Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels [2/13, 9:42 AM] Xayyeesherthul-humaerath: .*DOCTOR YUSUF*👨‍⚕️ Gajeran Labari *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS* LABARI DA RUBUTAWA: *Xayyeesherthul-humaerath* Tare da *Zeey ƴar Mutan Zazzau* *SADAUKARWA GA, SIRRIN'YAMACE* *MARUBUCIYAR:* BABU RUWAN SO (FREE) WASA DA SO (FREE) AZZAWAJUL-MUKADDAR (FREE) JAMEEL (200) MATAR POLICE (200) KUCHAKAR KISHIYA (FREE) HAYATIY (FREE) AMEENATOU (300) KWADAYI (FREE) ASHE HAKA SO YAKE (300) SAI NA AURI MARUBUCI (FREE) AND NOW DOCTOR YUSUF FREE *TSOKACI: bamu fara rubuta labarin nan ba sai da amincewar Dr. Don haka bamu yarda a juya mana labari ta kowace siga ba,sannan labarin gaske ne illa wasu abubuwan da zamu kara ko mu rage,bamu yi labarin nan da niyar tozarci ga kowa ba illa nishadantarwa mai cike da wa azantarwa ga wanda ya fahimta* PAGE-1 ********Yau ne Rana ta Farkon Kasancewata a makarantar GOVERNMENT SECONDARY SCHOOL BAUCHI (G.S.S.B) tun daga Wajen Makarantar Tsari da Yanayinta ya tafi dani, Dauke Da Murmushi a fuskata na karasa ga Ofishin Shugaban Makarantar nan take ba tare da mun tsaya wani zance ba bayan mun gaisa ya mun iso zuwa Ss3 domin kuwa mun gama komai tun ka fin in zo Makarantar. Da shigana idanuna suka fara tozali da kyakkyawar budurwa da ta sake mun Murmushi nan take ba tare da na ankare ba nima na sake mata. Kasancewar ta abancin gaba kuma ita ka dai hakan ya ba Shugaban Makarantar ba ni umarnin zama a bencin da take. Ba Musu na karasa gareta. Tare da yi mata sallama, cikin fara'a ta amsa mun tare da fadin, "Barkanmu Da Safiya Yayana." Saurin dagowa nai ina kallonta jin kalmar da ta furta, "Yayana." Murmushin nan dai ta kare sake mini wanda ya sanya Ni sunkuyar da kai na nan take. Ba mu kara yiwa juna magana ba,har Malami ya shi go a ka fara yi mana Lesson. Abun Mamaki lokacin da aka zo kiran Atendas Bayan an kira sunanta Fateema Isma'il sai ga shi an kira nawa Yusuf Isma'il. Malamin ne ya dago yana fadin, "Fatima daman Kina da Yaya A makarantar nan?" Maimakon jin Amsar Aa ji nai ta ce, "Eh Sir." Da Mamaki mu ka kalli juna amman a wannan lokacin ma, Murmushin dai ta sake mun ka fin ta ci gaba da rubutunta. A raina ban da sake-sake ba abun da nake da farko ta furta mun kalman Yaya ga shi an tambayeta ma ta kara tabbatar da hakan. Ban ji Mamaki ba sai da wata ta shigo tana kokarin zama a bencin da muke ka da bakin Fateema ta ce, "Surayya wannan desk Din mune da Yayana, Please ki duba na su Zainab su biyune." Ta karasa maganar tare da kawar da kan ta. Karfe 12 dai dai muka fito daga Lesson, mota ce na ga anzo daukan Fateema ya yin da ni kuma daman da Kekena naje. Ko da ta shiga motar lekowa tai muna hada ido ta a daga mun hannu alamar byee byee 🤤🤤Matan Sirri A ci gaba ko adaina?? Kar wata ta fadamun green magana wlh sai in hwada miki blue In dai kuna so in sha Allah zan kokarta cikin sati daya mu kammala. 08103080717 Urs Xayyeesherthou [2/13, 9:42 AM] Xayyeesherthul-humaerath: *DOCTOR YUSUF*👨‍⚕️ Gajeran Labari *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS* LABARI DA RUBUTAWA: *Xayyeesherthul-humaerath* *SADAUKARWA GA, SIRRIN'YAMACE* *MARUBUCIYAR:* BABU RUWAN SO (FREE) WASA DA SO (FREE) AZZAWAJUL-MUKADDAR (FREE) JAMEEL (200) MATAR POLICE (200) KUCHAKAR KISHIYA (FREE) HAYATIY (FREE) AMEENATOU (300) KWADAYI (FREE) ASHE HAKA SO YAKE (300) SAI NA AURI MARUBUCI (FREE) AND NOW DOCTOR YUSUF FREE *TSOKACI: ban fara rubuta labarin nan ba sai da amincewar Dr. Don haka ban yarda a juya mun labari ta kowace siga ba,sannan labarin gaske ne illa wasu abubuwan da zan kara ko in rage,ban yi labarin nan da niyar tozarci ga kowa ba illa nishadantarwa mai cike da wa azantarwa ga wanda ya fahimta* KU GANE DUK DA KASANCEWAR LABARIN DA AKA BANI ZAN RUBUTA AMMAN NOVEL DOLE YANA BUKATAR AKARA MASA ARMASHI SANNAN MASU CEWA DOCTOR MUTUM DAYANE😹WANNAN BA DAMUWATA BANE NI DAI YA BAN LABARI KUMA GA SHI ZAN RUBUTA MAKU AHTO. PAGE-2 ****** Washegari Misalin karfe 10 na shirya tsaf cikin manyan kayana, sanye da hula,kamshi kuwa ba sai an fada ba na san shi kadai ya isa bada sakon isata aduk in da zan kasance. Ban san dalili ba amman zuciyata ta zaku da in isa ga makarantar hakan ya sa duk da kasancewar karfe 10:30 ake fara lecture na tafi 10:00 kawai ko dan zuciyata za ta samu sukuni. Haka kuwa akai domin ko da naje ba kowa Makarantar Shiru,sai wajen 10minit ka fin mutane suka fara zuwa. Ina zaune ina zura idanu ta yadda zan ga Fateema ta bullo kamar kuwa ance kalli nan. Daga idanuna na ci karo da motarsu. Murmushi ne ya bayyana a fuskata wanda a baɗini mamakin hakan nake. Fitowa tai fuska dauke da fara'a kamar jiya,sai dai yau su biyune. Hada idon da muka yi ne ya sani saurin sunkuyar da kaina kasa. Ji nai anyi mun Sallama Hakan ya sani dagowa. Wata Yar budurwa ce kamar Fatima. Bayan na amsa ta kara da, "Na ce ka zo mu shiga ciki mana." Kan in ba da amsa muryar Fatima na ji karaf tana fadin, "Yayana muje ciki ko." Tsintar kaina na yi da bin bayanta ba tare da na ce uffan ba. Illa a yadda na lura wannan budurwa ta bi Fateema da kallon banza ya yin da ita kuma ta sake mata Murmushin ko in kula. Muna shiga suka zauna ita da kawarta ka fin ni na zauna a karshe kusa da Fateema. "Ina Kwana Yayana? Fatan mun tashi lafiya ya sanyi?" Cewar Fateema tana kallona. Na amsa mata da , "Lafiya lau, Alhamdulillah fatan ke ma kina lafiya?" Murmushi ta yi tare da juya kallonta ga kawarta ta tana, "Maryam Ga Yayana nan Yusuf da na baki labari jiya ba ki zo ba ya fara zuwa." Murmushi ita ma Maryam ta sake tare da fadin, "Barka dai Yayanmu ina kwana?" Fateema ta harareta. "Yayanku kuma? Yayana dai,Ya fi miki ki ce Yayan Fateema kawai." Dariya mu ka yi dukanmu har ni ta ce, "To Yayan Fateema." Daga nan Lesson Teachern mu ya shigo aka fara Lesson. ***** Wace ce Fateema Isma'il? Sannan Wane ne Yusuf Isma'il? Ku biyo ni domin jin su waye Jaruman Littafinmu. FATEEMA ISMA'IL ',Ya ce ga Alhaji Isma'il babban dan siyasa a jahar Bauchi, ta kasance 'Ya ta Uku kuma ta karshe a gareshi Yayunta biyu Mace da Namiji, Yana Matukar Ji da Fateema Kasancewarta Auta kuma sunan Mahaifiyarsa, uwa uba ta kasance mara son hayaniya domin ko cikin mutane bata cika shiga ba. Fateema ba za asata sahun farare ba kuma ba za asata sahun bakake ba,dagowa,mara jiki kyakkyawa ce dai dai gwargwado Mussamman da ta kasance mai fara'a a ko da yaushe. A yanzu tana kokarin Xana Jarabarwarta ta Neco ne domin ci gaba da karatu kamar yadda ta da ra ayi haka ma iyayenta Wannan kenan! YUSUF ISMA'IL 'Da ne ga Malam Isma'il Dan Kasuwa mai rufin asiri na shi daidai gwargwado, sannan shi kadai Allah ya ba su. Isma'il ba fari bane haka kuma shima ba ace da shi baki wuluk ba, tare da matsakaicin tsayi daidai gwargwado. Ya kammala karatun Secondary dinsa shekaru biyu baya kasancewar bai ci jarabawa ba ya sa shi kara zanawa awannan shekarar domin neman gurbi a jami'a tare da cika burin sa na kasancewa Likita. Dalilin zuwan shi makarantar su Fateema kenan. ****Ci gaban labarin. Duk da kasancewar Malami na aji amman hakan bai sa wannan yarinyar ta ci gaba da dallawa Fatema harara ba, Maryam ce ta ce, "Fateema wai kuwa ko kin lura da Zainab tun dazu ban da hararmu ba abun da take fa." Fateema ta ce, "Harara kuma? Ina ga ba da mu take ba,ki share kawai." Duk da cewa Fateema ta san da ita take amman ta zabi sharewan fiye da kulata. Assignment aka ba mu Fateema take fadin, "Ni kam Wallahi ban gane ba fa sam ban san ya zan yi wannan assignment din ba." Yusuf ya ce, "ai kuwa yana da sauki da kin fahimta." "To Yayan Fateema ko zaka dan kara mana bayani don wallahi ko ni ban fahimta ba." Cewar Maryam Yusuf ya kalli agogon hannunsa kan ya ce, "Lokacin ta shi ya yi, amman mai zai hana kumin magana a Wtsp group kawai sai in kara maku bayani." Da sauri Fateema ta furta "to bani numberka." Nan ya bata numbersa ta yi saving dai dai da lokacin ta shi kuwa. Tare muka fito daidai kofar ajin muka ci karo da Zainab tsaye ga dukkan alamu ta sa wani abu aranta. Fateema ta ce, "Excuse Zainab za mu dan wuce." Tana dagowa ta dallawa Fateema mari ..... Urs Xayyeesherthou [2/13, 9:42 AM] Xayyeesherthul-humaerath: *DOCTOR YUSUF*👨‍⚕️ Gajeran Labari *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS* LABARI DA RUBUTAWA: *Xayyeesherthul-humaerath* *SADAUKARWA GA, SIRRIN'YAMACE* *MARUBUCIYAR:* BABU RUWAN SO (FREE) WASA DA SO (FREE) AZZAWAJUL-MUKADDAR (FREE) JAMEEL (200) MATAR POLICE (200) KUCHAKAR KISHIYA (FREE) HAYATIY (FREE) AMEENATOU (300) KWADAYI (FREE) ASHE HAKA SO YAKE (300) SAI NA AURI MARUBUCI (FREE) AND NOW DOCTOR YUSUF FREE *TSOKACI: ban fara rubuta labarin nan ba sai da amincewar Dr. Don haka ban yarda a juya mun labari ta kowace siga ba,sannan labarin gaske ne illa wasu abubuwan da zan kara ko in rage,ban yi labarin nan da niyar tozarci ga kowa ba illa nishadantarwa mai cike da wa azantarwa ga wanda ya fahimta* Page 3 Kuyi hakuri mantawa nake bana sa feji ______ Cikin Harzuka Maryam ta daga Hannu zata ramawa Fatima, da sauri Fateema ta dago tana, "Aa Maryam bar ta Don Allah." Ta karasa maganar tana rike mata hannu. Har cikin Rana sam Isma'il bai ji dadin Marin da Zainab tai wa Fateema ba,domin a zahiri ma fuskar shi ta canja. Tsaki Zainab ta yi tana ci gaba da Harar Fateema, "Wallahi da kin bari ta tabani, ba ruwana da matsayin Ubanki agarinnan in ya so karshen zance kusa a kasheni,tsinannu masu shan jini." Cikin tsawa Isma'il ya furta, "Enough na ce ya isa ko? Ka da ki kyetare iyakarki Malama." Fateema ce ta ja hannunsa da na Maryam su ka bar wajen. Ita kuwa Zainab ta tsaya tsayuwar Mamaki,mai dauke da takaici. Tun daga Ranar doctor da Fateema suka kara shakuwa,ya yin da a kullum ban da harara ba abun da ke hada Fateema da Zainab. Kullum suna tare har ya kai ga Duk wanda ya riga wani zuwa sai ya jira dayan ya zo ashiga Lesson tare. Gabadaya yan Class kowa ya san Fateema da Isma'il, in kana son bacin ran junansu to ka taba wani aciki. Mussamman Fateema da ba ta kaunar Wata 'ya mace ta raɓi Isma'il ko kadan,nan da nan za ta sauya yanayi. Ko da sun koma gida, a weekend ko dare kullum ba sa da abun yi da ya wuce chatting da Kiran Waya. Ya kasance har yan gidansu Fateema ba wan da bai san labarina ba,duk da kasancewar basu taba ganina ba,amman a kullum ban da hirata ba abuj da take. _______Safiyar Monday da isa ta makaranta na tarar da Fateema na jirana kamar kullum. Murmushi a fuskar tare da wata bakar leda,mika mun ta yi tana, "Yayana yau ka kusan makara sosai fa, na kusa yin fushi." Ba tare da na bata amsa ba na bude ledar mai zan gani? Wani tsantsararen agogene da turare ido kadai ya isa baka amsar cewa ma su matukar tsada ne. Na dago ina kallonta tare da bude baki. Kan inyi magana ta ce, "Dadyne ya dawo daga tafiya ya kawo mana tsaraba, kuma Momy ta ce ka ki zuwa ku gaisa fa." Ta karasa maganar cikin salon shagwaba --- Urs Xayyeesherthou [2/13, 9:42 AM] Xayyeesherthul-humaerath: *DOCTOR YUSUF*👨‍⚕️ Gajeran Labari *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS* LABARI DA RUBUTAWA: *Xayyeesherthul-humaerath* *SADAUKARWA GA, SIRRIN'YAMACE* *MARUBUCIYAR:* BABU RUWAN SO (FREE) WASA DA SO (FREE) AZZAWAJUL-MUKADDAR (FREE) JAMEEL (200) MATAR POLICE (200) KUCHAKAR KISHIYA (FREE) HAYATIY (FREE) AMEENATOU (300) KWADAYI (FREE) ASHE HAKA SO YAKE (300) SAI NA AURI MARUBUCI (FREE) AND NOW DOCTOR YUSUF FREE *TSOKACI: ban fara rubuta labarin nan ba sai da amincewar Dr. Don haka ban yarda a juya mun labari ta kowace siga ba,sannan labarin gaske ne illa wasu abubuwan da zan kara ko in rage,ban yi labarin nan da niyar tozarci ga kowa ba illa nishadantarwa mai cike da wa azantarwa ga wanda ya fahimta* PAGE-4 🤒🤒IN GA RUWAN COMMENTS IN ANYI APPROVING DA WURI IN TURO PAGE-5 *****Murmushi ya sake tare da fadin, "Ya zame mun dole ma inzo inyi godiya ai,yanzu dai mu shiga class kin ga An fara Lesson." Fuska dauke da fara'a ta amsa mun da, "Tom Yayana Muje,amman tsaya." Har zasu shiga ya tsaya kallonta. Kara shagwabe fuska tai kan ta ce, "Yayana." Ya amsa da , "Naam Kanwata." "Ka min Alƙawari ba za ka kalli kowace 'Ya Mace ba yau in mun shiga Class." Murmushi Yusuf ya sake kan ya ce, "Angama Kanwar Yayanta Yau kaina na kasa kas ba motsi daga kallon White board sai kyakkyawar fuskar kanwata." Dariya Fateema ta yi sosai ka fin suka shige aji. Har lokacin tashi ya yi aka zo daukan Fateema. Kamar yau suka fara ganin juna, a kullum in za su Rabu Fateema sai ta yi tamkar tai kuka, sam ba ta son rabuwa da Yusuf shi ma kuma haka. _________Bayan kwana Biyu yau juma'a kuma ba Lesson sannan Yusuf ya yi wa Fateema Alƙawarin zuwa gidan su. Tun a gida Fateema ban da rawar kai da murna ba abun da take yau Yayanta zai zo, Antynta Sumayya ce ta galla mata harara, "Ni ko yau zan ga jarababben yaron nan da ake addabarmu akan shi." Auwal ma ya ce, "Ai kuwa sai rawar kai kai kace wani Alhaji ne zai zo Allah sa ma ba dan gidan laka ta kwaso mana ba." Fateema ta kalli Momy cikin shagwaba, "Momy kin ga suna ta zaganmun Yayana ko." Ta karasa maganar da niyar kuka. Da sauri Momy ta ce, "Sumayya, Auwal ku fita harkar Auta in ba haka ba wallahi ranku zai ɓaci koma ya yake muna son abun mu." Kamar wasa har dare babu Yusuf ba labarinsa,tun Fateema na kiran wayarsa har ta gaji da kira ta zauna ban da kuka ba abun da take yi. Su Yusuf da Sumayya kuwa an samu abun nema. Urs Xayyeesherthou [2/14, 10:27 AM] Xayyeesherthul-humaerath: *DOCTOR YUSUF*👨‍⚕️ Gajeran Labari *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS* LABARI DA RUBUTAWA: *Xayyeesherthul-humaerath* *SADAUKARWA GA, SIRRIN'YAMACE* *MARUBUCIYAR:* BABU RUWAN SO (FREE) WASA DA SO (FREE) AZZAWAJUL-MUKADDAR (FREE) JAMEEL (200) MATAR POLICE (200) KUCHAKAR KISHIYA (FREE) HAYATIY (FREE) AMEENATOU (300) KWADAYI (FREE) ASHE HAKA SO YAKE (300) SAI NA AURI MARUBUCI (FREE) AND NOW DOCTOR YUSUF FREE *TSOKACI: ban fara rubuta labarin nan ba sai da amincewar Dr. Don haka ban yarda a juya mun labari ta kowace siga ba,sannan labarin gaske ne illa wasu abubuwan da zan kara ko in rage,ban yi labarin nan da niyar tozarci ga kowa ba illa nishadantarwa mai cike da wa azantarwa ga wanda ya fahimta* Page 5 Washegari Da sassafe da ke bamu da Lesson kiran Fateema ne ya fara shigowa Wayata. Dagawa nai tare da sallama. Wanda anata bangaren shessheƙa take kamar zata yi kuka. Cikin shagwaba ta amsa tare da fadin, "Ni nayi fushi, na yi fushi wallahi." Da sauri na ce, "Fateem kiyi hakuri don Allah kiji uzurina,jiya matsala aka samu ban da Lokacin kaina ma bare na wayata,Mama ce ba lafiya muna asibiti tun safe sai dare muka dawo na kwanta barci,amman yanzu jiki Alhamdulillah zan zo anjima in sha Allah." "Uhumm Allah kara sauki ka mun alƙawari ba za ka ƙi zuwa ba kaji." Ta karasa maganar cikin shagwaba. Yusuf ya ce ,, "Ameen ya Allah,Karfe 5 za ki ganni da ikon Allah." Nan fa Fateema ta tafi da gudu tana fadawa Momy yau Yusuf ya ce zai zo jiyama ciwon mahaifiyar sa ya sa shi kin zuwa. Dariya Sumayya tai tana, "Karyar banza yau dinma ki gama wahala mu cinye." Ko kulata Fateema ba tai ba ta tafi kicin tun alokacin ta fara girke-girke kala kala wanda ba ta yi jiya ba ma tare da taimakon mai aikinsu. Kai kace wani hamshakin bako za ayi,kajine,shinkafa,Sinasir, drinks na katin dana hadin gida daban daban,doya ne, kifi abubuwa dai gwanin ban sha awa. Yamma nayi kuwa Fateema ta ci adon abayarta fara sol mai adon golden din stons, ba karamin kyau ta yi ba, jiki kuwa an feshehi da turare kamar ba ji, haka ma cikin gidan turaren wuta da na ruwa sai hamdala. ***A ɓangaren Yusuf kuwa wanke kekenshi ya yi tsaf abun da mai tsafta kai kace sabuwa ce, cikin manyan kayansa sun sha guga ga kamshi daidai gwargwado. Kasancewar yana da address din ta turomai kokarin hawa keken sa kenan sai ga kiran Fateema. "Yayana biyar da minti goma fa yanzu uhumm ni ka yi sauri." Murmushi ya sake azahiri kan ya ce, "To bani wani minti goman in sha Allah yanzu zaki ganni." Ajiye wayar tai tana sakin Murmushi tare da kara gyara fuskarta a madubi. Kamar Ya fada da bakin mala'iku biyar d a minti ishirin cif kuwa sai ga Yusuf a bakin get din su Fateema. Kiranta ya yi ta fito ta shiga da shi. Yusuf na shiga da er kekensa ya fara cin Karo da Yaya Auwal. Durkusawa yaiy domin gaida shi amman cikin isa ya amsa tare da kawar da kai gefe ya ci gaba da karantar jaridar shi. Jinin Yusuf ya yi sanyi ganin kallon da Auwal ya masa, ita ko Fateema inama ta lura damuwar ta su shige ciki kawai. Suna shiga Sumayya ta kalli Yusuf sama da kasa tai tsaki kan ta haye sama ko jiran gaisuwa ba tai ba. Momy kuwa tana jinsu ta fito da fara'arta , "Ah ma sha Allah yau yarona yayan Autane a gidan munyi babban bako gaskiya maraba da zuwa."cikin sakin fuska take mgnr Nan Yusuf ya durkusa suka gaisa daga nan aka fara jero masa abinci kamar yadda aka tsara. Da kyar ya iya cin shinkafar sauran ms kuwa ko tabawa bai va, shinkafarma sai da Fateema ta matsa. Jin fitar momy kadab ta dawo tare da fadin , "Auta bamu waje zamuyi magana da yayanki.". Hka aka yi kuwa Fateema ta basu waje ya yin da Momy ta fara maganarta kai tsaye, "Fateema ta fadamun komai dangane da soyayyarku kuma Alhamdulillah ina son abun da diyata ke so,sai dai inaso ta kammala karatu kan afara batun aure." Cikin mamaki Yusuf ke kallon Momy domin kuwa tunda yake basu tava mgnr soyayya da fateema ba,duk da kasancewar ya san aran shi yana sonta. Murmushi kawai ya yi wa momy tare da fadin, "In sha Allah Momy na gode sosai." Nan Momy na fita Fateema ta dawo muka fara hira kamar ba za mu rabu ba da kyar ta barni na baro gidansu ana kiran magriba. Bayan sunyi bankwana ta shige gida kwatsam Yusuf ya ga Yaya Auwal gaban sa da alamar dakatarwa. Nan take cikin Yusuf ya fara vurgawa. Urs Xayyeesherthou [2/16, 3:32 PM] Xayyeesherthul-humaerath: *DOCTOR YUSUF*👨‍⚕️ Gajeran Labari *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS* LABARI DA RUBUTAWA: *Xayyeesherthul-humaerath* *SADAUKARWA GA, SIRRIN'YAMACE* *MARUBUCIYAR:* BABU RUWAN SO (FREE) WASA DA SO (FREE) AZZAWAJUL-MUKADDAR (FREE) JAMEEL (200) MATAR POLICE (200) KUCHAKAR KISHIYA (FREE) HAYATIY (FREE) AMEENATOU (300) KWADAYI (FREE) ASHE HAKA SO YAKE (300) SAI NA AURI MARUBUCI (FREE) AND NOW DOCTOR YUSUF FREE *TSOKACI: ban fara rubuta labarin nan ba sai da amincewar Dr. Don haka ban yarda a juya mun labari ta kowace siga ba,sannan labarin gaske ne illa wasu abubuwan da zan kara ko in rage,ban yi labarin nan da niyar tozarci ga kowa ba illa nishadantarwa mai cike da wa azantarwa ga wanda ya fahimta* Page 6 Yaya Auwal ya kallesa cikin isa da yake magana, "Ka da in kuma ji,kuma kada in kuma gani, ka kula Fateema ko in ganku tare,kai ko awaya ma, shin ka ga alamun cewa ta yi kalarka kalar talauci? Shin ka ga alamun wata tawaya ajikinta? A misali ko da Fateema na da nakasa to wallahi tafi karfinka ta fi karfin shiga Ahalinku Ahalin talauci." Fixge kenan ya yi tare da wurgashi gefe kan ya ci gaba da magana, "da wata tsinanniyar gwangwan dinka har kana iya zuwa gidan mu ka shiga ban da raini ma irin naku na talakawa ina kai ina Fateema,maza ɓace mun da gani yanzu tun kan in ɓallaka gida biyu banza matsiyaci." Jiki na rawa gabadaya Yusuf ya ruɗe ya ja kekensa aguje ko waige baya yi ban da zufa ba abun da ke fita ajikinsa. Tsaki Auwal ya yi kan ya shige cikin gida. Yusuf na komawa gida sai ga kiran Fateema kasa dagawa ya yi ya tsaya kawai yana kallon wayar. Cikin mamaki mama ke fadin, "Lafiya dai Yusuf kamar kiranka ake fa?" "Bakomai Mama kiran bai da amfanine." Cewar YUSUF yana kawar da kai Mama ta ce, "Aa fa tun daga yanayin shigowar ka na fahimci cewa akwai matsala." "Mama gidansu Fateema na je,Mamanta ta tarɓeni harma munyi magana ,amman yayunta sun nuna rashin amincewarsu dani,har kashedi yayanta ya mun yanzu." Murmushi Mama ta yi kan ta ce, "Fateeman ta sani?. Aa Yusuf ya fada. Mama ta gyara zama,. "Wannan kadan ne daga cikin kalubale na rayuwa ina so ka cire komai aranka indai fateema na sonka ai ba ita tama laifi ba,sannan bana so ka sanar da ita maganar nan,ka ta addu'a,Allah zaɓama mafi Alkairi kawai." Yusuf ya ji dadin Nasihar mahaifiyar sa hakan ya sa shi komawa dakinsa domin kiran fateema. Waya suka yi tamkar ba abun da ya faru. ****Lbrn Yusuf da Fateema na daf da zuwa karshe kuna ganin mu kara masu karshen da kan mu ko a ƙyale yadda ya kasance kawai? Mu aura masu juna bayan rigimun matan sirri ko,ƙa-ƙa? Ina jiran ra ayoyinku [2/19, 1:48 PM] Xayyeesherthul-humaerath: DOCTOR YUSUF Page 7 Second to the last page. ***Ko da Yusuf yaje Lesson bai nunawa Fateema komai ba. Kamar yadda suke da haka suka kasance illa a kullum tsantsar soyayya na kara kulluwa tsakanin junansu. Abu ɗaya duk sanda Fateema ta kawo maganar ya zo gidansu sai ya nemo hanyar kaucewa,tun tana fushi har ta daina. Soyayya na ci gaba da kasancewa tsakanin su har suka yi jarabawar neco . A kullum suna manne da waya cikin begen juna. Fateema kuwa 'Ya'yan masu kudi sai bayyanowa suke gareta amman fir taki amincewa da su maganarta dai dayane Yusuf,hatta Abokin Yaya Auwal ya zo taki,ita Yusuf take so,hakan yasa Dady da momy yanke shawarar cewa da zaran ta samu admission Yusuf ya fito kawai a masu aure. Anan Auwal da Sumayya suka kara ƙula. ****Kwatsam wata Ranar Juma'a Yusuf na tafiya a kekensa gefen Titi Auwal na mota kamar ance ta daga kai,ya hango Yusuf,abun nema ya samu cikin zafin rai ya nufi inda Yusuf yake da motar da niyar bige shi. Aiko nan take ya yi ciro da Yusuf a tsakar titi,keke tai gefe Yusuf yayi gefe. Tsayawa Auwal ya yi sai da ya tabbatar sun hada ido da Yusuf kan ya yi tsaki ya fece da motar shi ko tsayawa bai yi ba. Cikin ikon Allah kurjewa kawai Yusuf ya yi,mutanen wajen ne suke taimaka masa ya dau kekensa ya koma gida,ko da yaje kuwa mama ta tambaye shi bai ce komai ba illa hatsari ya samu a hanya. Ana cikin haka sai ga kirin Fateema Sanar da Yusuf tai kan cewa Dady ya bada izinin aturo. Sosai YUSUF ya yi farin ciki har da Mama. Nan ba a bata lokaci ba kuwa dangi suka shiga lamarin, daga nan abubuwa suka fara sauyawa. Domin kuwa aduk ranar da YUSUF yaje zance gun Fateema sai Yayanta ya masa barazanar kisa. Amman hakan sam bai sa ya janye kudirinsa na aurenta ba. Daga karshe Tunda Auwal yaga Yusuf yaƙi ji ya koma barazana ga Iyayen Yusuf wanda har sai da ya kai ga ciwon hawan jinin Mama ya tashi an kaita asibiti. Cikin kuka mahaifiyarsa ke fadin, "Yusuf kai daya Allah ya bamu don Allah ka rabu da Fateema,Allah zai zaɓa ma mafi Alkairi bana son in rasaka in na rasaka tamkar na rasa rayuwata ne." Cikin kuka Yusuf ke fadin, "Mama wallahi ina son Fateema,ina son fateema,in ba ita bazan iya rayuwa ba." Ganin hawaye a idanun Mama ne ya firgita Yusuf,cikin sauri yake fadin, "Mama ki daina kuka na rabu da ita in sha Allah na miki alkawari yanzu xan kira in sanar da ita." Nan take Yusuf ya kira fateema da fara'arta ta dauka jin shessheƙar kukansa ne ya mata birki. "Fateema kiyi hakuri na barki,na barki har abada in sha Allah,ki goge number wayata mun rabu, Shikenan mun rabu." Yana katse wayar Fateema na waɗuwa kasa Sumammiya Saura kiris kowa zai fahimci meke faruwa😊 [2/19, 1:48 PM] Xayyeesherthul-humaerath: DOCTOR YUSUF Page 8 End Tuni aka yi asibiti da Fateema, dakyar akasamu ta farfado ko da ta farfaɗo ba wanda take kira Illa Yusuf. Zainab ce zaune kusa da ita tana, "To wai Meya faru ne,kin masa laifine zai ce ya rabu da ke?" "Aa zainab ni ban san me na masa ba." Cewar Fateema. Tashi Zainab ta yi ta dau wayar Fateema tana,"ina dan zuwa." Tana fita kuwa ta kira Yusuf awaya. Kamar ba zai dauka ba ya dauka. "Amman kai bakaramin mayaudari bane,me fateema tama zaka yaudareta? Ban da kaddara ma don Allah me xs ta yi da kai? Tur da hali irin naka kuma wallahi sai nayi posting a fcbk na ce ka yaudareta." Yusuf bai ce komai ba harta katse wayar. Ita kuwa Zainab shiga grp din SIRRIN 'YA MACE tai tayi posting da account din Fateema tare da tagging din Yusuf kan cewa ya yaudareta. Kamar ance Yusuf ya leka facebook kuwa karo ya fara ci da frnds rqst din mata da yawa, can kuma duk post din sa ban da zage zage ba abun da ake,ana kara gyato mutane kowa na fadin albarkacin bakinsa. Gabadaya ya birkice ya rasa meke masa dadi. Duk abunnan dake faruwa Fateema bata ma san anayi ba. *Wannan shine karshen abun da ya faru tsakanin Fateema da YUSUF shin akwai laifi acikin ɗayan su? Ko akwai wanda ya yaudari wani?* *Abun lura anan duk da cewa ba ya da laifin ammsn bai tsaya cecekuce ko fadan wata bakar magana kan masu xaginsa va,a karshe ma hakuri ya vayar, sannan ya tabbatar mun da cewa har yanzu zuciyarsa na dakon soyayyar fateema domin kuwa bai daina sonta ba,illa ba yadda xaiyi.* *Kamar yadda kuka bukata a tsaya daidai inda lbrn yake kar akara to ba a kara ba* *Duk mai son yi mun tambaya, SHARHI ko tsokaci kai tsaye zata iya yimun magana awtsp* Xayyeesherthul-humaerath 08103080717 Na gode 😘 Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels