Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels [26/11/2021, 18:57] Ameera Adam🌚: 36... Fulani Maryama turɓune fuska tayi dan ba ƙaramin haushin Jakadiya ta ji ba, gani take kamar raini ya fara shiga tsakaninsu dan haka ta ƙara ɓata fuska ta ce, "Jakadiya hawainiyarki ta kiyayi rama ta. Kar tarayyarmu da ke ta fara kaimu ga raini ki iya bakinki idan ba haka ba wallahi zan yi maganinki" Jakadiya ta saki hanci da baki tana ƙarewa Hallitar Fulani Maryama kallo dan ba ƙaramin muni tayi ba ga ranƙwalelen goshi kamar jirgi ya doso tasha ga fala-falan kunnuwa, cikin zuciyarta take mamakin yadda akayi Sarki Aminullah ya zaɓo Fulani Maryama a matsayin mata, matar tashi ma ta fari. Ganin kallon ya yi yawa yasa Fulani Maryama ta ɗan tsargu ta ce, "Lafiya kika kafe ni da idanu kamar kinga sabuwar hallita?" Jakadiya ta ce, "Yooo to Maryama me ya yi saura kuma ni da ke fa kar ta san kar ne, kinsan sirrina nasan naki babu wani isa da mallaka da zaki iya nuna mini yanzu, mu ci gaba da harkokinmu dan mu nemarwa kanmu mafita ina ganin zai fi, dan wallahi nikam na gaji da murmusasshen kannan nawa." Fulani Maryama kasaƙe tayi tana nazarin maganganun Jakadiya tabbas maganarta a hanya take amma wannan rashin bada girman da take mata yana baƙanta mata rai. Fuska ba walwala ta kalli Jakadiya ta ce, "Amma idan kina yi mini haka kina ganin mutane ba za su sa mana ido ba? Kinsan fa gidan nan komai kake yi ana ankare da kai. Matsawar kina yi mini haka wallahi za'a ɗora zarge-zarge akanmu, gara ma tun wuri ki sake tsari kuma ai koda girgiza kurna tafi magarya duk lalacewa dai ni matar Sarki ce ke kuma Jakadiya, kin ga kuwa babba, babba ne ko a gidan giya." Jakadiya da ta gaji ta zantukan Fulani Maryama a ƙagauce ta ce, "To naji amma dai ki nemo mana mafita wlh duk na shiga damuwa." Fulani Maryama ta ce, "Jakadiya bake kaɗai ba. Na ɗauka tafiyar yarinyar nan zai zame mini samun sauƙin lamura amma kina gani yadda lamarin yake kasance mana, ko dai zamu koma wurin marduska mu sanar da shi halin da muke ciki." Jakadiya ta miƙe ƙafafuwa ta ce, "Ai ni na kwana na hantse da tunanin wannan a zuciyata abin da ya fi kenan, dan Allah ya sani ba ƙaramin bankaɗar albarka ya yi mana ba" Fulani Maryama ta amsa mata sannan suka ci gaba da jajantawa a tsakaninsu. Tsaye take a gaban mudubi tana ƙara feshe jikinta da daɗaɗan turararrika, ita kanta ta ya ba da irin kwalliyar ta da tayi hawaye ne ya ciko idanunta nan take taji zuciyarta tayi rauni tana jin tausayinta, a hankali ta fara takawa zuwa runfar ɗakinta. Jakadiya ce ta shiga ta russuna cikin girmamawa ta ce, "Allah ya taimakeki an riga da annemar miki iso wajen Takawa a kowanne lokaci yana tsammanin zuwan ki." Fulani Zaliha ta gyaɗa kai sannan ta ce, "Ina godiya Jakadiya idan Allah ya kaimu safiya ki aiko a karɓar miki alkaki da zuma." Jakadiya zube wa ta yi tana godiya, "Godiya nake sarauniyar mata mai babbar fada a fadar Mai martaba, tauraruwar taurari a cikin dubbannin mata kece zarah. Ƴar Sarki jikar saki, Matar sarki kuma da yardar Allah ke zaki zama uwar sarki." Jakadiya ta dakata da bambaɗancinta tana jan ɗankwalinta gaba da yake niyyar sulluɓewa ta ci gaba da cewa, "Madara kike ko jaririn goye ya lasa sai ya ƙara lasa, Allah ya tsare mana Yarima Saif ya ƙara masa lafiya, Takawarki lafiya farincikin Takawa duk kin dakushe su zinariya..." Fulani Zaliha ta katse Jakadiya da cewa, "Jakadiya muna godiya a turo gobe a karɓi saƙon" Tana gama faɗa ta miƙe ta wuce ɗakinta. Jakadiya taɓe baki tayi tana binta da harara cikin zuciyarta ta ce, "Wannan yarinya anyi me baƙin halin tsiya. Ita ƴar hirar nan ma bata yarda ayi da ita, ita kenan kullin a ɗaki kamar munafuka." Tana tafe kuyangunta suna take mata baya har ta ƙarasa turakar Sarki Aminullah, tana zuwa ta sallame su sannan ta ɗan zura ƙafarta ɗaya tana jin wata irin faɗuwar gaba. Ji tayi ya yi gyaran murya da alamar yaji motsin mutum a bakin ƙofar, shiga ta yi bakinta ɗauke da sallama ta nemi kan lallausar dadduma ta zauna cikin girmamawa ta gaishe shi, "Barka da hutawa Ranka ya daɗe." Kafeta ya yi da kallo yana jin kewar matarsa, cikin zuciyarsa yake faɗin, "Na rasa me yasa nake jin Zaliha na da wani irin matsayi a zuciyata? Idan aka cire laifin turen kisa da tasa ayi mini bana jin akwai wani laifin da zan iya kamata da shi." Jin ya yi shiru ya sa Zaliha ta ƙara kallonsa tana cewa, "Ina fatan na same ka lafiya?" Sarki Aminullah ya sauke ajiyar zuciya yace, "Zaliha yau kece a gari? Yaushe rabonki da nan?" murmushi ta ƙirƙiro ta ce, "Allah ya taimakeka dama wata magana na ɗan ji ana ta raɗeraɗin ta." Shima murmushi ya yi ya lura har lokacin tana fushi da shi batasan maganar da ya yi mata, a zuciyarsa ya furta, "Mata kenan! Su dai tunaninsu daban yake. Wannan shi ne a dake ka a hanaka kuka. Ni da aka yi wa laifi kuma ni ake fushi da ni." Tashi ya yi daga kishingiɗen da yake yace, "Wacce magana ce Zaliha?" Fulani Zaliha ta ce, "Na ji ana ta raɗeraɗin wai yarinya da Maleek ya tafi da ita ba matarsa bace hasalima ance bata taɓa aure ba." Ba ƙaramin mamaki Maleek ya yi ba saboda ganin fitowar Takawa kaɗai ya isa ya tabbatar masa da lallai akwai ƙamshin gaskiya a tattare da maganar Sulaiman, cikin mamaki ya furta. "Ya ilahi wai me yake faruwa da masarautar nan ne? Ina na taɓa jin matacce ya tashi anya ba aljanu ne suke san yin wasa da hankulan al'umma ba kuwa?" A hanzarce ya ƙarasa wajen wanda ya yi dai-dai da ƙarasawar Sarki Abdallah, kutsawa ya dinga yi har ya shiga cen gaba-gaba. A zaune ya hangota tana sauke numfashi sama-sama da alama a wahalce take, waro idanunsa waje ya yi yana kallon ikon Allah, Mai babban ɗaki ya gani zaune a gabansa matar da ta shafe sama da shekara ashirin da rasuwa. Yana nan tsaye ta ɗago da kanta suna haɗa ido ta miƙa masa hannu tana cewa, " Wannan kamar Audul Maleek? Ashe zan ƙara ganinku a rayuwata?" gabansa ne ya yi mummunan faɗuwa yawun bakinsa na neman ƙafewa. Takawa ne ya ƙaraso wajen gabaɗaya matsawa suka yi suka bashi wuri, kallanta yake sosai yana jin wani yanayi a ransa, yana san ya yi mata yana fargabar kaidin magauta kar su yi amfani da wannan damar su halakar da shi. Wani tunani ya yi ya kalli Dogarawan wajen yace, "Ku ɗauke ta ku kaita ɗakin baya, a kira mini su Malam Liman yanzun nan." Kallan kallo suka fara yi a taakaninsu kowa ya daƙire yana tsoron tafiya. Jin muryarsa yasa Mai babban ɗaki ta ɗago da kai ta kalli Sarki Abdallah ta ce, "Audullahi baka yi murna da gani na bane? Nice fa kasan waye ya mayar dani haka? Matarka ita ta cutar dani na tsawon shekaru wata yarinya ce ta kuɓuto dani ta ce mini sunanta Muhaibish" Tari ta yi tana kare bakinta da busasshen hannunta mai tsananin dauɗa ta ci gaba da cewa, "Tsakanina da Matarka sai dai Allah ya isa, kuma umarni nake baka kayi mata saki uku rass idan ba haka ba wallahi sai na tsine maka" Gaban Sarki Abdallah ne ya faɗi musamman da yaji ta ambaci sunan Muhaibish, azuciyarsa yake maimaita sunan sannan yake ayyana anya ba aljanu ne suke neman wasa da hankulansu ba, kallan Dogarawan ya yi a ɗan fusace ya buga musu yace, "Ina magana kuna tsaye" Jiki na rawa suka fara kinkimarta suka wuce da ita cen ɗakin baya. Sarki Abdallah ya juya zai koma ciki saura kaɗan ya yi tuntuɓe da Hansatu matar Waziri tana kuka da birgima a gabansa tana cewa, "Wayyo ni wayyo gata na ya ƙare shikenan rayuwarmu ta zo ƙarshe Takawa, shikenan sun kashe mini shi ɗazu-ɗazu muka gama fita da shi amma wai babu shi sun kashe kai jama'a wallahi Allah ya isa tsakaninmu da duk wanda ya yi masa wannan mugun abun." Wani Dogari ne ya buga mata tsawa yana shirin magana Takawa ya dakatar da shi ya kalli Hansatu yace, "Me yake faruwa Hansatu?" Hansatu ta goge hawayenta da gefen rigarta cikin kuka ta fara magana, "Allah ya taimake ka lafiya ƙalau muna zaune muna hira da Babansu Rafi'u kawai sai ji nayi yana cewa ƙafarsa kamar almara haka naga jini na tsartuwa ta tsakankanin ƙafafuwansa, daga haka naji yana cewa Muhaibish ta gafarce shi ruɗin zuciya ne amma ta bashi dama zai gyara kuskurenshi, daga haka bai ƙara magana ba sai gani nayi bakinsa na talewa kafin wani lokaci anɓare bakinsa kamar na yankakkiyar tinkiya, wannan ban da aikin asiri ya za'ayi haka ta faru?" Tana gama faɗa ta sake rushewa da kuka tana buga ƙasa. Sarki Abdallah ji ya yi kansa ya yi nauyi duk dakiya irin tashi sai da ƙwallah ta zubo masa, cikin tausaya ya kalli wasu Bayi mata yace, "Ku ƙarasa gida da ita ku kwantar mata da hankali" Tun bai rufe baki ba suka ƙarasa wurin Hansatu suka kamata suka wuce da ita, har zuwa lokacin kuka take me tsuma zuciya. Kallan wani dogarinsa ya yi yace, "Aje a samu Galadima suyi masa sutura idan ankammala ayi mini magana." Yana gama magana ya fara takawa a hankali kamar Kazar da ƙwai ya fashewa a ciki. Maleek daskarewa ya yi a wuri shima a hankali ya fara takawa ya wuce har ya nufi hanyar sashensu ya tuna da masallaci zashi wanda tuni har an idar da sallahr yana tsaye ganin al'ajabi. Fulani Babba ban da zarya babu abin da take yi a tsakiyar ɗakinta sakamakon mugun labarin da ya iso mata, wanda ba ta taɓa tsammanin makamancinsa ba ko a mafarkinta. A fili ta furta, "Anya wannan Shukran da na sani ce? Me yasa zuwanta ya zame mini masifa da bayyanar al'amurana, tabbas akwai wani ɓoyayyan al'amari a game da ita koma menene dole na dakatar da ita kota halin ƙaƙa." Wani abu taji yana ɗan yi mata yawo a jiki da sauri ta kai hannu tana ƙoƙarin cire shi amma babu komai, haka taji ya fara mamaye jikinta ta ko'ina kamar tafiyar ƙadangare. Tun tana daga zaune harta miƙe tsaye tana karkaɗe-karkaɗe, kamar saukar aradu haka ta ji muryar wani Dattijo yana cewa, "Kin karya mana alƙawari karki zargi kowa game da abin da zai biyo bayanki idan kin tuna da yarjejeniyarmu a shekarun baya da suka wuce." Shiru taji kamar anyi ruwan sama an ɗauke haka taji mai maganar ya yi ɗiff komai ya ɗauke, daga ƙasanta ji ta yi kamar abu na zuba tana dubawa ta ga wani farin ruwa na ɗan tsiyaya me wari-wari. Tana nan tsaye ta ji wannan tafiyar ƙadangaren tana ci gaba da yi a jikinta ga fatar jikinta na mata wani irin tauna kamar ana yagar naman jikinta, cikin fitar hayyaci ta fice a guje tana kururuwar neman taimako. Bayinta da suka ga haka suma suka rufa mata baya suna ƙoƙarin kamota dan gudu take kanta ba dankwali ga zanin jikinta ta fara yagewa tana cewa, "Wace ce ke da zaki dagula mini lissafi?" Cak ta tsaya waje ɗaya tana ja da baya sai kuma ta ce, "Kika ce sunanki Muhaibish? Ba ke ce Shukura ba?" Zubawa ta ƙara yi a guje kamar zautacciya tana cewa, " Dan Allah ki yi haƙuri Shukura wallahi kuskure ne na tuba ki yafe ni, wayyo Allahna!" Tana faɗar haka tana ƙoƙarin tsige zanin jikinta har ta nufi fadar Sarki Abdallah daga ita sai fatarinta tana ƙoƙarin yage rigar jikinta. Sarki Aminullahi shiru ya yi yana nazari saboda shi kansa tun da su Maleek suka tafi da yarinyar kullin sai ya yi mafarki da ita kala-kala, mafarkai yake ba fasali shi kaɗai ƴan kwanakin nan ban da tunaninta babu abin da yake yi. Har mamaki yake akan me zai zauna yana tunani akanta bayan babu wani abu da ya haɗa da ita, sautari mafi yawan mafarkinsa yana mafarki yana cikin hatsari tana ƙoƙarin cetonsa. Sai dai duka mafarkinsa zai yi tare da Salman da ita amma Salman na ƙoƙarin cutar da shi ita tana yunƙurin ceton sa. Numfasawa ya yi kalli Fulani Zaliha da ta zuba masa idanu yace, "Zaliha kin san dai baza mu aikata abin da ba haka yake ba kuma idan ance haka yana nufin mun aikata haramci kenan?" Fulani Zaliha ta ce, "Allah ya huci zuciyarka a dai duba tambayata, ko a mafarki bana tunanin zaka iya aikata makamancin haka sai dai ko a cikin halin rashin sani, Allah ya baka yawan rai a bincika da kyau ina fatan ban ɓata maka rai ba" Shiru Sarki Aminullah ya yi yace, "Shikenan! Amma bama tunanin haka zata iya kasancewa tun da yarinyar da Mariƙiyarta sun amince. Amma zan kira Fahima naji halin halin da ake ciki." Ku kawo ɗauki Masarautar Adamawa tana cikin wani yanayi😂 _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [27/11/2021, 17:56] Ameera Adam🌚: 37... Fulani Babba na shiga fadar tun daga bakin ƙofa ta fara soshe-soshe tana ɗaga rigarta sama, a zabure Sarki Abdallah ya miƙe duk da kasancewar fadar babu mutane sosai bai fi mutum huɗu bane a ciki. Fulani Babba tunkarar Takawa ta fara yi tana cewa, "Dan Allah ka dakatar da ita zata kashe wallahi illatani take son yi, wayyo Allah jikina! Wayyo shukura zata kashe ni" tana nan tsaye Bayin ta suka shigo da gudu sai kuma suka yi carko-carko, Sarki Abdallah ya buga musu tsawa yana cewa, "Baku da hankali ne da kuna ganinta ba za ku iya mayar da ita cikin gida ba a wannan halin?" Da sauri suka matsa suna son kama Fulani Babba suna jin tsoro, dake wa kawai suka yi suka rirriƙeta suka fara kiciniyar wucewa da ita nan ta fara ihu tana faɗin, "Ku ƙyaleni na kaiwa mijina kuka shi kaɗai zai share mini hawaye na..." bata ƙarasa faɗa ba suka fice da ita. Sarki Abdallah komawa ya yi daɓass ya zauna ya dafe kansa yana nazari hankali a tashe, gabaɗaya baya cikin hayyacinsa saboda damuwa. Miƙe wa ya yi zai fice sai ga Dogarin da ya aika kiran Malam liman ya shiga yana cewa, "Allah ya taimakeka ya baka yawan rai Malam Liman yana cen ɗakin da aka kai Mai babban ɗaki" sai a lokacin ya tuno da aiken da ya yi bai iya tanka masa ba sai gyaɗa kai da ya yi sannan dogari ya fice daga fadar. Bayan wani lokaci jiki a sanyaye Sarki Abdallah ya fice zuwa ɗakin da Liman yake tare da rakiyar dogarawansa da suke take masa baya. Lokacin da ya shiga Malam Liman har ya gabatar da alwala ya fara yi wa Mai babban daƙi ruƙiyya, Sarki Abdallah gefe ɗaya ya ja ya zauna yana kallonsu, tana zaune cikin kojalallun kayanta jikinta futu-futu kamar wacce aka tono daga cikin rami. Malam Liman ya jima yana abu ɗaya sanann ya sallame ya kalli Sarki Abdallah ya ce, "Allah ya taimake ka ba na tunanin akwai shafar jinnu a jikin baiwar Allahr nan, sai dai tabbas akwai ɓoyayyan al'amari." Mai babban ɗaki ta ƙurawa Malam Liman ido ta ce, "Tabbas akwai ɓoyayyan al'amari domin kuwa matarsa ita ce silar shiga ta cikin wannan halin. Da saninta aka killace ni a kogon dutsen bokanta, na tabbata ba ta taɓa zaton haka za ta iya faruwa ba, ba ta yi tsammanin zan iya dawowa cikin ahalina ba" tana zuwa nan a zancenta ta rushe da kuka. Jikinsu ne ya yi sanyi Sarki Abdallah ya gyara zaman yace, "Amma sama da shekaru ashirin kenan da muka wayi gari da gawarki a ɗaki wannan lamari akwai rikitarwa." Mai babban ɗaki ta ce, "Idan kun tsaya kun fahimceni lamarin ba zai rikitar da ku ba, ka je ka duba matarka na san yanzu haka idan bata fara hauka da fisge-fisge ba tana kan hanya domin sharaɗin da bokanta ya gindaya mata kenan matuƙar na dawo masarautar nan" A firgice ya ɗago yana kallonta tabbas maganar da ta faɗa ta tabbata amma ya za a yi ace matacce ya tashi, gaskiya lamarin akwai rufa ido. Miƙe wa Sarki Abdallah ya yi yace, "Malam Liman anya lamarin nan babu shafar jinnu kuwa ina ganin rufa ido suke san yi mana" yana gama faɗa ya juya zai fice da sauri Malam Liman yace, "Allah ya taimake ka na tabbata ka san ƙur'ani zancen Allah ne, kuma idan har jinnu ne zasu bayyana kansu gaskiya ina ji a jiki akwai ƙamshin gaskiya a maganarta. Shi kansa a wannan lokacin ya fara gasgatawa amma abin da yake mamaki da shi ya za a yi matacce ya tashi, juyowa ya yi ya kalli dogarawan da ke tsaye yace, " A kira bayi mata su tafi da ita su gyara mata jikinta." yana gama faɗa ya fice daga ɗakin, bayan fitarsa Mai babban ɗaki ta fashe da kuka ta ɗago ta kalli Liman ta ce, "Wai yanzu ni Audullahi yake tuhuma da rashin gaskiya anya matar cen bata juya masa ƙwaƙwalwa ba?" Malam Liman cikin tausayawa ya fara lallashinta har tayi shiru babu jimawa Bayi suka ɗauketa suka tafi da ita. Da mamaki yake kallonta yana daɗa mamakin irin wannan ɗogon baccin da take yi kamar na rashin lafiya, bubbuga fulonta ya fara yi yana kiran sunanta jin ta yi shiru tana bacci lamarin da ya fara bashi tsoro. Hannu yasa ya fara ɗan dukan ƙafarta amma har wannan lokacin ko motsi bata yi ga kuma munshari nan tana yi kamar me bacci lakadan. Zama ya yi ya ɗago ta dukda yadda hannuwansa suke raɗaɗi, amma har lokacin bata buɗe ido ba, ruwa ya ɗebo ya fara yayyafa mata kamar wanda yake zubawa dutse haka ya ƙare zuba mata ruwa ba tare da ta motsa ba. Hankali a tashe ya nufi sashen mahaifiyarsa domin ya sanar da ita halin da ake ciki, yana zuwa ya samu ana ta kokawa da Fulani Babba ta yage kayan jikinta tsaf, sai wawurar mutane take tana kai musu cizo, Mahaifiyarsa ce da sauran matan mahaifinsa ne suke ta ƙoƙarin ganin sun tura Fulani Babba ɗaki sun rufe amma abin ya ci tura. A haukace take bin su tana cewa, "Wallahi shukura ko ni ko ke sai dai mu illata juna" tana faɗin haka tana yagar naman jikinta haɗe da kaiwa mutane warta. Maleek na zuwa ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba mantawa ya yi da tasa damuwar da yazo da ita, cikin dabara ya samu suka hankaɗata cikin ɗaki suka rufe kowa na mayar da ajiyar zuciya. Maleek na shirin jan mahaifiyarsa domin ya tambayeta abin da yake faruwa, daga cen filin Masarautar suka ji iface-iface da koke-koken mutane wasu daga ciki suna guje-guje, ban da kururuwar mutane babu abin da yake tashi a wajen. Gaɓaɗaya suka ari na kare suka fita a guje har ragowar matan Sarki Abdallah dake tsaye carko-carko, suna fita suka yi tozali da babban tashin hankalin da ya fi wanda suka ciki a cikin gidan, da gudu kowa ya fara gudun neman ceton rai. Maleek saboda firgici bai tsaya ko ina ba sai cen ƙuryar ɗakinsu, ya maƙale a cen bayan Maryo yana sauke ajiyar zuciya. Duk wannan abin da yake faruwa Maryo na kwance tana bacci hankali kwance. Maleek anya ka nemi maɓoye me kyau kuwa😂 Barka da hutun ƙarshen mako🥰 _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [01/12/2021, 17:12] Ameera Adam🌚: ANYA BAIWA CE? BONUS🌚 38... Ɗan shiru ne ya biyo baya babu abin da yake ta shi sai kukan ƙananan tsuntsaye, a hankali ta ɗago da kai ta kalleshi jin shirun da ya yi yana nazari. Idan idanunta ba ƙarya suke yi mata ba tabbas ta lura da matsananciyar damuwar da ke kwance a saman fuskarsa, suna haɗa ido ya tattaro murmushin ƙarfin hali ya ɗora akan fuskarsa wanda ake kira da yaƙe kafi kuka ciwo. Murya a sanyaye ta furta, "Allah ya taimake ka dama abin da ya kawo ni kenan. Ina me roƙo da ataimaka a dubi wannan roƙon da na zo da shi." Ta ƙarasa faɗa tana gyara zaman alkyabbar da ke jikinta. Ƙura mata ido ya yi yana jin kewar matarsa sai dai ya lura a yanzu idan ya tanka mata ta samu guri kenan dan ya lura da rashin walwalar da ke kwance a saman fuskarta. Shirun da ta ji ya yi ne yasa ta ɗago ta kalleshi sai kuma ta sunkuyar da kai ƙasa dan ba za ta iya jurewa kallon sa ba, a hankali ya motsa bakinsa kamar me ciwon haƙori yace, "Babu damuwa zamu duba mu gani, in sha Allah zan kira Fahima na ji halin da ake ciki tsakaninsu da yatinyar." Miƙewa ta yi cikin girmamawa tana faɗin, "Na barka lafiya Ranka shi daɗe." Tana gama faɗa ta yi gaba ya bita da kallo har ta fice daga turakarsa, lumshe ido ya yi dan ji yake yana matukar kewar Zaliha kawai dai ya rasa dalilin da yasa ya kasa yafe mata dukda kasancewarsa mutum mai sauƙin kai da rashin riƙo. "Maganar gaskiya Marduska na gaji wannan marmasasshen kan nawa. Ka duba ka gani fa yanzu da abin da zaka saka mana da shi kenan? Kawai daga ka buƙaci gashi sai ka aske mana kai. Ni wannan duk ba shi ya fi ɗaga mini hankali ba, tun bayan fitar gashin nan nake saka ran naji alamar wani sabo ya fara tofowa amma shiru kake ji kamar an shuka dusa. Gaskiya ka cuce mu wallahi baka taɓa ɓata mini rai kamar yau ba, duk fa saboda yarinyar nan nake wahalar banza amma ka duba ka gani na wayi gari da kai a sutale kamar bayan ludayi." Jakadiya da ke gefe sai gyaɗa kai take kamar ƙadangaruwa, ita kanta dan dai tana shakkun Marduska da tuni ta rufeshi da masifar ɗiban albarka. Marduska ƙuri ya yi da idanu yana kallon Fulani Maryama har ta gama masifar da take yi, miƙe busassun ƙafafuwansa ya yi masu kama da fusasshen itace ya ɗago ya dube ta da ƙwala-ƙwalan idanunsa masu matukar muni yace, "Maryama idan ban halakaki a nan take ba Allah ya tsine mini." Jakadiya ta dube shi a kaikace cikin zuciyarta ta ce, "Yoo dama me ya rage meye kai idan ba tsinannan ba." Ya ci gaba da cewa, "Har kya yi maganar cuta ke mutane nawa kika cuta a rayuwarki? Kuma mutane nawa kike kan cuta yanzu haka? Ko kin manta Salman ba jinin Takawa bane kike zaune da shi a matsayin ɗansa wanda a yanzu haka yana ƙudirin hallaka shi ta kowanne hali. Da kin ɗauka zan yi miki aiki a sadaka ne babu tukwici? Ahir ɗin ki da gaya mini maganar da ta zo bakinki idan ba haka ba wallahi ina iya mayar da gabanki ya koma bayanki, anan wurin da kike ina iya tsaface ki na ɓatar da ke kuma a manta da ke har tashin duniya. Idan za ki yi iskancinki ki san a inda ya dace ki yi amma ki tabbatar da kin yi na farko kin yi na ƙarshe a nan. Tun ranar da kika fara zuwa wajenmu muka sanar dake dokokinmu kika amince dan haka ki kama kanki, duk abin da kika ga ya biyo bayanki sakamakonki ne." Fulani Maryama tsoro ne ya kamata dan sai a lolacin ta fahimci wautar abin da ta aikata. Cikin nadama ta russunar da kai ta ce, "Tuba nake Marduska na yi kuskure ayi mini afuwa, ka san duk wani mai rai ajizi ne." Murmushin jindaɗi ya yi ya kalli Fulani Maryama yana hura boɗareren hancinsa kamar na botorami yace, "Fulani Maryama kenan kedai zuma ce sai da wuta. Babu komai an yafe miki amma ki kiyaye gaba, Kuma ki bar murna karenki ya kama zomo billahilazi a kodayaushe komai yana iya tashi kwaɓarki na iya yin ruwa. Bar ganin yarinyar nan ta bar masarautarku ki ɗauka zaki miƙe ƙafafuwa yadda kike so a kodayaushe nayi bincike ina ganin bala'i haɗe da tashin hankali a cikin masarautarku. Na gaya miki a wannan karan me sha da rayuwarsa sai wanda Allah ya tseratar, ina tunanin tarihi ne zai ƙara maimaita kansa sai dai wannan karan abun zai fi ƙamari da muni fiye da tunanin me tunani, ina matuƙar tausayawa Sarki Aminullah domin shi mutum ne me sanyin hali amma wani dalili daban kan iya tabbatar da wani yanayi a masarautarsa. Tabbas ƙaddara dole idan har Allah ya rubuta saukarta akan mutum, guje mata kamar gujewa mutuwa ne sai dai wataƙila tazo da sauƙi ko akasin haka. Amma bana ganin wannan ƙaddarar zata iya zuwa cikin sanyin hali ba tare da ta girgiza mazauna da wajen cikin masarautar ba. Abin da yake ƙara ɗaure mini kai ta yadda na kasa ganin daga ina wannan ƙaddarar zata soma shin Zulik ne zai fara taso da ita ko Rayzuta ko kuma mai dannaniyyar zuciya Furzaan. Lamarin tattare yake da sarƙaƙiya me ɗauke da ɓacewar tunani, ina ƙara haska miki hanya ne domin ki kwana da sanin tashin hankalin ba zai zo miki da sauƙi ba, zama bai ganki ba domin su tanadi suka yi na dubbanin shekaru ke kuma daga yanzu naki tanadin zai soma. Ki yi ƙoƙari kija Zulik a jikinki asirin bil adam a yanzu baya taɓa tasiri a jikinsu sai dai ki haɗa da kissa nafi tunanin wannan ce hanya mafi sauƙi a gare ki. Ki cusa masa soyayyar mulki da zaƙin da ke cikinsa dukda shima a haukace yake ta wannan fannin, amma hakan da zaki yi zai iya sa ki samu wani matsayi a wurinsa kamar wancen karnin. Ni da kika ganni ƙarƙari na yi miki bincike na kuma sanar da ke halin da ake ciki, domin su Rayzuta sun fi ƙarfina ba zan iya ja da su ba idan kuwa na zaƙewa lamarin halaka ni a wurinsu ba abu ne mai wuya ba." Ya ƙarasa maganar yana kafe Fulani Maryama da idanu. Jikinta ba ƙaramin sanyi ya yi ba duk tayi fiƙi-fiƙi kamar sabuwar munafuka, kamar wacce take da gyambo a baki haka ta ɗaga laɓɓanta a hankali ta ce, "Marduska a duk lokacin da na ziyarce ka maimakon ka kwantar mini da hankali sai dai akasin haka, na zo ne dan ka bani mafita amma koyaushe sai dai ka dilmiyar dani cikin tashin hankali. Ka sare mini gwiwa ta yadda nake ganin ba zan iya aiwatar da komai ba dukda zuciyata tayi tsayuwar gwamin jaki. Macece mafita akan lamarin ta ina zan fara?"Marduska ya zura hannunsa cikin wutar da ke zaɓalɓalawa kamar wacce ake watsa mata makamashi, waɗansu gwarwashi ya ɗebo guda biyu ya murje su a tafin hannunsa ya ƙura musu idanu sannan ya ɗago da kai yana sauke ajiyar zuciya kamar wanda ya yi tseren gudu yace, "Karki ki ji zafina ko kaɗan domin ba za ki fahimci amfanin zuwanki wurin nan ba sai gaba, idan har kin ɗauki shawarwarin da na baki na baya da wanda zan kuma baki a yanzu. Ni haska miki fitila nake wacce zata nusar da ke hanya me ɓillewa, shawara zan baki bansan yadda zaki ɗauke ta saboda kowacce ba lallai tayi miki daɗi ba, dan kowacce tana tafe da ƙalubale. Za ki iya fassara hakan da gaba kura baya damisa, ko kuma ki kira ta da gaba kura baya siyaƙi. Amma mafi muhimmanci a wurinki ki baje kunnuwanki domin ki ɗauki maganganun da zan sanar dake ɗaya bayan ɗaya. Nima fa bincike na yi sai kuma harsashe na bansani ba zai tabbata ko ba zai tabbata ba amma yana da kyau ki riƙe su, wataƙila Rayzuta ta dawo masarautarku wataƙila kuma ta tafi kenan dan ban ga yaƙinin juyowa masarauta a tattare da ita ba. Idan har ta dawo kiyi ƙoƙarin janta a jikinki, dukda nasan tsananin ƙiyayyar da ke tsakaninku. Ki kasance me ɓoye ƙiyayyarki a fili dangane da ita, idan ba haka Salman da kika haifa kina ji kina gani zai murɗe wuyanki har lahira. A haukace yake ya zauce akanta ta yadda baya ji bare gani akanta, duk wani abu da yake ƙoƙarin yi masa iyaka da ita yana iya hallakashi." Da sauri Fulani Maryama ta ce, "Ai tuni Maleek ya tafi da ita kuma lafiya ƙalau suke zaune.'Marduska ya ɗago jajayen idanunsa masu kama da gauta yace, "Wa yace miki suna zaune lafiya, Masarautar Adamawa na cikin ƙadamin da bil'adam bai isa ya dakatar da abin da yake faruwa ba a halin yanzu." Ya ƙarasa maganar yana nuna mata ƙwaryar dake gabansa nan take sai ga hargitsin masarautar Adamawa ya sauka aciki, shafe ganinsu ya yi sannan ya ɗago yace, "Idan kina tantama bayan ki koma ki kira ɗaya daga cikin masarautar zai sanar da ke halin da ake ciki." Fulani Maryama jiki a sanyaye kamar wacce aka zarewa laka ta ce, "Wai ba garin nake nufi ba. Na ji kace Zulik na iya hallaka kowa bayan kuma Maleek ya tafi da ita babu wani abu da ya biyo baya." murmushi Marduska ya yi har sai da ƙaton wawulon bakinsa ya bayyana sannan yace, "Ai ya san ba matarsa bace. Hasalima ya san duk tsanani babu wani abu da zai taɓa haɗata da Maleek, sai dai akwai wata ɓoyayyar alaƙa a tsakaninsu da ba kowa ne ya san da ita ba, wannan alaƙa ya sa Rayzuta ba za ta bari a cutar da shi ba abu na biyu da ya sa ba zai cutar da shi ba yaron na da riƙon ibada sosai, dan haka zai yi wuya jinnu su iya cutar da shi amma ban tabbatar ba. Abu na gaba da zan shaida miki idan har Zulik ya ƙara kawo miki ƙudurin aurenta ki goya masa ba har a samu ya mallake ta, ita kuma sai ki samu ki lallashe ta da yaudara har ta amince ta aure shi. Amma kinsan duk wannan ba zai yuwau ba har sai abu ɗaya ya tabbata." Da sauri Fulani Marayama ta ce meye shi." Marduska ya ce, "Maryama kenan. Ai duk gaggawar unguwar zoma ta bari a haihuwa kuma duk gaggawar asara ta jira samu. Kawai daga ganin hadari sai ki fara wanka da kashi?" Fulani Maryama a ɗan kunyace take faɗin, "Marduska na ƙagu ne na ji, amma ai naƙuda ga me tsohon ciki ba laifi bane?" Ya mayar mata da amsa da cewar, "Idan har cikin ya isa haihuwa ba idan kuma bakwaini ne kinga wataƙila asararsa za'ayi." Shiru ta yi tana kallon sa bata tanka masa ba dan ta san idan ta biye masa sun dinga yi kenan. Marduska ganin haka yasa ya ci gaba da cewa, "Ba za ki taɓa karya ƙadarin Rayzuta ba har Furzan wato Saif ya yi aure, idan ma bakya jan sa a jiki yanzu ki fara domin ki fahimci halin da yake ciki, na ga soyayya a ƙarƙashin zuciyarsa idan har kike cire dannaniyyar soyayyar da Zulik ya binne masa ya faɗa tarkon soyyaya, ki hanzarta goya masa baya ya yi aure muddin be yi aure ba bana tunanin zaki iya tanƙwara zuciyar Rayzuta hakan ma zai iya jawo miki allura ta tono garma. Idan kika samu zulik ya aureta wataƙila ki ci gaba da cin karenki babu babbaka, wata ƙila kuma ƙaiƙayi kan iya koma kan masheƙiya. Ku ta tashi ku tafi na yi iya yi na" Fulani Maryama zata ƙara magana ya katse ta da cewar, "Babu abin da zan kuma furtawa dangane da halin da masarautarku zata iya shiga, abu ɗaya na sani zan baku magani wannan garin ya daina zuba, dama ba komai bane kashin aljanin da yake latsar kanku ne idan kuka wanke kanku da maganin har abada bazai dawo ba, na gama magana bana buƙatar tambaya ko ƙarin bayani ku ta shi ku fice." Yana gama magana ya wurga musu wani garin magni, Jakadiya sai raba ido take Fualni Maryama na gaba tana biye da ita zugwai-zugwai kamar jela har suka fice daga kogon dutsen. Har bayan shigar Maleek ɗaki wurin Maryo bai daina jin iface-ifacen mata da ƙananan yara ba. Wata irin haniniya dokin yake me tsoratarwa wacce iskar da ke ta shi a wurin kaɗai abar tsoro ce, har lokacin jikinsa ban da rawa babu abin da yake yi musamman idan ya tuno halin da ya riski wani mutumi a ciki wanda har lokacin bai gane fuskarsa ba sakamakon yadda jini ya wanke ta. Daga bayan ɗakinsu ya ji kukan dokin kafin ya yi wani motsi yaji ya bigi katangar ɗakinsu har sai da wani sashe na daga jikin katangar ya zube. Kamar mace haka kuka ya ƙwace masa tare da furta, "Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un." da sauri ya faɗa kan gadon yana dukan Maryo yana kiran sunanta musamman daya tuna abin da dokin yake yi a waje yana gudun kar ya fashe ɗakin suma ya same su ya illata su. Abin da ya faru lokacin da su Maleek suka fita suna zuwa suka samu wani baƙin doki yana hauka, bakinsa ɗauke da wani mutum ya kafa masa haƙoransa ya riƙe masa gadon bayansa yana fyaɗa shi da ƙasa ban da jini babu abin da yake zuba a fuskar mutumin, wani babban tashin hankali da ban tsoro haɗe da ban ta'ajibi duk wurin da Dokin ya taka sai ƙasar wurin ta dagargaje ta tsage tana ƙoƙarin ruftawa ciki, duk waɗanda suke tafe a hanya haka ya dinga bangaje mutane suna faɗuwa a sume wasu kuma nan take kansu yake fashewa su mutu. Haka ya ci gaba da fyaɗa mutumin bakinsa da bango, ba shiri suna ganin haka kowa ya fara yi takai-takai domin neman ɓuya. Maleek cikin tashin hankali ya fara dukan Maryo yana cewa, "Shukra! Shukra wai me yake damunki wannan wanne irin bacci ne kike yi haka ki tashi mu tafi sashen Mai martaba zai fi nan saboda da alama dokin nan yana ƙoƙarin shigowa nan." Kamar gawa haka ya janyo Maryo ta yi yaraf ban da yana jin numfashinta zai iya rantsewa da Allah gawa ce a wurin, hannu ya sa da ƙarfi ya ɗan mari gefen fuskarta yana kiranta sunanta. Tun bai ɗauke hannunsa daga kan fuskarta ba jini ya fara ɗiga daga hancinta, buɗe dararan idanuwanta tayi suna haɗa ido da sauri ya wurgar da ita tare da ja baya, sakamakon ganin fuskar baƙin dokin da ya yi ƙuru-ƙuru ciki yana buɗe baki, gefen wajen da ya mareta da wajen da ya riƙeta tuni ya fara tsattsafo da jini, haka shima daga hannuwansa da gefen wajen da jikinta ya taɓa shi nan da nan ya yi burɗinɗin tare da yin taruwar jini. Yana daga gefe yana ƙoƙarin guduwa yaji ta fara magana cikin wata irin murya me amsa amo mara daɗin saurare, "Kana yawan shiga hurumin da ba naka ba, amma ina ƙara jan kunnenka da ka tsaya matsayinka. Ina ɗaga maka ƙafa ne saboda ɓoyayyar alaƙarmu banasan taɓa rayuwarka saboda gaba nima rashinka zai sani a matsala, jini na kai komo yana wucewa ta sassan jijiyoyin cikin jiki, baka kamaci zaka masoyi na gari ba idan aka duba zunzurutun soyayya da matsayinta, ka gaggauta shiga duniya wataƙila ka iya nemarwa kanka mafita amma ba wannan ba, domin mazaunin gida baya taɓa cimma nasara da muradin zuciyarsa. Ita soyyaya a duk inda take bata ɓuya karka kasance me raunatacciyar zuciyar da wata zata nuna mata jajircewa, kayi ta gudu kamar me laluben ƙarshen duniya akan nemo sahihiyar yalwatacciyar soyayyarka. Kada ka manta daraja ɗaya kake ci na ɓoyayyar alaƙarmu da tuni zancen wani ake ba kai ba. Karka ƙara dakatar da ni akan hukuncin da nake zartarwa dai dai da laifin masu aikata shi idan ba haka ba kaima ina iya bi ta kanka." Tana gama faɗa ta kuma yanke jiki ta koma bacci tare ta sauke ajiyar zuciyar kamar wacce tayi tseren gudu, wanda haka ya yi dai-dai da hankaɗe katangar ɗakin da Dokin ya yi ya kutso cikin ɗakin yana ɗaga ƙafafuwa sama tare da ci gaba da haniniya mara daɗin sauraro. Ga mu a wannan yanayin lamari dai ya ɗauki hazo, Masarautar Adamawa na cikin yanayi, ina fatana kalaman wannan shafin bai rikitar da ku ba🤣🤣 _LITTAFIN ANYA BAIWA CE? NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [02/12/2021, 18:01] Ameera Adam🌚: 39.... Maleek kusan mutuwar tsaye ya yi ban da karkarwa babu abin da jikinsa yake yi, runtse idonsa ya yi ya miƙa wuya ya saddaƙar da sai dai wani ya ƙara numfashi ba shi ba. Dokin bai saurara ba ya buga wata haniniya tare da buga ƙafafuwansa na gaba a ƙasa da ƙarfi, nan take komai da ke cikin ɗakin ya tsalle kamar waɗanda ake yi wa girgizar ƙasa. A cikin abubuwan da suka yi tsalle sama har da Maleek wanda tuni ya sarewa rayuwa, yana gabda faɗowa sama dokin ya cafe shi da bakinsa ya ci gaba da wata irin haniniya. Maleek jikinsa ne ya saki wanda yake nufi da ɗaukewar numfashinsa a take ya sume bai ƙara sanin abin da yake faruwa ba. Dokin na ganin haka ya yi wurgi da shi cen gefe sannan ya juya a haukace ya ci gaba da banke masu ƙararrarun kwana, waɗanda suke da rabon shan wahala kuma suna kwance kamar gawarwarki cikin jini, wasu ko numfashin kirki basa iya yi. A haukaci ya nufi sashen Mai martaba bugu ɗaya ya kaiwa katangar ɗakin ta rushe, sai ga haske rana ta dallare cikin turakarsa wace take a kusan cike ta maɓoye daga ƴaƴansa bayinsa harda dogarawansa da sauran mutanen cikin gida. Suna ganin dokin gabaɗaya jikinsu ya fara tsuma shiru suka yi kamar waɗanda ruwa ya cinye su, masu sakin fitsari na yi masu zawo a wando suna yi. Kafe su ya yi da idanuwa yana zaro harshe kamar zalamamman maye da ke gabda haɗiyar bil'adama, waige-waige ya dinga kamar me neman abu sai kuma ya fara takawa a hankali har gaban su Sarki Abdallah, miƙa kai ya dinga yi yana shinshimasu ɗaya bayan ɗaya. Duk wanda dokin ya kai kansa sai ya yi kamar zai mutu saboda tashin hankali. Sarki Abdallah tuni ya janyo rawanin har saman fuskarsa ya mayar da shi kamar hijabi. Dokin na zuwa kan wani Dogarin Sarki ya gatsawa kansa haƙora yana fisgoshi, ya fyaɗa shi da bango nan take ya faɗi ko shurawa bai ƙara yi ba, nan take ɗakin ya hautsine da hayaniya ban da ihun yara da manya babu abin da yake tashi a ɗakin, dan gabaɗaya sun saddaƙar da ƙara samun zuƙar iskar duniya. Suna tsaka da ihun ya sake fisgo wata baiwa dake rakuɓe acen gefe har ya ɗaga zai fyaɗa da ƙasa kamar daga sama suka jiyo muryar Maryo tana cewa. "Dakata! Ba mutuwa zai yi ba. A bashi wahala." Tun bata rufe baki ba dokin ya fara tumurmusar baiwar ban da ihu da ƙaraji babu abin da take yi, gabaɗaya hankulan mutanen wurin a tashe yake a lokacin da za a tsaga jikinsu wataƙila ba za a samu jini a jiki ba. Yana gama tumurmusa ta ya ƙarasa wurin Maryo da ke tsaye kyam tana ƙare musu kallo, russunar da kai ya yi a gaban ta cikin girmamawa yana jirana umarninta. Hannu ta sa ta fara shafa kansa tana murmushi sannan ta ɗago da kai ta kalli wurin ayarin mutanen, ta fara takawa a hankali cikin ƙasaita. Tana ƙarasawa ta fara kurɗawa cikin mutanen ban da zare idanu babu abin da suke yi.Hannu biyu ta sa ta riƙo Jakadiyar Sarki Abdallah ta ɗago ta, jikin Jakadiya sai rawa yake kamar mazari haka ta tsayar da ita tana ƙoƙarin faɗuwa saboda ƙafafuwanta sun ga za ɗaukarta. Kallon ta ta yi tana murmushi ta ce, "Alƙawarin da na ɗauka miki na cika miko shi tabbas wannan hukun da na yi musu bai kai azabtarwar da suka yi mana ba, amma ko babu komai sun ɗanɗana kuɗarsu." Ita dai Jakadiya tana tsaye kamar gunki sai raba ido take kamar shege a rabon gado. Hawaye ne ya ɗan zubo mata ta sa gefen hannunta ta goge sannan ta ci gaba da cewa, "Amma har gobe zuciyata ta gagara yafe musu bana tunanin zan iya manta abin da aka aiwatar gare mu." Jakadiya kamar fitar tusa haka ta tsinci bakinta yana faɗin, "Ita yafiya alama ce ta tsarkakkakiyar zuciya. Yafewa macuci ba aibu bane duba da muma muna yiwa Ubangijin da ya hallice mu laifi, kuma idan muka roƙe shi yana yafe mana, ki tausasa zuciyarki laifin wani baya shafar wani." Gyaɗa kai Maryo ta yi ta ce, "Saboda ke zan yi, saboda darajar bakinki amma ina neman yafiyar ki, amma tabbas sai ha hukunta Fulani Halimatu. Ta cutar da baiwar Allah na tsawon shekaru, ta yi tsammanin asirinta ba zai tonu ba wanda hakan ba ƙaramin kuskure bane. Ita ta killace Mai babban ɗaki a kogon bokanta sai ni na ɗauko ta, a shekarun baya kun wayi gari da gawar Mai babban ɗaki wanda sam ba ita bace rufa ido suka yi muku ita da bokanta, kuma billahillazi sai ta girbi abin da ta shuka. Kinsan darajarwa tasa na taimake Mai babban ɗaki?" Jakadiya kasa magana ta yi Maryo ta ci gaba da cewa, "Saboda Maleek ne! Akwai ɓoyayyar alaƙar da ke tsakaninmu. Ba za ku taɓa fahimta ba sai nan gaba. Na taimaka mata ne saboda duk cikin jikokinta ta fi ƙaunarsa, ta bashi kulawar da babu wani jika da ya samu haka." ɗaga kai ta yi ta kalli Sarki Abdallah ta ce, "Ka gaggauta mayar da ita ɗakinta domin Mai babban ɗaki ta fi ƙarfin zama a ɗakin baya, Uwa uwa ce babu na biyunta idan har kana san gamawa da mulkinka lafiya, kuma ka fara hukunta matarka kafin ta aminshi nawa hukuncin." Tana gama faɗa ta kalli Jakadiya cikin tausasa murya ta ce, "Ya Mahaifiyata zaman ki a nan ba dace ba ko za ki biyo ni mu tafi?" Da sauru Jakadiya ta fara girgiza kai ta ce, "A'a zan zauna a nan Allah ya yi miki albarka." Murmushi Maryo ta yi mata ta ce, "Ba zan takura miki ba. Amma idan akwai abin da kike buƙata ki sanar da ni." Jakadiya ta gaɗa kai, Maryo ta juya ta kama dokin ta kamar tsuntsuwa haka ta ɗafe kansa suka fice daga ɗakin. Idanu ya zuba mata har sai da ta fara tsarguwa ta sunkuyar da idonta ƙada tana murnushi, daga cen nesa Uwar bayi ce tafe tana kallonsu cikin takaici. Ji take kamar ta ƙarasa wurin da suke zaune ta damƙi wuyan yarinyar ta shaƙe kowa ya huta, hannunta na dama ta kalla wanda yake ɗauke da ƙwaryar fura da nono wanda yaji garin magani, amma idan ba a gabanka aka saka ba, ba za ka san da wani magani a ciki ba. Tana ƙarasawa wurinsu ta faɗaɗa fara'arta cikin girmamawa ta yi sallama tana faɗin, "Barkanku da hutawa ranka shi daɗe." Saif ya ɗago idanu ya kalleta yana cewa, "Barka dai Baba." Miƙa masa ƙwaryar furar hanunta ta ta yi ta ce, "Ga fura Bintu ta damo maka ta ce a kawo maka jikin nata ya ƙara warwarewa." Faɗaɗa fara'arsa ya yi yace, "Na gode Babah ita kuma Allah ya ƙara mata lafiya." Mayar da kallon sa ya yi wurin Abuh yace, "Kema za ki sha ko?" Gyaɗa masa kai ta yi sannan ya tura mata ƙwaryar yace, "Ga shi sha ki rage mini." Hankali a tashe Uwar bayi ta karaf ta ce, "Amma ai kai na kawowa." Kallon ta ya yi yace, "Ni da Abuh kusan ɗaya ne." Uwar bayi haɗiye mugun yawu ta yi dan bata so asirinta ya tonu yasa ta ce, "To shi ke nan amma ka tabbatar da ka sha fa." Kallonta ya yi yana nazartar maganar ganin haka yasa ta wayance da cewar, "Na ga idan baka sha ba Bintu ba za ta ji daɗi ba." Gyaɗa mata kai kawai ya yi bai kalleta ba yace, "Uwar bayi a bamu wuri." Sumi sumi ta tashi tana faɗin, "Na barku lafiya." Kallon Abuh ya yi yace, "Ba ni furar nan!" Abuh ta ɗan kwaɓe fuska ta ce, "Sha fa zan yi." Ya ɗan tsuke fuska yace, "Na ce ki bani." Miƙa masa ta yi ta wurga masa tambaya, "Dama Bintu har abinci take aiko maka?" ta tambaya tana kafeshi da idonta. Ɗagowa ya yi da manyan idanuwansa ya kalleta sai kuma ta ji ba za ta iya ci gaba da jurewa kallonsa ba, sunkuyar da kai ta yi ƙasa ta ce, "Amma kawai na yi mamaki ne." murmushi ya yi yace, "To me ya sa kika tambaya? Ko bakya son haka?" Bata san lokacin da ta gyaɗa masa kai ba, ya saki lallausan murmushi yace, "Saboda me?" Ta yi karaf ta ce, "Idan kana so ka bani na dinga yi maka." Kallonta ya yi yana jin wani irin farinciki cikin zuciyarsa yake tunanin, "Shin ko itama ta farajin abin da nake ji a zuciya ta?" kallonta ya yi yace, "Shi ke nan! Kin san Bintu ta yi wani irin ciwo me ban tausayi shi yasa nake tausayin yarinyar, amma yanzu ta warware. Ina tunanin sabon da muka yi yasa lokaci-lokaci take aiko mini da fura." Kallonsa ta yi sai dai a ƙasan zuciyarta bata ji daɗin abin ba. Gabanta ne ya yu mummunan faɗuwa da ta ayyana meye na ta na jin babu daɗi dangane da haka, tunowa ta yi da Maryo sai ta ji tausayin ƴar uwarta ya kamata. Ina ma yadda Saif yake sakar mata fuska haka zai yi wa Maryo. Tafa hannunsa ya yi a saitin fuskarsa yace, "Tunanin me kike yi?" Idonta ne ya kawo ƙwallah ta ce, "Ƴar Uwata Maryo." Tsuke fuska ya yi yana jan guntun tsaki, Abuh ta fara girgiza kai tana faɗin, "Me ya sa baka ƙaunar ƴar uwata alhalin ta fini kyawawan halaye." Fuska ɗaure ya kalle ta yace, "Na ce miki bata da kyawawan halaye ne? Ba na san damuwa fa." Daga haka bai ƙara tanka mata ba ya fara ƙoƙarin ta shi, da sauri ita ma ta miƙe tana faɗin, "Dan Allah ka yi haƙuri." Gyaɗa mata kai ya yi ya wuce kamar za ta yi kuka haka ta bi bayansa kamar jela. "Maryama lafiya na ga kwana biyu kina ɗari-ɗari da ni ko wani abu yana damun ki ne?" Sarki Aminullah ya faɗa yana ƙare mata kallo dan ba haka ta saba zuwa turakarsa ba ko da babu wani abu da yake haɗa su amma tana nuna masa kulawa. Murmushi ta yi tana kallonsa amma a ƙasa zuciyarta, ji take ƙirjinta na dukan uku-uku. Tattaro jarumta ta yi dukda a lokacin jikinta ya kusa jiƙewa da gumi ta ce, "Babu komai Ranka shi daɗe kaine dai ka ga haka." Sarki Aminullah yace, "Na sai wani sha mini ƙamshi ake ina jin sai na ƙara ƙwarƙwara." Fulani Maryama dukda ta san a yanzu Sarki Aminulla babu amfani da zai ƙara yi wa wata mace sai da ta ji babu daɗi a ƙasan ranta, amma da yake ta ƙwarai a kissa sai ta ce, "Allah ya baka yawan rai, wannan ai ba komai bane ka ga masu kula da kai za su ƙara yawa. Allah dai ya ƙara haɗa kanmu." Sarki Aminullah yace, "Allah ya yi miki albarka Maryama ke kam ta daban ce, shi yasa nake ƙaunarki saboda kyawawan ɗabi'unki." Murmushin jin daɗi ta yi ta ci gaba ta fari cikin kissa. Bayan sa ya kalla yace, "Maryama zo ki miƙe mini Jakar cen dan ina tunanin gobe ne tafiya ta ƙasar Gaya, miƙo mini ki zuba waɗannan kayan a ciki." Zuciya ɗaya Fulani Maryama ta miƙe ta je ta ɗauko jaka ta zauna daga ɗan nesa da shi tana ƙoƙarin buɗe jakar, shammatarta ya yi ya janyota jikinsa yana cewa, "Bahaushe yace duk wanda ya riga kwana zai riga ka..." sauran maganarsa ce ta maƙale ganin ɗan kwalin Fulani Maryama a ƙasa lokacin da ya janyo ne ya zame, a razane ya ja da baya cikin tsoro yace, "Maryama! Anya kece ko wata aka sauya mini?" 😂😂😂😂Takawa ya ga bayan silva😂😂😂😂 Kuyi manage pls _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [04/12/2021, 18:13] Ameera Adam🌚: 40... Kunyar duniya ce ta lulluɓe idanuwan Fulani Maryama dan bata taɓa tsammanin haka daga wurin Sarki Aminullah ba, sunne kai ƙasa ta yi cikin jin nauyi ta fara sharar ƙwallar munafurci tana faɗin, "Wani tsautsayi ne ya afka mini ranka shi daɗe." Cikin mamaki yace, "Tsautsayi? Meye silar fitar gashin na ki dubi fa ki ga yadda kan ya yi taƙwal kamar wacce aka yi wa aski da sabuwar aska." Fulani Maryama ta kuma goge ƙwalla a karo na biyu tana satar kallon Takawa, ta fara laluben ƙasa tana nemo ɗan kwalinta ta ji ya ƙara faɗin, "Wai ba magana nake yi miki ba?" Fulani Maryama cikinta ne ya kaɗa tsoro ya kama ta saboda yadda ta ga Sarki Aminullah ya yi mata magana, tattaro jarumta ta yi ta ce, "Rannan ne ina wayar gari na ga kaina haka gashin sauke a ƙasa na yi kuka kamar raina zai fita, amma ban sanar da kai ba saboda kar na ɗaga maka hankali." Sarki Aminullah ya ƙuri da ido yana ƙarewa hallitar Fulani Maryama kallo, tsarguwa ta yi musamman da ta tuna lokacin da Jakadiya take faɗin kanta kamar na jinjirin jaki. Sunkuyar da kai ƙasa ta yi tana wata sa hannun rigarta ta riski muryar Takawa yana cewa, "Sam wannan ba ma'askin dare bane dole a nemo masu magani." A firgice Fulani Maryama ta ɗago ta kalle shi kamar za ta yi kuka ta ce, "Haba ranka shi daɗe. Yanzu kamar ni a matsayin uwar garkenka sai a yi ta yayata abin da ya faru har da neman masu magani? Wai ba zai zama kamar abin kunya ba kuwa, dan Allah ka rufa mini asiri ka bar maganar nan." Sakin baki ya yi yana kallon Fulani Maryama dan a iya saninsa Maryama macece mai matuƙar ƙaunar gashi, amma wai yau ita take cewa a bar maganar nema mata maganin gashi? Tsare ta ya yi ido yace, "Tun yaushe hakan ya faru?" Sani ta yi idan ta gaya masa gaskiyar lokacin ba makawa sai ya nema mata masu magani, hakan ne yasa ta basar ta ce, "Shekaran jiya ne Ranka shi daɗe." Jinjina kai ya yi har lokacin idonsa na kan Fulani Maryama, a kaikaice ta kalle shi ta ce, "To wannan kallon fa ko munin matarka kake kallowa?" Sarki Aminullah ya kuma sakin baki da hanci yana kallom ɓoɗareren hancinta da sulluwar doguwar ƙeyarta yace, "Kin taɓa jin uwa ta hango munin ɗanta?" Fulani Maryama ta kwaɓe baki ita a dole shagwaɓa za ta yi ta ce, "To amma ai gani na yi kana kallona" Sarki Aminullah ya yi murmushi yace, "Dan na kalli matata aibu ne?" Girgiza masa kai ta yi ta ɗauko wani zancen da cewar, "Allah ya taimake ka ni kuwa me zai hana yaran nan kace su fito da matayen aure, yanzu fa lokaci ya yi da ya kamata ace su ajiye iyali, idan muka duba shekarunsu su tafi talatin-talatin fa." Sarki Aminullah ya numfasa yace, "Tabbas maganarki na kan turba amma kina ganin har Saif? Tun da kinga be daɗe da tashi ba." Wani murmushi ta yi wanda ita kaɗai ta san manufarsa ta mayar da kallon ta gare shi ta ce, "Haba Ranka shi daɗe ya kake faɗin haka kamar ba namiji ba, yanzu idan ƙanwata ta ji za ta ji daɗin abin da ka faɗa? Saif fa namiji ne kuma na tabbata ko kafin ya warke aka aura masa mace tsaf zai zauna da abarsa bare yanzu da ya samu lafiya rass da shi." Daɗi ne ya mamaye zuciyar Sarki Aminullah saboda yadda take bawa gabaɗaya iyalinsa muhimmanci, kallonta ya yi cikin ƙauna yace, "To me ƙanwa ai nima ba gulmar ta na yi ba gani na yi dai kamar a bari ya ƙara samun lafiya amma tun da kince haka shi ke nan, ai Saif da Salman duk ɗaya ne Allah ya yi musu albarka. In sha Allah zan tara su da maganar." Fulani Maryama ta kasa ɓoye farin cikinta a fili har sai da ta bayyana a sarari ta ce, "Allah ya tabbatar mana da alheri ka ga a ce har yanzu Yarima na yawo babu mata ne ai sai a saka masa rauni tun da shi jagoran al'umma ne." Gyaɗa mata kai ya yi ya faɗa duniyar tunani dan Allah ya sani yana faragabar ranar da za a ce Salman na riƙe da ragamar masarautar, dukda irin ƙaunar da yake ji zuciyarsa na yi masa. Amma haka kawai yaji yana fargaba. Ganin ya yi shiru yasa Fulani Maryama ta ce, "Tunanin me kake yi ranka shi daɗe?" Murmushi ya yi yace, "Ina tunanin yadda watarana za ku wayi gari da rashina, amma a kullin ina addu'ar Allah ya haɗa kan zuri'a ta." Duk yadda Fulani Maryama take da burin Salman ya samu nasarar ɗarewa kan karagar mulki, amma wannan kalaman na Sarki Aminullah ba ƙaramin raunata mata zuciya ya yi ba, har sai da ta ji idanuwanta sun ciko da ƙwalla ta dube shi da kulawa ta ce, "Me ya sa za ka sako mana wannan kalmar bayan muna cikin farinciki." Murmushi ya yi mata yace, "Maryama kenan! Ita mutuwa babu ruwanta da lokacin walwala ko akasin haka. Fata dai Allah ya sa mu yi kyakkyawan ƙarshe." Fulani Maryama ta amsa da, "Ameen" Sannan suka ci gaba da hira. Bayan lafawar ƙurar sannu a hankali mutane suka fara miƙewaa suna leƙen bakin hanya, gidan ya yi tsit kamar babu kowa a ciki ban da kukan tsuntsaye babu abin da yake tashi a wurin. Sarki Abdallah ne ya tashi wasu Dakaru dan su gano halin da gidan yake ciki. A ɗarare suka dinga fita suna leƙawa dan ganin abin da yake faru, sannu a hankali kowa ya watse sai kuma sautin koke-koke mutane ya fara tashi, saboda wasu an kashe musu iyaye wasu ƴaƴa ye wasu kuma matansu ne. Wannan lamari ba ƙaramin ɗaga hankalin Sarki Abdallah ya yi ba, a inda suka bar shi a zaune a nan ya jima yana nazarin makamar abin da ya dace ya yi. Lokaci-lakaci yake sauke ajiyar zuciya dan gabaɗaya kansa ya ɗau zafi, kamar wanda aka ɗanawa wuta haka ta zabura bai jira fadawansa ba ya wuce cikin gida, kai tsaye ya wuce cen turakarsa ta cikin babban sashe. Maryo na fita daga sashen ta nufi Dajin da yake bangaren wajen bishiyoyi, tana tafe tana jan dokin har suka ɗan yi nisa da jama'a. Kallonsa ta yi tana shafa shi ta ce, "Kudlifa mun gama aikinmu za ka iya tafiya" Juyowa ya yi a raunace ya kalleta, ita ji ta yi babu daɗi ta sauke kanta ƙasa ta ce, "Ba mu rabu ba ta yuwu zamu ƙara haɗuwa amma ko ba komai ya kamata ka ci gaba da bani ƙwarin gwiwa." Kamar mutum haka ya gyaɗa mata kai sannan ya kalleta ya wani irin rangaji da kai, murmushi ta yi masa ta ce, "Na gode da agajin ka mu haɗe wani lokacin." Tana gama faɗa ya zuba a guje cikin dajin be yi tafiya me nisa ba ya ɓace daga wurin. Juyowa ta yi cike da kewarsa sannan ya wuce cen sashen su inda ta bar Maleek yashe cikin wani hali. Kamar yadda ta fito haka ta koma ta same shi yana kwance kamar gawa, murmushi ta yi ta ɗebo ruwa ta kwara masa a fuska a firgice ya tashi yana nema fita da gudu, da sauri ta buga masa tsawa nan take ya tsaya cak wuri ɗaya yana rawar jiki kamar sabon ɗan bori. Kallonta ya yi ya fashe da kuka yace, "Shukra me ya sa kike son azabartar da ni me na yi miki ne?" Takawa ta yi a hankali zuwa bakin gado ta ɗora kafa ɗaya kan ɗaya yana kallonsa ta ce, "Tun farko na gaya maka ni ba matarka bace." Maleek cikin rawar murya yace, "Wallahi na sani dan na ga alama. To wacece ke." Miƙewa ta yi ta fara takawa har ta je bakin windowa ta ce, "Sunana Maryo ni ba Shukra ba ce hasalima ni ban taɓa aure ba, ruwan ka ne ka yarda ruwan ka ne kaƙi yarda, ni na riga da na ga wuri dan haka ban ga abin da zai fitar da ni daga masarautar nan ba. Ni kaifi ɗaya ce bana magana biyu, kun zaɓi dawo dani masaurautar nan akan barina na yi rayuwa da masoyina, ni kuma naci alwashin ko da a baɗini ne dole zan kasance a masarautar na." Maleek da cikin tashin hankali yace, "Dan Allah kiyi haƙuri wallahi na yi alƙawarin sadaki da masoyinki." Kallonsa ta yi idanunta na cikowa da ƙwalla ta ce, "Babu abin da haƙurin ka zai iya yi mini ka yi sabgar ka na yi tawa domin kai din wani mallakakken sashe ne daga ɓoyayyiyar alaƙarmu." _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [04/12/2021, 19:49] Ameera Adam🌚: 41... Maleek cikin rauni yace, "Wacce irin alaƙa gare mu da kike ta iƙirari alhalin kin ce ke va Shukra bace, ni wallahi babu wata alaƙar da ke tsakaninmu." Murmushi Maryo ta yi ta ce, "Lokaci na nan shi zai bayyana kansa na tabbata sai ka tuno da wannan ranar." Tana gama faɗa ta kwanta kan gado ta juya masa baya zuciyarta na tafarfasa saboda tuno da masoyinta da ta yi. Maleek ficewa ya yi zuciyarsa na rawa dan gabaɗaya ya rasa makama, yana fita saƙon Mai martaba na ƙarasowa wurinsa cikin gaggawa. A gaggauce ya ƙarasa wurin mahaifinsa cikin girmamawa ya gaishe da Mahaifinsa, tun kafin ya ƙarasa Sarki Abdallah ya dakatar da shi da cewa, "Kai Maleek! Wacce irin masifa ka kwaso mana muna zaune ƙalau? Tun da na zo duniya ban taɓa ganin tashin hankalin da na yi tozali da shi ba yau, maza tun wuri ka ɗauki yarinyar cen ka fitar da ita daga cikin gidan nan, dan ni ban taɓa nufar wani da tashin hankali ba ka ga kuwa ina zaman zamana ba za ta ja mini asarar rayuwa a ƙasa ba." Maleek shiru ya yi yana nazari shi kansa lamarin yarinyar ba ƙaramin tsoro ya bashi ba, amma a gefe ɗaya ga abin da ta faɗa masa. Yana tsaka fa tunani Sarki Abdallah ya katse masa tunanin da cewar, "Idan kuma so ya rufe maka ido ba za ka iya aiwatar da abin da na umarce ka ba, ka tattara kayan ka kai da ita ku fice mini da ƙasa dan bana ƙaunar abin da zai azabtar da talakawa na. Ka duba ka gani yau jini nawa aka zubar a gidan nan? Mun yi asarar rayuka sama da ashirin ban da waɗanda suke kwance cikin jinya, dama tun farko sai da na gaya maka ina tsoron aurenka da yarinyar nan tun da babu wanda ya san asalinta, amma ka kawo mana ƙabali da ba'adi ka ga abin da hakan ya haifar." Maleek jiki a sanyaye yace, "Allah ya taimake ka ta ce ita ba Shukra bace, hasalima ta ce mini ko aure bata taɓa yi ba." Sarki Abdallah baƙin ciki ya kama shi, yana ganin kamar Maleek na neman yi masa yawo da hankali, cikin tsawa yace masa, "Ba wannan na tambaye ka ba! Matarka ce ba matarka bace ba ni da matsala, dan haka na baku nan minti goma ko ta fice mini daga gida ko kuma ku fice mini gabaɗaya." Maleek ya marairace murya ya fara zayyanewa Sarki Abdallah yadda suka yi da Maryo, yana ci gaba da hawabi Takawa ya ɗaga masa hannu yana cewa, "Bana buƙatar ƙara jin wara magana daga gare ka, dan haka ku fice mini ko na sa a fitar da ku." Kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki haka Maleek ya fice daga turakar mahaifinsa ya nufi sashensa gabansa na dukan uku-uku. "Salman wannan maganar da na kawo maka na san dalilin da ya sa na kawo maka ita, haba ɗan arziƙi karka watsa mini ƙasa a ido mana." Fulani Maryama ta ƙarasa maganar tana fargabar abin da zai gaya mata. Ɗagowa ya yi ya kalle yana cije baki yace, "Wai kina cikin hankalinki kuwa da zaki ce na nemi wata matar na aura? Kin san dai ni Maryo ce zaɓina." Fulani Maryama yanyo shi ta yi tana masa raɗa a kunne ɗagowa ya yi da Kansa ya cikin farinciki yace, "Lallai matar nan kanki yana wuta ya zama dole na nemo aure ko da acikin ƴan shilolin cen ne, shima wancen kwantaccen dole na hura wuta a ɗaure shi da wata." FATAN ALHERI🥰🥰 _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [05/12/2021, 18:08] Ameera Adam🌚: 42... Wani yalwataccen murmushi Fulani Maryama ta yi tana kallon Salman har ta bayyana farincikinta a fili, saboda ko kaɗan bata taɓa tsammanin zai amince da buƙatarta cikin sauƙi ba, amma da ta tuna irin huɗubar da tayi masa sai ta ji tabbas dole ma ya amince, yana daga tsaye ya kalleta yace, "To wai ma ni wacce tsabar za a nema mini ne? Gaskiya ya kamata a nema mini auren ƴar babban gida dukda ba ita bace muradina ba." Fulani Maryama ta miƙe tsaye ta dafa shi tana cewa, "Wannan ba damuwa bace, zan yi wa Mai martaba magana ya nema maka a cikin ƴaƴan abokanansa, amma na fi son ya nema maka ƴar Sarkin Masarautar Gumel dam suna ɗauke da ɓoyayyar dukiya ne yawa ka san fa Mahaifinta ita kaɗai ya mallaka." Cikin rashin ladabi da ɗa'a yace, "Ke wannan ya dama dan da alama ke zalamammiya ce, ni mulki da mallakar Rayzuta ne a gabana. Wai wancen tsohon yaishe zai matsa ya bani wurina? Gaskiya idan na yi a aure a satin na biyu ko da tsiya dole na haye karagar mulki, ko lokacin tafiyarsa ya yi ko ma be yi ba dole na ƙara masa burki..." Da sauri Fulani Maryama ta rufe masa baki tun bai ƙarasa faɗar abin da yake furtawa ba a firgice ta ce, "Kai Salman me kake faɗa haka?" Takawa ya yi har ya je bakin ƙofa be tanka masa ba, ya juyo yace, "Ba zan iya zama na jira har sai ya mutu ba, zan datse numfashinsa ko na samu na haye mazaunina" Jikin Fulani Maryama har rawa yake ta ce, "Ka daina faɗin irin haka Salma. Ba na san mutane su dasa zargi a kanka dan Allah." Cikin halin ko inkula ya ɗaga kafaɗa yace, "Be dame ni ba ko kaɗan amma wallahi kinji na rantse miki muddin na yi aure ba zan rufa makwanni uku ban ɗare karagar mulki ba." Yana gama faɗa ya fice daga ɗakin. Wani irin gumi ne ya shiga ketowa Fulani Maryama dan har ga Allah tana matuƙar ƙaunar Takawa, soyayyarsa ce ma ta sa take bin bokaye dan ganin ta mallake shi ita kaɗai. Jiki a sanyaye kamar wacce aka zare wa laka haka Fulani Maryama ta zauna daɓas, bata damu da irin zafin da ta ji ba. Wani nazari ta yi sai kuma ta saki murmushi tana cewa a fili, "Dole na na karkatar da hankalinsa Salman, yaro man kaza." Daga cen bakin ƙofa ta ji sallamar Inna Habi, sai da ta mula ta mule sannan ta amsa mata a daƙile kamar me ciwon maƙogaro. Sai da ya shafe sama da minto biyar bata bawa Inna Habi umarnin shiga ba sannan ta ce, "Kya iya shigowa kin yi mini sandandan a tsaye kamar gungumen icce, uwar me kika zo yi mini yanzu?" Hawaye ne ɗigowa Inna Habi da sauri ta goge ta shiga cikin girmamawa ta russuna tana faɗin, "Allah ya taimake ki dama zuwa na yi na ji ko zan yi miki matsar ƙafar, saboda rannan na ji kin ce bakya buƙatar ɓata lokaci."Shiru ne ya biyo baya ba tare da ta tanka mata ba ta bi ta da wani wulaƙantaccen kallo ta ce, "Amma dai yau ba ki yi wanka ba ko? Daga shigowar ki tsami duk ya cika mini ɗaki." A raunane Inna Habi ta ce, "Allah ya taimake ki wallahi na yi wanka." Wurga mata harara ta yi ta ce, "Au ƙarya nake yi miki kenan? Tashi ki fice miki daga ɗaki kar ki kumburar mini da ciki maza fita sai na neme ki." Haka Inna Habi ta fita tana shayar ƙwalla saboda takaici har ta ƙarasa ɗakinta. Maleek na gabda ƙarasawa sashensu ta hango Maryo ta fito fuskarta ba yabo babu fallasa, tana tafe tana motsa ƴan yatsu kamar me lissafi. Ɗaga hannu ya yi kamar zai yi mata magana amma gabaɗaya tsoro ya hana shi furta ko da kalma ɗaya ce, Yana kallonta har ta nufi sashen Mahaifiyarsa. Gabansa ne ya yi mummunan faɗuwa jikinsa har rawa yake be san lokacin da ya bita a guje ba, don yana tsoron abin da za ta aiwatar a cen ba. Duk yadda yake sauri amma be cimmata ba kafin yaje tuni ta daɗe da shiga, tana shiga kai tsaye ta nufi ɗakin da aka rufe Fulani Babba. Da ƙafa ta hankaɗa ƙofar nan take ƙofar ta buɗe fuska a ɗaure ta damƙi hannun Fulani babba ta fisgota da ƙarfi suka fito daga ɗakin, Maleek na tsaye da sauri ya bi bayansu yana tambayarta amma ko waiwayonsa ba ta yi ba bare ya sa ran zata amsa masa. Fulani Babban ta fara cewa, "Don Allah ki..." Kallon da Maryo ta yi mata ne yasa ta ja bakinta ta rufe, tana tafiya kai tsaye ta wuce cen ɗakin da aka ajiye Me Babban ɗaki. Barka da hutun ƙarshen mako🥰 _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [06/12/2021, 19:46] Ameera Adam🌚: 43... Lokacin da suka isa ɗakin Me babban ɗaki tana kwance da alama hutun gajiya take fanshewa wanda ta manta rabonta da runtsawa a lallausan makwanci irin wannan. Maryo na shiga ta durƙusa gaban Me babban ɗaki ta ce, "Babah ta so muje fadar Sarki." Ba musu Me babban ɗaki ta miƙe ta bi Maryo na gaba riƙe da hannun Fulani Babba, Me babban ɗaki na biye da ita kamar jela. Lokacin da suka ƙarasa fadar babu kowa a ciki sai Dogarawan bakin ƙofa, lokacin da Maryo ta je shiga babu wanda ya yi gigin hanata shiga, sai ma ja da baya da suka yi a ruɗe saboda kowa shakkar Maryo yake. Sai da ta ƙarasa ta zaunar da Me babban ɗaki sannan ta juyo bakin ƙofar ta kalli wani Dogari fuska a haɗe ta ce, "Maza ka je ka kira mini Sarki Abdallah." A firgice ya kalle ta yace, "Shi Ranka shi daɗe ɗin za a kira miki?" Tsawa ta buga masa ta ci gaba da cewa, "Kace masa ya zo yanzu idan ba haka ba abin da ya faru ɗazu zai ƙara faruwa har na yanzu ya fi na ɗazu muni." Jiki na rawa Dogarin ya wuce cen sashen Sarki Abdallah." Yana zuwa ya ne mi iso da ƙyar ya samu aka barshi ya shiga sakamakon idan yana sashen iyalinsa ba a cika neman iso ba, sai da ya sanar da su abin da yake tafe da shi sannan suka bari ya shiga. Yana shiga ya fara inda-inda, ganin haka yasa Sarki Abdallah ya buga masa tsawa bakin sa na karkawa ya fara magana sai kuma wayar Sarki Abdallah ta fara ruri. Shiru ya yi har Takawa ya ɗauka bakinsa ɗauke da sallama, murmushin ƙarfin hali ya aro ya yafa a saman fuskarsa bayan sun gaisa Sarki Abdallah yace, "Siriki ina niyyar kiranka ka riga ni." Daga cen ɓangaren Sarki Aminullah ya yi dariya yace, "Na ji a jikina ai Siriki da fatan duk kuna lafiya?" Sarki Abdallah kamar wanda aka soso masa inda yake masa ƙaiƙayi har ya manta da Dogarinsa da ke tsugunne yace, "Ehto Siriki lafiyar fa da sauƙi." Gaban Sarki Aminullah ne ya faɗi a ɗan razane yace, "Ko shi yasa na kira Fahima ban same ta ba?" Sarki Abdallah ya sauke gwauruwar ajiyar zuciya yace, "Ko kana da labarin Me babban ɗaki ta dawo?" Sarki Aminullah yace, "Kamar ya Me Babaan ɗaki ta dawo kamar wacce ta yi tafiya? Siriki wannan wacce irin magana ce? Dama wanda ya mutu yana dawowa ne?" Nan take Sarki Abdallah ya zayyane masa duk abin da yake faruwa yana gabda ƙarƙare maganar, Maryo ta ban ko ƙofar ta yi tsaye a kansa tana faɗin, "Sarki Abdallah na aiko kiran ka na ji shiru ka wuce muje ina da magana me muhimmanci." Shiru ya yi yana kallonta ya ga babu alamun tsoro a tattare da ita, tarin da Sarki Aminullah ya yi ne yasa shi tunawa da wayar da ke kare a kunnensa. Gyaran murya ya yi yace, "Sirikina ina fatan ka ji muryar yarinyar da take magana?" Sarki Aminullah da mamaki ya gama cika shi murya a sanyaye yace, "Wai me yake faruwa ne?" Sarki Abdallah da ya gama ƙagauta yace, "Ina na sani. Maganar gaskiya yarinyar nan dole ta bar mana masarautar nan wallahi, ba zan iya ba yau Allah ne kaɗai yasan adadin rayukan da muka yi asara. Ina dalili shi kansa Maleek ɗin na gaya masa idan ba zai iya sallamarta ba ya bi ta su tafi cen, amma nidai su bar mini ƙasata ta zauna lafiya tare da talakawa ba tare da wata tarzoma ba babu gaira babu dalili." Sarki Aminullah shiru ya yi don har ga Allah shi ba sauraron sauran jawabin Sirikin nasa yake ba, fargabarsa ɗaya idan ta dawo tashi masarauta wanne irin tashin hankalin za su shiga. Yana tsaka da tunani ya ji Sarki Abdallah yace, "Ina matsanancin tausayin talakawa na saboda ba su ji ba basu gani ba babu yadda za a yi a dinga salwantar da rayuwarsu suna mutuwar wulaƙanci." Sarki Aminullah ya haɗiyi yawu da ƙyar yace, "To Allah ya rufa asiri." Daga haka suka yi sallama ya mayar da kallonsa ga Maryo da take tsaye fuska a murtuke babu walwala. Cikin izza da isa irin ta tsatson jinin sarauta ya kalleta ya saki murmushi yace, "Zan bi ki ne kawai saboda ina gudun zalincin da zaki aiwatarwa talakawa na, ko kaza bana fatan ƙara rashinta bare bil Adam." Yana gana faɗa ya miƙe tsaye yana gyara zaman rawaninsa sannan ya wuce, da sauri Maryo ta yi gaba fuuuuu har mamakin saurinta suke yi saboda wata irin tafiya take yi kamar za ta tashi sama. Lokacin da suka shiga Fulani Babba na tsaye ƙiƙam kamar gunki ko motsin kirki ta kasa yi, Me Babban ɗaki tana kishingiɗe a jikin lallausan daddumai. Mazauninsa ya je ya zauna ga mamakinsa sai ya ga mutane na ta hankaɗowa cikin fadar wasu har bakin ƙofa. Maryo ce ta miƙe tsaye ta fara kallonsu ɗaya bayan ɗaya, sannan ta juya ta kalli Fulani Babba ta nunata da ɗan yatsa sai a lokacin Fulani ta motsa tana sauke ajiyar zuciya kamar wacce ta yi tseren gudu. Kallon mutanen wurin ta yi ta ce, "Ke baƙar munafuka maza ki buɗe baki ki gaya musu mugun halinki da mugun abin da kika aikatawa waccen baiwar Allahr da bata ji ba bata gani ba." Fulani Babba ta durƙushe a wurin ta ce, "Don Allah ki rufa mini asiri" Tun bata rufe baki ba Maryo ta sa hannu ta matse bakinta nan take ta fasa ƙara sai ga haƙoran Fulani Babba suna faɗowa ɗaya bayan ɗaya kamar tsabar masara. "Allah ya taimake ka ya baka yawon rai, lafiya me yake faruwa ka nemi magana da ni kuma na ga duk kayi wani iri." Damuwarsa ce ta bayyana a fili ƙarara ya kalleta fuska ba walwala yace, "Masarauta Adamawa ce babu lafiya wani abun almara wai Me Babban ɗaki ta dawo." A razane ta kalle shi nan ya zayyane mata abin da yake faruwa, suka haɗu suna jajantawa. Sun jima suna wannan hirarar sannan Sarki Aminullah ya dube ta yace, "Zaliha na kira ki ne dangane da yaran nan." Da sauri ta juyo gabanta na faɗuwa ta ce, "Ina fatan ba wani laifi ya aikata ba?" Murmushin gefen baki ya yi yace, "Ba zamu yi muku maganarsa ba sai idan laifi ya yi?" Fulani Zaliha sai ta ji duk bata kyauta ba ta ce, "Tuba nake ranka shi daɗe" Sarki Aminullah ya ci gaba da cewa, "Lokaci ya yi da ya dace su fito da matan aure su yi aure. Saboda shekarunsu sun fara ja nima ina buƙatar ganin jika na na wurin ƴaƴana maza." Murmushi Fulani Zaliha ba ƙaramin daɗi ta ji ba ta ce, "Gaskiya na ji daɗin wannan maganar Ranka shi daɗe. Kuma dama kwana biyun nan ina zargin akwai yarinyar da ya faɗa soyayya da ita, amma in sha Allah zan tuntuɓe shi a daren yau ba sai gobe ba." Murmushi Sarki Aminullah ya yi yace, "Zaliha yaushe kika bar kunyar ki ta fulani ne? Kamar ba ke ce wacce ko kallona bakya iya yi, amma yanzu na ga sam kin canza." Murmushi ta yi ba don karta waiwayo da abin da ya wuce ba da ta bashi amsa, saboda tun lokacin da kowa ya yi watsi da su ita da Saif tun yana ƙarami ta cire kunyar idonta bata yi wa kowa kara akan Saif. Murmushi ta ƙara yi sannan ta ce, "Haba dai Ranka shi daɗe kawai dai haka ka gani." Daga haka suka ci gaba da hira cikin farinciki. "Saif Mahaifinku ya same ni wata magana." Kallon mahaifiyarsa ya yi cikin nutsuwa ya gyaɗa mata kai, ta ci gaba da cewa, "Yace kai da ɗan uwanka ya kamata ku fito da matan aure, idan kuma akwai wacce kake so sai ka sanar da ni ko ka sanarwa da mahaifinka." Murmushi ya yi ya fara yi wa mahaifiyarsa bayani kai tsaye saboda ya mayar da ita kamar abokiyar shawararsa, ya numfasa yana faɗin, "Ammi wallahi ni dai babu wacce nake so sai ƴar Abuh amma bansani ba ko za ta amince da ni." Farinciki ne ya lulluɓe zuciyar Fulani Zaliha ta ce, "In sha Allah za ta ma amince da kai, amma idan haka ta faru na fi kowa farinciki." MEYE HARSASHEN KU KO ABUH ZA TA AMINCE DA AUREN MASOYIN MARYO? 😢 _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [09/12/2021, 14:24] Ameera Adam🌚: 44... Murmushi Saif ya yi don ko ba komai Mahaifiyarsa ta ƙara masa ƙwarin gwiwa kuma za ta ƙaunace ta don ya hangi zallar ƙaunarta a idanun mahaifiyarsa. Miƙewa ya yi yana murmushi sai kuma ya ji duk kunya ta kamashi, da sauri-sauri ya miƙe ya fice daga ɗakin. Mahaifiyarsa ta kalle shi tana dariya a zuciyarta tana mamakin wai yau Saif ita yake jin kunya. Saif yana fita ya wuce ɗakinsa yana jin wani irin farinciki a zuciyarsa, wata irin ƙaunar Abuh ce take yunƙuro masa da shi kansa be san lokacin, da ya tsunduma cikin kogin sonta ba lumshe ido ya yi kamar a mafarki sai gani ya yi fuska Maryo raɗau a cikin ƙwayar idonsa. Da sauri ya buɗe idonsa yana sai yake jin kansa na juya masa, wata iska ya furzar me zafi yana jin ransa yana masa wani irin suya. Kwanciya ya yi yana jin ransa babu daɗi a hankali tunanin Maryo ya fara yi masa kai komo, ta shi ya yi zaune yasa hannu biyu ya rafka uban tagumi. Gabaɗaya mutanen wurin ido suka zuba mata hankali a tashe, tsit wurin ya ɗauka ban da ihun Fulani Babba babu abin da yake tashi a wurin. Sarki Abdallah ne ya kalli Maryo ya buga mata tsawa cikin fusata, "Ke! Wanne irin abu kike yi haka ne?" Maryo bata saurare shi ba ta kalli Fulani Babba da take cikin galabaita ta ce, "Muna sauraronki " Fulani Babba ta kalli Me babban ɗaki da ke zaune a gefe ta ce, "Don Allah ki gafarce ni Ranki shi daɗe ki yafe mini amma don Allah karku tona mini asiri." Muhsin a maza shi ne babban ɗan Fulani Babba, shekararsa Ashirin da biyar. Shigowarsa kenan fadar ya ga halin da mahaifiyarsa take ciki, wata razanannniyar tsawa ya bugawa Maryo da har sai da wasu daga cikin mutanen Fadar suka tsorata, a hassala ya ƙarasa ciki yana cewa, "Ke me kike yi haka ne baki da hankali ne?" Maryo bata juyo ta kalle shi ba kuma bata fasa abin da take yi ba. Kallon Fulani Babba ta yi fuska a haɗe, tun kafin ta fara magana Fulani babba jiki na rawa ta fara magana, "Don Allah ku gafarce ni amma tabbas na yi kuskure, wallahi tsautsayi ne da sharrin sheɗan." Me babban ɗaki ta ɗago ta kalli Fulani Baba ta ce, "Na tabbata ba ni ba hatta sheɗan ɗin sai an yi muku hisabi da shi saboda sharrin da kika yi masa, munafuka algunguma." Muhsin shiru ya yi yana mamakin wannan lamari Maryo ta kuma kallon Fulani babba tana gyaɗa mata kai, da sauri Fulani Babba ta haɗa hannuwa cikin tashin hankali tana roƙonta, "Don Allan ki yi haƙuri karki azabtar da ni wallahi zan faɗa." Maryo murmushi ta yi ta fara takawa a hankali a nemi wuri ta zauna, ta ɗebo manyan idanuwanta ta zubawa Fulani babba wanda da alama ta yi haka ne domin ta fara sauraron abin da za ta faɗa. Fulani Babba kallon mutanen fadar ta yi ta sunkuyar da kai cikin nadama, don ta rayawa zuciyarta gwara ta faɗi abin da ta aikata ko ta huta, don waccen azabar ma da ta yi mata bata gama sakinta ba. Ɗagowa ta yi ta kalli Sarki Abdallah idanunta suka ciko da ƙwallah, don ta san ƙarshen zamanta ya zo da shi ta fara da cewa "Shekaru talatin da biyar da suka gabata Sarki Abdallah ya kasance sarki a masarautar Adamawa, kuma ya gaji mahaifinsa ne wanda ya yi sarauta kafin shi, bayan rasuwarsa aka naɗa shi sakamakon shine ɗansa ɗaya tilu namiji. A lokacin da aka naɗa shi sarauta mu biyu ne kaɗai matansa ni ce uwar gida Fulani Maimuna amarya, a lokacin ƴaƴana uku duk mata ƴaƴan Fulani Maimuna biyu amma haihuwarta uku namijin ya rasu. bayan shekara biyar da hawansa karagar mulki sai ya auro Fulani Fahima ita ma da aurenta ko shekara ba ayi ba wan mahaifiyarsa ya bashi ƴarsa wato Fulani Sadiya. A haka dai idan ka ga zamanmu zaka rantse da Allah lafiya ƙalau muke zaune, amma a baɗini ba haka bane ta ciki na ciki ne, babban abin da ya fi ɗaga mini hankali yadda duka amaren da aka yi mana ba su jima ba kowacce tana ɗauke da juna biyu, kuma har lokacin babu wanda ya haifi ɗa namiji da ni da Fulani Maimuna. A da kafin ƙarin auren Sarki Abdallah ba ma zaman daɗi da Maimuna amma da ya yi aure sai na janyo Maimuna jiki muka haɗewa Fahima kai, tun Fulani Maimuna na ɗari-ɗari dani har ta saki jikinta muka ɗinke kamar babu wani da ya taɓa shiga tsakaninmu. A kwana a tashi har Allah ya sauki Fahima lafiya sai ga shi ta haifo ɗan ta namiji wato Abdulmaleek, a lokacin saboda baƙin ciki har ji nake kamar zan mutu, amma sai na danne na fara neman hanyar da zan halaka shi ta ruwan sanyi ba tare da wani ya zarge ni ba. Me babban ɗaki su biyu ta haifa daga Sarki Abdallah sai ƴar uwarsa Zakiya, a lokacin Me babban ɗaki haka ta shiga nannan da Maleek ita ce yi masa wanka da sauransa, tun ranar da aka haife shi ta ɗaga shi sama tana yi masa kirarin magajin sarki, wannan ba ƙaramin baƙantamin rai ya yi ba. Haka nima na sake aka ci gaba da nuna farinciki har da ni kamar babu abin da yake raina, har Maleek ya cika wata uku a lokacin ne kuma Fulani Sadiya ita ma haifo ɗan ta namiji kamar haɗin baki, a lokacin ne nida Maimuna muka shiga fafutukar neman yadda za mu kashe yaran amma duk inda muka je wurin bokaye sai ace mana Me babban ɗaki na jiƙa sanwa da sauran magunguna tsari tana wanke su da shi, don haka babu wani abu da za su iya yi akai, idan ma mutum ya matsa mugun abin da ya yi zai iya komawa kansa. Wannan lamarin ba ƙaramin ɗaga mana hankali ya yi ba, daga ƙarshe sai Maimuna ta same ni ta ce ita kam ta fauwalawa Allah lamuranta amma ta tuba ta daina harkar biye-biyen malamai da bokaye, gudun karta zarge ni ko wata rana ta tona mini asiri yasa nima na sauya yanayi na cikin damuwa, na nuna mata tabbas mun aikata kuskure amma mu watsar da komai mu fauwalawa Allah buƙatunmu, wanda sam a zuciyata ba haka bane. Haka na ci gaba da biye-biye na a sirrance wani kuma na tura Larai baiwata ta je mini, a haka har wata rana na je wurin wani boka wanda yace tabbas zai yi mini aiki amma da sharaɗi, ban damu da sharaɗin da ya gindaya mini ba nan take na amince, wata laya ya ciro daga bakin wani zomo da ke tsugunne a gabansa ya miko mini yace ina shiga gida karna kula kowa na wuce sashen Me babban ɗaki, ko na shiga karna yi mata magana kawai na damƙi hannunta na saka mata layar a ciki nan take ni da ita zamu ɓace daga wurin. Kamar ƙiftawar ido haka muka ɓace daga wurin sai gamu a ƙogon dutsen da boka yake, da mamaki Me babban ɗaki ta kalle ni ta ce, "Lafiya ina ne nan kika kawo ni?" tun kafin na bata amsa Boka ya ja hannunta ya zaunar da ita akan wani farin dutse, kallo na ya yi yace, buƙatarki za ta ci gaba da biya matsawar tsohuwar nan za ta rayu a cikin kogon nan, amma muddin kika bari ta koma masarautarku kashinki ya bushe. Ban damu da abin da ya faɗa ba na bushe da dariya na ce, " Wanene ya isa ya mayar da ita idan ba ni ba? n Ni kuwa ko a mafarki ba na jin zan aikata wannan saɓon." Boka yace mini, "Ba za ta taɓa komawa ba, amma ba za mu kashe ta ba. Sai dai za ta zama matacciya a cen masarautarku, yanzu kina komawa za ki ga me siffarta a mace muddin ba ke kika bada ƙofar da za a fahimci wani abu ba babu wanda zai gane ba ita bace." Murmushin jindaɗi na yi masa na juya zan tafi Me babban ɗaki ta fashe da kuka ta ce, "Don Allah karki yi mini haka..." na katse ta da murmushi sannan na yi ficewa ta, abin da ban sani ba ashe duk wannan lamarin da nake nima ina ɗauke da ƙaramin cikin wata uku, kuma ina dawowa na samu ana ta rusar kuka ina zuwa ɗakin Me babban ɗaki na ganta yashe a kwance har sai da na ja baya na razana, ina fargabar kar asirina ya tonu. Ga duk wanda ya ga halin da na shiga zai ɗauka kiɗimewar mutuwa ce ta sani haka, nan kuwa ba haka bane ina fargabar kar a wayi gari Me babban ɗaki ta dawo, Kuma a washegari ne ɗan wajen Fulani Sadiya shima ya mutu, Fulami Maimuna da take da ciki wata bakwai shima ta haifeshi babu rai, ashe cikin ɗa namiji gare ta, Maleek kuma ya kwanta jinya. Haka na ci gaba da kaiwa Boka ziyara Me babban ɗaki tana cikin kogon dutsen tun tana yi mini kuka da magiya har ta daina, tsuntsaye da namun dajin da Boka yake kamowa shi yake gasa musu suna ci ita shi, a haka aka ci gaba da rayuwa har Allah ya sauke ni lafiya na haifi ɗana namiji. Yadda na ɗauka Sarki Abdallah zai yi zumuɗi sai na ga sam ba haka bane, amma ban damu ba tun da nima na haifi namiji, idan aka cire Maleek duk wacce za ta haifi namiji a bayan nawa yake. A kwana a ta shi har yara suka girma duk bokaye na sun gagara kashe Maleek, sai na lura da Takawa yana jan Maleek a jiki har yana koya masa wasu al'amuran dangane da harkar mulki, nan take na sa boka ya yi aiki akansa don ya ja ra'ayinsa a harar karatun nasara to na san muddin ya karkata ana ko da nan gaba ne bayan mutuwar Sarki Abdallah, jagororin da za su yi naɗin sarauta ba za su naɗa shi ba za su ce ya fi karka da ilimin nasara be san abin da ya shafi sha'anin mulki ba. Wani tashin hankali dana shiga da boka ya sanar da ni akwai yarinyar da Maleek zai auro wacce za ta zame mini ciwon ido nan gaba, yace wai tana daga cikin FILSIFI, shi yasa ko da Maleek ya auro Shukra na fi kowa tsamari wurin kafa mata ƙahon zuƙa dukda dama kowa ba ƙaunarta yake ba. Duk ƙulle-ƙullen da na yi har ta bar gidan nan ashe ban tsira ba sai ga shi yanzu ta ƙara dawowa kuma ta bankaɗo abin da na ɓoye shekara da shekaru." Kamar haɗin baki haka Fadar gabaɗaya suka ɗauki salati cikin al'ajabi, Sarki Abdallah idanunsa ne suka yi jawur saboda ɓacin rai, a hankali hawaye ya fara gangarowa daga idanunsa. Tsam ya tashi ya ƙarasa wurin mahaifiyarsa ya rungumeta ya fashe da kuka, Dogarawan Sarki sunkuyar da kansu suka yi zuciyarsu babu daɗi, Muhsin wani irin abu ne ya turniƙe shi yana jin kalaman Mahaifiyarsa na maimaita kansu a cikin ƙwaƙwalwarsa. Maleek da ke gefe shiru ya yi ya kafe Fulani Babba da idanu, dan har lokacin mamakin abin ta faɗa yake yi gani yake kamar a mafarki ne, ɗan yatsansa ya tura baki ya ɗan gantsa cizo, jin zafin haƙoransa a hannunsa yasa ya tabbatar da gaskiya ne abin da yake faruwa. Maryo murmushi ta yi ta kalli Fulani ta ce, "Wanne hukunci kike so na yi miki? Kuma ki gyara bakinki ni ba shukra bace wataƙila wata filsifin ce ba ni ba." Fulani Babba ta ce, "Don Allah ayi mini afuwa, ki gafarce ni Shukra akan cutarwar da na yi miki." Maryo bata saurareta ba ta miƙe ta fara tsalleke mutane tana murmushi ta fice, tana fita Fulani babba ta zunduma ihu tana yage-yage haɗe da kaiwa mutane wawura. Haƙwaranta na ƙasa ta fara tsinta tana haɗiyewa tana gama cinye su ta danne wani Dogari tun kafin a yi wani yunƙuri, ta naushi bakinsa ta tura hannunta ta ƙwaƙulo haƙoransa ta fara wurga su baki ɗaya bayan ɗaya tana haɗiyewa. Da ƙyar aka ƙwaci dogarin fuskarsa har ta fara kumbura, da sauri Muhsin ya ƙarasa yana mata magana ta janyo shi za ta kai masa duka a baki, da kyar aka ƙwace shi ba a ɗau lokaci ba Sarki Abdallah ya bada umarni da akaita turu (Gidan mahauka) a cen ɗinma yace a ware mata ɗaki ita kaɗai don karta illata sauran. Cikin zumuɗi Fulani Maryama ta sanarwa da Sarki Aminullah yadda suka yi da Salman, shi ma ba ƙaramin daɗi ya ji ba. A nan yake sanar mata da Saif shima yana da wacce yake so daidaitawa kawai ya rage su yi, murna ta nuna a fili dan ita tana murnar ne saboda buƙatar kanta, da nishaɗi ta dube shi ta ce, "Allah ya taimake ka sai dai wani hanzari ba gudu ba, ka san fa Salman be cika kule-kule ba don yace ka nemo ɗaya daga cikin ƴaƴan abokanka in yaso sa daidaita." Sarki Aminullah ya ɗan yi jim har sai da gaban Fulani Maryama ya faɗi tana fargabar kar ya ƙi amincewa, ta ga ya kalle ta yace, "Eh to sai dai na yi wa Sarkin Gaya ko Sarkin Ƙaraye magana na san suna da ƴaƴa mata ko kuma Sarkin Rano." da sauri Fulani Maryama ta ce, "Allah ya taimake ka Sarkin Gumel ma kamar yana da ƴaƴa ƴan mata, na ce ko a cen za mu nemi iri don yaran suna da tarbiyya." jinjina kai Sarki Aminullah ya yi yace, "Babu damuwa zan duba na gani." Satar kallonsa ta yi tana addu'ar Allah sa haƙƙonsu ya cimma ruwa don idan Salman ya auri ƴar Sarkin Gumel kakarsu ta yanke saƙa. Kallon tsaf ya yi mata yace, "Maryama na aika a zo da Sarkin Wanzamai a sirrance ya baki magani don gaskiya na damu da ganin kanki haka babu gashi, wannan ba ƙaramar matsala bace ace haka kawai ka wayi gari babu gashi ko silli ɗaya, ko ma'askin dare fa ba haka yake yi ba." Fulani Maryama yaƙe ta yi ta amsa masa don kada ta yi gardama ta tonawa kanta asiri ana zaune ƙalau, gara ta zuba ido masu maganin su zo su gama abin da za su yi su tafi. Ta tabbata makarin komai yana hannun Marduska don Marduska ya wuce tunanin me tunani. Salman ya yi mamakin yadda ya sanarwa da Abuh amma babu ko ɗigon farinciki a tattare da fuskarta, amma kafin wannan lokacin ya tabbata ko mahaukaci ya san Abuh ta fara ƙaunarsa, be tursasa mata ba sai ma nuna mata ya yi da be fahimci abin da take nufi ba. Don haka ko da ya ga ta yi shiru ya kau da kai gefe don ƴan muskilancin ne akansa yace mata, "Zainab ki yi nazari akan abin da na sanar da ke amma ba zan tilasta miki ba, ina sauraronki zuwa nan da kwana biyu." Yana gama faɗa ya wuce, Abuh zama ta yi sai ga hawaye na bin fuskarta wannan shi ake kira da gaba kura baya siyaƙi. Idan har ta ce bata ƙaunar Saif ta yi ƙarya hasalima da shi take kwana take tashi a ranta, amma ta san hakan ba me yuwu bane. Ya za ayi ta auri mutumin da ƴar uwarta take begen shi babu dare babu rana. Girgiza kai ta fara yi tana faɗin, "Inaa sam wannan ba zai taɓa yuwuwa ba." Miƙewa ta yi da niyyar shiga sashen Fulani Maryama don ta sanar da mahaifiyarta halin da ake ciki amma tana gabda shiga ƙofa wasu dogarawa suka dakatar da ita, da mamaki ta kalle su da niyyar buɗe baki ta yi magana taji ɗaya yace, "Umarni ne daga Fulani Maryama ta ce kar a ƙara barinki ki shiga sashenta." Babu yadda Abuh ta iya haka ta juya tana jin zuciyarta babu daɗi, sashen su ta nifa zuciyarta da tunane-tunane, ta ɗaga labulen ɗakinta ta ji Fulani Zaliha ta ƙwala mata kira wanda ya yi daidai da faɗuwar gabanta, kamar mara jini a jiki haka ta juya jiki a sanyaye ta nufi turakar Fulani Zaliha ta russuna cikin girmamawa ta gaishe ta, "Barka da hutawa ranki shi daɗe" Murmushi Fulani Zaliha ta yi ta ce, "Barka dai ƴata ya ganki duk wani iri me yake damunki?" Abuh da sauri ta ɗago sai kuma ta ga sam ba za ta iya sanar mata da halin da take ciki ba don ta tabbata uwa uwa ce dole idon ta ce bata son Saif dole ba za ta ji daɗi. Don haka ta sunkuyar da kai ta ce, "Na je ganin Inna ta ne Dogarawa suka hanani shiga." Fulani Zaliha ta ce, "Kamar ya? Waye ya isa ya hanaki shiga ko Maryaman ce ta bada umarni?" A hankali ta gyaɗa mata kai. Ajiyar zuciya ta sauke ta ce, "Wannan ba hurumi na bane amma zan yi wa Takawa magana." Da sauri Abuh ta ce, "A'a don Allah karki gaya masa kar na yi wa Fulani Laifi." Murmushi Fulani Zaliha ta yi ta ce, "Zainab me ya sa kin fiye tsoro ne, yauwa ɗazu mun yi magana da Saif. Takawa yace su fito da matan aure shi dai yace kece zaɓinsa, ba ƙaramin daɗi na ji ba saboda ƴar gida za muyi amma ban sani ba za ki amince da shi?" Gabaɗaya Abuh dabaibayewa ta yi gumi ya fara tsattsafo mata, shiru ta yi ta faɗa duniyar tunani a duniya dai ta san Fulani Zaliha tana matuƙar ƙaunarta, bata taɓa ƙyamarta ba tana yi mata abin da uwa za ta yi wa ƴar ta. Jin shirun ne yasa Fulani Zaliha ta dafa kafaɗarta wanda shi ne silar dawowarta daga duniyar tunanin da ta faɗa, ɗagowa ta yi suka haɗa ido ta sauke kanta ƙasa, Fulani Zaliha ta ce, "Zainba! Na ɗauke ki tamkar ƴata idon bakya son Saif ki gaya mini ba zan miki dole ba, sai na sashi ya nemi wata." A hankali Abu ta ce, "Ba haka bane Ranki shi daɗe na amince." murmushin jindaɗi Fulani Zaliha ta ce, "Masha Allah, Tashi ki je Allah ya tabbatar da Alheri." Abuh bata iya amsawa ba ta miƙe a kunyace ta fice ta nufi ɗakinta, tana shiga ta fara zarya har lokacin gumi ne yake karyo mata. SHA BIYAR GA WATAN SATUMBA A SHERAR DUBU ƊAYA DARI TARA DA HAMSIN DA ƊAYA (15/09/1951) Wanda ya yi daidai da ranar Laraba a ranar ne Sarki Aminullah da Abokinsa Sarkin Gumel, suka sanya ranar auren Salman Aminullah Muhammad da Safiyya Yusuf Kabir sai Saifullah Aminullah Muhammad da Zainab Ya'u Me Nagge. An saka ranar aure wata uku farinciki wurin waɗanan iyalan abin ya ƙi misaltuwa. MARYO NA CEN AN YI WUFF DA MASOYINTA😢 _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [10/12/2021, 19:46] Ameera Adam🌚: 45... Lokacin da labarin sanya aurensu ya isa kunnuwan Abuh haka kawai ta ji gabanta ya yanke ya faɗi, tana daga ɗakinta a kwance ta ji Jakadiya tana ta zabga bambaɗanci da fadanci. Kasancewar Fulani Zaliha na cikin farinciki yasa ta kalli Jakadiya da murmushi ɗauke a saman fuskarta ta ce, "Jakadiya anjima a aiko a karɓi tukwici." Jakadiya sakin baki ta yi tana kallon Fulani Zaliha don Allah ya sani tun da take da ita sai da irga adadin murmushin da ta taɓa gani a saman fuskar Fulani Zaliha, hasalima tun da take bata taɓa daɗewa a sashenta kamar daɗewar da ta yi yau ba. A zuciyarta ta fara godia don ta tabbata tun da ta samu arziƙin sakin fuska, ba ƙaramar kyauta za ta samu ba. Wannan ya bata damar yashe baki ta ci gaba da bambaɗanci har Fulani Zaliha ta sallame ta. Jakadiya na fita bata zarce ko ina ba sai sashen Fulani Maryama, kanta tsaye ta yi sallama ta shiga. Tun daga tsakar gida Jakadiya ta fara rangaɗa guda, tana juyi a tsakar gida. Inna Habi dake ɗaura lalle daga ɗakinta tana hangota ta girgiza kai, don gabaɗaya ta gama fahimtar Jakadiya munfuka ce ajin farko. Kasancewar Fulani Maryama na cikin farin ciki yasa ta bawa Bayin ta damar kowa ya tafi sabgar gabansa na tsawon wunin. Jakadiya na shiga ta tsugunna nan ma ta fara bambaɗanci kamar yadda ta yi wurin Fulani Zaliha, sai da ta gama ta gyara zama ta ce, "Allah ya taimake ki wai ni kam don Allah wace tsiya ce ta ƙarewa Zaliha da Ɗanta, su rasa wacce zai aura sai ƴantacciyar Baiwa. Kai wallahi ni kam ba ƙaramin takaici na ji ba wannan ai salon ya ja wa Masarautar nan zagi ne saboda Allah, duk ƴaƴan Sarakunan ƙasar nan amma ya rasa wa zai so sai waccen figaggiyar ƴar Fulanin." Fulani Maryama da tun shigar Jakadiya Murmushi ne kwance a saman fuskar, ta kuma washe baki tana dariya me sauti ta ce, "Im muguwar kaza ta fara shiga akurki duk wacce ta zo sai ta tare ta. Don haka ni fes a gareni." Jakadiya ta yi murmushi ta ce, "Fulani Maryama kenan. Ba a sanin murnar karen da bashi da wutsiya." Fulani Maryama ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya cikin izza da isa ta ce, "Jakadiya duk Karen da bashi da wutsiya dube shi da kyau ƙwayar idonsa za ta gaya miki amsar halin da yake ciki." Jakadiya ta saki shewa ta ce, "Amma kin fi kowa sanin Zaliha Miskila ce cikin mata ba kamar sauran kishiyoyinku take ba, na tabbata wannan karen kallon ƙwayar idonsa za yi miki wahala." Fulani Maryama ta buɗe hannuwa alamar rashin damuwa ta ce, "Jakadiya kin manta da ko anci birnin Kura ba a ba kare dillanci, Maryama nake ginshiƙin dutse kowa karo da ni za shi ƙasa. Sam ban damu da wacce Saif zai aura ba ko da kuwa mahaukaciya ce burina na dai kawai ya yi aure shi da Salman, idan na fara cimma wannan matsayar sai na san yadda zan ɓullowa sauran lamura, domin shan tabar kwaɗo da baki da hanci yake." Jakadiya ta kalli Fulani Maryama tana jinjina kai ta saki murmushi ta ce, "Maryama ƙarfin gwiwarki da izzar ki yana matuƙar birge ni, ba kowa yake gane murmushin jaki ba wani idan ya gani ɗauka zai kuka yake wani kuma ya yi tsammanin cizo zai kai." Fulani Maryama ta gyaɗa kai kamar ƙadangaruwa ta ce, "Tabbas kuwa, domin kwana a gado daban da sabon kabari." Jakadiya ta sauya fuska zuwa yanayin jimami ta ce, "Oh! Sabon kabari me sa a tuna Allah. Maryama yaushe za mu tuba ne?" Fulani Maryama ta ce, "Lokacin da na gama biyan buƙatar rayuwata." Jakadiya ta kalleta a kaikace ta ce, "Ai kuwa buƙatar me rai bata cika sai kwana ya ƙare." Ɗaure fuska Fulani Maryama ta yi ta ce, "Wani me ran ya kan cika buƙatunsa sai kuma rai ya yi halinsa. Jakadiya idan muna raha ki bar sako mini zancen mutuwa." Jakadiya cikin zuciyarta take mamakin baƙi hali irin na Fulani Maryama da bushewar zuciya, da mamaki ƙarara asaman fuskarta ta ce, "Sarautar Allah kare a bakin kura. Maryama wacce irin zuciya gare ki." Kai tsaye Fulani Maryama ta bata amsa, "Wacce aka ciro daga jikinki aka liƙa mini." Jakadiya ta shi ta yi ta ce, "To Allah ya ƙwato ki don na lura kin yi nisa bakya jin kira." Fulani Maryama ba ta tanka mata ba, saboda ta lura idan ta biyewa Jakadiya sai ta ɓata mata rai alhalin tana cikin farin ciki. Jakadiya na fita bata zame ko ina ba sai ɗakin Inna Habi. Rangaɗa uwar sallama ta yi Inna Habi ta amsa mata ba yabo ba fallasa. Zama ta yi a gefe dokin ƙofa ta ce, "Uwar amarya sai kuma nake jin abun alheri." Inna Habi ta ɗauka murnar Salman take yi mata, murmushi ta yi ta ce, "Eh wallahi Yarima ya kusa girma, Allah ya nuna mana lokacin." Ganin kamar Inna Habi bata fahimci inda zancen ya dosa ba Jakadiya ta ce, "Ban da abin ki Habi na san dai Abu ai ba ta fari bace a wurinki, to karar me za ki yi?" Inna Habi ta yi murmushi ta ce, "Jakadiya karar me zan yi kuma?" Jakadiya ta ce, "Yooo na ga ina yi miki Allah sanya alherin Abu kina kaucewa, Allah na tuba ai farinciki za kiyi Namiji kamar Saif me nasaba da tushe har aka yi masa baiko da Abu ai abin nunawa duniya ne." Cikin rashin Fahimta Inna Habi ta ce, "Wace Abun aka yi wa baiko da Saif?" Jakadiya gulma na cinta ta ce, "Abuh ƴar wurinka mana ai duk tare aka yi musu baiko da Salman. Kuma ance yana mutuwar son Abuh ita ma tana ƙaunarsa, wai ke baki sani bane." Inna Habi ta fahimci bugun cikinta Jakadiya take don haka ta ce, "Na yi mamaki da Abuh ta zaɓi Saif ne, mun yi magana da ita ta ce akwai wani Yaro da suke taɗi. Kin san yaran yanzu baka gane alƙibilarsu." Jakadiya sam ba haka ta so ba ta miƙe tsaye tana faɗin, "Yooo ke kuwa ga wurin da za a haɗu da babban rabo, ko ba komai ai ta auri jinin Aminullahi."tana gama faɗa ta fice daga gidan. Al'ummar da ke zaune a masarautar Adamawa ba ƙaramin mamakin mugun halin Fulani Babba suka yi ba, saboda su dai a iya zamansu da ita basu taɓa kawo za ta aikata makamancin abin da ta furta da bakinta ba. A iya saninsu dai ita mace ce me son girma da son shugabanci, amma ba su yi zatan son matsayin nata har ya kai ga haka ba. Wunin ranar haka kowa ya wuni da ta'ajibinta, wasu na tsine mata wasu kuma suna ganin kuskurene da kowanne ɗan Adam yake iya aikatawa. Amma mafi yawa daga ciki sun fi danganta hakan da son zuciya, zalinci da rashin imani. Maryo na komawa ɗaki ta zauna ita kaɗai a ɗaki ta haɗa kai da gwiwa tana zubda wani irin hawaye me ƙuna, zuciyarta za fi take ga wani irin raɗaɗin ƙaunar Saif da yake ƙara nuƙurƙusar zuciyarta. Hannu ta sa ta dafe saitin zuciyarta ta kuma fashewa da kuka, nan take wani irin tari ya turniƙeta tun tana yi daga zaune har ta fara galabaita tana dafa bango tana ƙoƙarin miƙewa, feshin jini bakinta yake yi har ta fara fita daga hayyacinta. Dafa bango ta fara yi tana tafe tana labuben hanya hannunta ɗaya na kan ƙirjinta, hannu ɗaya tana laluben ƙofar fita. Tana zuwa bakin ƙofa ƙarfinta ya ƙare nan ta yanke jiki ta faɗi hancinta da bakinta na zubar da Jini. Lokacin da fadar ta watse jiki babu ƙwari Maleek ya miƙe kallon Mahaifinsa ya yi yana jin tausayinsa na mamaye zuciyarsa, musamman yadda ya ga har zuwa wannan lokacin yana rungume da Mahaifiyarsa yana zubda hawaye, ita ma hawayen take yi tana shafa kansa da rawanin kansa yake ƙoƙarin zamewa. Ganin hakan ne yasa Dogarawa suka sallami kowa harda su suka fita zuwa bakin ƙofa, ya zama ɗakin daga Sarki Abdallah, Me babban ɗaki sai ƴaƴansa maza guda Uku. Maleek ga ni ya yi ba zai iya ci gaba da gani ba don zuciyarsa ta fara karyewa, don kukan da Muhsin yake ba na farinciki bane. Yana kukan halin da Mahaifiyarsa take ciki da abin da ta aikata, don gabaɗaya ji yake ya tsani kansa yana kunyar fita ya haɗa ido da sauran al'umma. Lokacin da Maleek ya nufi sashensu gabansa ne ya ci gaba da faɗuwa don be san abin da zai je ya tarar, jiki babu ƙwari ya kamar marar laka a jiki haka ya fara takawa har zuwa bakin ƙofa, sama-sama yake jiyo nishinta tsoro ne ya fara kamashi don gani yake idan ya leƙa kamar zai iya ganin abin da zai kuma sumar da shi, kamar marar gaskiya haka ya fara tafiya saɗaf-saɗaf har ya zura kansa ya leƙa don ganin abin da yake faruwa. Zaro ido waje ya yi lokacin da ya yi tozali da halin da take ciki, da sauri ya ƙarasa hankali a tashe ya fara ƙwala mata kira amma bata iya buɗe idonta ba bare ya sa ran za ta kula shi ba. Hankali tashe ya ɗauke ta yana ƙwalawa Bayin da ke harabar sashen amma sakamakon abin da ya faru babu kowa a wurin, da sauri ya fice daga wurin ya nufi sashen Mahaifiyarsa da ita. Yana shiga ya same su jigun-jigun sam hankalinsa be kai ga yanayin da suke ciki ba, cikin damuwa yake faɗin. "Ummi! Shukra don Allah karta mutu aman jini take yi." Hankalinta ne ya tashi da sauri ta aika aka kira baushe nan take ɗan aiken ya dawo tare da Baushe. Kwantar da Maryo aka yi tana numfashi sama-sama, ƙura mata ido ya yi sanann ya jiƙa wani garin magani ya shafa mata a jiki ya ɗura mata sauran a bakinta. Numfashinta ne ya ci gaba da kaiwa da kawowa yana sama yana ƙasa, tarin ne ya ƙara rufeta ta fara yi babu ƙaƙƙautawa. Baushe ba ƙaramin tsorata ya yi ba, don be taɓa ganin ciwo irin wannan ba. A hankali Maryo ta buɗe idanunta da suka rune jawur, kallonsu take ɗaya bayan ɗaya hawaye na ƙwarara daga idanunta ta fara motsa bakinta a hankali tana cewa, " kowanne lokaci kowanne ɗan adam yana tafiya da yadda ƙaddararsa ta faro tun daga tsiron nufashinsa, ni tawa rubutacciyar ƙaddarar kenan. Allah ya ƙaddara ba zan sake cika burinmu na kasancewa ababen farantawa zuƙata ba, tafiyar ƙaddarata tafe yake da sauran ƙalubalen baya. Wataƙila tarayyata da shi bata da alheri shi yasa inuwar junanmu take ƙara nesa da juna." Tari ta ƙara yi jini na bin gefen bakinta ta ɗago ta kalli Maleek da ke gefe yana zubda ƙwallah, ta sakar masa murmushi ta ce, "Tabbas na aminta da yadda ka jiɓanci wani tsagi na daga sashena, haka tamu ƙaddarar take samun muradin abokin rayuwarmu na tafe da ƙalubale. Ka riƙe maganar da nake gaya maka har kullin, ni ba Shukra bace ka yi ta gudu me yawa kamar wanda yake laluben bangon duniya, tabbas za ka cinma muradinka idan har ka kasance baka wuri ɗaya a zaune. A duk lokacin da ka haɗu da Shukra ka bata wannan zoben na hannuna, wataƙila zata fahimci zanen ƙaddarata wanda yake tattare da ƙalubale." Hannu ta ɗaga da kyar jikin ta na karkarwa ta damƙi hannunsa da ɗan yatsenta yake ɗauke da wata azurfa, kuka na neman cin ƙarfinta ta ce, "Don Allah zan baka saƙo ka kaiwa Saif!" Hannu ta sa ta dafe zuciyarta da take barzanar faso ƙirjinta hawaye na zuba ta ci gaba da cewa, "Ka gaya masa ina ƙaunarsa fiye da tunanin ne tunani kuma ba zan fasa ƙaunarsa domin ƙaddararsa tafe take da tawa ƙaddara. Ka gaya masa na ci albarkar ƙaunar da nake masa ya sakawa ƴarsa sunana, sai ƴar uwa ta Abuh ka gaya mata ta tayani kishinsa saboda ta san yadda nake mutuwar sonsa, da zan iya da na shawarci ta zame masa mata sai dai banajin zan iya haɗiye wannan ƙaddarar. A dacen ma ban juri ganinsa da wata mace ba bare yanzu, ka isar da saƙona gare su na fatan aleri. Sai Inna Habi..." nan take tari ya sarƙe ta amai ya ci gaba da zuba daga bakinta. Numfashinta ne ya shiga yin sama da ƙasa ta fara wata irin shaƙuwa, da sauri Maleek ya ɗau ruwa ya fara ƙoƙarin bata amma sai ji ya yi numfashinta ya ɗauke, jikinta ya yi wani irin nauyi kanta ya langaɓe gefe ɗaya. Cikin tashin hankali ya fara ƙwallah mata kira amma babu alamun numfashi a tattare da ita, Fulani Fahima da sauran mutanen da ke wurin jikinsu ba ƙaramin sanyi ya yi ba, ban da hawaye babu abin da suke yi. Fulani Fahima zani ta janyo ta janye Maleek da ƙyar ta rufa mata, sannan ta aika aka sanarwa da Sarki Abdallah rasuwarta. R I P MARYO😭 A lokacin da zanen ƙaddarar wasu take ƙarewa a lokacin wasu suke farawa, ita ƙaddara kamar inuwa ce baka taɓa guje mata. Wani ƙaddararsa haɗe take da kasada ƙarshenma kasa, haka wani yake rayuwa ba tare da cimma burinsa na duniya ba. Bakowanne buri ne ake iya cika shi ba, wani duk yadda ya kai ga cimma burinsa zanen ƙaddararsa na katange burukansa. ALLAH SA KANKU BE KULLE DA YAWA BA😂😂😂😂😂😂 TO GAMU A WANI YANAYI ME DAƊI NE KO MARAR DAƊI CI GABAN LABARIN SHI ZAI IDAR DA HAKA, AMMA FA SAI DAI KU YI HAƘURI DA YADDA TSARIN LABARIN YAKE SABODA TAFE YAKE DA BAN TAUSAYI NA RASHIN CIKAR MURADI. _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [11/12/2021, 19:14] Ameera Adam🌚: 46... Inna Habi zuciyarta sai harbawa take jikinta ya yi wani irin sanyi, zantukan Jakadiya ne suke yi mata yawo a zuciya. Duk lokacin da ta kai aya a mamaita maganar Jakadiya sai ta ji ƙirjinta ya buga, janye masakin lallen ta yi gefe jiki a mace don yadda take ji da ace bata gama saka lallen ba babu yadda za a yi ta ci gaba da zama a wurin. Abu na cikin ɗaki haka kawai ta ji gabanta na faɗuwa musamman da ta tuna da Mahaifiyarta, zaro ido waje ta yi tana dafe ƙirji a fili ta ce, "Na shiga uku na! Wallahi Idan Inna ta sani na san kashe ni za ta yi. Na shiga uku." Nan take jikinta ya hau karkarwa tsoro na ci gaba da mamaye zuciyarta, ilahirin jikinta gumi yake tana fargabar haɗuwarsu da Mahaifiyarta don ta san ta aikata babban laifi domin ko da wasa bata taɓa yi mata hirar Saif ba. Ta ina ma za ta fara tun da bata manta yadda aka ƙarke da Maryo ba. Wani irin bugu ƙirjinta ya ƙara yi wanda har sai da ta yi saurin dafe zuciyarta tana jingina da bango, tunowa ta yi da cikin da ke jikin Maryo wanda take ta iƙirarin na Saif ne. Wani ƙulun baƙin ciki ne ya kamata ta a zuciyarta ta ayyana, " Kenan Saif ya taɓa sanin Maryo?" Nan take hawaye ya fara gangarowa daga idanunta, a gefe ɗaya tana jin haushin Saif da Maryo amma Maryo ta fi mugun bata haushi. Inna Habi jikinta har rawa yake tana gama wanke lallen ta fice daga gidan ko neman izinin Fulani Maryama bata yi bi, tana shiga sashen Fulani Zaliha ta nemi iso wurin Fulani Zaliha, ba a ɗauki lokaci ba suka yi mata iso tana shiga ta same ta a zaune cikin shiga ta alfarma. Russunawa ta yi ta gaida Fulani Zaliha, ta mayar mata da murmushi tana faɗin, "Barkanki da zuwa Inna Habiba ya aiki, ya bayan saduwa?" Inna Habi da kwarjinin baiwar Allahr ya mamaye zuciyarta ta tattaro jarumta ta ce, "Ranki shi daɗe sai alheri." Fulani Zaliha ta yi mata murmushi don lokaci ɗaya ta ji matar ta kwanta mata a rai. Ɗan jim Inna Habi ta yi Fulani Zaliha ta lura da yanayin da Inna Habi take ciki kamar tana cikin damuwa, gyara zaman ta tayi ta ce, "Inna Habiba ga dai abin alheri ya haɗamu." Inna Habi gabanta ya faɗi tana addu'ar Allah a samu saɓanin magana akan abin da Jakadiya ta sanar mata da shi. Jiki a sanyaye ta ce, "Ki gafarce ni ranki shi daɗe na yi jinkirin yi miki Allah sanya alheri." Fulani Zaliha murmushi ta yi mata ta ce, "Karki damu Inna wannan ba wani abu bane, na yi matuƙar farinciki da Abu za ta kasance matar Ɗana, Allah ya biya ki da gidan Aljanna sakamakon tarbiyyar da kika bata." Idanun Inna Habi ne ya ciko da ƙwalla gabanta na ci gaba da faɗuwa ta ce, "Amin Ranki shi daɗe." Abu da ke ɗaki jin muryar Innarta ba ƙaramin ɗaga hankalinta ya yi ba, tana ta zarya a ɗaki ta ji Fulani Zaliha ta aika da akira ta. Kamar mara gaskiya tun kafin baiwar ta shiga kiranta ta yi zaraf ta fito, ɗakin ta shiga tana sunne kai ƙasa tana zura ƙafarta ta ji ƙirjinta na bugawa. Murmushin yaƙe ta yi ta ƙarasa gefen Inna Habi tana raba ido ta ce, "Barka da zuwa Inna ran...amm... dama..." Haka ta fara inda-inda Inna ta yi murmushi ta ce, "Ba komai kawai dama na ce zan zo na yi wa Fulani Allah sanya alheri ne." Inna Habi ta miƙe ta kuma rassunawa ta ce, "A huta lafiya ranki shi daɗe." Fulani Zaliha ta amsa mata sannan ta ce, "Abu ki tashi ki yi mata rakiya mana." Kamar wacce aka zarewa laka a jiki Abu ta miƙe ta bi bayan Inna Habi tana raba idanu, tana zuwa soro Inna Habi ta juyo ta kife ta mari kafin ta ɗago ta kuma kife ta da mari sai kuma ta rufe ta da duka tana fashewa da wani irin kuka me tsuma zuciya. Sarki Abdallah wata tsawa ya bugawa Dogarin da ya same shi da mutuwar Maryo ya yi yana faɗin, "Yarinyar da ta bar waurin nan yanzu ita za ka ce mini ta mutu kana hauka ne?" Dogarin sunkuyar da kai ƙasa ya yi ya fara motsa baki don be san da wane yanayi zai gamsar da Sarki Abdallah ba. Ɗagowa ya yi zai yi magana Maleek ya shiga a haukace kamar mahaukaci sabon kamu, yana zuwa ya durƙushe gaban Sarki Aminullah yana kuka yana faɗin, "Wai shukra ta mutu yanzu nan fa ta fita daga wurin nan. Don Allah Ranka shi daɗe muje ka tashe ta, wallahi ba zan iya rayuwa babu ita ba." Jikin Sarki Abdallah ne ya yi sanyi don yadda ya ga Maleek tabbas babu ko tantama maganar da Dogari ya faɗa haka ne. Dafa kafaɗar Maleek ya yi yace, "Ka yi haƙuri Maleek amma duk wanda ka ga ya mutu kwanansa ne ya ƙare." Maleek ya ɗago da hawaye shaɓe-shaɓe yace, "Kwananta be ƙare ba wallahi idan muka je da kai za ka iya tashin ta." Da sauri Sarki Abdallah ya kife Maleek da mari, sai lokacin ya saita nutsuwarsa ya fasa wani irin kuka me tsuma zuciya, dan duk wanda yake cikin gidan ya san irin zallar soyayyar da yake yi wa Shukransa. Me babban ɗaki da tun shigowar Dogari tana jin saƙonsa ta fashe da kuka hankalinta na daɗa tashi. Sarki Abdallah tattaro jarunmta ya yi yana jin zuciyarsa na rauni ya kalli Dogarin yace, "A je a sanarwa da Jakadiya ta je su yi mata sutura." Jakadiya na shiga gidan gabanta ya faɗi, fuskarta ɗauke da hawaye ya ɗaga labulen ɗakin da Maryo take kwance. A hankali ta zame zanin bayan an kawo mata ruwan da za ta wanke Maryo da shi, idanunta na sauka kan Maryo ta zaro ido cikin tashin hankali. Waɗansu irin manyan tururuwai ne suka zagaye ta masu yawan gaske, daga cikin kunnenta jini ne yake ɗiga kaɗan. A hankali tururuwar ta fara zaizaiyar ƙasar wurin da maryo take a kwance, A hankali Jakadiya ta ɗora hannunta akan hannun Maryo ta ji shi sanyi ƙalau, wata tururuwa ce ta hau saman hannun Jakadiya cikin azaba ta fasa ƙalla ta fice daga ɗakin tana kururuwan neman taimako. A tsorace mutanen wurin kowa ya ɗiba da gudu don a tunaninsu Gawa ce ta riƙe ta, Jakadiya ban da juyi babu abin da take a tsakar gidan da ƙyar ta samu ta fisge Tururuwar da ƙarfin tsiya, sai ga shi ta haɗa da fatar wurin da ta ciza, jini ne ya fara gangarowa daga hannun Jakadiya yana ɗiga. Duk inda Jinin ya ɗiga da sauri Tururuwar za ta bi ta fara zuƙa. BARKA DA HUTUN ƘARSHEN MAKO🥰 _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [12/12/2021, 19:34] Ameera Adam🌚: 47.... Jakadiya tsaye ta yi cikin tsoro tana kallon ikon Allah saboda abu ne da bata taɓa ganin irinsa ba. Ganin Jakadiya a tsaitsaye yasa Sauran matan Sarki Abdallah leƙowa suna ganin abin da yake faruwa, ɗaya bayan ɗaya haka suka fara fitowa suna kalon hannunta da yake ɗigar da Jini, sannu suka fara yi mata suna tambayar ba a sin abin da yake faruwa. Nuna musu turuwar ta yi cikin haki ta ce, "Turuwa ce ta zagaye gawar, kinga wannan ita ta maƙale mini a hannu dubbi yadda hannun ya yi." Dafe ƙirji suka yi cikin ta'ajibi kowa tsoro ya kama shi. Fulani Fahima ce ta yi namijin ƙoƙarin cewa, "Jakadiya mu shiga mu gani mu biyu ko zamu iya sai a sauyawa gawar wurin kwanciya." Jakadiya ta yi tsalle gefe ta ce, "Allah ya taimakeki ni dai tun da muke da ke ban taɓa yi miki musu ba amma maganar gaskiya ba zan iya tunkarar gawar nan ba, don ni kaɗai na san halin da na shiga lokacin da Tururuwar nan ta hau kan hannuna." Fulani Fahima bata tankawa Jakadiya ta kalli wasu Bayinta mata biyu ta buga musu tsawa tana nuna musu ɗakin, jikinsu banda rawa babu abin da yake yi, haka suka ɗafa labulen ɗakin suka fara tozali da wannan tururuwar don ta yanzu har ta fi ta lokacin da Jakadiya ta shi ga rawa. Fulani Fahima dakatar da su sannan ta umarci da ɗauko fiya-fiya. Tana nan tsaye suka dawo da fiya-fiyan ta karɓa ta fara yarfawa, Maryo ce ta ɗago da hannunta wanda Furzaan ya taɓa saka mata zobe ta fara girgizawa alamar a'a. Da sauri duk suka ja ba Fulani Faliha saki kwalbar kalanzir ɗin ta faɗi ƙasa, a zabure Maryo ta ɗago da kai idanunta a rufe hanci da bakinta na ɗigar da Jini cikin ƙaraji ta ce, "Na gaya muku ku bari." Kalanzir ɗin na fara taɓa Tururuwar ta fara tashi sama kamar fari tana yo wa kan su Fulani Fahima." Cikin tashin hankali suka fice daga ɗakin a fice, kafin futarsu Wata turuwa ta maƙalewa Fulani Fahima a ƙafa, fara kuka ta yi saboda azaba Bayinta tuni suka fice a guje Jakadiya ta faɗa Turakar Sarki Abdallah ba tare da ta sani ba. Da ƙyar Fulani Fahima ta fisge Turuwar ta ɗauki kujera ƴar tsugunno ta makawa Tururuwar amma wani abun mamaki sai ji ta yi kamar ta makawa Dutse, Kamar mutum haka Tururuwar ta juya tana kallonta sannan ta koma ɗakin ta Maryo take. Fulani Fahima ɗingisawa ta yi ta fice daga sashen tana fita harabar gidan babu kowa sai wani Dogari, aikensa ta yi wurin Sarki Abdallah ta sanar da shi ya gaya masa duk abin da yake faruwa. Lokacin da saƙon ya isa kunnen Sarki Abdallah da sauri ya fito ya nufo sashen yana tafe Me babban ɗaki da Maleek na biye da shi, ganin Sarki Abdallah kamar baya saurin da ya kamata ya sa yasa Maleek zubawa a guje ya shige ciki. Maleek na shiga be tsaya tambaya ba ya faɗa ɗakin, kwance ya samu Maryo kamar gawa babu alamar numfashi a jikinta, zubewa ya yi a wurin yana wani irin kuka me tsuma zuciya yana faɗin, "Shukra don Allah karki tafi ki barni, meye wannan nake gani baibaye da jikinki..." Be ƙarasa faɗa ba Fulani Fahima ta leƙa ta ce, "Kai Maleek maza ka fito kar turuwarnan ta illata ka. Wannan ba Tururuwar gaske ba ce wallahi sai dai da wata a ƙasa." Wata Baiwa da ke gefe ƙasa-ƙasa cikin gulma ta ce, "Wa ya sani ko zalinci da ta yi wa wasu ne yaje bibiyarta tun kafin kabarinta." Tana rufe baki suka ji ta fasa ihu tana birgima a wurin. Maleek Kallon Mahaifiyarsa cikin Kuka yace, "Ummi da na yi rayuwa babu Shukra gara nima na bita ko me Tururuwar nan za ta yi mini zan jure." Kamar waɗanda ya faɗa akan kunnensa haka Tururuwar ta fara zagaye shi suka fara hawa jikinsa, tun yana runtsa ido saboda azaba har ya fara zubda ƙwalla, sannu a hankali Jikinsa ya fara ɗigar da jini a duk wuraren da Tururuwar ta cije shi. _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [13/12/2021, 19:22] Ameera Adam🌚: 48... Abu bata yi wani yunƙurin hana Inna Habi dukan da take mata ba, kuka take tun ƙarfinta tana durƙshe a wurin. Inna Habi sai da ta daketa har ta gaji sannan ta rabu da ita, jin shiru Inna Habi ta daina dukanta yasa ta ɗago ta kalli Inna Habi idanunta sun yi jawur, Inna Habi ta share hawayen fuskarta cikin takaici ta fara magana, "Abu tir da halinki ace wai kina soyayya da wani ni a matsayina na mahaifiyarki har ban sani ba, wani abun takaici wai har a saka miki ranar aure ina Mahaifiyarki ban samu wannan matsayin ba. Na gode da kike watsar da mutumci na, kwaɗayi dai mabuɗin wahala ne na tabbata kwaɗayin mulki da ƙyale-ƙyalen duniya ne ya kwashe ki, amma ke da kanki kin san kwaɗayi mabuɗin wahala ne. Amma tun da rayuwar da kika zaɓawa kanki kenan, ki je kiyi amma ban taɓa tsammanin za ki iya auren mutumin da ƴar uwarki take mutuwar sonsa ba, kin bani kunya Abu kin ci amanar ƴar uwarki sam ban taɓa tsammamin haka daga gare ki ba, na ɗauka za ki taya Maryo kishin abin da take so ashe ba haka bane? Na gode wa Allah da Allah ya sa ke ma be yi miko irin na ƴar uwarki ba." Inna Habi ta share ƙwallah cikin takaici ta ci gaba da cewa, "Ban san ta ina na gazawa tarbiyyarku ba, ban san ta ɓangaren da na samu naƙasu a harkar tarbiyyarku ba. Allah ya gani na baku tarbiyya daidai gwargwado, amma daga ƙarshe gabaɗaya ke da ƴar uwarki kuka watsa mini ƙasa a ido." Inna Habi na gama faɗa ta juya za ta fita da sauri Abu ta riƙo zaninta cikin kuka ta fara faɗin, "Inna don Allah ki yi haƙuri tabbas ban kyauta ba amma wallahi nima ban san da sanya ranar ba sai jiya, kuma an hanani shiga sashen Fulani Maryama. Amma Inna ni kaina ina ji a zuciyata ban kyautawa Maryo ba, sai dai ni kaina ban san lokacin da na faɗa soyayyarsa ba. Ina yi masa soyayyar da ni kaina ban san ya aka yi na afka ba, don Allah ki taya ni da Addu'a Inna Allah ya cire mini shi a zuciyata amma..." Bata ƙarasa faɗa ba Inna Habi ta fisge haɗe da hankaɗeta gefe ta ce, "Lokacin da kika fahimci haka kin yi shawara da ni, kije Abu tun da haka kika zaɓarwa kanki ni nawa ido ne Allah sanya alheri." Tana gama faɗa ta fice daga soron gidan, Abu durƙushewa ta yi tana wani irin kuka me tsuma zuciya don har ga Allah bata jin za ta iya rabuwa da Saif a wannan lokacin da take jin ba za ta iya rabuwa da wani Namijin ba bayan shi. A gefe ɗaya tana jin maganganun Inna na ci gaba da tururi a zuciyarta saboda zafin da suka yi mata, wannan shi ake kira da gaba kura baya siyaƙi tabbas ta lura da Inna Habi ta kai ƙololuwar ɓacin rai amma don ta san Inna ba macece me saurin fushi ba, amma idan ta yi fushi da abu kafin ta huce aiki ne. Ganin yadda jikin Maleek yake yi ba ƙaramin ɗagawa Fulani Fahima ya yi ba, kuka take ta shiga ɗakin tana janshi amma yana zaune kamar wanda aka ɗaure a wurin. Ana cikin wannan yanayin Sarki Abdallah ya shiga saboda labarin lamarin ya ishi kunnensa tun lokacin da Maleek ya shiga ɗakin da Maryo take, Me babban ɗaki ban da kuka babu abin da take yi donma an hanata shiga amma sau uku tana dumfarar ɗakin suna janyeta, Sarki Abdallah ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba ganin halin da su Maleek suke ciki, da sauri ya juyo ya bada umarnin kiran masu magani daga sassan wurare dake cikin garin Adamawa cikin gaggawa, tun da ya samu labarin Maryo bata mutu ba amma kuma tana cikin wani irin yanayi. Ba a ɗauki lokaci ba masu magani suka dinga zuwa suna gwada fikirarsu amma kowanne da Tururuwa ɗaya ta maƙale masa zai fice da gudu yana kuruwa ko waige baya yi. Maleek tun yana cikin hayyacinsa har ya daina gane abin da yake faruwa saboda galabaita. Haka masu magunguna suka dinga yi wasu ko ɗakin basa shiga suna ji ƴan uwansu masu magani sun fasa ihu za su fita suma a guje. Sarki Abdallah da Fulani Fahima haka suka fara cire tsammani da Maleek don Tururuwar gabaɗaya ta yanyame jikinsa, ko motsin kirki baya yi. Suna nan tsaye wani sarkin Maharba Me magani ya shigo, ɗan Dattijo ne hannunsa ɗauke da Jakar fatar Damisa, Sarkin Maharba ne shine shugabansu a wannan nahiyar. Yana ɗaga labulen ɗakin ya yi tozali da abin da yake faruwa, ƙurawa tururuwar Ido ya yi ya taka a hankali ya shiga ɗakin ya ɗauki Tururuwa ɗaya ya ɗora akan tafin hannunsa, duk tsananin zafin da yake ji a saman hannunsa be hanashi ƙurawa Tururuwar idanu ba, da sauri ya fara yarfe hannu saboda azaba yasa ƴan yatsu ya tsige ta, nan take wurin ya fara ɗigar da jini. Juyawa ya yi a hankali ya kalli Sarki Abdallah yace, "A samo mini ganyen tunfafiya da tsakin kuka." Tun be rufe baki ba wasu Dogari suka fice a guje, da sauri suka nemo abin da Sarkin Maharba ya buƙata. Suna kawo masa ya ce a nemo ƙwarya ƙarama a zuba ruwa kaɗan a ciki, kamar yadda ya buƙata haka suka yi. Karɓa ya yi ya zuba ganyen tunfafiyar a ciki da tsakin kukar yana murtsukawa, yana gamawa ya shiga ɗakin ya fara yarfawa akan Maryo da Maleek sai kuma wuraren da Tururuwar take bi. Suna nan tsaye suna ganin abin da yake faruwa, ɗaya bayan ɗaya tururuwar suka dinga faɗuwa suna mutuwa. Sannu a hankali Tururuwar duka ta mutu a wurin, Sarkin Maharba yace a ɗauke Maleek daga ɗakin. Da sauri Dogarawan suka ɗauki Maleek hannuwansu na zafi suka fito da shi harabar wurin aka kwantar da shi yana sauke numfashi kaɗan-kaɗan. Da sauri Fulani da taho za ta taɓa Maleek, wata razananniyar tsawa Sarkin Maharba ya buga sai kace ƴarsa domin har ya manta wacece ita a wurinsa, ba ita ba hatta Sarki Abdallah sai da ya kalle shi da mamaki. Sarkin Maharba be damu da kallon da suke yi masa ba, ya ɗebo wani garin magani ya fara barbaɗawa kan wasu daga cikin raunikan dake jikin Maleek sannan ya fara da cewar, "Kafin na barbaɗa maganin da ace wani zai taɓa shi a wajen nan to babu makawa dafin dake jikinsa zai dawo jikin wanda ya taɓa shi, tsananin da zai shiga har sai ya fi wanda shi Majinyacin yake ciki. Da ace yana cikin ɗakin haɗe da waccen." Sarkin Maharba ya nuna Maryo yace, "To da wani abu ba zai same shi ba, saboda ita ɗin FILSIFI ce. Kuma sai na baku magani wanda za ku jiƙa ku sha za ku amayar da dafin da ya taɓa ku." Jiki a sanyaye Me babban ɗaki da ta ci kuka ta godewa Allah ta ce, "Ita kuma yarinyar cen ya za a yi da ita? Domin ina ji a jikina ba ta tana buƙatar kulawa." Sarkin Maharba ya kalli Me babban ɗaki yace, "A wannan yanayin da take ciki duk abin da za a yi mata ba za ta taɓa farkawa ba." Da sauri Me babban ɗaki ta cukumi wuyansa ta ce, "Ƙarya kake me ya sa kake neman ka ɓata rawarka da tsalle?" Sarkin Maharba ya sauke hannun Me babban ɗaki yana gyara wuyan rigarsa yace, "Allah ya taimake ki, iya gaskiyar abin da na sani ita na gaya muku. Ku godewa Allah da Allah ya sa waɗannan Tururuwar ta mutu, wannan tururuwar da kuke gani a ido ba tururwa bace. Mutanenta ne suka zo ta ya alhinin halin da take ciki, Fusatattu ne za su iya halaka duk wanda ya kusance ta. Ba mutuwa tayi ba sai dai tana cikin wani irin hali na ban tausayi, wannan yarinyar da kuke gani zamu barta zuwa safiya a yadda take domin duk abin da za mu yi mata ba za mu iya dawo da ita cikin hayyacinta ba. Idan Allah ya kaimu zan dawo zuwa safiya, zan dawo da waɗansu garin magunguna wanda za a yi mata turare da wanda za ta dinga wanka da su." Sai a lokacin Me babban ɗaki ta gamsu da abin da ya gaya mata. Haka daga ɓangaren Sarki Abdallah da iyalansa. Sarkin Maharba ya tsaya a kan Maleek ya ɗauko wata kwalba da wani koren ruwa a ciki ya zuba a hannunsa ya murje sannan ya shafawa Maleek, tashi tsaye ya yi yace, "Yaron nan za ku iya ɗauke shi amma sai bayan sa'o'i uku, idan ya farko ku bari ruwan ɗumi ya sha daga nan babu abin da zai faru da shi, ita kuma yarinyar cen ku janyo ƙofar ɗakin ku rufe." Yana gama faɗa ya yi wa Sarki Abdallah sallama ya fice daga gidan. Bayan sa'i uku aka ɗauke Maleek aka kaishi ɗakin Fulani Fahima, bayan ya farka kamar yadda Sarkim Maharba ya faɗa haka suka yi masa. Kallonsu ya fara gi ɗaya bayan ɗaya har ya sauke idonsa kan Mahaifiyarsa, a hankali abubuwan da suka faru suka fara dawo masa a ka. Sai a wannan lokacin ya fara jin raɗaɗin ciwukan jikinsa. Kallon mahaifiyarsa ya yi kwallah na ciko idanunsa yace, "Ummi da gaske ne Shukra ta Mutu?" Tausayin ɗanta ne ya mamaye zuciyarta tana girmama irin ƙaunar da Maleek ya yake yi wa Shukra, wani tunani ta yi sai kuma take ganin don ya nuna ƙaunarta ba wani abu bane domin Shukra ta jure abin da ba kowacce mace ce za ta iya jurewa ba, Shukra ta yi jarumtar da sai an tara dubannin mata za a iya samun mutum goma a ciki. A jiyar zuciya ta sauke ta ce masa, "Abdulmaleek!" Da sauri ya ɗago ya kalle ta domin idan ba kunnensa gizo suke masa ba yau ce rana ta farko da ya taɓa jin Mahaifiyarsa ta ambaci sunansa na yanka. Kallonta ya yi yana tattara nutsuwarsa yace, "Na'am Ummi?" Ta ruƙo hannuwansa biyu ta ce, "Tabbas ke namijin da za a nunawa duniya ne. A lokacin baya na ɗauka Shukra hauka take yi na soyayyarka sai a yanzu na tabbatar da zallar soyayyar da kuke yi wa juna. Shukra bata mutu ba sai dai a wannan lokacin tana buƙatar hutu domin Me magani yace kar abar kowa ya shiga wurinta saboda kar a dawo mata da ciwonta sabo." Hannu biyu Maleek ya sa a kumatunsa yana kafe ta da idanu, maganar Maryo ce ta dawo masa da take cewa, "Ina ƙara tuna maka da cewar ni ba Shukra bace, kayi ta gudu me yawa kamar me neman ƙarshen duniya..." Ganin kallon da yake mata ya sa ta yi tunanin kamar ya gano ba ainin gaskiyar lamarin ta sanar masa ba, tana shirin magana ta riski muryarsa a sanyaye yana cewa, "Ummi ba Shukra bace! A da ƙaunar Shukra ta sa idanuwa sun rufe nake ganin yarinyar cen kamar Shukra ce amma sam ba Shukra bace, yanzu ma na ƙara rasa Shukra wataƙila ba zan ƙara rayuwa da ita ba. Yarinyar cen Maryo ce kamar yadda koyaushe take ankarar da ni, na yarda kama da wane bata wane. A fuska ne suke kamanceceniya da Shukra amma gabaɗaya halaye da ɗabi'unsu sun bambamta." Ita kanta ta fahimci abin da yake nufi don haka ta shafa sumaraa ta ce, "Na daɗe ina zargin haka, tun farko abin da ya faru a gidan nan zuciyata ta dasa zargin haka. Amma wacece ita?" A hankali ya wara mata hannuwa alamar be sani ba sannan yace, "Dole musan wacece ita amma ko da ba Shukra bace ina jin tausayinta a raina, jikina yana bata akwai wata ɓoyayyar alaƙa da ita kaɗai ta san wannan alaƙar kamar yadda take faɗa mini, ina tausayin yarinyar saboda halin da take ciki." A sanyaye Fulani ta ce, "To Allah bata lafiya, idan ra warware maji ainihin labarinta." Maleek ya amsa da Ameen yana kwanciya saboda yadda jikinsa yake masa raɗaɗi. Washegari kamar yadda Sarkin Maharba ya faɗa haka ya cika alƙawari, safiya na yi ya dawo Masarautar Sarki Abdallah kamar masu jiransa haka ya same su cikim shiri, lokacin da suka dunfari ɗakin Maryo take haka Bayi suka dinga leƙe kowa yana son kashe ƙwarƙwatar idanunsa, Sarki Maharba na tura ƙofar ya same ta a cen ƙuryar ɗaki ta zauna ta haɗa kai da gwiwa ta cusa kanta a ciki. Takawa ya dinga har ya je gabanta ya tsaya ya fara cewa, "Yarinya ɗago da kanki." Maryo shiru ta yi bata ɗago da kanta ba, sai da ya yi mata magana sau uku bata ɗago ta kalle shi. Hannu ya sa ya taɓa ta a tsorace ta miƙe tana lalube-lalube, da sauri ya sa hannu biyu ya riƙe sosai jin haka ya sa Maryo ta fara tattaɓa shi har ta kai ga fuskarsa, jin gashi a fuskarsa ya sa ta janye jikinta da sauri a ɗan tsorace. Sarkin Maharba jiki a sanyaye ya saketa ya juya a raunace, ganin haka ya sa Maleek ya saurin cewa, "Baba lafiya menene?" Sarkin Maharba yace, "Tabbas zanen ƙaddarar bawa baya taɓa gujewa ruhin me shi, ita ƙaddara tamkar yadda jini yake gudana a jikin ɗan adama haka ita ma take zaga sassan jikinsa. Wannan yana ɗaya daga cikin shafin ƙaddararta, gujewa ƙaddara kuwa kamar ƙoƙarin gujewa mutuwa ne. A yadda ƙaddara ta samu bawa mafi kyautuwa ya amsheta hannu bibbiyu, domin bijirewa ƙaddarar shi zai kai ga afkawa cikin ƙaddarar da baka yi tsammani ba. Wannan yarinyar da kuke gani ta riga da kurumce kuma ta makance wannan ma yana daga cikin shafin ƙaddararta." MARYO FANS! I FILL UR PAIN 😢 KWANA BIYU COMMENTS ƊINMA SHIRU🌚 _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [14/12/2021, 18:47] Ameera Adam🌚: 49... Cikin ɗimauta Maleek ya buga masa tsawa yana faɗin, "Ƙarya kake yi. Maryo bata kurumce ba, Malam ka fito ka faɗa mana abin da ka yi mata, Idan ba haka ba wallahi sai na hukunta ka." Murmushin Dattijon ya yi ya ƙara taku biyu zuwa gaban Maleek yace, "Yaro man kaza. Kana tunanin akwai wani abu na mugun abu da zan iya aiwatarwa wannan yarinyar? Ka san da wacce kake tare kuwa? Ita ɗin me matuƙar muhimmanci ce ba ɗaya take da sauran mutane ba. Bana tunanin akwai Ɗan adam mutum da zai iya sarrafa wani abu domin ya cutar da ita. A gabanku na buɗe ƙofa na shiga wurinta wannan ya isheku alƙalanci idan ma na yi mata wani abu, sannan kai musulmi ne na tabbata ka yi imani da ƙaddara me kyau da marar kyau. Ka sawa zuciyarka ƙaddarar da ta haɗaku ita ce ta jefa ta cikin wannan halin da take ciki." Jikin Maleek ne ya yi sanyi wani irin tausayin Maryo yake ji, kasancewarsa Jarumin gaske ba kowannen abu yake iya zubdawa ƙwallah ba sai ga shi a wannan lokacin idanunsa na shatatar da hawaye. A hankali ya zame ya zauna daɓas kamar wanda ya samu saƙon mutuwa, ban da hawaye babu abin da yake yi. Fulani Fahima da sauran mutanen wurin jigun-jigun suka yi saboda gabaɗaya jikinsu ya yi sanyi. Me babban ɗaki ce ta nufi ɗakin da Maryo take da sauri don tabbatar da abin da Sarkin Maharba ya faɗa. Tana shiga ita ma Maryo tana yunƙunrin juyowa hannunta na lalube-lalube, da sauri Me babban ɗaki ta riƙota tana cewa. "Ke yarinya kalle ni nan kina jina." Maryo laluba jikin Me babban ɗaki ta fara yi tana jin alamun mace ce ta faɗa jikinta tana rushewa da wani irin kuka. Duk yadda Fulani Fahima ta so daurewa sai da idanunta suka dinga zubda ƙwalla. Me babban ɗaki kuka take sosai tana faɗin, "Yarinya yanzu wai abin da mutumin nan yake faɗa mana gaskiya ne? Kaico rayuwa yau wane irin tashin hankali ne wannan muke ciki." Maryo da bata san me take faɗa ba ban da kuka babu abin da take yi, sai da ta yi kuka me isarta sannan ta ɗago ta lalubo hannun Me babban ɗaki ta kai saman fuskarta daidai kan manyan dara-daran idanunta, ta ɗora akai sai kuma ta sake fashewa da kuka tana ja da baya har ta jingina da bango ta zauna ta sake haɗa kai da bango tana ci gaba da ruskar kuka. Jiki a sanyaye Me babban ɗaki ta juyo ta fito ta same su carko-carko cikin alhini, cen bakin ƙofa ta nufa ta samu wani Dogari ta kira shi, da sauri ya ƙarasa ya russuna cikin girmamawa kamar me neman gafara. Me babban ɗaki ta dube shi fuska ɗauke da damuwa ta ce, "Maza ka je ka kira mini Audullahi." A zabure ya miƙe ya fice daga wurin. Ba a ɗauki lokaci ba Sarki Abdallah ya fito cikin takun ƙasaita yana tafe yana barbaɗar da izzar mulki, yana ƙarasawa Russunawa ya yi a gabanta cikin girmamawa. Me babban ɗaki ta ci gaba da sharce ƙwallah sannan ta sanar masa da abin da Sarkin Maharba ya sanar musu, Sarki Abdallah na gama jin bayaninta ya ɗago ya kalli Sarkim Maharba dake tsaye da jaka rataye a kafaɗarsa, sai wani zabgegen kwari da baka da yake rataye a wuyansa. Sarki Abdallah ya miƙe tsaye zuciyarsa babu daɗi ya leƙa ɗakin da Maryo take ya ji yadda take raira kuka, jin kukanta yake har cikin jikinsa. Kallon Sarkin Maharba ya yi yace, "Babu wani abi da za a iya domin taimakon halin da take ciki, idan da hali ko da idanunta ne a taimaka a bata maganinsu. Menene silar wannan kurumcewar ta ta?" Sarkin Maharba ya gyara zaman kwari da bakarsa yace, "Haihuwarta na tattare da ɓoyayyun lamura a zahirin gaskiya babu wani abu da zan iya aiwatarwa akanta saboda ita ba kamar sauran mutane bace. Tun lokacin da ta zo duniya ƙaddara ke bibiyar rayuwarta, ƙaddara da ta dawo da ita na fi tsammanin ita ta jefa ta cikin wannan yanayin. Daga ni har sauran masu maganin duniya babu wanda zai iya warkar da ita saboda wannan ciwon na ta ba irin ciwon da wani zai iya taimaka mata bane. Amma za ku iya jarraba neman masu magunguna ko za a dace domin ba a san inda rabo yake ba. Ina fatan za a yi mini afuwa ranka shi daɗe idan kalamaina sunyi kaushi" Me babban ɗaki na jin haka ta kuma rushewa da kuka. Babu wanda ya hanata sai da tayi me isarta sannan ta kalli Sarki Abdallah ta ce, "A ɗauke ta akaita sashena ta ci gaba da zama acen a turo mini Bayi uku waɗanda za su dinga yi mana hidima." Sarki Abdallah ya amsawa Mahaifiyarsa sannan ya juya ya sa a sanarwa da uwar Bayi buƙatar Me babban ɗaki. Maleek yana zaune a gefe kamar wani sakarai haka yake bin su da idanu, yana kallo wasu Bayi suka riƙo Maryo suka wuce Me babba ɗaki na gaba suna biye da ita a baya kamar jela, a lokacin fuskar Maryo ta yi jawur idanuwanta duk sun kumbura saboda kuka. Babu jimawa mutanen wurin kowa ya watse nan fa ƙananan maganganu suka fara zaga cikin gidan masarautar kowa na tofa albarkacin bakinsa, wasu na ganin alhakin waɗanda suka mutu da waɗanda suka jirkata ne ya kama Maryo, ya yinda wasu suke tausayin ta matuƙa. Musamman idan suka tuna yadda makanta ta same ta sama ta ka da girmanta. Bayan wasu kwanaki Fulani Fahima na zaune a turakar Sarki Abdallah suna hira, ya dube ta yana mata kallon tsaf yace, "Fahima akwai abin da yake daminki amma ban sani ba ko yanzu kin fara ɓoye mini damuwarki ne?" Kanta ta ɗora akan ƙafafuwansa ta ce, "Tabbas ina cikin damuwa matuƙa amma ban san ta ina zan fara ba. Ban san yadda za ka ɗauki maganar ba, bana jin ɗar dangane da amincewa buƙatar sai dai ban sani ba ko Me babban ɗaki za ta amince." Murmushi ya yi yace, "Hala akan yarinyar cen Maryo za ki yi magana?." Yunƙurawa ta yi ta tashi zaune tana gyara kallabinta ta kalle shi da kulawa ta ce, "A kan Maryo ne Ranka shi daɗe. Allah ya taimake ka gani nake ɓoyewa Yaya da Mariƙiyar yarinyar kamar be kamata ba, saboda Me maganin nan da bakinsa yace babu abun da zai warkar da ita, kuma ka ga an saka lokacin auren su Salman. Yanzu kana gani idan lokacin bikin ya zo ba zamu da ita ba, ko kuma su, su zo mana wata rana. Me zai hana kawai a sanar musu da halin da take ciki, ai su musulma ne dole su yarda da ƙaddara." Sarki Abdallah ya dube ta da yanayin damuwa yace, "Ban ƙi ta taki ba Fahima amma mu bari nan da ɗan wani lokaci mu ga ni, za mu ci gaba da neman magani don ba mu san inda za a dace ba." Jinjina kai ta yi ta ce, "To Allah ya datar da mu ya bata lafiya." Sarki Abdallah ya amsa da ameen, sannan ya kuma kallon ta yace, "Bayan wannan maganar sai wacce kuma don har yanzu bakinki da motsi." Kame-kame ta fara yi ya dafa kafaɗarta yace, "Fahima! Me kike son faɗa ki gaya mini." Fulani Fahima ta sunkuyar da kai ƙasa gabanta na bugawa ta ce, "Dama am akan Fulani Babb..." Wata razannaniyar tsawa ya buga mata jikinta na rawa ta ja bakinta ta tsuke, ganin yadda ranshi ya yi mugun ɓaci ya sa ta kalle shi ta ce, "Ina neman afuwa ranka shi daɗe tuba nake." Be kalli wurin da take ba yace, "Ba damuwa amma ki kula." Ta amsa masa sannan ta fara sako masa wata hirar tun yana ɓata fuska har ya sake suka ci gaba da hira. A kwana a tashi babu wuya haka rayuwa ta ci gaba da gangarawa Maryo ba ƙaramin kulawa take samu a wurin Me babban ɗaki ba, wani irin so take mata da ko sauran jikokinta bata jin su a ranta kamar ita. Ita kanta Maryo ta fahimci a wurin da wacce take, haka suke zaune koyaushe zaman kurame wani lokacin Me babban ɗaki har magana take gwada yi wa Maryo ta ga ko za ta kulata amma sai dai ta ji shiru. Tun Maryo na yawan koke-koke har ta fauwalawa Allah lamuranta, sai dai ta yi wata irin rama ta zabge fuskarta ta yi fayau. Kuma har wannan lokacin sau biyu ciwonta yana motsawa idan ya tayar mata kamar ba za ta yi raina ta dinga aman jini kenan. Sauƙin lamarin da suka samu da ake haɗa mata dana asibiti dukda da farko basu ɗauke shi da wani muhimmanci ba. (Note: ku tuna shekara saba'in baya Al'ummar hausawa ba kasafai idan ciwo ya samu suke yarda da na asibiti ba. Wannan labarin a matsayin ya faru shekaru saba'in baya da suke wuce ne. 1951) Sannu a hankali suka fahimci ci gaban da ake samu daga ciwon Maryo, kuma duk lokacin da ciwon ya tashi ana kaita asibiti bata ɗaukan kwanaki cikin ikon Allah take warwarewa. Sai dai abu ɗaya ne kullin Likitoci suke sanar musu da cewar yarinyar tana cikin matsananciyar damuwa, su dinga ƙoƙarin faranta mata. Wannan ba ƙaramin ɗaga musu hankali yake ba domin gabaɗayansu babu wanda ya san ta yadda zai tunkari Maryo ya yi mata bayanin yadda za ta gane, idan ance maganar kurame za a yi mata babu idon da za ta gani ta hankalici abin da ake gaya mata. A hakan dai Me babban ɗaki take bakin ƙoƙari wajen zama kusa da ita da yi mata ɗan abin da ba a rasa ba. A wannan yanayin ne har kwanakin auren su Salman suka zagayo. Shirye-shirye daga ɓangaren ta ko'ina sun fara kankama, Fulani Maryama sai shige da fice ake ana ta hada-hadar biki. Kamar wacce za ta aurar da ƴaƴa goma bata cen bata nan, ita ce gidan wannan Boka ita ce gidan wancen Boka. Duk wurin da za ta tafi ƙafarta ƙafar Jakadiya duk wani ƙulle-ƙulle tare suke yi. Fulani Maryama har sawa ta yi a yi wa iyayen yarinyar da Salman zai aura asiri, nan ne fa wani Boka suka je wurinsa ya kalli Fulani Maryama yace, "Buƙatar da kike nema ba za ta taɓa yuwu basaboda uwar yarinyar a shirye take fiye da tsammaninki, gara ma ki tsaya akan yarinyar wata ƙila idan kika mallake ta ki dinga samun alheri daga wurinta. Amma sam Mahaifiyar ba za ta mallaku ba." Fulani Maryama haka suka tarkato suka dawo ranar ba tare da ƙwarin gwiwa ba, amma a zuciyarta har lokacin bata jin za ta iya haƙura da ƙudurin da ke cikin zuciyarta. Daga wurin Fulani Zaliha sosai ta dage tana shirya Abu da kayan gyara kala-kala, sai dai gabaɗaya ta rame ta zabge saboda a kullin sai maganganun Inna Habi sun dawo mata tsakiyar ka. Ramar da ta yi ba ƙaramin damun Fulani Zaliha ta yi ba kullin ta tambayeta abin da yake damunta sai dai ta ce mata babu komai. Wannan dalilin ya sa Fulani Zaliha take tsammanin ko damuwar rabuwa da iyaye ce, tun yawanci duk amayar da za a yi aurenta sai ta yi wannan ramar. Lokaci na ƙara ƙaratowa baƙin ciki na ƙara cunkushe zuciyar Inna Habi, wani abu da yake ƙara ɗaga hankalinta yadda take munanan mafarkai da Maryo. Tun abin baya damunta har tashin hankalinta ya ruɓanya, a takaice abin har ya kai ya kawo bata iya baccin kirki. Saura Sati guda Ɗaurin aure lamarin ya addabi zuciyar Inna Habi, a wata safiya ta fice daga sashen Fulani Maryama kai tsaye ta wuce fadar Sarki Aminullah. Russunawa ta yi a gabansa cikin girmamawa ta kwashi gaisuwa. Sannan ta ɗora da cewa, "Allah ya taimake ka ya baka yawan rai ina neman izini akan a yarje mini tafiya Masarautar Adamawa." Kallonta ya yi ya numfasa yace, "Ko akwai dalilin zuwan?" Idanun Inna Habi ne ya kawo ƙwalla ta sa gefen mayafinta tana share ƙwallar ta ce, "Allah ya taimake ka kusan kullin ina yawan munanan mafarki da Maryo shi ya sa nake son zuwa na gano halin da take ciki." Sarki Aminullah yace, "Idan kin yi haƙuri rana ita yau tuni sun zo gidan nan biki." Ba haka ta so ba sai dai babu yadda ta iya, jiki a sanyaye ta russuna ta yi masa godiya ta koma sashensu, tana zuwa ta faɗa ɗakinta ta fara sakin kuka mara sauti gwanin tausayi. Fulani Fahima yadda take farinciki da shirye-shiryen tafiya sai ka rantse auren Maleek na farko za a yi. Saura kwana huɗu biki ta haɗa kayanta tsaf aka haɗa mata kekunan dokuna. Zaune take a ɗakin Me babban ɗaki lokacin Maryo na kwance idonta a rufe da alama bacci take yi. Me babban ɗaki ta kalli Fulani Fahima ta ce, "Audullahi yace wai za ki tafi da yarinyar nan Ƙasar Kano, sam ban lamunce ba. Ba za ki ɗauki yarinya ki ɗaukar mata baki ba ayi ta tanka ta ana cewa lalura ta same ta ba. Idan kin je an tambayeta ki ce ita da Audulmaleek sun yi tafiya." Fulani Fahima sam bata so haka amma sai ta gyaɗa kai ta ce, "Shikenan Ranki shi daɗe yadda kika ce haka za a yi." Daga haka ta miƙe ta fice daga ɗakin, babu jimawa aka fito da kayanta ita da ƴar Autarta Zuhra suka shiga rumfar dokunan suka ɗauki hanyar Ƙasar Kano. _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [17/12/2021, 15:28] Ameera Adam🌚: 50... Inna Habi tun da ta ji labarin zuwan su Fulani Fahima ta kasa zaune ta kasa tsaye saboda murna da farincikin za ta yi tozali da Maryo. Farincikinta har ya gaza ɓuya ƴan matan Bayin har tsokanarta suke suna yi mata tsiya, saboda yawanci sun ɗauke ta kamar kakarsu. A ɓangaren Abu kuwa tun da ta ji labarin su Fulani Fahima za su zo duk ta firgice, gabanta ban da faɗuwa babu abin da yake yi tana fargabar haɗuwarsu da Maryo da irin kallon da za ta yi mata. Sai dai ta yi imani da Allah duk ma juyin da za a yi bata jin za ta iya sadaukar da soyyayar da take wa Saif. Lokacin da su Fulani Fahima suka sauka haka ta dinga gaya musu Maryo lafiyarta ƙalau sun yi tafiya da Maleek amma bayan kwana biyu za su zo su yi Allah sanya alheri. Inna Habi sam ba ta ji daɗi ba don ta sawa zuciyarta ganin Maryo da halin da take ciki, amma kuma sai ta ji damuwarta ta ragu saboda ko ba komai ta fahimci Maryo na cikin kwanciyar hankali, tun da har ta saki jikinta tana bin Mijinta suna tafiya wuraren aikinsa. Da ƙarfi ƙirjinta ya buga sakamakon tunowa da cikin jikin Maryo da ta yi, a hankali ta furta, "Amma lamarin da mamaki ace duk waɗannnan watannin da aka kwashe ace har yanzu cikin jinkinta be bayyana ba. To ko ya zube ba tare da wani ya fahimta ba." Hannu biyu ta ɗaga sama tana addu'ar cikin jikin Maryo ya zube a gefe ɗaya kuma tana fargabar mummunan laifin da ta aikata, domin a ranar Juma'ar satin da ya gabata Sarki Aminullah ya yi tunantarwa dangane da, muhimmancin aure da ladabbansa tare da albarkar auren, a cikin hakane har ya gangaro kan iyayen da suke ha'intar mazan ƴaƴansu ta hanyar kwantar da cikin da wasu daga cikin iyaye suke yi idan ƴaƴansu suka samu cikin gaba da fatiha. Ya yi tunatarwa me za fi har sai da Inna Habi ta sharce ƙwallarta har ta ci alwashin samun Sarki Aminullah ta sanar da shi babban kuskuren da ta aika ta dangane da Maryo da Abdulmaleek. A wannan lokacin duk yadda Inna Habi ta so ganawa da Sarki Aminullah abun ya faskara saboda baƙin da yake yawan karɓa, don haka ne ta ajiyewa zuciyarta ana gama bikin su Saif duk halin da ake ciki sai ta samu Sarki Aminullah da maganar in ya so sai a gyara aurensu ta hanyar tantance ta tare da sake sabon ɗaura aure. A ɓangare ɗaya ko kaɗan bata jin wani farinciki dangane da auren Abu da Saif sai dai tana ta yi mata addu'a akan Allah ya tabbatar da alheri ya kuma ba su zaman lafiya. Saboda ita uwa ce bakinta kamar kaifin wuƙa ne ko yaya ta faɗi kalma mara daɗi akanta ta tabbata ko ba daɗe ko ba jima sai ya kamata. Don haka ta fauwalawa Allah lamuranta take yi mata addu'a domin ta san komai muƙaddarine daga ubangiji. Fulani Maryama kai ya fara ɗaukan zafi saboda baƙi daga ɓangare daban-daban take karɓa, gidan ba ƙaramin cika ya yi ba. Haka daga ɓangaren Fulani Zaliha sashenta cike yake da mutane sai dai gabaɗaya ta killace Abu a ɗakinta ta hana kowa shiga ɗakin a cewarta ba za a kalle Amarya tun kafin lokacin bikin ya zo ba. Ango Saif ba ƙaramin damuwa ya shiga ba saboda rashin ganin Abu ya jefa zuciyarsa cikin damuwa, saboda tun lokacin da aka tsayar da lokacin bikinsu Fulani Zaliha ta hana shi ganawa da Abu, duk yadda zai yi ya ganta su yi wata hira ta hana, ko da zai ganta sai dai idan yaje gaishe da Mahaifiyarsa. Ranar da aka yi kamun amarya da Ango ba ƙaramin tafiya hankalinsa ya yi akan Abu ba saboda wani irin gyaran jiki da aka yi mata. Ban da sheƙi da ƙyalli babu abin da take yi ga wankan lalle da aka yi mata haɗe ta waɗansu irin turararru masu masifar ƙamshi. Fulani Maryama haushi ne ya kamata ganin babu Salman a cikin kamun saboda Amaryarsa na masarautarsu bata kai ga ƙarasowa ba, da aka ce kuma za a yi musu kamun har shi a fusace yace baya buƙata ya fice daga gidan gabaɗaya. A daren ranar da aka yi kamu Saif ya kira Baiwa Laraba bayan ɗakin Fulani Zaliha, tana zuwa ta same shi a tsaye sai zarya yake kamar wanda ya yi wa Sarki ƙarya. Dukda duhun magriba be hana ta russunawa cikin girmamawa tana faɗin, "Allah ya taimake ka ranka shi daɗe an ce kana buƙatar gani na." Be ɗago ya kalle ta ba yace, "Ki kawo mini Zainab nan yanzu nan." Gabanta ne ya faɗi a firgice ta ɗago ta kalle shi ta ce, "Amma Ranka shi daɗe Fulani..." Ɗaga mata hannu ya yi saboda ya san ƙarashen labarin ba zai wuce a ce Mahaifiyarsa ta hana a fita da ita, don haka ya kalle ta fuska a tsuke yace, "Umarni ne na baki idan har aka kuskure mini na rantse har da Allah sai ranki ya mummunan ɓaci. Ki san dabara da za ki yi ki kawo mini ita." Baiwa laraba ta gyaɗa kai jiki na rawa ta wuce sashen Fulani Zaliha zuciyarta na zullimin ta yadda za ta kaiwa Saif Abu ba tare da asirinta ya tonu a wurin Fulani Zaliha. Tana shiga sashen Fulani Zaliha fara kame-kame da shige da fice, tana nan tsaye ta ga fitowar Abu sai dai tana shirin yi mata magana ta ga Amintacciyar Baiwar Fulani Zaliha tana biye da ita, gumi ne ya shiga keto mata kamar mara gaskiya saboda ta san Falmata amintacciyar Fulani Zaliha ce, duk wani abu bata iya ɓoyewa shugabar tasu saboda ba a taɓa haɗa kai da ita a ha'ince ta. Baiwa Laraba na tsaka da tunani ta ji Fulani Zaliha ta ƙwalawa Falmata kira, da sauri ta juya hakan ba ƙaramin faranta ran Laraba ya yi ba. Da sauri ta ja hannun Abu ɗakinsu Abu za ta yi magana Baiwa Laraba ta yi ƙasa da murya ta ce, "Allah ya taimake ki Me girma Saif yana bayan ɗaki yana jiranki don Allah ki yafa mayafin Bayi domin ɓadda kama, idan ban raka ki ba zan fuskanci mummunan ɓacin rai." Wani sanyin daɗi ne ya ratsa zuciyar Abu har sai da ta bayyana a fili, sauke wata nannauyar ajiyar zuciya ta yi ta ƙarbi mayafin me ɗauke da launin kayan Bayi ta yane kanta ta yadda ba za ka taɓa tsammanin ita bace. Har sun yi hanyar waje Laraba ta dawo da sauri ta janyo ƙauren banɗakin kamar da mutum a ciki ta rufe sannan suka tafi. Suna ƙarasawa Baiwa Laraba ta ce, "Allah ya taimake ka ya baka yawan rai a hanzarta domin Kar Fulani ta fahimci bata nan a samu matsala, amma a gafarce ni idan maganata ta yi kaushi." Kai ya gyaɗa mata yace, "Je ki zan neme ki." Tana tafiya ya ƙarasa wurin Abu da ke lulluɓe cikin mayafi sai zuba ƙamshi take, zame mayafinta ya yi zuwa wuyanta ƙamshin turaren jikinta ya ƙara dukan hancinsa. Lumshe idanunsa ya yi na ƴan sakanni sannan ya ware manyan idanunsa yana kallonta, kallon da yake mata ne ya sa ta ɗan tsargu har ta ɗago ta kalle shi, karaf idanunsu ya sarƙe da juna. Kashe mata ido ɗaya ya yi sai kuma ya shagwaɓe fuska yace, "Laifin me na yi? Me ya sa aka zaɓi haka domin azabtar tsokar da ke ɗawainiya da soyayyarki? Yau kusan tsawon wata biyu ban samu na yi tozali da kyakkyawar fuskarki ba." Abu sunkuyar da kai ƙasa ta yi tana jin bugun zuciyarta na tsananta saboda yadda kalamansa suke ratsa sassan cikin jikinta. Hannu ya sa ya ɗago haɓarta (Haramun ne) sai kuma ya janye hannun nasa da sauri saboda yadda ya ji wani irin yanayi da be taɓa jin irinsa ba. Jin ta yi shiru ya sa ya hura mata iska a fuska, cikin wani irin yanayi ta lumshe idonta Saif ya yi murmushi me sauti da sauri Abu ta ware idonta cikin jin kunya, ta shagwaɓe tana faɗin, "Ya Saif kar fa Ammi ta jini shiru." Ɗaga kafaɗarsa ya yi alamun rashin damuwa yace, "Sai ki ce mata kin je wurin mijinki." Da sauri Abu ta zaro ido ta ce, "Ammin zan gaya wa haka?" Murmushi ya yi yace, "Meye a ciki jibi ya rage ɗaurin aure fa." Juyawa ta yi za ta tafi da sauri ya sha gabanta yana ware hannuwansa, ɗan ɓata fuska ta yi haɗe da shagwaɓa ta ce, "Ya Saif Allah ka barni na tafi ni ba zan iya wannan rashin kunyar ba, idan aka ce mata an gammu ya zan yi?" Matsowa gabanta ta fara yi tana ja da baya har ta jingina ta bango ya matso gabda ita, har sai da ta kai suna jin numfashin juna yace, "Zainab!" Muryarsa ba ƙaramin kashe mata jiki ta yi ba a hankali ta ɗago ta kalle shi, shima ita yake kallo ya ci gaba da cewa, "Don Allah karki ƙara guje mini." Hannu ya ɗora a saitin zuciyarsa ya ci gaba da faɗin, "Rashin ganinki ba ƙarmin raunatar da rihina yake ba, ki yi mini alƙawarin duk daɗi duk wuya ba za ki guje mini ba domin ba zan iya jure rashinki ba." Abu ɗagowa ta yi ta kalli Saif tana jin wata irin ƙaunarsa na fisgarta, gyara tsayuwarta ta yi tana cewa, "Ya Saif! Kamar yadda jini yake da matuƙar tasiri a garkuwar jikin ɗan adam haka soyayyarka take zaga jini da tsokar jikina, ni ta ka ce bana tunanin akwai abin da zai kawo rabuwarmu idan ba mutuwa ba. Don Allah duk a halin da za mu kasance ka da ka guje ni saboda rashinka tamkar rasa numfashin da ke maƙale a gangar jikina ne. Ina neman alfarma a wurinka ban sani ba ko ina da wannan ƙimar a wurinka? Ban sani ba ko mutumci da darajata ta kai haka?" Hankali a tashe ya ɗago ya kalle ta bakin sa har rawa yake yace, "Wacce irin buƙata ce wannan faɗe ta matuƙar bata samawa mahalicci ba ni kuma na yi miki alƙawarin sai na biya miki ita." Abu ta ƙara narkewa tana narai-narai da idanu ta ce, "Don Allah ka da ka haɗa soyayyata da ta wata, ban zan iya ganinka da wata mace ba, wallahi ba zan iya jurawa ba saboda ina matsanancin kishinka bana jin zan iya jurar ganin ko da wata ta raɓi inuwarka ne " Ajiyar zuciya ya sauke yace, "Wallahi ba ƙaramin faɗar mini da gaba kika yi ba, na ɗauka wani muhimmin abu za ki nema a wurina. Indai wannan ne na yi miki alƙawari babu wata ƴa mace da za ta kaiki koda da ƙwayar zarra ce a wurina." Baiwa Laraba ce ta ƙaraso wurin jiki na rawa ta ce, "Allah ya taimke ka Fulani na cen tana cigiya don Allah ayi mini rai na mayar da ita." Saif zai yi magana da sauri Abu ta wuce gaba ta ce, "Mu je Labara don bana son a samu matsala Ammi ta yi fushi da ni." Babu yadda ya iya yana ji yana gani haka suka wuce, wani irin farinciki yake ji a zuciyarsa tare da fatan Allah ya nuna masa ranar ɗaurin aurensu lafiya. Abu na shiga soron gidan ita da Laraba suka yi dabara wuuf ta faɗa banɗaki, ba ta daɗe a ciki ba ta fito ta wuce ɗaki. Da kallon tuhuma Fulani Zaliha ta kalli Abu fuska a ɗaure ta ce, "Daga ina kike?" Abinka da mara gaskiya nan take ta fara kame-kame ganin haka ya sa Fulani Zaliha ta ce, "Wurin Saif kika je ko? Labari ya isa kunnena ance mini an gan ku tare. Karki manta nan fa gidan sarauta ne ko tusa kika yi me ƙarfi ana ankare da kai. Amma tun da na ga kamar kun matsu bari na je na samu Takawa nace ya tara mutane a ɗaure auren a daren nan kawai yanzu an gangaɗa akai ki kowa ya huta." Zaro ido waje Abu ta yi idanunta na cikowa da hawaye hannu bibbiyu ta durƙushe a wurin tana faɗin, "Don Allah Ammi ki yi haƙuri wallahi ba zan ƙara ba." Ganin yadda hankalin Abu ya ta shi ya sa Fulani Zaliha ta ce, "Shi ke nan je ki amma sai na yi nazari." Ƙara marairaricewa Abu ta yi ta ce, "Don Allah Ammi..." Fuska ba walwala Fulani Zaliha ta katse ta, "Ki wuce ɗaki akwai tukuɗin da na dama miki." Sum sum sum Abu ta wuce ciki jiki a sanyaye. Ranar juma'a wanda ya yi daidai da goma ga watan Jumada-Awwal a shekara ta dubu ɗaya da ɗari uku da saba'in da uku (Juma'a 10, Jumada-Awwal, 1373) wanda a kalandar bature ya yi daidai da sha huɗu ga watan sha biyu a shekara ta dubu ɗaya da dari tara da hamsin da ɗaya. (14/12/1951) Dubbanin mutane daga garuruwa daban-daban suka shaida ɗaurin auren Salman da Safiyya sai auren Saif da Abu, farin ciki wurin Sarki Aminullah abun baya musaltiwa. Mutane daga garuruwa ne suka halarci taron auren, har da baƙin turawa suka zo taya shi murna daga Ƙasar Ingila. Babu jimawa aka shiga kaɗe-kaɗe da wasannin Al'adu na gargajiya abun sai wanda ya gani gwanin burgewa. Duk wani abu na kayan auren an haɗa wa Abu wanda dangin gidan maza suke yi. Haka kayan ɗaki da duk wasu kayan al'ada da ake yi wa Ƴa mace Sarki Aminullah ya yi wa Abu, daga bayan gidan Sarki aka zaɓawa Saif da Salman wasu gidaje guda biyi iri ɗaya, sai dai suma gidajen suna cikin masarautar, haka ita ma Safiya ba ƙaramar dukiya iyayenta suka narka mata ba. Duk wani shagali da ake yi Salman baya farinciki da shi. Hasalima idan ka dube shi da kyau za ka fahimci sam auren kamar baya gabansa. Ranar da aka yi ɗaurin auren a ranar ne aka ɗauki amarya aka kaita ɗakin mijinta, Abu ta sha kuka sosai musamman da Mahaifiyarta take yi mata nasiha akan biyayyar aure, "Abu ki buɗe kunnenki da kyau ki ji ni, yanzu wani nauyi ya rataya a wuyanki me girman gaske. Igiyar aure ba abar wasa bace saboda matartabar da matar aure ke da ita ta ninka ta wacce bata da aure idan har ta riƙe mutumci, ƙima da martabarta. Ki sani ba soyayya kaɗai ita ce jigon aure ba, domin kar ki ɗauka yadda kuke soyayya a gida haka za a ɗore har cikin gida. A'a sam akwai bambamci saboda lokacin da ake waje neman fahimtar juna da samun kyakkyawar alaƙa a tsakani ake yi. Ya yinda aka yi aure kuma haƙuri da soyayya sune suke taka muhimmiyar rawa a zamatakewar aure. Yi na yi bari na bari ladabi da biyya sune jigo, haƙuri garkuwa ne kulawa ɗa'a ce godiya da girmamawa Tarbiyya ce. Duk abin da mijinki zai baki ki yi masa godiya zaman aure zo mu zauna zo mu saɓa ne, ba kodayaushe ake cikin farinciki ba. Wataran idan namiji ya guma miki sai ki ji duk duniya babu wanda ya tsaneki kamar shi, watarana kuma idan ya faranta miki ji za ki yi duk duniya babu wanda yake ƙaunarki fiye da shi." (Gara dai mu dinga gayawa ƴanmatanmu gaskiya 😂😂😂 ba wai kullin ace yayi kissing da romance da wacce tsiyar ake a gidan aure ba, wallahi duk wacce take ɗaukar huɗubar ƙaryar novel tana ruwa, ban ce kowacce soyayyar novel ƙarya bace amma akwai soyayyar da ke kanki idan kika karanta kinsan wacce zata faru da akasin haka. Ko munƙi ko munso Aure ɗan haƙuri ne duk fallin da wasu ƴan matan suke yi ba su shiga bane, saboda suna karanta littafi su ji ance bayan ta yi sallar asuba bata tashi ba sai sha biyu kafin ta tashi mijin ya gama komai tana tashi sun faɗa banɗaki an yi awa uku a toilet ana harka da soyewa 😂😂 ban da yaudarar kai wacce uwar za a yi shafe sama da awa uku ana yi a toilet? Wallahi mazanmu babu wanda zai yadda ki miƙe kullin a gado ace ya gama miki komai kina miƙe sai dai ya ruƙo hannunki ku faɗa toilet. Amma idan da me ja wata ta gwada gobe ta bamu labari 😂😂😂😂 Billahi na san karon ba zai yi da daɗi ba.🤣🤣) Abu ta ci kuka sosai haka ita ma Inna Habi har da share hawaye saboda rabuwar da za su yi da Abu. A ranar da aka kai Abu tare da wasu tsirarun ƙawayenta suka kwana saboda bisa ga al'ada hakan ake yi ga duk amaryar da aka kaita ɗakin mijin. Washegari aka yi buɗar kai tare wasu shagulgulan tsakanin ƙawayen amarya da ƴan tsirarun abokin Ango Saif saboda abokanansa biyu jal Huzaif da Haris, sune suka gayyato nasu abokan suka rufa musu baya. Washe garin buɗar kai Ango Salman ya shiga ɗakin amaryarsa Safiya haka daga ɓangaren Saif shima ya shiga ɗakin Amaryarsa tare da rakiyar abokansa. Shi kuwa Salman dama ba shi abokai shi kaɗai yake yawo kamar maye. Yana shiga ɗakin Bayin da ke zaune da Safiyya suka tashi suka fice, Salman gadan-gadan ya ƙarasa kan gadon ya janye hular alkyabbar jikin Safiyya. Dukda baya wani farinciki da auren amma ganin yadda Safiya ta sha kwalliya ba ƙaramin tafiya ta yi da shi ba, rungumota ya yi jikinsa yana shaƙar ƙamshin jikinta da aka wanketa cikin azababbun turarruka masu matuƙar ƙamshi. Ganin lamarin Salman na neman wuce gona da iri ya sa Safiya ta tattara ƙarfinta ta ɗan ture shi ta ce, "Yarima me ye haka?" Cikin kasalalliyar murya yace, "Me kika gani da idonki? Haƙƙina zan karɓa" Haushi ne ya kama ta ta ce, "Ko za ka karɓi haƙƙinka ai ka bi komai a sannu." Salman be jira cewarta ya fisge alkyabbar jikinta ya shiga neman ƙwatar haƙƙinsa. Da sallama ɗauke a bakinsa ya shiga ɗakin, daga bakin ƙofa ya tsaya ya harɗe hannuwansa yana kallonta cikin farinciki. Jin shiru babu alamun takowar mutum ya sa ta ɗago kai karaf suka haɗa ido. A kunyace ta sunkuyar da kai ƙasa tana wasa da ƴan yatsunta. A hankali ya fara takowa har ya zauna kusa da ita sannan ya zame hular alkyabbarta. Hannu ya sa ya ɗago haɓarta cikin tausasa murya yace, "Kunyar me ake ji." Abu shiru ta yi tana murmushi, goshinsu ya faɗa ya yi mata raɗa ƙasa-ƙasa sai gani nayi ta sunne kai ƙasa tana dariya, ɗago da kanta ya yi tana ƙoƙarin sunkuyarwa ta ji hannuwansa biyu ya tallafo fuskarta, yana goga hancinsu wuri ɗaya. kamar almara haka suka fara jin shassheƙar kuka daga waje Abu ce ta fara ɗagowa suka haɗa ido, tana shirin magana ya sa ɗan yatsansa akan bakinta yace, "Shiiii bari na duba na gani." Yana gama faɗa be jira cewarta ba ya ɗauki fitilar ƙwansu da ta kasance sabuwa dal da ita ya fita waje yana haske-haske. 🙄🙄🙄🙄🙄 Uban iya a dawo lafiya garin leƙe-leƙen idan ka kai kanka cen kai ka sani, ka fita ka bar Amarya Allah sa kar a gwada muku ɗiban albarka ba😂 Barkanmu da Juma'a🥰 _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [18/12/2021, 19:47] Ameera Adam🌚: 51... Takawa yake a hankali yana haskawa musamman wuraren da ya fi jin tashin sautin muryar me kukan, sashen hanyar banɗaki ya nufa daga cen bayan bishiyar Tsamiya yake jin tashin kukan mace, kukan ba ƙaramin taɓa zuciyarsa ya yi ba dukda be san wacce take kukan ba amma ya tabbata kukan na fitowa daga ƙaraƙashin zuciyarta ne. Abu da tun bayan fitowarsa ta fara jin tsoro na neman mamaye zuciyarta. Fitowar ta ya yi daidai ta hango shi da ta yi ya lula cen, da sauri ta ƙwala masa kira amma be waiwayota ba har sai da ya zagaya wurin bishiyar. Zuwansa ke da wuya ya ji ɗiff kamar an yi ruwa an ɗauke ya nemi kukan da yake ji ya rasa, sai ma kukan tsuntsaye da ƙananan ƙwari da ke tashi a wurin, juyowa ya yi yana daɗa haskawa daga cen jikin bango ya hango kamar inuwar mace a zaune ta cusa kanta cikin ƙafafuwanta. Yana ƙarasawa ya nemi inuwar ya rasa. Ganin haka ya sa Abu ta ƙara ƙwala masa kira a karo na biyi don haka ya juya da sauri ya nufi wurinta. Yana zuwa ta ja hannunsa cikin ɗaki a ɗan tsorace take kallonsa ta ce, "Ya Saif yanzu fa dare ne wallahi tsoro nake ji, a daren nan za ka je wurin bishiyar tsamiya ana zaune ƙalau." Jinjina kai ya yi yace, "Na leƙa in gani ko yara masu ganin ɗaki ne aka bar wata daga ciki." Abu ta kwaɓe fuska ta ce, "Gaskiya ni tsoro nake ji wallahi." Aljihunsa ya shiga lalube zuwa cen ya zaro wani ƙullin magani yace, "Bari na aika a kawo mana garwashi dama Ammi ce ta bani garin maganin nan na turare ne." Yana juyawa zai fita zaraf Abu ta bishi saboda ta gama razana da kukan da suka ji da farko. Babu yadda ya iya haka ya wuce yana gaba tana biye da shi, wani Dogari ya kira ɗaya daga cikin Dogarawan ƙofa ya aika aka ɗebo masa wuta suna zuwa ɗaki ya turara musu sannan ya ɗauko kazar da ya kawo musu ta amarci, a hankali ya fara bawa Abu amma saboda kunya ta kasa karɓa ta ci. Sai da ƙyar ta iya gutsira ta ci gutsire biyu daga haka ta ce ta ƙoshi. Saif ɓata fuska ya yi sai da ta ga ransa ya ɓaci sannan ta saki jiki ta suka ci gaba da ci. Bayan gama ciye-ciyensu suka gabatar da sallar nafila tare da addu'o'i sannan suka wuce kan gado suka ya da zanzo. Saboda gajiya Abu tana kwanciya bacci ya yi gaba da ita, Saif kwanciya ya yi a gefenta ya fara ƴan juye-juye. Abu cikin bacci ta fara jin baƙon lamari daga wurin Saif, da farko yi ta yi kamar ba ta ji shi ba amma daga baya da ta ji lamarin na neman gagar kundila ta shiga neman alfarmar ya ɗaga mata ƙafa. Gabaɗaya Saif birkice mata ya yi tun tana magiya har bakin ta ya yi laƙwas. (Bari mu wuce wurin kar na je na aiwatar da ɗiban albarka😂🤣) Washegari Salman tun farar safiya ya miƙe ya faɗa banɗaki ya tsarkake jikinsa, be bi ta kan Safiyya ba dukda yadda ta galabaita ko motsin kirki bata yi saboda ko kaɗan Salman be bi da ita ta lallami ba. Kai tsaye cikin gidansu ya nufa yana zuwa aka fara jansa da tsokanar ango-ango. Fulani Maryama na ɗakinta ta jiyo su ba ta kai ga miƙewa ba ta ji Salman ya shi ga wurinta, da mamaki ta kalleshi don gari ma be gama wayewa ba ta ce, "Salman lafiya da farar safiya haka? Ko Jakadiya sammako ta yi muku?" Yana daga tsaye yace, "Zuwa na yi na gaya muku a tura a gyara waccen yarinyar, gaskiya fa yarinya ta yi ƙoƙari don lokacin da nake tuki sai da na so wuce ƙofar mazugal..." A hassale ta katse cikin ɓacin rai ta ce, "Kai baka da hankali ne Salman ni Mahaifiyarka kake gayawa haka? Saboda rashin mutumci." Saif tun asuba ya taimakawa Abu ta gyara jikinta, ba ƙaramin tausaya mata ya yi ba, guntun tsaki ya ja ganin yadda zanin gadon ya yi da ya tuna dole sai ya ciro shi an shiga da shi cikin gida domin a tabbatar da amarya ta kai ƙimarta ko bata kai ba. Janye zanin gadon ya yi ya shimfiɗa wani sannan Abu ta hau ta kwanta ta koma bacci jikinta da ɗan ɗumi alamun zazzaɓi. SHAFIN DAI NA SAN BA ZAI MUKU DAƊI BA😢😢😢 AMMA KUYI HAƘURI HAKA YANAYIN LABARI YAKE GABA ZA KU FAHIMCI DALILIN HAKA, KAR KU MANTA A DUNIYA BA KOMAI MUTUM YAKE NEMA KUMA YA SAMU BA.😢 _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [19/12/2021, 12:46] Ameera Adam🌚: 52 Jakadiya da zumuɗi ta nufi gidan Amaren don tabbatarwa idonta tsegumin abin da aka umarce ta, da sallama ta samu shiga ɗakin Safiyya. Da fululluka ta fara cin karo da alkyabbar Safiyya, da ƙafa ta shure su ta fara kyaɓe baki ta ce, "Ƴar nan sannu kin ji. Girman kenan muma duk da haka muka zo nan. Yoo Allah na tuba ku ai da girmanku tun da ga alama daga ke har Abu kun kai sha biyar-biyar. Mu kuwa fa mu da sha bibbiyu aka haɗa mu da ƙaratan mazaje ai ba muyi ma langwaɓewarku ba. Tashi mu gani." Safiyya miƙewa ta yi a hankali da sauri Jakadiya ta ja gefe tana dafe ƙirji, Safiyya sai rangwaɗar da kai gefe take saboda azaba. Jakadiya ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "A'a lallai Salman gara da Takawa ya hanzarta aka yi auren nan. Allah na tuba da an ƙara wani lokaci wataƙila muma ya fara kawo mana farmaki, dubi yadda ya yi wa yar mutane tambaɗar rashin imani. Kai Amma dai Maryama ta haifi Jarababbe, ko dan ai be yar a ƙasa ba saboda lokacin Maryama da Takawa har guduwa yake tana nemansa saboda Jaraba." Safiyya ta gaji da surutan Jakadiya a ɗan fusace ta ce, "Kin zo taimaka mini ne ko surutu kika zo yi mini, ko kuma in sa a kira wacce za ta taimaka mini." Jadiya ta harareta a fakaice ta ce, "A'a wa kuma za ki kira a wannan yanayin da kike ciki wacce ta wuce ni." Jakadiya na surutu tana gyara gadon, sannan ta taimakawa Safiyya ta gyara jikinta. Tana gama gyarawa ta shimfiɗa wani zanin gadon, jikinta zafi zau da zazzaɓi ta koma kan gadon ta kwanta saboda ba ƙaramin jin jiki take ba. Jakadiya na gamawa ta wuce wurinsu Saif tana shiga ta tsaya a bakin ƙofa tana rangaɗa sallama, kasancewar ta ga takalmansa a bakin ƙofar. Saif ne ya fito yana ɗan murza idanu don shima baccin ya koma. Washe baki Jakadiya ta yi ta ce, "Allah ya taimaki Yarima, dama na zo ne domin na taimakawa Abu ta gyara jikinta sai kuma zanin gado da zan ɗauka, ka ga na matar Salman kai amma dai Salman an yi jarumin namiji, dubi yadda zanin gadonsu ya yi kaca-kaca da..." Cikin ɗaure fuska Saif ya ɗaga mata hannu yana faɗin, "Ban tambaye ki ba." Juyawa ya yi ya ɗauko mata zanin gadonsu ya miƙa mata yana jan guntun tsaki, yana shirin komawa ta ce, "Ai zan gyara Abu." Be juyo ya kalle ta yace, "Na gyara matata." Jakadiya ba haka ta so ba don ta so ta ga yadda Abu ta yi don ta ji daɗin isar da labari. Don haka ta ɗan tsuke fuska ta ce, "Amma ai ka san a ƙa'ida ni nake gyara duk wata sabuwar amarya." Saif ya kuma tamke fuska yace, "Ni na ɓata abata kuma na gyara ta." Yana gama faɗa ya shige ɗaki. Jakadiya haushi ya kuma turniƙeta ta juya ta mita da ƙunƙuni. "Eh ai ya nuna mini idonsa ya buɗe wai shi ya yi sabon aure, ai wallahi kamar kumbo kamar kayanta yaron nan babu abin da ya bari na Zaliha. Duk mugun halinta ya kwashe tsaf. Me babban ɗaki gabaɗaya ta shiga damuwa sakamakon ciwon Maryo da ta tashi da shi, wannan karanma ranga-ranga aka ɗauke ta zuwa asibiti. Sai da ƙyar Allah ya bada iko aka samu damar shawo kam ciwon nata. Ba ƙaramin faɗa likitan ya yi musu ba saboda yace tana cikin matsananciyar damuwa shi ya sa ciwon nata yake yawan ta shi akai-akai. Babu yadda suka iya a wannan karanma amsawa Likitan suka yi sannan suka ci gaba da bata kulawar da ta kamata. Ko kaɗan Sarki Abdallah be sanarwa da Fulani Fahima halin da Maryo take ciki ba, don ya san za ta shiga cikin matsananciyar damuwa. Lokacin da aka kai zannuwan gadon su Abu Inna Habi ba ƙaramin farinciki ta yi ba don ko ba komai, Abu ta kankaro mata daraja da ƙima a idon mutane. Sai dai tun daren ranar idanunta ya gagara bacci saboda miyagun mafarkan da ta dinga yi Maryo, wanda abun ba ƙaramin tsoro ya bata ba. Haka kawai zuciyarta take raya mata akwai damuwa saboda wannan mafarkan da take yi har sun fi na kwanakin baya muni. A daddafe take cinye kwanakin don ganin ƴan biki da sauran ƴan uwa da suka halarci bikin sun watse domin ta je ta tunkari Sarki Aminullah da maganar bakinta ayi wacce za a yi a ƙare, don ta ga ji da dakon zunubin da take yi ba dare babu rana. Bayan sati biyu da biki amare da angwaye ba ƙaramin murzar amarci suke yi ba cikin so da ƙauna. Safiyya babu yadda ta iya har ta fara sabawa da halin Salman saboda tuni zuciyarta ta afkawa soyayyarsa. A ɓangarensa shima ya ɗan rage wasu abubuwan yana ɗan lallaɓata wurin mu'amala ba kamar baya ba da yake yi mata ta ƙarfi da yaji. Sai dai babu wata hira me daɗi da take shiga tsakaninsu. Tsayawa gayawa me karatun soyayyar da ake ɓarza a gidan su Saif ɓata lokaci ne, amma a wannan lokacin ne Abu ta tabbatarwa zuciyarta babu wata ƴa mace da za ta iya samun gurbi a zuciyar Saif. Wani abun idan ya yi mata ita take jin kunya ba shi ba, saboda Saif gawurtaccen namiji ne a fagen iya soyayya, har mamaki take idan ya yi wani abun domin a baya ta ɗauka yadda yake shiru-shiru ta za ci babu wata duniyar gajimare da ya sani. (Maryo fans 😂 na san ji kuke kamar ku ɗebe mini albarka😂) Sarki Aminullah ba ƙaramin ɓacin rai ya shiga ba lokacin da ya gama jin zantukan da Inna Habi take gaya masa, kallonta ya yi ya ga yadda take zubda hawaye sai kuma ya ji ta bashi tausayi musamman da ya tuna yadda Maleek ya kafe kai da fata akan Maryo matarsa ce. Wayar salularsa ya sa wani Dogari ya ɗauko masa nan take aka danna lambar Sarki Abdallah, yana ɗagawa murya babu walwala Sarki Aminullah yace, "Sirikina ina buƙatar ganin yarinyar nan Maryo wacce Maleek yace matarsa ce, ina buƙatar ganinta cikin gaggawa daga yai zuwa gobe." Yana gama faɗar haka ya datse kiran. _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [20/12/2021, 13:01] Ameera Adam🌚: 53... *Amun afuwa pls saboda na ɗan yi kuskure wurin rubuta Sarki Aminullah ya ɗaga waya ya kira Sarki Abdallah, sai daga baya na farga wallahi idan kun duba yanayin shekarun labarin a lokacin babu wayar sadarwa. Yanzu mu barshi akan Sarki Aminullahi ya aikawa da Sarki Abdallah da takarda akan yana buƙatar ganin Maryo ciki gaggawa. Amun afuwa da wannan kuskuren*🌚 Sarki Abdallah jikinsa ne ya yi sanyi lokacin da ya gama karanta wasiƙar da aka aiko masa daga masarautar Kano, Fulani Fahima a lokacin tana zaune a gefensa ta ce, "Allah ya taimake ka wata muhimmiyar magana aka faɗa?" Kallonta ya yi yana nannaɗe wasiƙar hannunsa yace, "Sirikina ya buƙaci a mayar da Yarinyar cen cikin gaggawa saboda muhimmiyar magana. Hasalima ya tabbatar mini da cewar ba matar Maleek bace. Ba mayar da ne damuwa ta ba, babbar matsalar ta yadda za mu fuskance su da yanayin da yarinyar nan take ciki, kuma shin wani abu ya taɓa shiga tsakanin Maleek da ita? Kuma wanne jawabi za mu yi wa Me babban ɗaki wanda za ta gamsu?" Fulani Fahima ba ƙaramin daɗi ta ji domin dama ta jima da son haka, saboda ta san ko ba daɗe ko ba jima dole sai kowa ya san halin da Maryo take ciki don haka take ganin babu fa'idar ɓoyewa. Gyara zama ta yi ta ce, "Allah ya taimake ka ina ganin wannan ba abin damuwa bane. Mu fito mu gaya musu gaskiyar yadda ciwon ya same ta, ita kuma Me babban ɗaki sai mu nuna mata rubutacciyar samfefar da aka aiko. Wata ƙila ma damuwar da yarinyar nan take ciki zai yi mata sauƙi idan ta koma hannun mariƙiyyarta. Amma ina fargabar Allah ya sa babu wata mu'amala da ta shiga tsakaninsu." Jinjija kai yake cikin gansuwa da jawabanta shi ya sa yake ƙara ƙaunarta saboda duk wani abu da yake neman ɗaure masa kai ita take warware masa. Ba'a ɗauki lokaci ba ya sanarwa da Me babban ɗaki halin da ake ciki, da farko fitittike musu ta yi sai daga baya da ya lallameta sannan ta amince. Amma tun a lokacin da fara hawaye na rabuwa da Maryo saboda ba ƙaramin sabo suka yi ba, gabaɗaya kayan Maryo ta shiga haɗa mata tana haɗawa tana share hawaye gwanin ban tausayi. Ita kuma Maryo da take kwance akan ƙaramin gadon ƙarfe bata san abin da yake faruwa ba. Ɗan aiken Sarki Aminullah yana zaune yana jiran amsar da zai koma ya isarwa da shugabansa saƙon da aka ba shi, Sarki Abdallah ne ya umarci Dogari Lurwanu da ya rubuta amsar wasiƙar kamar haka. _Assalamu alaikum Sirikina fatan alheri a gare ka da fatan kuna cikin ƙoshin lafiya. Na riski saƙonka daga hannun Dogarinka Umaru, na yi matuƙar mamakin jin yadda wannan al'amari ya kasance, amma ina me baka haƙuri babu a dadi bisa ga wata larura da ta faɗawa wannan yarinya da ka aiko da takadda akan ta. Kasan duk abin da ya samu bawa rubutacce ne daga Ubangiji, kuma ba mu ɓoye maka saboda wata manufa ba sai don muna son nema mata magani na ɗan wani lokaci. In sha Allah za mu dawo da ita hannu da hannu da yardar Allah idan Allah ya kaimu rana ita yau me zuwa._ _SAƘO DAGA MASARAUTAR ADAMAWA_ Tambarin Masarautar Adamawa aka buga a jiki tare da naɗe farar takardar samfefar wacce aka yi rubutun ajami, aka bawa Dogarin da ya kawo takardar tare da guzurin da zai yi a hanya. Maleek tun da ya ji labarin tafiyar Maryo hankalinsa ba ƙaramin ta shi ya yi ba, dukda ya san ba matarsa bace amma idan ya kalle ta tana rage masa kewar Shukransa. Yana zaune a ɗakin Me babban ɗaki ita kuma tana lallaɓewa Maryo kanta, ya zuba mata ido yana tuna irin rayuwar da suka yi da ita da abubuwan al'ajabin da ta dinga yi kafin faruwar lalurarta, murmushin yaƙe ne ya suɓuce masa yana jin kewarta a zuciyarsa. Kallon ɗan bakinta da take cunowa gaba ya yi wanda da alama zafin kitson ne ya sa take ɗan tura baki don dai babu bakin magana ne, ta shi ya yi tsam ya ƙarasa wurin Me babban ɗaki yace, "Tsohuwa wannan kitson fa takura mata yake dubi yadda goshinta duk ya fito a bari sai an jima a ci gaba." Ya faɗa yana ƙoƙarin janye Maryo. Duka ta kai masa a baya ta ce, "Matsa mini daga gabana sakarkaru idan na biye ta yarinyar nan kanta a haka zai lalace dubi don Allah yadda fuskarta ta yi kyau amma da ta bar kai kamar na maza. Dududu kitson ƙwaya nawa ne ƙwaya takwas ne fa, na ƙi na sake ta ba zan saki kannan ba sai na gama." Maleek ficewa ya yi daga ɗakin yana mita don ya ga gaban goshin ta ya yi jawur. Lokacin da Saƙon Masarautar Adamawa ya samu Sarki Aminullah duk sai ya ji babu daɗi, dukda ya san komai muƙaddari ne amma yana jin kunyar a dawo da ita ga mariƙiyarta domin ta sha yi masa zarya amma ya ƙi bata dama. Lokaci ɗaya ya ji be kyauta ba a gefe ɗaya kuma yana fargabar irin larurar da za su yi tozali da ita wacce aka ce Maryo na ɗauke da ita. Kwanci tashi babu wuya a wurin Allah, kwanakin da Sarki Abdallah ya ɗiba sun cika. Sun shirya tsaf daga Me babban ɗaki, Maleek, Fulani Fahima, Maryo da Sarki Abdallah su kaɗai suka shirya tafiya don Fulani Fahima cewa ta yi ba za ta tafi da autarta ba ta zauna a wurin su Fulani. Duk budurin da ake Maryo bata sani ba sai dai jikinta yana bata akwai wani wuri da suke haramar tafiya. Maleek ne ya taimaka mata ta shi ga rumfar keken dokinsu wanda aka tanadarwa Me babban ɗaki amma ta ce fur ita da Maryo za su shiga, ganin haka ya sa Maleek shima ya shiga keken dokin na su Maryo. Fulani Fahima da Sarki Abdallah a wani keken dokin daban. Keken dokin Dogarai ne a gaba da suke ɗauke ba bindigogin farauta na sassaƙen itace, saboda koda za a samu farmakin wata dabbar, sai na su Me babban ɗaki yake bin su sannan na Sarki Abdallah yake biye da na su Maryo sai kuma keken dawakai biyu a baya da suke gadin su Fulani Fahima. Tafiya suka yi me nisan gaske sai da suka shafe wuni guda da rabin rana sannan suka ƙarasa Masarautar Kano me ɗumbin albarka. Maryo tun da ta ji tafiyar ta ƙi ƙarewa jikinta ya bata wataƙila Masarautar Kano suka nufa idan kuma ba cen bane to wani wurin ne me nisan gaske. Lokacin da suka sauka a ɓangaren Fulani Maryma suka sauka saboda duk abun Fulani Maryama tana matuƙar karrama duk wanda aka ce mata ya fito daga ɓangaren Sarki Aminullah ne, a wani ɓangaren kuma saboda ace ta fi sauran matan Sarki haba-haba da mutane ya sa take washe baki kamar wacce aka yi wa kyautar kujerar hajji. Me babban ɗaki tana riƙe da hannun Maryo har suka shiga ɗakin Fulani Maryama, shigarta ɗakin ke da wuya ta ji kanta ya yi wani irin sarawa, har sai da ta hannu ta ɗan dafe gefen kanta. Alamun zirarowar jini ta ji a hancinta, da sauri ta ɗauko ƙyallen wurin Saif ta fara gogewa. Fulani Maryama sai umarni take bayarwa ana jido kayan ciye-ciye da shaye-shaye ana direwa a gabansu. Tun da ta ƙyalla ido ta ga Maryo haka kawai ta ji gabanta na dukan uku-uku, suna haɗa ido da Maryo ta ji cikinta ya hautsine ita kuwa Maryo bata san ma me take yi ba. Ga wanda ya ga Maryo ba zai taɓa tsammanin tana da matsalar ido ba, saboda idanunta a buɗe suke tar za ta yi ta ɗan waige-waigenta kamar tana ganin abin da yake faruwa. Fulani Maryama bayan sun gaisa da su Me babban ɗaki tana son ta yi maganar Maryo tana jin tsoro ga shi ta ga sai kallonta take suna haɗa ido. Wani tsoron Maryo ne ya ɗarsu a zuciyarta haka dai ta ja bakinta ta tsuke. Inna Habi tun da ta ji shigowarsu Fulani Fahima ta kasa zaune ta kasa tsaye, daga cikin labulenta ta hango wucewar Maryo. Ta ga ta daɗa haske sosai sai dai ta ɗan rame hakan ne ya sa tsayinta ya ƙara fitowa sosai. Dabara ce ta faɗo mata don tana san ta shiga wurin Maryo ta san da zamanta a gidan tun da lokacin da Maryo ta tafi ba su koma sashen matan Sarki ba. Nakiyar da ta yi wa Fulani Maryama ta ɗauka ta nufi ɗakin bakinta ɗauke da sallama ta shiga, sai da ta ajiye musu a gabansu ta koma gefe ta fara gaishe da Me babban ɗaki. Tana shirin gaishe da Fulani Fahima suka ji an aiko da kiransu daga Fadar Sarki Aminullah. Inna Habi kallon Maryo take da mamaki duk sai ta ji ta muzanta don sun haɗa ido da Maryo ya fi a irga amma ba ta ga alamun za ta yi mata magana ba bare ta nuna ta santa. Jiki a sanyaye ta miƙe za ta fita Baiwar da ta isar da saƙon kiran ta tabbatar da ana nemansu har Inna Habi. Amsa mata suka yi sannan suka ta fice domin sanarwa da Dogarin da Sarki Aminullah ya aiko. Fulani Maryama ba ta so yadda aka ware ta ba amma ta tabbata koma meye akwai wani muhimmin abin da ya kawo su. Saboda da gama bikinsu Salman ko wata guda ba a yi ba kuma daga Fulani Fahima har Sarki Abdallah sun halarci bikin. Gabaɗaya suka hallara a cikin fadar Sarki Aminullah, Sarki Aminullah tare da Sarki Abdallah suna kan mazauni ɗaya. Cikin fadar iya waɗannan mutanen ne kawai sai Dogarawan da suke tsaron bakin ƙofar. Sarki Aminullah ne ya buɗe zaman nasu da Addu'a sannan ya gaishe da Me babban ɗakin cikin girmamawa. Kallon Inna Habi ya yi ya kalli jama'ar wurin ɗaya bayan ɗaya yace, "Maƙasudun wannan taron kusan za mu iya cewa ke ce kika jagorance shi, shin za ki iya sanar da mu gabaɗaya domin jin ta bakinki don sauran su tabbatar daga gare ki maganarnan ta fito." Inna Habi ta share ƙwallar idonta ta ƙara sanar musu da cewar Maryo dai ba matar Maleek bace hasalima budurwa ce ko auren fari bata taɓa yi mata ba. Jinjina kai gabaɗaya suka yi saboda labarin ba sabo bane a wurinsu tun da tuni an sanar da su a baya. Sarki Abdallah ya numfasa ya kalli Inna Habi yace, "Baiwar Allah amma kin san da haka me ya sa kika bari har muka tafi da ita, yanzu da wani abu ya shiga tsakaninta da yaron nan ya kike gani lamarin zai kasance, tun da mu gabaɓaya mun san matarsa Shukra kuma duk wanda ya san Shukra idan ya ga Maryo ba zai ce ba ita bace." Inna Habi jiki a sanyaye ta gaya musu dalilinta a lokacin iƙirarin cikin jikinta da Maryo take yi na Saif da kuma yadda ta ga Maleek ya dage akan Matarsa ce, ita a ganinta idan Maleek ya tafi da Maryo ba za a fahimci cikin jikinta ba shege bane. Gabaɗaya jikinsu sanyi ya yi musamman Sarki Aminullah, Sarki Abdallah ya kuma kallonta yace, "Ma sha Allah da kika fahimci kuskurenki kuma ba ki ji tsoron komai ba kika faɗi gaskiya, don kuskure kam an yi shi amma hamdalar da za mu yi da babu wani abu da ya haɗa Maleek da Maryo tun da na tuntuɓe shi tun a gida. Amma a yanzu muna so ki sanar da mu tsakaninki da Allah ya ya Maryo take a wurinki shin ke kika haifeta ko kuma ƴar riƙo ce?" Inna Habi ta kalli Maryo ta ji soyayyar yarinyar na ƙara shiga jikinta ci gaba da cewa, "Maryo dai ba ƴata bace hasalima babu wani dangi na Uwa ko Uba da muka haɗa da ita, sai dai Allah ya sani ina jin Maryo a cikin raina kamar ƴar da na haifa. Kamar yadda na sanar da Sarki Aminullah a baya mu fulani ne kuma fulanin tashi. Shekara goma sha biyar da suka wuce wata rana mun tafi kiwon awakai da shanun mun cikin daji, mun yi kiwo mun dawo kamar yadda muka saba a hanyar mu ta dawowa mukan tsaya a bakin wani rafi mu shayar da dabbobinmu ruwa. Mu kuma mu kan wanke jikinmu mu ɗebi wani mu zubawa jakkai su wuce mana da su gida. A ranar ma haka ina goye da Abu wacce a lokacin bata fi wata tara ba na ji fitsari ya matseni. Abu na miƙawa Goggota ta riƙe mini ita ni kuma na kewa na tsugunna domin kama ruwa, ina hanyata ta dawowa na ji kukan jaririya a bakin wata ƙatuwar bishiyar Kuka. Allah ya sani a lokacin na yi matuƙar tsorata sai dai kukan da yarinyar take yi ya sa nake ganin ba zan iya wucewa na barta a wurin ba. Jikina na rawa saboda tsoro ba ƙarasa wurin da addu'a a bakina na ɗauko ta tana ci gaba da tsanyara kuka. Na yi tsammanin ina ɗaukanta wani abun zai same ni amma sai na ji shiru, ina ɗaukata ta sa hannu a baki tana tsotsa. Da sauri na ƙarasa wurin su Goggo na nuna musu Maryo, suma ba ƙaramin tsorata suka yi ba don a nan take Goggota tace sai na mayar da ita ko ƴar aljanu ce na ɗauko. Baffa shi hana yace wannan ƴar mutane ce ta yuwu wata mara tsoron Allahn ce ta jefar da ita, kuma idan ma ƴar aljanu ce muna zuwa zai yi mata turare. Haka na rungumi Maryo muka tafi gida muka ci gaba da rayuwa na haɗa ta da Abu ina kula da su." Inna Habi ta ɗago ta kalli Maryo ta ci gaba da cewa. "Tun ranar da na tsinci Maryo Allah ya dasa mini ƙaunarta daidai da rana ɗaya ban taɓa bambamta ta da Abu ba, hatta su kansu ba su taɓa sanin ba ciki ɗaya suka fito ba sai lokacin da wannan maganar ta Maleek da cikin Saif ta tashi. Ni na riƙe Maryo tun tana tsumma har kawo girmanta, ban da tafiyarta Adamawa Maryo taba taɓa tafiyar kwana biyu ta bar gabana ba ita da ƴar uwarta."Sarki Aminullah ya jinjina kai cikin yabawa da kyawawan haki irin na wannan baiwar Allahr, a yanzu ya daina ganin laifinta saboda dama ɗan adam tara yake be cika goma ba don haka kowanne ɗan Adam yana kuskure. Maleek jikinsa ne ya gama sanyi yanzu ya ƙara tabbatarwa da Maryo ba Shukransa bace. Inna Habi kamar ta san abin da yake ransa ta ce, "Yaro bansan wacece Shukranka ba amma da alama kana matsanancin sonta. Don Allah idan ba za ka damu ba zan so na ji a wane gari Shukranka take ka ga idan aka bincika wataƙila a gano wurin da take." Maleek ya goge zufar da ke goshinsa yana zubar da hawaye yace, "Shukra bata da kowa sai ni, nine na zame mata Uwa da Ubanta. Kowa ya juya mata baya a lokacin da ni na kasa guje mata, Shukra ta karramani ta ceci rayuwata da ba don ita ba ta tuni ko gawata ba za a samu labarinta ba. Amma duk wannan karamcin da ta yi mini be sai da samu ko da kallon rahama ba daga ahalina. An azabtar mini da matata an baƙanta mata fiye da tunanin me tunani. Sai ga shi yanzu kowa nemanta yake a lokacin da ta yi mana nisa, wataƙila ma ta yi mana nisan da har abada ba za mu ƙara riskarta ba. Fulani Fahima ita ma hawaye take saboda tabbas sun nuna ƙyama ga Shukra sai ga shi suna nemanta ido rufe. Maleek sai da ya sha kukansa kuma babu wanda ya hana shi saboda a lokacin da yake wannan maganar ji yake kamar an kuma soso masa da tsohon gyambon da ke cikin zuciyarsa. Share hawayensa ya yi ya ci gaba da cewa, "Shekara biyar da suka gabata a cikin garin Shanono cikin wani ƙauye me suna Rigar Arɗo..." _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [21/12/2021, 19:32] Ameera Adam🌚: 54... "Shekara biyar baya da suka gabata a cikin garin Shanono cikin wata ruga me suna Rigar Arɗo. Rigar Arɗo riga ce me ɗauke da fulani wacce take cike da yalwar dabbobi da daga dangin shanu, awakai da tsirarun tsuntsaye. A wannan rugar muka yada zango ni da wani Baturen ingila me suna John da zo ƙasar Najeriya ya sauka a masarautarmu kasamakon akwai kyakkyawar alaƙa tsakanin Mahaifina da ɗan Sarkin ingila wanda ya kasance mahaifi a wurin John. Ya zo ƙasar akan binciken wata turɓaya wacce bincike ya nuna kasantuwarta a wancen yankin. Duk cikin masarautarmu nine wanda na bawa fannin ilimin boko muhimmanci, hasalima ni cikakken Jami'in Ɗan Sanda ne. Saɓanin ƴan uwana da suka fi karkata a harkokin da suka shafi sarauta. Zuwansa da bayyana manufar zuwansa ba ƙaramin daɗi na ji don ni mutum ne me yawan son binciken harkokin da ya shafi ilimin boko har ma da na addini. Lokacin da zai tafi wannan gari tare da shi muka tafi duk wani abu da yake yi ina ankare da shi. Lokacin da muka sauka a wannan rugar sai da muka nemi izini a wurin me garin wannan yankin, da farko Me gari be fahimci manufar John ba kuma duk cikinsu babu me jin turanci sai ni. Haka ya dinga bayani ina fassara musu, amma dukda haka be saki jiki da mu ba sai da na nuna masa tambarin masarautarmu sannan hankalinsa ya ɗan kwanta, don yana gudun abin da zai cutar da al'ummarsa. John ne ya fara yi musu bayani cikin harshen nasara ina fassara musu dukda nima ba kowanne turaci nake fahimta daga gare shi ba. "Ya kai wannan Shugaba ban zo domin cutar da mutanenka ba, na zo ne domin na yi bincike da aka tabbatar mini da cewar akwai wani taɓo a yankin afirka wanda bincike ya tabbatar da cewar a wannan yankin yake." Lokacin da Me gari ya ji haka kallo na ya yi da rashin fahimta yace, "Kai Yaro yanzu duk faɗin ƙasar nan a rasa inda za a yi bincken taɓo sai ƙasata an ya ba da wata manufa kuka zo ba?" Ganin yanayin da Me gari ya ke ciki ya sa John ya fahimci lalle akwai matsala don haka ya ciro wani ID kad ɗinsa ya miƙawa Me gari ya ci gaba, "Wannan kawai ya isa shedar da za ta tabbatar maka da babu wani abun cutarwa da muka zo da shi. Amma idan muka aikata muku wani abu duk hukuncin da ya dace ku ɗauka akanmu." A lokacin ban ji ko ɗar ba saboda na zaƙu na ga wanne irin bincike za a yo tun da hannunsa na ɗauke da wata ƙaramar na'ura da na lura yana zura ƙwayar idonsa a ciki. John ya ci gaba da bayani ina fassara musu, "Ba wani abu za mu yi ba da wannan na'urar zan haska domin gano shin wannan taɓon irin wanda muke buƙa ɗin ne ko kuma kamanceceniya ce." Ya ƙarasa magana yana curo wata ƴar ƙwalba yana nunawa Me gari yace, "A wannan ɗan muzubin zan ɗebi ƙasar daga nan zan koma ƙasa ta domin tabbatar da abin da muke bincike, idan har ita ce za ka ƙara ganin dawowarmu domin tattaunawa akan abin da ya kamata." Da ƙyar dai muka samu Me gari ya amince muka wuce cikin gari aka fara bincike-bincike. Duk wurin da muka wuce sai dai ka ga Fulani na faɗawa bukkokinsu suna ɓuya, wasu da suke ɗan jin hausa za ka ji suna faɗin, "Arna sun shigo" sakamakon ganin Baturen nan sanye da ƙananan kaya wanda hakan ya kasance baƙon lamari. Tun safe muke abu ɗaya tun ina marmarin abun har na ji na fara gajiya, haka Me gari tun yana biye da mu da Dogarawansa har suka ga ji suka juya suka barmu ni da John muna ta karakaina. Muna gabda ƙarasawa gidan Me gari bayan mu samu nasara ɗiban wani taɓo a wani ƙanƙanin rafi, Wata Matashiyar Bafulatana muka gani tana ganin mu taso daga rafin nan ta saki tulin hannunta a tsorace. Yarinya ce ƙarama don a lokacin ba ta fi shekara goma ba, tana shirin juyawa da gudu na ce, " 'Yan mata tsaya mana, ina za ki je?" Har lokacin ba ta gama sakin jiki da mu amma hakalinta ya ɗan kwanta da ta ji na yi hausa, cikin hausar da bata wadaci bakinta ba ta ce, "Hai gide mun banu, hai wannan rafin baƙin basa ɗiban ruwansa. Aradun Allah mun boɗare da ambaliyar ruwa. Ku yi ta kanku in ba haka ba shanye ku zai yi." Tana gama faɗa ta juya a guje ta koma ruga, ganin haka ya sa na fara tsorata na shiga yi wa John bayanin abin da ta sanar da ni. Ina gama yi masa bayani muka ji wata irin mahaukaciyar guɗa daga cikin ruwan har sai da muka ji kamar dodon kunnuwanmu za su doɗe. Hankali a tashe muka bazama da gudu kafin muje cikin gari tuni labari ya ba zu akan turawa sun taɓo baƙin rafi. Iska ce ta fara kaɗawa a garin tuni Fulanin yankin suka fara kaɗa shanayensu kowanne da ƴar jakarsa fatarsa a hannu. Haka zaman wannan rugar yake a duk lokacin da haka ta faru sai dai su bar cikin rugar, in ya so daga baya wasu fulanin su sai su yada zango a wurin, amma waɗannan idan suka tafi sun tafi kenan. Lokacin da muka zo wucewa ta wata bukka wannan matashiyar budurwar muka gani tana rungume da wata Dattijuwa, tana ta ƙoƙarin ɗora ta a kan amalanken Shanu. Da sauri na taimaka mata na cicciɓi Dattijuwar wanda da alama babu ƙoshin lafiya a tattare da ita. Muna ɗora ta muka jiyo hargowar tahowar ruwan da ya fara ambaliya da sauri muka iza shannun suka tafi da Dattijuwar na riƙe hannun yarinyar ƙam, John kuma ya riƙe hannuna muka dinga zabga gudu. Mun yi tafiya sosai sannan muka bar wannan rugar, sai dai babban tashin hankalin da muka gaza tsayar da wannan shanun wacce Tsohuwar nan take ciki. Suna gudu muna biye da su a baya cikin ikon Allah sai Shanun nan suka yi karo da wasu manyan bishiyoyi kamar wacce aka wurgo haka muka ga amalanken ya hantsila, sai ga wannan Baiwar Allahr ta faɗo kanta ya bugu da dutse har ya fashe. Da sauri muka ƙarasa wurinta na tallafota da sauri matashiyar budurwar ta ƙaraso da kuka tana fillaci haɗe da hausa tana jijjiga Matar, hawaye na ji a idanuna na ban tausayi ban yi aune ba na ji hannun Dattijuwar ta ruƙo hannuna tana faɗin, "Ka riƙe mini Shukura Amana don Allah. Ba ta da kowa a duniyar nan bayan ni, ni kuma da alama lokaci na ya zo don Allah ka riƙe mini ita da zuciya..." Maganarta ce ta maƙale lokacin da numfashinta ya ɗauke. Irin kukan da Shukra take yi duk wanda ya ga halin da take ciki sai ya zubar mata da ƙwallah. Da ƙyar na samu na lallashi Shukra shi kuma John yana gefe yana hawaye, nima hawayen nake yi don tun da nake a duniya ban taɓa shiga irin wannan tashin hankalin ba. A hankali na ƙarasa wurin amalanken na janyo wani zani na rufeta sannan na yi tafiya me ɗan nisa na ƙarasa wata ruga na sanar da su halin da muke ciki. Tare muka dawo da su suka taimaka aka ɗauki gawar Mahaifiyar Shukra muka ƙarasa da ita aka yi mata sutura. Kwananmu biyu a garin muka wuce cen Masarautarmu ya yinda acen hankalinsu ba ƙaramin tashi ya yi ba bisa ganin mun ɗebe kwanaki ba mu dawo ba, don har Takawa na shirin tura Dogarawa su bi sawunmu sai gamu mun koma musu a hargitse cikin tashin hankali, a gefe ɗaya kuma Shukra da babu abin da take yi sai kuka. Lokacin da muka je dana tambayi John kwalbar da ya ɗebi taɓo sai cewa ya yi she be ma san inda take ba, saboda gabaɗaya ya ruɗe ya shiga tashin hankali. A daddafe ya yi kwana ɗaya daga nan ya wuce ƙasarsu ta Ingila. Shukra duk gidan nan babu wanda take yadda da shi sai ni, saboda gabaɗaya a tsorace take da kowa kasancewar bata saba mu'amala a irin yanayin Masarautarmu ba. Sannu a hankali na fara fuskantar yadda mutanen gidanmu suke ƙyamarta, hasalima da farko komai tayi dariya suke yi mata saboda rashin wayewarta. Ko kaɗan haka baya mini daɗi kuma na fara nuna musu hakan, sai kuma suka fara chamfata wai tun ranar da muka dawo da Shukra baƙin al'amura suke faruwa marasa daɗi. Haka nake tausarta idan na ga tana kuka na yi ta bata haƙuri, tun abun yana damunta har ya zame mata jiki. Kuma wannan tsangwamar ba wai iya Mata da ƴaƴan Sarki ba har Mahaifiyata ba a barta a baya ba wurin nuna ƙyamarta ba. Shekararta biyu a masarautarmu tuni na faɗa soyayyar Shukra wanda ita ma tuni na lura da yanayinta. Ban sha wahalar bayyana mata sirrin zuciyata ba domin ita ma ta yi zurfi a soyayyata. Ban gayawa Mahaifiyata ba saboda na san ba ƙaunar Shukra take ba bare ta bani goyon baya. Mahaifina na sanarwa da buƙatata be yi wata-wata ba ya haɗa matansa ya sanar musu tare da hukuncin juma'a me zuwa zai sa a ɗaura mana aure. Kafin ranar kuwa ba ƙaramim ƙwarbai aka yi da Mahaifiyata ga Fulani Babba na ƙara zuga ta. Juma'a me zuwa aka ɗaura aurena da Shukra kuma wani ikon Allah a ranar da aka ɗaura aurenmu ranar muka samu takarda akan rasuwar Kakata wato Mahaifiyar Mahaifiyata, kafin Mahaifiyata su gama shiri Allah ya saukar mini da wata larura wanda na yanke jiki nan take ba tare da na san abin da yake faruwa ba. A wannan lokacin tsanani a ƙaru a wurin Shukra kowa ya tashi mayya yake kiranta saboda banda maita wai babu yadda za a yi ana ɗaur aure ango ya faɗi. Haka Shukra ta ci gaba da jinyata memakon rayuwar amarci amma wannan amaryar haka ta ƙare kwanakin amarcinta wurin wanke mini fitsari da kashi tare da wani irin amai na nake yi me warin gaske. Sai da na shafe shekara guda a haka sannan Allah ya kawo mini makarin ciwon a lokacin kowa ya gaza da ni babu me zuwa wurina sai Mahaifiyata da Mahaifina, ita ma takaicin ganin Shukra na bani kulawa ya sa ta ke kwashe kwanaki ba tare da ta waiwayo ni ba, saboda duk yadda ta so a raba aurena da Shukra Takawa cewa ya yi zai tambayi Shukra idan tana son a raba auren zai raba idan kuma bata so za mu ci gaba da zama a haka har zuwa wani lokaci idan anga ciwon babu ranar warkewa sai a raba auren, kuma ana tambayar Shukra ta fashe da kuka ta ce ita abarta tana sona a haka. Lokacin da na samu Lafiya Shukra ta fi kowa farinciki a gidanmu Amma warkewata be sa ta samu sa'ida daga wurin Mutanen gidanmu ba. A cikin kwanakin nan Takawa ya sa a ka hau yi mana ƴan gyara-gyare, ba a ɗauki kwanaki ba muka tare muka ci gaba rayuwarmu cikin farinciki. Shukra mace ce me haƙurin gaske duk irin abin da ake yi mata a gabana da bayan idona ba za ta taɓa nuna mini a fuskarta ba, muna cikin wannan yanayin da daɗi babu daɗi Shukra ta samu ciki. Nan tsanani ya ƙaru a wurinta daga wurin Mahaifiyata har wurin Fulani babba don dama a yadda na fahimta Fulani Babba ta fi tsananta mata fiye da Ummi. lokacin cikinta na da wata uku, Ummi da Fulani Babba suka sakata kwalemar ɗakunansu dukda bayin da suke cikin gidan nan amma Shukra bata gaza ba haka ta gama da ɗakin Ummi ta koma ɗakin Fulani Babba. Tana gama wannan aikin jini ya ɓalle mata a ranar ta yi ɓarin wannan cikin, shine ɓarin da ta yi har ta wuni ta kwana a sume." Maleek na zuwa nan a zancensa Sarki Abdallah ya saki salati ya kalli Fulani Fahima ta da take zabda ƙwalla yace, "Fahima ina yi miki kallon me hankali ashe kanki da saura, yanzu saboda Allah da yarinyar mutane ta mutu me za ku gayawa Ubangijinku?" Fulani Fahima ta share hawaye ta ce, "Wallahi sharrin sheɗan ne da muguwar huɗubar da Fulani Babba take yi mini." Cikin takaici Sarki Abdallah yace, "Ai shi ke nan ga shi ta bar muku duniyar sai ku ci karen ku babu babbaka. Wallahi na fara ɗora ɗan zargi akan mutuwar yarinyar saboda mutuwarta na ƙunshe da al'ajabi." Fulani Fahima ba ta tanka masa ba saboda ta san ko za ta haɗiyi Qur'ani ba za ta fita ba idan ta ce ba ita ta haddasa mutuwar ba." Maleek ya jingina da bango yana lumshe ido ya ci gaba da cewa, "Hutun da Shukra ta samu na ɗan lokacin da ta yi jinya ne amma ko sati ba ta yi da yin ɓarin ba aka koma ƴar gidan jiya. A wannan karan ne na magantu akan izayar da ake yi mata ta yi yawa, saboda tana auren ɗan Sarki amma ko wacce take auren Bawan gidanmu ta fita kwanciyar hankali. Ba'a ɗaɗe da yin ɓarinta ba ta kuma samun ciki shima cikin me matuƙar wahalarwa, don ko cikin da ta yi ɓarinsa be bata wahala kamar wannan ba. Da yake Allah ya yi cikin jikinta sai ya taka ƙasa a wannan rayuwar Allah ya sauke ta lafiya ta haifo Tagwayen ƴan biyu duk maza. Tun daga wannan lokacin Ummi ta fara sauke ƙiyayyar da take yi mata. Ganin haka ya sa na same ta a ɗaki na dinga yi mata nasiha a nan take ta nuna mini nadamarta, ba ƙaramin daɗi na ji ba don a lokacin ba ƙaramin kulawa take bawa Shukra da abin da ta haifa ba. Tun daga ranar suka fara raba gari da Fulani Babba don ba haka ta so ba. Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya har Allah ya kaimu ranar da ba zan manta da ita ba. Kasancewata ɗaya daga cikin Jami'in Ɗan Sanda ya sa ba ko yaushe nake zaune a cikin Masarautarmu ba, don bayan haihuwar Shukra da wata biyu aka yi mini canjin aiki zuwa Ƙasar zariya. A ranar da lamarin zai kasance haka kawai jikina ya bani na koma don ganin halin da iyalina suke ciki, sai dai wani babban tashin hankali dana ruska ina zuwa na samu sashen Shukra ya ƙone ƙurmus babu abin da aka iya fitarwa a ciki. Na shiga tashin hankalin da tun da na zo duniya ban taɓa shiga ba..." Maganar Maleek ce ta maƙale sakamakon kukan da ya ci ƙarfinsa. Jikin mutanen wurin ne ya yi sanyi, Sarki Abdallah ya zubawa Fulani Fahima idanu yace, "Fahima ki gaya mini tsakaninki da Ubangijinki me kike sani game da mutuwar matar yaron nan." Fulani Fahima da hankalinta ya gama tashi ta ce, "Ranka shi daɗe wallahi ko Qur'ani zan iya dafawa akan ban da masaniya dangane da mutuwar Shukra, abin da na sani gabannin asuba ƙaurin hayaƙi ne ya farkar da ni ina fita na samu Dogarai da Bayi carko-carko a tsaye wurin ruguzajjen kuma ƙonannan ginin da su Shukra suke ciki yana ci da wuta. Wallahi wannan ne gaskiyar abin da na sani." Sarki Aminullah ya numfasa ya kalli Maleek cikin tausayawa yace, "Maleek ina fatan za ka rungumi ƙaddarar da Ubangiji ya saukar maka. Addu'a za ka yi mata Ubangiji ya jiƙansu ya gafarta musu." Fulani Fahima ta kalli yayanta ta ce, "Allah ya taimakeka don Allah idan babu damuwa a aura masa Maryo don na san hankalinsa zai kwanta da ita." Sarki Aminullah ya yi wani irin murmushi da ta kasa gane manufarsa yace, "Fahima kenan, ƙarfin mulkinmu ba shi zai bamu lasisin zartar abin da muka ga dama ba. Yarinyar nan mutum ce kamar kowa babu yadda za a yi mu aurar da ita tana cikin lalura ba tare da mun ji ra'ayinta ba. A baya mun yi kuskure kuma wannan karon ba za mu maimaita ba, za mu ci gaba da kula da ita har Allah ya bata lafiya idan ta warware sai Maleek ya nemi soyayyarta, idan ta amince da shi falillahil hamdihi idan kuma ba ta amince da shi ba, ba za mu yi mata dole ba." A firgice Inna Habi ta ɗago ta kalli Sarki Aminullah ta ce, "Allah ya taimake ka wani abun ne ya samu Maryo?" Yanayin yadda ta yi maganar za ka fahimci tana cikin tashin hankali. Nana take Me babban ɗaki ta zayyanewa Inna Habi duk abin da ya faru da Maryo. Inna Habi bata san lokacin da ta matsa da sauri ta rungume Maryo tana fashewa da wani irin kuka ba. Kamar wacce ta fahimci Inna Habi ce a jikin nan hawaye fara bin idanun Maryo tana yi tana laluben hannun Inna Habi, aikiwa tana taɓo cindon da ke gefen ƙaramin ɗan yatsan Inna Habi Maryo ta saki wani irin kuka me ban tausayi don da alama ta fahimci a jikin wacce take yanzu. Sarki Aminullah duk yadda ya kai ga dauriya sai da ya zubar da ƙwalla, ganin suna ƙara karyar masa da zuciya yasa ya sallame su tare da Jaddada zaman Maryo a hannun Inna Habi kuma a ɓangaren Fulani Maryama. Fulani Fahima, Me babban ɗaki, Maleek da Sarki Aminullah kwanansu ɗaya suna juya Masarautar Adamawa. Maleek da Me babban ɗaki ba ƙaramin kuka suka ci ba don duk wanda ya kalli Maleek zai ɗauka mutuwa aka yi masa, Me babban ɗaki kuwa da ƙyar aka raba su da Maryo don a lokaci ɗaya duk ta fige ta fita hayyacinta. A haka suka yi sallama suka juya masarautarsu. Labarin dawowar Maryo da lalurarta lokaci ɗaya ya karaɗe Masarautar Kano, Fulani Maryama da Jakadiya farinciki a wurinsu kamar waɗanda aka yi wa albishir da gidan aljanna. Tsafi gaskiyar me shi. Fulani Maryama haka ta dinga hurawa Jakadiya hanci tana faɗin surukullenta ne ya kama Maryo har ta na nakashe. BAYAN WATA BAKWAI Abu ce zaune da tulelen cikinta ta marairaicewa Saif a shagwaɓe tana faɗin, "Don Allah Abu Nouf ka taimaka ka barni na je na gano ƴar uwata, dukda ina matuƙar jin kunyarta amma tun da na ji labarin dawowarta jiya a wurin Baiwa Nafi ko baccin kirki na kasa. Wallahi ban da sukuni tun da aka ce mini ga a halin da take ciki. Ina fargabar tozali da halin da take ciki, na san Maryo ita kanta ina na a ranta don Allah ka barni na je na gano ta ko na ji daɗi." Ta ƙarasa faɗa tana zubda hawaye don Allah ya sani duk duniya mutane uku ne masu muhimmanci a rayuwarta, daga Inna Habi, Saif sai Maryo. Jiya tana kwance a ɗaki ta ji Baiwa Nafi ita da Sahu suna hirar Maryo, karaf ta tambaye su anan suka ƙara mata haske. Ranar kuwa ta sha kuka kamar me haka ta kwana tana juyi tun Saif na lallashinta har ya gaji. Kallonta Saif ya yi yace, "Ba na ce miki kar na ƙara jin maganarta a bakinki ba? Idan kin ga kin fita daga gidan sai dai idan wanka za ki je gida." _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [22/12/2021, 18:29] Ameera Adam🌚: 55... "Maryama ko sama da ƙasa za ta haɗe wallahi sai na tafi da gudan jinina, don nima ɗan Adam ne kamar kowa ina buƙatar me tsaya mini tun da girma ya fara kamani. Idan na yi miki na miki idan ma waɗannan shekarun da aka kwashe ban yi miki ba ba damuwa ta bace. Na yi miki hallaci amma kika sak mini da butulci, dama wannan ranar nake jira domin na ci alwashin sai na tozarta ki. Amma kin ji na yi rantsuwa wallahi sai na tafi Saif, ba zan zauna kura da shan bugu Gardi da kwace kuɗi ba, ni da haihuwar yaro wani banza cen yana mora." Fulani Maryama ta zube bisa kan ƙafafuwanta tana faɗin, "Don Allah Ɗan magori ka taimakeni ka rufa mini asiri wallahi idan asiri na ya tonu na kaɗe har hanjina, duk duniya mutane biyu ne kawai suka san Saif ba Ɗan Sarki Aminullah bane. Daga kai sai Jakadiya..." Maryo ta katse mata maganarta da faɗin, "Sai kuma ni!" Hankali a tashe ta ɗago ta kalli Maryo a zabure ta miƙe tsaye tana nuna ta da ɗan yatsanta bakin ta na rawa ta ce, "Yanzu ma ke ce?" Maryo ta fashe da dariya ta gyaɗa mata kai cikin ƙwarin gwiwa ta ce, "Kina mamaki ne? Kin ɗauka za ki sha da wannan baƙin zalincin na ki? Kin yaudari kanki domin rana dubu ta ɓarawo rana ɗaya tak ta me kaya." Ɗan Magori ya hango Saif yana ƙarasowa ya damƙi hannunsa yace, "Wannan surutan banza ku ya dama amma tun da na ɗauki ɗana ku je cen ku ƙara." Saif ne ya ɗan fara turjewa Ɗan Magori ya kalle shi yanan murmushi ya nuna Maryo da ɗan yatsansa yace, "In dai kana son mallakar wannan ka biyo ni ni kuma na yi maka alƙawarin taimaka maka har sai ka mallaketa." Saif haka ya bi Ɗan magori kamar raƙumi da akala. Fulani Maryama ban da kuka babu abin da take yi. Maryo dariya ta fara sheƙa mata tun tana yi a hankali har dariyarta ta fara tsoratar Fulani Maryama. Firgigit ta farka daga mummunan mafarkin da take yawan yi a ƴan tsirarun kwanakin nan, gumi ta haɗa sharkaf jikinta har wannan lokacin be daina rawa ba. Ba ƙaramin tsorata ta yi da mafarkin wannan ranar ba, babban tashin hankalinta da duk mafarkin da za ta yi Ɗan magori take gani raɗau a cikin mafarkinta ga shi kuma na wannan ranar har da Maryo a ciki. Ɗan tsoron Maryo ne ya ɗarsu a zuciyarta sai dai kuma lokacin da ta tuna da lalaurar da ke jikinta sai hankalinta ya ɗan kwanta. A fili ta furta, "Ɗan Magori me ye dalilin bibiyar da kake yi mini a cikin mafarkina bayan ka shafe sama da shekaru masu yawa, me yake shirin faruwa da ni ne an ya ba wani abu ne yake shirin faruwa da ni ba?" Wani tsagi daga cikin zuciyarta yana nuna mata da tayi watsi da wannan mafarkin domin shirmen Mafarki ne. Baccin da Fulani Maryama ta gagara kowa haka ta zauna tana saƙa da warwarar yadda za ta ɓullowa waɗannan munanan mafarkan masu neman rikitar da ita lokaci ɗaya. Bayan kwana biyu Inna Habi na zaune tana yankewa Maryo farce, tana yi tana jin babu daɗi a zuciyarta saboda kusan kullin da kalar masu maganin da suke duba Maryo suna bata magunguna, wasu daga ciko har da turare. Sai dai duk ranar da aka yi mata turare kwana suke babu daɗi ba ƙaramin jiki take ji ba, haka Inna Habi take kwana akanta tana tofa mata addu'o'i sai a hankali jikin yake ɗan yi mata sauƙi. A ɓangare ɗaya kuma Salman ya tsira shigo musu ɗaki haka kawai bata yi aune ba sai ta riski ya faɗo musu ɗaki babu sallama, haka zai sa Maryo a gaba yana zabga dariya son ransa. Wani lokacin idan tana kwance har hannu yake sakawa ya tayar da ita zaune ya dinga leƙa fuskarta yana dariya. A wannan lokacin tana lura da yadda Maryo take fusata tana ƙoƙarin fisge jikinta, daga baya kuma sai ta fashe da kuka haka za ta wuni ta kwananda ɓacin rai. Wani abu da yake ɗaurewa Inna Habi kai ko da Salman be taɓa Maryo ba indai zai shiga ɗakin to ranar haka za ta wuni ta kwana tana kuka. Ranar da abin ya ishi Inna Habi Salman na shigowa ta ɗaure fuska ta ce, "Yarima maganar gaskiya abin da kake yi mini bana jin daɗi yau Maryo ko ɗan mutum ta kashe maka sai haka, da me yarinya za ta ji da lauluar jikinta ko da wannan dariyar da kake yi mata mara tushe?" Wata dariyar ya kuma saki yana nuna Inna Habi yace, "Ki iya bakinki idan ba haka ba wallahi sai na mayar da ke abar tausayi fiya da kike ganinta a wannan halin." Yawun bakin Inna Habi ne ya kusa ƙafewa nan take ta ɗora zargin ciwon Maryo akansa saboda furucin da ya yi da kuma yadda yake zuwa yana sheƙa mata dariya. Inna Habi ba ta ƙara tanka masa ba har ya gama abin da zai yi ya fice. Yana fita ta je ta rungume Maryo kusan lokaci ɗaya suka fashe da matsanancin kuka. Malam Liman Abdurrahman bn Safyan ne ya jagoranci yaɗa da'awa a ƙananan ƙauyukan da ke cikin birnin kano, ƙauyukan da suka kai wannan jihadin ga maguzawa a ƙarƙashin birnin Kano suke, irin su Doguwa, Zangon Dakata, Dawakin Tofa da sauransu. Cikin ikon Allah, suka nasara musuluntar da dubban Maguzawa da tsirarun kiristoci a ciki. Kasancewar boren da ƴan uwan waɗannan mutanen suka yi musu saboda karɓar addinin Musuluci ya sa suka taho da su cikin masarauta, kasancewar Sarki shi ne Uban kowa matsawar shi yake jagorantar wannan al'ummar. Yawan wannan mutane ya sa Sarki Aminullah ya umarci da a fara fitar da sabbabin gine-gine, domin rage cukoson Bayi a cikin ɗakuna. Saboda kafin zuwan waɗannan baƙin ana samu Bayi biyar har shida a ɗaki ɗaya. Wannan dalili ya sa aka shiga sare bishiyoyi da ƙananan sukoki aka shiga fitar da ɗakuna tare da faɗaɗa girman Masallaci, saboda samun wadatuwar gabatar da ibada yadda ya kamata. Tsugunne yake a gaban Mahaifiyarsa bayan sun gaisa take tambayarsa Abu da jikinta, a kunyace yake amsa mata daga haka suka shiga hirar duniya. Bayan ya yi mata sallama miƙewa ya yi zai tafi kawai sai gani ta yi ya yanke jiki ya faɗi. Hankali a tashe ta faɗa kansa tana ambatar sunansa, "Saif me yake faruwa be? Saif lafiyarka kuwa?" Wani irin gumi ne ya rufe shi na ƴan sakanni sai kuma jikinsa ya fara wani irin karkarwa. Duk abin da yake faruwa Saif be san Mahaifiyarsa na yi ba har sai da ya ji zafin na raguwa daga jikinsa, a hankali ya ɗago ya kalli Mahaifiyarsa yace, "Ammina!" Yana gama faɗa ya yunƙura zai ta shi ta taimaka masa ya tashi sai yace, "Ammi jiri nake ji." Fulani Zaliha bata amsa masa ba ta ci gana da tofa masa addu'o'in bakinta, ruwa ta miƙa masa ya sha sannan ta kalle shi ta ce, "Saif kana yawan yin azkar kuwa?" Murmushi ya yi saboda wani irin farinciki da ya ji yana ziyartar zuciyarsa, miƙawa ya ƙara yi yace, "Wallahi ina yi Ammi yauma tsautsayi ne." Duk yadda ta so hana shi fita be haƙura ba. Sallama ya yi mata ya wuce gida yana jin zuciyarsa fes. "Ke Sahura kalle ni da kyau, wannan garin maganin da na baki barbaɗa mata za yi a abinci ko ruwa, wallahi idan kika wuce yau sai na ɓatar da ke. Ki bani hankalinki nan idan kika bari asirinki ya tonu kece a ciki." Sahura da ta yi fiƙi-fiƙi da idanu ta ce, "Ba za a samu matsala ba ya shugaba ta." Fulani Maryama ta ci gaba da cewa, "Ki tabbatar kin ga ta fara naƙuda kafin ki fito, don babu yadda za ayi ta riga matar Saif haihuwa yana matsayin Yarima. Amma kika kuskura aka samu matsala ranki sai ya yi mummunan ɓaci." Jiki na rawa Sahura ta soke ƙullin maganin da bakin zaninta sannan ta fice daga gidan. Saif na zuwa gida ya faɗa kan gado yana lumshe ido, Abu kallonsa ta yi ta ce, "Abu Nouf an ya kana lafiya?" Kallonta ya yi sai ya sunkuyar da kai ƙasa yace, "Bani da sukuni sam saboda ina kewarta, ban san a wanne yanayi take ba amma jikina yana bani tana cikin damuwa." Cikin Abu ne ya kaɗa har sai da ɗan cikinta ya juya, mamaki ɗauke a fuskarsa yace, "Akan wa kake magana?" Kamar yana jiran tambayarta ya sake marairaice fuska yace, "Rayzuta! Na san wanda ya cutar da ita amma wannan karan dole na ɗau mataki akansa. Ita ce rabin rayuwata bana jin zan iya rayuwa da wata macen bayan ita, ba zan iya ci gaba da jin yadda take rayuwar ƙasƙanci ba, na rantse da girman Allah idan na har ya yi gangancin ciken jikinta ya samu matsala sai na datse rayuwarsa." Abu jijiga Saif ta yi hankalinta ba ƙaramin tashi ya yi ba ta ce, "Saif ni kake ambatar sunan wata a gabana shin wace ce wannan da ta asirce ka lokaci ɗaya? Me na yi mata da za ta raba ni da kai? Wacece wannan da soyayyarta ta rufe maka ido har ka gagara shakkata kake begenta a gabana." Hannuwa biyu ya sa ya tallafo fuskarta idanunsa ya zuba a kanta yana faɗin, "Ita ɗin rayuwata ce! Farincikana ce. Maryo ce wacce a duk bugun numfashina yana sauka ne da zallar soyayyarta." Abu dishi-dishi ta fara gani da ƙyar ta jingina da bango tana jin wani irin zafi a cikin zuciyarta, lokaci ɗaya kuma sai ta saki wani irin kuka me tsuma zuciya. Amun afuwa da errors ban tace shi ba. _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI_ [25/12/2021, 19:30] Ameera Adam🌚: 56... TUNA BAYA... *SHEKARA DUBU UKU BAYA* DAULATUL JINNUL SAHARA A wancen zamanin a cikin wannan Daular akwai wata gawurtaciyyar Masarautar Aljanu wacce take cike da tsantsar izza irin ta sarauta, Mulki irin na waɗanda suka gada iyaye da kakanni ba taka haye ba. Kamusul Birmi shine ainihin cikakken sunan wannan Sarkin na wannan Masarautar, ya gaji mahaifinsa ne bayan rasuwar Mahaifinsa. Asalinsu sun fito daga zuriyar Fararen fulanin Aljanun doron ƙasa, yawancin su Aljanu ne marasa haƙuri da sauri fushi sai Uba Uwa sun kasance masu matsanancin faɗa. Sai dai suna da matuƙar tausayi da tausasawa wanda yake da buƙatar taimako wala Aljani ɗan uwansu ko a cikin Mutane. Sarki Kimusul Birmi mafaɗacin gaske ne sai dai yana da saurin fahimta saɓanin ƴan uwansa. Mahaifinsa Birmil Ƙasi ya ga ji sarautar ne daga hannun Wan mahafinsa sakamakon Juddul Bahi yana da ƙaracin shekaru. Juddul Bahi ɗa ɗaya ne tulo a wurin Sarkin wancen nahiyar, ƙanƙantar shekaru da rashin ƙwarewa a mulki ya sa aka naɗa Mahaifin Kimusul Birmi. (Ku fahima da kyau kar gaba kanku ya kulle, Ai nihin sarauta ta gidan su Juddul Bahi ce wato Sarki Garzukul Juddu da ya mutu sai aka bawa Ɗan ƙaninsa Birmul Ƙasi. Da ya mutu aka bawa ɗansa na Fari Kimusul Birmi.) Kimusul Birmi yana da mata biyu Farratul Janwasu ita ce matarsa uwar gida tun auren saurayi da budurwa, Da mahaifinta da Mahafiyar Sarki Kisumul Birmi ƴaƴan mata suke auren gida aka yi musu. Sun shafe sheƙara sama da Talatin da aure babu wani labarin ciki daga wurin Farratul Janwasu, wannan lamari ba ƙaramin ɗaga hankalinsa ya yi ba yana ta taraddadin kar ya mutu be samu magaji ko magajiya ba. Ana haka har ya haɗu da Wurshil Ba'is ƴar Sarkin Buzayen Aljanun wancen lokacin. Lokaci ɗaya ya ji ya kamu da ƙaunarta ba a ɗauki lokaci ba aka ɗaura musu aure. Kasancewar Farratu Macece me sanin ya kamata ya sa babu wani abu da ya dame ta domin ta san haihuwa lokaci ce kuma Allah shi yake bayar da ita. Da auren su ko shekara biyu ba a rufa ba Wurshil Ba'is ta Haife kyakkyawar ƴarta, gwanin birgewa da ban sha'awa. A lokacin Masoyansa da dama ne suka nuna farin cikinsu ya yinda masu baƙin cikin suma ssuka shiga sahun masu nuna farinciki amma zuciyarau baƙiƙƙirin take kamar gawayi. Kisumul Birmi da kansa ya tambayi Farratu ta za ɓi sunan da ta ga ya dace a sakawa Jaririyar, sakamakon karamcin kulawar da take bawa amaryarsa saboda ya san son so fusabillahi take yi mata ba za ta cutar da ita ba. Farratu ba ƙaramin daɗi ta ji ba ganin irin wannan girmamawar da aka bata har da ƙwallarta sanan ta ce a saka mata suna RAYZUTA sunan ya matuƙar dacewa da ita, don haka aka shiga shagulgunan suna na ban mamaki tare da gayyatar manyan masaratun Aljanu na ko ina a faɗin duniya. Waziri Mardil Kibsan ɗaya ne daga cikin Masu himtawa Masarautar Sarki Kimusul Birmi, kuma babban aminin Sarki. Sun ta so tun suna yara tare suka yi komai har aure kusan lokaci ɗaya suka yi, amintarsu ta dabance shi ya sa duk cikin masarautar babu wanda Sarki Kisumul Birmi ya yadda da shi sama da Mardil Kibsan saboda duk rintsi baya taɓa fitar masa da sirrinsa. Yana da ƴaƴa biyu Mace da na miji Babban Ɗansa me suna FURZAAN sai me bin sa HIDRAT. Lokacin da aka haifi Rayzuta Furzaan na da sheka goma sha biyu a duniya, ya yinda ƙanwarsa take da shekara ɗaya rak a duniya. Balbutu shine shugaban bayin da suke hidima a ƙarƙashin Masarautar Daulatul Jinnul Sahara, Aljani ne kwaɗayayye me son zuciya da zalintar na ƙasa da shi a fakaice kuma ya kasance me mara kyakkyawar ɗabi'a. Duk wani mugun abu da miyagun halaye yana da su sai dai da yake ya iya takunsa babu wanda zai fahimci tsantsar halayyarsa. Yana da ɗa ɗaya tal a duniya me suna ZULIK sai dai kafin Zulik ya haifi ƴaƴa da yawa suna mutuwa. Bincike ya bayyana Bulbutu ya yi wa Mahaifiyarsa Fyaɗa har ta samu ciki shine ta haifi Zulik, bayan haihuwarsa baƙin ciki ya sa zuciyarta ta buga ta mutu. Wannan kenan! Duk in da nutsuwa da kwanciyar hankali suke sun yi baram-baram a cikin gidan Abu da Saif saboda baƙon al'amarin da Saif ya shigar masu da shi cikin gidan aurensu ba tare da Abu ta tsammace shi ba. Lokaci ɗaya ta zabge ta faɗa kamar wacce ta kwana biyu tana jinya saboda ko lokacin da ta yi laulauyi bata yi ramar da ta yi a wannan lokacin ba, ta rasa gane masa ba shi da magana sai ta Maryo, hatta doguwar hira baya iya yi da Abu wannan ya ƙara jefa ta cikin kogin tashin hankali. Za fi biyu ne ya haɗar mata na farko masoyinta annurin zuciyarta ya juya mata baya, na biyu kuma babu inda take zuwa bare ta samu sukunin sanar da Mahaifiyarta halin da take ciki. Lokaci ɗaya ta fara saka ɗan zargi akan Maryo take ganin kamar asiri ta yi wa Saif shi ya sa har ta fake da ciwon makantar ƙarya. Da daddare bayan sallar Isha'i Abu na zaune tana jiran shigowar Saif saboda tun safe da ya fice daga gidan be ƙara waiwayo ta ba. Tana jin motsinsa zumbur ta miƙe ta ɗaga labule tana murmushi amma ga mamakinta sai ta hangoshi ya nufi hanyar banɗakinsu yana zuwa bakin bishiyar Ɗorawar ya samu wuri ya zauna a wurin, shi kaɗai ya fara murmushi sakamakon tuna waɗansu irin abubuwan baya da ya yi. A hankali ya buɗe baki yana faɗin, "Ina ji a jikina kina kusa da ni, wannan ɓoyan da kike yi sam ba zai fisshe ki ba domin indan kika shiga hannuna sai na baki mamaki yarinya." Sai kuma ya marairaice murya yana faɗin, "Amma dai kin san azabatar da zuciyata kike yi, ni na san kina tare da ni amma duk ina kika na yi alƙawarin zan nemo ki domin kece farincikina." Abu ce a tsaye tana hawaye ta ce, "Saif!" Ɗagowa ya yi yana kallonta ta ci gaba da zubda hawaye tana faɗin. "An ya Maryo ba asiri ta yi maka ba? Da wannan daren za ka zo nan kana surutai. Ni kam indai asiri ne gaskiya Allah ya isa tsakanina da ita." Huci ya fara yi saboda yadda maganganun Abu suka yi masa zafi a zuciya, nuna ta ya yi da ɗan yatsa yana huci yana faɗin, "Ki gyara kalamanki akanta saboda ita ta musamman ce idan kika sake faɗa mata makamanciyar wannan maganar za ki gane baki da wayo, sakarai shashasha. Yana gama faɗa ya fice fuuu daga gidan. Abu durƙushewa ta yi a wurin tana fashewa da wani irin matsanancin kuka me tsuma zuciya, tana komawa ɗaki ta fara haɗa kaya tana cin alwashin zaman ta da Saif ya zo ƙarshe. Saif na fita sashen Mahaifinsa ya nufa, daga ɗan nesa ya hango Salman na tahowa fuska a murtuke. Saif ya yi niyyar yi masa magana ya ga hakan ba shi da fa'ida. Salman ne ya sha gabansa yana nuna shi da yatsa yace, "Na ga alamar ka samu kanka amma har yanzu da sauran rina a kaba." Murmushi Saif ya yi yace, "Idan ka ji mutum na tsoron dare ba a ɗaure shi ya kwance bane. Mu zuba ni da kai mu gani shege ka fasa. Wallahi idan baka yi wasa ba wannan karan sai dai gyatuma ta haifi wani." Wucewa ya yi ta gefensa ya wuce saboda zuciyarsa da ransa duka a ɓace suke. Salman ya yi saki wata dariyar ƙeta yana cewa, "Tarayya ke sa Zomo ya auri sarauniyar giwa. Amma baƙar wahala ita ke sa Shege ya nemi Ubansa." Ya sake waigawa yana kallon Saif yana sakin murmushi. Abu na tsaka da haɗa kaya Baiwa Tine ta shiga da sallama cikin girmamawa ta miƙawa Abu akushin da Fulani Zaliha ta aikota da shi wanda ta saba aika mata da abinci, karɓa ta yi ta ajiye a gefe sai kuma ta ji jikinta ya yi sanyi, musamman da ta tuna yadda Mahaifiyar Saif take ɗawainiya da ita. Wannan dalili ya sa ta fasa tafiya gida. Washegari Kamar daga sama Inna Habi ta ji Sallamar Maleek, bayan ya gaishe da Fulani Maryama ya ƙarasa wurin Inna Habi, sam Fulani Maryama bata so haka ba amma ta barwa kanta sai ya ta fi zata cancarewa Inna Habi. Gaisuwar mutumci suka yi da Inna Habi haka kawai ta ji tana ƙaunar Maleek saboda yadda yake bawa Maryo kulawa. Ido ya zubawa Maryo da bata san da zuwansa ba yana ji a zuciyarsa ina ma za ta iya ganinsa har ta buɗe baki ta yi masa magana. Ya jima suna hira da Inna Habi sannan ya tashi ya nufi sashen sauran Matan Sarki Aminullah. Sashen Fulani Zaliha ne ƙarshe ita ma sun jima suna hira sannan ya miƙe ya yi mata sallama. A soron tsakiya suka haɗu da Saif bayan sun gaisa Saif yace, "Ɗan uwa lallai ka miƙe da zumunci ina jin ko wata biyu ba ka yi ba rabonka da nan ya su Ummi." Maleek ya yi murmushi yace, "Kai kuwa ina da mara lafiya ai dole na zo dubiya." A ɗan hanzarce ya kalle shi yace, "Waye ba lafiya a nan?" Da mamaki Maleek ya kalle shi yace, "Maryo mana yarinyar da take kama da matata Shukra." Sunan Maryo ne ya yi masa wata irin kuɗa a kunne har sai da ɗan runtsa idanu, sai kuma ya damƙe hannun Maleek da ƙarfi yana faɗin, "Tana ina?" Maleek be yi mamaki ba ya ɗauka Saif na ta ya shi jimami ne kansa tsaye yace, "Mu ƙarasa na yi musu sallama tana wurin Babarta Inna Habi." A hankali Saif ya maimata, "Inna Habi dai Mahaifiyar Abu?" Maleek sam be ji shi ba sakamakon tuni ya yi gaba yana son ya yi musu sallama don daga nan Garin Zazzau zai wuce. Tun shigarsu gidan gaban Saif yake faɗuwa yana jin wani iri a jikinsa, a gaggauce ya gaishe da Fulani Maryama sannan suka wuce Ɗakin Inna Habi Maryo na kwance jikin Inna Habi tana tsefe mata kai. Maleek ne ya fara shiga Saif na biye da shi. Tun shigar Saif gidan a zabure Maryo ta miƙe tana lalube-lakube tana buɗe baki alamar tana son yin magana amma ta kasa, kawai sai ta fashe da wani irin tana ci gaba da lalubawa. Hankalin Inna Habi ba ƙaramin tashi ya yi ba tana ƙoƙarin kama Maryo amma tana kwacewa. Saif na arba ta ita da sauri ya ƙarasa wurinta cikin wani irin yanayi ya sa hannu biyu rungumeta a jikinsa, Maryo na jin haka ta sauke wata irin nannanuyar ajiyar zuciya sai dai ko kaɗan bata yi yunƙurin hanashi ba. Ɗago da kanta ya yi ya hurawa idanunta iska, ya sa bakinsa a daidai kunnenta ya hura iskar da ƙarfi nan take jikinta ya fara wata irin karkarwa. Ja da baya ta fara yi tana murza idonta sai kuma ta waiga wurin Inna Habi da take tsaye kamar gunki sakamakon tozali da abin da mijin ƴarta ya yi akan idonta. Da gudu ta tafi ta rungumeta tana faɗin, "Inna kece a gabana nake ganinki." Saif ya ƙarasa ga hanyo Maryo tana faɗawa Jikinsa yace, "Ni ba ki yi maraba da ni ba?" BILLAHI AKWAI ƘURA GIDAN SARKI AMINULLAH YA KUSA KAMAWA DA WUTA😂 _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI_ [30/12/2021, 17:38] Ameera Adam🌚: 57.... A kunyace Maryo ta sunne kai ƙasa don sai yanzu take jin nauyin abin da ta yi a gaban Inna Habi, kiciniyar kwace kanta take Saif ya haɗa goshinsu wuri ɗaya har yana jin yadda sautin ƙirjinta yake bugawa da sauri-sauri, kamar me yi mata raɗa a kunne haka muryarsa ta fara sauka tana ratsa sassan jikinta yana faɗin, "Ba dai guduwa za ki yi ba?" Kallon gefen da Inna Habi take ta yi ta mayar masa da amsa cikin sigar da ya yi mata magana, "Inna tana kallonmu fa." Sassauta riƙon da ya yi mata ya yi ai kuwa kamar me jira da sauri ta ƙwace kanta tana murmushi ta koma cen bayan Inna Habi ta rungomata ta baya tana ɗora kanta a gefen kafaɗarta. Ilahirin jikin Inna Habi ya yi sanyi saboda abu ne da bata taɓa tsammaninsa ba, a yadda ta lura babu wata damuwa a tattare da Maryo sai ma ta lura shauƙin da suke nuna juya kamar mata da mijin da suka yi shekaru ba tare da juna ba. Maleek da ke gefe gabaɓaya annurinsa ya ɗauke sai furzar da iska yake me zafi yana wurgawa Saif mugun kallo, takawa ya fara yi a hankali zai ƙarasa wurin Maryo a hargitse Maleek ya buga masa wata uwar tsawa yana faɗin, "Dakata! Wane irin shirme kake yi haka?" Nan take annurin da ke fuskar Maryo da Saif ya ɗauke kamar waɗanda aka isar musu da saƙon mutuwa. Saif ne ya zuba masa idanu sai da ya lumshe su ya sake buɗewa sannan ya kuma watsa masa manyan idanuwansa da suka fara sauya launi, da wata irin murya ya kalle shi yana faɗin, "Ina matukar ganin mutumcinka Ɗan uwa karka bari ya zube, domin na tabbata idan ya ɓare ko ƙwayar zarra ba za ka iya ɗiba daga gare ni ba. A wannan karon na yi alƙwarin duk wanda ya yi niyyar katange ni da ita na rantse da Allah sai na datse numfashinsa." Kamar wanda aka jefo daga sama haka ya faɗo musu ɗakin yana haki tamkar wanda ya wuni ya kwana yana tseren gudu. Fuskarsa a murtuke take babu ɗigon fara'a ya kalli Saif yana jin wata irin tsanarsa na mamaye masa zuciyarsa, sai da ya haɗiyi yawu me ɗaci sannan ya dube shi yana nuna shi da ɗan yatsa yana cewa, "A wannan karon ka kaini maƙurar bango amma zan nuna bakin rijiya ba wurin wasan makaho bane, kuma ko Kura ta rame ta fi ƙarfin gawurtaccen karen farauta. Na tabbata wannan karon idan aka ce ka dube ta da kallon rahama sai ka faɗi ka suma saboda irin izayar da zan wanzar maka..." A hassale Maryo ta katse shi da faɗin, "Ganin gida yake sa kare zagin Kura amma ba a daji ba. Kada ka manta kowa ya aikata son ransa zai ga ba daidai ba. Amma kuma zan ƙara tunatar da kai ko cikin tumaki rago ke zuwa fada. Ka yi yaƙi da dukkan jarumtarka ba da kaifin tsafi ba, idan baka manta ba a baya ina gaya maka kai ba me sa'a bane kuma ba za ka taɓa zama me sa'a ba." Wani malalacin murmushi Salman ya saki yace, "Zan rangwanta masa albarkacin soyayyar da kike yi masa, saboda azabtar da masoyi a gaban masoyi yana da matuƙar ciwo. Amma na yi rantsuwa na ƙara sai na nusar da ku Abubuwa da yawa suna ɓata a fada ba sai Takalmi ba." Maryo za ta sake magana Saif ya ɗaga mata hannu nan take idonta ya ciko da ƙwalla ta ce, "Don Allah a wannan karon karka dakatar da ni, ka fi kowa sanin wanene shi bana son ya ƙara nasara akanmu."Cikin sigar lallashi Saif ya dube ta ya sa hannu yana goge mata zirin hawayen da ya zubo mata sannan yace, "Wuƙar fiɗar giwa ba girma gare ta ba sai dai kaifi. Alƙawari na ɗaukarwa kaina duk rintsi ba zan bar me shirin yi mini iyaka da ke ba. Ki kwantar da hankalinki hargagin damusa baya firgita Namijin Zaki. Kamar baki san shi da hargagi ba ban son ki sawa kanki damuwa kin ji." Maryo gyaɗa masa kai ta yi tana watsawa Salman harara. Maleek da Inna Habi zama suka yi kamar mutum mutimi suna kallon ikon Allah, don yawancin wannan zaurancen nasu ba fahimta suke ba. Salman ne ya taka gaban Saif yana gyaɗa kai kamar na ƙadangare yace, "Wuya makarantar kare haka zalika wuya ita ke sa gawa sakin tusa. Amma ka sani alamar rago tana ga ɗaurin bante don haka idan kere na yawo zabo na yawo watarana za su haɗu." Yana gama faɗar haka ya fice daga ɗakin yana huci zuciyarsa na ƙuna. Bayan fitarsa babu jimawa Saif ya mara masa baya kowa ya yi hanyar gidansa. Sai a lokacin Maryo ta ɗan sha jinin jikinta yadda ta ga Inna Habi ta yi laƙwas tana binta da kallo. Abu ce ta faɗo mata a rai da sauri ta kalli Inna Habi ta ce, "Inna ina Abu take?" Ras gaban Inna Habi ta buga saboda kullin da wannan tunanin take kwana tana tashi, babban damuwarta ace idan Maryo ta samu lafiya ta wace sigar za ta fara sanar mata da mijin da ƴar uwarta take aure. Jin ta yi shiru ya sa Maryo ta ƙara cewa, "Ba dai har yanzu tana sashen Fulani Zaliha ba?" Jiki a sanyaye kamar kazar da aka jefa da gishiri ta ce, "Kin san fa ƴar uwarki ta yi aure tana gidan mijinta." Wani uban tsalle Maryo ta buga ta ɗane Inna Habi tana faɗin, "Don Allah Inna? Ina ne gidanta a rakani?" Maleek kallonta yake cikin birgewa yana mamakin wannan baiwa da ikon Allah, abu ɗaya zai rabata da Shukransa ita wannan ya lura tana da hatsaniya saɓanin Shukra da ko hira bata cika yi da mutane ba. Inna Habi ta yi mata hararar wasa ta ce, "Tun ba ki gama warware ba yau-yau fa kika samu lafiya, babu inda za ki sai kin ƙara warwarewa." Ɗan turo baki gaba ta yi ta ce, "Don Allah Inna ki sa a raka ni na kwana biyu ban ganta ba." Maleek ne ya yi gyaran murya yace, "Maryo babu magana kuma?" Kunya ce ta kama ta don sun haɗa ido da shi ya fi a ƙirga amma da yake a cikin shauƙi take ba su gaisa ba, a ɗan kunyace ta ce, "Ina Wuni!" Gyara tsayuwa ya yi, sai da zuba hannu a aljihu yace, "Lafiya ƙalau ya jikin" Ta bashi amsa, "Da sauƙi." ya mayar da akalar kallonsa ga Inna Habi yace, "To Allah ƙara sauki Inna ni zan wuce sai an kwana biyu." Ina ta ce, "Har tafiya Audulmaleek? To a gaida gida Allah ya tsare a gaishe da Fulani da Mai Babban ɗaki." Ya amsa mata tare ta yin gaba, zunguro Maryo ta yi a hankali tana ƙasa-ƙasa da murya ta ce, "Maza rakashi ko bakin ƙofa ne." Maryo ta yi gaba taba tura baki gaba ba don ta so hakan ba. Suna zuwa bakin ƙofa a gurguwa ta yi masa sallama ta dawo wurin Inna Habi. Waiwaye... Rayzuta ta taso cikin kulawa da soyayyar iyaye gaba da baya, tun bayan haihuwarta da wata uku Mahaifiyarta ta fara ciwo sama-sama. Tun ana ganin abin da wasa har lamarin ya fara ba su tsoro, saboda yanzu riƙon Rayzuta ya dawo hannun Farratu da zama, ba ƙaramin tausayin yarinyar take ji ba musamman ga ƙarancin watanninta ace Mahaifiyarta babu lafiya. Haka daga wurin Mahaifinta hankalinsa ba ƙaramin ta shi ya yi ba. Lokaci ɗaya labarin rashin lafiyar Wurshil Ba'is ya karaɗe cikin wannan Daula ta masarauta me ɗauke da ɗubin Aljanun a ciki. Ba a ɗauki lokaci ba aka fantsama neman magani cikin da wajen wannan nahiya. Koyaushe a cikin haɗa mata magani ake amma kullin ciwonta kamar ƙara gaba yake yi. Sarki Kisumul Birmi tun yana sa ran warkewarta har ya fara sare wa sakamakon yadda jikin nata yake ƙara rikicewa. Farratu ita take jinyar Wurshil Ba'is domin ta ce babu wanda za ta lamuncewa ya yi jinyarta, saboda jikinta yana bata akwai lauje cikin naɗi dangane da ciwon kishiyar tata. Wannan haɗin kai na Matan Sarki Kismul Birmi ba ƙaramin daɗi yake yi masa ba, a ɓangare ɗaya yana ƙara jin ƙaunar Uwar gidansa na ƙara mamaye zuciyarsa, yana jinjina karamci da kyawun hali irin nata. Burdamu Ita ce Mahaifiyar Furzaan, amintakar mazajensu ya sa ta su ta zo ɗaya da Farratu suka ɗinke saboda kusan halinsu ɗaya, wannan ta sa zumuncin su ya ci gaba da tafiya gwanin birgewa. Furzaan da Zulik tun suna yara suka taso da abotarsu sai dai bambamcin ɗabi'u da halaye da suke da shi tun suna ƙanana. Furzaan Yarone me nutsuwa ladabi da biyayya Uwa Uba girmama na gaba da shi, yana da saurin fahimtar abu. Yana da barkwanci sosai ta jin tausayin Mahaifiyarsa da ma sauran duk wani me buƙatar taimako. Saɓanin Zulik da ya ta so da haɗama, handama da babakere. Tun be yi wayon ba yake da hangen abin da wani yake da shi, sai dai da ya ɗora ido akanka muddin ya ga ka zarta shi da wani matsayi zai kawo hassada, ƙyashi da baƙin ciki ya ɗora akanka. Duk waɗannan ɗabi'u na Zulik Furzaan ya fahimce su saboda yana da saurin karantar yanayin da ƴan uwansa Jinsin Aljanu suke ciki. Don haka tun suna ƙanana kowa ya san halin kowa a cikinsu, saboda haka Furzaan yake cin maganin zama da Zulik don a zauna lafiya. Lokacin da Rayzuta ta kai shekara biyar a duniya lokacin ne ciwon Mahaifiyarta ya warke wato a ranar ne ta koma ga mahalicci, Farratu ta yi kuka ranar kamar ranta zai fita. Sarki Kismul Birmi sai shi ya dinga lallashinta yana bata haƙuri. Shiru ta yi ta faɗa duniyar tunanin irin wasiyar da Wurshil Ba'is ta bar mata a lokacin da take gabda da mutuwarta. (Bari mu taɓo yarensu🤪) "Jaskinbat minfartif basu kutminba Farratu banakul ginsatu lalbisfahu warga su minzanu kalmunsiban hurumi Rayzuta minzat falsibuhu zadigul basfu walkin." (Haƙiƙa ke ta daban ce Farratu ban taɓa jin kishiya me karamci kamar ki ba ko a tarihi, Allah ya yi ni ba me yawancin kwana bace don haka ga amanar Rayzuta nan ki riƙe kamar ƴarki ta cikinki.) Kuka ne ya kwacewa Farratu tana jin maganganun Wurshil Ba'is har cikin zuciyarta, share hawayenta ta yi ta ce, "Ki daina faɗin haka cuta ba mutuwa ba sai kwana ya ƙare." Murmushi Wurshil Ba'is ta yi ta ce, "Wannan karon ciwon haɗe yake da ƙarar kwana. Dama Kakana ya taɓa gaya mini tun ina budurwa cewa ƙaddarata za ta kawo ni Masarautar Jinnul Sahara, ya sanar da ni komai amma ba zan iya sanar da ku ba saboda gudun tayar da tarzoma, amma abu ɗaya zan sanar miki da shi akan Rayzuta ba don tana matsayim ƴata ba, ina baki shawara ne dangen da goben Ƴar Rayzuta. Don Allah idan yadda kina ɗauke ni har zuciyarki haka nake kada ki Aurawa ɗaya daga cikin zuri'ar Bulbutu, idan kuka yi wannan kuskuren na tabbata ƙasƙantattun Bayin cikin masarautar nan sai sun fi ku ƴanci a cikin Masarautar nan." Farratu ta kalli Wurshil Ba'is da mamaki ta ce, "Me zai haɗa zuri'ar Sarki Kisumul Birmi da zuri'ar Bawa Bulbutu, karki manta Rayzuta jinin sarauta ce su kuwa dangin Bayi ne." Murmushin yake Wurshil Ba'is ta yi ta ce, "A kwana a tashi ko bayan babu raina za ki tuna da wannan maganar. Ki sanarwa da Sarki wannan huɗubar tawa na tabbata ba zai watsa miki ƙasa a ido ba. Idan kika cire wannan zuri'ar na yarje duk wanda Rayzuta ta nuna tana so matsawar ba shi da wani aibu ku aura mata shi. Amma ina fargabar abin da Kakana Bundur ya sanar da ni dangane rubtacciyar ƙaddararta, wataƙila yin hakan ya dakatar da tasirin ƙaddararta sai dai..." Bata ƙarasa maganar ba numfashinta ya ɗauke nan take rai ya yi halinsa. Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya Rayzuta na hannun Farratu tana bata kulawa tamkar ita ta haifeta har Rayzuta ta fara zama budurwa, a wannan lokacin duk wasu al'amuran da ya shafi harkar Mulki Mahaifinta yana koya mata. Rayzuta nutsatssiyar yarinya ce sai dai ta taso da farin jinin duk kuwa da yadda Mahaifinta ya yi farin jini lokacin da yana matashi ta dame shi ta wannan fannin. Wata irin shaƙuwace ta shiga tsakaninta da Furzaan, a fannin iyayensu hakan ba ƙaramin daɗi ya yi musu ba. Ga wanda ya fahimci wannan alaƙa tasu zai fahimci shaƙuwar ta su ta rikiɗe zuwa soyayya. Zulik tun da Allah ya sa ya zama saurayi ya ji duk duniya babu yarinyar da yake ƙauna sama da ita. Babban burinsa ya ga an aura masa ita ya mori gangar jikinta, saboda Allah ya yi mata kyakkyawar sura cikin jinsinsu na Aljanu. Ganin hankalinta ya fi karkata ga Furzaan ya sa ya fara neman cusa soyayyarsa ƙarfi da yaji a zuciyar Rayzuta, wanda a lokacin har saɓani suka fara samu tsakaninsa da ita, don har sawa take Dogarawan ƙofa su dakatar da shi. Watarana yana zaune Mahaifinsa ya same shi a ɗaki ya ƙarewa Zulik kallo duk ya rame ya fara lalacewa, dama kuma ya daɗe da fahimtar halin da Ɗan nasa yake ciki kuma hakan ba ƙaramin daɗi ya yi masa ba. Zama ya yi a kusa da shi ya ambaci sunansa cikin wata irin murya da take tabbatar masa Mahaifin nasa yana son yin magana me muhimmanci da shi. "Zulik na fahimci ka faɗa tarkon soyayyar Rayzuta ƴar Sarki Kisumul Barmi, amma ka sani soyayya da ita kamar dawo da wanda ya mutu ne. Na san za ka yi mamakin jin haka daga gare ni kuma wannan ba abin mamakii bane idan ka duba matsayinka da nata." Bulbutu ya dakata da maganar yana kallon yanayin da Zulik ya shiga, cikin rashin ladabi Zulik yace, "Wacece Mahaifiyata? Ka fara sanar da ni wannan in yaso duk wani bayani sai ya biyo baya." Murmushi Bulbutu ya yi yace, "Mahaifiyarka ta rasu tun bayan da ta haife ka, Mahaifiyarka ita ce Mahaifiyata. Na hallaka mijinta wato Mahaifina sannan na haike mata a wannan tarraya ta mu da ita ta samu cikinka. Ka san dalilina na yin haka?" Zulik ya dube shi da kallon tsana ya girgiza masa kai sannan Bulbutu ya ci gaba da cewa, "Laƙani aka bani na yi amfani da shi domin kasancewata Sarkin gobe a wannan masarautar. Boka na ya sanar da ni cewar matsawar na yi tarayya da Mahaifiyata za ta haifi wanda zai auri ƴar Sarki Kisumul Birmi, amma indai ban yi tarayya da ita ba har abada ni da Saruta. Bincikensa ya nuna idan muka bi da dabaru tabbas za ka aureta kuma kana aurenta Mahaifinta zai baka Sarautar ka ga sai yadda muka yi da su. Sai dai ya sanar da ni wannan yaro Ɗan wurin Waziri zai kawo maka cikas, don haka ba da gaggawa za mu bi lamarin ba. Ka yi ƙoƙari ka daina nuna jin zafinka akan Furzaan za ka ga ta fara sauraronka, kuma a yadda na lura yarinyar tana da sha'awar harbe-harbe. Don haka zan turaka horon harbi na kwari da baka in ya so idan ka dawo sai mu yaudari Sarki akan za ka dinga koya mata Harbi, a wannan lokacin za ka cusa mata soyayyarka. Kaga kana aurenta ka zama Sarki me mulkar wannan Nahiyar ta Daulatul Jinnul Sahara." Duk yadda Zulik ya kai ga jin haushin Mahaifinsa sai ya ji zuciyarsa fes baƙin cikin da ke ciki ya yaye. Kallon Mahaifin nasa ya yi yace, "A farkon labarin ji nake zuciyata na tafasa kamar na datse numfashinka, amma daga ƙarshen labarin na hango nasara da cimma buri a ciki." Daɗi Bulbutu ya ji a ranar ya shiryawa Zulik tafiya ba tare da kowa ya sani ba, ya aikata cen Nahiyar Baƙaƙe Aljanin ƙarƙashin ƙasa. (JINNUL TARABIY) Domin amsar horon Harbi yadda ya kamata. Duk yadda Maryo ta so a raka gidan Abu Inna Habi ta ƙi yadda, a gefe ɗaya kuma tana fargabar rikicin da ka je ya zo. Suna zaune su biyu a ɗaki Inna Habi ta dubi Maryo tana cewa, "Maryo babu abin da za mu ce da Allah sai godiya. Cikin ikon Allah kina gani lokaci ɗaya idanunki da kunnuwanki sun buɗe, an ya lamarin nan babu sihiri a ciki kuwa. Ni fa ina ji a jikina tabbas akwai wani ɓoyayyen al'amari a ƙasa, amma meye haɗinki da Ɗan wurin Fulani Maryama? Sannan kuma me ya sa kika sakewa Namiji har yake iya rungumarki ke ba matarsa ba? Maryo na yi mamakin ganin haka saboda sam ban yi muku tarbiyyar son zuciya ba. Me kike tunani ga duk namiji da ya samu damar taɓa wani sashe na jikinki? Kina tsammanin zai aure ki ne?" Maryo jikinta ne ya yi sanyi ta kalli Inna Habi tana ƙarajin ƙaunar tsohuwar a zuciyarta tana faɗin, "Inna wallahi babu wani abu da yake tsakanina da Ɗanta, shi kuma Saif ba tun yanzu ba na gaya miki saurayina ne. Amma wallahi Inna ina ji a jikina shi ɗin kamar wani tsagina daga ɓangaren jikina, jikina na rayawa mini wasu al'amura musu muhimmanci dangane da rayuwata. Ciwon nan kuma yana daga Ubangiji Inna kar mu saka zargin kowa a zuciyarmu don kar a zoɓe ladan kankarar zununbin dana samu. Game da rungume ni da Saif ya yi na yi kuskure Inna amma duk hukuncin da ya dace za ki iya aiwatarwa a gare ni, na yi miki alƙwari In sha Allah hakan ba za ta sake faruwa a tsakaninmu ba. Amma wallahi ki yadda da ni Inna babu wani abu da ya taɓa haɗa ni da shi wannan ma kuskure ne." Maryo akwai iya falsafar zancen da sauke magana a inda ta dace, idan tana tsara maka magana za ka rantse da Allah wata babbar macece take yi maka magana. Inna Habi ce take mamakin yadda lokaci ɗaya kunyar Maryo ta yaye akan wannan Ɗan Sarki Saif, jiki a sanyaye ta dubi Maryo ta ce, "To ya kamata a kiyaye gaba saboda hakan baya daga tafarkin tsarin addinin musulunci." Maryo ta amsa mata cikin girmamawa, Inna Habi da har za ta tambayi Maryo game da cikin da take iƙirarin na Saif ne sai dai kuma ta fasa. Sannu a hankali tun Bayin sashen Fulani Maryama ba su san da warkewar Maryo ba, har suka hankalta. Wasu daga cikinsu sun ta ya ta murna ya yinda wasu kuma suke tsoron magana kasancewar sun fahimci Fulani Maryama ta kafa musu ƙahon zuƙa, ko gani ta yi kanfiye mu'amala da Inna Habi sai ta kira ka ta yanka maka kashedi. Lokacin da Fulani Maryama ta samu labarin faruwar wannan lamarin ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba, duk yadda ta so ganin Jakadiya a ranar abin ya faskara don Jakadiya na kwance maruru ya fito mata a hammata, tana kwance tana fama da hannu a sama don ko sauke shi ƙasa bata iya yi, saboda azabar da yake yi mata. Lokacin da Saif ya koma gida Abu na zaune a kan gado ta jingina da fuskar gado da alama baccin ɗaukarta ya yi ba tare da ta sani ba, Saif na shiga ya hangi Baiwa Sahura tana surfe. Ƙare mata kallo ya yi har sai da ta tsargu take ganin kamar ya lura da ta zuba wani abu a ƙofar ɗakin matarsa. Amma sai ta hau muzurai tana faɗin, "Barka da shigowa Ranka shi daɗe." A taƙaice yace, "Barka!" Har ya wuce gaba ya juyo ya sake kallonta yana bin hannuwanta da kallo, wannan karon tsoronta ya bayyana a fili sai ya wuce cikin gida. Tun daga bakin ƙofar ɗakin ya fara bin hallitun da yake gani a fili, kansa ne ya sara masa lokaci ɗaya idanunsa suka rune jawur ya kalle su fuska babu wallahi yana faɗin, "Maza ku koma wurin da aka turo ku muddin kuka saɓa mini wallahi babu wanda zai tsira daga gare ni. Saƙo na baku duk wanda ya ƙara gigin taɓa mini gudan jinina tabbas uwarsa sai dai ta haifi wani." Tun be rufe baki ba ɗaya bayan ɗaya suka fata ɓacewa, Baiwa Sahura da take gefe tana kallonsa yana ta surutai cikin zuciyarta take ayyana ko dai wani zancen zucin yake yi har ya fara fitowa fili. Fuska a tamke ya juyo gare ta jikinta har tsuma yake amma ga mamakinta sa ta ga ya nuna ta da Ɗan yatsa ya bushe da dariya, sai da ya yi me isarsa sannan yace, "Wannan ya zama na farko kuma na ƙarshe da za a baki mugun abu domin salwantar da abin da yake cikin Matata, idan ba haka ba wallahi zan baki mamaki. Kuma karna ƙara ganin ƙafarki a sashen nan." Baiwa Sahura ban da gyaɗa kai babu abin da take yi jikinta har rawa yake ta ci gaba da abin da take yi, Saif ya faɗa ɗaki ya kwanta a kan gado ya tsunduma kogin tunanin rayuwar abin da yake faruwa da shi. Sai a wannan lokacin ya tuna cewar Maryo ƴar Uwar Abu ce ji ya yi kansa ya yi wani iri. Ɗagowa ya yi ya ga yadda take bacci a wahalce, ta shi ya yi ya ƙarasa yana gyara mata kwanciya cikin tausayawa domin kwana biui kawai duk ta zabge ta rame. Bayan kwana biyu da warkewar Maryo ta gama tabbatarwa kanta dai suna zaune ne a sashen Fulani Maryama, ko kaɗan ba ta so hakan ba saboda gabaɗaya ta tsani matar don tun da take bata taɓa jin wani mutum da ta tsane shi farat ɗaya ba kamar Fulani maryama. Kamar kullin yauma ta saka Inna Habi da magiyar zuwa gidan Abu amma sai hanya-hanya Inna Habi take yi mata, babu yadda ta iya haka ta haƙura. Misalin sha biyun rana Inna Habi ta kwanta tana jan carbi har bacci ya yi awon gaba da ita. Hamdala Maryo ta yi don haka ta ja ɗauko mayafinta a hankali ta fito harabar gidan. Baiwa Sahura ta ga ni da sauri ta ƙarasa wurinta tana ƙasa-ƙasa da murya ta ce, "Sahura don Allah ina ne gidan Yayata Abu ki raka ni?" Sahura ta gwalo ido waje saboda kashedin da Saif ya yi mata, ganin haka ya sa Maryo ta ce, "Lafiya Sahura?" Sahura ta wanyance da cewa, "Fulani Maryama ce ta sani aiki sai dai in nuna miki gidan ba zan shiga ciki ba kar na daɗe na yi laifi a wurinta." Hannu bibbiyu Maryo ta sa ta riƙo hannun Sahura ta ce, "Na gode Sahura Mu je." Sahura tana gaba Maryo na biye da ita har suka ƙarasa ƙofar gidan su Abu, daga bakin ƙofa ta tsaya Maryo ta shiga tana rafka sallama. Tana shiga tsakar gidan haka kawai ta ji gabanta na faɗuwa amma sai ta yi tsammanin ko dan ta kwana biyu ba ta yi tozali da ƴar uwar tata bane. Bayin Abu ne suka amsa mata nan take tambayarsu Abu suka nuna mata ɗaki kasancewar duk sun san Maryo ƴar uwar Abu ce ya sa basu tsaya yi mata iso ba. Maryo sai da ta yi sallama a bakin ƙofa sannan ta ji Abu ta amsa mata sama-sama, ɗaga labulen ta yi ta shiga a zaune ta hangi Abu akan filo da turtsetsen cikinta. Jin yadda Abu ta amsa mata ya sa Maryo ta ɗauka ko don bata gane ta ba, amma lokacin da ta shiga da murnar ta ƙarasa gaban ƴar uwarta tana faɗin, "Abu kece haka yeeehh na kusa Ɗaukan Ɗana na kaina." Maryo har da ɗan tsallenta kamar wata ƙaramar yarinya, Abu dukda tana jin haushin Maryo a ƙasan zuciyarta ba ƙaramin daɗin ganin Maryo ta ji ba, sai dai kishin mijinta da take ji akan Maryo ya hanata amsarta hannu bibbiyu. Ɗauke kai gefe ta yi ta ce, "Maryo ke ce?" Maryo zama ta yi a sanyaye tana mamakin sauyin halin ƴar Uwarta don ta yi tunanin za ta yi farinciki da ganinta, basarwa Maryo ta yi ta ce, "Abu ya jikin ya Yayan namu?" Ras gaban Abu ya buga wani haushi ya sake turniƙe ta, sai da ta furzar da iska me zafi ta ce, "Duk muna lafiya." Maryo ta jinjina kai da yanayin mamaki ta ce, "Abu hala cikin nan yana takura miki ko bakya jin daɗi ne?" Abu ta watsawa Maryo wani Kallo tana shafa cikin jikinta ta ce, "Cikin da Masoyina ya yi mini har zan ce yana takura mini, sai kace wacce aka yi wa dole." Wannan karon mamakin Maryo be ɓoyi ba a hankali ta miƙe jiki ba ƙwari ta ce, "Abu ni bari na wuce gida Inna ba ta san na fito ba." Abu tana daga zaune ta ce, "Ki gaishe su." Maryo ta amsa tana ɗaga labulen za ta fita suka kusa gware da Saif hannunsa ɗauke da ledar kwakwar manjar da Abu ta ce masa tana buƙata, be lura da ita ba saboda da sauri Maryo ta yi baya tana faɗin, "Subhanallah ashe da mutum a hanya." Muryarta ce ta karaɗe dodon kunnensa da sauri ya saki ledar hannunsa bakinsa na rawa yace, "Ke... ke ce?" Mamakinta ƙarara ya bayyana ta ce, "Me ka zo yi gidan Abu." Abu da ke cen gefe ta yunƙura da ƙyar ta miƙe tsaye ta ce, "Kamar ya me ya zo yi mutum da gidansa, Maryo ko baki san Wannan ne Mijina ba." A hargitse Saif ya buga mata tsawa yana faɗin, "Lafiyarki Abu?" Kafin Abu ta yi wani yunƙuri Maryo da take jin jiri-jiri na nema ɗibanta ta ce, "Wai abin da ta faɗa haka ne kaine Mijinta?" Saif ya sunkuyar da kai ƙasa Abu da gayya ta ce, "Maryo na taɓa yi miki irim wannan wasan ne, idan ba ni ce matarsa ba kin san dai babu yadda za a yi Namiji kamarsa ya shigo mini ɗaki." A hankali Maryo ta fara jan kafarta ba tare ta lura da inda take jefa ta ba ta fita, da sauri Saif ya sha gabanta yana faɗin, "Don Allah ki tsaya ki ji yadda lamarin ya kasance wallahi..." Hannu ta ɗaga masa tana dubansa da rinannun idanunta ta sai kuma ta saki murmushin yaƙe da ya fi kuka ciwo ta ce, "Ba sai ka ce mini komai ba, don Allah ka bani hanya na wuce saboda ina yi maka kallon Yayana ba zan iya yi maka ranshin kunya ba kamar yadda bana taɓa yi wa Adda Abu." Tana kaiwa nan ta fice daga ɗakin tana tafe wani abu na dunƙule a zuciyarta hatta ƙafarta bata san inda take jefa ta ba. Yau na san Abu ta shiga uku🥺🥺 _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [07/01, 19:39] Ameera Adam🌚: 58... Lokacin da ta koma Inna Habi bacci take hankali kwance bata tashi ba, Maryo na shiga ta zube a ƙasa tana sakin kuka me tsuma zuciya. Sama-sama Inna Habi ta fara jiyo kukan Maryo a firgice ta tashi tana tambayarta abin da yake faruwa, Maryo ban da kuka babu abin da take yi hatta magana ta kasa iya furtawa. Inna Habi jikinta na rawa ta miƙe ta fita daga ɗakin tana dube-dube sai dai tsakar gidan shiru ma yake babu Bayin da ta bari suna aiki kafin ta kwanta bacci. Komawa ta yi ta zauna ta zubawa Maryo idanu don bata san me za ta yi ba, tun da ta yi mata tambayar duniya amma amsa ɗaya ce kukan da take rusawa. Sai da ta ci kuka ta gode Allah fuskarta jawur sannan Inna Habi ta sake tambayarta tana ƙasa da murya kamar me raɗa, "Maryo me aka yi miki? Ko yaron nan Ɗan wurin Maryama ne ya yi miki wani abu?" Maryo girgiza mata kai ta yi ta ce, "A'a ba shi bane." Kanta ne ya ci gaba da sara mata saboda tsananin ciwon kai ko idanunta bata iya ɗagawa, a hankali jini ya fara ɗiga daga hancinta tana shirin gogewa Inna Habi ta ruƙota cikin tashin hankali tana faɗin, "Me aka yi miki Maryo haka da har yake neman tayar miki da ciwonki?" Sai a lokacin Maryo ta iya faɗawa jikin Inna Habi ta fashe da wani irin kuka me tsuma zuciya. Inna Habi jin kukan Maryo take har cikin ranta tana ayyana wannan karan ta kai maƙurar tiƙiwa, ba Salman ba ko Fulani Maryama ce ba za ta iya ci gaba da ɗauka ba. Bayan fitar Maryo a hassale Saif ya ƙarasa wurin Abu ya fisgota da iya ƙarfinsa, gani ya yi ta kafe shi da idanu sai kuma ta bushe da wata irin dariya. Sunkuyar da kai ƙasa ya yi saboda baƙin ciki ya rasa wanne irin hukunci zai yi mata. Be ƙarasa tunanin da yake yi ba ya riski muryar da bata zame masa baƙuwa ba a cikin dodon kunnensa ana faɗin, "Wannan shi ne karonmu na farko da kai a taƙaice za mu iya kiran wannan da wasa farin girki." Yana gama maganar Abu ta sulale ta faɗi ta rubda ciki. A zabure Saif ya yi kanta yana kiransa sunanta, daga saman kansa ya sake jin bushewa da dariya yana ana faɗin, "Wannan karon za ka tashi biyu babu." Be saurara masa ba ya fara jijjiga Abu da lokacin tuni jini ya fara zuba daga jikinta. Ganin wannan ba zai kai shi ba ya sa shi fita da sauri gudu-gudu, kai tsaye ya wuce sashen Mahaifiyarsa. Da gudu ya faɗa ɗakinsa yana ƙwala mata kira, kai da ka ji irin kiran da yake yi mata za ka tabbatar ba na lafiya bane, kamar yadda sauran Bayi suka riski shigowarsa cikin tashin hankali." Hankali tashe Fulani Zaliha ta tare shi tana tambayarsa, ban da haki babu abin da yake saukewa yana faɗin, "Abu ce ta faɗi har ta fara zubar da jini." Ba ƙaramin tashin hankali Fulani Zaliha ta shiga ba da sauri ta aika aka kira mata Uwar Bayi da Uwar tuwo. Lokacin da suka ƙarasa gidan Abu ta fara fita daga hayyacinta, Saif sai kaiwa da kawowa yake yi yana nazarin irin hukuncin da ya dace ya ɗauka akan Salman. Kafin wani lokacin tuni unguwar zoman da aka kira ta ƙarasa ta fara duba Abu sannan ta jiƙa magani da turare aka bata na sha da shafawa sannan ka turara turare. Jikinsa ne ya bashi akwai abin da yake faruwa a ɗaki wurin da Abu take kwance yana shiga akin Uwar Bayi ta miƙe zumbur tana faɗin, "Ranka shi daɗe wannan ciwon mata ne ka fita duk abin da ya dace za mu yi..." Tun bata rufe baki ba ya ɗaga hannu ya maka mata a fuska Unguwar zoma na ganin haka jikinta ya fara karkarwa tun bata gama haɗa kayan magungunanta ta ɗauki jakarta ta fice daga ɗakin. Shaƙar wuyanta Saif ya yi da ƙarfin tsiya yana huci kamanninsa sun fara canja launi idanunsa sun fito sun yi jawur gashin jikinsa ya miƙe yana huci yace, "Ka kasar mini matata ko na illata ka, wallahi daga ita har abin cikinta idan ya samu matsala sai na kassara rayuwarka." Salman dake ɗauke da siffar Uwar bayi ya bushe da wata mahaukaciyar dariya yace, "Na yi tsammanin kanka baya ja ashe yana ɗaukan al'amura. Na gaya maka wallahi ba za ka iya ja da ni ba, sai na kashe ka da ranka kana kallo. A tashin farko ka ga na rabaka da Masoyiyarka na tabbata babu yadda za a yi ta ci gaba da ƙaunarka bayan tana muku kallon maciya amana kai da matarka. Sannan ka kwantar da hankalinka ba zan halaka matarka ba domin idan na halaka ta zan baku damar da za ku iya ɗinkewa har maganar aure ta shiga tsakani. Sai kuma abin cikinta bana tsammanin za ku same shi a yadda kuke da buƙata. Zan iya baka zaɓi idan ita ka zaɓa ko Mahaifiyarka, Mahaifinka, Matarka da abin da yake cikinta fansarta ne duk zan hallaka ku ɗaya bayan ɗaya. Idan kuma ka bar mini da ita za ka ci gaba da rayuwa da waɗannan mutanen dana lissafa maka. Dabara ta ragewa me shiga rijiya." Saif na jin haka sai kawai ya bushe da wata irin dariya yace, "Ai ban san irin wannan wasan kake so mu yi ba, amma tun da ka bani dama zan baka mamaki. Indan haka ne kaje nina san ta wurin da zan ɓullo maka. Amma ka rubuta ka ajiye na rantse da girman Allah duk abin da ya shafi waɗannan mutanen zan baka mamaki." Yana gama faɗa ya fyaɗa Saif da ke cikin siffar Uwar bayi da ƙasa ya sa ƙafa ya murje wuyansa har sai da ya buga wata uwar ƙara da ƙarfi sannan ya tashi da gudu ya fice daga ɗakin. A sace Bulbutu ya kai Zulik horon harbi ba tare da kowa ya sani ba, sai dai duk wanda ya tambaye shi yace ya kai shi dangin Mahaifiyarsa ziyara, sakamakon lokacin da cikin cikin Mahaifiyarsa ya fara bayyana ya sace ta kaita tsohon kogon Mirzu ya ɓoye ta a cen har ta haihu. Baƙin cikin ganin Ɗanta kuma Jikanta ya sa ta kwashe musu albarka daga Zulik har Bulbutu a take a wurin ta haɗiyi zuciya ta mutu. Lokacin da ya shiga masarautar da Zuliki yana jariri kowa bin sa ya dinga yi da kallo, kowa na san sanin wane yarona a hannunsa amma suna gundun irin fassarar da za a yi mishi. Ganin suna bin sa da kallon tuhuma ya sa ya ɗauki Zulik ya wuce Fadar Kamusul Birmi, yana zuwa ya zube ya yi gaisuwa sannan ya fashe da kuka. Babu wanda ya tanka masa sai da ya sha kuka me isar sa sannan Sarki ya dube da kulawa saboda a iya saninsa Bulbutu gawurtaccen sadaukin namiji ne, kamar ya san me yake zuciyar Sarki sai ya ɗago Zulik ya nuna masa ya sake fashewa da kuka. Fadawa tsawa suka buga masa sakamakon a gaban Sarki Kasumul Birmi ba kowanne sakarci ake iya yi ba. Hannu Sarki ya ɗaga musu jiki a sanyeye kamar kazar da aka jefa da kishiri yace, "Ku ƙyale shi! Ku amso mini yaron ku kawo shi." Tun be rufe baki ba suka cika umarninsa, wannan karan ma sai da ya jima yana kuka sannan ya ɗago ya fara wassafo karya kamar ba shi ya sha kuka ba. "Sarki me cikakken iko me maɗaukakiyar izza da babu irinta duk faɗin nahiyar nan, me ɗauke da tausayin talakawansa. A wannan karan na yi kuskure me girma ban san ta wacce siga za ka hukunta ni ba." Jin wannan bayanin nasa ya sa suka tattara hankulansu wuri ɗaya suna sauraronsa, ya goge hawaye ya ci gaba da cewa, "Na yi aure tun shekaru biyar da suka gabata a cen Daular Bahi da ke ƙarƙashin Jinnul Nariy, yarinyar da na aura ashe bata da lafiya basu sanar da ni ba har aka yi auren. Lokacin da na yi niyyar tahowa da Matata sai ciwonta ya tashi, haka na barwa zuciyata lamarin kuma na bar Matata a cen suna jinyarta, sai dai lokaci-lokaci ina ziyartarta amma ko kaɗan bata san wanda yake kanta ba. Ana haka bayan shekara uku da aurenmu sai ta sami lafiya ta dawo cikin hankalinta. Amma fa a nan take iyayenta suka ƙi amincewa da na taho da ifa sai dai kawai muka ci gaba da mu'amalar aure. Katsam sai ta samu ciki a ranar da ta haihu a ranar ciwonta ya tashi, nan take ta faɗi ta mutu." Bulbutu na zuwa nan a zancensa ya rushe da kuka, Bafadawa ne suka fara bashi baki yana gyaɗa kai, nan take ran Sarki Kisumul Birmi ya ɓaci ya dubi Bulbutu da kausashiyar murya yace, "A wane yanki wannan nahiyar take na aika fadawa a ɗebo iyayenta domin hukunta su, ba su barka ka ji da mutuwar matarka ba za su baka yaro ƙarami ka taho da shi." Cikin Bulbutu ne ya kaɗa yana ganin saura ƙiris asirinsa ya tonu don haka ya sake marairaice murya yace, "Sarki me adalci ba haka lamarin yake ba, kasancewar Kakar yarinyar ta taɓa bani labari cewar ita ma ta samu wannan ciwon ne sakamakon tana jaririya, shi ya sa na tsorata na ce su ba ni shi na kaiwa me ɗakina za ta ba shi kulawa. Da farko sun so hanani sai daga baya na yi musu jan ido sannan suka amince, mun yi magana da su akan duk bayan wani lokaci zan dinga kai shi wurinsu ina dawo da shi." Ajiyar zuciya Sarki ya sauke sannan ya tausasheshi da kalamai masu daɗi, da farko Sarki ya so yace ya bar masa yaron a wurinsa amma gudun shiga haƙƙi ya sa ya miƙa masa Zulik yana tambayarsa, "Bulbutu ka yi masa suna ne?" Bulbutu ya ci alwashin saka masa sunan da Bokansa ya sanar da shi ya san idan yace be yi ba wataƙila Sarki ya raɗa masa, don haka yace, "Kafin Mahaifiyarsa ta rasu ta bar wasiyyar a raɗa masa suna Zulik." Sarki Kisumul Birmi ya ɗan yatsina fuska don sunan sam ba na masu kyawawan ɗabi'a bane, sunan wani Shuɗaɗɗen aljani ne da Kakanin kakaninsu suke basu labarin zalincinsa, amma gudun kar ya yi shisshiga kuma ya ji ance wasiyya ce shi ya sa ya sa masa albarka. Tun daga ranar riƙon Zulik ya koma wurin uwar gidansa, da farko ta so bijire masa amma sanin halin mijin nata ya sa babu yadda ta iya ta amshe shi ta riƙe ba don ta so ba, sai don gudun kar ya ɓatar da ita. Zulik ya shafe kwana da kwanaki sannan ya dawo, Mahaifinsa ba ƙaramin daɗin ganinsa ya yi ba. Idan Zulik ya riƙe kwari da baka ya yi harbi Tsintsuwa duk nisan ta sai kibiyar da huda jikinta ta faɗo, sannu a hankali Zulik ya fara gwada basirarsa a cikin Bayi. Kafin kace wani abu tuni zance ya yaɗu a ko ina a cikin masarautar. Furzaan ba ƙaramim daɗi ya ji ba kasancewar Babban amininsa ya ƙware a fannin da babu Aljani ɗaya daya iya. Ban da ajiyar zuciya babu abin da Maryo take yi, a zuciyarta take ayyana me za ta iya gayawa Inna Habi bayan ta san Abu Ƴarta ce halak malak. Shin za ta ce mata ta je gidan Abu ta ga Saif ne mijinta ko kume. Inna Habi gabaɗaya jikinta ya yi sanyi kamar kazar da aka jefa da gishiri, bata yi aune ba ta ji Maryo na faɗin, "Me ya sa za ki yi mini haka?" Da sauri Inna Habi ta ce, "Maryo wace ce gaya mini me ta yi miki." Kallon Inna Habi ta yi cikin tausayawa don bata taɓa tsammanin zancen zucinta ya fito fili ba, ta hau girgiza kai sannan ta ce, "Inna wani Mafarki na yi da wata mata." Da mamaki Inna Habi ta furta, "Mafarki kuma Maryo?" Maryo ta gyaɗa mata kai, Inna Habi ta yi mata kallon tsaf tana nazartarta yanayin da take ciki. Girgiza kai ta yi cikin wata irin dakakkiyar murya ta fara cewa, "Maryo ni ce Mahaifiyarku kina da wacce za ki gayawa damuwarki bayan ni, tun kuna ƙanana na san halin kowa Maryo yaushe kika fara ɓoye mini damuwarki?" Maryo hawaye ne ya ci gaba da ziraro mata ta ƙara kwanciya a jikin Inna Habi ta ce, "Inna don Allah ki yi haƙuri amma babu wani abu da yake damuna." Inna Habi ta gyaɗa kai tana faɗin, "Shi ke nan duk lokacin da kika so sanar da ni za ki yi mini bayani amma ki sani ba zan lamunci ganinki cikin damuwa ba." Maryo ta ce, "Shi ke nan Inna ba za ki sake gani ba Insha Allah." Inna Habi ta ce, "Ta shi kije ki wanke fuskarki bana son ganin wannan haɓon na zuba." Maryo ta tashi ta fice daga ɗakin cikin damuwa. "Ya kai wannan Boka me karamci yanzu babu wani taimako da za ka iya tallafa mini da shi akan wannan Hallitar, na zautu ta yadda bana iya kallon kowacce mace a matsayi kyakkyawar hallita. Tun muna samun matsala da Matata har ta haƙura ta zuba mini ido, ka yi wani abu akai idan kuwa ka ce ba zan iya mallakarta ba na yi rantsuwa da girman Allah sai na kasheta sai dai kowa ya rasa. Na gwammaci na aiwatar da abin da ya faru a shekarun da suka shuɗe, domin muddin ban cika muradina ba, ba zan taɓa bari Saif ya mallake ta ba." Mutumin Tsoho ne tukuf me ɗauke da farin gashi a sassan jikinsa, kallo ɗaya za ka yi wa fuskarsa ka tabbatar da rashin tsoron Allah ya samu mutsuguni a kan fuskarsa. Kyakkyawan ne ajin farko ga duk wanda ya yi masa kallon kitse... dole zai ɗauka mutumin arziƙi ne. Murmushi ya yi yana kallon Salman da yake cikin damuwa yace, "Na gaya maka muddin tana cikin hankalinta babu yadda za a yi ta amincewa aurenka. Kiyayyarka daga jinin jikinta take ba za ka taɓa samun gurbi a zuciyarta ba, sai dai akwai mafita!" Da sauri Salman yace, "Gaya mini wacce iri ce duk girma da hatsarinta zan bi domin ganin na mallake ta. Na yi rantsuwa da girman Allah ba don bani da ikon sace ta da ƙarfin tsiya ba da babu yadda za a yi na zuba mata ido ina wahalar da kai." Murtuke fuska tsohon ya yi yace, "Karka ƙara ambatar sunan Allah a wurin nan domin nan wurin zaman ɓatattu ne, kamar yadda na baka wancen laƙanin ka binne masa haka wannan karon zan baka wani laƙanin amma wannan ya fi wancen hatsari. Amma zan ƙara tunasar da kai gabaɗaya ku ukun nan Filsifi ne, tasirin sihiri baya wanzuwa a jikinku har sai da haɗin kan ɗaya daga cikin jinsinku. Ina mu'amala da ɗaya daga cikin Bafaden Mahafin yarinyar nan don haka akwai wani taimako da zai yi mini wanda babu wani Bil'adam da zai iya aiwatar da shi." Salman ya kwantar da murya yana faɗin, "Tuba nake Bokan bokayen duniya, ina sauraron duk abin da kake faɗa kuma ko ta halin ƙaƙa zan aiwatar da abin da za ka umarceni." Wani tafasasshen jini ya ɗauko a cikin wata ƙwarya ya ɗaga sama sai da ya yi surutan tsafinsa sannan ya juya ya kalli Salman yace, "Me kake gani?" Salman ya zura kai yana kallon jinin nan take ya ji kansa ya sara har sai da ya sa hannu biyu ya dafe kansa sannan ya ɗago da kai idanunsa sun yi jawur yace, "Jini ne sai dai na kasa tantance ko na mene ne." Murmushi tsohon ya sake yi yana janye kwaryar ya mayar da ita gefe sai a lokacin kan Salman ya rage sara masa, Tsohon ya dube shi da kyau sannan ya ci gaba da cewa, "Ina taimaka maka ne kawai saboda akwai wani ɓoyayyen al'amari a tsakanimu, na san kai baka sani ba amma wataƙila nan gaba za ka fahimta. Wannan wani sirrinmu ne ni da mahaifiyarka da muka binne na tsahon shekaru, amma nan bada jimawa ba akwai lokacin da Ya za ta ɗakin Ƙanwa." Da mamaki Salman yace, "Mahaifiyata kuma? Kana nufin Mahaifiya ta san ka ko ta taɓa ziyartar ka?" Al'adar tsohon kenan koyaushe cikin murmushi yake sai dai baƙin halin da ke ƙunshe a zuciyarsa ya wuce abin a kwatanta. Murmushi ya kuma yi yace, "Mu ajiye wannan batun a gefe ka bari ka cimma burinka tukunna sai ka zo na yi maka cikakken bayani. Da farko dai laƙanin da zan haɗa maka magani da shi yana tare da kai wato da magani a gonar yaro..." Salman jikinsa har rawa yake ya miƙe tsaye yana faɗin, "Gaya mini ko mene ne na aiwatar maka da shi idan wanda zan ɗauko maka ne yanzu na kawo maka shi." Farin Tsohon ya saki dariya me sauti sannan yace, "Tabbas ko makaho ya shafa ka sai ya tabbatar da Barewa ba za ta yi gudu Ɗanta ya yi rarrafe ba, ko a ina jinin Maryama yake sai ya bayyanar alaƙarsu tabbas jini ba wasa ba na ƙara tabbatarwa da kai Jinin Maryama ne. Amma kuma duk gaggawar Ango ya bari a kai Amarya ɗaki, haka zalika duk gaggawar Unguwar zoma ta bari a haihu. Saurin me kake yi Salmanu." A hankali Salman ya koma ya zauna sannan tsohon ya ci gaba da cewa, "Matarka tana da Ɗauke da cikin Ƴa mace. Daidai lokacin da cikinta ya cika wata Bakwai nake son Jaririyar zan yi amfani da jininta, ita kuma uwar da jinin Biƙinta zan haɗa dole ita ma Maryo ka samo mini jinin jikinta kowanne iri ne. Idan ka kawo mini waɗannan zan haɗe su wuri ɗaya na zuba a cikin wancen ƙwaryar. Jinin ƙwaryar can da kake gani jininku ne na shuɗaɗɗun shekaru lokacin da aka yi ambaliyar Jini a daularku, shi ya sa kanka ya sara lokacin sa nuna maka, haɗakar Jananenku ne ku ukun. idan ka kawo mini zan haɗe su a cikin wannan shi ke nan burinka ya cika har abada Maryo ba za ta taɓa dawowa hayyacinta ba, amma da sharaɗi dole ka haɗo da jinin Saif daidai da ƙwayar zarra domin shi ɗin kamar inuwarta ne dole sai an haɗa jininsa idan ba haka ba ya dinga farmakarka kenan. Ni kuma a koyaushe na fi son ka kasance Me nasara." Farin ciki ƙarara ne ya bayyana a fuskar Salman lokaci ɗaya kuma damuwa ta sauka a fuskarta ya dubi Dattijon cikin damuwa yace, "Amma akwai ƴar damuwa!" Dattijon ya ɓata fuska kamar wanda aka isarwa da saƙon mutuwa yace, "Bana son ka dinga jin shakku a ranka domin abokin karawarka ya fi ka ƙwarin gwiwa, dukda ka fi shi kafar samun nasara be taɓa jin gazawa ko karaya a zuciyarsa ba." Salman ya sauke ajiyar zuciya yana faɗin, "Ba ina karaya bane sai dai duk ta sigar dana bijiro masa sai ya gane ni. Na bi ta siffar jikin Matarsa ya gano ni. Na yi siffar Unguwar zoma shima ban yi nasara ba. Idan zan ɗebi jinin jikinsu ta wacce sigar zan bi?" Tsohon ya ɗebi gasasshiyar wata hallita me ban tsoro ya watsa a baki yana tauna sannan ya fara magana, "Ka ci gaba da jarrabawa idan baka yi nasara yau ba za ka yi gobe. Sai dai ka ajiye a ranka shima ba zai taɓa zama haka ba. Karka manta cikin matarka watansa Shiga Ita kuwa Matarsa cikinta ya tafi wata tara. Ka yi ƙoƙarin ganin ka kula da Matarka ta yadda ba za a samu matsala da cikin jikinta ba, domin dole sai da jininka dana abin da za a haifa maka za mu yi aiki da shi. Bana buƙatar jin tambaya ko neman ƙarin bayani na gama magana ka ta shi ka wuce." Salman babu yadda ya iya haka ya miƙe a sanyaye kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki ya fice daga kogon dutsen. Bayan ficewar Salman daga ɗakin Abu kamar zautacce haka Saif ya ɗauki Abu da bata san abin da yake faruwa ba. Kamar matacciya haka kanta, ƙafafuwanta da hannuwansa suke raito, gudu-gudu sauri-sauri haka ya fice da ita daga ɗakin ya wuce sashen Mahaifiyarsa da ita hankali a tashe. Fulani Zaliha ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba ganin halin da Abu take ciki, har lokacin jinin jikinta be daina zuba ba. Hankali a tashe ta aika aka sanarwa da Takawa halin da Abu take ciki. Ba shiri ya bayar da Umarnin akai Abu Asubiti don ceto rayuwarta. Dole ƙanwar naƙi. Don dole aka sanarwa da Inna Habi halin da Abu take ciki, daga ita har Maryo tashin hankali ne ya bayyana ƙarara a fuskarsu, ba a ɗauki lokaci ba aka wuce da ita Asibiti rai a hannun Allah. Maryo da Inna Habi sai Uwar Bayi ne suka tafi asibitin sai sai wasu Dogarawa biyu da Sarki Aminullah ya umarce su da tafiya asibitin. "Maigida yau kuma ni kake yi wa barka da gida?" Murmushi ya yi yace, "To meye don na miki sannu da ɗinma da bana yi kuskure ne yanzu kuwa na gyara kuskure na." Ba ƙaramin daɗi Safiyya ta ji ba don a duniya tana son ta ga mijinta na bata kulawa musamman da Allah jarrabeta da mutuwar ƙaunar Salman, wani lokacin idan ya yi mata wulaƙanci har zama take ta ci kukanta ta godewa Allah, don haka take jin ta cikin farinciki da annushuwa. Salf da ke ɗauke da siffar Salman ya ƙurawa cikin jikinta ido lokaci ɗaya kuma sai ya ji tausayin Safiyya ya kama shi, don yadda ya ga tana ta murna da sannun da ya yi mata ya fahimci bata jin daɗin zama da Saif ko kaɗan. Tunanin irin halin da za ta shiga ya yake yi musamman da ya tuno da halin da Matarsa take ciki. Jikinsa ne ya yi sanyi ta dube shi tana cewa, "Maigida lafiya na ga kayi shiru." Murmushi ya saki yana cewa, "Mantuwa na yi a waje amma karki damu zan fita an jima." Safiyya ta saki murmushi tana faɗin, "Au ho ni kam na yi mamaki na ga tunanin ya yi yawa. Wai yau wani abu ne ya same ka na lura kana cikin farinciki." Ido ya sake zuba mata saboda ya san waye Saif zai iya azabtar da ita saboda soyayyar da yake wa Maryo, wannan karonma tausayi ta bashi don yana gabda shafar cikin jikinta amma jikinsa ne ya yi sanyi ya kasa aiwatar da abin da ya yi niyyar yi. Be kalleta ba ya juya ya fice yana cewa, "Ina zuwa." Yana fita ya koma siffarsa ta ainihi zama ya yi akan wani dakali ya haɗa kai da gwiwa cikin damuwa, domin ya san abu ɗaya zuwa biyu zai yi wa Salman ya wargaza masa farincikinsa. Na farko ya taɓa Mahaifiyarsa na biyu ya taɓa Matarsa, koda baya ƙaunarta yana yaƙinin zai so abin da yake cikinta. Don haka ya shiga domin shafar abin da ke cikinta amma tausayin Safiyya ya hanashi aiwatar da abin da ya yi niyya. Ba a ɗauki lokaci ba Likitoci suka shi ga bawa Abu agajin gaggawa, sun shafe lokaci akanta sannan suka samu nasara ceto rayuwarta. Ba ƙaramin galabaita ta yi ba fuskarta ta yi fayau ga wani haske bau da ta yi na zubar jinin da ta yi daga jikinta. Maryo ba ƙaramin kuka ta ci ba lokacin da ta yi tozali da halin da ƴar uwarta take ciki, Inna Habi ce ta dinga lallashin Maryo don tana tsoron kar ciwon Maryo ya ta shi su rafke mata gabaɗaya. Ba a barin kowa na shiga wurin Abu saboda Likitoci sun yi mata allurar bacci tana buƙatar hutu ita da abin da yake cikinta. Donma suna tsoron yi mata aiki a halin da take ciki da aiki za su yi mata su ciro abin da yake cikinta. Amma a hakanma idan ta samu lafiya za su yi mata aiki a cire yaron cikinta. Maryo na zaune a harabar Asibitin Inna Habi na tafi kama ruwa a banɗaki, Saif ne ya ƙarasa wurinta cikin shiga ta alfarma wacce da ka gani babu ko tantama za ka tabbatar da cewa jinin sarauta ne ne a cikinta. Takunsa kaɗai abin kallo ne me ɗauke da ɗaukan hankalin me jin da kallonsa. Yana ƙarasawa wurinta ƙamshinsa ya doki hancinta, gabanta ne ya yi mummunan faɗuwa, a hankali ta lumshe idanu wata irin ƙaunarsa na ƙara fisgarta. A hankali ta fara motsa bakinta tana faɗin, "Ya hayyu ya ƙayyimu!" Saboda ita kaɗai ce kalmar da za ta iya furtawa don samun sauƙin abin da take ji a cikin zuciyarta. Bakinsa ɗauke da sallama ya tsaya a wurinta yana ƙare mata kallo, lokaci ɗaya ya ga ta zabge ta faɗa. Ciki-ciki ta amsa masa tana ƙoƙarin barin wurin, sa sauri ya sha gabanta yana faɗin, "Ya me jiki!" Haka kawai ta ji haushin tambayar da ya yi mata amma babu yadda ta iya ta furta masa, "Da sauƙi!" Tana ƙoƙarin bi ta gefensa ya sake shan gabanta yana cewa, "Don Allah ki saurare ni Maryo. Wallahi ban auri Abu don wata manufa ba, ke nake so ke nake ƙauna bana jin akwai wata ƴa mace da za ta maye gurbinki. Ki yarda da ni aurena da Ƴar uwarki Ƙaddara ce ta tsananin rabo. Allah ne shaidata sam ban san yadda lamarin ya kasance ba, amma ko a yanzu a shirye nake na aure ki tun da ba ciki ɗaya kuka fito da ita ba..." Da sauri ta ɗaga masa hannu fuskarta a murtuke babu annuri a ƙasan zuciyarta wutar ƙaunarsa na ƙara ruruwa, idanunta ne ya ciko da ƙwallah ta dube shi ido cikin ido ta ce, "Saif!" Yadda ta ambaci sunansa kaɗai sai da ya razana ƴan hanjin cikinsa, kamar me ciwon haƙori haka ya amsa mata sannan ta ɗora da cewar, "Na rufe babin soyayyarka tun lokacin dana gano Ƴar uwata kake aure, ko kaɗan babu soyayyarka a zuciyata. Wallahi ko mazan duniya sun ƙare ba zan aure ka ba Saif." A haukace ya buga mata tsawa yana faɗin, "Kin san me kike faɗa kuwa?" Ita ma a ɗan tsawace ta ce, "Ka ɗauka hauka nake yi? Ina cikin hankalina Saif na gaya maka bana son ka bana ƙaunarka kuma wallahi ba zan aure ka ba. Muddin ka saki ƴar uwata ko ka wulaƙanta wallahi zan baka mamaki, amma na yi maka alƙawarin ba zan aure ka ba sai dai idan gawata za ka aura ba ni ba..." Bata rufe baki ba Saif ya ɗauke da mari yana faɗin, "Baki da hankali ne kin san me kike faɗa kuwa?" Kuka ne ya kwacewa Maryo ta tsugunna tana fashewa da wani irin kuka me tsuma zuciya, jikin Saif ne ya yi sanyi wata irin nadama ta kamashi, kwantar da murya ya yi ya tsugunna a wurinta yana miƙa mata farin hankicif ɗin hannunsa. Kallonsa ta yi zuciyarta na fisgarta akan ta amshi ƙyallen amma bata jin za ta iya karɓa saboda yadda zuciyarta take jin raɗaɗi akansa, kallonsa ta yi cikin kuka ta ce, "Me ya sa mafi yawancin lokuta Maza kun fiye san kanku ne, me ye laifina don na ce zan nemi zaɓin raina na aura. Me ya sa za ka hanani farincikina bayan kai ka auri zaɓin ranka, ko me za ka yi mini wallahi ba zan aure ka ba Saif. Babu yadda za a yi na auri mijin Ƴar uwar da nake jin ta har cikin jinin jikina, wane irin kallo mutane za su yi mini, ita kanta wane irin kallo za ta yi mini." Hannuwanta biyu ta haɗa alamu roƙo ta ci gaba da cewa, "Don Allah ka fita daga rayuwata, ka tsaya a matsayin Mijin Ƴar uwa zan ci gaba da baka girmanka na mijin Yayata amma muddin ka nemi wuce gona da iri za ka sha mamakina." 🥺 ANA WATA GA WATA😢 _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [08/01, 19:21] Ameera Adam🌚: 59... Idanu kawai ya zurawa Maryo yana jin kowacce kalma daga cikin bakinta na sauka a dodon kunnensa, duk kalma ɗaya ji yake tamkar ana buga masa guduma a tsakar ka. Samun kansa ya yi da kasa furta mata koda da kalma ɗaya ne domin zantukanta sun gama kashe gaɓɓan jikinsa ta yadda ƙafafuwansa ma Jansu yake ba tare da yana iya ɗaga su yadda ya kamata ba. Ikon Allah ne ya kai Saif gida yana shiga ɗaki ya faɗa kan gado kamar mace sai haka ya fashe da kuka me tsanani. Tun da yake a rayuwa waɗannan kalaman ne mafi muni da ya taɓa riska a rayuwarsa, tashi ya yi ya zauna ya zuba uban tagumi a fili a fara surutai kamar zautacce, "Me ya sa za ki guje ni a lokacin da nake da buƙatarki? Me ya sa ba za ki fahimci tasirin ƙaddara da faruwarta ba? Ke kaɗai nake so ke kaɗai nake ƙauna ba zan taɓa iya haɗa soyayyarki da wata ba. Don Allah ki ceci rayuwata kar ki bari magauta su yi mana dariya." Daga bakin ƙofa ya ji an ƙyaƙyace da dariya Salman ne ya ɗaga labulen ƙofar yana ci gaba da dariyar rainin hankali sannan yace, "Dariya kuma sai dai kar a kuma. Na gaya maka na raba ka da ita har abada ba za ta dawo gare ka ba, me zai hana ka nemi wasu ƴan matan ka aura kake wahalar da kanka a banza? Wannan shawara ce nake baka ka taimaki kanka ka sanawa kanka salama amma ina tunanin kafi kowa sanin irin kafiya da tsayawa akan magana ɗayanta." Saif murmushi ya saki yana tafa hannuwa sannan ya tsagaita ya kalli Salman da kallon ƙiyayya sannan yace, "Idan har baka manta da Kafiya da tsayawa akan magana ɗayanta ba, be kyauta ace ka amanta da tsantsar kiyayyar da take yi maka ba, kada ka manta kaine ka kashe mata mahaifi, ka kashe mace mafi muhimmanci a rayuwarta kana tunanin duk wanda aka yi wa wannan ɗanyan aikin akwi wata ƙauna ko soyayya da zai nunawa wanda ya aika masa haka?" Saif ya karka kai gefe yana murmushin ƙeta yace, "Tabbas na san ka fi kowa sanin wane ne ni, bana cin alwashi a banza don haka ka yi taka tsantsan." Yana gama faɗin haka ya fice daga gidan, bakin ciki ne ya turniƙe Salman ya shiga kaiwa da kawowa domin neman mafita. Kamar wanda aka ɗanawa wuta haka ya zabura ya fice, zuwa ya samu Bafade Sama'ila a gaggauce ya same shi ya bashi saƙo wurin Maryo don yadda yake jin jiri na ɗibansa zau iya faɗuwa kafin ya koma asibitin. "Sama'ila ka saurare da kyau bana san ka yi mini jinkiri a yanzu nake son kaje ka samu..." Ganin saƙon duk bata lokaci ne ya sa ya katse maganar da yake yi wa Bafade Sama'ila yana cewa, "Jeka kawai na fasa aiken." Kallonsa suka yi da tausayi lokacin da ya juya zai koma don duk wanda ya kalli Saif ya san yana cikin matsananciyar damuwa. A taunaninsu ciwon da Matarsa ne ya sa shi birkecewa sai dai abin ne ya haɗe masa goma da ashirin. Lokacin da Inna Habi ta dawo fuskar Maryo ta yi jawur duk wanda ya ganta sai ya gane taci kuka ta more. Inna Habi na ganinta ta ji babu daɗi zama ta yi a kusa da ita tana faɗin, "Dukda ba za ki gaya mini damuwar zuciyarki ba amma zai fi kyau a kodayaushe ki dinga ambaton Allah a zuciyarki, in sha Allah, Allah zai kawo miki mafita. Idan kuma ciwon ƴat uwarki ne Addu'a ita ce mafita ba kuka ba." Maryo gyaɗa kai ta yi tana goge hawayen idonta. Suna nan zaune guguwar iska ta fara kaɗawa sannu a hankali ta hango wani katon Jangwalagwada ya nufi ɗakin da Abu take kwance, jikinta har rawa yake da sauri ta tashi da gudu ta nufi ɗakin. Tana shiga ta ga ya tunkari wurin da Abu take kwance. Tsawa ta buga masa nan take ya tsaya tsam wuri ɗaya, A daidai lokacin ne Inna Habi ta ƙaraso wurin, Maryo ta so ta ce ya koma wurin da aka turo shi amma ta san muddin ta yi haka kwanciyar hankali ƙaura zai yi daga jikin Innar tasu. Ɗan kwalin kanta ta cire ta fara kaɗa shi tana faɗin, "Idan ka sake dawowa ni da kai ne." Kamar me jin abin da ake faɗa haka Ƙadangaren nan ya nufi har waje ya fice, da sauri Inna Habi ta matsa da mamaki tana faɗin, "Ikon Allah! Maryo me zai shigo da Ƙadangare ɗakin nan." Maryo ta yi yaƙe tana cewa, "Inna wataƙila guguwar nan ce ta gigita shi ya rasa wurin zuwa shi ya sa ya yo nan." Inna Habi zuciyarta ɗaya ta amince da abin da Maryo ta gaya mata bisa suɓutar baki Maryo ta ce, "Lallai kin ki magaryar tuƙewa a wannan karon zab nuna miki ba a taɓa mini ƴar uwa a kwana lafiya." Inna Habi da bata ji kalaman Maryo sosai ba ta ce, "Magana kike Maryo?" Maryo ta wayance da cewar, "A'a Inna muje kar Likitoci su shigo su same mu a ciki."nan take suka fice daga ɗakin. Suna gabda fitowa Uwar Bayi ta ƙaraso tana tambayarsu, "Na dawo daga bakin Asibiti aka ce mini kun shigo ko sun bari a shiga wurinta ne?" Inna Habi ce ta yi mata bayanin abin da ya kai su ɗakin sai ta yi jim kamar me nazari sannan ta ce, "Allah ya kyauta." Suna yin gaba Maryo ta waiga ta kalli bakin ƙofar nan take wasu Maguna guda biyu suka ratso daga jikin bango suka shiga ɗakin da Abu take kwance. Maryo sallama ta yi wa Inna Habi akan za ta je gida ta canja kaya, haka kawai Inna Habi ta ƙi aminta da abin da Maryo ta gaya mata, don ta san wace ce Maryo da maƙo babu yadda za ayi Abu na cikin wannan halin har ta iya komawa gida canja kaya, ta barwa zuciyarta akwai abin da Maryo za ta koma yi gida ba dai canza kaya ba. Amma bata tanka mata komai ba har ta isa ƙofar asibitin Idon Inna Habi na kanta har ta fice daga harabar asibtin. Maryo na gabda fita suka yi kaciɓus da Saif tsayawa ya yi a gabanta, za ta bi ta gefensa yace, "Ina za ki?" bata kalle shi ba ta furta, "Gida!" "Kin san akwia hatsari dangane da barinki asibitin nan." Saif ya faɗa yana zuba mata idanu. "Shi ya sa nake son zuwa na yi wa tufkar hanci." Maryo ta faɗa tana yin gaba. Juyawa ya yi yace, "Wannan me sauƙi ce zan ji da ita." Sai da ta waigo ta yi masa kallon tsaf sannan ta ce, "Alƙawari na ɗauka ba zan lamuncewa duk wanda yake ƙoƙarin cutar da ƴar wata kowaye." Saif ya saki murmushi da be yo niyya ba don maganarta ta ƙarshe kamar da biyu take faɗa masa wai, "Kowaye " Taku biyu ya yi zuwa gare ta yace, "Bana son ya cutar da ita ina tausayin halin da take ciki tun da bata ji bata gani ba, bana son haƙƙinta ya kamani." Maryo rasa wanne za ta yi farincikin Ƴar uwarta ta samu miji me kulawa da ita ko kuma kishin wanda take ƙauna yana faɗin kulawar da zai yake bawa wata. Dannewa kishinta ta yi don bata jin za ta nunawa Saif tana jin zafin ƴar uwarta, ta gyara tsayuwarta ta ce, "Ka yi aiki tuƙuri domin ganin ka kare martaba, haƙƙi, rai da lafiyar Matarka, ka zame mata mijinta da za ta yi alfahari da jarumtarsa. Ni na tsaya mata ne a matsayim ƴar uwarta Kaima ya kamata ka tsaya mata a matsayinka na mijinta." "Jarumta jinina ce juriya numfashina ce sadaukarwa rayuwata ce bana tunanin Ƴar uwarki za ta yi tsammanin ta yi zaɓen tumun dare. Ina son ki tsaya a gare ta saboda ke kaɗai na aminta da ke..." Tun be ƙarasa magana Maryo ta ɗaga masa hannu tana katse shi, "Kana nufin Mahaifiyarmu za ta cutar da ita?" Girgiza kai ya yi yace, "Ban taɓa kawo haka a kaina ba. Kin san waye shi yaci alwashin sai ya cutar da ita, kin san kuwa tun da ya furta Allah ne kaɗai ya san ta yadda zai ɓullowa lamarin." Maryo ta kalle shi a tsorace Saif ya gyaɗa mata kai, idanunta ne suka ciko da ƙwalla ta ce, "Na barta a hannun Allah na yi imani ba zai iya yi mata komai ba, zan je ga Maryama domin ta taɓo tsuliyar Dodo. Idan har ya yi kuskuren taɓa ta ko abin da yake cikinta na yi rantsuwa da girman Allah abin da ya faru na ambaliyar da aka yi a shekarun baya sai an maimaita ta." Tana gama faɗa ta yi gaba Saif ya wuce cikin asibitin zuciyarsa cike da tausayin halin da Abu take ciki. Salman da ke cikin siffar Likitan da ke kula da Abu yana ganin wucewarwa Maryo ya shiga ɗakin da Abu take kwance, Magunan da Maryo ta wakilta na ganinsa suka taso masa da gudu suka fara kai masa cizo da fiƙoƙinsu, nan take suka shiga artabu ganin za su ɓata masa lokaci ya shiga hura musu baƙar iska nan take suka ƙone ƙurmus. Tsaye ya yi a bakin gadon Abu da ke sauke numfashi sama-sama, duk wanda ya kalle ta zai tabbatar da baccin daɗi take yi ba, wata uwar dariya ya bushe da ita nan take ya rikiɗa zuwa suffar Maryo. Tashinta ya fara yana dukan kafaɗarta, buɗe ido Abu ta yi idanunta suka yi tozali akan fuskar ƴar uwarta. Da murnarta Abu ta yunƙura da ƙyar taba ƙoƙarin ta shi, cike da ɗoki ta furta, "Maryo ke ce nake gani yaushe kuka zo.?" Saif ya fara ɓaɓɓaka dariya yana faɗin, "Bana ƙaunarki tun da kika aure mini masoyina kuma sai na wahalar da ke." Yana rufe baki ya dunƙule hannu ya daki cikin Abu, nan take ta ƙwalla uwar ƙara har sai da su Inna Habi suka jiyo ihunta. BILLAHI HAR KUSAN KUKA NA YI WA ABU😢 AMUN AFUWA BAN YI EDITING BA _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [11/01, 14:23] Ameera Adam🌚: 60... Wani irin azababben duka ta ji cikin baccinta a firgice ta miƙe zaune tana waige haɗe da soshe-soshe, a razane ta sauke idanunta kan Maryo da ke tsaye a gefe ta zuba mata manyan idanuwanta fuskarta murtuk kamar ta fusataccen bujimin Sa. Da sauri Fulani Maryama ta ja da baya tana watso mata tambaya wacce ga dukkan alamu bata cikin hayyacinta, "Lafiya me kika zo yi mini waye ya baki izinin shigowa?" "Ki sani ina ragawa wanda ya nemi cutar da ni haka duk wata ɗan adam da zai cutar da ni bana ɗaukan wani mataki a kansa amma in wani ya yi yunƙurin cutar da wani nawa tabbas zan nuna masa iyakarsa. Ba na son ki fusatani ta yadda zan azabtar da ke da hukunci me tsanani. Na zo na yi miki jan kunne domin bakin rijiya ba wurin wasan makaho bane." Maryo ta faɗa tana ƙara haɗe fuska. Fulani Maryama ta saki murmushi domin ga duk wanda ya yi wa Fulani Maryama farin sani zai tabbatar ƙarfin hali irin nata, zai yi wuya farat ɗaya ka fahimci tashin hankalin da take ciki, tana dabƙwarin gwiwa fiye da tunanin mai tunani. Gyara zamanta ta yi ta kalli Maryo fuskarta kwance da murmushi tana cewa, "Yaro man kaza. 'Yan mata me kike faɗa haka ne?" Haushi ne ya ƙara kama Maryo ta furzar da iska me zafi nan take idanunta suka rine jawur, da sauri ta ƙarasa ta kama hannun Fulani Maryama ta damƙe shi da ƙarfin tsiya, wani irin zafi zumm! Ya ratsa cikin hannunta zafin har tsakiyar kanta. Wata uwar ƙara ta saki sannan Maryo ta saki hannunta ta ce, "Wannan gargaɗi ne na yi miki amma wallahi duk ranar da kika sake turowa 'Yar uwata wani mugun abin na rantse da zatin Ubangiji sai kin komai abar tausayi a gidan nan, na ƙata jadadda miki 'Yar uwata ba sa'ar yinki bace muddin kika nemi cutar da ita sai na kashe ki da rayuwarki, sai kin wulaƙanta kina ji kina gani babi uwar da bokayenki za su iya yi miki." Maryo na gama faɗar haka ta fice daga ɗakin, Fulani Maryama bata samu sukunin iya furta komai ba saboda tsananin azabar da take ciki. Jin ihunta ya sa Baiwarta shigowa a guje cikin tashin hankali ta tsaya a bakin ƙofar tana cewa, "Ranki shi daɗe kina buƙatar taimako ne?" Jin Fulani Maryama shiru ya sa Baiwarta ta faɗa ɗakin, da sauri ta matsa kusa da ita ganin halin da take ciki, a wahalce ta ɗago tana cewa, "A kwai yarinyar da ta fita ku maza ku ruƙo ta." Da mamaki Baiwarta ta ce, "Allah ya taimakeki muna zaune a rumfa (Falo) ba mu ji mostin kowa ba, babu wacce ta fita." Ɗagowa ta yi da idanu tana watsa mata mugun kallo a fusace ta ce, "Ƙarya nake miki kenan?" Matsawa baya Baiwar ta yi ta ce, "Wallahi Ranko shi daɗe babu wacce ta fita..." Cikin masifa Fulani Maryama ta ce, "Kina hauka ne yanzunan yarinyar nan Maryo ta fita ki ce mini babu wacce ta fita." Baiwar ta ce, "Bari na yi wa su Shafa'atu magana ko sun ga wucewarta." Tana gama maganar ta fice. Tun daga ɗan yatsanta har zuwa kafaɗarta hannunta ji ta yi ya yi wani irin sanyi ya sage mata, ɗayan hannun ta saka ta tallafo hannun sai jinsa ta yi ya yi wani sharaf. Tsoro ne ya fara kamata ta yi yunƙurin sake ɗaga hannun amma ta ji ya yi mata dum! Kamar an ɗora mata Dala da gwauron dutse. Hankalin Fulani Marayama ba ƙaramin tashi ya yi ba, nan take ta fara ayyana ko dai aljanu ne suka yi mata siffar Maryo tun da, da alama sun shanye mata hannu. Tana cikin wannan yanayin su Shafa'atu suka yi sallama suna cewar, "Allah ya taimake ki wallahi..." Da sauri ta buga musu tsawa tana cewa, "Ku fice mini ba na son ganinku!" Tun bata rufe baki ba suka fice a guje ko waiwaye babu me yi. Kamar ƙaramar yarinya haka Fulani Maryama ta tallaɓo shanyayyen hannunta ta rushe da wani irin kuka be man tausayi. A daidai lokacin da su Inna Habi za su shiga ɗakin da Abu take Saif ya diro kamar wanda aka jefo daga sama, saboda tsoron da suka ji har ja suka yi da baya. Bai kalle su ba ya faɗa ɗakin da gudu don ihun Abu jinsa yake har cikin jikinsa, a wannan yanayin da yake ciki baya jin ko ɗigon soyayyar Abu a zuciyarsa amma tabbas shi kansa ya san yana matuƙar tausaya mata, domin duk macen da ke ɗauke da Ɗa a cikin cikinta tabbas abar tausayi ce, bare macen da ke cikin mawuyacin hali irin wannan da bata ji ba bata gani ba kuma a aiwatar mata da rashin imani irin wannan. Yana shiga ɗakin a tsaye ya samu Salman da ke ɗauke da siffar Maryo, Abu ban da murƙususu babu abin da take yi, hannunta na dafe a cikinta. Saif na shiga ya ƙarasa wurinta ya rungumota jikinsa, yana ɗora hannunsa akan saitin wurin da ya ga tana dafawa. Wata irin shu'umar dariya Salman yake ƙyaƙyatawa a daidai lokacin su Inna Habi suka shiga sai kuma ya rikiɗe zuwa siffar Likita kafin su ankara da shi. Hankali a tashe Inna Habi ta ce, "Likita me yake faruwa me ya same ta." Sai a lokacin Saif ya fahimci yaudarar da Salman ya yi wa su Inna Habi, ganin yadda Saif ya yi wa Abu ya sa Inna Habi ta ja da baya ta fice daga ɗakin saboda kunya. Su Uwar Bayi ma fita suka yi tana cewa, "To bari mu basu wuri tun da mijinta na kusa duk abin da ya kamata sai ka sanar da shi." A wahalce Abu ta ɗago ta dubi Saif hawaye na zuba daga idonta, shima idanunsa ne suka ciko da ƙwalla ya sauke idonsa ƙasa yana haɗa fuskarsu wuri ɗaya. A daidai lokacin Maryo ta faɗo ɗakin bayan ta baro wurin Fulani Maryama. Tana shiga ɗakin ta kalli Salman cike da tsoro don ta tabbata ganinsa a nan ba alheri bane, da sauri ta nufi gadon da Abu take don ganin halin da take ciki, nan take ta yi tozali da Saif rumgume da Abu, wani abu ta ji ya soki ƙahon zuciyarta amma sai ta kauda kai gefe tana lumshe ido, a daidai lokacin Abu ta fara zubda ƙwalla murya can ciki ta ce, "Saif!" Ɗagowa ya yi ya kalleta hatta Maryo da ke gefe sai da ta kalle ta domin yadda ta faɗi sunan za ka tabbatar da tana cikin wani irin mummunan yanayi, ta ɗan cije bakinta saboda yadda take ji ta ci gaba da cewa, "Tabbas na aikata babban kuskure, na ɗauka soyayyar ita ce farincikin komai a rayuwar nan. Ta rufe mini ido a lokacin da take buga mini gangarta, ta yadda na kasa fahimtar kuskuren da hakan ke tattare da shi. Na makance a kan soyayyarka Saif ta yadda na manta soyayyar 'yan uwantaka, amma ban yi zaton hakan har zai ka ga 'yar uwata na neman halakani ba. Duk duniya ba ni da na biyun Maryo ta ƙaunace ni kuma na tabbata soyayyarka ce ta sa ta aikata mini haka." Hankali a tashe Maryo ta kalli Abu jikinta har rawa yake ta ƙarasa wurin Salman ta cukumi wuyansa tana faɗin, "Me ka aikata mata a siffata, wallahi muddin ka cutar da ita ba zan yafe maka ba. Ina ƙara gaya maka bana son zubar jini ya wanzu a masarautar nan amma da alama kana son tarihi ya sake maimaita kansa." Sai a lokacin Abu ta waigo suna haɗa ido da Maryo ta ji tsoronta ya sake kamata, Maryo tuni hawaye ya fara wanke fuskarta domin ta lura da irin zallar tsoron dake kwance a fuskar ƴar uwarta. Sake rungume ta Saif ya yi zata sake magana ya haɗe bakinsu wuri ɗaya, da ƙarfi ya shiga hura mata iska a bakin tun tana cikin hayyacinta har ta fita daga hayyacinta idanunta suka fara lumshewa. Sannan ya ɗauke bakinsa daga nata, kamar saukar ruwan sama haka ta fara kwara wani irin baƙin amai kamar za ta amayar da hanjin cikinta. Da sauri Maryo ta ƙaraso ta riƙe ta a ɗan fusace ta ce, "Me kake yi haka ne Saif?" Ido ya zuba mata sannan yace, "Hakan shi ne mafita idan na barta da gudar da ya zuba mata tabbas zai cutar da ita da abin da yake cikinta." Idonta ne ya ci gaba da zubda ƙwalla ta sunkuyar da kai ƙasa bata furta komai ba sai kuma ta yi gaba, da sauri Saif ya riƙo hannunta don ya fahimci abin da za ta aikata, juyowa ta yi a zafafe amma kallon yake yi mata ya saukar mata da kasala, hakan ya sa ta sunkuyar da kai ƙasa ta ce, "Don Allah ka sake ni!" Shiru ya yi mata bai tanka mata. Salman da ke gefe ya saki dariya me sauti yana tafi da hannunsa yace, "Ka bar murna karenka ya kama Kura." Saif ya ɗaga masa gira ɗaya yace, "Ka san ko kura ta rame ta fi ƙarfin gawurtattun karnuka." Maryo ta nuna shi da ɗan yatsa fuska babu walwala ta ce, "Duk a kaina kake wannan haukan ko? Ka ɗauka zan ƙaunace ka ne bayan kana barazanar halakar da ƴar uwata. Ka buɗe kunnenka ka saurareni da kyau ka ji, wallahi baka ci bulus ba na rantse da Allah sai na baƙanta maka da baƙin ciki me tsanani. Idan ma saboda Saif kake yi wannan haukan daga kai har shi babu wanda zan aura, na faɗa na ƙara wallahi babu mutum ɗaya daga cikinku da zan aura. Ka taɓa mini 'Yar uwata ni kuma na ɗaura ɗambar taɓaka tun daga yau har ƙarshen rayuwata." Abu ce ta jiyo ta kalli Maryo tana miƙa mata hannu, a hankali Maryo ta ƙarasa ta riƙe hannunta tana sunkuyar da kai ƙasa ta fara cewa, "Don Allah ki gafarce ni ƴar uwata ba ni na cutar da ke ba, kuma ba ni da burin cutar da ke daidai da ƙwayar zarra a zuciyata, duk wannan abin ya faru da ke ta sanadina ne don Allah ki yafe mini." Maryo ta faɗa tana kallon ƙwayar idon Abu, Saif ne ya taimaka mata ta tashi daga gadon da take kai zuwa wani gadon ya nannaɗe zanin gadon da ya ɓaci, a hankali Maryo ta bi ta kan sabon gadon ta sake zuba mata idanu don jin amsar da Abu za ta bata. Abu ce ta kalli Saif da ke hidima da kayan wurin ta ce, "Ba zan taɓa yafe miki ba har sai Saif ya yi mini alƙawarin duk abin da na buƙata a wurinsa zai aiwatar mini." Gaban Maryo ne ya yi mummuna faɗuwa, Saif ya tsaya cak sannan ya waigo ya zubawa Abu ido yana juya maganganunta. Gyaɗa masa kai ta yi, a hankali Saif ya furta, "In dai za ki yafe mata na yi miki alƙwarin biya miki buƙatarki matuƙar bata saɓawa addinin musulunci ba." Abu ta gyara kwanciyarta tana cewa, "Don girman Allah ka sauwaƙe mini ka auri 'yar uwata Maryo, wallahi ko baka sauwaƙe mini ba na yi alƙawarin ba zan koma gidanka ba." Jin maganarta ya yi dum! ya zuba mata idanu ya kasa furta koda kalma ɗaya ce. Da ƙarfi Maryo ta daki gadon da Abu take kai ta ce, "Yaushe kika fara hauka Abu ban sani ba? Kina cikin hayyacinki kuwa?" Abu ta saki murmushi ta ce, "Tun da muke baki taɓa gaya mini magana ta rashin girmamawa irin wannan ba, me ya sa don na faɗi abin da yake raina zamu fara haka da ke.?" Idanun Maryo ya kaɗa jawur ta ce, "Wa muke bautawa?" Abu ta ce, "Allah!" Maryo ta jinjina kai ta ce, "Na rantse da girmansa idan har Saif ya sake ki saboda wannan buƙatar taki babu ni babu ke, kin sanni farin sani idan ba bar abu na bar shi har abada kar ki janyo abin da zai rabani da ke. Karki manta komai rubutacce ne a wurin Ubangiji, kina tunanin bawa zai iya gujewa rubutacciyar ƙaddararsa? Kenan Allah ba zai jarabcemu ba ko mun fi Ubangiji sanin abin da ya kama? Ko kina gidan Saif ko bakya gidansa wallahi ba zan aure shi ba don haka idan kina son na ci gaba da ɗaukanki kamar yadda muke da ki bar wannan maganar." Abu ta lumshe ido ta ce, "Ina burin ganin farincikinki Maryo amma ki sani wannan ciwon nawa ba na tashi bane don Allah ki bari na ga aurenki da Saif kar sai lokacin da ƙasa ta rufe mini ido a yi babu ni, domin ina ji a jikin wannan cikin abokin tafiyata ne..." Da sauri Saif ya rufe mata baki idanunsa sun yi jawur saboda tashin hankali, Maryo jikinta na rawa ta ƙarasa wurim Abu ta ce, "Ya isa ki bari ki samu lafiya duk abin da kike so haka za a yi ba dai so kike na aure shi ba. To Allah ya baki lafiya." Kamar me shirin ta shi sama haka Salman ya fice fuuuu daga cikin ɗakin. Gabaɗaya suka bi shi da kallo babu wanda ya tanka masa. Abu ta ce, "Maryo meye alaƙarki da Likitan can har kuke musayar yawu." Nan take Saif ya sanar da ita abin da yake faruwa, Maryo ta kora mata bayanin burin Saif a kanta. Ganin ta shiga damuwa ya sa suka kwantar mata da hankali da nuna mata hanyoyin da za su shawo kan matsara. Maryo ta sanar da Abu za ta auri Saif ne domin ta lura idan ta biye mata sai jikinta ya sake rikicewa fiye da na baya, don ta lura da nadamar aurensa da ƴar uwar tata ta yi. Fulani Maryama ta gana tabbatarwa da kanta hannunta ya riga da ya shanye, ba a ɗauki lokaci ba ta sanarwa da Takawa duk abin da yake faruwa, lokacin da take yi masa bayani kuka ne a fuskarta shaɓe-shaɓe. Ba ƙaramin tausaya mata ya yi ba, amma abin da ya fi daminsa da ta ce Maryo ce ta shanye mata hannu sai dai an tabbatar da cewar tun da aka tafi da Abu asibiti babu wanda ya ga gilmawar Maryo, ganin yadda ta rikice ya sa Sarki Aminullah ya tabbatar da cewar tabbas aljanu ne suka shafe ta domin babu yadda za a yi ace mutum ɗan uwanka ya shanye maka hannu. A ranar ya aika ka fara gayyato masu magungunan gargajiya domin sun bata magani ko hannun ya miƙe. Kafin wani lokaci tuni shanyewar hannun Fulani Maryama ya karaɗe cikin Masarautar, wannan gayawa wancan gayawa wancan. Sauran kishiyoyinta sam maganar bata yi musu daɗi ba haka daga ɓangaren Jakadiya lokacin da labarin ya je mata sai da ta shiga banɗaki sau biyu sannan ta lallaɓa ta nufi sashen Fulani Maryama domin tabbatar da abin da kunnuwanta suka jiye mata dukda ita ma ba maruru na ci gaba da rarake hammatarta. Abu satinta Biyu a asibiti aka sallamota jikinta ya yi kyau sosai ta warware, cikinta ya ƙara tsufa da ƙyar take iya ɗaga ƙafarta, wannan dalilin ya sa Fulani Zaliha ta dakatar da komen Abu ta umarci a mayar da ita sashenta domin ta ci gaba da bata kulawar da Uwa take bawa ƴarta. Inna Habi na jin daɗin yadda Fulani Zaliha take ƙaunar Abu, Maryo ku san kullin tana wurin Abu domin idan damuwa ta yi mata yawa in taje can tana samun sauƙin halin da take ciki. Hakan yana yi wa Inna Habi daɗi domin damuwar da Maryo take shiga na raguwa, ana cikin haka Maleek ya kawo mata ƙoƙon barar soyayyarsa. Da farko ta so ta bijire masa amma sai ta yi tunani idan ba amince masa ta yi ba ba zata samu kwanciyar hankali a wurin Saif da Salman ba, domin ta san ita kanta Abu ta yi mata shiru amma ta jadadda mata baza ta koma gidan Saif ba ya fi a irga. Wannan labari ba ƙaramin daɗi ya yi wa Inna Habi ba dama kuma duk wanda ya ga yadda Maleek yake yi wa Maryo zai tabbatar da irin ƙaunar da yake yi mata. Ba a ɗauko lokaci ba Manya suka suka shiga magana, Mahaifin Maleek ya zo Masarautar Kano ya nemar Ɗansa auren Maryo a wurin Sarki Aminullah. Takawa sai da ya ji ta bakin Maryo domin yace wannan karan sai an ji daga gare ta, a kunyace ta amsa dukda za ta auri Maleek ne ba don tana sonsa ba sai don kyawun halinsa da kulawar da yake bata. Nan take Sarki Aminullah ya sanya musu rana wata biyu masu zuwa. Lokacin da Saif da Salman suka samu wannan labarin ba ƙaramin girgiza su ya yi ba, amma ga mamakin Maryo sai ta ga Salman bai nuna wata damuwa ba sai dai Saif da ya rikice mata yana nuna mata tsananin damuwarsa. BAYAN SATI UKU Ranar Laraba da daddare naƙuda ta kama Abu tun tana ɓoyewa har ta ji ciwon ya tsananta ta fara sintiri a ɗaki, Fulani Zaliha ce ta farka saboda jin motsin Abu da ta yi. Ku san kwana ta yi tana abu ɗaya sai bayan Asuba Allah ya sauke ta lafiya ta haifo santalelan Ɗanta namiji kyakkyawa kamarsa ɗaya sak da Saif. Fulani Zaliha ba ƙaramin farinciki ta yi bata jima tana kallon yaron sai take tuna lokacin da haifi Saif, rumgume shi ta yi tana godiya ga Allah bisa wannan kyautar da ya yi musu. Da kanta ta gyara Mai jego ta da jariri sannan ta mayar da su kan shimfiɗa Abu ta rungume Ɗanta suka koma bacci, sai a lokacin Fulani Zaliha ta aika Bayi da ta kira Unguwar zoma, nan take ta ƙaraso ta gyara wurin sannan aka fara sanarwa da mutanen kyakkyawan albishir. _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [12/01, 18:55] Ameera Adam🌚: 61... Waiwaye... Duk yadda Zulik zai yi ya janyo hankalin Rayzuta ya yi amma sam abin ya faskara, hasali ma 'yar gaisuwar mutumcin da suke yi ma ta yanke ta don ko ya zo cikin fadarsu idan tana zaune, ko ta tashi ko ta nemi wani uzurin da zai tashe ta daga wurin, abin sam baya yi wa Furzaan daɗi sakamakon Zulik abokinsa ne makusanci ba shi da na biyunsa. Hasali shi ba mai sha'awar tara abokai bane, wannan dalilin ya sa kodayaushe yana cikin masarauta idan baya sashen su to yana wurin ƙawarsa wacce ta rikiɗe zuwa masoyiyarsa. Wata ranar Juma'a suna zaune cikin lambum Mahaifinta suna hira Furzaan ya zuba mata ido lokacin da take ba shi labarin mafarkin da ta yi, Bari mu ɗan taɓa yaren nasu🌚 "Wurbankis guna bila kalbistu kinmansu walbisu fatgurin zakbistu..." (Ka bani goron albishir na baka labarin mafarkin da na yi, ka san mai ya faru...) Sai kuma ta katse maganar bakinta tana zuba masa ido har ta sa hannu a saitim fuskarsa, har sai da ta ɗan tafa hannunta a kan fuskarsa sannan ta ɗan ɓata fuska ta ce, "Wai dama ba saurarena kake yi ba." Shagwaɓe fuska ya yi yace, "A kodayaushe sauraron muryarki na sanya ni faɗawa cikin wani yanayi, har yanzu gani nake ina ta bilayi ban sani ba ko waiwayen da nake yi za a fahimci ƙishirwata. Sai dai a koyaushe idan na yi tuno da giwa ta yi wa barewa nauyi na kan ji karaya a zuciyata, sai dai bana jin zan iya jure kishirwar da nake ji ba tare da na kawar da ita ba." sai kuma ya marairaice murya kamar mai shirin yin kuka ya ci gaba da cewa, "Ba ta yi mini adalci ba kuma da zan iya tozali da na hukuntata da hukunci mai tsanani saboda bata shawarce ni ba. Na faɗa kogin soyayya ba tare da shiri ba sai dai bana jin zan samu gurbi domin bakin rijiya ba wurin wasa makaho bane. Wannan dalilin ya sa nake karaya..." "Karaya ga gawurtaccen jarumin maza sam bai dace da kai ba. Bana buƙatar saka jin kalmar daga bakinka domin sam bata dace da kai ba. Ta dace da gurbin zama shi ya sa ta samu sukunin zama a cikin zuciyarka. Kada ka taɓa tsammanin bata yi maka adalci ba domin ta ɗora ƙwarya a gurbinta. Ya za a yi ka hukuntata alhalin ta yi abin da ya dace domin duk abin da kake muradi yana tare da kai. Ka daina kewaye-kewaye domin ba zai haifar da Ɗa mai ido ba." Rayzuta ta faɗa tana kashe masa ido ɗaya. Mayar mata da martanin murmushi ya yi ya ruƙu hannunta, wannan ne karo na farko da haka ya fara faruwa a tsakaninsu, wani irin yaar ta ji a jikinta ta ɗago da idanunta karaf suka haɗa ido, rana ta farko kenan da ta gagara jurewa kallonsa a hankali ta sauke kanta ƙasa, tana cikin wannan yanayin ta riski muryarsa na cewa, "A yau zan bayyana miki abin da ya daɗe yana yi mini yawo a cikin zuciyata, Rayzuta!" Ya ambaci sunanta cikin wani irin yanayi mai wuyar fasaltuwa. Ɗagowa ta yi ta kalle shi sannan ta sunkuyar da ka ƙasa ya ci gaba da cewa, "Koda za ki sa a hukunta ni sai na furta domin barin kashi a ciki baya maganin yunwa. Na san ba zan samu matsayin da za ki amshi ta yi na ba domin bambamcin tsakanin ruwa da jini a bayyane yake. Rayzuta ina ƙaunarki tun ranar dana fara tozali da ke! Ina sonki fiye da tunanin mai tunani. Sai dai bana jin zan iya mallakarki a matsayin matar..." "Wa ya gaya maka?" Rayzuta ta yi maganar tana harɗe hannuwa a ƙirji sai ta ci gaba da cewa, "Na zura maka ido ne dama domin na ga iya gudun ruwanka. Furzaan! Na jima da dakon ƙauna da soyayarka, sai dai na yi kawaici ne domin mace da kunya aka santa. Duk wasu alamu na soyayya ina nuna maka amma kai sai ka nuna kamar baka gane ba shi ya sa na kame baki na." Farinciki ne ya lulluɓe masa zuciya lokaci ɗaya ya rungumota jikinsa ita ma ta kwantar da kanta tana jin wani irin farinciki a zuciyarta. Ɗago da ita ya yi yace, "Faɗa mini mafarkin da kika yi." Ta ku biyu ta ƙara sannan ta juyo ta kalleshi ta ce, "Na yi mafarkin ana ɗaura mana aure sai wani irin duhu ya mamayr wurin daga baya kuma sai na Takawa ya fara zubar da jini." Hankali a tashe ya furta, "Jini kuma?" Kanta tsaye Rayzuta ta ce, "Eh mene ne?" Murmushin yaƙe ya yi yace, "A'a babu komai!" Sauya fuska ta yi ta ce, "Amma sai na ga kamar baka yi farinciki ba." Hancin ta ya riƙe yana cewa,"Ke dai bakinki baya shiru." Ita da shi suka saki dariya lokaci ɗaya. Suna cikin wannan yanayin Zulik ya faɗa wurin hannunsa riƙe da kwari da baka, yana ganinsu a wannan yanayin ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba. Haɗiye yawu mai ɗaci ya yi ya ƙirƙiro murmushin yaƙe ya ɗora a fuskarsa ya ƙarasa yana cewa, "Barkanku da hutawa." Rayzuta na tamke fuska ta yi ta fara haramar wucewa, da sauri Zulik ya sha gabanta yana cewa, "Yau ba za ki bar wurin nan ba har sai kin sanar mini me na yi miki?" Da mamaki ta juyo ta kalleshi fuska a tamke ta ce, "Zan tunasar da kai kada harshenka ya yi gangancin furta abin da zai kaika ga mummunan hukunci, ka tuna wace ce a gabanka." Fuzaan ya tausasa murya yana cewa, "Rayzuta! Ki tsaya don Allah ki saurare shi." "Me kake so?" Ta tambaye shi a gajarce. Wani shu'umin murmushi Zulik ya yi domin ya san haƙƙansa ya kusa cimma ruwa, saboda duk maganganun da su Furzaan suka yi tun daga farko har ƙarshe yana laɓe yana jin su. Juyawa ya yi wurin Furzaan yace, "Duk cikin gidan nan ka fi kowa kusanci da Gimbiya kai ne babban abokinta don Allah ka roƙar mini alfarma a wurinta, ta taimaka ta amshi soyayyata duk duniya babu wacce nake so nake ƙauna sama da ita." Jin maganganunsa yake kamar saukar aradu, ido ya zura masa yana jin maganganunsa na yi masa yawo a tsakiyar ka. Yana shirin yin magaga Rayzuta ta ce, "Karka wahalar da yawun bakinka domin wannan buƙatar taka daidai take ta ɓillar ƙaho a tsakiyar kan ɗan tsako. Na riga da na samu masoyi na haƙiƙa domin na gwada shi ta hanyoyi mabambamta. Don Allah ina roƙonka ka bar wahalar fa kanka domin wannan ba abu bane mai faruwa. Tana gama faɗa ta yi gaba kafin ta fita ya sha gabanta da sauri ya sha gabanta ya saki murmushi yana cewa, "Wallahi sai na aureki kin ji na gaya miki bar ganin ina lallaɓaki amma sai na nuna miki idan na nemi abu dole sai na same shi babu ruwana da matsayinki abin da na sani..." Bai rufe baki ba ta ɗauke shi da mari. Ta nuna shi da ɗan yatsa tana cewa, "Ina ganin mutumcinka ne saboda kai abokin Masoyina ne, amma kana neman ka kaini magaryar tuƙewa idan ka sake yi mini makaman..." Bata yi aune ga ta ji ya rumgomata da sauri Furzaan ya janyota jikinsa ya ture Zulik cikin fushi yana cewa, "Ya isa haka karka fara ƙoƙarin wuce gona da iri. Tun da ta ce bata ƙaunarka ana dole ne?" Zulik ya saki murmushi sannan ya nuna su yana cewa, "Allah ko? To mu zuba mu gani ni da ku shege ka fasa. Wallahi sai na cimma ƙuɗurina a kanki." Yana gama maganar ya fice daga lambun. Wannan shi ne mafarin rashin jituwar Zulik da Furzaan... Kafin wani lokaci tuni labarin haihuwar Abu ta karaɗe ciki da wajen masarautar Kano, wannan labari ba ƙaramin faranta ran su Inna Habi ya yi ba. Saɓanij Fulani Maryama da wannan saƙo ya zame mata mummunan albishir, wannan saƙo ba ƙaramin ɗaga mata hankali ya yi ba dukda ta san wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa. Amma sam bata ji daɗin haka ba, amma a wannan karon tana shakar ziyarta ɗaya daga cikin Bokayenta saboda hannun da take fama da shi har gobe babu wani ci gaba da a ke samu. Masu magungunan gargajiya kala-kala sun zo kowa ya gwada basirarsa amma babu wani sauƙi ko canji. Canji ɗaya take lura da shi wato ta lura hannun nata ya fara tsotsewa yana ƙanƙancewa. Jakadiya maruru ya yi mata sauƙi har ya fara saɓa, da safiyar ranar da Abu ta haihu ta leƙa wurin Fualani Maryama bayan sun gaisa Jakadiya ta yi ƙasa da murya ta ce, "Fulani ashe mummunan mafarkin da na yi a daren jiya ba banza ba? Wacce yarinyar ashe haihiwa za ta yi? Ya a ka yi muka yi sake har wannan lamarin ya auku? Maryama kina me har ta haife cikin nan ba tare da an ɓarar da shi ba." Fulani Maryama fuska ɗauke da damuwa ta janyo shanyayen hannunta tana nunawa Jakadiya, da sauri Jakadiya ta yi baya tana zaro ido waje ta ce, "Na taɓa ki da alheri Maryama meye wannan nake gani ido biyu da farar safiyar nan?" "Jakadiya babu wanda zai yarda da abin da zan faɗa idan bake ba. Yarinyar nan Maryo ita ta tsotse mini hannuna." "Kamar ya Fulani kina nufin ture ta yi miki?" Jakadiya ta tambaya hankali a tashe. Fulani Maryama ta rausayar da kai ta ce, "Turen Ƙadangare na yi wa Sirikar Zaliha shi ne ta diro mini yadda na ganta ido biyu in ga Annabi, amma yaran nan kowacce sai cewa ta yi bata ganta ba. Wallahi yarinyar ba mutum ba aljana ce, idan ba aljan ba waye zai aikata haka matsa hannuna fa ta yi amma ji na yi kamar ta tura shi cikin wuta. Tun daga lokacin shi kenan bana jin komai." Jakadiya jikinta ba ƙaramin sanyi ya yi ba ta ce, "Maganar gaskiya Maryama ya kamata mu samawa ranmu salama akan yarinyar nan, ni fa ba tun yau lamarinta yake bani tsoro ba. Mu kawo ido mu zuba wanda muka yi a baya ma Allah ya yafe mana." Wani murmushi Fulani Maryama ta yi ta ce, "Jakadiya kina matuƙar ba ni mamaki, me ya sa kike saurun karaya ne?" Tsoro ƙarara ya bayyana fuskar Jakadiya a take ta miƙe tana cewa, "Maryama kin daina ba ni mamaki yanzu lamarinki tsoro yake bani, ni bari ki ga wucewata Allah ya baki lafiya amma duk yanda hannunki yake tsotsewa kamar an tsotse rake baki daddara ba." Wannan karan ko kyakkyawar sallama ba su ba Jakadiya ta fice ta faɗa sashen Fulani Zaliha. A cen ma bata daɗe ba saboda bata samu fuska ba, tana fita dagan sashen ta wuce sashen sauran Matan Sarki sannan ta koma sashensu. Inna Habi lokacin da aka sanar da ita ba ƙaramin farin ciki ta yi amma fir ta ƙi zuwa ganin Abu da Jaririnta (Saboda tsananin kunya irin ta mutanen da) Maryo ko bari a gama sanar da saƙon ba ta yi ba ta fice da gudu ko takalmi babu. Tana zuwa ko a gurguje ta gaishe da Fulani Zaliha, murmushi ɗauke a fuskar Fulani Zaliha ta ce, "Ai fa ba zama an ɗaurawa karya aure. Su Maryo an yi ɗa da alama ko takalma baki taho da su ba." Maryo na shirin bata amsa ta ji kukan Jaririn Abu da gudu ta faɗa ɗakin tana zuwa ta haye kan gadon ƙarfen ta karɓe Jaririn da ke ta mutsu-mutsi yana saka hannu a baki." Cak Maryo ta tsaya tana zuba masa ido sakamakon tsananin kamar da ta ga yana yi da Saif, wani irin farinciki ne ya kamata a zuciyarta take ayyana, "Tabbas ko ban auri Saif ba wannan ya zame mini abin farinciki. Yau Ɗan Saif ne a hannuna jininsa ne mallakinsa. Wannan shi ne murna biyu ga shi Ɗan 'yar uwata mahaifinsa kuma masoyi na." Ba ta san lokacin da ta rungume shi tsam a jikinta ba sai kuma ta faraa yi masa kissis cikin so da ƙauna. Wata irin kunyarta Abu take ji, kamar ta san abin da yake zuciyar Maryo. Ta ɗora hannunta a kan Maryo tana sunkuyar da kai ƙasa ta ce, "Bawa baya taɓa gujewa ƙaddaras sai dai wannan ƙaddarar ba ta zo mini ta sigar da nake buƙata ba. Ta yi mini yankan ƙauna domin tana neman yin katanga ga a tsakanin masoya. Maryo!" Abu ta kira sunanta cikin wata irin murya ta ci gaba da cewa, "Wannan yaron da yake hannunki Ɗanki ne halak malak ina raye da bana raye na mallaka miki shi koda mahaifinsa bai amince ba ni na mallaka miki tun da ni na san zafin naƙudar shi." Idon Maryo ne ya ciko da ƙwallah ta kalli Abu ta ce, "Tun da na zo duniya babu kyautar da na taɓa farinciki da ita irin wannan haƙiƙa ke ƴar uwace ta daban." Abu ta yi murmushi tana cewa, "Abu na gaba ina son ki janye maganar aurenki da Maleek idan har ina da matsayi a wurinki. Karki damu da ni na sha gaya miki zamana da Saif yanzo ƙarshe amma kina ɗaukar lamarin kamar wasa, wallahi ba zan koma gidansa ba..." Da sauri Maryo dakatar da ita tana cewa, "Don Allah ina tsaka da farinciki kada ki ruje mini shi. Na gaya miki ina ƙaunarsa ne da za ki tursasani aurensa. Me ya sa bakwason farincikina ne? Na samu mijin da zai bani kulawa miji mai ƙaunata ya kike so ki sa ni auren wanda bana so." Maryo na maganar hawaye na zuba. "Ƙarya kike!" Da sauri Maryo ta ɗago ta kalleta Avu ta ci gaba da cewa, "Kalmanki sun furta akasin abin da yake zuciyarki, kin manta cece Abu kin san na fi kowa karantarki da halin da kike ciki me ya sa za ki cuci kanki? Babu komai idan kun san wata ba ku san wata ba." Da sauri Maryo ta kalli Abu ta ce, "Me za ki yi?" Kai tsaye Abu ta ce, "Abin da ta dace!" "Don Allah..." Da sauri Abu ta katse ta, "Mu bar maganar tun da dai ba za ki aure shi ba shi kenan" Jikin Maryo ne ya yi sanyi don ta san Abu sarai ta san akwai abin da ta ƙulla. Kukan da Jaririn yake tsalawa ne ya sa Fulani Zaliha ta yi musu magana, a kunyace Abu ta karɓe shi ta fara bashi Mama. Maryo ta guntse dariyarta suna haɗa ido Abu ta ɗaɗa mata duka ta ce, "Munafuka faɗi abin da yake bakinki!" Maryo ta fashe da dariya don dama a cike take da ita, sai da ta yi mai isarta sannan ta ce, "Oh! Ni 'Ya su Abu wai kunya ta kike ji." Abu ta basar don ta san halin Maryo sarai idan ta gano lagonka ka shiga uku ta ce, "Kunyar uwar mai sai ka ce wata sirikita ke ni ko Fulani ba na jin kunyarta bare ke." Maryo ta riƙe baki ta ce, "Allah ya shiryeki na san za ki aikata abin fa ya fi haka." Abu daɗi ta ji har ciki ranta yanda ta ga ƴar uwarta ta saki jiki suna wasa da dariya a gefe ɗaya kuma ta ji haushin kanta domin da bata auru Saif ba babu wani abu da zai shiga tsakaninsu yanzu da tuni Ɗan Maryo ne a hannunta. Suna na zaune suna hira Jaririn ya tsanyare da wani irin matsanancin kuka jikinsa na wani karkarwa, a zabure Maryo ta miƙe tsaye ta karɓi Jaririn ta zuba masa ido sai kawai ta sake shi a ƙasa ya faɗi, bata bi ta kansa ba ta fice daga ɗakin. Sorry 4 the errors ban yi editing ba _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [13/01, 16:13] Ameera Adam🌚: 62... Da sauri Fulani Zaliha ta faɗo ɗakin domim kukan da Jaririn yake sam bana lafiya bane, Abu tana tsaye jikinta na karkarwa da sauri Fulani Zaliha ta ɗauke shi tana buga mata tsawa, "Wannan wanne irin sakarci ne kuke yi haka za ku yarda yaro kuna kuna tsaye kina kallonsa me yake damunki ne?" Abu kasa furta komai ta yi sai kawai ta fashe da kuka don yanayin da ta ga 'yar uwarta a ciki ya tabbatar mata da tabbas akwai abin da yake faruwa. Fulani Zaliha ce ta miƙa mata Jaririn a faɗace tana cewa, "Maza kaɓe shi ki ba shi ya sha." Shiru Abu ta yi kamar kurma sai da Fulani Zaliha ta maimata mata maganar sannan Abu ta sunkuyar da kai ƙasa ta amshi Jariri da ya ƙura mata ido ƙir (Waɗanda suka karanta littafina na Jariri ne kaɗai za su fahimci yanayin🤣) har sai da Abu ta tsargu tsoro ya ɗan kamata. Fulani Zaliha ta ce, "Abu wai ko wani abu na daminki ina yi magana kina ji na?" Abu ta sunkuyar da kai ƙasa cikin sanyim murya ta ce, "Ki gafarceni Ranki ya daɗe amma bana jin Maryo ta yi kuskure domin ba za ta yarda shi a banza ba, na tabbata tana da dalilin yin haka. Ina ji a jiki a kwai wani ɓoyayan al'amari a dangen da jariri..." Da sauri Fulani Zaliha ta katse ta a fusace, "Ba na son sakarci kina hauka ne? Karki sake ki furta kalma mara daɗi a kan jikana." A kan dole Fulani Zaliha ta tursasa Abu ta bawa Jaririn Mama, tana zama rai a ɓace ta fara bashi ya fara sha kawai sai gani ta yi Abu ta fara sanƙame wa idanunta suna niyyar kafewa. Wani babban tashin hankali sai ga jini ya ɓalle mata ya zuba kamar an buɗe famfo. Tuni Fulani Zaliha ta cire Jaririn da yake ta zuƙarta ta ajiye shi a gefe ta fita kururwar neman taimakon mutane. A daidai lokacin Saif ya shiga ya samu Mahaifiyarsa cikin tashin hankali, ba ƙaramin tsorata ya yi da ganin jinin da yake zuba daga jikinta ba. Dunƙule hannunsa ya yi yana ɗan girgiza kansa sai ya ɗora a saman kanta nan take ta sandare numfashi ya yi ƙaura daga gangar jikinta. Wata gauruwar ajiyar zuciya ya sauke yana dafe kansa, sai ya mayar da kallonsa ga Jaririn da yake kwance ya saki wani irin murmushi domin shi lamarin Salman ya fara ba shi dariya. A zuciyarsa yake ayyana, "Tabbas yaƙin ba iya a kan Maryo bane, saboda da a kanta ne ba zai yi mini haka ba. Tun da ya kwana da sanin ba da ni a ka saka mata rana ba. Amma wannan karon shi ne na farko kuma na ƙarshe." A gaggauce ya tashi ya je fita Mahaifiyarsa ta shiga ita da Jakadiya da Unguwar zoma. Bai saurare su ba ya yi gaba har ya kusa fita ya juyo ya ce, "Ammi Maryo ta shigo wurin nan ne?" Fulani Zaliha ta ce, "Eh yanzun nan ta fita." "Tana ɗakin abin nan ya faruwa?" "A'a ita ta yarda Jaririn dai a ƙasa sannan ta fice." Fulani Zaliha ta ba shi amsa. "Kar ku taɓa Abu ba za ta tashi yanzu ba Ammi." Yana gama maganar ya fice a gaggauce. Sororo suka yi suna mamakin furucinsa, Fulani Zaliha ta ce, "Unguwar zoma maza mu je ki duba ta ko wani abin za ki jiƙa mata idan kuma turare ne a samo garwashi." Unguwar zoma ta zurawa Abu ido ba don tana tsoron furta abin da ta gani ba da ta gaya musu gaskiya amma babu yanda ta iya haka ta yi gaba suna biye da ita a baya. Maryo tana fita babu in da ta tsaya sai fadar Sarki Aminullah ta shiga ko kyakkyawar sallama ba ta yi musu ba, ba ƙaramin mamaki suka yi ba domin ko hijabi babu a jikinta ƙafarta babu takalmi. Tana shiga bata tsaya a ko'ina ba sai ba gaban Sarki Aminullah, a tsaye take ƙerere sai ɗan russunar da kanta ƙasa da ta yi bata furta koda kalma ɗaya ba. Bafadawan da suke fadar suka fara buga mata tsawa, "Gyara dai hattara yarinya a yi biyayya." Kanta na sunkuye ta juyo ta kalle su Goge mai maganu da ke gefe suna haɗa ido gabansa ya faɗi. Mayar da kallon ta ta yi ta sake russunar da kai ƙasa ta ce, "Ka sa mini albarka." Mamaki ya kama Sarki Aminullah sai kuma ya saai murmushi domin lamarim Yarinyar a kodayaushe mamaki yake bata, ba sau ɗaya ba, ba sau biyu yana mamakin an ya jinnu ba su samu wurin zama a jikinta ba. Domim idan bai manta ba ita ce Baiwar aka tura ta kashe shi, sannan ita ce baiwar da yake a gani tana taimaka masa a mafarkinsa duk lokacin da ya ga Salman na yunƙurin cutar da shi. Kallonta ya yi yanayin ba ƙaramin mamaki ya bata ba ya saki murmushi yana cewa Fadawa, "Ku ƙyale ta" Mayar da kallonsa ya yi kanta yace, "Me za ki aiwatar da zan saka miki albarka?" Bata ɗago ta kalle shi ba ta ce, "Ka sa mini albarka, zan aiwatar da mihimmin abu amma na tabbata ba zai yi maka daɗi ba." "Mene ne shi?" "Ba buƙatar ka sani ka dafa kaina kawai nake buƙata..." A hassale Fadawan suka furta, "Yarinya Hattara..." Wara hannuwa ta yi tana nuna su kamar mai yin daƙuwa (Daƙuwa ta zagi) nan take bakinsu ya ɓame suka kasa furta koda kalma ɗaya sai wani irin yunƙuri suke yi. Sarki Aminullah mamaki ne ya kamashi yake ayyana, "Yaushe tsafi ya samu wurin zama a masarautar nan?" A gaggauce Maryo ta dube shi ta ce, "Lokaci yana ƙure mini ka dafa kaina." Shiru ne ya biyo baya, ganin haka ya sa Maryo ta fisgi hannun Sarki Aminullah ta ɗora a kanta tana runtse ido. Miƙewa ta yi ta fice daga fadar hat bayan fitarta bakin Fadawa nan bai buɗe ba. Sarki Aminullah ya kalli Goge, Goge ya sunkuyar da kai ƙasa don ya fahimci abin da Takawa yake nufi ya russunar da kai ƙasa yace, "Allah ya taimake ka babu abin da zan iya aiwatar dangane da ciwon Fulani, hasalima ita wannan yarinyar ita take da maganin ciwon nata domin tana da masaniya dangane da lalurar tata. Allah ya baka yawan rai ka riƙe ta hannu bibbiyu domin za ta taimaka maka fiye da yadda kake tsammani..." Sarki Aminullah ya katse da cewar, "Kana nufin ita ta cutar da Fulani? Idan haka ne meye makomar lalurarta me ta yi mata. Wane irin taimako za ta yi mana sannan ta ya za mu gasgata abin da ka furta?" Goje ya russunar da kai ƙasa ya ce, "Waɗannan amsoshin suna tattare da ita, abin da na sani dangane da ita ne kawai na sanar da kai amma idan kana shakku za ta iya tuntuɓarta." Fadawan da suka koɓa bebaye ne suka fara wanin gurnani suna son su yi magana amma harshansu ya naɗe. Sai a lokacin Sarki Aminullah ya fara gasgata abin da Goje ya faɗa domin biri ya yi kama da mutum amma saboda ya ƙara gasgatawa ya dube su yace, "Abdurrahman me kuke yi haka?" Bafade da aka kira da Abdurrahman ya fara yunƙurin yin magana sai ya kasa kawai sai ya fashe da matsanancin kuka. Wannan lamarin ba ƙaramin ɗaga hankalin Sarki Aminullah ya yi ba, jim ya yi kawai sai ya sallami kowa tare da sanar da su zai tsayar da lokacin da za a yi zaman gaggawa a cikin fada. "Ka fara yin galaba a kansu tun da mun fara taɓa matarsa da Ɗan da yake rawar kai an haifa masa. Amma mene ne ya sa dalilin da ya sa kaƙi haƙura da lamarin yaron nan Saif? Ina ce a kan yarinyar cen ne kuma ba shi zai aureta ba. Me ya sa ba za ka uzzurawa mai neman aurenta ba, tun da yanzu auren ma kwanaki ya rage." Farin Tsohon ya watso masa tarin tambayayi kala-kala. Salman ya saki dariyar ƙeta yace, "Ƙiyayyarasa a jinin jikina take ban taɓa jin ɗigon sonsa a zuciyata ba, tun yana nakasasshe har ya san wanene shi. Alwashi na ɗaukarwa kaina sai na ga bayansa tun da ka cw mini idan baan hau Karagar mulki ba zai iya ɗarewa. Wanda zai aure ta akwai dalilin da ya baya gabana domin duk yadda ya kai ƙunarsa na taɓa zuba masa wani haki a ruwan wanka ya bi jikinsa tun wancen tafiyar da ya yi da ita. Koda ya aureta zai gaji don kansa ya sake ta ko ka taɓa jin an yi zaman aure babu mu'amala? (Wannan ne dalilin da ya sa idan Maleek ya taɓa Maryo jini yake kwanciya a jikinta har jikinsu ya dinga raɗaɗi) "Lallai Bahaushe ya y gaskiya da yace gado ba karanbani ba. Barewa ta taɓa gudu ɗan da ya yi rarrafe ba. Tabbas ko yanzu mutuwa taa riskine zan yi alfahari da baya na na aiwatar da abin da fara." Dattijon ya yi magana cikin nishaɗi. Salman bai fahimci maganar tsohon ba ya ci gana da cewa, "Na san zamansu ba zai je ko ina ba shi ya sa ban tashi hankali na a kan haka ba.Na makantar da ita na kuma kurumtar da ita ne sakamakon ta fara ƙoƙarin yanke wata shawara, shi ya sa na dakusar da ita har zuwa lokacin da waccen kwantaccen ya a gano shiri na. Ka san dalilin da ya sa bata iya taɓukawa kanta komai ba?" "Saboda sharaɗi ne na gindaya mata na halakarwar da zan yi wa Al'ummar ƙasar Adamawa, zan yi musu kisa mai tsananin azaba domin saboda da farko shiga na yi jikin Dokin da yake mara mata baya, na dinga take mutane suna faɗuwa suna mutuwa sai da ta amince mini na fice daga jikinsa. Buƙata ta a nan gaba ta wancan tsohon ne dole ya mutu ya bani Sarautar saboda na gaji da jiran ya mutu don haka zan ƙarasashi." Ya yi maganar cikin ƙunan rai. "Ba za ka iya kashe shi ba muddin baka kawar da ɗaya daga cikinsu ba domin dukkansu suna ba shi kariya don kowannensu a cikinsu Mahaifinsa ne. Amma ka san wacece za ta taimaka maka dangane da cimma burinka a kanta." Da sauri Salman ya fara girgiza kai, Wani farin allon ƙarfe tsohon ya watsawa ruwa nan take hoton wata matashiyar mace ya fito raɗau a kan allon. Da mamaki Salman yace, "Ta yaya mai zai sa sai ita bayan ka san ba za ta taɓa bani goyon baya ba." Tsohon ya saki murmushi yace, "Ban san yadda aka yi jinin Maryama ya fi tasiri a jikinka ba, tabbas garaje da gaggawarku bata da maraba da juna. Sai tin kunnensa ya samu ya raɗa masa magana da sauri Salman ya ɗago yana zaro ido yace, "Tabbas a cikin gawurtattun bokaye kai na daban ne." Kyaklyawan tsohon mai mummunar zuciya ya saki murmushi yace, "Ni kaina ina tsoron kaina don ina gudun kar wata rama na yi wa kaina illa" "A ina zan ganta?" Tambayar da Salman ya jefa masa. "Tana gabda shiga Masarautarku, amma ina mai jan hankalinka karka bari ta shiga domin shigarta Masarautarku daidai yake da kwaɓewar al'amuranka." Kamar zai yi kuka Salman yace, "Ta zan san lokacin da za ta shigo?" "Maryo ce za ta baka tabbacin haka! Wannan aikin ya rage maka amma za ta samu wani sauyi daga yanayi har zuwa magana ta haka za ka gane. Idan kuma an riga da an yi aurenta da Maleek ka je bakin ƙofar fadarku ka ɗaga kanka sama za ka ga bishiyar hagu da ke bakin ƙofar ta bushe. Wannan shi zai baka tabbacin tana gabda shigowa wato tana nan harabar masarautarku. Duk ranar da ta shigo za a wayi gari da samun hargitsi da hayaniya tsakanin Inna Habi da Maryama. Don haka sai ka saka idanu ta shi ka bani wuri." Tsohon ya faɗa yana tattara kayan tsafinsa. Maryo na fita ta bata tsaya ko ina ba sai sashan Salman in da yake zauna da Matarsa Safiya. Tafiya take kamar za ta tashi sama duk inda ta wuce bayi da Dogarai sai sun bita da kallo, har ta ƙarasa soron gidan. Tsayawa ta yi a daidai kusurwar bango ta runtse idonta tana cewar, "Bimanatu ku fito gabaɗaya." Tana gama faɗan haka sai ga rukunin jerin 'yan mata sun suna fitowa sahu-sahu suka fito rairas babu adadi. Da hannu ta yi musu nuni da ɗakin Safiyya sai ga shi nan take sun fara tikiɗa zuwa siffar Safiyya kowaccen su na ɗauke da tsohon ciki. Tana gaba suna biye da ita har suka ƙarasa ƙofar ɗakin Safiyya. Da wata irin murya Maryo ta ɗaga labulen ta ce, "Safiyya!" Safiya da ke zaune a kan gado da sauri ta amsa don kiran ba ƙaramin razanata ya yi ba. Ta ɗago kai gabanta ya yi mummunan faɗuwa ganin Mata a tsaye masu fasalinta sak, wani irin ihu ta kwalla nan take ta yanke jiki ta faɗi sumammiya. Ɗaya daga ciki Maryo ta umarta da ta ɗauke ta nan take ta ɗaukota kamar jarirya sai kuma ta ɓace da ita daga wurin. Nuna musu ɗakin Safiyya ta yi suka fara shiga ɗaya bayan ɗaya sannan suka haɗe wuri ɗaya ta nuna musu wurin da Safiyya take a zaune suka zauna sannan ta ɗauki tafin hannunta ta ɗora akan fuskarta sai ta kalle ta kyau ta ce, "Bimanatu bana son a samu matsala kowacce iri ce saboda tafiyar mai nisa ce don haka ki kiyaye." Cikin girmamawa ta russunar da kai ta ce, "An gama ya shugabata" Daga haka Maryo ta fito daga gidan kamar wacce ake ƙarawa iska haka take tafe da sauri-sauri. Daulatul Jinnul Shaha... Zulik na barin Lambun Sarki Kasumul Birmi bai zar ce ko ina ba sai sashen Mahaifinsa, yana zuwa ya zauna yana huci kamar kumurcin maciji. Mahaifinsa Bulbutu ya dube shi yace, "Mai nema baya gaggawa domin shi jinkiri ga mai manufofi tamkar taki ne da ake zubawa tsirrai." Zulik ya kalli Mahaifinsa yace, "Tuni na isar da saƙona yanzu naka aikin ya rage. Da farko na ɗauka soyayyar ƙarya nake mata sai daha baya na tabbatar. Dole ka san abin yo domin na gama haukacewa a kan ƙaunarta komai zai iya faruwa." Hankalin Mahaifinsa ba ƙaramin tashi ya yi ba domin ya tuna tunatarwa da Bokansa yake yi masa da yake ce masa, muddin ya fara kuskura ya yi masa tsarki da ruwan maganinsa to zai matukar haukacewa a kanta, ta yadda a koyaushe zai rinƙa ƙoƙarin haike mata. Idan har kuwa a ka nemi hanashi ita to babu makawa tura zata kai bango har sai ya haike mata. Shi kuwa ruwan maganin da ya yi masa tsarki da shi da shi ne zai yi wanka duk ranar da Sarki Kisumul Birmi ya mutu. Kallon Ɗansa ya yi kai tsaye yace, "Me kake so a yi." Zulik ya sake tamke fuska cikin rashin ladabi yace, "Aurenta nake son yi a kwana kusa domin idan aka ja lokaci ba zan iya riƙe kaina ba." "Ka same ta ka gama. Ka ba ni nan da mako biyu na yi maka alƙawarin idan baka aureta ba ka datse kaina." Da sauri ya kalli Mahaifinsa sai ya tafi da gudu ya rungumeshi yace, "Na ji daɗi ƙwarai da wannan kalaman naka. Amma ka sani muddin wannan lokacin ya wuce baka aura mini ita ba to tabbas zan datse kanka kamar yadda ka buƙata." Bulbutu kansa tsaye yace, "Zan ta ya ka datse kaina da hannuna muddin ban aura maka ita ba." Rayzuta fusata ta yi bayan fitar Zulik ta fisge hannunta tana cewa, "Ka ga irin abin da nake gudu ko? Ni na san dalilin da ya sa sam bana buƙatar ya kunsanto kusa da ni." Gyara tsayuwa ya yi yana kwaikwaiyar muryarta yace, "Ki manta da shi kin san ya fiye shirme." "Shirme? Kana tunanin Zulik ya yi haka da wasa ne? Ina tunanin idan baka zama mutum na ɗaya wanda zai bayar fa labarinsa ba, ba za ka zama na biyi ba." Riƙo hannunta ya yi yace, "Na ji amma a bar maganar haka." Bin bayansa ta yi cikin shagwaɓa ta ce, "Kai dai baka son laifin Abokinka." suka fice cikin so da ƙaunar juna. Sai da ya raka ta har sashenta sannan ya wuce sashen Mahaifansa. Tun daga wannan ranar wata irin soyayya mai ƙarfi ta shiga tsakaninsu, yanda suke zama su yi ta hira a bin zai birge ka saboda soyayya suke mai tsafta. Tun ranar da Rurzaan ya riƙe mata hannu bai ƙara kuskuren haka ba. Sai dai duk wannan abin da yake faruwa Mahaifinta Sarki KIsumul Birmi bai san wainar da suke toyawa ba. Shi dai abin da ya sani Furzaan na zuwa biyawa Rayzuta karatun ƙur'ani bayan haka ya san 'Yarsa ƙawar Furzaan ce kuma sun yo matuƙar shaƙuwa. (Kun san suma kamar mutane fa suke yadda muke bautawa Allah suma haka suke yi.) Maryo na tafe suka haɗu da Saif, wuce za ta yi da sauri ya matsa sha gabanta yana haɗa hannuwa biyu alamar godiya yace, "Na gode da taimako Abu da Jaririnta." "Me ya sa za ka yi mini godiya bayan tun tuni na gaya maka wannan faɗan nawa ne? Kada ka manta Abu 'yar uwata ce abin da ta haifa Ɗana ne don haka ba buƙatar a godewa Uwa don ta kula da Ɗanta." Maryo ta ƙarasa maganar tana yin gaba abinta. Shiru ya yi kamar ruwa ya shanye shi, ya ji daɗin kalamanta don ko babu komai ta danganta Ɗansa da cewar Ɗanta. Cikin daji-daji da ke cikin Masarautar ta fara kutsawa bata tsaya ko ina ba sai bakin wata ƙatuwar bishiyar tsamiya. Zama ta yi ta sunkuyar da kanta ƙasa a hankali ta sa hannu ta fara ƙwaƙwular ƙasa sannu a hankali waɗansu irin manyan ƙudan zuma sula fara fitowa suna nufar hanyar Masarautar. Haka suka rinƙa fitowa babu adadi suna tafiya tun a hanya suka fara cin karo da Waziri. (Idan kun tuna akwai wani mutum mai zuwa wurin Fulani Maryama da daddare, wanda take kira da Ɓoyayyar fuska😷 ) Duk ƙudan zuma ɗaya idan ya ciji Waziri wurin fashewa yake jini ya fara tsiyaya. Kafin wani lokaci tuni Zumar da fara karaɗe cikin masarautar, ku san dul wanda ta faɗawa sai dai ya hau kururuwa yana kartar jiki jini ya yi ta fita daga wurin. Maryo na gama haƙar ƙasar wurin ta ɗauko dutse ta ɗora a kan ramin ta ɗebi ƙasar ta mayar ta rufe ramin sannan ta kalli sauran ƙudan zuman ta ce, "Idan ba wannan ramin ba ban lamimce muku mutuwa a kowanne wuri ba." Tana gama maganar ta kishingiɗa nan take bacci ya yi awon gaba da ita. *Maryo kam an yi taƙadiriyar muguwa*😂🤣 _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [15/01, 19:21] Ameera Adam🌚: 63... Waiwaye... Lokacin da Mahaifin Zulik ya samu Sarki Kasumul Birmi da maganar auren Rayzuta da Ɗansa Zulik ba ƙaramin mamaki Sarki ya yi ba tare da fadawansa. Amma Sarki bai nunawa Bulbutu ba sai yace zai tuntuɓi Rayzuta domin ya ji ta bakinta. Bayan Fada ta tashi Sarki ya samu Rayzuta ya gaya mata, ranta ba ƙaramin ɓaci ya yi ba a nan take ta sanar masa da bata son Zulik, kuma a wannan lokacin ta gaya masa wane ne zaɓinta. Sarki ba ƙaramin daɗi ya ji ba domin hankali da nutsuwar Furzaan ba ƙarmin burgeshi yake ba. Daɗin-daɗawa zumincinsa da Mahaifin Furzaan zai ƙara ƙarfi. Washegari Sarki Kisumul Birmi ya aika aka kira masa Bulbutu bayan ya gaida shi Sarki ya sanar masa da saƙon 'Yarsa. Bulbutu bai wani damu domin dama ya san da haka za ta faru saboda ko makaho ya shafa zamantakewar Rayzuta da Zulik ya san babu kyakkyawar alaƙa bare kuma soyayya ta shiga a tsakaninsa. Ya faɗawa Sarki Kisumul Birmi ne saboda wannan ya zame masa hujjar da zai kafa idan ya je yi wa Maƙiyan Sarki Kisumul Birmi mubaya'a. Daga cikin fadar bai zame ko'ina ba sai fadar Sarki Buzaag, Duk Fadar Sarki Kisumul Birmi kowa ya san irin tsananin ƙiyayyar da ke tsakanin Sarki Buzaag da Sarki Kisumul Birmi. Daɗaɗɗiyar ƙiyayya ce ta sahon shekaru, Sarki Buzaag mutum ne azzalumi mai tsananin son kansa tare da burin mallakar yankuna mabambamta. Wannan buri na shi, ya sa ya rinƙa farmakar ƙananan dauloli babu yanda suka iya haka suka rinƙa yi masa mubaya'a. A wannan lokacin ya kaiwa Sarki Ƙisumul birmi ta yi amma ƙarfin mulki ta tsananin jarumtar Masarautar da Jaruman cikinta ya sa suka gagari Sarki Buzaag. Wannan ya sa babu wata kyakkyawar alaƙa a tsakaninsu, kowanne ɓangare yana ƙullace da juna. Bulbuta na zuwa a ka sanarawa da Sarki Buzaag zuwansa, da farko wasu daga cikin Dakarun Sarki Buzaag sun so tasar masa sai wani Badakare ya dakatar da shi domin ya tabbatar ba zai yi zuwan banza ba. Bulbutu na zuwa ya sanarwa da Sarki Buzaag dalilin zuwansa da Mubaya'ar da zai yi masa domin ya gama tabbatarwa zai raba Sarki Kusumul Birmi da mulki ta ƙarfin tsiya, dabararsa ɗaya idan ya yi wannan badaƙalar zai raba shi da duk wani abun da yake taƙama da shi. Ya san zai yi wuya Mutanen Masarautarsu su bashi haɗin kai. Idan ya zo ya bawa Sarki Buzaag haɗin kai ya bashi sirrikan masarautar dole za su taimaka masa ya farmaki waccen masarautar ya murɗe mulkin ta ƙarfin tsiya. Ko banza ya san zai zama ɗaya daga Sarkin ƙanana Masarautu, tun da ya san ko suma yake Sarki Buzaag ba zai taɓa barinsa a babban Sarki kamar yanda Sarki Kisumul Birmi yake a kan karagar mulkinsa ba. Lokacin da Sarki ya sanarwa da Mahaifin Furzaan ba ƙaramin farinciki Aminan biyu suka yi ba sakamakon shima Furzaan ya sanarwa da Mahaifinsa abin da yake faruwa a tsakaninsa da Rayzuta. Babu ɓata lokaci aka tsayar da lokacin biki wata guda mai zuwa. Farinciki wurin Rayzuta da Furzaan baya musaltuwa soyayya suke zubawa cike da farinciki, kafin wani lokaci tuni maganar sa ranar Furzaan da Rayzuta ta karaɗe ko'ina a cikin Masarautarsu. "Masoyina lafiya ka kirani a tsohon daren nan?" Jakadiyar Sarki Kisumul Birmi mai suna Bizmatu ta faɗa tana kallon Bulbutu. Bizmatu ta hannun daman Bulbutu ce sakamakon suna soyayya a ɓoye ya mayar da ita tamkar matarsa kuma ita take bashi sirrikan Sarki. Ajiyar zuciya ya sauke yace, "Na kiraki ne domin ki bani haɗin kai akan Uban gidanki Sarki Kisumul Birmi. Ina son ki buɗe kunne ki saurareni idan har kika bani haɗin kai ni kuma na yi miki alƙawarin aurenki a lokacin da nake a matsayin Sarkin wannan Daular." Nan take Bulbutu ya sanar da ita halin da yake ciki da manufarsa dangane da Sarki Kisumul birmi. Murmushi ta yi ta ce, "Wannan ba abu ne mai wahala a wurina ba duk abin da kake buƙata ka min magana zan baka haɗin kai ɗari bisa ɗari." Daɗin haka ya sa ya rungomata nan suka ci gaba da masha'arsu. (Jakadiyar Sarki Bizamatu ita ce Fulani Maryama a wancan ƙarnin na su Rayzuta. Sarki Kisumul Birmi shi ne Sarki Aminullah a wannan ƙarnin na su Maryo. Balbutu shi ne Tsohon da Salman yake zuwan wurinsa a harkar tsafi da bokanci. Inna Habi ita ce Matar Baban Rayzuta wacce aka mutu aka barwa amanarta. Fulani Zaliha ita ce Matar Bulbutu Mahaifin Zulik, Ina fatan bakwa ruɗewa) Kafin wani lokaci tuni Ƙudan zuman nan ya addabi mutanen da ke cikin Masarautar, Lokacin da labarin zumar ya je kunnen Sarki Aminullah ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba, domin lokacin da ya leƙa da tagar fadarsa (Window) haka ya ya ga jama'a na faɗuwa jikinsu duk jinane. Waɗanda abin bai same su ba haka suka rinƙa rufe kawunansu a ɗaki. Saboda ko ɗaya idan ya yayimeka yana iya hallaka ka. Sarki Aminullah ne bada umarni da a kira masa Baushe, lokacin da Baushe ya zo shi kansa da ƙyar ya sha domin sai da jikinsa ya yi faca-faca da jini. Sarki da damuwa ɗauke a fuskarsa yace, "Baushe mun wayi gari da wata irin annoba da bansan wacce iri bace ta ƙudan zuma." Baushe ya nufasa sannan yace, "Allah ya taimake ka wanan zumar tun da Uwata ta haifeni ban taɓa cin karo da irinta ba amma ga tuarare a turara a gani idan ya magance ta za mu san wacce iri ce. Idan kuma bai magance ta ba sai mu san abin yi." Nan take Sarki Aminullah ya bada Umarni da a turara turaren a harabar Masararuta. Wuta aka hura da ita ce manya aka rinƙa zazzaga garin tuararen da Baushe ya ba yar amma wani babban tashin hankali hayaƙin na fara fita waɗansu irin Manyan ƙudan zuma suka fara fitowa daga cikin wutar suna yin kan Bayin da suka hura wutar. Bayi biyar ne a tsaye zumar na cizonsu jini ya fara fita daga jikinsu a wahale haka suka rinƙa faɗuwa nan take mutum huɗu suka rasa rayukansu. Sai guda ɗaya ce ta sha da ranta ita ma da rarrafe ta ƙarasa fada sai dai tun kafin ta je jikinta ya fara farfashewa yana ta tsartar da jini. Salman na ganin kudan zuman ya saki murmushi don ya san abin da ya aikatawa Abu da Jaririnta ne ya sa Maryo ta fusata, har ta aikata musu haka. "Wato ya tabbata Tarihi zai maimata kansa kenan." Ya furta yana gyara tsayuwarsa. Ayarin ƙudan zumar ne suka tunkare shi ya zuba musu ido don a zatonsa babu wani abu da za su iya aiwatar masa, sai dai ga mamakinsa ya ga sun fara cizonsa ta ko ina, kuma duk inda suka ciza sai dai jini ya yi tsartuwa ya fara zuba. Wannan ba ƙaramin ɗaga masa hankali ya yi ba domin ya ɗauka zai iya bawa kansa kariya sai ga shi wankin hula na neman kaishi dare. Abu sannu-sannu tun yana tsaye har ƙudan zuman ya tasarma hallaka shi sai da ya yi da gaske sannan ya samu ya gudu can sashensa. Baushe hankalinsa ya tashi matuƙa jakarsa ya kwance ya fara siddabarunsa na kiran aljanun da suke taimaka masa a cikin daji. Sai da suka bashi wasu magugunan sannan ya haɗa dana wurinsa yace a ƙara turarawa. Cikin damuwa Sarkin Aminullah yace, "Baushe ina fatan ba za a sake samun matsala ba?" Baushe ya rufe jakarsa yana cewa, "Allah ya taimakeka haka muke saka rai amma sai an gwada a kansan na ƙwarai." Lokacin da Dogarai suka fita don su haɗa wuta ba ƙaramin tsorata suka yi da ganin mutane baja-baja a yaryashe cikin jini. A tsorace suka fara zuba maganin domin suma suna yi zumar tana cizonsu sun daure ne kawai domin cika umarnin Sarki Aminullah. Fulani Maryama tana jin labarin saukar Annobar ta janyo ƙofarta ta datse, haka daga wurin Inna Habi domin ba ta san abin da yake faruwa da Abu da kuma ficewar Maryo ba. Abin da ta ayyanawa ranta ta san tun da Maryo ta tafi sashen Fulani Zaliha ba ta wuce wani wurin ba da har wannan kuɗan zumar za ta sauka a kanta. Fulani Zaliha kuka ta fasa lokacin da Unguwar zoma ta yi wa Abu duk abin da ya dace amma ko motso bata yi, suna cikin wannan yanayin annomar kuɗan zuma ta saukar musu wannan dalilin ne ya sa ba su yi wani yanƙurin fita ba suka zubawa sarautar Allah ido. Salman na shiga gida Kuɗan zumar suka sake yanyame shi wannan karon har faɗuwa ya yi suka rufu a kansa ta ko ina suke kai masa cizo a fusace. Tun yana iya ɗaga hannu ya kore su har ta kai ga ko ɗan yantsansa baya iya ɗagawa. Wani baƙin hayaƙinne ya turniƙe wurin bai jima ba ya ɓace tare da Saif sai ga wurin fayau sai ƙudan zuman sun farfaɗi suna motsi da ƙyar. Baushe da kansa ya ƙarasa gaban wutar yana ƙara maganin da ya bayar a turara, yana zubawa a hankali ƙudan zumar suka fara taurawa a gabansa wuri gudan. Wannan lamarin ba ƙaramin mamaki ya bawa mutane wurin ba. Sai da suka gama taruwa tsaf sannan ya umarce su da su koma wurin da suka fito. A hankali suka fara nufar hanyar wurin da Maryo take, Baushe ya fara binsu da sauri 'yan bani na iya suka rufa masa baya. Suna zuwa suka tsaya akan Maryo da ke kwance tana sharar bacci hankali kwance. Baushe tsaye ya yi yana kallon abin mamaki domin ko tantama baya yi dama ya san ba zumar lafiya bace. Bayi da Dogaran da ke biye da shi mamaki ne ya kashe su a tsaye, babu irin tashin da bai yi wa Maryo ba amma ko gezau bata motsa ba. Yana shirin taɓa ta ya ji wata irin guɗa a tsakar kansa har sai da kansa ya sara, wani Dogari ya umarta da ya ɗaga ta yanda shima ya ji haka Dogarin ya ji. Wani garin magani ya ɗauko ya shafe hannu da jikinsa sannan ya sunkuya ya saɓa Maryo a kafaɗa yana gaba ƙudan zuma na biye a saitin kan Maryo suka kuka. _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [18/01, 19:08] Ameera Adam🌚: 64... Tuna baya.... Bulbutu da ƙyar ya sha kan Zulik akan ya yi haƙuri ya ƙara masa lokaci, don cewa ya yi mai rabashi da datse numfashin Mahaifinsa sai Allah. Sai da ya sanar masa irin shirin da yake yi musu sannan ya haƙura. Domin ya lura da irin ci gaban da Mahaifinsa yake son kawo musu a rayuwarsu ta gaba. Haka ya ci gaba da warkajimsa cikin farinciki zuciyarsa ƙal babu damuwa. Duk wata ƙofar sirrin gidan sarautar Bulbutu ya buɗewa Sarki Buzaag ya samu ƙwarin gwiwa ne a wurin Jakadiya Bizamatu, domin duk wasu sirrikan Sarki Kisumul Birmi na fili dana ɓoye gabaɗaya ta sansu don haka ta rinƙa kwance masa su falle-falle a gaban Bulbutu shi kuma yana kaiwa Sarki Buzaag bayani a sirrin ce. Kwana uku da saka ranar Rayzuta, Bulbutu ne zaune da Jakadiya suna tattaunawa bayan sun gama suka faɗa masha'arsu. Matar Bulbutu na kawo kai ɗakin ta ci karo da abin da suke aikata, don haka ta fashe da kuka tana rufe Jakadiya da duka cikin takaici. Kallon tsana ta wurgawa mijinta tana cewa, "Duk mugun halinka da kake aikatawa na tsahon shekaru na yi maka shiru na zura maka ido, ina sane da ka haɗa kai da maƙiyan Sarki Kisumu amma hakan bai yi maka ba har sai ka sa Jakadiya ta ci amanarsa. Kai wanne irin azzalumi ne? Yanzu ka yi mini adalci da ka kawo mace har ɗakina kuke lalatarku?" Bulbutu ya bushe da wata mahaukaciyar dariya sannan ya murtuke fuska yana cewa, "Tabbas zan rage miki hanya domin da alama wuyanki ya fara kauri idan na zura miki ido za ki iya sanya kwaɓata ta yi ruwa." Yana gama maganar ya janyota ya toshe mata hanci tun tana kakari harta faɗi ta matu a wurin. Kallon Bizamatu yace, "Maza ki fice nima fita zan yi don kar a gano lagona." Ku san tare suka fice sai bayan wani lokaci Bulbutu ya koma ya fasa kuka sannan ya fito yana kuturuwar neman taimako. Kafin wani lokaci tuni mutuwar Matar Baban Zulik ta ratsa cikin masarautar, ba ƙaramin jimami suka yi ba kasancewar kowa ya yi mata shaidar mutuniyar arziƙi. Ranar da ta cika kwana uku da mutuwa ranar ne Sarauniya Rayzua ta kai gaisuwarta don fir cewa ta yi ba za ta ba, sai da Furzaan ya matsa mata sannan suka tafi tare da matar Babanta. Haka kawai ta ji gabanta ya fara faɗuwa amma ta dake ta ci gaba da harkar gabanta. Bayan sun yi gaisuwar suna ƙofar fitowa wasu baƙaƙen Dakaru suka nuna mata mazaunin keken doki. Kallosu ta yi da rashin fahimta ta ce, "Ku su waye?" "Ba dole sai kin su waye ba, umarnine aka ba mu na tafiya da ke ta lallami ko ta tsiya." Rayzuta tuni ta fara kiciniyar ƙwacewa da sauri Dakarun suka fara ƙoƙarin kamata, Matar Mahaifinta na ganin haka ta fasa kuka ta rungumeta tana ture hannuwansu. Dogarawan ƙofar Sarki Kisumul Birmi tuni aka haɗa baki da su a gabansu aka tafi ta Rayzuta da matar Babanta babu wani yunƙurin dakatarwa da suka yi. Farratu na rungume da Rayzuta domin ta san waɗannan mutanen ba alheri ne ya kaisu ba, da har sukai ƙoƙarin guduwa da Rayzuta. Lokacin da aka kaisu a wani ɗaki aka zuba su me duhun gaske, gabaɗaya a tsorace suke don ba su taɓa fuskantar haka a rayuwarsu ba. Bayan wani lokaci Sarki Buzaag ya sa aka fito da su, Rayzuta na zuwa ta hango Bulbutu a gefen Sarki Buzaag. Da sauri ta ƙarasa wurinsa tana fashewa da kuka, wani shu'umim murmushi ya yi ya fara shafa bayanta. Tana nan tsaye Zulik ya shigo fuskarsa ɗauke da murmushi yace, "Baba tun da nake baka taɓa faranta mini rai ba domin ka sa an kawo mini farincikina." Da sauri Rayzuta ta matsa tana nuna shi da hannu ta ce, "Dama da sa hannunsa aka kawo mu wurin nan?" Bulbutu ya bushe da dariya yace, "Da kina tsammanin zan zura ido a aurawa wani ke ba Ɗana ba?" Da sauri Farratu ta ƙarasa gabansa ta nuna shi da yatsa ta ce, "Tabbas ka bani mamaki kai macuci ne azaalumi maci amana..." Tun bata rife baki ba Zulik ya kifeta da mari yana cewa, "Shashashar banza uban nawa kike..." Rayzuta ce ta katsa shi ta wanke shi da zafafan mari har guda biyu sannan ta riƙo hannun Farratu tana rungumeta. Sarki Buzaag ne ya yi gyaran murya sannan yace, "Bulbutu mun cika maka naka alƙwarin saura namu." Bulbutu ya yi jinjina sannan yace, "A shirye nake ko yanzu zamu iya farmakar Sarki Kisumul Birmi." Farratu na jin haka ta yi kukan kura ta cukumi wuyan Bulbutu tana cewa, "Allah ya wadaranka dama kai ba masoyinmu bane babban maƙiyinmu ne bamu sani ba?" Bulbutu ya saki dariyar ƙeta ya nuna bakin ƙofa yace, "Ku ƙaraso daga ciki su kashe ƙwarƙwarar idonsu." Yana rufe baki Juddul Bahi (Shi ne wanda na ce muku mahaifinsa ne mai asalin sarautar Daulatul Jinnul Sahara.) da Jakadiya suka shigo. Jikin Rayzuta da Farratu har rawa yake saboda tashin hankali tabbas a wannan lokacin ne da suka tabbatar da mugu bai da kama. Suna shirin magana Sarki Buzaag ya bada umarnin tura Gwaraza su tafi Masarautar su Rayzuta domin farmakarsu kuma tun da dama Bulbutu duk ya gama siye su a sirrince. Zulik ne ya ƙarasa wurin Rayzuta yana lasar baki ya kai hannu zai taɓa ta, da sauri ta bige hannunsa tana ja da baya. Sarki Buzaag ne ya bushe da dariya yace, "Ƴan mata me kike yi haka ne? Maza ku kai masa amaryarsa idan kuma waccan tsohuwar ta hana ku datse numfashinta." Rayzuta na jin haka ta ƙanƙame Farratu ita ma ta riƙe ta gam suka saka kuka. Duk yadda Dakarun suka yi ƙoƙarin raba su abin ya gagara. Ɗaya daga cikin Dogarawan ne ya ɗauki wani ƙarfe ya bugawa Farratu a tsakiyar ka nan take jini ya fara tsartuwa ta yanke jiki ta faɗi. Kafin ta kai ga mutuwa ta kalli Rayzuta ta ce, "Da a kashe ki bayan an ci moriyar gangar gara a kashe ki kima mai kare martabarki ta 'Ya mace. Ba za su taɓa barinki ba koda kuwa kin ba shi kanki domin ba son ki yake ba gangar jikinki yake ƙauna." Tana gama maganar idanunta suka kafe nan take rai ya yi halinsa. Rayzuta durƙushewa ta yi a kan gawarta ta wani irin gursheƙen kuka, da ƙarfin tsiya Zulik ya fisgeta yana janta har cikin wani ƙayataccen ɗaki. Kamar gawa haka aka kwantar da Maryo a fadar Sarki Aminullah, hakazalika waɗannan ƙudan zumar ba su daina kuka suna tsaye a kanta ba. Wani Bafade ne ya zuba mata ido ya ɗago da damuwa ɗauke a fuskarsa yace, "Baushe shi wannan ƙudan babu yanda za a yi a koresu daga wurin nan?" Baushe ya yi masa wani kallo sannan yace, "Samun sararin kuturu gaɗa a cikin rama. Ina wa laifin da suka daina addabar mutane? Ai ka bari na yi muku jawabi yanda ya kamata." Sarki Aminullah haka kawai ya ji ya damu da halin da Maryo take ciki, bai san me ya sa yarinyar take da babban matsayi a zuciyarsa ba. Ya san shi mutum mai tausayi ne amma yana mamakin yanda yake jin yarinyar tamkar 'yar cikinsa. Kallon Bushe ya yi fuska ɗauke da damuwa yace, "Baushe bamu bayanin abin da yake faruwa da yarinyar nan!" Kafin Baushe ya yi magana Fadawa suka amsa da, "Baushe Mai martaba na buƙatar masaniyar lalurarta." Baushe ya russuna yace, "Allah ya taimakeka ba komai yake damunta ba face fusatar shuɗaɗɗun ruyukan wasu jinsi. Ba zan iya cewa ga jinsin ba amma abin da na sani tana cikin tsananin baƙin ciki domin wannan ƙudan zuman na taɓa cin karo da su shekara Ashirin baya a dajin Ɓaguru dake kudancin ƙasar nan. Aljanin da yake bani laƙani ya sanar da ni tarihinsu domin asalin wannan ƙudan da kuke gani ba kuɗan zuma bane, yana daga cikin ƙwarin wani jinsi amma wani binciki ya nuna a jimsin Jinnu ne wani kuma yace a jinsin ɓoyayyun dabbobi ne. Amma mafi rinjaye sun fi danganta shi da jinsin Aljanu." Sarki Aminullah ya yi tsai da tunani yana auna maganganun Baushe a mizani sannan yace, "Ina buƙatar sanin me ye alaƙarta da waɗannan ƙwari kuma a sallame su daga wurin nan." "Daga ni har sauran masu magungunan duniya babu wanda ya isa ya kore su kuma babu wanda zai ya tashin yarinyar nan daga bacci. Taimako ɗaya ne da nake da iko kuma na yi Ranka shi daɗe. Na haɗa kawunan Ƙwarin nan wuri ɗaya ga su sun taru a kanta suna jiran umarninta. Idan har ba ita ta basu umarnin ba za su taɓe a haka har sai ranar da ta tashi daga bacci, baccin da babu mai iya tashinta sai lokacin da ta farka ko kuma wani mai irin tsarim rayuwarta. Nima na samu nasarar ɗaukanta ne sakamakom Maganin dana shafawa jikina ba don haka ba tuni sun riga sun hallaka ni." "Haka zan tura ido suna hallaka mini talakawana? Ka san a ƙalla sama da mutum hamsin sun jikkata. An bani tabbacin mutuwar mutane ashirin da takwas har yanzu akwai waɗanda ba su san waye a kansu ba. Labari ya ishe mini ƙudajen nan sun fita har wajen masarauta suna ci gaba da farmakar Talakawa mutane sai faɗuwa suke." Bazan laminta ba!" Sarki Aminullah ya faɗa a kausashe da Babbar murya har sai da fadar ta amsa. Fadawan wurin da sauri suka ɗago suna kallonsa domin tun da suke da shi haka bata taɓa faruwa a fada ba. Wannan ne ya ba su tabbacin cewar Sarki Aminullah ya fusata da fushi mai tsanani, domin fuskarsa har haɗewa ta yi tai jawur. Ba su gama tsinkewa da mamaki ba suka riske shi ya miƙe tsaye ya fara takawa zuwa wurin da Maryo ke kwance, ba don numfashin da take yi ba za ka rantse da Allah gawa ce a wurin. Tsugunnawa ya yi a gabanta nan take Fadawa suka russunar da kansu ƙasa domin ransu gabaɗaya bai so haka ba ace Sarkin Sarakai, Sarkin da a ƙasarsa ta Najeriya (Nigeria) na alfahari da Masarauta kamar ta Kano mai cike da izzar mulki. Shugabansu da ke gefe ne ya ɗago da kai yace, "Allah ya ja ranka Ubangiji ya jiƙan Mai babban ɗaki, ina ganin a ƙara duba lamarin da maganin da za a yi mata. Muna mai roƙon alfarma ga adalin Sarki, Sarkin mai tausayin Talakawa da ya jinkirta zartar da hukun da zai gudanar yanzu.Tuba nake ranka shi daɗe idan magana ta ta yi tsauri." Sarki Aminullah ya ɗago ya kalleshi da manyan idanuwansa masu sanyan mutum shiga nutsuwar da bai yi niyya ba yace, "Haƙƙinmu mu kula da rayuka da dukiyar al'ummarmu. Ba zan lamunci ganin yanda jinin bayin Allah yake zuba babu ƙaƙƙautawa ba. Ko a tarihin iyaye da kakanni haka bata taɓa faruwa ba, don haka zan tashe ta inma ta tashi inma na kori waɗannan azzaluman da kaina." Yana gama magana ya saka hannunsa a kan ƙafarta yana ambatar sunanta. Sai da ya yi mata kira uku sannan jikinta ya fara wata irin karkarawa. Kamar wanda aka jonawa wutar lantarki haka ya ji hannunsa ya yi wani zum! Sai kuma ƙudan zumar suka fara yanyame shi suna ƙoƙarin kai masa cizo. A hargitsa ta miƙe zaune tana buga musu wata irin gigitacciyar tsawa tana cewa, "Ku dakata!" Kamar waɗanda aka ƙamar haka ƙudan zumar suka tsaya ƙyam kowanne a inda yake a nan ya tsaya. Tafin hannunta ta buɗe lokaci ɗaya suka fara dawowa kai suna hawa kan hannunta, sai da suka gama ta ruwa tsaf a hannunta ta ce, "Na sallame ku." Da gudu suka fice buuuu! Daga cikin Fadar, hawaye ne ya fara zuba daga idanunta ta kalli Sarki Aminulla da ke tsaye gabanta ta ce, "Daraja tana ga mai babban Matsayi da girma a gare domin kai ɗin ma daban ne. Me ya sa za ka yi mini haka? Sam ban ji daɗin haka ba domin ya kai ni maƙura." Sarki Aminullah ya taka a hankali ya koma mazauninsa Fadawa suka ruɗe da cewar, "Takawarka lafiya Ɗan toron giwa! Gaba salamun baya Salamun Sikari ba kai farin banza, bangon zuma mai nason alheri kowa ya raɓe ka sai lasa. Turare kake sha ƙamshi ƙamshinka ya yi naso har ɗakunan Talakawa." Wani Bafade ne ya tashi ya je ya gyara Sarki Aminullah zaman alkyabbarsa sannan ya kalli Maryo yace, "Wanne ne shi? Ɗan gidan waye kuma mai ya aikata miki?" "Bakin alƙami ya riga da ya bushe domin rijiyar da ke buƙatar agaji tuni da jima da ƙafewa. A baya ta nemi a gaji da tallafinka a lokacin da take ganiyar ɗaukinka amma sai ka wofantar da buƙatar hakan, alhalin bishiyar na buƙatar tallafi kafin ƙonewarta ƙurmus. Sanin wane ne shi me ya yi mini duk ba zai amfanar da mutum ɗaya daga cikin wurin nan ba domin, babu mutum ɗaya da hakanya shafa." Sai kuma ta fashe da kuka ta ci gaba da cewa. "Ka karya mini alwashina domin ba zan taɓa iya watsa maka ƙasa a ido ba domin kai ɗin mai muhimmanci ne a gare ni. Amma tabbas na ɗaukarwa kaina alwashin bai sha a banza ba." Tana gama maganar ta miƙe ta fice jiri na ɗaukanta taba tafe tana haɗa hanya kamar wacce ta aha ƙwaya. Mamaki ne ya mamaye Sarki Aminullah ya dubi Baushe yace, "Me ne ne matsalar yarinyar nan da take waɗannan maganganun marasa kan gado?" "Babu wani abu da yake damunta sai dai maganganunta cike suke da ɗaukan fansa. A fusace take da fushi mai tsanani amma tabbas yanda ta faɗa ɗin haka ne kai mai muhimmanci ne a wurinta Allah ya ƙara maka lafiya." Baushe ya faɗa yana kallon Sarki Aminullah. "A nema mata magani domin nan da kwanaki ƙalilan za a ɗaura mata aure. Don haka dole a san abin yi." Baushe ya yi jim yana nazari domin yana ganin da kamar wuya gurguwa da auren nesa, don haka ya ɗago yace, "Allah ya taimakeka a iya sani da laluben magunguna na har yau Allah bai sanar da ni irin maganin da zan bata..." Tun bai rufe baki ba Fadawa suka buga masa tsawa suna cewa, "Hattara! Hattara dai Baushe." Baushe ya russunar da kai ƙasa yace, "Allah ya taimake ka a gafarce ni amma maganar yanda take haka na faɗa. Domin bansan abin da zan yi mata ta warware ba." Yana gama maganar Sarki Aminullah ya sallame shi ƙarshe ya sallami zaman fadar gabaɗaya. Maryo na zuwa gida da sauri Inna Habi ta rungumo tana shafata jikinta da ya yi furu-furu da ƙasa tana cewa, "Maryo in ce dai babu wani abu da yake damunki wani labari ya ishe mini wai kin cen fada a kwance haka ne? Ina fatan dai ƙwarin nan ba su cutar da ke ba?" Maryo ta dafe kanta tana lumshe idanu ta ce, "Ba abin da ya same ni Inna kaina ciwo yake." Hannu Inna Habi ta kai ta dafa ta ji kanta ya yi rau saboda zafi da sauri ta kaita ɗaki tana fitowa ta samu mutane sun fara taruwa har da masu leƙe. Mamaki ne ya kamata amma bata furta musu komai ba saboda bata san abin da suke yi wa leƙe ba. "Ka tafka babban kuskure da ka tsaya, a tunaninka za ka iya tarar aradu da ka ne? Karka manta tasirinta ya rinjaye naka da ninki biyu. Ba ƙarfinku ɗaya ba domin da ka tsaya ja da bayinta na tabbata sai ta ƙone ka da ƙarfinta domin ta fusata fushi mai tsanani. Na aiko Gurubu ya ɗauke ka domin niyyarta ta hallaka ka gabaɗaya, saboda ka taɓa mata 'yar uwa da Ɗan da take jinsa tamkar nata." Tsohon ya faɗa ransa a ɓace. Salman ban da haki babu abin da yake yi don haka ya ɗago da rinannun idanunsa yace, "Wallahi sai na koya mata hankali saboda waccen abar za ta azabtar da ni haka?" "Bari ba shegiya bace da Ubanta. Amma idan ka shegantata akwai lokacin da za ka nemo mata uba ka saƙala mata. Yaƙi dan zamba ne domin ba a shigarsa sai da shiri don haka ina baka shawara da karka tunkareta gaba da gaba saboda za ka tunatar da ita babban ɓacin ran da idan ta ganka a gabanta sai ta cinyeka ɗanye." Salman ya dube shi yace, "Yanzu haka zan zura mata ido kenan ta ci bulus?" "Bata ci bulus ba sai dai bana san ka da yawan gaggawa domin wata ra zai kai ga danasani. Yanzu ka zauna a nan ka ƙarasa jinyar idan kuwa ka koma na tabbata sai ta illata ka. Haka zalika ka yi sake ɗan zaki ya girma domin tuni ta jima da kwaye maka baya, domin ta fahimci shirinmu tun da ɗauke maka matarka a yau ɗin nan. Maganar da nake yo maka a yanzu cikin da ke jikin matarka tuni babu shi saboda tsananin firgitar da ta yi. Sai dai mu bi ta wata hanyar ba wannan ba, domin wannan tuni da babu ita." Kamar wacce a tsikara haka ta mike ta nufi sashen Fulani Zaliha, bata kula kowa ba ciki har da Fulani Zaliha, tana shiga ta samu Abu a kwance cikin wani yanayi. Jaririnta yana gefe idanunsa a kakkafe suna kallon sama. Gabaɗaya ido suka zuba mata suna kallo abin da za ta yi. Kan Abu ta fara zuwa ta sa hannuwanta biyu ta dafe kanta da ƙarfi sai ta saka bakinta a saitin kunnenta ta hura mata wata irin iska, firgigit ta miƙe tana kalle-kalle kamar me matasalar ƙwaƙwalarwa. Sai kuma ta wata uwar ƙara ta ƙara zubewa a wurin. Hannuwa biyu Maryo ta ɗaga tana godewa Allah domin bata taɓa tsammanin haka ba. Ɗaukan jaririn ta yi ta ɗora shi a ƙafarta ta fara matsa masa ciki take wani farin ruwa ya fara fita daga bakinsa, zuwan can ya tsanyare da kuka sai da kyar Maryo ta lallashe shi bayan ya yi shiru ta miƙe za ta fita har ta je bakin ƙofa ta waigo ta ce, "Kar wanda ya taɓa ta zata warware ta farka da kanta, amma yaron za ku iya ba shi kulawa. Tana gama maganar ta furzo wasu duwatsu guda biyu daga bakinta ta murmushe su a wurin sannan ta fice. Tana fita ta ci karo da Saif kamar ita yake nema suna haɗuwa ya wurgo mata tambaya. "Me ya sa kika musu haka?" "Ta yaya zan barsu bayan kowannensu yana buƙatar jin ɗumin ɗan uwansu, idan ka yi haka kamar ka tsorata da lamarinsa ne. Kowacce Uwa ya fi kyautuwa gare ta da ta bawa Ɗanta kulawa." Ta karkaɗe hannuwanta sannan ta bi ta gefe ta wuce. Bayan wani lokaci Abu garau ta miƙe kamar ba ita, haka ta rungumi Ɗanta tana mamakin kwanciyarta a wurin sai dai babu wanda ya sanar da ita komai. Salman na wurin Dattijo yana ci gana da samun sauƙi, sai dai fir tsohon ya hana shi tafiya a cewarsa sai ya ƙara samun lafiya ya kintsa shi. Sarki Aminullah haka ya rinƙa kiran masu magana ana bawa Maryo don ganin ta warke ta samu lafiya garau. Marasa lafiyar da suka jikkata sakamakon ƙudan zuma suna samun sauƙi waɗanda suka mutu haka Sarki Aminullah ya aika aka yi musu sutura aka binne su tare da bawa iyalansu tallafin kuɗi da kayan abinci. Kwanci ta shi babu wuya an yi suna Yaro ya ci sunan Sarki Aminullah suna kiranshi da Naufal, ranar suna an sha shagali 'yan uwa da abokan arziƙi daga sassan garuruwa haka suka zo bikin taya murna. Fulani Zaliha farinciki a wurinta baya musaltuwa haka daga wurin 'yan uwanta na nesa da suka zo. Fulani Maryama saboda baƙin ciki ɗaki ta shige ta fashe da kuka Jakadiya na lallashinta tana bata baki, domin wannan shine ga ƙoshi ga kwanan yunwa saboda gabaɗaya ta rasa ta yanda za ta yi ta cutar da yaron. Kamar wanɗanda aka shafewa tunani da tunanin Salman haka kowa ya manta ta shafinsa, kuma tun daga wannan lokacin babu abin da ya sake faruwa akan Abu da Jaririnta ba. Lokacin da Maleek ya zo bayan suna duk wasu abubuwa na shirin biki da ya tambayi Maryo ce masa kawai ta yi ya yi duk abin da ya dace, saboda wani abin na shi ba ƙaramin kunya yake bata ba. Don yanda yake zumuɗin bikin yanda ka san bai taɓa aure ba. Sannu-sannu bata hana zuwa... Ranar wata juma'a bayan gudanar da sallar Juma'a aka gabatar da ɗaurin auren Maryo da Maleek a babban masallacin juma'a na gidan Sarkin Kano da ke cikin ƙwaryar garin Kano. Dubbannin mutane ne suka halarci ɗaurin auren wanda ya tara manyan mutane, attajira, 'yan siyasa da dai sauransu. Kafin ranar an gabatar da bukukuwa na al'ada kamar yanda yake wanda ya haɗar da kamu saka lalle da du abin da ya danganci shagalin bikin aure. Murna wurin Maleek abin baya musaltuwa, haka daga wurin Maryo dukda ta san ba wata zazzafar soyayyar take mata ba amma sai ta tsinci kanta cikin farinciki da annushuwa. Saɓanin Abu da take taya mijinta kishi, don Abu fushi take da Maryo sosai ko magana ta yi mata sama-sama take amsawa. Saif duk wanda ya kalle shi ya san yana cikin matsananciyar damuwa saboda yanda ya rame ya ƙanjame ya lalace. Da Fulani Zaliha ta takura da abin da yake damunsa ƙin gaya mata ya yi. Sai Abu ce ta sanar da ita abin da yake faruwa tun daga farko har ƙarshe, tausayin Ɗanta ne ya kama ta domin ta san idan ta ce za ta yi magana ita kanta ta san bata yi wa kanta adalci ba, kuma Fulani Fahima da wane ido za ta kalle ta? Wannan dalili ya sa ta kira Saif ta rinƙa tausarsa tana ba shi baki. Ranar ɗaurin aure da yamma Maleek ya aika kiran Maryo, da farko ƙin zuwa ta yi amma Inna Habi ta matsa mata. Tana zuwa ta same shi a babban zaure, mutane sai kallonta suke saboda yanda ta yi shar da ita sai zuba ƙamshi take. A kunyace ta ce, "Barka da yamma!" Shauƙin ƙaunarta yake ji har a zuvciyarsa, ya riƙo hannunta yace, "Da baza ki zo bane?" Ɗagowa ta yi tana shirin ƙwace hannunta ta ce, "Mutane suna kallonmu" Kashe mata ido ɗaya ya yi yace, "Sai me?" Shagwaɓe fuska ta yi ta ce, "Amma ai..." Wata murya ce ta katse ta sakamakon jin yanda ta ratsa gaɓɓan jikinsu gabaɗaya sautin muryar na faɗin, "Don Allah ku taimaka mini azzalumai ne wallahi cutar mu suke son yi." Saif da tsaye a bakin ƙofar ya kalle su yana sakin wani shu'umin murmushi. Jiki na rawa Maryo ta fisgota da ƙarfin tsiya ta maƙureta a bango tana cewa, "Wace ce ke?" 🌚Na baku gari kowa wace oho _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [19/01, 19:22] Ameera Adam🌚: 65... Da sauri Maleek ya ƙarasa yana ƙoƙarin cire Maryo da sauri ta waigo gare shi tana cewa, "Don Allah karka dakatar da ni bansani ba ko an turota ta illata ni, wataƙila kaidin Salman ne." Maleek ne ya sauke idanunsa a kan Matar kusan numfashinsa ne ya ƙafe ya shiga nuna ta da hannu bakinsa na rawa. Daga can ɓangaren matar ta zuba masa ido jikinta na rawa numfashinta na niyyar ɗaukewa ta ce, "Kai... Kai ne?" Tana faɗin haka ta zube a wurin. Da sauri Maleek ya ƙarasa ya tarota ta faɗa jikinsa yana jijjiga ta. Maryo ta kalli Saif da yake kokarin barin wurin tana son ta tambaye shi game da wannan macen da ta gani mai siffarta sai kuma ta haƙura. Kallon Maleek ta yi tana shirin tambayarsa ta ga ya saɓi matar ya ɗauke ta kamar jaririya ya wuce cikin gida. Can sashen Fulani Maryama ya wuce ta ita haka ya tafi ya bar Maryo a soro cikin tunane-tunane iri-iri, saboda gabaɗaya kanta ya gama kullewa. Kafin wani lokaci tuni gidan ya karaɗe da zancen Maleek ya ɗauko Amarya babu lafiya. Babban abin da ya ɗaure wa mutanen gidan kai bayan sun ga ankwantar da Maryo sai ga wata ta shigo. Sai da Maryo ta shigo suka tabbatar da ba ta farkon bace domin waccen sanye take da yagaggun kaya kuma Maryo ta fi ta haske da gogewar fata.Wannan maganganun da ake yi ne suka ƙarasa kunnen Inna Habi tana zuwa jikinta ya yi wani irin sanyi domin tun da take bata taɓa ganin matsananciyar kama irin wannan ba. Ita kanta Maryo abin ya matuƙar bata mamaki, sai dai tana tsaye ta kasa koda motsa ɗan yatsanta ne. Inna Habi ce ta sauke ajiyar zuciya ta ɗebo ruwa ta yayyafa mata domin ji take tamkar Maryonta ce kwance a wurin. Tana tashi ta fara bin mutanen wurin da kallo a hankali ta furta, "A ina nake nan." Tana tuno wanda ta gani ta zabura zata fice daga gidan da sauri Maleek ya kama ta ya riƙe ta gam, ido ta zuba masa ta hau kiciniyar kwacewa tana cewa, "Ina fatan wannan mafarkin kar ya zame mini gaskiya, Ya Allah ka farkar da ni." Maleek ya hura mata iska a fuska lokaci ɗaya ta sauke ajiyar zuciya ta ci gaba da kallonsa kamar ta samu sabuwar hallita. "A ina kika ɓoye mini tsahon shekaru kin barni ina bulayi?" "Waye kai?" Ta faɗa tana ƙoƙarin ƙwacewa. "Na san an cutar da ke amma don Allah ki karki watsawa soyayya ƙasa a ido, ki taimaka ki yi mata hallaci domin ta wahalar da ni fiye da tunaninki." Maleek ya faɗa mata a shagwaɓe kamar zai yi kuka. Idanun mutane yana kallonsu kowa na kashe ƙwarƙwatar idonsa. Maryo da ke gefe ta tsuke fuska ta ce, "Wace ce ita." Don ita gabaɗaya ta manta da cewar ya taɓa iƙirarin ita matarsa ce. Sai a lokacin ta juya ta kalli Maryo, zaro idanunta waje ta yi a tsorace domin ko a mafarki bata taɓa yin tozali da hallita mai matsananciyar kama da ita ba sai yau. "Shukra ce! Ita ce wacce soyayyarta ta haukata ni har ta makanta mini ido na ce ke ce matata." Inna Habi da ke gefe ta ce, "Wannan ba maganar tsaiwa bace ya kamata mu nemi wuri a yi zancen a zaune." Maleek ƙin sakin Shukra ya yi domin gani yake kamar za ta kwace ta gudu ya sake rasa ta, hannu ya ɗora a kan fuskarta yace, "Inna 'yan biyu suke?" Sunkuyar da kai ƙasa ta yi ta ce, "Suna can wurin Iyatu a bakin kasuwa." "Wace ce ita?" Maleek ya tambaya a ruɗe. "Wata tsohuwa ce da nake bar mata yara na tafi aikatau idan na dawo sai na karɓe su." Shukra ta faɗa tana ƙoƙarin kwacewa ta ce, "Lokacin tashinta ya kusa bari na je na karɓo su don idan banje ba sai na ƙara mata kuɗi." "Aikatau Shukra? Kece kike aikatau? Me ya sa haka me ya sa za ki yi aikatau alhalin kuna da gata?" Maleek ya yi maganar hankali a tashe. Shukra ta saki murmushin takaici ta ce, "Zamana a wurin nan ya fiye mini kwanciyar hankali Maleek, domin rayuwa nake yi mai cike da 'yanci saɓanin rayuwar da na yi a ba..." Tun bata rufe baki ba ya saka hannu ya rufe mata yana girgiza mata kai. Inna Habi ce ta riƙe hannunta suka wuce ciki Maleek ya rufa musu baya. Kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki haka Maryo ta bi su zuwa cikin ɗakin. Kafin wani lokaci tuni maganar Shukra ta ƙarasa har kunnen Sarki Aminullah, Sarki Abdallah da sauran waliyan Maleek waɗanda ba su tafi ba. Maleek ba ƙaramin tausawa Shukra ya yi ba dangane da tarihin rayuwar da suka fuskanta ita da tagwayenta. Inna Habi ta goge hawayen fuskarta tana kallon Maryo da Shukra, Maryo ta share hawayenta ta ce, "Amma da kin yi haƙuri kin zauna da mijinki ya fiye miki wannan wahalar da kika sha, sai dai duk abin da ya samu bawa daga Ubangiji mai kyau ne." "Duk abin da ya koro ɓera daga rami ya faɗa wuta to ya fi wutar zafi. Na so jure wa haka amma na ga ba zan iya ba domin neman rayuwata ake da abin da na haifa. A ranar da zan baro Masarautar Adamawa muna kwance cikin dare ni da 'yan biyu na ji katangar ɗakinmu ana rusa ta, ban yi aune ba na ji muryar da ko a mafarki ba zan manta da ita ba ƙasa-ƙasa tana cewa. Maza ku ƙone ta tana ciki da yaranta gabaɗaya. Inna jin haka da sauri na goya Hassan shi kuma Usaini na rungume shi na saka hijabi na fice da gudu a lokacin wutar har ta fara ci a ɗakinmu. A cikin daren nan haka na rinƙa gudu ko waiwaye bana yi har Allah ya sa na fice daga gidan. Na samu nasarar ficewa ne lokacin da aka tattara a bakin sahshenmu kowa na ta'ajibi. Ina ganin Sarkin ƙofa ya wuce na fice da sauri hannuna ɗaya rungume da Usaini ɗayan na toshe masa baki don lokacin wuya ta sa ya fara tsala kuka. Ina fitowa na haɗu da wasu fatake na nemi taimakonsu suna wuce da ni zuwa garin da za su yada zango. Haka na ci gaba da gwagwarmaya har Allah ya kawo ni garin Kano na rinƙa faɗi tashi har na samu gidan da zan riƙa yi musu aiki suna bani abinci muna ci nida yarana. A taƙaice kenan dalilin fitowa ta amma idan kece za ki iya ci gaba da zama kuwa." Maryo ta girgiza. Babu jimawa Sarki Aminullah ya sa aka kai Shukra Fada, bayan an karɓo 'Yan biyunta daga wurin Iyatu. Abu tsayawa ta yi tana kallonsu lokacin da ta ƙarasa ganin abin da ake ta jita-jita a kam maganar Maryo ta rikiɗa zuwa mutum biyu. Sarki Aminullah ido ya zuba musu yana kallo ya ɗauki lokaci mai tsayi sannan ya numfasa ya fara magana, "Dukkan yabo godiya sun tabbata ga Allah subhanahuwata'ala, wannan al'amarin ya faru ne cikin ikon Allah. Maleek ba za mu bar maka su gabaɗaya a matsayin matakan ba domin da alama akwai alaƙa mai ƙarfi a tsakanin Shukra da Maryo don haka sai dai ka zaɓi ɗaya." Takawa na gama magana Maryo ta gyara zama ta ce, "Allah ya taimake ka na haƙura na bar mata shi saboda dama rashinta ne ya sa alaƙarmu ta yi ƙarfi har da ta kai ga batun aure." Maleek da Inna Habi ba ƙaramin tausayin Maryo suka ji ba. Sarki Aminullah ya san za a yi haka domin idan bai manta ba rashinta ne ya sa aka bashi Maryo a matsayin Shukra. Wannan dalilin ya sa ya yanke wata shawara da cewar, "Bisa ga la'akari da abubuwan da ya faru idan aka warware aurenta da Maleek zan ɗaura mata aure da babban Ɗana kuma magajin wannan masarauta." Daga Maryo har Inna Habi a firgice suka kalle shi jikin Maryo har rawa yake tana tsaka da tunani ta ji Sarki Aminullah ya sallame su. Duk inda nutsuwa take ta yi gabas Maryo ta yi yamma domin tun da Sarki Aminullah ya furta haka shi kenan ta rasa nutsuwarta. A ranar labarin duk abin da ya faru ya karaɗe cikin masarautar. A ranar ne Saif ya kwanta rashin lafiya banda amai babu abin da yake yi yana ambatar sunan Maryo. Tun suna ɗaukan lamarin da wasa har abin ya fara gagarar Kundila. Kwanan su Maleek guda suka tattara zuwa garin Adamawa. A wannan karon SarkinAminullah ba ƙaramin damuwa ya yi dangane da ciwon Saif ba, da kansa ya aika aka kira masa Fulani Zaliha ya tambayeta abin da yake damunsa. Da farko ta yi niyyar ɓoye masa ganin ɓoyewar bashi da amfani ya sa ta sanar da abin da yake damunsa. Kwana biyu da yin maganar Sarki Aminullah ya sa aka kira masa Inna Habi, Maryo, Abu, Saif da sauran matansa gabaɗaya. Bayan ya gabatar da maƙasudin zaman na su ya kalli Maryo zai yi magana Abu ta yi karaf ta ce, "Allah ya taimakeka don Allah ka yi mini wannan alfarmar domin kai kaɗai ne za ka iya tabbatar da ita." Maryo ta dubi Abu ta ce, "Karma ki wahalar da bakinki domin hakan ba zai taɓa yuwuwa ba." _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [22/01, 16:55] Ameera Adam🌚: 66.... Waiwaye... Kafin wani lokaci tuni ɓatan Rayzuta da Farratu ya karaɗe ciki da wajen masarautar Daulatul Jinnul Sahara, hankalin Sarki Kisumu ba ƙaramin tashi ya yi ba. Nan take ya baza masu tsaron cikin Masarautar aka shiga bincike a tunaninsa bincike suke yi a baɗini kuma ninke shi suke yi domin kusan kaso casa'in da tara sun san yanda aka yi Rayzuta ta ɓace. Yana nan zaune Labari ya ishe masa a sirrance na tafiyar da aka yi da Rayzuta da mai ɗakinsa, wannan labarin ya same shi daga bakin Mahaifin Furzaan sakamakon wani amintaccen dogari da ya sanar masa. Lokacin da Furzaan ya ji labarin ji ya yi kamar ya yi hauka, nan take Sarki Kisumu ya bada umarnin zama na gaggawa a cikin fada. Ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba ganin yawan Dogarawa masu tsaron Masarautar ace wai har a ta fi da matarsa da 'yarsa ba tare da sun yi ƙoƙarin dakatarwa ba. Suna nan zaune yana tsaka da jawabi Furzaan ya miƙe jikinsa har rawa yake yace, "Ranka ya daɗe a yi mini izini na tafi Masarautar Sarki Buzaag na sare kanshi dana Bulbuta da ɗansa Zulik domin sun munafinci Masarautar nan dole ne a yi musu hukunci mai tsanani. Ka bani dama na je na taho da Rayzuta da Mahaifiyarta domin na yi rantsuwa sai sun girbi abin da suka shuka da hannunsu." Sarki Kisumu ba ƙaramin daɗi ya ji ba domin ya tabbata bai zaɓawa 'yarsa zaɓon tumun dare ba. Cikin ƙarfafa masa gwiwa yace, "Tabbas kai Ɗan halak ne kuma na ƙara tabbatarwa daga tsatson jinin Aminina ka fito. Amma ka sani kai kaɗai ba za ka iya karawa da su ba domin na san wane ne Sarki Buzaag ba tun yanzu ba. Ba za mu farmake su yaƙi ba matuƙar ba su suka fara kawo mana hari ba, don haka zamu zuba musu ido don ganin abin da suke da niyyar yi. Amma matuƙar suka cutar mini da iyali sai na yi mummunan ɓata musu..." Bai rufe baki ba wani Bawansa ya faɗo fadar jina-jina yana haki yana nuna ƙofa yana cewa, "Ranka ya daɗe ga Bulbutu can da rundunar Sarki Buzaag sun kawo mana hari sun kashe dubbannan mutane nima da ƙyar na..." Harbin kibiyar da aka sakar masa a baya ne ya katse maganar da yake yi nan take ya faɗi ya mutu. Hankalin Sarki Kisumu ya kai matuƙar ƙolokuwar tashi da sauri ya mike yana ɗaukan kayan yakinsa. Haka suma sauran mazauna wurin kowa ya fice a guje yana neman kayan yaƙinsa. Sanƙira tuni ya yi shelar ɗaura ɗamarar yin yaƙi saboda kowa ya kasance cikin shiri. Furzaan kamar jira yake tuni ta ɗauki kayan yaƙinsa ya fita ya fara ragargazar maza yana kai su ƙasa. Kafin wani lokaci tuni wuri ya hautasine da ƙura ban da ƙarar ƙasusuwan jikinsu da manyan miyagun ƙarafuna babu abin da yake tashi a wurin. Sai dai sarkin yawa ya fi Sarkin ƙarfi, munafukan Masarautar Sarki Kisumu tuni suka rikiɗa zuwa kaiwa tsagin Sarki Kisumi farmaki. Lokacin da Mahaifin Furzaan, Furzaan da Sarki Kisumu suka lura da haka sai yaƙin ya fara sauya salo. Ganin ana neman kai tawagar Sarki Buzaag ƙasa ya fusata su suka fara buɗe musu wuta wani Barde ne ya kawowa Sarki Kisumu suka Mahaifin Furzaan na ganin haka ya tare sukar ta huda cikinsa har zuwa bayansa. Nan take jini ya yi tsartuwa idanunsa suka fara kafewa, Sarki Kisumu ya wurgar da takobinsa ya ƙwalla ƙara ya rungumo abokinsa yana ci gaba da kuka kamar ƙaramin yaro yana cewa, "Me ya sa za ki mini haka? me ya sa ba za ka bari mu tafi tare ba." Wannan kukan da Sarki yake yi ne ya ja hankalin Furzaan ganin Mahaifinsa a ƙasa cikin jini ba ƙaramin ɗaga masa hankali ya yi ba. Da sauri ya ƙarasa ya rungume shi yana kiran sunansa. Daga cen gefe a fusace Babban Barden ya ɗauke Barden da ya kai wa Sarki suka mari yana cewa, "Baka da hankali ne ba ka ji sharaɗin da Mai gida ya kafa mana ba yace duk rintse kada mu kashe mutanen da ya lissafa mana yanzu da shi ka samu da ya kenan?" Furzaan na jin haka ya miƙe a fusace ya ɗau takobinsa ya fille kan Barden da ya kashe mahaifinsa nan fa faɗa ya ƙara ɗaukan zafi, Mahaifinsa yana gabda mutuwa ya kalli Sarki murya a shaƙr yace, "Kabar faɗin haka domin ba komai bane don Amini ya sadaukar da ransa ga amininsa. Na ji daɗi ƙwarai da ni zan fara tafiya na barka, amma ina me jadadda maka ko bayan raina ban yarje Furzaan ya auri wata ba bayan Rayzuta kuma ko zai mutu na fi son ya mutu a tafarkin jarumta ba jarumin da aka ci shi da yaƙi ba." Ya saki murmushin ƙarfin hali ya ci gaba da cewa, "Dama na gaya maka na girmeka tsaurin ido ne ya sa kake abota da ni amma na girmeka na riga ka aure, na riga ka haihuwa kuma yanzu ma sai na riga ka mutuwa. Yaro matsa gefe me gidanka na magana." Waɗannan kalaman tun suna yara ƙanana Mahaifin Furzaan yake gayawa Sarki Kisumu, tun ba su yi hankali ba har suka fara zama samari. Wani lokacin idan suna tsokamar junansu Mahaifin Furzaan na faɗin haka yake kashe bakin Sarki Kisumu. Don haka a wannan lokacin da mutuwarsa ta zo ya ƙara jajjada masa. Sarki Kisumu na jin ƙarashen zancensa ya rungume shi ya fashe da wani irin matsanancin kuka, duk wanda yake wurin idan ya ga irin gursheƙen kukan da yake yi sai ya tausaya masa. Tuno rayuwarsu ta yarinta ya rinƙayi da barkwancin Amininsa tare da sauƙin kai irin nasa. Kasa taɓuka komai ya yi ya rungume gawar Amininsa yana ci gaba da kuka. Ko a girgiza kurna ta fi magarya domin duk lokacin da ka daidai Giwa da ɗantsako banbancin a bayyane yake, Sarkin yawa ko cikin maye yake ya fi Sarkin Ƙarfi. Duk yanda Furzaan ya kai ga ƙoƙarin kashe Dakarun Sarki Buzaag sai da suka yi masa ƙawanya sannan suka ɗaure shi da wata murtukekiyar igiya. Kan Sarki Kisumu suka koma shima da ƙyar suka yakice shi daga jikin gawar Amininsa suka ɗaure shi, sanann suka yi ƙoƙarin tafiya da shi. Furzaan na gaba Sarki Kisumu na biye da shi, Masarautar ta yi tsit sai gawarwakin mutane da kukan mata da ƙananan yara. Daga bakin ƙofa ya hango Mahaifiyarsa a kwace cikin jini bata ƙarasa mutuwa ba tana ɗaga hannu alamar neman taimaka. Juyawa ya yi wurinta da sauri suka fisgeshi da ƙarfin tsiya kansa ya bugu da wani ƙarfe take ya faɗi sumamme. Suna ficewa daga masarautar ba su tsaya ko ina ba sai Masarautar Sarki Buzaag . Lokacin da Zulik ya shiga da Rayzuta ɗaki kallonta ya rinƙa yi yana lasar baki, sannan ya cire kayansa yana niyyar haike mata gadangadan. Kukan kura ta yi tare da jin wani irin ƙarfi ya zo mata ta hankaɗa shi da bango gefe ta kalla ta hango wani mulmulallan farin ƙarfe ta ɗauka tana nishi saboda nauyinsa ta buga masa. Dukda ya goce amma sai da ta same shi. Nan take ya fasa wata ƙara ya zube a wurin sumamme sai Dogarawan Sarki Buzaag ne suka shiga suka kai masa ɗauki. Ajiyar zuciya Rayzuta ta yi tana lumshe idanu, ta ci gaba da addu'ar Allah ya kawo mata mafita a cikin halin da take ciki. Har lokacin Sarki Kisumu bai daina hawayen rashin Amininsa ba, suna zuwa Sarki Buzaag ya kalle su ya bushe da dariya yana nuna Sarki Kisumu da ke cikin jini, Sai da ya tsagaita da dariya sannan Bulbutu ya shiga fuskarsa kwance da murmushi. Sarki Buzaag ya kalli Sarki Kisumu yace, "Dube ka abin tausayi, Sarki mai ji da izzar mulki amma yau ya koma ƙasƙantaccen mutum wanda Bawan Masarautar nan ya fi shi daraja. Mai zai hana ka taugunna na ɗora ƙafata a kafaɗarka ka nemu yafiyata na mayar da kai maɗaukaki koda ba ka kai matsayin da kake da shi a baya ba." Sarki Kisumu ya yi murmushin takaici yace,"Izza tamkar numfashi take, numfashi kuma a kodayushe shine ruhi kai ne ƙasƙantace ba ni ba domin ni na tsaya domin kare dukiya da talakawana ko a yanzu na mutu tabbas ban mutu a banza ba." Daga ɗakin da take ta fara jiyo muryar Mahaifinta da sauri ta fito tana zuwa ta faɗa jikinsa tana kuka. Sautin Kukan da take yi ni ya doko dodon kunnensa, wata gauruwar ajiyar zuciya ya sauke yana buɗe lumsasun idanuwansa. Tarwai ya ɗora su a kan fuskar Rayzuta, suna haɗa ido ta yunƙura za ta wurinsa da sauri Dogarawan suka riƙe shi suna dankwafar da kansa ƙasa. Bulbutu ne ya sa a ka janye Rayzuta gefe sai Zulik ya shigo yana ɗingisawa, wurin da Rayzuta take ya nufa ya dafa kafaɗarta yana murmushi. Wani irin abu ne ya tokare zuciyar Mahaifinta da Furzaan da sauri ta sa hannu ta ture Zulik tana matsawa gefe. Cikin Shammata Sarki Kisumu ya miƙe ya faɗa kan Sarki Buzaag ya damƙi maƙogaronsa iya ƙarfinsa ya matse da hannuwansa biyu. Kafin Dogarawan su yi wani yunƙuri tuni Sarki Buzaag ya mace har lahira. Da sauri suka janye shi suna kai masa duka ta ko'ina, ganin haka ya sa Furzaan ya yi kukan kura ya kwarma ihu ya yage igiyar da a ka ɗaure shi da ita. Nan take sabon faɗa ya rikice a cikin fadar. Furzaan sai da ya rufe duk wata ƙofa da yake da tabbacin wasu za su fahimci halin da suke ci sannan suka fara azababben yaƙi. Zulik na ganin haka ya fisgi hannun Rayzuta ya shige wani ɗaki da ita ya datse ƙofar. Bulbutu da ke cikin fargaba ganin za a iya cinsu da yaƙi ya sa ya zage damtse ya fara ƙoƙarin kare kansa. Anan cikin haka suka fara faɗa shi da Sarki cikin nasara Sarki Kisumu ya soka masara takobi a ciki har sai da ta huda bayansa. Amma ga mamakinsa sai gani ya yi Bulbutu ya fashe da dariya kallon cinyar Sarki yake wacce ya sara da wani sihirtaccen shu'umin gatarinsa saboda tsananin faɗa bai san da saran ba sai da ya ga Bulbutu na kallon wurin. Bulbuta ya fara shaƙuwa yana faɗin, "Ni da kai duk babu mai rayuwa domin wannan gatarin sunanshi Gaɓar mutuwa, tun da na sareka zai fara fitar da gaɓɓon jikinka, ka ga an yi ba a yi..." Bai ƙarasa maganar ba ya ji Sarki Kisumu ya ƙwallah ƙara sakamakon cinyarsa da ta fita daga gangar jikinsa, Bulbutu murmushi ya yi nan take rai ya yi halinsa. Haka gaɓɓan jikin Sarki Kisumu suka ci gaba da fita yana ƙwala ihu saboda tsananin azaba. Da sauri Furzan ya ƙarasa gare shi sakamakon ya gama da duk sauran Baraden da ke wurin. Zuwan sa ke da wuya Sarki Kisumu yace ga garinku nan. Cikin zafin nama ya tashi ya doka ƙofar ɗakin da Zulik da Rayzuta lokacin da ya shiga yana ta kiciniyar guduwa da ita ta ƙofar sirri. Ganin Furzan da takobi ba ƙaramin ɗaga masa hankali ya yi ba, Rayzuta na ganin haka ta fisge ta koma bayansa tana kaka. Ƙofar ɗakin ya rufe da ƙarfi sannan ya zaunar da ita a gefe nan suka shiga karawa cikin azabbaen yaƙi mai raunatar da zuciyar ƙananan jarumai. Zulik na ganin Furzaan ya tasamma halaka shi ya fice ta ƙofar sirri da gudu nan take ya ɓace cikin tsafin da Mahaifinsa ya yi masa kafin ya mutu. Furzaan bin bayansa ya yi da gudu amma ya neme shi sama da ƙasa ya rasa. Rayzuta ce ta biyo shi sakamakon jin bugun ƙofar da wasu dakaru suke yi. Kama hanunta ya yi za su gudu ta ja ta tirje tana cewa, "Furzaan ina za mu ta fi mu bar Mahaifina." Furzaan ya sunkiyar da kai ƙasa yace, "Ki yi haƙuri amma mun rasa Baba." Wata uwar ƙara ta ƙwalla ta zube ƙasa a sume. Ganin lokaci na ƙurewa ya sa Furzaan ya ɗauke ta cas ya rufe ƙofar da ƙarfi ya fara falfala gudu da ita cikin sararin samaniya. Wannan kenan! Sarki Aminullah ya tatattara hankalinsa kan Abu yace, " 'Yata ina jin ki." Maryo ban da harara babu abin da take wurgawa Abu, Abu ta russunar da kai ƙasa ta ce, "Allah ya taimakeka ina son ka sa Saif ya sauwaƙe mini." Da sauri Fulani Zaliha ta ɗago ta kalli Abu da ta sunkuyar da kai ƙasa don ta san wannan hukuncin ba zai taɓa yi wa Fulani Zaliha daɗi ba domin ta nuna mata ƙauna kamar ita ce ta haifeta. Sarki Aminullah ya kalli Saif da ke gefe duk ya rame ya lalace yace, "Ka ji abin da matarka ta ce?" Saif ya motsa baki ya fara magana, "Allah ya taimake ka ban san abin da na yi mata ba da har take son na sake ta." Nan aka ci gaba da tufkawa Abu na cewa Saif ya sake shi kuma yana faɗin bai san dalilinta na sa shi yin sakin ba. Abu duk yanda aka kaɗa aka raya ta faɗi dalilinta ta ƙi domin ta san idan ta ce tana son Maryo ta auri Saif ne za su ce mata Saif zai iya auren Maryo ko da bai sake ta ba. Bayan tafka wannan mahawarar Sarki Aminullah ya sako zancen Saif da soyayyar Maryo nan take Maryo ta tsalle ta dire ta ce sam bata ƙaunarsa. Haka aka tashi daga zaman babu daɗi kowa zuciyarsa a dagule ba tare da an cimma matsaya ba. Bayan kwana biyu da yin maganar aka wayi gari da ɓatan Abu babu ita babu jaririnta Naufal, wannan ɓatan na Abu ba ƙaramin ɗaga hankulan mutanen cikin gidan ya yi ba, musamman Saif da abin ya runcaɓe masa goma da ashirin. Tun daga ranar cin abinci ya yi ƙaura daga wurinsa, haka daga ɓangaren Inna Habi da Maryo duk sun fita hayyacinsa, haka labarin ɓatan Abu ya karaɗe cikin Masarautar gabaɗaya. Zuciyar Fulani Maryama fari ƙal don gani take wannan shi zai bata damar ganin na ta jikan ya yi rayuwarsa a matsayin Jikan Sarki na wurin Ɗa namiji. Haka rayuwa ta ci gaba da gungurawa da matsananciyar damuwar ɓatan Abu tun basa iya ci da sha har kowa ya fauwalawa Allah lamuransu suka ci gaba da rayuwa. Bayan ɓatan Abu da wasu watanni Saif ya samu Maryo a soron farko yace, "Ina mamakin yanda aka nemi baiwar nan aka rasa ina jin tsoron kar wani abin ya cutar da su." Ido ta zura masa ta ga duk ya rame sai ƙashi, lokaci ɗaya ta ji tausayinsa ya ratsa zuciyarta ta san ko ba a faɗa ba tabbas Saif yana ƙaunar Abu domin yanayi da alamunsa sun nuna. Cikin zuciyarta take ayyana, "Ya za a yi na yarda na auri wanda ya mace a ƙaunar 'Yar uwata" Ganin shirun ya yi yasa ya katse ta da cewar, "Tunanin me kike yi?" "Ina tunanin dalilin da ya sa 'Yar uwata za ta ɓace da ƙaramin goyo ko dai ka yi mata wani abin ne ban sani ba." Cikin suɓutar ba ki yace, "Me zan yi mata alhalin ina ƙaunarta da abin da ta haifa..." Harshensa ne ya sarƙe bisa jin nannauyar ajiyar zuciyar da ta sauke, wani irin abu ta ji ya turniƙe mata zuciyarta ta watsa masa harara ta ce, "Dama na san kana sonta ba sai ka gaya mini ba amma ba wannan na tambayeka ina tambayarka ne ko kana da masaniyar wurin da take." Gabaɗaya sai ya ji bai ji daɗi ba don bai san maganar za ta fito daga bakinsa ba, ya wayance sa cewar, "Ba ni da masaniyar wurin da take sannan don Allah ki dawowa da Salman matarsa domin ba laifinta bane." "Tun jiya suka dawo da ita sai dai an sami matsala domin ta rasa cikin jikinta. Bana tunanin tana cikin hayyacinta saboda firgitar da ta yi." Maryo ta faɗa tana neman wucewa, da sauri ya riƙo hannunta ta tura jikin bango yana kallonta yace, "Don Allah ki taimaka min ki amshi soyayyata. Me ya sa ba za ki yi haƙuri ba ko dan kin ga na mutu a kanki?" Matsawa ta yi gefe ta ce, "Me ka yi mini da za ka ba ni haƙuri? A gaskiya ka yi haƙuri amma ni ba zan aureka ba..." Wata gigitacciyar tsawa ya buga mata yana cewa. "Wallahi sai kin aure ni." A razane ta ƙanƙame jikinta a gefe don ta gama tsorata da yanayinsa, tsugunnawa ya yi ƙasa kamar ƙaramin yaro yana rusa kuka yace, "Shi ke nan tun da ba za ki aure ni ba amma ki sani ba zan taɓa yafe miki ba matuƙar na mutu kika yi mini kuka, ki je kawai nima zan je ban taɓa tsammanin soyayya na riɗewa zuwa ƙiyayya ba. Babu komai wataƙila wannan ita ce kalar tawa jarrabawar." Yana gama maganar ya miƙe ya wuce cikin gida, a hankali ta bi bayansa jiki a sanyaye tana runtse idonta wasu shuɗaɗɗun abubuwan baya suka sake dawo mata a cikin dodon kunnenta ta ji maganganunsa na baya na yi mata amsa kuwwa. "Wanda ya san mutumcin ƙauna baya yi mata riƙon sakainar kashi! Jikina yana bani wannan lokacin shine ƙarƙarewar numfashina! A duk bugun numfashi yana sauka tare da tsantsar ƙaunarki, iya zayyana kalaman da suke zuciyata ɓata lokaci ne. Amma Ƙaddara ta gindaye jindaɗinmu tabbas fitar ƙaddara tamkar fitar numfashi ce. Ki kula min da ajiyar da na yi a cikinka domin tabbas ina ji a jikina watarana zan dawo na karɓi a bata. Kaicon ragowar numfashina da ba zai iya aiwatar da jindaɗin rayuwarmu ba, amma na yi miki alƙawari tabbas sai na dawo na cimma sauran burina. Amma ki sani matsawar ban cimma burina ba shi kenan rayuwata babu sauran amfanin da za ta iya aiwatarwa don haka dole a koma 'yar gidan jiya." Jikinta har wani irin rawa yake sai dai tana shiga cikin gidan ta samu Fulani Zaliha ta fasa kuka Sauran Bayi na tayata a gefe guda Saif na kwance a ƙasa. Littafi ya taho gangara har na fara missing ɗinsu😢 _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [23/01, 19:35] Ameera Adam🌚: 67... Maryo na shiga ta samu Fulani Zaliha na Jijijjiga Saifa, kafin wani lokaci tuni labarin rashin lafiyarsa ya je kunnen Sarki Aminullah. Ba a ɗauki lokaci ba ya sa aka wuce da shi asibiti. Tuna baya... Furzaan bai tsaya a ko'ina ba sai da ya yi tafiya mai nisan gaske sannan ya sauke a cikin kogon dutse mai ɗauke da koriyar ƙorama da ƙananan tsuntsaye, a gefe ya kwantar da Rayzuta ya ɗebi ruwa yana shafa mata a fuska. Sai bayan wani lokaci ta buɗe idonta ta sauke su a kansa, hannu ta sa ta shafo fuskarsa idonta na zubar fa hawaye. A hankali ya fara lallashinta yana goge mata hawaye har ta tsagaita da kukan, ta yunƙura a hankali ta tashi zaune. Kallonsa ta yi ta kalli wurin da suke ta ce, "Yanzu shi kenan mu biyu muka rage? Ya kashe mini matar da nake yi mata kallon Mahaifiyata, sannan shima Mahaifina na rasa shi gatana ya riga da ya ƙara..." "Matsawar ina numfashi ba za ki yi kukan maraici ba domin ni zan maye miki gurbin Uwa da Uba. Addu'a za mu yi musu domin ta su ta riga da ta ƙare, na zaɓi mu yi rayuwa a nan ne domin na san waye Zulik ba zai taɓa barinki ba, ni kuma ina tsoron a samu akasi ya illata ki domin ke mace ce ƙarfinsa da naki ba zai taɓa zuwa ɗaya ba." Furzaan ya faɗa yana goge mata hawaye. Hancinta ne ya fara ɗigar da jini kanta na sarawa, da sauri ya sa abu ya tare yana tambayarta, "Lafiya me yake daminki? Dama kina yin haka ne ko yanzu ne abin ya same ki." "Ban taɓa yi ba, wannan ne karo na biyu karon farko Zulik ne ya buga mini kansa nan take jini ya fara ɗiga ta hancina, sai kuma yanzu da haka kawai na wayi gari da shi." Wanke mata ya yi sannan ya ci gaba da rarrashinta har ta fara sakewa. Haka suka ci gaba da rayuwa a wurin cikin soyayya da kwanciyar hankali, satinsu guda a kogon wani lamari ya gindaya a tsakaninsu kasancewarsu Mace da Namiji. Zaune suke kowa ya yi shiru fuska ɗauke da damuwa Furzaan yace, "Don Allah ki gafarceni wallahi na rasa yanda aka yi na kasa riƙe kaina?" Hawaye ta goge ta ce, "Babu komai domin na san ba za ka taɓa cutar da ni ba." Tun daga wannan lokacin babu wani abu da ya ƙara shiga tsakaninsu, haka suka ci gaba da gudanar da rayuwarsa. Sai dai babban abin da yake damunsu lalurar fitar jini daga hancin Rayzuta (Haɓo) da yake son zame mata jiki, ganin lamarin na ƙara ci gaba ya sa ya fara yanke shawarar nema mata magani. Bayan wata huɗu da faruwar lamarin, Rayzuta ta fahimci sauyin da take samu daga jikinta daga ƙarshe sula tabbatarwa kansu da cikin gare ta na tsawon watanni Huɗu. Ba ƙaramin murna suka yi ba haka Furzaan ya ci gaba da bata kulawa kasancewarta yau da lafiya gobe babu. Wata rana suna zaune Furzaan yace, "Idan Allah ya sauke ki lafiya zamu fita daga kogon nan muje a ɗaura mana aure." Murmushi ta yi masa ta ce, "Allah ya kaimu amma ni mace nake son haifa." Daga can gefe suka ji an ce, "Idan har kin haife shi ko? Alƙwari na ɗaukarwa kaina ba za ki haife cikin wannan abin ba, yana gama maganar ya fara hura iska ta ko'ina daga bakinsa, nan take sai ga masu siffar Rayzuta babu adadi kowacce ɗauke da ciki kamar, kowacce daga cikinsu jiran sunansa take tana kuka, Furzaan dafe kansa ya yi cikim damuwa, wata dabara kallon ƙasa ya fara yi, inuwar muce ɗaya ya gani wannan ne ya bashi tabbacin cewar ita ce Rayzutansa, da sauri ya ruƙota jikinsa ya kalli wurin da Zulik yake yace, "Me ya sa kake koƙarin..." Maganarsa ce ta maƙale masa jin wuƙa ta huda kayan cikin, ajiyar zuciya ya sauke ya ɗago yana kallonta daga can gefe ya ji wata ta fasa ƙara tana ta taho wurinsa, wacce ta soke shi da wuƙar ce ta ja baya ta riƙiɗa zuwa siffar Zulik, sannu a hankali waɗancan suk suka ɓace, Kuka Rayzuta take tana tallafe da shi a hankali ya dafa bango hannunsa ɗaya na kan cikinsa ya zare wuƙar ya dunfari Zulik suka fara faɗa. Sai dai zubar jinin da yake yi ne ya sa ƙarfinsa ya fara jin ƙasa jini na ɗaukansa. Babu yanda ya iya yana ji yana gani ya faɗi a ƙasa, sai dai duk da haka bai ƙaraya ba yana ƙoƙarin kai wa Zulik suka da wuƙa. Zulik na ganin haka ya fisgo Rayzuta ya maƙureta da bango, ya fara kiciniyar haike mata. Ganin haka ya sa Furzaan yunƙurawa a hankali zai tashi daga baya ya ga wasu masu siffar Zulik sun danne shi, suna soka masa makamai yana ji yana gani Zulik ya haikewa Rayzuta ban da kuka da kuruwar kiran sunansa babu abin da take yi. Bayan da Zulik ya gama abin da zai yi ya ƙarasa gaban Furzaan yace shafa fuskarsa yace, "Ashe haka kake kwasar gara shi ya sa ka killace ta a wurin na? Abin da baka sani ba lokacin da kuka shigo wurin nan ina biye da ku. Na baku wuri ne na koma wurin boka na dominnya tsumani da kayan tsafinsa kuma ga shi buƙatata ta biya, don haka zan ɗauke na kaita a cire cikin jikinta na killace ta domin biyan buƙatar kaina." Yana gama magana Furzaan ya hamɓare shi da ƙafa har sai da ya yi baya, Rayzuta ce ta taso ta bayansa ta ɗaba masa wuƙa a kafaɗa a gigice ya ƙwallah ƙara. A fusace ya koma wurinta ya kifeta da mari ta faɗa kan cikinta. Fita ta fara yi daga hayyacinta saboda azaba Furzaan na niyyar miƙewa Zulik ya burma masa ƙaho a ciki, nan take ya faɗi fuskarsa na kallon Rayzuta, Fisgota Zulik ya yi ya sake ƙoƙarij haike mata cikin rauni Furzaan ya fara magana, "Wanda ya san mutumcin ƙauna baya yi mata riƙon sakainar kashi! Jikina yana bani wannan lokacin shine ƙarƙarewar numfashina! A duk bugun numfashi yana sauka tare da tsantsar ƙaunarki, iya zayyana kalaman da suke zuciyata ɓata lokaci ne. Amma Ƙaddara ta gindaye jindaɗinmu tabbas fitar ƙaddara tamkar fitar numfashi ce. Ki kula min da ajiyar da na yi a cikinka domin tabbas ina ji a jikina watarana zan dawo na karɓi a bata. Kaicon ragowar numfashina da ba zai iya aiwatar da jindaɗin rayuwarmu ba, amma na yi miki alƙawari tabbas sai na dawo na cimma sauran burina. Amma ki sani matsawar ban cimma burina ba shi kenan rayuwata babu sauran amfanin da za ta iya aiwatarwa don haka dole a koma 'yar gidan jiya." Rayzuta ta fashe da kuka ta fisge ta ƙarasa ta rungomo shi jikinta tana kuka sai dai tuni alƙami ya riga da ya bushe rai ya yi halinsa. Jikinta na rawa ta miƙe zuwa wurin Zulik a fusace ta cire ƙahon da ya soka wa Furzaan ta shammace shi ta soka masa a ciki, kafin ta yi wani yunƙuri ta shigar wani abu ta bayanta har sai da ya ɓullo da cikinta, nan take suka faɗi gabaɗaya kowa rai ya yi halinsa, kamar tashin iska haka masu siffar Zulik kowanne ya ɓace daga wurin, wurin ya zama sai gawarwakin Zulik, Rayzuta da Furzaan. Wannan ne ƙarshen tarihin rayuwar su Rayzuta ta baya. Saif sai da ya yi ku san sati guda a asibiti sannan aka sallame shi, babu laifi jikinsa ya yi kyau sai dai har wannan lolacin baya iya cin abin, ci gaban da aka samu da ya farfaɗo amma yanda yake kullin haka yake. Satinsu uku da komawa gida wata ranar laraba a ka wayi gari da matsanancin ciwon Saif, wannan karon Fulani Zaliha ta ci alwashin duk yanda za ta yi za ta taimakawa Ɗanta domin ya samu Maryo ta aure shi. Wannan karon kafin su je asibiti abin na sa ya lafa. Inna Habi na zaune a ɗaki Fulani Zaliha ta shiga, Inna Habi na shirun gaida ta Fulani Zaliha ta zube mata a kan gwiwoyinta tana roƙonta. "Don Allah Inna ki taimaka ki shawo kan Maryo ta amince masa, shi kaɗai na mallaka shi kaɗai Ɗana Jikina ɗaya tilo shima kin ga yanda Ubangiji ya jarabce mu, Na san babu wani abu da zan iya aiwatar bayan in roƙi alfamarki na san idan kika yi mata magana za ta iya amincewa da buƙatata Don Allah ki taimaka mini kada na rasa shi." Tausayinta ba ƙaramin ratsa Inna Habi ya yi ba, ta wani fannin har kunyarta sai da ta kamata ace mace mai izza da mulki yau ita ce take russuna mata akan buƙatarta, tabbas Fulani Zaliha ta cancanci a yi mata halarci domin duk inda Ɗan halak yake Fulani Zaliha ta je wurin. Inna Habi ta ɗaga Fulani Zaliha zaune ta ce, "Ranki ya daɗe ki daina roƙona insha Allah Maryo za ta auri Saif zan yi magana da ita." Fulani Zaliha haka ta durƙasa sai zabga godiya take tana fita Inna Habi ta samu Maryo da maganar, da farko Maryo ƙin amincewa ta yi sai da Inna Habi ta yi mata nasiha mai ratsa zuciya sannan ta amince. Lokacin da Inna Habi ta sanarwa da Fulani Zaliha ba ƙaramin farinciki suka yi ba nan take Saif ya miƙe ya take ƙafafuwansa, Wata ranar juma'a da ta zagayo aka ɗaura auren Maryo Saif a bisa sadaki dubu biyar. (Ku san shekarun baya kuɗi daraja gare shi, dubu biyar ma sai gidan wane da wane.) Masarautar Zazzau ɗaya ce daga cikin muhimman Masarautun gargajiya na ƙasar hausa da ma yankin Afirka ta yamma. Tarihi irin na kunne ya girmi kaka ya yi nuni cewa, Zazzau wata daɗaɗɗiyar Masarauta ce wadda ta samo asali tun ɗaruruwan shekaru da suka gabata, wato daga lokacin Jahiliyya ko kuma kafin zuwan addinin Musulinci. Tana ɗauke da manyan jarumai masana fannin ilimin addini daban-daban. Yau typing sai da na gama ya goge wallahi sai dai ku karanta da hakuri _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI_ [28/01, 16:01] Ameera Adam🌚: 69... Masarautar Zazzau. Ganin Mutumin na neman ɓata musu lokaci ya sa Saif kiran Dogarawan bakin ƙofa, jikinsu na rawa suka shiga su biyu da bulali a hannunsu, russunawa suka yi cikin girmamawa suna faɗin, "Allah ya taimaki Yarima Allah ƙarawa mai jiran gado lafiya." Saif ya dakarar da su da cewa, "Kuna ina kuka bar wannan Mahaukacin ya shigo?" Sai a lokacin suka ɗaga kai suka mayar da kansu wurin Farin Tsohon da ke tsaye, da mamaki suke kallonsa sannan ɗaya daga cikinsu yace, "Allah ya huci zuciyarka Ranka ya daɗe wallahi ba bu wanda ya wuce mu a bakin ƙofa." Tsohon na jin haka ya bushe da dariya, ba ƙaramin tsoro ya basu ba don gabaɗaya yanayinsa kamar bana ainihin bil'adam ba. Sarki Aminullah ya kallesu fuska a ɗaure yace, "Maza a fice da shi tun kafin hukunci ya sauka a kansu." Tun bai rufe baki ba suka yunƙura za su kama tsohon da sauri ya nuna su da wani mushen muzuru nan take suka yanke jiki suka faɗi jikinsu na wani irin karkarwa. Ganin haka ba ƙaramin ɗaga hankalin Sarkin Aminullah da Saif ya yi ba, Sarki Aminullah na shirin magana Tsohon ya taka gabansa yana faɗin, "Ina son ka tara mini dukkan mutanen gidan nan domin ina tafe da muhimmiyar magana amma muddin ka ƙi amincewa haka na rantse maka yanda na halakar da waɗannan bayin naka sai na halakar da mutanen gidan nan gabaɗaya." Ganin da gaske yake ya sa Sarki Aminullah ya aika aka fara shela, ba a ɗauki lokaci ba sai ga jama'a damƙam sun cika faɗa. Sarki Aminullah fargaba ce ta kama shi domin tsohon ya fara ba shi mamaki, Tsohon na riƙe da hannun Salman kamar wani zai ƙwace shi, can gefe suka tsaya kowa ya zo sai ya kalle su. Bayan mutane sun hallara Sarki Aminullah ya sa aka kira masa tsohon gefen, ya dube shi da kallon nutsuwa yace, "Tabbas na lura kana tafe da muhimmiyar magana amma don Allah mene ne gaskiyar abin da ka faɗa dangane da yaron nan? Tabbas na san wacece Maryama ba za ta taɓa cin amanata ba, duk abin da nake so shi take so ko da bata ƙaunar abu idan ina so tana tayani ƙaunarsa. Amma ka zo mini da maganar da ta girmewa tunanina, don Allah idan har maganar ta shafi iyalina mai zai hana mu yi ta a sirrance." Kamar mutumin arziƙi haka Tsohon ya yi kasaƙe yana sauraron Sarkin Aminullah sannan yace, "Ba zan taɓa yin magana a sirrance ba matsawar akan abin da ya shafi ɗana ne don haka a yau zan fasa ƙwai kowa ya huta." Tsohon na gama maganar ya yi cikin fadar mutane na ganinsa suka fara matsa masa, kamar shine jagoran haka ya yi gaba, Sarki Aminullah na tafe jiki ba ƙwari shima ya shiga. Fulani Maryama tun da gari ya waye take jin ta kamar mara lafiya har kawo lokacin da sanarwa ta isa gare ta na kiran gaggawa da aka yi musu. Matan Sarki Aminullah gabaɗaya sun hallara a fadar, Fulani Maryama jikinta ban da rawa babu abin da yake yi tun da idanunta suka yi tozali da mutumin da ta jima da mantawa da babin rayuwarsa. Tun da ta sunkuyar da kai ƙasa ta kasa koda ɗagowa, Sarki Aminulla ya lura da haka amma saboda yanda ya bata yadda ɗari bisa ɗari ya sa bai kawo komai a ransa ba. Masarautar Zazzau. Asubar fari Abu ta ji alamun buɗe ƙofa da sauri ta tashi zaune tana mitseke idanu, hannunsa ɗauke da fitila ya shiga yana haska ɗakin, jikin Abu rawa ya ɗauka sakamakon ganin mutum sanye cikin wata ɓoyayyar shiga, hatta fuskarsa a rufe take, haskata ya yi nan take gabansa ya yi mummunan faɗuwa. Ƙura mata ido ya yi ya ga yanda take ta muzurai, tsawar da ya buga mata ce ta sata sake shiga hankalinta. Cikin wata irin Murya yace, "Ke!" Da sauri Abu ta kalle shi jiki na rawa ta ce, "Na'am Ranka ya daɗe" Tsugunnawa ya yi a gabanta yace, "Muga sarƙar wuyanki!" Jiki na rawa abu ta ɗago sarƙar wuyanta tana nuna masa, ƙarewa sarƙar kallo ya yi yace, "Wacece ke!" "Sunana Abu!" A tsawace yace, "Ba sunanki ba daga wace masarautar kike." Cikin abu ne ya bada sautin ƙuuuuuuu don har sai ya bayyana a fili, a zuciyarta take ayyana, "Shi kenan tawa ta ƙare me wannan yake nufi." A fili kuma ta ce masa, "Ni ba yar kowacce masarauta bace Hasalima ni marainiya ce iyayena duka sun mu..." Da sauri ya ɗauke ta da mari jikinsa na rawa ya nuna ta da ɗan yatsa yace, "Ki faɗa mini wacece ke ko kuma yanzu na tura ki fadar Mai martaba. Ganin yanayinsa da abin da ya faɗa ba ƙaramin ɗaga hankalin Abu ya yi ba jiki na rawa ta kwashe labarin abin da ta sani na tarihin rayuwarta da dalilin tahowarta har Allah ya sa, ta zo masarautar Zazzau a matsayin Baiwa." Hannu ya miƙa mata yana faɗin, "Ciro mini sarƙar wuyanki" A firgice ta ɗago ta ce, "Don Allah kark..." "Bana buƙatar jin komai daga gare ki." Babu yanda ta iya haka ta ciro sarƙar ta masa, yana karɓa ya juya har zai fita ya juyo yace, "Ki ta shi ki yi sallah a kowanne lokaci Mai martaba zai iya aikowa kiranki domin dole ki amsa tuhume-tuhumen da za a yi miki." Yana gama maganar ya fice daga ɗakin. Kuncin duniya tare da fargaba ne suka mamaye zuciyar Abu, saboda tashin hankali ji ta yi yawun bakinta na neman ƙafewa, don haka ta nemi kukan ta rasa. Wato kuka ma rahama ne, sai a wannan lokacin Abu ta tabbatar da haka saboda idanunta sun bushe ko ɗigon hawaye babu. Miƙewa ta yi ta tura ƙofar ta fita ta ɗauro alwala ta gabatar da sallar asuba. Bayan ta idar ta jima tana addu'ar Allah ya kawo mata mafita, ta jima tana roƙon Allah a kan ya yafe mata kuskuren da ta yi da wanda ta aikatawa mijinta na fitowa da ta yi ba tare da izininsa ba. Kallon Naufal ta yi ta ji wani irin tausayinsa ya kamata, a fili ta furta, "Kowanne bawa da tashi irin ƙaddarar ni kuma irin tawa kenan, Ya Allah ga yarona nan ka tallafi rayuwarsa kana ganin ƙaddarar da ta fito da ni, wata ƙila ma mutanen nan kasheni za su yi, Naufal ka yafe mini bisa sabuwar rayuwar da za ka fara fuskanta. Na baro ka da Mahaifinka da danginka da gatanka ga shi na kawo mu cikin sabuwar rayuwar da bamu taɓa zata ba." Tana ƙarasa maganar ta fashe da wani irin matsanancin kuka. Kukan da Abu take yi ne ya tashi Naufal daga bacci ya fara kuka, ɗaukansa ta yi ta rungume tana ci gaba da kuka gwanin ban tausayi. Tana nan zaune Bayin sashen Matan Sarki suka shiga tare da tafiya da ita can sashen da Matan Sarki suke. Sashen Mahaifiyar Yarima aka kaita, tana shiga ta tsugunna a bakin ƙofa, Matar zaune take cikin shiga ta alfarma ta yi kyau sosai ga ta da kwarjini, Abu na ganinta ta ji gabanta ya yi mummunan faɗuwa, tattaro ƙarfin hali ta yi ta gaishe da matar. Ba yabo babu fallasa ta amsa mata sannan ta ci gaba da jan carbin da take yi. Sai da gari ya waye sosai sannan Sarki ya aiko kiran Abu, wani sabon gumi ne ya shiga karyo mata ta ko ina. Haka ta saɓi Naufal ta fita tana share hawaye. Masarautar Kano. Sai da Sarki Aminullah ya yi Addu'a sannan ya gabatar da dalilin da ya tattara su a wuri, tun da Sarki Aminullah ya fara magana Ilahirin jikin Fulani Maryama yake rawa, Jakadiya da ke can gefe da tun shigarta wurin ta tabbatar da Fulani Maryama bata da gaskiya ya sa ta zuba idanu tana kallon yanda wannan lamarin zai kasance, Sarki Aminullah ne ya umarci Tsohon da ya fito ya yi jawabi. Miƙewa ya yi ɗaya bayan ɗaya ya fara kallonsu sannan ya sauke idanunsa a kan Fulani Maryama ya fara cewa, "Sanin sunana ba wani muhimmin abu bane da zai gamsar da ku domin ba wannan ne a gabana ba, Ina son jama'ar wudin nan su saurari abin da zan faɗa domin wataƙila zai iya yi muku amfani. Ni tantirin gawurtaccen Boka ne dana gaji tsafi a wurin Mahaifina tun kafin ya mutu, tun ina ƙarami na iya siddabaru don haka na yanke shekarun da yi zai yi matuƙar wahala. Shekarun baya Maryama na kawo mini buƙatunta akan Mijin wato Sarkinku da kuke kallo a yan..." Da sauri wani Bafade yace, "Hattara dai a gaban Sarki kake." Kallon da tsohon ya wurga masa ne ya sashi saurin tsoke bakinsa. Tsohon ya ci gaba da cewa, "Faɗin irin taimakon ban gushiri inbaka mandan da muke yi da Maryama abin ne da ba zai lisaafu ba, duk lokacin da Maryama ta kawon ziyara sai na yi mu'amala da ita domin duk abin da ta kawo mini duk wuyarsa sai na aikata mata shi..." Tun bai rufe baki ba Fulani Maryama ta yi zaraf ta ce, "Allah ya taimake ka wai me wannan mutumin yake faɗa ne, wacce Maryaman yake nufi? An ya ba mahaukaci bane?" Ga duk wanda yake wurin sai ya fahimci tsantsar rashin gaskiya a tattare da Fulani Maryama, Sarki zai yi magana Tsohon ya kalle ta yace, "Tabbas mai hali ba ya sake halinsa, a yanzu ne kika ƙara tabbatar mini da tabbas kina nan yanda na sanki Maryama." Nan take Fulani Maryama ta hau borin kunya tana zage-zage ganin haka ya sa Sarki Aminullah ya dakatar da ita ya umarci tsohon da ya ci gaba da magana. "Tun da nake ban taɓa aure ba har kawo yanzu, Salmanu shi kaɗai ne Ɗana a duniya dana mallaka don haka lokaci ya yi da zan mayar da abuna wurin zamana don na koya masa har tsubbuna kafin mutuwa ta riskeni. Salamanu Ɗana ne kuma babu wanda ya isa ya hanani tafiya da shi." Ƙananun maganganu ne suke ta shi a wurin, Jakadiya na daga gefe ta zubawa Fulani Maryama idanu zuciyarta fes don ta san babu ko tantama ranar da za a share hawayenta na mutuwar jikarta ɗaya tilo ya zo, da gayya ta sakarwa Fulani Maryama murmushi a fakaice ta mata, "An yanka ta tashi gasassa, Maryama sai a bi wani sarkin ba wannan ba." Sarki Aminullah ne ya yi gyaran murya yace, "Maryama kin ji abin da wannan mutumin yake iƙirari me za ki ce, "Fulani Maryama ta sunkuyar da kai ƙasa ta ce, "Karya yake ranka shi daɗe idan ina da wani mugun abu ma ai za ka fahimta." Sai suka ji ta fashe da kuka. Jakadiya da ke gefe ta yi zaraf ta ce, "Allah ya taimake ka tabbas abin da tsohon nan ya faɗa gaskiya ne domin na taɓa jin wani bokanta ya gaya mata tun shekaru sama da talatin baya da na yi mata rakiya wurin bokan nata. A gafarce Takawa amma tabbas ni kaina na aikata manyan laifika a gidan nan kuma kaso casa'in da tara duk akan buƙatun Maryama ne, na miƙa wuya Ranka ya daɗe duk hukuncin da ya dace a zartar a kaina, domin babu amfanin ƙin faɗar idan ma ban faɗa ba tabbas Maryama za ta tonani tun da nata asirin da ta jima da binnewa ya tonu." Fadar ce ta hautsine da hataniya kowa da abin da yake furtawa, bayan ɗan lokaci kowa ya yi tsit Sarki Aminullah ya dubi Fulani Maryama yace, "Me za ki ce game da Jakadiya." Da sauri Fulani Maryama ta ce, "Wallahi sai dai idan bakinsu ɗaya." Maryo da ke gefe ta saki murmushi tana kallon wannan diramar ta su. Jakadiya ta karkata kai tana mamakin ƙarfin hali irin na Fulani Maryama ta ce, "Idan tana musu Ranka shi daɗe a bani bani Fadawa muje ɗakin Maryama na ciro wurin da take zuwa wurin boka da su. Kuma jingar da Saif ya yi tun yana ƙarami ba da ita aka haifeshi ba..." Haka ta zayyane musu duk abin da ya faru tun ranar da suka fara zuwa wurin Marduska da ɗaukan Bayin da yake yi har mutuwar Mahaifin Maryama da askin kansu da aka yi musu. Jakadiya ta yi haka ne don ta kunyata Fulani Marayama a cikin mutane kuma a hukuntata saboda ta san sarai tun da asirinta ya tonu ita ma ba za ta barta ba don haka ta tona musu asiri gabaɗaya ta san ƙarƙari baya wuce hukuncin kisa, kuma ta saj ko ba yanzu ba idan asirinta ya tonu har Sarki Aminullah ya sa ita ta kashe masa Mahaifi hukunta kisa. Lokacin da Jakadiya ta zo a makaganar sai Fulani Maryama ta fashe da kuka ta ce, "Yanzu Jakadiya Sharrin da za ki yi mini kenan saboda na ce zan tona asirinki ke kika bawa Marigayi Mai martaba guba ya mutu." Jakadiya ta jinjina kai domin ta san za a rina... Ta kalli Fulani Maryama ta ci gaba da tonawa junansu asiri. Nan take Sarki Aminullah ya sa aka tasa ƙeyar Jakadiya har ɗakin Fulani Maryama. Duk wurin da Fulani Maryama take ajiyar kayan tsibbun ziyarar boka Marduska, Jakadiya ta sani ɗaya bayan ɗaya Fadawa suka fara fito da su sannan suka wuce can fada. _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [29/01, 14:11] Ameera Adam🌚: 70... Masarautar Zazzau. Tun da ta doshin Fadar gabanta yake faɗuwa amma babu yanda ta iya haka ta kutsa kai cikin fadar, bugun ƙirjinta ne ya tsananta sakamakon tozali da hamkimtaccen Sarki mai cike da kwarijini, mulki, haiba da kamala. Kallo ɗaya za ka yi masa ka tabbatar da tabbas an ajiye ƙwarya a gurbinta domin shigarsa ta alfarma ba ƙaramin amsar jiki da fuskarsa ta yi ba. Tana shiga duka idanun jama'ar da ke zaune a wurin suka dawo kanta, saboda ku san kowa ya hallara sai tsirarin mutanen da ba su fi mutum biyu zuwa uku ba, sakamakon wannan taron na gaggawa da ya tattara ya shafi iya iyalansa ne kawai. Abu sai da ta gaishe da Sarki Muhammad Safyan Bn Abdulwahab, sannan ta koma gefe ta yi ƙuri tana satar kallon Yarima da ke gefe ya haɗe girar sama da ta ƙasa. Babban abin da ya ƙara ɗaga hankalin Abu yanda ta ga fuskokin ahalin kowa babu walwala fuskarsa a tamke. Babu wanda ya tanka mata haka ta zaune ba ta yi aune ba sai ji ta yi hawaye na zuba a fuskarta. Tana nan zaune Fulani Maimuna da Fulani Badawiyya suka ƙaraso, Fulani Zannira da Fulani Batula duka a wurin ta same su. Sarki Muhammad Safyan ne ya yi sallama suka amsa masa gabaɗaya ban da Abu da take cike da zullimi, Sarki ya ci gaba da cewa, "Wani muhimmin labari ya same mu babu zato babu tsammani me ɗauke da sarƙaƙiya." Ya mayar da kallonsa wurin Abu ya ci gaba da jawabi, "An sanar mana daga masarautar da kike, kasancewarki sirika a gidan. Amma tabbas ba iya wannan alaƙar bace akwai wani ɓoyayyan alma'ari. Me ya sa za su aiko ki a zuwan 'yar leƙen asiri? Wace riba Aminullah zai samu bayan mun ajiye makamanmu kowa ya tafi harkar gabansa? Me ya sa zai yi mini haka, me ya sa zai cutar da ni ta hanyar da ban yi zato ba? Me ya sa zai biyo mini ta bayan gida alhalin tuni na riga da na manta da tsohuwar ƙiyayyar da ke tsakaninmu? Me ya sa zai ɗauki fansa akaina ta hanyar baƙantawa ahalina. Me ya sa za ki saka kanki a faɗan da tun kan kafin haihuwarki aka fara shi? Tabbas da kin aikata wani kuskure da kin cuci ƙuruciyarki don babu shakka ba za mu yafe miki ba." Abu shiru ta yi tana jin yanda ɗunbin tambayoyinsa suke ratsa dodon kunnenta, kamar mai gyambo a baki haka ta motsa baki ta russuna ta ce, "Allah ya taimakeka wallahi ban san duk tambayoyin da kake yi mini ba, abin da na sani shi na sanar da ku wallahi babu abin da ya kawo ni gidan nan face dalilin dana gaya muku, Allah ya kawo ni amma wallahi bani da niyyar cutar da kowa." Tun da Abu ta fara Magana Fulani Maimuna ta yi tsai da ranta tana sauraronta domin tana cikin zullumi sakamakon a daren jiya ta aika a kashe Abu amma ɗan aiken babu shi babu alamarsa har Sarki Muhammad Safyan ya haɗa taron gaggawa. Numfasawa Yarima ya yi yace, "Allah ya taimake ka ina ganin wannan ba maganar da za ta tsaya iya masarautar nan bane, Ina ganin a rubutawa Sarkin Kano wasiƙar neman izinin zuwanmu hakan zai fi domin idan aka ce abin zai tsaya a nan ba za mu samu mafita yanda ya kamata ba. Tabbas Masarautar Kano na da masaniya akan komai domin babu ko tantama akwai wata a ƙasa tun da sun turo wakikiyarsu ta zo a matsayin Baiwa." Cike da gamsuwa Sarki ya amince da maganar Yarima sannan ya ɗora da cewar, "Mun wayi gari da samun wani mummunan labari, amma wannan shi ne muhimmi a gare mu domin wancan mai sauƙi ne. Ban san lokacin da Masarautar nan ta zama haka ba, idan wannan maganar ta fita tabbas abun Allah wadai ne a gare mu ace a masarauta nan an tura wani yaje yin kisan kai. Tabbas zamu hukunta duk wanda yake da hannu acikin wannan lamarin ba za mu laminta ba domin wannan ba ƙaramin ƙalubale bane a gare mu." Jin haka ba ƙaramin firgita Fulani Maimuna ya yi ba, ita kanta Abu ba ƙaramin tsorata ta yi ba domin ta san ko shakka babu Fulani Maimuna ce ta aikata haka. Tana tsaka da tunani ta ji Sarki yace, "Zamu sa a rubuta wasiƙa zuwa Masarautar Kano idan Allah ya kaimu Juma'a mai zuwa za mu tafi can. A ci gaba da killace ta a maɓoyar sirri bana buƙatar jin wani labari mara daɗi a kanta daga baya. Masarautar Kano. Kamar wacce ruwa ya cinye haka Fulani Maryama ta yi kasaƙe kunya gabaɗaya ta dabaibayeta, sunkuyar da kai ƙasa ta yi ta fara rarrafawa wurin Takawa ta ce, "Don Allah ka yafe ni Ranka shi daɗe wallahi sharrin sheɗan ne don Allah..." Da sauri Sarki Aminullah ya katse ta da cewar, "Ya tabbata Salman ba ɗana bane kenan?" Gyaɗa masa kai Fulani Maryama ta yi ta ci gaba da cewa, "Tun lokacin na so sanar da kai sai..." A fusace Sarki Aminullah ya buga mata tsawa yana katse yace, "Bama buƙatar sake jin wata magana daga gare ki, kin cuce mu Maryama. Duk cikin matana babu wacce na bawa yarda ɗari bisa ɗari kamar ke, kin zalince mu domin kin munafurcemu kin kawo Ɗan da ba namu ba. Me muka rage ki da shi a masarautar nan? Me na yi miki da kika nemi halaka Jinina tun yana jariri." Jakadiya na jin haka ta yi farat ta ce, "Allah ya taimake ka, ka godewa wannan yarinyar." Jakadiya ta nuna Maryo da ke gefe ta ci gaba da cewa, "Ai bokan da ta sa ya yi mata aikin shi ya shaida mata baiwar da yarinyar take da ita kamar fa ƴar aljanu yarinyar duk wani siddabaru ta iya..." Sarki Aminullah ne ya dakatar da Jakadiya tuni ta kama kanta don ta lura babu alamun wasa a tattare da shi, wasa-wasa tun ana ganin Jakadiya na abu cikin hankali tana ta tona asirinsu sai abun ya fara zarce hankali domi zance take ta saki babu hankali babu fasali. Sarki Aminullah na shirin magana kamar saukar ruwan sama sai ganin mutum suka tsidik a gabansu cikin mummunar shiga kamar goggon biri, jikinsa gabaɗaya duk gashi. Ba ƙaramin tsorata suka yi ba don har sai da wasu suka fara ja da baya, Boka Marduska ne ya bayyana da kayan tsafinsa a fusace ya nuna Fulani Maryama yace, "Kin karya sharaɗinmu da ke dama na gaya miki duk ranar da kika fito da kayan tsafinmu a idon jama'a kashinki ya bushe, rufin asirinki shine namu asararriya domin kin tozarta aljanun suke yi miki aiki a idon jama'a dole ne su ɗauki mataki a kanki ke da ƴar korarki waccen la'anniyar, hukuncinki razanarwar fatalwa har ƙarshen rayuwarki." Boka Marduska ya faɗa yana nuna Jakadiya da wani baƙin ganye, Ihu Jakadiya ta zuba ta fara tsalle tana yagar kayan jikinta tana cewa, "Wayyo! Ku taimaka mini zai kashe ni ga shi nan da wuƙa zai yanka ni wayyo!" Ganin haka ya sa Sarki Aminullah ya yi wa wasu Fadawa magana suka kama Jakadiya suka yi gidan Turu (Gidan mahaukata) da ita, Marduska ya koma wurin Fulani Maryama yace, "Ke ma na ki hukuncin zai biyo bayanki domin ba za ki ci bulus ba." Yana shirin ɓacewa Farin tsohon nan ya yi dariya yace, "Ka ɗauka kaima za ka sha a banza ne, idan maye ya manta uwar Ɗa ba za ta manta ba. Ka tuna Boka Ƙurgen tsohon Maigidanka da ka ci amanarsa a shekarun baya? Dama na ci alwashin ba zan taɓa raga maka ba kawai na baka dama ne amma tun da ka kawo kanka ka rage mini aiki." Hankalin Marduska ba ƙaramin tashi ya yi ba, yana shirin guduwa Tsohon ya hura masa wata iska yace, "Ku bishi har can makwancinsa ku hallakashi, amma ku tabbatar da kun azabtar da shi da azaba mai tsanani kafin mutuwarsa." Tun tsohon bai gama magana ba Marduska ya fasa uwar ƙara har sai da wasu daga cikin mutanen wurin suka toshe kunnuwansu saboda rashin daɗin sautin, nan take ya ɓace daga wurin sannan Tsohon ya mayar da kallonsa wurin Sarki Aminullah yace, "Ba zama na zo yi ba na zo tafiya da Ɗana ne tun da kuma na bayyana maka kaina da matsayina shi kenan, idan kuma kana buƙatar taimakona zan iya taimaka maka domin ka yi mino halacci ka kula mini da Ɗana yanda ya kamata." Sarki Aminullah ya sauke ajiyar zuciya yace, "Babu inda za ka tafi da shi domin tafiyarka da shi ba alkairi bane, har yanzu ina jin Salman a matsayin Ɗana saboda duk abin da ya faru ba laifinsa bane, don haka ba za ka tafi da shi ka dilmiyar da shi kamar yanda kaima ka dulmiya."Tsohon ya ƙurawa Takawa ido yace, "Ba na son mu yi rabuwar rashin daraja ina ganin girmanka karka bari na cutar da kai..."Tun bai rufe baki ba Sarki Aminullah ya katse shi da cewar, "Babu mai cutar da wani bawa sai abin da Allah ya nufa, don haka ƙasƙantacce da kai zai iya cutar da ni ba."Nuno Sarki Aminullah ya yi da niyyar cutar da shi kamar ya sani ya yi a'uziya ya fara karatanto masa ayoyin tsari. Duk yanda Tsohon ya so cutar da Sarki ya kasa domin duk wani siddabarunsa ya kasa aiwatarwa, Salman da ke gefe a fusace ya juyo ta sokawa Tsohon ƙaho a wuya nan take Tsohon ya fara fita hayyacinsa. A fusace Sarki Aminullah ya miƙe ya wanke Salman da mari yana cewa, "Kana da hankali kuwa Salman me yake damunka?" Salman ya wurgar da ƙahon gefe yace, "Ranka shi daɗe sauran me ya rage mutumin nan idan mun barshi matsala zai zame mana musamman ni da yake so ƙarfi da yaji ya ɗauke ni, idan na barshi baƙin dajin nan zai mayar da ni." Jikin mutanen wurin ba ƙaramin sanyi ya yi hatta Fulani Maryama sai da ta ji ba daɗi domin duk lalacewar Ubansa bata taɓa tsammanin Salman zai iya kisa ba. Tsoro ne ya kamata domin gani take ita ma kamar zai dawo kanta ya hallaka ta. Wannan abin da Salman ya yi ne ya sanyaya jikin Sarki Aminullah don haka ya sa aka ɗauke gawar Tsohon ya bada umarnin da a haƙa rami a binneshi ba tare da wanka ko sutura ba, daga ƙarshe ya warware igiyar aurensa da Fulani Maryama, Kuka ta fashe masa da shi tana dana sani da nadama domin wannan ba ƙaramin abin kunya bane a gare ta, rarrafawa ta yi wurin Fulani Zaliha ta dafa ƙafafuwanta tana cewa, "Don Allah Zaliha ki yi masa magana ya mayar dani wallahi zai ji maganarki don Allah ki yafe mini keda Saif wallahi sharrin shaiɗan ne, kuskure ne ba zan ƙara ba." Ba ƙaramin tausayi ta bawa Fulani Zaliha ba domin saki a lokacin da baka tsammace shi ba na da matuƙar zafi, Fulani Zaliha ta dafa Fulani Maryama ta ce, "Ki yi haƙuri Yaya haka Allah ya ƙaddara miki, kuma ni da Saif mun yafe miki amma kin san ba a mayar da mace a saki uku matuƙar ba wani auren ta yi ba." Kamar Mahaukayi haka ta miƙe tsaye ta ce, "Wallahi zan yi indai zai mayar da ni ko waye zan aure shi." Yanda ta ruɗe take ruwan hawaye har sai da ta ɗan karya zuciyar mutane da yawa domin kowa ya san irin soyayyar da Fulani Maryama take yi wa Sarki Aminullah. Shi kansa Salman sai ya ji ba daɗi dukda matsanancin haushinta yake ji kasancewar ta yi masa iyaka da hayewa karagar mulki, amma ko sama da ƙasa za ta haɗe baya jin zai iya barwa Saif kujerar Masarautar Kano. Sarki Aminullah ya kalli Fulani Maryama yace, "Za mu yi miki alfarmar ci gaba da zama a cikin ɗakinki amma muddin muka lura da hatsaniya ko tashin hankali tabbas za mu ɗauki mataki a kai. Abin da kika aikata kin cancanci zuwa gidan horo amma darajar 'ya'yan dake tsakaninmu ba za mu iya aika ki ba domin idan mun yi haka kamar mun tozarta kanmu ne." Sarki Aminullah na gama faɗar haka ya kawo ƙarshen zaman taron tare ta yin nasiha mai ratsa jiki da jan kunne akan kiyaye dokokin Ubangiji. Kafin wani lokaci tuni fadar ta yi tsit kowa ya watsa cikin gida aka samu zancen tattaunawa. Masu kwashewa Fulani Maryama na yi masu yi mata addu'a suma suna yi. Kafin tashin taron sai da Sarki Aminullah ya ƙara jaddada cewar Salman na nan a matsayin Ɗansa kuma ko da wasa ya ji wani zance na ɓilla zau ɗauki mummunan mataki a kansu. _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI_ [30/01, 10:57] Ameera Adam🌚: 71... Masarauatar Kano. Abin duniya goma da ashirin ne ya haɗewa Sarki Aminullah domin idan yace ba ya son Maryama ya yi ƙarya, ita ce matarsa ta fari uwar 'ya'yansa ya bata dukkan yarda amma ta rasa da me za ta saka masa sai wannan miyagun ayyukan, tabbas lamarin akwai cin zuciya, juwa ce ta fara ɗaukansa don haka ya nemi wuri ya zauna. A yanayin da yake yana buƙatar mai tausarsa ta bashi baki amma wa zai kira? Gani yake duk wacce ya kira za ta ga ya yi kiranta ne saboda abin da ya faru. Yana nan zaune Fulani Zaliha da sauran matansa suka shiga kamar sun san abin da yake ransa. Fulani Bilkisu ce ta fara magana kasancewar ita ce matarsa ta biyu ita ce babba tun da babu Fulani Maryama. Ruwa mai sanyi ta ɗebo masa na cikin randa ta miƙa masa, bai musa mata ba ya karɓa yasha sannan ta fara da cewa,"Allah ya taimake ka ya baka yawan rai Sarki mai adalci Sarkin talakawa Sarki mai karamci da mutumci." Sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya gyaɗa mata kai ta ci gaba da magana, "Allah ya taimake ka a madadina da na iyalanka baki ɗaya muna ƙara jajanta maka da baka haƙuri bisa abin da ya faru." Kamar jira yake murya a shaƙe yace, "Me na yi wa Maryama da za ta saka mini da haka?" Fulani Zaliha ta karɓe zance da cewar, "Baka yi mata komai ba! Haka zalika karka ɗora damuwa da tashin hankali a zuciyarka. Ina me bawa Sarki haƙuri domin wannan yana daga cikin shafin jarrabawarka. Allah ya gwada kai ne domin ya jarabci imaninka." Sarki Aminullah ya miƙe tsaye sai da ya yi taku biyu yace, "Tabbas haka ne kuma muna godiya ga Allah (S.W.T) akan abin da ya jarabce mu da shi." Nan suka ci gaba da bashi baki sai da suka ga ya huce sosai sannan suka yi masa sallama suka fice kowacce ta wuce sashenta. Kwana biyu a tsakani sai ga saƙo daga Masarautar Zazzau lamarin ba ƙaramin girgiza shi ya yi ba domin banza bata kai zoma kasuwa. Bayan da Sanƙira ya gama karantawa Sarki Aminulla numfasawa ya yi ya kalli Ɗan aiken yace, "Ku bashi kyakkyawan Masauki zuwa wayewar gari." Ɗan aiken ya ɗago ya russhnar da kai ƙasa yace, "Allah ya taimake ka umarnine daga ubangidana cewar kar na kai wayewar a gari a Masarautar nan." Ƙura masa ido Sarki Aminullah ya yi yana son gano wani abu daga Bafaden amma ya gaza ganowa, Sarki Amullah ya ya kalli Sanƙira yace, "A rubutu martanin amincewa zuwansa sannan a bawa Bafaden guzuri kafin tafiyarsa." Gabaɗaya fadawa suka ruɗe da cewar, "Godiya yake Sarkin Musulunci, godiya yake Ɗantoron giwa, sikari ba ka yi farin banza ba, Sanƙira ya amsa shi ma ya yi godiya." "Ka kwantar da hankalinka Ranka shi daɗe in sha Allahu babu abin da zai faru sai alheri, wataƙila akwai muhimmin abin da zai kawo shi amma na tabbata ba tashin hankali bane, da tashin hankali ba zai aiko da ɗan aike ba." Sarki Aminulla ya jinjina kai domin yana jin daɗin yanda kodayaushe Fulani Zaliha take ƙarfafa masa gwiwa akan abubuwa da dama, kallonta ya yi ya ji kunyar ta duk ta kamashi. Dafa kafaɗarta ya yi da hannu biyu yace, "Zaliha!" Yanda ya kira ta shi zai tabbatar maka da muhimmancin maganar da zai furta mata. "Don Allah ki yafe mini ke da Saif domin na cutar da ku na zalince ku. Har yanzu zargin kaina nake kamar ban cancanci zama shugaban Al'umma ba tun da a tsakanin iyalina ma ban kwatanta adal..." Hannu ta sa ta rufe masa baki sai kuma ya sakar masa murmushi da cewar. "Hakan bai kyautu daga gare ka ba domin da a ce magauta za su ji wannan kalaman naka da abin da suke buƙata ne ya samu, wani ya yi rawa ballantana Ɗan makaɗi." Waro ido waje ya yi yace, "Waye haka?" "Wacce ta yi mini iyaka da farincikina ma yafe mata ballanta kai? Dama tun can bamu riƙe ka ba. Ɗan'adam ajizi ne ko kana nufin Allah ba zai jarrabce ka ba?" Matse mata baki ya yi yace, "Ni dai ban ce ba kar haɗani da Ubangiji." Gabaɗaya suka saka dariya Fulani Zaliha ta ce, "Ka san mene ne babban abin da ya fi faranta mini?" Sarki Aminullah ya girgiza mata kai ta ci gaba da cewa, "Da Allah ya bayyana gaskiya ina da ƙarashen numfashi, na ji daɗi da Maryama ta wanke mu dangane da kisan da ake zargin na tura Maryo ta yi maka. Tabbas wannan babban farinciki ne mun godewa Allah." Rungumota ya yi yana cewa, "Mu ajiye wannan maganar saboda kunyarta nake ji." "Mun barta, amma fa dole a nemi maganin lalurarka domin ko ba a faɗa ba Maryama ta yi mana jirwaye mai kamar wanka, don haka tun da lalurar ta cuta bace ba za mu ci gaba da zura maka ido ba." Haɓarta ya tallaɓo da hannu biyu yace, " Fillo wai yaushe kika fitsare idonki? Mamaki nake wai yaushe Zalihata ta zama haka." Fulani Zaliha ta yi dariya ta ce, "Tun ranar da ka fitsarar da ni." Yana shirin magana Fulani Zaliha ta ci gaba da yi masa magana. "Allah da gaske na ke a da mun ɗauka lalaurar daga Allah ce tun da har magunguna an nema ba a dace ba amma yanzu tun da mun fahimci sihiri ne mai zai hana a nemi magani tun da ai mun yi haƙuri shekara nawa muna tare a haka tun ba ma ni ba da aka cuceni, tun da ƙuruciyata ina jin na haifi Saif ko shekara uku bai yi ba ka haɗu da matsalar. Ni an ya ma ban fasa yafiyar da na yi wa Maryama ba." Ta faɗa cikin zolawa ai kuwa Sarki Aminullah mai zai yi ba dariya ba. Idan ka ga yanda yake yi wa iyalaninsa sai ka rantse ba wani mai sarauta bane. Ya dube ta yana riƙe kunnuwa sa biyu yace, "Kaina bisa wuya zan sa a nemar mini magani ko dan na wuce gori, ita kuma Maryama ba zan ce komai ba sai yanda kika ce." Fulani Zaliha ta ce, "To a hanzarta gaskiya tun kafin na yi maka bore! Yauwa Ranka shi daɗe na ke ganin mai zai hana yaron nan akai masa matarsa ina ganin take-takensa sai hanya-hanya yake yi mini da alama wallahi matarsa yake son akai masa kawai don bai fito ya faɗa bane." Sarki Aminullah gabaɗaya ya shafa'a da zancen Saif saboda ruguntsimin da aka yi, jinjina kai ya yi yace, "Haka ne tun da yau talata mu bari ranar Juma'a ranar albarka a kai masa matarsa ina ga haka ya fi." Fulani Zalina ta amsa masa sannan ta sauya murya zuwa damuwa idonta na cikowa da hawaye ta ce, "Allah Sarki Abu ko suna wacce duniyar oho? Allah ya tsare su a duk inda suke." Gabaɗaya suka amsa da Amin, shi kansa Sarki Aminulla duk sai ya ji babu daɗi. Fulani Zaliha da kanta ta rinƙa gyaran amarya, Maryo ba ƙaramin kunya take ji ba domin ba wani sabo ta yi da ita ba. Ba kamar Abu da take 'yar ɗakinta ba, ita kuwa Fulani Zaliha nunawa ta yi kamar ba ta lura da abin da Maryo take yi ba, Inna Habi ba ƙaramin daɗi take ji ba domin duk wanda ya ƙaunaci na ka kaima abin ka ƙaunace shi ne tana jin daɗi yanda Fulani Zaliha take ƙaunar 'yanmatan nata biyu. Saif tun da ya ga Maryo a sashen Mahaifiyar yaje zarya shine shiga ɗauko wannan mayar da wannan, yanzu ma Fulani Zaliha na zaune tana shafawa Maryo lalle a jiki ya shiga, lallan ba ƙaramin kyau ya yi mata a jiki ba abinka da farar fata jikinta sai sheƙi yake, daga ita sai ɗaurin ƙirji saboda gyaran da take yi mata kar ya ɓata kayan jikinta. Duk zaryar da Saif yake a tsakanin sauran ɗakunan yake yi wannan karon ne ya yi shahadar kutsa kai cikin ɗakin ya wayance da ɗaukan abu. Saif yana shiga har tuntuɓe yake yi yana waigen Maryo. Gabaɗaya kunya ce ta kamata ta sunkuyar da kai ƙasa, yana shiga ɗakin ya maƙale a bango yana leƙensu jin shirun ya yi yawa ya sa Fulani Zaliha ta ce, "Idan ka ga leƙen ka zo ka wuce tun ranka bai ɓaci ba." Kamar sabon munafuki haka Saif ya wuce sumi-sumi yana sunne kai ƙasa. Yana fita Fulani Zaliha ta saki murmushi tana mamakin wai yau Saifullahinta ne zai yi mata dabara. RANAR JUMA'A Duk abin da ya kamata a yi na gyaran ɗaki da duk wanda ake yi wa amarya an riga da an yi wa Maryo dare kawai ake jira ya yi akai amayar ɗakin mijinta. Tarba mai kyau Sarki Aminullah ya sa aka shiryawa baƙinsa matafiya daga ƙasar Zazzau, abinciccika aka yi kala-kala tare da tanadar kayan ciye-ciye da shaye-shaye. Sarki Muhammad Safyan shi da Yarima suka taho da ɗan wurin Fulani Zannira mai suna Umar, sai fadawansa da masu tsaronsa da masu yi masa hidima. A fadar Sarki Aminullah aka yi musu masauki sai da suka ci suka sha kamar wani abu bai taɓa shiga tsakanin Sarakunan biyu ba, sannan Sarki Muhammad Safyan ya bada umarnin a fito da Abu da take cen cikin keken doki hannunta ɗauke da Naufal, tun da ta ji sun sauka a Masarautar Kano take jin kamar ta yi tsuntsuwa amma ina babu wannan halin saboda yanda masu tsaronta suka kafa suka tsare. Saif yana zaune a a gefe bayan sun gaisa da su Yarima yana shirin tashi ya ga an shigo da Abu cikin wulaƙantacciyar shigar kayan Bayi. Wata irin saranda ya yi bakinsa na rawa yace, "Abu ke ce." Abu na jin haka ta fashe da wani irin kuka ta miƙa masa Naufa tana cewa, "Don Allah ka yafe mini Saif wallahi ban tabbatar da na aikata kuskure ba sai na masifu suka fara afka mini." Jikinsa na rawa ya sa hannu ya karɓi Naufal yana kallon yanda yaron ya yi wayo sosai kammaninsa dana Mahaifinsa sun ƙara fitowa. Sarki Muhammad Safyan ne ya katse musu magana sannan suka nemi wuri suka zauna, Sarki Muhamma d Safyan ya kalli Sarki Aminullah cikin wata irin murya yace, "Aminullah ta fe na ke da muhimmiyar magana ba da wasa na zo, a baya ka san irin abin da yake tsakaninmu amma ba wannan ne a gabana ba ina san ina. Ina tafe da tuhuma a gare ka kuma ina fatan zaka bani haɗin kai domin na fi som yanda muka lafiya a rabu lafiya." Fatan alheri 🥰 _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [31/01, 21:41] Ameera Adam🌚: 72... Sarki Aminullah tattara hankalinsa ya yi wurin Sarki Muhammad Safyan sannan yace, "Wannan wace maganace ina fatan ba za ta ƙetare iyaka ba." Ya yi maganar cike isa irin ta goggun Sarakunan da sarauta ta zame musu jinin jikinsu. Sarki Muhammad Safyan ya saki murmushin taici yana ƙoƙarin danne ɓacin ran da yake taso masa, mayar da kallonsa ya yi wurin Abu dake gefe sannan ya zaro sarƙar hannunsa wacce Yarima ya karɓa yace, "Wannan Sarƙar kince baki ita aka yi, yarinyar da take cikin Masarautar nan ce ta baki, Ina 'yar uwar Sarƙar da mai sarƙar suke? Me ya sa ka killace mini 'ya'ya tsawon shekaru? Me ya sa za ka ɗau fansa ta wannan sigar. Tabbas wannan Sarƙar ta Hasana ce ina ta Usaina da Usainar suke?" Sarki Aminullah ya dube shi cikin rashin Fahimta yace, "Ya kamata ka fito a mutum ka yi mini bayanin da zan gane abin kake nufi." Sarki Muhammad Safyan ya tamke fuska kamar ta fusataccen bijimin Sa yace, "An sace mini 'Ya'ya shekara goma sha Takwas baya! Wannan sarƙar da kake gani ba guda ɗaya bace guda uku rak aka sassaƙar mini su masu ɗauke da tambarin Masarautar Zazzau." Sarki Aminullah ya yi murmushin yaƙe yace, "Ta wannan sigar ka ɓullo? Muhammad Safyan!" Sarki Aminullah ya kirashi da wata irin kausasshiyar murya wacce take nuna tabbas maganarsa babu alamun wasa a ciki. Ya ci gaba da cewa, "A yanzu shekaru sun ƙaru girma ya ƙara kama mu bana tunanin abin da ya faru a baya zamu ƙara maimaita shi domin jiya ba yau bane. Wacce riba zan samu idan na rabaka da 'ya'yanka bayan nima na haifa, don Allah idan akwai abin da ya kawo ka ya kamata mu tattauna ba wannan ba." Sarki Muhammad Safyan ya harzuƙa cikin ɓacin rai yace, "Aminullah wannan karon a Uba na zo gare ka ba Sarkin Zazzau ba! Ina tsaye a matsayin Uban da zai tsaya kai da fata domin ƙwato haƙƙin ƴaƴansa. Ka gaya mini ina ka kai mini ƴaƴana?" Sarki Muhammad Safyan ya yi maganar a tsawace har sai da Abu ta tsora. Sarki Aminullah Ya jinjina kai yace, "Lallai da alama tura za ta fara kai bango amma da alama wankin hula zai iya kaika dare..." Da sauri Sarki Safyan ya katse Sarki Aminullah. Ganin lamarin na nema yamutsa hazo ya sa Saif ya tausasa harshe cikin kwantar da murya yace, "Allah ya taimake ka har yanzu bamu fahimci maganar da kake yi ba, mai zai hana ka yi wa Mai martaba..." Sarki Muhammad Safyan ya bugawa Saif tsawa yana cewa, "Dakata yaro! Wannan ba maganarka bace karka sake ka ƙara saka mana baki." Saif babu yanda ya iya haka ya ja bakinsa ya tsuke saboda da alama iyayen nasu biyu sun ɗauki zafi. Ganin an kara samun saɓanin rashin fahimta ya sa Sarki Muhammad Safyan ya kalli Abu ya buga mata tsawa yana faɗin, "Ke wa kika ce ya baki sarƙar nan?" A firgice Abu ta ce, "Wallahi Maryo ce kuma da kanta ta bani ana gobe zan tafi." Ƙirjin Saif ne ya buga da wani irin bugu mai tsanani. Sarki Aminullah ya kalleta cikin damuwa a zuciyarsa yana ayyanawa wannan wacce yarinyar ce da tun zuwanta gidansa ake ta samun matsaloli. Sarki Aminullah kallon Saif ya yi yace,"Maza ka je ka kira mini Matarka da Mahaifiyarta." Kamar jira Saif yake da sauri ya fita ya nufi sashen Fulani Maryama hannunsa ɗauke da Naufal, yana shiga wani irin wari ya fara dukan hancinsa da sauri ya tsartar da yawu yana rufe hanci. A gaggauce ya isarwa da Inna Habi saƙon Maimartaba ya fita yana waigen ɗakin fulani Maryama da tsirarun ƙuɗaje suka fara yanyame ɗakin. Inna Habi tun da suka samu saƙon kiran Sarki Aminullah suka yi hamdala domin warin da suka wayi gari da samunsa ba ƙaramin cika musu ciki ya yi ba. Ba su kawo komai ba amma kuma jin kiran ya basu mamaki domin a iya saninsu Sarki idan ya yi baƙi baya kiran wasu daga cikin gida zuwa Fada. Suna shiga tun daga nesa Maryo ta hango Abu a zaune sai dai duk ta yi baƙi ta rame. Kuka ta fashe da shi ta ƙarasa ta rungume Abu tana ci gaba da rusa kuka. Za ta fara magana Sarki Aminullah ya katse ta cewar, "Ya isa haka domin akwai muhimmiyar maganar da ke tafe da mu." Fadar ce ta tsit Maryo ta hau wara ido domin ba ƙaramin tsorata ta yi ba tana tsoron kada a ce mata Abu bata dawo da Naufal ba. Sarki Muhammad Safyan ƙurawa Maryo ido ya yi gabansa na faɗuwa, ita kanta Abu sai yanzu ta lura da wani abu. Tun ranar da ta fara tozali da Yarima ta rasa a inda ta san mai yanayin kamarsa, tsoro da fargabarsa ya hanata zama ta ƙare masa kallo. Sarki Aminullah ya miƙawa Maryo sarƙar da ya karɓa ya gani daga hannun Sarkin Zazzau. Da sauri ta karɓa tana murmushi ta ce, "Abu yanzu sai da kika cire sarƙar nan da kin ɓatar min fa kinsan ko Inna ba ta san na baki ba." Sarki Muhammad Safyan ya zuba mata ido yana ganin yanda take magana, amma gudin kar ya yi hanzari ya yi shiru. Sarki Aminullah ya katse Maryo da cewar, "Bama son sakarci a wurin nan." Shiru Maryo ta yi Sarki Aminullah ya ci gaba da cewa, "A ina kika samo sarƙar nan." Maryo ta yi shiru ta kalli Inna Habi domin ita kanta ba za ta ce ga inda ta samo ta ba abu ɗaya ta sani Inna na bawa wannan sarƙar muhimminci. Maryo ta sunkuyar da kai ta ce, "Allah ya taimake ka Inna ce ta siya mini tun ina yarinya." Kallon da Sarki Aminullah ya yi wa Inna Habi shi ya tabbatar mata da yana buƙatar ƙarin bayani daga gare ta don haka ta russunar da kai ƙasa ta ce, "Allah ya taimake ka kamar yanda na gaya maka a baya na tsinci yarinyar nan, a ranar da na tsince ta tare da wannan sarƙar na tsince ta sai wani murjani." Sarki Muhammad Safyan ya yi karaf yace, "Kika tsinceta ita kaɗai ko kika tsince su." Inna Habi ta ce, "Allah ya taimake ka Ita kaɗai na tsinta tana jaririya." Sarki Muhammad Safyan ya yi kabbara yana cewa, "Tabbas Allah shi ne abin godiya amma ya tabbata wannan yarinyar jinina ce, zo mu ga idonki matuƙar kina da tawadar Allah a idonki tabbas kece Hasana." Maryo da kanta ya gama ɗaurewa da waɗannan mutane masu dajara sai wurga idanu take tana neman da wacce yake magana. Sarki Muhammad Safyan da kansa ya tako wurin Maryo ya ɗago da kanta yana kallon ƙwayar idonta, Maryo sai gani ta yi ya rungumeta yana furta, "Alhamdullah Allah na gode maka da ka bayyana mini ɗaya daga cikin ƴaƴana da na rasa." Sai kuma ya raunana murya yace, "Ko a ina zan samu Usaina? Ina ma Allah zai bayyana mini ita kamar yanda nake ganinki a gabana." Daga bayansa ya ji ance. "Ita ma ka same ta domin ita ma tana nan da ranta." Sarki Aminullah ya faɗa murya ɗauke da ƙwarin gwiwa. Da sauri Sarki Muhamma Safyan ya miƙe ya ƙarasa wurin Sarki Aminullah yace, "Don Allah tana ina a wane wurin take." Sarki Aminullah yace, "Idan har wannna Hasana ce to babu ko tantama Matar Maleek ita ce Usaina." "Waye Maleek don Allah gaya mini shi, tabbas wannan Hasana ce wallahi Usaina tana da cindo a ƙafarta." Sarkin Zazzau ya yi maganar cikin ɗoki. Sarki Aminullah ya yi murmushi yace, "Ɗan ƙanwata ne yake aurenta." Sarkin Zazzau cikin farinciki yace, "Masha Allah yanzu yau ni nake jin daddaɗan labari akan tagwayena, Allah me iko yanzu Usaina har ta yi aure?" Sarki Aminullah ya yi dariya mai sauti yace, "Kana mamaki ne? Ita ma ta gabanka ga mijinta nan." Kunya ce ta kama Maryo da sauri ta sunne kai ƙasa tana murnushi. Haka kawai ta fara jin wani irin farinciki na ziyartarta ganin abin take kamar a mafarki wai yau ita ce take gaban Mahaifinta. Sarki Muhammad Safyan yace, "Ikon Allah ka ce da na yi abin kunya a gaban Siriki." Cikin zolaya Sarki Aminullah yace, "Idan baka yi a gaban wannan sirikin ba ka yi ai a gabana." Kallon rashin fahimta Sarkin Zazzau ya yi masa, Sarki Aminullah da ya fahimci haka sai yace, "Ina nufin ka yi abin kunya a gabana tun da ni sirikinka ne Ɗan wurina ne yake aurenta." Sarkin Zazzau ya saki baki da mamaki yace, "An ya Aminullah babu lauje cikin naɗi kuwa?" Sarki Aminullah sai yanzu maganarsa ta tsawon shekaru ta faɗo masa da ya taɓa gayawa Sarkin Zazzau lokacin da suka rabu baram-baram dutse a hannun riga. Murmushi ya yi ya kallin Sarkin Zazzau yace, "Dama na gaya maka cikin ikon Allah auratayya sai ta haɗa zuri'armu ta yanda duk wani rashin jituwa ya kau daga gare mu. Allah ne ya yi wannan haɗin kuma shi ya barwa kansa sanin alherin da ke tattare da haka." Abu da ke gefe wani irin daɗi ta ji domin ta san ko babu komai ta goge tabon ɓacin ran da ta dasawa Maryo a zuciyarta. Ko ba komai tafiyarta ta kawo abubuwan alheri da dama, silar tafiyarta ya sa Saif ya auri Maryo. Uwa Uba kuma ta sanadinta Maryo ta sadu da iyayenta. Har lokacin Sarkin Zazzau bai gama amincewa da a rashin sani aka yi auren Maryo da Saif ba, gani yake kamar yana da sa hannu wurin sace masa ƴaƴansa. Sai da aka bashi labarin Maryo tun daga ranar da Inna Habi ta tsinceta har zuwanta Masarautar Adamawa da abubuwan da ya faru. Ya matuƙar jinjinawa Inna Habi akan namijin ƙoƙarin da ta yi wurin rainon Maryo da yanda ta bata kulawar da ta dace. Nan take hira ta ɓarke aka ci gaba da ciye-ciye da shaye-shaye. Maryo na hannun Mahaifinta kamar wani zai ƙwace masa ita. Anan ya fahimci irin tsantsar shaƙuwar da ke tsakani Abu da Maryo abin ba ƙaramin birgeshi ya yi ba. Maryo tana son ta karɓi Naufal amma ta rasa ya zata yi saboda wata irin kunyar Saif da take ji, shi kuwa da sun haɗa ido zai kashe mata ido ya sakar mata murmushi. A wannan zaman ma sai da Abu ta jaddada maganarta na saki a wurin Saif don har ga Allah ta cirewa zuciyarta son ci gaba da zama da shi. Shiru Saif ya yi yana nazari ya riski muryar Sarki Aminullah yana cewa, "Saif ina gani ka sauwaƙewa yarinyar nan zai fi domin kana gani ta sanadin rashin sakin da baka yi mata bane har ta guje mana ta yi tafiya mai nisa, shi zaman aure na mutum biyu ne idan ɗaya ya nuna ba ya yi shi kenan." Saif ya gyaɗa kai sannan yace, "A yi mini afuwa ranka shi daɗe zan aiwatar da abin da take buƙata amma ba zan iya aiwatarwa yanzu ba." Hakan ba ƙaramin daɗi ya yi wa Sarakunan biyu ba, Sarkin Zazzau har a zuciyarsa ya ji ya aminta da nutsuwar Saif. Daga haka Sarki Aminullah ya sallami yaran ya rage sai sarakunan biyu. "Lallai Fulani Badawiyya a kwai murna a lokacin da ta yi tozali da ƴaƴanta. Don haka da Hasana za mu tafi kafin saƙo ya isa Ƙasar Adamawa." Cewar Mahaifin Maryo. "Ai kuwa ba za ta bika yai ba domin yau za a kaita ɗakin mijinta amarya ce ko tarewa bata taɓa yi ba." Ɓata fuska Sarkin Zazzau ya yi ai kuwa Sarki Aminullah yace, "Bar cika kana batsewa duk abinka, Maryo ba za ta bika ba domin yau za mu kaiwa Ango amaryarsa idan ba so kake mu yi masa ta leƙo ta koma ba. Ka bari lokacin da ƴan Adamawa suka ƙaraso sai a haɗasu gabaɗaya a tafi da su ita ma Mahaifiyarsh ta fi gasgatawa." Da wannan shawarar Sarkin zazzau ya amince akan bayan sati guda za su ƙara dawowa. Da farko ya nuna a bari ya kawo Mahaifiyar yarinyar kafin tariyar Maryo amma Sarki Aminullah ya ƙi amincewa domin ya nuna masa an jima da ɗaurin auren tariya ce ba ta tare da wuri ba. _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [10/02, 20:04] Ameera Adam🌚: 73... Duk irin baƙar wahalar da Abu ta sha sai da ta bawa su Maryo labari tun daga farko har ƙarshe, Inna Habi ba ƙaramin tausayawa 'yarta ta yi ba sakamakon yanda ta sanar da su da irin azabar da ta sha kafin zuwanta Masarautar Zazzau har zuwa miyagun ayyukan da Fulani Maimuna take saka ta akan Yariman Masarautar. Maryo ban da kuka babu abin da take yi don ƴar uwar tata ba ƙaramin rama ta yi ba ta lalace ta yi wani irin baƙi kamar wacce ta yi shekara da shekaru tana jinya. Maryo ce ta kalleta fuskar shaɓe-sheɓe da hawaye ta ce, "Abu me ya sa kika aikata wannan kuskuren? Yanzu da mutuwa ta riske ki me za ki gayawa Ubangiji dangane da haƙƙin mijinki da dana Yarona?" Abu ta goge hawayen idonta ta ce, "Maryo ba zan iya ci gaba da zama da Saif ba kin san yanda nake tun ina ƙarama, ada ma na ɗauki aurena da shi a matsayin ƙaddara da rabo wanda dole babu yanda zan yi har sai Naufal ya fito a tsakanina da shi. Babu yanda ban yi da ke ba akan ki amince da aurensa shi ya sauwaƙe mini amma gabaɗayanku kuka shafawa idonku toka, alhalin ko makaho ya san irin tsantsar ƙaunar da kuke yi wa junanku. Maryo!" Abu ta ambata da wata irin murya har sai da Inna Habi ta ɗago ta kalleta ta ci gaba da cewa, "Fitar da na yi, na yi ne bisa tsautsauyi sai ga shi Allah ya kawo alheri a cikinta. Tabbas na san na aikata kuskure wanda har abada ba zan sake aikata makamancinsa ba, Maryo ashe ba banza ba miskilancinki da son girmanki ba, duk sun samo asali ne sakamakon ku jinin Masarauatar Zazzaune!" Da sauri Maryo ta ɗaka mata duka a cinya tana wurga mata hararar wasa ta ce, "Bana son iskanci fa idan ba haka ba yasin na sa mayar da ke Baiwata." Abu ta saki dariya ta ce, "Idan ke baki mayar da ni ba ai wancen sanganrtaccen yayan naki ya mayar da ni, wallahi karki ga baƙar wahalar da ya bani hatta tsawa idan ya yi sai hanjin cikina ya kaɗa mugu kawai yana yawo tsalo-tsalo kamar tazuge." Maryo ta ƙunshe dariyarta ta ce, "Ɗan uwan nawa ne mugu a gabana Abu." Abu ta watsa mata harara ta ce, "Yoo meye idan ba mugun ba, wai ma tsaya kina nufin ƴan ubancin za ki gwada mini?" Maryo ta riƙe kunnuwanta biyu ta ce, "Ni na isa na ce wadon Sarki ba tazuge." Abu ta saki dariya ta ce, "Kin isa mana idan aka naɗa mijinki ya zama Sarki abin da ya fi tazuge ma za ki iya cewa babu. Meye a ciki kai da kaya ai duk mallakar wuya ne..." Maryo ta bige bakin Abu saboda kunyar da ta ji don Inna Habi na gefe tana jin su, ta harari Abu ta ce, "Wallahi ke dai bakinki ba shi da linzami ashe dai mai hali baya fasa halinsa." Gabaɗaya suka saka dariya. A hankali Abu ta fara tambayar su Inna Habi bayan tafiyarta abubuan da suka faru, nan take suka bata labari tun daga farko har ƙarshe har zuwa auren Maleek da Maryo da za a yi da kuma aurenta da Saif. Anan ta fahimci Maryo Amaryace shakaf ko tare wa bata yi ba. Sun jima suna hira Sannan Abu ta dubi Maryo ta ce, "Maryo maza je ki karɓo mini yarona a wurin Mijinki na san yanzu ya fara jin yunwa." Duk yanda Maryo ta so ƙin zuwa fir Abu ta ƙi bata dama babu yanda ta iya ta fita suwa sashen Fulani Zaliha. Bayan ta gaida Fulani kai tsaye ta ce, "Allah ya taimake ki dama Abu ce ta aiko a duba ko Naufal ya tashi daga bacci." Maryo ta faɗi haka ne don kar Fulani Zaliha ta yi zaton ko ta zo wurin Saif ne haka kawai. Tuni Fulani Zaliha ta harbo jirgin Maryo. Can sashen Saif ta nuna mata ta ce, "Shiga ciki tun ɗazu suna ciki." A kunyace Maryo ta miƙe ta wuce sashen Saif. Tun da ta shiga ta fara rafka sallama amma shiru kake ji babu amsa, a tunaninta ko gabaɗaya sun yi bacci tun da ta ji shiru ta san Naufal ya yi bacci. Ɗakinsa ta shiga tana sallama ta leƙa uwar ɗaki a cen kan katifa ta hango Naufal yana ta bacci hankali kwance. Murmushi ta saki ta ƙara ta yi masa kiss a goshi ta janyo zani ta rufa masa a jikinsa sannan ta taso ta fito zuwa rumfa, (Falo) kamar daga sama haka ta ci karo da mutum da sauri ta fara ja da baya. Murmushi ya sakar mata ya ƙarasa wurinta ta ƙara ja da baya har ta tokare da bango. Janyo ta ya yi da sauri yana cewa, "Dama yanzu nake shirin aikawa kiranki don ke na lura kamar ko a jikinki, an ya ba da gayya ba wannan zaman na ki ni fa ya fara isa ta." Zame hannunta ta yi tana bagarar da maganarsa ta hanyar cewa, "Dama na zo ɗaukan Naufal..." Bata rufe bakinta ba ta ji ya katse mata maganar ta hanyar sanya hannuwansa biyu a ƙugunta tare da faɗin, "Tun da Naufal ya yi bacci sai ki ɗauki Baban Naufal." Ɓata fuska ta yi tana kiciniyar ƙwace kanta amma ta kasa don haka ta dube shi ta ce, "Don Allah meye haka ne ka sake ni kar su ga na daɗe." Ido ya zuba mata yana kallon yanda take motsa laɓɓanta sannu a hankali, wata irin ƙaunarta ya ji ta ƙara mamaye ziciyarsa. Bai san lokacin da ya fara yawo da hannunsa cikin sassan jikinta ba, a hargitse ya fara ture hannunsa tana cewa, "Me kake yi haka Saif." Bai kalleta ba ya ci gaba da aika mata saƙonni masu wuyar fasaltuwa tun tana yunƙurin ƙwatar kanta har ta gagara taɓuka komai. Jin lamarin nasa na neman wuce gona da iri ya sa Maryo dakatar da shi ta hanyar gantsara masa cizo. Ɗagowa ya yi cikin wata irin murya yace, "Don Allah..." Bai ƙarasa magana ba ya ji bugun ƙofa daga can bakin ƙofa Baiwar Fulani Zaliha na rafsa sallama, hankali a tashe Maryo ta fara cikiniyar kwacewa, tabatuni hawaye ya fara ambaliya a idonta ta dube shi ta ce, "Ka ga abin da nake gudu yanzu idan aka gammu fa." Wara mata hannuwa ya yi alamun ko a jikinsa ya sake rungumota jikinsa yana cewa, "Sai me idan angammun ina ce ke matata ce ko haramun ne." Jin bugun ƙofar ba ƙaramin razana Maryo ya yi ba, a hargitse ta juya za ta fita da sauri yace, "Ki tsaya ki daidaita kanki kafin ki fita." Cak ta tsaya ta kasa gaba da baya, jin takunsa ta fara yi zuwa wurinta tana juyawa ya miƙa mata Mayafinta. Kunya ce ta kamata don gabaɗaya bata san lokacin da Mayafin nata ya faɗi ba, karɓa ta yi da sauri za ta fice. Janyota ya yi ya sa hannu ya ɗago haɓarta har suna jin numfashin juna sannan yace, "Na ta ya ki murnar bayyanar Mahaifanmu!" Ɗago ta yi ta kalle shi karaf idanunsu suka haɗu bata san lokacin da ta sakar masa murmushi ba don ko babu komai kalamansa sun faranta mata zuciya. Tabbas iyaye na daban ne jin ta take wani iri don gani take abun kamar a mafarki ne ace wai ita ce yau take da Mahaifa kamar kowa dukda Inna Habi bata rage ta da komai ba. Tana cikin tunani bata yi aune ba ta ji yana ƙoƙarin kai bakinsa cikin nata, da sauri ta ƙwace kanta tana ficewa daga sashen. Dariya mai sauti ya saki yana jin wani irin farin ciki na ratsa sassan jikinsa. Takawa ya fara yi a hankali ya ƙarasa ƙofar sashensa wacce tun shigowar Maryo ya rufe ta, tana tsaye ya same ta a bakin ƙofa yana zuwa ya yi mata dariyar ƙeta yace, "An jima za ki koya mini irin gudun nan na ki, domin na ji Takawa ya yi zancen tariyarki." Lokaci ɗaya Maryo ta yi saranda har ji ta yi ƙafafuwanta na gagarar ɗaukanta. Yana buɗe mata ba ta ƙara gigin tsayawa ba ta yi gaba domin magangunsa na yunƙurun kurumtar da kunnuwanta. Kamar sabuwar munafuka haka ta fice daga sashen Saif tana zuwa harabar gidan ta cin karo da Fulani Zaliha ta fara sunne kai ƙasa, a ɗan duburburce ta kalli Fulani Zaliha ta ga fuskarta murtuk ba fara'a ta ce, "Allah ya taimakake ki dama ɗaukan Naufal na..." Bata gama faɗar abin da yake bakinta ba Fulani Zaliha ta katse ta cewar, "Ina Naufal ɗin?" Maryo dum! Ta yi sannan ta ce, "Bacci... Yake." Fulani Zaliha ta saki murmushinsu na manya ta ce, "Idan ya tashi ki ce ya taho miki da Ɗankwalinki." A firgice Maryo ta shafa kanta don tabbatar da abin da Sirikarta ta faɗa, tana shafawa ta ji babu ɗankwali a kanta. Wata irin kunya ce ta kama ta da gudu ta fice daga sashen don tun da take bata taɓa jin irin kunyar da ta ji a wannan lokacin ba. Tana fita Fulani Zaliha ta saki murmushi haka kawai ta ji Maryo na ƙara birgeta a zuciyarta. Komawarta sashen su tana shiga wani irin wari ya ƙara mamaye ta saɓanin na da, da yake bugawa sama-sama. Hannuwa biyu ta sa ta fara toshe hancinta tana kallon sashen Fulani Maryama da banda warin da kukan ƙusaje babu abin da yake tashi. Tana shiga ɗakinsu ta samu Inna Habi na turara turaren wuta, ajiyar zuciya ta sauke dukda warin na doko cikin ɗakin. Abu na ganinta a hargitse ta saki murmushin ƙeta ta ce, "Ina Naufal ɗin" Nan take Maryo ta hau inda-inda daga ƙarshe dai ta ce, "Bacci yake kuma kin san ba a son tashin yara idan suna bacci." Abu ta riƙe haɓa ta ce, "To! Ko kema baccin ne ya ɗauke ki don na ji ki shiru kamar an aiki bawa garinsu." Maryo ta watsa mata harara don ta fahimci neman magana Abu take yi. Ɗauke kanta gefe ta yi ta ce, "Ni dai ban ce ba." Abu ƙasa-ƙasa ta yi da murya ta ce, "Ummm! Idan ma haka ne meye na musu mace da mijinta." Maryo na jin haka ta wuce uwar ɗaki ko bin ta kan Abu bata yi ba. Don ta san halin Abu da zolaya tun da ta gane lagonta ta shiga uku." Duk yanda Sarkin Zazzau ya so tafiya da Maryo Sarki Aminullah ya ƙi amincewa, akan dole yana ji yana gani haka suka juya masarautar Zazzau, sai dai kafin tafiyarsa sai da aka kira masa Maryo ya gabatar mata da Yarima a matsayin Ɗanwanta. Lokacin da za su yi sallama kamar kar ya tafi amma hakan da ya yi ya san shi ne daidai. Kafin tafiyarsa sai da aka rubutar doguwar wasiƙa aka tura Ɗan aike zuwa Masarautar Adamawa domin sanar da su halin da ake ciki. Sarki Aminullah sai da ya haɗawa Sarki Muhammad Safyan sha tara ta arziƙi, lokaci ɗaya kunya ta kamasu domin dukkansu sun aikata abubuwa na ɓacin rai a lokacin da suke kan matsananciyar gabar da take tsakaninsu. Gabar ta samo a sani ne bayan shekaru sakamakon wani farmaki da aka kai wa Masarautar Zazzau wacce a ka yi kashe da jikkada ɗunbin mutane, da sunan Masarautar Kano. Babu ƙwaƙƙwaran bincike Masarautar Zazzau suka mayar da martani nan fa faɗa ya ci gaba da wakana a tsakani har sai da Sarkin Musulmai na na takwas Sultan Muhammad Abu Ubaid daga Sokoto ya sasanta su tukunna. Dukada haka Masarautun ba wata jituwa suke ba sakamakon kowannensu an kashe musu wani sashen na daga danginsu. Sarkin Zazzau a wannan faɗan aka kashe masa Mahaifinsa Murabus ya yi aka naɗa Sarki Muhammad Safyan da Yayyansa mata biyu. Sarki Aminullah a wannan lokacin ne ya rasa babban Amininsa da Ƙannen Mahaifinsa biyu. Wannan rashin ba ƙaramin taɓa zuƙatan Sarakunan biyu ya yi ba. Daga ƙarshe Sarki Aminullah ya sauko har ya fauwwalawa Allah lamauransa ya watsar da dukkan makaman yaƙinsa. A wata ziyara da Sarki Aminullah ya kaiwa Sarkin Zazzau har lokacin bai wani tarbe shi da ƙima ba hakan ba ƙaramin ɓata ran Sarki Aminullah ya yi ba, a lokacin da zai yi masa sallama ya dube shi ya saki murmushin takaici yace, "Wannan gabar ta mu na tabbata watarana sai ta koma alkairi da ikon Allah sai mun haɗa zuri'a da kai domin Allah ya dubi zuciyata da ƙudurina." A hassalle Sarki Muhammad Safyan yace, "Allah ya tsare ni da haɗa zuri'a da kai idan ka ga haka ta faru sai dai idan bana numfashi, ko bana bumfashi duk wanda ya aurawa Ɗana ko Ƴata ahalinka sai mun yi shari'a da shi ranar gobe ƙiyama don ba da yawuna ba." Tun ranar da suka yi wannan rabuwar babu wani abu da ya sake haɗa su har aka shafe shekara sama da Ashirin, duk wani taro da zai haɗa su kowanne yana bakin ƙoƙari wurin ganin bai hallata ba ko ya saɓa lokaci don kar ya haɗu da abokin hamayyarsa. Wannan dalilin ya sa lokacin da Sarki Aminullah ya yi masa rakiya da Sarkin Zazzau ya nemi yafiyarsa gabaɗaya kunya ta kamata su. A ɓangaren Maryo kuwa tun da Inna Habi ta sanar mata da maganar tariyarta ban da kuka babu abin da take yi, lokaci ɗaya zazzaɓi ya rufe ta ruf ban da rawar ɗari babu abin da take yi. Lokacin da Sarkin Zazzau ya koma Masarautarsu da Farko ya so sanarwa da Mahaifiyar Maryo abin da yake faruwa, amma gudun kar ya tayar mata da hankali ya sa ya kwaɓi Yarima akan kar ya sanar mata har sai zuwa sati biyu masu zuwa wato ranar da za a kai su Maryo Masarautar da ƴar uwarta. Kamar tana da masaniya akan tafiyarsu haka Fulani Badawiyya ta yi ta tambayar Takawa abin da suka tattauna a Masarautar Kano amma fir ya ƙi sanar da ita. Mutumin da Yarima ya kama ya je kashe Abu ba ƙaramin duka ya ci ba, tun ana tambayarsa yana iya magana har sai da ta kai ga da ƙyar yake iya amsawa. Yarima ya yi wannan dabarar ne don ya kama Fulani Maimuna hannu bibbiyu domin ya jima yana zarginta akan miyagun abubuwa da dama, ya san wacece ita don haka ya san hujjar Abu kaɗai ba za ta fitar da shi ba. Lokacin da Mutumin ya ga mutuwa ido biyu nan take ya zayyana musu wacce ta tura shi da ƙwangilolin da take ba shi a baya har zuwa wannan lokacin da asirinsa ya tonu. Masarautar Kano Kimanin ƙarfe Takwas na dare Sarki Aminullah ya bada umarni aka ɗauki Amarya Maryo zuwa ɗakin mijinta Ango Saif, ba ƙarmin kuka Maryo ta sha ba haka Inna Habi tun tana dakewa har ta gagara ta fashe da matsanancin kuka, yanda take jin Maryo a zuciyarta tamkar ƴarta ta cikinta. Abu ce ta rinƙa lallashinta sannan ta yi shiru, ita ma ta wuce a ka kai Maryo da ita sai dai ba sashen da Saif ya zauna da Abu aka kai Maryo ba. Wani sashen daban Sarki Aminullah ya sa ka gyara mata tare da zuba mata dukiya tamkar ƴarsa ta cikinsa. Lokacin da aka kai Maryo wani irin abu ne ya tokare zuciyar Abu a hankali ta rinƙa furta, "Innalillahi'wa'inna'ilahirra'ji'un" Sannan ta ji salama a zuciyarta. Allah ya sani ita kanta ta san har lokacin a kwai ragowar soyayyar Saif a zuciyarta amma alwashi ta ɗaukarta kanta koda soyayyar Saif za ta kashe ta ba za ta sake zaman aure da shi. Jin hawaye na niyyar yin galaba a idanunta ya sa Abu saurin ficewa daga ɗakin ta koma sashensu domin ba ta burin wani ya yi tozali ta fuskarta har wani ya fahimci halin da take ciki. Saif buri ya ciki 😛 Amarya ta tare ina muku fatan alheri kuma ina neman afuwarku na jina shiru da kuka yi, sakamakon uzururruka da suka hanani typing. Na ga hirarrakinku wasu da alama sun ɗan tikice na ji suna ba su gane Mahaifin Maryo ba domin sun ji ance Sarki Aminullah Mahaifinta ne kuma aka ce Sarkin zazzau ma Mahaifinta ne. Idan kun tuna labarin tun a baya boka yace akwai yarinyar da bai san ya take ba mutumce ko aljan sihirinsa ya gagara nuna masa. Amma idan kun tuna yace za ta tashi da ruhi uku ta farko ƴar fararen aljanun ƙarƙashin ƙasa, ta biyu ya Sarkin baƙaƙen doron Ƙasa sai ta ukunsu da za ta zo a wannan zamanin wato Rayzuta. Idan ba ku manta na baku labari lokacin da Maryo take Masarautar Adamawa na Mahaifiyar Muhaibish wacce aka azabtar wacce ta kasance bil'adam to a wancen ƙarnin Wazirin Sarkin Adamawa ko Wambai ne na manta shine mahaifinta. idan ba ku manta ba shi ne har ta yi kashe-kashen nan a zuwan ɗaukan fansa tun da ruhikan azaaluman da suka zalinceta suma sun dawo. A masarautar Kano kuma Sarki Aminullah shi ne mahaifinta a wancen ƙarnin wanda ta kasance Ƴar Sarkin Baƙaƙen doron ƙasa, Ku fahimta Sarki Aminullah yana ɗauke da siffar Mahaifinta na wancen ƙarnin shi ya sa take yi masa kallon Mahaifinta, kuma abin da ya sa take kallonsa da ruhin Mahaifnta saboda ruhin Aljanu Biyu ne a jikinta. Tun da idan kun lura tana wasu abubuwa irin na jinnu. Sarkin Zazzau kuma shine ainihin Mahaifinta na zahiri wato Maryo wacce Boka ya kira da Rayzuta, to kunga ai ruhi uku kenan ina fatan babu sauran ruɗani amma idan da mai tambaya zai iya yi akan abin da ya shige masa dubu don ko ni labarin ya cakar da ni da yawa.🤣 _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [11/02, 17:52] Ameera Adam🌚: 74... A ranar da ka kai Maryo a ranar labarin warin da ke fita daga sashen Fulani Maryama ya riski Sarki Aminullah, da farko Bayinta ya fara tambaya take a ka sanar masa da gabaɗaya sun tafi babu wacce take bata kulawa sakamakon warin ya wuce misali. Da aka tambayi Inna Habi ita cewa ta yi ta shiga da safiyar ranar ta rinƙa buga ƙofar amma da Fulani Maryama ta amsa ƙin buɗewa ta yi sai ma zagin ɗiban albarka da ta rinƙa wurgo mata. A daren ranar aka mayar da Inna Habi da Abu sashen Fulani Zaliha Takawa ya aika Wasu Bayi sashen Fulani Maryama suka yi juyin duniya ta buɗe musu ƙofa ta ƙi. Lokacin da saƙon haka ya isa ga Sarki Aminullah ba ƙaramin fusata ya yi ba don haka yace a rabu da ita zuwa safiya. Maryo tun da aka kaita ban da kuka babu abin da take yi musamman da ta lura Abu tuni ta yi ficewarta, bayan kowa ya watse Ango shi kaɗai ya shiga ɗakin Amaryarsa bakinsa ɗauke da Sallama. A hankali ta iya amsa masa tana ci gaba da kuka mara sauti, ledojin hannunsa da wani ƙaton akushi ya ajiye a gefe sannan ya zauna a kusa da Maryo ya ɗaga mata mayafin da ke a kanta, yana ƙarewa fuskarta kallo ta kumbura suntum. Abin ka da farar mace tuni fuskarta ta yi Ja sai sauke ajiyar zuciya take. Farin kyalle ya ciro ya fara goge mata fuska lokaci ɗaya ta ji ƙamshin turarensa ya cika hancinta, lumshe ido ta yi ba tare da ta sani ba har sai ta bashi dariya. Jin shiru ya daina gogewa ya sa ta buɗe ido karaf suka haɗa ido ta ga yanda ya zuba mata idanu. Ba ƙaramin kunya ta ji ba da sauri ta ja mayafinta ta sinne kai ciki tana murmushi. Janyo ta ya yi yana faɗin, "Kunyar wai ta meye yanzu da kike ji? Ko kin manta lokacin da kike tsayawa kina yi mini tsiwa." Ɗago haɓarta ya yi yace, "Wannan bakin tsiwar ko hmmm" Miƙewa ya yi yace, "Ta so mu yi alwala mu gabatar da Sallah. A kunyace Maryo ta miƙe suka ɗauro alwala sannan suka gabatar da sallar Nafila. Akushin da Mahaifiyarsa ta bashi ya buɗe don shi kansa bai san meye a ciki ba, yana buɗewa ƙamshin farfesun kaji ya ciki ɗakin. Kunce ledar da ya zo da ita ya yi wacce ya siyo gasassun Kaji ya turawa Maryo gabanta yace, "Bismillah" Waro ido waje ta yi sai kuma ta girgiza masa kai. Ɓata fuska ya yi don dama ya san za a rina domin bahaushe yace "Alamar ƙarfi tana ga mai ƙiba" Hannun riga ya tattare ya gutsuro ƙatuwar cinya yace, "Buɗe bakin!" Da sauri da sunne kai ƙasa ta ce, "A'a zan ci da kaina" Murmushi ya yi yace, "To ko ki ci ko kuma na baki da kaina har sai kin cinye komai na wurin nan." Ganin da gaske yake ya sa Maryo ta zage don dole ta rinƙa ci. Kasancewar wunin ranar bata ci wani abincin kirki ba tun na safe ya sa ta ci farfesun sosai domin ba ƙaramin daɗi ya yi ba, kayan ƙamshi sai tashin ƙamshi suke yi. Sai da Saif ya ga ta ci ta ƙoshi sannan shima ya ɗan ci ba wani na kirki ba, kayan marmari suka sha Maryo ce ta fara ta shi sannan Saif ya ƙarasa. Bayan ta wanke hannunta can gefen gado ta koma, ta zauna sakamakon dare ya fara tsalawa, tattara kayan ya fara yi Maryo tana jikin gado a hankali bacci ya fara ɗaukanta. Jin baccin na neman cin ƙarfinta ya sa ta haura saman gado ta yi kwanciyarta ta duƙunƙune kamar mage, cikin baccinta ta fara jin Saif na aikamata da saƙonnin da suka girmewa tunaninta, tun tana yunƙurin dakatar da shi har ta haƙura. Asuba ta gari ban iya ɗiban albarka 🏃🏻‍♀️ Wani irin farinciki ne ya mamaye zuciyarsa har aka yi assalatu Maryo na rungume a jikinsa. Kiran assalatu ne ya tashe shi a hankali ya zame jikinsa ya je tsarkarke jikinsa ya gabatar da alwala sannan ya tashi Maryo, da kansa ya taimaka mata ta gyara jikinta. Ba ƙaramin tausayi ta ba shi ba saboda yanda ya ga yanayinta, tana idar da sallah ta koma ta kwanta bayan ya dawo daga Masallaci ya bi gefenta ya kwanta. Juye-juye yake saboda yanayin da yake ciki amma ganin irin wahallan baccin da take yi, ya sa akan dole ya haƙura, ga jikinta ya ɗauki wani irin za fi da alama zazzaɓi ne ya rufe ta ruf. Bayan gari ya yi haske da kansa ya tashi ya ɗumama musu sauran farfesunsu sai da ya kammala komai, sannan ya tashi Maryo tana ta shi ta fara yatsina fuska. Kallonta ya yi ya miƙa mata hannu ta sauko tana takawa da ƙyar, saitin kunnenta ya je ya raɗa mata, "Yarinyar nan kin fiya langwai an ya ba zamu koma na baki magani da kaina ba." Kamar jira take ai kuwa ta rushe da kuka tana maka masa fulo, ban da dariya babu abin da yake yi mata. Sai da suka yi wanka sannan suka zauna cin abinci, da kansa ya rinƙa bata abinci a baki tun tana sunne kai har ta zage ta rinƙa ci hankali kwance, daga daren ranar zuwa safiyar wata irin soyayya ake bugawa tsakanin Maryo da Saif. Lamarin Saif tun yana bata kunya har ya tuƙe ta saboda bata taɓa tsammanin Saif ya ƙware a fannin soyayya kamar haka ba. Abinci kala-kala Fulani Zaliha ta aiko musu wannan karon babu wanda ya tura wata wakiliya don bincikar yanda amarcin su Maryo ya kasance. Abu kamar wasa tun warin yana iya sashen Fulani Maryama har ya kai ga ya fara kaiwa gidajen da ke Maƙotaka da ita, a wannan karon Sarki Aminullah tura Fadawa ya yi tare da basu umarnin ɓalle ƙofa matuƙar suka yi magana bata buɗe musu ba. Kamar Takawa na da masaniya tun da Fadawan suka je suke yi wa Fulani Maryama magana amma sai ta rinƙa zaginsu ɗaya bayan ɗaya. Ganin haka ya sa jagoransu ya basu umarnin karya ƙofar. Tun ba su kai ga cire ƙauren ba wani irin wari ya doko hancinsu, da sauri suka ja baya aka fara tunanin wanda zai fara shiga amma duk wanda aka ce ya shiga sai ya noƙe. Mafi yawa daga ciki ba don sun ji muryarta ba ɗauka za su yi mutuwa ta yi gawarta ta fara wari. Ana cikin haka wani daga cikin Fadawan ya yi ta maza ya tura kansa ciki. Ganin haka ya sa sauran ma suka rufa masa baya, sai dai shigar su ba ƙaramin ɗaga musu hankali ya yi ba. A tsorace suka ja da baya kowa yana neman hanyar guduwa sakamakon abin da suka riski Fulani Maryama tana shukawa. Suna gudu tana biye da su a baya sai a lokacin jama'ar wurin suka farga da waɗansu irin manyan tsutsotsi da suke yawo a harabar wurin. Da gudu suka faɗa cikin faɗar, Fulani Maryama tana biye da su zawo na zuba, a bakin ƙofar wasu Fadawa suka tare ta don a yanayin da take ba za su taɓa barinta ta shiga Fadar Sarki Aminullah ba. Suna shiga Fadawan da suke cikin fadar suka fara cewa, "Hattara dai! Hattara." Mutumin da ya fara shiga sashen Fulani Maryama ne ya fara magana, "Allah ya taimakeka babu lafiya Salman ne Salman..." Ban da sauke numfashi babu abin da yake yi da ƙyar ya samu ya ci gaba da cewa, "Fulani! Fulani ta kashe shi ga shi can tana cin namansa. Gabaɗaya al'aurarsa ta tsige a hannunta muka same ta." Hankali a tashe Sarki Aminullah ya kalli Bafaden yana shirin magana ya ji Fulani Maryama tana cewa, "Kun ga laifina Ɗana ne fa yazo zai haike mini don na cire al'aurarsa na yi laifi. Wa zai taimaka mini ya dakatar mini da ita? Gudawa ce nake yau sati guda kenan ta ƙi tsayawa. Ku barni na je wurin Takawa an ce shine shugaban masu zuƙe gudawa, gara ya zuƙe mini ita na huta ko kun ga laifina don na zo ma'aikatar zuƙe gudawa?" Da kansa Sarki Aminullah ya miƙe ya tako zuwa bakin ƙofa don ganin halin da Fulani Maryama take ciki, don tun da ta zo ƙofar fadar wurin ya turniƙe da wani irin wari. Ba ƙaramin sanyi jikin Sarki Aminullah ya yi ba, lokaci ɗaya tsoron duniya da ruɗinta ya shige shi. Hawaye ne ya fara zubo masa ganin Maryama ƴar gayu mai ji da ƙwalisa tsaye a cikin jama'a, zawayi na bin jikinta kuɗaje suna yi mata gaɗa a kai. Fulani Maryama na hango Takawa ta buga tsalle tana ƙoƙarin kwaye zanin jikinta ta ce, "Wallahi kaine ko kaffara bana yi an ce kaine Shugaban masu zuƙe gudawa. Gudawa nake ta ƙi tsayawa amma Marduska yace na baka ka zuƙe ta, ka san me Salman ya yi? Shi fa ba Ɗanka bane wai ina Mahaifiyarsa ya zo zai haike mini ni kuwa na sa hannu na tsige abar, amma wallahi kaima idan na kamaka sai na tsige ta saboda ni ce na yi maka asiri baka iya taɓuka komai game da iyalanka, nima sai nake nuna na damu don kar a zargeni duk fa na yi ne don karka ƙara haihuwa, kuma dama Marduska ya faɗa kai da haihuwa sai a lahira." Fulani Maryama na gama magana sai ji suka yi tsuuuu! Wata gudawar na ƙara zirarowa ta gefen ƙafafuwanta. Hannuwa biyu ta sa ta fara kwasa tana turawa baki tana cinyewa ganin haka ya sa Sarki Aminullah ya bada umarnin a wuce da ita turu.(Gidan Mahaukata) Kafin wani lokaci tuni labarin abin da ya faru ya baza ciki da wajen Masarautar Kano wannan lamarin ba ƙaramin taɓa zuciyar mutane da yawa ya yi ba. Ɗaki guda aka ware aka saka Fulani Maryama a ciki, tun da aka kaita ban da gudawa babu abin da take yi. Idan ta yi abarta ta cinye kayarta tun tana cin iya zallar gudawa har ta fara yagar naman jikinta tana ci. Haka wasu daga cikin sassan jikinta suka fara ruɓewa suna wari daga ƙarshe da masifar abin ya taso mata haka ta saka baki ta rinƙa cizgar Nononta har sai da cire guda ɗaya. Hatta abinci ta daina ci koda an zura mata ta window bana ci sai dai ya lalace a haka, akwai ranar da Mai zuba musu abinci ta zura mata abinci ta window bata san Fulani Maryama na laɓe ba, sai ji da yi ta kafawa hannunta cizo har sai da ta cire mata Ɗan yatsa ɗaya. Tun daga ranar suke zuba mata abinci a leda suna wurga mata, tun da ta ji daɗin naman jikinta ta daina bi ta kan kowanne irin abinci. Duk wanda ya ga gawar Salman sai da ya zubda ƙwalla sakamakon irin kisan wukaƙancin da Mahaifiyarsa ta yi masa, saboda ya jima a mace jikinsa har ya kumbura ban da wari babu abin da yake yi. A haka aka sallace shi a ka kai shi makwancinsa aka binne shi domin jikinsa ya yi lalacewar da ba za a iya wanke shi ba. Bayan kwana biyar. Fulani Fahima, Maleek, Shukra, Mai babban ɗaki, da Sarki Abdallah sune suka dira a Masarautar Kano. Murna wurin Maleek kamar ya fi Shukra farin ciki da bayyanar iyayensu, babbar tarba aka yi musu sai da suka ci suka sha sannan aka fara mayar da labari. A nan suke jin labarin abin da ya faru da Fulani Maryama, duk irin mugun abun da ta aikata sai da suka ji tausayinta Fulani Zaliha da ke gefe har da hawayenta. Duk budurin da ake Maryo ba ta ji labarin zuwansu ba don Saif cewa ya yi sai sun zo zai sanar da ita. Tun da aka kai Maryo Abu take ta matsantawa Saif akan ya bata takardarta ya so ya riƙe su duka biyun a matsayin matansa amma fir Abu ta shafawa idonta toka, babu yanda ya iya a ranar da suke da kwana uku da aure ya aika mata takardarta ba tare da Maryo ta sani ba. Sosai Maryo ta zage take nunawa mijinta kulawa da soyayya, a cikin kwanakin har wani canjawa ta yi ta ƙara haske saboda kwanciyar hankali. Kamar daga sama haka Maryo ta ji sallamar su Shukra, tana fitowa ta hango ƴar uwarta. Wani uban tsalle ta buga ta ɗane Shukra tana yi musu barka da zuwa. Maleek da ke gefe ya yi gyaran murya yace, "Ki yi dai a hankali don ba ita kaɗai ba ce." Kunya ce ta kama Maryo ta ja ƴar uwarta suka wuce ɗaki. Bayan shigarsu ba daɗewa Fulani Fahima da Mai babban ɗaki suka shiga nan fa aka baje da hira. Mai babban ɗaki na maƙale da Maryo kamar wani zai ƙwace ta nan aka jajanta abin jajantawa, a ka yi san barka ga abin murna da farinciki. Kwanansu ɗaya a Masarautar Kano gabaɗaya suka ɗunguma zuwa ƙasar Zazzau, don tun a ranar da su Maleek suka dira Sarki Muhammad Safyan ya aiko da masu tarba haɗe da kekunan Dawakai waɗanda za su tafi da su gabaɗaya zuwa Masarautar Zazzau. Lokacin da suka sauka a wani babban falo aka tarbe su, falon cike yake da iyalan Sarkin Zazzau yara da manya Maza da mata. Tun da suka shiga Fulani Badawiyya take bin su da kallom sha'awa lolaci ɗaya ta ji yaran sun kwanta mata. A ɓangare ɗaya kuma tana kallon kamaninsu kamar ta san mai yanayin fuskarsu. _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [15/02, 18:03] Ameera Adam🌚: 75... 🔚🔚 ƘARSHE Gabaɗaya iyalan Sarki Muhammad Safyan kansu a ɗaure yake da wannan sabon yanayin da Mahaifinsu ya ɓullo musu da shi, ban da Yarima da babu wani mamaki a tattare da shi don ya san maƙsudin zaman. Abin da ya ƙara ɗaure musu kai shi ne saukar da a ka yi wa Sarkin Kano da tawagarsa, saɓanin baya da ko sunan Masarautar Kano ba a cika ambata a Masarautar Zazzau ba. Hankalin kowa a kwance yake ban da na Fulani Maimuna da tun tuni jikinta yake bata akwai wani abu a ƙasa, ga shi yanda ta lura kwana biyu Takawa baya bata fuska ko turakarsa ta je zai ce ta fita ta ba shi wuri. Daga ƙarshe ma idan ta aika neman iso baya bata izini, dukda ta san an kama ɗan aikenta amma tana da yaƙinin a irin kashedin da ta yi masa ba zai taɓa tona mata asiri ba. A ɓangare ɗaya kuma tana ganin koda ya tona mata asiri a yanda take da Takawa ba zai taɓa amincewa da maganarsa ba, kuma duk hanyar da za ta bi don ganin ta wanke kanta sai ta bi ta don haka fargabarta ta ragu. Amma haka kawai ta ji zuciyarta bata aminta da waɗannan tagwayen da ta gani ba hasalima ji ta yi duk duniya bata ƙaunar buɗe ido ta gansu a gabanta. Tun da suka zauna idon Saif yana kan Maryo motsi ɗaya biyu sai sun haɗa ido, suna haɗa ido zai sakar mata murmushi sai dai ta yi masa murmushi ta ɗauke kanta don da alama shi ya manta a wurin da suke zaune. Ta shi ta yi ta fita aka nuna mata makewayi don yin fitsari, tana fita Saif ya bi bayanta Fulani Zaliha har sai da kunya ta kamata don lamarin na Saif ƙara gaba yake yi. Tana fitowa daga banɗaki sai ji ta yi, ta yi karo da mutum a tsorace ta ja da baya za ta faɗi ta ji ya rungumota jikinsa yana dariya. Shagwaɓe murya ta yi tana kai masa dukan wasa ta ce, "Wallahi ka bani tsoro ban san kana wurin nan ba." Hannuwansa biyu ya sa ya zagayo da su ta bayanta yana jin bugun zuciyarta har cikin ƙirjinsa, kumatunta ya sumbata yace, "Na yi kewar Matata tun jiya aka nesanta ni da ita na gaza daurewa shi ya sa na biyo a bata." Hararar wasa ta wurga masa ta ce, "Ai kuwa ni da Kano sai na yi wata biyar don sai na sha Nono na ƙoshi." Kansa ya zura wuyanta yana ɗan hura mata iska yace, "Ai kuwa da na zauna sai a bamu ɗaki idan lokacin komawar ya yi sai mu tafi tare kin ga sai ki samo mana ɗan Zazzau." Da sauri ta hau kiciniyar ƙwacewa tana cewa, "Wallahi Habibi sam baka jin kunyar faɗa magana, sake ni na tafi kar wani ya ganni." Riƙe ta ya yi tsam sannan yace, "Ai gaskiya na faɗa! Da gaske idan aka ce za a riƙe mini matata sai dai a riƙemu tare." Suna na tsaye Maleek ya ƙaraso yana faɗin, "Laila Majnun idan kun gama ku ake jira." Maryo ba ƙaramar kunya ta ji ba tana shirin ƙwacewa ta ji Saif yace, "Kai kuma Ɗan sa ido ba sai ka tsaya daga baya ka isar da saƙon ba?" Maleek ya juya yana cewa, "Lallai Yaro wuyanka ya yi kauri bari na sanar da su Takawa abin da na gani ƙila su..." Da sauri Maryo ta yi gaba tana cewa, "Don Allah Ya Maleek kar mu yi haka da kai." Suka wuce gabaɗaya suna dariya. Sai da suka ci suka yi ƙat sannan aka shigo da wani mutum jikinsa jina-jina da ƙyar yake iya takawa a kan ƙafafuwans. Tsuggunar da shi a ka yi a gaban Sarki Muhammad Safyan sannan aka shiga da wata Tsohuwa, ita ma zama ta yi saitin wurin da Mutumin yake. Suna shiga wani Uban gumi ya jiƙe ta da sauri Fulani Maimuna ta sunne kai za ta fita, Sarki Muhammad Safyan ya dakatar da ita. Tun da ta yi tozali da Dillaliya hantar cikinta ta hau kaɗawa, ilahirin jikinta ban da rawa babu abin da yake. Bafaden da ke gefen daman Sarki Muhammad Safyan yana shirin magana, Takawa ya dakatar da shi ta hanyar ɗaga hannu sannan ya dubi mutumin da ke tsugunne, sai da ya buɗe taron da Addu'a sannan ya ci gaba daji cewa, "A wannan lokacin ina zaune a gabanku ne a matsayin Mahaifi ba Sarki ba, maƙasudin haka ya samo asaline ta wasu ɓoyayyayen al'amari, wanda zai bayyana a ta bakin wannan bawan Allahn. Kai yaro me ye sunanka muna son ka maimata abin da ka faɗa a kwanakin baya." A firgice Fulani Maimuna ta ɗago gumi na ci gaba da yanko mata, jikinta tamkar mazari haka yake kaɗawa da sauri-sauri. Mutumin ya sauke wahallalan numfashi sannan ya fara da cewa, "Da farko sunana Duna na shafe shakara da shekaru ina yi wa Fulani Maimuna aiki a sirrance, hasali dai ni tsohon Saurayinta ne..." Tun bai rufe baki ba Fulani Maimuna ta katse shi da cewa, "Ƙarya kake baƙin munafiki ko kalarka ban taɓa gani ba." Sarki Muhammad Safyan ya saki murmushi don ya san za a rina duk wani alamaun rashin gaskiya ya bayyana ga Fulani Maimuna, Duna bai kulata ba ya ci gaba cewa, "Fulani Maimuna ta sakani ayyuka da dama a gidan nan daga ciki har akwai Kisan Jakadiya Tine da satar tagwayen da Fulani Badawiyya ta haifa." Fulani Badawiyya da ke gefe ji ta yi kanta ya sara a firgice ta kalli Fulani Maimuna da sunne kai ƙasa, ba ta san lokacin da ta rushe da kuka ba ta dubi Fulani Maimuna ta ce, "Sakayyar da za ki yi mini kenan Maimuna bayan rufin asirin da na yi miki ashe ni za ki tura rana, ki manta lokacin da duniya ta juya miki baya ni na baki sutura? Kowacce mace na da kishi amma haka na danne kishin mijina na sashi ya aure ki amma kika aikata mini haka? Me na tsare miki." Ganin haka ya sa Sarki Muhammad Safyan ya dakatar da Fulani Badawiyya ta hanyar rarrashinta, sai da ta yi shiru mutumin ya ci gaba da cewa, "Ba ni kaɗai na gabatar da aikin ba domin a lokacin asirina zai iya tonuwa saboda satar yara biyu ba wasa ba. Dillaliya Kaltume ita ta taimaka mini muka sace Jariran a ranar da suka cika kwana uku cif da haihuwa, mun samu nasarar sace su cikin tsakiyar dare. Kaltume ita ta ɗauki Hasana ni na ɗauki Usaina, muna fita daga Masarautar Zazzau kowa ya yi nasa wurin ni na jefar na Usaina a ƙasar Shanono ita kuma Dillaliya ta nufi ƙasar Ƙatsina da ita." Mun yi wannan dabarar ne domin kar asirimun ya tonu don a lokacin na yi niyyar murɗe wuyan Usaina na kashe ta sai tausayin yarinyar ya saukar mini. Ita dama Dillaliya tashin farko ta ce ba za ta iya kashe Jariri ba dama guba za a bata za ta iya zuba mata. Amma don mu amshi ladanmu sai muka cewa Fulani za mu aiwatar da abin da ta umarcemu. Sanin bana bata matsala a aiki ya sa ba ta damu ba ta sallam mu da dukiya mai yawa ta kuma gargaɗi Dillaliya da ko da wasa ta dawo Masarautar Zazzau sai ta sa an hallakata. Nima ta yarje mini zamana ne saboda tana bani ayyuka kuma ina zartar mata. In taƙaice muku labari ba tun yau ta ba ni kwangilar kisan Yarima ba amma kullin na tunkare shi da niyyar kisa sai inji ya yi mini kwarjini, haka kawai na kasa zartar da ƙudurina a kansa. Sanadiyyar haka har sai da muka samu matsala da Fulani sai daga baya muka sasanta. Daga ƙarshe ta sanar da ni ta samu wacce za ta kashe shi idan ta kashe shi ni kuma sai na kashe ta. Ana haka har ranar da ta umarce ni da na kashe wata baiwa mai suna Abu daga nan asirina ya tonu. Amma don Allah a yi mini rai wallahi tsautsayi ne." Yana gama maganar Falon ya yi tsit ban da sautin kukan Fulani Badawiyya babu abin da yake tashi. Gabaɗaya jikinsu ya yi sanyi Maryo da Shukra sai hawaye suke kamar haɗin baki suka miƙe lokaci ɗaya suka ƙarasa wurin Mahaifiyarsu suka rungumota suna fashewa da kuka. Babu wanda ya hanasu sai da suka yi mai isarsu sannan Fulani ta ɗago ta kalle su da kallon tuhuma, cikin kuka Maryo ta gyaɗa kai tana cewa, "Mune Ammi" Da sauri ta waiga wurin Sarki Muhammad Safyan suna haɗa ido ya gyaɗa mata kai yana cewa, "Mun ɓoye miki ne ni da Ɗanki saboda na san ki da rikici sai ki ɗaga mana hankali kafin zuwansu." Fulani Badawiyya ta rungumo su tana godewa da Allah ya bayyana mata Tagwayenta, lokaci ɗaya farinciki ya mamaye zuƙatan ahalin Fulani Maimuna ta fashe da kuka ta rarrafa gaban Mahaifiyarsu Maryo tana neman yafiya. Sarki Muhammad Safyan da kansa ya miƙe ya ƙarasa wurinta. Hannu ya sa ya riƙota sai da ya kaita har bakin ƙofa sannan yace, "Ki fice mini daga ƙasata na sake ki saki Uku. Umarnin gaggawa na baki duk wanda ya ƙara ganin ƙafarta a ƙasarta a kawo mini ita hukuncinta zaman gidan ajiya da gyaran hali na dindindin." Yana gama maganar ya janyo ƙofa ya rufe, sanin halin Zafin Sarkin Zazzau ya sa ba ta yi wata-wata ba ta fice daga Masarautar yara na binta da dutse suna jifanta. Dillaliya cikinta ne ya kaɗa don ita bata san irin hukuncin da Sarki zai sa a yi mata ba, tana cikin tunani Sarki ya bada Umarni aka fitar da ita tare da tsula mata bulala hamsin. Shi kuwa Duna sakamakon ya yi kashen-kashen rayuka Sarki ya sa aka tura shi gidan yari ɗaurin rai da rai. Bayan an gama jimami nan ƴan uwa da abokan arziƙi suka shiga nunawa su Maryo kulawa da soyayya, nan aka shiga nuna musu dangi na kusa dana nesa. Matan Sarkin Zazzau huɗu, Mahaifiyar su Maryo ita ce Uwar gida sai bayan aurenta da shekara biyar da Haifi Yarima Kaleed tana cikin goyonsa Maimuna ta je ta same ta da buƙatar ta taimaka mata akan Sarki ya aureta saboda wasu ƴan Fashi sun yi mata fyaɗe lokacin da suke hanyar tafiya zuwa garinsu da ke Ƙasar Zamfara. Da ƙyar Mahaifiyarsu Maryo ta shawo kan Sarkin Zazzau ya amincewa auren Fulani Maimuna, an yi aurenta da shekara shida ta haifo ƴan biyunta duka mata. Mahaifiyarsu Maryo da Mahaifinsu Ɗan wa da Ƴar ƙanine dukkansu gadon jinin Sarauta ne na Masarautar Zazzau, su Maryo suna da Ƙanne biyu Mace da Namiji, Nurain da Nu'aima. Gabaɗaya ƴaƴan Sarki Muhammad Safyan goma sha huɗu maza bakwai mata biyar. Farincikin wurin ahalin Sarki Muhammad Safyna ba zai musaltu ba ririta su Maryo ake kamar tsoka ɗaya a miya, attajirai, ƴan kasuwa, ƴan uwa da abokan arziƙi sai dafifi ake yi wurin zuwa taya Sarkin Zazzau bayyanar Ƴaƴansa. BAYAN WATA BIYAR "Lafiya kike ta ɓata fuska waya taɓa mini ke Fulani na?" Sarki Aminullah ya faɗa cikin zolaya don da alama gimbiyar ta shi rikici take ji. Fulani Zaliha ta dube shi hawaye na ziraro mata ta ce, "Don Allah yanzu me ya fi wannan abin kunya? A ce Sirikata na da ciki ni ina laulayi." Kamar wanda aka yi wa busahara haka Sarki Aminullah ya washe baki cikin farinciki yana faɗin, "Da gaske kike?" "Duk wasu alamu sun gama bayyana yau wata biyu kenan rabona da baƙon wata ga alamomin cikine sun bayyana a jikina." Sarki Aminullah ya ɗaga hannuwa biyu yana godewa Ubangiji, tagumi Fulani Zaliha ta yi ta ce, "Amma kuma idan baka manta ba Maryama ta ce Boka yace ba za ka sake haihuwa ba an ya kuwa ma cikin ne?" Takawa ya ɗan ɓata fuska yace, "Kina nufin kema kin fara gasgata maganar Boka kenan, boka fa ba Allah bane da zai san gaibu. Aiki suke da aljanu suna tura su sama domin sato maganganun da Ubangiji yake yi da Mala'iku. Zancen boka zancan gaibu ne Allah shi kaɗai ya san abin da gaba za ta haifar. Kika sani duk haihuwa ku rinƙa jerawa da Matar Saif kina sauke mini tagwaye." Ai kuwa kamar ƙaramar yarinya haka Fulani Zaliha ta fashe da kuka tana girgiza kai. Sarki Aminullah yace, "Saƙo ya same na auren yarinyar nan Safiyya (Matar Salman) Ance mini Ɗan Sarkin Nufe shi zai aureta cikin wata mai kamawa." Fulani Zaliha ta faɗaɗa murmushinta tana faɗin, "Allah sanya alheri ikon Allah ka ga lamarin Ubangiji kenan." Tuni Abu ta riga ta gama iddarta har Yarima Kaleed ya yi maganar aurenta, da Farko ƙin amincewa ta yi sai daga baya ta amince aka ɗaura musu aure, lamarin ba ƙaramin daɗi ya yi wa Maryo ba haka ta tasa Abu tana yi mata shakiyanci kala-kala. Can Ƙasar Zazzau aka kaita cikin Masarautar Zazzau, ba ƙaramar kulawa take samu a wurin Fulani Badawiyya ta ɗauke tamkar ƴarta ta cikinta. Ba ƙaramin karamci Ina Habi take samu daga wurin Mahaifi da Mahaifiyar Maryo ba har ma da al'ummar Masarautar Zazzau bakiɗaya. Sun zama tamkar ƴan uwa sanadin ruƙon amanar da ta yi wa ƴarsu. Watan Abu biyu da aure aka ɗaura auren Sarki Aminullah da Inna Habi, da farko fir Inna Habi ƙin amincewa ta yi don har da kukanta akan maganar aurenta da Sarki Aminullah, sai da Fulani Zaliha ta yi mata nasiha da nuna mata muhimmancin auren a yanayin shekarunta tun da ba wuce auren ta yi ba, sannan ta amince. Babu wani lokaci da aka ɗauka aka ɗaura musu aure. Fulani Zaliha da kanta ta kai Inna Habi turakar Sarki Aminullah, lokacin da ta kaita sai da ta yi musu tsiya sannan ta fice ta basu wuri. Rayuwa suke cikin farinciki, zama suke na tsakani da Allah kamar ba kishiyoyi ba don dama Fulani Maryama ita kaɗai ce mai tsananin kishi duk cikin matan Sarki Aminullah. Cikin Maryo ya fito sosai dan har ta shiga watan haihuwarta, cikin ba ƙaramar ƙiba ya saka ba ta yi wani irin haske ta ko'ina ta yi ƙiba. Ganin haka ya sa Fulani Zalina ta sa Saif ya dawo da ita sashenta don a cewarta bai kamata Maryo ta zauna a gidanta ba saboda gudun Naƙudar dare. Ko kaɗan Saif bai ji daɗi ba amma babu yanda ya iya haka ya haɗa mata kayanta ta koma can, sai dai tun da Maryo ta koma shima ya tare a can kodayaushe yana can don wani lokacin Fulani Zaliha har kunya take ji. Sai da ta yi da gaske ta fara fatattakarsa sai ya yi kamar ya yi kuka saboda sam baya son abin da zai nesanta shi da Matarsa. Satin Maryo biyu a gida Allah ya sauke ta lafiya ta haifo santaleliyar Jaririyarta Mai kama da ita sak, Yarinyar babu inda ta baro Maryo a kammi sai dai ɗan duhun Mahaifinta da ta ɗauko. Farinciki wurin mutanen Masarautar Kano abun baya musaltuwa, lokacin da labarin haihuwar Maryo ya isa Masarautar Zazzau ba ƙaramin farinciki suka yi ba, saboda Murna Abu har ji ta yi kamar ta yi tsuntsuwa. Kwana biyar da haihuwa su Abu suka dira Masarautar Kano tare da kayan barka sha tara ta arziƙi. Abu saboda farinciki rungume Jaririyar ta yi kamar wani zai ƙwace mata. A lokacin da Maryo ta haihu Abu na da cikin wata uku, da daddare suna zaune su biyu a ɗaki Maryo ta dubi Abu ta ce, "Hajiyata ina ce kina kula mini da Ɗan uwa don ke dai na ga alamun yana baki kulawar da ta kamata, kin ga yanda kika zama uwar mata kuwa, don ni har gani na yi kamar da ajiyar mu a wurinki." Abu ta yi dariya ta ce, "Ƴar iska wai yaushe kika yi baki ban sani ba? Wallahi kin bani mamaki wai yau Maryo ke faɗin wannan maganar." Maryo ta kishingiɗa tana faɗin, "Sanin da kika yi mini amma yanzu kafin ki koma yarinyar sai na ƙara kintsaki yanda za ki bawa Ɗan uwana kulawa." Abu ta rafka salati tana tafa hannuwa ta ce, "A'uzubillah yasin kinfi ƙarfina bari na baki wuri, amma duk iskancin mutum sai ya yi arba'in biyu ko uku a gida." Maryo ta yi ƙasa da murya ta ce, "Wallahi da na bi mijina sahunmu a likafa mun wuce gida don an shiga haƙƙin masoya." Daidai lokacin Fulani Zaliha ta shiga ɗakin, Maryo ba ƙaramin kunya ta ji ba amma Fulani Zaliha ta yi kamar ba ta ji su ba ta kwantar da Naufal, kasancewar tun lokacin da Abu za ta yi aure ya koma wurin Maryo lokacin da cikinta ya fara girma sai Fulani Zaliha ta sa Saif ya kai mata shi. Ranar Suna Jaririya ta ci sunan Mahaifiyar Maryo aka saka mata Rabi'atul Badawiyya, a lokacin Shukra tana goyon Ɗanta Namiji Mai sunan Sarki Muhammad Safyan, an yi shagali na ban mamaki. Mawaƙa da makaɗa sun baje kolinsu suna ta wasanni haka aka yi taron suna aka gama lafiya. BAYAN KWANA HAMSIN "Fulani maganar gaskiya yaron nan matarsa yake yi wa jelan nan saboda kina gani da kaɗan-kaɗan ya kwaso kayansa ya dawo gidan nan, ya yi mana zuru ya ji shiru kin ga yace idan ya dawo ai a bashi matarsa su tafi." Ina Habi wacce ta koma Fulani Habiba ta yi maganar cikin ƙasaitacciyar shiga ta alfarma. Fulani Zaliha da cikinta ya fara fitowa ta ce, "Fulani rabu da shi so nake na gyarata sosai don sai ta ƙara sati biyu nan gaba." Inna Habi ta zaro ido waje ta ce, "Sati biyu! Tabdi lallai zan kai ƙararki wurin Takawa don wallahi wannan shiga haƙƙin ba za a yi wa Ɗana ba." Fulani Zaliha ta daidaita nutsuwarta sannan ta ce, "Wai don Allah da gaske yaron nan dalilin dawowarsa kenan?" Inna Habi ta saki murmushi ta ce, "Kina mamaki wallahi idan ba so kike a samo mana da cikin gida ba ki tattara matarsa ki kai masa, yau fa kwananta Hamsin da bakwai." Fulani Zaliha ta yi jim sannan ta ce, "Ai kuwa ba da ni za a yi wannan abun kunyar ba." "To kuwa gara ki mayar masa da matarsa tun wuri." Gabaɗaya suka saka dariya. Lamarin Fulani Maryama ya munana, duk mutum mai imani idan ya ga hakin da take ciki sai ya tausaya mata. A cikin wannan watannin gabaɗaya ta ciccizge jikinta, wasu rauninkan sun warke wasu kuwa guraren duk sun ruɓe, tsutsa duk ta fara cin ɓargonta ta rarake naman jikinta. Idan ka bi ta wurin ɗakinta ban da wari babu abin da yake tashi a wurin, lokacin da ciwon nata ya motsa da ta rasa wurin da za ta gaya ta ci, hannunta ta zura ta ƙwaƙwalo ƙwayar idonta tun bata kai ga cirowa ba ta fasa ƙara saboda azaba tana ihu, haka ta gama matagugunta babu wanda ya bi ta kanta, haka ta ci gaba da rayuwa cikin wulaƙanta da tagayyara. A ɓangaren Jakadiya kuwa hauka take tuburan sai dai abin da yake ƙara haukata ta, tsirowar gashin kanta a duk lokacin da gashin kantabya tsiro sai wani aljani ya zo ya kafa bakinsa a kanta har sai ya zuƙe duk wani silin ga shi. Ba a ɗauki lokaci ba Fulani Zaliha da kanta ta ƙara shirya Maryo da magungunan gyara, ba ƙaramun kyau ta yi ba jego ya amshe ita da ƴarta sun yi matuƙar kyau. Wata rana da daddare su Fulani Bilkisu suka mayar da Maryo ɗakin mijinta. "Wai wata sabuwar kunyata kike ji?" Ta cikin mayafi Maryo ta zuro kai tana leƙensa, da sauri ya fisgo mayafin yana janyota jikinsa yana cewa, "Kunnuwana basa amsar sarewar duk wani sauti face na zinariyar macen da babu kamarta, idanuwa na yi mini gizo a duk lokacin da na buɗe su matuƙar ban sauke su a kanki ba. Jikina ya yi maraicin rashinki domin a kowanne sakan gangar jikina na ambaton sunanki, na yi matuƙar kewarki matata amma sai nake ganin kamar ba ki damu da ni. " Kashe masa ido ɗaya ta yi ta ɗora kanta a jikin kafaɗarsa tana cewa, "Harshe na furta kalmomi ne domin bayyana saƙon abin da yake cikin zuciya, sai dai tawa zuciyar na bayyanawa ƴar uwarta saƙonta ne a kodayaushe domin zuciyata da taka a haɗe suke basa taɓa rabuwa. A duk bugun numfashina yana sauka ne da ɗumbin begenka! Mai zai sa na yi rashinka bayan ni da kai abu ɗaya ne? Tabbas so daban yake haka ma ƙauna! Ina ƙaunarka mijina farincikina mai faranta zuciyata." Maryo na gama faɗa ta lumshe masa ido tana kanne masa ido ɗaya, Saif ku san mutuwar tsaye ya yi ƙaunarta na ƙara fisgarsa, rasa abin yi ya yi kawai ya janyota ita da Rabi'a (Nimra) ya rungume su cikin farinciki. Tammat Bihamdullilah Komai ya yi farko zai yi ƙarshe a nan na kawo ƙarshen wannan labarin, masoya ina godiya da nuna kulawarku ta hanyar siyan littafina bani da bakin gode muku, sai na ce Allah ya bar ƙauna domin yabon gwani ya zama dole. Tabbas kuɗin ƴan amana ne wallahi na yi matuƙar alfahari da ku saboda ban taɓa ganin labarin nan a kowanne group ba. Na gode da yanda kuka riƙe mini amana Allah ya bar ƙauna.❤️❤️🥰🥰 _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels