Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ ⚜⚜⚜⚜⚜ ⚜ *AMRATU* *Written by* *Khadija Muhammad* *Ummusulymn* *And* *Fatima Aminu Ya'u* *F.A.Ya'u* *Bissimillah lahir-Rahmaneer-Raheem* Da gudu ta shigo tafada kan mami dake zaune wash mum nagaji wallahi tai dariya kin gaji kuma kike san karya ni ko haba mami sai kace wata mai kibar axo agani Aliyu dake gefe yana cin abinci ya wurga mata harara kaga ni kadaina hararar mun diya wallahi mum kina shagwaba yarinyar nan da yawa ace yarinya tana SS3 bata dena hawa cinya ba tunda dai ba cinyarka ta hauba ai saika xuba ido. Ke jeki ki daukon abincina kai yaya kai yaya ta fada tana xunbura baki aikifa nake ke nikike fadawa kina wani abu yakai hannu xai maketa tai saurin direwa daga kujerar mami dake shigowa tace kul karka sake ka daketa ta koma bayan mami tanai masa gwalo yakara kuluwa amman mami anman mai inajinku ace ka bi ka gallabi yarinya bakaga rubutu take ba baka ganin salame baka sata kenan mami ni ban isa in aiki kanwata ba kenan oho duk yadda kadauka. Kanwis mai ake dafa mana ne nafaji kanshi ko ina mutumin naka ne ah kice yau da gara yafada yana dariya maxa gama kixo kiga abinda na kawo miki tai dariya that's my yaya sulaiman shima yandariya😀yace that's my little sister shiyasa nake sonki suna shirmensu mummy ta shugo tare da murmushi matsalata daku akwae hankali Suhailat ta turo baki"haba mamy wlh ke kk ja Yaya Aliyu yake mana son ransa" Mummy ta"bige bakin ja'i'ra ba yayanki bane Amra ta fita kitchen a guje tana dariya. Amra ta wayi garin ranar litini da xaxxabi sbd haka bataje makaranta ba tana qudundune a blanket,mamy ta shugo dakin tare da fadin Babyn mamy ya naji shuru baki fito parlour ba har munyi breakfast, kuma nagani baki da niyyar xuwa skul ta yamutsa fuska wallahi mami bana jin dadi ne subhanallahi ta fadi gami da saurin kai hannunta goshin ta yadda taji jikin rau daxafi yasa ta mike maxa wannan ciwon bana gida bane maxa mike Ali yakaiki asibiti ta xaro ido gami da mikewa nawarke umma kinwarke kamar ya bansanfa shiririta kintaba ganin inda mutun yaxauna da cuta tafice bari naje kar shima ya fita inda abinda Amra ta tsana bai wuce wata wurda ta hadata da yaya Ali ba dan bata debewa ta dadi. Mami kinsanfa sauri nake kayi hakuri gadanga yanxu xata fito yakara duban agogonsa gami da xura hannu cikin aljihu ya ciro yan dubu dubu guda shida kibata kawai tahau taxi na makara ce maka akai bani da kudin bata ko kuwa motar hayace bansan ta hau inkuma ban isa insa kabane saika fada bahaka ne mami to maine yarinyarce yar rainin hankali kaga inbaxaka kaitaba ka iya tafiya yi hakuri ya fada atakaice gami da komawa mazauninsa mami ta mike tai sama inda dakin yar lelenta yake. Haba Amra ashe ko tashi bakiyiba Alifa yanacan ke yake jira kinsan halinsa nifa mami nace miki na warke kinci gidanku nace maxa mike ta mike alangabe mami ta ruko hannunta sukayo waje kallo daya yai mata ya dauke kansa ganin yadda take wani shagwaggwabewa kamar wata jaririya yabashi haushi jiyake kamar yaje ya maketa ganin yadda mami duk tabi ta daga hankalinta. Suna fitowa farfajiyar gidan ya galla mata harara dallah malama inxaki nutsu kinutsu bansan iskanci sanin yanxu ba mami ko dady masu tare mata yasa ta nutsu kai bakace Amra din da daxu tafiyama sai ana riketa tana wash wash da tafiya dakyar bace. Haba yar gidan dady kidaure kisha maganin ta turo baki ni wallahi shiyasa banasan akaini asibiti yaya Habule dake gefe yace haba kanwis sha xan sai miki wannan abun naki wayon ta fada mami tace daurewa xakiyi ai daman shi magani badan dadi ake shansa ba kinga kar dadinki yadawo yaga kinrame baxaiji dadi ba sulaiman yashigo rike da waya ya mika mata ungo ta kara akunne hello dady ta fada cikin miryar shagwaba haba baby Amra yanxu yayanki yake fadan baki da lafiya ance allura kinki ga maganinma kinki sha indai kina so mushirya to kisha kinji ko ta hannun daman to dadi phone din yaushe xaka siyon kisha maganin indawo sai asiya to dady karka ji komi xan sha promise promise dad love u dad love u dear ta mikawa sulaiman wayar gami da watsa kwayoyin abaki ya Abdul ya mika mata ruwa a glass cup ta kurbi kadan gami da ya mitsa fuska gabaki daya suka saka tafi kaga yar gidan dadinta da maminta sauran nadare Ali da tun daxu ke xaune kujerar gefensu yanajin abinda suke baice tatafus ba inbanda wayarsa da yaketa dannawa mintina zuwa mintina yakan sakin murmushi alamar hirar tasu da kaltum tanai masa dadi sai yanxu yamike dalla malamai kun cikani da tafin banxa ai dakun kyaleta karta sha waxai ji badadi in cutar ta keantar dashi suna basu ce dashi uffannba ya gama banbaminsa ya bar fallon suka bishi da kallo kaji dashi inji sulaiman ashe mutin bai da aiki sai abota da fada Abdul yace ai matar yaya Ali ta banu da fada waya fadama ai iribsu rakumi da akalane suka saka dariya gaki daya mami tace maxa ku mike lokacin sallah yayi sukai waje yayin da Amra tai bayi.... Amra kinko yi sallah eh mami to maxa tashi ki karya time din shan maganinki ya kusa wayyo mami yanxufa sassafene wane safe gomafa ta wuce ni wallahi baccin nan be isheno ba kaji ja'irar yarinya yanxu da lpyr ki kalau aida kina sch ta ruko hannunta maxa ni fito kinga ansamu zazzabin ya tafi inkika ki shan maganin zai iya dawowa. Dasauri ta mike zonan inazaki kuma baki gama cin a bincinba mami zuwa xan inkara tunawa yaya sulaiman sakona tai dariya se akace miki zama zai yaita jira harsaikin tashi ko to tun daxu ya fice oh my God na kwafsa kinga ba surutu zaki tsaya munba abinci zaki zauna kici ke nake jira zan shiga ciki. Zaune take tana kallo taji ancillo mata leda adan tsorace ta dako yaya sulaiman tagani yana dariya matsora ciya kawai ta daka tsalle shiyasa nakesanka yaya baka mantuwa yai dariya ina zan mance da sakon yar kanwata ta bude kai amnan yaya nagode Allah ya saka saunawa zance ki dena godemun innai miki abu kai anman wannan yafi ma wanda nace maka kyau ta mike da gudu tai dakin mami tana kwala mata kira ke lpy kike kirana haka saikin kashen dodon kunne kingani yaya sulaiman ne ya kawon takarba tana dariya kai anman yayanki ya birgeki mami ki tayani godiya. Kefa yar gata ce wallahi ji nake dama nice ke ko Allah maminki da dadinki nasanki yayyanki nasanki kowa ya kwaso alkairinsa naki ne tasa dariya Bilkisu ta kalleta kinsan Allah yayyanki ba birgeni musanman babban wanku yaya Ali ta turo baki tabdi mugun zakice ke nifa dabadan mami da dady ba ai kullun sai ya bugeni hakan ma sunai masa fada ya aka kaya aikedince wani xubin kinfiye abin haushi wallahi koni shagwabarki wataran sai a slow maryam tace kinji mu da bilki mutum bazai shana ba fada mata dai sis shiyasa nake sanki da yawa. Kinsan mai ni wata alfarma zakimun ki taimaka ki danmun hanya yaya Ali yasoni hhhhh waima rufan asuri kar budurwarsa tajini yanada budurwa tanaso na wallahi nifa harba k'agu yai aure yabar mana gida ma huta ace dad yace anan zai zauna tab ai wallahi saina saka yace yabar gidan kinsan mgn ta yakeji shiyasa yaya Alin kekishi dani. Mami wai yaushe dady zai dawo kya tambayeni keda kika san komi nasa kullun saiya cemun sai nanda sati ni haushina ma karmuyi candy bai gida haba aikema kinsan yanasane da ranar zai zo kodan gujema mitarki mami kema mai mita kike cemun tahawota da wasa nake yar gidan mami. Ke ungo sauran kiyi ta cikata da shirmen banxa kinji ko ta karba tabar gun dan sanin halinsa tana shiga daki tace aunty mukli yaushe xakixo daga can barin tace Amran mami kenan aina kusa zuwa na har abada anman kullum sai mami tace bakixo kin gaidata ba shikenan zanyi tunani shikenan ni zanxo intaho dake hooo amra sarkin rigima nidai zanzo to yaushe aisaidai ki ganni kawai to shikenan sunfi awa suna hira sannan sukai sallama ahankula take tafiya dan karta ganta harta shiga dakin ta aje masa wayar tana fitowa ta tsaya ta ajiyar zuciya alamar tasha saiji tai yace sai yanxu kika gama wayar tai saurin jiyowa tana rawar murya u a daman daman daman me kingama karar mun da kudi ce miki akai hako kudin nake yi hakuri yaya inbanyi mai kikeso nayi sai afkin kiyi barna ki bada hakuri bace mun dagani ni sunsun tabar gun hartakai kofa yace tsaya nashiga uku kije kitchen nakawo kifi mimun romonsa sauran kuma kisa asabe tayimun to yaya ta fice da sauri. Ita tai komai na girkinki inka dauke dakan sakwara da asabe tayi hadadden farfesu tai masa da yaji kayan yaji sai lemon citta kasantuwar tasan yanasansa dining takai masa sannan tai dakinsa yaya angama ya fito falon dakin rike da waya ina yake yana dining haka nace miki acan zanci ayi hakuri tace gami da ficewa tana fitowa ta hango yaya sulaiman yana kokarin zubawa da gudu tai gun ta rike masa hannu rufan asiri na yaya Ali ne yasa dariya kincika tsoron yayan nan kaidai barshi danyafa dady da mami basa ban shine yaketa sani wahala ina mamin ta tafi gidan umma Balara haba koda naji nidai yanxu raina ya biya wallahi aikodai saidai kaje kasameshi yasanma wa rufan asiri tasa dariya ashe dik kanwar ja ce akwai a kitchen kaje ka xube au baxaki zubonba ni wallahi na gaji da yawa to kawo na tayaki kaimasa ya daukar mata saida sukaxo bakin kofa ya mika mata nagode tace tashiga sallama akasan makoshi ya amsa ta ajiye gashi yaya baice komaiba ta mike me kike nufi ni xanma xuba wayyo ta fada me kika ce bakomai tai saurin fade ta mika masa gashi ajiye nan ta ajiye tadan zauna adan kaikaice ya kalleta lafiya daman ko kana buk'atar wani abu no zaki iya tafiya Nagode dasauri tabar dakin karya tuna da wani abu Sannu sis gaskiya na tausaya miki kaidai bari ni ba'abin inkai kararsa ba su kara tafiya ya hadan da duka ni wallahi dama kai mami ta fara haifa dana caba seka dunga zanenshi kodai cikin zamu koma ne tafara haifonin ta turo baki kajika yaya ana magana kana sako wasa yasa dariya. Wallahi mami nai missing dinki yaushema na fitan balle kice kefa kike ta cewa intafi karnai dare Ali yashigo ah dole kice kinyi missing dina dodon naki yana gida kenan tai saurin tashi zaune daga kan cinyar mami ganin yadda Alin ke zabga mata harara kai narasa wane irin mutun ne baka da aiki sai harara barshi mami idon ya fado ai ke nikike fadawa haka sa'anki ne ni yi hakuri tace ta faki idon mami ta mai gwalo mami kina ganinta ko me kuma nagani sarkin mita Allah mami yarinyar nan ta raina ni saita dinga mun abinda taga dama innai mgn ace na fiye fada aikaidinne komai fada me yasa sulaiman bai cewa ta raina shi tun ana tsoronka har sai an dena ya kada kai kawai ya bar gun. Tsaki yaja ni wallahi na gaji da jiran yarinyar nan kullum saita makarar dani banda abin Ali kwanan nan zata gama makarantar nan se ka dena kaita ina komai sulaiman ke mata kai makarantar ma kana mita ina yanxu waec suke ace saida aski yaxo gaban goshi zaka kosa kadaure ka karasa ladanka anman mami kina sane da bata makara a islamiyya bata makara dayake sulaiman ke kaita hakuri zakai da'ace zaka daure ka dena wannan fadan zakaga kun shirya tana makarane dan batasan kake kaita kinji ko mami kemafa dakanki kin fada baso na take ba rai dariya hoo Aliyu kaima kasan tana karama kai tafi so halinka ne bata so tana fitowa tace mami sena dawo to yar maminta Allah ya bada sa'a tace amin suka wuce. Wai dagaske kike yayanki yanada budurwa bilki kenan inma baki yadda ba to wallahi kixo jibi nakesan zuwa gaida ta semuje bilki tace Allah sarki ni nafa tausayama kaina nikam nai miki murna da bake wannan dan xafin zai aurava ni murnata ma ya barmana gida uhum bazaki gane bane Kawai anman dai zanje dan ganin wace me sa'arce. A gidansu muklisa budurwar Ali an karbi Amra da kawarta hannu bibiyu da yake ba bakuwa bace tsaraba kuwa da zasu tawo ba'a magana ke nifa inbanda so sone Allah banga me ya Ali zaida wannan ba Amra ta hade rai banfa san cin fuska kema kinsan ta ko'ina aunty mukli tayi ga mutunci sankowa kin wanda ya rasa kedai kice kina kishi kawai haba yarinya kema kinsan na wuce kishi da wannan ohoo dai kyaji dashi. Kinsan me mami sai kin fada aini shagali goma da ashirin gana bikin yaya gana candy ahlallai kice tarihi zaki kafa tai dariya ai wani abun sai ranar Allah dai yasa zamu gani amin Amratuna kaji mami bashi ne dan fariba ko kunya bakiji ba ungo nan ta watsa mata dakuwa yarinya sai zakulo zance tasa dariya aina girma candy zanyi ah lallai kin girma ni kike fadawa haka ko tai sama tana dariya. Motar sa data hango yasa ta cewa na shi na salim dake gefe yai saurin kallon gefe mts yasaki karamin tsaki yasan yanxu wannan yayan nata zai katse musu jin dadi yadda ya hade rai yakara bata tsoro sannu da zuwa yaya yawwa ya fada me kike anan gurin ba komi ta fada to maza wuce gida tai ciki da sauri tana kuka kai kuma saunawa zan ce maka karna kara ganinka anan ba yanxu xanu aurar da ita ba to yaya ya fada yai gun motarsa. Towo yar gidan mami keda wa mami ba yaya bane muna hira da salim yazo ya koroni shima ya koreshi to yo hakuri zaizo yasame ni. Yashigo yana huci mami sannu da gida bata amsa va tace Aliyu wai yaushe kakeson indena maka magana kan Amra takurar dakake mata tai yawa karka manta fa banazatai candy karka kara korar mata samari to mami zan kiyaye yai ciki yana huci gami da hararar amrar Dad nai missing dinka da yawa yai dariya ai nima nayi missing diyar tawa dad kasan ka dawo adedai ko eh mn gobe be final pape dinmu ai nasani ban mance shiyasa nadawo yau ayi komai a idona har suka isa gida suna hira me dadi dan ita da mami kawai suka samu damar taroshi. Agurin yaye su Amra tana daya daga cikin dalibai da suka sami kyautuk tuka na mai kokari tsafta da girmama malamai aikuwa dady da mami sai murna suke diyarsa ta zamo abar alfahari hotuna haka akai tayi kyautuktuka kam tasamesu daga gurin dangi da yayyenta suma kansu murna suke danma anbar nata taron sai ta hada da bikin yayanta anman hakan besa yan uwa sun zozzoba. Yau za'a kai kayan lefen Ali kana ganinsa kaga ango yadda yaketa washe baki sai tsokanarsa ake kai banda abinka kafin azo daurin aure har kafara shinning irin na angwaye dayake bai cika magana sai dai kawai murmushin sati hudu akasa bikin dan haka kowanne bangare wato amarya d ango shiri kawai suke . Yadda Amra ke zagewa kai kace itace amaryar komai ta bukata bata ake gyaran jiki takanas taje tai kyau sosai da biyu take wannan murnar bikin babban yaya sannan bikin su na farko gashi zai bar musu gida acewarta shanawa kuma ao ba kama hannun yaro. Biki kam ya gabato dan yau ake Diner kaf kawayenta Amra ta gayyacesu dan itama yau take party dinta na candy biki ne irin na kasaita bikin girma da girma kudi kam an kashesu. Yau take asabar yaushe ranar daurin aure Amra nacan na kwasar baccinta dan tace ita sai sha daya zata shirya ango yai kyau sosai yaci babbar riga milk komai milk kwarjininsa ya kara fitowa sosai . Waliyin amarya yace eh kunji yadda akace waliyyin ango yace to gaskiya saidai ku tsaya ayi magana da ango abinda yace to to aishike nan bari akirashi awaya ga mamakin Ali wayar uncle dinsa ce ke kiransa aransa yace towo lpy asaninsa uncle yana gun daurin aure kaji waliyyan matarka sunce zaka bar yarsu zuwa Malaysia dan karo karatu shiyasa nace abari kar adaura inji ta bakinka Ali yace ina ni bamu taba batun dasuba kenan baka amin ce ba eh kawu nima dai hk nagani ti kunji yace be amince ba to falillahi hamdan sai afasa aure afasa kuma eh to kutsaya in tuntubi iyayan yaro ko zasi saka ya yadda nan ya fito yasamu baban Alin ya fada masa shi kuna yace bari suyi shawara fa matarsa ya fita daga baya ya shigo yake cemasa afasa daurawa da mukli anman aure babi fashi. Abinda kunnuwansa suka jiyo masa yasa ya kara matsawa kusa bai yadda da abinda yaji ba kai Abdul wai me marokannan ke cewa cewa suke Alhamdulillahi an daura auren *Amratu* da angonta *Aliyu* What dagaske kunnena dedai yajiyo nima dai jinake shirme suke muje mu jiyo suka kutsa cikin jama'a duk inda sikai maroka na biye dasu kaga ango gun amratu bai san sa'adda ya doka musu tsawa pls ku kyaleni haka kun isheni iyye yai cikin masallaci yana hango kawunsa yai gunsa kawu wai da wa aka dauran aure ya washe baki da Amratu mana what waje yai Abdul yabi bayansa yasamu waje ya rafka tagumi Abdul yace abinnan fa da daure kai ina wa ya taba auren kanwa inaji dai ba amra kanwarka suke nufiba shi gabaki daya baijin me yake cewa ba abinda yake tunawa sai Alhamdulillahi an daura auren Amra da ....... Alhamdulillah an daura auran Amra da Aliyu kalman da yake ta maimaitawa knan tabbas in abun da yaji gsky ne xaifi jin dadin inama ace mafarki yake Muhammad ne ya dafa shi haba Aliyu mene haka karka sa sauran jama'a su zaci wani abun yadago idonsa wanda yakada yai jawur pls muhd kafadan gaskiya bacci nake ko idona biyu kaga dan Allah ka tashi mu shiga jama'a yaufa ranar farin ciki ce agunka haba muhd taya zaka kira wannan ranar ta farinciki eh kai agunka ranar bakin ciki ce anman kowa yana kallon ta amatsayin ranarka ta farinciki be a man pls kadaure haka yai tabashi baki har yadan saki ransa suka shiga jama'a yake kawai yake dan shi kadai yasan abinda yakeji aransa. Amra na kwance kamar kamar a mafarki taji wayanta na ringing xumbur ta tashi baccin me dadi da takeyi daddyne ya kirata yace ynxun nan yake son ganinta a falonsa saida gabanta ya bada dam a xuciyarta tana fadi meya faru Daddy kson ganina ynxun gashi ana biki ta bawa kanta amsa bb komai may be yanason ya sata abune tunda mummy mutane sunyi mata yawa da haka ta fito falon tunda tafito mutane ke rangada buda amarya ansha kamshi bata kawo komai aranta ba dan tunda aka fara bikin ma wasu kafi amarya suke kiranta tai bangaren dady. Shi kadai ta tarar adakin kamar yadda ta zata ta russuna ta gaidashi ya amsa cikin sakin fuska badai sai yanxu autan tawa ta tashi ba tai dariya ai nai sallah ok daman magana nakesan muyu ta fahinta to dady ta samu guri ta zauna. Amrah ya fada yanayin yadda ya anbaci sunan da iya saninta bai taba kiranta da shi ba yasa tai saurin dagowa na'am dady ni waye agurinki tace baba na ne ya kada kai yawwa daman alfarma na kiraki kimun tai saurin dagowa haba dady kadena cewa alfarma ka wuce ta aguna yafi kace umarni ashirye nake nabi duk abinda kace yai dan guntun murmushi irin nasu na manya kinsan yau ake daura auren yayanki ko ta daga kai yace yawwa adazu agun daurin auren andan samu matsala iyayen yarinyar sun bada sharadi mu kuma muka ga da cutarwa to hakan yasanya aka fasa auran tai saurin dagowa yace eh an fasa auren da muklisan hakan yasa muka yanke shawarar daura auranku keda Alin zunbur ta mike dady dan Allah karkace ba mafarki nakebe kafin yace wani abu tayi kasa yaraf inda yai dedai da shigowar mami batasan sa'adda ta watsar da ture dinba tai kanta tana jijjigata cikin kuka. *Tuna Baya* Alhaji muktar shine asalin sunan dady wanda yake haifaffen garin kano unguwar galadanci shine dana uku agidansu mahaifinsa wanda yake malamine ajami'ar bayero yayin da mahaifiyarsa take ma'aikaciyar jinya su su shida iyayaensu suka haifa yanayin yadda iyayensu suka tsara musu rayuwa yanayine mai ban sha'awa da birgewa ga kowa. Lokacin da muktar ya kammala secondry dinsa ne ya wuce ABU dake zariya danyin degree dinsa alokacin da ya kammalane aka turashi bautar kasa makarantar yan mata ta kwana dake garko anan Allah ya hada jininsa da wata yarinya me suna Aisha yanayinta na birgeshi yanayin kamalarta nutsuwarta da komarinta saidai yakada fada mata santa yake. Bai kuma yadda san yarinyar yakeba sai bayan sunyi candy dan sune shekarar karshe alokacin da ya dena ganinta ya fiskanci lallai ba karamar kwarar kansa yaiba abokinsa ne yabashi shawarar kafin ya gama service dinsa ya bincika ko zai samu address dinta yai sa'a ya samu batare da wani shan wahala ba yasamu soyayyarta yana kammala service dinsa sukai aure. Rayuwarsu rayuwa ce me dadi rayuwa irin ta yan boko masu illimin addini suna da shekara biyi da aure lokacin Aisha na level 200 ta haifi danta namiji me kama da babansa wanda yaci sunansa *Aliyu* murna gun muktar ba'a magana dan shima yazama baba. Aliyu nada shekara hudu ta kuma haihuwar danta namiji wanda yaci sunansa sulaiman tun daga nan haihuwa ta bude ta kuma hauhuwar Abdullahi bai shekara daya ba tai masa kani Ibrahim shima ta haifo masa kani umar sai yan autanta yan biyu usman da Bilal. Kasan tuwar Aisha bata da diya mace yasanya takesan ya mace kazalika yayanta da mai gidanta. Amra yarinya ce yar kimanin wata takwas tun haihuwarta Aliyu ke kula da ita diya ce ga makotansu in yadawo daga makaranta kan yaje gida ya shiga gidansu amra ya sabota akafada in ba makaranta ba ba abinda ke rabashi da ita sun shaku sosai yarinyar nasansa tun batai wayon cin abinci ba da yasamo kudinsa ai amra zai saima madara. Zaman Amra agidansu Aliyu yafi zamanta agidansu hakan yasanya tafi sabawa da yan gidansu Aliyun fiye da yan gidansu tasaba da dadynsu Aliyu balle kuma maminsu ko unguwa zasu tafi da ita suke tafiya dan yaye ma anan aka yayeta hakan yasanya wasu da dama basusan ba yar gidansu Aliyun bace sai na kusa kusa. Lokacin da zasu tashi daga unguwarne akasha rikici dan amra kuka Aliyu kuka kannensa kuka kai saida takai Amra da cuta iyayenta ganin zasu rasa diyarsu yasanya mahaifinta ranar wata juma'a yasa mamanta ta hada kaf kayanta yadauketa ita da maman nata sai kwanar ganduje nan gidansu Aliyun. Sun gaisa cikin mutunci Amra nata murna taxo gida dayake Ali bayyanan sulaiman ya shigar da ita ciki mami da day da iyayenta suka zauna afalon saka makon ganin shakuwar yarinyar nan daku yasanya naga dacewar in kawo muku ita bawai matsayin yar rikoba na baku ita ne duniya da lahira kuna da damar yin komi da ita tazama yarku mami kam harda kuka dan murna dan tanasan yarinyar da yawa dan ba yadda zatai ne yasanya ta tawo ta barta ko lokacin da suka zonan unguwar kullun da ita take kwana aranta. Sanadiyyar dawowar Amra gidan. Koda Ali ya dawo yai murna sosai koda amra ta isa shiga makaranta Aliyune ya kaita kudi kawai dady ya bashi saida sukai fada da sulaiman dan cewa yai shi zai dinga kaita Aliyu yace be yadda shine hakan yasanya aka raba shi zai dinga kaita boko sulaiman kuma islamiyya tun yana daukanta a hannu hartakai yana dauketa abakin mamaeanta ta karasa . Tasowar Amra agidansu Alitu tasowar gata ne abinda takeso shi ake mata yadda kowa keji da ita ko yayan gidan ba'aji dasu haka . Amra na primary 4 tayi commen inda yai dedai da gama secondry din Alitu an gama masa komi dan tafiya waje yin degree dinsa tun alokacin suka fara batawa da Amra dan baisain shagwaba ko kadan bare raini yayinda in ana neman shagwabbe karon farko asamu amra gashi babu dama adaketa yanxu mami ko dady sa hauka da fada. Lokacin da yazo hutu ne gaba daya alakarsu taja baya domin da yasata abu zata xunburi baki aiki nake ko kai yaya na gaji wannan kesawa yake doketa da yaga mami ko dady basa kusa hakan yasanya taja baya dashi ko yana guri bata zuwa sai in mami ko dady na gurin. Duk shagwaba da gatan da ake ma amra hakan besa duk wani aiki na gida da yakamata diya mace tayi ba ta iya dan mami gwanace bata yadda yan aiki suyi mata girkiba konai tare suke da diyarta tarbiya kuwa iya iyawa suna baima amra basu bari ta lalace ba . Hakan yasa tun tasowar amra mami ke burin Aliyu ko sauran kannensa wani ya auri Amra dan batasan yarinyar ta fita da ga zurriyarsu sai dai ina ko wannensu kallon uwa daya uba daya sukema junansu. Lokacin da dady ya buga mata waya yakeabinda ke ransa kenan fada mata yadda akai da iyayen mukli ne taga ga dama tadamu ta fadawa dady ra'ayinta akai sa'a shina ya amince dan shima abinda ke ransa kenan . Da yake maman Amra tabasali tazo gun bikin ananma ta kwana babanta ma yazo gun dauri daurin aure yasa mami da dady suka tun tubesu kan ya suka gani sukace ai bakomai diyarsu ce duk hukuncin da suka yanke yai dedai su yan kallone bako abata lokaci ba dady ya bugana wakilinsa wato kaninsa kan adaura auren da amr. *Ci gaban labari* Cikin kuka mami ke jijjigata da sauri dady ya bude firji ya dauko ruwa dabsauri ya balle kansa ya shafa mata ta saki wani ajiyar zuciya ahankula ta bude idanunta akan mami ta dorasu wadda ke faman sharar hawaye da sauru ta fada jikin mamin mami kice mun mafarki nake dan Allah mami ta dagota ba mafarki kike ba amra komai gaskene nice sila yanxu zansa a warware aurannan bansan zai cutar dakeba da sauri ta cire jikinta daga na mamin ta sa hannu tana goge mata hawaye mami ki dena kuka banasan ganin hawayenki na dena amra mami indai aurena da yah Aliyu farin cikinki nai miki alkawarin zama dashi har rayuwata ta kada. Dagaske kike yata haba mami kin wuce komai aguna tasaki murmushi naimiki alkawari ta shafa kanta maza mike muje kiyi wanka kafin an gwaye su fara shigowa ta mike da kwarin guwa duk dan farrantawa iyayen nata ta shige bayin dady. Shidai dady kallonsu kawai yake ya rasa ta cewa mami dakanta ta dauko mata kayanta ta kawo mata nan dakin . Koda amra ta shiga wankan zaman dirshan tai tasha kukanta ta koshi saida taji mami na cewa tai sauri ta shessheka ruwanta ta fito duda hawata kwalliya akai mata ba tai kyau sosai fiye da zaton me karatu iya yinta tayi dan kar agane tana cikin damuwa haka ta daure tana ta yake koda angwaye suka shigo haka akaita hotuna tun tana dari dari harta saki jiki. Yinin ranar yini amra tai tana kuka data saci jiki saitai inda ba jama'a ta kwashi kukanta ta a haka har lkcin daukan amarya yy Dady dakansa ya kamo Amra zuwa dakinsa Aliyu na zaune ya zaunar da ita da addu'a ya fara sannan ya fara yan nasihohi kamar yadda kuka sani yar tangar dar da'aka samu yasamu hada auranku dan kuma kaddararku ce zama ma'aurata bawai mun hafaku aure bane dan cin xarafin dayankubsai dan kara xumuncin dake tsakaninmu Aliyu kaine babba dole kaxamto me hakuri hakkin amra gabaki daya yadawo kanka auranta da kake bashi ke nufin xaka mata duk abinda kaga dama ba amra amanace agunka inka zalince Allah na gani xaka iya tafiya wani takaici yakara rufeshi wato ita bama za'a nuna mata matsayinsa ba wato tayi masa abinda taso gashi sarkin hakuri Ke kuma amta Ali mijinki ne ki guji abinda baiso kiyi masa biyayya aljannarki na karkashinsa kinji ko diyata insha Allahu dady tace daki daki yadinga kaita aka mata nasiha da kansa yasata amota direba yaja tunda suka fara tafiya take kuka tun ana bata baki har tsoffi suka fara fada. Ankai amarya an watse an barta daga ita sai halinta dan kawayenta sun gaji sun tafi tsoro duk ya cikata dan bata saba xama ita daya ba lokaci lokaci take daga ido tana kallon agogo 11:00 ta gani wani tsoron yakuma cikata shiko gogon nata yanacan dakyar abokansa suka sha kansa ya yarda zasu rakoshi tana cikin kukanta bata san abokanan ango sun shugo ba qasa qasa taji maganan su suna cewa amaryanmu barka da wannan lkcin,ba tayi musu mgna ba suka xauna daya daga cikinsu da suka kirashi da Ammar ya fara bude taro da addu'ah sannan suka yi musu nasihohinsu har suka karu surutunsu batace musu uffan ba kazalika angon nata suka gaju suka musu sallama ya fita tare dasu domin yi musu rakiya.Amra ganin sun fita tayi maxa tashi tare da sanyawa qofan makulli . Koda ya dawo ya tadda kofar akulle wani takaici yaxo masa wuya lallaima yarinyar nan ta raina masa hankali to mai ta maidashi xuciyarsa nace na mamajo yaja tsaki gami dayin nasa dakin. Da safe ta tashi bacci ta duba agogo innalillahi wanna wane irin baccin ne nayi past nine Amman banyi sallar asuba ba ta dirko daga gadon tare da wucewa bayi sannan tayo alwala ta wuce bedroom ta shinfida sallaya ta tayar da iqama idar da sallanta ke da wuya taji kaman ana kallonta ta baya juyawarta suka hada ido da Yaya Aliyu tace ina kwana yace"ban kwana ba xaki ganni da rashin tarbiyya yanxu akeyi sallan subhi?"tace"cikin murya kamar xatayi kuka Allah Yaya Aliyu vaccine kuma bansan nakai wannan lkcin ba "ya harareta ai dole kice haka tunda kin saba mummy ta shagwaba ki. Ni ba surutu nazo muyi dake ba naga jiya kin rufe kofa ai da baki wahalar dakanki ba kedin baki isa maceba aguna baki isa kallo ba aguna wallahi banxa kwaila inbanda abun iyayenmu mexanyi dake kema kinsani likamin ke akai bake nakeso ba inada wadda nakeso kuma kisani nan gidanane dan haka baki isa kizo kidinga mun abinda kika ga dama ba kinsaba komai saidai amiki nan gidan aurene gidan bauta kishiryama duk wata wahala dole kiyi aikin gida dan bani da ra'ayin yar aiki kuma inasan kisan dasanin daga rand kika shugo nan gidan kinyi ban kwana da kwanciyar hnkli saboda haka ki shirya wa tarban rashun mutunci daga gareni sannan kisani gidana sirrinane dan haka ki kiyayemin sirrin gida wallahi koda wasa naji maganar halin da muke ciki dake awaje saikin raina kanki koda kuwa gun su mami ne inkunne yaji jiki ya tsira fuuuuu yai waje Tunda yafara maganar batace uffan ba sai da ya fita taji saukan hawaye a fuskarta tabbas haka yake yah Aliyu bani ce wadda kakeso ba nakuma sani ban isa zama matarka ba zanyi hakuri zan jure duk abinda zaka mun indai zaisa iyayenka farinciki dan sun fice na guji jininsu akowane yanayi. Saida tai kukanta ta koshi sannan ta mike tai bayi dan wanka batason tai baki su zaci wani abun. Saida tai wanka tai kwalliya tai kyau sosai baxa ka taba cewa tana da damuwaba sannan ta hafo shayinta me kauri tafara sha tana cikin sha taji bugun kofa tana budewa taga su bilki da aunty Aisha sai murna da abincinsu suka tawo mata sako daga mami aiko tai murna taci tai dam sukai ta hira sai dare suka bar gidan. Tana kitchen taji bude qofa alamun mutun ya shugo ba taje ta dba ba domin yasan Yaya Aliyu ne can taji hayaniyar kamar bata mutun da ya ba ta leqa wa xata gani mummyne da daddy sai Aliyu ana hira bata San saboda murna sanda taxo ta dare cinyar mummy ba a guje mummy tace autata me yasa har ynxun bakya girmane tayi murmushi wlh mummy murnan qaninkune sannu da xuwa bari in kawo muku abinsha da ci ta wuce kitchen ta dawo sannan ta rarrafa wurin daddy tace"daddy ina wuni" yace "qlw 'yar daddy yau kuma tuta ta ta koma qasa tunda kk ga mummy ko kallon inda nake bakiyi ba" Tayi murmushi Allah daddy farin cikin xuwanku ne wlh duk ya rufe mini ido yace "Fatan dai kuna xaman lfy " Tace "lfy qlw daddy" Yace"in kinsan bakwa xaman lfy ki gaggauta sanar dani domin magance abun kunsa hausawa nacewa ta yaro kyau take bata qarqo so if there is any problem u are free to say it we are ur parent u can't hide any thing from us Tayi saurin dagowa ta kallo inda Aliyu yake shima ita yake kallo yako sakar mata harara tayi maxan saukar da kai tare da cewan Allah daddy bb komai inda da akwai tun kan kuxo xan buga muku waya in fada muku "toh Allah yy muku Albarka ya qare fitina a tsakaninku ya baku xaman lfy da xuri'a dayyiban" Aliyu yy saurin cewan ameen ameen daddy mungode harar da ya wurgo matane yasata cewa amin batare data shirya ba. Kafin daddy su tafi saida aka qara musu nasiha sannan suka rakosu har mota da xasu tafi Amra ta fashe da kuka😭kan lallai tare da ita xa'a tafi dakyar aka lallashe ta sannan suka tafi. Bayan tafiyarsu suna daidai bakin qofan shiga falonsu ya ja mata kunne Wanda saida tayi qara sannan ya sassauta ruqon tare da fadin Allah ya soki baki gaya musu ba da yau jikinki yy tsami yarinya kuma inaso in fada miki wallahi koda wasa wani ya kuma zuwa gidan bawai momy ko dady ba kika ce zaki bishi bawai kuka ba kawai zakiga abinda zan miki shasha kawai ya tureta yai dakins bai kula da kukan da take ba yai dakinsa yana tsaki. Da asuba ta sheqa wankanta taje tayi sallah.har qarfe tara ta bata bude dakinta ba,bayan ta idar da sallar walha ne ta bude dakin dan xuwa ganin menene xata sanyawa cikinta.A falo ta tarar dashi kwance daga shi sai singlet da dogon wando yana kwance yana kallon wani Indian film a zee cinema Player. Ta gabansa ta wuce ta shige kitchen ya bita da kallo yace lallai ma yarinyar nan.ta fito hannunta dauke da mug na tea tana juyawa sai da ta zauna sannan tace ina kwana yaya hara ya watsa mata gami da tsaki bata ce dashi uffan ba taci gaba da juya tea dinta .wani takaici yakara cikashi wato yari yar nan me ta maidani ke ya fada afusace tai saurin sauke kofin da take shirin kaiwa baki me kike nufi ne nanfa gida na ne nufinki ni zan shiga ingirka abinda xanci ko me kallonsa kawai tai gami da mikewa tai kitchen ruwan shayi ta hado masa hade da soyayyan chip agabansa ta dire yako watso mata shayin wato ga mahaukaci ko dan tsabar wula kanci bama xaki tsaya kiji abinda nake cewa ba balle samun matsayin kiji me zanci ko sa'arta daya akafa ruwan ya zubo mata yakuma dan huce hakan yasanya bata kone ba yi kofin ta dauke gami da durkusawa tana tsince dankalin tsaki yaja yai dakinsa sai da ta gama tsincewa ta goge ko ina sannan tai dakin data ga ya shiga da sallama ta shiga baya falon hakan yasata shiga ciki tsawar da ya daka mata ce tamugun firgita ta har batasan sa'adda tai hanyar fita ba ke dakata jikinta na kyarma ta tsaya me yajawo ki dakina daman daman ta fada tana rawar murya daman what daman tambayar ka zan me za'a dafa ma yaja tsaki inda abinda ke bata haushi be wuce tsakinnan ba banaso jeki kawai harta kai bakin kofa yace bakiji ba tai saurin juyowa ki hadan kunin gyada da kosai to tace tai waje. Da yake mami ta aiko mata da gyada hakan yasanya komai yaxo mata da saumi yunwa takeji sosai dan haka kaskon farko na kosan ta cinyeshi kunu tai mai gardi da zafinsa ta zuba akula ta fido kenan da zummar kai masa daki ta ganshi yana waya har ya wuce taga alamar fita zaiyi tai saurin cewa yaya abinci zankiraki taji yace daga bisani yace love u too sweat heart sannan ya cilla wayar a'aljihu bai juyoba yace kibaima almajirai bai jira me zatace ba yai ficewarsa wani hawayen takaici ya gangaro mata. Tunda ya zauna kamshin abincin ke kwakularsa dadinsa da yarinyar ta iya girki yana zaune ji yake kamar yaje yace ta kawo masa girman kai ya hanshi koda ta kawo masa cewa yai baya ci ya shiga kitchen danna tukunnyar ya maida yawunsa ya hado shayi yai dakinsa bata ko kalleshi ba ta cigaba abinda ya dameta. Zaune yake yana rubutu taxo tazauna adan kai kaice ya kalleta tace sannu da gida yaya bece da ita kala ba tace daman yaya magana naxo muyi nanma bece kala ba kusan minti biyar ya mike zai bar gun tace yah nace xamuyi magana ina kunne ne keji dolene sainayi magana ai dan kar inyi kahauni da fada eyye wato inhauki da fada ko watakan ga mahaukaci ta turo baki gami da juyar da kayya eyye lallai yarinyar nan. "Ki kiyayeni,wlh na kula baki sanni ba ko dan na lura mummy na tare miki fada shiyasa kk rainani?toh xaki san koni waye Aliyu very soon" yajuya zai shiga daki tako saki tsaki karaf akunnensa yako jiyo a fusace. Finciko ta yayi,saida hannunta yayi qara ya matse bakinta sosai har saida idonta yayi ja,ya hankade ta. . kadan kk ka gani ki kuma yimin tsami agudannan sai na fasa bakin naki mara mutunci kawai. Hawayen takaici ya kara zubo mata. Gaskiya yaya sulaiman nai fishi ace tunda aka kawoni sai yau zakaxo ganina yai dan murmushi kema kinsan kina raina abubuwa suka min yawa mun kusa fara final exam ne tasaki dariya kace mun kusa zama likitoci yai dariya ah kun kusa kam to Allah ya temaka ta mike bari na kawo maka abinci kai saidai ki xuban in tafi dashi axumi nake ta hade rai wato baxaka sha ruwa ananba yadanyi murmushi karkiji komai xanyi xuwa na musannan yini xanyi. Yanxuma dady ne ya aikoni yace ki bada takardunki jibi kuma zai turo kamal ya kaiki xakiyi register ta jamb tai dariya kace har anfara yace eh shinema yace naxo infada dan yasan baku sani ba inba nai fishiba tunda ashema da dady be aiko kaba vaxakaxo ke dai kin fiye mita kinga maxa ni dauko min xan wuce ai suna can gida kace mami ta duba durowar da nake ajiyewa duk komai na ciki ban tawo dasuba ya mike se naxo din to yahya ka gaida mami yafice da flask din data xuva masa abincin. Kwana Biyu bata sanya Aliyu a idonta ba,Sam abun bai taba damunta ba,ta tsaya tsayin daka ayi n ibadarta abu daya ke damunta tsoro dan baya shigowa sai dare ya tsala dabadan ma in ta tashi tanaganin kofa abude ba baxa ce agidan yake kwana ba. Ranar da yamma tana xaune da yamma tana sauraran wani wa'axin Sheikh kabeer Haruna Gombe akan biyayyar mata ga maxajensu da irin axabar da Allah ya tanadarwa matan da bata biyayya ga mijinta koda kuwa wani irin miji ke gareta ko talaka,mai kudi,dan iska,mara mutunci kar kiyi la'akari da abinda ke tsakaninsa da mahallicinsa ne,yau idan mijinki dan fashine ko dan yankan kai ne ya xamo wajibi kiyi masa biyayya kamar yanda Allah da manzonsa sukayi umurni iyakacin abinda xakiyi kiyi qoqarin xakulo shi daga axabar Allah addu'ah domin yin haka tamkar jihadine sbd haka 'yan uwanmu mata ya kamata mu dage Allah yasa mu dace. Amrah hankalinta ba qaramin tashi yayi ba dajin wannan bayanin domin tabbas ya xamo wajibi tayiwa Aliyu biyayya matuqar tana son saduwa da rahamar ubangiji...duk runtsi duk wuya. Fargabar amra daya itace yadda yah Ali zai karbi maganar karatunta dan ta fiskanci yanxu salo salo na mugunta yake fito dasu duk dan ya bata haushi da maganar take kwana take tashi ta rasa yadda zata fada masa cewar yau zata register na jamb. *Qarfe sha Biyu* Taji knocking a qofa taje ta bude was xata gani class mate dinta ne a secondary school su Zainab I Tukur,Ruqayya Abdullah, Nafeesa Shehu Lawal,Zee yabour,Hussy suka shugo tana mmki tace sannun da xuwanku Xee harda ke tace hmmmm ai wlh Amrah bamu taba sanin xaman da mukeyi dake kenan a skul ba ace auranki ya tashi bb gayyata kawai ji mukayi daga sama Hussy tace ke kuyi shuru ai Amrah ni nayi niyyan inxo in xaxxaga Miki nawa masifanne ace duk kirana mummy da kk yi wai daughter xata yi aure ban sani ba wannan ai abun kunyane kinason mutane suyi mana dariya koh daughter😡tayi mgnan cikin rashin jindadi. Amrah tace kuyi hqr abunne ba'ayi tsammani ba sannan tayi musu bayani sun jinjina lamarin tare dayin musu Allah sanya alkhair ya bada xaman lfy da qasantar daki tace ameen tagode tana jinjina kaman qaxantar daki a ranta wato 'ya'ya ta amsa ameen ne domin kar su San akwai wani matsala tattare da ita sannan kuma a ranta tayi alqawarin xama da Yaya Aliyu koda kan kullum xai dinga yanka naman jikinta yana ci. Sunyi hira sosai na tsakanin qawaye domin sai qarfe shida suka yi mata sallama kan cewan xasu tafi gida da xasu tafi kamar kada su rabu haka nan suka bata gift dinsu kan cewan suna tare kuma xasu yi xumunci ta rakasu suka tafi kowa da kewan dan uwansa Zaune yake yana hira da mukli dan duda sunyi aure da Amra ya kasa rabuwa da muklinsa kullun suna tare a waya danma bata kasar shiyasa nake sanki wallahi Amra dake tsaye tace yah yadago mata hannu alamar ina xuwa I will call u back sweat heart ya kashe wayar afusace ya kalleta ke lpy tace yah magana zamuyi shine xakixo ki damen ke bakisan mutun in yana waya ba yi hakuri tace sai afkin ki cuci mutun ki bashi hakuri me zaki cemun daman jiya yah sulaiman yaxo yace gobe yah kamal zaizo yakaini danyin register din jamb afusace ya kalleta kina nufin karatu xakiyi ba zaman aureba gabanta ya fadi cikin kin kina tace dady ne ya aikoshi to ni atsarina mata ta baxatai karatun jami'a ba kin gane to kawai tace tai daki tana kuka. Koda yah kamal yaxo tace masa ai ita ina yanxu bata sha'awar karatu yadda ya ganta yai tunanin da wata akasa yadda yasan kanwar tasu da dan banxan san karatu rana daya tace ta fasa koda yakoma gida ya fadama dady mami tace ina ai tasan Ali ne xai hanata hakan yasa dady kiransa ya ci masa mutunci dole ya hakura ya barta. Amra tai sa'a jamb tayi kyau dan taci maki sosai aiko murna bakama hannun yaro kasantuwar an soke post UTME yasa tunda akai jamb din akaga taci dady ke ta cuku cuku har saida yaga tasamu admission randa kuwa aka kawo mata admission ko bacci batai cikakkeba minti kadan sai ta juya ta dauki admission letter din takalla ta saki murmushi gani take kamar ma burinta ya gama cika. Amra yau xa'a fara daukan lectures a class da doki ta shirya cikin jin dadi yau an xama yan university😜ta gama shiryawa ta fito falo dan jiran Yaya Aliyu ya shirya ya kaita sbd yace matanshi ba xata yi driving ba taji shuru×2.kamar tayi kuka ta dai daure domin xuwa dakin shi taga lfy xuwanta ta tarar da yana bacci tayi turus ynxun kada in tashi masifaffe ya fara man fada ta kai batasan sanda ta shagala da kallonsa ba sai yau ta taba yima yayan nata kallon tsaf baccinsa yake cikin kwanciyar hankali sai yau ta yadda da su bilki da suke cemata yayanta me kyaune tsawar da ya daka mata ce ta dawo da ita daga hankalinta lpy kika wani xuban idanu cikin jin kunya tace daman yaya lokacin sch yayi naga baka tashi ba xan makara se akai yaya kuma kace baxan tuki ba ok jeki yanxu xan fito yah nafa makara nace kije ko tai waje yafi minti shida sannan ya fito dinning ya kalla me kike nufi ina abinci na yah nafa cema na makara ke kikaga xaki iya karatu ni auro ki nayi inkinga kin bar gidannan kin dafan abinci rai abace taje ta ta daba masa tsaye ta ganshi xuban a flask har bakin mota ta kaimai ta bude xata shiga yace na makara ki kirawo sulaiman ko wani a babban gida su kaiki bai jira amsarta ba yaja motarsa yai waje hawayen takaici ya xubo mata dan tana san makarantar ne da wallahi baxata ba haka ta kira yah nasir ya kaita sun sha hira nanma yake fada mata kwanaki mami bataji dadi ba tai ta mita tace xata je ko da daddare ne. Yana zaune yana cin abinci ta zauna kusa dashi baiko dago ba balle yasan da ita tace yah lpy yace daman yah Nasir yace mun mami bataji dadi ba shi ne nace dan Allah ko xaka temaka ka kaini daga nan inasan inje sabuwar kofa wato asalin gidan iyayenta ce miki akai ni direbanki ne eyyi tai shuru to ba inda zan kaiki bakuma xakije ba batace uffanba sai hawaye kawai da take yafi minti uku yana kallonta yaja tsaki shirya muje tasaki murmushi nagode yaya tai daki. Tayi shigarta dingin bingil material ce pink ta amsheta sosai,ta fito falo sai kamshi take yi shi har ya saba da cin abinci mai dadi da kallon kwalliyar kallo daya yai mata ya dauke idonsa yana gaba tana biye da shi. A can gidan mami hira suka sha ita da yan uwanta ji take kamar karsu tafi jin zata gida yasa mami hada mata tsara sosai dan kai musu. Acan sabuwar kofa ma dai sun taba fira dayake in kadauke shakuwa irinta jini basu wani saba ba kannenta ma bakuwa suke daukanta mamanta tace ina dai kuna zaman lpy tai dariya eh mama to Allah ya dawwamar bata ce uffan ba dan kunya yawwa inasan fada miki nasani Hajiya Aisha uwa ce agunki anman kisani Aliyu danta ne dole saikinyi hankula da kai mata kararsa ko sukarsa kinji ko diyata tai dariya to mama tare ma muke dashi babanta dake kan tabarma yna cin tuwo yace jaji ja'ira bakya bakya cewa yashigo wallahi baba nace yashigo yaki ya mike hara haje yana ganinsa ya durkusa yana gaisheshi haba Ali se kace wani bako yai dariya to muje mama na ganinsa tace dan nema wato surukuta kame damu kenan ai da kanka tsaye kake shigowa yai dariya yana sosa keya ananma sun sha fira sai goma suka koma goda..... ✍🏾✍🏾✍🏾✍🏾✍🏾✍🏾 *Ummusulym* *F.A.Ya'u* Dan ci gaba duba b fayau9.blogspot. Com ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ ⚜⚜⚜⚜ ⚜⚜ *AMRATU* *page 45➰50* *Na* *Ummulsulaym* *Da* *F.A Ya'u* fayau9blogspot.com fayau26.wordpress.com *Short and brief story* *We Dedicated this page to Xee Yabour,Husnarh(my hussy)Miss Xoxo,Miss Mjay,Miss Gorgeous, Memxiey,Tuartah Aberdah(Taurah😜),Also Noor Luv you so much kwando-kwando😜😘😘😘* Suna komawa gida lkcin ta gaji sosai da yake sun cika cikin su bata wani kalla kitchen ba tayi shigewata can bacci ya fara daukanta taji rankwsmashi ta tsakiyar kanta wani azababben zafi ya ratsata cikin magagin bacci tace haba wannan wane irin wulaqancine mutun yana cikin bacci sa aso a tasheshi...bata qarisa ba taji a murda bakinta tare da jan mata kunne keh tashi ai da sauri ta mitsika ido data tuna abinda tace batasan sanda gumi ya keto mata ba a ranta tana cewan lallai kashina ya bushe,yaci gama keh ni kk wa rashin kunya tabb yau jiki xaiyi tsami yaja mata kunne Wanda saida ta durqushe qasa ya qara jah da qarfi sannan yace dan wulaqanci ke na sane da kullum da daddare kafin in kwanta sai nasha ruwan Lipton Amman yau tunda kin rainani kk yi shigewarki gani dan iska kinyi shigewarki ba xaki dafa ba ko inyi duk abinda xanyi yana mgn ne hannunsa riqe da kunnanta cikin kuka tashe Allah Yaya Aliyu baccine bansan sanda ya kamani ba kawai gajiyane nayi yace "eyye wato kinma gaji ni kike cewa kin gaji ni nace ki kirkiro tafiyar ina seda nace bazaki ba kika sakan kuka ?" Tayi shuru toh ynxun muje ki hada maxa ki kawo minti biyar in ya wuce double punishment 😡aikam har kitchen ya rakata sannan ya sakar mata kunne ya tunkudata. Aranta tace Allah yah Ali mugune dan dai ruwan tea tunda nai bacci ai ya dafa ahaka tana tsaye har ya tafasa kanta ke mata wani irin ciwo sakamakon tsoratar datai da ya rankwasheta haka ta daure ta kai masa. ✨✨✨✨✨✨✨ Yana sana'ar tasa wato danne dannen laptop ta kawo saida yaja aji sannan ya daka mata tsawa tare da cewan da yake kin rainani koh dole ki yi mini tsaye akai saina amsa tunda ga sa'anki yana mgn jiki na rawa ta ijiye sannan sum sum ta tafi daki ta haye gado saida tayi kukanta 😭ma ishi sannan barci ya kwasheta. ✨✨✨✨✨✨✨ Da safe da xaxxabi ta tashi sbd a daddafe tayi sallah subhi sannan ta koma ta kwanta sbd jin kanta wani irin sarawa da yake yi ✨✨✨✨✨✨✨ Safiya lkcin tashi bacci yy domin Six take tashi tayi aiki da girki sannan ta shirya xuwa makaranta Aliyu ya kaita yau yajita shuru baiji alamun ana girki a kitchen ko wani alamun movement dinta yace "Ah lallai yarinyar nan wuya yy qwari amman xanyi mgninta sbd wulakanci sai munyi latti" Ya dai xauna shuru shuru bb alamun ta ya tashi da niyyar yaje yaci mutuncin ta yana qiyasta abinda xaiyi mata a ransa yana xuwa yy turus ya tsaya dalilin hangota da yy can quryar gado da qaton blanket sai rawan sanyi takeyi *Tuartah yar sa ido👁bata bari ya qariso ganin me ya samu Amrah ba har tayi saurin sako kai nai saurin turata baya to yar sa'ido ina ruwank 😜* ✨✨✨✨✨✨✨ A fusace ya yaye blanket din da niyar fara fadan da yasaba yadda ya ganta a dunkule tana rawar dari yasa shi fadin subhanallah ya dagota tai saurin janye jikinta yaja tsaki ke tun yaushe ne baki da lpy tai shuru koda yake ma ace mutun bashi da sana'a sai kuka ba dole jikinsa ya gaza ya fara cuta ba ya mike gami da ficewa. ✨✨✨✨✨✨✨ Ita dai tana kwance yadda ya barta ko motsawa ta kasa yi ya shigo rike da tea mai kauri da ya hada mata gefe guda kuma yana rike da magani ya dagota ahankula yake bata harta shanye ya bata maganin saida yai jan ido sannan ta iya sha aikuwa tana sha tayo amansa ajikinsa takaici ya kamashi ya mike gami dayin waje da tsumma ya shigo ya goge gun tas itama ya goge mata jikinta data bata sannan ya dauko mop ya goge gun ya kamata zuwa toilet da zunmar wanke mata jikinta data bata aiko yana kokarin xuba ruwan taga dai dagaske yake ta noke zan wanke ya tabe baki gami dayin waje. ✨✨✨✨✨✨✨ Karnin da yaji dakin nayi yasashi feshe shi da turare nan da nan kamshi ya bai baye ko ina data fito yace bara na kira doctor tace yah kabar na warke hararar da ya watsa mata yasata yin shuru kan doctor yaxo ya kammala girki dayake tun yana gida ya iya komai dan mami dan sun kasance maxa hakan besata kasa sanyasu aikin gida ba. Koda doctor yaxo yace ai gajiya ce kawai ba wani abu ba ta dan huta ya rubuta mata magani gami da tafiya aranar yini Ali yai yana mata hidima komai na gidan shi yai ita dai binsa kawai take da ido. ✨✨✨✨✨✨✨ Yah na shirya ta fada ya dan kalleta harta fada yace kin shirya me sch mana ya cigaba da abinda yake bai ce mata komi ba ta kuma daurewa yah nafa shirya zan makara adan fusace ya dago ke wai bakisan ciwon kanki bane na fuskanci zaman gidanne bakiso inba haka ba mutun bai da lpy yace sai yaje makaranta tace cikin raunanniyar murya wallahi yaya na warke kuma ganinai banyi reporting ba kar ayi attendance ko test eh kice karatu yafi lpyar ki to ba inda zaki tai rau rau da fuska zata sa kuka yace karki fara nafada miki batun yauba inda abinda yafi ban haushi dake to wannan kukanne ki koma daki ki kwanta kuma nashigo naga kina kuka Allah nida kene. ✨✨✨✨✨✨✨ Sai da tai bacci ta tashi ta tuna da maryam kawarta da sauri ta dauki wayarta dan kiranta ta fada mata bata da lpy ko dan ta sanar sai dai wayar bata shiga gashi number dinta kawai take da dan da ita kawai suka saba sosai taja tsaki itama dai maryam matsala ce wallahi ta fada gami da saukowa daga gadon toilet din dakin tashiga tai wanka gami da dauro alwala dan lokacin azahar yayi sai da tai sallah sannan ta fito da niyar dafa abinci. ✨✨✨✨✨✨✨ Ga mamakinta yauma kamar kullun tana fitowa falo komai tas kamshi kawai ke tashi wato yah Ali ya gyare gidan tas tai kitchen da zummar dora abinci ta akan tukunyar taga ya dora takarda da rubutu kamar haka _your breakfast in the dinning_ tai murmushi gami dayin waje komai yayi tana ci tana murmushi lokaci lokaci tana tubawa da yanayin Yayan nata. ✨✨✨✨✨✨ Jikinta yai sauki batajin komai dan yanxu tana riga yah Alin tashi ta kammala komai anman taga alamar har yanxu bai ga damar barinta taje sch ba hakan yasa yau tai niyar zuwa ta sameshi yana zaune yana kallo tazo ta zauna ko kallon inda take bai ba tace yah sannu da gida bai amsaba ta riga ta saba da halinsa tace yah dan Allah kaga fa na warke gobe ka barni naje sch pls yadda tai maganar yaso bashi dariya ya daure kije zanyi tunani pls yah to shikenan ki shirya tunda naga kin dena kuka tai murmushi gami da far da ido nagode yaya tai ciki. ✨✨✨✨✨✨✨ Ai kuwa a sch tasha ciwon baki bataxo ba kwana biyu anyi test hankalinta ya tashi dataji malamin dayai dan shi inbaka da test co direct aikuwa akan maryan ta hakke ita dai maryam hakuri ta dinga bata tace network ne ita wayarta kullun akunne take ita ce ma ankirata akashe. ✨✨✨✨✨✨ Dan Allah maryam in mungama lecture dinnan zaki rakani muje inroki malaminnan ko zai min test din ke nifa tsoronsa nakeji inji maryam pls kawas zainab dake gabansu tadan juyo kunsanfa halinsa kudena surutu karku jaza mn masifa kan tai shuru sukaji yace Amra Muhd Nasir stand up pls Amra ta kwalalo ido nashiga uku ina wannan mutumin yasanni Maryam tace ki tashi watakil yaga surutun da muke cikin Amra ya turu ruwa........ ✨✨✨✨✨✨ *Loves u Fans especially ummusulym and F.A.Ya'u group members* ✍🏾✍🏾✍🏾✍🏾✍🏾✍🏾 *Ummusulym* *F.A.Ya'u* [1/6, 8:45 PM] Fadima A. Ya'u(F.A.Ya'u)😘: ⚜⚜⚜⚜⚜⚜ ⚜⚜⚜⚜ ⚜⚜ ⚜ *Amratu* *50-55* *Na* *Ummusulym* *Da* *F.A.Ya'u* fayaublogspot.com Fayau26.wordpress.com Who is Amra nace jin ya fadi haka yasata dan colling down tunda ta gano be santa ba maryam ta taba ta ki tashi karyai fushi ko bataxo bane tai saurin mikewa gani sir yadan kalleta au da kina ma gabana kikai min shiru koda yake ai naga tun daxu firar ku kawai kuke sorry sir tace any way u are deceiving ur self not me kinga ba ma wannan ba ya gijin ya fada tai saurin kallonsa Yayanki yaxo ya samemu yace baki da lpy nai test ki shirya gobe xan baki make up baiji ta cewarta ba yai ficewarsa dan daman ya gama lecture dinsa ana ficewa ta fada jikin maryan tana murna kai anman naji dadi da tuni co direct tai dariya mantawa nai ban fada miki ba ai tun randa bakixo ba yayanki me kawoki wataran yaxo ni nama kaishi office din Hod tai dariya aranta tace yah Ali kenan miji nane ta fada a hankula what maryam tace da ita ita kanta batasan sanda ta furta miji nane ba kunya duk ta rufeta. ✨✨✨✨✨✨✨ Maryam ta riketa da gaske kike kina da aure tai dariya eh zance ne be tada zance ba tun kanna shigo nakeda aure kuma da gaske shine mujinki ta daga mata kai alamar eh kai anman kinyi dace wallahi ko yai dace ba suka sa dariya Allah ki yadda dani samin sa a miji ba karamin dace bane kinga ni mubar batunsa awwo kishi kike ko tai dariya 😃 kawai. ✨✨✨✨✨✨✨ Waiko ina yayan nan naki Nasir tai dariya kwayi kwa gama ai tuni na ganoku kuna wani kunbiya kunbiya shima tunda ya kyallara ya ganki ya hanani sukuni ganin ta rafkota yasata sauya zancen da wani ke yar gata ce Amra ko ta fada eh mana ko ina kikai yayu na biye dake ga mijinki me sanki aranta ta kuma mai maitawa gamijina me sona tai dariya kawai. ✨✨✨✨✨✨✨ Koda ta koma gida ta kammala komai ta zauna dan kallo anman ina tunanin Yah aliyunta ya cikata shi kawai take ganowa yayin da yake goge mata jiki lokacin da bata da lpy ita kadai taketa sakin murmuahi musanman idan ta tuno lokacin da yake fada. ✨✨✨✨✨✨✨ Yana zaune yana kallo ta zo ta zauna a kujerar datake kusa dashi tace yah sannu da gida yaya yawwa yace batare da ya kalleta ba ya ciga ba da abinda yake can ya dago ko da wani abunne a'a daman cewa xanyi na gama abincin na kaima dinning ok nagode wani dadi ya cikata yau yace ya gode ji take kamar yai mata wata gaga ruwar kyautakyauta. ✨✨✨✨✨✨✨ Yana ci tana kallonsa jefi jefi tana sakin murmushi shiko gogon nata ko ajikinsa dan bema san tanai ba yadan jiyo jin ajikinsa kamar ana kallonsa tai saurin dauke kanta yaso fuskantar wani abu ya tabe baki gami da ci gaba da cin abincinsa dan baya gajiya da cin abincin yarinyar mami tai mata horo wajen iya girki ganin zai ganota yasata mikewa tai daki. ✨✨✨✨✨✨✨ Yadda suke zaune ba yabo ba fallasa fada dai yaki dewa yayinda ita kuma taki dena shagwaba abinda ke bashi haushi da ita dan ko ayau ta hadu da mami sai tayi abinda be saniba jikinta ya saba tana iya kokarinta wajen san ta dena. ✨✨✨✨✨✨✨ Kai Abbakar ka cika natsala daga can daya barin bataji me akace va taji dai yayan nata yace to shikenan sai kaganmu ya kashe wayar ganin goma tayi wato time din baccinta yasata mikewa da zummar yin daki ke ya ce taja ta tsaya gobe ki shirya zamu gidan Abbakar to yaya tace tai ciki. ✨✨✨✨✨✨✨ Washe gari ta shirya tsaf tai kyau sosai ta fito baya falon tai dakinsa da alama alokacin ya fito daga wanka yana goge jikinsa kunya duk ta kamata ganinsa dagashi sai tawul tai niyar juyawa ya tsai da ita ina kuma xaki gani nai kana shiryawa yaja tsaki matsalarsa da yarinyat tafiye gida danci ok fadi me ya kawoki daman cema xanyi na shirya yadan kalleta ke na fuskance ki gabaki daya bakisan zaman gida wato danace zamu unguwa ai shikenan farin cikinki yaxo zaki shirya da wuri tasaki murmushi😃 kawai tai waje dan ta rasa me zatace ganewa ne beba ita ba unguwar takeso ba face fita dashi din dan ko bakomai in sunje gu baya shurun da yake mata agida zagewa yake ayi fira tare dashi ita ayanxu ba abinda takesan ji kamar muryarsa koda fadane shiyasa inta tarasa yadda zatai yai mgn take tsokanoshi yaita fada 😡tashige daki tai ta dariya.😂 ✨✨✨✨✨✨✨ Yai kyau shima cikin shigar shaddarsa blue komai yaji inji matasan yanxu yai mata kyau a ido jitake kamar karta dena kallonsa tadai basar sai ayanxu yadan kalleta muje ko tai saurin yin gaba yaja ya tsaya ke me kike nufi ne tadan tsaya gami dabkallonsa kina nufin da wannan shigar zaki fita takalli kansa me tayi bansani ba jeki ki sauya matar aure ce fake yah naga kai zaka kaimu ka dawo damu ya daga mata kuma naga kinga ni atsarina matata hijab xata sa ta turo baki anman ko bakomai taji dadi tunda dai ya dauketa matarsa tai ciki. Tafito sanye da hijab shi bega abinda ya sauya ba yaja tsaki suka tafi. ✨✨✨✨✨✨✨ Acan gidan Abbakar ansha fira da korafi kan Aliyun be kyauta ba ace tunda sukai aure ya kasa kai matar aagaisa mita kam yashata da yake sun saba da matar irin masu rahan nance tai tamasa tsiya eh kayi aure ka gujemu yace ke kuwa ba dole ba cewa nai ba huta da gori nima dai wane gori inkaga ka huta dashi sai kun aje mn babies kunya duk ta cika amra fuskantar hakan yasata janta zuwa ciki aiko tun tana sun sunkewa harta ware suka sha fira irinta gari dan Amra irin mutanannan ce da baka taba jin sirrinsu sai dare suka baro gida tare da jibgin alkairi daga Amina matar Abbakar. ✨✨✨✨✨✨✨ A hanya yake tambayar ta mene babu agidan tace aranta gida akwai komi saidai ginshikin gidanne babu afili tace akwai komi kifi da tumatir ne babu a jifato ya tsaya har ta fito da zummar binsa ko me ya tuna ohoo yace koma ki jirani. ✨✨✨✨✨✨✨ Da suka koma gida ta kaimasa tea dinsa tai dakinta wanka ta shiga tai wankanta gami da dauro alwala sunyi isha acan dan haka shafa'i da wuturi tai tafada gado dan tagaji sosai gashi gobe monday tanada lectute 8. ✍🏾✍🏾✍🏾✍🏾✍🏾 *Ummusulym* *F.A.Ya'u* [1/7, 3:44 PM] Fadima A. Ya'u(F.A.Ya'u)😘: ⚜⚜⚜⚜⚜⚜ ⚜⚜⚜⚜ ⚜⚜ ⚜ *Amratu* *55-60* *Na* *Ummusulym* *Da* *F.A.Ya'u* *In Dedication to Halima Dangado(Dangadoriasis)😘😘* fayau9.blogspot.com Fayau2626.wordpress.com Da wurwuri ta tashi ta kammala komai dan tanasan yau tashiga sch da wuri karfe bakwai dai dai ta fito ga mamakinta Yah Alin bai nan tai dakins sai takar da ta gani kan gadon da alama ita ya barma ta dauka abinda ta gani shine _Nashiga baki tashi ba jiya ban fada miki ba anturamu kaduna a gun aiki yau zan dawo ki kijira nace wani agida yaxo ya kaiki sch_ har ga Allah har ranta taji ba dadi tace Allah ya dawo dakai lpy aranta tai falo ko karyawa ta kasayi sai a flask ta zuba tana jiran me zuwa kaitan. ✨✨✨✨✨✨✨ Tadan russuna ta gaidashi Yah nasir ina kwana yaki amsawa shima yafan russuna kanwarmu ina kwana ta turo baki kai yaya nafa ce bana so nima nace ki dena gaishe ni kinki kefa matar yaya na ce Allah zanyi fishi dakai to ayi hakuri baxan kuma kaso ka makara yai murmushi bansan da zuwanba seda naga yaya sulaiman zaixo yace zaizo kai kine nace yabarshi na kaiki tai dariya kaji dashi dai yadan kalleta me xanji dashi tai darita ni muje ina makara. ✨✨✨✨✨✨✨ Ahanya yake mata maganar maryam tasa dariya ahaf ai nasani me kika sani ohoo gashi data fara wari mun faraji kinga ni bafa wasa nake ba pls ya za'ai ko number dinta ki ban tadan daga kai alamar tunani any way zanyi tunani haba aunty Amra ta tsuke fuska to wallahi zaka sanya infasa to nadena kanwarmu ta bude motar gami da lekawa inkaje ka gaida mami dan Allah kace wanda zaizo dauka na yaxo da wuri to yace tanxu number dinfa kabari zan tambayeta to shikenan se najiki. ✨✨✨✨✨✨✨ Bayan sun fito daga lecture Aisha taxo pls maryam yunwa nameji zoki rakani village Amra tace af kinga na mance naxo da abinci inxaki ci me zai hana yadda nakejin kudinnan nawa suka saka dariya dayake abincin da dan yawa tare suka ci su ukun Aisha sarkin jama'a ta mike ina zuwa tai gun dataga wasu na fira. ✨✨✨✨✨✨✨ Amra ta kalli maryam ban fada miki ba inajinki ai yau mutumin naki ne ya kawo ni tsaf ta gane wa take nufi ta basar wa kenan tadan kalleta ana so ana kaiwa kasu pls wa kike nufi ban gane ba waye inbanda Yaya Nasir tadan ja tsaki yaushe ta zama mutumina ohooo kya tambayeni kinga daman cewa yai inbashi contact dinki nace ai ankusa bikinki ta fadi haka ne dan ganin yadda zatai what inji uban...tai saurin rufe baki haba Amra yazaki min haka ke kika kusa bikin nawa aiko ankusa nasamu kama Nasir butsewa zanyi kaji yar newa to cewa nai zanmaki mgn abinda kika ce ynx zance ya kwantar da hankalinsa kema kina ciki haba ke kuma karki bada ni mana bama haka suka sa dariya vaki daya. ✨✨✨✨✨✨✨ Koda aka tashi Nasir ne yazo daukan Amrar sai da ya takura mata ta kira masa maryam dan ita tayi faculty din History dan dauko kanwarta da yake ita take driving aiko awayar tasha tsiya takusa minti goma bataxoba ta koma gefe dan kar yajita ke banfa san wulakanci yaysn nawa ma sai anja masa aji tai dariya yi hakuri ganinan. ✨✨✨✨✨✨✨ Anya kuwa kin kirata wallahi na kirata yaya tace kanwar tata ce bata fito ba ok ban wayar na kirata kan tace wani abu ya faketa ya kwace wayar yasa number din awayar tasa yana kokarin kira ta karaso Amra na kallonsu sai wani shassharewa Maryam take kasa kasa take musu dariya dan kar yagano wani abu. ✨✨✨✨✨✨✨ A gida gabaki daya ta kasa bacci duda bata iya wuce 10 sai gata har 11 idonta tan gararas sai 12 ya shigo gidan ga mamakinsa tana zaune ta rafka ta gumi bakuma kallo take ba dan ita din ba gwanar sa bace yazauna wash ya fada duda yai sallama bataji ba wash din data ji ne ya firgita ta tai saurin dagowa atsorace yasaki murmushi matsora ciya kawai tai dariya lah yaya sannu da zuwa yawwa ya fada ban ruwa ta mike jiki na rawa tai gun fridge yakar ba yasha tai dinning area ta hado masa abinci sai da ya fara ci ta mike gami da gada masa ruwa nakai maka toilet tadago yana murmushi me ya hanaki bacci kamar tacd rashinka ta daure tsoro to ynx na dawo jeki ki kwanta gobe da sch nagode Allah yai albarka amin ta fada gami dayin dakinta har bacci ya dauketa tana tunawa da dagowar dayai cike da murmushi fuskarsa maganarsa ke mata yawo aka to ynx na dawo jeki ki kwanta Allah yayi albarka. ✨✨✨✨✨✨✨ Da safe da wuri ta tashi ta gama komai tai makaranta A sch maryam ke mitar wallahi Amra baki da mutunci jiyafa kinso badani tai dariya tunda ban badake dinda ai shi kenan Allah da gaske nake inkina dariyar nan sai inna kalloki se inji nima kamar in sheke da darita kai dan Allah me yasa baki sheqe dinba mtseeew taja tsaki gami dayin gaba. ✨✨✨✨✨✨✨ Amra tabi bayanta ayi hakuri haba sis bafa ma haka dake ni ki kyaleni dole tasata dariya harta tsaya baki fadan ya kukai ba tadan tsuke fuska sirrinmu ne aha lallai masoya haka zaki ce eh haka zance to dai kiyi ahankula se inki baki shi ko sannu babarsa tasa dariya. ✨✨✨✨✨✨✨ Toma wai ke banda abinki Amratu ai ke zaki girmamani yayanki nake aute hoooo maryam Allah ya shiryeki wato ma harkin daura muku aure ahtoo ya ranki fari tas tace to bari yazo zaki sha mamaki tai aji tana dariya maryam tabita da sauri me zaki ce masa ah ohoo ki bari inyazo kyaji tai tai tafada mata taki. ✨✨✨✨✨✨✨ Agida suna zaune suna cin abinci ita abincin ma bawani ci takeba shi kawai take kallo wayarsa dake can kan kujera ta hau ruri yace mikon wayar can ta mike da hanzari bata duba wake kiranba dan kar kiran ya tsinke ta kawo masa yadan kalli screen din waya yawani saki murmushi kafin ta kara akunnensa taji yace Aminci agareki yake masoyita wani tukikin bakin ciki yazo mata wuya bataji me akace ba daga daya barin sai murmushi dataga yasaki tare da kara narke murya tare da naki afusa ce ta tashi tabar gun hartana faduwa dan ita kadai tasan me takeji aranta ya juyo ya kalleta ya tabe baki alamar i don't care yaci gaba da wayarsa...... ✍🏾✍🏾✍🏾✍🏾✍🏾 *Ummusulym* *F.A.Ya'u* ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ ⚜⚜⚜⚜⚜ ⚜⚜ ⚜ *Amratu* *60-65* *Na* *Ummusulym* *Da* *F.A.Ya'u* fayau9.blogspot.com Fayau26.wordpress.com Daki ta shige ta bugo kofar da karfi tana shiga kuka ya kwace mata ta jingina ajikin kofar kuka take maras sauti tun tana tsaye harta kai kas saida tai mai isarta sannan taje ta wanke fuskarta bata koma takan abinci ba ta hau gado danyin bacci anman bacci yace shi bai shirya ba. ✨✨✨✨✨✨ Zaune ta tashi to ma wai mene naki na damuwa dan yayi waya da wata zuciyarta ta fada mata wani barin yace mata kardai fa kin kamu dasansa ina ta fada baso bane afili can ta mike tahau zirga zirga inba so bane to mene kishi ta kada kai wata zuciyar tace ai mijinki dole kiyu kishinsa alwala tadauro ta dauko alkur'ani dan karantawa ko taji dadi aranta. ✨✨✨✨✨✨✨ Washe ruwan shayi kawai ta dafa sai kwai data soya ko dakinsa bataje ba bslle yasamu matsayin gaidashi shikansa yai mamaki be kawo komai ransa ba ya fito tana zaune akujera tadan kalleshi fuskarta adaure ina kwana tace ya amsa batare da tunanin komai ba yaje dan karyawa. ✨✨✨✨✨✨✨ Bai ce komi ba ya ci abincinsa ya mike muje ko tabi bayansa ko amota tunda ta sunkuyar da kanta bata dago va sai da yace zaki iya fita ta fice batare da tace kala ba ya kada kai kawai ya tafi aransa yana cewa yau yan shaga bar suka motsa dan yaga babu abinda tai agidan yadda ya kwanta yabarshi haka ya tashi yaganshi. ✨✨✨✨✨✨✨ Sakawa take tana war warewa ta rasa me zatayi a sch ma a sabule ta wuni har aka tashi maryam nata tambayarta me yasameta sai dai tace batajin dadi ne jitake kamar taje ta fasa wayar tasa. ✨✨✨✨✨✨✨ Koda ta koma gida indomi ta dafa ko ci batai ba ta ajiye masa a dinning tai dakinta da ya dawo yai mamakin rashin ganinta a falo be kawo wani abu ba yaci abincinsa sannan har ya kwanta ya mike dan zuwa yaga me yasa bata fito ba dan hankalinsa ya kasa kwanciya. ✨✨✨✨✨✨✨ Tana jiyo bude kofar tai saurin kwanciya alamar bacci take batasan ya ganta va tace au dankin dafa indomi shine zaki koma yar buya dani ta bude idonta dayai jawur sabida kuka tace kaina ke ciwo sub hanallahi kinsha magani tace eh Allah ya sawwake ya fada gami dayin waje. ✨✨✨✨✨✨✨ Yanayin waje hawaye ya zubo mata wato shi bemasan me take ma fishi ba shi yadauka shirmenta kawai take kaico na ta fada. ✨✨✨✨✨✨✨ Dasafe ta fara wucewa tai dakinsa yana wanka wayarsa ta gani kan bed side drawer nan hankalinta ya bata ta dauka da sauri ta dauka number din mukli ta nemo tai niyar gogewa se ta fasa tasa ta black list ta shiga watsap tai blocking dinta tai ficewar ta dan ta fuskanci ita take kiransa shi kuma na biye mata. ✨✨✨✨✨✨✨ Fes tajejin ranta dan ji take kamar ta rabasu tunda inta kira bata shigoba ta turo message be shigo ba intana da tunani ta hakura shi kansa yai mamakin yadda ta sauya cikin fara'a suka gaisa abuncin a flask ya tafi dashi suka fuce. ✨✨✨✨✨✨✨ Yau gidan a cike yake dan kannenta na sabuwar kofa ne suka zo dadi ya cikata sai nan nan take dasu tun safe sukazo sai dare zasu tafi koda Aliyu ya dawo dashi sukai ta fira dan sunma fi sabawa dashi kan yayar tasu. ✨✨✨✨✨✨✨ Da zasu tafi ta basu turarurruka Aliyu yadauke su dan maidasu sai da ya biya ta Sahad yai musu tsaraba sannan ya wuce dasu gida acan gida mama take ta mita ku yanxu daga ziyara sai wahala yai dariya ina wahalar take mama au haka zaka ce to kuwa zasu dena zuwa ayi hakuri yazauna suka taba fira ya wuce gida. ✨✨✨✨✨✨✨ Allah maryam nayi fushi ta kalleta me kuma nayi ace baki taba zuwa gidana ba ko sau daya ayi hakuri kimin uxiri tadan harareta uxiri fa kika ce haba Amra tarefa muke karatunnan dake kina kallo a sch muke wuni da kefa taushe fa baje gida natafi yawo au zuwa gidan nawa ne yawo ba komai ta kada kai tai dariya ayi hakuri ba haka bake nufu ba zaki ganni tsulum kedai ki tanadi kayan dadi yaushe to sai randa Allah yayi taja tsaki kice kawai bazaki xo tai dariya nidai bance ba. ✨✨✨✨✨✨✨ Yaya mezan dafa yadanyi shuru kiyi kome ma kika ga yadace to yaya tace tai kitchen da yake yau ba aiki suna gida dan shi ba gwanin yawo bane innyaje gida ma mami cewa take ya dawo gidan matarsa koda ba fira sukeba anman sun saba zaman guri daya duda kowa kowa da abinda yake. ✨✨✨✨✨✨✨ Bawani abinci me wuya taiba danbun kuskus tai sai dan lemo tana jerawa a dinning taji kamar ana taba kofa ta basar dantaji kamar iska ce kawai ta cigaba da abinda take tsaf take tai kyau cikin pink din diguwar riga alamar dai bugun da gaske ne har Aliyu ya mike zai bude ta wuce shi bari na duba. ✨✨✨✨✨✨✨ Wa zata gani muklisa wato tsohuwar budurwar Alin ce gabanta yai mugun faduwa ta daure Aunty mukli kece eh bakiyi tsan mani ba ko tadanyi murmushi ba haka bane ok me gidan yana ciki kamar tace a'a tace eh basu jira karashen amsar ba sukai ciki tabi bayansu da kallo tana sake saken abu buwa da dama..... ✨✨✨✨✨✨ *One love to Fans no word to express our appreciation*😘😘 ✍🏾✍🏾✍🏾✍🏾✍🏾 *Ummusulym* *F.A.Ya'u* ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ ⚜⚜⚜⚜ ⚜⚜ *AMRATU* *Page 65➰70* *Na* *Ummulsulaym* *Da* *F.A Ya'u* *Short and brief story* fayau9.blogspot.com Fayau26.WordPress.com Iya yinta tai ta daure ta saki fukarta gami da bin bayansu yn zaune ya miqe fuskarsa cike da mamaki Mukli ta kalleshi bakai farin ciki ba ko me kika gani yace naga kana mama kine yadanyi murmushi no ba haka bane kawai banyi zaton ganin ki a 9ja ba ne tai far da ido kace haka mn tunda ka gujeni tafadi haka tana zama. ✨✨✨✨✨✨✨ Amra ta zo dauke da lemo ta ijiye musu kamin itama tasamu guri ta zauna tadaure Aunty mukli ina wuni ta amsa a sheke ga lemo ta fada mata dayar da suke tare ta dauka tana tsiyayawa kanta ko ba'ai mn tayi ba ai masha ita dai bata ce musu komai ba Ali ya dube ta kawo musu abinci ta mike gami dayin wajen abincin koda ta gama jere musu tai dakinta takaici fal ranta. ✨✨✨✨✨✨✨ Da zasu tafi ya leko dakinta zasu tafi kixo kuyi sallama kamar tace bazata zo dinba ta mike ta hado musu turare cikin fara'a tace gashi mungode mukli tace ki barshi bashi mukazo karba kawar tata ta karbe ni inaso bari na rakasu bai jira amsar ta va yai fucewarsa. ✨✨✨✨✨✨✨ Ai tundaga wannan lokacin mukli ta maida gidan gidan zuwanta tun Amra na haquri har tafara kaita bango taci aniyar inta sake zuwa sai tai mata rashin mutuncin da bazata qara sha'awar zuwar mata gida ba. ✨✨✨✨✨✨✨ Tana daki dan yanxu ta rage zama inda yake danshi dinma haushinsa take ji tajiyi alamar maganar mace ta fito aiko muklin ce yau ita kadai ce ga mamakinta dinning take shirin hawa wato wuyanta har ya isa yankan da zata zo mata gida ta nuna isa da sauri ta karasa lafiya ta fada bata kalleta ba ta cigaba da qoqarin zuba abincin ke dallah malama dake nake ta dago au ashefa dani kike Yah Ali yace sakko mukli ta zuba miki ta kalleshi wa ai wallahi bazata ci abincinnan ba ta tureta na fuskanci bakisan mutunci ba wace macen ce zata dinga baro gidan iyayenta tana tawowa gidan saurayinta inba mara mutunci da tarbiyya va what ni kike cewa banda tarbiyya eh anfada ko xakiyi wani abunne ta daga hannu zata mare ta Ali yai saurin rike hannunta ke kuma mene haka pls zoki tafi gansan rigima Aliyu ni kake kora a gidanka No ba haka bane muje waje yajata waje ba haka Amra ta so ba tai daki tana kuka. ✨✨✨✨✨✨✨ Misalin biyu na rana Ali bayanan tajiyo bugun qofa taci kukanta ta koshi idonta ya kada yai jawur tai toilet ta wanke fuskar taje ta bude wa zata gani maryam ce kawarta dadi ya cikata. ✨✨✨✨✨✨✨ Takalleta lafiyar ki kuwa batasan Sanda hawaye ya kwace mata ba kuka fa kuka kike Amra nida nasan haka zan ganki da banzo ba wallahi sukai ciki maryam tai ta bata baki da nasihohi Amra batasan fadon matsalar ta anman inbata fada ba bazata ji sanyi ba nan ta baima maryam labarin komi tundaga aurensu har kawo yau. ✨✨✨✨✨✨✨ Maryam taja ajiyar zuciya kin ban mama ki Amra sai kace ba mace ba ki zauna da namiji kullun kuna tare ki kasa sanya masa sanki har ki bari wata tazo har gida tana kokarin nuna miki isa dan kawai tana takamar ita yake so inda nice da tuni an fice gun dole ki tashi tsaye ba boka ba malan da salonmu na mata ki kafa taki jam'iyyar agunsa gami da ture ta kowacce mace Allah ko tsaya kallon ruwa nan tai tabata shawar wari ita sai alokacin ma taga baiken kanta mata mu kula wani lkci mu ke kwaron kanmu ban baki shawaran bin boka ko mallan ba domin wannan hanyar ita ke dulmiyar da mata da yawa na wannan xamanin,da wuya kuga namji na asiri sai dai Wanda bai amsa sunansa na maxaje ba,ki cire duk wata tsana,kunya ko girman kai ki bawa mijinki kulawa kiyi masa biyayya. Sbd haka Amra ina mai shawartanki da ki kasance mai tsananin biyayya ga mijinki, ina tabbatar miki Allah xai da sa masa kaunarki domin dai ko ba komai hadisi yaxo daga manxon Allah (S.A.W)yana cewa. "An halicci xukata a bisa son wanda ya kyautata masu da kin Wanda ya munana mata" Idan kina kyautatawa mijinki ina mai tabbatar Miki sonki a kullum qaruwa xai dingayi,idan ke kuma yazama dole ki dena abinda baya so yadda kika ban labari tabbas Ali nasanki sedai be taka kara ya karya ba dole ke zaki tashi tsaye ki bunkasa sanki aransa ke burinki kullum ki bata masa rai toh tabbas bb shakka kullum sonki raguwa xai dinga yi a xuciyarsa,sbd haka 'yan uwa mata don Allah mu dage wurin kyautatawa maxa jenmu da jikinmu,da dukiyarmu,abin nufi da jikinmu shine tsabta,kula da gyaran jikinmu jan hnklin mijinki ta hanyar kwarkwasa domin kowacce mace ina tabbatar miki da jikinta jarintane muryanta jarinta ne,idonta jarinta ne. Abun nufi kuwa da dukiyarmu shine siyan kyale-kyale da abubuwan gyaran jiki,turaruka da sauransu da kudin mu ba sai mun jira mijinmu ya saya mana ba kamar ynda wasu matan ke aikata hakan,domin da wadannan karuwa ke mallake mana maxa jenmu Da fatan Amra xaki gane Allah ya baku xaman lfy kin ga lkci ya qure bari in tafi gida amman har ynxun ina shawartanki da ki qara dagewa da ibada,kuma komai ke tsakaninki da mijinki kikai kukanki gurin rabbi ixxati shine xai yaye miki,domin Allah shi yace Ku roqeni Xan amsa muku,Allah ya baki hqrin juriya na tafi sai mun hadu a skul Monday. Suka rabu tanatai mata godiya dan tajibdadin zuwanta ko bakomai ta tunatar da ita abinda ta mance tabvas ita take da lefi kuma zata gyara ta fada aranta. ✨✨✨✨✨✨✨ Tunda ta tafi ta xauna tana tunanin mgnar da sukayi da qawarta tabbas Allah ya bata kaifin hnkl Allah ya bata ikon juriya. Ta mike dan tunawa da ya kusa dawowa ko me ta tuna oho tasaki wani murmushi gami da yin dakinta. *LoVes You Fans* *Ummulsulaym* *F.A Ya'u* 🖊🖊🖊🖊🖊 ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ ⚜⚜⚜⚜ ⚜⚜ *AMRATU* fayau9.blogspot.com Fayau26.wordpress.com *Page 70-75* *Na* *Ummulsulaym* *Da* *F.A Ya'u* *Short and brief story* *Dedicated this luvly page to all Amratu fans mun gode sosai da qauna da kulawar da kk bawa wannan novel din Allah yabar mu tare luv yah😘* Kwankwasar da taji ne yasa ta miqewa taje ta bude. A tsaye yake,tayi masa sannu da xuwa ya qara murtuqe fuska sannan ya amsa ciki-ciki ya shige sashensa. ✨✨✨✨✨✨✨ Amrah tayi shuru tare da binsa da ido sannan ta shige nata dakin. ✨✨✨✨✨✨ Saida tayi wanka sannan ta tsala kwalliyarta cikin wasu shegun English wears coffee colour,ko dan kwali bb ta fita falo ta xauna tana duba jarida. ✨✨✨✨✨✨✨ Ya fito shima yy wanka yafi minti biyu yana kallonta,yana qiyasta abubuwa da dama a ransa,ita dai ko alamar dagowa bata yi ba sai can ta dago ta kalleshi murya qasa-qasa tace "abinci fa" ✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Fuska asake yace nagaji yau kawo mun nan ta mike yakuma binta da ido azahiri bawai yagajin bane kawai so yake yakare mata kallo duk inda tayi kuwa idonsa nakanta. ✨✨✨✨✨✨✨✨ Ta'aje masa taja gefe ta zauna yadan kalleta ki cika ladanki ki zuzzuba min ta zuzzuba masa ke bazaki ciba naci tun dazu tace oho ya fada ya kuma dagowa ya kalleta ya karatun lpy klau tace . ✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Kinsan me ya fada ta 'dago alamar tana jinsa duk kin sauya kin dena shagawa tadanyi murmushi oh my goodness tai saurin kallonsa yasakar mata murmyshi kinzama kurma ne ✨✨✨✨✨✨✨ Shuru tayi masa, Ta mike yaya gobe da lecture bata jira amsarsa ba tai dakinta tana taku dai dai ya bita da ido yakasa aje cokalin ko zuba abincin abaki rufo kafar dakin ta datai ne yadawo dashi hankalinsa yasaki wata nannauyar ajiyar zuciya. ✨✨✨✨✨✨✨ Yarasa meyasa yarinyar duk ta sauya masa komai nata ynx burgeshi yake salon data dauka ne yakejin bazai iya daika ba wato salon shiru. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Ada farkon auransu yakan dawo da niyyar ci mata mutunci anman da yadawo sai yaji yakasa yayin da ayanxu yake da burin kawai yadawo yaganta sai dai girman kansa yasa yakasa nunawa. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Haka ya gama cin abincinsa har ya xauna jira bb alamun fito warta ya gaji ya shige dakinsa. ✨✨✨✨✨✨✨ Ranar Monday ya tafi aiki abubuwa da yawa suna jiransa a office sai qarfe sha daya ya dawo,Amra na kwance a babban falo tana duba littafinta domin takaicinsa ya fara isarta duk wata dabara tayi bb nasara,gashi ynxun ita da kanta ta gane ta fara sonsa domin kullum wutar sonsa ne take ruruwa a ranta. ✨✨✨✨✨✨✨ Ya turo qofa ya shugo,ta mike tana kallonsa shi kansa kallon nata yakeyi. "Sannu da xuwa" Fuskarta a hade tayi mgnar ta hada littafanta ta miqe ta wuce sashenta,ya bita da kallo.kayan baccine a jikinta sun amsheta riga da wandone. Aliyu ya tabe baki ya shige sashensa. ✨✨✨✨✨✨✨ Tsananin takaici dajin haushinsa bai barta tayi bacci ba sai qarfe uku na dare bayan tayi nafilfilinta ta kwanta,don haka tunda tayi sallar asuba ta kwanta bama ta tunanin xuwa lectures a safiyar ranar sbd ynda take jin jikinta. ✨✨✨✨✨✨✨ Shi kuma oga Aliyu ya tashi da matsa kaicin xaxxabi a ranar domin ko yatsa baya iya motsawa sbd ynda jikinshi yakeyi. ✨✨✨✨✨✨ Amra ta fito da safe domin yin breakfast domin a xatonta oga ya tafi aiki har ta gama aikinta bata ga alamun ya fito ba wata xuciyar nacewa jeki duba lfy wata ta haneta dayin haka tadai fatattaki xuciyar ta nufi dakinsa tana daidai falonsa,taji kakarin amai alamun bb komai cikin mutun yana aman wahala a guje ta isa wurinshi ta taimaka masa ya tashi amman ina qarfin mace da Namiji ba daya ba kawai qarfin hali yasa,ya tashi dakyar sannan tasa masa filo a bayansa ynda xaiji dadin xaman tunda bb karfi sannan ta samu ta gyaran ko ina ta sanya turare yana kamshi ta iso gareshi Yayah Aliyu sannu ya daga mata gira alamun yawwa tace ina phone dinka a kira doctor yace da ita alamun da hannu ta duba drawer dinshi akwai mgni taje ta kawo sannan ta hada masa tea yasha ya danji qarfi a jikinsa sannan ta hada masa ruwan wanka ta taimake sa har qofan bayi kafin ya fito ta gyara,gadon ta dauko masa kaya marasa nauyi ya yi mata alamun. da hannu ya fito taxo ta taimaka masa ya qara so taje ta riqo hannunsa sannan suka iso gado tace ga kayanka nan na kawo kasa bara inje in dafa abinci in dawo. Ta tafi tayo masa,girki mara nauyi daidai buqatar mara lfy amman jefi jefi tana xuwa dakin ta leko shi harta gama ta kawo dakyar taci shima don yaga bacin ranta sannan yasha mgninsa ya kwanta. ✨✨✨✨✨✨✨ Itama a dakin ta kwana akan kujera amman motsi kadan yy yana kan idonta. ✨✨✨✨✨✨✨ Da safe ta shiga kitchen ta hada breakfast sannan tayi hidima dashi. ✨✨✨✨✨✨✨ Tsawon kwana biyu yadan fara murmurewa a ranar da taga haka saita kwanta a dakinta amman xuciyarta na dakinsa ✨✨✨✨✨✨✨ A Daren Aliyu ya dade baiyi bacci ba yana ta xuba ido yaga Amra Amman shuru domin dan takaitaccen xaman da sukayi da Amra ya tsaya masa a rai,a haka yata juye juye a gado har bacci ya daukesa. ✨✨✨✨✨✨✨ Da,safe ma Allah Allah Aliyu yake yaga Amrah Amman shuru shuru lkc lkc ya kalli agogo har goma tayi bb Amrah bb alamarta sai misalin sha,daya yaji alaman turarenta nan da nan yai baya ya lumshe ido kai kace bacci yake yi tayi sallama ciki ciki ya amsa,ta nemi guri ta xauna tana gayar dashi sannan ta shige bayin dake dakin ta hada masa ruwan wanka yana shiga ta miqe xuwa kitchen ta shga fiddo da kayayyakin abincin data,shirya tun tashinta kamar irinsu kunun gyada,arish ball da sauransu lkci qanqani daki ya dume da kamshin turare dana abinci😝don haka idan ka shaqa sau daya ba xaka so fita ba,Aliyu na fitowa daga wanka daman ta riga ta fiddo masa,da kayan da xaisa a qofan bayin ya dogara yana bin Amrah da kallo kwalliya tayi na fitan hankali daman gata da kyau amman yau tafi ranan aurenta kyau cikin qarfin hali ya dubi daddumar cin abinci data shimfida da varieties din abinci iri iri yace duk wa yy wannan?tace ni kadai yace kai amman aiki yy yawa,bana son ganin mace na aiki da yawa,don haka idan kinyi man abinci guda daya ya gamsar. Basai kinyi da,yawa ba. Bata amsa ba illa lumsassun idanunta da tayi alamun gamsar dashi tsigar jikinsa ya tashi yarrrr kallo ya bita dashi ta miqe xata fita yace ki dawo muci abinci idan ba haka ba,sai kuma yy shuru. ✨✨✨✨✨✨ Cikin kwana kin da suka shude muguwar shaquwa ta shiga tsakanin Amra da Aliyu Wanda har yasa duk cikinsu idan basu ga juna ba basa jin dadi kuma bb kwanciyar hankali. ✨✨✨✨✨✨✨ Mummy taxoqara duba lfyar Aliyu tagan shi ya qara murmurewa abun gwanin mmki a ranta tayi farin ciki tare da addu'ar Allah ya hada,kansu. ✨✨✨✨✨✨✨ Suna cikin hira Amrah taxo ta dan kanga jikinta jikin mummy kamar koda yaushe tace mummynmu ina wuni?Mummy ta shaqi kamshin Amrah ta murmusa acikin murmushin take cewa lfy qlw Amrah ta saki mummy sannan ta nemi three sitter ta xauna suka cigaba da hira harda,Aliyu sannan tayi masu nasiha da xata tafi har mota suka rakata sannan driver yaja ta tafi. ✨✨✨✨✨✨✨ A dakin Amrah sallamar Aliyu yasan Tayi saurin bude ido tare da Satan Kallon sa,a kullum qara kyau yakeyi cikin sauri ta suri hijabinta d ke gefe tasa yadan saki murmushi yadda tayin ya bashi dariya wannance rana ta farko da Aliyu ya Shiga bedroom dinta domin iyakarsa falo yadan qariso daidai lkcin daya saki labulen rigar bacci qaramace a jikinta domin. Ko cinyarta bata gama rufewa ba hannuwar rigar siraraine inka cire rigar bb komai a jikinta banda shower cap daman qa'idar baccinta knan sai kamshine kawai ke tashi na dum dum dum a jikinta yadan kalli gafen dakin komai yy masa hatta turarenwutar data jona ajikin burner ya burgeshi a hankali ya taka ya isa gefen gadonta.Amrah ya kira sunanta a maqoshinta ta amsa.... ✨✨✨✨✨✨ *Masu karatu kuyi hqr akan rashin jinmu da Baku yi kwana biyu ba* ✨✨✨✨✨✨✨ *Ummulsulaym 09039729270* *F.A Ya'u 09028287218* *For comment, correction or advice* ~Love you Fans~ ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ ⚜⚜⚜⚜ ⚜⚜ *AMRATU* *Page 75-80* *Na* *Ummulsulaym* *Da* *F.A Ya'u*. fayau9.blogspot.com Fayau26.WordPress.com *Dedicated this page to mah Luvly frnd Safiyyah H Aliyu Allah yabar so da qauna* *Short and brief story* Yadan jima yana kallonta kafun ta ce daman nashigo ne mudanyi fira naga ke kuma kamar bakya mara ko tai dariya no yaya kawai dai sai tayi shuru kawai dai na takura miki ko a'a wallahi to kawai dai me tadanyi murmushi gami dayin shuru any way tunda ba'a buka tata bari naje ya juya dan futa dasauri ta mike tabi vayansa haba yaya nifa bance katafiba to kinfada mn tanarkar da murya to pls kadawo ya dan kalleta sannan yace to muje. Suka sha firarsu wadda rabbinta ta rayuwa ce sai ta karatun amra wadda ya fuskanci tafi santa hakan yasa yaketa jawota sai wajan shabiyu ya kalli agogo kai gaskiya na jima adakinnan vari naje ko ta rako har bakin kofa sai dasafe ya amsa Allah ya tashe mu lpy ta turo kofarta ta rufe. Shoko gogon naku koda yakoma daki ai kasa bacci yai amrarsa kawai yake hangowa tana sakar masa lallausan murmushinta dakyar barawon yasace shi wato bacci. Da safe tashirya tsaf dan tafiya sch shi kawai take jira yayin dashiko tai zamansa adakinsa yana sane yaki fito wa so yake tashigo dakin yayin da ita kamar tasan abinda ya tsara taki shiga tai zamanta a falo lecture din 10 gareta ta daga ido taga hat 9:00 ta zaro ido kyashin tashi take ta mika hannu ta daiko phone dinta yah sunan da ta sanya masa kenan ta danna saida ta katse be dauka ba akaro na ukunne ya dauka cikin muryar shagwaba tace yah pls kafito ina makara zai mgn takuma ce pls yaya ta kashe wayar ba haka yaso ba yadai daure ya fito. Ita ko mukli ko da ta bar gidan Ali kasa tukin tai yau ita ce wata zata nuna ma iko akan Alin data ci buri akai kuma Ali yana kallonta ya kasa ce mata komai saima korarta da yai daga gidansa kuka ya kwace mata sai da tai me isarta sannan taja motarta zuwa gida. Agida ma yini tai tana kuka ba abinda tane tunawa sai janta da Ali yai zuwa gun motarta ya turata pls kije gida zamuyi waya kinga nan gidanta ne bansan rikici ba abinda yafi bata mata rai irin cewar da yai nan gidan Amra ne data tuna sai kuka tun ana rarrashinta agidan da tambayar ta mene suka hakura suka kyaleta. Amra nazaune tana rubutu duk kwakwalwarta tahau caji wani assignment aka basu a chemistry tayi tayi tayi ba idea wani abin takaici itace group leader gashi presentation assignment ne tashiga tunani sosai kallo ta kawai take gaban tan course dinsu tana baza ido yan group dinsu nata harararta batasan ma ya shigo ba sai jitai ansure ta atsorace ta dawo daga tunanin da take ya dire ta yana dariya matsoraci kawai tai dan murmushi lah yaya yaushe kashigo yai murmushi kinacan kina tunani harnaje daki na dawo sannu da zuwa tace yawwa ya fada atakai ce kawon abinci ta mike tai gun dinning ya dauki kayan karatun yana kallo tazo ta dure masa gashi ya aje yafara ci saida yaji ya koshi sannan yace wai tunanin me kike haka bakomai tace. Kedai fadi gaskiya wallahi wani assignment aka bamu ya cajan kai nakasa gashi gobe zamuyi presentation ya mike ina zuwa ya wanko hannunsa sannan yakarba sai da ya koya mata sannan yace ta amsa gyara kadan yai mata sannan yace sauran rehearsal na gobe ya zauna as student and sauran kujeru ya tsara mata yadda zai komai ta gwada ya tafa mata sannan suka koma wata firar. Aiko aschool da akazo sune yan group c group a sukai b sukai Amra ta fito dan yin nasu shi kansa malamin ta birgeshi dan zama yai yadda take kai kace lecture ce gashi babu ko tsoro da confidence dinta yadda tai ko ba dai dai bane sai ya basu maki dan kara mata karfin gwiwa balle koshi balallai yakoyar dadiban su gane haka ba daki daki sai tafi suke mata tana gamawa tace da me tambaya yan kwakkwafi suka fara sako tasu duk dan kayadda group dinnasu cikin ikon Allah ta amsa koda ta koma ta zauna malamin ya taso shima da tafinsa yace that's excellent dabadan bana bada maki duka ba da kunci 100% but ynx ma nayi kuru na baku 98% gabaki daya aji akasa ihuuu ahhh haba malan yace ko kun raina ne in rage yan vakin ciki wanda basu ci ba suka dinga cewa eh yace to naganeku nama kara musu 1 akasa dariya ya fice. Ai ana fita kowa yayo gunsu ai yasamu teacher ita dai amra dariya tai tayi suka fito ita da maryam dan tafiya gida yaya nasir tagani ta tambayeshi ina yaya Alin yace shine yace inxo inkaiki baze samu zuwaba takalli maryam ina zuwa tace tana matsawa suka shiga hurarsu irin ta masoya. Yau maryam bada mota tazo ba dan haka ita ce agaba Amra da kanwarta abaya anfara ta fiya maryam tace yayan ban fada ma tadan kallo mefa ai yau munyi lecture ta fada masa yadda amra tayi dadi ya cikashi ai daman kanwar tamu ba dama ce amra tai dariya yayar taku dai shima yai dariya sorry aunty suka saka dariya baki daya sai da yakai amra ya wuce kai maryam da kanwarta. Agida tunda Amra ta koma take baza ido taga Ali ya dawo dan masa albishir be dawo va tana kwalliya taji alamar dawowarsa da sauri ta fito dan murna batasan sanda ta fada jikinsa ba tana dariya tadan ja jikinsa yaya ban fada maka ba yakalleta alamar inaji munci aikinnan fa mune highest yana dariya kai anman na taya ku murna naso ina gunfa ta ce danma baka ganni ba nikaina nai mamakin yadda ha dake yasa dariya a'a amra banda yabon kai ta rufe fuska tana dariya. Haba mama yanxufa shekarata guda da aure anman baki taba zuwa gida na ba su khairi ma sau uku suka taba zuwa tana waya ne da ummanta mahaifiya can tace to shagwabarki ce zata sanya inzo ko me pls mama to shikeban zanyi tunani tasa kara yeeee to yaushe zaku zo kinga inkika isheni Allah zan fasa sorry tace suka koma wata firar . Azahurin gaskiya itama maman tanasan zuwa gidan yar tata sai dai alkunya irin tata tanaima mami alkunya dan tasani tanasan amra ta riketa kamar diyarta karshe ma ta baima danta ita wanda duk yayanta kowa yasan tafi san Ali shi yasa akulun take danne zucitarta wajan barma mami matsayin uwa ga Amran. Amra ce kwance kan doguwar kujerar dake falon tana bacci bama tasan sanda ya dauketa ba yayan nata take jira ya dawo da yake yau har six tana sch gashi tun eight ta futa tana dawowa ta dora girki agajiye take sosai hakan yasa bacci ya kwashe ta. Koda Ali ya dawo ya buga abata bude kofar falonba dan daman nan take kullewa harabar gidan da me gadi sai yasa makulli ya bude ya shigo zatonsa tana kitchen tunda yasa sulaiman ya daukota ya duba kitchen be ganta ba ya duba dakinta bata nan be kula da ita akwance ba yace towo ko sulaiman be daukota bane yayo falo dayake kujerar datake tana kallon dakinta yana fitowa idonsa ya dora akanta ya subhanallah ya fada ya matso daf da ita ya zuba mata ido ahankula yake yaye mata gashin da ya rufe mata fuska sai yau yaima yarinyar kallo na tsaf aransa yace lallai yakuma yadda Amransa me kyauce ahankula take bude idonta suka hada ido yasakar mata murmushi gami da daga gira tai saurin mikewa yadan rukota besan sanda hakinsa ya Furta *I Love You Amra* tai saurin kwace hannunta tai daki shidai anan yatsaya kamar sanda itako kunya ce ta rufeta ta kasa fitowa tunawa datai be ci abinci ba yasa ta daure ta fito. Yana kwance idonsa arufe tadan tabashi yaya abinci ya bude idonsa na koshi yace tai saurin kallonsa pls yaya dakyar tasa yasakko ya fara ci yadan kalleta duk atakure take aransa yace lallai inada sauran aiki sai na cirema yarinyar nan kunya. Sun dan taba fira kowa yai dakinsa Amra kasa bacci tai duniya tai mata dadi yau ita ce yayanta yace yanasanta jitake kamar ba ita ba. Mukli duk abubuwa sun hadu sun cabe mata inta kira Ali baya dagawa intai masa message sai dai ya turo mata am busy zan turo miki amsa anjima gashi gobe hutunta zai kare ji take kamar karta koma malay dinnan dakyar aka sha kanta ta yadda zata koma dan sauran semister daya ta gama ta dawo. Zaune take ita da kawarta Aisha cikin kuka take mgnar yanxu Aisha babu abinda zaki iya mun ko shawara inaji ina kallo wata zata kwacen masoyi tai danyi shuru ai matsalar go be zaki tafi ki bari in kin dawo tunda watanni ya rage ki kammaka akwai wani malan se muje Allah ko kedai Allah ya dawo dake lpy suka tafa suna dariya. Kinsanme ki kirashi dole sekina hadawa da kissina musanman ai kinga ita bama santa yake ba bakiga randa mukaje dakeba baya baya suke babu wata alamar shakuwa tsakaninsu takirashi yafi sau biyar yaki dauka ta mika mata tata wayar kirashi da tawa bugu daya da yake besan number dinba ya daga cikin yanga da jan hankali take mgn ina wani abu yace kafin ya kashe tasa kuka shi kuma inda abinda ya tsana yaga mace na kuka. Amra ce dauke da kayan Ali data wanke iya kayan ciki tun zuwanta ta dauki wannan hidimar dakinsa tai tana turawa ta jiyoshi yana fadin haba Mukli kinsan ba haka bane pls ki dena kuka bana so kina dagan hankali bata karasa jin mexai ceba tai waje. Dakinta ta shige tasha kuka wato yanasanta da yace karyane yaudara ce yanacan yana soyewa da masoyiyarsa haba shiyasa kullun se suna fira me dadi yace taje ta kwanta sch wani kukan ya kuma kwace mata. Tanajinsa ya bugun kofar tai mai banza yagaji yai dakinsa zatonsa ko tai bacci yana tafiya ta saki tsaki lallaima namiji dan rainin hankali ne ta fada ya maida ita me kenan abu buwa da dama zuciyar ke kitsa mata afusace ta mike danyin dakinsa bagaji tace dole kasakeni yau ka auro muklin inyaso kazauna da ita...... *Ummulsulaym* 09039729270 *F.A Ya'u* 09028287218 *For comments only* *Word can't express how Appie we are for ur cooperation fans sai dai muce mun gode mun gode Allah ya qara xumunci ameen Luv yah so much😘😘😘* .⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ ⚜⚜⚜⚜ ⚜⚜ *AMRATU* *Page 80-85* *Na* *Ummulsulaym* *Da* *F.A Ya'u* *Short and brief story* *Dedicated To Salma Ali Wada* Ta dan jima abakin kofar ta tura zata shiga kuma wata zuciyar ta haneta ta juyo ta dawo tuwa datai da mami da alkawarin data daukar mata yasata fasa kudirin nata ta koma ta kwanta. Gabaki daya haushinsa take ji zuciyarta kawai ta daure ta ci gaba da zama dashi dan ita irin matan nan ce masu kishin tsiya. Wani abu da ya kara bata haushi dashi shine dasafe da ta tashi sai ganin takarda tayi ya aje mata ni na fita nazo baki bude daki ba sulaiman zai zo ya kaiki sch tsaki taja gami da goge hawayen da ya kawo mata wato shi ko ajikinsa watakil ma gurin budurwar tasa ya tafi ko girki batai ba balle shafa mai hijabi kawai tasa tai farfajiyar gidan tana jiran sulaiman din. Ko da ta dawo nanma bata wani yi girki ba snacks kawai ta ci ta kora da madara me sanyi tai kwanciyar ta sai tara ya dawo sallamarsa kawai ta amsa itama a makoshi dan ta zama wajibi ne da bazata amsa ba yadan kalleta na tsawon sakanni kafin yai dakinsa sai da yai wanka ya sako jallabiya fara tas yana zuba kamshi kafin yazo kujerar dake daf da ita ya zauna gami da fadin wash wallahi yinwa nakeji bata ko kalleshi ba balle ta nuna tasan me yake yaga da alama baxata kawo abincin ba yace kawon abincina ban girka ba tace what yace tadago da niyar yimasa rashin mutuncin data tanada sai duk ya mata kwarjini a ido sai ta kasa ta koma ta rufe idon ta kawai mikewa yai yai kitchen indomie ya dafa ya dauko lemo me sanyi yayo falon tana inda ya barta ya dire kwanon sauko muci to tinda baki dafa ba nasan kinajin yunwa ta turo baki na koshi ai baki isaba ni harke na dafa wallahi sai kinci nifa na koshi nace ma kinga na rifa na rantse sauko malama tai banza dashi yakai loma biyu bakinsa wai bazaki sauko ba nace ta mike tai hanyar dakinta dasauri ya mike ya bi bayanta bata ankaraba akai sama da ita agaban kanon ya direta kanta ce wani abu ya tura mata taliyar baki ya rike lebbanta biyu hadiye nace tana hawaye ta hadiye yawwa na karya rantsuwata kya iya tafiya ta mike sai da tai kusa da dakinta ta burtsota wace mugu kawai kuma ban hadiye ba ta banko kofarta yai dariya Amra rikici kenan ya ci gaba da cin abincinsa. Washe gari asabar ya tashi yadda ya kwanta haka gidan yake ba abinda tai agidan yarasa wace irin yarinya ce Amra kamar me aljanu intana wani abin kamar ba ita ba haka ya gyare ko ina yasha tea yai farfajiyar gidan tanajin ya fice ta fito tai kitchen dan yunwa takeji sosai gashi tana tsoronsa abinda tai masa jiya waina ta soya sai tea data hada me kauri tai dakinta. Tana zaune suna waya da mami ya shigo dariya take sosai tana ganinsa tai kicin kicin da ranta bai nuna yasan tanai ba ya danna tashar da yakamo ta mike tai dakinta. Sai da ta gama wayar ta fito ta ajiye masa abincinsa agabansa bata ce masa uffanba shima baiko kalli flask dinba duda yunwa yakeji ya cigaba da kallonsa lokaci lokaci take kallansa taga ko zai ci abinci sai taga ko kallon be isheshi ba haushi duk ya cikata can ya mike yai dakinsa takaici kamar ya kasheta ta mike tai dakinta sai da tai sallah zata kwanta taga bata kyauta ba ta daure duda zuciyarta ba dadi tai dakinsa akulle yake bugun farko yace waye ta kuma mai maitawa waye ma lallai mutumin nan to dashi da waye agidan kamar ta juya tadai daure daman cema zanyi Abincinka ok na koshi kya iya tafiya iya wuya tazo tai daki. Shiko daman jira yake ta kwanta ko batazo ba zai ci abincinsa sai da ya dai daici tayi bacci ya fito yana sanda sama sama ya yada duk dan karta gane yaci yafiskanci sai yanayi yana rama abinda take masa zasu zauna kalau shi ya mance abinda yai ta mata ahankula yake tafiya karaf sukai karo ta fito daga kitchen kawai sai ya maze yai dakinsa yadda yai duk ya bata dariya tasaki dariya ya juyo ya kalleta yadda take dariya ya bashi haushi kawai ya dawo ya suri flask din yai dakinsa tunda ta ganshi meye na cin kadan ya fada aransa.... Da safe tai wankanta tsaf tai kyau tana zaune ya shigo ta sauko ba kamar jiya ba ta gaidashi tace Karin safe fa yadan hade rai na koshi tai dariya to bari naje daki ko adan diba akai daki shima dariyar yai bai ce komi ba yai gun dinning sai da ya gama karyawa yace da ita ki shirya anjima zamuje unguwa ina zamu Aisha ce ta haihu ni ba inda zani kinaso inkin haihu ke ma kar azo miki ko kunya duk ta rufeta tace cab wace zata haihun kemana ko bakisan haifon baby tai masa shuru daf da ita ya matso har tanajin nunfashinsa ya ruke mata hannu fadan Amra kina sona tai shiru naji ko bakya sona ki daure ki haifan baby kinji Amratuna ki kuma soshi ta daga ido takalleshi kin yadda zaki haifon baby batasan sa'adda bakinta yace ta yaya na baro ta ce kan yace wani abu ta kwace hannunta gami da yin dakinta shiko kasa motsawa yai yafi minti biyar ahaka kafin ya mike yai dakinsa yaso ta tsaya da yabata amsa anman bakomai ya fada gami dayin kwafa. Wai bazaki shirya ba nifa nace bazani ba to aishikenan kinma kanki daman har gidan Mami zamu yima dady sannu da zuwa da kuma sabuwar kofa yai ficewarsa dasauri tabi bayansa ina har ya fice ta doki goshinta kai anmanfa na kwafsa. Yana kwance akan doguwar kujera yana jiyo takunta ya rufe ido kamar me bacci tazo daf dashi tana tabashi pls yaya katashi na shirya yai kamar be jita ba bata ankara ba ya jawota jikinsa ta kwalla kara yai saurin sakinta mene haka katshi mutafi na shirya ni kuma vazani ba ta durkusa pls my yaya ya juyar da kai wato ke inkinasan abu kin iya ladabi ko tamai shiru to naji zamuje da sharadi ta zaro ido sharadi ya kada kai yes..... Ta waro ido what sharadi yai dariya eh ko bazaki iya bane abar fitar tadan rausayar da ido yazanyi inajinka indai kinga mun fita sai kinmin kiss kai yaya kai yaya zafakiyi lefi nace kidena yayan nan kinqi ko sorry hubbi anman dai abar kiss dinnan ya turo baki irin yadda take to shikenan sai musha zaman mu ta fakaiceshi ta bashi hot kiss tai daki tana dariya shima ya dafe gurin yana dariya yabi bayanta. To kuma maye na komawa daki sai ki fito mutafi ta mike tabi bayansa agidan mami suka rashe suka sha fira sai wajen goma suka taso. Wata kulawa ta musanman Ali ke baima Amra wadda hakan ya samar da shakuwa tamusanman tsakaninsu in tazauna ba abinda take tunani sai alinta sai yanxu take fahintar lallai da ita ba ma san Ali take ba sai yanxu da duk minti daya sai ta tunashi inbe dawo da wuri ba sai taji gabaki daya duniyar ta mata duhu. Zaune suke yana kowa da abinda yame yadan daga ido ya kalleta kafun ya kira sunanta ta amsa murya akasa yace mgn nakesan muyi ta ajiye littafin ta fiskance shi sosai Amra ni waye dinki tadan kalleshi sukayi sa'ar hada ido ya kada mata kai alamar go a head tace Yah na bacin wannan fa tai shiru ok ni mijinki ne ko ba haka bane tai shiru ya taso dab da ita haba amra nasan kinsan ni mijinki ne kuma nasan kinsan hakkin kowane miji kan matarsa amman kin take amra kiji tausayi na ta kalleshi da mamaki kamar zatai mgn ta fasa. Yah ga abincin yai kamar bejita ba ya cigaba da abinda yake taje dab dashi ta dauke system din ya hade rai kai kanwis wannan wane irin abune sai ynx ta gano lefinta ayi haƙuri bazan kuma kima kuma ɗin nafuskanci saina fara doke bakin tai dariya kawai. Iya kyau tayi kyau zaune take tana rubuta assigment ɗinta ya hankalinta gabaki ɗaya nakan littafinta har yashigo bataji ba pink ɗin dogowar riga ce jikinta sai gashinta da yayo baya ba ɗanƙwali kanta duda baiga fuskarta ba sai ta burgeshi yaɗan jima yana kallonta kafin yasake sallama ta amsa ahankula atare damai sannu da zuwa batare data ɗago ba sanin halinta yasa baiko damu da rashin ɗagowarba yai ɗakinsa sanye yake da doguwar riga mara nauyi yazo gabanta ya zauna kamshin turarensa ya daki hancinta tai saurin ɗagowa yai sa'a sukai ido cikin ido yasakar mata murmushi itama tai ɗan murmushi ƙanwis me akene aikine ta miƙe ina zuwa ya bita da kallo wani abu ya tsirgama ransa baisan ma ta dawoba tace yah ga abinci yai saurin cewa cika ladanki zubamin ta zuba tabashi ta cigaba da aikinta. Tunda yakwanta yake juyi ina bazai yiwuba ya faɗa gami da miƙewa ɗakin amra ya nufa danshi yaukam yagaji yai sa'a ƙofar abuɗe take yamurɗa yashiga tana kwance da alamu tanajin daɗin baccinta yajima yana kallonta baisan sanda ya sunkuwa yana gyara mt sumar kanta ba tai firgigit ta farka ganinsa yaƙara bata tsoro cool down my amra nutsu ba wani abin zan miki ba ta gyaɗa kaifuskarta na nuna alamar tsoro yaɗan zauna daf da ita kafin yace amra ni waye agunki tace yah na yaɗan haɗe rai bayan wannan tace babu yayi kƴau to me kike agidannan tace aure to waye mijin tace babu yaɗan kalleta da alamun gaske take yaɗan miƙe yai taku biyu zuwa uku kafin yafara mgn intaƙai ce muku wannaan dare dai yazamanto musu daren farinciki musanmam Ali yaita shima amra albarka kwance take tana bacci yana kallonta santa naƙara cika masa rai ji yake duniya bawanda yafishi sa'a ashe shi da soyai ya cuci kansa. Su Amra na level 3 cikinta ya tsufa haihuwa saura wata guda mukli ta dawo 9ja cike da murna kammala masters ɗinta sai dai abu guda da yafara bata tsoro shine kiran duniya taima wayar Ali sai ya rejecting ƙarshema sai yasata a black list hakan yasa bayanta huta tai gidansa ranar asabar. Tsaye take yaɗan sunkuya kasan cikinta shilallai hira suke da baby tana ta dariya ya dago shima yana dariya yajawo ta jikinsa inda yai dai dai da shigowar mukli gidan idonta karaf kansu dagyar ta iya saita kanta ta faka motar ko rufeta batai ba ta fito hawaye ɗaya nabin daya Ali ta faɗa baima jiba amra ta ankarar dashi ya juya lpy ya faɗa without showing any care nace lpy haba Ali amana vatace haka ba wace irin amana ban taɓa zaton zaka ci amanata ba shiii yace ke kina da bakin cewa naci amarki lokacin da kika tsallakeni kika tafi ai bamuyi Bazan aure ba kinga ni kizo kibarmin gida kuma pls karki sake zuwa kinaji na ko what Ali ni kake kora kan wannan banzar kwailar matar taKa kafin ta karasa ya bata mari ahir kul kika zo matagida kika zageta kike kiranta banza to bara kiji tafiye minke sai dubu wallahi daman dacan tsautsayi yasani rakito ki Ali ni ka mara kan wannan abar an marekin ko zaki rama kai bazan rama kankava tasa hannu ta share amra da mari aiko yahauta da duka dakƴar amra ta jashi ciki yanata hucu kamar wani kumurci mukli taja jikinta tavar gidan ba abinda yabata haushi fuye da ganin amra da ciki tai kuka me isarta kishi ya cikata. Ummanta ta kirata babsnki yace ki fidda miji yagaji da ganinki to kawai tace ranta na mata zafi tai ɗakinta wayarta ta ɗauka ta kira kawarta ba'ajima ba tazo ta faɗa mata komai tana kuka tasa dariya kinji kitsaya kina kuka kan namiji kizo inkai gun wani boka aikinsa kamar yankan wuƙa taja tsaki haba besty ke yanxu kirasa wace shawara zaki ban saita boka kibarni da lefukan danai basai na haɗa da shirka ba to kuwa kice bazaki auri abinda kike so ba eh wallahi na hakura yanzu inna aureshi a duniya ta shirka munyi rayuwar duniya tare alahira na shiga wuta mene anfanin hakan daman Allah yai ba miji na bane to kinsan haka kike damun kanki ai dolena nadamu kaina I love him alot sansa a jini na yake nasan har inmutu bazan dena sansa ba wlh. Dake nake mgn kufito da miji inba haka ba inzaɓamiki idonta jiƙe da hawaye ta ɗago su cikin kuka take mgn dady bani da wanda zan fito dashi daman Ali nakeso kuma shi zan cigaba daso sai dai lokacin da nakawoshi kun ce karatu dady nayi karatun gashibemin anfanin komi ba dady ka auran karatun yai kanta zai daka momy ta riƙeshi a'a Alhaji lefinmu ne tun asali yarinyar nan ta nuna aure take so ta kawo miji mukace karatu danmene yanzu dan bata kawo wani ba zamu daketa wato kinbi bayanɗiyar ki ko No Alhaji ba haka bane kawai dai gaskiya ce to naji zan kawo mt mijin taɗago dady ko waye zan aura anman dady bazan taɓa sansa ba san Ali shi zai kasheni nassni. Yau tunda amra ta tashi takejin jikinta ba daɗi daurewa take kawai Ali yaɗan fiskance ta bayan ta zuba ms abinci tai ɗaki jikinsa yabashi wani abu yabi bayanta aikuwa murkususu take tayi ya kwasheta sai asibiti hankalinsa atashe gani yake kamar mutuwa zatai cikin ikon Allah ta haifo ɗiyarta me kama da babanta murna gunsa kamar me kankace me duk ya bugama yan uwa waya asibiti ya cika maƙil To her suprise sunan ummanta ta asali yasama ɗiyar kowa yai murna ran suna aka sha taro Ummi na wata tara suna level 4 akasha bikin. Maryam Da yaya sulaiman biki iya biki lokacin amra nada ƙaramin ciki dan kwanika take ita ce ƙirjin biki bikin babbar ƙawa kanwa ga ango duda yanzu tazama yaya tunda tana auren yayan ango bikine iya biki amra ansha hidima. Duniya kenan kamar ba yau su amra suka fara bayero ba ya yau take ranar yayesu wato ranal convocation ɗinsu tunda suka tawo amota take tunawa da abubuwa da dama kamar ranar mstriculation ɗinsu ta shigo ita ɗaya yau zata barta tana da yara biyu da ciki hawayene suka gangaro mata yanzufa yadda ta kanmala sch ta barta haka zata kanmala rayuwarta ta duniya ta barta jitai ana goge mata hawaye Allah zamu koma yauce fa ranar murna ɗinki kuma sai ki dinga ma mutane kuka tai ɗan murmushi ayi hakuri. Tabbas amra tai murna duda batasan rabuwa da abokan arziƙi cikin yan department ɗinsu ta physics su ashirin da uku sukaƴi graduation su biyu keda first class ita da wani sai maryam da mutun takwas keda second class upper Shikansa Ali yai murna ganin yadda aka karrama abar santasa. Kasantuwar ta fita da first class bata shawuyar saminaiki ba shekarar ta biyu da farawa ta koma karatu lokacin tana da yara biyar tai masters ɗinta tana lecturing a faculty of scieces department of physic buk kankace me tai suna ɗalibai kowa nasanta kowacce ɗaba sai kaji tace her mentor was Amrat bata jima da yin phd ɗinta ba wato doctoring degree kasantuwar ta me yawan rubutu da bada gudunmawa fannin ilili musanma kan abinda ta karanta buk suka bata prof kankace me duk nageria kai africa naji da ita musanman gudunmawarta wajen tallafama mata da matasa suyi illimi. Amra na zaune tana duba wasu takardu duk yaran basanan ya shigo kamar yadda yasaba inyasan tsokana tace sannu da zuwa yawwa Robert hook ko brown zance ne kai yaya kai yaya what kikace yaya tasa dariya sorry babban yaya yabita dasauri tai ɗaki kaifa baka girma ya banko ƙofar au haka kika ce yana dariya . Nidai banbi su ɗakin ba Anan nake cewa Amra da Ali Allah ya taɗorar daku cikin wannan farin cikin Madadin ummu sulymn da ta tallafamin wajen rubuta wannan labari dani da mukayi tare natabbatar ankammala muke gode muku da karantawa fatan kuskuren da ke ciki za'ayi afuwa *_For comment_* 09028287218 09039729270 *_Note_* Whatsapp only Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels