Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels AL'AJABIN SO      (heart touching story) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN. (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* *Kowa Ya ga zabuwa..* *Diddigar ƙaya... Paid* *Rubutu a kan ruwa... Paid* And now.. *AL'AJABIN SO... Paid* *BOOK 1* *Page 1* SHIMFIƊA Tarihi yana nuna mana abubuwan da suka faru ne kafin mu a rayuwa! Rayuwar duniyar cike take da kalubale, haɗari, wahalhalu da musibu daban-daban, kusan in ka ga ka gujewa hakan to fa alƙalamin ƙaddara bata zana maka ita a shafin ƙaddararka ba, a lokacin da kaddara ke wasa da rayuwarka ya rage maka ɗaukan wannan kalubale a matsayin darasi, ka kuma yi haƙuri da jarabawar Allah (S.W.T) a gare ka. Ni Fatima ban taɓa sanin cewa igiyar ƙaddarar wani na iya shafan na wani har su sarƙe wurin zama abu guda ba sai da na tsinci kaina cikin alkaba'in rayuwa, zafi da kunci suka yawaita a gareni, farin ciki yayi min nisa irin tazarar dake tsakanin sama da ƙasa, na kasa tantance wai ƙaddarar wanene ya shafe ni, shin na mahaifiyata ne ko na mahaifina? Ko kuma nawa ne ni a karan kaina ba'a tsaga ni cikin masu rabauta da duniya ba? A mafi yawancin lokuta in har nayi irin wannan tunani, na kan samu kaina ne da yiwa gwanin halitta godiya da bai sa mana wani tabbataccen al'amari ba, farin ciki ko baƙin ciki yana da lokaci, komai kuma yayi farko to fa yana da karshe, wani karin maganar ma sai ya ce abinda ya baka tsoro a yau babu shakka ko tantama a gobe ya iya baka tausayi, rayuwar tamkar tafiyar hawainiya ce tana tafe tana chanza launi. Al'amuran da suka faru a rayuwata sun sanya min karsashin bayar da labarina. ***** Cikin matsakaicin speed motar ta shigo kayatacciyar harabar gidan, a natse take ratsa duk wasu shukoki da parking lots masu tsari da suka yi wa harabar kawanya zuwa ainihin kofar mashigar babban parlorn gidan kan ta dakata. Da hanzari kuma cikin sauri wata farar matsakaiciyar budurwa sanye da kayan dake nuni da cewa daga makaranta take don baƙar skirt ne jikin ta wadda iyakacinsa gwiwarta sai farar shirt da baƙar blazer ta ɗaura jan necktie daga wuyanta, farar doguwar safa ce a ƙasan baƙaken sau cikin ta wadda ya shiga har karkashin skirt din na jikinta, a kanta baƙar hula ce wadda ya rufe mata gashi tsab kan ta ɗaura baret dinta a karkace daga sama hakan sai ya baiwa kyakyawar fuskarta daman haskawa da kyau, a hankali ta taka zuwa seat na baya ta sanya tsiraran hannunta ta buɗe kofar. Wata buduruwar ce again da zasu iya yin sa'anni sanye da irin uniform din wacce ta bude kofar sak ta fito, da mugun kallo ta fara bin wacce ta buɗe kofar kan ta ja doguwar tsaki ta hankaɗeta ta wuce. Cikin sauri ta dafe motar don gujewa kaiwa ƙasa a kuma sanyi irin tata na tsantsar natsuwa da zaka hanga daga gareta ta ɗago kyawawan idanunta da suka cika tab da kwalla sbd a makaranta ita da friends dinta yau ba karamin mutunci suka ci mata ba, haka gun shiga mota saida ta zagi iyayenta kaman yadda suka saba sanin cewa hakan ne abun da ke ci mata zuciya yake kuma ƙona ranta a take sossai, gashi yanzu m... "Alayah...!" Firgigit ta maida idanunta kan drivern da ya ɗauko su ɗin ta amsa da "na'am baba Musa" Ya ce "kin mance jakar karatun taki ai yarinyar kirki" Murmushinta me kyau ta sakar masa tare da komawa inda ta fito ta buɗe ta duƙa ta dauki jakar tata ta rataye daga kafaɗarta guda tace "Na gode baba, bari na shiga ciki, a huta gajiya" Da murmushi ya bi ta har ta ɓace ta wani tsiririn hanya saɓanin wadda waccan yarinyar ta shige, sarai ya ga abin da ya faru ya kuma san ba mance jakar tayi ba sauri kawai take ta buɗewa Meelah kofa kar tayi laifi se gashi bata tsira ba. Ajiyar zuciya ya sauke tare da furta "Allah ya kyauta ya rufa mana asiri" daga haka be kara ba ya shiga motar ya kai ta ma'ajiyarta kan ya wuce bakin gate wurin hirarsu. Alayah kuwa saida tayi ɗan tafiya mai ɗan nisa kan ta isa ɗan wani karamin sashe a natse ta hau varender ɗin ta isa kofar tare da turawa bakin ta ɗauke da sallama duk da ta san babu me amsa mata, ta san anfanin hakan ne sbd an sha karantar da su cewa sallama a wuri kaman dole ce musamman in zaka shiga gida ko da babu wadda zai amsa a zahiri mala'iku zasu amsa kuma zaka samu ladar hakan. Idanunta take warawa tana neman hasken rayuwarta, majinginar ta kuma sanyin idaniyarta, ganin bata parlorn yasa tayi hanzarin nufar kofa kwalli ɗaya da sashen dake yanayi da kango wadda bazaka taɓa kawowa akwai irin wannan sashe a cikin tamfatsetsen gidan daga waje ba ke dashi. Tana sa kai idanunta suka sauka kan abinda take nema kayatacciyar murmushi suka sakarwa juna, kyakyawar farar macece wacce bazata haura 40yrs ba mai tsananin kyau da cikar kamala kai tsaye zaka iya kiran ta da mahaifiyar wannan buduruwar da aka kira da Alaya sbd fusgan kama da suke yi. Da hannu matar tayi mata alama da "kin dawo?" Murmushi cike da fuskarta wadda bazaka taɓa ganin ta dashi a wani wajen ba face nan cikin kangon nasu ta amsa da kai tana alama irin ta maganar kurame "eh ummi na dawo, ya gida?" Ba tare da ta tsaya sake jiran maganan ummin ba ta sake yi mata alama bakin ta na furta wa a hankali tace "Ummi bari nayi sauri na watsa ruwa na shiga cikin gida kar nayi laifi wurin mommy" Kai kawai ummin tata ta gyaɗa kan ta bita da ido har ta shiga bayin nasu, saida ta fara wanke uniform din nata ta shanya sbd bata da tabbacin samun lokacin kanta in har bata yi a yanzun ba kan ta watsa ruwan cikin hanzari, ta ɗaura alwala a bakin famfon da banda shi da matsuguni (squats) babu abunda aka bar musu a bayin na more rayuwa. Dukda hanzari take amma hakan Sam baya nunawa sbd sanyin ɗabi'a da natsuwa a jinin ta yake kaman gado ne tayi daga iyayenta duk su biyun, da kallo ummi ke bin ta har ta shafa mai ta nufi Ghana must go ɗin su da bayan katifa da sallaya se bakko guda biyun babu komai cikin ɗakin. Sallar azahar ta tayar wadda ta ja lokaci a cikinshi sossai tana sallamewa landline dake parlorn na ɗaukan ƙara har tuntuɓe ta ci garin saurin isa parlorn ta ɗaga kar ta kara laifi, sallama tayi a ɗarare gabanta na faɗuwa don ta tabbatar a kap rayuwarta bata taɓa ɗaga kiran alheri daga mutanen gidan ba. Ba tare da an amsa daga ɗaya ɓangaren ba aka soma magana cikin faɗa "Ke! Wato tsabar kin cika cikakkiya wani sabon rashin kunyar da kika tsiro dashi yanzu kullum kuka dawo makaranta se na buga na nemoki kan ki zo ki kama min ayyuka? To na rantse da Allah yau ne na karshe daga wannan an gama! in kin ga dama karki zo kin san kan wacce zan sauke iskancin naki...." Kit aka tsinke wayar, a hankali ta kai ta ajiye zuciyar ta Sam babu daaɗi, damuwa da gajiya na neman fin karfinta dama already sun fi karfin shekarunta ga raunin zuciyarta, a haka ta tashi ta samesu cikin wannan tsanani, a haka ta girma cikin bauta, hantara da zagi wadda bata san farkonshi ba bare karshen shi. Sau tari se tayi yunkurin yi wa ummintata magana akan wannan rayuwa da suke ciki se taji tausayinta ya danne mata zuciya, bata san daga ina matsalar take ba. Shin ummin tata bata da kowa ne bayan waennan azzaluman mutanen? Me yasa tun tashinta ummin kawai ta sani matsayin uwa, uba da danginta? Babu wadda zai so dawwama cikin ukuba bare ma irin nasun nan, bata da me bata amsa hakan ysa take iya kokarinta wurin taya ummin tata da addu'a kaman yadda ita karan kanta bata gajiya ba a neman mafita daga  mai kowa mai komai. Dafata da aka yi yasa ta ɗago tana kokarin maida kwallar da suka cika mata idanu.. "Kin gaji ko? Ko bakya jin daaɗi ne? Ki je ki kwanta bari naje Naji abinda zaki yi ɗin se nayi" Ummin tata tayi mata alama da hannu wadda tsab take fahimtarta sbd Kusan shi ne First language da ta fara koya a rayuwarta don har so yayi yayi affecing mind ɗin ta sai ta ga kaman magana da fatar baki ciwo ne a sadda tana yarinya karama. Da sauri ta girgiza kai tare da riƙe hannun ummin tace "Ummi da ina da dama da iko da ba zan taɓa bari ki je inda suke ko su kusanceki ba, ummi na fi jin zafi da ciwo a zuciyata idan naga suna ci miki mutunci suna jifanki da munanan kalamai fiye da abinda ni zasu yi min" Siririn hawaye ya gangaro mata ummin ta sa hannu ta share, ta ɗaga ido ta sanya cikin nata Dukda rauni da damuwa da suka bayyana mata sossai hakan be hanata sakarwa ummin tata murmushi mai ƙayatarwa ba tace "Ummi zan je kar na kara yin wani laifi" Sake mata alama da hannu ummin tayi "kin tabbatar kina dai lafiya ko?" Cikin murmushi tace "lafiya ƙalau ummi" Daga haka ta juya ta fice murmushin kan fuskanta na disashewa. Da kallo ummin ta bi ta har ta ɓace mata, da sallama ta tura kofar tamfatsetsen tsararraren parlorn da ya haɗu ya kuma gaji da haɗuwa, a share yake a kuma tsabtace kal kal kaman ka lashe tsabar kyau da walwalin da abubuwan ciki ke yi wadda duk aikin umminta ne tsabtar duk wani muhalli na gidan, wani corridor da shima ba'a bar shi a baya ba wurin kyale kyale da kwayayen fitilu masu kyau aka ƙawatar da cikinshi, akwai kofa guda ɗaya kitchen ne a hade da katon store kofar wurin dining shi suka fi bi nan ɗin na shigar masu gidan ne. Daga chan karshe ta buɗe wani kofa da ya sada ta da wani babban parlor wadda na matar gidan ne mommy kenan, kaman wanchan shima a share kuma a tsabtace yaji kujerun alfarma ga sanyi da raɓar Ac. A cikin lumtsuma-lumtsuman kujerun ta samu mommy zaune ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, tana sanye da wani ɗan ubansun lace na manyan mata taji adon gwala-gwalai hannaye da wuya, hannunta rike da waya kirar Samsung wadda ake cewa Fold tana latsawa, a kan gwiwowinta Alaya ta zube tace... "Mommy sannu da gida" Kaman ba da ita take ba, kaman ma bata san da zaman mutum a wurin ba saida ta bushi iska don kanta bayan kafafun Alayah sun fara tsami a tsugune kan ta ce "wato ke don uwaki tsabar kwakwalwar kanki a toshe yake kaman yadda kunnuwar uwarki kurma suke a doɗe Sau nawa zan faɗa miki in sake nanata miki karki sake ki haura mintuna talatin daga dawowarku daga makaranta zuwa ganin ki a parlorn nan?" Kanta a ƙasa idanunta cike da kwallah saide bata bari sun zuba ba tace "kiyi hakuri mommy sallah na tsaya yi" "ke a gidan uban wa na zama mommyn naki? Ban ce ki dinga kirana Hajiya ba? Ko kin ga nayi kala da uwarki? Sunnu limamiyar Makka! Tukuna ma me ya hanaki wankewa jameelah bayi yau da har ta kasa shiga bayan ta dawo daga makaranta sai na ɗakina taje ta shiga tayi wanka?" Bata ɗago ba a duniya babu fuskar da bata ƙaunar gani irin ta Hajiya Zeenat sai taga kaman idan ta kalleta zafin da zata ji daga zagi da cin mutuncin sai ya fi wadda take ji idan bata kallon ta. "Kiyi haƙuri Hajiya makara muka yi" Maimaicin abun da ta riga ta sani ne tunda tana hakimce Meelah na kwance kan cinyarta da safen ta kawo mata noodles and egg da shi ɗin tace ta dafa mata, bayan ta kawo kuma ta chanza zuciyarta chips da cripsy drumsticks guda biyar take so babu yadda ta iya ta koma ta sake farawa hakan ya makarar da ita sossai, kuma ta san idan ta kuskura ta saka Meelahn letti har aka taɓa ta a school Se Umminta ta mata gashin ruwan zafi sbd mahaifinta baya tolerating duk abunda ya shafi Jameelar. "Ki wuce kije ki wanke mata bayi, ki chanza mata beddings don ta ce ƙaiƙayi suke mata ki tattara laundry ɗin ta ki je ki wanke sannan ki zo ki ɗaura dinner don kurma ta riga ta ceceki tayi na rana ita me ƴa" Cikin ladabi ta amsa da "Toh Hajiya" Mikewa tayi ta nufi kofan hagu daga cikin parlorn shima yana da karamin parlor da dakuna biyu na hagu ta sake isa ta yi sallama, ba amsa, ta sake yi Dukda ta san Meelahn na jin ta amsawa ne bata yi niyyar yi ba, in kuma ta ƙusa kai ba izini ma wani maganan ne. A na huɗun ne ta riski wani tsawa... "Ke Dallah Muguwa kawai! Kin dameni da wani shegen murya kaman Drum so kike se kin kurmantar min da kunne kin maida ni kamar kurmar tsohuwarki ne ko kuma me? Mtseeew" Ba tare da tace komai ba ta buɗe kofar ta shiga, ko kurmar ne da take faɗa ta tabbatar ta shafa muryarta ta shafa na Jameelah ta san ta fita zaƙi da taushin murya nesa ba kusa ba. Tana zaune cikin ɗaya daga cikin kujeru guda biyu dake ɗakin hannunta rike da waya tana latsawa haka kunnuwanta sake da babban baby pink headphone saide bata tunanin tana using ganin baya haske, ba tare da tayi kwakwaran kwaraniya ba ta wuce toilet ɗin ta wanke shi tsab bayan ta gama ta dawo ɗakin bata sameta ba hakan ya sa ta fara cire zannuwan gadon ta chanza wani tare da gyare ɗakin tayi mopping da goge goge, hannunta dauke da kayan cikin laundry basket ɗin Meelahn ta fice zuwa chan baya inda suke wanki. Bayan ta zube su ta koma kitchen bayan store akwai wani karamin laundry room dauke da abubuwan shanya, washing mashings da sabulai da omo kala kala wasu a goruna wasu a ledoji, zaɓar waenda ake yi wa Jameelar wanki dasu tayi ta koma ta hau wanki, ta jima sossai tana yi sbd kayan da ɗan yawa saukinta ma babu wani datti sbd sawar mugunta ce sai a sa kaya kala uku huɗu a rana, tana gama sanyawa ta tsuguna a wurin riƙe da kanta dake sarawa, bayanta kaman ta cire ta ajiye sbd yadda yake yi mata wani irin ciwo, hawaye masu zafi ne suka zubo mata tana jan numfashi da kyar ta sa hannu ta goge, ta jima haka kan ta miƙe ta nufi kitchen wanke wanke ta fara na kwanukan rana da aka ɓata bayan ta gama ta goge ta shanya kan ta matsa ta duba time table na abinda zata yi na dare. Miyar ganda ce ta kan Sa sai tuwon shinkafa, fiddo naman kan tayi daga freezer ta sa a pressure pot ta zuba mishi ruwa me yawa ta ɗaura kan hot plate tare da kunnawa, chan gefe inda ta ga kular abincin su ta nufa ta ɗauka dama ta riga ta san ba daga tukunya yake ba wadda suka rage ne suka juye musu a kular da ya kasance nasu, sashensu ta koma ta samu umminta ta idar da Sallar la'asar kenan, zama tayi gefen ta cikin tsantsar gajiya ganin zaman baze yiwu ba ta zame ta kwanta a wurin tare da lumshe idanunta da suka fi yanayi da na Larabawa farare sol mai ɗauke da baƙi sidik ɗin kwayar ciki, zara zaran gashin har ya sauka fuskanta don tsawo da kyaun su. zuciyarta a chunkushe ta gaji iya gajiya da irin rayuwar da ta tashi ta same su da mahaifiyarta a kai, wasu kan ce abunda ka saba yau da kullum ya kan shiga jiki ya zame maka jini saide kai bata tunanin ana iya yin sabo da wahala, a hankali ta buɗe idanunta jin saukar hannun ummin ta bisa goshinta ta zubawa ummin idanu, banda rama da tsantsar damuwa babu abunda take karanta daga ummin tata. Murmushinta me kyau ta sakarwa ummi ko kusa ita karan kanta bata Fatan tashin ciwon ta don ta san ummin zata bari da wahala da kuma damuwa, cikin yatsina fuska ta miƙe zaune ta fara yi wa ummin tata magana "Ummi lafiya ta fa ƙalau na ga kina ta damuwa" Ummin tana mata kallon tuhuma itama tace "Ai na daena yarda da maganarki in har dae akan ciwon ki ne, sau nawa zaki ce hakan bayan kina nan kina shan wahala?" Murmushi ta saki sossai har saida fararen hakwaranta dake jere reras zuwa dimples ɗin ta guda biyu suka bayyana. "Ai ba wai ƙarya ba ce ummi bana so hankalinki ya dinga tashi ne" tana kai nan ta janyo kular abincin tana yi wa ummi alama da "wallahi Sallar nan ba zan iya yinshi ba matukar banji sauƙar abu cikin ƴar hanji na ba, yunwa nake ji kaman in ci babu". Murmushi kawai me cike da ma'anoni daban daban ummin da suke tsananin kama da Alayar sai en abu kalilan da bata ɗauko nata ba ta saki kan tayi mata alamar a ci dae da bismillah, inaaa ita kam tayi nisa a cin abincin ta, tunda take a duniya bata taɓa jin abincin da ya kai na umminta daaɗi ba, lokuta dayawa ta kan tambaye ta wai wani makarantar koyon girkin tayi? Lura da ta yi tambayar kan taɓo mata wani fanni chan na rayuwarta yasa ta daena. Sai da ta fara kai wa geji kan ta lura da ummin tata bata ma soma ci ba, da sauri ta dakata tare da ɗago idanunta farare sol ta dubi ummin da tayi nisa da kallon ta fuskanta dauke da murmushi sannan hawaye na zuba mata daga saman fuskanta. "Ummi.." Ta faɗa tana sa hannu ta taɓa kafafunta. Da sauri ta ɗauke kai tana share hawayen wadda nan take Alaya taji abincin ya fice mata daga rai, ba karamin So da shakuwa ne ke tsakanin su ba ko don basu da kowa ne sai junansu oho, amma abunda ta sani yanayin ɗaya baya chanzawa ba tare da ya taɓa na ɗayar ba. "Ummi menene?" Ta tambaya cikin tsantsar damuwa Dukda ba yau ne na farko da ta kan tsinci ummin tata cikin irin wannan hali ba. "Babu komai Alayah, kawai kin tuna min da mahaifinki ne da abubuwa guda biyu yanzu". Itama Alayar yanayinta ne ya sake sauyawa jikinta a sanyaye tayi wa ummin alamar "wani abu nawa na yanayi da nashi ko ummi?" Cikin murmushi me bayyana tsantsar ciwo ummi tace "Cin abincin ku iri ɗaya sak! Haka kuma bai taɓa zama cin abinci ba tare da ya tambayi inda na koya girki ba, wani lokacin ya kan sanyawa iyayena Albarka, na kan zauna cikin murmushi da jin daaɗi ina kallon yadda zai ke ta santin abinci na har ya gama ci, kai har ta kai ta kawo mahaifinki baya iya cin komai koma menene a waje, duk wata ƙasa da ze je se ya ɗauke ni mun tafi tare sbd girki kawai...." Katsewa maganar yayi ta sa bayan hannu ta ɗauke hawayen ta Allah sarki mutuwa, mutuwa baya barin wani don wani yaji daaɗi. A sanyaye Alaya tace "Allah ubangiji ya gafarta maka Abbana" Daga nan se walwalarsu ta kau, a koyaushe dama walwalar tasu bata wuce na dakiku, a duk sadda zasu tuna da jigon rayuwarsu kowa da abunda ze ke kitsawa a ran shi. "Ummi a duk sadda kika yi wani zance na Abba alamu su kan nuna Yana da dukiya, sannan yana da kirki ga mutane da kyakyawar alaƙa, yana da son mutane kaman yadda su ma suke son shi? Ummi ina dukiyar? Ina mutanen nashi? Ummi Don Allah mai ya ajiye mu anan cikin azaba da kuncin rayuwa??" Tayi maganar cikin zubar hawaye, da sauri ummin ta hadiye ƴar walwalarta cikin sanyi da siga na bada umarni tace "in kin koshi wuce kiyi sallah ki komawa aikin ki..." Kuka sossai Alayah ta saki kan ta tashi ta nufi bayi....... *karki manta book 2 paid ne a naira 500 kachal ze zo muku immediately after an gama book 1, zaki iya biya tun yanzu ta wannan asusun 3118518476 First bank Fatima Muhammad Gurin, se ki turo shedar biyan ki ta wannan layi *09039206763* #comment #Vote               🖤Gureenjoh🖤 AL'AJABIN SO (heart touching story) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN.                      (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* *Kowa Ya ga zabuwa..* *Diddigar ƙaya... Paid* And now.. *AL'AJABIN SO* *BOOK 1* *Page 2* Tana Sallar tana zubar da hawaye tana kuma adu'ar Allah ya sassauta musu ya gafartawa mahaifinta da take jin kila da yana nan da ba haka rayuwarsu zata kasance musu ba cikin rashin gata da galihu, wulakanci da tozarci ya zame musu ruwan sha don da yana tsiro da babu masaka tsinke jikin su, cikin matsanancin kaskanci da rashin Ƴanci, ta san ko menene zai tsaya yayi tsayin daka don samar musu walwala da rayuwa mai inganci a matsayinshi na mahaifi kuma miji ga ummin ta, mutuwa mai tonon asiri. Umminta gani take har yanzu ita ɗin yarinya ce ko gani take da already dama zuciyarta da aka haife ta da rauni na ciwo ba zata iya ɗauka ba shiyasa har yanzu bata iya bata labarinsu daga ita har mahaifinta ba, da yadda aka yi suke zaune cikin wannan baƙar gida, abubuwan da zata ce ta sani akan mahaifinta kalilan ne wadda take tsinta a wurin su baba Musa su ɗin ma se subutar baki ko in tayi wani abu da yayi yanayi da nashi, addu'a sossai tayi kaman kowani bayan sallah tana share hawaye da bayan hannunta se tayi looking very cute and adorable kaman baby. Ummi ta santa sarai da shegen shagwaɓa wadda rayuwar da suka tsinci kansu a ciki ya koya mata juriya, ta kure ta da ido tana banbance kukan ta ne na sakalta ko kuwa daga zuciyarta yake fita? Se ta fahimci wannan ɗin hawaye ne masu ciwo da dumbin damuwa, ajiyar zuciya ta sauke har Alayah ta miƙe ta mata alama da ta koma cikin gida ta kama aikin dare. Har ta fice ummin bata ce komai ba, Allah ya gani ba labarinsu bane bata son bata, sam bata so yarinyar ta sawa kanta kiyayya ko fansa ko wani abu makamancin haka a raunataccen zuciyarta da babu cikakken lafiya bare hutu, she cannot risk the life of her only daughter wacce itace hapiness ɗin ta a yanzu. Ita ko Alayah bayan ta koma kitchen din aikinta ta fara cikin son ture damuwowinta sbd umminta, cikin kwarewa da gogewa a girki da ta samu daga umminta ta haɗa Miyar kan San banda kamshi babu abunda yake tashi, a gefe ɗaya ta ɗaura tuwon shinkafarta, kan Ace an kira magarib ta gama ta kuma kimtsa kitchen ɗin tsab kaman ba'a yi komai ba, anan kitchen din tayi Sallar magarib, seda ta jira Masu gidan suka fito tukuna hajj Zeenat ta dibar musu abincin su, godiya tayi ba tare da ta samu amsa ba ta ɗauka ta fice. Kaɗan ta ci ta samu tayi isha da kyar sbd tsananin gajiya da baccin dake ɗawainiya da ita Dukda tarin assigments da take dasu gajiya be barta ta bi ta kan bokon ba, tunda ta kwanta a sallayar ko motsi bata yi ba haka bacci ya ɗauke ta. Ummi ta tsira mata idanu tana tuna chan shekara kusan 17 baya..... **** "Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!! Hawwa na gode.. Na gode" Abin da yake ta maimaitawa kenan tun a sadda kalmar likitar na tana dauke da ciki sati biyar suka shiga kunnuwanshi, ba zata ce ta taɓa ganin tsananin farin ciki a fuskanshi ba irin na ranan, ɗagowa yayi daga sujudushukr da yayi fuskarshi kamar gonar auduga yayiwa wannan likitar kyauta ta bajinta da ban mamaki.   Ko a wurin shiga mota shi ya buɗe mata kofar cikin kulawa ta shiga ya gyara mata laffayar da ta ɗaura kan wani tsadadden zani ya zauna mata sossai kan ya rufe ya zagaye ya shige ya tayar suka bar asibitin.    Hannunta ya kama ya riƙe cikin nashi cikin murmushi ya ce "hawwa ƴa mace mai tsananin kama da ke zaki haifarmin in shaa Allah in raine ta kamar sarauniya don ita ɗin zata zama princess kuma uwata" baki ta taɓe cikin murmushin ganin irin kwantaccen fara'a dake fuskanshi tace    "ni kuwa namiji nake so mai tsananin kama da kai ya zama jarumi, jajirtacce irin ka, mai kulawa da duk wani hakki na ubangiji, wadda ko kallonshi nayi zan tuna da sadaukin maza na." Cikin murmushi ya lakace mata hanci ya ce "We shall see! Allah ya bamu me albarka amma ina me tabbatar miki mamana na ajiye a nan" ya karashe yama me shafa ƙasan mararta da hannushi ɗaya, ɗayar na sarrafa stirring mota dariya suka yi a tare tana amsa adu'ar tashi.... ***** Tashin da Alayah tayi a firgice shi ya katse mata tunanin da ta tafi har tsorata tayi, sai ta ga tayi wurin landline da gudu tayi picking sbd saura kiris ya tsinke, da alamu kira ake ita ummin bata ji ba sbd babu kunnen, mintuna biyu taga Alayar ta dawo tare da ɗaukan hijab ɗin ta ta saka fuskanta sam ba walwala, da hannu ummi tayi mata alama..   "Menene? Ina zaki je a daren nan?" Seda ta sauke ajiyar zuciya tace cikin alamar kurame "Ummi Jameelah ke nema na wai dare yayi bazata iya cin tuwo ba in je in dafa mata indomie in soya mata plantain in kuma dibi Miyar as pepper soup in kai mata ɗakin ta" Shiru ummin tayi kan ta ɗago ta ce "Ki kwanta bari na je na yi mata" Da sauri ta girgiza kai tana mata alama "a'a ummi babu ta yadda za'ayi ina kwance kina chan kina yiwa Jameelah girki bari naje yanzu zan dawo" Kanta ƙasa har Alayar ta fice.. Lallai dukkaninsu Allah ya amsa adu'o'insu, ya bata mace me tsananin kama da ita kaman yadda mahaifinta ya roka, se kuma ya amsa nata wurin bata halayya mafi rinjayi na mahaifinta me haƙuri, juriya da kuma jin ƙanta, sanin kanta ne Alaya ta ci sunan inkiyarta na princess, smart and beautiful, kwata kwata bata son ganin ummintata na wahala Dukda a ciki ta tashi ta sameta, bata ƙaunar jin wani kalmar ɓatanci in har dae akan umminta ne, hakan ya sa wahalhalu dayawa takan ɗauke mata na ayyukan gidan da kankantar shekarunta, ɗaga hannu sama tayi tana rokon Allah ubangiji ya kawo musu karshen wannan rayuwa da suke ciki don suna tsananin jiggatuwa...     Cikin mintuna da basu fi arba'in ba ta gama tare da kai mata har daki, ba zata iya jira ba tunda ta san ko yau ko gobe din ne itace dae zata fitar da kwanukan don haka ta wuce sashensu, da kyar ta iya sauya kayanta ta koma bayan umminta ta kwanta a take bacci yayi awon gaba da ita se lokacin ummin ta juyo ta tofeta da addu'a kan itama ta shafa ta lumshe idanu tana sake sake har bacci ya ɗauke ta. Washegari da safe kaman yadda al'adarsu take a gidan suna Sallar asuba suka miƙe suka fice, ummi na tsaftace gidan yayinda Alayah ke ta zirga zirga a kitchen wurin haɗa breakfast, tayi nisa a aikinta tana cikin soya doya taji ƙarar fashewar abu a lokaci ɗaya ta tsinci gigitacciyar tsawar Hajj Zeenat wadda ta tabbatar umminta ce kawai take yiwa irin wannan tsawa, wani mummunan faɗuwa gabanta yayi wadda ya haddasa bugun zuciyarta tafiya fat fat fat kuma hakan barazana ce ga lafiyarta, da sauri ta saki cokalin hannunta tayi parlorn Dukda ta san laifi take shirin aikatawa amma bazata bar umminta ta muzanta gabansu ba, da gudu ta shiga gaban ummi marin da hajj Zeenat ke shirin sauke mata ya sauƙa kan fuskar Alayah ji kake tassss, tsabar zafin marin da karfin shi seda ta fadi jikin ummin ta baya baya, ko gama dawowa hayyacinta bata yi ba tayi saurin zubewa bisa gwiwowinta tana cewa.. "Mommy don Allah ki yi haƙuri, mun tuba ki yafe mana" Cikin faɗa me hade da ihu hajj Zeenat tace "ke har kin isa? Ke kika min laifi ko uwarki? Wallahi yau ko zata buɗi baki da kanta tace min yi hakuri ba zan hakura ba" Ummi da har lokacin ranta tafasa yake da marin da hajj Zeenat ta saukewa Alayah idanunta kan flower vase din da ta fasa wadda tunani ta tafi na sadda aka saye shi da yadda aka saya mistakenly ta ture shi ya faɗi ya tarwatse, idanunta gabaɗaya suka sauya duƙawa tayi ta ɗaga Alayah tare da juyawa da ita zasu fice, wani irin fusgowa da hajja Zeenat tayi mata seda suka juyo gabaɗaya ta ɗaga hannu da niyar tsinke fuskar ummin da mari taji karaf an riƙe hannunta. Da kallo ummi take bin su dukkansu biyu, shimfide cikin idanunta kana iya hangar zafi da turirin zuciya da take fama dashi a lokacin, soyayya da kulawa irin ta uwa ya wuce a ce a zabgawa ɗan ka mari me wannan zafi a gabanka ka kasa tabuka komai, wani irin zafinsu take ji barin ma shi, duban su ta sake yi a karo na ba adadi kan ta janye Alaya suka fice daga parlorn. "Me kenan kake kokarin yi Abban Jameelah? Ƙaskantar da ni a gaban waennan ƙaskantun mutanen? Ka kuwa san laifin da ta aikata min?" Hajj Zeenat ta faɗa a kufule "ban sani ba kuma bani da ra'ayin sani, abunda kawai na sani shine sau ɗaya tak kika yarda kika sauke hannunki kan hawwa ranki idan yayi dubu to se ya ɓaci, duk abunda kike kallonki kawai nake ba wai bani da ikon hanawa ko dakatarwa bane, ni na san anfanin da hakan ke min don haka ki kiyaye, don yarinyarta ban damu ki mata ko ma menene ba amma banda hawwa" Yana kai nan ya juya ya buɗe wani kofa da ze sada shi da sashen shi ya shige. Zaune hajja Zeenat ta kai tana jin zafin wannan abu da Alhj ke mata, wani irin turirin tsanar hawwa da Alaya take ji kaman ta shafe babinsu a duniya, a kan hawwa duk wani farin cikinta na gidan aure ta rasa shi, ga kuɗi har kuɗi amma bata da kwanciyar hankali, menene manufar Alhj akan hawwa ne da ya zuba ido shekara da shekaru ina mata yadda na so? Ta tambayi kanta daidai lokacin da Jameelah ta fito tana tambayar ƙaurin da take ji a gidan gabaɗaya. Da hanzari suka yi kitchen masifa sossai hajiya Zeenat ke yi na duk laifin Ummi ne gashi Alaya ta ɗaura tea a glass pot dinta ruwan ya ƙone har ya fashe, tambayarta Meelah tayi se take bata labarin abunda ya faru cikin jin haushin Alhj har yanzu.   "Ai ko wlh sun yiwa kansu yau azumin dole zasu yi babu me samun abun kari" Hajiya ta karashe da hakan, kwafa Meelah tayi tana tunanin yadda zata ci zarafin Alaya, mommyn ta saka ta dafa mata indomie da tea ta ci kan ta nufi ɗakinta don ƙarasa shiryawa, mommyn ma ɗakinta tayi tana danna kiran wayan aminiyarta Hajiya Fanta... A ta ɓangaren Ummi kuwa cike da tausayi irin na uwa take duba fuskan Alaya bayan ta zaunar da ita bakin katifarsu "Alayah me yasa kika shiga marin ya same ki? Kin dae san baki da wadataccen lafiya" "Ummi lafiya ta ƙalau i promise" tayi mata alama tana danne radadin zuciyarta. Shiru duk suka yi babu wadda ya iya sake cewa komai kowa da tunanin da yake a zuciyarshi, daga karshe Alaya ta miƙe tana cewa zata je ta ƙarasa breakfast kar ya zama laifi, ummi ta ce ta shiga tayi wanka ta shirya makaranta zata je tayi da kanta, komawa sashen ummi tayi ta fara soya doyar da Alayar ta fere, tana juyewa a kuloli Meelah ta shigo tsab a shirye cikin full uniform din ta, wani irin kallon kyama da tsana ta watsawa ummin kan ta nufi fridge ta buɗe ta dauki hollandia youghut da ta shigo ɗauka ta tsiyaye cikin wani bottle flask ta zuba mishi kankara ta juya ta fice. Ko da Alayah ta shigo Hajiya Zeenat bata fito ba bare ta basu abunda zasu ci, se kawai Alaya tayi wa ummi sallama akan se ta dawo kawai yanzu in ta ajiye Meelah Abbanta ze kusa kasheta.    Rayuwa baka samun yadda kake so, ga dae abincin ummi ta gama jujjuyewa saide babu halin su taɓa sbd gudun tashin hankali da tozarci, tana ji tana gani Alaya ta fice ba tare da ta karya ba.     Ko a makaranta Alaya bata yarda ta shiga sabgar Meelah ba duk da yadda sukan zage ta da kawayenta ko su zungureta bata ce musu ci kanku gudun fitina, karfe 1:30pm suka tashi daga makarantar hadari ne sossai ya haɗu a sararin samaniya banda iska babu abunda yake kadawa alamar ko da yaushe za'a iya tsugewa da ruwan sama, dubawa Alayah tayi taga baba Musa be kai ga zuwa ba hakan ya sa ta nufi masallacin su don gabatar da Sallar azahar kar ta je gidan ga aiki ga yunwa tana ji, banda ruwa babu abunda ta sakawa cikinta gabaɗaya yinin tana kallo a break yadda Meelah ke kashewa kanta da Ƙawaye kudi a cafteria, ita ba mai shiga mutane ba ita ba kawa ba don tana matukar kama kanta da tsayawa matsayarta, duk makarantar ƴaƴan masu hannu da shuni ne hakan ya sa tun farko ta kama kanta ta keɓe rayuwarta, duk duniya bata da kawar da ta wuce umminta.    Ko da ta fito ta duba agogo biyu saura mintuna sha biyar, da sauri tayi wurin ajiyar mota don duba baba Musa ko ya zo kar ta ajiye Meelah ta kara laifi duk dubawar duniya bata ga Meelah ba bare baba Musa da ta san har ta shiga masallaci bai zo ba, wurin gate man ɗin su tayi take tambayar motar gidansu ta fita? Makaranta ce me matukar tsaro hakan yasa babu motar da zai shiga ya fita ba tare da gate man ya tantance ba. "Eh sun fice tun mintuna biyar baya" Gabanta ya yanke ya faɗi sun tafi basu jira ta ba? Ya zata yi da nisar tsakanin unguwar su da makarantar? Ya zata yi da yunwar da take ji kaman ze kasheta? Bata da ko sisi babu dalili, ko bashi ta karɓa ina zata samu ta biya su? Su da suke rayuwa sai abin da aka tsakura aka basu.     Iskar ruwan dake shirin zuba at any moment ne ya kara karfi, takawa tayi ta sa hannu a karamin gate ta buɗe ta fice sbd Kusan duk school din babu kowa, takawa ta fara bata ko yi taku biyar ba aka soma yayyafi kan ka ce kobo ruwan ya tsuge a take ya kuwa sameta ba ɓata lokaci ya fara bugunta, bata tsaya ba kaman yadda bata fake ba sai tafiya take, daidaikun mutane dake neman mafaka se kallon ta suke, yayinda ita kuma tana ji bazata iya jiran ruwan ba, umminta zata shiga damuwar rashin ganinta sannan ya ayyuka zasu mata yawa. Ruwa ne ke zuba sossai ɗauke da walkiya da tsawa gudu yake tsugawa a bisa shimfidadden titin sbd karancin abun hawa kuma yana sauri, sam bai zaci ko tsammaci ganin mutum bisa titi ba a wannan yanayi na ruwan sama mai karfi dake zuba kawai se ganin halitta yayi kaman daga sama a gabanshi kuuuuuuuuuu haka wani irin ƙara ya karade wurin ya haɗu da wani tsawa da aka saki.... *Kar ku sha'afa Al'ajabin So book 2 is not free, a kan naira 500 kachal zaki same shi immediately after an kamallah book 1, zaki iya yin payment ta nan 3118518476 First bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya ta wannan layi 09039206763* #Vote #comment               🖤Gureenjoh🖤 AL'AJABIN SO (heart touching story) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN.                      (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* *Kowa Ya ga zabuwa..* *Diddigar ƙaya... Paid* And now.. *AL'AJABIN SO* *BOOK 1 *        *Page 3* A matukar tsorace cikin gigita ta tsaya kyam hannayenta bisa kunnuwanta idanunta a runtse jikinta kuma ya ɗauki kyarma, kaman yadda baƙar motar kirar jaguar XJ baƙa sidik wacce ba'a iya kallon komai nata ta tsaya chak, jin shiru motar bata bugeta ba har lokacin yasa ta sauke hannunta a hankali, idanunta dake rine ta ɗaga ta kalli gefen da mota yake ganin yana nan tsaye yasa ta miƙe a sanyaye, uniform nata a jike shakab ta cigaba da tsallakawa a hankali tunda ta tsira daga sharrin kaɗewar motar, har ta tsallaka bata ji motar tayi wani motsi ba seda ta bar kan titin gabaɗaya kan taji wucewar motar da karfi kaman iska, juyawa tayi ta bi motar da kallo na second kan ta cigaba da tafiyarta. Sai wuraren uku ta iso gida a lokacin yayyafi kadan kadan ake, jikinta babu inda baya rawan sanyi, gabaɗaya hankalinta a tashe banda tunanin umminta babu abunda take ta san tana nan tana jimamin rashin ganinta bayan Jameelah ta dawo tuntuni, karamin gate nasu ta kwankwasa Malam shazali ya zo ya buɗe ganinta ya sa ya kauce ba tare da ya ce komai ba ta shigo, cikin sassanyar murya tace "sannu da aiki malam shazali" Yace "sannu Alaya haka ruwa ya jika ki? Meyasa baki hakura ruwan ya tsagaita ba kan ki taho? Tun dazu baba Musa ke ta jimami akan ki wallahi Hajiya karama ta hana shi jiranki kaman yadda ta mishi barazana da aikinshi Idan har ya fita ya koma don ɗauko ki" Hawayen da ya gangaro mata ne ta share tace "ba damuwa malam shazali, ba zan iya zama ne ba tare da na san sadda ruwan zai tsaya ba ga ayyuka na tabbatar sun ma ummi yawa kuma na san itama hankalinta tashe bata ganni ba" Ya girgiza kai yace "zuwanta nan uku tana neman baba Musa kuma tunda ya sauke Hajiya karama Hajiya babba ta aike shi chan mariri har yanzu be dawo ba" "na gode bari na ƙarasa ciki" Ta faɗa kan ta wuce don shiga cikin gidan, kaman yadda ma'aikatan suke respecting nata da ummi haka itama take basu girma kasancewarta me tsananin biyayya da ganin girman na gaba da ita, kuma ko bayan haka ta kan zo wurinsu tana karama su yi ta mata wasa musamman Idan ayyuka suka yiwa umminta yawa kuma bata da abokin wasa, so kaman kusan iyaye ta ɗaukesu. Wucewa tayi zuwa sashensu tana shiga ta fara kokarin raba kanta da kayan jikinta sbd irin rawa da jikin nata ke yi na sanyi, da wasu kayan ta chanza tana kokarin tsugunawa don tattare kayan taji kirjinta yayi wani irin riƙewa, sunan Allah ta kira tana dafe kirjin da kaman ze tsage don azaba, cikin karfin hali ta ja ta isa kan gado ta janyo zannin ummi ta lullebe jikinta ta dunkule hannunta dafe da saitin zuciyarta tun tana dauriya har kuka ya kwace mata tana kiran ummi... Ummi kuwa Dukda aiki take sede hankalinta rabi da kwata baya tare da ita, gashi dae sun haɗu da Meelah sau biyu amma tsoron tambayarta Alayar take bama ta san ta yadda zata fara ba don mutunci be taɓa hada ta da Jameelah ko na minti ɗaya ba, in zata iya tunawa har miyau Jameelah ta taɓa zuba mata a fuska, wa kuma ya san irin zagin cin mutuncin da suke sha don ma bata da kunnen ji, a gaggauce ta gama wanke wanken da take ta nufi komawa sashensu don duba ko Alaya ta dawo. Karo ta ci da jikakkun uniform nata daga tsakar daki seda gabanta ya yanke ya faɗi da sauri ta ƙarasa ciki tabbas da tana da kunne zata iya jin irin kukan da Alaya take cikin ciwo, da gudu ta ƙarasa ta ɗago ta tana kokarin maganan su irin na kuramen nan sede babu abunda yake fita, hannun Alaya ta kama se taga ya chanza yayi wani abu blue tinge wadda a turance ake kira (cynosis) gabaɗaya ilahirin hannun, jijjigata tayi ta buɗe idanunta da kyar nan ma duka haka ne alamun ciwon zuciyarta ya tashi, ganin yadda numfashi ke shirin dauke mata kaman bazaka kyapta idanu ka buɗe ka sameta da rai ba yasa ummi Miƙewa da sauri tayi waje.. Tana fita motar Alhj Hassan Dala na parking a tsakar gidan da sauri ta nufe shi, a gabanshi ta tsaya hawaye na zuba mata, duban ta yayi na mintuna ya san in ya kalleta cikin wannan hali ƴar ta ce ba lafiya, baki ya taɓe kan ya koma motarshi  hankalinshi kwance yayi rubutu a jikin wani joter ya ɓalle ya fito, hannu ya sa a aljihu ya zaro kuɗin da baza su wuce dubu talatin ba ya watsa mata da papern, duƙawa tayi tana kuka tana tattarewa cikin sauri sauri daga haka ta miƙe tayi sashensu. A hannu ta riko Alayar dake tafiya da kyar da karfin hali don bata ma sanin tana ɗaga kafa sbd azabar ciwo, baba Musa da dawowarshi kenan yake tambayan shazali me gadi ko Alaya ta dawo shi kuma yana bashi labari ya hango Fitowar su duk hanaklinsu seda ya tashi ummi kuka Alaya kuka, baba Musa ne yayi kundunbalar fita ya samo abun hawa da kyar sbd irin tsaron unguwar, ya cewa malam shazali idan har aka tambayeshi ya ce ya tafi gida an kirashi iyalinshi ba lafiya. A napep din banda faɗa cikin tausayawa su ummi babu abunda yake, har yaushe wannan rayuwar zaluncin? Ina ma yana da wani iko da ko se ya ga abunda ya turewa buzu nadi akan iyalan Alhj Ahmad marafa, har hawaye yayi jin yadda Alaya ke kirar sunan Allah cikin azaban ciwo, asibitin murtala suka isa sbd nan ne su kan je idan irin hakan ta faru don basu da dalilin na kuɗi ɗan abunda yake basu idan ya ishesu Toh falillahil hamd idan kuma be isa ba sede su bar jinyar a haka idan har an ɗan samu sauƙi hakan yasa kullum Alayar take a wahale babu kuma ƙiba se rama.    Cikin hanzari aka karbesu aka fidda file ɗin ta aka yi emergency da ita, ummi zama tayi bakin wurin tana zub da hawaye masu zafi, ita kadai ta san irin tashin hankalin da take shiga a duk sadda ciwon Alaya ya tashi irin haka, ita kadai take dashi idan ta rasata ina zata saka rayuwarta?    Bata da tabbacin ko likitan zuciya ne ya shiga kan Alayar sun dae ɗauki lokaci a kanta kan suka fito, baba Musa yake tambayar su ya jikin nata? "Baba wannan ɗin ƴarka ce?" Ya amsa da"eh" "Kwanaki na bada shawarar zuwa wurin Dr philip sbd kwarewarshi a harkar zuciya chan meddy specialist hospital ban san Meyasa kuka kasa daukar shawarata ba, ina me tabbatar muku yarinyar nan tana kara shiga yanayi me hatsari ne a yawan attack da take samu idan mun iya tseratar da rayuwarta yau gobe babu abunda zamu iya, so prevention is better than cure" Baba Musa ya jinjina kai yace "in shaa Allahu zamu yi kokari akan hakan mun gode likita" Wucewa doctorn yayi yayinda ummi ke ta kallonsu cikin zakuwa da son jin me suke cewa sbd gabaɗaya hankalinta yana kan lafiyar gudan jinin ta, Juyowa yayi tare da yi mata bayani bata iya ta ce komai ba se hawayen da take sharewa a kai kai ba basu je Meddy din bane sun je sede irin kuɗin da suka ji daga karbar kati ma zuwa ganin Dr ba karamin kudi bane basu dashi babu kuma dalili. Ummi ce rike da hannun Alaya dake ta aikin bacci sbd alluran da aka yi mata lokaci lokaci ta kan kalli mutanen ɗakin, kowa da kalar ciwonshi, ward ne me ɗauke da gadaje kusan ashirin dogo ne sossai, Malam Musa ya samu ya tafi sbd gudun matsala zaninta ta kwance ta fiddo papern joter din da ta nannade ta ɗaure a wurin ta fara warewa a hankali. "Kaman yadda na faɗa miki a baya na kuma maimaitawa yanzu ma ba zan gaji ba zan sake faɗa, hawwa duk wani abunda yake faruwa daku laifin ki ne, lafiyar ƴarki a hannunki yake kaman yadda lafiyar kunnuwanki suke hannunki, Da kalma ɗaya tak! Zaki ƴanta ku zuwa sabuwar duniya amma kin kasa anfani da wannan dama, a yau Idan Fatima ta mutu karki ga laifin kowa se kanki, ke ce kika kasheta..." Dukunkune papern tayi tare da runtse ido da karfi hawaye na gangaro mata sossai, da sauri take girgiza kai kan ta ɗaura kanta jikin gadon Alaya ta saki sassanyar kuka, shin ya zata yi? Har abada bata jin zata iya abunda Alhj Alhassan Dala yake so, amma ganin ƴarta a hali irin na dazu ya sa take jin zata iya yin komai sbd samun lafiyarta, in tace komai tana nufin komai amma buƙatar Alhassan ya zarce da tunaninta, Allah ka min mafita... Abunda take ta nanatawa kenan a ranta. "Ummi!" Alayah ta faɗa tana me dafa ta idanunta da suka sauya sossai suke lumshewa da kansu ta zubawa ummin da ta ɗago take share hawaye a lokaci ɗaya tana tambayarta ta farka? Ya jikinta? Me take so? Duk cikin alamu irin ta maganan kurame. "Yunwa ummi, yanzu karfe takwas na dare babu abunda ya shiga bakina tun safe banda ruwa" Tayi alamar cikin tsananin jin yunwa ga ciwo, bakin ta duk ya bushe. Miƙewa ummin tayi tace mata tana zuwa ta fice, maida idanunta tayi ta kulle tana jin yadda surutan matan masu jinya da masu kula dasu na ta tashi kaman kasuwa hakan ne fa ya sa ta tsani asibiti, tana nan kwance har ummi ta dawo ta taimaka mata ta wanke bakin ta, da kanta ta wanke hannu take ciyar da ita dafaffen  doya da Miyar sauce ɗin da ta saya a bakin asibiti daga cikin ledar, bayan ta ci sossai ta ɓula farin ledar da aka kulla mata kunu ta bata ta sha sossai kan ta sha magungunan da ta sayo duk tana bacci lokacin ta sha. Rokar roba wurin makotarsu tayi ta saka ta tayi alwala ta rama sallolin da ake bin ta, ummin se kallon ta take tana tunanin wani shawara zata yanke, duk wadda ta zaɓa babu sauƙi... Kwanansu biyu asibitin banda ma'aikatan gidan babu ƙafar wadda suka gani a ahalin gidan dama sun saba Dukda da ciwo matuka, duk faɗar ka da mutum ai ciwo ya fi gaban komai, yanzu haka zasu koma su ɗaura musu da bauta ba tare da kyautatawa ko na minti ɗaya ya shiga tsakaninsu ba, banda abinci da shima se an ga dama a basu da kuma makarantar Alaya ba zasu ce ga wani abun arziki da suke tsinta a rayuwar gidan ba, amma ya suka iya? Ya kuma zasu yi? Nan ne kaddararsu kuma nan Allah ya zaɓar musu su yi rayuwa. Landline ɗin sashensu ne ya ɗauki kara ko gama tattare sashen ummi bata yi ba sbd tunda suka tafi babu wadda ya dawo se yau, ummin kuma ta hana Alayar kama mata sbd har yanzu jikin se a hankali, ƙarasawa tayi ta ɗauka Muryar Meelah ne ya karade kunnenta "Ki zo ki yi min gyarar daki" Shine abunda ta faɗa kan ta kashe babu ko amsa sallamar da tayi mata, ummi ce ta tambaya me take so? Nan ta faɗa mata, girgiza kai tayi tacewa Alayar ta je ta kwanta zata je tayi mata. Babu dae yadda ta iya ne haka tana gani ummin ta fice, zama tayi a wurin ta sanya kanta cikin kafafunta tana tunanin abunda kaddara ya zaɓar musu se yaushe ze wuce? Anya kuwa zasu samu chanjin rayuwa? Kwarai ummi tayi mamakin ganin irin yadda Meelah ta maida ɗakin a kwana biyu kaman ba mace ba? Duk wasu ledojin kwalamarta na zube tsakiyar ɗakin wasu kayan sawa wasu takalma duk gasu nan ɗaiɗai baje a ɗakin haka ta soma tattarewa a natse ta jima kan ta samu ɗakin ya dawo daidai ta juya ta fita ta tsaya parlorn ta gyara ta koma na Hajiya Zeenat ta fara kenan Meelah ta fita daga dakin uwarta tayi nata ba'a yi mintuna goma ba ta dawo ta tsaya kan ummi tana mata magana cikin tsawa. Ganin ba jin ta zata yi ba yasa ta dauko sandar mopper da ummin ke aiki dashi ta zungureta wai ita nan kyamar taɓa ummin take, Juyowa ummin tayi saide Meelah ba maganan kurame ta iya ba masifarta ya fito da Hajiya Zeenat "a'a Shalele mai ta miki ne?" "Mommy ina sarkar da Abba ya sai min last business trip din shi daga Lagos?" "Eh na zinarin nan" Mommyn ta amsa "Mommy daga shiga ta min shara kawai in fito ban ga sarka ba? Kan uban chan kayyasaaa! Wlh sai ta fitar min da sarkata " Meelah ta faɗa tana wani hararar ummi cikin tsantsar fitsara da rashin kunya. Mommy ta juya ga ummi tayi mata alama "ina sarkar da Kika sata a ɗakin Meelah?" Dafe kirji ummi tayi a firgice kan ta soma girgiza hannu da kai da sauri alamar ba ita ba ce, daidai lokacin Abba ya fito hakanan Shigowar Alaya don kamawa ummin aiki ta sani in sun matsa ko na awanni ne ayyukan da su kan samu a gidan ba na wasa ba bare har kwana biyu, kalaman da taji ne yasa hankalinta tsananin tashi da sauri ta ƙarasa ta rike hannun umminta tana kallon meela da mommy tace "Sata? Ummina fa?" Yadda tayi maganan a karye lokaci ɗaya hawaye na gangaro mata dole ta baka tausayi, wani sabon bita da kullin kuma za'a bisu dashi? *Kar ku sha'afa Al'ajabin So book 2 is not free, a kan naira 500 kachal zaki same shi immediately after an kamallah book 1, zaki iya yin payment ta nan 3118518476 First bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya ta wannan layi 09039206763* #Vote #comment                 🖤Gureenjoh🖤 AL'AJABIN SO (heart touching story) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN.                      (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* *Kowa Ya ga zabuwa..* *Diddigar ƙaya... Paid* And now.. *AL'AJABIN SO* *BOOK 1* *Page 4* "Hajiya! ummi bata saci komai naku ba, don Allah kar ku fara yi mana wannan sharri, ba halinmu ban...." Buge mata baki da Hajiya Zeenat tayi yasa ta saurin dafe bakin tana zub da hawaye kaman yadda ummi ma kanta ke ƙasa tana hawaye. Faɗa suke yi ta inda suke shiga ba ta nan suke fita ba har da zunguri Abban Meelah dae be ce komai ba yana tsaye yana nazarinsu, kansu ƙasa suna aikin zub da hawaye na wannan tozarci da ake musu da kazafi, suna cikin wannan masifar se ga Hajiya Fanta da ɗiyarta Zaliha suma suka shiga sahu har da aje a chaje sashensu. Meelah tace "ba wani sashe a nan jikinta zata ɓoye don ai bata fita ba" Hajiya Fanta tana dubansu cikin kyama tace "ku chaje ta maza maza toh in dae haka ne" Dukewa ummi tayi ƙasa tana rufe idanu a sadda hameeda da Meelah suka fara chaje jikinta suna yatsina fuska da sunan kyama yayinda Alaya ke kuka harda gunji, ganin irin halin da suka shiga yasa Abba da ya taɓe baki yana yiwa ummi kallon 'duk laifinki ne' yayi gyaran murya yana duban Meelah yace "my dota kyale su idan ma su suka sata zamu ga yadda zasu yi dashi idan don sarka ce zan sake sai miki wata.." Tura baki tayi harda hawaye sbd ba yadda ta iya tana kallo yayiwa su ummi alama da hannu akan su fice, kama ummi Alaya tayi suka fita daga parlorn zuciyoyinsu baƙi kirin, hajj Zeenat kuwa haushi sossai taji tana kallon sbd wani manufar ne Alhj Hassan ya sa suka tafi alhali sun musu sata bata damu da gaban ƴarsu ko baƙin su ba tace cikin faɗa "Haba Abban Jameelah ai wannan ka basu damar sake wa gobe ne, baka da hujjar saka su barin parlorn nan alhali ka san babu wadda zai saci sarkar nan in ba su ba in har dae ba da wata manufar ka tseratar dasu ba.." Wani irin kallo ya watsa mata kan ya juya har ya nufi barin sashen ya sake Juyowa "baki da hujjar tuhumata akan abunda yake ni na saya ko yanzu zan iya sayawa mamana Goma irin shi don haka ki daena shiga min hanci da kudundini" Gabas da yamma ta haɗa da fuskanta da ta turbune wadda yafi yanayi da na shanu zata soma sakin zance Hajiya Fanta ta ja hannunta suka yi ɗakinta. Meelah ta ja hannun Zaliha tana cewa "zo kawata mu je kiga wani guy da ya tafi da imani na a intsgram ban taɓa sanin akwai me kyau da charisma irin shi a duniya ba" Suna shiga ɗakin ta sa hannu bedside don ɗauko wayanta se ta sauke kan sarka da ya ɓuya a bayan flower portal dake daure bisa bedside dinta fiddo shi tayi tana nunawa Zaliha "Ai ke banza ta faɗi miki adana wannan daddynki ya sake sayo miki wata" "haka ko za'a yi" Ta ja bedside ta saka kan ta kamo instagram ɗin ta ta fara nunawa zaliha gayen ba Jameelah kadai ba har zaliha gayen ya tafi da imaninta sake kallon handle ɗin tayi a ranta tana maimaita "captain cold" wow ko sunan na daban ne. A ta ɓangaren su Alaya haka suka jima jugum cikin damuwa da tunani da Alayah ta gaji ta dubi ummi "Ummi don Allah bamu da kowa a duniyan nan ne? Ummi Meyasa kika dage sede mu cigaba da zama a wannan baƙin gida? Meyasa ba zaki bani labarinku da Abbana ba? Umm..." Dakatar da ita tayi "Ki adana tambayoyinki akwai lokacin da da kaina zan baki waennan amsoshi Alayah.." Hawayen ta ta share ba tare da ta sake cewa ummi komai ba. **** Tafawa suka yi suna dariyar su irin ta asalin Ƴan siyasa kuma waenda suka gogu da duniyanci, daga kallo ɗaya zaka san sun jiƙu da naira iya jiƙuwa da alama hirar tasu mai daaɗi ne... "Ai ina gaya maka Hon Hameed chanji a tafiyar da muke gab damo ke shirin isa ga harawa" Dariya suka sake sakewa kan Hon Hameed chanji ya ɗan tsagaita hankalinshi ya tafi ga wani tunani da yake damun shi a rai.. "Lafiya kuwa honourable?" "Wlh ina cikin wata ƴar damuwa ne, na san bazaka rasa sanin mukhy ba". "Ah taya ba zan san Mukhtar ba? Shine fa yaro ɗan babansa mafi soyuwa a cikin zuciyarka". "ka san a sadda na tura shi chan ƙasan waje karatu a maimakon karatun sai lalacewa yayi, ya faɗa shaye shaye, abun bai tsaya nan ba suka yiwa wata yarinya fyade sanadin kaisu gidan yari kenan, ka san chan ba kaman nan ba duk wata hanya da zan bi don ganin kuɗi sun fidda shi hakan ya gagara seda yaci prison na shekara takwas, daga nan suka koreshi a ƙasar lalacewar da Mukhtar yayi a prison yafi karfin wadda yayi kan zuwanshi da kyar na samu ya karanci business a Nile Abuja shima da laifuka iri daban daban, duk dae kuɗi nayi ta anfani wurin kashe su har ya kamalla na buɗe mishi kamfanin motoci ya fara business ɗin.." Kai Alhj Hassan ya gyaɗa duk wannan ya sani ai labarin tantirancin mukhy babu wadda be sani ba in har dae Kano kake. "Yanzu menene matsalar baya sana'ar ne?" "Hmm sana'a ba karamin karbarshi yayi ba yana samu ba na wasa ba sede kuɗin a banza yake tafiya Ƴan mata, abokai, Ƴan shaye shaye, su tatooo da ya cika jikinshi dasu da dai sauransu, da nake shawara da wani aboki na se yake ce min ai aure na nitsar da irin Muktar ni kuma ban cika son takura mishi ba duk abunda yake so shi nake so nayi ta bin shi ya kawo mata ya min kunnen uwar shegu, yanzu ina tunanin samun mace dalleliya wacce ba ze iya ƙin aurenta ba in aura mishi amma ban san wace yarinya zan samu ba, irin  yaran malaman  nan haka dae" Wani tunani Abba ya tafi kan ya dubi Alhj Hameed ya ce "ka kawo kuka gidan mutuwa abokina" Dariya suka yi a tare Alhj Hameed yace "na san ka abokina duk inda matsala take ka san maganinta, wacece wannan da iyayenta zasu iya aura mata mukhy?" "Fatima ɗiyar Amadu" Wani irin dariya suka yi sossai  kan Alhj Hameed yace "kana ganin wannan Hawwar zata yarda kuwa?" "Dole ma ta yarda, kai ko bata yarda ba ni na ba wa muktar auren Fatima kuma ka tabbatar wannan aure an yi an gama ka kwantar da hankalinka kaman kayi baƙo ya mutu" Kashewa suka sake yi suna dariya daga nan suka yi sallama, Alhj Hassan ya tashi don raka Hon Hameed se ga Alayah ta fito daga sashensu zata shiga sashensu Jameelar don ɗaura abinci sbd zazzabi ne ya rufe ummi... Har ta wuce Alhj Hassan yace "ke!" Da sauri ta iso ta duƙa a ƙasa ba tare da ta kalle shi ba ta gaida bakonshi ya amsa yana me kallon ta kan Alhj Hassan yace "je ki" Ta miƙe ta wuce. "Ka ganta nan bana tunanin Mukhtar ze iya ƙin irin wannan" Kai kawai Hon Hameed ya gyaɗa wannan ai ko shi ya samu irin wannan ba ze ƙi ba shar da ita ga kyau da natsuwa kaman nunanniyar gwanda... Ranshi kal yayiwa Mukhtar mata ya isa gida, parking driver ɗin shi yayi a kofar mashigar parlorn ƙawataccen gidan da ya tsaru ya gaji da tsaruwa, kofan parlorn ya buɗe ya shiga sanyi da kamshin da parlorn ke yi na asalin matan shuwa ya shaka ya lumshe ido, wannan kamshi da tsabtar na daga cikin abunda yake hana shi fushi me tsawo da hajj binta Dukda yadda take bakanta mishi rai a kullum tana mai dashi yaron goye. A kan kujera ya sameta kaman kullum cikin ado da kwalliyar da bata rabo dasu sanye da laffaya me tsadar gaske hannu da kafafunta sun sha jan kumshi gata fara sol kaman ka taɓa jini ya fito, ɗaga idanunta tayi ta kalleshi kan ta girgiza kai cikin hausar ta da har yanzu be zama cikakke ba tace "Alhj ban ji kayi sallama ba" Tsaki yaja yana yarfa hannu yace "woohuhu ke kam Binta Meyasa bakya rasa abun complain bane a kullum, ni na zo miki da labari me daaɗi ke damuwarki wata sallama" "Ai ko dae sallama na da matukar muhimmanci, kuma wajibi ne a musulunci" "to Naji Assalamu Alaikum shikenan?" "Wa'alaikissalam warahmatullah" ta faɗi tana kallonshi yana zama. "Na samarwa muktar mata" Da hanzari ta kalle shi "wani uba ne ze baiwa Muktar auren ƴar shi? Ko dae ƴar irin Muktar dinne?" Harara ya maka mata cikin takaici yace "Meyasa ke kam a kullum bakinki baya taɓa fadin alkhairi akan wannan yaro ne? Ƴar mutunci nitsatsiya kuma ya samu sai ki haɗiyi zuciya ki mutu" "Me yayi zafi Alhj? Ni dae na san uban kwarai ba ze taɓa ba muktar auren ƴarshi ba wallahi, kuma ni ban yiwa muktar baki ba a kullum adu'ata Allah ya shirye shi sannan wallahi ku guji hakkin ƴar mutane sbd wallahi haɗa ta da muktar zalunci ne mai girma, idan har ba ya chanza halin shi ba" Tsaki yaja yana Miƙewa "Babu anfanin faɗa miki Binta ki sani bukin ba ze dau lokaci ba in kin ga dama ki fara shiri, muktar dae ɗan ki ne da kika haifa da cikin ki babu abunda ze chanza hakan, fifikon ki na banza akan Umar yaron da be ma san kina yi ba" Daga haka ya wuce fuuu Da ido ta bishi a fili tace "Allah ya shirya to" A zuciyarta kuma tun kan ta san yarinyar tausayinta ya rufeta, muktar danta ne kaman yadda mahaifinshi ya gama faɗa saide duk halayen muktar babu na zaɓe, ga zafin zuciya da saurin fushi, ga shaye shaye idan ya bugu iya buguwa har ita bata tsira daga cin mutuncinshi ze iya zuwa tsakiyar parlorn nan ya gayamata duk maganar da ta zo bakinshi se abubuwan sun sake shi kuma ya zo yana neman yafiyarta yana cewa shi be san yayi ba, to taya ze iya zama da mace a haka? Ƴan matanshi har gidan nan suke zuwa neman shi mahaifinshi be taɓa ganin hakan a laifi ba se ma goyon bayan da yake bashi, duk da sana'ar da yake sede idan be nemi kuɗi a wurin mahaifinshi ba duk ywansu haka ze bashi ba tare da ya tambayi abinda za'a yi dasu ba, ko kwana nawa muktar ze yi a waje mahaifinshi baze taɓa tambayar inda yaje ba bare ya binciki me yayi tun ma be kai haka ba bare yanzu, duk wani faɗa na club mukhy amma uban ba ze taɓa tsawatar mishi ba sede ya biya kuɗi a kashe case ɗin, ita dake yawan yi mishi faɗa da nasiha se suka maida ita makiyiyarsu daga shi har mahaifinshi, kullum a ganin da yake mata bata ƙaunar Mukhtar wanene ze kaunaci ɗa duniya sama da uwa? Ajiyar zuciya me nauyi ta sauke tana girgiza kai... *** Yau sunday ummi na chan cikin gida tana aikin abincin dare yayinda Alaya ta gama yiwa Hajiya Zeenat da Meelah wanki ta shanya se ta nufi ɗakin su ta gyare tsab, ta fara tattare wankinsu don zuwa ta musu ta san idan ba yau din ba ummin ce zata yi idan ranakun makaranta suka shiga, taje ta fara kenan ta ɗauko wani zanin ummi dagawar da zata yi se taga wani ƙulli murmushi tayi tana ayyanawa kila ɗan chanjin asibiti ne ummi ta ƙulle a bakin zanin kaman wata tsohuwa warwarewa tayi don ta adana mata se taga paper ne, buɗewa tayi tana mamakin wani paper ne wannan ɗin.. Rubutun ta fara karantawa daki-daki gabanta ne ya faɗi ummi na da hanyar tseratar dasu daga wannan rayuwar? Menene wannan kalma ɗaya tak da zata faɗi don saya musu Ƴanci ta kasa? Gabaɗaya ta rude haka ta gama wankin tana Allah Allah dare yayi don ta tuhumi umminta akan abunda take boye mata, tana gama wankin ta nufi komawa sashensu don gab magarib ne ta san ummi zata gama abinci a lokacin ta koma sallah, da Abban Jameelah suka ci karo da sauri ta tsuguna kasa gabanta na faɗuwa sbd yadda take matukar tsoron wannan mutumi, ya azabtar da ita ba na wasa ba da tana yarinya ta ɗauka shine mahaifinta hakan yasa a duk sadda ta gansu da Jameelah se taje a kuma duk sadda taje da kuka zata dawo, tun tana zuwa har ta daena kwata kwata idan kuma wani abu ya hada su da Jameelah har suka yi faɗa to lallai jikinta se ya gayamata hakan ne ya koya mata respecting Jameelah karfi da yaji. har ze wuce se ya dakata yace "Ke! Idan kin koma ki fadawa mamarki na yi miki miji, a kowani lokaci za'a iya tada maganar aurenki don haka ku zama cikin shiri, sannan zaki iya amsar baƙuncin shi anytime from now don ze zo ya gan ki" Ji tayi kaman bata ji da kyau ba tsabar yadda maganar ya zo mata bagatatan, a razane ta ɗaga ta kalleshi tace "miji? Ni?" Harara ya zabga mata yana cewa "A'a ƴarki ta fari to uwarta" Da sauri ta maida kai ƙasa tana jin wani kullin tashin hankalin dake taso mata, ita ze yiwa aure? Me ta mishi? Meyasa? Akan me? Mulkin mallaka kawai? Da gudu a kuma kiɗime ta isa sashensu tana zuwa kawai ta faɗa jikin ummi da zata tada sallah kenan ta fashe da wani irin kukan tashin hankali... *Kar ku sha'afa Al'ajabin So book 2 is not free, a kan naira 500 kachal zaki same shi immediately after an kamallah book 1, zaki iya yin payment ta nan 3118518476 First bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya ta wannan layi 09039206763* #Vote #comment                 🖤Gureenjoh🖤 AL'AJABIN SO (heart touching story) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN.             (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* *Kowa Ya ga zabuwa..* *Diddigar ƙaya... Paid* And now.. *AL'AJABIN SO* *BOOK 1* . *Page 5* Kasa riƙe balance ummi tayi suka tafi tare zuwa kan gado, a gigice ta ɗago ta ganin tana zub da hawaye fuskanta da alamun gigicewa ko ɗimaucewa da bata taɓa ganinta dashi ba, cikin alamar kurame take tambayarta abinda ke faruwa, ta ma rasa da wanne zata fara, kuka kawai take na baƙin cikin kasancewar su a wannan gida kuma ummi na da yadda zata yi amma ta zaɓa musu wannan rayuwa da rayuwar ƴancin da ake tallata mata. "Alaya menene?" Ummin tayi mata alama bayan ta ɗago ta tana dafe da kafaɗun ta. "Ummi wai ni Abban jameela yake cewa zai yiwa aure nan kusa, ummi wlh in har hakan ta kasance ba zan iya cigaba da rayuwa ba! Ummi zuciyata zata buga da baƙin cikin wannan rayuwa..." Ummi da tafi Alaya gigicewa tayi saurin sake mata Alama "ban gane ba!" Bayani ta mata yadda suka yi cikin kuka ta kara da "Ummi karki ce in yi haƙuri wlh ba zan iya wannan aure ba, ba zan taɓa tafiya in barki cikin wannan gida ba!" Kasake ummi tayi zuciyarta na fin na Alaya bugu, maganar ya zo mata wani iri, aure? Wani irin aure? Me Alhassan ke nufi? Bata iya tayi magana ba illa kurawa Alaya idanu da tayi tana kuka sossai. Sai kuma ta warware papern tana nuna mata "Ummi wannan a kayanki na samu, me hakan ke nufi? Ummi zaki iya tseratar damu amma kika zaɓi ƙiyawa?" Karɓan papern ummi tayi ta dunkule bata cewa Alayar komai ba banda kanta da ta mayar ƙasa tana sauke numfashi. Daga magarib har isha sun yi shi ne kawai babu cikakken natsuwa dukkaninsu a tsorace suke da lamarin wannan aure da Abban yayi, sanin kansu ne babu kaunar su ko na second a zuciyar Abba to taya zasu yi tsamannin zai zaɓarwa Alayar ma miji nagari in ma ya kama ya zaɓar mata kenan, tambayar ma itace; Meyasa ze tsallake buduruwar yarinyar shi ya zaɓi Alaya? Me manufarsa? Har sun yi shirin kwanciya ummi da take wani nazari ta dubi Alaya dake ganin kaman duk wani abunda ke faruwa laifin ummin ne tunda tana da hanyar samar musu Ƴanci amma tayi shiru, ummin na kallo Alayar ta kwanta ba tare da ta sha magungunanta ba gashi sai zub da hawaye take har lokacin. Miƙewa tayi ta dauko magungunan da ruwa tazo ta ɓaɓallesu ta ɗago Alayar ta mika mata, karɓa tayi ta sha tare da sake komawa ta juyawa ummin baya, kaman yadda bacci ne ɓarawo ya dauki Alaya haka ummi da ta raya daren bisa sallaya tana zub da sassanyar hawaye na abubuwa masu yawa da suka faru a rayuwarta Dukda bata nadamar ko guda sede tana jin tsoron abunda hukuncin da zata yanke na gaba ze iya kawowa.. Washegari kaman yadda suka saba haka suka kama ayyukansu da sassafe saide duk jikkunansu a mace suke aikin babu wani kuzari, har Alaya ta kamalla breakfast ta shirya dining zata juya kenan sai ga Jameelah da Hajiya Zeenat sun fito, ƙasa ta duƙa cikin sanyin murya ta gaishesu babu wacce ta amsa ta miƙe ta ƙarasa ta ja wa Hajiya Zeenat kujera ta zauna, abincin ta fara serving nasu pepper soup na kayan ciki ne sai dankali da aka soya cikin kwai aka kuma yi mishi egg sauce da tea, pepper soup din Jameelah ta janyo ta sanya spoon ta kai bakin ta da sauri ta furzar tana zaro ido, a ruɗe Hajiya Zeenat ta miƙe kaman yadda Alaya ta zaro ido zuciyarta cike da fargaba. "Mommy harshena ze tsinke wannan baƙar muguwar zata kasheni da yaji!" Mugun kallo Hajiya Zeenat ta watsawa Alaya cike da gargadi tana kokarin bawa Jameelah evaporated milk da ta fasa. A ruɗe Alaya ta matso tana cewa "kiyi haƙuri wallahi ba...." Ƙara ta saki a lokaci ɗaya tana ambaton Allah sbd zazzafar pepper soup ɗin da taji a jikinta inda Allah ya taimake ta be kai fuskanta ba amma babu tantama wuyanta ya samu sbd radadin da ya ratsa ta a lokaci guda. Hawaye ke gudana a fuskanta tana jin faɗan da ya biyo bayan watsa Miyar har suka gama bata iya taji kalma ɗaya ba sbd radadin da jikinta ke yi, da sauri ta bar parlorn a sadda suka sallameta tana fita ta gamu da Ummi dake shirin shigowa ɗauke da kayan share share, bata tsaya yiwa ummin magana ba ta wuce ta da sauri, da hanzari ta ajiye abubuwan hannunta ta bi bayan ɗiyar tata ganin farin uniform dinta daga wuya har ƙasa ɓace da miya. Alaya na isa ta zube ta cigaba da kukanta tana jin radadin na ratsa ta, da sauri ummi ta ɗago ta tana tambayarta abunda ya faru amma bata amsa ba duk laifin ummin take gani, sai da ummin ta jijjigata da karfi tana mata alama bakin ta na irin ɓaɓatun maganan kurame dinnan "Alaya ki dawo hankalinki, duk abunda kika ga na yi sbd ke ne da rayuwarki, nima ba zan zuba ido a zalunceki a ɓata miki rayuwa da gangan ba, menene ya faru? Ki min magana..!" Alama take mata tana sakin wani kukan a haka ta bata labarin abunda duk ya faru, hijabin ummi ta zare mata abunka da farar mace nan da nan jikinta ya tashi yayi jajazir daga wuyanta har kirjinta, wani abu me ɗaci ummi ta haɗiye ta miƙe ta fice chan ta dawo da kƙullun kunu sbd ana yiwa Abban Jameelar tazo ta shafa mata duk wurin kunar ta zauna ta sanya ta a gaba tana kallo yayinda baccin wahala ya ɗauke ta. Bayan kwana biyu Tun daga randa ta ƙone bata kara fita daga sashen ba komai ummi ke yi Dukda damuwa da ya mata yawa, yake kuma cin zuciyarta hakan be hana tayi musu duk aikin da suka saba yi ba, Alaya kuwa tun ranar bata iya zuwa makaranta ba duk son ta da boko kuwa. Yau dae ta miƙe ta shiga cikin gidan don kamawa umminta aiki tana cikin jera abinci taji gyaran muryan Abba da sauri ta juyo se ta kai gwiwowinta ƙasa kanta kasa gabanta na tsananta bugu. "Muktar ze zo yau ku gaisa, make sure baki yi abunda ze zubar min da ƙima ba, parlorn baƙi na zaku zauna and ki tabbatar kin tsaftace kanki na rana ɗaya dae" Yana kai nan ya wuce abun shi. Bata iya ta miƙe daga tsugunon ba tsawon mintuna kan ta yunkura kitchen da bata koma ba kenan tayi chan baya ta fara zirga zirga... Na shiga uku na wai da gaske Abban Jameelah ke yi? Shikenan haka zamu kare kaman bayi a chan lokacin jahiliyya? Babu irin nazarin da bata yi ba har da tunanin ko ta gudu se kuma ta tuna in ta gudu umminta fa? In ma ta gudun ina zata? Bata san kowa nata ba banda gidan nan da makaranta sai asibiti bata tunanin ta san wani wuri a fadin birnin jihar Kano. Har aka kira la'asar bata iya ta taɓuka komai ba banda tunani da wani irin fargaba da ya cika mata zuciya fal, ganin lokacin Sallar na shirin fita yasa ta nufi sashensu sukuku da ita haka tayi sallah tana nan zaune ummi ta shigo ko kan tayi maganar yadda ta ganta ɗin taji sallamar iro me kula da shuke shuken gidan alama tayiwa ummi na ana sallama kan ta fice, a mutunce suka gaisa ya shaida mata tana da baƙo a sitting room na Alhaji.. Dawowa tayi tana share hawaye ta faɗawa ummi har abunda Abban Jameelah ya faɗa, bata ce komai ba har Alaya ta juya ta fice da kayan jikinta dogon riga da hijab da ya wuce mata gwiwa kaɗan, da idanu tayi ta bin zazzafar motar tashi kirar McLaren Mp4-12c wacce murafanta ma ta sama ake ɗagasu Red colour mirrors ɗin baƙaken sidik banda sheki babu abunda yake yi har ta isa kofar parlorn, ta dan jima anan tana daidaita bugun zuciyarta da fargaba hade da tsoro da suka cika ta kan ta tura kofar da sallama. Ba'a amsa ba kutsa kai tayi ciki bata yi gigin dagowa ba ta ƙarasa ta tsaya a tsaye tace ina yini? Ba tare da ta ko zauna ba. Buɗaɗɗiyar muryarshi da ta kara zurfi da amo sbd shaye shaye ya dira bisa kunnuwanta "Kin ƙara mintuna ashirin da biyar daga kiranki zuwa yanzu mind you next time karki kuma, ba'a ɓata min lokaci a banza!" Sai a lokacin ta iya ɗaga idanu ta kalleshi tana kokarin auna kalaman da yake faɗa mata cike da gadara da isa kaman shi ya ajiyeta, bata ce komai ba se kallonshi da take ba laifi don kyau kam kyakyawa ne na gasken gaske duk inda kake neman namiji wannan din da Abba ya kira da Mukhtar to ya kai, saide dressing dinshi na three quater da armless shirt ya bayyana munanan halayenshi kaman yadda baƙin lips ɗin shi ya nuna karara hayaƙi na aikinshi a wurin, daga kirjin shi zuwa dantsen hannun shi na dama tatoos ne da aka zana ya zanu sossai kaman kan zaki ko damisa ne oho.. Wani irin tsawa da ya daka mata yasa ta razana tayi baya tana wara kyawawan idanunta "ba'a yi min shiru in ina magana am I clear?" Bata amsa ba, hakan ya saka shi Miƙewa a harzuke ya nufeta gadan gadan, a tsorace ta fara ja baya yana kara matsowa har ta isa jikin gini ya matso sossai ya mata rumfa yana kare mata kallo "young, beautiful and stubborn!" Ya faɗa yana taɓe baki "ba laifi Dad ya iya zaɓe but kina bukatar sabbin karatuttuka a wannan lunatic brain ɗin" Ya faɗa yana dannan saitin brain ɗin da hannunshi kauda kanta tayi idanunta suka cicciko, ya sanya hannu ya shafa fuskanta a firgice ta Buge hannun tare da sauke mishi marin da bata taɓa tunanin tana da wannan karfin halin ba, kankame jikinta tayi sbd kusancinsu tana kokarin zamewa ya fusgota tare da fusge hijab ɗin jikinta, ƙara ta saki ya Buge mata baki da gwuiwar hannunshi har saida jini ya fita yana furta... "Shhhhh" idanunshi kaman garwashi da alama ma wani abun ya sha kan zuwanshi nan ɗin "Lallai yarinya kin yi kokari, Marin Muktar abu ne da ya kamata a tafa miki, trash like you, villager, wacce ke cike da rashin wayewa yau ke kika sa hannunki a fuskata, fuskar da mata dubu ke marari hmmm marin nan zan fanshe su ta hanyoyi daban daban ki rubuta ki ajiye the First one za ki tantance yanzu, sauran sai kin zo.." Ko kan tayi wani yunkuri ya sanya hannu ɗaya gaban rigar ta ji kake Kyaaaaat ya farke har farin vest dinta ya bayyana, ihu ta tsala tare da saka iyakar karfinta tana kokuwar kwace kanta sede shi ɗin namiji ne da gaske ko gezau ta kasa motsa shi, kuka da ihu take tana neman ɗauki daga Allah... Gaban ummi ne ke ta faduwa tun fitan Alaya ɗin ta kasa natsuwa, daga karshe sake aikin da take yi tayi ta nufi sitting room ɗin tana kuma jin gabanta na tsananta faduwa. Tura kofar da tayi ya ɗan yi karar alamar Shigowar mutum ne ya saka shi dakatawa daga abunda yayi niyya chakk, jajayen lumsassun idanunshi ya ɗago ya kalleta irin kallon zaki yi bayanin nan kan ya ja baya yana gyara wandonshi ya juyo, ita kanta ummin wani irin kallon banza yayi ta aika mata har ya isa daidai inda take kan ya daga hannu yayi mata alamar ta matsa, abunda ta gani ne ya daskarar da ita, idanunta na kan Alaya da ta zube bisa gwiwowinta tana gunjin kuka bata ankara ba taji an tureta an wuce, bata iya riƙe balance dinta ba se ta tafi a haka ta faɗi ƙasa sumammiya....! *Kar ku sha'afa Al'ajabin So book 2 is not free, a kan naira 500 kachal zaki same shi immediately after an kamallah book 1, zaki iya yin payment ta nan 3118518476 First bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya ta wannan layi 09039206763* #Vote #comment 🖤Gureenjoh🖤 AL'AJABIN SO      (heart touching story) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN. (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* *Kowa Ya ga zabuwa..* *Diddigar ƙaya... Paid* And now.. *AL'AJABIN SO* *BOOK 1* *Page six* A hankali ummin ke buɗe idanunta da suka yi nauyi, zuciyarta na bijiro mata da abin da ya firgitata, da ido ta bi environmemt ɗin sai ta fahimci a asibiti take babu tantama hawan jininta ne ya tashi. Idanunta ta kai gefen ta sai suka faɗa kan Alaya dake dunkule cikin kujera idanunta a lumshe kaman mai bacci duk sun kumbure alamun ba karamin kuka ta ci ba, wani irin tausayin ɗiyar tata ne ya rufe ta, lumshe idanu ta sake yi, ta gama yanke hukuncin amincewa Alhj Hassan da bukatar shi in har dae hakan shi zai sa ya kyale Alaya daga wannan mummunan rayuwar da yake shirin jefa ta, ko a mafarki kai ko a labarin tatsuniya bata fata ace wannan dodo da ta gani da idanunta yana shirin keta haddin ɗiyarta a cikin gidan ubanta ya zama mijin Alaya. Me yasa ta kasa rike amanar Ahmad? Me yasa mutuwa ta mata yankan kauna? Ita kadai babu yadda ta iya da Alhassan, dole abin da yake so din nan shi zata yi... Kuka ne ya kwace mata wadda ya saka Alaya da dama ba bacci take ba tunani take akan sabuwar ƙaddarar dake shirin riskarta tayi saurin ɗagowa da hannu take mata alamar ta tashi? Ya jikin? Ta dena kuka haka pls. Har malam Musa ya shigo da zumar tafiya dasu gida sbd likitan da ya fita yanzu ya sallamesu amma kaman yadda aka umurceshi Alhj Hassan ne ya kira ya sanar wa shi kuma ya turo malam Musa ummi bata ce komai ba ta dai bar zubar da hawayen sai azkar da take tayi, duk su biyu bayan su ubangiji ne kadai ya san abin da suke kullawa da warwarewa, suna sauƙa daga motar ummi ta dubi Malam Musa da yake mika mata wani takarda ta karɓa ta buɗe... "Idan kina da magana ki sameni yanzu a parlor na" Duban Alaya tayi tare da mata alama akan ta tafi, da kallo Alaya ta bita saide bata saba saɓa maganar mahaifiyarta ba haka ta wuce zuciyarta a kuntace cike da tunanin abin da ummi ke ɓoyewa a gareta sai taji bata ma son ji, kila rashin jin Alkhairin ta ne. A natse ta tura kofan parlorn ta sanya kai zuciyarta cike da addu'a irin adu'ar nan na fuskantar mummunan abu daga cikin halittar ubangiji wato a'uzubikalimatillahi tammat min sharri ma khalaka, daga tsaye ta tsaya tana kallonshi "hawwa kina da kafiya da taurin kai!" Ya mata alama yana taɓe baki. "Me kake buƙata?" Sai da ya dara kan yace "A tambayi kaza hanyar rafi kuwa? Hala kin mance tun ran gini tun ran zane, ba tun yau ba kika kwana da bitar bukatata a gare ki, da Kalma ɗaya tak zaki samar muku Ƴanci" "idan na amince maka na kuma yi maka duk abin da ka buƙata shine kadai zai sa ka fasa auren da kake shirin kakabawa Ƴa ta na tozarci da rashin galihu?" "Ko kin amince abu ne mawuyaci a fasa sbd yaro ya gani ya yaba, Marin da ta mishi kuwa daidai yake da ta yankarwa kanta tikiti na rayuwa dashi har abada, abu ɗaya na sani ko da kin amince nayi yadda nayi muka bar maganar auren nan to ɗiyar Ahmad bazata kara minti guda cikin gidana ba! Daga lafiyarta, cin ta, shan ta da karatunta duk sun yanke daga kaina babu abunda zan kara iya yi mata kuma a rayuwa sbd Ahmad be cancanci abubuwan da nake yi mata a yanzu ba.." "Me Ahmad yayi maka a rayuwa banda hallaci?  Kai butulu ne, kai azzalumi ne Hassan, ba zan taɓa bari ka samu abunda kake so a rayuwa ba zan barka da SON ZUCIYARKA cikin AL'AJAB NA SO kana ji kana gani ba zaka taɓa samun biyan bukatar ka ba in har dae akan SO ne ka aikata duk abunda ka aikata, Allah yana gani kuma ya san komai idan kaga Fatima ta auri wannan mutumi da ka kawo to haka yake rubutacce ne tun fil azal, ba zan iya chanza mata kaddara ba, addu'a kuma shine maganin komai..." Tana kai nan ta share hawayen dake gangara mata ta juya ta fice. Hajj Zeenat dake tsaye tana kallonshi yadda gabaɗaya yanayin shi ya sauya Ranshi ya kai kololuwa wurin ɓaci ta san ba komai bane sai danganta Ahmad dashi da Hawwa tayi har tana ikirarin cewa Ahmad ya fishi daraja da komai a idanunta, taɓe baki tayi ganin yadda ya wuce har yana buga kofa tace a fili "Kanku aje ji wai mahaukaci ya faɗa rijiya yace kanku aje ji ni wankana nake" Ko da ummi ta dawo bata iya tayiwa Alaya magana ba, kaman Alaya ta shiga ran ummi ta yagi fallen takarda daga takardar ta sbd so take ummin ta fahimci maganar daga zuciyarta yake rubutu tayi me ɗan tsawo kan ta ajiye mata ta tashi ta fice daga ɗakin. "Hawayen uwa abu ne me zafi da daraja a idanun ƴaƴa, ummi karki sake zubar da hawayenki akan wannan matsalar kin manta ke kika ce min Aljanna ana kewaye ta ne da abunda rai baya so yayinda ake kewaye wuta da abunda zuciya take so? Ko a makaranta an koyar dani cewa a cikin suratul baqarah Allah yana cewa zai kasance kuna matukar son abu sai ya kasance sharri a gare ku yayinda zai zamana kuna matukar ƙin abu sai ya zama shine alkhairinku, Allah shine mafi sani amma da na zurfafa tunani sai na ji ina da bukatar wannan aure watakila shi zai yi sanadin Chanza rayuwarmu, ba zan kara tambayar ki abin da baki so na sani ba na san in lokaci yayi zan sani, Don Allah karki sake yunkurin dakatar da Abban Jameelah akan auren nan idan har cutarwa yake nufinki dashi!" gabaɗaya hawayen Ummi ya gama jike takardar, kowace uwa bazata so jefa yarta cikin rayuwar da tafi wadda suke ciki ba amma ta san Hassan shu'umi ne zai iya anfani da wannan dama ya jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya kenan ko ta amince da kudurinshi sai ya san hanyar da ya bi ya muzgunawa Alaya saboda ita ɗin ɗiyar Ahmad ce. Haka suka kwana cikin wannan damuwa amma Alhamdulillah da yake sun fawallawa Allah sai suka tashi wasai da safe kaman basu da wata damuwa ayyukansu suka kama kaman yadda suka saba... **** Kishingide yake hannunshi rike da shisha Pen yana zuƙa sa'i da lokaci, ɗayar hannun nashi kuwa a kumatunshi daidai inda ta mareshi in ya shafa sai ya saki murmushi yana kallon fuskar yarinyar, Red eyes ɗin shi suka sake rinewa yana wassafa yanayin ƙirar jikinta yadda in tayi motsi komai nata yake girgiza, Allah ya zuba ƙira gata yarinya ƙarama, wannan in har ya same ta lallai yayi zarra cikin abokanshi, kaman yadda yake piya-piya a duk inda ya shiga baya jituwa da kananun kwari sai masu kumbar susa haka a aure ma, dole ne ya gayyaci duk wadda ya san zai iya gayyata ya nuna musu ya ƙere kowa... "bala'i! This gurl is morethan beautiful.." Gani yayi ba zai iya jira a dau lokaci ba hakan ya sashi Miƙewa daga kan sofa na rantsatsiyar club ɗin as usual sanye da kananun kaya three quater da shirt da bashi da maraba da vest, fitowa yayi cikin takunshi na nuna isa da jiji da kai wadda ze tabbatar maka da lallai shi wani ne ya isa ga motar shi ya shige tare da bata wuta yayi gida. Kaman yadda ya fita daga club ɗin haka ya shiga cikin parlorn sai de idanunshi da suka sauka kan mahaifiyarsu ne yasa ya ɗan seta kanshi.. "Sannu da gida Maami" Girgiza kai tayi tana kare mishi kallo ba tare da ta amsa ba, ze wuce tace "Mukhtar" Juyowa yayi ya dawo ya samu kujera ya zauna nesa da ita "wani magana ne nake ji daga bakin mahaifinka?" "Wai zancen aure? Na je na ga yarinya kuma na yaba ni yanzu ma so nake ko gobe ne tunda juma'a ne a ɗaura kawai" "ban gane a ɗaura gobe ba! Ƴar tsana ce? Ba ma maganan nan ba me kayiwa ƴar mutane da har zata mareka a cikin gidansu?" "Maami yarinyar nan fa dakikiya ƴar talakawa ce da alama kaskantacciya ce ko wayewa bata yi ba, daga in ɗan shafa fuskarta don tana da kyau da ɗaukar idanu shine fa" Tana girgiza kai cikin takaici tace "ba kawai bane, ta san girman mahaliccinta ne tana kuma tsoron fushinshi tana kiyaye azabarshi, innalillahi wainna ilaihi rajiun..! Wace ɗiyar mutunci ce zaku sa cikin bala'i da uku?" Yanayin fuskanshi ne gabaɗaya ya sauya ya miƙe yana yiwa mahaifiyar tashi wani kallo dama ya riga ya san ba son shi take ba, ba kuma ƙaunar shi take ba, mahaifinshi kawai ke son shi "Maami yanzu aurena ne bala'i da uku? Dama na san ba zaki taɓa farin ciki da cigaba na ba Maami ba ni kike so ba, wadda kike so yana chan yana aikin da kike ganin yafi na kowa a duniya, ni dae Allah na gani ba don kamanni ba kai tsaye zan iya cewa ke yaddikona ce...!" Miƙewar da tayi yasa yayi shiru tare da komawa baya sbd ya mata farin sani bata sake mishi sam, be kuma gameta yace ze faɗa mata wani abu ta tsinka mishi mari ba don ba yau suka fara ba "Ina maimaita maka wallahi Mukhtar kaji tsoron Allah ka sani komai zaka yi mai sauki ne da raina nin da kake, uwa nake a gareka baka isa ka faɗamin duk abunda ya ke bakinka in zuba maka ido ina kallonka ba don ba kai ka haife ni ba.." "Toh fa, waye ya taɓo rina uwar faɗa.." "Abba kaima ka sani in kana jin Muryar Maami a sama da ni ne ai Umar ba haka ake mai ba" Cikin takaici take kallon uba da ɗan, ta rasa Meyasa suke kunsa mata bakin ciki, Abbansun nan ya so muktar har ya wuce misali duk abin da zata yiwa muktar tun yana ɗan karamin shi gani yake ƙi ne har yaron nan ya zo ya kangare, abun takaici kuma har yanzu basu ganin abin da suke aikatawa ba daidai bane, runtse idanu tayi cike da tausayin wannan yarinya da ake shirin jefa ta cikin ka-ƙani-kayi tana ji sadda Mukhtar ya bijirowa da uban nashi shi gobe yake so a ɗaura mishi aure wadda ya zo ya zo, wadda be zo ba duk damuwar su a take mahaifin nasu ya amince akan zai ƙira Alhj Hassan yaji yadda za'a yi shi dae ya kwantar da hankalinshi. *** A natse ta sanya kafafunta ƙasa ta sauƙa daga cikin motar bayan driver ya buɗe mata kofar, karewa gidan kallo take tana nazari, gidan dae ya fi ƙarfin irin wannan aure da ake shirin aiwatarwa a gobe, tafiya take tana ɗan kalle kalle ko zata hadu da wani ko wata ta nemi iso, chan ta hango wata farar kyakyawar yarinya tana tafiya ne kawai amma daga dukkan alamu hankalinta yayi nisan kiwo, idan ta kula da kyau ma kaman yarinyar na sa yatsa sa'i sa'i tana dauke kwallah, sam yarinyar bata kula ba har seda tayi karo da ita kan tayi mugun komawa baya a firgice idanunta da suke fari tas a waje gabaɗaya. Alaya kam ita ta zata irin cikin kawayen hajj Zeenat ne yanzu su juye abu su ci musu mutunci, a tsorace ta zube ƙasa tana baiwa hajiyar da kai tsaye ta saka ta a top class hajiyoyi masu naira da isa haƙuri, bata taɓa ganin irin ta cikin ƙawayen hajj Zeenat ba don duk yadda zata misalta kyau da haiba irin na wannan mata me cike da annuri ba zai misaltu ba. Hannu ta sanya ta ɗago ta "Babu komai ai baki kula bane, yi min iso zuwa ciki ban taɓa shigowa gidan ba sai yau" Matar sam bata da girman kai irin na manyan masu kuɗi ɗin nan Alaya ta ayyana a ranta kan ta shige gaba Maami ta bi bayanta har cikin parlor, bata je kiran Hajiya ba seda ta kawo mata ruwa da ɗan abun motsa baki kan ta shiga wurin hajiyar ta jima a tsaye kan ta amsa mata ta dawo ta shige kitchen ta cigaba da aikin da take kan a kira sallah ta saki taje tayi. Cikin ƙasaita Hajiya ta fito Dukda ganin wannan gansamemiyar hajiyar ta san ba irin wacce za'a dagawa kai bane hakan be sa ta saita kanta ba ta samu wuri ta zauna a hakimce tana lura da kyau da kayan alatun dake jikin matar. "Sannu da zuwa" "yauwa Hajiya, kece mahaifiyar yarinyar da Abban muktar ya nemarwa aure?" Daidai Alayah ta fito don tambayar hajiyar abinda ta ce za'a ƙara bayan na time table yau. Idanu duka ta fitar kaman an danganta ta da wani mummunan abu tace "Allah ya tsare ni da haihuwar mugun iri, kin ganta chan sai ta dangana ki da kurmar uwarta tunda dae kun ji kun gani, a sauƙa lafiya in kin tashi!" Tana kai nan ta fice daga parlorn babu ko waiwaye, da farko jin irin gidan da za'a aurar da Alayah ta so ya haɗasu da jamila ne saide jin irin hallayyar yaron tayi tirrr da aurenshi, don a ganinta bashi da wani anfani, ko da uban ya faɗi ya mutu ko uwar dukiyar da zai gada bazasu je ko ina ba zasu ƙare a shaye shaye da bin mata, bata Gaza ba wurin tabbatarwa da Abban jameelar cewa in har dae suna da wani ɗan natsatse sai yayi kokari wurin ganin ya haɗa jamila da shi, be dae tanka ba amma ta san zai yi nazari akan hakan. A chan parlor kuwa, idanu mami ta zubawa Alayah da kanta ke ƙasa cike da kunyar matar sai a lokacin ma ta fahimci kamanni dake tsakaninsu da muktar din, amma me ya kawota? "Daughter ko zaki iya rakani wurin mamanki?" Ta tsinci Muryar hajiyar, da sauri ta ɗaga ta kalleta sai matar ta sakar mata kyakyawar murmushi, itama kakalowa tayi ta mayar mata kan tace cikin sanyin muryarta "Toh Hajiya mu je" Miƙewa Maami tayi ta bi bayanta har sashensu, da ɗan mamaki take kallon yanayin parlorn, kujerun da suka gama tsofewa duk dollof ɗin su waje Alaya ta nuna mata "bismillah bari na kira ta" Tana kai nan ta nufi kofa guda ɗaya dake sashen ta bar Maami da tsananin al'ajabi... *Kar ku sha'afa Al'ajabin So book 2 is not free, a kan naira 500 kachal zaki same shi immediately after an kamallah book 1, zaki iya yin payment ta nan 3118518476 First bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya ta wannan layi 09039206763* #Vote #comment                   🖤Gureenjoh🖤 AL'AJABIN SO (heart touching story) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN.                      (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* *Kowa Ya ga zabuwa..* *Diddigar ƙaya... Paid* And now.. *AL'AJABIN SO* *BOOK 1* *Page seven* Cikin tsananin tausayi da mamaki take kallon sashen nasu sai de tayi matukar kokari wurin boye yanayinta har ta kai zaune tana ɗan kallon kofan ɗakin da Alaya ta shiga, bata fi minti ɗaya ba sai gata da matar da bata bambance dayan biyu mahaifiyarta ce sbd kamanni Dukda Alaya ta zarta ta kyau nesa ba kusa ba. A hankali Alaya tace "Hajiya bazata iya jin ki ba" Tsananin tausayinsu ne ya kara rufe Maami tace "Sunana Maami bana so ki sake ce min Hajiya, tana iya karatu?" Kai Alaya ta gyaɗa. Jaka Hajiya binta ta buɗe ta fiddo joter da biro tayi rubutu kan ta mikawa Ummi da biro ɗin, ummi da yanayin matar ya kwanta mata ta karɓa ta karanta cikin tsananin mamaki ta sake ɗaga idanu ta kalli Maami sai yanzu take iya hangen kamannin, tattaunawa mai ɗan tsawo suka yi a rubuce, duk yadda Maami taso ummi ta nuna kirkiri bata son haɗin hakan bai samu ba sai ma bi da tayi ta wata siga irin ta mai hankali da sanin addini wadda hakan ya mugun yiwa Maami daaɗi, taji matukar daaɗin kasancewa dasu daga karshe ta fara jefawa Alaya tambayoyi yawanci akan karatunta ne kan tayi mata alkawari ko ta auri muktar karatun ba zai tsaya ba wadda hakan yayi mugun sata farin ciki tayi ta godiya, su ko cikin kunyar ko ruwan da zasu bata babu Alaya ta fara bata hakuri tayi saurin nuna ba komai da ta tashi tafiya kudi masu yawa ta fiddo ta ajiye duk yadda ummi taso ta bari ta ƙi haka ta tafi cike da tausayin waennan rayuka biyu da Allah ya tsirga mata. RANAR JUMA'A Tunda gari ya waye gaban ummi ke aikin faɗuwa sbd Maami ta faɗa mata a yau ne suka yanke za'a ɗaura auren, ta kwana kan sallaya ta kwana tana kaiwa Allah kukanta, da safen kuwa lokaci lokaci ta kan share hawaye, ba irin tunanin da bata yi ba idan har suka tsallake suka bar gidan nan shikenan tayi sallama da Ahmad da komai nashi, idan suka bar gidan saide su koma kaman sauran Abzinawa masu bara a titunan Nigeria, bata da wadda zata komawa a yanzu bata da kowa da zai iya rungumarta a wannan yanayi. Aiki take saide lokaci lokaci ta kan ɗaga idanu ta kalli Alaya hawaye na zuba a idanunta, daidai sadda Abban Jameelah ya shigo da karfi ya jefa mata ledar hannunshi wadda yayi sanadiyar watsewar alawa da goro dake ciki, a firgice Alaya ta miƙe tsaye tana kallonsu yayinda ummi ta runtse idanunta daidai lokacin da Abban ke cewa Alaya "Ga Alawar aurenki an ɗaura yau kuma ki shirya da dare zaki bar min gida, nayi matukar jinjinawa kokarin da nayi akan ki alhalin ke ɗin ɗiyar wadda ban taɓa so bane a rayuwata, ke ɗin ɗiya ce da mahaifinki bai taɓa ƙaunata ba, duk wani dama da ya ga zan samu ya kan yi hanzarin sha min gaba ya karɓe hatta kaunar iyayena bai barni da shi ba! Ki sani daga sadda kika fita daga gidan nan ko da sunan ziyara bana kaunar sake ganinki cikinta bare ki kashe aure ki dawo min, in kin fita duk abin da zai same ki ya kare a chan don Wallahi kika shigo min gida duk ya faru dake kiyi kuka da kanki" Razananniyar kukan da take ta yanke daga karshe tana kallonshi irin kallon da bata taɓa tsayuwa tayi mishi ba, kalamanshi ba abunda zata iya aiwatarwa ba ne taya yana tunanin zata tafi ta ƙi juya baya alhali ta san ta bar mahaifiyarta cikin wannan gida? "Alhaji mahaifiyata fa? Da kake wannan magana taya zan rayu cikin kwanciyar hankali in kasa waiwayen gidan nan alhali ka san duniyata na cikinta?" "Wannan kuma ke ya shafa Fatima, abunda na sani mahaifiyarki kamar mallaki na ce babu inda zata kuma ban amince ki shigo min gida ba and this is my final decision" Daga haka ya fice. Zubewa tayi akan tile ɗin kitchen din tare da ɗaura hannu a kai tana me sakin sabon kuka, da sauri ummi tazo ta ɗaga ta tare da sanya ta jikinta tana jin yadda jikinta ke ɗaukan rawa kuka take kaman ranta zai fita, bata san me tayiwa wannan rayuwa ba, shin ummi bazata faɗa mata abin da mahaifinta yayi mai zafi haka ba? Da kyar ummi ta samu hankalinta ya ɗan kwanta Dukda bata bar zubar kwallar ba, idanunta gabaɗaya sun sauya haka numfashinta da zafi zafi yake fita, wani mumman zazzabi da ciwon kirji ya kwantar da ita haka ummi ta saka ta a gaba tana zub da hawaye babu mai taimako, Dukda ta sha duk magungunanta saide hakan be kwantar da ciwon da ya fara barazanar ganin karshenta ba, addu'a ummi ta dinga yi har Allah yasa bacci ya ɗauketa na wahala. Haka ta koma cikin gidan ta ƙarasa aikin da suka bari ta dawo ta zauna jugum tana tunanin rayuwa, Dukda ta kasance marar gata irin Alaya saide aurenta bai zo a haka ba, aurenta da rufin asiri da kuma taron mutane aka yi shi, sallah ne kawai ke dagata har dab magarib kan Alaya ta farka, da taimakon Ummin tayi wanka ta sake shan magunguna abinci kam ya kasa shiga cikinta, a kwance kan cinyar ummin ta lumshe idanu bayan ta idar da sallolin da aka biyo ta ta fara jin Shigowar motoci da ƴar hayaniya kaɗan na mutane. Bata motsa ba har aka yi musu sallama, da gangan ta ƙi amsawa kila in bata amsa ba su juya su koma inda suka fito a yau me rabata da ummi kilan sai mutuwa bare in ta tuna irin furucin Abban Jameelah a kanta, Shigowar Maami ne ya sa Ummi sakin ɗan murmushi bayanta mata ne akallah zasu yi ashirin. Danginta ne kadan sai dangin mijin da suke ta kananun maganganu na mamakin zuwanta ɗaukar amarya alhali ɗan ta ne na fari kuma kowa ya san rashin jituwarsu saide tayi kunnen uwar shegu dasu kaman bata san suna yi ba wai an tsikari kakkaura, a hankali da taimakon ummi Alaya ta samu ta zauna tana zub da hawaye ta gaida Maami, cikin kulawa ta amsa kan tace "Binti ya baki shirya ba?" Murmushi me ciwo tayi ina wani kayan shiryawan mutanen gidan kaman basu san da zaman su ba bare su yi tunanin kyautata mata a yau dai ɗaya. "Maami bani da lafiya ba zan iya tafiya ba, ba zan iya tafiya in bar ummi a wannan gida ba Maami don Allah ki ce ya barni ban shirya aure yanzu ba, don Allah karki rabani da ummi wallahi zan iya mutuwa" Tayi maganan cikin sanyinta da kuma alamar roƙo da sallammarwa rayuwar gabaɗaya. Da kyar Maami ta iya mayar da hawayenta tana karbar farin takardar da ummi ta miƙo mata "ƴata na haifeta da ciwon zuciya! Don Allah ki kula min da ita da lafiyarta, ki riƙe min amanarta, ban san ko zamu sake haɗuwa nan kusa ba amma don Allah ina roƙon ki alfarma guda ɗaya a matsayinki na uwa kema, ki yi min kokari kan karatunta idan kika min wannan alfarma zan kasance me saka miki da addu'ar rahama da jin kan ubangiji har illa ma sha Allah..." Kasa rike hawayenta tayi ganin yadda Alaya ta koma jikin ummin ta rike hannunta gam tana kuka sossai, Aure yakin mata hakane amma wannan kukan na Alaya ba na auren bane kawai harda na taradaddadin yadda zata rabu da mahaifiyarta alhali an gindaya mata sharudar sake ganinta gashi ummi ba fita take ba, matan wurin dangin mijin Maami sai kananun maganganu suke wasu na taɓe baki saɓanin dangin Maami da tausayi da kuma jin kai aka raine su Dukda iyayensu suma masu arzikin ne sossai da sossai. Duk yadda Maami ta rarrashi Alaya ta kasa samun galaba a kanta, yadda ta rike ummi seda kowa yayi mamaki duk yadda akyi ta sake ta ta ƙi banda kuka babu abunda take, ummin ma sai hawaye take da kyar da sudin Goshi aka raba su ummi tayi saurin yin daki aka fita da Alaya a yadda take. Maami ta kasa yin shiru kaman yadda tayi niyya har a sadata da gidan ta ta kalli drivern tace "Ghali juya motar nan mu tafi gidana" Ƙanwarta dake gefen ta tace "Ah yaya binta gidanki kuma?" "Aisha sa hannu kiji jikin yarinyar nan, ciwon zuciya ke gareta in muka kaita Mukhtar da haukashi ya kashe wannan yarinya me zan cewa mahaifiyarta? Bana tunanin an yiwa waennan bayin Allah adalci wannan zalunci ne wallahi" Ta karashe tana share hawayen fuskanta tana kuma sake rungume Alaya da har lokacin kuka take sossai. Duk wasu kananun maganganu da aka yi tayi bata kula kowa ba kuma sun santa babu wadda ya fuskance ta yace komai har ta sada Alaya da ɗakin baccin ta ta kuma sallamesu akan sai ta shirya amaryar zata kaita da kanta. Bayan watsewar kowa ta koma ɗakin inda ta barta nan ta sameta dunkule bisa tsararriyar gadon na Maami, a natse Maami ta ƙarasa ta ɗago ta "Fatima.. Don Allah ki daena wannan kuka haka, kin san condition naki Its not good for your health kin ji?" Maamin ta faɗa tana share mata hawaye wasu sabbin na zuba tace "Maami hankalina ba zai taɓa kwanciya ba, ba zan taɓa farin ciki ba ba kuma zan taɓa daena zubar da hawaye ba matukar mahaifiyata na wanchan baƙin gidan, Maami zasu kashe min ita wallahi babu imani a zuƙatan su ko na second guda ya zanyi? Wani mataki zan bi in iya taimakonta a wannan rayuwa da na tsinci kaina? Wayyo Allah na na shiga uku!" "Baki shiga uku ba ɗiyata, umminki bazata mutu ba, abunda nake so dake shine ki fara ceton kanki da lafiyarki kan kiyi tunanin hanyar ceton umminki, babu ta yadda zaki iya yi mata komai idan har kika faɗa cikin wani hali, Fatima ina en uwanku? Ko na mahaifiyarki ko naki? Wani irin aiki ne wannan da babu encin kai a ciki?" "A yadda kika gan mu haka nima na tashi na same mu cikin wannan hali, Ummi bata magana alhali tayi magana a baya, ummi bata da dangi kaman yadda ta shaida min mahaifi na ma bashi da kowa, da ciwon zuciya aka haife ni me naci da ciwon gaske na tashi cikin tsangwama, kyara da mugunta iri iri, ummi bata taɓa bani labarin wani rayuwa nata na baya ko na mahaifi na ba, abunda dae kawai na fahimta shine me gidan na mugun jin zafina da tsana ta sbd wani abu chan da ya hadasu da mahaifi na kaman yadda yake da mugun nufi akan mahaifiyata, matar gidan ta tsani mahaifiyata fiye da kowa a duniya sbd laifin da har yau ban san menene shi ba, muna rayuwa akan wani baƙin siradi a cikin gidan yanzu ya min iyaka da gidanshi alhali na san kashe ummi na zasu yi da bauta wadda basu taɓa godiya akai ba, ummi karfinta ba kaman da ba Maami abubuwan zasu mata yawa, babu ta yadda zan iya ji daga gareta bare in san halin da take ciki, Maami taɓa zuciyata kiji ji nake kaman ze fita daga kirjina sbd azabar bugu da ciwo..." Hawaye Maami ta share tana shirin magana aka yi knocking a take ta bada izinin shigowa family doc din su ne da suka yi magana kan Shigowarta ta kuma bada umarni a chan kasa akan yana zuwa a mishi iso har ciki. Allurai ya haɗa yayi mata a take ta fara lumshe idanu kan wani baccin wahala ya sake daukar ta. "Hajiya ya kamata a kaita asibiti sbd yanayinta yana nuna tana wani stage me girma na ciwon nata kuma in tana sa damuwa a rai hakan ka iya kara shi fiye da yadda ya kamata ya tafi" "za'a yi yadda kace doc, in ta ɗan yi kwari zan nemi appointment ko a waje ne sai muje in shaa Allah" Godiya yayi kan ya fice. Ita kuwa ta shafa tulin gashin Alaya cikin tausayawa tace "zan taimakeku Fatima, zan taimaka muku iya yadda zan iya in shaa Allah" Ta faɗa hawaye na gangaro mata... Miƙewa tayi ta fito daidai lokacin da muktar ke shirin tura kofan ɗakin nata, hade rai tayi tana kare mishi kallo "lafiya?" "Ina fa lafiya Maami Meyasa kika hana a kai min matata chan gida aka kawota nan? Akan me?" "Toh Ubana ka shakeni sai kaji amsa, ɓace min a kofar daki tun muna shaida juna" Ashar yake shirin wawurowa tayi hanzarin kai hannu ta kuwa samu bakin ta Buge da karfinta, ni dae baya na matsa don na ga kokarin Maami chan fa sama take kallon muktar sbd tsawo da kuma murdewarshi don yana ɗaga karfe ba na wasa ba kuma shi ɗin dan dambe ne mafadacin gaske ne amma Maami ko a gyelenta yana shirin mata rashin kunya zata kai hannu, tana kuma saurin kwaɓarshi ne sbd gudun zunubin da ya ke tarawa kanshi yaji da iya na abubuwan da yake yi mana kar ya hada da fushin Allah akan taɓa iyaye iyayen ma uwa for that matter... Hanyar da ta nuna mishi take kuma kallonshi cikin fushi ya bi kaman zai tashi sama yana sauka yayi ɓangaren mahaifinshi da hanzari ya san shi kam ya isa da ita kuma zai kwatar mishi yanci wannan ai ba yi ba bane haka kawai yadda yaci burin wannan dare ta kama ta lalata mishi wlh ba'a isa ba, saide duk abunda ze faru ya faru har yana haki ya fara mayarwa Dad ɗin su yadda aka yi. "Wani lokaci Binta na abunda be dace ba wallahi ta bugeka akan matar da take mallakinka? Ai yanzu ko iyayen yarinyar ka fisu daraja a gaban Allah bare ita bintan, to baze yiwu ba sam, bari naje naji me take nufi? Don a saka ta a daki a kulle aka yi auren? Ina itace ta nuna bata son auren kuma yanzu don bakin ciki tasa ƴa a gaba ta kulle ta hana ka ita? Ina zuwa ko kuma wuce muje kawai.." Haka ya tasa ɗan a gaba suka yi ɓangaren Maamin. (hmmm wallahi maza mu ji tsoron Allah mu sani 'ya'yayen nan kaman amana suke a hannun mu, su ɗin kiwo ne da Allah ya bamu kuma ze tambayemu akai a ranar gobe, ba ina magana bane akan duka maza saide ina magana ne akan mazan da basu taimakawa uwa wurin tarbiyartar da yaro, iyaye mazan da suke wofintar da duk wani kokarin uwa akan ganin yaro ya zama nagari, iyaye mazan da duk abunda uwa zata yiwa yaro basu ganinshi as kauna sai mugunta alhali duk duniya babu wadda ya kaita son wannan yaro, iyaye mazan da suke gurbatawa yaransu tunani suke nuna musu babu kaunarsu a rayukan iyayensu mata alhali ba hakan bane, iyaye mazan da basa taimakawa uwa wurin tarbiyartar da yara. Wallahi mu gyara mu saka idanu akan ƴaƴanmu ko zamu samu rayuwarsu ta inganta... Single mothers Allah ya saka muku da alkhairi). *Kar ku sha'afa Al'ajabin So book 2 is not free, a kan naira 500 kachal zaki same shi immediately after an kamallah book 1, zaki iya yin payment ta nan 3118518476 First bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya ta wannan layi 09039206763* #Vote #comment                  🖤Gureenjoh🖤 AL'AJABIN SO (heart touching story) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN.                      (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* *Kowa Ya ga zabuwa..* *Diddigar ƙaya... Paid* And now.. *AL'AJABIN SO* *BOOK 1 *Page Eight* "Alhj for goodness sake kar ka sa na fara yi maka musu a gaban yarinyar da yau ne ta soma shiga cikin mu, yarinyar nan bata da lafiya kuma ciwon zuciya ke gareta idan ta mutu a yau wallahi Mukhtar bashi da asara tunda ba darajar ta ya sani ba, ni ban hana a kai mishi matarshi sbd jin daaɗi ba idan ta samu sauƙi da kaina zan sadata da ɗakinta" Maami ta faɗi hakan idanunta akan Alhj da ta janye shi zuwa ɗaya ɗakinta na saman. Dukda shi be wani ji tausayin yarinyar ba sede ya amince tunda bata da lafiya ne kuma ciwon irin ciwon da akan rasa mutum farar ɗaya ne don hakan yasa dole yayi shiru ya fito ya janyo hannun muktar suka yi ƙasa yana faɗa mishi situation ɗin cikin lallami kaman shine uban shi kuma Alhj ɗan, tana tsaye tana jin muktar da be gamsu ba yana alaƙanta hakan da son ranta ne in yayi ra'ayi sai ya kwana da mata sama da biyar a daren kuma ba abunda zai faru akan banzar talaka ana ƙona mishi rai. Duk da zafin kalaman da Maami taji hakan be sa ta barshi ya kai zuciyarta ba adu'ar shiriya ta mishi kan ta nufi ɗakinta, har asuba bata yi wani baccin kirki ba Sbd Alaya, cikin ikon Allah kuma da kanta ta tashi kiran farko tayo alwala ta zo ta fara nafila don ba'a binta sallah, da murmushi Maami ta shiga bayi tana godiya ga Allah, bayan sun yi sallah komawa Alaya tayi ta lafe sbd magungunanta da basa barinta ido biyu cikin sauƙi sam bata san ma fitan Maami ba, ba ita ta farka ba se 11 na safe. Wanka tayi ta sake mayar da kayanta ta zo ta zauna daga bakin gadon zuciyarta fal tunanin halin da umminta ke ciki lokaci lokaci ta kan share hawaye ta san ummi na chan aiki sun mata yawa ga jama'ar gidan sam basu san imani ba, Shigowar Maami ne yasa ta suluɓe ƙasa tana cewa "Ina kwana Maami?" "Lafiya klau bintie ya jikin dae?" "Bana jin komai maami". Karasawa Maami tayi ta kama hannunta ta miƙar da ita tsaye tace "kinga Ɗiyata ki daena wannan nuku nukun ki saki jikinki ki ɗauke ni tamkar umminki kinji?" Kai Alaya ta gyaɗa, Maami ta janye ta akan suje su yi breakfast suna tafiya tana kara nunnuna mata gidan tana sake jadadda mata ta saki jikinta nan ɗin kamar gidansu ne. Breakfast me rai da motsi Maami ta zuba mata itama ta zuba kaɗan sbd ta baiwa Alayar kwarin gwuiwar ci, saide inaa kaɗan taci Dukda daaɗin shi sbd tunanin ummi da yayi mata yawa ganin abincin kadai yasa ta fara tambayar kanta ko ummin ta ci? Yanzu kila tana kitchen tana wahalar dahuwar rana.. "Aji nawa kike a makaranta?" Maami ta katse mata tunanin da ta tafi, a hankali ta ajiye cokalin da dama jujjuyawa kawai take cikin abincin tace "SS3 muke First term" "Wani school ne?" Ta tambaya a take Alaya ta faɗa mata, lallai school me kyau ne. "Kina so a miki register ɗin waec a chan? Na san karshen second term dae zaku fara rubuta paper" Ɗan shiru tayi tana tuna yadda Jameelah ke tsangwamarta da friends dinta gashi babu wadda ya san an mata aure tana komawa sabon kyara ne ze tasar musu hakan yasa tace "a'a" "Ok zan bincika wani nan kusa sai a saka ki, amma wani course kike son karantawa in kin shiga jami'a?" Ɗan murmushi tayi "A da dae ina sha'awar likita saboda taimakon al'umma ta ɓangaren jinya sai kuma daga baya na zo na fara sha'awar law saboda samarwa mutane ƴancin su, matasa dayawa are physically, mentally and emotionally traumatize amma babu wadda ke iya noticing, mutum na da darajar da hatta ubangiji bai yarda ka ci mutuncinshi ba tunda da kanshi ya karrama mu, ina kuma Son business saboda ina so in yi kuɗi Maami, tunda har kuɗi ne ke sa a san da kai a kuma mutuntaka ko ba don Allah ba, ina son yin kuɗi.." Murmushi ne me kamar dariya a fuskan Maami tace "Toh Yanzu ke kam ma baki tsayar da abu daya ba, amma kuma duk abin da kika lissafa yana da kyau, wani ɓangare kike karanta secondary?" "Science" Ta bada amsa tana ɗan kallon Maami "kenan a abubuwan da kika lissafa likitanci ne kawai zaki iya yi, ki ƙara nazari da bincike duk abunda kike ra'ayi zaki yi in shaa Allah" Cikin murmushi tace "Na gode sossai Maami" Magana take shirin sake yi tana daga idanu sai idanunta suka faɗa cikin nashi, cike da tsananin tsoronshi tayi saurin sadda kai ƙasa, jan kujeran dining din yayi ya zauna "Maami good morning" "morning" Maami ta amsa mishi tana kallon yadda Alaya take ta wasa da fingers ɗin ta, cikin sanyin murya tace "Ina kwana?" "Lafiya" ya bata amsa yana ɗan jan tsaki, ai saida ya faɗa kawai Maami sbd ta kuntata mishi ne kawai tace yarinyar ba lafiya gata nan garau ɗin ta. "Muktar ka tura min kuɗi zamu je da Fatima mu haɗa mata lefe" Ta faɗa ba tare da ta kalleshi ba. Sakaka yake kallonta kan ya girgiza kai "amma ai bamu yi haka da gidansu ba Maami, ya daga zuwan yarinya zaki fara ɗaure mata gindi wurin raina ni? Me tazo dashi ita gado ko katifa? I thought wannan abu vice versa ne yi min in maka?" Da hanzari Alaya ta ɗaga kai tana kallonshi mahaifiyarshi yake magana da ita cikin kafin harshe da rashin tauna magana? Ya subhallah lallai akwai aiki me girma a gabanta innalillahi ta shiga nanatawa, Maami da ta jima tana kallonshi ta girgiza kai... "Kaje gidan naka ka gyara mata sashe allura ban amince ka saka ba, za'a kawo mata kaya saboda haka karka kuskura ko da wasa ka sake yi mata gori, kai kuma dole ne ka bada kuɗi enough a yi mata lefe" A wurin ya ɗaga waya yayi call ya bada umarnin gidan shi na jambulo a fitar da kayan part ɗaya da tsantsar mamaki Alaya ke kallonshi kallon dani kike zancen yayi mata kan yayi kwafa yayiwa Maami transfer ɗin kudi masu yawa, ta taɓe baki tace "duk sadda na shiryata zaka ganta, bintie tashi mu tafi" Kunkumi yayi tayi na wlh duk abunda Maami ke mishi akan yarinyar ze rama.. Da yammacin ranar Maami ta ja ta suka tafi kasuwa sayayya me tarin yawa suka yi, kasuwanni har uku suka je bata bar komai ba tsab ta haɗa mata lefenta kan ta saya mata wasu ready mades da kuma egyptian abayas da zata ke anfani dasu kan a yi mata dinki, daga nan suka tsaya wurin telan Maamin ta bada dinkunanta atamphopi masu tsadar gaske da kyau har goma sha biyar, se lesuna guda goma da shadda irin ta mata duk ta zaɓi irin zubin da take so guda biyar, tace sauran zata ɗinka a hankali. Lokaci lokaci Alaya ke kallon Maami tana yaba irin kirkinta ashe akwai masu irin wannan halin karamcin a masu kuɗi da suka saura a duniya? Lallai Maami mutuniyar kwarai ce Adu'a tayi ta mata a sadda suka tsaya shagon wayoyi ta zaɓa mata IPhone Xs max sai ta sayi wani tecno madaidaici take ce mata "gobe da kaina in shaa Allah zan kaiwa Umminki wannan sai ku dinga exchanging messages ko hankalinki ze kwanta" Adu'ar gamawa da duniya lafiya tayi ta mata da cikan burukanta na alkhairi. A gajiye tilis suka dawo duk kayan da ma'aikatan gidan suka kwaso ɗakin Maamin suka zube su yayinda duk suka yi alwala suka gabatar da magarib, suka dan yi karatu a tare sai bayan isha suka sauka dining. Alhaji hammad da Mukhtar na zaune suna cin abinci har ƙasa Alaya ta duƙa ta gaishe shi ya amsa ba yabo ba fallasa, ta ja kujera ta zauna tana jin idanun muktar a kanta, ita tayi serving Maami ta saka kaɗan zata juya Maami tace "Ah ina zaki daughter? Zauna nan ni fa har na gaji da faɗamiki yanzu duk daya muke we are family already" Zama tayi a kunyace ta soma ci duk ɗagowar da zata yi se ta haɗu da firgitattun Red eyes ɗin shi yana aika mata wani kallo, lokaci lokaci Maami kan yi magana da Alhj amma shi baya sa musu baki. Bayan sun tashi sama Alaya ta koma sbd gujewa irin kallon da yake mata, wayoyin su da ummi ta sa a chargy cikin murna take Allah Allah gobe yayi ko zata samu taji lafiyar ummin tata, a nan ta zauna gadinsu har Maami ta same ta ta ɗan zolaye ta kunya ya sakata Miƙewa taje ta fara shirin kwanciya bata yi ko mintuna biyar da kwanciya ba bacci me daaɗi ya ɗauke ta gabaɗaya jinta take cikin wani sabon rayuwa, sai yanzu take jin ta samu Ƴanci kamar kowa matsala ɗaya in ta tuna yake ɗaga mata hankali shine auren muktar dake kanta, da irin zaman da zasu yi sannan babban abunda ke damunta yadda baya baiwa mahaifiyarshi daraja, taya yake tunanin ganin haske a al'amuranshi ta lura babu wadda ya raina irin Maami, uwa tagari irin wannan Allah ya jarabceta da samun ɗa irin Muktar kuma kaman bata da wasu da akwai da kila ace zakka ya fita, saboda irin kyautatawar Maami garesu taji a ranta zata iya zama da muktar da zuciya ɗaya kila ta sauya shi zuwa mutumin kirki...da waennan tunannuka bacci yayi awon gaba da ita. Kaman yadda Maami tayi alkawari Washegari ta aika aka kaiwa Ummi wayar, Alaya dake ta kimtata lokaci a jikinta taji wayar ta isa hannun ummi da sauri ta rubuta text message sai ko ga reply na ummi tayi ta murna barin ma da ummin tace mata lafiyarta ƙalau kuma bata wani aikin sossai don an kawo sabbin ma'aikata girki kawai take musu, sai sannan hankalin Alaya ya kwanta ta miƙe kafa a gidan Maami ta ma manta da zancen aure in ba ta ga muktar ba, banda gaisuwa babu abunda yake hada su wani lokacin ma ko tayi niyyar sauƙa in taji muryarshi sai ta koma, sai ta tabbatar ya tafi ta fito. Satin ta biyu Maami ta kaita wani school me kyau fiye ma da ainihin school dinta aka mata registration ko da aka zo interview babu questions da bata amsa ba har Maami seda ta burgeta sbd akwai kwazo da tarin ilimi akan yarinyar, class ɗin ta aka barta bayan an bata uniform a makarantar Maami ta barta akan driver ze zo ya ɗauke ta in an tashi. Sossai take jin daaɗin makarantar sbd babu bullies ɗin ta su Meelah da kawayenta kuma kowa a makarantar harkar gabanshi kawai yake, yau juma'a da misalin karfe sha biyu na rana drivern da ya zama nata yayi parking kofar makarantar da ɗan hanzarin ta tazo ta buɗe ta shiga da sallama suka gaisa a mutunce kan suka kamo hanyar gida, a daidai parking lots yayi parking ta sauƙa tana mishi godiya tare da fara takawa don isa cikin gidan, spot car dake parke a tsakar gidan Red Color BMW a tunaninta ma ba kowa don bata ji karar injin motar ba se kawai gani tayi kofa ya buɗu, ko bata kai idanunta zuwa ga fuskar ba daga kafar ta riga ta shaida waye ne..... "Ke!" Ya faɗa a kausashe chak ta tsaya gabanta na faɗuwa tana da ilimi kuma ko makaho ya shafa ze san cewa muktar baya cikin cikakken hankalinshi. "Don kaza kazarki ba dake nake ba?" Ya antayo zagin yana kara kakkafeta da jajayen idanunshi, idanunta dake rawa ta sauke bisa tattos ɗin jikinshi Farin fatar shi tas duk ya lalata kaman akwai wani sabo ma daga wuyanshi.... "Na'am" Ta faɗa tana ɗan matsowa kaɗan a kuma tsorace "na biya sadakinki don ki zama min hoto ne? Ke wallahi tsohuwar chan tana jaza miki don sai na tabbatar na ladabtar dake bisa wannan biye mata da kike, sai kin zamto min kariya babu maganan wadda zaki iya ji idan ba na uban gidanki ba, wuce ki shiga mota mu tafi!" Ya daka mata tsawa Jikinta na tsuma tana rawar leɓe tace "Maami bata ce in tafi ba, and plz ka daure ka daena faɗin munanan kalamai akan Maami ko ba komai ta ɗauki cikinka na wata tara chur ta kuma yi nak....". "Shut up bloody fool, ke har kin isa ki gayamin abunda zan yi? U r like a servant to me, na aureki ne kawai don kyaun surarki ku kuma don kwadayi irin na talaka kun ga kuɗi kuka amince, for ur own information ko Asawanyarki bata kaini daraja ba don haka ke baiwa tace na fanshe ki kuma da kuɗi wuce mu tafi tun muna shaida juna.." Baya baya ta fara ganin yana nufo ta, kan yayi wani yunkuri ta runtumi na kare, taku biyu yayi ya..... *Kar ku sha'afa Al'ajabin So book 2 is not free, a kan naira 500 kachal zaki same shi immediately after an kamallah book 1, zaki iya yin payment ta nan 3118518476 First bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya ta wannan layi 09039206763* #Vote #comment 🖤Gureenjoh🖤 AL'AJABIN SO (heart touching story) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN.                      (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* *Kowa Ya ga zabuwa..* *Diddigar ƙaya... Paid* And now.. *AL'AJABIN SO* *BOOK 1* *Page Nine* Haki take saki tana juya bayanta ganin baya binta yasa ta dafe kirjinta, in wannan ɗan daban ya riƙe ta ai kashinta ya bushe, seda ta daidaita kanta kan ta kutsa cikin parlorn Maami ta gani zaune idanunta da hawaye, da sauri ta isa ta duƙa a gabanta kaman zata saki kuka aka ce zuciya tana son me kyautata mata jin matar take kaman Ummi tace "Maami me ya faru kike zub da hawaye?" Shiru Maami tayi, babu me fahimtar halin da take ciki se uwar da Allah ya jarrabe ta da ɗa irin Mukhtar, ace kana ji kana gani yaro ya nemi gagararka? Allah kaɗai ya san me ya je ya sha ya zo yake mata rashin kunya akan matarshi, duk zafinta akan muktar ne tana da sanyin hali da tausayi shima kuma da farko ta bi dashi da lallami da nasiha saide abun yaci tura, ganin hakan mahaifinshi ke mishi yasa ita ta karɓi ragamar zama uwa da uban saide duk a banza man kare, zafin dake kirjinta ya wuce misali bata fata ta mutu ba tare da ta ga chanzawar Mukhtar ba, tana mishi tsoron fushin ubangiji tana kwaɗaita mishi rahamarsa... "Maaami" Alaya ta kira sunan hawaye na cika idanunta. "Babu komai ɗiyata, je ki cire uniform ɗinki kizo ki ci abinci" Gudun musu da Maamin yasa ta miƙe ta tabbatar be wuce muktar bane matsalar Maami, saƙe-saƙe kawai take har ta watsa ruwa ta sauko ta ci abinci bata samu Maami ba kila tayi wurin Alhj, wayanta ta ɗauko ta fara texting ummi sun jima suna magana kan ta miƙe ta shiga kitchen, ita tayi musu girkin daren ranar sbd gujewa tunanukan Muktar da ya addabe ta ta rasa me take ji a game dashi, tsoro ne, tausayin Maami da halin da yake jefa kanshi da fushinta ne ko zeal na son ganin ta kyautatawa matar da duk duniya itace mace ta farko da ta fara kyautata musu a rayuwa? "woww daughter haka dama kika kware a girki?" Maami tayi maganan tana gyaɗa kai, murmushi me sauti kawai Alaya ke yi, Alhj ma yayi ta yabon girkin shi dae Mukhtar ci kanku be ce musu ba. Bayan gama cin abincin nasu ne Alhj ya mike yayi sama yana cewa "Hajiya in ganki mana minti biyu" Miƙewa tayi tabi bayanshi yayinda Alaya ke tattare kwanukan, tana kai na karshe zata juyo kenan taji tayi mugun karo da mutum, kafafunta suka Harɗe baya baya tayi zata faɗi yayi hanzarin riƙota, hannunshi yasa ya kama nata hannun ya matse kara ta saki tana me duƙawa kaɗan "Zafi Don Allah" "zafin dama nake so ki ji, wato ba zaki ji magana ta ba ko?" Hawaye ta fara sbd yadda yake murde hannun da tsantsar mugunta "Kayi hakuri" "ba hakuri nake son ji ba, sbd bani dashi kwata-kwata, abunda na sani shine kiyi gaggawar bin umarnina ko ki cigaba da karawa kanki laifukan da na rantse sai kin biya su ɗaya bayan daya" Idanunta a runtse hawaye wani na bin wani, ganin azabar yayi mata yawa ne yasa cikin kuka tace "Na amince wlh zan mata mag..." "MUKTAR" Maami ta katse shi tana jin kaman ta rushe da kuka ko ta rufe shi da duka ko zata ji saukin abunda take ji akan shi. "Ga nan irin abunda nake tsoron yasa na ki baka ita, amma zan kai maka ita cikin wani sati sai ka shirya ko ka riƙe ta saboda Allahn da ya halicce mu ko kuma ka zalunceta, Allah baya bacci kuma baya barin zalunci kuma ina faɗa maka kaji tsoron Adu'ar wadda aka zalunta don bashi da shamaki, fice ka bar min gida!" Ta karashe da karfi tana nuna mishi kofa. Tsayawa yayi yana kallonta sama da mintuna biyu kan ya wuce yana gunguni, da sauri ta ƙaraso wurin Alayar tana rike hannun tace "Sannu daughter, ya ji miki ciwo ko?" Girgiza kai tayi tana me Miƙewa tace bari ta shiga ɗaki. Da tunanin tarewar ta cinye satin ko fahimtar abin da ake yi a class bata yi tsabar tsoro, amma ya zata yi abu sede in ba'a sa mishi rana ba sai ga ranar ya zo, sisters ɗin ta guda biyu ta kira akan su rakata gidan ta don already an gama haɗa mata komai da komai har akwatunan an riga da an kai chan, tana kuka tana komai aka kaita gidan muktar a chan suka barta bayan doguwar nasiha. Ta jima zaune bisa gadon har ta gaji ta kwanta bacci ya fara fusgarta taji ana bugu kaman hauka, a tsorace ta tashi tsaye tana zare idanu ganin tsayuwar ba zai mata ba gashi sai karuwa bugun ke yi yasa da sauri ta fita, duba agogon parlorn tayi karfe ɗaya saura mintuna. "Waye ne?" Ta faɗa muryarta na rawa "Wayewa! Ke dallah ki buɗewa mutane kofa in zaki buɗe.." Muryar mace taji, a tsorace ta buɗe yarinyar na sarkafe da hannunta a kwankwason muktar ɗayan hannunshi na zagaye da kafaɗarta, ko be ɗago ba ka san ba karamin buguwa yayi ba, da sauri Alaya ta koma baya tana kama bakin ta da hannayenta, kukan sai ya ƙi zuwa sai idanu take bin su dashi har yarinyar ta shigo dashi tana karewa gidan kallo tana taɓe baki. "Ke wato kin raina mutane ko? Waye ya baki iz....nin rrrrufe kofar nannn" Cikin tsantsar maye yake maganar yana nuna ta da yatsa. Bata ce musu komai ba.. "Kai muky wace irin dakikiya ka auro ne? Kina kallon mu ba zaki kama shi ki kai shi ɗaki ba?" A tsorace taje ta fara kokarin riƙe shi yarinyar tayi tsaki tace "Muky am sleepy, good night" A maimakon Alaya taga ta fice sai gani tayi tayi wani ɓari na gidan wanda ba inda Alayar ta fito ba, tana tunanin tana layi sbd yadda yake sakar mata jiki shima kuma Layin ne yake yi, a haka suka nufi ɗakinta hawaye na wanke mata fuska warin giyar kamar zai kashe ta, galau galau suka yi kaman zasu faɗi kokarin tare shi take sai kawai taji amai a jikinta, wani irin tashin zuciya ne ya kamata, hawaye wani na bin wani haka ta jefa shi kan gadon bayan ya gama amaye mata jiki, bata iya ganin amai ba hakan seda yayi sanadiyar nata aman babu komai cikinta, tayi ta wahala a bayin kan ta fito tana kau da ido ta samu ta kwashe. Kayanta ta cire tayi wanka tana fitowa ta ganshi zaune yana kallonta. "Ke zo nan!" Har lokacin mayen be sake shi ba "na'amm" Ta ƙasan jajayen idanunshi yake kare mata kallo kan yace "kika bari na maimaita sai na lahira ya fiki jin daaɗi" Cike da tsoro take takowa ko kan ta ƙaraso ya fusgota kaman wata ƴar tsana haka ta faɗa kirjin shi, toshe hancin ta take sbd gudun sake amai warin giyar gigitata yake ga tsananin tsoron abunda zai iya mata ko kan ta gama tunani taji hannunshi ya fara yawo a jikinta, idanunta ta zazzaro cikin sautin kuka tace "Me...menene Ya muktar?" "Hakkina da kuka hanani zan karɓa" Girgiza kai take da karfi, tana kokarin Miƙewa ya matse ta yana cusa fuskanshi wuyanta, gigitaccen kuka ta saki ta fara cewa "A'a don Allah, Don darajar Allah ba yau ba, ba cikin wannan hali ba! Karka zaɓi tarayya dani da kazantar abubuwa dayawa a jikinka... Ya....ya Mukhtar aure fa muka y..." Bakinta ya rufe da nashi ta datse nata tana kakari sbd yadda abubuwan maye ke tashi a cikin bakin shi, kokarin kwatar kanta take Dukda ta san karfi ba ɗaya ba shima kuwa nuna mata ya fara yi cewa karfi ba ɗaya ba, dambe ne ya kaure a tsakaninsu, duk kokarin da tayi wurin ganin be samu abunda yake so ba ta kasa dakatar dashi, tayi kuka kaman zata cire ranta ta jefar, kirjinta yayi matukar nauyi, numfashi yayi mata wahalar shaƙa, ji tayi inama ta mutu a lokacin, be saurara mata ba seda ya samu natsuwa ya zube a kanta ya fara baccin hauka, nauyinshi ya kara mata nauyin kirjin da take ji, idanunta na kallon seiling yayin da hawaye ke ganganrawa gefen fuskanta wani na bin wani ta fara cewa cikin jiggata "Ya Allah kaine Allah, Allah kai kaɗai ka san dalilin hadani da Mukhtar a matsayin miji, Allah kana gani kuma na san kana ji na, ka bani haƙuri da juriya a kanshi ya Allah, idan kuma mutuwata ce hutu daga wannan radadin zuciyar ya Allah ka ɗauki raina a yanzu ya rabbi, idan kuma a rubuce yake a cikin kaddarata Ya Allah ka shiryar dashi ka kuma bani ikon yi mishi biyayya...." Kuka me karfi ta fashe dashi ta saka ɗan karfin da ya rage mata ta fara kokarin ture shi, saide ta kasa duk yadda ta so tashi ta kasa, kaman yadda taga rana haka taga dare tayi kuka har ta rasa hawaye, jikinta ya dauki zafi, numfashinta ya fara nisa sbd tsananin ciwon da zuciyarta ya ɗauka, cikin tsananin rauni cike da ban tausayi take cewa chan ƙasa ƙasa "Ummina ashe ba zan sake ganinki ba? Ashe ba zan taɓa jin muryarki a zahiri ba? Ashe ba zamu sake saduwa da ke ba! Ki yafemin in n...na taɓa saɓa miki, ummi ki yi min Adu'a zan tafi in samu Abbana....." Ta karashe cikin jan wani wahalalliyar numfashi. Mukhtar kuwa Ba shi ya farka ba seda gari yayi haske tarr, hantsilawa yayi gefen ta yana buɗe rinannun idanunshi ya zuba mata, ko motsi bata yi ba, fuskanta ya kurawa ido yayi wani haske yayi fayau, da sauri ya miƙe zaune ya ɗaga hannunta se yaga ya koma ya faɗi yaraf, kanshi ya ɗaura a kirjinta babu bugun zuciya..bai san sadda ya dirko daga gadon ba ya ɗauki boxers ɗin shi ya saka babu abunda yake tsoro se Maami, ya san idan har ya kashe yarinyar nan ko da me yake takama sai tayi shari'a dashi... Da gudu ya kaita mota bayan ya sa mata riga wacce be tantance bata da tsawo ba seda suka shiga asibiti, a asibitin ma da gudu aka karɓeta zuwa emergency, likitan da ya iso cikin hanzari ya fara examining ɗin ta, girgiza kai yayi, yana saurin riƙo hannunta ya fara jin pulse ɗin ta.... "YA RABB I'M AFRAID WE LOST HER..." Ya furta yana runtse idanunsa. *Kar ku sha'afa Al'ajabin So book 2 is not free, a kan naira 500 kachal zaki same shi immediately after an kamallah book 1, zaki iya yin payment ta nan 3118518476 First bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya ta wannan layi 09039206763* #Vote #comment 🖤Gureenjoh🖤 AL'AJABIN SO (heart touching story) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN.                      (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* *Kowa Ya ga zabuwa..* *Diddigar ƙaya... Paid* And now.. *AL'AJABIN SO* *BOOK 1* *Page Ten* "Dr Abdul what is the situation?" Wani Babban likita ya ƙaraso yana yiwa wannan doctor da ya runtse idanu tambayar sanin cewa shi wannan intern ne kuma be gama gogewa a aikin ba. Kallon Mukhtar dake tsaye ya zurawa gangar jikin Alayah idanu yayi yana cewa "wannan fa? What is he doing here?" Muktar da duk tunanin shi na ga Irin badakalar da zasu yi da Maami, sai kuma tunanin irin garɗin ni'imar da ya kwasa daga Alayah ace har ta mutu? Sau ɗaya kawai fa yayi?.. Idanunsa ya maida kan karamin likitar dake cewa babban "her heart stopped beating doc, babu wani pulse dake harbawa a jikinta" Maida kallonshi kan Mukhtar babban likitan yayi yace "Me ya sameta? Me ke damunta?" "blood?" Ya faɗa ba tare da ya jira amsar Mukhtar da har lokacin yake tsaye ba, kallon kallo suka yi suka sake kallon muktar zuciyoyinsu na bijiro musu da abubuwa daban daban.. "Dr is she alive or dead?" Yayi tambayar yana kallonta still. "Meke damunta? Did you raped her? Gsky ba zamu iya taɓa ta ba sai da Police, this case is serious" Tsawa ya daka wa doctorn "she's my fucking wife, do something if she's still alive tana da congenital heart defect..! Do something before Its too late" Jin hakan yasa doc saurin bawa nurses dake tsaye cirko cirko umarni, a take suka turo automatic external difibrillator, aka zuba mishi cream din ya dirza kan ya ɗaura mata a kirji, fusga tayi daga ita har gadon suka sake komawa yaraf, cikin gogewa a aiki ya sake murzawa ya danna mata ta kara jan numfashi tayi sama ta dawo kasa, a na huɗu ne ta ja wani dogon numfashi wadda ya dawo mata da numfashinta gabaɗaya, taimakon gaggawa suka fara bata yana kallon nurses biyu yace "We really need Dr Abdulrahman and Dr Eshrat here Its urgent!" Da gudu suka fita, shi kuma ya cigaba da abin da yake. Kaman mintuna goma sai ga wasu doctors guda biyu nurses din na biye dasu, rufuwa suka yi a kanta suka fara bata taimako barin ma Abdulrahman da ya kasance kwararren likitan zuciya, seda ta daidaita kan Eshrat dake gynae ta duba jikinta da sauri ta runtse idanu tana me Miƙewa tsaye, idanunta ta maida kan Muktar dake tsaye ya zura musu idanu bazaka tantance halin da yake ciki ba, a ranta ta raya dole hakan ta kasance daga kallo daya da ta mishi ta san yana apawa, ga ingarman jikinshi da ya watsawa tattoos na ban mamaki, cinyoyinshi dake waje sbd wandon jikinshi ƙarami ne a mummurɗe. "She needs stitches” ta faɗa tana kallon likitocin, Abdulrahman da ya gama daidaita mata bugun zuciya da taimakon Allah yace "She also need an urgent heart surgery, the heart is so weak and fragile" "yanzu da wanne za'a fara?" Likitan farko ya faɗa cikin tausayinta tana kwance banda oxygen dake taimakonta da numfashi da zaka iya cewa gawa ce kai tsaye in ka kalleta. "Dr Eshrat yi aikinki, before then relatives ɗin ta su yi duk wani abu da ya kamata har da blood da komai we will prepare for the surgery" Yana kai nan ya fice. Juyawa Drn farkon yayi wadda suke kira da Dr Ahmad ya kalli Mukhtar yace su je waje, ficewa suka yi zuwa office nashi, jallabiyarshi ya ɗauka ya miƙawa muktar wadda sabo ne tsaraba ce ma aka kawo mai sai ya mance a office ɗin, da wani irin kallo muktar ke bin jallabiyar shi fa ba sa irin abubuwan yake ba. "Babu daaɗi kana yawo a kan patients haka, you need to wear this ka zauna in maka bayani" Karɓa yayi ya bare a ledar ya saka, coffee Brown ce me sulɓi, wani irin amsarshi yayi shi ko se taɓe baki yake yana tsaki ƙadan kaɗan. Bayani likitan ya fara mishi sai ya nuna idan kudi suke bukata ko nawa ne ze iya bayarwa ayi komai, tsoronshi Allah tsoronshi Maami kuma baya so yarinyar ta mutu don yana da buruka a kanta, yana so ya nunawa abokanshi daban daban cewa ya kere sa'a, yana kuma kwadayin sake ɗanɗanata. Wani paper Dr Adam ya mika mishi bayan dogon typing, Miƙewa yayi ya fice zuwa reception anan ya biya duk abunda ake bukata, ko jinin ma seda wata nurse tace ko za'a gwada nashi yace a'a a saya a blood bank, bayan ya tabbatar babu wani abu ya fice abin shi. Gida ya dawo yayi wanka ya sa kananun kayanshi as usual wando baya kaiwa ƙasa in ko ya kai to irin wasu mahaukatan crazy jeans ne da suke nan kaman palazo, da karamar riga marar hannu, daga nan ya leka Rita buduruwarshi bata nan ya tabbatar tana club don haka chan ya wuce, hayaniyar ganinshi ta hautsina club ɗin a take ya fara rabar da kyaututtukan giya sai rawa en mata suke yana shafasu cikin kwarewa da barikanci. A asibiti kuwa aiki aka mata dukda anasthesia da take kai da kuma rashin hayyaci daga ka kalli fuskanta zaka san tana jin zafin stitches ɗin har aka gama, aka fara shirya batun surgery babu kowa nata aka shiga da ita theater, seda suka shafe sama da awanni bakwai kan suka fito, Alhamdulillah aiki yayi Kyau atleast zata ji saukin ciwonta ba kaman baya ba Dukda ba warkewa gabaɗaya tayi ba, abun mamaki har lokacin mijin be dawo ba kuma babu wadda yazo a family. Aminity da ya bada umarni after the surgery nan suke so aka turata babu abunda take sai baccin wahala da gajiya, wasa wasa har dare sede nurses su zo su duba ta su tafi haka ta kwana be dawo ba, Washegari da misalin karfe goma na safe ta fara buɗe idanunta cike da kokonton kasancewar ta a duniya har a lokacin, ɗakin take karewa kallo a hankali hankali se ta fahimci asibiti ne nan ɗin, ga wasu na'urori jikinta, lumshe idanunta da suka faɗa sossai tayi ta sake buɗewa daidai lokacin wata nurse ta shigo ganinta ido biyu yasa ta koma ta kira Dr. Checkup suka yi mata sossai kan suka rage na'urorin jikinta, Dr. Eshrat tace "Fatima..." Kaman yadda ta gani a rubuce a jikin file nata, da idanu Alaya ta bita. "Waye ne ya kawo ki asibiti? Ina nufin me matsayinsa a wurinki?" Tayi tambayar ne sbd su tabbatar da zancen Mukhtar kar karya ce ya musu gashi har yanzu yaki dawowa wani miji ne ze bar macen dake sharafan mutuwa ta yini ta kwana ta kuma hantse, har a mata surgry me hatsari irin na zuciya be dawo ba kuma ba aike? Ta san mutum na karshe da ta kasance tare dashi Mukhtar ne, runtse idanunta tayi da karfi tana jin kuka na son zuwar mata tuna irin azabar da tasha a daren, a hankali cikin rawar murya tace "mi..jinaa" Ajiyar zuciya suka sauke me karfi, Dr Abdulrahman yace "kina da iyaye a raye ko wasu Ƴan uwa?" Cikin rawar murya ta sake cewa a raunace "Ina da mahaifiya amma ba zan iya gayamata wannan hali da nake ciki ba, ku kira min mahaifiyar mijina" Da mamaki suke kallonta, taya mahaifiyar mijinta zata iya taimakonta alhali ɗan ta ne ke da kaso mafi girma cikin abunda ya faru da ita? Dr Ahmad ne ya karɓi Layin Allah ya sa ma ta riƙe sbd numbern special number ce, kira yayi cikin hikima ya sanar da ita komai nan take cikin tashin hankali tace gata nan zuwa. Ba'a yi mintuna Talatin ba sai ga Maami, hawaye tayi ta zubarwa na tausayin Alayah wadda seda ta saka Alayar kuka, ƙanwarta ta kira tasa ta dafa mata abinci irin na marar lafiya ta kawo mata yanzu, Alhj hammad ta kira ta sanar dashi halin da ake ciki, sam ta ƙi ambaton sunan muktar sbd gudun mummunar kalma akan shi, iyayenmu mata kenan(ki kasance me gudun mummunar kalami akan yaron ki musamman idan ya kuntata miki sbd duk maganar da zaki yi a lokacin walau sharri walau alkhairi Allah na iya amsawa a take). Har misalin sha ɗaya da wani abu sistern ta ta zo da abincin, da taimakon Maami tayi brush ta taimaka mata ta fara bata kakkauran shayin kan taci dankalin turawa da aka sarrafa shi cikin kayan ciki(offals) kaɗan, magunguna nurses suka zo suka bata, da wasu Iv injections aka sake ɗaura mata drip, wayan Maami ne yayi kira a hankali ta duba sunan se ta lumshe idanu kana ta sake buɗewa ta miƙe ta fice. Sama da kusan mintuna Talatin ta dawo, bayanta Alhaji hammad ne, shi karan kanshi be ji daaɗin abunda Muktar yayi ba, barin ma watsar da ita a asibitin da yayi yanzu da bata rike Layin Maami ba fa? Sede fa Dukda haka ba wai ze mishi faɗa bane ko ya nuna mishi rashin kyautawarshi tana bacci don haka be zauna ba ya fice, a harabar asibitin ya tsaya ya kira Layin muktar, dagawa yayi cikin alamun baya ma cikin natsuwar shi. "Kai kuma haka ake yi? Toh wlh ka tanadi abunda zaka kare kanka dashi a wurin maaminku ni kam ba ruwana" A ɓangaren Mukhtar wara Red eyes ɗin shi yayi yace "What? Maami tana asibitin? Ayyaa Abba duk bala'i karka bari ta rabani da yarinyar ba zan iya kyaleta ba" "karka damu ai tunda kaine ke da igiyar aure a hannunka zancen maaminku ta raba ku be taso ba, amma fa ranta ya ɓaci kuma ta zub da hawaye sossai" Cikin rashin nuna damuwa da hawayen mahaifiyar tashi yace. "Maami kuma hawaye na mata karanci ne Abba? Bari dae ina wani abu zan shiga asibitin zuwa anjima, duk bala'i babu zancen rabani da Fatima daga Asibiti kuma se gidana" Alhj hammad na gyara zamanshi yana kallon gefen titi sbd driver dake ja a natse yayi murmushi ya katse wayar, Abban Meelah ya kira ya sanar dashi an yiwa Alayah aikin zuciya sede be wani yi Adu'a ko nuna damuwa akan ciwon ba, kuma yace ba ze iya gayawa mamarta ba sbd baya so hankalinta ya tashi, sallama suka yi Alhj hammad na tayiwa Alhj Alhassan kirari. Mukhtar be tashi shiga asibitin ba sai dare, Maami ta tafi sai Aunty rukayya da me aikinta da zata kwana asibitin, an ɗan ɗaga gadon Alayah na kwance a kishingiɗe idanunta a lumshe amma ba bacci take ba, tana masifar kewar umminta gashi ko sanin halin da take ciki ummin bata yi ba, wayanta na chan gida bare tayi mata message ko bata faɗa mata ba ta ji lafiyarta, kai tsaye ya shigo ɗakin ba tare da ya damu da sallama ba tunda yayi knock. "Barka da dare Aunt" Ya faɗa idanunshi na kan Alayah da takara runtse idanu gabanta na tsananta faɗuwa har jikinta na ɗaukan rawa. Aunty rukayya dake ta kallonshi ta kasa cewa komai, kafada ya ɗaga yaje ya tsaya gaban gadon yana kallonta, sarai ya fahimci ba bacci take ba baki ya sake taɓewa, abunda ya hana shi zuwa asibitin kenan don be san uban da zs tsinana mata ba tana wannan abu kaman taga dodo, tsaki yaja ya juya ya fice abunshi a cewar shi yana da abin yi. Haka ta shafe kwanaki goma curr a asibitin duka duka zuwanshi biyu shima se chan dare lokacin me aikin dake kwana da ita ce kawai, Maami tayi kokari sossai wurin ɗawainiya da ita hakan yasa dole ta koyawa kanta shanye damuwarta saboda damuwar matar, fargabarta ɗaya yadda zata koma gidan muktar, zata iya kuwa? To in bata koma ba ina zata je ga Abunda Abban Jameelah ya faɗa mata, sannan kuma bata Yiwa Maami kara ba Dukda har lokacin Maamin bata ce mata komai akan abunda ya farun ba. Yau da take cika kwanaki goma sha biyu muktar ya zo da misalin karfe 12 na dare kai tsaye office na Dr in charge ya wuce "Ina so ka bani takardar sallamar matata" "wani irin sallama by this hour? Kuma ai tana da sauran medication da checkups" "Yau bazata ƙarasa kwana a asibitin nan ba, duk kuma abunda ya saura ko ma menene zata zo daga baya" Ganin fa baya ma cikakken hankalinshi kuma ze iya hautsina musu natsuwa anymoment sbd yanayin shi yasa babu yadda likitan ya iya duk yadda ya nuna mishi ya barta sai ko safiya ce ya ƙi haka ya bashi sallamar. Tana kwance bacci ya fara ɗaukar ta bayan doguwar hira da idanunta suke yanzu kawai taji Shigowar mutum, da farko ma ta zata nurses ne sai taji muryarshi yana ce mata "ke tashi mu tafi" Mummunan faɗuwa gabanta yayi, taji gabaɗaya numfashi na shirin barin jikinta, ko kwakwaran motsi bata iya yi ba bare ta buɗe idanunta har ta fahimci shin shi ɗin ne ko ba shi bane, kuma da ita yake yi ko da wata.... "Kika sake Kika bari na maimaita kaina wallahi sai na lahira ya fiki jin daaɗi.." *Kar ku sha'afa Al'ajabin So book 2 is not free, a kan naira 500 kachal zaki same shi immediately after an kamallah book 1, zaki iya yin payment ta nan 3118518476 First bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya ta wannan layi 09039206763* #Vote #comment 🖤Gureenjoh🖤 AL'AJABIN SO (heart touching story) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN.                      (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* *Kowa Ya ga zabuwa..* *Diddigar ƙaya... Paid* *Rubutu a kan ruwa... Paid* And now.. *AL'AJABIN SO* *BOOK 1* *Page Eleven* A hankali ta buɗe idanunta hawaye na gangarowa tace "Ya..Muktar ba zamu bari da sa...fe in Maami ta z..." Hannunta da ya fisgo ne ya yanke maganan, ta sauko ta sa takalami cikin tsananin tsoronshi, jan hannunta kawai ya dinga yi har motanshi ya buɗe ya jefata ya zagaye ya shiga, ya ja suka bar wurin da mugun gudu, har wani jiri da amai take ji sbd gudun da yake yi bata taɓa fuskantar irin shi da ita a cikin mota ba, a harabar wani Hotel ya tsaya chan wajen garin ya kife kanshi a jikin steering sbd baccin dake son kwashe shi... "Ya muktar..! Ya muktar..!!" Take kiran sunan a tsorace tana ɗan kalle kalle sai kuma ta kai hannu ta tattaɓa shi ko motsi be yi ba, hawayen da dama basu daena zuba bane suka ƙaru "na shiga uku na ni Fatima" Ta faɗa cikin karaya da tsantsar damuwa. Wani tunani ne ya faɗo mata, tayi saurin sa hannu ta murda handle ɗin sede motar a rufe, da sauri ta sa hannu cikin sanɗa ta duba wayanshi ta taɓa screen ɗin ba password, hannu ta kai jikin kofanshi ta buɗe motar daga madannin wurin, jikinta na rawa kaman wacce aka sato ta buɗe ɓangaren ta ta sa kafafunta waje hannunta dake rawa na dialing Layin Maami, kaman an tsikareshi ya farka wani irin fusgo hannunta yayi ta dawo da karfi har tana buguwa dashi ya tsinka mata mari yana kashe wayan da har ya soma ringing.. Kuncinta ta dafe tana kuka "Zan ɓaɓɓalla ki in baki rufe min baki ba... Wuce mu je" Ya fito ya zagaya ya fusgo hannunta suka yi ciki. Key ya karɓa alamar dae regular customer ne suka yi ciki, tana kuka ya cillar da ita a tsakiyar ɗakin "Meyasa kake min haka? Yaya Mukhtar kaji tausayi na mana... Am not a slav..." "Will you shut up! In ji wa yace u r not my slave? Ko baki san duk mace baiwa bace a gidan miji? Oya come and remove this clothes for me zan yi wanka" Miƙewa tayi gudun kar ya kara taɓa lafiyarta taje jikinta na rawa ta cire mishi, hannunta ya ja suka yi toilet wankan ma ita ya saka tana kuka ta mishi, yace tayi nata ta same shi yanzu. Haka tayi don miji irin Muktar ta fahimci in tace zata ke musu dashi watarana kakkarya ta ze umminta ce kuma da asara. A daren ma be barta ba ta sha wahala kwarai a wurinshi, haka ya zube ya cigaba da bacci ta miƙe da kyar ta shiga bayi ta gasa kanta da ruwan zafi, ta fito da alwala, akan sallaya ta tsaya tana sallah tana kuka, anya suna da rabon farin ciki? Sai kuma ta tuna maganan umminta "Fatima tun da nayi sallama da ƙasata na shigo wannan na san nayi sallama da farin cikin rayuwa, na fuskanci kalubale iri iri da damuwa kala daban daban kan Allah ya haɗa ni da mahaifinki ya maida ni tamkar sarauniya ya bani duk wani farin ciki da na rasa a baya amma shima Allah be bar min shi ba, tafiyar shi ga rabbissamawati ya sarar dani, na ɗauka nima zan bishi a kowani lokaci amma tunda na tsallake baƙar wahalar da na sha daga rasuwarshi zuwa haihuwar ki na sa a raina cewa komai ze zo ya zama tarihi, iko na rabbi ne kawai dawwamamme, na sa a raina zan raineki kila sirrin farin cikina na gareki, sai kuma gashi yadda kema Allah yayi dake. Dukda haka ban sare ba, kema ina me karfafamiki gwiwa da kwantar miki da hankali a kan cewa in shaa Allahu zaki wayi gari kiga duk wannan sun wuce, imani da yaƙini akan ubangiji yana riskar da bayi zuwa ga magantuwar matsalolinsu, wallahil azeem ubangijinmu na sane da lamuranmu kuma ina da tabbacin wata rana ze fidda mu daga cikin wannan jarabawa, ko ban riski lokacin ba in shaa Allahu wata rana zaki yi farin ciki, zaki yi murna zaki tuna kuma da cewa na faɗa miki hakan" Hawayenta ta share ta zurawa muktar ido, kila watarana shine ze zama farin cikinta, kila kuma karshen zaman su na iya zuwa ko kusa ko nesa, amma ka fin nan tayi alkawarin yunkuri wurin chanza shi, zata kasance me yi mishi Adu'a a ko wani motsinta zata taya mahaifiyarshi yakin mai dashi mutumin kirki da yardar Allah ko da kuwa ita baza ta samu ribar komai ba. Anan kan sallayan tayi bacci da asuba ma jin mutum kawai tayi ya ɗauke ta zuwa gado, bata mishi tirjiya ba ta hakura saide fuskanta be huta da ruwan hawaye ba don ba daaɗin abun take ji ba banda azabar ciwo, seda ta sake wanka na ruwan zafi sossai tayi na tsarki ta fito tayi sallah, yana kwance yana bacci, a hankali ta matsa kusa dashi ta sa hannu ta na ɗan bubbuga kafafunshi "ya Mukhtar! Ya muktar ka tashi kayi sallah don Allah, lokacin sallah na wucewa" Ko motsi be yi ba, da ta matsa mishi ya ja dogon tsaki tare da kaiwa hannunta harbi da kafa da sauri ta ja baya ya samu iska, tagumi ta zuba tana kallonshi har bata san sadda bacci ya kwashe ta a wurin ba. Sai misalin karfe goma ta tashi, yunwa ne ke dawainiya da ita kuma har lokacin bacci muktar ke yi, idanu ta zuba mishi tana aikin kallo, da zai shiryu muktar ba karamin kyau yake dashi ba, tana nan tana kallonshi tana sake-sake, ya buɗe idanu. "Wani maitar ne kike yi da zaki tasani a gaba kina kallo haka?" "Ba komai, ina jin yunwa ne" "Ni zaki cinye kenan sai ki koshi?" Da sauri ta girgiza kai, tsaki ya ja kan ya sauka seda ya tsaya wurin landline yayi call kan ya shige bayin, tana nan zaune har ya fito yayi wanka sede ya maida kayanshi ne don shima babu komai nashi anan ɗin, tsayawa yayi da niyyar sallah kaman kar tace komai sbd tsoron shi sai kuma tace "Ya Mukhtar namiji fa daga cibiyar shi zuwa guiwowinshine al'auranshi, Kaga zaka yi sallah kuma wandon be kai guiwa ba be kamata ba" Ta faɗa a tsorace "karki karɓa in nayi" ya faɗa yana jan tsaki tare da tada Sallar shi ita dae ta san sallahn nan kam se a hankali karfe sha ɗaya sallahn asuba sannan da gajeren wando. Knocking aka yi ta miƙe ta buɗe, tray ne me ɗauke da abinci kala uku da ruwa da wani energy drink, karɓa tayi ta zo ta ajiye ta zauna jiranshi har ya idar ya juyo. "Ɗauki abin da zaki iya ci" Ya faɗa ba tare da ya kalleta ba. Shinkafa jollof ta ɗauka da ruwa, ya ja sauran, tana ci tana satan kallonshi ga mamakin ta ya cinye duka abincin trayn nan bata ma yi rabin nata ba, energy drink dinshi yake sha sai wayanshi ya fara ringing don yanzu ya kunnata, dubawa yayi ganin Maami yasa ya ƙi dagawa kiran duniya ta mishi ya ƙi ɗauka, chan kiran Alhajinsu ya shigo mishi kaman kar ya ɗauka ba sai ya ɗaga. "Muktar ina ka kai ƴar mutane Maaminka ta kasa natsuwa? Kana so sai ka tayar mata da hawan jini ko?" "Dad naga dae matata ce, me nata?" "Ka amsa mini kuna ina? Taje gidan ku bakwa nan" "Hotel" Ya faɗa yana haɗe rai. Ita dae tausayin Maami ne ya rufe ta ta san duk don ita ne hankalin Maamin yake a tashe, a hankali tace "ya Mukhtar ka bani Maamin zan yi magana da ita don Allah" Harara ya zabga mata kan yacewa mahaifinshi da ya gama ce mishi su dawo yanzu "gaskiya ba zan dawo ta rabani da matata ba, ni ban rabata da mijinta ba haka kawai" "Don Allah yaya Mukhtar" Wayan ya jefa mata har yana dukan kirjinta ta dauka tana gaida Alhajin cikin girmamawa ya amsa yana tambayar lafiyanta tace da sauƙi Maamin na kusa? muryar Maamin ta ji tana cewa "Fatima? Kina lafiya kam?" "Lafiya ta ƙalau Maami, eyaa Maami ki mana alfarma ki kwantar da hankalinki kinji don Allah, in sha Allah babu abunda zai faru" Ta faɗa a karye cikin son karfafawa Maamin gwiwa, Maamin da taji hawaye na son zuba mata ne tace "Fatima ki yafe mana mun kuntata miki rayuwa" Girgiza kai tayi tana share hawayen da ya zuba mata "ko ɗaya Maami idan da ba don auren ba ai da ban sanki ba, amma yanzu na sameki bayan Ummina babu abin da ya kai hakan farin ciki a gare ni" "Ki bashi wayan" Maami ta faɗa, miƙa mishi ta yi. Karɓa yayi yana kau da kai daga kallonta yana taɓe baki "Ina kwana?" "Baka damu da kwana na ba ai muktar da ka damu da ba haka ba, ka ɗauki yarinyar nan ka maida ta gidanta ka bar Hotel da ita, sannan ka tabbatar ta cigaba da zuwa makarantar ta ranar Litinin" Tana kai nan ta kashe wayan, hawayenta ta share Alhj dake tsaye yace "menene kuma ne Maamin su? Ina dae yarinyar nan tace miki babu komai ki rabu da ita da mijinta mana" Cikin takaici ta kalle shi tace "Zurfin tunani da tarin tarbiyar da yarinyar nan take dashi she's too good for muktar wallahi" Tana kai nan ta miƙe ta bar mishi ɗakin. Su kuwa bayan ya ajiye wayan ya taɓe baki yace "Maami matsala" "Subhallah" Ta ambata chan ƙasa, ba don tana tsoron yin magana ya zama laifi ba da tace yayi saurin tuba da wannan kalma da ya je fi mahaifiyarshi dashi in har yana son rabauta duniya da lahira iyaye ba abin wasa bane amma inaa. "Ke! Tashi mu tafi" Da sauri ta miƙe tabi bayanshi, a cikin harabar gidansu yayi parking, ajiyar zuciya me karfi ta sauke ko ba komai zata je ta samu tayi magana da Mahaifiyarta, bata jirashi ba tayi ciki zuwa ɗakinta ta ɗauko wayanta ta fara turawa ummi text message. "Alaya ina kika shiga kwana biyu nayi sako shiru babu amsa? Kina lafiya dae ko? Ko ciwonki ne ya tashi? Ina ma ina da bakin kiranki in ji muryarki don tabbatar da lafiyanki... Don Allah kar ki min karya baki da lafiya ko?" Kuka ta fashe dashi a fili tace "Ummi bani da lafiya, ummi bana son wannan aure bana son shi, mugu ne, ummi marar tsoron Allah ne, bashi da ibada be san menene addininshi ba, ummi abubuwan da nake son faɗa miki kenan amma ba zan iya ba..." Typing tayi "na ɗan yi rashin lafiya amma da sauki Maami ta kula da komai yadda ya kamata" "Subhallah ya jikin? Allah ya sakawa Maami da alkhairi" "Alhamdulillah ummi babu komai yanzu, Ameen thumma Ameen kefa ummi? Babu wani damuwa? Su Hajiya Zeenat basa takuraki? Aiki be miki yawa ba ummi?" "Babu wani matsala Alayah, Allah ya baki lafiya" Tattaunawa kaɗan suka kara taji an turo kofan, da sauri ta ɗaga kai ta kalleshi.. "Ina da baƙi da dare ki shiga kitchen ki shirya musu abinci" A hankali tace "Toh" Har ya juya ya ce "Ki tabbatar mutane akallah ashirin zasu ci su koshi" Yana kai nan ya fice, bata kawo komai ba bayan tayi la'asar ta shiga kitchen dinta Allah ya sa tana jin karfin jikin nata sossai Alhamdulillah, sossai ta zage tayi girkin har kala biyu jollof nd fried Rice pepper chicken sai ta ɗan yi snacks ta haɗa fruit drinks masu daaɗi, dab Magrib ta fito daga kitchen din wanka ta sake da alwala ta zo tayi sallah, ta jima tana karatun alqur'ani da rokar wa kanta mafita a wurin rabbisamawati har aka yi isha ta tashi ta gabatar kaman wasa tana zaune nan ta soma jin hayaniya a ranta take ayyana baƙin sun zo kenan. Bata gama nazari ba ya shigo "Tashi ki shirya jarrey baƙi na na jira a yi serving ɗin su" A hankali tace "Amma Ya muktar abincin ai yana dining naga be kamata sai na fita na sassa......" "Kina so in wanka miki mari?" Shiru tayi ta miƙe shine ya shiga drawer ɗinta ya duba ya zaɓo wani pencil gown ya wulla mata, seda ta gama kallon kayan kan ta saka a hankali babu shape na jikinta da be nuna ba. Hijab ta fara dubawa yayinda shi kuma yake sake da baki yana kallonta don ba karamin gigita shi tayi ba sai gani yayi ta saka hijab "ke ina zaki je da wannan abin?" "Wurin baƙin naka ba?" Tsaki me karfi ya ja yarinyar nan an yi bagidajiya "ke kin san me sunana kuwa? PIYA-PIYA nake maganin kwari shine matata zata fita cikin abokaina da wannan abun a samu abun nuna ni? Kin cire ko kuwa?" Ya daka mata tsawa daga karshe "Ya Mukhtar ba zan iya fita da wannan rigan cikin maza ba hakan ya sabawa Addi...." Wani wawan mari ya sauke mata har seda ta faɗi "ke wai yaushe na zama sa'anki da zan faɗa ki faɗa?" Tana dafe da kunci cikin gunjin kuka ta miƙe "Babu biyayya a bijirewa ubangiji ya Mukhtar ba zan iya..." Sake kifa mata mari yayi ya ja hijab ɗin ya fisge ya yar kan ya janyo hannunta suka yi cikin parlorn tana tirjewa. Chak ta tsaya tana karewa parlorn kallo, mata da maza ne daban daban cikin shiga irin ta rashin sanin darajar kai wasu na rurrungume da juna yayinda kwalaben shiha suka yi bakwai a parlor hayaƙi har ya fara cika parlorn yana maida wutan wani fari fari baki baki, ganinsu tare yasa aka hau ihu sai kallon maita mazan suke mata da sauri ta koma bayanshi ta ɓoye. Rita wacce tsab Alaya ta gane ta ita ce ta kawo shi daren farkonsu a Buge tace "Ga dae kyau sede babu wayewa duhun kai yayi yawa" Shewa suka ɗauka don a yadda tayi maganan har da kishi. "Omoo kuna ganin kaya!" Wani ya faɗa yana zuƙar shisha ɗin shi yana wani karkata kai yana kare mata kallo. Fusge hannunta tayi da karfin tuwo ta juya da gudu tana ji suna mata ihu akan bayanta ta faɗa ɗaki ta rufe kofar da key ta zube a wurin tare da fashewa da matsanancin kuka tana squezing zuciyarta dake zafi da hannu biyu gwanin tausayi... *Kar ku sha'afa Al'ajabin So book 2 is not free, a kan naira 500 kachal zaki same shi immediately after an kamallah book 1, zaki iya yin payment ta nan 3118518476 First bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya ta wannan layi 09039206763* #Vote #comment 🖤Gureenjoh🖤 AL'AJABIN SO      (heart touching story) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN. (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* *Kowa Ya ga zabuwa..* *Diddigar ƙaya... Paid* *Rubutu a kan ruwa... Paid* And now.. *AL'AJABIN SO* *BOOK 1* *Page Twelve* *Sometimes idan muna karanta labari mu kan ji kaman almara har mu kan yiwa kawunan mu tambayar cewa anya hakan na faruwa? Wannan Page is a dedication to waenda suke cikin ibtila'in auren mashayi, masu haƙuri da juriya da kaddararsu. Sadaukarwa ce ga uwar da Allah ya jarraba da haihuwar ɗa wanda jarrabawarshi ta zama shaye-shaye, Allah kana ji kana gani ya Allah ka shirya mana zuri'a, ya Allah ka kara musu haƙuri da juriya, ya Allah Alfarmar annabi da alqur'ani ka musanya musu kaddarorinsu daga baƙi zuwa fari* (Ni kaɗai na san what i went to wurin rubuta wannan Page, a painful True life story) A wurin wani wahalallen bacci ya kwasheta ba ita ta farka ba sai da aka kira assalatu, Miƙewa tayi ta shige toilet ruwa ta fara watsawa kan ta ɗaura alwala tana jin yanda zuciyarta yayi mugun nauyi haka dae tayi sallah ta nemi magunguna ta sha kan ta kwanta, bacci ta sake yi ba ita ta fito ba sai karfe tara sanye da hijabin da tayi sallahn asuba dama da shi ta kwanta, a parlorn ta tsaya tana kallon yanda suka maida shi, kyamar parlorn gabaɗaya ya shige ta, haka dae ta daure iya dauriya ta soma tattare parlorn har ta gama ta share ta fesa air freshner kan ta nufi kitchen don neman abinda zata ci.      Bata gama dafa indomie din ba taji motsi, da sauri ta juya tana kallon kofan kitchen ɗin a tsorace sai suka haɗa idanu, babu kaya a jikinshi daga shi sai karamin wandon jeans, daga dukkan alamu har lokacin ba wai ya dawo daidai bane daga abubuwan da ya ɗurawa kanshi. "ke wato ma ina wasa dake ko? Ni zaki dizga? U are very stupid...don ubanki sau nawa na buga miki kofa kika barni shanye ana min dariya?" A tsorace take matsawa ganin yana kokarin cire belt din jikinshi muryarta na rawa tace "Kayi haƙuri, don Allah ka saurareni ya Mukhtar..." Tun kan ta sauƙe sunan ya fara zuba mata belt ɗin, be ji tausayinta ko na minti ɗaya ba sai da yayi mata duka har da kafa kan ya juya ya fice yana cewa gobe ta kara... "Innalillahi wainna ilaihi rajiun! Innalillahi wainna ilaihi rajiun" abinda take ta nanatawa kenan tana kuka, da kyar ta iya lallashin kanta ta miƙe ta nufi daki bayan ta kashe gas ɗin indomien da bata ci ba kenan, tana hawaye tayi wanka idonta ɗaya yayi jajazir jini ya kwanta gefen fuskanta ga shatin belt nan har kusan uku jikinta yayi wani irin Red abin ka da farar fata. Cikin uniform ta shirya don ta yankewa zuciyarta duk wuya zata yi karatu ko don nan gaba ta iya tsayuwa da kafafunta idan Mukhtar be yi sanadin ta ba, ji take kaman zata mutu kwana kusa a yanda take jin kirjinta da ciwonshi da ya dawo sabo fiye ma da na baya, tafin hannunta ta ware ta ɗan zubawa idanu kan ta gimtse tana sake ajiyar zuciya me nauyi na tsantsar damuwa a haka ta tafi makarantar, dayake bata kula kowa babu wanda ya damu ya tambayi me ya sameta ko ya akayi ta ji rauni har aka tashi bata iya ta ci komai ba. Bayan ta dawo ta haɗa custard ta sha ta sake shan magunguna kan ta janyo wayanta don jin lafiyar mahaifiyarta. Wani irin sabon baabin wahalar rayuwa ne ya buɗe mata, Mukhtar bashi da tausayi ko imani ko na miskala zarratin, ga zafin zuciya matukar ya sakata yin abinda ya saɓawa addininta in ta ƙi haka yake mata dukan mutuwa, marin shi a gareta ya zama kaman man shafawa da da matukar wuya a wayi gari a yini be kai hannunshi jikinta ba, ga bautar yi masa girki da abokansa wanda ba kadan ba idan suka tashi zuwa, a kullum se sun nemi ganinta ita kuma bata fasa ƙin fita ba ta kulle kofan ta gam shi kuma da safe ya mata dukan mutuwa, ko yaushe in yana bukatarta haka ze je mata walau yana hayyacinshi walau yana cikin maye, duk wani alwashi da ta ci a farko akan Mukhtar bata iya ta soma tabuka komai ba don gani take har Abada Mukhtar baze chanza ba, bata da lafiya sossai don zuciyarta ya sake rauni kan rauni sede babu wanda ta faɗawa haka take lallaɓawa kuma take karatu.      Yau suke gama waec ta yi jamb tun sati biyu da suka wuce, Alhamdulillah sun gama lafiya da Fatan jiran sakamako me kyau, a koyaushe tana jinjinawa Maami da irin jajircewarta a kanta Dukda wani sa'in idan muktar ya mata wani abin sai wata zuciyar ta raya mata dole ne ai Maami ta so ta don ta san zama da ɗan ta sai wanda iyayenshi suka sallama, da sauri kuma sai ta yi a'uziyya ta kawar da tunanin don ta san Maami da zuciya ɗaya take mata hidima kuma take tausayinta, babu wanda ze ganta ya shedata sbd wani irin rama da tayi a watannin da ta durfafi yi gidan muktar, tayi wani irin haske har kana ganin kalar green green a jikinta in kana kallonta, idanunta sun kara girma da haske haka hancinta ya sake fita zirrr, bata wani ado bare kwallaya in tayi wanka ta shafa mai ta sa kaya shikenan. Yanzu da ta gama Waec zaman gidan ya zame mata kaman wacce take rufe a prison na karkashin ƙasa, Rita a gidan take rayuwa daga parlor zuwa kitchen duk nata ne yayinda Alaya ke ɗaki a koyaushe abinda ke fitar da ita yunwa sai kuma idan shine ya zo ya sakata girki amma bata yi ta ajiye kam don ba lallai ma wasu ranakun yana kwana a gidan ba, kaman yau, gabaɗaya yinin tayi shi ne ba daaɗi sbd hayaniyarsu da suka yini yi bidiri kala kala a gidan, kaman wani kwarya kwaryar lifaya ne suke yi a gidan, daga inda take a ɗakinta babu irin warin ababen Mayen da bata ji, tana dukunkune kan gado, tana bukatar shan sassanyar iska marar surki irin wannan, ji take kaman zata mutu ne sbd wari da tashin zuciya. Kofan ta da ta kulle ne yinin ranar gabaɗaya don ko abinci bata iya fita ta nema ba taji ana bugawa da karfi, chan ta jiyo dakakkiyar muryarshi yana kiran ta da sunan da shine ya raɗa mata wato "ke! Ke!!" Gabanta ya faɗi, zuciyarta ya hau tseren bugu me zata mishi a wannan yanayi da yake ciki? Kallon jikinta tayi idan tana son lafiyan jikinta kuma abu me sauƙi shine ta bude kofan taji me yake tafe dashi sede tsoro kaman ta narke ta ɓacewa gani da sauraranshi ya lullubeta, jin kaman ze ɓalla kofan ne yasa ta sanya kafafunta ƙasa kaman wacce kwai ya fashewa a ciki ta nufi kofan hannunta ɗaya na kan zuciyarta da bugawarshi har ya shafi numfashinta, hannunta na kakkarwa ta miƙa ta buɗe, banko kofan yayi sai gata gabanshi ya fisgo ta riƙo na mugunta yayi mata "yarinya in ba zaki bi abinda nake so ba kina cikin wahala, buɗe bakinki ki karɓa" Girgiza kai tayi tana kauda kanta daga wani abu da yake shirin bata. "Ya..m...mukhtar menene?" Kashe idanu yayi yace "ko kin san menene ko baki sani ba dole zaki sha" Ya karashe yana janyota zuwa fili abokan shi suka ɗauki shewa. "Game muke kin san Truth or dare?" Be jira amsanta ba yace "an yi daring ɗina na bugar dake don haka buɗe baki malama" Idanunta gabaɗaya ta fitar, a lokaci ɗaya jikinta ya ɗauki mazari, me yaya muktar ke nufi? Shayar da ita abun maye ze yi? Hawaye ne suka soma zuba babu birki cikin girgiza kai tace "Don Allah yaya Mukhtar kar ka yi, kar ka cutar dani, ya muktar hannuna zafi...kirjina ciwo don Allah kar ka sa ni saɓawa mahallicina a dole, karka zalunceni dayawa mana have a pity on...." Bakin ya murɗe se sowa suke suna ambaton sunanshi ya soma bata, duk yanda tayi ganin ta kubce ko bata sha ba hakan be yiwu ba, gimtse hancinta yayi seda ta sha kaɗan kan ya sake ta ganin yana shirin kisa, a wurin ta zube ta tura yatsa cikin bakinta ta soma amai, tun tana yi har ta gigice ta fice hayyacinta gabaɗaya, wata ce a cikinsu da jikinta yayi sanyi da tausayin Alayar tace "Gaskiya baku kyauta ba, tunda bata sha me na shigo da ita cikin wannan game naku? Kullum baku da buri da ya wuce ku wulaƙanta ta, mu faɗawa kan mu gaskiya mana kai Mukhy kaine babban wawa, wanda be san abinda yake yi ba, taya zaka shigo da matar aurenka na sunna cikin wannan irin rayuwa, wani irin jahil....." Gigitaccen marin da Muktar ya sake mata ne ya saka ta kwala ƙara ta yanke maganan, kan tayi motsi saurayinta ya tashi ya rama mata, kwalba mukhy ya janyo ya rotsa mai, a take jini ya fara tsiyaya kaman wasa sai gashi wurin na shirin zama karamin Abbatoir don faɗa ne sossai ya kaure tsakanin saurayin chan da shima ɗan wani ne da kuma Mukhtar kowanne kuma yana da abokan zagi, ita dae Alaya ta samu ta rarrafa ta faɗa ɗakinta ta datse kofa a wurin ta kwanta, kanta se juyawa yake da alama de kayan Mayen ya taba ta, tayi kuka har ta rasa hawaye, tana ta rokon Allah ya yafe mata yana gani ba laifinta bane, an fi awa biyu kan taji gidan yayi tsit, a wurin tayi bacci Washegari ma seda ta kai wuraren sha biyu kan ta farka sbd buga mata kofa da ake tayi kaman za'a ɓalla. Dafe kanta dake sarawa tayi ko Sallar asuba bata yi ba, hawaye ya gangaro mata ta sanya hannu ta share kan ta motsa a hankali ta miƙe dafe da gini ta miƙa hannu ta buɗe kofan jin bugun ba na ƙare bane, woman Police ce tsaye tana kallonta "Madam ko zaki iya ara mana mintuna biyu a cikin lokacin ki?" Kaman bazata yi magana ba tace cikin dasashiyar muryarta "Lafiya?". "Shin kina cikin gidan nan gabaɗaya yinin jiya zuwa dare?" Kai ta gyaɗa ba tare da ta amsa ba "ko kin shedi hatsaniyar da ya faru a jiyan?" Nan ma ta girgiza kai tana kallon matar da take ta karantarta.. "Ba zaki samu ko wani sheda daga gareni ba, ko ma menene kike so pls ki samu waenda suka asassa abun, ina da uzuri se anjima" Ta ƙarasa a sanyaye kan ta tura kofan ta rufe ta juya zuwa bayi, seda tayi wanka ta zo tayi sallah tana rokon yafiyar Allah kan ta fita ta nemi abinda zata ci ta sake dawowa ta rufe ɗakin ruff ko bi ta kan wargajejjen parlorn bata yi ba, idan tace yanzu bata soma developing wani irin tsana na Mukhtar ba to wlh tayi ƙarya, a ƙasan ranta tayi ta ja mishi Allah ya isa kuma tana fata ya saka mata, ashe a chan kam case sossai aka yi sbd karfe da karfi ne suka haɗu sai da shudin Goshi case din ya mutu, nan Alhjnsu yayi ta mishi faɗa akan hakan ze iya ɓata mishi siyasa kar ya sake, ya dae ji ne ko da ya dawo ya tarar parlorn haka buga mata kofa yayi ta buɗe ba tare da ta kalleshi ba sai shima ya ji shakkan kallonta don fuskanta ba digon walwala ko farin ciki. "Ki je ki gyara parlorn nan" Yana kai nan ya juya ya fice, ta jima sossai kaman bazata yi ba se ta fito ta soma tattare parlorn incident ɗin jiya na dawo mata lokaci lokaci tana share hawayen baƙin ciki. BAYAN WATA ƊAYA Yammaci ne sakaliya tun safe bata fita daga ɗakin ba, bata jin karfin jikinta sam ganin yunwa ze iya mata illa don daga kwance ma jiri take ji yasa ta miƙe ta fito sanye da dogon hijab as usual ta shiga kitchen. Rabin taliya ta dafa da kwai dafaffe guda biyu ta zuba a plate, ta juya frigde don ɗauko ruwa se ga Rita ta shigo kai tsaye plate ɗin ta ɗauka zata fice, shan gabanta Alaya tayi tana jin ranta na ɓaci "Baiwar Allah lafiya?" Da mamakin tsaurin idanun yarinyar Alaya tace "ba lafiya ba kam, taya zan dafa abinci don na ci ki zo kawai ki ɗauka ba magana ba komai kaman zamanki nake?" Idanu Rita ta ɗan fitar cikin mamakin yau Alayar tayi magana haka ita bata taɓa ma jin dogon magana daga bakinta ba. "Karfi ya ci daru ya danne, bani hanya in wuce hai village girl kawai" Ranta ta sake ji ya zo mata wuya yarinya fitsararriya ta shigo har cikin gidanta tana zaune duk kauda kan da tayi be isa ba sai ta haɗa da zagi da cin zarafin ta ko da shi ke ba laifinta bane, cikin ɓacin rai tace "Ai kuwa gwara da ni sau dubu saba'in in ma na amsa ni village girl din kenan, ko ba komai village girl ta fi ashawo...." Watsa mata abincin gabaɗaya Rita tayi jiki yayinda ita kuma Alayah ta dauketa da zazzafar mari.    hango Mukhtar bayan Alayar yasa ta dafa kumatu ta saki razananniyar ihu, cikin kuka tace "Wallahi yau zan bar maka gidanka Mukhy, har ni matarka zata ɗaga hannu ta mareni akan banza taliya? Ni dae?" Da sauri Alayah ta juya zata yi magana ya kifa mata mari, yayi ball da ita bata san ta tafi kaman wacce iska ya ɗauka ba seda taji ta sauƙa a kafafun mutum, ɗagowa tayi bata gani daidai sai taga Maami ce da sauri ta miƙe ta faɗa jikinta ta soma kuka me cin rai, kan Maami tace tayi wani yunkurin kawai Alaya ta yanki jiki ta faɗi ƙasa... "Innalillahi wainna ilaihi rajiun Mukhtar ka kashe musu ƴa ka huta, nace ka huta.." Tana nufo shi ne take maganan "wani irin zuciya ne da kai? Wani irin baƙin zuciya ne Allah ya halicceka da ita? Ashe baka da tausayi Mukhtar dubi yadda yar mutane ta koma" Kwalan riganshi ta chakwamo "Allah ya saka mata, wallahi Allah se ya bi mata hakkin ta, Allah ya mata sakayya tun a duniya, mugu azzalumi.." Hawaye take yi bibbiyu, hannunta yake kokarin cirewa a wuyan shi tana sakin shi kuwa ta soma zuba mishi maruka hagu da dama tana kuka. Ganin hakan baze mata ba ta soma neman abinda zata kwada mai ko zata huta bata yi taku biyu ba itama ta yanki jiki ta faɗi ƙasa. Se a lokacin ya gigice cikin hanzari y dago ta yana kiran Maami Maami, sede Maami tayi nisa, daukanta yayi da gudu zuwa motanta driver ze ja yace ya jira shi, da sauri ya koma ya ɗauko Alayah da banda haushinta babu abinda yake ji dama tsakanin shi da mahaifiyar yaya gashi tana kara ɓatawa, ta wannan ne kawai zasu iya samun matsala da Abbansu don yana son matarshi. A motanshi ya saka ta yana gaba drivern Maami na bin su a baya har asibiti, cikin gaggawa aka Karɓe su emergency, likitoci suka rufu a kansu wasa wasa har aka yi Magrib kan suka samu kan Maami, Alayah kam se kusan bayan isha ma likita mace ta fito tana kallon Mukhtar "kaine mijinta?" Kai ya gyaɗa yana kallonta "Toh Congratulations matarka tana ɗauke da ciki na tsawon sati biyar sede akwai karancin nutrient a jikinta, and ciwon zuciyanta yana so ya tsananta kaman yadda jininta ke hawa duka wannan illah ne ga lafiyarta a gaskiya ya kamata ku kiyaye, a ka'idar aiki ma bayan an mata wanchan aikin zuciyar be kamata kuma ya sake hitting haka ba" Shi duk sauran jawaban ma baze ce ya ji ba banda batun cikin nan da ya ji. "Ciki???" Ya maimaita kan ya sake cewa "do you mean pregnency?" Kai ta gyaɗa, ya ja wani dogon tsaki ga ta inda ya tsani auren ai, yarinya ta zo banda gidahumanci babu abinda take mishi kwata kwata ko shekara bata rufa ba ace wani ciki, shiyasa ya fi son hulda da wayayyun mata shi be shiryawa haihuwa yanzu ba... "Look likita ina so ki zubar da shi ko nawa ne zan biya" "wannan ba aikina bane, kuma bama haka a asibitin nan amma zaka iya zuwa gaba se ayi maka" Har ta juya yace "ko don lafiyanta? What if cikin ne yake triggaring ciwon zuciyar? I th....." "MUKHTAR" Maami ta kira sunan, se kawai ta sulale ta zauna a wurin tana hawaye a ranta tana istigfari bata san me zata yiwa Mukhtar ya shiryu ba, babu me fahimtar ciwon ranta babu me gane abinda take ji da takaici da haushin ɗan da ta haifa a cikinta se wacce jarabawa irin wannan ya faɗarwa, muryarta a rarrabe tace "ka fice daga asibitin Mukhtar wallahi na tsani ganinka" Da sauri ya ɗago ya kalleta, ze yi magana ta daka mishi tsawa tana dafe kanta dake juyawa. "I Said Get outttt!" Miƙewa yayi ya fice, da sauri likitar ta ƙaraso ta riketa ganin tana shirin sake collapsing. "Se hakuri Aunty, Adu'a itace maganin komai ki kara akan wanda kike" Maami na hawaye tace "Wallahi ina yi Likita, ina yi bana bacci amma kaman bana yi astagfirullah Allah na tuba Allah" Tausayinta sossai ya rufe likitan, ita tayi ta kwantar mata da hankali amma ta koma ɗakinta firr ta ƙi tace zata zauna da Alayah gudun sharrin Mukhtar. Se kallon yadda kasusuwa suka yiwa yarinyar sarka take yarinyar gwanin tausayi, rayuwarta duk ya daidaice sbd Mukhtar, matakin da ta yanke kawai shine na riketa ta nema mata saki wurin Mukhtar shine kwanciyar hankalinsu duka, in ya ga dama ya tara matan duniya a gidanshi yana zina dasu tunda abinda yake so kenan, share hawayenta tayi ganin Alayah na motsi ta riƙe hannunta.... "binty kin farka?" Kai ta gyaɗa tana sake lumshe ido tace a hankali "Maami cikina kaman ana karta" "ai dole, taya me juna biyu zata zauna da yunwa sossai haka har ya fitar da ke hayyacinki? Ruqayya na hanya bari in kirata tayi sauri" "Juna biyu???" Bata san a fili ta maimaita ba seda Maami ta ɗago ta kalleta tace "Eh, kina dauke da juna biyu na tsawon sati biyar..." Dibbbbbb haka duniyarta ya tsaya, komai nata ya tsaya chakk kaman robot ta sake maimaita "Juna biyu dai?" *karki manta book 2 na kuɗi ne, da Naira ɗari biyar kachal zaki mallaka, a sha karatu lafiya* 3118518476 First bank Fatima Muhammad Gurin sai ki tura shaidar biya ta 09039206763*                        🖤Gureenjoh🖤 AL'AJABIN SO (heart touching story) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN.                      (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* *Kowa Ya ga zabuwa..* *Diddigar ƙaya... Paid* *Rubutu a kan ruwa... Paid* And now.. *AL'AJABIN SO* *BOOK 1* *Page Thirteen* *A cikin satin nan ina da hidima sossai so it depend da yanayin comments naku, in yi Page ban ga comments na arziki ba ga gajiyar hidima ga al'amuran yau da kullum gaskiya ba zan iya ba, sai in bari sai sati na sama in cigaba* Yanayin fuskanta sai ya so ba Maami tsoro don ƙiri-ƙiri ya nuna bata na'am da lamarin cikin, lumshe idanunta tayi tana jin hawayenta na sake yi mata nisa sbd tsabar zubar dasu da ta ke, sai ciwon zuciya mai tsanani da take ji kaman ko yaushe zai iya yin ajalin ta, sam bata yi farin ciki da cikin ba, ba wai bata so bane ba kuma wai ta tsani ɗan bane kawai bata shirya haihuwa da Mukhtar bane cikin wannan hali da suke ciki na rayuwa, bazata taɓa so ɗan da zata haifa ya tashi ta nuna mai muktar a matsayin mahaifi ba, sam be chanchanta ya zama uba ba bashi da nagarta da wannan nasabar taya zai iya baiwa yaronsu tarbiya da taimakon da ya dace? Dafata da Maami tayi ne ya sa ta buɗe rinannun idanunta ta kalleta "Binty Dukda ban san yanda kike ji a cikin ranki ba nayi imani baki son wannan ciki, na tabbatar ba don wani abu bane sai don hallayyar Mukhtar in har baki shirya yanzu ba sai a zubar a yi miki planning zuwa wani lokaci.." Da sauri kuma sai ta dafe cikin, gudan jininta za'a zubar? Girgiza kai tayi tana barin hawayenta zuba tace "Maami ba zan ɓoye miki ba, hasashenki gaskiya ne sede ba zan iya zubar da wannan ciki ba, tunda Allah ya bani ya san dalilinsa na yin hakan watakila sanadin shiryuwar Ya muktar din kenan don Allah a bar min" Murmushi Maami ta saki tare da shafa kanta tace "Allah ubangiji ya miki Albarka binty, Allah ya shirya muktar ya san cewa dami a akala ce ya tsinta kar daga karshe yayi faɗuwar baƙar tasa, a lokacin da nadama bashi da anfani" Shigowar ruqayyan ne ya katse su, da kanta ta zubawa Alayar abinci Maami ta taimaka mata ta zauna kan ta soma bata abincin, cikin natsuwa take karɓa har seda ta ƙoshi kan ta ce ya isa Maamin ta mika mata ruwa ta sha, kan ta sake kwanciya sai bacci, Aunty ruqayya ce tace "Amma yarinyar nan na da tsananin haƙuri Adda, ina tsoron kar shiga hakkin nata yayi yawa, idan mariƙinta ya mata muguntar haɗa ta da muktar mu da muka san halayyarsa maras kyau kuma be kamata mu zuba idanu tana shan wahalarsa ba kiyi hakuri in abinda na faɗa ya ɓata miki rai" Murmushi me ciwo Maami tayi tana kallon Alayar tace "a yanzu ruqayya zaman yarinyar nan da muktar ya fi cin raina fiye da yanda kike zato da asalin hallayyar muktar ɗin, tausayinta nake ji har ƙasan raina da ita nake kwana da ita nake tashi, amma in shaa Allah daga yanzu hakan ya wuce, Fatima ta gama zama da muktar in shaa Allahu, ko da mariƙin nata bai karɓeta ba ni zan zauna da ita har Allah ya kawo mata wani mijin da zai share mata wannan bakin cikin" Tattaunawa suka cigaba da yi duk akan matsalar Mukhtar, chan sai ga Alhj ya shigo yau kam seda yayiwa Mukhtar faɗa akan abinda yayi wanda hakan be wani ɗaɗa muktar din da ƙasa ba wayan ma ya ajiye a gefe hands free yana zuƙar shisha ɗin shi hankali kwance, bayan ya gama ya kashe. Ita Maami bata wani yi maganan Alayar da shi ba don ta san duk inda aka je aka dawo yana bayan Mukhtar don ba ganin laifin shi yake ba sam, saida ta kwana biyar a asibitin kan aka sallameta, a wannan karo Maami ita ke yini ta kuma kwana duk yanda ruqayya tayi da ita akan ta bari su kwana ko ta kawo mai aikinta su kwana ta ƙi tace bata so ko kusa Mukhtar ya sake yunkurin cutar da ita, daga asibitin gida suka yi direct ɗakin dake gefen nata Maamin ta mata masauki don ta sake. Da kanta ta tura aka haɗo mata kaya akwati har biyu da wayanta da take ta magananshi sbd son jin Umminta da take, ɗaki ne me girma da tsari babu abin more rayuwa na kuɗi da babu ciki, Maami ta mata umarni da ta dinga kulle kofan in an yi knocking sai ta tabbatar da waye kan ta buɗe don ta san Mukhtar farin sani, ita kuma zata cigaba da kula Dukda ta saka securities hana shi isa sashenta tace duk shigowan shi iyakaci sashen mahaifinshi bata amince ya zo mata sashe ba. Zaman Alaya a gidan ya matukar yi mata daaɗi duk wani kulawa na me juna biyu tana samu daga Maami, da kanta take shiga kitchen take dafa mata duk wani abu da ta san zai ƙara mata lafiya, haka a asibiti ma an yi recommending ta yawaita cin irin su vegetables, jan nama da dai sauransu, laulayinta ba mai yawa bane saide zazzafar zazzabin yamma, sai kuma wani sa'in amai shima ba sossai ba, kaman yadda ta ɓangare ɗaya Mukhtar ya gigice don duk yanda yake tunanin hukuncin Maami ya wuce nan tayi rantsuwa ko ya kawo mata takardar Alayah ko su haɗu a court ya bata ta karfin tuwo tunda yarinya bata son shi, Alhj hammad din ma bata ragar mai ba gashi yana ɗan busy sbd siyasa da ya kawo kai gadan-gadan. Damuwar Alayah guda ɗaya takkk na rashin jin mahaifiyarta duk text message da zata yi mata ba reply tayi ta kira tun yana shiga har ya daena, wannan na daga cikin abinda ya shigar da ita sabuwar damuwa da zaƙuwar son ganin mahaifiyarta, suna zaune da Maami suna ɗan taɓa hira yayinda Maamin ke chat kaɗan kaɗan tana murmushi me sanyi sbd da sanyin zuciyarta take magana, Dukda ɓacin rai yake nunawa ita kam lallashin shi take ta kuma lura har da Shagwaɓar da baya rabo dashi in dae yana gabanta kaman ba shi ba. Kira ne da ya shigo wayan ya sa ta gyara zamanta a natse tayi picking ta sanya a kunnenta cikin ladabi kaman tana gaban na cikin wayan ta soma miƙa gaisuwa cikin kulawa yake amsawa kan a natse yace "Faɗimatu yanzu mijinki da ɗan ki suka bar nan" Haɗe fuska tayi kenan kararta suka kai wurin baba. Kanta ƙasa tace "Baba kayi haƙuri na jin wani abu na laifina da kayi daga gidan aure saide ƙullin na da girma dole sai na warware maka zaka fahimceni, na san baka daga cikin masu goyon bayan zalunci da kai da me sunanka zuciyoyinku iri ɗaya ne a wanke a kuma dake, cike da gujewa duniya da kyamatar azzaluman cikinta, don Allah ka bani dama zan zo har gida ka ji uzurina" Ajiyar zuciya ya sauƙe yace "Ina fata ba hikiman zancen da Allah ya miki bane kika kanainaye ni da ita, ina jiranki" Daga haka ya yanke wayar, saukewa tayi ta saki ajiyar zuciya bata fata ko kusa baba yayi mata dole na ba Mukhtar Alaya sam bata wannan ra'ayin. Duban Alaya da sai juya wayanta take tayi tana karantar damuwar fuskanta kaman ma bata san da wayan da Maamin ta gama yi ba tace "Binty" Bata amsa ba ta sake cewa "Fatima.." Nan ma shiru, Miƙewa tayi ta isa gareta ta taɓa ta sai tayi firgigit ta zubawa Maami idanunta dake cike da ruwan hawaye, Maami tace "Binty yawan tunani hatsari ne ga lafiyarki, menene? Me damuwar?" Hawayen ta ne ya gangaro tace "Maami yau sati na uku ake shirin shiga ban ji daga Ummi na ba, hankalina a tashe yake ina tsoron kar dae wani abu ne ya sameta" Ajiyar zuciya Maami ta sauƙe kan ta dubeta tace "In shaa Allah lafiyanta ƙalau kila ɗan wani abu ne kalilan in shaa Allah jibi sai driver ya kai ki ki dubo ta don bana tunanin Alhj Hassan chanji yana nufin furucinsa akan ki" Murmushi mai ciwo Alaya ta saki ita kam ta riga tayiwa Abban Jameelah farin sani babu ko shakka abinda ya faɗa ɗin har ranshi ne sede zata je ɗin, ko yanka naman jikinta yake zata je taga mahaifiyarta. Washegari da misalin karfe huɗu na yamma Maami ta ɗauketa suka nufi family house ɗin su, babban gida ne me sashuka uku, matan gidan ba dae karamci ba haka ma'aikata da kalilan yara dake gidan wasu na kiran Maami yapendo yayinda wasu ke cewa Goggo ta fahimci duk masu ce mata Adda ɗin kannenta ne, anan taga daga inda Maami ta samu zuciyar daraja ɗan adam ko yaya yake, ba karamin kudi ne dasu ba daga tsarin ginin zuwa kayan ciki kaɗai ya isheka shedar hakan amma ji yadda suke Haba Haba da ita. A sashen mahaifiyarta suke dattijuwa ce me tarin ilimin addini, kana ganinta zaka iya kiranta da Ba'abziniya ko kuma shuwa cikin biyu dae kaman yadda Maami take kama da ita sak, haka ma Mukhtar, sai bayan Magrib baba ya aika kiransu. Cikin natsuwa suka zauna daga ƙasa a gabanshi, ita dae Alayah tayi farin gani don dattijon duk inda ake son samun kamillale natsatsen dattijo ya kai, wannan shine tsufa me riba a tsufa da mutunci karkashin inuwar addini, bayan sun gaisa ya dubi Maami yake ce mata yana sauraren ta, tiryan-tiryan ta soma bashi labarin abubuwan da suka faffaru nan ma bata san wasu ba kaman na ɗura mata kayan maye da yawan duka kaman jaka, ga siyar da mutunci. Ita dae Alayah kanta ƙasa ko daga shirun da wurin ya ɗauka bayan gama bada labarin Maamin ta san ran dattijon be mishi daaɗi ba "Muktar sam be kyauta ba, hukuncin da kika yanke ma ban ga laifinki ba, ba zai yiwu a bashi mace da ciki yaje garin duka ya raunatata ba, ina zuwa" Ya ɗaga waya ya kira muktar yace ya same shi a gida yanzun nan. Tambayoyi ya dinga ɗan jefowa Alayar tana amsawa da iyakar gaskiyarta akan gidansu da sauransu, duk abinda ta taɓa fadawa Maami haka ta faɗa mishi ba chanji, suna nan zaune sai ga Mukhtar, ba Alaya kaɗai ba hatta maami seda ta shiga tsantsar mamakin ganinshi da wani half jumpa blue yadi me taushi har da hula da ya rufe tsinannen askin kanshi, dama ta san duk duniya mahaifinta kaɗai yake iya yiwa wannan tsoro da ladabi, a hankali ya zauna gaban baban, bayan shiru na sama da mintuna biyu baba yace "Muktar na raina wayonka, kwarai baka kyauta ba anan ɓangaren dukan macen aurenka kuskure ne babba, Allah be amince da wannan ba ko kusa ko alama, mace da aka sani da rauni Abar a tausaya mata a riritata, a lallaɓa rayuwarta ita ce zaka dinga sakarwa kwanji? Haba Mukhtar! Yanzu da ka kawo ƙara me kake bukata?" Shiru yayi na seconds kan yace "a yi haƙuri hakan ba ze sake faruwa ba" Daga Maami har Alaya ba wai sun yarda da zancen shin bane sbd sanin hali da suka yi, duka wannan ladabin na en wiwi ne "Ashe baka san hadithin da yake magana akan dukkan shugaba abin tambaya ne akan kiwon da aka bashi ba? Kana tunanin in an ce shugaba ana maganar kawai masu mulki ko sarauta ne? La la la kowani mutum mai kiwo ne akan iyalansa kuma abin tambaya ne, shari'ar musulunci ta tsoratar akan duk wani me take haƙƙin wani ɗan uwansa na kusa ko na nesa kai hatta akan dabbobi bare matarka ta sunna, ka san wanene addinin musulunci ya ƙira da dayyus?" Kanshi a ƙasa jikinshi ya ɗan yi sanyi ya girgiza kai. "Wato sakarai, shashasha wadda baya kishin matarsa kwata kwata ya ɗauketa ne kawai a matsayin wacce zata mishi girki ya ci sai in bukatar shi ta tashi ya sauƙe ko kuma yaje yayi ta mu'amala da wasu matayen wannan sharri ne mai girma, domin irin wannan ne yake janyo shaidan ya ci galaba kan matar ko a samu akwai ƙarancin tsoron Allah sai itama ta halaka, ko ka san dayyus basa taɓa shiga aljanna? Ko kamshin ta bazasu ji ba, sahihin hadithi ne ya zo daga manzon Allah cewa mutane uku bazasu shiga aljanna ba an karboshi ne daga Abdullahi dan umar, mutane uku Allah ya haramta musu aljanna wadda ya dawwama yana shan giya har ya mutu..." Da sauri Alayah ta ɗaga kai ta kalleshi kaman yadda Maami ma da hawaye ya zubo mata take kallonshi, gabaɗaya kaman ruwa ya ci shi haka ya ɗago ya kalli matar tashi da mahaifiyarshi. Baba da ya kula da irin sanyin da jikinshi yayi ya cigaba "da kuma mai yawan saɓawa iyaye, sai kuma dayyus wanda baya kishin matarsa wanda yake tabbatar da ɓarna cikin iyalansa..." Kukan Alayah ne ya fito fili sossai a chan ƙasan ranta take maimaita innalillahi wainna ilaihi rajiun duk hallayyar Muktar ne a cikin nassi ɗaya, taya zata soma haihuwa da muktar da wannan hali? Taya zata iya cigaba da zama dashi alhali be san darajarta ba be san ƙimarta ba bare ya kare mata martaba? Idanunshi da suka sauya ya ɗago ya kalli baba da yake cewa "idan har ba tuba yayi ya daina dukkan waennan abubuwan da na lissafo ba, tuba na gaskiya da gaskiya tsakanin shi da Allah, Mukhtar kaji tsoron Allah! Ina ƙara nanata maka wannan kaji tsoron Allah a dukkan lamuranka ka tashi ka tafi zan neme ka da kaina" Baba ya ƙarasa! Shiru ya sake yi chan dae ya gyaɗa kai, ba tare da ya sake cewa komai ya miƙe ya fice daga parlorn. "Fatima!" Baba ya kira ta, shesheka take saki a hankali ta riga tayi developing tsanar Mukhtar bata son shi, bata ƙaunar shi, bata jin ko kaɗan zata iya son shi bayan duk abubuwan da yayi mata, bata tausayin shi saboda shine ummul aba'isin duk halin da yake ciki he's responsible for that don bazata ɗaurawa Maami ba mutumiyar kirki! Cikin muryan kuka ta amsa, gabanta na faɗuwa tana Adu'ar kar ya mata dole zama da Mukhtar a yanzu bata ko ganin ƙimar shi. "Fatima zaman aure ɗan haƙuri ne..." Idanunta ta lumshe da sauri ta dafe zuciyarta da yayi wani irin harbawa, zafi da raɗaɗi ya soma bin jikinta, numfashi ya soma yi mata wahalan fita wadda fusgan da take mishi yayi sanadiyar dakatar da Baba ya kuma maida hankalinsu gabaɗaya kan ta. *Kar ku sha'afa Al'ajabin So book 2 is not free, a kan naira 500 kachal zaki same shi immediately after an kamallah book 1, zaki iya yin payment ta nan 3118518476 First bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya ta wannan layi 09039206763* #Vote #comment                      🖤Gureenjoh🖤 AL'AJABIN SO (heart touching story) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN.                      (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* *Kowa Ya ga zabuwa..* *Diddigar ƙaya... Paid* *Rubutu a kan ruwa... Paid* And now.. *AL'AJABIN SO* *BOOK 1* *Page Fourteen* "Binty lafiya kuwa? Ko ciwon zuciyar ne?" Girgiza kai tayi tana riƙe hannun Maami da kyau, ruwa Maami ta zuba a cup da sauri ta bata ta sha, runtse idanunta ta sake yi da karfi tana sauƙe ajiyar zuciya a jere a jere, baba ya gyara murya kan yace "sannu Fatima, Allah ya baki lafiya" Maami ya duba yace "Faɗimatu ko zaku je asibiti ne?" Alayah ce ta girgiza kai tace "ba komai Baba ya sauƙa!" Ya so su je ta samu ta sha magunguna ta huta amma ta ce babu komai tana sauraran shi hakan ya sa ya cigaba. "Mace ga mijinta ta kan zama ƙyaure ne ko wani garkuwa wacce ba zata taɓa cimma rabautar aure ba idan bata haɗa da haƙuri da jajircewa ba, dukkan wasu iyaye ko yaya su ke baza su taɓa farin ciki da mutuwar auren ƴar su ba bare wannan da baku rufa watanni biyar ba, sannan ga rabo Allah ya kawo, na san abin da zan kawo zaki iya jinshi ba daaɗi sai de Fatima kaman yadda na ɗauki Mukhtar jinina jika a gareni haka kema na ɗauke ki ba zan taɓa miki dole zama da Mukhtar ba saide ina so ki je kiyi tunani, ki sanyawa zuciyarki natsuwa ki zama mai haƙuri duk da na san yana da matuƙar wahala sai dae fa yana da riba mai tarin yawa, duk yadda ka kai da son abu ko ƙin sa saida amincewar Allah shi kuma yana duba zuciyoyin mu ne wurin yi mana hisabi, idan kin koma ki yawaita tashin dare kina roƙon Allah a kan mijinki, ki fawwalawa Allah lamuranki ki zama mai ƙan ƙan da kai da zubda wa ubangijinmu hawaye, a duk bayan adu'ar ki ki haɗa da La'ilaha illa lahul azimul halim, La'ilaha illa lahul hakimul karim, La'ilaha illallah, subhallah, Rabbissamawatissaba'i wa rabbul arshil azeem, Alhamdulillahirabbil alameen. Kaman yadda na faɗa kiyi nazari sossai zan neme ki bayan sati ɗaya" Godiya sossai ta mishi Dukda ba daaɗi take ji ba a haka suka fice daga gidan, saida suka biya asibiti saboda Maami ta kasa gane mata a take likitan da take gani yayi referring ɗin su to meddy specialist hospital wurin Doctor Philips saboda ya tabbatar musu lamarin ta sai a asibitin za'a iya tackling ko kuma waje, godiya suka mishi daga nan suka yi gida dare yayi sossai so bata wani zama ba ta watsa ruwa ta kwanta, duk yadda ta so bacci ya ɗauke ta ma ya ƙi sai juyi take tana tunanin rayuwarta, ita bata zama mai sa'a ba sam babu mai mata ƙaunar tsakani da Allah bayan mahaifiyarta sai Maami haka zata cigaba da rayuwa? Shin ya zata je ta tarar da ummi? Wani irin tarba zata samu daga mutanen gidan barin ma Alhj Hassan dala? Wani irin ma tunani zata yi akan Mukhtar da zama dashi bayan ta riga ta sakawa ranta ba zata iya cigaba da zama dashi ba? Washegari haka ta yini duk jikin babu daaɗi da misalin karfe huɗu ta shirya tsab cikin atampharta da aka mata ɗinkin riga da skirt Dukda ramarta sai dae tayi haske yanzu ta ɗan yi kyau sbd karan hancinta da ya kara fitowa idanunta suka kara girma, she's so pale bata da wani walwala, daga ɗakinta ta fito sai ta tsaya chak tana shakar daddaɗar turaren da kamshin shi ya danne duk wani kamshi na Maami da baya rabo da babban parlorn saman, bata taɓa jin turaren ba, ko dae Mukhtar ne ya sauya turare? Da wannan tunanin ta tura ɗakin Maami ta shiga Maamin ce kawai zaune tana duba wani littafi da ya fi kama da na addini. Kamshin ya fi yawa a ɗakin hakan yasa tayi tunanin dae wani sabon turare ne Maami ta buɗe mai daaɗi, a gabanta ta zauna tana mata sannu da gida, cikin kulawa ta amsa tana tambayarta babu abin da yake damunta? Ta girgiza kai kan tace "Maami zan je dubo ummin" Maami tace "Toh Binty ki gaisheta kin ji? Sannan ga wannan dama tun jiya na tanada ki kai mata in akwai wani matsala kiyi gaggawar ƙirana kin ji?" Kai ta gyaɗa tana karɓar jakar tare da godiya da Adu'a ga Maamin kan ta miƙe, har ta isa kofa Maami ta kirata ta dawo. Kiran me aikinta tayi dattijuwar mata Maama Laami tace su tafi tare da Habu driver, babu gardama suka fice a tare. Banda faɗuwar gaba babu abin da take ji har dafe kirji take akai akai har suka isa gate ɗin gidan, Habu yayi horn shazali ya buɗe mai gate din ya kutsa kanshi ciki yayi parking, idanunta ne suka sauƙa akan Alhj Hassan dake zaune riƙe da jarida a rumfar shaƙatawarshi wanda hakan yasa gabanta sake bugawa da karfi, Habu ne ya buɗe mata kofa sai ta kasa sauƙa ganin Hajj Zeenat sun fito a tare da Jameelah kaman wani wuri jameelar zata ita kuma Hajiya wurin alhaji ta nufa bayanta me aikin da bata sani bane rike da tiren kayan marmari. Rashin fitan ta ya dawo da hankalin Alhj Hassan kan motar, har jikinta na rasa ta sanya kafa ta sauƙa daga cikin motar dukkaninsu Dakatawa suka yi suka zuba mata idanu, baba Musa ne cikin mamaki da wani ɗan farin cikin da ya bijiro mishi yace "Alayah kece?" Wannan suna da ya kira yasa dukkanin fara'ar fuskokin iyalan gidan ya kau, Miƙewa Alhj Hassan yayi ya nufo ta yace "Ke! Uban me ya kawo ki gidana? Me na faɗa miki randa aka ɗaura miki aure?" Kanta ƙasa ta ɗan duƙa tace "Ina yini Abba..." "Zan zazzage ki, zan kwalfe ki anan kika sake juya tambayata zuwa wani abu, nace uban me kika shigo yi min cikin gida?" Hajj Zeenat tace "zata nuna maka itama ta soma gwamutsuwa da masu maiƙo ba, wuyanta har yayi kauri..." Jamila dake gefe tayi wani dariya tace "abin da ya bani mamaki ma har wani buɗe mata kofa ake, ita gata surukar wani da dae ba'a san asalin balbela bane da sai ta ce daga Masar take, ko kuma da bamu san wani thug kike aure ba da shine za'a mana wannan feleke" Duk maganganun su bai dameta ba damuwanta ɗaya ta samu ta ga umminta ita ko gilamawanta ta gani ma Alhamdulillah ta san lafiyanta ƙalau, "Nace me ya kawoki gidana???" Ya daka mata tsawar da ya firgita ta cikin rawan murya tace "U..mm..i u..mmi..na na zo ga...ni" "da gaske kenan wuyanki kauri yayi da zan kafa miki doka ki take? Fitar min daga gida tun kan ban yi miki abinda kare ma baze ci ba in ya gani" "Don Al...." "I Said get out...!!" Ya daka mata tsawa yana yiyowa kanta, da sauri Maama lami ta riƙe ta tace "Hajiya mu tafi" Girgiza kai tayi tana me sakin kukan da take riƙewa "Maama mahaifiyata ce fa... A nan ciki... Ba..n sa..n ha..halin da take c..ciki ba, ba za.." Marin da Alhj Hassan din ya kawo mata ne ya sameta tayi baya saura kaɗan ta faɗi baba Musa da yake kusa ya tare ta chan ƙasa yace "idan akwai wadda zaki iya tara ya taimaka miki karki je ki zuba ido mu karan kan mu bamu da tabbacin lafiyar mahaifiyarki" Ɗagota yayi, hajj Zeenat tace "ka ganka Musa!! Kai shashashan ina ne da Alhj na hukunci zaka shiga? Da ka tare ta uban me ya haɗa ku da zaka bata kariya? Ashe ma goyon baya zaka bata tayiwa uban gidanka rashin kunya? Shiyasa na tsane ku ku din nan ma'aikatan tsakar gidan nan, akwai wani abu daban cikin ranku to ya ƙare a kanku" Habu da ya buɗe mota ne yayiwa Maami Laami magana tayi saurin saka Alaya da har lokacin kuka take tana tirjewa bata son tafiya cikin motar, yayi saurin shiga suka bar gidan hajjiya Zeenat na cigaba da surfa bala'in ta son rai. A jikin Maami ta zube tana kuka sossai "Maami kila sun kashemin ummi, Maami sun hanani ganinta, Maami ya zan yi? Ina zan sa raina idan wani abu ne ya samu ummi? Bani da kowa ban san kowa nawa ba ta ina zan fara ni Fatima?" Har shaking Muryar keyi saboda kuka. "Binty kiyi shiru in shaa Allahu ina tare dake, ina nan tare dake kuma ba zan taɓa bari su ida mugun nufin su ba, a jikina ina jin ummin ki babu abin da ya sameta, ki natsu kin ji? Kin ga ba ke kaɗai ba ce, ki bani hankalinki in shaa Allahu yanzu zan soma ɗaukar mataki" Ita dae ta san Alhj Hassan fuskantarshi ba abu bane mai sauƙi tunda Ummi nunawa take Abbanta ma ya gaza, sannan abokin Alhj hammad ne baban su Mukhtar baze iya bari Maami tayi wani abu ba, idan kuma bata yi ba shikenan ta rasa ummi kenan ko yaya? Ire-iren tunanin da ta zurfafa kenan ta daena kukan sai ajiyar zuciya, Maama lami ke faɗawa Maami duk yadda aka yi tana jinjina rashin darajar mutanen gidan, da lallamin Maami ta ɗan ci wani abu sai dawo mata maganganun baba Musa yake, yana faɗa mata ne akwai damuwa, har ta kwanta bayan isha sai saƙe-saƙe take bata da yadda zata yi, babu gata cikakke babu galihu, wanda hakan ya sakata kuka mai yawan gaske daga karshe ya haddasa mata zazzafar ciwon kai me tafe da zazzabi, da kyar ta ga safiya ko da Maami bata ganta ba bayan sallah saboda tana idar da sallah take zuwa gaisheta hakan yasa ta shigo ɗakin don dubata yanayin da ta sameta ne yasa kawai suka yi asibiti, gabaɗaya tausayin rayuwar Alayar ne ke rufe da Maami har kusan bayan awanni biyu ma kan Dr Philips din ya fito yake mata bayanin stage din da take na da hatsari tana bukatar kwanciyar hankali da natsuwa, hakan ne kawai zai sa da taimakon magani sai ta samu sauƙi tunda ba'a jima da mata aiki ba kuma it was successful. Duk Maami ta ji kuma ta san hallayyar Muktar gareta ne yayi triggaring ciwon da ya kamata ace ya lafa sossai da sossai, sai kuma wannan Alhassan ɗin da babu mugun abu nashi da bata sani ba, bashi da imani ko na miskala zarratin, godiya ta mishi kan ta ƙarasa ɗakin da aka kai Alaya din baba ne ya kirata don jin jikin Alayar sai ma yaji suna asibiti hakan yasa yayiwa Daada magana ta sa driver ya kai musu abin kari. Riƙe da hannunta Maami ta zuba mata idanu, wani irin tausayinta na sake ninkuwa a ranta, hawaye ta tsinci kanta da yi tana saka kanta a sahun Alayar, kiran da ya shigo wayanta ne yasa ta share hawayen kan ta miƙe ta fita tana danna recieve... *Kar ku sha'afa Al'ajabin So book 2 is not free, a kan naira 500 kachal zaki same shi immediately after an kamallah book 1, zaki iya yin payment ta nan 3118518476 First bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya ta wannan layi 09039206763* #Vote #comment                      🖤Gureenjoh🖤 AL'AJABIN SO (heart touching story) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN.                      (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* *Kowa Ya ga zabuwa..* *Diddigar ƙaya... Paid* *Rubutu a kan ruwa... Paid* And now.. *AL'AJABIN SO* *BOOK 1* *Page Fifteen* *Alhamdulillah Abdul ya samu sauƙi na gode da Adu'o'in ku* Wani nannauyar ajiyar zuciya ya sauƙe tare da buɗe idanunshi dake runtse tuntuni, club ɗin ya zubawa idanu a hankali yake bin mutanen wurin ɗaya bayan ɗaya da kallo kaman yau ɗin ne rana na farko da ya soma shigowa a rayuwarshi, daga masu tiƙan rawa rungume da Ƴan mata, zuwa kan masu kiɗan da suke buga beat suna ihu, zuwa kan waenda suke rage zafi da Ƴan matan da ba muharramansu ba babu wani kayan arziki zuwa masu busa hayaƙi da shan barasa, duk yadda yake tunanin anan yake samun natsuwa sai yaji gabadaya natsuwar ma ta ƙi zuwa, tsanar wurin ma yake ji a ranshi hatta da mutanen cikinta, idanunshi ya ɗaga sama yana shafa dadar kanshi tambayar kanshi yayi a lokaci ɗaya menene jin daaɗin wannan rayuwa? Mecece ribarta? Sake lumshe idanun yayi sai fuskan Maami ya faɗo mishi tana zub da hawaye tana mishi karyayyen kallo mai cike da tausayi, jimami da damuwa, da sauri ya buɗe yana kallon Rita dake tsaye a kanshi a maimakon ya ga fuskanta sai fuskar Alaya ce take faɗo mishi, magana take mishi amma sautin sassanyar Muryar yarinyar yake ji yana shiga kunnuwanshi, da karfi Abokin shi Pepe ya jijjigashi yana ƙiran sunanshi wadda hakan ya dawo dashi natsuwarshi "Kana lafiya kuwa?" Ajiyar zuciya ya sake sauƙewa kan ya ɗan girgiza kai sai kuma ya gyaɗa kawai. Rita tayi saurin cewa "Ko dai Maaminka ce ke pressurizing ɗin ka? Matar abin da take yi bata kyautawa, kaman babu zuciya a ƙirjinta? Anya ita ta haif..." "Shut uppp! U are very stupid mahaifiyata kike kokarin jefa da kalaman raini? I won't take that wlh kika sake ko da ambatan sunanta ne sai kin sha mamaki na.." Yana kai nan ya ture ta ya fice daga wurin kujerun ya koma gaban table da masu kula da wurin ke ta sarrafa barasarsu ana cigaba da bawa masu siye wasu har da ƙanƙara ciki. "Wadda ya fi kowanne ƙarfi" Abinda ya faɗawa bar attendant ɗin kenan, shi kuwa ya san waye mukhy ya soma haɗa mishi kaman yadda ya buƙata ya gama ya tura mishi, cup ɗin ya zubawa idanu ya jima yana kallo kan ya kai hannu ya ɗauka yana ɗan jujjuya shi a hannunshi da alama dae contemplating yake ya sha ne ko kar ya sha, bakinshi ya kai da nufin sha sai yaji kaman muryan Baba na ce mishi "Duk wadda ya dawwama yana shan giya har ya mutu Allah ya haramta masa aljanna, ko ƙamshinta ba zai ji ba bare ya shige ta" Jifa yayi da kofin ta tarwatse ya miƙe ya nufi waje kaman kumurcin maciji, motanshi ya buɗe zai shiga yaji an riƙe shi "mukhy Meke damun ka ne haka? Is something wrong?" Juyowa yayi sai ya kallesu har su uku ne, Pepe, smart da Nawwaz ne, Smart da yayi maganan ya maida hankali kanshi yace "I don't really know wlh smart, bana jin daaɗin komai i feel lonely, tired nd lost" Pepe yace "ko dai ka gaji da Rita kana son chanza Babe? Though na san Dukda kana tare da ritan kayi Ƴan mata dayawa." "Ko sha'awar jin sunansu bana yi bare har in raɓesu, I hate everything wallahi tun jiya ko runtse idanuna na kasa da sunan bacci" Shiru suka ɗan yi kan Nawwaz yace "maybe you need space for Little bit ka ɗan huta, da dai zaka iya da mun koma ka zama high sai ka fi samun natsuwa da bacci yadda ya kamata" Kai ya girgiza ya juya zai shiga mota smart ya riƙe hannunshi "ba zamu barka kake driving kai kaɗai cikin wannan hali ba, zamu dinga kasancewa tare da kai har ka dawo daidai ko ya kuka ce?" Ya tambayi saura suka ce hakane a tare suka shishiga motar, Smart ya ja suka fice daga harabar wurin. **** Hawayenta ta share tare da ɗaga kai ta kalli saman ɗakin mutane are very wicked a wannan zamani namu, su kan manta cewa duniyar kwata-kwatarta bata da wani girma kuma aron rai aka bamu muke zama cikinta, bata san me zata kira iyalan Hassan dala dashi ba, menene suke dashi against waennan bayin Allahn? Ko rantsuwa tayi bazata yi kaffara ba akwai tsantsar son zuciya, hassada da baƙar kyashi a tare dasu waenda duk mugayen ciyuka ne masu zaftare imani ya ɗaiɗaita natsuwa da farin ciki, godiya ta cigaba da yiwa Allah da ya sa umar na gari da bata san yadda zata fuskanci Alayah ba idan ta farka, dole hankalinta ya tashi ta shiga damuwa saboda uwa ai wata giɓi ce da rasa ta rayuwa babban asara ce wadda mai da irin ita babu har Abadan Abada. Banko kofan da aka yi ne yasa ta buɗe idanunta tana kallon Alhj hammad da ya shigo har huci yake sbd fushin da bata san a ina ya kwaso ba yake shirin zuwa kanta ya juye mata kwandunansu. "Lafiya kuwa Alhj? Ya zaka bangaje kofan asibiti haka kuma babu sallama ka s...." "Shut uppp!! Ki dakata min Fatima, uban wa ya baki izinin kutse cikin ahalin Hassan dala? Menene naki da rayuwar gidanshi? Ina ruwanki da komai na gidan?" Ranta ta haɗe tace "ban gane ba, saboda na ceci ran da yake gangaren mutuwa a hannun waenchan azzaluman laifi ne? Na san abokinka ne Dukda abotarku be taɓa burgeni ba hasali ma na tsani alakarku saboda Hassan zuciyarshi babu Allah cikinta na daɗe da fahimtar hakan to ba zan zuba idanu a cigaba da zaluntar bayin Allah nan ba ko me zaka ce sai dae ka ce" "kin san me kike kokarin aikatawa? Kin fa san siyasata idan ba Hassan kaman babu ita ne, taya zaki yi kokarin yi min asarar mutum irin shi a gab sa'ar da burin raina ke gab da cika? Har ki aiki wanchan banzan ɗan n..." Da sauri ta katse shi "Umar ba banza bane Muhammad, kuma ba zai taɓa zama banza ba, ina zuciyar imaninka ya shiga ne? Cikin fa najasar kashi da fitsari, ɗauke da zazzafar stroke da hawan jini ya haddassa wanda ya assassawa matar chan shiga cikin come ya fiddo ta, shin wannan be zama abin alfahari ba? Menene laifin umar da ka ɗaura mai karan tsana saboda kawai ya saka idanu kan al'amuranka ya kuma tsaya tsayin daka wurin hana ka aikata mummunan laifin illata rayuwar matasa a cikin al'umma? Kar ka zama Hassan din mana! Kar zuciyarka ta yaudare ka wurin auren duniyar nan mana Abban Mukhtar.." Ta ƙarasa da karyayyen hawaye. "Ina ruwanku? In ma abinda ya fi fitsari da kashi ne ko comar banza ne duk babu ruwanki, ina ce nine na ɗauki yarinyar nan na aurawa Mukhtar? Toh zan saka shi ya sake ta ki tattara ta da ita da uwar da kuka jajibo ku watsar don wallahi zaki fuskanci mummunan ɓacin raina idan kuka yi sanadiyar lalacewar siyasa ta" Ya ƙarasa kaman zai kifa da ƙasa don masifa, har ya juya ya nufi kofa yaji Maami na cewa "ko menene zaka yi yanzu kam sai dae kayi Abban Mukhtar yanzu case ɗin ba tsakanina da Hassan bane tsakanin Umar da Hassan ne, shi zaka ja wa kunne amma ba ni ba" Juyowa yayi ya watsa mata wani irin kallo kan ya juya ya fice yana sake buga kofar, kanta ta maida ƙasa ta sake silalar da hawaye kan ta share ta juya ta fice don duba Ummi dake ICU tun jiya ko motsi bata yi ba kaman yadda Alayar ma take ta bacci tun a jiyan don daga ta tashi za'a sake mata allura ta koma tana bukatar cikakken hutu. Maami na fita ta buɗe idanunta tare da kurawa kofan, hawaye ne taji yana cika mata ido wato in ka hangi Maami daga waje zaka rantse da Allah cewa ta gama samun komai a rayuwa tana cikin daula da hutu ga kuɗi masu maganin matsaloli amma ba hakan ba ce mai ɗaki shi ya san inda yake mishi yoyo, ashe bayan jarrabawar Mukhtar tsakanin ɗaya ɗan ta da mahaifinshi babu zaman lafiya? Amma kaman maganan ummi ake? Sai yanzu kalaman ya ɗaukota cikin najasar kashi da fitsari da stroke wanda hawan jini ya haifar sanadiyar hakan tana cikin coma da wani irin hanzari ta miƙe zaune tare da fisge ruwan ba tare da ta damu da jinin da ya cigaba da bin tsintsiyar hannunta ba tayi saurin saka takalmi tayi waje. Bayan Maami kawai ta hanga hakan yasa ta haɗa da gudu tana kiran sunanta, da sauri Maami ta juyo tana ganinta ta nufeta tana salati "Menene haka Alaya? Meyasa zaki fusge ruwa daga jikinki haka? Dubi fa jinin dake zuba?" "Maami Ummi na ce? Ummi ce kuke maganar Shiga coma? Me ya sameta ummi? Garin yaya? Taya hakan zata kasance.....innalillahi wainna ilaihi rajiun.."" Gabaɗaya ta ma ruɗe ta gigice "Ki natsu Alayah tana cikin salama in shaa Allah Adu'a kawai take buƙata a halin yanzu daga gareki ba wannan kukan da ɗaga hankalin ba, in shaa Allahu yanzu ummi ta dawo wurina kenan har Abada ko da tana so ba zan bar ta komawa cikin uƙubar da ta fito ba" Maami ta ƙarasa da alhini, da sauri Alayah ta rungumeta "Na gode Maami mun gode sossai Allah ya saka miki da alkhairi, Allah ya biya miki buƙatunki na alkhairi ya saka ki cikin aljannah maɗaukakiya" Har lokacin bata daena hawaye ba, tana cikin wani sabon damuwar duba da yadda saɓani ke shirin shiga tsakanin Maami da Abban saboda su kuma. Jan ta Maami tayi zuwa ɗakin da aka kwantar da ummin, daga jikin window suka tsaya Alayah ta ɗaura hannunta bisa kai tana sake zub da hawaye, ummin ta ce haka? Me ya faru bayan barin ta gidan? Taya duk waennan abubuwa suka faru ba tare da ummin ta sanar mata tun wuri ba? Ummin ta aka bari da najasa Allah andi tsawon lokacin da ta ɗauka a hakan, kuka ta sake saki. "Ashe ba zaki ji magana ta ba Binty? Ban ce ki daena ɗaga hankalin nan ba saboda yanayin ki? Toh shikenan kiyi ta yi" Ta ƙarasa tana juyawa alamar tayi fushi da sauri Alayah ta riƙe hannunta tana anfani da ɗayan hannun wurin share hawayenta tace "Na daena Maami, wlh na daina ki yi hakuri" "yauwa ko ke fa? Mu je ki kimtsa ki samu ki ci wani abu sai a ƙara duba ki ko?" Kai ta gyaɗa suka juya suka nufi ɗakin ta, wanka tayi bayan ummi ta haɗa mata ruwa ko da ta fito ma ta samu ƙannen Maami Aisha da ruqayyah tare da wasu ƴaƴan yayyunta maza sun shigo, da farin cikin ganinta hakan suka shiga amsa gaisuwar ta suna mata ya jiki? Tana amsawa da jikin da sauƙi sossai, abinci ta ci wanda yayi mugun mata daaɗi faten dankalin turawa ne aka saka mishi ugwu ya ji kifi ice fish, bayan ta gama nurse da Maami suka shigo ta kara dubata kan ta mayar da ruwan, kwanciya tayi tare da juya bayanta idanunta a lumshe. Bayan tsawon lokaci hira tsakanin en uwan na tashi Aisha ta dubi Maami tace "Adda Bintu yanayin ki kaman kina cikin damuwa, Mukhtar ne?" Girgiza kai tayi sai yanzu ma ta tuna da Mukhtar din tun jiya bata ganshi a nan ba, ta san ba zai taɓa chanzawa ba ai. "Aisha wato dukda abubuwan Mukhtar na damuna sai dae abinda ke damuna a yanzu ya shallake wanchan, na rasa wani hanya zan bi wurin shirya tsakanin Umar da mahaifinsu da basa jituwa sam sam, Dukda ban taɓa ganin laifin umar ba duk na Abban nasu ne sai de abin na ci min rai sossai wallahi" Ruqayya tace "har yanzu ne rashin jituwar nasu? Na zata bayan doguwar nasiha da faɗan baba komai ya wuce?" Maami tace "kusan an samu sauƙin hakan amma daga sadda umar ya kama masa wani kaya ya kirashi ya cicci mishi mutunci shi kuma umar yayi rantsuwar har Abada idan har zai yi wani hulɗa da ya shafe lalata rayuwar al'umma ba zai taɓa bari ba, daga shi har Mukhtar ko inuwa basa haɗawa dashi saboda kowa da abinda ya fassara irin kariyarshi, yana nuna jarumta akan lamarin sai dae na lura abin na damun shi shiyasa sam baya son zaman ƙasar nan" "Ya cigaba da haƙuri wata rana duk zasu fahimce shi in shaa Allah, yanzu ki duba irin taimakon da yayi a kan baiwar Allahn nan, kina tunanin ko Abbansu Mukhtar ya isa fidda matar chan daga gidan Hassan a yadda ya kafa tarko yake kuma da gogewa da duniya? In ba irin umar ba bana tunanin zata tsira cikin sauƙi haka" Cewar ruqayya a hankali. Aisha tace "Allah ubangiji ya kyauta amma tabbas akwai wata rana da duk zasu yi nadamar hakan" Lumshe idanu Alayah tayi ta sake maimaita sunan Umar a ranta, ya taimaketa ita kam bata da abin da zata saka mishi anan duniya sai dae da Adu'a, lallai zuciyarshi a wanke take ko bata ganshi ba tunda zai iya saka hannu ya ɗauki umminta cikin najasa ya sakata a motar shi har ya kawo ta asibiti bayan ya fuskanci barazana daga Abban Jameelah. A haka bacci ya sure ta, bata farka ba sai dab Magrib, a hankali take motsi ta ɗan shaki numfashi tana jin kamshin turaren da taji rannan a sashen Maami me daaɗi, waigowa tayi don ganin me wannan kamshi sai suka haɗa idanu da Mukhtar, wani kakkauran miyau ta haɗiye cikin kokarin danne fargaba da tsoron da ya bijiro mata musamman idan ta tuna abinda ya mata kwanaki a asibitin chan da aka mata aiki. Da idanu yake bin ta har ta miƙe zaune, muryanta ta ɗan gyara ta ce "Ina yini?" Albarkacin ya girme mata kuma ɗa ga Maami. Be amsa ba sai kallon da ya cigaba da bin ta dashi, chan ƙasa ta ja tsaki tana kokarin sauƙowa taji ya ce cikin buɗaɗɗiyar muryarshi "Ke! Ni kika ja wa tsaki???" *Kar ku sha'afa Al'ajabin So book 2 is not free, a kan naira 500 kachal zaki same shi immediately after an kamallah book 1, zaki iya yin payment ta nan 3118518476 First bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya ta wannan layi 09039206763* #Vote #comment                      🖤Gureenjoh🖤 AL'AJABIN SO (heart touching story) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN.                      (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* *Kowa Ya ga zabuwa..* *Diddigar ƙaya... Paid* *Rubutu a kan ruwa... Paid* And now.. *AL'AJABIN SO* *BOOK 1* *Page Sixteen* *Na riga na yi alkawari in ba haka ba ina zan iya typing karfe 12🥲 sorry guys class nayi da ba zan iya dodging ba* Bakinta ta tura gaba ba tare da tayi magana ba Dukda tsallen da ƙirjinta ke yi kaman ana dakan sakwara, sai dai abu ɗaya da ta lura dashi da ya bata lasisin hakan shine ba'a chake yake ba kuma idan hakan ne ta san zafin ran nashi da sauƙi, ba zata taɓa gigin yi mishi hakan ba idan yana buge don zai iya ƙas da ita a wurin ba tare ma da ya san ya aikata hakan ba, ƙarasa sauƙa tayi tare da sanya silifas ɗin ta "Ke! Ina miki magana kin mai da ni banza?" Nan ma bata ce komai ba taku biyu tayi ya sanya hannu ya fusgo ta tayi baya luuu ya mata masauki a kan kafafunshi hannunshi ya sa ya zagaye ta yana me kurawa fuskanta idanu for the First time a rayuwarsu irin kallon nan na kurilla yace chan ƙasa "ba da ke nake ba Fatee?" Ba tare da ta kalleshi ba ta zumɓura baki tace "to ai ni sunana ba ke bane, ba gashi da ka kira sunan na amsa ka ba??" Ta karashe tana ɗagowa ta kalli idanunshi da suke nan launin jaja kuma a lumshe, runtse su yayi yana jin yadda wani abu ke fusgar shi zuwa gareta, ji yake zuciyarsa na tsukewa wuri guda ga dukkan alamu ginin da babu shakka na so ne yake ginuwa daki daki cikin zuciyar shi, ɗauke kai yayi daga kallonta tare da ɗan tureta, ta kuwa sake taɓe baki alamun kai ka jiyo dama ba ni na ajiye kai na ba, toilet ta shige ko da ta fito ma bata same shi ba. Da yammacin ranar aka bata sallama, gida suka dawo Dukda ta so tsayawa asibitin sbd ummin ta amma kuma ba hali don har yanzu tana ICU ne ba'a yarda ba ma da isa kanta bare a fara jinyar ta, likitoci da nurses ne kaɗai ke zuwa kan ta, ko da suka koma gida ma bata bar zazzabin laulayi ba, kuma ta fahimci har lokacin babu shiri tsakanin Maami da Abba kai tsaye zata iya cewa sune sanadi, iya kokari Maami na yi wurin nuna mata komai lafiya ai dae bata san ta riga ta fahimta ba. Kwance take kan kujera hannunta yalo ne take ci Dukda wani irin zazzabi da ya rufeta tana dukunkune sai rawan sanyi take kuma ta ƙi kashe Ac ko rage wa, Maami ta fita sai mama lami ne ke zuwa jin ko akwai wani abin da take buƙata ta kawo mata, bacci ne ya fara fusgar ta sam bata san Shigowar mutum ba ashe har ya kashe Acn bayan taɓa fuskanta da yayi ya ji jikinta raurau, baya baya yayi ya zauna kan kujera Red eyes ɗin shi ya zuba mata a ranshi yana ayyana dama haka mata suke fama ne ko ita ce kaɗai? Tun da aka ce tana da cikin nan ba zai ce ga sadda ya risketa lafiya ƙalau cikin ƙarfi da kuzari ba, ko yaushe gata nan dai ajiyar zuciya ya sauƙe a hankali yake jin duk wani rayuwarshi na baya ya fita kanshi fit, iya kokari yayi na daina shaye-shaye haka matan ma rabon shi da mace zai iya cewa ya manta, bashi da wani aiki sai na tunanin wannan yarinyar, wani sa'in ma yana son zuwa ɗin ya kalleta sai kuma wani sashe na zuciyarshi ya mishi nauyi, kunyar Maami ya lalaɓo ya rufe shi ruff ta yadda baya so ko haɗa idanu su yi. Shisha Pen da smart ya bashi ya fitar yana ɗan jujjuyawa sun ce zai rage mishi wannan damuwan da ya shiga a kwanakin sai dai yana shakka don ya san zasu iya sa wani abu na bugarwa ciki, bakinshi ya kai kaman ya sha sai ya ja tsaki yana ƙoƙarin sauƙewa suka haɗa idanu, girgiza kai tayi tare da Miƙewa bata ce mishi ci kanka ba ta zo zata wuce yayi saurin riƙe hannunta kula da yayi kaman ranta ya ɓaci kuma hakan ya nuna har a fuskanta, fisgewa taso yi ta mance ma riƙon maza ba irin na mata bane...wani zafi ne ya ratsa ta mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin shanu a take ta fashe mishi da kuka sossai har sai da ya tsorata. "Ni ka sakar min hannu..." Da sauri ya miƙe yana kokarin duba hannun ko ta ji ciwo ne sam be san masu ciki da wannan mood swings ɗin ba ya haɗu kuma da wani tunani da tayi kanshi, ganin ya sake ta yasa ta nufi sama, taku biyu yayi ya tare ta "Menene? Kin ji ciwo ne a hannun?" "Ina ruwan ka da ni? Menene damuwarka? Ba tunani aka ce in yi akan auren mu ba? To na gama ba zan iya cigaba da zama da kai ba wallahi, tuban muzuru ne kayi ba na Allah da annabi ba..." Shesheka ta ja tana matsawa baya ganin ya matso ta sossai yana kokarin taɓa ta don sam be fahimci inda matsalar ta taso ba tace "kar ka taɓa ni, burin kowacce mace a rayuwa shine ta samu miji nagartacce, mai gaskiya da tausayi, wanda zata iya ƙarasa rayuwarta a tare dashi, sannan bayan aure su samu New wonderful family, burin kowace macece ta samu abokin rayuwa wadda zai agaza mata wurin cika duk burikan ta na rayuwa, ya taimaka mata a sadda take neman taimakonshi, ya so ta ya kasance mai kishin ta, sannan wadda zasu fuskanci duk wani matsalolin su a tare, ayi nishadi wasa da dariya, a yi salloli cikakku guda biyar a rana nd inspire one another to increase their deen, ayi respecting juna nd live peacefully in this nd the life hereafter, ka gayamin wanne kayi daga ciki? Ko kuma wanne kake shirin yi? Ya Mukhtar ɗan ka ne ke shirin zuwa duniya amma gaban idanunshi Shisha ne kake shirin sha wadda babu tantama na san flavor din ba zai rasa surkin abin bugarwa ba? Idan ba zaka ji kunyata ba ni karamar dangar ka da ka saba shawowa ka juye min shi be chanchanci kunyar ka ba? Maami bata chanchanci ka mata kawaici ba a cikin parlorn ta zaka yi shaye-shaye? Ka matsa min na wuce ka sha kayanka amma ka sani wallahi ni dae na gama zama da kai.." Hawayenta ta share kan ta zagaye shi tayi sama da gudu tana kuka. Kaman wadda kwai ya fashewa a ciki haka yake jan kafafunshi jin gwiwowinshi na shirin sagewa su butulce mishi wurin kasa ɗaukar gangar jikinshi, zubewa yayi kan kujera zuciyarshi na wani irin yamutsuwa tare da kwakwalwan kanshi dake ta aikin tariyo kalamanta, wani irin sanyi yaji yana ratsa shi a hankali zazzafar zazzabi ya soma sauƙo mishi, kalamanta sun mishi nauyi sossai, rashin fahimtar shi da bata yi ba sai ya so haukata shi, Miƙewa yayi don barin gidan ko zai shaki iska mai kyau sai ga Maami ta shigo. A hankali yace "sannu da dawowa Maami" Kallon shi tayi da mamaki don ba halin shi bane hakan, sai kuma ta kula kaman bashi da lafiya ne kaman bazata yi magana ba sai kuma tace "yauwa! Lafiya kake kuwa? Ko dai cikin shaye-shayen ka shayo abin da yafi karfin ka?" Idanunshi ya runtse da ƙarfin gaske wani zafin ya sake ratsa zuciyar shi, dama haka ake welcoming wadda ya ɗauki hanyar tuba? Dama wannan na daga cikin kalubale da illar shaye-shayen ko kuma daga mahaifiyarshi da matar shi ne? Be iya ya tanka ba ya fice daga gidan, da kallo ta bishi har ya bace kan ta haura stairs, ɗakin Alayah ta tura don dubata sai ta sameta zaune tana game a wayanta kaman ma bata yi kukan matsalar gidan aurenta ba, taji sauƙin abin sossai da ta samu fitar da abin da ke ranta kuma da gaske ta gama zama da Mukhtar. "Sannu da dawowa Maami" "yauwa binty ana hutawa ne?" Kai ta gyaɗa tana murmushi "Maami kin yi waya da asibitin? Sun yarda zasu bari a ganta nan kusa?" Kai ta gyaɗa tace "Eh mun yi magana, baba ma dai ya bada shawarar a fitar da ita waje kawai amma dai muna nazarin hakan da umar, kar ki damu zata samu sauƙi in shaa Allahu. Yanzu dae albishir" Murmushi ne kwance bisa fuskanta da ya ƙara mata kyau sossai tace "Goro Maami fari ƙal ma ba ja ba" "Kin samu admission a skyline university" Tsalle ta tashi zata yi da hanzari Maami ta riƙe ta tana dariya, rungume Maamin tayi hawaye na tsillo mata tace "Alhamdulillah Maami na gode, na gode sossai Allah ya saka miki da alkhairi ya shirya miki zuri'a, Allah ya amsa dukkanin Adu'o'in ki ya biya buƙatun alkhairi" Cikin murmushi ta amsa da Ameen, sai kuma ta ɗago ta "Amma me ya sa kika zaɓi cyber security bayan baya cikin duk courses da kika lissafo min kina so?" Cikin murmushi tace "haka kawai na ji ina son karantar shi, kila shine Allah ya zaɓa min" Har daren ranar murna take da samun admission nata, Allah sarki Da ummi na cikin koshin lafiya da sai tafi kowa murna ta tabbatar da hakan. Da dare ta isa jikin kofa don rufewa kenan taji kaman ana magana murya sama, idanunta ta lumshe babu shakka muryan Abba ne kuma ta tabbatar da Maami yake don kaman magana ne da ya dangancesu Dukda bata jin shi clearly, da jikin kofan ta jinginu ba zata taba son su kasance tasgaro ga rayuwar Maami ba, ita ce mutum na farko a rayuwarsu da ta nuna musu suma mutanene kaman kowa suna da muhimmanci kuma suna da Ƴancin rayuwa yadda kowane mutum ke yi, ita ta basu mafaka a sadda suke tsakiyar rana da kunar zafin ta, da ba don ita ba da kila yanzu babu Umminta don ta tabbatar ba jinya Abban meela ze yi mata ba, sannan ga damar karatu ta bata wadda zai sauya mizanin rayuwarta, amma su kuma suna kokarin dakile farin cikinta da zaman lafiyanta, tana jin irin barazanar Abba har da aurenta yayi mata kan ya zo ya wuce kaman iska. Ta jima tsaye wurin kan ta isa ga gadonta ta kwanta idanunta runtse tunaninta ya tafi gabaɗaya ga neman mafitar wannan matsalar kuma, cikin bacci ta ji ana buga mata da sauri kuma a ɗan tsorace ta miƙe zaune, idanunta ta kaikaya kan ta sauko gabanta na faɗuwa ta tsaya nesa da kofan "wa....waye?" Shiru aka yi sai aka sake knocking "waye ne?" **** Zaune su ke a club ɗin shi dae ko idanunshi baya buɗewa in banda ma matsawar su Nawwaz babu abin da zai kawo shi club ɗin amma sune kaɗai abokan shi su ne masu debe mai kewa cikin sabuwar rayuwar da ya tsinci kanshi, En matan dake ta damunshi ne ɗaya ta matso ta shafa shi "Mukhy whats wrong with you? We dont like this mukhy we want our old mukhy back, menene kake so? Ka zo mu debe maka kewa mu mantar da kai duk wani damuwa, mu baka farin cikin da ka jima baka samu ba..." Hannun da take shafa shi ya ture ba tare da ya buɗe idanun ba "don't you dare touch me again" Ya faɗa chan ƙasa ƙasa har yanzu kalaman Alayah ne ke farautar rayuwarshi, idanunshi ya buɗe ya sauke kan smart dake rungume da yarinyar da ta gama lafaza shi a yanzu tsaki ya ja me karfi barikin fa kenan, Tsam ya miƙe tare da miƙawa smart din hannu ya bashi key. Ture yarinyar smart yayi tare da Miƙewa "ka san bama barin ka driving cikin situation din nan muje in kai ka inda zaka" Nawwaz ma Miƙewa yayi suka fito su huɗu zuwa motar shi, da gudu suka bar club ɗin, sauran su biyu duk a Buge suke yayinda smart dake driving ke bankawa cikinshi Shisha, shi dae oga kwata Kwata na kishingide abin duniya ya dame shi, daidai wani unguwa motar ta tsaya chak, idanunshi ya buɗe ya dubi smart "ya dai?" "Wlh ban sani ba mukhy ko zaka duba mana don ko na je babu abin da idona zai gani?" Gaban motar ya buɗe ya fice yayin da smart ya buɗe mai bonet daga ciki, ganin ya ɗan jima yasa duk suka fito, wurin shiru sannan hasken wurin ba sossai bane, layi ne a chakude da gidaje kala uku akwai na masu kuɗi jefi jefi haka akwai na daidai misali sai kuma na talakawa da suka fi yawa. Wata yarinya ce da bata wuci 16 ba ta taho hannunta riƙe da tray tana kuka, kuɗin cinikin ta ta ɓatar gashi matar ubanta bata da sauƙi akan sana'arta shiyasa ta kai yi warhaka bata koma gida ba, ta sa baban ta da Yayanta yanzu sun dawo idan kum yaddikonta ta kanainayesu da maganganun ta ɗaure ta zata kara yi yau ta shiga uku da babanta tunda duk abinda yaddikonta ta faɗa daidai ne, har ta wuce su ma bata maida hankali kansu ba sbd nata matsalar. Nawwaz ne yace "kai yarinyar nan tayi smart, anya ba zamu latsa ba?" Area ɗin suka dudduba jin shiru sossai yasa babu wani tunani yadda suka saba kayansu sa'i da lokaci suka bi bayanta, da bakinta suka fara da karfi suka ɗaure suka jata gefen ciyayi, sam Mukhtar be san me suke ba don hankalinshi na kan duba motar sbd babu abinda yake so a yanzu irin ya je gida ya kwanta ya cigaba da tunani. "Smart tada motar mu ji" Yayi maganan ba tare da ya ɗaga kai ba, jin shiru ya sa ya ɗago ya dae san sun fito waje to komawa suka yi? Sake motar yayi yana zagayowa sai de be ga kowa ciki ba, jin kaman nishi ya sanya shi ɗaga kai da sauri ya kallesu chan da alama ma sun gama lalata rayuwar yarinya da gudu ya isa ya ture Nawwaz, ɗagowa yayi ya tsinkawa smart mari "Me kuka yi? Me kuka aikata? Innalillahi wainna ilaihi rajiun" Daidai lokacin yarinyar ta kwalla ihu sai ga hasken touch ana kiran sunan da basu gama gane na wacece ba, da gudu suka yi mota Nawwaz janye da Mukhtar da da alama tsayuwa ya so yi, ihu yaron ya fara yayinda tuni smart ya figi motar baban ne da yake gani dishi dishi ya riƙe plate number ɗin, babu shakka sun kassara rayuwarsu ko daga yadda yayan yarinyar ke kuka sossai yana dagota ya rungume ya san hakan.... *Toh fa, Mukhtar sawu ka taka ko ya abin yake ne?* *karku manta book 2 na kuɗi ne, muna gama book 1 zamu ɗaura in shaa Allah zaki iya yin payment ɗin ki anan kan a gama ɗin 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai shedar biya ta 09039206763 in shaa Allah za'a saka sunan cikin list na paid da muke dasu ƙasa. Thank you sai na ji ku 🖤Gureenjoh🖤 AL'AJABIN SO (heart touching story) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN.                      (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* *Kowa Ya ga zabuwa..* *Diddigar ƙaya... Paid* *Rubutu a kan ruwa... Paid* And now.. *AL'AJABIN SO* *BOOK 1* *Page Seventeen* "Me kuka aikata Nawwaz? Akan me zaku yi raping yarinya alhali kun bar yammata sama da hamsin waenda suke shirye da tayin ku? Why? Why??" Gabaɗaya hankalin shi ya tashi irin yadda ba'a zato, su karan kansu sun shiga mamaki, sun ga dae har a ƙasar da ma ya fi Nigeria tsaro da komai yayi raping yarinya wanda ma sanadiyar zamanshi prison kenan har aka kore shi ya dawo Nigeria da karatu, to me zai dame shi anan da ma ba lallai a bi diddigi ba ko ma an bi suna da kuɗi wadda sun tabbatar a ƙasar nan zai musu maganin komai. Ganin suna kokarin tursasashi maida komai ba komai bane yasa ya daka wa smart tsawar ya tsayar da motar kuma su fitar mai daga cikin mota, haka ya baɗe idanunshi da toka sai da suka fita ya zagaya ya figi motar kaman baya son ranshi, har lokacin wani irin tension yake ji a cikin jikinshi gidanshi ya ƙarasa a parlor ya zube, ya rasa ma kalar tunanin da zai yi me yaran nan suka aikata haka? Bai san iya adadin lokutan da ya ɗauka a haka ba, a hankali ya buɗe idanunshi da suka sake shanyewa wayanshi ya zaro ya duba sai ya ga biyu saura, contact ɗin shi ya shiga ya samo Layin Maami ya zubawa idanu, a hankali abinda be taɓa zaton ze yi ba a rayuwarshi tun tashin shi wato hawaye ya cika idanunshi, damuwar da yake ciki yana son jin ko da muryarta ne kila ya samu sassauci, kira ya danna mata ya zubawa wayan idanu ba lallai ta ɗauka ba, dab zai tsinke ta ɗaga, a hankali ya sa a kunnen shi ya ji muryarta cikin bacci tana furta "Assalamu Alaikum warahmatullah Mukhtar? Lafiya?" Idanunshi ya runtse hawayenshi suka zubo, a hankali yace "Wa'alaikissalam warahmatullah Maami..." Sai yayi shiru ya rasa ma me zai ce mata, bayan duk abubuwan da ya mata a rayuwa ya kuwa chanchanci ta taya shi shiga damuwa saboda damuwar shi? "Uhmm ya aka yi? Menene?" Uwa kenan, ya faɗa a ranshi yana sake jin wasu sabbin hawayen sharr, zuciyarshi na wani irin chunkushewa cikin tsananin damuwa da karaya, gaɓɓan jikinshi duk sun yi sanyi saboda rashin natsuwa da bashi dashi gabaɗaya kwanakin, har zafi zafi yake ji a cikin jikinshi kaman me masassara. "Maami ina cikin damuwa ne, na kasa bacci, na kasa samun natsuwar zuciya na rasa abin da zan yi na ji daaɗi, ki taimake ni please" Wani abu taji ya tsarga mata har cikin ranta, Allah sarki uwa bata san ta miƙe zaune ba, a hankali tace "baka da lafiya ne? Ka je asibiti?" Girgiza kai yayi "Maami lafiyata ƙalau kawai komai ne baya min daaɗi Maami" Shiru tayi na seconds kan a hankali cikin son tabbatarwa tace "ka sha wani abu ne da ya fi karfin ka ko?" Da karfi ya runtse idanunshi dama ya san zata yi tunanin hakan, kuma ya ji a jikinshi ba zasu taɓa fahimtar nadama da tuban shi a kusa ba, yayi mamaki ma da ta saurare shi, a hankali yace "Maami wallahil azeem rabona da in sha wani abu tun ranar da muka zauna gaban baba" Nannauyar ajiyar zuciya da har ya ji daga inda yake ta sauƙe. "Ka je kayi alwala ka faɗawa Allah matsalolinka in shaa Allah zaka samu natsuwa" Kai ya gyaɗa kaman karamin yaro kan yayi mata godiya suka kashe wayan a tare, Miƙewa yayi ya nufi ɗakinshi har ya shiga sai kuma ya tsaya kaman me nazari, wardrobe nashi ya nufa ya duba ya ɗauki three quater da wani armless Black shirt tare da sabon towel ya fice daga ɗakin don be yarda da ɗakin ba har wani kyamar ɗakin yake ji. Ɗakin Alaya ya shiga lumshe idanu yayi yana sake jin sabon hawayen tausayinta, anan ya mayar da ita prisoner a cikin wannan ɗakin ya shigo ya jata gaban abokai ya ɗura mata abin maye ba tare da ya damu da cewa ita ɗin tsarkakkekkiya ba ce, bayin ta ya nufa yayi wanka ya sanya kayan ya zo ya tsaya kan sallaya, a hankali ya ji Muryarta a sadda take ce mai a lokacin da ya ɗauketa daga asibiti zuwa Hotel zai yi sallah. "Ya Mukhtar namiji fa daga cibiyar shi zuwa guiwowinshine al'auranshi, Kaga zaka yi sallah kuma wandon be kai guiwa ba be kamata ba" Yana iya tuna yadda take mai magana a lokacin ma cike da tsoro. Ɗakinshi ya koma jallabiyar nan da Dr ya taɓa bashi kyauta ya ɗauka ya saka kan kayan ya dawo ɗakin ya kabbara sallah cike da Fatan Allah ya amsa ya sassauta mishi abin da yake ji yana damunshi. *** "Ki buɗe" Abin da taji kenan da ya sanya gabanta dokawa. Cikin rawar murya tace "Abba? Lafiya?" A harzuke yace chan ƙasa "na ce ki bude kofar nan" Hannunta na rawa ta buɗe da sauri ta ja baya ganin ya afko ya rufe "ke! wace irin mutum ce ke? Dama Alhassan ya min gargadi duk inda kuke babu alkhairi a tare daku musamman ma ke, kin san me kike shirin aikatawa?" Girgiza kai tayi tana jin tashin hankali na bijiro mata. "Zaki kashe auren macen da ta taimake ki ta taimaki mahaifiyarki ta so ki tsakani da Allah, kin mata adalci kenan? Kin san me uban su ya fi tsana? To babu abin da ya ƙi jini a duniya irin saki, barin ma na ƴar cikinshi, me kike tunanin zata fuskanta ta koma ga mahaifinta tsofai-tsofai da ita da takardar saki?" Zuwa wannan gaɓar tuni hawaye ya wankewa Alaya fuska, sai ta ji murnar karatunta ya koma ciki, in tayi wa Maami haka bata kyauta ba, sai dae ina zasu je? Ya zata yi da ummin ta? Kaman ya shiga zuciyarta yace "Zan ba ki makudan kudade da zai ishe ku rayuwa, kuyi nesa da mu da rayuwarmu dama Mukhtar ba soyayya tsakaninku zan sa shi sakin ki a gobe ku yi nesa da mu na har abada" Kanta ta mayar ƙasa hawaye ya silalo mata. "Kin amince?" Kai ta gyaɗa a sanyaye "daga yau bana so ki sake kwanar min cikin gida a gobe zan sallame ki" Yana kai nan ya juya ya buɗe kofa ya fita, a wurin da ya barta ta sulale ta zauna tare da fashewa da kuka, sake tura kofan da aka yi ne yasa tayi saurin ɗagowa a firgice ta miƙe tsaye! **** Mahaifin wannan yarinya da aka yiwa fyade ne ya riƙe hannun Yayanta dake kuka kaman ranshi, a hankali cikin lullube tsananin tashin hankalin shi yace "karka taɓa ta Bashir, barta bari na ƙira dan uwana" Cousin nashi ne comissioner of Police iyayensu mata sun haɗa uba, kuma kusan kaman abokai suka tashi Dukda tazarar arzikin ubanninsu ya banbanta nesa ba kusa ba, ringing uku ya dauka "Ɗan Uwana yau kuma da mu aka tuna?" Hawaye ya sirnanowa dattijon cikin karaya yace "Ɗan Uwana wannan kiran na neman agaji ne, ka taimakeni ina da da bukatar ka a yanzu, an wulakanta ni an tozarta rayuwar ƴata an illata min yarinya" Hankalinshi ya dugunzuma ya tashi jin dattijon na kuka sossai, tabbacin gashi nan ya bashi da ambulance bayan jin mummunan ta'asar da aka yi mata. Ba'a fi awa ɗaya ba sai gasu har lokacin daga baba har Bashir an rasa me ba wani haƙuri sai kuka suke yi, da ambulance da wasu polisawa aka zo, Allah sarki yarinya abin tausayi haka aka ɗaga ta zuwa motar asibiti da wasu Police mata ya haɗa su inda ya tsaya gun ɗan uwanshi don jin kanun zancen. Be ɓoye mishi komai ba duk ya faɗamai har da plate number ɗin, kwarai ya jinjina kokarin baban a take a daren suka soma bin hanyoyin da duk za'a bi don gane me wannan motar, abin ka da comissioner of Police ne ke ciki tsundum ba'a kira assalatu ba sai da aka gano motar Mukhtar ce, su ba ɓoyayyun mutane bane, don haka a take ya bada umarnin a je a kamo mishi Mukhtar dama kuma yana da ajiyayyen record a interpol, me hali ba zai taɓa fasa hali ba, maza maza a kawo shi. Makara yayi, a sadda ya buɗe idanunshi yaji ana sallama a masallaci, da sauri ya miƙe be tsaya wanka ba yayi alwala ya taho ya zo yayi sallah, anan ya zauna duk wasu Adu'o'i ba wai ya iya bane tunda karatun islamiyyar shi na je ka na yi ka ne yayi, zafin mahaifinshi yake ji har ranshi, yana tuna a lokacin in an bugeshi ya ce ba zai kara zuwa ba Maami na masifa haka Abba zai baɗe idanunshi da toka ya bashi goyon baya kuma ya hana shi sake zuwa sai ranar da ya ga dama, yana tuna har a gida an sha kawo malamai musamman don shi yana korarsu da sharri kala kala Abba be taɓa cewa hakan ba daidai bane, be taɓa gyara mishi ba, be taɓa tsawatar mishi ba... Door bell ake ta dannawa wanda hakan ya sa ya miƙe yana duba time, shidda ma be cika ba lafiya?" Yana isa ya buɗe sai idanunshi suka sauƙa kan polisawa kusan guda biyar dake tsatsaye gaban kofan parlorn they are even armed gasu manya manya, murmushin takaici yayi dama ya san hakan na iya faruwa, sai dae kuma gabanshi dake ta faɗuwa da tsoron halin da zai jefa Maami da Alayah idan maganan ya riske su, karamin ciki ne da ita idan yayi sanadin shi fa? Sai yanzu yake jin wani irin son abun cikin nata na shiganshi, bakin Police ɗin ya zubawa idanu a sadda yake cewa "Mukhtar hammad you are under arrest for the suspect of rape, u have the right to keep quit as anything you utter will be Proof against you in d court" Hannayenshi ya dunkule ya miƙa musu suka sanya ankwa, sai da suka fito ya ga ashe akwai wasu zagaye da motar da ya dawo dashi jiya, daga shi har motar aka ja sai Police station. *Kuyi hakuri da Page na yau, ban wani zauna bane. Thank you* *karku manta book 2 na kuɗi ne, muna gama book 1 zamu ɗaura in shaa Allah zaki iya yin payment ɗin ki anan kan a gama ɗin 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai shedar biya ta 09039206763 in shaa Allah za'a saka sunan cikin list na paid da muke dasu ƙasa. Thank you sai na ji ku 🖤Gureenjoh🖤 AL'AJABIN SO (heart touching story) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN.                      (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* *Kowa Ya ga zabuwa..* *Diddigar ƙaya... Paid* *Rubutu a kan ruwa... Paid* And now.. *AL'AJABIN SO* *BOOK 1* *Page Eighteen* *Ku yi haƙuri ku sa min Abdulraheem a Adu'o'inku please Allah ubangiji ya bashi lafiya gobe zamu yi tafiya zan kai shi asibiti, idan na samu sarari zaku ji ni in shaa Allah* "Maami" Ta kira sunan da tunanin kar ta ga fitan Abba daga ɗakin nata ne, gabanta ta iso ta riƙo hannunta.. "Binty me ya faɗa miki?" Shiru tayi kanta ƙasa ba tare da tayi magana ba sai hawayen da ya cigaba da zuba mata "kar ki damu na jima da tashi sanadiyar kiran Mukhtar to sai na kasa komawa bacci, ina cikin nafila na jiyo motsi da kuma buɗe kofa hakan ya sa na fito, har ya fice bai san da tsayuwata ba kuma ba zan taɓa faɗa mishi na ga zuwan shi ba, abinda kawai nake son sani shine me yake so da ke?" "So yake mu yi nesa da ku" Girgiza kai tayi ta sake riƙe mata hannu "kar ki ɗaga hankalinki Alaya, ban shigo rayuwarku don in lasa muku zuma a baki in kuma janye ba, na san kila har barazanar da yayi mini ɗazu ya faɗa miki don ki ji ba daaɗi karki damu na fi kowa sanin Alhj, gidan shi dae zaki iya bari amma ba dae rayuwar mu ba, mun riga mun zama en uwa, har gobe ni matsayin uwa nake a gareki yaya a wurin umminki kinji?" Rungume Maamin kawai tayi tana murmushi me haɗe da hawaye, Maami ta zama komai na rayuwarsu, da gaske Allah ya turo musu ita ne don ta taimaka musu ta fitar da su daga uƙubar da suke ciki, lallashinta Maami tayi ta yi har sai da ta ga ta koma bacci kan ta fice daga ɗakin, bata iya ta yi baccin ba ita kam haka ta kwana kai wa Allah damuwowinta, da asuba tare da masu aikinta ta shiga kitchen suka kama aikin breakfast, tsab suka gama ta bar su su shirya ta haura sama tayi wanka, tana fitowa Alaya ma na fitowa, gaishe ta tayi ta amsa fuskanta da fara'a as always tana mata ya jiki, ita dae Alaya na matuƙar mamakin hallayyar Maamin sam bata yarda da sa damuwa a ranta har ya nuna ga fuskanta ba. Suna isa dining da niyyar cin abinci sai ga Abba ya shigo, Maami ne ta fara gaishe shi ya amsa ba yabo ba fallasa, Alaya ma ta gaishe shi ya amsa da kyar, Maami ce tayi serving nashi ya ja gabanshi ya soma ci, ita dae Alaya juya spoon ɗin kawai take kaman yadda ta kula Maami ma ba wani cin kirki take ba, Tv dake aiki daga parlor ne aka soma labaran safiyar... Da wani hanzari duk su uku suka miƙe tsaye, Abba ne gaba wurin isa cikin parlorn daidai me kanun labaran na cewa "Mukhtar dai ɗa ne ga ɗan takarar Gomna wadda aka fi sani da honourable Hammad Abdulhameed chanji... In ba'a manta ba Mukhtar dae na da tabo a hukumar na en sanda inda ya ci firsuna na wa'adin shakaru takwas a ƙasar waje to dai gashi nan labari ya sake maimaita kanshi ku biyo ni don jin cikakken labarin" Kokarin zubewa ƙasa Abba yake Maami da ita ma take jin bata da wani karfi, firgici da damuwa haɗe da wani irin tashin hankali suka rufeta tayi kokarin tura shi a madadin ya kai ƙasa sai ya zube kan kujera yana jiƙewa da wani gumin tashin hankali. Alayah ce da ita ma karfin hali tayi wurin riƙe Maami suka zauna a tare, babu wadda ya iya magana sai tvn da suka ƙurawa idanu suna jiran kanun labaran kaman kuwa a mafarki aka hasko hannayen Mukhtar ɗaure da ankwa "A safiyar yau ne en sanda suka yi tattaki har gidan ɗan ɗan takarar nan honourable hammad Abdulmajeed chanji wato Mukhtar hammad chanji inda babu ɓata lokaci suka kame yaron nashi bisa zargin aikatawa yarinya karama ƴar shekara 16 fyade a daren na jiya, inda suka bar yarinyar cikin mawuyacin hali ga wakiliyar mu nan daga asibitin da aka kwantar da yarinyar" A take aka hasko iyayen yarinyar mahaifinta na kuka, haka en uwanta tsiraru da suke asibitin ɗaukewa aka yi aka dawo kan ɗan jaridan ya cigaba da cewa "a wannan lokaci da siyasa ke gab da wanzuwa a jibi jibin nan jama'a dayawa da suke ƙarƙashin tafiyar ta honourable sun soma janyewa, ga kaɗan daga bakunan jama'ar" Wani aka hasko yana cewa "mutumin da ya gaza ba ɗan shi tarbiya taya zamu yi zaton zae tafiyar da mulki, wannan halaka mu zai yi bama yi.." Na bayanshi suka amsa da bama yi bama yi, aka sake hasko wani haka dae aka yi ta hasko mutane suna fadin albarkacin bakin su duk babu wani daaɗin ji.. Wayan Alhj en jam'iyyarsu suka soma kira sai dae motsin kirki ya gaza, jikinshi banda rawa babu abin da yake, shikenan abin da yake gudu yana tunanin yana da ikon dakatarwa ya faru, wannan shine ta faru ta ƙare ga ƙoshi ga kwanan yunwa! Ya gama shiryawa da Alhj Hassan akan in ya kori su Alayah dole in sun tagayyara su koma mishi tunda shi kadai suka sani sai gashi ɗan da ya fifita ya ɓallo mishi ruwa, ruwan da zai mishi ɓarnan da baya tunanin zai taɓa taruwa ɓallewa zai yi ya shiga gari, da sauri ya ɗauko wayanshi dake ringing ya duba, chairman na party din su ne. Wani irin faɗa yake da masifa, akan me Abba ba zai tare danshi ba in ya san bunsuru ne yanzu suna ji suna gani haka partynsu zata ci kaye, sun yi duk yadda zasu yi sun danne batun baya amma wannan ya tashi musu kamar wutan daji kowa sai gani yayi a duniya, shi dae ya kasa cewa komai tunda hankalin Ƴan partynsu ya riga ya tashi haka wannan abu ba mai gyaruwa ba ne, Maami da ke zaune kaman mutum mutumi da Alaya da kanta na ƙasa zafin da ranta yayi ba sossai ba tunda dama ta riga ta cire rai da Mukhtar ta san ba zai taɓa gyaruwa ba, girgizan da tayi ma na don abun cikinta ne, hannunta dafe da cikin tana tunanin me wannan ɗa zai ɗauketa a rayuwa? Kawai sai faɗuwar Abba suka gani... **** "ba za kayi magana ba?" Shiru yayi yana kallon jibgegen ɗan sandan dake gabanshi cikin su biyar da suke tsaye, be tanka ba sai ma idanunshi da ya lumshe Allah kaɗai ya san abin da yake ji cikin ranshi, ina ma da zai iya saka hannu a kai yayi ta ihu ko duniya zasu fahimci tashin hankalin da yake ciki, duk yadda aka yi ya san zuwa yanzu magana ya riga ya kai kunnen Maami da Alayah, zasu sake yarda da shi a duniya? Menene wannan yake farautar rayuwar shi? Ko dai zunubanshi ne ya soma girba tun yanzu? Kulkin da aka sauƙe mishi a gwiwa ne ya saka shi buɗe idanun yana kallon Police ɗin ba tare da yayi motsi ba, ya tabbatar daga safiya zuwa yanzu da ake durfafan azahar da gwiwowin nan zasu fita da sun riga sun bar jikinshi, tun yana ma jin azaban dukan har ya daina ji, nauyin kirjinshi ya fi mishi azaba fiye da dukan, sai zullumi yake kila ciwon zuciyar Alaya ya tashi, kila Maami tana chan tana ta kuka watakila ma tana asibiti a kwance hawan jininta ya tashi, tsintar bakin shi yayi da furta "Astagfirullah! Ya Allah ka sassauta musu" Duk yadda suka yi yayi magana ya ƙi cewa komai, gabaɗaya idanunshi da fuskanshi sun sauya sai gumi yake jika shi, kafafunshi baya ko motsa su haka suka haƙura suka fice, suka je suka sanar wa comissioner, asibiti ya ƙira don jin ko ta farka aka tabbatar musu da ta farka sai dae ba kanta, statement din ta suke son samu su tura shi court don haka ya bada umarni a cigaba da mishi horror kala kala har sai ya faɗi gaskiya. **** Daga Maami har Alayah babu wadda ya motsa tun da suka shigo asibitin, dangin Maami da na Abba na nan birjik Abba na halin mutuwa ko rayuwa sbd jininshi da yayi hitting fiye da ƙima, Ƴan uwan Maami sai jimami suke yayin da Ƴan uwan Abba ke jefo kananun maganganu wadda kai tsaye Maami suke alaƙantawa da lalacewan Mukhtar, ita dae tana jin su bata tanka ba kuma ta gode Allah da yaddikonta dake wurin ta hana duk sisters din ta magana, Baba ne ya shigo ward ɗin da sauri Maami ta miƙe ta isa gabanshi hannunta ya riƙo "Faɗimatu!" Kaman jira take ya kira sunanta kawai ta zame ta fashe da wani irin kuka dake cin ta a rai, Mukhtar kila sai ya kasheta ne hankalin shi zai kwanta, in ta bar mishi duniyar sai ya fi jin daaɗinta, zuciyarta ya riga ya kuntata fiye da tunani, ita kaɗai ta san me take ji a ranta kunnuwanta kawai ke jin duniya gabaɗaya na tsinewa Mukhtar, kukanta sai da ya sa mutane dayawa kuka ciki har da Alayah, mahaifinta ya ɗago ta suka isa kujerun gefe guda suka zauna nasiha ya dinga yi mata akan jarabawar Allah, har misali yake bata da ƴaƴan annabawa suma Allah be bar su ba, ko ta manta jinin Annabi Adam shi ya fara kisa a duniya? Ta mance ƴaƴan annabi Yakub ɗan uwansu suka so halakarwa mahaifinsu yayi kuka har idanunshi suka makance? Ko ta mance ɗan annabi nuhu da ya kafurce yayi ikirarin hawa tsauni zai taimaka mishi wurin gujewa fushi da azabar Allah kuma Allah ya halaka shi a kan idanun mahaifinshi? Ta natsu ta cigaba da Adu'a idan yana cikin masu shiryuwar Allah zai shirya shi, sossai hankalin ta ya kwanta da nasihun baban, inda ya duba jikin Abba kan ya ɗauki yaddikonta suka tafi kafin ya tafi sai da ya sake kwantar musu da hankali ita da Alaya. Masallacin asibitin suka je suka gabatar da azahar, Adu'a sossai Maami tayi kan suka fito zuwa ɗakin abinci da aka yi ta kawowa ta saka Alaya a gaba ta ci ita kuma ta sha baƙin shayi, call ne ya shigo ma Aunty ruqayya ta duba kan tace "Allah sarki umar ne, kila labarin ya je mishi hankalin shi kuma zai dawo kan Adda ruqayya gashi jiya jiyan nan da safe ya koma" Maami ce ta mika hannu ta karɓa dama ita ma tunanin shi take a ranta, ɗagawa tayi tare da Miƙewa ta matsa daga inda suke sun jima sossai suna magana kuma shi ma ya sake bata kwarin gwiwa, so ma yayi ya zo Dukda ba don Yayan shi ko Abbansu zai dawo ba don Maami ne kawai to amma ba zasu bar shi a wurin aiki ba, abubuwa dayawa na hannunshi. Har zai kashe tace "Amma auta ka ji daga shi Mukhtar ɗin?" Daga chan ya ɗan yi shiru na seconds kan cikin natsuwa ya ce "Maami na ji, sai dae har yanzu ba wani abu be ce musu komai ba, kuma ba horon da basu mishi ba" Ajiyar zuciya ta sauƙe tace "Toh na gode sai anjima" A hankali ya sauƙe wayan ya bi da kallo, uwa fa kenan! Sai kusan la'asar Abba ya farka, ko magana ya kasa, abinci ma da kyar ya sha shayi, kab rayuwarshi be taɓa jin haushin Mukhtar irin na wannan karo ba, wani irin karta ranshi ke yi, Mukhtar da ya yarda dashi shine ya cuce shi, ya tarwatsa mishi siyasa, haushin da yake ji na kowa yasa mutane suka ɗan ragu, guards sun cike wurin sbd Ƴan jarida da suka taru kaman an kira su, ganin haka yasa Maami ta ce ɗan uwanshi ƙanin Alhjn a cikin mahaifinsu zaid ya zauna dashi ita zata koma sbd Alayah, har zata fita ta tsaya ta dawo da baya kadan tace tana kallon Abban da karyayyen kallo zafin kirjinta na fita har a kan harcenta. "Babu wata uwa da zata yi farin ciki da lalacewan ɗan ta, amma ko babu komai yau na ji daaɗi da muka raba ɗacin lalacewar Mukhtar wadda kai ne sanadi, ko babu komai Allah ya nuna maka ba sai ka zalunci wasu ne zaka yi nasara ko ka fadi ba, Allah baya zalunci kuma ba ya barin me yi, ko ka nufi gyara kuskuren da ka tabka daga yanzu ko kuma ka cigaba da girban abin da kai ka shuka dama na sha faɗa maka akwai ranan ƙin dillanci" Tana kai nan ta juya ta fice tana goge kwallar ta, idanunta ke haska mata kaman yau ne tana shirin tarbiyatar da yaronta Alhj na rusawa daki-daki, shi karan kanshi be ga laifinta ba sai ma kunya da nauyi da suka rufe shi, idanunshi gabaɗaya sun rufe ya cutar da rayuwar Mukhtar sossai wadda sai a yanzu yake jin be kyauta ba, kunyar mutanen duniya ya rufe shi, tsoro da shakkar kamuwar tsinuwar bakinsu ya lulluɓe shi, shine da kaso mafi tsoka ya sani amma shi a ganinshi duk soyayya ce ashe ba haka ba ne, hawaye ne ya gangaro mishi. "Yaya ka yi haƙuri kayi kokarin cire damuwa a ranka in shaa Allah komai zai wuce" Zaid ya faɗa, murmushi kawai yayi me ciwo be sake cewa komai ba. **** "ba mutum ɗaya ba ne...!" Ta faɗa da kyar a sadda ta farka cikin kuka, ƴar sandar ta gyara tace "Ki kwantar da hankalinki kin ji? Ki natsu babu wadda zai sake cutar dake yanzu kina hannun hukuma ne kuma ba sa zalunci bare cuta, ki gayamin duk abin da ya faru kin ji?" A hankali ta ba yar sandar labari ita dai ta san mutum uku ne, kuma sam bata lura da ko sun kai nawa tsaye a wurin ba hankalinta na kan kudin da ta batarwa yaddikonta sai a lokacin mahaifinta yake jin wasu abubuwan ma da be san suna faruwa da ita a gidan ba, kai tsaye wannan Police ta nufi office nasu. C.P ta kaiwa report din yana dubawa yace a je a sake tuhumar muktar har sai ya faɗi sauran, duk yayi ignoring calls da yake samu daga sama saboda wannan case ɗin ba mai kasuwa ba ne, ko ba familynshi aka taɓa ba sai inda karfinshi ya kare bare na gida ne, cikin kokarin cika umarni wasu daban suka sake nufan ɗakin na Mukhtar don tambayar shi da kyau.. *littafin nan paid ne book 1 ne kaɗai free Pay ur 500 through dis account 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai shaidar biya ta 09039206763* 🖤Gureenjoh🖤 AL'AJABIN SO (heart touching story) Fatima Muhammad Gurin (Gureenjo) Adabi Writers Association Book 1 *Page Nineteen* *Assalamu Alaikum warahmatullah, Fatan duk muna lafiya? Ina ganin ya kamata mu dinga yiwa juna adalci, ina nufin tsakanin makaranta da marubuta, lallai a tafiyar da muke zuwa yanzu na fahimci cewa makaranta ku ke da kaso mafi girma na sanya marubuta aran halin da ba nasu ba su yafa, kuma kun fi kowa yayata cewa marubuta na da girman kai, this and that, ina magana ne based on experience ba da ka ba so duk wadda be ji daaɗi ba yayi haƙuri kuma a gyara, Marubuci zai ɓata lokaci kwarai wurin bincike da rubutu, ya kashe duk wasu abubuwa masu muhimmanci nashi ya zauna don faranta muku dayawa kuna bibiya kuma ana ƙaruwa amma kalmar an gode ma ya zama matsala bare comment, ana tafiya dai a haka saboda burin kowani marubuci ya isar da saƙon da zai anfani al'umma, muna cikin wannan tafiyar na ce yarona ba lafiya zan kai shi asibiti billahi wasu ba su iya cewa Allah ya yaye ba, amma suna gaba gaba a wurin bi na Pc ana cewa ana ta jira shiru, a'a ana kashe musu kwarin gwiwar karatu, an shanya su this and that! Sister ashe babu daaɗi? Yanzu idan na buɗe na ga wannan saƙo saboda bin cewar Manzon Allah na ka faɗi alkhairi ko kayi shiru na ƙi magana sai fa a ce girman kai ne ko wulakanci ko? Toh Allah ya kyauta. Na kawo wannan ne ba don rashin ɗa'a ba don nan ɗin gidan tarbiya ne ba haufi sai don mu tattaru mu gyara, mu zama masu adalci a tsakanin juna, adalcin ne yasa duk ba zan yi Page ba sai na zo na faɗi dalili, don Allah mu karfafawa juna gwiwa wurin zamantakewa da kuma cigaban juna don kowa na da ƙaruwarshi a duk wani tafiya na duniya. Bissalam* •••• "Astagfirullah" Ya furta bayan ya shafa dogon adu'ar da ya jima yana yi tun bayan sallame Sallar asuba da ya gabatar, ya godewa Allah maɗaukakin sarki da ya kasance adalin adilai, maji ƙan bayi wadda bai taɓa tantance da yaren da za'a roƙe shi ya amsa ba, don da be san ta yadda zai fara ba, Sallar ma yayi shi ne babu tabbacin isar shi saide ya roƙa akan Allah ya shirya shi ya ɗora shi hanya madaidaiciya, ya kuma bashi ikon gyara kura-kuranshi tun kafin ya koma gareshi a zero, Shigowar wani kurtun Police ne ya sa shi sa hannu ya kare haske tarrrrr da ya bayyana mishi yana kokarin illata jijiyar ganinshi don ɗakin duhu ne yake zaune ciki. "Ana buƙatar ganin ka" Ya faɗa ya ja baya ya tsaya rike da kulkin shi, a hankali Mukhtar ya fito kafafunshi sun yi kumburar da baya iya taka su da kyau, dafe da gini ya dinga tafiya har suka isa office ɗin na C.p, kaman yadda be kalli duk jama'ar da suke kallonshi ba daga jami'ai har civilians haka be tanka maganganun da suke jifan shi dashi ba, ko da suka shigo be ɗaga idanunshi ba ya ja ya tsaya, a tunanin shi mahaifinshi ne zai sa a kawo shi ya ganshi alhali shi duk duniya a halin yanzu babu wadda ya tsani gani kaman mutumin da ya kawo shi duniya. "Mukhtar" Baba ya faɗa bayan ya gama kallonshi, babu abinda ya firgita shi irin tatoos na jikinshi kasancewar bashi da riga duk wani tatoo da ya kashewa makudan kuɗaɗe wurin zanawa gasu nan raɗau akan farin fatar shi, gashin kanshi da nashi ne yaje aka murde tsakiya ya zama dada aka kuma penta shi kalar ƙasa daga sama duk gasu nan zube har wuraren goshinshi, ɗaga idanu yayi ya kalli Baba ba tare da ya motsa ba, hannu baba ya miƙa mishi sai ya soma takawa kaman me tsoron tafiya ya isa gabanshi ya durkushe bisa gwiwowinshi a karo na biyu bayan fahimtar waye shi a duniya ya fashe da kuka me cin rai, kukan tsantsar takaicin rayuwarshi da nadamar abubuwan da ya aikata gabaɗaya rayuwarshi, kukan baƙin cikin kasancewarshi mashayi, mazinaci, azzalumi tunda yana iya zaluntar kowa ya kwana lafiya hakan kuma ya zamar mishi abin tinkaho a baya, hatta matar aurenshi ya zalunceta to me zai zauna duniyar yayi? Ya fi mintuna ashirin yana wannan kukan wadda duk jama'ar da suke wurin suka shiga tsantsar mamaki babu wadda zai yarda sbd wannan fyade ne yake kuka kaman yadda Baba ya katse mishi kukan da cewa "Mukhtar na tabbatar ba kukan halin da kake ciki ba ne kake yi, a duk abin da zai faru kana da yaƙinin mahaifinka zai fidda ka, shi ma kuma bashi da wani tunani in dae akan ka ne ko nawa zai iya kashewa tunda kudi ba matsalar shi bane, Mukhtar kalli jikinka kaman ba na mutane ba? Ka kuwa san haramci tatoo? Kalli gashin kanka irin askin da annabi ya hane mu dashi ka kwashe rabi da rabi ka bar tsakiya, Mukhtar baka tsoron hukuncin Allah a kanka? Baka tsoron fushin shi ya haɗu da na mahaifiyarka ya haifar maka da babban iftila'i? Ko ka san kuɗi ba zasu taɓa ceton ka daga fushin ubangiji ba?" Be iya yayi magana ba sai a sadda ya ji sassanyar Muryar mahaifiyarshi da ma sam be lura da ita ba tana cewa "Mukhtar kap rayuwarka cikin kowani rana baki na bai taɓa hutawa ba wurin yi maka nasiha akan abubuwan da kake aikatawa, ban taɓa gajiyawa ba da ɗaura ka akan hanyar Allah da manzonsa haka ban taɓa gazawa da kai kukana wurin Mahalicci ba da ya shirya min kai, Mukhtar ka san irin kunar da nake ji a zuciyata daga jiya zuwa yau kuwa? Wani irin rashin imani ne wannan ku haɗu har ku uku ku haikewa yarinya karama ku zalunci rayuwarta da na iyayenta, ku shafa musu baƙin fentin da ba zai taɓa gogewa ba a rayukansu? A yau ba don umar da kake ƙi ya roƙeni da mu zo ko zaka iya faɗa mana sauran abokan cin mushenka, ya kuma yi magana da shugaban yan sandan da ya ci alwashin ba zai taɓa bari ka sarara da azaba ba har sai ka bayyana sauran ka kuma amshi hukunci daidai da abin da ka aikata ba da baka ganni anan ba, ashe abin da ka aikata kenan ya hanaka bacci shekaran jiya?" Cikin sanyin murya ya ce "Kiyi haƙuri Maami, bani da kwarin gwiwar neman yafiyarki kasancewar na shafe tsawon rayuwata ina chusa miki baƙin ciki, amma ki yarda da ni kaman yadda na faɗa miki shekaran jiya tun nasihohin Baba ban sake kuskuren aikata wani abu marar kyau ba, na kasance cikin tsantsar nadamar abubuwan da na aikata, na kuma shafe kwanaki cikin tunanin ta inda zan fara gyara kurakuraina, haƙiƙa na san ba zan taɓa gujewa hukuncin ubangiji ba kasancewata me saɓo a gareki, na kuma san ko da kin yafe min zuban hawayen da nayi ta saka ki a baya zai iya bibiyar rayuwata a gaba, Maami ban san ko waninku zai iya yarda cewa ban aikata laifin da ake tuhumata dashi ba, hasali ma ban san sa'adda suka aikata ba Dukda ina a wurin, na bar hakan ne cikin soman taɓin girbe laifuka na, Allah shi ne shaidata sai kuma su da suka aikata" Idan Maami bata ce ta jijjiga da kalaman Mukhtar ba tayi ƙarya, sai de tana tsoron kar mafarki take, ko kuma wasa yake, shiriya take gani yana sauƙowa ɗan ta? Kuka ta fashe dashi na rasa abin yi, C.p, iyayen yaran da sauran manyan hukuma dake tsaye a wurin basu yarda da zancen shi ba, Baba kuwa hamdala yake adu'o'insu sun karɓu. "Kai da su waye ne?" Maami ta sake watso mishi tambayar Ya ɗaga kai kaman zai kalleta sai de kunyar kallonta yake ji, a hankali ya sake maimaita "Ban aikata ba" Baba ya ce "su waye ne?" A hankali ya faɗi sunayen nasu, tuni C.p ya kwashe ya kuma aika a kamo su, sun kuma ba wa baba da Maami hakuri akan za'a mayar da Mukhtar Cell dole dae su haɗu a court tukuna a tantance me gaskiya. Haka suna gani aka maida shi, Maami jikinta yayi sanyi sossai tana kallonshi har aka tafi dashi, ita da baba suka fito baba na sake yi mata nasiha har suka sauƙe ta gida drivern shi ya ja zuwa gidan shi. Zaune ta samu Alayah tayi zurfi cikin tunani, dafa ta tayi "Binty ban ce ki daina zama kina wannan tunane-tunanen ba?" Ajiyar zuciya ta sauke kan ta kakalo murmushi tace "Maami kun dawo?" "Eh mun dawo, ya cikin? Ba wani matsala ko?" Kasancewar tayi karyar ciwon ciki duk don gujewa tafiya ganin Mukhtar da ita ya sa ta kakalo murmushi "Eh Maami ya daina" Ajiyar zuciya Maami ta sauƙe, sai taji tana son bai wa Alaya labarin abin da ya faru "Ko kin san Mukhtar ya ce baya cikin waenda ake tuhuma da wannan al'amari?" Da sauri ta ɗago kai, one thing da zata iya cewa ta sani akan Mukhtar shi ne da matukar wuya yayi ƙarya "Kuma Maami a baya ya aikata irin haka aka ce?" Shiru Maami tayi sai Alayah ta ga kaman tambayar be dace ba "haka ne, maƙasudin ƙarasa taɓarɓarewar rayuwar shi kenan Alaya, kila da be aikata hakan har ya shiga prison a chan Kasar ba ya haɗu da manyan thugs kila da hakan be faru ba, kaddara ta rigayi fata. Amma a yadda Mukhtar yake magana a yau har cikin raina na gamsu na kuma amince da be aikata ba ɗin, Fatana shine Allah ubangiji ya sanya ya shiryu a gasken" Alaya ta amsa da Ameen. Sun ɗan tattauna akan jikin ummi inda Maamin ke faɗa mata umar ya ce bayan lafawar komai in har babu wani cigaba za'a fitar da ita waje, tana cikin total coma ne tsakanin rai da rayuwa. Alhj hammad Abdulhameed chanji a yadda al'amari ya zo mishi ta sa dole zuciyarshi ta durkushe, laifukanshi suka dawo suka lulluɓe shi, idanunshi sun rine kwarai a kwanakin da suka biyo baya a jere, kwanakin da suka kasance na zaɓe da kuma kirga kuri'u tare da faɗin sakamako, babu abinda ya fi girgizashi irin mummunar shedar mutane, yana ji yana gani ya faɗi wanwar hakan ta sa ya tafi tunanin kalmomi na karshe da suka haɗa shi da ɗan shi na biyu a lokacin da shi da Mukhtar suka sanya shi gaba da kyara da kuma hantara haɗe da baƙaken maganganu masu zafi don kawai ya dage da iyakar karfinshi wurin hana su saɓon ubangiji, yayi uwa yayi makarbiya akan duk wani mummunan sana'a da zasu yi, a lokacin gani suke kaman sanya idanu ne, toshe cigabansu ne yake tunda baya taɓa bari kayakin su ya shigo Nijeriya bare har ya shigo hannunsu su sayar, sun kasa tuna cewa yana da daman ɗaure su amma ya ki yin hakan a duk son shi su shiryu su dawo kan hanya, lallai da be raini Mukhtar bisa gurbatacciyar hanya ba duk wannan abubuwan ba zasu faru ba, kalaman mutane da shaidarsu a kan Mukhtar da ma shi da ake ɗaurawa laifi da mahaifiyarshi da bata ji ba bata gani ba baza su kawo karshen rayuwarshi ba kuwa? "Ban taɓa ƙin ku ba, ba kuma zan taɓa hakan ba, zan nesanta kaina da ku Dukda hakan ya zame min wani babban giɓi da abin baƙin ciki musamman in na duba cewa kun tura ni nesa da farin cikina wato mahaifiyata, hakan ba zai taɓa sa na bari kuyi abin da kuke so ba Abba, ku sani in har baku neme ni ba ni ba zan taɓa neman ku ba sai dae idanuna suna kanku, haka kuma a duk sadda na yi ra'ayi zan tako har cikin gidanka in ga mahaifiyata don ita bata ƙi ni ba, bata sanya min bakin cikin da zai farauci farin cikina da nesanta kaina da jama'a ba" Har ya miƙe sai ya juya yayi taku biyu uku kan ya ja tunga ba tare da ya juyo ba ya soma cewa. "Idan Yaro ya faɗi tashi yake ya ruga a guje, idan babba ya faɗi ya kan waiwaya ne ya ga me ya kayar dashi, idan ba ku yi nazarin jiya ba gobe ba zata taɓa yi muku kyau ba, ku daurewa zuciyoyinku kuyi rayuwar da zata zamto abin koyi ga na baya abin sha'awa ga na tare da ku, abin kishi ga makiya sannan abin alfahari ga dukkan masoyanku, ku kiyaye saɓani da mutane watarana za'a yi shaida walau da rai walau babu, wannan ɗin kusan saƙon mahaifiyata ne gareni inda take bani kwarin gwiwar zama Kunkuru cikin macizai na zaɓi na raba da ku ne saboda kuma ku rabauta... Na barku lafiya" Daga wannan rana ba zai ce ya sake ganin umar ido da ido ba, shekaru sama da Goma sha biyar, ya wofintar da rayuwarshi saboda kawai yana gyara musu tasu, umar ya kan zo har cikin gidan amma baya taɓa bari ko da a hange ne su hangi juna, hakan be taɓa damunshi ba sai a yau, hawaye kawai yake zubarwa motsin kofan shi ya ji, be damu da share hawayen ba har Maami ta shigo, kusan yanzu tana rayuwa dashi ne akan dole, haushi da takaicinshi karara yake gani cikin idanunta, abincin hannunta ta ajiye ba tare da ta tanka ba ta juya ta ɗauki na safe yadda ta ajiye shi be taɓa ba, taku uku tayi tace "Ban sani ba ko har yanzu wannan soyayya ta Mukhtar na nan dankare a zuciyarka, na shiga dumbin mamakin sanin cewa har yau baka iya zuwa inda yake ba baka kuma damu da halin da yake ciki ba, hasali ma maƙiyinku shine yayi uwa yayi makarbiya wurin ganin cewa ba'a zalunci ɗan uwanshi ko an illata shi ba, duk ba wannan ne ya sa na tsaya ba, na tsaya ne in ce maka gobe da misalin karfe takwas za'a shiga court an tsagaita sabd zaɓe, ban roƙi ka shiga lamarin don ɓinne gaskiya ba sai dae akwai buƙatar zuciya ta ɗanɗani azabar aikinta..." Tana kai nan tayi gaba, kanshi ya shafa yana huro iska, rudanin da yake ciki yasa be san komai akan abin da ke faruwa da Mukhtar din ba, be ba Mukhtar laifi duka ba ya raba ne a tsakaninsu hakan yasa ya mance Mukhtar din na ɗan lokaci, kuma a yanzu bashi da wani kwarin gwiwar fuskantar kowa da wannan lamari... COURT A yadda aka fito da su zaka yi tsammanin babu wadda ze iya magana cikinsu sbd yanayin wahala da suke ciki wadda ba sabon su bane, shi Mukhtar be iya ya kalli kowa ba, yayinda Alayah ta maida hankalinta kanshi tana kallonshi, har yau bata jin komai akan Mukhtar bayan ƙimar mahaifiyarshi da kakanshi, tunaninta na kai kawo ne akan shin ko shi ya aikata ko ba shi ya aikata ba zata iya cigaba da zama da shi kuwa? Zuciyarta ta riga ta kuntace shi, duk yadda tayi kokarin chusa tausayi da soyayyar Mukhtar a ranta ta kasa bata san cewa duk daɗewar sanda a ruwa baya taɓa zama kifi ba... "Shin kun amsa laifukanku?" Kusan shine tambaya na karshe da alkalin yayi bayan gabatar da duk hujjoji daga bangarorin lawyoyin masu kare wadda ake kara da masu kara, duk wasu shaidu sun fito karara, Nawwaz ne ya dubi mukhtar da har lokacin be ɗago kanshi ba, har yanzu basu faɗa cewa babu Mukhtar cikinsu ba, shima kuma tun da ya fada a gaban su Maami be sake furtawa ba, ko da suka zauna wuri ɗaya banda istigfari babu abin da yake yi, be musu magana ba duk kuwa irin surutan da suka dinga yi mishi, sun mishi adalci kenan idan suka sake dulmiya shi cikin damuwa bayan damuwar da suka san yana cikinta? "A ƙarshe bayan duk wasu hujjoji da shaidu da suka gabata, kotu ta yankewa waennan matasa huɗu shekaru goma goma gidan yari tare da azaba me tsanani, da kuma tarar naira miliyan ɗaiɗai daga kowannensu zuwa ga iyayen yarinya don a cigaba da kula da lafiyarta" Hannu ya sa ya ɗauki kulkinshi ya buga aka miƙe gabaɗaya, alkali ya juya don komawa office nashi hankali kwance. Yayinda polisawa suka yi kansu tare da ma'aikatan kotu don tabbatar da isansu prison lafiya. Littafin nan ba kyauta bane, book 2 na kuɗi ne a yanzu mun fara jin ƙamshin karshen book 1 ku hanzarta biya saboda yanzu muka soma tafiyan, zaku iya biya ta wannan asusun 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai shaida ta wannan layi 09039206763 🖤Gureenjoh🖤 AL'AJABIN SO (heart touching story) Fatima Muhammad Gurin (Gureenjo) Adabi Writers Association Book 1 *Page Twenty* "Ya mai girma me shari'a!!" Chak kowa ya tsaya a cikin kotun saboda yadda tayi magana da amo, fuskanta gabaɗaya ya cika da zallar gigita da kuma ruɗani wadda ta kasa ɗaura shi a mizanin hankali bare ta iya daidaita tunaninta, bata jira cewar shi ba tunda ya riga ya tsaya ta soma sauƙowa cikin sassarfa har ta isa gaban Mukhtar da ya zura mata idanu baya ko kyaftawa, zuciyarsa na wani irin fusga da wutar ƙaunarta da bashi da masaniyar sadda ta ruru har ta zame mishi wutan daji, ta cinye ilahirin zuciyarshi da duk wani sassa da jini ke gudana. Gabanshi ta isa ta kalle shi cikin idanu ta ɗago ta kalli alƙalin cikin Muryar roƙo da karaya ta ce "Don girman zatin Allah me shari'a ka taimaki macen da take dauke da juna biyu na wadda aka yankewa shekaru goma gidan firsuna, ka taimaki uwar da take shirin shiga tsananin tashin hankali saboda yanke wannan hukunci bisa kuskure, ka bamu dama ta biyu ina me tabbatar maka babu hannun mijina ciki..." Be tanka ba don yanayinta ya fi kama da mahaukaciya wacce take cikin sabuwar kamu, bata damu ba tunda dae yana tsaye ta juya ga Mukhtar da banda kallo babu abinda yake binta da shi ta sanya hannu ta riƙe nashi, cikin karyayyen murya me cike da tausayi a gauraye da son da bata san tana mishi ba saida taji hukuncin da aka yanke mishi ta soma cewa "Ya Mukhy a rayuwa muna kuskure, kowa yana kuskure kawai abinda ya kama ce mu a duk sadda hakan ta kasance shine muyi imani, mu kuma rayu da wannan consequences ɗin da kuskuren mu ya janyo mana, tunaninmu ya karkata ga tunanin tayaya! Ta kuma wani hanya zamu bi wurin gyara wannan kuskure" Hannunshi ta kara gimtsewa tana roƙonshi da idanunta "you don't have to blame yourself all for that Yaa mukhy, ba sai ka shigar da kanka cikin bala'in da baka da masaniya bane za'a san ka chanza wlh we all believe you... Ko Maami?" Ta juya tana kallon Maami da banda hawaye babu abin da take zubarwa sai ta gyaɗa musu kai, da sauri ta juyo tana mishi kallon ka gani ko? Sai ta sake cewa da sauri "Duk yadda kaddara ta zo a haka zamu karɓa mu kuma cigaba da rayuwa, karka nesanta kanka da mu da tunanin mun tsaneka, halayyarka ce bama so kuma ka sauya don Allah kar ka bari in haifi yaron da zai shekara goma cikin duniya ɗaya da mahaifinshi ba tare da ya san shi ba, maraici akwai ciwo Don Allah" Ta haɗa hannayenta wuri guda tana kuka. Da sauri ya sa hannayenshi duka biyu ya riƙo hannunta ya sauƙar ya mayar da ɗaya kan fuskanta yana share mata hawayenta a hankali cikin sanyi ya furta "Ban aikata ba Fatee, Na rantse da wadda raina yake hannunsa ban aikata ba..." Nawwaz da hawaye ke ta zuba mishi saboda sai yanzun ne yaji basu kyauta ba, barin ma da Alayah ta juyo kansu ta haɗe hannayenta "Don Allah kuji tausayin ɗan dake kwance a cikina, ku tausayawa mahaifiyar da ita kaɗai ta kan mance adu'a akanta wa kanta da rayuwarta saboda ta shagaltu wurin yiwa wannan ɗan nata Adu'a ku tsage gaskiya, kar ku kasance masu Son zuciya please" Nawwaz ne yace "Be aikata ba wallahi, hasali ma be san sadda muka yi hakan ba sai bayan mun gama" Smrt ma ya ce "hakane wallahi, Mukhtar baya cikin mu" Alkalin da gabaɗaya jikinshi yayi sanyi da tausayin Alaya da irin maganganunta sai ya dawo ya zauna, kowa ya koma ya zauna shari'a ta sake dawowa daga baya, kai tsaye duk su ukun suka bayyana gaskiya inda yarinyar m ta tabbatar da cewa mutum uku ne ba huɗu ba, shari'a saɓanin hankali sai gashi an wanke Mukhtar, Alayah kaman ta tiki rawa sai ta koma inda mazauninta suka rungume juna da Maami. Har suka iso gida bayan kammala komai Alaya bata iya ta ce komai cikin motan ba saboda yadda duk ya cike wurin, lallai natsuwa wani rahama ce ta daban, ɗakinshi na sashen ya wuce yayi wanka Maami ta tura a kai mishi Abinci, a chan ya ci ya kwanta bacci ba shi ya tashi ba sai azahar yayi wanka ya fito a wurin mashigar suka haɗu kiribb da Abba, kallon juna suka yi na seconds kan duk suka nufi ciki don karyawa. Abin mamaki wai na kwance ya faɗi yau Abba ne da Mukhtar suka hadu babu wadda ya iya yiwa dan uwansa magana, Alayah da Maami already sun ci hakan ya sa Alayah isowa gaban dining ɗin Sin serving ɗin su. "Abba ina yini?". Ya faɗa saboda gaisuwar kaman dole ce a gareshi "Lafiya..." "Ka kuwa san kana buƙatar neman yafiyata? Ashe duk hanyar da ka ɗaura ni kai ina ganin gata da soyayya ce babban halaka ne? Abba baka kyauta min ba sam, kaine sanadin duk wani kuskurena a rayuwa I hate you for that" Banda kallo da idanu babu abin da yace da Mukhtar din wadda hakan ya saka zuciyarshi hasala ya fara watsawa mahaifin nashi baƙaƙe maganganu cikin ɗaga murya, da gudu Alayah ta ajiye maheer ta tare Mukhtar tana mai rufe mishi baki a lokaci ɗaya tana girgiza kai cikin firgicin kalaman da yake jefawa mahaifin nashi... Ayi haƙuri da wannan wlh bacci ne ya ci karfi na. 🖤Gureenjoh🖤 AL'AJABIN SO (heart touching story) Fatima Muhammad Gurin (Gureenjo) Adabi Writers Association Book 1 *Page Twenty one* "Ya Mukhy ka dawo cikin hayyacinka Abba ne fa" Abba da yake zaune shiru ba tare da ya ce komai ba duk maganganun Mukhtar ɗin ne suke dawo mishi, a hankali ya ɗago idanu ya kalli Maami da ta iso wurin ta tsaya ba tare da tace komai ba, ashe haka take jin nauyi da zafi a ranta a duk sadda yake ba Mukhtar goyon bayan faɗa mata abinda be dace ba ba tare da kwaɓa ba, lumshe idanunshi yayi yana ambaton Allah kan ya buɗe ya kalli Mukhtar da ke ta huci har lokacin Alaya bata sauƙe hannunta daga kan lips ɗin shi ba yace "Fatima kyale shi, barshi ya faɗi duk abinda ke ranshi ko me zai faɗa na tabbatar babu ƙarya cikinta, na riga na cuci rayuwarshi na mishi illah, ban nemi yafiyarshi bane ba don ban yi nadama ba, nayi shiru ne saboda ban san me zan ce ba, ban kuma san ta wani hanya zan bi wurin taya shi gyara kuskuren da nine silar faruwarsa ba, amma ke ina rokon yafiyarki akan kalamaina na jiya" Cokalin ya ajiye ya miƙe zai fita Alaya tace "Abba!" Tsayawa yayi daidai kusa da Maami ba tare da ya juyo ba tace "abin da na faɗa a kotu ɗazu shi zan sake maimaitawa, kowa yana kuskure hakanan kowa na laifi saidai wadda ya fahimci laifin shi ya kuma tuba yayi niyyar gyarawa be yi kuskure ba, hasali ma abin da ake fata kenan, Don Allah karka saka damuwa a ranka Abba. Ya Mukhtar na fahimci yadda kake ji a ranka, sai dae ba hakan ne ya baka daman aibata mahaifinka ba, babu inda ya bamu wannan daman idan har da gaske ka gyara kuma ka chanza daga Mukhtar na da to kayi kokarin saita harshenka wurin magana da iyaye don Allah ya ɗaga darajarsu. Maami Don Allah da manzonsa kiyi haƙuri, fushi ko rashin yafiya duk ba zai chanza komai ba, mu haɗu duk mu gyara abin da ya ɓaci a baya adu'ar ki ce a yanzu Allah ya ƙarba, muyi kokarin zama one Big happy family Don Allah" Mukhtar da kanshi ke ƙasa hawayenshi na ɗiga bisa kan dining ɗin a ranshi yake jin Alayah is too good for him, be yi abinda Allah zai bashi ita matsayin mata ba, bayan duk abubuwan da suka faru ji yadda take magana kaman be gallaza mata ba, har ta yafe mishi kenan? Lallai idan zata iya yafe mai kuma har ubangiji zai iya yafe mai ya barshi da mace irin Alayah to shi me zai hana shi yafewa Abba? Maami ya ɗago ya kalla tana zub da hawaye itama idanunta na kan Alayah, har ranta take son yarinyar Allah ya mata baiwa na daban, idanunta ta maida kan Abba da jikinshi yayi matukar sanyi, kwarai suna bukatar cikakken farin ciki na tsawon shekarun da suka rasa a gidan ko da kuwa ba zai tabbata ba, shiyasa yake ganin gazawarshi ya kuma tabbatar komai ya faru tun farko daga shi ne, idanunshi ya lumshe yana jin kanshi na sarawa babu tantama hawan jininshi ne. Mukhtar ne ya yanke sad moment ɗin don tunda Alayah ta gama magana tayi shiru kowa da abinda yake saƙawa cikin ranshi, a hankali yake jan kafafunshi har ya isa gaban Maami ya zube bisa gwiwowinshi kanshi a ƙasa yace "Na san ni gagarumin me laifi ne a gareki Maami, tabbas a da na zama wawa, jahili, marar amfani na bi sahun waenda Allah ya ƙira da Ƴan wuta nayi ta saɓa miki cikin sani da kuma rashin sani, kin yi kuka har ba adadi, kin shiga damuwar da har ki kan yanki jiki ki faɗi, amma duk da haka baki tsane ni ba, baki daena min adu'ar shiriya ba, baki zare hannunki a kaina ba ba kuma ki yi min mummunan furuci ba saboda ke uwa ce! A yanzu ina tsananin jin kunyar kaina da na mahallacina, ina jin nauyin neman gafararki saboda abubuwan dayawa, Don Allah Maami ki yafewa Mukhtar ɗinki, ki yafe mini ko zan samu kwarin gwiwar tunkarar mahallacina da neman gafara, Maami ki ɗaukeni kaman jinjirin yaron ki da kika haifa a tsumman goyo in baki ragamar rayuwata ki yi min sabon tarbiya uwa ta gari, na tuba don Allah" Yadda yake kuka sai ya sa su duka kuka har Abba hawaye yake yi, kafaɗanshi ta kamo ta ɗago shi kawai ta rungumeshi Allah ya sani kukan farin ciki take, kukan jin daaɗi yau Mukhtar ya zama mutum, ɗagowa tayi tare da sanya hannu tayi cupping fuskanshi tana kallonshi cike da sabuwar soyayya tace "Na yafe maka Mukhtar, har Abada na yafe maka duk wasu laifukanka gareni da wadda na sani da ma wadda ban sani ba, Allah ya yafe maka... Ina so ka zama kaman ɗan uwanka a kusa dani duk abinda ya shige maka duhu a sabuwar tafiyar nan taka da zaka fara kar ka ji nauyi ko kunyar tambayata kaji?" Hugging ɗinta ya sake yi, Abba ya sanya hannu ya share hawayenshi kan yayi taku kaɗan ya ƙaraso gabansu, Maami ya kalla "Fatima ki yafemin na cutar dake a iya zaman mu, nayi kuskure me girma wadda ban farga ba sai a yanzu, bayan lalata tarbiyar Mukhtar na kuma nesanta ki da wadda zaki gani ki ji haske, lallai na tabbata mugu, azzalumi ban yi la'akari da cewar ke ɗin uwa ce ba, ban duba kasancewar ki mace me raunin zuciya ba ƴaƴa biyu da Allah ya baki duk na wargazasu na tauye farin cikin ki na tsawon shekaru na tuba" Kai ta gyaɗa tace "komai ya wuce Abba, in shaa Allah zamu ƙarasa sauran rayuwarmu wurin gyara duka waennan kuskuren" Mukhtar ya kalla zai yi magana sai yayi hanzarin rungumeshi, a rungume dashi yace "Abba kayi haƙurin kalamaina na dazu, na san duk abubuwan da kayi min a yadda ka ɗauki soyayya kenan baka min da niyyan zalunci ko don in lalace ba, hasali ma mune muka zalunci Umar, na riga na yafe maka Abbana, Allah ya bamu ikon gyara laifukan mu" Duk da Ameen suka amsa, sai a lokacin kowa ya iya sakin murmushi a cikinsu, dawowa suka yi Maami ta sake serving Abba sbd wanchan yayi sanyi, Alayah kuma tayi serving Mukhtar dake ta kallonta wadda hakan yake sakata jin kaman ta nutse cikin ƙasa. Basu zauna ba suka yi cikin parlor suka zauna da Maami, Maami ce ta nuna mata cinyarta sai ta zame ta kwanta tare da yin matashin kai da shi, a hankali ta zame dankwalin kanta tace "Binty dai Allah yayi ki irin Maaminku, kema bakya son kitso sam" Murmushi tayi tace "Maami ai tsoron kai ne da ni, daa ummi sai tayi da gaske take min kitso saboda rigima daga baya tace na girma in ma naki ni na sani, shikenan sai dae in wanke in shafa mai" Murmushi Maami ta sake tana cigaba da ɗan sosa mata kan tace "Lallai Binty ke ɗin wata haske ce a cikin rayuwarmu, ina Alfahari da samun ki matsayin ƴa Allah ya albarkace ki ya ba ummi lafiya" Tana lumshe idanu saboda baccin da yake son kwasheta don susan kan daaɗi yake mata tace "Bani da abin da zan saka miki Maami, illa iyaka a duk sallata na kan sanya ki a Adu'a Allah ya miki abin da zato be taɓa zato ba, tunanin ɗan Adam be taɓa kaiwa ba, Allah ya miki muhalli na musamman a cikin gidan Aljanna, haƙiƙa nayi matukar dacen samun ki a matsayin uwa" Murmushi Maami ta saki, a hankali ta ɗaga kai sai ta ga Mukhtar da Abba ma hira suke ɗan yi a hankali, idanunta ta lumshe ina ma da umar yana wurin da farin cikinta ya zama cikakke, amma ta san irin zuciyarshi ga yanayin aikinshi Allah ya sa ya yafewa babanshi da ɗan uwanshi har su yi zama da mutunci. Ko da Suka gama wurinta suka dawo, tuni Alayah tayi bacci kan kafafun Maami, hira suka cigaba da yi su ukun kaman komai be faru ba, shawaran karatuttukan da zai fara suka yanke inda a kullum da yamma zai tafi wurin baba sai goman dare ya dawo, tuni ya kira kakan nashi ya shaida mishi ze fara zuwa ɗaukar karatu har yar raha suka yi baban na cewa ya faɗi gaskiya ko furanshi na dare zai ke zuwa shanyewa kullum suka ɗan yi dariya, ya kula kowa so yake ya ja shi a jiki, kwarai hakan ya mishi matukar daaɗi don hakan ne kawai zai kasance ya san eh zai iya, zai iya zama na kirki, shima zai iya gyara kura-kuranshi, kuma he is accepted a welcome a familynshi. Idanunshi gabaɗaya zube a kanta, murmushi ya ɗan saki yana kallon yadda ta sake lafewa jikin kujeran kaman mage, haƙuri na musamman yake son bata, sai dae baya tunanin a yanzu ne zai yi hakan, duk yadda yake jinta a ranshi da yadda yake jin a yanzu ita ce bugun numfashin shi zai mata adalci, dole sai ya zama nagartaccen mutum kaman kowa zai iya sake fuskantar ta da kokon barar matsuguni a cikin ranta. Abin da be taɓa faruwa ba shi ya faru yau, sun yi hira sossai har la'asar cikin raha, sai tuno baya ake Maami na hiran yarantanshi yana dariya, dariyanshi ne ya tada Alayah, ta buɗe idanunta dake cike da bacci ta watsa mishi, shima da baya mintuna biyu be kalleta ba idanunshi na kanta, bakinta ta turo mai na tana baccinta me daaɗi ya tashe ta, murmushi me kyau da bata taɓa gani a fuskanshi ba ya sakar mata, da sauri ta ɗauke kai tare da kokarin Miƙewa zaune. "Sannu Fatima" Abba ya faɗa tayi murmushi, Maami tace "kin tashi Binty? Ko yunwa ce ta tashe ki? A kawo miki wani abu ne?" Jinta take ƴar gata, a da ana musu kallon kaskantattu marasa galihu babu wadda ya damu da damuwarsu, cin su, shan su ko lafiyar su amma duba a yau yadda waennan ahali suke mata, ai ko menene tayi musu bata faɗi ba. "Maami bari dae na shiga kitchen ɗin da kaina" Ta miƙe ta nufi kitchen ɗin, Masu aikin suna aikinsu cikin tsabta, Tabawa ce ta dubeta "Hajiya karama kina bukatar wani abu ne?" Tayi murmushi tace "A'a ki yi aikinki baaba, bari na haɗa da kaina" Indomie ta dafa guda biyu, anan ta zauna suna ƴar hira tana dariya har ta cinye kayanta, ko da ta fito ta samu duk basa nan a parlorn da alama sun je sallah, itama ɗakinta ta haura ta gabatar da la'asar din kan ta kwanta a wurin cikin tunanin umminta, Adu'a take tayi a ranta na Allah ya ba ummi lafiya, Allah ya tashi kafadunta don bata san ina zata kama ba in ba ummi, bata san kowa nasu ba, ko suna dashi ko basu dashi duk bata sani ba. Maami bayan ta idar da sallah Umar ta ƙira, a natse suka gaisa take bashi labarin abinda ya duk ya faru, ya taya ta farin ciki don da farin cikinta shima yake samun farin ciki. "Yanzu yaushe zaka shigo?" Ɗan shiru yayi kan yace "in shaa Allah zan shigo idan na samu sararin aiki Maamina kar ki damu" Ajiyar zuciya ta sauƙe tace "Toh Don Allah idan cikinsu wani ya ƙiraka ka ɗaga ka ji? Yafiya abu ne me kyau wadda dukkanmu muna son shi a wurin mahallici, ashe don mu mun yafewa junanmu bamu faɗi ba ko kaɗan, na san irin zuciyarka ka daure a maida komai ba komai ba ka ji autan Maami?" Murmushi ya saki me sauti har tana jinshi, saboda yadda ta ƙarasa maganan da lallami kaman ɗan yaro, ita ma murmushi ta saki suka yi sallama. Kofan ɗakin aka yi knocking ta bada izinin shigowa, Mukhtar ne ya shigo zai yi magana daga chan tayi saurin miƙa mai hannu ya iso ya riƙe ta nuna mishi kusa da ita bakin gado ya zauna, ta san sabo sai a hankali amma with effort komai zai zama tarihi. "Maami zan tafi wurin baba" Murmushi ta saki tace "Toh a kula, a kuma maida hankali banda tuƙin ganganci Allah yayi albarka" Wani irin farin ciki yaji marar misaltuwa Yace "in shaa Allah sai na dawo" Ya miƙe ya fito, ɗakin Alayah yayi knocking shiru ba response, ya sake yi shiru sai ya tura a hankali ya shiga tana nan kwance rigingine cikin tunani, a take yaji wani iri a jikinshi menene matsalar? A hankali ya isa ganganta ya tsuguna bata san zuwanshi ba sai hannunshi ta ji... *kar fa ku sha'afa tafiyar yanzu aka soma ta, akwai sauran rina a kaba, tsugune kuma bata ƙare ba, har ila yau dae muna nan book 1, book 2 zai muku a naira 500 kachal zaki iya biya ta wannan asusun 0545475847 Gt Fatima Muhammad Gurin Sai shaidar biya ta nan 09039206763 🖤Gureenjoh🖤 AL'AJABIN SO (heart touching story) Fatima Muhammad Gurin (Gureenjo) Adabi Writers Association Book 1 *Page Twenty Two* A hankali ta buɗe idanunta da suka sauya sossai ta zuba mishi su, zare hannunshi yayi daga goshinta chan ƙasa yace "Are you alright? Da wata matsala ne?" Da idanu ta amsa shi don bakinta yayi mata nauyin buɗewa. Gefe ya ɗan kalla sbd yadda idanun suke wani irin tasiri a jikinshi, Miƙewa zaune tayi a hankali tace "zaka fita ne?" Sai a lokacin ya ɗan kalleta yace "zan je wurin baba, me kike so in taho miki dashi in zan dawo?" Murmushi ta ɗan saki shima yayi, Dukda babu wani shakuwa na musamman a tsakaninsu babu tsoronshi a ranta kaman kwanaki, hasali ma tausayinshi ya fi komai tasiri a gareta sai kuma tausayin ɗan cikinta. "Nama" Ta faɗa a tsakanin lips ɗinta "wani iri?" Idanunta ta ɗan juya da alamun tunani kan tace "ko wani iri me daaɗi dai" "an gama maman unborn, na tafi" "Allah ya tsare" Ya amsa kan ya fice daga ɗakin, ajiyar zuciya ta sauƙe kan ta ɗan yi murmushi. Tuƙi yake a natse yana murza siterin motar tsakanin hannuwanshi, wani irin yanayi yake ji a jikinshi da ma zuciyarshi, jinshi yake sabon mutum a hankali ya miƙa hannu ya kunna karatun alqur'ani da ɗazu yayi downloading Dukda manyan surorin da be iya bane sai dae jinshi akwai saukar da natsuwa, gidan baba malam ya isa saida ya shiga ciki suka gaisa da kakkaninshi da wasu Aunties din nashi kan ya tafi parlorn baba, maraba ya mishi suka zauna aka kawo abinci fura kaɗai ya sha, da tambayoyi baba ya fara abubuwa dayawa be sani ba hakan yasa baba ɗauko komai daga farko, Allah ma ya sa shi ɗin akwai kwakwalwa da kam ba karamar wuya ze ci ba wurin koyon addini, kuma abin ka da wadda ya saka kai sossai ya natsu ya ɗauki karatuttukan ranan, sai goma na dare ya mishi sallama ya fito. Sai da ya tsaya ya sayi kaji gashin oven da aka yi su cikin wani hadaddiyar sauce na albasa da kuma Irish guda huɗu da su youghurt kan ya nufi gidan, a parlor ya sami Maami dake ta zuba ƙamshi tana kokarin tafiya part din Abba, da murmushi ta tare shi tare da wara hannunta ya matso yayi Hugging ɗinta tace "ka dawo?" "Eh Maami na dawo" "ya karatun? Fatan an yi abin arziki" Yana murmushi yace "Eh Maami, na koyi dayawa har fa baba na mamaki" Kai ta jinjina cikin jin daaɗin da ya kasa boyuwa mata tace "Masha Allah, Allah ya sa a ɗore a haka" Ya amsa da Ameen Ledar hannunshi me kaji biyu ya miƙa mata "Maami gashi a tafi wa Abba da shi" Karɓa tayi ta mishi Adu'a kan ta juya kitchen zama yayi yana jiran ta fita don kunyar haurawa wurin Alayah yake a kan idanunta, a tray ta haɗa musu kan ta fito ta mishi sai da safe. Sai da ta fice daga sashen ya miƙe ya shiga kitchen ɗin, yadda ya ga ta haɗa ya haɗa Dukda be iya ba duk ya ɓata jikin plate ɗin haka dae ya kokarta kan ya saɓi tray din ya haura sama dashi, a hankali ya ɗan yi knocking kan ya buɗe ya shiga tana tsaye ta gama saka night gown ɗinta kenan wadda dogon Cotton gown ne har ƙasa da tsagu gefe da gefe, cikinta ya ɗan tasa kaɗan akan rigar ya mata kyau sossai, murmushi yayi mata ta ɗan mayar mishi kan ta nufo shi ta karɓi tray din. "Sannu da dawowa" "yauwa fatee" A ƙasa ta ajiye tray ɗin kan tattausan rug carpet dake shimfide a wurin, ya ƙarasa ya zauna ita ma ta zauna, shi yake cire mata ƙashi sai ya bata tsoka, Dukda ba wani hira suke ba moment ɗin ya mishi daaɗi ashe haka samun cikakken natsuwa yake? Godiya kawai yake yi wa Allah da ya bashi daman zama mutum a karo na biyu, sai da tace ta ƙoshi kan ya kyaleta ta miƙe ta shiga toilet ta barshi yana ci, brush tayi ta fito ta isa kan gado ta kwanta lamo gabanta na faɗuwa Allah Allah take ya gama ya tafi, tana kallonshi ya gama ya tattare wurin ya kai bakin kofa ya ajiye kan ya dawo ya shiga toilet ɗinta ya wanke hannu tare da kuskure baki ya fito. Yana fitowa tayi hanzarin rufe idanunta tana damke blanket da take ciki dukda iyakarshi kan kwankwasonta ne, taku yake yana nufan gadon inda yake tafiya da bugun zuciyarta, murmushi ya saki ganin yadda take mirmisa idanun sai motsi gashin idanunta ke yi wai ita a dole tayi bacci, a ɗan space da ta bari ya ɗosana duwawunsa ya sanya hannu daga gefenta kan gadon ya tokare hakan ya bashi damar yi mata rumfa da faffadar kirjinshi, fuskanta ya zubawa ido yana ƙare mata kallo, tsawon dakika goma, kasa juran kallon tayi ta fara buɗe idanun a hankali har suka faɗa cikin nashi, murmushi ya ɗan saki yace "Me baccin ƙarya" Ta ɗan yi murmushi, idanunta ta kai kan hannunshi dake saitin kwankwasonta daga kan idon hannun har ya ɓace zuwa cikin half jumfar dake jikinshi wadda iyakacinshi damtsen shi daga sama duk tatoos ne a kwance, kallon hannun da take shima ya saka ya ɗan kalla, hannunta ta kai ta ɗan shafa tace tana maida idanunta cikin nashi "Yana fita?" Kai ya gyaɗa mata "A da ne ba'a samo technologyn cire shi ba, amma yanzu ana iya gogewa" Ta haɗiye miyau tace chan ƙasa kaman yadda shima yake mata magana "Da me ake gogewa?" "Da wuta kaman yadda aka yi shi da wuta" Idanunta ta ɗan zare "kuma ba zafi?" Cikin kwaikwayan maganan ta ya ce "akwai amma mijinki jarumi ne" Murmushi tayi, shiru ya ɗan ratsa su idanunshi dake ta yawo bisa kanta duk ya bi ya tsarga ta, har gwara suna maganan ma da suna zaune shirun nan. "Gobe in Allah ya kaimu zan fara zuwa makaranta" Kai ya gyaɗa yace "Allah ya kaimu in zan tafi Hameed auto motors sai in yi dropping naki from their za ki duba motar da ya miki sai mu fara koyon driving" Cikin jin daaɗi ta mishi godiya, idanunta ta ɗan lumshe ta sake cewa "in na tashi ina so zan je asibiti ne na duba ummi" Da sauri ya ɗan kalleta Sharp ya mance da zancen mahaifiyar tata, tunanin haduwarsu na farko kuma na ƙarshe yayi inda ya tureta a hanya har ta faɗi a sume, a take yanayin shi ya sauya, hankalinshi ya so tashi sai yaji hannunta kan kumatunshi ta ɗan shafa dole ta sa ya maida idanunshi cikin nata "Karka damu, ummi tana da sauƙin kai da fahimta, bazata ƙi ka ba musamman in ta farka ta samu ka sauya kana kuma kular mata da ni yadda ya kamata" Ajiyar zuciya ya ɗan sauƙe yace "in shaa Allahu kan ta farka ɗin zan tabbatar da na baki kulawar da ba zata iya gane ki ba ma ta ganki" A tare suka yi murmushi, hamma ta saki Yace "bacci ko?" Kai ta gyaɗa mishi, ya duƙa yayi pecking goshinta a hankali ya ɗago idanunshi akan lips ɗinta baya so ya kai nan don bashi da control a fannin, kuma ba zai iya kusantarta ba har sai ya je asibiti ya tabbatar da lafiyanshi, bargonta ya ɗan ja ƙasa yayi pecking cikinta tafin hannunshi ya ɗaura a kai, yace a hankali "Kuyi bacci cikin aminci, Allah ya bamu alkhairi" Ta ɗan yi murmushi tare da furta Ameen kan ya ja mata blanket ɗin har kirjinta ya sake pecking cheek ɗinta kan ya juya ya nufi kofa tana ta kallonshinshi saida ya dau tray din kan ya kashe mata wuta ya fice, ajiyar zuciya me karfi ta sauke a hankali ta furta "Alhamdulillah" Sake dunkule wa tayi a cikin bargon a take natsatsen bacci ya dauƙeta, shima yana isa ɗakinshi ya watsa ruwa ya kwanta saida ya sake bitar karatun su na ɗazu kan bacci ya ɗauke shi. Karfe huɗu da rabi alerm ɗin shi ya tashe shi, a natse ya miƙe ya shige toilet yayi alwala ya zo ya sanya Black jallabiya da ya mishi kyau sossai ya amshi skin dinshi dole yau zai je ya nemi kaya don da ya tsaya gaban kayakinshi na gidan duk babu na kirki, duka kyauta da su zai yi a yau, fita yayi ya tafi ɗakinta ya tashe ta kan ya fito, a haraba suka haɗu da Abba suka nufi masallaci dake kofan gidansu anan suka yi raka'atanil fajir wallahi be taɓa jin natsuwa irin na daga jiya zuwa yau ba a rayuwarshi, har suka yi sallahn asuba wani irin nishadi yake ji, ko da mutane suke fita shi qur'ani ya ɗauko ya cigaba da bitar ƙarin su na jiya, sai wuraren bakwai ya bar masallacin ya dawo ɗaki ya ɗan kwanta. Karfe goma daidai ya fito a shirye cikin half jumpa ruwan ƙasa da ya kama shi ya mishi kyau sossai, tuni ya aske kanshi don haka hular shi ta zauna sossai ya fito a babban mutum me cike da natsuwa da haiba, a parlor ya same su, itama ta shirya cikin baƙin lace me adon peach ya mata kyau sossai, gaishe shi tayi ya amsa yana tambayar lafiyanta kan ya duƙa ya gaida Maami itama ta amsa cikin kulawa "har kin shirya kina ta jirana ko?" Tace "A'a yanzu nima fitowana Yaya" Dining ya wuce ta miƙe don serving nashi sai murmushi Maami ke zabgawa tana kallonsu gwanin sha'awa. A chan ma cikin natsuwa yake shigar da kanshi gareta, har ya gama ci suka fito magana yake mata a hankali tana bashi amsa, anan ta yafa babban mayafinta ta ɗauki jakanta tace "Maami mun tafi" Maami tace "Allah ya tsare ya bada sa'a, sai kun dawo" Suka fice a tare gwanin sha'awa, shi ya buɗe mata hadaddiyar motar tashi sport car ce BMW ta shiga shima ya zagaya ya shiga ya ja suka fice, kaman yadda ya faɗa campanin motocin shi suka tsaya suka shiga, ana ta miƙa gaisuwa cike da tsoro saboda sanin shi masifaffen marar haƙuri, kuskure kaɗan kashin ka ya bushe, ga mamakin su yau sai gashi sai murmushi yake saki ba wannan hayaniya da hargagin, har kyautar kuɗi ya musu suna ta mishi godiya cikin jin daaɗin sauyin da suka gani a tare dashi. Wata coffee hyundai ta zaɓa ya mata kyau sossai, a take ya bada umarnin ayi wa motar duk wani checking kan yamma a kai mishi gida, daga nan school suka nufa duk yadda ta so ya barta daga haraba ya tafi zata yi duk abinda bata gane ba ya ƙi, a tare dashi suka yi ta yin komai, duk inda da bin layi zai nema mata seat ta zauna shi ya bi Layin sai an iso ya kirata ta zo su yi abinda zasu yi su kara gaba, kowa kallonsu yake gwanin sha'awa lallai haƙuri na da riba, duk masu yi mata kallon ta dace ta tsinci dami a akala basu san irin tsanin wutan da ta taka zuwa wannan wuri bane. Karfe ɗaya suka gama komai, sai da suka tsaya masallacin makarantar ta shiga ɓangaren mata shi ya shiga cikin masallaci suka yi sallah kan suka fito, restuarant me kyau ya kaita suka ci abinci kan suka nufi asibiti, har yau ba'a bari an shiga wurin ummi ba, hanganta suka yi ta fara hawaye tuni ya jinginata da jikinshi yana lallashinta, sun ɗan jima kan suka fito a reception yace ta ɗan jira shi anan yana zuwa, wayanshi dake ta ringing tuntuni yana rejecting yanzu ma shi ya sake ɗaukar ringing wayan ta bi da kallo har ya ɗan yi nisa kan ta ga yayi picking ya ɓace mata. "Rita i Said leave me alone! Ki kyale rayuwata na fita daga cikin sabgar rayuwarku daga ke har su Zee wacce ta sake kirana wallahi sai na mata rashin mutuncin da baku taɓa tunani ba, rubish" Yana kai nan ya yanke wayan ba tare da ya jira amsar ta ba sim zai chanza bazasu dagula mai lissafi ba, yana kokarin zare sim ɗin saƙo ya shigo, kalma ɗaya da ya gani shi ya ja hankalinshi wurin dubawa, wani irin jiri ne ya kwashe shi da sauri ya dafe gini don ƙoƙarin zubewa ƙasa yake, a take zufa ta karyo mishi a kan lips ɗin shi ya furta "Innalillahi wainna ilaihi rajiun.." *Kar ku sha'afa Al'ajabin So littafin kuɗi ne part 2 din zai zo muku akan naira 500 kachal har yanzu muna da gagarumin tafiya a gabanmu. Zaki iya biya ta wannan asusun 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya ta wannan layi 09039206763 Sai na ji ku* 🖤Gureenjoh🖤 AL'AJABIN SO (heart touching story) Fatima Muhammad Gurin (Gureenjo) Adabi Writers Association Book 1 *Page Twenty Three* Zaune a gaban Dr Ahmad dake ta murmushin ganinshi da yanayi na daban yace "Na zo ne ina bukatar a yi min tests ba zan iya haƙurin cire folder da sauransu ba please do the needful" Sarai ya gane shi their rude patients husband Dukda yanzu Meddy specialist sun karɓe musu ita sbd finsu kwarewa a harkar zuciya sai dae ya san Maami ya kuma san Umar tunda ta hannunshi suka karɓi ummi. "Wani iri kenan?" Numfashi ya ja kan yace "Komai da komai, precisely HIV/AIDS" Da sauri Dr Ahmad ya kalleshi, jingina yayi ya lumshe idanu yace "don't be suprise, it might be the product of my sins" Ajiyar zuciya Dr Ahmad ya sauƙe kan ya danna kiran wata ma'aikaciyar jinya ya bata umarnin zuwa da kayan diban jini, tubes biyar ya buƙata. Ko da ta kawo da kanshi ya tashi yayi sticking finger ɗin shi for the rapid antibody test na HIV kan ya saka syringe ya zuƙi jini sossai a tubes din nan, a na karshen ne ya ɗaga kwalban sama yana kallon jinin for seconds kan ya ajiye kan tray ɗin, rubutu yayi a kan plain sheet me ɗan tsawo da Mukhtar ba zai iya tantancewa ba sbd rubutun likitoci ba irin na normal mutane bane ya bata yace ta kai lab please. "Sai zuwa yaushe duk results din zasu fita?" Dr Ahmad yace "zai iya kaiwa five hours kan a kamallah komai sbd suna dayawa" Miƙewa Mukhtar yayi ya miƙa mishi hannu suka yi musabaha kan yace "Zan dawo ko zuwa anjima, nd I will make the payments yanzu in na fita thank you very much" Murmushi kwance a fuskan Dr. Ahmad shima ya bashi hannu kan ya juya ya fice, da kallo Dr. Ahmad ya bishi a fili ya furta "Masha Allah, he's indeed a changed person" Ko daga maganan shi ma ya fuskanci hakan. Yana isa wurinta ya sakar mata murmushi tare da miƙa mata hannu ta kama ta miƙe yace "Sorry madam na ajiye ki ko?" Girgiza kai tayi tana murmushi, bata tambayeshi abin da yaje yi ba sai dae ta fahimci kaman akwai abinda yake damunshi, yanayinshi ya sake sanyi har suka isa gida babu wadda yayi magana, a tare suka shiga parlor Maami na musu maraba da dawowa, duk amsa mata suka yi suka mata sannu da gida kan kowa ya nufi ɗakin shi don freshening, sai bayan la'asar ta fito ta zauna da Maami a parlor suna hira. Chan shima ya shigo yayi joining ɗin su Dukda ba wani magana yake ba, a kusa da Maami ya zauna ya ɗaura kanshi akan shoulder ɗinta, tsoro ne fal ranshi, hankalinshi rabi baya jikinshi rabuwa da Alayah shine fargabarshi a yanzu ba ciwo ba, Maami ta tambayeshi ko akwai wani damuwa ne yace babu, yana ji suna maganan Ummi akan yadda babu wani improvement saboda sun ce damuwa yayi mata over ta yadda jinin da ya tashi hitting yayi sama ba na wasa ba kuma laluranta ma na rashin ji da magana kaman musababbin BP ɗinta ne. Adu'ar samun lafiya duk suka mata, dab Magrib ya miƙe yace "Maami zan ɗan fita zan tsaya wani wuri ina ga daga chan zan wuce wurin baba kawai" Suka mishi Adu'ar dawowa lafiya ya fita. "Maami baki lura kaman yana cikin damuwa ba?" Alayah ta faɗa tana kallon Maami "Kwarai kuwa na kula, sai dae kila tunanin rayuwa ne with time zai sake in sha Allah" Zaune a gaban Dr. Ahmad bayan sun gaisa yace "ya ake ciki? Sun fito results din? "Yeah sun fito, for now babu HIV but ka san test na HIV yana ɗaukar 90 days ne kan ya zama successful, zaka dawo after 30days a sake yi haka after another 30 days again, sannan duk wasu STIs(Sexual transmitted infections) cututtuka da ake iya samunsu ta hanyar saduwa kaman su Syphilis da gonorrhoea da sauransu duk babu" Ajiyar zuciya ya sauƙe kan ya miƙa hannu ya ɗauki wani paper daban ya miƙa mai... Tsawon mintuna talatin ya ɗauka cikin office ɗin kan ya fito, a cikin asibitin yayi isha kan ya isa wurin Baba suka yi karatu, Dukda baba ya lura kwazonshi ba kaman na jiya ba sai dae ya maida hankali sossai da sossai, daga nan ya tsaya ya saya masu gasashen kifi yayi gida. **** Wasa wasa haka rayuwa ta zo ta sabar mishi da wani yanayi na daban, duk yadda yake karfafa zuciyarshi damuwarshi ba wani boyayye bane, yana iyakacin kokarin shi wurin bautar ubangijinshi kaman yadda yake matukar kula da Alayah da kuma Maami, bashi da wani buri illah ya shigo ya tarar dasu su biyu suna hira da raha hakan na kautar mishi da duk wani matsaltsalu na duniya, har ya sabar musu duk dare baya dawowa daga gidan baba hannu banza, ita kanta Alayah ta riga da ta saba bata cin komai sai ya dawo ya kawo ko balangu, tsire, kifi ko kaza gashi daban daban, yana riritata yana bata duk wani kulawa tsabar yadda hankalinta ke kwance Dukda yadda karatu yayi nisa wani irin kyau take narkawa tayi fresh abin ta. Ta fannin mu'amalar aure bai taɓa nemanta ba wata huɗu ake nema kenan bata damu ba kasancewar ita wahalar abin kawai ta sani, ya kan rage zafi idan ta ciyoshi da gaske Dukda yana yawan shan tea me lemon tsami da gishiri, bata da wani matsala banda ciwon ummi da har yanzu babu wani cigaba, jiya e yau, duk ta tashi makaranta shi yake zuwa ya ɗaukota daga nan wucewa suke yi koyon tuƙi tun bata iyawa har ta soma kwarewa wani lokacin ma ita ke dawo dasu gida, in tace a watannin nan basu yi wani irin shakuwa na ban mamaki ba tayi ƙarya, yana bata duk wani kulawa da mace take fata ko buri, cikinta ya shiga wata na bakwai kenan duk zuwanta awo a tare suke zuwa, har yau babu wadda ya mishi maganan su koma gidansu ko ya ɗauke ta su tafi saboda daga Maami har Abba basa so su takura shi, kila ya fi so su zauna nan ɗin don duk wani shakuwa da be samu ba da Maami a yanzu ya same shi Dukda ya san ba kaman na umar da ita ba, amma kwarai zuwa yanzu sun shaku matuka. Wani abu da yake yi yake ƙara burgesu shine yawan sadaka da taimako, har an san shi sai dae idan be ji taimako ba zai yi, abinci duk Litinin da juma'a yana ciyar da akallah mutane ɗari biyu zuwa uku, kuma lafiyayyen girki ba laga laga ba don a babban restuarant yake da contract, wani lokaci ma har ya ɗauketa su kai ziyara su orphanage, asibiti da sauransu a yanzu in ya ga rayuwarshi sai ya tsinci kanshi cikin zub da hawaye, lallai Allahnshi yana son shi. *** Tsaye take gaban dressing mirror tana shafe tattausan skin ɗin ta da mai fitowanta wanka kenan, wani irin zafi take ji sannan kirjinta ya tokare sossai wadda rabon da ta ji ciwon zuciyarta ya motsa ta mance sai dae rashin ƙiba da nauyinta na nan, ta dae murje ta ƙara kyau sossai, cikinta ya fito sossai sossai bayan ta gama ta feffeshe jikinta da turarukan ta mabanbanta a take ɗakin ya bule da sassanyar kamshin, night gown da be da wani nauyi da tsawo ta saka tana kokarin tufke gashin kanta ya turo kofan ya shigo, ta madubi suka sakarwa juna murmushi. A hankali ya ƙaraso ya ajiye tray din hannunshi kan ya nufeta slowly yayi Hugging ɗinta ta baya very tide yana zagaye hannunshi bisa kan cikinta a lokaci ɗaya ɗan cikin yayi motsi suka saki dariya a tare "ka ji min yaro da gulma" Yace "kyaleshi ya marabci babanshi watarana sai labari" Kallonshi tayi sai ta ga ya ɗan faɗa mata, sajen da ya tara ya mishi kyau ainun, tafin hannunta ta sanya ta ɗan shafa sajen tace "Ya Mukhy menene yake damunka? Jikinka da ɗan zafi kuma ramarka tun bata fita har tana nunawa, can you please share ur problem with me? Karka manta turawa fa sun ce a problem shared is a problem solved" Sakinta yayi ya karɓi ribbon ɗin hannunta yana tufke mata gashin yace "bani da damuwar komai Fatee, in da ina dashi ba zan ƙi faɗa miki ko Maami ba saboda har duniya ta nade bani da tamkarku" Bayan ya gama ya ja hannunta suka zauna bakin gado sbd zaman ƙasa na mata wahala yanzu, ya buɗe soyayyayiyar Irish da aka yi ta da liver sauce ya fara bata tana ci, sai da ta ƙoshi ta karɓi spoon ɗin ta dibo zata kai mai baki ya riƙe yana saukewa a hankali yace "bani da apetite ba zan iya ci ba" Tace "kuma dai? Ya Mukhtar kullum fa haka kake cewa da matukar wahala ka sha wani abu ma bare ka ci abinci me nauyi" Murmushi ya sakar mata. Miƙewa yayi zai fita da kwanukan ta riƙe hannunshi "zaka kwana anan? Ko in zo?" Ya kalleta yace "bari naje na dawo maman unborn tunda yau so ake a danne min kirji" Tana dariya ya fice, toilet ta shiga tayi brush ta ƙarasa kimtsawa tana zama yana shigowa sanye da jallabiya coffee Brown me taushi, jallabiyar ya cire ya saura daga shi sai dogon wandon bacci ya haye gadon ta kuwa samu masauki a kirjinshi suka yi Light off bata jima ba bacci ya sure ta. Sai da ya bari tayi nisa a baccin ya maidata kan pillow ya kwanta, baya so ya tashe ta cikin dare sbd ya san kanshi, juye juye kawai yake sbd baccin da baya samu a kwanakin gabaɗaya, chan kuma zufa yake ta karyo mai Dukda Ac dake ta aiki a ɗakin kusan kure wa tayi, ya yaye bargon yana cigaba da ɗan juye juye, wuraren sha biyu ta farka fitsari idanunta suka sauƙa kanshi. Taɓa shi tayi sai taji hannunta ya sauƙa kan zufan dake ta gangara a jikinshi, wuta ta kunna sai suka haɗa idanu "Ya Mukhtar zafi kake ji haka? Ko mu kunna standing fan?" Yace "No karki damu zan watsa ruwa yanzu ina jira ne ɗaya yayi gabaɗaya in miƙe nafilfili na" Sauƙa tayi ta shiga toilet tayi fitsari kirjinta ke damunta da ciwo tana tunanin dole gobe taje meddy, ta fito ta zo ta kwanta ya kashe wutan don ya san bata iya bacci da wuta a kunne. Bata iya ta yi baccin ba, tana ta kallonshi ga dukkan alama duk daren be yi bacci ba, ya kwana biyu da tayi noticing rashin baccin shi, in yayi ma baya wuce awa guda duk tsanani, tana ta kallonshi har ya sauka ya shiga toilet ya jima wadda ya tabbatar mata da wankan yayi kan ya fito ya sanya jallabiyanshi ya tafi wurin sallahnts ya fara nafilfili, tun tana kallon shi har bacci ya sure ta. Karfe uku ta sake tashi fitsari ta samu yana karatun alqur'ani da yanzu yayi nisa sossai kuma yana fitar da duk wani makharij da kiyayewa sossai a karatu, ta jinjinawa namijin kokarin shi don yanzu ko ita bazata nuna mishi ibada ba, taje tayi fitsari itama tayi alwala ta zo tayi raka'a huɗu kan ta koma ta kwanta, sai asuba ya tashe ta ya wuce masallaci. Ko da ya dawo a kitchen ya samu Maami tana shirin haɗa abin kari "barka da safiya Maami na" Tace "barka dae my son Fatan ka tashi lafiya?" "Alhamdulillah Maami yau ke da kanki ne a kitchen, to da me zan taya ki nima in samu ladan?" Cikin raha tace "Me ka iya? Da Kai da ɗan uwanka duk jirgi daya ya kwaso ku ruwan zafi wannan baku iya tafasawa ba in ba da kettle ba" Yana dariya yace "Ai kitchen ɗin nan sai ku mata Maami ina ganin kokarinku duk abu da ƙuna, yanka bani ciki" Sukayi dariya a tare, Maggi ta bashi yana ɓare mata chan yace "Maami autan ki zuciyarshi tayi yawa, har yau ya kasa sakewa da ni be san kuma bamu da wani lokaci ba" Itama hakan na damunta har yau be zo ba, babanshi ma na complain na ko ya kira daga sun gaisa shikenan "ko da shi ke ma Maami kyale shi, dama zaani ne ya tadda muje ni, ga hali kuma ga yanayin aikinshi" Ya katse ta don ya san tunanin amsar da zata bashi don kar yaga tana kare umar ne ta bar shi take yi. Wani hiran suka kama har ta gama breakfast din yana tare da ita, shi ne miko wannan miko wanchan, dibo ruwa. Masu aikinta ne suka fitar da abincin zuwa dining daga shi har Maami suka je suka yi wanka kusan a tare su huɗun suka fito, Mukhtar ya ja wa Abba kujera yana zama yace "Abba yau zaka ci girkina na san sai ya kai maka karo bari na tabbatar da lafiyar kujerar nan kar santi ya kwashe ka" Dariya suka yi Abba yace "tafi nan, da de bamu san asalin balbela bane kai yaushe ka iya ko kunna gas din ma? Ko binty ya iya?" Ya faɗa kaman yadda ya riƙe bakinshi saboda yawan faɗan Binty da Maami take. tana dariyar yadda ya kwabe fuska tace "Babu abin da ya iya Abba" Yace "Maami faɗa musu don Allah ba ni nayi ba?" Tace "kwarai kuwaaa" Yadda ta faɗa da alamun tsokana a muryarta yasa suka kwashe da dariya Abba na cewa "faɗi gaskiya dai daga jin wannan amsawan naki da walakin goro a miya" Abincin suka fara ci cikin natsuwa, jujjuya cokalin kawai Alayah take yi, Mukhtar da ya lura yace "Fatee lafiya? Ko wani abu na damun ki ne?" Shima ba ci yake ba ruwan zafi yake ɗan kurba. Maami tace "Binty akwai matsala ne?" A hankali tace "Maami kirjina ke ciwo sossai" Abba yace "Subhallahi Meyasa baki yi magana tun ɗazu ba? Mukhtar tashi maza mu wucenku asibiti" Duk abincin suka bari Maami taje ta ɗauko musu mayafi zuwa lokacin ko tsayuwa Alayah bata iya yi tuni suka yi meddy specialist hospital hankalinsu a tashe. *Har yanzu dae ana nan a free pages karku manta book 2 na kuɗi ne zaki iya biya ta wannan asusu 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin sai ki tura shaidar biya ta wannan layi 09039206763* 🖤Gureenjoh🖤 AL'AJABIN SO      (heart touching story) Fatima Muhammad Gurin (Gureenjo) Adabi Writers Association Book 1 *Page Twenty Four* Dr Philips ne ya yanke musu tsawon lokacin da suka ɗauka suna jiran tsammani, da hanzari duk suka isa kusa dashi kowa na rige-rigen tambayar ya take? "Akwai contraction between her illness nd the baby, dole za'a yi mata aiki a cire shi a watanni bakwai in ya so a bashi duk wani kulawa a incubator she cannot take it for completely nine months” Duk jikinsu yayi sanyi, sai da ya basu kwarin gwiwa ya tabbatar musu da ikon Allah in an cire they will be all safe, tuni aka kawo papers Mukhtar ya saka hannu. Bai sani ba ko don saboda firgicin da yake ciki ne ko kuma wani abu na daban wani irin hajijiya ya kwashe shi saura kiris ya faɗi Abba ya tare shi, suka zauna suka shiga kwantar mai da hankali, nurse ce ta fito tace zasu iya su ganta kan a shiga aikin, duk suka miƙe suka nufi ɗakin, murmushi ne kwance a fuskanta ta kalli Maami ta miƙa mata hannu, da sauri Maami taje ta riƙe Alayah tace "Maami ko a yanzu na mutu kun gama min komai, kun bani farin cikin da na rasa tsawon shekaru, Maami ko da wani abu ya sameni ina da tabbacin zaku cigaba da kulamin da ummi, idan kuma Allah yayi ikonsa bamu yi sallama ba ku tabbatar mata da cewa na mutu da ƙaunarta kuma ku ce don Allah ta yafemin" Da sauri Mukhtar ya sa hannu a bakinta ya rufe "Haba fatee wani irin zance kike yin nan? Mata nawa aka yi wa Cs suke cigaba da rayuwa har ma su cigaba da haihuwa, ki daena irin wannan furuci kin ji, zaki haihu lafiya zaki rayu ki kular min da baby har zuwa jikoki" Abba ma yace "zaki samu lafiya kin ji? Allah ya raba lafiya yasa ayi cikin nasara" Maami dae ta kasa magana sai shafa kanta da tayi tana mata Adu'a suka fice suka bar Mukhtar. Zama yayi ya riƙo hannunta tana kallonshi a hankali tace "Ya Mukhy ba zaka faɗa min abin da yake damunka ba ko? Kana so in mutu ban san menene matsalarka ba ko?" "Fatee na!" Ya katse ta, ta lumshe idanu shi kadai ne yake kiranta hakan a duk fadin duniya "Ya Mukhy" Yace "in kina so mu shirya karki sake maganan mutuwa, in shaa Allahu ba zaki mutu ba, not now not any moment from now..!" Bata yi mamakin ganin hawaye kwance cikin idanunshi ba, peck yayi mata a Goshi ya sake yi mata a lips yace "Ina sonki!" Murmushi me kyau ta saki tace "Nima ina kaunarka Yayana" Miƙewa yayi saboda Shigowar nurses ya sake mata peck a Goshi yana shafa kanta yace a hankali "Allah ya raba ku lafiya" Ficewa yayi ba tare da ya sake kallonta ba sbd hawaye dake zuba mishi, ashe yana da rabon ganin ɗan shi ko ƴar shi, ajiyar zuciya yake ta saukewa a kai a kai. Wayan Abba ne ya ɗauki ƙara bayan tsawon lokaci suna zaune, dubawa yayi sai ya ga Umar ne, ɗagawa yayi da sallama suka gaisa yake tambayarshi Maami fa tun asuba yake kiran wayanta ba'a picking. "Muna asibiti ne da matar Mukhtar za'a yi mata Cs, ga Maamin naku" A hankali yace "Allah ya raba su lafiya" Maami ta karɓa suka gaisa ta ɗora da "Lafiya kuwa auta kake ta kira tun asuba?" Don ta ji maganansu da Abban ta sake ɗorawa da cewa "tunda nayi sallah na bar wayan ɗaki zuwa kitchen ko da na gama abin kari ma naje nayi wanka ban duba ba kuma ka ga daga wurin karin ne muka yo nan asibiti ko abincin bata ci ba baiwar Allah" Nannauyar ajiyar zuciya ya sauƙe ta ɓangaren shi tana jin sautin iska da ya fesar yace "Ummi!" Don haka ya ji Maamin na kiranta, da sauri ta miƙe tsaye "Me ya sameta? Sun ƙiraka daga asibitin ne? Me suka ce?" "Calm down Maami, ta farka ne cikin dare, farkawan kuma be zo daidai ba sai jikin ya rikice, tun 2 suka ƙira ni akan if possible ayi gaggawar fita da ita i don't want to call you that time so we arranged emergency craft aka ɗauketa daga nan zuwa saudi saboda chan ya fi kusa da nan Lyon, am presently at the hospital Doctors basu fito ba dai tukuna". Ajiyar zuciya ta sauƙe tana zama cikin sanyi ta soma jero mata adu'ar samun lafiya tana kuma godiya wa autan nata, ta san ko Abban shi ne zai yi wannan dole za'a samu delay ba kaman shi ba da yake da connections masu yawa, bayan sun kashe take yiwa su Abban bayani adu'ar samun lafiya suka yi mata da kuma burin a fito da Alayah lafiya bayan ta warke su tafi chan gabaɗaya. Some hours later Dawowansu Abba daga Sallar azahar kenan likitoci suka fito suna musu albishir samun ƙaruwar ɗa namiji yana ma nursery a incubator zasu iya zuwa su ganshi. Mukhtar yace "maman fa?" Cikin murmushi suka ce itama lafiyanta ƙalau bacci ma take, sai a lokacin tsantsan farin cikinsu ya bayyana a take Maami ta karbi wayan Abba ta soma kiran en uwa tana gaya musu matar mukhtar ta sauƙa lafiya, an sha mamaki kam don bakwaini ne aka haifo musu, kan ka ce karfe biyu en uwa da abokan arziki na ta zuwa sai dae a ga yaro a incubator tarr kamanninshi da Mukhtar kaman an tsaga kara. Shi kam ba'a tantance wani yanayi yake ciki, yana nan zaune tare da Alayah har bayan la'asar ma Abadan kan ta farka, lafiya ƙalau ta tashi jikin kuma da ɗan ƙarfi dayake plaster ne aka mata ba ɗinki ba, ta ji daaɗi kwarai da ta samu labarin ɗan ta lafiyanshi ƙalau, saida aka kimtsata ta ɗan ci wani abu kan Mukhtar ya taimaka mata zuwa nursery don yaron ya ci abinci sai kuka yake, sun so ta matse aje a bashi sai dae Maami tace gwara dae ya ji ɗumin mahaifiyarshi. Da ita da shi ne gaban incubator ɗin wata nurse ta ciro musu babyn, Mukhtar ne ya soma karbar shi ya rungume a kirjinshi sassanyar hawaye na bin fuskanshi a kan lips dinshi yake ta furta "Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!" Adu'a yayiwa yaron don musamman ya koya saboda burin kaiwa ranar da zae ga ɗan nashi a duniya Dukda bashi da wani kwarin gwiwa. Miƙa mata ɗan yayi saboda nurse ta gama taimaka mata ta wanke bakin nonon kar yaro ya sha bacteria saboda kula irin tasu barin ma wannan da yake bakwaini dukda lafiyayye ne, saida ya ba yaron zamzam da dabino kan ya taimaka mata ta soma feeding nashi Dukda zafin da ya ziyarceta, ya sha kuwa yana ta sauke ajiyar zuciya. Sun jima sossai wurinshi dab Magrib suka fito, ya kaita har ɗaki kan ya wuce masallaci. Kan ka ce kwana bakwai tuni ta koma normal tana komai da kanta har wanka, sai su sa leda a bakin wurin su ɗaure da zani ta yadda ruwa ba zai taɓa ba tayi wankanta, yaddikon Maami ce ta zauna da ita tana kula da ita sossai kuwa, kullum asibitin a cike, Mukhtar ya ce ba za'a yi taron suna ba walima ce a ci a sha ayiwa yaro Adu'a so a gidan Maami aka yi dukda ba yaro bare mahaifiyarshi, yayi hakan ne saboda sanin cewa haka annabi ya umurta da a yi ba irin na yanzu ba da za'a tara jama'a a saka dj wurin suna bayan albarka ake nemawa yaron. Kowa ya shiga mamakin jin sunan ɗan wai Mukhtar sai dae babu wadda ya ce don me tunda uban shi ne ya sanya mishi hakan, ganin bashi da wani matsala a duk checkups da aka yi sai kawai suka sallame su bayan sun ƙara week kuma har lokacin Alayah bata san ummi bata ƙasar ba, a duk sadda Maami zata yi waya da Autanta ficewa take kuma yana tabbatar mata da tana samun sauƙi sossai yanzu har tana iya gane wadda ke kanta. A sati biyun sau wurin uku yana zuwa daga wurin aikinshi a Lyon ya koma, taji daaɗi kwarai yadda ya ɗauki ummin da muhimmanci Dukda be san ma wacece ita ba bayan surukar gidansu, wannan tausayi a jininshi yake. Yau bayan Maamin ta gama yiwa baby komai yayi bacci a lokacin tabawa suka fito da Alayah daga bayi a bakin gado ta zauna ta soma kokarin shiryawa, ɗakin banda ƙamshin turaren wuta babu abin da yake fitarwa, wani kalar kunu ne da bata ma san ko sunanshi ba banda wani fitinannen kamshin kayan yaji da yake babu abin da yake Dada ne ke aiko mata kullum kuma tana jin daaɗin shan shi, ƙamshin shi da taji ne yasa ta kalli gefen gadon Maami ta tsiyaya mata sai turiri yake murmushi ta saki, jegon gata take ita kam bata da abin cewa ga Maami don ko ɗiyar da ta haifa a cikin cikinta karshen abin da zata yi kenan. "Oya hanzarta kar kunun ya huce" Ta amsa da to kan Maamin ta fice, agogo ta kalla karfe goma da rabi, sam bata ji motsin Mukhtar ba yau don haka ta nufi ɗakinshi, a kwance cikin bargo ta same shi zazzaɓi mai zafi ya rufe shi banda rawan ɗari babu abin da yake, da sauri ta ƙarasa kanshi ta yaye bargon tana cewa "Subhallahi Mukhtar zazzaɓi kake yi shine ka shigo ɗaki ka kwanta kai kaɗai haka? Tashi mu tafi asibiti maza" Tana kokarin juyawa ya riƙo hannunta, a hankali ya buɗe idanunshi da suke lumshe wa da kansu yace "Maami ba wani abu bane ba fa, in na watsa ruwa na sha panadol zan samu sauƙi" Girgiza kai tayi tace "inaa ba zai yiwu ba Mukhtar, wannan ne kake cewa ba wani abu ba? Yaushe rabon da ka ci abinci a cikinka? Ina fa kula da al'amuranka zazzabin nan ya jima a jikanka kake yin shi tsaitsaiye ga rama marar dalili gwara dae mu je asibitin sai ya fi" "Maami don Allah dae ba sai na je ba, bari na ƙira Dr Ahmad ma kawai zai zo ya duba ni a gida" Ba don ta gamsu ba ta miƙa mishi wayan ya ƙira Dr Ahmad akan ya zo gida ya duba shi please, shakuwar dake tsakaninsu a yanzu ya wuce na patient da Dr sai na friends sun zama abokai sossai don a yanzu bashi da abokin da ya wuce Dr. Ahmad, ko kayan suna na ban mamaki ya aiko matar shi dashi kuma sau kusan uku tana zuwa asibiti da abinci niki-niki wa me jego har za'a iya cewa sun ɗan saba da Alayah. Komawa ɗakin Alayah Maami tayi ta samu ta gama shan kunun, dubanta Alayah tayi tace "Maami ya jikin Ummi? Har yanzu ba wani chanji ko? Kullum da ita nake kwana nake tashi har na haihu ummi bata sani ba" Ta ƙarasa hawaye na gangaro mata "Ummi ta farka Alayah tana cigaba da samun kulawa" Wani irin zabura tayi "tana iya magana? Tana iya gane komai? Maami don Allah zan je asibitin na ganta! Na san tana chan tana tunanina babu bakin da zata ce a kira ni" Maami tace "in shaa Allahu zaki je Alayah, yanzu dae ɗauki Wannan mijin nawa ku je ya gaida babanshi babu lafiya likita ma na hanya" Tana cikin farin ciki kwarai da jin ummi ta farka tana samun kulawar da ya dace, Adu'a tayi ta yiwa su Maami, cikin jin daaɗi ta miƙe ta saka kayanta plain riga da zani, duba system ma dama take son yi sbd lectures dake ta wuce ta nan ma don farkon semester ne da a tsakiya ne ta haihu da ta ga bone, ba laifi kuma dayake tana da fahimta sossai ko a hakan tana ganewa sossai, dama su suna online class sossai sbd yanayin course na su. Yaron ta ɗauka yana ta muimui da baki, ta lakaci hancinshi da sak na babanshi tace "dube shi, yanzu ya sha baccin shi anjima yace bamu isa mu yi bacci ba" Murmushi ne kwance a fuskanta in ta ga wannan yaron sai tace oh yau ni Alayah ce na haihu, ni ke da yaro kyakyawa irin Wannan Alhamdulillah! Ɗakin Mukhtar ta nufa, a natse ta sanya hannu zata tura kofan ta ji yayi magana da ɗan ƙarfi "Dr. Ahmad Don Allah ka kyaleni ba zan yi ba! Ba zan yi ba nace! Me ya saura? Kar ka sake min barazana da sanar da iyalina saboda a yanzu bana buƙatar tashin hankalinsu, don Allah ka rabu dani da zancen nan..." "Mukhtar ka yiwa Allah ka bari a gwada, sai fa an gwada ake samun dacewa, zamu dace don Allah ko ɗan uwanka mu sanar wa in ya so ko ba anan ba sai ayi, its getting late please don't let it be worse than this u really are sufferring" Mukhtar zai yi magana kawai suka ganta a kansu? "Me za'ayi? Menene ba'a so mu sani? Me kake ɓoyewa ya mukhy?" ***** Zaune take cikin tantsamemen parlorn nasu, iyayenta na kan dining suna cin abinci, a yanzu ta san babu wacce ta kai mommy jin daaɗi saboda hankalin Abbanta da ta kawar kan Waenchan banzayen, yanzu burinsu ya cika suna rayuwa cikin jin daaɗi su ukun su babu wata matsala, hankalinta ya rabu gida biyu tana jin hiran irin kayen da Abban su Mukhtar ya sha saboda abinda Mukhtar ya aikata Dukda daga baya an gane ba sa hannunsa sai dae baƙin alƙalami ya riga da ya bushe. Mommy tace "ko dae farar kafafun waennan sadaka yallar da ya kwasa ba, ai sun ban mamaki daga shi har matar tashi da basu san menene ma'anar arziki ba ai arziki shine a ci a sha a nunawa talaka wutsiyar rakumi tayi nesa da ƙasa" Abban Meelah yace "nayi mamaki daga baya wai akan mutanen nan Alhj Hammad Abdulhameed yake gayamin magana hmm gashinan nan wadda be ji bari ba ya ji hoho" Wani irin Miƙewa da Meelah tayi tare da buga salati tana wani zazzare idanu shi ya firgita su suka yi kan tilon er ta su a rikice suna tambayar me ya faru? Ta kasa magana sai kawai ta sake fasa ihu "Jameelah menene? Menene a wayan?" Abba ya ƙarasa ya ɗauko sai ya ga rubutu ne kawai ta riƙe Mommyn tana ta zare idanu chan da kyar ta fusgo maganan "Mommy....Captain cold.. Captain cold!" "Na gane Captain cold naki, wadda kike matukar so amma baki gama bincike a kansa ba me ya same shi? Ya rasu ne?" "A'a mommy be rasu ba! Mommy sai dae kila na rasa shi, mommy Captain cold complete name ɗin shi Umar Hammad Abdulhameed chanji... Ƙanin mijin Wannan shegiyar.. Mommy Meyasa kuka bari kuka ɓata da babanshi? Abba ka yi mishi magana don Allah ku shirya ina son Umar ba zan taɓa aure ba in ba shi na aura ba" Duk ta rikice ta rikita iyayen nata, "Wai kina nufin ɗan Alhj hammad chanji shine Captain din naki? Meyasa baki faɗa da wuri ba?". Abba ya ce yana riƙo ta. "Abba personal information ɗin shi are very very confidential saboda yanayin aikinshi, na shafe sama da shekara ina nema na kashe kudade masu yawa don kawai ko full name nashi na samo. Wayyooo na shiga uku!" "Baki shiga uku ba! Zaki aure shi Jameelah na miki alƙawari!" *Kar dae ku manta book 1 na gab da karewa wadda be wuci shafi biyu bane suka saura in ma na samu lokaci a goben zan gama su, ku yi hanzarin yin payment don karatu na gaba, in shaa Allah ba zaku yi dana sani ba. 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai shaidar biya ta nan 09039206763 500 Naira kacal* 🖤Gureenjoh🖤 AL'AJABIN SO (heart touching story) Fatima Muhammad Gurin (Gureenjo) Adabi Writers Association Book 1 *Last Page of book 1* Ba zata ce ga yadda aka yi aka gama duk wani formalities na karɓar gawa ba, ba zata iya fasalta halin da take ciki ba har aka gama komai da ya kamata a yi, idanu kawai take bin taron mutanen da kaman yayyafinsu ake, a take ilahirin gidan Maami ya cika maƙil wasu na Adu'a wasu na zub da hawaye, lallai duk wadda ya san Mukhtar a watanni bakwai zuwa takwas da yayi bayan shiryuwar shi ya san ya rabauta, gabaɗaya alkhairanshi na kwanakin ake tunawa, da kyar take fidda numfashi bata sanin duk abinda mutanen da suke zagaye da ita ke cewa, ita dae gata nan ne ga yanayinta. "Ina matarshi? Ta zo suyi sallama" Wani ɗan uwan Abba ya leƙo bayan sun ƙira Maami ta jima a chan, Aunty ruqayya ce ta kama ta ta miƙar tsaye sai taji kaman kafafunta ba zasu iya daukar ta ba, abin mamaki kuma sai ta ganta tana tafiya ɗin kaman a iska har zuwa gaban gawan Mukhtar, a kan gwiwowinta ta zube, da kyar tayi kokarin fusgo kalmar "Innalillahi wainna ilaihi rajiun shikenan ko? Shikenan kai kuma ka tafi ka bar mu da wannan ruɗaɗɗiyar duniyar, ya Mukhtar Meyasa yanzu?.." Tayi saurin yanke maganan tace "Astagfirullah na san baka yi sauri ba, muma bamu yi jinkiri ba kowa lokacin shi yake jira da yayi babu me karfin ikon hanaka tafiya, Allah ya gafarta maka Ya Mukhtar, Annabi rahama ya san da zuwanka lallai ayar Allah tayi aiki akan ka..." Su baba ta kalla tace "Ashe ba'a yankewa bawa tsammani? Ashe babu mahalukin da ya isa shiga tsakanin bawa da mahaliccinsa? Alhamdulillah in shaa Allahu naka yayi kyau, Ba zan maka kuka ba kaman yadda na yi maka alƙawari, ba zan yi ba.." Tana maganan ne a rarrabe hawaye na bin fuskanta da tsananin gudu, gabaɗaya ta ɗimauce, babu wadda ya hanata kowa yayi ƙasa da kai yana zub da hawayen tausayinta. Adu'o'i ta cigaba da jera mishi ana amsawa, saida taji bata iya jan numfashi kan ta dakata, babu wadda ya tsaida ta saida ta gama da kanta ta kai zaune tare da ɗaura hannunta akan gawan ta saki sanyayyiyar kuka da ya kara ɗaga hankalin mutanen wurin, Maami ce da itama hawaye take ta zo ta ɗaga ta, haƙiƙa mutuwa akwai ɗaci kuma akwai zafi sannan aya ce me girma a garemu ga duk wadda ya san labarin Mukhtar zai gasgata faɗin Allah na ɗayanku zai kasance yana aikata sharri har sai gab da zai mutu sai ya aikata alkhairi ya shiga aljanna, haka idan babu rabo ɗayanku zai kasance yana aikin alkhairi dab zai mutu sai ya aikata sharri ya shiga wuta. Allah ka sa muna da rabo a aljanna. Suna ji suna gani dumbin al'umman musulmi suka sallaci Mukhtar bayan an idar da sallahn juma'a aka tafi da shi gidan gaskiya, gidan da kowa zai je shi, a jikin Maami numfashin Alayah ya ɗauke rushing ɗinta aka yi zuwa hospital sanin condition ɗinta. **** A hankali take buɗe idanunta da suka yi mata nauyi ainun, dishi dishi take gani hakan ya sa ta ɓata lokaci sossai idanun nata zube a ceiling kan ta fahimci asibiti take, daki-daki haka hoton rayuwarta daga farko zuwa yanzu ke dawo mata kaman wacce aka kunnawa magiji(television) har zuwa kan fitar da Mukhtar da aka yi wadda shine ƙarshen abinda zata iya tunawa, idanun ta maida ta lumshe hawaye na bin gefe da gefen kuncin ta, hannu taji ana share mata a hankali ta waiga sai idanunta suka faɗa cikin na Meelah. Bata san ina ta samo ƙarfin tashi zaune ba tsabar mamaki da ya so kasheta daga kwance. "Jameelah?" Ta maimaita a kan lips ɗinta Da sauri Aunty ruqayya dake zaune kan sallaya ta miƙe "Alayah? Kin farka? Sannu ya jikin?" Kallonta tayi ta sake kallon jameelar dake ta zabga mata murmushin da ya fi kama da na mugunta ko na makirci a hankali tace "da sauƙi Aunty" Ficewa Aunty ruqayya tayi da niyyar kiran Dr yayinda Jameelah tace "Sannu Sis, sai kawai kika ganni, mun samu labarin rasuwar mijinki ne yasa nace bari na zo na miki gaisuwa sai kuma muka tarar kema ba lafiya gashi har yau kwananki goma sai dae ki farka ba cikin hayyaci ba a sake miki allura ki koma, sannu Allah ya gafarta masa" Ta ƙarashe da fuskan damuwa. Dukda abin da take ji ya tokare mata zuciya hakan be hana ta yin murmushin dake bayyana zallar takaici ba, wannan kuma wani sabon salon wasan kwaikwayon ne? Baya ta matsa ta jinginu da gini a hankali kan ta furta "Ameen" A kan labbanta bata sake magana ba har likitan ya shigo, ko duniya zata naɗe bazata taɓa yardar wa kanta saboda Allah ne Jameelah take zaune a wurin ba, ta riga ta san su farin sani son zuciyarsu kawai ke kaisu gangar wadda suka ɗauka makiyi, kuma ita bata ga dalilin sake shigowa rayuwarsu da take kokarin yi a karo na biyu ba ka guji soyayyar maƙiyi don da matukar wuya ya kai zuci. Sossai Dr Philips ya dubata kan ya cire mata karin ruwan yace ta watsa ruwa ta ci wani abu sai a mayar, Jamila ta miƙe don taimaka mata tayi saurin ɗaga mata hannu, a ranta ta saka zata nunawa jameelar yanzu da da akwai bambanci komin ƙanƙantarshi kuwa, duban Aunty ruqayya tayi tace "Ayyah Aunty ruqayya ɗan taimakeni zuwa bayin" "Ok Binty" Kusan haka bakinsu ya riƙe sbd yadda Maami ke yawan kiranta da hakan, da taimakonta ta shiga bayi tayi wanka da ruwa mai zafi, ko da ta fito ta samu Maami a ɗakin da Mukhtar Junior da kuma Tabawa, sannu duk suka mata har ta zauna sai a lokacin Jamila ta musu sallama ta fice, da kallo duk suka bita kan Alayah ta kalli Maami "Maami ko me ya kawo ta?" Maami tace "yadda kika gansu haka na gansu Alayah, Abbanku ma har mamakin ganin Alhj Alhassan ya zo gaisuwa yayi itama matar tashi tana zuwa gida, bamu dae ce musu komai ba kuma ina so ki kiyaye don bamu san da wani sharrin suke tafe ba" A hankali Alayah tace "In shaa Allahu Maami" Daga nan ta shirya aka ɗaura mata Mukhtar Junior kan kafafunta ta soma bashi abincinshi ya ƙarba kuwa da gudu bawan Allah, haka ta zubawa fuskanshi idanu ranta na kunar tuna Mukhtar sai dae tayi alkawari bazata sake mishi kuka ba don haka bata yin ba sai Adu'a da tayi ta mishi a ranta. Haka ta ƙara kwanaki kusan biyar a asibitin kan aka sallameta ta dawo gida, Takaba take ga goyo hakan yasa lokaci ɗaya ta chanza rama ya sake mata sallama Dukda Maami na kula dasu sossai, kullum da tunanin Mukhtar take kwana take tashi, karatunta da take online ma sai da Maami tayi da gaske kan take ɗan bibiyan wasu abubuwan da tace sai de tayi deffering, kowa ya san yadda mutuwa yake a hankali ta rungumi kaddara da sabuwar rayuwar da littafin kaddara ta buɗe mata, burin ta guda ɗaya yanzu shine ta fita takaba ta ziyarci mahaifiyarta wadda Maami ta mata alƙawari tana fita takaba ba zasu kara sati biyu ba zasu tafi. A lokacin da zata fita ɗin a lokacin zata soma exams kuma paper takwas zata yi cikin sati biyu zasu gama sai su wuce, sossai take kula da mukhtar Junior da yake girma so masha Allah. Tana kwance akan sallaya Maami ta turo kofa da sallama ta shigo ɗakin, a hankali Alayah ta miƙe zaune tana gyara hijabin jikinta hannunta na cigaba da jan casbinta. "Sannu Maami" "yauwa binty, wannan yarinya ta zo wurin ki" Sama Alayah ta ɗan kalla da alamun tunani don bata san wace ba sai da Maami ta ce "Jamila" Gira ta haɗe in confused way tace "Me yarinyar nan kuma take nema da rayuwata?" Maami ta matso ta zauna bakin gado tace "shiyasa ban barta ta iso har nan ba, ina so ki yi taka tsan-tsan da lamarin ta don haka kawai ba zata soma shige miki ba bayan abubuwan da suka faru a baya, ki kiyaye kin ji?" Kai Alayah ta gyaɗa ai ko Maami bata faɗa ba bazata taɓa son mutanen ba, da ma ita kaɗai suka kuntatawa da sauƙi amma har mahaifiyarta babu irin cin kashin da basu mata ba sannan yanzu su zo suna buɗe mata haƙori kuma ta aminta dasu? Never. Miƙewa tayi ta fito a hankali ta sauƙa stairs tana kallon Jamila dake zaune cikin kujera hannunta riƙe da juice da aka kawo mata tana sha, tana ganin Alayah ta hau murmushi "sannu sis" Ita Alayah dariya ma abin yake bata ikon najahu ji take abin na mata banbaraƙwai wai namiji da suna Hajara shine wannan. "Yauwa sannu" "sai kika ganni, zan ɗan wuce ne nace bari na shigo dae mu gaisa" Alayah da take ta kallonta abubuwan da suka faffaru wasu na dawo mata ta girgiza kai "eyyah na kuwa gode" Shiru ne ya ratsa wurin kan Jamila tace "yauwa ni ko nace akwai ƙanin mukhtar da tunda nake zuwa ban haɗu dashi ba na kuwa so in mishi gaisuwa a matsayin relative naki" Sai a lokacin ma wani suna umar yayi clicking mind ɗin ta, murmushin takaici tayi ita ma bata ganshi ba bare Jamila, haushin shi ma taji tana ji da wani irin takaici da ta rasa na menene, babu shakka kila na abubuwan da yayiwa Mukhtar ne bayan tuban shi, kuma ace har Mukhtar ya mutu bata ji labarin ya zo gaisuwa ba. "Eyyaaa kin ga kuwa baya nan, ya ma koma ƙasar da yake aiki" Tana kai nan tayi shiru, duk shiru suka yi don ba sabo bane tsakaninsu, hasali ma Jamilar kaman forcing magana da smile din duk take. "Oh Ayyah, to bari na zo na wuce sai na sake shigowa" Ba tare da Alayah ta miƙe ba tace "Allah ya kiyaye a gaida mutanen gida" Da kallo ta rakata har ta fice, girgiza kai tayi ta miƙe ta koma sama. Wasa wasa sakanni kan juya ya zama minti, mintuna su juye zuwa awanni, awanni su zama kwanaki, kwanaki zuwa satittika zuwa watanni wai yau Alayah take cika watanni huɗu da kwana goma cifff da mutuwar Mukhtar inda a yau din take fita takaba, kaman yadda al'adarmu take an yi mata hidima na kayayyaki sossai da kyaututtuka kan aka yi sadaka aka ɗan taru aka yi Adu'a, sai a lokacin Abba ya aika a kira Alayah. A natse ta shigo babban parlorn baba ne da wasu da bata sani ba waenda suka haɗa da aminan baban sai en uwan Abba da wasu abokan shi sai Maami, a ƙasa ta zauna kanta ƙasa, haka kawai ta tsinci kanta da matsanancin faɗuwar gaba. Bayan sallama da ƴar nasiha da kuma Adu'a da aka sake bin Mukhtar da ita Baba ya dubi Alayah yace "Mun kira ki nan ne akan abubuwa guda biyu zuwa uku Fatima, muna fata zaki bamu haɗin kai" Kai ta gyaɗa baba ya cigaba "akan maganan gadon Mukhtar, kasancewar yana da ɗa kuma namiji kowa anan ya san dukiyar kusan duka nashi ne illa iyaka za'a cire miki naki sai na iyayenshi, menene kike tunani akan gadon yaron?" Kanta a ƙasa tace "Baba da ni da Junior duka muna a ƙarƙashin ku ne, duk abinda kuka yanke daidai yake a gareni" Kai ya gyaɗa kan yace "Masha Allah, haƙiƙa ban taɓa alfahari da Mukhtar ba irin na lokacin da yayi min rantsuwa da alqur'ani cewa arzikinsa babu haram ciki, nayi murna kuma da Naji jajircewar ɗan uwansa a kansa ne ya hana shigar haram cikin dukiyarsa sai kuma karfin adu'ar uwa, a shawara ta shine a bar wa umar ya cigaba da kula masa dashi zuwa ya mallaki hankalin kanshi na tabbatar ba zai taɓa cin amanar dan uwansa ba" Kowa yayi na'am da haka sai de ita Alayah ta ɗan ji wani iri, Allah ya sani zafin wannan umar ɗin take ji. Abba ne ya karbe zancen "sai abu na gaba, alfarma muke so mu nema a gareki wadda muke fata zaki yi mana shi" Kai tsaye tace "Abba tsakanina daku babu alfarma, ku matsayin iyaye kuke a gareni a lokacin da duniya ta yi mini kunci, rayuwa tayi zafi komai na cikinta yayi tsanani na rasa madafa ku kuka tallafeni kuka bani inuwa, kuka kula da maraicina kuka kula da mahaifiyata babu kyama ba kyara, kuka so ni fiye da ɗan da kuka haifa, in har umarninku be saɓa na mahallacina ba, ba ma sai na ji ba na amince, wallahi na amince" Maami tayi murmushi dama ta san Alayah ba zata watsa musu ƙasa a ido ba, Baba yace "Masha Allah, dama amincewar shine babba je ki Maaminku zata miki bayanin komai a ciki" Miƙewa tayi ta fito yayinda maami ta bi bayanta, a ɗakin Maamin suka zauna don gidan akwai tsirarun en uwa, hannunta Maami ta kama a hankali tace "Fatima hakika mahaifiyarki tayi matukar kokari wurin gina miki tarbiya, kowacce uwa zata yi fatan samun sirika irin ki wacce zata taya ta son ɗan ta ta kuma taya shi gyara tsakanin shi da Zuri'ar shi, wacce zata kula da dukiyar shi ta kare martabarshi, wannan nagarta naki na duba na ga ba zan bari nayi asarar ki ba, ba zan bari Junior yayi agolanci ba, ba zan iya bari ki subuce mana ba hakan yasa na nemi da a ɗaura miki aure da umar a yau kuma Alhamdulillah baki bani kunya ba kin amince, nayi matukar farin ciki ina kuma fata da burin mutuwa ce zata raba ku...." Tun da Maami ta ambaci aure da umar bata sake fahimtar sauran zantukan ba saboda wani irin tashin hankalin da ya ziyarce ta... AURE? bata dawo daidai ba ɗan Aunty Aysher ya shigo da hanzarin shi yana ba Maami Alewa "Maami gashi yanzu Abba ya bani wai na auren Uncle umar?" Murmushi me kyau Maami ta saki tana furta "Alhamdulillah har an ɗaura kenan" Wani irin sarawa kan Alayah yayi jiri taji tana gani. Gwarama! *jama'ar Allah jama'ar kwarai anan na kawo karshen book one1, kaman yadda muka sani book 2 na kuɗi ne zai zo muku akan Naira ɗari biyar kachal har yanzu akwai sauran tafiya akwai kuma tufka da bama mu fara warware shi ba, shin umar ya san da zancen auren? In ya sani zai karɓa kuwa? Ita kanta Alayar ba farin ciki tayi da wannan aure ba, ita kenan haka ƙaddarar ta? In shi umar din na da wani hali fa kaman yadda aka haɗa ta da Mukhtar a farko karfi da yaji? Ya labarin umminta zata farfado kuwa har ta warware musu tufkar dake tsakanin Hassan da Ahmad mahaifin Alayah? Ina Ƴan uwa da danginta? Shin kuna ganin Jamila zata yi hakuri ta bar wa Alayah Captain Cold ko kuwa haka zata ƙare kaman yadda mahaifiyarta ta kare cikin AL'AJAB Na So? Ta yadda tana ji tana gani abinda take so ya fi karfinta? Ku biyo ni ku sha karatu* 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin 09039206763 🖤Gureenjoh🖤 Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels