sabeeha dear wallahi Mama a zuciyata nake jin zafin hakan," Sameeha kuwa cak ta tsaya da maganar da ta yi niyyar fad'a domin a tare ita da Sabeeha suka dafe kuncin su Abba kuwa rintse idanu kawai ya yi domin baya so yasa baki a maganar. A hankali Sabeeha ta ja baya ta sulale a k'asa jikin kujera ta had'a kanta da gwiwa ta cigaba da kuka. A hankali Abba ya mik'e ya nufi wajen Doctor da ta ture Sabreen daga jikin ta tana aika mata da harara jan Doctor jikin sa ya yi ya rungume a hankali ya ce "Maryam ki samu nutsuwa kinji wannan Sam ba hanyar da ta dace ki nunawa aminiyata kuskuren ta bane," a hankali Doctor ta yi ajiyar zuciya ta ce "Na nuna musu kuskuren su dai domin nasan duk tare suka yi komai ai ka fini sanin halin su," d'an girgiza Kai Abba ya yi ya ce "Please mana Doctor ki fahimce ni ni nasan ba haka kawai aminaina suka yi hakan ba ki duba aminiyata halin da take ciki tana cikin damuwar da tafi tamu lokacin da nake neman auren ki shin kin tuna wahalar da muka sha kafin mu mallaki juna?kina ganin wannan ce hanyar da ya kamata mu bi wajen taimako yarinyar mu?" A hankali Doctor ta girgiza kai. Ajiyar zuciya Abba ya sauke sannan ya ja hannun Doctor suka zauna a kujera ya ce "Aminaina kuzo nan," Sabreen da Sameeha ce suka zauna gaban su Sabeeha kuwa har lokacin tana gefe ko d'aga Kai ta kasa damuwar ta d'aya Maleek. Abba ya kalli su Sameeha ya ce "Aminaina k'arya ba halin ku bace ku fad'a mana asalin abinda ya faru," basu b'oye komai ba suka fad'awa su Abba duk abinda ya faru tun lokacin had'uwar Sabeeha da Nasreen a part d'in Ummi har zuwa sakin da Maleek ya yiwa Nasreen duka. A d'an tsorace Doctor ta kalli su Sameeha jin abinda Nasreen taso aikatawa mijin ta Wanda take so to Ina ga 'yar ta da zata je a matsayin kishiya duk da tasan Aysha Mai kular mata da Sabeeha ne fiye da yadda ita kanta zata kula da ita amma abun da kamar wuya auren Sabeeha da Maleek ya yuwu duk da ta lura soyayyar sa tayi nisan da dakatuwar ta zai zama babban abu wanda bazai yuwu ba. Kallon Sabeeha dake zaune tana kuka Doctor ta yi cikin tausaya mata tabbas yarinyar ta bata da laifi domin duk ta yi hakan ne domin ceton rai da Kuma kare 'yan uwan ta da take jin baza ta bari wani Abu ya same su ba a kansu tak'i yadda da soyayyar Maleek duk domin su zauna lafiya lallai Sabeeha ta musamman ce. Muryar Abba ta ji ya ce "Kinji ko Maryam yarana basa abu kai tsaye dukan su Allah ya basu fahimta da Kuma sanin daidai suna son junan su fiye da tunanin ki su kan sadaukar da farin cikin su domin farin cikin d'ayan su tun suna yara haka suke Kuma Allah ya kare mana su domin rashin mahaifiyar su hakan bai sa sun rasa tarbiyya ba," a hankali hawaye ya zubo daga idanun Doctor take ta ji abinda ta yi bata kyauta ba a hankali ta tashi ta nufi inda Sabeeha ke zaune ta dafa ta da sauri Sabeeha ta d'aga kai ta kalli mahaifiyar tata da idanunta da saika rantse dama can a haka suke saboda jan da suka yi. A hankali hawaye suka gangaro daga idanun Doctor ta bud'e baki ta ce "Yarinya ta kiyi hak'u...," Saurin rufe mata baki Sabeeha ta yi tana girgiza mata kai sannan ta fad'a jikin ta ta rungume ta Doctor ma rungume ta tayi a jikin ta cikin matuk'ar so 'yar tata ta ce "Allah ya yi muku albarka 'yan uku na," a tare suka amsa da "Ameen," A hankali Sabeeha ta d'aga Kai ta kalli Doctor ta ce "Mamana uhm," sai Kuma ta yi shiru ajiyar zuciya kad'an Doctor ta sauke sannan ta kalli agogon hannun ta ta ce "Sabeeha dare fa k'arfe tara fa," langab'ar da kai Sabeeha ta yi k'walla taf idanunta. Tausayi taba mahaifiyar tasu ta ce "Shikenan kuje ku Kira driver a waya ya fito ya Kai ku and kar kuyi dare okay?" Noding Kai Sabeeha ta yi sannan ta yi saurin tashi mayafin kanta kawai ta gyara suka yi waje. Driver suka Kira yazo suka bar gidan a hanya Rinaz ta Kira Fauwaz shi ya sanar da su cewar suna asibitin su Ummi direct can suka nufa ko gama daidai ta parking driver bai yi ba Sabeeha ta fice sai sauri take yi domin burin ta bai wuce ta ga halin da sahibin nata ke ciki ba su Sabreen na biye da ita. Guards tare da sojojin da suka gani ne suka tabbatar musu da Maleek na wajen a k'ofar shiga Sabeeha ta kalli Salman da idanun sa suka yi jajir domin b'acin rai domin duk Fauwaz ya sanar da shi abinda ke faruwa jijiyoyin jikin sa duk sun fito rud'u_rud'u kallo d'aya zaka yi masa kasan a tunzure yake ran maza ya b'aci amma ganin halin da Sabeeha ke ciki ne yasa ya bita da idanu cikin kallon tausayi. Tana shiga ta hangi Ummi Daddy da Kuma Fauwaz a k'ofar ICU ko wanne ya kasa zaune bare tsaye Nasreen kuwa Uncle takanas ya aika driver yazo ya d'auke ta zuwa gida. Sabeeha na k'arasawa direct gurin Ummi ta wuce ta rungume ta a hankali ta saki kuka ta ce "Ummi wane hali ya Maleek ke ciki?" Shafa bayan ta Ummi ta yi cike da k'arfin hali ta d'ago ta daga jikin ta ta ce "Daughter ki kwantar da hankalin ki insha Allah Son zai samu sauk'i kinji?" Noding Kai kawai Sabeeha ta yi tana share hawaye da bayan hannun ta. Sai da ta ji su Sabreen na yin gaisuwa ne sannan ta waiga ta ga suna gaida Daddy a hankali ta zame ta tsugunna k'asa ta gaida Daddy ya amsa musu ba yabo ba fallasa domin shima zuwa lokacin hankalin sa a tashe yake ganin har lokacin ko likita d'aya bai fito ba sai dai sai kallon Sabeeha yake yi ganin a yanayin da ta zo asibitin hakan ya lurar da shi damuwar da yarinyar ta yi da d'an sa sharewa kawai ya yi ya kalli tsadadden agogon hannun sa. A hankali su Sabeeha suka zauna a kujerun dake wajen Fauwaz kuwa ko magana ya kasa banda dafe kansa da ya yi domin saran da kan ke yi masa. Sabeeha kuwa ji take yi kamar ta tashi ta lek'a ta ga halin da yake ciki ta glass d'in dake k'ofar d'akin amma gaba d'aya ta kasa domin jin nauyin Daddy da take ji domin yana da matuk'ar kwarjini a hankali ta d'aga kai ta k'ara kallon Daddy shi baya kama da Maleek kama yake yi da Fauwaz da Kuma Rinaz fari ne shima sosai Sam bai da jikin tsufa sai kace bai haifi Maleek ba ma. Kasa daurewa ta yi ta mik'e ta ta nufi jikin k'ofar ta lek'a gaban ta ne ya yi matuk'ar fad'uwa ba k'aramar razana ta yi ba ganin Maleek kwance kamar gawa ko Ina nasa baya motsi fuskar sa ta yi wani mugun haske oxgyen ne a hancin sa sai wasu wayoyi da aka sassa masa a k'irjin sa ga wasu allurori da taga sai yi masa ake yi manya manya amma har lokacin ko yatsan sa bai motsa ba da sauri ta ja baya hannun ta rufe a bakin ta domin kar kukan da ya taho mata ya kufce jin ta yi ta buge mutum ta baya ne yasa ta waigawa ta ga Sabreen ce rungume Sabreen d'in ta yi murya a sanyaye cikin kuka ta ce "Sabreen dear baya motsi wallahi baya motsi," Fauwaz ne ya tashi zuwa inda suke cikin k'arfin hali ya ce "Sabeeha kiyi hak'uri tun sanda muka kawo shi har yanzu a haka yake babu wani canji sannan har yanzu babu wani bayani," "Haba Abbana haka ya kamata ka sanar da su domin kwantar musu da hankali Kinga yarinya ki kwantar da hankalin ki Son zai samu lafiya," Daddy dake daga gefen su ya fad'a hannunsa duka sanye cikin aljihu shima a cikin damuwar yake amma wannan ai yarinya ce k'arama ba haka ya kamata ace anyi mata magana ba Daddy ke fad'i a zuciyar sa tare da d'an hararar Fauwaz da ya yi saurin yin k'asa da kai. Sabeeha kuwa hararar da Daddy ya yi ne ya k'ara tuna Mata da Maleek Daddy ya ce "Ki kwantar da hankali okay?" A hankali Sabeeha ta yi noding kanta. Sun Kai wajen mintuna talatin a wajen sannan likita guda d'aya ya fito a tare suka yi wajen sa tun kafin su yi magana ya kalli Daddy da Ummi ya ce "Yallab'ai Doctor muje office," girgiza kai Daddy ya yi ya ce "No Doctor why not ka fad'a mana a nan I hope there's no big problem?" Likita ya ce "I can said that cuz har yanzu ba wani bam_bamci a gaskiya Yallab'ai yana cikin wani hali domin zuciyar sa tana gab da ta yi buga Wanda hakan na nufin we can lose him cigaba d'aya aka samu daga d'azu zuwa yanzu dogon suma ya yi Wanda ciwon sa da ya tashi ne ya ja hakan a yanzu zuciyar sa ta fara bugawa amma yadda take beating is too fast gaskiya Yallab'ai Ina ga MG na buk'atar special care ba Ina nufin nan bamu da halin kulawa da shi ba Doctor u already known all about MG kamata ya yi a fitar da shi waje a can zai fi samun kulawar da ta dace da shi domin sun fimu k'wararrun likitoci a wannan fannin that's all," Daddy ya ce "Ok no problem ina ga gobe zamu je kawai amma bari na Kira friend d'ina a waya babban likita ne a wannan fannin domin shi yake duba son lokacin yana school a dubai," daga haka Daddy ya zaro wayar sa daga aljihu ya ciro wayar sa ya yi kira tana fara ringing aka d'aga daga can Doctor ya ce "The most architecture person in the world," dariya Daddy ya yi ya ce "Ka fara ba Doctor Kamal where are you now hope you are in Dubai now?" Daga can Doctor ya ce "i dey Egypt now any problem?" "Yeah Son is in unconcious now we need you urgently," daga can Doctor yace "Subhanallah jikin son ne ya tashi ya ilahi naje duba governor na can ne sai next week zan dawo," Daddy ya ce "Ok no problem zamu jira dawowar ka sai mu shigo," Doctor Kamal ya ce "Ok worry don't I will do my possible best to scz the days," Daddy ya ce "Thank you friend," Dariya Doctor ya yi ya ce "The architecture amma ka bani wayar likitan dake kula da shi akwai shawarwarin da zan basu domin kula da shi kafin na dawo insha Allah," Daddy ya ce "Ok zan bashi wayar ka," daga haka suka yi sallama. Doctor ya ce da Daddy "Yallab'ai wai dama Doctor Kamal is your friend amma ka kawo MG wajen mu?" "Doctor yanzu ai ga amfanin kawo son gurin ku domin Kamal baya Dubai zuwa next week zai dawo zan baka wayar sa zaku yi magana," cikin jin dad'i doctor ya ce "to to ngd," bashi number d'in Daddy ya yi ya wuce office. Bayan tafiyar Doctor Daddy ya kalli agogon sa sannan ya kalli Ummi ya nuna mata su Sabeeha da ido Ummi ta ce "Daughter dare ya yi ya kamata kuje gida zuwa gobe sai ku dawo ko?" Noding kanta Sabeeha ta yi sannan suka tashi. Daddy ya ce "Abbana kuje a kai su gida," Sabreen ta ce "Daddy da driver muke," Daddy ya ce "Ok ku gaida Mamar ku," suka ce "To," suna fita Fauwaz ya bisu. Sun bud'e mota zasu shiga Fauwaz ya k'arasa wajen kallon jikin su duk a sanyaye yake ya ce "Please ku kwantar da hankalin ku anything will be right," ba Wanda ya iya magana a cikin su domin yanayin da Maleek d'in ke ciki ya wuce a kwantar da hankali. Sabreen ce tayi k'arfin halin yin murmushi ta ce "Ok bakomai sai da safe idan mun dawo," jinjina kai ya yi sannan ya juya ciki su kuma suka shiga mota suka tafi. Fauwaz na komawa ya samu Ummi da Daddy sun zauna gefen Ummi ya zauna ya ce "Ummi naga kun zauna ke da Daddy dare fa ya fara kuje gida ku huta zan zauna a nan d'in," a tare suka kalle shi Daddy ya ce "No Ummin ku ta tafi ni zan zauna," Ummi ma girgiza kai tayi. Fauwaz ya ce "Daddy Ummi kuyi hak'uri kuje gida Daddy yau fa ka dawo daga tafiya," shiru Daddy ya yi "Ummi please kuje tare," Fauwaz ya fad'a yana kallon su. Mik'ewa Ummi ta yi ta ce "Shikenan gobe da safe zamu dawo," tashi Daddy ya yi suka tafi har wajen mota Fauwaz ya raka su sannan ya juya wajen da Salman ke tsaye ya k'arasa ya ce "Ya Salman mu k'arasa ciki," binsa Salman ya yi zuwa ciki. Sabeeha kuwa suna zuwa gida suka samu Abba da Doctor a zaune a falo da alamu dawowar su suke jira sai dai da kallo su Doctor suka bisu ganin su duk jikin su a sanyaye guri suka samu suka zauna babu me yin magana a cikin su Abba ya ce "Ya jikin Abdul-maleek d'in?" Sameeha ce ta ce "To da sauk'i dai za a ce Abba amma har yanzu bai farfad'o ba Doctor yace sai dai a fitar da shi waje saboda ciwon sa ya tashi sosai," Abba da Ummi ma take hankalin su ya k'ara tashi domin ba su yi tunanin jikin nasa ya kai haka ba. Tashi Sabeeha ta yi ta nufi stairs idanunta taf hawaye wani tausayin kansu ita da Maleek ne ya kama ta tana shiga d'aki wanka ta yi tare da alwala tana idar da sallah ta kwanta saman gado ta fad'a tunani Sabreen ce ta shigo ta zauna gefen ta ta ce "Sister kiyi hak'uri mu ma muna cikin damuwar da kike ciki amma hak'uri Zaki yi yanzu ki tashi muje kici abinci," d'an tashi zaune Sabeeha ta yi daga kwancen da take ta ce "Sabreen na rasa nutsuwa ta bansan me yake shirin faruwa damu ba sweetheart yana asibiti a wani yanayi ta ya ni zan iya cin abinci Sabreen me Uncle yake nufi da maganar sa suna nufin bazai aure ni ba kenan?" "Please dear ki dawo cikin nutsuwar ki idan Allah ya tsara ke matar Ya MG ce babu wanda ya isa ya hana calm down please," shiru Sabeeha ta yi tana nazarin maganganun Sabreen tabbas gaskiya ta fad'a a hankali ta ji sanyi a ranta sai dai duk yadda Sabreen ta yi da ita akan suje ta ci abinci k'in yadda ta yi haka ta kyale ta. Su Ummi suna komawa gida suka samu Rinaz kwance ba lafiya Ummi ce ta duba ta ta bata abinci da magani tasha. Washe gari su Sabeeha suka shirya har da Doctor da ita dama asibitin zata da Kuma Abba suka tafi asibitin suna zuwa suka samu su Ummi suna nan cikin fara'a su Ummi da Daddy suka tare su suka gaisa tare da tambayar mai jiki suka amsa da cewa da sauk'i. Su Sabeeha suka gaishe da su da tambayar mai jiki Ummi ta ce "Da sauk'i yarana," Daddy ya kalli 'yan uku ya ce "Aysha kina nufin wad'an nan yaran Maryam ne?" Ummi ta ce "Eh wannan Kuma mahaifin su," jinjina kai Daddy ya yi ya ce "Masha Allah," ya fad'a yana kallon su Sabeeha domin mamakin kamannin su. Tashi Sabeeha ta yi ta nufi k'ofar d'akin da Maleek ke ciki ta lek'a yana nan inda suka barsa jiya hawayen dake taho mata tayi saurin mayarwa sannan ta juya ta koma gefe ta zauna Fauwaz ne da Rinaz suka shiga asibitin domin Fauwaz ya je ne domin yin wanka. Zama Rinaz ta yi ta gaida su Doctor sannan ta k'arasa wajen Sabeeha dake gefe ta zauna kallon ta Sabeeha ta yi bata ce komai ba ganin haka Rinaz ta fara kwantar mata da hankali sai dai ko uffan Sabeeha bata ce ba domin duk abinda zai fito daga bakin ta kuka ne shiyasa kawai ta yi shiru ba magana. Tashi Doctor ta yi tare da Abba tace da Ummi "Aysha bari na shiga office," Ummi ta ce "To zan shigo," tafiya suka yi suna tafiya ba dad'ewa Umar ya isa asibitin shima hankalin sa a tashe domin sai lokacin Salman ya Kira shi a waya ya sanar masa. Haka suka yi ta zaman asibiti da yamma da Doctor ta tashi daga aiki ta ce da 'yan uku su tashi su tafi gida mak'e kafad'a Sabeeha ta yi ga idanu ya ciko da k'walla Doctor bata ja maganar ba tayi tafiyar ta ta barsu dan tasan su Sabreen ma ba binta zasu yi ba. A haka har aka kwana biyar kullum su Sabeeha suna asibitin har dare amma duk abinda ake yi Uncle bai je duba Maleek ba haka ma Hajiya Asiya Nasreen ma hanata zuwa suka yi. Ranar kwana na shida Daddy ne ya fito daga part d'in Ummi yana amsa waya da Doctor Kamal suke waya yana sanar da shi yau zai koma Dubai Daddy ya ce "Ok zuwa gobe zamu shigo to," da haka suka yi sallama. Har Daddy zai shiga mota motar Uncle ta tsaya saitin sa fasa shiga motar Daddy ya yi ya tsaya har Uncle ya fito ba yabo ba fallasa Daddy ya gaishe shi amsawa Uncle ya yi tare da cewa "Ya jikin yaron?" Kamar Daddy bazai yi magana ba sai Kuma ya ce "Yaya kenan aina d'auka Maleek d'an ka ne sai gashi ka nuna mun ba haka bane tunda yau kwanan sa shida a asibiti amma ko da wasa baka je ka ga jikin sa ba amma bakomai tunda kai kaga dacewar hakan," Daddy na fad'ar haka ya shige mota suka tafi karo na farko kenan da yaji d'an uwan nasa baya kyautawa. Uncle kuwa motar Daddy yabi da kallo baki bud'e yana mamakin Daddy yau shine da fad'a masa magana irin haka wata zuciyar ta ce ka manta d'an gold fa ka tab'a tab'e baki Uncle ya yi a fili ya furta "Aikuwa d'an gold d'in zai ci uban sa," daga haka ya shige mota. Daddy kuwa yana zuwa ya samu Sabeeha zaune kusa da Ummi tana ganin sa ta tsugunna har k'asa ta gaishe shi cikin fara'a ya amsa domin zuwa lokacin 'yan uku sun gama shiga ransa ya ce "Yarinya ya gajiyar ku?" K'asa Sabeeha ta yi da kanta bata ce komai ba. Zama Daddy ya yi ya ce "Aysha gobe zamu wuce Dubai doctor zai koma yau," Ummi ta ce "Ok Allah ya kaimu," mik'ewa Sabeeha ta yi ta ce "Ummi bari naje gida zan dawo yanzu," Ummi ta ce "To sai kin dawo," fita ta yi gate d'in asibitin domin samun abun hawa domin ba wanda yasan ta taho sakamakon mafarkin Maleek da ta yi ta ji tana tashi shi take son gani. Tana tsaye mota ta tsaya a gefen ta ko kallon motar bata yi ba sai dai ta ga kamar motar daga cikin asibitin ta fito bud'e motar aka yi Salman ya fito ya k'arasa wajen ta ya ce "Sabeeha Ina zaki haka?" Ganin Salman ne ta ce "Dama gida zani," ya ce "Ok muje," bud'e mata motar ya yi ta shiga ya shiga ya ja suka tafi. Tana shiga falon ta samu su Doctor suna breakfast gaishe su ta yi sannan ta wuce stairs da kallo Doctor ta bita ganin yadda itama Sabeehan ta rame saboda rashin cin abinci da damuwa tana shiga d'akin su wanka ta fad'a tana wankan ta ji wayar ta na ringing ko da ta fito bata bi takan wayar ba mirrow ta nufa tayi shafe-shafen ta ta bud'e drower ta d'auko doguwar rigar atamfa irin ta jikin su Sameeha tasa ba ko kwalli a fuskar ta ta ta nannad'e gashin ta waje d'aya ko d'an kwali bata tsaya d'aurawa ba ta d'ora mayafin saman kanta ta d'an fesa turare wayar ta ta ji ana sake kira juyawa ta yi ta d'auki wayar tayi sallama tana zura plat shoes a k'afar ta wani ihun murna ta saki sannan ta fice daga d'akin da gudu. Falo ta sauka da gudun ta tana zuwa ta rungume Doctor ta ce "Mama ya farka," ko ba su tambaya ba sun san Maleek ne ta kalli su Sabreen ta ce "Sister ya farka," a tare suka ce "Alhamdulillah," domin sun ji dad'in hakan sosai musamman da suka ga Sabeeha na farin ciki haka domin tunda Maleek ya kwanta cuta ko murmushi ba yinshi Sabeeha ke yi ba. Hanyar waje ta yi tana cewa "Dear ku taho mu tafi," "Sabeeha abinci Kuma fa?" Cewar Doctor Sabeeha da ta riga ta yi gaba ta ce "No Mama," mota suka shige driver ya ja sai hospital. Yana yin parking suka fita da sauri Sabeeha har da gudu take had'awa saboda d'okin zuwa ganin sweetheart d'in ta. Kai tsaye tasa kanta cikin d'akin cak ta tsaya tana kallon mutanen d'akin su Sabreen ma dake bayan ta tsayawar suka yi. [10/25, 8:43 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️ RUBUTAWA DAGA HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ) SADAUKARWA GA MY DAUGHTER SABEEHA BILKISU Z.YA'U (🅱️K) AISHA MAGAJI DABO (AMA) Page 20 D'akin babba ne sosai Daddy na zaune a gefen Maleek dake jingine jikin pillow sai Ummi da Fauwaz dake zaune a gefe da Rinaz daga d'ayan gefen kuwa Uncle ne zaune shi da Hajiya Asiya sai Nasreen tasha uwar kwalliya ta k'wama black glass a fuskar ta. Kasa k'arasawa ciki Sabeeha ta yi sai dai idanunta na kan Maleek da ya rame ya k'ara haske a hankali yake sauke numfashi yana d'an rintse idanu alamun yana cije pink lips d'in sa alamun yana jin jiki shima kallon Sabeehan yake yi kamar ranar ya fara arba da ita. Tunani Sabeeha ta yi a zuciyar ta ko dai suna magana ne tasu ta family a hankali ta juya zata fita daga d'akin "Sabee na," ta ji muryar sa ta fad'a da sauri ta waiga tana kallon sa ba ma ita kad'ai ba kowa na d'akin da kallo ya bisa domin tunda ya farka ake yi masa magana amma ko sannu yak'i amsawa har an fara tunanin ko wata matsalacce ta daban amma sai gashi ganin Sabeeha ya yi magana hawaye ke shirin saukowa Sabeeha a fuska ya girgiza mata kai d'an murmushi ta yi. Nasreen kuwa cire glass d'in fuskar ta ta yi tana jifan su Sabeeha da wani mugun kallo Sabeeha kuwa ko lura bata yi ba domin bata ita take yi ba k'wafa Nasreen ta yi ta dunguri Uncle tana nuna masa Sabeeha da ido. Ummi ta bud'e baki zata yi magana Uncle ya kalli su Sabeeha ya ce "Lafiya zaku zo ku tsaya mana a nan kunga kuyi waje muna magana ne ta ahali bama buk'atar bare a nan," kallo ne ya koma kan Uncle domin mamakin abinda ya fad'a. Maleek kuwa rintse ido ya yi yana d'an girgiza kai shi kad'ai yasan abinda yake ji amma Uncle na neman k'ara masa wata damuwar. Har sun juya zasu fita Maleek ya kalli Fauwaz alamun ya yi magana domin shi ba halin yi domin yanayin da yake ciki. Fauwaz ya ce "Sabeeha ku shigo ga guri ku zauna ba wata magana da ake yi," baki sake Uncle ke kallon Fauwaz ya ce "Dan uban ka ni sa anka ne da zanyi magana kayi?" Bai gama rufe baki ba Rinaz ta ce "Me ku ke jira ne ku zauna mana Nan asibiti ne ba family meeting hall ba," "Ya isa mamana!" Daddy ya fad'a cikin d'aga murya sannan ya kalli su Sabeeha ya ce "Ku zauna kunji," sai lokacin su Sabeeha suka zauna a sanyaye. Daddy ya ce "Alhamdulillah mun godewa Allah da wannan cigaba da muka samu dama gobe muke sa ran tafiya Dubai domin duba lafiyar ka," shiru d'akin ya d'auka Daddy ya cigaba da cewa "Gobe insha Allah zamu je domin a duba mana lafiyar ka," Sabeeha kuwa k'asa ta yi da kanta. Maleek kuwa rintse idanunsa da suka ji jajir ya yi sannan ya rik'o hannun Daddy ya damk'e hannun sa sosai murya na sarkewar ciwo ya ce "Daddy idan har baza ka amince na auri Sabeeha ba ba amfanin a fitar dani ko Ina domin nasan hakan bazai amfanar da komai ba," "Aikuwa sai dai ka mutu domin wannan yarinya baka isa ka aure ta ba kuma ni da mahaifin ka mun riga mun yanke magana batun yau ba Kuma Kai baka isa ka canja mana ra'ayin mu ba," kallon Daddy Ummi ta yi domin jin me zaice amma shiru bai ce komai ba. Hawaye ne ya gangaro a fuskar Sabeeha a hankali tasa hannunta ta goge Maleek dake kallon ta ji ya yi kamar ana zuba masa tafasasshen ruwan zafi a zuciyar sa ganin hawayen ta take jikin sa ya d'auki wani mugun zafi jikin sa ya fara rawa ya rik'o Daddy ya ce "Please Daddy Ina sonta zan iya rasa rayuwata idan babu ita," take ya fara wani irin numfashi jikin sa kuwa rawa yake yi sosai a rud'e Ummi ta yi wajen sa tana kuka Fauwaz kuwa da gudu ya fita domin Kiran Doctor. Cikin hawaye Ummi ta kalli Uncle ta ce "Wallahi idan har yarona ya rasa rayuwar sa bazan tab'a yafe maka ba kai waye da zaka haramta abinda Allah ya halatta ko ita 'yar ka ta daban ce da baza a yi mata kishiya ba to idan har na isa da d'ana to sai ya auri Sabeeha," Daddy cikin fusata ya ce "Aysha kina hauka ne Yaya ne fa," d'aga masa hannu Ummi ta yi sannan ta juya inda yake ta ce "Kai shaida ne akan tsanar da yayanka da matar sa suka yiwa yarona wanda daidai iyawar sa yana yi masa biyayya cikin biyayyar sa ne ma ya yadda da auran Nasreen duk dan farin cikin ka ba tare da ya ja lokaci ba amma shi yau gashi a kwance akan gadon asibiti cikin mawuyacin hali akan abinda yake so amincewar ka kad'ai yake buk'ata amma ka kasa amsa masa bayan ba haramun zai aikata ba baza ku kashe mun yaro ba meyasa baza ka fahimci halin da yake ciki ba ni fa uwa ce Ina da hakk'i akan Maleek Dan nayi shiru na zuba ido ba hakan na nufin bana son shi bane nima Ina so na ganshi cikin farin ciki ina so na faranta masa kamar yadda yake faranta mana," Ummi ta fad'a tana hawaye sannan ta cigaba da cewa "Nasan ba kasan dalilin sakin Nasreen da ya yi ba saboda lokacin an hana shi fad'a to ya sake ta ne saboda k'ok'arin kashe shi da take yi ita da mahaifiyar ta wanda wacce ku ka hana ya aura itace ta cece shi," Nan Ummi ta fad'awa Daddy kaf abinda ya faru sannan ta d'ora da cewa "A wannan karon bazan tauyewa yarona hakk'in sa ba idan har Ina raye saina bawa Abdul-maleek farin cikin da yake buk'ata abin nan ya isheni haka kamar yadda yake son yarinyar sa to ni fiye da haka nake son yarona," Ummi ta fad'a tana share hawaye. Uncle kuwa gumi ne ya keto masa domin jin yadda Ummi ta gama tonawa 'yar sa asiri haka ma Hajiya Asiya duk ta jik'e da gumi ganin irin mugun kallon da Daddy ke jefan su da shi. Juyawa Daddy ya yi ya kalli Maleek dake kwance da likita a kansa ya rik'o hannun Maleek hawaye na zuba a idanun Daddy na tsabar tausayin d'an nasa ya ce "Allah ya yi maka albarka son da yi mun biyayya sannan na yadda ka aure ta na amince," duk da baya hayyacin sa sai da ya yi saurin bud'e idanunsa ya kalli Sabeeha ya yi mata murmushi sannan ya mayar da idanun sa ya rufe saboda alluran da likita ya yi masa. Kallon Ummi Daddy ya yi ya ce "Nagode Aysha da tubatar dani abubuwa da dama da ki ka yi," sannan ya taka har gaban Sabeeha ya ce "yarinya Allah yayi miki albarka Nagode da ceton d'ana da ki kayi," a hankali Sabeeha ta ce "Bakomai Daddy," Tashi Nasreen ta yi tana buga k'afa ta ce "Wallahi ba a isa ba bazai aure ta ba Daddy kana jin abinda ake fad'a ko?" Fauwaz ya nuna mata k'ofa ya ce "Zo ki fita tun kafin nayi miki duka domin nan ba filin hauka bane," fuuu Nasreen ta fice Uncle da Hajiya Asiya suka bi bayan ta. Suna fita su Ummi su ma suka fita Sabeeha zuciyar ta fal farin ciki ko zama kasawa ta yi ta kalli Ummi ta ce "Ummi zamu je gida," Ummi ta ce "To daughter ku gaida maman ku," suka ce "To," sannan suka tafi. Da gudu ta shiga falon ta fad'a jikin Doctor ta ce "Mama finally Daddy ya amince da maganar aure na da ya Maleek," murmushi Doctor ta yi ganin yadda Sabeeha ke farin ciki ta ce "To naji mara kunya ni tashi mun a jiki," tashi ta yi tana dariya ta haye stairs da gudu. Washe gari Daddy Ummi Maleek suka shirya sai Dubai Rinaz Kuma ta tafi gidan Mama. Suna zuwa Airport motocin sojojin Maleek tazo da Kuma motar asibiti direct asibitin suka wuce suna zuwa ba b'ata lokaci aka fara duba shi domin ansan da zuwan su. Sai da su Ummi suka ga an fara duba shi sannan suka nufi gidan Daddy dake can suka yi wanka da cin abinci sannan suka koma asibitin. Sai yamma sannan doctor Kamal ya fito tare da ragowar likitoci kallon Daddy ya yi ya ce "Friend muje office," bin bayan sa suka yi suna shiga office d'in bayan ya zauna ya kalli Daddy ya ce "Gaskiya friend bai kamata ace ciwon son yana yin gaba haka ba akwai abinda yasa a ransa sosai nasan koma meye shi zai samu nasan ba abinda ya rasa nasan zaku ji da wannan amma dai gaskiya wannan shine mak'asu din fad'awar sa a wannan halin wanda munci nasarar shawo kan matsalar domin munyi masa wani k'aramun aiki sai dai a kiyaye fad'awar sa a irin wannan halin nan gaba domin idan hakan ya kasance komai ma zai iya faruwa yanzu dai yana bacci zuwa gobe zai farka zamu bashi kulawa a nan zuwa sati d'aya," ajiyar zuciya Daddy da Ummi suka sauke sannan suka ce "To doctor mun gode," murmushi kawai ya yi sannan suka fita zuwa d'akin da Maleek yake. Maleek kuwa sanda ya farfad'o ba laifi jikin sa da sauk'i anan Ummi ke masa albishir da cewar Daddy ya amince da auran sa da Sabeeha ba k'aramun farin ciki ya ji ba har hakan ya kasa b'oyuwa. A Nigeria kuwa kullum sai su Sabeeha sun Kira Ummi sunyi mata ya me jiki. Da haka har suka kwana biyar a asibiti jikin Maleek kuwa ya ji sauk'i sosai kamar da gashi ya wani k'ara kyau domin ya kwantar da hankalin sa sosai ga wata kulawa da yake samu daga Daddy da Kuma Ummi. Sallama likita ya basu suka koma gida Maleek kuwa sai farin ciki yake yi domin so yake gobe ta yi ya je ya ga sahibar sa. Tun dare da suka Kira Ummi ta sanar da su gobe zasu dawo dan haka su shiryawa tarbar su ranar da wuri su Sabeeha suka yi bacci domin su tashi da wuri su yi shirin tarbar su. Washe gari tunda suka yi Sallah basu koma bacci ba wanka suka yi sannan suka fita driver ya d'auke su zuwa gidan Ummi suna zuwa ba b'ata lokaci suka fara gyara part d'in duk da ba dirty fes suka k'ara gyarawa sannan suka shiga kitchen har Fauwaz da fitowar sa kenan shima kitchen d'in ya shiga ayi da shi. Cikin k'ank'anin lokaci gidan ya cika da k'amshin soye_soye da dafe dafe lemuka kuwa sun had'a ya kai kala biyar suna gamawa suka jere komai a daining sannan suka gyara kitchen d'in suka tafi d'aki domin yin wanka. Tsaf suka shirya cikin shiga ta alfarma kamar ka sace su ka gudu tsabar kyan da suka yi Sabreen Sameeha da Rinaz ne suka fito falo daidai lokacin motocin su Maleek na yin parking a k'ofar part d'in Ummi. Da sallama suka shiga falon da gudu Rinaz ta rungume Maleek tana murnar ganinsa shi kuwa sai murmushi yake yi wajen su Sabreen ya kalla da suke gaishe da su Ummi ya yi ya ga ba Sabeeha kafin ya yi magana Fauwaz ya fito daga d'akin sa rungume juna suka yi da Maleek. Gaishe da Maleek su Sabreen suka yi tare da tambayar sa jikin sa ya ce "Alhmadulillah," Sabeeha da ta gama d'aurin ta ta nufo down stairs tasha kyau sosai cikin green d'in less kamar amarya. Tana fara taka matakalar benen idanunta ya sauka akan Maleek da ya yi matuk'ar kyau cikin shigar complete bak'i da ya yi shima kamar ance ya d'aga Kai ya hangota da idanu ya bita har ta k'arasa cikin falon har k'asa ta tsugunna ta gaida Ummi da Daddy tare da yi musu ya mai jiki. Daddy ya ce "Lafiya daughter mai jiki yaji sauk'i gashi nan," waigawa ta yi ta kalle shi ya hard'e hannayen sa a k'irji yana kallon ta ita kunya ya bata ma. Stairs Daddy da Ummi suka nufa kallon sa Sabeeha ta yi ta ce "Ya jikin ka?" Sai da ya gama kallon ta sannan ya numfasa ya ce "Alhamdulillah Sabee na," murmushi ta yi shima hakan ya yi hanyar waje domin zuwa part d'in sa. Wanka ya yi ya dawo part d'in Ummi ya same su a daining baza idanu ya fara domin ganin ta inda zai hango Sabeeha amma babu ita Daddy ya ce "Son yadai k'araso mana," daining d'in ya k'arasa ya ja kujera kusa da Rinaz ya zauna sannan ya ce "Daddy Ina su Sabee na suke?" Ummi ta ce "Sun wuce gida munyi dasu su tsaya sunk'i," shiru kawai ya yi Daddy ya ce "Ci abincin mana Son," abincin ya fara ci yaci sosai domin abincin ya yi masa dad'i haka ma Daddy girkin yayi masa dad'in gaske. Yana gamawa ya mik'e ya nufi hanyar fita daga falon Ummi ta ce "Ina zaka Kuma?" "Ummi wajen ta zani fa," Daddy ya ce "Zonan Son," juyawa ya yi ya koma ya zauna yana kallon Daddy domin jin abinda zai ce. Ajiye cup d'in zob'on dake hannun sa Daddy ya yi sannan ya ce "Son ka sanarwa da daughter cewar zamu je wajen mahaifin ta Ina so ne muje nema maka auren ta zuwa," washe baki Maleek ya yi ya ce "Wow thank you Dad ai da kaina ma zan sanarwa Mama," hararar wasa Ummi tayi masa ta ce "To ba kai muka ce ka sanar musu ba sarkin zumud'i," dariya Maleek ya yi da ta k'ara masa kyau dimples d'insa suka lotsa sosai ya ce "To Ummi," Waigawa Daddy ya yi ya kalli Fauwaz dake gefe yana danna waya yana kora kunun aya ya ce "Abbana," ajiye wayar ya yi ya ce "Na'am Daddy," "Dama kaima na fad'a maka ka fito da mata nasan kuma kana da ita 'yar gidan waye?" Fauwaz ya ce "Eh Daddy Sabreen ce sister d'in Sabeen Yaya," washe da baki Daddy ya ce "Masha Allah to insha Allah zuwa jibi zamu je nema muku auren su," jefa hannu sama Fauwaz ya yi ya cafke ya ce "Yes can't wait," dak'uwa Ummi ta aika masa ta ce "Marar kunya kawai," Dariya Maleek ya yi ya mik'e ya yi hanyar barin falon zuciyar sa fal farin ciki. Sabeeha ce zaune gefen gadon su sai murmushi take saki domin ganin Maleek yau cikin k'oshin lafiya ba k'aramun faranta mata ya yi ba ga wani fallele da ya k'ara zama. Sabreen ce ta shiga d'akin ta fara dube-dube ta ce "Dear kinga earphone d'ina?" Girgiza kai Sabeeha ta yi cigaba da dubawar ta yi Sameeha ce ta shiga d'akin ta fad'a kan gadon ta yi shiru. Kallon ta Sabeeha ta yi ta ce "Sister lafiya kuwa?" Mirginawa Sameeha ta yi ta d'ora kanta saman cinyar Sabeeha ta ce "Dear guess what?" Girgiza kai Sabeeha ta yi Sabreen ma barin abinda take yi tayi ta zauna gefen Sameeha. "Hmm ya Umar ne fa yace na sanarwa da Abba zai turo iyayen sa," ihun murna suka saki Sabreen kuwa tashi ta yi ta rawa tana cewa "Wayyo dad'i kice mun kusa mu kwashi kodumo abinmu," Sameeha kuwa tun ihun su na farko ta tashi zaune ta tank'washe k'afar ta tana kallon su. Daga zaune Sabeeha ta k'waso shoky sannan ta rungume Sameeha ta ce "Congratulations dear," Doctor ce ta shiga d'akin da sauri tana gyara d'aurin d'an kwalin doguwar rigar jikin ta ta ce "Lafiya ku ke aminan Abba irin wannan ihu haka?" Gurin ta su Sabeeha suka yi suka rungume ta suna nuna mata Sameeha. Sabreen ta ce "Mama ya Umar ne yace zai turo iyayen sa ayi maganar auren su da Sameeha dear," Sabeeha ta ce "Mama ki sanar da Abba ko mu zamu fad'a masa?" Girgiza kai Doctor ta yi ta ce da Sabeeha "Ke ni cikani marasa kunya wato kune zaku fad'a masa ko," sakin ta Sabeeha ta yi tana dariya wayar ta ce ta fara ringing d'agawa ta yi daga can Maleek ya ce "Sabee na Ina waje," ta ce "Ok gani nan," ta kashe wayar ta d'auki mayafin ta ta fice tana cewa "Mama ki fa fad'awa Abba karki manta," murmushi Doctor ta yi cikin jin farin ciki mara misaltuwa. Sabeeha tana fita ta hange shi tsaye a jikin motar sa da gani sabuwa ce fara sol da ita ya hard'e hannayen sa a k'irji yana kallon ta har ta k'arasa ta ce "Barka da zuwa," har lokacin kallon ta yake yi kamar ranar ya fara ganinta juya idanu ta yi ta ce "Lafiya kuwa irin wannan kallo haka," ya ce "Ina sanki," murmushi ta yi ta ce "Love you more sweetheart mu k'arasa ciki," gaba ta yi yana binta a baya har cikin wani falo mai kyan gaske zama ya yi ita Kuma ta nufi fridge ta kawo masa drinks da ruwa ta ajiye sannan ta zuba a cup ta koma gefen sa ta zauna ta mik'a masa. Karb'a ya yi ya yi sipping kad'an sannan ya ajiye Yana kallon ta ya ce "Farin cikin me ki ke yi ne haka Sabee na?"yar dariya ta yi ta ce "Farin cikina a yau na farko shine ganin ka da nayi yau cikin k'oshin lafiya hakan ba k'aramun faranta mun ya yi ba then Abu na biyu shine ya Umar ne ya ce zai turo iyayen sa ayi maganar auren su da Sameeha dear wayyo farin ciki," ta fad'a tare da mik'ewa tana yin juyi domin ita tsabar farin ciki ma ta manta gaban waye take. D'an tsalle ta yi ta ce "Ai na fad'a maka lokacin nan zamu sha shagali," dariya Maleek ke yi mata domin video ma yake mata bata saniba. Jin shiru ba magana ta d'an waiga saurin nutsuwa ta yi ta koma ta zauna tayi k'asa da kanta dariya ya yi ya ce "Ya ki ka zauna Kuma na d'auka ai rawar bikin zaki fara yanzu," ya fara mata dariya. Had'e fuska ta yi ta ce "Ka ga ka bari," ta fad'a tana tura baki wata dariyar ya yi ya ce "Ok bara kiga wani Abu," d'an matsawa kusa da ita ya yi ta nuna mata video d'in da ya yi mata hannayen ta biyu tasa ta rufe fuska. Mik'ewa ta yi yasa lallausan hannunsa ya rik'o nata ya mik'e sannan yasa hannayen sa biyu ya zaunar da ita ya zauna gefen ta ya ce "Bud'e fuskar to na fad'a maki wata magana," bud'ewa ta yi sai dai idanunta na k'asa. "Nikam idan bara ki kalleni ba na fasa sanar miki," Maleek ya fad'a yana kallon ta a hankali ta d'aga kyawawan idanunta ta sauke a nasa ajiyar zuciya ya sauke ida nunsa cikin nata ya ce "Sak'o daga Daddy," gaban ta ne ya yi wata muguwar fad'uwa ta yi saurin rintse idanu ta mik'e tsaye muryar ta na rawa ta ce "Ya fasa amincewa da auren mu ko?" Ta fad'a k'walla taf a idanunta. Gaban ta Maleek ya tsaya ya ce "Calm down Sabee na," hawayen idanunta ne suka zubo ta ce "How should I calm down my man bayan kunnuwana na so su ji mun abinda bazan tab'a mantawa da shi ba a rayuwata," ajiyar zuciya Maleek ya sauke tare da rik'e k'ugu da hannunsa d'aya d'ayan hannun kuma a goshin sa yana d'an sosawa a zuciyar sa kuwa ya ce wannan wace rigima ce haka Kuma. Kallon ta ya yi ya ce "Kinga Sabee na ki saurare ni bawai abinda ki ke tunani bane Daddy fa cewa ya yi na sanar miki ki fad'awa Abba zasu zo nema mun auren ki jibi," da sauri ta kalle shi ga hawaye a idanunta amma murmushi take yi ta yi tsalle tana yarfa hannaye ta ce "Dagaske sweetheart?" Jinjina kai ya yi Yana kallon yadda take tsallen kamar baby doll. Ya ce "Kinyi farin ciki?" Ta ce "Kai sosai fa kenan zan zama matar ka?" "Eh mana baby ko baki son hakan?" D'an hararar sa ta yi ta ce "Ni kuwa nake so," bari ma naje na sanar da Mama Kiran ta Maleek ke yi amma ko waige bata yi ba tabar falon da gudu girgiza kai ya yi ya kalli agogon sa yabi bayan ta domin tafiya gida ya huta. Tun kafin ta shiga falon take k'wala kiran "Mamana Sabreen sister Sameeha dear," duk a tare ta same su a falon Doctor kuwa dafe Kai ta yi ta ce "Ya ilahi wad'an nan yara nawa rabbi ya shirya mun ku," fad'awa jikin ta Sabeeha ta yi ta ce "Mamana albishirin ki," kafin Doctor ta yi magana ta nufi Sabreen ta rungume ta ta ce "Dear congratulate me na kusa aure Sameeha dear Sweetheart ya ce su Daddy zasu zo neman aure na," ta fad'a tana rungume Sameeha. Ihun su na murna da suka saba suka saki suka fara rawar su ta murna har da Sameeha da itama rawa take yi kamar wacce ta samu fitaccen kid'a. Doctor kuwa kallon yarab nata kawai take yi ganin yadda suka sata a gaba suna rawa cikin farin ciki itama murnar take yi. Wayar Sabreen ce ta fara neman agaji ta d'auka daga can Fauwaz ya ce "Amarya ta," dariya ta yi ta ce "Yau Kuma amarya na koma my heart?" Cikin farin ciki ya ce "Dagaske kin kusa zama amarya ta su Daddy zasu zo nema mun auren ki har ma da na yaya," "Wayyo dad'i kace na kusa zama amarya," ta fad'a tana buga tsalle bata jira ya k'ara magana ba ta katse Kiran suka cigaba da budiri domin su Sabeeha suna jin abinda suka tattauna da Fauwaz nan fa suka k'ara rikita gidan 'yan aikin gidan fitowa suka yi suna kallon yadda 'yan uku suka saki kid'a suna cashewa domin abun ya yi musu dad'i. Sallamar Abba ce yasa su saurin nutsuwa suka kashe kid'an suka zazzauna kamar basu suka gama zubar da galan-galan na rawa ba. Zama Abba ya yi Sabeeha ta je ta kawo masa ruwa suka ce "Sannu da dawowa Abba," ya ce "Yawwa," ya kalli Mama ya ce "Doctor yau dai kam daga ke har aminaina na ganku cikin farin ciki ku fad'a mun meke faruwa," kallon 'yan uku Mama ta yi a tare suka yi k'asa da kai. Mama ta ce "Ooh ni ku ka raina kenan ko to shima ku fad'a masa mana marasa kunya kawai," sannan ta kalli Abba ta ce "Yanzu suka gama rawa nan a gabana saboda Maleek Umar da Fauwaz sunce zasu turo maganar auren su," washe baki Abba ya yi ya ce "Masha Allah aminaina girma ya taho Allah ya kawo su lafiya ai kuna son su ko?" A tare suka ce "Sosai ma kuwa Abba," baki bud'e Doctor ke kallon su da sauri suka tashi suka bar falon. [10/25, 8:46 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️ RUBUTAWA DAGA HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ) SADAUKARWA GA MY DAUGHTER SABEEHA BILKISU Z.YA'U (🅱️K) AISHA MAGAJI DABO (AMA) Page 21 D'akin su 'yan uku suka koma kowaccen su cikin farin ciki. Rana d'aya su Daddy tare da wakilan Umar suka je wajen Abba a take aka kammala komai aka sa rana wata d'aya saboda Maleek takurawa Daddy ya yi akan asa bikin wata d'aya saboda nan da wata biyu zai koma Dubai hakan ne yasa akasa bikin wata d'aya har da na Fauwaz Umar ma wata d'ayan yace asa domin a shirye yake. Haka 'yan uku da masoyan nasu suka cigaba gudanar da soyayyar su cikin farin ciki da son junan su da kuma bawa juna kulawa kowannen su na jin idan ba d'ayan su bazai iya rayuwa ba. Uncle kuwa sai daga baya Daddy ke sanar masa cewar ansa ranar bikin Maleek wata d'aya abin ya matuk'ar bawa Uncle mamaki domin bai tab'a tunanin Daddy zai yi wani Abu ba tare da sanin sa ba ko da Nasreen ta ji labari ranar wuni ta yi kuka domin tasan idan har Maleek ya auri Sabeeha sunanta sorry domin tasan bata da sauran k'ima da daraja a wajen Maleek duk da dama ba ganinta da mutunci yake ba already Hajiya Asiya kuwa har lokacin bata fasa yiwa Nasreen hud'ubar shaid'an ba. Kawu Bala ne kwance saman wata yagalgalalliyar tabarma idan ka kalle shi sau d'aya baza ka so ka k'ara ba ya rame ya yi bak'i idan har ka San shi da ka kalle shi yanzu sai ka rantse bashi bane saboda uwar rama duk ya canja kamanni daga gefe kuwa Lantana ce zaune ta zabga uban tagumi tana kallon Kawu Bala cikin tausayawa rayuwar su ta ce "Malam ka daure kasha kunun nan ka ga yau gaba d'aya baka sa komai a bakin ka ba duk da kunun nan kad'ai gare mu Wanda shima dakyar na samu aka bamu bashin sa balle ayi maganar siya maka maganin cutar ka," Kawu dake kwance sai ka rantse bacci yake yi sai dai tsabar jin jiki ne yasa ko idanunsa baya iya bud'ewa a hankali ya ce "Lantana nayi nadama na cuci d'an uwana Wanda bani da kamar sa gashi halin da na shiga garama na mutu na huta," kuka Lantana ta saka ta ce "Ka dena fad'ar haka malam insha Allah sai mun had'u da Maryam da Habu harma da yaran su mun rok'i yafiyar su domin samun sauk'i wajen ubangiji," Zainabu ce ta fito daga d'aki sai ka rantse ba haihuwar ta d'aya ba duk ta fita hayyacin ta ta zama tsohuwar k'arfi da yaji ta zauna gefen Lantana ta ce "Lantana ko zaki sanwa habibu kunun nan ya tashi daga bacci sai kuka yake yi," d'an girgiza Kai Lantana ta yi ta ce "Zainabu kunun nan malam na karb'owa yasha," Kawu dake magana dakyar ya ce "Bata Lantana shi yaro ne baisan babu ba," mik'a mata Lantana ta yi ta karb'a ta koma cikin d'akin su da ba komai a cikin sa taba Habibu mai 'yan watanni kunun yasha. Bikin 'yan uku sai tahowa yake yi yayinda Rinaz dakyar Daddy ya yadda yabar ta sai bayan biki sannan zata tafi karatu tayi kukan ta yi magiyar har ta gaji haka ta hak'ura. B'angaren 'yan uku kuwa gyaran jiki Mama tasa ake yi musu bata barin su fita ko Ina ko yaushe suna gida abinsu. Kawu Bala ne ke tafiya Yana layi kamar yasha wani abu domin zaka iya cewa shaye-shaye ya yi sai dai ba haka bane tsabar yunwar dake damunsa ce tasa shi hakan tafiya yake yi baya kallon gaban sa yazo tsallaka titi wata babbar mota data taho da gudun gaske ta yi gaba dashi ya fad'i a wajen matacce. Firgigit Abba ya farka daga bacci da salati a bakin sa Mama dake kwance a gefe yadda ta ji Abba ya tashi zumbur ne yasa itama ta tashi tare da kunna bedside lamp ta ce "Abban 'yan uku lafiya?" Ajiyar zuciya Abba ya sauke domin ya tabbatar da mafarki yake yi ya ce "Maryam mafarki nayi Yaya yana cikin mawuyacin hali sannan mota ta bige shi ya mutu gobe dole ne naje k'auyen," Doctor ta ce "Gaskiya ne hakan ya yi goben sai muje tare," Abba ya ce "Allah ya kaimu," ta amsa da "Ameen," daga haka suka koma baccin su. Washe gari da safe 'yan uku nayi breakfast a daining idan ka kalle su saika k'ara saboda wani azababben kyau da suka k'ara brown skin d'insu ta k'ara kyau sai shining take yi ga k'amshin su da falon ya d'auka. Abba ne da Doctor suka fito daga d'aki sunyi wanka na alfarma Doctor ta yi kwalliya cikin less coffee colour da milk takalmi da jaka da mayafi less d'in ya matuk'ar yi Mata kyau kasancewar ta fara Abba kuwa tsadaddiyar shadda yasa fara sol babbar riga sai k'amshi suke yi. Tunda suka fito su Sabeeha ke kallon su cikin burgewa waya Sabreen ta d'auka ta fara fella mutu hotuna Sabeeha na taya ta har suka k'arasa daining d'in suma suka zauna domin karyawa. Gaida iyayen nasu 'yan uku suka yi suka amsa cikin fara'a sannan suka cigaba da karyawa suna gamawa Abba ya kalli agogon sa ya kalli Mama ya ce "Doctor muje time na tafiya," "Abba Ina zaku je?" Sabeeha ta tambaya Abba ya ce "Aminiya zamu je k'auye ne wajen Yaya," Sabreen ta ce "Abba Dan Allah zamu je," Doctor ta ce "No Kun manta ne na hana ku fita?" Sameeha ta ce "Please Mama kuje damu," Abba ya ce "Kyale su mu tafi Doctor ku yi sauri kuzo mu tafi," Doctor ta ce "Kuma kuna dad'ewa tafiya zamu yi. Da sauri suka nufi stairs suka yi Shirin da baza a rasa ba domin already sunyi wanka kaya iri d'aya suka sa dogayen rigunan pich color d'in shadda suka sa da blue mayafai da takalma da jaka duk blue. Da gudu suka sauka down stairs kamar su Abban zasu gudu su barsu girgiza Kai Doctor ta yi ta ce "Allah ya shirye ku mu tafi to," gaba suka yi suna fitowa suka samu driver na jiran su. Doctor ta kalle shi ta ce "Yawwa sabi'u idan Faisal na kusa Kira mana shi yanzu," Sabi'u driver ya ce "To madam," ya fad'a tare da juyawa ya nufi wata hanya dake gidan can sai gashi tare da Faisal suna zuwa Mama ta nunawa Faisal wata dank'areriyar bak'ar mota ta ce "Zaka yi driving 'yan uku zamu je k'auye ne," ya ce "To madam," Bayan mota Abba ya bud'e Doctor ta shiga shima ya shiga sabi'u ya shiga ya ja motar. Bud'e bayan mota Sameeha ta yi ta kalli Sabreen dake gefe tana waya ta ce "To dear sai kin taho dan mu mun tafi," da sauri Sabreen ta shige motar tana yiwa Sameeha hararar wasa yayin da Sabeeha ta shiga gaban mota tana yin chart da Maleek. Jan motar Faisal ya yi yabi bayan motar su Abba sai k'auye. Suna shiga k'auyen daidai lokacin gidan Kawu Bala ya kama da wuta sosai wutar ta fara ci ganga_ganga ba tare da sunsan dalilin kamawar ta ba rabon su da d'ora tukunya a gidan ba sun manta shekarar ballantana ace wutar murhu ce ta haddasa. Dakyar suka fito daga gidan suna neman agaji tuni 'yan gari suka hallara aka fara k'ok'arin kashe wutar domin karta shafi mak'ota dakyar aka samu aka kashe wutar sai dai gidan ya yi k'urmus 'yan garin sai tausayin Kawu Bala suke ji domin duk wani Mai imani idan yasan halin da Kawu ke ciki sai ya tausaya masa ballantana yanzu da gidan nasa da shi kad'ai ya rage masa ya k'one. Tun daga nesa suke hango tarin jama'a wajen gidan Kawu Bala Abba ya ce "Maryam duba kiga taron jama'a wajen gidan Yaya lafiya kuwa," Mama da itama mamakin hakan take yi ta ce "Insha Allah lafiya lau," "Dear Kinga mutanen garin a tare a gidan Kawu Allah yasa dai lafiya," Sameeha ta fad'a cikin Sabeeha da Sabreen babu wacce ta kulata domin su mugun haushin Kawu Bala suke ji. 'yan k'auyen ganin manyan motoci yasa su baza idanu suna kallon motocin daga nesa da mutanen kad'an suka yi parking sannan suka firfito daga motar. Nan fa mamaki ya kuma kama mutanen saboda ganin wad'an da suka fito daga motar musamman wad'an da suka san Abba da Kuma sanin halin da yake ciki da amma yanzu gashi cikin tsadaddiyar mota ga wani canjawa da ya yi kamar ba shi ba haka ma 'yan uku sai kallon su ake yi ganin yadda suka zama bama a zancen Doctor domin ko gane ta 'yan garin basu yi ba zuwaira mai abinci dake lek'e ta katanga ce kad'ai ta gane ta. Hanya mutanen wajen suka bud'a musu suka wuce zuwa k'ofar gidan turus suka tsaya suna kallon yadda gidan ya k'one saurin juyawa Abba ya yi ya kalli Malam Saleh ya ce "Malam Saleh ina Yaya?" Domin Abba Sam bai lura da Kawu Bala dake gefe ba. Da hannu malam saleh ya yiwa Abba nuni da Kawu Bala dake gefe a durk'ufe idanunsa sai zubar da hawaye suke yi domin tausayawa rayuwar su halin da zasu shiga yake yi damuwar sa d'aya a Ina Lantana da Zainabu da d'anta zasu dinga zama shi bata kansa ma yake yi ba domin shi namiji ne. Sai da Abba ya tsorata ganin wadda aka nuna masa a matsayin yayan sa yasan dai yayan sa dogo ne sannan yana da k'iba amma a nuna masa wannan siririn mutumin matsayin yayan sa su kansu 'yan uku da maman su sunyi mamakin hakan sosai ga Zainabu rik'e da d'anta sai kallon su take yi kamar ranar ta fara ganin su yayin da su ko gane ta ma basu yi ba. A tsorace Abba ya nufi inda Kawu yake durk'ushe yana kukua ya dafa kafad'ar sa a hankali Kawu ya juya domin ganin Wanda ya dafa shi da sauri Abba ya cika shi tare da ja baya cikin rud'ani ganin yadda yayan nasa ya koma gaba d'aya fuskar sa sai k'ashi da fata. Ganin Abba ne da sauri Kawu ke k'ok'arin tashi tsaye domin tabbatar da abinda ya gani amma ya kasa da sauri Abba ya k'arasa ya d'ago shi ya mik'e idanun kawu Bala na zubar da hawaye ya ce "Habu," Abba bai damu da yadda jikin Kawu yake tumu_tumu ba ga wani tsami da yake yi na rashin wanka da wanki ba ya rungume kawu shima yana hawayen ya ce "Yaya me yake faruwa da kai haka ne?" Rungume Doctor Sameeha ta yi itama tana kukan tausayin Kawu Bala su ma su Sabeeha ya basu tausayi sosai. Kawu Bala ya bud'e baki ya ce "Habu kayi hak'uri nasan nayi maka ba daidai ba," saurin rufe masa baki Abba ya yi ya ce "Ya isa Yaya a cikin mutane muke yanzu muje mu tafi," Zainabu ce ta taso da d'anta a hannu tana kukan haka ma Lantana. Doctor kuwa ta kasa cewa uffan tana rungume da Sameeha dake aikin kuka wajen ta Lantana ta nufa tana kuka ta ce "Maryam kece," Doctor ta ce "Ni ce lantana," haka ma Zainabu ta k'arasa tana wani zare ido harara Sabeeha ta galla mata bawai bata tausaya mata bane a'a sai kawai tunawa da irin cin mutuncin da Zainabu tayi musu da ta yi Sabreen ma tsaki ta ja. Tuni jikin Zainabu ya yi sanyi Doctor kuwa wani kallo ta yiwa Sabreen jin tsakin da ta ja Sabeeha kuwa mazewa ta yi ta fara danna wayar ta yayin da Sabreen ta kalli wani gefe daban. Abba ne ya rik'o hannun Kawu ya k'arasa gaban su Doctor ya ce "Doctor Ina ga mu tafi gida kawai," juyawa suka yi suka nufi motor yayin da 'yan gari kowa ke jinjinawa Abba da abinda ya yi sanin yadda Kawu ke muzguna masa. Doctor kuwa duk da haka sai da suka gaisa da zuwaira Mai abinci sannan suka wuce zuwa mota yayin da Sabeeha fafur tace bazata shiga mota d'aya da Zainabu ba duk da hararar da Doctor ke yi mata ganin tana neman tara musu jama'a kamar k'aramar yarinya yasa Abba cewa shikenan kuzo mu tafi a nan. Gaban mota Sabeeha ta shige Sabreen ma ta shige bayan mota ta zauna Wai itama bazata zauna mota d'aya da su kawu ba Sameeha ce kawai ta shiga gaban motar yayinda Kawu Lantana da Zainabu ke bayan motar da su Sabeehan suka zo a ciki suka tafi. Tun a mota Doctor ta fara yi musu fad'a baji ba gani Sabeeha sai tura baki take yi Sabreen kuwa shiru ta yi tana sauraren yadda Doctor taita fad'a kamar ta ari baki Abba dai shiru ya yi baice komai ba domin yasan cewa tabbas 'yan uku sun wahala sosai wajen kawu Bala dan haka da wuya sun karb'e su da wuri da haka suka k'arasa gida. Idanu waje Kawu Lantana da Zainabu ke kallon gidan domin ganinsu suke yi kamar a k'asar turai suna gama parking Sabeeha ta bud'e mota ta fice ta shige cikin gidan da kallo Doctor ta bita ta girgiza kai kawai Sabreen ma kallo su Kawu basu ishe ta ba ta shige cikin gidan. Doctor ta kalli Sameeha dake gefe a tsaye ta ce "Daughter shiga ki Kira mun Halima kuzo tare wad'an can 'yan uwan naki kuwa ni da su ne," Sameeha ta ce "Mama kiyi...," "Kinga ba abinda na saki kenan ba wuce ki tafi," shigewa falon Sameeha ta yi Mama ta waiga ta kalli Kawu ta ce "Amma Yaya kamar baka da lafiya ko?" Lantana ta ce "Eh Wallahi wajen sati biyu kenan," Doctor ta ce "Ayyah me yake damun ka?" Nan Kawu ya yi mata bayanin yadda yake ji take Doctor ta gane ulcer ce ke damun Kawu mai zafi Sameeha da Halima ne suka k'arasa wajen Doctor ta kalli Halima ta ce "Yawwa Halima ga bak'i munyi kije da su wancan k'aramun part d'in nasan a gyare yake ki nuna musu yadda ake amfani da kayan toilet d'in zasu yi wanka sannan ku basu abinci suci yanzu zan ba Faisal kud'i ya siyo musu kayan sawa kafin zuwa gobe mu fita shopping Faisal idan ka dawo kaba Halima kayan ta Kai musu sannan ke kuma idan zaki Kai musu abinci ki sanar dani na baki magani ki kaiwa Yaya yasha kafin gobe muje hospital," sannan ta kalli Kawu Bala ta ce "Yaya idan Kun kammala sai ku shigo ciki," Kawu Bala kuwa kasa magana yayi domin mamakin halin kirki irin na Maryam. Kud'i Doctor ta zaro a jakar ta ta bawa Faisal ta ce "Ka dai ji bayani na ko?" Ya ce "Eh madam," Doctor ta ce "Ku je Halima," ta ce "To madam," suka tafi Doctor Kuma ta ja hannun Abba dake mamakin ta shima suka shige cikin falon. [10/25, 8:46 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️ RUBUTAWA DAGA HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ) SADAUKARWA GA MY DAUGHTER SABEEHA BILKISU Z.YA'U (🅱️K) AISHA MAGAJI DABO (AMA) Page 22 Har d'aki ta ja Abba sannan ta shige bathroom ta had'a masa ruwan wanka ya shige domin yin wanka Doctor ma ta tafi d'akin ta tayi nata wankan. Sabeeha kuwa tana shiga d'akin su cire kayan jikin ta tayi ta d'aura towel ta fad'a wanka tana fitowa ta samu Sabreen zaune tana danna waya wuce ta Sabeeha tayi zuwa gaban mirrow ta yi shafe_shafen ta ta zira wata doguwar riga marar hannu maroon tasa hula a kanta maroon tayi kyau kamar yar baby gashin gaban goshinta ya kwanta luf gwanin sha'awa ta kalli Sabreen ta ce "Dear wallahi zuciyata tak'i yin sanyi yau da naga Zainabu sai naji tsanar da nake mata tafi ta ko yaushe har tsanar da nake mata tafi ta Kawu saboda mun girme ta amma hakan baisa ta raga mana ba," ajiye wayar Sabreen ta yi a gefe ta ce "Wallahi kuwa nima haka amma ki duba yadda Sameeha dear ta kama kuka kamar ta manta sanda Zainabu taso kashe ta ba," Tashi Sabeeha ta yi ta ce "Ah to nima dai abinda nagani kenan ni bara na fita," daga haka ta fice daga d'akin Sabreen kuwa ta shige toilet don yin wanka. Sabeeha na sauka down stairs lokacin Mama ta fito daga d'akin ta zata je na Abba "Ke zonan," Doctor ta fad'a wajen ta Sabeeha ta nufa ta ce "Gani Mama," hararar ta Doctor ta yi sannan ta ce "Kunsan Allah ku kiyayeni a cikin gidan nan ku abinda ku ke yi haka ku ka ga ya dace Yaya fa yayan mahaifin ku ne Zainabu yar uwar ku ce ku duba halin da suke ciki haka ya kamata kuyi musu?" Tura baki Sabeeha ta yi ta ce "Mama basu da mutuncin fa dukan su," "Rukayya Wallahi ki fita a idona na rufe matsa mun a nan ko yanzu ranki ya b'aci Wallahi," kitchen Sabeeha ta nufa tana buga k'afa ajiyar zuciya Doctor ta sauke tana bin Sabeeha da kallo a zuciyar ta ta ce yaran nan sai a hankali zasu sauko nasan dama za ayi haka ta nufi d'akin Abba. Abinci Sabeeha ta zuba ta koma d'akin su ta ci sannan ta tashi ta yi alwala ta yi sallah ta kwanta saman gado take bacci ya d'auke ta. Tana baccin ne ta ji ana tashin ta juyi ta yi ta bud'e idanunta ta sauke su akan Sameeha ta ce "Dear yadai?" "Kizo inji Mama tana down stairs kuma yanzu fa," tana fad'ar haka ta juya ta fita tashi Sabeeha ta yi ta gyara zaman hular ta tabar d'akin. Tunda ta fara sauka ta hango su Kawu Bala a falon d'an d'auke kai Sabeeha ta yi ta ja k'aramun tsaki ta k'arasa falon kusa da Sameeha ta zauna ta ce "Mama gani," shiru Doctor ta yi mata. Abba ya kalli Kawu ya ce "Yaya lafiya kace duk mu taru anan bayan baka da lafiya ai kamata ya yi ka kwanta ka huta," Kawu Bala kuwa hawaye ne ya zubo a fuskar sa ya ce "Habu dan Allah ka gafarce ni kuyi mun aikin gafara nayi maka abubuwa da dama a rayuwa nasan ban cancanci yafiya a wajen ku ba tun muna yara nake k'untata maka har zuwa girman mu Habu duk farke maka shagon da ake yi nine nasa da hannuna a ciki," sai da Abba ya razana girgiza Kai kawai ya yi domin bai tab'a tunanin Kawu ne ya yi masa haka ba domin a tunanin sa d'an uwan sa ai sai dai yaso cigaban sa amma gashi d'an uwan nasa ne da hannu cikin kashe masa wajen sana'a. Kawu ya cigaba da cewa "Sannan Maryam ki gafarceni neman Maryam da akayi aka rasa mune sila domin mune muka je wajen bokanya ta yi mana aiki akan a b'atar da ita sannan a mantar da ita k'auyen da duk mutanen k'auyen ballantana mijin ta da yaranta amma da Allah yaso asirin mu ya tonu sai rana d'aya bamu barbad'a maganin da ta bamu ba akan musa kullum ba daga nan bokan ya ta tabbatar mana cewa dole Maryam zata dawo sannan zamu d'and'ana talauci mai zafi haka kuwa aka yi abinci ma gagarar mu yake yi duk wata kadara ta mu sai da muka siyar ga Kuma Zainabu a gida saboda itama asirin da muka yiwa Sadam ya karye shine ya korata gida Dan Allah ku yafe mana munyi hakan ne saboda sharrin shaid'an da Kuma hassada saboda Sanin Maryam wacece da Kuma kud'in iyayen ta hakan ne yasa mana hassada da rashin son cigaban ku amma munyi nadama," Abba duk sanyi AC dake falon amma goge gumi yake yi jin aika aikar da yayan sa ya yi Doctor ma jikin ta duk ya yi sanyi a hankali hawaye suka zubo kan fuskar ta jin akan wani Abu na duniya ake neman hallaka ta ga rabata da 'ya'yan ta da aka yi da kuma mijin ta a lokacin da tafi buk'atar su a lokacin da ta rasa nata mahaifan gaskiya su Kawu sun cutar da ita a rayuwa. Lantana ta ce "Duk abinda malam ya fad'a gaskiya ne amma Dan Allah ku yafe mana dan girman Allah munyi nadama tun ba yanzu ba," wata uwar harara Sabeeha ta zabga Mata domin wata sabuwar k'iyayyar su taji a ranta domin jin duk sune silar jefasu a wata rayuwar a baya wacce ba dan Allah ya tsare su ba da sun fad'a wata rayuwar daban. Sameeha kuwa hawaye ta dinga gogewa Sabreen kuwa itama tsanar su ce ta ninku a ranta tab'e baki ta yi ta kauda kanta daga kallon su. Zainabu ta ce "Dan Allah ku yafe mana ba dan halin mu ba mun aika ta laifi dukan mu ko Lantana?" Harara Sabeeha ta wurga mata taja wani dogon tsaki jin yadda 'ya ke gatsa sunan mahaifiyar ta kamar ta Kira sa'ar ta. Da kallo mutanen wajen suka bita Zainabu kuwa sai wurga ido take yi tana k'arewa falon kallo domin yafi Wanda aka kaisu kyau tana ganin can d'in kamar ba a Nigeria ba sai ga Wanda ya fi shi gashi sunci abincin da basu tab'a cin mai dad'in sa ba ga kaji sai da suka bar su da lemuka. Abba ya yi ajiyar zuciya ya ce "Yaya tabbas kun cutar da rayuwar mu da ta yarana Amma bakomai Allah ma munayi masa laifi ya yafe mana mun yafe Allah ya yafe mana baki d'aya," suka amsa da "Ameen," Kawu Yana hawaye ya ce "Nagode Habu nagode," Doctor ma ta ce "Nima na yafe muku," godiya sosai suke yi sannan suka kalli 'yan uku tun kafin su yi magana Sameeha ta ce "Mun yafe," "Kin yafe dai," cewar Sabreen Sabeeha kuwa wayar k'arya ta fara ta mik'e tabar falon domin idan ta ce zata yi magana to maganar da zata fad'a baza ta yi dad'i ba. Doctor kuwa ita kunya ma suka bata ta kalli Kawu ta ce "Yaya kayi hak'uri," Kawu ya ce "Bakomai Maryam yarana ne ai Kuma a abinda nayi musu a hakan ma ba k'aramun hak'uri suka yi ba," Doctor kuwa kallon Sabreen dake zaune ta yi kicin-kicin ta yi ta yi k'wafa. Abba ya ce "Yaya kuje ku huta nasan kun gaji nima zan fita ne," tashi su Kawu suka yi zuwa part d'in da aka sauke su Abba Kuma ya hau mota ya fita. Da daddare har d'aki Doctor ta samu su Sabeeha ta fara yi musu fad'a baji ba gani sai da ta gama fad'an ta sannan tabar d'akin. Sameeha ta ce "Dan Allah ku fahimci Mama maganar ta gaskiya ne ku yafe musu ko mu muna yiwa Allah laifi Kuma ya yafe mana duk abinda suka yi mana ba gashi sunyi nadama ba Kuma da sunsan wannan ranar na tafe da baza su aika mana haka ba," tab'e baki Sabeeha ta yi ta fice daga d'akin domin ita tana da wani hali rik'o ne da ita sosai sannan idan tayi fushi akan abu to ana shan wuya kafin ta sauko. Har Sabreen zata tashi Sameeha ta rik'o hannun ta tana hawaye da sauri Sabreen ta zauna ta ce "Subhanallah dear ki dena kuka please," cikin hawaye Sameeha ta ce "Haba dear kuna ganin ya dace Mama tayi fushi da ku laifin fa da su Kawu suka yi mata yafi namu girma rabata suka yi da duk wani farin cikin ta suka rabata da mu duk da kuwa soyayyar dake tsakanin uwa da yaran ta Amma ta yafe musu meyasa mu bazamu yafe musu ba bai kamata mu zama d'aya da su ba," ajiyar zuciya Sabreen ta yi ta ce "Nagane dear," "Yawwa sister me muje mu bawa Mama hak'uri," Sameeha ta fad'a tare da jan hannun Sabreen suka fita daga d'akin a falo suka samu Sabeeha nan itama suka kashe mata jiki da maganganun su tashi ta yi suka tafi bawa Doctor hak'uri amma ta k'udurta a zuciyar ta babu ruwan ta da su Zainabu. A d'aki suka samu Doctor tana waya da Ummi sai da ta gama sannan ta kalle su ta kawar da kai tashi Sabeeha ta yi ta zauna gefen doctor ta yi Mata side hug ta ce "Kiyi hak'uri kinji Mamana baza mu k'ara ba," Sabreen ma ta rungume ta ta d'aya side d'in ta ce "Please Mama we promise that we will not do it again," ajiyar zuciya Doctor ta yi ta ce "Shikenan na hak'ura ku rungumi 'yar uwar ku ku koyar da ita abinda bata saniba idan tayi ba daidai ba ku nuna mata kuskuren ta bata da wad'an da suka fi ku Allah ya yi muku albarka," suka amsa da "Ameen uwa ta gari," daga haka suka fita daga d'akin. Washe gari da safe Doctor Abba da Kawu suka je asibiti aka duba shi aka bashi magunguna aka yi masa allurai sannan suka koma gida da yamma Doctor ta kira 'yan uku suka same ta a falo ta ce "Yawwa amininan Abba ku tafi da Zainabu kuyi musu shopping," suka amsa da "To," sannan suka tafi domin shiryawa. Suna fita compound d'in gidan Sabeeha ta ce "Kuje ku kira ta mu tafi domin nidai bazan je ba," basu ce Mata komai ba suka nufi part d'in da su Kawu suke. Da Sallama suka shiga falon Lantana da ta k'urawa TV idanuwa ta waiga tare da amsa sallamar tana ganin sune ta washe baki tana yi musu Sannu da zuwa k'arasawa cikin falon suka yi suka gaishe ta ta amsa tana washe baki tab'e baki Sabreen ta yi domin gani ta yi daban da lantana nayi musu fara'a domin ba saba ganin hakan suka yi ba ta ce "Ina Zainabu fa zamu fita ne," Lantana ta ce "Tana ciki Zainabu!," Ta k'wala mata kira. Daga ciki Zainabu ta amsa ta fito tana ganin su Sameeha ta k'arasa da sauri ta tsugunna ta ce "Ina wunin ku," abin ya basu mamaki amma suka basar suka ce "Lafiya," Sameeha ta ce "Ki shirya zamu fita shopping yanzu," ta ce "To," sannan ta juya zuwa d'akin ta. Wayar Sabreen ce ta fara ringing Sabeeha ce ke kiranta picking ta yi ta ce "Dear," daga can Sabeeha cikin masifa ta katse ta "Wai me ku ke jirane ku ka barni a waje ba dai wannan banzar ku ka zauna jira ba Wallahi ku ka yi wasa bazan je ba mtsww," ta ja tsaki dafe Kai Sabreen ta yi ta ce "Ya Salam calm down dear," "Ank'i ayi calm down d'in," Sabeeha ta fad'a tare da hanging d'in Kira ta bud'e gaban motar ta zauna tana jan tsaki sai gasu sun fito sun nufo motar. Bud'ewa suka yi suka shiga Zainabu ta kalli Sabeeha ta ce "Ina wuni," banza Sabeeha ta yi mata ta sake cewa "Ina wuni," tsaki Sabeeha ta ja ta ce "Kinga dalla malama karki dameni nace miki banji bane," shiru Zainabu ta yi Sameeha zata yi magana Sabeeha ta d'aga mata hannu hakan ne yasa ta ja bakin ta ta yi shiru. Har suka je ba Wanda ya yi magana suna shiga suka fara siyayya Sabeeha kuwa kujera ta samu ta zauna tana waya da Maleek can ta mik'e wani ring ne ya d'auki hankalin ta ta d'auka sannan suka nufi wajen biya suka bi ya sannan suka bar wajen. Direct wajen tailor d'in su suka wuce suka bayar da d'inkuna sannan suka wuce gida har cikin falo Zainabu ta bisu suka samu Doctor tana danna laptop ta ce "Kun dawo "yammata na?" Suka ce "Eh Mama," zama suka yi Zainabu Kuma ta zauna a k'asan carpet ta ce "Mama mungode Allah ya saka da alkhairi," Doctor ta ce "Bakomai ai kema 'yata na d'auke ki," tsaki Sabeeha ta ja a ranta ta ce baki iya fad'awa uwar ki Mama ba sai na neman suna. "Lafiya kuwa?" Mama ta tambayi Sabeeha Sabeeha ta ce "Kaina ke mun ciwo Mama Bari na shiga ciki," tana fad'ar haka ta d'auki hand bag d'inta ta haura stairs. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya Sam Sabeeha bata shiga harkar Zainabu ko gaisuwar ta bata amsawa duk da Zainabu yanzu part d'insu take wuni amma ko kallo bata ishi Sabeeha ba su Sabreen kuwa sosai suke fira da ita sannan suna son yaron ta Habibu da suke Kira Habibi itama Sabeeha tana kula shi amma idan Zainabu bata wajen haka ma Lantana tana zuwa part d'in su yi fira da Doctor. Kawu Bala kuwa ya warware tare ma suke fita da Abba inda Abba ya mallaka masa d'aya daga cikin super markets d'insa farin ciki wajen Kawu Bala ba a magana sannan 'yan uku ma sun sake da shi Banda Sabeeha da iya gaisuwa ke had'a su da haka har suka yi sati biyu lokacin bikin 'yan uku ya taho. Sabeeha ce ta fita compound d'in gidan saboda Kiran da Maleek ya yi mata a tsaye ta same shi yasha kyau sosai cikin k'ananan kaya farare ya had'u sosai sai k'amshi yake zabgawa gashin kansa sai shek'i yake yi k'arasawa ta yi ta ce "Barka da isowa sanyin idaniya ta," murmushin da ya bayyana dimples d'insa ya yi ya ce "Yawwa barkan ki da fitowa matata," Zainabu ce Ke tahowa domin zuwa part d'in doctor ta hangi su Sabeeha tsaye ita da wani balarabe suna fira suna dariya murza idanunta ta yi tana so ta tabbatar mafarki take yi ko da gaske ne ba indiye ne a gaban ta a hankali take takawa kamar tana jin tsoro sai da ta k'arasa wajen su ta kasa wucewa ta tsaya kallon Maleek da baisan da ita a wajen ba. Sabeeha na ganin ta had'e fuska ta ce "Ke Kuma fa zaki wani zo ki tsayawa mutane a nan dalla janye tsunmar rayuwar ki kibar nan," d'an kallon Zainabu Maleek ya yi da sauri ta durk'usa ta ce "Ina wuni," Maleek ya ce "Lafiya," mamaki Zainabu ke yi a zuciyar ta ta ce kunji yana jin hausa sannan ta kalli Sabeeha ta ce "Ina wuni aunty," tsaki Sabeeha ta ja bata amsa ba tashi Zainabu ta yi tabar wajen da sauri kafin wani wulak'ancin ya biyo baya. Kallon Maleek Sabeeha ta yi ta ce "Mu k'arasa ciki," binta ya yi suka wuce suna shiga falon ya zauna ta kawo masa drink da ruwa ta zauna kujerar dake facing Wacce yake kai ya ce "Baby waccan d'in wacece?" Tab'e baki ta yi ta ce "Yarinyar Kawu ce," take Maleek ya gano Kawu da Kuma abubuwan da Kawu ya yi musu hakan na nufin kenan Sabeeha na rama abinda aka yi musu ne basar da tunanin ya yi ya ce "Me tayi Miki haka?" "Tayi mun abubuwa da yawa wallahi a rayuwa ita ta fara fad'a min maganar da ta hargitsa mun tunani wallahi sannan yarinyar bata da kunya," d'an murmushi ya yi ya ce "San girma ko?" Dariya ta yi ta ce "Haba na girme ta fa dan dai kawai ta rigani aure ne," zare ido Maleek ya yi ya ce "Kina nufin tana da aure ne?" Gyad'a kai ta yi ta ce "Har da yaro ma yanzu dai basa tare da mijin nan dai ta bashi labarin sadam," jinjina kai Maleek ya yi ya ce "Lallai wannan d'an rainin wayau ne any way zansan abinda zanyi," daga haka suka canja firar tasu zuwa ta soyayya. Washe gari Sabeeha na zaune a d'aki tana kallon wani American film a wayar ta Zainabu ta shiga d'akin da Habibu a hannunta sai kuka yake yi bata. Kallon Sabeeha ta yi batasan wacece ba a cikin 'yan uku ta ce "Aunty Sameeha ce?" Banza Sabeeha ta yi da ita saima tab'e baki da tayi hakan yasa Zainabu ta fahimci Sabeeha ce ta ce "Ina wuni Aunty," Nan ma Sabeeha taba banza ajiyar ta juyawa ta yi a sanyaye zata fita daga d'akin Sabeeha ta ga yadda Habibi ke kallon ta yana kuka sai yaron ya bata tausayi sosai gashi dama tana son yaron sosai. Zare earphone d'in kunnen ta ta yi ta ce "Ke zonan," waigawa Zainabu ta yi ta k'arasa gaban Sabeeha ta zauna a k'asa ta ce "Gani," tashi zaune Sabeeha ta yi ta ajiye wayar ta gefe inda pretty ke bacci ta ce "Lafiya Habibi yake kuka kuwa?" Cikin mamaki Zainabu ta ce "Wallahi aunty bansani ba tun d'azu yake kuka yak'i yaci komai amma naji jikin sa da zafi," d'an jinjina Kai Sabeeha ta yi sannan ta mik'e tsaye ta ce "Mama tana asibiti kuje ki shirya mu kaisa asibitin su Sameeha dear sun fita unguwa," Zainabu ta ce "To," sannan ta fita daga d'akin Sabeeha ma wanka ta shiga tana fitowa ta shirya a gurguje cikin doguwar rigar less d'inkin buba orange color tasa red d'in mayafi ta d'auki handbag d'in ta da jakar ta ta fice. A compound d'in gidan ta samu Zainabu na jiran ta Faisal ta Kira suka shiga motar ya jasu zuwa hospital suna zuwa Sabeeha na fita daga mota idanunta ya sauka akan Maleek da Salman ya bud'ewa mota da alama daga cikin asibitin yake. Shima kamar ance ya kalli gurin suka yi ido hud'u a tare suka sakarwa juna murmushi. K'arasawa wajen sa Sabeeha ta yi Zainabu ta gaishe shi ya amsa yana kallon Sabeeha ya ce "Sabee na kinzo yin mene a hospital?" Juya fararen idanunta ta yi ta ce "Munzo wajen Mama ne ta duba habibi baya da lafiya," jinjina Kai ya yi. "To kaima me kazo yi nan?" D'an murmushi ya yi ya ce "Nazo wajen Ummi ne," ta ce "Ok bara naje na gaida ta," Maleek ya ce "Bari na raka ki," sannan ya kalli Salman ya ce "Salman ka raka wannan office d'in Mama zamu same ta a can," ya fad'a yana nuna Zainabu Salman ya ce "Ok sir," ya juya suka jera zuwa cikin asibitin. Tafiya suke yi suna fira suna dariya abinsu d'an gefen su Maleek ya kalla ya ga wani matashi ya d'auki hoton sa shi da Sabeeha basarwa ya yi sai kuma lokaci guda ya sake kallon inda mutumin yake ya ga wayam babu shi d'an shiru Maleek ya yi yana tunanin to meyasa mutumin ya d'auki hoton su Sabeeha ta ce "My lafiya kuwa?" Girgiza kai ya yi ya ce "Nothing muje," ya fad'a tare da yin gaba yana waige ko zai hango mutumin. Tura k'ofar office d'in Ummi ya yi suka shiga da Sallama ya zauna kujerar dake gaban Ummi. A hankali Ummi ta d'aga Kai tana ganin shine ta dafe goshi ta girgiza kai ta ce "Ya salam yanzu kuma wacce rigimar ka dawo sauke mun?" Washe baki ya yi tare da nuna mata Sabeeha da ido kallon ta Ummi ta yi ta ce "Daughter dama tare ku ke shine ka barta a tsaye zauna kinji daughter," zama kan d'ayar kujerar Sabeeha ta yi ta ce "Ummi Ina kwana?" Cikin fara'a Ummi ta amsa ta ce "Ba dai har gida wannan sarkin rigimammun ya je ya taho dake ba akan wannan maganar ba?" Kallon Maleek Sabeeha ta yi ya langab'ar da kai yana kallon Ummi kamar mai shirin yin kuka ya ce "Ummi kiyi shiru," hararar wasa ta yi masa ta ce "Bazan yi shirun ba dole ne na tambayi daughter nata ra'ayin," Ummi ta fad'a tana kallon Sabeeha. Sabeeha ta ce "A'a Ummi a waje muka had'u da shi," jinjina Kai Ummi ta yi ta ce "Nan yazo yasa mun rigima ai wai next week idan an d'aura auren ku wai Dubai zaku wuce tare ni kuma nace a'a tunda yana da damar da zaku yi wata d'aya a nan d'in gara ku yi tunda idan kun tafi ba ranar dawowa ko kun shirya hakan da shi ana d'aura auren zaku tafi?" Kallon Maleek ta yi ya kashe mata ido ya yi ta kalli Ummi ta ce "A'a Ummi," "Sannan bayan hakan ya kuma kawo zancen to wai idan aka d'aura aure a sabon gidan sa da ya gina a nan Kaduna zaku zauna nan ma ban amince ba domin yasan akwai shirin da na shirya idan ku ka dawo daga Dubai ida zaku tare shiyasa nace ya bari sai kin dawo sai ku zauna a d'aya daga cikin gidajen sa ko ku zauna a can gida a part d'insa tunda na wata d'aya ne kawai ko kinfi so ki tare yanzu idan an d'aura auren Dan na gaji da rigimar wannan," Ummi ta fad'a tana dungure masa Kai nan ma signal Maleek ya dinga yi Mata da ido alamun tace Eh amma ta basar kamar bata ganshi ba ta ce "A'a Ummi yadda ki ka tsara d'in yafi zan zauna a can gida tare da ku," cije pink lips d'insa Maleek ya yi ta basar. Mik'ewa ya yi fuska a had'e ya ce "Tashi mu tafi," mik'ewa Sabeeha ta yi ta ce "Ummi zamu je wajen Mama," Ummi ta ce "To ku gaishe ta," fita ya yi tana binsa a baya. Tunda suka fita ko kallon ta bai yi ba wai shi fushi yake yi da ita ta ce "My kana jina?" Banza ya yi da ita ta yi murmushi tare da shan gaban sa ta tsaya ta ce "Ka ga ai bai kamata mu rusawa Ummi Shirin ta ba," hararar ta ya yi ya murgud'a baki ya wuce ta gefen ta. Binsa ta yi tana kunshe dariya ganin yadda ya murgud'a mata pink lips d'insa ta ce "Ka saurareni please," d'an tsayawa ya yi ya ce "Me kuma zaki ce mun Sabee na ba dai ke bakya so ki rusawa Ummi Shirin ta ba to ni kin rusamun nawa shirin Wanda na dad'e da had'a shi kinsan dalilin da yasa na fad'awa Ummi duk haka to duk domin kece nasan kin manta cewar bake kad'ai ce matata ba to Ina so ne mu tafi Dubai tare tun ana d'aura aure amma kince a'a a gidana na Nan ma kince a'a da kanki ki ka zab'i zama cikin gidan mu Wanda nasan dole ne a raba kwana tsakanin ki da Nasreen Wanda idan aka yi hakan idan lokacin kwanan ta yazo a lokacin tafiya ta Dubai to da ita zan tafi kuma kina gani ba ruwana amma da kin yadda ana yin auren mun tafi shikenan," yana fad'ar haka ya wuce ya barta. D'an tsayawa ta yi tana nazarin maganar sa ita Sam dagaske ta manta da wata Nasreen ji tayi kamar ta koma ta fad'awa Ummi ta yadda da maganar Maleek Amma ba dama a sanyaye tabi bayan sa. Tana shiga ta same shi a zaune suna gaisawa da Mama itama zaman tayi a sanyaye kamar wacce aka yiwa duka kallon ta Mama ta yi ta ce "Ke Kuma fa lafiya?" Kallon Maleek ta yi idanunta har ya cika da k'walla bata ce komai ba hararar wasa Maleek ya yi mata d'an tab'e baki ta yi kamar k'aramar yarinya na shirin kuka. Doctor ta ce "Kinga idan kuka Zaki sani a gaba kiyi min to ki fita mun a office sannan ga Zainabu can a motor tana jiran ki gaba d'aya kwanan nan rigima kike ji," Maleek ya d'an yi murmushi ya ce "A'a Mama may be baby bata jin dad'i ne ko baby?" Tashi kawai Sabeeha ta yi ta fice daga office d'in binta da ido Doctor ta yi ta girgiza Kai ta ce "Allah dai ya shirya son zaka yi fama," dariya Maleek ya yi ya ce "Sai anjima Mama," ya fice yabi bayan Sabeeha. Tafiya take yi tana share hawaye haka kawai take jin wani mugun kishin Maleek na nuk'urk'usar zuciyar ta Wai a hakan ba tun kafin a kaita gidan. Tana fitowa wajen asibitin daidai lokacin wata jar mota ta yi parking a gaban Sabeeha aka bud'e motar wata budurwa ta fito cikin shigar riga da wando wata ce ta fito daga gaban motar da gudu ta wuce Sabeeha d'an waigawa Sabeeha ta yi ga mamakin ta budurwar da gudun ta ta je ta rungume Maleek. [10/25, 8:47 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️ RUBUTAWA DAGA HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ) SADAUKARWA GA MY DAUGHTER SABEEHA BILKISU Z YA'U (🅱️K) AISHA MAGAJI DABO (AMA) Page 23 Wani takaicin ne ya sake had'arwa Sabeeha a zuciyar ta da gudu ta k'arasa motar su ta bud'e ta shiga ta ce da Faisal "Muje," ya ja motar suka tafi. Maleek kuwa janye wacce ta rungume shi daga jikin sa ya yi ya kalli fuskar ta ya ce "Yammatan Momcy saukar yaushe," budurwar Mai suna Haneefa ta ce "Yaya yanzu muka zo fa Ina My sweet mom wajen ta muka zo," kafin ya yi magana d'ayar ma tazo ta rungume shi ta ce "Oyoyo Yaya," ya ce "Hanfa har yanzu bakwa girma ko?" Sakin sa wacce ya kira da Hanfa ta yi ta tura baki ta ce "Kai Yaya duk fa murnar ganinka ce Ina sweet momma fa Ashe har yanzu baka hana momma zuwa hospital ba to yaushe zaka Kai mu wajen auntyn tamu?" Ajiyar zuciya ya yi ya ce "Kun fara ba Ummi na ciki a office gashi nan garin rawar kan ku zaku kashe mun aure," "Aure fa Yaya har an d'aura ne Ina take Kuma ita Sweetheart d'in," Haneefa ta fad'a d'an tsaki ya ja ya ce "Kunga ta ga kinyi hugging mijin ta in front of her and batasan alak'a ta dake ba then dama rigima take yi shiyasa ta tafi ni dai yanzu zan wuce," Hanfa ta ce "To Yaya ka kaimu wajen ta," tafiya ya fara ya ce "No idan Kun koma Rinaz ta Kai ku," daga haka ya wuce su Kuma suka nufi office d'in Ummi. Sabeeha kuwa tana komawa gida direct d'akin su ta wuce tana share hawaye tana shiga ta samu Sabreen Sameeha da Aysha da Kuma Dija waje ta samu ta zauna tare da saurin sai ta nutsuwar ta. Dija ta ce "Daga Ina haka Sabee?" Ajiyar zuciya ta sauke ta ce "munje hospital ne wajen Mama Habibi ba lafiya so munje an duba shi tare da Zainab," kallon mamaki Sabreen da Sameeha ke yi Mata jin yau ta kula Zainabu har ma sun fita tare basarwa ta yi ta ce "Ina Rinaz Habibty fa?" "Hmm mun Kira ta fa ta ce zata zo akwai wasu bak'i da take jira su zo may be basu zo bane shiyasa," Sabreen ta fad'a Sabeeha ta ce "Babe's lafiya ku ke kuwa wad'an nan kayan fa?" Dariya Aysha ta yi ta ce "Duk mun siyo su ne saboda mu fitar da anko," girgiza Kai Sabeeha ta yi ta kwanta abinta bacci ne ya kwashe ta. Lokacin da ta tashi ta tarar basa nan toilet ta fad'a ta yi wanka tare da alwala sannan ta shirya cikin pink d'in riga da siket na kanti tasa farar hula a kanta gashin gaban goshinta ya kwanta luf luf gwanin burgewa ta d'auki wayar ta ta nufi down stairs tun kafin ta sauka take jiyo hayaniyar su. Tana fara sauka duk suka juya suna kallon ta Sabreen Kalli su Hanfa da tun zuwan su da Rinaz suke tambayar amaryar Maleek ta ce "To ga amaryar Yaya MG can saukowa," da gudu Haneefa ta je ta rungume Sabeeha ta ce "Nice to meet you sweetheart," kallon ta Sabeeha ta yi ta ce "Nice to meet you too," sannan ta kalli Hanfa da ta tsaya tana kallon ta tabbas wannan ita ce na gansu a asibiti tare da wacce ta rungumi Ya maleek kenan wannan ce Sabeeha ta fad'a a zuciyar ta tana kallon Haneefa. Bata gama tunani ba Hanfa ta rungume ta ta ce "Gaskiya naji dad'in had'uwa dake sis hany Kinga wata kama a tsakanin su kamar mutum d'aya?" Haneefa ta ce "I see sis Hanfa I'm very surprised kamar ma ta b'aci," d'an murmushi Sabeeha ta yi sannan ta ce "Mu k'arasa," suka koma cikin falon suka zauna. Hanfa ta ce "Ya MG yace kinyi fushi muna baki hak'uri a madadin sa," murmushin yak'e ta yi ta ce "No bakomai," Haneefa ta ce "Ni sunana Haneefa wannan Hanfa mu yaran Aisa ne k'anwar Ummin Ya MG," jinjina kai Sabeeha ta yi a zuciyar ta kuwa ta ce na jinjinawa surutun ku. Rinaz ta ce "Sabeeha dear ki taya mu zab'a mana wannene ya dace da Kamu da Kuma dinner?" Kallon kayan Sabeeha ta yi sunyi matuk'ar kyau sai walwali suke yi daga gani kaya ne masu tsada materials ne d'aya pich color d'aya kuma dark green sai walwalin silver color d'in zaiba suke yi. Sabeeha ta ce "Pich d'in na kamu green Kuma na dinner duk da silver head ya yi?" Dija ta ce "That's my Sabee abinda nake fad'awa babes d'in nan kenan Kinga wannan milk d'in less d'in ranar dinner d'in su Ummi da suka had'a tare da Maman ya Umar then wannan dark blue material d'in kuma ranar d'aurin aure bayan munsa wannan atamfar a lokacin walima da yamma tunda already dama wannan shaddar da safe zamu sa lokacin d'aurin aure," tafi wajen ya d'auka jin tsarin Dija ya yi Sabeeha kuwa shiru ta yi tana jin ikon Allah anko wajen kala biyar sannan ko wanne d'aya a ciki ya haura 20k kallon Zainabu dake can gefe ta yi ta yi tsuro tausayi ta bata amma ta basar. Doctor ce ta yi sallama a falon suka amsa suna yi Mata sannu da zuwa Hanfa da Haneefa kuwa har da zuwa su rungume ta domin su haka suke sun saba suka gaishe ta ta amsa cikin fara'a sannan ta wuce bedroom d'in ta. Haka aka cigaba da gudanar da hidimar bikin 'yan uku kullum su Rinaz suna gidan su Sabeeha suna shiri Sabeeha kuwa fushi ta yi da Maleek ko wayar sa bata d'agawa hakan ya damu Maleek amma ya basar a zuciyarsa yana fad'in Zaki zo hannu ne yarinya saura k'iris. Ummi tare da Aisa mamar su Hanfa da momyn Umar da maman Salman ne suka shirya suka tafi Dubai Landon domin had'o lefen 'yan uku. Aikuwa lefe suka had'o nagani na fad'a lokacin da suka dawo suka samu gida cike da dangi da 'yan uwa haka ma gidan Doctor gidan a cike yake da K'awayen Doctor duk da ba babbar k'awar ta wato Ummi kasancewar itama tana can da nata bak'in sannan 'ya'yan Kawu Bashir ma sunzo da yaran su 'yammatan duk suna wajen 'yan uku. Ana saura kwana biyu a fara biki ranar Aisa da Umman Salman tare da wasu daga cikin dangin Ummi suka tafi kai lefen 'yan uku tarba mai kyau su Doctor suka yi musu a babban falon gidan akwatuna aka fara shigarwa cikin falon tun ana k'irgawa har aka dena domin yawan su akwatunan kala biyu ne maroon guda ashirin da hud'u haka ma pink d'in ashirin da hud'u abu sai Wanda ya gani ana haka masu Kawu lefen Sameeha ma suka isa da akwatunan su suma ashirin da hud'u su Kuma kalar coffee haba nan fa aka rasa Wanda za a gani domin kaya ne na gani na fad'a masu matuk'ar tsadar gaske ga sark'ok'in cikin akwatunan daga na gold saina diamond hakama agogunan ciki Kai Abu ba a cewa komai haka 'yan kai lefen suka tafi suna tambayar amare domin suna san ganin su sunji ance 'yan uku ne Doctor ke sanar musu ai suna Salon suka ce bakomai zasu had'u idan aka fara shagalin bikin haka suka tafi suna yaba halin karamci na Doctor. Haka ma su Doctor suke yaba dangin Ummi da su Umar da Kuma yaba kayan abinda basu saniba duka akwatunan 72 Ummi ce tayi musu da duk wani Abu da aka gani a ciki duk Ummi ce ta siya a cewar ta ai lefe ita ya kama domin zata aurar da yaranta wad'an da daga su bata da wasu wad'anda zata had'awa sai dai ita a kawo mata idan bikin Rinaz ya tashi sannan tana matuk'ar ji da yaran nata maza sannan tana son 'yan ukun ta domin 'ya'ya ne a wajen ta Dan haka dole ne ta had'a musu kaya na gani na fad'a domin su yan gata ne sannan kuma gasu surukan ta dan haka ba sisin su Maleek duk ita ta fitar da kud'in abu d'aya tasan Maleek ya yi shine ya bada car keys guda uku da Kuma sababbin wayoyi iPhone 12 pro max guda uku an saka a kowacce akwatu. Lokacin da su Doctor suka ga car keys mamaki ne ya cika su su gani suke yi abin Kuma yayi yawa har da motoci abinda basu sani ba shine motocin ma suna waje da su ake tafe. 'yan uku suna shiga gidan idanun su ya sauka akan motocin da suke ta kyalli suna sauka direct wajen motocin suka nufa Sabreen ta shafa farar ta ce "Wayyo Allah amma fa motar nan ta ware da tunanina Dan Allah kalli Sameeha dear," dariya Sabeeha ta yi ta ce "To da tayi kyan ai ba taki bace ni Kinga wannan maroon d'in ce tayi gabas da hankalina," dariya suka shek'e da ita Aysha ta ce "A lallai ne ai dama best color naki ne maroon," Sameeha ta ce "Nima ai ga best color na nan ta fad'a tana shafa bak'ar motar," Rinaz ta ce "Kunga kubar wannan abun mu shiga ciki," Hanfa ta ce "Gaskiya nabi zab'in ki anty," Haneefa kuwa ta kalli Sabeeha ta ce "Ni kuwa na dangwalawa zab'in ki sweetheart," Sabeeha ta ce "Nagode," Dariya Dija ta yi har da rik'e ciki ta ce "Na jinjinawa shashancin ku Wallahi especially you 'yan uku babes ya daga ganin motar mutane may be bak'i Mama ta yi su Sabeeha dear har da godiya," Dariya suka kwashe da ita suka shige falon. Suna shiga falon ya d'auki gud'a su Lantana ne gaba wajen rangad'a gud'a Doctor ce ta lek'o da waya a kunnen ta ta ce "Aminan Abba kuzo nan," d'akin suka nufa yayin da su Rinaz kayan lefen suka yi gabas da tunanin su sai kalla suke yi. Suna shiga lokacin Ummi ke cewa "Haba Aysha kayan sunyi yawa," daga can Ummi ta yi magana amma basa ji Mama ta ce "To shikenan sai anjima," ta katse wayar ta kalle su ta ce "Yanzu ba sai anjima ba maganin da na baku d'azu kuje ku shanye tun kafin ranku ya b'aci aina duba naga baku sha ba," tuni kowacce ta had'e rai sai kumbure kumbure suke yi suka juya zasu fita. Doctor ta ce "Baku jiba ga lefe can ankawo yanzu muka yi waya da Aysha ta sanar mun ke Sabreen maroon ne naki mayyar Maroon ke kuma Sabreen pink d'in ne naki Sameeha ke Kuma cofee d'in sannan haka ma motocin dake waje Aysha ta sanar mun kowacce da tata basai nayi muku bayani ba kowacce tasan tata domin kowacce tasan zab'in ta," ihu suka saki suka rungume Doctor suna murna. Doctor ta ce "Kai ni ku cikani Karki yar da ni saura kuma ku fita kuna wannan shashancin cikin mutane Wai ma dama kunsan za a sa muku car keys a lefe?" A tare suka girgiza kai Sabreen ta ce "Ni dai nasan lokacin da muke gidan Ummi mun tab'a fita da my one naga wata farar mota nace ta burgeni har ya tambaye ni inason farar mota ne nace eh," Sameeha ta ce "ni dai tambaya ta ya Umar ya yi Wai meyasa nafi cewa yayi kyau idan yasa bak'ak'en kaya shine nace masa ai shine best color d'ina black and coffee," jinjina kai Doctor ta yi ta kalli Sabeeha ta ce "kefa shugabar 'yan rigima?" Tura baki Sabeeha ta yi ta ce "To nidai bansani ba," doctor ta ce "To kuje," fita suka yi suna ji kamar su je a kalli lefen da su amma ba dama suka wuce zuwa d'akin su. Rinaz ce ta shiga d'akin ta ce "ga phones d'in ku ku rik'e a wajen ku saboda kar a fasa muku," cikin murna suka k'arbi wayoyin Sabreen ta ce "Rinaz Habibty ashe motors d'in wajen namu ne," Rinaz ta ce "Ai kune baku saniba amma Ina jin sanda Yaya ya yi yawa yace a kawo masa motoci guda uku ya fad'i colors d'in wayoyin Kuma yace duk farare" Sameeha ta ce "Allah ya saka masa da alkhairi," Sabreen ta ce "Wayyo dad'i Allah yabar mana ya MG ya saka masa da alkahiri ya biya masa buk'atun sa," suka amsa da "Ameen," A b'angaren Maleek yasha godiya wajen Fauwaz da Umar sannan suka had'u suka yiwa Ummi godiya. Da daddare su Sabeeha na kwance a d'akin su ta mik'e Sabreen ta ce "Dear sai Ina kuma?" Sabeeha ta ce "Ina zuwa," ta zira hijab d'inta ta fice. Direct part d'in su Lantana ta wuce da sallama ta shiga falon Zainabu dake kallo ta amsa sallamar tana kallon Sabeeha domin bata gane wacece a cikin su ba tab'e baki Sabeeha ta yi ta ce "Ke wannan kallon fa?" Take Zainabu ta gane Sabeeha ce saboda ita ce take ce ke. Ta ce "Barka da dare anty," murmushi Sabeeha ta yi ta ce "Yawwa Zainab dama magana nazo muyi dake," ta ce "To anty zauna mana," zama Sabeeha ta yi gefen ta ta ce "Zainab," ta amsa "Na'am," Sabeeha ta ce "Kina son Sadam?" Kallon ta Zainabu ta yi ta ce "Amm...," D'aga mata hannu ta yi ta ce "Just answer my question kina son Sadam?" A hankali Zainabu ta ce "Eh anty," jinjina kai Sabeeha ta yi ta ce "Ya matsayin auren ku yake?" "Cewa tayi na tafi gida," kallon ta Sabeeha ta yi kamar mai yin nazari ta ce "Kina nufin ba sakin ki yayi ba," gyad'a kai Zainabu ta yi. Ajiyar zuciya Sabeeha ta yi ta ce "To dama ranar nan da ki ka ganmu da my ya yi mun maganar ki sai nake bashi labari shine yace zai yi wani Abu akai Kinga dai ni yanzu aure zanyi Kuma akwai shirin da muke yi ni da shi domin gyara rayuwar ki amma fa sai kinyi hak'uri kin Kuma kawar da kanki da Kuma soyayyar da kike wa Sadam Kinga aike kina son shi sab'anin shi da auren ki kawai ya yi ba don Yana sonki ba sai dan saboda anbi ta wata hanyar Zainab zaman ki haka bai kamata ba shiyasa nake so mu shirya plan d'in Sadam zai so ki fiye da yadda ki ke son sa k koma d'akin ki ko dan Habibi domin yanzu ko aure ki ka sake yi babu lallai ki samu Wanda zai kula da Habibi sama da mahaifin sa amma kamar yadda na fad'a Miki sai fa kin cire soyayyar da kike masa a lokacin ungo wannan wayar na baki ita da ita zamu dinga yin magana dake," karb'a Zainabu ta yi tana hawayen farin ciki ta ce "Nagode anty Allah ya saka da alkhairi," Sabeeha ta ce "Babu komai Zainab ai ke kanwata ce duk abinda nayi miki ban fad'i ba ko lokacin da ku ka dawo gidan nan bawai na tsane ki bane har ga zuciya ta tun lokacin na yafe miki abu d'aya ne yasa nake yi miki haka Zainab saboda yadda ki ke gatsa sunan mahaifiyar ki wanda hakan bai dace ba mu kina Kiran mu da aunty amma Kuma mahaifiyar ki ki gatsa sunan ta karfa ki manta itace silar zuwan ki duniya ko kin girmama ta baki biyata ba ke fa yanzu uwa ce baza ki so Habibi ya tashi yana gatsa sunan ki ba Zainab karki zama d'aya daga cikin yara marasa d'a'a da tarbiyya ki zama 'ya ta gari wacce iyayen ta zasu yi alfahari da ita kinji?" A hankali tana hawaye ta ce "To anty insha Allah na dena," Sabeeha ta ce "Yawwa Nagode da kika fahimce ni Ina Habibi ko ya yi bacci ne?" Ta ce "Eh ya yi bacci," Lantana da ke jiyo su a d'aki ta fito ta zauna Lantana ta ce "Barka da fitowa Umma," cikin mamaki da jin dad'i ta ce "Yawwa," gaishe ta Sabeeha ta yi ta amsa cikin fara'a ta ce "mun gode Sabeeha Allah ya biya ki da gidan aljanna tabbas ku na daban ne kuna kyakkyawar zuciya Kuma wankakkiya fes saboda duk abinda muka yi muku a baya baku d'auke shi a komai ba Kun rungume mu baku kyamace mu ba mungode," ta fad'a tana share hawaye Sabeeha ta ce "Bakomai inna ai Zainab kanwata ce," Kawu dake k'ofar shigowa tun farkon shigar Sabeeha tas yaji maganar da suka tattauna da Zainabu ya shiga da Sallama amsawa suka yi ya samu waje ya zauna Sabeeha ta gaishe shi ya amsa cikin fara'a ya ce "Yarinya ta Allah yayi miki albarka yasa aljanna makomar ki tabbas 'yan uku ku na daban ne a baya har karuwai na Kira ku nayi Shirin yi muku auren dole sannan bayan haka Kuma na kashe miki naki auren amma yau kece ke son 'yata ta yi zaman farin ciki a gidan auren ta sannan ki ke nuna mata hanyar da zata sada ta da aljanna Allah ya raba ki da naki iyayen lafiya ya yi miki albarka," ta ce "Ameen Kawu," tashi Kawu ya yi ya nufi d'akin sa yana share hawaye da babbar rigar sa. Tashi Sabeeha ta yi ta ce "Inna na tafi sai da safe," daga haka ta fice. Tana shiga falon su Sameeha ta rungume ta tana murna ta ce "Dear zo kiga kayan da Abba ya siya mana na fitar biki," janta Sameeha ta yi har tsakiyar falon inda kayan suke akwatuna ne guda hud'u manya manya kusa da Sabreen ta zauna ta d'auki wani less maroon mai adon flowers silver color ta ce "Wow Abba angode Allah ya saka da alkhairi ya k'ara bud'i," ya ce "Ameen aminiya," Sabreen ta ce "Abba dama haka ka iya zab'e?" Cikin farin ciki Abba ya ce "Ai doctor ce ta tayani zab'ar muku su domin Wad'an da ke mun oder nasa suka nemo mun su domin ku kad'ai 'yan ukuna gashi nan kowacce d'aya d'ayar Kuma ta Doctor," godiya suka dinga yi domin kayan kana ganin su kasan kud'i mai suna kud'i akasa aka siya lesses ne masu kyau da atamfofi da takalma masu tsadar gaske da sark'ok'i na gaske ga materials abin ba a cewa komai. Doctor ta ce "Abban 'yan uku mu k'arasa waccan falon ka ga lefen kuma ku taso domin nasan ko ban gayyace ku ba sai kunzo," tashi suka yi suka je domin ganin kayan yayinda bak'i ke can b'angaren bak'i saboda Abba ya sake da iyalan sa abinku da 'yan boko wayayyu. Bubbud'ewa suke suna santin kayan. Wani takalmi Sabreen ta gwada ta mik'e tana kwatanta yadda zata yi tafiya idan tasa dariya sosai Abba ke yi shi da Doctor haka suka dinga sa iyayen nasu dariya Abba kansa yasan zasu yi missing yaran nasu shi da Doctor. Gajiya suka yi da ganin kayan suka tashi ba dan sun gama gani ba sai dan gajiyar da suka yi dan ko rabin rabi basu yi ba haka suka tafi domin su kwanta. ana i gobe Kamu Daddy ya Kira Maleek falon sa gaishe shi Maleek ya yi ya amsa sannan ya ce "Son dama dalilin Kiran ka magana ce akan Nasreen d'azu muka yi magana da Yaya domin yanzu ma ta koma d'akin ta," Maleek ya ce "To Daddy," Daddy ya ce "Yawwa Son Allah ya yi maka albarka," ya amsa da "Ameen," sannan yabar falon. 'yan uku ne kwance a d'akin su cikin kayan baccin su iri d'aya Sameeha na amsa waya Sabreen na chart Sabeeha kuwa na kallo a laptop sun sha kyau ba k'arya k'afa da hannun su ya d'au kyau da jan lalle da bak'in da akayi musu kansu yasha gyara d'an gaske fatar su sai fitar da shek'i take yi juyi Sabeeha ta yi tayi k'wafa Sabreen ta ce "Dear lafiya kuwa?" K'aramun tsaki ta ja ta ce "Sabreen bansan me Ya Maleek ke nufi dani ba wallahi," "Me ya yi miki?" Sabreen ta tambaya furzar da numfashi Sabeeha ta yi ta ce "Ranar da muka je fa hospital ni da Zainab ne muka ganshi,' nan ta basu labarin abinda ya faru kaff Sameeha da ta gama waya tana sauraron ta ta ce "Amma dear ai laifin ki ne meyasa zaki k'i picking calls d'insa bayan kin gano relationship d'insa dasu Hanfa?" Tab'e baki Sabeeha ta yi ta ce "I don't know am only know that Ina matuk'ar kishin sa sannan shi kuma sai bai sake Kira ba," Sabreen ta ce "Ki kwantar da hankalin ki sis ai saura k'iris wai maye ya yi amarya," dariya Sameeha ta yi ta ce "Aikam dai," haka dai suka dinga fira abinsu. [10/25, 8:48 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️ RUBUTAWA DAGA HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ) SADAUKARWA GA MY DAUGHTER SABEEHA BILKISU Z.YA'U (🅱️K) AISHA MAGAJI DABO (AMA) Page 24 Washe gari suka tashi da shirin yin Kamu hidima ake yi sosai a gidajen guda biyu hakan ne yasa 'yan uku suka had'a abubuwan da zasu yi amfani da shi suka tafi gidan Auntyn Dija. Fauwaz ne ya shiga falon Ummi tare da Ahmad Ashraf da Abdul_alim sai Usman duk 'ya'yan yayyen Ummi ne maza sa'annin Fauwaz nan dangi suka dinga ga ango ga ango washe baki kawai Fauwaz ke yi abinsa. Hanfa ce gaban Aisa k'anwar Ummi wato mahaifiyar su tana buga k'afa cikin shagwab'a ta ce "Please Momcy munsan hanya fa ko sis hany?" Haneefa dake zaune gefen Momcy ta ce "Eh Momcy mun iya fa ta fad'a kamar zata yi kuka," Ashraf dake bayan ta kuma shi zai aure ta cak ya d'aga ta ya ajiye ta gefe ya ce "sweet momma karki yadda da wannan yarinyar wai ma akan me ki ke rigimar?" Tura baki Hanfa ta yi tana hararar sa. Haneefa kuwa wajen Fauwaz ta yi ta rik'e hannunsa ta ce "Please bro kasa baki Momcy ta bamu key d'in motar munfa san hanya," "Ke kuwa Hany Ina zaku kuma?" Fauwaz ya fad'a yana kallon Momcy ta ce "To gidan su amare zamu fa," Momcy ta ce "To kwata_kwata yaushe suka san gidan da zasu je su kad'ai?" Alim ya ce "Kai babe's ba inda zaku Sweet momma karki basu," Haneefa ta ce "Hmm zaka sani wlh," d'aga kafad'a Alim ya yi ya ce "Indai ba fasa aurena Zaki yi ba ai shikenan gashi bama wannan ba My hany nasan ku fa bakwa driving a hankali," Fauwaz ya ce "Shikenan amma ai su my heart basa gidan Mama suna gidan su Dija bari nasa Alasan ya kai ku," Jan hannunsa Hanfa ta yi ta ce "To muje kuma babu ni ba wani ehe," ta fad'a tana kallon Ashraf Haneefa ma ta bisu Alim ya ce "My fav inzo na raka ki?" Harara Hany ta zabga masa ta ce "Baza ni da kai ba kuma baram-baram," daga haka suka fice. "Wallahi MG wani mahaukacin farin ciki nake ji a zuciyata Wai zan mallaki Sameeha," "Allah koh?" Cewar MG dake juya wayar sa yana so ya Kira Sabeeha ga Kuma mugun son ganinta da yake yi. Umar ya ce "Wallahi fa gashi yau wajen kwana biyu bangan ta ba saboda suna busy amma fa yau zan ganta domin na sanarwa da Mummy sai dai a kama mu dukan mu," tab'e baki MG ya yi ya ce "Dama ana kama maza ne?" "Oho idan ma ba ayi sai a fara ta kanmu," dariya falon ya d'auka Arif yayan Alim ya ce "Gaskiya ne babban ango," Umar ya kalli Aiman yayan Ashraf ya ce "Aiman ya kace," cikin dariya Aiman ya ce "Banga laifin ka ba kuwa," D'ayan mai Suna Muhseen yayan su Hanfa Wanda magana ma bata dame shi ba shiru ya yi yana jin su baice komai ba Maleek ya kalli Umar ya ce "Mu kam baza ka ja mana raini ba," suka kwashe da dariya haka suka dinga fira abinsu. B'angaren 'yan uku kuwa duk zaune suke a wani falo suna fira wayar Sabreen tayi k'ara tana d'agawa ta ce "Angon saura k'iris," daga can Fauwaz ya ce "Haka yake saura k'iris ki zama tawa su Hanfa sunzo nan kuwa?" Ta ce "No basu K'araso ba," ya ce "Aha to suna hanya," "Ok to sai sunzo," Sabreen ta fad'a tare da kashe wayar. Da yamma aka fara shirin zuwa wajen Kamu make up sosai su Dija suka d'auka sannan suka shirya cikin ankon su sunyi kyau ba k'arya zaune suke a falon suna jiran fitowar 'yan uku domin sun dad'e a cikin d'aki make overs d'in da Doctor ta d'auko suna gyara su. Sun dad'e sosai sannan aka bud'e k'ofar d'akin wani k'amshi ne ya hure falon gaba d'aya Wayyo kuzo ku ga kyau iya kyau wajen 'Yan uku kamar ka sace su ka gudu sunyi kyau sosai cikin shigar dark blue d'in dogayen rigunan code net da suka yi fuskar su tasha make up sosai Nan fa aka fara ruwan hotuna su Dija sai yaba kyan da suka yi suke. Da haka suka fita suka shiga motocin da aka kawo musu domin zuwa kamu. Hall d'in da aka kama ya yi kyau iya kyau yasha decoration ko Ina ka kalla kaskon turaren wuta ne da aka zuba turaren ciki gurin sai tashin k'amshi yake yi ga 'yan uwa duk sun hallara ba b'ata lokaci aka fara gudanar da shagali. A b'angaren su MG kuwa hana Umar zuwa yayi dan dole ya hak'ura. Haka aka gudanar da Kamu Wanda ya k'ayatar aka tashi bayan daga nan kowa ya koma gida abinsa. Washe gari da daddare kuwa aka fara shirin party k'awayen amarya sunyi kyau cikin ankon su dark green Mai adon silver hakama head d'in da suka d'aura silver color amare kuwa wedding gown suka sa farare sunyi kyau sosai ba k'arya sai ka rantse mutum d'aya ce saboda tsanin kama. Hotuna suke yi sosai wayar Rinaz ta fara ringing d'agawa ta yi daga can Fauwaz ya ce "Beb ku fito fa muna waje time na tafiya," ta ce "Ok," kallon su Sabeeha ta yi ta ce "Dear muje suna jira," dukan su suka yi hanyar fita yayinda amare ke tafiya a hankali a haka suka fita har compound d'in gidan nan suka ga motoci reras. Fauwaz ne ya fito daga bayan wata bak'ar mota yasha kyau sosai cikin farar shadda sai k'amshi yake zabgawa ya kalli Rinaz ya ce "Matar Yaya ga motor d'in da zata shiga can," ya fad'a nuna wata farar Bugatti Hanfa ce ta rik'e hannun Sabeeha har zuwa wajen motar ta bud'e mata back seat a hankali ta shiga motar wani k'amshi ta ji ya daki hancin ta tabbas tasan shine dan haka bata waiga inda yake ba ma ta jingina da jikin kujerar ta lumshe idanunta. Maleek kam a hankali ya saki wata ajiyar zuciya tare da gyara zaman sa yana k'arewa fuskar ta kallo yana jin wani farin ciki mara misaltuwa a zuciyar sa a jikin ta ta ji kallon ta ake yi lokaci guda ta bud'e idanunta suka had'a ido murgud'a masa baki ta yi tare da d'auke idanunta ta k'ara matsawa can jikin murfin motar. Murmushi yayi mai sauti wanda yasa dimples d'insa suka lotsa jin sautin murmushin sa ne yasa ta kalli b'angaren da yake sai da gabanta ya fad'i saboda ganin tsanin kyan da ya yi sanye yake cikin farar gizner shadda d'inkin riga da wando da babbar riga ya matuk'ar yin kyau kamar kwana biyun da ta yi bata ganshi ba k'ara masa kyau akayi. Ganin shima ita yake kallo yasa ta d'auke idanunta a kansa bawai Dan ta gaji da kallon sa ba sai dan fushin da take yi da shi cikin burgewa Maleek ke kallon babyn tasa domin shi duk abinda zata yi burge shi take yi. Da haka suka k'arasa hall d'in da za a gudanar da party da tunda suka shiga compound d'in wajen suke jiyo kid'a na tashi a jere motocin suka yi parking. Firfitowa su Dija suka yi Sabeeha na tsaka da danna wayar ta aka bud'e k'ofar side d'in ta a hankali ta d'aga kanta ta kalli Wanda ya bud'e motar Aysha ce ta ce "Dear ku fito an K'araso," bata amsa ba ta d'auki pose d'in ta dake gefen ta sannan a hankali ta zira k'afar ta waje ta fita. Lokacin har Umar ya fito rik'e da hannun Sameeha haka ma Fauwaz yana rik'e da hannun Sabreen. Zagawa b'angaren da take Maleek ya yi ya tsaya sannan a hankali yakai lallausan hannunsa ya rik'o nata da sauri ta rintse idanunta saboda wani yarr da ta ji yayin da a cikin hall d'in da yake cike da 'yan uwa da abokai da k'awaye suka fara jiyo MC na sanar da shigowar angwaye da amare. A tsakiya akasa su sannan suka fara takawa a hankali zuwa cikin hall d'in yayinda masu d'aukar hoto ke yi masu video nayi har 'yan gidan televisions duk sun hallaci wajen domin ansan da bikin tun ana sati bikin ake sanarwa a kafafen yad'a labarai da jaridu. A haka suka shiga cikin hall d'in da ya gaji da had'uwa domin decoration yasha cikin farin yadi da dark green gurin sai bada kalolin fitilu yake yi duk inda ka kalla sai kyalli yake yi yayinda wata had'add'iyar wak'a ke tashi a wajen Mai suna lamba ta destiny boy tuni Dija Aysha Hanfa da Hany sun fara taka rawa yayinda su Alim suka rufe su da lik'i suma suna taka tasu rawar. Sabreen kuwa mantawa ta yi da ita amarya ce ta fara taka tata rawar yayin da Fauwaz ke ta yata wajen ihu ya d'auka lik'i kuwa yinsa ake yi kamar ba a son dukiyar Maleek kuwa hayaniyar har ta fara damunsa gashi an rufe su sai lik'i ake musu a hankali ya janye Sabeeha suka je suka zauna. Su Sabreen kuwa sai da suka gama tashewa sannan suka je suka zauna Sameeha ma bata yi rawa ba sai Umar da shima sai da ya taka rawar farin ciki sannan suka zauna. Ba b'ata lokaci aka fara gudanar da party amare tare da angwayen su har sai da suka gaji da fita tsakiyar fili suka dena fita yayin da Hanfa da Ashraf Hany da Alim banda rawa ba abinda suke yi ana yi musu video lik'i kuwa sun sha shi kamar ba gobe Dija da Aysha ma ba a barsu baya ba yayin da idanun Arif ke kan Dija domin shi har ga Allah sonta yake yi haka aka gama tashewa aka tashi yayinda DJ yaji dad'in bikin domin kud'in da ya samu yafi k'arfin tunanin sa domin Maleek har dollar ya lik'awa Sabeeha duk da ko motsa jikin ta bata yi ba da sunan rawa. Amma duk da haka a gajiye ta fito daga wajen ga wani wahalallen bacci da take ji jan k'arfar ta kawai take yi Maleek da kansa ya bud'e mata motar ta shiga ya rufe sannan shima ya zagaya ya shiga. Tunda ya shiga motar idanun sa suke a kanta kallo d'aya ta yi masa ta d'auke kanta ita a dole har lokacin bata sauko daga fushin ba shi abun nata ma ya koma bashi dariya Aikuwa kallon ta ya yi ya fara dariya ya juyar da kansa. Sheshshek'ar kukan da ya ji ne yasa ya yi saurin kallon b'angaren ta ya ga dagaske kukan take yi sai goge fuskar ta take yi da bayan hannunta a hankali ya k'ara matsawa kusa da ita murya k'asa k'asa ya ce "Mene?" Kallon sa ta yi ta k'ara volume d'in kukan nata. A hankali ya Kai hannun sa ya ja ta zuwa jikin ta ya rungume ta ya ce "Is okay fad'a mun mene?" Luf ta yi a jikin sa tana hawaye ta ce "Ba kai bane," murmushi ya yi ya ce "Ni ne koh me nayi to?" A hankali ta d'an daki k'irjin sa ta ce "To ba kaine ba ka manta dani ba ka dena kirana ba," ya ce "Ayyah sorry baby bazan k'ara ba kinji?" Noding kanta ta yi domin yasan idan ba hakan ya yi Mata ba ta dinga yi masa rigima kenan. A haka suka k'arasa gidan Auntyn Dija ana tsayar da motocin mutanen dake ciki motocin suka fita Fauwaz ne ya bud'e b'angaren da Maleek ke zaune ya ce "Yaya mun k'araso," gyad'a kai Maleek ya yi sannan ya Mai da kallon sa kan Sabeeha da tuntuni ta yi bacci a jikin sa saboda gajiyar da ta yi. A hankali ya zame jikin sa daga nata ya cire babbar rigar sa da dama ta ishe shi ya mik'awa Fauwaz sannan ya fita daga motar su Dija da su Hanfa tare da su Alim su Arif da Umar duk kowa na wajen. A hankali ya d'auke ta cak ya fito da ita daga motar kamar ya d'auki 'yar baby kallo ne ya koma kansu Sabreen kuwa jikin ta har yana rawa wajen d'aukar su a hoto har tana samun mata ya. Ganin haka Dija ta bud'e masa k'ofar baya tana gaba yana binta a baya har d'akin ta a hankali ya kwantar da ita a kan makeken gadon yana k'arewar kyakkyawar fuskar ta kallo ya kalli Dija ya ce "Ki tashe ta ta canja wannan rigar," ta ce "To," daga haka ya fice daga d'akin. Yana fita compound d'in gidan ya bud'e mota ya shiga tare da Muhseen da Kuma Arif sai Umar suka tafi. Su Sabreen ma bayan sun gama firar su suka shiga cikin gidan a gajiye suka d'akin suka samu Sabeeha sai baccin ta take yi cikin kwanciyar hankali. Dija ce ta fara tashin ta a hankali ta bud'e idanunta ganin ta kwance a gado yasa ta saurin tashi zaune tana kallon su d'aya bayan d'aya dariya Sabreen ta yi ta ce "Dear yadai?" "Wane ya kawoni nan Kuma?" Sameeha ta ce "Mijin da zai aure ki mana kunga yadda ku ka yi kyau kuwa da ya d'auke ki," Sabreen ta ce "Bari ki gani," ta fad'a tana nuna mata hotunan da ta yi musu kuma sunyi kyau bata ce komai ba ta mik'e tare da cire rigar jikin ta ta d'aura towel ta shige toilet ta yi wanka tare da alwala. Maleek kuwa direct part d'in sa suka nufa suna shiga ya zauna akan kujera tare da d'aukar ruwan dake kan center table ya bud'e yasha ya ajiye Arif ya kalli Umar ya ce "Umar yau fa munga love," Umar ya ce "Wallahi kuwa MG irin wannan caring haka?" Tab'e baki Maleek ya yi ya mik'e ya nufi stairs yana cewa "Sa ido sana'ar banza," su kuma sai dariya suke yi masa. Washe gari ya kama Dinner d'in da Ummi tare da Doctor suka had'a domin taya yaran nasu murna hidima ake yi sosai a gidajen mummyn Umar ma ba a barta a baya ba wajen yi hidimar bikin d'an nata tilo. Shiri ake yi sosai domin amare ba k'aramin kyau suka sha ba cikin maroon d'in lace Wanda Abba ya yi musu Mai adon silver takalmin su tare da pose d'insu duk silver color mai kyalli haka ma net d'in da aka rufe musu fuska shima silver kyan da suka yi bana wasa bane sai k'amshi suke yi. Yayinda k'awayen su suka shirya cikin milk d'in lace da coffee head sunyi kyau har da Zainabu wacce itama aka yi Mata kwalliya kamar ba ita ba. Motoci ne reras a k'ofar gidan antyn Dija sai wacce ka zab'a zaka shiga motocin suka shiga sai hall d'in da za a gudanar da Dinner d'in Wanda yafi na jiya tsaruwa. Suna yin parking Ummi da kanta tare da Maman Umar su suka fito tarar su Sunsha kyau cikin wani red d'in code net mai followers yellow duk da ba wata kwalliya ce a fuskar su ba amma sunyi kyau har k'asa 'yan uku suka tsugunna suka gaida surukan nasu suka amsa cikin fara'a tare da rungume 'yan uku daidai lokacin motocin su Maleek na shiga wajen Ummi kuwa hannayen 'yan uku suka ja zuwa cikin hall d'in da ya gaji da had'uwa yasha decoration ba k'arya ko Ina sai walwali yake yi da kyalli fitilu kaloli na kawowa a wajen hatta wajen da suke takawa wasu fitilu suke kawowa dangi kowa yasha anko cikin code net coffee da milk head ga table table Nan na zama a can gefe kuma wajen zaman couples d'in ne da ya gaji da had'uwa can kuwa gurin da aka tanadi abinci ne da masu zubawa sai abinda ka zab'a domin girki aka yi kala kala da farfesu kala kala ga gashashshen naman rago dana sa. 'yan uku kuwa sai baza idanu suke domin ganin ta inda zasu hango Doctor can suka hango ta zaune a wajen wasu kujeru uku gurin an k'awata shi sosai da alama gurin su ne ita da maman Umar da Kuma Ummi direct wajen ta suka nufa da sauri. Doctor da batasan da zuwan su ba unexpected ta ji sunyi hugging d'in ta Suna murnar ganin ta murmushi Doctor ta yi tare da ajiye wayar ta kan table ta kalle su ta ce "Ku nutsu mana a gaban mutane ku ke fa," tura baki Sabeeha ta yi ta ce "Mama fa duk murnar ganin ki ce," ta yi dariya ta ce "To naji shugabar rigimammu," dariya su Sameeha suka sa yayin da su Maleek da suka shiga wajen suke kallon su cikin burgewa haka ma mutanen wajen ba k'aramun burge su 'yan uku da mahaifiyar su suka yi ba. K'arasawa su Fauwaz suka yi yasha kyau cikin farar Shadda yayinda su Ashraf tare da abokan Maleek suka sa milk d'in Shadda mai aikin coffee Maleek tare da Umar suma farar Shadda suka sa sunyi kyau ba k'arya sai k'amshi ke tashi. Ummi ce ta je ta ja 'yan uku zuwa wajen da aka tana da domin su ta zaunar da su kallon ta Fauwaz ya yi ya ce "Ummi naga kin had'a su su ukun?" Hararar sa Ummi ta yi ta nuna musu d'an gefen da 'yan uku suke ta ce ga wajen zaman ku can tura baki Fauwaz ya yi ya nufi wajen ya zauna haka ma Maleek da Umar suka je suka zauna kusa da Fauwaz da sai kumbure-kumbure yake kallo d'aya Maleek ya yi masa ya shiga hankalin sa. Bayan kowa ya zauna Ummi ta nufi kan step tare da k'arbar microphone daga hannun MC ta ce "Firstly i thank almighty Allah countlessly for the special gift that he has given to me it's today my son's became the groom's so I'm very happy and I congratulate them to have a beautifuls bride's so I pray Almighty Allah to bless them with fine fine babies," tafi wajen ya d'auka yayin da Sabreen da Fauwaz suka had'a baki wajen cewa "Ameen," Ummi ta cigaba da cewa "I welcome everybody here and thank for your love and caring thank you once again," tafi wajen ya d'auka. Haka ma Doctor da maman Umar suka yi nasu gabatarwar cikin harshen turanci daga nan Ummi ta kalli gold watch d'in hannun ta ta kalli hanfa da Hanifa ta ce "it's your turn time na tafiya," tashi Hanfa da Hany suka yi suka hau kan stage d'in karb'ar microphone d'in Hanfa ta yi ta d'anyi gyaran murya ta ce "Akwai wata game da muka shirya sannan a yanzu zamu gudanar da ita a yanzu muke so ko wanne ango a ciki zai tashi ya k'arasa gaban amare sannan ko wannen su zai nuna mana amaryar sa kamar yadda ku ke gani amaren mu they're identical triplets saboda haka we shall see what happens," tafi wajen ya d'auka sannan Hanfa ta ce "Let us start with Ya MG Bismillah Ya MG," d'aga Kai Maleek ya yi ya kalli Hanfa ta ce "Yes you sweetheart," ajiye wayar ya yi a kan table d'in dake gaban sa ya mik'e cikin takun k'asai ta ya k'arasa gaban hanfa ya tsaya. Kallon mutanen wajen ta yi sannan ta ce "Like we see zamu fara da Ya MG Bari na raka shi sannan Kuma kuna gani wazai zab'o mana," ta fad'a tana jan hannun sa har zuwa gaban 'yan uku da yake ganin kamar ranar kamar su tafi zama d'aya. Kallon su ya fara yi d'aya bayan d'aya ya fara takan ta farko sannan ya kalli ta tsakiya ya kalli ta d'aya gefen murmushin gefen Baki ya yi Wanda ya bayyana dimples d'insa sannan a hankali yakai hannunsa ya rik'o hannun ta tsakiya. Dariya Hanfa ta yi ta ce "Even me Hanfa bansan wacece ba sai dai bari muji daga bakin amaryar mu shin meye sunan ta," ta fad'a tana Kai microphone d'in saitin bakin ta. A hankali cikin sassanyar muryar ta ta ce "Sabeeha," Ihu wajen ya d'auka ana tafi juyawa Sabeeha ta yi ta kalle shi ta sakar masa murmushi nan fa aka fara ruwan yi musu hotuna dama already 'yan gidan televisions suna nan Hanfa ta ce "Bari muji me ya MG zaice da amaryar sa Wanda ya shafi abinda ke cikin zuciyar sa," ta fad'a tana mik'a masa abun maganar karb'a ya yi sannan ya fuskanci Sabeeha da ta yi k'asa da kanta a hankali ya ce "Look at me baby," a hankali ta d'aga Kai ta kalle shi idanunsu ya had'e da juna murmushin ya sakar mata Wanda ya k'ara masa kyau sannan ya ce "U already knew that I love you and I can't stop telling you that from now up to rest of my life in the morning evening or night in the rain or sun I will tell you that I love you I really love you with every breath i take and i can't leave you forever you know my heart beats for you only you,your love is all i will ever need," tafi wajen ya d'auka da ihun samarin wajen Sabeeha kuwa batasan sanda murmushi ya kufce mata ba abin maganar ya kai bakin ta cikin sassanyar murya ta ce "Me too my heart love you and it will never stop loving you,i love you with all my heart," ai Maleek baisan sanda ya rungume ta ba ya sakar mata kiss a forehead d'inta ihu wajen ya d'auka ana tafi. Hanfa ta ce "Wow this couple so amazing," Jan hannunta ya yi zuwa gefe suka zauna. Hanfa ta ce "kunga dai Ya MG ya tsallake so bari mu ga shin bro Fauwaz zai wuce ko a'a taso bro," Haneefa ce ta rik'e hannun sa Hanfa na binsu a baya har gaban Sameeha da Sabreen dake zaune yayin da mutanen wajen kowa ke baza idanu ya ga yadda abun zai kasance. Dam gaban Fauwaz ya fad'i saboda shi gaskiya idan har suna tare baya iya gane Sabreen d'an dafe Kai ya yi tare da rik'e k'ugu yana k'are musu kallo hannu ya kai a hankali zai rik'o hannun Sameeha Sabreen ta kanne masa ido d'aya ya yi saurin rik'o hannunta duk abinda ya faru a wajen mutanen Aikuwa waje ya kaure da ihu Hanfa ta ce "Tofah kunga bro Fauwaz ya kasa gane amaryar sa anya a kaita gidan sa kuwa?" Dungure mata kai Fauwaz ya yi ya ce "Sai ki hana a kaita 'yar rainin wayo kawai," ya fad'a tare da k'wace microphone d'in hannun ta ya fara fallasawa Sabreen sirrin zuciyar sa akan son da yake mata itama haka ana ta yi musu tafi sannan suka wuce suka zauna. Dariya Hanfa ta yi sannan ta waiga sai kawai ta ga Umar rik'e da hannun Sameeha zare ido ta yi ta ce "Ya Umar to ai ba a yi game d'in ba kawai ta zauna sannan su zama su Uku sannan ka zab'o sarauniyar taka," harara Umar ya aika mata ya ce "Ai ko su goma suke kama sai na gano ta a cikin su," ya fad'a Yana kallon Sameeha da ta yi k'asa da kanta tana murmushi. Hanfa ta ce "To kamar yadda ku ke gani Ya Fauwaz da Ya Umar wayo suka yi mana saboda haka basu yi nasara ba especially ya Fauwaz saboda haka ya MG shi ke da nasara," ta fad'a tana mik'awa Umar abun maganar ya yi yana hararar ta. Shima bai b'ata lokaci ba ya fara kwararawa Sameeha kalamai masu sanyaya zuciya haka itama ta mayar masa Nan aka dinga yi musu hotuna sannan suka zauna. Hanfa ce ta ce "Congratulations once again ya MG zaka k'arbi gift d'in ka daga Ummi immediately after dinner and this the end of this game," tana fad'in haka ta mik'wa Haneefa abun maganar. K'arba Hany ta yi ta ce "Da farko Ina so naga Ya Alim a nan," Alim dake can gefe ya taso yasha kyau cikin milk d'in Shadda kyakkyawa ne fari domin Mahaifin sa ya yi domin duk gidan su Ummi farare ne so dukan su yaran haka suke farare kyawawa a hankali ya k'arasa gaban Hany ya tsaya tare da kanne mata ido d'aya abun magana shima aka bashi. "Hany ta ce yanzu zamu gabatar da drama just for our happiness," kallon Alim ta yi ta ce "Start," tana fad'in haka ta juya masa baya ta fara tafiya cikin yanga tare da had'e fuska tafiya take yi kamar zata k'arye saboda rangwad'a gashi ta rik'e k'asan doguwar rigar ankon jikin ta dake Jan k'asa tana taku a hankali. Yayinda Alim ke binta a baya cikin sauri ya ce "Exuse me," banza Hany ta yi masa hakan ne yasa ya yi saurin shan gaban ta cak Hany ta tsaya tare da yi masa kallon up and down ta ja tsaki tare da kawar da fuskar ta gefe bata ce komai ba. Murmushi Alim ya yi ya ce "Gaskiya harara ba k'aramun kyau ta yi Miki ba baby," d'an zare ido ta yi tana mamakin abinda ya fad'a sai dai nan ma bata ce komai ba. Numfasawa ya yi tare da gyara tsayuwar sa ya ce "Komai ki ka yi kyau yake miki na tabbata samun kyakkyawar mace zabgegiya mai kyan tafiya irin ki abune mai wuya a gaskiya daga kallon farko da nayi miki naji kin yi gabas da tunanina please accept my love baby," Wata uwar harara ta watsa masa ta rik'e k'ugu ta ce "Ni Kuma bana tunanin kana d'aya daga cikin mazan dake burgeni so find your way out of my own way," tana fad'in haka ta cigaba da tafiya abinta. Tagumi Alim ya zabga tagumi sannan ya Kuma binta ya ce "yammata a gaskiya Ina sonki,son ki shine abu mafi k'arfi daka iya juya gami da sarrafa gangar jikina ya zuwa aikata duk wani abu daya danganci so da k'auna," shiru ya yi sannan ya dawo gaban ta yana kallon cikin idanunta ya ce "Ba kowane ya cancanta ya zamo sarki ba sai jinin sarauta Kuma mai ilimi gami da natsuwa hak'ika kin cancanci zama gimbiya Kuma sarauniya a cikin zuciyata," sakin ido Hany ta yi tana sauraron kalaman sa wad'an da lokaci guda suka ja ra ayin ta ta saki murmushi ta ce "Amma meyasa kake sona bayan baka sanni ba you don't know even my name?" D'an murmushi ya yi ya ce "Abinda ya ja hankali na a gare ki nutsuwar ki hankalin ki da Kuma kyawawan halayen ki kina da qualities d'in da duk namijin da ya ganki zai ji kin kwanta masa a zuciyar sa tabbas kin cancanci a so ki I really love you Please I beg you to accept my request please," ya fad'a tare da tsugunnawa a gaban ta irin a taimaka masa d'in nan. Rik'e k'ugu ta yi tare da juya idanunta a zuciyar ta take fad'in uhm uhm fa Hany karki yiwa kanki ki rasa wannan santalelan saurayin gashi kyakkyawa dogo fari ga iya kalamai sannan ga hankali da nutsuwa k'ara kallon sa ta yi sannan ta ce "Meye sunan ka," da sauri ya ce "Sunana Abdul-Aleem amma zaki iya kirana sweetheart," ihu da tafi wajen ya d'auka banda iPhones ba abinda ke tashi a wajen ana yi musu video bayan yan gidan televisions dake nasu. Alim ya ce "Amma ya sunan sarauniyar tawa?" D'an murmushi ta yi ta ce Sai ka tashi sannan zan sanar maka mak'e kafad'a ya yi ya ce "No bana so na tashi a nan har sai kinyi accepting d'ina a matsayin masoyin ki," dariya ta yi ta ce "Ban tab'a had'uwa da saurayin da naji zuciya ta ta aminta da shi lokaci guda ba sama da Kai a wannan lokacin bazan iya dakatar da kaina ba wajen fad'a maka Ina sonka ba yanzu ne na k'ara tabbatarwa gami da gasgata cewar zab'i mafi girma da nayi a rayuwata shine dana zab'e ka sannan Kuma na amince da irin soyayyar da ka ke yi mani Alim bana tunanin yanzu da Kuma nan gaba wani zai bayyana daka iya sauya akalar zuciyata daga son da nake maka nayi dace nayi sa'a da bayyanar ka a rayuwata Ina son ka sannan sunana Haneefa amma zaka iya kirana da matar ka insha Allah," mik'ewa Alim ya yi tare da yin wani juyi ya d'aga hany sama yana juyi da ita a wajen. Su Ummi na gefe sai dariya suke yi hakama sauran jama'ar wajen abun ya burge su sai tafi ake musu. Saurin k'arasawa wajen Hanfa ta yi ta karb'i abun maganar ta ce "mun gode kwarai da gaske da wannan nishad'antar damu da ku kayi sannan ku b'ace mana da gani wannan lokaci ne na cin abinci dan ni na matsu," duka wajen aka kama dariya. Daga haka aka fara gudanar da dinner kowa sai abinda yake so sannan yake ci yayin da Fauwaz ya dage sai ciyar da amaryar sa yake yi shi da Umar yayinda Maleek da Sabeeha ke zaune suna fira abinsu suna dariya ruwa kawai da lemo suke sha da haka aka kammala cin abinci sannan Ummi ta je ta gabatar musu da gift d'in su wasu rings ne guda biyu ta umarci Maleek da ya sawa Sabeeha haka kuwa akayi ya d'auki ring d'in da sai kyalli yake yi ya zira mata a yatsar ta ana yi musu tafi sannan itama ta d'auka tasa masa nan ma akayi tafi tare da hotuna sannan aka tashi kowa ya shiga motar sa zuwa gida. 'yan uku kuwa mota d'aya suka shiga da Doctor domin a gida zasu kwana saboda gobe d'aurin aure. [10/25, 8:48 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️ RUBUTAWA DAGA HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ) SADAUKARWA GA MY DAUGHTER SABEEHA BILKISU Z.YA'U (🅱️K) AISHA MAGAJI DABO (AMA) GODIYA TA MUSAMMAN A GARE KU HAFSAT YAHYA (NAMECY) SISTER MARIYA Nagode sosai da kulawar ku a gareni Allah yabar zumunci ya barmu tare sannan wannan page d'in na sadaukar da shi a gareku masoyan kwarai🥰 Page 25 Suna zuwa gida d'akin su suka nufa a gajiye wanka suka yi sannan suka shirya cikin kayan baccin su iri d'aya kamar yadda suka saba sai dai kowaccen su a zuciyar ta tunani take yi yanzu shikenan daga yau bazasu k'ara kwana tare ba duk sai suka dinga jin ba dad'i Dija ce ta shiga d'akin ita da Rinaz da kallo suka bi 'yan uku ganinsu duk jikin su a sanyaye. Dija ta ce "Beb's ya akayi ne nagan ku haka what wrong?" Ta fad'a tana zama gefen Sabreen dake kwance ruf da ciki ta zabga uban tagumi kamar wacce aka yiwa mutuwa Sabeeha kuwa tana zaune akan gado daga gefe ta had'a kai da gwiwa yayin da Sameeha ke zaune tsakiyar su ta tank'washe k'afa ta yi tagumi. Rinaz ce ta ce "Wai lafiya ku ke kuwa meke faruwa?" Ta fad'a fuskar ta d'auke da damuwa sai lokacin Sabreen ta yi juyi ta kalle su ta ce "Hmm sisters ku bari kawai gobe ne auren nan ko?" "Eh fa da wata matsalar ce?" Dija ta tambaya tana kallon Sameeha da har k'walla ta taru a kyawawan idanunta "Wallahi ni duk sai nake jin ba dad'i shikenan daga yau mun dena kwana tare da su dear zamu raba gida?" Sabreen ta fad'a tana goge hawayen da ya zubo mata. Sameeha kuwa tuni ta fara kuka domin itama tunanin ta kenan tashi Sabreen ta yi zaune ta rungume Sameeha suka cigaba da kuka kamar wad'an da aka yiwa mutuwa su Dija sai aikin rarrashi suke yi. Tashi Sabeeha ta yi tabar d'akin idanunta sunyi ja sosai da alama itama tana cikin yanayin da 'yan uwan ta ke ciki domin itama tana jin ba dad'i a zuciyar ta. Falo ta koma ta zauna ta d'ora uban tagumi wayarta dake gefen ta ce ta fara ringing ganin me Kiran ne yasa ta yi picking ta kara a kunnen ta ba tare da ta ce komai ba. "Baby," Maleek ya fad'a cikin in his sweet and cool voice d'in sa lumshe idanu Sabeeha ta yi sannan a hankali ta ce "Uhm," ya ce "Lafiya kuwa," kamar tana gaban sa ta girgiza kai alamun a'a. Kamar yasan me tayi ya ce "Ok fad'amun meye damuwar kinji sweetheart na?" Ai kamar jira take yi ta saka masa kuka har da shesshek'a tashi zaune ya yi daga kwancen da yake tare da shafa tulin sumar kansa ya ce "Ya salam please baby kibar kukan nan ki fad'a mun mene damuwar," Bata bar kukan ba sai ma k'ara volume da tayi cikin kukan ta fara magana kukan da kana jinsa kasan na tsantsar shagwab'a ne ta ce "To ba shikenan ba zamu rabu da su Sameeha dear ba shikenan na dena ganin su kullum," ajiyar zuciya ya sauke sannan ya yi k'asa da murya cikin sigar rarrashi ya ce "is okay wannan ne ya saki kuka uhm?" Gyad'a kai ta yi a hankali ta ce "Eh," Murmushi ya yi a zuciyar sa yana fad'in na bani ni Abdul yanzu tun yau baby ta fara kuka lallai zanyi fama da rigimar ta a fili kuma ya ce "Shikenan yi shiru abinki kullum fa zan dinga kai ki wajen su ammafa idan kinyi shiru," Da sauri ta share hawayen fuskar ta ta ce "Nayi shiru," "Yawwa that's my baby to yi dariya naji," dariyar kuwa ta yi kamar ba ita ta gama kuka ba sannan suka d'ora da firar su. Washe gari tun safe jiniya ke tashi a garin kasancewar rana ce ta musamman ga babban soja wato MG Abdul-maleek dan haka tun safe manyan sojoji ke dira a garin Kaduna daga wannan jiniya sai waccan jiniya Maleek kuwa tun safe suke zirga_zirgar tarbar bak'i shi da su Umar. Daddy ma a nasa b'angaren haka take domin shima sai amsar bak'i yake su Ummi ma haka sai hidima suke yi. Yan uku kuwa haka suka tashi sukuku Doctor na lure da su sai dai bata ce musu komai ba tana ta fama da bak'i. K'arfe Sha d'aya da rabi aka d'aura auren Rukayya Abubakar da Abdul-maleek Hamza mai Dala sannan aka d'aura na Umar Aliyu da amaryar sa Sadiya Abubakar sannan na Muhammad Hamza mai dala da Hajara Abubakar akan sadaki dubu d'ari-d'ari. D'aurin auren ya samu halattar manyan manyan sojoji ma'aikata da 'yan siyasa dama sauran jama'ar gari angwaye kuwa duk Wanda ka kalla a cikin su fuskar sa fal farin ciki gashi sunyi kyau sosai cikin ankon farar shaddar da suka yi. Reception aka yi bayan d'aurin auren a wani babban hall sai hotuna ake yi duk inda ka kalla masu d'aukar hotona ne da marok'a Maleek kuwa tare da Salman suka tafi mayar da sojojin da suka zo zuwa masaukin su. Daga can gida suka wuce direct part d'in sa Maleek ya nufa can ya samu su Umar sun baje a falo suna ganinsa Muhsin ya mik'e yana gyara babbar rigar jikin sa ya ce "Yawwa guy dama kai muke jira mu wuce zuwa part d'in sweet momma," Maleek baice komai ba sai juya da ya yi ya nufi k'ofa suka bi bayan sa zuwa part d'in Ummi. Suna gama parking suka nufi cikin falon suna shiga aikuwa falon ya d'auki gud'a nan suka fara gaggaisa da mutane. Can Maleek ya hango Ummi zaune kan kujera sai kallon sa take yi tana murmushi kallo d'aya zaka yi Mata kasan tana cikin tsantsar farin ciki tasha kwalliya sosai cikin light blue shadda hannu da wuyan ta sun sha adon gold ba k'aramun kyau tayi ba ba zaka tab'a cewa ta haifi d'a kamar Maleek ba hak'orin makkah na bakinta sai walwali yake yi. Takawa Maleek ya yi har gabanta ya tsugunna akan lallausan carpet d'in dake falon ya ce "Ina wuni Ummina," murmushi ta yi ta shafa sumar kansa kasancewar ya cire hular dake kansa ya rik'e a hannu ta ce "Lafiya lau Son an d'aura aure Allah ya sanya alkhairi," kallon mutanen dake falon ya yi domin kunyar su ya ke yi kifa kansa ya yi a jikin Ummi sannan ya ce "Ameen Ummina," gud'a Aisa ta rangad'a mik'ewa Ummi ta yi ta d'ago shi daga tsugunnen da yake ta rungume shi ta ce "Allah ya yi maka albarka," ta fad'a tare da k'arbar hular shi dake hannun sa tasa masa ya ce "Ameen Sweet mother," "Son d'ina," Aisa ta fad'a waigawa wajen ta ya yi ya ce "Na'am sweet momma na," ya fad'a tare da rungume ta ta ce "Allah ya sanya alkhairi ya yi muku albarka ya kawo zuri'a d'ayyi ba," kafin ya amsa Umar ya rigashi. "Yawwa ku haura sama Hajiya na nan," Ummi ta fad'a ya ce "To," saman ya haura yabar su Umar suna gaisawa da su Ummi. Da sallama ya shiga d'akin Ummi Hajiya dake zaune tana cin farfesun kaji ta amsa sallamar fara ce tas bata tsufa ba sosai dagargar take idanunta sanye da farin glass k'arasawa wajen ta ya yi ya zauna gefen ta ya ce "Hajiyata Ina yini?" Harara ta aika masa tare da kawar da kai murmushi ya yi ya ce "Haba Hajiyata laifin kuma menayi?" Ya fad'a yana langab'ar da kai tare da d'ora kansa a kafad'ar ta. "Kai ni d'agani kazo ka wani danne mutane kuma dana sani ma da banzo ba ko da yake ma ai ba dan kai nazo ba dan Fauwaz nazo saboda shi kad'ai ke ziyarta ta amma kai har manta kamannin ka nake," Maleek da ya k'ura mata ido yana kallon ta ya yi murmushi ya ce "To amma dai kinsan bana k'asar ko hadda wani kin manta kamata to yanzu ya akayi ki ka ganeni jikin ki Kuma ki rik'e abinki ni da zan hau wanda yafi naki," dariya su Umar dake zama suka yi Hajiya kuwa rik'e hab'a ta yi ta ce "Tabdijan ni kuwa yaushe ka zamo mara kunya haka a lallai gara da Hamza ya yi maka aure ko da yake ai dama kana da wata matar sannan ko ka turo ta ta gaishe ni ko?" Tsuru ya tsaya yana kallon Hajiya domin shi Sam ya manta yana da wata Nasreen banda yanzu da aka tuna masa tab'e baki ya yi ya yatsina fuska baice komai ba. "To 'yan miskilancin ne zasu tashi kenan ai kai da wannan bansan wa ku ka yo ba," ta fad'a tana dungurewa Muhsin kai shi Kuma ya harare ta salati Hajiya ta saka ta ce "Yanzu Muhsin ni ka ke harara to ai dukana ya kamata kayi wannan matar ka ta shige su da Kai," shiru Muhsin ya yi mata dan shi yafi Maleek miskilanci. Mik'ewa Maleek ya yi "Ni ku taso mu tafi gidan Mama domin so nake naje na ga baby na before anjima a kawomun abata," "Ah lallai Audul ka k'aro rashin mutunci Allah sarki yarinya zata yi hak'uri da fitina da uban miskilancin ka" dariya ya yi ya nufi k'ofa yana fad'in "Waye ya gayamiki ai ita ta daban ce baza ayi mata ba," ya fad'a tare da ficewa yabar Hajiya na masifar ita ya raina kenan. Direct gidan Doctor suka nufa Hanfa da Ashraf suka samu a compound d'in gidan suna fira ita tayi musu jagora har cikin babban falon dasu Doctor ke ciki itama ta yi kyau sosai cikin shaddar ta irin ta Ummi domin anko suka yi Lantana tunda suka shiga take rangad'a gud'a su kuma suka zube suna kwasar gaisuwa. Rinaz ta kalli su Sabeeha da suka yi mugun kyau cikin wani farin less Mai blue flowers sun sha kwalliya ta ce "Beb's da alama su Yaya sun iso ya kamata mu fita domin yin pictures," tashi suka yi suka nufi down stairs. Tunda suka fara sauka kallo ya koma kansu kallon Sabeeha Maleek ke you babu ko k'iftawa wani farin ciki yake ji mara misaltuwa a zuciyar sa idan har ya tuna yanzu fa ta zama matar sa mallakin sa ga wani mugun kyau da tayi masa itama a nata b'angaren haka take domin ba k'aramun kyau ya yi mata ba kallon juna suke yi ba tare da d'ayan su ya d'auke idon sa ba. Gud'ar da aka rangad'a ne yasa yin k'asa da kansa saboda tunawa da yayi a gidan surukai yake sannan ya mik'e ya fita bayan sun fitane su Sabeeha ma suka fita suka fara hotuna bayan sun gama har mota Sabeeha ta raka Maleek sannan ta koma cikin gida. Da misalin k'arfe biyu Doctor ta shiga d'akin su 'yan uku suna tare da k'awayen su ta ce "Yammatan Abba ku shirya Aysha ta yi mun waya zata turo a d'auke ku saboda lokacin walima ya kusa," suka ce "To," sannan suka tashi suka sake yin wanka suka zauna aka fara yi musu kwalliya. Doctor kuwa d'akin Abba ta shiga ta same shi yana amsa zama ta yi gefen sa jikin ta duk a sanyaye katse wayar Abba ya yi ya kalle ta ya ce "Doctor na lafiya kuwa?" "Wallahi Abban su ji nake yi babu dad'in rabuwa da su," murmushi Abba yayi ya ce "Nima Ina cikin irin yanayin da ki ke ciki Doctor amma wannan ne gatan da zamu yi musu saboda haka muyi ta musu addu'a Allah ya zaunar da su a gidan mazajen su lafiya tare da yara na gari," Doctor ta ce "Ameen ya rabbi," Shiryawa 'yan uku suka yi cikin wani tsadadden material purple mai adon farin flowers a jiki sunsha kwalliya sosai alkyabba suka d'ora saman kayan sunyi kyau sosai motocin da Ummi ta turo musu suka shiga tare da 'yan uwan Doctor wad'an da zasu walimar da Kuma k'awayen su da suka sha kyau cikin atamfar anko. Suna zuwa su Ummi suka tare su cikin farin ciki a cikin gidan daga wani b'angare za ayi walimar gurin ya tsaru sosai ansa runfuna da kujeru har wajen zaman su su Ummi suka yi musu rakiya yayinda kansu ke k'asa suna tafiya a hankali sai tashin k'amshi suke yi. Ba b'ata lokaci babban malamin da aka gayyato ya fara da walima da nasihohi ga amare dama sauran jama'ar da suka halacci wajen jikin amare duk ya yi sanyi domin wa'azi da Kuma nasihar malam ta shige su sosai. K'arfe biyar aka tashi daga Walimar Ummi tasa aka mayar da 'yan uku gida domin fara shirin Kai kowaccen su d'akin ta. Maleek kuwa hotel d'in da Abokan aikin sa suke ya tafi sukai ta fira da dariya da Kuma wasu tsare-tsaren wani soja ne ya shiga d'akin da sauri ya mik'awa Maleek waya ya ce a cewar Ahmad daga Dubai yana kira. KUYI HAK'URI DA WANNAN BA YAWA. [10/25, 8:50 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️ RUBUTAWA DAGA HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ) SADAUKARWA GA MY DAUGHTER SABEEHA BILKISU Z.YA'U (🅱️K) AISHA MAGAJI DABO (AMA) Page 26 Shiru d'akin ya d'auka mik'a hannu Maleek ya yi ya karb'i wayar yana tunanin lafiya kuwa da yasa Ahmad bai kira tasa wayar ba kara wayar ya yi a kunnensa. "Barka da wannan lokacin sir," gyad'a kai kawai Maleek ya yi Ahmad ya cigaba "Sir gaskiya akwai matsala," "Meye matsalar yanzu?" Maleek ya fad'a yana gyara zaman sa. "Gaskiya a yanzu akwai wata matsala mutanen yanzu suna yawan yin meeting sannan shi ogan su yana gab da dawowa suna yawan yin waya da shi a meeting d'in sannan duk maganar da suke yi cikin wani yare suke yi da bansan wanne yare bane domin yaren iya nasu ne sannan abinda nake tunani suna shirye shirye ne akan kayan da zasu shigo da su," Maleek da ya gama sauraron Ahmad ya ce "Ahmad ka cigaba dasa ido a lamuran su sannan abu d'aya dana fuskanta shine akwai Wanda ke kai musu information akan plan d'in mu hakan ne yasa suka canja yare wannan kuma zansa a kula da lamarin," "Ok sir an d'aura aure Allah yasa alkhairi ya bada zaman lafiya," "Ameen Ahmad," daga haka ya katse kiran zuciyar sa fal tunani ajiye wayar ya yi sannan ya mik'e ya nufi k'ofar fita daga d'akin ba tare da ya yiwa kowa magana ba. 'yan uku kuwa tunda Ummi ta shiga d'akin su tace su tashi su yi wanka su shirya dare nayi suka fara kuka dakyar suka yi wankan sai dai tunda suka yi wankan ko mai basu shafa ba suka zauna suna ta aikin kuka su Rinaz na rarrashin su daga baya itama Rinaz ta fara nata kukan Dija kuwa tagumi ta zabga ta kalle su ta ce "Yanzu Beb's meye amfanin kukan da ku ke yi look at you beb ke da zaki rarrashe su kema kin fara stop it please aure fa ba mutuwa bane sannan kuna gari d'aya fa zaku dinga ganin juna," "Beb's munzo duniya tare komai tare muke yi bama tab'a rabuwa da juna kullum a tare muke kwana muna jin motsin juna hatta kayan mu iri d'aya muke sawa komai namu iri d'aya ne muyi kuka tare mu yi dariya tare duk inda zamu tare duk wannan shak'uwar ace rana d'aya zamu rabu rabu da juna ya zaki ganmu?" Sabreen ta fad'a tana k'ara sakin wani kukan Wanda tasa su Sabeeha k'ara nasu volume d'in. Wata k'awar Doctor ce ta shiga d'akin ta same su suna ta kukan sai da suka bata tausayi zama ta yi tana rarrashin su amma basu yi shiru ba dakyar dai ta samu suka shafa mai ba batun kwalliya wani tsadadden less suka sa pich color takalman su da jakar su da mayafi duk dark pink sai k'amshi suke yi sunyi kyau sosai sai dai idanunsu sunyi ja Kuma har lokacin basu dena kukan ba jansu ta yi zuwa down stairs. Falon Abba ta kaisu inda Abba da Doctor ke zaune tsugunnawa suka yi a k'asan carpet d'in kansu a k'asa suna zubar da hawaye. Gyara zama Abba ya yi cikin yin k'asa da muryar sa ya ce "Aminaina," basu iya amsawa ba sai gyad'a kai da suka yi shima Abba ji yake ba dad'i haka ya dinga yi musu nasiha mai ratsa jiki yana Kuma jaddada musu su yiwa mazajen su biyayya ba abinda kake ji sai shesshek'ar kukan su. Doctor ta ce "Aure ibada ne tabbas nasan baku da matsala sannan na haifi yara masu biyayya da tsafta da girmama na gaba da su Rukayya Sadiya Hajara ku girmama mazajen ku ku zauna da su lafiya ku nuna musu ku masu tarbiyya ne ku nuna musu kunsan ya kamata dukda zaman tare zomu zauna ne zo mu sab'a amma Dan Allah ku kula sannan ku yi ta addu'a ku rik'e sirrin mazajen ku Allah ya baku zaman lafiya tare da zuri'a d'ayyi ba," basu iya amsawa ba sai kukan da suke yi mai sauti. "Rukayya kina da abokiyar zama saboda haka Yaya ce a gare ki girmamata dan Allah karki zamo silar fitina a gidan auren ki duk abinda zai faru kiyi hak'uri ku zauna lafiya Allah ya yi muku albarka," suna kukan suka amsa da "Ameen Abba," "Ku shigo mana," Ummi ta fad'a tare da ajiye wayar k'arasawa wajen ta 'yan uku suka yi suka rungume ta suna kuma sakin wani kukan itama dauriya kawai take yi saboda yadda suke kukan har zuciyar ta take jinsa daga nan suka tafi gurin Abba shima suka rungume shi suna kuka shafa bayan su Abba ke yi yana rarrashin su. Wasu daga cikin k'awayen Doctor ne da danginta da lantana suka shigo domin motocin d'aukar amare sun iso 'yan uku kuwa k'ank'ame Abba suka yi suka k'i sakinsa sai kuka suke yi. Doctor ta ce "Kuyi hak'uri ku tafi ana jiran ku zaku fara zuwa gidan Aysha ne," har lokacin basu saki Abba ba domin shak'uwar da suka yi da shi basu yi da Doctor ba. Tsawar da Doctor ta yi musu ne yasa suka saki Abba suna kuka Jan hannunsu aka yi aka tafi dasu suna kukan rabuwa suna fita daga d'akin Doctor ta fad'a jikin Abba tana kuka ajiyar zuciya Abba ya sauke ya ce "Maryama kiyi hak'uri kinji dole za aji ba dad'i kukan ya isa haka please," shiru Doctor tayi jikin Abba tana sauke ajiyar zuciya. 'Yan uku kam har a mota basu bar kuka ba har suka je gidan Ummi bayan motocin da suka kawo su wajen guda ashirin sunyi parking sannan aka fara shiga falon Ummi. Tarba ta mutunci su Ummi suka yi musu Lantana da Zainabu kuwa sakin idanu suka yi suna kallon aljannar duniya wato duk had'uwar gidan Doctor ga Wanda yafi nata nesa ba kusa ba su ai irin wannan gidajen a televisions suke ganinsa Zainabu kuwa kallon Ummi take yi a zuciyar ta tace ashe ba iya gidan ne na k'asar waje ba su kansu indiyawa ne da haka suka zazzauna Ummi kuwa gata ga 'yan ukun ta a zaune sai farin ciki take yi. An d'an tab'a fira sannan Ummi taja 'yan uku taja hannun 'yan uku zuwa cikin d'akin ta wani ruwan wanka tayi musu ruwan yasha wasu kayan k'amshi ta ce su yi wanka kowacce ta yi wankan duk sunyi wani irin mai Ummi ta basu ta ce su shafa kamar turare tsabar k'amshin sa sai da suka gama Ummi ta d'auko wani yadi shi ba code net ba ba less ba mai k'ananun zane kamar material kowacce best color d'in ta Ummi tasa aka d'in ka mata dogayen riguna ne fitet gownt tare da mayafi bayan sunsa ta feshe su da wani turaruka masu dad'in k'amshi. Sannan Ummi ta fara yi musu tata nasihar sannan ta k'ara da cewa karsu d'auke ta a matsayin suruka su d'auke ta a matsayin uwa karsu dinga b'oye mata wata damuwar komai k'ank'antar ta Hajiya ce ta shiga d'akin tana fad'in "Ina kishiyoyin nawa?" Ummi ta yi dariya ta ce "Gasu nan," zama ta yi gefen Ummi. A hankali suka gaishe ta ta ce "Lafiya k'alau ya kamata dai naga fuskar wad'an da zasu k'wace mun mazaje," a hankali suka yaye fuskar su Hajiya kuwa sakin baki ta yi tana kallon su domin ganin tsananin kamar su ta ce "Masha Allah Ina ta Audul ne?" Ummi na dariya na nuna mata Sabeeha "A lallai Masha Allah amma fa sai kinyi hak'uri da wannan yaron dan naga kansa rawa yake yi," k'asa Sabeeha ta yi da kanta bata ce komai ba. Waya Ummi ta d'auka ta yi Kira ta ce "Haba me kuke jira ne dare fa ya fara," daga can Maleek dake d'aura agogo a hannun sa ya ce "Ummi gamu nan," daga haka ya katse kiran. Turare ya fesa a jikin sa harya gaji da yin kyau kallon Umar ya yi dake gefe sai murmushi yake yi shi kad'ai ya ce "Umar muje nifa kwana biyun nan na lura cutar murmushi Kai kad'ai ba tare da wani dalili ba ta kamata sai kace wani k'wark'war," dariya Umar ya yi ya ce "MG banson iskanci fa duk wanda yake da Mata kamar Sameeha ai bashi ba fushi ko k'unci shiyasa kake ganina always in smile," ya fad'a yana k'ara washe baki kallon sama da k'asa Maleek ya yi masa ya girgiza Kai ya ce "Na tausayama," daga haka ya fice. Mota suka hau zuwa part d'in Ummi cikin falon suka shiga da Sallama daidai lokacin Fauwaz ya fito daga part d'insa ya sha kyau ba k'arya take falon ya rud'e da gud'ar ganin angwayen gaggaisawa suka yi da mutanen wajen sannan suka wuce zuwa stairs. Da sallama suka shiga d'akin Ummi amsawa ta yi sannan suka k'arasa cikin d'akin idanunsu nakan 'yan uku dake zaune kansu a k'asa d'ayan gefen Ummi Maleek ya zauna idanunsa na kan Sabeeha da tasha kyau cikin doguwar riga maroon color wacce tayi mata kyau jin kamar ana kallon ta ta d'aga kanta Aikuwa suka had'a ido shima shaddar jikin sa maroon ce Kuma suma Ummi ce ta yi musu. Tana kallon sa hawaye ne suka ciko idanunta ta yi saurin yin k'asa da idanunta wata k'aramar ajiyar zuciya ya sauke sannan ya mik'e ya k'arasa gabanta ya tsugunna a gabanta wani k'amshi ne ya daki hancinta itama a nata b'angaren haka lumshe ido yayi ya bud'e su a kanta a hankali ya kai hannunsa ya d'ago fuskar ta yana kallon idanunta da suka yi jajir ga Kuma wata k'wallar a cikin su girgiza mata kai ya yi a hankali ta lumshe idanunta take hawayen ciki suka zubo hanky ya zaro a aljihun sa ya fara goge mata yana magana k'asa k'asa "Please kukan ya isa haka karki rashin lafiya uhm kibar kuka okay?" A hankali ta gyad'a kanta a hankali ya jawota zai rungume ta Hajiya ta yi gyaran murya. D'an waigawa ya yi ya kalle ta yana mata kallon tambaya ita Kuma ta harare shi tab'e baki ya yi ya yatsina fuska ya ce "Sannu fa Hajiya," yana fad'ar haka ya rungume Sabeeha yana yi Mata a magana a kunnenta a hankali "Please Baby ki dena," ita dai ajiyar zuciya kawai take saukewa a jikin sa ga kunyar rungume tan da yayi. Ummi kuwa kallon su tayi tana murmushi tabbas tasan Maleek na son Sabeeha kamar yadda itama ke son sa ta tabbata zasu ba juna kulawar da ta dace ta ce "Son lokaci na k'urewa ku dai ba saina ce muku komai ba illa iyaka ga amanar yarana nan na damk'a ta a hannunku nasan baza ku cutar mun da su ba sannan nasan yarana masu biyayya ne saboda haka ku Kuma kuyi musu adalci ku kula da su," suka amsa da "Toh Ummi," "Ina ga yanzu ya kamata Fauwaz Kai da Umar zaku wuce da matan ku sannan akwai dangi da zasu raka su saboda haka kuje lokaci na k'urewa saboda kowa ya koma gida da wuri," da sauri Fauwaz ya ce "To Ummi," ya fad'a tare da mik'ewa Umar ma bakinsa dai har lokacin yak'i rufuwa sai jefawa Sameeha wani kallo yake yi. Su Sabeeha kuwa ba k'aramun tashin hankali suka shiga ba jin abinda Ummi ta ce a tare zuciyoyin su ke bugawa dagaske dai rabuwar zasu yi ai tuni kamar ansa remote control an kunna su suka fara kuka a tare har Sabeeha da har lokacin tana jikin Maleek. Sabreen da Sameeha kuwa rungume juna suka yi suna kuka Ummi kanta ta tausaya musu tashi kawai ta yi tabar d'akin domin tausayin su saboda bazata manta lokacin da za a kawosu gidan ba da Sabeeha ta ce indai ba tare da 'yan uwanta ba ta fasa aikin da kuma farkon zuwan su gidan da suka ce a d'aki d'aya zasu zauna amma yau ga ranar da zasu raba gida ka ga kuwa kuka dole. Tana fita Fauwaz ya k'arasa wajen su ya janye Sabreen da ta rik'e Sameeha ya ce "Sorry my love zo muje," ya nufi k'ofa rik'e da hannunta. Umar ma rik'e hannun Sameeha dake hawaye yayi suka nufi k'ofa yana mata magana k'asa-k'asa juyawa Sameeha ta yi tana kallon Sabeeha. Wasu hawayen ne suka Kuma zubowa Sabeeha cikin kuka da kuma muryar ta da ta dashe ta ce "Please My zan raka su," k'ara rungume ta ya cigaba da kukan ta yi shi kuma ya waiga ya kalli Umar alamun su wuce kawai fita suka yi. Nan aka tafi raka su Sabreen da Sameeha gidajen su Wanda fad'in had'uwa da tsarin gidajen b'ata lokaci ne tsarin gidajen irin na k'asar turai ne ku dai yi imagine yadda gidajen wad'an nan 'yan gatan 'yan bokon masu ji da kud'i zai kasance haka dangi suka tafi ana yaba gidajen da Kuma dukiyar da aka narkar wajen zuba furnitures d'in gidan da kayan kitchen domin gidan Sameeha da Sabreen bedroom uku uku ne Wanda kowannen su yasha furnitures nagani na fad'a falon kuwa guda hud'u hud'u kamar sun had'a baki ga garden da su swimming pool abun dai gwanin sha'awa. Sabeeha kuwa tana jikin Maleek sai sauke ajiyar zuciya take yi tashi Hajiya ta yi tayi hanyar fita tana cewa "Kai dai Audul baka da kunya," baice mata komai ba sai tab'e baki da ya yi ta fita. Sabeeha kuwa bacci ne ya d'auke ta a jikin sa jin yadda take sauke numfashi ne yasa ya gane bacci take yi a hankali ya d'ago fuskar ta yana kallon kyakkyawar fuskar ta data jik'ata da hawaye share Mata ya yi yana murmushi sannan ya mik'e da ita a hannun sa ya kwantar da ita kan gadon Ummi ya fita daga d'akin zuwa down stairs. Yana sauka Ummi ta ce "Son Ina kuma zaka Ina Daughter?" Kallon agogon hannunsa ya yi sannan ya kalli Ummi ya ce "Ummi bacci ta yi yanzu zan dawo bak'i ne ke kirana ba dad'ewa zanyi ba," yana fad'ar haka ya fice. Hotel d'in da Abokan aikin sa suke ya je a nan suke sanar da shi gobe zasu wuce amma kafin nan suna so su gabatar da parate domin taya shi murna bai musa ba ya ce Allah ya kaimu da haka yayi musu Sallama ya nufi gida. A part d'in Ummi ya tsaya a falo ya samu su Ummi ya ce "Ummi wai bata tashi ba?" Kafin Ummi ta yi magana Aisa ta ce "Eh saboda haka ka kyale ta kawai ta kwana a nan," zare ido ya yi sannan ya langab'ar da kai ya ce "A ji tausayina mana sweet momma," dariya ta yi ta ce "Wasa nake yi," murmushin da ya bayyana dimples d'insa ya yi sannan ya nufi stairs. Tura k'ofar d'akin ya yi ya shiga har lokacin baccin ta take yi domin dama tunda aka fara shagalin bikin su bata samun hutu hayewa gadon ya yi ya zauna yana k'are Mata kallo wato ita komai kyau yake yi mata hatta bacci ma a hankali ya kai hannunsa ya shafa fuskar ta mik'a ta d'anyi sannan ta bud'e idanunta masu d'aukar hankali ta sauke su a kansa daidai lokacin Ummi ta bud'e k'ofa ta shiga d'akin hararar wasa ta yi masa ta ce "Wato sai da ka tashe ta ko son," d'an tura baki ya yi ya ce "To fa Ummi tafiya zamu yi," girgiza Kai kawai Ummi ta yi. Sabeeha kuwa tashi zaune ta yi Ummi na fita ya sauka daga gadon ya mik'ar da ita tsaye ya gyara mata zaman mayafin kanta yayin da d'ankwalin ke rik'e da a hannunsa ya rik'e hannun ta suka nufi waje. Sun fara sauka stairs rigar ta ta tad'iye ta ta tafi luu zata fad'i yayi saurin rik'o abar sa ta fad'a jikin sa a tare suka saki ajiyar zuciya yayinda mutanen falon hankalin su ya yi wajen su kallon rigar ya yi har jan k'asa take yi furzar da iska ya yi daga bakin sa ya d'an juya idanunsa cikin k'asa da murya ya ce "Kinga wannan rigar zata kayar mun da ke ko?" Ai kafin ta yi magana cak ya d'auke ta ya fara sauka stairs. "My please ka sauke ni da mutane fa," ta fad'a cikin dashashshiyar muryar ta sannan hawaye na taruwa a idanunta ganin yawan mutanen dake wajen shi kuwa ko a jikin sa baice komai ba. Hanfa da Haneefa kuwa tuni suka fara aikin nasu wato d'aukar hoto Ummi kuwa girgiza kai kawai ta yi Sabeeha kuwa ganin ya nufi cikin falon da ita yasa tayi saurin b'oye fuskar ta a k'irjinsa ya kalli su Hanfa ya ce "Ku bakwa gajiya ko," daga haka ya yi hanyar fita Aisa ta ce "To Son masu rakiyar fa?" Bai waiga ba ya ce "No sweet momma mun yafe," gud'a wata cikin su ta rangad'a shi kuwa ya fice. Sojojin sa suna tsaitsaye bai ko kalle su ba ya zagaya gaban motar Salman ya bud'e masa ya zaunar da ita a ciki sannan ya zagaya ya shiga ya ja motar zuwa part d'insa inda Nasreen ke ciki. Tafiya yake yi a hankali ya d'an kalli Sabeeha ya ce "Baby yadai," kallon sa ta yi sannan ta yi masa harara ta ce "Meyasa zaka d'auke ni gaban su Ummi Kuma Hajiya ma na nan harda mama Aisa ma," ta fad'a tana marairaice fuska. D'age gira ya yi yana kallon ta sannan ya ce "Manta kawai Baby kina ganin kayan jikin ki zasu yar dake beside ma mene danna d'auki baby na Kuma matata ni ba ruwana da suna nan saboda i can't hide your love infront of koma waye," murmushi ta yi kawai bata ce komai ba. Har suka k'arasa aka bud'e masa gate ya shiga ya yi parking sannan ya fita ya zagaya ya bud'e inda take ya bud'e ya d'auke ta kamar 'yar baby ya nufi cikin gidan da ya gaji da had'uwa Sabeeha ma kallon gidan take yi saboda ko da wasa bata tab'a zuwa part d'in ba. Suna shiga cikin falon suka samu Nasreen kwance akan kujera 'yan aiki na zagaye da ita suna mata tausa wata arniyar riga ce a jikin ta iyakar ta gwiwa gata wata shara shara jin sallamar Maleek ne ya sata tashi zaune da sauri domin rabon da ta ganshi ta manta sai dai ganin ya d'auko Sabeeha ne yasa ta had'e fuska ba Kuma ta amsa sallamar ba. Kallo d'aya ya yi Mata ya d'auke kai domin wani fauu da ta yi kamar a gudu sai k'ananun idanu a wajen banda ma tana da dogon hanci da ana kaita china ba mai gane ita ba 'yar china bace. Stairs ya nufa da yayinda 'yan aikin suka bisu da kallon birgewa itama kanta Nasreen ta ga sun mugun dacewa amma ganin yadda 'yan aikin suke kallon su kamar sun samu TV yasa ta daka musu tsawa cikin masifa ta ce "Uwar ku ku ke kallo ku b'ace mun da gani tun kafin raina yafi haka b'aci," da sauri suka bar falon suka barta sai huci take yi. Maleek kuwa yana shiga falo cikin bedroom ya wuce ya zaunar da ita a kan gado ya ce "Baby bari naje nayi wanka," ya fad'a tare da sakar mata kiss a forhead d'in ta ya fita lumshe ido ta yi tana jin farin ciki a ranta. Yana fita itama ta tashi ta cire kayan jikin ta ta d'aura towel ta nufi gaban mirrow ta ta had'e gashin kanta waje d'aya ta samu wani k'arfe dogo ta soke shi sannan ta nufi toilet d'in da fad'in had'uwar sa b'ata lokaci ne ta watsa ruwa ta fito ta nufi mirrow ta shafa mai sama sama mai k'amshin gaske gashi taji garin akwai sanyi sosai iska sai kad'awa take yi. Wata sleeping dress tasa ruwan hoda doguwar riga ce mai wani d'an siririn hannu ta d'ora ta samanta wata falmaran mai igiya bata tsaya d'aure igiyar ba ta zira dogon hijabi har k'asa brown color mai haske sallolin da ake binta ta yi tana nan zaune Maleek ya shiga d'akin cikin wasu kayan bacci farare da kallo ya bita domin ba k'aramun kyau hijabin ya yi mata ba gashi hijabin kalar fatar ta zama ya yi gefen gadon har tayi addu'a suka shafa tare ta kalle shi ya ce "Kin idar ba?" Gyad'a kai ta yi. "Ok taso muje," mik'ewa ya yi ya rik'e hannunta suka fita down stairs a inda suka bar Nasreen a nan suka same ta tana cin jallop rice yatsina fuska yayi saboda da ganin abincin ba dad'i zai yi ba sai uban curry zama ya yi ya zaunar da Sabeeha gefen sa. Ya kalle ta ya ce "Ke!," Kallon sa ta yi ta ce "Yes," wani haushi ya kama shi wato shi take wani cewa yes ya share ya ce "Kamar yadda ki ka sani nayi aure sannan ga Baby nan a wannan gidan bana son tashin hankali wannan shine kawai abinda nazo na sanar miki kinsan bazan d'auki iskanci ba kija girman ki," yana fad'ar haka ya mik'e rik'e da hannun Sabeeha zasu koma d'aki. "Banji kayi maganar kwana ba?" Harara ya aika mata ya ce "Ashe ki manta da magana dake a ranar da aka kawo ki gidan nan ko?" Wani haushi ya kama Nasreen ta ce "Ban manta ba Kuma hakan da kake k'ok'arin yi ba adalci bane kawai ka raba mana kwana ehe," Daga bayan sa k'asa k'asa Sabeeha ta ce "Please My do as he said tana da gaskiya," ajiyar zuciya ya sauke ya kalli Nasreen ya had'e fuska ya ce "Bayan mun gama cin amarci kowacce kwana biyu ne kwananta," yana fad'ar haka ya juya yaja hannun Sabeeha suka yi d'aki. Nasreen kuwa tsaki ta ja ta ce "Aikuwa Wallahi sai yarinyar nan taci uwar ta a gidan nan wato ita zaka bawa kanka amma Wallahi Allah ya isa ko da yake Arfat ne babban shege Kuma wallahi saina nuna muku real color na," ta fad'a tare da shigewa d'akin ta. Maleek kuwa suna shiga d'aki ya ce "Ina zuwa," falo ya fita ya shiga kitchen ya sai gashi da lemuka da su fresh milk da kaza ya ce "Zo baby kici nasan baki ci komai ba," ba musu ta zauna da kansa ya bata taci ta k'oshi tasha fresh milk ta kalle shi ta ce "Kaifa?" Girgiza kai ya yi ya ce "No baby na k'oshi," d'aukar kayan ta yi ta Kai kitchen Wanda ya gaji da tsaruwa ta fito. Tana shiga d'akin ta zauna lokacin Maleek ya shiga toilet yin alwala yana fitowa ya ce "Baby zo muyi sallah," ta ce "To Ina zuwa," toilet ta shiga ta yi brush sannan ta fito ta samu ya shimfid'a prayer mat a saman lallausan carpet d'in d'akin ya jasu Sallah raka'a biyu suka yi addu'a sannan ya dafa kanta yayi Mata addu'a ya yi Mata tambayoyi sannan suka hau gado domin yin bacci bayan sun kashe k'wan d'akin. Nan fa suka tsunduma wata duniyar ta daban domin Maleek hanata sakat ya yi abinka da farin shiga tab'o can tsotsi can ita kuwa sai nok'ewa take yi daga baya kuwa da ta tsumu da salon sa ta fara biye masa sai da aka zo ganawa da babbar fada sannan ido ya raina fata domin ta wahala ba k'adan ba duk da tana da dauriya amma sai da tayi masa kuka yayinda shi kuwa gaba d'aya tayi gabas da hankalin sa sai addu'a yake shek'a mata. A b'angaren su Umar kuwa Sameeha zazzab'i ne ya rufe ta magani Umar ya bata sannan suka kwanta tana manne a jikin sa har bacci ya kwashe su. Sabreen kuwa tun a mota take zuba suna zuwa gidan bayan mutane sun tafi Fauwaz ya jata d'akin sa suka yi wanka sannan suka ciyar da juna suka yi sallah sannan tun a wajen suka fara kashe juna da romance sannan suka haura zuwa bed tofah masu rawar Kai biyu sun had'u aikuwa sai durzar juna suke yi daga k'arshe wiwi Sabreen ta fara kuka tana cewa Wallahi ta hak'ura ita ya kyale ta Fauwaz kuwa baima San me take yi ba domin ya shiga babbar fada. NI KUWA NACE ASUBA TA GARI SABEEHA DA SABREEN. [10/25, 8:51 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️ RUBUTAWA DAGA HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ) SADAUKARWA GA MY DAUGHTER SABEEHA BILKISU Z.YA'U (🅱️K) AISHA MAGAJI DABO (AMA) Page 27 Washe gari tun asuba zazzab'i ya rufe Sabeeha tana kwance ga azabar da k'asan ta ke mata kamar an yayyanka mata da reza sai hawaye take yi tana kwance jikin Maleek da tunda yayi mata wanka shima ya yi ya kasa matsawa ko ina ko sallah ranar a gida ya yi sai sannu yake jera Mata. Tashi ya yi ya shiga kitchen domin sama mata abinda zata ci sai dai shi sam bai wani iya girki ba dakyar dai ya dafa ruwan tea ya soya dankali da kwai ya nufi d'akin ya zauna gefen gadon tare da shafa sumar kanta ya ce "Baby taso kici abinci kinji?" Girgiza kai tayi har da hawayen ta ganin dagaske fa ba cin abinci zata yi ba yasa ya fara k'ok'arin cire rigar jikin sa yana cewa "Tunda baza kici ba bari na k'ara yi," a firgice ta girgiza masa kai ta ce "Wallahi zanci," murmushi ya yi ya ce "Yawwa baby na," d'aukar ta ya yi cak ya d'ora ta a cinyar sa ya d'auko tea d'in da ya had'a yana bata tana sipping a hankali sai da ta ce ya isa sannan ya kyale ta. Dankalin ya d'ebo da fork ya kai bakin ta sai ta shagwab'e fuska ta ce "Uhm uhm da zafi fa," ta fad'a tana k'ifk'ifta idanunta da har lokacin da k'walla a cikin su. Sarai yasan rigimar ta ce sai ya fara hura mata abincin kamar yadda akewa yara yana bata sai dai bata ci da yawa ba ta ce ita ta k'oshi sannan ya rabu da ita ya zaunar da ita ya d'auke kayan ya kai kitchen yana dawowa tabi shi da idanu gira d'aya ya d'aga mata "Da wani abune Baby?" Noding kanta tayi ta ce "Ina so nayi brush ne," d'aukar ta ya yi ya kaita toilet tayi brush d'in ya dawo da ita cikin d'akin. Lokaci ya kalla sannan ya d'auki wayar sa ya kira wayar Rinaz Hanfa ce ta d'aga wayar ta ce "Hello Yaya good morning," "Morning," ya fad'a a tak'aice "To Ina sweetheart tana lafiya?" Kallon Sabeeha ya yi sannan ya ce "Hanfa ina Ummi?" "Yaya Sweet momma fa ta tafi hospital," Hanfa ta fad'a cikin jin mamakin maganar Hanfa ya ce "Ok ba matsala," ya katse wayar ya fita daga d'akin. Sai da ya jima da fita sannan ya koma cikin d'akin cikin wata blue light d'in shadda sai kyalli take yi ya yi kyau sosai kallon sa Sabeeha kansa ba hula sai tulin sumar kansa dake shek'i fuskar sa fayau gwanin sha'awa bakinsa ya k'ara pink ga girar sa data kusa had'ewa ta yi bak'i sosai kamar gashin kansa haka ma zara-zaran gashi idanunsa. Kashe mata ido d'aya ya yi ita Kuma ta yi k'asa da kanta murmushin sa mai tsada wanda ke bayyana dimples d'insa ya yi mata sannan ya nufi drower ya ciro wani dogon Hijabi coffee color ya zira mata saman milk d'in doguwar jikin ta yasa mata takalmin ta cak ya d'auke ta ya yi hanyar fita da ita. Kallon sa ta yi ta ce "Ina zamu je?" "Hospital kinga baki jin dad'i sosai," ya fad'a tare da bud'e k'ofar falon ya fita. Nasreen dake zaune a falon tana jinsu su dai basu san da halittar ta a wajen ba tsaki ta ja tana jin wani Abu ya tokare mata k'irji sai kawai ta kama kuka tana jin kamar ta kashe Sabeeha ta huta. A mota ya sata ya zagaya ya shiga yaja motar yabar gidan gaba d'aya a hanya Sabeeha ta kasa yin shiru ta ce "Amma wanne asibitin zamu je?" "Na su Ummi mana," ya fad'a hankalin sa na kan titi "Ni dai gaskiya kar muje nan me zaka cewa Ummin to?" Ta fad'a tana marairaice fuska dariya ya yi ya ce "Ce mata zanyi Ummi mota ce zata shiga ma ajiyar ta ma'ana garaje Kinga ai gurin already nata ne so sai wani gini yaso bata matsala lokacin da take k'ok'arin shiga d'akin ta sai kawai wannan motar ta rusa ginin shine muka zo a duba mana wajen da fatan ba matsala," ya k'arasa maganar tare da yin murmushi. Shiru Sabeeha ta yi tana tunanin maganar sa ta ce "Mota ta rusa gini kuma shine zamu a dub...," Zare ido ta yi tana kallon sa saboda ta gano abinda yake nufi ta ce "Please My kar muje wajen Ummi Wallahi kunya nake ji," ta fad'a k'walla na zubowa a idanunta. "Ok shikenan sai muje wajen Mama ai," kuka kawai tasa masa girgiza Kai ya yi ya ce "Nabani Baby me ya faru kuma?" "Haba Dan Allah baby saboda mune sarakan rashin kunya kawai sai muje wajen su mu fad'a musu wannan abun?" Ta fad'a cikin kuka. "To sai me kinga nifa su kad'ai zan iya fad'awa wannan sirrin bedside ma nifa ko mace 'yar uwarki bazan je wajen ta ta duba ki fa Aha garama kiji," ganin dagaske yake maganar yasa ta cigaba da kukan ta har suka k'arasa asibitin ai a nan ta tabbatar dagaske yake. Zagayawa ya yi ya bud'e b'angaren da yake zai d'auke ta ta zare ido ta ce "Please ka barni zanje da kaina," had'e fuska ya yi ya ce "To naji fito kiyi tafiyar mugani," a hankali ta zura k'afafun ta waje ta fito tana rintse idanu hannun ta ya rik'e suka fara tafiya sai dai sai runtse idanu take yi k'walla ya cika idanunta. Ganin haka yasa Maleek d'aukar ta yana cewa "Kin fiya rigima baby kina irin wannan tafiyar ai sai kija hankalin mutane wajen mu idan Kuma na d'auki matata ina ruwan wani dani," luf kawai tayi a jikin sa domin ita kad'ai tasan me take ji. Ai kuwa duk inda suka gifta sai an kalle su shi kuwa ko a jikinsa har suka k'arasa k'ofar office d'in Ummi ya murd'a handle d'in ya shiga rintse idanu kawai Sabeeha ta yi saboda wata kunya da ta saukar mata. Da sallama ya shiga office d'in Ummi ce tare da Doctor ne a zaune suna yiwa juna ya gajiyar taro suna d'an tattaunawa ganin Maleek d'auke da Sabeeha ne yasa su sakin baki suna kallon su wucewa ya yi da ita kan doguwar kujerar dake cikin office d'in sannan ya k'arasa gaban su ya gaishe su suka amsa. Kallon juna Ummi da Mama suka yi sannan suka mayar da kallon su kan Maleek Ummi ta ce "Son lafiya kuwa me yake damun Daughter d'in?" D'an k'asa ya yi da kansa sannan ya kalli Ummi yana d'an sosa kai bai yi magana ba. "Uhm hum Kai muke sauraro," a hankali ya tashi ya zagaya kujerar da Ummi ke zaune ya kai bakin sa saitin kunnen ta ya ce "Ummi a d'an dubana wajen ko fa tafiya ta kasa," hararar sa Ummi ta yi sannan ta tashi da sauri ta k'arasa wajen Sabeeha da har lokacin ta kasa bud'e idanunta saboda kunya ta zauna gefen ta. Tashi Doctor ta yi ta kalli Ummi ta ce "Aysha ni na tafi office," bata jira cewar Ummi ba ta fice jin muryar maman su yasa ta kuma jin wata kunyar ta kuma kamata dariya Ummi ta yi ta ce "To ai Maryam d'in ta fita bud'e idanunki Ummin ki ce fa," a hankali ta bud'e idanunta masu d'aukar hankali eyelashes d'inta duk sun jik'e da hawaye ta kalli Maleek sannan ta kalli Ummi tana hawaye. D'an rungume ta Ummi ta yi ta ce "Sorry kinji yarinya ta Son ne ko?" Gyad'a kai Sabeeha ta yi. "To yi hak'uri kyale shi ko ya fita?" Nan ma gyad'a kai Sabeeha ta yi Ummi ta kalle shi ya k'urawa Sabeeha ido ta ce "To daughter ta ce ka fita saboda haka ayi waje," "Ni koh baby?" Ya fad'a yana nuna kansa a hankali ta ce "Eh," ta fad'a tana maida kanta k'irjin Ummi. Tashi ya yi yana cewa "Idan fa na tafi bazan dawo ba," tashi Ummi ta yi ta ja hannun sa ta tura shi waje ta rufe k'ofar sannan ta dawo wajen Sabeeha ta kwantar da ita ta fara dubata. Gaskiya kam ba laifi ta ji jiki dan yaji mata ciwo d'inki kad'an Ummi ta yi mata tare da allurai tana yi mata sannu suna nan Maleek ya yi knocking Ummi ce ta bud'e masa k'ofa ya shiga sai hararar wasa yake aikawa Sabeeha. "Yawwa Son ina ga kawai mu tafi zuwa gida," ya ce "Toh," k'arasawa ya yi gaban Sabeeha ya d'auke ta ya yi hanyar fita Ummi na biye da su a baya har wajen mota ta bud'e masa gaban motar ya zaunar da Sabeeha sannan ya zagaya ya shiga Ummi ta ce "Yawwa kuje bari zan taho a tawa motar," gaba suka yi ta bisu a baya. Suna zuwa a k'ofar part d'in Ummi ya yi parking Ummi nayin parking ta k'arasa ta ce "Son muje ciki akwai magungunan da ya kamata tasha," cikin falon suka shiga yana d'auke da Sabeeha direct d'akin Ummi ya kaita sannan ya koma falon inda su Aisa suke. "Ai dama tunda naga Audul na rawar kai nasan sai yayi ba daidai ba," Hajiya ta fad'a tana hararar Maleek yatsina fuska ya yi ya ce "To ke Ina ruwanki sannan ni a dena b'ata mun suna nikam ba sunana Audul ba Abdul nake ehe idan baki iyawa kice Maleek," "Rabu da Hajiya Son zonan kusa dani ka zauna bari na kawoma abinci nasan baka samu kayi break fast ba," ta fad'a tare da mik'ewa ta nufi kitchen ta had'o masa breakfast a tray ta janyo k'aramun center table ta ajiye masa a kai ta zauna gefen sa. Side hug yayi mata ya manna mata kiss a check d'inta ya ce "Thank you sweet momma na," ya fara cin abincin yana kallon Hajiya da ta saki baki tana kallon su. Ummi ce ta shiga falon bata kalle su ba ta wuce kitchen ta had'awa Sabeeha breakfast ta nufi stairs tana shiga daidai lokacin Sabeeha ta fito daga wankan da Ummi ta had'a mata ruwa tasa ta yi a hankali take takawa ta zauna gefen gadon ta shafa mai dasu humra Ummi ta bata wata had'add'iyar tsadaddiyar atamfa d'inkin doguwar riga up shoulder tasa atamfar ta yi Mata kyau fara ce da blue Ummi da kanta ta gyara mata gashinta ta kitse mata shi ta gefe kan bata sa mata ribbom ba saboda kar ya dame ta ta fesa mata turaruka sannan Ummi da kanta ta bata abincin taci sannan tasha magunguna ta ta d'auki abubuwan abincin ta fita. Ummi na fita su Rinaz suka shiga d'akin ita da su hany "Sannu dear ashe kin maguzu," Rinaz ta fad'a cikin sigar tsokana "Sannu Sweetheart kunsha aiki ke da Yaya," hany ta fad'a Sabeeha kuwa da harara kawai take binsu. Ummi ce ta shiga d'akin ta ce "Ku Kuma ya akayi ku ka zo ku ka samun yarinya a gaba?" Ta fad'a tana kallon Sabeeha da take kallon Ummin idanunta taf k'walla. "Kunga ga hanya nan bana son takura oya kuyi waje then kuje part d'insu ku gyara musu tas kunji ba?" "To Ummi ba mu car key d'in ki," Hanfa ta fad'a mik'a mata Ummi ta yi suka fita. "Kwanta ki huta kinji daughter," Ummi ta fad'a sai da ta ga Sabeehan ta kwanta sannan ta fita tare da ja Mata k'ofar d'akin. B'angaren su Sabreen kuwa itama ta gurzu ba laifi bayan sunyi wanka sai shagwab'a Sabreen ke sauke masa dan ko abincin da Ummi ta aika musu cewa ta yi ita baza ta ci ba sai dai ya girka mata wani ba yadda ya iya haka ya shiga kitchen ya girka mata dan mugun ji yake da ita motsi kad'an ya ce mata sannu. Su Sameeha kuwa da safe sumul ta tashi zazzab'in ya sake ta hakan yasa suna gama breakfast Umar ya fara shishshige mata duk sai ta gama tsorata sai tattab'e ta yake yi kamar zata yi kuka ta ce "Ni dai ka barni ko na fad'a ka da Ummi," cikin zare ido ya ce "Kice mata me bayan tasan ke d'in mallakina ce," ya fad'a yana d'aga mata gira d'aya tura baki Sameeha ta yi ta ce "Toba dama ta ce idan kayi mun ba daidai ba na gayamata ba?" "To amma nima ai tace ki girmamani sannan kiyi mun biyayya ko ba a sanar dake hakan ba bugu da k'ari kuma Ummi tace ki rik'e ni gam saboda haka kawai ba mutunci a bani hakk'ina," shiru Sameeha ta yi tabbas maganar sa gaskiya ce sai ta marairaice fuska irin a tausaya mata d'in nan ta ce "To shikenan naji amma ka bari sai da daddare ka ga yanzu ban gama samun sauk'i ba," sarai yasan taji sauk'i garau amma sai ya basar ya ce "To shikenan naji na kuma yadda," daga haka suka cigaba da fira. Sabeeha kuwa bacci tayi sai azahar sannan tayi juyi ta bud'e idanunta daidai lokacin Maleek ya shiga d'akin tsayawa kallon ta ya yi domin ta yi kyau sosai cikin atamfar itama kallon sa take yi ya canja wanka cikin wata farar shadda yayi kyau sosai ba aiki a kayan sai wasu bak'ak'en bottles da aka har wajen aljihun sannan rigar iyakar ta cinya sai dogon hannu da ya sawa Link's bak'ak'e kansa ba hula sai k'amshi yake yi gashi kansa ya zubo har goshin s. Shi kuwa gashin ta da aka kitse mata shi a gefe shi ya tafi da shi domin ba k'aramun kyau ta yi ba a hankali ya taka wajen ta ya haye gadon daf da ita yana kallon ta ya ce "Sannu baby kin tashi?" Gyad'a kanta ta yi kamar an tsikare ta ta ce "Wai My d'azu da Ummi ta kore ka a asibiti ina kaje?" Hararar wasa ya yi mata saboda tuna masa da tayi ya ce "Waya naje nayi da budurwata a mota," take had'e fuska har k'walla na had'ar mata a fararen idanunta ta kawar da kanta gefe "Baby," ya Kira ta amma bata kalle shi ba sai ma hawayen da ya zubo mata. Ummi ce ta shiga d'akin kallon Sabeeha ta yi sannan ta kalli Maleek cikin had'e fuska ta ce "Zuwa kayi ka dame ta ko oya fitar mun a nan," tura baki ya yi k'asa-k'asa ya yi magana yadda Sabeeha ce Kawai zata ji shi ya ce "Ki ka bari Ummi ta sake korata wayar zanje na sake yi da Surayya," daram gaban Sabeeha ya fad'i ta kalli Ummi ta ce "Ummi ki kyale shi kawai," "Ok kaci darajar daughter," Ummi ta fad'a tare da barin d'akin tana fita Sabeeha tasa bayan hannunta tana goge hawayen da ya b'ata mata fuska. Cikin k'asa da muryar cikin sigar rarrashi yasa hannun sa ya juyo da fuskar ta suna facing juna ya ce "Is okay ya isa uhm ni wasa nake yi miki da kika sa aka koreni wajen Mama na tafi muka yi fira," ajiyar zuciya ta sauke shi kuma ya rungume ta a k'irjin sa yana jin wutar sonta na k'ara ruruwa a zuciyar sa ita kuwa luf ta yi a jikin sa domin tana jin dad'in d'umin jikin sa a hankali ya ce "Ya jikin naki?" "Ya warke fa yanzu ba inda ke mun ciwo," ta fad'a tana zagaya hannunta a bayan sa murmushi ya yi tare da bata kiss a goshin ta ya ce "Masha Allah kenan yanzu zamu iya k'ara yi?" Ya fad'a yana kallon cikin idanunta. Harara ta aika masa ta ce "Idan kashe ni kake son yi ba to ni ban warke ba," ta fad'a tana jamewa ta d'ora kanta a cinyar sa dariya ya yi tare da yin wasa da gashin ta. Wayar sa ce ta fara ringing cikin wani sauti mai dad'in gaske d'aukar wayar ya yi ba tare da ya yi magana ba can ya ce "Okay ba damuwa gani nan zuwa," daga haka ya katse kiran. "My Ina zaka?" Juya idanu ya yi ya ce "Zani wani waje amma yanzu zan dawo ki shirya saboda za ayi wani taro yanzu saboda mu kingane?" Gyad'a kai ta yi sannan ya manna mata kiss ya fita da ido ta bishi tana jin soyayyar sa na ratsa ta. Yana fita compound d'in gidan ya samu su Salman sai gyara wurin da za ayi taron suke yi suna ganinsa suka taso d'aga musu hannu ya yi kamar baya son magana ya ce "Ku cigaba da aikin ku zani ni d'aya," yana fad'ar haka ya fad'a mota ya jata yabar gidan. Hotel d'in yaje suka d'anyi tsare-tsare sannan ya koma gida part d'in Ummi ya shiga ya tarar sai hidima ake yi Ummi ya hanga ta nufi stairs wajen ta ya nufa ya ce "Ummi ga wannan kayan su Baby zata sa," kallon kayan ta yi na sojoji ne ta karb'a ta ce "Amma ai kasan bata da lafiya ko ba lallai ta iya zuwa," "No Ummi tace ta warke fa zata iya zuwa," "Shikenan bari naje amma fa idan tace bazata iya ba bazata fito ba," Ummi ta fad'a tare da haurawa stairs shi kuma ya juya ya fita. Ummi na shiga d'akin ta samu Sabeeha ta fito daga wanka sai dai har lokacin tafiyar ta bata dawo daidai ba k'arasawa ciki Ummi ta yi ta ajiye kayan saman gado ta ce "Idan kin shirya wannan kayan Zaki sa saboda taron da za ayi," kallon kayan Sabeeha ta yi ta ce "Toh," "Zaki iya ai ko?" Ummi ta tambaya gyad'a kai kawai Sabeeha ta yi "To Bari na aika a d'auko mai make up tayi miki," Ummi na fad'ar haka ta fita. Zama gefen gadon ta yi wayar Ummi dake ringing Sabeeha ta kalla Daughter ta gani rubuce a screen d'in d'auka ta yi tare da sallama "Sabeeha dear," Sabreen ta fad'a cikin farin ciki "Na'am sweetheart," Sabeeha ta fad'a tana murmushi. "Lafiya kike kuwa naji muryar ki haka ko da yake dama haka ya kamata naji ki kasancewar ki sabuwar amarya saboda ehem kinsan kuwa hmm bari dai nayi shiru," Sabeeha da tunda ta fara magana take murmushi ta ce "Allah ya shirye ki amma dai zaku zo?" "Eh muna nan muna shiri yanzu muka gama magana da Sameeha dear ma itama shirin suke yi," Sabeeha ta ce "Ok sai kun shigo daga haka ta katse Kiran," har zata ajiye wayar sai kuma ta Kira Doctor. "Hello Aysha," Doctor ta fad'a "Ni ce Mama Ina wuni?" Sabeeha ta fad'a Doctor ta ce "Lafiya lau 'yar rigimata ya jikin?" Cikin jin kunya ta ce "Da sauk'i Mama amma ai zaku zo ko?" "Me ake yi?" Doctor ta tambaya "Taro zasu yi ne Ummi please kizo Ummi tace zaku zo ai," shiru Doctor ta yi ko shine taron da Ummi ke fad'a Mata a asibiti sai ta ce "To shikenan zamu zo," "To sai kun zo," tana fad'ar haka ta katse Kiran Ummi ce ta shigo tare da me make up ba b'ata lokaci aka fara ranga'awa Sabeeha Kwalliya yayinda take jiyo jiniya na cika gidan. Lokaci kad'an aka gama tsantsara mata kwalliya Mai masifar kyau eyelashes ne kawai tace kar asa mata itama mai kwalliyar bata yi tunanin sa mata ba saboda tana da gashin ido sosai wani ma sai yace eyelashes d'in tasa irin dogayen nan taje mata shi da mascara kawai akayi. Kayan sojojin tasa wad'an da suka yi Mata matuk'ar kyau gasu cif daidai jikin ta tana gama sawa make over d'in a zuciyar ta ta ce Masha Allah, Allah yayi halitta a nan ga kyau ga sura. Tana gama sa kayan ta koma ta zauna make over d'in ta fara gyara mata gashinta inda yasha mayuka sai kyalli yake yi aka d'aure mata wani a tsakiyar kanta cikin milk and army green d'in ribboms aka sake shi har gadon bayan ta sannan aka zubo mata da wani ta gaban goshin ta aka lank'wasa shi aka had'e dana bayan sannan aka sa mata wata hula army green mai kyau mai wasu kunnuwa biyu a gaba yayinda tsakiyar kan yake a bud'e domin band ce hular gashin gaban goshinta ya kwanta luf luf a gwanin sha'awa. Sannan tasa wani hill d'in takalmi army green wayyo ba k'aramun mugun kyau tayi ba kamar ka sace ta ka gudu kayan zuwa kwalliyar sunyi mata azababben kyau kamar 'yar baby turaruka ta fesa masu dad'in k'amshi ita kanta tsayawa kallon Sabeeha ta yi ta ce "Masha Allah kinyi kyau," Sabeeha ta ce "Nagode," sannan ta juya ta kalli mirror itama tsayawa kallon kanta ta yi saboda tunda aka fara shagalin bikin su zata iya cewa bata yi kyau ba kamar yau ba hatta d'an kunnen ta army green ne da agogon ta. Ummi ce ta shiga d'akin tasha kwalliya cikin wani less milk tayi kyau tana ganin Sabeeha ta ce "Masha Allah daughter na kinyi kyau sosai," murmushi Sabeeha ta yi ta ce "Nagode Ummina," Kallon make over d'in Ummi ta yi ta ce "Nawa ne kud'in ki," ta ce "Dubu d'ari ne hajiya," Ummi ta ce "Gaskiya yadda kika fito mun da daughter na haka zan biyaki dubu d'ari biyar," nan ta fara godiya sannan Ummi ta fita daga d'akin. Ummi na fita ba dad'ewa Maleek ya shiga d'akin cikin uniform d'insa na sojoji da a kullum yasa su kamar k'ara masa kyau ake yi yasha kyau gashin kansa sai walwali yake yi ga askin dake kansa da k'ara masa kyau sosai sai tashin k'amshi yake yi. Sallamar sa ce tasa Sabeeha waigawa ta kalle shi sai da numfashin sa ya d'auke na wasu seconds saboda tsabar kyan da ya ga ta yi a zuciyar sa sai hamdala yake yi da ya same ta matsayin abokiyar rayuwa itama kallon sa take yi yadda ya yi kyakkyawan kyau. Make over dake zaune kallon Maleek ta yi a zuciyar ta ta ce haba dama wannan falleliyar ai sai wannan had'adden guy d'in gaskiya sunyi matching gaskiya za a ga yara a nan wai kallon da Maleek ya yi Mata ne yasa ta mik'e ta fita tana waigen su. A hankali ya k'arasa gaban ta ya mik'ar da ita Yana kallon cikin idanunta sannan ya rungume ta a tare suka saki ajiyar zuciya. "Kinyi kyau sosai Baby," murmushi ta yi sannan ta d'aga kanta tana kallon fuskar sa kasancewar ya fita tsayi ta ce "Kai ma kayi kyau My," murmushin ya yi dimples d'insa suka lotsa hannu ta Kai ta tab'a wajen ta ce "Bani d'aya My," dariya ya yi ya ce "Ai wannan ma naki ne amma zan bawa yaro ko yarinyar da zamu haifa," dariya tayi wayar sa ya zaro ya fara rangad'a musu hotuna. Suna rungume da juna Ummi ta fito ta ce "Son ku fito time na tafiya mutane sun taru fa," jan hannun Sabeeha ya yi suka fita. Tunda suka fara sauka stairs idanun mutane ya yi kansu iPhones kawai ke tashi a wajen ana yi musu hotuna kowa na fad'in sun dace a haka suka k'arasa sauka. Aisa ta k'arasa gaban su ta rungume Sabeeha ta ce "Masha Allah Daughter kinyi kyau," ta ce "Nagode Momma," su Hany Hanfa da Rinaz sai hotuna suke musu har su Ashraf Alim da su Muhsin da Aiman da suka shiga falon sai pictures suke musu domin sun burge kowa. Daidai lokacin Sabreen da Fauwaz suka shiga falon sunyi kyau ash shadda Fauwaz yasa Sabreen kuwa Ash less tasa Mai adon silver sunyi kyau ba k'arya daga bayan su Kuma Umar da Sameeha ne suma sunyi anko Umar cikin bak'ar shadda yayi kyau Sameeha Kuma bak'in less sunyi kyau sosai Sabeeha na ganin su ta cika da farin ciki. Rungume ta Sabreen ta yi ta kalli fuskar ta ta ce "Wayyo dear Kinga yadda ki ka yi mugun kyau Wallahi kin had'u ba k'arya," dariya Sabeeha ta yi ta ce "Thank you dear," sannan ta rungume Sameeha ta ce "I miss you sis," "Same here dear kinyi kyau," Sabeeha ta ce "Thanks," sannan suka gaisa da su Fauwaz nan aka cigaba da hotuna su Dija ma sunje cikin ankon su dark blue material irin na jikin su Rinaz. Su Mama da Lantana da Zainabu tare da sauran dangi sunje Mama kuwa anko suka yi da Ummi Aikuwa sunsha pics 'yan uku kuwa sai murnar ganin juna da Doctor suke. Da haka mutane kowa ya fita wajen taron banda su Maleek sai can sannan suka fita suna fita sojojin da suka yi layuka biyu sai hanyar da suka bayar a tsakiya suka sarawa su Maleek da Sabeeha ga masu video da hotuna na aikin su domin tunda aka fara bikin kullum sai sunje. Maleek rik'e da hannun Sabeeha suka fara tafiya akan carpet d'in dake shimfid'e a wajen kalar army green a hankali Sabeeha ke tafiya saboda har lokacin tafiyar ta bata dawo daidai ba Wanda a zahiri tafiyar ta bada style. Yana rik'e da hannunta suka k'arasa gaban wani dogon table inda manyan sojojin da suka dira a yau suke zaune cikin uniform a tare Maleek da Sabeeha suka sara musu gurin ya d'auki tafi sannan suka k'arasa wajen da Daddy tare da Abba ke zaune da Kuma Kawu Uncle kuwa yabar k'asar ma. Sabeeha kuwa cikin mamaki take kallon Abban su dama har da shi ko da yake ai taron bana yara bane bayan sun gaishe su suka tafi wajen da aka tana da domin su suka zauna. Table d'in yasha lemuka iri iri da snacks da Kuma fruits plate-plate. Ba b'ata lokaci aka fara gabatar da program d'in bayan manyan wajen sun yiwa ango da amarya fatan zama lafiya da yara na gari aka fara parate Wanda ya k'ayatar da mutane 'yan gidan televisions sai aikin su suke yi hakama masu hoto bayan sun gama sannan aka fara bawa amarya da ango gifts Wanda basu san adadin kud'i da motoci da gidajen da suka samu ba daga manyan ma'aikata abokan Daddy da suka je wajen ba da Kuma manyan sojojin da suka halacci taron ba harma da k'awayen Ummi da Doctor da Abokan Abba Kai sun kwashi dukiya ba kad'an ba. Su dai sai aikin godiya suke yi ga wata kulawa da suke bawa juna musamman Maleek da duk juyin da Sabeeha zata yi a idon sa mutanen wajen ma sun lura soyayya ce me k'arfi tsakanin su. Microphone aka bawa Maleek domin jin me zai ce karb'a ya yi ya mik'e tsaye cikin salon sa da sweet voice d'in sa ya yi sallama ya ce "All praise be to Allah subhanahu wata ala really I don't have any word that show you my happiness to everybody here I'm really appreciated then I wish all of you here to go back safely and thanks for attending this program thank u once again our soldiers wish u a safe journey," kallon Sabeeha ya yi kallo mai cike da so da k'auna ya ce "I really thanks Allah for special gift that he has given to me Rukayya u are special gift from Allah so I promise to take care of you like baby and I promise support you my lovely wife," murmushi kawai Sabeeha ke yi ga hawayen da ya taho mata ya Mai da kallon sa ga mutane ya ce "thank you once agains," tafi wajen ya d'auka. Kallon Sabeeha ya yi ya mik'ar da ita tsaye ya k'ara mata microphone d'in a bakinta a hankali ya ce "Say something dear," murmushi ta yi sannan cikin sassanyar muryar ta ta yi sallama ta ce "As my lovely husband say we thank to almighty Allah countlessly and everyone here thanks for your love our soldiers and our parents thank for ur supporting," tafi wajen ya d'auka sannan ta kalli Maleek ta ce "Let me use this opportunity to give a special thank to my hero my husband my happiness I love you more and more thank u for ur supporting then me too I promise to love u i promise to respect u in every condition," ta fad'a hawaye na zuba a idanunta hannu yasa yana share mata sannan ya rungume ta suna jin wani sanyi na ratsa su tafi aka dinga yi musu da hotuna. Da haka aka rufe taro da Addu'a cak Maleek ya d'auki Sabeeha duk da mutanen dake gurin ya nufi cikin gida da ita a kan gadon Ummi ya ajiye ta sannan ya ce "Baby bari naje na raka bak'i airport ko?" Mak'e kafad'a ta yi ta ce "Uhm uhm sai dai muje tare nima ai bak'i na ne," Zare ido ya yi ya ce "No baby stay here yanzu zan dawo fa," kukan shagwab'a tasa masa dole haka ya rik'e hannun ta suka fita suka aka bud'e musu bayan mota suka shiga suka nufi airport jiniya kawai ke tashi a garin wajen motoci talatin sukayi a haka suka k'arasa airport soldiers d'in suka su Kuma suka juya zuwa mota duk inda suka gilma sai an kalle su suka koma gida tare da sojojin Maleek d'in. [10/25, 8:52 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️ RUBUTAWA DAGA HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ) SADAUKARWA GA MY DAUGHTER SABEEHA BILKISU Z.YA'U (🅱️K) AISHA MAGAJI DABO (AMA) Page 28 Suna zuwa gida ana gama yin parking ya d'auke ta cak zuwa cikin part d'in Ummi bai damu da mutanen dake falon ba ya wuce Kai tsaye zuwa stairs. Sabeeha kuwa tuni ta b'oye fuskar ta a k'irjin sa saboda ganin su Mama da Ummi da Kuma Hajiya da ta yi ga su Sameeha da Sabreen da su Rinaz duk a falon. Zainabu kuwa idon ta kamar ya fad'i k'asa saboda kallo haka ma Lantana. Yana shiga d'akin Ummi ya zaunar da ita gefen gado "To sarkin jin kunya bud'e idon mun shigo d'aki," bud'e idon ta tayi tana yin murmushi. Ummi ce ta shiga d'akin tana yiwa Maleek hararar wasa dariya ya yi ta ce "Gaba d'aya kai ka zama mara kunya ko?" "Ummi ai ban jin kunya indai akan baby ne," girgiza Kai ta yi tare da fad'in "Kai ni bani waje ba wajen ka nazo ba," ta fad'a tare da k'arasawa wajen Sabeeha dake yiwa Maleek gwalo shi Kuma sai cika yake yana batsewa. "Yawwa Daughter bari na had'a miki ruwan wanka ko," kafin Sabeeha tayi magana Ummi ta shige toilet d'in ta had'a mata ruwan wanka da yasha kayan k'amshi da kayan gyara ta fito ta tana fad'in "Tashi kiyi wankan," daga haka ta fice. Tashi tsaye Sabeeha ta yi ta fara b'alle bottles d'in shirt d'in rigar sojojin dake jikin ta saurin rik'e hannunta Maleek ya yi sannan ya fara b'alle mata da kansa sai da ya gama sannan ta cire rigar saura farar t_shirt d'in ciki kawai ya Kai hannu zai cire mata tayi saurin rik'e hannunsa tana girgiza Kai "Ni ka kyale mun zan cire da kaina," "Ni kam bazan bari ba ni ne zan cire miki," shagwab'e fuska ta yi ta ce "Dagaske fa zan cire," shima ya ce "Uhm uhm fa ni zan cire miki," d'an juya idanu ta yi ta ce "Laa My kaji Ummi na Kiran ka," dariya ya yi ganin wai Sabeeha ce zata yi masa wayo ya ce "Ni banji ba," Jan hannunsa hanyar k'ofa ta yi ta ce "To zo muje kaji," suna zuwa k'ofar ta bud'e tana rik'e da hannunsa suna fita ta zare hannunta ta koma cikin d'akin da gudu tasa key. Dariya Maleek ya yi tare da girgiza Kai sannan ya nufi down stairs. Yana fita su Sabreen suka tashi da sauri suka nufi stairs domin tun shigowar su part d'in suke so su je su gana da 'yar uwar su amma Mama ta hana su ganin Maleek na d'akin. Sabeeha na wanka ta ji ana knocking ta jima sannan ta fito d'aure da towel ta bud'e musu k'ofar ganin su yasa ta sakar musu murmushi sannan ta nufi gaban mirrow ta zauna tare da fad'in "Sabreen dear dan Allah ki Kira Rinaz ta waya kice ta kawomun kaya," Sabreen bata ce komai ba sai da ta Kira Rinaz d'in bayan ta sanar mata sannan ta kalli Sabeeha ta ce "Dear wankan na meye?" Ta fad'a cikin sigar tsokana murmushi Sabeeha ta yi ta ce "Na shiga turakar miji ne," sai Kuma dukan su suka tuntsire da dariya. "Wallahi sister abun nan da wuya yaseen," dariya Sabeeha ta yi sannan ta ce "Ai garama ke sis Wallahi," Sameeha kuwa tsuru-tsuru ta yi da ido bata ce komai ba domin ita maganar su ma ta gama tsorata ta "Ke Sameeha dear yadai?" Sabreen ta fad'a tare da kallon Sameeha itama Sabeeha ita take kallo. "Dan Allah sisters da wuya?" Sameeha ta fad'a idanunta taf k'walla "Bangane da wuya ba kina nufin Wai jiya ba abinda ya faru?" Sabreen ta tambaya cike da mamaki. "Amma dear jiya da zazzab'i na kwana fa," cewar Sameeha har Sabreen zata yi magana Sabeeha ta rigata da cewa "Kinga manta sister ba wani wuya," ajiyar zuciya Sameeha ta sauke Sabeeha kuma ta cigaba da tufke gashin ta da ribbom. Rinaz ce ta shiga d'akin da kaya a hannunta a kan gado ta ajiye tare da fad'in "Sabeeha dear ga kayan," tana fad'in haka ta fice tana dariya k'asa-k'asa. Bin k'ofar da kallo Sabeeha ta yi sannan ta d'auki kayan ta bud'e zare ido Sabeeha ta yi ta ce "Me Rinaz habibty ta mayar dani da zansa wannan rigar," ta fad'a tana d'aga rigar da idan tasa baifi iya gwiwa ba gashi rigar d'aya dogon hannu ne d'ayan Kuma siriri sannan bayan rigar a wawake yake sai igiyoyin d'aurewa rigar dark blue ce sai wasu duwatsu masu kyalli daga saman rigar. Jefar da rigar saman gado Sabeeha ta yi tana tura baki ta ce "Ni dai kam gaskiya bazan sa wannan arniyar rigar ba," dariya Sabreen tasa ta ce "Amma fa rigar ta yi kyau fa sosai dear to meye matsalar da baza ki saka ba?" "Haba dear har yaushe na zama mara kunyar da zan saka wannan rigar Kuma a part d'in Ummi haba mana sis," "Sabeeha dear da rigima kike Wallahi to kisa mana sai kisa hijabi," Sameeha ta fad'a ita dai shiru ta yi ba kuma alamun zata sa rigar sai ma d'auko hijabi da tayi tasa ka ta zauna suka d'ora da fira har magriba lokacin suna d'aki suna fira har su Doctor sun tafi basu saniba. Sallah suka yi suna zama aka k'wank'wasa k'ofar d'akin k'amshin turaren Umar kawai Sameeha ta ji da sauri ta mik'e ta yi hanyar toilet tana cewa "Dan Allah kuce mishi bana nan wallahi tsoron binsa nake yi," kafin su yi magana har ta sige ta tura k'ofar. Sabeeha ce ta ce "Shigo," tura k'ofar d'akin ya yi ya shiga suka gaisa da su Sabeeha sannan ya ce "Sisters Meeha fa?" Da sauri Sabreen ta ce "Tana ciki wai gudar maka tayi," dariya ya yi sannan ya k'arasa k'ofar toile d'in ya murd'a handle d'in k'ofar a bud'e take ya rik'o hannunta ya fito da ita yana fad'in "Meeha meye na gudun taho mu tafi gida ko?" Shiru Sameeha ta yi sai raba idanu da take yi. "Sabreen sister Sabeeha dear sai da safe," Sameeha ta fad'a "To asuba ta gari dear," cewar Sabreen girgiza Kai Sabeeha ta yi ta ce "Sannu fa," Ummi ce ta shiga d'akin tana fad'in "Wai me ku ka zauna yi a bedroom har yanzu kofa abinci baku ci ba," Sabreen ta ce "A'a Ummi ni da Sameeha dear munci d'azu wajen taro Sabeeha Sister ce Kawai bata ci ba," Fauwaz da sigowar sa kenan ya ce "My love an gama firar haka ki taho mu tafi," tashi Sabreen ta yi ta ce "Ok muje my heart Ummi dear sai da safe," ta fad'a tare da bin bayan Fauwaz. Kallon Sabeeha Ummi ta yi ta ce "Daughter bari na kawo Miki abinci," bata jira cewar ta ba ta fita bata dad'e ba sai gata da ture Mai d'auke da flask d'in abinci da drinks ta ajiye a kan k'aramun table d'in dake d'akin ta zuba mata jallop d'in shinkafar da coslow a plate sai peppe chicken. Daidai lokacin Maleek ya shiga d'akin sai bulbula k'amshi yake yi ga wani kyau da ya yi ciki k'ananun kaya blue black trouser da white riga ya yi kyau sai wata blue black da ya d'ora a sama Mai kamar ta sanyi domin iska ake a garin ga Kuma hadari ya had'o a garin. Tunda suka amsa sallamar sa idanunsa na kan Sabeeha kusa da ita ya zauna sannan ya karb'i plate d'in hannun Ummi da take mik'awa Sabeeha ya ce "Ummi kawo na bata," Ummi bata ce komai ba ta bashi sannan ta bar musu d'akin tana fita Maleek ya d'ebi abincin a spoon ya ce "Oya bud'e bakin baby," ba musu ta bud'e ya fara bata har sai da ta k'oshi sannan ya ajiye ya bata ruwa ta sha. "Baby taso mu tafi," shagwab'e fuska ta yi ta ce "To ba ba kayana a nan ba," ta fad'a kamar zata yi masa kuka "Wannan fa baby?" Ya fad'a yana kallon rigar dake gefen ta ta ce "Wai fa Rinaz habibty nace ta kawo mun kaya shine ta kawomun wannan rigar kumama ni baran iya sawa ba," murmushi ya yi tare da d'aga rigar ya ce "Wow baby rigar tayi mun kyau kisa please," d'an shiru ta yi sannan ta ce "To zansa but sai ka fita sannan," d'an zare ido ya yi ya ce "Haka fa d'azu ki ka kore ni dan haka yanzu ba inda zani," ya fad'a yana wani had'e rai ita dariya ma ya bata ta dake ta ce "Ok shikenan Bari naje bathroom nasa," ta fad'a tare da mik'ewa shima mik'ewar ya yi ya rik'e ta ya ce "Ba fa inda zaki kawo rigar nasa Miki," bai jira cewar ta ba ya amshi rigar ya fara k'ok'arin cire mata dogon hijabin jikin ta. Rintse idanu kawai ta yi domin bata so su cigaba da sa'in sa tana ji ya zare mata towel d'in jikin ta yana k'arewa surar ta kallo jin shiru baisa mata rigar bane yasa ta tura baki tana bubbuga k'afa cikin shagwab'a ta ce "Ni dai kayi sauri ka samun fa Ina so na bud'e idona," ajiyar zuciya ya sauke ganin yadda duk jikin ta ke motsawa saboda buga k'afar da take yi sannan ya sa mata rigar. Yana gama sa mata ya ce "Wow u are so cute baby looking so amazing my wife," ya fad'a tare da yi Mata wata kyakkyawar runguma ya ce "Oya open your eyes cutie look at ur husband," a hankali ta fara bud'e kyawawan idanunta masu d'auke da zara-zaran eyelashes ta kalle shi shafa sumar kanta ya yi ya ce "Muje ko," ya fad'a tare da sa mata hijabi tasa takalmi suka fita daga part d'in ba tare da sun yiwa Ummi sallama ba. Bud'e musu mota aka yi ya shiga driver seat ita kuma front seat ya jasu suka tafi direct d'ayan part d'insa shi kad'ai ya nufa bata ce da shi komai ba suna shiga falon Sabeeha ta baje saman kujera Maleek Kuma ya haura stairs yana fad'in "Time d'in sallah ya yi bari naje nayi alwala na wuce masjid," noding kanta kawai ta yi. Tana zaune har ya fito ya tafi masallaci har ya dawo tana wajen sai dai har ta fara bacci d'aukar ta ya yi ya nufi bedroom da ita ya kwantar da ita tare da zare mata hijabin yana binta da wani irin kallo cire shirt d'in jikin sa ya yi wayar sa ce ta fara ringing ya d'aga daga can Ummi ta ce "Wato shine ka ja daughter ku ka tafi ko to zo ka amsar mata maganinta sannan kar a sake a sake maimata irin ta jiya a barmun daughter ta huta," tana fad'ar ta katse wayar shi Kuma ya nufi k'ofar fita. Yana fita babu dad'ewa Sabeeha ta tashi domin ita idan har bata yi sallah ba bata iya bacci sai kawai ta d'auro alwala ta shiga dressing room d'insa ta d'auki wani wando robber tasa tayi sallah sannan ta mayar masa ta koma ta kwanta domin baccin da take ji. Ko da ya dawo ya samu har bacci ya fara d'aukar ta fara Kiran ta ya yi "Baby ki tashi Kisha magani," ai jin an ambaci magani yasa ta k'ara rintse idanunta kamar wacce bacci Mai nauyi ya yi gabas da ita. "Idan fa baki tashi ba ko yaseen sai nace sai nayi irin ta jiya," kafin ya k'arasa har ta mik'e zaune tana tura masa baki baice komai ba sai maganin da ya bata tasha sannan ya mik'e ya shiga bathroom ya yi wanka sai da ya gama Shirin sa ya feshe jikin sa da turare sannan ya kwanta kusa da ita ya jawota jikin sa ya rungume k'ara mak'alk'ale shi ta yi domin tana jin dad'in jinta a jikin sa sosai a haka bacci ya kwashe su. Sameeha kuwa duk zillewar ta sai da taba Umar hakk'in sa tab aikuwa langwai ta dinga yi masa Yana aikin rarrashi. Tom haka dai rayuwar su ta cigaba da kasancewa cikin farin ciki da k'aunar junan su har aka yi sati biyu da bikin. Sabeeha ce zaune akan kujera a babban falon part d'in su riga da wando ne a jikin ta duk pink ta yi kyau har ta gaji ta kitse gashin ta a gefe kanta apple take ci sai earphone da tasa tana sauraro wak'ar jaywillz (medicine) gyad'a kai take yi a hankali domin wak'ar tayi mata dad'i sosai. Maleek ne ke saukowa daga stairs yaci gayu sosai cikin wata maroon shadda ba k'arya sai Nasreen dake bayan sa domin daga d'akin ta ya fito tana biye da shi har suka k'arasa cikin falon. Tunda suka k'arasa falon idanunsa ke kan Sabeeha da Sarai taji takun tafiyar su sai dai bata kalli inda suke ba b'ata san dalilin da yasa take jin ba dad'i ba duk sanda Maleek ya kwana a d'akin Nasreen ba gashi Nasreen d'in duk sanda ya kwana d'akin ta ta dinga iyayi kenan duk sanda ya fita haka zata je wajen da Sabeeha ke zaune tana fad'in "Wash Amma yau ya Maleek ya wahalar dani sai dai ya lashi zumar da bai samu ba wajen wata ya fad'amun cewar Yana jin dad'i na sab'anin wata," haka zatai ta magana tun abin na damun Sabeeha har ta dena damuwa domin ita Sam ba mai son rigima bace. Zama kusa da ita Maleek ya yi ya zare mata earphone d'in dake kunnen ta had'e da fad'in "Baby baki ga mijin ki bane," murmushi ta sakar masa ta ce "Ina kwana," "Lafiya cutie," ya fad'a tare da karb'ar apple na hannunta ya fara ci Nasreen dake gefe a tsaye ta cika tayi fam kallon ta Sabeeha ta yi ta ce "Ina kwana," tsaki Nasreen ta ja bata amsa ba Sabeeha bata damu ba domin dama duk sanda zata gaishe ta bata amsawa. "Baby zan fita saina dawo," "Amma My ai baka yi breakfast ba," Sabeeha ta fad'a tana kallon cikin idanunsa juya idanunsa ya yi ya ce "To baby ya zanyi bayan ba a bani ba zanje wajen Ummi nayi before na fita amma ki dafa mun abinci idan zan dawo," ta ce "Ok shikenan," kiss ya bata a check d'in ta sannan ya mik'e saurin sha gaban sa Nasreen ta yi ta ce "Bangane tayi maka abinci ba ai ba girkin ta bane," "D'an bani hanya mana nifa kinsan bazan ci abincin ki ba domin baki iya ba tun farko ke kika yiwa kanki da baki tsaya kin koya ba," yana fad'ar haka ya matsar da ita gefe ya fice. Nasreen ta ce "To munafuka Wallahi sai kin bar nan gidan sannan idan har kin isa na ganki kina yi masa girkin," ko kallon ta Sabeeha bata yi ba ta mik'e ta nufi hanyar stairs tabar banza a wajen. Tsaki Nasreen ta ja sannan ta zauna akan kujera ta zabga tagumi sai Kuma ta fashe da kuka sai da ta gama kukan ta sannan ta mik'e ta shige bedroom d'in ta. Sabeeha kuwa tana shiga d'akin ta ta zauna gefen gado ta Kira Sabreen suka yi firar su sannan ta tashi ta d'auki dogon Hijabi tasa ta d'auki wayar ta ta fice ko da ta fita falo bata samu Nasreen ba sai kawai ta fita. Tana fita driver tasa ya kaita har k'ofar part d'in Ummi da sallama ta shiga falon Ummi kad'ai ta samu a falon kasancewar weekend ne bata fita office ba Daddy kuwa tun bayan biki ya koma Dubai Rinaz Kuma ta tafi karatu India dan Daddy cewa ya yi dole ne ta tafi makaranta tana kuka tana komai haka ta shirya ta tafi. A k'asan carpet ta zauna ta gaida Ummi cikin fara'a Ummi ta amsa ta ce "Daughter kin tashi lafiya?" "Lafiya lau Ummi," Sabeeha ta fad'a tare da mik'ewa ta nufi kitchen tana fad'in "Ummi bari naje kitchen d'in ki yunwa nake ji," ta fad'a tare da shigewa cikin kitchen d'in ta samu kuwa akwai abubuwan ci kala kala zubawa ta yi ta fita falo ta zauna ta fara ci sai da ta k'oshi sannan ta mayar da plate d'in kitchen ta fito suka yi ta fira da Ummi har Fauwaz ya shiga ya same su gaisawa suka yi sannan ya zauna aka cigaba da firar da shi. Sai yamma sannan Sabeeha ta yiwa Ummi sallama ta tafi tana shiga part d'in su ta samu Nasreen a zaune kan kujera 'yan aiki zagaye da ita sai wani karkad'a k'afa take yi kallo d'aya Sabeeha ta yi Mata ta d'auke Kai ta nufi stairs. Tana shiga d'aki hijabin ta kawai ta ajiye tana zama ta tuna da girkin da Maleek yace tayi masa da sauri ta mik'e daidai lokacin wayar ta ta fara ringing ko ba a fad'a Mata ba tasan shine domin ring tone d'in sa daban ne d'aukar wayar ta yi sannan ta nufi kitchen tana cewa "Hello my," Daga can ya ce "Wato Baby ni kika manta ko?" Ya fad'a kamar wani k'aramin yaro mai shirin kuka "Ayyah sorry My ina wajen Ummi ne shiyasa," "Ohk kina wajen Ummi shiyasa ki ka manta dani ba?" Zare ido ta yi ta ce "No ba haka bane kasan dai bazan manta da Kai ba koh ayimun afuwa," ta fad'a tana sakin murmushi. D'an shiru ya yi sannan ya ce "Shikenan an hak'uran Miki amma idan ki ka k'ara fa?" Wannan karon dariya tayi ta ce "Sai a yafe mun," shima dariyar ya yi ya ce "Zaki yi bayani ne yarinya," haka suka cigaba da yin waya tana yin aikin ta yana jinta sannan suka yi sallama ta ajiye wayar ta cigaba da aikin ta. Sai da ta gama tas sannan ta jera komai a daining d'in dake falon ta ta fad'a toilet tayi wanka tare da alwalar sallar magrib tana fitowa ta shafa mai ta zira wata rigar atamfa bak'a ce atamfar sai ratsin ja a jiki hijabi ta saka tayi sallah sannan ta zauna d'auki k'aramun veil ta yafa a kanta ta fita falo ta zauna tare da kunna TV. Jin k'arar bud'e gate ne yasa ta gane Maleek ya dawo bata motsa ba domin tasan ba girkin ta bane bare taje tarar sa cigaba da shafa jikin pretty tayi wacce tayi b'ulb'ul kamar ka sace ta ka gudu. Maleek kuwa da sallama ya shiga falon ko amsawa Nasreen bata yi ba sai zuwa da tayi cikin iyayi tana niyyar rungumar sa hararar da ya aika mata ce yasa ta tsaya ya yi Mata kallon up and down ya wuce zuwa cikin d'akin sa. Wanka ya yi yana cikin shiryawa Nasreen ta shiga d'akin ko kallo bata ishe shi ba ya fesa perfumes a jikin sa wayar sa ce ta fara ringing ganin Mai Kira yasa shi sakin murmushi ya d'aga daga can Sabeeha ta ce "Na kawo ma abincin nan?" Ya ce "No gani nan zuwa a gurin ki zanci," daga haka ya kashe kiran ya nufi hanyar fita da kallo Nasreen ta bisa har ya fice. Da sallama ya shiga falon ta da tun kafin ya k'arasa shiga k'amshin sa ya daki hancin sa amsa sallamar Sabeeha ta yi sannan ta tashi a hankali ta isa gare shi ya bud'e mata hannu ta fad'a jikin sa ya rungume ta ta ce "Sannu da dawowa," "Yawwa Sabee na," ya fad'a tare da jan hannunta zuwa cikin falon yana fad'in "Baby yunwa," har daining suka k'arasa tayi saving d'in sa abinci ta tura masa plate d'in gaban sa sai ta ga ko kallon abincin bai yi ba ta ce "Yadai my kace kana jin yunwa ga abincin nan," hararar wasa ya yi mata yana niyyar mik'ewa zare ido tayi ta ce "Sorry my zauna na manta," zaman ya yi ta fara feeding d'in sa abincin har ya k'oshi sannan shima ya bata har ta k'oshi sannan suka koma cikin falon ya zauna ya zaunar da ita saman cinyar sa suna fira sannan ta zame ta kwanta a jikin sa yana shafa lallausan gashin kanta. Nasreen dake lek'en su ta koma d'akin ta ta fara zage-zage ta d'auki wayar ta ta kira Hajiya Asiya ta fad'a mata aikuwa itama ta dinga masifa tare da cewa gobe zata je har gidan. Sabeeha kuwa bacci ne ya kwashe ta a jikin sa tayi wajen minti talatin tana baccin sannan ta d'anyi juyi saurin rungume ta ya yi a jikin sa gudun karta fad'i k'asa jin an rik'e ta ne yasa ta yin mik'a a jikin sa wanda hakan ya tafi da imanin sa bud'e idanu ta yi ta kalle shi sai ta kuma zare idanu domin ita ta ma manta a inda ta yi baccin murmushi ya sakar mata ita kuma ta mik'e tsaye tana murza idanu ta ce "My dama kana nan baka tafi ka kwanta ba?" "To kin danne mun jiki kina bacci ta ya zan tafi?" Tura baki tayi ta ce "To ka tashi kaje ka kwanta ka ga fa dare yayi," hararar ta ya yi tare da fad'in "Au korata ma kike yi?" "A'a ba korar ka nake ba fa kawai dai naga dare ya fara ne Kuma ka ga ai Nasreen zata jira ka karta ga ba ayi mata adalci ba," tashi ya yi bai ce komai ba ya tsaya a gaban ta tasan me yake nufi Dan haka ta rungume shi tare da kissing d'in sa ta ce "Goodnight and sweet dreams my husband," "Same to you Sabee na," ya fad'a tare da ficewa binsa ta yi da ido har ya fita sannan itama ta shige bedroom d'in ta ta yi alwala tayi sallah isha'i sannan ta canja kayan jikin ta zuwa na bacci ta kwanta kusa da pretty dake ta bacci. Washe gari da wuri Maleek ya fita domin suna da meeting lokacin da ya shiga d'akin Sabeeha bacci ma take yi Dan haka ya fita ko Break fast bai yi ba domin Sabeeha ce mai yi masa Kuma itama bacci take. Tana tashi kuwa dama tayi sallah da asuba d'akin ta fara gyarawa sai da ta gama tas ta turare ko Ina da turaren wuta sannan ta shiga kitchen ta d'ora breakfast tana gamawa ta jera komai a daining ta shiga d'aki tayi wanka sannan ta fita falon tana mamakin jin Maleek shiru wayar ta ta d'auka ta fara Kiran wayar sa yana d'agawa ta ce "My kana lafiya naji har yanzu baka fito ba?" Dariya ya yi ya ce "Baby ina NDA ne fa muna da meeting amma na kusa dawowa," ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce "Amma ko ka tashe ni nayi maka breakfast ko kaci wani Abu ne?" "Ba abinda naci Kuma Ina jin yunwa," ya fad'a kamar zai yi mata kuka ita Kuma cikin rarrashi ta ce "Ayyah sorry baby kayi sauri ka dawo kaji kaci abincin," "To baby amma fa bayan abincin har da ke kinsan nayi kewar kwana biyun nan," dariya tayi ta ce "Ba kada case My sai ka dawo d'in," daga haka ta ajiye wayar ta nufi down stairs jin ana k'wala mata kira. Hajiya Asiya ta gani a tsaye sai huci take yi bata damu ba ta k'arasa ta ce "Ina kwana?" Ko amsa gaisuwar bata yi ba ta fara sirfa masifa "Ke dan uwar ki daughter sa'arki ce da duk ranar girkin ta ki ke yiwa mijin ta girki ko ce Miki aka yi ita bata iya ba?," Sabeeha cikin jin hausin zagar Mata mahaifiyar ta da aka yi ta ce "Eh," wani wawan mari umman Nasreen ta sauke mata a fuska daidai lokacin Sabreen ta shigo da sauri ta k'arasa ta ba tare da shakkar komai ba ta d'aga hannu ta wanke fuskar Nasreen da mari zazzafa sannan ta nuna Hajiya Asiya da hannu ta ce "Darajar girman ki ne kawai yasa bazan ramawa Sabeeha dear marin da ki ka yi mata a fuskar ki ba amma na rama a fuskar jakar 'yar ki dan Wallahi sai na baki mamaki akan Sabeeha," daga Umman nasreen har Nasreen d'in mutuwar tsaye suka yi domin rashin kunyar Sabreen ta wuce tunanin su. Sabeeha kuwa hawaye ne kwance a fuskar ta domin Marin ya shige ta sosai wajen ta Sabreen ta koma ta fara share mata hawayen fuskar ta "Lallai kun d'ebo ruwan dafa kanku ina tabbatar muku sai na gyarawa dukan ku zama," Hajiya Asiya ta fad'a harara Sabreen ta zabga mata ta ce "Allah ya tsinewa Wanda ya fasa," daga haka ta ja hannun Sabeeha suka nufi stairs. Suna shiga falon suka zauna Sabreen sai huci take yi ta ce "Tunda na tashi naji kawai ke nake so nagani na takurawa my one sai da ya kawoni ashe dama abinda zan tarar kenan yanzu ke dear dama abinda suke Miki kenan ki ka zuba musu ido to Wallahi indai suka Kuma yi miki kivi uban 'yan iska Wallahi har uwar ta karki ragawa," share hawaye Sabeeha ta yi ta ce "Bana so Ina kula su ne saboda a zauna lafiya kinsan halina idan na fara ramawa baza a ji da dad'i ba," Sabreen ta ce "Ai gara ki dinga ramawar domin shirun da ki ke yi ne yasa suke to miki hakan domin sunga suna cin banza," Sabeeha ta ce "Baza ki gane ba dear duk sanda nayi niyyar ko fad'awa Nasreen magana ne sai nasihar su Abba ta fad'o min a rai shiyasa nake kyale su ba wai dan sun fi k'arfina ba," ajiyar zuciya Sabreen ta sauke ta ce "Shikenan amma ya kamata ki duba lamarin," Sallamar Maleek ne yasa suka mayar da hankalin su wajen sa da sauri ya k'arasa wajen Sabeeha yana tambayar ta lafiya domin da ganin ta ba saika tambaya ba taci kuka ta k'oshi. Hawayen da suka zubo Mata ta goge ta ce "Bakomai fa kawai kaina ke mun ciwo," "Amma Baby yanzu fa muka gama waya dake lafiya?" Ya fad'a domin bai yadda da abinda ta fad'a ba. Jikin sa kawai ta kwanta zata yi magana kenan Sabreen dake gefe ta ce "Wallahi Ya MG k'arya dear take yi yanzu na shigo na samu Nasreen da mahaifiyar ta sun sata a gaba ita babar Nasreen d'in har da Marin ta," Da sauri ya d'ago fuskar ta ya kalla aikuwa gurin yayi ja har da shatin yatsu baice komai ba ya mik'e Sabeeha na Kiran sa amma ko waigawa bai yi ba ta kalli Sabreen ta ce "Meyasa zaki fad'a masa dear," ko a jikin ta Sabreen ta ce "Saboda nasan ko zai yi hak'uri akan komai banda a kanki hakan ne yasa na fad'a masa domin ya yiwa tufkar hanci danni ba mutunci na fiya ba indai a kanku ne," shiru kawai Sabeeha tayi ba magana. A zafafe Maleek ya shiga d'akin Nasreen inda suke zaune suna kitsa makirci ita da mahaifiyar ta ba Nasreen ba hatta Hajiya Asiya sai da ta tsorata da ganin da ganin yanayin Maleek. Saurin tashi Nasreen ta yi ta ce "Ya Male..," Marin da ya sauke mata ne ya hanata k'arasa maganar da zata yi ya nuna ta da yatsa ya ce "This is the first and last warning da zanyi miki akan Baby ki fita hanyar ta domin a kanta saina iya d'aukar ko wanne irin mataki a kanki domin bazan d'auki iskanci ba kin kuma San da hakan then ki jawa mahaifiyar ki kunne Ina ganin girman ta nan ba gidan ta bane nawa ne saboda haka karta kuskura na sake ganin k'afar ta a ciki idan kuwa ba haka ba zan d'auki mataki," daga haka ya wuya ya fita ba tare da ya kalli inda Umman Nasreen take ba. Kuka Nasreen ta fashe da shi ta ce "Kin gani ko Umma Wallahi baya sona yafi son waccan yarinyar ko da da nake yi masa abubuwa bai tab'a marina ba sai yau ko k'ok'arin kashe shi da muka yi bai yi tunanin dukana ba amma ki duba akan waccan jakar yarinyar har marina ya yi hakan yana nuna tsantsar soyayyar da yake Mata ne ke kanki yace karki sake zuwa kawai ki Kira Uncle ki fad'a masa," Cikin takaici Hajiya Asiya ta girgiza Kai ta ce "Ba sai an fad'awa mahaifin ki ba Ni da ke k'adai ya isa muji da Sabeeha tare da 'yar uwar ta mahaifin ki kuwa ko ban ce komai ba dama Yana Nan yana gudanar da aiki akan wannan wawan yaron nan da lokaci k'alilan Zaki ga abinda zai faru Wanda zai tarwatsa rayuwar sa da ta iyayen sa da duk wani Wanda ya dangance sa ke wannan yarinyar da ki ke gani mune ajalin ta har shi mijin nata dama na fad'a Miki ba k'aunar ki yake yi ba har da ki ke zancen komawa gidan sa yanzu Kinga abinda nake fad'a Miki?" "Na gani Wallahi nagani Umma Kuma na goyi bayan ki ke da Daddy kuyi duk abinda ya dace," wata shegiyar dariya Hajiya Asiya ta yi ta ce "Ai kin da zamu baki na Nan kusa Kuma zamu yi nasara a kansu sai sun gwammace kid'a da karatu ni zan tafi duk yadda ake ciki zan yi miki waya domin bazan sake zuwa ba kinsan wannan d'an iskan ba abinda bazai iya ba akan waccan aljanar yarinyar kafin mu tarwatsa musu rayuwa ke dai abinda nake so dake kafin wannan lokacin ki hana gidan nan zaman lafiya," gyad'a kai Nasreen ta yi ta ce "An gama," suka yi dariya har da tafawa sannan Hajiya Asiya ta fita. Maleek kuwa d'akin Sabeeha ya koma ya same ta a zaune inda ya barta janta jikin sa ya yi ya rungume ya ce "Kiyi hak'uri kinji baby Kuma na rama miki," shiru tayi ba magana ya ce "Kinyi breakfast kuwa?" Girgiza Kai ta yi ta ce "Muje suna daining," dukan su suka nufi daining daidai lokacin Fauwaz ya yi sallama tare dukan su suka nufi daining d'in suka yi breakfast sannan suka koma falo suna ta fira Sabeeha dai tana mak'ale a jikin Maleek. Ranar yini suka yi a gidan sannan suka tafi da daddare kuwa masoyan biyu Maleek da Sabeeha sun faranta ran juna da daddad'ar soyayya. Washe gari tun safe Nasreen ta cika gidan da kid'a kamar gidan zai tsage duk dan neman ayi rigima amma ko Maleek baice komai ba duk da kid'an ya dame shi wanka suka yi sannan suka shiga kitchen tare suka yi breakfast suka ciyar da juna sannan suka koma falo suka zauna kad'a kai Sabeeha ta fara domin kid'an ita dad'i ma ya yi mata ta tashi ta fara rawa abinta Maleek kuwa sai dariya yake yi mata. Haka tai ta rawa har ta gaji sannan ta fad'a jikin sa a gajiye peck ya bata a check d'in ta ya ce "Sannu da aiki Baby," tura baki ta yi ta ce "Bayan baka tayani ba," dariya ya yi har dimples d'insa suka lotsa sosai ya ce "A'a ai naga abin na manyan k'wari ne," itama dariyar ta yi ta ce "My muje wajen Ummi," ya ce "To muje," hijabin ta tasa suka fita hannun su rik'e dana juna ta gaban Nasreen suka wuce basu ko kalli inda take ba wani k'ululun bak'in ciki ne ya turnik'e mata zuciya. Shi yayi driving d'in su har k'ofar part d'in Ummi suna shiga suka samu Ummi zaune tana danna laptop gefen ta suka zauna suka gaishe ta ta amsa cikin fara'a ta ce "Daughter jiya gaba d'aya baki lek'o ni ba," dariya Sabeeha ta yi ta ce "Ai Ummi yau a nan zan kwana," harara Maleek ya aika mata ya ce "Ummi karki yadda k'arya take yi," "A'a ni d'iyata bata k'arya na ma fad'a maka," Sabeeha ta gyad'a Kai irin fad'a masa d'in nan "Yawwa Son nasan baku je kunyi wa Maryam gajiyar biki ba ya kamata kuje," "Insha Allah zamu je," ranar dai yinin part d'in Ummi suka yi a nan Sabeeha tayi musu girki suka ci sai dare sannan ya ce "Baby taho mu tafi," mak'e kafad'a ta yi ta ce "Ka manta yau a nan zan kwana kuma a tambayi Ummi ma," Ummi na jinsu bata ce komai ba had'e fuska ya yi ya ce "Ki tashi fa nace," aikuwa ta k'ank'ame Ummi ta ce "Ni dai bazan bika ba," Ummi kuwa mik'ewa ta yi ta nufi d'aki saboda Kiran da Daddy ya yi mata. Cak ya d'auke ta yayi hanyar fita daga part d'in sai wutsil-wutsil take yi ya ce "Yarinya Zaki sani ne," a mota ya sata sannan shima ya shiga suka nufi part d'in su. Yana yin parking ta fita daga motar ta nufi k'ofar shiga babban falon gidan ita a lallai ta yi fushi Dan ya hanata kwana part d'in Ummi tana shiga bata lura da b'awon banana da aka zub'e su da yawa a k'ofar falon ba Aikuwa ta taka abinka da tiles ya jata zuuu ta tafi luuu zata fad'i saurin rintse ido ta yi domin tasan dole ne ta Kai k'asa sai Kuma ta jita a jikin mutum a tare suka sauke ajiyar zuciya saboda yadda ya ga ta tafi da ta fad'i tabbas sai ta karye a hankali ta bud'e idanunta ta sauke su a kyakkyawar fuskar mijinta sannan ta kalli k'asa domin ganin me ta taka. Kana kallon yadda b'awon bananar da yawa kasan da gayya aka zube su a wajen kallon gefe ta yi can ta hangi Nasreen tana lek'e ta k'ofar kitchen ko ba a fad'a mata ba tasan aikin Nasreen ne "Me kike kallo ne haka?" Maleek ya tambaya ta ce "Bakomai mu tafi," wata 'yar aiki Maleek ya ga ta fito daga kitchen nan ya fara balbala masifa akan sunbar waje da dirty irin haka duk ranar da suka Kuma a bakin aikin su zubewa ta yi tana bashi hak'uri bai damu ba ya ja hannun Sabeeha taku d'aya ta yi tasa masa kukan shagwab'a a rud'e ya ce "Baby da wata matsalacce?" Bubbuga k'afa ta fara yi ta ce "Toba k'afana ke yi mun zafi ba ni bazan iya tafiya ba sai dai ka goyani," kallon ta ya tsaya yi yasan ba wani k'afar ta dake zafi tsabar rigimace kawai irin na ta ya ce "Wannan ai shi yafi komai sauk'i," ya durk'usa ta haye suka nufi stairs. Nasreen dake lab'e kuwa wani bak'in ciki ne ya turnik'e ta a fili ta ce "Ai Wallahi gara ma duk ku mutu a huta," wata 'yar aiki dake bayan ta ta ce "Hajiya su mutu Kuma?" Da sauri Nasreen ta juya ta kalli Jamila dake tsaye domin batasan a fili ta yi maganar ba ganin Jamila ce Kuma ta aminta da ita sai ta ce "Eh Jamila so nake su mutu kinsan Ina son Ya Maleek ai ko?" "Eh sosai ma kuwa ranki ya dad'e," Jamila ta fad'a tana russunawa "To amma shi baya sona yafi son waccan aljanar saboda haka sai naga bayan su," Jamila irin jahilan k'auyen nan ce ba wata babba bace Amma ta girmi Nasreen 'ya'yan ta biyu suna wajen mahaifiyar ta ta ce "Ai ranki ya dad'e nima lokacin da nake da aure haka babban yarana ya auro wata ya nuna Mata so fiye dani sai kawai nabi dare na kashe shi kowa ma ya rasa," dariya Nasreen ta yi ta ce "Gaskiya za aje dake Jamila dan haka zan had'a kai dake," Jamila ta ce "Baki da matsala domin har yanzu ba Wanda yasan ni na kashe mijina an d'auka b'arayi ne," Nan suka cigaba da firar su. Maleek kuwa suna shiga d'aki ya ajiye ta saman gado sannan suka shige wanka bayan sun fito ko kaya basu tsaya sawa ba suka shige blanket suka fara farantawa juna rai. A haka aka yi sati d'aya kullum da irin tsokana da neman fad'an da Nasreen zata yi amma basa kula ta domin sun Mai da ita mahaukaciya Maleek kam baisan kulata ne domin idan yace zai biye mata sai ya karyata ya zubar. Maleek ne zaune a d'ayan part d'insa shi da Salman ya kalli Salman ya ce "Salman a yau nake so kuje ku yi abinda nasa ku kuje," Salman ya ce "Ok boss," Yana fad'ar haka ya fice. Mota biyu na sojoji suka yi suka nufi k'auye suna zuwa nesa da gidan sadam suka yi parking suna cikin mota basu fito ba wani mak'ocin Sadam ya fito daga gidan sa Horn Salman ya danna masa kallon wajen mutumin ya yi aka Kuma yi masa horn wajen motar ya nufa Yana jin d'ard'ar sai da ya kusa da motar sannan ya tsaya ya nannad'e hannun rigar sa da k'afar wandon sa a zuciyar sa yana fad'in saboda ko abun gudu zai kama sai inda maina ya k'are. Yana k'arasawa wajen Salman ya sauke glass ganinsa da kayan sojojine yasa mutumin k'ara rud'ewa Salman ya bashi hannu suka gaisa sannan Salman ya ce "Sunanka fa?" Mutumin ya ce "Sunana Sunusi," jinjina Kai Salman ya yi ya ce "Dama munzo nan ne domin mu nemi mai yi mana aiki mutum d'aya kamar yadda ka gani mu sojojine sannan aikin ba wamu za ayi shi ba ogan mu ne yake so a samu Mai yiwa mahaifiyar sa aiki," jinjina Kai sunusi ya yi ya ce "Kai amma naso ni ne zani aikin nan amma ba dama domin a gidana da iyalaina da mahaifiya ta Kuma nine komai nasu bazai yuwu na barsu ba," "Ka ga malam sunusi ba lallai fa sai Kai ba," Salman ya fad'a domin ai dama aikin su ba a kansa bane. Sunusi ya ce "Shikenan amma akwai wani Mai suna sadam aikin yi yake nema ido rufe ko wanne iri ne saboda duk garin nan da ba Wanda ya Kai shi kud'i yanzu Kuma yafi kowa talauci sannan kum...," Salman ya ce "Is enough Kira mana shi," juyawa sunusi ya yi a zuciyar sa yace is enote d'in yake nufi oho da ganinsa dai d'an gayu ne sallama ya rangad'a k'ofar gidan Sadam daga ciki Salman ya amsa ya fito duk ya canja kamanni kamar ba shi ba bayan sun gaisa Sunusi yayi masa bayanin abinda ke faruwa cikin jin dad'i Sadam ya fara yiwa sunusi godiya shi kuwa sunusi sai wani hura hanci yake yi Wai shi a lallai ya yiwa wani hanyar arzik'i. Wajen motar suka nufa ba tare da b'ata lokaci ba Sadam ya ce "Sunusi ya fad'a mun komai na amince muje kawai," bud'e masa akayi ya shiga yana d'agawa sunusi hannu. [10/25, 8:52 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️ RUBUTAWA DAGA HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ) SADAUKARWA GA MY DAUGHTER SABEEHA BILKISU Z.YA'U (🅱️K) AISHA MAGAJI DABO (AMA) Page 29 Sabeeha ce zaune a falon ta tana yin waya bayani take yi Mata akan plan d'in su ita da Maleek akan daidai ta auren Sadam da Zainabu Doctor ta ji dad'in hakan da haka suka gama wayar tana ajiye wayar Maleek ya fito daga bedroom d'in ta da waya mak'ale a kunnensa shima da alamar yake. Hanyar fita ya nufa "Am Sweetheart," tsayawa ya yi tare da katse wayar k'arasawa ta yi ta shagwab'e fuska ta ce "Ina Kuma zaka?" Shafa kyakkyawar fuskar ta ya yi ya ce "Zani waje ne yanzu zan dawo," gyad'a kai ta yi ta koma cikin falon shi Kuma ya fita a falo ya samu Nasreen da Jamila suna magana suna ganinsa suka yi shiru bai damu ba ya fice abinsa. Yana fita Salman tare da sauran sojojin sa suka sara masa ya ce "Salman ya ake ciki?" "Boss yana cikin motor," gyad'a kai Maleek ya yi tare da shafa sajen sa ya ce "Yanzu abinda za ayi Salman kuje dashi gidan Mama tasan komai," Salman ya ce "Angama boss," hararar sa Maleek ya yi ya ce "Boss or friend," dariya Salman ya yi ya ce "Dukan su," murmushi kawai Maleek ya yi ya juya cikin gidan. Nan ma yana shiga kamar d'azu su Nasreen suna ganinsa suka yi gum sharewa ya yi har ya fara taka stairs sai Kuma ya tsaya tare da waigawa ya kalli Jamila da jikin ta har ya fara rawa ya ce "Ke Dan uwar ki tashi kibar gidan nan idan na sake ganin ki sai kin gane naki wasa ne," jiki na rawa ta mik'e ta yi waje har tana had'awa da tuntub'e. "Haba ya male..," Maleek ya yi saurin d'aga mata hannu ya ce "Karki kuskura wallahi Nasreen kice mun wani Abu a nan if not you see what happens stupid," yana fad'in haka ya k'arasa hayewa stairs d'in. Tsaki Nasreen ta ja ta ce "Wallahi zaku gane kuren ku da Kai da 'yar gold d'in taka mtswww," Salman kuwa suna gama parking daidai lokacin Mama na fitowa daga part d'in ta zuwa part d'in Kawu Bala k'arasawa suka yi wajen ta tare da Sadam gaishe ta suka yi ta amsa cikin fara'a Sadam kuwa tuni ya zube Yana kwasar gaisuwa amsawa Mama ta yi tana k'arewa sadam d'in kallo sannan ta kalli Salman ta ce "Zaku iya tafiya," ya amsa da "Toh," sannan suka shiga mota suka tafi. Kiran Faisal a waya Mama ta yi akan tana son ganinsa ba b'ata lokaci sai gashi ya gaishe ta ta amsa ta ce "Am Faisal kuje da wannan ya yi wanka sannan kazo ka amsar masa abinci wajen Halima then ga wannan kaje botique ka siyo mas kaya," ta fad'a tare da bud'e jakar ta ta deb'o kud'i masu yawa ta bashi ya ce "Tom madam," Sadam kuwa godiya ya fara kamar ya ari baki Mama ta ce "No bakomai komai nayi maka ai bazan iya biyan ka abinda kayi mun ba aikin ka shine bawa flowers ruwa," ya ce "To ranki ya dad'e," daga haka ta wuce zuwa part d'in su Lantana Sadam Kuma yabi bayan Faisal yana tunanin to shi me ya yiwa Doctor da tace komai tayi masa baza ta iya biyan sa abinda ya yi mata ba. Doctor kuwa itama tafiya take tana tunani tare da k'udurar niyyar kyautatawa Sadam saboda abinda ya yi Mata babba ne ya d'auki d'awainiyar 'yan ukun ta duk da ba wai haka kawai ya yi ba Dan yana son Sabeeha ne amma duk da haka taji dad'i domin ba don ya d'auki d'awainiyar su ba Kuma basu da kud'in yiwa kansu hidima zasu iya fad'awa wata hanyar gashi kuma ya yi abinda baza a iya biyan sa ba domin ba dan shi ba tasan yaran ta basu yi karatu ba haka zasu taso with empty brains amma ta sanadin sa sunyi primary da secondary sai Kuma cigaba da wannan tunanin ta k'arasa part d'in Kawu. Da sallama ta shiga Zainabu dake zaune ta ce "Sannu da Zuwa Mama," "Yawwa Zainab ya Habib?" Zainabu da ta kashe d'auri cikin doguwar rigar atamfa ta ce "Yana nan lafiya bacci yake yi," gyad'a kai Mama ta yi. Lantana ce ta fito daga kitchen domin ta jiyo muryar Mama ta zauna suka gaisa Mama ta sake yi musu bayani akan zuwan Sadam d'in Zainabu kuwa jin Sadam na gidan ba k'aramun dad'i taji ba. Wayar Doctor ce ta fara ringing tana dubawa ta ga Sabeeha ce tayi picking daga can Sabeeha dake kwance jikin Maleek ta ce "Mamana Sadam ya iso ko?" Doctor ta ce "Eh ya iso," "To Mama Ina Zainab?" Sabeeha ta tambaya tare da tsotsar lips d'in Maleek "Gata," Mama ta fad'a tare da mik'awa Zainabu wayar karb'a ta yi ta ce "Hello Aunty," daga can Sabeeha ta ce "Zainab kina jina," "Eh," Zainabu ta fad'a tare da barin falon zuwa bedroom d'inta. "Abinda nake so dake shine kamar yadda na fad'a Miki a baya sai fa kin matsar da soyayyar da kike wa Sadam gefe idan har kina so ki samu taki soyayyar ki dinga kwalliya kina ado kinji ko?" Zainabu ta ce "To aunty zanyi yadda ki kace," Sabeeha ta ce "Wannan shine ke dai macece ba saina tsaya koya Miki komai ba sai anjima," "To Nagode Aunty," Zainabu ta fad'a ba tare da tasan Sabeeha ta ma kashe kiran ba saboda wasan da suke yi da Maleek ne yafi k'arfin ta. Kwanan Sadam biyu a gidan amma har ya fara dawowa hayyacin sa yaci mai kyau yasha mai kyau Wanda ko a da baicin kamar sa domin ko da ruwan pure water yake sha amma gidan Doctor har gate man ruwan jarka yake sha ga kaya masu tsada da Mama tasa aka jido masa da takalma sannan tun washe gari ya fara aikin sa na ba flowers ruwa. Yanzu ma gama aikin sa kenan ya zauna kusa da Malam Musa gate man suna fira sai kawai ya hango wata ta fito kamar Zainabu da sauri ya mik'e tsaye ya ce "Zainabu!," Gate man ya ce "Ka santa ne?" Sadam kuwa ya ma kasa magana. Zainabu kuwa fitowar ta daga part d'in su kenan zata je part d'in Mama tasha kyau cikin riga da skirt na shadda ta yi kyau ba laifi domin ta waye ta yi fresh abinta ta iya kwalliya yanzu ma Tasha kwalliya ta yi d'aurin ta da malha tana taunar chewing gum kunnen ta mak'ale da earphone. D'an kallon wajen ta yi ta ga Sadam ya saki baki da hanci da idanu Yana kallon ta itama tsayawa kallon sa ta yi ko me ta tuna Kuma sai ta tab'e baki tare da jan tsaki tayi gaba abinta yayin da Sadam ya bita dana mujiya. Ganin ta b'acewa ganinsa yasa ya koma dab'ar ya zauna ya kalli Musa ya ce "Malam Musa wannan ba Zainabu ta bace?" Kallon baka da hankali Malam Musa ya yi masa ya ce "Bangane Zainabun ka ba kwata-kwata yaushe ne kazo nan gidan da zaka kirata taka ko da yake bansani ba amma wannan dai sunanta Zainab Kuma 'yar gidan nan ce," shiru Sadam ya yi sannan ya ce "Wannan ma sunanta Zainab d'in ce ni Zainabun da nake magana matata ce tsautsayi ya rabamu Amma dakyar idan wannan ita ce domin ita tawa ramammiya ce Wannan ta fita k'iba sannan tawa bak'ace sosai Amma wannan baza a kirata fara ba sannan baza a Kira ta bak'a ba Kai gaba d'aya ma wannan tafi tawa komai da wayewa da komai nifa tawa 'yar k'auye ce Kai nasan kamace kawai," dariya malam Musa ke kyalkyalawa kamar wani mahaukaci sabon kamu Dan har wani kwanciya yake akan bencin da suke zaune sannan ya ce "Kai Sadam banda ma kai bagashare ne yaushe sifofin daka zayyano na Zainabun ka za a had'a shi dana wannan Zainab d'in mu?" Tsaki kawai Sadam ya ja baice komai ba shi a lallai an ciwa Zainabun sa mutunci. Zainabu kuwa can wajen Mama ta zauna suka yi ta fira har sai da ta ji an Kira sallar azhar sannan ta yiwa Mama Sallama ta tafi domin tasan lokacin Sadam ya tafi Masallaci domin wannan Shirin Sabeeha ne domin ta ce sau d'aya tak a rana zata dinga bari tana had'uwa da Sadam. Shi kuwa Sadam tunda ya ga shigewar Zainabu shigewar part d'in Doctor ya zauna ya zubawa k'ofar ido domin ganin fitowar ta amma shiru Kiran sallar da akayi ne yasa ya tafi masallaci yanzu ma Yana dawowa ya Kuma samun waje ya zauna shi lallai yana jiran fitowar ta amma har dare shiru sallah kad'ai ke tashin sa ga wata uwar yunwa yana ji tun d'azu Faisal yace an kai masa abinci amma yak'i zuwa yaci. Duk abinda ke faruwa Zainabu na gani ta window dariya ita ya bata ma har ta gaji ta kwanta bacci Sadam kuwa sai da ya fara gyangyad'i sannan ya hak'ura ya tafi b'angaren su. Washe gari da yamma ma yana cikin bawa flowers ruwa ya kuma ganinta ta fito daga part d'in su zuwa part d'in Doctor taci kwalliya cikin black d'in doguwar riga sai k'amshi take yi abinta tiyon hannunsa ya fad'i k'asa da ido ya bita ji yake kamar ya yi mata sai dai yana shakkar hakan har Zainabu ta wuce yana kallon ta ajiyar zuciya ya sauke. Malam Musa dake bayan sa ya kyalkyale da dariya ya ce "Zainab d'in mu ba Zainabun ka bace," tsaki Sadam ya ja sannan ya gama aikin sa ya samu waje ya zauna Yana aikin kallon k'ofar part d'in Doctor ko Zainabu zata fito amma shiru kake ji. Zainabu kuwa wajen su Halima ta je suka fara fira kasancewar Doctor ta tafi hospital aiki ta taya su sai da aka shiga sallar magrib sannan tabar part d'in lokacin Doctor ta dawo. Sadam kuwa Yana dawowa ya cigaba da aikin jiran fitowar ta amma ranar ma shiru sai Malam Musa ya Kai ya kawo ya kalle shi ya kyalkyale da dariya ya ce "Zainab d'in mu ce ba Zainabun ka ba," shi dai Sadam shiru Dan shi baisan yana son Zainabu har haka ba sai yanzu da ya ga Mai kama da ita dan har yanzu bai tab'a had'uwa da Kawu Bala ba da Lantana ba bare Kuma Abba da yanzu baya samun zama. Ranar ma har dare shiru damun sa da malam Musa ya yi ne da "Zainab d'in muce ba Zainabun ka ba," yasa ya tafi flat d'in su zuciyar sa fal tunani. A haka har akayi sati kullum sai Sadam ya ga Zainabu sau d'aya cikin kwalliya da k'amshi ga wani aji da take ja masa ko kallon sa bata yi shi kuwa idon sa na kanta gashi ko Habibi bata fita da shi Yana cikin gida wajen Lantana haka zai ta zama Yana jiran ta amma shiru ita kuwa suna shiga sallah take guduwa part d'in su abun ya damu Sadam gashi ba rashin ci da sha da sutura amma har ya rame saboda damuwa har ya fara tunanin komawa k'auye neman Zainabun sa domin yanzu mugun sonta yake yi gashi wannan Zainab d'in kullum sau d'aya yake ganinta sannan shakkar yi Mata magana yake balle ya tambaye ta ko fuska ma bai gani ba sai dai kullum malam Musa ya dame shi da "Zainab d'in muce ba Zainabun ka ba," "Na bani ni Sabeeha yanzu Ina pretty take yau fa tunda na tashi banganta ba," Sabeeha ta fad'a tare da rik'e k'ugu cigaba da pretty ta yi tun daga bedroom har toilet da falo da kitchen da store tana Kiran ta amma shiru domin da tana nan tana jin an Kira sunanta zata je da gudu idon Sabeeha har ya fara tara k'wallah k'aramun veil d'inta red ta d'auka ta yafa saman kanta bak'ak'en riga da wando ne a jikin ta tayi kyau sosai ga kanta yasha gyara sosai sai k'amshi take ta yi k'iba ga wani haske da tayi down stairs ta nufa tana k'wala Kiran "Pretty my pretty," Amma shiru. Cikin falon ta k'arasa turus ta tsaya hango pretty da tayi kwance a gefe ga jini duk jikin ta a gefe Kuma Nasreen ce tsaye da wuk'a a hannunta wuk'ar duk jini domin yanzu ta k'una bata tsoron k'auri domin duk neman fitinar ta basa kulata hakan ne yasa yau ta tab'o pretty wacce tasan Sabeeha na sonta sosai. Wasu zafafan hawaye ne suka zubowa Sabeeha a ido da gudu ta k'arasa wajen pretty ta d'auka tana jijjigata amma Ina pretty rai yayi halin sa kuka sosai Sabeeha ke yi. Daidai lokacin Maleek ya yi sallama jin muryar sa yasa Sabeeha ta tashi tayi wajen sa da gudu ta rungume ta fashe masa da kuka gaba d'aya ta gama mak'alk'ale shi a rikice ya ce "Ya Salam baby what happened me yake faruwa?" Ta kasa magana sai kukan da take yi rik'e fuskar ta ya yi da duka hannayen sa ya ce "Please ki fad'amun meya faru," cikin kuka muryar ta har sark'ewa take yi ta ce "P...ree..tty," ta fad'a tare da nuna masa inda gawar pretty take. Da sauri ya k'arasa wajen kallo d'aya ya yiwa magen yasan ta mutu Kuma yankata aka yi da wuk'a take idanunsa ya yi jajir domin shima Yana son magen akwai ta da shiga rai. Nasreen Ba tasan ta aikata kuskure ba sai da ta ga yadda fuskar Maleek ta koma take jikin ta ya fara rawa. Cikin d'aga murya Maleek ya ce "Waye!! Waye ya aikata hakan?". [10/25, 8:55 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️ RUBUTAWA DAGA HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ) SADAUKARWA GA MY DAUGHTER SABEEHA BILKISU Z.YA'U (🅱️K) AISHA MAGAJI DABO (AMA) Page 30 Wuk'ar dake hannun Nasreen ce tsabar tsoro ta fad'i k'asa wajen Maleek ya kalla ganin yadda jikin Nasreen d'in ke rawa ga kuma wuk'ar da ta yar duk jini ya tabbatar masa da Nasreen d'in ce ta kashe Pretty. Gudurin ta ya nufa a zafafe ya d'aga hannu ya zabga Mata maruka har biyu k'asa ta durk'ushe tana kuka kamar cristiano Ronaldo ke buga k'wallo haka Maleek yayi ball da Nasreen har sai da ta Kai wajen stairs case wata razananniyar k'ara ta saki wacce tasa Sabeeha dake durk'ushe tana kuka rintse idanunta Hawaye suna zuba daga idanunta ba k'akkautawa. Wajen Nasreen Maleek ya nufa ya jata k'i zuwa sama Yana cewa "Wallahi karki kuskura ki cikamun kunnen mata da ihu," har cikin d'akin ta ya shiga da ita yasa key ya d'auki belt ya fara dukan ta iya k'arfin sa Aikuwa Banda ihu ba abinda Nasreen ke yi taji dukan jarumin soja ihu take yi iya k'arfinta kamar zata fasa mak'ogaron ta. Ihun ta yasa duka 'yan aikin ta fitowa su yi cirko_cirko a falo ba damar zuwa ceto sai da ya yi Mata lilis ya fito kai tsaye falon ya koma har lokacin Sabeeha na durk'ushe a gaban gawar pretty tana kuka k'arasawa wajen ya yi ya d'ago ta ya rungume ta ita rungume shi tayi sosai tana k'ara sakin wani kukan domin ba k'aramun so take yiwa pretty ba ga Kuma sabon da suka yi da ita shafa bayan ta Maleek ke yi a hankali cikin k'asa da murya ya ce "Sorry please baby kukan ya isa haka," maimakon ta yi shiru sai ma k'ara volume da tayi. Kallon 'yan aikin dake zagaye da su ya yi ya ce "Me ku ke jira ku gyara wajen," ya fad'a tare da jan hannun Sabeeha su nufi stairs shima kansa Maleek farar shaddar sa ta b'aci da jini Sabeeha kuwa waigen pretty da Jamila ke niyyar d'auke ta a wajen wasu zafafan hawaye ne suka Kuma zubo mata. Suna shiga falon ta zauna aka kujera tare da kifa kanta jikin hannun kujerar ta cigaba da kukan ta tausayin ta duk ya cika Maleek bedroom ya wuce domin tsaftace jikin sa. Wayar Sabeeha ce ta fara ringing ganin Mai kiran ne yasa ta d'aga wayar Sameeha ta ce "Dear kin shiga Ina na nake ta Kiran wayar ki Baki yi picking ba?" Kuka kawai Sabeeha tasa rikicewa Sameeha ta yi ta ce "Me ya faru dear?" Nan ma shiru ba magana sai kuka da Sabeeha ke yi tambayar duniya Sameeha ta yi Mata amma tak'i magana sai gajiya Sameeha ta yi ta katse kiran. Tana nan zaune har Maleek ya fito yana cewa "Wallahi Umar Nasreen ce ta kashe mata magen ta," daga can Umar ya ce "Kai amma wannan anyi 'yar iska Wallahi shegiya Kai kamar murhun giya ai da Meeha ta kira 'yar gidan ka taji tana kuka ka ganta itama sai kukan take yi shiyasa ba shiri na Kira naji ko lafiya amma Nasreen an yi shegiya ice ko dai kaci uwar ta?" D'an murmusawa Maleek ya yi ya ce "uhm uhm fa," "Mtsww Amma Wallahi MG ka kwafsa ai da ni ne da tuni ta kwashi kashin ta a hannu," wannan karon dariya Maleek ya yi ya katse Kiran. Daga can Sameeha ta ce "Please me yake faruwa Hubby?" Ajiyar zuciya ya yi ya ce "Wai Nasreen ce ta kashewa sister d'in mu Mage," ware ido Sameeha ta yi hawaye na zubo Mata ta ce "Kenan ta kashe preetty?" "Pretty," Umar ya maimata sannan ya ce "May be ita ce kam," kuka sosai ya ga Sameeha tasa nan yaita aikin rarrashi dakyar ta yi shiru. Maleek kuwa k'arasawa wajen ta ya yi ya durk'usa a gaban ta ya ce "Please baby kibar kukan haka kinji," bata d'aga Kai ta kalle shi ba sannan bata bar kukan ba dafe kansa ya yi ya ce "Ya Salam meyasa Nasreen zata yi mun haka ne dama batasan kwanakin nan rigima kike ji ba mtsww," d'an dafata ya yi ya ce "Sorry taso muje na siya Miki wata," sai lokacin ta d'aga Kai ta kalle shi ya ce "Yes let's go," ya fad'a tare da rik'o hannunta ta mik'e suka shiga d'aki tasa hijabi yana rik'e da hannunta suka fita. Mota ya bud'e Mata ta shiga sannan ya shiga har zai ja Salman ya ce "Sir bai kamata ka fita kai d'aya ba," ba tare da damuwa ba ya ce "No karku damu yanzu zamu dawo," daga haka ya ja motar suka bar gidan. Nasreen kuwa da taimakon Jamila ta farfad'o daga suman da ta yi ta taimaka mata tayi wanka ta gasa jiki tasha magani sai dai zazzafi ya rufe ta kwanciya ta yi har lokacin kuka take yi abinka da 'yar gata ita fa ko mari Sabeeha ce ta fara Marin ta a rayuwar ta. Maleek kuwa yana yin parking suka shiga gurin parking ya yi sannan yana rik'e da hannun ta suka shiga gurin ma'aikatan wajen kallon su ya yi ya ce "Na kawo ta ne ta zab'a wacce ranta yake so," suka amsa da "To ranka ya dad'e," fara zagaya wajen suka yi Sabeeha sai zuba jajayen idanunta take yi tana kallon kyawawan magunan wajen wad'anda suka fi pretty kyau sai dai ita lallai sai irin ta ganin babu aikuwa ba kunya ta zama ta kama kuka har da shura k'afafu. Ware ido Maleek ya yi yana kallon ta domin yayi mamakin wannan aikin da take yi wannan wacce iriyar rigima ce ya fad'a a ransa sannan ya d'auke ta cak ya fara tafiya yana fad'in "Baby wannan wacce iriyar rigima ce haka?" "Ni kawai kace matar ka ta biyani pretty ta kuma na ga Wanda ya bani yace na kula masa da ita sosai," ta fad'a tana k'ok'arin sauka ya ce "Ya isa ai na zab'a miki mai kyau zasu kawo miki gida," mak'e kafad'a ta yi "Ni banso kawai matar ka ta biyani," "Toh shikenan amma Baby Wanda ya mutu fa baya dawowa fa ji mana ba sai kun kawo mana ba Queen d'in tawa ta dena ra'ayi" ya fad'a yana kallon ma aikatan wajen sannan ya bud'e mota yasa 'yar rigimar sa ya zagaya ya shiga suka nufi gida ranar dai kwana Sabeeha ta yi kuka Maleek na aikin rarrashi. B'angaren Sadam kuwa zaune yake yana jiran fitowar Zainabu zuwa part d'in Doctor domin wannan karon yace sai ya yi Mata magana duk abinda zai faru ya faru domin ya lura indai ya ganta sau d'aya a rana baya sake ganinta gashi hak'urin sa ya k'are. Yana cikin tunanin ne sai gata ta fito cikin doguwar rigar material red tayi kyau kam da sauri ya nufi wajen ta yana cewa "Zainabu! Zainabu!" Tsayawa ta yi cak sannan ta juya ta kalle shi sannan ta keb'e baki ta ce "Me kace?" "Zainabu ki saurareni Wallahi nayi nadama," "Mtsww waye kuma Zainabu ni Zainab nake," daga haka ta cigaba da tafiya sake shan gaban ta ya yi ya durk'usa a gabanta ya ce "Zainabu ki tausaya mun Wallahi nayi nadama nasan kece matata please ki tausayamun Wallahi Ina sonki Ina son yarona yana Ina?" Banza ta yi masa zata tafi ya rik'o k'aramun veil d'in kanta a fusace ta waiga ta zabga masa mari ta ce "Kai har wani d'a gare ka ka ga ka fita a rayuwa ta ni bansan ka ba haba," daga haka tayi shigewar ta ta barsa a wajen a tsugunne. Dafa shi malam Musa ya yi ya ce "Na fad'a maka Zainab d'in mu ba Zainabun ka bace gashi ka jawa kanka mari yi hak'uri ka taso tunda ta ce ba ita bace ka kyale ta," tashi kawai Sadam ya yi suka je suka zauna shida gate man. Zainabu kuwa tana shiga falon zama ta yi ta fashe da kuka tabbas taji tausayin sa sai dai idan ta tuna abinda ya yi Mata sai taji tana jin haushin sa duk da kuwa soyayyar da take masa sai da ta ci kukan ta sannan ta fita zuwa part d'in su kunnuwan ta suka jiye Mata Sadam na fad'in "Musa bazan iya zama a gidan nan Ina kallon Mai kama da matata ba kawai zan tafi neman matata wacce nake k'auna idan har ban same ta a k'auye ba to bazan dawo nan ba a k'auyen ma bazan zauna ba zan shiga duniya Musa na aikatawa Zainab kuskure Amma nayi nadama ta haifar mun yaro amma banko tab'a ganinsa ba nayi nadama," wuce su tayi tana jin ba dad'i a ranta tana shiga part d'in su ta Kira Sabeeha ta kora mata jawabin abinda ke faruwa Sabeeha ta ce "Manta kawai ba abinda zai faru insha Allah kinji," Nan dai ta kwantar mata da hankali sannan suka yi sallama. Bayan kwana biyu Sabeeha ta tashi da wani zazzafan zazzab'i ba b'ata lokaci Maleek ya d'auke ta suka je wajen Ummi ta dubata ba b'ata lokaci aka yi gwaje_gwaje inda Ummi ta tabbatar musu da Sabeeha na da ciki na sati hud'u babu ko kunya gaban Ummi suka rungume juna suna murnar samun cikin ita Kuma Ummi nayi musu dariya. Haka Maleek ya ninka kulawar sa akan Sabeeha ita Kuma tana ajiye masa rigima iri_iri ta ce Bata cin wannan sai wancan shi Kuma yana biye mata zancen ciki kuwa ba Wanda bai ji shi ba Nasreen kuwa tunda Maleek ya yi Mata mummunan duka take mugun jin tsoron sa ko zaman falo ya gagare ta kullum tana d'aki sai dai suna nan suna k'ulla makircin su ita da Jamila. Bayan one week Maleek da Sabeeha suka shirya domin zuwa gidan Doctor sunyi kyau sosai ba k'arya cikin shadda light blue shadda kamar ka sace su ka gudu Sabeeha tayi using da pich color d'in takalmi da jaka da mayafi sai k'amshi suke yi. Mota aka bud'e musu suka shiga suka d'auki hanya jiniya kawai ke tashin a garin har k'ofar part d'in Doctor suka yi parking suka shiga Sabreen suka hanga akan daining tana cin aminci sai Sameeha a gefen Mama. Sameeha na jin sallamar su ta k'arasa da gudu suka rungume juna da Sabeeha suna murnar ganin juna haka ma Sabreen sai da suka gama murna suka gaida Maleek sannan Sabeeha ta k'arasa gurin Doctor da gudu ta fad'a jikin ta tana cewa "I really miss you Mamana," "Ku dai bakwa girma Wallahi ni d'agani," kwab'e fuska tayi ta kalli Sabreen ta ce "Wai sister haka Kuma Mama tayi muku," dungure Mata kai Doctor ta yi ta ce "Ku fa kiyayeni," tura baki ta yi ta koma can kusa da Maleek ta koma tana tura baki su Sabreen na Mata dariya Aikuwa sai tasa kuka su abin ma mamaki ya basu duk da sun santa da saurin kuka amma abin bai kai haka ba. Rarrashin ta Maleek ya fara ya ma manta a inda yake sai rungume ta yake yi Mama kuwa kunya ma suka bata. "Yarinya da anyi magana sai kuka kamar wata jaririya," Doctor ta fad'a cikin fad'a. "Dan Allah Mama kiyi hak'uri saboda ba ita kad'ai bane shiyasa,' ihun murna falon ya d'auka Domin ba Dan Maleek ba da rawa zasu taka a wajen. Doctor Kuwa girgiza Kai kawai ta yi tana murmushi ranar dai wunin gida Mama suka yi sannan suka koma gida. Sadam ne zaune ya zabga uban tagumi a wajen malam Musa sai Kuma kamar an tsikare shi ya mik'e "Ina Kuma zaka irin wannan irin zumbur haka ko kashi kake ji," harara Sadam ya aika masa ya ce "Ka ga Ni ka kyale ni kayana zan d'auko yanzu ba sai anjima ba zanbar gidan nan," yana fad'ar haka ya fara tafiya. Daga d'aki Zainabu ta fito ta kalli Lantana dake zaune ta ce "Umma Habib fa ya fito a d'aki Yana Ina?" "Ke yanzu Banda ke shashasha ce Zainabu yaro ya fito sai yanzu Zaki biyo bayan sa bayan kinsan k'ofar fita a bud'e take," Zainabu ta ce "Wallahi Umma na d'auka yana ta wajen ki ne amma bari na duba shi," tana fad'ar haka ta yi hanyar fita da sauri tana neman Habibi kasancewar rarrafe yake yi. Tana fita ta hange shi yana rarrafawa compound d'in gidan d'an girgiza Kai ta yi ta nufi wajen sa da sauri ta d'auke shi tana fad'in "Kai kuwa yaro ka fito waje haka," waigawar da zata yi suka yi ido hud'u da Sadam dake bayan ta Yana kallon ta tare da yaron hannun ta da ko ba a fad'a masa ba yasan d'ansa ne saboda kamar da ya ga yaron nayi da shi. Sharewa ta yi zata tafi ya yi saurin cewa "Zainab ki saurareni Dan Allah karki yi k'ok'arin raba miji da matar sa da Kuma d'ansu please," bata ce komai ba ta juya ta shige. Ya dad'e a tsaye yana tunani sannan ya nufi wajen gate ya zauna ya kalli Malam Musa ya ce "Waye yace maka Zainab d'in ku ba Zainabu ta bace to itace matata domin yanzu na ganta da yarona a hannunta," tab'e baki Malam Musa ya yi shi lallai bai yadda ba. Aikuwa ranar Sadam ya ga Kawu ya shigo gidan nan ya tare shi Yana yi masa kuka Yana rok'an sa hakan ne yasa Kawu ya jashi har falon su ya Kira Abba a waya har da Doctor suka zauna aka yi sasanci sannan Abba ya yiwa Sadam kyautar gidan da zasu zauna sai godiya yake yi shi da Zainabun sa Nan da sati d'aya zata koma. Bayan wata abubuwa sun faru ciki har da komawar Zainabu gidan Sadam inda suke shan soyayya. Sabeeha ce Zaune a falon su lokacin Maleek baya nan saboda yanzu baya samun zama saboda yawan meeting da suke yi yau ma tun safe ya fita zaune kawai Sabeeha take amma gaba d'aya bata jin dad'in jikin ta ga yawan fad'uwar gaban da take yi a 'yan kwanakin kawai tana daurewa ne jin zaman ita kad'ai ya dame ta ne yasa ta tashi ta zura hijabin ta ta fita zuwa part d'in Ummi. Har zata hau Mota da yanzu ta iya sai Kuma ta fasa ta tafi da k'afa wata bak'ar mota ta gani ta yi parking a k'ofar part d'in Umman Nasreen haka kawai taji hankalin ta bai kwanta da motar ba can sai Uncle ya fito daga motar da sauri kamar zai kifa ya shige cikin part d'in. Mamaki ne k'arara a fuskar Sabeeha to meyake faruwa da Uncle haka ta fad'a cikin zuciyar ta sannan Kai tsaye nufi sashen gaban ta na fad'uwa a daidai window d'in cikin falon ta lab'e. "Eh daughter ta yi wannan aikin tun jiya da daddare sannan idan har ya taka maganin to zuwa yanzu ya fara jin sauyi a jikinsa domin 3 hours maganin ya fara aiki sannan sai matar sa kamar yadda ka fad'a a daren yau za a d'auke ta," Uncle ya fad'a sannan Kuma ya kyalkyale da dariya ya ce "To dama Baba me aka yi aka yi uban Abdul-maleek ma ballantana shi Maleek d'in ai kawai kasa a ranka munyi aikin mu mun gama," ya fad'a yana fashewa da wata muguwar dariya. Zare ido Sabeeha ta yi tasa hannunta ta toshe bakin ta saboda kukan da ya taho mata a hankali take ja baya a zuciyar ta ta ce wanne magani suka sawa sweetheart me yake nufi da maganar sa da wani mugun gudu tayi part d'in Ummi tana shiga ta fad'a jikin Ummi tasa wani kuka Mai ban tausayi. A rikice Ummi ke tambayar ta maiya faru amma ba amsa sai kukan da take yi kamar mak'ogoron ta zai fashe. Maleek da fitowar sa kenan daga meeting cikin kakin sojojin sa ya yi kyau har ya gaji sai dai wani iri yake ji a jikin sa kamar anyi masa duka gashi kamar ana tsotse masa jinin jikin sa a haka ya k'arasa gaban motar sa Salman ya bud'e masa ya shiga ya zauna wayar sa ce ta fara ringing d'agawa ya yi. "Yallab'ai akwai matsala dafatan dai baka shiga motar ka ba saboda ansa mata magani a ciki Wanda idan ka taka shi shikenan zaka kamu da cutar mutuwar b'arin jiki ba abinda zaka ji ko anyi maka magana sannan baza ka yi magana ba Yallab'ai wallahi akwai matsala domin idan ka kwanta shikenan zasu samu damar shigo da kayansu Nigeria sunyi shiri sosai," katse Kiran kawai Maleek ya yi ya lumshe idanunsa sannan ya bud'e idanunsa ya kalli inda k'afafun sa suke tsirawa gurin ido ya yi sai lokacin ya lura da wani garin magani bak'kk'irin a inda k'afar sa ke Kai gaban sa ya yi muguwar fad'uwa bai iya cewa komai ba har suka isa gida ya kalli Salman ya ce "Salman yi parking k'ofar part d'in Ummi," ana yin parking ya fito daga motar. Ya tsaya ya kalli duk sojojin sa da suka zagaye shi sannan cikin muryar sa mai dad'i ba tare da wani tsoro ba ya ce "Na samu labarin shigo da makamai k'asar nan kwanan nan abinda nake so daku a yanzu kuje jaji da NDA ku had'a duka runguna ta ku rabu duk wata hanya da ku kasan zasu iya biyowa Salman Kai kuma zaka zauna a tare dani su Kuma dukan su zasu tafi yanzu wish you all the best," har Salman zai yi magana ya d'aga masa hannu su Kuma sojojin suka shiga shiga motocin su suka bar gidan. Waigawa Maleek ya yi ya kalli Salman "Sir me yake faruwa ne haka?" Hawaye ne suka fito daga idanun Maleek abun ya matuk'ar tsorata Salman. Bayanin abinda ke faruwa Maleek ya yiwa Salman sannan ya ce "Salman na fad'a maka hakane saboda yaddar da nayi maka sannan na damk'a amanar family na a hannunka kar wani abu ya same su sannan kar wani yasan da wannan maganar sannan ko bayan na kwanta kar Wanda ya yi k'ok'arin nema mun magani domin hakan bazai yi amfani ba," kuka sosai Salman yasa kamar ba soja ba sannan ya rungume Maleek shi kuwa Maleek yana yin da yake ji a jikinsa ya fara fin k'arfin sa a hankali yana jan k'afa ya shiga falon Ummi. Da gudu Sabeeha ta je ta rungume shi ta fashe da kuka a hankali kamar ana Shak'e shi ya ce "Baby meya faru?" Kasa magana ta yi jin yadda muryar sa ke fita. Kafin kace me ya sulale k'asa a wajen baya yin motsi da gudu Ummi ta k'arasa wajen tana Kiran sunansa Sabeeha kuwa jikin sa ta fad'a tana fashewa da kuka. [10/25, 8:55 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️ RUBUTAWA DAGA HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ) SADAUKARWA GA MY DAUGHTER SABEEHA BILKISU Z.YA'U (🅱️K) AISHA MAGAJI DABO (AMA) Page 31 Iya rud'u rikici da tashin hankali Ummi da Sabeehs sun shige shi ganin yadda Maleek ke kwance kamar gawa Salman dake bakin k'ofa ne ya jiyo kukan su kai tsaye ya shiga falon shima ganin halin da Maleek d'in ke ciki ya tashi hankalin sa sosai. Da sauri ya k'arasa wajen yana salati suka d'auke shi suka kwantar da shi saman kujera har lokacin kuka suke yi "Salman meya faru da son haka dama ya sanar maka baida lafiya ne ko ya sanar maka wani abun na damun sa," Ummi ta fad'a tana sharar hawaye. Shiru Salman ya yi Sabeeha kuwa tana so ta sanarwa da Ummi wayar da taji Uncle nayi sai dai bata da kwarin gwiwar hakan domin sanarwa Ummi na nufin ninkuwar tashin hankalin ta ne Maleek kuwa hakan zai k'ara masa damuwa. "Ummi bakomai dama muna Shirin yin wata tafiya ne tare da Yallab'ai to shiyasa yace ayi masa wata allura wacce tana da had'arin da idan jinin mutum bai da k'arfi takan kwantar da mutum cutar paralyse ta tsawon lokaci sannan ta hana magana da kuma ji nayi tunanin hana Yallab'ai amma bai saurare ni ba tun a hanya yake sanar dani Yana jin yanayin jikin sa na sauya masa," ya fad'a hawaye na zuba a idanunsa. Sai lokacin Maleek ya bud'e idanunsa sai dai ya yi k'ok'arin d'aga hannun sa hakan ya faskara kallon Sabeeha da Ummi kawai yake yi ganin yadda suke zubar da hawaye ji ya yi kamar ruwan zafi a zuciyar sa k'ok'arin bud'e bakin sa yake yi domin rarrashin su sai kawai ya ji kamar an d'ora masa wani k'aton dutse a bakin wasu zafafan hawaye ne suka zubo a idanunsa kansa kad'ai yake iya juyawa duk su Ummi basu lura a halin da yake ciki ba gaba d'aya zubawa Salman ido suka yi cikin tashin hankali "Ya sunan allurar Ina so nasani," Ummi ta tambaya jikin ta har rawa yake yi. Da sauri Salman ya kalli Ummi domin ya ma manta cewar Ummi likita ce har ya yi mata wannan k'aryar kallon Maleek ya yi suna had'a ido Maleek d'in ya lumshe idanunsa ya bud'e ya gane me yake nufi sai ya ce "Ummi bansani ba," domin Maleek na fuskantar me suke fad'a idan ya kalli bakin su kallon ban yadda da Kai ba Sabeeha ke yi masa sannan ta kalli Maleek ganin idanunsa a bud'e ta ce "My dagaske ne abinda Salman yake fad'a," a hankali ya gyad'a kansa wani sabon kukan Sabeeha tasa ta ce "Yanzu baza ka iya tashi ba kenan jikin ka bazai motsa ba?" Ta fad'a tana kwantar da kanta saman jikin sa. Ummi kuwa gaba d'aya ta rasa tunanin da zata yi ta ce "Salman mu tafi asibiti kawai zanyi bincike," Nan ma da sauri ya kalli Maleek da ido Maleek ya fad'a masa kar ya bari aje. "A'a Ummi kar muyi hakan saboda aikin da yake tunkaro mu," "Haba Salman akan me zamu zauna da shi a gida yana cikin wannan yanayin?" Sabeeha ta fad'a idanunta sun kumbura tsabar kukan da tasha Dan ajiyar zuciya Salman ya sauke ya ce "Ba Ina nufin kwata kwata kar a Kai MG asibiti bane amma Kai shi a yanzu Yana nufin duniya zatasan halin da yake ciki Wanda hakan zai dakatar mana da aikin mu na tsayar da shigo da makamai k'asar mu ba kuma idan har labari ya Kai musu hankalin su zai karkata ga tunanin ta yadda zasu bi MG asibitin su kashe shi yayin da a gefe kuma zasu shigo da kayan," shiru suka yi Ummi kuma kuka ta saka tare da rungumar Maleek ta ce "Ya Allah ga bawan ka Allah Ina rok'on ka da ka bawa yarona lafiya ka kare mun shi daga sharrin masu sharri," suka amsa da "Ameen," Maleek kuwa hawaye ne kwance a idanun sa domin ganin hawayen Ummi na tayar masa da hankali hakan ne yasa shi d'an yin murmushi yana girgiza mata Kai. "Ummi bai ci abinci ba kafin fitar sa," Sabeeha ta fad'a tana kallon Ummi da sauri jiki na rawa Ummi ta tashi ta nufi kitchen sai gata da tray da abinci a center table ta ajiye sannan dakyar suka zaunar da Maleek tare da jingina shi a jikin kujerar Ummi da kanta take bashi abincin. Tashi Sabeeha ta yi ta nufi stairs da kallo Maleek ya bita so yake ya yi Mata magana amma ba dama domin yasan tana shiga d'akin zata cigaba da kukan ne kawai. Tana shiga d'akin Ummi ta fara Kai da komawa a d'akin hawaye na bin fuskar ta gaba d'aya kanta ya kulle tama rasa abinda zata yi wayar ta ta d'auka ta Kira wayar Sabreen ana d'agawa daga can Sabreen ta ce "Hello dear," cikin dashashiyar muryar ta ta ce "Sabreen Ya Fauwaz na gida?" "Eh yana nan amma lafiya kuwa naji muryar ki haka?" Sabreen ta tambaya "Ni dai Dan Allah kuzo tare yanzu gida ina jiran zuwan ku," daga haka ta katse Kiran ta zauna ta d'ora da kukan ta. Tafi minti talatin a zaune a wajen sannan ta sauka down stairs ta shige kitchen sannan ta fice ta k'ofar baya zuwa part d'in su tana shiga ta samu Nasreen da Jamila zaune suna fira abinsu ko ta kansu bata bi ba ta haura stairs a falon ta zauna abubuwa da dama nayi Mata yawo a kwakwalwar ta. Batasan shigowar su Sabreen ba sai da ta ji an dafata ta sannan ta yi saurin kallon Sabreen idanunta cike da k'wallah Sabreen kanta ta tsorata da ganin yanayin da 'yar uwar ta ta ke ciki ta ce "Subhanallah dear meya faru ne? Da wata matsalar ce?" Rungume Sabreen kawai Sabeeha ta yi ta saka kuka ta ce "Dear mun shiga Uku," Da sauri Fauwaz da shigar sa kenan ya k'arasa da sauri ya ce "Me yake faruwa ne?" Ganin Sabeeha da ya yi a jikin Sabreen. Kome Kuma Sabeeha ta tuna sai tayi saurin tashi zaune ta share hawayen ta ta kalli Fauwaz sannan ta kalli Sabreen ta ce "Akwai matsala sister muna cikin wani hali ina buk'atar taimakon ku Dan Allah," gaba d'ayan su basu fuskanci me Sabeehan ke nufi ba Fauwaz ya ce "Sister ki nutsu ki yi mana bayanin abinda ke faruwa ko tsakanin ki da Yaya ne?" Girgiza Kai tayi sannan ta ce "Ya Fauwaz maganar da zan fad'a yanzu ta zama sirri a tsakanin mu dan Allah wato abinda ke faruwa da safe My ya shiga wanka wayar sa na hannu na sai kawai naji shigowar text sai kawai na duba rubutu ne ansa MG ka shirya rasa matar ka a yau da daddare abun ya tayar mun da hankali ina gani sai nayi sauri na goge text d'in sai dai abun ya dame ni a raina sosai My yaso ya fuskanci cewar ina cikin damuwa sannan nima nayi tunanin sanar da shi abinda ke faruwa amma ganin yana sauri yasa banyi masa maganar ba har ya tafi ni kuma nasa a raina cewar yana dawowa zan sanar da shi abinda ke faruwa," "Yanzu Ina shi Yayan ni Bari naje na sanar da shi," Fauwaz ya fad'a tare da niyyar nufar hanyar fita. "A'a ya Fauwaz sanar dashi yanzu akwai matsala saboda shi ma Yana cikin wani yanayi," Sabeeha ta fad'a tare da sanar da su rashin lafiyar Maleek d'in daga ita har Sabreen da Fauwaz hawayen suke yi idanun Fauwaz har sunyi jajir zuwa fuskar sa Sabreen rungume Sabeeha ta yi ta ce "Yanzu dear wanne taimakon ki ke so a gare mu?" "Dan Allah sister Ina so ki zauna a nan gidan sannan a matsayina ni kuma su zo su tafi dani?" "Kamar ya?" Sabreen da Fauwaz suka fad'a a tare. "Ku fahimce ni yanzu My yana cikin mawuyacin hali idan har na sanar da shi wannan hankalin sa zai fi haka tashi sannan kunsan cewar Yana da ciwon zuciya gashi kamar yadda na sanar muku ba a so asan da wannan rashin lafiyar tasa a gari hakan kan iya jawo masa matsalar da rayuwar sa zata kasance a cikin had'ari Ummi damuwa zata yi Mata yawa ga tunanin rashin sanin halin da nake ciki ga Kuma rashin lafiyar sa so nake kawai ni su yi mun duk abinda su ga dama idan ma kashe ni zasu yi su aikata hakan amma ku ku zauna lafiya," Kuka Sabreen ta fashe da shi ta ce "A'a hakan bazai yuwu ba ni nan zanje a madadin ki kinji?" Girgiza kai Sabeeha ta yi ta ce "A'a dear ni ya kamata naje," "Dukan ku ba Wanda zai je bari na Kira Daddy na fad'a masa a d'auki mataki a Kai," Fauwaz ya fad'a tare da k'ok'arin ciro wayar sa a aljihun sa "A'a Ya Fauwaz fad'awa Daddy halin da ake ciki na nufin My da Ummi kenan su San halin da ake ciki bana son ciwon My ya tashi sannan bari na fad'a muku gaskiya na fuskanci idan ba haka nayi ba baza ku fahimce ni ba wannan cutar da My yake yi sune silar jefa shi a ciki asiri suka yi masa sannan sun tabbatar a text d'in da suka yi masa cewar ba malamin da ya isa ya karya wannan asirin idan har basu suka warware shi da kansu ba wanda zuwana ne kad'ai zai sa su warware asirin ni d'in Kuma suna buk'ata tane kawai domin su rik'eni a wajen su su hana My dakatar da shigo da makamai da hodar cocaine Nigeria ni Kuma Ina so naje ne domin sun tabbatar mun da cewar suna d'auka ta zasu warware asirin jikin sa Kuma kunga yana samun lafiya zai samu damar k'wato ni da Kuma dakatar da k'udirun su ni dai ku taimake ni," Zama Fauwaz ya yi tare da dafe kansa da yaji yana sara masa. "Na amince dear amma Ina tsoron su cutar mana dake Wallahi baza mu iya jura ba," Sabreen ta fad'a tana hawaye mik'ewa Fauwaz ya yi tsaye ya ce "Na fahimci komai sister duk wannan Yaya bai saniba sannan baisan sanadin ciwon sa ba hakan ne yasa akace allurar sojoji aka yi masa domin kwantar da hankalin mu ko?" Gyad'a Kai Sabeeha ta yi. "Shikenan Nima na amince da hukuncin ki sai dai ina tsoron abinda zai je ya dawo," cikin jin dad'i ta ce "Insha Allah ba abinda zai faru kawai ku tayani da addu'a," Fauwaz kuwa Sabreen ya kalla sannan ya juya ya ce "Bari naje na ga Yaya," ya fad'a tare da fita daga d'akin. Sabeeha Kuma ta kalli Sabreen da har lokacin hawayen ta bai tsaya ba tasa hannu ta goge mata ta ce "Haba dear ki bar kukan haka mana ki zama jaruma na zab'i na fad'a Miki ne saboda nasan kinfi Sameeha dear jarumta ko da wasa karki sanar da kowa wannan lamarin ko da Mama ce da kuma dear saboda gudun halin da zasu shiga," gyad'a Kai kawai Sabreen ta yi ta ce "Ta ya zan iya zama a matsayin ki a tunanin ki Ya MG bazai gane ba?" "Eh bazai gane ba idan har kin bi hanyoyin da zan sanar dake," "Wanne hanyoyi ne?" Sabreen ta tambaya "Bari na fayyace Miki komai Kinga dai My bashi da lafiya nasan ba ta yadda za'ayi ya yi tunanin yin wata mu'amullar aure sannan zansa a yanzu a dawo da shi nan part d'in saboda a can za a iya samun matsala sannan karki kuskura ki Kira shi da Yaya domin hakan na iya sawa ya gane cewar ke d'in bani bace sannan abu Mai muhimmanci da ya kamata ki sani shine My yana gane Ni a cikin ku idan har ya kalli cikin idanuna da kansa ya sanar dani hakan dan haka kada ki bari ku dinga had'a idanu da shi sannan baza ki samu damuwa ba saboda yanzu ko magana baya iyawa," gyad'a Kai kawai Sabreen ke yi. "Yanzu muje part d'in Ummi," cewar Sabeeha ta fad'a tare da rik'e hannun Sabreen suka nufi k'ofar fita. Nasreen dake lab'e tsahon lokaci ta nufi d'akin ta tana wata shegiyar dariya Jamila ta samu a d'akin ta kalle ta ta ce "Jamila kinsan wani Abu?" Girgiza kai Jamila ta yi ta ce "A'a ranki ya dad'e sai kin fad'a," wata dariyar Nasreen ta yi sannan ta fad'awa Jamila komai ta d'ora da cewa "Kinga yanzu na samu damar gyarawa itama Sabreen zama lallai Sabeeha ta burgeni da ta tsara hakan sannan abinda bata saniba shine idan ta tafi baza ta tab'a dawowa ba sai dai gawar ta," suka shek'e da dariya Jamila ta ce "Meye Shirin ki na gaba ranki ya dad'e?" "Shirina na gaba shine bana so Umma tasan cewar Sabreen na gidan nan ita da Kawu daga sannan ni Kuma zan koyawa Sabreen hankali daga lokacin da aka kawo gawar Sabeeha su Aysha da Hamza da shi kansa Maleek zasu gane cewar Sabreen ce zaune a matsayin Sabeeha sannan kafin nan sai nasan yadda nayi har Maleek ya yiwa Sabreen ciki Kinga daga nan zaman lafiya ya k'are daga nan Kuma shi kansa Maleek Daddy zai sa a kashe shi har da ma iyayen sa da kowansa Kinga shikenan mu Kuma mu gaje abinda suka mallaka daga nan Daddy ya warke har mu kanmu babu mu ba talauci," ta fad'a tare da tafawa ita da Jamila suka tuntsira dariya. Sabeeha kuwa ta k'ofar kitchen ta shiga falon Sabreen Kuma ta k'ofar shiga Fauwaz suka samu jikin Maleek yana kuka kamar k'aramun yaro domin bai kawo abin ya Kai haka tsamari ba haka ma Sabreen kukan take yi. A hankali Sabeeha ta k'arasa falon inda suke kusa da Maleek ta zauna tana kallonsa shima ita yake kallo hawaye ne ya gangaro mata girgiza mata kai ya yi sai tayi saurin goge hawayen ta Ummi dake gefe abubuwa sun dame ta ta ce "Bari na Kira Daddyn ku na sanar masa," a tare Sabeeha Sabreen da Fauwaz suka kalle ta. Fauwaz ne ya yi saurin cewa "A'a Ummi karki sanar masa domin d'azu muka yi waya da Daddy ya sanar mun cewar akwai aikin da yake yi mai muhimmanci da ya tafi gabatarwa a london idan ki ka sanar masa hankalin sa zai tashi sosai mu bi komai a Sannu," jinjina Kai Ummi ta yi yayin da Sabeeha ta saki b'oyayyar ajiyar zuciya. "Amma dai na sanarwa Maryam," ta fad'a tare da d'aukar waya ta sanarwa Doctor abinda ke faruwa hankalin Doctor ya tashi sosai Dan ko iya yanayin muryar Ummi da ta ji ya isa ya tashi hankalin ta ba shiri ta nufo gidan. Ko da tazo itama sai da ta yi kukan tausayin halin da Maleek ke ciki itama cewa ta yi su je asibiti amma da Ummi ta yi mata bayani kan yanayin aikin su Maleek sai itama ta yi shiru da maganar. Suna Nan zaune har dare Sabeeha ta kalli Ummi ta ce "Ummi mai zai hana mu koma can part d'in sa saboda nan ba wani sirri," Doctor ta ce "Haka ne Aysha can ya kamata su koma," Ummi ma ta yi na'am da hakan. Dad'a matsawa kusa da shi Sabeeha ta yi alamun tana son fad'a masa wani abu fahimtar da Maleek ya yi ne yasa ya zubawa bakin ta idanu a hankali ta ce "Zaka yi wanka?" Gyad'a Kai ya yi kallon Ummi Sabeeha ta yi ta ce "Ummi wanka yake so," Ummi ta ce "To bari Salman ya dawo," tana rufe baki Salman ya yi sallama tare da wheelchair ba b'ata lokaci suka d'ora Maleek a Kai tsaye part d'in Fauwaz suka nufa saboda nan ne a down stairs Sabeeha ce ta yi masa wankan dakyar ta iya sannan ta tura shi zuwa cikin bedroom d'in Fauwaz ta shafa masa mai sannan tasa masa wata riga fara tas tare da farin 3quater ta taje masa kansa ta fesa masa turare ya yi kyau sosai. Maleek kuwa zuciyar sa fal tausayin Sabeeha ganin harta fara hidima da shi gashi bashi da bakin yi mata godiya ganin ya kafeta da idanu yasa ta sakar masa murmushi ta tura shi zuwa cikin falon. Suna fita waje suka fita akasa Maleek a mota sannan aka nufi part d'insa dake cikin gidan ba Wanda Nasreen ke ciki ba suna zuwa dama d'akunan dake down stairs a gyare suke d'aya a ciki aka shiga da maleek aka kwantar da shi saman k'aton gadon Sabeeha na gefen sa a zaune. Mama ta yi musu Sallama Salman ya kaita gida. Har lokacin suna d'akin Nasreen ta shigo d'akin da gudu har haki take yi tana zuwa ta fad'a jikin Maleek ta saka kuka kamar gaske ta ce "Shikenan na shiga uku na lalace Ya Maleek Mai ya same ka dama baka da lafiya yanzu Ina zansa kaina?" Ta fad'a tana cigaba da ihu kamar sabon kamu Sabeeha dake gefe duk ta gama k'ulewa ga wata muguwar tsanar Nasreen dake zuciyar ta ta kalle ta ta ce "Kinga Dan Allah kiyi mana shiru ai My bashi da mak'iyiyar da ta wuce ki dalla malama d'aga mun jikin miji idan ba haka ba Wallahi sai kin gane bani da wani mutunci," Gaba d'aya mutanen wajen kallon su ya koma wajen Sabeeha hatta ma Nasreen d'in jin abinda Sabeeha ta fad'a. Sabeeha kuwa ba ma tasan maganar ta fito daga bakin ta ba sai kawai ta mik'e ta fice daga d'akin ashe tana fita sai Nasreen ta kalli Ummi ta ce "Ummi Ina so na dawo nan part d'in nima saboda kula da shi idan ranar girkina yazo," ba tare da wata damuwa ba Ummi ta ce "Bakomai ai kema mijin ki ne ki dawo," ta ce "To Bari naje na shirya," ta fad'a tare da fita a falo ta samu Sabeeha tana kuka kallon ta ta yi tare da yin dariya ta fice. Cikin d'akin ta koma sannan ta kalli Fauwaz ta kanne masa ido ganin har sha biyu ta yi ya kalli Ummi ya ce "Ummi ya kamata kije ki kwanta Kinga dare ya yi?" Ummi ta ce "To ku ma ya kamata ku tafi dare ya fara" Fauwaz ya ce "To Ummi bari na Kai ki," tashi Ummi ta yi ta kalli Maleek da har ya yi bacci ta k'arasa wajen sa sumbace shi a goshi sannan ta fita tana ji kamar ta kwana a wajen sa sai dai ba dama ganin da matan sa har biyu a part d'in. Suna fita Sabeeha ta kalli Sabreen ta ce "Dear muje can part d'in sai ya Fauwaz ya same mu a can," tashi Sabreen ta yi suka nufi d'ayan part d'in suna shiga suka samu Nasreen zaune a falo tana cin kaza tana korawa a falo ko kallo bata ishe su ba suka haura stairs wanka Sabeeha ta fad'a tana fitowa ko mai bata shafa ba ta zura wata black d'in doguwar riga ta yi parking gashin ta kallon ta kawai Sabreen ke yi ga cikin ta har ya tasa take tausayin Sabeeha ya kama Sabreen ta ce "Sister ki zauna ni su tafi dani Kinga bake kad'ai bace kar su cutar dake tare da yaron ki," shafa cikin Sabeeha ta yi hawaye cike a idanunta sai Kuma ta d'an yi murmushi ta ce "Insha Allah ba abinda zai faru dear," daga haka ta zira hijabi abinta ta kalli Sabreen ta ce "Sister kiyi wanka," ba musu ta shiga toilet ta yi wanka ta fito tasa wata doguwar rigar Sabeeha blue sannan suka fita falo suna zama Fauwaz ya yi sallama suka amsa sannan ya zauna ya ce "Sister kina ganin abun nan zai yuwu kuwa?" Gyad'a kai Sabeeha ta yi ta ce "Eh abinda kawai zan fad'a shine ka dinga kula da Sabreen saboda Nasreen," gyad'a Kai Fauwaz ya yi sannan suka tashi suka fita daga part d'in zuwa part d'in Maleek ko shiga Fauwaz bai yi ba ya ce "Zai wuce gida," rungume shi Sabreen ta yi ya shafa bayan ta ya ce "Sai na dawo gobe My love take care," noding kanta Sabreen ta yi sannan ya shiga mota ya tafi su Kuma suka shige part d'in. D'akin da Maleek yake suka shiga sun dad'e a d'akin a zaune sannan Sabeeha ta kalli agogon hannunta ta ga d'aya saura sai ta tashi ta kwanta jikin Maleek wani kuka ne ya kufce mata ta dad'e tana kukan sannan ta mik'e suka rungume juna da Sabreen suna kuka sun dad'e suna aikin abu d'aya sannan Sabeeha yi jarumtar cewa "Dear ni zan tafi ki kula sosai," gyad'a Kai Sabreen ta yi sannan ta mik'awa Sabeeha k'aramar wayar ta ta ce "Sister kije da wannan akwai kati sosai a ciki ki kasance tare da ita Dan Allah ki dinga Kiran mu ko hankalin mu zai kwanta," karb'a Sabeeha ta yi ta ce "To Nagode na tafi," ta yi hanyar fita tana waigen Maleek. Tana fita Sabreen ta zauna ta saka kukan tausayin 'yar uwar ta. Sabeeha ma tana tafiya tana sharar k'walla d'akin ta ta shiga ta kwanta sai dai ta kasa bacci. Sabreen ma kwanciya tayi saman kujerar dake d'akin. Duk cikin su ba Wanda bacci ya d'auka daga Maleek har Sabreen da Fauwaz da Ummi da Salman ballantana Sabeeha da sai juyi take yi. Misalin k'arfe biyu da rabi Sabeeha dake yin Sallah ta ji an bud'e k'ofar d'akin ta bata damu ba domin dama tasan zasu zo tana sallar suka shigo cikin bak'ak'en kaya manya ne sosai su hud'u sun rufe fuskokin su ganin tana yin Sallah sai suka tsaya jiran ta tana yin sallama d'aya a cikin su ya zaro bindiga ya nuna Sabeeha da ita sai lokacin ta ji wani tsoro ya kamata ta ce "Su waye ku?" "Zaki san ko mu su waye taso mu tafi kawai ko yanzu mu fasa kanki da wannan bindigar," da sauri jiki na rawa ta mik'e domin iya muryar mutumin abun tsoro ce haka suka tasa Sabeeha a gaba har mota ta shiga suka ja motar da gudu suka bar gidan. [10/25, 8:56 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️ RUBUTAWA DAGA HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ) SADAUKARWA GA MY DAUGHTER SABEEHA BILKISU Z. YA'U (🅱️K) AISHA MAGAJI DABO (AMA) Page 32 Tunda suka hau titi suke zabga gudu Sabeeha kuwa wasu hawaye ne suka zubo Mata a idanunta domin rashin sanin abinda zai faru ga rayuwar ta tabbas taji dai Uncle yana zancen za a d'auke ta sannan tasan basu d'auke ta dan komai ba sai dan su raba ta da ranta shikenan yanzu hakan na nufin ta rabu da mijin ta da take matuk'ar k'auna shikenan ta rabu da iyayen ta shikenan yanzu ta rabu da 'yan uwan ta da suke matuk'ar son ta sannan a hankali ta shafa cikin ta wasu zafafan hawayen suka sake zubo mata saboda tunawa da babyn dake cikin ta da ta yi tabbas aka kashe ta Maleek ya yi asarar Babyn sa. Ajiyar zuciya ta sauke sai Kuma tunanin ta ya koma kan tunanin meyasa Uncle yake son kashe Mata miji wata zuciyar tace shin kin manta labarin da Maleek ya Baki akan rayuwar sa ta baya take ta bawa zuciyar ta amsa akan cewar tsanar da Uncle kewa Daddy da Ummi ne har ya shafi Maleek tana cikin tunanin ta ga an yanki wata hanya a cikin daji sai da aka yi nisa sannan ta ga wani gida guda d'aya tak a dajin da alama ma gidan gona ne bud'e musu gate aka yi suka shiga suka yi parking sannan suka bud'e motar suka fita suka ce Sabeeha ma ta fito ta fito wani mugun tsoro ne ya kama ta ganin gaba d'aya gidan a zagaye yake da wasu manyan murd'a_murd'an mutane masu tsayi da k'iba bak'ak'e k'irin da su cikin bak'aken kaya har da bindigu a hannun su. "Kee! wuce muje" wani a cikin Wanda suka zo tare ya dakawa Sabeeha tsawar da sai da ta firgita ta fara tafiya cikin gidan suka shiga bakowa a gidan sai wata mata tsohuwa a zaune tana shan taba da mamaki Sabeeha ke kallon ta ganin tsohuwar mace irin wannan da shan sigari sannan kanta ba kitso wacce tsohuwar a k'alla zata yi shekara 65. Tashi matar ta yi ta k'arasa gaban Sabeeha sannan ta d'aga hannu ta zabgawa Sabeeha mari har biyu ta ce "Uban waye yace miki ana kallo na haka?" Saurin k'asa da Kai Sabeeha ta yi hawaye na bin fuskar ta domin Marin ya shige ta ba k'arya damk'ar gashin kanta da matar ta yi ne yasa ta sakin k'ara amma duk da haka matar bata sake ta ba ta fara janta har zuwa wani d'aki ta turata fad'uwa Sabeeha ta yi kanta ya buge da tiles take wajen ya fara jini rintse idanunta ta yi tana jin wata azaba na ratsa ko Ina na jikin ta ga wani sanyi da yake ratsa ta da baya-baya ta ja sannan ta jingina jikin wata kujera dake d'akin wacce duk fad'in d'akin ita kad'ai ce a ciki curewa waje d'aya ta yi ta kifa kanta da gwiwa tana kuka a hankali. Matar dake bakin k'ofa ta ce "Kee!! Kiyi mana shiru a nan idan kuwa ba haka ba na lahira sai ya fi ki jin dad'i," wayar matar da ta fara ringing ne yasa ta d'aga cikin ladabi ta ce "Allah ya ja da ran Yallab'ai," sannan ta ce "Eh an kawo ta to Yallab'ai zan ganar da ita azaba kamar yadda ka buk'ata shikenan angama," daga haka ta katse wayar ta ja k'ofar d'akin ta rufe da key Sabeeha kuwa addu'a kawai take jerawa cikin ranta. A gida kuwa asuba a idanun Sabreen ta yi saurin tashi ta yi ta shige toilet ta d'auro alwala ta yi sallah ta dad'e tana addu'ar Allah ya kare mata 'yar uwar ta sannan ta tashi ta fice daga d'akin duk Maleek na kallon ta direct part d'in su Sabeeha ta nufa tana sauri har tana yin tuntub'e tana shiga falon ta tarar ba kowa cikin bedroom d'in Sabeeha ta shiga sai ta ga wayam sannan bata ji motsin ta a toilet ba hakan ya tabbatar mata kenan mutanen sun tafi da Sabeeha zama ta yi gefen gadon ta saka kuka tana tunanin shikenan yanzu an tafi da 'yar uwar ta yanzu basu San a halin da take ciki ba shin tana raye ne ma ko sun kashe ta suna nan garin ko ma sunbar k'asar da ita oho shin ko tana raye zasu sake ganinta ko kuwa shikenan sun rabu kenan da saurin Sabreen ta fara girgiza Kai kamar wata tab'abb'iya a fili ta furta "Bazai yuwu ba ba abinda zai faru dake Sabeeha dear zaki dawo gare mu zamu yi rayuwar farin ciki," ta k'arashe maganar cikin kuka. Ta dad'e tana kukan sannan ta tuna Maleek fa ya farka sannan fito Yana kallon ta ba tare da tace masa komai ba karfa ya gane ba ita bace Sabeeha da sauri ta mik'e ta nufi hanyar fita tana sauka down stairs sai ta ga Nasreen a tsaye kallon tsaf ta yi mata sannan ta ce "yammata ya jikin mijin ki?" Banza Sabreen ta yi Mata ta yi hanyar fita shan gabanta Nasreen ta yi ta ce "Ya Ban gama magana dake ba za ki wani tafi?" Nan ma Sabreen ta kasa cewa komai. "Ke ko Wai rashin maganar mijin ki ne ya dawo kan ki Kuma fa Ina ganin daga wannan cutar zaku wayi gari ku ga sai gawar sa," wani mugun kallo Sabreen ta watsa mata sannan cikin harzuk'a ta ce "Wallahi karki kuskura ki ce zaki shiga sabga ta domin hakan bazai miki kyau ba idan Kuma Kinga zaki gwada ki cigaba ni kuma zan nuna miki tawa haukar tafi taki stupid kawai," Sabreen na fad'ar haka ta fice tabar Nasreen a tsaye sake da baki. A fili ta ce "Stupid," sai kuma ta kyalkyale da dariya ta ce "A sannu zan nuna miki karawa da Nasreen ba abune mai sauk'i ba Sabreen," tana fad'ar haka ta haye stairs abinta. Da sallama a bakin ta ta shiga d'akin kallon ta kawai Maleek ya yi a hankali ta k'arasa wajen sa ta tsaya ta kasa furta ko da kalmar a ce shi kuwa d'auke kansa ya yi sai Kuma kanta a k'asa ta ce "To yanzu ta ya zata iya yin sallah?" Shiru ba magana daidai lokacin Ummi da Fauwaz suka yi sallama a hankali Sabreen ta sauke ajiyar zuciya tare da amsa musu sallamar suka shiga suka zauna gaishe su ta yi yayin da idon Fauwaz ke a kanta baya ko k'iftawa ganin idanunta sunyi jajir alamar ta yi kuka. Suna had'a ido ta ce "Dama za shi toilet ne," tashi Fauwaz ya yi ya nufi wajen Maleek ya kalle shi murya a raunane ya ce "Sannu Yaya," lumshe masa ido kawai Maleek ya yi Ummi ma wajen sa ta nufa ta zauna gefen sa ta shafa lallausar sumar kansa ta ce "Sannu kaji Son Allah ya baka lafiya," jinjina kai ya yi a zuciyar sa kuwa ya amsa da Ameen Ummina. Salman ne ya shiga d'akin Umar na binsa a baya ganin halin da Maleek d'in ke ciki ya k'arasa da sauri yana salati kamar k'aramun yaro haka Umar ya saka kuka domin shi Salman ya yi masa bayanin anahin abinda ke faruwa. Ummi ke rarrashin sa dakyar ya yi shiru Maleek kuwa da kallo yabi Umar ganin irin kukan da yake yi ya gane tabbas Salman ya sanar da shi abinda ke faruwa girgiza masa Kai kawai Maleek ya yi. Har da Umar suka sa shi a wheelchair sannan Umar ya tura shi zuwa toilet ya cire masa rigar jikin sa sannan ya d'aura masa towel a k'ugunsa sannan ya zare masa boxer d'in jikin sa ya fara masa brush sannan ya yi masa wanka sannan ya rufa masa wani towel d'in a jikin sa ya tura shi domin fita daga bathroom d'in. Jin motsin za a bud'e k'ofar yasa Sabreen saurin cewa "Ummi Bari naje nayi masa breakfast," kafin Ummi tayi magana har ta fice daga d'akin. Kitchen ta shiga ta fara had'a breakfast har ma dasu Ummi da Fauwaz da tasan babu abinda yaci gamawa ta yi tas sannan ta jera a babban tray ta nufi d'akin da sallama ta shiga da sauri Fauwaz ya k'arba yana yi Mata Sannu. Zama tayi gefen gadon lokacin har an shirya Maleek cikin bak'aken k'ananan kaya ya yi kyau sosai abincin Ummi ta zuba a plate ta mik'awa Sabreen ta ce "Ungo Daughter bawa Son," ta mik'a hannu zata karb'a sai Fauwaz ya yi wuff ya karb'a ya ce "A'a Ummi bani ni zan ba shi," Ummi bata kawo komai a ranta ba Fauwaz kuwa gefen Maleek ya koma ya fara bashi abincin. "Daughter kema ya kamata ki ci abincin," Ummi ta fad'a tana kallon Sabreen da dama yunwa take ji rabon ta da abinci tun jiya da rana a hankali ta ce "To Ummi," zuba abincin ta yi a plate tana ci kamar wata mara gaskiya. Kallon ta Maleek ke yi a zuciyar sa Kuma mamaki yake yi yaushe Sabee ta fara cin chips saboda tunda ta samu ciki ta dena cin chips ko k'amshin sa amai yake sata amma yanzu gashi tana ci sannan Kuma yanzu bata so suna had'a ido sannan wannan ba d'and'anon girkin ta bane mai ya ja hakan wata zuciyar tace may be rashin lafiyar ka ne ya ja Mata wannan canjin. Kallon spoon d'in chips da Fauwaz ya kai bakin sa ya yi ya girgiza Kai alamun ya k'oshi sannan ya ba shi ruwa ya sha. "Ya Fauwaz Kai baka ci abincin ba ko kaci wani Abu ne?" Sabreen ta fad'a tana kallon sa girgiza Kai ya yi ya ce "A'a sister bara dai naci yanzu," ya fad'a tare da fara cin ragowar da ya bawa Maleek. Tashi Umar ya yi ya kalli Fauwaz ya ce "Fauwaz Ina Sabreen ne?" Daram gaban Sabreen da Fauwaz ya fad'i. "Amm Ya Umar tana gida," Umar ya ce "Dama Meeha ce ke son ganinta ka sanar da ita sai na biya ta gidan muje saboda bata da lafiya ne," Fauwaz da har ya fara zufa ya ce "Ai da...ma ita ma bata da la..fiya ne shiyasa," ya k'arasa maganar cikin in Ina jinjina Kai Umar ya yi ya ce "Ok ba damuwa zan sanar mata bari naje zan dawo anjima insha Allah," Ummi ta ce "To ka yi Mata Sannu Allah ya bata lafiya," ya amsa da "Ameen," tare da ficewa. "Mai yake samun Daughter d'in?" Ummi ta fad'a tana kallon Fauwaz d'an ajiyar zuciya Fauwaz ya yi ya ce "Ummi tun jiya da muka koma gida tace mun kanta na yin ciwo daga baya Kuma sai zazzab'i ya kama ta," Ummi ta ce "Ayyah Allah ya bata lafiya Kira mun ita a waya nayi mata sannu," da Sauri Sabreen dake kallon sa ta fara girgiza kai fara lalubar k'aryar da zai yi Fauwaz ya fara Sabreen ta yi saurin cewa "Laaa Ummi ai jiya nan Sabreen ta manta wayar ta," Fauwaz ya ce "Au dama nan ta manta wayar ai mun d'auka fad'uwa ta yi kinji ashe ma tana nan amma Ina komawa zan fad'a mata kina yi mata sannu," Mik'ewa Sabreen ta yi ta fice tana fita hanyar part d'in su Sabeeha ta yi domin zuwa tayi wanka tana shiga bedroom d'in ta cire rigar jikin ta ta d'aura towel ta shige wanka tana fitowa ta nufi mirrow ta zauna. Mik'ewa Fauwaz ya yi ya ce "Ummi bara na d'an shiga ciki na dawo," gyad'a Kai kawai Ummi ta yi sannan ta kalli Maleek cikin tausayin sa ta ce "Son muje asibiti ko?" Girgiza mata kai ya yi saboda ya fahimci abinda tace masa. Fauwaz kuwa direct part d'in su Sabeeha ya shiga Kai tsaye ya shige bedroom ya hangi Sabreen ta mik'e tsaye domin ko Mai ta kasa shafawa ta baya ta ji an rungume ta a tare suka saki ajiyar zuciya sannan Fauwaz ya ce "Nayi missing d'in ki My love," waigawa ta yi ta kalle shi sai Kuma tasa kuka. Rikicewa Fauwaz ya yi ya ce "Subhanallah meya faru?" Cikin kuka sannan ta rungume shi tsam ta ce "My heart Sabeeha dear bamu San halin da take ciki ba sun tafi da ita me zasu yi mata tana da ciki fa," Sai lokacin Fauwaz ya tuna da cewar fa Sabeeha na da ciki amma suka yarda tasa kanta a had'ari ya ce "Ya Salam Allah ubangiji ya kare ta daga dukkanin sharri," Sabreen ta ce "Ameen amma meyasa kazo nan karfa wani ya ganka," ya ce "Ba Wanda ya ganni ni gurin matata nazo," shiru kawai Sabreen ta yi a jikin sa su n dad'e sannan ta shirya ita ta fara fita sai da ta dad'e sannan shima yabi bayan ta. Nasreen ce ta zauna gefen gadon ta ta kyalkyale da dariya a fili ta ce "Wannan ma wata hanyar ce da zan tarwatsa duk wani Shirin ku domin tunda Fauwaz mayen Sabreen ne zai cigaba da biyo ta nan part d'in dan Haka sai nayi musu video na nunawa Maleek da uwar su daga lokacin kuwa asirin su zai tonu," Da sallama Umar ya shiga bedroom d'in Sameeha tana kwance cikin blanket gefen gadon ya zauna jikin sa a sanyaye a hankali ta ya ye bargon sannan ta matsa kusa da shi ta shige jikin sa ta ce "Hubby me yake faruwa ne Dan Allah ka kaini naga Sabeeha dear saboda tun jiya nake yin munanan mafarkai a kanta Dan Allah ka kaini na ganta ko tana lafiya," ajiyar zuciya Umar ya yi sannan ya shafa kanta zuwa bayan ta ya ce "Ki kwantar da hankalin ki Meeha Sabeeha na lafiya yanzu ma daga can nake Sabreen ce Kawai Fauwaz ya ce mun bata jin dad'i zan Kai ki wajen Sabeehan amma sai kinji sauk'i kinji?" Noding kanta ta yi amma har lokacin hawaye take yi domin a mafarki ta gani cewar Sabeehan su na cikin wani hali sai wata zuciyar ta ce Wannan ba komai bane illa rashin lafiyar Sabreen da mafarki ya hargitsa Miki komai ya danganta hakan da Sabeeha sai Kuma ta ji hankalin ta ya d'an kwanta. Sabeeha kuwa tunda asuba ta yi ta fara buga k'ofar d'akin da take ciki wannan tsohuwar ta bud'e tana aikawa da Sabeeha wani mugun kallo. "Dan Allah baba ki taimake ni ki bud'e ni nayo alwala nayi sallah," tas fas ka ke ji matar ta wanke fuskar Sabeeha da maruka sannan cikin d'aga murya ta ce "Uban waye ya sanar dake Zaki yi sallah a nan gidan da har Zaki tashe ni Ina bacci to kinyi na farko Kuma da k'arshe," ta fad'a tare dasa k'afar ta ta daki cikin Sabeeha. Baya Sabeeha ta yi ta fad'i dafe da cikin ta tare da sakin wani ihu saboda wani abu da taji ya mugun tsira mata a cikin ta saka kuka tana murk'usu su matar Kuma ta ja tsaki ta ja k'ofar d'akin ta rufe ta bar wajen. [10/25, 8:56 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️ RUBUTAWA DAGA HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ) SADAUKARWA GA MY DAUGHTER SABEEHA BILKISU Z. YA'U (🅱️K) AISHA MAGAJI DABO A (AMA) Page 33 Sosai cikin Sabeeha ya fara ciwo mararta na murd'a mata gaba d'aya ta fita hayyacin ta daga nan bata sake sanin inda kanta yake ba. Ruwan da aka kwara Mata a jiki ne yasa ta farfad'o daga sumar da tayi k'ok'arin tashi zaune take yi amma ta kasa tsohuwar ta gani a kanta a tsaye tana aika mata da wani mugun kallo. Dakyar ta iya tashi zaune tana rintse idanu kallon banza tsohuwar ta yi mata sannan ta ce "Tashi yanzu muje ki d'ora mana girki," kallon ta Sabeeha ta yi a zuciyar ta ta ce girki Kuma sai ta fara k'ok'arin tashi tsaye dakyar ta iya tashi tsaye tana dafa bango matar ta juya ta yi hanyar fita Sabeeha na binta a baya har zuwa kitchen suna shiga matar ta ce Yanzu muke buk'atar kiyi mana girki ga kayan nan daga haka matar ta fice daga kitchen d'in. Zama Sabeeha ta yi dafe da cikin ta dake yi mata ciwo tana kallon shinkafar da aka nuna mata a k'alla tayi kwano uku. Tunawa tayi da wayar da Sabreen ta bata ta yi da sauri ta lalubo wayar ta fara neman layin Sabreen. Sabreen dake zaune kan kujera tana facing Maleek wayar ta ta fara ringing kallon wayar ta yi tana ganin number d'in ta gane ta da sauri jikin ta har rawa yake yi ta ce "Hello dear," k'asa_k'asa cikin muryar wahala ta ce "Sabreen dear Ina My ya jikin sa?" Maleek kamar yasani sai kallon Sabreen yake yi ba ya ko k'iftawa. Hawaye ne ya zubowa Sabreen saboda jin muryar Sabeeha kamar tana cikin wahala a hakan ma batasan saita muryar Sabeeha ta yi ba. "Dear lafiya ki ke kuwa Mai yake faruwa ne Sameeha dear yaushe Zaki zo sannan ya yanayin abun yake har yanzu mu ba muji wani sakamako ba," take Sabeeha ta gane cewar Sabreen na cikin mutane sannan ta fahimci inda tambayar ta dosa a hankali cikin muryar azaba ta ce "Dear kina tare da My ne?" A hankali Sabreen ta ce "Eh," "Shikenan sai na k'ara Kiran ki ki kwantar da hankalin ki zandawo very soon," daga haka ta kashe wayar gaba d'aya ta b'oye sannan ta kalli wata k'ofa ta bud'e sai ta ga ashe toilet ne da sauri ta shiga a gurguje tayi alwala ta fito ta kalli inda take tunanin nan ne alk'ibla ta tada sallah tana idar ta fara k'ok'arin had'a itace a cikin k'aton murhun dake kitchen d'in haka ta cigaba da aikin tana dafe cikin ta dake mata tsananin ciwo idanunta Kuma yana zubar da hawaye ga hayakin itacen a haka ta k'ok'ar ta ta d'ora k'atuwar tukunyar a haka dakyar ta dafa jallop d'in shinkafar sannan ta bubbuga k'ofar kitchen d'in matar ta bud'e tare da ture Sabeeha ta shige cikin kitchen d'in ta bud'e tukunyar iya k'amshin da taji ne ya tabbatar mata da girkin bana wasa bane wajen dad'i. Kallon Sabeeha ta yi ta ce "Wuce mu tafi," fita ta yi matar na binta har d'akin da take ciki ta tura ta ciki ta kulle malala Sabeeha ta kwanta saman tiles d'in d'akin ga cikin ta da yake ciwo ga yunwar dake damun ta domin rabon ta da abinci tun jiya da safe gashi goshinta da ta buge a jiyan shi ya haifar Mata da wani ciwon kai ta dad'e sosai a kwance sannan tsohuwar ta bud'e k'ofa ta shiga har gaban Sabeeha ta k'arasa ta ajiye mata wani k'aramun kwano da abincin da bai fi loma biyar ba sannan ta juya ta fice. Abincin Sabeeha ta kalla ta fashe da kukan tausayin kanta ta dad'e tana kukan sannan bacci ya d'auke ta a wajen domin tunda ta samu cikin yawan bacci ne da ita. Dukan da taji ta ko Ina shi ya tashe ta daga baccin a mugun firgice tana kallon matar cikin d'aga murya matar ta ce "Waye ya Baki izinin yin bacci tashi yanzu muje ki d'ora abincin dare," gaban Sabeeha ne ya fad'i jin abinda matar ta fad'a sai dai bata da damar musawa sai kawai ta tashi tana tafiya a hankali saboda yanayin da jikin ke ciki ga gajiyar dake damunta. Har kitchen din matar ta rakata sannan ta kulle ta a ciki da sauri Sabeeha ta shiga toilet d'in da ta shiga d'azu tayi alwala ta yi sallar Azahar da la'asar da bata yi ba sannan ta d'ora girkin wannan karon Mai da yaji ta yi musu sannan aka mayar da ita d'aki aka kulle. Ko abincin ba a Kai Mata ba haka taci Wanda aka Kai Mata da rana saboda yunwar da take ji ga hannunta sai rad'ad'i yake yi saboda dakan yajin da ta yi haka taci abincin tana kuka tare da tuna gida. Haka rayuwar Sabeeha ta cigaba da tafiya kullum ita take yin girkin gashi wata sabuwar muguntar da ake mata kullum da daddare sai matar nan ta yi mata duka a cikin sati d'aya gaba d'aya Sabeeha ta fita daga hayyacin ta ta yi duhu sosai saboda rashin wanka ga k'aurin da jikinta yake yi saboda girki ga kanta duk a hannunta saboda dake dake ga babu isashshiyar k'oshi gashin kanta duk yayi datti idan ka ganta sai ka tausaya mata sosai. A b'angaren Sabreen kuwa abubuwa sun dame ta sosai ga rashin Sabeeha gashi har yanzu Maleek babu wani canji a wani b'angaren Kuma ga matsalar Nasreen kullum sai sunyi cacar baki jin dad'in ta d'aya da ko da yaushe Umar da Fauwaz da Ummi na part d'in dan haka ba ita ke kai Maleek toilet ba ba ita ke yi masa wanka da Shirin sa ba. A b'angaren Maleek kuwa gaba d'aya ya gama gamsuwa da cewar wannan ba Sabeen sa bace saboda kulawar da Sabeen sa ke bashi baza a tab'a had'a ta da ta sabeen sa ba abubuwa da yawa sun dame shi a ransa dan dai ba yadda zai yi ne kullum ko da idanunsa biyu zaka ganshi idanunsa a rufe ya fad'a duniyar tunani. Sabreen ce ta fito daga kitchen da tray a hannunta ta nufi d'akin su tana shiga Nasreen da Jamila dake lab'e suka tuntsire da dariya harda tafawa "Ai Jamila Ina fad'a miki ba paralysed ba kome waccan d'an iskan ke yi yau sai ya tashi ya sadu da yarinyar can kuwa ba haka ba ciwon mara ne ajalin sa yau," Jamila ta shek'e da dariya ta ce "Aikin ki na kyau ranki ya dad'e," daga haka suka juya suka bar part d'in. Sabreen kuwa da sallama ta shiga d'akin Fauwaz ya tare ta tare da karb'ar tray d'in hannunta ya ajiye sannan da kansa ya zuba abincin a plate yasa cokali sannan ya zauna gefen gado kusa da Maleek inda yake zaune akan wheelchair ya fara bashi abincin har sai da ya k'oshi Sabreen ta kalle shi ta ce "Abincin fa?" Girgiza Kai ya yi ya ce "Na k'oshi sister," bata ce komai ba ta mik'e ta fita daga d'akin ta nufi part d'in su Sabeeha kayan jikin ta cire ta d'aura towel sannan ta fad'a toilet domin yin wanka ta dad'e tana wankan sannan ta fito. Fauwaz ta gani zaune a gefen gado yana ganin ta ya mik'e da sauri ya nufe ta jikin sa na rawa ya rungume ta a d'an tsorace ta ce "My heart lafiya kuwa ka bari mana," k'ara k'ank'ame ta ya yi ya ce "Bazan iya ba my love bazan iya jure rashin ki a kusa dani ba kullum ina cikin buk'atar ki yanzu na kasa jurewa ne please help me," kallon tausayi ta yi masa tasan tabbas ya yi hak'urin rashin ta sannan ya yi kewar ta kamar yadda ita tayi kewar sa sai kawai ta zame towel d'in jikin ta suka fara sarrafa juna. Sun dad'e sosai suna aikin abu d'aya sannan suka yi wanka suka shirya Fauwaz shi ya fara fita sannan ta bi bayan sa daga baya. Tun kafin ta sauka down stairs take jiyo shewar Nasreen ko kallon ta Sabreen bata yi ba tayi hanyar fita sai dai har tasa k'afar ta waje ta ji Nasreen na fad'in "A yau sai na tonawa maciya amana biyu asiri ashe haka ake cin amanar Maleek ba a sani ba saboda a ganshi a kwance sannan ya auri jarababbiyar mata saboda haka vedion nan har a social media saina d'ora shi," daram dam gaban Sabreen ya fad'i ta yi saurin juyawa ta nufi inda Nasreen take. A tsaye kan Nasreen ta tsaya tare da lek'a wayar Nasreen d'in tabbas video d'in ta ne ita da Fauwaz d'azu da suna tare wani k'ululun bak'in ciki ne ya taso mata a zuciyar ta tana fad'in wannan wacce iriyar masifa ce a d'auki Mata a mijin ta a waya a lokacin da suke saduwa da junansu wannan ai haukane da jahilci. A harzuk'e Sabreen ta fisge wayar sannan ta dage ta bugata da k'asa ta tarwatse sannan ta kai hannu zata d'auki memoryn take hannun ta Nasreen ta yi da k'arfin gaske domin idan har Sabreen ta d'auke memoryn tabbas ta rasa hujjar ta domin ta rasa video d'in kenan har abada. Sosai Sabreen ta ji zafin taka ta da Nasreen ta yi dan haka da k'arfi tasa d'aya hannun ta tankad'a ta baya har sai da ta fad'i sannan ta d'auke memory card d'in tasa shi a baki ta taune shi tas sai da ya lank'washe ya k'arye sannan ta fito da shi tayi jifa da shi k'asa sannan ta kalli Nasreen ta ce "Wannan shine kashedi na k'arshe da zan yi Miki akan cewar ki fita a sabga ta idan kuwa ba haka ba sai na nuna miki wacece Sabreen," a harzuk'e Nasreen ta kaiwa Sabreen mari. Rik'e hannun Sabreen ta yi ta ce "Wannan shine kuskure na farko da zaki fara aikatawa a rayuwar ki ni da ki ke gani nafi k'arfin mari daga wulak'antaccen hannu irin naki," daga haka ta yi jifa da hannun Nasreen ta juya zata bar falon. Wani k'aton kuttun fulawa na k'asa dake gefe Nasreen ta d'auka tabi bayan Sabreen da shi. Sam Sabreen bata ji tahowar Nasreen ba sai ji kawai ta yi an buga mata abu a kanta k'ara ta saki ta fad'i a wajen sumammiya ba numfashi. Jifa da abun Nasreen ta yi a tsorace ganin Sabreen kwance babu numfashi ga jini na zuba a kanta a hankali Nasreen ta ce "Na shiga uku Allah dai yasa Sabreen bata mutu ba domin idan ta mutu na tabbata Fauwaz Kashe ni zai yi," Fauwaz da ya dad'e da komawa wajen Maleek ya ji shiru ba Sabreen ba alamar ta gashi Kuma tunda ya shiga d'akin ya lura da Maleek d'in bai da lafiya bayan rashin lafiyar dake damunsa domin sai rintse ido yake yi yana cije lips sannan yana d'an juya kansa maganar duniya Fauwaz ya yi masa amma yak'i kula shi daga k'arshe ma ya lumshe idanunsa domin shi baisan ta Ina zai fara yiwa Fauwaz bayanin abinda ke damun sa ba ko da yana baki balle babu bakin magana sannan ko da akwai baya tunanin zai iya fad'awa kowa abinda ke damunsa indai ba matar sa. Gashi kuma baida lafiyar da zai iya biyawa kansa buk'ata hawaye masu zafi ne suka gangaro masa daga idanunsa. A rikice Fauwaz ya ce "Subhanallah Yaya me yake faruwa ne meke damun ka?" Shiru ba magana domin idanun Maleek a rufe suke ma balle ya kalli bakin Fauwaz ya fahimci abinda yake fad'a Wanda ko da ya gani babu bakin magana. Fauwaz kuwa duk ya rud'e ga halin da yayan sa ke ciki a wani b'angaren Kuma har yanzu Sabreen shiru bata dawo ba. Gaba d'aya hankalin sa a tashe yake tunanin sa yak'i ba shi daidai akan k'in shigowar Sabreen da sauri ya mik'e ya yi hanyar fita direct part d'in su Sabeeha ya nufa domin dubo Sabreen. [10/25, 8:57 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️ RUBUTAWA DAGA HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ) SADAUKARWA GA MY DAUGHTER SABEEHA BILKISU Z.YA'U (🅱️K) AISHA MAGAJI DABO (AMA) Page 34 Babu ko sallama ya shiga falon ya samu Nasreen a zaune a kan kujera ta had'a uban gumi duk da kuwa AC dake falon kallo d'aya yayi Mata ya haura stairs kai tsaye. Yana shiga falon ya fara Kiran ta "My love! My love!" Amma shiru hakan yasa ya fara nemanta amma bai ganta ba nan fa hankalin sa ya k'ara tashi down stairs ya dawo har zai fita sai Kuma ya kalli Nasreen fuska a matuk'ar sannan a had'e ya ce "Kee! Kingan ta?" "Wafa?" Ta tambaya, ba tare da wani tunani ba kansa tsaye ya ce "Matata mana," duk da tana cikin tashin hankali sai ta ce "Dama tazo gidan nan ne?" Wani banzan mahaukacin kallo Fauwaz ya aika mata sannan cikin had'e fuska da kumbura murya ya fara fad'in "Dalla can malama karki raina mun hankali ina matata nace?" Jikin ta har ya fara rawa ta ce "Wallahi bangan ta ba," tsaki Fauwaz ya ja ya ce "Iskancin banza," ya fad'a tare da ficewa daga part d'in gaba d'aya. Sai da ya fita Kuma ya fara tunanin shin ina Sabreen zata je a wannan lokacin wata zuciyar ta ce ko tana part d'in Ummi ne Kai tsaye ya nufi can d'in domin dubata da sallama ya shiga falon da yake tsaf-tsaf sai tashin k'amshi yake yi Ummi dake saukowa stairs ta amsa masa sallamar sannan ta ce "Ina Shirin zuwa can wajen ku sai ga ka lafiya dai ko?" Ya ce "A'a Ummi Sabreen tazo nan kuwa?" Kallon tambaya Ummi ta yi masa sannan ta ce "Sabreen tazo nan ne dama?" Da sauri ya ja bakin sa ya yi shiru sannan ya ce "Sorry Ummi Sister zance matar Yaya," "Bata shigo ba lafiya dai ko?" Dakyar ya iya k'ark'aro murmushi ya ce "Eh Ummi bari naje," bai jira cewar ta ba ya fice abinsa da kallo Ummi ta bi shi tabbas tasan akwai abinda ke faruwa tunda ta ga yanayin Fauwaz haka sai kawai tabi bayan sa. Yana shiga d'akin da Maleek yake da sauri ya k'arasa ganin yadda Maleek d'in ya had'a uban gumi sai cije pink lips d'insa yake yi da suka k'ara pink tsabar wuya "Yaya mai yake damunka ne haka?" Maleek kam ba bakin magana sai bud'e idanunsa da ya yi da suka zama jajir tsabar wahala ya kalli Fauwaz baice komai ba Ummi ce ta yi sallama a d'akin itama da sauri ta k'arasa ta ce "Subhanallah Son lafiya kuwa?" Itama ta yi tata tambayar duk da tasan babu bakin amsa mata sai kallon ta itama da Maleek d'in ke yi ja da baya Fauwaz ya yi ya zauna akan kujera ya lumshe idanu. Zama Ummi ta yi gefen gadon da Maleek ke kwance tana cigaba da tambayar sa abinda ya faru ta ce "Kanka ke ciwo?" Ya girgiza mata kai "Ciki?" Ta tambaya gyad'a mata Kai ya yi a hankali ta kai hannunta kan cikin sa wajen tsakiya ta ce "Nan?" Ya girgiza kai wajen marar sa ta Kai hannun ta ce "Nan ne?" Gyad'a mata Kai ya yi yana rintse idanu. Ummi ta ce "Bari na Kira Doctor yazo ya duba ka," Nan ma ya girgiza kai Ummi ta ce "Shikenan bari na kira Umar shi yazo ya duba ka," Nan dai shiru ba magana. Number d'in Umar Ummi ta kira Yana d'agawa ta sanar da shi tana son ganinsa ya ce "To Ummi," Tana ajiye wayar sai Ummi ta kalli Fauwaz ta ce "Wai Ina Daughter d'in?" Da sauri ya bud'e idanunsa ya kalli Ummi sannan ya ce "Bari na duba ta," daga haka ya tashi ya bar d'akin ba dan yasan inda zai je duba Sabreen d'in ba. Bayan fitar Fauwaz da sauri Nasreen ta mik'e ta fara safa da marwa a falon domin jan Sabreen ta yi ta kaita wani d'aki ta kulle sannan tasa Jamila ta gyara wajen da jini ya b'ata. Sabreen kuwa dake kwance a k'asan tiles sanyin da tiles d'in ya d'auka ne yasa ta farfad'owa ta motsa hannunta sannan ta bud'e idanunta k'ok'arin mik'ewa take yi amma ta kasa saboda mugun sarawar da kanta keyi mata ji take yi kamar buhun sumunti aka d'ora mata akan nata idanunta sunyi jajir tsabar wahala dakyar ta iya mik'ewa tsaye tana dafa bango sannan ta nufi k'ofa sai ta jita a rufe bubbugawa ta fara yi Nasreen dake falon jin ana bubbuga k'ofar ne yasa ta jin wani farin ciki ta nufi k'ofar da sauri ta bud'e. Dakyar Sabreen ta d'aga idanu ta kalle ta sannan cikin muryar wahala ta ce "Wannan d'in ba shi ki ka ci wallahi sai kin gane kuren ki," tana fad'ar haka ta nufi hanyar fita tana dafe bango. Dakyar ta iya Kai kanta part d'in Maleek tana bud'e k'ofar Fauwaz ta hanga kwance a kujera ya lumshe idanunsa tunani ne fal zuciyar sa akan Ina Sabreen ta tafi. Ita kuwa tafiya take yi ga wani jiri na d'ibar ta domin har lokacin jinin bai tsaya ba Sam Fauwaz bai ji tahowar ta ba sai ji kawai ya yi ta fad'a jikin sa a sume. Da sauri ya bud'e idanunsa yana kallon ta hankali a matuk'ar tashe ya ce "My love meya same ki haka?" Jin ba amsa sannan kamar bata numfashi yasa shi kwantar da ita a kan kujerar ya nufi fridge ya d'auko ruwa sannan ya shafa mata a fuska wata ajiyar zuciya ta saki sannan ta bud'e idanunta a kansa a hankali ta ce "My heart," kafin ya yi magana Ummi ta fito jin motsi a falon da ta yi da sauri ta k'arasa ganin halin da Sabreen d'in ke ciki ta ce "Subhanallah Daughter meya same ki haka ya kamata muje asibiti yanzu tana buk'atar taimakon gaggawa," Fauwaz da duk ya gama rud'ewa ya ce "A'a Ummi zamu je tare da ita ke kin zauna wajen Yaya shima yana buk'atar wani kusa da shi bari muje wajen Mama," tabbas maganar Fauwaz haka take sai kawai Ummi ta ce "Ok kuje to," ta fad'a tare da juyawa cikin d'akin ganin haka sai kawai Fauwaz ya d'auki Sabreen cak ya nufi hanyar waje da ita. A mota ya sata sannan ya ja motar zuwa asibiti yana driving yana kallon ta so kawai yake ya ji meya faru da ita haka sai ya ce "My heart garin ya hakan ta faru?" Rintse idanu ta yi sannan a hankali tana juya kanta da take jin ya yi mata nauyi ta ce "Nasreen ce," "Whatt!!?" Fauwaz ya fad'a tare da jan burki babu shiri Allah yaso ma babu motar dake binsu a baya da sai sun ja accident ta ce "Mu tafi My love kaina ciwo yake mun," Jan motar ya yi suka cigaba da tafiya bai k'ara cewa komai ba sai k'wafa kawai yake ja yana jijjina kai domin bazai tab'a bari hakan ya tafi a banza ba. Har suka je asibitin bai ce komai ba direct cikin office d'in Mama ya nufa Yana shiga Doctor ta tashi da sauri ta ce "Subhanallah meya faru da ita haka shigo da ita ciki," Mama ta fad'a tare da shigewa wani d'aki dake cikin office d'in ta Fauwaz na biye da ita akan gadon dake d'akin ya kwantar da Sabreen sannan ya ce "Mama a toilet na same ta a kwance Ina ga fad'uwa ta yi," jinjina Kai kawai Doctor ta yi ba Dan ta yadda da hakan ba domin yanayin ciwon baya nuna alamun fad'uwa ta yi treating d'in ta kawai ta fara yi Fauwaz na zaune a gefe. Yana zaune har aka gama Sabreen d'in ma ta samu bacci ya mik'e ya kalli Doctor ya ce "Mama Bari naje gida na kawo mata abinda zata ci," girgiza Kai Doctor ta yi ta ce "A'a bari na Kira Halima ta kawo kawai," ta fad'a tare da d'aukar wayar ta kan table ta kira Halima ta ce yanzu Faisal ya kawo ta hospital ta taho da abinci Halima ta amsa da "Toh Mama," daga haka Doctor ta ajiye wayar ta zauna tana tunanin to garin ya ya Sabreen ta ji irin wannan ciwon haka. Fauwaz ya mik'e ya kalli rigar jikin sa da ta gama b'aci da jini ya ce "Mama Bari naje na canja kaya," ta ce "To sai ka dawo," fita kawai ya yi domin damuwar sa ba akan ya canja kayan bane illa ya je ya ci uwar Nasreen kawai. Mota ya shiga a matuk'ar fusace yake driving har ya je gidan direct a can part d'in ya yi parking sannan ko tsayawa kulle k'ofar bai yi ba ya shige cikin falon. Nasreen dake daining area tana zuba abinci a plate ba tasan shigar Fauwaz sai kawai ji ta yi anyi ball da ita ta bugi fridge d'in dake wajen abinci muka ya k'ife Mata a jiki wata k'ara ta saki Fauwaz ya zare belt ya fara dukan ta baji ba gani sai ihu take yi bai kyale ta ba sai da ya ga ko motsi bata iyawa sannan ya kyale ta ya ce "Kuma Wallahi akan matata sai naci uwar ki Wallahi shegiya dak'ik'iya Kuma wallahi kallon banza ya sake had'aki da Sabreen ba ke ba Uwar ki da ubanki ma sun shiga uku," Yana fad'ar haka ya juya ya fice yabar banza a wajen da k'aton k'ulu a gaban goshi. Yana fita mota ya shiga zuwa part d'in Ummi ya yi wanka ya canja kaya sannan ya nufi asibitin. Umar ne ya fito daga bedroom Sameeha na biye da shi ya kalle ta ya ce "Meeha kiyi hak'uri mana ki k'ara jin sauk'i sai muje," bubbuga k'afa ta fara yi cikin tsantsar shagwab'a ta ce "Uhm uhm nidai sai na bika naji sauk'i fa," ya girgiza Kai ya ce "Ban yadda ba," k'arasawa wajen sa ta yi ta shige jikin sa ta rungume shi sosai ta hana shi tafiya ya ce "Meeha rigima to ki cikani na tafi mana Kinga Ummi na jirana," ta ce "Uhm uhm ni sai ka je dani," "Is okay d'auko hijabin ki mu tafi to," cikin farin ciki ta sake shi ta nufi bedroom har zata shiga sai ta tsaya ta waiga ta kalle shi ta ce "Hubby kar fa ka gudu ka barni," murmushi ya yi ya ce "Bazan tafi ba," ta ce "Promise?" Ya ce "Yes I promise dear," juyawa ta yi cikin bedroom d'in ta milk d'in hijab ta d'ora saman cofee shadda dake jikin ta ta d'auki hand bag d'in ta da takalmi ta fito ya rik'e hannunta suka bar gidan. Da sallama Fauwaz ya shiga office d'in Doctor ya samu Sabreen zaune suna fira da Mama da sauri ya k'arasa ya zauna gefen ta ya ce "Sannu My love," ta ce "Yawwa My heart ka dawo?" Ya ce "Eh na dawo," "Yanzu zaku iya tafiya ai tunda ta ji sauk'i," Mama ta fad'a tana had'a takardun gaban ta Fauwaz ya ce "To Mama My love taso mu tafi ko saina d'auke ki ne?" Tashi ta yi tana dariya ta ce "A'a zan iya," ta fad'a suna nufar hanyar fita Doctor kuwa da kallo ta bisu tana girgiza kai. Mota suka shiga suka nufi gidan Ummi har k'ofar part d'in su Sabeeha ya yi parking suka shiga tare hannun su rik'e da na juna a falon suka samu Nasreen zaune a saman kujera sai kuka take yi Jamila na gasa mata jiki kallon ta Sabreen ta yi sannan ta kalli Fauwaz da sauri ya kawar da fuska irin baisan zancen ba Sabreen kuwa tunda ta ga haka tasan aikin sa ne sai kawai ta kyalkyale da dariya ta ce "Nasreen ya ki ka ga aikin mijina abun Sona aina fad'a Miki ba shi kika d'auka wawiya kawai," Tana fad'ar haka suka haura stairs. Kayan jikin ta ta cire sannan ta d'aura towel suka shiga toilet Fauwaz da kansa ya yi Mata wanka sannan ya shirya ta suka fita mota suka shiga zuwa part d'in Maleek da sallama suka shiga d'akin. Suka samu Umar da Sameeha a d'akin Sameeha na ganin Sabreen ta mik'e da sauri ta nufi Sabreen tare da fad'in "Sabreen dear Mai ya faru dake haka?" Gaba d'aya mutanen wajen suka bi su da kallo har Maleek dake kwance sai da ya kalli wajen Ummi ta ce "Sabreen Kuma?" Sameeha ta ce "Eh Ummi Sabreen dear ce," [10/25, 8:58 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️ RUBUTAWA DAGA HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ) SADAUKARWA GA MY DAUGHTER SABEEHA BILKISU Z.YA'U (🅱️K) AISHA MAGAJI DABO (AMA) Page 35 "Dear Mai ya faru dake haka?" Gaba d'aya kasa magana Sabreen ta yi Ummi ta ce "Sameeha wannan fa Sabeeha ce," kafin Sameeha ta yi magana Fauwaz ya ce "Eh fa may be dan ta gan mu tare ne ta yi tunanin ko My love ce," kallon Sabreen d'in Sameeha ta yi domin duk duniya babu mai fad'a mata 'yan uwan ta tasan Sabreen haka ma Sabeeha amma ita Ina Sabeeha dear take da ake Kiran Sabreen da sunan ta Kuma meye dalilin da yasa Sabreen take amsa sunan Sabeehan haka ta dinga tunane tunane a zuciyar ta. "Kai dear su abun Kuma har da k'in gane ni ai Sabreen dear na gidan ta bata jin dad'i ne," Sabreen ta fad'a tare da kashewa Sameeha ido ba tare da kowa ya lura ba. Sameeha ta ce "Sorry dear na bangane ki da wuri ba," Ummi ta yi dariya ta ce "Daughter wato har kin fara manta Sabeeha ko?" "Ai kyale ta kawai Ummi nima zan rama," Sabreen ta fad'a tana dariya Maleek kuwa idanunsa ya mayar ya lumshe. Umar kuwa bayan ya duba Maleek ya gane cewa desire tablets yasha amma abin tambayar shine waye ya ba shi bayan ga halin da yake ciki bai yi tunanin fad'awa ko da Ummi abinda ke faruwa ba ya dai yi masa allura tare da magani sannan ya kalli Sabreen ya ce "Sabeeha zan d'an ganki yanzu," ya fad'a tare da barin d'akin bin bayan sa Sabreen ta yi a falo ta same shi a zaune zama ta yi ta ce "Ya Umar gani," "Dama so nake na sanar miki cewar ki dinga kula da abincin da MG zai dinga ci saboda a bincike na naga desire tablets aka zuba masa a abinci ya kamata kisa idanu akan Nasreen sosai domin babu shakka ita tasa masa," jinjina Kai Sabreen ta yi domin wani tausayin Maleek ne ya rufe ta saboda bai yi dacen mata ba sannan mai son sa tsakani da Allah bata nan ba asan halin da take ciki ba. Tashi Umar ya yi ya fita daga part d'in gaba d'aya domin shima mugun tausayin Maleek yake ji. Komawa cikin d'akin ta yi babu Wanda ya tambaye ta yadda suka yi da Umar itama bata fad'a ba Sameeha ta tashi ta kalli Sabreen ta ce "Dear yunwa nake ji muje ki bani abinci," ta fad'a tana fita daga d'akin. Sarai Sabreen tasan ba wata yunwa da Sameeha ke ji kawai so take yi su keb'e akan batun Sabeeha bin bayan ta Sabreen ta yi suka nufi d'ayan part d'in a falo suka ya da zango. "Dear kiyi mun bayanin abinda ke faruwa Ina Sabeeha dear take?" Hawaye ne ya zubowa Sabreen ta ce "Bansani ba dear bansan inda Sabeehan mu take ba," "Kamar ya kenan Sabreen sister me ki ke nufi da ba a ga Sabeeha dear ba?" Sameeha ta fad'a itama tana hawaye. Tas Sabreen ta kwashe abinda Sabeeha ta fad'a musu ita da Fauwaz ta sanarwa Sameeha. Zuwa lokacin kuka sosai Sameeha take yi mai sauti cikin kukan take fad'in "Why why Sabreen sister meyasa ke da Sabreen sister zaku b'oye mun wannan d'in Sabreen akan meyasa zaku bar Sabeeha dear ta tafi bakwa tunanin samun matsala ga rayuwar ta ko cikin dake jikin ta kinsan munanan mafarkan da nake yi akan ta kuwa?" Sosai k'arar kukan Sabreen ya k'aru ta rungume Sameeha suka cigaba da kuka babu Mai rarrashin wani a cikin su. Cikin kuka Sameeha ke fad'in "Sabreen dear yanzu shikenan ba wani labari akan Sabeeha dear ki duba fa halin da Ya MG ke ciki shin idan har wani Abu ya faru da Sabeeha wane hali ki ke tunanin zai shiga mu ma ya rayuwar mu zata kasance babu rabin jikin mu?" Ta Kuma sakin kuka. Daidai lokacin wayar Sabreen ta fara ringing ganin number d'in Sabeeha yasa ta saurin d'agawa tasa a handsfree ta ce "Hello dear," Daga can Sabeeha dake rakub'e murya a wahalce ta ce "Dear kuka ki ke yi Mai ya faru dake?" Wani kukan ne ya Kuma kufcewa Sabreen saboda tausayin 'yar uwar ta domin ko da sau d'aya mutum yasan muryar Sabeeha ya ji ta a yanzu yasan tana cikin mawuyacin hali yasan a wahalce take amma bata damu da halin da take ciki ba sai ma tambayar Sabreen d'in da take yi meyasa take kuka Sameeha ma jin muryar Sabeeha na fita dakyar ne yasa ta sakin nata kukan. "Dan Allah kar ku k'ara tayar mun da hankali meya faru ku ke yin kuka Sabreen dear maiyasa zaki fad'awa Sameeha?" Ta k'arasa maganar a wahalce. "Meyasa Sabeeha dear akan me zaki tafi a lokacin da muke buk'atar ki a lokacin da Ya MG yafi buk'atar kulawar ki?" Hawaye ne suka zubowa Sabeeha ta ce "Ya My d'in yake yanzu?" "Da sauk'i dear ki fad'a mana inda kike muzo mu ma please," Sabreen ta fad'a kamar tana gaban su ta fara girgiza kai domin ko mak'iyin ta baza ta so ya shiga irin halin da take ciki ta ce "A'a dear kawai ku cigaba da tayani da addu'a ita kad'ai nake buk'ata a halin da nake ciki yanzu," ta fad'a tari na sark'e ta a tare suka ce "Maiya faru dear Mai ya same ki?" Kafin ta yi magana suka ji k'arar mari "fass tass!!," "Ke!! Ke da uban waye kike magana Kuma dame kike maganar Zaki bani ko saina gana Miki azabar da tunda kike baki tab'a fuskantar ta ba?" Tsohuwar ta fad'a tare da buga kan Sabeeha a bango hakan yasa ta saki wata razananniyar k'ara ta fad'i sumammiya. A tare Sabreen da Sameeha suka sa hannun su a baki domin hana kukan dake niyyar kufce musu fitowa suna kallon wayar Kiran ne ya katse. Kuka sosai Sabreen da Sameeha ke yi kamar ransu zai fita Sameeha kuwa da gudu ta yi hanyar fita daga falon tana fita wajen part d'in taci karo da Umar jikin sa kawai ta fad'a tana sakin kuka a rud'e yake tambayar ta meya same ta amma ko magana ta kasa hakan ne yasa ya bud'e gaban mota ta shiga shima ya shiga ya ja motar suka bar gidan gaba d'aya. Suna zuwa ya fara rarrashin ta tare da tambayar ta meyasa take kuka amma ta kasa fad'a masa haka ya hak'ura da jin dalilin kukan sai rarrashin ta da ya cigaba da yi har tayi shiru sai dai zazzzab'i ya rufe ta. Sabreen ma a haka Fauwaz ya same ta tana kuka fuskar ta duk ta kumbura idanunta sunyi jajir da ya tambaye ta bata b'oye masa ba ta fad'a masa abinda ke faruwa shima hankalin sa ya tashi sosai amma haka ya dake ya rarrashi Sabreen amma itama zazzab'i ne ya rufe ta. B'angaren Sabeeha kuwa tsohuwar ce ta d'ebo ruwa cikin bokiti ta juyewa Sabeeha a jikin ta a razane Sabeeha ta tashi zaune gaba d'aya ta fita hayyacin ta ko gane ta idan Wanda ya santa bazai iya ba kamar dai wata mahaukaciya. "Dan kutmar ubanki zaki bani abinda ki ke magana da shi ko saina sauyawa fuskar ki kamanni?" Shiru Sabeeha ta yi domin bata jin zata iya bada wayar nan. Duka sosai matar ta yiwa Sabeeha duk ta ji mata ciwo a jiki amma Sabeeha bata ba da wayar ba hakan yasa matar ta zaunar da Sabeeha kan kujera ta d'aure ta tamau d'auri na mugun ta dan har k'ara sai da Sabeeha ta saki sannan ta mannewa Sabeeha baki yadda baza ta iya magana ba sannan ta ce "Na ga ta bakin da zaki iya magana shegiya aljana," ita kuwa hawaye kawai take yi domin jin jikin ta take yi kamar wacce aka yiwa wanka da markad'add'en attaruhu. A gaban ta matar ta d'auki waya tayi Kira kamar tana gaban ogan nasu ta tsugunna ta ce "Allah ya biya oga dama wannan yarinyar ce na kamata tana yin magana a d'aki to yanzu dai ga ta na d'add'aure ta ba irin dukan da banyi Mata ba amma tak'i bani wayar," "To abinda za ayi gobe dukan mu gang zamu zo nan domin kawai yarinyar nan kashe ta kawai zamu yi," tsohuwar ta ce "To,to ku iso lafiya," daga haka mutumin ya kashe kiran. Tass Sabeeha ta ji abinda mutumin ke fad'a tashi matar ta yi ta fice daga d'akin. Washe gari da safe Fauwaz ne ya shiga falon part d'in Maleek ya samu Ummi zaune ita da Doctor ya gaida Doctor sannan ya kalli Ummi hankalin sa a tashe ya ce "Ummi Daddy fa yazo gashi nan shigowa nan," kafin Ummi ta yi magana Daddy ya shiga falon cikin wata blue suit ya yi kyau har ya gaji kullum kamar k'ara masa kyau ake yi da gayu sai k'amshi yake yi mik'ewa kawai Ummi ta yi tana kallon sa har gaban ta ya k'arasa dakyar Ummi ta iya cewa "Sannu da dawowa," "Yawwa Aysha yadai naga kamar baki farin ciki da dawowa ta ba ko dai da wani Abu ne?" Ya fad'a yana shafa kwantaccen sajen sa Doctor ce ta gaishe shi ya amsa cikin fara'a. Sabreen ce ta fito daga cikin d'akin da kallo Doctor ta bita har zata tambaye ta me take yi cikin bedroom d'in Maleek sai Kuma ta yi shiru ganin da mutane a wajen. Har k'asa Sabreen ta gaida Daddy ya amsa cikin fara'a "Ina son fa?" Daddy ya tambaya yana kallon Ummi. "Yana ciki baya da lafiya ne," Ummi ta fad'a domin yanzu baza ta iya b'oyewa Daddy cutar d'an nasu ba. "Subhanallah me yake damun sa bari na ganshi," Daddy ya fad'a tare da nufar d'akin Kai tsaye su Ummi suka bi bayan sa. D'akin ya shiga da Sallama ganin Maleek d'in kwance baya motsi sannan bai amsa sallamar sa ba sai kallon mahaifin nasa kawai da yake yi yasa Daddy k'arasawa da sauri ya ce "Innalillahi Son what wrong with you," gaba d'aya Daddy ya gama rikicewa yama rasa abin yi ya kalli Ummi ya girgiza Kai "Yanzu Aysha Son yana cikin wannan halin amma you can't even tell bayan muna waya dake and you Fauwaz you can't even give me a call Nagode muku sosai mu shirya mu tafi asibiti kawai," girgiza Kai Maleek ya fara daidai lokacin Salman ya shiga d'akin da sauri bai lura da Daddy ba Maleek ya kalla ya ce "Boss labari na samu yanzu daga Ahmad cewar an samu nasarar shigo da kayan nan Nigeria ta wata hanyar da mu bamu San da ita ba yanzu haka suna k'asar nan a wani waje da mu ba musan ina bane yanzu haka sojojin daka tura nayi musu waya cewar su dawo gida," jiniyar dawowar sojojin ce ta cika gidan gaba d'aya Maleek ya shiga tashin hankali jin abinda Salman ke fad'a duk ya ma rasa abinyi. Nasreen ce tayi dariya ta kalli kalli Jamila ta ce "Da alama gidan nan yau akwai labari domin nasan zuwa yanzu burin Daddy na na gab da cika bari naje naga wainar da ake toyawa," ta fad'a tare da barin falon gaba d'aya direct part d'in Maleek ta same shi cike da mutane domin lokacin Sameeha da Umar ma sunje guri ta samu ta k'ace tana wani kad'a k'afa ita ga 'yar iska. Kowa idanunsa na kan Maleek dake kwance ya lumshe idanu kowa tausaya masa yake yi Daddy kuwa guri ya samu ya zauna Sam ya rasa tunanin da zai yi kallon Maleek kawai yake yi idanunsa sunyi jajir yanzu d'ansa da ya fi k'auna ne a wannan halin amma ba Wanda ya fad'a mishi. B'angaren Sabeeha kuwa ko rintsawa bata yi ba har safiya gashi igiyar da aka d'aure ta sai ci mata jiki take yi tana cikin wannan halin kawai ta jiyo wata murya a falon gidan kamar tasan muryar tana fad'in "Goggo! Goggo ta!!" Motsin bud'e k'ofa Sabeeha ta ji aikuwa ana bud'e k'ofa tabi wacce ta bud'e k'ofar da idanu tabbas Rashida ce da suka yi aiki da ita a gidan Yallab'ai khamis. Sam Rashida bata gane Sabeeha ba domin a tunanin ta ko mahaukaciya ce da sauri Rashida ta k'arasa ta ce "Na shiga uku Ashe har yanzu Goggo bata bar wannan halin nata ba wannan Kuma a Ina ta same ta?" K'ok'arin yin magana Sabeeha ke yi amma ba dama ganin hakan ne yasa Rashida d'ayewa Sabeeha abinda aka rufe mata baki da shi. "Rashida ni ce Sabeeha sun kamoni ne dan Allah ki taimake ni," cike da mamaki Rashida ke kallon Sabeeha ba tare da ta yadda ba ta ce "Kina nufin Sabeeha 'yan uku dana sani?" "Eh eh ni ce kar tazo please ki taimake ni," Sabeeha ta fad'a tana hawaye Rashida ta ce "Ni yanzu wanne taimako zanyi miki Sabeeha duka gidan nan a zagaye yake goggo ta kama mu har da ni zata had'a," "Rashida kwance mun hannuna," ba musu Rashida ta kwance ta duk a tsorace suke jiki na rawa Sabeeha ta d'auko wayar ta da Sabreen ta bata jiki na rawa ta fara rubuta number d'in Maleek ta fara Kira amma ba a d'aga ba a fili ta ce "Please My ka d'aga wayar," Kira na biyun ma ya katse ta sake Kira tana hawaye. Maleek dake kwance bai kalli inda wayar take ba ma saboda tunda ya kwanta cuta yana ji ana Kiran sa baya iya d'agawa Kira ne ya sake shigowa wayar a karo na hud'u Salman dake kusa da wayar a tsaye ya tura wayar kusa da Maleek domin ya ga mai kira. A hankali ya Kai duban sa kan screen d'in wayar kawai ya ga ansa "Sabee na," zare ido ya yi sannan ya Kai duban sa inda Sabreen da Sameeha ke zaune. Abun mamaki kawai sai gani suka yi Maleek ya tashi zaune zumbur ya d'auki wayar cikin cool and sweet voice d'in sa ya ce "Sabee na," duka mutanen wajen sun shiga rud'ani da al'ajabin abinda ya faru na tashin Maleek. Daga can Sabeeha cikin muryar Kuka ta ce "My kazo please," A rud'e ya ce "Kina Ina ne ina ki ka tafi?" "Bansan ina bane amma mutanen da ka ke nema duk suna hanyar zuwa inda nake bari na bayar a fad'a ma address," Sabeeha ta fad'a tare da mik'awa Rashida wayar. Kwatancen wajen ta yiwa Maleek jinjina Kai ya yi sannan ya mik'e tsaye ya kalli Fauwaz ya nuna masa Nasreen ya ce "Karka barta ta fita ko Ina," daga haka ya fice da sauri Salman ya bisa a baya. Suna fita ya kalli sojojin sa ya ce "Ku shiga motar muje," bud'e masa motar aka yi ya shiga suka ja motar da gudun tsiya. [10/25, 8:58 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️ RUBUTAWA DAGA HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ) SADAUKARWA GA MY DAUGHTER SABEEHA BILKISU Z.YA'U (🅱️K) AISHA MAGAJI DABO (AMA) Page 36 Gaba d'aya hankalin Maleek a matuk'ar tashe yake gaba d'aya wannan lamarin yasa shi a duhu. Sabeeha kuwa suna gama waya da Maleek ta kashe wayar duka ta b'oye sannan ta kalli Rashida ta ce "Rashida ga matar nan ta taho ki k'ulle ni kar ta zo ta tarar kin kwance d'aurin," k'ulle Sabeehan ta yi. Daidai lokacin tsohuwar ta shiga d'akin da kallo tabi Rashida ta ce "Ke kuma me ki ke yi a nan?" Murmushi kad'an Rashida ta yi ta ce "Dama neman ki nake yi shiyasa na shigo nan amma gwaggo me wannan baiwar Allah tayi miki ki ka canja mata kamanni haka?" Rashida ta fad'a idanunta na kawo k'walla. "Au dama kin Santa kenan ko me?" Saurin girgiza kai Rashida ta yi ta ce "Amma gwaggo wannan zalinci ne fa ku...," D'aga mata hannu tsohuwar ta yi ta ce "Rashida wallahi idan kina shiga harkar sana'a ta zanci kutmar ubanki," Jan baki Rashida ta yi tayi shiru k'arar motoci kawai suka fara ji a wajen gidan suna ta parking iya k'arar motocin ya isa ya sanar da kai cewar motocin masu yawa ne. Jiki na rawa Tsohuwar ta k'arasa gaban window ta lek'a da sauri ta dawo ta kalli Rashida ta ce "Maza ki shige wani gurin ki b'oye domin idan har Oga ya ganki a nan sai dai wata ba ke ba ke ba ma ke kad'ai ba har ni zai had'a domin baison asan da wannan gidan," tana gama fad'ar hakan ta fara kwance Sabeeha da gaban ta banda fad'uwa ba abinda yake yi. Tana gama kwance ta ta damk'i gashin kan Sabeeha da hakan yasa ta sakin k'ara saboda azabar da taji a kan nata amma tsohuwar bata damu ba haka ta ja Sabeeha har babban falon gidan. Turus Sabeeha ta tsaya tana kallon Uncle dake zaune ya d'ora k'afa d'aya kan d'aya a k'alla sun kai su ashirin a wajen magidan ta ne sai masu gadin su manya manya kallo d'aya zaka yi musu ta tsorata saboda tsabar girman su gasu bak'ak'e wuluk da su idanun Sabeeha ne ya Kai kan wani babban mutum Wanda ke zaune a tsakiyar mutanen tunanin Sabeeha ne ya katse lokacin da taji wannan matar ta yi wurgi da ita a tsakiyar falon har ta bugu da center table Wanda hakan yasa ta sake buge goshin ta take jini ya b'alle a goshin ta wata azaba ce ta ratsa jikin ta ga wani jiri da take ji tana daga kwancen Mai da idanunta ta yi ta rufe ruf. "My son wannan yarinyar ce ta hana jika ta sakewa a gidan mijin ta?" Cikin girmamawa Uncle ya ce "Eh father," wata mahaukaciyar dariya oga ya yi sannan ya ce "Zan sa a keta mata mutuncin ta sannan na kashe ta kafin shi kansa MG ya biyo bayan ta domin jikata na riga nayi Mata miji," jinjina Kai Uncle ya yi. Wani a cikin su ya ce "Boss amma ya batun kayan mu dake cikin gidan nan," kallon sa Oga ya yi ya ce "Wannan ba damuwa bane a yau idan mun kammala kashe wad'an nan biyun zamu fita dasu sannan mu aiwatar da aikin mu," daga fad'ar hakan Oga ya juya ya kalli tsohuwar dake tsaye ya ce "Ke Sailuba a yanzu ba sai anjima ba Ina so ki fito mun da jikarki da ke cikin gidan nan," take jikin wannan tsohuwa mai suna Sailuba ya fara rawa sanin duk Wanda ya Musa maganar Oga sunan sa gawa yasa ta juya jiki na rawa ta shiga d'akin da Rashida ta b'uya ta fito da ita har falon take wasu cikin wannan dabar suka fara lashe baki ciki kuwa har da Uncle domin shi ma lamba d'aya ne wajen neman mata. Dariya Oga ya yi ya ce "Sailuba kin karya mun dokata ta cewar bana so wani yasan da wannan gidan domin sirrina ne amma ke ki ka karya mun ita sannan sarai kinsan hukuncin Wanda ya bijirewa umarnina saboda haka kema shekaru ashirin da muka d'auka kina aiki a k'ark'ashina hakan bazai sa na kyale ki ba tabbas kina yi mun aiki yadda nake so hakan ne ma yasa zan baki zab'i cikin biyu ki zab'i d'aya," tuni tsohuwa Sailuba ta zube a wajen domin tasan kashin ta ya bushe rok'o take akan ya yi hak'uri amma ko kulata ba Wanda ya yi Rashida kuwa kuka sosai take yi jin abinda Oga ya fad'a. "Ki zab'a ko na sadu da jikar ki sannan na kashe ta ko Kuma ke na shek'e ki," a razane Tsohuwa Sailuba ta kalli Oga idanunta fal da nadamar aiki da Oga sannan ta kalli Rashida dake kuka tabbas tana son Rashida domin ita ta raini Rashida tun daga yaye sakamakon rasuwar iyayen Rashida amma Kuma ai itama tana son rayuwar ta sai kawai ta ce "Na bayar da Rashida," bud'e da ido Rashida ke kallon tsohuwar sai dai ta kasa fad'ar komai. Wata dariyar basawa Oga ya yi sannan ya kalli inda Sabeeha ke kwance jini ya wanke mata fuska ya kalli wani k'ato cikin yaran sa ya ce "D'auke mun wannan abun daga nan kaje na baka ita kayi amfani da ita domin ni tayi mun k'azan ta da yawa duk da tafi waccan sura mai kyau," ya fad'a yana nuna Sabeeha dake kwance tana d'ibar azaba. Maleek kuwa suna isowa wajen daga nesa suka hangi gidan dan haka ya kalli Salman a matuk'ar rud'e ya ce "Park here," take Salman ya yi parking da sauri Maleek ya bud'e mota ya fita tare da zaro bindigar sa daga aljihun motar sa har biyu ya soke su a jikin sa sannan ya yi gaba sojojin sa na binsa a baya. Sabeeha kuwa jin abinda Oga ya fad'a ba k'aramun tayar mata da hankali ya yi ba saurin bud'e idanunta ta yi sai kawai ta ga wannan k'aton mutum a gaban ta k'ok'arin tashi take yi amma ta kasa hannu yasa ya rik'o na Sabeeha ya mik'ar da ita tsaye sannan ya fara janta zuwa wani d'aki tana tirjewa domin akan ta aikata abinda ake nufi da ita gara gawar ta. Maleek kuwa zagaye gidan suka yi kamar karare haka suka dinga karya k'asusuwan yaran su Uncle murd'e musu wuya kawai zaratan sojojin ke yi ba tare da sun sha wahala ba. Maleek kuwa idan ka ganshi zaka yi tunanin ba shi kad'ai ke aikin ba saboda kamar yana murd'e wuyan kaza haka ya dinga murd'e wuyan 'yan daban ko mai k'arfin su yana yin jifa da su kamar karare. A zuciye ya nufi k'ofar falon yasa k'afa ya yi mata duka d'aya ta karye ta fad'i da k'arfin gaske Wanda hakan ya ja hankalin mutanen wajen inda yake. Idanunsa ne ya sauka kan wannan k'aton mutumin dake jan Sabeeha tana tirjewa Sabeeha kuwa kallon inda Maleek yake ta yi cikin kuka ta ce "My ka taimake ni," a razane Maleek ke kallon ta cikin wani mugun yanayi domin shi Sam bai gane wannan sabeen sa bace saboda gaba d'aya kamanin ta sun sauya ga jini ya wanke mata fuska. Marin da mutumin ya yiwa Sabeeha ne yasa ta fad'uwa a wajen a sume bata numfashi. A wani mugun harzuk'e Maleek ya nufi wajen da Sabeeha take kwance kawai wani k'aton mutum ya sha gaban sa tare da kawowa Maleek wani mugun punch a fuska saura k'iris naushin ya sauka a fuskar Maleek ya yi saurin sa tafin hannunsa ya tare dukan sannan ya murd'e hannun ji kake "k'aras b'as k'as," ya karya hannun sannan duk girman mutumin ya d'aga shi sama ya yi jifa da shi a kan k'aton center table d'in dake falon take wata k'ara ta cika falon. Daidai lokacin sojojin Maleek suka shiga falon tare da zagaye falon tare da saita ragowar mutanen falon da bindigogi take yaran suka zubar da makaman su da da sun saita Maleek da su suna jiran umarni su sakar masa harbi tako ina. Maleek kuwa duk da ya ga mutumin baya motsi sai da yasa hannun sa ya jawo shi ya rik'e d'aya hannun nasa ya karya. Kallo d'aya zaka yiwa Maleek kasan cewa ransa idan ya yi trillion ya b'aci saboda jan da idanunsa suka yi jijiyoyin damtsen sa da goshin sa sun tashi. Kai tsaye wajen Sabeeha ya nufa da gudu ya tsugunna a gaban ta yana kallon ta wasu zafafan hawaye suka zubo masa janta jikin sa ya yi ya rungume a hankali ya fara Kiran sunanta "Sabeeha Sabee na please open your eyes Maleek is here your husband is with you please baby," wani irin jan numfashi Sabeeha ta yi Sam Maleek bai damu da daud'a da Kuma k'arnin jinin da Sabeeha ke yi ba ya rungume ta tsam a jikin sa. Sannan ya kalli fuskar ta da tayi bak'ik'irin tsabar datti gashin kanta duk ya hargitse kamar na mahaukaciya ya ce "Open your eyes dear," a hankali Sabeeha ta bud'e idanunta da take jin sunyi mata mugun nauyi ta kalle shi hawaye na zuba a idanunta ta Kai hannunta da ya gama b'aci da jini ta shafa sajen sa a hankali cikin muryar azaba ta ce "Na godewa Allah ka samu sauk'i My," daga haka ta sake rufe idanun ta ba numfashi dad'a hugging d'in ta Maleek ya yi wani azababben son ta na k'aruwa a zuciyar sa. Cak ya d'aga ta ya nufi kujera ya kwantar da ita sannan ya yi wata iriyar juyawa tare da zaro bindigun sa biyu ba abinda ka ke ji sai k'arar harbi idanunsa a rufe yake harbin sai da ya gama sannan ya yi jifa da bindigun. Mutanen dake falon duka rintse idanunsu suka yi jin yadda MG ke harbi idanunsa a rufe sai dai ga mamakin su suna bud'e ido gaba d'aya 'yan daban dake falon da a k'alla sun Kai talatin gaba d'aya ya harb'e su gaba d'ayan su sun zama gawa. A hankali ya k'arasa gaban Uncle ya yi masa kallon Sama da k'asa hawaye taf idanun sa ya ce "Why Uncle meyasa zaka aikata haka meyasa zaka yi hakan akan me zaka jefa mu a irin wannan halin Uncle meka rasa a rayuwar ka da ka zab'i kashe bayin Allah tare da cutar da su meyasa Uncle," Maleek ya fad'a yana fashewa da kuka kamar k'aramun yaro cikin k'aramun lokaci Kuma ya kalli gefe guda tare da share hawayen sa da babban yatsan sa ya kalli Uncle ya ce "Ka da ka tab'a tunanin zan tausayawa Wanda yake cutar da al'umma," daga haka ya bar gaban Uncle ya koma kan Oga kwata kwatan su ya tsaya a gaban sa ido cikin ido Maleek ya kalle shi ya yi murmushin gefen baki ya ce "Alhaji sammani miji ga mahaifiyar Uncle marigayiya Hajiya Hauwa'u ashe dama kaine the most criminal person da Nigerian army bamu sanka ba a gaskiya na tausaya maka da case d'inka yazo hannun MG Abdul-maleek Hamza mai dala domin kashin ka ya bushe tabbas naji dad'i da granny baza ta kawo wannan lokacin da idanunta zai gane mata mutuwar mijin ta da d'anta ba Ina tabbatar muku wasan ku yazo k'arshe," daga haka ya matsa gaban wani mutum. Sai da Maleek ya k'are masa kallo ya ce "Alhaji Hamisu kwangila uba ga Arfat yaro d'aya daka mallaka a duniya sannan Kuma minister ashe da hannun ka wajen rusa mana k'asa hmm ku jira result d'in ku," haka Maleek ya gama yi musu zayyana kaf d'in su sannan ya juya musu baya tare da zura duka hannayen sa a aljihu idanunsa akan Sabeeha ya ce "Sabeeha yarinya Mai hankali da nutsuwa sannan Kuma mata ga MG Abdul-maleek yarinyar da nake so Kuma nake matuk'ar k'auna kamar rayuwata Kai fiye ma da rayuwata yarinyar da nake so na riritata na gatata ta na ji da ita kamar 'yar tsanar zinare amma hakan ya gagara saboda ku d'in nan," ya fad'a tare da nuna su sannan ya jinjina Kai kamar Yana yiwa yaran sa fad'a ya ce "A bisa hakan nake yi muku albishir da cewar dukan ku zaku karb'i results d'in ku tun a nan duniya kafin ku had'u da ubangijin mu," daga haka ya kalli sojojin sa cikin bada umarni ya ce "Salman dukan su ku sasu a motor zuwa gida," daga haka ya nufi inda Sabeeha take ya d'auke ta ya yi hanyar fita har ya Kai k'ofa ya waiga ya kalli Tsohuwa Sailuba ya ce "Har da wannan," daga haka ya fice ya nufi motor ya bud'e ya shiga aka rufe akaja motar zuwa gida. [10/25, 8:58 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️ RUBUTAWA DAGA HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ) SADAUKARWA GA MY DAUGHTER SABEEHA BILKISU Z.YAU (🅱️K) AISHA MAGAJI DABO (AMA) Page 37 Tunda suka d'auki hanya zubawa fuskar Sabeeha ido kawai Maleek ya yi cikin tausayin ta a hankali ya shafa gashin kanta da ya yi uban dirty kamar an shekara uku ba a wanke shi ba. Suna shiga gate d'in gidan sojojin sa suka k'arasa gaban motar sa da gudu Salman ne ya bud'e masa motar tare da Sara masa fita daga motar Maleek ya yi d'auke da Sabeeha a hannun sa "Salman aje dasu waccan b'angaren ka tabbatar jikin su ya fad'a musu," Maleek ya fad'a tare da fara tafiya. "Amma sir Uncle fa har da shi?" Wani banzan kallo Maleek ya aikawa Salman wanda bai tab'a yi masa makamancin sa ba ya ce "Shi Uncle d'in shi waye shi to har da shi nake nufi," yana fad'ar haka ya shige part d'in Ummi. Da sallama ya shiga ya same su kowa cirko cirko a tsaye Daddy ne kawai a zaune da glass cup a hannun sa Yana shan ruwa amma ragowar mutanen falon kowa kansa a kulle yake da abinda ya faru. Ganin shigar Maleek ne yasa kowa binsa da idanu ganin wata a hannun sa domin duk ciki ba Wanda ya gane Sabeeha ce direct kujera ya nufa ya kwantar da ita yana kallon ta. A tare Sabreen da Sameeha suka nufi wajen domin dole sunsan wannan 'yar uwar su ce suna kallon ta wani tashin hankali ya ziyar ce su saboda ganin halin da Sabeehan su ke ciki. Sameeha kuwa fad'uwa tayi sumammiya a wajen Sabreen kuwa da sauri ta waiga ta rungume Fauwaz dake bayan ta ta fashe da wani irin kuka ta ce "Na shiga uku my heart duba fa ka gani yanzu da gaske wannan Sabeeha dear ce?" Shima kansa Fauwaz hankalin sa a tashe yake. Umar kuwa da sauri ya nufi inda Sameeha ke kwance ya d'auke ta zuwa b'angaren Fauwaz ya kwantar da ita a saman gado ya shafa mata ruwa da kuka ta farfad'o tana Kiran sunan Sabeeha dakyar Umar ya shawo kanta tayi shiru sannan ya ja hannunta suka koma falon. Ummi kuwa k'arasawa wajen da Sabeeha ke kwance ta yi tana kallon ta itama take hawayen tausayin Sabeeha ya wanke mata fuska mik'ewa Maleek ya yi ya dafe goshin sa take hawaye ya zubo masa hankali a tashe Daddy ya k'arasa wajen sa fad'awa jikin Daddy Maleek ya yi ya saka masa kuka kamar k'aramun yaro shi kansa Daddy dauriya kawai yake yi domin duk wanda ya ga halin da Sabeeha ke ciki sai ya tausaya mata cikin dauriya Daddy ya ce "Be strong Son insha Allah Daughter zata samu lafiya okay?" Maleek kam ko magana ya kasa sai gyad'a kai kawai da yake yi hawaye wasu na bin wasu a hankali Daddy ke buga bayan sa alamun rarrashi sannan ya kalli Umar ya ce "Umar zaka iya treating daughter a nan ko sai munje hospital?" "Daddy Ina ganin muje hospital kawai," a hankali Maleek ya zare jikin sa daga na Daddy ya share hawayen sa ya k'arasa inda Sabeeha ke kwance ya d'auke ta cak ya yi hanyar fita da ita Umar Daddy Ummi na biye da shi. Har mota suka k'arasa Umar ne ya shiga driver seat Daddy Kuma front seat yayin da Ummi ta shiga back seat Maleek kuwa motar sa aka bud'e masa ya shiga suka nufi hospital. Direct office d'in Ummi suka shiga da Sabeeha Ya kwantar da ita saman gadon dake d'akin Ummi da Umar ne a kan Sabeeha suna treating d'in ta har lokacin a sume take ja baya Maleek ya yi ya jingina da k'ofar d'akin yana share hawaye daga k'arshe ma ya fita daga office d'in gaba d'aya. A zuciye ya fita daga office d'in Ummi ko bari a yi driving d'in sa k'in yadda ya yi ya fad'a mota ya jata da wani masifaffen gudu kamar mai Shirin tashi sama zuciyar sa banda tafasa ba abinda yake yi ikon Allah ne kad'ai ya kaisa gida lafiya. Ko gama sai ta parking bai yi ba ya fice daga motar ya shige part d'in Ummi a zuciye gaba d'aya da kallo mutanen falon suka bi shi. Direct wajen da Nasreen take a rakub'e Maleek ya yi gaba d'aya ta gama jik'ewa da zufa da Kuma fitsarin da ta yi domin tasan yau gashin ta ya bushe kallo d'aya zaka yiwa Maleek ka fahimci zuciyar sa a kusa take. Nasreen na ganin ya yo ta wajen ta tashi da gudu domin samun wajen b'uya sai dai kafin ta yi wani yunk'uri Maleek ya d'amk'i hannun ta ya yi wurgi da ita a jikin bango wata razananniyar k'ara Nasreen ta saki saboda wata azaba da ta ratsa bayan ta zuwa k'eyar ta Sam Maleek bai damu ba ya k'arasa inda take ya fara ball da ita tana ihu da neman ceto amma tsakanin Fauwaz Sabreen da Sameeha ba Wanda ya yi k'ok'arin taimakon ta. Sosai Maleek ke ball da Nasreen tana ihu shak'ar da Maleek ya yiwa Nasreen ce tasa Fauwaz yin wajen da sauri ya rik'e hannun Maleek d'in ya ce "Please Yaya ka sake ta haka zata iya mutuwa fa," saboda duk Wanda aka yiwa wannan shak'ar mutuwa ce k'arshen sa Nasreen kuwa har numfashin ta ya fara guduwa idanunta sun firfito shi kansa Maleek yasan shak'ar mutuwa ya yi mata Sameeha da Sabreen su ma abin ya tsorata su yanzu rintse idanu Sabreen ta yi Sameeha kuwa k'ara ta saki ganin MG na niyyar yin kisa. Wurgi da ita gefe ya yi ba dan komai ba sai dan ganin hankalin Sabreen da Sameeha ya tashi huci kawai yake yi Nasreen kuwa suma ta yi ko ta kanta bai bi ba ya fice zuwa part d'in sa wanka ya yi ya fito a gurguje ya shirya cikin wata farar shadda d'inkin zamani sumar kansa sai shek'i take yi yana zabga k'amshi sai dai fuskar sa babu annuri a tamke take kamar bai tab'a dariya ba. Car key d'insa ya d'auka tare da wayoyin sa ya fita direct asibiti ya nufa har lokacin Sabeeha bata farfad'o ba guri ya samu ya zauna ya zuba mata idanu Yana kallon ta har magrib ta yi tashi ya yi shi da dad suka tafi masallacin dake cikin asibitin suka yi sallah a hanyar komawar su ne Fauwaz ya yiwa Maleek waya akan cewar suna so su je asibitin ya ce "Ok kuzo d'in but wannan abar ka kulle min ita a part d'in ka," ko ba a fad'a ba Fauwaz yasan Nasreen ake nufi sai ya ce "Okay," ya yi hanging up. Ba su dad'e da komawa d'akin ba sai ga Fauwaz da Sabreen da Kuma Sameeha su ma zama suka yi suna kallon 'yar uwar tasu hankalin su a tashe kowa tausayin ta fal zuciyar sa a haka har dare ya fara Maleek ya kalli Fauwaz ya ce "Ina ga kuje gida dare ya yi Ummi kema da Dad kuje gida," Sabreen ta girgiza Kai ta ce "Zan zauna a nan," Sameeha ta ce "Nima haka," Ummi da Daddy ne kawai suka tafi Amma Fauwaz Sabreen da Sameeha har ma da Umar a asibitin suka kwana. Wasa wasa Sabeeha sai da ta kwana biyu bata farfad'o ba a safiyar kwana na biyun Maleek ya nufi gida domin yin wanka domin wankan kawai yake iyawa sai sallah amma batun abinci kuwa babu shi bacci ma baya yi kwana yake a zaune. Yana zuwa part d'insa ya wuce ya yi wanka ya shirya cikin k'ananun kaya jajaye ya yi kyau har ya gaji ya d'ora red p-cap sai dai fuskar sa a had'e take sosai asibitin ya koma. Da sallama ya shiga d'akin daidai lokacin Sabeeha ta motsa tare da bud'e idanunta da sauri ya k'arasa wajen gadon ya zauna gefen ta fuskar sa d'auke da farin ciki ya ce "Sabee na," idanunta ta sauke a kansa baisan hawaye yake ba sai da ta girgiza masa kai tare da nuna masa su Sabreen da idanunta sannan ya share hawayen ya rungume ta sosai a jikin sa. Su Ummi ma da sauri suka k'arasa wajen su suna hamdala su Sabreen kuwa har da hawayen farin ciki ita dai Sabeeha da idanu kawai take binsu ita kanta tasan tayi missing d'in su over kamar ranar ta fara ganinsu haka take binsu da idanu tare da k'ara kwanciya jikin Maleek. Kallon Ummi ta yi ta ce "Ummi zanyi wanka," Ummi da kanta ta had'a mata ruwan wanka ta tashi a hankali ta nufi toilet d'in ta dad'e a toilet d'in tana gurzar jikin ta kanta kuwa tayi masa wanki yakai goma take ta dawo Sabeehan ta ta da towel ta d'aura ta fito ta samu d'akin ba kowa sai Maleek kad'ai. Yana ganin fitowar ta ya k'arasa wajen ta da sauri ya d'auke ta cak ya k'arasa da ita gefen gadon ya zaunar da ita ta tsane jikin ta da kansa ya shafa mata mai me matuk'ar k'amshi sannan ya gyara mata kanta ya d'aure mata shi sannan ya bata wata doguwar riga red tasa ta yafa mayafin rigar ya feshe ta da turare a hankali ya Kai hannunsa saman cikin ta da ya d'an fito lumshe ido ta yi sannan ta bud'e su a saman kyakkyawar fuskar sa ya ce "I really miss you my wife," A hankali ta ce "Miss you more," sumbata ya bata a check d'in ta sannan ya zauna tare da zaunar da ita akan cinyar sa ya bata abinci ta ci ya bata magani tasha sannan ya ce "Yanzu me yake miki ciwo," girgiza Kai ta yi cikin sassanyar muryar ta ta ce "Bakomai sai gajiya kawai," ta fad'a tare da kwanciya kan gadon su Ummi ne suka shiga d'akin. Gaishe su Sabeeha ta yi suka amsa tare da tambayar ta jikin ta ta ce "Da sauk'i," kowa da kalar tambayar da yake son yi sai dai ba wajen da ya dace ayi tambayar bane sai kawai kowa ya yi shiru abinsa. Sameeha da Sabreen kuwa rungume 'yar uwar tasu suka yi suna murnar ganin ta samu sauk'i "Ummina zamu iya tafiya gida ai ko?" Maleek ya fad'a yana kallon Ummi. "Eh zamu iya tafiya," Ummi ta fad'a tare da mik'ewa ta fara dialing number d'in Doctor bayan sun gaisa Ummi ta ce "Maryam yarinya ta bata da lafiya fa ya kamata kizo ki dubata," daga can Doctor ta ce "Tom Insha Allah zanzo," "To sai kinzo," Ummi ta fad'a tare da katse wayar suka had'a koman su suka fita wajen asibitin. Maleek da kansa ya bud'e mata gaban motar sa ta shiga ya zagaya ya shiga yayinda Sabreen da Sameeha ke back seat motar baya Kuma Fauwaz ke driving sai Umar a front seat Ummi da Daddy na back seat haka suka nufi gida bayan sunyi parking direct part d'in Ummi suka nufa a falo suka zazzauna. Basu dad'e ba da zama Mama ta yi sallama a falon Sabeeha ce a gaba wajen rungume Doctor tana murnar ganinta bayan ta zauna ne aka gaggaisa sannan falon ya d'auki shiru daga Ummi har Daddy suna so su ji wata magana gamsashiya daga bakin Maleek. Maleek ya yi gyaran murya tare da cire p-cap d'in sa ya ajiye sannan ya kalli Fauwaz ya ce "Fauwaz zo da wannan yarinyar," tashi Fauwaz ya yi ya bud'e part d'insa ya fito da Nasreen tana fitowa suka had'a ido da Maleek da gudu ta juya zata koma cikin d'akin domin yanzu mugun tsoron Maleek d'in take dan gara taita zama a part d'in Fauwaz baci ba sha da ta gauraya da shi. Tsawa dodon nata ya daka mata ya ce "Zonan!" A d'ard'ar ta nufi cikin falon tana raba idanu kowa a falon da kallo ya bita kallo d'aya zaka yi Mata kasan bata da gaskiya saboda raba idanu da take tana sosa k'eya tana k'asa da idanu. Guri ta samu can nesa da Maleek d'in ta zauna mik'ewa Maleek ya yi ai tana ganin ya mik'e ta saki ihu ta tashi da gudu ta b'uya bayan Ummi tayi mata wani mugun rik'o shi dariya ma ta bashi domin ba wajen ta zashi ba Ummi kuwa ta ce "Kinga cikani karki karyani," Maleek kuwa ficewa ya yi direct inda yasa akai su Uncle ya nufa. Yana shiga wajen sojojin dake wajen suka Sara masa kallon su Uncle ya yi duk sun gama galabaita tsabar wuya har sun cire manyan rigunan jikin su murmushin gefen baki ya yi ya kalli Uncle ya ce "Uncle zan ganka yanzu," ai har da gudu Uncle ya had'a wajen zuwa gurin Maleek ya rik'e hannun sa tamau ya ce "Gani Dan Allah kace su kyale mu haka ka duba matsayina a wajen ka," kawar da Kai gefe Maleek ya yi tabbas Uncle uba ne a gurin sa sannan yana son sa sai dai Uncle d'in ya kasance mai laifi Maleek har zuciyar sa yake jin ba dad'i amma ya basar ya ce "Uncle d'an sake ni mana," Da sauri Uncle ya ce "To to to Wallahi na sake ka," wani tausayin Uncle d'in ne ya dirar masa a zuciya jiki a sanyaye ya ce "Muje," ya fad'a tare da yin gaba Uncle na binsa a baya har falon Ummi. Tunda suka shiga Maleek ya samu waje ya zauna sai lokacin idanun Sabeeha ya sauka akan Uncle ai da azamar gaske Sabeeha ta fad'a jikin Maleek ta k'ank'ame shi domin wani mugun tsoron Uncle d'in take ji shafa bayan ta Maleek ya yi saitin kunnen ta ya ce "Ki kwantar da hankalin ki Sabee na ba abinda zai miki okay?" K'ara mak'alk'ale shi Sabeeha ta yi har da rintse idanu. Daddy kuwa ganin yadda yayan nasa ya koma ne duk fuskar sa a kumbure yasa shi mik'ewa da sauri ya ce "Yaya lafiya Mai ya same ka?" Uncle kuwa sai kallon Maleek yake yi cikin jin tsoran sa Daddy ma Maleek d'in ya kalla ya ce "Son just tell me what happens?" Ajiyar zuciya Maleek ya sauke ya ce "Daddy ka zauna domin maganar da zan fad'a yanzu bata tsaiwa bace domin zaka iya fad'uwa," babu musu Daddy ya koma ya zauna sai dai har lokacin idanunsa na kan d'an uwan sa d'aya tilo da bai da kamar sa Yana so ya ji Mai ya faru da shi. Maleek ya fara magana da cewa "Daddy iya sanina tun ina yaro Uncle baya k'auna ta bai tab'a Sona ba duk da matsayin sa na uba a gare ni baya son cigaba na baya son farin cikina Wanda k'iyayyar da yake maka ne ta shafeni Daddy ka fini sanin halin d'an uwanka domin tare ku ka rayu a iya sanina Uncle baya sona ne saboda kawai nazo a matsayin d'an ka sannan na kasance namiji Kai Kuma baya sonka ne saboda a komai kaine gaba da shi a ko da yaushe ina addu'ar Allah ya ganar da shi gaskiya amma Uncle bai tab'a tunanin cewa abinda yake yi ba daidai bane kullum burin sa shine ya ganni a matsala ya aura mun 'yar sa ta dole bana sonta amma nayi muku biyayya domin faranta ranku Daddy a ta kowacce hanya Uncle so yake ya ga bayan mu ba dan komai ba sai dan dukiya," d'an shiru Maleek ya yi yana bin mutanen falon da kallo sannan ya sauke idanun sa akan Nasreen dake rakub'e a bayan kujera. Ya ce "Daddy Uncle ya shirya kashe ni sannan ya had'a da Sabeeha," "What?" Daddy ya fad'a da k'arfi idanunsa akan Uncle da ya yi k'asa da Kai gyad'a Kai Maleek ya yi ya ce "Hakane Daddy domin da kunnena naji yana fad'awa Nasreen a waya cewar ta tabbatar tasa mun maganin da ya aiko mata cikin motata maganin da idan na taka shi shikenan zan kwanta paralyse Wanda bazan warke ba har sai sanda suka so sannan idan na kwanta cutar zasu samu damar rabani da numfashina sannan Ku ma su kashe ku domin su mallake duk abinda muka mallaka Daddy Uncle ya zubar mana da mutunci Uncle safarar miyagun kwayoyi yake yi da makamai Wai dasa hannun Uncle wajen kashe al'umma da jefa su cikin mawuyacin hali Daddy bansani ba shin daidai na aikata ba ko laifi dana kama uba a gareni matsayin mai laifi," Daddy hawaye ne zafafa suka zubo masa a idanunsa kowa dake falon kansa a kulle yake shin mamaki zasu yi ko kuma al'ajabin abinda yake faruwa zasu yi. Wata ajiyar zuciya Maleek ya sauke ya ce "A lokacin da naji wayar Nasreen da mahaifin ta sam banyi mamakin jin hakan ba a daren idanuna na kanta har lokacin da ta je har cikin motata ta zuba maganin bayan ta gama ni Kuma a daren nasa aka kawomun irin motar sak aka ajiye nasa aka fitar da d'ayar saboda ba damar na hau wata daban domin zasu gane ba ita nahau ba ni Kuma Ina so suji a ransu aikin su ya yi hakan ne yasa nasa aka kawo mun wata motar washe gari Ina gani Nasreen na lek'en fitata ta window bayan zuwana meeting na fito na yanke shawarar yin pretending domin na nuna musu cewar aikin su ya tafi daidai Wanda na tabbata hakan ba k'aramun dad'i ya yi musu ba Sabee na kad'ai nayi niyyar fad'awa gaskiyar abinda ke faruwa sai dai abu d'aya daya tsaya mun a zuciya shine ta ya Sabee na ta je gare su tabbas lokacin da nake kwance na gane Sabreen ce zaune a matsayin Sabee na abun ya d'aure min kai matuk'a Umar kad'ai yasan abinda ke faruwa shi kad'ai ke d'awainiya wajen nemo inda Sabeeha take amma ba labari ni kuma ba damar na tambaya domin idan har wani ya gane cewar na samu sauk'i na tabbata maganar zata kai wajen Uncle na damu sosai da rashin ganin Sabee na hankalina ya tashi sosai sai dai dole nasan Sabreen tasan wani game da hakan ita da Fauwaz," Sabreen ta ce "Eh Ya MG Sabeeha dear ta sanar damu cewar wayar ka na hannunta aka yi maka text akan cewar za azo a d'auke ta a daren ranar daka kwanta ciwo kuma har sai an d'auke ta ne sannan za a warware asirin dake jikin ka hakan ne yasa na zauna matsayin Sabeeha dear kafin ta dawo sai daga baya Kuma muka gane munyi kuskuren barin Sabeeha dear da muka yi ta tafi saboda duk lokacin da muke waya da ita muna jinta cikin mawuyacin hali ranar da Sameeha dear tazo ta Kira mu ranar hankalin mu ya tashi sosai saboda jin wata mata ta buga ta da bango tana dukan ta," Sabreen ta fad'a tana hawaye. Sabeeha dake mak'ale jikin Maleek sai lokacin ta d'aga kanta ta kalli Maleek ta ce "Ka gafarceni My lokacin da ka fita meeting na fito zuwa wajen Ummi naji Uncle nayin waya yana magana akan zuba mata magani da akayi a motor Wanda zaka kwanta ciwo sannan Ni Kuma a daren ranar zai turo a sace ni sannan a kashe ni sannan kaima a kashe ka har ma da su Ummi hankalina ya tashi sosai na nufi wajen Ummi domin fad'a Mata abinda ke faruwa sai dai ganin dawowar ka ba lafiya ya hanani sanar mata saboda gudun kar hankalin ta yafi haka tashi sannan ga Kuma halin da My yake ciki hakan ne yasa na yanke hukunci gara kawai na Bari su tafi dani ba tare da Ummi ko my sun saniba saboda gudun afkawar su a damuwa My ga rashin lafiya Ummi Kuma ga rashin lafiyar sa ga Kuma sace ni hakan ne yasa na fad'awa Sabreen dear haka ita da ya Fauwaz na b'oye musu ainahin gaskiyar saboda gudun karsu shiga halin rashina sannan nasa Sabreen zama a madadina saboda kada kuyi tunanin bana nan sun azabtar dani sun so su cutar da rayuwa sunso su rabani da farin cikina ranar da suka shirya kasheni a ranar Allah ya turomun Rashida ita ta kwance ni daga d'aurin da suka yi mun harna Kira ka domin ba dan ita ba nasan shikenan zai sun aiwatar da abinda suka yi niyya a kaina sannan naji ana maganar shigo da kaya k'asar nan," ta fad'a tana kallon sa jawota jikin sa ya yi ya rungume ta yana jin sonta na ratsa duk wata jijiya dake jikin sa da jinin jikin sa tabbas Sabeeha macece ta gari a gare shi ita ta daban ce saboda ta yarda ta rasa rayuwar ta domin farin cikin ahalin ta. Doctor kuwa share hawaye ta yi a zuciyar ta kuwa tana yabawa 'yar tata haka ma Ummi hawayen take yi na tausayin Sabeeha ga Kuma wata sabuwar soyayyar ta da ta dad'u a idon Ummi su Sabreen ma da su Umar sai da suka ji ta burge su domin ba kowane zai iya abinda ta yi ba. Daddy kuwa kansa ya dafe da yake juya masa ta bakin Maleek tabbas da a tsaye yake dole sai ya fad'i domin maganar ta girgiza shi sosai maganar ta tashi hankalin sa fiye da tunanin mai tunani idanunsa sun kad'a sunyi jajir tsabar b'acin rai ya kalli Uncle ya ce "Why Yaya meyasa zaka aikata hakan shin tsanar da Kai mana ne ya Kai har haka kome yanzu meye ribar abinda ka aikata yanzu kaji dad'i kenan da case d'in yake a hannun d'anka?" Share hawaye Uncle ya yi ya ce "Nayi nadama tabbas na aikata kuskure babba na biyewa zuciya ta da nayi amma ku gafarceni san abin duniya ne ya jefani a wannan halin amma Wallahi bansan cewar miyagun kwayoyi ake Shirin shigo dasu k'asar nan ba," Da mamaki Maleek ke kallon Uncle sannan ya ce "Kamar ya kenan?" Uncle ya share hawayen sa ya ce "Alhaji sammani mijin mahaifiya ta shi ya kirani har gida yace tunda an koreni daga wajen aiki na zuba hannun jari a kasuwancin sa sanin bazai cutar dani ba yasa ba tare da nayi bincike ba nasa kud'ina akan cewar za a dinga shigo da kaya daga k'asar waje a dinga siyarwa sannan zamu dinga raba ribar nayi farin ciki sosai na yi masa godiya," tun daga lokacin sai dai kawai na dinga ganin alert a wannan lokacin n kuma ya kirani yake sanar dani cewar sunyi meeting tare da abokan kasuwancin mu kasancewar ni basu tab'a yin meeting d'in su dani ba yake sanar dani akwai kayan da za a shigo dasu Kuma akwai riba sosai a kayan sai dai akwai matsala wajen shigo da kayan saboda idanun Nigerian army na kan kayan saboda haka tunda Kai d'a ne a wajena na sanar da Kai ka bayar da izinin wucewa da kayan ni Kuma na sanar da shi bazan iya rok'ar alfarma a wajen ka ba hakan ne yasa ya kawo shawarar a zuba maka wannan maganin amma Wallahi bansan kwayoyi aka safara ba da makamai ko ranar da ka same mu a can ranar dai ya sanar dani cewar kaya sun iso amma dai nazo domin a ranar za a yankewa matar ka hukunci ita kuma na goyi bayan kashe ta ne ba dan komai ba sai domin farin cikin daughter amma nayi dana sanin abinda na aikata dan Allah ku yafe mun," D'an shiru Maleek ya yi sannan ya mik'e tsaye ya kalli Uncle ya ce "Uncle kenan Alhaji sammani da kake ganinsa ba mutumin kirki bane Nigerian army na da tarihin sa ya dad'e Yana aikata laifuka marigayiya Hajiya Hauwa'u ita ce mata ta biyar da ya aura Kuma kowaccen su ya bayar da ita ne wa k'ungiyar asiri ciki kuwa harda mahaifiyar ka da ya bada jinin ta nasan ba kasan da hakan ba ko?" Rud'ani firgici nadama da dana sanine suka saukarwa Uncle a lokaci guda jikin sa har rawa yake yi idanunsa sunyi jajir shi kansa Daddy ya girgiza da jin wannan lamarin Maleek kuwa ko a jikin sa bai Kuma damu da yanayin Uncle d'in ba ya ce "Abu na gaba Alhaji Hamisu kwangila da kake gani d'ansa Arfat ya taka muhimmiyar rawa wajen tarwatsa rayuwar 'yarka d'aya tilo shi ya fara raba ta da budurcin ta dukkan wasu kud'ad'e da kake bata shi take kaiwa sannan duk wata kadara tata daka sani gida ko fili duk ta siyar ta Kuma bashi kud'in ita kanta batasan nasan da hakan ba sarai mahaifin Arfat yasan da wannan abun amma bai yi k'ok'arin hana yaron shi ba duk da cewar suna da dukiya a tak'aice dai Uncle kana zaune da mak'iyan ka ne baka sani ba Ni Kuma a daidai wannan lokacin zan yanke wani hukunci game da rayuwata domin na dad'e da Dena kallon Nasreen a matsayin matata saboda haka na yanke duk wata igiyar aurena dake kanta dama nayi Mata d'aya saboda haka na sake ta saki biyu," Uncle kuwa tashin hankalin da ya shiga baya misaltuwa sai kawai gani aka yi ya yanke jiki ya fad'i a wajen. [10/25, 8:58 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️ RUBUTAWA DAGA HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ) SADAUKARWA GA MY DAUGHTER SABEEHA BILKISU Z.YA'U (🅱️K) AISHA MAGAJI DABO (AMA) 🇸🇦 ZAMAN AMANA WRITERS (Gidan zaman lafiya da amana Insha Allah)🤜🤛 Page 38 Da sauri Daddy da Ummi Nasreen da Doctor suka yi wajen Uncle dake kwance tare da Umman Nasreen da shigar ta part d'in kenan. Maleek kam ko motsawa bai yi ba haka ma su Fauwaz yunk'urawa Sabeeha ta yi zata je wajen Maleek ya yi saurin rik'e ta tare da rungume ta a jikin sa yana girgiza Mata kai hawaye ne suka zubo mata domin Uncle ya bata matuk'ar tausayi k'ara mak'ale Maleek ta yi tana kuka k'asa k'asa. Ruwa Daddy ya zubawa Uncle take ya sauke wata nannauyar ajiyar zuciya ya tashi zaune sai kawai ya fashe da kuka idanunsa akan Daddy da shima nasa idanun suka yi jajir ya ce "Yaya kana lafiya dai ko?" Daddy ya tambaya hankalin sa a tashe Uncle kuwa hawayen sa ne suka k'aru sai yanzu ya k'ara tabbatar da cewa Daddy masoyin sa ne na gaske duba da abubuwan da ya yi masa kuma Daddyn ya sani amma shi Sam hakan bai d'aga masa hankali sosai ba kamar lafiyar d'an uwan nasa bayan Yana da damar rama fiye da abinda Uncle d'in ya yi masa sai dai shi zuciyar sa kyakkyawa ce ta gaske. Uncle baisan sanda ya rungume Daddy ba yana kuka ya ce "Dan girman Allah Hamza ka yafe mun nasan na aika maka laifuka da dama naso na cutar da rayuwar ka kai da iyalan ka amma Dan Allah ka yafemun kafin a yanke mun hukuncina Wanda nasan na kisa ne," a razane Daddy ya kalli yayan nasa sannan ya juya yana kallon Maleek da har lokacin rarrashin Sabeen sa yake yi. K'asa k'asa cikin muryar Kuka ta ce "Please My ka taimaki Uncle ka duba nadamar da ya yi ka duba shima cikin tashin hankali yake I beg you please save his life," shiru kawai Maleek ya yi Yana sauraron inda take kukan ya ce "Zanyi yadda ki ke so amma idan kin daina kukan," shirun ta yi tana sakin ajiyar zuciya. Daddy kuwa gaba d'aya ya zama speechless ya rasa abin cewa sai kallon Maleek kawai yake yi Umman Nasreen kuwa kwanciya ta yi flat ita da Nasreen suna rok'on Maleek akan ya ceci Uncle Ummi da Doctor ma suka sa baki ga Sabeen sa ma. Shiru ya yi na d'an lokaci ya kalli Uncle tabbas nadamar sa ta gaskiya ce ya ji a ransa shima yana son taimakon Uncle ko dan soyayyar da mahaifin sa ke masa ko dan nadamar da ya yi ko dan iyalan sa baya ga haka ma akwai k'amshin gaskiyar cewar Uncle ba Mai laifi bane. Ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Shikenan za ayi bincike," daga fad'in hakan ya yi ficewar sa yabar falon. Yana fita mota ya shiga Kai tsaye NDA ya nufa tare da sojojin sa ya je suka zauna meeting ya yi musu bayani akan abinda ke faruwa sosai suka jinjinawa k'ok'arin Maleek anan ake bayanin cewar dukkan masu laifin da aka kama Nigerian Army da kanta zata yanke musu hukunci amma sai bayan anyi bincike game da Uncle bayan sun gama tattaunawa akan hakan sannan suka tashi suka nufi gidan gonar Alhaji sammani. Sunyi motoci sun Kai hamsin jiniya kuwa ta cika garin na KD suna zuwa basu tsaya wata wata ba suka zubawa gidan fetur suka k'one shi k'urmus suka bar wajen. A gida kuwa bayan tafiyar Maleek Daddy ya d'ago Uncle bayan ya gama neman yafiyar su Ummi har ma da Sabeeha suka yafe masa suka nufi upstairs Umman Nasreen ma ta nemi yafiya tare da Nasreen d'in kanta ba su yi wani tunani ba suka yafe musu suna ta godiya. Doctor kuwa sallama ta yi musu ta tafi har mota 'yan ukun ta suka rakata ta tafi sannan suka koma ciki Sabeeha kuwa bedroom d'in Ummi ta tafi ta kwanta tana kwanciya bacci ya d'auke ta. Sabreen da Sameeha kuwa kitchen suka shiga suka fara yin girki Fauwaz kuwa ya koma office haka ma Umar. Sai Yamma sannan Sabeeha ta farka daga baccin da take yi mik'a tayi tare da yin salati ta kalli agogon dake d'akin zare ido ta yi ta tashi da sauri ta fad'a toilet ta yi wanka tare da alwala ta fito ta kuwa samu an kawo mata kayan ta a gurguje ta shirya cikin wata black d'in atamfa mai touches d'in light blue bata yi kwalliya ba ta zura hijjab ta yi salolin dake kanta sannan ta gyara d'akin Ummin tsaf ta yafa light blue veil sai k'amshi take yi ta fita zuwa down stairs falon ya gauraye da k'amshin girki da air freshener ga Ac na aikin ta fararen kwayayen dake falon sun haska falon sosai. A hankali ta taka zuwa falon ta samu Ummi da su Sabreen da Sameeha Ummi ta ce "Daughter kin tashi zonan kusa dani," wajen Ummi ta zauna tana amsa sannun da su Sabreen ke yi mata ta kalli Ummi ta ce "Ummi yunwa nake ji," da sauri Sameeha ta tashi ta had'o mata abinci da ruwa da drinks ta kai mata. Kallon ruwan ta yi ya gaji da yin sanyi take ta tuna Maleek ya hana ta shan Abu mai sanyi a zuciyar ta tace tunda baya nan gara nasha abuna tunda inaso da wannan tunanin ta fara kai lomar abincin bakin ta Maleek ne ya yi sallama a falon yana amsa waya da alama ya d'an jima da dawowa saboda ya canja wanka cikin wasu complete ash color d'in k'ananan kaya ya yi kyau k'amshin sa ya cika falon d'an tsayawa ya yi Yana kallon Sabeeha dake ta kai loma ba ruwan ta d'an murmushi ya yi da ya bayyana dimples d'insa ya shafa tulin kwantacciyar sumar kansa ya ce "Ok Daddy gani nan," ya fad'a tare da nufar upstairs. Da sallama ya shiga falon Daddy ya amsa masa sallamar kallo d'aya Maleek ya yiwa mahaifin nasa ya ga har ya d'an rame kusa da Daddy ya zauna ya gaishe shi amsawa Daddy ya yi tare da shafa kan Maleek d'in ya ce "Son hankalina yak'i kwanciya akan case d'in Yaya yanzu ya binciken naku ya kasance?" D'an juya idanu Maleek ya yi ba tare da damuwa ba ya ce "Daddy sai dai fa kayi hak'uri domin Uncle dai da hannunsa dumu dumu a wannan harka dan haka ma ku fara yafar juna," salati Daddy ya yi cikin matuk'ar damuwa. Tashi Maleek ya yi daga kusa da Daddy yana dariya ya ce "Dama so nake naga yadda zaka yi Daddy munyi bincike mun gane Uncle na da gaskiya bai da laifi," ajiyar zuciya Daddy ya sauke yana hararar Maleek tare da d'aukar pillows d'in kujera ya fara jifan Maleek yana cewa "Marar kunya sai ka bar aikin soja tunda mai daku yake marasa tausayi," da sauri Maleek ya nufi k'ofar fita yana dariya ya ce "Kwantar da hankalin ka Dad ka kusa tashi daga mahaifin ga MG Abdul-maleek zuwa mahaifin Marshall Abdul-maleek Hamza mai dala domin girma za a k'aramun," ya fad'a tare da ficewa. Murmushi Daddy ya yi Allah ya sani har zuciyar sa yana matuk'a k'aunar Maleek saboda yaron ya yi tako Ina ga biyayya ga kyautatawa ga taimako ga son nasa komai lalacewar sa ga misali kan Uncle duk tsana da muzgunawar da Uncle ya yi masa amma bai damu ba sai ma taimakon sa da ya yi lallai wannan miji da matar 'yan aljanna ne da izinin ubangiji Daddy ya ayyana a ransa. Maleek kuwa down stairs ya sauka Sabeeha na ganin sa ta yi saurin d'auke ruwan ta b'oye a bayan ta su Sabreen nayi mata dariya kallon su ya yi sannan ya juya idanunsa kan Sabeeha ya zauna gefen ta itama shi take kallo d'aga mata gira ya yi tayi saurin girgiza Kai alamun babu komai ya ce "Sure?" Noding kanta ta yi ta ce "Yeah," "Hmm! Ok zanci abincin nima," kallon plate d'in ta yi sannan ta kalle shi ta ce "Wannan fa nawa ne ni kad'ai nake so na cinye shi," d'an zare ido ya yi yana k'ara kallon abincin da ko rabin sa bata ci ba amma tana zancen duka zata cinye ya gyad'a kai ya ce "Uhmm! Lallai na jinjinawa rowar ki baby yanzu duka za ki cinye?" "Eh fa," ta bashi amsa tare da cigaba da Kai loma "Amma shi wannan hannun fa da kike b'oyewa a bayan ki fa ko yana ciwo ne?" Girgiza kai ta yi da sauri ta ce "A'a a'a My a haka yake so ya zauna tun d'azu kafin kazo nake dawo dashi daidai amma yana cakud'awa baya abinda za ayi kawai kyale shi za a yi idan ya gaji sai ya dawo da kansa," dariya ta bashi ma ya jinjina kai yana kallon ta tana murmushi. Itama murmushin take to amma na yak'e sake kallon hannun ya yi ganin yadda take motsa shi tana wani k'ifk'ifta idanunta kamar babyn roba d'age girar sa d'aya yayi Yana kallon ta yana kallon hannun nata yana kallon fuskar ta sannan ya mayar da kallon sa kan k'aramun center table d'in dake gabanta hollandia yogurt ne kawai a kai yayin da plate d'in abincin ke kan cinyar ta. "Allah dai yasa kar My ya gane," "Sabee na kince wani Abu ne?" Da sauri ta ce "A'a bakomai," juya idanunsa ya yi dariya na cinsa Sarai ya ji abinda ta fad'a ya mik'e tsaye tare da rik'e k'ugu ya ce "Sabee na meyasa kuma kike cin abinci ba ruwa kusa," k'asa ta kalla tana juya idanun ta sai Kuma ta kalle shi ta yi murmushi ta ce "Dama ai zan sha...," Tari ta fara tana wani rik'e duk a wayon ta na son ganin ya d'an matsa daga gurin ya je d'auko mata ruwa kafin ya dawo ita kuma ta d'an kora mai sanyin. Sarai yasan akwai abinda take b'oyewa domin ita bata cin abinci ba ruwa a kusa ganin bai ko motsa ba daga inda yake sai ma tsayawa kallon ta da ya yi ya d'age gira d'aya cak ta tsaya da tarin ta ce "My tari fa nake ka samo mun ruwa na sha," d'an zare mata ido ya yi ganin tarin nata ya tsaya sai Kuma ta cigaba da tarin. Wannan karon kam sai da ya murmusa har fararen jerarrun hak'oran sa suka fito ya ce "Ayyah Hubbyna sannu wannan tarin naki amma latest ne ko domin naga kamar ana controlling d'in sa da remote," ya fad'a tare da kama kafad'un ta da hannayen sa duka ya mik'ar da ita tsaya har lokacin hannunta na bayan ta tana rik'e da gorar ruwa. Ya kalli su Sameeha da suke guntse dariyar su ya ce "Sabreen dear d'aukowa Baby ruwa," tashi Sabreen ta yi ta nufi fridge d'in dake daining zata d'auko ruwa da kallo Sabeeha ta bita har zata bud'e ya ce "But not cool one," "Toh," Sabreen ta amsa tare da d'auko mara sanyi ta nufe su Sabeeha kuwa sai juya idanu take irin na marasa gaskiyar nan hannu Maleek yasa ta bayan ta ya rik'o hannunta da ta rik'e ruwan ya karb'a yana murmushi ya ce "Hubbyna Shan ruwan sanyi na da illa ga babyn mu," ya fad'a tare da ajiye ruwan saman center table ya karb'i na hannun Sabreen ya tsiyaya a cup ya Kai Mata baki kwab'e fuska ta yi zata yi masa kuka sannan ta kawar da kai gefe ita a dole baza ta sha ba. "Haba mana baby na please ki sha ruwan nan," mak'e kafad'a ta yi juya idanunsa ya yi ya ce "Shikenan bari na tafi da shi ni," ya fad'a tare da Kai hannu zai d'auke Mai sanyin ta yi saurin rik'e hannun nasa ta ce "Tofah shi nake so nasha," kallon ta ya yi har ranta take son shan ruwan ya ce "Ok amma kad'an zaki sha sannan da kaina zan zuba miki kin yadda?" "Eh eh na yadda ta fad'a da sauri," gyad'a Kai ya yi ya zuba Mai sanyin rabin cup ya Kai bakin ta da sauri ta rik'e cup d'in tare da had'awa da hannun sa ta shanye ruwan tas har da sauke ajiyar zuciya. Murmushi ya yi ya ajiye cup d'in ya kalli Rolex watch d'in hannun sa ya ce "Bari naje masallaci," ya fad'a tare da d'aukar ragowar ruwan sanyin ya fice. Ummi kuwa tana kallon su tana dariya k'asa-k'asa. [10/25, 8:58 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️ RUBUTAWA DAGA HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ) SADAUKARWA GA MY DAUGHTER SABEEHA BILKISU Z.YA'U (🅱️K) AISHA MAGAJI DABO (AMA) 🇸🇦 ZAMAN AMANA WRITERS (Gidan zaman lafiya da amana Insha Allah)🤜🤛 Page 39 Bayan fitar Maleek ta zauna sai tura baki take yi tana hararar su Sabreen dake yi mata dariya kamar an tsikare ta ta mik'e ta nufi kitchen bata dad'e ba sai ga ta da abinci a hannun ta har da ruwa mai sanyi ta fito da kallo su Ummi suka bita k'ofar fita ta yi "Ina Kuma za ki dear?" Sabreen da Sameeha suka fad'a a tare kallon su ta yi ta ce "Yanzu zan dawo," tana fad'a ta fice daga falon. Tana fita ta fara kalle kalle Salman ta hango shi da Adam gurin su ta nufa suna ganin ta suka Sara Mata d'an murmushi ta yi ta ce "Salman ko zaka kaini wajen da masu laifin nan suke," ba musu ya ce "Ok muje," daga haka ya yi gaba tana binsa a baya har wani b'angare a gidan d'akin da suke ya b'ude mata a d'an tsorace ta shiga d'akin gaban ta sai da ya fad'i da ta ga inda aka sauya musu halitta da duka d'auke kanta gefe ta yi tana kallon tsohuwa Sailuba dake shimfid'e a gefe ko motsin kirki bata iyawa saboda dukan da ta sha su kuma ganin Sabeeha da kular abinci ne yasa su tsura mata idanu saboda mahaukaciyar yunwar da suke ji. Kai tsaye wajen tsohuwa Sailuba Sabeeha ta nufa a hankali ta tsugunna a gaban ta duk da kuwa tsoran ta da Sabeehan ke ji ta ce "Ga abinci," ai kafin Sabeeha ta gama fad'a har tsohuwa Sailuba ta wafce kular ta bud'e ta fara ci tab'e baki kawai Sabeeha tayi tare da ajiye ruwan hannun ta ta mik'e zata tafi "Nagode 'yannan kin yi mun alkhairi," waigawa Sabeeha ta yi ta kalle ta ta ce. "Karki damu nayi Miki hakan ne dan Allah sannan da Kuma darajar Rashida," tana gama fad'in hakan ta fita daga d'akin. Tana fita su Alhaji sammani suka k'wace abincin suka cinye suna dannawa tsohuwa Sailuba zagi. "MG Ina so ka saki mahaifina ni Kuma ko nawa ne zan biya," wata muguwar harara Maleek ya narkawa mai yi masa maganar sannan ya gyara tsaiwar sa ya ce "Arfat kenan to ba Kai ba ba Kuma mahaifin ka ba duk duniya babu Wanda ya isa ya sani abu domin baku da kud'in da zaku nuna mun Kai kanka kasan gidan su kazo saboda haka tun kafin hukuncina ya biyo ta kanka kabar nan," ganin yadda Maleek d'in ya canja masa fuska ne zuwa had'e rai yasa shi fadin "Shikenan sai anjima," daga haka ya shige motar sa ya tafi. Tsaki kawai Maleek ya ja tare da juyawa domin shiga part d'in Ummi sai ya hangi Sabeeha da sauri ya k'arasa wajen ta ya ce "Sabee na daga Ina haka Kuma?" Shiru ta yi tana kallon sa shima kallon nata yake yi domin jin abinda zata fad'a d'an murmushi ta yi ta ce "Dama..dama na kaiwa waccan matar abinci ne," girgiza Kai kawai ya yi yayi gaba ta bishi a baya zuwa cikin part d'in Ummi. Da daddare Umar da Fauwaz suka d'ebi matan su suka tafi gida. Washe gari kuwa aka sojojin k'asar Nigeria suka yankewa su Alhaji sammani hukuncin kisa inda kowannen su aka harbe shi ya mutu. A gajiye Maleek ya shiga part d'in Ummi ya zauna akan kujera Sabeeha ce Ke saukowa stairs wajen sa ta k'arasa bayan ta d'auko masa ruwa mai sanyi da cup ta tsiyaya a cup ta mik'a masa tare da fad'in "Sannu da dawowa My," ya ce "Yawwa Sabee Ummi fa?" D'an juya idanu ta yi ta ce "Ummi tana office," jinjina Kai ya yi ya ce "Zo muje ki rakani part d'in mu nayi wanka mana," mak'e kafad'a ta yi ta ce "Uhm uhm nikam bazan bika ba," mik'ewa ya yi tare da d'aukar ta cak ya nufi k'ofar fita yana cewa "Aikuwa yarinya baki isaba ladan ne bakya so ki samu," ita dai Sabeeha sai zillewa take yi domin tsoron had'uwar su take ji saboda an kwana biyu ba a gamu ba. Ko ta kan mota bai bi ba a k'afaya nufi part d'in Yana rik'e da ita kamar jaririya duk inda suka gifta idanun ma'aikatan gidan na kan su suna kallon su cikin burgewa bai ajiye ta ba sai da suka shiga bedroom d'insu sannan ya ajiye ta akan gado ya fara cire Mata kayan jikin ta ta ce "Allah fa My ni nayi wanka na," bai ko damu ba ya ce "Na sani wani nake so ki k'ara yi," bata sake magana ba har ya cire Mata kayan ya d'auke ta zuwa toilet. Sun dad'e sosai a ciki sannan suka fito d'aure da towels Sabeeha sai tura baki gaba take yi shi Kuma yana you mata dariya "Dama nasan ba wani wanka da zaka Bari ayi ai," "To yarinya ko iya haka ai kin samu lada," ya fad'a tare da jawota jikinsa ya zare towel d'in jikin ta ya ce "Yanzu Kuma ladan da Zaki samu yafi na d'azu," ya fad'a tare da kwantar da ita saman gadon ya fara aika mata da wani irin kissing Mai tsayawa a rai tun tana basarwa har itama ta biye masa suka fara bawa junan su farin ciki. Sun dad'e suna aikin abu d'aya abinka da an dad'e ba a gamu ba sannan suka sake yin wanka suka shirya cikin k'ananun kaya Maleek riga da wando farare Sabeeha Kuma pink d'in doguwar riga sai k'amshi suke zabgawa hannun su rik'e da juna suka fita dga part d'in. Suna zuwa part d'in Ummi suka samu ta dawo nan fa suka zauna zaman fira a nan Maleek ke sanarwa da Ummi cewa gobe zasu tafi dubai shi da Sabeen sa Ummi tayi musu fatan alkhairi tun daren ranar suka had'a kayan su tsaf washe gari 'yan uwa da abokan arzik'i suka yi musu rakiya airport tare da zugar sojoji suka hau jirgi sai Dubai. A gajiye suka k'arasa gida kamar wad'an da suka je a k'asa wanka suka yi suka ci abinci sannan suka kwanta baccin gajiya rungume da juna abinsu. Zuwan su Dubai ba k'aramun kwanciyar hankali suka samu ba ga wata kulawa da suke bawa juna more especially ma Maleek da yake ganin Sabeen sa ba ita kad'ai bace hakan ne yasa shi zage damtse wajen ninka kulawar sa a kanta kullum sai sun fita yawo abin su yau suna shopping gobe suna shan icream ko cinema jibi suna restaurant. Babyn su kuwa kamar zasu saye Dubai Mall gaba d'ayan ta saboda siyayyar da suka yi masa duk wani Abu na buk'atar jariri da wasan sa sun siya sun ajiye kullum suna kan hanyar siyayyar baby a b'angre guda Kuma su Ummi da Doctor ma ba a barsu baya ba wajen siyayyar harma da Daddy da Abba da suke murna sun kusa samun jika ko ince jikoki domin Sabreen da Sameeha ma suna da shigar ciki. Rinaz da take India ma kullum cikin yi musu waya take ballantana Sameeha da Sabreen su ji labari haka ma Zainabu itama tana Kira harma da mutanen Abuja su hanfa abun mamaki kuwa Kira harda su Nasreen domin ta yiwa kanta karatun ta nitsu daga ita har iyayen ta dan Uncle ma yabi Daddy Landon a can Daddy yasa baki aka mayar da Uncle bakin aikin sa yadda ya cigaba da aikin sa cikin mutunci da amana. Haka rayuwar ta cigaba da kasance musu cikin farin ciki a kowanne bangare a haka har cikin Sabeeha ya shiga watan haihuwa lokacin ne Kuma Ummi ta fara damun Maleek da waya akan cewar lallai ya d'auki Sabeeha su koma Nigeria saboda ta haihu a gida. Yanzu ma zaune suke a falo Sabeeha na kwance jikin Maleek sai sauke masa shagwab'a take yi shi Kuma yana wasa da gashin kanta ya ce "Baby meye sirrin ne naga fa sai wani k'ara kyau ki ke yi kullum?" Far tayi da idanunta ta ce "Kai haba My sai kace kai kullum fa k'ara maka kyau ake yi kasan dawa ka ke kama kuwa?" Girgiza Mata Kai ya yi yana dariyar maganar sai da ta tsaya kamar mai tunani sannan ta kalle shi tare da shafa sajen fuskar sa ta ce "Kana matuk'ar kama da actor d'in Bollywood d'in nan Mai suna Mahesh babu," d'an juya Mata idanunsa ya yi alamun au hakane ta gyad'a Kai ta ce "Yes bambamcin ka da shi shine ka fisa kyau saboda ka fisa idanu shi idanunsa ba manya bane Kai Kuma naka manya ne sannan Kuma yana yin jikin ku ba d'aya ba Kai jikin ka irin na Rehan Ahmad khan ne na series film d'in nan na shu'uma sai dai shima ka fisa tsayi," kallon ta kawai Maleek ke yi yana murmushi. "Yawwa My idan Kuma kayi dariya kasan kuwa cewar hak'oran ka irin na Amman Junaid Khan ne sai dai dariyar ka tafi tasa kyau and then Kai kana dimples su Kuma duk basu da shi sai dai gashin kanka kam sak na Rehan Ahmad khan ba bambamci haka ma fatar ka wow gaskiya My ka had'u ga sajen ka mai kashe ni da kyansa," wannan lokacin dariya kawai Maleek ya ke yi mata tura baki kawai ta yi ta ce "Au dariya ma na baka to yadda na fad'a maka ma a hakan kwatantawa nayi domin duk ka wuce nan Wallahi," Sai lokacin ya ce "Ok ok na yadda ai baby ke Kuma duk kinfi haka," ya fad'a tare da Kai hannun sa yana shafa cikin ta a tare suka kalli juna suna dariya ta ce "My kaji babyn yana motsawa dama fa daga ji baya ji fitinanne ne," dariya ya yi ya ce "No nikam ki dena cewa yarona mai fitina," "To kullum fa sai ya yi ta yi mun wasa a cikina yana naushi na," dariya Maleek ya yi ya ce "To yi hak'uri kinji hubbyna bazai sake ba," ya fad'a Yana kai kansa wajen cikin ya ce "Babyn papa ka dena naushin momman ka a ciki kaji d'an albarka," Nan ma cikin ya Kuma motsawa rungume juna suka yi suna dariya. "Yawwa My yaushe ne zamu koma gida nayi missing kowa," "Uhmm ba rana nifa nafi so mu zauna a nan," zare ido ta yi ta ce "Nikam ban yadda ba Kuma ba Ummi ta ce mu tafi gida ba," "Shikenan jibi zamu wuce shikenan?" Noding kanta ta yi cikin farin ciki tana sakin masa wani lallausan murmushi shi Kuma ya sakar masa kiss akan soft lips d'in ta tare da mayar da ita jikin sa ya rungume ta yana jin sonta na ratsa ko wacce gab'a ta jikin sa. Washe gari sai da suka sake fita duk da ba yadda Maleek bai yi da ita ta zauna a gida ya je ya dawo ba Amma tak'i yadda har da yi masa kuka ganin yadda tasa shi a gaba tana ta aikin kuka ne sai ya ce ta tashi su tafi shopping suka fita inda suka yiwa mutanen gida tsaraba kala-kala sannan suka koma gida bayan sun biya restaurant sunyi take away na kayan ciye ciye suna komawa gida wanka suka yi sannan suka zauna suka yi dinner sannan Sabeeha ta kunna TV tana kallo Maleek kuwa danna laptop d'in sa yake yi. Ta ce "Yawwa Husby wai meyasa ka ke zaune a nan meyasa baza ka koma 9ja da aikin ba kayi zaman ka a office kawai tunda dama kace Kai zaman office ne naka?" Kallon ta ya yi sannan ya d'an ture laptop d'in ya ce "To Hubbyna ai nan d'in ma a office nake ko kinfi so na koma can?" Gyad'a Kai ta yi ta ce "Eh saboda bazan so ka dinga yi mana nisa ba ni da babyn ka," ta fad'a hawaye na zubo mata. D'an zare ido ya yi ya ce "Ya Salam! Baby rigima please Bari kukan to Kuma kema ai kinsan bazan dinga barin ku a 9ja na taho nan ba ko," "To idan muka taho ai zanyi missing su Ummi Mama da su Sabreen dear," ajiyar zuciya ya sauke ya d'an sosa forehead d'in sa ya furzar da iska ya ce "Ina ga zan cigaba da aikina a nan amma zan koma can d'in ma nan Kuma na dinga zuwa idan buk'atar hakan ta taso kin amince?" Gyad'a Kai ta yi ta ce "Eh na yadda," ranar sun dad'e suna fira abinsu. Sai dai lokacin da zasu kwanta Sabeeha ta fara jin cikin ta na juya Mata especially ma mararta mazewa kawai take yi bata bari Maleek ya lura da hakan ba har suka kwanta taje duk ta mak'alk'ale shi da marar ta ta juya sai ta k'ara k'ank'ame shi ya ce "Baby da wani abu ne?" Girgiza masa Kai ta yi bai Kuma magana ba ya rufe idanun sa Mai d'auke da zara-zaran eyelashes domin bacci ne sosai a idanunsa saboda ya gaji da yawa. Sai ya yi nisa a baccin sa zai ji ta k'ank'ame shi sai mutsu mutsu take yi ba tare da ya bud'e idanun sa ba ya ce "Baby da wata matsalacce?" A hankali ta ce "Uhm uhm fa," "Ok ki barni nayi bacci ke baki gaji bane kwanta kiyi bacci abinki kinji," ya fad'a tare da d'ora kanta saman k'irjin sa yana shafa bayan ta ita kuwa dad'a yin luff ta yi a jikin sa saboda d'umin jikin sa da ya ratsa nata jikin. Dakyar wani bacci ya d'auke ta amma tana yi tana farkawa idan mararta ta murd'a mata wajen k'arfe uku na dare ta tashi ta sauka k'asan gadon ta dafe cikin ta tana yarfe hannu saboda azabar da take ji sai da aka yi sallar asuba sannan taji cikin nata ya lafa ta tashi ta yi alwala ta yi sallah tana zaune saman prayer mat Maleek ya tashi shima alwala ya yi ya yi sallah sannan ya sata a gaba Yana kallon ta ganin idanunta sunyi ja ya ce "Lafiya ki ke kuwa baby?" Gyad'a Kai ta yi ta ce "Ina kwana," "Lafiya ya babyna?" Kallon cikin ta yi da ya yi k'asa sosai ta ce "Yana lafiya yana gaida Daddyn sa," tashi tsaye ya yi sannan ya d'auke ta cak ya kwantar saman gado ya ce "Maman baby na da baby na su koma bacci," ya fad'a tare da kwanciya gefen ta Sabeeha kuwa dama bacci take ji idanunta har rurrufewa suke yi ta cire hijabin jikin ta ta shige jikin sa a haka bacci ya d'auke ta. Maleek ya riga ta tashi dan haka ya yi wanka ya shirya cikin wata had'add'iyar tsadaddiyar shadda brown color ta yi masa kyau sosai har hula yasa wajen gidan ya fita yasa d'aya daga cikin soldiers d'in sa ya je ya kawo musu abin breakfast domin baya barin Sabeeha girki sannan ita baza ta ci na 'yar aikin gidan ba sannan shima baza ta barshi yaci ba. Bayan ya koma cikin gidan zama ya yi saman kujera yana danna wayar sa Kiran Ummi ne ya shiga wayar tasa da mamaki yake kallon wayar sai ya d'aga ko bari su gaisa Ummi bata yi ba ta ce "Kun fara shiri kuwa?" Murmushi ya yi ya ce "Ummi muna kan shiri ne anjima kad'an zamu taso insha Allah," "Allah ya kaimu ina Daughter d'in?" K'ofar d'akin ya kalla ya ce "Bata tashi ba Ummi," "Ok sai kunzo," Ummi ta fad'a tare da kashe wayar Sabeeha kuwa wani mugun ciwon mara ne ya tashe ta daga baccin da take yi a mugun firgice ta tashi daga baccin ta zame ta sauka k'asan dafe da cikin ta tana yarfe hannu ga wata uwar zufa da ta had'a duk da sanyin AC da d'akin ke yi sai juya Kai take yi Kira take son k'walawa Maleek amma da ta yi k'ok'arin bud'e bakin ta sai ta ji cikin ta ya murd'a a hankali ta Kai hannun ta ta laluba saman gadon ta jiyo wayar ta ta d'auko ta danna number d'in Maleek wanda tayi saving da Life partner ta yi dialing. Maleek dake zaune a falo ganin kira daga soulmate yasa shi kallon wayar sai Kuma ya yi picking yana d'agawa ta ce "Wayyo My zan mutu," da sauri Maleek ya mik'e tare da nufar d'akin da sauri. A durk'ushe ya same ta tana kukan wahala ya ce "Subhanallahi Baby bari mu tafi asibiti kawai," ya fad'a tare da k'ok'arin d'aukar ta. Yunk'urawa ta yi da d'an k'arfin ta tare da sakin wani nishin wahala abin mamaki sai jin kukan jaririya suka yi a tare suka kalli juna sannan suka Mai da kallon su kan baby girl d'in dake ta tsala kuka wata nannauyar ajiyar zuciya suka sake a tare Maleek da kansa ya yanke ciki tare da k'udundune yarinyar a wani lallausan towel Sabeeha kuwa zubewa ta yi a wajen tana maida numfashi Maleek kuwa bai damu da jinin dake jikin yarinyar ba sai ma sumbata da yake ta aikawa yarinyar tako ina. Shi da Sabeeha suka yi k'ok'arin gyara wajen domin Alhamdulillah ta haihu lafiya ba inda ke mata ciwo a haka suka gyara wajen tsaf sannan suka gyara babyn cikin wasu kayan sanyi masu matuk'ar kyau da laushi kalar purple mai haske. Yarinyar suka kwantar sannan Maleek da Sabeeha suka shiga toilet shi a lallai sai ya taya ta wanka bata iya ba haka ta hak'ura ya taya ta ta yi wankan ta gasa jikin ta sannan suka fito ta fara shiri shima ya koma toilet d'in ya yi nasa wankan suka fito suka shirya sosai suka yi kyau abinsu Sabeeha cikin atamfa doguwar riga mai mad'auri ta gaba atamfar blue light ne da fari sai Baki a jiki ta yafa mayafi fari da takalmi da jaka Maleek kuwa cikin light blue shadda ya yi kyau har ya gaji sai k'amshi. Shi dai Maleek bakin sa yak'i rufuwa sai kallon jaririyar tasu yake yi yana jin irin sonta mara misali a zuciyar sa ya jawo Sabeeha jikin sa sai sakar mata kiss yake yi ita kuwa sai dariya take masa ya ce "Baby muje asibiti a duba mun ke sannan mu wuce airport," zare ido ta yi ta ce "Hospital fa My nifa lafiya ta k'alau," girgiza Kai ya yi ya ce "I know amma dai duk da haka sai munje," bata sake magana ba har suka gama Shirin su suka fita compound d'in gidan da yake cike da sojoji da Kuma motoci. Suna tsaye har aka gama zuba musu tulin kayan su a mota suka shiga sai Airport jiniya kawai ke tashi a Dubai sojojin kansu mamakin haihuwar suke yi. Sai da suka biya asibiti aka tabbatar da ba abinda ke damun baby da mamanta sannan suka wuce Airport suka shiga jirgi suka d'aga sai 9ja. Jirgin su na landing suka samu zugar family tare da sojoji na jiran isowar su a hankali suka fara sauka daga matakalar jirgin fuskar su d'auke da murmushi. A gefe Kuma Ummi ce da Doctor tare da Sameeha Sabreen da Umar sai Fauwaz har ma da Nasreen da Umman ta burin su kawai suka fitowar su Maleek d'in Aikuwa sai gasu sun fito cike da mamaki suke kallon Maleek rik'e da baby a hannu ga Kuma Sabeeha ba ciki. Ai da matuk'ar murna suka k'arasa wajen su Sabeeha kuwa bata damu da hill takalmi dake k'afar ta ba da gudu ta nufi Ummi ta fad'a jikin ta ta rungume ta sannan ta saki Ummi ta fad'a jikin Doctor ta rungume ta tana dariya yayin da Sabreen Sameeha da Nasreen har ma da su Fauwaz suka nufi Maleek suna kallon kyakkyawar yarinyar dake hannun sa mai kama da baban ta sak. Wajen su Maleek ya k'arasa ya gaishe su suka amsa cikin fara'a Ummi bakin ta yak'i rufuwa ta ce "Son me nake gani kamar new baby?" Yana dariya ya ce "Eh Ummi Baby ce ta haihu d'azu," ai barin sa suka yi a tsaye suka nufi wajen su Sabreen dake rik'e da yarinyar suna murna har sun rasa inda zasu sa yarinyar. Waigawa Maleek ya yi ya kalli Sabeeha dake gefen sa ya ce "Kin gani su Ummi ba ta mu suke yi ba zo mu tafi domin na gaji da yawa," hararar wasa ta yi masa ta ce "Lallai ma My d'in nan sai kace kaine ka haihu," dariya ya yi ya ja hannun ta ya karb'i key hannun Adam ya shiga driver seat Sabeeha ma ta shiga suka d'auki hanya ba tare da su Ummi sun ankara ba ya ja motar da gudu yana fad'in "Yanzu sai ki ga 'yan jarida sun cika airport d'in nan ni kuma hakan ne banso," ajiyar zuciya Sabeeha ta sauke ta ce "Nima kam baso nake yi ba kana ganin ranar da zamu tafi inda suka zagaye mu a airport d'in nan," dariya ya yi ya ce "Ke Kuma ki ka so ki nuna musu ke rigimammiya ce ba kuka fa na ga Zaki yi," dariya itama ta yi ta ce "Allah husby naga ba Kai suka fiya ba," haka suka k'arasa gida suna fira abinsu ga mamakin Sabeeha Rashida suka samu a part d'in Ummi tare da su Hadiza suna jera abinci a daining su suka tarbe su. A airport kuwa yarinyar nan tana ganin so daga hannun wannan sai hannun waccan yarinya kuwa ba dai wayo ba duk Wanda ya d'auke ta sai ta yi masa k'urr da idanu tana kallon sa Sabreen Bata damu da cikin dake jikin ta ba ta yi tsalle ta ce "Wayyyo my heart kalla ka ga blue eyes gare ta wayyo kyau," Sameeha ta ce "Wow nikam dama a barmun," Fauwaz ya ce "Masha Allah yarinyar kama take yi da Yaya har tafi Yaya kyau ma," Umar dake gefen Fauwaz sai aikin hoto yake wa yarinyar ya ce "Gaskiya MG ya iya haihuwa wannan kyakkyawar yarinya haka ita ba yar indiya ba ita ba balarabiya ba," "Sameeha dear dai ta iya haihuwa," Sameeha ta fad'a tana k'ara kallon yarinyar "Ummi mu wuce gida ina MG d'in?" Umar ya fad'a suna waigawa suka ga ba Sabeeha ba Maleek sai tulin 'yan jarida da suka gani wajen. Dakyar suka samu suka zille suka shiga motocin su suka tafi gida sai dai yarinya tasa hotuna da videos. Ga mamakin su suna zuwa suka samu su Sabeeha har sun yi wanka suna zaune a daining suna cin abinci abinsu suna dariya. A falo su Ummi suka ya da zango da baby girl da wutsil-wutsil da hannu da k'afa take yi Yarinyar daga ganin ta akwai wayo a wajen Umman Nasreen ce ta shiga falon itama ta karb'i yarinyar tana yaba kyan ta itama sai farin ciki take yi domin yanzu Allah ya shirye ta. Kafin kace me su Fauwaz da Sabreen sai waya suke yi suna fad'ar haihuwar Rinaz dake India kuwa da su Hanfa da Hany har an cika musu wayoyin su da pictures d'in baby. Su Zainabu kuwa suna jin haihuwar suka tafi gidan Ummi Abba da Daddy har ma da Uncle sai waya suke yi suna tambayar baby domin suma labari ya Kai musu. Haka Baby da Maman ta ke samun kulawa a ta kowanne bangare ko yaushe gidan zaka samu ana farin ciki ana fira da dariya yayin da baby tana yin kuka hankalin kowa a gidan idan ya yi dubu ta tashi saboda so da k'aunar da ake nuna Mata a haka har ranar suna ta kusa inda ake ta yin shirye shirye ba kama k'afar yaro. Ana I gobe suna Rinaz ta sauka a 9ja nik'i nik'i da tsarabar da ta yiwa baby su Sabeeha sai murnar ganinta suke yi da daddare Kuma su Daddy suka dira a k'asar har falon Uncle aka Kai musu baby a take Uncle ya yiwa yarinyar kyautar car key domin ji ya yi yarinyar ta shiga ransa sosai. Washe gari suna gidan a cike yake da bak'i na kusa dana nesa su Hanfa duk sunzo da Mama Aisa har ma da su Aleem domin lokacin ansa ranar hanfa da Ashraf Hany da Alim saura wata d'aya. Yarinya taci sunan Ummi Aysha amma suna Kiran ta da Alizah kaya kuwa yarinya tasha shi har iyayen ta sun rasa wajen sawa kyauta har da su car keys d'in da ta samu da yamma aka yi gagarumar walima ta gani ta fad'a anci ansha ba k'arya 'yan jarida da gidan televisions suka cika gidan uwar 'ya ta ci kwalliya kamar wata amarya domin idan ba fad'a maka akayi ba baza ka ce ita ta haihu ba. Walimar babba ce domin har Nigerian army sunje inda a nan ne aka k'arawa Maleek girma daga MG zuwa Marshall social media ko Ina ka shiga su ake d'orawa a haka aka tashi yarinyar da iyayen ta sun samu kyauta babu k'arya. Ranar da daddare Ummi tasa Sabeeha ta shirya tare da Baby alizah zuwa gidan Doctor domin su yi wankan gida Doctor su Ummi suka yi mata rakiya inda lantana ta tare su cikin farin ciki can aka cigaba da basu kulawa kullum Maleek na gidan hakama su Sabreen da Zainabu kowa ya d'orawa Alizah soyayya. Satin su d'aya a gidan aka kawo kud'in auren Rinaz tare da saurayin ta Faruk aka sa rana one month hakan na nufin idan akayi nasu Hanfa da sati d'aya kenan Amma Daddy ya ce a had'a kawai a yi. Haka rayuwa ta cigaba da kasancewa har Sabeeha ta yi arba'in da haihuwa inda a lokacin Kuma zasu tare a sabon gidan su. Haka suka tare a sabon gidan su da ya gaji da had'uwa Ummi ce ta zuba komai na gidan tun daga compound d'in gidan za kasan mai gidan ba wasa b'angaren kud'i saboda motocin dake parking space baza su irgu ba da nasa dana matar sa da Kuma na baby Alizah balle ka shiga ciki fad'ar had'uwar gidan ma b'ata lokaci ne su Sabreen sai santi suke yi d'akin baby Alizah kuwa ba a cewa komai saboda tsabar had'uwar sa yaji kayan wasa komai na d'akin baby pink ne gwanin sha'awa haka aka watse akabar masu gidan. A haka bikin su Hanfa ya matso tare da na Rinaz gaba d'aya su Ummi tarkatawa suka yi suka tafi Abuja har dasu Sabreen da su lantana har ma da su Uncle domin dama suna da family house nan za ayi bikin gida ne mai girman gaske Mai d'auke da wajajen hutawa da swimming pools da iska Mai dad'in gaske kasancewar gidan ya yi bayan gari ba abinda kake ji sai kukan tsintsaye sai duwatsu Kai wajen gwanin burgewa. A nan aka yi shagalin bikin su Hanfa bikin ya k'ayatar ba k'arya kasancewar bikin ya samu gidan naira anyi harkar girma hakama ango faruk ba dai uban dukiya ba haka aka yi biki aka tashi lafiya aka Kai kowacce gidan ta Rinaz ma gidan ta dake Abuja aka kaita kafin subar k'asar zuwa India inda dama a can faruk ke aiki sannan dama Rinaz d'in bata gama karatun ta ba tayi kuka har ta gaji lokacin da su Ummi zasu koma kaduna sai dai ba yadda ta iya haka suka tafi suka barta da angon ta su Hanfa kuwa ba wacce ta yi kuka domin suna ganin basu bar gida ba gasu ga yayyan su Kuma mazajen su sai ma duniyan cin da suke yi gaban mutane. Bayan komawar su Ummi gida da sati d'aya Arfat tare da mahaifiyar sa suka je suka samu Uncle da Daddy akan cewar a taimaka aba Arfat auren Nasreen inda su Daddy suka ce ba ruwan su su sami Maleek har gida kuwa suka je suka sami Maleek akan maganar da ya nuna Sam bai yadda da hakan ba Mai hankali da nutsuwa zai ba k'anwar sa sai da Sabeeha tasa baki tare da nuna masa cewar Arfat fa nasan Nasreen sannan itama tana son sa sannan da baya sonta bazai jawo mahaifiyar sa har wajen sa ba tunda har ya riga ya samu abinda yake nema a wajen ta da Dan wani abu yake son ta da haka Sabeeha ta shawo kansa ya yadda inda yace sati d'aya kawai za asa bikin Arfat kam bai Musa ba tunda bai da matsalar komai akwai naira aikuwa sati nayi ba a yi wata bid'i a ba sai dinner aka Kai amarya gidan ta. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya kowanne gida suna cikin farin ciki da nishad'i. BAYAN SHEKARA UKU abubuwa da yawa sun faru ciki kuwa har auren Salman da Aysha ta wajen aikin hajiya fulani da Kuma bikin dija da Muhsin d'an yayan Ummi da suka had'u a bikin 'yan uku Sabreen kuwa ta haifi twins duk maza kyawawa masu kama da 'yan uku anyi shagali ba kama k'afar yaro yara sunci sunan Daddy da Abba ana Kiran su Aiman da Ammar yaran sun ga gata ba k'arya Sameeha kuwa mace ta haifa Mai kama da Umar sai dai ita fara ce yarinyar kyakkyawar gaske taci sunan Doctor Amma suna Kiran ta ni'imatullah. Sabeeha ce a kitchen tana aiki ta ji shigowar Alizah da gudu cikin falon ta nufi stairs tana k'wala Kiran "Momma! Momma," cikin hausar ta ta yara da bata gama iyawa ba. Dafe Kai Sabeeha ta yi ta ce "Wayyo ni Sabeehan Mama naga ta kaina," ta fad'a tare da fita falon ta ce "Alizah me kika dawo yi kuma?" Kyakkyawar yarinyar dake saukowa stairs tasha kyau cikin farar riga da k'aramun black skirt da toms d'in takalmi da farar safa da necktie da alama daga makaran ta take kallo d'aya zaka yi Mata kasan fitina ta ratsa yarinyar da wayo an gyara mata gashinta kanta an yi Mata two babies da shi ya zubo har kafad'ar ta Tasha jan ribbom ta ce "Momma na manta biro ne a gida ne nazo d'auka," ta fad'a tare da washe bakin ta fararen hak'oran ta suka bayyana dimples d'in ta ya lotsa. Hararar ta Sabeeha ta yi ta ce "Duk laifina ne da na saki a makarantar dake kusa da gida sai ki dawo sai uku kafin a tashi," k'ifk'ifta blue eyes d'in ta ta fara ta zare idanunta Mai d'auke da zara-zaran eyelashes ta ce "Sorry momma karki ce Zaki canja mun school," "Sai Kuma kiyi yarinya canja makaranta ba fashi," Sabeeha ta fad'a tare da komawa kitchen d'in Alizah kuwa hanyar fita ta yi da gudu tana cewa "Na tafi Mama ta see you later," Sabeeha na jinta girgiza Kai kawai ta yi. Da yamma da Maleek ya dawo ya samu Sabeeha zaune saman kujera tana chart da Sameeha ajiye wayar ta yi ta rungume shi tana masa sannu da zuwa zama ya yi a gajiye ta kawo masa ruwa ya sha ya ce "Ina Alizah fa?" Kafin ta ce wani Abu sai ga Alizah ta fito da gudu daga sama tana k'ara itama Sabeeha ganin haka ta yi tsalle ta b'uya a bayan Maleek ta b'oye fuskar ta a bayan sa ya ce "Baby Aliz lafiya kuwa," raurau ta yi da ido ta ce "Papa wani Abu ne a d'akin momma zo muje ka gani Ina wasa na kawai yazo," sai lokacin Sabeeha ta kalli Alizah zare ido ta yi ta ce "Kam bala'i ka gani ko My ni kawai Wallahi ka d'auki yarinyar nan ka kaita wajen Ummi ko Mama ko ka kaiwa Sabreen dear ka ga fa inda ta yiwa jikin ta wanka da Mai har ma da jambaki," Sabeeha ta fad'a kamar zata yi kuka. Shiru Maleek ya yi Yana kallon Alizah shi kansa ya jinjinawa fitinar Alizah ya ce "Yanzu Aliz haka kika b'ata jikin ki," "Ni ba wannan ba My kullum ita ce dawowa daga school sai ta dawo sai uku sau hud'u kafin tashi hatta teachers d'in su complain suke akan ta Ni kawai na gaji gara ka Kai ta wajen Umman Nasreen," Maleek kuwa jin Alizah na gudun makaranta take ya had'a rai saboda shi duk fitinar ta bata dame shi ba amma jin tana dawowa daga school sai ya ji bai ji dad'i ba ya ce "Kee! zonan," zare ido ta yi ta ce "Sorry papa ban Kuma ba kaji," "Kizo fa nace!," Ya fad'a a d'an tsawa ce Sabeeha kuwa dariya take musu k'asa k'asa a zuciyar ta ta ce gara ya yi maganin mara jin magana Aliza kuwa a hankali ta k'arasa wajen sa. Jawota ya yi ya d'orata saman cinyar sa ya ce "Oya kiss your daddy," kiss ta bashi a check d'in sa tana dariya shima dariyar ya yi ya bata kiss a forehead d'in ta ya ce "Gobe ma zamu wuce Dubai a can Zan saki school kamar yadda nayi karatu primary da secondary d'ina a can haka ma my Aliz zata yi sannan maman ki ma school zata koma," Sabeeha dake tura bakin jin haushin k'in dukan Alizah ta buga tsalle ta ce "Wayyo da gaske My?" D'aga mata gira ya yi nan kuwa su Sabeeha har da rawar murna ya ce "Ku je ku shirya muje yiwa su Mama Sallama," ba b'ata lokaci suka yi wanka suka shirya suka fice. Da gidan Mama suka fara sannan gidan Ummi a can suke jin Rinaz ta haifi namiji sunyi murna sosai sannan a can suke jin auren Rashida da Faisal driver d'in Doctor next week sun dad'e a gidan sannan suka nufi gidan Umar Sameeha ta tare su cikin farin ciki suna ta fira abin su Alizah kuwa sai da ta yi musu fitina domin kaca kaca ta yi da kayan dressing mirrow d'in Sameeha. Bayan sunbar Nan sai gidan Sabreen can suka yi dinner suna ta kwasar fira inda Alizah ta mak'ale sai ta d'auki Aiman yaron da ko da kud'i aka had'ata bazata iya d'auka ba kan Sabeeha ta hana a bata ta dinga kuka har da cewa sai ta gayawa Uncle da Daddy dakyar suka rarrashe ta ta yi shiru da kukan ta da kana ji kasan na shagwab'a ne. Suna barin gidan Nasreen shopping suka wuce bayan sunyi siyayya suna fitowa suka yi ana Kiran sunan Sabeeha suna waigawa suka ga Yallab'ai khamis tare da fareeda har ma da yara uku gaisawa suka yi cikin fara'a sannan su Yallab'ai suka yi Mata Allah ya Sanya alkhairi kowa ya shiga motar su suka tafi Alizah na damun su da tambaya "Momma na papa wancan Uncle d'an lukutin waye?" "Malama ki yi mana shiru ke bakya gajiya da surutu ne tunda muka fito baki yi shiru ba," Maleek dake yiwa dramar tasu dariya ya ce "A'a baby kyale ta ta yi tambaya ai abinda Bata sani bane," shiru Sabeeha ta yi bata Kuma magana ba domin tasan yanzu sai su had'e mata Kai. Nan Alizah tai ta jera tambayoyi domin ko a school haka take shiyasa teachers d'in su ke ji da ita gata da k'ok'ari da uban surutu shiyasa Maleek yasa ta school da wuri a haka suka koma gida. Washe gari suka d'aga zuwa Dubai inda aka samarwa Alizah wata private school aka sata haka ma Sabeeha ta koma makaranta ya yinda Maleek ke zuwa office abinsa haka rayuwar su ta cigaba da gudana cikin farin ciki da k'aunar juna. ALHAMDULILLAH Anan na kawo k'arshen littafina Mai suna 'YAN UKU kuskuren da nayi a ciki Allah ya yafemun Allah ya bamu ikon amfana da abinda littafin ya kunsa Allah ya yafe mana kurakuren mu Allah yasa mu cika da imani ameen. Ina jaddada godiya ta ga masoyana Allah ubangiji yabar zumunci ya barmu tare Allah ya sake had'a kanmu Nagode Nagode daga taku a ko da yaushe HAFSAT MAGAJI DABO SHANONO (RUHAZ). Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels