Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels *GAWA TAFE* (Zombies story) On2025 *©Zahra Royal Star* *ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION* *EPISODE 1* *General hospital Katsina State Nigeria* "Innallihi wa'inna alaihir raju'on, Farida waye ya take ki da mota har hannunki ya k'arya haka?" Kuka Farida kawai keyi mai cike da tsananin rad'ad'in zuci da azabar da hannunta ke mata. Kwance take akan gadon marassa lafiya, irin na asibitin. Hannunta ta kalla ganin yadda ya kunbura har yayi fushi da waya, wani miyau mai zafi ta had'e a mak'oshinta tana kallon abokiyar zaman Mahaifiyarta wacce duk ita ce silar shigarta cikin wannan wahalar, domin da baccin bata d'ora mata tallar da bata so ba, da duk hakan bata faru ba. "Inna Zubaida wani ne a mota ya bige ni, kuma bai tsaya ba, yayi tafiyarsa, sai wasu Mutane k'alilan ne suka kawo ni asibitin nan" "Dalla can rufe min baki, ai ni wallahi ni ce kika jama asara, yanzu ubanwa zaije wajan aikin ki? Kin kuma san inda kike aikin nan bafa mutumci ne dasu ba, kuma na rantse bazaki ja min salalan tsiya ba, domin idan aka kore ki daga gidan Alhaji Sammani B Radda Mai Naira ai na shiga uku na, dan haka yanzun nan kima tashi ki kama hanya mu wuce, dama tallar baifi ta wuni d'aya kike zuwa min ba, shine yanzu kinje kin shige ma titi kinja masu hannu da shuni sun bige ki kin barni da aiki". Wata doctor ce da tun maganar Inna Zubaida ta farko take kallonta cike da mamaki, ta kasa hakuri ta kalleta ta ce. "Baiwar Allah amma da alama bake ce kika haifi wannan yarinyar ba ko?. Domin da ki ce kika haifeta bazaki fara mata zancen rashin zuwanta wajan aiki da zatai na y'an kwanaki ba. Ke burinki kawai ta kawo miki kud'i kawai, baki gudun ma ace yau anje wani ya lalata mata rayuwa gaba d'aya?, miye zan....... "Ke Kinga baiwar Allah, babu ruwanki a cikin sha'ninmu, ina ruwanki? Ke ke rik'eta ko ni? Ko kuwa ke ke d'aukar cinta ko shanta?. Kinga Malama ki sallame mu ma mu wuce gida". Inna Zubaida ta k'are maganar tana hararar likitar kamar idonta zasu fad'u. Girgiza kanta kawai likitar tayi tana sake duban Inna Zubaida ta ce. "A sallame ku ai bai taso ba, saita samu sauk'i tukunna". Rai a b'ace cike da da harguwa Inna Zubaida ta fara cewa. "Ai ko kun samu mai biya mata magani, domin na rantse da Allah ko sisina bazatai ciwon kai ba, yawwa, gara ma ku sallame mu wuce a'ato, idan ma baku bamu sallama ba, yanzun nan zamu wuce sai naga ubanda ya isa ya hanamu tafiyar". Likitar zata sake magana aka bud'e k'ofar d'akin aka shigo. Shuru tayi tana kallon wacce ta shigo d'in. "Doctor Halisa mike faruwa ne" Kallonta Halisa tayi tana cewa. "Uhuhmm wannan matar ce marar imani mana, Doctor Anam an kawo wannan yarinyar da k'araya a hannunta wani shima marar imanin ya bigeta, ko tsayawa baiyi ba yayi tafiyarsa ya barta, shine wasu bayin Allah suka kawota asibitin nan, mun samu da kyar an gyara k'aryar hannun nata, shine ta bada number wannan matar an kira ta mai maikon ta zo ta nuna tashin hankalinta, sai ma ta fara cewa zata jaza mata asara mine-mine, da dukkanin alamu ba ita ce ta haife ta ba in...... "Kinga Malama dan Allah babu ruwanki a ciki, miye na wani tsayawa ki gaya mata abunda ya shafi rayuwarmu ne, kawai ku bamu sallama mu wuce inda dare yayi mana, ni wallahi bana son shiga sharra ba shanu". Inna Zubaida ta k'are maganar tana banga masu harara gaba d'aya. Wani duba sosai Doctor Anam tayi ma Inna Zubaida kamin ta matsa kusa da Farida dake hawaye har lokacin tana kallon abunda Inna Zubaida keyi. Ta ce "ki daina kuka kinji?, zaki iya gane motar data bige ki, ko number motar?". Da shashshekar kuka Farida ta ce. "Na dai rik'e sunan da na gani a jikin Motar". "Yawwa fad'a min miye kika gani?". "Naga ansa *Al'ameen Galadima B Radda* a jikin Mo..... Saurin yin shuru tayi jin yadda Doctor Halisa tayi saurin fad'ar sunan data kira. "Tabd'i jam ubanwaye bai san Y'an gidan B Radda ba, dan ubanki ubanwa ya kaiki sallaka titi kinga irin motocin Y'ay'an Gwamnan Jihar nan zasu wuce, baccin baki da halkali ai gidan da kike aiki ma gidan K'aninsa shashasha ke dan...... "Haba baiwar Allah ki bita a hankali mana?". "Ke Kinga baiwar Allah babu abunda ya shafeki Dani, kuma da kike mata tabbayar ta rik'e number mota ko sunan dake jikin number Motar, mi kika isa kiyi ma wadda ya turmusheta a titin?, kina dai ji babu ubanda bai san Y'an gidan B Radda ba, sune fa da Nigeriar gaba d'aya, Y'ay'an k'usoshin k'asar nan ne fa, ita fa ba y'ar kowa ba ce face y'ar gidan Malam Dauda Mai Faci, dan haka karki sake ki wani sa mata rai da d'aukar mata mataki akan abunda ya faru da ita. Ke kinga Farida maza tashi mu wuce gida, mun gode da irin taimakon da kukai mata". Ta idasa maganar ta kamo hannun Farida mai lafiya ta jata keee suka fice daga asibitin gaba d'aya. "Kashhh wallahi Allah wasu basu da tunani da hankali, ai ta bari taji miye zaki ce ne ko, bata san kema y'ar gidan wuce ba". "Uhuhmm". Doctor Anam ta ce kawai tana cire rigar doctors dake a saman kayan data sa. Tana duban Doctor Halisa ta d'an dafe kanta. Kamin a hankali ta ce "Na rasa miye yasa Y'ay'an Daddy B Radda suke haka, kodan sunga ubansu shine akan muk'amin Gwanan Jahar nan why zasu rink'a taka duk wadda suka ga dama ne?". Dafa ta Halisa tayi tana sauk'e numfashi ta ce. "Banga laifinsu ba, amma abunda suke yayi yawa gaskiya, kiyi hakuri akan abunda zan fad'a dan na sani da ciwo tunda Y'ay'an K'anin Mahaifinki ne, amma su guje ranar da zasuyi muguwar nadamar da bata da anfani wallahi. Kinga kamar ke babu wadda ma zai kalle ki a yanzu ya ce ke y'ar wani ce a K'asar nan, baki d'auki kanki komai ba, aikin dake gabanki shine kawai kike, shi yasa wallahi kike sake birgeni idan ma kin fad'a ba babu wadda zai ce ke y'ar gidan B Radda ce". Shuru kawai Doctor Anam tayi domin ranta sosai ya b'ace akan abunda yake faruwa a cikin family nasu. _____________________ "Why Dad mi yasa su Faruk B Radda da su Al'ameen G B Radda zasu rink'a d'aukar kansu da nesa haka ne?, wata fa yarinya ya bige da mota amma ya wuce kamar wadda ya bige Dabba ba D'an Adama ba, rayuwa zata tafi a haka ne?". Dad dake zaune akan Darning table su duka Y'an gidan ne, Anam Sai K'anwarta mai bi mata, sai Mom ita dake zaune daga gefen Dad. Ya d'an zare gilashin idonsa yana duban yarinyar ta shi zaiyi magana Mom ta rigasa. "Anam shin wai ina runki da rayuwar su ne?. Suyi yadda suke so lokaci ne, ni banga wani aibun abunda suke yi ba, matsayi ne Allah ya basu d'aukaka ce Allah ya basu, girma ne Allah ya basu kud'i ne Allah ya basu, sana haka zalika kema dukkanin abunda ya basu kema Allah ya bawa naki Mahaifin, kema kiyi yadda kike so mana, amma sai wani tauye kanki kike kin hana kanki shak'atawa, kin hana mutane su san wacece ke, kin wani je asibitin talakawa asibitin Gwamnati kina aiki kamar ke haba, wallahi idan na tuna wannan abun karki ji yadda nake jin haushinki sosai, shi yasa ta wani wajan K'anwarki Hanan tafi ki sanin mi cece rayuwa da matsayinta". Tab'e baki kad'an Hanan tayi tana cewa. "Mom ai ni banzan iya zubar da class d'ina kamar yadda Aunty Anam ke yi ba wallahi, ina banga d'an talakan da zai raina ni na kyale shi ba wallahi" "Ke da'aAllah rufe ma mutane baki a nan wajan, ansa dake ne marar kunya? Duk ba halinku d'aya da su Ameen d'in ba, duk ba dake suke zuwa yawan banza aje waccar k'asar aje wannan k'asar kullum kune y'an yawo K'asashe k'ashe, kuma wallahi Allah kin kusa daina fita kwata-kwata ma kuwa". Cewar Anam rai ba b'ace tana kallon Hanan dake turo baki gaba. Mom ta dafa Hanan ta ce. "Rabu da ita kinji Autata babu wadda zai hanaki shakawata wallahi, kema ai ba hanaki akai ba, kece kika tauye kanki, dan haka bazai yuwu kuma ki ce zaki tauye wani ba". Dad dake kallon kowa a cikinsu yayi shuru, Anam ganin Dad shurun nasa yayi yawa yasa ta kwab'e baki tana cewa. "Uhum uhum haba Dad ka ce wani abu mana, kayi shuru". Murmushi ya d'an saki kad'an kamin ya ci gaba da cin abincinshi hankalinsa kwance ya ce. "Ni duk banga abunda tada hankali ba Anam, kiyi rayuwarki yadda kike so, suma ki barsu suyi yadda suke so, kinga dai ni K'anin Babansu ne, banda ikon ce ma ubansu gashi-gashi, kuma kinfa san bana son shiga harkar wasu, so please kima daina d'akko irin wannan damuwar kina gaya min please". "Yawwa Dad shi yasa nake sonka wallahi, baka da takura ko kad'an, amma Aunty Anam kin cika shiga abunda babu ruwanki a.....kwaffffff Anam ta bige bakin Hanan dake maganar. Tab'e baki Hanan tayi da sauri ta saki wani kukan sangarta, domin ba wata bigewa ba ce Anam d'in tayi mata, amma shine harta wage baki tana sakin kuka. Tashi Mom tayi tana kallon Anam ta ce. "Kinga Anam daga yau gaskiya karki sake d'akko damuwar wasu ki kawo ta cikin gidan nan, kije can ke ta shafa, tunda ke ce kika je can cikin talakawa kika d'akko ta, karki sake bigar min yarinya akan wasu talakawa can". Juyawa Hanan tayi zata bar wajan Darning d'in kawai suka ci k'aro da Farida mai aiki. Tassss K'arar mari ya k'arad'e wajan. Da mugun sauri Farida ta dafe k'uncinta tana rik'e hannunta wadda ya samu karaya tana jin wani zugi da rad'ad'i domin bata lura bane ta sawo kai wajan, suka yi karo da Hanan, hasalima Hanan d'in ce ta bangaje ta har tana bangaje mata hannun data kare dashi, amma shine kawai ta d'auke ta da mari. "Ke wacce irin dak'ik'aya ce ne? Ku wai rayuwarku komai zakuyi sai kunyi na rashin hankali da gidadanci ne?, idan kikai wasa zakiyi ta bakin aikin ki wallahi shashashar banza kawai". "Dan girman Allah Ranki ya dad'e kiyi hakuri, wallahi banga kin sawo kai bane, ai da bama zan biyo ta inda kike ba". "Dalla can ni rufe min baki". Hanan ta k'are maganar tana sakin wani dogon tsaki ta wuce ta tana jefa mata kallo irin na k'as-k'anci. Anam zatai magana Mom tayi mata wani kallo wadda yasa dole ta shanye abunda take son fad'a d'in. Dad kuwa tashi yayi ko a kwalar rigarsa ya haye sama, domin shi baiga wani aibun abunda Hanan d'in tayi ba, danya saba ganin hakan a wajanta ko Mom, Anam ce kawai baya ganin tana ma masu Aiki tsawa kota kyare su. Farida ta d'ago, sai fuskarta ta cika da mamaki ganin Doctor Anam, tunda ta fara aiki tsawon sati biyu a gidan, basu tab'a had'uwa ba, sai a asibiti sai kuma yanzu data san cewa y'ar gidan ce. "Keeee dalla can ubanmi kike kuma a tsaye har yanzu? Da ba zaki fara aikin daya kawo ba?". Cewar Mom data mik'e tsaye itama. "Kiyi hakuri uwar d'akina" "Da anyi magana kiyi hakuri, rik'e hakurinki Malama. Sana miya hanaki zuwa da wuri yau?, kina so ki rasa aiki ne?". Da sauri Farida ta fara girgiza kanta bakinta na kyarma ta ce. "Dan Allah Haj kiyi hakuri, wallahi ina kan hanya ta ta zuwa gidan nan Mota ta kad'e ni, shine yasa banzo da wurin ba, kin gani Haj har karyewa nayi amma a ha...... Saurin yin shuru tayi ganin Mom ta d'aga mata hannu tana cewa. "Kinga Malama dakata please, wannan keta shafa, bana son yawan surutu kin sani, ki fara aikin dake gabanki kawai". Ta k'are fad'ar haka ta bar wajan itama, aka bar wajan daga Anam Sai Farida tsaye. Sauke ajiyar zuciya Farida tayi wasu hawayen tausayin kanta da duk wadda yake cikin hali irin nata, na aiki k'ark'ashin wa'inda basu san darajar D'an Adam ba, dole yasha wahala irin haka. Jin an rik'o hannunta yasa ta d'an firgita, sai kuma ta ja wani dogon lumfashi tana kallon Doctor Anam data rik'o hannun nata. "A madadinsu ina mai baki hakuri kinji?, yanzu a hakan kika taho aiki?". "Uhuhmm Haj kenan ai babu komai rayuwa ce fa, karki damu idan ma banzo ba wahalar da zan sha a gida ai sai ya fiye min alkhairi gara na zo nan d'in kawai. Ashe Ranki Ya dad'e ama gidanku nake aikin rashin sani?". "Uhuhmm ai tun lokacin da kika fad'i sunan Dad nasan gidanmu kike aiki, ban dai nuna bane kawai". "Lallai Ranki ya dad'e wallahi halinki ya banbanta da saurin Y'an Family naku, ke kam kinji dad'i abunki, Allah yasa ki d'ore da halin nan naki". A cikin zuci kawai Anam ta amsa da amin. Da sauri Farida ta d'an zabura ta ce. "Ranki ya dad'e bari na fara aikin nan, na barki lafiya". Ta k'are maganar tana tattare darning table d'in duk da hannunta d'aya bata iya aiki dashi, haka take cije baki da kyar take k'arfafa ma kanta gwaiwa take aikin, domin idan ma bata yi ba tasan abunda zai iya faruwa da ita, to gara taji wannan azabar da hannunta ke mata zai daina ne na d'an lokaci ne. _____________________ *Government House Katsina State Nigeria* "Asabee!! Asabee!!" Da mugun sauri har Asabe na tuntub'e ta k'araso wajan tana zubewa k'asa akan gwaiwowinta. Bakinta na kyarma wajan cewa. "Ranki ya dad'e ga ni". "Ke wai wacce irin jahila ne? Sau nawa zance miki a rink'a goge kujerun nan sau biyar idan aka tashi? Dubi d'akin nanma wani k'arni nake ji, hatta toilet d'in nan bai min yadda nake so ba". "Dan Allah kiyi hakuri Ranki ya dad'e za'a sake aikin yadda kike so kiyi hakuri". "Mtswww, wallahi daga yau idan na sake fitowa na iske ba dai-dai ba to ki kuka da kanki". "Baza'a sake ba Ranki ya dad'e da yardar Mai Sama". Wani Tsakin Amal tayi tana zama kan gadonta wadda ya gaji da had'uwa iya had'uwa. Danna wayar take saiga Sa'ade wata mai aikin ta shigo da rawar jiki, a k'asa ta duk'a ta fara cire mata takalmi ta kama k'afar tata ta saka cikin wani ruwa da yaji kayan k'amshi da turaruka, tana wanke mata k'afar, had'e da yanke mata farce, tana yi tana taka tsantsan sai ka ce tana wanke kwai. D'an rantse ido da sauri Amal tayi jin kamar dan zafi a k'afar tata, d'agowa tayi tana cewa. "Keee Kee Kee Sa'ade baki gani ne ke?, ke makauniya ce ne?, ki rink'a yin abu da hankali mana, na kusa asa a sake min ke tunda naga kullum so kike kiji min ciwo haka kawai a banza". Jiki na rawa Sa'ade ta ce. "Haba uwar d'aki na, kimin rai dan Allah kiyi hakuri za'a gyara wallahi". "Mtswww na dai gaya miki". "Wallahi naji ranki ya dad'e za'a kiyaye" Sake mik'a k'afar tayi Sa'ade ta ci gaba da yi mata yadda take so. Sun shafe kusan awa d'aya ana wanke k'afa kad'ai, ita ko sai faman danna waya take tana cin biskit mai d'auke da wata irin Zuma a ciki da Madara had'e da wani lemo da aka aje gefe guda. Ta d'auki kusan awa uku kafin ta gama shiryawa gaba d'aya ta sakko k'asa. Kallon su Faruk tayi tana d'an tab'e baki ganin yadda suka ci ka Darning table d'in da surutun su. K'arasowa tayi tana taku d'ai-d'aiya, kamar wacce ke tsoron taka k'asa. Kallon K'anwar tasu su Ameen suka yi har suna had'a baki wajan cewa. "Wow My K'anwa dole ne ki rink'a cizon gayu fa, shi yasa muke ji dake a family namu ke da Hanan Allah kun san miye kuke yi fa, Banda waccar Anam d'in ita kwata-kwata bata waye ba wallahi". "Uhuhmm" Kawai Amal ta ce ta ja kujera ta zauna tana aje y'ar k'aramar jakar hannunta had'e da key d'in mota dake hannun tana kallon su ta ce. "Shi yasa ai bama jituwa da ita, sai ka ce Y'ar daji kwata-kwata bata da class Aunty Anam, wallahi tana bada mu, ni k'ara jin haushi na ma, ta rasa inda zatai aiki wai sai asibitin marassa gata". Al'ameen ya d'an tab'e baki yana cewa. "Ai ita hakan da take ba wani abu bane take gani a tunaninta wai hakan shine wayewa, so take muma mu koma irinta fa". Da sauri Amal ta ce "ai ina itama tasan bazai yuwu ba, babu yadda za'ai na iya zama irinta, domin ni bana son raini ko kad'an a cikin rayuwata, bazan iya bari wani d'an talaka ya zo dai-dai dani ba wallahi" Faruk ne ya d'an sauk'e lumfashi kad'an kamin ya d'an d'age k'afad'arshi kad'an ya ce. "Ku manta da zancanta please. Wai ya maganar tafiyarmu Gowa ne? Yaushe kuke ganin zamu yi tafiyar nan ne?". "Wow Y Faruk kasan harna sha'afa da tafiyar nan ma?. Kan uba zamu fa rak'ashe a Gowa d'in nan fa, ina son yanayin K'asar, shi nida Jasmin da Hanan zamuyi tafiyar nan, sai kum.... Al'ameen ne ya katse Amal da cewa. "Sai kuma wannan ana can Saurayin nan naki nasan zaki ce". "Ke ma fa Amal ta wani wajan kina kwafsa mana fa, kina biye wadda bai kai Mahaifinki kud'i ba, waye ubansa a k'asar nan, kamata yayi ki samo D'and'anan wani K'usa a k'asar nan, amma sai kika b'ige ga Wannan gyu d'in Faisal". Cewar Faruk. "Uhuhmm Y Faruk bazaka gane ba, Faisal yayi ne, wai baku ganin tsananin kyansa ne da gayunsa, yayi kota ina yana da class shi yasa nake sonshi, kuma ai shima ubansa yana da kud'i kawai dai bai kai kud'in nawa uban bane, shine kawai kuke ganin ya kwafsa". "Hmmm shikenan dai nima da tawa budurwar zanje yawon shak'atawar nan dole ne na kira Hana da ita za'a wannan tafiyar". Fad'in Al'ameen. Ai ko Faruk najin haka yayi saurin cewa. "Ohhh D'anwaken zagaye za'a min kenan?, ai ko nima dole ne zamu tafi da tawa Babyn Jonal". Tab'e baki Amal tayi tana kallon Faruk ta ce. "Ka rasa wacce zaka rink'a ma'ala da ita sai Kristan?". "Uhum Amal kenan sunfi dad'in sha'ani ai". Shuru sukai jin Momma ta sakko wajan, masu aiki ne suka masu suka fara zuba ma kowa abinci suka fara ci, suna wasa da dariya da Momma saika rantse cewa ba ita ce ta haife su ba, domin kwata-kwata jikinta bai nuna hakan ba............. *GAWA TAFE* (Zombies story) On2025 *©Zahra Royal Star* *ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION* *EPISODE 2* "Bana buk'atar fita da kowanne jami'in tsoro, da'aAllah ku matsa ku bani waje na wuce" Wani daga cikin jami'an tsoron ne ya d'an duk'a har k'asa yana cewa. "Please Ranki ya dad'e Amal mai gida ne ya hana duk d'ayanku da zai fita, a tabbatar an basa wani jami'an tsoro koda mutum d'aya ne ya fita dashi, kiyi hakuri ga Anjali kuje tare please kar muyi laifi wajan mai girma Gwamna". Wani tsaki taja tana duban Anjali dake gefenta, sanye take da kayan jami'an tsoro itama, dama kuma ita ce mai bata kariya, duk inda take to zaka ga Anjali a wajan. Key d'in mota ta wurga ma Anjali ta duk'a k'asa ta d'auka, da sauri ta bud'e mata gidan baya ta zauna, ta maida murfin ta rufe ta zagaya gidan gaba wajan mai toki taja motar suka fice daga gidan. Basu dad'e da fita ba su Faruk suka fito, su dama sunfi so idan zasu fita ayi masu Jiniya, jami'an tsoro suna take masu baya, sai idan zasuje wajan shashanci sune hatta kansu jami'an tsoron basu san lokacin da suke sab'ewa suyi tafiyarsu harsu dawo basu sani ba, saboda akwai b'arauniyar hanya a gidan gwamnatin, wadda sune kad'ai suka san da ita. Kiiiiiiiiiiiii "Ohhhh My God" Anjali ta furta da k'arfi. mugun sauri Anjali taja wani uban birki motar ta tsaya, har Amal dake baya ta d'an bige da jikin Motar. A yamutse cike da masifa Amal ta d'ago tana cewa. "Wannan wane irin hauka ne Anjali?, baki da hankali ne so kike ki kashe ni da raina?". "Ranki ya dad'e please kiyi hakuri dan Allah, wata Tsohuwa ce ta shigo mana gaba zata tsallaka titi ne". Zaro ido waje Amal tayi cike da tsallar jin haushin ko wacece ta shige masu gaba, ta kai dubanta gaban titin ganin Tsohuwar har yanzu sai wani d'angyasa k'afa take had'e da sandarta tana dogarawa, har sun ma d'an bigeta tana k'ok'arin tashi da kyar. Rai a mugun b'ace cike da tsanar talaka a cikin ranta Amal ta wani bud'e mota ta fito. A wulakanci Amal ke kallon Tsohuwar ganin zata dafa masu mota tana son mik'ewa, Amal tayi saurin saka k'afar ta hanb'arar da Tsohuwar tana tofa mata miyau akan fuskarta tana cewa. "Kee da'aAllah magidajiyar Tsohuwa kawai, saboda tsabar gidadanci irin naku na talakawa kawai ki shigo titi tsabar rashin hankali da wayewa, titin na gidanku ne da zaku rink'a hawansa kara zube haka?, sana karki sake k'azamin hannunki ya sake tab'a min Mota aikin banza kawai". Amal ta k'are maganar tana nuna Tsohuwar dake d'uke a yanzu tana mata kallon tsallar mamaki. Mutane da yawa sun tsaya suna kallon abunda ke faruwa, wasu y'an mata ne dake nesa da wajan suna tafe zuwa wajan suna cewa. "Kee wa nake gani kamar d'iyar B Radda Gwamnan Jahar nan?". "Yo ita ce mana, gata can tana wulakancin nata da ta saba, dama kuma na dad'e ina jin ana cewa duk Y'ay'an Gwamnan nan mai ci yanzu basu da mutumci wulakanci ne dasu, idan ka bari wata hud'd'a ta had'aka dasu, sai sun k'ask'astar da kai sun nuna maka kai ba kowa bane". "Yo ubanwa zasuyi mawa, ai Mulki ba hauka bane wallahi, kuma suje ai duniya ce tafi Bagaruwa iya jima wallahi. Ki duba irin d'ibar albarkar da take ma waccar Tsohuwar miye laifinta? Dan kawai tazo tsallaka titi motarsu ta shawo Kai?, Ai suma da laifinsu tunda ba toki suke na kwanciyar hankali ba". Irin wannan maganganun ke tashi a wajan. Anjali ma fitowa tayi tana son yima Amal maganar abunda take ba dai-dai bane, amma tana shakkarta. Tsohuwar da kyar ta mik'e wata mata na kamata Tsohuwar tana kallon Amal dake dod'e hancinta tana yamutse fuska ta ce. "Uhuhmm yarinya kenan, kibi duniyar a hankali, saboda ba matabbata ba, ce ku guji ranar da zaki nemi taimakon wani kuma kina ji kina gani ya kasa taimaka miki har ki halaka kina ji kina gani da idon ki..... "Ke kinga baiwar Allah ki rik'e wa'azinki na saba jinsa daga bakunan jama'a, dama ku talakawa ba abunda kuka iya sai y'ar k'aramar murya, wai dan kawaii aji tausayinku. Ke Anjali dalla shige muji, mubar wajan nan wari ma wajan keyi mtswww". Ta k'are fad'ar haka tana shigewa motar da sauri, mutanan dake wajan sun saki baki da hanci suna jin d'ibar albarkar da wannan y'ar yarinyar ke masu. ______________________ "Baby na mike faruwa ne?, kin iso ranki duk a b'ace". Kallon Faisal tayi tana narke fuska, ta kalli Anjali tana d'an b'ata fuska ta ce. "Please Anjali d'an bamu waje ko?". Matsawa Anjali tayi kawai tabar wajan bata ce komai ba, tana kallon yanayin wajan da suka zo d'in. Waje ne irin na shak'atawa, irin na Y'ay'an masu hannu da shuni ne kad'ai ke shawagi a wajan, kowa ka kalla yana ji da kanshi a wajan. Kamo hannu Faisal Amal tayi a shagwab'e ta ce. "Honey wata Tsohuwar banza ce ta b'ata min rai a hanyarmu ta zuwa wajan nan, wai mi yasa shi talaka fakiri ne ba abunda ya iya sai shashanci da k'auyanci, shiga fa tayi a gaban motar mu kawai ta wani hau titi sai ka ce titin na ubanta ne mtswwwww". Murza hannunta yake yana sake shigewa mata, yana wani shinshinar wuyanta had'e da hura mata iska, a hankali taji ya had'e bakinsu waje d'aya, bata hanasa ba saima wani d'an murmushi da saki tana tallafo kansa itama. Jama'a karku ce wasu sunma hangi miye suke yi, saboda da yawa wajan wayayyu ne, rayuwa ake kamar ta turawa, kowa ga gani a wajan d'an iskan kanshi ne. Sakinta ya d'anyi yana jifarta da murmushi ya ce. "Manta da wasu talaka Babyn, ya maganar tafiyarmu Gowa?". "Ohh abunda na zo mu tattaunawa kenan, mu y'an gidanmu su Faruk mun gama tsara yadda za'ai tafiyar, kaga ni da kai sai Jasmi na kira wayarta itama zata zo nan zamu had'u yau zamu gama tsara yadda za'ai". "Yawwa Baby ki shirya zuwanmu Gowa zaki bani kyautar..... "Na sani ba sai ka fad'a ba ai" Murmushi ya saki na shak'iyaancin yana kanne mata ido d'aya. "Wow My friend ashe har kin rigani isowa?". Zama Jasmin tayi tana fad'ar Hakan. Tafawa sukai Amal ta ce. "Shegiya K'awata wannan muguwar shiga haka, kina lokaci fa". Dariya Jasmin tayi tana kallon wani D'an iskan wando data saka da wata y'ar riga ko cibiyarta bata rife ba. Ta ce "kema kinsan bana son kaya masu nauyi just bana son takura. Yawwa wai yaushe ne zamu bar K'asar nan ne na K'usa fa Guys?". "Maganar da muketa yi kenan, inaga bamu wuce cikin Satin nan gaskiya". Fad'in Amal. Jasmin ta d'aga kai ta ce "wai ina shegiyar nan ne Hanan?". "Hhhh ai ko yanzu kin ganta wajan nan itama ai duk da ita za'ai tafiyar". Cewar Faisal "Ki ce zamu rak'ashe da yawa a Gowa, Gowa zatai d'ibar Y'ay'an Manyan K'asar Nigeria". Fad'in Jasmin tana murmushi da d'okin tafiyar. *HANAN POV* "Ke Farida kiyi saurin had'omin Copi, ina sauri ne zan fita pls". Hanan ta k'are maganar tana zama d'aya daga cikin kujerun babban parlon gidan nasu, tana latsa waya, bata kalli inda Farida ke goge a parlon ba. Farida da rawar jiki ta amsa tana shigewa k'aton kitchen d'in parlon. Duk da yawan ma'aikata dake kitchen d'in amma ita ce kad'ai suka yadda da girkinta, shi yasa tana aikatuwa a cikin gidan ba d'an kad'an ba. Da rawar jiki ta k'araso inda Hanan take a zaune, rik'e da cofi na copin data had'u mata. "Gashi Ranki ya dad'e an gama". Hannunta ta mik'a again tana latsa wayarta ta amshi k'ofin dake hannun Faridar. Kaiwa bakinta tayi tana latsa waya, kurb'a d'aya tayi da mugun sauri a zabure ta furzar dashi sai akan fuskar Farida. A zabure Farida ta saki k'ara tana mik'ewa tsaye, domin taji zafin copin ta furzar mata akan fuskarta. Hanan rai a b'ace tana nuna Farida da yatsa tana cewa. "Kan uba, so kike ki kashe ni Farida?, kinji zafin abunda kika had'u min kuwa?, waike mi yasa komai zaki yi sai kinja an zagi ki?, wannan wane irin jakanta ce haka, ace mutum kullum sai ance baiyi dai-dai ba, sai ka ce wacce ke da Kwakwalwar kifi". Zubewa Farida tayi a k'asa tana had'e hannunwanta waje d'aya alamar neman afuwa tana cewa. "Kiyi haku...... "Dalla can rik'e hakurinki Malama". Ta k'are maganar tana sakin kofin a hannunta ya fad'i k'asa ya tarwatse, ta nunata da yatsa ta ce. "Ki kiyaye a nan gaba, idan ba haka ba kin san sauran, kuma ki fara shiri domin dake zanyi tafiya Gowa, domin ki rink'a min hidima a can, saura idan munje can d'in ma ki rink'a min Jakanta kamar yadda kike min nan". Rasssssss Farida taji gabanta ya yanke ya fad'i lokaci d'aya, haka kawai taji gabanta ya ci gaba da bugawa, jin abunda Hanan d'in ke fad'i, bata san mi yasa taji ta tsani ayi tafiyar nan da ita, tasan zasuyi tafiya tabbas zasu bar K'asar zuwa shak'atawa amma b'ata tab'a tunanin cewa wai da ita za'a tafi ba, b'ata tab'a ganin irin haka ba ita kam, zaka je shak'atawa tsabar sangarta har sai ka tafi da mai maka hidima? "Tsayuwar uban mi kike kuma a nan?". Fad'in Hanan tana ma Farida wani duba. Da sauri Farida ta katse tunanin data fad'a jiki na rawa ta ce. "Yi hakuri Ranki ya dad'e". Ta fad'i hakan tana barin wajan. Anam ce ke sakkowa tare da Mom har Anam na kyarmar fad'in. "Mom kinji miye waccar yarinyar ke fad'i ko?". "Naji mana, to miye a ciki?, idan ta tafi da Farida, ai zata rink'a mata wasu abubuwan ne a can". "Nooo Mom bai kamata ma ki bari taje wani yawan shak'atawa ba wallahi why Mom d...... D'aga mata hannu Mom tayi dai-dai sun idasa sakkowa k'asan ta ce. "Kinga Anam bana ce miki ki daina shiga harkar da babu ruwanki a ciki ba?, so please ki kyale yarinya tayi yadda take so mana, kuma nake ganin ai ba ita kad'ai zatayi tafiyar nan ba, ita fa dasu Amal da kuma su Al'ameen Yayyunta, zasu tafi, kinga kuwa banga abun tada hankali ba ai". "Mom ki ce kawai shashancinsu zasu tafi wallahi, ai duk inda aka sami su Amal dole akwai shashanci a ciki, Mom dan Allah kima Dad magana ya soke masu Tafiyar nan, ni haka nan tunda suka fad'i tafiyar na ji kwata-kwata bata kwanta min ba, suyi hakuri da ita mana zuwa wani lokacin". Hanan dake kallon Anam ji tayi kamar ta shik'e mata wuya, tsabar jin haushinta. Ji mata da'aAllah nason masu bak'in ciki k'iri-k'iri. "Kinga ko Aunty Anam babu abunda ya sha miki kai da tafiyarmu, ai bamu ce dake zamu je ba dai ko?". "Ki rufe min baki Hanan, ni yama za'ai nayi tafiya irin wannan daku Allah ya tsare ni wallahi, kuma zaki ci ubanki ne idan ina magana kina sak'o min wannan shegen bakin naki". Kwab'e fuska Hanan tayi tana murgud'a mata baki. Mom data zauna akan kujera tana d'aukar romot d'in Tv ta canza tasha tana cewa. "Kwantar da hankalinki Autata babu wadda ya isa hanaku tafi Gowar nan, tama yi ta gama" Sakin baki kawai Anam tayi tana duban Mom, can ta sauke wani lumfashi tana gyara tsayuwarta ta ce. "To tunda dole ne ance tafiyar ta su, Mom karta sake ta ce zata d'auki Farida su tafi tare, domin banga dalilin da zaisa dole sai an d'auki Farida ba". Wani kallo da Mom ta jefa mata ne yasa ta d'an had'e wani miyau daya tsaya mata a mak'oshinta, tana sake kallon Mom d'in. "Anam kifa fita ido na rufe tom, da ita d'in zata tafi, ko ke ce kika d'auke ta aiki ne ban sani ba?" "Ni Mom bani na d'auke ta aiki ba, am... "Kinga zo ki wuce wajan aikinki ya fiye miki, domin b'ata ma kanki lokaci kawai kike a yanzu". Ranta babu dad'i ta juya ta fice daga parlon. Mom na kallon ta fita taja wani lumfashi duk da itama tafiyar bata wani kwanta mata ba, amma kamar an d'aure mata jijiyoyin jikinta da bakinta ta kasa furta ainafin abunda ke cikin ranta. A hankali ta ce. "Ace ayi mutum yayita shiga abunda babu ruwansa". Hanan dake murmushin cin nasara ta rungume Mom tana cewa. "Mom wallahi shi yasa nake k'ara sonki, bari naje su Amal na can suna jira na, zamu tattaunawa akan tafiyar da zamuyi Gowa". "To sai kin dawo, am.... "Haba Mom karki ce komai, kawai sai na dawo d'in dai". Ta k'are maganar tana kai mata kiss a goshi tayi saurin ficewa daga parlon, domin ta lura kamar Mom d'in na son yarda da maganar Anam d'in. _______________________ *HARUN POV* a hankali yake juya y'ar kujerar da yake zaune akanta. Sanye yake da kakensa na Soja, wadda suka k'ara haska fatarsa Chocolate color, dara-daran idanuwansa ya lumshe yana sake bud'e so. Dokar daji ce suke, yak'i ne akai Babban gaske, daka kalli yanayin wajan da suke zaka shaida hakan, saboda gawawwakin dake yashe a wajan, da wasu tsirarun Sojoji dake wajan, sai wasu Gawawwakin Sojoji suma dake kwance a wajan cikin jini. "Harun Yaya dai?". Kallonsa ya kai inda yaji kiran nashi a hankali ya sake ware idanuwansa sosai akan abokinsa shima dake sanye da kaken Soja. Cike da tsananin gajiya ya ce. "Noo ba wani abu Captain Joha" "Dole Harun jikinka yayi ciwo, ban tab'a ganin mai k'ok'arinka ta fanin yak'i ba, dubi fa irin mutanan da kashe wajan aikin nan, yama kamata muzo mubar cikin jejin nan gaskiya" A hankali ya d'an mik'e akan kujerar da yake kai duk jikinsa jini ne sai wasu y'an ciwuka da baza'a rasa ba. Kujerar daya tashi Joha ya kalla domin irin kujerar Mota ce data rugugguje ta fita daban, a dai-dai lokacin daya kashe wani d'an daba wadda ya addabi mutane da dama, sunsha artabu da Harun kamin Allah ya basa damar kashe sa, yana kashesa kuma ya fad'a kan kujerar yana sauke wani lumfashi mai cike da gajiya. Ganin Harun d'in yayi nisa ya barshi ga jirginsu dake shirin tashi domin barin Jejin, da sauri da d'an gudu-gudu ya k'arasa inda yake, kusa a tare suka shige jirgin ya d'aga dasu suka bar cikin Jejin dake ci da wuta ga gawawwakin jama'a nan, sun bar wasu Sojojin na aikin jidar wa'inda suka rasa ransu a wajan............. *GAWA TAFE* (Zombies story) On2025 *©Zahra Royal Star* *ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION* *EPISODE 3* "Why Amal zaki je tsakiyar titi ki fito kina ma mutane tsawa?. Ki duba video yadda y'an adawa ke yad'ashi suna magana marar dad'i akai na da iyali why mi yasa?". Fad'in Abbie dake tsaye yana nuna ma Amal wayar dake hannunsa ransa a b'ace yake maganar. Amal kuwa dake tsaye shagwab'e fuska tayi tsabar ta saba masa sangarta ta ce. "Sorry Abbie wallahi banyi hakan dan b'ata siyasarka ba, kasan talakawa ba abunda suka iya sai shige ma masu kud'i, kawai fa Abbie muna tafiya tsakiyar titi wata banzar Mata ta shigo mana gaba, ni kuma shine...... "Shine ke kuma kika tsaya tsakiyar titin kina d'iyar Gwamnan Jahar nan kina cece kuce da jama'a, kuma dama kin san magauta kiris suke jira su yad'a abunda bashi kenan ba. Yaushe ne tafiyarku Gowa?". Wani murmushi ta saki na tsallar murna ta ce. "Yesssss Abbie cikin weekend zamu tafi". "Noo na dawo da tafiyar taku zuwa gobe, gara ki bar K'asar keda wa'innan Yayyun naki kuje can ku d'an huta, saboda maganar mutane akanku yanzu tayi yawa, gara ku tafi can, dan in kina ganin mutane irin na K'asar nan dole hakan zata rink'a faruwa, canfa duk masu kud'i ne ke zuwa K'asar shak'atawa, so kamar nawa kuke son tafiya dashi?" "Wayyo dad'i Abbie Allah ya saka, Abbie kamar Million's...... Faruk ne ya yayi saurin katseta da shigowarsu kenan parlon suka ji maganar Abbie ta k'arshe inda yake tabbayar kamar nawa zasu ishe su tafiyar. "Abbie kamar Million's biyar-biyar ko wannan mu ta ishesa nake gani ko guys?". Ya fad'i yana duban su Amal da Al'ameen. "Yesss Abbie saboda muda friend d'in da zamuyi tafiyar dasu" Cewar Amal tana kallon Abbie dake kallonsu. Abbie ya juya wajan P'A d'insa yana basa umarnin ya turowa kowannan su naira million shidda-shidda ta account d'in kowa daga cikinsu. Wani tsalle Amal ta daka tana rungume Abbie jin harda k'ari yayi masu akan wadda suka tabbaya d'in. Murmushi ya d'an saki yana cewa. "But sai kun rink'a lura idan zaku fita cikin gari, kusan inda ya dace ku rink'a abubuwa, saboda yanzu sai kuga abu k'arami magauta na son mayar dashi babba, yanzu miye dan kawai kin fito kin tsawatarwa wannan Tsohuwar?, why mutane yanzu kamar jira suke su fara zaginka, dama nasan shirrin mak'iya ne kawai, sai ku kiyaye gaba d'ayanku, baima kamata kuna bi Local waje irin wadda zaku rink'a had'uwa da wa'inda basu san miye duniyar take ciki, just ku rink'a ma K'anwarku fad'a Faruk". Da to suka amsa ya haye sama P'A d'insa yana take masa baya. Yana bin Y'ay'an gata da kallo, lallai giyar Mulki na d'ibar wasu mutanan, dubi dan Allah yadda yayi kyauta Millions shidda ga kowannan su, kamar yayi kyauta naira biyar. Fad'in P'A d'insa a zuci yana bin bayansa yana maganar zuci. _____________________ *1100pm Umaru Musa Yar'Adua Airport Katsina State Nigeria* Gaba d'ayansu ne tsaye a filin jirgin. Wasu matsiyatan kaya suka saka kusan zan iya cewa duk iri d'aya ne, saboda k'ananun kaya ne wadda sukai masu mahaukacin kyau. Daga gefen Amal harda Anjali za'a tafi saboda ta rink'a tare mata wasu abubuwan, tana kula da ita, sai Jasmin. Hanan ma tare suke da Farida wacce aka bata kwancan kaya, shigarta itama ta k'ananun kayan ne, dan dai ita ko ina a jikinta a rufe yake. Daka kalli yanayin fuskarta zaka shaida cewa ba dan tana so za'ai tafiyar nan da ita ba. Domin sai da sukai uwar watsi da Inna Zubaida a sadda ta koma gida take shaida mata zasuyi wata tafiya da ita k'asar waje, ita gaskiya zata ce masu ta daina masu aikin, bazata wani bisu zuwa K'asar da bata sani ba, tafiyar ce kwata-kwata bata kwanta mata ba. Ai ko tasha zagi da kwashe albarka sai cewa mata take "Sannu y'ar bak'in ciki irin tsiya dangin tsiya sannu kinji na ce. Ai ko ko kina mutuwa kina farfad'owa billahir azim Farida sai kin bisu ko da bangon duniya ne kuwa, shi uban naki da bai da aikinyi sai Faci ba gashi can a bakin titi ba, kullum ba abunda ya iya sai maula, ni ce dai rufin asirinku gaba d'ayanku, to wallahir azim baki isa ba, garama tun wuri ki fara shirin tafia, ke baccin ma baki da tunani da hankali za'aje dake k'asar waje kina wani k'i, tsabar dama ke ta daji ce, ba abunda kika sani sai k'auyenci, yo ina laifin wadda ya ce zai kaika inda baka tab'a zuwa ba ko a mafarki, baki tab'a tsammanin zaki fita wata k'asar waje ba, ke ko Niger wannan dai ta kusa damu, ubanki baida arzik'in kai ki, bare ance k'asar turawa zakuje". Inna Zubaida ta dad'e tana zagin Farida kamar zata rufeta da duka. K'arshe dole Farida ta yarda da tafiyar, tana kuka ta koma gidan aikin nata, tana tunanin da Mahaifiyarta na raye wallahi tasan ko za'ayi mi, bazata tab'a bari taje ma aikatau d'in ba, bare harta had'u da wa'inda basu san darajar mutum ba, bare kuma ace za'ayi wata tafiya da ita. "Keee wai wacce irin sakarai ce ne, komai sai ance kiyi ne? Ko kuwa komai sai an nuna miki yadda zakiyi? Tsabar k'auyenci irin naki?". Fad'in Hanan tana banka mata harara. "Kayi hakuri Ranki ya dad'e banji miye kike cewa ba?". "Ya za'ai kiji mi nake cewa, tunda kin lula duniyar k'auyenci, sai wani bin mutanan wajan nan kike da ido". K'asa tayi da kanta, ita harga Allah tana dai kallon jama'a ne amma wani abu can take tunani a ranta, ba wai kallon mutanan wajan ba. "Sai ki mai da hankalinki sosai za'a fara kiran sunaye, idan kinji naki Zaki iya biyo bayanmu, bana son yawan magana na gaya miki". "Insha Allah Ranki ya dad'e za'a kiyaye". Tsaki kawai Hanan taja tana k'ara gyara y'ar jakar dake hannunta irin ta gayu, sai wayar da take shirin sakata a ciki. Amal ta kalli Hanan ta ce. "Ashe kema haka kike fama da irin gidadawan mutanan?". Ta k'are maganar tana kallon Farida da kanta ke a k'asa tana jinta. " Wallahi fa kin dai gani, ai ni uban mutum nake ci wallahi a zauna lafiya, domin ni bana d'aukar shashanci". "Hhhhh haba k'awata, nima sai ka ce baki san wace ni ba, ni ai inaga na fiki rashin d'aurkar raini wallahi". Dariya zaku saki a tare suna kai dubansu wajan su Faruk da wanne cikinsu yake nanik'e da budurwarsa, sai ka rantse ka ce wasu ma'aurata ne. Suna cikin haka aka fara kiran sunayen fasinjojin jirgin, wadda zai d'aga k'arfe sha biyu dai-dai. Gaba d'aya kusan sune suka fara shiga jirgin kwansu da kwarkwatarsu Y'ay'an manyan k'asar ne, abun kamar had'in baki ma, babu wani d'an tagajan-tagajan a cikin jirgin. _____________________ *ANAM POV* A hankali Doctor Halisa ta dafa kafad'ar Anam cike da mamakin yadda ta dad'e tana mata magana amma shuru ba amsa, shine yasa ta d'an dafa kafad'arta. D'an firgita tayi tana dawowa yaccinta. "Lafiya kike kuwa Anam?" "Uhuhmm da sauk'i dai Halisa" Zama Halisa tayi tana duban Anam d'in cike da mamaki tana aje wasu takardu dake rik'e a hannunta ta ce. "Mi yake faruwa ne?". Sauke ajiyar zuciya Anam tayi tana zare wani abun Doctor's dake rataye a wuyanta kamin ta ce. "Akan Family namu ne kawai, wai wata tafiya suka shirya kawai don suje yawan shak'atawa, wai yau da safe har Dad yake ma Hanan kyautar Million biyar, why Fisbilillahi kamar Hanan y'ar haka da ita za'a rink'a mata kyauta Million biyar?". Zaro ido waje Halisa tayi tana had'e wani miyau a zuci take cewa "wayyo Allah dama nice a matsayin ku". A fili kuma ta d'an maze tana cewa. "Tabd'i jam gaskiya anaji da Hanan d'in nan taku, to ai ni Doctor Anam banga abunda shiga damuwa ba a nan". Wani kallo Anam tama Halisa tana cewa. "Amma wallahi ban tab'a tunanin jin haka daga gare ki ba, da nasan abunda zaki ce kenan da bazanyi gaggancin sanar dake damuwa ta ba, haba baki da K'anwa ne a gidanku Halisa?, kamar Hanan ana bata irin wannan mak'udan kud'ad'en, ya za'ai bazata lalace ba, gata tana mace, dama ace namiji ne wannan komi yayi ido ne, ita fa?". Bata san hawaye take ba sai da taji saukar hannun Doctor Halisa akan fuskarta tana d'auke mata su. Jiki a sanyaye Halisa ta rik'e mata hannu ta ce. "Ko kad'an ba abunda kike zargi bane, ni a nawa tunani kawai ki bita da addu'a shine ya kamata, dama a gida ana samun zakka a ciki, ki rink'a sata a cikin addu'o'inki insha Allah komai zai wuce, zaki ga kamar batayi ba insha Allah". Sauk'e lumfashi Anam ta rink'a yi saboda hawayen dake mata zuba sai ma wani k'ara gudu da suka rink'a yi. Rungumeta kawai Doctor Halisa tayi tana d'an bubbuga bayanta. _______________________ *HARUN POV* Gaba d'aya d'akin taron ne aka d'auki tafi, jin an kira sunan Harun. A hankali cike da natsuwarsa ya tashi yana nufar inda shugabansu na Sojoji ke tsaye cike da izzarshi yake tafiya mai jan hankali da class. Kai tsaye inda shuban nasu yake ya tsaya yana Sara mashi. Wata number yabo shugaban ya d'akko ya ratayama Captain Harun, yana saka masa aka sake d'aukar wani tafin mai k'arfi sauran Sojoji dake tsaye kuma suka Sara masu. Number yabo aka basa mai girma tare da k'arin matsayi mai girma a cikin Sojojin. "Mtswww" Kallon na kusa dashi Captain Joha yayi wadda sarai yaji tsakin da ya saki a lokacin da shugaban Sojojin ke k'ara gode ma Harun tare da jinjina akan namijin k'ok'arin da yake yi ta fannin yak'i. Joha ya kasa hakuri ya kalli Abbakar ya ce. "Abbakar ya da tsaki kuma?". "Mtswww nifa na tsani bawan Allahn can wallahi, ace komai sai shine zai zo na d'aya, komai za'asa dashi shine akan gaba, sai kace ba tare Muka zo dashi Hukumar Soja ba, matsayinmu d'aya dashi ada amma yanzu ya k'are mu". Wani murmushin gefen baki Joha ya saki yana kai dubansa inda su Captain Harun suke tsaye, a yanzu ya amshi abun magana yana d'an jawabi cike da muryar nan tashi mai kauri had'e da natsuwa. "Banga abunda Captain Harun ya tsare maka ba Abbakar, sai nake ganin kamar hassada kike masa kana bak'in ciki da ci gaban da Allah yake basa ne, ya kamata zuwa yanzu ka daina duk wannan indai akan Harun ne zaka mutu da ciwo a ranka kuwa". Wani dogon tsaki Captain Abbakar ya saki cike da jin zafin Captain Harun ya mik'e ya bar masu wajan, yana ji a ransa ko wuk'a ya samu ya sami dama kuma zai iya kashe Harun wallahi. Captain Joha ya bisa da kallo yana masa Add'aur shiriya, duk da ya kasance shi ba addini d'aya suka had'a ba, baya bak'in ciki da d'aukakar da Allah yayi ma abokinsa, ko da da rana d'aya ne kuwa, duk da cewa kusan matsayi d'aya suka fara aiki a tare a Hukumar Sojan, amma gashi yanzu Captain Harun d'in ya kare su nesa bama kusa ba, bai tab'a jin wani abu saboda da haka ba, ace sai d'an uwansa wadda suke addini d'aya ne yake jin haushinsa haka. Kusan abokai ne harda Abbakar d'in Kuma duk tare suka zama Sojojin. ______________________ *Airport Rd, Dabolim Goa* A hankali Fasinjojin jirgin daya sauka a filin jirgi dake K'asar Gowa ya sauka a dai-dai k'arfe takwas na dare. Gaba d'aya suka fara fitowa d'aya bayan d'aya. Kusan zan iya cewa Farida ce k'arshen fitowa ita da Anjali suna rik'e da akwatunansu gaba d'aya. Farida ba abunda take sai tasbihi ga Ubangiji wadda shine mamallakin komai dake cikin duniyar nan tamu da kowa a cikinta, gaba d'aya garin Gowa ya tafi da imanin Farida, tsabar yadda ya had'u iya had'uwa, zata iya rantsewa da Allah b'ata tab'a ganin garin da yake dad'in ace zaka shak'ata kamar Gowa ba, lallai bata ga laifinsu Amal da suka dage sai wannan K'asar zasu zo yawan shak'atawa ba, K'asar tayi kyau kam iya kyau, an tsarata ta tsaru. Garin kalle-kalle Farida harda su tuntub'e saura kad'an ta kife a k'asa, tsawar da Hanan ta buga mata ce ta kusan sata idasa zubewa a k'asa bata shirya ba. "K'auyencin zaki fara nuna mana ko?, ki natsu ki shiga hankalinki wallahi Farida". Da rawar jiki Farida ta d'aga kanta maganar ma ta kasa, da gudu ta k'araso inda wasu motoci suke parking a wajan. Motoci ne sunkai biyar ko wanne ya hau wacce yake da ra'ayi dama kuma tarbarsu aka zo yi. Farida kanta ai bai k'ara kwancewa ba sai da taga sun iso wani matsiyacin Hotel wadda tunda take a duniya b'ata tab'a ganin irinsa ba. Hotel ne amma yadda kasan kana cikin gidan ubanka. Kai zata iya cewa babu ce kawai babu a hotel d'in, iya had'uwa D'akunan da suka kama sunyi kyau na k'in k'ari. Kowanne cikinsu tare da wa'inda suka taho suka kama d'akuna. Su Faruk da Baby's nasu d'aki d'ai-d'aiya suka kama kowanne, sai kuma Amal da Faisal d'aki d'aya, abun ya so ba Farida mamaki tunda dai ai take ganin ba ma'aurata bane, amma su ko a jikinsu, ita da Anjali aka kama ma d'aki d'aya, ita kanta Hanan sai yanzu ne ma Faridar ta lura da wani saurayi da Hanan ta taho dashi, ita wallahi da duk bata lura dashi ba, sai yanzu da ake shirin had'a d'aki d'aya dashi d'in. Ita kam yau tana ganin ikon Allah, sufa a haka gani suke wayewa ce ba wani abu bane kwana d'aya da namiji wadda ba maharramunka ba ko?. Irin wannan tunanin take a zuciyarta. A cikin daren sai da suka d'an huta, kamin suka fara shiga wanka aka fito aka d'auki wani shegen wankan, ana shirin fita yawo tun a ranar. Duk d'aukar su Anjali sai zuwa safiya zasu fara fita yawon, sai kawai suna zaune aka buga masu k'ofar d'aki suna fita Amal ta basu umarnin su fito zasu d'an fita daga gari ne a kamin gobe da safe ayi mai gaba d'aya. Da mamakinsu taje ta sanar da Farida. Farida harta fara wani wahalallan bacci taji an tayar da ita. Ba dan ta so ba ta fito suka iske su suna jiransu. Hanan sai fad'a take tana masifar sun barsu a tsaye sai ka ce wasu sa'anninsu. Basu da ikon cewa komai suka shige mota suka nufi cikin garin Gowa. Sunsha yawo cikin daren, kamar bazasu dawo makwancinsu ba. Iya gajiya Farida ta gaji ai nun, amma ba damar nunawa, tana kallon Anjali ita ko a jikinta, tunda zan iya cewa ta saba dama da irin hakan ita. Kiiiiii Gaba d'aya motocin suka ja birki. Fitowa suka rink'ayi gaba d'aya suna kallon motar su Amal dake gaba ita da Faisal wadda sune suka ja birkin suka tsaya. "A'a ya naga kunja birki mi ya faru ne?". Fad'in Jasmin. D'an kallon ta Amal tayi tana zare hannunta daga na Faisal dake kallon abunda ke gabansu wani Kare ne tsaye a wajan saura kad'an su take sa ma. Tsaye yake sai kunji yake bakinsa yayi daje-daje da wani bak'in jini, idonsa kuwa jawur kamar garwashin wuta, kamar Kuma wuta naci a cikinsa. Farida tana kallon yanayin Karen gabanta ya yanke ya fad'i har sai da ta d'an ja baya tana addu'a a zuci, haka kawai taji mugun tsoro Karen. "Wallahi wai Kinga wani Kare ne ya shige mana gaba, shine yasa muka ja birki saura kad'an mu take sa ma Allah ya tak'aita" Fad'in Amal itama tana mai do dubanta wajan da Karen yake ganin Faisal ya nufi inda yake yasa ta d'an ja da baya tana sake cewa. "Kaii kaii Honey please karka matsa inda yake, kasa dutse ka jefesa ya bamu waje kawai mu wuce dan Allah, ni haka nan ban yarda da Karen ba". Haba ai baima jita ba nufar Karen kawai yake yana wani murmushi irin ya saba da Karnukan nan yana cewa. "Haba Baby ba abunda fa zai faru, baki ga Karen turawa bane babu ruwansu da fad'a ma bare suji ma mutum ciwo". Ya k'are maganar zai kai hannunsa jikin Karen. Kamin ya kai hannunsa jikinsa kawai kamar an harbo Karen yayi wani kukan kura ya fad'a jikin Faisal yana kafa masa hakura a dai-dai k'afarsa. Wani bala'in ihu mai k'arar gaske Faisal ya saki, jin wata azaba da tayi ma Kwakwalwar kansa sallama mai shirya ba. Gaba d'aya zaro ido waje sukai wasu na komawa baya, Farida ko wani zawo ne taji yana shirin zubo mata. Da kyar wasu Y'an Sadda suka k'araso wajan, suka kori Karen daga wajan yayi cikin daji yana lashe jinin daya tsotsa a jikin Faisal. Faisal da kyar ya mik'e idonsa jawur na tsabar azaba tunda yake bai tab'a jin cizo mai zafi da rad'ad'in azaba irin na wannan d'an iskan Karen da ya cije sa ba. Da kyar Amal ta rik'e masa hannu yana d'angyasawa, suna ta masa sannu, sai dai kawai ya girgiza kai yana d'aga masu hannu alamar yaji. Kai tsaye Wani Babban Asibiti suka nufa dashi domin gyara masa cizon da Karen yayi masa, domin harya fasa masa fata sosai sawon hak'oran Karen b'aro-b'aro a cikin k'afar Faisal inda ya kai masa cizo. Doctor's sunyi mamakin yadda wajan da Karen ya cije sa yake komawa wata color daban, wani irin bak'in jini wajan ke zuba. An masa allurar bacci tare data kashe rad'ad'i domin Faisal wani ihu ya rink'a masu na cewa wajan na masa wani irin azababben rad'ad'i, dole tasa Doctors yi masa allurar kashe zafi. Amal sai kuka take kamar wacce aka ce ma mutuwa zaiyi........... *GAWA TAFE* (Zombies story) On2025 *©Zahra Royal Star* *ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION* *EPISODE 4* *V.M Salgaocar Super Speciality Hospital Goa* Zaune suke a d'akin jinyar da aka kwantar da Faisal, sunyi jingum jigum kowa da abunda yake tunani a ransa. Hanan ce ta d'an matsa kusa da Amal dake zaune bakin gadon da aka kwantar da Faisal wadda yake wani dogon bacci har zuwa biyu na dare Shuru kake ji bai farka ba. "Ya kamata wasu daga cikinmu suje Hotel d'in da muka sauka su d'akko mana kayan anfani, ba zai yuwu mu kwana gaba d'aya a asibitin nan ba". Fad'in Al'ameen yana duban su gaba d'aya. Hanan data k'arasa inda Amal take ta ce. "Ni gaskiya ina nan nida K'anwata sai dai kai ka tafi kaida Garl d'inka" Shuru ya d'anyi, haka kawai yaji baya son tafiya ya barsu, cikin k'arfin hali Al'ameen ya dafa kafad'ar Faruk yana cewa. "D'an uwa da kai zamu wuce ne ko kana nan?" "Why not mu zauna gaba d'ayanmu zuwa safiya, sai mu wuce mu dawo?" *Farida & Anjali POV* Su Farida dai na daga waje k'ofar d'akin da aka kwantar da Faisal suna kallon yanayin asibitin. Wata y'ar hayani ce ta fara kusanto inda suke, hakan yasa da mugun sauri Farida ta zabura ta mike da kyar Anjali ta rik'e mata hannu ganin tana neman banka masu cikin d'akin jiyar. Zaro ido waje tayi tana kallon Anjali tana cewa. "Wallahi Anjali kwata-kwata hankali na ya kasa kwanciya da inda muke, ke gaba d'aya ma K'asar ce bata kwanta min ba, ki duba ki gani daga isowarmu har wasu abubuwa marassa dad'i sun fara faruwa damu fa, yanzu ki dafa k'irji na kiji yadda yake bugawa da k'arfi har ya wuce misali, zuciyata da ruhi na dank'are suke da tsoro na rasa mi yasa Hakan". Sauke wani gajeran lumfashi Anjali tayi tana jin wani iri a ranta kamin ta ce. "Kusan nima zan iya cewa ina jin kaso mafi girma da fargaba a raina, duk da ba yanzu ne karo na farko dana bar K'asar Nigeria ba, no a ko da yaushe muna tafiya irin wannan da su, amma wannan sai nake ji ta banbanta da sauran, kwata-kwata, bana jin tafiyar a raina, ki natsu insha Allah babu abunda zai faru kinji". Suna cikin magana wasu Doctors guda biyu suka nufo inda suke tsaye, zasu wuce hankalinsu a mugun tashe da harshen turanci Anjali ta ji kamar suna cewa. "Akwai babbar matsala a cikin gari ya kamata ayi gaggawar kulle hospital d'in nan, kamin matsalar ta shigo ciki". Hankali a mugun tashe d'ayar keba d'aya amsa daga cikinsu tana cewa. "Akwai fa marar lafiyar da aka kawo yanzun nan D'an Sanda ne wai wani mahaukacin Kare ya cijesa a hannunsa, kuma da alama kamar Karen shine ke son yad'a wata cuta, dan yanzu haka ance cikin garin Goa ba lafiya cutar da Karen ke yad'awa ce, yaje ya sake cizon wata mata ita kuma matar ta tafi gida ciwo nata cinta, k'arshe kawai mijina ta kama tana cizo had'e da yagar naman jikinsa tana ci, a labarin dana na gani ma ta cinye rabin gagar jikin mijin nata fa, hatta Yaronta k'arami ta cije sa, amma ance shi ya gudu dashi da ita ne suka rink'a cizon mutane har cutar ta fara yawa a cikin gari, shine ina cikin kallon abunda ke faruwa kika shigo min da maganar ana son kulle hospital d'in nan gudun kar cutar ta iso cikinsa, to amma fa...... Tsaye suka tsaya inda su Farida suke, Farida sai zare ido take tana binsu da kallo ganin yadda suke magana hankali a tashe suna rik'e da hannun juna, tana dai jinsu ne amma kwata-kwata bata fahimtar yaranda suke yi, sai Anjali dake jin komai tana fahimtar su, itama k'irjinta sai bugawa yake, idonta da hankalinta kacokam yana gare su, ta tsaya sake da baki tana jin abunda suke cewa ji take abun kamar a cikin film ko labarin wani littafi. Farida ce ta kamo hannun Anjali tana d'an girgiza ta tana cewa. "Dan Allah kina jin miye suke cewa?, naji a jikina kamar abun suke fad'a ba alkhairi bane, kamar zai shafe mu ne, dan Allah ki sanar dani miye suka tattauna a Kai". Zatai magana taga d'ayar Doctor d'in ta ce. "Ohhh my God kina nufin wadda aka kawo yanzun nan shima cizon Karen ne?, to ai wannan d'akin ma wadda aka kawo shima cizon Kare ne an masa allurar bacci ne shine ma zanje na dubasa yanzu, Doctor Darniyal ne ya bani umarnin zuwa na gani ko ya farka". Ta k'are maganar tana nuna d'akin da aka kwantar da Faisal. Kai gaba d'aya fa Farida ta rud'e, tun kamin taji abunda suke tattaunawa akai, y'an cikinta sai kuka suke, mararta tana ji ta cika da wani fitsari na tashin hankali. Har suka shige d'akin da aka kwantar da Faisal Anjali na binsu da kallo, har sai da Farida ta d'an mata magana a tsawace sana ta dawo hayyacinta. Wata irin nannauyar ajiyar zuciya Anjali ta fara saukewa tana kallon hanyar da wa'innan Doctors d'in suka biyo, ji take kamar hayaniya na nufo inda suke again, ji take kamar wani tashin hankali na kusanto su. A hankali ta furta. "Akwai matsala babba Farida, dake faruwa a wajan Hospital d'in nan da garin Goa baki d'aya" "Innallihi wa'inna alaihir raju'on, dama na ce wallahi tunda jikina bai aminta da wannan tafiyar ba nasan akwai wani abu marar dad'i da zai faru, dan Allah mike shirin faruwa ne?". Farida ta k'are maganar hawayen tsananin tsoro na kwace mata a fuska. "Ki natsu dan Allah Farida, naji suna cewa Karen da ya ciji Faisal ne wai yake cizon jama'ar gari, kuma wata cuta mai ban tsoro ce take kama gangar jikin mutum ta cin naman mutane". Wani irin jaaaa da baya Farida tayi ido a waje kamar zasu fad'u, daga kalli k'irjinta yadda yake d'agawa zuciyarta ce ta sake shiga rud'ani mai tsananin gaske had'e da wani masifaffen tsoro ya sake rufeta, bakinta na rawa take fad'in. "Miye hakan kike cewa Anajali?, ko dai baki ji da kyau bane?, taya za'ai mutum ya kamu da cutar da zai rink'a cin naman D'an uwansa?, haka kawai zai turmushe d'an uwansa ya kama yagar naman jikinsa yana ci ko mi kike nufin cewa ne?". Kamo ta Anjali ke k'ok'arin yi tana son k'ara mata bayani, amma Farida na sake ja da baya, gani take kamar Anjali d'in ma cinye ta zatai a yanzu. "Abunda naji suna cewa kenan nima Farida, komai na iya faruwa Farida, saboda dama ko wacce asalin cuta ana iya samunta daga Dabbobi dama, kuma Kinga Karen daya ciji Faisal fa kamar wani abu ne yaje ya ci ko yasha shima kamar naman mutane yake bi yana ci ko yasha jinin mutum". Muryar Farida har tana tashi tsabar kid'ima da tsananin razanar gaske, wata irin zufa gaba d'aya ta gama wanke mata jiki, take fad'in. "Kaii inahhh ya za'ai hakan ta faru?, ban tab'a ji ko gani ba, ya za'ai da hankalinka ka kama D'an uwanka ka ci namansa?, ni dai kawai nasan akwai Mayu akwai kuma Y'an k'ungiyar asiri, amma su ai ba ta haka suke halaka D'an Adam ba". "Bazaki tab'a fahimta ta ba Farida, nima fa abunda naji ne nake sanar dake, nima yadda kike cikin tsananin rud'ani haka na shiga a sadda suke bayanin abunda ke shirin faruwa da K'asar Goa". Kamar jira ake Anjali ta rufe bakinta Doctors suka fito a guje daga d'akin da aka Kwantar da Faisal suna cewa. "Wallahi kowa yayi ta kansa shima wannan ya gama kamuwa da cutar nan, ayi Maza a kira Sojoji ko Y'an Sadda duk wadda ya kamu da cutar a harbeshi kawai, Maza-maza muje a sanar da Doctor Darniyal ya sanar da jami'an tsoro cutar ta gama shigowa hospital d'in nan". Wata irin zabura su Anjali da Farida sukai suna k'ank'ame juna zuciyoyinsu na harbawa. Sunma kasa motsawa daga cikin d'akin suna iya jiyo ihun su Amal bare muryar Amal dake fituwa had'e da ihun azo a taimake mata zai kashe ta, kamin su gama tantance mike faruwa suka ji k'arar an bugama mutum k'arfe a saman kai sai kuma sukaga suna fitowa da mugun gudu daga cikin d'akin. Faruk ne rik'e da hannun Amal da Faisal ya danna mata cizo a tsintsiyar hannun nata jini sai tsiyaya yake a hannun nata. Farida kallonta kawai take wani masifaffen tsoro gaske na sake rufeta ganin Al'ameen ya jawo d'akin ya gark'ame had'e da sauk'e nannauyar ajiyar zuciya yana dafe k'irjinsa. Sake waro ido Farida tayi tana ganin inda Faisal ya ciji Amal har jinin dake zuba ya d'auke, sai wata irin color ta jinin daya sauya, daga ja zuwa blue, da wajan ke canzawa yana komawa Blue jijiyoyin wajan sunyi mugun tashi rad'au a wajan, fatar wajan kanta ta koma blue itama, gashi sai yamutse fuska take tana fad'in akwai zafi sosai wajan ke mata, wani shegen zafin wajan da Faisal d'in ya cije ta take ji, gashi sai wani irin kuka take mai tab'a zuciya tana kallon d'akin da masoyinta yake. "Tunda nake a duniya ban tab'a ganin tashin hankali irin wannan ba, ya kama muyi gaggawar barin Asibitin nan gaskiya, domin naji Doctors d'in can da suka fita daga d'akin nan suna cewa cutar ta gama shigowa hospital d'in nan gaba d'aya". Cewar Faruk yana rik'e da budurwarsa dake mak'ale a bayansa. Matan sai kuka suke Hanan ma tana rik'e da hannun nata saurayin mai suna Ahmad, ai tana jin wani sabon tashin hankali na rufeta, sai yanzu ta gama fahimtar cutar da Faisal ya gamu da ita, cutar dake yad'uwa kamar wutar daji dandanan take kashe gari komai yawan jama'ar dake garesa kuwa. Al'ameen da hankalinsa shima baya jikinsa ya k'ank'ame hannun budurwasa yana yin gaba domin fita harabar Asibitin yana cewa. "Ya kamata muje, zama waje d'aya ba namu bane ana cikin wannan hali, domin shi kansa Faisal zai tashi a kowanne lokaci ban tab'a ganin k'arfi irin wadda Faisal ya nuna yanzu ba, kamar wani Zaki, na rantse da kyar na shammace sa fa na buka masa k'arfin gado a kai, shine fa ya suma ba wai mutuwa yayi ba". Bin bayansa sukai suna tafiya a hankali kamar wadda za'ace masu gasu nan su harta na kare. Amal sai kuka take tana turjewa wai ita bazata tafi tabar Faisal a haka ba, sai da Faruk ya wanke ta da wani gigitaccan mari sana ta nutsu tana kuka mai sauti, ya rik'e hannunta suna nufar harabar Asibitin. Kamar jira ake su fito harabar Asibitin idonsu yayi masu tozali da wani gaggarumin tashin hankalin daya kusa sa zuciyarsu bugawa. Domin k'atotan Get d'in Hospital d'in Doctor Darniyal ke shirin bada umarnin rufesa, kamin akai ga rufesa ma Dondozen Zombies wadda suka gama kamuwa da Cutar sun danno kai cikin Asibitin, gaba d'aya masu tsaron Get d'in suka watse suna gudu had'e da ihun neman taimako da tsira da ransu, suna ganin yadda idan Zombies suka kama mutum suke yagar naman jikinsa suna ci kamar sun samu abinci, da sun saka farcensu suke yago fatar naman jikin mutum sai dai kaga ta taho kamar ansa al'makashi an yanko ta haka take yi. Sabon tashin hankali sai da suka ga wata mace ta zama Zombie itama ta nufi inda Doctor Darniyal yake k'ok'arin harta na kare ta cafke masa hannu ta kafa masa hakura sai jini suke gani yayi wata irin tsartuwa, ihu yake yana sun kwace jikinsa sai ma wani k'arfi data sa ta kaisa k'asa ta turmushe, dai-dai cikinsa ta kafa hak'uranta sai dai kawai sukaga ta farke cikinsa tana d'ebo y'an cikin nasa tana cusawa a bakinta, tana wani irin gurnani da gunji babu dad'in ji, tun yana shure-shuren zafin fitar rai had'e da wani ihu wadda baya fita harya daina kwata-kwata, suna gani ta cire hannunsa da k'afarsa gudu d'aya yadda kasan ba naman mutum suke ci ba, kamar sun samu naman Dabba wacce aka gyara domin ci kawai. Farida dake jikin Anaji ta fasa wata gigitacciyar k'ara had'e da sumewa a jikinta. Da kyar Anjali ta iya tarbeta sosai a cikinta dake rawa na tashin hankali itama. Zan iya cewa ba Farida kad'ai ce ta suma ba, harda Hanan, Ahmad ne ya kinkimeta ya sab'a a kafad'arsa, da gudu Anjali ta d'auki Farida dake sume a hannunta tana nufar wata Motar Asibitin tana cewa. "K'uyo sauri zasu iya dawowa inda muke, kuma bana jin zamu iya k'are kanmu, tunda bamu d'auke da wasu makami a hannunmu". Ai tun kamin ta dire maganar, Zombies wasu da suka gama cinye wasu, wasu ma nan take suke mik'ewa suma sun zama irinsu suke take masu baya. Da gudun gaske suka fad'a cikin motar, Faruk ne ya shiga mazaunin Driver sai Al'ameen mai zaman banza, sauran kuma suka shige bayan motar, domin Motar tana da zurfi. Zasu rufe murfin baya na Motar kawai wata Doctor tare da wani namiji suka shigo bayan a guje, har suna fad'uwa. Ganin sun shigo suka jawo murfin a tare suna sauke lumfashi. Ba wadda yayi magana, sai kallon harabar Asibitin suke yadda lokaci d'aya ya koma ya hargitse kamar wata mak'abarta, ga Zombies dake son yayyab'e Motar suna buga gilashin Motar suna son ba'lleshi, da mugun k'arfi suke buga gilashin, ba abunda suke buri sai cimma wa'inda ke cikin Motar, sai wani shin-shine suke suna jiyo k'amshin Bil Adam a ciki, sai hauka suke suna wani gunji marar dad'in ji. Da kyar Faruk yaja wani uban birki had'e da zubar da Zombies d'in da suka yayyab'e Motar da suke ciki, wasu nan take ya bi ta kansu ya latse, yaba Motar wuta, wajan Get d'in fita ba sai da yabi ta kan wasu, suka fice daga Asibitin, Asibitin da zasu iya cewa duk mutunan da yayi saura a yanzu kam sunansa GAWA, Domin har motocin dake parking lot na Hospital d'in sun fara ci da wuta, suna kallon yadda wasu Zombies dan naci suka biyo motar a guje, wasu kuwa tafiya suke a slowly suna mik'a hannunsu gaba suna tafiya suna shin-shine, jini yana dalala a bakunansu. Su Faruk dake gidan gaba, suna bin K'asar Goa da kallo na tsallar mamakin yadda a y'an awanni cutar ta gama yad'uwa a wasu sassa na cikin garin Goa d'in. "Kai Malam na rantse munga bala'in yau, wannan Cutar bala'i ce wallahi, duka fa k'arfe uku na dare ne yanzu duka yaushe muka kawo Faisal bamuyi fa awa uku cikakka ba, amma dubi yadda garin ya koma kamar Mak'abarta, dan Allah duba ka gani". Fad'ar Al'ameen yana nuna garin gaba d'aya. A bayan Motar Anjali dake rungume da Farida tasa hannunta a bayan rigarta Allah ya so tana d'auke da wata roba ta ruwa, ta kwance ta tana watsa ma Farida ruwan akan fuskarta. Saida ta watsa mata ruwan ya kai sau uku sana taji taja wani irin lumfashi. A zabure kuma a kid'ime ta farka. Tana wata irin jijjiga na tsallar tashin hankali. Sai da d'aya daga cikin Doctor d'in da suka shigo motar daga baya Macen ta matsa inda suke, tana d'an dubata, a hankali ta rink'a murza tafin hannunta, har ta samu ta d'an dawo dai-dai. Wani murmushi Anjali ta saki tana kallon Matar ta ce. "Thanks" Murmushin yak'e kawai Matar ta saki a hankali ta matsa daga inda suke tana komawa inda namijin yake, jikinta a sanyaye tana kallon gilashin Motar yadda Zombies ke shawagi a cikin garin, wasu ma suna gaf motarsu suna tab'a ta da son cin masu, dan ma a hakan wani irin matsiyacin gudu Faruk d'in keyi dasu, shi yasa ko sun shige masa gaba ta kansu kawai yake bi. Farida dake wani irin nishi kamar mai shirin kamuwa da wata cuta, da kyar ta iya bud'e baki ta ce. "Wai ba mutuwa nayi ba dama?" Ta k'are maganar hawaye masu zafi na sake yanke mata a fuska. Wata uwar harara Hanan ta banka ma Farida ta ce. "Sai tsoron masifa cike da ciki, harda su sumewa mutane, wallahi baccin Anjali da sai dai mu barki a can su cinye ki kowa ma ya huta" Wani kallo Anjali tayi ma Hanan ta kasa hakuri ganin shi Saurayin nata Ahmad ya kasa fad'a mata itama fa suman tayi, kawai ta farka ne da kanta, ta kuma riga Farida farkawar. "Kema fa Ranki ya dad'e suman nan kikayi, ko ni nan kad'an ya rage zuciyata bata buga ba, wannan tashin hankalin ai dole yasa Kwakwalwar kanka tab'uwa, ban tab'a ji ko labarin irin wannan abun da nake gani a yanzu ba, ace mutum nacin naman D'an uwansa" Wani kallo Hanan ta watsama Anjali tana d'auke idonta daga kansu tana wani basarwa, ganin Anjalin na son tuna mata asiri a gaban y'ar aikinta. Kamar saukar aradu suka ga Amal ta mik'e tsaye ta fad'i k'asa tana wata jijjiga had'e da wani irin ihu had'e da gunji, ga wani sauti dake fito daga jikinta kamar ana k'arya k'asusuwan jikinta, domin ji kake k'assss k'assss k'ak'k'asssss. Gaba d'aya zabura sukai suna mik'ewa tsaye, mutuwar tsaye kawai sukai suna duban yadda Allah yayi da Amal, zuciyoyinsu na harba da k'arfin gaske, ga wata zufa data wanke masu jiki. Kai Jasmin tafa kasa hakuri ta ce. "Gaskiya a tsayar da Motar nan a fitar mana da Amal, idan ba haka ba kuma zata halaka mune muna ji muna gani, ni kuma tsakani da Allah ban shirya mutuwa ba wallahi". Ta k'are maganar cike da tsananin tsoro tana sake ja da baya sosai. Zan iya cewa Amal ta ji duk abunda k'awar tata ke fad'i, domin wasu zafafan hawaye ne suka yanke mata, tana jin wani mugun rad'ad'i a zuciyarta, ga jikinta dake sauyawa dan har ta fara jin k'amshin naman mutane itama, tana son ci, ji tayi ba abunda take mugun son ci kamar naman Bil Adam, harta fara y'an shin-shine, kamin ta gama fita daga yaccinta gaba d'aya ta tuno da maganar da Tsohuwar nan tayi mata a sadda suka bigeta, inda take cewa, "ta kuka da duniya, wata rana zata had'u da wata matsalar zata nemi taimakon na kusa da ita, Kuma tana ji tana gani zasu kasa taimaka mata, gudunta ma zasu rink'a yi, kuma babu yadda ta iya da su", jikinta yayi wani irin mugun sanyi na zallar nadamar da bata anfani a yanzu. Gaba d'aya jikinta ya koma fari tass kamar wacce aka shafama ruwan toka. Suma tayi suka jita shuru, sake zabura sukai har bakin Hanan itama na kyarma wajan kiran su Faruk, da mugun sauri suka ja wani matsiyacin birki kiiiiiiiiiiiiiiiiiii, jin uban kiran data kwala masu, ga dondonzon Zombies dake son cin masu a wajan da suka ja birkin............. *GAWA TAFE* (Zombies story) On2025 *©Zahra Royal Star* *ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION* *EPISODE 5TO6* dafa Faruk Al'ameen yayi yana cewa. "Karka sake ka fita, bari ni naje bayan Motar naga miye ke faruwa". D'aga kansa kawai Faruk yayi, Al'ameen da zuciyarsa ke bugawa ya d'auki wani k'arfi dake a gaban Motar k'ark'ashin Motar ya zaro shi yana b'alle marfin Motar ya fito zuwa waje. Zuciyarsa ce ta halba da k'arfi ganin wani Zombies ya rik'e masa riga da fitowarsa, sauran Zombies da hankalinsu baya Kai, sukayo kanshi kamar suna jira. Yana zufa ya daddage iya k'arfinsa yana buga masu k'arfen dake rik'e a hannunsa. Wasu su watse wasu kuwa su k'ara tashi suna kawo masa hari. Da kyar da sub'in goshi ya isa bayan Motar da mugun sauri har yana shirin kifewa k'asa ya bud'e marfin Motar na baya, yayi wani tsalle ya fad'a cikin motar. Yayyab'e bayan motar sukai, da kyar suka taru harda Ahmad suka rink'a dukan hannayen Zombies da suke shirin shigowa bayan Motar kamin da kyar da dabara suka rufo bayan Motar. Idon Al'ameen ne ya sauka akan Amal dake yashe a k'asa har yanzu cutar bata gama kama jikinta gaba d'aya ba, amma color d'in jikinta gaba d'aya ta sauya, ta koma kamar horror ga wasu zak'o-zak'on farce da suka fara fito mata a y'an yatsunta. Zuciyarsa na bugawa da tsananin k'arfi zai nufi inda take Hanan tayi saurin rik'e hannunsa tana cewa. "Dan girman Allah Al'ameen kayi hakuri ku fitar da Amal daga motar nan, idan ba haka ba muna cikin had'ari in....... Tasssss ya wanke fuskar Hanan da wani gigitaccan mari idonsa a waje na tsabar tashin hankali da b'acin rai mai tsananin gaske, bakinsa na rawa na tsallar masifa yake nuna Hanan da yatsa yana cewa. "Ni kike gaya ma na fitar da y'ar uwata cikin annoba, su cinye naman jikinta, nin.......ni.....ni zan iya kai y'ar uwata a inda za'a gama da ita?, kar wadda ya sake ce min na fitar da ita daga cikinmu, sai dai duk mai buk'atar raba hanya damu k'ofa a bud'e take zai iya barin cikin Motar nan ga hanya nan". Ya k'are maganar yana nuna bayan Motar, kamin ma ya sake wata maganar, Ahmad ya ci kwalar rigarsa yana cewa. "Karka sake sa k'azamin hannunka ka ce zaka tab'a Hanan. Kuma ai gaskiya take fad'a, ya za'ai mubar ajalinmu a cikinmu, muna ji muna gani, bazai tab'a yuwu ba wallahi baka isa ba, sai dai kune zaku fice mana daga Motar nan amma ba dai mu ba". Zan iya cewa yadda naga jikin Al'ameen na d'aukar rawa had'e da wani irin huce da yake na tsananin b'acin rai komai na iya faruwa a tsakaninsa da Ahmad. Gafe gudu Farida har yanzu ta kasa motsi dan ita hankalinta gaba d'aya ma baya tare da ita, hankalinta kacokam yana ga bala'in dake tunkaro su, amma su jiba kwata-kwata sunma manta da irin halin bala'in da suke ciki, suna shirin had'a kwanji. Kamar ance Farida ta waiga inda Amal take kwace, zan iya cewa dama kusan rabi hankalinta naga Amal d'in, sai kuma rigimar da su Ahmad keyi, kamar zasu cinye junansu d'anye. A mugun-mugun zabure had'e da wata irin gigitacciyar k'ara Farida ta saki, tana toshe bakinta, nuna inda Amal take, Amal d'in ta wani tashi kanta a karkace hannuwanta sun lauye hatta k'afafuwanta sun bandare, wani kalar jini bak'ik'k'rin dashi yana dalalar mata a baki, wani irin shegen gunji take tana wage bakinta dake d'auke da wasu tsiraran hak'ora irin na horror masu shan jini, bakin nata kanshi ya koma baki gaba d'aya kalarta ta gaba sauyawa daga D'an Adam zuwa dodo. Gaba d'ayansu zabura sukai suna duban Amal data zame masu abun tsoro. An rasa wadda zai fara fita daga motar, gashi Zombies kamar k'ara Koro su ake inda motarsu take a tsaye, daga can gaba kuma Faruk ganin haka ya tayar da Motar yana zan wani uban birki yaba Motar wuta, suna jin yadda Zombies ke wani irin ihu yadda Faruk d'in kebi ta kansu yana latsewa. Suda ke baya kuma fad'uwa sukai a sadda yaja birkin da k'arfi, da wani mahaukacin sauri su duka suka zabura suka mik'e ganin yadda Amal ke neman kawo masu farmaki. Allah ya bata sa'a ta kamo k'afar Doctor d'in Mace dake jikin namijin d'an uwanta, wadda suka shigo motarsu suna gaf barin Asibitin da aka kwantar da Faisal. Wani razanannan ihu had'e da wata irin murya mai k'arfi ta kama cewa. "Na shiga uku na, ku taimaka min karta shafa min cuta wayyo Allah zata kashe min rayuwa, Ina ji ina gani wayyo wayyo wayyo Allah na". Da harshen turanci take fad'ar Hakan. Abunda take iya fad'i kenan Doctor d'in, iya k'arfinta take furta Hakan. Gaba d'aya an rasa wadda zai nufi inda suke, shi kansa Al'ameen mai tada jijjiyoyin wuya akan Amal d'in ya kasa koda motsawa daga inda yake, ido a waje yake duban Amal dake son kaima Doctor cizo da bala'i. Ai d'ayan Doctor d'in da suke a tare bai san lokacin daya fara waige-waige ba, yana son gano wani makami domin cetan y'ar uwarshi ba. Ai ko yana cikin dube-dube ya hangi wani k'arfi mai kauri a cikin Motar, yasa k'arfinsa ya fisgo shi bai tsaya wata-wata ba, ya d'aga shi sama yana ihu iya k'arfinsa saboda k'arfin yana da wani irin shegen nauyi, dan da kyar ya daga shi, ya kuwa sauke ma Amal shi a tsakiyar kanta, nan take kamar kyaftawa da Bismillah kanta ya rabe gida biyu, jininta yayi wata irin tsartuwa yana feshe na kusa da ita akan fuskarsu, ko shurawa Amal batai ba nan take ta zube babu rai a tare da ita. Gaba d'aya zan iya cewa wa'inda ke wajan sumen tsaye sukai gaba d'aya sun runtse idonsu zuciyoyinsu na harbawa da k'arfin gaske, zufa na tsiyayo masu ta kota ina a jikinsu. Farida zan iya cewa nan take ta sulale ta zube ta sake wani sumen. Al'ameen ko kamar wadda aka zarewa rai a tare dashi, domin yana tsaye ne amma baya motsi. Sai zuwa can suka ji ya fasa wata gigitacciyar k'ara ya zube a wajan shima a sume. Duk wadda keda sauran motsi a cikin Motar sunyi jingum-jigum kamar basa numfashi suma, ido kawai ke motsi a tare dasu. Hanan ce ta fara fasa wani irin azababben kuka mai tab'a zuciya, tana sa tafukan hannunta ta rufe fuskarta dasu, wani irin kuka take na tsananin tausayin Amal da rasata lokaci guda da sukai. Mi zasu gaya ma Abbie?, ya ma za'ai su fara tunkararshi da maganar babu Amal a fad'in duniyar nan a yanzu?, to suma suna da tabbacin zasu bar Goa a raye ne?, mi yasa basuyi dogon tunani ba kamin suyi tafiyar nan?. Muryarta na rawa da kuma kuka take fad'in. "Wayyo Allah na, ashe Aunty Anam abunda kike hango mana kenan na wannan tafiyar ba alkhairi ba ce?, kika so hana tafiyar nan dani, mi yasa Aunty Anam baki kulle ni d'aki kika bige ni ba, ko k'ila na fahimci abunda kike hango mana?, shikenan nasan nima mutuwa zanyi wallahi tunda naga gawar Amal nasan nima tafiya zanyi inda taje". Ta k'are maganar bakinta na rawa wajan furta kalmar. Kusan gaba d'ayansu maganar da Hanan d'in keyi ta saka su kuka, domin daka kalli gaba d'aya fuskokinsu hawaye ne ke kwaranya akansu. Doctor d'in nan data mik'e tana rungume d'an uwanta likitar nan, sai kuka suke suma, duk da sunji da Yaran da Hanan d'in tayi magana da Hausa tayi, basu ji miye take cewa ba, to amma yanayin yadda take kuka tana jijjiga take maganar, zaka san mai tab'a rai ce. Faruk dake baya ya sami wani waje inda ba Zombies sosai ya faka, jin shuru a bayan Motar ya b'alle marfin Motar ya fito, yana bige wani Zombie dake son kamo hannunsa, shi kad'ai ya gani a kusa, sai wasu tsiraru dake nisa da inda yayi parking d'in motar, da sauri ya b'alle marfin ya shige gidan bayan. Juyowar da zaiyi bayan ya mai da marfin ya rufe, kawai ya hangi tashin hankalin dake yashe a k'asa, ga gawar Amal data yi raga-raga Kwakwalwar kanta ta fashe jini mai yawa kalarsa bak'i na zuba a tsakiyar motar. Sai Al'ameen dake zube a sume. Zan iya cewa Faruk Kwakwalwarsa ta kusa zarewa domin girgiza kai ya rink'a yi yana wani murmushin daya fi kuka ciwo, yana nuna Amal yana magana marar kan gado yana cewa. "Kai amma dai Amal wasa kike ko?, ki tashi ki maida kwanyar kanki mana, mi zai sa ki cirota daga kanki, kina son mutuwa ne?, tashi mana. Kai kuma Al'ameen daga shigowarka bayan Mota sai kaje kayi zamanka?, au bacci ma kike kenan?, to Maza ka tashi kaima ko mun bar wajan nan". Wani irin kuka mai sauti Jasmin ta fashe dashi itama, Hanan da Anjali na taya ta ganin Faruk na son haukace masu. Anjali ce ta kamo shi tasa shi a jikinta tana tallafe kansa take magana. "Dan Allah Faruk karka birkice Amal ta mutu bazata dawo ba, shi kuma Al'ameen suma yayi, ba sai na tsaya ina maka baya ni ba, Kasan an riga da an Ciji Amal tun kan mu baro Asibiti, dan Allah ka dawo hayyacinka". D'ago kansa yayi daga jikinta, yana girgiza kansa wasu zafafan hawaye suka shiga zuba masa. D'ukewa yayi k'asa yana sakin kuka mai sauti, d'aga kansa yayi sama yana kurma wani uban ihu. Kamin ya dawo da dubansa inda gawar Amal take. Nunata yake yana cewa. "Ya zaki mana haka Amal?, mi kike so muje mu gaya Abbie?, mi yasa da kika kamu da cutar baki zo gare ni ki cinye naman jikina ba?, bazan iya hanaki ba ai, mi yasa baki cije ni ba?, muka koma iri d'aya, why why why why Amal?". Yadda yake kuka jikinsa na jijjiga had'e da wata irin kyarma da jikinsa keyi yasa Anjali jawoshi jikinta ta rungume suna kukan a tare. Jasmin ce mai k'arfin halin d'aukar wani sauran ruwan da Anjali ta tab'a watsama Farida a sadda tayi suman farko, ta d'akkosa ta watsama Al'ameen shi, amma shuru bai tashi ba, ta kusan k'are ruwan a jikinsa, da kyar yaja wani lumfashi, yana bud'e idonsa akansu. Matsawa tayi tana watsama Farida itama akan fuskarta, sauran ta d'aure gudun sake suman wani a cikinsu. Kallonsu kawai yake yana binsu dana mujiya, kamar ya fice daga hankalinsa kwata-kwata shima, domin wani murmushi ya rink'a jifansu dashi yana duban gawar Amal shima yana magana yana nuna Faruk dake jikin Anjali da ya d'an zame yana kallon d'an uwansa daya farka, zuciyarsa cike da tsananin tsoron kar D'an uwansa ya haukace gaba d'aya, gara shi ya d'an dawo tunaninsa amma ba sosai ba. "Faruk kana gani wai Amal wasa take mana da hankali, ka ce mata ta tashi dan Allah, miye hakan take yi?, ji wani abu data shafa akan fuskarta tana mana wasa, ka ce mata bamu saba irin haka da ita bafa". Wani irin rauni ne ya rufe Faruk yana kallon Al'ameen dole tasa ya danne duk wani tashin hankali da yake ciki yabar jikin Anjali ya matsa inda d'an uwansa yake ya rungumesa yana basa baki, amma kamar sake hautsina Kwakwalwarsa ma yake, hauka fa tuburan Al'ameen ke neman yi gaba d'aya. A gefe guda kuma Farida na farkawa batai wani ihu ba, sai binsu da take da kallo, jin abunda su Al'ameen ke cewa da ganin yadda Al'ameen Kwakwalwar kansa kwancewa yasa Farida sakin kuka mai sanyi tana curewa waje d'aya, gaba d'aya tausayin kansu da kansu ne ya rufe mata jiki da ruhi, wannan wacce irin masifa ce haka?, wacce irin jarabawa ce Allah ya jarrabe su da ita?. Faffasss fafffassss fasss kake ji had'e da wani gunji marar dad'in sauti ke k'ara kusanto inda suke. Kamin ma suyi wani yink'uri kamar an harbo wasu dondozen Zombies masu yawan gaske suka yayyab'e Motar, kamar had'in baki tako ina tururuwar haye motar suke. Da k'arfin da Allah ya zuba masu suke shirin kifar da motar gaba d'aya. Wani irin sabon tashin hankali ya rufe na cikin motar, duk da haka har yanzu Al'ameen hauka yake yana fad'ar wasu kalami marassa kan gado. Hanan da Jasmin kuka suka sake fashewa dashi suna k'ank'ame samarinsu, har suna had'a baki wajan cewa. "Dan Allah ku taimaka mana mubar wajan nan, kunga fa sun gama yayyab'e mu, gashi babu kowa a gaban motar, shikenan mun mutu wallahi". Farida ma k'ara curewa waje d'aya tayi jikinta na rawa, sai wani irin kyarma jikinta keyi tana girgiza kai, dan itama ji take kamar Kwakwalwar kanta nasan haukacewa. Faruk ne yayi jaruntar tashi yana mik'ama Anjali Al'ameen ta rik'eshi, domin ko iya tsayuwa baiyi. Kamin yayi wani uba, kawai suka ga an jirkitar da motar su, ta kife a k'asa. Gaba d'ayansu suka fad'i a tsakiyar motar suna k'undun bala, har suna bigewa da junansu da kuma jikin Motar. Gummmmm wata k'ara Farida ta saki jin yadda ta bige a goshi a sadda motar ta jirkice da su, tafe take da wajan, tana sa d'ayan hannunta tana dafe inda take kwance. Faruk ne yayi k'arfin halin sake mik'ewa a jirkicen da suke, bakin window d'in motar ya rarrafa ya nufa, rik'e da k'arfin da Doctor d'in nan ya kwad'ama Amal shi. Ya bud'e ya fito, kamar jira Zombies suke suka yayyab'e shi. Jikinsa rabi na cikin motar sai rabi na a waje. Iya k'arfinsa ya yakice wasu, ya dage yana d'aga k'arfen da k'arfi ya rink'a kwad'ama duk wani Zombies dake yayyab'e da jikin Motar. Ya d'auki lokaci suna yak'i da Zombies d'in, kamin Allah ya basa sa'a ya d'anci galaba akansu. Da sauri ya koma cikin motar yana basu umarnin kowa ya fito daga motar ta window d'in daya fara fita, sunyi sauri da hanzairin barin cikin Motar domin gaf take da kamawa da wuta. Shine ya fara ficewa da Al'ameen, sai su Jasmin dasu Farida. Gefe d'aya suka tsaya suna gani Motar ta kama da wuta gawar Amal na ciki. Sai lokacin Al'ameen ya saki wani kuka mai sauti yana d'ukewa k'asa. Babu wadda ya ce masa danmi yake kukan?, saima suka rabu dashi yayi mai isarshi. Sun dad'e a tsaye a wajan, kamin da sauri kamar an tsikari Faruk ya kamo hannun d'an uwansa, suka fara tafiya, taka k'afarsu kawai suke duk inda suka sa gaba, basu san inda suke nufa ba, tafiyar kawai suke cike da tsananin tsoro, danma a haka wai asuba ta kusa yi masu. Sai zuwa yanzu ne ma Farida taji y'an cikinta sun kad'a jin wata irin azababben k'ishirruwa da mak'oshinta ya bushe k'amas ko miyau babu sosai a bakin nata, sai kuma yinwar data ke ji a yanzu, duk da bata ji yinwar ba, sai yanzu da k'ishirruwa ta addabe ta, yo dama idan kana cikin tashin hankali wata yinwa ai ba ta ita kake bama. Dafe cikin nata tayi jin yadda ya d'aure mata waje d'aya, a d'uke take tafiya, tsabar wata azaba da cikin nata ke mata a yanzu, ga sallolin dake kansu bata jin tunda suka shiga wannan iftila'in sun tuna da sallah, sai ita da abun ke damunta a ranta. Kamar ance ta waiga ta hango wani gida d'an k'arami, da aka gama canza masa kamanni, duk an fasa gilassanshi na jikin widows dake gidan, duk an faffasa su, hatta jikin bangon gidan jini ne ke zuba, suna tafiya suna taka gawawwakin jama'a wa'inda Zombies suka gama dasu. Da sauri batai nauyin baki ba wajan cewa. "Please y'an uwa ga wani gida can a can, muje dan Allah ko sallah muyi, mu rok'i Ubangiji daya kawo mana d'auki, mu rama sallolin dake akanmu". Yamutse fuska Jasmin tayi tana d'an dafe cikinta itama jin wani k'ungin yinwa daya yi mata itama. Ba wadda ya ce k'ala suka nufi gidan, zuciyarsu na fargabar shiga cikinsa. Farida ce tayi namijin k'ok'arin bud'e k'ofar gidan, da aka gama k'aryawa tana dafa k'ofar ta fad'i a wajan, har sai da suka d'an matsa daga jikin k'ofar gidan. Shiga sukai suna faman dube-dube, zuciyarsu ta d'an buga lokacin da suka yi tozali da Gawar mutum biyu a cikin gidan, wani Yaro ne shida Mahaifiyarsa daga gani, gawar tasu yashe a k'asa sai gawar wani mutum da suka hanga a yanzu zaune akan kujera, gawawwakin nasu bama kyan gani kwata-kwata, domin wani an cire masa ido d'aya an yayyaga fatar fuskarsa ba kyan gani, gaba d'aya jini yayi dame-dame akan fuskarsu, kai gaba d'aya ma halittar da Allah ya zuba masu an sauyata zuwa abun tsoro. Da kyar suka samu suna neman inda zasu zauna, Farida ko batai Sanya ba, ta nemi ban d'aki tana shiga ta saki wani ihun daya jawo hankalinsu, Anjali ce tayi saurin nufar toilet d'in. Ganinta a tsaye ta rufe bakinta tana ihun, ta kai dubanta ganin Gawar wata mace ta gani a toilet d'in babu kyan gani, domin gawar tata tafi ta sauran Muni wacce suka gani a parlon gidan. Hawaye kawai Farida keyi tana kuka dafe da bakinta. Sauke ajiyar zuciya Anjali tayi tana dafe da k'irjinta, bata ce mata komai ba, ta dawo zuwa parlon, ganin yadda duk suka shiga halin tsoro, yasa ta d'an masu jawabin babu komai su kwantar da hankalinsu. Zata iya cewa kusan duk taji irin ajiyar zuciyar da duk suka sauke kusan a tare. Tana gani Jasmin ta nufi kitchen d'in gidan, ta d'an samu biskit tana ci su duka ma abun tab'a baki suka samo suka d'an tusa a cikin nasu, ba dan suna jin dad'insa ba, sai dan kawai su kori yinwar dake sasak'ar y'an hanjin cikinsu. Farida da kyar ta fito daga toilet d'in, tana zuwa tasa d'ankwalin kanta ta saisaiti alk'ibila ta kabbara sallah, ta dad'e tana sallah, tana idarwa ta d'aga hannunta sama tana hawaye tana kai kukanta wajan Mahaliccinta. Suma sallar suka gabatar bayan sun d'auro alwala. Anjali ce ta matso inda Farida take ta mik'a mata wani biskit da ruwa, amsa tayi tana ci kawai har yanzu hawaye take, tana ji yadda idonta ke mata wani rad'ad'i na tsananin kukan data sha, da kuma hawayen da suka k'i daina zubar mata har yanzu............. *GAWA TAFE* (Zombies story) On2025 *©Zahra Royal Star* *ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION* *EPISODE 7TO8* Tunda sanyin asubahi su Farida suka bar gidan da suka yada zango a cikinsa, domin idan ma basu barshi ba yana gaf da gazawa, domin har sai da Faruk ya kwad'e wani Zombies, kwana saukai babu bacci, shi yasa duk sun fita yaccinsu, ido yayi zuru-zuru. Suna cikin tafiya Farida cikinta ya sake d'aurewa gefe d'aya ta d'uke k'asa tana kiran sunan Allah. D'an dakatawa sukai gaba d'aya suna dubanta, Hanan ranta a d'an b'ace da Faridar ta ce. "Ke wai Farida miye haka kike k'ok'arin yi ne?, zaki tashi mu cigaba da tafiya ko kuwa mu barki a nan, kinga ko sunanki GAWA". D'an mik'ewa tsaye tayi a hankali ta fara takawa tana runtse idonta had'e da cije leb'enta. Jasmin ma tsaki taja suna yin gaba suka barta ita ce k'arshe. Da d'an gudu-gudu suka k'araso kusa da wata k'aramar Mota, suna kallon yanayin unguwar da suka shigo jiya cikin dare gabanin asubahi, babu yawan jama'a a unguwar, amma yanayinta tayi kaca-kaca Malam, babu kyan gani, duk an hargitsa unguwar duk kyan ganinta amma ta koma kamar Mak'abarta, motoci ne birjit a tsakiyar titin unguwar wasu sunyi had'ari sun kama da wuta, wasu ko mutane ne a ciki zombies sunyi masu mummunan kisa. Faruk ne ya fara shiga motar Al'ameen ya shige gaba shima, Motar fa na neman masu kad'an kowa kuma burinsa ya shiga kar a tafi babu shi a ciki. Wani gunji suka fara jiyowa suna cikin kokowar shiga motar, gaba d'aya zuciyoyinsu ne suka buga da k'arfe har suna rige-rigen waigawa bayansu. Abunda suka gani ne yasa suka saki baki da hanci suna kallo, zuciyoyinsu na wani irin tsalle na tashin hankali. Wasu Zombies ne su kusan guda biyar a jere a bayansu, suna dubansu, duk jini ya b'ata masu jiki, fuskarsu ba kyan gani, wani tsabar muninsa ma babu ido d'aya, wani an cinye rabin fuskar, wani babu hannu guda d'aya, sai gundinmin hannun kawai, amma a haka suke jan k'afa suna sun cin masu. Doctor d'in nan ne yake son bangaje su ya shige Motar, yana baya amma yana k'ok'arin bangaje kowa ya shiga Motar, ai ko daga bayansa yaji y'ar uwar nan tashi ta fasa wata gigitacciyar k'ara had'e da kiran sunansa da k'arfi. Ai bai san lokacin daya dakata da niyar shigewa motar da yake niyar yi ba. Juyowa yayi gaba d'ayansa yana zaro ido waje k'irjinsa na d'agawa na tsananin kid'ima da razana. Wani uban ihu ya saki yana nufar inda y'ar uwar tashi take, Anjali ce ta rik'e masa riga, ganin yana son kai kanshi inda zai halaka. Fad'i yake "wayyo Allah ku taimaka ma y'ar uwa ta zasu kasheta, wayyo Allah bazan iya rayuwa babu ita ba, wayyo Allah. Ki sake ni na ce naje inda take" Suna gani Zombies d'in nan suka rufa akanta, sunyi mata kaca-kaca, kamin su rabu da gangar jikinta data daina motsi. Suna jin k'amshin Bil Adam suka barta suna niyar kamo wani su turmushe. Faruk ne ya fito daga Motar yana komawa daga bayansu cikin hikima, k'arfe ya samu ya daddage iya k'arfinsa ya rink'a sauke masu shi a bayansu wani a tsakiyar kai, nan take suka zube a sume, domin su kansu su Faruk d'in sun lura idan ba b'are masu kai kayi ba ya rabe gida biyu, to kuwa ba mutuwa suke ba, suma ne suke kawai da an d'auki lokaci zasu tashi. Sauke k'arfen yayi yana sauke ajiyar zuciya yana dafe da bayansa, sai jan iska yake a bakinsa, suna kallonsa cike da tausayi. Shiga motar sukai gaba d'aya, sai Doctor d'in nan dake tsaye bai da alamar ma zai shiga motar sai hawaye yake, ga Zombies dake sun rufe unguwar a yanzu, domin duk inda wani mutum yake kamar k'amshinsa suke jiyowa duk nisansu dashi kuwa k'amshin zai kai har inda suke. Suna kallonsa Al'ameen ya kwala masa kira, zaro ido sukayi ganin Doctor d'in nan wacce Zombies suka gama bidirrinsu da ita, ta mik'e ta koma Zombie itama. Jikinsu ne ya kama rawa ganin duk yadda Zombies d'in nan suka ji mata ciwoka a jikinta duk d'aukarsu mutuwa zatayi amma ji yadda ta mik'e itama ta zama irinsu. Suna gani Doctor d'in nan ya nufi inda yake yana hawaye yana tsaye inda take, harta k'araso ta cin masa kawai ya wani rungumeta, ita ko dai-dai wuyansa ta kafa masa wani uban cizo tana wani irin gunji had'e da gurnani. Juyowa tayi dashi saitin da suke, suna jin ihunsa had'e da mik'a hannunsa yana alamar a ceceshi, sai ihu yake ita kam har lokacin bakinta yana wuyansa sai tsotsar jininsa take had'e da yago fatar wajan tana ci. Yo ko kallonsa sun sake yi, Faruk ya tayar da Motar jin su Jasmin suna cewa. "da'aAllah Faruk ja mota muje, kaji d'an rainin wayo Malam, a sadda muke kiransa ya dawo mu tafi ba k'i yayi ba, sai da yaji azaba zai wani nuna a taimakesa yake, ai ga k'auna nan ya gani, nikam banga wadda zai zama Zombies ba na kashe kaina akansa ba wallahi". Gaba d'aya samarinsu ne suka dubesu, ba wadda ya sake magana, dan suma kusan zan iya cewa abunda ke zuciyarsu kenan, kowa tashi ta fishsheshi ake kawai. Wani irin matsiyacin gudu Faruk keyi dasu, dan duk inda suka bi suka wuce Zombies ne keta shawagi a cikin garin Goa, sai mutanan da baza'a rasa ba a mab'oya, amma duk wadda idonka zai gane maka shi a tsakiyar garin to ya riga da ya zama Zombies. Wani munafikin burki Faruk yaja har saida su Farida Dake baya suka bige da jikin Motar. Hanan dake dafe da goshi inda ta bige ta d'ago tana niyar magana kawai idonta ya hasko mata wasu dondonzon Zombies da suka tare masu gaba, yawansu ya zarce masali ma, dan tsananin yawansu basa jin zasu iya bi ta kansu. Ko wanne ka kalla daga cikinsu ido a waje ga wata irin zufa data rufe masu jiki gaba d'aya, yadda kasan an watsa masu ruwa a jikinsu. Kowa ya kasa magana sai bakunansu dake bud'e a hangame tsabar tashin hankali. Anjali ce tayi k'arfin halin fisgo magana daga bakinta tana cewa. "Faruk kabi ta kansu kawai, Allah zai bamu ikon wuce su da yardar shi". Tayar da motar yayi yana bata wuta, sosai yaja da baya kad'an kamin ya jata da k'arfi yabi ta kan Zombies, amma duk da haka wasu sun watse wasu ko sai da suka manne a jikin Motar. Sai da ya rink'a jijjiga motar had'e da samin wata bishiya ya rink'a goga motar a jiki ne wasu wadda suka mak'ale suka zube suna wani irin ihu. D'aga kai Farida tayi jin yadda wani Zombies ke buga tsakiyar motar da suke ciki yana daga can samanta ya mak'ale sai gunji yake da gurnani kamar wani Zaki. Faruk yaja birki bai tsaya ba, cike da kwarewa ya rink'a juyo da Motar wai dan dai Zombie d'in nan daya mak'ale ya fad'o k'asa, duk sun jigatu sun wahala, saboda uban gudun da ake dasu, gashi sai wurwura su ake cikin Mota, da kyar Allah yasa ya fad'o ta gaba Faruk bai tsaya ba yabi ta kansa ya latse suna iya jiyo ihunsa. Gaba d'ayansu sauke ajiyar zuciya sukai, duk da sun san zasu iya gamuwa da wani iftila'in zombies d'in a gaba, domin sun san duk inda zasu shiga a yanzu Zombies sun gama karad'e gaba d'aya K'asar Goa. Motar ce kawai suka ga ta tsaya tak'i baya bare gaba, Faruk sai sun tayar da ita yake amma ina. Wani tsaki Faruk ya saki had'e da kai ma sitiyarin Motar wani naushi yana cewa. "Ohhh My God, mai d'in Motar ne ya k'are, ya kamata muyi hanzarin sauka daga cikinta, kar wata masifar ta rufe mu muna ciki". Ai kamin ma ya dire maganar gaba d'aya sun b'alle marfin Motar suna ficewa daga cikinta. Sai da suka gama sakkowa suna dube-duben inda ya kamata su fara nufa a yanzu kuma. Wani company nin yin shinkafa suka ci karo dashi Al'ameen ya nufi wajan yana fad'in. "Kuzo muje ko mun d'an huta a cikin wancan Company d'in da nake gani a gabanmu". "Kai kam Al'ameen ai bamu ga hutu ba, ni wajan ne ma bai wani kwanta min ba, dan Allah mubar wajan nan". Fad'in budurwarsa dake mak'ale dashi, sai wani waige-waige take, idonta a waje na tsananin tsoro. Ko magana bai mata ba suka biyo bayansa domin suma a mugun gajiye suke. Shiga sukai cikin Company nin suna kallon irin illar da Zombies sukai a cikinsa, kusan GAWA tafi a k'irga suka rink'a cin garo da ita ta mutane gasu nan cikin jini, gashi wajan yayi wani irin shuru sai wata iska dake busuwa a wajan, wacce saita sa mutum tsorata dan ji kake shuuuuuuuuuuuuu kamar kana cikin Mak'abarta nan, kai gaba d'aya ma garin haka ya koma. A hankali Farida ke tsallake Gawar mutane tana ware idonta waje, zuciyarta na bugawa wasu hawaye na tsananin tausayin kanta dama wa'inda suke tare dasu, duk da tasan sune suka ja masu wannan shiga masifar. A haka kuma idan ka ce zakai magana su ce zasu rufe ka da fad'a, sufa ta lura ma wasu daga cikinsu har yanzu ba nadama a tare dasu. Kamar jira ake Farida ta tsallake wata Gawar mace dake yashe a k'asa. Budurwar Al'ameen ce a bayanta, ta zo tsallaka gawar da Farida ta tsallake kawai kamar saukar aradu gawar nan ta tashi tana rarumo k'afar budurwar tana k'ok'arin kai mata cizo. Wani uba-uban ihu ta saki wadda yasa gaba d'ayansu toshe kunnuwansu, domin ihun da mugun k'arfi ta sake sa, wani irin ihu take tana kiran sunan Al'ameen. Duk ya gama rud'ewa ya rasa ta inda zai fara kawo mata d'auki shima. Su Jasmin ko da Hanan k'ara matsawa suke daga inda suke suna dafe da k'irjinsu dake bugawa sosai na tsallar tsoro da wata irin razana da sukai. Wata k'arar ta kuma kwalawa a sadda taji saukar hak'oran matar akan k'afarta, wani shegen zafi da rad'ad'i ne yayi ma Kwakwalwar kanta dirar mikiya, ta saki wata k'arar tana kiran. "Wayyo Allah na shikenan ta kashe ni wallahi, shikenan nima na koma irinsu, na shiga uku wannan wacce irin masifa ce, Allah ya isa tsanina dakai Faruk duk kaine silar shigowarmu wajan nan, ashe ajalina na cikin wannan company nin, wayyo Allah na, wayyo wayyo wayyo". Matar ce ta mik'e tana gunji kamar Mage ta samu b'era tana niyar sake kai mata wani cizon suka ji k'arar saukar wani k'arfe da Al'ameen yayi nasarar samu a wajan basu lura ba ya kwad'a mata shi a a tsakiyar bayanta, tana sake juyowa garesa tana niyar kamosa shima tana son kai masa cizo had'e da d'an wani ihu da gunji irin nasu na Zombies idan suka ji azaba. Ya d'aga abunda ya kwad'a mata ya sake kwad'a mata shi a tsakiyar kanta, sai a lokacin ta zube a sume. Kamo hannun Budurwar tashi yayi yana mik'ar da ita. Sai aikin kuka take domin ita kam tasan nan da wani lokaci zata koma Zombies. Wani kallo Jasmin take binta dashi batai wani nauyin baki ba wajan cewa. "Tsakani da Allah Al'ameen asan yadda za'ai da wannan budurwar taka, Fisbilillahi wallahi bazata zauna damu ba, haka kawai bamu ankara ba ta zama irinsu ta zo ta ce zata farmaki wani daga cikinmu, nifa gaskiya a yanzu ban yarda da kowa ba, tunda k'anwarku ta mutu, to ya kamata kowa ma aka ciza to ku kyale shi kawai wallahi". Rushewa da kuka budurwar tayi tana bak'in cikin abunda Jasmin ke fad'a. A zuciye ta nufi inda Jasmin take tsaye tana cin kwalar rigarta tana cewa. "Ashe Jasmin kece mutum ta farko da zaki fara gudu na?". Wani d'an iskan kallo Jasmin ta jefa mata, tana saka hannunta ta yakice ta daga jikinta, tana nunata da yatsa ta ce. "Karki sake wannan jikin naki ya ce zai sake tab'a jikina, kuma baki ji miye na ce tun muna a cikin mota a hanyarmu ta zuwa wannan wajan bane?, ke ko uwata ce ke na rantse da Allah yau sai mun raba hanya dake, bare babu uwar da muka had'a dake". Cike da tsananin mamakin Jasmin Farida ke kallonta, tana zare ido waje, uwafa?, anya Jasmin nada hankali kuwa?, bata gudun itama gobe a cije ta?, amma ta manta da hakan, sai wani tayar da jijiyoyin wuya take, sai ka ce tana da tabbas d'in ita Zombies d'in Allah ba zai basu sa'ar su cije ta ba. Cike da bak'in ciki da jin zafin Jasmin budurwar ta wanke ta da wani Mari, wadda Jasmin ta zabura a kid'ime domin Marin yazo mata a bazata ne, bata lura da lokacin data d'aga hannu ta kai mata marin ba. Dafe k'uncinta tayi tana fiddo idonta waje bata tsaya b'ata lokaci ba wajan d'aga hannunta itama tana sauke mata wani gigitaccan mari har biyu wadda ya ci uwar nata zafi wadda tayi mata. Ganin suna son had'a jiki suyi dambe yasa Al'ameen shiga tsakiyarsu ransa a mugun b'ace yake cewa. "Wai mi yasa ku mata k'aramin tunani ne da ku?, miye abun fad'a muna cikin wannan halin?". Nunata Jasmin take da yatsa a yadda take magana zaka san lokaci d'aya ta tsani budurwar Al'ameen d'in, fad'i take. "An gaya miki ni sakarya ce dolowa irinki, da zan tsaya ki mare ni ban rama ba, ai ko ko uwar data haifeki tayi kad'an ta ce zata mari Jasmin bata mara ba, ki kiyaye a nan gaba". Abu biyu ya taru yayi ma Budurwar nan yawa ga zafin cizon da aka danna mata, ga bak'in cikin ta kusa komawa Zombie, ga kuma tsanar Jasmin da take ji idan batayi sanadiyar zamowar Jasmin Zombie ba, ko tayi sanadiyar mutuwarta, to gaskiya bata haifo ba, hankalinta bazai tab'a kwanciya ba. Wani kukan kura Budurwar tayi, Jasmin bata ankara ba Budurwar ta kamo wuyan Jasmin dai-dai fatar wuyanta tasa farce ta yakoshi Jasmin d'in, wacce bata lura da yakoshinta tayi ba, dama gashi tana tara farce zak'o-zak'o a hannunta. Kuma dama tasan tunda yanzu jinin jikinta ya gama kamuwa da cutar, to tana da tabbacin idan ta yakoshi mutum a yanzu zai iya zama Zombies shima a ko wanne lokaci. Jasmin zata kai mata duka a baki Faruk ya hankade Jasmin daga wajan, har yanzu Jasmin bata ji wani zafi ko rad'ad'in ciwon da Budurwar ta ji mata ba. Fahimtar hakan da budurwar tayi ta saki wata shegiyar dariya, wacce tasa su Farida mamakinta, kai har Jasmin d'in, batayi gigin nuna mata wata illa da tayi mata ba, sai ma nunata da take da yatsa tana dariyar tsananin mugunta. Gaba d'aya Jasmin sai taji ta tsargu, ta kama duba jikinta, amma babu abunda ta gani a jikin nata. Kamar jira ake kawai sukaga budurwar an fyad'ata da k'asa, jaa da baya suka kama yi gaba d'ayansu, suna kallon yadda take komawa lokaci d'aya, jikinta ya kama sauyawa yana komawa color blue, jijiyoyin jikinta sun fito rud'u-rud'u, fatar jikinta ta koma ruwan toka. Farida tana kallon yadda take wage baki tana ihu lokacin da k'asusuwan jikinta ke kakkaryewa, hak'oranta sunyi wani masifar tsini, na gaban bakinta. Wata irin mik'ewa tsaye tayi tana layi, kanta ya jirkice kafafuwanta ma haka. Da gudu suka fara ficewa daga company nin, kusan zan iya cewa Jasmin ce farkon arta na kare. Sauran suka take mata baya. Kamar jira ake su fara fita, suka fara ganin Zombies masu yawa suna fitowa daga wasu sassa na company nin, kota ina kamar zaro su ake suna fitowa suna niyar fitowa daga cikin company nin. Faruk ne yayi azamar idasa ficewa kusan shine k'arshe, yasa iya k'arfinsa yana son rufe k'ofar company nin, domin idan wa'innan Zombies d'in suka fito da suke gani suna b'allowa daga cikinsa, to komai na iya faruwa. Al'ameen ma ya taimaka masa da kyar suka datse k'ofar Zombies na gaf k'arasowa wajan k'ofar. Suna jin lokacin da suka iso bakin k'ofar suna bubbuga k'ofar a hankali suna suna girgiza k'ofar da son b'allata. Kamar ance Faruk ya waiga yaga wani k'aton duram mai cike da fetur a cikinsa. Da sauri ya k'arasa inda yake yana ma Al'ameen alamar ya taimaka masa. Bai san abunda yake nufi ba, sai da yaga Faruk d'in yasa inda duram d'in yake iya k'arfinsa ya jirkitar da Duram d'in fetur d'in da ke ciki ya fara malale k'ofar Company nin. Ja da baya suka soma yi sosai Faruk ya d'akko wani dutse na k'ank'ara iya k'arfinsa ya irink'a had'e dutsen da d'an uwansa, suna bada wani sauti, can saiga wuta suna kawowa, idan ya had'esu waje d'aya. Suna bada wutar yayi tsalle ya jefar dasu a cikin fetur d'in daya malale a k'asa. Ai ko nan take wuta ta fara ci a wajan, kamar wutar daji ta fara kamawa da yawa tana nufar cikin company nin. Suna tsaye nesa da wajan suna gani a sadda wutar ke k'ara ci sosai harta kama cikin company da yawa suna iya jiyo ihun Zombies dake ciki, had'e da kururuwarsu. Wutar har wani tashe take sama, saboda zuwa lokacin ta gama kama gaba d'aya wajan, har sai da su Faruk d'in suka had'a da d'an gudu suna son barin wajan................ *GAWA TAFE, NA KUD'I NE AKAN NAIRA D'ARI HUD'U KACAL #400, DAGA EPISODE 9TO10, ZAI TSAYA FREE PAGES D'IN, KARKU BARI A BAKU LABARI, SALON LABARIN NA DABAN NE, BA SAI NA TSAYA INA MAKU DOGON SHIRHI BA, KUMA KUN RIGA DA KUN SAN AL'K'ALAMINA BAYA RUBUTUN BANZA* *Zaka iya turo kud'inka ta wannan number d'in*👇 8130479973 Fatima Rabi'u Opay bank Saika turo shaidar biya ta wannan number d'in 👇 08130479973 *GAWA TAFE* (Zombies story) On2025 *©Zahra Royal Star* *ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION* *EPISODE 9TO10* *END OF FREE PAGES* *G.R.A. Estate Residential Area, Katsina State Nigeria* *ANAM POV* Da mugun gudu Anam ta sakko k'asa tana duban Mom dake tsaye hankali a tashe rik'e da waya a hannunta, sai kiran waya take amma ana cewa wayar a kashe. "Mom wallahi nima sai kiran wayar Hanan nake ita da su Faruk amma a kashe, ya za'ai su bi su kashe wayoyinsu wannan wane irin hauka ne haka Mom?". Mom dake cikin halin rud'ani itama ta sake gwada kiran nasu again a kashe, sauke wayar tayi kawai tana dafe kanta ta kalli Anam tana cewa. "Please Anam ina cikin rud'ani, ki barni da abunda nake ji, gaba na fad'uwa yake amma kinzo kaina sai hayaniya kike min". "Haba Mom nima fa hankali a tashe yake, ya kamata ace tun sadda suka isa su kira mu ko?, amma har yanzu shuru" D'aga kanta Mom tayi ganin Dad ya shigo Parlon a rud'e yana kallon Anam duk ya rud'e yana cewa. "Maza-maza Anam kunna min Tv, an kira ni waya wai na kalli Labarin duniya na yanzu da ake haskawa akwai matsala da alama". Gaba d'ayansu gabansu ne ya yanke ya fad'i bare Mom ido a waje take bin Dad da kallo ta kasa cewa komai. Hannun Anam na rawa ta d'akko romot tana kunna Tv had'e da kamo tashar labarin duniyar. Muryar mai labaran ce ta karad'e parlon a inda yake cewa. "A labaran namu na yau zaku ji cewa a K'asar Goa wata muguwar annoba ta kunne kai a gabashin k'asar gaba d'aya, a inda yanzu haka cutar na dad'a yad'uwa kamar wutar daji, a inda shugabannin K'asar ke bada labarin cewa suna buk'atar taimakon K'asashen dake kusa dasu, kai harma da K'asashen duniya baki d'aya, a inda suke buk'atar kwararrun Likitoci wa'inda suka kware ta fannin aikinsu, domin suna son gano maganin da zai warkar da wannan Cuta, sai kuma buk'atar Sojoji wa'inda suka kware ta fannin yak'i domin yak'in wa'inda suka riga da sun gama kamuwa da ita wannan annobar, wacce idan mutum ya kamu da ita cutar yake cin naman mutum d'an uwansa. To sai dai muce Allah ya kyauta, kuma Allah yasa K'asashen duniyar suji Koken K'asar Goa domin tallafa mata wajan iyakance wannan annoba data riske su in....... Kamin ma su idasa jin k'arshen labarin Mom ta sulale a k'asa a sume. Anam dake kusa ta lura da ita ce ta saki wata gigitacciyar k'ara had'e da bazawa da gudu tana tarbo Mom a jikinta. Kuka ta rushe dashi tana jijjiga Mom. Dad kansa ya d'auki zafi yama rasa miye ya kamata ya farayi, dole su zauna da Gwamna da kuma, shuban K'asa, asan yadda za'ai suma su tura Sojojinsu had'e da Doctors domin cuto Y'ay'ansu dake a K'asar Goa. Zufa kawai ke yanko ma Dad ba shiri ya cire babbar rigarsa, ya nufi inda Mom take da hannunsa ya kinkimeta sai waje. Mutanan dake cikin gidan, ganin Dad ya fito da Mom a hannunsa bata motsi, yasa gaba d'ayansu rud'ewa ga Anam dake biye a bayansa sai rusa uban kuka take kamar wacce aka ce Mom d'in ta mutu. Da kansa yaja Motar, bayan yasa Mom a baya sai Anam data shiga tana rungume da Mom, da gudu yaja Motar suka fice suka bar y'an aikin gidan da zullimin abunda ke faruwa. _____________________ *HARUN POV* Babban d'akin taro ne na Hukumar Sojan K'asar Nigeria, gaba d'ayansu ne zaune a wani k'aton Table kowanne mutum dake zaune an aje masa ruwa a gabansa. Gaba d'ayansu sun mai da hankalinsu ne ga Shugaban Sojojin da yake masu wani mahimmin jawabi kamar haka. "Mun had'a wannan mintin d'in ne, a bisa shugabannin K'asar nan da suka bada umarnin tura wasu daga cikinmu zuwa K'asar Goa". Sai kuma yayi shuru yana sake kallonsu, wata Tv ce a gabansu tana tsaye yana nuna jikin Tv d'in yana sake kallonsu yana sake cewa. "Wata annoba ce ta riski K'asar Goa, a yadda muka samu labarin cewa cutar ta gama ma K'asar Goa babbar illar da har suke neman taimako a k'asashen duniya, wa'inda suke da halin taimaka masu k'ofa a bud'e take, suna buk'atar Likitoci wa'inda suka san aikinsu, sai kuma Sojoji wa'inda suka kware ta fannin yak'i. To shugaban K'asar nan ya bada Umarnin mu tura Sojojinmu na nan k'asa Nigeria domin kai masu d'auki, had'e da Likitoci manya na K'asar nan. A labarin da naji cewa akwai Y'ay'an Manyan K'asar nan da suka tafi Goa bada dad'ewa ba, shi yasa abun ya shafi Manyan K'asar yasa har suka bada umarnin ayi gaggawar kai masu d'auki". Ya sake d'an yin shuru yana dubansu gaba d'aya sun bada hankalinsu suna sauraran abunda yake cewa, sai d'aga kai suke alamar suna fahimtarsa sosai. Ya sake nuna jikin Tv d'in dake a gabansu yasa wani manuni yana nuna yadda K'asar Goa ta fara komawa kamar Mak'abarta yana cewa. "A nan zaku ga irin illar da cutar ke yi a jikin D'an Adam, cutar dai tana kama mutum ne idan mai cutar ya cije ka ko kuma yasa farcensa ya yakusheka, cutar tana sa ka rink'a cin naman mutum, akwai had'ari sosai a wannan tafiyar da muke shirin turawa wasu daga cikinmu. Kai Captain Harun kai zamu tura had'e da Y'an group naku, domin Hukumar Soja ta yarda da kai da y'an term d'inka, tana da tabbacin baza ku bamu kunya ba, shi yasa ma kai tsaye muka yanke kune zakuyi wannan tafiyar". D'aga kansa kawai Harun yayi alamar tabbatarwa, da amsawa Kuma. Taron ya tashi a inda aka ware y'an group d'in Captain Harun ciki harda Abbakar da kuma Captain Joha, sai wasu kusan su goma Sha harda mace Maza sunfi yawa a ciki. _____________________ Momma dake zaune sai rusa uban kuka take har jikinta na rawa tsabar tashin hankali, a rud'e Abbie ke mata magana yana cewa. "Haba ya kamata ki daina kukan nan haka nan, nasa fa za'a tura Sojojinmu na K'asar nan had'e da Doctors domin cuto Y'ay'anmu, insha Allah babu abunda zai faru dasu ki kwantar da hankalinki kinji?". Kuka ta sake rushewa da shi, tana kuka tana cewa. "Wallahi hankali na bazai tab'a kwanciya ba, baccin gaba d'aya Y'ay'ana suna K'asar da wannan cutar ta b'arke da ita, ya za'ai na iya kwantar da hankalina?, kana fa gani aka nuno yadda idan mutum ya kamu da cutar yake cin naman D'an uwansa, wannan wacce irin cuta ce haka, ni ban tab'a ji ko gani ko labari akwai irinta ba, Innallihi wa'inna alaihir raju'on, nikam da nasan hakane bazan tab'a bari suyi wannan k'addarar tafiyar ba, dan...... Toshe mata baki yayi ganin yadda take magana cikin kuka har tana shid'ewa, cikin kwantar da murya Abbie ya ce. "Mu dukanmu bamu da sani da abunda Allah ya hukunta faruwarsa ai, addu'a ya kamata mu bisu dashi, dan Allah kibar kukan nan haka nan karki sama kanki wata cuta daban Kuma". Cikinsa kawai ta shige tana sake rushewa da kuka, domin tashin hankalinta gaba d'aya Y'ay'anta suna Goa. Taji labarin an kwantar da Mom a asibiti kwata-kwata bata da kwarin gwaiwar zuwa asibitin dubo ta, ji take dama ita ce ta suma ko ta samu sassaucin abunda take ji a ranta, dan ita sadda ta riski labarin komawa tayi kamar wata zararra, da kyar aka samu ta hawaye suka fara subo mata, daga nan ne kuma ta rink'a kuka mai sauti kamar ba gobe. _____________________ *ANAM POV* Rik'e take da hannunsa Mom da farkawarta kenan Anam sai kuka take tana kiran. "Dan Allah Mom karki sake suma, kina bani tsoro, kuma nima dani za'aje domin ceto y'an uwa na, yanzu nake samun kira da Hospital namu ana son ganinmu gaba d'aya, kuma ana ji dani a asibitin da nake aiki, nasan zaiyi wuya ba'a ce za'ayi tafiyar dani ba". Rik'e hannunta Mom tayi da k'arfi tana girgiza kanta, Dad na kusa ya d'an rik'e d'ayan hannun nata yana dubanta jin tana cewa. "A'a a'a ban yarda kije K'asar nan ba, kema so kike na rasa ki?, ban amince kije ba, itama Hanan nayi danasanin barinta zuwa, ashe dama abunda kike ji a jikinki kenan?, shi yasa kike ta k'ok'arin nuna min kar na bar Hanan taje, amma nak'i, bazan barki kije ba Anam bazan iya ba, idan na bari kika tafi kamar banyi adalci ba". Hawaye take tana maganar, Anam ma wasu hawaye ne suka sake wanke mata fuska ta girgiza kanta tana cewa. "A'a Mom dan Allah karki ce karna je, ina son nima nayi taimakon bayin Allah, ko Allah zai ji tausayinmu ya k'are Y'an uwana dake cikin k'asar da annobar take, please Mom ki gane abunda nake nufi, ba abunda zai faru dani Mom please". Mom zata sake magana wayar Anam ta sake d'aukar k'ara, cirota tayi ganin Doctor Halisa ke kira yasa ta kalli Mom tana cewa. "Ki gani ko Mom?, kirana ake daga Asibitin da nake aiki mitin ne na gaggawa zamu shiga, please Mom ki barni naje dan Allah" Dad ne ya katse hanzairin Mom dake son sake turjewa ya ce. "Please ki barta taje nima na barta taje insha Allahu zata dawo lafiya ita da Y'an uwanta". Ba dan Mom taso ba ta d'aga masu kai kawai hawaye na sake zubo mata akan fuskarta. D'auke idonta tayi daga Anam d'in tana zare hannunta daga na cikin Anam d'in. Dad ne yayi ma Anam alamar ta tafi kawai zaiji da Mom d'in, dan sun lura Mom bata gama amincewa da Anam d'in taje Goa ba. ____________________ Gaba d'ayan Doctors ne a zaune a wani d'akin taro a asibitin da Doctor Anam ke aiki, kusan ita d'aya ake jiran isowarta wasu har sun fara jin zafin ta, ciki harda wata Doctor Asiya sai cika take tana batsewa, a inda har ta fara surutu ita da wata K'awarta Doctor Sa'adha tana kallon k'ofar d'akin turon da suke tana cewa. "Wai ya za'ai anzo an wani aje mu akan wata can bata k'araso ba, mi yasa baza'ai mana jawabin abunda ya taramu ba?, ko kuwa dole sai shafaffiya da mai d'in can Anam ta zo za'a fara?, dan wallahi na tsane ta, ta cika iyayen tsiya da son asani". D'an tab'e baki Doctor Sa'adha tayi tana gyara zaman gilashin idonta, tana d'an yin magana k'asa-k'asa yadda ita da Doctor Asiyar ne kad'ai zasu ji ta ce. "Ai ko zaman jiranta ake yi yanzu, danni nima fa wallahi haushi take bani, ashe ba ni kad'ai ce ke jin kwata-kwata batai min ba". Asiya zatai magana Anam ta fad'o d'akin, kamar an jefota. Doctor Fahat ne ya kalleta kusan shine shugaban asibitin, dan shine ma zaiyi bayani akan abunda ya tarasu. "Mi ya tsayar dake ne Anam?, kin bar mutane a zaune". "Am sorry Doctor Fahat, wallahi an kwantar da Mom d'ina ce a asibiti, ga abubuwa da suka cakud'e mana a family namu, amma yanzu na iso zamu iya fara abunda ya taramu". Nuna mata wajan zama yayi ta zauna ya d'an kallonta cike da sonta da birgewar da take masa. Su Doctor Asiya dake gefe kusan a tare suka tab'e baki. Tana zama Doctor Halisa dake kusa da ita ta d'an mata rad'a a kunne wadda yasa Anam d'an sakin murmushi kad'an. Gyaran muryar da Doctor Fahat yayi ce yasa gaba d'ayansu suka mai da hankalinsu gare shi. "Kamar yadda kuka sani a safiyar yau ne muka ji labarin wata Annoba ta kunno kai a K'asar Goa, wacce ta hallaka mutanan k'asar da yawansu, dan hakane manyan k'asar Goa d'in suke neman taimakon manyan Doctors wa'inda suka san aikinsu had'e da taimakon Hukumar Soja, ga duk K'asar dake son taimaka masu k'ofa a bud'e take. Mun samu umarnin cewa shugaban k'asamu Nigeria ya bada Umarnin tura Sojojinmu had'e da Doctors a kowanne asibiti dake fad'in k'asar nan zasu iya bada kamar mutum uku, abunda yasa mukayi gaggawar taraku a nan kenan, mun rigada mun gama zab'ar wa'inda za'ayi tafiyar dasu, ga duk wadda muka je muka dawo lafiya dashi, shugaban k'asa ya ce zai bada gagarumar kyauta wacce zata girgiza mutum, dan haka mun zab'i Doctor Anam had'e da Doctor Halisa sai kuma Doctor Asiya sai kuma ni da za'ayi tafiyar". Shuru wajan ya d'auka kamin kuma a fara y'an k'ananun maganganu, wasu sunji haushin cewa bada su aje ba, domin jin cewa ai shugaban k'asa yayi albishir d'in zai bada gagarumar kyauta, kyautar ce kawai da suka ji za'a bada ta rud'e su, sai cece kuce suke akan wa'inda aka yanke dasu za'aje, wasu ma kai tsaye suke maganar son kai aka nuna a cikin wa'inda aka zab'a za'ayi tafiyar dasu. Sai da Doctor Fahat ya d'an buga table d'in dake gabansa, sana suka yi shuru. "Idan akwai wadda yake da magana k'ofa a bud'e take, ga duk wadda aka zab'a idan baida ra'ayin zuwa zai iya fad'a a canza wani a madadinsa". Kowa shuru yayi domin wa'inda aka zab'a kowa dama so yake aje dashi. Doctor Sa'adha ce ta tab'e baki ita ce farkon tashi ta fice daga d'akin taron tana jin zafin ba'a sa da ita ba a tafiyar. Doctor Asiya ce ta take mata baya, domin suna d'asawa da ita. "Haba k'awata ya da haka Kuma?, ba'a gama taro ba kin tashi". Tsayawa Sa'adha tayi tana kallon Asiya kamin ta ce. "Dole zaki ce haka man, tunda kin san an zab'e ki a tafiyar". "Noo wallahi na so asa dake a ciki, amma dan Allah kiyi hakuri, ni kwata-kwata ma jikina ne yayi sanyi, kamar na ce ma fasa zuwa ma, kinga fa inda zamu kamar lahirarmu ce muka kai kanmu, kinji bayanin da Doctor Fahat yayi ai?, wa'inda suka kamu da Cutar fa cin naman mutum suke da ransa fa, abun ya d'an so ya bani tsoro, ba dan naji za'a bada number yabo ga duk wa'inda akai tafiyar dasu aka dawo lafiya su za'a basu kyauta had'e da number yabo, wallahi da ba abunda zaisa na amince ayi tafiyar dani". Wani tsaki Doctor Sa'adha ta saki tana bankama Doctor Asiya harara, tayi gaba tabar Asiya da sakin baki. Au yanzu haushinta take ji duk bayanin data tsaya tayi mata?, gani take kamar bak'in ciki Sa'adhar ke mata dan kawai an zab'e ta, ita kuma ba'a ce da ita ba. Tab'e baki Asiya tayi tana d'aga k'afad'arta, alamar Doctor Sa'adhar taji dashi dai. ______________________ *Umaru Musa Yar'Adua Airport Katsina State Nigeria* Gaba d'aya Hukumar Sojojin Nigeria ne had'e da Kwararrun Likitoci wa'inda aka tantance zasu tafi zuwa K'asar Goa, wadda K'asar Goa d'in ta riga da tasan da zuwansu a yau d'in, sosai kuma suka jinjinama Nigeria d'in a bisa taimako na farko da aka fara kowa masu, Nigeria ce ta farko wacce ta fara amsa zata turo mutananta domin taimakon k'asar. An riga da an shirya tarbarsu a can, da duk kayan aikin da zasuyi anfani dashi. Da sun sauka kai tsaye gidan shuban K'asar Goa d'in za'a sauke su, domin a fadar shugaban k'asar ce kawai Zombies basu gama cimmata ba, amma suna gaf shiga fadar shi yasa suka nemi taimakon K'asashen duniya. Jirgin Sojojin Nigeria ne ya fara tashi kamin kuma Jirgin Doctors nasu Anam ya d'aga sararin samaniya shima. Su Anam jirginsu na d'agawa ta kama sauke ajiyar zuciya, jin wani bala'in tsoro yana rufe mata gangar jiki, kai bama ita d'aya ba dukkansu sai yanzu ne suke jin anya basuyi gaggancin amincewa shiga K'asar da annoba ta gama halaka mutanan cikinta ba kuwa?. A wajansu Harun ma kusan hakane, Abbakar kuwa akwai bak'in k'uduri a ransa na son kawo k'arshe Captain Harun a wannan tafiyar yayi ma kansa al'k'awarin bazai tab'a bari Harun ya dawo da ransa ba............ *Tofa jama'a masoya na masoyin wannan book d'in nawa, laifin dad'i aka ce k'arewa, a nan duka-duka na kawo k'arshen Free pages, Maza-maza ka-ki tura kud'inka domin karanta ci gaban labarin, yaya za'a kwashe a wannan tafiyar dasu Captain Harun suka yi had'e dasu Doctor Anam?, shin zasu dawo da ransu kuwa?, shin wai ma zasu had'u da y'an uwansu a k'asar Goa?, K'asar da ke da yawan jama'a, ya za'ai su fara neman su lokaci d'aya?.* *Kai nima fa zanso sanin ya zata kasance a wanga book wallo.* *GAWA TAFE, NA KUD'I NE AKAN NAIRA D'ARI HUD'U KACAL #400, DAGA EPISODE 9TO10, ZAI TSAYA FREE PAGES D'IN, KARKU BARI A BAKU LABARI, SALON LABARIN NA DABAN NE, BA SAI NA TSAYA INA MAKU DOGON SHIRHI BA, KUMA KUN RIGA DA KUN SAN AL'K'ALAMINA BAYA RUBUTUN BANZA* *Zaka iya turo kud'inka ta wannan number d'in*👇 8130479973 Fatima Rabi'u Opay bank Saika turo shaidar biya ta wannan number d'in 👇 08130479973 Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels