Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels [3/11, 3:41 AM] Mummy: *1-5* *RAINA* *(The beautiful princess)* © *HUMAIRAH (melody)* *Alhamdulillah rabbil alamin nagode Allah mai kowa mai komai daya bani ikon dawowa dawani taska wacce nake fatan Allah yabani ikon idar da wannan sako banyi don cin zarafi ga kowa ba koh batanci ga kowa ba Allah yasa mu amfana da juna Amin.* _INA KAUNARKU_ *UMMU SABREENA* *FIRDAUSI SODANGI* *ANEESA A RIMI* *LUBBIE MTFSR* *AUNTY SIS*💞 *SERDEYERH*😘 _KUNA RAINA_ *ABEEDA* *MARDIA NIJAR* *SARAH* *ZAINAB DUBAI* *MISS XOXO* *FATTY AZLAND* *HAULERT SKT* *MARYAM M SADI* *FATTY NASHUKA* *MIENERH HAMIDAN* _JINJINA GA FAMILY AND FRIENDS_ *YARA MANYAN GOBE SADIQ & FARUK(Twins)* *MUHAMMAD* *AMINA MAID* *SAIF KT* *AHMAD MS* *SUHAILA* *BEAUTY BOMO* _SANYIN IDANUNA MUSTAPHA (Abba)_ *IYAYENA DR MB SHEHU DA HJY MALAMA DIJE WADA MANZO LOVING YOU IS MY PORTION MAY ALLAH BE WITH YOU FOR EVER AN EVER AMIN.* _Bismillahir rahmanir rahim......_ *BABI NA DAYA* Dan sarki ne magajin sarki duk Dan bakin ciki saidai ya mutu babu wata mata cikin gidannan dazata fini rawan gaban hantsi kuda haihuwa sai dai kuji a makota badai cikin gidannan ba ehe duk me magana tafito ina dai-dai da kowacce bora, Wata matace yar k'arama sanye da alkyabba rikeda jariri a hannu dabai wuci wata biyar zuwa shida ba matar daganinta batada kunya babu sauran mutunci a fuskarka koh imani, Gimbiya Maimuna ce tafito tafiya take cikeda SARAUTA babu Wanda zai ganta bai kara kallonta ba saboda tsabar kyau kaman zai zube. “Maryam ke baki isa ki kirani bora ba wallahi kinyi tsururu, me akeda agola kowa acikin masarautar nan yasan cewa badan sarki bane saidai idan kin zama shawo maida Dan wani naka yau koh mutuwa sarki yafadi yayi bashi da gado kinga koh sai kisawa kanki salama da kwanciyan hankali” Duk cikin matan dake cikin gidan babu wacce ta iya tofa wani abu sai Maimuna wacce tasha SARAUTA ta koshi gabanta da bayanta. Haka suka gama cece kucensu kowacce tashige sashenta. Maryam ce tsaye cikin falo ga kuyanginta sun zagayeta kowacce tana tarairayanta ta koh ina *Danish* kuwa sai tsala ihu yakeyi hankalinta yayi matukar tashi tarasa abunda yakeda buk'ata binta ce ta russuna cikin ladabi tace “ranki yadade mai zai hana kibani rainon yarima ko kya samu ki huta” Dariya maryam tayi. “Gashi binta nabaki amanarsa cinsa shansa duk nabaki ragamar komai sannan na baki wancan b`angaren kizauna aciki daga ke sai yarima don naga kina jidashi takowani fanni, daga ranan danish ya koma hannun Binta saboda tsabar kaunarsa Data keyi. Sarki *MAMUDA* ne yashiga inda danish yake yana yimishi wasa cikin dabara shiko sai dariya yakeyi, yana bangale baki Hajiya Maimuna ce tsaye tana kallonsa, tuni taji takasa controlling kanta hawaye kawai yake ambaliya a idanunta. “Tabbas mai martaba kana bukatan ganin k'wanka aduniya saboda nasan duk wani ikoh da MULKI na maryam zai ragu saboda dole mai martaba ya raba son da yakema danish gida BIYU. Maryam ce tazo wucewa taga Maimuna a tsaye a taga tana kaiwa da komowa dafata tayi tare da cewa. “Allah sarki juya aci ai kashi ki kwantar da hankalinki danish yariga zuwa duniya kuma babu yadda zaki iya da ikon Allah saboda shine yarima mai jiran gado koda SARAUTA saida MULKI” wucewa tayi tunkafin Maimuna ta lalubo amsar dazata bata amma ina kafin duk wani kalami ya shiryu Maryam tayi gaba. ****** *BAYAN SHEKARA GOMA* Ana cikin takun sak'a da maryam da Maimuna. K'watsam ciki ya baiyana ajikin Maimuna tuni jakadiyar sarki tayi fadan sarki aguje danta sanar dashi Abun farin ciki abunda ya dad`e yana nema ruwa ajallo ido rufe, Tana shiga fada ta zube a k'asa ta kwashi gaisuwa tace “Ranka ya dad`e gimbiya kuma sarauniya Maimuna tana dauke da juna biyu a gwaje gwajen da akayi likita yace cikine da ita”Farincikinsa yakasa boyuwa tuni yace, “Kibi sasa sasa ki shelanta ma kowa cewa yar sarki jikar sarki matar sarki mamuda tana daukeda juna biyu sannan duk wata bukata ta duniya jakadiya na biya miki likita nabashi kyautar mota da kujeran makka” jakadiya tace “Godiya nake Allah yakara Nisan Kwana Allah yakara ma sarki lafya da karama takawarka lafya rijiya ba wajen wasan yara bane kafara dai” Haka jakadiya tagama kirarinta tayi waje guda kawai takeyi, Tayi yakaina tsawon minti goma bayi da kuyangu duk aka fito matan sarki koh an kasa kunne Duk sun baza kunnuwa jakadiya tayi kirari tayi kirari, kowa ya zak'u dajin abunda zata fada, Maryam kuwa tanajin gud'a tuni ta kasa zaune tak'asa tsaye takai gauro takai mari gabanta sai faduwa yakeyi dukda murnan saukan Al'quranin danta Danish, tuni fuskarta ta sauya zuwa akasin haka. *_MELODY_*😍 [3/11, 3:41 AM] Mummy: *6-10 RAINA* *(The beautiful princess)* *_BY_* © *HUMAIRAH (Melody)* *BABI NA BIYU* Jakadiya tace “Mun samu k'aruwa acikin gidan nan gimbiya kuma sarauniya maimunatu tana daukeda juna biyu ance in shelanta Sarki yace a tayashi farinciki Ashe yanada rabon ganin k'wansa a duniya, Ras gaban Maryam ya yanke yafad`i takasa zaune ta kasa tsaye kowa Na murna amma banda ita har bak`in ciki take nunawa a fili bata b`oyewa saboda rashin tunani, Haka ake rainon cikin cikeda kulawa lokaci guda Maimuna tazama wata katuwa Abu abinda ba'a girka mata daga zogale, rama, lansir Dan gauda duk abunda tace haka jiki ke rawa za'ayi mata. Safiyar lahadi ne mai martaba yashirya zuwa kilisa kamar yadda yasaba a bayan gari, Haka kowacce tafito take yimasa adawo lafya ciki harda Maimuna Wanda ciki yafito yayi titsitsi. Dubansa yakai gareta yana mai yalwata murmushin sa yace “Ki kulada kanki da abunda ke cikinki ki kwanta ki huta don yanzu ke yar hutu ce Indai *SARAUTA* ce kin gada,” Charaf Maryam tace. " *MULKI* kuma shi muka gada saidai akaimu bola” Dariya yayi don yasan halin Maryam saboda mugun kishin datake da maimunatu saboda ita ke bimata, Jakadiyace tace, “Uwar gida yakamata kidinga motsa jiki kin Dan zagayawa koh zaki dinga samun kuzari” dariya tayi tace “toh” Tafiya take itada kuyanginta suna zagaye suna bata labari mai sanyaya zuciya sai dariya takeyi, Maryam dake d`aki tasa Danish ya ruga da gudu ya tokari cikin ya zube haka ya rugo tuni kuyanginta suka tareshi sukace, “Ranka ya dad`e yarima lafya waya biyoka da gudu ”? saboda gaskiyarsa yace, “Mum ce tace inzo da gudu in bige miki ciki kuma Na gayamata ni inason ki haifamun kani yadda zamu dinga kilisa tare” Tab`e baki yayi kamar zaiyi kuka. Maimuna ta kalleshi saboda yarima Danish yashiga ranta tun ranan dayazo duniya taji sonsa ya mamaye mata ilahirin zuciya ko d`an bata haifa bane Allah kadai yasani, “Karka damu danish kazama yaro mai gaskiya da rikon amana sannan kazama mai tausayi saboda Allah yanason mutane masu tausayi da imani, Ji tayi kamar daga sama ance, “Wane hud`ubar akewa d`ana? Fisgan danish tayi tana huci karki sake koda wasa ki sake tabamun da saboda ba tsaran abunda zaki Haifa bane wayasani koh cikin bayi kika samu wani yayi miki ciki kikace Na mai martaba ne? Maimunatu tayi dariya Wanda yake bak'anta ran Maryam “Allah kadai yasan uwar kwaddo” Tana gama magana tayiwa kuyanginta magana suka ci gaba da tafiya suna shewa suna dariya, Maryam ta mace a tsaye dole tace “In samu mafita akan wannan cikin saboda banaso tazo duniya da rai koda tazo da rai saina San yadda nayi aka fitarmun da ita daga cikin gidannan” tana juyowa taga binta tsaye ta rike haba tace, “Uwar dakina meyasa kike damun kanki? Maiyasa kike tada hankalinki akan waccan abun hmmm tunda ki keda Binta saina share miki hawaye duk wani makirci daya kwana ya hantse nasan shi wani darene jemage bai ganiba?”maryam tace Daren haihuwarsa. Anata shirye shiryen saukar danish gida yayi tankam da mutane haka akayi saukar aka gama washe gari aka wuceda Danish k'asar madina inda acan zaiyi karatunsa daga sakandiri har jami'a, nan akabar Maryam da kewa hakan yakara bata daman shirya magun abunta dabazai kaita ga komai ba sai halaka Haka suka dinga k'ullawa suna k'wancewa itada kuyangarta binta suna cikin zancenne jakadiya taji komai ta kulle a hab'ar zaninta, ranan da watan haihuwar Maimuna ya tsaya sune gaba gaba wajen zuwa clinic din cikin gidan, inda aka kira likitan bayan ta haihu ne aka samo matacciyar ya mace akasa mata tuni binta ta Goya yar ta gudu da ita koh wanketa ba'ayi ba. Haka aka sanar da maimartaba wannan mummunan labarin amma tuni jakadiya ta karbe tace karya akeyi tuni ta kwashe komai tafadi, Inda mai martaba yashiga cikin rud`ani don zan iya cewa harda kuka saida yayi kowa Na gidan yayi kuka tuni aka kama Maryam da dakta akayi wani akurki dasu inda a k'aidar al'ada duk Wanda aka damk'a da laifi nan ake kaishi koda mai girman muk`ami ne a masa rautan, Rayuwa tayi musu kunci amma suka fawwalawa Allah komai. *_MELODY_*😍 [3/13, 12:53 PM] Melody🎤🎤: *11-15 RAINA* *(The beautiful princess)* *_BY_* © *HUMAIRAH (Melody)* *BABI NA UKU* Tun tafiyar Binta basu sake sata a idoba bare labarinta, haka Kullun iyayenta suke kukan rashinta mahaifiyar Danish kuwa tashiga tsaka mai wuya axabar yau daban nagobe daban, tundaga haihuwar Raina baa sake wata haihuwa ba, daman tun kafin tazo duniya yasa mata suna RAINA wato beautiful princess _( Kyakkyawar Gimbiya)_ kuma hakan take...... ****** *Tushen labarin* Wai sai yaushe zakiyi hankaline ne ke Kullun saina miki magana kan ki daina shigowa gida kina ihu kin mata cewa ke macece namiji aka Sani da karaji ba mace ba maza kiyi yadda nace farayi ingani, Abu gwanin ban dariya duk Wanda yaga yarinyar da ake koyawa bariki saiya rik'e baki saboda tabar mamaki yarinyace yar kimanin shekara goma da ko irgan dangi bata faraba illah iyaka Dan jiki datakeda shi, “Raina kalleni haka zakiyi da ido duk Wanda yakiraki sai kinyi yauki kannan zaki bashi cikin yanga” haka inna yalwa tadinga koyawa RAINA abubuwa daban daban dabarun bariki iri iri daga bisani ta daura mata mashe Wato wainar gero zuwa tashan garin Wato zangon Mati, inda ake cinchirindo wajen kawo abun soyarwa, haka fuskar Raina taji mai sai sheki take ga wani digi digo datayi kamar wata aljana, tana tafe tana yanga harta isa runfarsu da zuwanta yara suka dinga kwashe kayansu, suna ya mutsa fuska suna cewa ke mutashi kinsan halin wannan shegiyar dabatada uba, wata tace wayasani ba koh yar tsintuwa ce? Oho sukayi tafi sukayi shewa. RAINA batako tankasu ba ta kallesu ta watsar tace “Banda abunku *MULKI* baya Koran *SARAUTA* yara saidai saurauta ta kori *MULKI* saboda ita mulki wa'adi gareta *SARAUTA* kuwa saidai tayita zagaye mtwwww” taja tsaki taci gaba da saida mashenta kan kace me RAINA ta siyar duka bokitin ta dauka ta juya ta kallesu tace “Shegiya ta siyar tabar masu uba da dangi” tafe take tana taunar cingam Wanda ya Dade tana ci salon ya fafe mata ciki, bakin shagon Kb ta faka ta siya gero Na wainar gobe sannan ta wuce gida tana shiga ta ajiye bokitin ta mikawa inna yalwa kudin tace “Inna waini meyasa yara suke cemun shegiya Mara uba? Nidai inna waye ubana?” tafadi tareda buga kafa, taba zunbura baki uwa durin jaka, Inna tace “Tabbas ke kaskan tacciyace Mara usuli shiyasa suke cemiki haka ina ruwanki dasu kifita harkarsu kiyi rayuwarki ke kadai koh tare dasu kukazo duniya?”. RAINA tace “Ah ah” Haka suka ci gaba da rayuwa cikin talauci da kaskanci inna yalwa tazama kamar karya itace fada da wannan fada da waccan kima Duk akan RAINA akeyi, saboda iyayen yara sunce basuso RAINA tana shiga cikinsu karta bata musu tarbiyan yara, Indo ce kawai take kula RAINA saboda jinisu yayi masifan haduwa da juna. Raina dai bata zuwa makarantar boko bare islamiyya zagon Mati babu makarantar arabi bare ta boko tsantsar jahilci ke dawainiya dasu yaron mai garine kawai yaje birni karatu wayo FU'AD. Tunda sanyin safiya inna yashiga ta watsawa raina ruwan tsanyi a gigice ta mike “Ubanwa ya baki Hutu maxa ki mik`e kikai nik'a” Jitayi gabanta yayi mugun faduwa tace “Inna wallahi banason kai nik'a matan gidan kyarata sukeyi," "Sucemun Mara usuli abunda yake batamun rai kenan haka zakiga yara sunata kallona suna yamutsa fuska wai inna meyasa bazasu gane cewa ba laifina bane? Kaddara ce tafada mam”kuka ta barke dashi inna yalwa koh kallo bata isheta ba tace “Yida jiki kije ki dawo kar gari ya gama wayewa” Haka takai nik'an ta dawo ranta babu dadi, inna yalwa Kullun batada wani buri sai Na RAINA ta kawo mata kudi tako wani hanya shiyasa take koya mata duk wata baraka, tuni Raina ta baci dason kudi idan taga kudi jikinta har b'ari yakeyi. Yauma kamar Kullun ta dauki talla da barkakken zani silipas din Duk ya sud'e, RAINA babu zancen sallah bare salati saboda bata iyaba tafe take cikin layi tazo wucewa ta k`ofar gidan mai gari tun daga nesa Musalle yake tab`a abokinsa “Kalli RAINA yar gidan inna yalwa mai waina inason yin harka da ita saboda nasan zatayi maik'o” lashe baki yayi itakoh sai wani rangwada takeyi kamar wata tsohuwar kilaki, tana isowa wajensu tace “Zaku siya?” da sauri musalle yace eh zan siya haka ta sauke tana wani juya idanu wanda gaba dayansu saida sukaji wani tsar. Sun dauki waina ta murtala suka siya sukace tajeta dawo tabiya ta shago, tana siyarwa ta wuce sai shagon musalle ta tsaya ta rik'e k'ugu “Ah ah raina yan mata har an dawo shigo ki amsa kudin” Haka ta shoge tace itadai ya miko mata haka yadinga janta harta shiga ta zauna irgan kudi yakeyi sulalla tuni ta zauna don tana ganin yau zatayi chamama haka yace ta tayashi irga kudin tanayi tana sokewa a haban zani, duk yana kallonta tana gamawa yace “nawane?” Raina tayi far da ido tace “Na murtala biyarne” batasan yarigada ya irga murtala shida da goma bane ta zari talatin, Musalle bai damuba saboda yanaso yaga yayi nasara cewa yayi “Raina yan mata dauki kudin duka nabaki” ba musu babu Jan aji ta karbe yadauko murtala kudin waina yabata shima ta karbe “Musalle kenan haka kakeda kudi?” “Hmm Raina kenan inda zakizo shagona da dare kinga wayannan kudin wallahi duka zambaki” tuni ta zare ido tafita sai gida sallaman datayi ne yajawo inna ta waigo “har an siyar haka nakeso maza shiga ciki biskin ki nanan kidauka, RAINA tace toh tana fadawa ta zuba kud`in cikin baki *_MELODY_* 😍 [3/13, 12:53 PM] Melody🎤🎤: *16-20 RAINA* *(The beautiful princess)* *_BY_* © *HUMAIRAH (Melody)* *BABI NA HUDU* Tadawo tanemi guri taci biskin ta, “Goggo wallahi Laure zatayi aure kuma kinga zanyi anko Dan Allah kiyimun kinsan cewa duk cikin karkaran nan bayarda takesona sai Laure idan banyiba bazataji dadi ba kwata kwata” “Ke dalla rufemun baki ba anko ba ankoko kina ganin zan iya baki biyar cikin kudinnan? Toh koh sile inzaki tashi ki nema ki nema kinada abun bayarwa sisi bazan miki koh chokali ba idan kika tashi aure” Baki sake RAINA ke kallon Goggo yadda take magana kamar ba ita ta kawota duniya ba, misalin karfe bakwai saurane Raina ta tuga batareda Goggo ta saniba tuni ta mik'a layi sai wajen musalle, tana zuwa tundaga nesa taganshi tareda wansa Wato Fu'ad suna Alwala haka ta k'arasa jiki ba gwari, “Musalle wajenka” Kamar daga sama yaji maganarta cikin rudewa da rashin gaskiya tashi yayi yaje kusa da ita ya tsaya tace, “Musalle nazo ne akan maganan dazu inacikin matsala zan iyayi maka komai donka bani kudin dakace idan nazo, Kaine kaidai zaka iyayimun maganin lalurata”. Musalle duk ya muzanta agaban wansa Fu'ad duk yaji ya tsani kansa, “Amma ke wace irin macece Mara aji mak'aryaciya Kawai ni an gayamiki irin sauran mazane yan iska masu laguda yayan mutane banda kin rainani yaushe nace kizo” Mtswwww yaja tsaki cikeda borin kunya, “Haba musalle yaza kayimun haka bacin kaida kanka kace inzo Dan Allah shine zaka cimun mutunci?” “Ina kikaga mutunci inda kinada mutunci kamarni Dan Dan mai gari zakizo kinamun wannan maganar salon bata suna” Ji yayi an dafashi tuni yasan ko waye Fu'ad kuwa ya tsare Raina da ido a rayuwarsa yana masifar sonta sona hakika amma gaba daya kwarjini takemai, “Musalle sai yaushe zaka daina fasikanci da yayan mutane koh kamanta Zina bashi ce wataran saika biya, musalle zaiyi magana ya katseshi dacewa Mazinace baya arziki koyayi saiya talauce kuma mazinaci mak'aryacine duk amintarsa da mutane saiya haincesu, Sannan Allah yana fushi damaiyinta, duk abunda Raina tafadi na cewa tazo kafadi dabaka fadiba babu yadda za'ayi karamar yarinya kamar ta tazo wajenka” musalle tuni yanade tabarmar kunya da bori ya K'ara gaba. “Ke kuma akanme kika zabi saida mutuncinki darjarki da kimanki akan kudi kudinda bazasu yimiki wani amfani ba, Zina musibace Raina kuma duk Wanda ke Zina baya tareda Allah kuma tabbas yacika Mara imani” Raina taji duk ta tsani kanta duk Goggo ne taja mata sai cije cije takeyi tana kwarkwasa takasa cewa uffan. “Raina duk abunda kikeso zanyi miki koya yawansa yake namiki Alkawari fatana shine ki kama kanki abunda kika dashi kenan dazai sai miki mutunci a gidan mijinki kenan, Yanzu meye matsalarki? Kin gayamun in miki maganinta yanzu Duk a zangon Mati banga yar da nakeso ba saike wallahi inada burin ki kasance masoyita abokiyar rayuwata ke bake jira raina” Far tayi da ido saboda tsananin dad`i ance ana sonta “Daman ankon Laure nakeso nayi kuma bansan yadda zanyiba abincima ya kyar mukeci bare anko kuma kawatace sosai idan banyiba zataji haushi na tace bata kwawancen dani” “Raina yan mata muje toh in rakaki har gida koh suna tafe tana wasada kara ta tsinta wannan ta tsinta wannan tanata tsalle tsalle abunka da yarinta, har kofar soron gidansu sukazo ya dauki jaka biyar yabata yace tayi amfani dashi kuma duk in tanada bukatan Abu tayi mishi magana zaiyi mata haka ta shige gida tana dagamai hannu shigarta keda wuya taga Goggo labe a zaure tace, “Zonan dan ubanki nawa yabaki kawosu nan” Haka ta fizgi d`ari biyu raina tace “Aiko kin dauki rabonki kuma mekikeyi a labe anan wallahi Goggo kezaki siyamun mutunci a garinnan amma Kullun kekike watsani shiyasa mutane sukemun cin kashi keda kika haifeni baki tarairayeni ba kin soni sai mutan gari ni inada shakkun cewa bakece uwata ba saboda duk wata uwa tanason danta harta jashi ajiki” Kwab kakeji Goggo ta bige mata baki harsaida yayi jini “Kajimun yar iskan yarinya Dan ubanki saboda sanadiyyan haihuwanki kika koranmun kostamomi kika hanani rawan gaban hantsi, kuma har jigila nake dake kar inji kar ingani wallahi. Kuka raina takeyi maicin rai tarasa abunda yake mata dadi amma babu yadda ta iya saidai ta rungumi kaddara. Haka Gwaggo yalwa taci gaba da yiwa Raina hud'ubar shaid`an tanata sata hanyar halaka nan Goggo taje wajen Malam ALU ta ansoma Raina maganin farin jini Dana Wanda samari zasu bata kudi, haka ya had`a mata yace jaka zata bada tace, “wooooo jaka fa kace toh zan aiko raina” A cikin ranta cewa take ai saidai tabada kudin don sisi bazan kashe mata ba. *_MELODY_* 😍 [3/17, 7:41 AM] Melody🎤🎤: *16-20 RAINA* *(The beautiful princess)* *_BY_* © *HUMAIRAH (Melody)* *BABI NA BIYAR* Haka ta tafi gida tana isa bata tadda Raina a gidaba, tadinga kwala mata kira amma shuru tana dasa mazaunenta RAINA tashigo aguje tana haki, Goggo Ta dubeta tace, “Ke lafiya kika fadoma mutane gida babu koh sallama kuma a guje, na hanaki wannan abun amma kinki kiji sai kiyitayi Sai kace wata namiji ina gayamiki mace rangwada takeyi ba guduba” bata gama rufe bakiba taji ana doka sallama ai tuni RAINA ta haure takan Goggo tayi dakinsu mai shegen duhu ta boye cikin tsumma cikeda kudin cizo, Goggo tace “Lafiya kike gudu haka ubanwaye ta biyoki? Mutumin dake waje yace “Leko ki gani dakeda wannan shegiyar yar taki sai nayi karanku matukar bata fita harkan yayana ba” “Daman Kaine ka biyomun ya toh bari kaji yadda kake tutiya da cewa yayankane haka itama yace, don haka kakai kara kotun koli muzuba nidakai shege kafasa, wallahi bakasan tsiyaba zan nuna maka idan baka bar kofar gidannan ba sainayima sharrin da Allah kadai zai iyama amma ba mutum ba” Sanin halinta yasa shi barin kofar gidan don yalwa makirar macece wacce nasan shedan dakansa yana tsoronta, Ciki tashiga ta kama RAINA tayi mata d`an banzan duka “Narabaki da shiga tsabgarsu amma kinki kiji ke kika sani banza Mara Yanci Mara gata Mara galihu shegiya bakar banza, maxa kidauko jaka daya cikin kudinnan kikaiwa Malam ALU” Hararan ta tayi tace “Hmmm Goggo kenan kudinnan babusu nasai anko nabada dinki saidai kisan yadda zakiyi wallahi don ni ban aikeki wajen ALU ba keda kikaje aike zaki biya kudi” “Iyeeh haka kikace kinji shegiyar yarinya Dan ubanki bazan biyaba” “Goggo taraki nakeyi duk randa kika sake cemun shegiya saikin nunamun ubana a garinnan kinji na gayamiki don abun yafara isana Kullun saikin shegantani, Duk abunda naxama aduniya Goggo kece sila” fit tafice tayi zaune a soron gidansu tana wasa da kasa Fu'ad ne tsaye akanta yace “Barkadai sarauniyar kyau da kamala, tunda nake bantaba ganin budurwa mai cikar zatinki ba Raina idan ban gankiba zuciyana kuna take idan na ganki sai inji kaman anasani a gidan Aljanna, Raina idan ban aureki ba tabbas mutuwa nayi” Waiwai wai sai kunga raina wani far far datakeyi duniya inaxata sa kanta saboda dadi batasan lokacin data wani kayataccen murmushi ba da hakoranta sunyi jawur saboda rashin yin brush, ga doyi da bakin yakeyi amma koh ajikin Fu'ad saboda kaunarta dayakeyi, nan suka zauna suna zance Goggo ta leko tace “Wai wayene yake bibiyarmun ya ne babu wani kwakkwaran zance toh ki tabbatar da yabaki yan chanji” Raina taji kamarta nutse don kunya haka da Fu'ad zai tafi yabata Dari biyar da cewa zai dawo gobe, Haka RAINA taci gaba da tallanta duk da Fu'ad bayaso babu yadda ya iya da Goggo, Da sanyin safe Raina ta tashi koh wanke baki ba tayiba bare sallah don xan iyacewa bata sallah bare ita uwar gayyan wato Goggo yalwa koh karatun fatiha basu iyaba don babu makarantar arabi bare na boko. Wanke gero tayi ta kainik`a duk sakko datayi saida ta taradda layi har kofar gida ajiyewa tayi kawai taje ta haye kan dutse ta zabga uban tagumi kamar wacce batada iyaye koda yake meye marabanta da maraya rashin uba, Motoci taga sunata wucewa kamar daga sama taji anata horn dagowa tayi tana kallon motar har suka gama wucewa ta a zuciyarta tace “Daganin wannan bak'on sarkine saboda sarewa da aketayi daga birni suke waiyo Allah hmmm duk wani Dan birni dadi yakeji babu ruwansa da talla saidai boko”. Da wannan tashiga ta dauki nikanta sai gida sankirane yaketa shela cewa mai gari ya aikoni yace maxa da mata manya da yara kowa ya halacci fada saboda Sarki yazo daga birni akwai jawabi daza'ayi, haka yaketa kwakwazo, “Goggo kinji fah anata shela nasan yau kwantai zanyi saboda yau garin babu kowa duk zasu tafi fadan mai gari” Goggo ta harareta tace “Sai kinje idan kika zauna mezamuci har fadar zakikai saboda mutane idan yunwa ta addabesu zasu siya” Haka RAINA tayi fushi harta hakura kwaskwarima tayi tasa wani barkakken skirt tasa rigar wata atampha daban Dan kwali daban, sannan ta bada hoda tayi mata busu busu fusk'arnan taji digo digo ita ala dole ta hadu, haka ta dauki botikin wainar ta wuce sai fada da isarta ne ta nemi guri ta zauna duk cikin mutanen babu Wanda yayi abun siyarwa sai yalwa saboda son kudi, Jawabi Sarki yafara kamar haka amma gaba daya hankalinsa nakan Raina data shagala da kallonsa don tana ganinsa taji wani iri ajikinta, shima kuma haka “Assalamu alaikum jama'ar Zangon Mati ina gaisuwa ga yara da manya da kuka halicci wannan taron Wanda babu komai aciki sai Alkhairi. *_MELODY_* 😍 [3/17, 7:41 AM] Melody🎤🎤: *21-25 RAINA* *(The beautiful princess)* _*BY*_ © *HUMAIRAH (Melody)* *BABI NA SHIDA* Munzo muku da wani daddadan labari gwamnatin Mu maici tabada kwangilan a Gina ma mutanen Zangon Mati makarantar boko da da islamiyya sannan sa masallatai, sannan ita Zara kawo kwararrun malamai donsu koyarda yaranku, Dan mun duba mun hanga kuna bukatan dauki, fatanmu shine muga yaranku sun zama abun alfahari suzama chiyamomi, yan majalissu, likitoci malamai, Harma da shugaban k'asa baza'a rasaba acikin karkaran nan, talla ba abunyi bane dakwai sana'o'i Wanda a gida za'azo asiya, amma kudubi wannan yarinyar ya nuna RAINA wacce tuni jikinta yafara kyarma, umurni yabata data taso saboda tsabar raxana saida robar wainar ta zube a k'asa ta watse riketa yayi yana k'watance da ita amma gaba daya yarasa meyasa yakeson yarinyar, ya sunanki?” ```“Sunana *RAINA* ”.``` Haka Sarki ya k`ara jin gabansa yayi mugun fadi Ya maimaita sunan acikin ransa yace “ *RAINA*? Indai raina tace ai Maryam tace sawa tayi a tafi da ita a kashe” kowa na wajen tsayawa yayi yana kallon sarkin sakinta yayi yasa abata kudi naira dubu goma hannu na rawa RAINA ta amsa koh godiya tana fita ta runtuma a guje sai gida, Haka aka gama jawabi kowa ya watse, Sarki ya tafi ransa a ba dadi. Da shigar *RAINA* gida tanata haki ta zauna tana maida numfashi, Goggo tace “Ke wai lafya ina kika samo wayannan kudin masu uban yawa? Raina takasa magana duk a tsorace take inna tambaya take ina robar wainar, Saida tabari raina ta natsa sannan ta fara yimata tambayan abunda yabata tsoro? “Goggo mai martaba ne yabani wannan kudin bayan yakirani yayi Kwatance dani akan a daina daurawa yara talla” Dam!!! k`irjin Goggo ya buga duk ta rude tace, “Raina barin garinnan zamuyi Mu kama gabanmu Mu koma wata siyyan, saboda zamanmu a garinnan hatsarine” RAINA dai kallonta takeyi meyasa Goggo ta rude tunda taji na ambaci sarki? Tabe baki tayi ita tasani. “Goggo babu inda zamu zama daram acikin garinnan, kodan Fu'ad Dan wajen mai gari bazan iya yin nisa dashi ba saboda yana sona sosai” “Ke rufemun baki kawo kud`innan mun samu na chefane kwana biyu ” Haka raina ta mika mata kudin yarone ya shigo yace ana kiran RAINA Goggo tace yace gatanan zuwa saura idan kikaje kiyita Abu kamar Goyon gwaro. Fita tayi cikin natsuwa suka gaisa da Raina yace da ita, “Nazone akan zuwa makaranta kinsan kwanan nan za'a gama so inaso insaki na islamiyya Dana boko, saboda kikara wayewa kizama yar birni sannan kisan hukunce hukuncen addinin musulunci” Dadi kamar zai kashe ta tace “Kai naji dadi kwarai kuma nayi murna sosai, amma Fu'ad kana ganin Goggo zata yarda kasan ina mata talla kuma shine rufin asirinmu” Kamar daga sama sukaji maganar Goggo “Mezai hana in yarda matuk'ar zaka dinga ciyardamu duk abunda mukeda bukata zakayi mana ai zuwa makaranta koh fashi bazatayi ba” Raina taji haushi kwarai amma saita boye shi kanshi Fu'ad saida yayi kunya ba raina kadaiba kansa yasa k'asa ya gaidata ta amsa sannan tace “Zanje gidan karime mai haja ga gari chan ki kwada kici kafin indawo”. Raina ce tace “Kayi hakuri halin Goggo sai ita amma Fu'ad ina ganin baxamuyi aureba saboda kyarmar da akemun na cewa ni shegiyace, nasan cewa wata rana sainayi kuka saboda nasan cewa rabamu za'ayi ina tsoron zuwan wannan ranan nasan cewa ni Mara dangice banida kowa bansan kowaba nasan cewa dayawa kallon kaskantacciya takemun bata hanyar aure aka haifeni ba” Kukane yaci karfinta sosai harta kasa magana “Dan Allah kiyi hakuri kidaina kuka wallahi ina matuk'ar sonki banda abunki raina aka auri karuwa bare ke", Zanyi duk yadda zanyi iyayena su fahimceni kuma aure dani dake babu fashi fatana kirike mutuncinki na ya mace toh kingama mun komai a rayuwa” Fu'ad kenan ai saidai kayi hakuri don ina ganin gwara nima inbi hanyan da aka samoni inyi bushasha na in samu duniya kamar yadda Kullun Goggo take gayamun idan nayi kudi na wuce raini. Hure mata ido yayi yace “Tunanin me kikeyi bayan gani a tareda ke?” Dariya tayi Wanda yafi kuka ciwo sukayi sallama yadauko kudi yabata. ******* Yanzu RAINA tanada shekara goma sha hudu a duniya haka Fu'ad yasata a makaranta tana zuwa, Kullun saiya yimusu cefane safe da rana hard a dare sannan yabata kudin Tara amma Kullun Goggo babu godiyan Allah, haka shagonsa yayita karewa amma bai daina yimusu hidima ba, har RAINA tafara jin gwara yadinga basu abincin rana kawai saboda shagonsa ya lalace babu kaya gashi duk wata saiya yimata dinki Wanda zata dinga kwalliya ga littafan makaranta dayake siyamata duk term. Tuni labari ya ishe Mai gari mahaifin Fu'ad _*MELODY*_ 😍 [3/19, 4:01 PM] Melody🎤🎤: *26-30 RAINA* *(The beautiful princess)* _*STORY & WRITTEN BY*_ © *HUMAIRAH (Melody)* *BABI NA BAKWAI* Hankalinsa yayi k`ololuwan tashi, Aii bai tsaya bata lokaci koh Neman shawaran wani ba ya d`ebi yan fad`ansa sukayi musu diran mik`iya, Sallama suketa kwad'awa amma shuru kakeji Inna tana labe taga ko waye amma taki ta amsa saida taga suna niyyan shigo mata gida tayi sauri tafito koh mayafi, Tuni ta zube a kasa tana kwasar gaisuwa “Dakata tsohuwar najadu, tsohuwar karuwa, makira addababba, Kina tunanin Duk ayar da kike shek'ewa keda yarki banida labarune? Toh kin yaudari kanki kuma saikin bar Garinnan keda shegiyar yar taki Marar uba yar kwararo, Ina akuya zata da kayan tankai me zuwan biri da gada Dana baxai auri yar ki ba koda itace autar mata kisani, Duk wani bin boka dabin malamai nasan babu Wanda baki iyaba toh ahir d`inki akan D`ana, Kun me damun da saniyar tatsa dakeda shegiyar yarki Duk kun cinye mishi jari saboda son abun duniya toh koh Duk ranarda naga Fu'ad da RAINA take kowa sainayi holi daku daga garinnan, dayawa mutane suna kawomun k'ararki saboda fadanki da rashin mutuncinki inazan hada zuri'a daku mutanen da ba'asan Asalinku ba, nan kikaxo Allah annabi nabaki guri Ashe a kaina zaki kare” Yana gama magana ya wuce batareda ya saurari Goggo yalwa ba. Tsaye tayi tana maida numfashi Niko mezanyi banda dariya Ashe gaba da gabanta Aljani ya taka wuta, ciki gida ta koma taga RAINA zaune tanata razgan kuka babu ji babu gani sai sheshek'a takeyi, “Lafiya kike kuka? Indai akan Fu'ad ne karkisawa kanki damuwa tunda kinadani kin gama samum komai mai gari dani yake Batu yanzu wajen ALU zani ya rufemun bakin shegu saidai suga yana bauta mana basuda ikon magana” Sai a lokacin raina tayi murmushi taji dadi Fu'ad shine namijin daya fara furta mata kallaman *LOVE* shiyasa take ganin shine karshen maganarta, shi takeso ta aura Duk runtsi amma ina tana ganin ta makara saboda iyayensa sun fara nuna kyamarta a fili. “Yanzu ni narasa gane me Kalmar shegiya take nufi ance banida uba taya aka sameni nasan dai saida namiji ake haduwa asamu da toh ita Goggo a ina Tasha kodai a randa tasha? ```Ohh Allah magani ni RAINA ina cikin gararin rayuwa, bansan suwaye dangina ba gashi Goggo tak`i ta nunaman mahaifina koda baxai amsheni ba nasan k`ila dashi nake kama don babu wata kama danayi da Goggo”``` Da wannan tunanin ta k'are har Gwaggo tadawo tace, “Maza kije ki daga wancan dutsen kisa layarnan” tana sawa sukaji sallama ana kiran RAINA lokaci guda bugun zuciyarta ta karu Goggo tace tana zuwa kace waye Tashi tayi ta wanke fuskarta da tasha kuka ta mustsuka mai da hoda tafiya, Tsaye taga Fu'ad ya k`ure ta da kallo Wanda yake nuna tsantsar son da yake mata. “Raina inaji ajikina wani Abu yafaru karki boyemun kisanar dani wallahi sai inda k'arfina yak'are, akan ki raina zan iya amfani da numfashina na karshe in yaki Duk Wanda ya keda niyyan bata miki rai. Shuru tayi tana kare masa kallo tace “Fu'ad kenan inajin wannan mutumin baxaka iya fito na fito dashiba saboda yagama maka komai a Rayuwa tunda ya kawo ka duniya, inajin watan rabuwarmu tazo saboda dazu yace bani bakai mezakayi da shegiya Mara uba kaskantacciya Irina katafi kar aje a gayamai ya koremu Dan bansan inda zamu dosaba danida Goggo ba”. Kuka takeyi sosai har saida tasa Fu'ad kuka saboda indai zata zubar da hawaye baiga abinda zai hana shi ya zubar da nashi hawayen ba, “Kiyi hak`uri ga wannan kiba Goggo hak`uri abubuwan sai a hankali ne jarin nawa duk ya narke ga kudin tara na gobe kiyi sammamako naji ance baki zuwa islamiyya toh kidage saboda anan ne zaki samu aljannanki” “toh” tace Tashige gida shikuma ya wuce wajen IDI abokinsa donya sanar dashi abunda yake faruwa amma sai akasamu sabani bayanan, Haka ya karkata ya wuce gida fuskarsa babu koh walwala bare fara'a daki yashiga ya kwanta yafada kogin tunani tsaki, Yayi yace “Bahaushe mai ban haushi da uwarka da ubanka ya shegantaka mai makwan yace bada aure aka haifeka ba sai yace mata shege kuma abun haushi babu Wanda aka jeho daga sama wallahi wallahi aure danida RAINA babu fashi saidai mutuwa kamar daga sama yaji ance “Saidai ka mutu don baxan hada zuri'a da yar maceba wacce batada asali wake daya shike bata gari Fu'ad wani irin makanta zuciyarka keyi ka amince ma waccan yarinyar toh kasani bakai ba ita kuma ka shirya nanda sati zan daura maka aure da marka koh kanaso koh bakaso”. *EDITED BY SERDERYERH*😘 _*MELODY*_😍 [3/19, 4:01 PM] Melody🎤🎤: *31-35 RAINA* *(The beautiful princess)* _*STORY & WRITTEN BY*_ © *HUMAIRAH (Melody)* *BABI NA TAKWAS* Fuuuu ya fice yabar Fu'ad k'wance hawaye ke zuba a gurbin idanunsa sai tsiyaya yaketa gefen ido ni humairah nace hawayen masoya ta gefe yake kwarara, Haka ya kwana baici wani abinchin kirki ba banda kuka babu abunda yake masa dadi a rayuwa, washe gari koh sallah yakasa zuwa acikin daki yayita yakoma ya kwanta tsawon kwana biyar babu wanda yasashi a ido illah satar hanya da RAINA takeyi ta kawo mishi abinchi, daya ganta saiya warke tana tafiya zai shiga cikin k'unci da tunani “Malam wai kwana nawa Fu'ad bai shigo ya gaidamu ba koh lafya, indai lafya Fu'ad bazaiki shigowa ba yadda ya keda k'awa zucci” “Banda abunki meyasa zaki damu kanki yaron dabaida tunani Mara hankali mezaiyi dawata shegiya Mara uba kaskantacciya bafatada usuli inajin akan maganar danayine na cewa ya rabu da ita kuma aure da marka ba fashi shine yake azabtar da kansa don naji ance koh kasuwa baya zuwa” Inna tashi tayi tace “Haba Malam idan baa auren shegu ya za'ayi a rage irinsu agari, Inhar ana k`yamarsu ya za'ayi a daina haihuwar su karka manta ina daya daga cikin shegun duniya kuma haka ka aureni amma ace yau kaike k'yamar wacce bata da uba? Kayi kuskure hakan ya nunamun cewa abisa kaddara kake zaune dani badon soba hmmm malam kenan inhar ina numfashi aure sa shegiya sai anyi” Mai gari yace “Toh bada yawuna ba wallahi kuma bada kudina ba inyanada kudi zanje in nema masa auren yaje chan ya k'arata, Dakike zancen kema irinta ce toh kisani mahaifiyarki agaban iyayenta take harna ganki na aura kuma kaddara ce kuma sun baki tarbiya wacce tadace shiyasa har nayi shaawan aurenki kuma banyi Dana saniba”. Fitt ya fice haka tashiga Dakin taganshi kwance danuwansa a sama sallamar ta ne ya ta saka shi tashi murmushi yayi amma ga rama da damuwa fal acikin ransa, “Fu'ad Ka daina kuka kaje ka nemo kudin aure mahaifinka ya aminche, wani tsalle yayi saboda murna yace “ya Aminche in auri RAINA? Alhamdulillah Amma naji dadi inna Allah yaja kwana Kiga jikokinki yanzu zanje in sanarda RAINA don nasan tana cikin irin wannan damuwan, Aii takalmi yasa tuni yayi waje garda gudu yake k'arawa nace Allah sarkin dadi soyayya maisa zumudi, soyayya mai sanya nishadi. Yana isa k`ofar gidansu RAINA ya tadda tana zaune a zaure tana cin Dan gauda, sallama yayi tana ganinshi taji wani dadi Wanda baxai misaltuba tace, “Fu'ad bakaji irin sanyin danaji ba Danaga kana murmushi yadda kasabayi mani ada kafin komai ya rinchabe” Murmushi yayi yace “Mai gari ya aminche da za'a turo akawo kudin aurenmu shiyasa kikaga naketa dariya saboda burina yakusa cika RAINA akanki na kizama uwar yayana” Dad`i kamarya kashe RAINA Goggo ma tayi farinciki dajin wannan batun, Bayan kwana biyune Fu'ad ya yanke shawaran ya siyar da kayan shagonsa yakai kudin auren raina saboda inba haka yayiba bashida inda zai samu kudi bare harya iya biyan kudin Neman aure, da sanyin safiya ya isa kasuwa yakira Idi abokinsa suka nemi guri suka keb`e, Nan Idi yadinga kod'ashi idan ba raina ba sai rijiya rijiyarma mai k'walabe, Na Raina bada kanka asare aje gida kace yafadi, ina kafito RAINA ina zaka RAINA. “Fadi ka kara Idi amma dakwai abunda nakeso kayimun, Inaso kasiya sauran kayan shagona inaso zankai kudin aurena da RAINA sauran kuma inaso zani birni karatu daga nan kaga sai'in kama wata sana'ar, koh NCE ce kaga sai inje inyi tunda inada k'walin sakandiri, inaso Raina taji dadi ne inaso wata rana indauketa inmunyi aure inkaita birni” Dariya Idi yayi yace “Lallai abokina kayi nisa lallai RAINA tasace zuciyanka Allah yasa karta watsama k'asa a ido don mata halinsu saisu, ka kare akansu sukare akan wani banza chan dayazo daga D'oshe, muje shagon muyi lissafi muga nawa kayan suka kama” Haka akayi lissafi kaya dubu hamsin da biyar ni humairah nace aiba wasu kud`in arzik`i bane ma, haka ya k'washe kaya zuwa shagonsa yamik'a masa kud`i yayi mishi fatan Alkhairi sannan sukayi sallama, Ankai kudin aure wanda Goggo ta amsa batareda wani namiji ba abundai babu kyan gani majina a gefen hanci. *EDITED BY SERDERYERH😘* _*MELODY*_😍 [3/19, 4:01 PM] Melody🎤🎤: *36-40 RAINA* *(The beautiful princess)* _*STORY & WRITTEN BY*_ © *HUMAIRAH (Melody)* *BABI NA TARA* Murna duk ta ishi RAINA dan duk ta k`osa Fu'ad yaxo suyi hirar soyayya tunda sunkusa zama daya amma wani K'arin bakinciki Fu'ad yaxo ma RAINA dawani sabon labari na cewa zashi makaranta a birni tuni gabanta yafadi taji takasa jurewa kalamansa tace “Yanzu kana nufin bazan kara ganinka ba yazakamun haka Fu'ad kasancewa Kaine Gatana acikin wannan karkaran idan ka tafi wazai dinga bamu abinchi gaskiya nidai saidai ayi auren indauki Goggo na mutafi tare kasan yadda kowa ya tsaneni Kaine kawai kake faranta mana rai” “Kiyi hakuri RAINA hakan ne zaisa inci gaba inzama wani Abu daxan iya rikeki dakeda Goggo, Gashi bawata Sana'a gareni ba amma zan dinga yimuku aike akai akai ga dubu goma kiba Goggo kice mata nan bada jimawa ba zan dawo, Inaso kiyi man Alk`awari duk runtsi duk tsanani baza ki manta da Fu'ad d`inki ba mai k'aunarki badare ba rana, kici gaba da zuwa makaranta kinji Raina ta karki dinga kula maxa idan ba hakaba yaudaranki zasuyi su lalata miki Rayuwa kiji idan kikamun haka babu abunda zaki nema duniya banyi miki ba” RAINA tayi tsalle tace “Dagaske kasan me nakeso kabani Aljanna" Dariya yayi yace “Raina kenan banida wuta banida Aljannan sannan kisani Allah ne yake da mutum a Aljanna idan yayi aikata aikin Alkhairi, sannan yasa mutum a wuta idan yayi aikin sharri kinji raina shiyasa nakeso kici gaba da zuwa makarantar islamiyya don achan zaki koyi komai nadaga Addini kifito da wuri idan zan wuce mutafi tare kinji” haka ta amsa da toh sannan sukayi sallama ya wuce gida, Kafin yakai gida haka mutane suketa nunashi wai Dan maigari zai auri yar mace uwa uba shegiya, shiko Fu'ad koh ajikinsa wai an tsikari kakkausa yaci gaba da tafiya yanata surutai, Washe gari sammako yayi yayi sallama da kowa ya wuce birni, Amma saida ya biya gidansu RAINA suka wuce tare Goggo tayi mishi fatan Alkhairi, Suna tafe suna hirar bankwana amma ransu babu dadi haka suna zuwa maraba sukayi sallama, Yadauko dubu d`aya yaba ta ta wuce cikeda kewan Fu'ad. Anshafe kwanaki da dama ba Fu'ad ba aike inna tafara shiga wani hali haka tayita yiwa Raina fanfo nacewa lokaci yayi dazata fara saida kanta danta samo musu kud`i tun RAINA tana ki harta fara daukan hud`ubar Goggo, Ranar litinin ne RAINA tayi lattin zuwa makaranta saboda saitaje tallan safe take tafiya da shigarta cikin makaranta taga ba kowa tayi saurin shiga aji ta xauna, Ashe malamin su yana kallonta haka ya tsamota yace ta tsaya gaban aji, jikinta sai Bari yakeyi kamar iska na kad'a bishiya yadaka mata tsawa ya janyota kawai basaiga Nonuwa ba, yan aji kowa ya rufe ido saboda kunya shiko Aymel ya tsaya yana kallonta yana lashe baki tuni abunsa ya mike babu abunda yake buk`ata sai keb`ewa da RAINA, “Meyasa bakisa riga ba kika xo makaranta Wato ke yar iska koh?" Tuni ta zare ido tafara kuka tace “Babu Omo ne ban wanke rigarba kuma sauran kayan suma babu wanki shiyasa nasa hijabi kuma ba muda kud`i” Hak'ik'a Aymel yaji tausayinta Amma ya k`udiri aniyar sai ya lalata mata rayuwa don yaga idonta a bude yake k`ilama tasaba da maza, Wurga mata hijab din yayi tayi sauri tasa yace “Idan an tashi kizo Office dina” Babu musu koh gardama “Toh malam” Haka kunya ya isheta har aka tashi taki sakin jiki, saida kowa ya watse RAINA ta kutsa cikin office din tana mai jin tsoro, “Uncle ina wuni” Juyowa yayi yana murmurshi yace “Raina harkinzo zoki zauna akan k'afana” Haka ta dinga tafiya kamar wacce kwai ya fashe mata a ciki zama tayi ya dinga yimata tambayoyi, Daga nan ya dinga matsa mata d`an k`irgan dangin data fara gashi mugun zafi suke mata amma babu yadda ta iya tunda yace zai bata kudi, Tuni yakawo dayake jarababbe ne d`an gidan abun k`wari. _*EDITED BY Serdeeyerh*_😘 _*MELODY*_😍 [3/19, 4:01 PM] Melody🎤🎤: *41-45 RAINA* *(The beautiful princess)* *STORY & WRITTEN BY* © *HUMAIRAH (Melody)* *BABI NA GOMA* Haka yaciro kudi yabata babu koh Jan aji bare godiya fita tayi tana mai mugun farinciki aranta Allah yakawo mata dauki “Daganin Aymel Dan gidan masu hannu da shuni ne, Suna da k'umbar Susa aiko kamar Goggo taji irin wannan abun arziki hmmm ai Aymel soyayya dakai ba fashi me akeda wani Fu'ad shid`in banza” ``` _Niko humaira saida cikina ya murda nace gwarama kenan wannan shine Bankad`an,_``` Da gudu tashiga gida tana kwalawa Goggo kira haka tafito xane a hannu sai fatari sai lalitar boye kudi wacce akasawa suna MATA SUNWAYE,🤣 “Lafya kiketa kirana saikace kin makance?” Tsalle takeyi nonuwan suna sama suna k'asa “Goggo hakarmu takusan cimma ruwa kinga wayannan kudin Uncle Aymel ne yabani wai insai sabulu in wanke kayana, kuma karya nayi Goggo rigarce ban ganiba”. Tuni ta anshe kudin tace “Haka nakeso yata takaina ai ina gayamiki saimun tatseshi mun kwalkwale shi tsaf kannan zamu sakeshi yasha ruwa, Ki maza kije ki siyo mana nama muyi dagwargwajiya” RAINA Tuni aka hau sukuwa da gudu taje tasiyo aranan su Goggo rai fes ba hawan jini ba ulcer bakincikin da namiji ya kwaranye, Da yamma lis Uncle aymel yazo ya aika aka kira RAINA ciki na kyarma ta mik'e zata zuba aguje, Goggo tadawo da ita ta dankwafar tace “yau naji yar iskar yarinya sai wani sukuwa kikeyi saikace wacce tasha baliyon( kwayar doki) tashi ki gyra tafiya sannan kinatsu bakije kiyita magana kamar injin din markadeba, Dan farin ma kin daina da rangwada”. Ya mutsa fuska tayi tace “Haba Goggo inayi mana kema kinsani haka tafita tana rangaji, sunan wata haleema Rangaji, Aymel tagani tsaye ya harde hannun sa jingine da mota wani murmushi yasakar mata abunda ke kara fito da zunzurutun kyawunsa, Aymel kyakkyawa ne ajin karshe farine dogo amma ba kwarai ba idanunsa farare kal kamar madara, Bakinsa kam jawur tamkar yasa chougzuh wani jambakine da yan China suke sawa, Gashinsa luf luf kamar bakarabe Amma zuciyarsa batada wani Alkhairi illah sharri, Kuma haka yasamo Asaline daga wajen iyayensa ganin shikadai suka Haifa hakan yasa suka kasa bashi tarbiya ta kwarai, “Barka da fitowa ya ma'abociya k'yau da kwarjini, ganinki kadai yana Sani nishadi ganinki yanasani zama wani sarki, Murmushinki kadai yana sanyaya zuciyana” dariya tayi taji wani ni'ima ya ziyarceta takasa boye farin cikinta ga hak`oran ta jawur sai doyi yakeyi banda kaxanta babu abunda Raina bata taraba duk talauci ai tasa gawayi da gishiri ta gurje bakin don haushi har na juya zan tafi naji muryar, Aymel yana cewa _“will you marry me”?_ Wani abune ya doki kunnena nayi saurin juyowa kafin yaci gaba da magana “RAINA kisoni Kiga gata kisoni Kiga yadda duniya zata sanki cikin k'ank'anin lokaci, Mahaifina gawur taccen mai arzik`ine gidajen mansa sunfi a k`irga duk sati a makka muke ummra duka gidanmu, sannan yace innemi kowacce yarinya zai auramun ita duk talaucin su don haka ki aminche in daukeki in kaiki birni ki gaida iyayena ” Nidai ina tsaye Nace wannan shine Zubit din amma Dana duba fuskan RAINA sai naga gaba daya ta rude chan kuma naga ta bata rai duban daxan kara mata naga ta turbube fuska, “Uncle Kaine mutum na biyu daka taba cewa kana sona bazan iya cewa ah ah ba amma akwai kudin aurena da Fu'ad, Basan yadda zanyiba kusan shekara biyu babushi babu labarinsa amma inaso kabani daga yau zuwa gobe zanyi shawara” Sallama suka yi ya d`auko kud`i naira Dubu goma yaba ta, Hannu na rawa koh godiya tana juyawa Aymel yace “Hmmm nagane laggon Ku kunada son abun duniya, toh kashin ku saura kad`an ya bushe don saina fanshe kud`ina ajikin ki RAINA” _*Gwarama kenan muje zuwa...........*_👌🏻 _*MELODY*_😍 [4/7, 6:26 PM] Melody🎤🎤: *46-50 👸🏻 *RAINA* *(The beautiful princess)*👸🏻 © _*STORY & WRITTEN BYHUMAIRAH (Melody)*_ BABI NA SHA DAYA Washe gari an tashi daga makaranta tafe take tana wasa da yatsunta, Sadiya tace “Raina daman inata so inyi miki magana yau naga gaba daya kin canza yadda kike walwala yanzu babu meye dalili?”Raina tayi murmushi tace “Sadiya tunani nakeyi wazan zab'a? Tsakanin Fu'ad da Aymel a gaskiya ina son Aymel yanzu fiyeda Fu'ad, tunda Fu'ad ya tafi yakasa koh sau daya yazo ya ganni baisan a wani hali nakeba shiyasa na yanke hukunci Uncle Aymel ya turo gidanmu muyi aure” “A gaskiya Raina idan kikayi haka kinyi tsantsar butulci kar kizama butulu mana ki tuna irin hidimar da Fu'ad yake miki amma ace saboda baixo ba zaki auri wani meyasa kikayi mishi Alk'awarin zaki rike mishi amana? Kiyi tunani dakyau ki tuna saboda ke ya tafi birni Neman ilimi don Ku tsira da mutuncin ku amma kiyi hakuri idan na bata miki rai”Sadiya tana gama magana tayi wayi hanyar gidansu batareda ta karabi takan RAINA ba. Tafe RAINA take tana lissafe lissafai horn taji Tuni ta juyo a firgice har Aymel saida yagane RAINA tana cikin tsananin tunani, packing yayi yafito yace “Dafatan lafya yadda naga kike tafe bakisan Wanda ke bayan ki ba, shiga mota inkaiki gida” Tsaye tayi don inzaa yankata batasan yadda ake bude motarba ga girman kai rawanin tsiya tak'i tace bata iyaba gajiya yayi ya fito ya bude mata motar ta shiga kannan ya shiga wajen direba, RAINA tayi kaman ruwa ya cinyeta saboda tsabar tsoro bata taba shiga motaba, Tuni ta fara rawan Dari saboda tsabar sanyin AC Allah Allah tayi su isa kofar gida, suna isa ya bude mata murfin motar tafito kamar wacce ruwa ya cinye ya dawo da ita, “Gimbiya ina sauraren amsa daga gareki saboda na kosa in kaiki ga iyayena” gyara tsayuwa tayi tana shirin magana k’watsam ta hangi Idi abokin Fu'ad. Tuni ta bata rai ta hade giran sama Dana k’asa ta isa wajenshi tace “Malam lafya kazo kofar gidanmu? Mekazo yi kallonta yakeyi ido cikin ido yana mamakin Raina ce take gayamai wannan maganan? Dariya yayi yace “Saboda kina tareda wancan matin ne kike wani hura hanci mtwww yaja tsaki kinsan ke kinyi kadan inzo wajenki banza Mara tarbiya Goyon mace gashi Fu'ad yace inbaki” Watsa mata kudin yayi yana huci yace “Yadda kikazo a wulakance haka ga kudinnan na watsa miki a wulakance banza yar Mara asali banda kaddara me Fu'ad zaiyi dake Taxi kawai motar kowa da bamusan Asalin angulu ba saitace daga missra ta taho” Fuuuu ya kama hanya zai wuce ta gaban Uncle Aymel Tuni yasamai kafa saiga Idi warwas a k'asa haka Aymel yayi biji biji da Idi harsaida mutane suka zo ceto saboda kar ayi kisan kai, kudin dake kasa ya kwashe yaciro kudi bansan iya yawansu ba yace “Gashinan” ya watsa mishi yace “Kasani Kaine Mara mutunci da ka kasa ganinta a matsayin kaddara wacce ta Riga fata, meyasa kuke sheganta abunda Baku San asalin zance ba bari kaji babu wani shege a fadin duniya kowa da ubansa da uwarsa Allah ne kadai bashida uwa bashida uba bai haifaba ba'a haifeshi ba” Miyau ya tofawa Idi sannan ya juyo yace “Gayamun abunda kikeso ki gayamun kam zuwan wannan garban?” Gyra tsayuwa tayi “Uncle Aymel na aminche zan aureka katuro manyanka zuwa gidanmu” Wani dadi Aymel yaji ya juyo yace “Wa yakeda suna Fu'ad kowa? Kace mishi yayi lissafin abunda ya kashema RAINA zan biyashi, sannan ina gargadinka banaso in k’ara ganinka bare fuskarka koh a hanya inba hakaba saina takeka da mota, duk abunda akeyi nida Aysha sayedi muna gefe kowacce ta rik'e haba tana jin karfin hali irinna Uncle Aymel. Haka sukaci gaba da soyayya kamar da gaske, har Aymel yasa ranan da Raina zata gaida iyayensa haka Goggo ta aminche, yayimata siyayya nagani na fada a gari komai too match, nikaina saida na roller. [4/8, 8:17 PM] Melody🎤🎤: *51-55* 👸🏻 *RAINA* *(The beautiful princess)*👸🏻 © _*STORY & WRITTEN BYHUMAIRAH (Melody)*_ BABI NA SHA BIYU A gari kowa gulmansu yakeyi yar makarantar da Raina ke zuwa bata zuwa haka kauyen Zangon Mati yaci gaba kowa kagani burin dansa yaje makaranta, Haka y'ay'a mata cikin kashi Dari kashi 85 sun rage talla, Babu wani Abu da iyaye zasuba yayansu Wanda ya wuce TARBIYA don shine ya kori komai a rayuwa matuk'ar kinbawa danki tarbiya toh kisani ko bayan ranki wallahi tamkar baki mutuba, saboda komai sukayi na Alkhairi ke za'a yabawa keda kika daurasu akan turba mai kyau, yau Uwar gida\iyaye ina dadi ace yau an wayi gari baki bakya numfashi Ace ga danki chan yana zagi koyana fada kinga kinbarmai abun fade babu abunda zai fito bakin jama'a sai suce ai Uwarsu ce bata basu tarbiya ba, wallahi koda Dan gaba da fatiha ne kika bashi tarbiya wallahi yaxama na k'warai zakiga yadda mutane suka sha'awarsa Alfaharinki ke uwa ki ba yayanki tarbiya saisu zama abun kwantance musammam yaya mata saboda sune rayuwarsu take cikin hadari wajen fuskantar rayuwa. Ranan wata ladi ne Raina ta shirya tsaf cikin lace mai ruwan madara sai shek'i yakeyi komai too Match Goggo tsaye take gwada mata yadda zatayi tafiya da magana idan taje gidansu Aymel babu komai aciki sai fitsara keda zaki ganin surukai har wani dama gareki babu wani kunya bare kunyan sarkin gari Allah kasa mudace, Raina da Goggo sunyi nisa ba'a cewa komai. “Goggo saimun dawo”Goggo ta rakata da d'umi fita tayi ta iske Uncle a waje sai dariya yakeyi yana kod'a Raina saboda kyau datayi, nikaina mai karatu ban ganeta ba saboda takoma Rainan gaske bata Zangon Mati ba, Suna tsaye mashine yazo wucewa da Fu'ad abun mamaki yaga raina tana shirin shiga mota da sauri yace mai machine ya saukeshi, cikin sassarfa ya Isa inda Raina take yana dariya “Raina kece haka Alhamdulillah gani na dawo wannan waye” duk a Jere yayi mata wannan tambayar tsawa ta dakamai tace “Dakata Fu'ad wannan da kake gani shizan aura shine annurin raina shine miftahul Qalbi na shine nake burin yaxama uban yayana, kafadi kudin daka kashe akaina abiyaka don ba talaka bane irinka, mai shiga rana yasamo” Da mamaki Fu'ad ke kallon RAINA cikin tashin hankali yace “Raina kar kiyimun haka” “Na nawama”cewar RAINA “Kiyimun rai idan kika rabu Dani raina ina zansa Kaine kece farincikina, RAINA zan iya rasa raina idan kikamun haka Raina kalleni nine masoyinki na asali Nina chanchanta da'in zama Uban yayanki, Kituna Raina munyi Alkawari sannan nabaki amanar soyayyana meyasa kike kokarin badamun kura a ido, kisani Allah dakansa yace duk Wanda yaci amanar wani toh tabbas Amanar Allah saita ci mutum, RAINA Alkawari kayane duk Wanda ya dauka burinsa ya sauke, Raina banida wani tunani sai naki ki taimakeni, Raina ciwonso bashida magani Wallahi Daganin wannan ba aurenki Zaiyi yaudarace tsantsa acikin idonsa” Kuka kawai Fu'ad keyi Wanda nikaina naso in tayashi don nasan zafin rabuwa da Masoyi babu dadi, Raina kuwa watsa mishi kallo tayi tace “Banida lok'aci haka ta shige mota batako saurari Fu'ad ba haka Aymel ya figi mota wani kurane ya tashi Wanda Tuni Fu'ad ya fadi kasa yana wani irin tari abunka gamai ASMA, Tuni mutane sukayo kansa aka daukeshi sai gida. ★★★★ Raina ce cikin mota suna tafiya banda k'yauyenci babu abunda take zubawa, Shiko Aymel yana dariya kamar yaga wawan zama, Da haka Raina tadinga murna ganin sun shigo cikin birni tsundum, Cikin garin Kaduna ne a Isa kaita road, wani layi mai suna kafur road, wani katon gidane Wanda ya amsa sunansa gida ya tsaru iya tsaruwa, babu ne kawai babu acikin gidan, “Allah sarkin dadi inji barawon mando” [4/9, 10:20 AM] Melody🎤🎤: *56-60* 👸🏻 *RAINA* *(The beautiful princess)*👸🏻 © _*STORY & WRITTEN BYHUMAIRAH (Melody)*_ BABI NA SHA UKU _*Wannan shafin nakune masoya RAINA Allah yabarmu tare Yakaremu da katewarsa Allah yayi mana tsakani da mugaye Amin Basira ce Allah yabani ba don wayona ba ko iyawana ba*_LYSM😍😘❤ Cewar RAINA dake tafe tana shafa bango babu kowa acikin gidan Dan ko motsin mutum guda banjiba bare na tsuntsaye, ciki suka shiga suna shiga wani Parlour Raina tayi wani ihu tace “Aljanna kenan” “Ah ah sweet ba Aljanna bace wannan cewa zakiyi Aljannar duniya ” Wani daki suka nufa banda batan baseerah irinta raina kiga gida Empty ai dole ranki yabaki wani Abu amma abunka da hakki Duk bata kawo komai ba “Waw home sweet home RAINA wannan gidanki ne ke kadai sai yaran dazamu Haifa Ki sakata ki wala kinga idan kika huta anan zuwa anjima saimuje gidan Mu idan yaso saimu koma Zangon Mati ” “hahaha Toh aiba matsala ni koh anan kabarni ainaje kauyenmu inba Sadiya labari dukda naga bakin ciki takeyi da soyayyarmu” Tashi yayi “bari inje insiyo miki abinchi da abun sha koh??????” Haka ta amsa ficewa yayi yabi kafur road gaban BT motors yasiyo mata naman rago daganan yasiyo mata abun sha tafe yake naga ya tsaya gaban wani chemist wallahi bazan iya cewa ga abunda ya siyaba, saboda acikin envelope akasa mishi. Gidan ya koma ya tadda raina zaune koh sallah batayiba bare salati, Sallah bata cikin agendan Raina saboda uwar dakinta batayiba bare tasata tayi, yar islamiyyan datake zuwa tasha ruwan waladaina, haka ya mik'a mata naman yakara ficewa haka taci tayi gytsa “Inama Goggo tana nan kusa dana kaimata ta dangwala Arziki” kan me karatu yasha ruwa yadawo karatu raina ta dinga k'wada uban hamma Wanda saida ta jera ashirin, daganan kuma bacci yayi shillo riya da ita don har garinsu Mardia takai Wato nijar, koh minti goma batayiba da k’wanciya Uncle Aymel yashigo wani dariya yayi na mugun ta Tuni ya ida mugun nufinsa akan RAINA saida tayi mata facha facha da gaba wani ya rantse yace wuk’a aka chacchaka mata yadda jini ke zuba ni humairah saidana tsorata tsigar jikina ta tashi nace bai dace a hada mazan dawaki waje guda da matan dawaki ba saboda tabbas za'ayi batatta, abunda yafaru yafaru haka uncle Aymel ya kadawo bujensa iska ya barta k'wance tana bacci kamar matatta, inta k'aitama mai karatu pills Aymel yabata Wanda ake sharan Awa ashirin da hudu ana gantali a sararin samaniya. Washe gari ne RAINA ta wastsake tasan me duniya take ciki kannan tafara kuka maikama da sautin wak'a, tana Kurma ihu saboda ganin halinda take ciki ba wuya tabbas yau ranar bakinciki ce agareta saboda abunda yafaru yafaru kuma abunda tarasa ta rasashi har duniya ta nad'e, “Nashiga uku ni Raina Allah Kaine gatana Goggo duk kece silar komai nashiga uku yanzu shikenan nazama bola a idon duniya kenan waiyo duniya Tabbas Allah ba azzalumin kowa bane sai Wanda yaso ya zalumci kansa, Fu'ad wannan ishara ce nagani tabbas dole innemi yafiya a gareka, Ashe gaskiya kake gayamun Dana Sani daban biyewa zuciyana ba Allah shizai isarmum tsakanina da Aymel” bata gama rufe bakiba taji ana bude kofa cikin sauri ta waigo tana kallon mai shigowa, wani k'aton mutum tagani baki sidik babu alaman rahma a fuskarsa, ga wasu majiya k'arfi a gefensa da alama take masa baya sukeyi, tsawa suka daka mata “Keeeeeee!?!!! In Wanda kuke tare dashi? Halama ke karuwarsa ce koh kwana wuni mukayi dashi gashi har kwana kukayi toh kudina zai bani ko kuma asan yadda za'ayi ” RAINA a tsorace takallesu tace “Wannan gidan na Aymel ne akan me zakuzo kuna kumfar baki? Dan Allah kuyi gaggawan fita inji da abunda yake damuna”wani daga cikin yaran yace “yarinya yaudaranki yayi kuma kisani bamu taba saninsa ba Dan garin Adamawa ne bakone zuwa yakeyi yayi holewarsa da yan mata yakara gaba ke karuwarsa ce koh” Raina tace “Wallahi niba karuwa bace” daganan dukta labarta musu komai mai gidan yace saiya fanshe kudinsa haka ya tube ya kara hayewa kanta ai Tuni RAINA ta daina numfashi. [4/9, 12:10 PM] Melody🎤🎤: *61-65* 👸🏻 *RAINA* *(The beautiful princess)*👸🏻 © _*STORY & WRITTEN BYHUMAIRAH (Melody)*_ BABI NA SHA HUDU Inda mutumin nan bai saurareta ba haka suma yaransu suka dinga hayeta inta kaitawa mai karatu nidai gani nayi har numfashi raina batayi, bayan sun kammala ne suka dauketa cik suka sata cikin mota gudu kawai sukeyi babu alaman zasu tsaya, awata maraba suka tsaya suka turo RAINA waje suka k'ara gaba koh tausayi babu, haka rana tagama dukanta daga bisani ta farka da kyar take tafiya duk Wanda tagani saita daga mishi hannu amma ina duniya tazama abunda tazama babu maison taimako, ana yar tsoron tsoro. Wani mutumine ya tsaya ganin halinda take ciki yayi matukar tausaya mata a yadda yaganta tana bukatar taimako, “Yan mata lafya meya sameki haka” Raina tayi karfin hali tace “Fyade wasu mutane sukayimun shine na farka naganni a bakin dajinnan ka taimaka kakaini wajen Goggo na inma mutuwa zanyi in mutu a gabanta” Mutumin achan kasan zuciyansa yace Dubi yarinya wacce shekarunta basu wuci sha takwas ba amma an lalata mata Rayuwa kaico duniya Tabbas da yata akayiwa haka na tabbata mutuwa zanyi daganin wannan yarinyar dakwai nak'asu a rayuwarta wajen rashin samum isassan tarbiya daga iyayenta sannan da rashin kula da yayan da Allah yabasu don muyi Alfahari dasu. Haka yataimaka mata tashiga cikin motan sannan ta gayamai inda zasu nufa Wato Zangon Mati, da shigarsu mutane sai kallon motar sukeyi cikeda tuhuma saboda motar bakin mudubi gareta, har kofar gida ya sauketa yashiga da ita Goggo na ganinsu tayi wata zabura tace “Raina lafya ina kika shiga meya sameki haka” Raina takasa magana illah kuka da takeyi maicin rai tasan cewa rayuwarta ta gama lalacewa, “Goggo abakin hanya na samu yarki cikin bukatar taimako shine na daukota nizan wuce amma inaso Ku kula da baiwar da Allah yabaku saboda Allah zai tambayeku ranan gobe ” Goggo tayi magana Tuni ya fice nan raina tace “Goggo duk kece silar lalacewar rayuwata a doron duniyannan kekika lalatani da son abun duniya har ya kaini ga sadaukar da rayuwanta amma tabbas namiji Dan kunama ne amma kuma tsakanina da namiji tamk'ar kifi da kaska zamu zama kura da nama babu sauran sassauci tsakanina da namiji sannan sainayi silar rusa ma duk namijin da yashigo Rayuwa, duk Wanda yashiga tarkona Allah kadai zai fiddashi badai mutum ba” tana gama magana ta kara rushewa da kuka Wanda aranta tasa sai kowani namiji yayi kuka da ita dago idanunta tayi jajaye ta mike tayi waje bata zarce koh inaba sai inda zata ga Idi da Fu'ad tabasu hakuri, ilai ta aika yaro bata ce injita ba saboda tasan halin Idi yana iya cewa bazaizo ba, Da isowarsa taji wani kyamar RAINA yakeyi “Lafya naganki koh koh wani sharrin kika kullo in nemi tsari dake?” “Ah ah Idi nazone kaya tani ba Fu'ad hakuri tabbas nasan ban kyauta mishi ba Dan Allah kataimakeni tabbas duniya ta rudeni Idi” dariya Idi yayi yakuma daure fuska. “Raina kenan yau da iska ta kad'a gashi munga takashi kaza, kin makara kinzo lokacin jirgin ya d'aga, inda kinsan halinda kikabar Fu'ad na tabbata saikin tausaya masa saida aka hada da rokon Allah kannan yasamu kanshi, yanzu dai duk labari yakare Fu'ad yana kasar India saboda gwamnati ta kaishi karatu kuma daman cewa akayi yazo yatafi da matarsa kinga yanzu kin lashe bai tafi da mataba amma zai dawo nan bada jimawa ba, dazu jirginsu ya daga RAINA adinga Sara ana duban bakin gatari, kisani cewa duk kyau rakumin dawa bazai kaiga na gidaba” Kafin tasamo abun cewa Tuni ya wuce ysbar ta tsaye da cizon yatsa, ai da gudu takoma gida koh zafi bataji tana shiga ta fad'a kan Goggo tana kuka sosai “Goggo nashiga uku inaxan sa kaina duniya nashiga uku meyasa rayuwata tazo da sabani kala kala, inhar jarabawa ce wannan inna yaci ace nafara cinta ba inta faduwa ba” “Raina kaddara ce kidauka” “Wane irin kaddara Goggo meyasa bataxo tuntuni ba sai yanzu tabbas nayi ladama akan wulakancin danayiwa Fu'ad nasan cewa baxai taba yafemun ba, nasan cewa Alhakinsa ne yake binmu”haka aka gama kakabi uncle Aymel dai yasha tsinuwa k'wando k'wando wajen Goggo haka ta gyra RAINA tadinga dafa mata sassaken baure da bagaruwa da ganyen magarya tana tsomata tana ihu haka akayi kwana bakwai kannan RAINA takoma daidai, tafara tafiya daidai, akaci gaba da rayuwa. [4/10, 2:52 PM] Melody🎤🎤: *66-70* 👸🏻 *RAINA* *(The beautiful princess)*👸🏻 © _*STORY & WRITTEN BYHUMAIRAH (Melody)*_ BABI NA SHA BIYAR ★★★ BAYAN WATA BAKWAI Raina ce tafito aguje tafada b'agirarran ban dakinsu tanata k'warai amai kamar wacce yan hanji zasu fito Goggo dai tsaye tayi tana ganin ikon Allah meyake shirin faruwa dasu Fitowan Raina ne Goggo taga tayi wani mugun fari goshinta sai kyalli yakeyi riketa tayi suka zauna tace “Raina lafya kike kuwa kodai ciki gareki?” “Idanma cikine inna ai basaikin tambayi inda na rakito shiba koh?” Inna tace “Watanki nawa bakiga jinin al'adan kiba?” Raina ta tabe baki ta cije tayi far da ido “Goggo kusan wata bakwai kenan banayi kwata kwata koh digo kuma sai inji nauyi a cikina gashi zazzabi nakeyi da dare” Goggo tayi salati tasanarda uban giji tace wannan wane irin kurman cikine? Toh yanzu zaibar duniya yanzu zan burgeshi ai abun gorin sai yayi yawa “Goggo babu inda zaki burgemun ciki haka kawai meyasa kafin ki haifeni baki burgeni ba kika barni ina rayuwa adoron kasa toh shima wannan cikin inaso kibarmun abuna in haifa ai babu Wanda baida uba kuma nasan ubansa haihuwa kamar nayi saidai idan yazo duniya ki maidashi yadda bakiji kunyan yin cikina ba haka nima bakaina farau ba kuma ba kaina karau ba” Kwaf kakeji Goggo ta bige mata baki “Toh kisani koh kinaso koh bakiso sai na zubar dashi” Daki tashiga ta hado abubuwa da dama cikin kwanon sha taba RAINA dole tasha cikin mintuna Raina tafara juyi kamar zata mutu chan saiga jini ya balle Tuni raina ta daina motsi Goggo ta rude a dagudu tayi makota, Allah yaso mijinsu yanada mota aka dauketa sai Asibiti Zangon kyauta, nan aka shiga da ita emergency akayi mata taimako Goggo sai muzurai takeyi kamar wacce tayi karya, likita ne yafito yace “Waye mijin wannan yarinyar?” Malam Musa yace “Likita batada miji budurwace fah” “Kace budurwace toh waye yayi mata ciki shi muke nema” nan Goggo taji kamarta nutse ga matan Malam Musa ai kowa saiya koma yar kallon kallo. Nan akace hantarta tasamu matsala sanadiyyan maganin datasha na gargajiya, sai anyi mata aiki ai Tuni Malam Musa da matansa suka bar asibitin haka Goggo tadinga tumami tana kuka maicin rai da zuciya, likita yace “Baba hakuri zakiyi wannan yariga yafaru kisamo kudi muddin kinaso yarki ta rayu” haka aka kwana biyu kwatsam saiga Fu'ad acikin Asibiti shida Idi ai Goggo wani kunya taji haka Fu'ad yabiya musu komai harda raran dubu Dari sannan yayi mata fatan samum sauki suka wuce, Anyi aiki RAINA tayi garas, kwanansu ashirin da hudu aka sallamesu garine yacika tundaga shigowarsu, “Inna lafya naga gari yacika kodai mutuwa akayi koh sarki ya kara dawowa ne?”Goggo tace wane irin sarki kuma mexaizo yayi? Wani suka tambaya akace musu Fu'ad ne Dan gidan mai gari yake aure RAINA tayi saurin cewa “Kana nufin Fu'ad ne yake aure wacece ya aura? ” Yaron yace “Sadiya ya aura yar gidan lanti mai kwakumeti yau zasu wuce Kasar India ma don naji ance achan yake aiki” Ai jinkin ta kaura yayi la'asar Ni HUMAIRAH nasan Fu'ad baxai auri RAINA ba saboda sun cutar dashi sun kasa gane cewa Allah shike azurta bawa sun manta cewa Allah ke fidda shugabsn k'asa daga mahaifar uwarsa, sun kasa gane cewa bawa da arzikinsa yake zuwa duniya, gida suka wuce cikeda kakabi haka Raina ta rame ta kanjame har cewa ake cutar zamani gareta, duk suka dode kunnensu. ★★★ BAYAN WATA DAYA Da asuba aka doka uban sallama goggo ta fita taga mai gari tsaye shida mutanensa “Sannun Ku ” “Dakata tsohuwar kilaki wakika maida yaro acikin garinnan babu yar data taba cikin shege sai yarki toh kisani zaman ki a garinnan ya kare karuwar banza karuwar wofi makira addababba kawai nabaki awa ashirin da hudu kibar gidannan idan ko kikaki sainasa anyi holi daku, kafa kafa muka taimakeki muka baki gurin zama amma kingawo mana annoba zata bata mana tarbiyan yaya, tsohuwar yar bariki toh ki kara gaba ” Raina dake bayan Goggo dukta gama jin abunda mai gari yafada ta kutsa ta tsaya a gaba cikeda tsiwa da tashanci tayi guda tace “Tafi nono fari maigari baka burgeni ba dakace awa ashirin da hudu naso kace yanzu Mu tattara yanamu yanamu da sai ince koh zaka tayamu daukan gidan, don nasan siya mukayi da kudi toh kasani in kaga munbar garinnan sai munsamu mai siyan gidan an bamu kudi kannan mutafi, Dakake kirana shegiya naji labari matarka itama yar k'wararo ce don haka karka cire rai da sumun shege koh shegiya, duk mai zagin Dan wani shima saiyaga jarabawa, Maigari adinga Sara ana duban bakin gatari, wannan Abu tamkar saukar malkade muna jira ayiwa gida kudi Mu kara gaba” tsaki RAINA taja tace “Goggo Mu shiga daka ciki” [4/11, 4:39 PM] Melody🎤🎤: *71-75* 👸🏻 *RAINA* *(The beautiful princess)*👸🏻 © _*STORY & WRITTEN BYHUMAIRAH (Melody)*_ BABI NA SHA SHIDA Haka Raina taja Goggo data kasa cewa komai abun duniya ya isheta, shiko magari tsaye yayi yace “kumu tafi daman barewa batayi gudu danta yayi rarrafe ba shine da Fu'ad yake shirin jajibomun irin tsiya irin jaraba da haka zata dinga tsigeni nida marwa” haka suka koma Tuni akayiwa gida kudi Fu'ad ne yasiya har naira dubu Dari biyar badan komai ya siyaba saboda RAINA dayasan cewa duk abunda yafaru da ita daga Allah ne amma yajin baxai iya hada zuria da RAINA ba, haka aka kaimusu kudi washe gari tunda duku duku suka tashi basu sauka koh inaba sai Wani gari *Dinya* Gaba da SOBA inda akwai matattaran karuwai da masu zaman Kansu, haka suka samu hayan daki daya k'ato suka sai katifa Dadai sauran kayan aiki, nan RAINA tafara baje gwanjon tsiya itada yan gidan saboda samari suna kawo mata bara cewa suna sonta ita kuma kowa yitake dashi, indai zaka sak'ar mata kudi yan dubu dubu farare, Goggo itace magajiyarsu itake ba RAINA duk wani salon yaudara da samun kudi Haka basu zauna ba wajen bin bokaye don Neman sa'a, Raina koh tajik'u sosai da mugunguna don tace bariki tun ina k'arama na iya toh yanzu nasa kafa wancan sharan fage nayi, kowacce mercy kallon docas nake mata, Goggo batada wani buri saina ganin Rayuwar raina ta Daidai ce saboda kin jininta da Tayi tun zuwanta duniya kawo yanzu. Raina dai tazama abar kwatance a gari tazama maiji da kanta a shekara Ashirin RAINA ta mallaki gida da mota Wanda babu kamar sa acikin garin soba da kewayenta haka bangare daban tayiwa Goggo sannan aka girke rikakken malami koh ince boka, Shike mata aiki don duk namijin daya kawo kansa gidan Sunanan sa sorry don bata amsan kudi a hannu sai Check dukda ba arabi ba boko wani yaga Raina zaice tayi digiri harda digir gir Abu yayiwa raina yawa ga sata ga maita, ga zina ga madigo babu Wanda batayi Alhaji bello shine Wanda ya tsarewa RAINA komai na rayuwa sannan ya hanata mu'amala da kowa wata rana k'watsam Matarsa takira shi don taji rade radin ya ajiye karuwa, kin dauka yayi saboda tsoro, RAINA tana kwance daga ita sai yar shimi sai pant nashiga Swimming pool ta dauki wayar ta kara a kunne “Hello Ranki ya Dade uwar gida saurautar mata mai suna biyu lafya mijin naki bacci yakeyi pls kiyi hakuri zuwa gobe koh jibi don banison takura bare damu” Kafin matar tace wani Abu an kashe wayar gaba daya haka Raina tafada kan jikinshi tana shafa mishi katon cikinsa tana mishi hirar love shiko Tuni ya sakankance yabada kai bori ya hau yana gamawa yashiga wanka yace zai wuce RAINA tace “Miliyan daya nakeda bukata inaso zanyi yan wasu hidimomi ne kafin ka dawo daga England koma Mu wuce tarene?” Alhaji yayi dariya “Hmmm RAINA kenan sonki kawai nake kaunarki tana dibana mezai hana mutafi tare Visa akayi mata rana guda saboda dakwai kudin haka suka wuce kasar England saida suka Shari wata daya suka dawo, Ni humairah nace Raina tauraronki yana haskawa yanzu toh wata rana saiya dusashe yakoma hasken gulob daganan hasken rechargeable gaba gaba harken fitilar kwai sai kuma na aci balbal mai hayaki sai kuma dundim, komai yanada lokaci Allah yasa mugane ngd Allah daya bani iyaye masu kula ba irin Goggo ba daman batasan zafin haihuwa ba sannan batasan zafin lalacewar rayuwar da ba, zeenert ce kishingide akan kujera tana waya tana gamawa ne RAINA tace “Zeenert kenan dole in tsula tsiya yadda nakeso saboda inada wacce ta tsayamun sanadiyyan Uncle Aymel rayuwata ta lalace sannan kinsan wacece silar? Goggo, babu wani makircin daban iyaba babu salon daban iyaba zeenert Abu daya nakeso shine a duniya yanzu in Sani waye ubana sannan yar wace Garice ni haryau Goggo taki gayamun amma nasan wata rana dole ta sanar dani komai” Zeenert tace “Tabbas kuma ai ranar wanka ba'a boyon cibi” “Maganarki dutse yar uwa ” [4/12, 6:55 PM] Melody🎤🎤: *76-80* 👸🏻 *RAINA* *(The beautiful princess)*👸🏻 © _*STORY & WRITTEN BYHUMAIRAH (Melody)*_ BABI NA SHA BAKWAI _*I DEDICATED THIS HUMBLE PAGE TO ALL ONLINE HAUSA WRITERS MOST Especially my noble once Aneesa AR, Aunty SIS💞, Umma yahya Goyon kaka, Fatty Azland, Samrah, Hajja ce, Firdausi sodangi, Fatima Nashuka, Jannart, Asykhaleel, Xarahbukar, Ummi Aysha, Miss XOXO, Mjay, Husnat, Abeeda, basira, Mrs umar, tytrlorh, Aisha sayedi, Lots of more Tsintsiya madaurinki daya🤝LYSM😘😍 you ladies are wonderful😄*_ Cewar Raina haka taci gaba da kazan tacciyar Rayuwa wacce kowa yake gudunta ita zina bashi ce kowa yacita saiya biya koh ba jima koba Dade, faden Allah ne yace “Ku kare iyalinku da zuri'arku daga halaka ” sannan yace “Mukare farjojin Mu daga zina” amma ina wasu basu ganewa sukanyi Zina kamar baza'a mutuba, yanzu Zina taxama ado baga matan aureba baga yan mataba hatta samari musibar dake dawainiya Damu kenan, meye ribarki yar'uwa idan kinyi zina? Kudin za za'a baki dabai zaisiya miki daraja a idon mutane ba, bare sabulun dazaki wanke kaxantar data zuba ajikinki, mezaisa kiyi abunda kike boyewa mutane Dakin gansu ki boye saboda kar ace anganki muji tsoron Allah tun kafin lokaci ya k'ure. Dambe Raina take kwasa itada wani saurayinta, datakai mai ziyara yaci bai biyaba, tadinga gwanjon siya Akan titi kowa yana kallonsu gashi ta chukume mishi kwalar tiga ta rikemai wando “Wallahi saika bani kudina aiba a banza zaka hayeni kaki bani asiba nidai zamuga mai naci” Wani magidancine yazo wucewa yaga mutane sun taru sai dariya suke musu “Baiwar Allah meye ribar dambe da mijinki a titi?” Mutane suka fara ihu ba mijinta bane dadironta ne. “Wa'iyazu billah Allah ya shirya haka sukaci dambe tundaga ranan Kasuwar Raina tadawo kasa babu wasu samarin arziki sai yan kuci kubamu, Goggo koh babu alaman ladama illah kara tunzura RAINA zuwa aikin assha, daga karshe gidan aka siyar suka koma daki daya suci banxa suci wofi, daga karshe wani Dan masu kudi yazo da niyyan zai auri Raina lokacin tanada shekara 22 a duniya, Amma kema dagas tak'i amma *Farid* yanace saboda auren dole za'ayi mai shikuma yace gwara ya auro karuwa mai zaman kanta ya shiryar da ita suci gaba da rayuwarsu ta so da kauna. Goggo taga kudi Tuni ta zuge Raina da shawarwari haka aminche, tafara zaman istibra'i harna tsawon wata Uku bata zuwa koh ina amma fah acikin duhu takeyi saboda babu wani Neman tuba datakeyi, saidai taci tasha tayi bacci babu sallah babu salati, *Farid dai Dan gidan Ambassador GARBA BUBA ne Hamshakin mai arzikine kyakkyawan mutum ne son kowa kin Wanda yarasa, Sun hadu da Raina ne a filin jirgi dake mumbai lokacin datake shirin zuwa K'asar India don Neman Fu'ad Dan gidan mai gari amma haka tagama holewa ta dawo, danginsu Farid babu talauci gasu da kyau kamar su sukayi Kansu ga isa da iya MULKI, shiyasa aka hada Farid da farida aure saboda shakuwar da sukayi kowa ya dauka soyayya sukeyi dukkansu basuda buk'atar juna shiyasa suka bijirewa iyayensu akan cewa babu wata ALAK'A a tsak'aninsu illah so na yan'uwan taka, Mazauna garin Kaduna ne a malali sukeda zama, haka Farid yasanar da farida cewa shifa yasamu mata Farida tayi murna tace “me sunanta?”Farid yace “Nawa zaki biya don sunanta mai tsadane”tuni ta marairaice tanaso tayi kuka nanya sanar da ita cewa Sunanta RAINA* Tsalle Farida tayi tace “Wat a Nyc name bro kasan ma'anar sunanta kuwa?” Farid yace “No saikin fada” “Beautiful princess” wani dadi yaji yace “Amma fah xan gayamiki gaskiya Raina zaman kanta takeyi da itada Goggonta inta kaita miki wannan zance basan waye ubanta ba kinga koh akwai bikin zuwa babu zani, acan wani gari take kibari zuwa jibi zamu kiganta” Farida tayi murmushi sannan ta figi Motarta sai gida. Farid ne tsaye cikin falon mahaifinsa yanata kaiwa da komowa Chan yaji motsi har kusada stir case din benen yaje tarbo mahaifinshi, “Barka da fitowa Daddy Allah yataimakeka, zama yayi akan cushion shiko Farid ya durkusa yace “Daddy daman inaso in sanar dakai cewa nasamu wacce nakeso zan aura Ku gafarce ni daddy nasan cewa nidane nagari amma kudubamun Kuga halinda zan shiga Farida tanada Wanda takeso kuma babban abokina ne baxan iya aurenta inci amanar Abokina ba pls daddy kaikadai ne zaka sharemun hawayena daddy save the poor little boy pls” Wata muryace ta katseshi da cewa “Farid inhar Nina haifeka saika auri Farida itace matarda naxaba maka do or die saika aureta” “Dakata Hajiya tasallah abunda Farid yakeso shiza'a yimai koda karuwa yace yanaso zan auramai matukar zai sanyata hanyar da Allah ya tanadar ma kowani mumini” “Alhaji baxan yarda ba”shikuma Yace “Bazan dauka ba danane inada right akansa narigada na gama magana saboda yakawomun duk wasu dalilai nasa kuma na yarda dasu na aminche aure kuma rana ansa sati biyu kifara shiri” [4/14, 7:37 PM] Melody🎤🎤: *81-85* 👸🏻 *RAINA* *(The beautiful princess)*👸🏻 © _*STORY & WRITTEN BY HUMAIRAH (Melody)*_ BABI NA SHA TAKWAS Juyawa tayi afusace yashige daki tana keta uban zufa “yanzu ni Farid zai watsawa kasa a ido lallai saina hanashi kwanciyan hankali acikin gidansa muddin ina raye” Wayarya ce ke kara tana duba tankamemen Screen din iPhone 7 dinta taga ansa unman Farida gabanta yafadi tace Allah yasa ba sun fasa bane don inkan bakana, karaf ta dauka tace “Hello hajiyar Allah ykk ya sirikata?” “Hajiya babu lafya fah Farida tace itafa batason Farid tace itafa tanada Wanda takeso tace do or die aure tsakaninsu da Farid babu gata tanata masifa tana farfasa kayan gida” Jikake tas tas tas Ni humairah dake labe don kar a jehomun flower vase ai tuni na fita aguje, katse wayar sukayi kowa yana jimami, Tuni suka shirya sai garin Dinya inda RAINA suke zaune dayake sunbar gidan karuwai, Raina itace karuwa mai ladabin kunama, RAINA yayi musu girki kala kala iri daban daban amma babu dadin sisi bare kwabo, Haka akayimusu tarban girma, tunda Farida taga Raina taji gaba daya ta kamu da sonta tana jinta tamkar yar'uwarta tajini haka sukayi hira mai kwantar da zuciya, Farid kuwa saboda tsabar kwaliyan RAINA har kasa magana yakeyi bare yayi mata kallon minti biyu ji yake kamar ya dau hannu ya tabata, Raina dai jar fata ce son kowa kin Wanda ya rasa siririyar fuska gareta ga saje ta kowane gefen fuskanta, Bakinta bawani karami bane kamardai nawa, hancinta shima Dan daidai Wanda za'a iya misaltashi da dogo amma ba kwarai ba, idanuwanta kanana kamar maijin bacci, sannan sun danuwanta kamar na maciji yayi shape sosai, Raina dai baxamu kirata gajera ba haka baxamu ce mata tanada tsawo ba tana tsaka tsakiya, gashin kanta baida wani yawa bacin acuci datakeyi ai sai a gudu saboda kamar hammatan San iska yake, Wannan kenan. Misalin karfe uku Farid yace “Princess zamu wuce duk abunda muke ciki zakiji sannan karkiji komai sannan ina umurtanki dakiji ki kiji saboda akwai wasu matsaloli, haka sukayi Exchange din number da farida suka wuce sai Kaduna, Fitarsu keda wuya Raina takoma ciki tace “Goggo yanzu yaxamuyi kina tunanin kezaki amsa kudin aurena kamar yadda kika amsa na Fu'ad? ”Goggo tace “K'warai nizan amsa Susan cewa ke mara galihu ce Mara usuli bare tushe, koh kinada Wanda zai amsane bayanni?” Goggo ce ke magana cikeda iko da isa da MULKI Raina tace “Goggo kinsan cewa mulki baxai kori SARAUTA ba? Kinsan da haka toh inaso kisani baki isa ki amshi kudin aurena mutukar bazaki nemomun ubana ba saboda ba kimata bace bare daraja ace kece zaki amshi kudin aurena baxai taba yuwuwa ba, idan kuma kince ah ha maxa ki nemomin mahaifina, nasan cewa bazai ki jininsa ba”Tuni Goggo tafara ba RAINA hak'uri tana lallashinta haka Goggo tasamo mutane uku Wanda sune suka amshi kudin saboda kimarsu da darajarsu saida Ambassador Garba Buba yayi musu kyauta, Sadaki dubu dari aka bada da akwatina guda goma cikeda kaya. Bayan tafiyarsu ne Goggo ta fito daga inda ta boye ta amshe kaya tayi musu godiya abunda yabata musu rai kenan, har saida kyauta ya tsaidata yace “Me kike nufi tsohuwar kilaki koh kin manta yarda mukayi ne miko” Hannu ya mikawa Goggo haka ta debo kudi tabasu adai rabu lafya, Ranan sati biyu akasa sannan a masallaci za'a daura auren, Bayan k'wana Uku da kawo kaya hajiya tasallah tamatsa sai ankaita taga Raina sannan hankalinta zai k'wanta, Farid bashida yadda zaiyi haka yakira Raina yasanar da ita komai haka ta shirya cikin tsadadden lace tayi makeup komai yaji, Sauraren zuwansu Farid kawai takeyi, Dazasu wuce saida farid yabiyata gidansu farida yace tafito su wuce tare, sai garin Dinya. “Farid wai ina kuke shirin kaini ne kar dai kacemun yarinyar anan take?”saboda yana tuki yarasa wace irin amsa zai bata shuru yayi baice komai ba “Farid magana nakeyi kayi shuru”? “Hajiya me kikeso ince miki kinsan dai Asalin kowa kyauye don wannan garin birnine akan wasu kyauyukan” tundaga haka bai kara cewa uffan ba farida kuwa Adu'a kawai takeyi kar umman farid ta wulakanta RAINA don raina bazata raga mataba saboda yar bariki ce. [4/14, 8:06 PM] Melody🎤🎤: *86-90* 👸🏻 *RAINA* *(The beautiful princess)*👸🏻 © _*STORY & WRITTEN BY HUMAIRAH (Melody)*_ BABI NA SHA TARA Da isarsu Hajiya tasallah ba abunda takeyi sai yatsina fuska ta window raina ta hangi matar acikin ranta tace kindade baki yatsina fuskaba Daganin matar nan yar bala ce amma sainayi maganin iskancin mata ciki suka shiga sukayita k'wada Sallama ta fito tayi musu sannu da zuwa suka shiga, kan Chinese carpet suka zauna hajiya sai toshe hanci takeyi Farid sai kyafta mata ido yakeyi amma ina koh kallon bai isheta Raina tace “Ina wuni hajiya kinzo lafya”? Hajiya tasallah tace “Daban zo lafya ba zaki ganni wannan wane irin dakine farid saikace Masai sai doyi takeyi, wannan ai saiya janyo maka cuta akasa gane maganinta a Asibiti. Ai tuni Farid ya dafe kai saboda tsabar kunya farida kuwa arsnta tace ai nasan a rina, Raina tacika da mamaki k'warai bin Hajiya takeda wani shu'umin kallo tace “Hajiya ga ruwa ga abinchi” ai tuni Hajiya ta watsawa Raina ruwan da abinchin Raina tayi dariya lokacinda Farid ya tashi don zuwa kusa da ita tace “Basaika zoba Farid dadin abun mulki koh arziki baya tasa SARAUTA gaba saidai SARAUTA tasa mulki da Arziki gaba, Farid kai nakeso ba mahaifiyarka ba Kaine jin dadina ba wannan matarba, karkace naji haushi ah ah kodaya don na fuskanci Rayuwa wacce tafi wannan zafi dacin rai, Sannan kisani Duniya tafi bagaruwa iya jima, Ban nufin kowa da sharri sannan bana saka sharri da sharri sai in tura takai bango”. “Farid daman irin wannan yarinyar zaka auro harta zama surikata toh bazata sabuba bindiga a ruwa, wane ni da daura zani uwar miji na yawo tsirara. Fuuu ta fice batareda ta koh waiga ba kafin su gama rarrashin Raina ai hajiya tayi Nisa suna fita da mamaki babu ita babu labarinta, haka sukaci yawo wajen nemanta amma babu ita babu labari Raina aranta tace “Yar iskan mata haka kawai ki addabi mutane wallahi danice baxan nemeta ba saidai ta bace mtwwwwww” Nikoh HUMAIRAH nace Raina ba laifinki bane bakisan dadin uwaba bakisan soyayyar uwaba shiyasa kike tunanin kowa ya wulak'anta uwarsa.. “Farida Princess gaskiya daganan I can go beyond nan wajen am tired so tired yakamata Farida mukama hanya saboda bamusan abunda zai faru da hajiya ba” Kallon Raina yayi cikeda so da k'auna yace “bari Mu tafi kinji saura dakwai kudi Dana ajiye miki banda bukatan komai na kayan daki ke nake bukata ranan daurin aure da'an daura kisa aranki zamu wuce kaduna, Goggo kuma nasama mata gida ita kadai Sannan na bude mata shago Wanda zata dinga siye da siyarwa, RAINA believe me you are my destiny you are my life I love you toh the moon and back” Pec yayi mata yashiga mota Raina sai daga musu hannu takeyi, haka ta gyra kanta iya gyra amma sabo daban yakeda second new (Wato tsoho) amma Farid ya yarda ya aminche daduk yadda zai sameta, Da isarsu gida farid ya kutsa hancin Motarsa cikin gida abunda ya tada mishi da hankali shine ganin fuskar kowa na gidan babu fara'a babu walwala, lokaci daya taji gabanta ya fadi tafiya sukeyi kaman kwai ya fashe musu aciki wucewa sukaje yi Ayman daya kasance Yayan Farid yace “Dakata Mara mutunci Mara tarbiya zaka bige a yarinya fitsararra, wacce batada wani usuli yar cikin shege” . Lokaci daya cikin k'araji Farid yace “Karka sake Yaya karka kuskura ka sheganta mun mata ita nakeso kuma ita zan aura, Ku kukace inbidi mata kuma nasamo sai kuma yaxama abun gori Duk abunda Raina tayiwa hajiya ita taso kuma ta siya da tsabar kudinta don haka let me be on my own after ol inada madogara idan kukace inbar gidannan zan Bari koda kuwa yin hakan sabo ne yaya na gwammace in dauwama cikinsa” Tas tas kakeji Ambassador Garba ne ya kwashe Farid da mari yace “gobe za'a daura maka aure kuma a gobe zakabar gidannan don naga abun naka harda cin mutunci” Farid yarike kunci yana zubda hawaye yace “Nagode kwarai daddy nagode da duk wata dawainiya dakayi dani daga haihuwa zuwa yanzu Allah yasaka muku da Alkhairi nagode” wucewa yayi yasamu wayar mahaifinsa yayi transfer din kudi naira Miliyar Goma ya ajiye kamar baiyiba, Sannan yashiga daki ya hada komai nasa Farida sai kuka takeyi Rumgumeta yayi yace “Takwarata kar kiji komai Allah yana taredani a duk inda nake kuma jihadi zanyi na auren Karuwa mai zaman kanta, kuma ta dalilina indai me shiriya zata shiryu kukanki yana dagamun hankali” Shuru Farida tayi nadan lokaci a inda take sauraren wayarda Farid yakeyi tasan bada kowa yake wayaba saida RAINA, [4/16, 8:05 AM] Melody🎤🎤: *91-100* 👸🏻 *RAINA* *(The beautiful princess)*👸🏻 © _*STORY & WRITTEN BY HUMAIRAH (Melody)*_ BABI NA ASHIRIN _*ASSALAMA DAFATAN ALKHAIRI GA MASOYA JINNINA GA MARUBUTA, Dayawa mutane sunamun tambayan cewa meye dalinlin dayasa bana cikin kowacce kungiyar ta MARUBUTA? Dalili shine banida ra'ayi sannan ban fiyeson gutsuri tsoma ba koh kuma munafunci shiyasa na kiyayi kaina Saboda I don't want to be Dis-honoured🙅🏻 But tunda dayawa suna zancen yakamata inshiga zan shiga Wanda ya dace Idan kuma mutanen ciki zasu amincemun zanji dadi, sannan kohda ban shiga wata kungiya ba inada Manyan marubuta masu bani sha'awara daga cikinsu Akwai ANEESA AR sannan da dadewa akwai RASHKARDAM, Haka MIEMIEBEE she was one of the best, Sannan ga Uwar Arziki AUNTY SIS💞 Akwai ILILEE the chief baker😜 ALLAH YASA DAYAWA SU FAHIMCENI👏🏻.*_ #ANAMUGUNTARE😍😘 Washe gari haka aka daura auren Farid da Raina bikin bawani armashi abokansa dai duk sunyi mai kara sunzo kowanne cikinsu saida ya yaba da kyau irinna Raina, sannan sunga tsantsar SARAUTA acikin idanunta, motoci ne nagani nafade bayan kowa ya watse ne Ayman yace “Mijin karuwa inada buk'atar mukullin motarnan saboda kasan da cewa yanzu you are not part of us” Damamaki Farid yace “Bakada hurumin amsan mota a wajena my man yafadi tareda dafashi, don bakai ka siyamun ba kabari Wanda ya siyamun ya amsa my people if you guys are ready muje kafin sugama shiryawa” Kad'a kansa yayi shida abokansa sukabar Ayman tsaye, misalin karfe hudu zukazo daukan amarya, haka Goggo tadinga yiwa Raina hudubar k'anzon kurege da matacce da rayayye itakoh raina wani kasurgumin tunani takeyi wai itace tayi aure shin meye aure me aure ya kunsa? Duk wayannan tambayoyin ni HUMAIRAH nace bansaniba Raina saikin shiga zaki tantance komai. K'awarta zeenert itace ta rakata har garin Kaduna, a bypass gidanta yake babu ne babu acikin gidan komai yaji daidai ruwa daidai kurji, haka zeenert ta wuce nata waje acikin garin kaduna, abokai duka suka k'ara gaba, daga Raina sai Farid hankalin farid ya k'wanta “Amarya bakya lefi yau gaki a sabon waje dole muyi hakuri da juna dole kiji kiki ji, yanzu inaso inyi miki wasu tsmbayoyi gameda Addini xaki bani amsa yadda yakamata daga bisani saimuyi Sallah Mu godewa Allah daya nuna mana wannan rana” Ras Gaban Raina yafadi don tasan cewa kashinta ya bushe don babu abunda tasani, Farid ne yaci gaba da cewa “Amarya raina inaso kimun Karin bayani gameda wankan tsarki Sannan sunnoni da mustahabban Sallah, Sannan da farillai saikum hukunce hukuncen musulunci”? RAINA tayi kwalkwal da ido tarasa abunda zatace yau k'ayarta ta k'are, Shuru tayi nadan lokaci daga bisani ta sauke girman kai “Farid bazanyi karya donka soni ba a gaskiya banida wani Sani dangane da tambaoyinka , k'yauyen Dana tashi bamuda makarantar islamiyya bare na boko yadda ka ganni haka nake, fanko na sai tarin jahilci don haka inaso ka koyardani komai gameda Addina musulunci” Farid yayi mamaki k'warai _*ni humairah nace Tabbas da'ace maza da dama idan sunyi aure suna tambayan matayensu irin wannan tambayoyin da suka shafi addini toh da yanmata dayawa sun rage girman kai sun koma mak'arantar islamiyya don samun ilimin addini don dayawa yanmata basu damuda zuwa islamiyya ba, sai kallo da karsnce karance toh kusani komai yanada lokaci mutuk'ar munaso Mu tsira da mutunci mu, gidan aure ba gidan shargalle bane zamane na har abada Sannan ibada ne, aure is not all about eating food, having sex all day all night, Sleeping and also gidan aure is not a club wajen gulma da tsegumi, dayawa mata basusan wannan ba, Allah yasa mudace da mazaje nagari Amin.*_ “Hmmm RAINA kenan naji dadi k'warai dakika sanar dani zan koyar dake komai gameda musulunci haka suka kashe wannan dare wajen fadakarda Raina abubuwan dasuka shafi wankan janaba haila dadai sauransu, Sannan suka gabatar da sallah Sannan Yakama gashin kanta yayi mata Adu'a yakori duk wani sharri daxai fada musu, Sannan Raina ta canza kaya duk kunyarsa takeji, ni humairah nace Ashe yan bariki Nada kunya? Kwanciya tayi shima ya k'wanta ya rugumeta ajikinsa haka yadinga sarrafata daga bisani raina tafara baje nata baseerah, A wannan dare sun farantawa juna rai gashi yadda farid yake tunani ba haka bane, tunda Asuba Farid ya tashi ya samusu ruwan zafi sukayi wanka raina ta sauya kaya. Haka raina taci gaba da bautar aure kudinda Farid yake takama dasu komai ya kare basuda komai gashi kowa ya juya mishi baya, Raina Kullun faranta mishi rai takeyi haka zaije yayi dako yaciyar da ita amma duk bata damuba, har aka koresu daga gidan dasuke saida nayi musu kuka, amma hakan baisa farincikin su ya gusheba, daki daya suka samu a unguwan nufawa nan suke zaune dayake ba tsada duk wata Dari biyar ake biya amma wani lokacin sai farid yakaiga cin bashi gashi abokansa duk sun gujeshi bashida kowa sai Allah saikuma raina da farida. [4/16, 7:56 PM] Melody🎤🎤: *101-105* 👸🏻 *RAINA* *(The beautiful princess)*👸🏻 © _*STORY & WRITTEN BY HUMAIRAH (Melody)*_ BABI NA ASHIRIN DA DAYA _*Dedicated to Fatima(Maman Beauty) From Kd Tnx for the love and care, And also masoya na over the world i shout out my greetings😘😘😘*_ Yasaida komai nashi bashida abun tunk'aho gashi babu wani abu da iyayensa sukeyi akai, haka zaman su yaciga babu tsana bare tsangwama, Raina ce zaune itada matar wani mai kudi a kusa dasu wacce suka kulla k'awance don har abun Alkhairi takewa raina, “Jamila babu abunda yakai aure daraja, nayi bariki tun ina yar k'ank'anu wata amma wannan Rayuwan da nake ciki tafimun komai dadi mijina yana sona yana mun komai Wanda bai gazawa karfinsa ba, dalilina iyayensa suka gujemu suka daina yimishi komai saboda ya aura karuwa” kuka raina takeyi Wanda ni Humairah nace da ace Raina kinsan koke wacece wallahi dabaki damu kanki ba, amma muje zuwa mahaukaci ya hau kura. Jamila ta tsareta da ido tace “Raina dakinsan irin wahalar danake sha cikin gidannan sai kinyi mamaki Raina nasan zakiyi tunanin cewa mai Jamila tarasa dazata damu kanta kanta babu abunda Abban Abrar bayamun daga sutura, abinchi, kayan more rayuwa duk akwai amma narasa farincikin mijina, babu kwanciyan hankali bakin cikin yau daban na gobe daban ga kudi ga arzik'i amma idan babu farinciki Raina duniya takan zamemun Wuta nikadai nasan abunda nake fuskanta, idan Abban abrar ya mula sai inyi wata uku bansa shi a idoba, wallahi Raina na gwammace irin rayuwarki da tawa”. Raina tace “gaskiga Ummin Abrar ganin miji kusada kai wani niima ne na daban Wanda bakowa yasani ba, amma dayawa mata sunfi ga kudi koda miji bayanan, nima ina daya daga ciki amma yanzu nasan meye duniya take ciki, dole idan mace taci takoshi ga kudi ka abubuwan more rayuwa amma Dole ta nemi namiji a kusada ita matukar tanada lafya Ummin Abrar Kiyi hakuri komai yayi farko zaiyi karshe kiyita yimishi Adu'a Allah ya dawo miki da natsuwan mijinki gareki toh Tabbas zakiga abun mamaki Allah maji rokon bawane.” Ummin Abrar tayi mata godiya sannan ta wuce gida fitarta keda wuya Farid yashigo kayan jikinsa kacha kacha kamar Wanda yayi dambe da kura gaban Raina ya yanke yafadi da gudu ta nufi inda yake tana kare masa kallo shiko Farid yakasa kallonta “Mijina daga ina kake suwaye sukayi maka wannan ta'asar? Me kayi musu? Kayimun magana don ina iya fito nafito daduk Wanda yayi maka wannan raunin”? Kallonta yakeyi ido cikin ido tausayin Raina kawai yakeji “Raina muje daki zan gaya miki komai” ledar hannun sa ta amsa suka shiga Daki zaunar dashi tayi ta zauna a gabansa ta zabga uban tagumi yace “Akan hanyata nadawo wa gida ne nahadu da gungun matasa suka k'wace Dan kudin dana samo sannan suka yankamun gefen wuya amma saida mukayi damben mutuwa daga bisani sukaci nasara kunsan ance sarkin yawa yafi sarkin karfi” Raina ba k'aramin tausayi yabata ba haka tasa ruwan dumi tagasa mai jiki haka sukaci kanzon tuwo data jik'a suka k'wanta. Washe gari Farid yatashi da k'arfinsa dukda yankannan baisa yaki fitaba Dukda Raina bataso ba haka itama zazzabi ya rufeta bayan tafiyarsa, sai uban amai take kwarawa kamar da bakin k'warya haka mutanen gidan babu Wanda yace bari yafito, Ummin Abrar ce tashigo kwatsam da gudu ta isa wajenta tace “RAINA da lafiyarki kuwa irin wannan amai haka” Goya Abrar tayi tafara wanke mata baki takaita daki sannan ta share koh ina, “Raina lafya kike meke damunki”? “Wallahi bansani ba jinayi zuciyana na tashi ga zazzabi mai zafi cikina ciwo yakemun” Ummin Abrar tace bari taje gida ta dawo PT test tayiwa Raina saboda ta karanta Auxiliary nurse shiyasa Ta iya Dan gwaje gwaje harda amsan haihuwa, bayan minti biyu yanuna Raina tana daukeda juna biyu Farinciki wajen Ummu Abrar ba'a magana Raina itama ta nuna farincikinta gidan Raina Ummin Abrar ta wuni sai dare da Farid yadawo tayimishi albishir, a gsban Ummin Abrar farid ya rungume Raina saboda farinciki magani Ummin Abrar ta rubuta Dari uku gareshi haka yaje yasiyo. [4/17, 11:21 AM] Melody🎤🎤: *106-110* 👸🏻 *RAINA* *(The beautiful princess)*👸🏻 © _*STORY & WRITTEN BY HUMAIRAH (Melody)*_ _*This page goes toh AUNTY SIS💞 Thanks for all the love and care you hv for me am very greatful you are a QUEEN MOTHER👑 U'R different among odas Glory be to Allah may Allah continue to Guide and protect you from all Hypocrite and all Evil May you be the Shining STAR in our daddy's EYES Amin👏🏻*_LYSM😍 BABI NA ASHIRIN DA BIYU Jiki na rawa yakawo, akwana a tashi wajen Allah ba wuya, ciki sai girma yakeyi yana dad’a fitowa yayi titsitsi zama da kyar tashi da kyar amma hakan baisa sun daina rayuwar aure ba don ba haramum bane a musulunci idan kinada ciki daga randa yashiga har ranan da zaki haihu an yarda miji yayi jima'i da matarsa saidai idan shine bashida buk’ata koh ita matar wallahu ta'ala wa'alam. Farid sai fafutukan Neman aiki yakeyi da kwalin degree dinsa don har masters yayi k'watsam yasamu aiki Raina tayi murna da farinciki k'warai, Albashin farko farid a matarsa yak'are da dansa me shirin zuwa duniya Sannan ya saya musu kayan abinchi da sutura lokaci daya duka murmure Farida ce zaune cikin Dakin Raina tazo tayasu murna dukda Farida na gida batayi aureba, saboda duk Wanda ta kawo sai suce baimusu ba harta hak'ura, amma Kullun cikin Adu'a takeyi Allah yazaba bata da Alkhairi, haka ta yini kannan ta wuce gida. Kwatsam wata safiyar Asabar Raina tana k'wance kan kafar mijinta yana mata tausa mugun kofa sukaji na rashin hankali Farid yace “Raina waye wannan yake buga mana k'ofa kamar ya zautu? Raina ta tsbe baki tace “Mijina kaje ka duba”. Yana budewa hajiya tasallah yagani Wato mahaifiyar Farid sanye take da Atampha Super Aura mai ruwan bula ga jaka handbag tayi kyau kwarai amma fuskarta babu sauran annuri illah huci datakeyi Raina dake tsaye Farid ma tsaye yake Amma yakasa motsi bare yayi magana, “kun kafeni da ido koh bazaku bani hanya bane in wuce?”ai tuni suka matsa tashiga ta tsaya tana karewa dakin kallo cikeda tsana Gaisheta Farid yayi koh kallonsa batayiba Raina ta durk'usa a gabanta tace “Sannu da zuwa hajiya kinzo lafya?”. A fusace hajiya tasallah ta juyo ta daka mata tsawa “Ke dallah rufemun doyin bakinki har kinada bakin gaisheni bayan kin rabani da dana Allah wadaranki matsiya ciya kawai yar tasha” hamb'are Raina tayi batareda taga cikin ba Farid da sauri ya daga Raina “Haba hajiya bakiga halinda take ciki bane tsohon ciki gareta kika tureta Dan Allah hajiya karkiyi sanadiyyan kashe mana da Wanda zaiyi mana Adu'a bayan ranmu” Hajiya tasallah ta kurewa Raina kallo tabbas cikine ajikin wannan makirar, “Raina har wani ciki gareki ? Waya miki cikin? Kina nufin jikanane? Kina nufin kinada rabo ajikin dana? Kodai cikin shegene har kinsamu k'wanciyan hankali harda daukan ciki? Toh kisani wannan cikin ba jikana bane tun wuri ki nemamai uba” Raina ta gama rudewa dafe cikin tayi tana kallon farid da idanunsa sukayi jawur yace “Hajiya ina rok'onki da karki sake sheganta mun da ciki nawane nida Raina Hajiya irin kwanciyan hankalin da muke ciki shugaban kasa baya ciki yadda kuka kujeni saboda Raina babu gudu kuma babuja dabaya ina tareda Matana da dana, kusani da Allah kuke jayayya shiyace Mu auri karuwai musasu a hanyar k'warai wannan yanuna cewa mutum yayi jihadi kuma ladansa dabanne”. Hajiya ta mutu a tsaye tace “Kasani yau zama tsakaninka da wannan jarababban yakare, keda uwarki kun taru kun lashemun da dangin maita wayasani koh mayune Ku toh kisani wannan cikin saidai kiyimai uba amma ba jinina bane, koda kasuwa zaki Haifa kin Dade baki haifaba kaska kawai kisani yau kafana kafar dana” hannu Farid ta rike ta jashi waje tace “Mutafi” Zare ido yayi yace “Hajiya intafi kike nufi inbar Raina da ciki? Saidai Kiyi hak'uri matata bata fikiba amma kuma bazan iya tafiya inbarta ba” komawa Farid yayi yarike hannun raina wacce take kuka kamar Ranta zai fita tace “Farid Dan Allah karka tafi kabarni kadubi Girman Allah ka taimakeni da rayuwar abunda ke cikina” tunu mutane aka taru kamar anacin dank'o Ummin Abrar itama hayaniya tajiyo tafito ganin Raina na kukane tasan cewa ba Lafya ikoh hajiya sai masifa takeyi “Karuwa kawai kin mannewa dana kin rabani dashi kisani saidai hawayenki su k'afe ko kuma suzama kogi don yawa amma Farid saiya barki dakeda shegen cikinki, woooo dakeda uwarki wayasani koh mayune” Kara zuwa tayi taja hannun farid takaishi bakin mota tace yashiga amma Farid yak'i RAINA tace “Farid karka tafito kabarni ka tausayawa abunda ke cikina ” dawowa yayi hajiya ta dak'atar dashi tace “Muddin ka koma wajenta saidai kazaba koh ni koh ita ko kuma in tsine maka kabi duniya” ai Farid cik yatsaya Raina kuwa toshe baki tayi saboda kada kukan yafit. [4/17, 10:16 PM] Melody🎤🎤: *111-115* 👸🏻 *RAINA* *(The beautiful princess)*👸🏻 © _*STORY & WRITTEN BY HUMAIRAH (Melody)*_ BABI NA ASHIRIN DA UKU Tsaye yake tace “Ga takadda inaso ka saketa saki uku babu kome” Raina tak'ara sakin wani kukan Farid kam shima kuka yakeyi kamar Ransa zai fita Hajiya tak'ara cewa “gashi rubuta” “Hajiya saidai Kiyi hak'uri gaskiya bazan iya sakinta Matata ba saboda addini baice hakaba, Malamai da dama sunce inhar matarka tana cutarda Mahafiyarka kuma tace ka saketa toh ya halasta ka saketa saki daya idan babu cuta kabata hakuri cewa bazaka saki matarka ba, in tsinema tace zatayi toh tabbas tsinuwanta bazai taba tasiri akanka ba muddin kana kyautata mata don haka Kiyi hakuri Hajiya kibarni da Raina, bazan iya sakinta ba itace jigon rayuwata kidubi girman abunda ke cikinta Hajiya” ya marairaice “Farid muddin baka saki waccan k'arfar ba toh saidai kazaba koni koh ita kana iya sauya mata amma uwa bazaka sauyaba” Jin haka yasa Raina tace “Farid kabi umurnin mahaifiyarka kabita amma kasani wannan cikin inhar yazo duniya karka kirashi da danka don bazaka sake ganina ba bare har kaga danka ke kuma uwar banza kinyi abunda kike buri kinji dadi inhar wannan cikin shegene Allah yana gani inkuma Farid danki shine ubansa toh insha Allah bazaki taba ganin jika daga wajen Farid ba”ta fadi hakanne badon batason mijinta ba ah ah saidon Mahaifiyarsa taga ishara Allah baya Goyon zalunci. Juyawa Raina tayi har takusa shiga gida ta juyo tace “Bani takadda ta” hannu ta mik'a Farid yabata saki daya yana kuka “Allah yagani inason matata da dana Amma hajiya kin tauyemun hakkina yanzu idan Allah ya amshi Aduar Raina kina ganin duniya ban muzanta ba?”Raina ta juyo wajen Hajiya tace “Ayyiiiiriiiiiii Jama'a gobe kuje Kaduna isa kaita road koh kafur ana auren Farid da uwarsa hajiya tasallah hajiya saiki zuba ruwa akasa kisha inaso ki aurawa Farid mace mai gindin gwal wacce tafini gata da iko harma da mulki, Uwar banza kisani kin Haifa kuma duk abunda kaiwa Dan wani toh wallahi rubutacce ne sai anyima” tsaki taja Wanda saida ni humairah na tsorata don yakai kusan second talatin haka hajiya ta turashi cikin motan sannan tace “Ai farid koh mai gindin azurfa yace zai samu me akeda Kaska mai bak'ar kafa irinki andaiji kunya dakeda uwarki yan iska” hajiya yasa kai suka wuce suka bar *RAINA* cikin damuwa amma yata iya da Ikon Allah, cikin wata guda Raina ta haihu yara biyu mace da namiji Wato yan'biyu acikin gidan Ummin Abrar data rik'eta bisa yarda da amana itace cinta Shanta har mijinta yasan da zamanta don haka tana haihuwa tacewa Ummin Abrar “Nagode k'warai da kulawarku keda mijinki saidai wani hanxari ba gudu ba nabaki yarannan bisa amana karki taba cewa nice uwarsu saboda zamana yak'are a cikin Kaduna zan koma Dinya wajen Goggo Kiyi hak'uri nabaki aiki amma ke kadai kika chanchanci wannan kyautar” Abban Abrar yayi murna saboda yana k'aunar yan'biyu haka suka bata kud'ad'e suka kaita tasha ta tafi badan batason yaranta ba ah ah tabarsu wajen dazasu samu gatane Sanadiyyan yan'biyu Komai ya daidaita gidan Ummin Abrar, sunan yan biyun FA'IZ DA FA'IZA son kowa kin Wanda yarasa kyawawa ajin karshe duk inda suka kutsa sai an tanka haka aka dage dayimusu adu'a. *DINYA* Goggo na zaune tana karta itada tsaffi a zaure k'watsam Raina tagani tsaye tace “Goggo barka da hutawa” Sannan ta wuce jiki ba k'wari ai tuni karta ta watse Goggo tafada gida tana mamakin yadda Raina takoma kamar wacce ta haihu zama tayi dirshan tace “Ke lafya na ganki kamar daga sama lafya dai koh” Raina ta fashe da kuka tasa kanta a kafan Goggo tana kuka ta labarta mata komai duk abunda yafaru har cikin data haifa, Goggo tace “lallai nema tace wani Abu karki damu yanzu bari afara wankan jego ki murmure kiyi fes acigaba daga inda aka tsaya” Goggo wai yaushe zata natsu tasan me duniya take cikine tambayan danake yiwa kaina kenan batada wani buri saina lalata rayuwar RAINA wacce batasan me ake cikiba tun zuwanta duniya, Akwana a tashi wajen Allah ba wuya Raina ba karamin kyau tayiba a shekarunta Wanda basu wuce Ashirin da shida ba, amma wani ya rantse yace tsakiyan sha shida take tuni ta juya kambunta ta koma ruwa tsudum kamar yadda tasaba fita tadawo haka ta iske anyi chinchi rindo a kofar gida da isowarta mutane sukace gata ga mamaki naga ansa mata handcuffs a hannu motoci sai jiniya sukeyi abunda ya daure mata kai ganin Goggo dabatayiba, haka suka isa police station saida akasata a bayan kanta kannan ake sanar da ita abunda yafaru, ASP yana zuwa yaga Raina sai yaji tabashi tausayi k'warai tuni yace a fito da ita suka shiga office yayi mata nasiha har yace yana sonta amma bafa so irinna holewa ba don a rayuwarsa karuwa bata bashi shaawa asali ya tsani karuwa Amma a zaton Raina sone na hakik'a haka Kullun saita kirashi bayan ya sallameta wata rana ne taje office dinshi ta matsa kusa dashi tayi hugging dinsa lokaci guda yaji ransa yayi mugun bace ai jikake Tas tas mari takota ina Raina tuni tashiga rudu matsananci yace “Kina tunanin inada lokacin yar iska irinki wacce batada kima bare daraja a idon mutane kina tunanin sonda nake miki na so ne? Me zanyi da karuwa irinki kisani koh mata sun kare bazaki taba zama uwar yayana ba tunda anasha a nono, this is the First and the last koh ahanya karki kalleni bare kice kinsanni get out of my office” karuwa kenan Mara kamun kai rayuwarta daman ta gaji rashin mutunci daga kowa babu Wanda yake ragamata saurayi yadaka kuma gobe yazo yace saurayi nake tabudemai kafa, tazama bola kowa ya zuba kazantarsa aciki Allah kasa mudace Amin. [4/17, 10:58 PM] Melody🎤🎤: *116-120* 👸🏻 *RAINA* *(The beautiful princess)*👸🏻 © _*STORY & WRITTEN BY HUMAIRAH (Melody)*_ BABI NA ASHIRIN DA HUDU Haka rayuwarsu Raina da Goggo yaci gaba saboda tsabar iskancin Raina gari gari take zuwa bata Abuja bata Port Harcourt bata Tafa wata ranan asabar ne aka tashi da fada acikin gidan da Goggo take inda aka samu wata mai suna BELA ta zage Raina tas tayi mata wankin katon bargo sannan tayi mata gorin dangi hardana yan'uwa RAINA bayau aka asaba yi mata gori ba hakan yazame mata tamkar Riga yar shara haka tashiga daki ta tasa Goggo dole ta sanar da ita inda danginta suke kodan tanunawa duniya ta wuce gori kuka take babu kakkautawa, Goggo ce zaune shurum takasa cewa k'ala bare tayi motsi mai karfi jiki ba k'wari tace “Raina kinaso kisan asalinki?” Raina tace “kwarai Goggo maizai hana Ido rufema kuwa” Goggo ta yunk'ura tace “Jeki bayan layi siyo mana k'osai idan mukaci muka gama sai in sanar dake inda yan uwanki suke batareda bata lokaci ba” haka *RAINA* ta mike badon ranta nasoba ta fice ai koh second sittin batayiba Goggo ta mik'e ta k'ulle kayanta ta k'washi yan kudi a lalitan RAINA kafa mainaci ban bakiba Goggo nafita ta tare Dan achaba tace yakaita cikin gari Dawowar Raina keda wuya ta kutsa daki da mamaki ba Goggo babu labarinta saida ta zauna tsawon minti Goma a tunaninta kewaye tashiga amma shuru kakeji Malam yaci shirwa. RAINA ce tafito a hargitse tacema wata K'aruwar Gidan “Dan Allah koh kinga Inda Goggo tayi?” Budar bakinta tace “Tafita da kullin kaya akai batayiwa kowa magana ba illah wuce mu datayi” RAINA tayi ihu ta tuma a kasa tace “Waiyo nashiga uku ni Raina Goggo Dan Allah karki tafi kibarni ina zan dosa kiyimun rai Goggo kece gatana kece abun alfaharina yanzu idan kika tafi Zargin Mutane ya tabbata akaina duniya banida wani gata kashe kaina zanyi in huta Waiyo kaico duniya Ni Raina naga takaina” kuka mai tada hankali Wanda saida wasu suka tausaya mata Tana cikin burari ne wayarta tafara k'ara cikin hanzari ta dauka ganin lambar Goggo tace “Hello Goggo Dan Allah kidawo” harda dariyarta amma saitaji namiji ne yake magana Murna saita koma ciki. “Baiwar Allah idan da namiji kuzo bakin kasuwar soba anyi hatsari kuma matar RAINA kawai take kira” karaf aka kashe RAINA ta hauk'ace kuka takeyi mara sauti da gudu ta fice gudu kawai takeyi tana zuwa taga Goggo k'wance acikin jini wani ihu tafasa ta mance da salati bare yadda akeyi. “Goggo Dan Allah karki mutu idan kika mutu inazansa rayuwana Goggo kar kice yadda nazo duniya haka zan koma Goggo ke kadai nasani a duniya idan kika rasu inazan dosa Karyata tak'are Goggo ki tashi Dan Allah” jijjiga Goggo takeyi amma batasan halinda take cikiba zuwan Roads safety ne yasa akasa Goggo a mota sannan ga police da mamaki Raina tana daga ido tayi arba da ASP Ahmad Yari tuni taji sonsa ya karu cikin zuciyanta har suka isa Asibiti RAINA takasa daina Kallonsa saboda shak'uwar dake tsakanin zuciyarta da Asp, haka aka shiga da ita Emergency room inda likitoci sukayi cha akanta anata iyakar kok'ari haka Raina ke leken Yadda Goggo ke burari waiyo kawai takecewa babu alaman Rahma a tattare da jikinta bare sauki Babu Adu'a bare salati saboda mugun abunta daman karshen azzalumi kenan mutuwar Fuji'a mutuwar gaggawa Asiri Goggo, Zina Goggo, makirci Goggo, zalunci Goggo abun yayi mata yawa wai shege da hauka, Itadai RAINA fatanta Goggo tasamu sauki donta sanar da ita tushenta koh kuma Asalinta........ Bayan wasu awowine Goggo ta Umurci dason ganin RAINA haka ASP yakirata tafe take hawaye na k'waranya acikin gurbin idanunta tana zuwa ta rungume Goggo tace “Allah yabaki lafya Goggo kece abar Kallo inji dadii karki mutu kinji” Dariya Goggo tayi Wanda bata taba irin taba tace cikin Murya k'asa k'asa “Raina mutuwa tazama dole Kuma nan bada jimawaba zan bakunci inda kowa saiyaje kiyafemun Saboda nayi miki laifi wanda girmansa yana iya wuce dutsen Mambilan” Tuni Asp *Ahmad yari* yadauko Biro da takadda saboda ya dauki Statement din Goggo Taci gaba dacewa “RAINA ke yar Gata ce gaba da baya Duk wani kaskanci Nina jawo miki dana rabaki da iyayenki alokacin dasuke matuk'ar bukatanki Sunanan na Asali Binta kuma ni kuyanga ce acikin masarautar mahaifinki Wato *Sarki MAMUDA* Saboda tsabar makircina Yasa na saceki adaidai lokacin da Mahaifiyarki Maimuna ta haifeki Mahaifinki yafi kowa bakinciki Haka naji labari har ciwon hawan jini gareshi itako mahaifiyarki saboda kuka idanunta basu buduwa sun shiga matsanancin rayuwa wanda nake fata ki rokanmun su Alfarma su yafemun” Raina da ASP dama likitoci sunyi masifar razana kallon Raina kawai sukeyi saboda ga kamanan wacce bata boyuwa Goggo taci gaba da labari................... [4/18, 9:16 PM] Melody🎤🎤: *121-126* 👸🏻 *RAINA* *(The beautiful princess)*👸🏻 © _*STORY & WRITTEN BY* *HUMAIRAH (Melody)_* BABI NA ASHIRIN DA BIYAR “Maryam itace tasa na saceki saboda nata Manufar, tabbas idan tabarki a cikin gidan Danta *DANISH* bazai samu wata kulawa ba saboda sarki MAMUDA bashida wani buri Wanda ya wuce ganin k'wansa a duniya Shiyasa muka kulla wannan makircin muka musanyaki da matacciya na gudu dake akan kudi kalilan Wanda basu amfaneni da komai ba, shiyasa nakasa baki tarbiya mai kyau saboda banaso kizama abun alfahari a duniya, tarine ya sarke Goggo Wanda saida tayi wani amai harda jini, ASP yace “Ko zaki iya sanar damu inda zamu samu gidan Sarki MAMUDA?” Goggo da kyar take magana tace “Yana cikin garin Kaduna dazama a k'aramar hukumar Kajuru.......... Tana gama magana tayi shak'uwa har sau uku daganan tasaki wani razanannen kara ai sai kuma akaji shuru, RAINA wani irin kara tayi ta rungume Goggo tana kuka tana “Goggo maiyasa zaki mutu kibarni? Dan Allah ki tashi” ikon Allah kenan kudubi girman laifinda Goggo tayiwa RAINA amma soyayyar Goggo yana cikin ranta harda zuciya nasan duk Kukan da Raina takeyi na tsantsar shakuwane, haka aka lullube Goggo cikin Zanen Asibiti, tuni yan sanda suka nufi Kaduna tun safe sai dare suka dawo saboda tsabar nisa jiniya kawai nakeji abun mamaki ina lekawa cikin harabar Asibiti motoci nagani convoy bak'ak'e wani mutumi nagani black beauty yana tafe cikeda kasaita cikin Alkyabba. Ana takamai baya suna shiga Dakin da Goggo keciki sukayi tozali da RAINA jiyayi gabansa yayi mugun fadi kallon kallo kawai sukeyi kujera aka sa masa ya zauna RAINA koh takasa kuka takasa dariya saboda tsabar farinciki, Danish ne tsaye yana kallon raina jiyake ya tsaneta saboda tundaga kallon fuskarta yaga dukta kone saboda tsabar bilicin, Kirari kawai ake yiwa Sarki MAMUDA haka likita ya budema sarki fuskan Goggo yana gani yace “Ai wannan binta ce” tuni ya Umurci RAINA data matso kusa dashi haka yadafa kanta yacema likitoci ayi gaggawan yimata sutura don su daganan Kaduna sukayi komin dare, haka aka yiwa Goggo sutura Harda ASP a wucewa kajuru kafin isarsu gida yacika yayi makil sai sarewa akeyi da kalangu abinchi kuwa kala kala saboda tarban Gimbiya RAINA, basu isa garin kajuru ba sai misalin Asuba amma gidan yadda kukasan rana, Haka raina tafito harabar tank'a sheshen gidansu acikin ranta cewa tayi yanzu Ashe nimai gatace amma aka shiga dani duniya na wulakanta? Kaico duniya Allah Kaine gatana, kuyangune sukazo suka wuce da Gimbiya RAINA zuwa bangarenta da tunkafin zuwanta duniya aka killa ceshi. Ciki Raina ta kutsa kai tashiga Tunda take bata taba katari da kayataccen daki irin wannan ba kalle kalle kawai takeyi wata daga cikin kuyangin tace “Ranki yadade wannan shine dakinki mune masuyi miki hidima duk abunda kikeda buk'ata muzamuyi miki , suna cikin magana akayi sallama jakadiya ce tsaye daukeda wasu kaya masu kyalli da shek'i “Gimbiya ranki yadade Allah yaja kwana Wayannan kayane saga sarauniya Maimunatu mahaifiyarki tace ki sanya idan kin kammala wanka” kuyangin ne suka amsa suka ajiye tuni aka hada mata ruwa mai tsafta turaruka kuwa sunkai kala goma da'aka acikin bath din ciki tashiga tayi minti Talatin tana wanka ita kanta tasan tayi wankan dabata taba bata lokacinta wajen yiba, fitowa tayi tuni kuyangin suka dau towel suna tsane mata jiki zama tayi tana shafa mai masu kamshi sannan ta shirya cikin kayanda aka kawo mata har bayan Sallah Asuba hidima akeyi gari na wayewa fada tacika makil da Al'umma haka aka kawo RAINA tafe take jitake kanta yakara girma, Jitayi tabbas SARAUTA tafi mulki kuma SARAUTA ajini take baa kudi koh dukiya ba, haka akayi Adu'a akayiwa Gimbiya barka sa dawowa daular mai martaba sarkin Kajuru. [4/19, 8:31 AM] Melody🎤🎤: *126-130* 👸🏻 *RAINA* *(The beautiful princess)*👸🏻 © _*STORY & WRITTEN BYHUMAIRAH (Melody)*_ BABI NA ASHIRIN DA SHIDA *DEDICATED TO YOU MY VERY OWN LOVE YOU ALOT😍😍 MISS XOXO THANK FOR FOLLOWING MY NOVEL BIT BY BIT😍❤👏🏻 LYSM😘* Bayan kowa ya watse ne aka gabatar da RAINA ga dan'uwanta Wato DANISH Wanda gaba daya yaji ya tsaneta tunda yaji ance Karuwa ce, bayan RAINA ta koma shahenta ne aka aiko jakadiya cewa ASP zai wuce in tanada abuncewa, cikin Zumudi tace kwarai tanada bukatan magana dashi tunda Maimartaba yace Idan tsnada Wanda wakeso tafito dashi itakuma duniya ASP Ahmad yari take muradi dukda cin mutuncin da yayi mata Haka aka rakata kofar dazai sadata da Lambun da Asp yake da isarta tayi wani kasaitaccen murmushi tace “Ranka yadade banida abun cewa sai godiya kayimun karamci Wanda babu wani mahaluki a zamaninnan dazaiyimun irinsa inada magana mai muhimmanci danakeso muyi kasan ance zuciya kabata abunda takeso duk girman abun Asp bantaba ganin namijin daya kwantamun arai irin kaba inasonka ina kwanarka ka ceci rayuwana banida burin daya wuce in aureka kazama uban yayana”. Tsawa ya dakama raina yace “Dakata malama dakata hakanan Karki yaudari kanki don bantaba jin sonki acikin raina ba kamar yadda na sanar dake a baya babu abunda zanyi da karuwa irinki mara mutunci karkiyi tunanin mahaifinki Sarki ne toh kisani uwa tagari nakeso insama ma yarana wacce babu wani aibu acikin rayuwanta koh nakasu wacce duniya yake kallonta a matsayin mutuniyar Arziki, bani ba auren karuwa irinki kaskantacciya maxa nawa sukayi amfani dake suka zubda Wato gani Mara wayau koh toh kinyi a banza sonki nakeyi a matsayin kanwata amma baa masoyiyaba” Hawaye ne kawai ke zuba daga gurbin idanunta, ranta yayi bala'in baci da munanan kalamansa tace “Asp wannan shine karo na karshe daxaka gayamun munanan maganganu meka maida karuwa? Waya gaya maka karuwa bata auruwa? Meye aibun karuwa Idan tace ta tuba? Amma inaso kasani ba laifina bane amma kuma babu komai kaje duniyace ta ishi kowa karka chire rai dasamun Irina acikin zuri'arka sai inga wanda zai auri taka y'ar mtwwwww Guards” sai gasu cikin hanzari tace “sonake ku fitarmun da wannan Mara mutuncin kuma aka nakeso ku daukeshi” haka kartin suka daukeshi sai waje gurshekin kuka kawai raina keyi “tabbas Goggo kinyimun Illah kin wulakantamun rayuwa tsakanina dake Allah saiya isarmun kin shegantani da iyayena kaico duniya inazanga Farid shine silar farincikina a duniya bayaga iyayena a yanzu”. Ciki ta wuce rikeda doguwar rigarta mai bayan dawisu dakinta tashiga tayiwa kuyanginta izini dasu fita tanaso ta kadaice cikin yini daya ta fige koh abinchi takasaci, tun zuwanta gidan sau daya ta sa mahaifiyarta a ido abunda ke damunta kenan, ★★★★ BAYAN WATA DAYA Maimartaba Yakira Danish yasanar dashi buk'atan sa na auren RAINA hankalin danish yayi kololuwar tashi saboda babu macen daya tsana irin RAINA kuma, “Mai martaba inaso abani lokaci inyi tunani ” “Babu wani tunani umurni nabaka ba shawaranka nake nemaba koh tunani ba kashirya nanda sati biyu”yana gama magana yamik'e danish saida yayi kuka Wanda nikadai nagani sai kunkuni yakeyi “maxanyi da karuwa wacce gaba daya rayuwanta ta hulakance”. Yini yayi yana tunani yadda zai bijirewa umurnin Mai martaba amma yakasa ni HUMAIRAH nace dole ka aureta saboda uwarka itace silar lalacewar rayuwan RAINA, kwanci tashi cikin kankanin lokaci RAINA ta kilance tayi kyau amma ta kudiri aniyar Yau saita nemi hanyar zuwa wajen mahaifiyarta tanemi afuwanta don taga kaman fishi takeda ita saboda takasance karuwa Mara galihu ada, Zuhra itace ta rakata har kofar Dakin mahaifiyarta kutsa kai tayi tashiga cikeda fargaba kuyangin sasan sai gaisheta sukeyi amma bataba kowa amsaba cikin Dakin mahaifiyarta zata shiga aka hanata wai sai an tambayi sarauniya Maimuna, wani wawan Mari tayiwa kuyangar tace “Ke wacece dahar zakice bazanga uwata ba? Ke kin isa toh kisani wannance rana ta farko kuma na k'arshe inada daman shiga koh ina bangajeta tayi tashiga ta taradda ita zaune ana mata fifita durkusawa tayi tagaidata cikin ladabi sannan tayi shuru nadan lokaci, Sarauniya Maimuna tace _*KUYI HKR WAJEN NUMBER JIYA NAYI MISTAKE PLEASE 121-125 zansa nasa 121-126 bear with me*_. [4/20, 6:46 AM] Melody🎤🎤: *131-135* 👸🏻 *RAINA* *(The beautiful princess)*👸🏻 © _*STORY & WRITTEN BYHUMAIRAH (Melody)*_ BABI NA ASHIRIN DA BAKWAI “Kiyi Hakuri Raina nasan kina cikin rudani nasan kina cikin matsanancin damuwa na Rashin Adalci dana nuna miki tun zuwanki cikin gidannan nayi hakanne saboda wani kunci dake dawainiya Dani, amma naji matukar dadi dakika zo inda nake hakan yanuna cewa kemai kaunar uwar data kawoki duniya, dakwai wata magana mai matukar muhimmanci Wanda nakeso inyi dake Ansa ranan aurenki nanda sati biyu keda dan'uwanki DANISH amma kisani yanada mata mai Suna Unaiza tana zaune acikin garin Kaduna ne” Ras RAINA taji gabanta yayi mummunan faduwa taji duniya ta tsani Danish Wanda shima take ganin alaman ya tsaneta budar bakinta tace “Ummi A gaskiya banida raayin yin wani aure saboda nayi banji da dadi ba sannan Danish bayasona saboda babu wata magana data taba hadani dashi koda cikin Garden na shiga saiya watsamun kallon tsana yabar wajen Dan'uwanka mai sonka kuwa Janka zaiyi a jiki ganin yafaranta maka rai amma duk abunda kuka yanke a shrye nake da inyi muku biyayya a matsayin iyayena” Maimuna taji dadi tabbas da ace RAINA a gabana ta tashi nasan data zama abun kwatance saboda daga dukkan alamu tanada ladabi da biyayya. Nan sukayita hira amma koda wasa RAINA bata taba fadin tanada yara har biyu ba rayuwa ta sauya RAINA taxama yar gari takan fita domin shakatawa tana samun kulawa daga mahaifinta sosai haka mahaifiyarta, kwatsam hanya tabiyo da ita ta wani labi dake cikin gidan kawai batayi auneba taci karo da mutum dagowan daxatayi taji an dauketa da mari, Agigice ta dago ganin Danish ne itama ta daukeshi da gigitaccen Mari Wanda saida taga taurari sannan RAINA tace “Kul agolan gida kabi a sannu don karkaga kanka na rawa kayi tsammanin kafi yar masu gida iko da mallaka kul Dan mulki wannan yar saurautace a gabanka, Uwata yar sarki jikan sarkice kuma matar sarki uwar Gimbiya RAINA Idan ka mance in tuna maka yau shine rana na karshe dazaka sa wayannan doyan hannun naka ka mareni Ina umurtanka daka bani hanya kafin inbaka kunya” tsayawa yayi ya rike kunci yana mamaki RAINA yar karamar yarinyar dayaba shekara goma bangajeshi tayi ta wuce tana wasa dayan yatsunta, bangarenta ta wuce tafada kan royal bed dinta ta fada kogin tunani “Dole inyi biyayyar aure Idan harna Auri Danish tabbas gwarzon namiji ne maijida kansa kyakkyawa ne ajin karshe ohhhh toh niwai meyasa Abbi ya zabamun Danish a matsayin miji da gudarin tunani ne bacci yayi awon gaba da ita, misalin karfe hudu ta farka Sallah kawai tayi akayi sallama cewa malaminta yazo mai koya mata duk wasu hukunce2 musulunci lokaci guda ta rikesu Kullun cikin istigfari take tana Neman gafaran ubangiji haka take sanarda Malam kan maganar aurenta. Haka yayi mata Karin bayani akan Zaman *Istibra'i* da mace takeyi tsawon wata uku matukar tayi yawon bariki koh tayi zaman kanta sannan tana holewa da wasu maxan don haka yabata babban Sha'awaran a k'ara watannin aurenta zuwa wata uku da komai zai kammala, haka akayi bata zuwa koh ina daga gida sai gida babu wani namiji dayake zuwa inda take sai Azumi takeyi sallar dare kuwa kamar akanta aka saukar da Aya Abun gwanin ban shaawa kowa yayi mamakin Gimbiya RAINA yadda lokaci guda ta canza saidai batason raini koh nuna isa, Dayawa cikin family dinsu tsoronta akeji, Tuni aka fara nemawa RAINA gurbin karatu Wanda ake cewa yaki da jahilci Raina gata babu irin wacce bata samuba a halinda take yanzu. ************* BAYAN WATA UKU Komai ya daidaita Anfara shirin biki Gidajen radiyo babu inda ba'a shelanta ba, Zainab kuwa jin mijin ta zai kara aure kaman zatayi hauka saboda tsabar Rainin wayo irinna Danish bai sanar da itaba yace taji a gidan rediyo, Shida abokinsa ne mai suna Shureim ne suka zauna cikin wani folo dake kirada Tarazo suka aika ayi musu iso da RAINA batayi mamakiba haka ta tambaya waye akace da ita yarima Danish ne, saida tayi wanka tashirya cikin wata bakar doguwar Riga tayi mafla da gyale Green, tasa takalmi Shika Green tafito tareda rakiyar kuyanginta tana isa falon tace sukoma ciki ta kutsa kai Shureim ne kadai ya iya amsa sallamar RAINA harya kalleta shiko Danish wani garwashin tsanane ya turnukeshi babu abunda yake tunawa sai Marin data taba yimai........ [4/21, 6:38 AM] Melody🎤🎤: *136-140* 👸🏻 *RAINA* *(The beautiful princess)*👸🏻 © _*STORY & WRITTEN BY HUMAIRAH (Melody)*_ BABI NA ASHIRIN DA TAKWAS _*Zakuyimun hakuri don baxaku jini ba kwana biyu saboda makaranta Allah yasa ku fahimceni LYSM my FANS*_😘 *DIX Page goes to my co-writer BADI'AT IBRAHIM kina kamshi inabinki da Humrah Allah yasa kifi haka yak'ara daukaka da laifin baseerah LOVE YOU SWEETHEART❤* Sannan ganinta yake a matsayin karuwa har yanzu acikin zuciyansa guri ta nema ta zauna fuskarta babu yabo babu fallasa illah wani murmushi datake Wanda nikaina nakasa dangantashi dana farinciki koh akasin haka gaishesu tayi Shureim ne ya amsa da “Amarya bakya lefi ta yarima bada kanki asare Idan bashiba sai rijiya rijiyarma mai kwalabe” Tuni Danish ya zugureshi alamun bayaso Shureim yaci gaba da magana “Amarya Mai sunan yan gayu daman munzo ne gameda hidiman biki kidakwai abunda kikeda buk'ata koh kuma wani shagali da kikeso ayi a ranan bikin” RAINA ta kare mishi kallo tace “Amatsayinka na aboki kuma Wanda yasan yakamata nabaka dama kaje ku yanke duk shaawarar data dace don as you guys can see am in a heast don haka left to you”Kafin ta tashi Danish ya tashi yaja uban tsaki ya fice saura kiris yataka mata Dan yatsa, Tashi tayi zata fita Shureim yabita yana bata hakuri dacewa saitayi hakuri da abokinsa budar bakin raina tace “Shureim kenan yadda danish yake ikirarin bayason aurena dashi haka nima banaso biyayya kadai zanyiwa iyayena sako nabaka zuwa gareshi don kansa yadaina daukan huci koh ince zafi koh kuma rawa” haka ta fice tabar Shureim Wanda yake ganin tabbas RAINA macece mai klas k'warai gata da wani boyayyan kyau dake kwarara tayaya zanyi nasaran ganarda Danish cewa wannan itace zata share mishi hawayen dake zuba tsawon shekara biyar da aurensa, da wannan yafice anata shirin biki amma RAINA batako daukin bikin illah tunanin rayuwar aurenta da FARID Wanda yakasa gushe mata daga kwakwalwa.. RAINA ce zaune gaban mahaifinta Wanda yake tambayarta nawa take so kudin sadakinta? Haka tasanar dashi naira dubu Ashirin kacal ya isa Albarkan akeso sannan ita tasan a yadda rayuwarta take bata wuce hakan ba, Sarki MAMUDA ne yabada umurnin ashiga cikin garin Kaduna adawoda Unaiza cikin gidan saurauta matukar tanason aurenta ya daure da Danish wannan labarin daya isketa tayi masifar razana bin jakadiya kawai take da kallo tace “Kina nufin DANISH aure zai k'ara kuma maimartaba ya Umurci da in koma masarautar kajuru?” jakadiya tace “Kwarai ranki yadade umurni ne daga mai girma sarki MAMUDA Allah yakara mishi Nisan kwana kuma yar Sarki MAMUDA zai aura RAINA kyakkyawar Gimbiya”tsawa Unaiza ta dakawa jakadiya tace “Nisan kwanan sarki kuya dama mijina kawai nake tunani RAINA koda itace sarauniyan kyau wannan ba matsalata bane don nasan saidai kyau na SARAUTA amma bana MULKI ba kubaiwa Maimartaba hakuri nanda kwana uku ashirye nake da'in koma kajuru Kufita banda bukatar ganin ku sai nanda kwana UKU” Ai jiki na rawa suka fice koh waige haka suka koma sarki ya Aminche Unaiza Kullun cikin kiran danish take abunda bata tabayiba tsawon lokacin dasuka diba na zaman aure, shiko koh kallo wayar bata isheshiba sometimes har kashe wayar yakeyi. ★★★★ *WACECE UNAIZA?* Unaiza dai yar Ambassador MB shehu ce Wanda yayi suna a fagen kulada yan Nigeria dake a kasar Amurka Susu uku iyayensu suka haifa kuma itace ta karshe Wato Auta duk wani iya shege akanta yak'are kuma duk abunda tayi a wajen iyayenta daidai ne, yadda uwarsu ta maida ubansu mijin tace haka suma suka maida mazajensu, Danish dai a wajen biki suka hadu inda yaji duniya Unaiza yakeso har ta kaisu ga aure Unaiza batada lokacin danish bare harta yimishi abinchi kafin a kaiga wajen k'wanciyansu nanma saiya sha daga sometimes har kudi yake ajiyemata kannan ta aminche mishi babu kwayar biyayya takan fita lokacin data so tadawo lokacin dataso haka ta Tara K'awayenta suyi bishasha yadda sukeso bashida ikon magana tace tafishi baki, harta wanki shara da wanke wanke shiyakeyi, har abokanansa suka daina zuwa gidansa saboda haushinsa kawai sukaji yadda mace ta rainashi kuma duk a sunan shike aurenta koh kusa dashi Unaiza bata zuwa data samu ciki saitasha pills ta zubar dashi kwata kwata babu biyayyan aure Wannan kenan. [4/22, 7:21 PM] Melody🎤🎤: *141-145* 👸🏻 *RAINA* *(The beautiful princess)*👸🏻 © _*STORY & WRITTEN BY HUMAIRAH (Melody)*_ _*Wannan page din nakine MARIYA AHMAD ILIYASU Son da nake miki is different ngd da karamcinki gareni @Anatare 😍😍 lets keep chillingGulx💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻*_ BABI NA ASHIRIN DA TARA Akwana a tashi wajen mai rai RAINA babu abunda take zullumi sai gamuwarta da DANISH Wanda k'wata k'wata bayasonta haka ranar daurin aure ya rage saura kwana uku, UNAIZA ta dawo cikin gidan sarautan wajenta dabanne nesa da inda RAINA zata zauna, Unaiza ce tsaye a bakin taga inda take hangen masu kaiwa da komowa hankalinta yayi kololuwar tashi “Yanzu nice zaayiwa kishiya? Tab lallai daman hakan nuwaira taji lokacin da AB zai kara aure?” Jitake kaman zata hadiyi rai ta mutu saboda tsabar son danish datakeyi sai yanzu tasan cewa miji mijine wacce ta raba miji da wata tayi gagarumin sake. Wata sain ba sake bane kaddara ne kuma rubutaccen Al'amarine ana gobe daurin aure Unaiza ta fita mike k'afa ga gida ya cika dankam da mutane bata zarce koh inaba sai hanyar dazai sadata da bangaren RAINA tafe suke itada Kuyanginta da'aka bata don yimata hidima suna isa k'ofar RAINA tayiwa kuyanginta umurni dasu jirata koh sallama babu ta banka kofa, Raina tana sama itada zeenert k'awarta tafitowa tayi da sauri lokacin duk kuyanginta basa kusa, daga saman bene tace “Wace yar akuyarce Mara tarbiya bare dabi'a take shigomun falo ba sallama? Koh bataje islamiyya bane?” Unaiza data kulu tace “Kul yar tasha ragowar bariki Karki kuskura ki zageni har kinada bakin zagin wani mara tarbiyya gaki BABBAR Mara tarbiya wacce rayuwarta ta kare a bariki inaso kisani igiyar rak'umi tayi nesa dana kaza kiyi gaggawan rabuwa da mijina kafin a haifi da Mara ido”. Raina ce tafe zata sakko zeenert kuwa tana sama tana kallon abun al'ajabi, saida RAINA ta zagayeta sannan tayi guda tace “koh ba'a mijiba danish dan'uwana ne kuma inada right din aurensa tunda ba nono daya mukasha ba sannan Kuma ba uwa daya uba daya mukeba bare kice ba aure, kisani saikinyi kishi da Raina kafin in irga uku kiyi gaggawan fita inba hakaba kiji kunya ” Unaiza shuru tayi don abun yasha karfinta kishi da Baban miji Fita tayi a fusace cikin sauri kuyanginta ke biyeda ita tana shiga daki ta fada kan gado zufa kawai takeyi abun duniya ya isheta Kuyangarta ta aika aje a nemo mata Danish ace tanason ganinsa amma Ina abun yaci tura yana cikin garin Kaduna gidan Ab abokinsa, Unaiza tak'asa rintswa takai gwaro takai mari har misalin shadaya nadare lokacin dataji gunjin motar Danish bata tsaya bata lokaciba tafita da gudu tayi inda yake fadawa jikinsa tayi lokaci daya ya hankadata batareda yasan itabace yace “RAINA ina kyautata zaton kinyi kuskure wajen zuwa ki rungumeni dis is the First and the last kisani banza kawai kina tunanin zan iya hada jiki dake toh kisani *Auren jeka nayika zamuyi* ba auren Darai yake muradi ba”. Yana gama magana Unaiza tace “Baby ba RAINA bace nice matarka Unaiza kayimun rai kazo gareni ka ceceni don duniya ina cikin duniyar ladama nayi dana Sanin yimaka wasu abubuwa a baya pls forgive me i dont mean to hurt your feelings any more Darling” wani gigitaccen tsawa yayimata Wanda saida taji kaman zata gudu Yace “Unaixa kinyi kuskuren zuwa inuwata bari Kiga yadda ake ganar da mutum irinki kuskurensa, kin manta cewa kinyi rantsuwa bazaki sake zuwa inda nakaba?” ai rufe baki tayi tana gunjin kuka Ai batayi auneba saijin belt tayi tako ina sai hambareta yakeyi babu imani koh tausayi saboda Unaiza ta cutardashi ta inda mai karatu baya zato, Danish yana masifan son Unaiza lokacin da yakamata tayi amfani da damarta lokacin ta watsar saboda sonshi yafi nata tasiri, Akan Unaiza bata biya masa hakkinsa yafada ga aikata zina duk lokacin daya buk'aci mace saidai yaje waje tur da halin Unaiza wacce sanadinta mijinta yashiga halaka mata muyi imani mu kare hakkokin mazajenku. [4/24, 6:40 AM] Melody🎤🎤: *146-150* 👸🏻 *RAINA* *(The beautiful princess)*👸🏻 © _*STORY & WRITTEN BY HUMAIRAH (Melody)*_ BABI NA TALATIN _*Wannan page nakune yan group dina Wato Melody novel group Allah ysbar zumunchi yabar kauna LYSM😘😍*_ Ai da gudu ta wuce cikin gida tana kuka washe gari Aka daura auren DANISH DA RAINA a babban masallacin dake kofar gidan Sarki MAMUDA inda manyan Mutane suka halatta daurin auren ciki harda sarki KAMAL Wanda shima sarkine Wanda ake jidasu a fadin Nigeria, Gida sai hidima akeyi Sarauniya Maimuna kuwa bakinta har baka gida yacika da jinin sarauta takoh ina harma jinin mulki ni humairah saida nagani abun masha Allah Amarya da Ango sunyi kyau Unaiza saboda bak'in ciki kamar zatayi kashi ajiki babu kowa a bangarenta saboda kowa ganin laifinta yakeyi dabata hana danish aure ba tafita zakka cikin yayan gidan Ambassador MB shehu, Misalin karfe uku ne aka wuceda Amarya nata sashen a al'adarsu mace bata Sallar La'asar a gidan iyayenta sai a gidan miji Nidai saboda tsabar son ganin Dakin amarya mai karatu saida naci tuntube, A gaskiya RAINA tazama ya mai gata mai yanci duniyace tayi mata kamun kaxan kuku lokacin datake matukar buk'atan iyayenta a kusa da ita babune babu acikin bangarenta yaji kaysn kwaliya na zamani wani bangaren na yar saurauta kirari kawai ake mata *Yar Sarki jikar sarki yar sarauniya Maimuna takawarki lafya Allah yakara ma Yarima Danish lafiya Allah ya tsole idon makiya mahassadanki fadawanki kyakkyawar Gimbiya tun kan zuwanki duniya akasa miki suna kikazo duniya sunan yabiki Duniya Mai yadda yaso da bawa ke macece mai kamar maxa masu irin imaninki sai an tona Allah yasa muji albishir mai dadi Uwar yan biyu in Allah ya yarda* Tunda Jakadiya tace yan biyu raina taji wani mugun faduwan gaba yaranta kawai ta tuna amma tasan yanzu sun zama na wasu bata burin karbarsu Amma tanajin irin sonda take musu har kokon zuciyarta kuka kawai tasaki Wanda babu Wanda yasan dalili. Bayan an shiga da itane aka gama yan Al'adarsu ta masarautan kajuru, daga bisani akabarta daga ita sai jakadiyarta sai kuyangu tunda dole tasamu jakadiya saboda tazama matar aure al'adarsu, Zaune take bisa katon gado Wanda yasha ado Royal bed ne Wanda kansa ya kusa rabi da k'watan bango sai fifita ake mata misalin karfe Goman dare lokacin da Danish yadawo abun mamaki tana zaton inda take zaizo amma saitaga Akasin haka Jakadiyace tashigo hannunta rikeda wasu kayan bacci masu kyau da tsada “Gimbiya kitashi kisa wayannan kayan muje in rakaki wajen Mai girma yarima” cikeda mamaki baki bude raina tace “Jakadiyya kinada hankali kuwa? Mutum yana sonka yaka k'are dashi bare kuma bayasonka kakai kanka? Nifa bazansaba inace miji kebin mace har dakinta?” ta zunburo baki ta mike ta nade hannu tana kai gwaro takai mari, jakadiya ce a durkushe tafara magana cikin siga mai kashe jiki Nanta labartawa RAINA irin rayuwar Auren “Gimbiyata mai zai hana mu gwada tamu baseerar saboda gani yake matan duk saya suke kije Gimbiya ta kidaure har hakarmu ta cimma ruwa” haka raina ta shirya cikin kayan ta sanya Alkyabba suka kama hanya jakadiya daga kofa ta koma RAINA kuwa gabanta sai dukan goma goma yake, tayi minti biyu a tsaye kannan ta zauna a gefen gado da alaman mutum a cikin Dakin cire Alkyabba tayi ta kwanta ta juyawa toilet din Dakin baya tasan duk yadda akayi wanka yakeyi. Tanajin motsi tayi saurin rufe ido DANISH daya fito saura kadan ya arta a guje saboda bai taba ganin mace mai kira irinta RAINA ba, lokaci guda ya gusar da tunanin hakan a ransa yana Neman tsari da shaidan din sake Neman yin tasiri acikin Ransa Juyowa RAINA tayi tace “Barka da fitowa ranka ya Dade yayana yarima mai jiran gado Allah yabaka sarki ka nadani Sarauniyar masarautanka” tafadi tana murmushi ta sakko mai yake shafawa tayi saurin amsa cikeda kissa zata shafa masa tunda wani darene jemage bai ganiba dakatar da ita yayi yace “Malam bansakiba banason Shishigi maxa ki tashi daga gabana kafin inyi ball dake ” RAINA tayi saurin dagowa takasa cewa komai ba laifin Wanda take gani sai nata dana jakadiyya bakin gado takoma sai satar kallonta yakeyi Barcine tayi awon gaba da ita shiko sai daukanta hoto yakeyi yadda tayi masifan kyau cikin silk milk din kayan baccin amma fah yarasa meyasashi daukan hotonta *Koh me karatu yasani?*misalin karfe biyu da rabi raina ta tashi DANISH dai motsi yaji Alwala tayi ta shimfida sallaya ta dubi gabas tafara kiyamun lai Shiko Yarima Danish kallonta kawai yakeyi wai daman RAINA tana sallah? Tsmbayar kansa yakeyi nida mai karstu mukace Ah ah Batayi tunda Kaine kadai musulmi a duniya. [4/25, 6:30 AM] Melody🎤🎤: *151-155* 👸🏻 *RAINA* *(The beautiful princess)*👸🏻 © _*STORY & WRITTEN BY HUMAIRAH (Melody)*_ BABI NA TALATIN DA DAYA Yana zaune yana kallon ikon Allah RAINA bata bar kan sallaya ba har saida tayi sallar Asuba ta daga hannu sama tayi adu'a ta shafa bata zarce koh inaba sai dakinta inda doguwar hanyace ta rabata da inda turakan Danish take wanka tayi tasa kaya marasa nauyi ta kwanta sai bacci. Bayan yadawo daga Masallaci yanemi RAINA yarasa wani haushin kansa yaji Wata kujera yafada yana yamutsa gashin kansa tako ina ya buga hannunsa akan tebur anan shima bacci yayi awon gaba dashi misalin karfe shabiyu ya tashi lokacin am hada mishi duk abun kari kallon jakadiyyarsa yayi kaman zai tambayeta saikuma yafasa yaci gaba dacin abinchi badon yanaso ba ya tabbata da Raina tana nan zaune dayaci Dayawa don yanzu sonta yake amma kuma yaci damarsn sai taji kaman tace bata auren, itakoh zaune take tana kallo Bayan tayi Karin kumallo inda taketa ganin bak'i suna shiga suna fita itadai iyaka tayi musu sannu kuyangu ke kula daduk wani harkar sasan nata Wayarta ta dauko kiran Infinix 0 ta latsa lambar Mahaifiyarta tana dauka tace “Ummi Barka da rana” cikin sigar shagwaba. Sarauniya Maimuna tayi dariya tace “Amarya kenan dafatan kin tashi Lafya kinjini shuru koh ai nasan kina tattare da gajiya shiyasa bankiraki ba Allah yayi miki Albarka yasa kusamu zuriar dayyaba” “Amin” RAINA tace chan kasan makoshinta Sarauniya Maimuna takara da cewa “Abu na biyu danakeso dake shine ki rike ibada sannan kibi mijinki da abokiyar zamanki sau da kafa” RAINA ta tabe baki tace “Umm Ummi naji Abby yana kirana” karaf ta kashe tayi huci “Hmmm duk Wanda yaso azauna Lafya shiyaso don Bazan dau ko wane irin cin kashi ba yadda ta nunamun haka zan nuna mata” Kiran mahaifinta tayi yana dauka tace “Allah yakara maka Lafya Abby Kaine dawisu abun kallo zaki sa gabanka inda kakeso ranka yafi nawa dadewa Abby Mahassadan ka fadawanka kataka a sannu adon kowa” dariya sarki MAMUDA yayi abun yayi mishi dadi “Ina kwana beautiful princess dafatsn kin tashi Lafya ya Bakunta Allah ya kauda idon makiya yayi miki albarka keda zuriarki baki daya ngd da gaisuwa kirari yayi dafatan bakida wata matsala?” RAINA ta gyada kai kamar yana kallonta tace “Babu gaskiya Saidai inaso inji a ina maganar Karatuna ya tsaya?”dariya yayi yace “Karki damu insha Allah xaki cigaba” haka sukayi sallama. Yauma kamar Kullun jakadiyya ce tashigo hannuta daukeda wasu kayan baccin masu kyau da sheki son kowa kin Wanda yarasa rigar dai wasu igiyoyine sukasa aka kirata da riga haka ma short din shima kulleshi akeyi RAINA tana ganinta ta tamke fuska cikin ranta cewa take Niko naga takaina ji irin wulakancin da bawan Allah nan yamun amma wai kuma yau in kara komawa tabdi jam. Jakadiyya ce ta katseta da cewa “Lokacin bacci yayi koh kina iya sanya wannan in rakaki?” babu musu Raina tasa suka kama hanya Tana shiga taji babu kowa amma kuma sai taji saukan ruwa kofar toilet din ta bude ganin Danish cikin kumfa yana wanka a baf matsawa tayi yace “Barka da dare ranka ya Dade dafatan ka wuni Lafya Idan bazaka dumuba bari in tayaka goge kafa” fadi tayi tana fari daman na abun nema bane wajen RAINA tun tana karama ta iya fari, Sa hannunta keda wuya yaji wani iri sha'awarsa ta tashi wani banxan kallo yayi mata yace “Waike meyasa kin fiye shishigine nifa Karki manta badan bariki bane irinki don haka kiyi gaggawan cire hannunki kafin inyi maganinki sakarya kawai Mara zuciya yarinya saikace karya?” Raina kanta a kasa yake don cin mutuncin danish bayau yafara ba amma nayau yafi kowanne muni dayace mata yar bariki, Tsame hannunta tayi tayi waje ta rufe fuska sai kuka saida tayi mai isanta ta nemi guri ta kwanta kamar Kullun ta mike donyin. Ibadanta sai taga Danish zaune yana kallonta batayi saurin bude idoba saida tayi motsi ya kauda idonsa RAINA tace acikin ranta “Hmmmm lokacin ka ne Danish amma nawa yananan tafe” Alwala tayi tazo tayi sallah har saida tayi Asuba Bayan tafiyansa masallaci ne kafin ya dawo babu RAINA babu labarinta “Wai me take nufi daga sallah saita wuce sasanta?”saida RAINA tayi kwana bakwai Danish yana mata wulakanci amma dukta jure mai martabane ya aiko a kira danish saboda yaune ranan dazai Tara matansa ya raba musu kwana Danish ya gamsu amma kuma dakamar wuya wai gurguwa da auren nesa shi bazai taba kiran Unaiza ba saidai ysba jakadiyya sako ya raba kwana biyu haka akayi Unaiza taji dadi don yau kwana takwas ba Danish babu alaman sa dadinta daya bayason RAINA, Nanta fara shirye shirye amma ni humairah nace Allah yarabaki da Tsiran makaho. [4/26, 7:53 AM] Melody🎤🎤: *156-160* 👸🏻 *RAINA* *(The beautiful princess)*👸🏻 © _*STORY & WRITTEN BY HUMAIRAH (Melody)*_ *BABI NA TALATIN DA BIYU* Unaiza ta tanaji komai don mijinta amma da dare yayi sai taga akasin haka babu shi babu diriyarsa nan hankalinta ya tashi bata tsaya bata lokaci ba sasan danish ta wuce taganshi zaune dagashi sai boxer wani dadi taji aranta wucewa ciki zatayi danish ya janyota har saida kanta yakusa haduwa da gini a tsorace take kallonsa “Amma Unaiza saiyau nasan cewa kina yaudaran kanki sannan Kisani ban yarda da shigo shigo ba zurfi ba kina tunanin zakizo mun cikin daki hakanan baysn iskancin dakikayita yi a baya Kisani kafin in kiraki matata sai kinje Asibiti anyi miki tests din STD( Sexual transmitted diseases) Sannan ki koyi ladabi oh Allah mai yasa mata masuda kunyane daga kunga anyi muku kishiya koh kunya saiku fara abunda da bakuyi toh Kisani Unai bazaki taba yaudarana ba kuma ki bacemun naji yau girkinki ne Amma kuma ngd bana bukatan zuwanki” Duk abunda suke Duk a kunnen Raina sukeyi Unai tabata Rai bata iya cewa komai ba tasan cewa Allah ne yake sakawa Danish abubuwan datayi mai a baya wasu hawayene suka kwararo daga idanunta durkusawa tayi har k'asa “Mijina ka tausayamun kayi hkr kabani dama in nuna maka cewa yanzu bada bane daman duk rudin shedan ne” “Tir da wannan shedan din Unaiza kuma karkiyi amfani da shedan wajen kare kanki don kina daya daga cikin shedaniyar kanki ki tashi kafin ranki ya baci banza kawai wawuya sakarya dubabki kaman wata tsumma a randa mtwwwew”. Tashi yayi ya dauki jaridarsa ta Daily trust ya shige falonsa Ya b'ame kofa bam yabarta zaune a kasa tana kuka, haka akayi kwana biyu Unaiza bata samu wani rabo daga jikin Danish ba kwanan Raina ne yau amma bata wani dauki taci Alwashi saita gwara kansa tunda ya wulakantata a matsayin mace mai Aji da Sanin yakamata yau yaci ace tazo inda yake amma danish shuru yakeji har misalin karfe biyu na rana, Sai safa yakeda marwa saida yaji wani jiri yarasa meyasa yakejin Raina har kokon zuciyansa itakoh Azumi takeyi dayake yau litinin har ta wajen sasanta yaje kozai ganta amma babu ita babu alamarta sallamar jakadiyya ne ya katse mishi tunani ya juyo da sauri kamar zai mata tambaya sai yayi shuru Jakadiyya tace “Ranka ya Dade Abinchi yana dinning room koh zamuje kaci abinchi” Kallonta yayi yakasa hakuri “Wai yau Lafya Gimbiya koh motsinta banjiba koh Lafya?” Dariya tayi “Kamanta tana axumi ko bata sanar dakai bane?” Danish yarasa mezaice “Eh ta gayamun na mancene kinsan abunda yawa kitafi zanci abinchin” fitarta keda wuya yayi wani k'ara lallai nema shine zatayi Axumi takasa ta sanar dani saikace ba mijinta ba? Danish dai yakasa cin abinchi hankalinsa bai k'ara tashiba saida yaga dare yayi RAINA batazo dakinsa kwana ba ai tuni yaji kaman zai haukace ganinta ma kadai yana sashi nishadi dukda hantara dayake mata.. Itako koh ajikinta don bata tashi sannan tayi Alkawarin sai yarima Danish ya nemeta, Misalin shabiyu yafita zuwa sasan RAINA da mamaki yaganta zaune tana kallon TV tana dariya daga ita sai kuyanginta guda biyu Wanda kusan tare suke barci, Hangenta yayi ta tagansu dayake kirar ginin na tura wane mai fakada2 Windoji toh yana ganinsu wani dadi yaji yajingina da bango jiyake kaman yayi sufa yadauko Raina acikin ransa yake cewa Wai kota dauka kwana uku nace? Da har yanzu takasa zuwa dakina mu k'wanta, Ni humairah nace namiji kenan lokacin da damar tazo kayi wasa da ita sai yanzu data kubuce? A ranan Danish bacci yayi harda su sumbatun kiran Raina amma kafin baccin ya k'washeshi saida yakai kusan Asuba, Tunda safe RAINA ke shirin zuwa Kaduna donyin siyayya a *IBRAHIM KANGIWA STORE* dake kaduna wayarta ta dauka ta tura ma Danish sakon kamar haka *Slm dafatan ka tashi cikin koshin Lafya da kwanciyan hankali Ina Neman izini zani garin Kaduna siyayya sainaji reply* Kirimmmmmm wayar Danish tayi k'ara ganin lambar dabai saniba a tunaninsa Unaixa ce wani tsaki yayi yakoma ya kwanta yana juyi “Ji sakarya koh ina ruwanta da tashina Lafya koh ba Lafya ba kifi ruwa gudu ina ruwana wani sabon salone kiran sallah da husir kiwanice mun zaki fita da kina gayamun ne”. [4/27, 7:02 AM] Melody🎤🎤: *161-165* 👸🏻 *RAINA* *(The beautiful princess)*👸🏻 © _*STORY & WRITTEN BY HUMAIRAH (Melody)*_ *BABI NA TALATIN DA UKU* _*SADAUKARWA GA Abeeda, Baseerah, Habiba Aliyu, Sarah, Umeegee, Huraira, Red butterfly, dafatan duk kun wayi gari cikin koshin lafya😘😘*_ Jiyayi ana busa sarewa ana takawarki lafya yar sarki jikan sarki matar Yarima Danish Allah yakaiki lafya yadawo dake lafya Uwar biyu insha Allah kamar a mafarki Danish ya leko taga Ashe RAINA ce zata fita cizon yatsa yayi yace “Kash da nizan kaita ai nayi tunanin waccan yar iskarce Unaiza” kallon Raina yakeyi kamar zai cinyeta ta shigewarta cikin mota ta k'ara gaba tabarshi tsaye bayakoh motsi koya zasu kare da raina idanta dawo koh zata Dakin nasa... *Cikin Kaduna* Raina ce tafe da kuyanginta da fadawa guda biyu suna mata kirari tuni ta dakatar dasu tace “Kubari Idan muna masarauta kuyi amma inhar nabar masarauta koh Gimbiya banaso a kirani dashi cikin plaza suka shiga kwando suka fara dauka suna zagayawa abun mamaki RAINA taga wasu yara guda biyu mace da namiji kamarsu ta baci kuma abun mamaki sai tattakawa sukeyi gwanin sha'awa tuni ta shagala da kallonsu duk inda sukabi saita bisu sukuwa kuyangi da fadawa kallon abun al'ajabi sukeyi kodai Gimbiya RAINA tasan yaranne kuma kamarsu ta baci da ita saidai su fararene tas wannan maganar da kuyanginta keyine na fadawa. Tana isa kan wani kwana sai tayi arba da Ummu Abrar wacce tayimata halacci lokacin da take cikin tsanani wacce ta sadaukarwa yayan cikin wani ihu RAINA tayi ta rungume Ummu Abrar tace “Ashe rai kanga Rai Ummu Abrar Ashe zan kara haduwa dake a duniya Kaico duniya ya Allah ka dauwamar damu acikin jin dadinka ya Allah kayi mana k'waron damuwa ya Allah” saita fashe da kuka tana tuna rayuwar data shude Abban Abrar shima sai gashi lallashinta sukeyi harta labarta musu irin Rayuwar data fada harda mutuwan Goggo da haduwanta da iyayenta da matsayin ta a yanzu na jinin sarauta matar yarima, Ummu Abrar tace “Duniya labari kana naka Allah yana nashi Ya Bayan saduwa? Kin tafi kinbarmu da k'ura Farid yadawo wai inakike ina cikin dakike dauke dashi ai tuni nace mai ai kintafi da ciki yaje ya nemeki achan inda ya auroki kinga yan biyu da faiz da faiza sun girma k'warai” Juyawa RAINA tayi taga fadawan sunyi nesa da ita tace “Idan bazaku damuba mugama siyayya muje kajuru in nunawa mahaifina ku amma Karki sake kice yayana ne” Haka akayi suka kammala siyayya Raina ita tabiya masu Ummu Abrar komai yan biyu kuwa sai murna sukeyi sunga Aunty sai surutu suke mata RAINA tana kallonsu cikeda So da k'auna, fitowansu keda wuya RAINA taga Farid tsaye shida wani mutum Kallo daya tayiwa farid taganeshi shima haka yake kallonta, cikin mota suka shige Lokacin farid ya rugo aguje yana ihun RAINA amma ina tuni fadawa sukayi kansa suka fara duka “Kasan matar waye kake kiran sunanta gatsau ba Gimbiya ba komai kul matar yarimace yar sarki jikar sarki” itakoh RAINA tana cikin mota tinted batakoh damuba sai da taga ana cimai mutunci da yawa ta saukarda window tace “Pls ku kyaleshi yafadi abunda zai fadi” Farid kamar zaiyi hauka yace “Raina kice kin yafemun kozan samu Ganin k'waina a duniya tun Bayan rabuwanmu nayi aure amma har yanzu matsala muke samuda matata pls RAINA ” wani kallo ta watsamai tace “Direba muje Dan Allah” haka RAINA tabar Farid durkushe yana kuka wiwi, sai kajuru da isarsu aka bude musu wani katon gate kaman na gidan Yari Ummu Abrar da Abban Abrar mamakine ya kashesu a zaune lallai Idan baka mutuba baka gama ganin hikimar ubangiji kuyangune suka zagayesu suna masu marhabin lale sarewa kawai ke tashi abun gwanin ban sha'awa sai Ummu Abrar taji inama ace itace, jakadiyya aka aika wajen mai martaba tuni yabada izinin ashigo dasu sunga karanci iri daban daban saboda a Rayuwa sarki MAMUDA idai ka taimaki Raina a rayuwa toh tabbas kaime Arziki ne, haka ya rungume yan biyu jinsu yakeyi har cikin ransa RAINA dukta fuskanta amma tace acikin zuciyanta Saidai ku kirani da uwarku ta lahira amma bata duniya ba. Haka aka maidasu da alkawarin zasu dinga zumunchi tunda ga Gari sun sani sun tafi da dukiya k'warai duk wainar da ake toyawa Danish yafita cikin gari. [4/27, 4:49 PM] Melody🎤🎤: *166-170* 👸🏻 *RAINA* *(The beautiful princess)*👸🏻 © _*STORY & WRITTEN BY HUMAIRAH (Melody)*_ *BABI NA TALATIN DA HUDU* _*Dedicated to UMMI HAMBALI & UMMI AISHA*_LYSM😘👍🏻 Bayan tafiyanzu ne RAINA ta wuce sasanta dayake tana azumin tsofaffi ne datayi alkawarin zatayi guda hudu, toh shirye shiryen dafe dafe kawai akeyi ayi wannan yayi wancan Danish Dai kamshi ya isheshi gashi wata irin yunwa yakeji kamar zai mutu da mamaki ana gamawa yaga ana shigo dasu ana jerawa kan dinning ai kafin ayi mishi tayi ya isa dinning din saida yaci yayi kat kannan ya tashi ta wuce masallaci saida yayi sallan magariba da isha yadawo amma shuru kakeji babu RAINA babu labarinta, tana shan ruwa tayi sallah ta nemi guri ta k'wanta kuyanginta nabata labari daga bisani ta haye saman bene, Danish daya kasa hakuri yace “Wai me take nufine saikace ba aure mukeba?” ni humairah nace kaikuma meye matsayin wulakanta ta dakakeyi?. Kasa zaune yayi ya kasa tsaye ai tuni ya zura jallabiya yayi sasan RAINA yana isa a tunaninsa babu kowa ai tuni ya kutsakai k'watsam saiya hangi kuyanginta zazzaune suna tatsuniya sadaf sadaf yazo zai wuce sai kuysnga mimxe tace “Ranka ya Dade yarima mai jiran gado Gimbiya hutu takeso tace koda mai martaba ne abashi hakuri tayi Azumi ta gaji” wani mashi yaji ya sokeshi acikin zuciya jiyake kaman ya bige kuyangar lokaci guda yaji kunya ta kamashi juyawa yayi yana cizon yatsa mai yasa yabari suka ganshi acikin Shashenta? Aiba girmansa bane haka ya dinga kiran wayarta amma no answer daga karshe switch off Danish yashiga rudani tuni ya haukace yana sunbatu. Danish yaji ransa kaman zai fita wani zazzabi ne ya damk'eshi sai k'yarma yakeyi amma saboda karfin hali irinna namiji saiya daure koh sallan Asuba yakasa zuwa Mai martaba yashiga rudani k'warai saboda rashin ganin Danish dukda yasan yanada iyali amma duk me iyali ai Asuba nayi zai mike Idan najasa ce ai yaci ace yayi wankan tsarki yafito masallaci haka ya aika jakadiyya wajen RAINA donya tambayi lafiyar yarima, Raina tace ita batasan ko meya hanashi ba saboda bacci ya dauketa saboda gajiyan Azumi. Haka aka kira wayansa shine yake sanarda Mai martaba cewa bashida lafya ne tuni aka kira likita yadubashi yabashi maganin bacci tsawon kwana biyu yace baida bukatan kowa gashi Unaiza keda girki Raina kuwa koh ajikinta wai an tsikari kakkausa, sai hidimarta takeyi Randa RAINA zata amshi girki ne tun wuri Danish yasa akira mishi RAINA amma taki amsa kiran, dare nayi Danish yacire kunya Bayan yagama cin abinchi yayi sallah zai fita kenan yaci karo da Unaiza tace “Munafiki mak'aryaci kasan abunda ka shuka ma kanka kwana biyu danakeda girki ka kirkiri ciwon karya amma dayake RAINA ce zata amshi girki har binta zakayi dakinta koh abinci na ka kasa ci kace baka buk'atan kowa a kusa dakai kasani Duk abunda kayi kasani adalci nakeso kayi tsakaninmu karka manta cewa ance kayi mata daya Idan zakayi adalci kayi biyu har zuwa hudu amma meyasa zaka kasa abunda Allah ya daurama?”. “Dakata dallah malama Karki cikani da surutu Ashe ke malama ce banda labari yaci ace kin bude makarantar Islamiyya don koyarwa” mtww Yana gama magana yayi wucewarsa sai inda RAINA, Unaiza tayi kwafa takoma daki taci kuka kamar ranta zai lula, yana shiga sama ya wuce daidai ya zauna don ganin ta ina zata fito Raina ce tafito daga toilet tayi daurin kirji bata sanda mutumba kawai taji motsi da gudu takoma kafin takai toilet Danish ya ruk'ota sai a kan kirjinsa tayi wani lamo shiko tuni jikinsa yafara kyarma, jiyayi kamar ba'a duniya yakeba tunda ya auri Unaiza sau biyu yataba kasancewa da ita haka, RAINA sai kici kici take amma ina Danish yayi mata rukon da bazata iya koda motsawa ba, tuni yashigar da ita wani yanayi Wanda sai Wanda yagani don ban ganiba sumbatar bakinta yakeyi tuni ya k'wance towel din da yake sanye ajikinta ai bai k'ara rudewa ba saida yayi ido biyu da dukiyar fulaninta ya wani cutsa kansa yana murzawa yana tsotsa ai tuni RAINA ta fara baje nata kolin. [4/29, 7:37 PM] Melody🎤🎤: *171-175* 👸🏻 *RAINA* *(The beautiful princess)*👸🏻 © _*STORY & WRITTEN BY HUMAIRAH (Melody)*_ BABI NA TALATIN DA BIYAR. _*Ina mika TAAZIYYA ga Family din Nasiru hayin Malam Alhaji bisa ga Rahin daya daga cikin yan biyunsu UMAR FARUK dasukayi Allah ubangiji yasa mai cetonmu ne ranan gobe Allah yabaku hakuri Rashi Allah yakawo masu amfani Allah yasa ya huta Amin*_ I,MISS YOU FARUK😭😭 Haka kolin saida taga Danish yafara fita hayyacinsa kannan tayi karfin hali ta yakice kanta tabarshi Yanata sumbatu acikin ransa yace“tabbas Raina macece tanada duk wata niima da ake bukata atareda mace Amma kuma mai yasa Saida tabari nashiga cikin kogin mararinta kannan zata zabi ta raba jikinta da nawa?”wani irin haushi yaji itakoh raina tuni tafara shiri cikin kayan baccinta, saida ta shafa maya mayai kala sunfi uku ga sure, ka body spray, ta fesa turaren baki Sannan ta nufi gado zata k'wanta, tuni danish yayi fuskan tausayi ya matsa kusada ita yace “Pls honey karkiyi mun haka wallahi bantabajin cewa inasonki ba saida kika kaurace mun kece farincikina Raina Dan Allah ki tausayama bawon Allah kizama mace ta farko dazata shayar danin ruwan dadi kizama Mace ta farko dazata tabbatarmun da cewa nayi aure haba mana RAINA kalleni Narasa duk wani farinciki tun ranarda na auro Unaiza banida wani iko a matsayina na namiji.....”. “Dakata Malam ka isheni da surkullen ka pls ka tashi kafita bacci nakeji”RAINA ta bata rai badon tanaso ba tanayine donta rama abunda Danish yayi mata lokacin datake tsantsar bukatarsa Danish ba kunya ya matso inda Raina yafara gayamata kalamai masu dadi da ratsa jiki ai tuni suka fada kogin maliya ni humairah bashir na rufe kofa nafito don Abun ya girmi kakata a lahira, Washe gari da Asuba Raina ce k'wance bata koh iya daga hannu bare tayi magana saboda irin gashin dataji daga wajen Danish shiko babu abunda yakeyi sai lallashi ya tabbatar da cewa yau shi namiji ne daga bisani yace acikin zuciyansa Ashe haka Yan bariki suke tabbas Idan haka suke zan bawa mutane da dama shawara su nemi irinsu su shiryar dasu kodan suyi shahada su samu lada kan lada, Tashi yayi ya dauketa cik sai toilet inda ya hada mata ruwa ya taimaka mata wajen gyra jikinta Sannan yayi nasa wankan sarkin Sannan yayi norml wanka na sabulu, Sallaya RAINA ta shimfida don gabatar da sallah shiko batareda bata lokaci ba ya wuce masallaci, Yana dawowa dakinsa ya wuce don bayaso yakoma inda Raina take yahadu da koda kuyanginta guda daya. Raina ranan wuni tayi bacci haka Shika Danish don basu sukayi breakfast ba sai misalin karfe Sha biyu na rana lokacin abincin rana na shirin sauka, Ranan sun shayar da Kansu ruwan soyayya mai dadi inda Danish yayi nasaran maye mata gurbin farid acikin rayuwar raina abun sai Wanda yagani, k'wana biyu RAINA keda girki suna shanawa suna zaune a falone Unaiza ta aiko tanada bukatan ganin yarima amma sai cewa yayi kuce mata ina falo tazo da kanta abunda ya batawa Unaiza rai tace “wato nizai wulakanta a gaban matarsa Wato ni banida yanci acikin gidannan Allah yasa ba karuwa yaganni ya auroni ba”kafinta k'arasa magana Danish ya kwasheta da mari gigitacce yace “Am warning you for the first time you brat Wannan yazama ranan karshe dazaki sake kiran RAINA da karuwa Idan kika zageta tamkar kin zagi mijinki ne kuma kisani matuk'ar ban yafe miki ba Wallahi Bake ba rahamar ubangiji” daka kafarsa yayi yakara da cewa “Kingani toh saina daga zaki shiga Aljanna kisani tunda naga giyar Hauka da jahilci yana reto dake a sararin rashin tarbiya”. Yana gama magana yayi wani kwafa Tuni RAINA tasha gabansa tace “Yayana kuma mijina ba girmanka bane ka tsaya ka saurareta kohba komai matarka ce pls” kallon RAINA yayi yadda take magana a natse babu hayaniya aciki bare hargagi irinna Unaiza yace “Gimbiya sarautar mata kisani koh a lahira wani yakanci Albarkan wani haka ma a duniya taci darajarki”komawa yayi dabaya yace “Yar mulki ina sauraren ki koh mushiga daga cikine?” tuni tayi saurin cewa “Ah ah Dan Allah kayi hakuri bisa ga kuskuren danayi maka kayi hkr ka yafemun” Kallonta yayi acikin zuciyansa yace “Bari alalan gwangwani kowa yaci yakoshi sai yace ya iya hmmmm Unaiza kenan bazaki taba yaudarata ba har saimunje anyi miki gwajin STD” RAINA ce ta katseshi tace “Wai har yanzu maganar bata kareba? Karfa aci da rabona tuni ya sallami Unaiza suka koma cikin falo inda suke kallon *The reach for the star* Da yammane lokacin muftarin Girkin Unaiza yashiga yakirata dacewa ta shirya yanaso su fita tayi shiri wanda Baku zato ta shiga cikin mota suka fita tareda fadawa RAINA tana garden taga wucewar yarima Danish saida taji wani iri amma tasan bakacin rabonka kaci na wani. _*Toh masu karatu ga littafi yazo gangara koh me karatu zai iya wani tsokaci akan littafina RAINA, Room abude yake wajen amsan duk wata shawara?*_ Danish dai sun fita shida niyyan zuwa Asibiti ita kuma Unaiza da niyyan outing acikin ranta ko wacce lalura likita zai fadi kubiyo ni yar mutan zazzau. [5/2, 4:26 PM] Melody🎤🎤: *176-180* 👸🏻 *RAINA* *(The beautiful princess)*👸🏻 © _*STORY & WRITTEN BY HUMAIRAH (Melody)*_ _*Ina kaunarku masoya Kuna raina akullun farinciki ku shine nawa Allah yakara mana son ma'aiki, Sannan ina baran Adu'arku Zazzabi ne yatasani saboda tambaysn da ake shiyasa na daure nayi muku Wannan Allah yasa mudace*_Amin LYSM😘😘😘 BABI NA TALATIN DA SHIDA Tafe suke tareda yan rakiya Wato fadawa cikin motoci tinted glass baka ganin kowa sai kanka haka sukazo wani babban Asibiti da ake cewa *GIWA HOSPITAL* Asibiti ne Wanda ya amsa sunansa koh a kasar waje sai haka ganin hospital yasa Unaiza saurin juyowa tace “Nan inane mine?” wani kallo yamata yace “Me kika gani? Koh asaran kudin Tara akayi da akaje England karatu? Hospital ne to malama Idan baki gane ba” shuru tayi don tasan komai yana iya faruwa, Fitowa tayi tana yake shima kuma irinta yake mata suka shiga reception OPD nan suka bukaci ganin Doctor Moddibo Wanda abokin Danish ne lokacin da suke k'asar Saudiyya cikin wani office suka shiga suka zauna koh minti uku basuyiba sai gashi dariya yayi suka gaisa yace Unaiza ta biyoshi tafiya take amma kallon Danish takeyi shiko tuni ya kauda kansa, wani guri suka shiga nidai naga ansa *Laboratory* nasan dai wajen gwaje gwajene haka aka dauki jijinta Sannan akasa mata wani Abu kamar cotton bud acikin Vigina dinta, aka lakuto wani Abu kamar madara koh ince koh koh nan aka umurceta data sakko suka fita tareda Doctor. Tafe suke zasu koma office Unaiza ta kalli doctor moddibo tace “Wai gwajin me akamun ne doctor Saikace wata mai daukeda citar kanjamau?” shima da yake doctor moddibo ya tsani Unaiza tun wani zuwa dayayi yaga ta yara daban kawayenta suna lalacewa harda yimusu dariya yaji batayi masa ba yace “Ai baxamu iya saniba sai result yafito ba kanjamau kadaiba harda wasu abubuwa da dama zamuyi gwaji akansu don haka kina iya shiga gaba muje” Mamakin maganar sa tayi maiyayi zafi Shiba huta ba, tabe baki tayi suka kutsa ciki da mamaki Suka nemi Danish suka rasa amma Wannan plan din nasune tsakanin doctor da danish kallon doctor Unaiza tayi tace “Doctor ina Yarima yake inace nan muka barshi?”doctor ya tabe baki yace “Bakida MATSALA inace Yarima Danish ba yaro bane? Duk inda yaje zai dawo ” wani irin kallo Takeyiwa doctor saboda taga sai wani bak'ar magana yakemata tuni tafara lashe baki tana wani irin k'warkwasa doctor ya dauke kansa kaman baisan tanayiba shiko Yarima Danish yana labe yana kallon abun mamaki yace “Biri yayi kama da mutum abunda ake gayamun ya tabbata cewa Unaiza yar *PLS CALL ME* ce”. Tashi tayi tace “Doctor pls inaso kayimun taimako daya I need you ka tausayamun mijina baya kulani baya kusantata pls let's have fun” magana takeyi cikeda iyawa da bariki tana wani bude gyale tareda bude kirjinta da dukiyar fulaninta suka fito saida takai kusa dashi Sannan ta zauna akan tebur din tana shirin shafashi tuni ya daka mata wani tsawa Wanda saida naga kirjinta ya buga yace “Amma ke banzace Wallahi kina tunanin irin mazan dakike yaudarane kina tunanin ni irin sauran abokan mijinki ne wayanda babu abunda sukasa gaba sai ashararanci toh kisani ni inada mutunci ban bari ya zubeba ke kiji tsoron haduwarki ga Allah don shine kadai gatanki a duniya harma a lahira sakarya kawai” “Lallai ne kace wani Abu Moddi meyasa baka wayeba? Pls stop shouting at me Idan ba hakaba sainayimaka sharrin da bazaka taba fitarda kanka ba” Bude kofa taji nanta fara kukan karya cewa moddibo yace zaiyi lalata da ita Danish yabita da wani k'azantaccen kallo lok'aci guda ya tsinketa da mari yace “Bantaba sanin cewa ke bara gurbi bace cikin mata nayi ladamar aurenki kisani duk abunda kikayi naji kuma nagani kijira sakamako daga LAB matukar kina daukeda cutar Kanjamau anan cikin Asibiti zan koreki kije gidan ubanki ki karasa guntun rayuwaki daman duk yan gidan naku taron tsintsiyane ba shara kowacce miji ya sakota kar kiyi tunanin banda labari inajin komai kisani”ai tuni jikinta kaura yayi la'asar sai kuma gabanta yafara dukan uku uku sai kunya tabiyo baya. [5/2, 7:43 PM] Melody🎤🎤: *181-185* 👸🏻 *RAINA* *(The beautiful princess)*👸🏻 © _*STORY & WRITTEN BY HUMAIRAH (Melody)*_ _*Dedicated to FATIMA ADAMAWA (Ummin Alkasim)❤ Ngd da kaunar novel dina dakikeyi Keta dabance Allah ya Albarkaci rayuwanki dana baby*_❤ BABI NA TALATIN DA BAKWAI Tuni doctor yafita yaje amso sakamako cikin minti goma yadawo dauke da fayal ya nemi guri ya zauna yabasu umurnin suma su zauna, Saida ya duba takaddun kannan yace “Yarima matarka bazata taba conceiving baby ba (Wato bazata taba haihuwa ba) hakan yafaru sanadiyyan shaye shayen magunguna Da takeyi ba bisa ka'idaba wayanda suke hana daukan ciki, Sannan tana daukeda Wannan cutar ta sanyi Wato toilet infection Wanda ake samu wajen saduwa Wato STD sexual transmitted diseases dagashi batada wani cuta”. Yarima ba k'aramin razana yayiba saboda jin cewa Unaiza bazata taba haihuwa ba, wani kallo yake mata Wanda yasata shiga taitayinta takasa koda motsi “Yanzu munada buk'atan magunguna Wannan infection din don yanzu zamu dauki hanya kasan batada kyau” haka aka basu magunguna suka wuce gida kajuru babu mai cewa kowa komai, suna isa gida sukayi parking yarima Danish yafito ya rike hannun Unaiza yana janta kamar wata akuya bai wuce koh inaba sai wajen sarauniya Maimuna mahaifiyar RAINA wacce takasance mahaifiyarsa Bayan rabuwansa da tasa uwar, Kwance take ganin Unaiza ne a gabanta yasata mikewa tana tambaysn lafya “Ummi gatanan ki tambayeta kitambayeta banida abun cewa Amma Unaiza Wannan bani kadai kikayiwa mugunta ba harda kanki kuma bani ba sakinki Wannan kadai ya isheki kunci acikin ilahirin rayuwarki oh Unaiza you are now a barring ” Babu abunda Unaiza keyi sai kuka Wanda nikaina saida Naji tsantsar tausayinta ya ziyarceni. Nan yabaiwa sarauniya Maimuna labarin komai Wanda hakan ya tada hankalinta sosai haka tayi musu sulhu tayi musu nasiha mai ratsa jiki kannan suka wuce suka fice dakinsa ya wuce saboda tsabar bakin ciki har mancewa yayi da abun faharinsa kuma sanyin idanuwansa Wato Gimbiya RAINA. *BAYAN SHEKARA BIYAR* RAINA ce nagani zaune daganinta cikine ajikinta yayi girma iya girma haihuwa yau koh gobe, Unaiza zaune a gefenta tayi tagumi tana kallon RAINA wacce aka dauke mata hankali da labarai masu debe kewa, Hawayene ya fara kwarara cikin gurbin idanunta tuni ta mike tayi sasanta tashinta ne yadawo da hankalin RAINA tacema daya daga cikin kuyangin lafya kuwa naga Yar mulki Unaiza ta tashi?” budar bakinta tace “Ranki yadade ai tunda ake baki lbr take kallonki inajin hakan yasata kuka”Ai tuni RAINA ta mike tace su jirata tana zuwa amma saboda umurnin da yarima yabasu akan kulawa da ita yasasu binta. Tana shiga taga Unaiza zaune tana kuka Mara sauti cikin sauri ta matsa kusada Unaiza tace “Kidaina kuka Yar'uwata Dane mukayi zaman marina amma yanzu mun zama daya Kidaina kuka komai kikaga yasamu bawa toh da Sanin Allah kuma kidauki kaddara damai kyau da Mara kyau shine cika makon musulunci kisa aranki Wannan abunda ke cikina nakine duk ranan dayazo duniya nayi miki Alk'awari saidai inke kikace bakiso” cikin sauri Unaiza ta dago tace “Kina nufin kice zaki bani Dan dake cikin cikinki?”raina ta kada kai alamun Eh ran Unaiza yayi fari kal jitayi kaman ta Goya RAINA daganan Unaiza tafara dariya. ********* Farid ne zaune yana yiwa mahaifiyarsa kuka tareda tuna mata baya da maganganun RAINA “Hajiya tabbas bakiyimun Adalci ba kin tauyemun duk wata dama lokacin da matata take tsananin bukatata lokacin kika datse duk wata halak'a yanzu kinga irin iftila'in daya riskeni, ga dukiya babu abunda ban tarashi ba a duniya amma Narasa dukiyar datafi komai muhimmanci a rayuwa Wato DA' tabbas hajiya RAINA batada Alhakin mu mukeda alhakinta kuma HAKKI SHIKE BIBIYARMU”. [5/3, 2:47 PM] Melody🎤🎤: *186-190* 👸🏻 *RAINA* *(The beautiful princess)*👸🏻 © _*STORY & WRITTEN BY HUMAIRAH (Melody)*_ _*This page is dedicated to my Friend my sister MARYAM MACCIDO daughter to Safiya Aliyu and EX-Provost FCE Zaria indeed we have to be remembering you May your gentle soul continue to rest in perfect peace may Aljannah firdausi be your final abode Amin😭*_ BABI NA TALATIN DA TAKWAS “Kai dallah rufemun baki shashashan banza RAINA itadin banza inzaka rungumi matarka ka runguma saboda itace wacce ta dace dakai ba wata ba Muneera itace zabina” wani irin tuk'uk'in bakin cikine ya riskeshi tashi yayi yana rikeda kirjinsa ai yana zuwa kofar falo saiya fadi aman jini kawai yakeyi, tuni hankalin yan gida ya tashi hatta hajiya saida abun ya tabata jitayi da tanada abun goge cikin zuciyan mutum saita goge sunan RAINA daga cikin zuciyan Farid, basu zarce dashi koh inaba sai giwa hospital inda akayi cikin emergency dashi Farid dai baisan Wanda ke kansa ba itakoh muneera hankalinta ya tashi saboda babu Wanda takeso irin mijinta burinta guda taga sun samu Zari'a a tsakaninsu amma tsawon shekara fin biyar babu ciki babu alamansa duk Asibitin da sukaje sai ace lafiyarsu kalau, Wannan abun ke damun muneerah hajiya ce tsaye Ambassador Buba kuwa sai kaiwa yake da komowa Wato mahaifin Farid cikin kankanin lokaci likita yafito yace “Kushigo cikin Office inaso mu tattauna” ai rige rige akeyi suka kutsa suka nemi guri suka zauna hajiya tasallah cewa take “Likita ka gayamun halinda Farid yake ciki?”. Likita ya numfasa yace “A gaskiya Farid yana cikin matsanancin hali halinda bazan iya misalta muku ba yana cikin tsantsar damuwa yana bukatan farinciki a tattare dashi koh kunada masaniyan cewa zuciyarsa gab take da bugawa? You are his parent dole kunsan damuwarsa?” Hajiya tayi fiki fiki da ido lokacin da Ambassador ya kafeta da ido yace “Likita ka ganta duk itace silar rugujewar rayuwar Wannan yaron ta rabashi da matar daya gani da idonsa yace yana SO sukayi aure ta rabashi da ita lokacin da take tsananin buk'atan taimako lokacin da yaron cikinta yake gabda fitowa duniya, tayi kokarin rabashi da matarsa da zafin hakan yasa yarinyar tayi masa bakin cewa saiya nemi DA' ido rufe yarasa ilai hakan tafaru gashi yana son haihuwa Allah bai bashiba likita ya kake tunanin uwar datayiwa wata uwa haka Allah zai duba lamarinsu?” Likita ta numfasa ya jinjina girman maganar yace “Ita matar tasa ina take? Kuma ina abunda ke cikin cikinta? Bakuda masaniyan inda take koh mahaifarta?”. Suka kada kai hajiya tafara magana “Yarinyar ta kasance yar bariki ce don haka bamuda masaniyan inane garin nata ada nasan tana Garin Soba don achan aka daura aure kuma Bayan wasu lokuta farid yasha zuwa amma babu ita babu labarinta har makociyarta an tambaya amma tace batasan inda ta nufaba”likita ya jinjina kai yace koh zaku iya Sanin sunanta kila asa cigiya koh Allah zaisa a ganta?”Hajiya tace “Eh kwarai nasan sunanta farin sani” “ko zaki iya sanar dani sunanta?” Hajiya tace “Sunanta RAINA” Dam Likita yaji gabansa yayi mugun fadi da mamaki masu karatu zasuce waye Wannan likitan toh ba kowa bane face abokin Yarima danish Wato Doctor moddibo, kallonsu yakeyi ido cikin ido yace “Kunaso kucemun Gimbiya RAINA yar sarkin kajuru MAMUDA?”da mamaki hajiya ta kalli Likita tace “Bafa Gimbiya bace sunanta RAINA wata yar bariki ce wacce taba bariki gaba ba bayaba tananan da wata tsohuwar kilakin uwarta wai ita Goggo” Likita yace yana zuwa wayarsa ya dauko ya budo hoton RAINA da yarima Danish yace “Hajiya ki kalli Wannan hoton itace RAINA da kike magana? Don nasan itama Wannan ta taba fadawa irin Wannan halin ta sanadiyyan saceta da wata mata tayi a daidai lokacin da uwarta ta haifeta” da sauri suka amsa wayar Suna dubawa da mamaki hajiya tasallah tace “Biri yayi kama da mutum ai Likita lokacin tsaida ruwan miya yayi itace Wannan Wallahi itace babu tantama” Likita ya amshi wayarsa ya maidata chargi, yaci gaba da cewa “Amma inhar Wannan ce yar sarki ce kuma batada wani da banda cikin dake jikinta haihuwa yau koh gobe abokina take aure kuma shine yarima mai jiran gado, kuma ban tabajin labarin tanada wasu yaya ba kuma ni dinnan babu inda bana shiga babu wasu yara acikin gidan Wanda yake bako a wajena”. [5/3, 7:29 PM] Melody🎤🎤: *191-195* 👸🏻 *RAINA* *(The beautiful princess)*👸🏻 © _*STORY & WRITTEN BY HUMAIRAH (Melody)*_ This page goes to my Entire family which is MANGUTA @BIDA GBAKO LOCAL government may Allah continue toh shower his blessings unto my family Much love with my beloved sisters' MARYAM SHEHU MUHAMMAD, FATIMA SHEHU ABDULLAHI, SAHURA SHEHU AMEENU, SADIYYA SHEHU ADAMU love you all❤😘😍. PROUDLY NUPE💃🏻💃🏻💃🏻 BABI NA TALATIN DA TARA Shuru hajiya tayi ta kasa koda motsi cikin ranta tace kaji rabo na minallahi daman yar sarki ce bansaniba kaico na duniya shiyasa wulak'anta Dan Adam bashida dadi tabbas nayi dana Sanin yiwa RAINA Wannan cin mutuncin Tabbas nasan bazata taba yafemun ba, Ambassador Buba yace “Likita duk yadda akayi itace Wannan koh zaka iya yimana kwatancen inda zamu samu RAINA?” Likita yace tabbas da kunje kajuru kukayi tambaya gidan sarki MAMUDA toh babu tantama gidansu raina za'a kaiku” sunyi godiya daga bisani wata nurse tafito tace musu Mara lafya ya tashi ai tuni suka fara rige rigen shiga kwance suka taradda Farid baya koh iya magana bare kuma yakaiga daga hannu kallon muneerah yake cikeda tsana tunda sukayi aure babu abunda ya tsinta illah tulin kaxanta daga ta jiki harta kaya zuwa abinchi ga tsantsar rashin kunya datakeyi mai babu girmamawa tsakaninsu daya fita itama zata fita Kullun tonon Asiri takeyimai wajen yan',uwa da k'awaye duk yadda sukayi dashi a gado saita fallasa abunda akace sirri ne tsakaninka da mijinka, hawayene suka zubo a girbin idanunsa lokaci daya ya kalli hajiya ya kauda kai tuni hajiya tafara kuka Likita yace “Baya bukatan kukanku face adu'a itace magani Ambassador Buba mahaifin Farid ya matsa kusadashi yace “Be a man and always be a strong hearted man men don't cry but women does DAT is the different btwn a man and a woman kasha kuruminka lokaci yayi dazamu he wajen RAINA mu roketa gafara Sannan ta sanar damu yadda tayi da Dan cikinta” ai Farid baisan lokacin daya tashi daga kan badon Asibiti ba yace “Dad are you serious dagaske kake kasan inda Raina take? Allah yasa RAINA ta aminche dani a karo na biyu tazamo matata koh zuciyata zata samu sa'ida”. Tausayin Farid ne Yakama hajiya tace “Farid dole kadauki komai a matsayin kaddara data riga fata RAINA matar aurece babu kai babu aurenta yanzu haka tana daukeda juna biyu na mijin datake aure don haka hakuri yaxama wajibi a garemu baki daya” farid ji yayi ransa ya baci dajin kalaman hajiya acikin ransa yace “hajiya kece silar komai daya faru dani Allah ubangiji kasa RAINA ba zubarda Dan cikinta tayiba duniya dana muzanta Fatana Allah yasa Raina ta yafe mana nida mahaifiyata”ai tuni Farid ya warke suma dayake masu tsohuwar dukiyane haka akayi convoy na motoci sai garin kajuru abakin kofar gidansu RAINA Daga saman bene RAINA ta hangi motoci a kofar gida an bude musu kofa mamaki bai gama cikata ba saida tayi tozali da Hajiya tasallah Sannan ga farid da farida ga yayan farid sai kuma mahaifinsa mutum gudace raina bata ganeba Wato muneerah wacce babu tantama kila matar Farid ce RAINA ta gyra zama tana shan madara wacce itace abun Shanta tunda cikinta ya tsufa. Cikin fada Sarki MAMUDA yace su shiga suka zazzauna sai kirari akeyiwa sarki nan hajiya tasallah ta natsu saboda Sarauta ta wuce gaban wasa gashi fadar ta tsaru iya tsaruwa nan suka gaisa da Ambassador buba daga bisani Ya labarta mishi dalilin zuwansu da abunda ya kawosu sarki MAMUDA yayi matukar mamaki a inda yake Sanar dasu cewa RAINA bata taba aureba bare haihuwa yarima shine Wanda ta fara aura, Tuni Farid ta durkusa gaban sarki MAMUDA yace “Ranka yadade Allah yaja zamani RAINA matata ce wacce nafara aure tun farkon kuruciyana” nan shima Farid yasanar da mai martaba komai, lokaci guda yasa aka kira mishi sarauniya Maimuna cikin gaggawa jakadiyya tadawo tace “Allah yakarama imani Gatanan tafe” haka yasa aka kira mishi yarima shima akace gashinan tafe Gimbiya yar sarki kuma sarauniya Maimuna ce tafe cikin kayan kasaita fifita kawai ake mata tana tafiya kamar mahauniya dukda girma yazo bai hana kyawunta fitowa ba. [5/4, 7:07 PM] Melody🎤🎤: *196-200* 👸🏻 *RAINA* *(The beautiful princess)*👸🏻 © _*STORY & WRITTEN BY HUMAIRAH (Melody)*_ _*Wannan shafin nakine Mai Nicky din mummy na Wato (HAJJA CE) Allah yabar zumunchi yabar kauna Sannan kema kina RAINA🤔 ROOKIE KAX Wish you Allah's blessings😘*_ BABI NA ARBA'IN Tana isa ta nemi guri ta zauna a kan kujerar zaman mutum guda sai kirari ake mata yar sarki jikan sarki matar sarki uwar Gimbiya RAINA Allah ya kara miki lafya da Nisan kwana, Hannu kawai tayi musu sukayi shuru ai hajiya tasallah sai aka kara sakin baki Allah magani sarki MAMUDA ne yayiwa Sarauniya Maimuna bayani abun yayi matukar bata mamaki tace “Ai Wannan maganar cikin mu bamuda Wanda zai bamu amsar maganar nan da cikakken bayani sai RAINA don haka inajin Wannan ba lokacin magana bane saboda a halin da ake ciki Raina tana matakin da batason wani hayaniya saboda juna biyun datake dauke dashi kunsan mai ciki babu abunda takeso sai kula da tarairaya don haka ku kuje sai ta sauka hankalinta yadawo jikinta sai ayi magana Ranka yadade ina fatan banyi maka shisshigi ba koda yake ai mijinta shima yanada abun cewa” Shima Danish haka akayi mai bayanin komai cikin razana da rashin fahimta yace “Ranka ya Dade Wannan ai zancen banza sukeyi zancen wofi inda RAINA tazo da DA' koh ta taba haihuwa koda bada aureba yaci ace mun sani amma yadda Ammi tace haka za'ayi kuje har saita haifamun Dan dake cikin cikinta saboda banaso wani koh wata suyi mana sanadiyyan salwantar abunda ke jikinta” hajiya tasallah tace “Allah magani yau nan nake ganin iko da mallaka dank'ari uwarta da mijinta sunyi mana haka inaga uwar gayyan ai inajin saita tsireni hmm nan ake son DA' Niko danayi ruwa nayi tsaki ai gashi hau ta hauni Allah na tuba kayafemun ” haka yarima danish ya tashi aka bishi da kirari itama Sarauniya Maimuna ta mike koh sallama batayi musu ba saboda sun bata mata rai” mai martaba ne ya basu hakuri yace suje sa dawo wani loton, Farid sai sake sake yakeyi acikin ransa yana cewa “Hmmm lallai ne yarima kake kowa inajin duniya baka taba son RAINA irin yadda nasota ba amma Bai laifina bane rabuwa da ita haka baka kaini son Dan cikin RAINA ba dukda ba cikina bane amma Allah ka dubi zuciyana ka haskaka mun da haskenka kabani haihuwa ya Allah banida laifi. Haka akayi musu rakiya haka da Ambassador buba da sarki MAMUDA sukayi Exchange na lamba don Susan lokacin da Raina tasamu lafya, farida haushin hajiya kawai takeji suna shiga mota tace “Yanzu dai *Ruwa cikin chokali ya ishi mai hankali wanka* Wannan saiya zama darasi Allah ba azzalumin kowa bane kuma duk abunda ka shuka komin girmansa zaka girba Sannan kuma *Alhaki kwikwiyone* kuma baishi yakeci batareda yayi tambaya ba” Hajiya ta bige mata baki tace *“Ke Ubanwa kikewa jirwaye mai kamar wanka kisani ban taba son raina ba kuma bazan sota ba koh zuri'a banason hadawa da ita bare wani nata Wannan ma inayine saboda Wancan sakaran da yakeji kaman zai kashe kansa ga matar Arziki chan muneera*” muneerah dake gefe tace “Hajiya bakida abun cewa a halin yanzu dole ki durkusa kiba RAINA take kowa hakuri ta yafe muku koh inada rabon ganin k'waina tareda annurin zuciyana Wato Farid a duniya hajiya yaci ace kin saduda kisani inhar nakara shekara ban samu cikiba Wallahi aurena da Farid yakare jiba juya ba amma a tauyeni lallai”hajiya bakaramin haushin zancen muneerah tajiba amma saita basar tana yake mugun kuka tace “Aunty munee ai ba'ayi hakaba insha Allah kaman kin haihu me kikeci na baka na zuba?”farida tana jinsu saida aka kai wajen unguwansu tace “Toh nidai zan sauka daman Idan mutum yaki sharan masallaci zaiyi ta choci” Haka ta sauka sukuma suka wuce. *GARIN SOBA* Jamila ce Wato Ummu Abrar zaune yara sun zagayeta abun mamaki dana irga naga yara iri daya kala uku Bayan abrar da fai'z da fai'za dana sani zaune take ta tasasu tanayimusu ta tatsuniya daka gansu zaka gane suna cikin walwala ga wani kara kyau da Jamila tayi suna cikin wasanne Abban abrar yadawo da gudu yaran sukaje suka rungumeshi haka itama Ummu abrar ta rungume shi abun gwanin ban sha'awa ta amsa kayan hannunsa tana yimai barka da zuwa tanayimai sannu abunda yasa a koda yaushe yakejin tsantsar son Jamila kenan tun baysn samuwar farinciki a tsakaninsu, haka yaran suka wuce falonsu don yadda ta koyar dasu dazaran mahaifinsu yadawo sukayi mishi sannu da zuwa toh sauran lokacin natane, saboda bataso su samu tangardan tarbiya dukda yaysnta mata basuda yawa, dakin mata daban na maxa daban dukda suna kanana don babu Wanda take shayarwa, sai kuma katafaren falonsu Wanda aka kawatashi da kayan wasa iri daban daban basu kallon wani film inba carton ba har sun saba, saboda Jamila tace barin yara suna kallace kallacen film din India, america, Philippines, Nigeria film harma dana Hausa yana taimakawa wajen gurbata tarbiyan yaro Allah yasa iyaye muyi koyi da Ummu abrar Amin. [5/6, 6:07 PM] Melody🎤🎤: *201-205* 👸🏻 *RAINA* *(The beautiful princess)*👸🏻 © _*STORY & WRITTEN BY HUMAIRAH (Melody)*_ _*Kuyu hak'uri k'wana biyu makaranta ne ya boyeni amma nakusa karasawa in huta kuma ku huta😜 LYSM😘*_ *BABI NA ARBA'IN DA DAYA* Falo yashiga ta taimakamai wajen gyra kansa donyin wanka da su cin abinchi saida ya natsu yafara sanar da ita labarin daya samu daga RAINA akan su fa'iz da faiza bakaramin razana tayiba tace “Haba ai wasane yana ganin zamu bashi yayane a banza dole hukuma ta shigo Wannan maganar kohda munyi don Allah toh saimun kwato ma RAINA darajarta da kima yasancewa da ba abun wulakantawa bane da gashi har uwarsa data shirya muguntar” Abban abrar yace “meye naki na tada jijiyoyin wuya? Iyeh ai saisunyi dasun Sanin amsansu koh ince zasu samu ysyansu da tsada”nan sukayita shawarwari nan suka zauna da shirin zuwan amsan yara. *********** Raina ce kwance tana salati ciwo ya isheta sai sumbatu yakeyi tana kiran sunayen Allah saida Raina ta lissafasu daga farko har kashe gaba daya gida ya rude ga jini sai malala yakeyi tuni RAINA ta suke yarima Danish kuwa da Unaiza hankalinsu ya tashi adu'a kawai sukeyi cik aka dauketa aka sata acikin mota babu inda aka yi da ita sai Giwa hospital inda nanne folder din ilahirin zuriarsu take nan aka shigar da ita Emergency batasan Wanda yake kanta ba Danish karatu kawai yakeyi mata yassara duk abunda ya sauwak'a Unaiza kuka take rusawa acikin ranta tace “Ashe haka haihuwa take tabbas mata abun tausayawa ne ya Allah ka dubi zuciyana inaso koda irin Wannan azabarce ta nakuda inaso inyini inayi inxan haihu” ni humairah nace yar sheba kawai Ashe dai kinason haihuwa. Doctor nuraini ne yafito daukeda wani fayal yace “Ina mijin patient dinnan?” da sauri danish yace “Gani” “Inaso kasa hannu a Wannan fayal din Saboda matarka aiki zamuyi mata don da alamu batada karfin daxata iya haihuwa”cikin sauri danish yasa hannu fadawa da kuyangu suma adu'a sukeyi Unaiza kuwa babu um ba um Ummu sai ido dake zubarda hawaye cikin ranta tace “Matsayine danka koh ya sukiraka da Mama saboda irin azabar da iyaye kesha wajen haihuwa tabbas duk macen datasan zafin haihuwa dole takara imani dason uwarta”. Saida akayi awa biyu ana aiki duk aikin da akeyi ni humairah banga abunda RAINA ta Haifa ba Sannan naga alamun tana numfashi a cikin talabijin din dake manne a bango, likitane yafito fuskarsa babu wani walwala koh murmushi yace “Munada buk'atan jini kaman Leda uku so samu kuma yanzu da gaggawa?”Danish yace “Likita muje inbada nawa wai Likita har yanzu bata haihu ba?” Unaiza tayi sauri tace “Likita koh nima za'a gwadani Idan jinin yazo daya sai a diva?” Danish yayi mata wani mugun kallo yace “Ke asuwa *KALAN DANGI* dallah ja chan nine dan'uwanta kuma jinina za'a diba asa mata mtwww barren kawai” Abunda yayi masifar batama Unaiza rai shine yadda Danish bayajin kunya koh nauyin cemata juya nida mai karatu mukace tsuntsun dayaja ruwa shi ruwa kan duka gefe takoma taci gaba da Adu'a Allah yasauke RAINA lafya ko badon tabata da' ba, suna shiga wani Daki akayi gwaje gwaje amma sai Likita ya kada kai yace “Ranka ya Dade jinin matarka baya bukatsn wani jini sai irin nata kuma irin nata yana wahala” Danish yace “then Likita mai kake nufi? Kana nufin cewa jijina bazaiyi wa RAINA ba Nifa jininta ne kuma Dan uwa sosai” “It doesn't mata my man blood group dinku ba daya bane koda uwa daya uba daya kuke” “yakamata Asama Wanda zaa samu jini irin nata koh aje bank asiyo Wanda zai mata” Danish yayi tsalle yace shifa Allan baran bai yarda ba waya yaciro yasanar ma gida Sarki MAMUDA da Sarauniya Maimuna suka hallara raina dai ana cikin tiyata room anacin kwakwa. [5/6, 8:08 PM] Melody🎤🎤: *206-210* 👸🏻 *RAINA* *(The beautiful princess)*👸🏻 © _*STORY & WRITTEN BY HUMAIRAH (Melody)*_ _*WANNAN PAGE DIN NAKUNE k'awayena abokan Arzuk'a, Abeeda Tautah, Mardia mossa Allah ya raba lafya, Zee Maman Suhailah, Hababi Aliyu T\W, Hauwa Salisu, Samrah, Hussnat, Maryam RUKOJI, Farida, RABI GOMBE, KHADIJA LAWAL ALIYU, Sannan tukwici ne ga MELODY NOVELS GROUP Allah yabar kauna LYSM❤😘*_ *BABI NA ARBA'IN DA BIYU* Suna isowa aka shiga dasu ciki abun Allah babu Wanda jininsu yazo daya Likita yace toh mezai hana baza'a kira waccan matar dake wajeba koh jininsu yana iya zuwa daya ai Danish yace sam baza'a sa mishi jinin Unaiza a jikin mataba saida Maimuna ta daka mishi tsawa tace “Kai meye Kakeyi lafiyar RAINA itace muke nema yanzu koh me za'ayi ayi acetomun rayuwar yata Likita akirata”ana fita aka kira Unaiza aka dibi jininta aka gwada saigashi jinin yazo Daidai dana RAINA ai baayi wata wata ba aka k'wantar da ita aka diba, tuni aka shiga inda sauran likitocin suke kanta ana Abu daya tuni aka fara fid'a Abun mamaki aka Ciro yara uku akayi gefe dasu sannan aka fara dinketa saida aka gama tsaf sannan aka fito da ita zuwa Dakin Hutu Doctor Nuraini ne yafito fuskarsa cikeda murmushi kowa ya mike ana tambayan lafya aituni yayi musu albishir da cewa ta haifa yara uku amma har zuwa yanzu nurses basu fadi me aka samuba wani kara Danish yayi yace “Doctor pls koh zamu iya shiga ciki muganta?” Likita yace “No ba yanzu ba bata bukatar komai sai Hutu Karin ruwa ake mata dana jini bata bukatan abinchi mai nauyi harna tsawon kwana bakwai sannan dazaran anji tayi tusa toh aiki yayi kyau”. Sannan ya wuce hajiya Maimuna koh ince sarauniya tuni tafara kira tana yadawa, tuni takoma gida aka shiryo masu hidima, RAINA dai ta haifi mata biyu namiji daya murna wajen Unaiza ba'a magana duk Wanda yaganta yasan damuwarta ta kau kallon Danish tayi tace “Nasawa mace da namiji suna” wani kallo yayi mata yace “ke kuma asuwa fi'ili fadi inji zugwai” Cikin jin tsoro Unaiza tace“nasawa namijin Abdul-Jabbar macen kuma Amatul-jabbar” dariya yayi yace “Gaskiya dole inyi miki kyauta sunan mahaifina waw wonderful nasawa dayar suna MARYAM” tuni suka kutsa inda Jariran suke akayi musu huduba Raina taga gata wai donma ance babu cin abinchi mai nauyi ga dogarai tsaye da an kwashe wayannan wasu ake kawowa kuyangu kuwa hmm ba'a magana Haka aka gyrawa RAINA gida komai Sabo ba aikin kowa bane saina uwarta da danginsu, kohda aka sanarda RAINA sunan yara tayi charaf tace “Uban kuturu yayi kadan ai ba'a isaba dole asa sunan uwata” tuni tasa aka kira Danish yana zuwa tace “Inaso asake huduba sunayen basuyimun ba a ka'ida Idan za'a sawa da suna sai an sabarda uwa inda sunan datakeso sai awani zabi suna batareda sanina ba?” Ai batareda bara lokaci ba aka sake wata hudubar Allah yaso baa yadaba Danish yace “Gimbiya ranki yadade wani suna kikeso a chanxa?” RAINA ta damre fuska tace “Aciremun Maryam asamun Maimunatu(QUEEN)” ran Danish yayi masifan baci amma sai yayi shiru raina ta kara da cewa “Indai nizan tsugunna in haifi ya toh baza'a taba samum Maryam acikin zuriata ba kasani daga rana irinta yau” Danish yace “tabbas ramuwar gayya yafita gayyar zafi yanzu cin mutuncin da raina ta tsnada zatamun kenan Ashe har gobe batason Rabin Raina Wato Ummi na?”ni HUMAIRAH nace fadi ka kara da Wannan kadai dole jama'a mu koyi darasi Dan maye yaci ya mance uwar diya bazata manceba. Kwanan raina Tara a Asibiti aka sallameta dayake babu ruwan nono Bata fara basu nono ba suna zuwa gida bayan kwana biyu Raina ta sanarda Ummin ta akan zata bawa Unaiza da daya ta Aminche tace “Kinyi tunani Raina tabbas dole Allah yaduba lamuranki Fatana Allah yayi miki kyakkyawar masauki”Raina taji dadi tasanarda mahaifinta shima ya aminche amma da sharadi sai mijinta ya aminche don shikeda iko dasu gaba daya........ [5/10, 9:26 PM] Melody🎤🎤: *211-215* 👸🏻 *RAINA* *(The beautiful princess)*👸🏻 © _*STORY & WRITTEN BY HUMAIRAH (Melody)*_ *BABI NA ARBA'IN DA UKU* Saida dare ya tsala Yarima Danish yadawo gida Dayake tunda Raina ta haihu a Dakin Unaiza yake kwana har sai tayi ARBA'IN kafin ta amshi girki haka Idan tanaso ta amsa babu Wanda zai hanata, Zaune take kuyangi suna daukeda yara suna jijjigasu tashi sukayi suka basu waje Danish ya kalli Unaiza a wulakance yace “ke malama ubanme kikeyi anan juya kawai get out” Raina tace “Kaga irin abunda banaso wai ba Allah yake badawa ba kuma inhar kana ganin ita tayiwa kanta illah meyasa nibanyiwa kaina illah ba nida nayi zaman bariki pls kabari banaso” Danish yace “Inhar bakibar nan wajen ba sai ranki yayi mummunan baci”Allah sarki mai karatu zaice meyasa Danish yakewa Unaiza haka? Toh kusani Danish yanason Unaiza dalilin Yin haka shine yanaso taji kuncin abunda tayiwa rayuwarta ne tayi data sani inajin a hasashen HUMAIRAH ba son Unaiza ne bayayi ba ah ah halinta ne bayaso amma yana kunshe dason matarsa kutuna Itace First LOVE dinsa a rayuwarsa kuma shiya gani yakeso. Haka Unaiza tafita Kamar munafuka shiko yanemi guri ya zauna Saida suka gaisa Unaiza tace “Sweet inaso muyi magana kuma akan wayannan yaranne inaso zanbawa Unaiza QUEEN saboda in rage mata radadin rashin haihuwa datake fama dashi Ummi ta aminche haka Abby” Wani tsalle Danish yayi yace “Toh ni ban aminche ba kuma ban lumunta ba kisani kibarta da radadin daman banaso tasamu sauki tunda haka taso da rayuwarta” Raina tace “Saidai kayi hak'uri don koh nono ban fara basuba za'a saboda wannan dalilin don haka kafin ranar da aka tsara nayin suna za'a sama mata magani ita zata shayar da Queen kasani don Allah zanyi badon wani kato koh katuwa ba ehe dole abunda zakamun itama sai kayi mata a matsayinta namai jego kasani kota dalilin haka Allah ya dubi duminiyata pls..........” Mamaki ne ya kashe Danish yace ikon Allah. Anyi shagalin suna Unaiza ta karbi QUEEN hannu bibbiyu Sai kula da take samu Kamar kwai koh kuda ba'a bari ya tabata haka Raina taci gaba danata rainon abun gwanin ban shaaawa. ********* *Bayan Wata uku* Sarki MAMUDA yakira Raina donsu tattauna gameda zuwan dasu farid sukayi “Raina Karki boyemun kisanar dani komai inhar kin boye mana bazaki bayewa Allah ba meye Wannan batun ya kunsa me kika sani kifada gani da Mahaifiyarki ga mijinki ga waziri ga maga takadda ka kilishi zaune” Ai kawai hawaye sukaga yana zuba a gurbin idanun Raina ta cije baki tace cikin muryan kuka“Allah yak'ara maka lafya Duk abunda suka fada gaskiya ne Amma koda duniya da abunda suke cikinta zasu hadu baxan taba bawa Farid da Uwarsa yayana ba saboda basu chanchanta basu cika iyaye ba hajiya tasallah itace silar rugujewar rayuwana ta rabani da mijina lokacin da nake tsantsar bukatansa akusa dani ai nida ita har abada bana yafiya ga Wanda ya cutar dani”kukane yaci karfinta Jakadiyya ce keta faman rarrashi tana bata baki, Sarauniya Maimuna tace acikin ranta “Tabbas Yata Raina ita kadai tasan ciwon da takeji komaye Wannan abunda yasa tace hajiya tasallah da danta basu chanchaci zama iyayeba?”. Saida Raina ta natsa kannan Sarki MAMUDA yace ta sanar dasu mafarin maganar datayi nacewa bazata bada yaraba sannan ina yara suke? “Tun kafin muyi aure hajiya tasallah ta nuna bata sona Amma haka danta yaji yagani yana sona, babu irin sunayen dabata kirana Tacemun Karuwa tacemun kilaki dukna jure har saida wataran tazagi Goggo, Ansa ranar aurenmu anyi aure, bayan aure aka kwace komai da mijina yake dashi ta dalilin mahaifin shi Dan gidan damuka mallaka muka dawo babu” Raina tana magana tana kuka kowa a wajen saida ya tausaya mata ciki harda mijinta dayaji Kamar ya kashe farid da uwarsa “Daki DAYA muka samu a tundun nufawa nan muke zaune mijina sai yayi dako mukeci mukesha hakanan muke zaune babu tashin hankali sai so da mutunta juna damukeyi har makota suna kwatance damu duk talaucin farid bai daina farantamun ba sai yakici yaga naci harda abun cikina BAYAN WATA BAKWAI. [5/10, 9:29 PM] Melody🎤🎤: *216-220* 👸🏻 *RAINA* *(The beautiful princess)*👸🏻 © _*STORY & WRITTEN BY HUMAIRAH (Melody)*_ *BABI NA ARBA'IN DA HUDU* _*SECOND TO THE LAST PAGE DEDICATED TO ALL MY FANS OVER THE WORLD🙋🏻🙋🏻🙋🏻*_ LYSM😘😍 Wacce wata Ranan lahadi tazama ranar bakin ciki ranarda bazan taba mancewa da itaba Aranan naga tsantsar kiyayyar uwar miji inda ta tasa danta gaba da cewa saiya rabu dani babu irin zagin da batayimun ba ina kuka ina rokonta amma ina mutane sun taru ana ta dubi abunda ke jikina amma tace Cikin shegene haka farid yasakeni saki daya toh kutayani figa yarannan sun halatta suzama yayansu? Nikuma nacema Farid karya sake ya nemeni sannan karya sake yakirasu da yayansa kuma inhar banida hakkinsa sai Allah yasaka mun baxai taba haihuwa ba bare yasamu mai ce mishi baba, Jamila mutuniyar Arziki itace ta dauki dawainiyata har rananda na sauke abunda ke cikina na haifi yaya biyu *FA'IZ DA FA'IZA* na bawa Jamila Wato Ummu abrar halak malak na umurcesu dakarsu sake suce basu suka haifesu ba”. Tuni guri yayi tsit saboda Kansu ya kwance da kalaman Raina, Kuka take amma tana magana taci gaba da cewa “haka na barsu nakoma Soba wajen Goggo haka nayi wankan jego har ARBA'IN biyu bayi sannan nakoma ruwa Wanda zan iya kira da tuban muzuru har zuwa rananda na bukaci Goggo tasanar dani asalina wannan kenan” Kowa saida yayi ajiyan zuciya waziri ya katse shurun yace “Mai martaba dole ne wayannan mutanen su fiskanci horo kuma yaya bazamu bayarba saimun kaisu kotu ta kwatanma wayanchan mutane Hakkin cimusu da yaya dasukayi kannan duk abunda Alkali ya yanke fakat” Danish yayi charaf yace “ai karyarsu tasha karya babu yayanda za'a basu irin wannan cin zarafi haka” Sarauniya Maimuna tace “Duk surutu bai tasoba a kirasu suzo su amsa laifinsu basai ankaiga zuwa Kotu ba wannan ai salon tonon silili ne ayi duk abunda za'ayi anan komai ya watse”. Haka akayi washe gari suka halicci fada dasu da zuriarsu gaba DAYA anyi muhawara sosai haka aka kira Jamila da mijinta suma suka hallara da yara kyawawa son kowa kin Wanda yarasa farare tas tas da ganinsu kasan yan Hutu ne sunyi girma a shekaru sunyi shekara Goma a kiyasi, farid koh da muneerah kaman su cinye yaran, faiz yace “mummy wai suwaye wayannan? Ina mukazo bamu taba zuwa waje mai tarin mutane ba mummy kalli wannan matar tayi looking ugly bata dariya”. kakarsa yake nunawa Wato hajiya tasallah acikin ranta tace Wannan katon mai gashin baki shine mummuna. Lauya aka kira mai zaman kansa yazo yayita da wajewa Da sharadi duk wajen wanda yara sukaje toh sune da yaya koda ba nasu bane haka akayi aka kashe wuta akace faiz da faIza su nemi iyayensu, Faiz yanada lalura wacce yake yawan Amai musamman indan sunyi tafiya mai nisa a mota acikin duhun faiz ya kwara amai dukya bata jikinsa yana zuwa wajen Farid Wato mahaifinshi da sauri yaja baya saboda shi daman akwashi da kyankyani haka faiz ya juya yakoma wajen Abban abrar aka tura faiza ita kuma tasha sweet hannun ta duk Danko Farid na taba hannunta Yayi sauri ya saketa itakoh sai shigemai take ai tuni ta juya sai inda dan'uwanta sai kwai aka kunna wuta da mamaki saiga yara duka wajen Abban abrar Lawyer yace Wannan ya nuna cewa kaiba uba bane shiko Abban abrar ya damukesu dayake yasaba sai a lokacin Farid ya farfado Daga baccin dayake aka barma Abban abrar yara da sharadin Farid zai dinga tallafa musu amma ba haka ransa yaso ba Raina kuwa dadi kawai takeji yan'uwan farid sukace wannan bayi bane Alkali yace “Yaya nasane amma baisan zafinsu ba don haka he deserve to be childless until the end of his life” haka aka watse kowa Yakama gabansa. *BAYAN SHEKARA GOMA* Su Farid sun shiga jami'a sunyi masifar sabawa da farid mahaifinsu saboda ziyarar dayake kawo musu har aka sanar dasu labarin komai sunji tausayin shi dana uwarsu wacce itama take kula dasu, amma abun mamaki basuda inda suka dosa sai gidan iyayensu basu yadasu ba Sucewa ubansu Uncle sucewa uwarsu Aunty, Gaba DAYA aka zama daya har aikin hajji sarki MAMUDA yabiya musu suna kasa mai tsarki Allah yayi masa rasuwa tuni aka Nada Yarima Danish yazama sarki. Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels