Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels [9/7, 10:40] bintaumarabbale: _MAJNUN!_ *'BOYAYYAN -ATTAJIRI* _NA_ *_BINTA UMAR ABBALE🍒_* _MANAZARTA WRITES ASSO_ _________ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ _*DOCTOR MS AGADAS*_ _(MARA'KISIYYA)_ INA GAISUWA🙏🏻🥰 _NA BAKI KYAUTAR WANNAN SHAFIN_💜 *19&20* Duk da Baban ta amince da abinda takeso hakan bai sanya ta kwantar da hankalinta ba, kullum cikin damuwa take duk saboda rashin sanin takameman gurin da mahaukacin ya sauya da zama, domin ita duk a tunaninta tsokanar da yara ke masa ya sanya ya bar gurin, a rana ta kan je bakin kasuwar sau uku ko fiye da haka tayi ta dube-dube ko Allah zai sanya ta ganshi, babu shi babu dalilinsa sai tarin tarkacensa dake karkashin matacciyar mota (a kori kura) da yake kwanciya a karkashinta. Da azumin arfa a bakinta daf da za'a sha ruwa ta faki ido ta fita daga gidan kai tsaye bakin kasuwar ta nufa. Baba Asabe ta fito daga kicin da muburgi a hannunta, Saliha ce kadai a zaune a tsakar gidan tana had'a musu lemo, tace." Ina Shahida ita kuma sai tazo ta soya mana awara kada asha ruwa mu rasa abunda za musa a bakin salati." Tabe bakinta tayi tace." Yanzu ta fita." Cike da mamaki tace." Ta fita kamar yaya ina taje."? Tace." To ni kya tambaye ni, nima ban sani ba, na san dai sa'i da lokaci tana fakar idonki ta fita." Baba Asabe bata kawo mummunan abu a ranta ba, tafi tunanin cewa Shahidan bakin kasuwa take zuwa gurin mahaukacin data dauki son duniya ta dora masa. A fili tace." Allah yasa ya tafi kenan ba zai dawo ba domin kuwa na fara zargin mutumin nan idan ba aljani bane to babu shakka maye ne." Ta daga labulan daki ta shiga tana cigaba da maganar da alama al'amarin yana damunta. Yau ma ba sa'a domin kuwa gurin zaman nashi ma dabbobi (awakai) ne a kwance a gurin duk sunyi masa kashi ga ruwan saman da akayi jiya ya jika masa wasu kayan nasa, babu shi a gurin sai dabbobin da suka maye gurbinsa. Wasu zafafan hawaye suka ciko idonta, ko'ina mutumin nan ya shiga? "Watakila ya mutu a wani guri." Zuciyarta ce ke raya mata hakan. Ta girgiza kai gabanta na wani irin fad'uwa! "Insha Allahu bai mutu ba." Ta furta hakan a fili. Da sauri tasa hannu ta goge hawayen da ya zubo ta kira wani yaro da hannunta. Yaro yazo ya tsaya gabanta da ledar kankana da lemo a hannunsa da alama aikensa akayi kuma da azumi a bakinsa yana sauri ya isa gida yace." Gani." A sanyaye tace." Don Allah ko kasan inda Baban-baba ya koma da zama." Cike da rashin fahimta yace." Waye Baban-baba."? Ta nuna masa tsohuwar motar da fadin." Mutumin dake zama a waccan motar." Ya kalli gurin da take nuna masa ya juyo da tsoro a tare dashi yace." Ni ma ban sani ba.'' bai jira jin abinda za tace ba yayi saurin barin gurin yana waiwayenta. Ba ta hakura ba ta sake tarar wani yaron tana tambayarsa, yaron irin marasa kunyar nan ne, kawai sai ya fashe da dariya yana gwada irin maganarta ta kurame! "habbbaba! ya nuna ta da yatsa yana kyalkyala dariya ta bishi da kallo tausayin kanta da kanta ya lullubeta, wai shin ita din abar tausayi ce ko kuma Baban-baba! Hawaye masu zafin gaske suka ciko idonta, tayi namijin kokarin hanasu zuba, da saurin gaske ta bar gurin tana addua a zuciyarta. Koda ta koma gidan ma 'bacin rai ne! don fad'a ta riska, Baba Asabe ta inda take shiga ba ta nan take fita ba har da cewa idan ba tayi a hankali to za ta kai ta asibitin dawanau a duba kwakwalwarta, to itama a lokacin da Baban ke fadin hakan ba taji haushi ba domin ta fara zargin kanta anya kuwa bata samu matsalar kwakwalwa ba. Washe gari aka tashi da sallah, jama'a nata walwala da farin ciki mussaman wanda Allah ya hore wa abin layya ciki har da Baba Asabe domin babban (rago) na dubu sittin ta siya tayi layya dashi, wadatar zucci ne da ita tare da kokarin faranta ran jikokinta dake gabanta. Uku ga sallah ta shirya tsaf fuskarta babu walwala ta fito daga daki da hijab dinta a hannuta. Baban ta kalleta da fadin." Kin shirya kenan nace Saliha ta shirya kuje tar.....Salihan ta katse ta da fadin." Ni babu in da zani bacci zanyi na huta da yamma Kamalu zai zo muje gidan yayarsa ziyara." Kamalu shine saurayinta wanda akayi musu baiko. Baban tace." Ayyo! to shikkenan Shahida kinji abinda tace." Babu damuwa a tare da ita tace." Babu komai.'' Hanyar fita ta nufa da fadin." Sai na dawo." Tace." Ki gaishe su ba dan halinsu ba, maganar naman sallah kuwa ba zan ce ki tafi musu dashi ba dalili na fi kowa sanin waye Jamilu da burgar tsiya yanzu idan baki take ba yana nan ya kayar da manyan shanu yana neman suna a unguwa." Bata tsaya taji karshen maganar ba tayi saurin fita daga gidan, a ranta tana jin haushin irin cin mutuncin da Baban ke wa mahaifinta. Ilai kuwa tana shiga gidan taga zahiri domin kaca-kaca ta same su suna ta aikin suyar nama tare da daka dambu a k'aton turmi Hadiza ce mai wannan aikin. Can gefe kuma ganda ce tare da kan sah! da rago a babbake akan buhu an shanya k'udaje sai tashi a gurin da wari mara dadi. Jamila ce kawai ta amsa sallamarta tana fara'a tace." Aunty Shahida ashe kece dama kwana biyu kina raina." Ta saki fuskarta da fadin." Nima saboda ke nazo gidan." Hadiza ta kalleta da fadin." 'Yar iska bebiya kawai." da yake a hankali tayi maganar ba ta ji ba ta dai ga bakinta na motsi a lokacin da take maganar amma Talatun da sauran 'ya'yanta duk sun ji." Babu wani kulli a cikin ranta tace."Talatu ina kwana anyi sallah lafiya."? A dakile ta amsa ta cigaba da juya zallar sokar naman dake cike da kaskon suya. Jamila ta shimfida mata tabarba tana zama ya shigo gidan fuskarsa a tur'bune! kamar koda yaushe yana sanye da tsadaddiyar shadda wacce taji uban aiki irin na manyan mutane, hula da takalmi da agogo duka babu na banza kamshinsa kuwa tuni ya cika gidan. Gabadaya su kayi masa sannu da zuwa ya amsa babu walwala ya bude dakinsa ya shiga babbar rigar ya cire ya rataye ya zauna kasan kafet zugum! daka gani yana da damuwa. Sallamarta ce ta katse tunaninsa, ya amsa yana bin ta da kallo har ta samu guri ta zauna tana sake gaishe shi. Ya amsa yana mata wani irin kallo kafin yayi kwafa da fadin." Sai yau ki kayi ra'ayin zuwa in da nake."? Shuru tayi tana wasa da yatsun hannunta. Ya cigaba da cewa." Maganar aure ce bakya so nayi miki shiyasa ki ka dauke kafarki daga gidan nan ko.''? Ta kalleshi da fadin." Baba aure nufin Allah ne idan lokaci yayi zanyi aur......ya katse ta, ta hanyar daga mata hannu da fadin." Ni zaki fadawa lokaci? zaman me kike kin zama uwar mata shekara ashirin kanwarki Hadiza saura wata uku bikinta ga Jamila nan itama nayi magana da yaron da yake son auranta mun tattauna da mahaifinsa, ke da kike babbarsu kina zaune to wannan itace magana ta karshe da zanyi miki wata biyu kacal na baki ki fito da mijin aure tunda kin kammala secondary kinyi saukar al'kur'ani to kuma me ake nema."? Tana shashshekar kuka tace." Wallahi Baba tunda nake babu wanda ya ta'ba cewa yana sona, duk wanda yake so nayi aure ba kamar ni ba, na dai fi tunanin saboda lalurata maza suke gudu na." Ya girgiza kai da fadin.'' Mace bata kwantai matsalar ki ba zai hana ki auruwa ba, ki na da duk abinda ake bukata saboda haka ni ban yarda da wannan maganar taki ba." Sai ta kasa ce masa komai domin duk abinda zata fada masa ba zai yarda ba, bahaushe yace." Mai daki shi ya san inda yake masa yoyo, gaskiya ne tunda ta taso babu wani namiji da ya taba cewa yana sonta. Hannu tasa ta goge hawayen fuskarta, ta kalleshi har yanzu fuskarsa bata sassauta ba." "Zan tafi Baba." tafada tana kokarin tashi. yace."Ki bari sai yamma idan an kammala soya naman ki tafi da naki." Ya sosa mata in da yake mata 'kai'kayi cikin fargaba tace."Baba ina ka samu kudi ka yanka *SAH!* har da rago ." Ya kalleta yana sake tamke fuskarsa." Ke ni kikewa wannan tambayar don ubanki." Ya fada yana zazzare mata ido! A sanyaye! tace." Kayi hakuri." Hanyar fita ya nuna mata da hannu cikin tsawa! yace." Tashi ki fita ki bani guri." Da sauri ta tashi ta fita gabanta na wani irin fad'uwa! akwai dalilin da yasa ta tambaye shi saboda sanin halinsa mugun dan rigima ne zai iya zuwa yaci bashin mutane duk domin yazo yayi bajinta burga! da neman suna a cikin unguwa babban burinsa ace masa ya isa shi mai kudi ne. Hasashenta ya tabbata domin kuwa bayan fitar ta, ya zurfafa cikin tunanin hanyar da zai bi gurin ganin ya biya mahaucin da ya kar'bi *SAH!* da ragon a gurinsa. Yayi nazari ya hanga ya hango a yanzu dai bashi da dubu dari uku da hamsin din da zai biya mutumin idan ba gidan da yake ciki a zaune zai daga ya siyar ba. Dama yasa ran samun wasu kud'i ne sai kuma asara ta same shi, domin hak'ansa bai cimma ruwa ba, a gurin sana'ar tasu shine ya tashi fanko fayau!(ziro) hatta da motarsa bata tsira ba sai da aka kwamushe haka ya dawo gida a motar haya. Kwabo yanzu babu a cikin account dinsa sai 'yan canjin dake hannunsa, gabadaya tunaninsa ya ta'allaka gurin ganin hanyar da zai biya mahaucin kud'insa. Ta shiga dakin tana gyara daurin zanin jikinta da yayi muguwar daud'a sai karni take fuskarta na maiko. Kerere ta tsaya a kansa da fadin." Babu icce ya 'kare ga kuma uban 'kashi can da za'a soya yanzu dai abunda ake bukata icce da man gyada." A sakarce ya kalleta yaji wani mugun takaici ya turnuke shi, ta tsaya masa aka kerere! ba ta san halin da yake ciki ba, girgiza kansa yayi yace." Je ki zan fito yanzu na bada kudin." Ta juya ta fita bagazan-bagazan! Ya fito tsakar gidan yana nazarinsu. babu Shahida a cikinsu ta tafi, wato da yace ta tsaya ta tafi da nata rabon shine ta kama hanya ta tafi, shikkenan ai tayi wa kanta, waje ya fita minti biyar ya dawo gidan tare da zaratan samari biyu, a yanzu dai bashi da kudin icce ballantana wani man gyada, saboda haka ya yanke shawarar bada sadakar naman da niyya biyu. Ganin abinda yake shirin faruwa yasa ta fito afujajan! baki na rawa tace." A'a ya haka kuma." ? Bai saurareta ba ya cigaba da loda tsoka da k'ashi cikin buhu yana fadin gidajan da za'a kai musu. Talatu kamar ta dora hannu ta kurma ihu! jikinta sai rawa yake tana fadin." Ya haka ina za'a kai kuma."? Yace." Na bayar sadaka dama haka Allah yace ayi saboda haka wannan na cikin kaskon ya ishe ku." Idonta ya ciko da ruwan hawaye ta dinga zabga masa harara! wannan ai wulakanci ne! duka na cikin kaskon bai fi ya cika bokin fenti ba. Su Hadiza ma jikinsu ne duk ya mutu saboda ganin yankan kaunar da mahaifin nasu yake musu. Kaf ya kwashe naman ya bayar, ya bar musu kadan hatta da kawunan dabbobin da gandar dake shanye a buhu bai bari ba sai da ya bayar, dalili baya bukatar ta sake zuwar masa da wata bukata ta siyan icce ko man gyada da makamantansu. *LITTAFIN NA KUDI NE #500 SPECIAL 1K 0542382124....BINTA UMAR GTBANK, IDAN KATI ZAKI TURO #600 KIYI MIN MAGANA TA WHATSAPP DA WANNAN NUMBER 07084653262.....MUTANAN NIJAR DALA DARI SPECIAL JAKKA DAYA KATIN AIRTAL KO MOV* [9/7, 10:41] bintaumarabbale: _MAJNUN!_ *'BOYAYYAN -ATTAJIRI* _NA_ *_BINTA UMAR ABBALE🍒_* _MANAZARTA WRITES ASSO_ _________ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ *21&22* Talatu tare dasu Hadiza kamar su mutu saboda takaicin da Hujaj ya k'unsha musu, babu shakka ya cutar dasu, domin naman da ya bar musu bai taka kara ya karya ba, da 'kyar zai kai sati d'aya, gashi sun ci burin ajiyar nama saboda bayan sallah idan kwadayi ya tashi su fito dashi su gyara abinsu, Talatu dai kasa hakuri tayi ta shige daki tana matsar hawayen bakin ciki, tunanin hanyar da zata kuntata masa take. 'Bangaran sa kuwa har ya manta abunda ya aikata domin wanka yayi ya shirya cikin sabon yadi mai tsada anyi aikin kufta a wuyan rigar da hannuwa, ya dora hula zannar bukar a kansa ya fito yana kamshin tsadaddan turaransa. Yaran ya samu sunyi jugum-jugum! kamar anyi mutuwa. Ya kallesu na minti biyu kafin ya girgiza kansa ya kama hanyar fita ba tare da yayi musu magana ba, Jamila ce kawai ta iya yi masa a dawo lafiya Hadiza da Amina kuwa harara suka bi shi da ita yana fita Hadiza taja tsaki ta mike tsaye tana kunkuni! daki ta shiga, Jamila ta bita da kallon mamaki! ita kuwa Amina bakin kasko ta nufa ta juya naman dake kan wuta kafin ta tsamo katuwar tsoka tasa a bakinta tana taunawa tare da hure zafin dake barazanar 'kona mata dadashi. *** Jiki a sabule ta koma gida. Abin duniya yayi mata katutu! matsalar Baban-Baba ita tafi damunta, sai kuma matsalar mahaifinta, sharadin daya gindaya mata na fito da mijin aure cikin wata uku yayi mata tsauri! ba ta da madogara sai Allah domin kuwa babu wani namiji da ya nuna yana sonta ballanatana har su kai ga maganar aure. Sallah ta wuce da sati biyu da yawa daga cikin wa'inda sukayi layya sun cinye naman su, har sun fara siyan na miya, ita kanta Baba Asabe da ta yanka RAGO a yanzu bata da nama sai diddiga da kakide domin ba tayi son zuciya ba tayi sadaka da naman kamar yanda Ubangiji ya umarta Saliha ma tuntuni ta cinye nata, Shahida ce kawai mai nama a gidan ta kime shi a cikin kakide ta boye a karkashin gado ita bata ci ba, ba kuma ta bawa wani yaci ba yana ajiye. Tana zaune a tsakar rumfa tana taimakawa Baban da daurin gishiri taji motsi a cikin uwar daki. Haka kawai jikinta ya bata wani abu, da sauri ta ajiye gishirin dake hannunta ta shiga dakin wanda yayi dai-dai da lokacin da Saliha ta janyo kwanon naman da ta boye a karkashin gado. Suka had'a ido Saliha ta diriri ce! sai ta wayance da fadin." Ke ni ba naman ki zan ci ba ina neman warin takalmi na ne." Tsaki taja ta dauke kwanon naman da fadin." Saliha ko kinfi kud'a maita wannan naman yafi karfinki wallahi domin wanda na ajiye wa ya fiki daraja a guri na." Saliha ta fusata! "Ni ce mayya." Tace." Me yasa to zaki zo kina min binkice naman nan an raba an baki naki kin cinye, sai kuma ki dinga bibiyar nawa." Tace." Don Uwarki sharri zakayi min naman banza naman wof.......! Shigowar Baban ya katse maganar tace." Menene wai ? tun daga soro nake jin hayaniyarku." Cikin yanayin maganar ta tace." Nama na zata satar min shine don na ganta take borin kunya." Cike da mamaki tace." A ina ki ka samu nama ke kuma."? Tace." Wanda ki ka bani ne na boye abina." Tace." Meye amfanin boye wa sai ya lalace yanzu lokacin zafi ne gwara ki fito dashi ki cinye ni bana san neman fitina." Kai tsaye tace ." Baban-Baba na ajiye wa." Gabadaya suka zuba mata ido. Baban ta sake maimaita maganar." Ki kace Baban-Baba ki ka ajiye wa ."? Ta gyada kai alamun "E." Ba ta iya cewa komai ba kawai ta kama hanya ta fita daga dakin da tunanin wani abu a ranta, lallai dole ne idan Kawu Musu yazo ta sheda masa abinda ke faruwa domin ta fara zargin wani a cikin ranta. *ABUJA* Tun daga bakin Estate din zaka gane lallai mazauna gurin manya mutane ne, gida hudu ne kacal sai tarin sucurites wanda suke kai kawo a gurin, can gefe kuma wasu lafiyayyun karnunaka ne biyu a kwance da alama suna rama bashin baccin da suka ci. Gida daya a cikin hud'un yafi tsaruwa da burgewa yanayin ginin zai baka sha'awa sosai babu shirman kyale-kyale irin na almubazzaranci. Daga saman babban gate din da ya katange gidan anyi ado da suna Annabi Muhammad SAW da gold an rufe da wani irin glass mai mutukar daukar ido daga ciki wasu irin fitilu ne da suke bada haske kala-kala sai dare abin yake sake k'ayatuwa da jan hankali. Ginin tsakiya ne wanda yake dauke da bangare uku sai filin ball dake can gefe da parking spece a in da yake dace, sai kuma gurin hutawa wanda akayi masa ado da wasu irin kujeru masu kyau da daukar hankali. Suna tsaye sanye da bakaken kaya a bakin kofar suna dakwan fitowarsa, Adamu ne da Sule Escort dinshi. Yana zaune a gabanta kafafunshi a tankwashe kamar karamin yaro da alama Umarninta yake jira." Hajiya Saude ce kakarsa wacce ta haifi mahaifinsa ita kadai ce ta rage masa a duniya ita kuma yake gani yayi farin ciki duk mai son yaga walwalarsa ya mutunta ta, mai san ganin dariyarsa ya daraja ta. "Hajiya lokaci na tafiya." Ya fada yana duba tsadaddan agogon dake daure a hannunsa. Ta kalleshi tana ya tsine fuska kafin tace." Habu." ita kadai ce take kiransa da wannan suna *HABU* tun yana yaro, Asalin sunansa Abubakar-Assadiq mahaifinsa ne kadai ke kiransa da Assadiq sai kuma abokan karatunsa, amma da yawa daga cikin 'yan uwan mamansa kuwa suna kiransa da *DAN GASKE* wanda mahaifiyarsa ta sanya masa dalilin yaci sunan mahaifinta da kuma alkunya irin ta dan fari, wannan dalilin yasa 'yan uwanta suka boye sunan domin daraja sunan mahaifinsu, sunansa ya 'bace gabadaya a famliy idan zaka kwana kana kiran ainihin sunansa babu wanda zai gane wanda kake nufi mutukar baka kira *DAN GASKE!* ba. Ta cigaba da cewa." Na ce wai kai ina zaka kai kudi ne? kullum baka gajiya, kai ne can kai ne nan, a duniyar nan babu 'kasar da baka taka ba, wannan kudi dai haka zaka tafi ka bar su, ka naji kana gani Shukura ta zama magajiya tun da ita kadai ka ajiye gemai-gemai da kai da gemu da furfura kana zaune babu aure." Sai ta fashe da kukan bakin ciki ta cigaba da cewa." Ya jama'a ba zasu zarge ka ba, Habu nima na fara zarginka kana neman matan banza a waje." Ya sunkuyar da kansa yana sauraran kukanta dake mutukar tafarfasa masa zuciya! zubar hawayenta yana nufin abubuwa da yawa a tare dashi, dole ya rarrasheta domin duk irin bayanin da zai mata ba zata yarda ba bahaushe yace (mai daki shi ya san in da yake masa yoyo) duk ta san gwagwarmayar da ya sha a baya, ya tabbatar da cewar ba za tayi masa uzuri ba tunda kullum fadi take ai matan ba duka suka taru su ka zama daya ba." "Ki kwantar da hankalinki Insha Allahu zanyi aure very soon." Hanci taja kamar wata karamar yarinya murya na rawa tace." Alhaji Habu ni nafiso ka dawo da Fatima Uwar Shukura domin matar fari itace rufin asiri." Lokaci guda fuskarsa ta sauya! idonsa yayi jah! kansa ya girgiza da fadin." Hajia kada ki sake min maganar Fatimah idan kina so mu shirya.'' Ta kalle shi ganin yanda kwayar idonsa ta sauya yasa taji tsoro kada ciwonsa ya tashi dama can Fatiman ce *SILA* tace." To yanzu ka samu wacce zaka aura din kuma 'yar wane gari ce? domin wannan karon ba na so ka fita daga Najeria kaje wata kasa neman aure." A cunkushe yace." Ina dubawa tukkuna tunda nace miki na kusa aure to kisa al'amarin a cikin ranki kuma ki taya ni da addua." A sanyaye tace ." Allah ya tabbatar da alkairi.'' Ya amsa da "Ameen hankalinsa na kan agogon dake daure a hannunsa. Tsaye ya mike wanda yayi dai-dai fa fitowar Shukura daga dakinta. "Daddy yau fa duka kwananmu biyar da dawowa ba zaka zauna ka huta a gida ba." Hannunta ya ri'ke da fadin.'' Daughter ku kwantar da Hankalinku ba nisa zanyi ba KANO na nufa insha Allah zan duba ma'aikatu na (company's) domin ganin abinda yake gudana." Ita da Hajiyan suka sauke ajiyar zuciya domin duk a tunaninsu sun d'auka zai bar 'kasar ne kamar yanda ya saba tafiye-tafiye. *LITTAFIN NA KUDI NE #500 SPECIAL 1K 0542382124....BINTA UMAR GTBANK, IDAN KATI ZAKI TURO #600 KIYI MIN MAGANA TA WHATSAPP DA WANNAN NUMBER 07084653262.....MUTANAN NIJAR DALA DARI SPECIAL JAKKA DAYA KATIN AIRTAL KO MOV* [9/7, 10:41] bintaumarabbale: _MAJNUN!_ *'BOYAYYAN -ATTAJIRI* _NA_ *_BINTA UMAR ABBALE🍒_* _MANAZARTA WRITES ASSO_ _________ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ *23&24* Cikin nutsuwa yake musabaha da jama'a bayan idar da sallar asubahi a massalacin dake jikin gidanshi wanda ke unguwar giginyu, ya fito daga massalacin da cazbaha a hannunsa yana sanye da farar jallabiya mai karamin hannu kanshi sanye da hula mai raga-raga irin ta larabawa kamar ko da yaushe ya nad'e kansa da farin rawani. Can tsallake ya hangi wasu matasan samari a tsaye, jikinsa ya bashi cewar shi suke jira ya fito daga massalacin, aikuwa dai gabanshi suka zube suna gaishe shi, ya saki fuskarsa tare da basu umarnin tashi. Bayan sun gaisa sai kuma su kayi shuru suna sunkuyar da kai dukkaninsu da alamun magana a bakinsu. Gyaran murya yayi cikin kamala da dattako yace." Ko meye yake tafe daku kada kuyi shakkar fada min ina sauraranku." Na farkon yace." Alhaji Taimako nake nema a gurin ka, kayi min suttura kamar yanda Allah yayi maka, tabbas nazo gurin da za'a share min hawaye na." Da rawar murya yake maganar. Ya dafa kafadarsa da fadin." Menene bukatarka? fadi kanka tsaye." Yaji kwarin gwiwa a tare dashi yace." Mata ta ce ta haihu yau kwana bakwai kenan bani da abin hakika da goro da Alawa hankali na ya tashi sosai Alhaji domin maula ba hali na bane, kawai don bani da yanda zanyi ne kasancewar gwamnati ta yanke min albashi na, babu laifin tsaye bare na zaune wannan dalilin yasa wahala tayi min yawa yara na biyar gashi karamin ma'aikaci ne albashin duka dubu talatin da biyar nake dauka amma yanzu tsayin wata shida kenan da gwamnati ta zabge rabin albashin ya koma dubu goma sha bakwai, to wannan dalilin yasa duk wani karamin ma'aikaci yake cikin tashin hankali." Ya dinga girgiza kansa yana jin wani irin zafi a zuciyarsa. ido ya tsurawa mutumin yana tunanin wani al'amari daya faru a cikin shekarun da suka gabata lokacin ma da duniya take kwance kenan Malam me za'ayi da mulkin Najeria. Numfashi ya sauke kafin yace." Kada ka damu komai yana da sanadi kuma kowane bawa akwai hanyar abincinsa saboda haka ni zan taimaka maka daidai gwargwado Allah ya rufa mana asiri." Gabadaya suka amsa da "Ameen." Ya kallesu kafin yace."Abokansa ne ko kuma tafiyar kowa daban."? Hada baki sukayi gurin bashi amsa da cewa." Abokansa ne." Sai yayi murmushi wanda yake fitar da zahirin kyawunsa ya umarce su da su bi bayanshi zuwa gida. Dubu dari cash ya bashi da fadin." Ya je yayi hidimar haihuwa, ya kuma yi masa addua sosai. Shi da abokansa suka rasa bakin godiya. To ganin gari ya soma haske yasa a gaggauce ya shige cikin gidan ya bar su a bakin gate tare da masu gadi sai godiya suke na irin alkairin da akayi musu. **** Yau haka kawai ta tashi da kwadayin cin wainar gero, kuma mai soya wainar a can bakin titin Jakara take. Ta fito tsakar gidan ta same su, a zaune suna karyawa da kunu da kosai jawur dashi, sam bai bata sha'awa ba, wainar geron dai take kulafuci. Ta kalleta da fadin." Baba bani dari zan siyi waina yau kwadayinta nake ji." Ba tace komai ba ta zuge zif din lalitar dake daure a jikinta ta dauko 'yan hamsin biyu ta mika mata. Kar'ba tayi da sauri tasa hijab d'inta ta fita tana adduar Allah yasa ta samu kada taje ta tarar ta 'kare tunda yanzun tara ta wuce ana zancan goma. Wani mugun farin ciki ne ya ziyarce ta sakamakon tozali da tayi dashi a kwance a k'asan mota akan wani tattararan buhu wanda yayi datti da kasa da kazanta har da kashin awakai." Mantawa tayi da abunda ta fito siya, ta tsallaka titin kai tsaye gurinsa ta durfafa fuskarta cike da annuri. Yana daga kwancen ya hangota sai yayi saurin rufe idonsa kamar mai bacci. Tana isa idonta ne ya sauka kan kafafunsa, gabanta ya fadi! ta tsurawa kafafun ido tana mamakin abinda ta gani. wata lafiyayyar kafa ce kamar bata taka k'asa, jikinta yayi sanyi lokacin da take kallon fuskarsa da hannuwansa kamar sansanin kanikawa saboda tsabar baki da maik'o sai ka rantse da Allah cewa kafafun ba'a jikinsa suke ba. Tsoro yasa ta dan ja baya amma ba ta daina kallonsa ba, kuma ba tayi masa magana ba. Ya bude idonsa tare da kokarin tashi zaune, fuskarsa a murtuke yake kallonta. Bakinta na rawa ta kirayi sunansa. Uffan bai ce mata ya dauki wata tsohuwar buta dake kasan motar yasa bakin kazantacciyar butar da ko arzikin murfi babu a bakinsa ya gumtsi ruwan ciki ya fesar dashi har sai da ya same ta a kafafu. Ya sake kafa bakinsa a bakin butar yana kokarin shan ruwan dake ciki. Cikin rauni da tausayi tace." Kada kasha wannan ruwan bashi da kyau zai maka illah.'' Ko kallonta bai yi ba ya kafa baki ya sha ya ajiye butar a gurin da take. Tsigar jikinta gabadaya ta tashi, sam bata san kallon butar saboda yanda zuciyarta take tashi. Komawa yayi ya kwanta ya rufe idonsa yana takure jikinsa, taji wasu zafafan hawaye suna kokarin kwace mata, wallahi da tana da yanda za tayi akansa da tuni tayi ta samar masa nutsuwa da makwanci mai kyau. Can gurin mai siyar da wainar geron ta nufa. A ka ci sa'a wainar bata k'are ba. to koda ta siyi wainar a maimakon ta nufi gida kai tsaye gurinsa ta koma domin ba ta tsammanin za ta iya sanya wani abu a cikinta mutukar ba tabbatar da cewa shi din yaci wani abu ba. daf dashi ta tsuguna da ledar wainar a hannunta, cikin yanayin tsoro ta kirayi sunansa, ya bude ido yana kallonta, tace." Ga waina za ka ci ko.? ya bi hannunta da kallo lokacin da take mi'ka masa ledar wainar. Ta fara kokarin kwance ledar tana fadin." Ga ta nan da zafi kaci bari na je gida na kawo maka kunu ka had'a." Kallonta kawai yake bai sa hannu ya kar'bi wainar ba. Ta marairaice fuska kamar za tayi kuka tace." Don Allah ka ci wallahi tausayi kake ba ni.'' Tsigar jikinsa ce ta tashi jin abinda tace. Ya tsira mata idanuwansa yana jin wani irin tausayinta, ya lura da yarinyar ta na sonshi sosai kuma duk abinda ta fad'a gaskiya ne. Hannu yasa ya karbi wainar a takaice yace." Na gode." A hankali yayi maganar shi yasa ba ji ba, amma ta fahimci godiya yake mata. Ta mi'ke da fadin." Bari na je na dawo." Bai ce mata komai ba, ta tsallaka titin ya bita da kallo yana ayyana abubuwa da yawa a kanta. Cikin farin ciki ta shiga gidan, lokacin har sun fara aikace-akaice abincin siyarwa Baban tana yanka kabewa ita kuma Saliha na gyara alayyahu. Da farin ciki a tare da ita tace." Baba akwai kunun ko."? Tace." Eh saura naki a kadai gashi can a jug." Tace." Baba yau dai na ga Baban -Baba a bakin titi wallahi dadi ya rufe ni.' Ta harareta da fadin." Matsalarki ce wannan Shahida ni abinda nakeso ki zo ki daka min gyadar miya domin yanzu zan hura wuta na dora miya." Tace." Shikkenan yanzu zan zo nayi." Ba ta sake magana ba, kawai sai gani su kayi ta shiga daki minti biyu ta fito da kwano a hannunta, ta dauki jug din kunun ta kama hanya ta fita. Saliha tace." Wallahi Baba idan ta dawo da kwanukan kada kiyi amfani dasu domin ba kowa za ta kai wa sai wannan mahaukacin.' Tace." Saliha ya zanyi da Shahida, na yi magana cibi ya zama 'kari, na zuba mata ido kawai amma ya zama dole idan mahaifinki yazo mu tattauna dashi domin ina wani tunani a kan yarinyar." Tana 'yar dariya tace." Wallahi lafiyarta lau tsabar iskanci ne wai ita mai tausayi watarana sai taje ya buga mata dutse idan haukan nasa ya motsa." Ta girgiza kai da fadin." Allah ya rufa asiri. "Wannan naman sallah ne na kawo maka, wannan kuma kunu ne in sha Allahu da rana ma zan kawo maka abinci." Ya kalleta kafin ya kalli abubuwan da ke gabansa, hannu yasa ya bude kwanon naman babu abinda yayi suyar tayi kyau sosai sai kamshi yake. Rufe wa yayi kafin ya bude jug din kunun shima da zafinsa sai kamshin lemon tsami yake, sosai kunun ya bashi sha'awa, amma bai nuna a fuskarsa ba. Sunkuyar da kansa yayi ba tare da yace mata komai ba. A sanyaye tace." Sannu ko baka da lafiya ne?" Ya daga mata kai alamun ."Eh." gabadaya jikinta ya mutu kamar za tayi kuka tace." Zazzabi ko ciwon kai.? Ganin tana shirin fashewa da kuka yasa ya sassauta fuskarsa yace." Babu ko daya jikina ne yake ciwo." Ta sauke ajiyar zuciya da fadin." Sannu Allah ya sawwake amma ka daina kwanciya cikin lema dubi abin shimfidar ka a jike ga 'kazanta da kashin awakai dole lalura ta kama ka." Shuru yayi bai ce komai ba. Tace." Ka sha kunun sai na tafi na siyo maka magan........Ya buga mata tsawa a burkice yace."Ke! tashi ki bani guri bana so." Ta tsorota ta mi'ke tsaye tana kallonsa, gabad'aya idanunsa sun jirkice! ya dauki robar ruwan paro ya jefa mata, wanda ya janyo hankalin yara gurin. Aikuwa suka fara ihu! "Baban-baba mahaukaci! Baban Baba mai annakiya." wasu suka fara tsintar duwatsu suna jifansa tare da tofa masa yawu, sai su ruga a guje suna dariya. 'Karkashin motar ya shige ya takure jikinsa guri daya yana makyarkyata! Ita kuwa zuciyarta a 'kuntacce ta bar gurin wani k'atoton abu ya tokare mata a wuya tana shiga gidan kai tsaye daki ta nufa ta kwanta saman gado tare da fashewa da wani irin kuka! Kuka taci ta koshi ta fito idanunta jawur! babu wanda ya tambaye ta abinda ya sa ta kuka aikin gabansu kawai suke, murya a dashe tace."Baba ina gyadar take.? Da hannu ta nuna mata. ta cigaba da aikin gabanta zuciyarta cike da kunci da takaicin halin da yarinyar take 'kokarin jefa kanta. **** "Wai ana sallama da maigidan." muryar wani yaro kenan, yayin da aka aiko shi yayi sallama da Hujaj. Jamila ce ta fito da fadin." Ba ya nan.'' yaron ya juya ya fita, minti biyu ya dawo da fadin." Wai idan ya dawo a fada masa cewa Saminu abbatuwa yana nemansa." Tace." To za'a fada masa. Da ya dawo gidan Talatu ta sheda masa cewa wani yazo nemansa mai suna Saminu Abbatuwa, ko gezau bai yi ba ballanatana ya razana, cin bashi dai ba akansa aka fara ba, kuma sai yana dashi zai bayar. Hankalinsa a kwance ya cire babbar rigar jikinsa ya rataye, ya kashingida yana tunanin yanda za'ayi kudi su shigo masa, kwana biyu kamar wanda a kayi wa baki gurin sana'ar tasu haka yake dawowa babu ko sisi a aljihunsa, hakan kuma baya ha nashi gobe ya koma da wani abun nashi domin samun nasara da nin ka abinda ya bayar. *LITTAFIN NA KUDI NE #500 SPECIAL 1K 0542382124....BINTA UMAR GTBANK, IDAN KATI ZAKI TURO #600 KIYI MIN MAGANA TA WHATSAPP DA WANNAN NUMBER 07084653262.....MUTANAN NIJAR DALA DARI SPECIAL JAKKA DAYA KATIN AIRTAL KO MOV* [9/7, 10:42] bintaumarabbale: _MAJNUN!_ *'BOYAYYAN -ATTAJIRI* _NA_ *_BINTA UMAR ABBALE🍒_* _MANAZARTA WRITES ASSO_ _________ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ *25&26* Bacci ne ya fara fizgarsa kamar a mafarki yaji muryata a kunnansa, ya bude ido yana kallonta tana tsaye 'kerere a kansa. cikin 'bacin rai yace." Wai ke Talatu yaushe zakiyi hankali ne.? tabe baki tayi ta nannago 'bakar magana ta ya'ba masa domin har yanzu da ragowar haushi da takaicin abinda yayi musu, haka kawai ya kwashe nama ya bayar, sun tashi a tutar babu. Babu ladabi a maganarta tace." sai ranar da akayi hankali nima zanyi." Ya tsira mata ido yana kallo. Tace." Tun shekaran jiya wannan mutumin yake zuwa sallama da akai, ya ishi mutane nace yau dai tunda kana gidan sai ka tashi kaje domin kaji abunda yake tafe dashi." Yana kokarin tashi zaune yace."Ki aika Jamila ta fada masa cewa bana nan." "Wane irin na aika Jamila bayan na sheda masa cewa kana nan, shin ko dai baka da gaskiya ne."? Yana kokarin magana su kaji wani yaro ya shigo yana fadin." Wai Saminu Abbatuwa yana tsaye fa yana jiran Maigidan a waje." Hadiza dake zaune a tsakar gidan tace." Dallah kaje kace gashinan zuwa." Yaron ya fita yana k'unk'uni. Talatu ta kalleshi taga duk ya had'a zufah! sai muzurai yake, tace." Da alama dai wannan mutumin kudi yake bin ka." Ya kalleta da fadin." Talatu wannan mutumin kudi yake bina kimanin dubu dari uku da hamsin gashi bani dasu a yanzu wannan ne dalilin da ya sanya nake shakkar fita gurinsa. Tace." Kai har mai ka siya da wannan kudin? Jamilu ka girma baka san ka girma ba har yanzu ba zaka daina d'aukowa kanka bala'i ba, kana da surukai a cikin unguwa masu bukatar auran 'Ya'yanka ko kunyar hakan ba ka ji." Yace." Kin ga kada kiyi min maganar banza fita ki bani guri." Ta buge zaninta da fadin." Ko ba kace na fita ba ai zan fita dama, Allah dai ya shirye ka." Ta kama hanya ta fita daga dakin tana surutai. Jallabiya yasa ya fita. Wani shirgegen katon mutum ne tsaye a jikin bango fuskarsa sai mai 'ko take, gashi da wasu irin ido mitsi-mitsi duk kwantsa a ciki, Saminu Abbatuwa ne. Ya mika masa hannu da fadin." Barka da yamma Saminu kwana biyu kana ta zuwa baka samu na wallahi na d'an yi wata 'yar tafiya ne yau din nan na dawo." Ba tare da ya rike hannun da ya mika masa ba yace." Alhaji Jamilu ka bani mamaki wallahi ban ta'ba tunanin haka halinka yake ba." Ya sosa kai yana 'yar dariya da fadin ." Haba Saminu ai ka bari mu gaisa tukkuna kaji Uzuri na, ni ba 'karamin mutum bane da zan dinga wasa da hankalinka." Ya d'aga masa hannu da fadin." Babu wani Uzuri naka da zan duba domin ba haka mu kayi da kai ba, ni mutum ne mai girmama al'kawari shiyasa bana mu'amula da wanda bai san muhimmancinsa ba, ban d'auka za kayi min haka ba wallahi, kazo neman alfarma a gurina nayi maka duk da cewa a lokacin akwai wa'inda suka zo da kudi a hannunsa domin na siyar musu na'ki na ajiye maka alhalin baka bani ko kwabo ba, na rufa maka asiri, shine ni zaka tona min nawa asirin." Ya k'arasa maganar yana numfarfashi tare da taruwar wata kumfa a gefan bakinsa. 'Yar dariya yayi irin wacce ya saba yace." Allah ya huci zuciyarka! na san dole wannan al'amarin ya 'bata maka rai amma kasa ranka a inuwa insha Allah yau da daddare zanzo har gida na kawo maka kudinka ni kaina nafiso muyi rabuwar arziki saboda haka ka samu nutsuwa kuma kada ka yarda da jita-jita mutane a kaina, ni mutum ne mai cika alkawari, matsala aka samu wallahi nima hakan bai min dadi ba. Ya sauke ajiyar zuciya yana dan jin sassauci a zuciyarsa, amma dai duk haka babu fara'a a tare dashi yace." Jama'a da yawa sun yi min magana mara kyau a kanka, amma a yanzu a karo na biyu zan kara yarda da kalamanka, mutukar baka cika alkawari ba to duk abinda ya biyo baya kada kayi kuka da kowa kai ka janyo, don haka yau da daddare ina jiran zuwanka." Ya dafa kafad'arsa da fadin." Kada ka damu mutumina zamu rabu lafiya da ikon Allah." Ba tare da yace masa komai ba ya kama hanya yana tafiya tinkis-tinkis naman jikinsa yana rawa ya bishi da kallo yana hango yanda kansa yake zuba k'yalli digon gashi babu kan sumul sai uban kyalli yake. Sai da ya 'bace da ganinsa sannan ya sauke zazzafar ajiyar zuciya ya shiga gidan yana tunanin hanyar da zai bi domin ganin ya samu kudin da zai biya mutumin hakkinsa. **** Tana so tayi magana amma tana gudun abunda zai biyo baya, da yammacin ranar Kawu Musa wato mahaifin Saliha yazo gidan ya ci mata mutumuci har dasu zagin mahaifinta, duka ne kawai bai yi ba, saboda kawai tana taimakawa Baban-baba, shine suke kiranta da mahaukaciya. Ta goge wasu hawaye masu zafi da suka gangaro a saman fuskarta. Wai shin meye laifinta anan? don ta taimaka masa, a ganinta shi din abin a tausaya masa ne, to wai mahaukaci ba mutum bane? ita fa har yanzu ba ta dauke shi a wannan matsayin ba, har yanzu kallon mai hankali take masa. A sanyaye ta kira sunanta." Baba." ta juyo da muburgin kad'a miya a hannunta, yau towo tayi sha'awa shine ta tu'ka musu na masara." "Don Allah kada ki biye maganar Kawu Musa Allah ne kad'ai ya san irin ladan da kike samu gurin ciyar da wannan bawan Allah ki daure ki cigaba da bashi abinci." Saliha ta dinga zabga mata harara can kasa tace." Banza mahaukaciya kawai k'arshen so ki aure shi kawai zaki dinga damun mutane." Ita kuwa Baban jikinta ne yayi sanyi tace." Shahida ba wai bana so bane. Aa ni bana son kina zuwa gurinsa duniyar nan babu yarda har yanzu mutumin nan bai kwanta min a raina ba wallahi." Tace." Ni kuma wallahi bana mugun tunani a kansa, domin nayi imani da cewa babu wani abu da zai min wanda zai yi tasiri tunda ni alkairi nai masa, to bana tsammanin sharrinsa zai yi tasiri a kaina." Ta gyada kai da fadin." Ai shikkenan Allah ya sawwake." Shuru tayi bata amsa ba ita kuwa Saliha sai maganganu 'kasa-'kasa ta keyi, ba tayi da 'karfi ba wanda ta san idan taji to ba zasu kwashe lafiya ba. Ta kalleta da fadin." Ki dauko kwanon da aka ware masa na zuba masa abincin." Da sauri tace." To.'' ta tashi tana jin dadin yanda Baban ta fahimci ta. Baba Asabe wani lokacin tana da tausayi sai dai wani sa'in Kawu Musa yana sauya mata ra'ayi domin shi din wani irin mutum ne mara kan gado. Ta zuba masa towon da yawa da miyar 'kubewa kafin ta kawo miyar tattasai da nama mai yawa ta zuba masa har da manshanu. Shahida dadi ya lullu'beta ta je ta sanyo hijabi ta fito da azama ta dauki abincin za ta fita, Baban ta kalleta da fadin." Anya Shahid ba za'a samu almajiri ya kai masa ba. Ta girgiza kai da fadin." Yanzu zan kai masa na dawo idan almajiri ne zai iya zama a wani gurin ya cinye ya dawo yace ya kai masa. Tana gama maganarta da gaggawa ta fita domin ba ta son Baban ta sake wata maganar. **** Saminu Abbatuwa yayi ta tsumayin zuwan Hujaj kamar yanda yayi masa alkawari, shuru malam yaji shirwa, bangaran Hujaj din kuma yana can suna bugawa, har yanzu nasarar bata fad'o kansa ba, ya cire tsadaddan agogon dake daure a hannunsa ya ajiye aka cigaba da fafatawa, cikin hukuncin Allah abokin karawarsa ya ci agogon, gumi mai zafi ya dinga karyo masa, babu abunda yai saura a jikinsa sai riga da malin-malin, sai kuma takalmin kafarsa, dan tun a karon farko ya cire hular kansa ta kimanin dubu ashirin da biyar ya ajiye aka cinye. Bai saduda ba, zai sanya tsadaddiyar wagambarin dake jikinsa wacce taji ubar aiki, shaddar wankin ta d'aya a kiyasi da shaddar da dinki sun tasar wa dubu arba'in! Ya kalli alkalai da fadin." Wasan yanzu muka fara na sanya wannan kayan na jiki na, saboda haka muje zuwa. Ba tare da 'bata lokaci ba suka cigaba da bugawa. *Tofa wannan sana'a dai ta marasa tunani ce😳* *LITTAFIN NA KUDI NE #500 SPECIAL 1K 0542382124....BINTA UMAR GTBANK, IDAN KATI ZAKI TURO #600 KIYI MIN MAGANA TA WHATSAPP DA WANNAN NUMBER 07084653262.....MUTANAN NIJAR DALA DARI SPECIAL JAKKA DAYA KATIN AIRTAL KO MOV* [9/7, 10:42] bintaumarabbale: _MAJNUN!_ *'BOYAYYAN -ATTAJIRI* _NA_ *_BINTA UMAR ABBALE🍒_* _MANAZARTA WRITES ASSO_ _________ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ *27&28* Hakika duk wanda ya siyi rariya ya san za ta zubda ruwa, zahiri kuma wanda ya hau motar kwadayi to babu shakka za ta sauke shi a tashar dana sani, Hujaj cikin rashin kima da rashin arziki ya nufi gidanshi, da gashi sai singlet da gajeran wando domin ko da sanya tufafin jikinsa don ganin kamar zai samu nasara, sai gashi cikin hukuncin Allah an kwamushe shi, bashi ga tsuntsu bashi ga tarko haka ya nufi gidansa cikin rashin kuzari da rashin kwarin gwiwa, in da Allah ya rufa masa asiri ma dare ya tsala babu wanda ya ga ne shi a hanya sai da ya zo shiga gidan ne sukayi arangama makocinsa mai suna Malam Habu yana nannade tabarma zai shiga gidansa, da sauri Hujaj din yayi nufin shiga gidan, ya ji Malam Habu din yana magana amma saboda kunya bai saurare shi ba, yayi saurin banko kofar gidan ya sa sakata ya kulle kana ya ja tsaki da fadin munafiki kawai. Malam Habu ya girgiza kai ransa a 'bace da irin zubda mutuncin da makocin nasa keyi a gari, ko shakka ba ya yi daga can gurin sana'ar tasa ne aka wulakanta shi irin wannan, in banda zubda mutumci da son duniya mai za'ayi da sanar cha-cha! jahili shine ya dauke ta sana'a har yake fankama da ita, gidansa ya shiga da tunanin yanda zai tunkari makocin nasa da maganar zuwan Saminu Abbatuwa sannan kuma dole ne ya nuna masa kuskuran abinda ya ke aikatawa wannan shine zaman amana a tsakaninsu. Fitowar ta kenan daga daki da buta a hannunta za ta shiga bandaki ya shigo gidan kamar wani 'barawo sai sand'a yake, shi kansa kunyar kansa yake tunda ya fara sanar ca-ca! bai ta'ba wulakanta irin yau ba. Ta kalleshi da mamaki a tare da ita ta ce." Mai zan gani ni Talatu."? Bai saurare ta ba ya nufi dakinsa da saurin gaske, ba ya so tayi kwakwazo har 'ya'yansa su tashi a bacci su san abinda yake faruwa. Ta ja mutsiyacin tsaki da fadin." Allah ya shirye ka Jamilu wallahi na yi nadamar auranka." ranta a 'ba ce ta shiga bandakin tana tur! da halin mijin nata. Wa she gari ya tashi zuciyarsa a 'kuntacce fargabarsa kada Saminu ya zo ya ritsa shi a gidan sai sauri yake fita. "Wai ana sallama da mai gidan." Wani ne yaro ne yake magana a gidan. Gabansa ya fad'i! wai shin ya zai yi da wannan mutumin ne? Luf yayi a dakin bai ce komai ba yana jin lokacin da Talatu ke fadin." Ka ce gashi nan zuwa." Ya nemi gefan gado ya zauna yana tunanin k'aryar da zai girbawa mutumin. Ta shigo babu sallama ballanatana gaisuwa, ta ce." Ka ji ana sallama da kai a waje ko.''? Ya kalle da dan firgici a tare da shi ya ce." Na ji zan fita na same shi." Ta ja dogon tsaki ta fita tana surutai, gabadaya Talatu ta raina shi, bashi da wata 'kima a idonta. Kayan sa ya sanya ya fita yana cin kunu! sai dai yanayin yanda ya sami Saminun ya firgitashi, mutumin bai ta'ba bashi tsoro ba irin yau ba! amma sai ya jajurce yayi ta ma za! hannu ya mika masa da fadin." Malam Saminu barka da asubah." Ba tare da ya amsa ba ya ce." Hujaj haka mu kayi da kai ."? Yayi shuru bai ce masa komai ba. Ya girgiza kansa yana hura katoton hancinsa ya ce." Lallai yau zan nuna maka asalin waye ni."! Cike da burga da rashin gaskiya ya daga masa hannu da fadin." Ka ga Saminu ba fa za ka zo har k'ofar gidana ka fada min bakar magana ba, mai akayi akai dubu dari uku da hamsin da har za ka ishe ni da sallama wallahi na fi karfin haka." Ya fusata! yana numfarfashi! fuskarsa na maiko ido cike da kwantsa ya ce." Kai har kana da bakin wata magana anan gurin wallahi i dan ba kayi wasa ba zan dau'ke ka na damfara ka da 'kasa! ni ba'a rai na min hankali." Jin abinda ya ce yasa ya d'an tsorata amma bai nuna masa a zahiri ba, ya ce.'' Na so mu fahimci jun.......Ya katse shi da fadin." Jiya na zo da daddare ban same ka sai na barwa makocinka sallahu saboda haka bani da lokacin sauraran maganarka a yanzu." Wayarsa ya fito da ita "Eh gani a kofar gidansa ku 'karaso." Ya kashe wayar ya mayar da ita aljihu! Malam Habu ya fito da shirin tafiya kasuwa ya ga abinda ke shirin faruwa 'Yan sanda sun zagaye Hujaj daya na kokarin daura masa ankwa a hannu. "Subahanallahi." Wannan kalmar ya furta yana kallonsa, kafin ya ce." Haba Saminu har an kai ga haka kuma? kayi hakuri ku fahimci juna mana.'' Ya ce." Malam Habu na dawo daga rakiyar wannan mara mutuncin bashi da gaskiya mugun makaryaci ne, saboda haka hukuma zata raba ni dashi." Hujaj ransa idan yayi dubu ya 'baci sai gumi yake ya gaza furta komai bai ta'ba tsammanin mutumin zai masa haka ba. Ya kalli yanda jama'a suka fara taruwa a gurin suna kallonsu abinda ya tsana kenan zubewar mutumci mutane na kallonsa da kima da mutunci amma Saminu ya ci masa mutunci a gari. Hayaniya tasa Jamila fitowa kofar gidan, can ta hange su sun tasa k'eyarsa domin tafiya ofis dashi, da sauri ta koma gidan tana shedawa Talatu abinda ke faruwa, ko a jikinta ta cigaba da sabgoginta a fili ta ce.'' Shi ya janyo wa kansa cin mutumci saboda haka babu abinda ya shafe ni shi ya siya." Yaran suka zauna jugum!-jugum! duk lalacewar sa, ba za su canza shi a matsayi a ubansu ba. Wai a kace labarin duniya ba ya 'boya har gida labari ya same ta, da yake sana'arta ta jama'a ce, duk wanda ya zauna sai ya jajanta mata wasu kuwa munafurci ne ya ke sanya su maganar. Shahida kam daki ta shiga ta ci kukanta ta koshi, ta rasa yanda za tayi da rayuwarta kunyar fitowa take saboda irin kallon da mutane ke mata dole sai sun nuna ta da tambayar Baba Asabe ita ce 'yar Hujaj wanda bai san ma shine mahaifinta ba to a ranar ya sani. *** "Ranka ya dad'e iyakar hakuri nayi kawai abinda nakeso ku sanya shi ya biya ni kudi na domin akwai hidima a tare dani." Officer ya ce." Saminu kaje kuyi sulhu a tsakaninku mu za mu shiga cikin al'amarin mutukar bai cika alkawarin da ya dauka ba, tunda dai ya ce yasa gidansa a kasuwa yana jira a bashi kudin a karshen wata to zamu zuba ido lokacin ya cika, idan ya sa'ba alkawari za mu shigar da 'kara kuto." Fuskar nan a murtuke! ya ce." Ranka ya dad'e aure nakeso nayi a wannan lokacin nima ina da uzuri gaskiyar magana kenan wannan mutumin makaryaci ne na daina yarda da maganarsa." Ya kalleshi da fadin." Saminu ni ne fa nayi alkawari cewa 'karshen wata ana bani kudin gidana zan biya ka kudin ka amma cin mutuncin da kake min ya isa haka muna gaban hukuma anyi komai a rubuce da kuma sharad'i ka kwantar da hankalinka zamu rabu lafiya insha Allahu." Ya d'an sassauta amma bai saki fuskarsa ba tana tanan kamar hadarin dake dab da zubda ruwa, ya kalli Officer din da fadin." Na amince da hakan amma ayi komai a rubuce da sanya hannuku sannan kuma a fada min ranar da zai bani kudi na domin nima na shiryawa hidimar dake gabana." Officer din ya kalleshi da fadin." Hujaj kaji bayanin Saminu yana bukatar sanin rana da kuma kwanan watan da zaka biya shi hakkinsa." Yayi jim yana nazari wannan maganar ya shata ne kawai ya fad'a amma babu wani dilalli da sukayi cinikin gida dashi kawai ya fadi hakan ne saboda ya kubtar da kansa yana kuma hasashen kafin zuwan lokacin sa'a ta fado kansa a gurin sana'ar tasu. Ya ce." ashirin da takwas ga watan uku ya kama ranar lalata kenan insha Allahu zan biya Saminu kud'insa." Officer ya rubuta ya sanya hannu, ya mika masa shima ya sa hannu. Ya kalli Saminun dake tsaye ya sa katon ciki a gaba, ya ce."Kai ma kasa hannu akan wannan yarjejeniyar ni ne sheda." Ya kar'bi zungureriyar takardar yayi jagwlgwalonsa a kai domin dai bai san me ake nufi da singing ba. Bayan kwana biyu 'kura ta d'an lafa ya nufi can abbatuwan in da Saminu ke kasuwacinsa na siyar da nama ya same shi da wata sabuwar magana. Bayan ya gama sauraransa sai ya hau shafa 'katoton cikinsa yana dan murmushi wargajejen wawulonsa ya bayyana ya ce." Eh to Hujaj ban k'i maganarka ba zan iya amincewa da manufarka mutu'kar yarinyar ta kwanta min a raina, saboda haka zan je na duba ta na gani idan ta cancanta sai mu fanshe kawai." Ya sanya dariya da fadin." Ai wannan yarinyar tawa ba ta da makusa cikakkiyar macace san kowa kin wanda ya rasa, matsalar kunne kawai ke da ita amma bata da wani nakasu." Shima yana dariyar ya ce." Ai ni babu ruwa na da matsalar rashi ji daga gare ta, idan tana da abubuwan da nake bukata daga jikin mace falillahil hamdu.'' Ya bashi hannu suka tafah! kafin ya ce." Kawai ka je ka same ta a can gidan kakarta dake bakin titin jakara 'yan gurasa ai gidan ba 'boyayye bane Baba Asabe kowa ya santa a kan sana'arta." Ya ce." Babu damuwa insha Allahu gobe da daddare zan je na duba ta yanda ya kamata." Su kayi sallama cikin barkwanci kamar ba su ta'ba samun matsala ba, Hujaj ya nufi kasuwa cike da farin cikin rabuwa da nauyin Saminu dake kansa, yana da tabbacin cewa yarinyar za tayi masa kamar yanda yake bukata, tunda duk in da ake bukatar cikakkiyar mace to ta kai gurin. *Turkashi!* *LITTAFIN NA KUDI NE #500 SPECIAL 1K 0542382124....BINTA UMAR GTBANK, IDAN KATI ZAKI TURO #600 KIYI MIN MAGANA TA WHATSAPP DA WANNAN NUMBER 07084653262.....MUTANAN NIJAR DALA DARI SPECIAL JAKKA DAYA KATIN AIRTAL KO MOV* [9/7, 10:43] bintaumarabbale: _MAJNUN!_ *'BOYAYYAN -ATTAJIRI* _NA_ *_BINTA UMAR ABBALE🍒_* _MANAZARTA WRITES ASSO_ _________ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ *29&30* Da wuri ya dawo gidan, ya umarci Jamila cewa ta shirya da sauri kada magariba tayi ta je ta kira masa Shahida maza su zo tare yana nemanta. Tunda Talatu ta ji haka ta san da wata a kasa. sai ta bishi dakin ta same shi a kishingide yana zan can zucci. Gefan sa ta zauna da fadin." Na ga ka aika a kira maka wannan yarinyar a jikina na ji ruwa baya tsami banza." Ya kalle ta na second biyu kafin ya ja tsaki da fadin." A nan ki ka fi kauri gulma da tsugudidi dube ki don Allah kamar ba mace ba, wannan tufafin na jikinki idan ban mance ba yau kwanansa hudu a jikinki." Hannu ta daga masa da fadin." Ya isa kada ka ci min mutunci, shin da kake wannan maganar ka siya min sabulun wanka ko omon wanki ne."? Shuru yayi mata banda hararar ta babu abinda yake. Tace." Da fatan dai yarinyar nan ba gidan nan za ta dawo da zama ba domin wallahi ba zan iya rike ta ba nima naji da nawa." Tsakaninta da Allah take maganar. Ya gyara zamansa da fadin." Aure zanyi mata itama ta huta da wannan cin mutuncin naki." Tabe baki tayi kafin ta ce." Au ashe ta samu mijin aure amma babu labari." Ya ce." Wannan mutumin ne da yake bina bashi zan bashi kyauta a madadin kudinsa, kin san yarinyar nakasashiya ce za'a sha wahala kafin a samu mai auranta shiyasa na yanke shawarar aura mata Saminu tunda dai shi din ma kansa d'aya da rabi ne. Farin ciki ya cika zuciyar Talatu, babban burinta a duniya a ce Shahida ta wulakanta, a maimakon ta nuna masa kuskuran abinda yake shirin aikatawa sai ta cigaba da karfafa masa gwiwa cewa hakan da yayi daidai ne, domin shi yake da iko da 'yarsa. Cikin wannan halin Shahida da Jamila su kayi sallama a gidan. Talatu ta fito daga daki tana washe baki, abin mamaki cikin sakin fuska ta amsa gaisuwarta, ita kanta Shahidan abin ya bata mamaki mutuka. Durkushe take a gabansa gabanta in banda faduwa babu abinda yake, tun kafin yayi mata magana ta karanci komai a fuskarsa, labarin gizo baya wuce na koki saura kwana uku wa'adin da ya bata ya cika, wasu zafafan hawaye suka shiga tsere a saman fuskarta. Fuska a murtuke ya daka mata tsawa! da fadin.'' Ba kuka na ce kiyi min ba Shahida ki saurare ni da kyau! kina jina ko."? ya k'arashe maganar da karfin gaske wanda har sai da su Talatu su ka ji sautin muryarsa. "Ina fatan baki mance magana ta dake ta karshe ba."? Murya na rawa da yanayin maganarta ta ce." Ban man ce ba Baba." Ya ce." Wa ki ka tsayar a matsayin wanda za ki aura."? Kai tsaye ta ce." Babu kowa." Ya jima yana kallonta kafin ya ce." To ba zaki mayar da ni mutumin banza ba, kina yawo godai-godai a gari ni ba shashashan uba bane, tunda kin kasa tsayar da mijin aure ni a matsayi na na wanda ya haife ki zan aurar dake ga wanda ya cancanta, saboda haka ki zauna cikin shiri ki kuma shedawa kakarki cewa nayi miki miji zan had'a ku tare da Hadiza na aurar daku a lokaci guda." Wani irin kuka ne ya k'wace mata murya a sarke ta ke fadin." Baba ka da kayi min haka mana kayi min adalci ka sake bani dama a karo na biyu insha Allahu zan fito da wanda na keso." Kafin ma yayi magana Talatu ta bankad'o dakin ta shigo domin duk abinda ke faruwa suna ji ita da yaranta, ta ce." Wa ne irin adalci ki ke so ayi miki ? ai ki godewa Allah tunda har ki ka samu wannan bawan Allah ya amince da cewar zai aure ki a matsayin ki na muskiniya, ki daina daukar kanki cikakkiyar mutum kamar kowa." Maganganun Talatu sunyi mata zafi sosai! a shari'ance ma sunyi tsauri da yawa, jahili ne kadai ya ke bambamce jinsin mutum wanda Allah ya hallita mai lafiya ko mara lafiya, duk wata hallita da Allah yayi akwai manufa kuma ba don baya sonka ya hallicce ka hakan ba, shi ya fi so ya gan ka a hakan ne. Da k'yar ta iya yunkurawa ta tashi. hanyar fita kawai ta nufa hannunta kunshe a bakinta kukan da take dannewa ya'ki dannuwa sai fita yake hawaye kuwa a saman fuskarta sai tsare suke. A bakin titi adaidaita sahu ya sauke ta, yanayin tashin hankalin da take ciki ya sanya ba ta lura dashi ba, yana daga can tsallaken da jarkar ruwa a hannunsa zai je ya samu ruwan alwalwa a tuka-tuka! shi ya gan ta a firgice! hankalinsa kuma ya tashi ainun! ganin yanda take kuka! ya bi ta da kallo lokacin da take karya kwanar layin gidansu, sai da ta k'urewa ganinsa sa'an nan ya tsallaka titin cikin damuwa ya nufi in da tuka-tukar take yana tunanin abinda ya ke damunta. Cikin matsanancin tashin hankali da damuwa ta shiga gidan, kai tsaye rugume kakar tayi tana rera wani irin kuka mai tsuma zuciya! duk da ta kasance nakasashiya ba zata so ayi mata irin wannan auran ba, gabadaya al'amarin bai kwanta mata a rai ba wannan shine dalilin da yake sanya ta zubda hawaye. Baba Asabe ta rike ta suka shiga daki a tare, ita kuwa Saliha ko a jikinta ta'be bakinta ma tayi ta cigaba da aikin gabanta. Da kyar Baban ta rarrasheta ta dora da fadin." Dama tun da naga wannan kiran na gaggawa na san akwai abinda zai faru, Jamilu ba shi da kirki ko kadan kiyi shuru ki fada min abunda sukayi miki." Tasa hannu ta goge hawayen dake gudana a saman fuskarta, ido jawur! ta kalle ta da fadin." Wai aure zai yi min ." Baban ta zuba mata ido cike da mamakin maganar "Aure kamar yaya ."? ta sake tambayarta domin jin cikakken bayani. Murya na rawa da yanayin maganarta ta fara sheda mata hukuncin da baban nata ya yanke a kanta cewa lallai zai had'a ta aure da wanda yayi ra'ayi. Baba Asabe tayi tsalle ta dire! ta fara surfa bala'i ta in da take shiga ba ta nan take fita ba, ta ce." Wato yanzu ne zai nuna iko a kanki saboda bashi da kunya an gama yi masa wahala kin girma kin zama mutum shine zai shigo da wannan maganar to wallahi bai isa ba mutukar ina raye ba za'ayi wannan auran ba." Kawu Musa ya shigo gidan ya riski maganar ya zauna Baban tana sake jadadda masa cewa Jamilu bai isa ba yayi kadan sai dai duk in da za su shiga su shiga amma ba zata bari ba. Ya ce." Baba musulunci ne ya bada damar hakan, ai budurwa ce mahaifinta na da ikon za'ba mata mijin aure bazawara ce kadai ke da 'yancin za'bar mijin da take ra'ayi, saboda haka babu ruwanki, ki cire kanki daga wannan maganar." Ta ce." Ka san Allah ba zan lamunta ba, domin dai yarinyar nan ba ta da cikakkiyar lafiya to ba zan bari garin san zuciyarsa ya aura mata bara gurbi ba, a jikina nake jin akwai dalilinsa na aikata wannan abu." Ya ce." To shikkenan yanzu abinda za'ayi shine zanyi binkice akan lamarin idan ya kasance shi wanda ake so ayi auran dashi mutumin kirki ne ya tara duk abubuwan da ake da bukata haka akeso, amma idan akwai mishkila a tare dashi nima ba zan bayar da goyon bayan tabbatuwar al'amarin ba." Ta ce." Eh hakan yayi na baka wuka da nama kayi min binkice akan shi Jamilun da kuma dalilin da yasa yake so ya aura mata wanda ba ta so." Ya mike da fadin." In sha Allahu zanyi kokarin gano yanda al'amarin yake. A daran ranar Shahida ba ta iya rintsawa ba sallar dare ta kwana ta nayi tana kuka da rokon Allah yayi mata za'bi na alkairi a cikin ranta take jin za ta iya auran Baban-baba akan dai ta auri mutumin da mahaifinta yake kokarin aura mata, tun bata ganshi ba take masa wata irin tsana! Da yamma tana daki a kwance tana tunanin rayuwarta ta tsinkayi muryar yaro." Wai ana sallama da Shahida in ji Saminu Abbatuwa." Gabanta yayi mummunan faduwa! Baba Asabe ta harari yaron a fusace! ta ce." Ka je ka ce bata nan." Yaron ya juya ya fita yana dariya! daman ya san za'a rina, tunda mutumin ya aiko shi gidan zuciyarsa ke raya masa cewa ba zai samu ganin budurwar da yake so ba duba da irin hallitarsa da tarin munin da Allah yayi masa. A she bata hakura hijab ta zura a wuyanta ta kama hanyar fita tana surutai akan al'amarin, so take ta ga mutumin tayi masa cin mutunci! Shirgegen mutum ta gani da katon ciki a tsaye a kofar gidan nata. Ta kalli tafkekekiyar kafarsa da dunduniyar take waje sakamakon takalmin da yayi masa kad'an farce zako-zako kafafun sunyi wata irin daud'a da kaushi da faso abin babu kyawun gani! Ta kalli sumulmulallan kansa da fuskarsa dake zuba uban kyalli 'kwayar idonsa jajawur gasu cike da kwantsa da alama dai yana da matsalar ido. Hankalinta bai tashi ba sai da ya wangale bakinsa yana dariya babu ha'koran sama dana kasa sai turame a gefe da gefe! mummunan wawulo ne dashi! ya zube har kasa yana gaisheta. Gefe ta matsa gabanta na dukan uku-uku! lallai Jamilu bashi da mutunci ina yarinya kankanuwa kamar Shahida za ta kai wannan katoton mutumin. Ta gaza furta komai sai kallonsa take tana tunanin yanda zata bullowa al'amarin. ''Baba Asabe Ina wuni." Maganarsa ta dawo da ita hayyacinta. Ta amsa "Lafiya lau kai ne kake sallama da Shahida."? Ya ce." Eh ni ne sunana Saminu Abbatuwa ina sana'ar siyar da dabbobi a kasuwar Abbatuwa dake cikin wannan gari namu mai albarka." Ta girgiza kai da mamaki a tattare da ita ta ce." Waye ya turo ka gurin Shahida? ko kuma kai ka ganta ka ga kana so."? Yayi shuru yana nazarin maganar, fuskarsa ta sauya da bacin rai! ashe hujaj bai daidaita komai ba amma yasa shi zuwa domin a ci masa mutumci. Ta sake maimaita masa tambayarta ta farko "Shin turo ka akayi ko kuma kai ka ga yarinyar kake so."? Ya ce." Mahaifinta ne ya fansar min da ita a madadin kudin da nake bin sa." Gabanta yayi wani irin fad'uwa! dama tasan ruwa baya tsami banza! Ta kalle shi rai! a 'bace ta ce." To ka koma ka sheda masa cewa ni Asabe yayi 'karya bai isa ba ya sanya yarinya a caca na Shiriya zuwa kotun koli dashi a kan wannan al'amarin." Ya sa hannu ya sharce gumin dake saman goshinsa ya kalle ta da mummunar fuska ya ce .'' Dama ba ni na nema ba shine yayi min kyautar ta a madadin kudin da nake bin sa kimanin dubu dari uku da hamsin saboda ya kasa biya na, don haka yanzu daga nan gidansa na nufa domin muyi wacce za muyi." Ta ce." Wannan kuma ya rage naku." gida ta shige tana bambami da mamakin al'amarin. Dawowarsa kenan daga kasuwa Saminu yayi masa dirar mikiya. Tunda ya fito ya ga yanayin fuskarsa ya tabbatar da cewa lallai akwai matsala ya bude baki kenan zai yi magana ya katse shi ta hanyar fadin...... *LITTAFIN NA KUDI NE #500 SPECIAL 1K 0542382124....BINTA UMAR GTBANK, IDAN KATI ZAKI TURO #600 KIYI MIN MAGANA TA WHATSAPP DA WANNAN NUMBER 07084653262.....MUTANAN NIJAR DALA DARI SPECIAL JAKKA DAYA KATIN AIRTAL KO MOV* [9/7, 10:43] bintaumarabbale: _MAJNUN!_ *'BOYAYYAN -ATTAJIRI* _NA_ *_BINTA UMAR ABBALE🍒_* _MANAZARTA WRITES ASSO_ _________ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ *31&32* "Ka ga dakata Malam." ya katse shi ta hanyar daga masa hannu. ya cigaba da cewa." Ashe dama ba ka gama daidaita komai ba ka sanya ni zuwa aka tozarta ni." Cikin tsantsar bacin rai ya kai karshen maganar. Hujaj! ya girgiza kai a cikin ransa ya san hakan sai ta faru, to wannan karan dole ne ya nuna iko akan 'yar sa, babu wani mahaluki da isa yayi masa karan tsaye akan abinda yake da iko dashi, yarinya dai shine ubanta saboda haka zai ga wanda ya isa ya hana shi iko da ita. "Ka gan........bai bari ya k'arasa abinda yake shirin fada ya sake katse shi a karo na biyu ya ce." Na gaji da wannan yawo da hankali Hujaj nayi hakuri iyakar hakuri saboda haka na rantse da zatin Allah yau ba zaka kwana a gidan nan ba sai ka fito min da kudi na." yana huci! da numfarfashi yake wannan maganar bai kuma jirayi jin ta bakin Hujaj d'in ba fuuuuu! ya bar gurin kamar kububuwa! Wani zazzafan gumi! ne yake karyo masa! yasa hannu ya share na saman goshinsa hankali a tashe ya shiga gidan! Talatu ta bishi da kallo a lokacin da yake kokarin shiga dakinsa, duk yanda akayi akwai matsala ganin yanda ya shigo gidan cikin tashin hankali. Yana 'kokarin fitowa daga dakin ta shiga "Wai lafiya na gan ka duk a hargitse? Ya ce." Baba Asabe ce take nema ta tona min asiri a gari saboda haka yau zan nuna mata karfin iko na a kan 'ya ta." Ta ce." Me take nufi to? Yana kokarin ratse ta ya wuce ya ce." Yanzu bani da lokacin yi miki bayani saboda Saminu ya fusata! komai yana iya faruwa idan ban yi wa tufkar hanci ba saboda haka sai na dawo za muyi magana." Ta biyo bayansa tana surutai "To ai 'yar ka ce don ka yanke hukunci a kanta sai ya zama laifi gaskiya wannan karan ka nuna mata cewa ba fa ita ce take da iko da yarinyar ba kai ne ubanta dole ne ayi hakuri da hukunci da ka yanke." Bai ce mata komai ba ya kama hanyar fita yana gyara babbar rigar jikinsa. kai tsaye can gidan Baba Asaben ya nufa. Dama ta shirya masa koda ya gaishe ta a dakile ta amsa ta cigaba da sabgogin gabanta, ya juya ko'ina bai ga Shahidan ba sai Saliha dake wanke-wanke a bakin rijiya ko kallonsa ba tayi ba ballananta ya samu arzikin gaisuwa. Fuska a tur'bune ya ce." Kan maganar yarinyar nan ne na zo na tafi da ita domin na yanke hukunci a kanta wanda hakan alkairi ne a gare mu baki daya." Ta kalle shi a wulakance kafin ta ce." Rufe min baki shakatafe! shashasha wanda bai san ciwon kansa ba, ai dama na shirya zuwanka saboda baka da mutunci shine ka sanya yarinya a cha-cha wato kai abin kunya gaba ka bashi ba baya ba, ka turo wani mummunar hallita da sunan mijin aure kaji kunya Jamilu wallahi kayi faduwar 'bakar tasa."! Gumi! ya dinga karyo masa! ransa yayi masifar 'baci da irin cin mutuncin da take masa ya ce." Wai shin ke kika haifar min yarinyar nan ne da kike min iko da ita, iya kawaici da kara nayi miki mai zai sanya ki dinga kokarin wuce gona da iri, ki zauna a matsayinki mutukar kina so na cigaba da ganin mutuncinki." Ta ce." Jamilu cin mutuncin ka ai ba sabo bane a guri na, ka saba dama kai hanyar da mutunci yake baka bi gurin ba, to bari kaji na shirya tsaf wallahi tallahi ba zaka wulakanta yarinyar nan ba sai in da karfi na ya 'kare akan hakan." Ya ce." Auran da zanyi mata shi ki ke kira tozarci! a tunaninki waye zai aure ta da wannan lalurar? yarinyar fa ba cikakkiyar mutum ba ce wannan ma sa'a aka ci da zai aure ta." Fashewa tayi da kuka ta nuna shi da ya tsa da fadin." 'Yar cikin ka ce fa Jamilu, saboda Allah ya halliceta a haka sai kake neman kai da ita har ka sanya ta a cha-cha! mai yasa baka sanya daya daga cikin 'ya'yan Talatu ba kada fa ka manta duka kai ka haife su kuma ranar lahira sai Allah yayi muku hisabi." Ko gezau! ya ce." Ni dai na gama yanke hukunci wannan yarinya ba ta da miji sai wanda na za'ba mata a matsayi na na ubanta yana da kyau a bani hakkina wannan shine magana ta daku ta karshe ku zauna a shirye daga nan zuwa sati biyu komai zai guda na.'' Shuru kawai tayi tana kallonsa hawayen tausayin yarinyar na tsare a saman fuskarta tunda take a duniya bata ta'ba ganin maciyin mutunci irinsa ba, shekara da shekaru yake 'kunsa mata 'bakin ciki har yanzu ta rasa maganinsa. Shi kuwa rigarsa ya buge! ya fita daga gidan cike da cin alwashi akan abunda ya niyyata. Saliha na kife kwanuka a kwando ta ce." Wai Baba ina ruwanki ne! don Allah ki kyale shi yayi iko da 'yarsa mutumin nan bai da mutunci wallahi saura kiris na d'ura masa ashar saboda takaici! Tana goge hawaye ta ce." Saliha har yanzu kuruciya na damunki baki san duniya ba amma mutumin da yake kokarin hada aure da Shahida bai cancanta ba." Ta ce." To ai gwara shi akan wancan mahaukacin na bakin titi, kamar yanda ya fadi hakane yarinyar nakasashshiya ce da wuya ta samu mijin aure dole sai mara galihu." Girgiza kanta kawai ta ke hawaye na zuba a saman fuskarta, saboda kawai yarinyar na da matsalar kunne shikkenan ba ta da wani farin ciki da jin dadi a duniya ba za a duba cancanta da abinda ya da ce ba, to ita muddun tana numfashi ba zata bari ayi mata auran tozarci ba. Tana fitowa daga kantin Shu'aibu ta hango shi ya fito daga gidan. Gabanta yayi mummunar fad'uwa! sam ganinsa ba alkairi bane mussaman yanda ta hango tsantsar tashin hankali a fuskarsa. Babu damar guduwa tunda ya riga ya gan ta, fuska a turbene ya k'arasa in da take ta sunkuyar da kanta cikin rawar murya take gaishe shi. bai amsa ba kawai ya rike hannunta ya ja ta sukayi gaba. Jan ta yake tana bin sa har suka fita bakin titi bai ce mata komai ba gabanta sai faduwa yake tana kiran Innalillahi wa'ina ilahi raji'un! Suna tsaye a bakin titin suna neman abun hawa Baban -Baba ya 'karaso gurin dugujaja! ya tsaye gefen ta. Hujaj din ya razana kad'an! yana kallonsa ita kam ba ta tsoro ta da ganinsa ba, sai ma wani irin kallo da take masa hawaye na sauka a kumatunta tafi jin tausayinsa akan kanta." Kallo guda yayi masa ya sha jinin jikinsa idan ba mahaifinta ba to wani shakiki ne a gurin ta saboda yanayin kammani da ya gani a fuskokinsu. Da yake mutum ne mai kyauta sai yasa hannu cikin aljihu ya dauko dari biyu ya bashi domin shi duk a tunaninsa abinda yake bukata kenan.'' Girgiza kansa yayi kafin ya ce." Ina zaka kai min matata?" Maganar ta dinga yi masa amsa kuwwa! a kunne "Ina zaka kai min matata? ya sake maimaita maganar, itama ta tsorata da jin furucinsa hawayen idonta ya bushe ta dinga kallonsa gabanta na dukan uku-uku! "Kai ba na son hauka! kar'bi nan ka matsa ka bani guri." abinda ya fad'a masa kenan ya sake mi'ka masa gudar dari biyun. 'Kin 'karba yayi maganar dai ita ya sake maimaitawa "Ina zaka kai min matata."? Cikin fad'uwar gaba ya ce." Don Ubanki waye wannan maukacin! meye hadin ki dashi.? Da yake da karfi yayi maganar yasa da sauri ta ce." Ba mahaukaci bane sunansa Baban-Baba a 'karkashin waccan motar yake kwana Baba Asabe tana bashi abinci." Ya ce." Okey shiyasa kuka k'ulla soyayya a tsakaninku.? ido ta tsura masa tana auna maganarsa. Ya buga mata muguwar tsawa! da fadin." Ba zaki bani amsa ba.? ta ce." Ba soyayya muke ba Allah ne kawai ya hada jininmu nake tausayin........Ya wanke fuskarta da wani azababen mari! yana huci! ya ce." Ni zaki mayar mutumin banza ko? wannan d'an iskan mutumin ban yarda dashi ba kina tausayinsa shi zai iya cutar dake saboda haka aure zanyi miki, kai kuma ka saurare ni da kyau." Ya tsura masa idanunsa dake cike da tsantsar b'acin ran marin da yayi wa yarinya ya ji ciwon hakan har cikin ransa. Cikin isa ya cigaba da cewa." Wannan yarinyar tafi 'karfinka ba zan baka auranta ba domin ba ka da komai mahaukaci kawai." yana kai karshen maganar ya ja hannunta suka shiga motar da ta tsaya a gabansu. Ya jima a tsaye a bakin titin yana nazari da tunani akan al'amarin, can kuma na ga ya tsallaka titin ya bi wata hanya ya mi'ke...... "Ranka ya dad'e ina sauraranka. daya daga cikin yaransa dinshi ne ke wannan maganar yayin da yake tsugune a gabansa. Ya ajiye jaridar dake hanunsa a nutse ya ce." Sule kai ne kasan gari sosai kasan wata unguwa Ja'in a cikin garin nan.''? Yayi jim na minti biyu kafin ya ce." Eh ranka ya dade ina dai jin sunan unguwar amma ban ta'ba shigar ta ba amma wani lokaci muna bi ta hanyar tare da kai idan za muje babbban kamfanin ka na sumunti dake sharad'a." Ya ce." To ai ta kwana gidan sauki tunda ka san hanyar wani aiki za kayi min akan wani mutumi ina so kayi min binkice sosai a kansa. Ya ce." To ranka ya dad'e babu damuwa ya sunan mutumin."? shuru yayi na minti biyu, sunansa Jamilu idan bai manta ba domin can da dadewa ya taba bugun cikin yarinyar ta fada masa sunansa da kuma unguwar da yake zaune. "Sunansa Jamilu amma akwai wani suna da jama'a ke kiransa ya kwanta min a rai amma hakan ba zai zama matsala tunda mutumin sananne ne a cikin unguwar binkice a kansa ba zai yi wahala ba." Ya ce." To babu damuwa ranka ya dade insha Allah zanyi kokari sanin wanene mutumin domin kawo maka cikakken labari a kansa." Ya ce." To Allah ya taimaka ina tsumayinka daga nan zuwa gobe da safe. Ya mike da fadin." Insha Allah ranka ya dade .'' da sauri ya nufi parking spece ya fito da mota domin cika umarnin maigidan nasa. Na jima ina kallonsa ina hango nagarta da dattijantaka a tare dashi, cikakken mutum ne kamili a zahiri da badini domin yanda yake tafiyar da rayuwarsa a nutse shine zai tabbatar maka da cewa ya san abinda yake. *LITTAFIN NA KUDI NE #500 SPECIAL 1K 0542382124....BINTA UMAR GTBANK, IDAN KATI ZAKI TURO #600 KIYI MIN MAGANA TA WHATSAPP DA WANNAN NUMBER 07084653262.....MUTANAN NIJAR DALA DARI SPECIAL JAKKA DAYA KATIN AIRTAL KO MOV* [9/7, 10:45] bintaumarabbale: _MAJNUN!_ *'BOYAYYAN-ATTAJIRI* _NA_ *_BINTA UMAR ABBALE🍒_* _MANAZARTA WRITERS ASSO_ __________ *33&34* Cikin matsatsun kaya ta fito da wani 'karamin mayafi a kafadarta wanda dashi gwara babu. hannunta rike da mukkulin motarta tare da handbag tana wani irin kamshi mai fizgar hankali. Ganinsa a zaune ya sanya jikinta yayi sanyi sai ta hau duru-duru! ya kalle ta tun daga kasa har sama! yanayin fuskarsa ya sauya da 'bacin rai! Yarinyar na so ta zubar masa da mutunci a gari domin ya jima yana hana ta shigar kaya irin wannan amma taki ta daina a kullum burinta ta fitar da tsaraicin ta waje. Cikin 'bacin rai ya ce ." Shukura ba kya jin magana ko ."? A sanyaye ta ce." Daddy kayi hakuri don Allah." Ya daga mata hannu da fadin." Koma cikin gida." Sai ta fashe da kuka tana bubbuga k'afafunta! "Daddy kayi hakuri ka bar ni don Allah." A shagwabe take maganar. Ya duba a gogon dake d'aure a hannunsa shida da rabi na yamma daf ake da a kira sallar magariba. Ya ce." Ina za ki ji."? Hanci ta ja da fadin" Bikin 'kawata a can karkasara." Girgiza kansa yayi da fadin ." Ki koma gida babu in da za ki je." yanda ya fadi maganar babu wasa ya sanya ta juya a guje! tana kuka! Ta zube a jikin kakar uban tana gursheken kuka. Hajiya Saude hankalinta ya tashi a duniya ta tsani 'bacin ran yarinyar ta dinga rarrashinta kan tayi shuru ta fada mata abinda yake faruwa Ta ce." Daddy ne ya ha na ni zuwa kuma kin fi kowa sanin yanda nake da Samira 'kawata ce sosai ai bai kamata Daddy ya hana ni zuwa bikinta ba. Ta ce." Aikuwa bai kamata ba wallahi, shiyasa wani lokacin bana son zamansa a gida saboda yana matsanta miki da yawa bari ya shigo na ji dalilinsa. Tana rufe baki ya shigo da niyyar d'aura alwala. ta dakatar shi ta hanyar kiran sunansa "Alhaji Habu." Ya amsa tare da tsayawa yana sauraranta. "Meye dalilin da ya sa zaka hana yarinyar nan zuwa bikin 'Kawarta kana fa matsantawa yarinyar nan Alhaji Habu." Babu wasa a fuskrasa ya ce." Hajiya wane irin biki ne wannan ? wanda sai magariba za ayi shi, to ba zan lamunci wannan shashanci ba, bayan haka kuma dubi sutturar da take jikinta tuntuni na hana ta sanya dinkuna irin wannan amma taki ta dai na wannan dalilin ya sanya na hana ta zuwa kowane irin biki ta hakura dashi tunda ba ta jin magana." Ta kwantar da kai da fadin." Ai ba za ayi haka ba yarinyar nan Samira 'kawarta ce tare sukayi karatu ya kamata ace Shukura ta halarci bikinta kayi hakuri ka bar ta taje ba don halinta ba sai dai ni nake nema mata alfarma." Ya sauke ajiyar zuciya da fadin." To shikkenan amma ta sanja kaya lallai kuma ki sanya hijabi a jikinki kafin ki fita." Da sauri ta daga kanta da fadin." Insha Allah Na gode Daddy." ba tare da yace komai ba ya bar gurin. Kamar gaske ta fito da k'aton hijab har k'asa tayi wa hajiyar sallama ta fita, tana shiga mota ta cire hijab din tana jan tsaki ! karamin mayafin dake ciki jakarta ta fito dashi ta rataya a kafad'arta sannan ta kunnar motar ta fige ta da karfin gaske. **** Tashin hankali kenan! tun a bakin titi a ka tare shi aka sheda masa abinda yake faruwa, bai gazgata ba sai da ya karya kwanar layin gidan ya ga zahiri! tun daga nesa yake hango jama'a cike a kofar gidansa ga katakwaye da katifu da sauran abubuwan amfaninsu nan a watse a gurin, tonan silili Saminu ya zo yayi a gidan bayan fitarsa yasa zaratan Samari suka dinga watso musu kayan su waje, Hadiza da sauran 'yan uwanta sai kuka suke, ita kuwa Talatu tana zaune a kofar wani gida abin duniya ya dame ta, ma'kota da 'yan uwanta sai bata baki suke, Saminu yasa k'aton kwado (dan mukkuli) ya kulle gidan yayi tafiyarsa. Hujaj tunda yake bai ta'ba tozarta irin yau ba, ya rasa da wane ido zai kalli Jama'ar dake gurin, kawai sai ya huce! fushinsa akan Shahida ya dinga gaura mata mari yana fadin." Kin ga irin abinda ki ka janyo min ko? kin ga tozarcin da ki ka janyo min ko."? ya dinga kwashe ta da mari yana haurinta da kafarsa har sai da ta durkushe a gurin tana wani irin kuka! da kyar aka janye shi daga gurin ana bashi hakuri. Malam Habu makocinsa ya ja shi gefe yana bashi baki da fadin ." Haba Alhaji Jamilu ka nutsu mana ita kuma wannan yarinyar da kake dukanta meye laifinta da zaka huce fushinka a kanta dama tuntuni nake fada maka ka gyara kuskuranka saboda irin wannan rana to yanzu ga abunda ya faru." Ya cire hular dake kansa yana firfita da ita ya ce." Malam Habu wallahi ban taba tunanin Saminu zai yi min wannan tozarcin ba, amma babu komai tsinanniyar yarinyar can ce ta janyo min domin da ta amince da bukata ta da tuni haka ba ta faru ba kamar ni a ce an tozartani irin haka.'' Malam Habu Ya ce." Yanzu dai mu bar wannan maganar insha Allahu komai zai daidaita, akwai daki da rumfa a cikin gidana zan baka aro ka shiga ka zauna kafin mu ga abunda Allah zai yi." Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke da fadin ." Na gode sosai Malam Habu Allah ya saka da alkairi." Ya ce." Babu komai bari yanzu nasa yara su kwashe kayan su shiga dasu Allah ya kiyaye faruwar hakan anan gaba .'' Ya amsa da "Ameen yana bin gurin da kallo, manya da yara sun cika sunyi dafifi a gurin kowa na tofa albarkacin bakinsa. **** "Ranka ya dade wallahi na dauka binkicen da ka sanya ni zai bani matsala sai gashi cikin hukuncin Allah komai ya zo da sau'ki don lokacin dana shiga Unguwar ban sha wahalar sanin waye Alhaji Jamilu ba." Zamansa ya gyara a nutse ya ce." Sule nima nayi farin ciki da haka ina fatan zan samu kyakykyawan labari daga gare ka." Fuskarsa ta sauya da alhani da kuma jajantawa. Ya ce." Yallabai al'amarin mutumin dai babu arziki babu kuma kima da mutunci.'' "Ina sauraranka." Ya fada tare da mayar da hankalinsa gare shi. Cikin rashin jin dadin abubuwan da ya gani da idonsa ya shiga warware masa abunda ya faru ya kuma dora da bashi labarin da ya samu daka bakunan mutane da sauran jama'ar dake makotaka dashi, domin ya tabbatar masa da gaskiyar binkicensa ya nuna masa hotonan da ya dauka a lokacin da yake ta zazzabgawa yarinyar mari ana ta bashi hakuri. Ya karbi wayar yana duba hotonan ransa yayi masifar 'baci ganin yanda yake dukan yarinyar har da kafarsa, babu shakka wannan mutumin bashi da mutunci kuma bai san darajar dan adam ba, kuma jahilci shike da damunsa ba wani abu ba, hakika ya ji ciwon yanda ya ke tozarta yarinyar a gaban jama'a amma bai nuna hakan a fuskarsa ba, ya mika masa wayar da fadin." Goge hotonan daga wayarka." Da sauri ya goge gabadaya kamar yanda ya umarce shi. Ya kalle shi a nutse ya ce." Da safe idan Allah ya kai mu ka je ka nemi shi mutumin da yayi tozarcin domin jin cikkenan karin bayani daga gare shi, ina so ya tabbatar maka da iya adadin kudin da yake bi daga baya sai mu ga ya za'ayi ." Ya ce." Insha Allahu zanyi kokarin ganin hakan ya tabbata." Ya ce." Ma sha Allah ka tashi ka je kawai sai Allah ya kai mu goben ." Ya mike yana godiya sannan yayi masa sallama ya tafi. A daran ranar bai kwanta ba sai da yayi Istahara akan al'amarin, ya wayi gari da yarinyar a cikin ransa, yana tausaya mata sosai yana kuma so ya aure ta amma yana tunanin wani abu a cikin ransa, duk da hakan ba haramun bane amma yana ganin kamar yarinyar tayi masa 'kan'kanta da yawa idan anyi duba da matakin shekarunsa, yayi mata girma domin yana kallonta ne kamar 'yar sa Shukura a zahiri shekarunsu na iya zuwa d'aya. **** Sule ya zo masa da cikakken bayani akan Saminu ya warware masa komai da yanda Hujaj din ya dinga yaudararsa har yayi masa alkawarin bashi auran 'yar sa, daga baya kuma ya dinga yi masa yawo da hankali wannan shine dalilin da ya sa ya yanke wannan hukuncin. Ba a ja dogon lokaci ba ya Umarci Sulen da kudi dubu dari hudu ya je ya kai wa Saminun domin kashe wutar yace koma lallai ya je ya bude gidan ya kulle. amma ya gargadi Sulen cewa kada ya kuskura ya sheda masa cewa ga wanda ya biya kudin. Saminu ganin har da riba akan kudinsa yasa da saurin gaske yasa rigarsa ya fito kai tsaye gidan Hujaj din ya nufa, lokacin ya fita yawon Malamai burinsa kawai a daure bakin Saminu sannan ya wulakanta a duniya kamar yanda ya wulakantashi. Sai Malam Habu ne ya kar'bi mukkulin ba tare da ya bi ba'asin komai ba ya bude gidan, yasa yara suka dinga kwashe kayan suna shiga dasu. A gari ya ji cewa Saminu ya dawo da mukkuli har iyalinsa sun koma ciki, sai ya sake gazgata karfin aikin malamin da ya taimaka masa, domin duk a ganinsa aikin malamin ne yayi tasiri. 'Bangaran Baba Asabe kuwa da kyar ta wayi gari, domin tunda Sha'aibu mai kanti ya sheda mata cewa Hujaj ya tafi da Shahida hankalinta ya tashi mutu'ka! har tayi niyyar zuwa gidan suyi wacce za suyi Kawu Musa ya hana ta yace a rabu dashi su ga iya gudun ruwansa. Kasa hakuri tayi washe garin ranar da yamma ta shirya ba tare da tayi shawara da kowa ba ta nufi gidan, domin bata tsammanin zata zubawa mutumin ido yayi abinda ya keso a kan marainiyar Allah, dole sai tayi masa karakare! sannan za su daidaita. _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ *LITTAFIN NA KUDI NE #500 SPECIAL 1K 0542382124....BINTA UMAR GTBANK, IDAN KATI ZAKI TURO #600 KIYI MIN MAGANA TA WHATSAPP DA WANNAN NUMBER 07084653262.....MUTANAN NIJAR DALA DARI SPECIAL JAKKA DAYA KATIN AIRTAL KO MOV* [9/8, 09:41] bintaumarabbale: _MAJNUN!_ *'BOYAYYAN-ATTAJIRI* _NA_ *_BINTA UMAR ABBALE🍒_* _MANAZARTA WRITERS ASSO_ __________ *35&36* Lokacin da ta isa gidan baya nan, amma kuma daf yake da dawowa domin shiri na mussaman na zuwa mahad'arsu. Babu yabo babu fallasa Talatu ta karbe ta. suka gaisa sama-sama kafin ta bar ta zaune a gurun. Jamila ta shigo gidan hannunta rik'e da 'bakar ledar dake dauke da kayan miya gwalagwaji. ganin ta yasa ta washe baki da fadin." Baba ke ce a gidanmu."? Ta saki fuska da fadin." Ni ce Jamila ai na jima da zuwa ina zaune ina jiran dawowar babanku." Ta ce." Aikuwa yana kan hanya domin lokacin dawowarsa yayi." Talatu ta fito daga kicin ranta a 'bace ta harare ta da fadin." Sarkin shishshigi da cusa kai a maimakon ki kawo min aiken da nayi miki shine ki ka tsaya kina neman suna ko.'"? A sanyaye ta ce." Kiyi hakuri." Tsaki taja da karfi ta fizgi ledar dake hannunta aikuwa ta yage kayan miyan suka watse a gurin, sai kawai ta hau d'ura mata ashar! ranta a a bace tayi saurin barin gurin tana turr!! da halin mahaifiyarsu sam bata da d'abia mai kyau. Shahida ta fito tsakar gidan da alamun bacci a idonta, Jamila ce da ta shiga dakin ta tashe ta daga baccin tana sheda mata zuwan Baba Asaben. Ganinta yasa zuciyarta karyewa sai kawai ta zube a jikinta ta fashe da wani irin kuka mai sosa zuciya. Jin kuka ya cika gidan ya sanya tayi gaggawar Fitowa daga kicin da ludayin miya a hannunta nan ta iske Baban na rarrashinta da fadin." Tayi shuru ta share hawayen ta mutukar tana raye babu mahalukin da ya isa yayi mata auran dole. Karaf ta bude baki ta ce." Wannan fa ba hurumin ki bane Baba kina nema ki wuce gona da iri a akan wannan yarinyar." Ta daga mata hannu da fadin." Saurara haka kada kiyi min rashin kunya ba gurin ki na zo ba gurin mijinki na zo kuma shi nake zaman jira saboda haka kada ki kuskura ki kara wata magana a cikin wannan al'amari." Ta ja dogon tsaki tana surutai kasa-kasa ta juya ta shige kicin domin cigaba da aikin dake gabanta. A gaggauce ya shigo gidan kawai yayi tozali da ita a zaune tare da yarinyar a kusa da ita, kallo daya yayi mata ya san da abinda ta zo. A tsaye ya gaishe ta fuska a daure ta amsa, da sauri ya nufi hanyar dakinsa ta dakatar dashi ya tsaya tare da soka hannuwansa a cikin aljihun rigarsa. Ta ce." Ba wani abu ne ya kawo ni gidan ka ba sai wannan yarinyar domin na zo ne na tafi da ita saboda ba zan ta'ba yarda ka cutar da ita ba." Ya ce." Kin taba ganin uban da ya cutar da abinda ya haifa."? Ta ce." Sau nawa kuma sai dai idan ba a sa son zuciya ba." Ya girgiza kai da fadin "Shikkenan Baba ni ba naso mu dinga jayayya da juna, zan baku dama da lokaci dake da yarinyar domin ni ba mutumin banza bane nayi nufin yi wa 'ya ta aure kin hana to wannan ce dama ta 'karshe a gare ku sati uku kacal ya rage bikin Hadiza kuma so nake na had'asu duka na auran, a cikin wannan satikan nakeso Shahida ta tsayar da miji idan ba ta tsayar ba wallahi tallahi zan had'a ta aure da duk wanda nayi ra'ayi. Cike da alhani da jajantawa yarinyar Tace." Wai shin Jamilu kai wane irin uba ne mara tausayi da jin kai? shin baka ganin halin da yarinyar nan take ciki ne, bata da koshin lafiya wane namiji ne a wannan zamanin zai iya da lalurarta" Ya ce." Tunaninki daban da nawa, ni a ganina duk wannan ba matsala ba ce kuma wanda zan bawa auranta zan sheda masa matsalarta cewa kurma ce to sai kuma me? tana da duk abinda da namiji yake bukata a jikin mace matsalar rashin ji ba zai ha na komai ba, saboda haka wannan shine hukuncin dana yanke." yana kai karshen maganarsa yayi gaggawar bude dakinsa ya shiga. Jiki a sanyaye suka koma gida, duk da cewa ba duka taji komai ba amma ta tsinci wasu maganganun, hawaye kawai take sharewa ta je ta kudindine a kan gado zazzabi mai zafin gaske ya rufe ta. Kawu Musa ne ya kai ta chamis aka duba ta tare da bata magani, a wannan lokacin ya tausayawa yarinyar sosai amma ya za suyi da abinda yafi 'karfinsu Jamilu shi yake da iko da 'yarsa ko'ina aka je shiyasa da yaji Baba Asaben tana ikirarin kaishi kotu ya hana ta ya ce tayi hakuri kawai kanta za ta bawa wahala Jamilu yafisu rinjaye da yarinyar. Kwananta biyar a kwance tana jinyya kafin ta warware ta rame fuskarta tayi haske da tafin kafarta da hannunta alamu sun nuna tana bukatar ruwa a jikinta. Ta fito da hijabi a wuyan ta. Ta kalle ta da fadin." Shahida Na ce ." Ki bari yara su kai abincin nan tunda har yanzu jikinki bai gama dawowa daidai ba kiyi hakuri ki koma ki kwanta. Zumbura baki tayi cikin yanayin da Allah ya halliceta Ta ce." Ni dai idan kin zuba masa kawai ki bani na tafi na kai masa." Tayi murmushi da fadin." Shahida ko dai wannan mutumin dashi za ayi ne.? Murmushi tayi tana kawar da fuskarta. Wani irin tausayin yarinyar ya lullube ta idan ba sharrin zuciya ba mai zai ja hankalinta kan mahaukacin da bashi da asali kawai ganinsa akayi rana tsaka, wannan yana daya daga cikin sharrin *SO!* dole tayi wa yarinyar uzuri. Ta mika mata kwanon abincin da fadin." To gashi nan amma kada ki ce zaki zauna a gurinsa kamar yanda ki ka saba zaki janyowa kanki jifa da tsokanar yara domin dai duk wanda ya gan ki tare dashi zai dauke kema irinsa ce." Ajiyar zuciya ta sauke da fadin." Yanzu zan dawo insha Allahu." Hanyar fita ta nufa, sai ta bita da kallon tausayi da jimami! **** Yana can cikin k'arkashin motar a kwance kafafunsa kawai take hangowa sunyi 'kura sosai amma babu kaushi ko faso! a tafin 'kafar sai dai daud'a. Da d'an karfi ta kirayi sunansa "Baban-Baba." Jin muryata a cikin kunnansa yasa da sauri ya bude idonsa ya fara kokarin fitowa daga kasan motar. Ido ya tsira mata yana mata wani irin sihirtaccen kallo, kaunarta yake har cikin kokon ransa. Murmushi tayi ta dan tsuguna kusa dashi ta ajiye kwanon abincin a gabansa, a nutse Ta ce." Ina wuni." 'Kin amsawa yayi kawai ya kafe ta da kwayoyin idanunsa wanda ta so ta fuskanci wani abu a tare dashi, sai kawai ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da yatsun hannnunta. Ba zato ta tsinkayi maganarsa." Kin tafi kin barni da tunaninki." Kallonshi tayi tana so ta tabbatar da maganarsa. Ya lumshe ido tare da daga mata kai "Nayi kewar ki My dear." Gabanta ya fad'i ta dinga kallonsa tana mamakin kalaman dake fitowa daga bakinsa kamar ba wannan mai tabin hankalin ba. A sanyaye Ta ce." Ga abinci nan kayi hakuri nima kwana biyu bani da lafiya shiyasa ban zo ba." "A jiki na naji hakan domin tare muka kwanta ciwo nima bani da lafiya my dear amma ganinki a yanzu ciwon ya tafi." A d'an tsorace ta ce ." Don Allah waye kai nifa har yanzu zuciyata bata amince min da cewa kana da tabin hankali ba, haka kawai nake tausayinka. Shuru yayi bai ce mata komai ba. A lokacin ta fahimci sauyawa daga gare shi, sai ma ya shige 'kasan motar ya bar ta a tsugune a gurin. Ta mike tsaye tana 'karkade jikinta tana juyawa taga yara sun fara taruwa a gurin, da sauri ta tsallaka titi ta shiga layinsu cikin sassarfa. Washe gari ma da safe ita ce ta kai masa abin kari, sai dai lokacin da ita isa bakin titin baya nan, sai dabbobi a kwance akan buhun da yake kwanciya duk sunyi kashi da fitsari! gurin sai wari yake ga shara nan birjik da bawon lemo da sauran tarkace! Tsigar jikinta ta tashi! ta tsani ganin kazanta a rayuwarta, wai yanzu a ce mutum mai rai! wanda Allah ya daraja shike kwanciya a gurin, ta girgiza kai tana kokarin mayar da kwallar dake kokarin zubo mata, kofin kunun ta ajiye a can gefe in da babu k'azanta! ta juya gaba da baya tana duba gurin, da yake yanzu garin ya waye babu mutane sosai amma dai wandanda ke sana'a a bakin kasuwar sun fara fitowa yara 'yan makaranta da wanda ke cikin ababan hawa suna ta wuce wa suna kallonta lokacin da take kokarin korar dabbobin dake kwance a kan shimfidar buhun nasa. Wani almajiri ya zo ya tsaya da roba a hannunsa. Kallonsa tayi idonsa cike da 'kwansa da alama tashinsa kenan daga bacci ya fito neman abinda zai sa a bakinsa. Cikin yanayin da Allah ya halliceta take masa magana." Ya ce." A she baki sani ba ai jiya da daddare wani mutumi ya zo wai ashe shine mai wannan motar." Ya fada yana nuna katuwar akori kurar da ta jima a gurin. ya cigaba da cewa." Ya gargadi Baban-Baba cewa lallai ya kwashe tarkacensa daga gurin zai turo kanikawa su kwance motar ya siyar da ita. Gabanta ya dinga dukan uku-uku! baki na rawa." Ta ce.'' Yanzu ina yake."? Cike da rashin fahimta ya ce." Waye."? Murya a sama ta ce." Baban-Baba." Wata hanya ya nuna mata da fadin." Ni dai waccan hanyar na ga ya nufa." A take hawayen da take dannewa suka 'kwace suka fara gudana a saman fuskarta, jikinta sai rawa yake tana bin hanyar da kallo! "Shin ina yake ne a yanzu? wane irin hali yake ciki? wannan tunanin take a zuciyarta idonta kurr! akan hanyar da almajirin ya nuna mata. A sanyaye Ya ce." Kiyi hakuri ki daina kuka nima nayi nawa kukan na gaji." Ta kalleshi da ragowar hawaye a fuskarsa ta ce." Saboda me zan daina kuka d'an Malam ina tausayin mutumin nan." Ya ce." Yana da kirki kullum sai ya bani abinci na ci na 'koshi, shiyasa da aka kore shi daga gurin nan ban san ya zanyi ba." Hannunta tasa a kafadarsa Ta ce." Kayi hakuri ka ji ko insha Allahu Allah zai sake had'a mu dashi, maganar abinci kuma ni zan cigaba da baka ai kasan gidan Asabe mai abinci ko."? Da sauri ya daga kai da fadin." Eh na sani." Ta ce." To kullum ka dinga zuwa kana karbar abincin. Cike da murna da farin ciki Ya ce." Na gode sosai Allah ya shi albarka. Ta ce." Bude robar abincin naka." Da sauri ya bude ta juye masa kunun da zafinsa da sugar sannan ta bashi fulas da kosai a ciki ta ce." Idan ka gama karyawa sai ka kawo fulas din gida." Ya dinga godiya kamar zai fashe da kuka. Cikin mutuwar jiki da muguwar damuwa ta tsallaka titin ta shiga layinsu cike da jimami da fad'uwar gaba. _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ *LITTAFIN NA KUDI NE #500 SPECIAL 1K 0542382124....BINTA UMAR GTBANK, IDAN KATI ZAKI TURO #600 KIYI MIN MAGANA TA WHATSAPP DA WANNAN NUMBER 07084653262.....MUTANAN NIJAR DALA DARI SPECIAL JAKKA DAYA KATIN AIRTAL KO MOV* Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels