Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels 🏡️🏡️🏡️🏡️🏡️🏡️🏡️🏡️🏡️🏡️🏡 πŸ€ΉπŸΏβ€β™‚οΈ *ALKAWARIN MASOYA* πŸ€ΉπŸ»β€β™€οΈ ~ Na ~ πŸ‚ *Rukayya Ibrahim* πŸ‚ ✨Tsokaci ALKAWARIN MASOYA na kudi ne gamai bukata naira 300 ne kacal ki zama mace mai aji ki karanta abinda kika sayaπŸ‘Œ Free page🀧 *EXQUISITE WRITER'S FARUM* Page1⃣&2⃣ Safiya ce da misalin karfe 7:10pm Ahlin gidan tsohon minister ne, zaune Akan daining babba mai d'auke da kujeru sama da 12 karyawa suke kowa ka gani cikin shirin sa yake na zuwa aiki koh makaranta inka cire matan gidan, Abba ne zaune a kujeran daining inda ke tsakiya, zaikai Akallah shekara 65 sai hajiyoyin dake zaune akan kujerun gefensa, manyan matane masu ji da aje naira da izzah, sanye suke cikin shiga na atamfa dukansu. mamu uwar gida akallah zata kai 50 sai ummu Amarya mai shekaru 40 sai babban d'ansa Anwar d'an mamu ne zaikai shekara 35 zaune yake cikin shigar office(doctor). sai mai binsa shareef mai shekara 31 shima yana sanye da suit baki (lauya), sai umaima dake sanye cikin dogon rigan kanti da gyelen sa, daga kaga irin wankan ta kasan yar jami'a ce, zata kai shekara 25 dukan su d'akinsu d'aya ne. sai babban d'an ummu uzaifa da zaikai 20 yana sanye da jamfa da riga da wando na shadda, kansa babu hula(student). sai munira mai shekara 17 sanye take da uniform tare da kanwarta zulaihat mai shekara 15 ita tana sanye da uniform, Abinci suke ci hankali kwance yayinda kujeru uku yakasance empty babu kowa akansa. Addayiya dake zaune a tsakiyar falo ta mimmike kafa tsohowace sosai Amma jin dadi ya boye shekarun nata, sanye take da zani da riga sai d'an kwali data aje a gefe bata d'aura ba tulin gashenta daya rine zuwa fari a bayyane, Abinci take ci kwai ne da Arish sai tie ga bread a gefe, cin Abincin ta take hankali kwance. Turo kofar da akayi shiya ja hankalin kattafanin su dake falon harda daining Area, duk da kamshin turaren sa ya sanar dasu wake shirin fitowa, Amma hakan bai hanasu juyawa don tabbatar wa kansu shin da uniform ya fitoh koh Ah ah. Fitowa yayi a kofar, wow masha Allah watoh in Anace maka black is beauty, bazaka tabbatar ba sai kaga wannan Hallintar koh shakka bazakayi ba, bakine mai sheki irin bakikkirin nan, fatar nada masifar laushi har maiko-maiko fatar keyi sanye yake da wando baki, mai roba a kasar wandon, pencil ne ya kamasa sosai bai rufe masa idon sahu ba. sai boot fari tas baisa wa kafarsa socks ba, hakan yasa ana kallon idon sahun nasa, t-shirt ne a jikinsa white sai rigan da ya daura akai mai hula da dogon hannu, Amma ya bude zip in wanda yasa ake kallon rigar ciki. ga wani d'an iskan Aski dake kansa ya raruke gefe yabar sakiya da yawa, gashine mai laushi da yawan gaske irin na fulani, ga kwancecen sajensa mai hade da gemu, duk da bai cika masa fuskar ba, Amma daga gani Ana ji da gemun irin na tsiran farkon nan ne na tashe balaga. Bakin sa pink ne mai kyau dan kankani, hancin sa mai tsahone sosai ga idanu manya kamar na mata, kwayar idanunsa bakine sosai wanda ke matukar rikita mutune a duk lokacin da ya zare maka su yayin da mabi da kwayar ya kasance fari tas gashin giransa mai yawane blutooth ne fari makale a kunnensa d'aya. Yana da tsawo sosai Amma ba irin har shan innan ba, gashi da kira mai kyau duk da yanzun yake tashen sa, Amma kallo d'aya zaka masa ka gane za'ayi namiji, baxai wuce shekara 18 ba. Taku yake irin na isasun yaran nan masu ji da lokacin su hade da kuruciya, duk da ya gansu zaune a falo, Amma hakan baisa sa ya nuna ya gansu ba nufar kofar falo kawai yayi. Addayiya dake zaune a tsakar falo tana cin kaza da romonsa wanda yar aiki ta aje mata, ta mike kafa. da gangan ya nufi ta saitin da take zaune kamar baiganta ba, ya d'aga kafarsa kamar zai taka kafarta da sauri taja abinta cikin masifa take kallon Lahab. Amma yaron nan Anyi jarabebbe kai in gari ya waye baka sani surutu ba bakajin dadi, nida gidan mijina da d'ana, bani da sakat sai in baka nan, toh yau duk bala'inka bazan kulaka ba, d'an-banza kawai. yi yayi kamar baisan ma tanayi ba tafiyarsa yaci gaba dayi. Abbu dake zaune tunda lahab ya fitoh yake binsa da kallo Ganin yanda yazo ya wuce su, yau koh break in ma bai tsaya yiba, kwala masa kira yayi ganin yana kokarin bude kofar, Lahab!!!Lahab!! *ALKAWARIN MASOYA Naira 300 ne vie 2185602275 Rukayya Ibrahim UBA bank, koh katin Airtel zaki tura ta wannan layin 08084453785 tare da shaidan biyan ki* had'a fuska Lahab yayi jin yayansa na kiransa juyowa yayi ya dawo cikin falon har wajen daining Area, ya tsaya a bakin steps in. Abbu ganin ba gaidashi Lahab zaiyi ba yasa sa kallonsa, Anya lahab rayuwa zaiyu a haka kuwa? kai kenan in gari ya waye sai an maka fad'a, daga safe zuwa dare sai ka samu surutu a gidan nan, mekake so Lahab da ban maka ba? kara had'a fuska yayi jin Yayan nasa zai fara masa fad'ar daya saba a idon yaransa, "babu" toh Yanzun ka kyauta kenan ina fa kallonka saura kad'an ka taka mini kafar mahaifiya da wa'inan shegun takalman nan naka? Addayiya fa ba kakarka bace, koh su Anwar basa mata abinda kake mata a gidan nan. jin Abinda Abbu yace yasa Addayiya fashewa da kuka, kuma fa umar tun farko saida na nunawa ubanka banason Auren sa da wannan figeggeyar yarinya, Amma dayake budurwar zuciya ne dashi,kaima kabi ka sani a gaba da wa'azi, gashi shi ya tafi ya barni da jaraba ga uwarsu shan tayi auren ta tana jin dadi ni An barni da ciwon baki, Allah sarki. haushi ne ya kama lahab cikin masifa yace"oh Ashe kishi kike tayi aure bakiyi ba, kema ai bawanda ya hanaki saiki fitar da miji a miki" kuka Addayiya ta sake, nikam na shiga uku ni Maryamu, toh bara kaji uwarka ce kwad'ayayiya ita da ubanta, ba kunya tazo ta likewa tsoho. dariya jama'ar dake wajen suka sake Abbu ne kawai baiyi dariya ba saima haushi dayaji ya rasa meyasa kullun sai sunyi fad'a, kuma Lahab ke tsokanar ta daga karshe kuma ya sata kuka, Habba don Allah Addayiya wannan wani irin magana ne a idon yara? jin abinda Abbu yace yasa Addayiya had'a fuska taci gaba dacin Abincin ta, tana share hawaye. kallon Lahab Abbu yayi, yanzun menene Amfanin abinda ka matan nan ta tsufa ma bazaka barta ta huta ba?koh so kake ka d'aura mata hawan jinine? "kayi hakuri yaya bazan kara ba" rufe mini baki karawa na nawa kuma lahab,kuma ban gane ba na ganka da wa'innan kayan ina uniform in? kafun ma lahab yayi magana Umaimah tayi caraf tace Haba Abbu inda sabo yaci ka saba da halin small uncle ka hutawa ranka, kai yaranka basu baka ciwon kaiba zaka sawa kanka ciwo akan sa. ai Lahab najin abinda tace cikin masifa ya nunata da yatsa"wallahi zanci uwarki umaimah daga yau in ana mini magana kika sake saka bakin ki a ciki yar iska kawai". mikewa shareef yayi kai wallahi ya isheka haka Lahab mun gaji da iskancin ka a gidan nan? wani hayyakowa lahab yayi cikin masifa kamar irin zai iyya dukansan nan"toh koh dukana zakayi matsiyacin lauya" tura kujeran daining in shareef yayi zai sauko da sauri Abbu ya nuna masa kujera da hannu, go back to ur seat shareef, Lahab bappan kane respect him banason haka? shi ya fara baka respect naka tukunnan kaida kake yayansa, kuma a girme ka haifesa Amma bayajin maganar ka, bayajin kunyar ma su ummu rashin mutunci saini ne dukan sa zai gaggareni. ai jin yace duka yasa lahab harzuka zai zage shareef sai kuma yayi shuru jin takun sahun kafa a falon, wanda koh shakka babu yasan wanda ke tahowa. Allahu Akbar tsarki ya tabbata ga Allah, hatta tafiyarsu iri d'ayace kai daga zaran ka gansu basai an fad'a maka ba, zaka bawa kanka amsa da tagwayene, babu abinda ya banbanta su sai abu biyu hali da kuma gyaran gashin su, Amma bayan wannan da koh a cikin gidan su baza'a samu mai banbantasu ba, a hakan ma mutanen waje ba iyya banbantasun suke ba. karasowa yayi gaban daining in bayan sun gaisa da Addayiya a falo, gaida Abbu yayi da ummu da mamu, yaran Abbu suka gaidashi dukansu duk da mazan sun girmesa hakan bai hanasu basa girman saba. kallonsa Abba yayi cikin farin ciki, sanye yake da uniform, wandone navy blue, sai riga fari da boot fari na makaranta a kafar sa, hannunsa sakale da school back sai wasu litattafai daya rike, Rahab na tura zuhaihat kafa biyu kazo mu karya, wai kana wanka? murmushi yayi saida fararen hakoran sa sak irin na Lahab suka bayyana, Eh yaya Assigment nayi da safen nan shiyasa nad'an makara ban shiga wanka da wuri ba. ok get a seat ka zauna oyya kayi break? gaskiya Yaya nayi laten almost 7:32 yanzun fa?zan wuce kawai. hannu Abbu yasa a Aljuhunsa ya zaro 1k mikawa Rahab yayi, gashi ka shiga school cafe ka sai abin break ka tabbatar kafun ka shiga aji ka karya? d'an rusunawa Rahab yayi ya karbi 1k in hade dama yayan nasa godiya, kallon Anwar yayi, doctor Ya Alkawarin mu na kudin hadisi gobe islamiyya, in ka samu aban yanzun zanbi islamic bookshop in muna dawowa? hannu Anwar yasa a Aljuhu ya zaro lalitarsa 10k ya zaro ya mikawa Rahab. hannu yasa ya Amsa cikin murna yace, doctor kudin sunyi yawa hadisin fa 500 ne? na sani Rahab sauran chengen ka rike a a hannunka. Lahab dake tsaye a gefe tun fitowar Rahab bai kara magana ba, sai binsu da ido yake, ganin kudin da Aka bawa Rahab yasasa shammatar su ya fizge 11k in ya b'anb'ara da gudu ya nufi kofar falo, a tamanin Rahab ya bisa a guje zuciyar sa na tafarfasa don shi daman mutun ne mai karamin zuciya, duk irin kwala masa kira da suke akan ya dawo kin sauraron su yayi. Addayiya dake zaune har lokacin fuska a hade, nufar kanta gadan-gadan Lahab yayi da azabebben gudu. ai mikewa Addayiya tayi jiki na rawa ganin sa ya nufota da gudu itama gudun tasa ta nufi............. ******************* ENUGU STATE......... zaune take a kan bench ita kad'ai, kuma benchin a kusurwan aji, ita kad'ai aka ware wa wajen tana zama, gabaki d'aya ta tattara hankalin ta akan malamin dake koyar dasu Math's duk da ba kallonsa take ba. sanye take da wani kod'aden uniform dogon rigane wanda ya tsaya mata iyya gwuwa, farace irin farin nan da ake kira light, kyakkyawace na bugawa a jarida siririya ce Amma fa Akwai kaya duk da tana zaune akan kujera hakan bazaisa mutun ya kasa gane irin baiwar da Allah ya mata ba, kirjinta a cike yake tam wanda yasa gaban rigan matseta har gaban kirjinta ya kasa rufuwa har ana kallon farin vest inta datasa a ciki shine ya hana ganin Kirjinta a waje, kanta ba hula sai gashinta mai yawa da aka masa kitso uku ya zuba har gadon bayan ta. Ebo ce irin fararen masu kyau innan toh haka take ita ma, bakinta jajazur maikyau ga hanci mai tsaho, duk da idanunta na boye a cikin medicated glass, hakan bai hana ganin kwayar idanunta dake kallon Allo ba. masha Allah idanun nan ne irin wanda ake kira da cat eyes kwayar idanunta sky blue ne, gasu masu girma, wanda sanadin su wasu ke kara gudun ta. kiliilii....killiiliii bugun bell shiyasa malamin fita a ajin, ya rage ita kad'aice a class babu kowa, yamusheshen jakanta ta zaro a lokan benchi budewa tayi ta leka ciki. kulenta(magge koh kenwa)zaune a kan takardunta abin tausayi, shima jin An bude boron yasa sa kallon ta. sosai ya bata tausayi yanda bata karya ba, haka shima yau babu abinda yaci, hannu tasa a gefen jakan ta zaro naira talatin jujjuya kudin tayi a hannunta, aje jakan tayi ta mike tsaye ta fita a ajin. tafiya take kanta a duke fuska a hade sosai, wanda hakan dabi'arta ne bazaka taba ganinta cikin fara'a ba, koh kaga tana surutu da wani, duk inda tazo wucewa haka yara zasuna watsewa Inda sabo ta saba, hakan yasa abin bai damunta sosai. tun kan ta karaso wajen mai kayan shagon tuni ya ruga a guje ga fita a keus nasa, itama bata wani damuwa ba hannu tasa daga wajen shagon ta ballo madaran 20 da pure water 10 aje masa kudin tayi ta juya ta koma class. zama tayi a inda ta tashi hannu tasa a boron ta d'auko kulen ajesa tayi akan kujeran, bude madaran tayi ta bula ruwan ta zuba a madaran saida yazo har bakin laidan madara, kafun ta aje pure water kallon kulenta tayi yana zaune kamar mutum ya kurawa madaran ido, d'aukarsa tayi ta aje akan cinyarta tana basa madaran. sai da ya kusa shanyewa kafun ya Rufe bakinsa Alamun ya ishesa, sauran kad'an in ta shanye batare da taji kyeman bakinsa ba. haka a daddafe take saboda tsananin yunwar da ke cinta, karfe 2 Aka tashi a school, duk yara suka fifita, itakam zama tayi a class taki fita saboda tasan mundin ta fita, haka yara zasuyita gudu har su shiga kauyen su, shiyasa take jiran su d'anyi nisa kafun itama ta kama hanya. 2:27 ta fitoh a class nasun hannunta rike da jakanta wanda kule ke ciki da takardu, yaran makarantan duka sun watse koh malamai babu, A haka take tafiya A hankali, Nnenna irin mutanen nan ne masu saib'i. tafiya take Da kafa hankalinta gabaki d'aya yayi gida, ganin yanda hadiri ya hadu sama yayi bakikkirin sai iska dake kad'awa, doguwace sosai tana da wadatantun mazaunai masu d'aukar hankali, iska na kad'awa sai suka kara fitowa sosai. babu kowa a hanyar wanda hakan bai dameta ba sanin yaune Ake biki a makwantan kauyen su, lokacin da ta tsallake ruwa tazo wajen gonaki. ji kawai tayi an fizgota ta baya a matukar kid'ime ta juya wazata gani? wasu yan iskan kauyen sune chukwudi da onyebuchi akalla zasu kai 25, fizge riganta tayi taci gaba da tafiyan ta hankalin ta a tashe, sanin halinsu gashi yau babu kowa a hanya. binta sukayi Chukwudi cikin yaren Ebo yake mata magana, ke Nnenna Mayya mufa ba ruwan mu da maitancin ki, cinki yau zamuyi saboda kin hadune bana wasa ba, gashi bamu taba samun target namu yatafi daidai ba irin yau. jikinta na rawa ta kara sauri onyebuchi ne yasa hannu ya damko gashin kanta, fusge kanta tayi, da sauri ya wanketa da mari wanda yasa glass nata faduwa. rumtsa kyawawan idanunta tayi cikin tashin hankali ta sake budesu, gabaki daya dishi-dishi take kallo sam bama zata iyya kane fuskar su ba a yanzun. da sauri ta tsunguna a kasa tana lalubar glass nata, chukwudi ne yasa kafa ya take glass in dake gefe. jin karan fashewan glass yasa da sauri tasa hannunta ta saitin wajen tana laluben glass in, tana najinsa ta d'auka, tattabasa tayi, Kawai saita fashe da kuka ganin idanun glass ya bararraje. dariya suka sake a tare cikin iskanci onye yace mata, yaufa koh Jesus ne ya sauko bazai ceceki ba(wa'iyyazu billah) bare mutum gwanda ki bimu a hankali mu gama abinda muke so, a wajenki mu barki ki wuce, koh kuma mu kasheki kika mana gardama ya karasa maganar da zaro sharbebbeyar wuka. dubansa tayi idanunta na zubarda ruwan hawaye, sam ba kallonsu take sosai ba, tadai san gasu a gabanta Amma bata kallo normal kamar kowa "Tabbas kowa zai mutu Amma fa ka sani kai yau kwanan ka ya kare, kafun na mutu kai zaka fara mutuwa, Ajalinka na kusa wannan ALKAWARI ne, ALKAWARIN mutuwa"ta karasa maganar cikin tsantsan bacin Rai. jin Abinda tace yasa chukwudi sake wanketa da mari mai zafi saida ta zube a kasa, jakarta ya fade Allah ya sota ba'akan jakan ta fadi ba data illata kulenta, jinine ya balle a hancinta. A take ruwa ya sako da karfin gaske, hannu yasa yajawo riganta sai da ya yage,da karfi ta turesa ta kwashe jakanta da gudu ta ruga. suma binta sukayi sosai suke tsere har sukazo bakin titi koh gabanta bata kallo saboda rashin glass, gudu kawai take wanda ta fadi yafi a kirga haka zata daure ta mike, da gudun tsiya ta tsallaka titin daya ratsa kauyen su. suma da gudu suka zo tsallaka titin, ji kake kauuuuuuuuuu wata babban roka tabi ta kansu . Nnenna dake gudu jin karan yasata tsayawa da sauri ta dafe kirjinta tuno warning inda papa ya mata kafun ta fitoh.............. SANARWA!!!!SANARWA!!!!SANARWA!!!SANARWA!!! BABU UPDATE NA ALKAWARIN MASOYA EVERY WEEKEND ✨Ruqeenjalal✨ πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€ πŸ€ΉπŸΏβ€β™‚οΈ *ALKAWARIN MASOYA* πŸ€ΉπŸ»β€β™€οΈ ~ Na ~ πŸƒ *Rukayya Ibrahim*πŸƒ Free page🀧 *EXQUISITE WRITER'S FARUM* Page3⃣&4⃣ in bata manta ba papa yace mata mundin ta fita gida, sannan ta d'auko masa magana jikinta zai gaya mata, asalima umurni ya bata akan ta rufe bakinta, har taje ta dawo karta kuskura tayi magana da kowa, gashi tajawo wani rigimar kuma. kuka ta sake mai karfi gashi sai ruwa ake ga rashin glass ga iska na shigar mata ido, gashi bata ganin gabanta sosai, tafiya kawai take hankalinta a tashe, ta rasa ina zata nufa ba ganin hanya zatayi ba sosai ga ruwa, tafiya take a hankali ga jakanta a sakale a kafad'arta, gajiya tayi ga yunwa yasa ta zauna a jikin wani bishiyar da batasan bishiyar menene ba. kamar minutes 5 da xaman ta taji abu ya fado a jikinta da sauri ta kwala kara ta matsa gefe, don ta tsorata ainun zuciya mai sake-sake harta saka mata wani abin cutarwa ne. jin abin bai motsa ba yasata lalubar jakar ta ta bude kulenta dataji yana kuka, aiko tana budesa da gudu ya nufi inda Abin nan yake d'aukowa yayi da bakinsa ya matso kusa da ita ya aje mata a jiki, hannu tasa ta tattaba jin ayabane yasa ta murmushi, duk da ita a d'abiyarta sam batacin abinda ba'a bata ba koh yayane, Amma yunwar da takeji bazai saurara mata ba rabonta da abinci tun jiya. barewa tayi a hankali tana kai dubanta zuwa ga kulenta mika masa tayi Amma taji bai karba ba alamu dai bazaici ba, daman tasan Bayacin Ayaba, cin Abinta ta shigayi dayake bari guda ya fadi kusan k'walli 15 ne a manne waje d'aya. bayan ta gama cin ayabar ta, zuwa lokacin ruwa ya d'auke mikewa tayi da jikekken uniform nata a yage, jakanta ta bude ta saka kulenta a ciki shima duk ya jike, tafiya ta cigaba dayi tana kallon dishi-dishi dayake hanyar ba bakonta bane koh babu ido garanti zata gane kauyen su. tunda ta shigo kauyen jikinta ya fad'a mata ba lafiya, sanin da tamusu war yanzun suna bakin bishiya wasu na caca wasu nashan giya, Amma yau sit kakeji, duk inda ta wuce binta ake da ido wasu yaran kam gudu suke suna bata hanya. a haka ta iso kofar wani yamusheshen d'akin falange wanda akayishi ciki da falo, sai tsunmokaran su a rarrateye a jikin kwanukan gidan kome nasu a waje yake kama daga bandaki wajen girki kamar dai gidajen inyamurai babu katanga koh makewayi daga an fita a daki toh kamar an fita a kofar gidane. tura kofar d'akin tayi kamar yanda ta tsammani hakance watoh a bude kamar kullum, da takalmi a kafarta ta shige ciki. falone d'an kankani sai kujera da katifa mai masifar datti a gefe da tufafi a rarrateye sai risho da takalma da kwalaban giya, wucewa tayi kofar dake tsakar falon, tana shiga dakine karami babu kome sai taburman ta karami da kullin kayanta data d'aure mai datti tamai dashi filo. aje jakan kulen tayi a gefe ta bude sa a ciki da sauri ya fice a dakin yayi falo, itakam kaya ta cire ta d'aura zani a kirji uniform jikekken ta fitar ta aje a gefe, takardun ta duka ta ciresu ta d'au jakan ta rataya akan igiyar kayanta dake dakin, hannu tasa a gefen katifarta ta fitoh da wani karamin akwatin karfe budewa tayi hannu tasa ta d'auko wani glass in, jujuyasa tayi a hannunta tana tunanin shine kadai ya rage mata in tsautsayi ya rafkawa glass in shikenan bata da wani, sakawa tayi a idanunta, kayan makaranta ta d'auka a hannu tayi waje dashi. boket nasu dake falo ta d'auka ta fita waje dayake basa shan ruwan sama, sai Amfani dashi kawai suke Amma yau koh tarewa basu samu sunyi ba, ruwan jarka data ibo jiya ta tsiyaye kasancewar tasan tabbas bata da omo bata da kudin su, yasata wanke kayan haka da ruwa zallah ta shanya su. Ruwa ta ibo takai bandaki duk irin sanyi da ake haka ta kwara ruwan ta fito, dakin ta shiga ganin kulenta rakube yanajin sanyi zani ta d'auka ta lulluba masa, kwanciya tayi akan taburman ta,har bacci ya d'auketa ga kulenta a gefenta shima a kwance. Nnenna!!!Nnenna! Papane ke kwala mata kira da karfi tun kafun ya shigo falon. Bude idanunta tayi da sauri jin kiran mahaifin nata, glass nata dake gefe ta dauka ta saka, sanye take da Jess da t-shirt, kod'andu da sauri tafito a d'akin jin ya shigo falon. "Yes papa barka da dawowa" tace cikin yaren Egbo hade da karban laidan dake hannunsa. "Yauwa Nnenna ga Abinci saiki ci saya miki nayi a kasuwa yau na d'an samu kudi na sai miki Abinci saikici ai karki mutu da yunwa? Shuru tayi batayi magana ba ganin yau papa da mutunci ya dawo, harda sai mata abinci zama tayi a falon bayan ta dauko plate, ta bude laidan tuwon Amala ne ta fitar ta juye a plate, bude laidan miyan tayi zata juye sai kuma tasa a hancinta ta tsuntsuna. Da sauri ta aje laidan tana kakarin amai jin miyar Akwai naman kare a ciki. Papa dake kallon ta cikin jin haushi yace,kee Nnenna bazakici abincin nan ba kenan again koh dai da gaske ke mayyar ce, naga dai miyace babu nama a ciki koh Alamun nama? "amma ai miyar naman ce?kuma naman ma na kare ni banzanci nama ba" Keee mu Egbo ne munacin aladu da kare ke waye da bazakici ba? "Ni namane kwai banaci koh miyar nama"tace tana Aje miyar a gefe ta kama cin tuwon zallah yayin da papa ke zaune a kan kujera, kallonta yayi sai kuma yace Nnenna? Yes ta amsa masa Koh kinsan meya faru da onye da chukwudi kuwa? Gabanta ne ya fadi Amma ta maze cikin basarwa tace, "no pappa" Thank god daya kasance babu ruwan ki a maganar nan, babu wanda yace akwai hannunki, kinsan kuwa d'azun da rana onye da chukwudi babban roka tabi kan onye ta markad'a masa kai atake ya mutu, chukwudi kam ya samu karaya uku yana asibiti har yanzun baisan wake kansa ba. "Mai motar ya tsayane"? No bai tsayaba gudu yayi, akwai wasu mutane a bakin titin sune suka gaggauta kaisu asibitin cikin Enugu. "Toh god ya basu Lafiya" Emeen daughter god bless u yarinyata bata da rike kowa a zuciya duk abinda suke miki a kauyen nan kina musu Addu'an samun sauki? Shuru kawai tayi tacigaba dacin tuwonta yayinda kulenta ke lashe miyar. ********************* Ta bangaren Lahab da gudu ya haye Addayiya data ruga gefe ta zauna Amma tsabar masifa saida yabi ta kanta ya haye, Rahab kam gefe yabi. Da gudu ya bude kofar falon ya b'anb'ara bakin get tun daga nesa yake kwalawa mai gadin get akan ya bude masa kofa. Jin hakan yasa Rahab shima yiwa mai gadin warning akan karya bude kofar, Amma ina mai gadi kam duk ya rikice, driver dake tsaye yana jiran yan makaranta da ido ya bisu ganin yanda sukazo suka wucesa kamar walkiya da gudu lahab ya bankade kofar get in ya fice a tamanin. Turus Rahab ya tsaya rai a bace yana maijin bakin cikin abinda lahab ya masa, gashi yasan tunda lahab yafita a gidan shikenan badai ya iyya kamasa ba. Kamar zai fashe da kuka haka ya koma cikin gidan cikin bacin Rai,Abbu ne ya kallesa Rahab waton rashin hakuri koh? Rahab kiranka muke Amma ina zuciyarka ta kasa hakuri koh?ai da wannan zuciyar kullum lahab ke galaba akan ka. Shuru yayi fuskar nan tayi kirim Kamar zaiyi aman wuta, Addayiya dake gefe har yanzun tana salati akan hayo mata kai da Lahab yayi tace, wallahi Allah ya isa tsakanina da uwar yaran nan ta cuceni data aure mini miji. Cikim haushi RAHAB ya juya gareta,kinga wallahi kimin shuru Addayiya karki sake zagar mini uwa banaso wallahi bala'inku ya tsaya iyya kan Lahab ba mamata ba. Baki suka sake gabaki d'ayan su suna kallonsa da mamaki, sau dubu lahab zai masa abu in aka zagesa sai kuma ya nuna bacin ransa. Babu wanda ya sake magana sai tashi da sukayi daga kan daining Area in, shareef ne ya mikawa Rahab 10k, gashi uncle ka sai littafin? Karba Rahab yayi yana sabar jakarsa ya fita a falon, su munira sukabi bayansa dayake duk school d'aya suke dasu lahab. Motar school da Ake kaisu suka shiga, Rahab ya shiga gaba munira da zulai suka shiga baya, driver yaja suka bar gidan, shareef da Anwar mototin su suka hau, haka ma umaimah da dan uwanta duk suka wuce school. Lahab kam da gudu ya fita a gidan haka bai tsaya ba saida ya dangana da karshen layinsu, kafun yaja birki yana numfashi, sai kuma ya sake dariya tunawa da yanda yanzun Zuciyar Rahab ke tafarfasa. Boom yaci ya kama tafiyarsa kamar bashi ba tun daga nesa ya hango Adewale tsaye sanye yake da uniform, wando da riga, wandon pencil ya d'amesa sosai sai rigan uniform in koh botur bai rufe ba wuyansa sanye da sarkan cross mai sheki sai hannunsa dake sanye da abin hannu na maza. Yana kallon Lahab daga nesa ya kama baki cikin tarin mamaki, jesus nashiga uku me zan gani haka Lahab ina kayan makarantar yake dan iska?duk cikin hausar sa dabai nuna ba ya tambaye lahab. "Kallon banza lahab ya masa kai na fasa zuwa school in" Wannan wani irin iskancine lahab kace mana jiya zaka school kasa yau na buga uniform zaka wanice baxaka ba? "Eh bazani bane kawai yau in ma" Amma baka da mutunci yanzun so kake nayita yawo da uniform ai danasan bazaka ba bazan saka ba. "Basai ka koma ka cire ba" Aikin banza momy na gida zakace na koma na cire uniform? "Sorry ina Nabeel yake wai bai fito bane har yanzun, nifa na samo kudin jesen nan" Kallonsa Adewale yayi, nima ai na fito dasu yace yana zaro kudi a Aljuhunsa ka gansu nan 10k ne cip. "Kai anya ba satosu kayi ba daga magana jiya harka samo" Kowa barawo ne irin ka, an gaya maka ni dady ne ya bani dana ce masa a school aka bukace kudin kaga kuma uniform na saka ga kekena ma, shiyasa ya yarda makaranta zani, yace yana nunawa lahab kekensa dake gefe a fake, kekene mai masifar kyau da tsada. Murmushi kawai lahab yayi yace"aiko kudin Rahab na rarumo" Toh kaikam Allah ya shiryeka? "Ameen shige Ade muje mu dubo nabeel koh tsohowar nan ce ta tsayar dashi" Kekensa Adewale ya hau Da sauri lahab ya rike bayan keken ganin Adawale na kokarin jan abinsa"wallahi Ade baka isa ba ka wuce a sama ka barni a kasa" Turesa ade yayi yaja kekensa da karfi ya bule lahab da kura ya kara gaba. Cikin jin haushi lahab yake bin kuran bayan keken ade har kofar gidan su Nabeel, irin gidan nan ne na block da block sai d'an karamin kofar falange ga ade a tsaye a kofar gidan yana jiran isowar Lahab. Koh kallon ade baiyi ba ya tura kofar gidan, da sauri Adewale yabi bayansa. Da sallama suka shigo tsakar gidan, amsa musu mubeena dake zaune a tsakar gidan tana wanke wanke, sanye take da xani na Atamfa riga daban zani daban, sai hulan bacci data soka gashin kanta a ciki, amma hakan bai hana ganin gashinta dake kwance a gaba goshinta ba. Sai kakar Nabeel inna dake zaune a taburma tana tsefe kanta, Kallon Su lahab inna tayi sai kuma Adewale, dake gaidata Amsawa tayi ciki ciki ganin lahab bai sanya uniform ba, tasan daker ne yau su leka makarata. Jin yanda ta wani Amsa ma Ade gaisuwarsa yasa lahab kin gaidata, d'akin ya nufa Adewale na binsa a baya. Ku dawo nan karku kuskura ku shiga d'akin nan yan iskan yara fitinannu Addan Nabeel dake wanke wanke tace. Koh kulata lahab baiyi ba ya wuce d'akin, yayin da Ade ya tsaya kamar yanda Mubeena tace, jingina yayi da jikin ginin dake gefen wajen wanke wanken nata. Mikewa Inna tayi ta sabe bokatin wankan ta ta shiga ban dakin, batace musu uffan ba. Ganin ba kowa yasa Adewale fisgo Mubeena dake tsaye tana kokarin d'aukar kwandon kwanukan ta, had'ata da bango yayi ya rufa mata jiki da nasa, ya kasance tana jikin bango yana gabanta, yasa hannu akan ginin dake bayanta. Da sauri ta kallesa sai kuma cikin bacin rai tasa hannu ta ture sa amma koh gezau baiyi ba, yana mai duban cikin kwayar idanunta, a hankali ya bude baki yace, Akan ki na koyi sallama a gidan koma waye in zan shiga mundin musulmine,Amma na fahimci ke baki ganewa koh?kin matsamin. Cikin jin haushi tace karka kuskura banason wasan banza don Allah sakeni?ni sa'arkace nifa Aunty kuce? Hhh dariyanya sake tare da cemata, auntin nabeel da lahab dai, badai niba kuma shekara nawa kika bawa nabeel in? Amma sai son girma. Hannunta tasa ta make masa kumatu da mari amma irin mara zafin nan. Da sauri ya riko hannayen ta cikin zafin nama ya murd'a mata su. Ihu tasa da karfi Kamar daga sama sukaji ance mezan ganin nan haka Da sauri ya saketa yana kallon mai maganar................ pls Subscribe!!!! πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€ πŸ€ΉπŸΏβ€β™‚οΈ *ALKAWARIN MASOYA* πŸ€ΉπŸ»β€β™€οΈ ~ Na ~ πŸƒ *Rukayya Ibrahim*πŸƒ Free page🀧 *EXQUISITE WRITER'S FARUM* Page5⃣&6⃣ Lahab ne tsaye yana kallonsu cikin mamakin Abinda Ade yake ma Mubeena, fuska ba walwala ya tako wajen da suke tsaye, Itakam jikinta sai rawa yake don ta tsorata bata d'auka lahab bane. Karasowa yayi kusa da Adewale a daidai lokacin wani farin matashi bazai wuce sa'ar su lahab ba, sanye da kayan gida a jikinsa wando 3queter da riga duk da kayan da gani sun d'an sha ruwa, kallonsu lahab yayi cikin tuhuma ganin su a tsatsaye harda Addansa ma, kai lafiyarku? Har suna had'a baki wajen basa Amsa ba kome, da sauri mubeena ta sabi kwandon wanke-wanken ta har lokacin jikinta na bari ta shiga kitchen nasu dake gefe. Kofar gidan suka nufa har sun iso bakin kofa sukaji muryar inna data fito daga bandaki, kai nabeel!! Da sauri dukansu suka juyo gareta suna kallonta. Ina zaka??banaji kace makaranta zaka da safen nan ba? yana ganka a haka sannan dumamen dana aje maka bazaka d'auka bane kaci sai ulcer ya kamaka. gaskiya Inna ki basar kawai ni bazani makarantan nan ba. akan me bazaka ba?koh don uban gidanka(lahab) baxaije bane? ai tunda na gansa ba uniform nasan za'a rina, toh ka tsaya na fad'a maka gaskiya, tun duniya bai fad'a maka ba, kaga wannan yaro lahabu da wannan d'an yorobawan?su suna da gata iyayen su nada hali koh basuje makaranta ba, rayuwa bazata musu tsami irin naka ba, Amatsayin ka na maraya ka rike maraicin ka kayi karatu ka samu na tallafawa rayuwar ka damu duka, in bakayi karatuba ka samu madogara wazai zamo gatan mu nida yar uwarka nabeel? jin kalar fad'arda akema nabeel yasa Su fita a sulale suka bar gidan, suna fita kallon Ade lahab yayi"Adewale menene tsakaninka da mubeena Addar Nabeel"? shuru ade yayi sai kuma ya ce ba kome. cin serious lahab yayi, karka fara karka kuskura duk rashin jin mu baikai nan ba, koh zamuyi iskanci banda Ahlin mu a ciki, dangin nabeel tamkar nawa nake ganinsu kuma bazanso wani abin ya samesu ba, haka naka dangin bazan yarda a tuzartasu ba, don haka karka kuskura ka bari nabeel yaga irin abinda kayin nan, don Wallahi nasan karshen relationship naku yazo karshe kenan, kadaisan halinsa"? Promise u hakan bazai kara faruwa ba, amma fa bada niya nayi ba kawai abinda tamin ne banji dadi ba? "sai kuma aka.......shuru lahab yayi bai karasa ba ganin nabeel ya fitoh daga gidan fuska a hade. Ade ne ya kallesa toh ina dumemen(dumame)yake koh bazaka fito mana dashi bane? daga lahab har Ade dariya suka sake tuno Yanda abokin nasu ya tsane dumamen tuwo. kallon banza ya musu ya kama tafiyar sa, da sauri sukabi bayansa ganin ya nufi gangaren layinsu, " kai nabeel ina zakane"? kamar bazai amsa ba sai kuma yace, shago "wani shagon"? shagon dinki mana da mamaki lahab da Ade sukace shagon dinki?har suna had'a baki, don rabon nabeel da shago ai an kwana biyu duk da ya iyya dinki, Amma fa banda had'a kura babu abinda ya iyya inya kakkarba kayan mutane sai ya daina zuwa shago" Amma dai yau mafarki kayi wata zata karka akan kudinta koh"? kallon Lahab yayi sai kuma yayi murmushi kawai hade dacewa, kun manta kudin jesen jiya da mukayi daku zamu saya. "eh mun tuna" toh shiyasa yau zanje shago tunda mun fasa shiga school in naga koh Allah zaisa na samu kafun yamma. amma Nabeel taya zaka samu 10k a rana d'aya kuma a d'inki gaskiya da wuya. lahab kam baice kome ba jin Amsar da Ade ya bawa nabeel yasa sa ciro 11k innan a Aljuhunsa mikawa Abokin nasa kudin yayi, "gashi 11k ne ka d'auki dubu goma kuje da Ade kusai jese shima kudinsa na hannunsa 1k in ku hau transport" da mamaki Ade ke kallon lahab daman haka kullum yake mundin D'ayansu baida abu tsakanin shi da Nabeel haka lahab zai d'au nasa ya basu, toh yanzun kai ina zaka? da sauri Nabeel ma ya jefo masa tambayar sa shima, toh lahab inna karbi kudin nan kai kuma ka saya dame? "kallonsu yayi toh tambayar wa zan fara amsawa a cikin ku"? dukan mu suka basa amsa. " toh gidan mamina zanje koh zaku rakani ne"? da sauri sukce Ah ah ok toh sai kuma maganar kudi, ina da wasu kuje kawai da wannan in, kai kuma Ade bani keken nan naka naje dashi a cikin 1k innan Nabeel ya saya abinci tunda bai karya ba. godiya nabeel ya masa, bai amsa ba sai harara ya dallara masa, cikin wasa yace"babu godiya a tsakanin mu Abokai ai yiwa kaine, ya karasa maganar da hawa kan keken yaja ya kara gaba, suma da ido suka bisa sai kuma suka wuce bakin titi suka tare keke napep zuwa kasuwa. lahab kam unguwan da maminsa ke aure ya nufa, unguwane mai kyaun gaske packing yayi a kofar wani tangamemen get, gidane mai kyau Amma baikai gidan su kyau ba, hannu yasa ya bubbuga get in hade da danna hon na kekensa. maigadi dake zaune a d'akinsa jin bugu ba gaggautawa yasa da sauri ya mike takalminsa ya saka cikin sassarfa ya nufi kofar, kokarin bude kofar yake hade da tambayar wanene. shuru lahab yayi baiyi magana ba, mai gadin nad'an bude kofar zai leka yaga waye ne da gudu lahab yaja keken yayi cikin gidan saura kad'an ya kade maiganin, da sauri ya basa hanya tsayawa kawai yayi yana bin lahab da ido hade da mamakin ganinsa yau don duk da baya ganesu da d'an uwansa, Amma mundin lahab yazo saiya ganesu a d'abi'a da d'an uwansa ne yana zuwa gaidashi zaifara ba kokarin kad'esa ba, komawa kawai yayi ya rufe kofar ya zaune a benchin dake gefen d'akinsa. lahab bai tsaya da keken saba har ya wuce compound na gidan sai da ya iso har bakin kofar falon in ya tsaya da kekensa, sauka yayi ya jingina keken ya haura baranda, tura kofar falon yayi koh sallama babu ya duro kansa ciki. mami dake zaune Akan kujera tana shan fruit salad ne ta bisa da ido harya karaso tsakar falon, fuska ta hade tana kallonsa, koma kayi sallama. tsayawa yayi kikam yana kallonta ganin yanda ta had'a fuska, bazaka fita bane koh yaya?ta sake maimaita wa. juyawa yayi a hankali wallahi badon bukatar sa bace ta kawosa da inya fitan nan badai ya kara shigowa ba, komawa yayi ya tsaya a bakin kofar, da karfi ya kwala sallama. Girgiza kai kawai mami tayi jin mannin hauka da lahab yake, amsawa tayi tare da bashi izinin shigowa, ba musu ya shigon, zama yayi a cikin d'aya daga cikin kujerun falon yana kallonta"ina kwana mami"? Lafiya lahab ashe ana ganin ku? "Eh mami bagani ba" Ah ah bukatar ka dai ta kawoka ba zuwan Allah Annabi bane wannan, yasu Addayiya da sauran yan uwan naka da iyaye? "Suna lafiya mami sun mace suna gaidake" kadaiji tsoron Allah wallahi taima ma babu wanda yasan kayi hanyar gidan nan, gashidai safiyar jumma'a ce kowani yaro yana makaranta war haka amma kai kana gantali da abokan shashancin nan naka? "Wallahi mami yaune na tashi kafad'ata na ciwo shiyasa Abbu yace kar naje makaranta" rufemini baki shashasha kawai Abbun kake ma karya koh sa'anka ne taya za'ace kai kullum cikin case kake, kai ba zuwa makaranta ba kai ba sana'ar baki ba bare fari, sai yawon kamar kare, da ball kai koh kishi bakaji yanda kowa ke yabon yalin d'an uwanka Rahab. Had'a fuska yayi don shi a duniya ya tsani in za'a masa fad'a ace ya kwaikwayi Rahab abin haushi yake basa. Ka had'a fuska da kyau, gaskiya na fad'a ai yaron nan ya fika hankali babu ranan jumma'a da yamma daba zaizo wajena ba ya gaidani, yanzun kai tsakani da Allah rabonka da gidan nan tun yaushe? Fuska a hade yatsungunar da kai, shuru yayi baice kome ba shidai sai Allah Allah yake kartazo ta hanasa kudin nan,"kiyi hakuri mami zanna zuwa kullum insha Allah" ALKAWARIN KA ai ba Alkawari bane sau nawa kana mini Alkawari kana karyawa, Yanzun sau nawa kanace mini xaka daina saka Addayiya surutu Amma ka daina inne? hatta jiya da Umaimah tazo gidan nan saida ta bani labarin abubuwan da kake musu a gida anya lahab zakayi hankali kuwa, shekara 18 ace mutum baisan inda ke masa ciwo ba? Shuru yayi yaki tanka mata don shi irin mutanen nan ne da holo baya damunsu sam ga rashin zuciya, koh fad'a kukayi da lahab zuwa anjima ya watsar abinsa, ya cigaba da rayuwar sa baya sakawa kansa tention. Ganin yanda yayi zuru yana sauraronta kamar radio yasa ta yin shuru kawai, tana kallonsa. Shima d'aga ido yayi ya kalleta jin ta daina fad'ar had'a ido sukayi da sauri ya sunkuyar da kai yana kaikaya gashin geyarsa"uhmm ayya mamina my only mother ki taimaka mini da 20k mana momcy"ya karasa maganar cikin Alamun a tausaya masa. Kama baki mami tayi tana kallonsa, uban me zakayi da 20k lahab? "Wallahi mami so nake na sayi wasu kayane" Kaya lahab?wani irin kayane baka dashi a gidan ku?daga na banza harda na kirki sanan kazo kace na baka kudi, badai kaya bakam kadaisan me zakayi da kudin, toh bara na fad'a maka lahab bazan baka koh sisi ba kaji na fad'a maka, bazaiyu Yayan ka yana kirana yana mini masifa ina bata ka da kudi b, a badani ba kaji na fad'a maka. Mikewa lahab yayi tunda yaji mami tace bazata bayar ba toh fa magana ya kare kenan, tafiya ya fara cikin jin ba dadi. Dawo nan lahab, ba musu ya dawo ya tsaya ka karya kuwa? "Ah ah" Toh wuce kitchen akwai abinci ka iba. Girgiza kai kawai lahab yayi alamun bazaici ba. Ina wasa da kai? "Ah ah mami" Toh karkasa na maimaita kalamaina wuce akwai abinci a kitchen ka iba kazo ka zauna kaci nasan tunda ka fito ba uniform toh nasan baka karya ba, Shiyasa nake Allah Allah muzammil ya dawo shine daidai da kai wuce ka bani waje... Wucewa yayi cikin kitchen in, bude kulanda ya gani mai kyau a zaune a kitchen in yayi plate ya d'auka ya iba, dankalin hausane soyayye da miyar tattasai sai shayi a kofi ya had'a da soyayyen kwai akai, fitowa yayi da plate da cup in a hannunsa zai zauna akan daining. Kawo abincin na gani lahab?mami tace tana kallonsa. Tsayawa yayi yana zullumi had'e da kallon plate in, dankaline da bai wuce yanka bakwai ba, sai kwai da biya kad'an. Bakaji me nace bane? "Naji mami ina zuwa na manta ban saka miya ba"yace da sauri yana komawa kitchen in karo dankalin yayi da yawa saida plate ya cika ya fito a kitchen in, ya nufo wajen da mamin ke zaune. Mika mata plate in yayi, ba tare da ta kalli plate in ba tace, zauna kaci a kusa dani na gani. Ba musu lahab ya zauna akasan cafet in, cin abincin yake cikin rashin walwala don sam basirar sa ta toshe baisan ina zai samo kudin jese ba, yana kammala ci mikewa yayi ya kai kwanukan kitchen, yana fitowa ya kama hanya zai bar falon. Kiransa mami tayi, ya Amsa yana kallonta, wuce kitchen kaje ka wanke mini kwanukan da sukayi datti oya. "Wanke wanke kuma mami?ni ina na wani iyya wanke wanke don Allah fa" Toh yau kai zaka mini koh baka iyya ba ka koya. "Amma dai mami gaskiya ni kuma, ina yan aikin naki toh"? Oho wuce kitchen ka bani waje, ba musu ya shiga kitchen in, zaman sa yayi ya zaro wayarsa yana chatting abinsa. Mami dake falo kamar tasan abinda yake aikatawa mikewa tayi da saurinta ta nufi kitchen in, tana tura kofar da sauri ya mike tsaye yana kokarin boye wayar, amma ina tuni harta raftosa, ban wayar nan?tace tana mika masa hannu. Ba musu ya mika mata wayar, nuna masa kwanukan tayi da hannu wanke. Zare rigan saman shirt nasa yayi ya soma wanke kwanukan, shiyasa bayason zuwa gidan ta akwai matsawa mutum, a haka ya ringa wanke kwanuka harya gama haka mami tasaka sa sake wankewa wai bai fita ba. Yana gamawa haka tasaka sa aikace aikacen kitchen, tana girki yana mika mata kayayyaki har suka gama abincin rana tare, lokacin kusan 12:00 saura na rana, Abincin ma kinci yayi gashi duk kaurin girki yake. Wanka yayi a d'akin kaninsa mahraz, bayan ya fito d'aure da towel, bude wardrop in yayi yana duba kayanda zai saka don bazai iyya maimaita kaya mai datti a jikinsa ba bayan yayi wanka, rasa ma kayanda zai d'auka yayi don duk kayan sun masa kad'an, daker ya samo wata jallabiya fara sol ya zura sai wando baki pencil dayabi jikinsa ya kwanta irin roba-roban nan ne. Turare kawai ya fisa ya fita a d'akin falon ya shiga zuwa lokacin mami ma har tayi wanka tana zaune akan siter. Baiyi mata magana bama kofa kawai ya nufa itama in batayi magana ba, harya fita baranda sai kuma ya dawo tsayawa yayi a gefe ba walwala yace"mami a bani wayan" Mara kunya aida wuceni kayi, don haka koma ka sako hula a kan shegen gashin kan nan naka. Baison magana kawai juyawa yayi ya koma ya d'auko hula ya saka akan sa, fitowa yayi ya tsaya ba tare daya ce kome ba, wayar ta mika masa. "Hannu yasa ya amshi wayar hade da kallon mamin nasa"ayya mami kitaimaka mini mana mami na ki bani koh 10k ne don Allah"? Wuce mini daga gani in abin arziki zaka saya zan baka Amma banda na shirme. "Don Allah mamina kiyi hakuri na tuba alalubo abani" Lahab bazan bayar ba kaji koh nace bazan bayarba.....shuru mami tayi jin an turo kofar falon. Wani d'an dattijo ne ya bude kofar sanye yake da suit baki, sai yara dake binsa a baya sanye da uniform su uku da gudu suka rugo cikin falon ganin lahab da sauri suka rungumesa suna oyoyo yaya Rahab, don su sam d'auka sukai akan Rahab ne ganin yau shigen mutunci ne a jikinsa. Da dauri ya turesu a jikinsa cikin masifa yace "don Allah ku matsamin a jiki karku batamin farin kaya. Da mamaki yaran ke kallonsa suna mamakin meya faru da yaya Rahab donsu basu kawo lahab bane. Kallonsa dattijon yayi, ah ah Rahab yau ziyaran jumma'ar da wuri akazo mana kenan, aiko saika jiramu mu tafi tare koh? Kauda fuska lahab yayi ya nufi kofa baice kome ba. Kwala masa kira mami tayi lahab dawo nan........... Pls subscribe https://youtube.com/channel/UCsYHQSbZF_5kKSbjvZTYXHg πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€ πŸ€ΉπŸΏβ€β™‚οΈ *ALKAWARIN MASOYA* πŸ€ΉπŸ»β€β™€οΈ ~ Na ~ πŸƒ *Rukayya Ibrahim*πŸƒ Free page🀧 *EXQUISITE WRITER'S FARUM* page 7⃣&8⃣ Ba musu lahab ya dawo ya tsaya cikin had'a fuska yake kallon kannen nasa dake gefe sunyi xuru suna kallon sa. Lahab waye wannan?mami ta tambaye sa tana nuna masa Dattijon. Kallon mutumin lahab yayi sai kuma yace"dadyn su mahraz ne" Eyeee watoh dadyn su mahraz kai ba dadyn kaba kenan koh?shiyasa dake kallosa kamar banza?anya lahab kana da tunani kuwa mahraz ba kaninka bane koh bani na haifesa a cikina ba dabaza girmama ubansa ba? Shuru kawai yayi baice kome ba. Gaidashi lahab? Ba musu lahab ya dubi dattijon"ina wuni Dady"? Lafiya lahab yasu Yayan naka da d'an uwanka, kwana biyu kayi mana retaya baka zuwa? "Lafiyan su klau dady"yace sai kuma yayi shuru baice kome ba. Mahraz dake gefe zaikai shekara 13 tun d'azun sai kallon Lahab yake tunda yaji momy tace ba Rahab bane yaja gefe ya tsaya abinsa gudun karyasha duka a banza. Sai kayi tafiyarka ai koh na rike ka ne? "Bai bawa mami amsa ba kawai ya juya zai fita sai kuma ya sake kallon mamin yanzun mami bazaki bani ba"? Mami koh Amsa masa bata sake yiba,tayi shuru abinta,dady ne ya dube lahab in, mekake so lahab? Da sauri mama race,Kaga Dadyn mahraz kuwuce muje ku shirya time na gudu yaufa have day ne, kusamu ku shirya kafun a fara tafiya jumma'a. Kallon lahab dady yayi me kake so ta baka? "Kudine dady kuma tace bazata bani ba" Nawane kudin lahab? "Murmushi yayi yana kallon mami,yace 30k ne" Ok jirani ina zuwa kawai dady yace yana shigewa ciki, da mamaki mami tace lahab yaushe zaka fara tsoron Alalh ne?yanzun na karyata ka agabansa yace banason yana kyautatawa yarana,Amma lahab allah ya shiryeka. "Ameeen mamina" Ba'a jima ba saiga dady ya fito daga sashin sa,kudi ya mikawa lahab, da sauri yasa hannu ya Amshe kudin cikin murna yake masa godiya ganin kudin kamar zaifi 30k ma. Fita yayi a gidan keken sa ya d'auka, tuda mai gadi ya gansa ya fitoh da sauri ya bude get in ya basa waje ya wuce, bai fita ba saida ya kirga kudin 50k ne cipcip da murna ya soka kudin a Aljuhunsa na jallabiya, wayarsa ya duba aiko kamar yanda ya tsamma nine kusan 10 miss call na Adewale da nabeel suka kirasa bai d'auka ba, buga kekensa yayi ya kara gaba. Yana fita a get in gidan, haryayi nisa a layin kamar daga sama yaga ade da nabeel zaune a kofar wani gida su biyu dukansu sun shanja kaya alamu dai jiransa suke. Tun daga nesa da suka hangosa gabaki d'ayan su suka mike suna kallonsa ganinsa sanye da jallabiya harda hula abinda ba d'abiyarsa bace saka kaya manya ba, durun wa, kaji manyan gari nebeel yace ganin lahab ya kusa isowa kusa dasu. Da gudu lahab yayo kansu da keke ai a dari suka watse suna zaginsa shege d'an iska meye haka kaje ka wani zauna ka barmu a tsaye, munata kiran wayan ka ba'a picking, wallahi saura kad'an mu ware mu barka. "Hhhh yan iska meyasa baku shigo ciki ba, kuma uban wa yace muku ina gidan tun safe" Hh ai tunda mukaji kace xaka gidan mami nace badani ba, don nasan inkaje baka ga ta dawowa yanzun ba. "Kai nabeel baka da mutunci mamar tawa? Sorry aboki wallahi mamin kan nan nasan yau saita kare mana tanadi a gidan ta shiysa nace bazani ba. "Naji yanzun ina muka nufa" Adewale ne yace Masjid mana bayau friday ba?kuma naga time ya kusa almost 1:00 yanzun fa? "Ok yanzun ya zamuyi da keken nan don nidai sai dai na ware na barku kuhau machine" Wallahi nan ne kuma baka isa ba, sai dai mu shiga gidan su duwaisu mu aje keken in mu tafi duka a keke napep in? Ba musu lahab ya yarda suka aje keken a gidan wani abokin makarantan su, suka shige masallaci lokacin da suka iso masallacin a bakin titi suka bar adewale bakin wani shago ya zauna, yana jiran su yayin da su kuma suka wuce cikin masallacin. Bayan an idar da sallah kasuwa suka wuce, don sam nabeel da ade basu sayi jesen ba aje kudin sukayi sai lahab ya samu saisu had'a su saya tare. Jese suka sasayawa kansu kala d'aya, lahab ya had'a da socks da takalmi duka, haka suka ringa yawo basu sukayi niyar komawa gida ba sai kusan 5 na yamma, nabeel da lahab harda ade wale kowa na rike da laidan kayansa, sukabi gidan su Duwaisu suka karbo keke. Ade suka fara rakawa gida, a bakin get suka tsaya, kallon su yayi sai kuma ya mikawa nabeel kayan sa, gashi nabeel ka rike mini gobe in zamu tafi zanzo na karba? Hhh"kace dai kana tsoro"lahab yace yana dariya Shuru kawai yayi ya shige gidan da kekensa ganin motar baban sa na nufosu alamu dai dawowar sa kenan, ade na shiga gida, suma su lahab suka juya zasu tafi da sauri baban ade ya sauke glass na motar sa, hiii kuzo nan ya kirasu cikin turanci. Da sauri suka karaso inda yayi packing gai dashi sukayi bai amsa ba sai binsu da yayi da kallo idanunsa suka sauka akan lahab, kaiiii yaron nan daga ganin idanunka baka da kunya. Shuru lahab yayi baice kome ba yana jinsa ya cigaba dacewa, toh bara kuji daga yau sai yau karku sake koh da sunan wasa naji koh na ganku da yarona especially kai bakin nan,ya nuna lahab, watoh ku gaku yaran hausawa muslim zaku mayarmin da yaro irin ku ku cutar mini dashi koh?yan ta'adda toh yafi karfin ku mugaye ku wuce ku bani waje munafukai kawai? Sumui sumui suka juya suka kama hanyan layinsu gabaki d'ayansu basu sake magana ba koh gulman baban ade, don su haka suke gabaki d'ayan su suna girmama iyayen abokan su, sam don d'aya daga cikin su don iyayen su sun zage dayan su baya damun su duk da zagin da baban adewale ke musu yayi yawa harya wuce iyyaka. Gidan su nabeel suka je aje kayan sa shima lahab yayi a wajen nabeel kafun ya nufi gida. Tafiya yake hankalinsa kwance harya iso kofar gidan su, hannu yasa xai tura kofar get, sai kuma yaja da baya ganin ana kokarin bude kofar ta ciki, Abbu ne ya fitoh cikin jallabiya hannunsa rike da calbi sai yaransa dake binsa a baya harda Rahab dagani dai masallaci zasu don an fara kiran sallan mangariba, sunkuyar da kai yayi ya basu hanya. Dubesa kamar mutumin kirki, shige mu tafi masalaci, Abbu yace yana masa pointing da yatsar sa, ba musu lahab ya juya yabi bayan su. Bayan an idar da sallah haka Abbu ya sakasu a gaba suka kamo hanyar gida don masallacin baida nisa da gidan su, asalima ginin gidan su manne yake da masallacin, tun a hanya yaga yanda Rahab yayi banza dashi sai wani shamasa kamshi yake amma koh a jikinsa. Don shi harya ma manta da zancen 11k na safiya wallahi sai yanzun dayaga yanda rahab ke had'e da fuska ya tuna amma dai baice kome ba har suka shiga gida. Bude kofar lahab yayi don wannan karo shine a gaba, mamu da ummu ne zaune a falo dukan su suna sanye da hijab dagani dai sun idar da sallan mangari bane, wuce su lahab yayi, ya nufi kofar daya fitoh da safe. Tura kofar yayi ya shiga wow babban falone mai dauke da manyan kujeru na gani na fad'a sai d'akuna sama da bakwai dake falon, nufar d'aya daga cikin kofofin dake falon yayi, tura kofar yayi ya shiga d'akin da sallama. Dakine babba mai d'auke da kayyaya ki irin na samaru kan zamani, wardrop ne guda biyu sai manyan katifu guda biyu d'aya a kusurwar daki, dayan ma haka an gyara katifun sun matukar kayatu da zanin gado, sai mirrow dake d'auke da kayan kamshi irin su turare da mayuka, labuleye sun kewaye rabin d'akin, shiga yayi ya tura kofar ya rufe. Toilet direct ya nufa wanka yayi babu jimawa sai gasa ya fitoh, wardrop in ya bude wando da riga na bacci ya d'auka ya saka fisa turare yayi ya koma d'aya daga cikin katifar dake kwance akasan tiles na d'akin ya kwanta, lumshe idanunsa yayi kawai yayi shuru duk da yasan yanzun ne lokacin cin Abincin dare Amma bayaji zai iyya cin kome gaskiya. Turo kofar d'akin Akayi da sallama, bai bude idanunsa ba ya amsa. Tsayawa umaimah tayi tana kallonsa ganinsa da kayan bacci kuma a kwance, small uncle wai inji Abbu kazo muci abinci? Kallonta yayi irin kallo mai kama da hararan nan"ke kuma munafuka watoh gidan mamina kike zuwa kina kai gulma koh"? Hhh dariya ta sake da karfi tana rufe bakin ta, ashe yau gidan mami akaje shiyasa ya shareef yace min yaganka da jallabiya kum......da sauri ta kwala kara ta ruga a guje ta bar d'akin, ganin lahab ya mike harya sabi bell nasa zai nufota. Kwafa kawai yayi cikin jin haushi ya koma ya kwanta, sai kuma ya mike da sauri jakan makarantan Rahab ya bude takardunsa ya fitar English And maths ya d'auko yana dudubawa. Bude kofar d'akin akayi, Amma bai dago ya dubi waye ya shigo in ba, ji kawai yayi an fizge littafin Hannun sa, da sauri ya d'ago yana dubansa, Amma baice kome ba. Wallahi karka sake taba mini littafi lahab?daga yau sai yau tunda baka da mutunci bakasan idon sani ba harni zaka fizgewa kudi? don kaje ka kashe a banza da abokan banzan ka?in karatu kake so kaje makaranta ni ba bawanka bane. "Don Allah ya isheka haka d'an iyayi kawai zakazo kana tsayamin akai zaka mini rashin mutunci, lahab sosai ya rufe D'an uwansa da masifa, shuru kawai Rahab yayi ya koma kan katifarsa da littata fansa, Aje littatafan yayi ya d'au system yana dannawa. Tsaki lahab ya sake ya koma ya kwanta cikin bacin rai don shi ya tsani abin haushi a rayuwar sa, shi gabaki d'aya ma ya manta da zancen fad'arsu na safiya, tuni ya watsar Abinsa, kwanciya shima yayi yana kallon d'an uwansa dake rike da system haushi yakeji sosai don sam Kin saya masa akayi, aka saima d'an uwansa kome aka tashi Rahab ake bawa koh a basa abu, Amma shi ba'a masa. ************* Nnenna zaune take akan kujera, kwalli d'ayan dake falonsu,littatata fanta take dubawa Ta rasa me zatayi ga yunwa ga kewa, ita kad'anta take rayuwa a d'akinsu Babu uwa ba kawaye Babu kowa sai kulenta dake gefe a zaune,ji kawai tayi an banko kofar falon. Da sauri ta mike papane ya shigo cikin mayye Yana tangadi hannunsa rike da laida baki karami,cikin magana irin na Yan kwaya yake k'wala Mata Kira,Nnenna!! "Yes papa"tace tana toshe hanci Jin irin gasar da mahaifin nata keyi ga wari,Mika Mata laidan yayi da sauri ta karba don Wallahi yunwa takeji Tana Kai hannu ta Amshi laidan kawai ya kwararo Mata Amai a jiki da sauri ta matsa gefe tana fashewa da kuka ganin Alelen Akwai dake laidan ma ya Fadi a kasa Amai ya tabasa ga jikinta duk Amai,da kuka ta fita waje da gudu. Papa dabaya cikin Hayyacin sa kiranta kawai yake Nnenna!!Nnenna!!Ina zaki?? Kasa basa Amsa tayi da sauri ta kwabe rigan dake jikinta. Tabar vest don ita ba brz bane da ita,ruwa ta iba da sauri tayi bandaki. Tana wanka tana kuka a hakan harta kammala, ita abinda yafi Bata Takaici Abinda zataci Daya baci da Amai yafi kome Mata ciwo,falon ta shiga tana kallon Papa dake kwance Kamar macece Ga Amai a zube a gefe. Tsumma ta d'auko da ruwa ta share simintin don d'akin ba kome a kasa sai simintin kwashe Aman tayi ta rufe musu kofar falo,kulenta dake gefe a rakube ta d'aukosa hawaye na cika Mata ido, yau hakan zasu kwana da yunwa kenan. Kwanciya tayi tare da zare glass nata ta aje a gefe,kulen ta d'auka ta kwantar a gefenta,A sannu sannu har bacci ya d'auke ta. Misalin karfe 1:30am na dare,dare ya tsaga, A hankali kulen Nnenna(Kiki)ya mike daga kwance, sauka yayi akan taburmar ya girgiza jikinsa da karfe a take ya sauya Kama daga fari zuwa baki kirim, kwayar idanunsa ya sauya shima zuwa jajazur,da hanzari yayi hanyar kofar d'akin fita yayi Zuwa falo, kallon Papa yayi sai Kuma y.............. ✨Ruqeenjalal✨ πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€ πŸ€ΉπŸΏβ€β™‚οΈ *ALKAWARIN MASOYA* πŸ€ΉπŸ»β€β™€οΈ ~ Na ~ πŸƒ *Rukayya Ibrahim*πŸƒ Free page🀧 *EXQUISITE WRITER'S FARUM* page 9⃣&πŸ”Ÿ Sai kuma ya ruga yayi kofar falon ganin papa na motsi kamar xai farka, yana isa kofar kamar walkiya a take ya bace batt. Nnenna dake bacci jin wani irin sarawa da kanta yayi wanda yasata farkawa a gegece kama kan tayi gam tana Kiran jesus, ji take kamar ana tsikara mata kwakwalwa da Allura, gashi d'akin duhu don koh touch basu dashi mai kyau sai fitila shima ya mutu. Jin abin ya saketa kad'an yasa ta mikewa a hankali hannu tasa a duhun tana lalubar glass nata har Allah yasa ta gane, d'auka tayi tasa a idanunta Amma abanza don kamar yanda bata kallon kome da bata saka ba haka ma yanxun. Cire glass in kawai tayi ta lallaba ta mike tsaye da sauri ta dafe kanta jin juya mata da kan keyi, ga wani irin jiri dake dibarta, da sauri ta dafe jikin falangen d'akin nata, da babu shakka zatasha kasa. Kuka ta fara a hankali ta rarrafe zuwa kan katifar ta, kwanciya tayi sai kuma ta mika hannunta zata taba kulenta, amma bata jisa ba kiransa tayi cikin muryarta mai dadin sauraro cikin rauni"kiki!!kiki!!" Ke Nnenna bazaki mini shuru ba saikin cikamin kunne aikin banza, taji muryar papa daga falo cikin magagin bacci. Shuru tayi tana tunanin taima kulen ya chanja wajen kwanciya ne. Haka tayita fama da motsen kai har 3 na dare kafun ta samu bacci ya d'auke ta. **************** Asuban farko Lahab dake kwance a katifarsa lulube da blanket ga sanyin AC dake dukansa, ware idanunsa yayi a hankali ya yaye blanket inda ke kansa, bakinsa d'auke da Addu'an tashi daga bacci ya mike zaune. Hannu yasa a drower dake gefen katifar ya kunna hasken wayansa,zuro kafarsa yayi a kasan cafet inda ke shimfid'e a kasan tiles na d'akin, mikewa yayi tsaye a hankali hade da mika, toilet ya nufa, ya bude ya shiga kunna hasken ban d'akin yayi,brush yayi ya hada ruwan dumi ya watsa a jikinsa, Ya d'auro Alwala ya fita a bandakin. Kan katifar da d'an uwansa ke kwance ya matsa sai kuma ya koma toilet in da sauri, ruwa ya tara a buta yana zuwa yaja kafar Rahab kasan tiles ya dundula masa ruwan sanyin. Ihu Rahab ya tsake hade da salati ya mike tsaye ganin Lahab ne, ya masa wannan rashin mutunci daman ya saba masa. Tsaki kawai yayi ya juya ya wuce toilet don shi sam bai iyya fad'a irin lahab ba sai zuciya. Shimfid'a sallaya lahab yayi ya sauya kaya zuwa wando da riga, hawa sallayan yayi ya tada sallan nafila,Rahab na fitowa a daidai lokacin yajin An fara kokarin shiga masallaci hakan yasa Lahab sallamewa. Masallaci suka wuce dukansu mazan gidan, basu dawo ba sai 6:30 Abbu kam komawa bacci yayi haka yaran giyan kaf daga matan har maxa inka cire tagwaye sai ma'aikata ke zarya, Rahab zaune yake yana bitan haddansa, yayinda lahab ya sanya kayan ball wandone dogo na roba, sai riga da boot ya sanya sai towel ya rataya a wuyansa fita yayi a d'akin. Firij na falo ya bude ruwa gora d'aya ya d'auka ya nufi kofa da jogging, gudu yake a hankali harya fita a gidan su a haka ya gangara layinsu har kofar gidansu adewale. Aiko yana tsaye sanye da wandon ball guntu da riga sai takalmi alamu shima jiransa yake hannu ya bawa lahab suka kashe, tare da tambayar ya suka waye garin yau, daga nan gidansu Nabeel suka nufa da sallama suka shiga gidan. Addar nabeel ne xaune a tsakar gidan tana banbaran masara, Amsa musu tayi ba tare da ta d'aga ido ta kallesu ba, lahab ne ya wuce d'akin yayin da Adewale ya koma kofar gida ya tsaya ganin irin kallon banza da mubeena ke masa,lahab na shiga ya samu nabeel sai bacci yake koh sallan asuba bai tashi ba, Ruwa ya ibo a randan inna yazo ya kwara masa a jiki, mikewa yayi cikin masifa yake zagen lahan, shima yana ramawa, sai da yayi da gaske kafun ma suka samu yayi sallah suka fita tare. Da misalin karfe 8:00 lahab ya nufo gida jikinsa duk ya jike da gumi alamu dai dawowarsa kenan daga jogging, kofar get nasun ya bude ya wuce cikin gida, tura kofar falon yayi koh sallama babu, Rahab ne dasu munira da zulai ke karyawa cikin uniform na islamiyya yayinda rahab ke sanye da jallabiya fari da hula, su kad'ai ke zaune akan daining in, dayake Al'adan gidan su ne ranan weekend kowa na baccin safe sai su yara dake zuwa islamiyya, da ma'aikata hatta Addayiya bata tashi a weekend. Good morning uncle? Kallon xulaihat Lahab yayi kamar baxai Amsa ba Amma kuma saiya basar ya amsa mata da "lafiya " don karya yarfata, kawai ya wuce Abinsa. D'aki ya shiga direct ya wuce toilet wanka yayi ya fitoh daure da towel wando kawai ya saka dogo, yad'au waya yakira mai aikinsu, ta kawo masa Abinci. Ba'afi 5 minutes ba sai gata d'auke da tire zata kai shekara 50, da sallama ta shigo D'akin Amsa mata yayi, har gaban katifarsa taxo zata aje masa abincin. "Subhanah Gogoji lafiya kuwa"Lahab yace da mamaki ganin saura kad'an ta xubar da abincin. A sanyaye tace lafiya klau ta juya tana tafiya, harta fita A d'akin lahab kallonta yake, haka kawai yaji a ransa akwai abinda ke damunta. Abincin ya bude macaroni ne da miyar kaxa sai ruwan tie, karyawa yayi yana kamawa ya d'an xauna kad'an Abinvin ya sauka before ya kwanta abinsa, A hankali har bacci yayi Ahon gaba dashi. **************** Nnenna bata farka ba sai kusan 7 na safe dayake yau babu school share d'akinta da falo har waje tayi, tsummo karansu ta tattaro masu datti, bunu guda ta aje a waje, ta dawo falon kallon papa tayi dake xaune a kujera" good morning papa" Morning daughter? "papa abani kudi nasai omo zan mana wanki"? Ah ah daughter ina naga kudin omo yanzun sai dai ki bari gobe na baki kudin in mun dawo church sai ki wanke? Ok papa kawai tace tana mikewa tsaye. Daughter ga wannan ki dafa mana doyane da manja sai magi? Hannu tasa ta karbi laidan dake hannunsa sai doya dake gefe ta d'auka ta fita waje, kara-karan dake bola shita ibo tazo ta hura wuta dashi, d'aura tukunya tayi ta zuba ruwa tasa magi da manjan ta rufe, fere doyan tayi shima ta zuba. Bayan ta sauke girkin ta ibawa papa nasa itama ta saka nata sai kulenta dake gefe ta zuba masa nasa, zama tayi a wajen tanaci tana kallon jama'ar dake zuwa wucewa in sun ganta a zaune sai su koma, gabaki d'aya tausayin kanta da kanta take don Abincin ba dadine dashi ba, in kuma bataci ba waxai bata. Papa na karyawa yasa kafarsa ya fita a gidan, d'aki ta koma ta kwanta tama rasa me zatayi haka ta wuni har dare a d'akin sai kusan 11 papa da yadawo a buge Yau koh Abincin bata samu ya sayo mata ba haka ta kwanta. Washe gari Sunday da safe lipton ya sai musu da sugar suka sha shayi baki, Nnenna na sanyi da wani kod'aden siket iyya gwuwa da riga, sai sandal na makaranta dake kafarta don bata da Wani takalmi sai wannan, kanta babu hula sai tsifeffen gashinta dake kwance babu gyara, hannunta d'auke da bable. Papa ma sanye yake da kodeden suit nasa na gwanjo da wata kifefeyar takalmi da hula a kansa, rufe gidan sukayi zasu churchi, da gudu kulenta yataho kusa da ita ya tsaya,da masifa papa yace. Nifa na fara gajiya da wannan cat in naki ace tsawon shekara goma kina tare da Abu bai mutu ba, sanan har magana ya fara ji, I swear bazaki fita dashi ba. tsungunawa tayi tana shafasa"kiki zamuje church ka xauna a gida saina dawo", aiko kamar maijin magana haka ya koma gefe ya tsaya yana kallonsu har suka wuce, a tare suke tafiya da yarsa duk inda ta wuce sai a ringa gudu wasu su shanja hanya. Da suka isa church in ma kin bari pasto yayi Nnenna ta shiga, Papa ya buga ya buga Amma yace bazata shigo ba, karshe haka ta koma gefe da bable inta dake hannunta ta zauna, Amma duk da haka pasto nan yace sai dai ta koma bayan church ba gaba ba kartana kallon yaran mutane daga nesa. Ba musu ta koma shan bayan church ta zauna a kan wani dutse tana kuka ta rasa me yasa mutane suka tsaneta ne wai haka? Ba'a taso church ba sai 12:38 su kuma basu suka bar church in ba sai da jama'a suka watse duka wannan umurnin pasto ne. Sai kusan 1 suka kama hanya har gida yauma bata samu na rana ba sai omo da papa yasai musu na 50 ya bata ta dawo tayi wankin a gida zai wuce , saida ya jaddada mata kar taje kogi wanki, amsa masa kawai tayi da "toh"ta karbi omo tace Tana komawa gida wankin ta harhad'a gayyane guda tana tunanin ina omon hamsin zai isa Amma tuna a kogi zata wanke koh ba omo zata sa a ruwa ta cire, don basu da ruwa a gidan in kuma zatana ibowa a kogi harta cika jarakuna, Abin ya mata yawa gwara ta tafi da wankin kawai. Tattara wankin tayi ta sabi kulenta tasaka sa cikin kayan wanki ta d'aura akan ta,kogi ta nufa kamar yanda tayi tsammani hakance watoh jama'a a tare a kogin kamar me,daga masu wanki masu kama kifi, gefe daban ta samu babu kowa sai yashi mai kyau da haske juye kayan tayi a gefe , tad'au boket ta ibo ruwa ta dawo ta zauna agun tana wanki ga kulenta a gefe yana zaune. Sosai take wanke kayanta bata damu da marmatsawa da wasu masu dauraya sukayi daga gefenta ba, duk da suna da nisa da ita Amma haka suka kara marmatsawa sosai, tana cikin wanki kamar daga sama taga an tsaya a kanta. Da mamaki ta d'ago tana kallon yaran, yan matane guda hudu, katti katti irin inyamurai manyan nan gasu bakake, gabanta ne ya fadi tunawa da yaran ba mutunci bane dasu gashi a kauyen su taji papa na cewa Yan zaman gindin dutsene sai sufi wata basu dawo kauye ba. Kee kece mayyar da ake magana koh? Shuru tayi bata basu Amsa ba sai raba ido take. Haushi rashin Amsa wata taji a cikinsu, hannu kawai tasa ta kifar da ruwan omon Nnenna. Da sauri Nnenna ta tsunguna tana tsine kayanta dake cikin ruwan omon kuma sun zubar a yashi, sai da suka bari ta tsine duka ta saka a boket, sai wata ta sabi boket in da gudu ta nufi kogi. Da gudu Nnenna ma ta bita tana kuka tana bata hakuri don a cikin kayan harda school uniform nata, kuma shi kad'aine da ita tasan papa bazai taba sai mata wani ba gashi weac ma kasa biya mata yayi haka ta sake maimaita ss 3 don batason zaman gida kullum kewa na damunta shiyasa take zuwa makaranta, an koreta har an gaji an barta. Kamata sauran yara ukun sukayi tana kuka tana rokon d'ayan akan ta dawo mata da kayanta Amma ina sai da ta juye su a ruwan kogi, tana juyewa suka saketa suna dariya haka jama'an dake kogin dadi sukeji ana wulakanta ta. Da gudu tayi cikin kogin tana bin kayanta zata cire Amma ina ruwa kam sai tafiya yake da kayan ta, haka tanaji tana gani ruwa ya gudu da tufafinsu sai na papa data samo kala uku,Amma itakam na jikinta ne kawai ya rage mata. Dawowa bakin kogin tayi tana kuka ga jikinta na tsintigon ruwa, boket nata biyu dake gefe ta d'auka zata tafi, da sauri suka fizge boket in,har suka jimata ciwo da karfen boket in a hannu,d'ayan ta had'ashi da dutse a take boket in ya fashe, cikin dariya tace bake mukaji anacewa mayya ba toh mu mun fiki Hassabibanci. Kuka ta sake da karfi don ita a duniya babu abinda ke bata mata rai irin a kirata da mayya, abin na mata ciwo, hannu kawai tasa ta sabi kulenta, fizgo kulen wance ta zubar mata da kaya tayi ta wurwura kulen zata jefar a ruwa. Da karfi Nnenna tayi tsalle ta taka kirjin yarinyar da kafarta, A take yarinyar tayi wani irin zubewa a kasa saida kasan wajen ya girgiza take ta sandare babu Alamun Rai a tatare da ita......... ✨Ruqeenjalal✨ πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€ πŸ€ΉπŸΏβ€β™‚οΈ *ALKAWARIN MASOYA* πŸ€ΉπŸ»β€β™€οΈ ~ Na ~ πŸƒ *Rukayya Ibrahim*πŸƒ Free page🀧 *EXQUISITE WRITER'S FARUM* page 1⃣1⃣&1⃣2⃣ Sam yarinyar bata motse idanunta sun kakkafe a sana ga hancinta na xubar da jini, ihu jama'a suka kwala aka rufu akan yarinya. Hankalin Nnenna a tashe Don yau tasan ta shiga uku, gashi papa ya hanata xuwa Amma taki ji wai ita tabi sauki, gashi taje tasa kanta a masifa, da sauri ta sabi kulenta da ya jefo a gefe, ganin hankalin mutane baya kanta yana kan yarinyar dake kwance. Yasata banbarawa a guje jikinta sai rawa yake tunda take bata taba jawo rigima kiri kiri irin na yau ba, sai dai taga an mata Aiki Amma yau ta baiwa kanta mamaki mai girma. da gudu ta baro kogi har ta shigo cikin kauye direct gidan su ta nufa tana xuwa ta bude kofa ta mayar ta rufe jikinta na rawa tayi cikin dakin aje kulentayi ta zauna dabas a kasa ga kayan jikinta a jike. Kuka take sosai gabaki d'aya hankalinta a tashe yake ta rasa meke mata dadi yau dai tata ta kare ta shiga uku. ***************** Lahab bashi ya farka ba sai kusan 11 na rana, mikewa yayi daga kwancen ya d'auko laptop na Rahab ya kunna data, har 12 yana dakin jin muryar su rahab a falo yasa kasa mikewa da sauri ya kashe system in ya mayar ya aje. Fita yayi a d'akin ya wucesu a falo babba suna xaxxaune Ana hira, kitchen ya nufa yana bude kofar kitchen in sai kuma ya tsaya ganin gogoji mai aikin su tana duke Tana kuka. Harya karaso cikin kitchen in bata ma san ya shigoba shima dukawa yayi a tiles in kamar yanda yaga tayi, ya dafata tare da kiran sunan ta"gogoji"? Da sauri ta d'ago tana kallon lahab sai kuma da sauri ta kama goge hawayen ta da bakin dankwalin ta. "Gogoji tun da safe nasan akwai abinda ke damunki, Amma haka kika boye mini dana tambaye ki kikace lafiya, ke ba'a mai aiki na d'auke ki ba kawai a gidan nan, a matsayin uwa nake kallonki tunda nayi wayo na bude ido na ganki a gidan mu, koh zan manta da hidiman kowa wallahi baxan manta dake ba kin mana goma sha tara wanda koh mahaifiyar mu bata kula damu ba kamar yanda ke kika kula damu, don Allah ina rokon ki ki sanar dani abinda ke faruwa"? Shuru tayi tana kallon lahab sai kuma a hankali ta kamo hannunsa, lahabu bawai banason fad'a maka bane nasan halinka ne shiyasa? "Insha Allah babu abinda xai faru waye ya zageki koh wani abin aka miki"? Lahabu babu abinda aka mini a gidan nan daman yarona kuda d'aya da Allah ya bani ne yana da sikila tunda aka haifesa yake fama da jinya ba'a wata biyar sai an daura masa laidodin jini, duk Albashina a jinyansa yake karewa Kanaga dai Abinci ma na gidan nan nake ci natafi masa da nasa. "eh sai mai yafaru gogoji"?lahab ya kara tambayar ta jin tayi shuru. Shine wannan karo koh wata biyu baiyi ba daga jinya aka sake bukatar wani jinin don tun jiya yana asibiti gashi bani da wasu kudin a guna, shine nacewa Mamun ku akan tamin magana da Alhaji ina son magana dashi don Allah. Shine ta tambaye ni meyasa nakeson magana dashi saina gaya mata akan inaso ya taimake ni da kudin aikina na wata biyu zan ma d'ana jinya in ya samu lafiya saina cigaba da aikin har na gama na wata biyun ma. Shine tace wai baza'a bayar ba kuma na kuskura na gayama Alhaji a bakin aikina tunda daman ita ta d'aukeni aiki, kuma bazan tafi ba saina gama aikina nayau, ta karasa magana cikin kuka. "Ran lahab a bace yace, kenan yanzun d'anki na asibiti kikazo kina aiki kika barsa"? Don Allah Lahab karka nema mini magana kabar maganan nan kawai na yafe insha Allah zanje na samesa lafiya. "Wani irin koshin lafiya bayan kin zabi aiki sama da d'anki, taya zaki amince da abinda mamu ta fad'a bayan kinsan Imani bai wadace taba"? Don Allah lahab kayi shuru ka daina magana da karfi kar ajimu, yanzun innaje naxo na rasa aiki fa a ina zan samu wani aikin da zan tallafawa rayuwar d'ana? "ki tashi ki fita a gidan nan ki jirani a kofar gidan su adewale ina zuwa"ya karasa maganar da mikewa tsaye. Da sauri gogoji tace, mezakayi lahab na rokeka karka jawowa kanka wani rigimar kuma? kadai san mamu akwai iyya munafurci abinda bakayi bama tana kitsawa ta fadawa Alhaji bare kayi. "Karki damu gogoji kedai ki jirani kawai ina zuwa inta tambaye ki ina zaki kice Kiranki akayi daga asibiti jikin yaronki ya tashi kuma karki kuskura ki tsaya koh tana miki magana ne, muje oya"yace yana kama hannunta suka fita a kitchen in, bayan ya kashe gas data ke girki dashi.. Bai saketa ba saita suka zo mahaden falo ya sake mata hannu tare da nuna mata hanya ba tare da yayi magana ba, itama ba musu ta d'auki hIJAB nata ta wuce falon. Shikam sashin su Mamu ya wuce tura kofar sashen yayi a hankali yana bin koh ina da kallo tsarin gininsu ba irin nasu bane duk da suna flat d'aya, amma an tsara musu bangaren su, kofofine guda uku a falon tura kofar mamu yayi ya shiga ciki. Bincike ya fara mata daga akwati har wardrobe, drower koh ina sai da ya bincika amma ina shuru bai samu koh sisi ba zagin mamu yake a ransa na mako irin nata ita kullum saidai ta samu a jikin Abbu amma baxata ci nata ba. Jakan hand-back nata ya d'auka ya bude ATM ya gani har guda uku, zaban master card nata yayi ya soka a Aljuhu tunawa da yayi ranan ta aiki Rahab bank dashi, kuma yaji Rahab na tambayar ta ta waya menene pin in ATM in a lokacin suna d'aki. Da sauri ya fita a d'akin maimakon yabi hanyar falo babba, sai yabi baya wata kofar ya fita a falon su mamu, sai ya bi kofar lambu ya fita a flat in ta baya, ya zagoyo ya fita ta get da sauri ya nufi gangaren layinsu har kofar su Adewale, aiko gogoji na tsaye tana jiran sa. "Gogoji muje koh"?. Ina xamuje Lahab? "Kekam muje mana bakin yiwa mamu sallama ba"? Eh na mata sallama dayake ma Alhaji na falon bata tambaye ni ina zanje ba, danace mata zan koma gida tace ba damuwa. "ok muje to"ba musu ta bisa har suka tsallake titin unguwan nasu sai da suka iso wani shagon POS, mika ATM in yayi tare da fadar Pin in yace kuma a cire masa dubu dari uku a ciki. Ba musu masu Pos suka cire masa kudin dakad'an kadan har suka gama a take ya mikawa gogoji, data sake baki tana kallonsa dubu 150k"gashi gogoji ki masa jinya karki sake dawowa har sai yaji sauki in ma kin dawo ta koreki sauran changen ki kama sana'a dashi Allah ya basa lafiya" Kuka ta sake Ah ah lahab Aina ka samu kudin nan, dakake bani karfa kaje kasa kanka a rigima nasan halinka? "Ba wani rigima kudina ne danake tarawa duk randa aka d'auke mu ball a kasar waje sai na tafi dashi" Toh Allah yayi Albarka na gode maka Allah ya rayaku Lahab ya rage maka fitina "Kai gogoji zafa mu samu matsala dake tunda kema irin su mami zaki zama"? Ah ah d'an gidana ba'zama ayi haka ba, kaga tafiyata. "Am gogoji d'an tsaya don Allah nace ba karki fadawa kowa na baki kudi kinji"? . Toh saboda me ? "Nidai na fada miki, in ba haka ba zaki saka kanki a matsala ehen" kawai yace ya juya ya kara gaba ya barta tsaye agun tana binsa da ido. Lahab bank ya wuce yasake maida sauran kudin daya cire a Account nasa, master card nata kam wurgarwa yayi a kwalben abinsa bai koma gida ba, ya wuce shagon su nabeel don yasan war haka baya gida, aiko bai samesa a shagon ba, wai Adewale yazo sun fita tare. Komawa gidan su Nabeel in yayi ya kwanta a dakin sa, bai saurare masifar inna ba kona mubeena. Bacci yayi sai kusan azahar suka dawo, anan suke sanar dashi ai sunje gidan su ance musu bayanan gashi kamar yan gidan ma neman sa suke, sai kawai suka wuce gona. "Me kuka samo a gonar"? Rakene sai yalo, Nabeel ya basa amsa "lallai fa ai gwara da banje ba yanzun ina abinda kuka sinkon yake"? Yana tsakar gida inna tace sai dai mu fitar mata dashi a gida bazataci kayan sata ba. Aiko ku tashi muje wajen audu mai rake ya saye su koh zamu samu na kashewa "allah ya sauwaka nafi karfin 10k yanzun bare wani banzan rake sai kun dawo"? Shuru sukayi suna kallon lahab tunda suka ji yace haka sunsan ya nada kudine, shiyasa ba musu suka fita su biyun suka sabi rake da tunben buhun yalo sukayi kofar gida, inna sai kutuma musu zagi take mubeena na tayata. Suma basu dawo gidan ba har yamma sai kusan 3:30, a waje suka hadu da Lahab daya fitoh masallaci, dukan su a gidan su nabeel sukayi wanka suka shanja kaya zuwa na ball inda suka saya jiya gabaki d'ayan su sanye suke da jese fari sai takalmi baki da socks na ball fari daya kai musu kusan gwuwa, wayar Lahab sai kara take Amma yaki d'agawa harsu Adewale na tambayar sa dalili Amma shuru ya musu, ya kashe ya aje a dakin nabeel Ball lahab ya rike a hannunsa suka fita a gidan, Kekenapep suka hau zuwa filin ball inda ke tsallaken unguwan su a cikin wani makarantan gwannati don ball zasuyi da yan ungwuwan. *************** Nnenna na duke a cikin daki tayi kuka harta gaji jikinta sai rawa yake, jin An banko kofar falon yasata mikewa da sauri. Nnenna !!!! Nnenna come Out? Jikinta na rawa ta fito a dakin cikin kuka tazo tayi lingdown a gabansa, had'e hanneyenta tayi tana rokonsa, Amma ina kwasheta yayi da kafa ta fadi warwar a kasa kafun ta mike ya rufeta da duka, cikin masifa yake cewa kin cuceni ada ban yarda da duk abinda za'ace mini ba akanki, saboda babu wanda ya taba kamaki kinyi kisa da hannunki sai yau zakije ki kashe yar mutane? banace miki karkije kogi ba ashe sai da kikaje, finzgota yayi ya maka da jikin gini a take bakin ta ya fashe jini ya soma dalala ga glass nata daya fadi a kasa. Cigaba da dukanta yayi, ashe kece kika kashe onyebuchi yau chukwudi ya farka yake sanar da iyayen sa ke kika ma onye Alkawarin mutuwa shegiyar yarinya duk kin sani a bala'i nayi dana sanin sanin ki wallahi a duniya kin rabani da kowa nawa. Kuka kawai Nnenna keye tana kare dukan, da gudu wata tsohowar mata ta shigo dakin nasu cikin tashin hankali tazo ta amshi Nnenna a hannun papa kallon sa tayi rai a bace tace. Mr Obinna duka bashi bane zai gyara kome kuma ina so kasan cewa yarka bata da laifi kai koda tana dashi yau bai kamata kaima ka nemi halaka taba, toh bara kaji yanxun haka yan kauye suna tinkaro gidan ka da niyar kashe yarinyar nan kai ya dace ka taimaka mata. Cikin tashin hankali papa ya daura hannu akai yana kiran jesus, sai kuma ya ruga da gudu yayi d'akin Nnenna biro da takarda ya d'auko yayi rubutu a ciki da sauri ya fitoh falon. Nnenna dake kuka a jikin matar ya mika hannu ya kamata ba tare dayayi magana ba ya nufi kofa da ita da sauri ta fizge hannunta tayi wajen kulenta dake zaune kansa a kasa kamar mutum haka ya duka, d'aukar sa tayi da sauri tabi papa a baya. Suna fita a kofar su da gudu suka kama hanya zasu bar gari koh rabin kauyen basu fitaba suka ga tawaga na binsu na matasa da mata da mazan kauye wasu na rike da sanda wasu wuka wasu jarkan petur. Gudu papa suke da Nnenna jama'a na binsu ganin suna basu wahala yasa wasu bin shunkut suka tarosu ta gaba sosai jama'a suka kewaye su, wasu mazaje majiya karfine suka tinkare Obinna(papa) suka kamasa rike sa sukayi a gefe suka bar Nnenna a fili tsaye da kule a hannunta idanunta koh glass babu kuma ba kallonsu ma take sosai ba tadai san yau suna cikin tashin hankali da ba'a saka masa rana. Tana cikin tunanin halinda yau xata kasance kawai taji ihun papa yana had'asu da jesus karsu kona masa yarinya suyi hakuri zasu bar kauyen zasu tafi a garin suyi musu gafara. Bata ma gama fahimtar kome ba taji an kamata janta sukayi tana kuka tana kome suka daureta da jikin bishiya wasu suka kwarara mata petur a jiki daga sama har kasa,Nnenna kuka ta saka tare da rimtsa idanunta gudun kar ya shigar mata ido. Kara papa ya sake ganin wani ya kunna leta tun daga nesa ya jifo mata, Amma abin mamaki wutan na faduwa a cikin petur kawai ya musu, sun gwada hakan yafi sau biyar Amma wuta yaki kamata. Wani daga cikinsu ne ya zaro sharbebeyar wuka cikin zafin rai yake cewa tunda bazaki kama da wuta ba wallahi sai nayi ajalinki jinin sister na bazaki sha bulus ba, da gudu yayi kanta baiyi wata wata ba kawai ya d'aga wukar ya burma mata, kara ta sake da karfi ganin wanda wukar ya caka shima yaron ihu ya sake hade da kama kansa ganin abinda ya aikata wa............................ ✨Ruqeenjalal✨ πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€ πŸ€ΉπŸΏβ€β™‚οΈ *ALKAWARIN MASOYA* πŸ€ΉπŸ»β€β™€οΈ ~ Na ~ πŸƒ *Rukayya Ibrahim*πŸƒ Free page🀧 *EXQUISITE WRITER'S FARUM* page1⃣3⃣&1⃣4⃣ Papane wukar ya caka a ciki ashe lokacin da wannan guy in ya tinkare Nnenna papa ya rugo da gudu unexpected ya shiga gaban Ta, wukar ya sauka a cikinsa. Ihu Nnenna ta sake da karfi a take tayi tsalle ta fizge igiyoyin dake jikinta, a take suka tsintsinke, cikin hanzari ta taro papa dake kokarin kaiwa kasa. Kuka take cikin yare take magana, pls papa karka tafi ka barni bani da kowa sai kai, me yasa baka bari An kasheni ba kai kayi rayuwar ka Meyasa??meyasa?? tana maganar tana kuka. Cikin magagen mutuwa papa ya kama hannunta yasa mata paper dake hannunsa, a hannunta cikin Azaba ya soma mata wasiya, Nnenna ke ya dace ki rayu bani ba, don ni tawa ta kare wannan Address na d'an uwa nane yabar kauyen nan shekaru da dama ki bar garin nan ki tafi wajensa, sai kuma tari ya sarke masa. Sai da ya sakaita kafun ya cigaba da magana jini na biyo bakinsa, ki rike Addininki kinga AREWA zaki tafi, zakiga abubuwan da suka sabawa Al'adun mu ki iyye bakin ki aduk inda kika tsinci kanki, kiyi hakuri da rayuwa sannan ki xamo mai kawaici domin fushin ki Ajalin wasu ne, naso na sanar dake koh da wani abune a game dake kafun nabar duniya Amma hakan baxaiyu ba lokaci na yayi, Amma nasan wata rana zaki san kome koh bajima koh ba dade, in jesus name? "Emeen papa bazaka mutu ba asibiti zan kaika" ta karasa maganar hade da kokarin kamasa ya mike tsaye, Amma ina rai yayi halinsa. Ihu ta sake da karfi sai da ya Amsa amo kuka take da karfi tana rungume da papa. Inyamuran nan basu wani ji d'ard'ar ba, suka sake yunkurin d'aureta Amma abin mamaki duk wanda ya taho gareta sai dai kawai aga yana faduwa macece yayin da ita kuma ke duke cikin tsananin bacin rai. Ganin abinda ke faruwa yasa sauran mutanen gudu sosai, kauye ya kashame da guje guje, yayin da Nnenna ke tsungune a gindin bishiyar rike da papa har lokacin kuka take tana maijin wani irin ciwo da fushi a ranta. Dafata taji anyi da sauri ta d'ago domin ganin wanda ke tsaye a kanta, tsohowar d'azun datazo ta sanar da papa za'a kasheta ne, tsaye tana hawaye, Nnenna kiyi hakuri kinji rayuwa haka take tafiya da kaddara iri iri abinda yafi miki ana shine kiji maganar Obinna kibar garin nan ki tafi inda ya turaki. D'aga mata kai Nnenna tayi tana mamakin kallon matar da take zarzar tunda aka cakama papa wuka ta koma kallo kamar kowa gashi ba glass a idanunta"bani da kudi ki dubi kayan jikina akwai petur bazan iyya tafiya a haka ba "? Ina zuwa kawai tace, ta koma cikin kauye, ba'a jima ba sai gata da kaya dogon riga ta had'a da kudi 10k ta mikawa Nnenna, gashi kisa kayan wannan kudi kiyi kudin mota. Karba Nnenna tayi sai kuma ta kara kallon matar, momy ni zan jira a binne papa dani kar abar gawansa a wulakance"? Karki damu daughter ki tafi na miki Alkawari gawan papan ki zai kwanta a mutunce? Mikewa tayi a hankali ta juya ta kama hanyar fita a kauyen gabaki d'aya, daman sun riga sunyi nisa tana kuka tana tafiya rike da kaya da kudi a hannu sai da ta kusan fita a kauyen kafun ta shanja kaya, kudin ta saka a Aljuhun rigan har lokacin warin petur take. A haka ta ringa fasa hanya zuwa lokacin At least 5 na yamma zaiyi tana fita bakin titin ta samu machine mai kafa biyu, ta tare akan tanaso ya fitar da ita zuwa tasha, shikam mai machinen haka kawai yaji shakkan ta da tsoron d'aukar ta ganin kyau inta yayi yawa karfa yaje ya d'auki Aljana gashi hanyar ba mutane. Ganin kamar bazai d'auke ta ba yasa ta zaro masa 2k ta nuna masa akan zata biyasa mundin ya kaita, inyamuri da kudi ba musu yace ta hau, harta hau machine zai ja da mamaki kawai taga kulenta a gindin machine a zaune yana kallonta ita harga Allah ta manta da zancen kulen ma tsabar tashin Hankali. Da sauri ta sauka ta ciccibesa ta hau suka ja, basu suka isa tasha ba sai 6 gashi babu mototi kowa ya tashi kudi ta biya mai machine in ta koma wani rumfa ta xauna a bakin shagunan wasu masu manja da suka kulle. Har dare ya raba tana wajen a zaune koh motsawa batayi ba har aka fara yayyafi kamar wasa aka fara zuga ruwan sama sosai tun baya samunta har ya fara tabata. Ruwa akayita jugawa har 9 na dare zuwa lokacin gabaki d'aya tashan babu kowani maluki sai ita kad'an ta kowa ya kara gaba ga sanyi ga yayyafi. Tana zaune kanta a duke sai digar da hawaye take tana tuno Abubuwan dake faruwa a rayuwar ta, wai menene laifin ta meyasa sai ita kad'ai Abubuwan nan ke faruwa da ita, avinda ke yawo a ranta kenan, jikawai tayi an haskata da touch, Amma koh d'ago kai batayi ba tanajin sahon kafar mutane, Amma hakan baisa taji koda d'an tsoro ba, don zuciyarta yanzun yariga ya kekashe duk wani tashin hankali, gani take kamar ta riga ta gama ganinsa a kauyen su, tunda har wanka da petur aka mata za'a cinna mata wuta. Kamar da wasa taga maza hudu akan ta dagani dai irin yan iskan nan ne, kama mata hannu dayan yayi cikin maganar yan kwaya yake cewa, kai baby ya haka naji kina warin petur Amma dai duk da haka bamu damu ba, zamu iyya a hakan ma. Fizge hannunta tayi kawai ta mike tsaye kulenta ta d'auka, Zata kara gaba da sauri d'ayan ya sha gabanta hannu yakai zai taba mata kirji, ai ji kawai yayi anyi sama dashi an buga a kasa ya sake kara da karfi jin kamar kafarsa ya karye, ita karan kanta a tsorace take ganin abinda ya faru duk da a duhune, tsere suka shigayi ita da yan kwayan ana rige-rige kowa gudu yake don ita ma arcewa tayi, bata tsaya ba sai gonan wani dake yankin wajen ta shiga ta kwanta a cikin ciyayi. Har asuba Nnenna idanunta biyu, yau dai idanunta sun koma kallo kamar ko wani mai lafiyar ido, sai kuma ta tsinci kanta da rashin jin bacci kwata kwata koh tashin Hankali ne yasa ta kasa baccin ne oho. **************** Lahab basu dawo daga ball ba sai kusan 6 na yamma, bai saya bin gidan su nabeel ba direct ya nufi gidan su, haka ma adewale gidan su ya shiga, da sallama ya shigo babban falon sai kuma ya saya yana bin kowa da kallo ganin gabaki d'ayan su a tsatsaye alamu dai shi ake jira ya shigo. Basarwa yayi kawai ya shigo falon irin koh a jikinsan nan ya kama hanyar bangaren su. Lahab!!!Abbu ya kira sunan sa tsayawa yayi yana kallonsa ba tare da ya Amsa ba, jin abinda Abbun ya cigaba da fad'a, Lahab ka d'auko card in Halima ka bata sannan ka fitoh mata da kudin ta? Hade fuska yayi sosai ya tamke tamau irin ba wasa a cikin nan"A gaskiya a gidan nan ana mini abinda bai kamata ba, ace ni shikenan an mai dani agola nida gidan ubana bani da sakat, yanzun rabona da cikin gidan nan tun yaushe Amma a rasa wanda za'a d'aurawa sata sai Lahab saboda an mai dani barawo"? Da sauri Addayiya ta cebe zancen ai barawon ne, koh karya aka maka baka sata? "Karki kara cema d'an uwana barawo Addayiya kikiyaye bakin ki? tayaya zakuce shiya d'auka mata abu batare da anyi bincike ba, kuma taya ma zai d'auki ATM nata Alhalin baisan pin in ba, ai sai a tuhume ni da yaranta tunda muke cire mata kudi bashi ba? Da mamaki kowa ke kallon Rahab kiri kiri Lahab xaiyi abu Amma haka xai goya masa baya kuma sun tabbatar lahab ne kad'ai xai iyya aikata abin nan. Kuka mamu ta sake da karfi tana nuna Lahab, cikin masifa take cewa, wallahi kai zaka aikata tunda naga Rashida tace mini zata tafi bayan shigan ka kitchen zuciya ta ta rayamin kaine zaka sace mini kudi? Da mamaki shareef yace mamu me kike nufi bamu gane ba? Kwashe yanda sukayi da Gogoji mamu tayi ta sanar dasu, salati abbu ya sake ya farama mamu holo akan abinda tayi da wasa da rayuwar wasu wannan ai rashin imani ne taya d'an mata na cikin Ciwo tazo a taimaka mata Amma har tana mata barazana da rasa aikin ta, aiko kyauta yaci ta baiwa gogoji tayiwa d'anta jinya, sosai fad'a ya koma kan mamu maimakon Lahab da ya baro ta. Sosai taji bakin ciki da kara tsanar Lahab a ranta fiye da da, especially da Abbu yace su shirya bayan isha'i suje su duba yaron gogoji su bata kudi tayi hidimar jinya. Lahab cikin murna ya cinna mamu ya wuce d'akin su yau koh holo bai Amsa ba, wanka yayi ya ibi abincin da Rahab ya kawo masa yaci abinsa bayan isha'i sukaje asibitin, sun samu jikin yaron da sauki, Abbu ma ya bawa gogoji kudi sosai haka ma ummu da Addayiya, tare da sanar da ita babu zancen kori a tsakanin su sun zama d'aya ai tsawon shekaru ba wasa bane. Itama bata fad'a musu Lahab ya bata kudi ba. Suna dawowa lahab ya xauna a falon su yana kallon ball, don ya manta da wayan sa a gidan su nabeel, gabaki d'aya ya tattara hankalin sa akan kallon. Anwar daya fito dakin sa sanye da rigan bacci da wando, hannu yasa ya d'auki remote ya chanja tasha zuwa news, da mamaki Lahab ke kallonsa ganin ya zauna yana wani abu isa-isa,mikewa yayi yana kallon Anwar ya mika masa hannu hade da cewa"bani remote"? Innaki baka fa sai me? "Sai kowa ma ya rasa"lahab ya basa Amsa Au haka koh toh a rasa kace koh? karamin mara kunya d'an iskan karya wallahi tarawa nake ina jiran uncle muzammil ya dawo ya mana maganin shege. "badai shege ba kace shegu, kuma inya dawo in sai me mala'ikane shi da zanji tsoron dawowar sa koh gidan ubansa ne"? Kama Baki Anwar yayi, ubansa ka zaga lallai abin naka nayi ne lahab wallahi kadaiji kunya baza'aje boko ba baza'aje arabic ba ahaka dai za'a kare "Inna kare a haka uwarka ce ta kare" Jin Amsar da lahab ya basa yasa bacin ransa karuwa akan nada, don yaji haushin abinda lahab da rahab suka ma mahaifiyar sa, da kunyatata da sukayi a gaban kishiyar ta da surkuwar ta ga yara, gashi kowa baiga laifin saba saina mamu, hannu yasa zai tsinke lahab da mari. Da sauri lahab ya cabe hannun Anwar hade da wurgarwa, da gudu ya b'anb'ara, sanin da yayi koh ya saya in zasu daku ma shine zaiji a jikinsa, shima Anwar da gudu yabisa. Gudu Lahab keyi Anwar na binsa harya nufi kofar d'akin su da sauri yasa kafa ya bangaje kofar ya shiga, cikin sauri ya maida kofar zai rufe daidai lokacin shima Anwar ya kawo kai zai shiga, buga masa kofar Lahab yayi a fuska ji kake kauuu sai salatin Anwar dake tashi da karfi yana innalilahi Lahab ya cire masa hakoriiiiiii ******************* Nnenna sai da asuba ta mike a hankali jin muryoyi na tashi a tasha, bakko mai datti ta gani a gonar d'auka tayi ta tsunduma kulenta a ciki ta fita a gonar ta nufi tashan, Abinci ta saya hade da kifi ta baiwa kulenta itakam ta kasa cin kome don mutuwar papa ya shiga jikinta bana wasa ba. Duba takardan da papa ya bata tayi wanda jiya ta cusa a Aljuhun riganta, budewa tayi tana dubawa gani tayi ya rubuta mata Gombe state da kuma unguwa da address na gida hade da sunan mutumin Coulis Appa, nunawa masu motar tayi akan tana neman motar gombe? Bata samu ba sai dai sunce ta shiga a sauke ta a wani state, ta hau wani mota ba musu ta shiga ganin wannan ya amince zai kaita don wasu mutanen koh magana ta musu sai dai suki kulata haka mai abinci ta koreta wai tana warin petur karta jaza mata masifa, wasu yarane ta roka suka sayo mata, haka motar ma tana shiga mutane suka ringa toshe hanci wasu na tufar da yawo. Ganin haka yasa driver ce mata ta sauka, kuka ta sake tana basa hakuri daker ta samu ya yarda Amma sai dai ta zauna akan injin mota daman bus ne. Ba musu haka ta zauna tana maijin azaba bad'an kad'an ba,kafun mita ya cika, karshe dai da taga za'a tada motar Kawai tace zata koma boot cikin kaya ta zauna agun bazata iyya zaman kan inji ba, da murna mutanen motan sukace ta shiga boot in, a haka akayi ta tafi sai kusan 4 aka sauke su a wani gari wanda itama batasan ina bane agun inyamuri mai motar ya had'ata da wani akan zata gombe. Tana bakke da bakkonta ta shiga motar gombe akaja suka kama hanya gabaki d'aya tayi ligis kafufunta sun kukkumbura don ita bata taba tafiya irin na yau ba, shiyasa sai zare ido take, tana kallon mutane, suma suna kallonta sauran abincin data saima kulenta yaci ya rage shitasamu ta afa a bakinta jin yunwa na shirin kasheta. Har dare suna kan hanya basu isa ba, ga dare ya fara rabuwa wasu har bacci suke Amma banda Nnenna dake zaune rungume da bakkon ta, suna gaf da shiga garin gombe, kamar daga sama sukaji karan bindiga tauuutauuutauuu sai sukaji tayan motarsu ya fashe, musulmai dake cikin motar ne suka fara Ambaton Allah, yayin da Christoti na ihu suna kiran jesus, Alamudai sun shiga riskun yan Fashiiiiiii ✨Ruqeenjalal✨ πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€ πŸ€ΉπŸΏβ€β™‚οΈ *ALKAWARIN MASOYA* πŸ€ΉπŸ»β€β™€οΈ ~ Na ~ πŸƒ *Rukayya Ibrahim*πŸƒ Free page🀧 *EXQUISITE WRITER'S FARUM* page 1⃣5⃣&1⃣6⃣ Nnenna kam jikin ta rawa ya fara ganin yanda hankalin jama'ar motar ya tashi don ita ba fahimtar kome tayi ba tadai san Tabbas akwai abinda ke faruwa. Motar ce ta tsaya a take barayin suka saitasu da bindiga tare da basu izinin fitowa daga motar, ba musu duk jama'ar motar suka fifita harda Nnenna. Ashe basu kadai aka tare ba ga mototi da yawa har biyar, kallon wata mata Nnenna tayi da mijinta da gani dai musulmai ne masu arziki matar na d'auke da ciki babba, haihuwar yau koh gobe ga mijinta a kusa da ita sai rokon barayin yake akan suyi hakuri akwai kudi a mota, Amma karsu cutar masa da mata. Wani daga cikin sune ya daga ma su Nnenna tsawa akan su kwanta, kamar sauran babu musu duk suka kwanta, mutumin kuma wani ya buga masa gindin bindiga a kafad'a. Matar ganin Halinda mijin ta ya shiga a take hankalinta ya tashi nakuda ya ballo mata sabo, Salati take sauran matan dake gefen tane suka fahimci haihuwa zatayi da sauri wata ta miki zata nufe ta ganin tana nakuda kuma a zaune. Tsawa suka kwadawa matar akan ta koma inda take mijin ma jansa akai gefe aka bar matar ita kadai tana ta fama da azaba. Caji suka fara daga mota har jikin mutane An samu wasu da kudi sai a ware su a gefe wanda ba'a samu kome agun saba Harbesa ake, Hakan yasa wasu da dama mutuwa tun ma ba'azo kansu ba suka hadeye rai suka musu. Nnenna karan kanta Hankalinta ya tashi don ta fahimce Abinda ke faruwa a wajen watoh bakin rai bakin fama, Allah sarki mai nakuda nan nata fama da wahala kowa agun saida ya tausaya mata kuma da gani haihuwar fari ce. Gaskiya Yan fashin nan basuda imani suna gani matar nan ta haihu Amma koh a jikinsu daker suka bari wata tsohowa ta yanke ma jaririya Cibi, Uban yarinyar ne ya roke Alfarmar a barsa yaga yarsa, Amma barayin nan haka suka ki. Nnenna dake gefe a kwance Wani kato yazo kanta yana lalubar ta aiko banda naira dubu uku dake hannunta bai samu kome ba, janta yayi ita da bakkon ta gefe tare da bada izinin akai masa ita ciki tunda bata da kudi dole su fanshe kaya. Kamata wasu sukayi wani yaja bakkon ya yar a take kulenta ya bayyana, Fizgo kanta Nnenna tayi da gudu ta nufi matar dake kwance cikin jini ga jaririyar a gefe dukawa tayi ta d'au jaririyan tare dama matar magana da turanci akan zata kai mata yarta har inda suke ta fad'a mata inane garin su? Da mamaki barayin da mutanen wajen suke kallon Nnenna ita kamma koh a jikinta babu Alamun tsoro koh tashin Hankali, wani daga cikin sune ya harzuka da sauri ya nufi wajen da Nnenna ke duke tana jin maganar da matar ke fad'a mata, ga jakanta purse data bata akan inta shiga gombe sai ta binciki jakan tare da bata d'ankwalin kanta ta sanya jaririyar a ciki. Ba musu ta Amsa daida lokacin barawon ya daga bindiga da karfi zai buga ma Nnenna akai cikin hanzari ta gauce ba tare da ya dame taba. "Karka kuskura ka fusatani nama mahaifina Alkawarin xan danne xuciyata karka hasalani" tace tana nuna mutumin da hannu. Hannu kawai yasa ya kwasheta da mari tau saida ta fadi a kasa daga tsungune, mikewa tayi da jaririyan a hannunta sai kuma ta daga kanta da karfi jin yana mugun sara mata. Bata dawo hayyacin taba saida taji guje gujen mutane Ana ihu ana gudu daga maza har mata ga karan harsashe kamar ruwa, d'ago kanta tayi cikin matsanan cin Nauyi tana kallo dishi-dishi kamar dai Nnennan da babu glass. Bata Ankara ba taji An kama hannunta da sauri an jata sun kama gudu Ashe wai yan sandane suka diro suke musanyan wuta da yan fashi. Tsungunawa tayi da gudu ta sabe kulenta da jinjira a haka suka ringa gudu bata masan wanene ya riketa ba, ga jaririyar sai kuka take kamar ranta zai fita dole tasa suka tsaya a wani wajen ganin sun tsira sunyi nisa da Dajin. Su biyune da bawan Allanan da zaikai shekara 40 jijiga yarinyar Nnenna kiyi Amma ina yarinya taki shuru mutumin ma ya karbeta ya jijiga Amma ina kuka take bilhakki da gaskiya abin ya kwabe musu sun rasa yaya zasuyi da ransu Ga dare ga kukan yarinya. Mutumin ne ya mike hade da cewa Nnenna bara ya dubo koh ruwane a samu a bata tunda kamar sun shigo kauyukan Gombe babu musu tace masa toh. Yana tafiya yarinya sai kuka take harda had'a gumi sosai ta bawa Nnenna tausayi tunawa da tayi ana baiwa jarirai nono yasata saurin kwantar da yarinyar a cinyanta ta sauke kulenta ta aje a gefe. Riganta ta matsar kasa kad'an hannu tasa ta zaro breast nata manya kuma tsayayu, babu wani tsoro ta kafawa yarinyar nipple a baki, jikin yarinyar har bari yake ta kama da sauri sauir take jan maman. Duk da babu kome a cikin nono babu ruwa Amma hakan baisa yarinyar ta sake ba, sai ma Nnenna da zafi ya dameta ta zare bakin nonon ta, aiko yarinyar cinyara kara tayi da karfi, Nnenna ma da sauri ta maida mata tana rumtsa ido saboda zafi. A haka har yarinyar tayi bacci mutumin bai dawo ba ita ma bata damuwa ba ta maida kirjinta ciki, tana mai tausaya ma jaririyar, sai da ta sake jimawa sosai kafun mutumin ya dawo d'auke da ruwa a tundi. Da mamaki yake tambayar Nnenna ya haka yarinyar tayi bacci, Amsa kawai ta basa da yarinyar ta gaji da kukane har tayi baccin, ruwan ta karba shima ya cire rigansa ga baiwa Nnenna tana tsomawa a ruwa tana gogewa yarinyar jiki harta gogeta ta fita kamar yanda yace tayi. A wajen suka kwana yarinyar ta farka da dare haka Nnenna ta damka mata nono a cikin duhu ba tare da mutumin ya gane ba a tunaninta batasan shikam yasan me take ba, washe gari mutumin ya fita bakin titi ya tare musu motar suka shiga har cikin gari. Tunda Nnanna ta shigo cikin gombe take bin koh ina da kallo duk da bata kallo garau Amma tana iyya gani dishi dishi, ji take kamar ta shigo sabuwar duniya gata rike da kule da jaririya ga riganta a bace kaca kaca station mutumin yace su nufa gudun matsala. Report mutumin ya shigar akan suna d'aya daga cikin matafiya da aka ma fashi daren jiya a mashigar gari, daman yan sandan sunsan da fashin, jakan hannunsa daya d'auka wanda matar ta baiwa Nnenna ya bude ID card na matar ya fitar ya baiwa yan sandan, tare da musu bayanin jaririyar. Akan su nema musu matar ga jaririyar ta a hannun su koh wani yan uwan ta kona mijinta, babu musu yan sanda suka karba aka fara bincike basu bar Station in ba saida aka samo Iyayen matar ashe ma ba boyayyu bane manyan mutane ne, karbar jaririyar su sukayi suna ta godiya, jin Abinda Nnenna tayi, wasu sai kuka suke don tun jiya hankalin su yake a tashe gashi basu san halin da yarsu da mijinta suka shiga ba, daman garin su mijin suka fitoh. Nnenna kamar tasa kuka don haka kawai taji tana son jaririyar Amma ya ta iyya haka ta basu yarsu, kakan jaririyar kudi ta baiwa Nnenna masu yawa akalla zai kai 500k kin karba tayi sai da mutumin yasa baki kafun ta karba tana musu godiya. Mutumin ya mata sallama zai tafi sai kuma ya dawo ya tsaya ganin yanda ta rike kudi a hannu sannan tana bakke da kule ta tsaya a gefen station. Tambayar ta yayi lafiya take tsaye bataza ta tafi gida ba? Kuka Nnenna ta sake cikin jimami take sanar dashi ita bakuwa ce kuma bata san kowa ba takarda kawai baban ta ya bata ta taho wajen uncle nata daga Enugu, kuma yanzun bata gani sosai, bata da glass a ido. Karban paper mutumin yayi yana dubawa sai kuma yace mata tazo suje kudin ma karba yayi yasa A Aljuhunsa ba musu ta bisa a baya, Abinci yasai mata a tsallaken titi Amma taki ci sai kulenta kawai yaci don batacin nama sam koh Abinci mai nama, ya sai mata medicated glass a wani shago ta sanya a idanunta. Keke napep mutumin ya tare musu suka hau ba musu tana ta binsa. Sunyi tafiya mai d'an nisa kafun suka iso wani unguwan talakawa har kofar wani gida sukayi packing,mutumin sauka yayi kamar d'azun ya zaro change daya saya mata abinci ya biya mai machine in tare dama Nnenna iso a cikin wani kwarmadeden gidan jan kasa....... ********************* Lahab yana d'aki a kwace bayan ya rufe kofar dakin su, yanajin lokacin da Anwar ke ihu har zuwan su Addayiya da Abbu yana cewa yaga bakin Anwar in, sai kuma yaji Rahab nace wa ashe ba hakorin sa bane yacire, bakine da Goshi ya fashe duk yanajin Ana ta hidimar Anwar har kaisa asibiti da akayi da irin zagin da Mamu da Addayiya keyi Amma koh a jikinsa kofar ya sama kwado. Ranan Rahab ma a dakin su Uxaifa ya kwana, washe gari da Asuba Lahab koh a jikinsa ya fita da asuban yaje masallaci agun ya hadu dasu Abbu Ga bakin Anwar ya sunduma gwanin tausayi, Lahab kam koh a jikinsa yayi kamar ma bai gansu ba. Daga masallaci gidan su adewale ya wuce suka fita jogging, sai 8:00pm suka dawo,gidan su nabeel ya shiga yayi wanka ya sanya kayan sa da yake bari a gidan su nabeel wata rana in yayi wanka a gidan. Adewale gida ya koma ya ibo musu abincin karyawa a kula lafiyayye suka karya daganan suka shiga gari yawo. Bashi ya dawo ba sai yamma ya kamo hanyar gida don duk rashin jin Lahab baya wuce mangariba a waje haka baya fita koh ina da dare shiyasa suke kara godewa Allah baya yawon dare iyyakar sa rana. Turo kofar falon yayi ya shiga ciki har yayi rabin falon sai kuma ya tsaya ganin mamin sa zaune a falon tana hira da Addayiya, tsayawa yayi yana kallon Addayiya da mamaki ganin yanda take washe baki, kamar ba ita ke zagin mamin su ba kullum. Mami dake kallon sa ita ma tun shigowar sa jin baiyi sallama ba yasa ta nuna masa kofa ba tare da tayi magana ba, shima baice kome ba ya koma bakin falon ya tsaya amma baiyi sallamar ba, meya tunane oho ya juya ya zagaya ta bayan ginin flat nasu, ya shigo sashen su ta d'ayan kofar falon su. D'aki ya wuce yayi wanka abinsa wando yasa 3quater sai Armless, jin an kira sallah yasasa yin Alwala ya fita masallaci ta kofar da ya shigo ana idar da sallan shagon mai Abincin tsallaken titin su ya shiga yasai abinci Agun ya zauna yace har isha'i yayi sallah ya shigo gida kamar d'azun yabi kofar baya. Kwanciyar sa yayi abinsa yana chat gabaki d'aya hankalin sa nakan wayar sa. Mami dake bakin kofar dakin hannu tasa ta tura kofar da sallama ta shigo, da sauri Lahab ya mike zaune daga kan katifar sa yana kallon mami sosai cikin sa ya duri ruwa ganin fuskar ta babu koh digon walwala. Wallahi Lahab kabi duniya a Hankali Lahab kaji tsoron bakin jama'a lahab ina rabaka da Halima da yaranta, Lahab bakama jin Abinda nake fad'a maka koh? inka ma Addayiya koh yayan ku Umar su naka ne babu yanda suka iyya,hakuri ya zamo musu dole Amma wallahi ina rabaka da Halima(mamu)da taba mata yara don baka da hankali zaka d'aukar mata kudi har 300k sannan ka buga mata fuskar yaro sai da ya kumbura, Anwar Abokin wasan kane, bafa cousin naka bane d'an yayan kane akan me zakayi wasan banza dashi. "Habba mami nifa bani na d'auka mata kudi ba, wani munafukin ne ma yaje ya sanar dake wannan sharbeben karyan"? Ungo naka?mami ta masa dakuwa. Kumbura fuska yayi "nifa mami ban d'aukar mata kudi ba" Rufe mini baki in bansan halinka bane sai na yarda baka d'auka ba, wallahi Lahab ka shiga hankalin ka ka jima yaro ciwo Amma bazaka iyya zuwa ka duba sa ba, bare ma ka basa hakuri koh neman yafiyarsa. "Kai mami" yace yana kallon ta Duka mami ta kaimai da karfi a baya ji kake domm, ihu ya sake yana sosa bayan sai kuma da sauri ya sauko a katifar. Bar kallona rasa kunya beran danga, wuce muje ka duba Anwar in kuma wallahi ka basa hakuri. Ba yanda ya iyya haka yanaji yana gani mami ta saka sa a gaba har d'akin Anwar da sallama suka shiga d'akin. Zaune yake a bakin gado ga abinci a gabansa saman center table, Amma ya kasa ci inka gansa sai ka tausaya masa kofar ta buge fuskar sa sosai ga goshi ya kumbura, Amma lahab koh a jikinsa tsayawa yayi a gefe yayin da mami ta nemi kujera dake dakin ta zauna tana kara ma Anwar ya jiki tare ba basa hakuri Akan rashin Hankali da Lahab ya masa. Murmushi kawai yayi cikin sanyin jiki yake sanar da ita babu kome, kome ya wuce wallahi sai a lokacin Lahab yaji tausayin d'an-d'an uwansa, Jin yanda yayi maganar gwanin tausaya, takowa yayi a hankali ya matsa wajen da Anwar ke zaune a bakin gado shikam tsungunawa yayi a gaban Anwar in ya kama hannunsa, Cikin wasa yace "Son Am so sorry for what uncle do it for u, nasan Abinda ke damunka kar fa'iza ta ganka haka da kumburarun lebuna koh, tace a sauke sartin biki"? Ya karasa maganar yana dariya Shima Anwar d'an dariya yayi a hankali saboda bakin sa, jin turancin da Lahab ya masa kamar wani d'an primary, kaga koh Lahab shiyasa nace ka koma makaranta turanci babu dadi. Dariya lahab yayi daman shima burinsa kenan yaga Anwar ya sake jikinsa, hira suka soma akan budurwar Anwar fa'iza, Abincin da aka kawo wa Anwar lahab ya d'auka yaja kujera ya zauna yana bawa Anwar kadan kadan A baki ganin haka yasa mami yima Anwar sallama jin mijinta yazo zasu tafi. A ranan tare Da Anwar lahab ya kwana gado d'aya, da safe ma shiya taimaka masa yayi brush harda karyawa ya basa a baki dayake bazashi Office ba, lahab ma zama yayi a dakin ya d'auko wani English novel yana karanta wa Anwar duk jaraban Mamu saida ta barsa..... ************* Nnenna na bin mutumin A baya har suka shigo cikin gidan da sallama a bakin sa. amsa masa wasu yara dake zaune a tsakar gidan sanye da uniform Suka mike da gudu suna oyoyo baba, jin Abinda yara ke cewa yasa matar gidan saurin fitowa daga bayi hannunta d'auke da buta. Fuska ba walwala take kallon mijin nata sai kuma ta kalli Nnenan dake gefe kama baki tayi hade da cewa mijin nata, kai shayibu menene haka zaka shigo gida daga kai sai wando da vest duk datti ga wata Arniya da guntun riga tana binka a baya wanan shegen kulenfa uban me yasa aka shigo mini dashi cikin gida? Girgiza kai mijin yayi yana kallon Ma'u, haba ma'u ya daga dawowa na koh waje baki bani na zauna ba baki bani ruwa koh wani abu da zansha na dawo hayyacina ba, zaki tareni da irin wa'innan xantuka, keda tun daren jiya nace miki ina hanya Amma kika ga shuru ban dawo ba, koh a jikin ki? Eh koh a jikin nawa wani abin kake tsinana mini ne da in ka dawo zan damu sannan wacece wannan tace tana nuna Nnenna. Bai bata Amsa ba sai kallon yaransa da yayi wa'inda suka sakesa da sauri suka koma kusa da Nnenna suna lakutar jikin kulenta sai kuma su ruga da gudu su koma baya suna dariya, sai kuma su sake dawowa su taba duk sun cika gidan da ihun su, daka musu tsawa ma'u tayi, kai shegu ku rufe mana baki kun cika mini kunne? Kai ma'u Allah ya shiyeki nace miki banason kina zagen yarana da shegu Amma baki ji, sanan meya hanasu zuwa makaranta har yanzun suna zaune da uniform a jiki? Tsaki ta sake hade da kallon su, kai me ya dawo daku ku fad'a masa da bakin ku? Ba musu suka sanar da baban su an koresu kudin petiA ne basu biya ba aka korosu. Girgiza kai kawai yayi don kudin kwata kwata naira 100 ne, koh wani mutum daya shi kuma yau koh sisi bai dawo dashi ba dan kudin daya tara a kudun ma gashi ya hadu da iftilahi. Kallon Nnenna yayi cikin turanci yake ce mata ta zauna bara ya ibo mata ruwa sai tayi wanka koh, gyada kai tayi ta nemi gefen dakali ta xauna shima boket ya d'auka da sauri ya nufi kofar gida. Cikin masifa ma'u tace kai shayibu ban gane ba?me nake ganin yarinyar nan ta aje min gindin ta a dakalina? Wa'iyyazu billah dake ma'u da rashin iyya magana, toh zama zatayi bakuwa ce tare muka samu iftikahin barayi a hanya? Bata da gidan yan uwane da bazata tafi ba zata biyoka gida?oh na gane watoh sabon iskanci ne kenan daka saba xa'a kawo mini har gida toh wallahi bazata zauna mini a gida ba, sai dai ka zaba koh ni koh ita, wannan daga ganinta ma karuwa ce........... . ✨Ruqeenjalal✨ πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€ πŸ€ΉπŸΏβ€β™‚οΈ *ALKAWARIN MASOYA* πŸ€ΉπŸ»β€β™€οΈ ~ Na ~ πŸƒ *Rukayya Ibrahim*πŸƒ Free page🀧 *EXQUISITE WRITER'S FARUM* page1⃣7⃣&1⃣8⃣ Juyawa shayibu yayi yana kallon ma'u, shikam Allah ya gani rashin kudi da bin umurnin Iyaye,sune silar da yake hakurin zama da ma'u Amma wannan karon zai nuna mata ikon Miji akan matar sa, Ma'u baki da hankali a gaban yaran ki babu kunya kike irin wannan magana, toh bara na gaya miki koh kibi Abinda nace koh kuma ga kofa ki tafi duk inda yafiye miki nan. Waro ido tayi tana kallon shayibu sannan ta maida kallon ta gun Nnenna dake xaune gabaki d'aya kanta a duke duk da ba Hausa takeji ba, Amma daga Kaga muhawaran da suke kasan fad'a ne, toh wallahi bara kaji xama kam daram dam, in ma burinka kenan na tafi na barmaka gidan kuji dadin iskanci toh bazan tafiba tace tana shigewa daki Abinta. Shima bai kara magana ba ya d'auki jamfansa a igiya ya saka, ya fita bai jima ba sai gasa da ruwa a boket d'aya hannun nasa d'auke da sabulu sai take Away a Abinci. Da sauri Nnenna ta mike ta karbi boket inda ke Hannun sa ta aje a gefe,nuna mata bayan gida yayi cikin turanci yace ta kai ruwan ciki ba musu takai ta aje. Yaran sa kam kulen suka tasa a gaba suka maida abin wasa,Abincin ya mikawa Nnenna yayi yace mata taci, ba musu ta karbi take Away in tana budewa da sauri yaran suka rugo zuwa inda take alamu dai suma ba karyawan sukayi ba, Aje laidan Nnenna tayi a kasa ta bude, shinkafane da miya sai nama d'aya akai da sauri ta kauda fuskar ta, iba tayi a laidan takeAway in ta mikawa kulenta sauran ta baiwa yaran Shayibu. Da mamaki yake kallon ta sai kuma ya kasa hakuri ya tambaye ta dalilin da yasa batacin duk abinda ya sai mata?girgiza kai tayi sai kuma a hankali tace masa ita batacin nama koh abinci mai nama. Da mamaki yake kallon ta sai kuma ya wuce d'akin matar sa, zani da riga ya d'auko harya fitoh da sauri ma'u ta biyosa da gudu tazo ta fizge kayan kuma tace Nnenna bazata saka mata kaya ba. Fita yayi bai jima ba sai gasa da siket da riga na gwanjo har guda hudu, ya baiwa Nnenna ta shiga wanka, Alele ya sayo mata ba musu taci ya nuna mata dakin yaransa akan ta shiga ta kwanta tunda jiya basu samu bacci ba, ba musu ta shiga ta kwanta abinta sai bacci. Bata farka ba sai kusan 3:00 na yamma nan ma masifar Ma'u ne ya farkar da ita akan bazata ci Garin kwaki ba yau ta gaji sai dai ya bata kudi ta sayo musu Shinkafa a dafa koh dafa duka ne(jalof). mikewa tayi ta fitoh a d'akin jin ma'u ta shiga ciki kallon Shayibu tayi sai kuma tace, "sir pls in zamana ne Bataso sai na tafi"? Murmushi yayi watoh mutun koh baya jin yare Allah ya basa baiwar gane abinda ke gudana, haba Nnenna bafa akan xamanki bane? "Toh akan menene sir tunda nazo kuke fad'a"? Kudi ne takeso na bata ta sai Abinci ni kuma bani dashi shiyasa kinji ki koma daki koh? "sir haba ka d'auki kudin dake hannunka kasai abinda ya dace" taya zanna taba miki kudi, badon bani dashi ba da dasafen nan ma hidimar ki duk ni zan d'auka basai na taba kudin ba? "No sir nikam na bar maka kudin ka rike a hannunka ni damuwata kawai ka kaini wajen uncle nawa"? Sosai yaji dadin girmama sa da Nnenna tayi gashi dai yarinya kirista tana da Hali mai kyau da tunani, ok kawai yace yana fita a gidan tsintsiya Nnenna ta d'auka ta share musu gidan kwanuka masu datti data gani a watse duk ta had'asu waje d'aya haka ta wanken babu omo, tana cikin wanke wanken sai ga shayibu ya dawo da laida baki ajewa yayi yana kallon Nnenna da mamaki, Daughter kece haka da aiki? "Ba kome sir is my pleasure" Ma'u ma'u yana kwalawa matar tasa dake d'aki kira, Amma tayi biris dashi koh Amsawa batayi ba gashi yaransu sun dawo makarantan Allo sunyi jigon-jigon a gefe duk yunwa na damunsu ga mangariba ya kusa. Fitowa tayi tana yamutsa fuska, gani lafiya kaketa kwalamin kira haka? Kedai kika jiyo da halinki ga shinkafan nan saiki d'aura mana da wurwuri akwai wake yaran nan yunwa sukeji? Ita wannan menene Amfaninta da bazata d'aura ba, sai ni zan daura ita kuma tana yawo da siket kai ba dankwali kana kare mata kallo, ta karasa maganar da nuna Nnenna dake xaune tana d'aureye kwanuka. Amma dai kinsan yarinyar nan yar Kudu ce koh? Abincin mu daban da nasu haka ma yanayin girkin mu sannan koh da ace ta iyya ai bai dace ki sata aiki ba bayan wanda take miki. Dakata shayibu banason maganar banza abinci ne nace bazan iyya girkawa ba. Ya miki kyau kawai yace yana wucewa madafan Gawayi ya kunna daker lokacin ana kiran sallan mangari ba ya samu ya fara kamawa, wucewa yayi zuwa masallaci da yaransa maza biyu macen ma buta ta d'auka tayi Alwala ta shimfida sallaya tana sallah. Nnenna sai kallonta take don Abin sabo ya xamo mata kauyen su babu musulmin da xaiyi sallah a sarari haka suna kallo, Asalima inka musulunta koranka ake a kauyen. Ruwan xafi ta d'aura a gaushin ganin ya kama, sai ga shayibu ya dawo tire ya d'auka yana gyaran wake yayinda Nnenna ya bata dakan barkono yaransa na gefe da kule, gabaki d'ayan su suna zaune har bayan isha'i ya gama girkin, xubawa Nnenna yayi a kwano d'aya da yaransa ya zubawa kulenta a wani tsohon kwano ya xuba nasa daban ya xubawa Ma'u nata babu kunya tazo ta d'auka tayi daki. Suna gama cin Abincin Nnenna tayi wanka yace musu su tafi daki su kwanta, suna shiga Nnenna ta tambaye yaran takardun makarantan su, firfitarwa sukayi tana ta musu lesson, tama d'ayar Assigment nata sai kusan 9 suka kwanta. Washe gari da asuba shayibu yazo ya buga musu kofa yaran sukayi Alwala sukayi sallah Nnenna wanke-wanke ta had'a shayibu yasai musu omo da yawa yaran sukayi shara shi kuma ya musu karyawan taliya dafa duka da manja. Suna karyawa yasa yaran a gaba zai kaisu makaranta, daga nan zai wuce GRA neman gidan Coulis Appa, Suna barin gidan Ma'u ta ibo kayanta masu datti dana yaranta tazo ta jugawa Nnenna a gaba hade da bata boket ta jido ruwa ta wanke musu kaya. Haka koh akayi Nnenna tayi jidon ruwa tun daga rijiyan unguwan har ta cicika randa kafun tazo ta dukufa akan daurayan harda na shayibu ma'u ta had'a saban mugunta, Nnenna ba ita ta gama Aikin ba sai kusan 5:30 lokacin ta gama wankin jikinta duk yayi tsami gashi ma'u bata bata na rana ba tanaji tana gani ta gama dafawa ta zubama yaranta da suka dawo makaranta Amma ita kaman ajalinta, ga gajiyan d'auraya. Shayibu na dawowa ya tawo mata da kyakyawar Albishir yau wuni yayi yana binciken gidan Coulis kuma ya samu a kasan GRA yake har kofar gidan yaje sai gobe in Allah ya kaimu zai kaita da safe. Nnenna murna sosai tayi ba kad'an ba har Allah Allah take gari ya waye tabar gidan nan, da dare ma Albarkacin shayibu ta samu dan tuwo ta saka a bakinta. *************** Lahab da jama'an gidan sune zaune a babban falon gidan kowa na sha'anin gaban sa, Lahab ne zaune yanacin Ferfesun kifi da tuwon gurka(akoro),a kwano d'aya shida Addayiya suke zaune a tsakar falo suna ci suna fad'a, wai Addayiya na shan miya Ah ah tana cin kifi da yawa. Sai fad'a suke yayinda abbu ke zaune a kujera yana karanta jarida sauran matan hira suke yayinda Su Anwar ke zaune da laptop a hannu munira kam Assigment nasu suke, Umaimah ne ta kalli Abbu sai kuma ta marairaice murya, Abbu Na ayya nace ba? Zare glass in idanunsa Abbu yayi yana kallon umaimah toh mamata menene fadi ina jinki? Yauwa Abbu daman Ina son a bani kudi ne xanyi abu? Wani kudi zai baki yar batalon uba, uwarki bazata baki kudin da zaki yiwa saurayin ki cefene ba sai ubanki ya baki tsabar makon uwarki, Addayiya tace cikin masifa. Hade fuska umaimah tayi, toh Addayiya ina ruwanki nasa bakin ki a ciki ne? Kul mamana banason haka yaushe kika fara zama mara kunya mamar tawa kike fadawa haka? Shuru tai sai kuma ta mike cikin fusata tayi hanyar falon su. Zo nan mamata?Abbu yace Dawowa tayi ta tsaya a gefe, ki shiga falona akan center table akwai ATM nawa ki d'auka in Allah ya kaimu gobe lafiya sai driver yaje miki kasuwan don banason yawo. Cikin murna tace thank you Abbu na. Shima dariya kawai yayi, yana kallon Rahab dake ta fama da haddansa na Alkur'ani a gefe koh shiga sabgar su baiyi hankalin sa naga abinda yake. Tsaki Addayiya tayi cikin fad'a fad'a tace kaidai ka jiyo umar da sakarwa y'ay'an ka kudi sakaka har Atn(ATM) kake basu su cire abinda sukaso batare da ka ka'ide musu ba. Kiyi hakuri Addayiya Ummu tace yayinda Mamu ta hade fuska sosai jin yanda Addayiya keta zazzaga masifa, don an baiwa Umaimah card. Kallon Lahab Addayiya tayi d'an kusan wa ka tashi ka karo mana miyan, duk kazo ka kanainaye mini abinci gashi duk ka cinye mini kifi kabar kayuka d'an kwad'ayi kawai. "Wallahi bazan karo ba wani irin na cinye kifi?Ai naga dai Abincin gidan mune kene ma zan ma gori miji ya mutu anki a koma inda aka fitoh" Nashiga uku nida gidan d'ana dan uwarka ina zanje kaida uwarka ta kasa zama daku tayi auren ta abinta, ta watsar daku badon niba ai da yanzun kun watse. "Wallahi badai mu watse ba sai dai ki watse" Ungo naka Lahab wallahi zanji maka tashi ka karo mata miyar, bana son shirme Abbu yace yana ma Lahab gargadi da yatsa, ba musu lahab ya mike da kwanon miya a hannu yana zuwa kitchen ya aje kwanon abinsa ya wuce sashen su bai karo miyar ba. Daki ya wuce abinsa yayi wanka ya chanja kaya, ya kwanta wayan sa ya d'auka ya kunna data ya shiga groups nasu na whatsApp suna hira da Abokan sa, har kusan10:00 sai da Rahab ya shigo d'akin kafun ya kashe wayar suka kwanta tare kamar kullum. Washe gari da safe yaran gidan gabaki d'ayan su sun tafi aiki wasu kuma sun tafi Office in aka cire Anwar da baiya zuwa saboda ciwon sa, Lahab ma tun safe daya karya ya fita bai dawo ba. ************** Ta bangaren Nnenna ma da safe bayan ta gama aikace aikacen gidan tayi wanka tama yaran ma'u, suka tafi makaranta tana karyawa ta cicibi kulenta ita da shayibu suka fita a gidan. Bakin titi suka nufa Nnenna na rike da laidan kayan ta, da Shayibu yasai mata jiya, Tare musu keke napep yayi suka shiga. Kwatance yama mai keken har unguwan GRA daidai kofar wani gida mai kyau sosai, amma irin gidan nan na Christian ne ba'a kewaye flat in ba gashi gidane mai kyau gidan sama da kasa gashi yasha glass na Ameniun sai shuke-shuken flowers sai karafuna da aka kewaye gidan dashi, karnuka ne manya manya kwakwance a tsakar gidan wasu na shawage. Nufo get in karfen dake rufe sukayi suna taba get in karnukan suka mike da gudu suka nufosu cikin haushi........ ************** Umaimah da kanta taje kasuwa tare da driver tayi sayayya sosai, saboda saurayin ta da zaizo yau tare da iyayen sa, za'azo tambayan Auren ta, amma sai gobe iyayen zasu shigo gidan don har bauchi suke kuma in suka iso a yau zasu sauka a hotel su huta sai gobe zasu shigo, Amma Angon yace mata zaizo wajen ta da yamma. Sayayyya tayi sosai harda wanda gobe za'a dafa musu, ba ita ta dawo ba sai 11 tana, ta tsunduma akan girkin da kanta ba ita ta kammala ba sai la'asar, wanka tayi shafshaf ta zauna ta fara tsantsara kwalliya. Lahab da suka fitoh yawo tun safe ga yunwa gidan su Adewale suka fara biyawa Amma basu shiga ciki ba gudun masifa don iyayen sa sun tsane su, gani suke duk taurin kan Adewale su lahab ke koya masa, Abinci ade yaje ibo musu Amma momin sa ta koro sa akan bazata basu ba har dashi ma baxaici ba. gidan Inna suka biya Amma basu samu ba, karshe dai gidan su lahab suka nufo don lahab baida koh sisi a hannunsa bai fita da kudi ba bare su sai abinci, suma basu da koh sisi a hannu a waje suka tsaya shi kuma ya shige cikin gidan, yana shigowa direct kitchen ya nufa. Kuloli ya gani a jere sai kamshi ke tashi bubude kulolin yayi Abinci ne mai kyau da kayatarwa a ciki, da sauri ya sabi babban kulan mai d'auke da Rice sai d'ayan kulan dake dauke da Soyayyen kaxa da miya. D'aukar guda biyu yayi da sauri ya fita a kitchen in, nufar falo yayi zai fita sukayi kicibis da zulai, da sauri ta tsaya tana kallonsa sai kuma tace uncle kulanda ka d'aukan nan fa abincin Aunty umaimah ne tama Yaya sadeeq yau xaizo. Hararan ta yayi cikin masifa yace "wallahi ki ban waje na wuce kona bangajeki yar banza mai gulman tsiya, a gidan uban wa sadeeq in ya zama yayan ki kalen dangi koh"ya karasa maganar da tureta sai da ta fadi akan 2 sita. Ihu ta sake tana kwalama umaimah kira, wayyo Aunty ga uncle lahab ya d'aukar miki kulan Abincin yaya Sadeeq, mamu kuzo kuzo zai gudu. Ai jin haka yasa umaimah rugowa a guje daman yanzun take kokarin fitowa ta tarbo sadeeq dake compound, ai da gudu ta kwala kara ta bude kofar da sauri, tana kiran mamu. Jin muryar umaimah yasa Lahab rugawa a guje da kuloli a hannunsa yayi kofar gida yayinda Sadeeq ke jingine a jikin motar sa, da sauri ya tashi tsaye daga jinginar da yayi ganin mutum ya banbaro a guje yayi kofar get, sai kuma ya juya da sauri jin muryar wance ta bisan tana had'asa da Allah ya da............... ✨Ruqeenjalal✨ πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€ πŸ€ΉπŸΏβ€β™‚οΈ *ALKAWARIN MASOYA* πŸ€ΉπŸ»β€β™€οΈ ~ Na ~ πŸƒ *Rukayya Ibrahim*πŸƒ Free page🀧 *EXQUISITE WRITER'S FARUM* page1⃣9⃣&2⃣0⃣ Akan dan Allah ya dawo, Amma ina Lahab koh juyawa baiyi ba harya fita a get, yayinda Umaimah ke tsaye a bakin baranda kamar ta hadiye zuciya ta mutu,haka ta ringaji bare ma sai yanzun da taga sadeeq gabaki d'aya ta manta yana compound ta biyo lahab. Murmushin dole ta kirkiro hade da karasa wa kusa dashi, tana tsunkuyar da kai suka gaisa irin na masoya tambayar ta yake mai ya had'ata da Rahab yau koh tsayawa baiyi sun gaisaba. Cikin yake take ce masa su shiga ciki pls,bata basa amsa ba, ba musu yabi ta a baya hanyar da suka saba zama, watoh garden xama sukayi da sauri ta turawa Rahab dake cikin gida sako akan Lahab ya d'aukar mata abincin bako ya taimaka ya fita ya sayo mata shinkafa da miya da kaza a restaurant. Yana dawowa aka juye a wani kulan, mai aiki takai musu garden, Amma cika kam Mamu da umaimah sun shaka, jira kawai yau mamu take Abbu ya dawo ayita ta kare ta gaji da hakuri da Halin Lahab. Lahab yanda ya fitoh a guje haka su nabeel suka rufa masa baya don sun sam tabbas akwai abinda ya b'aro kenan shiyasa ba tambaya, gudu yake da kuloli suma suna binsa a baya har suka shari kwana, kafun Lahab ya tsaya aje kwanukan yayi yana maida numfashi. Kai menene haka duk kabi ka d'aga mana hankali ka sakamu gudu kaman barayi? kallon sa Lahab yayi sai kuma ya kyalkyale da dariya"aiko wallahi barayin ne don sato mana abincin umaimah nayi saurayin ta zaizo ta masa delicious" Habba Lahab meyasa zaka d'aukar mata?kai shikenan kullum gidan ku ana case naka. Tsaki lahab yayi yana bude kulan shinkafan yace"don Allah rufe mini baki munafuki in zakaci kazo kaci banason munafurci" Zama koh sukayi a wajen ruwan fanfo suka tara suka wanke hannunsu, had'a miyar yayi a shinkafan ga kaji suka soma ci hankali kwance. Abinci sukaci dayake ba kad'an bane har suka rage ga kaji duka, Almajirai Lahab ya gani a bakin titi ya kirasu ya juye musu sauran Abincin. Kulan ya sab'a su Adewale suka rakasa har get na gidan su ya kwalama mai gadi kira. yana fitowa ya basa kulan ya shigar cikin gida shikam baici ta shiga gida yanzun ba. ***************** Nnenna bata gudu ba tsayawa kawai tayi tana kallon karnukan dake tinkaro ta yayinda shayibu ya ruga a guje ya koma kwanar layin ya tsaya yana kwalawa Nnenna kira akan ta gudu. Kin gudun tayi ta tsaya don ita ba tsoron kare take ba sam, abune da sun riga sun saba dasu duk da wa'innan mazajen karen, ta fahimci suna da fad'a da zafin nama. Turus suka tsaya a gabanta suna maida numfashi yanda karnuka keyi ba tare da sun mata kome ba, juyawa tayi tana kallon shayibu sai kuma ta nuna masa da yatsa akan ya tawo su shiga, ba musu ganin babu abinda yan iskan karnukan suka mata, ya karaso wajen Yana mamakin yanda kule yaga kare Amma bai wani razana ba, suma karnukan badu nuna yunwar su ba. Nnenna ne a gaba hannu tasa ta tura kofar karfen shayibu na binta a baya karnukan ma suka bisu, tsayawa Nnenna tayi a tsakar gidan tana bin koh ina da kallo wai wannan gidan ne zata xauna a ciki?koh a mafarki bata taba tsammani ba. Kofar falon shayibu ya isa yayi knocking kusan sau uku kafun suka koma gefe suka tsaya, sai da aka jima kafun sukaji ana kokarin bude kofar, ana budewa dukansu suka dubi na bakin kofar mace ce Christian budurwa a kalla zata kusa 25 sanye da zani guntu sai t-shirt koh ba'a fad'aba daga mutum ya ganta yasan yar aiki ce. Da sauri taja baya tana kallonsu suma da sauri suka gaidata, Amsawa tayi a yangace tare da tambayar su lafiya me suke bukata? Kallonta shayibu yayi cikin turanci yake ce mata ta musu iso a wajen pastor Coulis Appa wajen sa sukazo, kamar bazata ba sai binsu take da kallo, kafun ta koma ciki sai da ta jima kafun ta dawo tace musu su shigo ciki. Ba musu Nnenna tabiyo ta a baya shayibu na binsu har suka shigo falon, wow falone mai kyau d'auke da Jere na zamani kujeru da kayan Alatu daidai karfin masu gidan don baza'ace azabebben kyau ba, zama yar aikin tace suyi a falo ita kuma ta wuce kitchen. Daga Nnenna har shayibu a kasa suka zauna watoh kasan tiles, basu hau kujera ba, sai kallon falon Nnenna keyi daga ka ganta kasan bakauyiya ce. Sai da suka d'auki akalla 1 hour a zaune duk sun gaji kafun suka ji karan takalmin mutum a upstair's, Gabaki d'aya suka bi matakalar da kallo, wani mutumi ne baki d'an lukuti ga tumbi ke saukowa daga ka gansa kasan lallai irin pastotin nan ne rikako, kamar yanda suka zura masa ido shima haka ya zura musu ido yana kallonsu har ya gama saukowa musamman ma daya ga shayibu don dagani babu tambaya Annurin musulunci daban ne. Kallon Nnenna yake ganinta babu d'an kwali ga wando a jikinta na gwanjo da t-shirt sai dai basu kamata ba, hakan ya tabbatar masa ba musulma bace kuma yayi matukar mamakin kamarta kyaun nata na taban ne koh nace na musamman. Zama yayi akan kujera yayi bake-bake yana binsu da kallo da sauri shayibu ya sunkuyar da kai yana gaidashi, Amsawa yayi kamar bayaso, hade da tambayar su lafiya suke neman sa? Gyara zama shayibu yayi ya koro masa bayanin haduwar sa da Nnenna tare da takardan da ta basa tana neman d'an uwan babanta daga Enugu, rike baki yayi yana kallon Nnenna sai kuma ya nunata da yatsa, kee kece yar Obinna taya kika zama Yar Obinna dubeki fa. Kuka ne ya kwace wa Nnenna a tunanin ta koh in tazo zata samu tarba mai mutunci itama karshen wahakar ta kenan ta huta da wahalan rayuwa ashe ta gudu ne bata tsira ba. Mika hannu yayi, ku bani takardan ai zan gane rubutun Obinna duk da shekaru da dama rabona dashi Bana tunanin zan manta? Ba musu Shayibu ya zaro paper ya basa, ba musu ya karba yana bin rubutun da ido sai kuma ya d'aga kai yana kallon Nnenna, yaren Egbo ya fara mata don tabbatar wa kansa yar d'an uwan sane, tambayoyi yake mata tana basa Amsa harda tambayar ta mahaifiyar ta fa, tace masa bata san taba, amma bata sanar dashi ana mata kazafin maita ba, hade da mamakin halinsa na koh in kula da jin labarin mutuwar Obinna gashi dai ita tunda take bata taba ganinsa a kauyen suba, Amma ga kaman nin papa nan a fuskar sa. Koh godiya baima shayibu ba na kula da Nnenna da yayi jiya sai ma kwalama mai aiki kira yayi, Akan tazo ta nunawa Nnenna d'akin baki dake kasan falon, yana maganar ya haura sama abinsa, da sauri ta fito hade dama Nnenna iso suje ta kaita dakin. Mikewa shayibu yayi bayan fitan coulis hannu yasa a Aljuhu ya zaro kudin ya mikawa Nnenna girgiza kai tayi a hankali cikin dauriya tace,"Am sory sir da abinda Uncle nawa ya maka nasan bai kyauta ba, kudin nan kuma ka rike a hannunka kayi business dashi na baka rabi kudin nima ka juya mini nawa nima, wata rana in bukatar kudi ya kamani nasan gidan ka zanzo" Kin karba yayi sai da tayi da gaske kafun ya karba yana mata godiya tare da mata Alkawarin zuwa ya dubata hade da mata nasiha akan hakuri da rayuwa aduk yanda yazo mata. Rakasa tayi har kofar get in hannunta d'auke da kulenta ta dawo falon, kofar da taga mai aikin ta shiga tun d'azun gun ta nufa ta bude, dakine d'an madaidaici mai d'auke da gado daidai na mutum biyu, sai labulaye da aka zaga d'akin dashi, fita mai aikin tayi, da sauri Nnenna ta matsa jikin labulen ta kama ta yaye sai kuma ta rike baki ashe glass dake wajen nan cikinsa ne, dakin ta tan kallon unguwan baki d'aya daga dakin ta inta yaye labule, sosai taji dadin dakin koh banza zai rage mata kewa. Turo kofar akayi da sauri ta juya tana kallon mai aikin hannunta d'auke da tiren abinci aje mata tayi akan tiles tare da nuna mata wardrop dake gefe akan tasa kayanta dake laida a ciki, tare da nuna mata bayan gida da yanda zatayi amfani da kayan ciki fuska ba walwala yar aikin ke mata magana, tana gamawa ta fita daman ita Nnenna koh fuska bata sakar mata ba daman ita ba ma'abociyar fara'a bace bare ta damu. Aje kulen tayi akan gado da sauri ta bude abincin Arish ne da kwai sai bread da tie sosai taji dadi wallahi gyara zama tayi ta fara cin abincin ta har lumshe ido take don ba sabawa tayi da cin suba, daga ita har kulenta sukeci tare a kwano d'aya. Tana gama ci toilet ta shiga tsintsiya ta d'auko tazo ta share dakin ga basket a ciki ta juye sharan, wanka tayi ta gyara gadon ta kwanta abinta tana maijin dadin sauyin rayuwa data samu da fatan kasancewa cikin kwanciyan Hankali. Har dare tana d'akin bata tashi ba duk da taji tsayuwar mota a tsakar gidan don duk abinda ke faruwa a waje tana d'anji kad'an-kad'an saboda glass. Yar aikin ne ta shigo tare da sanar da Nnenna tafito ana nemanta a falo, da sauri ta mike sanye take da dogon riga d'aya daga cikin wanda shayibu ya sai mata, kofa ta nufa zata fita ai da sauri kulenta dake kwance a gadon ya mike zai bita. Da sauri ta nuna masa gadon cikin yare tace masa ya koma ya kwanta, ba musu kuma ya koma ya kwantan Abinsa kamar yanda tace, bin yar aikin tayi har falo, ji tayi zuciyar ta ya tsinke ganin mutanen dake falon, uncle Coulis ne zaune akan 3sita da wata tasha bleching ga attech akanta, sai wasu yara mata biyu dake zaune da kananun gajerun wanduna d'ayan zata kai shekara 23 sai karamar mai shekara 17, sai namijin dake zaune a 1sita daga ka gansa kaga dan iska bakin nan bakikirim irin na yan kwaya sai ido jajazur zai kai 30, daga ka gansu kaga irin shagwababun yaran nan babu kob'a, gashi tunda Nnenna ta fito yake binta da wani mayace cen kallo yana lasar baki. Rakuba tayi a gefe cikin rawan jiki take gaida matar"good Evening ma"? Amsa mata tayi hade da sanar da ita ba ma zatace ba mom yaranta ke kiranta, ta karasa maganar cikin yanga kai kawai Nnenna ta daga mata alamun taji gaida sauran yaran tayi harda uncle nata. Kallon ta Dady yayi cikin yare ya nuna mata mom, ga wife ina sunan ta chidimma Doctor ce, sai wannan ya nuna na mijin sunan sa ibraham yana karatu a kasar waje Amma yanzun ya dawo hutu, my first born. Nuna yaran matan yayi wannan sunan ta Sarah ta kusan kammala digree inta sai mai binta jennifer tana sss 3, ni kuma pastor ne, na fada miki ne don ki san mu da kyau, kuma zansa a je amin bincike a kauye kamar yanda Dr tace saboda na tabbatar dake din yar uwa tace, ganinki da nayi da muslim nan hankali na bai kwanta dake ba? Gyada kai tayi hawaye na taruwa a idanunta tsoro take ji kar yaje yaji zancen mayyace ita shima ya korata a gidan nasa, bata dawo daga tunaninta ba mom ta kalleta cikin gatse tace ke tashi kije ki jera mana abinci a daining ba zaman banza zakiyi a gidan nan ba dole yanzun na sallame Lakwanti ke ki maye gurbinsa a ayyuka, keda peace kun isa tayi na kitchen kiyi na gida. Gaskiya ne mom bazayu tana yar kauye muci mu kwanta ita ma haka ba, sarah tace tana yamutsa fuska cikin rigima, guy innan kam maida Nnenna yayi madubi sai kallonta yake yayin da jennifer taji wani irin tsanar Nnenna a ranta ganin yarinya yar kauye tazo ta fita kome da kome gata kyakkyawa, bare ma yanzun dataji dad na cewa bayan anyi bincike ya tabbtar yar obinna ce har makaranta zai saka ta. Da murna Nnenna kece masa takardun ta na gidan su pls in za'aje garin nasu a d'auko mata. Tsawa mom ta daka mata ke yar kauye dakata menaji kike cewa? ta tambaya tana nuna Nnenna, yaushe kika samu waje har zaki bada order shege ya. Sosai Nnenna ta razana don itakam harga Allah batason tsawa, nuna mata kitchen mom tayi wuce kije ki taya Peace aiki, ba musu ta mike a hankali take tafiya Ibraham sai binta yake da ido kamar tsohon maye. Tana shiga kitchen in ta tsaya tana kallon peace dake shirya Abinci a kuloli, tana gama zubawa ta bawa Nnenna umurni akan taje ta jera a daining don duk abinda ke wakana a falon tana ji, ba musu ta cicibe kulolin takai daining ta jerasu, tare da su plante suna gamawa kimtsawa, familin suka zo suka zazzauna akan daining, saving nasu peace take Amma Ibraham yace lallai sai dai Nnenna tazo ta zuba masa. Ba musu Momy tace tazo ta zuba masa matsawa tayi fuska ba walwala sam, tazo ta d'auki plate kaman yanda taga peace tayi haka itama take, zuba masa tuwon tayi da miyar naman Alade, sai kauda fuska take saboda bata koh son ganin naman. Shikam kafa yasa ta karkashin table in ya taba mata tsintsiyar kafa, sake plate in tayi jikinta na wani irin bari kamar mazari, da sauri ta juya ta dafa jikin bangon Area in kanta na wani irin sarawa kamar zai rabe biyu. Da sauri suka mimmike suna tambayar ta menene.............. ✨Ruqeenjalal✨ πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€ πŸ€ΉπŸΏβ€β™‚οΈ *ALKAWARIN MASOYA* πŸ€ΉπŸ»β€β™€οΈ ~ Na ~ πŸƒ *Rukayya Ibrahim*πŸƒ ✨Tsokaci ALKAWARIN MASOYA na kudi ne gamai bukata naira 300 ne kacal ki tuntube ni ta layin nan whatsApp only 07044407979πŸ‘Œ Free page🀧 *EXQUISITE WRITER'S FARUM* page2⃣1⃣&2⃣2⃣ Kasa Amsa musu tayi saboda tsananin ciwo da kanta keyi ga wani irin fushi dake taso mata tana kokarin dannewa. Tsawa mom ta daka mata,kee ba magana ake miki ba kin wa mutane banza? Shuru kawai Nnenna tayi jin jirin ya lafa mata yasa ta nufi barin Area in cikin damuwa, sukam da ido suka bita suna mamakin halinta na ko in kula ga had'a fuska da mannin hauka. Tura kofar d'akin ta tayi ta shiga da sauri ta zauna a bakin gado, ranta a jagule ta kwanta tare da lumshe idanunta, anya zaman nan zai mata dadi kuwa?wai itakam bazata samu farin ciki bane a rayuwar ta, shikenan bata da sukuni, wai menene a jikinta da yake rud'ar maza harsu kasa hakuri sai sun nuna maitar su a fili tayi tunanin koh in ta dawo Birni zata ga change ashe abun ba haka bane. A haka tana kwance har bacci ya d'auke ta ba tare dataci na dare ba daga ita har abin kiwon nata. ******************** Lahab kam gantali suka tafi abinsu bashi ya dawo gida ba sai yamma kamar kullum yau ma xama yayi a masallaci, agun yayi Alwala ya shiga harsu Abbu ma suka shigo suka same sa daga yanayin kallon da abbu ya masa sai da yaji cikin sa yayi kuka. Suna idar da sallah yabi bayan su har cikin gida tsaya yayi a falo yana bin falon da kallo, mamu ne zaune ita da umaimah inka gansu a lokacin kad'ai ya isa ya sanar da kai akwai matsala, tsawa abbu ya buga masa, Lahab nemi waje ka zauna. Ba musu ya nemi gefen kujera ya zauna kamar na Allah ya hade kafa waje d'aya, zama Abbu yayi haka ma su Uxaifa, saiga Addayiya ta fitoh sanye da hijab, yauwa Umaru jarabebben ya samu isowa kenan, ai tunda naji muryarka nace d'an kusan wa ya dawo, ta karasa maganar da zama a 1 sita. Hararan ta Lahab yayi da suka had'a ido Amma batace kome ba, sai maida hankalin ta da tayi a wajen abbu dake magana, wallahi wallahi lahab ka shiga taitayinka dani a gidan nan, kar kaga duk abinda kakeyi an zuba maka ido babu mai hukunta ka sai muxammil, ka d'auka koh tsoron ka akeji. kallon Abba yayi cikin hade fuska yace"toh ni me nayi koma?koh nace me aka sake kullamin"? Tsawa abbu ya kara daka masa sai da ya razana wallahi irin unexpected in nan, wallahi summa tallahi lahab ka kiyaye kanka da bacin raina zaka ga ba daidai ba randa ka kaini bango?banda rashin hankali da rashin tunani ace saurayin diyarka yazo, ta masa girki sai kazo ka sabe ka kara gaba dashi? Muna barin ka da yunwa ne a gidan nan koh me? da bazaka tambayi abinci ba saika d'auki abinda ba naka ba ina rabaka da d'aukar kayan mu a gidan nan. Kayi hakuri Abbu, Rahab yace hawaye na cika a idanunsa ji yake kamar shi yayi laifin, sabanin lahab dako a jikinsa TV kawai ya kurawa ido kamar pusta. Amma dai kai Lahabu anyi shegen gari ana maka fad'a shine zaka basa keya kana kallon d'an iskan TV? Juyawa yayi yana kallon Addayiya cikin masifa da haushi yace, "wallahi addayiya ki fita harkana nace miki koh? koh dole ne sai kin shiga abinda babu ruwan ki"? Kai na shiga!! nace na shiga!! d'an batalon uba, yanda kake baki haka zuciyar ka take. Kwarai kuwa addayiya ni wallahi inso samu ne ma kawai a mayar dashi wajen dadyn su Taimiya. Kama baki Addayiya tayi tana kallon mamu dake maganar nan, Eh lallai halima sai yanzun nasan zaman da kike da yaran nan, sai kuma ta fashe da kuka tana rufe fuska da gefen hijabi, toh wallahi bari kiji na sanar dake da kowa ma na gidan nan wallahi koh bayan raina ban yafe maka ba umar in yaran nan tagwaye suka bar gidan nan mundin ba aure koh karatu koh son ransu bane yasa su fita sai masifar Matan ka koh yaranka. Wallahi koh bayan Ran mijina bazan wufantar da amanar da ya bamu nida umar ba, ai yasan da Jafar in yace umar ya kular masa da yaransa,ta nuna mamu ke asuwa da zakice yabar gidan uban sa? ai kece ma zaice ki kara gaba, in kin manta bara na tuna miki lokacin da umaru ya tashi auren ki yar haka kike kamar kishiyar mayya. Amma dubeki yanzun kin zama buhu kici ki koshi kiyi kashi kice zaki raba zumunci, wallahi baki isa ba kai lahab tashi ka tafi abunka ka d'au abincin dan uwar ki umaimah bazaiici kayan yayan sa ba, sai ya zama zaraba toh yaci din Lahab tashi ka tafi. Mikewa Lahab yayi cikin kuri ya nufi kofa yayin da mamu taji kamar ta tona kasa ta shiga musamman ma dariyar da ummu ta sake, irin dariyar nan na jin dadi. Abbu kam sai ido, ya rasa meke damun Mamar tasa itace tayita uzzura Abinda lahab yayi, sannan yanzun tazo ta juya zance kuma, duk da abinda mamu tace bai dace ba sam shima baiji dadin abinba d'an uwa ba wasa bane. Lahab na shiga d'aki kwanciyar sa yayi koh abinci baici ba. Washe gari jafar da babban d'ansa, Taimiya suka diro tun safiya a d'akin su Anwar Taimiya ya sauka dayake duk sa'o'ine, sai abokan Abbu, tun safe su mamu ke shirye shiryen tarban baki. Sai da yamma iyayen sadeeq suka zo anyi kome a mutunce sun kawo goro da Sadaki tare da yanka sarti duka, saboda nisan dake tsakanin sun, gari ba daya ba. sonyi kome lokaci d'aya, ya rage saura kayan aure da rana, daman sadeeq da umaimah sun jima tare jira yake ta kammala karatu gashi yanzun har ta fara zana final exam nata. A Ranan ma Lahab koh wuni baiyi a gidan ba sanin da yayi mamin sa na zuwa kuma yasan tabbas tazo ta samesa zuwa school ya kamasa kenan. ***************** Nnenna dake bacci hankali kwance ji tayi kamar ana son tabata kamar da mutum a kanta don ita duk nauyin bacci muddin mutum ya tsaya akan ta tana farkawa, bude idanunta tayi da sauri yayin da ta damko hannun mutum dake kokarin kaiwa jikinta. Ware ido tayi da kyau ganin Abraham ne duke akan ta sanye yake da gajeren wando da single, wantsalowa tayi gefe tana kare jikinta, hade da masa mugun kallo. Shikam sai kara matsowa kusa da ita yake, baby ya naga kina kwana da wuta gashi koh sleeping dress babu? Mikewa tayi tsaye tare da nuna masa kofa cikin bacin rai tace," get out Abraham wallahi ka fita koh na illataka" Da mamaki yace nida gidan mu zakice zaki illata ni kina mace ina namiji har akwai wata illar data wuce nina miki? "Tabbas akwai don ni illar da zan maka na har abada ne babu sauran gani bare wata rana ka manta, fitar miki a wajen kwana naji gidan kune amma d'akin nan ance nashiga don haka fita kaban waje"tana maganar cikin fad'a fad'a tsawa tsawa. Zaro ido yayi da mamaki don shikam bai d'auka haka yarinyar take ba gashi dare ne kar tayi ajisu da sauri yayi mata magana kasa kasa, ke menene haka? "Fita"!!!!!!!!!! Da sauri ya juya ya fita, itama Nnenna mikewa tayi ta rufe kofar duk da bata iyya ba amma haka ta tura da karambani ta murd'a ki tare da zarewa ta aje a gaban katifar ta koma, zata kwanta sai kuma ta kalli makwancin kulenta, zaune yake yana kallonta alamu madai ya jima da farkawa. Wutar d'akin ta kashe ta kwanta tare da rungumar kulenta. Washe gari da misalin karfe 3 na asuba taji ana buga mata kofa da karfi ana kiran sunan ta, mikewa tayi ido duk bacci, haka ta mike zaune da lalube ta kunna hasken d'akin, key ta d'auka tana kokarin bude kofar aka bankosa ta waje, sai da ya buge mata goshi kara ta sake tana dafe wajen, kafun ma ta dawo hayyacinta taji an sake mata dundu mai zafi a baya hade da zagi. Ke yar kauye ai bacci bai kamaki ba yar wahala muna bacci kina bacci fita zakiyi ki share gidan nan tsaf, har compound kiyi mooping kiyi wanke wanke in peace ta fitoh breakfast zata had'a miki d'aurayan da zakiyi. Gyada kai kawai tayi amma batace kome ba sai bin bayan jennifer tayi har tsakar falon tsintsiya ta watso mata da sandan mooping da sauran kayan gyara, ta koma dakin ta ta kwanta, Allah ya kyauta don ta azabtar da baiwar Allah kawai ta tashi. Tsintsiyar Nnenna ta d'auka ta share falon har wajen compound unguwan tsit babu motsen kowa sai kukan karnuka ga sanyin asuba dake tashi haka Nnenna ta share gidan tas da falo, amma ta rasa ya xatayi mooping karshe ma jika musu falo tayi da ruwa tirim. Wanke-wanke tayi a kitchen lokacin gari ya fara waye wa 5:30am na asuba saiga Peace ta fito a kofar d'aken kusa dana Nnenna sanye da kayan kitchen, bin falon tayi da kallo sai kuma ta sake kallon Nnenna da kyau, ke wace irin wawo yace ya zakizo ki jika tiles haka da kumfa? Nnenna kam shuru ta mata don ta rasa me yasa take da bakin jini ne, koh ina taje bata farin jini, karban mopper in Peace tayi ta gyara tiles in falon tare da nuna mata yanda zatayi mooping in kayan falon karta narkawa kayan wuta ruwa. Tana aiki peace na girki a kitchen, tana gama aikin d'auraya peace ta lafta mata a waje,ta had'a mata da sabulu da omo ga dam a gefe na ruwa. Tun tana tsammanin gamawa da wuri har d'aurayan ya fara shiga jikin ta, wanki take tun safe tana kallon yanda yara 'yan makaranta keta wucewa daga musulmai har Christian da ma'aikata, har lokacin da Dady ya fita shima ba'a jima ba saiga momy itama ta fita aiki, jennife ma ta fitoh zata makaranta ita da sarah tana sanye da uniform a jikinta, Abraham ne karshen fita, yana fitowa wajen da Nnenna ke zaune ya nufa zama yayi a bakin barandan kamar yanda tayi, beauty kin tashi lafiya Am sorry da abinda na miki daren jiya? Kala batace masa ba sai mikewa da tayi tana shanya kaya a igiya, shima mikewar yayi sai magana yake mata yana binta Amma taki kulasa, peace dake tsaye tun d'azun a bakin falo sai binsu take da mumunan kallo especially ma Nnenna, tsaki taja da karfi wanda ya jawo hankalin su duka harda Abraham. Amma baice kome ba ya juya ya shiga motar sa yaja yabar gidan, itama wanki ta cigaba dayi sai kusan 12:00 ta gama sauran omon ta wanke kayanta kala biyu da sukayi datti daman kayan kala hudu ne, uku shayibu ya sai mata da wanda ta shigo gari dashi. Cikin gidan ta nufa a gajiye direct ta wuce kitchen don yunwa take ji sosai, peace ce tsaye tana had'a lunch, koh kallon Nnenna batayi ba itama bata wani damu ba ganin kula a rufe yasata nufar wajen ta bude farfesun kazane, rufewa tayi da sauri ta bude d'aya kwanon taga taliya ne, rufewa kawai tayi ta had'awa kanta tie a kofi sai kulenta data ibawa naman kazan kadan a kwano, ta fita a kitchen in bata damu da tsakin da peace ke bugawa ba. Tana shiga d'akin ta ajewa kulen abincin sa itama ta kama shan shayin ta, turo kofar akayi koh excuse babu, d'aga kanta tayi ganin Abraham ne yasata maida kan kasa taci gaba da abinda take. Shigowa yayi ya zauna a kujeran mirrow hannun sa rike da laidodin kaya, hiii baby yace yana murmushi. Nuna masa kofa Nnenna tayi da hannu. Da mamaki yace korina kike Nnenna? "No fita zakayi don baka nemi excuse nawa ba ka shigo" Amma ai naga gidan mune koh? "Na sani koh d'akin momy ne ya dace a nemi excuse " Ba musu ya mike ya koma bakin kofar ya nemi Izini ta basa kafun ya shigo, direct bakin gadon yazo ya zauna kusa da ita, da sauri ta matsa gefe tana hararan sa. Sorry yace yana d'aukar laidan ya aje kusa da ita, kallon laidan tayi tare da tambayar sa menene? Kayane na sai miki masu kyau da kayan amfanin ku na mata? "Bana bukata" Saboda me? "Nawa ya isheni" Amma menene laifi don Brother ya sai ma sistern sa kaya? "Toh ai kai ba brother na bane cousin ne" Amma ai duk d'aya ne koh? "Ba d'aya bane kowa da matsayin sa" Nidai kiyi hakuri d'an Allah ki karba" Kallon sa tayi sai kuma ta tuna in fa bata karba ta wata rana kaya zai gagare ta, amma bata son ta basa kofar da zai na shiga jikinta"OK thank you"tace tana d'aukar kayayyakin ta maida gefe mikewa tayi tsaye hade da ce masa zata shiga wanka. Ba damuwa ki shiga ki fita ina jiran ki kinga ma saiki gwada kayan na gani? Wani mummunan kallo da Nnenna ta masa baisan lokacin da ya mike ya bar dakin ba, yana fita da sauri ta bisa ta rufe kofa, laidodin ta bude kayan ta juye akan gado, tana dagawa tana dubawa jeas ne pencil kusan hudu sai t-shirts harda towel da brush da maclen ga shampoo duka, dasu turaru ka, tad'an ji dadi kad'an jera kayan tayi ciki wardrop harda vest da lagies. Wanka ta shiga tayi brush, tana d'aure da towel ta wanke kayan da ta cire a toilet in ta fitoh dashi a boket, mai ta shafa ta sanya wando tasa vest ta d'aura riga akai, duk wanda ya ganta yasan bata saka brz ba saboda yanayin yanda kirjinta ya fitoh sosai gashin kanta dake tufke koh warware sa batayi ba saboda wahalar kimtsawa da yake bata, boket in ta d'auka cikin jin dadin shigarta na yau don bata taba saka kaya mai kyau irin na yau ba, gashi tana jinta free ba kamar kananun siket ba koh dogon riga wannan wandone har kasa, ga silifas na roba mai flower a kafarta irin na yayin nan akalla zaikai 3k. Tana fitowa falo tayi kicibis da peace na jera kuloli a daining cikin haushi take binta da kallo itakam koh a jikinta shanya kayanta tayi a waje ta koma daki. Da yamma lilis dady da jennifer suka dawo, aiko tana dawowa haka ta ringa masifa sai Nnenna ta cire kayan jikinta bazata saka ba saida Abraham ya mata kaca kaca kafun ta natso, sai kuma tace sai Nnenna ta tattaro kayan da ta wanke ta gogesu. Haba jennifer muna da injin wanki menene nasa ta ta wanke sannan yanzun bazaki bari gobe ta goge ba sai kice yanzun. Jin abinda dady ya fad'a yasa jennifer fashewa da kuka irin na sangartatun nan a take baban sa ya rikice ya fara rarrashin ta tare da baiwa Nnenna dake gefe umurnin taje ta tattaro kayan ta goge. Mikewa tayi Abraham ya bita da kallon tausayi, taje ta tattaro shanyan dakin guga ta wuce taje ta fara goge kayan nasu daga ita sai kulenta suke zaune a ciki. Har dare tana guga karshe ma bacci ne ya d'auke ta a dakin ba tare da ta gama gugan ba. Washe gari ma da bautan ta tashi haka ta ringa rayuwa a gidan cikin bakin takura na Abraham da jennifer har gwara sarah sau dubu akan momy, ga dady baya cewa kome akan abinda suke mata. Dady Ya tura ayi bincike akan Nnenna kuma ya samo cikekken bayanai akanta da abubuwan da suka faru da ita harta gudo zuwa gombe, sosai ya shiga shock karfa da gaske mayyar ce, amma bazai iyya kin riketa ba tunda shine kad'ai nata da ya rage. Kasa fad'awa momy gaskiya yayi don yasan tabbas, zaman Nnenna bazai yuba tare dasu, sai dai ya kira Nnenna ya mata warning akan inta kuskura ya kamata da wani laifi na maita koh na illata wani zai d'auki babban mataki akanta,don nan birni ne ba kauye ba kana kashewa za'a kasheka bare suna Christian a cikin musulmai dumu dumu ta iyye bakin ta. Kuka take tana gyada kai koh banza ya taimaka mata, tunda ya amince zai rayu da ita a karkashin sa, neman Alfarmar koma wa makaranta ta nema duk da ta sanar dashi ta gama SS 3 Waec ne batayi ba amma tana son ta cigaba da zuwa har lokacin waec yayi. Ba musu yasa aka d'auko mata result nata a kauyen su, washe gari ya aike Abraham kasuwa ya sai mata kayan makaranta ya kai dinki,yasai mata sabon eye glass mai kyau da tsada, da sauran abubuwan da zata bukata akan zuwa Monday zasu kaita school a mata Interview duk ajin da ya dace a sata sai a sata, don su sun d'auka bata da kokari sosai. Jennifer kamar ta wura wuta ta shiga jin Nnenna xata shiga school inda take sosai ta haukace wa momy akan ita bata yarda ba wallahi, momy ma ta nuna akan sai dai a sata a govorment school Amma Dady yace ya gama magana. Wannan abu yama momy ciwo a karon farko dady ya bijirema bukatar ta, amma kuma tasan me zata kulla koh Nnenna ta shiga school in sai taji bata kaunar xama tare da jennifer. ************************ Lahab yau ball suka tafi tun safe bai dawo gida ba, daga ball suka je gidan su adewale da yake iyayen sa sunyi tafiya acan sukayi wanka suka saka kayan sa dukan su, suka wuce birthday party wani school mate nasu, sai yamma lilis ya nufo gida tun daga nesa ya hango sa zaune, sai da gaban sa ya fadi sanye yake da 3quater na sojoji sai t-shirt baki, yana zaune a bakin get kan kujeran roba. Ai da sauri yaja ya tsaya shikenan yau dai tashi ta kare, Amma yan gidan nan munafukai ne ace babu wanda zai sanar dashi uncle muzammil na zuwa yau, ya wuni a gida sai aki sanar dashi da yau ai ya kaima islamiyya ziyara. Ji yayi kamar ya juya Amma babu hali dole tasa ya nufi get in zuciya na duka, Amma san koh nuna alamun ya gansa ma baiyi ba, ya sa hannu zai bude kofar. Lahab!!!!!!! Muzammil ya kwala masa kira da karfin gaske. Aiji yayi kamar an tsikare ransa da tsinke, cikin sauri yace"na'am uncle daman wallahi ban ganka bane" Na tambaye kane lahab ka ganni koh baka ganni ba? "Kayi hakuri don Allah uncle" Hakurin uwar ka?ina kaje? "Uhmmm naje lesson ne gidan su adewale" Ina takardun? Kallon hannunsa yayi sai da ya hadeye yawo"uncle nabar takandun a gidan su" Gyada kai muzamminl yayi, oh watoh boko yafi Arabic kenan? "Ah ah uncle" Ok toh me kake nufi naga dai islamiyyar so biyu ake zuwa a sati kai kuma naga a karshen satin ma kaje lesson koh? "dan Allah uncle kayi hakuri"? Hakuri?meka mini ai duk abinda kayi kanka kama bani ba, ka wuce muje sallah bazaka shiga gida yanzun ba muje, yace yana nuna ma lahab hanya babu alamun wasa a fuskar sa, da sauri lahab yayi gaba muzammil na binsa a baya har bakin masallaci. Alwala yayi suka zauna har aka kira sallah kafun yan gidan su suka fito tun daga nesa suke gulman lahab suna dariya ganinsa zaune samo samo kamar na Allah. Ana idar da sallah suka shiga gidan da sauri lahab ya nufi kofar falo, tsawa muzammil ya daka masa, Lahab dawo nan ban sallame kaba? Ba musu ya dawo ya tsaya a jikin motan kaman yanda yaga uncle in yayi, bude kofar motan Muxammil yayi ya shiga hade da basa umurni ya shiga. Shiga yayi yaja motar suka nufi barin gidan, suna fita shagon aski suka nufa tunda lahab yaga anyi packing a bakin shagon yaji ransa yayi mummunan tashi ba shakka yau gashin da yake ta kashewa kudine za'a cire masa. Fita yayi a motar yabi bayan muzammil cikin shagon, sun samu layi dole tasa suka zauna har akai isha'i, sukaje sallah a masallacin bakin shagon suka dawo kafun layi yazo kansu, nuna ma mai shagon kan lahab uncle yayi tare da ce masa ya aske kan kwalkwal a cire gemu. Ihu lahab ya sake kamar an burma masa Allura"wallahi uncle ban yarba ba haka kawai a aske mini gashi kamar wani kafuri kwalkwal,kuma a cire mini gemu duka? ai gemun sunnah ne manzon Allah ne yace abar gemu. Mikewa muzammil yayi lokacin da lahab ke surutun ji kawai yayi an wanke masa fuska da mari mai azaban zafi, dafe kuncin sa yayi yana mai duban uncle in nasa, da tsananin mamaki wai shi lahab har yanzun ake duka. Kallon mai shagon yayi, aske masa kamar yanda nace, kallon uncle mai asken yayi pls oga kayi hakuri nad'an rage masa gashin sosai yayi daidai, gemun kuma a bar masa don Allah yace cikin d'ari-d'ari fahimtar da yayi ran sojane ya baci, ba tare da muzammil yayi magana ba ya basa izinin yayi hakan da hannu. Zama Lahab yayi akan kujera har lokacin hannun sa dafe da kumatun sa, mai asken ya fara aikin sa. Gashi mai tsawon nan duk an aske yayi daidai da kan nasa sai gyaran goshi da aka masa sosai askin ya masa kyau ba kad'an ba, muzammil dai sai kallon mai kaman harara yake masa. Ana gama askin suka nufo gida, bayan sun tsaya uncle ya sai gasheshen kaza kusan biyar, suna isa gidan da sauri lahab ya balle marfin motar ya nufi kofar falo, kwala masa kira Muzammil yayi akan yazo ya d'auki laidan kazan ya shigar ciki, Amma lahab koh juyawa baiyi ba kuma sarai yasan uncle yasan yajisa. Yana turo kofar falon, family ne zaune a tsakar falon ana ciye ciye harda Nazeefa matar muxammil da yaransu Tirmizi da islam, nufar kofar sashen su kawai yayi koh amsa wa matar muzammil dake masa magana baiyi ba, don daman ba shiri suke da ita ba, kamar yanda baya shiri da mijinta, dariya 'yan falon suka sake da karfi ganin kan lahab yau a aske sai gashi kad'an, don kan Rahab ma yafi nasa gashi. Yana shiga d'akin akwatin sa ya d'auka ya aje a kasa tiles, ya fara iban kaya a wardrobe yana zubawa a ciki, don Wallahi gudu zaiyi ya koma wajen yaya jafar nasa haka kawai ya zauna wannan mugun soja ya kashesa a banza bai isa ba, don wallahi mami batace masa jika ka gani ba. Turo kofar akayi da sauri ya soma boye kayan gudun kar wanda ya shigo yagani, amma ina kafun ma ya boye har an shigo, tsaki yayi ganin Rahab ne. Da sauri ya karaso kusa dashi, Lahab lafiya yana ga kana had'a kaya a jaka? Kallon biyun nasa yayi da kyau hatta magana in sunayi iri d'aya ne,"wallahi rahab bazan zauna a gidan nan ba, sai muzammil yabar sa ya wani ibo 'ya'yan sa da shegeyar matar san nan zasu zo su sani a gaba" Yanzun lahab tafiya zakayi ka barni ni kadai kenan? "Tafiya kam kaman nayi na gama babu uban da ya isa ya hanani" Sai dai in bana gidan nan?sukaji magana daga bakin kofa, da sauri lahab ya sake kayan dake hannun sa ganin wanda ke tsaye a kofar ga dukan alamu ya jima a tsaye............. ✨Ruqeenjalal✨ πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€ πŸ€ΉπŸΏβ€β™‚οΈ *ALKAWARIN MASOYA* πŸ€ΉπŸ»β€β™€οΈ ~ Na ~ πŸƒ *Rukayya Ibrahim*πŸƒ ✨Tsokaci ALKAWARIN MASOYA na kudi ne gamai bukata naira 300 ne kacal ki tuntube ni ta layin nan whatsApp only 07044407979πŸ‘Œ Free page🀧 *EXQUISITE WRITER'S FARUM* page2⃣3⃣&2⃣4⃣ Uncle nasu ne fuska ba walwala ya karaso tsakiyar d'akin, kallon lahab yayi da kyau, amma wallahi ka bani mamaki dom na damu da rayuwar ka kake zagar mini mata da shege ya? Dam-dam haka yaji kirjinsa ya buga amma bai nuna ba"nifa bada kai nake ba wallahi uncle" Kala baice masa ba illah nuni da yayiwa lahab da hannu akan ya wuce su fita a dakin, ba musu yayi gaba uncle na binsa a baya, daining zaka nufa. Aiko daining in ya nufan yana isa ya nemi kujera yaja ya zauna hade da zuba tagumi ya kurawa waje d'aya ido. Muneera!!! Muzammil ya kwala mata kira. Yes uncle, tace tana mikewa ta taho wajen su da sauri ta tsaya tana kallon su. Ki zuba masa abinci, da sauri ta d'auki plate ta zuba masa aje masa tayi a gaba shima uncle ta zuba masa nasa ta aje, shukali kawai lahab ya d'auka ya soma cin abinci duk wanda yaga fuskar sa yaga tsantsan bacin rai harda na sai dawa. Addayiya dake zaune a falo tun d'azun sai kallon su take fuska a hade don gaskiya abin na muzammil yayi yawa taya zai sawa amanar ta a gaba haka?kuma babu halin magana. Abinci ne dai sai da ya cinye tass, kafun ya barsa ya tashi mikewa yayi ya nufi dakin su yana shiga wanka yayi ya sanya kayan bacci zama yayi yana zullumin yanda zai bullowa lamarin uncle, take ya sake murmushi watoh yasan abinda zai kulla musu ai in sun san wata basu san wata ba. Takardun Rahab ya d'auko yana dudubawa, sai kuma ya aje da sauri jin wayar sa na ring, d'auka yayi ya dube mai kiran nabeel ne ke kiran sa, picking yayi ya kara a kunnen sa. "Hello nabeel" Ta d'aya bangaren aka amsa masa, kai shegen ba nabeel bane . Oh Adewale uban me kake da wayar nabeel kuma war haka"? Yazo tayani kwana ne shine nace koh kaima zaka fatso mu kwana tare? "Amma dai baka da hankali wallahi tunda nake da kai na taba yawon mangari ba" Amma ai naga gidan mu zakazo koh? "Toh Bazan zo ba " Jin Amsar da lahab ya basa yasan lallai akwai matsala, guy lafiya kuwa koh file naka aka girgiza ne? Harya bude baki zai sanar dashi muzammil yazo sai kuma yayi shuru, wallahi yanda yaji a jikinsa suma sai sunji a jikin su, shuru zaiyi Allah yasa gobe suyi gangancin xuwa gunsa suma su kwashe rabon su. Misalin karfe 10 cif Rahab ya shigo d'akin tare da Tirmizi, kallon yaron Lahab yayi cikin zare ido yace"kai ina xaka ka shigo mana daki"? Uncle a dakin ku zan kwana? Ai jin amsar da tirmizi ya basa yasa sa mikewa da sauri, Allah sarki yaron na ganin haka dayake ya saba da gudu ya ruga ya nufi kofar d'akin cikin gudu ya bude kofa yafita. Koma wa lahab yayi ya kwanta a shimfidar sa, Rahab kam girgixa kai kawai yayi baice kome ba gudun masifa don yasan yanzun D'an uwan nasa a cike yake dam jira kawai yake a tabosa ya sauke. Wanka yayi yazo ya kwanta, amma baiyi bacci ba har kusan 11 ganin da gaske Lahab ba kwanciya zaiyi ba yasa Rahab tambayar sa, lahab bakajin bacci ne? "Kaga malam kayi baccin ka kawai ni ba yanzun zan kwanta ba" Kamar ya ba yanzun zaka kwanta ba, lahab bayan mun saba kwanciya tare kuma bama kai warhaka? "Yau kuma nace banaji koh? ka rabu dani mana" Kwanciya yayi tare da kashe wutar dakin, amma bai kwanta ba ganin lahab a xaune yana danna waya. Har 12 yau basu kwanta ba tun lahab na d'aukar abin da wasa, Rahab keyi harfa ya fahimci da gaske yake, in bai kwanta ba shima baxai kwantan ba, kwanciya yayi hade da rufe jikinsa ya kashe wayar yayi likimo kamar yayi bacci, aiko ganin haka yasa Rahab shima gyara kwanciyar har bacci ya d'auke sa. Misalin karshe 1 na dare wanda yayi daidai da nauyin baccin rahab, mikewa lahab yayi da sauri ya kunna wayar sa ya haska lahab don kara tabbatar wa yayi baccin da gaske. Toilet ya nufa da sauri ya d'auko abubuwan aski, zama yayi a gefen Rahab daman shikam akwai nauyin bacci d'aga kansa yayi kad'an yasa clever yana aske masa gashin kai, sosai ya rage daidai irin nasa, gemun ma ya gyara sa sosai kamar yanda tasa yake yana gamawa da sauri ya maida kome toilet. Jan Rahab yayi ya maida shi kan katifar sa ya lulube sa, ya d'auko jakan Rahab ya juye takandun sa a nasa boron, ya sanya nasa ana Rahab, sai kuma ya kakkabe katifar rahab ya kwanta akai. *************** Nnenna ce zaune akan gado ta fifitar da kayan makarantan ta tasa a gaba tana kallo, koh abincin dare bata ciba ga gajiyar aiki da tasha, amma ta kasa bacci ji take kamar inta kwanta ta tashi da safe za'ace mafarki take. Turo kofar akayi tare da Neman excuse, riganta ta d'auka da sauri ta saka jin muryar Abraham ne, tana sanyawa ta amsa masa ya shigo, kallon ta yayi ya sake kallon kayan sai kuma yayi murmushi yazo ya zauna a bakin gadon, beauty hope kayan sun burgeki? Gyada kai tayi kawai tana tattara kayan tana ajewa a gefen gadon cikin zumudi shima baice kome ba, sai kallon ta yake sai kuma ya mike tsaye ganin ta sa hannu ta kashe wutar dakin ta kwanta ba tare da tayi masa magana ba, yana fita ta rufe kofar ta kwanta har bacci ya d'auke ta. ***************** Misalin karfe 4 na asuba Muzammil ya farka kamar yanda ya saba, daman lokacin tashin sa kenan, mikewa yayi ya sanya kayan sport a jikin sa. D'akin su lahab ya nufa hannu yasa ya tura kofar kaman yanda ya tsammani basu rufe ba, shiga yayi ganin dakin da duhu yasa sa lalubar makunni ya kunna wutan d'akin, katifar Lahab ya nufa, yasa hannu ya d'ana masa duka a baya ji kake dom. Innalilahi Rahab yace da sauri yana mikewa zaune cikin Al'ajabi yake bin uncle in nasu da ido, uncle lafiya? Uwarka ne tashi ka sanya kaya mu fita jogging? Ni kuma Uncle? Eh koh akwai wanda nace wane bayan kai? Amma uncle ai naga l..... Bai bari ya karasa ba ya daka masa tsawa, mike nace koh jikin ka ya gaya maka. Mikewa yayi cikin magagin bacci don shi baima fahimci katifar ba tasa bace da sauri ya nufi wardrop nasa, ya d'auko wando da riga na basketball ya sanya toilet ya shiga ya wanke bakin sa. Fitowa yayi tare da marairaice murya Ayya uncle nifa banason jogging in nan Lahab nefa ke zuwa. Zaro ido muzammil yayi yana tambayar Rahab, wani Lahab in bayan kai kuma, ni zaka mannawa hauka d'an iska? Wallahi uncle bani bane ga lahab a kwance. Make masa keya muzammil yayi, shige muje banason karajin wata magana a bakin ka, shasha sha kawai kullum musu a cikin ka, watoh na fita jogging kafun na dawo ka sa kafa kabar gidan koh? shige nace. Tsamo-tsamo haka Rahab ya ringa binsa a baya ga sanyi kamar yayi me sai yanzun ya gano Abinda lahab ya masa especially daya taba kansa yaji ba gashi. Lahab dake kwance yana jinsu jin sun fita yasa sa kyalkyalewa da dariya don daman tunda Uncle ya shigo yake matse dariyar karta fitoh,dawowa katifar sa yayi, gyara kwanciyar sa yayi yaci gaba da baccin sa. Rahab kam a gaba Uncle ya sashi suka ringa zagaye tun daga unguwan su har round about suka sake bin bayan layin su basu suka gangaro gida ba sai 5 In mutum yaga Rahab sai ya tausaya masa gabaki d'aya ya shanja yayi wujiga-wujiga dashi. Suna shiga gidan a lokacin jama'ar gidan keta Alwalan asuba,umurni ya bawa Rahab akan yaje yayi wanka, ya basa 5 minutes shap-shap yana maganar yana shigewa d'akin sa dake gidan. Rahab na shiga dakin daidai lokacin Lahab ya fitoh toilet sanye da gajeren wando da gani Alwala ya d'auro, shakosa Rahab yayi cikin masifa yace, me yasa Lahab zaka aske mini gashin kai?meyasa zaka maidani shimfidar ka meyasa? yana maganar yana girgiza sa da karfi. Turesa Lahab yayi cikin shekiyan ci yace"kowa kai yake so, kowa kai yake gani a matsayin nasa, ni babu mai sona a gidan nan hatta mamin mu kai tafiso dani, a wannan karon kaima zansa kaji yanda nake ji" Nina hanaka ka zama na kirkine koh ninace karsu soka?tayama zasu soka a haka, yace yana nuna lahab da yatsa. "Ok shikenan gani gaka kaima sai ka d'an d'ana abinda nake ji" ya karasa maganar cikin bagu ya taka har bakin katifar sa ya zauna ba tare daya saka kaya ba. Da sauri Rahab yayi wanka ya fitoh jallabiya yasa fari sai hula shima fari silifas yasa a kafarsa ya fita a d'akin yabar Lahab har lokacin zaune akan katifar sa. Ganin ya fita yasa lahab mikewa da sauri bude tasa wardrop in yayi ya zaro jallabiyar sa fara kal sabuwa irin na Rahab dan daman koda yaushe in za'a sai musu kaya iri d'aya ake saya, indai na sawa ne a baiwa kowa nasa, amma shi sai dai ya ajesu yasai irin nasa, saka jallabiyar yayi ya d'auki hula ya saka irin na Rahab ya sanya takalmin sa irin na d'an uwan nasa. Murmushin mugunta yayi sai kuma da sauri ya fita a d'akin jin uncle na kwala masa kira a falo, fitowa yayi ya kalli Uncle in, "ah ah uncle barka da asuba Lahab fa ya fita masallaci yanzun nan"? Ok toh muje Rahab na d'auka koh bai fita bane ai d'an banzan yaro sai nayi da gaske kafun nabar gidan nan, don naga su yaya sun zuba masa ido yana abinda yaga dama. Da sauri lahab yace"wallahi kam uncle koh school baya zuwa" Karka damu ai yau kafata kafarsa har makaranta d'an iska, sawa zanyi a shanja masa aji bazai zauna da abokan shashancin nan nasa ba. "Hakan ma yayi uncle"ya karasa maganar daidai da isar su bakin masallaci, shiga sukayi aka tada sallah. Ana idarwa suka fifito daga masallacin sai kuma su Abbu suka bisu da ido cikin mamaki ganin su yau sak iri d'aya, uncle ma zaro ido yayi kai menene haka yau kuka sanya kaya iri d'aya?sai kuma ya nuna rahab kai shige muje. Zaro ido Rahab yayi wallahi uncle bani bane ga lahab nan, da sauri lahab ya nuna sa da ido, "kai lahab ka shiga taitayin ka banason iskanci fa, uban wa yasa kasa kaya irin nawa" Kama baki Rahab yayi bangane ba bani na fara fita a d'akin na barka zaune ba?.. Kafun ma Lahab yayi magana da sauri Uncle yace d'an banza watoh kaika fara fita ka barsa a dakin kenan, dashi mukazo masallaci shige muje nace maka koh? Ba yanda Rahab ya iyya haka yabi Uncle a baya yayin da Lahab yabi su Amma cikin natsuwa, kamar na Allah suka nufi babban falo yayin da uncle ya wuce da Rahab garden. Suna shiga ya tsunguna kamar yanda Rahab keyi ya gaida Abbu sauran yaran suka gaggaishe sa gaida Addayiya yayi dasu mamu kafun ya wuce d'akin su, kwanciya yayi abinsa har bacci ya d'auke sa. Da misalin karfe 7 Rahab ya shigo d'akin jikinsa duk tabo Alamu dai gyaran flowers sukayi kafa yasa da karfi ya tunkude Lahab dake kwance, mikewa yayi da sauri ya kalli Rahab sai kuma ya ruga da gudu yayi toilet saboda Agogon bango daya gani, wanka yayi ya fitoh yana kallon Rahab"sannu biyu na zoka wuce kaje kayi wanka, Tsaki kawai Rahab yayi ya wuce toilet, mai Rahab ya shafa a jikinsa ya d'au uniform nasa ya saka, wando ne nevy blue sai riga fari tas mai dogon hannu, neck-tie nevy blue ya d'aura a wuyansa, socks ya d'auko baki ya zauna a bakin katifar sa ya sanya, sai boot nasa baki mai igiya ya d'aura a kafar sa, agogo ya d'aura shima baki sai jakan makarantan sa shima baki ya rataya turaren Rahab ya fesa da sauri ya ruga yayi waje jin motsen d'an uwan nasa na kokarin fitowa daga toilet. Yana fita a d'akin daidai lokacin tirmizi ya fito a d'akin su uzaifa, harda uzaifan ma da sauri lahab ya kwala masa kira kamar yanda Rahab keyi"kai angon addayiya wannan wanka duka nata ne"? Hade fuska tirmizi yayi aini uncle babu ruwa na da kai, tunda dai jiya kuka koreni a dakin ku? "Ayya ango kayi hakuri kaji ni babu ruwana" Amma ai uncle Lahab ne, meyasa baka masa magana ya barni ba kana gafa har son dukana yayi? "Yi hakuri zo muje daining koh"koh bazaka daina fushi dani bane"? Na d'aina uncle, yace yana kama hannun lahab suka fita a falon su zuwa babban falo, gabaki d'aya mutanen gidan ne zazzaune a daining inka cire matan gidan dake zaune a falo suna cin abinci, sai Rahab da uncle da basu fitoh ba, da sauri Lahab ya gaida Nabeela harda kiran ta da aunty nabeela, amsa masa tayi tana yabon hankalin sa. Zama yayi akan kujera zulaihat ta zuba masa breakfast nasa ya soma ci duk a tsammanin su Rahab ne. Uncle muzammil ne ya fitoh cikin shirin jamfa da riga harda hula, da sallama ya shigo falon Amsa masa akayi duka aka sake sabon gaggai sawa, bin falon yayi da kallo har idanun sa suka sauka akan lahab dake zaune hankalin sa kwance yake yagar kazar sa yana ci, kai Rahab ina d'an uwan naka. "Wallahi uncle yana ciki taima baza shi makarantan bane" Da sauri mamu tace, aiko wannan karamin aikin sa kenan daman ba zuwan yake ba aini nagode Allah na godewa muzammil. Gyada kai muzammil yayi ya juya ya nufi kofar falon su Lahab, yana shiga lokacin Rahab ke sanya uniform nasa, ai uncle na zuwa ya rufesa da masifa yana tsaye har ya gama kimtsawa gabaki d'aya hawaye ya cika masa ido, shidai ya shiga uku ace wai jama'a bazasu iyya gane saba koh banban tasa da lahab. . A gaba Uncle yasa sa har falo zama sukayi akan kujera suka soma karyawa, kallon Lahab zulai tayi, uncle Rahab ina assigment ina. Da sauri Rahab dake gefe yasa hannu a jakan sa zai d'auko takardan Zukaihat duk da bashi ta tambaya ba amma yasan shi ta baiwa takardan ta, yana sa hannu kawai yaga takardu da ba nasa ba budesu yayi dakyau koh shakka bayayi takardon lahab ne. Mikewa yayi tsaye hade da kallon lahab dake mikawa zulai takardan ta, lahab wallahi wasan kwaikwayon nan ya isheni haka ka bani takardu na, koh na maka mugun duka agidan na. "Kallon sa lahab yayi, wai menene haka lahab tun asuba saice mini kake wai nine kai menene riban ka tsakani da Allah fa"? Wani irin fusata Rahab yayi da mugun haushi ya sake takardun makarantan sa ya nufi lahab, don yana ga duka kawai zai iyya masa yaji sanyi a ransa, kai mara kunya????yaji uncle yace cikin bacin rai, wallahi lahab ka kuskura ka tabasa saina mugu-mugun saba maka munafuki daman ka aske masa kaine don kayi basaja.? Tsayawa kawai yayi yana bin kowa dake falon da kallo, sai kuma kawai ya sabi jakan nasa ya nufi barin kofar, kiransa Uncle yake amma yaki juyowa, da sauri muzammil ya bisa yana kokarin fita a falon ya fizgosa wanke masa fuska yayi da lafiyayun mari wanda yasa gaban Lahab dake zaune faduwa bai d'auka abin zaikai harga duka ba amma dai baice kome ba. Kai karamin d'an iska ina maka magana kana tafiya saboda kaje ka hadu da yan iskan abokan nan naka ku shiga gari koh? toh yau kafata kafarka har makarantan naku abincin ma bazaka ciba. Shuru kawai Rahab yayi yana dafe da kumatun sa yana kallon d'an uwansa yana mamakin Faruwar Al'amarin. Suna tsaye har aka gama karyawa Uncle ya durasu a mota dukan su rahab ne lahab ne muneera da zulaihat, yaja motar suka nufi school nasu..... *************** Nnenna tun asuba ta farka da sauri tayi brush ta sanya d'aya daga cikin kayan da Abraham ya sai mata, dogon riga ne bai iso koh gwuwa ba, sai hulan sanyi data saka, fitowa tayi cikin murna ta fara aikin ta, watoh share-share da goge-goge har tsakar gidan ta goge tiles duka, wanke-wanken dake kitchen duk ta tattara ta wanke tas. Daki ta shiga tai wanka, uniform in ta sanya siket ne nevy blue sai riga mai dogon hannu, stokin na rigan tayi a cikin siket in, hannu tasa tadau nect-tie nata blue ta sanya dayake tasan yanda ake nade abin tunda papa na makalawa, socks tasa fari sai boot nata nevy blue, empty jakan ta nevy blue shima ta d'auka, amma babu takardu a ciki kulenta dake gefe ta d'auka ta sanya a jakan, barect nata ta kafa akai daman gashin ta a tunkushe yake bata warwarewa ma bare. Agogo ta kallah karfe 7:00pm daidai ta fito a d'akin taku take a hankali tanajin ta wani iri cikin kayan uniform nata, tana isa falon gabaki d'ayan su suka bita da ido, ganin wani irin azabebben kyau datayi kamar dan ita akayi uniform in, jennifer turmude fuska tayi cikin hassada, Abraham kam kamar ya taso ya rungume ta haka yakeji koh zaiji sanyi. Tsungu nawa tayi akan gwuwar ta tana gaida dady dake zaune akan daining, Amsawa yayi sai kuma ta gaida Abraham ya amsa da sauri haka ma sarah ta amsa ba walwala, sabanin momy da Jennifer da sukaki Koh amsa mata ma. Kallon ta dady yayi, daughter gashi yau dai zaki fara zuwa makaranta, abinda nake so na fad'a miki shine kinga makarantan da zakije ba irin na kauye bane? wannan makaranta ne na birni sannan Muslim and Christian ne, babu ruwan ku da yaran hausa wa kar naji kar na gani, kika kuskura naji labarin an ganki da yaran Hausa wan nan, toh sai na cireki kuma banda kawayen banza,kiyi abinda ya kaiki kinji koh? Dukar da kai tayi sosai"i promise u Dad bazaka sameni da sab'anin hakan ba" Ok daughter ni zan fita ga Abraham zai kaiku school na basa kudin da za'a cherge ku. "Thank you Dad" Ur welcome daughter yace yana mikewa tsaye ya sabe jakan dake zaune akan kujera ya bar falon, kallon ta abraham yayi, Beauty kije kitchen ki ibo abinci time na gudu. Mikewa tayi da sauri mom ta daka mata wata uwar tsawa, koma ku zauna yar iska bakauyi ya, babu inda zaki duk rawan kafarki yau bazaki school din nan ba,nuna jennifer tayi ke Jennifer tashi brother ya kaiki school karkuyi late. Kallon ta Abraham yayi, haba mom ya haka bakiji Dad yace na kaita school ba? Naji, ni kuma nace bazata ba, kuma wallahi ka kuskura ka sanar da mahaifin ku saina saba maka. Jin abinda mom tace, yasa Nnenna sake kuka da karfi shikenan murnar ta zai koma ciki..................... ✨Ruqeenjalal✨ πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€ πŸ€ΉπŸΏβ€β™‚οΈ *ALKAWARIN MASOYA* πŸ€ΉπŸ»β€β™€οΈ ~ Na ~ πŸƒ *Rukayya Ibrahim*πŸƒ ✨Tsokaci ALKAWARIN MASOYA na kudi ne gamai bukata naira 300 ne kacal ki tuntube ni ta layin nan whatsApp only 07044407979πŸ‘Œ Free page🀧 *EXQUISITE WRITER'S FARUM* page2⃣5⃣&2⃣6⃣ Kuka Nnenna take Amma koh tausayi babu haka mom tasa Abraham d'aukar Jennifer zuwa school sarah ma makaranta abinta ta tafi, mom yau koh aiki bataje ba, dole tasa Nnenna komawa daki ta kifa kanta tana kuka sosai, koh karyawa batayi ba a haka tayita zama a daki. Shima Abraham da sauri ya aje jennifer a tunanin sa mom ta tafi hospital, amma me yana zuwa yaga mom xaune a falo, haka ya sake komawa da baya yabar gidan kawai. Har azahar Nnenna na xaune a dakin tana kuka koh kayan bata cire ba. Dad dake wajen aiki ne, Abraham yaje ya samu ya sanar dashi abubuwan dake faruwa, sosai yaji Ransa ya baci matuka bai taba zaton yawan amsa wa mom bukatun ta babu musu shiyasa ta d'auka koh tsoron ta yake ji. A fusace ya nufo gida cikin bacin rai... ******************* Lahab kam suna isa makaranta haka yayita bin makarantan da ido rabon sa da zuwa school tun komawar muzammil barrack, suna isa makarantan daman shike zaune a baya dasu muneera Rahab na gaba tare da muzammil in. Yana packing duk suka sassauka, hannun Rahab muxammil ya kama suka nufi office in principal, yayin da su lahab suka shishige Ajujuwan su. Lahab na shiga ajin wajen da Rahab yafi zama watoh benchin gaba agun ya zauna tare da fiffito da takardun Rahab ganin maths teacher nasu ya shigo. Ta bangaren Rahab kam suna shiga office in Muzammil ya bada sanarwa akan so yake a shanja ma Lahab aji a ciresa daga A zuwa B class sannan su saka masa ido duk lokacin da ake lesson baya aji a kirasa kuma a tabbatar ana binciken littatafan sa, yayi rubutu koh ah ah, 20k ya baiwa disple master nasu akan lahab, zaina zaman extra lesson da hadda, in yazo tun safe sai 5 na yamma zaina komawa gida. Rahab kam hawaye ne kawai yake bin kumatun sa lokacin da disple master ya tasa keyar sa zuwa B class. Muzammil na komawa gida zama yayi ya karya,suna hira shida addayiya a falo, don matar sa ta tafi gidan su da yaran sa ba kowa a gidan sai su ummu suma suna daki,ji sukayi ana kwala sallama a bakin kofar falo, addayiya ce ta amsa duk da ta gane masu muryar amma bata nuna ta ganesu ba sai ma tambayar su datake akan su wane ne su shigo. Muxammil kam mikewa yayi da sauri yabar falon, aiko suna shigowa suka soma gaida Addayiya, yamutsa fuska tayi ta amsa ba yabo ba fallasa, lafiya kuwa yan duniya na ganku anan? Nabeel ne ya bata Amsa, lafiya addayiya munxo wajen lahab ne, da safe bai fitoh jogging ba gashi wayar sa munyita kira ba'a d'agawa da safen nan. Ok toh ku shiga d'akin nasa ku duba taima yana aikin nasa watoh bacci. Mikewa sukayi suka nufi dakin su lahab, suna shiga suka ga ba kowa a d'akin, toilet Adewale ya nufa hannu yasa zaiyi knocking kawai yaga toilet in ya budu, tsaki yaja mtwsss wallahi nabeel ba kowa a dakin nan, sai Allah ina ya shiga yau kuma tun safe. juyawa sukayi zasu fita a dakin sai kuma suka ja da baya ganin Muzammil tsaye ya harde hannu. Da sauri dukan su suka tsunguna suna gaidashi, d'aga musu hannu yayi ba tare da yayi magana ba ya musu nuni da hannun sa akan su biyo sa. Fita yayi a d'akin suna binsa a baya saida sukazo falo, sai kum ya tsaya tunawa da yayi karfa ya fita dasu compound su arce a d'ari don halin sune dagasu har abokin nasu lahab gudu ba abin kunya bane a wajen su. Kofar dake falon ya turasu wanda zai kaisu har garden, suna dai binsa a baya har garden yayin da ransu in yayi dubu ya baci watoh lahab yasan kwanan zancen amma bai sanar dasu boss ya dawo ba, bare ma nabeel ya shaka sosai. Zama yayi akan d'aya daga cikin kujerun gabaki d'ayan su yasasu linkdown, kallon su yayi, meya hanaku zuwa makaranta? Uncle munzo duba lahab ne koh lafiya yau bamu gansa da asuba ba, daman in muka dubasa sai mu wuce school. Ok daman kun daina sa uniform ne? Ah ah uncle daman in mun zo mun dubasa sai mu koma musa ne. Makarya ta yace ana d'aukar bell nasa dake gefe, ya zubawa adewale da karfe,kafun ma nabeel ya ruga shima aka zuba masa aiko zurawa sukayi a guje yana binsu abinka da soja tuni ya shawo kansu, ya soma sakasu tsallen kwado daga bakin gate har garden. Haka ya sasu a gaba sunayi yana binsu a baya akalla saida sukayi kusan 2 hour's har yakai basa iyawa suna farawa suke zubewa kafafu sunyi tsami, nabeel kam har kuka ya fara da gaske kafun muzammil yabar su hade da musu kyakkyawan kashedi akan wallahi gobe in yaje makaranta yaji labarin basuje ba, koh sukaje suka tafi geto koh yagansu tare da Lahab sai jikin su ya gaya musu, babusu babu haduwa da lahab sai an dawo makaranta. Sudai amsa masa suke da eh kawai, nuni ya musu dasu wuce su tafi, wallahi haka suke tafiya a hankali kafafu duk sun mutu kafun su isa get sai da suka huta a baranda, suna fita ma saida suka huta a kwalbet na kofar gidan, kallo adewale nabeel yayi, wallahi adewale daga yau bazan kara yarda muxammil ya dakeni ba, daman ina rage masa ne Albarka cin lahab, amma tunda dai yace baya bukatar muna haduwa da kanin sa, wallahi daga yau na rabu da lahab kuma makarantan ne dai baxanje ba. Haba nabeel karfa ka manta yanda xai iyya dukan lahab haka zai iyya dukan mu, menene innar ka da mubeena basama lahab ne?harda zagi amma kaga ya nuna bacin ransa, yar uwarka da shekara 2 ta girme lahab amma bai taba tanka mata ba, sau nawa dad nawa na xagin ku lokacin da muke yara ma sau nawa yana dukan ku akaina, in kuka shigo gidan mu amma na tabbata lahab bai taba cewa zai rabu dani ba, haba nabeel? Kai kaga zaka iyya nidai nace bazan iyya ba, dukan mun nan munason zuwa school amma saboda lahab bazaije ba haka zamu ki zuwa duk saboda shi, shine yau shi zashi makaranta mukuma munzo muji lafiya bamu gansa ba,wani banzan yayansa ya mana irin wannan duka, lahab in ubana ne.? Shuru kawai Adewale yayi don yasan wannan surutu da nabeel keyi duk cikin zafin ciwo ne da haushi, amma yana wuce iyya ka ya tabbata wallahi badon Albarkacin lahab ba yasan da sun dade da rabuwa dashi koh don yanda nabeel ke nuna masa banbancin Addnin wasu lokutan, amma lahab babu ruwan sa da nuna fifiko gashi baida zuciya sam koh yayi fushi da abu zai huce ya dawo. Wucewa sukayi direct gidan su nabeel don kafar nan tasu sai an gasa ta, gashi adewale bayason komawa gida iyayen sa na hanya kar su dawo suga kafar su yasan ba karamin bala'i za'a buga da baban sa ba akan maganar nan. Tunda suka nufo kofar gidan su nabeel ran adewale ya kara baci ganin mubeena tsaye da wani saurayi suna hira a dakalin kofar gidan su. ******************* Lahab kam zama yayi a class kamar Rahab daman shi akwai kwakwalwa sosai rashin karatu ke damun sa da wasa ga rashin maida hankali, amma Rahab bazai nuna masa ilimi koh fahimtar abuba, sai dai in baisa kansa ba sosai yau ya maida hankali ana rubutu yanayi ana karatu yana tambayar question kaman dai yanda d'an uwan sa keyi. Ta bangaren Rahab ya rasa meke masa dadi abokan zaman sa dake A class babu su anan gashi disple daya tasa sa a gaba duk waiga warsa sai ya gansa zaune a bakin window akan kujera yana kallon sa, kwata-kwata ya rasa meke masa dadi ga yunwa dake damunsa. Misalin karfe 10:00pm aka buga break, mikewa lahab yayi ya fita a ajin magana abokan Rahab ke masa ya musu banza ya fita abinsa, cafe ya shiga yayi ordern abinci a takeAway ya sai nasa ma daban, fita yayi ya nufi B class. Rahab ne zaune ya kurawa wayar sa dake hannun sa ido ga dukkan Alamu waya yayi da wani, dafasa Lahab yayi, da sauri ya buge hannun nasa duk da bai d'ago yaga waye ba amma yasan tabbas lahab ne. "Haba lahab yanaga kazo ka zauna a aji baka fita break ba koh so kake yunwa ya ramar dakai ne a banban tamu" lahab yace ma Rahab cikin zolaya. Kallon sa kawai rahab yayi amma baice kome ba ya cigaba da danna wayan sa, bude laidan lahab yayi ya zaro takeAway ya aje akan loka "ga abinci kaci don wallahi yau dai wuni zakayi har yamma in ma bakaci ba jikin kane zai gaya maka, ga wannan yace yana mika masa 500. Kin karba Rahab yayi ya masa banza, aje masa kudin lahab yayi"gashi kaci abincin Rana"yana maganar yana fita a ajin. Misalin karfe 1:30 aka tadasu sallah, lahab ya hadu da rahab a masallaci amma baice masa kome ba, suna idar da sallah suka koma class. Sai 3 cip aka tadasu muzammil ne yazo d'aukar su, daman Rahab kam baima fita a ajin ba don yasan yini xaiyi har yamma yana hango su suka shiga mota suka tafi, karfe 4 suka shiga Extra lesson, na awaya d'aya 5 suka tafi massallaci hadda bashi ya dawo gida ba sai kusan 5:40 na yamma. *************** Dad kam daga wajen aiki gida ya nufa lokacin mom na dakin ta, ransa a bace ya bude kofar falon ya shiga ganin ba kowa a falon ya nufi d'akin Nnenna ya tura ya shiga. Har lokacin zaune take da uniform a jikin ta tayi kuka har taji babu dadi gashi daren jiya ma bataci kome ba, kanta ciwo yake mata, girgiza kai yayi ya kirata, my daughter. Da sauri ta d'aga kanta tana kallon dad sai kuma ta fashe da kuka dana durku sawa daga zaune da take. Daughter menene in maganar zuwa makaranta ne ki kwantar da hankalin ki gobe goben nan zaki tafi makaranta da kaina zan kaiki kiyi shuru karki sawa kanki wani cutan kuma? Cikin kuka ta mike da sauri tazo ta rungume Dad, tana sakin kuka haka kawai yau takejin kewan iyayeta da ace tana da iyayen ta a raye baza'a mata yankan kauna irin na yau ba. Haba daughter ki kwantar da hankalin ki, yace yana bubbuga bayan ta. Sake sa tayi ta koma bakin gado ta zauna tana mai dafe kanta don wallahi ciwo yake mata, daughter kinci abinci kuwa? Girgixa kai tayi batare da tayi magana ba, fita dad yayi a d'akin yana kwalawa peace kira da sauri ta fitoh tana gaidashi, ba tare da ya amsa ba yace ta kaima Nnenna abinci. Juyawa tayi ta koma kitchen in, shima dakin ya koma ya lallabata tatashi ta shiga wanka, yana fita bayan ta fito toilet in ta d'auki abincin da peace ta kawo mata taci, kadan ta baiwa kulenta saura kaya tasa a jikin ta, ta koma kan gado ta kwanta don tanaji yaukam bazata iyya aikin kome ba. Dad yaje ya samu mom sosai ya nuna mata haukan sa tare da mata Warning mai kyau akan Nnenna, jennifer ma sosai ya zazzage ta ba kad'an ba wannan abu shiya karawa Mom tsanar Nnenna. Har dare Nnenna bata fito ba abinci ma a daki aka kaimata amma bataci ba saboda nama da aka saka a ciki sai kulenta ta baiwa gashi yan gidan har yanzun basu fahimci batacin nama ba. ********************* Lahab tunta ya dawo makaranta bai fita koh ina ba gudun kar a zarge shine lahab don Rahab baya yawo daga masallaci sai gida koh makaranta, hakan yasa sa zaman gida sosai ya kule a dakin su, yana ta bitan litattafai gudun kar azo a samu matsala a gane bashi bane. A haka Rahab ya dawo goshin mangari ba ya same sa, yana turo kofar dakin kawai ya zube akan katifar sa yana maida numfashi don wallahi wahala kam yau yasha, wuni cur a makaranta ba lafiya bane. Sai da ya jima a kwance har an fara kiran mangariba kafun ya shiga wanka daidai ya fitoh ma har lahab ya sanya jallabiya ya tafi masallaci, da sauri ya sanya kaya yabi bayan sa, ana idar da sallah suna fitowa masallaci sukayi kicibis da yaya jafar watoh yayan uncle muzammil kanin Abbu, gaisawa sukayi sosai yana ta yabon Lahab a tunanin sa Rahab ne don yanzun rahab koh musawa mutane bayayi am mai dashi lahab karfi da yaji. Gida suka shiga Aka zauna cin abinci ana hira gwanin sha'awa, ana kiran isha'i gabaki d'ayan su suka nufi massallaci sallan isha, tunda aka idar da sallah Aka duba ba'aga Rahab ba, amma tabbas tare dashi aka idar da sallah amma an nemesa ba'a gansa ba sosai ran uncle ya baci ton shi a tunanin sa lahab ne ya tafi yawo. Shima lahab ya damu don yasan Rahab baya yawon Rana ma bare dare, gida suka shiga Muzammil sai masifa yake yana kwatanta irin dukan da yau zaima lahab inya dawo shidai lahab na zauna yana bitan qur'ani a gefe zuciyar sa a tsinke. Yaya jafar karan kansa wannan tashin hankalin bai bari ya tafi ba, har 9 na dare shuru-shuru babu Rahab ba labarin sa, gashi sun kasa zaune sun kasa tsaye, bare ma lahab yafi kowa shiga tashin hankali kiran waya aka fara gida-gida ana neman Rahab koh yazo amma shuru, a take Amwar ya fita neman sa har gidan su nabeel yaje lokacin yana kwance kafa ba lafiya. Anan ma sukace basu gansa ba rabon su da lahab tun jiya, yauma da sukaje dubosa tsaraban duka suka samu jin haka yasa baima je gidan su Adewale ba. Uncle muzammil ne zaune akan kujeraya harde kafa hannunsa rike da bell jira kawai yake aga Lahab jikin sa ya gaya masa, don shi yafi ta'allaka abin akan gudu Lahab yayi don yaga yana takura masa koh kuma wajen shashancin su yaje Ji sukai an turo kofar cikin sallama, mikewa sukayi suna amsa wa har suna had'a baki, mami ce ta fara shigowa sai Rahab dake binta a baya yayin da mijinta ke jiran iso, da sauri muzammil ya mike cikin zafin rai yake nuna Rahab, yau zakasan kasa kafa kabar gidan nan lahab watoh gidan uwarka kaje koh?toh yau babu mai hanani dukan ka a gidan nan koh a gaban tane sai na bugeka. Kallon uku saura mami ta masa don daman tun husul basa shiri da muzammil, tun suna yara lokacin tana matar baban sa, don Allah dakata mini malam akan me zaka dakar min d'a? baijiba bai gani ba aiko abu yama Albarka cin idona zaka sassauta masa saina tafi bare bai maka kome ba. Ok iko zaki gwada mana akan yaranki maryam, kinsan kina son sune kika tafi kika barmu dasu? Na nuna ikon kaji tunda nina haifi abuna babu wanda ya haifa mini?koh duk abinda kake musu na taba saka bakine?ina tambayar ka nace na taba saka bakine, saboda da nasan kanayi ne akan gyara lahab, Amma taya zaka kama Rahab kana azabtar dashi abanza da sunan lahab wannan Adalcine nace adalcine?dabazan nuna ikona na uwa ba saina zuba ido ka bugesa akan abinda ba laifinsa ba. Da sauri Abbu ya dakatar da cece kucen ganin muzammil na son bata amsa, kai muzammil wallahi ka kuskura naji kace wani abu saina nuna maka bacin Raina? Sai kuma ya kalli mami maryam bamu gane zancen ba kimana yanda zamu fahimta mai lahab in yaje yace miki? Kallon lahab tayi dake sanye da jallabiya yana tsaye a gefe sai fiki-fiki yake da idanu,ya bata tausayi sosai abinka da uwa da 'ya'yan ta, don tasan yau Allah ne kad'ai zai kwacesa a hannu muzammil............. ✨Ruqeenjalal✨ πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€ πŸ€ΉπŸΏβ€β™‚οΈ *ALKAWARIN MASOYA* πŸ€ΉπŸ»β€β™€οΈ ~ Na ~ πŸƒ *Rukayya Ibrahim*πŸƒ ✨Tsokaci ALKAWARIN MASOYA na kudi ne gamai bukata naira 300 ne kacal ki tuntube ni ta layin nan whatsApp only 07044407979πŸ‘Œ Free page🀧 *EXQUISITE WRITER'S FARUM* page2⃣7⃣&2⃣8⃣ Bafa Lahab yake hukunta wa ba Rahab ne? Sake baki muxammil yayi yana kallon Lahab dake tsaye, lahab da gaske ne abinda maryam tace? Shuru lahab yayi baice kome ba, aiko abin ya mugun kara batawa muzammil rai fizgo lahab yayi ya wanke sa da lafiyayun mari guda biyu, amma ko gizau lahab baiyi ba bare ma ya bada hakuri. Kai muxammil sake yaron nan koh mutuwa na kunyan idon uwa bare kai ka sake sa, Addayiya tace ganin yanda muzammil ya finciko lahab zai fita falon dashi. Kin tsayawa muxammil yayi sai jan kwalan jallabiyan lahab yake, amma lahab koh hakuri koh alamun nadama babu a fuskar sa. Yaya jafar ne ya tsaida muzammil,sake yaron nan kadai san duka baya gyara koh?lahab yanzun ya girma ace shekara 18 namiji ana dukan sa aiko mace ne ta wuce duka. Addayiya fashewa tayi da kuka, wallahi muzammil ka sake yaron nan marayan Allah zaka cakume kaje ka illata sa. Kyalesa yaje ya kashe sa addayiya koh an bar lahab baxai hana gobe yayi abinda yafi haka ba, tunda dai zai iyya kwakwayon d'an uwan sa har ana gallaza masa, mami tace tana share hawaye bawai abinda xa'ama lahab ne yasata kuka ba sai tuna mahaifin su lahab, da ace yana raye babu wanda ya isa ya d'aura hannu akan 'ya'yan sa. Muzammil koh kulasu baiyi ba kawai ya bude kofar zai tura lahab, da gudu Rahab yazo ya kama kafar sa tare da dukar da gwuwar sa a kasa cikin kuka yake magana don Allah uncle kayi hakuri na rokeka ka taimaka, wallahi ni naje na fad'awa mami ne badon a buge lahab ba, kuma nayi farin ciki daya gyara halin sa a kwana d'aya ya zama kamata, dan Allah uncle kayi hakuri karka bugesa gobe nama Alkawari zaije makaranta. Tsayawa muzammil yayi yana kallon lahab dake tsaye ya wani lonkosu ya rike kwankwaso da hannu d'aya, d'aya hannun kuma ya dafa jikin gini, kana ganin sa kaga taceccen gagare koh alamun nadama babu a fuskar sa, duk da akwai tsoro aran sa amma sam baima bari an gane ba.. A gaskiya Rahab yau in ban ma lahab duka ba zan zame hannu na a lamarin yaron nan, don naga duk abinda yake kuke d'aure masa gindi yake duk abinda yaso. Shuru duka falon sukayi don wallahi sun san mundin sukace a kyale lahab toh muzammil ya daina saka sa a gaba kenan don sun san muzammil kaifi d'aya ne, basu san wazai jawa lahab birki ba. Mami ce ta kalli mijin ta Alhaji muje koh tana maganar tana nufar kofar falon, koh kallon muxammil batayi ba tanajin wani irin zafi a ranta, daman haka uwa keji mundin za'a taba lafiyar d'anta koh da kuwa shine da laifi sai dai ta danne xuciyar ta a hukunta shi. Binta mijinta yayi a baya suka bar gidan uncle jafar ma tafiyar sa yayi Rshab kam sai kuka yake a falo, ganin muzammil yaja lahab zuwa sashen sa. Extra room na falon sa yakai lahab bell ya d'auka ya dinga laftar sa, amma abin bakin ciki lahab baya kuka kuma baya bada hakuri sai dai kare kansa da yake, sosai Muzammil ya bubuge lahab bana wasa ba ga sashi tsallen kwado da ya ringayi da machine in yamasa taurin kai ya rufasa da duka. Lahab fa iyya jikita ya jinkita amma taurin rai bai bari ya nuna nadamar sa ba, ruwan sanyi muzammil yaje ya ciko a boket yazo ya kwara masa a jiki cikin daren nan, haka yana zaune bayan wahalar dashi da yayi a haka lahab ya kwana a zaune kuma a jike bashi ya sake saba sai kusan 4 na asuba. Kasa tashi lahab yayi da rarafe ya ke tafiya kamar yaro mai tete , a haka ya fita a falon ga jikin sa duk ya farfashe amma fuskar sa bai samu kome ba sai idanun sa da suka kumbura na wahala da rashin bacci, a haka har ya ido kofar falon su duk a bude aka bari sanin da akayi yana wajen muxammil, a zaune yasa hannu ya bude kofar da rarrafe ya isa kofar falon su, yana shiga yaga Rahab zaune har lokacin kuka yake d'aga fuskar sa yayi da yayi mugun kumbura ya kalli Lahab da sauri ya mike ya isa garesa. Lahab sannu wallahi tunda uncle ya wuce da kai ban samu bacci ba, gashi mami ma sai kira take akan ya barka ka dawo amma bai barka ba sai dukan ka yake koh? "Kamani muje d'aki"lahab yace ba tare daya basa amsa ba, da sauri Rahab ya kamasa da taimakon sa suka shiga dakin daman ba kaya a jikinsa sai wando muzammil ya kwabe jallabiyar. Har toilet Rahab ya kaisa, " jona mini kettle Rahab" Da sauri Rahab ya d'au butan ya cika ruwa a ciki ya jona, wandon jikin lahab ya taimaka masa ya cire, ya rage daga shi dai gajeren wando, ganin yanda jikin sa ya zama yasa Rahab kara fashewa da kuka yana d'aukar wayar sa dake ring mami ce. Hello mami rahab yace cikin muryar kuka Da sauri mami tace Rahab lahab in ya dawo ne? Eh mami gashinan wallahi duk uncle ya faffasa masa jiki koh tafiya baya iyyawa mami. Bashi wayar, mami tace tana hawaye. Mika ma lahab wayar yayi amma kememen lahab yaki amsar wayan sai ma mugun kallo daya watsawa Rahab. Kashe wayar kawai lahab yayi yana zare socket na ruwan zafin ajewa yayi ya zaro karamin towel ya aje a gefe, tura kofar yayi ya fita da sauri ya nufi babban falo, Yana shiga kitchen boket ya d'auko a store da roba karami sai gishiri, yana fitowa sukayi kicibis da addayiya. Da sauri take tambayar sa lahab ya dawo? gyada mata kai kawai yayi ya cigaba da tafiyar sa,itama da sauri tabi bayan sa har dakin su lahab, rahab ya tura kofar toilet in suka shiga. Ganin jikin lahab yasa addayiya kama baki ta fara kuka tana dafa kirjinsa, wayyo na bonu amanar umar ne haka, amma muzammil anyi azzalumi haka yayi maka lahab tana maganar tana had'a ruwan zafi. Kala lahab baice ba kansa na sunkuye koh d'agowa baiyi ya ganta ba don itama yau wani mugu-mugun haushin ta yake ji. Addayiya da rahab su sukayi ta wanke lahab suna gasa masa jiki zuwa 5 na asuba jikin ya d'anyi sauki, Alwala sukayi dukan su a dakin Rahab ya sanyawa lahab wando 3quater addayiya ta shimfida masa sallaya ta fita a dakin. Daga Rahab har lahab ranan kin zuwa masallaci sukayi a daki sukayi sallah abbu na dawowa sallah ya shigo dakin nasu, a yanayin da yaga jikin lahab yasa sa saurin kiran likita, yazo ya basa maganguna da allurai a take bacci ya d'auke sa, shima Rahab baccin ya koma don jiya baiyi bacci ba kuma yasha Alwashin koh kashesa za'ayi yau bazashi makaranta ba sai lahab yaji sauki. Gari na waye wa muzammil ya nufo dakin nasu da niyar ya korasu makaranta, yana budewa ya gansu kwakwance a kan katifa, sai addayiya dake gefe a zaune tana gyangyadi jin an budo kofa yasa ta saurin zabura ganin muzammil ne yasa ta mikewa tsaye tana masa nuni da hannu akan ya fita a dakin, fuska a d'aure shima baija zancen ba ya juya ya tafi abinsa. **************** Ta bangaren Nnenna yau ta tashi a sab'ule koh d'okin zuwa school in batayi ba, tana tashi tayi ayyukan ta kamar ko yaushe kayan makarantan ma bata saka ba sai da Abraham ya shigo ya kara jaddada mata yau zata school. shiryawa tayi jiki ba kwari ta ibi abinci taci kad'an Dady da kansa ya d'auke ta xuwa school, , jennifer kam kin binsu ma tayi tace bazata bi dady ba mom zata kaita. Nnenna tunda suka nufi makaranta zuciyar ta ke tsinkewa, wanda bata san dalili ba tana ji kamar akwai wani abu mai muhimmanci dake tinkaro rayuwar ta anan gaba. Makaranta ne na manya in akace manya ana nufin yayan masu akwai sosai, makaranta mai kyau da tsada daga yanayin ginin makarantan da uniform inda ke sanye a jikin su kome clean ne, ajujuwa ne sama da kasa bini mai hawa uku gashi reshe-reshe gefen science daban Art ban, Amma senior ne kawai babu primary koh jenior. Packing Dad yayi a packing space na makarantan a hankali Nnenna ta bude marfin motar ta fita Dad ma fita yayi, yana kallon ta tare da sakar mata murmushi, daughter muje koh yanzun fa Almost 7:39pm gyada kai tayi tabi bayan sa har office in principal. An gama kome harda interview aka mata kuma sun yaba da kokarin ta, ga speak a bakin ta, a take Dad ya mata registration, aka bata takardun makaranta tare da sanar da ita akwai Labrary basai an bata textbook ba, sai da aka gama mata kome kafun aka mikata a sss 3 A. Tunda Nnenna ta shigo ajin gabaki d'aya 'yan ajin suka bita da kallo sosai suke kallon ta kamar sun samu wata sabuwar halitta, a bench na gaba aka ajeta itama karan kanta ta sargu ganin yanda yara keta binta da ido daga maza har mata. Wata yar inyamura ce ta matso bench da take cikin yare ta soma mata magana ganin ta Christian kuma kykkyawa haka, atunanin ta Egbo ce, duk da kyawun nata yayi yawa sosai, cikin yare take sanar da ita sunan ta Amarachi? Gyada kai Nnenna kawai tayi tana kallon yarinyar amma batace kome ba, don dad yau saida ya kara ja mata warning sosai akan mu'amala da mutane ta kuma iyye bakin ta. Sake tambayar ta yarinyar tayi ita kuma menene sunan ta? mikawa yarinyar takardan ta tayi, ba musu yarinyar ta karba ta duba, sai kuma ta d'ago tana kallon Nnenna, ok ur name is Nnenna obinna from Enugu state abie? Gyada kai again Nnenna tayi batace kome ba itama Amarachi bata damu ba koh banza zatayi kawance da kyakkyawa,wasu yara biyu ma duk suka zo sukayi joining na Amarachi sai hira suke ma Nnenna, tana binsu da ido kawai duk cikin turanci suke wasu har takardu suka fiffitar, note nasu suka bata wai ta copy aiko da sauri ta karba tana copy abinta. A haka Jennifer ta shigo class in fuska ba walwala kallon Nnenna tayi dake rubutu sai yara dake gefen ta mata uku maza biyu sai hira suka mata sosai, ranta ya baci ganin daga zuwan Nnenna zata kwace mata jama'a a ajin su,tsawa ta dakawa Nnenna tare da nunata da hannu ke yar kauye tashi mana a bench banza mabaraciya kawai. Mikewa Nnenna tayi yayin da d'aya daga cikin mazan yace ma Jennifer amma dai ke mahaukaciya ce, ya daga zuwan yarinya zaki wani fara zaginta ubanki yazo da benchi daga gidan kune. Badai gidan mu ba sai dai gidan ubanka. Ai kankace me fad'a ya barke tsakanin Jennifer da yaron , sosai yake bugun jennifer kafun aje akira teacher tayi laushi sosai, kafun akazo aka jidesu dukansu akayi staff room dasu. Ranan koh darasi d'aya jennifer bata samu ba saboda hukunta su da akai a staff aka barsu wuni kas don su school in basa duka sai dai su horar. *************** Lahab basu suka farka ba sai kusan 11 na safe suna farkawa suka tarar da addayiya na zaune har lokacin a d'akin, watoh dai gadin su take, Lahab jiki yayi sauki da kafar sa ya shiga toilet duk da kafar bawai ya daina tsami bane, wanka yayi da ruwan zafi da addayiya ta had'a masa yana fitowa ya samu ta zuzzuba musu abinci a plate. Zama yayi a bakin katifar tare da jinginar da jikinsa a jikin ginin dakin, da sauri ta kawo plate in ta aje masa a gaba, kallon plate in yayi shinkafa ne da salad sai miya,"gaskiya nifa addayiya bazan iyya cin abincin nan ba bakina ba dadi" Ok toh lahabu mekake son ci? "Kwai kawai zaki kawo mini soyayye sai ruwan tie ba madara" Da hanzari ta mike ta fita a dakin, abincin da lahab yaki ci shi Rahab ya d'auka ya kama ci, koh 30 minutes ba'ayi ba saiga addayiya da tiren abinci aje masa tayi a gaba ga dukkan alamu yanzun ma ta d'aura tie in harda suyan kwai. Kad'an lahab yaci ba yawa ya koma ya kwanta tare da d'aukar wayar sa, nabeel ya kira amma har ya gama ring bai d'auka ba haka ma adewale abun ya basa mamaki don da wuya ka kira d'aya baka samesa ba. Aje wayan yayi kawai ya lumshe idanun sa yana sauraron hiran da addayiya keyi da rahab. **************** Nnenna a rana d'aya tayi winning na heart in yara, daga malaman har daliban saboda kwakwalwar ta da kyaun da Allah ya bata gashi students mata sai janta labrary koh cafe suke ayi ciye-ciye, koh suce suje ta musu wani Assigment, duk da ba fuska ta sakar musu ba tana d'ari-d'ari da kowa kuma abinda ya bata mamaki shine sam yaran musulmai basu rabeta ba gwara maza wasu sun mata magana albarkacin zaman tare, amma matan kam kowa d'aga kai tayi abinta kamar basu san da ita a class in ba. Yayin da bakin ciki ya gama gashe jennifer ganin rana d'aya Nnenna ta kwace mata kawaye, da aka tashi makaranta da driver yazo d'aukar su jennifer hanata shiga tayi driver yaja mator ya barta a tsaye. Haka Nnenna ta ringa takawa da kafarta tun daga school har gida, gashi 3 aka tashi koh karyawan kirki batayi ba gashi taki cin abinda students suka sai mata, ga tafiya duk da hanyar sabone a wajen ta hakan bai hanata gane gida ba sai kusan 4:30 ta isa gida. Tana tura kofar falon ta tarar da Mom zaune a falo sai sarah dake duba book nata koh kallon ta mom batayi ba, harta shiga d'akin ta wanka tayi ta ibo kayan uniform nata ta wanke su a waje ta shanya, kitchen ta nufa zata ibi abinci haka mom ta hanata iba, akan tunda Jennifer ta dawo makaranta ta kulle kanta a d'aki koh abinci taki ci sai kuka take don haka itama bazataci ba. Sai dare aka samu Jennifer ta bude kofa anan take sanar da mom nata abinda Nnenna ta mata aiko mom ba karamin bacin rai taji ba, amma tace ta bari gobe in Allah ya kaimu zasu je school in tare ayita ta kare. Haka koh akayi washe gari da safe Mom da kanta taje school in su Nnenna ita da jennifer yayin da suka bar Nnenna a titi tana takowa da kafa, Nnenna batasan me su mom sukazo suka kulla mata ba, tadai tazo school late har anso korarta gida, m amma daga baya principal yace a barta jin dalilin late in nata, sannan ya shaida mata tabar A class an maidata B. Haka ba musu ta koma B da zama, amma sam ta daina jin dadin makaranta saboda mugun tsanar ta da aka soma ba gaira ba dalili gashi wulakanci jennifer take mata sosai, wani lokacin sai dai ta buya tasha kukan ta koh zaman aji bata iyya wa in aka fita break saboda ihu da ake mata da hausa wanda bata san mema suke cewa ba amma ta tabbata zagine. A haka ta ringa zuwa school a kafa kuma a wahale kullum sai ta buga late allah ma ya sota ba'a duka a school in sai dai horo mai tsanani irin su wanke toilet da dai sauran su. Daga an buga break kuma sai dai ta tafi bayan ajujuwa wajen gonakin makaranta ta xauna abunta ita kadai sai kulenta har a dawo break. Gidan ma ba dadi yake mata ba sai in Abraham nanan koh dad suke d'an shiga harkar ta kad'an, nan ma ba sosai bane ga yunwa dake cinta abinci ba koh yaushe take samu taci abinda ranta ke so ba, har wani tari ta fara wanda bata san kansa ba in tanayi kirjinta har zafi yake mata haka numfashin ta ke fita da sauri sauri. **************** Lahab sai da ya kwashe kwana 3 Rahab da addayiya suna jinyansa kafun ya samu ya murmure har yana zuwa masallaci da kansa muzammil yaso su koma makaranta amma addayiya tayi kukan kura ta dire tace jikin lahab bai warke ba, shikam da wannan yayi amfani wajen kara longo bewa don da gaske ciwo kan sun bushe sai dai baza'ace sun warke ba. Yau dai yana fita sallan asuba bai zarce koh ina ba sai gidan su adewale, Amma maigadi yace masa adewale baya nan, sai ya gangara gidan su nabeel don shikam gaskiya yasha mamaki kwarai wallahi ace yau kwanan sa hudu basu gansa ba su kasa zuwa neman sa koh suje gidan su. Yana zuwa gidan su nabeel suka gaisa a inna harma tana tambayar sa lafiya baizuwa kwana biyu? (D'an mutum kenan duk yanda kake kinsa randa baka gansa ba sai kaji wani wuri naka sakayau)anan yake sanar da ita baida lafiya ne. Tare da tambayar ta su nabeel, ce masa tayi ai sun tafi jogging, fita yayi a gidan ya nufi hanyar filin ball da suke zuwa exercise aiko yayi sa'a tun daga nesa ya hangosu suna motsa jiki, hannu ya d'aga musu yana kwana musu kira, amma gabaki d'ayan su sukayi kamar basu gansa ba abin yayi mugu-mugun basa mamaki lokacin da ya iso inda suke yaga nabeel na kokarin barin wajen, da sauri ya rike hannun sa "haba guys kwana biyu baku ganni ba amma kuka kasa nema na"? Wani kallo nabeel ya masa cikin yaushi yace, mtwsss eh taya zamu neme ka bayan kana school sannan a gidan ku ba'ason mu rabe ka, toh muma yanzun m................ ✨Ruqeenjalal✨ πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€ πŸ€ΉπŸΏβ€β™‚οΈ *ALKAWARIN MASOYA* πŸ€ΉπŸ»β€β™€οΈ ~ Na ~ πŸƒ *Rukayya Ibrahim*πŸƒ ✨Tsokaci ALKAWARIN MASOYA na kudi ne gamai bukata naira 300 ne kacal ki tuntube ni ta layin nan whatsApp only 07044407979πŸ‘Œ Last Free page🀧 *EXQUISITE WRITER'S FARUM* page 2⃣9⃣&3⃣0⃣ Don haka muma yanzun bamu ba kai? "Wai menene niban gane ba kunje gidan mune daman"? Munje mana wannan d'an iskan yayan naka ya........., ai lahab bai bari nabeel ya karasa ba ya wanke sa da lafiyeyen mari cikin hakin bacin rai yace" wallahi karka kuskura ka sake zagan mini yaya kaji na gaya maka duk rashin kunyan ka a bayana kake, don uwarka na taba zagin wani naka ne don ya kuntata mini. Hannu nabeel ya d'aga ya wanke lahab da mari shima jin ya zagi uwarsa, aiko take lahab ya shuresa ya buga a kasa take fad'a ya barke a tsakanin su, sosai lahab ke jibgar nabeel adewale yayi iyya kokarin sa don raba fad'an abu yaki lahab na jibgar nabeel, shikuma zuciya na cinsa yaki barin fad'an daga karshe dai har jama'an dake gefe suna exercise, aka zo aka kakka masu amma nabeel yaki barin fad'an sai zagin wa'inda suka rirrikesa yake, wai sai dai a barsa ya buge lahab. Wani ne a cikin su yad'au waya ya kira Bappan sa a waya, akazo aka jasa aka tafi dashi kafun mutane suka watse, kallon lahab adewale yayi, gaskiya friend nayi mamakin abinda nabeel ya aikata maka? "Manta dashi kawai adewale gani yake yafi kowa zuciya baisan akwai maza bisa kansa ba, wai ma meya farune Adewale ban gane abinda yake ma masifa akai ba, me uncle ya muku ne"? Wallahi lahab munzo wajen ka kawai ya kikirbemu wai bamuje school ba, shine shi kuma nabeel yad'au zafi baka sanar damu yazo ba mukaje gidan ku neman ka, ashe ka shiga school koh note babu, nima banji dadi ba gaskiya? "Am sorry amma ban zati don brother na ya buge nabeel zai hau haka ba, ka dube jikina"lahab yace yana kwabe rigan sa. Jesus menene haka lahab mezan ganin nan? "Wallahi kaga jikina dukan da muzammil ya mini kenan kwana biyu bakwa gani na" Cap Allah ya sauwa ka amma guy ka daku fa iyya dakuwa ma kuwa. "Ka bari kawai Adewale ai shiyasa nace wallahi bazani makarantan ba sai dai ya kasheni" Da mamaki Adewale ke kallon lahab, gaskiya aboki wallahi kana da taurin kai na rantse nidai gobe school zani, bansan koh nabeel zashi ba? "Kai karka sake kira mini sunan shegen nan a kusa dani" Ok yanzun ina muka nufa kenan da sassafen nan lahab? "kai muje gidan ku ka chanja kaya mu fasa gari wallahi na gaji da zaman banzan nan zama waje d'aya ba dadi sam" Ok muje lahab amma fa kasan old man na gida fa? "Toh ni ina ruwa na tsoron baban naka nake ne"? Ah ah yi hakuri man muje. Kama hanya sukayi suka nufi fita a filin ball in har sun bar filin kamar daga sama suka ga Muxammil a tsaye a gaban su fuska ba walwala, hade fuska yayi sosai yana kallon lahab, amma kai dai lahab Allah ne kadai zai gyara maka ka, shige mutafi tun raina bai baci ba. Bin gefen muzammil yayi ya nufi layin su ba tare da yace kome ba, kallon adewale uncle yayi, ka wuce kaje ka sanya uniform wallahi naje school naku bakaje ba, nida kai yana maganar yabi bayan lahab da sauri gudun karya arce. Lahab na gaba Uncle na baya a haka suke tafiya har suka shigo cikin gida yana tura kofar falon ya shiga, Addayiya ce zaune sai Abbu ga inna ma zaune sai masifa take. Karaso mutumin banza, addayiya tace tana kallon lahab. Hararan ta yayi"wallahi nidai ba mutumin banza bane atoh" Rufemin baki koh namaka abinda yafi na jiya d'an iska zauna anan, yana maganar yana nuna masa kasan tiles, kin zama lahab yayi sai da abbu yasa baki kafun ya zauna. Kallon sa abbu yayi, yanzun lahab ka kyauta kenan kaje ka kama abokin ka kamasa duka kasan yaron laulayine dashi haka ake abota da dambe? "Wallahi yaya shiya fara wai fa akan uncle ya bugesa shikenan yace wa yaya d'an iska shine na babbuge sa" Kallon sa muxammil yayi nine dan iska kuma nabeel ne yace? "Eh yaya" Kamin daidai tashi ka tafi ka sanya uniform maza-maza 'yan uwan ka sun tafi makaranta. Ai jin haka tuni inna ta soma bala'i don an gansu talakawa shine za'a cucesu a hanasu kuka, Allah ya isawa jikan ta, addayiya dai sai hakuri suke bata ita da Abbu amma muzammil kam mikewa ma yayi yabi lahab d'aki yana jiran sa ya gama shiryawa yakai sa makaranta. ******************* Nnenna daren jiya koh lafiyayyen bacci bata samu ba wani irin tarine yake damun ta tanayi tana aman yawo mai yauki,haka ta tashi da safe da taren kamar zata mutu, koma bata fad'awa kowa ba, haka take ta fama da azaba. Tana tashi da safe koh aikin sharan ta kasa don tana farawa da kura ya shigar mata hanci ji tayi kamar numfashin ta zai d'auke. Hakan yasata kasa aikin gashi Dad bai kwana a gida ba sunje wani gari yad'a addinan su, gashi Abrahama bai isa ya shiga harkan ta mom nanan ba. Yau peace doya ta soya musu da miya, har Nnenna ta iba mom ta kwace ta mayar kitchen tace tunda batayi aiki ba bazata bata abinci ba, Allah sarki rabon Nnenna da abinci tun daren shekaran jiya amma jiya cur abinci mai nama ake koh ta iba ba ita keci ba. Ba yanda ta iyya haka ta sanya uniform nata ta d'au jakan ta datake jinsa yau ya mata mugun nauyi harda kule a ciki don har yanzun ba'asan tana zuwa makaranta da kule ba, fita tayi a gidan tana takawa da kafa ga kirjinta dake mata nauyi sosai ga tari ga nauyin jaka kallonta ma yau ya kara duhu duk da akwai glass a fuskar ta ga jiri dake dibarta, a haka take tafiya kad'an ta huta ta tafi kad'an ta huta. ******************** Lahab na sanya uniform abinci ma muzammil ya hanasa ci haka ya tura keyar sa har cikin mota suka wuce school. Suna isa office suka fara nufa sosai ya kara jaddadawa disple kula da lahab, tare da karban number sa, har class ya raka Lahab kafun ya tafi, yana tafiya lahab dake zaune a bench sai malamin su dake koyar dasu, ga disple a tsaye a window, shammatar su lahab yayi ya hau window d'aya kusurwar ajin ya dirka. Disple ma da gudu yabi ta cikin ajin ya hau window ya dirka yana bin lahab da gudu lahab na gudu, a haka suka soma zagaya makarantan sai da suka shigo tsakiyar makaranta disple ya fara cewa malamai a taro masa lahab, aiko take aka fara tare-tare sai lahab yazo saitin ka sai ya kauce yabi d'aya gefen, abinka da mayen ball, ana haka disple saura kad'an ya kama lahab kawai ya shammace sa ya kauce take disple ya fadi ji kake timmmm. Me yara dake classes nasu zasuyi in ba dariya ba, da gudu lahab yayi cikin gonaki, daidai wani bishiyan gadina yahau har reshen sama ya zauna. Disple na samu ya mike cikin burga ya bi bayan lahab cike da kunya, amma yayi iyya dubawan sa bai fahimce inda lahab ya nufa ba, dole tasa sa komawa cikin makaranta, amma yaki kiran muzammil kaman yarda sukayi duk abinda lahab yayi a kirasa a sanar dashi, gudun kar muzammil yaki kara masa kudi kamar yanda yace masa muddin ya saka lahab zaman class duk wata yana da 10k. Lahab kam gyara zaman sa yayi akan bishiya ya zaro wayar sa yana dannawa duk da yana jin yunwa amma baici ta sauka yanzun ba don get na school in d'aya ne. ************************* Nnenna ba ita ta isa school ba sai kusan 10 na safe, lokacin an fita break ma tana shigowa mai gadi ya hanata shiga duk yanda tayita masa magiya ki yayi karshe ma sai yaje ya kira principal, yana zuwa yace mata bafa zata shiga school in ba, haka tanaji tana gani aka hanata shiga. Zama tayi a bakin get na school in sai tari take da amai, wanda yasa maigadin bude karamar kofa ya lekota tambayar ta yayi lafiya koh dai bata da lafiya ne? Kuka ta sake tana had'asa da iyayen sa akan yabarta ta shiga ciki, amma yaki karshe dai daya tausaya mata yace zai barta amma karta shiga aji tunda dai principal ya hana bai kamata ya barta ba. Gyada masa kai tayi ta sabe jakanta tashiga cikin makarantan direct hanyar da ta saba zama watoh gonar makaranta gunta nufa a hankali take tafiya tana dafe kirjinta harta iso gonar, nusawa tayi ciki sosai har gindin bishiya ta zauna tana haki. Lahab dake saman bishiyar jin motse yasa sa kara labewa da kyau gudun kar a gane akwai mutum akai. Tari Nnenna ta fara da karfi tana amai ga kuka data fashe dashi na wahala, jin kukan mace da tari yasa lahab leko kansa ta gindin bishiyar, ga mamakin sa mace ya gani zaune ga dukkan alamu Christian ne kanta a duke tana amai. D'aga kafad'a yayi irin ba ruwan san nan yaci gaba da abunda yake, amma dai ya kasa samun nutsuwa jin yanda take tarin tana kiran jesus. Daga kan bishiyar yaji karan bugun bell da sauri ya duba agogon hannun sa 10:30 watoh sai lokacin aka koma break kenan, amma har lokacin Nnenna tari take tana haki kasa hakura yayi ya kama reshen ya dirko daga saman itacen. Nnenna dake duke koh d'ago kanta batayi ba saboda hakin da takeyi, binta da ido kawai lahab keyi zuciyar sa na wani irin wawan bugu, tsungu nawa yayi a gabanta,"ke baiwar Allah lafiya"? Koh D'agowa batayi ta kallesa ba, duk da taji mutum a kusa da ita harma magana yake cikin hausa don ita bajima take ba, amma halin da take ciki bazai bari ma ta saurare waye bane. "Ke ba magana nake miki bane kin mini banza sai kije shan ki mutu tunda baki san hanyar clinic b......bai karasa ba ya dakata saboda d'ago ido datayi ta kallesa, gaban sane ya fadi cikin tsananin tarin mamaki da Al'ajabi wannan kuma yaushe ta shigo school nasu ga kyaun ta har yanason yafi karfinta. Da sauri ya mike zai bar wajen, cikin gegeta Nnenna da numfashin ta ya soma d'aukewa ta kamo hannunsa, magana take son masa amma tari yaki barinta sai sarke ta yake, kara matsowa kusa da ita yayi shima yayi linkdown kamar yanda tayi, yana rike kafad'ar ta ganin jikinta sai bari yake,"wai lafiya baiwar Allah ba baki da lafiya bane? kije clinic mana" Baya baya tayi luuuu zata fadi, da sauri yasa hannu ya tarota ta fado a kirjinsa, bugawa kirjin nasa yayi da karfi fiye da da, wannan abune daya zo masa a bazata koh yace sabo a rayuwar sa, tunda ya girma yayi wayo koh wasa da mata bayayi bare ma har su taba masa jiki, inka cire muharraman sa, sai yau ga yar inyamurai dumu-dumu a kirjinsa. Hankalin sa a tashe ya soma girgizata jin gabaki d'aya ta sake numfashin ta baya fita, "nashiga uku kar yar mutane ta musu a hannuna" yana maganar yana mikewa tsaye ciccibar ta yayi da dukkan karfin sa ya wanshakalar da boronta da wayan sa ya goyata a bayan sa da gudu ya nufi school Area da ita. School clinic ya nufa da ita Allah ya sosa ma an koma break babu dalibai a waje, kuma hankalin su bai kawo kansa ba, da gudu ya shiga cikin clinic sai kwalawa Dr kira yake su karan kansu Dr da nurse hankalin su ya tashi ganin Nnenna koh motse babu. Kwantar da ita akayi a gado bayan karban ta da akayi a bayan lahab, a take likita ya rufu a kanta, pharmacy aka je aka karbo ruwa dasu Allurai shap-shap aka d'aura mata ruwa nurse tazo ta d'auki jinin ta zuwa lab. Lahab dai na zaune a Kan kujera a bakin d'akin ya zabga tagumin tausayin baiwar Allah nan kome ke damunta sai Allah, yana nan zaune sai ga principal ya shigo da sauri yana tambayar wace yarinya ce aka kawo, anan lahab ke sanar dashi shima bai santa ba. D'akin da take kwance ya shiga ganin Nnenna ne yasa sa fita da sauri yad'au waya ya kira mom, amma kusan 2 hour's babu wanda yazo daga gidan su Nnenna, karshe dai dole tasa principal d'auko wani Dr daga babban asibiti sukayi su biyu ana ta kokar tawa sai kusan 1 na rana Nnenna ta gane hankalin ta. Likitan ne ya fitoh a d'akin kallon lahab yayi dake zaune a kujera ya buga tagumi, kai ne ka kawo ta? "Yes sir nene ya jikin nata"? Da sauki iyayen ta sun zo ne? "ah ah sir principal yace ya kira mom nata amma har yanzun shuru ba wanda yazo shiysa ma na zauna nake jiran su zo kar na tafi a nemi wani abu bamai sayowa" Karka damu duk abinda za'a mata daman d'awainiyan makaranta ne, don daman a cikin school fees naku akwai kudin jinya, sannan ka sameni a office zamuyi magana. "Ok Lahan yace ya mikewa yabi bayan Dr. Suna zuwa office likitan ya masa nuna da kujera ya zauna, ba musu lahab ya zauna yana kallon likitan jin tambayar da ya jefo masa wai yasan Nnenna? "Gaskiya Dr ban santa ba" Ok koh ka san gidan su koh wani nata? "Gaskiya Dr ni ban taba kallon ta bama sai yau wani abun ne ya faru"? Gaskiya kam ga dukkan alamu yarinyar nan bata tare da iyayen ta. "amma likita meyasa kace haka"? Lahab dole nace haka kaga yarinyar ulcer ne ya kamata tana zama da yunwa, koh nace ana mata horo da yunwa don ba yanda za'ayi mutum najin yunwa yakicin abinci har ya masa illah haka, a kalla rabon ta da abinci Almost 24 hour's kenan, bataci kome a cikin taba kuma tana jin yuwa banda hakan ma, tana zama da yunwa sosai gashi ulcer ya mata mugun kamu. Lahab kam"subhanallah kawai yace yana mamaki ace yarinya za'a iyya sata a school nasu amma ace a binda zataci ma y gagare ta gashi daga gani kaga yar manya ba wahalalliya bace. "toh yanzun likita ya za'ayi principal yace min ya kira mom nata har yanzun batazo ba nima ina tantama anya a wajen iyayenta take kuwa"? Will yanzun dai zata iyya farfado wa zuwa karfe 3 koh 4 so anason daga ta tashi in aka zare mata ruwa a samu a bata wani abun taci mai d'an ruwa ruwa bamai nauyi sosai ba, don hanjin nata ya murde dole sai an samu abu mai sauki-sauki an bata daidai yad'an warware. Lahab dake sauraron sa yace "toh likita kamar me dame zan sai mata kake ga wanda ya dace taci" Eh kaidai abinda baida nauyi sannan baida yaji baida sanyi kuma baida tsami zaka iyya bata. Da sauri lahab ya mike ya fita a clinic in kama hanyar cafe yayi cikin hanzari jin ana kiran sallan azahar kawai saiya nufi masallaci Alwala ya tsunguna yake sai ga Rahab da mamaki yake kallon d'an uwan nasa har ya matsa kusa da shi, Lahab daman kana cikin school inne? "Oho shine amsar daya basa, yamike yayi cikin masallaci a ciki ma ya hadu da nabeel amma kamar bai gansa ba, ana idar da sallah ya nufi cafe hannu yasa a Aljuhu zai taba wayan da sai yaji wayam"subhanallah da sauri ya nufi gona yana Allah-Allah kar wasu sunje wajen sun kwashe masa waya a kasa. Aiko yayi sa'a kamar yanda yabar wayar haka ya dawo ya same sa harda jakan Nnenna da glass nata daya fadi, duk ya d'auko bakka jakan yayi yafi toh a wajen, direct cafe in ya wuce yana tura kofa suka had'a ido da Adewale dake zaune akan kujeran daining dake wajen shida nabeel, d'aga masa hannu kawai lahab yayi ya nufi wajen mai abincin. Ordern ferfesun kaza yayi sai fruit salad da kwai dafefe a take Away duka tare da ruwan gora mara sanyi, sai kuma yayi ordern doya dafeffe da zaici da miyan kazan shima. kudi ya biya ya karbi laidodin ga jakan makaranta a bayan sa, yazo zai fita a cafe in mikewa Adewale da Rahab sukayi sukabi bayan sa, da sauri suka tsaida shi suna tambayar sa lafiya laidodin hannunsa nan fa, ga jakan mata a kafad'ar sa bangaje su yayi ya wuce abinsa dukan su suka bisa da ido harya mule. Yana isa clinic in, direct dakin da aka kwantar da ita ya nufa yana d'aga labule idadunsa suka sauka akan ta, ita kadaice a dakin tana kwance akan gado tana bacci an cire mata takalmin kafarta aka bar socks, rigan ma an zare mata na uniform daga ita sai vest gabaki d'aya gashin kanta a wargaje sai fuskar ta dayayi fayau fari tas. A hankali ya karaso bakin gadon aje boron yayi a kasa sai abincin daya aje akan drower kusa da magangu nan ta, zuciyar sa na bugawa ganin ta a haka yasa sa d'aukar zanin gadon dake nade a gefe ya lulubawa kafafunta zuwa kirjinta ya kara gudun fankan sanin da yayi saboda zafine taima ba'a rufeta ba. Zama yayi a gefe koh abincin ya kasa ci, bayan awa d'aya likita yazo ya kara dubata sannan ya cire mata laidan ruwan dake hannunta. Sai kusan 4:30 har Lahab yaje sallan la'asar ya dawo ya zauna kafun nan Nnenna ta farka, Alhamdulilah tana farkawa bata farka da tari ba, a hankali ta bude idanunta tana yawo dasu asaman silif na dakin, ganin duhu-duhu take, hakan yasa ta taba idanunta taji ba glass da sauri ta fara yunkurin mikewa. Lahab dake zaune ganin ta farka kuma tana son tashi yasa sa mikewa da sauri ya iso bakin gadon yana mata sannu cikin turanci. Gyada kai kawai tayi bawai don tana kallon saba, harta mike zaune, yaye zanin gadon tayi ta zauna ta jingina da gini kafafunta na lilo a bakin gado, tare da dafe kirjinta jin har yanzun nauyi yake mata. "Sannu ya jikin naki" "A hankali a karon farko ta basa Amsa da sauki" Allah kara sauki yace, yayin da ita kuma tayi shuru batace ameen ba don ba haka ta saba ba. "Pls help me, ka bani glass nawa in yana kusa" Glass in ya d'auka ya mika mata hannu tasa a hankali zata karba by mistake hannunta ya taba hannun nasa da sauri ya sake glass in jin wani bakon Al'amari mai kamar shock da special feeling. Subhanalalh yace yana kallon glass in ganin fashewa yayi a tiles"am sorry wallahi glass in ya fashe fa"? "What kana nufin kace min Goggles ina ya fashe kenan? Shika d'aine dani fa haka kakeso na ringa tafiya bana kallo sosai" "Kiyi hakuri in aka sallame ki zan sai miki wani" "Toh kai wanene bansan kaba sannan nan inane na ganne akan gado gashi ina jin warin asibiti" "Asibiti na kawo ki baki da lafiya" Shuru tayi tana tunanin lokacin da take gindin bishiya tana tari tadai san akwai mutum agun amma batasan wanene ba, kallon sa tayi duk da bata kallon nasa tass sai yama-yama"ayya jakana"? "Karki damu jakanki na nan" ya karasa maganar da mika mata roban takeAway dake d'auke da ferfesun kaza. Hannu tasa ta amshi roban da sauri kuma ta maida masa tare da girgiza masa kai idanun ta na zubar da hawaye. Da mamaki lahab yace"menene tsoro kike zan cutar dake koh me"? Ah ah banason wannan ne kawai tana maganar tana nuna kwanon dake hannunsa da yatsa. "Ikon Allah bakin ce baki gani sosai ba? ya akai kika kare wa kwanon kallo har kikasan meke ciki"? Ai ina da hanci kuma yanajin kamshi, ta basa amsa tana mamakin kanta da surutun da take, kamar ba Nnenna Obinna ba. Aje roban yayi ya d'au na fruit salad ya mika mata da sauri ta karba ta soma sha a hankali bai wuce shukali uku tayi ba ta yamutsa fuska ta aje roban a gefe, shima bai tambaye taba illa bare kwai dafefen yayi kuda uku yasa a marfi ya aje mata a kan cinya. Komawa yayi ya zauna jin yunwa na neman hallaka sa bude doyan yayi ya zuba miyar kazan a ciki yadau shukali ya soma ci. Kukan kule da motsen da jakan Nnenna keye a kasan tiles ne ya basa mamaki, "ke menene a jakan nan naki"? Ya tambaye ta. "Oh my god cat nawa ne a ciki" Cat?yasake maimaita tambayar cikin mamaki yasa hannu ya bude zip na boron da sauri ya koma baya ganin kulentan nan haka kawai suna had'a ido yaji tsikar jikinsa na tashi gashi kulen shi sam baima masa kama da fuskan kulen gaskiya ba, ganin fuskar kamar zubin fuskar mutum. Da sauri kulen yayi jump daga cikin jakan ya fitoh da gudu yayi kan kwanon abincin lahab baki yasa zai d'auki naman, cikin zafin nama lahab yasa kafa yayi shoot dashi sai da ya had'asa da jikin ginin d'akin, wani irin kara kulen ya sake kamar ba kukan dabba ba ya fade tim a kasa, a take yamike kwance kamar wanda yayi dogon suma. Kara Nnenna ta sake tana kokarin sauka a gadon tana tambayar lahab meyake faruwa meya sami kiki. Kin magana lahab yayi ya barta tayita zagayen dakin tana neman kulen amma bata gane inda yake ba, kuka ta sake da karfi wanda yasa Nurse's dake zaune a station nasu sukayi saurin shigowa dakin suna tambayar lafiya? Itace ta basu amsa tana neman kulenta yayin da lahab ya koma yayi zaman sa yana cigaba da kallon abin al'ajabi koh yunwar da yake ji ma sai yaji bazai iyya cin abincin da kule yasa baki zaici ba. Da mamaki likita ya shigo yana kallon ta lallai jikin mara lafiyar mu yayi kyau harma neman kule take, ita dai batace kome ba sai da nurse ta d'auko kulen ta mika mata mata, tattabasa tayi sai kuna ta kara fashewa da kuka jinsa a longobe kamar sumemme. Lahab kam cikin jin haushi yace"Dr asallame mu kawai naga kamar taji sauki gashi yanzun kusan 5 ake nema na yamma " Ah ah lahab jikin dai da saura ka bari na d'aura mata karamin ruwa bazai wuce 1 hour ba. Ok kawai yace yana mikewa tsaye ya fita a dakin itama da taimakon nurse ta koma kan gado ta zauna, shinfid'a kulen tayi a gefe ta kwanta kusa da shi. Lahab na fita shop yaje ya sai mata sabon glass,yana dawowa ruwan na karewa bata glass in yayi ba musu ta karba cikin murna ta sanya a idanunta tana masa godiya. Sallamar su likita yayi lokacin 6 yayi na yamma ana ma shirin kiran mangariba gabaki d'aya hankalin lahab na gida yasan dai yau baisan wace karyar zai suburbud'a ba bare ma yanda ya ringa ganin call na jama'an gidan su, amma yayi biris bai d'auka ba harda na muzammil. Rigan ta Nnenna ta saka tare da d'aukar kulenta lahab yad'au mata jakan suka fita a d'akin shidai sai binsa take da kallo, koh ba'a fad'a mata ba tasan musulmine, koh yaushe ana sanar dasu musulmai mugaye ne, amma ita mutum biyu ta hadu dasu masu kyawawan halayya suna taimakon ta. Makarantan ba kowa shar kake ji sai maigadi hatta malamai babu. Haka sukazo suka wuce suka fita get, tsayawa sukayi a bakin kwalta lahab ya tsaida keke, tambayar Nnenna yayi don shifa har yanzun bawai sanin sunan ta yayi ba,"baiwar Allah wai a wani unguwa kike ne"? "Ka bar kudin ka kawai nagode zan iyya zuwa da kafa" "Oh lallai ki tashi daga gadon asibiti kice wai zaki taka, bawai fa kinji garau bane Dr yace gobe ma zaki amshi ruwa" "Nace ka bari zan iyya zuwa" "Mtwss kinsan Allah kina bata mini rai ki shiga keke mu tafi" Ba musu ta shiga ta zauna don daman karfin hali take kawai ba iyya takawar zatayi ba, shima shiga yayi tare da kallon mai keken"kaini GRA gidan mu xan kaiki tunda baki san gidanku ba"yace ma Nnenna. Da mamaki Nnenna ta kalle sa"a GRA kake"? "Oho bansani ba nima" "Am sorry nima unguwan mu kenan amma mu muna layi na biyu" Kala baice mata ba,itama shuru tayi mai keke sai tafiya yake, sunzo wajen round-about ga Go slow ya hade musu, gashi sai kiraye kirayen mangariba a ke hankalin lahab duk a tashe so yake ya samu sallah a gida, gashi sai kara cakud'uwa suke koh sunce zasu koma baya bazaiyu ba, gashi basu kusa da unguwan suba bare su taka da kafa Nnenna ma jikin nata kamar yanason tashi. Kallon ta yake tayi ganin itama gabaki d'aya hankalin ta na gefen da take ta kurawa waje d'aya ido, shima wajen ya kalla wani dattijo ne fari tass a kallah zai kai shekara 90 ya tsufa sosai ga idanun sa manya masu girma d'auke da kwayar ido sky blue sak irin na Nnenna a duke yake kamar mai kusumbi yana rike da sanda, fuskar sa d'auke da farin gemu babu digon baki haka ma gashin kansa,hannun sa rike da roban bara, irin tsofafun nan ne masu bawa yara tsoro da tsufar su. Had'a ido lahab yayi da tsohon ga mamakin sa kawai sai yaga tsohon ya nufo inda suke, da sauri Nnenna ta zabura ta juya ta kalli lahab suka had'a ido amma batace kome ba har tsohon ya kuda isa inda suke. Bara ya soma yi a saitin lahab yana abasa na Annabi,tun ma bai iso ba, hannu lahab yasa a Aljuhu ya zaro gudan 200 zai mikawa tsohon, da sauri Nnenna ta damko hannun sa cikin rawan murya tace"karka basa" "Akan me zakice karna basa" ? "Akan nasan wanene shi wallahi ka basa abin hannun ka sai kayi dana sani, dana sani mafi muni a rayuwar ka, bako yaushe kyautatawa wasu yake zama Alkhari ba" "Amma baki da hankali, oh haka akace muku a addinin naku bakyau kyauta"? Kaga Ina maka maganar gaskiya kana d'aukar maganar addini, wallahi ka kuskura ka basa abin hannun ka toh ina mai tabbatar maka ka shiga tarko, yau ka fara shiga rayuwa ta, ka shigone da kyautatawa da tausayi a gareni bazanso kaddarata ta shafe kaba karka basa kudin nan" Tsaki kawai lahab yayi yana mikawa tsohon daya iso kusa dasu kudin yana cewa,mu musulmai muna kyauta don Allah sannan babu abinda zai faru damu sai da izinin Allah, insha Allah Allah zai dubi niyata koma menene bazai basa ikon cutar dani ba..................... ✨Ruqeenjalal✨ *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki* Page 31&32 Bai idasa maganar sa ba Nnenna cikin zafin nama tasa hannu ta fizge kudin, cikin jin haushi lahab ya juya gareta"ke wai meye hakane? da babu kyau taimako da zan taimake kine da Allah ban kudi na"? Kin basa kudin tayi cikin jin haushi yasa hannnu zai fizge kudin da sauri Nnenna ta boye hannun ta mai kudin a bayan ta, hannayen nata duka biyu ya kama da karfi zai kwace kudin abu kamar kokowa har mai keke yasa baki su bari amma ina lahab naci na cinsa, sai da ya amshi kudin sa, juyawa yayi zai mikawa tsohon, amma me wayam babu kowa agun, bai kawo kome a ransa ba illah mutumin yayi wucewar sa. Nnenna dake rike da kulenta garin fad'a harta yarda shi a kasan keke, da sauri tasa hannu ta d'auke sa tana kallon lahab, shima kallon ta yayi irin kallo mai hararan nan"ke lafiya kike kallo na gashi ma tsohon ya tafi" Girgiza masa kai kawai tayi tare da nuna masa kulenta dake kwance kamar mara lafiya, da hannu cikin fuskan tausayi amma batayi magana ba. "Mtwss kuna da aiki a gabanku ace mutum ya kama kiwon kule, har makaranta Allah ya kaimu gobe kikazo da kulen nan insha Allah zan kai karanki wajen principal" Shuru ta masa again bata sake magana ba Shima gyara zama yayi ganin an sake hanya"don Allah mai keke kaja wuta sosai sauri muku" Kai d'an samari ba gudun da zan kara Ehen ga mangariba yayi har kana cewa na kara wuta? Ganin fa mai keken nan d'an jarabane yasa lahab yin shuru, ganin sai mita yake masa akan yace ya kara wuta. Ana kiraye kirayen Sallah Mangariba suka shigo GRA, har kofar gidan su Nnenna mai keke yayi packing bayan kwatance da ta masa na gidan nasu, sauka tayi a hankali jiri na ibarta ta dafe karfen get nasu a take karnu kan suka zaburo, ganin ta ya sasu komawa suka kwanta. Mikawa mai keken kudi lahab yayi shima ya sauka agun, jakan Nnenna ya d'auka ya rike, "muje koh"? Da mamaki tace" zuwa ina"? "Cikin gidan naku mana koh zaki iyya rikon jakan ne? muje nayi ma Mom naki bayani akan rashin cin abincin da bakiyi" Girgiza masa kai tayi tana mika masa hannu"ka bani jakana bani da mama, duk uwa baza'ace mata diyar ta ba lafiya taki zuwa ba tun safe, ni nan ba gidan mu bane" "Da gaske kike? toh meyasa baza kije gidan kuba" "Kaga ka bani jaka na kawai" Mika mata jakan yayi daker ta bakka sa a bayan ta ta juya tana kallon sa a sanyaye tace" Thank you for Everything" Murmushi kawai yayi yana shafa kansa, itama batajira amsar saba ta bude get in ta shiga har tayi nisa taji yace mata"bakiji ba"? Juyowa tayi tana kallon sa amma batace kome ba. "Wai nace baki fad'amin sunan kiba"? Kai tsaye tace" Nnenna Obinna" Ya mutsa fuska yayi cikin raha yace, Labiba nice name" Waro ido tayi jin sunan daya kirata dashi, hannunta ta ware Alamun tambaya. Shima girgiza mata kai yayi hade dace mata"ki tabbatar kinsha maganin da Dr ya bamu yana jakan ki, sannan ki daure kici abinci ki huta" Juyawa kawai tayi ta nufi falon duk yana tsaye har ta bude ta shiga, ganin ta bace masa yasa sa juyawa shima ya d'auki hanyar layin su, zuwa lokacin an shiga sallan mangariba hakan yasa sa yin Alwala ya shiga masallaci kawai bai isa gida ba. Ana idar da sallah yabi 'yan gidan su zuwa cikin gida, zama sukayi a falo abba ya kallesa da kyau, lahab ina ka shiga yau? "Yaya ina makaranta ne"? Wani irin makaranta lahab bayan 'yan uwanka sun dawo makaranta tun 3 na yamma, kai sai 6:00 sannan kace mini makaranta ka fitoh? "wallahi yaya ka tambaye Rahab yau a school na wuni fa" Muxammil ne ya tare abbu da sauri yace, Rufe min baki inka wuni a school sai akace kayi mangari ba ashan, ya za'ayi mutum na makaranta jakan sa ya dawo gida? "Kash sai ma yanxun ya tuna da zancen school back nasa, kuma yasan Rahab ne kawai zai kawo masa" uhmm yaya nina bawa Rahab ya kawo mini nad'au littatafai a library" Allah ya shirye ka lahab tashi kaje. Mikewa yayi ya wuce dakin, wanka yayi ya sauya kaya, ya nufi daining yau kam harda shi ake dinner, umaimah ke raba abincin wa kowa, harta zo kan lahab tuwon shinkafa ne miyar Shuwaka ga kifi manya manya na yawo a ciki,tana gama zuba masa a hankali ya gusiri tuwon ya tallah miya harya sa tuwon a baki sai ya dakata yana tunanin Nnenna da yanzun ta fad'o masa a rai. Koh tashi abinci yanzun?koh tasha maganin ta? koh me take iwar haka Allahu Alamu? sosai yayi zurfi cikin tunanin moment nasu na yau, ji yayi an kwace tuwon hannun nasa, da sauri ya d'aga kansa ya kalli wannan, Rahab ne dake zaune a gefen sa sai jama'ar daining in da suka bar cin abinci gabaki d'ayan su suka zuba masa ido suna mamaki yau Rana ta farko kenan da suka ga Lahab yayi zurfi haka a tunani, don shi kome nasa a watse yake baya ajewa kansa damuwa a xuciya gashi yau sunga sabanin hakan. Binsu da kallo shima yake kamar yanda suke kallon sa har idanunsa suka sauka akan uzaifa, cikin eiiii eiiina yace"kai menene haka? ka wani zubomin ido kaci abincin ka mana maye" Muzammil ne ya karbi zancen, ba maye zaka ce ba mayu zaka ce, watoh uzaifa ne marainin wayon ka shiyasa ka yabashe, tukunna ma tunanin uwar me kake? Tambaye sakam koh wani abun ya b'aro koh wani masifan ya jawowa kansa waya sani, mamu tace cikin harare harare. Addayiya dake xaune a falo tana jinsu da sauri ta mike tsaye, Keee halima masifa ya kare akan ki banda Amanar umar babu abinda zai faru sai Alkhari aniyarki ya biki mai mugun baki kawai. Don Allah ya isa haka addayiya ke kuma Halima bazaki kama kanki ba ina hanaki shiga abinda ba ruwan ki kinayi koh? wata rana zakiga ba daidai ba, abbu dake wanke hannunsa yace yana mikewa a daining in. Lahab kam abincin ma kasa ci yayi haka kawai yaji bazai iyya ciba batare da yasan halinda Nnenna ke ciki ba, kudur tawa yayi a ransa yana fita sallan isha zai kwace jiki yayi layin nasu, ana idar da sallah har yayi nisa yaji Muzammil na kwala masa kira ji yayi kamar ya zura a guje, wallahi da rana ne baxai tsaya ba gudun sa zaiyi, dawowa baya yayi har inda muxammil in ke tsaye a bakin get. Lahab yawon dare ka fara ne koh me? Girgixa kai yayi cikin haushi yace"Adewale ne ba lafiya shine xanje na duba sa" Makarya cin banza Adewale dana gani da yamman nan a hanyar filin ball, nuna sa yayi da yatsa, wallahi lahab ina tausayin ka baka tausayin kanka, kafun na rufe idona na bude ka bace mini da gani. Da sauri lahab yayi cikin gidan direct kan kujeran babban falo yahau ya kwanta, likimo yayi kawai yama rasa meke masa dadi yau jinsa yake wani incomplete, kamar yanda aka saba duk dare za'a zauna a falo babba ana hira kafun aje a kwanta sai asha fruit, yauma hakan take d'aya d'aya ake zuwa har aka cika falon kowa na abinda ke gaban sa, lahab na kwance ya juyawa mutane baya yana fuskantar kujeran harde kafafun sa yayi waje daya yayi filonda hanneyen sa. Yau fa jama'an gidan na ganin sabon salo agun lahab, nitsuwar sa na yau ya dame su koh don bai saba nutsuwar bane, koh baida lafiya lahab baya nutsuwa waje d'aya. ******************* Nnenna na shiga falon su taci karo da jennifer dake tsaye a bakin window sai mom dake kan kujera koh kallon su bata kara ba tayi hanyar dakin ta, dukan su da tsaki suka rakata. Tana shiga dakin daman ji take kamar xata mutu da sauri ta kwanta akan gadon koh uniform bata cire ba, kulen ma ajesa tayi duk da shima ba lafiyar bane dashi lahab ya halbi besa, har kusan 9 na dare tana kwance bata koh rimtsa ba gashi bakin ta ba dadi maganin ma bata sha ba, maganar lahab ne ya fado mata, ta mike da sauri towel nata ta zaro a saman kofar toilet ta shiga wanka, ta dauro towel in ta fitoh tare da jika kayan makarantan ta a boket Allah ma yasa kala uku aka dinka mata. Koh mai bata shafa ba ta bude wardrop na kayan ta, wani siket pencil mai tsagu a baya ta saka sai riga mai yale-yale, socks ta sanya a kafarta ta fitoh daga d'akin, tafiya take a hankali-hankali harta fitoh falo amma yanzun babu kowa a ciki. Kitchen ta shiga bubude kulolin tayi ta mayar ta rufe, tare da jan d'an karamin tsaki, tukunya ta d'auka ta tare ruwa ta d'aura a gas, binciken liptop tayi ta zuba a ciki sai sugar ta rufe, tana tsaye a wajen har ya tafasa juyewa tayi a cup tasa shukuli, d'auka tayi ta nufi barin kitchen in. Tsayawa tayi ganin jennifer a bakin kitchen in sai girgiza kwankwaso take cikin masifa ta soma magana,wannan gidan ubanki ne koh?da zaki dafa abinda kika ga dama, oh watoh a binda aka dafa bai miki ba shine zaki dafa naki daya ke ubanki ke cefene. Rana Nnenna ya baci sosai amma sai kokarin danne wa take ba tare da ta kula Jennifer ba ta nufi gefen ta zata wuce, shan gaban ta jennifer ta sake tare dasa hannu zata kwashe cup na tie in, jan cup in tayi Nnenna kuma taki sakewa, kara ja da karfi jennifer tayi, a zuciya Nnenna ta sake mata cup in, a bazata kawai ruwan tie tafasheshe ya watsu mata a kafafu, abinka da jikin mai shafe-shafe take ta sake kara da karfi, wanda yasa mom da sarah rugowa daga d'aku nan su suna tambayar meya same ta. Nnenna gefe ta koma ta tsaya batace kome ba, cikin kuka jennifer kece musu Nnenna ce ta zuba mata ruwan zafi, a hassale mom ta nufe Nnenna cikin zafin Rai zata kwad'a mata mari, cikin zafin nama Nnenna ta cafke hannun ta cikin xafi tace"karki kuskura kice zaki sa hannun ki a jikina don abin bazai miki kyau ba. Tana gama maganar ta hurgar da hannu mom ta fita a kitchen in, gabaki d'ayan su da ido suka bita suna mamakin wannan Al'amari daman Nnenna nada bakine haka?ake ganin ta salaha. Peace na tsaye a kofar dakin ta tana sauraron duk abinda ke faruwa amma bata iso cikin kitchen in ba, Nnenna ma yi tayi kamar bata san da mutum a tsaye ba, dakin ta shiga ta maida kofa ta rufe harda makulli. Kwanciya tayi tana jin babu dadi na missing in lesson data yi yau, jakan ta dake gefe ta jawo takardun ta, soma cirewa tayi 1 by 1 tana ajewa akan gado da niyar bitan su don ta gaji da zaman kad'aici,hannun ta ta dakatar dake cikin jakan jin ya tabo laida, jawo laidan tayi tana kallo da mamaki glass nata ta gyarawa zama, tana bude laidan ganin laidan kaman na wajen sai da kayan ciye-ciye, bude laidan tayi taga laida babba a ciki bude laidan tayi tare da ware ido, cake ne babba d'an madaidaici Amma baikai na birthday girma ba, sai d'an card a gefe a manne. Bude card in tayi letter ne Lahab ya bar mata, anyi rubutu mai shegen kyau da black pen " FOR YOU"maimaita wa tayi for u, b'are laidan tayi ta aje cake in akan gado, ta d'au wukar dake makale a gefen ta yanka, tana d'aukan kad'an-kad'an tana ci sosai cake in ya mata dadi bana wasa ba, tana tsaka da ci ta tuna da kulenta yayyanka masa tayi ta aje masa amma kememen yaki ci, har tayi mamakin hakan amma ta basar. Ta samu taci cake in da yawa sauran ta lulube sa da laidan sa ta aje a cikin drower, wanke hannunta tayi ta shiga toilet ta taro ruwa a pampo tasha maganin dashi, kwanciyar ta tayi hade da kashe wutar ta lumshe idanun ta a hankali har bacci ya d'auke ta. ******************** Lahab kam jin surutun su ya ishesa yasa sa mikewa da sauri yayi cikin d'akin, kwanciya yayi kawai yama rasa meke masa dadi, kara wayar sa yayi ya d'auka ya duba, ganin Adewale ne yasa sa daukar wayar ya kara a kunnen sa" hello guy" Hiii ykk? "Normal friend yasu mom" Klau suke, yau an tashi school mun nemeka bamu ganka ba, gashi kuma har geto munje shuru? "Oh naje wani waje ne" Ina kenan? "Mtwss rabu dani dasa idon nan naka ka isheni" Amma dai Lahab bawai fad'an ku da nabeel bane yasa ka ware mu gefe bako? haba lahab ban sanka da riko ba bayau kuka fara samun damuwa ba, daga karshe kaje ku sasanta amma naga koh damuwa da fad'ar ma bakayi ba? "Kaga Ade ina da abubuwan yi da yawa ka barni naji da abinda ke damuna karka karamin zafi kan zafi haka kawai"? Allah baka hakuri daman kawai na kirane naji inda ka shiga, gobe in zaku school na biyo kane mu wuce? "no ku tafi a binku" Kashe wayar kawai Adewale yayi bai sake cewa kome ba. Lahab ma kwaciya yayi har Rahab ya shigo duk yana kwance, gefen sa yazo ya zauna hade da da zuba tagumi yana kallon lahab. "Kai lafiya kazo ka zauna ka zubamin na mujeya"? Hmmm lahab ba dole na zuba maka ba, yau gabaki d'aya naga kamar wani abu na damunka ne? Shuru lahab ya masa sai surutu yake amma lahab bai kulasa ba, harya gaji don kansa ya koma ya kwanta. Bashi ya samu bacci ba sai kusan 1 na dare ya samu bacci ya d'auke sa. Tsaye yake a cikin wani gursungumin daji mai d'auke da manyan itatuwa hade da korayen ganye masu ban tsoro da duhu, ga kogi a gaban sa mai girman gaske yayin da ruwan cikin sa ya kasance jaaaaa kamar jini,da karfi yaji an hankad'a sa cikin ruwan cikin ikon Allah ya kauce bai fadi ba ya fadi a gefe. Kallon bayan sa yayi don gani wanene ke son turasa ruwa,wani mummunan hallitane sanye da kaya jaaajazur koh kyaun gani bai dashi, hannu yasa zai kamo sa da gudu ya mike tsaye ya ruga da gudu yayi cikin dajin, Wannan mummunan halintan ya rufa masa baya gudu yaje yana ganin dajin na jujjuya masa, ga wasu manyan kuleluka bakake dake takawa hallintan nan baya, wasu na saukowa daga saman itatuwa suna kai masa hari yana kaucewa. A kallah yakai 2 hour's yana gudun kafun yaja birki ganin tsoho mai farin furfura a gaban sa tsohon da in bai manta ba ya hadu dashi kafun nan, tsayawa yayi yana dariya tare da nuna sa da hannnu sai kuma ya hurgar da sandan sa, ya wani nannade jikin sa ya zama mukeken maciji ya nufi kansa shima. Riki cewa yayi ya rasa ina zai nufa gaba maciji, baya kuma hallintan nan da kulelu kan nan suna kara kusanto sa, tsungunawa yayi kawai ya kama kansa yana Ambaton innalilahi wa'inna'ilaihi raji'un. D'aga kansa macijin nan yayi zai sare sa, a take ta bayyana cikin shiga na mayaka, wukar dake hannun ta ta d'aga da karfi zata sare kan macijin, kafun wukar ya same sa tuni ya bace batt. Da sauri ya d'ago kansa jin hannun mutum a kafad'ar sa ya taba sa, zaro ido yayi ganin wance ke gaban sa, cikin tsawa take ce masa"ka tashiiiiiiiiiiii ka tashiiiiiii naceeeeee makaaaaaa kaa........... *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki* *Kuyi hakuri babu yawa sai in Allah ya kaimu gobe da rai da lafiya yau ma da yamman nan na daure nayi typing duk saboda far in cikin ku don naso sai gobe zanyi* Page 33&34 Ka tashiii naceee???ta yi maganar tare da dafa kafadunsa duka biyu ta girgiza sa da karfi. Hasbinallahu wani'imal waken shine abinda lahab ya furta lokacin da ya farka daga wannan mumunan mafarki mai cike da rud'ani, abinda Nnenna tace masa ne a cikin keke napep ya dawo masa akan karya baiwa tsohon nan sadaka toh wanene shi wannan tsohon, dahar yayi mafarkin sa yau kai akwai dai abu a kasa. Jin motse ta wajen window yasa shi lalubar wayar sa da sauri ya kunna tare da haska wa, baiga kowa ba sai glass in windon su dake bude wandan yake da tabbacin rabon su dasu bude glass harya manta,mikewa yayi da sauri ya isa wajen windon zai rufe, amma me? yana isa ya hango kule baki a tsaye a bakin window, gaban sane ya fadi amma bai wani nuna razana a fili ba, don tsoro na d'aya daga cikin abinda yasa ake galaba akan mutum. Window ya rufe da bismillah ya sake labule, jima yayi baccin ma ya daina ji kwata kwata, toilet ya bude ya shiga Alwala yayi yazo ya shimfida darduma, lokaci ya duba karfe biyu ne daidai na dare, tada sallah yayi. Rahab da fitsari ya ta dashi mikewa yayi ya sauka a katifar sai kuma ya tsaya da mamaki ganin Lahab na kiyamun laili yau harda kiyamun laili?Shiga toilet in yayi yayi uzurin sa ya dauro Alwala shima yazo ya tada sallan. Raka'a shida yayi ganin sallan lahan in bana karewa bane yasa sa sallame wa ya koma katifar sa ya kwanta abinsa. Sallah lahab yayi tayi har kusan hudu na asuba kafun ya sallame, yana idarwa ya saka sports wear nasa ya Riga uncle FIta abinsa, jikin sa yau duk a sanyaye na mummunar mafarkin da ya Afku jiya abin ya tsaya masa a rai. Ga kuma tsananin son sanin halinda Nnenna take ciki, gangarawa layin su yayi har kofar gidan su Nnenna, ya tsaya yana tsumayin zata fito ya ganta. Har kusan Biyar amma fara kiraye kirayen sallan asuba yana tsaye a kofar gidan su har lokacin, kamar mafarki ya hange uncle muzammil ya nufo Layin, ai da gudu ya kara gaba ya sake zagayawa yayi Layin su. Jan birki yayi a kofar gidan su yana haki don ba karamin gudu yasha ba, amma kuma duk da haka yaki shiga gidan sai da ya bari muzammil ya shigo Layin kuma ya tabbatar ya gansa kafun ya tura kofar ya Shiga hankalin sa kwance. Tura kofar falon su yayi cikin Sauri ya Shiga falon direct kofar sashin su ya nufa yana Shiga dakin ya tadda lahab na kokarin Sanya jallabiya a jikin sa. Jin mutum ya shigo dakin bako sallama yasa Rahab saurin juyawa, lahab INA ka shiga da asuba uncle yazo Neman ka? "Kala lahab baice masa ba don shi a ganin sa manna masa hauka Rahab yayi ya zai gansa da Mayan sport kuma yana tambayar sa INA ya fito, shiyasa baice kome ba kawai ya wuce bayi abinsa wanka yayi yayi alwala yazo ya zura kayan ya wuce masallaci. Bayan sun idar da sallah gabaki dayan su yauma Kamar kullum Suka jero a jere xuwa cikin gidan,gabaki dayan su dakin Addayiya Suka shiga Suka gaidata sannan kowa ya wuce dakin sa zai d'an kwanta daidai lokacin fita sun dan rintsa. Kasan cewar gogoji(Mai aiki)Bata dawo aiki ba har yanzun don abbu yace ta Bari har d'anta ya samu cikekkiyar lafiya tukum,dole tasa mamu da ummu Suka Fara shiga kitchen da kansu, Kuma yau girkin ummu ne shiyasa ta shiga kitchen bayan idar da sallan asuba. Lahab dakin su ya shiga shida dan uwan sa, harya kwanta a katifar sa da sauri ya Mike ya fita a dakin,Rahab Kam da Ido ya bisa ya rasa meke damun dan uwan Nasa ba, daga jiya xuwa yau duk yabi ya susuce baida cikekkiyar nutsuwa Kamar yanda yake, duk da Mai rawan Kaine Amma wannan azarbabin NASA yafi nada yawa. Shikam lahab Yana fita a dakin kitchen ya wuce ya tura kofa ya shiga, ganin ummu a ciki yasa Shi tsayawa Shi baiyi abinda ya kawo Saba Shi bai fita ba. Ummu Kam ganin ba gai data zaiyi ba yasa ta watsa Masa mugun kallo cikin Jin haushin sa, da Kuma haushin kin dauko wata Mai aikin da abbun yayi gashi su umaima kiwiya ne dasu dakin aikin asuba sam,Kai lafiya kazo ka tsayamin a gaba Kamar an baka sallahu Akaina? Dan tsotsa Kansa yayi sai Kuma ya jingina da jikin kitchen in cikin murmushin Nan nasa maikyau ya bude Baki ya Soma mata magana"Aunty me ake girka Mana ne yau munji dadin mu"? Wani shegen kallo ummu ta Masa irin kallon Nan na ka Raina mini wayo cikin haushin tace"Kai da Allah gafara mini anan kullum da ake girki baka taba tambaya ba sai yau Don Neman iyayi kome? Cikin dariya-dariya na wuce haushi lahab ya kamayi"Haba Big aunty daga tambaya sai kuma ki sauke a kaina naga dai bani nakar zomon ba rataya aka bani"? Kala batace masa ba ta cigaba da aikin ta Shima bai sake magana ba ya wuce cikin store Nasu yana tunanin shin mai ya dace ya dafa mata kome tafi so? don shi gaskiya ya shiga damuwa sosai na ciwon ulcer nan nata ace kamar Nnenna da irin gidan da take ciki da gatan ta, ace yunwa na Neman kashe ta a banza, tunawa yayi Mara lafiya yafison abun kwadayi-kwadayi hakan yasa sa d'aukar indomie manyan laida guda biyu sai kwai biyar dasu vegetables. fita yayi a store hannun sa sheke da kayan girki a basket, ajewa yayi yana kallon ummu dake ta kallon sa kamar ta samu madubi ganin sa da kaya Niki naki sai dai batace kome ba ta kauda kanta. Shima bai mata magana ba ya nufi wankakun bujuwa dake sit nasu ya dau daya sai kuma ya tsaya tunawa da yayi baisan ma ta ina zai fara ba, gashi koh zai mutu ummu bazata taimake saba. Aje bujuwan yayi da sauri ya fita a kitchen in, ya nufi falon ba kowa sai mai aikin share share dake ta fama, kofar dake gaban kofar sashen su ya tura yasa kai, wow masha Allah falo ne mai kyau da kayatar wa kamar Nasu, sai dai banbancin abin ado. daya cikin kofofin dake cikin falon ya nufa harya kama zai bude sai kuma ya daga hannunsa a hankali yayi knocking in kofar har sau uku kafun yaji muryar zulaihar cikin muryar bacci tana tambayar wanene? kin amsa mata yayi don yasan mundin suka San shine bazasu bude ba cigaba yayi da bugawa. Cikin dakin kam muneera ne ta Mike zaune cikin bacin rai jin sai bubuga kofar ake an hanata bacci gashi xulaihat taki bude kofar, kallon ta tayi cikin masifa tace, ke zulaihat don Allah tashi kije ki bude kofar nan an hanani bacci? Cikin haushi zulaihat ta mike don harga Allah daker ta samu bacci ya dauke ta koh minutes biyu batayi ba sukaji bugun kofar, tana isa kusa da kofar hannu tasa da Sauri ta bude jin bugu ake kamar za'a balla musu shi. Ja da baya tayi ta rike Baki again, tana bin lahab da kallo don koh ba'ace ba tasan lahab me xaiyi irin bugun kofar tasan ba rahab bakam. Murmushi ya sakar mata ya cusa Kansa a dakin kamar zai bangajeta ya ratsa gefen ta ya wuce, kallon muneera yayi dake kwance alamu ma ya nuna tun daren jiya bata tashi ba sai yanzun kuma ta koma"muneera muneera" Mikewa tayi zaune ciki hade rai take kallon sa da mamaki ganin sa yau a dakin su, menene uncle da asuban nan don Allah ka bari, koma menene inna farka sai naji. Jin amsar da ta bass yasa shi shammatar ta da Sauri ya fizgota gabaki dayan ta daga kan gadon, yana Jan hannunta kafun ma ta Ankara har sun Fita a dakin, ganin hakan yasa zulai hanzartawa ta maida kofar ta rufe harda sa sakata ta koma ta kwanta. Cikin Bacin rai ta fizge hannun ta, wai me hakane uncle banson wulakanci fa wallahi zan had'aka da uncle muzammil? Hada fuska yayi jin abinda tace cikin masifar sa da yake ta kokarin dannewa yau, don shi maganar mafarkin nan nasa ma harya tattara ya watsar Sanin da yayi mafarki ba gaskiya bane, kuma baison sawa Kansa tention a banza. 'Yauwa bondin ummu so nake ki taimaka kimin girki kinji"? Wani kallon uku saura ta masa, uncle yau cewa akai baza'ayi girki bane kome? kuma ni dai gaskiya bana Shiga kitchen da asuba kuma ma bacci nake ji wallahi rabu dani, ta karasa maganar tana kokarin juyawa. Hannu yasa ya sake fusgota domin yanzun ransa ya soma baci, da don baison zuwa gun mai shayi ba da wajen zaije yasai abinsa ya huta da takaici, kuma yasan muneera da ban haushi take amma ya Santa da shegen son yawo kamar masifa, rage murya yayi a hankali yace"ke wawuya yau kwad'ayin indomie nake kuma so nake me ki dafamun da kanki, inna dawo makaranta Zamu fita tare dake yawo" Washe Baki tayi kamar gonar auduga cikin farin ciki tace da gaske uncle zamu fita zaka kaini gidan zoo da wajen shakatawa? "Kwarai ma kuwa muneera harda ice cream zan sai miki kisha a gun" Wani tsalle ta daka da Sauri ta nufi kitchen shima ya Mara mata baya, suna Shiga, ummu kam kala batace ba kamar d'azun sai aikin ta take duk da ta cika da mamaki amma batayi magana ba. Nunawa muneera basket in yayi ya nemi waje ya zauna, yana kallon ta harta gaba dafa indomie da vegetables ga kwai data soya a gefe, ummu ta dade da FIFA, ganin itama miners ta kusa kammala wa yasasa mikewa ya Shiga store dake manne a kitchen in ya dauko roban takeaway, yazo ya juye indomie a dayan har sai da ya cika tam kafun ya rufe, haka d'aya roban ma ya zuba kwai soyayyan a ciki sai dan karamin flask mai d'aukan kofin shan shayi biyu a ciki, na Silva ne ya zuba coffee a ciki ya rufe, laida fari mai kyau na shopping ya dauka ya Jere abubuwan a ciki harda cups da spoon ya dauka yabar kitchen in. dakin su ya Shiga a gurguje ya kalli agogon dake like a bangon ganin 7:00 yasa sa aje laidan da Sauri ya nufi toilet, kama kofar yayi zai bude yajisa a rufa, tsaki yaja jin saukar ruwa alamu wanka Rahab ya Shiga, tsabar sauri da yake yau yana Allah Allah ya bar gidan kafun Nnenna tabar gidan su. ***************** Ta bangaren Nnenna Bata fargaba sai kusan shida na safe,mikewa tayi a hankali ta yayi blanket in dake jikin ta cikin natsuwa ta same kafafun ta izuwa Kasan tiles in, mika tayi sai kuma ta mike ta nufi toilet wanka tayi ta fitoh, jikin ta daure da towel fari, fuskar ta Sam babu walwala ga wani irin kasala dake damun ta da mutuwar jiki stool na mirror ta jawo ta zauna tana mai kallon kanta a madubi, sai kuma ta kalli hannun ta dake d'auke da Allurar ruwa. Murmushi ta sake data tuna Da yaron jiya daya taimake ta gashi koh sunan sa bata rike ba, drowa ta bude ta dauko Cake in jiya, yaye laidan tayi a hankali tasa hannunta ta yanko kad'an tasa a bakin ta tana taunawa, fuskarta dauke da murmushi ta wani lumshe ido, ada ta d'auka musulmai mugayen mutane ne kamar yanda takeji a kauyen su amma ta hadu da mutane uku masu kirki Wanda hakan ya tabbatar mata ba duka bane aka taru aka lalace ba. Da sauri ta ware idanun ta jin an sa makulli ata wajen kofar an murda mikewa tayi da Sauri jin yanda aka bangado kofar, bata kara tsinkewa ba saida taga mutanen da suka shigo Wanda koh ba'afada mata ba tasan babu imani a fuskar su kuma ba lafiya or kawo zuba, jiki na bari tace policeeeeeeee *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki* *Kuyi hakuri babu yawa sai in Allah ya kaimu gobe da rai da lafiya yau ma da yamman nan na daure nayi typing duk saboda far in cikin ku don naso sai gobe zanyi* Page 33&34 Ka tashiii naceee???ta yi maganar tare da dafa kafadunsa duka biyu ta girgiza sa da karfi. Hasbinallahu wani'imal waken shine abinda lahab ya furta lokacin da ya farka daga wannan mumunan mafarki mai cike da rud'ani, abinda Nnenna tace masa ne a cikin keke napep ya dawo masa akan karya baiwa tsohon nan sadaka toh wanene shi wannan tsohon, dahar yayi mafarkin sa yau kai akwai dai abu a kasa. Jin motse ta wajen window yasa shi lalubar wayar sa da sauri ya kunna tare da haska wa, baiga kowa ba sai glass in windon su dake bude wandan yake da tabbacin rabon su dasu bude glass harya manta,mikewa yayi da sauri ya isa wajen windon zai rufe, amma me? yana isa ya hango kule baki a tsaye a bakin window, gaban sane ya fadi amma bai wani nuna razana a fili ba, don tsoro na d'aya daga cikin abinda yasa ake galaba akan mutum. Window ya rufe da bismillah ya sake labule, jima yayi baccin ma ya daina ji kwata kwata, toilet ya bude ya shiga Alwala yayi yazo ya shimfida darduma, lokaci ya duba karfe biyu ne daidai na dare, tada sallah yayi. Rahab da fitsari ya ta dashi mikewa yayi ya sauka a katifar sai kuma ya tsaya da mamaki ganin Lahab na kiyamun laili yau harda kiyamun laili?Shiga toilet in yayi yayi uzurin sa ya dauro Alwala shima yazo ya tada sallan. Raka'a shida yayi ganin sallan lahan in bana karewa bane yasa sa sallame wa ya koma katifar sa ya kwanta abinsa. Sallah lahab yayi tayi har kusan hudu na asuba kafun ya sallame, yana idarwa ya saka sports wear nasa ya Riga uncle FIta abinsa, jikin sa yau duk a sanyaye na mummunar mafarkin da ya Afku jiya abin ya tsaya masa a rai. Ga kuma tsananin son sanin halinda Nnenna take ciki, gangarawa layin su yayi har kofar gidan su Nnenna, ya tsaya yana tsumayin zata fito ya ganta. Har kusan Biyar amma fara kiraye kirayen sallan asuba yana tsaye a kofar gidan su har lokacin, kamar mafarki ya hange uncle muzammil ya nufo Layin, ai da gudu ya kara gaba ya sake zagayawa yayi Layin su. Jan birki yayi a kofar gidan su yana haki don ba karamin gudu yasha ba, amma kuma duk da haka yaki shiga gidan sai da ya bari muzammil ya shigo Layin kuma ya tabbatar ya gansa kafun ya tura kofar ya Shiga hankalin sa kwance. Tura kofar falon su yayi cikin Sauri ya Shiga falon direct kofar sashin su ya nufa yana Shiga dakin ya tadda lahab na kokarin Sanya jallabiya a jikin sa. Jin mutum ya shigo dakin bako sallama yasa Rahab saurin juyawa, lahab INA ka shiga da asuba uncle yazo Neman ka? "Kala lahab baice masa ba don shi a ganin sa manna masa hauka Rahab yayi ya zai gansa da Mayan sport kuma yana tambayar sa INA ya fito, shiyasa baice kome ba kawai ya wuce bayi abinsa wanka yayi yayi alwala yazo ya zura kayan ya wuce masallaci. Bayan sun idar da sallah gabaki dayan su yauma Kamar kullum Suka jero a jere xuwa cikin gidan,gabaki dayan su dakin Addayiya Suka shiga Suka gaidata sannan kowa ya wuce dakin sa zai d'an kwanta daidai lokacin fita sun dan rintsa. Kasan cewar gogoji(Mai aiki)Bata dawo aiki ba har yanzun don abbu yace ta Bari har d'anta ya samu cikekkiyar lafiya tukum,dole tasa mamu da ummu Suka Fara shiga kitchen da kansu, Kuma yau girkin ummu ne shiyasa ta shiga kitchen bayan idar da sallan asuba. Lahab dakin su ya shiga shida dan uwan sa, harya kwanta a katifar sa da sauri ya Mike ya fita a dakin,Rahab Kam da Ido ya bisa ya rasa meke damun dan uwan Nasa ba, daga jiya xuwa yau duk yabi ya susuce baida cikekkiyar nutsuwa Kamar yanda yake, duk da Mai rawan Kaine Amma wannan azarbabin NASA yafi nada yawa. Shikam lahab Yana fita a dakin kitchen ya wuce ya tura kofa ya shiga, ganin ummu a ciki yasa Shi tsayawa Shi baiyi abinda ya kawo Saba Shi bai fita ba. Ummu Kam ganin ba gai data zaiyi ba yasa ta watsa Masa mugun kallo cikin Jin haushin sa, da Kuma haushin kin dauko wata Mai aikin da abbun yayi gashi su umaima kiwiya ne dasu dakin aikin asuba sam,Kai lafiya kazo ka tsayamin a gaba Kamar an baka sallahu Akaina? Dan tsotsa Kansa yayi sai Kuma ya jingina da jikin kitchen in cikin murmushin Nan nasa maikyau ya bude Baki ya Soma mata magana"Aunty me ake girka Mana ne yau munji dadin mu"? Wani shegen kallo ummu ta Masa irin kallon Nan na ka Raina mini wayo cikin haushin tace"Kai da Allah gafara mini anan kullum da ake girki baka taba tambaya ba sai yau Don Neman iyayi kome? Cikin dariya-dariya na wuce haushi lahab ya kamayi"Haba Big aunty daga tambaya sai kuma ki sauke a kaina naga dai bani nakar zomon ba rataya aka bani"? Kala batace masa ba ta cigaba da aikin ta Shima bai sake magana ba ya wuce cikin store Nasu yana tunanin shin mai ya dace ya dafa mata kome tafi so? don shi gaskiya ya shiga damuwa sosai na ciwon ulcer nan nata ace kamar Nnenna da irin gidan da take ciki da gatan ta, ace yunwa na Neman kashe ta a banza, tunawa yayi Mara lafiya yafison abun kwadayi-kwadayi hakan yasa sa d'aukar indomie manyan laida guda biyu sai kwai biyar dasu vegetables. fita yayi a store hannun sa sheke da kayan girki a basket, ajewa yayi yana kallon ummu dake ta kallon sa kamar ta samu madubi ganin sa da kaya Niki naki sai dai batace kome ba ta kauda kanta. Shima bai mata magana ba ya nufi wankakun bujuwa dake sit nasu ya dau daya sai kuma ya tsaya tunawa da yayi baisan ma ta ina zai fara ba, gashi koh zai mutu ummu bazata taimake saba. Aje bujuwan yayi da sauri ya fita a kitchen in, ya nufi falon ba kowa sai mai aikin share share dake ta fama, kofar dake gaban kofar sashen su ya tura yasa kai, wow masha Allah falo ne mai kyau da kayatar wa kamar Nasu, sai dai banbancin abin ado. daya cikin kofofin dake cikin falon ya nufa harya kama zai bude sai kuma ya daga hannunsa a hankali yayi knocking in kofar har sau uku kafun yaji muryar zulaihar cikin muryar bacci tana tambayar wanene? kin amsa mata yayi don yasan mundin suka San shine bazasu bude ba cigaba yayi da bugawa. Cikin dakin kam muneera ne ta Mike zaune cikin bacin rai jin sai bubuga kofar ake an hanata bacci gashi xulaihat taki bude kofar, kallon ta tayi cikin masifa tace, ke zulaihat don Allah tashi kije ki bude kofar nan an hanani bacci? Cikin haushi zulaihat ta mike don harga Allah daker ta samu bacci ya dauke ta koh minutes biyu batayi ba sukaji bugun kofar, tana isa kusa da kofar hannu tasa da Sauri ta bude jin bugu ake kamar za'a balla musu shi. Ja da baya tayi ta rike Baki again, tana bin lahab da kallo don koh ba'ace ba tasan lahab me xaiyi irin bugun kofar tasan ba rahab bakam. Murmushi ya sakar mata ya cusa Kansa a dakin kamar zai bangajeta ya ratsa gefen ta ya wuce, kallon muneera yayi dake kwance alamu ma ya nuna tun daren jiya bata tashi ba sai yanzun kuma ta koma"muneera muneera" Mikewa tayi zaune ciki hade rai take kallon sa da mamaki ganin sa yau a dakin su, menene uncle da asuban nan don Allah ka bari, koma menene inna farka sai naji. Jin amsar da ta bass yasa shi shammatar ta da Sauri ya fizgota gabaki dayan ta daga kan gadon, yana Jan hannunta kafun ma ta Ankara har sun Fita a dakin, ganin hakan yasa zulai hanzartawa ta maida kofar ta rufe harda sa sakata ta koma ta kwanta. Cikin Bacin rai ta fizge hannun ta, wai me hakane uncle banson wulakanci fa wallahi zan had'aka da uncle muzammil? Hada fuska yayi jin abinda tace cikin masifar sa da yake ta kokarin dannewa yau, don shi maganar mafarkin nan nasa ma harya tattara ya watsar Sanin da yayi mafarki ba gaskiya bane, kuma baison sawa Kansa tention a banza. 'Yauwa bondin ummu so nake ki taimaka kimin girki kinji"? Wani kallon uku saura ta masa, uncle yau cewa akai baza'ayi girki bane kome? kuma ni dai gaskiya bana Shiga kitchen da asuba kuma ma bacci nake ji wallahi rabu dani, ta karasa maganar tana kokarin juyawa. Hannu yasa ya sake fusgota domin yanzun ransa ya soma baci, da don baison zuwa gun mai shayi ba da wajen zaije yasai abinsa ya huta da takaici, kuma yasan muneera da ban haushi take amma ya Santa da shegen son yawo kamar masifa, rage murya yayi a hankali yace"ke wawuya yau kwad'ayin indomie nake kuma so nake me ki dafamun da kanki, inna dawo makaranta Zamu fita tare dake yawo" Washe Baki tayi kamar gonar auduga cikin farin ciki tace da gaske uncle zamu fita zaka kaini gidan zoo da wajen shakatawa? "Kwarai ma kuwa muneera harda ice cream zan sai miki kisha a gun" Wani tsalle ta daka da Sauri ta nufi kitchen shima ya Mara mata baya, suna Shiga, ummu kam kala batace ba kamar d'azun sai aikin ta take duk da ta cika da mamaki amma batayi magana ba. Nunawa muneera basket in yayi ya nemi waje ya zauna, yana kallon ta harta gaba dafa indomie da vegetables ga kwai data soya a gefe, ummu ta dade da FIFA, ganin itama miners ta kusa kammala wa yasasa mikewa ya Shiga store dake manne a kitchen in ya dauko roban takeaway, yazo ya juye indomie a dayan har sai da ya cika tam kafun ya rufe, haka d'aya roban ma ya zuba kwai soyayyan a ciki sai dan karamin flask mai d'aukan kofin shan shayi biyu a ciki, na Silva ne ya zuba coffee a ciki ya rufe, laida fari mai kyau na shopping ya dauka ya Jere abubuwan a ciki harda cups da spoon ya dauka yabar kitchen in. dakin su ya Shiga a gurguje ya kalli agogon dake like a bangon ganin 7:00 yasa sa aje laidan da Sauri ya nufi toilet, kama kofar yayi zai bude yajisa a rufa, tsaki yaja jin saukar ruwa alamu wanka Rahab ya Shiga, tsabar sauri da yake yau yana Allah Allah ya bar gidan kafun Nnenna tabar gidan su. ***************** Ta bangaren Nnenna Bata fargaba sai kusan shida na safe,mikewa tayi a hankali ta yayi blanket in dake jikin ta cikin natsuwa ta same kafafun ta izuwa Kasan tiles in, mika tayi sai kuma ta mike ta nufi toilet wanka tayi ta fitoh, jikin ta daure da towel fari, fuskar ta Sam babu walwala ga wani irin kasala dake damun ta da mutuwar jiki stool na mirror ta jawo ta zauna tana mai kallon kanta a madubi, sai kuma ta kalli hannun ta dake d'auke da Allurar ruwa. Murmushi ta sake data tuna Da yaron jiya daya taimake ta gashi koh sunan sa bata rike ba, drowa ta bude ta dauko Cake in jiya, yaye laidan tayi a hankali tasa hannunta ta yanko kad'an tasa a bakin ta tana taunawa, fuskarta dauke da murmushi ta wani lumshe ido, ada ta d'auka musulmai mugayen mutane ne kamar yanda takeji a kauyen su amma ta hadu da mutane uku masu kirki Wanda hakan ya tabbatar mata ba duka bane aka taru aka lalace ba. Da sauri ta ware idanun ta jin an sa makulli ata wajen kofar an murda mikewa tayi da Sauri jin yanda aka bangado kofar, bata kara tsinkewa ba saida taga mutanen da suka shigo Wanda koh ba'afada mata ba tasan babu imani a fuskar su kuma ba lafiya or kawo zuba, jiki na bari tace policeeeeeeee *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki* Page 35&36 Su biyu suka shigo ciki yan sanda ne mace dana miji sai mom da ta shigo a bayan su, tare da Jennifer da Sarah, gatanan Ku kamata don ubanta?mom tace tana pointing in Nnenna datayi mutuwar tsaye d'aure da towel mamaki na Neman hallaka ta. d'ayar police in CE ta nuna Nnenna da yatsa, ke sa kayan ki, jikin Nnenna na bari ta bude baki har rawa yake ta soma bawa mom hakuri"pls mom am sorry karki sa su tafi dani pls"tana maganan tana kuka, wani kallon banza mom ta watsa mata, police in ta daka mata wani uban tsawa, keee kisa kayan ki muje shegiya barauniya. Waro ido Nnenna tayi jin an kirata da barauniya ita yaushe ma ta dau abin wani harda za'a kirata da barauniya? jin matar ta sake daka mata tsawa yasa jiki na bari ta bude wardrobe inta ta zaro dogon Riga sai kuma ta nufi bandaki, ba musu suma basu hanata ba suka barta ta shiga. Harta bude kofar sai kuma ta juya ta kalli kikin ta dake rabe a gefen gado don yau kwata-kwata bata gane yanayin jikin saba kamar baida lafiya. Bude kofar tayi ta Shiga don harga Allah bata taba Shiga Matsala irin nayau ba, kayan tasa cikin rawan jiki ta zura dogon Rigan, amma ta kasa fita daga toilet in jingina tayi da kofar ta lumshe idanun ta bata son misbehave ta jawo wata matsala koh magana batason yi bare wani abin ya faru. Ji kawai tayi an bankado kofar da karfin gaskiya Wanda ata dalilin bankadar har takai ga faduwa a kasa, mom ce ta shigo batayi wata-wata ba ta shakota tare da janta da karfin ta tafito da ita daga cikin toilet. Kuka ta soma da karfi Amma sai da mom ta fito da ita daga toilet in ga hannun ta dake dauke da allura, da Sauri police in tazo ta tasa keyanta tana janta har suka fito falo, suka nufi kofa da ita, daidai lokacin Abraham ya turo kofar falon ya shigo, da mamaki ya tsaya rike da kofa yana bin su da kallo ganin Nnenna a hannun yan sanda ga mom a tsatsaye a falo alamu dai babu lafiya. Mom Ya haka lafiya me Nnennan ta musu? Koh kulasa mom batayi ba sai ma bawa police in daman fita a kofar ba tare da ta amsa masa ba, shima ganin da gaske fitan za'ayi da ita yasa sa sa hannu ya fizgo ta rai a bace ya sumo magana, haba mom wai menene haka me yarinyar nan ta tsare miki ne mom? Wanke sa da mari mom tayi cikin zafin rai ta soma masifa, kai harka isa nace Abu kace ba haka ba, eh bana sonta kuma yau sai tasan ta taro March. dafe kumatun sa yayi da mamaki yake kallon ta wai yau mom ce ta mare sa rabonsa da a mare sa ai harya manta, mom ni kika Mara? Yes na made ka koh zaka ramane? Girgiza Kansa yayi,mom bazan rama ba amma wallahi bazan bari a tafi da ita ba har sai an gayamin abinda tayi za'a tafi da ita. Rike baki Sarah dake tsaye tun dazun tayi kafun tace, wai kai Abraham INA ruwan ka da itane?koh abinda mom ta mata toh sata tayi. Kallon ta yayi sai kuma ya dubi Nnenna dake kuka, meta sata mata? Wani shegen kallo ta jefa masa, baza'a fada ba, harsai munje station. toh a gaskiya mom Indai hakane ba'a mata adalci ba ya za'a dau mutum baisan abinda yayi ba, sai kuma ya kalli yan sandan fuska a hade, tare da nuna muzu kofa, kunga yallaboi kuje kawai mu tattauna a waje, ba musu suka bisa waje,ga wannan ya mika musu kudin daya zare a Aljuhun sa kuyi hakuri abinda ya shafi family ne?don shikam harga Allah bai yarda da abinda mom tace ba, Ba musu suka karbi kudin suka tafi, Dawowa falo yayi yanuna wa Nnenna kofar dakin ta yayi, shege kisa uniform kizo na sauke ki a school, da Sauri kuwa ta nufi kofar ta shiga, mom kam bakin ciki ne kamar zai kashe ta wai ya zatayi da Abraham ne yabar Shiga harkar yar iskan yarinyar nan rai a bace ta zauna a kujera tana mai bakin cikin rugujewar plan nata, Jennifer ma zama tayi tana wani langobe kafar data kone jiya, Sarah kam tsaki kawai tayi ta koma room nata Dan yau bata da lecture shikam yana tsaye yana jiran fitowarta. ***************** tsabar sauri kasa hakuri lahab yayi ya sabi towel nasa ya fita a dakin ya nufi dakin uzaifa, da sallama ya tura kofar daidai lokacin shima uzaifa ya gama shirin sa tsap yana fefesa turaren sa ganin lahab yasa sa dakata wa ya bisa da kallo ganin sa d'aure da towel ya shigar masa bandaki, girgiza kai kawai yayi ya sabi jakansa yayi waje. Shafshaf lahab yayi wanka da Sauri Sauri ya fito dakin ya nufi Nasu harda dan gudu gudun sa, daidai lokacin Rahab ma ya fito cikin shirin sa sanye da uniform a jikin sa, kallon lahab yayi kai yasa ya fita a dakin, shima lahab Shiga yayi da sauri yad'au uniform nasa yasa jakan sa da laidan abincin ya saba ya fita a dakin cikin hanzari ya maida kofar falon ya rufe, a sannu sannu take ratsa falon Nasu har kofar falon hannnu yasa ya bude kofar ya fitoh babban falon gidan. Zazzaune suke kamar kullum akan dinning harya wuce su baiyi magana ba sai kuma ya dawo da baya tunawa da yayi da akwai fa uncle a dinning in,gashi ba addayiya bata fitoh ba, Dan rusuna wa yayi yana gaida Abbu"good morning yaya"? Kallon sa Abbu yayi da mamaki yau shine sanye da uniform ba tare da anyi hali ba gashi wai harzashi makaranta, morning Lahab sai ina haka kake ta saurin nan? Murmushi yayi ya dan tsosa keyar sa" wallahi yaya school zani Sauri nake na makara yana maganar yana kallon agogon dake manne a tsintsiyar hannun sa. Dukan su suka zuba masa ido da mamaki wai yau lahab ke cewa zaiyi late, gyada kai kawai Abbu yayi bai kara magana ba, juyawa yayi ya gaida uncle dake hade da fuska yana cin abinci lahab yayi, kin amsa masa muzammil yayi sai nuna masa kujeran dake gefen sa da yatsa Wanda koh bai tambaya ba yasan me hakan yake nufi. Kin zaman yayi cikin sanyi yace "uncle so nake daman na wuce da wuri ga abinci na nan a laida yana maganar yana daga laidan hannun sa. Kallonsa muzammil yayi, kai wani Sabon salone cin abinci a kula ka fara koh me? da Sauri ummu tace, Nima dai abin yaban mamaki yau tun asuba yake kitchen ya tasa muneera a gaba ta soya masa kwai da indomie. Harara lahab ya maka mata a fakaice cikin jin haushi ya mike" gaskiya nifa ana samin ido a gidan nan abinci ne dai nace zan fita dashi kuma makarantane zanje sai kuma akama mini wani tambayoyi" Kama baki mamu tayi"kema dai wallahi da naki Ina ruwan ki inyaga dama ma ya ya dau gas ya tafi school yana girki ashan me naki" d'aga musu hannu Abbu yayi ganin in aka sake fadar zai koma na manya,kunga ya isheni, kai kuma lahab saika jira yan uwanka suci breakfast sai Ku tafi tare. "Gaskiya ni yaya zan tafi da kaina wallahi banson tafiya dasu a mota zan hau keke" Kasan Allah lahab in baka rufemin baki ba kaje waje ka zauna ba zan mugun saba maka shashasha kawai, muzammil yace yana masa mugun kallo. Ba musu lahab ya sauka a falon zama yayi a one sita yana kunkuni ciki-ciki don shi so yayi yau su hade da Nnenna in so samu ne suje tare amma sunzo sun bata kome. Bini-Bini saiya duba time yaja tsakin haushi a haka har suka kammala ci baima wani saurare suba ya fita daga falon, bin kofar falon yayi yana bin compound in da kallo har idanun sa suka sauka akan motar da driver ya packa yana jiran su, nufar motar yayi ya bude gidan gaba ya zauna koh gaida malam habu baiyi ba shima bai wani damu ba Inda sabo ya saba da halin lahab. Ba'a jima ba munira da zulaihata da rahab suka fito daga falon kowa rataye da school bag Nashi, bubbude motar sukayi suka zazzauna, malam habu yaja motar bayan mai gadi ya wangale musu gate. "Don Allah ka kara gudu zamuyi lattin fa" lahab yace yana kallon driver don shi ji yayi kamar motar bata sauri. malam habu tafi a hankali mu ran mu na mana dadi, Rahab yace fuska a hade. "Kaga malam sauke ni anan" lahab yace ma malam habu. karka sauke sa in ba haka ba wallahi Zan Kai karanka wajen yaya, rahab shima ya maida martani yana kallon dan uwan nasa. Shima lahab baice kome ba yaja bakin sa yayi shuru tunawa ma da yayi koh ya nace ya sauka ba dole bane ya samu Nnenna by this time. A haka har suka isa makaranta a bakin gate malam habu yayi packing dukan su suka sassauka kamar yanda sauran students dake ta Shiga school gate in, suma Shiga sukayi, da Sauri lahab ya wuce clinic direct don shi a tunanin sa Nnenna tazo tuntuni. Rahab daga nesa yake kwala masa kira ganin ya nufi hanyar clinic har hankalin sa ya tashi koh d'an uwan nasa baida lafiya ne? Tsayawa Lahab yayi jin Kiran da Rahab ke kwala masa, baice kome ba har Rahab ya karaso kusa dashi, lafiya lahab ina zakaje kuma naga ka nufi clinic? "Mtwsss kai d'an sa ido yau kuma ni ka tsare da tambaya kamar wani kanin ka kaji Dan Rai nin since kawai" Juyawa kawai Rahab yayi ba tare dayace kome ba, shima lahab kara gaba yayi abinsa ya wuce clinic in, yana isa bakin block in ya Haura steps dake barandan yana Hawa a hankali ya taka har bakin kofar hall in ya tura tare da Shiga ciki. *************** Ta bangaren Nnenna ma da Sauri ta Shiga dakin uniform ta d'auka Harta tube kayan ta zata sa rikan uniform sai kuma da Sauri tai"shiiiiii"tare da duba hannnun nata jin wani rad'adi agun, alluran ne ya tsoketa tun lokacin da mom ta ja hannnunta ta damke ga jini na malala, kuka ta sake a hankali ta aje rigan dake hannnunta tasa d'aya hannnun a hankali ta zare Allurar ta aje a kasa da Sauri ta dauko dankwalin ta tasa raiza ta yanka ta daure hannnu, kafun ta lallaba ta Sanya kaya a jikin ta, jakanta ta d'auka ta sanya magangunan ta tare da tattare cake Inda yayi fata-fata da cake Inda ya wargaje a kasa. Kulenta ta d'auka tasa a jaka tare da tattara magangunan ta duka tasa a jakan da Sauri jin Abraham na kwala mata kira daga falon. Da Sauri ta fita sai kuma ta soma tafiya a lalube a hankali ta shigo falon, ganin ta yasa Abraham nufar kofa yabude mata a hankali ta fita ya rufa mata baya ba tare da ya saurare warning Inda mom ke buga masa ba suka fita hannun Nata ya kalla tare da karban jakan dake hannun ta ya rataya ba tare days kula da ciwon taba. Bude kofar gaba tayi ta Shiga shima ya bude drive sit ya zauna tare dajan motar suka Lula. Suna isa school in ya sauke ta a kofar makaranta tare da zare 2k ya mika mata amma kememen Nnenna taki karban kudin Sam yayi yayi amma taki karshe haka ya barta ta fita a motar ta nufi gate, har lokacin bai tafi ba yana tsaye har yaga shigan ta. A hankali take tafiya kamar iska zai hure ta saboda ciwon kwana da kwanaki dake cinta sosai ta rame, maimakon ta nufi clinic kamar yanda Dr yace, saboda ita Sam batason missing na class in yau ma. Lokacin data bakin class ma first period ne har anyi nisa dole yasa ta tsayuwa a kofa bata shiga ba. Uncle maths dake teaching juyawa yayi ya ganta sai kuma ya yafitota da hannu, ba musu ta karasa cikin ajin ta tsaya a gefe Yana gaidashi, cikin tsawa yake tambayar ta ba tare daya amsa gaisuwar ba, kee meyasa kullum kike lettin ne? "A hankali tace, sir am sorry bansan zanyi Lettin ba"? Oh late in ma sai an sani ake? Durkusawa tayi da gwuwowin ta a kasa tana basa hakuri daker dai ya hakura tare da nuna mata bench dake can tsakiya, go an sitdown my friend. Da Sauri taje ta zauna a take yaran dake zazzaune kusa da bench in duk suka marmatsa abinsu. ************ Lahab kam yana shiga hall in direct ya wuce corridor dake dama da falon sannan ya tura kofa mai number 4 Wanda a ciki jiya aka kwantar da ita, yana Shiga da mamaki ya tsaya yana bin dakin da kallo. Ba kowa asali ma dakin tsap yake an gyara an kimtsa kome alamu dai bama mutum a ciki, Fita yayi ya nufi office in likita, yayi knocking sai da aka basa izinin shiga kafun ya tura kofar ya Shiga da sallama,"Assalamu Alaikum" dago kai Dr yayi tare da amsa masa" waalaikumu salam ah ah lahab shigo mana get a sit? Zama lahab yayi a hankali ya soma gaida Dr "good morning Dr"? Amsa masa yayi, morning lahab yamai jiki? "da sauki Dr daman nazo naji koh an chanja mata dakine"? Da mamaki Dr yace, Ah ai bata iso ba,ai dana ganka ma na d'auka koh tare kuke? "au Dr bata zo bane" Murmushi Dr yayi, maybe lahab an kaita wani hospital inne. "Anya kuwa Dr munyi da ita fa jiya nan zata dawo" Kai lahab ka sani koh iyayen ta sun bukace kaita gaba, koh dai koh dai??ya karasa maganar yana dagawa lahab gira. Tsotsa keyan sa yayi tare da mikewa tsaye cikin kunya yace"toh Dr mungode" Ba kome lahab daga nan dai ka wuce aji karka ce zaka fita school yanzun don nasan halinka Sarai? Gyada masa kai lahab yayi tare da bude kofar falon ya fita, kujerun dake hall in na silver,akan guda daya ya zauna don shi yafi ta'allaka rashin zuwan nata da late tayi shiyasa yace bari ya jira ta. Lahab na zaune har 9:12pm na safe shuru babu Nnenna babu mai kama da ita haka ya miki ya fita a block in, harya nufi gate sai kuma ya dakata, da Sauri ya juya ya kama hanyar block na SS class. A window ss 1A ya tsaya ba tare daya damu da malamin dake ciki ba ya soma jejjefa ido yana duba ta, amma bai ganta ba haka dai bai karaya ba ya ringa bin class by class yana checking nata har yazo kofar ajin da aka maidashi ss 3B kamar a mafarki yana laika Kansa ya hangota zaune kanta akan dex tana rubutu. Ai da sauri ya nufi kofar class in ba tare daya nemi excuse ba kawai ya Shiga abinsa hannun sa danke da laidan takeAway nasa. Uncle physics dake note a board ya juyo yana kallon sa yana mamakin rashin kunyar yaron, ace banda iskanci ya gansa a tsaye a cikin class amma haryana da confidence na shigowa kai tsaye. Lahab kam koh takan sa baibi ba da Sauri ya nufi wajen da Nnenna ke zaune, yayin da yan ajin gabaki d'aya suka bar abinda suke suka zuba masa ido harda Nnenna data daga kai zata ga board kawai sukayi 4 eyes da lahab a take fara'ar dake fuskar ta bayyana, Barin rubutun tayi tana jiran karasowar sa, ganin wajen ta ya nufa. Aiko yana isa gareta dayake binci mai d'aukar mutum daya ne kowa da lokansa da sit nasa hakan yasasa, tsayuwa a kanta ba tare daya zauna akan binchin dake kusa da nata Wanda yara suka marmatsa suka barta. Nufar sa teacher yayi rai a bace cikin tsawa yace, kaiii stupid ways baka izinin dazaka shigo aji ba tare da Neman izinina ba who I u ya karasa maganar cikin hargowa. Nnenna Kam ta sure sosai sabanin lahab dako a jikin sa saima Zama yayi akan bincin dake gaban nata yayi cross lag........... *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki* Page 37&38 Damko kwalan Lahab yayi rai a bace ya Soma jansa Yana buga Masa tsawa,I say get out from my class? Kowa yasan yanda ss 3 suke feeling lokacin da suke Sabon Shiga gani suke kansu daya da malamai ne yanzun gasu da gemu,gashi a lokacin yaran ke tashen balaga ji suke kashin su na daidai dana kowa,toh hakan take a wajen Lahab daman gashi da karfi Kamar doki Koh uncle muzammil dake jibgarsa albarkacin kanin uba yakeci,kwace kwalar sa yayi da karfi tare da bangazan coper in don bazai wuce 25 ba"Akan me Zan bar class in"?Lahab ya tambaye sa Yana haki. Mari coper in ya wanke sa dashi tare da cewa,saboda bana ubanka bane. Habawa daman Lahab a duniya ba abinda ya tsana irin a zagi ubansa Koh don uban bai raye ne oho,Amma shi gwara ka zagi uwarsa daka zagi ubansa,kafun coper(uncle physics) ya sauke hannnun sa tuni Lahab ya d'aga hannu ya sharara Masa Mari,a take suka rungume juna da fad'a. Kacemewa ajin yayi da ihu Nnenna sosai ta tsorata ganin irin dambe da ake bugawa gabaki dayansu fada suke da dukkan karfin su Kuma bamai kwaran wani, Lahab bai basa daman da zai bugeshi,Kuka take tana tattara jakanta dana Lahab da laidan, ta ruga gefe ganin sun koma fadan akan bencuna. Ihun dalibai shiya d'auki hankalin malamai dake makarantan da dalibai duk take sauran classes Suka fifita a ajujuwan su Suka nufi Nasu Lahab ciki harda su muneera dasu Adewale da Nabeel da rabon su da Lahab tun jiya,ganin fada ake da Lahab yasasu shigar Masa,take su ukun Nan Suka Soma jibgar coper Nan da karfin da Allah ya musu,daman ance sarkin yawa yafi sarkin karfe,zuwa lokacin Kare kansa coper Nan ya suma Amma baya iyya maida martani ganin malamai sun nufi ajin Yasa sauran students fara ihu suna ga principal ga disple Master. da gudu Suka sake bawan Allah Suka nufi windonan hannnun daman ajin Suka hau Suka tsallaka daidai lokacin malamai Suka shigo da gudu suma Suka nufesu,Amma Ina kafun ma su sauka tuni su Lahab sunyi Nisan zango,sun dosi cikin gonakin makarantan Amma duk da hakan Basu hakura ba Suka rufa musu baya suma. Ta bangaren class Kam kuka Nnenna take tayi don ita ta gama sadakarwa shikenan yau Lahab ya shiga ukun sa,daidai lokacin Rahab ya iso wajen bayan su muneera sunje sun Kai Masa rahoto sosai Shima ya shiga damuwa sanin da yayi lallai yau jikin Lahab zai gaya masa in aka kamasu,Yana Isa ya samu sun ma gudu juyawa yayi bai shiga ajin ba ya Kama hannnun zulai tare da muneera Suka bar wajen,warning ya musu akan karsu kuskura yaji sunyi hiran abinda ya faru Koh da Wasa Koh fadawa wani a gida,munira ce ya kallesa,insha Allah uncle bazamu fada ba Amma ni ina tsoron matakin da xa'a d'auka akan uncle Lahab? Girgiza Kai Rahab yayi,karki damu munira abin zaizo da sauki Allah ya Mana Mai kyau. Zulai dake kuka sai share hawaye take akai akai ita tayi magana,ni toh uncle Mai yasa yake haka ne. Kin cika surutu zulaihat ya Isa haka kudai duk lokacin da kukayi sallah kusa uncle naku a Addu'a Allah ya shirye sa. dukan su da Ameen suka amsa Masa kowa ya koma class nasu. Su Lahab Kam da gudu Suka fasa cikin gonakin makarantan ganin har lokacin ba'a daina binsu ba yasa su Kama katangan makarantan Koh tsoron wayan danger dake mammakale basuji ba Suka d'ale da gudu Suka dirka ta bayan makarantan,Inda Allah ma ya sosu yashine a bayan wajen suna dirka Suka Kara gaba abinsu ,dole tasa malaman juyawa ganin su Lahab dai sun tsira. Koran yara a ajin su Lahab teachers in sukayi sai Yan aji kawai aka Bari,Kama coper dake sheme akasa sukayi don gaskiya ya daku wallahi dole tasa aka nufi clinic dashi. Nnenna Kam komawa tayi kan des nata ta zauna har lokacin jikinta baibar rawa ba don it's Sam duk abin tashin hankali bason sa take ba. Su Lahab Kam d'aga Nan hankalin su kwance don harma sun manta sunyi fada tsakanin su su biyu da Nabeel,hirane ya barke tsakanin su sunayi Suna dariya,Amma wallahi Lahab baka da mutunci wai ma tsaya uban me ya hadaku ne wai? Cikin dariyan shekiyanci Lahab ya dubi Nabeel dake Masa wannan tambayar"Kai za'a tambaya d'aga kanin Muna fada sai kawai kuzo ku shiga abinda ma bakusan kansa ba. Hararan sa Adewale yayi toh sai mu Bari a jibgeka ne Koh Yaya? "Wallahi kunsan nafi karfen muyi dambe aci zalina"ya karasa maganar Yana kallon Nabeel Yana dariya Shima Adewale kwashewa yayi da dariyan tunawa da dukan da Lahab yamasa last time. Aiko Nabeel ya Shaka sosai har ya kasa hakuri ya yunkura zai kaiwa Lahab naushi da gudu ya zura tare da fashewa da dariya Nabeel ya Mara Masa baya Suka ringa guje guje a titi Kamar tababbu. tun da abin ya faru ba teacher d'aya daya shiga ajin su Nnenna, don malaman sun rantse bazasu sake shigaba harsai an dauki kwakwaran matakin akan su Lahab don bazai yu suna matsayin malamai har dalibi ya samu daman dambe da malami abarsa ba hakan raini ne sosai Kuma in aka bar abin a haka toh tabbas an bawa dalibai satan amsa ne,duk Wanda malami ya buga zaice zai rama tunda Lahab ma yayi ba'a Masa kome ba,suma daliban Koh a jikinsu saima Dadi da sukaji yau babu lesson,sai hirar abinda ya faru suke duk an cika ajin da surutu group group akayi wasu mata zallah wasu Maza da Mata,wasu na zagin Lahab wasu nacewa ya burgesu daman copern haushi yake Basu wasu Kam labarin gagarancin Lahab suke musamnan Yan kusa da Nnenna Kuma sunayi Suna gaurayawa da turanci hakan yasa tana dan fahimtar abubuwan da suke cewa. 10:00pm dai dai aka buga break duk daliban ajin Suka Fara fita da d'ad'aya har gabaki dayan su Suka fita,sai Nnenna dake zaune rakube Kuma wallahi sosai takejin yunwa rabonta da abinci Mai kyau tun Wanda Lahab ya saya Mata jiya sai Kuma cake da taci shikuma ba abinci bane Mai nauyi bare ma ita data tashi d'aga jinya Koh magani anfison aci a koshi kafun asha,kwantar da kanta tayi a des in sai Kuma ta tashi jakanta ta bude ta fito da kulen nata a hankalin ya ajesa akan bincin da Sauri Kiki ya sauka ya nufi laidan Lahab dake aje a kasan bincin tun lokacin da ta sje batabi ta Kai ba kansa yasa Yana tsuntsuna laidan Yana soka kansa. Da Sauri Nnenna ta d'auke sa sai Kuma ta hada fuska ganin sai kokarin sauka yake zai koma wajen laidan"Kai Kiki menene haka ka daina Mana"tana maganan tana sake rikesa gam abinka da dabba maijin yunwa da kwadayi take ya Soma kukan Nan nasu na kuleluka,tsorata tayi gudun Kar wani yaji ta shiga matsala da Sauri ta dauki laidan ta bude da mamaki abinci ta gani sai dan paper karami dake d'auke da note,haka kawai taji ranta nason karanta abinda ke rubuce,hannnun tasa a hankalin ta dau paper warwarewa tayi,"wow shine abinda ya fito a bakin ta Ganin wani nice note dake rubuce, rubutune Mai shegen kyau Kamar na computer. "Good morning Labiba(Nnenna)" Shine abinda ta Fara gani a farkon shafin,murmushi tayi don tasan kaf duniya babu Wanda ya taba kiranta da sunan Nan sai mutum daya, amma Bata tsammani lettern nata bane. "How was your night hope kintashi lafiya ya karfin jiki,meyasa Baki koma clinic ba alhalin kince min Zaki dawo a Kara duba lafiyar ki"? "Ok fine ga break na kawo miki Yana laidan Nan pls karkice no and promise me zakisha maganin ki,nasan indai har na shigo ajin Nan ba lalle in samu magana dake ba shiyasa na tsaya na rubuta miki letter na shigo dashi"" "Kici abinci Kisha magani and kije clinic" "See you tomorrow byeeeeee" Hannnunta tasa ta rufe bakinta tana murmushi watoh abinda ya faru Nan daman Lahab ya riga ya tsara kenan kafun ya shigo,Jakarta ta bude a hankalin ta aje papern a cikin litattafanta, cire barrect nata tayi ta aje a gefe laidan ta bude tana maijin dadi Sam ta rasa meyasa indai Lahab ya Bata Abu har marmarin karba take,Koh Abraham dake dan uwanta bata karban abin hannunsa. takeAway in ta fitar duka biyu budewa tayi ganin daya indomie ne dayan Kuma kwai hakan yasata aje kwai in ganin akwai bread ma,indomie ta bude ta zubawa Kiki a marfin roban ta aje Masa akasan binci ya sauka ya kamaci,flask in ta bude don tasan yanda ake budewa akwai irinsa a gidansu. Tsiyaye coffee tayi a cup fork ta d'auka Shima na roba ne ta Soma cin indomie cikin happy tana hadawa da coffee inta hankali kwanci sosai taci indomin Harta rage don daman Saida ya cika roban dam,karshe rufe sauran tayi ta maida cikin laidan ta,Ana dawowa breakfast haka sukaci gaba da Zama babu malami har azahar musulman suka fita sallah itakam kwai da bread ta d'auka taci ta koshi. Misalin karfe 3 na yamma aka tashi makaranta dayake yau ba extra lesson kasancewar abinda ya faru yasa su tun karfe ukun akace su tafi gida,duke take tana tattara litattafanta data fitar tana bitawa saboda ita dai abinda ya faru bai Mata dadi ba da asaran lesson nayau dabasu samu ba,Amma ta lura yan ajin Koh a jikinsu Basu wani damu ba. Excuse me senior,taji muryar wata yarinya dake tsaye a kanta d'aga Ido tayi ta kalli yarinyar black beauty ce kyekkyewa sosai Yar doguwa bazata wuce 15 ba Koh kasa da haka"yes" shine abinda Nnenna tace tana kallonta don d'aga gani juniorn sune. Am daman nace Koh jakan dake zaune a gaban des Nan naki ne? Girgiza Mata Kai Nnenna tayi"no ba nawa bane na class mate nawa ne. Murmushi zulaihat tayi,ok sister na uncle nawa ne Bari na d'auka. "La ba kome Nnenna tace tana d'auka da kanta ta Mika ma zulaihat in don ganin yanda ta tsaya sai kallonta take Kuma tana magana idanunta akanta. da Sauri zulaihat tasa hannu ta karbi boron tana kallon laidan abinci dake gefe Amma dai batace kome ba tama Nnenna sallama tabar ajin,Nnenna ma jakanta ta d'auka tare da laidan ta fita a ajin. Zulaihat Kam tana fita ajin su Rahab ta nufa ta Kai Masa jakan Kamar yanda ya umurceta kafun ta wuce masallaci domin sallan la'asar suci abinci kafun su Fara hadda by 4 O'clock. Harta nufi gate sai ta tuna Lahab yace taje clinic juyawa tayi ta nufi clinic in,tana Hawa block in ta samu wasu Yan coper guda biyu sun fitoh d'aga ciki suna yare, alamu dai ya nuna wajen uncle physics nasu Suka fitoh shiga clinic in tayi direct ta nufi office in likitan knocking tayi shuru ba'a Bata izinin Shiga ba,gajiya tayi da tsayuwa kawai saita yanke shawarar tafiya abinta, juyawa tayi saura kadan suci Karo da Dr daya kawo Kai,da Sauri tayi baya hade da dukawa, "good afternoon Dr"? Afternoon Nnenna Koh? gyada Masa Kai tayi, toh muje ciki sai muyi maganar,Yana karasa maganar ya bude kofar office in ya shiga,biyosa tayi a baya Zama yayi a kan kujerar sa tare da nuna nata kujeran kaban Des nasa,sit down Mana Nnenna? gyada Masa Kai tayi hade da Zama akan kujeran dake gaidashi tayi Shima ya sake amsawa kafun ya daura da cewa,gaskiya Naga jikin yayi kyau sosai ashe shiyasa ban ganki da safe ba. "Sorry Dr naji saukine sosai shiyasa" Ok Amma ai zakizo mu cire kanula in Aiko,ya karasa maganar Yana kallon hannnunta. "Dr Na zare Allurar ai"ta karasa maganar tana kallon sa What???meyasa Zaki cire kina aikin asibitine ban hannun mu gani. Mika Masa hannun tayi,da kansa ya warware tsumman zare Ido yayi Ganin yanda hannnun ya kubura alamu ma sun nuna jini ya zuba,Aiko take yahau masifa irin dai yanda Dr kema majinyata in suka jika musu aiki,take yadau waya yayi magana ba'ajima ba sai Suka ji knocking izinin Shiga ya bada,aka turo kofar wata kyakyawar budurwace sanye da kayan asibiti. Cike da girmamawa tace,sir gani Yauwa sister farida ga wannan kuje da ita pharmacy kusai Allurar Nan saiki Mata tare da dressing in hannun nan nata Kisa Mata plaster,yakarasa maganar da Mika Mata Dan paper daya rubuta Mata allurar. da Sauri ta karba cikin girmamawa. Am sannan ke Nnenna kina Shan magani akan Kari Kam Koh? karki kuskura kiyi Wasa da magani kinji Koh? Gyada Kai Nnenna tayi tare da mikewa tabi nurse in a baya,fuskarta a hade don wallahi ta tsane Allura. Haka ba yanda ta iya ana kammala Mata allurar aka wanke hannun nata aka manna Mata plaster ta fita a clinic in, lokacin kusan 3:30 yayi haka ta fita a makarantan Koh sisi Bata dashi haka ta ringa takawa da kafa har gida duk tabi ta gaji ta jirkita gabaki d'aya. Ta bangaren su Lahab haka Suka ringa yawon su har rana yunwa data Kama Lahab abinci Suka saya dukansu Suka ci,d'aga Nan sai Kuma yamma Suka Kama hanyar gidan su Nabeel. Da sallama dukansu suka shiga gidan Inna ce zaune tana kwaba lalle zata daura sai yayar Nabeel dake rataye da jakan makaranta a kafadar ta sanye take da dogon riga na atamfa Wanda yasha wanki da guga duk da yasha ruwa Amma tas yake sai gelenta fari medium rataye a kafadar ta,ta rataya hand bag nata maikyau a kafadarta fuskar ta ba kome sai powder data shafa,tunda Suka shigo Adewale ke binta da kallo itakam kallo daya ta musu ta kauda kanta tare da zura takalmin ta ta nufi kofar fita. "Ah ah big Aunty sai Ina Lahab yace Yana kallonta" Mtwss Inda ka aikeni, shine amsan da ta bashi tana fita a gidan Inna Kam Ido kawai ta zuba musu irin kallon Nan na tuhuma da haushi don haryanzun Bata bar Jin haushin abinda Lahab yama jikanta ba gashi Kuma yau ta gansu tare duk buga Masa gargadi datayi bashi ba Lahab d'aga yau. Adewale Kam saurin juyawa yayi tare da zaro wayarsa yahau wayar karya Yana fita a gidan Lahab Kam da kallon tuhuma ya bisa Amma Nabeel bai kawo kome a ransa ba ya nufi dakin sa Lahab na binsa a baya harsun kusa Isa dakin da Sauri Inna ta Mike kaiii lahabu dakata Ina zakaje badai dakin jikana ba kamko???Mara mutunci. Dakatawa dukansu sukayi suna kallonta da mamaki bare ma Lahab Inda sabo dai ya Saba da masifar ta Amma bata taba koransa ba,"oh Inna yanzun ni kike kora a gidan Nan"? Eh na koreka lahab,shine amsar da ta basa tana Masa kallon uku saura kwata. "Kaga Nabeel shiga ka dauko mini kayana na shanja" Shiga dakin Nabeel yayi Kamar yanda Lahab yace Masa don baison shiga rigimar su da Inna,kayan ball in Lahab da yake bari a gidan su ya dauko Masa da takalma duk ya fitoh masa dashi,kallon Inna yayi dake tsaye ta rike kugu yayi kawai ya girgiza Kai tare ta mikawa Lahab kayan,gasunan Lahab. Amsa Lahab yayi ya aje akan dogon igiya dake tsakiyar gidan ya makala kayan ya aje takalmin a gefe,rigan uniform dake jikinsa ya cire tare da vest ganin addan Nabeel Bata gida yasashi Kwabe wando ya rage dagashi sai gajeren wandon jikinsa salati Inna ta buga,innalilahi wa'inna'ilahu raji'un mezan ganin nan dan duniya tsirara kayi a gaban jama'a nashiga ukuna,tana maganar tana tafa hannaye. Shikaran kansa Nabeel mamakin iskancin Lahab yake wallahi ace mutum baya shakkan kowa. Bucket Lahab ya d'auka batare dayabi takan masifar Inna ba yaja ruwan sa ya wuce bayi bayan yadau kayan daya makala a igiyan, wanka yayi ya zura kayan ball in abinsa ya fitoh daidai lokacin Nabeel ya dauko musu kwanon alele da Inna tayi a kitchen aje musu yayi a tsakar gida ya shimfida musu taburma,Lahab ga abinci fa ka fara ci Bari nima nayi wanka. gyada Masa Kai Lahab yayi ya zauna tare da tambayar sa"wai har yanzun Adewale bai shigo bane"? Nabeel najan ruwan Yana basa amsa,wallahi bai dawo ba nayi tunanin Koh fa ya wuce gidane. "Anya kuwa Nabeel kasan yaufa akwai show bazai koma gida ba" Kai gaskiya hakane fa Bara nayi wanka kaci alelen ka rage Mana daidai na fito wanka maybe ya dawo. Bandaki Nabeel ya Shiga yayinda Lahab ya bude kwanon yayi Bismillah ya Soma cin alelen da Miya Inna Kam sai hararansa take makokonta cike yake tam da haushi ita da gidan ta ta kasa koransa. Ta bangaren Adewale Kam Yana fita ya hangeta a bakin titi da Sauri ya nufeta,Assalamu Alaikum Gimbiya mubeena sai Ina haka. Kallon sa mubeena tayi, waalaikumu Salam lafiya Kam? Lafiya mubeena nace Ina Zaki? Cikin yanga tace school zani wani abun me? No ba kome Kuma in ba damuwa Zan iyya rakaki? Kallon sa tayi da kyau itafa lamarin dan yarobawan Nan ya Fara isarta,akan me zaka rakani cema akayi bansan hanyar bane Koh me? No ba hakan bane mubeena me laifi dan na nuna Zan rakaki school Naga dai duk Inda kaga kyautatawa da kulawa alamune na.................sai Kuma yayi shuru Yana kallonta kamar yarda ita ma ta juyo gabaki daya tana mamakin mezai ce kenan. Uhmm uhmm a gaskiya mubeena nagaji da boye abinda ke Raina na gaji da hakuri da abinda ke cutar dani,nagaji da lallashin kaina wallahi Ina cutuwa mubeena bazan iyya daurewa ba nayi iyya yina Amma nakasa juriyar hakan. Zuciyar ta bugawa take sosai Wanda har Saida ta dafe kirjin ta kafun ta daga idanunta tazuba Masa a hankalin ta bude bakinta ta Kara tambayarsa a Karo na biyu,menene wannan abin Adewale??........... *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki* Page 39&40 Ina sonki Ina kaunar ki Ina bukatar ki a rayuwata,dan Allah karkice ah ah zuciyata bazata jure hakan ba ki tausaya min, Adewale yakarasa maganar cikin wani yanayi na fargaba. Wani irin gyara tsayuwa mubeena tayi cikin Al'ajabi da mamaki take bin yaron da kallo don Koh a cikin su ukun shine karami su Lahab da Nabeel sun Dan girmesa kusan da shekara daya ma Koh watannni,Amma Kai dai baka da hankali Koh ince baka da mutunci yanzun Kai Inba tsaurin Ido da samun wuri ba ka rasa wance zaka kalla kace kanaso sai ni? sa'ar kace Koh tsarar kace ni toh wallahi d'aga yau sai yau magana makamancin wannan ta sake shiga tsakanin mu sai nayi mummunan Saba ma aikin banza kawai da wufe,ta karasa maganar tare da juyawa tana tsaida Mai keken da zai wuce. Adewale dayayi mutuwar tsaye a wajen ganin Mai keken ya tsaya har tana kokarin Shiga yasasa saurin Kama Mata hannu,pls Mubeena ki tsaya ki saurare ni don Allah zuciyata bazata juri wannan horon da kike Mata ba. Tasss kakeji mubeena ta wanke Adewale da Mari tare da fizge hannunta ta shiga keken tare da cewa Mai keken,malami dan Allah ja muje. Adewale na dafe da kumatunsa Yana bin keken da kallo Harta cila,dafe kansa yayi a take yaji Kan na Masa wani irin ciwo kirjinsa na mugun bugawa juyawa yayi zai tsallaka titin,Sukayi Ido biyu da Lahab dake tsaye a nesa ya zuba Masa Ido alamu ma ya Jima agun. Lahab Kam tunda Nabeel ya Shiga bandakin haka kawai taji hankalin sa ya kasa kwanciya ta fitar Adewale Kuma ya tabbatar bin mubeena yayi,hakan yasasa kasa hakuri har Saida ya rufe kwanon alelen yasa silifas din mubeena dake waje duk da ya Masa kadan Amma haka yasa. Inna sai masifa take,Kai lahabu cire takalmin Nan wannan kafa naka kamar doya manya manya zaka saka Mata a takalmin ta Mai number 10 da rabi so kake ka tsinka Mata ai kafarka sai number 11 da rabi. Kin kulata yayi ya wuce ya fita don ya gaji dasa boot takalmin ball in Kuma so yake inyasa Kar ya cire saiya dawo ball,fita yayi a gidan sanye da kayan ball in jikinsa tun d'aga nesa ya hangesu tsaye Suna magana hakan yasa shi jingina da ginin kofar gidan su Nabeel in ya hade hannu a kirjin Yana kallon su Amma baijin abinda suke cewa,bai Gama Shan mamaki ba Saida yaga mubeena ta wanke fuskar Adewale da Mari. takowa Lahab yayi har Inda Adewale ke tsaye hannunsa ya Kama suka ye bakin wani dakali Suka zauna dafa kafadar sa Lahab yayi,"Adewale Koh baka fadamin ba na fahimci meya faru tun farko abinda na Fara guje maka kenan nace maka ka maida abinda kake kokarin bayyana wa saboda babu alamun nasara a tare da hakan. Haba Lahab yazakace haka sannan laifine dan na nuna Ina son mubeena dahar zata d'aga hannu ta mareni,saboda na Kama Mata hannu Koh don nace Mata Ina sonta zata gaggayamin magana Koh saboda ni kabila ne kuke kyamata? Kaga Adewale maganar gaskiya Zan fada maka,ni bana kyamar ka bama Kai ba duk wani mutum Mai hali irin naka ba abin kyama bane Kuma maganar banbancin kabila babu shi Koh na addin dazan nuna maka,kowa da addinin sa da kabilar sa Amma nasan mu Yan kasa dayane,kaima shaida me da ace mun nuna maka da bamu kai warhaka tare ba, Amma fa ka sani Ade mu a addinin mu bai halatta mana mace musulma ta aure Christine ba sai dai an hallata ma namiji musulmi auren Ahlil kitab,kaga Kenan a addinin mu bai halatta Mana ba,kaga kenan babu amfanin Neman soyayar mubeena tunda babu aure a tsakanin ku,sannan bayan Nan ka dubi shekarunka ka dubi nata atleast ta Baka 3 years a yanzun ita take bukatar abokin rayuwa,Kai yanzun ka aureta Ina zaka kaita nasan zata iyya kula da hakkin ta na aure don namiji baya kadan muddin ya balaga,Amma fa ka tuna cinta Shanta sannan iyayen ka kana tsammanin hakan zaiyu aikin me kake da zaka riketa? All this well Addinin mu bai hallata Mata ba don haka maganar gaskiya ka janye maganan Nan kodon cigaban alakarka da Nabeel don kasan in yasan zancen Nan Abu bazai maka kyau ba na tabbatar mubeena bazata fada Masa ba Amma Inka cigaba da yada manufarka gareta wata rana zai gane" Bude Baki Adewale yayi zai Yi magana Lahab ya girgiza Masa Kai tare da Masa alamun yayi shuru ganin Nabeel ya nufo su,guys ya haka dukan ku kun fitoh kunzo kun zauna a waje gulman wa kuke? Murmushi Lahab yayi cikin basarwa yace"Kai Nabeel aimu munfi karfin gulmar mutum sai dai mu tinkaresa da zance"bai bawa Nabeel daman magana ba ya kalli Adewale tashi muje Ade ka chanja uniform Nan mu wuce ball yamma na karayi fa"? Ade dake zaune dafe da Kaine yace,gaskiya kuje ni yau babu Inda zani tare da mikewa tsaye gaskiya ninama wuce gida sai goben ku,Yana karasa maganar ya ratsasu ya wuce,da Ido Suka bisa Harya tsallaka titin ya wuce layin su,Yana bace muzu Suka juya a tare Suka kalli juna cike da mamaki Nabeel yace,lafiyan Adewale kuwa meyake faruwa ne? d'aga kafadar sa Lahab yayi irin Shima baisanin nan ba,shuru kawai Nabeel yayi bawai don ya yarda ba,Mikewa sukayi suka koma cikin gidan, alelen da Basu karasa ciba Kenan Suka fita filin ball. ta bangaren mubeena Kam tana shiga keken napep kuka kawai ta kamayi tama rasa meke damun ta guda da'ya Wai ita Adewale keso wannan shine so maso wani. Baiwar Allah nidai Zan Baki shawara a matsayina na babba karki sake d'aga hannu ki dake namiji irin haka baida kyau zuciya baida Kashi wani inkin maresa ya barki wallahi wani bazai barki ba,Mai keken yace Yana kallon ta ta madubi. Toh baba na gode amsar da ta basa kenan tana share hawaye dake bin kumatunta. Adewale na Isa kofar gidan su hannu yasa ya tura get in ya Shiga har cikin falon su ya Kama hanyar corridor dazai sadasa da dakin sa idanu jazir. Ade Ade mamar sa data fitoh d'aga kitchen rike da plate d'auke da nama soyaye. Tsayawa yayi Yana kallonta sai Kuma ya kauda fuska,good afternoon mama. Uhmm,cikin yare tace,toh yau Kuma ni kake gaidawa toh ma tsaya inaka fitoh ne? School ya Bata amsa har yanzun idonsa na kasa. School??ok Ina schoolbag first,shi sai yanzun ma tuna da school bag nasu shi da Nabeel Amma ya tabbatar friends nasu zasu daukar musu,mama banjin dadine shiyasa nabarwa Nabeel ya wuce min dashi. Ok Amma yaushe ka Fara wuni har 4:00 a school,bude kofar dakin nasa kawai yayi ya shiga ba tare daya Bata amsar taba,Zama yayi a bakin gadon sa ya buga tagumi abin duniya ya damesa. Mama dake tsaye aje plate in tayi tabi bayan dan nata,turo kofar tayi ta shiga a yanayinda ta gansa ya mugun d'aga Mata hankali Ade ne ke kuka ya rufe fuskarsa da tafukan hannayen sa, Jesus Ade what happen??meyasa kake kuka? Da Sauri ya goge hawayen sa, nothing mom kawai kaina ke ciwo. Kanka na ciwo Adewale yauka Fara ciwo ne? da bansan kaba me zakace ciwo ne ya saka kuka. Nace Miki nothing mama,girgiza Kai mama tayi sai Kuma tayii murmushi tace,wace ce?? Kuma tace Bata sonka Koh? Da mamaki yake kallon maman nasa shikaran kansa wani lokacin Yana mamakin yanda take saurin karantansa,Kwabe fuska yayi mama... Shiii ba wani mama,nace wacece? Shuru yayi sai Kuma ya rufe fuska Yana dariya hawaye Nabin kumatunsa. Ok tunda bazaka fadamin ba is ok bazan takura maka ba Amma nasan wata Rana da kanka zaka fada basai na tambaye kaba,yanzun dai ka tashi Maza kayi wanka ka cire uniform, tana maganar tana shafa Masa Kai. Mikewa yayi ya nufi toilet in ta bisa da kallo Harya bude kofar sai Kuma ya juya ya kalleta mama ya akai kikasan na Fara sonta Kuma tace Bata Sona.?? Hhhh Adewale kenan nice fa na haifeka nafi kowa sanin son nawa nasan babu abinda zaisaka kuka haka da damuwa sai so saboda nasan yarona ba rago bane sai a soyayya. Murmushi yayi cikin Jin dadi ya shiga bandakin,mikewa tayi ta fita a dakin Naman ta d'auka dake plate ta wuce kitchen abinci ta zuba Masa ta shigo dakin aje Masa tayi tare da ruwa,fita tayi a dakin ganin har lokacin bai fitoh ba. Adewale na fitowa yasa night Wear nasa abincin ya d'auka yadan ci duk da babu testing Koh kadan a bakin da Amma saboda Kar hankalin mama ya tashi yasa sa d'an Sakura yaci ya kwanta Yana ta tunane tunane abinsa. ta bangaren Nnenna tana Isa gidan nasu dakinta ta shiga tayi wanka ta chanja kayan ta ta sanya wando fari da rigan t-shirt sauran indomie Mai sanyi ta baiwa Kiki yaci laidan ta d'auka ta nufi kitchen,falo ba kowa wanke Robobin tayi ta zubar da coffee dake flask ya Soma baci tayi ta dauko takai dakin ta ta aje, zata fita kenan saiga mom ta Shigo,keee Yar iska saiki fitoh ai Koh? peace taje kauyen su don haka ki fitoh ki daura Mana dinner tunda ba hutu kikaxoyi gidan Nan ba ai. Gyada Kai Nnenna tayi tare dabin bayan mom data fita,tana binta a baya har kitchen,cikin store mom ta shiga,keee ki shigo store in Mana kin tsaya a kitchen Kamar na ubanki. Shiga Nnenna tayi ta tsaya tana sauraron lissafin da mom ke Mata, ga yam ki Mana sokora da miyan Stew kisa tsokar kaza a ciki sannan miyan Mai zakiyi karki kuskura Naga Mai yayi kadan Koh yawa hakama Magi Koh pepper,wallahi in abincin Nan bayi Dadi ba nida ke. Gyada Kai Nnenna tayi again ta tsunguna tana daukar doyan,ke magana zakiyi min ba gyada Kai ba,ok mom kawai tace tana fita a store in itama mom fita tayi ta wuce falo ta zauna tana girgiza kafa. Nnenna Kam doyan ta fere ta wanke ta kunna gas ta zuba a bujuwa ta daura tare da sa ruwa ta rufe,tattasai da tumatur sai tarugu da Albasa Mai ganye(lawashi) ta had'a ta gyara ta zuba a blander ta markad'a a take lawashin ya rinjaye colour tattasan ya zama green,bude fridge tayi ta dau kaza ta wanke ta yayyanka ta zuba a bujuwa Albasa da attarugu ta yanka a ciki ta zuba kori kadan da tafarnuwa kadan tasa Magi da gishiri tare dad'an shitta da masoro ta daura a huta ta rufe daidai lokacin Kuma doyan ta ya nuna saukewa tayi ta dauko wani bujuwan ta d'auka ta zuba Mai a ciki ta yanka Albasa Yana soyuwa ta zuba nikekken kayan miyanta ta fitoh da turmi tana zuba doyan a ciki tana dakawa gabaki d'aya ta hada gumi gashi daman ba isheshen lafiya bane da ita kanta ma wani ciwo yake Mata da hannunta gurinda aka da Mata ruwa. ta daka doyan ta rage kadan Wanda zata ci sakwaran ta mulmulasu a laidan ta zuba a kula kayan miyan ta ringa juyawa Yana Shan wuta ta ibi kadan ta zuba a kwanon Miya ta aje a gefe ta zuba Naman Kazan ta Kara soyawa kafun tasa ruwan zafi a ciki Magi ta Kara kadan ta rufe miyar. Doyan da ta ragen tasa a plate tadau miyar data zuba a kwano tasa a Kai tare da Barbara Magi ta Kama cin kayan ta Saida tacinye doyan duka tass kafun ta wanke hannunta ta duba miyar ya nuna saukewa tayi ta juye a kula yayi kyau sosai gashi ganyen albasar ya kawata miyar,tare da daukar daya bayan daya tana fitarwa a kitchen in tana jerawa a dinning Harta gama ta jera su plate da cups spoon ta goge kitchen in ta share, lokacin ma kusan 6:30 na yamma a gajiya ta wuce dakinta ba tare data wanke kanukan ba don wallahi ta gaji tana shiga ruwa ta d'auka tasha maganin ta ta kwanta sai baccin gajiya. Ta bangaren Lahab Kam d'aga filin balls Basu dawo gida ba sai kusan mangari ba wucewa gidan su Nabeel yayi yayi wanka yadau jallabiyar Nabeel ya sanya lokacin mubeena na alwalan mangariba fuskar ta tamke Koh kallon arziki basu samu ba masallaci Suka nufa sukayi sallah mangari ba d'aga Nan Nabeel yace su koma gidan su suci abincin dare Amma Lahab yaki yace shi zai wuce gida. Ok yanzun Kai Lahab gida ka nufa kenan? "No Nabeel yau dai gidan Yaya jafar zani nida gidan mu Kuma sai muzammil ya Barta" Au laifi kayine kake tsoron zuwa gida? "Kutt Kai harka manta abinda yafaru kenan Nabeel toh nidai ban manta ba kasan maganar dole xai dawo gida don haka bani ba komawa gida" Kai Kuma fa hakane Lahab, toh shikenan sai da safe Amma dai gobe ba Shiga school kenan Koh? "tam Nabeel kenan in kaga zaka jeka nidai nayi Nan" Dariya Nabeel yayi yabi Lahab da kallo Harya share kwana. ****************** Adewale Kam Yana kwance har 7 na dare Yana dakin sa a zaune Kamar d'aga Sama yaji papan sa na kwala Masa kira Adewale Adewale..... Mama dake zaune a falon da Sauri ta Mike ah ah papan Ade ya haka d'aga dawowar ka Koh hutawa bakayi ba koh daki baka shiga ba ka Fara kwalawa yaro Kira. Kinga tsaya nifa na Fara gajiya da halin kin Nan duk abinda yaron Nan yake aikatawa harda daurin gindin ki Nasha fadamiki banason Ina kallon Adewale da yaran hausawan Nan na tsane su banason ganinsa tare dake Amma ke nafahimci Koh a jikin ki ma Koh?? Kai papan Ade yanzun me nawa a cikin maganan Nan Kuma?Naga dai yaran Nan tun Suna yara suke abota duk abinda zakayi ka rabasu kayi Amma Basu rabuba sai yanzun da Suka Fara girma,Kuma a irin wannan age yara irin su basa bukatar fada Koh duka Koh tsawa Nasiya da lallashi daja a jiki sukafi bukata a yanzun. Do Allah rufemin Baki nonsenses wance batasan ciwon kanta ba Taya zakice bazan ma yarona fada ba who I u?? Am ur wife Kuma uwar Ade Amma tunda kace hakan shikenan Allah baka hakuri yanzun dai meya faru??? Ina yake na tambaye ki ya dawo ne Koh bai dawo ba? Ya dawo Yana bedroom,ai da Sauri ya nufi dakin yana surfa masifa binshi tayi a baya har cikin dakin. Adewale tun Kiran farko ya Mike ya zauna Yana Jin duk cacar bakin da suke har nufo dakin Nashi,Yana jiran isowar papan Nashi,turo kofar tayi da karfi ya shigo tsayawa yayi akan Adewale Kai who I u da zanna kiranka kana jina ka kasa fitowa Kai wanene? Kauda fuska kawai Adewale yayi donshi bai taba ganin baba masifaffe irin nasa ba ace mutum baida sassauci Kuma Wai a hakan shi pastor ne guda Amma baisan ya sassautawa iyalansa ba. Ina magana ka manna mini hauka? Am sorry papa Sorry for ur self,me ka aikata a school principle naku ya kirani dazun da rana akan gobe yanason ganina Kuma na tabbatar tare da Kai zanzo. Haba papa yazaka zo kana tambaya ta ai shugaban makarantan zaka tambaya bani ba? Kai Ade kul karka sake gayawa baban ka magana like this,mama tace tana kallon sa. gyada Mata Kai yayi,papa Kam cewa yayi keee barshi bayana ji da tashen balaga ba dole ya fadamin abinda ya fitoh a bakin sa. Mikewa Ade yayi domin ransa ya Fara bace,kaga papa pls a hate noise tunda dai kazo ka tambaye nace ban sani ba pls u can leave now na gaji da surutun Nan ka barni naji da abinda ke damuna. Kaiii Ni da gidana kake cemin na fita a dakin dana gida da kudina? Bude kofar toilet in kawai Ade yayi ya Shiga hade da banko door in da karfi ya rufe Wanda Saida mama ta dafe kirjinta alun sanun tabar daki Bata Kara magana ba sai papa dake ta surfa masifa Yana zagin Ade.......... *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki* Page 41&42 Masifa papa yayita surfawa,Ade na toilet kin fitowa yayi Kuma yaki tanka Masa Harya gaji ya fita a dakin don kansa. Jin ya fita yasa Ade ya fitoh yazo ya rufe kofar dakin sa ya kwanta. ************ Lahab Kam Keke napep yahau har unguwan su Yaya jafar"a kofar wancan gidan zaka tsaya Mai Keke" Kallon gate in Mai keken yayi gate ne tankameme Mai shegen kyau da daukar hankali gaskiya kudi yayi kuka a gidan sauka Lahab yayi ya zaro lalitar sa ya Ciro dari biyu ya mikawa Mai keken,nufar kofar gate in yayi yasa hannu ya kwakwasa da karfi,ba'a Jima ba security yazo ya bude kofar Yana sanye da bakaken Kaya Kuma d'aga ganin sa madakin katttine,Yana ganin Lahab ya fadada fuskarsa,ah ah Rahab sannu da zuwa shigo Bismillah. Shiga Lahab yayi ba tare daya mabi takan maganar Saba ya Soma ratsa tsakiyar gidan rufe gate in security yayi yabi bayan Lahab Yana Masa magana Amma Lahab Koh takan sa baibi ba yayi kofar falo dake manne a flat babba Wanda yafi Koh wanne kyau a gidan tura kofar yayi bakin sa d'auke da sallama, "Assalamu Alaikum"shuru babu amsa bin Koh Ina na falon yayi da Ido ganin ba kowa yasashi nufar upstairs dake falon ya Haura sama,Harya Isa babban falo dake saman binin bai hadu da kowa ba dan tsiririn corridor dake falon yabi direct ya bullar dashi wani kayatacen falo madaidaici Mai d'auke da kayan alatu na mure rayuwa. "Assalamu Alaikum"ya Kara sallama a Karo na biyu Jin motsi a dinning area dake falon, waalaikumu Salam yaji an had'a Baki aka amsa Masa don ba kallon mutanen yake sosai ba,saboda labule daya karesu da falon Amma ana ganin alamun mutane a zaune,muryar wa nakeji kamar ta Rahab ka karaso Mana ka tsaya a falo kaman Bako? takawa yayi a hankali zuwa dinning in hannu yasa bayan ya haura dan steps dake wajin ya yaye labulen,Yaya jafar ne sai matarsa nenne da yaran sa guda hudu Fatima da Hashim sai Aisha sai autan su Abdulmajid(gagararre),laa Uncle Rahab sannu da zuwa, shine abinda Fatima tace tana jawo Masa kujeran dake gefen ta, ba musu Lahab ya matsa wajen kujeran ya zauna,"Ina kwana Yaya Ina kwana nanne"? Lafiya Rahab ya gida yasu Addayiya da Hamma Umar(Abbu)? "Lafiya Yaya sun ma ce a gaida Kai"? Rahab ya gida ya kwana biyu shuru Koh lekamu bakwayi harma gwara Kai da dan uwan ka Kam rabona dashi ai harna manta Koh gidan naku naje bancika samunsa ba. "Alhamdulilah nenne kowa Lafiya"kawai Rahab yace don baison maganar tayi Nisa hannu ya baiwa Hashim sukayi musaba'ha sai Abdulmajid daya Mike yazo ya rungumesa"Kai man kwana biyu bama haduwa Koh wajen ka nazo uncle bai Bari na ganka ranan naje school naku ma Mai gadi ya hanani shiga, Wai Ina labarin Rahab ne mun kwana biyu da shegen wallahi? "Kai da Allah sakeni karka karyamin kafadu ka bar Addayiya da wahala"Lahab yace Yana banbare Abdulmajid daka kafadar sa sake sa Majid yayi ya koma ya zauna Yana dariya gaisawa yayi dasu Aisha,kafun Fatima ta Mike tazo ta zuba Masa abinci ba musu yayi joining nasu Suka Soma cin tare. Suna tsaka da cin abincin suka jiyo takalmi na kwaras kwaras alamu dai wani na taka tiles na falo kaf nasu babu Wanda ya dago Kai ya dubi Mai tahowan kowa cin abincin sa yake sabanin Lahab daya dago Kai ya kalleta, budurwace zatakai shekara 17 Amma kallo daya zaka Mata kasan akwai rawan Kai bana Wasa ba Koh d'aga yanayin tafiyarta ma kadai zai nuna Mata stubborn ce. Shima sauke kansa yayi yaci gaba dacin tuwon dake gaban sa yayin da hankalisa ya Soma tafiya tunanin Nnenna Koh yanzun me take warhaka,wani hali ya tafi ya Barta a school ya jikin nata Kai Amma gaskiya ya Zama dole gobe da safe yaje ya ganta,Jin mutum a kansa yasa sa saurin kallon Kan nasa, yarinyar d'azun ce tazo ta tsaya Masa akai tana sanye da wasu matsatsun Kaya dinkine na riga da zani. "Kee da Allah lafiya zakizo ki tsayamin akai in Zaki zauna akaina Zaki xaunane Koh Yaya"? gabaki d'ayan su kallon Lahab sukayi Suna mamakin masifar sa don Sunsan Rahab na zuwa Amma babu ruwan sa da CeCe kuce asalima shi bai kaiwa mangariba a gidan d'aga yamma yayi yake tafiya gashi yau yazo da mangariba Kuma a fusace. Amrat Kam kallon sama da kasa tayi Masa Amma dai batace kome ba taja kujeran ta zauna tadau plate ta zuba abinci ta kamaci gabaki d'aya wajen yayi shuru sai Karan shukula dake tashi wajen masu cin shinkafa Lahab Kam tuwo yake ci shida ya jafar. Ringing wayan Ya jafar shine ya katse musu shurun nasu kallon Aisha yayi,ke dauko min wayata akan kujera,mikewa tayi da Sauri ta nufi falon daidai ta isama har wayar ta tsinke d'auka tayi ta kawo Masa,ganin Mai Kiran nasa yasa sa d'auka da Sauri ya Kara a kunne, waalaikumu Salam muzammil. Jin an abbace muzammil sai da gaban Lahab ya Fadi Amma dai haka ya dake abinsa Yana sauraron abinda yayan nasa ke cewa. Lafiya Alhamdulilah sai Kuma yayi shuru Yana sauraron muzammil in,eh Naga Rahab dai yazo dazun Nan yanzun ma Muna tare dashi akan dinning,shuru ya sakeyi sai Kuma yace oh Lahab ne Aiko gashinan nima saida na tuna nace lafiya da mangariban Nan ok ok ka dai Bari gobe da safen sai kazo Amma yanzun dai ka barshi ya kwanan,shuru ya sake sannan ya cigaba,ok Allah ya kaimu lafiya babu damuwa shikenan Zan kula. Sauke wayar yayi a kunnen sa yakai duban sa ga Lahab Amma baiyi magana ba Shima Lahab abinci ya cigaba daci bai wani damu kansa ba,sai da Suka kammala ci nanne ne ta Fara tashi sai Lahab ma ya Mike,koma ka zauna,shine abinda yayan nasa yace Masa tare da kallon sauran yaran,ku bamu waje gabaki dayan su Suka Mike harda Amrat itama mikewa tayi da plate nata a hannu tabar dinning in don Yaya bai yarda Yama kannensa fada a gaban matan sa Koh yayan Saba,kallon Lahab yayi, Lahab? Dago Kai yayi a hankali ya kalli yayan ya amsa "na'am" Meya faru Koh ince Meka sake ma yayan naka Wanda yasa ka kasa komawa gida? girgiza Kai yayi Kamar mutumin kirki"babu abinda na Masa Yaya" Ah ah Lahab nasan ka nasan halinka nasan abinda zaka iyya da abinda bazaka iyya ba kadai San zaman ka a gidan Nan bamai yuwa bane Koh? Addayiya bazata yarda ba sannan muzammil bayason kana had'a inuwa daya da Abdulmajid saboda gani yake Kamar xai Kara Bata Kane Kuma Koh Ni Dana haifi Abdulmajid Yana matsayin d'ana nasan baijin magana,don haka gobe da safe muzammil zaizo ku wuce na nemi Alfarmar ya barka ka kwana. "Shikenan Yaya nagode Amma Ni gaskiya bazan koma ba ai Nan ma gidan mune" Eh gidan kune Amma nasan tabbas zaman ka a ciki bazai yuba ban hanaka zuwa ba Amma gaskiya Banda ikon ja da maganar da Hamma zaice Kuma nasan Koh yace ka zauna muzammil bazai amince ba don haka bazance kome ba. Shuru Lahab yayi yana tunanin abinyi don shi harga Allah baison Zama a gidan yafison sai muzammil in sun koma kafun Shima ya koma,mikewa kawai yayi ya fita a dinning in,bangaren su Hashim ya wuce direct ya bude kofar dakin ya shiga zaune ya samu Majid a Kan kujera Yana waya ga dukkan alamu da mace yake wayar sai wani make murya yake kamar kwarto,kwanciya Lahab yayi akan gadon Yana wani irin jinsa incomplete Yama rasa tunanin me xaiyi na damuwar abokin sa Ade Koh na Nnenna dake son samun waje a zuciyar sa. Ok baby Zan kiraki anjima ok Love you too,Majid yace Yana yanke wayar in kallon Lahab yayi,Kai mutumina kwana biyu baka lekomu ga Uncle ya samin Karan zuga shiyasa na daina zuwa gidan ku kwata kwata. tsaki kawai Lahab yayi sai Kuma yace"mtwssss kaga aramin wayan Nan naka kabarni da abinda ya dameni" Mika Masa wayar Majid yayi,a gaskiya Lahab kana ganin takura wannan uncle muzammil Nan anyi mugu wallahi shiyasa bana ma yarda na hadu dashi last dana hadu dashi ma a kofar school namu na gansa lokacin Muna level100 kaga an Jima Kuma ba zuwa gidan Nan nake ba. "Taya zaizo Majid bayan basa shiri da nannen ka kasan shifa duk Wanda xai taka Masa birki akan hukunci toh fa sun Kulla tsama kenan" gaskiya Kam don nanne ta dade da manta rikicin Nan Amma shi har gobe Yana Kan bakansa na gaba. dariya kawai Lahab yayi Yana Kara wayar a kunnen sa bayan ya loda number Adewale a ciki, ringing uku yayi ba'a d'auka ba karshe ma rubuta Masa messagei yayi ya tura Masa. ************* Adewale dake kwance abin duniya ya damesa ya rasa ma da wanne zaiji da masifar papa Koh da matsalan mubeena don shidai bai wani d'aga hankalin sa ba Akan Case in school Sam,yaji ringing in wayan sa Amma ya kasa tashi ya d'auka gani yake duk Mai kiransan Nan baida damuwa ne,Amma Jin shigowar sako yasa sa mikewa zaune a hankali tare da dafe Kan nasa Jin yanda yake azaban ciwo sosai hannu ya Mika ya kunna wutan dakin wayar nasa ya d'auka ganin an turo Masa sako da Sabon number,"Ade Lahab ne pls pick the call kaji" tsaki kawai yaja don harga Allah haushin Lahab yakeji ganin harda Shima baiyi supporting na soyayyar sa ga mubeena ba. Komawa yayi ya kashe wutan dakin ya kwanta tare da aje wayan a gefen sa wasu kiranne Suka ringa shigowar Yana basarwa gajiya yayi Kuma ya kasa hakuri sanin da yayi in dai har Lahab nama mutum nacin Kira haka toh da biyu me, daukar wayar yayi ya Kara a kunne,Hello.. Ta bangaren Lahab Kam sai Kira yake duk da Ade bai d'auka ba Amma haka bai hakura ba bai Kuma kula Majid dake masifa ba Wai dole ne sai babyn nasa tadau call in ya Kira so daya bai Isa ba. Jin Adewale yayi picking Yana cewa hello"Ade fushi kake dani"?shine tambayar da Lahab ya Fara Masa. Eh Lahab fushi nake dakai. "Akan. Me toh"? Au tambayana ma kake Lahab bakasan me kamin ba? "Indai maganar dazun ne kayi hakuri Amma gaskiya na fada maka" Jin abinda Lahab yace yasa Ade uhmm kawai baiyi magana ba. Shuru Lahab yayi Jin bai basa amsa ba a hankali yace"baka da lafiya ne friend"? Babu abinda ya shafe ka da rashin lafiya ta Koh lafiya na yanzun dai ka Fadi abinda yasa ka kirani in Kuma baka da abin fada na kashe wayata? rike Baki Lahab yayi cikin mamaki don shifa bai d'auka Ade zai dau maganar daya fada Masa da zafi ba,a ganinsa me amfanin zaman tare in baza'a fadawa juna gaskiya ba"shikenan Ade Allah ya baka hakuri Amma wallahi kaf duniya Mai sonka ne kadai zai fada maka gaskiya Amma tunda ka nuna baka so is ok,daman maganan da Zan fada ma shine daman zance maka akan Case na makaranta gobe Kar Wanda yaje. Jin abinda Lahab yace yasa Ade kase wayar ya kashe gabaki d'aya ya wurgar Yana tsaki Yana cikin wannan matsalan da zullumin soyayya har Yana da bakin kawo Masa wani case na school in banza. Bayan Lahab ya aje wayan kallon sa Majid yayi yace,toh Wai nikam Lahab me dan Arnen Nan yake bakane da har zaina ma wulakanci Ni wallahi na tsani yaron Allah. Koh kala Lahab baice Masa ba sai kwanciyar sa da yayi,mikewa Majid yayi ya dawo gefen Lahab,yau akwai birthday party na wani friend nawa yau da da dare Koh zakazo muje? Kallon uku sauran kwata Lahab ya masa cikin masifa yace"a daren nan kake maganar muje fati ka gannin nan Ina dawowa sallan Isha bacci Zan kwanta nayi banson damuwa" Kutt sai kace mace Kai dai wallahi anyi matsoraci menene a ciki don munje partin dare? Mikewa kawai Lahab yayi ya wuce toilet yayi Alwala tare da kallon Majid,toh nidai babu Inda zani kaida kaga zaka iyya sai kaje,Yana karasa maganar ya wuce masjid. Bayan sun dawo kwanciya Lahab yayi Amma Ina ya kasa bacci gabaki d'aya ma ya rasa meke Masa dadi ya rasa nutsuwarsa kwata kwata so yake yajisa cikin kwanciyan hankali Amma Ina ya kasa sosai,Yana kwance likimo yayi a blanket Yana kallon Majid ya wuce bandakin xaiyi wanka ganin 9 na dare yayi. Lahab dai na kwance har ya fito wanka yazo Yana shiryawa Harya Gama zai fita sai Kuma Lahab ya mike"dan jirani Majid mu fita wallahi na gaji da kwanciyar Nan nama kasa baccin kwata kwata" Kadaiji dashi lokacin dana ce kazo mu tafi aiki kayi sai yanzun dana shirya zaka wani ce in jiraka toh bazan jira ba,don zaka sani late a banza. Da Sauri Lahab ya mike"kama Isa party makaranta ne Koh ma'aikata da zakace kayi lattin"Yana karasa maganar ya shiga toilet Zama yayi Yana jiran Lahab. Shafshaf ya fitoh ya bude wardrobe in Majid ya zaro kayan Majid in wando da riga Mai azabebben kyau wando baki sai riga fari da takalmi Baki yayi kyau sosai Suka fita tare Amma abinda ya bawa Lahab dariya da mamaki Ashe Wai Bata gate zasu fita ba"Wai Majid ya Naga haka baga kofar falo ba Naga Kuma kana bin wannan corridor in Ina zamu" Mtwss rabu dani pls Lahab yanzun nufin ka ta kofa zamu fita toh Bari kaji Daddy yace Kar security su Kara barina na fita sai da izinin sa. "Toh yanzun ta Ina zamu fita in ba ta kofa ba"? Kazo Mana zaka gani Suka Isa bakin wani kofa key guda uku a hade ya zaro a Aljuhun sa yasa wa kofar ya bude tare da kamawa ya wangale kofar. Fita yayi Lahab ma ya fita kafun ya maida kofar ya rufe Lahab Kam bin wajen yayi da kallo bayan flat nasu ne Wanda ba kowa zai d'auka akwai kofa a wajen ba kasancewar garden ya kewaye wajen Harya boye kofar,gaba Majid ya Kara Lahab na. Binsa a baya har Suka iso wani kofar gate Wanda ake Kira da back door na gidan Nan ma key Majid yasa ya bude kofar Suka fita kafun ya maida kofar ya rufe harda Murda key. Bayan layin su Majid Suka bullah Wanda nisan sama daga babban gate na gidan zuwa Inda Suka bullah tafiya ne Mai tsawo sosai. Waya Majid ya d'auka yayi Kira ya kafa a kunne,yes na fitoh ka karaso muna kusa da wajen suya,Yana aje wayan ya kalli Lahab dake ta kallon sa don shi wallahi sosai yake mamakin abin ashe duk rashin jinsa Majid ya damasa ya shanye tunda shi baitaba ya fita gida a boye ba cikin dare,muje Koh Lahab wajen Mai suyan Nan mujirasa a wajen. takawa sukayi sukayi danyi tafiya kafun Suka iso wajen wani Mai nama Zama sukayi a gefen sa Suna jira Kamar yanda Majid yace. Ba'a Jima sosai ba sai ga wata azabebben mota tayi packing a gaban Mai nawan kadan mikewa Majid yayi ya kalli Lahab,muje. Mikewa Lahab yayi yabi bayan sa,bude gaban motar majid yayi ya shiga Lahab ma baya ya shiga yaron dake tuka motar bazai wuce 21 ba zasuyi tsara da Majid ma Yana tukin Suna shekiyanci da Majid d'aga ganin sama dan gata ne sosai Kuma dan manya,Dan juyawa yayi ya kalli Lahab,sannu Lahab Koh? ai Majid na bani labarin ka sosai Amma bamu taba haduwa ba sai yau. "Ayya,kaiwai Lahab yace Yana bin titi da kallo ta glass in motan don shi yanzun ba surutu bane a gaban sa,kyelesa kawai faruk Abu ke damunsa shiyasa ka gansa sai wani basarwa yake,Majid yace don yaji kunyan abinda Lahab yayi Masa yanda yake bawa faruk labarin sa ba haka ya gansa ba. toh Allah ya gyara Mana shine abinda faruk yace sukaci gaba da hiran Yan Mata sunata surutun su Amma Lahab baice kome ba Yana daijin sune kawai. 20 minutes ya kaisu wani kayatancen hotel Mai shegen kyau tun d'aga gate zaka gane lallai ana party Kuma na manyan yara yaran ma matasa shiga gate in sukayi faruk yayi packing a packing space dake hotel in duk Suka bude kofofin Suka fitoh,bin wajen kawai Lahab yayi da kallo tunda suke shida su Ade basu taba zuwa waje irin wannan ba ga yan Mata Kota Ina ga matasa Nan birjib wasu na shiga Hall wasu na fita wasu na Hira a waje. Zuwan su Lahab shiya d'auki hankalin matasan dake wajen a take Suka Soma ihu suna sowa,gaaa MJ ga MJ da fazey. Wani doro majid yayi Yana wani dan iskan tafiya irin na Yan iskan Nan shida faruk har Suka Shiga cikin hall in tsabar fasa Kai sun ma manta da Lahab,shikam ganin wasu kujerun plastic dake kusa da flowers da aka kayata hotel in dashi yasa sa matsawa ya zauna akan kujerar Yana bin Koh Ina na haraban hotel in da kallo har idanun sa Suka fada kanta tana tsaye sanyi da wani Y'an iskan wando da riga sun matukar matseta sai gashin attach dake zube a gadon bayan ta fuskar Nan Tasha make-up sosai. Kara Ware Ido yayi dakyau ya Kara kallon ta sai Kuma ya mike tsaye don Kamar mafarki yake ba a zahiri bane daman haka takee......................... *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki* Page 43&44 Ba kowa bace face farida budurwan Anwar Koh ince matar da Anwar zai aure don har date na auren an yanka,mamaki ne ya kusa kashe Lahab don itace Amira a islamiyyar su Kuma sosai iyaye ke Alfahari da ita ana nuna wa Yan Matan islamiyyar su suyi koyi da halayen ta ashe abin ba haka yake ba kullum tana cikin hijab har kasa ana taboda zatace Allah yace annabi yace Ashe fuska biyu gareta lokacin da Anwar ya fitar da ita akan matar da zai aura babu Wanda baiyi na'am da abin ba. da Sauri ya juya musu baya ganin ta kusa kamasa Yana kallon ta gashi hall in Suka nufa agogon hannun sa ya duba karfe 10:39am,mikewa yayi da Sauri yabar wajen tsayawa yayi a jikin mototin dake pack Yana kallon ta harta shiga ciki,hannu yasa a Aljuhunsa wayam babu waya sai yanzun yake Jin haushin rashin waya a hannun sa yabar wayan sa a gidansu. Shiga ciki yayi Yana bin hall in da kallo Maza da matane ana ta rawa ga yan matan musulmai da Cristian nan cikin bad dress sai faman Mika wuya yake Yana Neman su Majid Aiko acan wani table ya gansu zazzaune da Yan Mata ana ta Hira ana mammatse su tacan gefensu ma faridan ne tsaye Suna magana da wani,Wanda a dukkan alamu birthdayn nasa ne,dole yasa sa bin cikin mutane Yana tafiya Yana sunkuyar da Kai Harya iso kusa da Majid juya Mata baya yayi yanda baza taga fuskar Saba sai bayan sa,ya zauna akan kujerar ya Bata baya,amsar wayar Majid in yayi ya kunna camera tare da karban hulan faruk pcap ya rufe fuskarsa sosai. Tashi yayi ya koma tables in baya ya zauna sosai yake bin duk wani abinda take,mc ne ya Soma magana bayan an Saida kid'a,Muna ma manyan bakin mu barka da zuwa,sannan Muna son ganin shi kb uban gayyan a fili tare da zazzafar budurwar sa fereey su karaso Muna son ganin su. farida ne ta shigo fili da wani yaro da bazai wuce 23 ba Yana rike da hannun ta Suka Haura Kan step in,zasu yanka cake,aka kawo aka aje musu kb ya d'auki wuka ya saita Kan cake in yayin da farida ta daura hannunta akan nasa,shi Kuma Lahab sai daukar hoto yake da vedio tunda Suka taso,gashi jama'a sun mimmmike tsaye Suna musu wakan we wish u happy birthday. Yanka cake in sukayi kb ya d'auka ya Samata a baki itama ta basa kafun ya Kama bakin ta ya bata hot kiss take wajen ya kashame ta ihun su Majid da tafin su,Waka aka sake Wanda mutum zaijishi har tsakiyar kansa kafun aka kashe wutan Hall in habawa basai aka Kama iskanci ba, duk namijin da ya Kama mace take zai danneta a wajen, Lahab da zuciyar sa ke bugawa da Sauri ya ringa lalube Yana Neman hanyar kofa Jin wani ya kamasa Yana ta jansa ihu ya Fara Yana namiji ne ba mace ba Amma ina sai ma ji da yayi mutane biyu sun shuresa sama. Wani irin wainuwa yayi ya kadawa dayan cizo har sai da wayar hannusa ta Fadi kasa garin Sauri yaji ya taka ta ta subuce tayi wani wajen,dole baida wani zabi sai na fita a hall in da gudu Yana tattaka mutane ya samu ya fita a ciki duk yabi ya had'a gumi jakaf ya fitoh, direct gate ya nufa Amma abin bakin ciki bai samu Koh tsuntsu a titi ba garin shuru babu motsen kome,agogo ya duba karfe 12:19 na dare hankalin sane ya Kara tashi ba dan kadan ba, daya sani dayasani dabai biyo Majid ba da hankalinsa kwance a gida Kai dama ya sani da gidan su ya koma Koh kasheshi muzammil zaiyi yayi da wannan tashin hankali,gashi bata kofar gate Suka fita ba baisan ta Ina zai shiga ba in yaje ya buga kofa aka bude Masa baisan amsar da zai baya yayan Saba Kuma Koh giyan wake yasha bazai kuskura ya koma gidan suba jingina yayi da ginin hotel in duk abin duniya ya damesa. Yana Nan tsaye a wajen har 1 na dare kafun ya Fara ganin yara na fitowa daya bayan daya dayake darene babu Wanda ya lura da mutun agun sai can kusan 1:27 yaga motar su Majid na kokarin fita a gate in da Sauri yazo yasha gaban su tsayawa faruk yayi a mugun zuciya Lahab ya bude kofar ya shiga ya maida kofar ya rufe da karfi"Amma wallahi Majid Allah wadaren ka Ashe iskancin da kukasan zakuzo kuyi kenan kace na biyoka sai yanzun na gane dalilin dayasa Yaya baison xamana tare da Kai ashe hakan Alkhari ne" Kaga Lahab dakata bafa jawoka nayi da karfi ba Kuma in kasan Kai karamin dan iskane meyasa ka shiga ciki. "Majid Ni kake Kira dan iska"?Lahab ya tambaye sa ransa na kara soyuwa,ga bakin cikin batar wayar Nan ta Majid shikenan ya rasa wannan vedio,yasan duk abinda zai fada akan farida bamai yarda don kaf unguwan su yabonta ake,yaso yayi amfani da vedio wajen Hana auren ta da Anwar saboda baya kaunar ta yanzun yaji ya tsane ta kwata kwata Kuma baya fatan ta aure dan dan uwan sa. Keeeeee kakeji faruk ya taka birki da karfi suna salati da Majid don saura kadan ya buge wani tsoho Allah ya Sosa. Lahab Kam dafe kirjinsa yayi haka kawai zuciyar sa ta tsinke da Sauri su Majid Suka fita a motar Suka nufi tsohon dake duke a kasa jikinsa na rawa. dagosa faruk yayi yana basa hakuri tare da tambayar sa abinda yafin dashi a daren nan shikam tsohon sai kallon glass in motan yake ta Inda Lahab ke zaune yayi sumar zaune ganin tsohon jiya da Nnenna ta hanasa basa kudi Kuma yazo yayi mafarkin sa kin fita yayi a motar Yana dai ganin su Suka basa hakuri tare da tsallakar dashi titi Suka taho motar ja faruk yayi Suka bar wajen. Kamar yanda faruk ya daukosu haka ya maidasu lokacin dare yayi sosai wajen shuru babu motsen kowa gabaki d'aya Lahab ya shiga damuwa Allah Allah yake yagansa a daki Kar wani ya gansu. Bude back door in Majid yayi Suka shiga ya maida kofar ya rufe kirim Kamar yanda ya bude tafiya suke a garden kaman barayi Suna zazzare Ido,suwaye a garden Nan su wanene???sukaji muryan daya d'aga cikin security na gidan ya nufo garden in da toshi Mai haske. Habbawa Majid da Lahab kafa me naci ban baka ba gudu saka saka Jin gudun kafafu yasa security hura usur dake wuyan sa a take sauran ma suka nufo garden in tashin hankali yasa su Lahab kasa bude kofar ganin an kusan cin musu yasasu Hawa bishiya suka labe Lahab sai tsinewa Majid kawai yake a ransa. Security's Kam sosai sukayita checking na gidan Amma basu samu kowa ba sunyi iyya dudubawan su Amma shuru sai daga baya wani yaga shatin takalma a tabon dake garden in hakan ya Kara tabbatar musu akwai mutanen da Suka shigo garden in bin shatin sukayi har hanyar back door duk da Basu Zargi wani bane ya shigo kofa a rufe sai dai a Yan gidan. Hakan yasa Suka Kara tsananta tsaro da sa Ido Suka yada zango a garden in wannan tashin hankali duk su Lahab nakan bishiya Suna jinsa,hannu ya d'aga yaga time dayake agogon Mai wutane 2:31am na dare. Wannan dare dai mutane uku sun kasa bacci Mubeena Lahab Adewale don shi Majid tuni ya jingina da jikin reshe ya Kama bacci abinsa Koh a jikinsa Kamar a gadon sa yake kwance Banda Lahab da Sauro suka tasa sa a gaba ga fargaba dake damun sa. Su Lahab na garden a zaune akan bishiya d'an bacci ne ya sace Lahab. Mafarki............ Kwance yake Yana bacci akan bishiya wani gawurtancen macijina Mai girman gaske Baki kirim Yana ratso ganye da reshe Yana tafiya Yana fidda harshe Hawa Kan Lahab yayi yasa bindinsa yasa ya nade Lahab kamar taya yayin da tsohon Nan ya bayyana a gaban Lahab Shima hannnun yasa cikin dariya ya damko makogoron Lahab da karfe gaske Wanda yasa sa farkawa a cikin mafarkin. Ihu yake yana Neman taimako yayin da tsohon yake Kara damkar Masa makogoro har Yana Jin numfashin sa na d'auke wa. Bayyana tayi a kasan bishiyan Wanda ya kasance Mai Nisan d'aga kasa zuwa saman bishiyan haryakai sai dai a ringa hangan mutum dan kadan a kasa,ihu take tana cewa Lahab, "Lahab ka farka Lahab ka farka ka farka na rokeka bazan iyya kwacan ka ba ka farka kamin nisa sai Kuma ta Kama bishiyar tana Hawa Amma tamkar ana Kara Nisan tsakanin gindin bishiyar da ganye. Wani ihu ta Masa da karfe Wanda Lahab yaji sa har tsakiyar kansa,a take ya farka a zahiri ya jika sharkaf kallon Inda yake yayi da gaske a bishiyar yake ga wani motse da yakeji a saman reshen gefensa wuyansa da aka Shaka gani yake kamar da gaske don wani irin radade yake ji a wuyan nasa hannu yasa Yana shafa wuyan ai da Sauri ya dirko d'aga Kan bishiyan Jin ana kiraye kirayen sallan asuba jikinsa sai rawa yake. Bai Koh tashe Majid ba ya wuce cikin massalacin dake gidan yayi Alwala a pampo ya shiga ya zauna,Kamar 30 minutes sai ga Yaya jafar da Hashim sun shigo da mamaki suke kallon sa ganin ya fitoh da wure Amma sai suka kauda mamakin tunawa da Lahab nason ibadah bai cika Wasa da sallah ba,Kai Lahab Ina Majid kun kwana tare Amma kazo massallaci Ina yake? "Yana daki na barsa Yana Alwala zai fitoh"shine abinda yace kawai yaja bakinsa yayi shuru security ma sun shigo aka tada sallah dasu ana idarwa aka gaggaisa anan daya daga cikin security ke sanar da Yaya jafar akwai Wanda ya fita a deren jiya don sai karfe 1 ya dawo Amma sun rasa ta Ina ya shiga Koh ya fita. Hade fuska ya jafar yayi ya nufi cikin gida direct dakin su Majid ya shiga wayam baiga Majid ba ya sake duba toilet babu kowa fitowa yayi a dakin daidai lokacin su Lahab Suka shigo falon kallon Lahab yayi Yana kallon dressed nasa da takalmin kafarsa rai a bace yace Ina Abdulmajid Lahab karka kuskura kamin karya ya kwana a gidan Nan Koh bai kwana a gidan Nan ba sannan Ina kukaje? Shuru Lahab yayi Yama rasa ta Ina zai Fara shikam ya shiga uku wallahi dama ya sani dabai zo gidan Nan ba kwata kwata. daka Masa tsawa ya jafar yayi Wanda yasa sauran yaran da nenne fitowa suji Koh lafiya da asuban Nan,, kaii Lahab badakai nake magana ba Ina Abdulmajid?????? *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki* Page 45&46 Lahab Kam shuru yayi yakasa magana baison yace kome akan majid. Lahab Ina magana kamin shuru?ya jafar ya Kara daka Masa tsawa Amma Ina Lahab Kam yaki magana nenne ne tasa Baki, Lahab kayi magana Mana Ina Abdulmajid in daman ba tare kuke ba? Kafun ma ya Bata amsa Suka ji motsin bude kofar da rufewa a sashen su Majid in,juyawa ya jafar yayi ya nufi kofar sashen su nanne ma Suka Mara Masa baya,ya jafar na bude kofar daidai lokacin Majid ke tura kofar dakin su zai shiga,dakata Majid tsayawa yayi Jin muryar dadyn sa. Nanne ne ta tafa hannaye innalilahi nidai na Shiga uku Majid Ina zaka sa kanka ne Wai ashe da gaske ne jite jite danake ji a gari ana cewa kana kwana a hotel Majid yaushe ka tafasa har zaka kone yaushe na haife ka majid har kasan kwanan waje watoh shine kaja Lahab kuka fita tare Koh? Sunkuyar dakai Majid yayi,ya jafar Kam ransa in yayi dubu ya bace,hannu ya mikawa Majid,bani key Inda kaje ka d'auka har kana fita ta back door watoh Majid Ni ban Isa da kaiba har barayi kake nunawa kofar sirri na gidan ku? Hannu Majid yasa a Aljuhu ya zaro key in ya mikawa dady ba alamun damuwa a fuskar sa,juyawa ya jafar yayi ya koma falon daya bar lahab,har lokacin Yana tsaye kallon sa yayi, Lahab Bari kaji zaman ka a cikin gidan Nan bazaiyu ba bazaiyu kazo ka zauna ku taru ku lalace ba don haka kaje daki ka jira muzammil anjima zaizo ku tafi,Yana karasa maganar ya juya yabar falon. Nanne da ya Hashim kam fada Suka rufe Majid dashi kafun Suka juya Suka bar Masa wajen,dakin sa ya shiga,Lahab dake tsaye a falon Shima dakin Majid in ya tura ya shiga. Majid dake tsaye a tsakar dakin ne ya kallesa,sannu Lahab haka mukayi da Kai sai ka tashi ka shigo gida bazaka tadani ba ai shikenan hankalin ka ya kwanta ai yanzun,ban wayata? Koh kallon sa Lahab baiyi ba ya bude wardrobe nasa yadau jallabiya tube kayan jikinsa yayi ya zura jallabiyar,ga kansa dake Masa ciwo ciwo na rashin bacci da bai samu ba jiya. Magana fa nake maka Lahab,shuru Lahab yayi bai amsa Masa ba ya nufi kofar dakin shakumosa Majid yayi cikin zafin Rai yace,kaban wayata daman Lahab a cike yake tam jiran kadan kawai yake ya fashe a take ya bangaje Majid Suka kaure da fada fada suke sosai ya d'aga Majid ya buga da tiles wani Kara Majid ya sake da karfi Yana Kiran nenne. Nanne dake zaune a falo tana bama Mai aikin ta ordern abinda zata d'afa musu na karyawa da Sauri ta Mike Jin Majid na kwala Mata Kira da karfin cin tuwo,da Sauri ta nufi falon nasu tana shiga ta tura kofar dakin sa ta shiga,subhanallah me Zan gani haka Lahab sakesa Mana tace tana kokarin shiga tsakanin su Amma Ina Lahab yayi zuciya sosai kin barin fadan yayi da gudu nanne tayi dakin Hashim tana kwala Masa kira da karfi tana salati,bude kofar yayi fuska ba walwala don duk abinda suke Yana jinsu Sarai tunda dakin na manne da nasa da gangan ya barsu suyita dakuwa. Hashim fitoh kazo ka raba yaran Nan Lahab zai kashe Majid ka Sansa da zuciya baisan Bari ba kayi Sauri tace tana Kama hannunsa Suka shiga dakin tare,da taimakon Hashim aka raba fadan Amma dai Majid ya daku Kam. Juyawa kawai Lahab yayi ya fita a dakin bayan ya hashim ya rabasu fadan,fita yayi a flat in gabaki d'aya ya nufi gate budewa yayi ya fita ya tare Mai keke napep ya hau direct gidan mamin sa ya nufa don yasan muddin ba gidanta yaje ba baisan Inda zaije da sassafen Nan ba, knocking na gate in yayi sau uku kafun Mai gade yazo ya bude ganin shine yasa sa basa hanya ya wuce tare da maida kofar ya rufe. Bude kofar falon Mami yayi a hankali yasa fuskarsa ya leka falon ganin ba kowa yasa shi Shiga cikin Sauri ya nufi wani kofa dake falon. tura kofar yayi ya shiga extra room ne ba kowa a ciki ya maida kofar ya rufe zare jallabiyar jikinsa yayi ya kwanta akan gadon yaja bargo ya luluba Koh 3 minutes baiyi ba wani wahalallen bacci yayi awun gaba dashi. ta bangaren Nnenna Kam tun 4 na asuba Mom tazo ta tada ta haka ta Mike jikinta ba kware ta shiga toilet ta wanke fuskar ta, jikinta da sauki sai dai hannun tane takejin sa ba dadi,sharan falon tayi da kitchen da baranda tayi mopping duka ta share tsakar gidan duka,wanke wanke dake kitchen duk ta wanke gidan shuru kowa na bacci sai ita kadai kawai tana aikace aikace,sai misalin 6 na safe ta Fara daura breakfast golden yam ta soya musu sai tie ibawa Kiki tayi tadau roban takeAway in Lahab ta zuba rabonta a ciki tasa tie a flask nasan Kamar jiya ta jera a laidan ta aje,kulolin ta jera musu a dinning lokacin karfe 7:00 yayi,daki ta shiga tayi wanka ta sanya uniform nata ba tare data tsaya taga saukowar jama'ar gidan ba ta sabe jakanta da laida tabar gidan. Adewale haka ya kwana bai rumtsa ba sai kusan 4 na asuba ya samu yadan kwanta,misalin karfe 7:30 papa yazo ya Fara surfa Masa matsifa akan ya tashi su tafi makarantan su Kamar yanda principal yace,shi Kuma Adewale yace babu Inda zashi baida lafiya sosai rikici ya barke mama ta rasa bayan wa zatabi na Ade Koh na papa,karshe ma da Adewale ya gaji fita yayi a gidan yabar papa sai masifa yake Wai ya raina sa. Ade na fita d'aga gidan su rasa ma Ina zaije yayi bazai iyya zuwa gidan su Nabeel yanzun ba saboda mubeena haka Koh gidan su Lahab bazai jeba,gidan su David dake kusa da gidan su ya Shiga dayake David irin yaran Nan ne da iyayen su ke musu part nasu daban hakan yasa sa wucewa part nasu David in yaje ya kwanta don duk basa Nan sun tafi makaranta. Mubeena yau haka ta tashi jiki ba kwari kome take a sanyaye Wanda har inna sai da ta gane Mata Amma ta Mata tambayar duniyan Nan amsa daya take Bata shine babu kome,shiryawa tayi cikin abaya baki da gyalensa ta rataya school bag nata a kafada kallon Inna tayi,Inna Ni Zan wuce!! Au yauma akwai makarantan ne shine kike kome a sanyaye? Eh Inna akwai makaranta yau Muna da paper da safe. Ke Kika San paper ni ban Sansa ba yanzun dai ga wannan saikiyi kudin machine chanjin ki rike a hannun ki,karba mubeena tayi tare dama Inna godiyan. Har tasakai zata fita a kofar saiga bappan su,tsungunawa tayi ta gaidashi,Ina kwana bappa? Lafiya mubeena sai Ina haka da sassafen Nan? Makaranta zanje bappa. Toh Allah ya bada sa'a Amma nidai bason wannan karatun nake ba kawai ki sanar da Ahmad in ya turo don Ni na gaji da wannan fikilin da sunan karatu in so yake kiyi karatun toh ya aureki Mana kicigaba a dakin ki baifi ba Amma ace budurwan shekara 20 tana gantali a titi wai ku yaran zamani Yan boko. Shuru kawai mubeena tayi Harya kareshie mitarsa tamar sallama ta wuce abinta. Bappa Ado da sallama ya shigo cikin gidan,amsa Masa Inna tayi,ah ah lale lale Ado ne yau a gidan mu wata Sabon gani. Hmmm Inna kenan wallahi abubuwan ne sai a hankali Amma Ni Karan kaina Ina son shigowar akai akai. Kaidai ka jiyo ganinan dai Nina haifeka sai kafi wata baka takoni ba gamu baki da hanci amma dayake ita asabe uwar matar kace gaka koh wani juma'ar Allah sai kaje gaisheta. Yanzun dai Inna don Allah kiyi hakuri Kuma wani munafukin ne ya kawo miki wannan gulmar? Nice munafukar dana jiyo gulmar Ado,shine amsar da Inna ta basa don ranta ya Soma baci. Kiyi hakuri inna? Daman baka mini kome ba duk Wanda yayi na gari dai don kansa ne,yanzun meke tafe dakai don nasan in ka taki kafarka a gidan Nan nakane ya kawo ka. Sunkuyar dakai yayi cikin kunya yace,Inna daman jiyane principal in makarantan da yaron nan Nabeel ki ciki ya kirani akan yau yanason ganina dashi Nabeel in duka shine yanzun nazo mu wuce muje muji Koh lafiya? tafa hannaye Inna tayi,watoh wani abin Nabeel ya sake jawowa kenan don in kaga irin wannan Kira daga shugaban makarantan kasan bana lafiya bane oh ni fatu Naga ta kaina,Bara na Kira maka shi Yana daki Yana baccin asara shi bai tsaya ya muri arziki yayi karatun ba shi baije shago ya nemi kudi ba tunda ya iyya dinkin Nan sai Kura dayake hadawa kansa,ya dawo gida ya zauna ya zanyi da wannan yarone Ni fatu tunda Nina haifi ubansa Kuma maraya dole dai Ni Zan zauna dashi in ba don hakan ba ardun Allah Koh hanya Ado bazan yarda mu had'a da yaron Nan ba, tana maganar tana nufan dakin Nabeel. tura kofar falangen tayi ta yaye yamusheshen labulen kwance yake akan katifarsa dake zagaye da kayan sawan sa Mai datti duk Akan katifar yake titd'awa in dare yayi ya kwanta akan su,daka Masa duka tayi a gadon baya Kai Nabeel tashi don uwarka. Mikewa yayi Yana yamusa fuska haba Inna wannan wani irin zalunci ne ace mutum na kwance Amma zakizo ki tasheshi da sassafen Nan Kamar na daukar Miki kudi Koh naci bashi? rufe min Baki shashasha ba gwara ma ka daukar min kudin ba Koh fitinan zata tsaya iyya kaina. toh yanzun dai menene da Zaki ta dani. Bappa Ado dake sauraron duk abinda suke cewa daga waje, d'aga murya yayi yace,melene dan kaniyanka innar tamu kake fadawa haka don baka da mutunci toh Maza saka kayan makarantan ka ka fitoh muje muji Kiran me ake Mana. Waro Ido Nabeel yayi da Sauri Jin muryar bappan sa da Kuma abinda yake cewa Wai suje school shap? ya tabbatar yau Ade da Lahab ba zuwa zasuyi ba karshe hukunci ya Kare a kansa shi kadai wallahi Bai Isa ba wane shi. Wai Ina nabeelu ne,ganinan bappa Ina zuwa ,sai Kuma yayi kasa da murya cikin magiya yace,don Allah innata kice Masa bari nayi wanka kinji dan Allah? Hararan sa Inna tayi tare da fita a dakin,Shima mikewa yayi ya dau rigansa yasa wayar sa dake zaune a gefe ya d'auka yasa a Aljuhu tare da daukar soson wankan sa Kamar gaske,ya fitoh a dakin tsungunawa yayi ya gaida bappan nasa,amsawa yayi sama sama,lafiya kaga Nabeel kayi Sauri kayi wankan kazo mu tafi nabar shagona a rufe fa. toh bappa yace da Sauri ya Mike yadau bokati ya ibi ruwa ya wuce bayan gida,Yana shiga aje ruwan yayi ya Kama ginin bayan gidansu daman guntune ya d'ale abinsa ya dirka ta lungun unguwan su,karkade wandonsa yayi ya Kara gaba abinsa. Yau ne gobe ne Nabeel bai fito ba tun bappa Ado na tsaki Harya Fara mita Yana kwalawa Nabeel Kira,gajiya yayi da jiran nasa ya tashi ya tsaya a hanyan kofar bandakin,Kai Nabeel chanja fata kake ne Kome?wanka Kamar wankan amarya,shuru make ji ba'a amsa ba. Inna Kam wani tunanin tayi sai Kuma ta girgiza Kai,Ado shiga ban dakin nan ka duba in dai na canki daidai toh Nabeel baya gidan Nan yanzun. da mamaki Ado yace kamar ya Inna baya gidan Nan? Kaidai shiga ka duba,ba musu ya shiga Aiko ba kowa sai ruwa da soso fitowa yayi Yana masifa,wallahi Inna Nabeel ya Raina Ni Sam baya ganina da gashi harni zai rainawa wayo toh na fasa zuwa makarantan ina da abinyi Amma saboda shi nabar kome nawa nazo muje naji dalilin Neman sa shine zai min iskanci? Ah ah baza'ayi haka ba kayi hakuri kaje kaji dalilin Neman naka karka Zama irin sa Mana shi yaki zuwa Kai kaki zuwa ai sai ran shugaban makarantan ya Kara baci kaje kaji in. Shikenan Inna saina dawo,toh Allah ya dawo dakai lafiya Ado,fita a gidan bappa Ado yayi. *********** Mubeena Keke napep na tsaidata a kofar school nasu ta d'auka biyan sa kudin sa tayi ta Soma takawa a hankali jiki a sanyaye tana ratsa makarantan tafiya tayi Mai nisa sosai kafun ta iso department nasu,Hawa block in tayi ta shiga Hall in lokacin dalibai sun cika tim a ajin ana jiran lokaci yayi wasu na zaune wasu na karatu wasu na hira wasu na tsatsaye a window d'aga kaga irin cikan nan kasan lokacin jarabawane Koh test kawai ake wannan sammakon da yawan,acan kujerun tsakiya ta hangi kawarta Ruky zaune da wasu friends nasu biyu Suna Hira ana dariya. Nufarsu tayi tana kiyastawa Ina ma inama itama tana da daman walwala Mana kamar da,ai data mure,Assalamu Alaikum. Amsa Mata sukayi dukansu Suna had'a Baki tare da kallon ta hannu Suka Bata Suka gaisa tare da matsa Mata itama ta zauna,kallon ta Ruky tayi,ya fama da karatu bestie? Alhamdulilah Ruky,shuru tayi kawai tana sauraron surutun su Ruky Amma ita Bata saka musu baki ba illa takardan ta data fitar tana bita kafun lokacin shiga jarabawan su ya cika. Misalin karfe 10 lecture in ya shigo,Suka Soma jarabawan,Basu Suka fitoh ba sai 11:30 gabaki dayan su suka zazzauna akan kujerun dake gindin bishiyar gefen block nasu don Suna da jarabawa anjima,daya kawar tasu ce ta Mike tare da musu sallama zataje hostel ta dawo. Kallon mubeena Ruky tayi sannan ta Soma Mata magana cikin hikima,mubeena meke faruwa? na fahimci tun jiya kike cikin damuwa duk da kina kokarin boye mini Amma ai labarin zuciya a tambaye fuska meya faru? dan murmushin yake mubeena tayi,babu kome Ruky kawai dai gajiyane da rashin samun isheshen bacci kinsan in exam yazo bani da nutsuwa sai anyi an gama? Haba mubeena Koh Zaki boyewa kowa kome bazaki iyya boye mini ba sai dai in Baki yarda dani ba, Koh Baki daukeni a matsayin aminiyar da Zan Baki shawara ba?ta karasa maganar ranta adan bace don tana Jin matukar haushin halin mubeena wasu lokacin akwai zurfin ciki da muku muku. Mubeena sauke ajiyar zuciya tayi Uhmm Ruky bansan ta Ina Zan Fara ba kinsan kaf duniya bani da kawa Kuma aminiya sama dake Amma akwai abinda baki sani ba guda d'aya, daya Jima Yana damuna Ina boyewa saboda kunya kaina da kaina nake,amma a Y'an kwanakin Nan na rasa meke tadomin dashi ga wani irin tsoro da fargaban rasa abun da nake. Wani Abu kenan da ban sani ba? gyara Zama mubeena tayi,tace Ruky a gaskiya bazan boye Miki ba zuciyata bata kaunar Ahmad? Kamar ya mubeena bata kaunar Ahmad daman bason Ahmad in kike don Allah ba kike tare dashi kike nuna wa duniya kina sonsa?Koh dai kin samu Wanda ya fisa kin wuce chaptern sa yanzun kina son sauyawa da wani? bara na fada Miki wallahi mubeena zakiyi dana sani a rayuwar ki ki dubi irin d'awainiya da Ahmad yake dake duk wani fadi tashi nasa akanki ne shine yau rana tsaka Zaki kawo min wani zance Wai baki sonsa? a zahiri ne Ruky kuke ganin haka amma a can cikin zuciyata bashi nake so ba na saurare Ahmad ne saboda nace mini da yake da irin yanda yake nuna tsananin Sona,na karbesa ne a matsayin masoyi saboda a tunanina Koh bashi dama da zanyi a rayuwata ya canja min ra'ayin dake zuciya ta amma fa ki sani tun kafun nasan Ahmad na Fara sonsa. Son waye kenan kike Kuma? bangane kin baiwa Ahmad dama dan ya chanja ra'ayinki ba kimin bayani yanda Zan gane manufarki da kyau. Mikewa mubeena tayi tsaye ta juyawa Ruky baya tayi dan taku kadan kafun ta tsaya hade da hade hannayen ta biyu waje daya hawaye ne Suka cika a idanunta har Suna sheki da zummar saukowar Kan farin kumatunta. Itama Ruky mikewa tayi ta matso gareta ta dafa kafadun ta,lalle wannan al'amari Mai girmane mubeena wakike ma wannan so haka wanene shi. Juyawa tayi Suna fuskar tan juna, hawaye Nabin fuskarta ta Soma magana,Ina sonsa najima da sonsa Ina Jin kunyar sa nayi iyya kokarina na ganin na binne abinda ke Raina ba tare da kowa ya sani ba amma Ina na kasa. Ki sani mubeena barin Kashi a ciki baya maganin yunwa wa kike son? Ba kowa bane illah lahabbbbbbb............. *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki* Page 47&48 Wani Lahab kike nufi mubeena ban gane ba? daman bazaki taba ganewa ba Ruky ni Karan kaina ban ganewa kaina ba. Ki fahimtar dani wani Lahab kuma. Kinsan kanina Nabeel? Kwarai nasan Nabeel Mana sau nawa Ina zuwa gidanku Ina samun sa Yana tsananin Kama dake fari sol kamarke in ban manta ba?. Yauwa akwai wasu yara biyu da Zakina ganinsu tare da dashi yawanci a gidan mu ma mutum yazo da wuya yatafi bai gansu ba. gyada Kai Ruky tayi,tabbas na gansu su biyu sa'o'in juna dayan black beauty sosai handsome dashi ruwan Fulani sai dayan Kuma wankan tarwad'a amma Kamar kabila kabila. Yauwa Ruky kin musu kyakkyawan sani,wannan black in shine Lahab Brown in shine Adewale,wannan Lahab in nake so sannan jiya Kuma Adewale ya tare Ni da wata magana daya matukar tayarmin da hankali don furtashi baraza nane gareni da Kara nisan tani da abinda nake so. Ruky Kam tama rasa wani hauka ne mubeena take,yanzun mubeena kina nufin wannan yaro friend na kaninki inne kike so sannan wannan kabilar daba musulmi bama kikace yace Yana sonki? Eh Ruky na Fara son Lahab ne tun da jimawa dayake tare Suka taso da Nabeel Kuma rashin jinsu daya tun Suna yara suka Soma abota,lokacin da Lahab yakai shekara 16 a lokacin sai na Fara Jin wani yanayi daban a tare dashi in har baizo gidan muba sai naji na matukar damu duk lokacin da yazo sai in jini cikin farin ciki na tsane Naga yazo gidan mu zai tafi sai inji tamkar na bisa mu rayu tare a duk lokacin da Suka samu matsala da Nabeel Suka daina ma juna magana Koda kuwa na wuni gudane sai naji tamkar na shekara ne, gashi ba zuwa nake gidan suba duk saina birkice na rasa meke damuwa har sai na gansa natsuwata take dawowa. A lokacin da na Kara girma saina fahimci babu abinda ke d'awainiya dani face son Lahab,nashiga tashin hankali nayi kuka na roke Allah ya ciremin sonsa a raina Amma Ina kullum Kara Jin sonsa nake na jiya yafi na yau,Yaya zanyi Ruky taya Zan fuskance duniya in d'aga yatsa in nuna Lahab a matsayin Wanda nake so So ma irin na aure? dole tasa na daina sakar musu fuska na ringa nuna Masa hali Koh Allah zaisa na daina damuwa dashi Amma na kasa na kasa Rukayya,sai kuma ta fashe da matsananci kukan tana dukawa akan gwuwuwin ta. Itama Rukayya dukawa tayi ta kamo kafadar mubeena ta mikar da ita,hannunta ta Kama suka koma Kan kujera Suka zauna ganin hankalin mutane ya Fara dawowa kansu. Ke share hawayen ki mubeena shifa so haddin Rabbine,Allah shike dasa so a zukatan bayinsa ba wayonki Koh dabarar ki bace zai rabaki da abinda kikeji ba, illah Addu'an Allah ya zaba Miki abinda yafi Zama Alkhari a gareki. mubeena hannu tasa ta share hawayen fuskarta insha Allah kuwa Ruky,sannan ta cigaba da Bata labarin,toh ganin sonsa sai dad'a ninkuwa yake gaba d'aya,bangaren Ahmad Shima Yana mutuwar Sona duk irin wulakancin da Zan Masa haka ya nace mini,d'aga karshe dana zauna nayi tunanin Mai zurfi saina gano lallai Ahmad najin zafin abinda nakeji taima ma Harya fini tunda Ni so kawai nake Ina hauka na Ni kadai shi kuwa ya furta Amma bai samu karbuwa ba? Hakan ne yasa na basa dama,tun a farko da zancen aure yazo hakan yasa na Soma Masa kolo kolo nace saina gaba secondary bayan na gama ne ya sake tada maganar akan shi yanzun Yana son aure ne,Nan ma nace saina juna gaba da secondary saboda irin son da yake min yasasa amince wa duk da kullum Yana sanar dani mahaifiyar sa na nuna Masa bacin randa akan kin Saida maganan auren sa da baison Yi. gashi yanzun na samu shiga college duk Kuma a cikin Aljuhunsa kome nawa shike min Kama d'aga kudin makaranta suturu duk shike saimin in Kika cire Inna da itama tanamin daidai gwargwado Amma Yan uwan babana dana mamata basu San Koh a sallah su saimin turmin zani ba. Amma fa ki sani har gobe son lahab na d'awainiya dani Kuma ganin da nayi mundin na aure Ahmad shikenan Zan daina ganinsa,shine dalilin na na kasa baiwa Ahmad daman aure na har yanzun,ga Kuma Adewale daya bullo Wai Yana Sona Kuma na tabbatar Lahab zaisan maganan Nan saboda duk wani Abu da Ade zaiyi saiya shawarce Lahab sama da Nabeel Yaya zanyi Rukayya wallahi kirjina zai fashe zuciya ta ta kasa mini Adalci taso abinda bazata samu ba taso abinda zai Bata wahala wayyo Allah na,tana maganar tana kuka ita kanta Ruky Saida hawaye ya cika Mata a ido. Handkerchief nata ta d'auka tasa a fuskar mubeena tana goge Mata hawaye kafun a hankali ta fara Mata magana,mubeena da ace Lahab da Adewale sun dai 25 ko 30 kinsan shawaran me Zan Baki? girgiza Mata Kai mubeena tayi. toh da sai nace Miki ki hakura da Lahab kiyi accepting na Adewale Koh don saboda soyayyar ki dake ransa zai Zama sular musulun tansa in Yana da rabon musulunci,Kinga kema kinyi jahadi,Amma Kinga Lahab baisan kinayi ba sannan baisan kina sonsa ba ga aminin sa na sonki kinsan da wuya ya amince,nidai Zan Baki shawara karki kuskura kiyi Wasa da daman ki sama sau daya yake zuwa wa mace na zaben mijin da taga dama tana so daga xaran shekaru sunja sai dai fa a koma Addu'a Allah ya bada mijin Koh ma yayane. Kin gannin Nan mubeeena a shekarun baya ba irin sonda Nazeer Bai nuna mini ba yasoni Kamar hauka Amma kullum cikin wulakantashi nake yasha turo abokansa suzo su min magana akan irin tsananin son da yake min Amma na kekashe kasa naki kememen na nuna bana kaunar sa Amma Sam ba haka bane a cikin zuciyata Ina sonsa na Kuma kasa sanin me yasa bana nuna Masa son. A karshe wata cousin nasa ya aura Wance ta fini kyau da kuruciya nayi bakin ciki nayi kunci,gashi yanzun Koh da kudi aka basa akace ya aureni bazai yarda ba gashi nima yanzun babu wani tsayaye gajiya da zaman gida yasa mahaifina sani a college,gashi haryau babu Wanda yake zuwa da sunan Sona a kofar gida sai dai samarin online. Ki dubi malamar mu Nan ga ilimi ga kyau ga kudi Amma babu miji,sannan naji labarin ta a wajen aunty laure tace min lokacin da suke Yan Mata baiwar Allah Nan tayi farin jini Kamar na hauka kowa yazo tace sai boko ita bazatayi sure ba wasu sun yarda zasu aureta ta cigaba a gidan ta Amma taki,ki dubeta a yau ta haura 30 da wani Abu Amma babu miji. don haka kima kanki karatun ta natsu tun duniya Bata Miki ba karkice Zaki biyewa kawa zuci ta kaiki ta baroki in ba rashin tunanin ba Ina ke Ina Lahab bare Ade Suna da abinda zasu rike kansune bare su rike ki? duk da Suna yaran masu kudi Koh dangin su zasuyi maraba dake?in Kuma kikace Zaki jirasa sai ya girma toh shi Kuma a lokacin zai zabo santaleliyar yarinya ya aura a barki da dana sani. Dan Allah Rukayya ki dakata ya haka kina ta zancen lokaci lokaci karfa ki manta aure nufin Allah ne duk wayo Koh sakaci Koh dabara baya Hana aure baya saka aure don haka kawai in zaki bani shawara ki bani Kuma har yanzun akan bakana nake Ina son Lahab tamkar numfashina Kuma ba'a haifi Wance zata rabani dashi ba muddin Ina numfash.....kafun ta karasa sukaji faduwar mutum a bayansu ji kake timmmmmmm ****************** ta bangaren gidan su lahab daman tun da su muneera suka dawo makaranta ba Lahab muzammil ya tambaye su sukace yaje school Amma da aka tashi yabi su Nabeel Sam sunki fadawa kowa gaskiyar abinda ya faru. principal na makarantan su Lahab ne ya Kira muzammil akan gobe Yana son ganin su shida kanin sa a school day safe,hakan ya tabbatar wa da muzammil lallai akwai babban abinda Suka aikata kenan tunda gashi har yamma lilis bai dawo gida ba. Wasa wasa har mangariban ba Lahab hakan yasa hankalin Abbu tashi don yasan duk yawon Lahab baya dare a waje, waya ya d'auka ya Kira Mami Amma tace Lahab baya wajen ta,take ya tuna toh Koh gidan jafar yaje, muzammil ne ya d'aga waya ya kira ya jafar Kuma ya tabbatar Masa Lahab nagun su yaso a daren yaje ya dauko sa Amma jafar yace ya barsa ya kwana da safe yazo ya d'auke sa. Washe gari misalin karfe 7 na safe a gidan jafar ya samesa amma Ina ya makara kafun yazu ma Lahab ya Kara gaba abin ya Kara kula muzammil sosai ya cika tim gashi yazo yaji labarin sunje party sun kwana a bakin Hashim don Hashim daman haushin su yakeji kaf familyn su su ukun Nan sun ishesu Amrat Majid Lahab,Kuma yanajin dadin yanda muzammil kecin ubansu sosai. muzammil da kansa yaje har gidan Mami lokacin mijinta baima fita ba Suna karyawa a dinning da yaransu ya shigo Alhaji kawai ya gaishar don daman basa shiri da Mami sam,Amina Ina Lahab? Wani kallo Mami ta Masa Jin tambayar da ya Mata yasa ta kin kallon sama, sai mijinta daya basa amsa, muzammil Lahab Bai zo ba Allah dai yasa lafiya Koh? Juyawa yayi fuuuuuu ya fita a gidan mami kam da dogon tsaki ta rakasa dashi. ************* A makaranta yau Nnenna tayi ta zuba Ido da tsammanin ganin Lahab Amma shuru babu shi babu alamar sa gashi itama yau ta zubo Masa abincin gidan su ta kawo da zimmar zaizo. A office in principal Muzammil ne da pastor baban Adewale sai bappa Ado,gabaki dayan su babu Wanda yazo da students in nan guda uku hakan ya Kara kular da malaman a ganinsu tunda har su Lahab basa Jin maganar iyayen su babu amfanin a bar musu su Lahab a makarantan. Principal ne ya mike Rai a bace yace tunda har abin ya koma haka Ni d'aga yau bana son ganin yaran Nan a cikin makarantan naaaaaaaa ************** Lahab na kwance Yana sharara bacci bashi ya farka ba sai kusan 10:30 na safe Nan ma yunwa ce ta tashesa bawai don ya koshi da baccin bane a hankali ya mike zaune Mika yayi a tsaye tare da hautsana gashin kansa Mai yawa da laushi,agogon dake dakin ya kalla,ganin 10 yasan yanzun babu kowa a gidan sai Mami hakan yasa sa fitowa a dakin d'aga shi sai wando 3quiter dake jikinsa bude kofar yayi ya fito falon Yana kaikaya gashin kansa. Mami dake zaune akan kujera tana feeding na yaron ta Mai kimanin shekara 1 fari Sol dashi kyakkyawa, Lahab ne koh dai ba Kai nake gani ba? "Dan tsayawa yayi sai Kuma ya shagwabe fuska yace nine mami" Kardai kace min a gidan Nan ka kwana na bunu yayan ka yazo neman ka nace baka Nan? "Matsowa yayi kusa da mamin ganin kaninsa dake Kan cinya ya sake no-no Yana ihu Yana Mika Masa hannu Wai ya d'auke sa,sa hannu yayi ya dauki yaron ya wurgashi sama ya cabe ai a take ya shiga babbaka dariya har hakoransa guda biyu na kasa suka bayyana. Murmushi Mami tayi,kasan Yusuf ya d'auka Rahab ne harda marmarin ka dagasa,don kai dai bantaba ganin ka d'auke sa ba da sunan Wasa. "Aikam Naga alama Mami na Yana maganar Yana Kara wullah yaron sama. Kai Lahab ban yarona karka zoka kadamin shi a banza,tace tana kwace yaron,dariya yayi kawai ya zauna akan daya d'aga cikin kujeran da Yusuf a hannunsa don yaki sakema mamin shi,itama kitchen ta nufa abinci ta Iba ta kawo wa yaron ta Kuma dan farinta Mafi soyuwa a ranta,sarkin rigima Lahab,Jan center table dake tsakiyar falon tayi zuwa kusa da kujerar da Lahab ke Kai ta aje masa. gyara zama lahab yayi da Yusuf a kafan sa ya soma cin taliyar da mami ta aje masa, itama mamin zama tayi a gefen lahab suka soma hira na tsakanin d'a da uwa, wai lahab meka yiwa muxammil ne yazo yana nemanka a fusace, Lahab kai me kake so ka zamane da bazaka natsu kamar dan uwanka ba?ka duba yanda kowa ke maganar rashin jinka Sam banajin dadin abinda kake,ga taurin kai ga kin zuwa makaranta. Kwarewa yayi garin zai baiwa Mami amsa da Sauri ta mike ta ibo masa ruwa da kanta ta kafa masa kofin a baki, hannun sa ya daga ya daura akan hannun nata yana sha,Yusuf dake kan cinyansa hannu yasa akan plate in taliyan ya dumbula wai zaici, dan janye bakinsa akan cup in lahab yayi ya kama hannun Yusuf in. Zama mami tayi ta aje kofin ruwan hade dasa hannu ta karbi Yusuf in tana cewa lahab, maza kaci abincin saika amsa min meka yiwa muzammil. dan shuru yayi sai kuma ya aje spoon in hannunsa kallon mamin yayi a hankali hace"mami nasan kaf duniya koh zan fadi Abu Aki gaskatawa indai gaskiya ne na tabbata zaki yarda dani koh"? Kwarai kuwa Lahab, Mami tace "toh mami na fada miki wani Abu"? Eh fadamin naji Lahab. "Wallahi mami jiya farida matar da Anwar zai aura na gani a hotel taje party har 12 na dare" Mikewa mami tayi tsaye har Yusuf na subuce mata a hannu ta tarosa ta soma tambayar sa, Lahab kai meya kaika hotel harka ganta karfe 12 na dare.........???? *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki* Page 49&50 sunkuyar da Kai Lahab yayi bai bawa Mami amsa ba,wanke sa da Mari tayi cikin bacin rai tace,bazaka fadamin mai ya kaika hotel a lokacin? Lahab me kake son Kan Zama ne,ashe shiyasa muzammil keta nemanka ruwa a jallu? dafe kumatun sa yayi Yana kallon Mami dake ta surfa masifa meya kaisa hotel,mikewa yayi Koh riga babu ya Kama hanyar fita,kwala Masa Kira Mami tayi,Lahab Lahab Ina zaka Ni sa'ar kace da Ina maka magana zaka wuce ka fita,toh ka dawo Nan,ta nuna Masa kujerar daya tashi,kin dawowa yayi ya bude kofar falon ya fita ya maida kofar da karfi ya rufe,shi abinda yafi Bata Masa rai ba kome bane illah Marin da ta Masa Amma in badon haka ba da dakansa zai gaya Mata kome. Fita gate na gidan yayi gashin kansa a yamutse jiki ba riga,a haka yayita tafiya duk Inda ya wuce sai an bisa da kallo mutum lafiyayye amma ace Yana yawo ba cikekken tufafi,a hakan ya gangaro kasan unguwan gidan su abokin sa da ranan Suka aje Keke ya shiga,ya karbi riga,Keke napep ya hau bai zarce Koh Ina ba sai gidan yayan mamin sa uncle muneer Keke na sauke sa a kofar gidan ya biya Mai keken ya shiga gidan. ******************* Nnenna tayi ta tsammanin ganin Lahab amma shuru shuru har 2 na Rana bata gansa ba dole yasa ta cin doyanta,bayan an tashi makarantan ita kadanta ta Kama yanda da kafa tana tafiya tana tunanin Ina Abraham ya shiga kwana biyu bata ganin ziryarsa a gidan. Lahab Kam baisa mu uncle a gida ba Yana kasuwa, wanka yayi yasa Kayan mansur dan uncle muneer ya fita a gidan direct hotel in daren jiya ya koma daker aka barsa ya shiga Hall in,amma Yana shiga ya samu an gyara Hall in an share haka yabi sit by sit Yana duba wayar amma bai gani ba,wajen manaja hotel in ya nufa, office in ya tura ya shiga bayan an basa izini, "Assalamu Alaikum" Waalaikumu Salam Bismillah ka zauna? Zama Lahab yayi Kamar yanda manaja ya bukata,an wuni lafiya"? Lafiya Alhamdulilah ince dai lafiya Koh hall kazo kamawa?muna da hall masu girma da tsari Kama daga na birthday har na program in biki "No ba hall nazo kamawa ba sir jiya nazo party a hotel Nan a cikin hall naku na kusa da packing space so na manta wayata ne ta Fadi a karkashin kujera shine nazo na tambaya Koh Allah yasa cleaner naku sun gani wayan is very important to me ne shiyasa na dawo. a gaskiya banace ba saboda Ni da safe na tura cleaners suje su share Hall in sai dai bara a Kira su a tambaye su Koh sun gani? "Ok toh ba matsala yallaboi" Waya manaja ya d'auka yayi Kira ba'afi 10 minutes ba sai ga ma'aikata masu share share sun shigo su biyar ne,Suna shigowar suka gaida manajan kallon su yayi,a cikin ku su waye Suka share Hall in kusa da packing space? Mune sir wasu guda biyu sukace mace dana miji,kallonsu again manaja yayi kafun yace,akwai phone da aka manta a hall in koh akwai Wanda ya d'auka a cikin ku? duk kansu biyu girgiza Kai sukayi da Sauri macen sai wani zare Ido take tana tsinne kai,mikewa kawai Lahab yayi ya fita a office in Jin manaja nace Masa su Basu ga wata waya ba taima ma a cikin wa'inda sukazo party wani ya d'auka,Yana fita a hotel in machine Lahab ya hau zuwa makarantan su har sun kusa da makaranta ya hangi mace na tafiya sanye da uniform Kuma Yana kyautata zaton Nnenna ne d'aga tafiyan ta ya gane ta sauka yayi a keken ya biya Mai keken kudinsa yabi Nnenna a baya ba tare da ya Mata magana ba. dan dakatawa Nnenna tayi haka kawai jikinta ke bata ana kallonta juyawa tayi tana kallon bayanta,Kamar a mafarki idanunta ya shiga cikin nasa waro Ido tayi cikin happy tana kallon sa,Shima kallonta yake Yana murmushi ji yake Kamar yayi shekara Bai ganta ba sosai yake kewanta. matsowa yayi kusa da ita har lokacin fuskar sa d'auke da murmushi,hannun damansa yasa ya Kama haggunta,da Sauri ta zabura tare da kokarin fusge hannunta Amma Ina ta kasa don riko ya Mata na gam gam,sakeni shine abinda take cewa tana dad'a fisge wa,"kee ki natsu Mana"Jin abinda Lahab yace Mata yasa ta d'aga Idonun ta tasa a cikin nasa sosai take bin fuskarsa da Ido,ka sakarmin hannu yamma yayi Zan koma gida. bai bata amsa ba sai hannu daya sa ya dau jakanta dake kafadarta ya bakka a bayansa har lokacin bai sake Mata hannu ba ya Soma tafiya tana binsa a baya tafiya suke babu Mai magana,tsallake titi sukayi ya nufi wani babban restaurant kallon wajen Nnenna tayi sannan ta sake kallon sa,Inane Nan? Koh ma inane muje in mun shiga Zaki ganewa idanunki,shiga wajen sukayi har lokacin hannunta na cikin nasa Zama yayi akan kujeran dinning dake wajen yaja Mata nata"ki zauna" "Nifa bana Jin yunwa" "Uhmm Koh bakiji sai kinci" Abinci aka kawo musu fried rice sai ferfesun kaza,plate biyu aka jera musu,shokali Lahab ya d'auka ya Mika Mata ganin bata d'auka ba karba tayi ta rike tana bin abincin da kallo, Lahab Kam harya Soma cin abinsa Amma hankalinsa na kanta ganin har lokacin bataci kome ba yasa sa magana,"Wai bazakici abincin bane in Kuma bai Miki ba sai kiyi magana a kawo abinda kikeso" girgiza Masa Kai kawai tayi ta saka shokali a plate in shinkafan ta Iba sosai takebin shinkafan da idanu sannan a hankali ta matso dashi kusa da hancinta da Sauri ta maida shi cikin plate in"ni nace maka na koshi fa" abincin sa Lahab ya cigaba daci sai Kuma ya dakata Jin tambayar da Nnenna ta Masa,shin "meyasa bakazo makaranta ba yau"? "Hakan kawai"shine abinda yace Yana daukar cinyar kazar yanaci. "Naji jite jite ance Wai an koreku"? Hhhh korata Kuma Labiba?Aiko an koreni anyi a banza bayau aka Saba ba Kuma nake komawa. "Kamar ya kenan bangane ba"? "Jira nake case in yayi sanyi saina dawo" Uhmm meyasa toh kaki komawa gidan ku?Nnenna ta tambaye sa again da Sauri ya kalleta da mamaki yace"waya fadamiki bana gida? dan sassaita kanta tayi shuru,Kara tambayarta yayi shuru ba amsa Shima bai wani damu ba don yasan bazai wuce a bakin Yan gidansu Koh malamai zancen ya fitoh ba. Yago kazar yayi ya nufi bakinta Yana cewa"haiii bude Baki na saka Miki"kin bude bakin tayi sai wani kallo da take Masa Shima yaki sauke hannun nasa dake d'auke da tsokar kaza,a hankali ta Soma magana"nace maka banaci banaci dole ne"? Sauke hannun nasa yayi Kamar ya hakura sai Kuma ya shammace ta da Sauri ya tura Mata namar a Baki,ai a take tasa hannunta ta buge hannun nasa sai da ya Fadi daka kan kujerar zuwa kasa yayin da ita Kuma ta duke a wajen tana tufar da kazar dake bakin nata,sai Kuma ta dago da Sauri Jin yanda Lahab ke Nishi abin mamaki kwance yak har lokacin ya kasa tashi sai wani had'a zufa da yake Yana rike da hannunsa. *************** Juyawa su mubeeena sukayi da Sauri Suna duban Wanda ya fadin ba kowa bane face Ahmad kwance a kasa ya Suma uhu mubeena ta sake ta nufesa da gudu tana kuka,dukawa tayi a kusa dashi tana girgiza sa tana kuka,don Allah ka tashi Ahmad in wani Abu ya faru dakai bazan yafewa kaina ba. Rukayya Kam da gudu tayi gate na makarantan nasu Keke napep ta tare ta shiga Suka dawo makarantan har wajen da mubeena suke Suka matso sauka tayi tare da rokon Mai keken napep in akan ya taimaka masu asa Ahmad a aciki,da taimakon Mai Keke da wasu samari aka sa Ahmad a Keke napep Suma su mubeena suka shiga,asibiti aka wuce da Ahmad direct d'aga zuwansu aka basa gado,gashi su mubeena nada paper gashi sai kuka take daker dai rukayya ta lallabata tare da karban wayanta daman akwai number kanwar Ahmad Kira Rukayya tayi ta sanar da ita an Kama yayanta a gadon asibiti,basu Kai Koh 20 minutes ba saiga kanwarsa da mamansa da babansa sunzo,Suna tambayar abinda ya samesa mubeena ta kasa magana sai kuka sun ma rasa me zasuce sai rukayya ce tace musu Suma Basu sani ba kawai ganin sa sukayi ya yanke jiki ya Suma a makarantan su. Ok toh Allah ya basa lafiya shine abinda baban sa yace,Suma Su mubeena Addu'a samun sauki Suka Masa sannan Suka fita a hospital in mubeena taso ta koma gida amma Rukayya tayita lallabata daker ta amince Suka koma school Suka rubuta paper,sai yamma lilis mubeeena ta nufi gidan su tunda ta sauka a Keke napep ta hangesa tsaye a kwanar layinsu,Yi tayi Kamar Bata gansa ba har tazo saitinsa zata geftashi taji ya Kira sunan ta,mubeena mubeena. Shuru tayi bata amsa Masa ba takowa yayi Suka Soma jerawa tare har lokacin bata kulasa ba,dan Allah mubeena ki saurare ni mana wannan wulakancin duk saboda nace Ina sonki ne? dakatawa tayi tare da Soma magana,kaga Adewale ka fita d'aga harkata da rayuwa ta banason dogon zance in Kuma kaki wallahi saina shimfida maka dana sanin da zakayi nadama. Nadama fa kikace mubeena menene abin nadama a sonki da nake. dan Allah dakata son banza kenan toh bari na fada maka Ni bana sonka bana sonka bana sonka wannan kalma jinsa yayi tamkar kifiya haka yajita a Randa sosai maganar ta Masa zafi Wanda yasa sa kasa binta sai Ido daya zuba Mata har ta shiga gida. Da sallama mubeena ta shigo gidan nasu, Assalamu Alaikum Waalaikumu Salam mubeena sai yanzun? Eh wallahi Inna kinsan exam muke shiyasa ban dawo da wuri ba. Toh ki Shiga ciki ki Kwabe kayanki ga abincin ki Nan saiki zo ki d'auka. Toh Inna shine amsar da mubeena ta bata tana shiga dakin Kwabe kayan jikinta tayi ta daura fellen zani a kirjinta ta fitoh a dakin kitchen ta shiga ta dauko kwanon abincin nata ta zauna a gefen taburman da Inna ke zaune akai bude kwanon tayi dan wake ne yaji burkono da Mai gaurayawa tayi tayi Bismillah ta soma ci a hankali bawai don tana ra'ayi ba sai gudun kada Inna ta zargi wani Abu,ta danci kadan kafun ta rufe kwanon alamun ya isheta. Badai Harya isheki ba mubeena? Wallahi Inna na koshine. Wani irin kin koshi mubeena abincin da kikafi sone fa na girka Miki sannan Koh shokali biyar lafiyayye bakiyi ba kicemin kin koshi? Mikewa tayi ta dau bucket ta nufi rijiyan dake tsakiyar gidan ta zura guga tanajan ruwa ba tare da ta baiwa Inna amsar taba itama innar bata Kara magana ba sai binta da kallo da take gabaki d'aya yarinyar ta susuce ga tarin damuwa a fuskar ta amma tasan halin mubeena da zurfin ciki shiyasa bazata sake tambayar ta damuwar taba sai in tayi ra'ayi da kanta ta fada Mata, bucket in na cika ta shiga daki tadau kwandon sosonta ta sabe bucket in tayi cikin bayan gida. Bappa Ado ne ya doko cikin gidan Koh sallah babu tsabagen yanda ransa ke bace,ah ah Ado menene haka ya kana girma kana Kara shiga daji aka sallamar ma ya gagara zaka Fado Mana cikin gida Kai tsaye. dan Allah Inna kiyi hakuri raina ne duk a bace. In ranka ne a bace Ado sai ka shigo waje ba sallama,Zama yayi agefen ta wajen da mubeena ta tashi tare da cewa Inna,wallahi Inna yaron Nan Nabeel ya raina mu? Meya faru Kuma me yayi akace maka a makarantan?Inna ta tambaye sa. Inna Wai kinji abinda shugaban makarantan su yace Ashe Nabeel da Yan iskan abokan San Nan Suka hadu Suka bugi malamin su. Da mamaki Inna ta ce,dukafa kace Ado Kai Amma wa'innan yara anyi marasa kunya shi Kuma Nabeel ShaShaSha su duk abinda Suka aikata Suna da gata shi Kuma fa Ado kana ganin kudin makarantan su yaron Nan dubu darine fa duk tam(team) su suke biyan Masa maimakon ya tsaya ya more su yayi karatun sa saiya tsaya shashanci su sukiyi Shima yaki. Gyara Zama Ado yayi,wani irin karatu ma Inna bayan an koresu. An koresu fa kace Ado? Kwarai ma kuwa anan ya fada Mata duk yanda akayi da principal sosai Inna tayita mita kawo Ado sallama yayi Mata ya tafi abinsa. Nnenna Kam kuka ta sake sosai ganin halin da Lahab ke ciki sai had'a zufa yake Yana dafe da daya hannun nasa yama kasa Koh mikewa zaune,da Sauri ta matso wajensa tasa hannu ta dagosa zaune, customers dake cikin restaurant in gabaki dayansu hankalin su ya tashi ganin halinda Lahab ke ciki ga kukan da Nnenna keyi su Karan kansu ma'aikata sun tashi hankalinsu ganin wani ya Shiga matsala a cikin shagonsu. Mutumin dake zaune kusa da table in su Lahab ne ya mike a hankali ya nufi Nnenna ganin mutanen wajen sai zaginta suke akan kome ya samesa itace sanadin kome harda cewa su fitar musu a shago,karasowa yayi kusa dasu yasa hannu ya dago Lahab tare da kallon Nnenna dake ta kuka jikinta sai rawa yake harga Allah Bata bugi hannunsa da niyar cutar dashi ba mutumin da ya taimaketa a rayuwa yau an waye gari ita ta cutar dashi,dau jakanki muje asibiti don ina tunanin ya samu matsala a hannun sa,shine abinda mutumin yace Mata Yana tafiya da Lahab bayan ya tallafesa. Da Sauri tadau jakanta tabi bayan mutumin daya riga ya fita waje,amma abinda ya bata mamaki shine tana fita kawai ta nemi mutumin da Lahab ta rasa,hankalinta a tashi ta Soma tambayar mutanen dake tsatsaye a bakin restaurant in Koh sunga wani mutumin sanye da farin jamfa da wando Yana rike da wani dan makaranta?amma kowa cewa yake baigansu ba dawowa tayi cikin restaurant in ta tambaye su Koh mutumin bai fita bane amma Suka tabbatar Mata ya fita Mana harma tabi bayan sa,dafe kanta tayi da karfi jikinta na rawa sai Kuma ta Mike da mugun gudu ta fita a cikin restaurant in................. *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki* Page 51&52 Sosai ta rikice tana bin wajen shagon da Ido sosai jikinta na rawa kallon wani Forest dake gefe da shagon tayi,da Sauri ta nufi dajin tayi cikin bishiyoyin kaman ance ta dubi damanta kawai taga mutumin nata Sauri da Lahab Kamar ma baya hayyacinsa,da wani irin mugun gudu ta nufi mutumin unexpected tasa hannu ta bangajesa har Saida Lahab Shima ya Fadi timm a Kan wasu ciyawe wuyan mutumin ta shake da karfi sosai ta had'a bayansa da jikin wani bishiyan zaiti,sosai ya shaku Wanda a take kamanninsa Suka Fara sauyawa zuwa na wannan tsohon sosai jikinta ya Kara d'aukar rawa Shima sai kokarin kwatar kansa yake a wuyanta ga tari na caarkesa Kamar xai mutu,ki taimaka karki illah tani ki sakeni ki sakeni Zaki cutar dani akan wannan yaro,shine abinda tsohon yake fada har lokacin ya kasa kwatar wuyansa. Hawaye ne sun cika idanun Nnenna ta soma magana"na maka gargadi na sake na maka gargadi akan Hassan ka fita daka hanyan sa amma kaki na fada maka kabar zuwa Masa a mafarki kaki sannan yanzun ka koma farautar sa"? Jin abinda tace yasa sa zabura cikin zafin nama yasa kafa ya tunkudeta sai da ta Fadi a kasa a take ta Mike tsaye tana binsa da mugun kallo,tabbas dole na bibiye sa tsawon shekaru muna baki kariya akan me rana tsaka zaizo ya chanja Maki zanen kaddarar ki d'aga tsarin mu zuwa nasa. "rufemin baki ku kun Isa ku zanamin kaddarar rayuwata kun Isa babu Wanda ya Isa ya tsara wa mutum abubuwanda zai faru dashi bace abinda God ya tsara wannan karyane" Bari kiji bazamu lamunce Hassan a rayuwar ki ba bazamu lamunta ba tsawon shekaru kin rayu bisa tsarin mu baki Isa ki kauce ba ata dalilin sa ba ki kaurace Masa muddin kina sonsa a raye. "taya Zan rabu dashi tunda nake bantaba samun Wanda ya damu da damuwa ta ba ban tana haduwa Koh Samun Wanda yakeson kasancewar dani a tare dashi ba,sai yanzun Hassan ya rabeni ya nuna min tausayi shida shayibu mundin kanason kanka da lafiya ka fita harkan sa ka fita harkansa ka fita wannan ne gargadi na karshe da Zan maka na rantse ka Kara rabarsa nice ajalinka kaji ka fada musu iyya wuya Ina tare da shi"tana karasa maganar ta tsunguma ta cicibi Lahab abin mamaki ba tare da ta wani ji nauyinsa ba abayanta ta goyasa ta dau jakanta ta juya tana tafi ba tare da ta sake kallon Inda tsohon yake ba har ta bar Forest in. Maharbi dake tsaye tun d'azun a cikin wasu ciyawe da Ido yabi Nnenna Harta bace sannan ya dawo da kallonsa ga tsohon amma Ina baigansa ba girgiza Kai kawai yayi yaci gaba da tsintar maganin sa. Nnanna har bakin titi ta fitoh da Lahab a bayanta Keke ta sayar Mai keken tsayawa yayi Yana tambayar ta Inda zai kaita ganinta d'auke da mutum a bayanta ga hannunta rike da jaka. "Asibiti nake so ka kaini" Nnenna tace cikin turanci. Ke in zakiyi hausa kimin hausa. Shuru Nnenna tayi don bata fahimce me yake nufi ba gashi bata iyya hausan ba,Mai Keke Kam Jan kekensa yayi ya Kara gaba ya na masifa. Ta Jima a wajin kafun ta samu wani Mai keken dan niga-niga dashi,tace Masa asibiti zai kaita. Cikin dan gaya gayan turancin sa yace mata meya samesa naga baya motse. Kawai malam ka kaimu asibiti,shine abinda tace kenan tana kallonsa. shiga muje,a hankali ta sa Lahab a cikin keken itama ta Shiga,wani asibiti Zan kaiku?Kowan ne ma maikyau sannan don Allah kayi Sauri. Karki dawo da gudu ya fege keken bai tsaya Koh Ina ba sai wani Private hospital ya faka. Sauka Nnenna tayi tare da rokonsa ya Kama Mata Lahab su shiga ciki. dazun waya d'auka Miki shi da yanzun Zaki wani ce na rike Maki shi da Allah ban kudina na Ware. Waro Ido tayi sai ma yanzun ta tuna bata da ko sisi a hannunta,kaga ka taimaka ka Kama mini shi mushiga saina karbi kudinka na baka,cikin masifa yace daman kudin nawa bake Zaki bani bama kenan? Shuru tayi taki kulasa Shima cikin haushi yazo ya Kama hannun Lahab da Sauri ya zabura domin hannun ne Nnenna ta buge Masa,"Kai malam menene haka nace maka hannunsa zaka kama ne" don Allah rufemin Baki Yar banzan inyamura In ba hannu ba Ina kikeso na Kama Masa,Bata kulasa ba tasa hannu ta cicibi hakarkarin sa ta cirosa a keken wani cleaner ne yazo da gudu ya taimaka Mata ganin Kamar zata fadi. Cikin asibiti Suka shiga da gudu akazo aka karbi Lahab akayi wani daki dashi,Zama tayi a hall in Mai Keke sai masifa yake akan ta basa kudin sa kin kulasa tayi har hankalin mutane ya dawo kansu wani mutumine ya tambaye sa kudin sa yace 200 ne yasa hannu a Aljuhu ya zaro 500 ya Mika Masa. Canji Mai keken ya basa Amma yace Masa ya bari kawai, sosai Mai keken yayi ta godiya ya juya ya tafi,kallon ta mutumin yayi,Kinga Yaya karki Kara shiga abin mutum in baki da kudin biyansa hakan babu kyau gwara ki roka ya kawoki a kyauta kinjiko? Kallonsa Nnenna tayi Kamar Mai gane abinda yake fada tadai fahimci Holo yake Mata hakan yasa ta gyada Masa Kai ba tare da tayi magana ba ta Mike Jin ana niman Wanda ya kawo patient asibiti,mikewa tayi tace itace kiranta nurse in tayi tare da Mika Mata takarda ta Sayo abinda aka lisssafa,daukar jakan makarantan ta tayi ta karbi takardan tana sake saken ina zata samu kudi ita Kuma har tayi nisa sai Kuma ta dawo tunawa da d'azun taga Lahab yasa hannu a Aljuhu ya zaro kudade a restaurant da Sauri ta shiga nurses station ta roki nurse in akan tanaso taga lahab. Kee yanzun dai doctor na ciki Kuma tsagewan Kashi ya samu za'a daura Masa hannu sannan kizo kice Zaki gansa bama ta abinda akace ki siyo kike ba. dan rusunawa tayi tace"sorry ma bani da kudi a hannusa shiyasa nake son ganinsa Zan dau kudi a Aljuhunsa"Jin abinda Nnenna tace yasa nurse in cewa,bara na Shiga na dauko Miki mma ke babu halin ki shiga yanzun. Toh shine abinda Nnenna tace tana tsaye har tashiga dakin Bata Jima ba sai gata ta dawo hannunta d'auke da Kudi harda ATM card nasa duk ta had'a ta mikawa Nnenna, karba tayi ta fita a hall in kirga kudin tayi 12k ne sai ATM pharmacy ta shiga ta basu list in ta sayi duk abinda aka bukata sannan ta koma cikin clinic in takai kayan aiki daidai lokacin aka soma kiraye kirayen sallan mangariba Zama tayi akan kujera. Sai kusan 8 na dare kafun likita ya fita a dakin sannan ya tura a kirata,tashi tayi tabi nurse in har office nasa,musulmi ne dan gatane sannan daga ka gansa kaga dan kwalisa tunda Nnenna ta shigo yake binta da wani shegen kallo Yana bin sharaban kafanta dake waje da kallo dayake uniform ne har lokacin a jikinta,get a sit my friend Yana maganar Yana nuna Mata kujera Zama tayi sannan nurse in ta fita,am kece Kika kawo Hassan Alhassan?yayi Mata maganan cikin hausa dan gyara Zama Nnenna tayi duk tana wani Jin kanta uncomfortable tarasa me yasa bata iyya sakewa da Koh wani namiji in ka cire papan ta sai Lahab"pls can u speak English? Sake Baki yayi Yana kallonta da yanda take magana Kamar yanga take Masa donshi a ganinsa iyayine kawai bawai batajin hausa ba amma sai ya basar ya soma mata magana,am Zaki iyya shiga daki Mai number 7 Yana ciki sannan zai iyya tashi 3 Koh 2 na dare za'ana shiga ana dubasa in Kuma ya farka babu wani a kusa kizo ki sanar da nurse. Ok sir kawai tace tana kokarin mikewa Am sister why not ki Kira gida azo a kula dashi ke Kuma ki koma ki kimtsa naganki sanye da uniform ga school bag maybe ma Koh gida Baki koma ba. Kala batace ba ta bude kofar ta fita shikam sai kallon kofar yake tunda yaji hausan ta ya tabbatar ba Yar Arewa bace sannan ga tsananin kyaun da take dashi gata tana yawo ba hijab Kuma ta kawo musulmi asibiti me alakarsu kenan?. tana fita d'aga office in tabi daki daki tana duba number har tazo Kan number dakin nasa tura kofar tayi ta shiga,kwance yake sanye da vest sai wandon jikinsa an cire Masa rigansa dayazo dashi sai hannunsa da aka daure da farin bendeji a hannunsa,takowa tayi a hankali zuwa bakin gadon kurawa fuskarsa Ido tayi fuskarsa tayi fayau sai dan tsukeken bakinsa da yayi jajazir ga dogon hancinsa a tsaye sosai ta Kura Masa Ido sai Kuma taji hawaye ya cika Mata Ido"Hassan ka shiga rayuwar ta batare da kasan Koh Ni wacece ba kayi hakuri na raunana ka hannu da yaban abinci bai cencenci karaya Koh tsageba. Sai Kuma ta Mike ta dauko kujerar dake dakin fari na roba ta aje kusa da bakin gadon aje school bag nata tayi a kasa ta zauna akan kujeran ta bude jakanta ta dauko littafin ta tana dudubawa,aje littafin tayi ta zuba tagumi tana tunanin kikin ta da yau haka kawai taji tanason ajesa a gida ashe rabon zasu hadu da Lahab ne don tun Randa ya nuna Mata ta daina zuwa school dashi. Zafi ake sosai ga gari ya gume Hatta fankan dake dakin Hura zafi yake botur in rigan uniform nata ta soma ballewa Harta gama hannu ta cire ta Kwabe rigan jikinta ya rage daga ita sai vest in jikinta sai siket hannu tasa ta zare sandal nata ta cire socks in ta duka ga wani gyangyade take ta zare glass in fuskanta ta aje akan drawern dake gefen gadon ta zare barect in kanta ta warware gashin nata ya sauka har gadon bayan ta don ita bata son bacci da gashi a kuller,gyara Zamanta tayi ta kwantar da kanta a bakin gadon jikinta nakan kujera tare da lumshe idanunta a hankali bacci ya fizgeta Mai dadin gaske. ****************** ta bangaren Mami sosai taji hankalinta ya tashi meya Kai Lahab hotel a daren jiya me yasa muzammil ke neman sa kasa hakuri tayi tadau waya ta Kira muneera ta tambaye ta Koh Lahab ya koma gidan amma muneera ta bata tabbacin Lahab bai dawo ba Zama tayi ta buga tagumi tayi shuru kawai da misalin karfe 8 na dare zaune suke a falo ita da mijinta da yaranta sunata Hira Inka cire Mami data buga tagumi tayi shuru abin duniya ya dameta sau biyu tana Kiran muneera amma amsa daya take Bata Bai dawo ba Alhaji sulaiman daya fahimci tunda ya dawo akwai abinda ke damunta shuru kawai yayi saboda yara bai tambaye taba amma yanzun Kam kasa hakuri yayi ya kalli mahraz dake zaune Yana zana mutum a caborn paper,Mahraz tashi kuje dinning ka xuzzuba musu abinci kuci Muna zuwa daga baya nida mamin ku. da Sauri Mahraz ya aje pencil in hannuda tare dasa hannu ya dau Yusuf dake kan cinyar kanwar sa wasila suka wuce dinning,kallon Mami Alhaji yayi sannan ya soma magana,Amina meke damunki tunda na dawo na fahimci kina cikin damuwa matuka Koh? dan shuru tayi don ita kwata kwata batason ta tattauna matsalan y'ay'anta da mijinta tafi sakewa tayi zancen su Lahab da su Addayiya da sauran Yan uwan tsohon mijinta da y'ay'ansa Amma Bata sonyi da mijin nata shiyasa ma yanzun ta dan murmusa tare da cewa,babu kome dadyn Mahraz kawai dai bana danjin dadin jikina ne. Uhmm Amina kenan nafi kowa sanin halinki Koh kin manta tare muka tashi tun kina yarinya namiki kyakkyawan sani nasan yanda kike in kina farin ciki bakin ciki damuwa da Kuma ciwo,Amina damuwa ne a ranki ba ciwo ba in ma matsalar da bazaki iyya sanar dani bane Ina rokonki akan ki sawa kanki natsuwa in ma matsalar yayanki ne bazan hanaki boye mini ba,tunda bani na haifeki ba amma ki sawa kanki natsuwa kowa da kalan yarantan sa da Kuma tashensa dole iyaye su kasance masu hakuri dama yayansu addu'an shiriya bawai kisawa kanki damuwa ba Amina? Nagode kawai tace ta tashi ta Shiga dakin ta,waya ta d'auka tama rasa wa zata tambaya haka kawai yanzun gidan yayanta muneer dan tasan kaf Yan uwan babansa bazashi gunsu ba tunda zasu sanar da gidansu yaje tasan Yan uwanta sune zai nufa,bugawa ya muneer waya tayi ta Kara a kunnenta. Tana jinya d'auka tayi sallama, Assalamu Alaikum Waalaikumu Salam taji muryar yayan nata ya amsa An wuni lafiya ya munir? Lafiya Amina ya maigidan naki da yara? Lafiya sai godiyan Allah Masha Allah haka akeso ince dai lafiya Kika kirani a daren nan? Lafiya klau daman Zan tambaya ka Koh Lahab na wajen ka? Ah ah Amina d'azun dai dana dawo kasuwa salamatu tace min yazo yayi wanka ya fita tun da yamma ince dai lafiya koh dai wani abune ya faru? Gudun karta d'aga Masa hankali yasa ta ce Masa babu kome kawai d'azun face min zaizone shine na Kira na tabbatar Koh yazo kasan yaron Nan baijin magana. toh Amina Allah ya bamu Alkhari sai da safe shine abinda yace Yana katse wayar,juyi tayi akan gadon ta rafka tagumi tana tunanin Ina danta ya shiga a daren nan hakan yasa ta daukar waya ta ringa kiraye kirayen tana tambayar Yan uwanta da duk tasan Lahab zai iyya zuwa wajen su Amma duka amsa dayane bai zo ba. da misalin karfe 2 na dare dakin shuru gashi ba haske babu motsen kome saina Karan gudun fanka ga wani irin hadiri daya karade sararen samaniya yayi bakikkirin sai walkiya dake tashi ya haska duhun hadirin dan motsene ne ya Fara dan tashi a jikin window tare da yayewar labulen window,wani kasurgumin kulene ya shigo dakin idanunsa jajazir yayi wani irin super daga bakin window zuwa Kan Lahab kafun kafafunsa su sauka akan lahab...............,. *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki* Page 53&54 Nnenna dake kwance da Sauri ta zabira duk da dakin da duhu hakan bai hanata ganin abinba da Sauri ta kwanta akan lahab tare da Masa rumfa ta bashi kariya d'aga sauka akansa da kulen zaiyi da Sauri kulen ya sauka a gefen gadon bai Fado akan bayanta ba sannan da Sauri ya juya ya fita ta window,mikewa Nnenna tayi a hankali ta zare jikinta a nashi lalubar glass nata tayi ta saka sannan ta kunna wutan dakin daidai lokacin aka soma yayyafe yafyaf bargo dake kusa da gadon ta d'auka ta warware ta lullube Lahab dashi Jin an Fara sanyi sosai riganta ta d'auka ta maida jikinta sosai takejin sanyin Hawa gadon tayi ta zauna Wai zatana gadon Lahab don ita tasan tabbas akwai abinda ya shigo dakin Kuma ta gansa, jingina tayi da jikin ginin dake manne da gadon a take bacci ya shureta. Misalin karfe 3 na asuba Lahab yadan Murda tare da Ware idanunsa yana bin dakin da kallo,ganin duhu yake gani yasa sa dan d'aga hannun nasa Kara yadan sake don shi Yama manta ya samu karaya in ba yanzun ba hannu Mai lafiyan ya d'aga ya Kama blanket in ya yaye a jikinsa tashi yayi zaune yasa hannu Yana Tattaba gadon,a bazata yaji hannunsa ya taba fatar mutum Mai shegen laushi. cikin zafin nama Nnenna ta damko hannun Lahab dake Kan cinyanta har lokacin Yana shashafa wa don ya gaza ganin jikin wa yake tabawa don bai kawo a ransa itace be sai da yaji muryar ta, bayan ta rike Masa hannu tace"Lahab ka tashi"? Shuru yayi bai bata amsa ba sai ma yanzun ya tsoma Jin haushin abinda ta Masa gashi Nan taje ta karyasa a banza d'aga make Masa hannu sai tsagewar Kashi mace Kamar Mai Kashi daya amma ta wani bangaren yaji dad'i kula data nuna Masa gashi har kwana zatayi dashi,Koh dayake ma ai ita ta raunana sa,,Yana jinta tana Kara tambayarsa amma baibata amsa ba,sai kokarin sauka yake akan gadon,itama da Sauri ta sauka ta nufi switch na dakin ta ketta take haske ya gauraye dakin d'aga Ido yayi ya kalleta sai Kuma ya maida kansa a tiles in Yana Neman takalminsa don baison taka tiles in asibiti. Fahimtar abinda yake nema yasa ta saurin matsowa garesa ta cire sandal in kafarta ta tsunguna hade da kama kafar nasa Wai zata saka Masa takalmin, shuru kawai yayi baiyi magana ba Harta gama sawa mikewa yayi ya nufi toilet,itama Zama tayi akan kujera tayi shuru duk sai taji ya shiga damuwa sosai wallahi,bai wani Jima a bandakin ba ya fitoh Hawa Kan kadon yayi ya kwanta tare dasa hannunsa Mai lafiyar ya lulube jikinsa duka harda Kai. Mikewa tayi ganin ya kwanta taje ta kashe wutan dakin duk da Dr yace inya tashi takirawo nurse kin kiransu tayi,a hakan dai tana Kan kujera ga kafarta a waje har bacci ya dauketa shikam kasa baccin yayi dan zazzabi zazzabine a jikinsa kwata kwata yaji baccin ya Kare Masa,a hakan yayita jujjuyawa har aka Kira sallan asuba mikewa yayi daga Kan gadon ba tare daya kunna wutan ba ya Shiga ban daki Alwala yayi duk da zazzabin da yake ji Amma bai sawa hannun ruwa ba. Dudu ba dakin yayi baiga sallaya ba dan tsaki kawai yayi yakai dubansa ga Nnenna dake bacci a zaune gashi bazai iyya zuwa masallaci ba har lokacin ana yayyafin ruwa rigansa ya d'auka ya shimfida a kasan tiles in ya Kama sallah Yana idarwa daidai lokacin nurse ta shigo ganin ya farka yasa ta cikin fara'arta tace,ah ah Hassan ka farka ne? "Eh na farka sister"Yana mamakin Ina tasan asalin sunan sa waya fada Mata sunansa? Ok Baku da sallaya ne Naga kana sallah da riga bara na kawo muku amma yanzun akwai Inda ke maka ciwo ne? "dan zazzabi zazzabi nakeji ga nauyin da kaina ke mini" Ok toh bara na Kira doctor,tace tana fita a dakin, Nnenna da tun tashin Lahab ta farka shuru kawai tayi Harya idar da sallan,bude Ido tayi ta kallesa a hankali ta sauka akan kujerar tasa gwuwuwinta a kasa ta hade hannayinta sannan ta soma magana"kayi hakuri Lahab badon niba badon halina ba ka yafe mini nasan ban kyauta ba Kuma wallahi Koh Ni ban d'auka zaka cutu har hakanba pls forgive me" Kauda fuska yayi Koh kala baice Mata ba,itama ganin hakan yasa jiki a sanyaye tace"ya jikin naka"?Nan ma shuru ya Mata Kamar ta shuka dusa,turo kofar da akayi yasata mikewa ta koma Kan kujerar da ta tashi likitane ya shigo nurse in dazun na binsa a baya hannunta d'auke da sallaya, Assalamu Alaikum "Waalaikumu Salam"Lahab ya amsa tare da gaishe da likitan. Amsawa likitan yayi ya daura Masa laidan ruwa ita Kuma nurse in ta aje sallayan a gefe tace, sister ga sallayan Nan sai Kuna amfani dashi daidai. Lahab ne ya Mata godiyan don ita Kam Nnenna bama tasan me take cewa bama sai wani harhada fuska take ganin yanda likitan sai binta yake da Ido duk yabi yasata susuce,ashe Shima Lahab ya lura da hakan sosai ya had'a fuska tare da kallon laidan ruwa da aka saka Masa tunda yake ball kullum mami na Masa bariya akan yabar ball yana Karya mutum Amma gashi yau ball bai karyashi ba Nnenna ta tsaga Masa Kashi ba'a taba daura Masa laidan ruwa ba tunda yake har wani fariya yake babu kamarsa a gidan su gashi yau tasa an daura Masa sannan ga wani shegen kallo da yaga likitan ke Mata ita Kuma tabar kafafu a wajen ganin likitan ya fita yasa sa CE mata,"keee dan kallon sa tayi ganin yanda ya wani had'a rai irin ba wasan Nan yana kiranta mikewa tayi tazo bakin gadon ta saya batayi magana ba,"in tambaye ki Mana? "Ina jinka" "Wai a addinin ki ance ki ringa saka suturan da zaina fallasa tsiraicin kune"? Itama had'a ran tayi tana Masa kallon mamaki amma batace kome ba Shima ganin bata da niyar basa amsa yasa ta ce Mata"ATM nawa da Kika amsa jiya ki fita bakin asibiti baza'a rasa shagon Kaya a wajen ba kije ki sayamin Kaya so nake na chanja na jikinta,kema ki sai naki kibar daukar Alhakin Maza. Jin ya gama maganar yasata juyawa kawai Bata ce kome ba ta bude jakan makarantan ta ta zaro card in da flask nasa dayake school dashi ta nufi kofar"zo taji yace dawowa tayi ta tsaya tana sauraron sa"ki sayi abinci"toh tace ta fita a dakin komawa yayi ya kwanta . **************** Hmmm gidan su Lahab da sun shiga tashin hankali na rashin d'ansu domin Wasa Wasa Saida muzammil ya ringa bin gida gidan Yan uwa Yana tambaya Amma sai suce Basu ga Koh keyar Lahab ba,Mami ma ta Kira Addayiya ta sanar da ita Lahab yazo wajen ta amma ya fita,Wasa Wasa har dare ba labarin bawan Allah Nan Addayiya kuka ta Soma tana amanar umaru ya bata me zaicewa ubangiji an basa amana yaro ya Bata gidan su Adewale da Nabeel duk anje sunce su rabon su da Lahab tun shekaran jiya da Suka bugi malami a school Rahab shi Karan kansa kuka yake amma fa Abbu ya bada guarantee Lahab ba bata yayi ba,akwai dai Inda ya shiga yanzun yanda kowa ke ruruta rashin jinsa aka fitar da zancen ba'a gansa ba wasu zasu ce duniya ya shiga Koh Kuma yafi karfin iyaye da yayunsa tunda daman shi dan Adam baka iyya masa haka baka guje masa kome abin magana ne. Muzammil Kam yasha alwashi idonsa idon Lahab kashesa ne kawai bazaiyi ba Amma Shima ya mugu mugun shiga damuwa sosai. ta bangaren gidan su Nnenna Suma sunsha mamaki ganin har dare babu Nnenna especially da yanzun ita ke musu girki gashi dady zai dawo gobe duk mom ta rikice batasan me zatace wa Dad ba tunda Bata San takamemmen Inda ta shiga ba a daren haka yayita sake sake,washe gari da safe Dad ya Kira ta ya sanar da ita Yana Kan hanya kitchen ta shiga ta girka musu breakfast sukaci kafun Sarah da Jennifer Suka tafi makaranta. Mubeena a daren nan ta kwana a zaune ga wani irin bugawa da kirjinta yake ta rasa meke Mata dadi tabbas da tasan Ahmad zaiji abinda tace wallahi da Bata fadawa kowa ba tabar abin a ranta yanzun wani hukunci Ahmad zai yankewa alakarsu Koh banza Mai kyautata maka randa bashinan sai kaji ba dadi,bare Ahmad daya Mata kome a rayuwar baicacanci wulakanci Koh ki ba haka bataso yaji kome ba,washe gari hakan ta tashi idanunta a kumbure sosai Wanda hakan ya matukar damun Inna ajeta tayi ta tambayeta meke damun ta Amma kememen mubeeena tace ba kome. Toh Koh kunyi fada da Ahmadun ne?Inna tace Mata. Babu abinda ya hadamu Inna. Toh Amma Naga jiya baizo ba Kuma nasan Ahmad in ba ruwa ake ba babu abinda ke hanasa zuwa. Inna nace Miki babu kome fa shuru kawai Inna tayi bawai don ta yarda babu abinda ke damun ta bane,da misalin karfe 8 na safe sai ga Rukayya ta doka sallama a kofar gidan nasu tare da turawa ta shigo. Waalaikumu Salam barka da zuwa takwara,Inna ta amsa Mata tana shimfida Mata taburma,yauwa Inna Ina kwana mun tashi lafiya tayi maganar tana Zama a taburman Zama itama innar tayi tana amsawa lafiya Alhamdulilah ya jatumar Taki? tana lafiya Inna mubeeena na Nan kuwa? tana Nan yarnan gata can kunshe a daki duk abin duniya na damunta Kuma Taki fadamin ki shiga ai in akace maka mutum bafulatani an gama magana. Murmushi Rukayya tayi ta nufi dakin tana tsokanar Inna,ai kawancen ne aka daina dake kin tsufa Bari Kiga na shiga fadamin zatayi. dariya kawai Inna tayi yayinda Rukayya ta Shiga dakin kwance ta tarar da mubeena Koh sallamar da tayi ma Bata amsa ba Zama tayi a bakin gadon a hankali tasa hannu ta girgiza ta,firgigit ta farka d'aga nannauyan tunanin data tafi,Haba mubeeena Zaki kashe kanki ne Koh Yaya irin wannan tunanin da damuwa da Kika daurawa kanki da wannan kwanciya naki da Alwala kikayi kikayi sallah Kika roki Allah ya yaye Miki dayafi? Uhmmm Ruky bazaki gane halinda nake ciki ba ni kadai nasan yanda nake ji. Koma me kikeji ba daidai bane ace kina sakanki a damuwa har kinsa tsohowa ma a cikin damuwa haba mubeena? Ruky dole na damu bantaba Jin kunya irin na jiya ba da wani Ido Zan Kara ganin Ahmad tana maganar tana kuka. Mubeeena ki kwantar da hankalinki yanzun ma zuwa nayi ki tashi muje asibiti mu duba jikin nasa ya ya kwana tunda yau bamu da exam. Haba Ruky wallahi bazan iyya zuwa ba innaje nace meye? Kinga mubeena gwara dai ki tashi muje ki dubasa Amma rashin zuwanki ma wani rauni Kika fame Koh iyayen sa zasuyi mamakin ki in Baki je ba karfa ki manta Koh ciwon Kai kikayi haka Yan uwansa zasu yita zuwa dubaki dan Allah ki daure muje kinji Koh? Mikewa zaune mubeena tayi jiki ba kware ta fita a dakin tabar Ruky ita kadai ruwa ta Iba tayi wanka ta shirya Suka ma Inna sallama Suka fita a gidan,tun d'aga nesa ta hangesa tsaye a wajen jiya gabaki d'aya yabi ya rame itama Kara had'a fuskarta tayi daman a hade yake tafiya suke yayinda ya zuba Mata Ido shi Kuma tun d'aga nesa,har suka karaso Inda yake zasu shari kwana matsowa yayi kusa dasu tare da musu sallama Kamar cikekken musulmi, Assalamu Alaikum Waalaikumu Salam Rukayya ta amsa Masa mubeeena Kam Koh kallo Bai isheta ba bare ta amsa Masa sallaman ma sai ma kokarin geftasu da take da Sauri yasha gaban ta tare da Ware hannayen sa ya tare Mata hanya sannan ya Soma magana, mubeeena bancancanci wulakanci a wurinki ba mubeeena bazan gaji da fada Miki wannan kalma ba Ina sonki Koh da bazaki karbi soyayya taba dan Allah ki sakar min fuska Koh Zan samu sassauci da sukuni a zuciya ta. Adewale ka bani hanya na wuce na fada maka bana son ka banason ganinka ana dole ne ?Koh Ni sarar kace?ta karasa maganar tare da zagayesa ta wuce d'aga shi har Ruky da Ido Suka bita Harta tare Keke napep tahau bata ma saurare jiran Ruky ba. Kallon Ruky Adewale yayi ya Soma Mata magana,Ina kwana kawarmu? dan murmushi Ruky tayi,lafiya Alhamdulilah Adewale Koh? Hh ta Baki labarina kenan? Eh toh banace ba. Hh pls kawarmu ki taimaka ki ringa nunawa mubeena abinda ya dace bazan iyya cigaba da jure abinda take minin Nan ba. Karkaji kome kaima Ina so kayita Addu'an Allah ya zaba muku abinda yafi Zama Alkhari ka Kara hakuri Ade mubeeena nacikin damuwa ne a Yan kwanakin Nan. Da mamaki yace damuwa Kuma?meke damun ta? Kaidai abar zancen kaga Bai Kamata na Fadi abinda Bata sani ba Amma kana Mata uzuri. Ba kome nagode,wucewa Ruky tayi tana maijin haushin halin mubeena Keke itama ta tare,tana Isa clinic Keke ya dauketa ta Shiga gate in mubeena ta gani tsaye tana jiranta Koh kallonta Ruky batayi ba ta wuce ciki mubeena tabi bayanta. Suna Isa kofar dakin da aka kwantar dashi jiya Ruky tasa hannu ta bude kofar bakinta d'auke da sallama. amsa Mata kanin Ahmad yayi fuskarsa a washe shigo sukayi ya mike ya Basu kujera Suka zazzauna Ahmad dake kwance tun shigowar su yake bin mubeeena da kallo kawai kalllo ne irin na mamaki,kanin sa fita yayi ya basu waje, Ruky ne ta katse shurun da gaidashi,Ina kwana ya Ahmad ya jikin naka? ajiyar zuciya ya sauke,lafiya Alhamdulilah da sauki. Jikin mubeeena a mace Daman tunda ta Shiga dakin bata yarda sun had'a Ido ba kanta a kasa yanzun ma muryarta har rawa yake ta soma gaidashi,i........in...naa...kwana? Lafiya shine kadai abinda yace sannan dukansu sukayi shuru mikewa tayi ta aje laidan fruit data saya a hanya don ta fahimci hankali bai Gama isar mubeena ba,am rukayya ki zauna maganar da zanyi ya shafeki kema no need ki bamu waje Ahmad yace ganin Ruky zata fita a dakin. ras ras haka gaban mubeena ya Fadi,komawa Rukayya tayi ta zauna a hankali Ahmad ya Soma magana,a gaskiya ban taba tunanin bana fahimta ba sai jiya tun farko mubeeena ta nuna bana kauna na amma na nace na kasa rabuwa da ita saboda tsananin sonta da Allah ya daura mini,a lokacin da na Fara ganin tana sake mun fuska sai nayi tunanin toh Koh ta Fara sonane ashe hauka nake Ni kadai,sai Kuma ya kalli mubeeena meyasa mubeeena Baki gayamin akwai wani a ranki ba da tun farko ban nace lallai nayi so maso wani ba,amma ba kome Alhamdulilah tunda yau nasan matsayina,insha Allah d'aga yau mubeeena bazan Kara tinkarar ki da rokon so Koh maganar so ba. Kukane ya kubcewa mubeena tasa hijab ta rufe fuskarta wani irin zafi takeji da Kuna a zuciyarta especially da taji abinda yace,sannan ke Rukayya na Jima banga mace Mai tunanin Mai zurfi da fadin gaskiya da girmama soyayya ba irin ki a yau Ina Mai rokon Alfarmar so a wajen ki inkin amince daman iyayena sun takura min Kuma sun ban lokaci na fitar da Mata Kuma a yau Naga matar da ta dace dani Ina so Zan aure kiiiii.............. *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki* *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki* Page 55&56 Aure aure fa kace Ahmad?wannan wani irin abune kana saurayin kawata kazomin da wannan zance Ahmad?Ruky CE tayi maganar tana mikewa tsaye. tabbas Rukayya aure ba Kuma auren huce haushi Koh auren tushi zanyi dake ba so nake na nema a wajenki in Zan samu amma ba roko nake ba don nayi hakan banga da kyau ba, maganar kawa Kuma ai ba a bayan idanunta akai komai ba a gaban idanunta ne shiyasa na fada a gabanta karma ta kiraki Maci amana, Rukayya naji kince lokacin Abu ayishi mutum in yasamu dama a dama dashi bance ki aure Ni don naji bakida manemi ba illah gaskiya da naji kike fada Mata dan haka nake son ki Amince dani na Zama shugaba a gareki na biya sadaki mu shiga d'aga ciki. dakata Ahmad wani irin magana ne wannan kake haka kasan kuwa wacece a gabanka Rukayya kawar budurwar ka haba dan Allah ana barin hallas dan kunya. Ah ah Rukayyatu karki ce haka abinda Addini bai haranta ba aikatashi bai Zama aibu ba na Jima tsaye a kofar dakin nan Ina Jin duk abinda kuke cewa,tabbas naji dadi Kuma na amince da abinda Ahmad yace tabbas ya cika dan halak daya rabu da mubeena Nasha nuna Masa yarinyar Nan bata ra'ayinsa Amma ya nace kullm cemin yake Wai kunya takeji dason boko amma d'aga zaran ta jona gaba da secondary komai zai daidai,na nagode Allah daya fahimtar dashi ya ganewa idanunsa me za'ayi da macen da Bata sonka,maman Ahmad tace tana karasowa cikin dakin. Mikewa mubeeena tayi ba tare da tayi magana ba ta fita a dakin da Sauri gudu gudu ta fitoh a clinic in ta tsaya a bakin titi har lokacin hijab nata na Kare a fuskarta Rabin fuskar kawai ake kallo,Ruky ganin mubeena ta fita yasa ta mikewa da Sauri ta nufi kofar itama duk Kiran da Ahmad ke Mata bata tsaya ba,da Sauri ta nufi mubeena da ta soma tafiya da kafa tana rurufe fuskar ta Wanda Koh shakka Ruky batayi kuka mubeena keyi. dan gudu gudu tayi ganin mubeena ta Mata rata mubeeena dakata don Allah ki tsaya Ina kike tafiya ne haka kindai san d'aga Nan zuwa gidanku bazaiyu da kafa bakan Koh? dan tsayawa mubeeena tayi tana sassaita fuskarta gudun Kar Ruky ta fahimci abinda take ji,mubeeena nasan yanda kike ji Sarai Koh baka son mutum muddin akace wani ya karbesa sai kaji wani iri mubeena Ina Mai baki shawara daki kyautatawa Mai sonki haka zalika ki sassaita Masa sai Wanda kike mutuwa a kansa Shima ya sassauta Miki,Ki dubi abinda Kika ma Adewale dazun Sam baki kyauta ba yaya zakiji randa kikaji Lahab yace bai sonki gaba da gaba toh haka Shima Adewale yake ji,bazan gaji da baki shawara ba ki koma ku sasanta da Ahmad. Kallon ta mubeena tayi sannan tace,wani irin mu sasanta bayan kinajin abinda mahaifiyar sa tace sannan Shima yace kuje kawai Nina hakura Allah ya zabawa kowa rabon sa. Me kike nufi mubeeena kina nufin kema kin janyewa Ahmad in kenan? Kwarai Ruky na janye Allah yasa hakan shine Mafi Alkhari a gareni. Shikenan mubeeena Amma Ni bazanyi gangancin da kikayi ba nayi Wasa da damata a baya Amma a wannan Karo ban shirya cigaba da zaman gida ba Kamar yanda nayi a baya karfa ki manta kaf kawayen mu sai aure suke mu ba yaran manya ba bare ace za'a somu don kudin iyayen mu don haka Ni naji na gani Zan amince wa Ahmad ya aure Ni don banga wani aibu a garesa ba. Juyawa kawai mubeena tayi ta tsallake titi tabar Ruky a wajen tare keken dayazo wucewa tayi cikin sa'a kuwa ya tsaya ba tare da tayi magana ba ta shiga tare da cewa muje Mai keke, Ruky da Ido tabi keken har Suka mile,mubeeena Kam wani irin kuka ta sake a cikin Keken Mai ciwo tama rasa meke Mata dadi a duniya gabaki d'aya Wai Ina zata sa kanta ne taji sanyi tayi iyya boye son Lahab Abu ya gagara gashi tayi rashin masoyi na gari innalilahi wa'inna'ilahu raji'un Allah ka kawo mini mafita. Subhanallah Wai baiwar Allah lafiya haka kike ta rusa kuka a cikin Keke in ma mutuwa aka Miki kiyi hakuri kullunafsin za'ikatul maut,shine abinda Mai keke ya fada Mata don shi gani yake wani nata ne ya mutu take kuka shiyasa lokacin daya sauke tama yace ta tafe ya yafe Mata kudin sauka tayi tasa hannu ta Kara Jan hulan hijab in ta rufe fuskarta sosai tana tafiya hawaye na zuba tana gogewa a hakan har ta shigo gidan Koh sallama babu Inna dake zaune tana tsinka zogale da mamaki take tambayar ta ganin daga shigowar ta tayi daki kawai babu sallama bare na dawo,ke mubeeena ince dai lafiya Kam Koh kin shigo fuska a kulle Wai harkun dawo makarantan ne duk da yau asabar bansan me kukaje d'auka ba? Mikewa tayi da Sauri ganin mubeeena bata bata amsa ba tabi mubeenar cikin daki,samun ta tayi zaune ta Kwabe hijab in jikinta abinka da farin fata lokaci daya idanun ta da fuska sunyi jawur ganin Inna ya sata Kara fashewa da kuka,jikin Inna har bari yake ta matso kusa da mubeena,ke mubeena menene meke damunki?saurin rungumarta mubeena tayi tana wani irin marayan kuka ita Karan kanta Inna ta shiga damuwan tunda take bata taba ganin mubeena cikin wannan tashin hankalin ba don Koh rasuwar iyayen ta bata da wayo sosai,don Allah mubeena ki natsu nasan ke yarinya ce Mai zurfin ciki Ni na haife mahifinki Kuma Nina raine ki tun kina da shekara biyar a duniya mahaifanki Allah ya musu rasuwa keda dan uwanki duk a hannuna kuka tashi ban rareku da kome ba duk abinda na samu bana Fara sawa a bakina har sai Naga ku kunci meyasa meyasa mubeena Baki d'auke Ni a matsayin wance zakiyi shawara da ita ba wance Zaki fadawa damuwan ki kuyi Alhini tare tun kina yarinya Koh Abu na damunki baki fadamin sai dai Inna gane nayi kokarin magance Miki Amma bazaki fadamin da bakin kiba sai Kuma ta fashe da kuka Mai tsuma rai tana Zama a bakin gadon tasa bakin zaninta ta rufe fuskar tata. da Sauri mubeena ta sake rungumar Inna cikin kuka take magana,kiyi hakuri inna bawai haka bane wallahi kaf duniyan Nan bani da Kamar ki na tabbatar Koh iyayena ne Suka dawo bazan musu son da nake Miki ba dake na Saba Ina boye Miki damuwa tane don gudun sakaki kema a damuwa. in dai bakison sani a damuwa toh mubeena ki daina boye mini damuwar ki hakan na mini zafi gani nake Kamar akwai wani abinda nake Miki Wanda yasa kike gudun naji sirrin ki. girgiza Kai mubeena tayi sai Kuma a hankali ta soma magana hawaye na bulbulowa,Inna Ahmad ya rabu dani s...sa...saboda.......sai Kuma ta kasa karasawa saboda kuka daya ci karfinta,mikewa Inna tayi cikin bacin rai tace,kaii badai akan wannan yaro kike zubda hawaye haka ba tukunna ma maiya hadaku daman duk son da yake gwada Miki na shekaru duk karyane munafukin Allah toh wallahi babu Wanda ya Isa ya yaudari jikata ya kwana lafiya tana karasa maganar ta gyara daurin zaninta hade da daukar hijab a jikin kofa tasa tana kokarin fita a dakin sai surutai take,shagon sa zanje saina ci Masa mutunci sai yasan ya taba kayyu yau Innan don ubansa har gun uwarsa sai naje na shata Mata layi Ni za'a rainawa wayo in gama tattali Ina jiran biki zaizo yace ya fasa. Inna ki dakata don Allah,Amma Ina Inna bata saurare mubeena ba sai takalmin ta data saka tsabar Sauri ma hagu ta sama dama dama ta sawa hagu ta nufi kofar gida. Inna ki dakata nace Miki Koh kunje shagon sa bazaki samesa ba haka zalika gidan su saboda yana asibiti,dakatawa Inna tayi ta juya tana kallon mubeena,wani asibitine kenan har can Zan bisa Koh Yana danjan mutuwa ne saina nuna Masa bacin Raina harni zai cutarwa Jika,ta juya abinta zata fita. Inna ki dawo Nina ce bana sonsa bana sonsa ne don bashi bane a zuciya............. *************** Alhaji sulaiman da Mami da yaranta ne zaune akan dinning dayake yau weekend ne babu makaranta gabaki dayan su abinci suke ci Kuma d'aga yanayin cin kadai zaka gane Suna Jin dadin sa,sabanin Mami dake ta sai jujjuya shukali take abin duniya ya dameta gabaki d'aya jin abincin take Kamar mad'aci,Mami Mami Mami mahraz ya kirata har baki uku Amma shuru Bata ma San yanayi ba. Mufeeda dake kusa da itane tasa hannu tadan tabata,Mami ya mahraz nata Miki magana baki amsa Masa ba?dan firgigit tayi cikin yake ta kalli mahraz , na'am mahraz Meka ce? Mami meke damunki ne Koh Baki da lafiya ne? Ah ah mahraz lafiyata klau Meka gani? Uhmm kawai yace bai Kara magana ba don Shima yanzun ya Fara wayo sosai yasan me ake Kira tunanin shiyasa daya fahimci bata son tambayar ya Barta kawai badon ya yarda ba,Alhaji sulaiman Kam girgiza Kai kawai yayi tare da kallon mamin,mamin mahraz tunda yau weekend ne sai kije gidan su lahab in ki barmin yaran a gida. Dan dago Kai tayi ta kallesa watoh Koh bata fada Masa ba ya fahimci matsalar Lahab ne,toh shikenan dadyn mahraz,tsagal wasila tayi tace,nidai gaskiya Mami Zan biki kinji? kallon ta Mami tayi Jin mahraz da mufeeda ma sunce Suma zasu,Kinga bafa jimawa zanyi ba Kai Kuma mahraz da girmanka zaka wani cewa zaka bini toh Yusuf ma a gida Zan barsa,Aiko Yusuf dake Kan cinyar wasila Kamar yasan me mamin ta fada Kwabe fuska yayi sai Kuma ya sake kuka da karfi Yana kokarin sauka d'aga Kan kafar wasila Yana mikawa Mami hannu,gabaki dayan su Saida sukayi dariya hannu tasa ta dau Yusuf in ta daura akan kafarta Aiko take yayi shuru abinsa Costan sa da aka dama Masa a cup ta janyo daga gaban wasila tana Iba tana basa. Suna gama cin abincin mufeeda ta goya Yusuf ganin yayi bacci a bayanta yasa Mami ta tashi ta shirya fitowa tayi hannunta d'auke da car key's,toh Ni Zan wuce sai na dawo tace tana kallon Alhaji dake zaune rike da jarida ga yaransa a kusa dashi,toh a dawo lafiya Mami yaran suka had'a baki,yauwa Yan Albarka sannan Kai mahraz ka karbi Yusuf a bayan mufeeda ka kwantar dashi a tsakar gado kasa Masa filo a gaba da bayan sa Karya fadi? toh Mami saikin dawo,Allah yasa tace tana bude kofar falon ta fitoh compound na gidan parking space ta wuce ta bude motar ta ta shiga tare da maida murfin ta rufe ta tada motar. da Sauri gate man ya walgale Mata gate Yana Mata a sauka lafiya. ***************** a gaskiya sadeeq kayi hakuri maganar kawo laifen Nan a ajesa a gefe yanzun hankalin gidan mu ba'a kwance yake ba bare ayi wata maganar lefe,umaima dake jingine da motar sadeeq a cikin compound na gidan su tace fuskar ta babu walwala. Sadeeq dake zaune a gaban mota kofa a bude fitowa yayi gabaki d'aya a motar Yana kallon umaima,Wai umaima Mike faruwa ne na kasa gane kanki tun fa jiya na shigo garin ku na kiraki a waya akan ina zuwa da daddare Zan Miki Albishir na musamman saboda maganan Nan na taso daga baushi nazo gombe amma har zakice Wai a sauke maganan kawo laife ranan Monday bangane me kike nufi ba? Unmmmmm sadeeq kenan bazaka gane bane shiyasa amma nidai na riga na gama magana. Wai tsaya umaima bangane Kin gama magana ba akan me zakice Kar a kawo Kuma baki gayamin gamsheshen amsa da Zan Kai gidan mu nace ba, meke faruwa ne?Koh dai son nawa ne Kika daina d'aga jiya zuwa yau? dan murmushi tayi tana kallon sa watoh shi tanan ma tunanin sa ya sako Masa Kenan,sadeeq dan uwan mahaifina yau kwana biyu bai kwana a gida ba sannan ba'asan Inda ya shigaba taya hankalin mu zai kwanta har a karbi kayan auren ka? Subhanallah wanene a cikin su ya batan?ya tambaye ta don yasan bazai wuce small uncle's nata ba. Wallahi hubby Lahab ne ya bata ta basa amsa tana kallon gate Jin horn na mota Mai gani ne ya taso ya bude kofar. ton Allah ya bayyana sa,sannan Kayan aure na Koh na auren ki ai inta nine a yafe kayan. Shuru tayi bata basa amsa ba tana kallon Mami data shigo da motar ta gidan parking tayi a kusa dasu ta fitoh a motar tsungunawa sadeeq yayi har kasa ya Soma gaidata. Amsa wa Mami tayi umaima ma ta gaidata ta amsa sama Sama ta nufi flat nasu don hankalin ta ba'a kwance yake ba da sallama ta bude kofar ta shiga Addayiya ce zaune a kasan cafet sai rusa kuka take yayinda muzammil dasu Abbu keta bata hakuri amma Ina sai Kara volume take Jin sallamar Mami yasa ta share hawayanta tare da amsa sallamar Kamar yanda sauran Yan falon Suka amsa shigowa Mami tayi ta nemi waje ta zauna gaggausawa sukayi anan ake ta jajanta lamarin. toh Ni anawa shawarar uncle Mai zai Hana akai case Nan hannun Yan sanda babu amfanin muyi shuru da sunan gudun magana shifa mutum ba'a iyya masa kome aka Masa baza'a gujewa maganar sa ba,shareef dake zaune Akan 1 sita yace Yana kallon uncle. da Sauri Mami ma tace eh wannan gaskiya ne nima nayi tunanin haka Kar Muna tunanin wuta a makera mu ganta a masaka Muna tunanin Lahab gudu yayi Alhalin Kuma b'ata yayi Koh wani abin ne ya samesa don Ni wallahi jikina ya bani ba lafiya bane jiya Koh bacci ma banyi ba. Wani dogon tsaki mamu tayi cikin makirci ta soma magana,Haba Amina wani irin magana akai ga Yan sanda waye baisan halin Lahab ba aje asa hukuma a ciki karshe a kamasa a logi(hotel) Koh club ya kunyata mu abarshi dai ai duniya ce tafi gabaruwa jimawa Kuma duk Wanda yabar gida da kafarsa zai dawo. Wani irin bacin rai ne ya ziyarci Mami Jin munanan kalamai da take fadawa gudan jikinta,keee Haleema dakata banason shshigi ai basai kinyi haka Zaki nunawa duniya baki kauna ta da y'ay'ana ba wannan Kam kowa ya Jima da sani,Ina d'aga Miki kafane Albarkacin yayan ki amma wallahi wannan karon in Kika Kara shiga harkata wallahi Zan nuna Miki shuru shuru ba tsoro bane. Itama mamu mikewa tayi Koh kunyar su Anwar batayi ba,keee Amina inkin fasa baki cika yar halas ba sannan menene abin ki a tsotsonki banda kwadayi dason abin duniya in ba kwadayi ba meya shigo dake tsakar rana cikin ahli Kika Haifa musu masif........tas tas kake ji Mami ta wanke fuskar Mami da wasu mahaukatan Mari guda biyu daidai lokacin umaima ta shigo falon mikewa Anwar yayi jikinsa har rawa yake ya nuna Mami da yatsa,mahaifiyata Kika Mar.............. *************** Nnenna na fita a bakin asbitin ta samu wani shagon Kaya shiga ciki tayi ta zabi riga da wando kala uku na Lahab sai itama ta dauko wando kala biyu da riga biyu sai vest ta saya Masa da boxes ita Kam bata samu vest na Mata ba towel ma duk ta saya mikawa Mai shagon ATM nasa tayi yasa a POS ya cire kudin sa wani shagon dake gefe ta shiga tasai maclen brush da soso harda sabulu da turare abinci Kam tama rasa wanne zata sai Masa wajen Mai shagon bakin asibitin taje ya had'a Mata shayi a flask Kofi biyu sai kwai daya soya Mata, tasai bread sai doya soyayye data musu takeAway,komawa cikin asibitin tayi hannunta Niki Niki da Kaya ta tura kofar dakin ta shiga kwance yake Kuma Sarai yaji shigowar ta amma bai wani motsa ba Yana kwance a yanda tabarsa,aje kayayyakin hannunta tayi tare da daukar laidan suturar da ta sai musu ta matsa bakin gadon"Lahab ga kayan na sai maka ka duba Koh ya maka"? Kala baice Mata ba sai mikewa da yayi daga zaunen da yake sandal Nata yasa a kafarsa ganin haka yasa ta saurin dauko Sabon silifas Inda ta sayo ta aje a gaban sa,cire sandal in yayi yasa silifas in,mikewa yayi a hankali ga hannu an daure harda igiya aka daura Masa a wuya zuwa hannu saboda hannun kada ya ringa Lilo sauka yayi a gadon ya finciko laidan hannun nata da hannunsa Mai lafiyar wando ya d'auka da vest ya Kama hanyar toilet in da Sauri Nnenna ta kallesa sai Kuma tace"Amma dai ba wanka zakayi bako"? Har lokacin baiyi Mata magana ba sai kokarin bude kofar da yake da hannun sa na hagu Yana jinta Sarai yaki tamkawa,"Lahab kasan ba'a wanka in aka samu rauni irin wannan Koh"? Bauuuu kakeji ya maida kofar toilet in da karfi ya rufe shuru kawai Nnenna tayi takoma ta zauna sai Kuma ta Mike da Sauri Jin Karan faduwar a toilet tare da ihun mutumin nata......... Page 57&58 da gudu ta shiga bandakin zaune ta gansa akan tiles kayan daya shigo dasu a watse a kasa tsayawa kawai Nnenna tayi tana kallon Lahab dan sauke ajiyar zuciya tayi ganin babu abinda ya samu hannun nasa dan ita tama tsorata ta d'auka Koh hannun ya samu matsala ne"menene ya faru kake ihu"? dan dagowa yayi ya watsa Mata wani kallo cikin masifa-masifa yace"oho ban sani ba yanzun a yanda Kika gannin Nan Har kina tambayar meya faru? Koh ma meyafaru aikece sila". Shuru kawai tayi bata kulasa ba har lokacin tana tsaye"bazaki kamani na tashi bane"?da mamaki take kallon sa Jin abinda ya fada Wai ta kamasa matsowa tayi a hankali ta duka a gabansa ta sanya gwuwuwinta a tiles in hannunta ta zura a hakarkarin sa a hankali,dan zabura yayi don wallahi sai yaji Kamar jakulkule ta Masa"ya haka malama Zaki wani ciccibeni Kamar Zaki d'aga dan yaye Kama min hannu zakiyi"Lahab yace cikin d'an rawa rawan murya don dan tabasa da tayi yanajin wani iri a tattare dashi. Nnenna bata kulasa ba unexpectedly ta dagosa daga zaunen da karfin Allah,zaro Ido yayi"keee Wai Naman jaki kike cine Koh me mutum sai karfi Kamar shariya Kamar ba mace ba haba " tura Lahab in tayi Kamar xai Fadi sai Kuma tasa hannu ta rikosa tare da pushing nasa ya zauna akan toilet sit,ba musu Shima Lahab in baiyi kokarin tashi ba sai hannun sa na hagu daya sa Yana kokarin cire vest in jikin sa amma ina ya kasa saboda hannun sa dole sai dai a yaga vest in"Wai tsayuwar me kike ne da bazaki taimake Ni ba Koh jira kike na Kwabe kayan nayi wanka a gaban ki"?Lahab ya karasa maganar yana hararanta. Hhhh dariya Nnenna ta sake a karon farko shima yaga dariyar ta sosai dariyar ta Mata kyau ga wasu cute white teeth nata da suka bayyana,girgiza Kai tayi cikin dariya ta fizgo vest in jikinsa har sai da ya barke ihu lahab ya sake Yana ce Mata"Wai menene haka ke Baki da hankali ne ki natsu Mana"Amma Ina zare Masa yagegen vest in tayi Lahab Kam da hannu daya yake ta Kare jikinsa Yana daka Mata tsaka ganin tasa hannu ta Kwabe botul in wandon jikinsa tana kokarin zaresa d'aga waist nasa,jikinsa har wani irin rawa yake yasa hannun sa Mai lafiyar ya fizgota har Saida ta fado a kansa"wash yace Yana Kara sa hannu ya mannata a jikinsa sosai Yana wani irin sauke a jiyar zuciya akai akai. Jinta a jikin namiji a karon farko a rayuwar ta mutumin da take sakewa dashi fiye da mahaifinta da ace wanine ya rungumetan Nan da sai wani ikon Allah badai Shiba,dan muskutawa tayi tana son tashi d'aga jikin sa Jin yanda gemun dake fuskarsa ke taba Mata wuya gata dama-dama akan kirjinsa Mai d'auke da kwantancen gashi baki duk da bamai yawa bane sosai amma ga dukkan alamu shekaru yake jira su dan Karu Shima ya Karu saboda kallo daya Zama ma Lahab kasan irin mutanen Nan ne masu halittan gashi da yawa a jiki"so kike kimin tsirara da gaske"?Lahab ya tambaye ta Yana kwantar da kansa a wuyanta. Kokarin turesa take amma Ina ta kasa saboda da karfi sosai ya riketa,cusa hannunsa yayi ta wajen cikinta ya zagayo dashi bayan ta tare da rike waist nasa,ihu ta sake tana cewa ya sake ta ya saketa amma Lahab gam ya riketa sosai Yana dad'a mannata a jikinsa. ganin da gaske bazai saketan ba yasata dan sake jikinta kadan a nasa tare da dago kanta ta kalli fuskar sa hannu ta d'aga a hankali ta shafa fuskar tasa da Sauri ya lumshe idanunsa Wanda tun dazon yake kanta,dan bude Ido yayi Yana kallonta itama kallon nasa take"yunwa nakeji"Lahab yace Yana Kara bin fuskarta da kallo. Uhmmm kawai tayi ta lumshe idanunta kafun ta basa amsa"nida Kai wa aka rike? "Ke kike rikeni"ya Kara amsa Mata Yana dan shashafa Mata waist,hannunta tasa akan nasa tana turewa"ka sakeni Mana sai kayi wankan kaci abinci kaji"? Dan muskutawa yayi yace"so kike na sakeki watoh Kinga Banda hannu ki kwabemin Kaya Koh"? "ah ah Wasa nake maka mezaisa na Kwabe maka Kaya a gabana Kuma ai saina makance" Jin abinda tace yasa sa sa hakorin sa yadan ciji kafadarta da dan karfi"Jesus ka kasheni"tare da ture hannunsa ta sauka a jikinsa tana shashafa wajen tsungunawa tayi ta kwashe kayan daya shigo dashi bandakin suka zube a kasa ajewa tayi a bandakin cikin boket da Sauri ta bude kofar ta fita shikam da Ido ya bita Yana dan murmushi,bata jima ba sai gata ta dawo da wani Sabon wando da rigan harda towel ajewa tayi ta ciki ruwan dumi a boket in ta aje Masa a gabansa tare da daukar karamin towel tasa a cikin ruwan hade da bude sabulu ta aje Shima juyawa tayi zata bar wajen,hannunsa yasa da Sauri ya rike nata,tsayawa tayi bata juyo ta kallesa ba ganin hakan yasa sa Kwabe fuska"kizo ki Kama min wando ki cire wallahi kafar baya fita sai da laida"(kaji iskanci dazun da za'a cire mekace😏) Juyawa tayi ta kalli kafar wandon ta sake kallon fuskarsa"Wai menene haka kike wani kallona toh ma waya raunanani ne ai kece don haka ki kula dani malama"kala batace ba Shima mikewa yayi ya zare wandon a kugunsa ya saukar kasa rumtsa Ido tayi da karfi ganin boxes nasa a waje ga cinyoyin sa masu tsoka gasu bakikkirin ga gashi a kwance akai"kijamin kafar wandon Mana hai"? tsungunawa tayi ta kamo kafar Lahab in ta daura akan cinyarta kallon yatsotsin tayi gasu dogaye tsirara dasu ga kafar Mai tudu da nama Kamar kafar mata hannu tasa ta Kama wandon tana ja ja take da karfi amma Ina wandon pencil Kam yaki fita sam"Wai menene amfanin sayan wando Alhalin Kai Mai kudin baka huta ba ace ka sai wahala da kudin ka Wai da sunan gayu"Nnenna tace tana Jan wandon da karfin gaske Wanda har lahab dake zaune ya biyo wandonsa Suka zubu a kasa daga shi har Mai cire masan"innalilahi wa'inna'ilahu raji'un wayyo hannuna yace kamar irin ya bugen Nan cikin tashin hankali ta Mike tana dubasa"sannu sannu Lahab Inga hannu Jesus hannu Mai ciwo. sassake jikinsa Lahab yayi yana wani irin narkewa Kamar maijin jiki,da Sauri Nnenna ta Mike ta nufi kofar"bara na Kira likita suzo su dubaka hannunka ya fame"kizo ki gyaramin jikina bazan iyya ba sai mu fita a bandakin kafun kikirasu"dakatawa tayi Jin abinda Lahab yace da Sauri ta dawo ta taimaka Masa ya tashi ya zauna bucket in ta jawo sai Kuma ta fita da Sauri ta dauko laida Baki da aka sa Mata su soson wankan a ciki ta dawo bandakin ta tsunguna a gaban Lahab ta sanyawa kafarsa a laidan kafun wandon ya fita aje wandon tayi a gefe ta tsoma hannunta a bucket In ta tsamo towel dake ciki ta matse sosai kafun ta sanya towel in a gadon bayan sa tana goga Masa lumshe Ido Lahab yayi,a sannu sannu tayi ta goge Masa jiki sai dai bata goge kafa ba iyya sama kawai ta wanke, hannu tasa ta lakace sabulu tana goga Masa a fuska a hankali gudun Kar ruwa ya taba Masa hannu har lokacin idanunsa a rufe Yana ji tana tattaba Masa gashin fuska wanke Masa fuskar tayi tasa towel ta goge Masa fuskar sosai take kallon fuskar NASA gashin gemunsa ya jike tare da sajensa ya wani irin kwantawa gwanin sha'awa. Aje towel in tayi"ka karasa sauran da kanka Zan jira ka a waje kayi Sauri abincin na sanyi"ta fita a ban dakin ta barsa. kallon abin wankan Lahab yayi sai Kuma ya cire gajeren wandon sa ya karasa wankan da kansa towel ya daura ya fitoh a bandakin,mikewa Nnenna tayi ta bude laidan kayan ta Mike Masa karba yayi ya koma bandakin ya sanya wando dogo na roba vest Kam bazai Shiga ba saboda yanayin hannunsa fitowa yayi ya aje rigan dake hannunsa ya zauna a bakin gado"meyasa baka saka rigan ba Koh vest"?sai naje na Kira Dr ya duba hannun tunda ka fame. "bazan sa ba a hakan kikeso nasa kayan ne Koh Yaya nidai kiban abinci naci"mikewa Nnenna tayi ta dau cup guda daya ta Iba Masa tea in tasa spoon ta Mika masa,"make kafada yayi tare da kallon ta Yana Wani shugwabe fuska"nifa bazan iyya Sha da kaina ba Kinga dai hannun damana ne"?Kika tsagamin. Zama tayi a kusa dashi a bakin gadon ta aje cup ta dau takeAway in kwai dana doya soyayye da Miya duk ta kawo ta aje masa tayi sosai sannan ta dau cup in tasa Masa a Baki kurba yayi a hankali Yana kallon fuskarta itakam Koh kallon sa batayi ba ta yago wainar kwai in tasa Masa a baki,atakaice dai Saida Lahab yaci ya koshi kafun Nnenna ta Mike daga Kan gadon laidodin abincin ta aje a jikin drower ta dauki Kaya ta shiga bandaki wanka tayi ta daura towel Inda Lahab ya cire tare ruwa tayi a bucket tayi ta soma wankewa harda na Lahab tas ta wanke kayan ta tsame a bokati,kayan da ta shigo dashi ta saka wandone da riga t-shirt ta dau bucket in tare da bude kofar toilet in ta fitoh. Lahab Kam tunda Nnenna ta shiga ban dakin ya koma ya kwanta ba tare da ya maida ruwan daya cire a hannunsa ba,haka kawai sai Yana Jin wani irin shauki ji yake Kamar rayuwar aure suke da Nnenna Suna rayuwarsu a daki daya ta basa abinci ta Masa wanka duka da ace matarsa ce janta kawai zaiyi su kwanta tare yaji yanda masu aure suke ji ashe haka rayuwa da mace yake da dadi"Allah ka aurar damu"shine abinda Lahab yace Yana gyara kwanciyarsa Jin Karan bude kofar toilet daidai lokacin aka bude kofar dakin da sallama aka shiga,d'aga Lahab har Nnenna dake bakin toilet dago Kai sukayi sukaga Mai shigowar ................. ****************** Ruky ta Jima a tsaye a bakin titi bayan wucewar mubeena ajiyar zuciya ta sauke itama ta tare Keke tare da sanar dashi sunan unguwan su shiga keken tayi Mai keken yaja Suka cillah 30 minutes Keke yai parking a bakin lungun su Rukayya saboda cabalin da unguwar tayi ga ramuka shiyasa masu Keke basa yarda su shiga sai dai a sauke su a bakin lungu,sauka tayi tadau 50 kudin keken ta Mika Masa gangarowa tayi cikin layinsu tana tafiya tana bin Koh Ina da kallo kowa harkan gaban sa yake unguwane na masu karamin karfi sosai,kallon gefen wani madalisa dake gabanta tayi cike yake da jama'a tim,sai tebur dake d'auke da manya manyan kuloli akai kannen Rukayya ne su biyu Wance take binta tana zuba abinci dayan na karba tana rarrabawa matasan dake zazzaune a rumfar,share hawayen fuskar ta kawai tayi ta wucesu ba tare ma da ta d'aga Ido ta Kara kallon madalisan ba suma basu wani lura da wucewar Yar uwar tasu ba saboda ciniki da suke. tafiya taye kadan kafun ta iso kofar gidansu,gidane irin na da mai Jan block Koh kofa babu sai wani yamutsetsen taburma da aka Kare kofar shiga gidan dashi sai wani tsohon shagon gugan babanta dake kusa da gidan su leka shagon tayi tama baban ta dake guga da dutsen cakwal,baba sannu da aiki? da fara'arsa ya juyo fuskarnan sharkaf da zufa,yauwa mamana harkin dawo gidan kawar Taki dazun da nashiga gida mamarku kece min kinje gidan kawar Nan taki mema sunan ta farar Nan? Hhh sunan ta mubeeena baba? Mubeena Kuma mamana wannan Suna ai sunan yan gayu saiku zaku iyya rikewa. dariya kawai Rukayya tayi ta nufi kofar gidan nasu d'aga taburman tayi da sallama ta Shiga. Addanta bazawara dake duke tana sana'an wankau ce ta amsa sallamar ta tare da Mata sannu da zuwa itama Rukayya sannu da aiki tama yayar tata ganin uban wanki da take tana ta shashanyawa,Zama tayi a bakin dakali,mamar tane ta fitoh kitchen da Sauri hannunta d'auke da kullin awara data tsame yanzun daga tukunya ajewa tayi a bakin dakali tare da daura Masa babban dutse akai. Sannu da aiki mama? Yauwa Rukayya sannu harkin dawo? Eh na dawo mama,yauwa tunda Kim dawo ga kwanuka da tukanen abincin Nan kije ki wankesa kafun lokacin fitar kanwarki tuyar awaran yayi kin kimtsa kayan aiki,mikewa Ruky tayi ta Shiga dakinsu ta Kwabe kayan jikinta ta sanya wani kodadden zani ta fitoh bucket ta d'auka ta fita gidan ruwa ta ibi kafa uku saboda yanayin yawan kwanukan abinka da gidan masu abinci da tuya kwanuka bana Wasa bane buhun omon su ta dauko ta aje tasa kujera ta Fara wanke wanken. Sai can yamma kannenta guda biyu Suka shigo gidan, Almajirai nabinsu da robobi da kulolin abincin nasu,faggawa Almajiran sukayi a mawanki ita Kuma Yar autarsu ta dau awaranta a bucket da abubuwan tuyanta ta fita kofar gida, cefene maman su tama Rukayya saboda itace Bata sana'an kome sai aika da wanke wanke da zuwa cefene in bataje school ba Amma su biyar Mata kaf su hudun Suna da abin yi. Bayan sallan mangariba zazzaune suke gabaki dayansu a tsakar gidan sauran abincin da bai Kare ba na sairuwa shi gabaki dayan su suke ci shinkafane da Miya sai Kuma tuwo da miyar alaiyahu da aka duma, Ruky duk da abinda ke damunta kokarin boyewa take bata son kowa a gidan su ya fahimci halin da take ciki,Jin ana kiraye kirayen isha'i yasa baban su mikewa ya fita masallaci sauran yaran ma duk Suka mimmike Suka dau buta Suna Alwala. Bayan sallan Isha zazzaune suke ana Hira a tsakar gida ita Kam Ruky rike take da handout nata tana karatu hannunta rike da dan wayarta Abba gida-gida,yaro ne ya shigo da sallama tare da sanar dasu wai wani na sallama da Rukayya a waje kallon kallo akayi don rabon da azo ace a Kira Rukayya ai an kusan shekara kenan,kaje kace wanene Addan Rukayyar tace,juyawa yaron yayi baijima ba sai gashi ya dawo Wai inji Ahmad,mikewa zaune Ruky tayi duk da tana danjin kunyar babanta dake wajen,ta fahimci wani Ahmad ne cikin sanyi tace kaje kace bana Nan? Ke tashi dan Allah Mara hankali wani irin aje ace bakenan Mike Maza,-maza Kafun tacewa yaron kai jekace tana zuwa maman ta tace tana zarewa Ruky Ido,mikewa Ruky tayi tadau hijab nata cikin kunya ta fita a gidan. tsaye yake a jikin ginin gidan su ya hade hannayen sa a kirjin duk da dare ne hakan bai hanata ganin raman da yayi ba, Assalamu Alaikum. Waalaikumu Salam Rukayyar barka da dare? Uhmm barka dai Ahmad ince dai lafiya na ganka a irin wannan lokaci Kuma a kofar gidan mu? Hh lafiya klau Rukys menene zai kawo saurayi irin wannan lokaci wajen budurwa in bada maganar so ba?tukunna ma ba wannan ya Kamata ki tambaye Ni ba jikina ya Kamata ki Fara tambaya. Kaga dan Allah Ahmad Ni wannnan Wasa ya isheni haka Ina son kawata Ina son alakarmu duk da Koh shekara bamuyi da haduwa ba kaika sani a makaranta muka hadu amma Ina jinta a raina sosai bazan so ka Zama tsilar rabuwar mu ba Koh Ni na Zama tsilar rabuwar ku. Haba sau nawa Zan sanar dake cewa babu wannan zance na nine sula Koh kece tsila babu wannan magana abu daya na sani shine bamu sabawa shariya ba Kuma ita da kanta tace bata Sona tana da Wanda take so? Eh hakane amma fa ka sani bazan iyya auren ka ba duniya zasu zageni. Wani irin zagi?ana gujewa mutan ne Koh bayan aure zasu zo har gidanki su fiddaki ne,Koh zagi Yana mannuwa a jikin mutum ne? Ni abinda nake so dake Ruky ki sani bawai zanyi abin nan dan kuntattawa mubeena bane ah ah wata daya ya rage in ba haka ba baba na ya rantse sai ya auramin Yar kanwarsa Ni Kuma tarbiyarta baimin ba amma kefa na sanki tuntuni bana bukatar tsayawa tantance dabi'unki sai abinda baza'a rasa ba. dan sauke ajiyar zuciya Ruky tayi,yanzun Ahmad y........baibari ta karasa ba ya dakatar da ita,Kinga Ruky ba zuwa nayi muyita maida zance ba Zan baki Nan da kwana uku kije kiyi shawara Zan dawo ranan talata na amshi amsata duk abinda Kika yanke wallahi bazan Kara akansa ba don haka ki shiga cikin gida Sai da safe. gyada Kai kawai Ruky tayi ta juya ta shiga gida,tana shiga ta samu baban ta ya tashi yayi cikin dakin sa itama dakinsu ta shiga da Sauri taje ta zauna akan katifar ta ta rufe fuskarta da hannunta cikin damuwa. Mikewa Addan Ruky tayi ta biyota dakin Zama tayi a bakin katifar ta dafa kafadar ta,Ruky meke faruwa meyasa tsawon shekara kina Neman mashinshini sannan yau kin samu wani yazo shine Zaki ki fita Ruky watoh har yanzun bakiyi karatun ta natsuba kin manta sake da kikayi da Nasir ya tsubce Miki,haba Ruky kinfiso dukan mu mu taru mu zauna kenan Koh me? Uhmmm Adda Koh kinsan Ahmad Nan dayazo wajena shine zai aure mubeeena? Rukayya wata mubeena? Kawata mubeeena fa. What??wannan ai shirmene akan me zaizo wajen ki bayan Yana tare da kawarki,Zama Ruky tayi ta warwarewa addan ta kome,toh kinji abinda ke faruwa. Mikewa Adda tayi ta kalli Ruky, Rukayya indai haka abin yake toh Ina Mai Baki shawara ki yarda ki amince da Ahmad wannan shine Allah ya kashe ya Baki......... πŸ™„*Ruqeenjalal* *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki* Page 59&60 Haba Adda wani irin Allah ya kashe ya bani? karfa ki manta banine a ransa ba mubeena ce wallahi Koh shakka banayi Koh na aure sa bazan samu kulawar da mubeena zata samu a wajen sa ba. Uhmmm Rukayya kema har yanzun yarinyar ce Ina ruwanki da yafi sonta a kanki,shuru kawai Ruky tayi tana kallon Yar uwar tata sai zuzuta zancen take da Kara jaddada Mata akan ta amince dashi, Rukayya nidai Ina Kara gaya Miki wallahi kiyiwa kanki karatun ta natsu ai dukan kune zakuyi biyu babu ke baki aure sa ba itama ta rasa don haka nidai Ina gaya miki ki amince kinji? gyada Kai Ruky tayi tace,insha Allah Adda Zan amince Masa Allah yasa hakan shiyafi Alkhari a garemu baki d'ayan mu. Ameen Adda tace ta Mike tabar dakin,ajiyar zuciya kawai Ruky ta sauke tare da kwanciya akan katifar ta. Adda na fita daga dakin nasu wajen mama takoma Zama tayi tafara ma mama magana,uhmm mama kinsan Ruky da rashin hankali Wai harxata samu Mai sonta da aure ta tsaya tana yanga? Mikewa zaune mama tayi d'aga kwance da take a taburma,kaji Yar banzan yarinya zata sake reshe ta Kama ganye watoh abinda ya faru tsakanin ta da Nasir baisa tayi hankali bako? Kedai Bari mama Wai saurayin kawar Nan tata mubeena take Koh wa? tace batason Yaron shine fa shi Kuma yaga Rukayya Yana so Wai ta tsaya tana lagwa-lagwa Yar banza in tayi aure Ina zataga ita mubeenar bare ta tuna saurayinta ta aura? Uhmmm lallai Rukayya bata gaji da zaman gida ba Aiko wallahi Koh bataso Ni Zan ma baban ku magana in yaron ya sake dawowa ace ya turo don ubanta a halin da muke cikin Nan Nan gaba ma kudin makarantan nata ba iya biya zamuyi ba sannan ta samu Mai son auren har zata tsaya wani kafli da badi mubeenar kanwar uwarta ne Koh na ubanta? dariya ne ya kufcewa Adda Jin yanda mama ta zage sai masifa take harda cewa zata shiga dakin nasu ta samu Ruky taci Mata mutunci daker Adda ta samu ta sassauta masifar tare sayin Alwala ta wuce dakin ta bayan tama yaran Saida safe, daman baba ya shiga tuntuni,Adda ne ta Mike taje ta rufe kofar gida ta karkata kannen nata zuwa cikin dakin su kwalli d'aya da suke kwana dukansu su biyar a ciki, Nan ma ta mayar da yaranta biyu kenan gidan baban su shiyasa Suka samu saukin matsin da suke ciki na wajen kwana don daki biyu garesu daya na mama da baba daya nasu. ******************* Mahaifiyata Kika Mara?kallon Anwar Mami tayi kafun tayi magana,eh na mareta Anwar na mare uwarka Koh zaka rama Mata ne nasan lalle kunsha a no-no? Umaima data shigo durkusawa kawai tayi a wajen tana kuka Anwar har lokacin Yana Nan a tsaye yayin da Shareef ya sunkuyar da kansa a kasa uwa uwace duk da mamarsu ce bata da gaskiya amma yaji mugun haushin Mami na marar Masa uwa bare ma Mami da kadan ta girme Anwar don kwata kwata bata wuce shekaru 35 ba a duniya ba. Mamu da tayi mutuwar tsaye hannunta dafe da kumatu tana bin yaran nata da kallo ganin gabaki dayan su babu Wanda ya yunkura zai rama Mata hawaye ne ya cika a idanunta lokacin da takai dubanta ga Abbu muzammil da Addayiya babu Wanda ya nuna Koh damuwa a fuskarsa,da gudu tayi kitchen ba'ajima ba sai gata ta fitoh da tabarya tayi Kan Mami, wallahi yau sai nayi ajalinki saikin gane baki da wayo harni Zaki mara,ta d'aga tabaryar da karfi zata bugawa Mami,gabaki d'aya Yan falon mikewa sukayi cikin bacin Rai Abbu ya daka Mata tsawa,wallahi halima in Kika buga Mata tabaryar Nan a bakin auren ki na gaji da halayen ki a gidan Nan, shekaru sunja amma ke banga hankalinki ya daidaita ba. Mamu Kam kafewa tayi da tabarya a hannu har lokacin kunnenta baibar jiyo Mata da abinda Abbu yace Mata ba, a tsawon zaman su bai taba Mata wasan saki ba bare barazana sai yau,Wai Ina zata sa Mami ta daina kallonta ne? ga ummu itace kishiyarta amma batajin kishinta Kamar mami,Wai inkin buga Mata a bakin auren ki?ita Haleema Kuma a gaban yaranta. gabaki d'aya jama'an falon sun girgiza da maganar Abbu sosai Wanda hakan yasa Addayiya kasa hakuri hartayi magana,Kai Umaru wannan wani irin rashin hankali ne mekake cewa haka so kake ka dasawa yaran ka wani tunanin daban a ransu ne Koh Yaya?kace zaka saki uwarsu akan uwar wasu,yau Haleema da Amina Suka Suma tsama ne da zaka Fadi haka kul bana son sake Jin magana irin wannan. Jan numfashi Abbu yayi sannan a hankali ya koma Kan kujera ya zauna tare da dafe kansa shikaran kansa yasan hakan bai kyautu ba amma ya zaiyi ransa ne ya baci yasan halin Halima da rashin hakuri,ummu Kam Koh a jikinta yima tayi Kamar bata San meke faruwa ba sai daddan na wayanta take,Mami Kam juyawa tayi zata bar falon da Sauri Lahab ya kirata,Mami ayya jirani Ina zuwa minutes biyu tsayawa tayi shikuma da gudu ya mike yayi cikin falon su daki ya shiga a hargitse ya zaro akwatin kayansa ajewa yayi a kasa tare da bude wardrobe na kayansu jido kayayyakin sa yake Yana jugawa a akwatin Koh takan Nade baibi ba takalma duka ya zuzzuba har Saida akwatin ya cika yaja zip da sauri ya dau jakar makarantan sa ya goya tare dajan akwatinsa ya fita a dakin kofar falonsu ya bude ya fita. duka Yan falon da Ido Suka bisa ganin sa. D'auke da Kaya Niki Niki ya nufi mami hannunta ya Kama Suka nufi kofar ba tare da yayi magana bama,Kai Rahab Ina zaka kayan Nan fa?Abbu yace Yana kallon sa a tsorace don harga Allah baison ganin fushin Rahab gara Masa na Lahab kunayin abu anjima ya watsar amma wannan shegen rikone dashi da d'acin Rai. Juyowa Rahab yayi cikin girmamawa yace,kayi hakuri yaya ban taba sanin cewa zaman na da dan uwana shiga hakkin ku muke ba sai yau,ga gidan Nan mun bar Mata sai ta rayu daga ita sai yayan ta da wa'inda takeso ba shikenan ba? Kai ba shikenan ba dan uwarka kana da gidan da yafi wannan ne Koh gidan da zaka yanzun na ubanka ne?Addayiya ce tayi maganar a zafafe Shima Rahab a zafafe ya Bata amsa,bana ubana bane amma Ina da tabbacin babu Wanda zai goranta mini daki a gidan Koh uwata Koda kuwa shekaru dubu zamuyi a cikin sa,mikewa muzammil yayi Jin bakar magana da Rahab kewa mahaifiyar sa,nufo Rahab yayi Kamar wani zaki Yana huci Shima Rahab bai Koh mutsa ba Yana tsaye domin a wannan lokaci ransa yayi kololon baci hannu muzammil in ya d'aga zai kwadawa Rahab a kumatun da Sauri Rahab ya riko hannun nasa jikinsa har rawa yake ya Soma ma muzammil magana cikin kaushin murya,ka tsaya iyya matsayinka na Yayana karka wuce iyyakarka wato na baiwa mahaifiyarka amsa kaji haushi?Ina ga Ni danayi hakuri da irin cin Kashi da kake Ma tawa mahaifiyar baka kallonta da daraja amma a hakan Muke kiranka da wa,don haka baka Isa nima yau kace zaka bugeni akan taka uwar ba,kaji na rantse maka d'aga yau bazan sake bari hannunka ya taba jikina da sunan duka ba in ko ka gwada hakan toh tabbas Zan rama nima karfin Nan babu wanda bai dashi don haka ya isheka haka ya isa bazan lamunta ba bazan lamunta ba kaji na rantse,Yana karasa maganar ya sake hannun muzammil yayi mutuwar tsaye agun Wai shi yau Rahab kecewa inya buga zai rama gara ma in Lahab ne ya fada Masa haka toh bazaiyi mamaki ba amma yau wannan ne ke fada Masa da kansa lallai abin nayi ne,Ni kake cewa zaka buga ai bazanga laifin kaba tunda uwarka bata nuna maka Ina da mutunci ba. Jin abinda muzammil yace yasa Mami harzuka,Kai muzammil karka kuskura karka soma wallahi in ba haka ba Zan rufe Ido inci ma mutunci kasan Ni nasanka wallahi Ni nafi karfin na nunawa yarana su Raina barema bare dan uwansu kaida yake dama mugun Hali gareka dole kana kallon kowa ma haka,nuna Rahab tayi Kai wuce muje ta bude kofar falon ta fita Rahab na binta a baya da kayansa,mamu Kam sosai taji dadi ganin fadan yabar kanta ya koma na muzammil da Mami gashi Rahab yabar gidan don ita a duniya babu abinda takijini Kamar ta bude Ido taga Mami a duniya da yayan ta Suna walwala Koh cigaban su bataso. Kuka Addayiya ta sake kafun ta soma magana, yanzun umaru kana ji kana gani amanarka zai bar hannunka karfa ka manta kafun mahaifinku yabar duniya sai da ya baka wasiya Koh bayan ransa y'ay'an sa su zauna a hannunka shine yanzun zaka wani barshi yabi uwarsa yaje Yana agolanci a gidan uban wasu,sai Kuma ta Kuma sakin wani Sabon kukan. Abbu Kam da kansa ke kasa ji yake Kamar Kan zai tsage ace Yana matsayin babba ga mahaifiyarsa duka zaune Suna fadace fadace a gabansa sannan ga damuwar rashin Inda karamin kaninsa ya shiga na tsawon kwana biyu ga kukan da yanzun Addayiya keyi,dan Allah Addayiya ki rufamin asiri kiyi shuru mubi kome a hankali. Kin shuru Addayiya tayi muzammil Kam ji yake Kamar ya ketta wa kansa aShana Wai yau shine Rahab yama rashin mutunci gaskiya ne da hausawa sukace karka Kai Mai hakuri bango. ***************** ai da Sauri Inna ta juya ta kamo kafadun mubeena da karfi ta girgiza cikin masifa tace,keee mubeena ashe baki da mutunci oh baki sonsa toh uban wa kike so nace uban wa kikeso? ki fadamin Mara hankali munafuka kawai Inna tace tana girgiza mubeena dake ta kuka durkusawa tayi a wajen tana wani irin kuka Mai cin Rai da tsoro. Inna ma Zama tayi a wajen ta Kama Kai tana kuka tana magana,mubeena kin cuci kanki mubeena mekike nema a wajen namiji Wanda Ahmad bai dashi yaro Mai sonki Mai kaunar ki yamiki goma Sha,yanzun da abinda Zaki saka Masa kenan wai kice baki sonsa toh wallahi sai kin fadamin uban wa kike so din? Shuru mubeena tayi bata yi magana ba haushi ne ya cika Inna Jin sai magana take Mata ita Kuma taki bata amsa,nace Miki wanene In kike so da har Zaki rabu da yaron kirki Mai kawo min goro duk juma'a Ina tambayarki kin min shuru,shuru mubeena bata bata amsa ba hannu Inna tasa ta wanke fuskar mubeena da Mari daidai lokacin Nabeel ya shigo gidan akan idanunsa Inna ta wanke Yar uwarsa da Mari cikin tsoro ya karaso Inda suke ganin su cikin wani irin yanayi na damuwa,Inna lafiya meya faru Aunty mubeena meke faruwa ne? gabaki d'ayan su shuru sukayi babu Mai magana sai kuka da mubeena keyi Inna na tayata,wallahi ku fadamin meke faruwa Koh Kuma Bari naje na Kira bappa Ado yace Yana mikewa don harga Allah ya tsorata ya d'auka wani babban al'amari ne ya faru bai kawo Koh a ransa akan Ahmad bane. ganin zai fita yasa Inna dakatar dashi,tsaya Nabeel basai ka Kira bappan kuba zauna kaji abinda munafukar yarinyar Nan tace mini bayan ta gama munafurcinta sannan tazo tasa kanta a damuwa ai ba kuka zatayi ba Murna zatayi. dan tsaki Nabeel yaja,Kinga Inna Ni kimin bayani yanda Zan gane Mana menene mubeenar tayi Kuma,kunzo kun hadu Kuna kuka Koh wanine ya mutu? Jin tambayar da yayi yasa mubeena girgiza Kai ta Mike tsaye Shima mikewa yayi ganin ta nufi Kan taburma ta zauna Shima Zama yayi yasa hannu ya Kama nata sosai ya rike cikin nasa a tausashe Kamar ba Nabeel abokin Lahab ba ya soma magana,Kinga mubeena kibar kukan Nan haka ya Isa kimin bayani duk kunbi kun rudani meke faruwa ne?shuru mubeena batayi Masa magana ba sai kallon kasa da take har lokacin idanunta na zubar da hawaye,Taya zata maka magana bayan bata da gaskiya. Kinga Inna in Zaki fadamin ki fadamin kawai Kuna dad'a rudani fa? ba kome bane yasamu cikin wannan Hali illah abinda Yar uwarka da bata rike maraicin ta ba ta aikata Wai har yarinyar Nan zataga tsabar idanun yaron Nan Ahmadu tace bata sonsa yaron da yayi d'awainiya da ita tun bata Kai haka ba watoh yanzun ta Zama Yar collegi(college) zatazo ta nuna Masa wayewa banda rashin tunani irin nata ai shiya sata a makarantan. sauke ajiyar zuciya Nabeel yayi Jin abin ba wani babba bane amma duk da haka Sosai abin ya basa mamaki har Saida ya kasa boyewa,Inna kikace Aunty mubeena tace Miki sun rabu da Ahmad Kuma ita tace bata sonsa?tunda Kika ga hakan Kika sani Koh akwai abinda ya Mata shiyasa tace bata sonsa,tsawon shekarun Nan batace bata sonsa ba sai wannan Karo gaskiya da sakel. Jin amsar da Nabeel ya baiwa Inna yasa mubeena ta Fara magana a hankali har lokacin kanta a kasa,babu abinda ya hadamu da Ahmad daman bashi nake so ba Ina da Wanda nake sone. Wakike son kenan sannan tsawon shekarun Nan bakisan baki sonsa ba kuke tare Koh yanzun ne kika ga Wanda kike son Inna tace Aunty mubeena ki kwantar da hankalin ki ki Mana bayani d'aga Ni har Inna nakine babu bare in baki fada Mana damuwan ki ba wa Zaki fadawa kenan Yar uwa?kinsan mu masu goyon bayan abinda kike sone mundin zai saki farin ciki amma fa in bai sabawa shariya ba. Sosai maganar Nabeel ya baiwa mubeena karfin gwuwar fadin abinda ke ranta daman tsoro take taya zasu d'auke al'amarin a hankali ta soma magana,daman tun da dadewa bashi nake so ba ku............. πŸ€ *By Ruqeenjalal* πŸ€ *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 08084453785tare da shaidan biyan ki* Page 61&62 Uhmm Aunty mubeena munajin ki ya kikayi shuru Kuma? dan shuru tayi sannan a hankali tace,toh banace bana sonsa bane Kuma ban d'auka zaiji ba ashe yazo wajena a makaranta bansani ba shine ya yanke jiki ya Suma..........................................daga a har z mubeeena ta sanar dasu duk abinda ya faru amma bata sanar dasu Lahab ne take son ba ta boye musu tadai ce tana da Wanda take so,ajiyar zuciya Inna ta sauke Jin dogon bayanin da mubeena keyi,toh ke mubeena yanzun duk maye saki a damuwa?ai tunda ya hakura abinda ya dace yanzun saiki fitar da Wanda kike son yazo a muku aure bashi kenan ba Shima yaje ya aure takwarana in ba? hawaye ne ya zubowa mubeena Jin abinda Inna tace,toh yanzun Inna fisabililahi sai Ruky tana kawata sai ta yarda zata aure sa kenan? toh dan kaniyar ki sai taki ne Koh Yaya a zamanin da ake innan ana haba haba da mijin aure har zata ga bonus ta bari ne?kince baki sonsa don haka kicewa Wanda kike son ya fitoh, nagaji da ganin ki a zaune ba aure in ma karatunne ya ajeki bamuda kudin biya miki yanzun. Haba Inna da wanne zataji ne Wai guda daya haka, Nabeel yafada wa Inna sannan ya juyo ga mubeena,Kinga Aunty mubeena yanzun kiyi shuru ki kwantar da hankalin ki ki Mana bayani shin Menene ya saki kuka da damuwan so kike Ahmad ya dawo ne?Koh Kuma bakison Rukayya ta aure sa wanne ne baki son guda daya? girgiza Kai mubeena ta sake tare dajan numfashi Jin tambayar da Nabeel ya antayo Mata Wanda bazama tace eh ne Koh ah ah ba ta rasa wanne ne d'aya? tace bata son Ahmad amma tanajin haushin auren Ruky da xaiyi,nifa ba wa'innan ke damuna ba kawai dai makaranta nane gashi Rabin kayana duk shiya dinka min bazan iyya cigaba da amfani da abinsa ba,sai Kuma ta fashe da kuka Kuma Wanda nake son baisan Ina sonsa ba. Ai Jin haka yasa Inna mikewa cikin masifa tace,keee maimuna don baki da hankali har kina maganar makaranta ai Ni koh Ni da kaina bazan sake barinki kije makaranta ba aure zakiyi,sannan Kuma kice Wanda kike son baisan kinayi ba, me kike nufi kenan mu Zaki mayar Yan iska Koh Yaya? don girman Allah Inna ki barsu shiyasa Aunty mubeena bata son gaya Miki matsalan ta maimakon ki natsu ki bata shawara Koh Nasiya saiki Kama Mata ihu aikin gama dai ya gama Koh Ni Karan kaina banji dadin abinda tayi ba amma ya zanyi bazan iyya ganin Yar uwata ta aure Wanda bata so ba,shuru Inna tayi ta koma Kan kujeran da ta tashi ta zaune,ganin tayi shuru yasa Nabeel cigaba da magana,indai akan makaranta ne karkiji kome Aunty Ni Kuma insha Allah daga yau xanna xuwa shago xanyi aiki yanda ya Kamata xan nemi kudi na biya Miki kudin makaranta Koh da kuwa Ni Zan hakura da nawa karatun daman Lahab da Ade me biyamin, sannan Koh Ni bazan so ki cigaba da amfani da abinda Ahmad ya baki Koh yayi Miki,amma fa dole ne Zaki bar wasu kiyi amfani da wasu kamar sutura dole ne kisa nasa amma makaranta insha Allah Ni Zan cigaba da biya Miki ke Kuma ki maida hankali akan jarabawanki insha Allah kome zai daidai. dan shuru mubeeena tayi tana kallon Nabeel in kafun tace,amma fa Ni babu ruwana da Rukayya daga yau, Kuma Zan maida Masa da wayarsa dake hannu na yanzun? Inna ce ta tareta kafun ma Nabeel yayi magana,babu wani ba ruwanki da kawarki ai ita bata Miki kome ba, Kuma Koh tayi kece Kika ja maganar waya Kuma baza'a maida Masa ba ki bawa Nabeel yaje ya sayar dashi sai ya sayo Miki wani kala Kinga Koh anga waya a hannunki ba nasa bane. gaskiya ne Inna bai Kamata ma ta nuna abin ya Mata zafi ba Kuma nima na tabbatar yaso auren kawartata ne don ya kuntata Mata badon Allah ba sai Kuma maganar Wanda take so, Aunty mubeena mu Maza Muna da wani dabi'a shine in mace ta nuna tana son mu Koh auren akayi bata mutunci a idanun mijin nata sai Wanda yasan abinda yake in Allah ya hadata da namiji Masanin Alkur'ani da hadisai don haka Ina Mai shawartar ki akan kibi kome a hankali sannan ki rike ajinki na y'a mace. Insha Allah Nabeel Zan kiyaye tace cikin Jin dadi ganin basu matsa sai sun San wanda take son ba,Kuma taji dan sanyi data samu ta tofa abinda ke damunta. Inna Kam cikin dan sake jiki datayi tace,toh yanzun mubeena haka Zan tasaki a gaba sai dai in gari ya waye kiyi wanka ki tafi makaranta Wai da sunan kina jiran Wanda yake sonki yazo auren ki wannan abune da xaiyo kuwa?,nidai Ina fada Miki gwara kiyi abinda zai fansheki Nabeel baisan kome ba sai shashanci. Jin abinda Inna tace yasa mubeena mikewa ta shiga dakinta Cikin Jin haushi Nabeel yace haba Inna menene haka don Allah ya zakina fadar magana irin wannan yanzun Nasiya da magana Mai dadi Aunty take bukata amma abinda kike matan Nan baida kyau wallahi. don Allah rufemin baki Wawa kawai. Mikewa Nabeel yayi yasa takalmin sa zai bar gidan don yaga duk ta Inda zai bullowa Inna bazata hakura da masifar Nan ba dan dakatawa yayi Jin Inna na Masa zancen Lahab akan jiya muzammil yazo Neman sa baya Nan,Kai Inna inaga dai baikoma gida bane don yace min zashi gidan yayan sa jafar taima ma yanzun sun gansa amma bara nake gidan su Ade in yaso sai muje mu duba sa a gidan yayan nasa nima nayi missing nasa kwana biyun nan wallahi. Ku dai kuka jiyo daman in kun hadu ba'ajin Alkhari amma daya ke kwana biyu baku haduba har dan hankali ka Fara,Jin abinda Inna tace, murmushi kawai yayi ya fita a gidan nasu,mubeeena dake daki tana jiyo duk abinda suke cewa dafa kirjinta tayi tana tari a cikin kwana biyu da bata sa Lahab a idanunta ba abin ba karamin nukurkusanta yake ba. ********************** Mami Suna fita a gidan parking tayi a bakin titi tare da sauke ajiyar zuciya tana kallon Rahab dake zaune a sit in Mai zaban banza dake kusa da ita gabaki d'aya taga yaron nata yayi sanyi sosai wallahi,Rahab ta Kira sunansa amma shuru bai amsa ba hannu tasa ta shafa kumatun sa dan juyowa yayi Yana kallonta sai Kuma ya kalli titi shi baima San tayi parking ba,Mami ya Kika tsaya Kuma Koh motar ta lalace ne? ba lalace wa tayi ba Rahab magana nake son muyi a gaskiya abinda kayi yau Innan banji dadi ba Sam, na kuma Yi shuru ne badon ka burgeni ba nayi shurun ne saboda na barka ka Fadi abinda ke nukurkusan ranka amma fa ka sani kaf duniya baka da gidan da yafi wannan gida da kake ciki sai Wanda zaka mallaka Nan gaba,baka da wasu Yan uwa Kuma Ado a gareka daya fisu barinka gidan Nan bazaiyu ba,in har kabar gidan toh burin mamu ya cika na rabaku da yan uwanku Kuma muzammil yayan Kane banji dadin abinda ka Masa ba. da Sauri Rahab yace,nima Mami ai banjin dadin abinda yake Miki,meyasa Koh don albarkacin mu bazai mutuntaki ba kina matan baban sa taya Zan cigaba da basa girman sa Mami? Kaga Rahab wannan tsakanina da shine bana son kasa kanka a cikin wannan maganar,sannan bazan goyi bayan kabar cikin gidanku ba Yan uwanku zasuga Kamar Nike zugaku Koh Kuma so nake na karbe ku,don hakan yanzun dai muje station daga Nan sai na kaika gidan yayan ka jafar ka zauna acan. Haba Mami ni wallahi bazan zauna a gidan Yaya jafar ba wata rana nanne tamin gori itama,baga irinsa ba Mami kinje kin aure tsoho karshe muntashi a wahale da ace mahaifin mu na raye na tabbata bazan tsaya tunanin Inda Zan...............daka Masa tsawa Mami tayi cikin Jin haushi tasoma magana,yanzun kaima Rahab maganar da zaka fadamin kenan Wai meyasa mutane suke min haka ne, watoh kaima ka kawo Kai har kana da bakin fadawa uwarka maganan ta aure tsoho Koh? sai Kuma ta kifa kanta a siterin motar tana Mai girgiza kanta tana alhenin abubuwan da Suka shude duk mahaifinta ne yaja Mata duk shiyasa ta cikin wannan matsalan,da Sauri ta kauda tunanin tare da istingefari tunawa tayi karfa tayi sabo kome na duniya dama Rubuceccen Al'amari ne. don Allah Mami kiyi hakuri bazan Kara ba wallahi bawai rashin kunya na Miki ba amma abin na damuna Inna d'aga Ido Naga ya Umar da ya jafar da Aunty shamsiyya a matsayin yayuna ne su duka duk sun tsufa gwara gwara ma ya muzammil ga yawan gori da Addayiya da Mami ke Mana akanki abin baimin dadi Sam. d'aga kanta Mami tayi daga Kan siterin ta kunna motar ba tare da tayi magana ba tafiya suke babu Mai magana har Suka Isa station Suka mikawa Yan santa case in Lahab daga station in titin gidan ta Mami ta nufa da Rahab,ganin haka yasa sa saurin dakatar da ita,Mami Ni bazan zauna a gidan ki ba ki kaini gidan uncle muneer saina zauna a wajen sa kafun Lahab ya dawo saimu koma gidan mu Koh? tad'anji sanyi a ranta Jin yanda yaron nata ke Mata magana watoh ya hakura da fushin barin gidan nasu,amma bata nuna Masa ba sai Kara tamke fuska da tayi tayi rebas ta Kama hanyar unguwan su Uncle muneer in 30 minutes ya kaisu unguwar gangarawa tayi har kofar gidan tayi parking bude motar tayi ta fita Shima Rahab sauka yayi a motar ya bude baya yadau jakansa yabi Mami cikin gidan. da sallama Mami ta Shiga gidan amsa Mata salamatu tayi,ah ah wa nake gani Kamar Hajiya Amina sannu da zuwa Bismillah,dan murmushi Mami tayi sannan ta shiga falon gidan Zama tayi a Kan kujera yayin da mustapha dake kwance Yana danna waya ya mike Yana gaidata tare da fita a falon Jin muryar Rahab a tsakar gidan Yana sallama,amsan kayan Rahab in yayi ya nufi dakin sa dake kusa da sauron gidan ya shigar da kayan wajen,dan leko falon Rahab yayi ya gaida salamatu sannan shima yabi mustapha dakin,bai bi mamin falo ba. Salamatu daki ta Shiga bayan sun gaisa da Mami ta Kira Mata yayan ta muneer sannan ta basu waje sosai Mami Suka znta da yayan ta Kuma Shima ya Mata fada sosai data sanar dashi Lahab yaje wajenta Harya fusata yabar gidan nuna Mata yayi shi yaro Mai rawan Kai da lallama ake binsa daja a jiki daga karshe Kuma ya nuna Mata babu kome Rahab yazo su zauna ai dashi da mustaph duk daya suke a wajen sa sosai taji dadin hakan tare da mikewa tama yayan nata da matarsa sallama fitowa tayi a falon tasa takalminta ta nufi Sauro zata fita yayin da salamatu ke binta a baya Suna dan Hira,tsayawa tayi a kofar dakin mustapha ta kwalama d'an nata kira. Rahab dake zaune a dakin mustapha nata zuba Masa hira,ya amsa Mata tare da mikewa ya fitoh ganin ya fiton yasa Mami nufar kofar gidan tana ma salamatu sallama itama salamatun asauka lafiya ta Mata ta koma cikin gidan,bayan sun fita wajen bude purse nata Mami tayi ta zaro ATM card nata guda daya ta mikawa Rahab ba tare da tayi magana ba,amsa yayi da Sauri Yana godiya,nasan zakaji sauyin rayuwa a gidan Nan don ba irin gidan ku bane daka Saba da laushi da AC ga card Nan Koh zaka bukace wani abin saika zare ka saya ban baka don kayi almubazzaranci dashi ba. Insha Allah Mami Allah dai ya bayyana dan uwana duk da Ni Mami gani nake kamar wallahi ba b'ata Lahab yayi ba mu munsa Kan mu a damuwa,kindai San iyya shegen sa. dan sassauta fuska Mami tayi,toh yanzun Rahab in ba b'ata yayi ba meyasa har yanzun bai dawo ba sannan tunda yake bai taba barin gida ya kwana wani waje ba tare da sanin yayan ku ba sai wannan Karo nidai gani nake Kamar akwai abinda ya samesa. Mami ki kwantar da hankalin ki taima ma gidan wasu abokan nasa yaje yayi zaman sa kinsan fa yayi laifi Kuma ya tabbatar za'a hukuntashi Koh hakan ma zai hanasa zaman gidan. Toh Allah ya shiryesa koma me ake ciki zanji a wajen Yan sanda. Ameeen ya Allah Mami Rahab yace, Yana tsaye Harta shiga motar ta tabar layin unguwan sannan ya juya ya koma cikin gidan. ********************** Dr ne ya shigo cikin fara'ar sa gaidashi Lahab yayi itama Nnenna ta gaidashi amsa musu yayi sai wani irin kallo yake Mata ganinta sanye cikin wando da riga sunyi azaban karbanta ta fito Ras da ita a cikin kayan,Lahab Kam ji yayi makokonsa ya cika amma baice kome ba,itama Nnenna aje bucker in tayi ta zauna a kujera. Dr ne ya maida dubansa zuwa ga hannun Lahab Yana Masa ya jiki da mamaki yabi hannun da kallo sanna ya kalli karfen ganin ruwan Koh rabi baiyi ba gashi Kuma ya cire,ah ah Hassan ya haka yanaga an cire maka ruwan Kuma wace nurse ce ta cire? cikin dan basarwa Lahab yace"am nine na cire naje nayi wanka ne naci abinci" Meyasa ka cire sannan wani irin wanka kayi a irin wannan yanayin da kake ciki ai ba'ason kana wanka akai akai goge maka jiki za'a nayi ba wanka ba, muga hannu Koh ruwa ya shiga,ai saika bata Mana aiki. Mika Masa hannu Lahab yayi likitan ya dudduba sai fad'a yake Kamar bashi ya shigo da fara'a ba shidai Lahab shuru kawai yayi har likitan ya karasa masifar sa kafun ya maida Masa da ruwan tare da Karin wasu Alluran,ya rubuta musu magani ya basu akan su sayo,amsan takardan Nnenna tayi sannan ta koma ta zauna,Shima likitan fita yayi a dakin. Mikewa Nnenna tayi ta matso kusa da Lahab a hankali ta soma Masa magana"Lahab Lahab"ya jita Sarai amma yaki amsa wa haka kawai takejin haushin likitan ga masifar da ya gama surfa masa"kayi hakuri Lahab amma fa gaskiya Dr ya fad'a ya Kamata kabi ka'idar likita saika samu lafiya karfa ka manta tsagen kashine a hannunka kayi Wasa da hannun Nan sai kaga hannunka ya lalace" Wani irin juyowa Lahab yayi cikin haushi Jin abinda tace Wai hannunsa ya lalace"aiko wallahi hannuna inya lalace kece sula Ina zaman xamana tsabar mugunta daga Miki abin arziki saiki sa hannun Nan naki na samudawa ki kwade hannun na Saida Kashi ya tsage sannan kice min innayi Wasa da hannu na ya lalace"? Sake baki tayi tana kallon sa da mamaki tana Al'ajabin lamarin sa,dan Jan numfashi tayi kafun ta soma magana"toh shikenan"sai Kuma ta juya zata fita a dakin ganin hakan yasa sa tambayar ta"Ina zakije Kuma"? tsayawa tayi bata juyo ba"zanje wajen likitane ya taimaka min da waya na kawo maka ka Kira gidan ku ka sanar dasu halin da kake ciki kada hankalin su ya tashi kaga nima saina samu na koma gidan mu" "Zonan shine abinda Lahab yace Yana kallonta juyowa tayi ta dawo bakin gadon ta tsaya binta da Ido yayi sannan ya nuna ta da yatsa,"yanzun kina nufin a hakan Zaki fita kina yawo kina tallan jiki a cikin asibiti Maza na kallon ki Wai meke damunki ne baki da kayan da Zaki saya saina haukan Nan,bama wannan ba ce Miki nayi kije ki karbo min waya"? bin jikinta tayi da kallo sannan ta Kara kallon sa"meya samu kayan jikin nawa da kake cewa Ina tallan jiki,sannan maganar ka aikeni Koh baka aikeni ba duk zanje na amsa wayar na kawo maka"tana karasa maganar bata jira Mai zaice ba ta juya zata bar wajen, hannun sa Mai lafiyar Kuma ke d'auke da laidan ruwa yasa da karfi ya riko hannunta tare da ingizata har Saida tayi baya tagaltagal zata Fadi Kara Jan nata yayi Saida ta Fado akansa. Kallonsa tayi fuska a hade Kamar yanda Shima ke kallon ta"meyasa kake Wasa da lafiyarka ne"? baibata amsar tambayar da ta Masa ba sai wani tambayar da Shima ya jefo Mata"kingaji da jinyata"?girgiza Masa Kai tayi tana son tashi akansa don har lokacin baisa riga a jikinsa ba"amma meyasa kikeson na Kira Yan gidan mu sannan kema kikeson ki koma gidan ku"? "saboda hankalin Yan gidan ku ya kwanta na gidan mu ma ya kwanta" Maidata kwancen yayi daga kokarin tashin da take yasa bakin sa a kunnenta"kinsan wanene Ni"?ya tambaye ta a hankali. Ah ah bansani ba"toh bari kiji na fada miki Ni da kike ganin nan d'an tsohon minister ne sannan yayana babba,shararen dan kasuwa ne d'ayan Kuma gawurtancen soja ne dayan Kuma kusan gwannati ne,in Kika kuskura sukaji labarin kece Kika tsagamin Kashi burbudinki ma Y'an gidan ku bazasu gani ba bare gudan ki,gwara ki rufawa kanki asiri kiyi jinyata harna warke na koma da kafata hannuna sumul" wani kallo take bin fuskar sa dashi kafun a hankali tace"Ni kasan wacece"?dan murmushi yayi sanna yace"wacece ke"bude Baki tayi a hankali zata Yi magana sukaji gyaran murya a dakin alamu mutum ne........................ πŸ€ *by Ruqeenjala* πŸ€ *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki* Page 63&64 da Sauri Nnenna ta sauka akan Lahab tare da kallon kofar dakin, nurse in jiya ne a tsaye ta Kura musu Ido,kunya ne ya Kama Nnenna sosai akallah nurse in zata Kai shekara 30 shima dai Lahab tad'anji kunyan kad'an amma saiya basar ya lumshe idanunsa tare da juyawa dakin baya tare da lullube jikinsa da bedsheet,d'an gyaran murya nurse in tayi cikin mamaki don ita ta kasa gane menene tsakanin yaran Nan guda biyu wallahi,kun sai maganin da likita yace min ya rubuta maka? Nnenna ce ta bata amsa"ah ah yanzun ne zanje na Sayo"tana maganar tadau bucket na kayan tare da daukar pepar da card na Lahab ta juya zata tafi"Kinga zonan Labiba"Lahab ya Kirata dawowa tayi kanta a kasa don har lokacin nurse in na dakin tana had'a Masa magangunan sa"kidau abinci kici sanan banason ki fita a haka kizo ki zauna in ruwan ya Kare Zan fita da kaina na sayo" kallon Lahab nurse in tayi sannan ta kalli Nnenna kafun tayi magana"sister jeki dau breakfast naki kici ashe baki karya bama,Kai Kuma Hassan bai kamata ka fita ba kadai barin ta karya sai taje pharmacy in Naga ma harda Kaya takeson ta Shanya Koh? gyada Kai Nnenna tayi sannan ta aje bucket in ta zauna akan kujera ta jawo laidan abinci ta soma ci"gaskiya sister nafi dai son ta zauna in ninaje na sayo Kuma na Shanya kayan"? Kallon Lahab ta sake,saboda me bazata fita ba? "Kalli kayan jikinta fa a hakan takeson ta fita" dan zaro ido Nnenna tayi kafun tace"Kai Wai Ina ruwan ka da shigena ne Kam"? "Keee Ina ruwa na kikace?toh a kwai ruwana Kuma wallahi bazaki fita a hakan ba" Shuru Nnenna tayi tana cigaba dacin abincin ta murmushi nurse in tayi wallahi ita sosai take mamakin yaran Koh menene tsakanin su don basu Mata Kama da Yan uwa ba especially datazo taga Nnenna akan lahab hakan ya Kara tabbatar Mata ba Yan uwa bane,meyasa baka son ta fita a hakan? "Sister ki kalle kayan jikinta fa Kai Koh dan kwali ma babu" Juyawa nurse in tayi ta kalli Nnenna Jin abinda Lahab yace"toh ke meyasa Zaki fita haka bazaki sa dankwali da Kaya Mai kyau ba? Nnenna hadeye doyan dake bakinta tayi kafun ta bata amsa"nifa Christian ne bansan meyasa ya damu saina sa Kaya irin naku ba" Jin abinda Nnenna tace yasa nurse in dan waro idanunta tana kallon Nnenna dawalakin goro a miya ashe shiyasa tun jiya take yawo da gajeren sikit toh shi Kuma wannan a Ina yasamu Yar inyamuran Nan kauda tunanin tayi da Sauri tana sauraron abinda Lahab kecewa Nnenna"toh saiki fadamin a Ina akace ku ringa shigen banza donke ba musulma ba sai akace ki ringa yad'a alfasha"?kaga Hassan tsaya menene haka ya zaku zauna Kuma cecekuce akan addini Maison gyara ai baya fada Koh zuciya. Shuru Lahab yayi Kamar yanda Nnenna itama tayi duk Suna sauraron holon da nurse in ke musu,Kunga duk ku rufemin baki ke Kuma kina bibiye Masa bayan Kinga ba lafiya bane ma dashi kinsan Mai jinya da rawan Kai,amma fa abinda yace baiyi laifi ba bai Kamata ki fita a hakan ba nan Arewa ne Muna da al'adu da kunya,don haka ki tsaya bara naje na kawo Miki abaya ta danake zuwa da ita Ina daurawa akan uniform saiki sa da dankwalin sa ki fita ki Shanya kayan kije pharmacy duka,ba shikenan ba na raba gardaman? kallon Nnenna yayi sannan ya kalli nurse in"eh shikenan ki kawo Mata ta saka mungode sosai"ba kome Hassan Amma bara muji daga bakin ta Koh ta amince karma takurata?gyada Kai Nnenna tayi alamun itama ta amince,fita a dakin nurse tayi bata Jima ba sai gata ta dawo da abaya baki da igiyan sa sai dankwalin sa karba Nnenna tayi tana Mata godiya,ba kome tace sannan Kai Kuma Hassan ya Kamata ka rage b'uruntun Nan haka kaji da lafiyar hannun ka.? Insha Allah Zan kiyaye"fita tayi a dakin ta barsu itama Nnenna mikewa tayi bayan ta gama karyawa rigan ta zura a jikinta ta daura da igiya sai dan kwali data makala a kanta tadau bucket in kayan da card tayi waje. Bayan fitar Nnenna baccine ya d'auke Lahab bayan yasha magangunan da nurse ta aje Masa bacci ya dauke sa baima San lokacin da Nnenna ta dawo ba. da misalin karfe 8:20am na dare Lahab ne zaune akan gadon sa Yana cin gasheshen kaza da ya aike Nnenna ta soyo Masa bayan masifar da ya rufeta dashi akan bata iya kula da Mara lafiya ba ya za'ayi ya samu tsagen Kashi ace tun safe baici nama ba,shine fa ta fita ta sayo Masa gasheshen kaza biyu sai milk ita Kuma ta saiwa kanta fruit salad data gani a bakin asibitin don duk abinda ake sai dawa a restaurant na wajen akwai nama a ciki,kallon Nnenna yayi sannan ya kalli Naman sa so yake yace Mata tazo suci amma Kuma inya tuna abinda ta Masa sai yaji bazai bata ba daurewa kawai yayi ya yagi cinya ya Mika Mata,ganin bata masan yanayi ba yasa sa Mata magana da baki"ki karba ungo"? Kallon hannun nasa Mai lafiyar tayi sai Kuma tayi murmushi tare da mikewa d'aga Kan kujeran da take ta matso Kan gadon Zama tayi a bakin gadon tasa hannu ta amshi cinyar kaza dake hannun sa har lokacin, bakin sa ta nufa da naman,girgiza Mata Kai yayi tare da nuna Mata bakin ta watoh ita zataci"kaci samun kashinka ya koma yanda yake" Hararan ta yayi"ce Miki akai Zan iyya cinye kaji biyu ne duka d'ayan ma bazan iyya ci duka ba shiyasa na tsammiki" "Kaga Ni Kuma banacin nama"dan zaro ido yayi Yana kallonta"kina da ciwon hanta ne"?girgiza Masa Kai tayi. "Ciwon hanji"Nan ma girgiza Masa Kai tayi"toh Koh Naman kazane bakici bakinki ya Saba da naman karnuka da aladodi"?wani kallo ta Masa Jin kalar tambayar da ya Mata bata ma basa amsa ba ta Mike zata bar bakin gadon,da Sauri ya Kama hannunta,kallon hannunta daya kamata tayi ta kalli nasa sannan ta dago ta kalli fuskarsa fuska a hade "yau tun safe kina Kan kujera why not yanzun ki kwanta ki huta"? A Ina Zan kwanta na hutan"? Nuna Mata gadon yayi"toh Kai Kuma ka kwanta a ina,"gefen gadon ya sake nuna Mata"oh so kake mu kwana tare kenan koh"?eh haka nake nufi" fizge hannunta tayi ta rike kwankwaso tana kallon sa kafun ta soma magana"d'azun da safe a dakin nan ka Kare min tanadi kace Ina yawo ba Kaya Mai kyau gashi Kai Kuma yanzun kana cewa nazo mu kwanta? nima bari na tambaye ka a addinin naku ance ku kwana da mace gado daya ne ba aure"? Kama baki yayi Yana kallonta sai Kuma yace"ah ah "toh don haka in kanason na kwanta na hutan ka amshi waya ka Kira gidan ku Koh ka ban address na gidan kun tunda kace a unguwan mu kake,sai yanzun naje na sanar kaga nima saina samu na koma gida yau kwana daya kenan ban bawa Kiki na abinci ba Ina tsoron Kar yunwa yasa ta Kama dabbobi taci fa"? Komawa yayi ya kwanta Yana mita"aiko saidai kiyita kwanan kujera karki huta in indai nine Zan Kira Yan gidan mu Koh aikan ki tunda dai ke Kika karyani ya zama Miki dole kiyi jinyata,Kiki Kuma inyaga dama yaci mutane ma ba dabbobi ba"komawa tayi ta zauna taci gaba dashan fruits nata har karfe 11 idanun su dukan su a bude basuyi bacci ba Nnenna Kam gabaki d'aya taji bayanta da hips nata har wani kamawa suke ta gaji da zaman kujerar bata samun isheshen bacci Mai dadi akai, gashi bata San kasuwa ba da sai taje gobe tasai taburma da filo,ga tunanin Kiki da take da halinda yake ciki,amma bata damu da Yan gidan su ba tasan babu Mai damuwa da rashin ta tunda dady baya Nan. 12:11am ta Mike a hankali ganin Lahab ya sake sosai gashi sai sauke numfashi yake Kamar Mai bacci,alhalin Kuma idanunsa ras suke ba bacci yake ba,leka fuskarsa tayi ganin idanunsa a kulle sai sauke numfashi yake a hankali hannu tasa ta kashe wutan dakin a hankali cikin Sand'a ta hau Kan gadon kwantawa tayi a bayan sa wajen dan filin da ya rage hannunta ta nade tayi filo dashi Koh minutes 10 batayi ba bacci ya dauke ta,mikewa zaune Lahab yayi duk da duhune amma Yana kallon ta filon sa ya matsar kanta a hankali ya d'aga Kan ya daura akan filon tare da gyara Mata hannayen ta shima kwanciya yayi yasa kansa a filon ya Zamanto dukan su biyu ke kwance akai, Addu'an bacci yayi baijima ba bacci yayi gaba dashi. ****************** Nabeel bai zarce Koh Ina ba sai gidan su Ade yana Isa gidan hannu yasa ya kwankwasa kofar Mai gadi ne yazo ya bude ganin shine yace bafa zai bude Masa ba don papa yace karya sake bude Masa shida Lahab,ganin da gaske bazai buden ba yasa sa rokonsa akan Yama Adewale magana Yana waje yanason magana dashi,daker dai Mai gadin ya yarda tare da nufar cikin gidan. Bai wani Jima ba saiga baigadin sai Ade daken binsa a baya bude kofar yayi cikin fara'a,ah ah shegen yaka saya a waje kashigo Mana Yana maganar Yana wangale Masa kofar shiga gidan,Nabeel Kam sosai ya kurawa Adewale Ido ganin yanda yayi mugun rama daga gani kasan baida lafiya ne,ah ah Adewale Nan ma ya Isa basai na shigo ba. Kama Isa kazo mu Shiga kawai guy? dan Jim Nabeel yayi bawai gidan su Adewale bane baison shiga ah ah yau weekend ne taima baban sa na gida yaje yaci Masa mutunci a banza don baida matsala da maman Adewale,no Ade Nan ma is ok daman nazo na tambayeka labarin Lahab ne nayi missing nasa kwana biyun nan Koh na Kira wayarsa baya shiga shine nace bara nazo wajen ka Koh zamuje gidan ya jafar mu dubo sa amma Naga kaima Kamar Bakajin dadi ba ma amma Koh notice babu nazo na dubaka. Sai murmushi Ade keyi Yana sauraron zuban da Nabeel ke Masa ba gaggautawa sai da ya bari yakai Aya kafun yace,toh yanzun dai wanne Zan amsa a cikin tambayar Nan naka? Koh ma wanne ka Fara amsa wa. Ok toh nidai babu abinda ke damuna maganan Lahab Kuma wallahi koni banjin labarin sa jiya ma naje gidan su aka cemin Wai ba'amasan Inda yake ba wallahi Lahab zai kashe Yan gidansu duk ya d'aga musu hankali Kuma Nina tabbatar Lahab ba b'ata yayi ba iyya shegene kawai ke damun sa. Uhmmm lallai Kam amma kana nufin ba'ama San Inda Lahab yake ba kenan? Kwarai ma kuwa Nabeel hakan nake nufi. toh yanzun gidan wa Lahab yashiga kenan? Wallahu alamu Ina Zan sani Nabeel Kallon sa Nabeel yayi Jin yace wallahu alamu watoh Koh Yaya Christian ya zauna a cikin musulmai sai ya kwaikwaye maganar bakin su,ok bara na wuce Allah ya sauwaka don nasan dai tabbas baka da lafiya kawai boyewa kake. Yanzun bazaka zo mu shiga ba? No Ni bazan shigaba kaga ma tafiya ta sai anjima,Nabeel yace ya Kama tafiya abinsa. Toh ka gaida Inna. toh zataji,komawa Adewale yayi cikin gida su. MAFARKI................. Assalamu Alaikum wani mutumine kyakkyawa fari tas sanye da farin Kaya hannunsa d'auke da Sanda Yana dogarawa yayi Masa sallama. Waalaikumu Salam ya amsa Masa sallaman nasa daga zaunen da yake tare da d'aga Ido zai kalli tsohon amma Ina ya gaggara saboda hasken dake kashe Masa idanun. bazaka iyya kallona ba Hassan tsohon yace Yana wani irin murmushi Mai dan Sauti. Sosai zuciyar Sa ya tsinke har Saida ya dafe kan kahon zuciyar tare da kokarin d'agowa daga duke da yake Yana son tashi tsaye Kamar yanda tsohon yake a tsaye amma Ina ya kasa ji yayi gabaki d'aya jikinsa ya wani irin daskarewa waje daya sosai yaji wani tsoro ya mamaye Masa zuciya. Bazaka iyya mikewa ba saidai wani ikon Allah Hassan ka kwantar da hankalin ka bazan cutar da kaiba,magana nake so nayi dakai. Jikinsa na rawa ya daina yunkurin tashi daga wajen sai dan dago kansa da yayi ya kalli gaban sa katon kogi ne fari tass Mai d'auke da ruwan koramu masu gudana daaga cikin dutse Mai tsawon gaske hannu ya Mika a hankali zaisa a cikin ruwan kogin saboda tsananin sha'awa daya basa yaji an hanka d'asa tare da amon murya ana Masa gargadin kada ya kuskura ya taba ruwan,ja da baya yayi ganin ruwan ya rikide daga fari zuwa ja jazer dutsen dake wajen sun koma bakake. Hassan kaga kogin Nan?tsohon dake bayan sa har yanzun ya fada. "Eh na gani" toh haka kaddarar ka take abu Mai kyau zaka gani ka zata abin sone amma fa ka sani kaddarar kace kaddarar kace tana tinkaro ka tabbas abinda Allah ya tsara dole ne saiya faru amma Ina Mai baka shawara akan duk halin da zaka tsinci kanka Nan gaba kayi hakuri ka dogara da Allah kasawa ranka kome jarabawa ne daga mahallincin mu,kayi kokarin ganin ka cinye jarabawar ka insha Allah Allah zai musanya maka da Mafi Alkhari akwai zazzafar kaddara a rayuwar ka haka zalika akwai kyakkaywar sakamako amma sai kayi hakuri sai kayi hakuri kayi hakuri Hassan.......ka zamo Mai tawakkali.....Allah na tare da Masu hakuriiiiiii...............wani irin zabura Lahab yayi ya mike zaune daga mummunan mafarkin dayayi duk zufa ya jika Masa jiki. Nnenna dake zaune tun d'azun a kansa tana binsa da kallo ganin sai wani jujjuyawa yake da kansa ga zufa na sassafo Masa,saurin Mika hannunta tayi ta dafa sa ganin ya mike zaune a razane cikin damuwa take tambayarsa"menene mafarki kayi ne Mika gani a mafarkin naka"?kasa bata amsa yayi sai"innalilahi wa'inna'ilahu raji'un dayake ta maimaitawa,itama mikewa tayi da Sauri ta nufi wajen socket ta kunna wutan dakin tare dakai dubanta garesa ganin ya mike da Sauri zai nufi kofa,da gudu tasha gaban sa tare da nuna agogon bango dake makale a dakin"Lahab ka duba lokaci karfe 1:30am na dare Ina zakaje Kuma"? "gidan mu zanje bansan meke faruwa dani ba a Y'an kwanakin Nan mummunan mafarki nake zanje wajen Mami na"ganin Kamar baya hayyacinsa yasa Nnenna kin basa hanya sai rungumarsa da tayi tabaya ta soma magana"ka kwantar da hankalin ka babu abinda zai sameka sai Rubuceccen Al'amari wannan bani da iko a kansa amma bazan barka ka fita a daren nan ba. Fizge jikinsa yayi da Sauri ya nufi kof.............. πŸ€ *by Ruqeenjalal* πŸ€ *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki* Page 65&66 Nufar kofar toilet yayi ya bude ya shiga,komawa Kan gadon Nnenna tayi ta zuba tagumi,Lahab na shiga wanke fuskar sa yayi da ruwa sannan ya zauna akan toilet sit gabaki d'aya damuwa ne shimfide a ransa tunda yake bai taba ire-iren mafarkan Nan ba sai a 'Yan kwanakin Nan haka zalika yasan mafarki ba gaskiya bane amma mafarkin yau ya matukar rud'asa ya Kuma tsaya Masa a wuya,shiru kawai yayi yayi Jim dashi a zaune shi bai fita ba Shi baiyi kome ba. Nnenna kallon agogo tayi sannan ta Mike ta nufi kofar ban dakin tasa hannu tadan tura kofar Jin a bude yasa ta dakata wa kafun ta soma magana"Lahab lafiya har yanzun baka fito ba"shiru bai amsa ba itama tura kofar tayi ta leko cikin ban dakin Allah ma ya sota akwai wuta,har lokacin Yana zaune shuru,takowa tayi ta shigo ciki a hankali take tafiya Harta iso kusa dashi hannu tasa a hankali ta kamo hannun sa lafiyayyen"Lahab meke faruwa mafarkin me kayi"? Kallon ta yayi sai Kuma yaji baison sanar da kowa abinda yake mafarki especially na yau,mikewa tsaye yayi har lokacin hannunta na nasa ya nufi fita a kofar binsa tayi a baya har Suka fitoh Zama yayi a bakin gado tare da kallon ta ya nuna Mata gefen sa gyada Kai tayi ba musu ta hau ta kwanta,kashe wutar yayi shima ya kwanta gabaki dayan su shiru sukayi amma kowa yasan dan uwansa baiyi bacci ba. Har asuba Basu rumtsa ba kowa da abinda ya damesa Wanda rashin baccin nasu lokaci daya ya saukarwa da Lahab da zazzabi a jiki,da asuba ma da taimakon ta ya samu yayi alwala ta shimfida Masa sallaya yayi sallah Yana idar da sallan Dr ya shigo ya daura Masa ruwa da Alluran bacci ganin jikin nasa yayi zafi ga rashin bacci yayi musu fad'a sosai ,bacci ne ya d'auke sa itama Nnenna bacci tayi akan kujera. ******************* a gidan su Nnenna bayan dady ya dawo da yamma har dare baiga wullawan Nnenna ba gashi dai weekend ne bare ace taje school kasa hakuri yayi ya tambaye mom anan take ce masa tun jiya Friday Suka nemi Nnenna Suka rasa ,Sarah taje school nasu akace taje amma tashi da ita. Aiko ranan mom taga bala'in Dad Wanda bata taba gani ba ta Inda yake shiga batanan yake fita ba sai cewa take daman bata son Nnenna taimama ita ta b'atar da ita Wasa-Wasa fada ya zamo na manya station dad yaje yakai kara Yar d'an uwarsa bakuwa ta bata,sun karbi hoton ta da suna aka Kai gidan TV Koh Allah zaisa wani ya ganta tunda ance bakuwa ce kilan bata tayi Abraham ma daya dawo daga Lagos yaji wannan labari hankalin sa ya tashi sosai. Nabeel na barin gidan su Adewale shagon dinkin su ya nufa da sallama ya shiga shagon ogan sane da sauran yaran shagon Suka amsa masa Suna binsa da kallo rabon shi da shagon har sun manta sai dai yazo da abokan sa suyita hira,Zama yayi akan keken sa bayan yadau wani tsumma ya kakkabe kuran dake Kai ganin haka yasa ogan sa mikewa tsaye ya Soma magana,kaga Nabeel Mike tsaye bazaiyu kazo ka zauna a shago ba don nasa d'ayan biyu ne wata kil watace zata kawo maka dinki shiyasa kazo ka zauna watoh ka karbi kayan jama'a ka yanke zuwa shago daga karshe yara suzo Suna min rashin kunya a shago tare dajan Allah ya isa,don Kai Allah ya isa bai dameka ba don hakan Mike kabar shagon Nan. Sunkuyar da Kai Nabeel yayi,don allah oga kayi hakuri wallahi dinki ne zanyi daman akwai wasu Kaya da nake son dinkawa ne. Wa???badai a shagon Nan ba sai dai kadau keken naka ka tafi gidan ku dashi kaje ka dinka acan bazan iyya ma halinka ba Nabeel. don girman Allah kayi hakuri oga wallahi dinki zanyi kudi nake su a Yan kwanakin Nan Inna bar shago Ina Zan samu tsoffen customers nawa. Kai Nabeel wani tsofen customer Kuma bayan bana tunanin akwai Wanda xai sake baka dinki indai yasan ka kayan jama'a guda nawa ne a wajen ka na Allah ya isa?watoh kana son kudi Koh,shiyasa ka dawo ka yago kudin mutane? Haushi ne ya tsoma Kama Nabeel hakan yasa sa mikewa ya fita a shagon baijima ba sai gasa da Mai bairo Kan keken sa ya d'auka da bodyn keken duka yasa a bairo wasu turaman zanin daya aje a shagon duk ya tattara ya loda a Keke,baibi takan maganan da ogan nasa yake Masa ba ya Soma tafiya Mai bairo na binsa a baya. Suna isowa kofar gidan su wangale kofar yayi Mai bairo ya shigo da keken cikin gida,mubeena dake zaune ta tasa tuwo a gaba amma bataci ba don kwata kwata taji bata sha'awan cin kome musamman data ji labarin b'atan Lahab don zuwa lokacin labari ya guma unguwan kwana uku ba'a gansa ba,sai Inna dake zaune tana tatan kamu,dukan su da Ido Suka bi Nabeel har ya shigo tsakar gidan sauke keken sukayi damai bairon kudi ya zaro naira 30 ya mikawa Mai bairon. gaskiya abokina talatin yayi kadan kadai ban 50,kallon sa Nabeel yayi a karkace cikin dan Jin haushi daman ya gama kuluwa da abinda ogan sa ya Masa,Kai da Allah karba ka Ware wani irin na baka 50 daga shagon mu Nan nan kasan layin Nan xaka wani CE na baka 50 sata kake Koh neman kudi kajimin almajiri da iyayi. ran Alamajirin ne ya baci shima cikin zafin yace,kaga malam ban 50 na ai hakki nane in Kuma bazaka bani ba na barka da Allah. Inka fasa jamin Allah ya isa Kai shege ne Nabeel yace Yana maida 30 in cikin aljuhun sa,da Sauri Inna ta Mike ganin Mai bairon ya juya jiki a sanyaye ya nufi kofa,Kai yaro tsaya Inna tace tsayawan yayi ita Kuma Inna matsowa kusa da Nabeel tayi tasa hannu a aljuhun sa ta zaro kudi da Sauri shima yasa hannu Yana kokarin Kama hannunta amma Ina ta rigasa d'auka,kudine akalla zai Kai 5k gayan 1k da 200 100 duk a Ciki,naira 100 ta d'auka ta mikawa Mai bairon ihu Nabeel ya sake Yana wallahi Inna ki ban kudina bana so wallahi Inna karki basa dari na,mikawa Mai bairon tayi da Sauri shima ya karba tare dajan bairon sa da gudu yabar gidan cikin Jin dadi. Zama Nabeel yayi a Kan dutsen dake kasan wajen Yana ma Inna wani kallo tare da Mika Mata hannu ba tare da yayi magana ba,itama dongora masa sauran kudinsa tayi tana surutu,wallahi Nabeel karin ga Jin tsoron Allah Kai Koh tsoron ace an barka da Allah bakaji Koh a jikinka indai akan Allah ya isa ne, Wai a Ina ka Sami wannan mugun haline nacin abin Allah ya isa? Mtwwwss wallahi Inna ki daina min irin wannan banason sheshege ke babu halin Kiga Ina magana da mutane sai kinsa baki? Nasa Nabeel nace nasa don kaniyar ka Ina fa rabaka da abin Allah ya isa don wallahi wata rana zakaci abinda zai dameka,Oho dai yanzun ba wannan ba menene yasa ka dauko keken ka ka dawo dashi cikin gida Koh mutuwar zuciyar ce yasa ka dawo dashi gida tabbacin ma babu cigaban zuwa shago kenan Koh? Kinga Inna nifa ba haka bane abinda yasa Kika ganni ogana ne ya sallameni a shago Kuma fa Inna wallahi tallahi aiki najeyi kinsan nace Miki daga yanzun Ni zanna biyawa Aunty kudin makaranta amma wannan d'an wahalan malam sadam(ogan sa). Kama baki Inna tayi Jin Nabeel ya Kira ogan sa da wahalalle,amma in ana Neman Mara kunya in an sameka an gama yanzun Koh tsoron Allah bakaji kake ganin tsabar idon rana kace wa sadam wahalalle lallai nabeel? Nidai duk yanzun abar maganan nan so nake kije ki basa hakuri yayi hakuri na koma shagon kinji inna ta. Hararan sa tayi kafun tayi magana,Kai Nabeel babu Inda zani bakace Masa dan wahala ba sai ka nemi uwar da zataje ta basa hakuri tana karasa maganar ta nufi bucket in kamunta ta cigaba da tatanta bata ma kara bi ta kansa ba,shima mikewa yayi ya gurgura keken nasa da ker zuwa cikin dakin sa gudun Kar azo ayi ruwan dare,mubeena Kam har lokacin tana zaune a taburma batace musu komai ba. washe gari da sassafe mubeena na tashi ta kammala aikace aikacen gidan na safe Koko Inna ta dama musu Nabeel ya sayo musu kosai Suka karya dashi kayan wanki mubeena ta fitar duk da jikin nata babu dadi amma haka ta daure take aikace aikace gudun Kar tasa dan uwanta da Inna a damuwa tunda suma basa iyya sakewa mundin tana cikin damuwa,Kuma hakan ya musu dadi dukan su don Nabeel na tashi bayan sun karya keken sa ya fitar tare da wasu zanuwan daya saya musu kayan aiki baiyi dinkin ba ya dauko Yana dinkawa ga mubeena a gefen rijiya tana dauraya yayin da Inna ke kwance a taburma tana fifita da mafici a hannunta. *********************** da misalin karfe 8 na safe Nnenna ce ta fitoh daga ban daki ta canja Kaya bayan tayi wanka ta wanke kayan jikinta,rike bucket in tayi ta fita a dakin,tsakar asibitin ta fitoh zuwa wajen garden Inda ta Shanya kayan su na jiya cire kayayyakin tayi ta shanja sabo ninkesu tayi ta dawo dakinta aje,har lokacin Lahab bacci yake bai farka ba kudi ta d'auka ta fitoh bakin asibiti takeAway ta musu,mutumin dake kusa da shagon Saida abincin sosai yake binta da kallo sai Kuma ya zaro wayarsa da Sauri ya Kara kallon screen in ganin ta tsallako titi zata shiga asibiti yasa sa binta a baya shima har yaga dakin da ta shiga sai Kuma ya fitoh da Sauri ya tare Keke napep yahau. Nnenna na shiga dakin Γ je abincin tayi ganin Lahab zaune matsowa tayi kusa dashi tana kallon sa gabaki d'aya ya sauya hatta fuskarsa ta kumbura hannu tasa ta taba goshin sa shidai sai Ido dayake ta binta dashi,da Sauri ta dau brush nasa tasa maclen "kazo muje kayi brush sai ka samu kaci abinci kasha magani time na wucewa"mikewa yayi Kamar yanda tace a hankali ya nufi bandakin binsa tayi a baya Suna shiga ta basa brush in yayi ta goge Masa jiki tare da fita ta barsa ya karasa sauran da kansa. Zaune suke Suna cin abinci kowa da tunanin da yake bare Lahab dake ta Sakuran abinci don shi gabaki d'aya yau Innan so yake ya gansa kusa da mamin sa yaji kewanta da son ganinta ya samu ya fada Mata abinda ke damunsa Koh zaiji sauki a ransa,aje spoon in hannunsa yayi ya kalleta"Labiba ki karbo min Aron wayan na Kira gidan mu. ba musu ta Mike tsaye dan kwalin abayan nurse in ta d'auka ta yafa zata fita a dakin sai Kuma ta tsaya Jin abinda Lahab yace"karki karbomin na Dr Nan ki karbomin na nurse in dake yawan shigowan Nan"? Ok tace ta fita a dakin bata wani Jima sosai ba sai gata ta dawo da rantsatsen waya Mai kyau touch screen Mika ma Lahab tayi ta koma ta zauna,jujuya wayan yayi a hannunsa Yana tunanin number wa zai Kira yaso yasa na mamin sa ya kirata amma daya tuna yanda Suka rabu akan maganar farida sai yaji shakkan kiranta,dan murmushi yayi ya Soma sanya number dan uwansa ya Kara a kunne tare dakai dubansa ga Nnenna dake cin abinci batama kallon direction nasa. ******************** Rahab bayan sunci abincin dare da mustaph kwanciya sukayi tun mustapha na Masa Hira har bacci yadau mustapha Rahab Kam na kwance idanunsa biyu abinda ke damunsa ya hanasa bacci Koh Ina Lahab ya shiga ga Kuma abinda ya faru a gidan su abin yazo ya damesa Sam baiji dadin abinda Yama muzammil ba duk da muzammil nacin zalinsu Amma fa soyayyar sa ta gaskiya da gaskiya ne duk Wanda zakayi ba daidai ba ya hukunta ka yagama maka kome amma shi ransa ne ya baci Sam baijin dadin abinda yayan NASA kema mamin sa. Sai can dare ya samu bacci ya dauketa,washe gari da safe salamatu ta Gama musu dumamen tuwon nasara miyan karkashi gashi daman Rahab baison miyan yauki a rayuwar sa tada Masa da zuciya yake dayake salamatu tasan halinsa tun Yana yaro yasa ta aikan mustapha ya sayo Masa dan wake,ya kawo Masa Rahab yaso yakici amma yasan bazasu ji Dadi ba don tun jiya sai rawan kafa suke dashi Suna haba-haba dashi suke yasan in yakicin abincin su baza suji Dadi ba Sam hakan yasa sa karban dan waken yayi yaci sosai Suna Gama karyawa yabi mustapha garejen su Zama yayi Yana kallon yanda suke ta aikace aikacen su na Neman halak sosai yaji zuciyarsa ta tsinke daman haka talakawa suke Shan wahala lallai Allah ya musu gata Koh Basu da mahaifi a raye sun samu gata zasuci zasu Sha sutura Mai kyau makwanci Mai kyau,amma ga wasu da iyayen ma suke nema wa kansu abinda zasu sa a bakin salati tagumi yayi Yana bin jama'an wajen da Ido daga dai ka gansa kaga yaron masu hali Wanda bai Saba da wajaje irin wannan ba. Wayar sane tayi Kara hannu yasa a Aljuhu ya zaro wayar tasa kallon number yayi ganin new number yasa sa kin dagawa ya maida wayar aljuhu. tsaki Lahab yaja ganin ya jerawa Rahab har 3 miss call Amma yaki dagawa"Kai Allah ya kyauta maka ace mutum bazai dauki Sabon layi ba Kamar wani dan film sai kuma ya tura Masa sako Kamar hauka"ka dau wayar Nine" Jin Karan shigowar sako yasa Rahab budewa"ka dau wayar Nine"sosai ya kurawa message in Ido Yana nazari da Sauri Kuma ya Kira layin,dan murmushin Lahab yayi ganin Rahab ya kira, picking in call in yayi yasa a kunne. Assalamu Alaikum,Rahab yace kamar Mai son tabbatar da abinda yake zargi,shuru Lahab yayi bai amsa ba,mikewa Rahab yayi Jin shuru ba'a amsa ba yasan babu Mai Masa wannan abin sai abokin haihuwar sa, Lahab nasan Kaine Kaine Dan Allah kayi magana Lahab? "Rahab...... Lahab ya Kira sunan sa ta cikin wayan,jikin Rahab har rawa yake ya Soma magana,laaa dan uwa Kaine Ina ka shiga kasan tashin hankalin da ka samu a ciki kuwa kana Ina ne? "Ina makama hospital"Lahab ya basa amsa. What??? hospital fa kace Lahab meya faru dakai meya Kika hospital Kuma na shiga uku. "Kaga ka kwantar da hankalin ka ba wani abuba ne tsagen Kashi na samu shekaran jiya" Waro Ido Lahab yayi Wanda yasa mustapha dake gefe Yana gyaran mota ya taso ya taho gare sa,Jin Rahab na cewa,eehh kace tsagen Kashi ka samu innalilahi wa'inna'ilahu raji'un. Katse wayar Lahab yayi Jin dogon salati da rahab ke zabgawa,ta bangaren rahab Kam tambayar sa mustapha ya Fara meke faruwa ne rahab meya samu Lahab in amma Ina lalubo number Mami yayi ya Kira tafiya ya tsoma Jin number nata na ringing,sai Kuma yaji ta d'auka sai muryar ta tana sallama........ πŸ€ *By Ruqeenjalal* πŸ€ *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki* Page 67&68 Mami dake zaune a tsakar compound na gidan ta ita da yaranta da mijinta Suna buga basketball gabaki dayansu sanye suke da sports wear nasu,yaranta da Alhaji ne suke ball itakam zaune take a gefe Kan cafet Inda ta shimfid'a tana amsa wayar Rahab,sai Yusuf dake zaune akan keken sa na yara,mikewa tsaye tayi cikin zumudi tace, na'am Rahab meka ce?ta bangaren Rahab sake maimaita mata yayi,Mami Lahab ya kirani. Wai meya ce maka daya kira kan,Wai Ina yake? Yana hospital Mami ya samu tsagan kashi ne. Subhanallah tsagen Kashi Kuma garin yaya,tukunna ma kana Ina ne Kai in yanzun? Ina garejin su mustapha ne yanzun Zan wuce asibitin. da Sauri Mami ta dakatar dashi,karka hau Keke ka jirani ganinan zuwa yanzun zanzo na d'auke ka a wajen karka tafi ka jirani bata jira Mai zaice ba ta katse wayar tare da nufar flat nasu,bata ma sanar da Alhaji ba dama hankalin su baya kanta kwata kwata Yana ga kwallo da suke bugawa. tana shiga cikin falon sai Kuma ta tuna bara ta sanar da yayan su babba(Abbu) number sa ta Kira ta Kara a kunne Yana dagawa Suka gaisa tare da sanar dashi Lahab na asibiti shima sosai yanuna alhinin sa tare da cewa shima gashinan zuwa,wanka Mami tayi ta sauya Kaya daga wando da rigan jikinta zuwa atamfa riga da siket,hijab nata ta jawo ta rufa tare da d'aukar key in mota da Sauri ta fitoh,dai dai lokacin Alhaji sulaiman Suka sakaita da ball in Suna hutawa dukan su akan cafet Inda ta tashi,nufosu tayi tana magana,Abbin mahraz zani hospital yanzun yanzun Rahab ya kirani Lahab na asibiti ba lafiya? Subhanallah meke damunsa haka mamin yara?ya tambaye ta. Wallahi Wai ya samu tsagen Kashi bazai wuce a filin ball bane. toh ai dakin tsaya kin jiramu saimu shiga mu kimtsa mu tafi duka da yaran mu duba jikin nasa? ah ah bazan iyya jiranku ba kudaiyi hakuri in yaso kuje ku dubasa da yamma Koh da daddare bazan dawo da wuri ba mahraz ya dafa muku spaghetti tana basa amsan ta juya zata nufi parking space nasu,ihu Yusuf ya kurma ganin mamin sa da hijab Kuma ta nufi hanyar waje,kin sauraron sa tayi don tasan daga zaran ta fita a gidan zaiyi shuru ganin tane yasa yake kuka,Kinga dawo kizo ki d'auke sa don Naga kwanan Nan kin tsiri fita kina barin sa a gida Alhaji yace Yana mamakin irin sonda Amina kewa yaranta akan yaranta bata da kawaici especially tagwayen ta don sonda take musu Bata ma yaransa shi. ba musu tabi umurnin mijinta dawowa tayi ta karbi Yusuf in tare da bude motarta ta shiga ciki aje Yusuf tayi a sit taja tabar gidan hanyar garejin su mustapha ta nufa. tsaye yake a bakin titin garejin Yana bin mototin dake tahowa daga nesa yayin da mustapha ke zaune a cikin garejin nasu ya sauya Kaya daga na aiki zuwa Mai kyau shima zaibi Rahab asibitin su dubo Lahab,haka zalika shima ya Kira baban sa ya sanar dashi asibitin da Lahab ke. tun daga nesa Rahab ya hango motan mamin sa fadada murmushin sa yayi Yana daga hannu Kamar wani Bako, murmushi mustapha yayi d'aga cikin garejin ya Masa magana,toh ka hango goggo Aminan kenan?gyada Masa Kai kawai Rahab yayi, parking Mami tayi da Sauri Rahab ya matsa kusa da motar ya bude gaba yadau Yusuf ya shiga ya zauna ya daurasa akan cinyarta Yana Masa Wasa mustapha ma ya bude bayan motar ya shiga rufewa yayi Mami taja motar. Ina kwana Goggo Amina? Lafiya mustapha ya aiki? Mungode Allah,ya Bata amsa kallon Rahab tayi Kai Kuma bazaka gaidani bane Koh me? murmushi yayi Kai Mami na wallahi zumudi ne kiyi hakuri Ina kwana? Shuru tayi bata amsa ba shima bai sake cewa kome ba Suka cigaba da tafiya. ***************** Abbu Suna gama waya da Mami ya mike yad'au Kaya ya sanya a jikinsa fita yayi a dakin tare da shiga dakin Addayiya da sallama,amsa Masa tayi bayan ya zauna yake sanar da ita Lahab na asibiti,sosai ta tsorata tana salati tare da daukar hijab nata have Sunnah tasa tare da gyele ta yafa a kafada tana Masa magana,tashi Maza umaru muje mu duba sa muga ya jikin nasa Allah sarki dan maraya Koh garin yaya hakan ya faru ne? Abbu daya mike tsaye yace Mata,nima wallahi bansani ba shiyasa nake son naje naji yanzun-yanzun naji garin yaya,kinsan nima uwan nasu ce ta kirani tace min itama dan uwansa ne ya kirasa. Muje-muje Maza muga ya jikin nasa fita sukayi babban falo yaran ne zaune da iyayen su mata dayake ranan hutune Kuma sunyi baccin su harsun gaji suka fiffito falo Suka zauna,da mamaki suke kallon Abbu da Addayiya ganin su cikin Shirin fita kasa hakuri mamu tayi ta tambaye Abbu,lafiya kuwa Abbu na ganku haka cikin Shirin fita? Koh amsa Mata Abbu baiyi ba don har yanzun haushin ta yakeji na abinda ya faru jiya,Uzaifa ne ya Kara magana ganin baban nasu da Addayiya na kokarin fita a falon, Addayiya sai ina? Sai uwarka Kai asuwa da zan fita kace Ina zani? Haba Addayiya sofa nake nima na biku don nasan fita da Abbu Alkhari ne yayi Mata dadin baki don ta samu ta fad'a musu,Abbu Kam Harya fita a falon Addayiya ta washe baki,Kai Uzaifa Maza zo mu tafi dan albarka bappan ka Lahab ne Yana asibiti ba lafiya zamuje,ai Jin haka yasa muneera mikewa da Sauri daman akwai gyale a jikinta takalmi kawai ta d'auka tabi bayan Uzaifa dayabi Addayiya a baya da Sauri. Mikewa umaima tayi da dankwali a hannunta zata dau hijab nata akan kujera da niyar binsu daka mata tsawa mamu tayi,uwar Y'an iyayi sai Kuma Ina Zaki? Jiki a sanyaye tace,mamu Zan bisu muje duba Uncle ne? Uban kine shi ba uncle ba Yar iska Mara zuciya watoh abinda uwarsa tamin jiya harkin manta Zaki bisu kuje toh babu Inda zaku daga ke har Anwar da Shareef in,tsaki ummu taja ta Mike ta shiga dakin ta tad'au mayafinta tazo ta wucesu a falon tabi bayan mijinta da yaranta tabar na mamu a falon Wanda kallo daya zaka musu kasan suna son zuwa babu yanda Suka iyya ne,munafukar banza zai Kare a tsuliyan ku keda yaran naki ai indai Amina ne Muna Nan dake a gidan Nan Zangan ku a Rana kina binta a gindi a gindi babu uwarda take tsinana Maki,ita dai ummu Koh takanta bata biba ta fitoh compound lokacin Abbu da su muneera duk sun cika motar sa harzasu fita a gate sai gata ta fito tana d'ago musu hannu tsaya sukayi ta bude gaba ganin uzaifa yasata rufewa ta bude baya tare da Zama kusa da Addayiya don muneera ce ta gefen kofa Addayiya a tsakiya itama ta zauna a gefen Addayiya Abbu yaja motar Suka bargidan. ******************** Adewale yau tunda ya tashi da safe bai Fara karyawa da kome ba sai da bala'in papan sa ta Inda yake shiga ba tanan yake fita ba daga yace Masa ya shirya zasu tafi Church,shine Adewale yace bazashi ba baijin dadi,shikenan papa ya Soma ruwan bala'i daman baison zuwa church yaran hausa people na zugasa yabar addinin sa,Jin abinda yace yasa Adewale kasa hakuri ya tamka Masa,haba papa wannan wani irin magana ne haka Ni tunda nake da abokai na basu taba zagin addinina ba Koh suce wani Abu a ciki ba daidai ba Koh na daina. Rufemin baki Wawa kawai stupid kawai Wanda baisan ciwon kansa ba yanzun ace duk yaran Christian basu isheka abota ba saika had'a da Yan iskan yaran? Komawa Ade yayi bakin gado ya zauna papa na tsaye Yana jaddada Masa ya tashi ya shirya amma Koh gixau baiyi ba hakan shiya Kara kular da papa Harya sashi mikewa ya fizgo Bell in Ade dake yashe a kasan d'akin ya nufesa ai da gudu Ade ya mike ya rufi kofar bayangida binsa papan yayi tsabar rudewa kasa bude kofar yayi ganin papa ya kusa kamasa yasa sa nufar kofar dakin da gudu ya bude ya falfala a guje yayi falo,maman sa ce dake kwashe kwanuka a dinning ta nufosa tana tambayar sa lafiya? tsayawa yayi ya tsoma magana idanunsa nakan kofar dakin sa ganin har lokacin papa bai fito bama,mama nifa kaina na ciwo bazan iyya zuwa church ba this week gaskiya? uhmmm haba Ade Kai duk weekend saika kirkiro abinda zai hanaka zuwa church kafasan dole ran papan ka ya baci Yana matsayin pastor ace d'ansa guda bai zuwa church abin zai Zama abin magana Koh ana cewa kafi karfinsa hakan baida kyau ka tashi kaje ka shirya shap-shap kazo mu tafi? Zama yayi akan kujeran ganin papa ya fitoh Yana maida numfashin gudun da yayi daga dakin Ade zuwa falon,nifa kaina ciwo yake fa mama? duk naji amma ka tashi haka zaka daure mu tafi abinda by 12:00 ma zamu tashi. Kai mama har 12:00 Ina zaune ai sai ciwon ya Karu,tsawa papa ya daka Masa ganin sai lallabasa mama take shi Kuma sai botsarewa yake,Ade Zan mugun Saba maka a gidan Nan fa wallahi yau Koh zaka mutu sai kaje church. Mikewa maman nasa tayi ta kamo hannun sa ta nufi dakin sa dashi Bata tsaya ba har toilet ta shigar dashi kafun ta basa umurni babu Wasa a fuskar ta,kaga Ade kayi wankan Nan na baka 15 minutes ka shirya ka samemu a falo wallahi in ba haka ba Zan Saba maka kanason ka jawa mahaifinka hawan jini Koh? Kaya ya Soma cirewa ba tare da yayi magana ba hakan ya nunawa maman tasa zaiyi wankan kenan,fita tayi taja Masa kofa,bayan yayi wankan ya shirya Saida ya bata lokaci sosai don mama kafarta uku a dakin sa kafun ta samu ta fitoh dashi,anan ma Saida akayi daru don Ade 3quiter yasa papa Kuma yace bazashi church Yana d'ansa da gajeren wando ba daker dai aka samu ya canja,mota papan ya fitar Suka shiga sai church. ********************** Lahab na sauke wayar a kunnen sa Nnenna ya mikawa"gashi kema ki Kira gidan ku"yace Yana Kara Mika Mata. Mikewa tayi ta matsa kusa da jakanta tana harhada kayanta da takardun ta tana basa amsa"ban haddace number kowa a gidan mu ba" dan zare Ido yayi kafun ya sake tambayar ta cikin dariya"hhhh kina nufin kaf gidan ku babu wanda Kika haddace number sa"? Wani harara ta maka Masa tana rufe zip na jakanta tare da matsowa kusa dashi tana Mika Masa hannu"ban wayar na maida Mata innazo fita akwai Kaya a garden basu bushe ba,Mika Mata wayar yayi tayi Kamar zata karba sai Kuma yayi baya da wayar tare da Kama hannunta ya rike Yana bin fuskarta da kallo ya Soma magana a hankali"tafiya zakiyi ki bar patient" Fizge hannunta tayi,"toh ba ka Kira Yan gidanku ba me Kuma Zan tsaya Yi maka"? "Ki jira suzo saiku gaisa" Jin abinda yace yasa ta zaro ball eyes nata waje tana kallon sa tana magana"eh kace mu gaisa"? Hhhh kina tsoron karsu zo suga Wance ta tsagamin Kashi koh?toh ki kwantar da hankalin ki bazan fad'a musu ba kinji"?yayi maganar fuska a hade ganin Harta juya zata fita a dakin bata saurare Saba ma"bazaki min sallama bane sannan ga wayar nurse in ma baki d'auka ba Zaki tafi Kuma ki barni"? bata Koh saurare Saba tasa hannu zata bude kofar sai Kuma ta koma baya da Sauri ganin an turo kofar da karfi, dady ne ya shigo sai mutane guda biyu dake bayan sa,waro Ido yayi da Sauri ya shigo dakin tare dasa hannu ya riko nata Yana dudubawa Yana magana, Nnenna meya sameki Ina Kika shiga meya kawoki asibiti iye talk to me Mana daughter? dan sunkuyar da Kai tayi tama kasa magana d'ago Kai Dad yayi ya bin cikin dakin da kallo har idanun sa Suka sauka akan Lahab dake zaune akan gadon Kara kallon Nnenna yayi, daughter wanene wannan?ya nuna Lahab. Calm down sir ka bari mube kome a sannu tunda dai mun ganta,sai Kuma ya kalli Nnenna Harya bude Baki zaiyi magana sai Kuma ya kalli kofar dakin Jin an bude, Dr ne ya shigo Yana binsu da kallo, Assalamu Alaikum? Amsa Masa Lahab da d'aya mutumin sukayi dayake sune musulmai a dakin Dad Kam kasa hakuri yayi ya sake tambayar Nnenna nace wanene Kuma meya kawo ki hospital? "Accident muka samu a Keke Muna dawowa makarantan daga lokacin bansan Inda Kaine yake ba Saida na farka na ganta ashe ita ba abinda ya sameta shine ta taimakeni tana jinyata"Lahab ya basa amsa ganin Nnenna ta kasa ma magana duk tabi ta sure. What?don kayi accident sai akace ta zauna a wajen ka har 2 days Kai baka da iyayene? "Ina dashi ranka ya dade shiyasa ma dazun na kirasu Suna Kan hanya" binsa da kallo duk Yan dakin sukayi especially Dad don dagajin amsan da Lahab ya basa ya fahimci yaron baida kunya amma zai nuna Masa karshen rashin kunya,Kai Ina magana har kana da bakin bani amsa lallai Zan nuna maka karshen iskanci kallon d'ayan mutumin yayi sai na kulle yaron Nan Kan yata? wani shegen dariya Lahab ya sake ya nuna kansa da yatsa"Ni za'a Kama Ina kwance cikin jinya sai Kuma ya kalli Dr kana ji za'a zo a ciccibeni a hospital naka toh wallahi daidai yake da ka shiga rigimar Nan" ran Nnenna ne ya tsoma baci ganin Lahab nason raina Mata kanin mahaifi Kama hannun Dad tayi"kayi hakuri Dad bansan haka abin zaiyi zafi ba da ban tsaya ba na dawo gida tausayi ya bani babu Wanda yasan halinda yake ciki gashi Mai keken ya gudu gashi babu waya a hannun sa shiyasa na zauna dashi" Police in dake sanye da suit shima ya goyi bayan Nnenna, gaskiya ne sir bai Kamata a halinda yake cikin Nan a kawo maganar kamasa ba,duba da baida wani laifi ga Kuma abinda ya faru dashi Kai Kuma Dr ya Kamata in kun samu jinya irin wannan kurin ga sa hukuma a ciki bawai ku karbi majin yaci ire iren na accident haka kawai,don Kuna private hospital. da Sauri Dr yace insha Allah sir za'a kiyaye muma ganin su da uniform nayi tunanin abin bana accident bane. Dad Kam kamo hannun Nnenna ya sake ya bude kofar ya fita Yana ta masifa don Koh Ido ba mudu bane yasan kima kallo d'aya Yama yanayin Lahab ya gane ba irin yaran da zai Kama Kuma a rufe bane. suma mutanen binsu sukayi a baya Dr Kam matsowa yayi kusa da Lahab Yana tambayar ta,daman bakusan juna da yarinyar bane? Kallon gefe Lahab yayi kafun ya basa amsa"bama accident nayi ba" Ah ah Hassan daman karya kayi ba accident kayi ba sannan menene tsakanin ku da yarinyar Koh kasan uniform na wani school ne a jikinta? Komawa Lahab yayi ya kwanta bai baiwa Dr amsa ba hakan shiya Kara kular da likita tare da kudurtawa a ransa bazai Kara Koh daura Masa ruwa ba sai ya koyi yanda zaima babba magana juyawa yayi yabar office in. Su Nnenna na sauka a block na clinic in daidai lokacin motar Mami ke kokarin shigowa cikin gate na hospital in kusan tare Suka iso dasu Abbu parking tayi a lokacin suma su Nnenna motar su ya tashi gabaki d'aya Kamar ruwa ya cita ta tsinke da abinda zataje ta tarar a gida don taga Kamar abin ya bata wa Dad rai sosai. Mami ne ta fito a mota tare da rufewa hannunta d'auke da key,Rahab ma budewa yayi ya sauka da Yusuf a hannunsa sai mustapha,tsayawa Mami tayi tana bin motar Abbu da Ido ganin sunyi parking,fitowa dukan su sukayi fad'ad'a murmushin ta tayi ta nufi Inda suke tana Isa ta mikawa ummu hannu tare da sallama, Assalamu Alaikum amsa Mata sukayi gabaki dayan su gaggaisawa sakeyi ana jajanta abin mustapha ma ya matso ya gaidasu banda Rahab dake ta kakkauda fuska don shi saima yanzun yake Jin kunyar Abbu da abinda ya musu,shiyasa ma ya kasa gaidasu bare matsowa kusa dasu. Muje ciki Amina Abbu yace shima yayi Kamar baiga Rahab in ba, Addayiya dake gefe ne ta matsa Inda Rahab yake hannuta tasa ta dau Yusuf dake hannunsa don yaron kowa ya gansa sai yayi sha'awar d'aukarsa fari tass gashi bulbul dashi,tayi gaba sauran suka bita a bay shima Rahab binsu yayi a hankali. Suna shiga cikin hall in gabaki d'aya jama'ar dake wajen Suka bisu da Ido don duk hassadan Mai hassada inya ga ahlin Nan sai sun burgesu tun daga suturan su har ga fatansu ga matan dake d'auke da hakoran gwal a baki Suna dan Hira sama sama Suna tafiya,nurse uzaifa ya tsayar Yana tambayar ta Koh zata nuna musu layin majinyatan Kashi. Dan shuru tayi kafun ta tambayesa,Menenen sunan Mara lafiyan? Hassan Alhasan,ya bata amsa. dan Jim tayi sai Kuma ta sake tambayar sa,wani irin rauni ne hannu ne Koh kafa Kuma yaushe aka kawo sa? Fad'a Mata uzaifa yayi,shekaran jiya da Sauri ta ce kwarai ta ganesa,kubi wannan barandan direct har dakin Mai number 1. Toh mungode yace Mata, itama ta wuce su Kuma Suka nufi barandan tafiya Sukayi kad'an kafun Suka iso dakin Mai number 1 hannu muneera dake gaba tasa ta Kama kofar zata bude,tura kofar tayi ta bude gabaki dayan su Suka sa Kai daya bayan daya Suna shiga dakin da sallama...................... πŸ€ *By Ruqeenjalal* πŸ€ *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki* Page 69&70 Mikewa zaune yayi daga Kan gadon yanabin familyn sa dake shigowar da Ido,gabaki dayansu shiga sukayi Suka tsatsaya Suna kallon sa Rahab daya shigo daga Baya da gudu ya nufi dan uwan nasa bai tsaya duba matsalan hannunsa ba ya ruga yaje ya rungume Lahab sai Kuma ya fashe da kuka, murmushi lahab yayi Yana kallon fuska irin nasa dake kuka su Mami ma matsowa sukayi bakin gadon cikin soyayya don kaf cikin su an rasa Mai magana sai kallonsa da suke,"Wai menene haka Rahab kana kuka kamar mace"?Lahab ya tambaye sa Yana Kara rungumar dan uwan nasa. dan janye jikin sa daga na Rahab in yayi yad'aga Ido ya kalli Mami sai Kuma abba,murmushi Abbu yayi yasa hannu a Cikin tulin gashin dake kansa ya Soma magana,inkun gama rungume rungumen sai muma muyi magana,murmushi duk Yan dakin sukayi,ya jikin naka?"da sauki yaya"ya basa amsa. Addayiya ne ta mikawa muneera Yusuf itama ta matso wajen Lahab in tasa hannu ta Kama hannu Mai ciwon dan Kara Lahab ya sake yace"haba Addayiya ya haka ai saiki karasa ni"? Uhmm sannu ya jikin naka? "da sauki"sauran Yan dakin duka suka masa ya jiki yayin da Rahab ya d'ale Kan gadon ya kwanta Kamar shine Mara lafiya gasu uzaifa da muneera duk sun d'ad'd'ane Kan gadon sun Sasa a sakiya sai Hira ake,Mami Kam kasa cewa kome tayi sai bin Lahab in take da Ido a y'an kwana biyun nan har wani Yar rama yayi tace,Wai Lahab garin Yaya ka samu raunin Nan ne Allah dai yasa ba a filin kwallo bane? A wajen ne Mana kinsan babu Inda zai samu irin raunin Nan in ba a wajen ba, Addayiya tace Lahab ne ya had'a fuska kafun yace"da Allah dakata Addayiya nifa ba a wajen kwallo naji ciwon Nan ba karki min sharrin da Kika Saba"Jin abinda yace yasa Mami Masa dakuwa da yatsun hannunta tace,ungo naka Addayiya ke maka sharri don baka da kunya. Addayiya tace uwarka ce Mai sharri bani ba,sannan Kai umaru ka wani tsaya tsololo dakai kanajin abinda yaron Nan Mara kunya Yake gayamin bazaka bubbuge min bakinsa ba tunda uwarsa ta kasa bugewa, murmushi Abbu yayi sannan yace,kiyi hakuri Addayiya Kinga ba lafiya bane dashi amma inyaji sauki duk abinda ya Miki Ina tarawa muzammil xai maganin sa kinsan daman akwai punishiment dake jiransa. Hade fuska Addayiya tayi Jin abinda Abbu yace tace,kaga ba wani ponushmant(punishment)da za'a Masa abinda ya wuce dai ya riga ya wuce Kuma in maganan abinda yake min ne Ni bana rikesa na yafe masa,langwabe Kai yayi Jin abinda Addayiya ta fada sai Kuma ya kalli yayan nasa"Yaya nifa gaskiya na gaji da zaman hospital Nan kawai a sallameni,wani kallo Mami tayi masa tace,wani irin a sallame ka a yanda kaken Nan kasan jinyan Kashi kuwa?toh babu Inda zaka,ummu ce tace,ah ah Amina da dai an sallame San in yaso yayan nasa sai ya dauko Dr n Kashi Yana zuwa har gida Yana dubasa,da Sauri Addayiya tace,Anya za'ayi haka kuwa in ba hospital ba Anya Lahab zai zauna a Masa jinya har yaji sauki?insha Allah zai zauna in ma bai zauna ba hannun sane zai lalace bari naje office in Dr muyi magana,Abbu yace Yana fita a dakin,mikewa uzaifa yayi yabi bayan sa. Abbu yaje office in likitan ya nemi sallama duk da Dr baiji dadin haka ba amma yanemi alfarman shi zaina zuwa duk safiya kafun ya fito clinic yazo ya dubasa afternoon zaizo Koh da evening,ba musu Abbu ya amince sanan aka sallame sa,dakin ya shigo yana cewa muneera ta hada kayan dakin zasu tafi,kallon ta Lahab Yaya yace"Kinga akwai garden a hospital Nan inkin fita akwai Kaya dake shanye guda biyu wando da riga na mata dana Maza sai abaya baki,kallon sa duka Yan dakin sukayi har Mami ta kasa hakuri harta tambaye sa,kayan mace Kuma meya hadaka da kayan Mata Kuma,shuru yayi bai bata amsa ba har muneera ta fita a dakin,turo kofar akayi nurse innan ce ta shigo wanda koh sunanta bai sani ba, gaida su Yan dakin tayi kafun ta kalli Lahab tace,Hassan ya jikin na....makalewa maganar yayi lokacin da Rahab ya fitoh daga toilet in da Sauri ta kallesa ta kalli Lahab,d'aga Mata gira Lahab yayi Yana murmushi,bude Baki tayi zatayi magana Lahab ya rigata da cewa"Hussain sunan sa"Hussainin ka?ta Kara tambayar da? Zuwa Rahab yayi ya zauna kusa dashi baice ma nurse in kome ba sai Addayiya data nuna Mata mami"ga maman su Ni Kuma matar baban suce saida na tsufa mijina ya aureta ga y'ay'an su shararren dan kasuwane in gaya Miki yaran Nan tun Suna kanana Allah yama mahaifinau rasuwa Allah sarki,murmushi kawai nurse in tayi ta kalli Mami, gaskiya hajiya kin iyya haihuwa Allah ya rayasu nima kisani a Addu'a Allah ya ban tagwaye irin su masu Kama wallahi Suna ban sha'awa? Insha Allah kawai Mami tace juyawa nurse in tayi tana kallon Lahab tare da tambayar sa jiki. "da sauki sister amma sallame mu"zaro Ido tayi da mamaki tace,an sallame kafa kace Hassan?amsa ya bata"eh an sallameni za'a cigaba da dubani a gani,sai Kuma ya dau waya da abayan ta ya Mika Mata harda sallaya,gashi mungode sister Allah ya bar zumunci"hannu tasa ta amshi wayar tace,kabar sujud in da abayar na bar mata. "Ah ah ki amsa sister ai ta riga ta tafi"da mamaki tace,ta tafi Kuma Hassan tafiya babu sallama? murmushi yayi ya shafa kansa a hankali yace,tafiyar ce tazo babu tsammani,Mika Masa wayarta tayi ungo kasamin layinta sai muyi zumunci,amsar wayar yayi yasa Mata layin sa don baisan me zaice Mata ba karbar wayar tayi ta musu sallama ta fita Y'an dakin Kam sai mamaki suke don su basu gane wa ake nufi ba Amma Basu ce kome ba,har bakin mota nurse da Dr Suka rakasu,kallon Abbu mami tayi tace,yayan su nace Koh Zan wuce da Lahab Ina kula dashi a wajena daidai yaji sauki? Wani kallo Abbu ya Mata amma baice kome ba sai Addayiya ce tayi magana,lallai Amina Baki da mutunci harmu Zaki nunawa son d'a da iyya kula dashi watoh mu bazamu iyya ba kenan Koh me?toh bara na tuna Miki inkin manta tunda Kika yaye yaran Nan Kika dawo Mana dasu nake kuladasu dani da yarana sai yanzun Kinga ya samu matsalan Kashi Zaki wani jajubo jiki Wai a baki shi kiyi jinya toh baza'a bada ba,hannu tasa ta tura keyar Lahab da karfi tana cigaba da masifa,wuce muje bazaka bita ba Shi dayake binta yaje can yayita bin nata kaidai bazaka ba munafurcin banza da wofi, baki ummu dasu muneera Suka sake Suna kallon ikon Allah kasa hakuri Abbu yayi cikin alhini yace,haba Addayiya itace fa ta haifi abinta ta fimu iko da yaranta tana da ikon tafiya da Lahab ta kula da lafiyar sa don haka ki barsa ya bita. tsayawa Addayiya tayi amma har lokacin bata sake Lahab ba saina rike Masa kafadu da tayi da kyau Kamar xa'a kwace ta a hannunta tace,wallahi bazai bita ba ai da mahaifinku zai bar duniya yasan da Amina a duniya ai yace Kai ya baiwa amanar y'ay'an sa ka kular Masa dasu, toh akan me zaka barsu a gidan uban wasu wallahi bazan bayar ba ai Ni da Y'ay'ana aka barwa yara ba wata b'akutuwa ba tana karasa maganar ta Kama marfin mota tana kiciniyar budewa amma saboda bala'i tama kasa budewar shidai Lahab baice kome ba Kuma bai tayata budewa ba sai da ummu ta bude Mata Suka shiga Mami Kam kala batace ba ta bude motar ta ta shiga ita dasu mustapha Suka bar asibitin. Parking Abbu yayi Suka bubbude kofar motan Suka fiffito har lokacin Addayiya batayi shuru ba sai mita take,in ma bakin cikin kajin da za'a kakkawone take hassada tace zatayi jinyar Lahab, kashinsa da fitsarin sa lokacin da nake dawainiyar su Ina ita Aminar take da uwarta sai da yara Suka kawo Kai za'a nuna muna fin karfi,badai Wanda ya kulata shikaran kansa Lahab baice kome ba har Suka Shiga cikin gidan, ba kowa a falo har lokacin Addayiya na makale da kafadar sa,bude kofar dakinta tayi Suka shiga su Abbu Suka zauna a falo,Suna Shiga dakin da Sauri ta sake sa tasa hannu ta rufe kofar harda makulli bude wardrobe nata tayi ta Ciro Sabon zanin gado ta feffesa Masa turare ta yaye nakan gadon ta shimfida Sabbi tana chanja pillow tace,ai gwara na canja Kar azo dubaka aga zanin gadon ba yanda yake tana gama shimfidawa Lahab ya kwanta, sake share dakin tayi ta feffesa turare,matsowa tayi kusa da gadon tace,Kai lahabu Mai Zan dafa maka Naman kazane Koh ganda Koh kifi Zan maka kasan ance in mutum ya samu matsalan Kashi so ake a ringa dafa Masa nama Amma karfa kaci Kashi? Shuru Lahab bai amsa Mata ba leka fuskar sa tayi taga yayi bacci fita tayi a dakin taja kofar ta rufe tare da nufar kitchen dake babban falo,har yamma mamu da yaranta basu shiga sun duba Lahab ba sai Anwar daya fake idanunta ya shigo ya duba Lahab in tare da Masa ya jiki yayi zaman sa a bakin gadon Yana daddanna wayar dake hannun sa jifa jifa Suna Hira da Anwar in,Addayiya ce tayi sallama tare da leko cikin dakin amma bata shigo ba,had'a Ido sukayi da Anwar sai Kuma ta had'a fuska tare da turo kofar ta shigo hannun ta d'auke da food flask Mai shegen kyau guda biyu ajewa tayi akan table dake dakin ta had'a rai ta zauna akan kujera tana hararan Anwar tace,Ni don Allah tunda mutum yazo dubiya Kam basai ya duba ya tafi ba me na Zama Kuma zai sawa mutane Ido aka abincin ma mutum bazaici ba sai an wani zuba Masa na mujiya salon ya kware,murmushi Anwar yayi ya mike tsaye yace,toh Addayiya basai kince na tafi bakison naci amincin da Kika Masa ba ai shikenan Yana maganar ya bude kofar ya fita,kallonta lahab yayi kafun yace"Wai ke Addayiya menene haka"? Hararan sa tayi tana d'auko kulolin tana ajewa akan gadon tace,uwarka ce amsar da ta basa kenan tana bude kula babban tuwon shinkafa ne fari tass gashi ya dawo sosai laida biyu ta dauko ta bude tare da ajewa a plate in dake gefe karamin kulan ta bude lumshe Ido Lahab yayi,kazane tayi ferfesun sa sai kamshin citta da tafarnuwa yake zubawa tare da tsokokin a kwanon Miya,ta aje a tsakanin su tare da mikewa ta taro ruwa a roba ta Mika Masa,hannun sa yasa ya wanke a roban kafun taje ta zubar ta dawo ta zauna kusa dashi Suka Soma cin abinci hankalin su kwance. mami na barin hospital in bata tsaya dasu mustapha ba duk da yaso su tsaya ya sauka amma Mami tace ah ah sai dai ya bita suje gidan ta,Suna shiga gidan dukan su suka sauki a motar sukayi cikin gidan zaune Alhaji yake da yaransa a falo Suna Wasa da sallama Mami ta shigo falon yaran na binta a baya gaggaisawa sukayi Rahab da mustapha Suka zazzauna gabaki d'aya Rahab so yake ya koma gidan su,amma ya rasa ta Yaya Yana son Zama da dan uwansa waje d'aya,hijab Mami ta cire tayi cikin kitchen Alhaji ma mikewa yayi yayi part nasa yabar su a falon mikewa Rahab yayi ya shiga kitchen in ya dauko musu kayan marmari ya dawo falon ya aje musu shida mustapha... Abinci Mai Rai da lafiya Mami ta dafa miyan ganda ta dafa da tuwon rogo,tana gamawa tadau Sabon kulanta Mai kyau ta zuba abincin a ciki ta rufe ta dau sauran ta jera a falo,wanka tama yaranta Suka shirya tsab harda shi Alhaji Kiran sallan azahar da akai shiyasa sasu wucewa masallaci bayan sun dawo ne Suka zazzauna a dinning Sukayi lunch gabaki dayan su. Bayan sun gama ci hijab Mami ta daukowa wasila da mufeeda Alhaji na rike da Yusuf sai mahzar dake d'auke da kulolin abincin da Mami tace ya dauko a kitchen,mota biyu Suka shiga d'ayan mami keja daya Kuma Alhaji Suka nufi gidan su Lahab. ************************ Adewale basu Suka dawo church ba sai kusan 12:30 Suna dawowa kwanciya Adewale yayi Yana maida numfashi don harga Allah ba lafiya bane dashi turo kofar mama tayi ta shigo dakin ganin sa a kwance yasa ta karasowa kusa dashi tasa hannu tana taba jikin sa tace,Wai Adewale bansan meke damun kaba jikinka zafi gashi yanzun kome sai kanayi a sabule what wrong with u?matsowa yayi ya daura kansa akan cinyarta hannu tasa ta shafa Kan nasa tace,Wai har yanzun dai akanta ne Koh Hala?uhmmm har yanzun mama bansan matsayina a gunta ba? Murmushi tayi tace,in baka shawara son?gyada Mata Kai yayi baiyi magana b kara shafa kansa tayi ta soma magana,ur too young sosai yanzun ace ka Fara soyayya a dan wannan shekarun naka karatu ya dace kayi ka samu ka Zama cikekken mutum kafun ka Fara maganar mace?kaga yanzun zaka b'ata future naka ne a banza Kota amince da soyayyar ka auren ta zakayi? d'ago kansa yayi ya kalleta yace,toh mama basai ta jirani na gaba makaranta ba sai muyi auren Koh Kuma keda papa kumin aure sai mu cigaba da rayuwa tare? Dariya abin ya baiwa mama amma batace kome ba don tasan komame zatace bazai fahimce taba saboda so ya rufe Masa Ido ita Kuma bata San me zata ce Masa ba. Mikewa Adewale yayi ya shiga ban daki Bai jiba ba sosai ya fito ganin mama tabar dakin yasa sa daukar key in machine nasa ya bar gidan akan machine in roba-roba direct gidan su Nabeel ya nufa Harya share kwana sai Kuma ya tsaya ganin Shareef tsaye a bakin rumfar kayan marmari dake kusa da tsallaken layin su Yana sayan kankana,Jan Machine NASA yayi zuwa Inda Shareef in ke tsaye da sallama ya faka machine in hade da mikawa Shareef hannu,juyawa Shareef yayi ya kallesa sannan ya kalli hannun kin bawa Ade hannun sa yayi sai amsawar da yayi a gatseΓ±e Yana kokarin barin wajen. danne zuciyar sa Ade yayi yace,Shareef yakake?lafiya klau kawai yace Yana kokarin bude motarsa da Sauri Ade ya sauka a machine in ya nufesa yanace Masa,ayya nace Koh anji labarin Lahab Koh Inda yake? shekeke Shareef ya tsaya sai Kuma ya bude motar ya shiga yaja kofa ya rufe kafun ya sauke glass yace ma Ade dake tsaye har lokacin Yana binsa da Ido,eh ya dawo Yana gida baida lafiya,da Sauri Ade ya matso kusa da glass in har Yana tuntube yace,ba lafiya meya samesa,oho kashin hannunsa ne ya tsage daga haka yaja motar da Sauri Ade ya matsa gudun karya taka masa kafa, machine nasa ya hau ya gangara gidan su Nabeel paka Machine in yayi a kofar gidan ya cire key tsayawa yayi a bakin kofar gidan Yana kwada sallama. Nabeel dake Kan Keke sai dinki yake don yau tun da safe Banda sallah babu abinda ya dagasa akai sai cin abincin Rana da yayi ya samu ya dinka riga yanzun ma siket yake dinkawa yaji muryar Ade Yana sallama amsa Masa yayi,ka shigo Mana sai kace Bako,turo kofar gidan yayi ya shigo kansa a kasa,sai Kuma ya dago Kai da Sauri Jin Karan Keke da mamaki ganin Nabeel akai yace,yau wani Rana Nabeel dinkin wace Mai sa'a ce hake kake dinkawa?mtwsss kaga ga kujera zoka zauna bana son wani surutu gabaki d'aya mutane Basu da adalci gabaki d'aya kunsa min Ido,dariyan karfin hali Ade yayi ya juya kitchen Jin muryar Inna na Masa magana,ah ah wa nake gani Kamar bayarbe kwana biyu nace Koh Lagos kuka nufa ai? Ah ah inna Ina Nan wallahi bandaiji Dadi bane sai yau ya gida? Alhamdulilah Adewale ya jikin naka Ina labarin lahabu bawan Allah Wallahi Inna nima yanzun Nan na hadu da dan yayan sa Shareef nake tambayar sa labarin sa yake cemin Wai an gansa Yana gida ya samu tsagin Kashi a hannu zaro ido Inna da Nabeel sukayi kafun suyi magana sukaji Karan Abu a bayan su gabaki dayansu suka juya mubeena ce ta fito wanka daure da zani a kirjin kanta da jikinta naaaaaa........................... πŸ€ *By Ruqeenjalal* πŸ€ *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki* Page 71&72 Kwandon soso dake hannun tane ya Fadi dukansu kallonta sukayi, tana had'a Ido da Adewale da Sauri ta juya ta koma ban dakin tana tsaki batasan zata fitoh ta gansa ba da Bata fito a hakan ba,sunkuyar da Kai Adewale yayi Yana Jin abinda Inna ke cewa,kee mubeena kin haukace ne Koh me?Kai Kuma bayarbe garin Yaya abokin naku ya samu wannan rauni haka? Wallahi Inna ban sani ba shiyasa ma na biyo tanan muje mu dubasa da Nabeel, Adewale yace Yana sauraron abinda Nabeel zaice, Ade mu Bari zuwa dare sai muje mu dubasa,da mamaki Inna tace wani irin a bari sai dare Nabeel meyasa baka da mutunci ne Lahab nefa baida lafiya kace sai dare zaku?Kai Inna sofa nake na gama dinka wannan kayan daman Mai kayan taban kudin dinkin rabi Inna Kai Mata sai taban sauran Kinga saimu samu mu sai Masa koda kaza ne. Murmushi Adewale yayi yace,kaga Nabeel in zamuje mu dubasa muje mu dubasa maganar kaza Koh abinda zamu Kai wannan bazai hanamu zuwa ba kaga saimu koma da daren,gyada Kai Nabeel yayi yace shikenan muje in ba matsala. Sauka yayi akan keken NASA sukayiwa Inna sallama Suka fita a gidan Suna fita mubeena ta fito daga bayin fuska a hade tare da dukawa ta dau sosonta daya Fadi ta kalli Inna da har lokacin tana Kan taburma tace,nifa gaskiya Inna bana Jin dadin abinda yaron Nan yake Mana?da mamaki Inna tace ke mubeena meya Miki da har baki Jin dadi bansani ba Kuma Ni gani nayi yaron Nan baida matsala. Murguda baki tayi tace nifa gaskiya Inna banson Yana shigowa gidan Nan Kai tsaye irin haka duk abinda zaiyi Koh yakeso ya tsaya a waje Nabeel in ya fita ya samesa acan Akan me zaina shiga haka Kai tsaye yanzun fa wanka na fitoh fa a haka dagani sai zani na gansa a tsakar gidan Nan hakan ya dace kenan Muna barin wannan arnen Yana Kare Mana. Rike baki Inna tayi cikin mamaki tace,lallai baki da mutunci mubeena yaron Nan sama da shekara goma Yana zuwa gidan Nan sai yau kikasan ya Fara Kare Mana kaji Mara kunya? Yanzun dai duk ba wannan ba Inna yaushe zamuje mu duba Lahab in,wani kallon mamaki Inna ta Mata tace,keee na hanaki zuwa ki dubasa ne Koh yanzun kikeso shiga ki kimtsa kizo ki wuce nidai sai gobe da safe zani,wucewa kawai mubeena tayi ta shiga daki batace kome ba. ******************** Bude kofar gate in Mai gadi yayi Alhaji sulaiman ya danna hancin motar sa zuwa cikin compound in na Mami na binsa a baya, parking sukayi gabaki dayan su suka fito,tsayawa Alhaji yayi da mustapha a parking space Mami da sauran yaran sukayi cikin gidan tura kofar Rahab yayi suka kusa Kai ciki,babu kowa a falon nufar kofar sashin su Lahab Sukayi har Mami zata bude kofar aka rigata uzaifa ne ya fitoh da fara'arsa ya Soma gaidata,amsa wa tayi tana tambayar sa jikin Lahab,ai Yana dakin Addayiya baya Nan ku Isa, kofar falon Addayiya Suka nufa tura kofar sukayi da sallama babu kowa a falo kofar dakin Suka nufa gabaki dayan su suka tsattsaya a kofar dakin Rahab yasa hannu Yana bubbugawa Yana kwada sallama, Addayiya dake zaune ana yagan kaza Jin ana bubbuga musu kofa kamar Kuma muryar Rahab yasa ta Fara masifa,Kai haba karka ballamin kofa Mana ka jira azo a bude maka banason gaggawa haba?mikewa tayi tana tsude hannu tazo ta bude kofar,waro Ido tayi sai Kuma ta washe baki tace,ah ah wa nake gani Kamar hajiya wasila? Nine Addayiya Ina wuni?matsawa Addayiya tayi ba tare da ta amsa gaisuwar ba tace ku shigo Mana kin tsaya a tsaye,shigowar dukansu sukayi Suka zazzauna aje kulan mahraz yayi ya matso kusa da dan uwan nasa Yana Masa ya jiki,Mami ce tace, Addayiya da Alhaji mukazo Yana waje zai shigo ya duba Lahab,hijab Addayiya ta d'auka tasa tare da cewa, Bismillah ya shigo fita Rahab yayi yashigo dashi,su Mami basu tashi barin gidan ba harsu Nabeel ma Suka shigo sosai mutane keta shigowa abin sai ya baiwa mutum mamaki duk da kowa baijin dadin Lahab amma Allah ya Masa farin jinin mutane kuma duk Wanda zaizo saiya riko Masa Abu kulolin kaji Kam yafi biyar aka cikawa Addayiya a daki sai yamma sosai Mami Suka tafi amma Rahab bai bisu ba,bayan wucewar su kasa hakuri Lahab yayi ya tambaye Rahab"Wai Rahab lafiya Kam Naga gabaki d'aya kana Nan uncomfortable yau innan meke faru tunda na dawo Banga umaima Koh Shareef sunzo sun dubani ba Koh basa gidan ne"? Shuru Rahab yayi ganin Addayiya ta shigo dakin shiya hanasa magana,kallonta Lahab yayi yace"Wai Addayiya Ina Yaya muzammil ne Koh fushi yake dani har yanzun bai shigo ya dubani ba haka ma Aunty nabeela"?uhmm ajiyar zuciya ta sauke tare da Zama a bakin gadon ta had'a giran sama da kasa ta kalli Rahab tace,malam fita ka bamu waje zamuyi sirri don Ni yanzun bani ba kai. Waro Ido Lahab yayi yace"Kai Addayiya Rahab nefa kike kora Koh idanun nakine Suka samu problem"?zanci mutuncin ka lahabu?Jin abinda tace yasa Rahab Hawa Kan gadon ya kwanta Aiko da masifa ta Mike tana cewa sai ya fitar Mata a daki ya tashi ya fita amma haka yaki fita ta gama nacinta da masifarta kafun ta d'ale Kan kujerar dakin ta kwanta harda filo ta daura a kanta Kara tambayarta Lahab yayi ganin bata basa amsa ba"Addayiya Ina uncle ne yau kwata kwata ban gansa ba" Ya koma tace Masa,zaro ido yayi cikin happy yace"ya koma fa Kika ce haba dai da gaske ya koma Amma Baya ce sai bayan auren su umaima zasu koma ba"? Eh haka yace amma abinda dnn uwanka ya Masa shiya fusatashi ya tattarasu da sassafen Nan suka koma Inda suka fito,Kama baki Lahab yayi Kamar mace yace"bangane ba Addayiya meya faru meya hadasa da Rahab Kuma"?gashinan a kusa da Kai ka tambaye sa?juyawa yayi ya kalli Rahab dake kwance yayi Kamar baijin abinda suke cewa maka Masa kafada Lahab yayi yace"Kai tashi ka fadamin meya faru"? Manna Masa hauka Rahab yayi bai basa amsa ba hakan ya Sasa kallonta yace"waini don Allah kumin magana Mana menene haka na Mannin hauka,turo kofar akayi zulaihat ce ta shigo hannunta dauke da plate,uncle sannu ya jiki sai Kuma ta Mika Masa plate in hannunta gashi inji ummu waina kawo maka,karbar plate in yayi yace"gaskiya kice Mata na gode"budewa yayi gasheshen Naman ragone yasha yaji sosai yana kamshi ga cabbage a Kai rufewa yayi ya aje don harga Allah ya gaji da ciman Nan yau yaci nama haryafi a kirga hannun zulai ya rike ya ajeta a gefen sa yace"zauna anan muyi magana"zaman tayi cikin Jin dadi tana kallon sa"meya faru jiya a gidan Nan har Uncle muzammil ya tafi meya had'asa da Rahab"shuru tayi tana kallon sa tunani take ta fad'ane Koh karta fada ga Kuma Rahab da Addayiya dake wajen fahimtar hakan yasa sa mikewa hade da kamo hannunta Suka bar dakin,Zama yayi akan kujeran falo itama ya ajeta yace"toh yanzun ai saiki fadamin abinda ya faru naji"Zama ta gyara a hankali ta soma magana,ba jiya bane Wai Mami ta Mari mamu shine sai Mami ta zageta ran Uncle Rahab ya baci ya tattara kayansa zaibar gidan zaibi Mami shine uncle Rahab yace............................tass ta mayar Masa da yanda abin ya faru duk da a farko Lahab yayi farin cikin barin muzammil gidan Amma yaji haushin abinda Rahab ya Masa,sai kuma ya basar yace"Ni gaba ta kaini tunda bani na zagesa ba bare a sani a gaba"ya mike ya koma dakin yayi kwanciyar sa abinsa. *********************** Fuskar dady babu walwala daga hospital in station sukaje yayi sign sannan Yama mutumin da yakai rahoton ya ganta a asabiti kyautar 3k amma mutumin yaki karba Sam yace ya yafe wallahi daga Nan gida Suka nufa har lokacin Dad baice Mata kome ba parking yayi a kofar gate na gidan su,bude kofar motar Nnenna tayi da Sauri ta sauka ta tura karamin gate in ta shiga a take karnuka Suka mimmmike Suka nufota itama bata wani damu ba ta soma kiciniyar bude babban gate tsuntsunata sukayi sannan Suka koma Suka kwanta wangale gate in tayi dad ya shigo da motar sa parking yayi ya bude ya fita baibi ta kanta ba ya bude kofar falo ya shiga,binsa tayi a baya a hankali jikinta duk yayi sanyi bataso ta Bata Masa ba itama batasan ransa zai baci har haka ba,mikewa su mom sukayi dake zazzaune a falo cikin alhini,shigowar dad da Nnenna yasa Suka Mike Suna tambayar sa a Ina yaganta kala baice musu ba sai tura kofar Nnenna da yayi ya shiga ya zauna akan stoll na dakin yayi shuru,kanta a kasa ta gaida mom kasa amsawa tayi itama Nnenna Bata damu ba tabi dad dakin nata shiga tayi tana tafiya Kamar Wance kwai ya fashewa a ciki zamowa tayi ta zauna akan tiles har lokacin kanta a duke wani irin tsawa da bata tabajin dad Yama Koda yaran cikinsa bane ya sake Mata"keeee meya hadaki da wannan yaro Mara kunya dan hausa people innan am asking you for the last time wallahi ki gayamin gaskiya. A hankali tace"am so so sorry Dad ban d'auka haka yake ba don Allah kayi hakuri nima ban Sansa ba accident muka samu lokacin baya hayyacin sa shiyasa na d'auke sa da taimakon Mai Keke mukaje asibiti bai farfado ba sai yau"tana gama maganar ta rumtsa idanunta da karfi saboda karya data fetsawa mahaifin nata duk da ba dabi'arta bane karya amma yau Lahab ya saya tayi. A fusace dad yace,watoh kece uwar tausayi duk musulmai dake wajen a rasa Mai taimaka Masa saike uwar gwaninta sannan da wani kudi kike kula dashi a hospital in tunda har waya ma baidashi? Duk da taso tadan rikice amma ta dake tace"akwai kudi a Aljuhunsa masu yawa dasu nayi amfani"Jin abinda tace Sam baiyarda ba ga wani bacin Rai daya tinkaro sa don shi a rayuwar sa yaki jinin musalmai da Christian ta taimakawa dayafi kowa murna,d'aga hannu yayi zai mare ta da Sauri ta Kare fuskarta shima hannun nasa tsayawa yayi Bai mare ta ba don sai Kuma yaji baison Marin nata komawa yayi ya zauna ya sassauta muryar sa ya Soma Mata magana,Kinga Nnenna Nan ba Enugu bane rayuwar Nan daban dana Shan banason ki jajibowa kanki matsala bana son kina mu'amala da ire iren mutanen Nan Baki ganin su Sarah da Jennifer kin taba ganin Koh maganar kirki ya hadasu da musulmai kina ganin layin mun Nan kwata kwata christoti Bamu da yawa Amma bama shiga harkan su don haka bana so karki Kara karki sake daga yau ma Zan nema miki drive da zaina kaiki makaranta tunda Naga Gloria da Abraham amanar da na Basu na tafi ba iyya rikewa suke ba,Yana Gama magana ya mike yabar dakin. shuru tayi tana tunanin meyasa Wai kowa yake cewa musulmai Basu da kirki ne amma ita Bata ga rashin kirkin su ba ta hadu da shayibu(mijin ma'u) da Lahab Bata ga wani abin aibu a tare dasu ba amma tunda uncle Nata yace ta bari toh zata barin tunda bata San dalilin da yasa yace Mata haka ba wata Kila Suna da wani haline da ita Bata gane ba,mikewa tayi ta soma dube dube a dakin tana Neman Kiki kiransan ta somayi a hankali tana dubasa,,banko kofar dakin akayi mom ce ta shigo ranta a bace ta Soma magana harke kin Isa a dauko Miki d............................. πŸ€ *By Ruqeenjalal* πŸ€ *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki* Page 73&74 A d'auko Miki driver Jennifer da take Yar masu gida ba'a kawo Mata drive ba saike banza toh wallahi Baki Isa ba ita dai Nnenna na tsaye kanta a kasa shako wuyanta tayi tace,kee magana nake Miki fa kin manna min hauka watoh kin gama karuwan cin ki shine Zaki dawo kuma a nema miki who a u?fisge riganta Nnenna tayi ta bude kofar toilet ta shiga tare da banko Mata kofa,sosai mom ke masifa ita dai Nnenna batace kome ba hartaji mom ta fita a dakin kafun ta fito tana kuka tana Kiran kiki,tsunguna wa tayi tana leka kasan gado duhu ne babu kome bayan wardrobe duk ta dudduba amma Bata gansa ba. gajiya tayi ta koma bakin gado ta zauna tare da zuba tagumi tana tunanin Koh dai Kiki ya mutune da yunwa toh amma inya mutu Ina gawan sa ai da zata gani,kuka ta Soma a hankali tana cewa"ka taimaka Kiki ka fitoh tsawon shekara 10 Muna tare sanan yau kawai saika tafi ka barni,ta sake sabon kuka da karfi turo kofar akayi Abraham ya shigo dakin da Sauri ya karaso bakin gadon ya zauna hannu yasa zai Kama nata cikin tashin hankali Yana tambayar ta meyake faruwa hannu tasa ta buge nasa tare da mikewa rai a bace tace"fita mini a daki banason ganin ka ka fita nace"tana magana tana kuka sosai. zamowa yayi daga Kan gadon yayi kneel a kasa ya Soma magana,haba sister meyayi zafi haka zakice Baki son ganina menene laifina kinsan irin tashin hankali dana Shiga kuwa?na rashin ki a kusa dani naji tsoro sosai,komawa tayi ta zauna tana cigaba da kuka Koh banza tad'anji sanyi ashe akwai wa'inda Suka damu da rashinta a duniya,matsowa kusa da ita yayi sosai cikin lallami yace,kiyi hakuri ki sanar dani Ina Kika shiga wallahi na damu rashin ki na samu Dad amma yaki ya kulani pls tell me Ina Kika shiga? dan shuru tayi sai Kuma tace"accident muka samu a hanyan toh Wanda mukayi accident in dashi ya samu rauni sosai shine na taimaka na zauna agunsa Ina jinyar sa"da mamaki yace toh meyasa ran Dad ya baci saboda dan abinda kikayi Nan sannan nasan saboda baki da wayane da Zaki Kira ki fada Mana amma Bari na fita Zan sayo Miki Sabon system?girgiza Masa Kai tayi shima girgiza Mata yayi yace,saboda me?meyasa duk lokacin da Zan Baki Abu saikin Raina ne?da mamaki tace"raini Kuma"eh mana ya bata amsa dan rufe fuska tayi tace"nifa ba Raina wa nayi ba kawai ka barshi don nasan in mom ta sani ranka da nawa ne zai baci. Mikewa yayi daga durkusen da yake har lokacin idanunsa na kanta yace,kawai amsa nake son naji kinaso Koh ah ah?nifa bawai bana so bane kawai dai.........dakatar da ita yayi ta hanyar cewa,nifa banson kice kome waya dai Zan sayo Miki sauran aiki ya rage naki,dubeki Kamar Mai wayo amma babu,Yar kauye kawai duk abinda aka baki dole ne saikin nuna an gani kawai boyewa zakiyi kina amfani da abinki Koh su Sarah karki bari su gani kinji ?"toh nagode"tace tana Kara zuba tagumi har ya bude kofar zai fita sai Kuma ya dawo ya tsaya again yace,meke faruwa ne sister Naga Kamar kina cikin damuwa? "Banga cat nawa ba brother"tace tana Kara fashewa da kuka tana dad'a rufe fuskar ta da hannu, murmushi yayi yace,kiyi hakuri toh Zan samo Miki wani new cat in,d'aga kafada tayi tace"Ni bana son wani kawai so nake na gansa"bude kofar kawai yayi ya fita baice kome ba,jakan makarantan ta ta bude ta dauko uniform nata dake ciki ta aje akan gadon takardunta ta Soma fitarwa sai Kuma ta zaro Ido ganin abinda ya Fadi hannu tasa ta d'aga tana duddubawa ATM in Lahab ne"wash na manta dashi kwata kwata ban basa ba toh yanzun ya zaiyi da bill na hospital gashi babu kowa nasa?"sai Kuma ta danyi murmushi idanunta na zubda kwalla tace"ashe fa ya Kira Yan gidan su,gobe Zan Kai Masa a hospital in duba jikin nasa. ******************** bayan isha'i umaima dake dakin ta a zaune wayarta ne yayi tsowa mikewa tayi ta dau wayar ta Kara a kunnen ta,sallama akayi ta amsa cikin happy tace"ok harka iso ok toh ganinan fitowa,katse wayar tayi ta aje mikewa tayi ta dau hijab nata ta dau turare ta feffesa a jiki sannan ta zura,ta fitoh a dakin nasu kallon su muneera dake zaune a falo tayi ta nufi kofar ta fita. Tsaye yake Kamar kullum a kusa da motar sa karasowa tayi tana murmushi"barka da warhaka Rabin Raina",da murmushi yace"yauwa dear ya Mai jikin? Da sauki Rabin Raina Yana ciki muje Bismillah Bude motar yayi ya dau laidodi manya dake ciki,da Sauri umaima ta matso tasa hannu zata karbi laidan,kaucewa yayi Yana dariya ya rufe motar yace"Kinga Bari Zan idar da ladana basai kin tayani ba"kaga ka bani kawai bakon ka annabin ka kana son mu shiga ciki Addayiya tamin fada ban karbe abin hannu Bako ba, murmushi kawai yayi ya bata laida daya shima ya rike daya Suka jera tare Suna tafiya itace a gaba Yana binta a baya. Zaune suke a dakin Addayiya kansa a kasa irin anzo gidan surkunayen Nan kansa a kasa suke gaisawa da Addayiya sai umaima dake zaune a bakin gado,Lahab da Rahab nakan gadon a zaune"gaskiya mungode Abubakar Allah yabar zumunci Allah dai ya nuna Mana ranan bikin Nan ayi a wuce wajen, Addayiya tace Kara sunkuyar da Kai sadeeq yayi Yana ma Lahab ya jiki amsawa yayi rahab ya gaidashi ya amsa da fara'a mikewa umaima tayi da Sauri Addayiya tace"Ina Kuma Zaki kibar Abubakar in kuma"zanje na sanar dasu mamu Wai zai shiga falo ya gaidasu" ta bata amsa ba tare data jira abinda zata ceba tafita a dakin,itama Addayiya mikewa tayi tadau laidan daya kawo Mata ta bude wardrobe nata tasa ta rufe tare da fita a dakin,ganin babu kowa daga shi sai tagwaye yasa sa d'aga kansa ya kalli Lahab yace"am in babu damuwa small uncle Niko so nake muyi magana da Kai wata Alfarma nake nema. "Wace irin Alfarma kenan sadeeq ince dai lafiya"? Lafiya Lahab daman akan maganar kawo lefe ne abinda ma ya dagoni kenan zuwa gombe nazo na sanar Mata akan ranan talata za'a kawo lefe toh saina zo na tarar da abinda ya faru Allah ya kiyaye na gaba,Ameen Lahab da Rahab sukace Suna cigaba da sauraron sa,shine tace a aje maganar kawowa, yau na tashi da niyar wuce wa sai ga kiranta tace min an ganka harma ka dawo gida,dana Mata maganan kawo Kaya shine tace Wai babu Rana sai Randa kaji sauki gashi mom nata kirana akan maganar lefen nakasa ce musu kome pls kasa baki akan maganar na rasa wazan tinkara ga umaima da taurin Kai? Rahab ne yace kana nufin ita tace babu maganar lefe ba ranna kawowa bayan Kuma date na biki saura wata daya"?cikin dan annashuwa ganin ya samu goyon baya yace"eh wallahi nima shine hankalina yadan tashi"karka damu Zan ma Addayiya magana karku fasa kawowa ranan Tuesday in Ina jibine ma"?eh sadeeq yace sai Kuma yayi shuru ya fasa maganar da zaiyi ganin umaima ta shigo tsayawa tayi tana kallon su ganin Kamar wani abin suke kullawa tace"ka taso muje ku gaisa"mikewa yayi yabi bayan ta Suka fita a dakin,Suna fita saiga Addayiya ta dawo a lokacin Lahab ya sanar da ita abinda ke faru Aiko tace zata samu mamu da Abbu duk da ajesu akan maganar lefen. Mamu taji haushi matuka na zuwan sadeeq gaida Lahab amma bata nuna Masa a fuska ba sai bayan ya fita sosai tayita zagin umaima,washe gari da safe Rahab da sauran yaran Suka shirya cikin kayan makaranta suka tafi Abbu ya gama Shirin office NASA harzai fita Addayiya ta kirasa shida mamu ta musu bayanin akan za'a kawo lefen umaima gobe Tuesday sosai abin ya baiwa mamu mamaki ace Kamar ita uwar umaima bata San da zancen lefe ba sai da Addayiya ta Kira ta ta sanar da ita lallai yau zataci uban umaima,mikewa tayi a fusace zata bar dakin Abbu ya daka Mata tsawa tare da Bata izinin komawa ta zauna komawar tayi ta zauna Rai a bace Abbu yace"Abba haleema bazaki taba hankali ba tunda har yanzun Baki da hankali ya uwata na tsaka da magana Zaki tashi ki fita wannan ai raini ne"? Rabu da ita ai haleema halinta sai Allah Inda sabo na Saba da shi nasan babu abinda ya Bata Mata Rai sai zancen lefe gobe Kuma ta Fara ji a bakina Addayiya tace tana girgiza Kai,Abbu yace haba Addayiya ai a tunani na Koh ke Zaki iyya tarban masu kawowan basai haleema tasa Baki ba Amma menene don kin sanar da ita Kuma ni naji dadin hakan Koh banza iyayen yaron Nan sun girmama mahaifiyata"bama su bane Umar yaron ne daya zo duba Lahab yau yake sanar dani akan Suna so zasu kawo Kaya Amma umaima tace karsu kawo sai Lahab yaji sauki.......ai bata gama magana ba mamu ta amshe da cewa"yanzun akan yaron Nan har umaima na cewa a d'aga kawo lefen don bata da hankali Ni na tabbatar wallahi Koh mutuwa nayi na tabbata yayan Amina bazasu fasa abinda sukayi niyar Yi ba akan me zatace haka wallahi yau sai ta gane kuranta. Addayiya tace don Allah haleema inkin tashi Mata hukunci ki kasheta har lahira bake kince baki da kunya ba Bismillah jeki tabata Ni Kuma Zan nuna Miki karfin ikona a gidan Nan ShaShashar banza Mara hankali,Abbune ya Soma bawa mamar tasa hakuri itakam mamu mikewa tayi tabar dakin,tasan Koh hauka take yanzun dai bazata lakato wata maganar ba shiyasa ma bata bi takan umaimar ba Kuma batace Mata kome ba sai dai fuskarta kawai mutum zai gani ya gane tana cikin bacin Rai,d'aga waya tayi ta Soma kiraye kirayen kawaye da Yan uwanta akan gobe za'a kawo kayan auren umaima,duk Wanda ta Kira sai yayi Mata mitan akan sai yau za'a sanar dasu hakuri kawai take basu. Abbu na fita a dakin Addayiya compound ya nufa zai bar gidan da Sauri mamu tabi bayan sa har ya shiga mota ya hangota yaso yaki tsayawa amma ya daure yaji dame tazo,abinka da Mai jiki dan Sauri da Tayi yasa ta sauke numfashi akai akai bayan isarta jikin motar sa ta Soma magana daker daker"daman Alhaji Naga fita zakayi bakace min kome ba?kallon banza ya Mata kafun yace toh me kike son nace Miki haleema? Haba Alhaji kana fa zaune kanaji Addayiya tace gobe za'a kawo lefe amma baka bani kudin da zanyi sayyayyan abubuwan tarban Baki ba kasan wannan shine aure na farko da zamu d'aga a gidan Nan auren umaima da Anwar gaskiya bana son Abinda zaisa a Raina mu nafison kome a wadace,shikam Abbu Yana mamakin irin jaraban karya dason kudi da Haleema ke dashi a rayuwar ta amma baice Mata kome ba har Saida yaja dan lokaci ita dai tana tsaye tana kallon sa yace"Haleema wa'inda zasu kawo kayan Nan fa ba a gombe suke ba a bauchi ne Koh danko zaku dafa musu ai kye bari gobe yayi a dafa xuwa yamma ai ya dafu Koh? Jin abinda yace yasa ta hade rai tace"haba dan Allah kafa San yau nake son naje nayi sayyayyan kayan aiki irin su kaji da sauran su kaga gobe in Yan uwa Suka hallata sai su Fara aiki kawai,zaro Ido yayi ya nunata da yatsa yace"yanzun haleema da bakin ki kike cewa Zaki kasuwa sayyayyan kayan abinci wallahi karki kuskura Kuma kudi ne dai bazan bayar ba saina dawo office Yana karasa maganar yaja motarsa yayi gaba ya barta a tsaye agun tana juyawa zata koma cikin gida Kamar ance ta kalli bini sukayi Ido hudu da ummu dake saman bini tana kallon su,a fusace mamu ta shiga falo ta nufi upstairs don wallahi yau saita nunawa ummu bacin ranta na sa Mata Ido da take a gidan. Ummu dake sama da Sauri ta Soma saukowar daga saman jin takun steps a fusace yasa ta bude dakinta dake sama ta shiga tare da maida shi ta rufe da karfi ta murza key harga Allah masifar mamu ya isheta haka bata son cecekuce a gaban yara. ******************** tun da sassafen mubeena ta kasa nutsuwa yau Monday sunada paper batason zuwa makarantan balle ta hadu da Rukayya ita Soma tayi Inna ta tashi suje su duba Lahab amma tace sai ta dawo makaranta sai suje ga Nabeel dake ta surfa Mata nacin ta shirya yau da kansa zai Rakata makaranta lura da yayi duk jikinta a sanyaye,ruwa ta Iba taje tayi wanka shima Nabeel wanka yayi ya goge kayan sa bayan ta shirya dumamen tuwon daren jiya sukaci,Nabeel ya dauko kayan daya dinka jiya da niyar kaima Mai kayan tunda jiya bai samu ya karasa da wori ba sallama Suka ma Inna dukan su Suka fita a gidan tafiya suke Suna dan taba Hira kowa ya gansu yaga Yan uwa gasu farare tass farin nasu daya ne ga Kama na jini,sunkai almost 30 minutes basu samu Keke da zai kaisu makarantan su mubeena ba in Kuma Suka ce drobe basa samun Wanda ba mutane kowa yasan yanayin garin gombe in gari ya waye especially ranakun makaranta akwai go slow sosai hakan ya taimaka wajen Kara lattin nasu sosai hankalin ta ya tashi ganin lokacin shiga jarabawan bai wuce 40 minutes ya rage ba,Nabeel wayar sa ya zaro a Aljuhu ya lalube number Ade ya Kara a kunnen sa. ***************** Adewale na tsakiyar falo da papansa sai jaraba yake zubawa akan rashin zuwa makarantan da Ade yake"Wai papa mekake so nayi ne ba dai an koreni a makarantan ban menene Kuma zai kaini"? papa yace mezai kaika kake tambaya na ai in mukaje na Basu hakuri albarkaci na za'a Mai dakai amma dayake Kai Wawa ne kafison kayita yawo a gari kana galantoyi kaida abokan shashancin ka"ringing in wayar Ade shiya dakatar da papa ganin Mai Kiran yasa Ade picking ya Kara a kunnen sa Yana sauraron abinda Nabeel ke cewa Kamar haka,"pls Ade nace kana gudane so nake ka aramin machine naka wallahi Auntina ce tayi late gashi Suna da exam Nan da 40 minutes"ba kome Bara na fitoh wait for me Ina zuwa yanzun Nan Yana karasa maganar ya katse Kiran tare da kallon papa yace"nifa gaskiya papa na gaji gani nayi mu yanzun sss 3 ne Kuma Muna second term no need na dame kaina da karatu Koh zuwa makaranta Koh naje Koh Kar naje duk daya ce revision ake fa Kuma Koh ban samu Avr ba ban damu ba tunda bazai hanani registration na weac ba,Yana maganar Yana tafiya Harya bude kofa ya fita binsa a baya papa yayi Yana zagin sa Ade bai wani tanka masa ba ya shiga garejin gidan su key machine dake aljuhun sa ya zaro ya tsokawa machine in zai tayar papa daya iso wajen hannu yasa ya zaro key machine in tare da juyawa ya koma cikin gidan,da Ido kawai Ade ya bisa sai Kuma ya dake banban machine in da karfe ya sauka akai bude gate yayi ya fita da kafa Yana Kara duba time ganin kusan 6 minutes da Kiran sa da Nabeel yayi ya shige gidan su David ya shiga da Sauri ya nufi flat nasu Allah ya Sosa sun fito kenan zasu fita sai gashinan alfarman machine na kanin David ya nema ya basa aro amma bai samu ba saboda zashi makaranta dashi sai mota da David ya basa,karba Ade yayi duk da Suna koyan mota da Lahab Kuma sun Kai kusan shekara amma bai taba Hawa ya fitoh cikin gari ba,amsar key yayi ya bude motar ya shiga tare da kunnata yayi reverse yaja zuwa bakin gate Mai gadi ya bude Masa ya fita,tafiya yake Yana duba time ga kirjinsa dake bugawa na rashin Sabon tuki da yake yanzun Yana taka tsamtsam gudun karyayi kuskure,gangarawa kwaltan su Nabeel yayi tun daga nesa ya hangosu Suna takowa da kafa har round about nasu. Parking yayi a gaban su gabaki dayan su Suka ja baya tare da basa hanya Suna kaucewa zasu wuce sake Shan gabansu yayi Wanda hakan ya fusata Nabeel har ya Soma dura zagi akan Mai motar nason kadesu,sauke glass Ade yayi yace"toh sarkin masifa washe baki Nabeel yayi yace"durun wa Kaine mutumina irin wannan harka haka wannan motar fa"Kai shigo da Allah time na tafiya,da Sauri Nabeel ya bude gaban motar yana kallon mubeena dake hade da fuska tunda ya Kira Ade take wani ciccin magani ita a dole bai Mata daidai ba yace"Aunty kizo ki shiga ya kaiki lokaci na wucewa Ni Kam Zan wuce gidan su Nadiya na Kai Mata dinkin nata. ranta badon yaso ba ta shiga gaban motan tana hararan kanin nata,shikam Nabeel ya maida murfin ya rufe Bai damu ba Ade Kam sai wani murmushi yake yau zasu kasance tare da juna Kuma a kadaice matsawa baya Nabeel yayi Yana musu a sauka lafiya har Suka bacewa ganin sa shima tsallaka titin yayi ya nufi gidan su Nadiya customern sa. Adewale tuki yake amma gabaki d'aya hankalin sa na kanta wankan ta gabaki d'aya ya tafi dashi duk da ba walwala a fuskar ta amma ba laifi tafito ras da ita dan gyaran murya yayi ya juya ya kalleta kadan,juyawa tayi ta kallesa amma batace kome ba ganin har lokacin kallon ta yake maida kanta kan titi tayi sai Kuma ta zare Ido jikinta na rawa tasoma Kiran innalilahi wa'inna'ilahu raji'un da Sauri tayi super ta rungumesa tare da rumtsa idanunta jikinta na mugun b'ari........................... πŸ€ *By Ruqeenjalal* πŸ€ *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki* Page 75&76 Wani irin Jan birki Ade yayi Wanda har Saida Kan mubeena dake Kan kirjinsa ya koma gaba ya bugu kara ta sake da karfi bawai na zafin buguwar bane ah ah na tsoro ne,sauke ajiyar zuciya yayi ganin Allah ya takaita abin saura kadan ya buge motar dake gabansa,bude Ido tayi ganin babu abinda ya faru yasa ta sauka a jikinsa cikin bacin Rai tace"Wai menene haka wannan ai hauka ne in kasan baka iya driving ba ya zaka d'auke Ni a mota ka nemi kashe Ni a banza,kala baice Mata ba bai Kuma tada motar ba bai Kuma fasa kallon ta ba a fusace tasa hannu zata bude motar amma ta ji a rufe gim da Lock,juyawa tayi ta kallesa suka had'a Ido ta cilla Masa harara cikin Jin haushi tace"malam ka bude min Mota na sauka nayi late,bai saurare taba yayi ma motar key,fusata tayi ta Soma Masa ihu ya sauke ta Koh kulata baiyi ba sai zuba gudu da yake a kwalta bini bini Yana kallon agogon dake d'aure a tsintsiyar hannun sa,saura minutes 6 a shiga jarabawa Kuma daidai lokacin suka iso gate na makarantan itama Karan kanta mubeena hankalinta a tashe yake"ta Ina ne department naku,nuna Masa tayi da mugun gudu ya kwasa Wanda Saida yaja hankalin dalibai dake geftawa, parking yayi a gaban block nasu mubeena saban Sauri bude motar tayi ta ruga da gudu tayi cikin hall na exam nasu hango lecture dake tawowa zai shiga,tana sa kanta a hall in taga Rukayya tsaye hankalinta tashe da waya Kare a kunnen ta ganin mubeena yasa ta saurin nufota tana cewa"mubeena lafiya kinsan halin malamin Nan baida mutunci sannan Kika buga late gashi saura minutes 2 fa a fara,Koh rufe Baki batayi ba malamin ya shigo hakan ya sata hakuri da Sauri ta nufe kujeran da ta Kama musu ita da mubeena,kauda fuska mubeena tayi ta zauna a wani kujera daban ba tare da tabi ta kanta ba sai kokarin boye bacin ranta take Bata son bayyanawa. Ade da Ido kawai ya bita ganin yanda take gudu cikin tashin hankali dariya kawai yayi sai Yana shafa kansa sai Kuma idanunsa suka sauka Akan wayarta daya Fadi lokacin da Suka kusa accident tashin hankali Bai Bari ta d'auka ba dukawa yayi yadau wayar Yana jujjuyawa sabuwa ce Kiran hot 6 kunna wayar yayi ganin akwai Lock yasa sa jan tsaka ya aje wayar tare dajan motar yabar school in. ***************** Tun da sassafe Nnenna ta Soma share share don peace ta dawo ta karbi aikin kitchen share tsakar gida take hankalinta ba'a kwance ba ga idanunta da Suka kukkun bura jiya Koh isheshen bacci bata samu ba na rashin Kiki abin ya mugun d'aga Mata hankali sosai sabo, da kule harna tsawon shekaru ace yau an waye gari baka gansa ba dole zakaji ba dadi kwashe sharan tasoma tana zubawa a basket dake gindin bishiyar goiba tacan bayan zaro Ido tayi ganin Kiki a cikin shara yayi lame lame dashi gashin jikinsa duk ya yamutse ya yarda kai Kamar macece hannu tasa ba kyama ta dagosa hawaye na zuba a idanunta Koh ba afada ba daga gani ruwan da akai shekaran jiya akan sa ya Kare kenan? da Sauri ta nufi cikin gidan dashi Allah ya sota ba kowa a falo da gudu ta Shiga dakinta. Maida kofar bayin tayi ta rufe ruwan zafi ta had'a a bucket ta Soma wanke kiki Kamar mutum harda soap tass ta wanke gashin jikinsa tadau towel nata ta lullabesa da gudu ta fito a toilet in ta ajesa akan gadon fita tayi a d'akin da Sauri har Suka kusa cin Karo da peace dake kokarin fita a kitchen ita Kuma tana kokarin shiga matsa Mata peace tayi cikin Jin haushin ta ita Kam Nnenna batabi ta kanta ba ta shiga kitchen in fridge ta bude ta dauko milk ta fita,zubawa Kiki tayi a ciki plate na abincin sa data aje a daki tana zuba Masa abinci kullum wanke plate in tayi ta tsiyaye madaran da Sauri tahau Kan gadon ta dauko sa tura Masa plate in tayi a saitin bakin sa amma dib kakeji kiki ya kasa latsar madaran,bude Masa Baki tayi ta dau Goran ta kafa Masa a Baki daker da tsuden goshi yasha kadan rufe Goran tayi da Sauri ta shiga ban dakin shashaf tayi wanka tazo ta zura uniform nata jakan makaranta ta d'auka ta cicibi kiki dake cikin towel har lokacin Kuma ita Bata cire Masa ba ta nufi barin gidan, Abraham dake kokarin shigowa ne a gate ya tsaya Yana kallonta da mamaki yace"ba Dad yace zai dauko Miki driver ba ki daina fita ke kadai"brother cat nawa ba lafiya so nake nakaisa clinic a dubasa"uhmm kawai yace ya bude Mata kofar motar tare da Bata izinin Shiga ba musu ta shiga ya data motar Suna barin layin su waya ya d'auka ya Kira Dad ya sanar dashi yadau Nnenna zai Kaita makaranta,Suna gama wayar ya tambaye ta"Hope de da Kika tashi fita clinic in dabbobin kinsan a Ina yake Koh"?girgiza Masa Kai tayi amma Batayi magana ba shima baice kome ba ya cigaba da tukin cikin kankanin lokaci yayi parking a gaban wani shago Kamar chemist,sauka sukayi dukan su Suka nufi cikin shagon glass in kofar ya bude Suka shiga. Sosai akayi treatment in kiki harda allurai aka Masa Dr n yace a bar Masa shi taje school ta dawo, Abraham ne ya biya duk kudin da aka kashe a clinic in daga Nan makaranta ya kaita tare da sanar da ita akan ta jirasa zaizo ya dauketa in aka tashi,zaune take a class tana tunanin yanda Lahab ya kwana da jiki taci burin zuwa ta dubasa sannan ta Kai Masa card nasa amma Bata samu hakan ba gashi tsoro take ji kada ace bazata Kara ganin sa ba tunda ance an koresu gashi yanzun batasan gidan su ba,ga Dad zai nema Mata driver tunawa da zulaihat data taba zuwa ta karbi jakan Lahab a hannun ta in bata manta ba Yar junior set ce Kuma ba shakka zata game fuskar ta da Sauri ta Mike ta fita a class in ta sauka a barandan su. Block in junior ta shiga class by class amma koh Mai Kama da zulaihat bata gani ba sauka tayi a baranda har tazo tsakar compound na makaranta motar gidan su Lahab ta danno Kai cikin makarantan muneera ce ta balle marfin motar sai Rahab daya fitoh a gidan gaba sosai Nnenna ta daskare a wajen tana bin dan uwan nasa da kallo cikin Al'ajabi don ita a zatonta Lahab ne yazo makaranta da Sauri ta nufesa ganin zai hau block in class nasu tace"Lahab tsayawa yayi Yana kallon ta da mamaki duk da yasan ba shi ta sani ba amma ya cika da mamakin Inda tasan Lahab don shidai bai taba ganinta a school in ba"ya jikin naka Wai har an kunce hannun ne"?ta ce tana kallon sa, murmushi kawai yayi yace Mata"da sauki sosai amma baizo ba"waro Ido tayi kenan wannan ba Lahab bane lallai kam,card data dauko da niyar baiwa zulai ta Mika masa tace"gashi na Lahab ne Inka koma ka basa" hannu yasa ya karbi ATM in Yana jujjuyawa juyawa tayi tana tafiya shidai Yana tsaye har lokacin Yana binta da kallo Harta shiga aji shima juyawa yayi ya wuce nasu ajin. *************** Adewale na barin makarantan su mubeena gidan su Lahab ya wuce,zaune suke a daki Suna Hira kallon Adewale Lahab yayi yace"Wai Ade lafiya yanaga duk kabi ka ramene ga wani fara'a daka shigo dashi Kamar Wanda aka baiwa auren mubeena"kyelkyelewa da wata bazawaran dariya Ade yayi shima Lahab dariya yayi a hankali Yana kallon abokin nasa Addayiya ce ta turo kofar dakin fuska a hade tace"Kai Kunga banson hauka ya zaku zo ku zauna min a daki kunamin ihu bare ma Kai Mara lafiya surkuwar haleema tazo dubaka tana falon su zata shigo sannan kazo kana dariya a sama sama Kamar zararu"shuru sukayi gabaki dayan su basu kulata ba itama juyawa tayi ta bar dakin. "Bazaka gayamin meke maka Dadi Yana saka rama be Wai"?cikin murmushi Adewale yace"kasan yau Nina Kai mubeena makaranta a mota"waro Ido Lahab yace mota kwal uba yaushe ka samu mota Ni ban samu ba ai wallahi da sakel"kaga kwantar da hankalin ka Lahab ba nawa bane na David ne"? "Toh ya akai ta yarda ka dauketa wannan sarkin taurin Kai"murmushin dake fuskar sa har lokacin na Nan yace"Nabeel ya kirani Nan take ya sanar dashi yanda Suka Kaya,sosai Lahab yaji dadi ganin abokin nasa na cikin farin ciki yace"aiko aiki ya sameka Ade sai kayita fama aiki ya sameka soyayya ne Koh wahala"hararan sa Ade yayi ya zaro wayar ta ya nunawa Lahab yace"tabbas zata kirani kaga na samu hanyar communication da ita"gyada Kai kawai Lahab yayi Yana murmushi don shi soyayyar su dariya yake basa. muryan Addayiya sukaji tana cewa"Bismillah ki shigo Yana ciki shigo farida Sannu da zuwa,sai Kuma aka turo kofar Addayiya na gaba farida dake sanye da hijab har kasa babba sai socks dake kafarta kanwarta na gefe sanye da gyale,Suka shigo Zama farida tayi a kasan carpet in dakin duk yanda Addayiya taso ta zauna a kujera ki tayi shikam Lahab tunda ta shigo ya mugun hada rai Yana Mata wani kallo na bacin rai gata dai a fuska mutuniyar kirki har kwatance iyaye keyi da ita akan yaransu suyi koyi da halinta a unguwan amma basusan Kura bace da fatar akuya,ita Karan kanta jikinta yayi sanyi don kaf gidan Banda Anwar babu Wanda yake supporting in soyayyar su sosai irin Lahab so dubu in Suka hadu ya ringa tsokanar ta kenan San bai rike girman sa na surkinta bappan mijin da zata aura ba,amma abin mamaki yau Koh kallon arziki bata samuba amma ta alakanta abin da ciwon dake damunsa ne kawai amma ganin yanda ya juya ya Kama hira da Ade sai taji ranta ya baci sallama Tama Addayiya Suka tafi. Bayan fitar su juyawa Ade yayi ya kalli Lahab yace"Wai Lahab wannan ba Amiran islamiyyar ku bace ustaziyar unguwan Nan Kuma matar da Anwar zai aura Kodai ba ita bace"ita ce Ade Meka gani"?da mamaki yace gani nayi kana Mata magana kamar maijin haushin ta Kuma Naga ba hakan kuka Saba magana ba last haduwar da nasan munyi da ita ma in ban manta ba ta fito islamiyya mu Kuma mun fito ball har kake cewa dole a auren su ayi program Kai babu ruwan ka da ustazanci ta ajesa sai bayan aure"? Kai wallahi Ade yanzun nayi mugun tsabar yarinyar munafuka ce Mai 2face ce"Kamar Yaya ban gane ba ya Kara tambayar sa nan Lahab ya zayyana Masa duk abubuwan da suka faru tare da kudurinsa akan wargaxa auren sai Kuma warning da Mami ta buga Masa akan zancen"rike Baki Ade yayi yace"gaskiya Lahab ba haka zakayi ba kawai ka rabu dashi ya aureta taima watakil auren ya zamo tsular shiriyarta sai kaga ta shiryu"wani kallo Lahab yayi Masa yace"kana nufin auren ta da Anwar zai nutsar da ita macen da aka sa date na auren ta har zata iyya fita hotel tsakar dare tana can akan me Koh kaffara bazanyi ba Anwar ba mazinaci bane akan me Zan bude Ido Ina kallo ya aure Mai dattin Mara tazo ta Haifa Masa yara Yan iska karfa ka manta duk abinda mace ta aikata zata gani a kwartar tuwon ta sai Wanda Allah ya sosu suke ganin daidai amma mace batayi iskanci bama ya ta Kare bare tayi Kuma Ni abinda ke dad'a batamin Rai shine fuskar mutanen kirki da take dashi wallahi saina tona Mata asiri don ubanta" Sosai Ade ke kallon Lahab Yana mamakin soyayar dake tsakanin su da Yan uwan sa yace"kaga nifa yanzun shawaran da Zan baka d'aya ne karka tona Mata asiri a bayyyane baka da hujja in dai baka iyya Kama barawo ba shi saiya Kama ka Mami nada gaskiya gwara kayi shurun kawai"wallahi bazanyi shuru ba"Lahab yace,ok in bazakayi shuru ba toh kasani indai zaka Hana auren ka Hana a zahiran ce ba a nuni ba kasa Anwar ya ganta da kansa"sosai Lahab ya zagu yace toh ta Yaya kenan"Baki Ade ya bude zaiyi magana saiga Kira ya shigo wayar mubeena dake aljuhun sa zaro wayar yayi Yana kallon screen in waya. Mubeena mikewa tayi tayi summit na paper ta da wuri tana Allah Allah Kar Rukayya itama ta Mike tana mikawa da Sauri gudu gudu ta fita a class in rataye da jakan ta bayan hall Inda ba mutane sosai ta nufa don ta tabbatar in taje cafe Ruky zata iyya ganinta itakuma yanzun batason wani alaka ya sake shiga tsakanin su da juna tafison tayi rayuwarta Kamar da Kamar batasan Ruky a duniya ba Zama tayi akan kututturen itace dake gindin bishiyar leam dake wajen jakan ta ta bude tasa hannu zata dau wayarta wayam kake ji bataga waya ba hankalin tane ya tashi ta shiga dube dube tana zaro material nata dake cikin jakan dan dakatawa tayi tana wani nazari in dai bata manta ba Kamar lokacin da suke tawowa Yana hannunta time to time tana duba lokaci sai Kuma kusan accident in da sukayi daga lokacin Kuma ta kasa tuna yaya wayar ma yayi "Allah dai ya Soni Kar a wani wajen na yatsar da wayar" da Sauri ta Mike ta Kama hanyar hall tana shiga lokacin an gama summit gabaki d'aya ajin sai dalibai daidaiku dake tsattsaye wasu a zaune Suna jiran next paper ganin ba Ruky a cikin hall in ya sata karasowa wajen da ta zauna tana dudduba wajen Koh Ta bar wayanta a wajen amma babu,lawiza dake zaune ita da wani Suna duba jotter ta matso wajen su tayi da sallama tare da rokon lawizan ta Ara Mata wayarta zata Kira wayarta,Mika Mata lawizan tayi da Sauri ta amsa ta loda number ta a ciki tare da karawa a kunne,daidai lokacin Ruky da tunda mubeena ta fita itama ta kammala da Sauri tabar ajin sosai tayi ta yawon Neman mubeena Amma Bata ganta ba tana ta tambayar mutane,sai Kuma ta hango mubeenar ta shiga Hall na exam da Sauri tamike daaga Inda suke tsaye ta nufi hall in..................... πŸ€ *By Ruqeenjalal* πŸ€ *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki* Page 77&78 Kauda idanunta tayi daga Kan na Ruky Jin an d'aga wayar tayi sallama, Adewale dake Kare da wayar a kunne amsawa yayi cikin Jin dadi Jin muryarsa yasa ta tamke fuska ta sabe jakanta a kafa hade dama lawiza nuni da hannu tana dawowa,tare ta Ruky dake tsaye tayi tace"haba mubeena yau throughout nayi ta neman ki a school Nan ban ganki ba sannan yanzun kin gannin Zaki wuce"?fuska mubeena ta sake Kamar ba kome tace"waya zanyi Kuma Ina bukatar sirri tana karasa maganar ta rabata ta wuce Ruky Baki ta sake tana binta da Ido hartabar hall in mamaki na cikata Koh Ahmad a gabanta mubeena ke waya dashi tunda suke mubeena bata tana zakud'awa da sunan amsa call ba koma waye ya kirata sai yau Zama tayi a kusa dasu lawiza tana sauke a jiyar zuciya kallon ta lawiza tayi sai Kuma ta tabe Baki batace kome ba. Adewale dake Kare da waya a kunne Yana Jin duk abinda Suka fada, murmushi yayi yace"wake magana ne"?aikafi kowa sanin wake magana na d'auka wayar faduwa tayi tunda Yana hannun ka Inna dawo school na samu a gida"tace Masa cikin gara-gara shikam hade fuska yayi Kamar tana gabansa yace"kee Ni kike bawa umurni inkai wayarki gida kafun ki dawo toh in kikayi Wasa ma wayar tasha kenan Naga ta tsiya"waro Ido tayi tace"Kai Ni kake ma magana haka"?an Miki nace an Miki ke karfa ki Raina Ni don nace Ina so ki Ni ba irin mazan Nan bane bita zaizai"katse wayar mubeena tayi cikin bacin rai ta zauna a bakin baranda tana kitsema rashin mutunci da zata maka Masa duk lokacin da Suka hadu,mikewa tayi ta shiga Hall in har lokacin Ruky na ciki, mikawa lawiza wayar tayi Mata godiya ta juya tabar ajin. Sauke wayar yayi a kunnen sa yakai duban sa ga Lahab dayayi tagumi hannu bibbiyu Yana kallon sa"Kai menene haka ka tasani agaba Kamar TV"?ba dole ba Adewale Ina ganin ikon Allah kalar soyayyar Nan taku tana ban dariya Kai a dole kayi waya da masoyiya sai Kuma ya kwanta ganin Ade Bai kulasa ba Yana sake Kiran number da mubeena ta kirasa dashi. Lawiza ce ta zaro wayar tata tana kallon number Kamar bazata d'auka ba sai Kuma tayi picking call in ta Kara a kunne tare da sallama amsa mata Ade yayi Jin ba muryar ta bane yasa sa cewa"am dan Allah Koh mubeena na kusa ki bata wayar"lawiza tace"am sorry ta fita amma inta shigo na bata ta kiraka"no ki bari kawai basai kin bata ba in ba damuwa Zan iyya sanin time in da zaku kammala paper ku na yau"?dan shuru tayi tana tunanin ta fada Masa ne Koh karta fada Masa sai Kuma tace"3:30 afternoon zamu tashi, ok toh na gode katse wayar Adewale yayi ya mike tsaye Yana kallon Lahab sai Kuma ya nufi kofar Yana ce Masa"kaga nayi tafiya ta sai anjiman ka Allah ya Kara sauki"kala Lahab baice Masa ba Harya fita a dakin. Misalin karfe 3:30 Ade ne cikin mota zaune a haraban makarantan Yana wowola Ido ata Ina zai ganta Kamar daga samq yaga ta fito a class tana Sauri ga dukkan alamu akwai Wanda batason ya ganta ne, fitowa yayi a mota ya tsaya Yana jiran karasowar ta itakam ma baka kula dashi ba hartazo zata gifta ta gaban sa,yace"malama dan dakatawa tayi sai Kuma ta kallesa wani harara ta watsa Masa tacigaba da tafiyar ta binta yayi Yana magana amma fir taki sauraran sa kasa hakuri yayi yasa hannu ya riko nata,da Sauri ta juya hade da d'aga hannu zata watsa Masa Mari sai Kuma ta tsaya tana bin fuskarsa da kallo ganin yanda ya rumtsa idon Yana jiran tsammanin ma rabbuka. dai dai lokacin su Ruky Suka fito da sauran friends nasu tsayawa sukayi Suna kallon show in dake gudana a tsakanin Ade da mubeena sauke hannunta tayi taso fusge hannun da ya rike amma ta kasa saima janta da yayi da karfi ya bude gaban motar ya jefata,ya maida murfin ya rufe kokarin bude motar take amma ta kasa da Sauri ya zagaya ya bude driver sit ya zauna tare da tada motar bai kula da masifar da take Masa ba. Tafiya suke shuru babu Mai magana hannu tasa ta bude jakan makarantan ta ta zaro memo nata tana lissafe lissafe tare da list in abubuwan da zata saya kwata kwata 3k ne kadai ya rage Mata shima cikin Wanda Ahmad ke bata tana Tarawa ne so take Tama Lahab delicious Mai dadi insun tashi zuwa dubasa takai Masa,tama rasa mezata saya tasan kaza dai intace zata saya da sayyayyan sa sai yafi 3k Yanke shawaran saya masa ice fish da sweet potatoes list takeyi tana gogewa sai ta gama inta buga calculate sai ya bata sama da 3k tsaki kawai taja ta cilla paper gefe ta dafe kanta tama rasa Mai zata saya na marmarin tasan kome ta sayo Masa akwai fiye da hakan a gidan su. Adewale da duk hankalin sa na kanta Yana kallon duk wani movement nata"tsaya Zan sauka anan tace daidai lokacin Suka iso titin kasuwa tsayawa yayi yasa hannu ya dau paper kokarin kwacewa tayi yayi Sauri ya boye Yana murmushi yace"ke behave yourself Mana me haka"batayi magana ba sai kokarin fita da tayi tana fita shima ya fita ya rufe motar tare dabin bayan ta ganin ta nufi tsallaken titin,binta yayi a baya Yana kallon list in dan dakatawa tayi Harya karaso kusa da ita tace"Wai ya haka ne Mena Bina a Baya"kin kulata yayi Yana Kuma tsaye Kara footsteps tayi again ya bita abun haushi ya Bata sosai hakan ya sata Neman waje ta zauna shima zaman yayi Koh a jikin sa,ganin lokaci na gudu har ana Neman 4 na yamma yasa ta mikewa bata kulasa ba tayi cikin kasuwa Yana binta a baya,rumfan dankwali ta nufa tare da zaro 1k tace a Bata,kallon Mai rumfan Ade yayi yace a zuba Mata na 5k Aiko da Sauri Mai rumfan ya Fara zubawa kallon list in Ade yayi Yana Masa lissafin kayan gwari dake rumfan sa Wanda ta rurubuta,Kuma da yawa yawa yake saya itadai mubeena yunkurin barin wajen tayi yasa hannu ya damko hannunta zaro Ido tayi ganin yanda idon mutane ya dawo kansu abinka da cikin kasuwa tsoro ne ya kamata tahau rokon sa da Allah bai sakar Mata hannun ba Saida tamar alkawarin bazata tafi ba. Gyada Masa Kai tayi ta fizge hannunta tare da jingina da kantin sayayya tana tsinewa Nabeel a ranta daya hadata da wannan fitina,sayayya yayi sosai sannan ya kalleta hade da cewa muje Koh binsa tayi a baya har wajen Mai kifi kusan guda shida manya manya na dari biyar biyar ya saya musu,tafiya suke bayan sun fito a kasuwar babu Mai magana har Suka iso unguwan nasu har kofar gidansu ya kaita Yana parking ta Mika Masa hannu hade da cewa"ban wayata Adewale"kin bata yayi sai bude motar da yayi ya sauka hade da bude boot Yana sauke laidodin cefenen juyawa kawai tayi ta nufi cikin gida batabi ta kansa ba dayake ta kwala Mata Kira akan ta tsaya ta dau cefenen amma Bata saurare Saba. Bayan shiga gidan mubeena tsaye yake a kofar gidan nasu Sam ya kasa shiga haka kawai yaji baison shiga yafi 20 minutes a wajen ya hangi Nabeel ya fito matsallaci yana nufo gidan nasu tun daga nesa ya hangosa karasowa yayi cikin fara'a ya dake kafadar Ade hade da cewa"mutumina ya na ganka tsaye da laidodi baka shiga ba Kuma" Kaga Nabeel mubeena na dauko daga makaranta muka tsaya a kasuwa tayi tsayya Wai kawai don na biya shine taki karban kayan,wani kallon tuhuma Nabeel ya Masa yace"kana nufin ka koma ka daukota kenan"?dan cijewa Ade yai gudun karya bada kansa yace"eh na koma na dauketa saboda wayarta data Bari a motar Yana maganar ya Mika ma Nabeel wayarta karba kawai Nabeel yayi sannan Bai gamsu da zancen ba amma dai baice kome ba ya karbi cefenen ya shiga gida sauke ajiyar zuciya yayi ya shiga motarsa yabar arean nasu. Aje cefenen Nabeel yayi a gaban mubeena dake cin abinci a tsakar gida hade da d'osana Mata wayarta akan cinyarta baice kome ba ya shiga dakin sa,mikewa Inna tayi tana tambayar mubeena hade da bude laidan tace"ya haka Nabeel zaka kawo Abu bazaka Mana bayani ba saika aje ka tafi Kamar ka samu wahalallu washe baki tayi ganin kifi manya da dankali ga kayan Miya enough"ah ah ikon Allah Nabeel wannan tattakwashin fa na menene Koh dai laidan cefenen wani ka sato don nasan Kai tsoron Allah Bai wadace kaba"? Lekowa yayi daga cikin dakin NASA fuska a daure yace"waini me Kika maida nine toh cefene dai ba nawa bane na mubeena ne sako aka ban na kawo Mata in Kuma bataso ki amsa kawai rabonki ne"juyawa Inna tayi ta kalli mubeena da kyau Jin abinda Nabeel yace tace"kee Yar nema waye Kika aika Koh ya bada sako a baki,Ni ban aike kowa ba,da mamaki Inna tace Nabeel kanaji Wai Bata aike kowa ba toh Kai waya baka"?fitowa yayi gabaki d'aya daga dakin nasa yace"Adewale ne yace sunje kasuwa shine tayi cefene ya biya itakuma taki amsa" Mikewa kawai Inna tayi ta shiga daki tabar cefenen a wajen shima Nabeel keken sa ya hau ya Kama dinki bai sake magana ba tana gama cin abinci sallah tayi tadau cefenen tayi kitchen dashi ta Soma girki. ******************** 5:26pm mota ce tayi parking a tsakar gidan sauka Yan makarantan sukayi duk a gajiya kowa na goye da school bag nasa a baya zulaihat ce a gaba Kamar zataci da Baki saboda fitsari daya cika Mata Mara Kuma batayi a makarantan ba Saida Suka shiga mota ta farajin sa sosai shigowa falon sukayi ita da muneera sukayi sashen su,shima Rahab nasu sashen ya nufa tura kofar yayi ya Shiga wanka yayi ya sanya kayan gida da Sauri ya fita a dakin kitchen ya shiga Suka kusa cin Karo da muneera d'auke da plate na abinci a hannunta matsa Masa tayi ya shiga kafun itama ta fita abinci ya zuba a plate ya dau drink Mai sanyi ya fita a dakin Zama yayi a babban falo Yana cin abincin sa,Saida ya gama tas kafun ya mike baidau kwanon bama ya tafi ya barsa a wajen. Zaune Lahab yake gabaki d'aya ya tattara hankalin sa Akan TV dake aiki a dakin ball take kallo gabaki d'aya wasan ya tafi da imanin sa aka turo kofar dakin,d'ago kansa yayi ganin Rahab ne yasa sa maida Kan ga TV,Zama Lahab yayi a gefen sa Yana kallon sa a hankali yace"aikin kenan baka bawa kome muhimmaci sai ball wallahi Lahab gwara ka gyara rayuwar ka wannan bayi bane"wani kallo Lahab ya Masa sannan yace"Kai da Allah dakata nifa kana kallo na innan insha Allah abinci na na cikin kwallon kafa Kuma Kai da kanka ka San na iya"da mamaki Rahab yace shi kwallon kafan ne abinyi"?kwarai ma kuwa Kai kasan kudin da yan kwallon suke samu kuwa Kuma Ni Koh ba kudi yake kawowa ba nidai Ina da sha'awar Yi"? Mika Masa card nasa kawai Rahab yayi yasan duk abinda sai gaya Masa Lahab ba ganewa zaiyi ba"amsar card in Lahab yayi da mamaki yace"a Ina ka dauko ATM nawa"? Tashi tsaye Rahab yayi yace"ita ta bani a school"zaro Ido Lahab yayi yace"ita wa"?Wance ka baiwa card in Mana Koh kana nufin baka bata bane"?shuru Lahab yayi bai amsa Masa ba shima Rahab bai motsa ba sai Kuma ya koma ya zauna tare da fuskan tar dan uwan nasa yace"wacece don Allah"? remote Lahab ya d'auka ya Kara volume na TV ya mimmmike kafa ya cigaba da kallon sa Bai saurare Saba. Bayan mangariba zazzaune suke akan dinning Suna dinner gabaki dayan su Lahab da Addayiya ne kawai basa dinning in don tunda Lahab ya dawo basu cika cin abincin da aka dafa ba shida tsohowar tsabar irin girke girken da ake kawo musu na namomi gashi yauma mamin sa ta turo su mahraz sun kawo Masa pepper chicken,ya jafar ne da iyalan sa Suka kwada sallama a falon amsa musu akayi gabaki d'aya cikin farin ciki zazzaunawa sukayi a falo mamu ta Mike taje ta dauko musu drink's da water ta aje musu gaggaisawa akayi Majid ya mike direct ya nufi dakin Addayiya don sunyi waya da lahab,tura kofar yayi Koh sallama babu zaune Lahab yake Yana cin kwai dafeffe,mikewa Addayiya tayi da plate na nama a hannunta ganin Majid yasa ta sakin tsaki amma batace kome ba ta koma ta zauna tana holo yashigo ba sallama Kamar dan kafurai shidai bai kulata ba sai zaman da yayi akan gadon ya kwace plate na kwai dake gaban Lahab ya d'auka ya Soma ci,da Sauri Addayiya ta kwace tace"Kai majidu baka da kunya Meka kawo Mana bare kazo ka samu dan marayan Allah Yana fama da jiki ba tausayi ka dau kayan jinya kana lashewa ai wannan mugunta ne? Kala baice Mata ba sai kallon Lahab dake kallon sa yayi ya kalli Addayiya sai Kuma ya mike tsaye yace"don Allah ka tashi muje dakin ka menene na Zama a dakin tsohowar nan duk warin tsufa"uwarka da ubanka ne masu warin tsufa bani ba dan banza kawai gagare"ganin fad'an nason girma don sai CeCe kuce suke yasa Lahab mikewa ya nufi kofar Yana ma Majid magana akan suje sashen su,Majid Saida ya Bari Lahab yabar dakin kafun ya fizgo laidan kazar dake gefe ya fita da gudu a dakin. *************** Kafun mangariba mubeena ta kammala girkin ta dankalin turawa ne ta soya sai ferfesun kifi ice fish,duba kwanukan nasu tayi gabaki d'aya sun tsufa Basu da kula sabo raba abincin tayi ta zubawa Inna nata da ban Nabeel da ban tasa nata sauran data keda niyar kaiwa lahab,hijab nata ta rufa ta fita gidan wata amarya dake kusa da gidan su,Kuma tayi sa'a ta samu Sabon kula guda biyu na tuwo dana Miya,sabo gal Mai kyau dawowa tayi ta zuba dankalin daban kifin daban ta aje a kwando,ita dai Inna da Ido kawai take binta,wanka tayi Koh abinci ta kasa ci bude akwatinta tayi ta dau wani less nata Mai kyau purple zani da riga gyale fari ta d'auka da takalmi ta yafa fitowa tayi a dakin a Karo na hudu tana duba Inna amma abin haushi har lokacin batayi niyar mikewa ba kasa hakuri tayi ta tama inna magana tana cewa"haba Inna dare fa nayi don Allah ki tashi mu tafi Mana Ina da karatun da zanyi fa"kallon ta da kyau Inna tayi tace Wai ke yaushe kuka Fara shiri da Lahab in har kike rawan kafa zakije ki duba sa ga wani uban cefene da kikayi Kamar Zaki gidan surkunaye"gabanta ne ya yanke ya Fadi Jin Inna ta jefo jirginta amma ta dake tace"shikenan nama hakura da zuwa"tayi Kamar zata koma daki amma a cikin zuciyar ta Allah Allah take kada Inna taki tsaidata. Wallahi baki Isa ba tun yamma kike uzzuramin sannan yanzun kice kin fasa zuwa, bari ma nadau hijabina muje,dakatawa mubeena tayi ta hade rai ta tsaya tana jiran Inna data shiga daki dauko hijab nata,kulan abincin ta d'auka ganin Inna ta fito rurrufe kofofin su mubeena tayi Suka fita a gidan,tunda Suka dotse gate na gidan su Lahab gabanta ke faduwa rabon ta da ta Shiga gidan Harta manta tun wani Shiga da tayi Mami taci Mata mutunci tun Suna yara Bata sake taka gidan ba sai bana da zata yanda suke nufo gidan haka dukan da kirjinta keyi yake daduwa,wutan lantarki ne Kamar rana yake tsaye a kofar gidan ga flowers dake shiki,hannu Inna tasa ta bubbuga gate na gidan.................................................... πŸ€ *By Ruqeenjalal* πŸ€ *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki* Page 79&80 da Ido Mai gadin ya bisu sannan ya bude gate in tare da matsa musu saboda ya gane Inna ba yau ta Saba zuwa ba Akan Case in Lahab da Nabeel tun Suna yara,tafiya suke mubeena na binta a baya duk inda Suka wuce sai mubeena ta Kara waigawa ta kalla da kyau gidan gabaki d'aya ya chanja Mata ganin irin daular da yake ciki yanzun sama da da,tsayawa sukayi a kofar falo Inna nata kwada sallama dayake daman kofar in ba bell aka danna ba ba Jin mutum za'a Yi ba in Yana magana hannu mubeena tasa ta danna kararrawan. Kallon ya Umar ya jafar yayi yace"gobe in Allah ya kaimu za'a kawo lefen yarinyar Nan umaima Koh"?kwarai ma kuwa gobe ne insha Allah"toh Allah ya kaimu saiku tashi mu tafi dare nayi sai Allah ya kaimu gobe in zaku dawo ma saiku dawo,mikewa dukansu sukayi harda nenne duk da yaran sunso a barsu su kwana amma ya jafar yaki yace gobe akwai school,kallon nanne yayi yace"Ina Majid in da Aisha kuma"mamu ce tace wata kil Majid na wajen Lahab ita Kuma Aisha bazai wuce tana can tana like da umaima ba, kasanta da zancen zuwa biki daga auren mutum ya tashi zata Fara like Masa"Addayiya dake zaune ne tace,kaji Shashashar banza ke zulai shiga ki kirata Kai Kuma uzaifa kirawo Majid in yazo mu tafi"ring na bell Inda sukaji shiyasa Anwar mikewa ya nufi kofar kamawa yayi ya bude sai Kuma ya waro Ido yace"innan Nabeel yau Kuma me Lahab yayi kin fa San baida lafiya Koh fita bayayi karma kice Yama Nabeel kaza"?hararan sa tayi da murmushi a fuskar sa ya matsa Mata ta shige mubeena na binta a baya tad'anji sanyi ganin yaran gidan har yanzun Basu da girman Kan masu kudi in ka cire Shareef yafi kowa mugun hali da murd'adden hali a gidan. Ah ah sannu da zuwa wa nake gani Kamar Inna kayyu?da murmushi Inna ta karaso cikin falon ta zauna akan kujeran da Addayiya ta tashi tana nuna Mata ta zauna mubeena Kan kanta a kasa tazame ta zauna a kasan carfet"nice hajiya Asma'u"gaskiya ne barkanku da zuwa haba Yan Mata ya da Zama a kasa ki hau Kan kujera Mana kin hawan mubeena tayi sai wani susunkuyar da Kai take komawa zaune ya jafar yayi Suka gaggaisa dasu Inna, fitowa umaima tayi da hijab a jikinta sai Aisha dake gefenta Suna magana a hankali Suna dariya tare da muneera da aka aika ta Kira Aisha kallon umaima mamu tayi tace"ke Kuma meye haka Ina Zaki"dan rausayar da Kai umaima tayi batace kome ba sai Aisha ce tace"mamu Wai zata bimu gidan mune kinsan gobe za'a kawo Kaya shine Wai tanajin kunya"rike Baki Addayiya tayi tace"kunya Kuma Koh munafurci koma menene kwadaiji dashi,mikewa ya jafar yayi again Yana kallon uzaifa daya fito babu Majid kallon sa yayi ya tambaye sa Ina majid in?Wai shi Anan zai kwana"shuru kawai Addayiya tayi Albarkacin su Inna dake falon da wallahi Majid bazai kwana musu a gida ba,fita ya jafar da iyalan sa sukayi su ummu da sauran yaran Suka rakasu compound har gaban mototin su, Bismillah kuzo muje kugansa Yana dakin su,mikewa sukayi Suka bi bayan ta tana gaba Suna bayan ta har lokacin hannun mubeena d'auke da kwandon kwanuka gabaki d'aya jikinta yayi sanyi zuwa da tayi ta tarar da plates na kaji Baja Baja a falon da abinci Mai Rai da lafiya Wanda aka kawowa su nanne,sai taji ta muzanta ita da ferfesun kifin ta da dankali. Zaune suke da Majid Suna Hira system na Rahab ne a gaban Lahab Yana chatt nasa sai Majid dake Masa Hira Yana cin kazar daya d'auka a dakin Addayiya,turo kofar dakin a kayi Addayiya ta shigo Inna na binta a baya waro Ido Lahab yayi da Suka had'a Ido da mubeena"Bismillah ku zauna ga waje Addayiya tace musu Zama sukayi"kallon Inna Lahab yayi ya gai data ta amsa tare da Masa ya jiki mubeena ce ta Fara Masa ya jiki ya amsa hade da cewa"big Aunty mekika kawo minine haka Naga kulan sabbi alamu dai abun ciki ba karamin dadi zaiyi ba"?dariya Inna tayi tace aiko ka canka daidai kasan Ni bazan tsaya bata lokaci wajen maka girki ba"da murmushi Lahab yace"kaiyya Inna Ina ma Kika iyya bare yayi dadi"dariya dukan su Yan dakin sukayi Majid Kam Inna kawai ya gaidar idanunsa Kam akan mubeena Wanda yasa Lahab sa hannu ya mintsine Naman cinyan sa dan Kara ya sake ya sauka akan katifar ya koma kasan carfet ya zauna Yana jama Lahab Allah ya Isa,kallon kulan Lahab yayi sai Kuma ya mike ya dawo kusa da mubeenar hannu yasa ya bude kulan sai Kuma da Sauri ya kalli mubeena,mikewa yayi ya dawo bakin gadon da kulan ya aje sai Kuma ya sake budewa yadau marfin ya zuba dankalin akai yasa miya ya Kama ci,Yana gyada Kai sosai mubeena taji wani mugun dadi ganin Lahab yaso abinda ta kawo duk da sunada fiye da hakan a gidan su,duk kankantan kyauta da mutum Yama Lahab baya botsaresa sosai yake nuna Masa ya kaunace abin Koh da kuwa bai Masa ba baya nunawa. Mikewa Inna tayi tace toh hajiya mu zamu tafi Allah ya kiyaye na gaba"Ameen Suka amsa duk da mubeena bata ji dadin tafiyar da Inna tace zasuyi yanzun ba amma ba yanda ta iya haka sukayi sallama da mutanen gidan Suka tafi,Suna fita a dakin Lahab ya aje plate in don harga Allah ba yunwa yakeji ba kawai dai yayi hakan ne don nuna Mata Jin dadin sa Sarai yasan halin mubeena haka zalika karon farko data dau Abu ta basa cikin mutunci babu masifa"da Sauri Majid ya dawo kusa dashi Yana bin kofar da kallo har lokacin sai Kuma yace"Kai wannan fa wacece Ni fuskar tama familiar ne gareni"hararan sa kawai Lahab yayi baice kome ba naci sosai Majid ya ringawa Lahab a Kan mubeena amma bai kulasa ba gajiya Lahab yayi yace Masa"kaga Majid banason surutu haba don Allah Kai baka Isa kaga Mata ba jikinka sai ya ringa rawa toh ka kiyaye kanka wallahi"tsaki kawai Majid yaja da Sauri Lahab yace"yauwa don Allah Ina so ka taimake Ni"wani banzan kallo Majid yayi Masa shima baice kala ba matsowa kusa dashi yayi Yana rokon sa. Hannu Majid yasa ya hankada Lahab Sora kadan yafadi akan hannun sa mikewa Lahab yayi ya shiga toilet bucker ya cika da ruwa Majid na kwance kawai yaji an kwarara Masa ruwan sanyi kafun ma ya dawo hayyacin sa Lahab yabar dakin da gudu yayi dakin Addayiya tare da maida kofar ya rufe yahau Kan gadon ta ya kwanta sai bacci. ***************** Zaune take rike da wayar da Abraham ya kawo Mata tare da dogon gargadi kada ta bari kowa ya gani sosai take jujjuya wayan babba be babu laifi Kiran Tecno danna wajen da yace Mata zatanayi in zata kunna tayi take haske ya kawo sosai take kallon screen in wayan tama rasa ta Ina zata Fara wannan shine Karo na farko data rike waya nata na kanta papa nada waya amma karamace ba irin wa'innan ba,shige shige ta Fara kasancewar ta Yar makaranta waya bazai bata wahala sosai ba shige shige tayi tayi har dare sosai,kafun ta kashe wayar kiki ta d'auka ta basa magani ta kwantar dashi itama ta kwanta abinta. Washe gari da safe tun asuba ta tashi share gidan tayi da wuri Kamar kullum ta Gama aikin ta na safiya ta shirya ta tafi makaranta Kamar jiya yauma Abraham ne ya kaita duk da mom bata so amma babu yanda ta iyya ganin yanda Dad ya Soma chanjawa a Yan kwanakin Nan. ********************** Bayan sallan asuba gabaki d'aya Yan gidan sun koma bacci sai kusan 7 Suka hallara akan dinning yaukam harda Lahab abinci sukeci Majid ya kalli Abbu yace"Abbu wallahi jiya Lahab jika katifar da Zan kwanta yayi ya jikani da ruwa karshe ma dakin Shareef na kwana"shuru Abbu yayi nadan wasu minutes kafun yace"Kaga Majid kaci abinci kawai ba'aci ana magana tsakanin ka da Lahab Kuma bansan Wanda yafi wani ba"yunkurin magana Majid yayi Abbu ya d'aga Masa hannu alamun ya mishi shuru kenan,shurun yayi Suka cigaba dacin abincin d'aga Ido Abbu yayi ya kalli mamu dake zaune fuska babu walwala hatta yaran Karan kansu sun fahimci akwai abinda ke damun ta,mikewa Abbu yayi cikin Sauri yadau jakan system nasa da Sauri muneera itama ta Mike hade da karban jakan ta nufi kofa,mikewa mamu tayi a fusace ta nufi sashen su ganin Abbu Harya nufi kofa baice Mata kome ba don jiya ma ba girkinta bane amma haka taje ta samesa akan kudin sayayya ya koreta gashi yau yayi ficewar sa bai bata ba,yaran Kam binta kawai sukayi da Ido Harta mule musu, amma basu ce kome ba duk da sunyi mamakin yau ranan kawo lefen umaima amma fuskar mamu ba walwala. Mikewa sauran yaran sukayi Suna fiffitowa da d'ad'aya d'ad'aya Inka cire Majid da Lahab dake zaune har lokacin a dinning Kuma sune kadai bazasu makaranta ba(gagararu)Kamar an mintsine sa da Sauri ya mike gudu gudu Sauri Sauri ya fitoh a falon Aiko yayi sa'a su Rahab basu tafi ba, wajen sa ya matso yasa hannu ya jawo sa kusa dashi cikin kasa kasa da murya yace"don Allah Rahab so nake ka hadani da yarinyar da ta baka card jiya zamuyi magana ne a waya"wani juyawa Rahab yayi da kyau ya kallesa sai Kuma ya girgiza Kai ya shiga motar ya rufe baice kome ba aka ja motar Suka bar gidan komawa cikin gidan Lahab yayi ganin motar Dr ya shigo gidan nasu ya daura Masa ruwa da Allurai. Mamu na shiga daki rai a bace ta zauna akan gadon ta tana kintsema irin wulakancin da Abbu ya Mata duk da tana da kudin itama Abba tanajin zafin kashe kudinta,Kamar ance ta d'aga Ido kawai taga card nasa akan pillow da Kuma pepar da Sauri ta matsa wajen ta dau card in take murmushin ya bayyana a fuskar ta ya yalwata sosai bude takardan tayi tana karantawa Kamar haka"toh sarkin son kudi Naga kin tashi sai wani harhada Rai kike waike Halima tunda nace Zan baki kina tunanin bazan bada bane toh ga card Nan banyar da ki kashe sama da dubu dari biyu ba don nasan ki"?da murmushi ta Mike ta dau wayar ta kiraye kirayen kawaye ta ta Shiga da kannen ta Akan suzo suje Mata cefene Kamar wani bikin ake. Gidan su Lahab yanda kukasan gidan biki Kamar yau za'a daura aure saboda yawan kawaye da mamu ta gayyata karban Kaya sai zuzzuta zancen kayan take da kawayenta, Mami Kam batama San zancen kayan ba sai da azahar data shigo gidan taga Mata birjit gashi sai girke girke ake ana suyan kaji,da mamaki take gaida kawayen mamun da kannen ta amsa wa suke a daddage,Shiga cikin falon tayi hannunta dauke da laida hallo cikin ma da Mata gidasu tayi ta wuce sashen su Rahab zaune ta yarda Addayiya a falo sai ummu dake zaune Suna hira,karasowa falon tayi ta zauna Suka gaida sanan tace"Wai Addayiya meke faruwa ne Naga gidan a ciki"?meke Kuma faruwa banda Yar Nan umaima yau dangin yaron Nan sadeeq zasu kawo Kaya shine duk tazo ta cika Mana gida da jama'a Suna shewa Suna suya"da mamaki Mami tace"yanzun Addayiya haleema za'a kawo kayan yarta amma ba Wanda zai sanar dani"?ummu ne tace"Kinga Amina muma bamusan da maganar kayan ba sai da Addayiya ta fada"mikewa mamin tayi ta shiga dakin Lahab kwance yake hannunsa d'auke da ruwa shikadai ne don Majid ya fita,shigowa tayi ta zauna a bakin gadon tasa hannu ta taba wuyansa bude Ido yayi ganin Mami me yasa sa komawa baccin da yake. Har zuwa yamma Mami na gidan duk da taso shiga ciki ayi aiki da ita Amma Jin yanda ake tsoka Mata magana yasa ta zame jikinta ta dawo tayi joining su Addayiya da ummu a falo Suka cigaba da zaman su,wanka yan Koran mamu sukayi akasha less da zanunuwa ansha d'auri ana jiran baki,da misalin karfe biyar na yamma lokacin yaran gidan wasu sun daddawo makaranta harsunyi wanka mazan Kam tuni Suka bar gidan bayan sunci lunch nasu. Lahab sai hararan Rahab yake don bai hadasu da Nnenna ba bai kuma ce Masa kome ba,mami taso tafiya ganin har yamma ba'a kawo Kaya ba,amma ummu ta hanata gudun kada ummu tace hassada ce ya hanata Zama don tun safe zance daya mamu keyi yaudai makiyanta sai dai su mutu saidai su rufe idanun su yarinyar ta tayi goshi insha Allah kayan da za'a kawowa umaima har a gama aurar da yaran gidan baza'a kawo musu irin Shiba, danta Anwar ma akwatuna 12 ta had'a Masa za'a Kai wani sati Kuma tasan sadeeq zai had'a sama dashi. Wangale gate na gidan akayi mota daya ya shigo rufe gate in Mai gadi yayi aka bude motar wasu matane guda uku Suka fito a motar,Jin mota ta shigo yasa mamu mikewa tabar falon ta shiga dakin ta Yan uwanta ne da kawaye suka tarbo bakin shigowa sukayi namijin daya kawosu shiya Fara shigo da akwatunan baza Ido manyan matan sukayi Suna kirga a kwatunan ganin mota daya ne ya shigo basu tsammace hakan ba Saida ma Suka ga an aje akwatunan duka,daidai Nan Mami da ummu Suka fito falon,kwata kwata guda biyar ne da karamin kit................................ πŸ€ *By Ruqeenjalal* πŸ€ *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki* Page 81&82 Zama Mami sukayi matan Suka Soma sauke kayan akwatunan, ba laifi sadeeq yayi kokari sosai zanunuwa kam masu kyau akwai na dubu hamsin da ishirin ga lace masu kyau babu laifi Kam, finda kayan suke su Mami na kirgawa sukam kawayen mamu Jan jiki sukayi Suna shan kamshi Koh kallon arziki basu ma bayin Allah Nan ba,mikewa kawar mamu tayi ta nufi sashen su Mamun zata Kai Mata rahoto da Sauri yayar mamu ta Mike tabi bayan matan Harta kusa isa kofa ta kwala Mata Kira tsayawa tayi har yayar mamu ta iso kusa da ita tana cewa"ina Zaki hajiya Hanifa badai wajen Halima Zaki ba"?wajen tane Mana zanje na sanar da ita abinda ke faruwa"da Sauri addanta tace"Kinga hanifa mu koma falo kinsan halin Halima Sarai zata iyya bamu kunya akan kayan nan muje ku ibo abinda aka tanadar musu ku Basu suyi Subar gidan kafun Haleema tasan zancen kayan lefen Nan"haba adda taya zamu d'au abinda muka had'a da kusan rabin kudin lefen da suka kawo mu d'auka mu Basu haba dan Allah"da Sauri Adda ta nufi kofar Jin ana kokarin bude kofar mamu itama Hanifa da Sauri tabi bayan Adda. Mamu da taji surutu na tashi kadan kadan a corridor nasu shiyasa ta fitowa ganin ba kowa ya sata koma daki,su Karan kansu Yan uwan sadeeq jikin su yayi sanyi ganin yanda aka tarbesu Sam basuga fuska a gunsu ba saisu Mami dake Nan da Nan dasu Mami ce ta bude jakanta tadau gudan dubu duba sabbi guda ishirin ta Basu a matsayin kudin tukuici,Adda ce ta Mike ta shiga kitchen da kanta ta Soma d'auko Robobin kaji dasu donot da eggroll tana shigowa dasu falo ganin hakan yasa sauran Yan uwa mikewa da Sauri Suka shiga kitchen in daman robobi biyar suka shirya musu ganin Adda ta fitar da uku yasasu zuwa Suka dau biyun Suka saka a store Suka rufe duk yanda Adda tayi tayi dasu akan su bada biyu a Kai amma Suka ki,mikewa bakin sukayi sunata godiya Mami da ummu da Adda su Suka rakasu har mota. Mamu najin tashin mota daman tana bakin window da Sauri ta fito a dakin ta ta nufi falo,idanunta ne Suka sauka akan kawayen ta da Sauri ta karaso saboda Zama da sukai Suka tasa akwatunan a gaba shiya hanata gani magana ta Fara"Alhamdulilah yaudai Zan kwanta cikin kwanciyan hankali an kawo kayar diy...........kasa karasawa tayi kanin akwatunan da Sauri ta karaso tsakiyarsu tana nuna kayan da hannu tana tambayar su"wannan fa menene?Ina sauran akwatunan dakina fa za'a kai?da dariya Mai Kamar tura haushi Mami tace"kayan umaima ne da matan gidan Nan kaf bazasu samu irin Shiba shine aka kawo Kuma iyya kacinta kenan"jikin mamu har rawa yake tasa kafa tayi ball da akwatunan Kamar mahaukaciya tana rantse rantse wallahi sai an maida musu kayan su ita yarta ba Yar agwagwa bane da zasu aurar da ita haka da wasu shegun Kaya. Mami Kam tafiyarta tayi Koh a jikinta ummu Kuma tayi dakinta taje ta kwanta,sauran kawayen Mami abincin Robobin suka deddeba Suka bar gidan Suna kananun magana bayan sun zuzzuga mamu akan karta yarda karsu karbi kayan,Koh sallama basuma mamu ba saboda haukar da ta ringa zubawa akan kayan auren karshe ma tace baza'a Kai Mata daki ba Addayiya ce tadau kayan takai dakin ta,har dare mamu na dakinta ta kulle kanta bata tabajin kunya irin na yau ba da tasan kayanda za'a kawo wa umaima kenan wallahi da bata gayyi kowa yazo ba dama bazata bawa kanta wahala wajen kashe kudin dafe-dafe ba,Abbu da yara tunda Suka dawo basu ga Mamu a waje ba Wanda hakan yasasu sanin tabbas akwai damuwa kasa hakuri Anwar yayi Saida ya tambaya,mikewa Addayiya tayi tabawa su zulai da muneera umurnin su dauko Mata akwatunan dake dakin ta,ba musu Suka daddauko ajewa tayi a tsakar falon Yan gidan duka na zaune a wajen umaima ce kawai Bata nan. Nuna kayan Addayiya tayi tace"kaga kayan Nan umaru shi aka kawowa umaima shine uwarta ta d'aga hankalin ta har tana rantsuwa za'a maida musu"da mamaki Abbu yace a maida musu akan me kenan"?da Sauri ummu tace"akan bai Mata ba Mana Alhaji"girgiza Kai kawai Abbu yayi yace wa Addayiya"Ina ga yaran Nan zasu dau kayan sukai sa sashena su aje Zan rufe kayan a wajena bana bukatar wasu suzo da Suna ganin Kaya a gidan Nan bakuma za'a fitar da kayan ba sai ranan da aka daura auren"Yana gama maganar ya mike rai a bace yabar falon,Shareef ne ya ciccibi akwatunan da kannen sa Suka Kai dakin mahaifin nasu suka rufe. Kwance Lahab yake akan katifar sa sai Rahab dake gefe Yana assignment"yanzun Rahab da gaske baka kirani ba ka hadani da yarinyar Nan"tsaki kawai Rahab yaja baice kome ba sai Shan Kuma yace"eh ban hadaku ba in kanason magana da ita kaje da kanka Mana ba maka Kama da Dan aika ne"shuru Lahab yayi baice kome ba daidai lokacin Majid ya fito daga wanka don har lokacin bai koma gidan su ba bude wardrobe na Lahab yayi ya dau kayan baccin sa ya saka,sannan ya dawo Kan katifar tasa ya kwanta kallon sa Lahab yayi yace"Wai don Allah Majid kasan yarinyar Nan farida"?Jin maganar mace yasa Majid sauren tashi zaune Yana washe baki yace"wace yarinya kenan"am yarinyar Nan da mukaje birthday party saurayinta"Jin maganar da suke yasa Rahab barin abinda yake ya juya Yana kallon su da kyau. Oh baby ferry kake magana haba Lahab me zakayi da wannan second hand in, karka bada kanka Mana bazaka nemi yarinya fresh one ba d'anta sai kilakin Nan ai taimaka girma wallahi abokai na da yawa sun hayeta fa"waro Ido Rahab yayi sai Kuma ya girgiza Kai yamike ya bar dakin tare da bugo musu kofa da karfi,Suma basu bi ta kansa ba sai Lahab yace"Kai tambayar ka nake ka santa bawai dogon magana Koh bayani nake so ba" Eh na Santa mugun sani ba,amma Kai meyasa kake maganar ta"?tashi zaune Lahab yayi yace so nake na ganta don Allah Koh akwai wani party dakasan zata very soon"?eh toh gaskiya babu kasan fa ta wanke wani gara aure zatayi amma naji friends nawa nacewa za'a Mata na bankwana a Ranan za'a murzata na karshe"amma Kai meyasa kake son ganin ta?gyada Kai Lahab yayi ya cije baki baiso ace tonawa farida asiri yayi nisa har kusan aure ba, yaso ace tun yanzun kome ya kunce"karka damu kaide duk lokacin da aka saka date da venue na wajen ka sanar dani"ok shikenan ba yawa lahab, kwanciya sukayi dukan su biyu don Rahab Kam tunda ya fita a dakin Bai dawo ba. Washe gari da safe sai ga goggoji Mai aiki ta dawo bakin aikinta daman girkin mamu ne gashi bata fito ba tun jiya hakan yasa tana zuwa ta fada kitchen bayan sun gaisa da mutanen gidan,bayan sunyi breakfast Abbu da kansa ya mike ya nufi dakin mamu hannu yasa ya tura kofar dakin ya shiga zaune take a bakin gado ta zuba tagumi sosai tayi nisa a cikin kogin tunani da ta shiga,Zama yayi a gefenta hakan ya sata dan birkita sai Kuma ta koma ta zauna tana kallon mijin nata Kamar yanda yake kallon ta,ajiyar zuciya ya sauke sannan ya Soma magana a tausashe yace"Halima meke faruwa ne"? Kamar ya?tace Masa tana dad'a tamke fuskar ta"Kamar ya Kuma zakice ai a tunani na kinfi kowa sani miya faru, na tambaye ki Wai meke faruwa ne Naga tunda na dawo jiya har yau ban saki a idanuna ba gashi yanzun nazo na sameki acikin damuwa"?shuru tayi sai Kuma ta fashe da kuka ta Soma magana"gaskiya Ni wallahi a maida musu kayansu taya za'a ce yarka guda za'a kawowa lefe akwatuna biyar da wani banzan kit daya haba haba don Allah kofa zanin sama da dubu hamsin babu a ciki"? da mamaki Abbu yace"toh Halimatu yanzun ya kike so ayi indai maganar lefen ne baiyi ba babu damuwa Ni Zan iyya Kara Mata wasu set ma a had'a Mata da wannan,wani irin kayane umaima bata daura ba a gidan nan,abinda nakeso dake dan Allah ki kwantar da hankalin ki inke kin nuna irin wannan dabi'ar ita Kuma diyar taki ya kike so tayi kenan,amma in Kika nuna Mata albarkan aure yafi kayan tarkacen Nan na tabbata itama bazata nuna bai mata ba" Wani zabura mamu tayi ta tashi tsaye ta Soma magana a harzuke"kasan Allah Alhaji nifa bazan yarda ba haba don Allah akwatuna 6 Kamar Wanda zai aure Mai tuyar awara da sakel gaskiya da sakel a maida musu da kayan su in Kuma bazasu Karo wasu ba saidai a sauke maganar auren Nan ai bashi bane kadai autan Maza kanaga fa,wannan yarinya Jamila ita da ba kyau ne da ita ba kaga gidan ubanta Koh gate babu amma ka dube kayan auren da aka kawo Mata sai tawa Yar za'a kawowa wannan tarkacen"shima Abbu tashi yayi ya nuna mamu da yatsa yana magana cikin fada"kee halima bafa tsoron ki nakeji ba karkiga Ina binki da lallama kice Zaki takani yanda kike so zancen aure Kuma Koh kiso Koh kiki wallahi baza'a fasa ba Koda kuwa yaron baiyi Kaya ba bare yayi sai in shine yace ya fasa,Yana karasa maganar yabar dakin cikin bacin rai. Lahab Kam fita yayi a gidan hannun sa daure sai Mai lafiyar dake d'auke da kulan mubeena da niyar zai kaimata, ya gangara layinsu Nnenna da kafa don bazai iyya tuka Keke ba gwara ma in hannun hagune yake da matsala ba dama ba,Zama yayi a kofar gidan dake kallon nasu Nnenna sosai ya zurawa tsakar gidan ido Yana jiran fitowar ta duba agogo yayi karfe 7:12 ne daidai,Harya Soma tunanin Koh dai Harta wuce makaranta ne,amma saiya tsinci kansa da kasa tafiyar,sai kusan 7:30 yaga an turo kofan nasu tunda daman gidan nasu ba'a kewaye yake da gini ba, karafuna ne mutum na tsaye a wajen Yana hango cikin gidan. Abraham ne ya fito yasha wanka cikin wasu arnan wando da riga na gogaggun Yan iska masu tashen kwaya, Nnenna na binsa a baya rataye da jakan makarantan ta bude mota yayi ya shiga itama ta bude gefe ta zauna yaja Suka bar gidan har sunzo saitinsa zasu gifta Kamar ance ta kalli gefen glass sukayi Ido hudu dashi da mamaki ta waro idanunta,shima bai tashi ba ganinta da yayan ta,har Suka share kwanar layin Yana zaune bai tashi ba"brother nayi mantuna nabar assignment book nawa a gida gashi yau zanyi summit pls ka tsaya Zan koma na d'auka"tsayawa yayi ya juya Yana kallonta yace"basai kin sauka ba bari mu juya mu koma saiki d'auka"da Sauri tace"ah ah ka tsaya dai na koma da Sauri Zan dawo karna baka wahala Bata jira mai zaice ba ta sauka da Sauri ta nufi layin su hangosa tayi a zaune har lokacin ya sata Kara Sauri tana dan gudu gudu kad'an hakan ya baiwa sassan jikinta daman kadawa da kyau,ganin ta yasa sa mikewa tsaye Yana murmushi Harta karaso Inda yake fuskar ta d'auke da murmushi itama tace"Lahab Kaine kaji sauki kenan"?hararan ta yayi irin na wasan Nan yace"eh nine lallai baki da kirki Labiba ace kin karyani amma baki nemi sanin yanda na Kaya ba nasan Koh Shakka banayi baki koma asibiti dubani ba" Marairaice fuska tayi tace"kayi hakuri wallahi kana raina naso zuwa amma saboda abinda ya faru yanzun ba'a barina nafita makaranta Ni kadai"da gaske Ina ranki"ya tambaye ta Yana d'aga Mata gira daya,shuru tayi tana dai tsaye tana kallon sa"oh kina nufin makaranta kawai kike zuwa ne Koh Yaya"?dan rufe fuska tayi tace"eh wallahi tunda nazo garin Nan sau d'aya nayi yawo a gari amma kullum makaranta nake zuwa"Ware Ido yayi Wanda ya zame Masa jiki yace"cap kifin rijiya kenan"? "Next week zamu Fara CA test pls kazo makaranta"ke makaranta zanzo a haka da hannu na"ya tambaye ta,ka dai daure pls bari na wuce ana jirana byeee"ta juya tana d'aga Masa hannu da Sauri ya riko hannun nata zai Mata magana sai Kuma yayi shuru ganin Dad dake tsaye a kusa da motar sa Rai a bace Yana kallon su. Ganin sa yasa Nnenna fizge hannunta ta kwasa a guje tabar layin shidai Lahab na tsaye hannunsa d'auke da kula,harya karaso kusa dashi yatsa ya nuna wa Lahab a fuska a mugun bace yace"Kai Kuma again a kofar gidana Kuma da daughter ta bana maka last warning akanta ba tuna hospital don Kai baka da mutunci shine zaka biyota har Nan kana rike Mata hannu"? Juyar da Kai Lahab yayi Yana karewa layin kallo Yana magana"wannan ne kofar gidan ka"?wannan ai kofar gidan wani ne nake tsaye kofar gidan ka gashi chan tsakanin sa da Inda nake tsaye akwai titin gonnati ma a sakani don haka kaji da kyau Nan ba filin ka bane,Yana karasa maganar ya juya ya Soma tafiyarsa Dad na binsa da Ido Harya bar layin sosai yaji mugun tsanar yaron a ransa. ******************* Tura kofar maman nasa yayi ya shiga,zaune ya tarda ita a gaban mirror tana shafe shafe cikin shigan suit na aiki ga jakanta a gefe sai Sauri take tana shafa powder Jin an bude kofa yasa ta juyawa ta kalli kofar ganin sa yasata maida kanta ga mirror hade da d'aukar agogo tana daurawa a hannunta,matsowa yayi kusa da ita yayi Hugging nata ta baya ya daura kanta akan kafadarda Yana kallonta ta mirror hannu tasa ta ture sa ta baya amma yaki barin jikinta yace"Kai mama ki Bari na lale bayan Mana" Rankwashin ta sake masa ta kansa da Sauri ya saketa Yana Susa wajen Yana turo Baki,mikewa tayi tsaye ta dau jakanta tace"kaga Adewale Naga baka da aikin yine yau shiyasa kozo kana likemun gardi da Kai matsamin na wuce papan ka na jirana a compound"haba mama magana fa nazo muyi fa shine Zaki shareni ki wuce"?tsayawa tayi tana kallon sa sai Kuma ta zauna a Inda ta tashi tace"toh Fadi naji in maganan kudine bani dashi in Kuma wani maganar ne kayi Sauri" Yauwa mama na daman nace ayya Koh Zaki gidan su Lahab ne ki dubasa ayya mamata kije don Allah kije mamata ki dubasa tunfa jiya nasanar dake amma bakice kome ba"? Kaga Adewale ni Karan kaina Ina son zuwa dubasa amma banson samun matsala da mahaifinka,shiyasa ban Masa zancen zuwa ba tunda yace bayason ka da yaran Nan ai ya Kamata kaima kaja jiki dasu"had'a fuska yayi yace"haba mama don Allah ace ke kome zakiyi Saida izinin papa gani nayi tunda Zaki office maizai Hana inkin tashi ki shiga ki dubasa shafshaf Mana" Ah ah Adewale maganin Kar ayi Kar a Fara kadai bari Inna dawo saika Kira Lahab in na gaidashi a waya ai zaifi amma bazan bi abinda kake so nazo na samu sabani da mahaifin ka ba"? Kenan mama ace kullum sai abinda papa yake so zakiyi menene a ciki Nan Nan baki da hanci bazaki ki dubasa ba"eh bazata dubasan ba Mara kunya Mara hankali duk abinda kake cewa Ina jinka sannan ke Kuma wallahi kin fanshe kanki don dako labari naji kinje gidan su yaron Nan ninasan abinda Zan Miki shige mu wuce kin sani nayi late a banza Kai Kuma saikayita zaman banza daka Saba stupid kawai,papa na karasa maganar yabar dakin mama na binsa a baya Suka barsa a tsaye Baki bude. turo kofar gidan yayi ya Shiga bako sallama,mubeena dake zaune da takardu a gabanta tana bita don yau basu da pepar Koh dankwali babu akanta da Sauri ta d'au gyale dake gefe ta yafa a kanta,karasowa yayi cikin gidan yaja kujera ya zauna tare da kallon Nabeel dake ta faman dinki baima San da shigowar sa ba Saida yaja ya zauna tukunna ya tsaida dinkin Yana kallon Lahab da mamaki harma ya kasa hakuri yace"Wai Lahab Kaine ka fito a haka kaida baka da lafiya" Kayya Nabeel wallahi na gaji da Zama waje daya,Inna zauna har wani zafi zafi nakeji a mazaunai na haba"mikewa mubeena tayi tana Jan tsaki don harga Allah maganar ya bata kunya Kuma ta fahimci Lahab bai dashi,dariya Lahab ya sake fahimtar abinda yasata shiga dakin,hararan sa Nabeel yayi yaci gaba da dinkin sa Inna ce ta fito daga bandaki tana kallon Lahab sai Kuma ta girgiza Kai tace"Lahab nake gani Koh bashi ba"? Nine Inna ga kulanku na dawo muku dashi gaskiya abinci yayi dadi,d'aukar kulan Inna tayi ta shiga dashi kitchen,har yamma Lahab na gidan nasu daga Nan yayi gidan su Adewale,sai goshin mangariba ya koma gida sosai Abbu yayita Masa fada don ini kas baisha magani ba bare Allura kafar Dr biyu a gidan bai samun sa. ******************* da misalin karfe 2 na dare Nnenna ce ta farka daga bacci saboda matsanancin kishin ruwa daya farkar da ita,mikewa tayi daga Kan gadon nata ta sauka,taka tiles na dakin take a hankali tasa hannu ta dau wayar ta,kunna wutan wayar tayi,tana sanyi da kayan bacci wando da riga hannu tasa ta bude kofar dakin ta ta fita,tafiya take a hankali kasancewar falon shuru ba motsen kowa kasancewar daman ita da peace ce kadai a downstairs sauran mutanen gidan Suna upstairs ne, kitchen ta shiga har lokacin bataji motsen kome ba ta bude fridge ta dau ruwa Mai sanyi a cup tasha ta maida cup in ta aje,mikewa tayi takama hanyar dakinta Harta gifta kofar dakin peace sai Kuma ta dawo baya, Jin surutai na tashi kasa kasa ga Nishi Nishi da take ji. Matsawa kusa da kofan tayi ta kasa kunne sosai tana son ganin mike faruwa toh Koh dai peace bata da lafiya ne,Jin Karan mutum yasata Sauri sa hannu ta bude dakin tare da haska ciki,wani irin ihu ta sake da Sauri ta juya da gudu ta nufi barin wajen a guje har tana tuntube da flower dake zaune a kusurwar step in sauka a dakin................................ πŸ€ *By Ruqeenjalal* πŸ€ *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki* Page 84&85 da Sauri Abraham ya mike hade da daukar gajeren wandon yasa shima da gudu yabi bayan Nnenna data Jima da Isa kusa da kofarta a hankali yake kiranta gudun kada iyayen sa Koh Yan uwansa dake sama su jiyosu,dakin ta shiga da gudu jikinta na rawa ta maida kofar ta rufe harda murza ki tayi Kan katifarta ta kwanta hankalinta tashe. Yakai 10 minutes a tsaye a bakin kofar gabaki d'aya jikinsa yayi sanyi tunda yake Bai tabajin kunyan abinda yake aikatawa ba irin na yau ba, juyawa yayi jiki a sanyaye ya nufi dakin peace ya bude ya shiga,har lokacin tana kwance ba sutura a jikinta don gabaki d'aya babu kuzari a jikinta,kayansa ya Soma tsinewa binsa tayi da kallo sannan tace"ya haka Abraham kafasan halinda nake ciki shine zaka tafi ka barni a hakan"wani dogon tsaki yaja tare da barin dakin baice Mata kome ba,damke lips nata tayi na kasa ta cija cikin Jin takaicin abinda Nnenna ta musu gabaki d'aya ta katse musu jindadi. Cikin sati daya sosai Nnenna ta sauyawa Abraham bana Wasa ba ga gudunsa da take don kwata kwata Bata yarda su hadu makaranta ma tun asuba take saka uniform Koh karyawa batayi ta tafi da kafa kafun 7 na safe ta Isa,gabaki d'aya taji zaman gidan Bai Mata ba ga takurin mom a gida gana Jennifer a makaranta,ga wani irin kiyayya da peace ke gwada Mata especially da Abraham ya fita a harkanta tun daga randa ta kamasu red hand yaji gabaki d'aya ya tsane kansa da peace in gabaki d'aya. ************** Lahab ne tsaye a dakin su Yana Santa uniform don yaune za'a Fara CA Kamar yanda Yama Nnenna Alkawarin zaizo gashi yazo shiyasa tun jiya ya ishi Dr dake dubasa har Saida sukaje hospital aka kunce hannu Kuma Alhamdulilah hannun yayi kyau sosai saidai baya iyya aiki dashi sosai sai dai a hankali. Fitowa yayi a dakin ya nufi dakin gidan zazzaune suke ana karyawa amma babu mamu da umaima don a cikin satin nan gabaki d'aya sun sauya a gidan shigowa Lahab yayi ya zauna akan dinning in tare da d'aukar plate da spoon ya ibi abinci cup na tea ya d'auka ya Soma karyawa,kallon sa Abbu yayi yace"yau Kuma school zaka kenan"?eh Yaya makaranta xani"dan murmushi Anwar yayi yace"ka manta an koreka a makarantan ne"kallon sa Lahab yayi shima yayi murmushi hade da kallon Abbu da Sauri Kuma ya kauda kansa ganin shima kallon NASA yake yace"ai da babban Yaya zani"wani kallo Abbu ya Masa sai Kuma ya mike tsaye ummu ta dau Masa jakansa Suka nufi kofar,ganin haka yasa Lahab mikewa da gudu yabi yayan nasa a baya har compound Saida ya bari ummu ta aje Masa jaka ta juya kafun Lahab ya nufesa da Sauri ya bude gaban motar ya Shiga. Fitamin a mota Lahab?"Ni gaskiya Yaya muje ka bawa principal hakuri kafa San yau za'a Fara CA"?CA fa kace CA nawa ne yazo ya wuce da exam bakayi ba"?wallahi Yaya da gaske nake don Allah kaje ka basu hakuri daga wannan jarabawar fa sai dai mu Kira weac" Shuru Abbu yayi na d'an wani lokaci kafun ya d'aga waya ya Kira su Rahab dake falo su fito yau da kansa zai kaisu makaranta cikin happy muneera ta Mika har Suna rige rige Suka fita Rahab na binsu a baya,bude motar sukayi Suka shiga Abbu yaja suka bar gidan,Suna Isa makaranta sauran yaran Suka nufi class nasu,Abbu a gaba Lahab na binsa a baya Kamar Wanda kwai ya fashe Masa a ciki Yana binsu a baya,har cikin office na principal Suna Shiga Suka tarar da bappa Ado da Nabeel sai papa da Adewale,fuskar kowa ba walwala Kamar hadin Baki gabaki dayansu yau Suka tattaro 'ya'yan nasu a gaba,Zama Abbu yayi Yana fuskantar principal da fuskar sa dake d'auke da fushi kwata kwata babu walwala a fuskar tasa toh haka Suma kaf babu fara'a. Kallon su principal yayi cikin masifa yace"Kunga bayin Allah ku tattara yaranku nidai nace ya isheni bazan iyya ba akwai makaranta a gombe kuje ku nemi wani ku sasu"da Sauri bappa Ado yace"haba malam wani irin mu sasu a wani kwata kwata wata nawa ne ya rage su kammala karatun shekara biyu da wani Abu kuke fama dasu sai saura Yan watannii ku rabu ma gabaki d'aya shine bazaka iya hakuri su dawo ba"?wani shegen kallo principal ya Masa yace"in zamu rabu sai akace muyi rabuwar tsiya dasu coper fa Suka buga gabaki d'aya kace nayi hakuri akan me? sunan makaranta ta suke so su b'ata Koh me"?Kai nifa na gaji da wahala Nan daman team Nan ya rage musu kawai suje suyi zaman gida su jira register weac da neco in yaso kwa musu a wani makarantan ba nawa ba"sosai principal yayi ta zuba tijara su Lahab bazasu dawo makarantan ba har Saida ran papa ya Soma baci sukayi kaca kaca yayi zuciya zasu koma gida shida d'an nasa, Abbu ganin abin ya Zama haka yasa baki akan zancen dayake mutum ne Mai natsuwa da dattako lokaci d'aya principal ya sauko Suka daidai ta amma fa da sharadin su Lahab na Kara jawo wani abin zasu bar Masa makaranta,papa Kan cewa yayi a raba Adewale dasu a class kowa da ajinsa haka Koh akayi daman Lahab ya koma B aka bar Adewale a A shi Kuma Nabeel aka kaisa D class. Zaune take tana duba text book in biology data d'auko a Lab tana checking nasa,Zama yayi a kusa da bincin ta har lokacin Bata d'aga Kai ta kalli wanda ya zaunan ba don kwata kwata hankalinta ba'a Kam class yake ba yana ga littafin tane,hannu yasa yaja book in da Sauri tasa hannu zata kwace,sannan ta dago Kai ta kallesa,had'a Ido sukayi da Sauri ta sakar Masa littafin da mamaki tace"yaushe ka shigo"taya za'ayi kisan na shigo hankalinki Naga book duk karatun da kikayi a gida bai isa ba sai kinzo kin dad'a anan,duk nacin kidai baza kici πŸ’― ba"murmushi kawai tayi batace kome ba shima gyara zaman sa yayi ganin malamin su ya shigo,mikewa sukayi dukan su Suna gaidashi amma banda Lahab shima malamin Bai damu da gaisuwar nasa ba shiyasa yayi Kamar bai gansa a zaune ba,Zama Yan ajin sukayi ya Soma raba musu Questions paper dake hannun su da answer shep,zaro pen sa Lahab yayi dake Aljuhu ya Soma rubutu da hannu Mai ciwo. 30 minutes after yara Suka Soma fita Suna summit shidai Yana zaune Yana rubutu sai Kuma ya aje pen in yayi zaman sa, Nnenna data gama rubuta amsan ta dan masowa tayi kusa dashi murya kasa kasa tace"ka bani papern ka ka karbi nawa bansa Suna akai ba,tana maganar tana Mika Masa papern ta kasa. Kin juyowa yayi sai magana take Masa har malamin biology su ya ganta ya kwace papern nata bayan ya sata ta rubuta Sunanta ya karba tare da korarta waje da d'add'aya da d'add'aya Yan class suke tashi har aka bar saura mutum biyu Lahab da wata yarinya,lokaci ya kusa karewa Nan da minutes uku Zan karba paper"shine abinda malamin ya fad'a Yana muzurai da Sauri yarinyar ta tashi ta Mika Masa nata ta fita,bayan minutes uku da kansa yaje Kan table in Lahab ta kwaco nasa ya fita. Mikewa Lahab yayi ya fita a ajin,kusan cin Karo sukayi da Nnenna da duk tabi ta shiga damuwa ganin bai gama ba aka karba"Lahab meyasa Ina ta maka magana ka karbi paper ta kaki"?shine abinda ya Fara fita a bakinta, d'an gyara tsayuwar sa yayi yace"ke ai abin kunya ne Ina namiji mace taban Satan amsa don hakan maganar CA ajesa a gefe muje restaurant muci abinci nasan wata kila baki karya ba Kar ulcer ki ya tashi"ah ah nagode Lahab zanje na maida biology Nan na Kuma duba Civic kasan shine second paper mu"?shuru yayi sai Kuma yace"ok asha karatu lafiya ya wuce,itama tafiyar ta tayi tana Isa lab in ta aje biology tadau Civic da notebook Inda ke hannunta tana dudduba wa,aje Mata laida yayi a Kan table Inda take rubutu yaja kujera Mai facing nata ya zauna tare da harde hannun sa"itama barin rubutun tayi tana kallon sa,hannu yasa ya bude laidan Pizza a kwalin sa babba dashi bude kwalin yayi ya dau yanka daya yasa a Baki tare da tura Mata sauran ya soka ear_P insa a kunne ya aje wayar a gabansa Yana latsawa. Jawo pizzan tayi duk da bata Saba ci ba hakan bai hanata son ci ba don yanzun batajin shakkan cin Abu a gabansa tunda sukayi zaman asibiti. ***************** Yau satin sadeeq d'aya kenan baiji muryan umaima ba da farko inya Kira layinta bata d'agawa daga Baya Kuma sai aka kashe wayar gabaki d'aya,abinda ya d'aga Masa hankali kenan ya dawo gombe ba shiri yaji Koh lafiya amma abinda ya Kara basa mamaki yau kwana biyu Yana zirga zirga a gidan su Lahab baya ganin umaima daga ace Masa bata da lafiya bazata iya fitowa ba sai ace Masa Batanan tana makaranta dayake itama tana final Exam nata zuwa next week zasu Gama sai ayi bikin da sati biyu kenan yanzun kwata kwata bikin nasu saura sati uku. Yaje makarantan su amma Baya ganin ta abinda Bai sani ba shine duk lokacin da umaima ke makaranta in yazo mamu zatace ace Masa Bata da lafiya in Kuma tana gidan sai ace tana makaranta haka bawan Allah Nan yayita gantali a gidan nasu akalla a Rana zaizo sau uku kamar yau ma yazo da safe akace Bata Nan,yanzun ma misalin 12 na Rana Yana compound na gidan tun d'azun yazo ya aike Mai gadi aka cemai Bata da lafiya bazata samu fitowa ba"don Allah baba Koh zakaje kayi musu iso Zan shigo na dubata"dan shuru Mai gadin yayi don yasan harga Allah babu abinda ke damun umaima haka zalika yasan sadeeq tunda sun jiya da umaima Yana zuwa gidan Kuma Halo yaron ya basa tausayi. daurewa yayi yace toh bara naje na sanar dasu,horn na mota da akayi ne yasa baba maigadi juyowa daga kokarin Shiga falon da yake zuwa wajen gate,da Sauri ya Kama gate in ya bude,motar su Lahab ce ta parking gabaki d'ayan su Suka fitoh,dukan su Suka gaida sadeeq sukayi da fara'a ya amsa hade da baiwa Rahab hannu sukayi musaba'a Yana Masa ya jiki,nuna Masa Lahab daya kusa Isa kofa yayi yace Masa gashi can Mai jikin"dan Allah toh in ba damuwa kamin magana dashi"gyada Masa Kai kawai Rahab yayi yabi bayan su zuwa ciki,har Lahab ya Kwabe riga Rahab ya shigo dakin Yana sanar dashi sadeeq nason magana dashi,Jan dogon tsaki yayi yace"nifa na Fara gajiya haba akan me zaina takuramin inyana da matsala ya nemi yayan yarinya Mana bani ba"da Sauri Rahab yace"haba Lahab Kai kana ga duk gidan Nan banda Kai wazai taimake sa kana tunanin Anwar Koh Shareef zasu sauraresa Kamar yanda zakayi Masa ne"?fita a dakin kawai Rahab yayi ransa a bace don shi harga Allah sadeeq ya Soma isarsa,karasowa yayi kusa dashi ya jingina a jikin motar sa. Am daman akwai wata Alfarma da nake nema ne Lahab nasan na dameka Koh"?kallon sa yayi babu walwala a fuskarsa yace"in ma ka dameni sadeeq Yana iya kana ga dai makaranta na fito Kuma yunwa nakeji amma ba kome fad'a muji"ajiyar zuciya sadeeq ya sake sannan yace"Lahab wallahi bansan meke faruwa ba kwata kwata umaima yau sati banji muryarta Koh ganinta ba nazo garin Nan ma ganin ta ya gagareni"? a gajiye Lahab yace"toh Ni yanzun mekake so nayi maka ai wannan magana Abbu zaka tinkara dashi kaga maganar lefe ma daka min karshe abin ya Zama babba ance Wai daga bakina magana ya fito ba daga bakin umaima ba"?da damuwa sadeeq yace toh yanzun Lahab Yaya za'a Yi akan Yar maganar Nan in sake ya tafi har wajen manya bai dace ba ya Kamata mukashe maganar iya nida ita basai iyaye sun shiga ba". dan shuru Lahab yayi sai Kuma yace"toh ya kake so ayi"?yauwa Lahab nida so nake dan Allah duk yanda za'a Yi Ina son ganinta ne nazo ance min bata da lafiya in ma fitan ne bazata iya ba Ni Zan iya shiga"karkata Kai Lahab yayi sai Kuma yace Ina zuwa,ciki ya koma har dakin umaima Saida ya dudduba amma baiga Koh Mai Kama da ita ba dakin su muneera ya shiga ya tambaye su sukace Bata dawo makaranta ba fita yayi Yana tunanin mezai cewa sadeeq don harga Allah baison karyata mutanen gidan su ya zubar musu da kima a idon surkinsu tunda sunce bata da lafiya Kuma yasan mamu ce, alhalin Kuma tana makaranta,karasowa wajen sadeeq yayi Yana tunanin mezaice Masa gabaki d'aya basirar sa ta kwace in yace tana ciki sadeeq zaiso ya Shiga in Kuma yace Masa tana makaranta wato Yan gidan sun Masa karya kenan,a hankali ya bude Baki yace"eh sadeeq daman dai umaima......sai Kuma yayi shuru ganin motar da ya shigo cikin gidan....................... πŸ€ *By Ruqeenjalal* πŸ€ *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki* Page 86&87 Motar umaima ne yayi parking bude kofar tayi ta sauko tare da daukar school bag nata ta rataya Yi tayi Kamar Bata gansu ba ta Kama hanyar shiga ciki,baki sake sadeeq yake binta dashi don gaskiya tayi mugun rame Masa sosai ta Kara haske Kamar dai maijin yan gaskiya Alhalin Kuma damuwa ce kawai ke cinta,ai ganin ta giftasu yasa sa binta da Sauri yasha gaban ta cikin damuwa yace"umaima lafiya kwana biyu bana samun ki ya jikin"?a gajarce tace lafiya da sauki sosai"sai Kuma ta yunkura zata Kara step da Sauri Kuma ya sake tareta haba umaima ya Kamata mu samu waje mu zauna akwai maganar da nake so mu tattauna dake ne"? Shekeke take kallon sa tace"yanzun dai makaranta na fito Kuma Banda isheshen lokaci bazan iya magana da yawa ba"da saurin sa yace toh shikenan amma dan Allah meya faru Inna Kira wayarki Baki d'auka daga baya Kuma na jisa a kashe na shiga damuwa sosai wallahi"wayar ce ta Bata ban ganta ba shiyasa"da mamaki yace haba umaima in waya ya Bata bazaki d'au Koda na muneera bane ki sanar dani in yaso na Aiko Miki da kudi kisai wani"wani kallo ta Masa a fakaice,Wai ya turo kudi ta sai sabo Ina shi Ina saya Mata wayar da take rikewa tunda ya kasa had'a kayan auren azo a gani"ka Bari kawai Abbu yace nabar maganar wayar zai saimin sabo"ah ah umaima Nina dace Dana saya Miki,yanzun dai duk ba wannan ba so nake muje mu samu waje kiban Koh 10 minutes ne muyi magana akan programs Inda zakiyi anan gombe da Kuma kudaden da Zan Baki na gyara da dinki"shuru ta Masa Saida ya gama maganar kafun tace"basai ka kashe kudinka ba na gode duk abinda nake bukata an riga an tanadar mini dinki ma na riga na Kai maganar programs Kuma guda uku zanyi Kuma duka ango baya zuwa so ba bukatan ka sani tana karasa maganar ta zagaye sa ta wuce abinta har lokacin Yana tsaye Yana kallonta Harta bude kofa ta shiga ta maida ta rufe. Lahab dake tsaye a bayan su kad'an kallon su kawai yake Bai zakud'a daga wajen da sadeeq ya barsa ba,juyowa yayi ya dawo wajen da Lahab ke tsaye yace"Wai Lahab akwai abinda ke faruwa ne Koh yake damun umaima"?kafada Lahab ya d'aga Masa irin shima Bai sanin Nan ba,karban number wayan sa sadeeq yayi kafun ya tafi. Komawa cikin gidan Lahab yayi direct ya nufi kitchen abinci ya Iba a plate shinkafa da Miya sai cabbage Zama yayi akan dinning Yana ci,goggoji ne ta fito daga sashen Addayiya d'auke da kwanuka masu datti tazo zata shiga kitchen ganin Lahab a dinning yasa ta tsayawa Suna gaisawa tambayar ta labarin d'anta yayi da jikin sa tace Masa da sauki harma an basa Mata a garin su sosai ya Taya ta murna harda tsokana Wai zata Zama uwar Miki Banda sawa surkuwa Ido"da Wasa da dariya ta wuce kitchen. Bayan isha'i zazzaune suke gabaki dayan su a falo Abbu ya karkato su dukan su,sai dai har yanzun umaima da mamu Basu fitoba,wayarsa dake gefe ya d'auka cikin bacin Rai ya Kara a kunnesa Saida ya kusa tsinkewa mamu ta d'auka"keda yarki ku fito yanzun Nan maza kafun na Bata muku rai"Bai jira abinda zatace ba ya kashe wayar sa, ba'a dau lokaci ba saiga Mamu da umaima sun fito Zama mamu tayi a daya kujeran Kamar yanda ummu da Abbu da Addayiya ke Kai umaima a kasa ta zauna,Anwar Shareef uzaifa ku fita compound ku bude booth na motar dana shigo da ita akwai Ghana must go manya guda uku kowa ya dau d'add'aya ku shigomin Nan dashi,mikewa sukayi da Sauri Shareef sai zumbura Baki yake Yana hararan tagwaye dake zaune su ba'a ce musu suje ba. Shigo da kayan sukayi Suka aje a tsakiyar falo umurni Abbu ya Basu su bude bags in su fiffito da abinda ke ciki,zannuwa ne manya manya masu tsada hadaddu da lufaya lace harda materials a daya Ghana must go in dayan Kuma shadodene tirim da hula da takalmi sai Kuma daya bag in dake d'auke da zannuwa colour uku Amma sun Kai turmi hamsin a ciki,kallon Addayiya yayi yace ta xabi turmin zani a cikin bakko dayan da bana anko ba matsowa tayi ta xabi zanuwa masu kyau kala uku Abbu yace Mata ta Kara Amma taki tace wannan ma ya isheta Allah yayi albarka itakam zanuwa ai Wanda take dasu ba'a dinka bama yawane dasu gasu can make a wardrobe. Mamu itace na biyun zaba kala bakwai ta d'auka harda less dasu materials ta hada,sai ummu ita Kuma tadau kala biyar,anko abbu yace muneera ta zulaihat suzo su d'auka duka kala ukun Suka d'auka Koh wanne d'add'aya sai lufaya da Suka d'auka cikin bakko su Mamu da gyale da takalmi,sauran ankon Abbu yace su d'auka su rabawa Yan uwa gida gida kafun bikin su tabbatar sun kaiwa su nanne nasu gobe goben Nan sai Anwar ango kala goma Abbu yace ya d'auka shadda dasu boyel sauran yaran Suka daddauka Lahab Saida yadau kala biyar biyu nasu Adewale uku nasa,umaima ki Kira goggon ki na tura Mata kudi saikuyi magana zata Miki order Kaya daga Kano za'a dinka Wai a Shan don haka saiki kirata ki gaya Mata kalan kayan da Zaki saka a biki da Wanda za'a Kara Miki ta waya,sannan wa'innan Kuma Haleema kidau goma kema haka ummu sai ku baiwa Addayiya sauran zata rarrabawa kawayen ta Kuma haka sai kudin dinkin daya Basu Amma Anwar yaki karba shida Shareef sunce zasu biya a aljuhun su, Yana karasa maganar ya mike yabar falon Addayiya na binsa da sanya albarka. Mikewa Lahab yayi ya dau shaddan ya Kai dakin su ya aje wanka yayi ya kwanta,washe gari a makaranta sunyi Math's da chemistry dayake sunada paper uku ne harda Islamic aka had'a musu,dayake makarantan basa bada paper a rarrabe sai an gama CA duka suke hadawa gabaki d'aya a raba a Rana daya. Bayan ya dawo gida da yamma sadeeq ya kirasa tare da rokon sa akan ya fito wajen gate don baison shiga gidan sako zai basa ya baiwa umaima zai wuce bauchi ne,bayan ya fito kwalin waya ya Mika Masa tare da rokon sa akan ya taimaka ya baiwa umaima sannan dan Allah ta kirasa,ba musu ya karba hade da Masa alkawarin insha Allah zata kirasan,bayan wucewar sadeeq cikin gidan Lahab ya dawo har dakin umaima ya shiga hannu yasa ya tura kofar dakin nata zaune take cikin kayan bacci wando da riga sai dai ba Mai bayyana tsiraici bane Yana da duhu da laushi,kanta d'auke da holan bacci rike take da wayarta Kiran iPhone 11 chatt suke da goggon ta sumayya da Abbu yace ta nemeta suyi magana hotonan materials da zata sai Mata dasu purse da sauran surutun da zata saka a program's take turawa,taji an turo kofar a tunanin ta muneera ce Koh zulai don Mamu bata cika shigowa ba saidai ta kirata ita taje ta samesa hakan yasa bata bar abinda take ba har Lahab ya shigo dakin Zama yayi kusa da ita yasa hannu ya karbi wayar hannunta Yana jujjuya wayan hade da kallon ta. Mika Masa hannu tayi fuskarta babu walwala tace"ka bani wayata baka ga Abu Mai muhimmaci nake bane"?eh Naga abinda kike amma fa ki sani duk muhimmacin sa baikai sadeeq bakoh"? Mikewa tayi Rai bace zata bar dakin da Sauri shima ya mike ya Isa kusa da kofar da Sauri ya rufe hade da zare key in ya rike a hannun sa yace"umaima zauna magana zamuyi dake"hararan sa tayi tace Kai asuwa da Zan tsaya na saurare ka kaga nifa banson damuwa yanzun"hhh bakison damuwa nidai yanzun kawai ki zauna muyi magana malama"Zama tayi tana kallon wani direction daban"umaima Zan fada Miki gaskiya duk da da ciwo amma fa ki sani kaf duniya babu masoyin ka sama damai fada maka gaskiya Zan tambaye ki tsakanin ki da Allah umaima meyasa Kika chanjawa sadeeq"? Shuru tayi bata basa amsa ba har lokacin bata Kara kallon sa ba"umaima tambayarki nake meye faru a tsakanin ku har Zaki Masa karya kice wayarki ya bata Alhalin Kuma gashi a hannunki kin Sasa ya sai Miki wani haba umaima duk wannan na menene"?Koh akan kayan auren ne kema Bai Miki ba"?hawaye ne ya cika Mata Ido a hankali tasa hannu ta goge wa'inda Suka zuba Mata cikin shesheka tace"haba Lahab ya zanyi da Raina ne Taya za'a ce sadeeq zaimin Kaya haka a ganina Yana da kudin da zaimin fiye da hakan amma ya kasa"toh ke umaima yanzun abinda ya dameki shine kankantan kayan?a tunanina babu kayan da za'a Miki ya d'aga darajan ki bayan Wanda Kika saka a gidan Nan sannan kinsan dalilin sa nayi Miki kadan inne"?kuka ta fashe dashi tana magana"Ni duk ba kankantan kayan bane yafi Bata min rai Kamar d'aukan kayan da akayi a waya aka had'a da hotona ana yadawa a online Wai duk girman kaina ga lefen da aka min,sannan haka maganar yake ta yawo a school namu abin shiyafi mini ciwo wasu kawayena ma don su tabbatar yasa su zuwa da sunan kallon Kaya,amma Basu samu kallo ba don Abbu yahana a fitar,shine suke cewa Wai kunya ya Hana a fitar jama'a su gani" girgiza Kai kawai Lahab yayi yace"ke dai umaima sai kace yarinya karfa ki manta yanzun fa 25years kike dashi Amma kin kasa magance dan matsalan Nan"ke Banda abinki yanzun a tunanin ki in sadeeq ya Miki wannan Kaya har abada bazai Miki Wanda ya fisa bane Nan gaba karfa ki manta Mata da yawa sun samu kayan aure na bugawa a jarida amma auren baiyi lastic ba meye amfanin sa,ba yawan Kaya bane aure ah ah albarka ake nema kawayen ki masu Miki dariya yanzun haka a cikin su wata da sadeeq zai nemi auren ta Koh babu lefe ba goro sadaki kawai in zai tabata da gida wallahi tanason,kina ga guy kyakkyawa dashi ustaz ki tsaya kina Masa yanga,amma shikenan in Baki so ni Zan iya zuwa na samu Abbu a fasa bikin kawai sai yayi lefe 24 box's shikenan"?ya karasa maganar tare da jefa Mata kwalin wayar akan gado da wayan ta duka. Da Sauri ta Mike tsaye ganin zai fita a dakin a shagwabe tace"toh Ni yaushe nace maka bana sonsa Kuma ai Vance a sauke sarti ba"?juyawa yayi ya kalleta cikin Serious yace"nifa na gama magana mundin sadeeq ya kirani yace Baki kirasa ba wallahi tallahi saina gayawa Abbu,Bai saurareta ba ya fita a dakin ya maida kofar ya rufe. Washe gari Lahab ya d'au Kaya yakai dinkin duka kala ukun sa ya baiwa Adewale da Nabeel nasu Suma Suka Kai dinki don kowa da telan sa saboda yawan rikicin su da teloli daman Nabeel telan matane vana maza ba,zancen Ruky da Ahmad har manya sun shiga iyayen Ahmad sun kawo kudin goro naira dubu 50 cicib aka saka musu sarti Nan da wata biyu masu zuwa Nan take ahlin gidan su Ruky da Ahmad Suka Soma shirye shiryen biki,mubeena data tsinci zancen zuciyarta ne kawai Bata hadiye ta mutu ba amma har ciwo Saida ta kwanta na kwana biyu tsabar damuwa. kuma rukyn ce ta tura Mata message ta what'sApp akan an saka ranar auren ya zancen anko da zasu fitar, Bata Mata reply ba sai ma blocked inta da tayi don ita gani tayi Kamar cin fuska Ruky ke Mata, daman sun riga sun kammala exam nasu Suna hutu yanzun. ******************* Yau Alhamis saura kwana daya a Fara biki gidan su Lahab cike yake tam da jama'a bakin da sukazo aure abinka da d'aga bikin farko a family sosai Yan uwa ta kowani kusurwa Suka allara gida ya cika makil da Yan uwa Mata,Lahab ne ke shirga kayan sa a jaka zai bargidan saboda karancin dakuna da sukayi kadan dan su hudu suke kwana a dakin ga mata a sauran dakunann Koh bacci basa iyawa saban surutun jama'a daga asuba dana kuke kuken yara daman shi Anwar tuni ya koma gidan sa tare da zugan abokan sa don har sun Fara program na biki umaima ne sai gobe laraba za'ayi kamu. daukar jakansa yayi Rahab dake zaune a gefe mikewa yayi ya dau NASA daya jima da hadawa,fita sukayi Suna ratsa jama'ar dake falon Suka fitowa tsakar gidan matane make tirim sai muneera dake zaune a gefe ga dukkan alamu kuka ta gama ga idanunta a kukkumbure,yafitota Lahab yayi da hannu ba tare daya tsayaba ya fita kofar gida. Biyosu tayi har waje kallon ta Lahab yayi sannan ya tambaye ta meya faru wani kuka ta sake da karfi tana cewa"toh ba mamu bane ta aikeni tun safe Ina Kai katuna gidan kawayen ta shine fa ban samu lalle ba har Mai lallen ta tafi kafun na dawo, Kuma nacewa ummu ta ban kudi naje saloon Amin tace Wai bazata bayar ba. "yanzun ke da girmanki Zaki tsaya kina kuka a gaban mutane amma wallahi kinji kunya duk yanzun ba wannan ba nawa ne kudin lallen"?cikin murna tace 3k ne uncle hannu Lahab yasa ya zaro 3k ya Mika Mata da murna ta karba tare da juyawa ta koma cikin gidan da Sauri zata dau mayafinta. Gidan su ya jafar Lahab suka nufa don su nanne ma duk sun zo gidan su maza ne kadai a gidan ya jafar in, jakansa kawai Lahab ya aje Suka Shiga gari da Majid dinkin sa yaje ya karbo daga Nan Suka wuce cinima sai kusan 6 na yamma suka koma gida,abinci Suka samu an turo musu daga gidan biki Mai Rai da lafiya bayan sunyi dinner ne Majid ya kallli Lahab sannan yace"Lahab yaufa akwai casu"cikin rashin fahimtar Lahab yace kamar ya akwai casu ban gane ba"? murmushi Majid yayi ya mike tsaye tare da bude wardrobe nasa ya fito da wasu arnan jeans da longsleeve tare da wani jacket Mai uban kyau ya wurgawa Lahab a fuska Yana cemai"yau za'a Yi partyn ferry za'a kwana ana shashewa da Yan Mata Kai yau akwai casuuuuu da Sauri Lahab yace"kana nufin yau za'a ayi partyn auren nata"?kwarai ma kuwa shiyasa na Mana shopping ba tare dana sanar da Kai ba gasu maza by 10 o'clock Muna hotel. Mikewa tsaye Lahab yayi zai fita a dakin da Sauri Majid yace Ina Kuma zaka bayan nace maka karfe goma zamu fita yanzun Kuma Ina zaka"bazan Jima ba waje zanje Ina zuwa yanzun Nan,Yana karasa maganar ya bude kofa ya fita,da Sauri ya zaro wayar sa lalubo number Anwar yayi jikinsa har wani rawa rawa yake, ya Kara a kunne amma Harya tsinke Anwar bai d'auka ba Kara Kira yayi again har Saida Yama Anwar five miss call kafun yaji an d'au wayar abokin sane ya d'auka yace Yana wanka amma inya fito zai kirasa.......................................... πŸ€ *By Ruqeenjalal* πŸ€ *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki* Page 88&89 Komawa cikin gidan Lahab yayi ya samu har Majid ya shiga wanka, agogo ya kalla 8:30 ne na dare fitowa majid yayi Yana goge kansa yake cewa Lahab"kaga kayi Sauri wallahi tara yayi muna cikin gidan Nan fita zai Mana wuya kasan Daddy dasa Ido"?girgiza Kai kawai Lahab yayi ya bude bandakin ya Shiga Bai Jima ba ya fito Kaya ya sanya Suka fito har lokacin Anwar bai kirasa ba bini-bini sai ya duba wayar sa har Majid ya kasa hakuri ya tambaye sa meyake dubawa a wayan sane Wai"?akwai Wanda zai kirani ne Kuma har yanzun bai Kiraba"toh Kai ka kirasa Mana"na Kira baya d'auka ne"oh kawai Majid yace Yana tura gate in ya rufe tsallake titi sukayi,motar dake Parke a gefen titin Majid ya bude baya ya shiga shima Lahab budewa yayi ya shiga mutum biyu ne a ciki saurayin da ranan yazo ya dauke su sai wata budurwan dake zaune a gefen sa Tasha wanka cikin English wear. tafiya suke Majid da abokan Shashancin sa sai Hira suke akan party yau da kayatuwar da zaiyi,wani kayatatten Hotel Lahab yaga sun nufa gate aka bude Suka danna hancin motarsu ciki,tun Kan su Isa parking space sukejin yanda kide-kide ke tashi Kamar ba dare ba ga matasa na shigowa da mota wasu da machine harda Wanda masu xuwa da kafa ma, parking sukayi suka sassauka dukansu nufar Hall in sukayi Lahab na binsu a baya har Suka danna ciki wa'iyyazu billah Mata da mazane shakude ansha wanka cikin banzan Kaya bama Kamar matan Wanda Rabin tsiraicin su ke waje,Zama su Lahab Sukayi don ita uwar gayyar Bata shigo ba. Tsabar kid'an dake tashi shiya Hana Lahab Jin ringing in wayarsa dake Aljuhu,mikewa tsaye matasan sukayi suna ihu ganin shigowar farida cikin wasu shegun Kaya wando damamme sai riga da kwata kwatansa kasan kirjinta ga Rabin mamata ta sama a bude kannan yasha attachment ga eyelashes fuskar nan d'auke da makeover,tafiya suke ita da saurayinta da akayi birthday partynsa ranan hannun su cikin na juna da Sauri Lahab yasa hannun sa a Aljuhu ya zaro wayarsa sai a lokacin yaga miss call in Anwar,vedio ya Soma Mata har sukaje suka zauna har lokacin hannun su a cikin na juna sai wani lillikewa a jikin juna suke saving in vedio yayi ya mike da Sauri ya fita a Hall in. Saida yayi nisa da hall in yanda zaiji abinda Anwar zaice Masa Kiran Anwar in yayi bayan yayi picking yace Masa"Lahab ka kirani d'azun Ina wanka dana fito muhsab yake cemin ka Kira Niko ban kiraka ba sai dazun baka d'auka ba ince dai lafiya"lafiya Anwar don Allah kana Ina"? da mamaki Anwar yace"kace lafiya Kuma kana tambaya ta Inda nake"Kai dai ka fadamin kana Ina yanzun"?kallon agogo Anwar yayi yace Ina gidana"ok toh ayya in baka wani Abu zanzo akwai maganar da zanyi da Kai"dan shuru Anwar yayi sai Kuma yace"a daren nan zaka fito? kadai Bari gobe da safe kazo Mana"nidai dan Allah kace min eh babu ruwan ka da dare yayi"shikenan sai kazo,katse wayar sa Lahab yayi da Sauri ya nufi gate Keke ya tsayar tare da fada Masa unguwan da Anwar yake. Sauka yayi a keken ya zare 500 ya Mika ma maikeken tare da bar Masa changen gate na gidan ya tura yaji a rufe hannu yasa ya ringa dukan gate in da karfin gaskiya don unguwan sabuwar unguwa ne ba mutane sosai,bude kofar akayi Anwar ne tsaye Yana kallon Lahab dake kallon sa shima"Wai da gaske zakazo Lahab"? "Eh man Anwar da gaske nake yana maganar ya bi gefen Anwar ya shiga gidan Anwar ma bayan sa yabi,juyawa Lahab yayi ya dawo wajen gate in yasa hannu ya bude babban kofa ya wangale,zaro Ido Anwar yayi yace Wai kanka daya kuwa ana Neman karfe 10 kana wangale gate Aiko da Rana ba'a irin wangale wannan"Ina key motan ka"?shine tambayar da Lahab ya Masa"wani banzan kallo Anwar ya Masa yace kana nufin abinda ya kawoka kenan kazo ka amshi mota a daren nan toh wallahi badani ba bazaka jazamin masifa a wajen yayunka da Addayiya ba. Had'a fuska Lahab yayi yace"ba Aron mota nazo ba zuwa nayi in d'auke ka muje wani wajen da zaka Sha mugun mamaki"hararan sa anwar yayi yace kaga nifa yanzun haka a kule nake fa"meya faru toh Lahab ya tambaye sa"d'an tsaki yaja sannan yace"waifa Saida muka gama arrangements na kome farida tace Wai bazatayi bidi'a a auren taba taki yarda da kamun da za'ayi gobe,gashi na tara friends. zaro Ido Lahab yayi cikin Al'ajabi lallai farida ta shahara kuma insha Allah yau asirinta sai ya tonu,lallaba Anwar Lahab ya Fara daker da sudin goshi ya samu Anwar ya amince zai bisa wajen Amma da sharadin bazasu Kai 20 minutes ba,nuna Masa hanya Lahab yayi Suna tafiya a mota da mamaki Anwar yace ganin hotel Inda Lahab ya nuna Masa Wai su shiga yace,mezan dauka a cikin wajen Nan Kuma,anya hankalinka kalau kuwa"?kaidai muje mana bakace minti 20 ka bani ba Abu Zan nuna maka sosai ran Anwar ya baci don shi gabaki d'aya ransa ya baci ganin shirmen da Lahab ke Masa paka motar sukayi ya fito hannunsa kawai Lahab ya Kama Yana tafiya Anwar na binsa a baya har suka iso bakin hall in Shiga sukayi gabaki d'aya hall in ya hargitse da hayakin wewe,farida na tsakiyar wasu maza biyu gabaki d'aya sun sata a tsakiya sai mammatseta suke,wani Kara Anwar ya sake da karfi ya dafe kirjinsa. Jikinsa har rawa yake ya suma ratsa mutane Yana son karasawa Inda farida take Lahab Kam wayarsa ya kunna Yana vedio,fincikota Anwar yayi daga Kan cinyar guy in kafun ta Ankara tuni ya wanketa da wani irin bahagon Mari,muryarsa na rawa ya Soma magana"farida kin cuceni da ace nayi gangancin auren ki danayi nadamar da bantaba tsammani ba ashe ke munafuka ce Mai fuska biyu Allah ya Isa Allah ya Isa min,gabaki d'aya Hall in ya d'auke shuru DJ ma ya kashe kid'an dake tashi saboda abin ya d'au hankalin jama'a jin ango da kansa ne a wajen. saurayin tane yasa hannu ya zaro wukar dake kugunsa ganin mutuwar tsaye da farida tayi bana zafin Marin bane illah na tashin hankali data saka kanta a ciki,ya kaiwa Anwar yanka da Sauri ya tare da tsintsiyar hannun sa wukar ta samu Naman wajen shaa jini ya ballo da Sauri Lahab ya katse vedio ya kusa cikin taron ganin wasu gayu sun kakkama saurayin,ganin yana da niyar karama Anwar yanka, Anwar da mugun shock da farida ta sashi da Kuma yankan daya Sha shiya sakasa Kama Kai da karfi sai Kuma ya sulale ya yanke jiki ya Fadi a wajen da gudu Lahab yayi kansa cikin Kara yana kuka. Security ne Suka shigo Jin hayaniya a hall in da gudu sukazo Suka ciccibi Anwar ganin jini a hannun sa gashi ya Suma ga saurayin farida da wuka a hannu sosai Suka tsorata sun d'auka Koh kisan Kai akayi,Aiko ganin abinda ya faru daman police station na kusa waya sukayi lokaci kankani Yan Sansa Suka shigo wajen Aiko take aka Soma guje guje wasu sun gudu wasu an kamasu cikin wa'inda aka Kama harda farida da saurayin ta,Majid dai ya matso wajen Lahab sukace Yan uwan Anwar ne Kuma Yan sandan sunga Kama na jini sosai sukayi asibiti,da isarsu aka karbe Anwar hankali tashe Lahab ya d'au wayarsa ya Kira Abbu karawa yayi a kunne Harya tsinke bai d'auka ba agogon hannun sa ya duba 11 saura na dare yasan war haka Abbu ya Jima da kwantawa, Zama yayi a reception na asibitin Majid dai har lokacin Yana tsaye Yana aikawa da Lahab mugun kallo wallahi baisan farida itace matar da Anwar zai aura ba da bazai yarda ma Lahab yasan da zancen party ba, number Shareef ya Kira d'auka Shareef yayi baiyi magana ba sai Lahab ne ya Fara sallama amsa Masa yayi Yana tambayar sa lafiya?,ce Masa Lahab yayi Anwar ba lafiya Yana hospital tare da tura Masa address in asibitin. cikin kankanin lokaci Shareef ya iso tare da tambayar ba'asin cutar nasa anan Lahab yake sanar dashi abinda ya faru"Kan bala'i lallai wannan yarinya ta cika algunguma Ina vedio yake"?Mika Masa wayar sa Lahab yayi da Sauri Shareef ya karba Majid dake gefe cikin damuwa yace Shareef me zakayi da vedio?Koh kallon sa Shareef baiyi ba ya d'au wayar sa ya tura vedion a take ya sake a internet tare da Karin jawabi,ya mikawa Lahab wayan sa. Lahab Koh a jikin sa a asibitin Suka kwana su uku,washe gari maganar farida Wasa-Wasa Saida ya baza online Koh Ina ka Shiga zancen ake Kota Ina zagin farida ake wasu mazan na comments akan Koh Mata sun Kare in sune Anwar bazasu aure taba bare ma da Shareef ya had'a da hotonan ta na islamiyyar da labarin ta da irin yabonta da ake. A gidan su Lahab Kam tun daren jiya Yan Mata Suna Fara gani kankace kala tuni magana ya baza unguwan daga zaran wani ya bawa wani labari sai ace a nuna vedio Koh a tura musu a haka abu ya Fara yaduwa sai ga Kiran Shareef yake sanar da Abbu nasu Anwar na asibiti bayan Abbu take asibiti lokacin Anwar na bacci gabaki d'aya gidan bikin ya Zama wani iri kowa ka gani fuska ba walwala,11pm Anwar ya farka nurse ta fito ta sanar dasu daman ba'a fadawa matan gida halin da yake ciki ba,Abbu da Lahab sai Majid da Shareef ne Suka nufi dakin,Suna shiga Anwar ya fashe da kuka ganin mahaifin nasa,matsowa kusa dashi Abbu yayi da Sauri ya rungumesa Yana magana yana kuka yace"don Allah Abbu karka sani auren ta Dan Allah Abbu a fasa auren Nan wallahi inna aure ta Zan mutu ka taimaka min Dan Allah. Duk da ya bawa Abbu tausayi amma sai ya maze yace"ah ah Anwar hakuri zakayi mu rufa Mata asiri yanzun inka fasa auren Nan nasan kaida aure kuma sai wani ikon Allah yanzun fa karka manta kana da shekaran 35 ba aure, yaushe zakayi kenan in ba'a Yi yanzun ba don hakan zancen aure ba fashi"da Sauri Shareef yace haba Abbu dan Allah Mana in dai aka ma ya Anwar haka wallahi ba'a Masa adalci ba na rantse" Shuru Abbu yayi baice kome ba"kuka Anwar ya sake Yana cewa"wallahi Abbu na amince zanyi aure Koh Mata hudu ne na amince amma dan Allah banda farida"kana da Wance kake so a hadaku ne banda yarinyar"? Girgiza Kai yayi yasa hannu Yana share hawayen dake bin fuskarsa ganin Abbu ya sauka babu zancen farida yace"ah ah amma Ni Koh Wance ka aura min Koh zaka aura min na amince wallahi"sosai yaron ya baiwa mahaifin sa tausayi sosai"toh shikenan yanzun dai tunda ka farfado Bari likitan yazo yayi discharge naka mu tafi. Kafun azahar an sallamo Anwar a asibiti amma an dinke hannun sa don wukar ya shiga karfin haline kawai gidan suka koma saboda tsananin damuwa dayake ciki ga abokan sa dake ta maida zancen amma dai Alhamdulilah tunda ba'a d'aga biki ba,mamu tafi kowa shiga tashin hankali ganin ta samu Anwar zaiyi sure ga Kuma abinda ya faru amma Koh banza taji dadi sosai da Allah ya taimake ta ba'ayi auren ba. Family meeting na gaggawa Abbu ya had'a duk Wanda ya dace Kuma d'an uwa Koh Yar uwa na kusa-kusa duk an hallara zazzaune ake manya nakan kujera yara na kasa,da Addu'a Abbu ya Fara bayan an shafane ya Soma jawabi Kamar haka"Alhamdulilah yabo da godiya su tabbata ga Allah mad'aukakin sarki daya kawo mu wannan Rana Mai albarka,Wanda yake kunshe da abubuwan mamaki da Kuma jimami,a gaskiya abinda ya faru tsakanin Anwar da yarinyar Nan farida a gaskiya bamuji dadin abinda ya faru ba dukan mu,haka zalika yad'a abin a kafan sada zumunta. Anwar ya nuna bazai iyya yarda da auren yarinyar ba, Wanda Koh baifad'a ba nida nake mahaifin sa da yan uwana bazamu amince ba,nida jafar munje takanas ta kano har gidan su mahaifin ta Kuma mun Musa bayani,bai nuna wani bacin ransa akan abinda muka je dashi ba don dama labari ya riga yaje musu,ga akwatunan sa sun hadamu dashi mun dawo. Nida d'an uwana tare da goyon bayan kanwar mu sumayya mun yanke hukuncin had'a Anwar aure da Yar uwar sa A...................................... πŸ€ *By Ruqeenjalal* πŸ€ *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki* Page 90&91 Zamu had'asa aure da Yar uwarsa Aisha"Koh rufe Baki Abbu baiyi ba mamu tayi wani irin zabura ta Mike zatayi magana"Abbu bai bari ta furta kalla daya ba ya d'aga Mata hannu da Sauri fuskar nan tasa babu fara'a Sam don tunda take dashi Bata taba ganin bacin Rai a kwance a fuskarsa irin na yau ba sosai tasha jinin jikinta hakan yasata koma ta zauna"kuka Aisha ta sake da karfi tana rufe fuska Jin abinda bappan nata yace kamar a mafarki Wai za'a aura mata Anwar,rufe fuskar ta tayi da hijabin dake jikinta,Anwar Kam tunda ya sunkuyar da Kai Bai d'ago ba har Abbu ya kammala jawabin sa tare da cewa Suje su cigaba da buki aure ba fashi. Jiki a sanyaye Anwar ya mike yabar falon bayan fitan mahaifan nasa, Aisha Kam tama kasa tashi a wajen har lokacin bata bar kuka ba wasu daga cikin yan uwa ne Suka Soma bata baki Suna nuna Mata muhimmaci da ribar biyayya ga iyaye,nanne da wasu Yan uwansu Suka d'au Aisha Suka nufi gidan ya jafar da ita aka kafa Sabon biki a gidan dole yasa Yan uwa rabuwa Kashi biyu wasu Suka koma gidan jafar,sosai Yan uwa sukayi murnan wannan hadin shikam Anwar daga Nan gidan sa ya koma ya kwanta duk nacin abokan sa Bai saurare suba illa bar musu dakin da yayi ya Shiga wani dakin daban ya kwanta gabaki d'aya ya kasa manta abinda farida ta Masa. Misalin karfe 4 na yamma mototine cike a kofar gida Koh wace Mata Koh Yan Mata zaka ganta cikin anko ansha wanka iya wanka ana shishiga mota,alAmarya umaima dake d'aki, Masha Allah tayi wani irin kyau cikin material dinta Golden colour dinkin buba akayi zanine normal sai riga da aka d'aura zani akai kannan yasha d'auren turban ga wani yadi Mai sheki da aka rufe kanta dashi sosai tayi kyau kowa ya ganta yasan kudi yayi kuka a cikin suturan dake jikinta Banda golagolai dake wuyanta da hannu da kunne. Wata babbar mace ce ta shigo dakin tare da cewa Amarya inta gama Shirin yanzun za'a fitar da ita ganin ta a shirye yasa ta fita sai gata ta dawo da wasu matan biyu Suka dau Amarya kawaye dake cikin anko Suka Mara musu baya a haka aka ratsa gidan da ita har bakin gate,zazzafar mota baki dake tsakiya aka nufa da ita, budewa akayi ta Shiga sannan matan Suka shiga,Suma kawayen mota daban Suka shiga ba wannan ba. **************** Lahab daya gudu daga gidan ya jafar ya dawo gidan su Jin hayaniyar tafiyar kamu ta lafa yasa sa mikewa wanka yayi ya sanya Sabon shaddan sa Ash colour sabuwa Kal da ita takalmin soso ya zura ya fito daga gidan gabaki d'aya gidan shuru sai daddaiku da baza suje bane aka bari amma gabaki d'aya gidan babu hayaniya nufar gate yayi sai Kuma ya dakata Jin ana kwala Masa kira,juyawa yayi da mamaki yake kallon Mai Kiran nasa uzaifa ne"tsayawa yayi har uzaifan ya karaso kallon sa yayi da mamaki yace"Lahab baka tafi ba ai na zati ka tsufa a wajen"tunda aka Fara program ka gannin a wajen"?shine tambayar da Lahab ya Masa. Ah ah ban ganka ba Kuma nayi mamakin haka kwarai"yauwa toh ka gannin Nan bazan iyya zuwa biki, duk Inda na juya Ina had'a Ido dasu Mami ba, ban Isa ba Ni Jiran dinner nake da d'aurin aure su zanje"Kama Baki uzaifa yayi Yana dariya kafun yace"Aiko dadai ka jira daurin aure kawai,dinner Kam bana tunanin zaiyu"? "Akan me dinner bazai yuba"eh in gaya maka ya Anwar da Aisha wallahi dukan su kin zuwa sukayi ba yanda abokan ya Anwar basuyi ba yaje kamu yaki itakuma Aisha anyi anyi tayi Koh lalle ne taki sai hauka take musu ran nanne ya baci taci kaniyarta"hhhhhhhhhhhh wani bazawarin dariya Lahab ya sake Yana bude gate in ya fita baikara cewa uzaifa kome ba,Yana tsallake titin layinsu kaman ance Masa ya waigo kawai ya hangi Nnenna na tafe sanye da uniform. da sassarfa ya bita a baya a hankali-hankali,har lokacin bata juyo ba,Yana Isa bayan ta unexpectedly yasa hannu ya rufe Mata Ido,tsayawa tayi kana tasa hannunta ta tattaba nasa,sai Kuma ta hade fuska hade da cewa"Lahab sakar min Ido a bakin titi muke mutane na kallon mu"da mamaki ya sakar Mata Ido juyowa tayi garesa Suna facing in Suna"amma dai daman kin gannin Kika wani fusge Kamar baki ganni ba"da murmushi a fuskarta Wanda tunda ta hadu da Lahab tasan tana da yawan murmushi tace"banganka ba amma dana taba hannun ka na gane wanene Kai sai Kuma ta Soma bin kayan jikinsa da kallo Kamar Mai nazarin wani Abu shidai yayi shuru yana binta da Ido Kamar yanda take bin kayansa kana tace"aure ake a gidan kune"?da mamaki yace"ah ah me Kika gani "girgiza Kai kawai tayi tace"babu kome"amma me yasa Kika ce ana aure a gidan mu"ba nace bane na tambaya dai. boron ta dake bayanta yasa hannu ya cire yana cewa"ke kullum makaranta makaranta ana revision in ma bazaki sassautawa kanki ba"hade fuska tayi ta Kama tafiya tana cewa"in banje makaranta ba Ina zanje kenan"?kamo hannunta yayi kawai ya nufi kofar gidansu Adewale dake gabansu,waro Ido tayi cikin tsoro tace"Ina zaka kaini sakarmin hannu menene haka banason"kin sakin nata yayi yasa hannu ya tura gate in ya shiga,ihu ta Soma Masa tana cewa ya saketa bazata shiga ba amma yaki sakin nata maida kofar yayi ya rufe ya nufi bakin flat in hannu yasa da karfin cin tuwo ya bugawa, kofar falon,Adewale dake kwance a falo ya mike da Sauri don shi kad'aine a gidan iyayen sa sunje garin su. da Sauri ya mike Yana masifa Akan za'a balla musu kofar ne,budewa yayi sai Kuma ya sake baki da Sauri Yana cewa"kutt Kai sai Kuma yayi shuru ganin mace a bayan Lahab Yana rike da hannun ta"da Sauri ya matsa ya Basu hanya shigowa Lahab yayi har lokacin Yana rike da ita,shigowa sukayi ta fizge hannunta da gudu ta nufi kofar da har lokacin Adewale na tsaye rike da kofa baki bude idanun sa har lokacin nakan su,ganin yanda ta nufo kofa a guje yasa Ade matsawa da sauri,Lahab daya biyota shima a guje ya fincikota tare da matseta a jikin ginin kofar da karfi Yana zagin Adewale akan meyasa zai masa Mata ta wuce. da masifa Adewale yace"Wai uban mi zakayi da itane ka shigo Mana gida sannan kana wani matse Yar mutane da Allah saketa"saketa Lahab yayi da Sauri ya nufi kofar ya rufe harda makulli Zama yayi akan kujera har lokacin Adewale da Nnenna dake manne a bango Rai bace Basu zauna ba"malam yau tun safe banci kome ba ka ban abinci"amma dai Lahab bakajin tsoron Allah ba ana biki a gidan ku ba yanzun ma haka Shirin tashi nake nashirya zuwa wajen kamu". Mtwsss Lahab yaja tsaki yace"shikenan don ana biki a gidan mu sai Kuma naki cin abinci, Koh me kake nufi dan Allah kawo mun abinci"yanuna Nnenna sannan yace mata"kizo ki zauna Bari ya kawo Mana abinci"kin Zama tayi"Adewale kam kitchen ya shiga duk da baida kome dafaffe a gidan Kuma badon Albarkacin Nnenna ba bazai saurare dafa Masa abinci ba,Lahab Kam kwanciya yayi yadau remote ya chanja tasha Nnenna har lokacin tana tsaye a Inda take. 30 minutes saiga Adewale ya fito da plate d'auke da dafaffen indomie sai tururi yake kowa yasan yanda yaran yorubawa suke girki,dangolawa Lahab yayi a gaba ya koma ya zauna,mikewa Lahab in yayi ya dau plate na indomie Yana cewa Ade"Kai haka zaka kawo abinci babu ruwa ba drink's Kuma plate daya ita Kuma fa"?shuru Ade yayi baiko kalle Saba sai Kuma ya mike yabar falon,shima Lahab mikewa yayi da Sauri ya nufi Nnenna ganin haka ya sata rugawa zata gudu daga wajen da sauri,binta yayi Suka ringa zaga falon a guje aje plate na indomie yayi ya kwala ihu Yana nuna Mata kofa kamar irin yaga abin tsoron Nan,juyawa tayi zata ga Inda ya nuna matan kawai ya damkota damka bana Wasa ba. Jawota yayi ya aje akan kujera yunkurin tashi tayi ya maidata zaune daukar indomie yayi ya daura Mata akan cinya Yana bin kafafunta dake waje da kallo,hade rai yayi yace"yanzun meye amfanin wannan sutura ace mutum yasa Kaya kafa a waje cinya a waje Wai Ansa uniform"hannu tasa ta tura kirjinsa baya tana cewa"Wai meye hakane don Allah d'agani Ni banjin yunwa bazanci ba Kuma babu ruwan ka da kayana. "Komawa daya kujeran yayi ya dau indomie ya Kara daura Mata a kafa"wallahi saikin ci kici kawai sai mu tafi Ni babu abinda Zan Miki kinji"hararan sa tayi ta dau plate in ta bude ta Soma ci a hankali saukowar yayi shima yadau spoon yazo ya zauna a kasan carpet in yasa ya Soma ci,dago Kai tayi Suka had'a Ido sai Kuma ta maida kanta kasa tana cigaba dacin abincin nata 5 spoon tayi ta aje spoon in tana daukar ruwa da Lahab yasha ya aje ta Sha mikewa tayi tsaye tare da aje Masa plate in a gaban sa"ka tashi ka bude min kofa Zan tafi gida Dad nawa zai nemeni yamma yayi sosai" Kin mikewa yayi yaci gaba dacin abincin sa har lokacin Ade bai fito ba,komawa tayi ta zauna tayi mugun hade rai wayarta ne yayi ringing hannu tasa ta dau jakanta dake kasa ta bude wayar ta zaro ta duba Mai Kiran nata Abraham ne tsaki kawai taja ta maida wayar a jaka, indomie ya cinye tass ya dau plate in yakai kitchen dakin Ade ya shiga zaune ya samesa ya tasa wayar sa a gaba Yana kallon screen. Hannu yasa ya fisge wayar dake hannun Ade da Sauri ya zabura sai Kuma Yana tsaki tare da kwace wayar NASA"dariya Lahab yayi yace"wato Kai haryau kana fama da wannan makauniyar soyayyar"?in soyayyata makauniyace toh kaima ka Fara makancewar"da shekiyanci Lahab yace"Kamar ya nima na Fara makancewar"? Wani murmushin gefen Baki Ade yayi ya nuna kofa yace Masa gata a falo"da Allah waya cema soyayya nake"in ba rami Lahab meya kawo zancen Rami ai nima bance ba"juyawa kawai Lahab yayi Yana cemai kaga na tafi sai kaci gaba da kallon hotonan nata ban ma San a Ina ka samo pictures in ba nadai San ba ita ta baka ba malam" Fitowa sukayi a gidan boronta Lahab ya bude yadau wayar ta number sa ya saka ya Kira wayar sa ya maida Mata itadai tana kallon sa batace kome ba tsallake titin sukayi har lokacin Yana binta Suka nufi layin su,tayi tayi dashi ya koma amma ya ki tun daga nesa ta hangi Dad Mom da sauran Yan gidan tsaye a compound na gidan daga ka gansu kasan hankalin su ba'a kwance yake ba Abraham nata surutu,da Sauri Nnenna ta dakata tare da rokon sa akan ya koma kada iyayenta su gansu tare. Tsayawa kawai yayi ita Kuma ta wuce amma Yana iyya hangota tunda ta nufi cikin gidan gabaki d'aya Suka zuba Mata Ido tana shiga Dad ya wani zabura cikin bacin Rai Suka rufeta da fada mom Kam tsinketa da mahaukacin Mari tayi Nnenna ta dafe kumatun ta tana hawaye,ashe abinda su Lahab basu sani ba lokacin da ya rike hannunta Abraham dake cikin mota ya hangosu harda shiga gidan su Ade da sukayi shine ya dawo ya sanar da iyayen sa ya kirata Kuma taki d'agawa sosai Dad ya zazzage ta tare da cewa duk randa ya Kara ganinta da wani dan hausawa sai ya cireta a makaranta Kuma ta bar Masa gida. ************************ Friday gidan su Lahab yau Koh matsakin tsinke babu yau ne d'auren aure, jama'a ne kamar kasa,kayatattun abincin dauren aure ake shiryawa a takeAway Masa ne da miyar ganda sai drink's ana arrange na abubuwa da gift na d'aurin auren sosai gidan ya hargitse da jama'a especially da yanzun kwata kwata bai wuce 3 hours ya rage a daura auren ba bayan sallan juma'a,Lahab dake daki ya fito wanka daure da towel,da mamaki yace"Rahab ya na ganka har yanzun da towel baka shirya ba harna fito wanka"? Juya fuska Rahab yayi yace"Ina ruwanka ne Wai ma"?babu ruwa na Kam shine abinda Lahab yace Yana shafa Mai a jikinsa bayan ya goge, wayar sa dake gefe ya d'auka ya Kara Trying number ta a Karo na ba adade Kamar yanda ya Saba haka yaji a kashe,mikewa yayi ya bude wardrobe nasa farin shaddan sa ya zaro sabo gal dashi sai maiko yake zura wando yayi yasa rigan have joppa ne, liss yasa a hannun sa baki yad'au takalmin sa sabo shima Baki ya sanya bayan yasa socks Baki hula ya saka Baki ya sanya ya daura agogo kallon kansa yayi a madubi yayi wani mugun kyau ga kwarjini daya bayyana kirikiri a fuskar sa ga sajen Nan NASA ya taju yayi kyau turare ya d'auka ya feffesa,had'a Ido sukayi da Rahab dake kallon duk abinda yake,hararan sa kawai yayi baice kome ba ya sa Kai ya fita a dakin,ganin har 1:30 yayi. A hankali yake tafiya Harya nufi corridorn Abbu Yana dube dube gudun kada wani ya gansa dayake sashen Abbu babu Baki a wajen gashi abbun ya tafi masallaci,bude dakin yayi da Sauri ya Shiga wajen drowern mirror ya nufa ya bude Key's na car insa daya sabuwar ya d'auka da Sauri ya nufi kofar Harya bude kofar sai Kuma ya koma baya da Sauri ya nufi cikin cotton na dakin ya boye ummu ce ta shigo dakin hannun ta d'auke da food flask Mai kyau d'auke da abinci ta aje a dakin ta juya ta fita da Sauri shima ya fito tare da nufar kulan ya bude kazane aka soya Masa sai tuwon shinkafa da akayi miyan shuwaka aka tsoma Kazan a ciki spoon yasa ya dauko cinya daya ya maida kulan ya rufe fitowa yayi a dakin bayan ya cinye cinyar ya bude kofa ya fita Inda Allah ya Sosa Harya iso babban falo ba Wanda ya gansa kofar baya ya nufa ya bude sai gashi ya fito a bayan flat nasu. garejin ya nufa ya bude,wata babban Jeep ya nufa ya bude duk da akwai Kura kad'an haka ya kunnata bayan ya shiga yayi reverse yaja motar,ya ratso tsakar gidan da mamaki mamu tace"ah ah waya dau motar Alhaji Kuma bayan ya fita amma wallahi Shareef bayajin magana Sam Sam kullum ina fada Masa ya daina daukar motar baban sa Amma bai dainawa"sai Kuma ta nufi motar ganin ya tsaya Mai gadi na bude Masa gate. da Sauri wata kawarta tace"haba Amina yaufa daurin auren yayan sane ki barsa Mana Kika sani Koh zai d'auko Yan daurin aure Jin abinda sukace yasa ta komawa ta zauna Suka cigaba da hiran su ana kimkimtsa abinci. da gudu Lahab yake fasa unguwa duk Inda ya wuce Saidai kaga Kura fuuuuuuuuu yabi motan a baya jama'a sai kallon motar suke Suna salati a guje ya nufi kofar gidan su Nabeel tun daga nesa Suka Fara dariya don su wallahi kallo daya suke ma motar da Lahab ke tukawa su gane shine daga gudun motar kawai zaka gane, parking yayi Saida motar tayi gaba kadan ta dawo baya kafun ta tsaya,matsowa kusa da motar sukayi Nabeel Yana cewa"don girman Allah ka baiwa Adewale key ya tukamu wallahi Lahab tsoron hawan motar da kake tukawa nake ji nake Kamar ajalina na tinkaro a cikin motar . glass baki Lahab ya dauko ya kwaba a fuskar sa yace"kaga Ade shigo muje lokaci na kurewa don Allah karna rasa sallah bude gaban Ade yayi ya shiga,Nabeel Kam badon ransa yaso ba ya bude baya ya Shiga ya zauna har Lahab ya tada motar saiga mubeena ta fito daga gida da Sauri ta nufi motar cikin zakuwa dason ganin abinda take so tunda taji Nabeel yace Lahab zaizo su tafi masallaci tayi wanka ta zauna tana jiran sa"Lahab Ina kuka nufane"da Sauri Adewale yace masallaci zamuje in akwai Inda kike son zuwa shigo mu sauke ki" "Masallaci zamu Kuma mun makara don haka kawai big Aunty ki nemi motocycle,bude bayan motar tayi ta shiga tana cewa"wallahi sai ka kaini Zan sauka a kofar gidan su Fati dake hanyar tudun wada Kuma ai Naga sai kunbi wajen kafun ku Isa massalacin"kala Lahab baice ba yaja motar Suka cillah,tafiya suke motar shuru babu hayaniya sai wakar da Lahab ya sake duk ya cika musu kunne Nabeel Kuma Allah Allah yake su sauka lafiya bini bini mubeena sai ta kalli madubin gaban motar amma abin takaici maimakon taga Lahab sai su had'a Ido da Ade. Sun aje mubeena a tudun wada kafun suka wuce masallaci Ade kawai Suka Bari a mota,su suka Shiga ciki after jumaat prayer,kofar gidan su Lahab mazane a cike tim don auren Aisha ma anan za'a d'aurashi dole waje ya cika d'auren aure biyu za'a Yi gashi d'aga bikin na farko ne,bayan an daura auren kowa ka gani fuskar nan Kamar gonar auduga kada ma sadeeq yaji labari Wanda aka daura nasu akan sadaki naira dubu 100k cicib,Anwar kam yake kawai yake Amma kowa ya gansa zai zaci baida lafiya ne gabaki d'aya yayi sanyi sai yawo yake a cikin gare. Tund'a zun da Lahab ya Parka motar Abbu Abbu ya gansa kawai yayi shuru ne Albarkacin idon mutane amma kaffa kaffa yake da Lahab kada ya bar wajen da motar sa Lahab dake rarrabawa jama'a laidodi daya d'auko daga cikin gida a cike a basket babba duk Wanda ya baiwa sai kaji ana cewa wannan ba dan Alhaji Al'hassan dogo Mai naira tsohon minister,Kai Masha Allah tagwaye sun girma yau da gobe yafi karfin wasa,shikam Lahab rabon sa kawai yake da kalandun daurin aure Kamar ance ya kalli gabansa Rahab ne ya fito da basket gifts a hannun sa, sak irin shigar da Lahab yayi shine shima yayi Inka gansu a lokacin karyar ka banbantasu kome na Lahab Rahab yasa hatta turaren sa sai yanzun Lahab ya fahimci dalilin dayasa Rahab yaki saka Kaya Harya bar dakin, Adewale dake gefen sa shima Yana rabawa mutane takeAway yaji an fizgo sa da Sauri ya juya sai Kuma ya sake laidan hannun sa ganin Wanda ya rikesan ba kowa bane illah.......................... πŸ€ *By Ruqeenjalal* πŸ€ *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki* Page92&93 Papa ne ya wanke Ade da wani irin Mari ya hau masifa hakuri jama'a Suka Soma basa ana cewa yayi hakuri ya bar Ade amma Ina keyar Ade ya tasa a gaba Suka bar wajen,Lahab Karan kansa ransa ya baci bana Wasa ba Sam baijin dadin irin yanda papa ke nuna masu kiyayya Kiri-Kiri babu Koh boye-boye,rarraba abinci suka cigaba dayi shida d'an uwan sa Koh Ina Suka wuce sai kaji Wa'inda Basu sansuba Suna cace Kai tagwaye masu Kama wa'inda suka sansu Kuma sai suce ga yaran Al'hassan marigayi yara sun girma. bayan d'auren auren karfe 3 akayi walima a babban hall had'a Aisha da umaima akayi aka musu walimar har lokacin Aisha taki yarda Koh lalle a Mata sai hauka take,bayan an tashi a waliman saiga mototin Yan bauchi da niyar a ranan zasu wuce da Amarya,dagewa kawayen mamu sukayi sai dai a bari gobe da safe a wuce,su Kuma dangin sadeeq sukace yau zasu wuce basu shirya kwana ba anan dai akayita kace nake karshe Abbu da kansa ya fito ya dau umaima ya danka musu bayan Nasihat da ya Mata ya Kira mamu sukayi sallama da Addayiya da sauran wa'inda Suka face. Yan uwa Suka Mata rakiya sosai zata baka tausayi in kaga irin kukan da take Kamar ana yankata,rabuwa da iyaye akwai jimami,aka wuce da ita Lahab Kam tun a wajen daurin aure ya d'au mota abinsa bai tsaya a gida ba yawo Suka ringayi da Adewale Nabeel tunda ya samu Suka dawo massalci yace wallahi bai sake Hawa don Sam,shikuma Lahab yaki yarda ya koma gida gashi anata Kiran sa a waya amma yaki d'auka. da misalin karfe takwas na dare Lahab ne da Adewale a mota sai bada wuta Lahab yake, unguwan su ya jafar ya nufa tun daga nesa ya hangi mototi a cike da kofar gidan tim, parking shima yayi a gefe wasu Yan Mata suka bude Suka shiga don su sun d'auka motar d'aukan aure ne Saida mototi Suka cika kafun aka Fara tafiya,Amarya Aisha aka Kai gidan mijinta angonta Anwar har lokacin kafarta fari fat ba lalle daker aka samu aka fitar da ita don kuka take bil hakki da gaskiya,Lahab haka ya ringa daukar mutane Yana juyewa Yana dawowa har kusan karfe 9 na dare. bai koma gida da ba Koh maida motar ba saima gidan ya jafar ya koma yaje ya fakata sanann ya hau Keke napep,gidan su Nabeel ya nufa agun ya kwana,washe gari da safe bayan sun dawo masallanci ya koma bacci don a gidan kaf babu Wanda yasan ya kwana Saida asuba da Inna ta fita sallah ta gansa a duke yana Alwala. *************** ringing in wayarsa shiya farkar dashi bude idanun sa yayi a hankali yasa hannu ya lalubo wayar dake gefen dollof,daukar wayar yayi bai wani kalli screen in ba ya danna tare da karawa a kunne,da Sauri ya mike zaune Yana Ware Ido tare dasa kafa ya shurar da kafar nabeel daya daura Masa a kafada Jin muryar Maminsa ta cikin wayar cikin bacin Rai take tambayar sa Inda ya kwana"Mami Ina gidan su Nabeel nefa"ka taso yanzun yanzun Nan kazo ka sameni a gidana wallahi ka Kara minutes 20 baka zo ba sai nayi mummunan Saba maka nonsense kawai"tana gama maganar ta yanke wayarta. Sake Baki Lahab yayi Yana bin wayar da kallo cikin mamaki sai Kuma ya mike zaune da Sauri wandon sa dake Kan kayan Nabeel ya jawo ya sanya Akan gajeren wandon dake jikin sa wankan da yake son yayi ma fasawa yayi ya d'au rigansa da Sauri ya bude kofar dakin ya fita,cikin kankanin lokaci ya Isa unguwar su Mami gate na gidan ya buga da karfi Mai gadi ya bude Masa,cikin gidan ya shiga da sassarfa don shi Sam yasan bawai Kwanan sa a wani waje bane ya d'aga Masa hankali illah yanda yaji Mami tamar magana ne yasan babu lafiya. tura kofar falon yayi ya shigo sai Kuma yayi turus ya tsaya ganin Wance ke tsaye a tsakar falon,a hankali ya karaso ciki mamin sane zaune akan kujera sai Alhaji sulaiman shima a zaune yake ga Rahab a zaune akan carfet,farida(budurwar Anwar na da)ce tsaye kallo daya zaka Mata kaga ainahin Kamar ta na rashin mutunci gabaki d'aya ta zafge sanye take da lafcecen hijab har kasa sai nikaf data daga shi sama fuskar ta a bayyane,nuna farida yayi da yatsa Yana yamutsa fuska yace"wannan Kuma wacece Mami me take a gidan Nan ba auren ance an fasa da ita ba metake mana anan" Juyowa farida tayi fuska jawur idanunta a kumbure sumdum ta Soma magana Kamar haka"wallahi tallahi Lahab tunda ka rabani da farin ciki ka rabani da walwala ka Haddasa min bakin ciki na rantse da Wanda Raina yake hannun sa Koh zanyi yawo tsirara Lahab saina Haddasa maka kaima bakin ciki ka rubuta ka ajiye nazone na baiwa uwarka sallahu tunda har kayi sanadin da bakin ciki ya kashe mahaifiyata ta bar duniya jiya Kuma akan abinda kayi bazan barka ba. Mikewa Mami tayi tace"ke karamar Yar iska, ya kashe Miki uwa Koh bakin cikin ki ya kasheta shasha Sha karamar Yar bariki zakizo kice bazaki bar dana ba a gabansa, toh wallahi bazan bar maganan Nan ba sai mun danganta da kotu sai an rubuta Kamar yanda Kika ce duk abinda ya Sami d'ana kece sula ba Baki da mutunci ba Zan gwada Miki yanda ake rashin mutunci Mami na karasa maganar da Sauri ta shiga dakin ta,ganin hakan yasa farida barin gidan da Sauri tana rantse rantse bazata barsa ba. Lahab Kam da Rahab duk shuru sukayi suna mamakin yanda farida tasan Lahab ne ya tona Mata asiri,fitowa Mami tayi a dakin tana waya da wani barrister akan zata Kai kara station yanzun za'a turo su kotu,kofar falon ta nufa hannun ta d'auke da hijab har lokacin hannun ta Kare da waya a kunne,da Sauri Alhaji ya mike Yana dakatar da ita akan babu Inda zataje ta koma ta zaune bude Baki Mami tayi tace"taya zanyi na zauna wannan shegiyar yarinya Harta Isa ta shigo gidana a gabana tana ma yarona warning harda Shan Alwashin bazata barsa ba kasan me zata Masa gaskiya ban yarda ba wallahi dole nasan abunyi. Nace ki dawo ki zauna Amina Kika San Koh zafin mutuwar mahaifiyar tane yasa ta fadin haka dame zataji yanzun da mutuwar Koh da abinda Zaki Mata yanzun"d'aga Masa hannu Mami tayi cikin masifa tace"wani irin Bata hayyacin ta Bata hayyacinta ne zata gayamishi haka watoh nabar maganar ta wuce,daga baya nazo Naga d'ana cikin wani Hali bada Ni ba" Kinji na rantse Amina babu Inda Zaki na gaji nagaji wannan wani irin abune haka fisabililahi,ban Isa dake ba kenan Koh ban Isa nace kibar Abu ki Bari ba,sai Kuma ya mike tsaye cikin bacin Rai yasa Kai yabar gidan,komawa tayi Kan kujera ta zauna ta dafe kanta,da Sauri Lahab da dan uwan sa Suka nufi mahaifiyar tasu ganin Kamar kuka ta Fara rungumar ta Lahab yayi a rikice,da Sauri ta turesa tare da wanke sa da Mari ta Soma magana cikin kaushin murya"matsa min daga jikin Lahab ya zanyi da Kai ya zanyi da Kai duk abinda na fada maka bashi kake aikatawa ba kwata-kwata Bakaji Koh don mahaifin ku baya rayene,ni Kuma bana tare dakune shiyasa kuke abinda kuka ga dama so kake hawan jini ya Kamani nima na mutu na barku............. da Sauri Rahab ya rufe Mata Baki hawaye na bin kumatun sa yace"don Allah Mami kada kice haka, ki sanya Mana albarka don shi mukafi bukata a Yanzun insha Allah Koh babu mahaifin mu a duniya zamu zamo abin kwatance da Alfahari bazamu taba yin abin Allah wadai ba Abbu ya jafar ya muzammil Suna iyya bakin kokarin su wajen ganin sun tsaya a Kan tarbiyar mu Mami in bazaki yaba musu ba,Bai Kamata kiga gazawar su ba akan muba. Rungumar dan nata tayi Lahab dake zaune a kasa tunda ta turesa daya sunkuyar da kansa har yanzun bai daga ba,Saida yaji abinda mamin nasu ke cewa"Lahab tun farko Nika Fara kawowa zancen farida nace maka ka bar zancen ashe Lahab baka bari ba Saida ka bibiye yarinyar Nan,ka tona Mata asiri yanzun Kuma tazo tasha alwashin bazata barka ba meyasa kake son damuwa da wa'inda basu damu da kaiba kake son gwaninta wa wa'inda gwanintar taka ba ganin sa zasu Yiba meyasa-meyasa nace meyasa Lahab"ta tambaye sa da karfi. dagowa yayi idanun sa jajer yace"Saboda d'an d'an uwana ne bazan so mugun iri a cikin zuriyar mu ba Kuma na tabbata Koh nine Anwar shine Ni sai Inda karfin sa ya Kare wajen Hana wannan aure, murmushin takaici Mami tayi tace"lallai yaro baisan wuta ba saiya taka da ace kasan wacece Halima da bazaka d'aga Ido ka kalli yaranta so biyu ba Halima ta musguna min a rayuwa Halima tamin sharri kala kala bata da makiyiya kamar Ni,amma nasan baka San tarihin gidan ku ba illa Suna da ka sani da yan uwan ku,a yau Zan baka labarin tushen aure na da mahaifin ku da Kuma dalilin auren nasa yana babban mutum Ina yarinya. **************** WAIWAYE ADON TAFIYA............... Alhaji Al'hassan dogo Mai Naira shine cikekken sunansa ainahin su Fulani gombe ne haifafun cikin gombe Alhaji Al'hassan tagwaye ne dattabai masu sananin Kama da junan su Wanda a lokacin zaiyi wuya kaga tagwaye tsofafe masu Kama irin shida d'an uwan sa Al'hassan tare Suka taso kome iri daya suke Hatta karatu course d'aya Suka karantaAlhaji Al'hassan nada Mata d'aya kwallin gwal,Hajiya Aisha Wanda yaranta suke kiranta da Addayiya auren saurayin da budurwan sukayi da ita har Allah ya azurtasu da Y'ay'a guda biyar Umar(abbu) sai da Umar yayi wayo ya Soma zuwa makaranta kafun aka haife jafar saboda haihuwar Aisha tana da tazara sosai Saida jafar ya girma kafun ta haifi sumayya (goggo) sai autan ta Muzammil (uncle). Alhaji Al'hassan kudi sun zauna sosai haka ma Al'hussain shima yayi aure amma har tsawon shekaru matarsa bata taba haihuwa ba,duk da Al'hassan yasha basa shawara akan ya Kara aure amma kememen yaki yace haihuwa na Allah ne Kuma Koh baida rabon Y'ay'a a duniya y'ay'an Al'hassan Suma sun isheshi da haka yake kashe Masa Baki. Umar yayi aure bayan ya kammala karatun sa har mahaifin nasu ya gina Sabon kamfani Kuma ya basa manager a company in yana gudanar da ayyukan ciki,Umar nada yara uku da matar sa Halima(mamu)d'ansu na farko Anwar sai Mai binsa Shareef da kanwar sa umaima,bayan haihuwar umaima ne ya Kara aure ya aure ummu ta Haifi d'anta na farko uzaifa a lokacin. Jafar yayi aure shima ya aure Khadija (nanne) Yana aikin gonnati,Yana da yara hudu Hashim Fatima sai Aisha(Amaryar Anwar)sai auta Majid a lokacin ma Yana jinjirin sa,sumayya(goggo)tayi aure ta auri sarkin katsina tana zaman aure a shan, muzammil lokacin an Fara Zama saurayi har an shiga jami'a ana karatu a cikin gombe. Al'hassan mutum ne Mai hakuri dattako dajan nasa a jiki sosai, An basa minister of labour and employment,kudi ya zauna sosai hakan yasa sa gina babban gida yadau 'Ya'yan sa da d'an uwan sa(Hussain)ya maida su cikin gidan,gidane da ake zaman lafiya Kuma babban gida sai abinda baza'a rasa ba mamu(halima)macece Mai masifar tsiya da kasa hakuri yayin da ummu ta kasance Yar ba ruwa na hakan yasa zaman su yayi sanyi don Koh mamu ta hau ummu Bata kulata, Addayiya akwai gajeren hakuri sai dai macece Mai tausayi matuka tana kaunar mijinta da Masa biyayya sosai sannan babu ruwan ta da sawa surkunaye Ido daman part nasu daban tsakanin tama dasu akwai rata shiyasa ba'a Jin kansu,gogo badawiyya(matar Alhussan)daman ita macece Mai sanyin hali ga yawan shuru shuru shiyasa gidan baida hayani Kamar gidan yawa. A wata Litinin Alhaji Al'hassan da tawagan sa Suka je wani kauye na Fulani usul dake karamar hukumar bajoga dake cikin gombe,wani rikici ne daya hafko tsakanin Fulani da manoma,sosai akama Fulani barna Kuma ya mugun tausaya musu shiyasa ya taso takanas yaje rugan,minister ya mike ya shiga rarrabawa jama'a kudi sosai Yan kauyen Suka cika da murna ga kayan masarufi da aka sauke musu mota babba ana rarrabawa buhuhunan shinkafa da masara,tun daga nesa ya hangota d'auke take da Robobin nonon ta akai dawowar ta kenan daga cikin gari ta Kai tallan no-no tana dawowa su uku ne suke tafe tana tsakiyar su,ganin yanda ake rabon abinci da kudi yasa sauran abokan tafiyar tata Suka aje Robobin su da gudu sukayi wajen motar da Kuma dattijon dake raba kudi,tunda ta d'aga Ido ta kalli wajen bata Kara kallo ba tafiyar ta kawai ta cigaba dayi. Mikawa PA nsa kudin hannun sa yayi ya cigaba da rabawa,ya nufi barin wajen da Sauri security Suka mimmmike zasu bisa,ganin hakan ya Sasa shiga mota kawai ya zauna amma bai rufe murfin ba Yana kwanton yaran da suke tare da ita,yafito security yayi ya sanar dashi akan ya Kira masa yaran da suka d'au buhun shinkafa ta gwannati akan sun Nan su biyu,Kiran su security sukayi duk da kowa yasan yan kauye da tsoro hakan bai hanasu zuwa ba,Jin Wanda ya raba musu kudine ya kirasu aje shinkafan sukayi da Sauri Suka nufi motar. Kabo na Isa gida ta aje roban nonon ba tare da ta saurare masifar da innon ta ke Mata ba akan ta San ana raba Abu bazataje ta karbo ba ai in bata samu ba,yayan ta zai samu in Kuma Suka samu dukan su karuwan sune,daki kawai kabo ta shiga ta fito da soson ta sai sabulun sodan ta dan kankani taja ruwa a rijiya cikin k'walla ta nufi kewayen nasu,Aminatu shine cikekken sunan ta yarinya ce da bazata wuce shekara 16 ba kyakkayawar bafulatana ce Fara Sol da ita sai kauyanci daya Kara boye sirrin kyawun nata sosai. Amina(kabo)y'ace ga malam jibril marigayi Mai Almajirai da matar sa Rabi(inno)tun Amina na karama Allah ya ma mahaifinta rasuwa su biyu iyayen ta Suka Haifa ita da dan uwan ta muneeru,Aisha irin yaran Nan ne masu tsananin son karatun boko hakan ya sa ta sanyawa ranta son karatu sosai,duk da bata makarantan amma haka take sanya uniform data sayawa kanta tana zuwa tun ana koranta saboda iyayen ta basuzo sun sata ba har malaman Suka hakuri abinka da makarantan kauye taci gaba da zuwa(kuyi hakuri Yan kauye karkuce Ina ci muku fuska labari ne) Sulaiman shine kadai saurayin kabo(Amina) sulaiman na tsananin son Amina fiye da tunanin Mai tunani da farko Amina Bata sauraron sa don ita kwata kwata soyayya baya gaban ta kowa yazo zata saka bori tace Bata sonsa sa'o'inta duk an aurar dasu sosai ake zagin inno a rugan su akan taki aurar da ita ta barta tana yawo,sulaiman yaro ne Mai hankali kowa ya shaida hakan shiyasa lokacin da Amina ta Soma sauraron sa sosai inno taji dadin abin. Sulaiman dan makaranta ne yana karatun sa a birni na gaba da secondary abinda yasa Amina ke dada sonsa kenan kullum Suka hadu sai Hiran Makaranta take Masa daya koya Mata kaza kaza a hakan ya samu Shiga a wajen ta hardai Suka Soma soyayya kowa a kauyen ya sani ata dalilin Amina sulaiman ke komawa rugan su duk sati sati juma'a zaizo da yamma sai Kuma ranan lahadi ya koma da yamma,Inna kullum matsawa Amina take akan zancen sulaiman ya turo amma duk lokacin da ta kawo Masa zancen sai yace tayi hakuri ya kammala karatun in ya samu aiki sai suyi aure, in bai samu ba Kuma ya dawo kauyen su ya cigaba da kiwo kamar yanda ya taso. Wannan shekarar ya kammala karatun sa ya muneeru da kansa yaje ya samu kawun sa sukaje wajen iyayen muneeru akan auren sa da Amina,amma sulaiman yace suyi hakuri zai tafi NYSC a kasar inyamurai a bar zancen auren saiya dawo insha Allah za'a Yi kome a gama sai ya cigaba da zaman sa a gida,badon ran inno yaso ba ta hakura,a takaice dai yanzun Amina na rugan su sulaiman na kasar inyamurai. Bayan kabo ta fito wanka daidai lokacin muneeru ya shigo gidan da buhun masara a bayan wuyan sa daker daker yake tafiya da Sauri Inno ta Mike tsaye Tama gyara daurin xanin ta,tana magana,haba muneeru ya zaka dauko masara haka a kanka bazaka nemi amalanke ba,sauke masaran yayi Yana Bata amsa da fullacin"inno am hatou mi hebata ai dinka mi Ronda tam,da murna ya zaro kudin aljuhun sa wanda a kalla zaikai dubu goma ya nuna Mata Yana cewa ashan Aka Basu wani Mai kudine yazo kauyen nasu,da Sauri Inno tasa hannu ta fizgo kudin tana kirgawa tana washe baki tare da daukar 1k ta mikawa muneeru tana tsoka sauran a bakin zanin ta,girgiza Kai kawai Amina tayi ta shiga daki tana mamakin irin son kudin inno. Bayan sallan la'asar saiga kawo shehu yazo gidan su kabo Bata San meya tattauna da inno ba tadai ga inno sai fara'a take tana Nan da nan da ita itadai Amina Bata tambaye ta ba,yaro ne ya shigo gidan Koh sallama babu ya Soma karade gidan Yana cewa Wai ana sallama da Kabo a waje,da murna Amina dake daki ta fito tare da zare gyalenta dake saman Zama ta yafa a zatonta sulaiman ne yazo hutu don yace Mata wata uku zaiyi yazo hutu Kuma gashi an cinye wata biyu. Inno dake tsaye a bakin madafa da Sauri ta kwala Mata Kira ganin zata fita kofar gidan,dawowa Amina tayi cikin kunya don wallahi Bata zati inno na waje ba sunkuyar da Kai tayi,itakam inno cewa tayi akwai wani turare da muneeru yaje binne ya sayo min tafi wata na boyeta kije ki dauko a cikin kwalba ki fitsa ki shafawa kafar Nan Taki vasilin,da mamaki kabo ke kallon ta tunda take inno Bata taba sata fisa turare ba sai yau amma batace kome ba ta shiga ta dau turare ta shafa,mulkawa kafarta Mai da Sauri ta fito tana lekan labule ganin inno ta shiga bandaki da Sauri ta fito ta nufi kofar gidan. tsaye yake a jikin zanan kofar gidan ya jingina da bishiyan cabbulle dake manne da zanan,tunda ta fito yake binta da kallo ganin sai kalle-kalle take had'a Ido sukayi ta kauda fuska tana cigaba da dube-dube Kamar tana Neman wani Abu,cikin taushin muryar sa yayi Mata sallama,amsawa tayi sama-sama tana cigaba da abinda take,Gimbiya Aminatu kabo nine bakon da kike nema" Wani irin juyowa tayi a kaikaice tana Kara kallon mutumin Wanda a haife yayi jika da ita Wai shine Wanda ya tura a kirata toh Koh Tayi Masa laifine ita da ba sanin sa tayi bama bare,toh Koh ta Masa Kama da Yar aikane da zai turo a kirata ya aiketa kenan........................ ................. *In na samu charge zakuga update da dare* 🀸🀸🀸🀸🀸🀸🀸🀸🀸🀧 πŸ€ *By Ruqeenjalal* πŸ€ *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki* Page 94&95 tsayawa tayi daga nesa tana kallon sa da mamaki sai Kuma ta durkusa har kasa ta Soma gaidashi"Kaka Ina wuni"d'an murmushi yayi yace taso Mana Aminatu mun wuni lafiya"tasowa tayi tana tambayarsa da lafiya yake Kiran ta,babu d'ard'ar Koh Jin kunya anan take ya bayyana Mata soyayyar sa da Kuma niyar sa na auren ta,wani irin harara Amina ta maka Masa sannan tace"yanzun Kai banda rashin tsoron Allah bawan Allah daga kawai kazo garin mu ka Mana kyauta sai Kuma ka Soma bin yara gida,Kai Koh kunya Bakaji ba tsofe-tsofe da Kai kazo kace kanason yarinya Kamata amma dai wallahi anji kunya girma ya Fadi Niko yanzun me zanyi dakai gemu duk furfura toh wallahi Bari kaji tun ban nuna maka halina ba ka kwashi kafafun ka kabar Mana kofar gida. Sosai Alhassan yayi mamakin yanda Amina ke zuba Masa tsiwa amma a maimakon yaji d'ar akan son da yake Mata saima yaji son ya karu sosai yake Jin son Amina a ransa bana Wasa ba shi Karan kansa yasan yazo neman aure a Inda bai dace dashi ba yarinya kankanuwa Kamar wannan yasan abun kunya ne zai jawa yaransa da matansa amma ya zaiyi,shi so haden Rabbi ne lokaci d'aya yake shiga amma fitar sa Bata da iyaka,yanda takejin yarinyar kaf duniya banda iyayen sa da Suka mutu babu Wanda zai hanasa auren yarinyar Nan sai wani ikon Allah babu ruwan sa da abin kunya tunda addini bai haramta ba. tsaki Mai karfi Amina ta sake ta juya fuuu ta koma cikin gidan nasu ranan haka ta kwana Koh abincin dare bataci ba washe gari da safe ta tafi makaranta tana dawowa tadauki tallan nonon ta,da yamma bayan ta dawo daga tallah ta nufi gida tun daga nesa ta hange mutum zaune a kofar gidan su abin mamaki ba kowa bane sai mutumin jiya,Yi tayi Kamar Bata gamsa ba tazo zata wucesa da Sauri ya mike yabi bayanta Yana Mata magana ganin tana Shirin shiga gidan"haba minatuwa Baki ganni a tsaye bane tun fa 12 na Rana nake zaune anan bayan nazo akace min kin tafi tallah nake zaune Ina jiranki amma shine Zaki ganni ki wuce. dan dakatawa kawai tayi Saida ya gama maganar sa kafun tace"wallahi tsoho ka rabu dani Koh bakaji menace maka bane Wai"?naji Mana amma Ni bazan iya hakura dake ba gaskiya"sosai Amina taci Masa mutunci iyya mutunci kafun ta barsa tsaye a wajen ta Shiga cikin gida inno dake labe tana Jin duk irin cin mutuncin da Amina ke Masa,tana shiga daki inno ta bita da sharbeben d'anyen Kara duka ta rufe Amina dashi tana cewa"ke Harkin Isa kimin bakin ciki in Kika Kore wannan in wazaizo ya aure ki Koh so kike kiyita jazamin magana a gari,toh wallahi Bari kiji Koh sulaiman ne ya dawo bazai Hana a fasa auren ki da Alhaji Nan ba Yar banza hutu yazo Mana Zaki min bakin ciki tunda mahaifinku ya rasu Nike jegele da gida yanzun da Allah ya amshi Addu'a ta Dana Dade inayi shine Zaki min hassada,da gudu muneeru dake dakin sa ya shigo yazo ya kwace ta, ganin irin dukan da inno kema Amina kamar zata yankata ga Amina da taurin Rai Koh ana dukanta Bata gudu. Fizgota yayi da Sauri ya shigar da ita dakin sa ganin inno nason karyo wani Sabon bulalan rufe kofar bukkan nasa yayi,Zama Amina tayi tana kuka sai rarrashin ta muneeru keyi yana bata baki shidai baice Mata kome Akan Alhaji ba, yadai nuna Mata tayi hakuri insha Allah kome zai daidaita sai Wanda takeso zata aura insha Allah zai tsaya Mata, Jin hakan yasata ta danjin sanyi-sanyi Saida fa zazzabi ya rufeta ainun kwanciya tayi a katifar yayan nata, shikam fita yayi ya dauko Mata jikekken maganin su dake gindin Randa ya tsiyaye Mata a kwanon Sha ya kawo Mata kin sha tayi don ita Bata kaunar jikekken magani sam. Wasa Wasa Abu ya Zama gaske tun Amina na d'aukan abin a shirmen Abu ya Fara girma sosai Alhaji ke surfa Mata naci ba ranan da baya zuwa Koh karyan ciwo tayi sai inno ta tasata a gaba harsai ta fita inta fita babu abinda ke had'ata dashi sai cin mutunci sosai take Masa rashin kunya shikam Bai karaya ba Sam,muneeru baison aure saboda harga Allah yasan ba'a ma Yar uwarsa adalci ba ya tinkare inno da maganar amma ta rumtsa Ido tace aure sai anyi,abinka da magana a ruga lokaci d'aya zance ya karade gari Amina ta samu Alhaji zai aureta baza'a bawa sulaiman ba sosai iyayen sulaiman Suka Soma gaba da gidan su Amina,Allah sarki Amina Kam hankalinta yafi na kowa tashi Bata San ya zatayi ba gashi sulaiman baya na. A bangaren gidan minister Suma sunsha mamaki da sukaji an baiwa Alhassan Mata a zaton su ma babbace tsohowa Kamar Addayiya,amma duk da hakan Addayiya ta nuna kin amince warta akan me zai Karo Mata Amarya bayan Saida Suka riga Suka tsufa da Yaya da jikoki wannan ai abin kunya ne Amma me rumtsa Ido yayi yace yaji ya gani y'ay'an sa gabaki d'ayansu sun nuna basa kaunar auren Amma yaki hakura dan uwan sa Saida ya bashi shawaran hakura ganin gidan nason rikicewa,amma yace babu Mai hanasa auren Amina. Zancen aure ya kankama Kaya na Alfarma minister yayi ma Amina Wanda yasa Yan kauye Suka ringa CeCe kuce akan inno zata saida Amina saboda tsabar son kudi irin nata amma inno ta toshe kunnen ta ta musu ta uwar shegu,saura sati daya biki duk Wanda yaga Amina sai ya tausaya Mata ta rame ta zabge tayi kuka tayi kuka harta fawwalawa Allah lamuran ta amma fa bawai ta hakura bane, sosai take Jin wani irin tsanar Alhaji a ranta tare da kudurta irin abubuwan da zata shuka Masa in yayi gangancin auren ta. tirkashi ana wani ga wani cikin wannan Hali sulaiman ya Fado a cikin rugan su yazo ya tarar da wannan mummunan labari sosai ya birkice Kamar tababbe da kansa ya shigo har cikin gidan su Amina yazo ya dafa kafar inno Yana rokonta akan kada su rabasa da Amina amma inno tace aikin gama ya gama wajen kawu shehu yaje amma Ina babu alamun nasara don ba karamin kudi Alhaji ke sakarwa inno ba,yaso ya rusa gidan su Amina kafun aure ya musu na zamani amma inno tace a Bata kudin kawai abin magana baya kad'an a kauye har jikokin su sai amma gori. Sulaiman tunda ya dawo yake bin Koh wani hanyoyi don ganin ya hadu da Amina amma inno ta datse Amina Koh Nan dashan Bata fita ta kasa ta tsare,sulaiman bai samu ganawa da Amina ba sai a daren da za'a daura Mata aure misalin karfe Sha biyu na dare ta farka don da Rana kanwar sulaiman tazo ta sanar da ita akan yayan ta zai jirata a Sauro da daddare ta fito zaiyi magana da ita a sirri karta fadawa kowa,tun karfe 9 na dare take son fita tana tsoro, gudun kada wasu su ganta Koh inno ta farka ta Kamata zata fita. tafiya take a hankali cikin duhu gudun kada a jiyota kofar gidan su ta nufa a hankali taji muryar mutum a bayan ta da Sauri ta juya hade da kwala ihu da Sauri sulaiman yace nine Amina karkiyi a jiyo mu,jikinta ne ya daina bari anan Suka zauna Suka soma tattaunawa Suna muhawara don sulaiman cewa yayi ta tashi su gudu daga rugan suje suyi aure a can Inda yake NYSC,ita Kuma tace bazata jawa iyayen ta abun kunya ba akan me zata bisa suje suyi aure su shiga duniya ita bata yarda ba amsar da ta basa shiya kuntata Masa Rai, anan fad'a ya barke a tsakanin su sosai sulaiman ya gaggasa Mata magana akan itama tana son auren Alhaji shiyasa ta Fadi haka Ashe ba soyayyar gaskiya take Masa ba taga Mai kudi zataje birni. Komawa cikin gidan tayi tana kuka ta shiga dakin ta ta kulle wani irin zafi takeji a ranta har Addu'a take Allah ya dauke ranta kafun gobe ta huta Kar taga wannan Rana da za'a ce an daura Mata aure da tsohon nan,. ********************* Rana bata karya saidai uwar d'iya taji kunya ayau dubban al'umma Suka shaida dauren auren Alhassan Muhammad dogo Mai naira tare da Amaryar sa Aminatu kabo jibril Akan sadaki naira dubu Ashirin,tunda aka kafa rugan ba'a taba daurin aure irin na ranan ba jama'a mn Kamar kasa Yan birni sosai Suka cika kauyen hatta yaran ango da jikokin sunzo daurin auren kakan su,Amina dake daki,kafa yasha yaben bakin lalle da hannu sai kuka take tunda gari ya waye Koh wanka taki tashi tayi Jin lasfikan masallaci iska ya kado zancen daurin auren nata dib taji ta d'auke wuta bata Kara sanin me ake ciki ba Saida ta farka ta ganta a cikin mota ana tafiya da ita,watoh ashe data Sumama bata tsira ba a sumen aka sata a mota bama ta lafiyar ta ake ba ta zancen aure suke sai yanzun take takaicin rashin yarda da abinda sulaiman yace Mata tayi,data bisa Koh bangon duniya ne suje. **************** tafiya suke sosai ganin haka yasa ta hakura da iFace iFace da take ta nutsu waje d'aya har lokacin hawaye baibar bin kumatunta ba idon Nan Kamar garwashi,tsayawa motar yayi itakam har lokacin bata dago taga Inda suke ba bude motar akayi da Sauri wata goggon ta ta lulube Mata fuska Wai gudun kada a ga fuskar tata ba'a sayi Baki ba. Jidai kawai tayi Suna tafiya amma Bata San Inda take sanya kafarta ba har suka nufi cikin sashen nata ajeta sukayi akan gado Suna jin Mata sai shigowa suke Suna fita ana gaggaisawa da Yan uwa ta,abinci aka kawo musu aka aje duk matan dakin Suka fita aka bar amarya dayan uwan ta sosai Yan uwan nata Suka Soma cin abinci basu Koh damu da halin da Amina ke ciki ba Suka hau zagin mutanen gidan Wai Suna musu kallon wulakanci Kamar sunga Kashi ga wani d'add'aga hanci da uwar gidan take,ai maganin inno kenan ba kwadayi ba sai ta Kai yarta ga mahallaka Koh wajen yan Yankan Kai,inji wata tsohowa a cikin su itadai Amina har lokacin tana lullube Bata yaye mayafin ba. da yamma akace za'a Yi budan ka gidan minister sosai ya cika da Baki duk da auren sirri yayi amma bai buyaba zancen auren Kuma kowa yaji sai yace zaizo yaga matan da Alhassan ya Kara da gangan aka kirkiro budan Kai don ayi maganin tsohowar d'aya aura,wanka Amina ta sake Alhassan ya turo matar Alhussan tazo ta kawo Mata kayan da zata sa don duk gidan babu Mai supporting auren Nan nasu sai ita hatta dan uwan sa baiso. Ba karamin mutuwar tsaye goggo badawiyya tayi ba data ga Amaryar tsohon nan,amma batace kome ba haka ma bata fadawa kowa ba ta kawo Mata zani da Sabon mayafi ta yafa,tanama Yan uwan Amina da aminar jagora har tsakar gida wajen budan Kai,lokacin da aka bude Kan Amina kowa ya Sha jinin jikinsa Addayiya kuka ta fashe dashi tana cewa Alhassan ya kunyatata ya rasa wance zai kawo Mata a wannan shekarun sai jikarta?da jikarta zatayi zaman kishi sosai fa magana ya bazu a gari akan zancen auren nasu. Bayan kwana biyu baki masu zuwa kallon Amina da Yan gulma duk sun dan ragu Addayiya har ciwo tayi akan zancen auren Amina kafun daga baya ta fawwalawa Allah,tsakanin Amina da Alhaji babu abinda zamuce sai dai muce rabon wahala ne ya sasa auren ta don ba karamin rashin mutunci Amina ke Masa ba a gaban kowa nuna wa take bata sonsa auren dole aka Mata ga rashin kunya takewa kowa a gidan,duk da ba halinta bane amma auren duk shiya birkitata sosai take nuna Masa kiyayya shima abin na Masa ciwo amma hakuri yake Yana danne zuciyar sa don duk abinda zata Masa bazai fasa Zama da ita a hakan yake sonta. Alhassan fa yaga ta kansa don gabaki d'aya Amina ta birkita masa gida rashin kunya takewa mutane na bugawa a jarida Inka cire Alhussan da matar sa badawiyya don su basa ma zuwa Inda take bare tagansu tace zata musu rashin kunya, muzammil yayi mugu mugun tsanar yarinya ga Kuma abinda take musu,ummu bata fada da ita Saida babu abinda ke hadasu sabanin Addayiya da mamu sosai suke gaba gashi duk lokacin da akayi fada sai Alhassan yadau gaskiya ya bata cewa yake duk Mai son zaman lafiya dashi toh ya fita harKan Amina. Amina bata da aiki a gidan sai dai taci ta kwanta tasha gwada gudu amma security ne birjit KoNan dacan bata iya zakudawa a cikin compound sai sun bita da Ido Suna duba Inda zata,Alhassa nada hakuri shiyasa yake zaune da Amina Yan garin su nadan zuwa kadan kadan ya musu hisani su tafi akwai wata Rana kanwar sulaiman tazo gidan ta a boye da letter (wasila) ta Bata akan sulaiman ne yace ta Bata sannan itama ta rubuta Masa reply kanwar tasa ta koma Masa dashi, Amina ta karbi wasikar shikenan tun daga ranan sai sulaiman ya dau kanwar sa suzo cikin gari don yaki komawa service,yan kitsa Mata rashin mutunci da zatana ma Alhaji ta yanda zaisa shi sakenta amma Abu ya gagara harsai wata Rana mamu ta Kamata suna magana da kanwar sulaiman plan in yanda zata fita su hadu da sulaiman, anan take ta sanar da Alhassa sosai ransa ya baci bana Wasa ba Kuma ya bincike dakin Nan ya samu wasikun da take Tarawa na sulaiman a ciki da durowan ta sosai Yama Amina fada akan martabar aure,da Kuma Hana security barin kowa daga kauyen su indai ba mutane uku bane, kawu inno da muneeru tunda har waya aka kawo aka Bata. Yau surkin Alhassa sarkin katsina ya shigo gombe sannan ya iso gidan surkin nasa sauke sa a babban falo Alhaji yayi cikin mutunci kowa na gidan sai haba-haba yake da surkin nasa ana kawo abin Sha daci ana jerawa kowa Saida yazo ya gaidashi daman alhassan ya gargadi Amina don Allah kada ta kuskura tazo ,Aiko ita daman abinda zai kuntata masa shi take so tayi Masa,Suma tsaka da magana ta Fado falon mikewa Alhaji yayi Yana tare ta da cewa suje waje sai suyi magana amma Amina taki ta fita,saima ta hau Kan kujera ta kame. Kunya Kamar ya kashe Alhaji sai lallabata yake ta tashi su fita surkinsa ne karta kunyata shi amma abin bakin ciki mikewa Amina tayi tasa kafa ta shurar da kulolin abincin dake gaban sarki ta Soma masifa akan bazata tafi ba saiya saketa bazata zauna dashi ba,dafe kansa yayi cikin takaici sai Kuma ya sulale ya Fadi Koh motse bayayi salati muzammil daya shigo gidan kenan dawowar sa daga makaranta Addayiya ke sanar dashi sarki na falon babansu yaje ya gaidashi,ya jima a bakin kofar Yana Jin duk abinda ke faruwa amma baice kome ba don yasan Koh yayi magana baban sa zai gwatsele sa akan Amina. da gudu ya shigo dakin yayi Kan mahaifin nasu sai Kuma ya sake kuka yana kwalama mutanen gidan Kira ya mike da gudu yabar falon sarki ma mikewa yayi yana salati ya matso wajen alhassan in bayan ya dauko ruwa yana shafa Masa amma ina shuru,saiga muzammil da fadawa da suke tsatsaye a kofar flat in da sauran Yan gidan suka shigo falon da gudu cikin tashin hankali Amina dake gefe da Sauri tayi hanyar kofa jikinta na rawa bata taba Shiga tashin hankalin da ta shiga ba, karfa mutuwa Alhaji yayi. Mikewa muzammil yayi yabi bayan ta da gudu tana kokarim dannawa kofa sakata ya bango kofar ya shigo bell nasa lafiyayye ya Soma lafta Mata da iyya karfin sa Daman ya girmeta da shekara biyar a lokacin Yana da 21year,mugun duka ya rufeta dashi baji ba gani duk takaicin da take dura Masa a gidan yau shiyake sauke Mata, dukanta Yake Yama cewa kafun ta kashe Masa uba shi zai Fara kasheta har lahira inyaso ana binne ubansa ana tona kabarinta a gefe................................. πŸ€*By Ruqeenjalal*πŸ€ *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki* Page 96&97 babu Wanda hankalin sa ya kawo wajen dukan da muzammil kema Amina asibiti aka wuce da minister,mamu ce ta hankalta bayan an wuce da Alhajin asibiti Kara zuga muzammil tayi,shikuma yayi ta kirban Amina ba karamin duka Yama Amina ba Saida ya faffasawa Yar Fulani jiki kaca-kaca kafun ya Barta korata shida mamu sukayi a gidan har bakin titi mamu ta yafa mayafinta ta kora Amina muzammil na rike da bulala, sulaiman daya maida kofar gidan wajen zaman sa tunda aka Hana kanwarsa shiga shikenan ya maida wajen wajen zaman sa kullum Yana tsumayen wata Rana Amina zata fito Kamar a mafarki yaga Mai Kama da ita an hankadota daga cikin gidan,hankali tashe ya mike ya bi bayan su daidai lokacin muzammil ya watsa Mata bell da Sauri ya tare dukan tare da cakumar muzammil da dambe security dake kofar gidan da gudu Suka nufosu ganin wani na dambe da Dan minister a takaice dai daga Amina har sulaiman ranan jikin su yayi tsami bana Wasa ba. Allah yaso sulaiman yana da kudi a wajen sa,dashi Suka hau mota zuwa kauyen su gabaki daya zance ya baza kauye sulaiman ya kashewa Amina aure inno batayi binciken kome ba ta hau fushi da Amina Koh sauraron raunukan dake jikinta batayi ba,sai muneeru dake Kai kawo a kanta. ta bangaren gidan minister sai bayan tafiyar Amina sukaji labarin dukan da Muzammil Yama Amina,Amma babu Wanda ya damu don ba sonta suke ba Daman Kuma abinda tama mahaifinsu ya musu zafi,hawan jini ya samu sosai Koh hayyacin sa Bai dawo ba sai bayan kwana biyu ya Fara bude Ido,a ranan daya bude Ido da zancen Amina ya farka sosai ran Addayiya ya baci ita ta sakasa a wannan Hali sannan har Yana da bakin Kiran sunan ta bama yaki taba,baida magana saina Amina batazo ta dubasa ba Koh Bata da lafiya ne,da haushi ya ishi muzammil Anan yake ce Masa tana garin su ya koreta Aiko ranan sunga me ake Kira bacin Rai iya bacin Rai rikice musu yayi akan lalle lalle sai an sallamesa yaje ya dauko matar sa a kauye. Abin fa ya wuce tunanin Mai tunani dole tasa alhussan tashi tare da basa Baki akan shi zaije ya daukota shi Kuma yayi hakuri ya zauna a asibiti sai jikin sa yayi sauki kafun yace zai bar asibitin. Alhussan badon ransa yaso ba yaje garin su Amina,sosai inno tayita basa hakuri lokacin da ya zana Mata abinda Amina ke musu, daki ta Shiga ta jawo Amina tare da Mata kashedi Koh bayan ranta ta sake Masa makamancin abinda akace, indai ta rabu da Alhaji Allah ya Isa Bata yafe Mata ba Amina tasha jinin jikinta bana Wasa ba especially furucin inno gareta haka ta bi alhussan har asibitin halin da taga bawan Allan a ciki sosai jikinta yayi sanyi shikam cewa yayi ta zauna a asibitin kin Zama tayi saboda yanda kowa yazo sai taga irin tsanar da yake nuna Mata abayyane, komawa gida tayi sai dai tazo ta dubasa ta koma shikam yad'anji dadi kad'an ganin ta dan sauya Hali tayi sanyi ba Kamar da ba, ba'a San garin Yaya ba wani ya sanar da Alhaji dukan da Muzammil ya Mata sosai ya birkice yace muzammil kada ya sake taka Masa gida ya tattara yanasa yanasa ya koma hostel,wannan shine mafarin gabar da muzammil keyi da Amina ata dalilinta mahaifin sa ya bude Baki yace kada ya tako Masa gida akanta. Alhaji yaji sauki inno da muneeru sunzo sun dubasa Kuma sun Kara basa hakuri akan abinda ya faru,su Umar hankalin su ya tashi haka zalika ransu ya baci na abinda mahaifin su yayi na korin muzammil,gashi yaran duka sun tsani Amina sosai,Umar jafar su Suka tattara yaran su da Suka Fara wayo sosai, muzammil Anwar Shareef da Hashim Suka turasu abroad karatu gabaki d'aya bama sun sanar da mahaifin nasu ba Saida yaran Suka tafi,sosai Alhassan yaji ba dadi Amma baice kome ba, gidan ya kasance yarane kananu kadai a cikin sa masu wayon duka basa Nan. Amina tayi sanyi kad'an Kuma ta Soma kula Alhassan harma suyi Hira hakan ya samu mafari ne da takardu Koh jaridu dayake kawo Mata Yana karanta Mana tare da koya Mata yanda ake wasu abubuwan a boko shikenan ta Soma sanyi haka zai sayo littatafai in yana gida su zauna Yana karanta Mata Yana fassara masa,ganin yanda take kaunar karatu yasa sa shigar da itama makarantan secondary akaita a daukota, a sannu sannu soyayyar sulaiman tayi sanyi aranta bawai son alhassan ta Fara ba ah ah tanajin farin ciki yanzun in tana tare dashi a hankali hankali zaman su ya sauya daga tsana zuwa kulawa. Bayan wasu watan Ni saiga ciki kusam ya fito daga wajen Amina abinda ya zamo abin mamaki da Al'ajabi da kunya a wajen ahlin gidan Inka cire uban gayyan dayafi kowa murna murna yake Kamar Bai taba samun Y'ay'a a duniya ba sai Nan Nan yake da Amina kome take so jiki na Bari yake Mata,itakam Amina kunya sosai yake damunta haka zata kunshe ciki musamman lokacin da ya fito tayita boye boye batason Koh fita tsakar gidan. Lokacin da cikin ya girma hatta tafiya Amina bata iyyawa sosai duk tsanar da Addayiya da sauran yan Gidan Suke Mata Saida Suka dawo tausaya Mata Amma Banda Mamu dake ta radawa mutane cikin jikin Amina bana surkinta bane,saurayinta ke binta makaranta daga Nan su wuce iskancin su shine tayi ciki ana cewa Wai na alhassan ne,magana fa ya fito fili Wanda yasa alhassan mugun fusata tare da jawa Umar dogon layi akan ya Shiga tsakanin matar sa da Amina maganar datayi girma Saida Umar ya sake halima,ganin yaka yasa jafar tattara matarsa da yaransa Suka koma cotes na ma'aikatan gonnati Suka bar gidan. daker da sudin goshi mamu ta dawo dakin ta,cikin Amina ya girma girma bana Wasa b,sosai alhassan yake kula da ita da abinda ke cikin ta baya duba tsufansa Koh girma yake tattalan matar sa,lokacin da cikin Amina ya shiga wata tara,Alhassan ya Soma ciwon da ba'a gane kansa ba,da fari ciwon ciki ya Fara anje asibiti sukayi gwaje gwaje aka basa magana Koh sati baiyi ba sai Kuma tashi ya gaggara haka aka ciccibesa aka Kai asibitin likitoti sukace su basuga ciwo ba,hankalin family Nan ya tashi bana Wasa ba dawo dashi gida sukayi ganin yanda yake ramewa. Alhassan ya rame ya Kade gashi a kwance sai abinda aka Masa magana ma ya daina saidai kawai aga yana zabura Yana Shure Shure hawaye Nabin kumatun sa,abun fa ya d'agawa Amina hankali ganin tunda ya kwanta sai aka hanata shiga Koh dakin da yake,mamu ta Soma zuga Addayiya Wai Koh Amina ce da saurayin ta Suka Masa asiri,Nan fa Addayiya ta tada hankalin ta aka Fara Neman maganin hausa,Koh wani malami aka kawo daga yace iska sai yace asiri aka Masa,Nan danan magana ya Fara nisa Amina ce ta Masa aSiri ai Fulani daji me(shiyasa akeson Koh baka son mutum ka boye kiyayyar a idanun mutane inko ka bayyana toh Koh Abune ya samu mutumin in badai Yana da tauyidi ba kana cikin matsala). Yau Amina ta tashi da nakuda sosai take cikin halin ciwo,tun safe tana daki tana fama da jikinta don tunda Alhaji ya kwanta ciwo babu Wanda yake bi ta kanta abinci ma kuku zata kawo Mata ta aje Mata ta fita duke take a bakin gado sai jujjuya kanta take tana damke da bakin gadon sai salati take tana kuka. Muzammil dasu Anwar da labarin ciwon Alhassan ya riskesu duk da Muzammil na fushi da abinda mahaifin nasa ya Masa Amma halinda akace yake ciki ya tada Masa da hankali bayan isarsune suka tsinci zancen ai Amina ne ta Masa asiri abinka da maza su Basu wani yarda da zancen ba,amma Mata Kan sosai suke zuzuta abin,cikin wannan halin da Amina take ciki badawiyya(matar Hussain)ta shiga falonta da sallama don ita Sam yau hankalinta Bai kwanta da shurun Amina tun safe Koh tsakar gida Bata fita ba. tana shigowa falon taga kulan abinci a aje budewa tayi taga Koh ci batayi ba sallama ta Soma Mata Amma shuru ba amsa bkin kofar taje ta tsaya tana Kiran Amina,Nishi dataji Yana tashi shiya mugun d'aga Mata hankali,haihuwane gadan gadan janta tayi sukayi bayan gida wahala iyya wahala Amina tajishi har Allah ya dauketa lafiya ta haife yaranta tagwaye kyawawa masu Kama da mahaifinsu sak hatta skin nasu Basu dau hasken taba. Bayan badawiyya ta Gama kimtsa yaran kwantar dasu tayi ta taimakawa Amina tayi wanka bayan fita da tayi taje part nata ta daura ruwan zafi tazo ta kimtsa ta da yaranta,Allahu Akbar lokacin da badawiyya ta sanar da haihuwar Amina duk da Muzammil baya kaunar Koh ganin Mai Kama da Amina amma jini yafi ruwa kauri,Saida ya taka kafarsa har dakinta ya dau jariran sosai jikin familyn Alhassan yayi sanyi ganin yaranda Amina ta Haifa like father like son,anan take muzammil ya d'au yaran ya Kai har dakin mahaifin su,da hannu ya nunawa muzammil ya nuna Masa yaran, facing nasa yayi ya nuna Masa yaran a take hawaye ya cika Masa Ido,tare da Mika hannu daga kwance dayake ya karbi yaran ya kwantar dasu duka a kirjinsa,a hankali ya bude bakin sa ya Soma magana"muzammil kiramin Amina"da mugun mamaki muzammil ya mike Yana cewa"Abbi magana kake kaji sauki"?gyada Masa Kai Alhassan yayi da gudu muzammil ya fita Kiran Amina cikin gaggawa duk da Bata da karfin jiki Kuma hutu take bukata amma hakan bai hanata gaggawar mikewa zuwa Kiran mijinta ba. Tunda ta shigo dakin ta fashe da kuka ganin yanda Alhassan ya koma in baka Masa kyakkyawan sani ba bazaka ganesa ba,daga tsaye da take yasa hannu ya rike nata tare da jawota kadan ta zauna a bakin gadon har lokacin yaransa na jikinsa sai bacci suke yatsan su a baki"Amina na gode da wannan kyautar da Allah ya Mana ke Kuma Kika Haifa mini, Amina Koh a yau na mutu Banda asara tunda har Kika haifamin yara a tsotsonki,Ina sonki Amina Allah ya Miki albarka ga yara Nan na musu huduba da Sunan Hassan da Hussain Kamar yanda nake nida dan uwana"Kuka ta fashe dashi tana rufe Baki sai Kuma ta zamo bakin gado ta Soma rukon sa gafaran abinda ta Masa, murmushi kawai yayi yace"Niya dace na nemi yafiyar ki Amina na cutar dake na aureki na dole badon ranki naso ba Baki tabamin wani Abu na bacin Rai na kwanta dashi ba ba tare da na yafe Miki ba Amina ki yafe min..........Bata Bari ya karasa ba ta rufe Masa Baki da hannu tana hawaye tace"babu abinda kamin bare ka nemi yafiyata Alhaji Allah ya baka lafiya"Ameen ya amsa Mata Yana lumshe idanunsa dake cike da hawaye. Addayiya ne ta shigo dakin tare da Muzammil dasu Umar daman sumayya(goggon katsina) ma na gidan,karasowa sukayi Jin muzammil yace muzu Alhassan na magana Aiko gashi sun ganewa idanunsu Zama sukayi Suka kewaye sa saiga Hussain ya Shiga dakin shida matarsa Hawa Kan gadon yayi ya rike hannu dan uwan sa cikin tsananin tausayin sa,suke Masa sannu hannun dan uwansa ya Kara damkewa a nasa,a hankali alhussan yasa hannu ya d'aga yaran akan kirjinsa shima ya rikesu a hannun sa,gyara kwanciyar sa Al'hassan yayi ya Soma magana Kamar haka"Umar ya Kira sunan babban dansa da Sauri Umar ya matso kusa dashi hawaye na cika Masa Ido,nuna Masa jariran yayi yace"Umar Koh bayan Raina zanyi Alfahari dakai mundin karike min y'ay'ana ka Basu tarbiya ka kularmin dasu Kamar yanda kake kula da yaranka,gasunan Amana na bar maka"kuka Umar ya fashe dashi Yana cewa mahaifinsa bazai mutu ba insha Allah zai tashi da kansa zai kula da yaransa. "Ah ah Umar banajin haka a jikina muzammil jafar inaso kumin alkawarin Koh babu Ni banason ku Ware yaran Nan a cikin ku Koh ku nuna masu banbanci, Alhussan ga Umar da kannen sa na barmaka ragamar kula dasu a hannunka ka zame musu uba tamkar kaika haifesu duk abinda kaga sunyi ba daidai ba ka sawatar musu,gabaki dayan ku Allah ya musu albarka duk abinda kuka min Wanda na sani da Wanda ban sani ba duk na yafe muku duniya da lahira yayana nima kuskuren dana muku kuyi hakuri..............Bai karasa ba sumayya tace"babu abinda ka Mana Abbi insha Allah babu abinda zai sameka, Addayiya Kam kuka take lokacin da taji mijinta na cewa ya yafe Mata duniya da lahira itama ta yafesa,sosai Alhassan ya karya musu da zuciya kuka Kam shi suke Alhussan kasa hakuri yayi har Saida ya zubada kwalla karban yaran Alhassan yayi daga hannu Hussain ya kwantar akan kirjinsa Suma yaran Koh kuka basuyi ba Suna bacci,shima baccine ya daukesa Yana kankame da yaran,ganin haka yasasu Fara fita dakin d'aya bayan d'aya Kama Amina badawiyya da sumayya sukayi Suka fitar da ita a dakin aka Kira likita har gida tazo ta dubata tare da daura Mata ruwa. da misalin karfe 1 na rana Addayiya ce ta leko a Karo na uku tun baccin Alhaji da yaran Nan Bai farka ba har yanzun,Hassan(Lahab)ya farka sai kuka yake yasata shigowa hannu tasa a hankali zata dau yaron tana mamakin wani irin nauyin baccine ya d'auke mijinta yaro na sanyara kuka amma baiko motsa ba bayan Kuma tasan sa da yawan ji Koh bacci yake mutum ya shigo dakin sai ya farka, janye hassan(Lahab)daga jikinsa tayi sai taga hannun dayasa ya rungume yaron yayi baya ya sake Yana Lilo a Bakin gado waro Ido tayi jikinta na bari ta Soma maimaita kalmar innalilahi wa'inna'ilahu raji'un sai Kuma tasa hannu ta dau Hussain (Rahab) shima ta kwantar dasu a gefen gadon Aiko take ya farka suka Soma kuka su duka biyun a tare da Sauri tasa yatsanta biyu a bulin hancin Alhassan (mahaifinsu) sai Kuma ta sulale a kasa ta sake wani marayan kuka. ********************* Allahi Akbar rayuwa kenan yaudai Alhaji Alhassan Muhammad dogo Mai naira ya zamo tarihi,Allah daya hallice abinsa yau ya dau kayansaAlhassan an kaisa gidan sa na gaske,mutuwar Nan tayi mugun dukan Amina ashe haka rayuwa take Koh baka kaunar mutum Randa aka waye gari babu shi sai kayi alhini bare ita dake kyautata masa sosai ta Shiga wani irin Hali na atausaya Mata,dole tasa inno zuwa akan zata tafi da ita kauye Amma Umar ya Hana yace ta zauna a dakin ta tayi wankan jego,Aiko dole tasa inno zama a gidan tana kula da 'yarta. Amina ta Zama abin tausayi sosai tayi sanyi bana Wasa ba tayi nadamar abubuwan da tayi Masa a rayuwa,Allah sarki duk irin kiyayyar da aka nuna Mata a gidan Albarkacin y'ay'anta ta samu sassauci sosai suke nuna kaunar yaran nata bana Wasa ba,kullum matar Alhussan haka zatazo ta daukesu su wuni a part nata no-no kawai ke dawo dasu wajen uwar su. Tunda Alhassan ya rasu shikenan lafiya tazamo sai a hankali a wajen dan uwan NASA sosai ya Soma ciwace ciwace na ba gaira babu dalili yaje asibiti likitoti sun gargadesa akan damuwar da yasawa ransa ya rage,Amina ta kammala jego cikin koshin lafiya Amma babu zacen barin gidan Umar yaki inno ta koma kauyen su,tabarta anan,shekaran Yaran d'aya Allah Yama Alhussan rasuwa,rasuwar da ya tada ciwon mutuwar Alhassan mutuwar ya zamo musu sabo fil,don shikadai ya rage musu suke kallo a matsayin uba,Amma ya Suka iyya babu Wanda yake ja da hukuncin ubangiji. Bayan rasuwar Alhassan, badawiyya ta Soma laulayi Ashe rabo ya shiga duk tsawon shekarun Nan Bata taba koh batan wata ba,sai bana dahar sun cire tsammani Allah ya Bata taso ace kafun mijinta yabar duniya yaji wannan albishir amma harya bar duniya baisan da cikin ba...................... πŸ€ *By Ruqeenjalal* πŸ€ *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki* Page 98&99 Bayan rasuwar badawiyya Amina taso ta cigaba da shayar da yarda badawiyya ta Haifa ta rasu ta barta aka maida Mata sunan mahaifiyarta ana kiranta da Amrat,Amma su Yan uwan badawiyya sunki sun nuna Akan zasu rike yarinyar a wajen su Tasha Madara,Kuma ba musu aka barmusu yarinyar a wajen su. Bayan Amina ta yaye yaran ta anan tace zata koma gidan su don rasuwar mijinta shekara biyu kenan,gadon su Lahab a kallah yakai million biyar biyar Koh wannen su ga gidaje biyu biyu da Suka tashi dashi,da gonaki,Amina an Bata kasonta Saidai na yaranta ta barma Umar a hannun sa,ya sanya Dana muzammil Yana juyawa a cikin kasuwancin sa kudin na dad'a habbaka,ta dau tata gadon ta ta koma garin su, y'ay'anta ta barsu a hannun Addayiya ita tacigaba da kular Mata dasu. Hassan da Hussain wa'inda aka lakabawa Lahab da Rahab har sunan su na ainahi ya buya don kowa kunyan Kiran yake sunan iyayene,yaran sun tashi kowa da halin sa, Lahab yarone Mai hakuri ga Wasa ga saurin yafiya ga rawan Kai dogon hakuri farfar da mutane babu ruwan sa talaka Koh Mai kudi shikam duk daya suke a gunsa Amma akwai rigima da taurin kai,sabanin Rahab daya tashi da sanyin Hali amma akwai zuciya ga riko ga saurin fusata gashi d'an ba ruwana ne sai yaga dama yake shiga harkan mutane in baiga dama Amma akwai yawan gaisuwa kam, Lahab akwai Wasa fara'a rawan Kai hakan yasa yafi Rahab yawan jama'a da wuya kaje unguwan kace Lahab wani baice yasan Saba. Amina na komawa garinsu Daman sulaiman ya kammala makarantan sa babu aiki haka yaci gaba da kiwo a kauyen su,zuwa lokacin ya hakura da zancen Amina Amma Bai Kara zancen aure ba dawowar Amina ita ta sake tada Sabon sonta a ransa,Suka cigaba da soyayyarsu suka daura daga inda suka saya. Iyayen sulaiman sunso Hana d'ansu auren Amina a matsayinta na bazawara Amma sulaiman ya nace tare da rantsewa in ba'a Bari ya aure Amina ba bazai taba aure ba,babu yanda iyayen Suka iya haka aka daura musu aure da Amina bayan d'aurin auren nasu ne Amina tadau million daya daga cikin gadonta ta baiwa yayanta muneeru akan ya cigada da kula da gidan su sauran biyun ta baiwa mijinta sulaiman tare da rokonsa su koma cikin gombe yanda zata ringa ganin y'ay'an ta akai akai Allah sarki akace Mai sonka dole yaso naka,baiyi musu ba Suka tattaro Suka dawo cikin gombe haya ya Kama musu,da kudinta data basa ya Kama shago Yana Saro Kaya daga kasar inyamurai Yama zubawa Yana sairuwa. Cikin kankanin lokaci Sulaiman yayi kudi na ban mamaki sosai harziki ta bude Masa Harya biya Amina(Mami)kudinta ya tsaya da kafafunsa,Amina ta koma makaranta ta cigaba da karatun ta sannan duk sati tana zuwa taga yaranta inta tashi tafiya haka zasuyita kuka zasu bita,wata Rana ta daukesu suje su kwana wata Rana Kuma saidai ta barsu. Amrat(badawiyya karama)ta taso a wajen dangin mahaifiyarta cikin rashin isheshen kula don yarinyar ta taso ba'a Mata kwaba Bata da kunya wani zuwa da jafar yayi dubata a can garin su badawiyya(Adamawa)yaje ya tarar da irin rashin kunyar da Amrat ke zubawa a ranan ya tattarota Suka dawo gombe da karfin Isa don dangin sunso hanawa ya nuna musu suke da iko da Amrat,daga lokacin rikon Amrat ya dawo hannun jafar wanda a lokacin sun bar cotes ya dau daya daga cikin gidajen da ya mallaka na mahaifinsu ya koma ciki. Mami ta sake haihuwa bayan auren ta da sulaiman,sun samu Yaya hudu bayan su Lahab,Mahraz mufeeda wasila sai Yusuf karami da ake shayarwa yanzun,rayuwa tama wannan masoya dadi kudi iya kudi sulaiman nadashi tuni yabar harkan kasuwa ya tsunduma a gomnati ana damawa dashi sosai ya kera gida Mai kyau suka koma ciki,itama Amina yanzun ta Zama Hajiya Matan manya ga business nata da take a cikin gida kudi na shigowa hannunta sosai, d'aga inno da dan uwanta tayi ta dawo dasu cikin gombe gida ta sai musu Mai shegen kyau daman muneeru ya Jima da aure tun kafun a haifi su Lahab Yana d'a daya mustapha,da matarsa salamatu sosai zaman salamatu da inno ya kasance wani iri abun ba dadi Sam lokacin da Mami ta kawosu birni sai abin yafi lokacin da suke kauye sosai inno ta tisa salamatu a gaba ranan da salamatu ta kasa hakurin zagin da inno ke Mata ta shiga ramawa. Shigowar muneeru kenan ya tsinkayi zagin da salamatu kema uwar sa Nan ransa ya baci yace saita bar Masa gida ganin irin kukan da dansu dayayi wayo yake Jin abinda baban sa yace,yasa muneeru hakura amma fa ya tattara yanasa-yanasa da salamatu da dansu sunbar gidan,karamin gida Mami ta basa kudi ya saya suka koma ciki,daman Yana kasuwan ci,suka cigaba da zaman rufen asiri da matarsa bakin su alekum. Iyayen sulaiman sunki dawowa birni a ganinsu bazasu iya barin tushen suba gida ya kera musu a can rugansu Mai kyau Suka koma rayuwar birni a kauye. ******************* Inda asalin abotar su Lahab ta samune ata dalilin unguwan su daya tun Suna yara Lahab nason zancen ball haka yake Sasa kullum sai ya zame jiki ya fita arean su Nabeel suje suyita buga ball kullum in sun hadu da Nabeel sun buga ball basa gamawa lafiya sai sunyi fada Wasa Wasa har abota ta Fara atsakanin su suyi fada su shirya Lahab kullum in sun gama Wasa sai yabi Nabeel gidan su suci abinci wata Rana Kuma Addar Nabeel mubeena ta koresa. Kullum in ya fita haka Abbu zaiyita fada akan a daina barin sa Yana fita hakan bazai hana gobe ya fita ba,a hankali suka Fara wayewa da juna Nabeel nad'an zuwa gidan su Lahab shida addan sa,Amma haka Mamu zata koresu ta hanasu shigo musu gida Wai y'ay'an talakawa,makarantan su Nabeel government ne tana manne da private Inda Lahab ke ciki wata Rana da aka kawo Lahab makaranta aka saukesu a gate saiga Nabeel da addan sa zasu Shiga makarantan su Aiko abin nema ya samu tun daga Nan Lahab ya gane gudu a makarantan su yazo nasu nabeel,su Kuma malamai su korasa akan ya koma makarantan su daga ya fita Nabeel zai sulale ya bisa su shiga yawo unguwa unguwa,kutsam aka kawo Sabon dalibi dan yarobawa a ajin su Lahab Mai shegen taurin kai. Lahab Adewale Nabeel abotar su taci gaba dakin karatunsu sai yawan yawo tun Suna primary 4,duk irin tsanar da baban Ade ke gwada musu da kyankyami da Mamu ke nuna musu baisa su sun rabu ba kullum abotar su Kara gaba dake,saidai Kuma duk yanda kake da mutum biyu Dole zakafi Jin d'aya sama da d'ayan toh hakan take a wajen su Lahab yafi kaunar Adewale haka yafi yin sirri dashi Abba baya nuna wa a gaban idon Nabeel dan Adewale ba karamin kauna yake ma Lahab ba. An dawo labari...... ***************** Lahab Kam shuru yayi kansa a kasa har Mami ta gama zayyana musu labarin Family su,sai yanzun ya gane dalilin dayasa ta aure mahaifinsu Wanda kullum Addayiya da Mamu ke goran ta musu mamin su Yar kwadayine,Amma yawancin abinda ta fada yasassan su. Mikewa yayi a hankali ya nufi kofar,kiransa Mami tayi ba musu ya juyo ya dawo kallonsa tayi tace,Lahab ka fita a harkan yaran Mamu Ina rabaka da yaran matan Nan,sannan ka dawo anjima zamu fita bafa Zan hakura da zancen Nan yasha a banzaba"?gyada Mata Kai kawai yayi yabar gidan Yana fita a kofar gidan ya durkusa ya Soma kuka bilhakki da gaskiya sosai yakejin wani irin tausayin mahaifin su don duk da ya rasu Suna da hotonsa dashi da baban Amrat(Alhussan),ashe haka babansa yasha wahala akan Mami sanan har Mami tanada bakin cewa Mamu Bata kaunar ta,duk irin abubuwan da ita ta Mata ai tun farko ita ta Fara jawo fadan. Alhaji sulaiman daya sharo layin nasu ganin Lahab duke Yana kuka yasa sa parking na motarsa ya sauka a motar in,karasowa yayi kusa da Lahab yasa hannu ya dago kansa da yayi shabe shabe da hawaye a tunanin sa Rahab ne"haba Rahab ya zakazo ka zauna kamar an maka wani Abu Koh mamin taku tace maka wani Abune"?girgiza Masa Kai kawai Lahab yayi baice kome ba"toh Koh akan Hana maminku Kai Kara ne kake kuka"rasa abin cewa Lahab yayi kawai ya d'aga Masa Kai alamun eh"toh tashi muje ciki saimu fita da mamin naku,ba musu ya mike suka Shiga cikin gida har lokacin Rahab da Mami na falon. Anje station Mami ta shigar da korafi akan abinda farida tace wa danta, police da kansu Suka shiga mota sai gidan su farida amma Kash da zuwan su Suka tarar da mutuwar mahaifiyarta ana zaman makoki sannan annemi farida an rasa,karshe dai dole Mami tayi hakuri da maganar bayan yarjejeniyar da aka aje duk wani mummunan Abu daya faru da d'anta alhakinsa na wuyan farida za'a neme mahaifinta. Bayan bikin su Anwar gida ya koma Kamar yanda yake sai Kewan mutane biyu da ake musamman umaima,gwara Anwar ana gari d'aya,Hankalin Mamu ya kwanta yanzun babu kowa a gabanta sai Shareef shi Kuma ya girma,su Lahab sun Fara jarabawan second term,yau Friday ayaune sukayi last paper nasu na English Kuma kwalli daya sukayi. Bayan sati daya da jarabawan yau Tuesday ayaune sukazo karban report card nasu gabaki dayan su SSS 3 Suka taru waje d'aya ana hotona photographer musamman aka Kira ana d'add'aukan hoto harda malamai masu manyan waya irin su Lahab duk sunata d'auka da nasu, coper da Lahab Suka Masa duka Yana staff room su Lahab Suka nufi staff in dukansu uku Suka duka suna basa hakuri don daga wannan Rana ba lallai bane a sake haduwa don wasu ba'a makarantan zasuyi paper ba, shima coper in zai koma garinsu ya gama service sukaran kansu ss3 daga wannan time babu tabbacin zasu dawo third time babu grante Don a lokacin zaman gida ake turasu suyi ace su jira register waec,sosai copern yaji dadin hakurin da Suka basa Harya zaro wayarsa ya fito waje yace suzo su tsaya, ya baiwa wani malami ya daukesu zai aje na tarihi, Lahab ma wayarsa ya bayar a d'auka dashi sosai sukayi hotona bana Wasa ba. Zame jiki Lahab yayi a cikin yara ya nufi ajin su, Nnenna ne zaune waje d'aya kowa ka gani da abinda yake wasu na Wasa wasu na hotona wasu na karban number juna sabanin ita zaune babu wanda yace tazo suyi hoto Koh taje suyi,karasowa Inda take yayi yasa hannu ya Kama nata tare da mikar da ita ya Soma tafiya tana binsa,daman jakanta na bayan ta"Ina wayarki"shine tambayar da ya Mata Mika Masa wayar tayi"har Kan floor insu yajata Suka tsaya wayarsa da nata ya bayar yace a daukesu sosai aka shiga daukar su sannan wasu na shiga hoton anayi dasu kankace me duk yawancin class mate nasu duk sunyita daukar hoto da Nnenna da Lahab,su Adewale ma sunzo sun shiga hoton Nabeel nata mamakin alakar dake tsakanin Lahab da Nnenna duk da ya tambaye Lahab Lahab yace Masa friendship ne a tsakanin su amma baice kome ba saidai shikam Sam Bai kaunar Nnenna da Lahab kwata kwata amma tunda dai school life ne dole wata Rana zasu rabu. Ba karamin bakin ciki ne ya kashe Jenifer ba,sai kusan 10 na safe aka had'a musu assembly abinda yayi mugun bawa mutane mamaki da Al'ajabi shine first position da Lahab ya d'auka a ajinsu sosai abin yayi ta saka jama'a a mamaki,sai Nnenna tazo na biyu wayyo Allah Ina wuta Jennifer ta jefata,daga Nan aka Shiga rarrabawa wa'inda suka dau position na daya zuwa na uku kyaututukan Lahab ya tashi da kyautar Award Wanda aka Mika Masa yayinda dalibai ke kashe sa da cameran wayansu,bayan an basa award na jajirtancen dan kwallo,don yafi kowa hazaka a makaranta in akace za'a buga ball da wasu school,aka had'a Masa da kyautar Keke sabuwa Mai kyau duk da yafi karfin Keke amma akace kyautar bajinta daban yake acikin sauran kyauta, Nnenna an bata kyautar laptop sabo,sauran ma aka babbasu nasu,Lahab a ranan murna Kam Baki har kunne,lokaci d'aya aka ringa post na hotonan su da sukayi da keken da aka basa,mikawa Nabeel yayi yace ya Kai Masa gidansu award in Kuma ya baiwa Rahab yakai Masa gida. Tafe suke da Nnenna yau Koh abin Hawa Bai tare musu ba Suna tafiya Suna Hira kallon ta yayi yace"shikenan yanzun bazamuna haduba sai an dawo hutu"?tana Wasa da yatsan hannunta tace"eh man Inba haka ba toh a Ina Zan ganka"toh waike Baki zuwa Koh inane"ah ah bana zuwa daga gida sai makaranta Kuma kaga yanzun babu zancen makaranta Kuma sai zaman gida. Gyada Kai yayi yace"Aiko gyara Miki ma da Baki yawon,bare yanzun kin samu laptop saikiyita using na abinki"gaskiya ne"shurune ya ratsa sakanin su ganin shurun yayi yawa Lahab yace"bayan weac namu wani school kike da burin shiga"?dan shuru tayi Kamar Mai nazari sai Kuma ta juya ta kallesa ta sake kauda fuska sannan tace"Ina son na karancin medicine sannan na Zama soja"waro Ido Lahab yayi sai Kuma ya Soma dariya har Yana dafe cikinsa Kallon sa tayi ta had'a fuska tace"toh dariyan Kuma na menene kake min"dole na Miki dariya hajiya ke kince Zaki Zama Dr sannan soja a hakan"ya nunata a gatsine nifa tambayar ki nayi wani makaranta kikeson shiga after graduate kiwani cemin soja da Dr"ganin yanda ta had'a fuska bata basa amsa ba yasasa dan tsakaita dariyan yace"toh Yi hakuri yanzun dai fadamin menene dalilin ki nason Zama soja dama-dama Dr Zaki taimake Mata"? "Zan Zama soja ne saboda Ina da sha'awar Zama security yanda zanna hukunci a dokance"harara ya Mata mata Ya tamke fuska yace"toh ke Kika Zama soja wazai aure ki a hakan"nima ai bance Ina son aure ba,a takaice ma Ni bazanyi aure bama"shuru yayi baice kome ba Amma fuskar nan babu fara'ar d'azun a hakan suka ringa tafiya harsaida sukazo daidai kwanar layin su Nnenna kafun ya tsaya saboda rokonsa da tayitayi akan ya koma Kar Yan gidan su su ganta da ita kwalin laptop nata ya Mika Mata daman Yana hannun sa kin amsa tayi tace"ka rikemin a gunka Inna tashi Zan karba"akan me Zan rike Miki Kuma Baki da hannune Koh Kuma gidanku babu wajen ajiya"? Bata basa amsa ba ta cigaba da tafiyanta Bata saurare abinda yake cewa ba Wai zai bar Mata kwalin a wajen shima yayi tafiyarsa, baibar wajen ba Saida ya leka yaga ta shiga gida kafun yadau laptop in yayi gidan su dashi,daga isan sa gida yaga yanda Addayiya keta washe baki tana nan da nan da shi sai a lokacin ya tuna ashe fa yazo na daya yau babu kamarsa duk tarihin karatunsa report card nasa Bata da kyaun gani saboda rashin maida hankali ga karatu dakin zaman rubuta jarabawa, amma yau ya baiwa kowa mamaki,sai wani huhura hanci yake a dole yau babu kamarsa. Abbu daya dawo yaji labarin abinda ya faru Nan Dadi ya kashesa tare dama su Lahab da Rahab Alkawarin muddin sukayi weac da neco nasu yayi kyau yamusu Alkawarin zai Basu damar zabar duk kasar da sukeso suje suyi karatu Nan Dadi ya Kama Rahab sabanin Lahab da jikinsa yayi sanyi yasan tabbas baida buri da ya wuce yaga Yana buga ball a kasar waje Amma bazaiso ace ya tafi karatu yabar abokin Saba yasan Adewale zasu iyya tafiya tare tunda iyayen sa nada kudi Nabeel da Nnenna sune yake jimamin rabuwa dasu a karon farko an kasafa Masa abinda bazai iya biya wa Nabeel ba don makarantan da suke ciki shida Ade suke had'a kudin hannun su su biya Masa school fees batare da Yan gidan su sun sani ba sai nasu nabeel kawai,daman ba zuwa makarantan suke ba tunda Suka biya Masa su kum ma daga gida ake biya musu ana asara basa zaman aji. ganin yanda Abbu yaga rashin murna a fuskar lahab Kamar yanda yayi tsammani,hakan yasasa kasa hakuri Saida ya tambaya"Lahab Koh baka murna ne Koh akwai Inda kake son karatun ne"da Sauri Rahab yace"Abbu ya wuce akan ball ne kafa San shi inso samune yafison ya Kare a bautawa kwallo"mikewa tsaye Lahab yayi yacewa Abbu"insha Allah zanyi karatu Kuma Zan dage sosai ganin na cinye jarabawan"Yana karasa maganar ya bar wajen da Ido Suka bisa Suna mamakin Koh meke damun sa oho. ********************** Nnenna na Shiga gida ta samu Jennifer zaune dasu mom tunda ta shigo zaginta suke batabi ta kansu ba daki ta shiga ta aje jakanta tare da d'aukar kiki dake tsakar dakin ganinta yasasa,rugawa yazo yahau jikinta ita Kuma ta daukesa ta rike a hannu,sai Kuma ta saukesa ta shiga bandaki,Jennifer ce ta shigo dakin don laptop da aka baiwa Nnenna a makaranta ya saya Mata a wuya shigowa dakin tayi ganin ba kowa ya sata sa hannu ta bude jakan Nnenna ta juye kayan jakan akan gado Allah yasa Nnenna bata ajiye wayarta a cikin takandu Yana aljuhun jakan shiya Hana Jennifer gani ball tayi da kiki ganin bataga laptop in ba don tayi niyar d'auke sa. Fitowa Nnenna tayi sai Kuma ta tsaya tana kallon Jennifer da mamaki tace"mekike nema da Zaki shiga daki kina wargaza min Kaya"mtwsss Naga dai gida da dakin duk na ubana ne Ina da ikon shiga duk Inda nakeso"amsar da ta baiwa Nnenna kenan hakan yasa ta kin kula Jennifer tazo ta bude wardrobe nata tana maida kayan da Jennifer ta wurwurgar a kasa"keee Ina laptop in kin Isa ubana ya saki a makaranta Kuma ki samu kyauta kiri ke,ke kin Isa ki rike laptop ban rikeba? Kala Nnenna Bata ce Mata ba ta gama tsayuwar ta ta bar dakin,har dare Nnenna na daki a kwance bayan ta kammala duk abubuwan da ya zame Mata jiki,wayar ta ne yayi Kara d'auka tayi ganin lahab ne tayi pick up ta Kara a kunnen ta sallama ya Mata ita Kuma tace Hello, murmushi kawai yayi yace"Wai harkin Fara bacci ne"?ah ah ban kwanta ba"ok ki hau online"toh tace tana katse wayar WhatsApp ta hau ya tutturo Mata hoton su na yau Suna ta Hira sai kusan 12 ya Mata sallama shima badon ya gaji ba sai don bacci datace Masa tana ji Yana yanke wayar ta gyara kwanciyarta sai bacci. Kiki dake kwance mikewa yayi ya koma bakikkirin ga idon sa ya Kara zarowa sunyi jajer dasu,tafiya ya koma da kafa biyu na baya ya tashi Yana tafiya da kafarsa yana Isa kusa da window ya Manne da jikin glass na window take ya bace batt,misalin karfe 1 na dare aka bude kofar Nnenna a hankali shigowa akayi cikin tsanda aka nufi Kan gadon nata,hannu Wanda ya shigon yasa zai tabata cikin duhun dakin,da Sauri tayi wani irin zabura ta farka daga baccin da take tare da matsawa gefe hannun nasa ya sauka akan gadon............................................. πŸ€ *By Ruqeenjalal* πŸ€ *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 08084453785 tare da shaidan biyan ki* Page 100 Kafa tasa ta hankade sa tare da mikewa da Sauri ta kunna wutan dakin ga mugun mamakin ta ba kowa bane illah Abraham cikin maye yasha ya bugu,faduwa yayi sai Kuma ya mike cikin maganan Yan iska yake cewa tazo kusa dashi ya take gudun sa sonta fa yake Yana Kara matsowa kusa da ita Yana layi sosai. Nnenna sosai taji tsoro don tunda ta kamasa da peace shikenan taji Koh magana batason Yana hadasu,ganin yanda ya maso kusa da ita yasa tayi Baya da Sauri,hannu yasa ya fizgota da karfi ya maka akan gado tare da fadowa a kanta,wani irin juyi tayi ta wantsalar dashi a gefe ta tashi tsaye jikinta ne ya Soma bari bana Wasa ba karkar Kar haka Naman jikinta yake Bari hannu ta d'aga tana nuna sa dashi hankali tashe take cewa"Abraham fitamin a daki ka fita tun kafun na illataka"rigan jikinsa ya Kwabe ya Soma kokarin cire wando da mugun gudu ta nufi kofar amma kafun ta kiftashi yasa hannu yaja vest in jikinta da nufin jawota baya rigan ya barke take kirjinta rabi ya fito subhanallah aiko take hankalin Abraham ya Soma tashi itakam hannu tasa ta tare kirjin nata cikin wani irin Hali na bakin ciki. da gudu ta nufi kofar Amma kafun ta Isa tuni ya Sha gabanta tare dasa hannu ya damke damtse hannunta Yana kokarin janta sai layi yake lokacin da ya d'aura hannun sa a jikinta a lokacin idanunta ya rufe tama manta waye a gaban ta bed lamp ta d'auka ta kwada Masa a Kai take kannan ya fashe tare da lamp in duka jinine ya fantsama Wanda tashin hankali yasa Abraham fasa wani irin giggitancen ihu Mai amsa amo duk Wanda yaji ihun Abraham a lokacin yasan Yana cikin wani irin zafi na radade faduwa yayi akasa ya Kama Kan yana shure-shure. Su mom dake sama da gudu suka sauko Jin muryan gudan jinisu Yana ihu bilhakki da gaskiya sai Kuma ya soma gurnani Basu tashi ganin tashin hankali ba Saida suka jiyo sa a dakin Nnenna Kama kofar sukayi zasu bude amma kofar taki buduwa,ashe lokacin da ya shiga dakin ya maida kofar ya rufene ta ciki. Cikin tashin hankali Nnenna ta sabe wayarta da boron makarantan ta Koh riga Bata tsaya ta d'auka ba don tashin hankalin da take ciki bana Wasa bane, window dakin ta ta waje shita bude,tana bude glasses in ta hau ta dirko ta waje tana dudduba kiki don Bata gansa a dakin ba,take karnukan Suka hafto Jin motse da gudu tabar gidan Suna binta Wanda kukan karnukan shiya jawo hankalin su mom dake falon kasa Suna tsattsaye a kofar dakin Suna bugawa tare da kwalama Abraham Kira, Suka hankalta da kukan karnuka a waje. da gudu Nnenna tabar layin karnukan basu bar binta ba har Saida ta Shari kwanar barin layin kafun suka koma baya Bata damu da dare bane gudu kawai take tana sa hannu tana Kare kirjinta don gudun da take kirjin zafi yake Mata,layin su Lahab ta Shiga duk da Bata San gidan su ba amma haka kawai jikinta ya Bata Nan ne layin nasu tunda yace mata unguwan su daya,amma Bata canki gida ba a kofar wani gida ta tsaya Inda babu wuta don sauran gidajen kofar gidan solar ne aka kafa haske Kamar Rana ita Kuma a yanda take Bata bukatar tsayuwa a haske Koh dankwali babu daga ita sai wandon bacci da yageggen vest,rasa Ina zata tayi babu Wanda ya Fado Mata a Rai sai Lahab. So take ta kirasa amma Kuma inta kirasa tace Masa meye?a daren nan,wayarta ta d'auka ta danna Masa Kira Harya Fara ringing da Sauri Kuma ta kashe, mannuwa tayi da ginin tana tunanin in wani Abu ya samu Abraham Ina zata Shiga in Dad ya koreta daman ya Mata kashedi tun farko zuwan ta Amma bazata iyya zuba Ido ya keta Mata mutunci ba.. Lahab dake zaune akan sallaha idar da sallansa kenan don yau mummunan mafarki yayi shiya farkar dashi daga bacci,yayi Alwala yazo yayi sallah raka'a shida,Kamar ance ya d'aga kansa kawai yaga wayarsa dake gefen katifar sa tana wuta don wayar na silent ne, da mamaki ya mike toh wazai kirasa war haka agogon dakin ya haske karfe 2:20 ne na dare mikewa yayi ya dau wayar,ganin Nnenna ne yasa sa bin Kiran. da Sauri ta dau wayar ganin kirann sa kafawa tayi a kunnen ta"Nnenna"ya Kira sunan ta fashewa tayi da kuka a hankali tace"na'am Lahab"meya faru Kika kirani yanzun lafiya Kam"shuru ta Masa tana nazarin ta fada Masa gaskiya ne Koh ah ah"Jin shuru batace kome ba yasa sa duba wayar ganin tana Kan layi ya sake tambayar ta"lafiya Nnenna"kasa basa amsa tayi saboda gaskiya yau taji tsoro fiye da lokacin da yan fashe Suka taresu yayin shigowar ta gombe,hankalin sa ya tashi wanda ya Sasa mikewa tsaye"lafiya Nnenna kina inane"a hankali tace Ina layinku. Waro Ido yayi yace"layin mu fa kikace are u out of ur sense kinsan karfe nawa yanzun"?kikace kina layin mu?eh Ina Nan Lahab ka taimake Ni kaf duniya banda Wanda zai taimakamin sai Kai"?ai baisake cewa kome ba ya bude kofar su a hankali cikin tsanda ya fita a dakin tafiya yake a hankali a hankali,Harya iso kofar falon nasu budewa yayi ya fita da Sauri ya karaso bakin kofar gate nasu gate in a rufe yake kirim,hannu yasa yana kokarin bude sakatan gate in irin Mai karfin Nan ne in ka taba sakatansu zasu tona maka asiri. Maigadi dake bacci da Sauri ya zabura tare da lalubar toshinsa Mai hasken gaske ya fito a dakin nasa Yana cewa wayene daidai lokacin Lahab ya bude kofar ya fita Aiko da gudu Mai gadi ya biyosa a baya tsayawa Lahab yayi ya jirasa Harya karaso kusa dashi Yana tambayar sa Inda zashi"kaga rufe gate Nan Ina zuwa Zan dawo yanzun yanzun Kuma bance ka fadawa kowa ba kanajina Koh baba"amma in............baibari ya karasa maganar ba ya d'aga Masa hannu yace "don Allah kaje nace Koh"ba yanda maigadi ya iya haka ya koma cikin gidan ya rufe gate yayi zamansa bai koma bacci ba Yana tsammanin dawowar Lahab da Kuma Inda zashi. Lahab na fita ya kunna wayarsa kiranta yayi tana Masa kwatance Harya karaso Inda take kallon ta yayi sau d'aya Bai Kara marmarin kallon taba sai korin shaid'an yake a zuciyarsa jallabiyar jikinsa ya zare ya Mika Mata,karba tayi ta saka,"meya fitar dake a daren nan Kuma a haka babu suturan kirki"?hawaye ta share ta sanar dashi duk abinda ya faru da mamaki yake tambayarta daman Abraham ba yayanta bane Dad ma ba babanta bane,gyada Masa Kai tayi,tunani ya shiga yasan Koh hauka yake bazai dau Nnenna yakai gidan su ba Kuma tace Masa daga Enugu tazo. A wajen Suka nemi dutse suka zauna sai misalin karfe uku na asuba Lahab ya mike tare da cewa ta jirasa Yana zuwa,gida ya koma lokacin da ya shigo har lokacin idon Mai gadi biyu da Sauri ya shiga dakin nasu har lokacin Rahab na bacci wandon baccin jikinsa ya cire yasa wani wando da riga ATM card NASA ya d'auka,ya bar gidan shidai maigadi sai Ido babu halin tambaya gashi yace Masa Koh Abbu zai nemesa yace Masa ya fita sallan asuba da wuri,da kafa Lahab Suka ringa takawa da Nnenna har wani karamin hotel dake gaban unguwan su kad'an, kama musu Roomi and falo yayi na kwana daya lokacin da suka shiga dakin ce Mata yayi taje ta kwanta a bedroom tunda jiya Bata samu bacci ba shima kwanciya yayi a falo. Kasa bacci Nnenna tayi har 8 na safe idanunta biyu,Lahab dake bacci Jin Karan knocking in door ya farkar dashi mikewa yayi ya Isa bakin kofan, room service ce ta kawo musu breakfast amsa kawai yayi ya maida kofar ya rufe har ya koma zai kwanta sai Kuma ya mike ya nufi bedroom in,da mamaki yake kallon ta ganin ta a zaune ta zuba tagumi kallo daya zaka Mata kasan tana cikin damuwa. Xama yayi a kusa da Ida tare dasa hannu a hankali ya Kama nata yace"Labiba ki kwantar da hankalin ki kinji insha Allah Zaki koma gidan ku"?gyada Masa Kai tayi tace"daker ne wallahi mom ta barni na Kara xama tare dasu kaga yanda kansa ya fashe kuwa"?mikewa yayi tsaye yasa hannu ya mikar da ita bandaki ya shigar da ita ya ajeta a toilet sit ruwa ya Iba ya wanke fuskar ta sosai yajawo towel ya goge Mata tare da cewa"tunta bazakiyi bacci ba ai shikenan sai kizo kici karyawa ga yanda idanunki Suka kukkumbura fa"? Banajin yunwa,da Sauri yace ai Baki isaba wallahi shige muje da karfin dole ya fito da ita falo har lokacin jallabiyar sane a jikinta abincin ya bude Mata shinkafane da doya,tura Mata yayi a gaba hannu tasa badon taso ba ta Soma Sakura tanaci shikam komawa yayi zai kwanta sai Kuma yaji wayansa na ringing daukar wayar yayi ya Kara a kunne amma baice kome ba sai Kuma yace"ah ah Ade ban hau online ba meya faru"?ok ok kawai yace ya katse wayar tare da mikewa yadau remote ya kunna TV. Kara Nnenna dake zaune ta sake da karfi tana ihu jikinta na rawa shi Karan kanshi Lahab yasha jinin jikinsa bana Wasa ba gawan Abraham ne kwance cikin jini kansa a faffashe ga shatin wuka da aka daba Masa a ciki,tare da Karin bayani akan an kashe matashi Mai Suna Abraham Godwin a cikin gidan su sai Kuma aka nuna mom tana kuka tana cewa Nnenna ta kashe Mata d'a sannan ta gudu a cikin daren ba'a San Inda take ba sai Kuma aka Nuno hoton Nnenna boro boro a screen in TV, innalilahi wa'inna'ilahu raji'un shine abinda ya Fara fita a bakin Lahab ya mike tsaye tare da nuna Nnenna da yatsa Yana cewa"keee Daman kisan Kai kikayi kikeson ki sani a matsala"wani irin kuka tafashi dashi tana kafa gwuwowinta a kasa tana cewa"bani na kasheshi ba Ni ban kashe Shiba buga Masa lamp nayi aka Amma wallahi ban soka Masa wuka ba,tana kukan jikinta na rawa tana cewa"shikenan nikam rayuwata ta lalace,gwara ma kawai na mutu na huta da ganin wannan bakin cikin. tana karasa maganar ta Mike da gudu ta zaro wukar dake Kan center table akan plate na fruit da aka had'a musu dashi zata cakawa kanta da mugun gudu Lahab yayi kanta hannun yasa ya Kwabe wukar da karfin gaske ya murza hannun nata tare da had'ata da bango ya bita ya danne da jikinsa har Suna Jin numfashinal juna da Sauri Sauri kuka Nnenna ta Soma tanayi tana ihu akan ya Barta ta kashe kanta shi Kuma Lahab tashin hankalin sa d'aya shine Halin da ta fada ga Kuma kuka da take Masa gudun kada wasu suji a shigo dakin,wani ihu ta sake tana cewa ya saketa saita kashe kanta turasa tayi yayi baya Kamar xai Fadi da gudu ta nufi wajen wukar dake kasa tana dukawa ta dau wukan. ta baya ya rungumeta da karfi jikinsa na rawa yasa hannu zai fizge wukar suka Soma kokowa sosai suke ta dambe a kasa cikin tashin hankali ya fizgota ya maka a bango daga zaune da suke,tana bude Baki ya danna lips NASA acikin nata,take jijiyoyin jikinsa Suka mimmmike Naman jikin na wani irin rawa,a zabure ya damke lips nata na kasa ya Soma tsotso da zafi zafi Yana maida numfashin dake kokarin barin jikinsa gabaki d'aya. Hannunta dake damke da wukar batasan ya akai ta sake wukan da kanta ba hankali tashe ta Soma sauke kanta kasa har lokacin bakinsa na cikin nata Yana aikin tsotsar tausashen lips nata dukar da kanta take a hankali shi Kuma Yana Kara tallafo Kan sama da hannun sa,a hankali ya zame bakin sa daga Kan lips nata a hankali Yana tsude damshin yawonsa dake manne a lips Natan,a sanyaye ya zamo Kansa daidai kirjinta ya kwantar tare da Kai hannunsa ta bayanta ya mannata sosai a jikinsa Yana Jin yanda kirjinta ke mugun bugawa ya Soma magana cikin mutuwar jiki"Labiba duk abinda ya samu vawa jarabawace daga ubangiji meyasa bazakiyi hakuri da jarabawar ki ba,nasan ke ba musulma bace Amma babu addinin duniya daya hallata kisan Kai don an Shiga kuncin rayuwa na yarda dake na amince bazaki iya kashe kowa ba,Koda duk duniya zasu gujeki Ni Zan kasance a gefenki na Baki kariya. Kwantar da kanta tayi a bango ta rumtsa idanunta da karfi,Sun Dan Jima a haka kafun ya zare jikinsa a nata,ba tare da ta kallesa ba ta Mike tsaye sai Kuma da Sauri ta dafe bango Jin jiri nason ibanta,ta nufi kofar da Sauri yasha gabanta tare da Kare kofar da jikinsa,ba tare da ta Bari sun had'a Ido ba tace"ka ban hanya na wuce"Ina zakije"?shima ya tambaye ta. "Zanje na gayama su mom bani na kashesa sa"cikin damuwa Lahab yace"tun farko kin Bata kome da ace lokacin da abin ya farune Kika tsaya Baki gudu ba duk abinda zai samesa kina da bakin kare kanki,amma yanzun kin taka sahun barawo ne kina zuwa saidai a yanke Miki hukuncin kisa"ban damu ba don rayuwa ta daman Bata da wani amfani"da Sauri ya rungumeta sosai ya manna bayansa da jikin kofar tana jikinsa dan dagata yayi a hankali Bai damu da fizge-fizge da take ba,har Saida ya dangana ta da bedroom turata yayi da Sauri ya dawo da kofar ya rufe ta Baya sannan ya fita a falon. Fita yayi a dakin ya tsaya a bakin dakin dake kallon nasu in Bai manta ba jiya kusan tare Suka Kama dakin da couple in Suka shiga dakin su Kuma suka shigo Nan, knocking yayi Saida ya Jima kafun aka bude dakin mutumin ya tsaya Yana tambayar sa lafiya,dan kaikaya keyansa Lahab yayi a hankali yace"Dan Allah madam ta taimaka min da veil daya Dan Allah,kallon sa sosai mutumin yayi sai Kuma ya girgiza kansa Yana mamakin abinda ya had'a yaro da Bai wuce 18 years ba da mace a Hotel Amma baice kome ba ya koma dakin Yana kitsema iskancin yaran yanzun daga xaran balaga yazo musu dai macece a ransu. hijab in ya kawo Masa babba har kasa sosai Lahab yayita godiya da Sauri ya shiga dakin bude kofar dakin yayi ya Shiga zaune ya saketa sai kuka take,jakanta dake yashe ya d'auka ya dau wayar ta ya maka da bango don yasan daker ne in ba'a bi diddigin layi ba shiyasa ya cire sim in ya karya yadau hijab in ya zura Mata akan jallabiyar dake jikinta irin hijaban Nan ne da akece musu Mai Corona ya rufe Mata Rabin fuska hannunta ya Kama ya goyi jakan nata a bayansa Wanda babu kome a ciki sai tarkacen takardunta fita sukayi a hotel in da Sauri ya tare musu Keke Suka shiga Yana tunanin Ina zai kaita to yasan dai yanzun fita a gari bazaiyu ba,kallonta yayi a cikin keken yace"akwai Wanda Kika sani anan ne"?girgiza Masa Kai tayi"Mika Mata wayan sa yayi yace kisa number parents naki muyi magana dasu don ya Kamata Susan abinda ke faruwa. Kuka ta Soma a hankali Wanda yasa Mai Keke Dan juyawa ya kalleta,da Sauri Lahab yace"kimin shuru karki taramin jama'a"shurun tayi tana shesheka,"tsaya anan"Lahab yacema Mai keken ganin yanda yake juyowa Yana kallon Nnenna Bini-Bini duk da ba Dole bane mutum ya ganeta ba,sauka sukayi ya basa kudin sa wani keken ya tare ya fada Masa Inda zai kaisu,Suna Isa bakin layin Bai yarda ya shiga da Mai keken ba ya zare kudin sa ya basa hannu yasa ya kamo na Nnenna Suka Soma tafiya har Suka iso kofar wani gida Mai Jan tabo sosai irin gidan Nan na talakawa tsayawa yayi a bakin kofar gidan Yana sallama. Amsawa akayi daga ciki babu Jimawa saiga yaro saurayin a kalla zaikai 25 ya fito sai Kuma ya waro Ido yace Rahab sannu da zuwa,shafa kansa Lahab yayi yace"Lahab ne"Aiko da Sauri yaron yace masa su shigo ciki Bismillah ba musu Lahab ya kama Nnenna Suka shiga ciki shimfida musu taburma yayi Suka zauna bin gidan Lahab yayi da Ido sai Kuma ya kalli yaron yace"goggoji ta tafi aiki ne"da Sauri saurayin daya mike ya ibo musu ruwa a kofi ya aje Yana amsa Masa da eh Lahab Bai barota a gida ba"?share tambayar Lahab yayi sannan ya nuna Nnenna yace"Dan Allah faruq in babu damuwa Ina son ta zauna anan zanje gida nayi magana da goggoji don Allah Kar a barta ta fita sannan ta zauna a daki banason mutane Suna shigowa Suna kallonta ga wannan ya Mika Masa 5k ka sama Mata abinda zataci pls,da Sauri faruq yace haba Lahab abinda zataci sai ka bani kudin karfa ka manta daga gidan ku goggoji ke zuwa da abinci haba haba wallahi bazan karba ba,duk yanda Lahab yaso faruq ya karbi kudin ki yayi,mikewa yayi zai tafi da Sauri Nnenna ta Mike hade da tsayawa a gefensa zaro Ido yayi yace"ya haka"?wani kallo take Masa duk da bataji abinda sukace ba don bajin hausa take ba Amma ta fahimci a gidan yake nufin zata zauna Taya zata zauna gida daya da faruq ba Mata a gidan. da turanci take fada Masa bazata zauna gida babu mace ba,anan Lahab ke ce Mata ai matar gidan na tafiya aikine shima faruq Yana zuwa shago don haka ita kadai zatana wuni kin yarda Nnenna tayi da zaman sai da Lahab yayita Mata masifa kafun ta amince a idanunsa faruq ya bude Mata kofar dakin goggoji ta shiga shi Kuma yabi Lahab a baya ya rufe gidan ta baya kamar yanda Lahab yace Masa. Lahab na Isa gida ya tarar da har Yan gidan sun karya masu zuwa aiki ma sun wuce aikinnsu Amma sauran yaran nagida tunda yanzun ana holiday ne, bayan dakunan gidan ya leka anan ya tarar da goggoji Zama yayi babu boye boye ya zayyana Mata abinda ya faru da Kuma Nnenna dake gidan ta tare da tabbatar Mata Batayi kisan Kai ba sanan Dan Allah duk abinda zaije ya dawo kada ta sanar da kowa Nnenna na gidan ta sanann tasa Mata ido,babu abinda lahabbl zai nema Wanda Bai sabawa shariya ba goggoji ta kasa Masa don ya taimake ta a rayuwa badon Shiba da d'anta kwalli daya faruq daya Zama tarihi. da yamma saiga Adewale da Nabeel hankali tashe sukazo gidan su Lahab Nabeel zai tsinewa Nnenna yake Wai ashe makashiyace Mai fuska biyu shi wallahi tunda ya ganta shikenan yaji ya tsaneta Allah yasa a Kamata a ratayeta wani irin Abu Lahab yaji ya tsoki zuciyarsa hatta yawun bakinsa wani daci daci yake Masa wani Abu Mai kamasa gundura tsana yaji ya dirar Masa a makwashi na Nabeel,Amma baice kome ba Adewale ma kallon Nabeel kawai yake Saida ya Bari ya kammala zaginta tas kafun yace"haba Nabeel kana da tabbacin ita tayi kisan ne wai meyasa mutane suke hakane gashi duk gari ya gume ta kashe Dan marikinta ka sani Koh ba haka abin yake ba"hayayyako Masa Nabeel yayi yace cewa za'a Mata karyane in tasan tana da gaskiya meyasa ta gudu ana Neman ta, mikewa Lahab yayi ya nunawa Nabeel kofa hade da cewa"tashi ka fitar min a daki Nabeel"? Da mugun mamaki Nabeel ya mike tsaye yace"Ni kake kora Lahab"kofar lahab ya Kara nuna Masa a zafafe yace"tun Kan Raina ya baci Nabeel kabar dakin Nan"mikewa Nabeel yayi yace"insha Allah bazan Kara shigowa gidan bama bare dakin ka ya bude kofar ya fita"mikewa Adewale yayi ya matso kusa da Lahab tare dasa hannu ya dafa kafadar sa Yana bashi Baki akan ya kwantar da hankalin sa taima ma duk abinda ake fada akan ta karyane,shidai Lahab baice kome ba Harya Gama surutun sa yabar gidan. Bayan kwana biyu Da yamma bayan Lahab yaje ball ya dawo kamar zaibi gidan goggoji yaga ya Nnenna ta kwana sai Kuma ya dawo gida yadau laptop nata,bayan yayi wanka yaje gidan goggoji ya duba Nnenna Kuma yaji dadin yanda yaje ya sameta tayi wanka harma ta sa Sabon Kaya daya baiwa goggoji kudi ta sai Mata,Amma dai tadan rame kad'an Zama yayi a kusa da ita tare dasa hannu ya taba wuyanta buge hannun tayi,shikam Dan murmushi yayi ya aje Mata laptop in a gefen ta Bata kallesa ba ta juya fuskar ta gefe daban irin tayi fushin Nan,sai da yayita faman lallama kafun ya samu ta hakura ta sauka daga fushin da take dashi na kwana biyar dabaizo ya dubata ba, faruq ne ya shigo gidan da Sauri ya karaso Kan taburman ya dau laptop in Yana jujjuyawa. Washe garin ranan da yamma Lahab ne zaune a dakin sa Yana karanta littafin physics don yanzun da gaske ya dage Yana karatu, yaji an turo kofar dakin sa da Sauri da Sauri ya mike tsaye ganin uzaifa ya shiga hankali tashe Yana cewa Lahab ya fito ana Neman sa,shekeke lahab yayi yace "don ana nemana saika min irin wannan shiga daki cikin tashin hankali"Bai rufe Baki ba saiga Abbu ya shigo dakin da kansa hankali tashe yace"Wai Ina Lahab inne ka fito Mana fitowa lahab yayi da Sauri Abbu ya kamo hannun sa har babban falo,sake Baki Lahab yayi Yana bin wa'inda ke falon nasu sai Kuma idanun sa ya sauka akan Dan uwansa da ke tsakiyar wasu mutane guda uku cikin dumbin mamaki,yaji Abbu na cewa bakun ga dayan ba Y'an biyu ne,gaLahab in wannan dake wajen ku Rahab ne ince dai lafiya kuke neman sa,babu walwala a fuskar dayan ya kalli Lahab yace"Kaine Hassan Al'hassan dogo Mai naira?gyada Kai Lahab yayi sai Kuma wani daga cikin mutanen ya zaro ID card insa ya nuna tare da cewa"Ni sunan wisdom timoti jami'in sirri na farin Kaya zamu tafi da Lahab office in mu akwai tambayoyi da mukeso ya amsa mana"Lahab yaci niiii"? Yes ur under arrest................................................ Alhamdulilah Alhamdulilah Alhamdulilah πŸ€ *By Ruqeenjalal* πŸ€ *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 08084453785 tare da shaidan biyan ki* Book 2 Page 1 Innace muku hankalin Y'an gidan su Lahab ya tashi toh yafi gaban tashi yayi sosai suka shiga rudani duk yanda Abbu yaso su Masa bayani tun a cikin gidan sukace ah ah saidai yabisu office nasu aiko take ya shiga ya dau keyn mota Rahab da tunda yaji ance za'a tafi da dan uwansa yake ta faman rusa kuka yazo ya rungumi Lahab,amma babu Imani aka fincike sa tare da tasa Lahab a gaba suka bar falon ji kawai sukayi timmmmmmm Rahab ya sulale a wajen,hankali tashe Abbu ya d'aga waya ya Kira ya jafar ya samesa a office in jami'an ya barwa su Shareef Rahab shi Kuma yabi bayan jami'an. Bayan isar su Abbu anan ne yaji dalilin Kama Lahab akan wata yarinya da tayi kisan Kai Kuma ana zargin dasa hannun Lahab,aiko Nan Abbu yace uban kuturu yayi kad'an bare na makaho kaninsa Koh kuda bazai iyya kashewa ba bare tai guda,Kuma babu abinda ya had'asa da wata Yar arna,magana ta Zama babba Mami da Rahab na gado don gabaki d'ayan su faduwa sukayi,lokacin da labari ya riske mubeena Aljanunta ne Suka tashi rike-rike sai ihu take daker aka samu aka daddan neta Suka kwanta,daga baya Kuma sai aka koma asibiti ganin ciwo ne ya nufeta lokaci d'aya,su Inna sunyi mamakin surutun da tayi lokacin da take cikin kukan iska akan a fito Mata da Lahab kaza-kaza tunanin da yazo ma Inna taima tausayin sane ya sata haka tunda case na kisan Kai ba Wasa bane. Papa Kam sosai ya dawo gida Yana ta masifa akan baga abinda yake gujewa Ade ba akan yaran hausawan nan makiyansu ne Amma baya ganewa gashi yaro ya kashe Cristian duk yanda Adewale yaso Kare Lahab a wajen iyayen sa abun ya gagara don Yana tare papa zaiji an buga Masa baki,kowa yaji zancen Nan sai ya karyata duk da Lahab bayaji amma wallahi kowa ya shaida Lahab bazai kashe mutum ba Koh taimaka wa wata ta kashe mutum. Duk yanda Yan Sanda sukayi da Lahab akan ya sanar dasu Inda Nnenna take amma ya murza idanun sa akan shi baisan Inda take ba,gashi an Hana taba lafiyar sa da karfin iko da kudi yayun sa Suka daukaka Kara za'ayi shariya akan kazafin da ake son d'aurawa kanin su,duk wani masoyin Lahab ya Shiga tashin hankali lokacin da zancen yaje kunnen Nnenna goggoji ne ta dawo tana sanar Mata hankalin ta tashe ta Soma kuka tare da mikewa tsaye tana cewa zata,tace musu babu ruwan Lahab basai an Shiga kotu ba,hankali tashe goggoji tace bazaiyu ta barta ta fita ba Lahab bazai yafe Mata ba ta fahimci Yana kaunar yarinyar sosai ita da faruq Suka yita nutsar da ita tare da Bata tabbacin insha Allah Lahab xai fito ai Yan uwansa nada kudi Kuma Godwin bazai iya winning akan suba in zancen kudine zuriyan su Lahab sun damasu sun shanye daker dai da sudin goshi Suka samu ta yarda zata zauna laptop nata ta dauko ta baiwa faruq ya sitting na kome a ciki ta Fara Hawa yanar gizo tana kallon abubuwan dake gudana a duniya da Al'amarin case nata kowa na fadin Albarka cin bakin sa. Mami tafi kowa Shiga tashin hankali Allah sarki uwa gabaki d'aya ta rame ta fige duk da an sallamota amma bata Jin garau Kamar dai mubeena itama ta Dan warware ga Kuma bikin Ahmad da Ruky da ake a wannan satin duk abubuwan sun hadu sun Mata yawa,Lahab ya wahala zaman gidan yari Koh babu duka ba zagi azabane, ya Kara Baki ya rame sosai sai Ido da hanci da tsawo duk sun fito sosai amma saboda taurin rai Lahab yaki ya basu duk information da ya sani akan yarinyar. Monday morning kotu ya cika makil da Jama'a Koh matsakan tsinke babu sosai sai dan surutai dake tashi kasa-kasa shigowan Alkali shiya nutsar da Al'umma kowa yayi shuru tare da mikewa Harya zauna kafun jama'ar Suma Suka zauna Yan uwan Godwin (Dad) dana mom sai Family Lahab Suna da yawa sai Yan jaridu da Kuma Yan kallo after few minutes lauya ne ya Mike ya gatabar da kansa na lauyan dake Kare Wanda ake tuhuma sannan lauyan su mom shima ya mike ya gabatar da kansa tare da Neman izini ya matsa kusa da Lahab ya tsaya sannan ya kalle sa yace" Koh zaka iyya fadawa kotu cikekken sunan ka"? d'ago jajjayen idanun sa yayi ya kalli lauyan yace"Sunana Hassan Al'hassan dogo Mai Naira"jinjina Kai lauyan yayi sannan ya Kara jefo Masa tambaya"Koh zaka sanar da kotu wace alakace tsakanin ka da Wance ake zargi da kisan Kai Nnenna obinna"?sunkuyar da Kai yayi sai Kuma yace"bamu da wata alaka ta jini friend nawa ce a makaranta"wani shegen murmushi lauyan yayi ya gyara rigansa kafun yace"kana nufin bakwa haduwa sai a makaranta sanann duba da a'ladunku na Arewa babu friendship tsakanin mace dana miji"mikewa lauyan dake Kare Wanda ake tuhuma yayi Yana cewa"objection my lo... barrister Yana kokarin cusawa Wanda ake zargi magana a baki taya zaice a Arewa babu abota tsakanin namiji da mace"gyada Kai Alkali yayi yace wa lauyan a kiyaye,sannan yaci gaba dama Lahab tambayoyi Yana basa amsa har aka gangaro Kan na Randa abin ya faru"Koh Hassan zai iyya sanar da kotu a ranan 30/1/202.........meya fitar dashi da misalin karfe 20:20am daga gidan su, alhali Kuma dokan gidan su yara basa fita muddin 9 na dare ya gotta.? Sosai zuciyar Lahab ta tsinke bama Kamar lokacin da ya dago ya kalli Mami da Abbu da Suka zuba Masa Ido Suna jiran amsar da zai bada,a hankali yace"da misalin karfe biyu na dare Nnenna ta kirani a waya.......................tsab ya Fadi abinda ya faru a ranan har hotel Inda Suka sauka a ciki amma bai sanar dasu yasan ana tuhumar Nnenna da kisan Kai ba haka zalika baice musu ya kaita gidan goggoji ba yadai ce sun bar hotel in ya bata kudin mota akan zata koma garin su"jijiga Kai lauyan yayi sannan ya nemi izinin zama ya koma ya zauna. Koh lauyan dake Kare Wanda ake tuhuma Yana da tambaya Koh shaidan da zai nunawa kotu Hassan bashi da hannu a kisan Abraham?mikewa lauyan yayi ya sake rusunawa kafun ya dawo wurin Lahab ya Soma magana"a ranan da akayi kashe Abraham Wanda ake zargin Yar uwarsa Nnenna obinna ce ta kashe sa,abisa binciken likita sai da aka raunana gawar da duka akai kafun bayan Yan minutes aka daba Masa wuka daidai karfe 1:30 na dare Wanda anan Kuma Mai gadi ya tabbatar ma da kotu karfe 2:21am Lahab ya bar gidan su,kotu in tayi duba da wannan al'amari Lahab bayida hannu a kisan Abraham duba da cewa Saida aka kashe Abraham kafun ya bar gidan su. Yana karasa maganar Alkali yace Yana da takardan hujjan likita amsawa yayi ya mika aka mikawa Alkali,sannan yaci gaba da bada gasheshen bayani akan babu abinda ke tsakanin Lahab da yarinyar sai abota Kamar yanda yace duba da cewa ajinsu daya a makaranta,haka zalika yarinyar da aka bibiye tushen taa korarta akayi a kauyen su saboda zargin maita da ake binta dashi,Kai a takaice dai an fafata shariya sosai kowa yanason yaga ya kada d'aya, Alkali ya d'aga shariyar sai Nan da sati shida sannan lauyan su mom ya tabbatar daya nemo hujoji masu karfi Wanda zai tabbatar wa da kotu Lahab nada hannu dumu-dumu Koh boye Nnenna,bayan kammala shariyar aka maida Lahab Inda aka d'auko sa don Abbu yayi yayi a sakosa su dawo gida Amma kotu Bata bada dama ba. Bayan sati shida Zama na biyu,tsaye lauyan su Abraham yake a gefen Lahab daya gama kodewa ya Zama wani iri dashi ya jefo Masa tambaya"shin Koh zaka sanar damu dalilin da yasa kuka fasa kwana a hotel in alhalin Kuma kudin kwana ka biya tun farko"?gyara tsayuwar Lahab yayi yace"saboda a hotel in ba'a Kama wuni sai kwana sannan na jawota ne don na ajeta daidai safiya na maidata gidan su Don ni bansan cewa ba iyayenta take tare ba" Kana nufin duk abotar ku da ita bata sanar dakai cewa ba iyayenta bane Mr Godwin da matarsa ba"? "Kwarai Ni Bata sanar Dani ba" Amma me tace maka bayan sanar dakai cewa ta bugawa Abraham lamp"?cemun tayi ya shigo dakin ta cikin dare Yana kokarin afka Mata shine garin Kare kanta ta buga Masa lamp"ok a lokacin kasan cewa ba yan uwa bane Koh Kuma tace maka menene a tsakanin su"a kufule Lahab yace nace maka bansan bada parents nata take tare ba Saida abin ya faru. Murmushi barrister yayi sannan ya nemi izinin gabatar da shaid'an sa na biyu, peace ya Kira ta taso tazo ta tsaya gabaki d'aya idanunta a kumbura kallo daya zaka Mata kasan cewa wannan mutuwar ta shigeta ta Soma amsa tambayar da aka jefo Mata,shin akwai wani Abu na rashin fahimta Koh tsana Koh Kara tsakanin Abraham da Nnenna,girgiza Kai tayi sai Kuma hawaye ya cika Mata Ido tasa hannu ta share ta Soma magana a hankali"babu wani Abu a tsakanin su sai dai Kuma Nnenna batason shishige Mata da Abraham keyi Kamar ma ta tsane sa,sosai dai akayi ta fama da shariyar aka Kira mom Dad Jennifer Sarah sukazo sukayita bada shaidan gaskiya da karya akan Lahab bayan kammala nuna hujjojin barrister Solomon jefau ya koma ya zauna,mikewa lauyan Dad yayi ya matso kusa da lahab. Hassan shin mutanen dake zaune da Nnenna sun taba kallonka Koh sanin wani alaka a tsakanin ku"amsa Lahab y basa"kwarai ma kuwa uncle Nata ya taba ganina a asibitin haka zalika cousin nata Jennifer mate namu ce don haka Ina da tabbacin sun sanni"gyada Kai Barrister yayi ya Kira peace tambayar da ya Fara jefo Mata shine menene alakarta da Abraham,dan rikicewa tayi cikin eii eiiina tace babu"dan murmushi barrister yayi yace a bincikin da kotu tayi tagano cewa akwai soyayya Mai zafi a tsakanin ki da mamacin kafun Nnenna ta dawo gidan da Zama,sai gabaki d'aya hankalinsa ya Soma komawa kanta,daga Nan ya shiga kyautata Mata ke Kuma tun daga lokacin kikaji kaf duniya babu Wanda Kika tsana Kamar ita"da Sauri tace Ah ah ni babu wata soyayya a tsakanin mu"karkiyi Wasa da kotu don Nan bamusan Wasa ba sannan ya Kara jefo Mata tambaya wata daya kafun mutuwar Abraham kunje hospital dashi saboda zazzabi da kike na shigan ciki,gane hakan yasa ya Miki dadin Baki akan zai kaiki a Baki magani daga Nan aka baki na zubar da ciki Wanda shi ya sani kece Baki sani ba Saida cikin ya zube,Kika koma kauyen ku jinya Saida Kika Kai wata Kika dawo"kukane ya kwacewa peace ta tsunguna tana kuka"amsa Zaki bawa kotu"kwarai haka akayi Kuma naji matukar zafin zuban cikin. toh Zaki iya komawa ki zauna ganin irin kukan da take komawa tayi ta zauna sannan aka Nemo mom tambayar farko da aka jefo Mata shine waya Fara Jin kukan Abraham Kuma waya Fara Shiga dakin da Kuma waye karshen shiga a lokacin da abin ya faru peace na Ina dakuma dalilin da yasa Abraham Shiga dakin Nnenna cikin daren Allah,duk amsa daya ce peace ce tayi bayan shiga sannan itace farkon fitowa na jiyo kukan NASA haka zalika bata San abinda ya shigar dashi dakin Nnenna ba Ina son wannan kotu Mai adalci data dubi hujojin da aka gabatar a gaban kotu in tayi duba da cewa Abraham ya shiga dakin Nnenna tsakar dare Kuma cikin maye Wanda bincike ya tabbatar Mana daga dakin peace ya fito don yabar hulansa da wayarsa a dakin peace tare da goran syrup daya Sha bugu da Kari peace bata shiga dakin ba sai bayan minti uku da mutuwar sa haka zalika Nnenna tayi kokarin Kare kanta na yunkurin raping nata da take kokarin Yi,mikewa Barrister Solomon yayi yace Barrister Yana yanke magana babu hujja,sosai akayita shariya daga karshe aka wanke Lahab daga zargin da ake Masa tare da Kama peace a matsayin Wanda ake tuhuma kuka peace ta fashe dashi tana rantse-rantse ba ita ta kashe Shiba,sannandasa Ido Mai tsanani wajen ganin hukuma ta shafko Nnenna obinna. Wanka Lahab yayi yaci abinci kafun ya samu ya farfado gabaki d'aya zuriyan su ranan sun cika gidan ana ta maida zancen abinda ya faru wasu Nasiya suke Masa akan abinda ya faru ya Zama iznah a garesa Mami Kan cewa tayi duk Randa taji labarin an gansa da wata wallahi sai tayi mummunan Saba Masa zata basa mamaki,Abbu Kam security ya zuba a gidan sunfi goma ya Karo mototi haka zalika yanzun shiga gidan su Lahab baida sauki haka zalika fita ma banda Shareef babu Wanda ake Bari ya fita shi kadai sai da driver da security zakaje ka dawo malami aka dauko musu Yana karantar da yaran Arabic a gida gashi daman ana Holiday gabaki d'aya Lahab yaji Kamar zai mutu an kwace Masa waya an hanasa fita gwara kowa ma za'a barsa yadan fita shikam Koh kofar gida bai zuwa damuwa sosai yake ransa sai dai Yana d'anjin labarin Nnenna a wajen gogoji amma hakan bai wadace saba so yake ya ganta face to face Koh xai danji dadi gashi abokansa ma duka an hanasu shigowa gidan babu Mai shigowa sai family su Koh gogoji Mai aiki da sauran ma'aikatan sune keda daman shiga da fita ta sauki. *********** Yau satin Lahab d'aya da dawowa ba laifi yadan murmure sai fama da jinya yake tunda ya dawo abinka da Wanda ya Saba da dadi yaje wahala,kwance yake akan katifar sa Addayiya na gefe a zaune,ruwa Dr yake daura Masa bayan ya gama ne ya fita a dakin Addayiya ma fita tayi Lahab dake kwance bude Ido yayi Jin an turo kofar Rahab ne ya shigo sanye da jampa sai qur'ani a hannun sa yanzun malamin ya sallame su,aje Qur'ani yayi akan sett ya matso bakin gadon da Lahab ke kwance,hannu yasa ya taba goshin Lahab, dan bude Idon da ya lumshe Lahab yayi ya kalli dan uwan nasa sai Kuma ya maida idanunsa ya rufe. tagumi Rahab yayi yanda Lahab ya rame haka shima ya rame sabar damuwar da yagani a fuskar dan uwan nasa,kasa hakuri yayi yace"Lahab ya Kamata kayi hakuri akan abinda ya faru ka manta da kome ka dawo da fara'ar ka Mana dan uwana Koh nima Zan dawo yanda nake,Kama hannunsa lahab yayi a hankali ya Soma kokarin mikewa zaune tashi Rahab yayi ya taimaka Masa ya tashi xaune,a hankali yace"Rahab dan Allah ka taimaka mini"wani kallo Rahab ya Masa sannan yace"wani irin taimako Zan maka amma fa ka sani indai akan karya dokan da Abbu yasa a gidan Nan ne bazan taimake kaba"fuskar tausayi Lahab yayi yace"dan Allah Rahab ka taimaka min da waya zanyi Kira"da Sauri Rahab yace dan Allah rufemin baki akan me Zan baka waya kayi Kira wallahi badani ba shiyasa ma Abbu ya raba Mana daki yanzun kwana kawai yake kawoni Nan". Hawaye ne ya cika idanun Lahab a hankali yace"shikenan Rahab tunda kowa zai nunamin fifiko a gidan Nan cikin Suma harda Kai bakome Randa na mutu ai kun huta"da Sauri Rahab ya mike tare da zaro wayarsa ya mikawa Lahab Jin Lahab ya ambace mutuwa cikin damuwa yace"gashi nan karba kayi Kiran dan Allah ka daina min Wasan mutuwa bana fatan ka mutu ka barni na daina ganin Mai irin fuskata a duniya"?karbar wayar kawai Lahab yayi a hankali ya mike tare da zare ruwan dake hannun sa,ya mike tsaye a daddafe ya bude toilet ya shiga tare da maida kofar ya rufe shidai Rahab Ido ne nasa yabisa dashi Harya rufe kofar. d'an jingina yayi da tiles na toilet in ya loda number Adewale don shi Sam baida number goggoji a wayan sa Kira yayi Saida ya tsinke ya Kara Kira na biyu kafun Ade ya d'auka karawa yayi a kunnen sa yayi sallama amsa Masa Ade yayi daga Jin muryar tasa ya shaida shi da Sauri yace"Lahab nayi missing naka so much wallahi babu ranan da bana zuwa kofar gidan ku amma security sun hanani shiga duk na shiga damuwa wallahi gashi layinka bata shiga"a hankali Lahab yace"nida fita Kam bansan ranan Saba Abbu ya rantse bazan Kara fitaba sai lokacin weac Ina kammalawa results na fita yace bazan Kai sati a kasan Nan ba duk banjin dadin rayuwa ta wallahi"dan shuru Ade yayi Saida ya gama sauraron sa kafun yace"toh yanzun Lahab ya zakayi dolen ka kabi abinda yayan ka yake so,dan Allah karka sake shigar da kanka wani rigimar Kuma kayi hakuri saura wata nawane kwata-kwata muyi weac in, kaga in mukabar kasan Nan karyan dai ace za'a sa Mana Ido. Ajiyar zuciya Lahab yayi sannan ya Kara kasa da murya yace"Ni duk ba wannan bane damuwa ta"da mamaki Ade yace toh menene damuwarka Banda Wanda kake ciki har akwai wani abin ne"eh akwai Ade so nake kaje gidan goggoji....Ade Bai bari ya karasa ba da Sauri ya sake jefo Masa tambaya wace goggoji Kuma"?a hankali Lahab yace Wacce ke Mana aiki har muka taba zuwa gidan ta muka duba yaonta"?da zullumin Ade yace"toh mezai Kaine gidanta Kuma" Sauki ajiyar zuciya Lahab yayi yace"yau kwana biyu batazo aiki ba hankalina ya kasa kwanciya Ina ji a jikina akwai abinda ya same Nnenna duk da Addayiya tace min wai faruq ne ba lafiya kasan sickle cell ne"da mugun mamaki Ade yace"wace Nnenna Kuma"?a sanyaye yace Nnenna da aka ikirarin tayi kisan Kai"wani dogon salati Ade ya sake kamar wani musulmi ya Kara da cewa"kana nufin duk ukubar da ka shigan Nan yarinyar nan tana wajen goggoji toh wallahi babu ruwana bazaka sani a matsala ba in gaya maka babbu Inda zani Yana karasa maganar ya yanke call in...................................... πŸ€ *By Ruqeenjalal* πŸ€ Cike da damuwa ya Kara Kiran Adewale amma sai ya danna Masa user busy,baiyi zuciya ba ya tura Masa message dan Allah ya d'auki wayar sa daker dai ya samu Adewale ya dau wayar sannan ya amince zaije ya dubo Nnenna amma daga wannan kada ya sake sakasa a shirgen Nnenna babu ruwan sa,katse wayar Lahab yayi Yana hamdala sannan ya koma cikin dakin har lokacin Rahab na zaune yana jiran sa,yana fitowa ya Mika Masa hannu wayan nasa ya basa sannan ya maida ruwan jikin sa ya kwanta. da daddare Koh abinci Lahab ya kasa ci sai tsumayen Kiran Adewale yake amma shuru sai kusan 8 na dare Adewale ya Kira Rahab Rahab ya kawo Masa wayar amsa yayi da Sauri ya tashi Kamar d'azun ya shiga ban dakin Kara wayar yayi a kunne ya Soma mita sai yanzun Adewale zai kirasa tun d'azun Yana zaune Yana tsumayen Kiran nasa amma shuru"?yanzun zaka tsaya na fada maka abinda na ganone Koh zaka tsaya min mita na kashe wayata"?da Sauri Lahab yace toh kayi hakuri fadamin inji meya faru"? Ajiyar zuciya Ade yayi yace ka duba WhatsApp na tura maka hoton ta kaga halinda naje na sameta a ciki zuciyar Lahab Saida ta buga cikin tsoro yace meya sametan,baidai basa amsa ba kawai ya katse wayar,jikinsa har rawa yake ya bude data ya shiga WhatsApp zubewa yayi a kasa ya zauna tabas saban shock Nnenna ya gani kwance Kamar gawa Ido a rufe jikinta gabaki d'aya ya sauya daga fari zuwa yellow sosai ga bakinta yayi jajer dashi rabin fuskarta har wajen wuyanta jijjiyoyine bakekkerin Suka fito rudu-rude jikinsa ne ya cigaba da rawa ya fita da Sauri wayar Ade ya Kira Yana d'auka ya Soma Masa magana"Adewale mutuwa tayi ne meya sameta"kaga Lahab karka sa kanka a matsala nidai goggoji tacemin yau kwana biyu kenan da Fara ciwon Nan nata sun tsorata ainun don numfashin tane kawai zai tabbatar maka tana da rai"innalilahi wa'inna'ilahu raji'un kawai Lahab yace ya katse wayar da gudu ya fito daga ban dakin wardrobe ya bude ya fito da kayansa sakawa yayi ya zaro takalmi zai sa yaga Rahab ya shigo da mamaki yace"Lahab sai Ina zaka a haka Kuma"? "da Sauri Lahab yace fita zanyi"fita fa kace wani irin fita kake nufi Koh ka manta ne baka da daman fita a gidan Nan yanzun"da Sauri shima Lahab yace Ina da Kai Koh ka manta ne dan Allah Rahab kaje ka kwanta a matsayi na Ni Kuma na fita a madaden ka ka taimaka min wallahi akwai babban matsala"wani kallon tuhuma Rahab ya Masa sannan yace wani irin matsala kenan? Nidai ka taimaka min kin taimaka Masa Rahab yayi daker ya samu ya shawo kansa kafun ya amince kwanciya yayi akan katifar Lahab yayin da Lahab Kuma yasa Kai yabar dakin Yana zuwa compound na gidan nasu security Suka tashi shiga mota yayi Suma Suka shiga aka jasu suka Soma tafiya gidan ya jafar Lahab yace a kaisa Suna Isa yace su tsaya a kofar gidan basai sun Shiga ba bude kofar yayi ya shiga gidan da Sauri ya nufi falo gashi yammane Kuma goshin mangari ba falon ya bude da sauri ya Shiga babu kowa sashen su Majid ya nufa Yana bude kofar yaga babu kowa Kamar falo sai kida dake tashi a dakin Majid bude dakin yayi da Sauri Majid ya juyo ya kallesa sai Kuma ya juya yaci gaba da rawansa. Xama Lahab yayi a hankali yasa hannu ya kashe mp in a kufule Majid yace"kaga Rahab banson surutu tashi kabar min daki da Allah"Majid Lahab ne"zaro Ido majid yayi yace kana nufin kaida aka sawa Mari Kaine ka fito"?nidai ba wannan ba taimakona zakayi security na kofar gida so nake ka taimaka nabar gidan Nan ba tare da sun sani ba"kallon sa Majid yayi da mamaki yace"so kake nayi fiffige da Kai mu tashi ta samane Koh yaya Ni ta Ina Zan iya fiddakai"? "Shuru Lahab yayi sai Kuma yace back door ka taimaka min"d'an dakata Lahab nifa karkazo ka sani a matsala munddin aka nemeka aka rasa Ni za'a zarga karka kiramin ruwa babu ruwana wallahi"dan Allah Majid ka taimaka min Dan Allah nace fa"dan shuru yayi sai Kuma yace Ina zuwa fita yayi a dakin Bai Jima ba sai gashi ya dawo da key yana cewa Lahab ya bari a Shiga sallan mangariba. Ana shiga sallan mangariba backdoor Lahab ya nufa da Majid bude Masa yayi ya fita harda waya Lahab ya karba a wajen sa Yana barin layin Adewale ya Kira akan ya fito gida Yana bayan GRA,Bai wani Jima ba saiga Adewale daga Nan gidan su goggoji Suka nufa da yake darene babu Wanda ya gane Lahab Shiga gidan sukayi har dakin da Nnenna ke kwance abin tausayi gabaki d'aya kammanin ta sun sauya ta chanja hannu Lahab yasa ya bude kwayar idanunta Saida ya koma baya da Sauri saboda yanda jini ya taru a idanun tim goggoji ya tambaya garin Yaya ta Soma ciwon"wallahi Lahab kwana uku batacin abinci a kwana na hudun ne na matsa Mata akan saita d'anci abinda na kawo daga gidan ku daga saka abinci a Baki Koh hadeyewa bata gama yiba Naga ta damke makogoronta tana amai harda jini a ciki shikenan ta yanke jiki ta Fadi Ido ya rufu har yanzun bata budewa kwana biyu kenan. Mikewa yayi da Sauri ya nufi kofar gidan Keke napep ya tare sannan ya dawo gidan da Sauri ya ciccibi Nnenna da jikinta ya bushe ta sandare,da Sauri Ade dasu goggo Suka Soma tambayar sa lafiya Ina zaije da ita gudun kada a ganeta a Kamata,kala baice ba yayi kofar gidan da Sauri Ade da goggoji Suka Shiga keken Suma aka bar faruq a kofar gida a tsaye,wani private hospital na kudi Lahab ya kwatantawa Mai keken directly Suka karasawa asibitin ya d'auketa sai ciki ganin halinda take ciki yasa likitoti rufuwa a kanta. da misalin karfe 12:30am na dare Lahab da goggoji ne a asibitin don Ade tun 9 na dare papa ya kirasa yanata masifa akan ya dawo gida,likitane ya Kira su vayan sun shiga office nasa ya Soma musu tambaya Koh akwai abinda ke damun tane daya shafi iska-iska girgiza Kai goggoji tayi shidai Lahab shuru kawai yayi Yana Jin abinda Dr ke cewa Wai Basu gane Kan cutar ba sun saka Mata ruwa ma ruwan baya gudu haka Allurar ma sun saka amma ruwan yaki shiga a jikinta,su d'auketa kawai jinyan Nan bana asibiti bane,mikewa Lahab yayi da gudu yayi dakin da aka kwantar da ita Yana zuwa kuka kawai ya fashe dashi ya zauna a bakin gadon hade da kamo hannun ta Yana hawaye. Goggoji ce ta turo kofar ta shigo ta zauna akan kujeran tana kallon Lahab sai Kuma tace"Lahab yarinyar Nan ta Fara bani tsoro gaskiya mezai Hana ta koma wajen danginta kaga halinda take ciki fa"hawaye ya share sanann yace"gaskiya goggoji bazan iya barinta a halinda take ciki ba gaskiya tunda yace abar musu hospital nasu da safe sai mu kaita wani"? Kaga Lahab Kai suspect ne haka ma ita nasan dai ba kowa bane zai gane Nnenna tunda ita gabaki d'aya jijiyoyin fuskarta sun sauya Mata kamanni bai Kamata ana ganinka haka barkatai ha bugu da Kari Kuma halinda yarinyar Nan take ciki bana asibiti bane gobe in Allah ya kaimu sai muje nida faruqu kauyen mu akwai wani babban malami acan gaba da kauyen, insha Allah koma menene zai kawo karshen sa,d'an shuru Lahab yayi sannan yace"muje dai tare goggoji shi faruq ya zauna a gida bai Kamata na bar Miki d'awainiya haka ke kad'ai ba" amma Lahab baka gani akwai damuwa na barin gari yanda tsaro yayi yawa a kankan Nan"?karkiji kome goggoji Allah ya kaimu goben"ameen ta amsa,washe gari tun asuba Lahab Suka bar cikin gombe Kuma cikin hukuncin ubangiji Basu samu wani matsala a tafiyar tasu ba,haka zalika baibi takan Kiran da Majid keta danna Masa ba sosai suke ta shiga cikin kauyuka wasu kauyukan ma da machine suka shigesa kafun su Isa kauyen da zasu Saida Suka hau kuran shanu kafun Suka iso wani rugan Fulani. Zaune suke a gaban wani dattijo ne babba sosai tsohone ga farin gemun shi,Lahab da goggoji ne a gabansa a cikin bukkan sai Nnenna da aka shimfidar akan wani taburman kaba,magana ya Fara a hankali cikin nutsuwa yace"Alhamdulilah Ramatu naji dadi matuka da yanda Kika taimake wannan baiwar Allah Nan ba tare da kinsan wacece ita ba haka zalika Kai Lahab kayi matukar kokari Allah ya saka maka sannan ya kalli goggoji yanzun Ramatu inaso ki sanar dani menene ya faru da ita Koh Kuma me tayi ta Soma ciwon"a hankali goggoji ta rusuna tace abinci kawai na takura Mata taci"wani irine abincin"?shinkafa ne da Miya"a nutse yace dakwai nama a ciki"?gyada Kai tayi ganin haka yasa Lahab saurin cewa ai batacin nama"da mamaki goggoji tace Koh shiyasa Inna Bata abinci Mai nama sai takici amma Bata taba fadamin ba ranan ma nina matsamata taci bata gama hadewa ba abin ya faru. Mikewa tsohon yayi ya nufi Kan Nnenna masowa yayi sosai yasa hannu ya bude kofar idanunta"sai Kuma ya girgiza Kai tare da d'auko wani magani ya bude xamxam ya juye a ciki ya zuba magani Addu'a yayi sosai ya tofa sannan ya Kira goggoji taxo ta Kamata ya bude bakinta ya Soma zuba Mata maganin tana Sha wasu na zuba sai kawai sukaga ta zabura ta Mike ta Soma aman jini babu gaggautawa harda guda-guda sai Nishi take amai tayi bana Wasa ba,har lokacin idanunta a rufe komawa tayi ta kwanta shi Kuma ya mike ya d'auko magani ya kwaba da man shanu yace ta shafa Mata aduk Inda jijiyar ya fito,Dole tasa Lahab ya fita waje shida dattijon don jijjiyar daga fuskarta ya gangara har wuyanta har Kan kirjinta na hagu ya sauka har kafarta na hagu,fita sukayi goggoji ta gama shafa mata kafun Suka dawo gaushi aka kawo a kasko ya zuba magani a ciki maganin na turnuke dakin Nnenna ta Mike tana wani irin ihu da surutai da Sauri goggoji ta Fadi kasancewar tana da marabai,ya aike Lahab ya Kira wasu sukazo Suka fita da ita shi Kuma ya cigaba da fama da Nnenna Harya samu ta natsu sannan ta koma ta kwanta Lahab kam na bare a waje duk abin duniya ya damesa ya kasa nutsuwa yasan war haka ana neman sa. *************** Bayan sati d'aya Alhamdulilah jikin Nnenna yayi sauki sosai amma har yau Bata dawo hayyacinta ba gashi idanun nata yadan washe daga jini-jinin zuwa fari tass amma Bata tashi ba jinya dai ake Mata sosai goggoji ta koma cikin gombe tabar Lahab a kauyen su,duk sati faruq na zuwa ya dubasa sannn Yana kawo Masa labarin irin Neman sa da ake Kamar me,dayake garin babu Network Sam tsawon sati d'aya kenan isheshen bacci Lahab baya samu sosai,zaune yake a kusa da ita hannunsa d'auke da kwaryar no-no Wanda aka dama da magani,iba take a ludayi Yana sanya Mata a baki a hankali in Kuma ya gangaro sai ya dau tsumman gefensa ya goge mata Inda ya gangaran a haka ya samu tadan sha kad'an,sai Kuma yaga ta Soma tari sosai tana kwarewa mikewa yayi ya dagata zaune ya jinginar da ita take ta Soma kwarara amai sosai take aman bakikkirin, kaman bakin Mai sosai tayi aman duk ta bata jikinta ta bata Masa jiki babu kyankyami ya Kamata harta gama kafun a hankali ya maidata kwance ya mike yadau babban tsumma ya goge wajen ruwa ya ibo ya wanke abinda ta batan ya Shanya ya had'a da kayan jikinsa ya wanke kayan jikinta matar malam ne tazo ta canja Mata don malam yace haka zatayi tayi ta aman har sai ta dawo aman abinda tasha wato in tasha no-no tayi aman nono. A kallah Lahab yakai wata yanzun a kauyen Suna jinyar Nnenna Kamar kullum Yana zaune kusa da ita Qur'an ne a hannun sa Yana karanta mata,Kamar a mafarki yaga tana dan motsa hannunta Bai wani yi mamaki ba tunda dai ta Saba motse kawai dai Bata hayyacinta ne,sai Kuma yaga tana d'an bubbude idanunta harta budesu tar a hankali ta Soma magana Wanda yasa Lahab rufe Qur'an in ya matso kusa da kunnen ta Yana sauraron abinda take cewa Jin yanda take Kiran sunansa yasa sa damko hannunta jikinsa har rawa yake yake ce Mata"Nnenna ki kalleni ganinan kusa dake kinji Labiba"? Hawaye ne ya Soma bin kumatunta da Sauri tasa hannu ta daura a jikinsa tare da jingina a kafadunsa tana kuka take cewa Lahab bata gani ya Bata glass nata da Sauri ya mike tsaye Jin tace bata gani kuka ta fashe dashi itama ta Mike tsaye tana lulubar hannnun sa kamo hannun nata yayi da Sauri ta damke hannun har tana kokarin faduwa na rashin kuzari,kamota yayi Yana cewa ta koma ta zauna amma Ina tace karya tafi ya Barta Dan Allah karya sake barinta"shigowa malam yayi sai Kuma ya tsaya Yana kallon su kauda fuska yayi yace Lahab ya zauna,Zama Lahab yayi itama ta zauna tana rike Masa hannu sai Kuma tambayar da ta jefo Masa"Lahab inane muke waya shigo dakin Nan? bana kallo Lahab bana kallo fa?Ina goggoji ta Miki min glass nawa. Ki natsu shine amsar da malam ya Bata natsuwar tayi Lahab yadau wulan Fulani dake gefe ya aza Mata akai don gabaki d'aya gashin nata duk sun wargaje sunyi datti,kallon ta malamin yayi babu Wasa a fuskar sa yace"Zan tambaye ki Kuma Ina so ki ban amsa babu karya a ciki abinda Zaki cemin"jikinta har wani rawa take tasa hannu ta rike rigan Lahab da karfi ta gyada Masa Kai"ganin yanda ta rikice yasa Lahab sa hannu ya riko hannunta Yana dan Mata magana a hankali"ki natsu Mana babu abinda zai Miki kawai tambayar ki zaiyi fa"shuru tayi tana Jin abinda malam yake fada Mata. Koh Zaki sanar dani sunan ki"Sunana Nnenna obinna"ke wace kabila ce"a hankali tace Igbo"toh tambayar da Zan Miki yanzun shine menene halakarki da Mafi'a(secret code)"zaro Ido Lahab yayi sai Kuma yace"haba malam ya zaka..........d'aga Masa hannu malam yayi yace"karka kuskura na sake Jin bakinka a cikin tambayar da Zan Mata karka kuskura"shuru kawai Lahab yayi Nnenna Kam jikintane ya tsoma rawa a hankali ta Soma hawaye sai Kuma ta fashe da wani irin kuka ta koma da baya timmm kakeji ta yanke jiki ta Fadi tayi wani irin sandarewa"salati Lahab ya sake yayi Sauri ya matso gareta ya tallafo kanta Yana Kiran sunan ta amma shuru bata amsa masa ba. Mikewa malam yayi ya dauko wani magani yazo ya Shaka Mata a hanci saiga jini ya Fara bulbulowa Kamar bakin fanfo Kara Lahab ya sake Yana kuka yana cewa a taimaka Masa karta mutu"Kai ka kwantar da hankalin ka wannan jinin dake fita a jikinta warakane a gunta ka natsu sosai,natsuwa yayi aka maidata Kan shinfidar da ta tashi ,fita malam yayi yace Lahab ya biyo bayan sa bayan sunfita Zama yayi a kasan bishiyar tsakar gidan Zama yayi a gefen sa,magana malam ya Soma Masa Kamar haka"Lahab a gaskiya yarinyar Nan tana cikin gagarumin hatsari bana Wasa ba wanda in aka cigaba da hakan zata iya rasa ranta gabaki daya Dan soyayya ya Fara tasiri a zuciyarta. Waro Ido Lahab yayi yace"mutuwa fa kace malam dan Allah ka taimakamin kada ta mutu don Allah fa"tabbas Lahab zata iya mutuwa in ba dai wani ikon Allah ba muddin ba'a samu ta dawo hayyacinta ba hakan Kuma bazaiyu ba harsai ta samu wani muharraminta kusa da ita wato miji muddin aka d'aura Mata aure karfinta a kungiyar su zai raunana rauninta zaisa ta samu sassaucin ciwon da take ciki in ba haka ba naman daya wuce cikin tannan zai iya Zama ajalinta...................... *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 08084453785 tare da shaidan biyan ki* πŸ€ *By Ruqeenjalal* πŸ€ Waro Ido Lahab yayi yace"malam kana nufin bazata tashi ba sai an Mata aure"?gyada Kai malam yayi yace eh tabbas aure zai rage Mata hatsarin da take ciki, ya Kamata a Nemo Yan uwanta suxo asan abinyi,a hankali Lahab yace"gaskiya malam bansan Inda Yan uwanta suke ba Wanda na sanin ma yanzun nemanta suke ruwa ajallu"anan take yabawa mallam labarin haduwarta dashi sosai malam ya jinjinawa kokarin Lahab tare da Masa Nasiya akan bijirewa dokar da aka kafa musu a gida da yayi ya rage rashin jin magana"sannan daga karshe Lahab yace a daura Masa aure da ita"kallon sa malam yayi yace"gaskiya Lahab bazan iya hadaka aure da yarinyar Nan ba tare da izinin mahaifan kaba gudun Shiga hakkin su a matsayin su na iyaye zasu iyya tuhumata akan waliyin auren ka danayi bada izininsu ba. Hawaye Lahab ya share cikin alhini yace"yanzun malam sai a barta ta mutu kenan baza'a taimaka Mata ba dan Allah"za'a taimaka Mata Lahab,shine a Nemo iyayenta suzo da kansu kaga yarinyar Nan ba musulma bace auramaka ita sakaka a matsala za'a Yi kaga ita ma bada izininta ba da Sauri Lahab yace"dan Allah malam a daura Mana auren kaga iyayenta sun mutu haka akace a kotu Kuma Yan uwanta bana tunanin zasu taimaka Mata a yanzun"in ma maganar auren ne babu damuwa inta farfado sai na saketa ba shikenan ba in batason aure. Girgiza Kai kawai malam yayi Yana jinjina yarantan Lahab wato shi bai damu da abinda zaije ya dawo ba gaba gadi yake abinsa"kaga Hassan aure fa ba abin Wasa bane haka zaliki ba'a yinsa da niyar a sake,da kyakkyawar Niya ake da fatan raya sunnah manzon mu fiyayyen halitta dan haka karka sake furta saki da bakin ka"toh malam yanzun haka za'a rufe Ido dan Allah a barta ta mutu ka taimaka insha Allah babu abinda zai faru sai Alkhari" Lahab kayi kankanta da zaka d'auke wannan kasadar haka zalika Inka aureta Ina zaka nufa da ita daga Nan"?malam saura min Yan watan Ni nabar kasar Nan gabaki d'aya so nake mubari tare da ita insha Allah kafun na dawo kome zai daidaita Zan sanar da Yan uwana Kuma Ina da tabbacin zasu amince"dadin Baki sosai Lahab yayita ma malam shidai malam kallon sa kawai yake baice Masa kome ba haka zalika Bai nuna Masa ya amince da bukatarsa ba yadai zuba Masa Ido kawai Yana kallon sane kawai. Bayan kwana uku haryau malam baicewa Lahab kome ba shima Lahab Bai sake magana ba ana dai cigaba da jinyar ne har lokacin tana Nan Kamar gunkiya,yau tun safe Lahab yabi yaran dake tafiya kiwo sosai sukayita yawo da shanukai sai yamma likis Suka dawo cikin rugansu gabaki d'aya Lahab ya rame kowa ya gansa yasan a wahale yake daga abincin da yakeci ma ba cimarsa bane kwata-kwata d'add'aure shanukan sukayi sannan ya debi ruwa a kwalla yaje yayi wanka kayan Fulani wando da riga ya sanya sannan yazo ya zauna Yana cin tuwon da matar malam ta zuba Masa,babu abinda zaice musu sai godiya dan malam Koh sisi Bai karba ba na jinyar Nnenna haka zalika Suka juya Suna ciyar dashi. bayan sun dawo sallan isha'i malam ya kirasa cikin dakin sa bayan ya zauna malam ya Soma Masa magana cikin serious note yace"Hassan in Allah ya kaimu gobe juma'a bayan sallah za'a daura muku aure tare da yaran rugan mu da za'a daura musu gobe in Allah ya kaimu da rai da lafiya Zan daura auren Nan ne saboda halinda yarinyar Nan take ciki Kuma Naga alamun da gaske ne Bata da wani tsayaye haka zalika bai Kamata kaci gaba da Zama anan ba"wani irin fara'a ne ya karade fuskar lahab sosai ya Soma godiya Kamar bakin sa zai taba kasa"haka zalika zaka d'auki yarinyar Nan in taji sauki ka kaita gidan ku ka musu bayani"? da Sauri Lahab yace"wallahi malam gidan mu bazasu taba yarda da ita ba asalima sai an kaima hukuma ita"shikenan Lahab duk lokacin da kake bukatar sanar da gidan ku ka sanar dani zan tashi da kaina naje na Kara musu bayani"gyada Kai Lahab yayi cikin happy ya mike dakin da aka kwantar da Nnenna ya Shiga kwance take Kamar kullum matsowa yayi kusa da ita sosai yasa hannu ya janye gashin ta daya zubo ta gaban goshinta duk a hargitse hannunta ya Kama a hankali ya Soma Mata magana"Labiba in Allah ya kaimu gobe za'a daura Mana aure zamu dawo karkashin inuwar aure ki yafe min batare da Neman yardan kiba Ina Addu'an Allah yasa auren ya zame Mana Alkhari ya Zama silar warakarki"sai Kuma ya sake hannun nata tare da tofa Mata Addu'a ya fita a dakin. Washe garin da safe tun asuba ya Kama hanyar zuwa cikin local government in samun ya samu network aiko Yana shiga charge ya bada aka dan Masa zuwa takwas ya karba hade ta Kiran ade,Yana d'auka ya Soma Masa magana Kamar haka"innalilahi Lahab Ina ka shiga ka saka Yan gidan ku a cikin tashin hankali wasu nacewa anyi kidnapped naka wasu sukace Wai ka gudu a gida ne Lahab na koma asibitin Nan bakwanan naje gun goggoji na samu itama Bata Nan kwana na uku Ina sintiri sai a na hudun na sameta tace min wai itama bata San Inda ka shiga ba an turaku wani asibiti. gajiya Lahab yayi da surutun Adewale ya dakatar dashi"dan Allah Ade enough yanzun duk ba wannan ba so nake kaje gidan goggoji ku hadu da faruq ya rakoka kauyen da nake kace Nina kiraka kuzo tare don Allah kafun 2 na rana"tambayar sa dalili Ade zaiyi Lahab yace Masa urgent ne yayi gaggawan zuwa ya katse wayar sannan ya koma cikin rugan su malam. Bayan sallan juma'a jama'an rugan ne gabaki dayan su daga yara har Manya Amma maza zallah zazzaune a masallacin juma'ar Lahab na gefe da wasu yaran Fulani sanye yake da kayan da yazo garin dashi a wanke tass,bini bini Yana dube-dube Koh su Adewale sun iso Amma shuru,daura sure aka Soma daya bayan d'aya Saida aka daura na Mata biyu maza hudu kafun ya hangi Ade da faruq harda goggoji it'a goggo ta nufi hanyar gida sabani su faruq da Suka nufo masallacin sukaji ana cewa za'a daura auren Hassan waliyinsa ya matso su kwata-kwata Basu gane daurin auren wani Hassan ma ake ba,mikewa Lahab yayi ya kamo hannun Ade da bai gansa ba magana zai Masa ya nuna Masa yayi shiru kawai,jansa yayi Suka zauna faruk ma ya zauna a hankali Lahab yace Adewale aurena za'a daura yanzun"da mamaki Ade yace aurenka fa kace sai Kuma yayi shuru Jin an Fara daurin auren da Sauri Lahab ya baiwa faruq wayansa ya Masa vedio aiko take ya kusa cikin masallacin yaje Yana daukar daurin auren da ake. Bayan d'aurin aure jama'a sai zuwa suke Suna mikawa Lahab hannu ana Masa Allah tayasa riko duk faruq yana d'auka abinsa da Sauri Ade yazo ya fizge hannun Lahab ya matsa gefe dashi fuska babu walwala ya Soma magana"Lahab ka haukace ne Koh me?aure ka daura da yarinyar da baka sani ba Lahab ka lallata future naka,duk sonda nake ma mubeena a yanzun bazan iya auren ta a boye ba akan me zakayi haka Kai kana Nan kana shirme Yan uwanka nacan hankalin su a tashe"hannu Lahab yasa ya banbare hannun Adewale dake kwalar sa kafun yace"Ade bazan zuba Ido ta mutu ba haka zalika bazan gaji da taimakon taba Koh wani Hali na shiga sularta bana dana sani daga yau in bazaka taimakeni ba karka kuskura ka aibata ta bana so dan daga yanzun matata ce" Gyada Kai Ade yayi cikin zafin Rai ya juya yabar kauyen ransa a mugun bace Lahab Bai taba Masa abinda ya Masa zafi irin nayau ba iskancin Lahab bai zati yakai harga aure bada izinin magabata ba sai yau,Lahab Kam Koh a jikinsa duk da yaji babu dadi abinda Yama abokin sa haka zalika jikinsa yayi sanyi Wai shi Lahab yau shine Mai aure lallai ya yarda kome nufin Allah ne,haka ya wuni cikin zullumin,da daddare malam ya kirasa Allo ya basa da alkalami da tawada tare da addu'o'inda zai rubuta karba yayi ya Soma rubutun Kamar yanda malam yace shida kansa zai rubuta,Yana kammala rubutun malm ya sashi wankewa sannan ya Sasa d'aga kanta ya bata ruwan tasha, kana ya basa magangunan ya had'a a ruwan wanka hade da fita a dakin yace Lahab ya Mata wanka dashi Kuma ya tabbatar Koh Ina a jikinta ya samu maganin. Zama Lahab yayi ya tisa Nnenna a gaba Yama rasa ta Ina zai Fara hawaye ne ya cika Masa Ido a gaskiya Yana tausayin wannan baiwar Allah haka zalika baijin d'ar na kasancewar ta Yar Mafia ba,malam ne yazo bakin kofar ya tsaya hade da tambayar Lahab ya Fara ne Koh yana shashanci"uhmm gyaran murya yayi sannan yace yanzun Zan Fara malam"kaga Lahab kayi Sauri ba'a son dare yayi sosai bakayi Mata wankan Nan ba"?toh malam yace Yana nade hannun rigansa,hulan kanta ya zame a hankali gashin ta masu datti ya bayyana,hannun sa na Bari yasa ya zame Mata rigan jikinta rumtsa idanu yayi saiga hawaye Shar da ace lafiyarta klau Allah ne kadai yasan halinda zai shiga Amma dayake Bata da lafiya ne wallahi baiji kome ba sai tausayi,ruwan magani ya deba a hankali ya shafa Mata a Kai ya sake Iba ya shafa Mata a wuyanta da yayi fari tas Iba ya sakeyi a hankali ya watsa Mata akan kirjinta Wanda ke d'auke da manya manyan maman ta jajer dasu gasu a tsaye sunyi bulbul fresh dasu Kuma free ga lahab da Sauri ya rufe idanun sa ya Soma iban maganin Yana wankewa harda Kan cikinta da Sauri Kuma ya jingina da bangon dakin Yana matse kafafunsa jikinsa nason badashi ya kasa jure tabasu da yake da farko baijin kome da ganin su Amma fa ta wannan bangaren ya kasa. Jan jikinsa yayi ya sake matsowa jikinsa gabaki d'aya hankalinsa a tashe yake wallahi tun a Kan Kwabe rigama hankalinsa nason tashi,rufe idanunsa yayi kawai ya daure ya Soma kwara Mata a jiki a hankali yasa hannu zai kwance zanin jikinta Amma ya kasa kwance mad'aurin zanin Ido rufe dole tasa sa bude Ido a hankali Yana kakkauda fuska akan kirjinta hannu yasa yayi yayi ya kunce Abu ya gaggara abinka da zanin Fulani Kuma d'auri gangataran matan malam ta Mata runkofawa yayi a hankali yasa hakorinsa a madaurin zanin sai kiciniyar kuncewa yake, daker da tsudin goshi ya samu zanin Nan ya warwaro har had'a zufa yayi sharkaf warware zanin yayi Yana bin laps nata fari Tass fatar wajen har wani sheki yake gashi fresh dashi idanu ya zaro daidai saman maran ta ta sama ba kome bane sai wani tattoo da ya gani na hoton skeleton (danger) shafa tattoo in yayi a hankali Yana Kara bin abin da Ido Kaine sai katsushuwan kafa da akayi cross dashi. Lumshe idanunsa kawai yayi ya zare Mata pant in jikinta ya Soma Mata wankan Saida ya game jikinta da maganin tass kafun ya sanya Mata Sabon sutura duk idanunsa a rufe yake kome, gudun kada yaga abinda zai hanasa control na kansa yanzun in ma dauriyace kawai dagota yayi daga Kan taburman ya maidata Kan gado,ya kwantar tare da mikewa ya fita waje malam in ya Kira yazo ya basa no-no ya Bata Bata nonon yayi Mai magani"ka zauna a wajen ta ku kwana tare insha Allah zuwa can dare zata farfado saika Bata ruwan rubutun Nan tasha" amsa Lahab yayi Yana ta ma malam godiya. Zama Lahab yayi bayan fitar malam ya dau kur'ani Yana karanta Mata a hakan har bacci ya daukesa zaune rungume da kur'ani a hannu baima San bacci ya fizgesa ba can dare ya bude Ido da Sauri Jin kakkarin amai mikewa yayi ya kunna Kwan fitila dake gefen gadon, Nnenna ce ke ta amai kur'an ya aje Kamata yayi ya saukar da ita a gadon Karan ya dukar da ita tana ta amai Aman no-no ne fari tass tana gamawa ya dauko Mata butan dake dakin ta wanke bakinta a daren ya goge wajen hade da fidda abubuwan da ta Bata Koh kyankyami babu. Zaunar da ita yayi Yana Mata sannu gyada Masa Kai kawai take ya mike zai dauko rubutu da Sauri ta rike hannun sa, d'an murmushi yayi yace"ki kwantar da hankalin ki dare ne karkiji kome babu Inda zanje na barki gyada Masa Kai tayi ta koma ta kwanta shi Kam ruwan maganin ya d'auka yayi Bismillah ya kafa Mata a Baki sosai Tasha sannan ya janye ya maidata ya kwantar"Lahab meyasa ka yarda ka aure Ni ba tare da ka tuna abinda zai biyo baya ba"da mamaki yace"kina nufin kinsan abinda ya faru yau"?kwarai ma kuwa Lahab duk abinda ya faru Ina ji kawai bana iya sarrafa jikinane,Lahab kayi kasada a kaina da yawa Bai Kamata kayi wannan b......Bai Bari ta karasa ba yasa hannu ya rufe Mata Baki yana cewa"yanzun duk wannan surutun baida amfani burina shine ki samu lafiya haka zalika ki koma kallonki Kamar da wannan shine burina" Gyada Masa Kai tayi ta gyara kwanciyarta shima kwanciyar yayi a haka idanun su biyu dukan su har asuba, sallah Lahab ya fita a masallaci yake sanar da malam ta farka daga Nan dakin in Suka shigo dukan su lokacin tana kwance Kamar Mai bacci da sallama malam ya shigo dakin ya nemi waje ya zauna sannan ya Kira sunan ta shuru tayi Bata amsa Masa ba matsowa kusa da ita Lahab yayi ya leka fuskarta sannan ya kalli malam yace"malam tayi bacci"girgiza Kai Mal yayi yace"idanunta biyu ki mike kimin bayani sanann ki amsa min tambayata wannan shine Karo na biyu Kuma na karshe muddin Baki gayamin alakarki da Mafia ba zaku tattara ku bar gidan Nan Banga amfanin zamanki a ciki ba"? A hankali tasa hannu ta riko na Lahab gamgam ta rumtsa idanun ta da karfi kafun ta Soma magana"nice mataimakiyar shugaba a kungiyar mu haka zalika na kasance daya daga cikin su tun shekaruna bai..................................... *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 08084453785 tare da shaidan biyan ki* πŸ€ *By Ruqeenjalal* πŸ€ tun shekaruna bai kaiba amma wallahi ban taba Shan jinin dan Adam ba"wani kallo malam ya Mata babu Wasa yace"taya Zaki kasance cikin mabiyan Mafia Kuma kice min baki Shan jini"kuka ta Fara a hankali wani tsawa malam ya daka Mata ya Kara jefo Mata tambaya"nace ki min bayani menene alakarka da Mafia"?jikinta har rawa yake ta Soma magana"nima ban sani ba abinda na sani shine da Rana zanyi rayuwa a cikin Yan uwana mutane in dare yayi kuma na kwanta bacci sai na Kama rayuwa Kuma a cikin wasu mugayen mutane bansan yaushe na Shiga ba nadai San sunce Ni Yar uwarsu ce haka zalika sunce Ina da gadon mukami Mai girma a kungiya" Kina nufin kice min Baki San kome akan kasancewarki a cikin su ba"da Sauri tace wallahi malam bansan kome ba tun da nayi wayo in dare yayi na kwanta sai na halakci taro duk ranan lahadi haka zalika ansha kashe mutum asha jini a gabana amma Ni tunda nake ban taba Sha ba bansan ya ake Sha ba haka zalika ban taba kashe kowa ba"da mamaki Lahab yace taya zakice baki kashe kowa ba Kuma kina cikinsu ana kashewa a gabanki"?hannu malam ya d'aga Masa sannan ya kalle Nnenna"inaso ki fadamin wanene ke kiban labarin ki" dan kwantar da kanta tayi a kafadun Lahab tanajin wani irin ciwo a kirjinta a hankali ta Soma magana"Ni Karan kaina bansan wacece Ni ba abinda na sani kawai shine na tashi na tarar da papa na shine kome nawa yace mahaifiyata ta rasu tun Ina kankanuwa Ni ban ma santa ba Koh hotonta ban taba kallo ba,sannan kowa a kauyen mu guduna yake ana cewa Wai Ni mayya ce"malam tambaya ya Kara jefo Mata"meyasa ake ce Miki mayya"dan sunkuyar da kai tayi cikin zullumin tace"saboda duk lokacin da na Fadi mummunan Abu akan mutum sai ya faru dashi haka zalika Inka nemi cutar dani zaka mutu Wanda ni Banda wani masaniya akan mutuwar su"gyada Kai malam yayi sannan yace shin akwai wani abinda kike kiwo Koh dabban da kike tare dashi a gidan ku"? da d'an murmushin damuwa tace"eh Ina kiwon kule"yakai shekara nawa a hannun ki"kusan shekara goma"yanzun Ina yake"?nima ban sani ba malm tunda nabar gidan mu ban Kara kallon sa ba"toh Ina so daga yau Koh kin gansa karki d'aukesa haka zalika karki sake kiwon Koh wani dabba a yanzun har sai jikinki ya warke rass"toh malam mikewa yayi ya fita kallon ta Lahab yayi yasa hannu ya taba gashinta sannan yace"kanki yayi datti sosai Koh muje waje na wanke Miki tunda kinji sauki"? Gyada Masa Kai tayi ya Kama Mata hannu Suka mike,waje Suka fita ta zauna a gefe yaja ruwa ya dau babban kwarya yazo ya aje a bayan ta omo da matar malam ta basa ya jika ya saukar da Kan nata ya Soma wanke Mata, tass ya wanke Mata Kai sannan ya debo wani ruwan yakai Mata bandaki ya dauko Mata wani wankeken Kayanta ya makala Mata kafun ta fito wanka ya wanke Mata kayan data cire da nasa da Wanda ta bata duka ya Shanya matar malam sai tsokanarsa take Wai tun ba'a lale amarya ba an Zama mijin hajiya shidai sai dariya yake,bayan ta fitone ya Kama hannunta harkan shimfidar da ya Mata a waje, kwanciya tayi shi Kuma ya zauna a gefenta Suna dan Hira kad'an kad'an malam ne ya shigo gidan hannun sa d'auke da kaza mikewa Lahab yayi yace ya tashi ya gyara Kazan mikewa yayi matar malam ta tafasa ruwan zafi ta basa bai taba gyara kazaba sai yau haka yayita fama matar malam na tayasa Suka gyara Kazan ta daura Masa a wuta Yana daka tana hura wuta,malam ya kawo magani ya Basu Suka dafa dashi lumus Suka dafa Naman juyewa sukayi a kwano Suka kaiwa malam amma sai yace wa Lahab ya kaima Nnenna taci da mamaki Lahab yace"malam ka manta batacin nama"? Ka Kai mata nace Kuma ka tabbatar taci toh Lahab yace ya dau kwanon aje Mata yayi a gaba sannan yace ta Mike mikewar tayi yasa hannu ya yago Naman cinyar ya nufi bakinta dashi da Sauri ta rike Masa hannu tana girgiza Kai amma batayi magana ba"kici malam ne yace"?ba yanda ta iya haka ta amshi Naman cikin tsoro ta Soma taunawa tana rumtsa Ido tunda take a rayuwata Bata taba cin nama ba haka zalika ma batasan dandanon nashi ba sai yau kwata kwata sai taji Bai Mata ba Bai Mata Dadi ba ranan dataci shinkafa Mai miyar nama a gidan goggoji ciwonta ya tashi toh yafi Naman saukin rashin dadi"kauda fuska tayi tana yamutsa fuska sai Kuma amai ya biyo baya Aman Naman tayi na naman data ci sosai take amai Kamata yayi Saida ta Gama Aman kafun ta koma ta kwanta Naman ya tasa a gaba bai damu da maganin dake ciki ba ya cinye tass ya aje kwano. da malam ya tambaye sa taci,cewa yayi ita taci malam bai Kara magana ba tun kallo d'aya daya Masa, washe gari baru malam ya yanka aka sake dafa Mata da magani aka bata Nan ma taci tayi amai amma baikai na jiya ba akalla Saida akayi sati ana bawa Nnenna nama a hankali ta Fara daina Aman Kuma dandanon ya Fara Mata kad'an kad'an sai dai har gobe idanunta Basu budu ba,yau malam ya kirasu dukan su bayan sallan isha'i kallon Lahab yayi yace"ya Kamata ka koma gida Lahab Bai Kamata ka cigaba da Zama anan ba yanzun haka ana Neman wata biyu da wani Abu jikinta yayi sauki sai abinda baza'a rasa ba bazan iya cewa kome akan taba? dan Ni Karan kaina bazan iya cewa wani abuba tunda bansan gaskiyan lamarin taba abinda na sani kawai d'aya ne tana da alaka da Mafia haka zalika abinda ta fada gaskiya ne Kuma insha Allah wata Rana kome zai warware muku kafun Nan Ina so ka koma gida Zan baka maganin da zaka dinga diga Mata a Ido sai Kuma ya juya harshen fulatanci yaci gaba da magana don baison Nnenna taji"idanunta bazasu bude ba har sai ranan da kuka rabe juna a matsayin ma'aurata Kuma cikin tsigar shauki da sha'awar juna dukan ku dan haka bazan tilasta muku ba duk randa kuka ji zaku kasance da juna in Allah ya yarda kome zai daidai ta"sunkuyar da Kai Lahab yayi wani irin mugun kunya ya lullubesa itadai Nnenna sai Ido don bajin abinda suke fada take ba haka zalika hausar ma ba iyawa tayi ba duk abinda malam ke tambayarta cikin turanci yake Wanda Lahab yasha mamakin iya turancin malam Harya kasa hakuri ya tambaye matar malam anan take cemai babu Inda malam baya zuwa bada magani amma ada sai yanzun da tsufa ya kamasa kafun ya zauna waje d'aya,sosai malam ya musu Nasiya bana Wasa ba,ya hadasu da maganguna harda Wanda Lahab zaina yiwa kansa na wanka na hayaki harda nasha Dana digawa haka zalika yace duk abinda zai sake tashi suzo su sanar dashi godiya sosai Lahab ya ma malam cikin Jin Kewan rugan washe garin tun safe sukayi wanka sukabi gida gida Suna ma 'yan rugan sallama sabo tirken Wawa d'an wata biyun nan sosai Lahab ya Saba da jama'ar garin. ***************** tafiya suke akan keken Shanu daya d'aukosu daga cikin rugan jugudun Lahab yayi cikin damuwa da zullumi sai yanzun yake tsoron abinda zaije ya tarar a gida,saukesu akayi a wani kauye da zasu samu machine ya fito dasu cikin local government in Hawa sukayi sanan Lahab ya d'au wayarsa kunnawa yayi ganin network ya dawo ya bugawa Adewale amma bai d'auka ba Saida ya Masa kusan five miss call kafun ya d'auka baidai ce kome ba Lahab ne ya Soma magana"Ade Dan Allah Koh zaka shigo local government in Nan kazo k d'auke mu"a gatse Ade yace au baka San hanyar gidan bane Koh baka da kudi"?Dan sauke ajiyar zuciya yayi ya kalli Nnenna dake rike da hannun sa gangataran tamkar Wance akace zai gudu ya Barta yace"Adewale kasan Shiga gari da Nnenna tare dani akwai matsala ka dai zo dan Allah"katse wayar Ade yayi baice zaizo ba haka zalika baice baraizo ba. Mikewa Lahab yayi ya dago Nnenna da niyar su shiga mota kawai koma mezai faru ya faru tunda yanzun har yamma yayi Suna tsallaka titi ya hango Adewale ya bude marfin mota ya fito karasawa yayi kusa da Aden Yana rike da hannun Nnenna kallo daya Ade ya Masa sai kuma ya kauda fuskar sa,Lahab baiyi zuciya ba yana rike da hannun Nnenna ya bude bayan mota ya sata kana ya bude gaba shima ya shiga ya rufe bai cewa Ade kome ba Ade bude kofar yayi shima ya shiga kawai yaja motar Suka Lula dan juyawa yayi Suka had'a Ido da Lahab murmushi Lahab yayi yace Adewale kanajin haushi na Koh"?girgiza Kai Ade yayi yace"akan me xanji haushin ka Kuma bayan abinda kaga dama kake"haba Ade ka juya kaga halinda yarinyar Nan take ciki yaci a tausaya mata" Ade dai baice kome ba tafiya Suka cigaba dayi cikin hukuncin Allah har Suka Shiga gombe ba'a gane Nnenna ba kwata kwata saboda shigar Fulani dake jikinta ga gashinta da kitson dake kanta, parking Ade yayi Kamar yanda Lahab yace tunda Suka nufo cikin tsakar gari sauka yayi tare da cewa Ade yakai Nnenna gidan goggoji Jin hakan yasa Nnenna kiransa da Sauri bude kofar yayi ya shiga ya Soma Mata magana a hankali cikin lallama"Kinga ki bisa kuje gidan goggoji Ni gidan mu zan nufa Kuma Banda tabbacin zamu gana Nan kusa ki kula da kanki Allah ya Baki lafiya magani na Booth"gyada Masa Kai kawai tayi hawaye na taruwa a idanunta,Ade Kam Jan motar yayi baice kome ba. Lahab tunda ya tare machine ya shiga ya nufi unguwan su zuciyarsa ta Soma bugawa wallahi baisan amsar da zai Basu gamshashiya ba akan Inda ya Shiga gashi bayason musu karya Koh kad'an a hankali ya sauka a keken Yana bin kofar gidan nasu da Ido kudi ya baiwa Mai keken a hankali ya nufi kofar hannu yasa ya kwankwasa sai Kuma ya tsaya Jin muryar Mai gadi na cewa wanene Yana bude kofar sai Kuma ya tsaya Yana kallon Lahab da kayan jikinsa sai Kuma yayi shuru kwata kwata yanda Lahab ya fige Bai Masa kama da Rahab Inda ya gani d'azun a cikin gida ba da Sauri yace Lahab? Murmushi Lahab yayi ya gyada Masa Kai aiko da Sauri ya bude kofar ya Soma salati cikin Al'ajabi ya ruga cikin gidan da gudu Yana kwalama Abbu kira da iya karfinsa Lahab Kam binsa yayi a baya a hankali,Yana tura kofar ya dan tsaya ganin kattafanin jama'ar gidan su a tsaye Suna jiran karasowar su don Mai gadi tuni ya kusa ya tsaigunta musu sunkuyar da Kai yayi lokacin da yayi Ido hudu da Abbu bawan Allah har wani Rama yayi na rashin amanar sa,da gudu Rahab ya tawo yazo ya rungume dan uwan nasa dan dukawa Lahab yayi a hankali ya Kara makale dan uwan nasa da karfi kowa yaga kaunar Nan yasan na sakanin jini da jini ne,da Sauri ya sakesa Jin Addayiya na salati fitowarta kenan daga dakin ta hannunta rda canula. Kuka ta fashe dashi ganin Lahab a hankali ta Soma takawa tana nufo su da Sauri Lahab ya mike ya nufeta fadawa kawai yayi a jikinta ya sake kuka Wanda shima baisan kukan menene ba,zazzaune suke sun tasa Lahab a gaba tun ana lallaman sa ya fad'a musu Inda ya shiga har ran muzammil ya baci Wanda zuwan sa kenan yau don B'atan Lahab in tun ana daukar Wasa Abu ya Zama gaskiya sannan anzo ana Masa tambaya ya mannawa mutane hauka mikewa yayi Rai bace Yana zare bell in jikinsa ya Soma magana"wallahi Lahab inka kuskura ka batamin Rai jikinka ne zai gaya maka dan iska kawai"da Sauri Abbu ya d'aga Masa hannu tare da cewa kada Wanda ya sake tambayar sa Inda yaje duniya ce duk abinda ka shuka shi zaka girba sudai sunyi iya bakin kokarin su a kansa duk Wanda ya zagesu Allah ya Isa sai Kuma yace daga yau Kar Wanda ya sake tambayar Lahab Ina zashi duk Inda yaga dama yaje duk lokacin da yaso ya dawo Yana karasa maganar Rai bace ya mike yabar falon da d'add'aya kowa ya watse don Abbu baiya fushi amma in yayi abin Baya kyau Sam. Zama Lahab yayi akan katifarsa lokacin da ya Shiga dakin nasu lumshe Ido yayi rabonsa da ganin haske haka Harya manta sai Kuma ya mike ya shiga wanka wanka yayi sosai ya kimtsa jikinsa cikin kayan baccin sa wando da riga kwanciya yayi ya lumshe idanun sa,turo kofar dakin akayi Addayiya ce d'auke da plate na abinci sai drink's mikewa yayi da Sauri ya karbi plate in ya aje a gefe itama Zama tayi tasa hannu ta shafa kansa a hankali ta Soma magana"Lahab Sam banji dadin abinda kayi ba ka d'aga Mana hankali haka zalika kasa mu a damuwa karka Kara Mana irin haka Kamar yanda yayan ka yace karmu sake tambayar ka bazan tambaye kaba amma dan Allah karka sake irin wannan?gyada kansa yayi ya kwantar da kansa a cinyarta hawaye na taruwa a idanun sa hannu tasa ta dauko abincin ta bude tare da d'aga kansa tana cewa ya tashi yaci ba musu ya karbi plate in ya Soma cin abincin daya Dade baici ba. tunda ya kwanta yake juye juye Sam ya kasa bacci tunanin matar sa yake"Lahab yaji Rahab dake katifar sa ya kirasa"amsawa yayi tare da mikewa zaune shima Rahab mikewa yayi ya ce"bakayi bacci ba har yanzun"eh banjin bacci ne dan uwa"uhmmm kasan me"ah ah saika fada"Abbu ya Mana registration na weac da neco insha Allah zuwa next week za'a Fara waro Ido Lahab yayi yace kana nufin yanzun an rufe biya kenan"?kwarai ma kuwa. Rumtsa Ido Lahab yayi yaci burin ya biyawa Nnenna duk da Bata kallo sai ya bada a Mata duk da yasan hakan prohibited ne a exam,komawa yayi ya kwanta Rahab ma kwanciyarsa yayi Bai Kara cewa kome ba ba,a cikin kwanakin Nan da Lahab yayi babu Wanda ya Kara tambayar sa Inda yaje Mami ma batazo ba shima ya kasa zuwa wajen ta saboda tsoro gashi yau satin sa daya ya muzammil ma ya koma a yau Suka Fara jarabawar neco babu Wanda ya sanar dashi zancen jarabawar Koh yaje yayi sai Rahab don yanzun Abbu baya Masa magana Koh gaidashi yayi baya amsa wa,sun cigaba da zuwa school harda Adewale Nabeel ma duka Yana zuwa duk da Lahab baisan waya biya Masa kudi ba yadai ganshi shima a hall Kuma ya tambaye sa Inda ya shiga sharesa kawai Lahab yayi Bai ce Masa kome ba Kuma sosai yaji ya Kara son Ade watoh duk da sun samu rashin jituwa akan Nnenna amma babu Wanda ya sanar wa da labarin auren sa. Kamar kullum yau sun tashi jarabawar har yamma Suna fitowa lahab ya dan kalli Adewale ganin Nabeel hankalin sa baya kansu yasa sa kama hannun sa Suka zagaya bayan exam Hall shidai Ade Ido kawai yake binsa dashi Jin abinda yace"dan Allah so nake ka daukomin Nnenna ka kaimin ita garden City mu hadu a acan bayan mangariba dan Allah"wani kallo Ade ya Masa kafun yace"Kai me yasa bazaka je ka dauketa ba?kaga Lahab ka daina Sakani a shirgen ka da yarinyar Nan fa bana so" Kawa Allah kayi hakuri Ade kasan Abbu yace naje duk Inda Naga dama ya cire security na gidan mu Amma abinda na gano wallahi yasa ana bibiyata duk Inda na shiga muddin aka ganni naje gidan goggoji za'a sawa zuwan ayar tambaya"shuru Ade yayi sai Kuma yayi tsaki ya juya yabar wajen murmushi Lahab yayi ya shafa kansa sannan yabi bayan abokin nasa, Nabeel ya hango tsaye Yana dubasu ganin su yasa sa matsowa kusa dasu yana cewa "muje gidan mu ka gaida Inna duk ta damu a kanka ga Adda mubeeena kamma ba'a magana"girgiza Kai Lahab yayi yace"kayi hakuri Nabeel bana fita tunda na dawo amma in Allah yasa muka gama exam lafiya zanje. Ba kome shine abinda Nabeel yace Yabi bayan Ade Suka bar school in Lahab Kam gida ya koma wanka yayi ya tafi sallan mangariba daga Nan wani mall ya wuce sayyayyan Kaya ya Mata sosai ya had'a da kayan ciye ciye laida guda daidai ya fita a mall in ana Kiran isha'i tsayawa yayi yayi sallah kafun ya nufi wani tukuban nama yasai kaza sukutum guda biyu Keke napep ya hau Yana kallon motar dake binsa a baya tsaida keken yayi a kafar wani gida ya bude gidan ya shiga suturan jikinsa ya Kwabe yasa wani sabo daya saya sanin da yayiwa gidan Mai kofa biyu ne irin gidan Nan guda biyu da ake musu kofa a katangan tsakiya bude daya kofar yayi ya fita abinsa ta wani layi ma ya fito Yana dan dube dube ya tare Keke sai garden City. Yadan jima kad'an kafun Adewale Suka karaso rike yake da hannun Nnenna had'a fuska Lahab yayi Yana kallon hannun har Ade ya karaso,cikin masifa ya Soma magana"wannan wani irin Abune ya zaka rike Mata hannu"?da dariya a fuskar sa duk da baison Yi amma wallahi Lahab ya basa yace"idan ban rike Mata hannu ba Lahab Ina Zan rike gani nayi Bata amfani da Sanda Kuma haka zalika bazan barta haka ba Koh ya kake so nayi maka ne Wai"hararan sa yayi ya fizge hannun ta ana Ade ya rike Yana magana kasa kasa Yana cewa matar aure zai rike kaza kaza shidai Ade wani table ya nema ya zauna nesa dasu ya zaro wayarsa Yana dannawa. Zaunar da ita yayi akan dardumar daya shimfida musu a kasa Yana bin kayan jikinta da Ido kayan ya kode sosai,gaidashi tayi ya amsa Yana cewa"Labiba kiyi hakuri ki Kara hakuri da jarabawar ki Allah ya bamu ikon cinyewa kinji"amsa Masa tayi da toh kana ya bude laidan Kazan,Naman ya yago yasa Mata a baki bude bakin tayi ta amsa ta Soma ci,ya Kuma dauko hanken ya goge Mata gefen bakinta sannan ya sake yago wani Naman Yana Kai Mata Baki daidai lokacin yaji tsayuwar mutum a kansa da Sauri ya d'aga Kan nasa sai Kuma ya zaro Ido cikin mamaki Wanda ya gani agun............................ *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 08084453785 tare da shaidan biyan ki* πŸ€ *By Ruqeenjalal* πŸ€ Farida murmushi tayi tace lallai ma Lahab Ni ka shekemin tawa soyayyar Kai Kuma kana raya taka Koh? sai Kuma ta gyada Kai tare dayin kwafa tabar wajen binta yayi da Ido harta mule kafun ya maida kansa ga Nnenna data jefo Masa tambaya "Wai wacece?shuru yayi Yana daukar drink ya kafa Mata a Baki kin bude bakin tayi ta rufe sa gangataran d'an dakatawa yayi Yana kallon ta da mamaki yace"bazaki karbi juice in ba"?nace maka wacece"?dariya ya Soma cikin dakewa yace "kishi Koh"? babu wani kishi kawai dai naji yanayin da tayi magana Kamar tana Jin haushin Kane duk da ba yarenku nakeji sosai ba"ba kome shine abinda yace Mata sannan ya Kara da cewa"Nnenna mun Fara exam naso na biya Miki amma Allah baiyi ba"ba kome Lahab hakama na gode matukar babu abinda zance maka sai godiya kamin goma Sha akan wannan basai ka ce kome ba"amma naso na biya Miki wallahi"dariya ta danyi tace toh Inka biyamin ka fadamin da wani idon zanyi exam"?kamo wani hiran yayi sukayita Hira har Saida Ade ya gaji da Zama ganin 10 na dare yayi yazo yace ma Nnenna ta tashi su tafi,kayan Lahab ya bata da sauran tarkacen Ade ya d'auke sai gidan goggoji. Lahab bai koma gida ba sai kusan 10:30 na dare babu Wanda yace Masa kalallahu haka ya shiga ya kwanta,sannu sannu kwana nesa su Lahab harsun kammala exam nasu Suna jiran result har yau Lahab baije gidan su mubeena ba Kuma bai hadu da itaba haka zalika bai yarda yaje wajen Mami ba in ma yaji tazo baya fita nukuwa yake a daki harta tafi sosai yake Jin shakkar haduwar tasa da ita dan baida amsar da zai bata,duk lokacin da take son kallon Nnenna Yana rokon Ade ya d'auko Masa ita, in Kuma yaji Yana son Jin muryarta wayar goggoji yake Kira ta hadasu sosai soyayya Mai zafi da tsafta ya shiga tsakanin su daidai da rana daya Lahab bai tabajin dana sanin tarayyar su da Nnenna ba Yana sonta bana Wasa ba duk da kalaman soyayya har yanzun bai shiga tsakanin su ba Amma akace labarin zuciya a tambaye fuska. Abbu ya kirasu yace su ukun Nan su fada Masa school Inda suke son shiga a abroad uzaifa ya kammala degree insa a gombe zai Kama Master's shima a abroad Abbu yace su nemi kasa d'aya takamemme, Rahab yace India shi Kuma uzaifa yace Canada shidai Lahab shuru yayi Yana jinsu Suna da CeCe kuce har Abbu ya gaji yace suyi applying na school biyu duk Wanda akayi accept nasa shiken,Aiko Lahab yaji dadin zabi biyun Nan duk da baiyi magana ba ya rasa ya zaiyi da ransa wallahi baison tafiya yabar Nnenna gashi result nasu yayi kyau gabaki dayan su harda Ade,wanka yayi ya fita a gidan directly gidan su Ade ya shiga da yake yau lahadi ne iyayen sa Suna church,zaune ya samu Ade a falo Yana karyawa Zama yayi Suka Soma magana"ah yanzun Lahab bakajin kome ne Wai kayi aure gidan ku basu sani ba Kuma Koh a jikinta"? d'aga kafada Lahab yayi yace"nikam Koh a jikina wallahi yanzun ma duk ba wannan ne ya dameni ba"da mamaki Ade yace wata sabowa meya sameka Kuma"?badai Akan matsalar yarinyar Nan Bako?dariya Lahab yayi yace"wallahi kasamin Ido na rantse da Allah toh akanta ne"?hararansa Ade yayi yace zaka mutu akan ta wallahi"in mutun Mana Ina ruwan ka"babu ruwana Kam Lahab Ashe na manta"in serious Lahab yace"ya maganan makarantan mune Wani kasa ka zaba"?dan shuru Ade yayi sannan yace "Kai wanne kake so?na bar maka zabi "yace yana jiran yaji me Lahab zaice"tunani ya shiga kafun yace Ina son zuwa University of Canada Koh Kuma London a cikin biyun Nan nake son daya Rahab yace India uzaifa yace Canada zashi Ni Kuma banida burin tafiya school dasu dukansu biyu nafison na tafi da Nnenna abroad bana tunanin Zan iya barinta a kasar Nan bansan halinda zata shiga ba bayan babu Ni"wani banzan kallo Ade ya Masa kana yace kana nufin kacemin wai da yarinyar Nan zaka bar kasan Nan Ina ka samu kudin da zaka biya Mata kudin jirgima bare na tafiya"? Balance Lahab yayi yace"wallahi Ni Karan kaina na rasa Ina Zan samu kudi ban damu da kudin kome ba irin jirgin da Zan biya Mata shine na yanke shawara Koh zanje na samu Abbu a cikin kudin gadona yaban million daya"da Sauri Ade ya mike cikin masifa yace amma wallahi da zakayi haka kaf duniya babu Wanda ya kaika rashin ta Ido, mutumin da tun kuna yara har kawo yau da kudinsa yake d'aukar d'awainiyar ka bazakaji kunyar tambayar sa gadonka a yanzun ba? wallahi kaban mamaki kabi a hankali Lahab kada makauniyar soyayya ta kaika ta baroka a banza"shuru Lahab yayi har Ade ya Gama masifar sa ya koma ya zauna Yana huci sanan yace toh Ade ya zanyi yanzun dan Allah dai?kawai ka barta anan mu tafi karatun mu shine kawai magana"amma Ade a halinda take cikin Nan tana bukatar kulawa na musamman duk da nasan goggoji zata riketa Amana harna dawo, amma duk da hakan ma gaskiya banjin Zan iyya barinta"da haushi Ade yace toh saikayita fama Allah ya baka sa'a sannan ya mike yabarwa Lahab falon gabaki daya,mikewa Lahab shima yayi ya wuce gida. Washe garin da safe saiga Adewale yazo wajen Lahab shidai Lahab baice kome ba,wuri Ade ya nema ya zauna kafun yace"nama papa maganan Inda nake son karatu kasan abin mamaki ashe Wai yasa an Masa bincike anji xaku tafi India karatu shine yace na xabi Koh Ina amma Banda India"hhhh dariya kawai Lahab yayi yace shikenan saimu wuce London"gyada Kai Ade yayi yace gaskiya Lahab bai Kamata mu tafi mubar Nabeel ba kasan shi har jamb yayi baici ba kasan abin sa'a ne"d'aga kafad'a Lahab yayi irin I don't care innan yace,"kaga yanzun ta kaina nake bata wani Nabeel ba abinda muka Masa a baya Allah ya saka Mana amma yanzun bazan iya ba in kaga zaka iya Bismillah kayi" Da lallama Ade yace,haba Lahab gaskiya hakan bai dace ba tare fa muka tashi Kuma kome muka saya sai mun raba tare,da masifa Lahab yace"Wai gidan uban wa Zan samu kudin da Zan biya Masa karatu a London Harya gama ne kanaga kudin da Zan biyawa matata ma bandashi kudin jirgi kawai"da mugun mamaki Ade ke kallon sa Yana mamakin Al'amarin Lahab Baki a ciki bako Jin kunya Wai matansa,ai sai yanzun na ganoka watoh tunda Nabeel yace ya tsani Nnenna Naga gabaki d'aya ka chanja Masa wallahi wata rana har tambaya ta yake Mini, Wai ya kasa gane kanka kwata-kwata yanzun baka shiga shirgin sa"tsaki Lahab yayi baice kome ba Ade ya Kara cewa"Wai Lahab nace Koh zaka ma Abbu magana Koh zai dau nauyin Nabeel kasan Ni Koh hauka nake bazan Fara gayawa papa haka ba,kaga inya yarda Ina da dan million daya a account nawa saina biya Masa Koh kudin flight ne"wani harara Lahab yake ma Ade cikin harzuka yace"Kai Ade kaje Kama Abbu da kanka karka sake cewa na roke kowa kudi babu ruwana an maidani wani dan iska kome Ni ai abbun yafini sanin abinda ya dace in yaga zai iya biyamar ya biyamasa in yaga bazai iya ba bazansa bakina ba"karshe dai haka Ade ya hakura da maganar Nabeel. After few weeks Lahab ya samu gurbin karatu a London shida Ade amma ba tare da ya fadawa kowa ga kasar da yayi applying ba har Saida yaji Rahab nacewa Abbu zai musu visa kowa ya kawo passport NASA abin mamaki Bai gama kashe Yan gidan ba Saida Lahab yace shi a London ya samu makaranta da mamaki Rahab yace kana nufin ba India zamu ba kenan ranan na tambaye ka kace wajen zaka har uzaifa ya hakura shima ya nemi Nan?Lahab shuru yayi baiyi magana ba Abbu Kam sai kallon sa yake Ido cikin Ido da Sauri Lahab ya sunkuyar da Kai"kai dawa zaku London in"?Abbu da Adewale ne"gyada Kai Abbu yayi baice kome ba sai nuna Masa da yayi ya aje passport in,Aiko take Rahab ya dire yace shima sai London Saida Abbu ya nuna Masa jan Ido kafun ya hakura amma ya zage Lahab Kam iya zagi ya kirasa munafuki duka Lahab Bai kulasa ba dan yasan bai kyautawa dan uwan nasa ba dan tunda Suka tashi sutura wannan Rahab yafison yasa irin NASA shine ke kin yarda suyi anko haka ma makwanci da Lahab baya bacci sai ya Mannu dashi daga baya ne Lahab ya ringa gudun sa har Suka raba shimfida. Alhamdulilah su Lahab visa insu ya fito saidai su Rahab zasu riga su Lahab tafiya tun saura sati su Rahab su tafi gabaki d'aya ya birkice yace ya fasa tafiyar shi bazai tafi yabar Lahab ba daker aka samu ya natsuwa amma haka kawai inya zauna sai kaga ya buga tagumi ya Fara tunani Wasa Wasa ya Soma ciwo yau ciwon Kai gobe zazzabi kullum Yana like da Lahab Dole aka d'aga tafiyar tasu har yaji sauki,yau saura kwana uku tafiyar su Rahab Lahab Kuma sai Nan da sati daya,wanka sukayi tun safe yau Kaya iri daya Lahab ya yarda Suka saka jamfa da wando yau harda hula,motar Shareef Lahab ya karya su uku harda uzaifa Suka shiga Suka Soma bin gidan Yan uwa Suna musu sallama, lokacin da sukaje gidan ya jafar 100k ya baiwa Koh wannen su nanne ma ta dan Basu wani Abu daga Nan gidana Anwar Suka biya sun samu Aisha na fama da laulayin ciki Anwar ma ya basu kudi har 30k Koh wanne suka Masa godiya daga Nan Suka ringa yawon sai kusan yamma Suka Isa gidan Mami. tunda Suka shigo da Lahab ya gaidata Bata Kara bi ta kansa ba sai Hira take da uzaifa da Rahab sun dan Jima a gidan lokacin da sukazo tafiya, ta saidasu ciki ta shiga sai gata ta dawo da laida manya manya biyu ta mikawa uzaifa daya daya ta mikawa Rahab tana cewa zata zo ranan da zasu tafin insha Allah godiya Suka Mata sai Kuma Rahab ya kasa hakuri yace Mami Ina na Lahab wani mugun kallo data Masa Bai sake cewa kome ba Suka bar gidan haka Suka ringa yawon gidan Yan uwa sai goshin mangariba Suka nufo gida har sun wuce kofar su Nabeel da Sauri Rahab yace Lahab dan dakata Bara na shiga gidan Inna na Mata sallama rabona da gidan su bazan iya tunawa ba?ba musu Lahab ya tsaya dukansu Suka fito a motar cikin gidan Suka shiga da sallama. Amsawa Nabeel dake zaune Yana wanki yayi tare da mikewa ganin su dukansu inna ma fitowa tayi Suka zauna ana gaggaisawa Lahab ne ya kalli Inna yace"Inna daman zamu tafi karatu abroad ne shine mukazo mu muku sallama"waro Ido Inna tayi tace inane abmro Kuma"?dan murmushi yake Nabeel yayi yace Inna kasar waje,da Sauri yace ah ah ikon Allah haba shiyasa naganku dukan ku rabona da Rahab yazo gidan Nan harna manta sai yau"murmushi sukayi tare ana ta Hira duk da su Inna ba wani gane Rahab da Lahab sukayi ba kasa hakuri Nabeel yayi yace"daman Ashe zaku bar nageria amma Ade bai fadamin ba"kauda fuska Lahab yayi baice kome ba yasan so Nabeel yake ya gane sa a tsakanin su sai Rahab ne yace"eh wallahi xamu tafi mu gata zamu tafi Lahab da Ade sai next week"gyada Kai Nabeel yayi,mikewa Lahab yayi suma su uzaifa Suka mike Suna ma Inna sallama tsaidasu tayi tace Bara ta Basu kudi ba yawa kin karba sukayi amma Inna tace sai sun karba 150 ta Basu Wai kowa 50 hamsin sannan Nabeel ya rakasu kasa hakuri Lahab yayi ya tambaye sa mubeena yake ce Masa Bata Nan ta tafi makaranta. Sauka Lahab yayi yace su Rahab su koma akwai wani gidan abokin sa da zaije,Suna wucewa yad'au wayar sa ya Kira faruq akan ya kawo Masa Nnenna,ya Masa kwatancen restaurant da zaizo,zaune yake akan table in an musu ordern abinci Kamar ance ya d'aga kansa ya hangota sanye cikin hijab har kasa Mai hannu fuskarta d'auke da glass Baki wallahi ba karamin kyau ta Masa ba faruq na rike da hannunta Suka karaso ciki hannu Lahab ya d'aga musu,sanann ya mike Suna karasowa ya Kamata ya aje a kusa dashi faruq kin Zama yayi yace zaije ya dawo Yana barin restaurant in cikin alhini Lahab ya kamo hannun Nnenna yace"Labiba"na'am ta amsa masa a hankali"Labiba Zan tafi"da mamaki tace Ina zakaje ya d'aga isowata kace wani zaka tafi"? Labiba ba irin tafiyar Nan bane dana Saba Zan tafi karatu wani kasa"hannu tasa ta zare glass Inda ke fuskarta saiga hawaye Shar da Sauri yasa hannu Yana share Mata hawaye Yana cewa"bazan wani Jima ba zanna dawowa hutu karki damu kinji"?yanzun kana nufin saina Jima kafun na Kara ganinka"ya zanyi Labiba nayi-nayi kokarina na ganin muntafi tare amma bani da halin haka Koh bashi da kudi Zan karba nasan babu Mai bani bashi"a hankali yace kudine zai Hana mu tafi kenan?kanason tafiya dani"?da Sauri yace sosai ma"d'an shuru tayi tana tunanin wani Abu,da Sauri yasa hannu ya zare tagumin dake fuskar ta Yana cewa"tunanin me kike"da Sauri tace in kanason zuwa dani Zan iyya biyawa kaina kudin jirgi............................. *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 08084453785 tare da shaidan biyan ki* πŸ€ *By Ruqeenjalal* πŸ€ *BUZHUWA EmphireπŸͺπŸͺ* Assalamu Alaikum,Barkanmu da wannan lokacin ,Sannun mu da shigowa Halarar mu na buzaye.... Albishirin ku matan AureπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ BUZUWA EMPIRE ta taho maku da sirrika na MALLAKAR mijin ki yar uwa a hannun ki ba tare da boka ko malam ba. Matan da yawa na fuskatan matsalolin su da maxajen wato kalubalen a gidan auren mu...kuma irin wannan maganin matan Asha tabaje...mene wani shirme wani gayinan dai ,bashi ne ba... Ina macen da daga zarar mai gida yy sallama gaban ki keda yara ya hau fadi?. Ina macen da mijin ta kullum idanun shi na akan matan banxa?. Ina macen da ga kudin mijin yanada amma babu ci sai dai duniya suci yy kyautan riya? Kai duk wani matsalan ki na gidan Aure kizo taskar BUZUWA EMPIRE. zata baki mallaka ta hanyar sirorin kur'ani da dai sauransu. Mallaka ta hanyar kwai Mallaka ta hanyar nama ,madara ,kifi , yan shila da dai sauran su.. Ga kuma mallaka ta hanyar suratul yusuf . Mallaka ta hanyar jauhara. Mallaka ta hanyar Yaseen Mallaka ta hanyar fatiha umul qur'an. Mallaka ta hanyar turaruka da dai sauran su... Ina Yammata marasa farin jini ?πŸ’ƒ Kuzo kuma da naku ,sai kaji ana gata mummuna baka kirin amma sai farin jinin manyan alhajazai masu jifa jifai kome take dashi oho..!! Kuji ita tasan inda tazo ta taho taskar BUZUWA EMPIRE . sai kin taho yar uwa gaba daya sirrin nan na farin jini dana mallaka 5k ne duka . Idan kuma mallaka ne kadai munayin na 2k da kuma 3k. Na farin jini kacal 3k ne ,gamasu bukata zasu tuntu6a wannan number 08081202932 09061466409 Ina Zaki samu kudin jirgi kinsan nawane kuwa"?gyada Kai tayi a hankali tace"akwai Wanda na aje kudina a wajen sa"had'a fuska yayi Jin tace wani Wai Kuma ta aje kudi a wajen sa"ganin yanda yasha mur sai taji jikinta yayi sanyi a hankali tace"toh shikenan na hakura da tafiyar hararanta yayi yace"toh wa Kika baiwa kudin Kuma a Ina Kika samu kudin da Kika aje"labarin shu'aibu da haduwar su harma da Alkharin da aka Mata na 500k shuru Lahab yayi sannan yace Zaki iya gane unguwan Kuwa"?Koh sunan sa tunda Baki gani"?murmushi tayi anan take sanar dashi sunan unguwan mikewa yayi faruq ma ya mike tsaye kallon sa Lahab yayi yace"ka maidata gida Ni akwai Inda zani". Unguwan su shu'aibu Lahab ya wuce daker da kwatance ya gane gidan shayibu bayan yayi sallama Nan wani mutum ya fito yake sanar dashi ai shayibu ya Jima da barin gidan yanzun yayi kudi yana wani unguwa Alfarma Lahab ya nema mutumin ya had'asa da yaron da zai kaisa gidan shu'aibu,Suna Isa kofar gida kwankwasa kofar sukayi maigadi ya leko tare da tambayar su wa suke nema Mai gidan Lahab ya bukaci Gani ba musu ya barsu Suka shiga,zaune Lahab yake a falon gidan yakai kusan minutes Sha biyar kafun wani matashin magidanci ya fito da fara'arsa Zama yayi Suka gaisa da Lahab Yana tambayar sa Bai gane sa ba anan Lahab ke sanar dashi labarin Nnenna da kudinta da zai karba a hannun sa,cikin bakin ciki shu'aibu yace,eh wallahi yaji duk abinda ya faru Kuma ya tausaya wa Nnenna, ya Kuma yiwa Lahab Alkawarin zai basa kudin Nnenna ya Kai Mata haka zalika a Aljuhunsa zai biya Mata kudin jirgi don ba karamin business yanzun yake ba account numbern Lahab ya karba a take ya tura Masa 500k cib da Nnenna ta basa rance yad'au 200k ya aje Mata 300k,amma ya had'a duka ya bata lokacin da Lahab ya Soma zancen kudin sunyi yawa shayibu yace babu abinda zai biya Nnenna dashi sai fatan Alkhari domin itace sular arzikin sa. Lahab na komawa gida waya ya d'auka ya Kira faruq akan gobe yakai Nnenna a Mata passport za'a nema Mata visa,cikin yardan ubangiji an kammala shirye shiryen tafiyar Nnenna sai rana kawai ake jira,yau ne su Rahab zasu tafi Koh bacci ya kasa na dare bini-bini sai yazo katifar Lahab ya leke fuskar sa sanann ya koma ya kwanta a hakan har asuba tayi sukaje sallah gabaki d'aya mood nasa ya canja yayi wani sanyi dashi,bayan dawowar su sallan asuba ya zauna ya buga tagumi yayi shuru,akwatin Rahab Lahab ya janyo ya Fara had'a Masa kayansa ganin Zama yayi Kuma flight in safe zasubi,kallon sa Rahab yayi a hankali yace"kana murna zamu rabu Koh"? Da mamaki Lahab yace akan me zanyi murna Koh ka manta ba hakan na nufin mun rabu bane fa,zamuna dawowa hutu haka zalika zamu sada zumunci ai Ni nama fika Kewan rabuwar mu"wani banzan kallo Rahab ya Masa cikin haushi yace da kana kewata bazakayi munafurcin tafiya Kai kadai ba dariya Lahab ya Fara hade da kamo hannun dan uwan nasa har toilet kafun ya fita ya barsa a ciki. **************** Da misalin karfe 8 Mami ne da yaranta Suka shigo gidan harda Anwar da Aisha duk sunzo rakiyar su Rahab gidan a cike,daga Nan airport Suka wuce gabaki dayan su suka musu rakiya lokacin da Rahab yazo rabuwa da Lahab baisan lokacin da kuka ya subuce Masa ba da Sauri ya rungume Dan uwan NASA haka kawai Lahab yaji gabansa ya Fadi ganin yanda Rahab ya nuna kin son tafiyar,sai da Abbu yasa baki Jin ana Kiran passenger sake Lahab Yayi ya rungume Mami ya had'a da Addayiya sai Kuma ya Kama kafadan Abbu ya runguma kana ya sake su yajuya ya Soma tafiya sai yayi nisa sai Kuma ya juya ya Kara daga musu hannu Harya shiga jirgin,Basu bar airport ba har jirgin ya d'aga suka Lula sararen samaniya kafun Suka koma gida gabaki dayan su. After one week yau su Lahab zasu tafi tun safe yasha wankan sa yaci abinci ya zauna a Kan kujera ya tasa akwatunan sa a gaba yana duba agogo Allah Allah yake 12:30 yayi Koh su Abbu zasu fito,Maigadi ne yayi sallah a falon amsawa yayi ba tare da ya kallesa ba"am Lahab wata ce ke sallama dakai a waje"waro Ido Lahab yayi yace sallama dani Kuma nidin"?kwarai ma kuwa" farace Koh baka"?farace tass"toh wacece haka sai Kuma yayi tunanin Koh Nnenna ce. Mikewa yayi da Sauri ya fita wajen da mamaki ya bude kofar gate nasu amma baiga kowa ba harya juya zai koma ciki sai yaji an Kira sunan sa a kofar wani gidan makwacinsu da mamaki yakebin mubeena ganinta tsaye gabaki d'aya ta rame Masa wallahi,"Aunty kece Kuma Kika tsaya a waje Baki shigo ciki ba"?girgiza Kai tayi a hankali tace"basai na Shiga ba Nabeel yacemin Wai yau zaku wuce ga wannan Ina maka fatan Alkhari Allah ubangiji ya baka duk abinda kaje nema muddin Alkhari ne"hannu yasa ya amshi laidan Yana Mata godiya tare da bude laidan Yana kallon meyake ciki sai Kuma ya dago Suka had'a Ido murmushi yake tayi tace"sai wata Rana"murmushi shima yamaida Mata cikin fara'a yace toh sai wata Rana Aunty mubeena Allah sadamu da Alkharin kilama kafun na dawo kinyi aure tunda kince bakison abokina"murmushi yaga tayi sosai yaji mamaki yasan mubeena batason Wasa Sam amma yau ya tsokonota sai Kuma tayi fara'a"sai Kuma ya tsaya ganin har lokacin bata da niyar tafiya sai kallon sa take. juyawa yayi zai shiga gidan da Sauri ta kirasa cikin dan murmushi tace ga number ta Inka Isa Koh zaka kirani sai muna gaisawa?"la Aunty mubeena Ina da number ki insha Allah Zan kiraki sai Kuma ya d'aga Mata hannu ya shiga gidan, kuka mubeena ta Soma tana tafiya tana share hawaye,Allah sarki uwa uwace duk irin haushin Lahab da Mami keji kasa hakuri tayi tazo rakiyar sa Saida Suka iso airport kafun ta d'aga hannu ta maka Masa dundu Mai zafi Wanda ya sashi Kara Yana kallon ta magana ta Soma kamar haka"watoh Lahab harka Kai matsayinda zaka min abu inji haushi Kuma ka kasa bani hakuri Lahab zaka sa kafa kabar kasar Nan da haushin uwarka Kuma kana tunanin zakaci nasarar abinda kake bukata" Rungumarta yayi yace"mamina Nina San kin Jima da yafemin Kuma sai hadamun fuska kike shiyasa na kasa baki hakuri"zungurar sa tayi yace"Koh da wuka nake rike dashi Lahab zaka kasa bani hakuri,girgiza Kai kawai yayi ya nemi yafiyar kowa daga danginsa sukayi sallama ya nufi jirgi, Ade dake gefe Suna buga rikici da papa don papa badon kudinsa daya kashe da kamawa Ade gida acan dayayi ba aradu da Ade bazai tafi da Lahab ba baisan da zancen tafiyar ba Saida ya hade da Yan gidansu yanzun a airport ganin Lahab ya nufi jirgi shiyasa Adewale mikewa yabi bayan sa bai damu da masifar papa ba, tunda sunyi sallama da mahaifiyarsa. tunda Lahab ya juya Yana tafiya Bai Kara waigowa ba Koh sau daya Harya shiga jirgi shigowarsu Kenan ya Soma rarraba Ido Yana neman sit Inda Nnenna ke zaune don shu'aibu yace Masa yabar kome na tafiyar Nnenna a hannun sa har cikin jirgi zaisa a kaita amma Bai ganta ba saboda girman jirgin gajiya yayi da dubawa ya juya zai koma waje amma aka hanasa fita Ade kam na zaune baisan dawan garin ba don sit nasu ba daya da Lahab ba Yana gaban Lahab,Jin rikicin Lahab da ma'aikatan jirgi ya Sasa mikewa yazo Yana tambayar ba'asi da Kuma dalilin dayasa Lahab keson fita waje,kin basa amsa Lahab yayi ya koma ya zauna a filin sa shima Ade komawa yayi ya zauna. Rumtsa Ido yayi da karfi gaske wannan shine karonsa na farko a jirgi Kuma zaiyi tafiya har wata kasa gashi baida tabbacin Nnenna na cikin jirgin. Jirgin su Lahab ya sauka lafiya klau a babban birnin London cikin dare, passenger ne Suka Fara fita d'aya bayan d'aya mikewa Adewale yayi Yana kallon Lahab ganin baiyi niyar mikewa ba kala baice ba ya d'au akwatunan sa ya fita waje mikewa Lahab yayi ganin mutane nata fita,da mamaki yaga an bude private sit dake ciki saiga ma'aikaciyar cikin jirgin ta fito tana rike da hannun Nnenna waro Ido yayi da Sauri ya karaso wajen cikin farin ciki ya riko hannun ta da Sauri ma'aikaciyar tace"Kai ya haka ya zaka kama mata hannu?kafun ma yace wani Abu da Sauri Nnenna tace"shine Wanda nace ki dubomin kikace baki ganesa ba,au toh gata shine abinda tace tana Mika Masa jakunkunan Nnenna da shu'aibu ya Mata shopping sosai. Sauka suke a steps na jirgin a hankali sunyi wani irin masifar kyau sanye take da abaya baki shi Kuma yana sanye cikin kananan Kaya jakunkunan su na hannun ma'aikatan Suna sauko musu dashi,Baki sake Ade yake kallon su daga inda yake tsaye Yana salati cikin tashin hankali ganin Nnenna tare da Lahab a London bai taba kawowa ransa wannan abun ba. Juyawa yayi ya wuce ba tare da ya jirasu ba dayake Yana da address in Inda zasu sauka Hawa taxi kawai yayi ya Mika Masa address in,Lahab Kam Yana rike da hannunta Suka fito cikin airport in ya tare taxi shima ya hau ya d'ura kayansu Suka d'auki hanya,har sunyi nisa yace wa bature ya kaisu Inda zasu samu abinci watoh restaurant,abinci Lahab yayi order harda laidan Abraham, unguwa ne Mai kyau Mai d'auke da ginunuka iri d'aya akallah kofa-kofa yakai sama da hamsin Kuma Hawa uku,sauka Lahab yayi ya ringa dudduba number floor har Allah yasa ya samo numbern dakin nasu a Hawa na uku suke,nufar wajen Nnenna yayi Yana korafi a ransa wannan ai sai wata rana ya manta dakin nasu ace Hawa har uku dakuna sunkai sama da hamsin amma ace kome iri daya kamo hannun Nnenna yayi yabar jakan nasu a kasa ya Soma haurawa upstairs in da ita Suna taka steps in a hankali Hawa na biyu Suka hau gabaki d'aya taji ta gaji Zama kawai tayi tace zata huta,komawa kasan yayi ya dauko musu kayan su ya hauro dashi har lokacin tana zaune a matakalan,aje kayan yayi ya ciccibeta duk yanda tayita cewa ya sauketa ki yayi Saida ya kaita har kofar dakin su hannu yasa ya bude dakin ya shigar da ita,falone madaidaici sai wasu steps guda uku Wanda Koh ba'a fada Masa ba yasan kitchen ne a wajen ai dakuna guda biyu a falon sauketa yayi ta zauna akan kujera shi Kuma ya koma waje ya dauko bags nasu,kome akwai a falon TV fridge AC abubuwan more rayuwa duk akwai dakin dake hannun hago ya bude Adewale ne zaune akan kujera ya zuba tagumi Yana kallon gefe bude kofar baisa sa ya juyo yaga Wanda ya buden ba shima Lahab rufewa yayi ya bude na dama alamu shine dakin sa. Ajeta yayi a bakin gadon kana ya aje akwatunan su a gefe,Zama yayi a bakin kujeran dakin ya zare takalmin Boot dake kafarsa ya zame black socks in duka kayan sa ya cire ya rage daga shi sai wando dogo toilet ya shiga yayi wanka da Alwala ya fito bude jakansa yayi yadatu darduma tare da kallon Nnenna dake zaune a bakin gado Yana cewa ta jirasa bari yayi sallah ya kawo musu abinci"gyada Kai tayi tace"so nake nayi wanka tukun na"ok yace ya tada sallah yana idarwa had'a Mata ruwa yayi a toilet kayanda zata sa tare da nuna Mata ma ajiyinsa,fita yayi falon ya d'auki laidan abinci dakin Ade ya bude ya aje Masa laida daya baiyi magana ba ya sake fita. Kitchen ya shiga shima kayatance Mai dauke da dinning a ciki irin tsarin turawa haka yake plate ya d'auka da cup ya fita dakin nasu ya Shiga har lokacin bata fito wanka ba bude akwatinsu yayi yadau maganinta yasa Mata a cikin fresh milk daya sayo musu, yasa nasa maganin ya aje juye abincin yayi duka ya zauna ya Soma ci Sam abincin Bai Masa dadi ba saboda dandano daya banbanta da cimarsa sosai amma saboda gayu haka yake taci,bude kofar toilet in akayi Nnenna ta fito da towel tana tafiya tana tattaba waje dakatawa Lahab yayi ya daina motse harta shigo dakin Kan gadon ta zauna tana tattaba kayan da ya aje Mata d'auka tayi sai Kuma ta Soma warware towel in jikinta da Sauri yayi gyaran murya itama a rikice ta Kara tamke towel in da Sauri ta nufi toilet Wai zata koma kawai ta gwaro da jikin wardrobe Kara ta sake ta durkusa tana dafe goshinta. da Sauri ya mike yazo ya Kama goshin Yana ta masifa wai ai zata hallaka kanta a banza fita yayi a dakin ya jirata tasa kaya kafun ya dawo ciki Suka ci abinci dayake darene kwanciya sukayi tana Kan gado Yana Kan kujera. Washe gari da safe,har 9 Lahab na bacci tunda ya koma bayan sallan asuba Bai tashi ba Nnenna ta farka amma saboda kartayi motse ta tadashi ya sata kin tashi tana kwance akan gadon,bubbuga kofar akayi da karfi,shiya farkar da Lahab mikewa yayi Yana tsaki ya nufi kofar budewa yayi Ade ne tsaye cikin Shirin tafiya makaranta Yana bin Lahab da mugun kallo sai Kuma yace"zakaje ne Koh nayi tafiya na"?da mamaki Lahab yace"haba dan Allah jiya fa Muka diro kasar Nan ka Bari gobe muje school in mana"juyawa Ade yayi yace"course namu daban Kai zaka iya Zama sai goben"da Sauri Lahab yace dan Allah d'an jirani Ina zuwa"?,dakin ya shiga da Sauri ya Wasa ruwa ya sanya Kaya da Sauri ya dau school bag NASA ya fito,a falo ya samu Ade na zaune Yana jiran sa kallonsa yayi yace"Wai Ade haka Zan tafi bazan karya ba"nuna Masa kitchen da hannu Ade yayi da Sauri ya Shiga bude abinci yayi sai Kuma ya dauka da gudu ya nufi dakin su aje Mata yayi a kusa da gado ya kawo ruwa ya aje Yana gaya Mata ya tafi school, sanan ya fito a dakin kala Ade baice ba Suka wuce makaranta. Ranan Lahab na farko a makaranta ta Masa dadi don yaga chanji da school nada nada sosai anan babu takura babu tsawa Ade ya wuce department nasu yayin da Lahab ma ya wuce nasu dan Adewale zai karanta engineering me yayin da Lahab xaifara karanta pharmacy daga zuwan Lahab class har yayi abokai guda uku yayan turawa,biyu maza d'aya mace,Suna fita a class dayan yaja Lahab wajen training na football nasu a school babu kauyanci Lahab ya shiga cikin yaran turawa ana buga ball dashi,cikin sati guda Lahab ya sassaba da mutane da yawa haka zalika abokan sa masu son karatune shiyasa Koda yaushe yake cin serious Kuma ba laifi sosai suke ganewa gashi yanzun ya Zama daya daga cikin members na yara masu kwazo wajen football ga kyakkyawan horo da suke samu daga coach nasu haka zalika Yana yabawa da gogarin Lahab. Wasa Wasa Lahab sunyi wata a London babu laifi Adewale yadan sauko da fushin Nnenna da yake ganin Lahab na karatu haka zalika yarinyar nada Hali Mai kyau,har yau Lahab bai had'a sim Koh waya ba Ade na Kiran gidansu amma Lahab saban Zama yayi Masa dadi Koh tunanin sayan sim baiyi ba,Kamar yau zaune suke da daddare a falo gabaki dayan su, karatu Lahab yake da Ade sai Nnenna dake gefe tana sauraron abinda suke cewa wayar Ade ce tayi Kara ya mike tare da daukar wayar ya Kara a kunne ganin new number ne Kuma number nageria gaisawa sukayi da Wanda ya kirasan kafun da Sauri yace gashinan,mikawa Lahab wayan yayi, ba musu yasa hannu ya karba duk da baisan da wake Kiran nasa ba,karawa yayi a kunne Jin muryar Abbu yasa sa washe Baki Yana cewa Abbu Kaine"eh nine Lahab tunda Kai baka San ka nememu ba mukam munsan mu nemeka"am sorry Abbu wallahi karatune ya maidani gabaki d'aya busy shiyasa"da Allah rufemin baki Kai Inne zaka Kira sunan karatu mutum ya yarda Ina dai fada maka in kace zaka tsaya shirme wallahi babu ruwana Suna Korinka zaka tattaro ka dawo gida kazo ka zauna kamar yanda kakeso"dariya Lahab yayitayi Abbu nata Masa masifa daga baya ya baiwa Addayiya Suka gaisa da sauran yaran gidan sannan ya jaddada Masa ya sai SIM Rahab ya damesa da Kira akan Dan uwan sa dan haka ya nemeshi a waya da zaran ya samu sim card,insha Allah Abbu Zan saya gobe da safe"Allah yasa sai da safe"Allah ya kaimu lafiya Ameen katse wayar Abbu yayi. Su Lahab sun Soma exam karatu yayi musu zafi sosai gashi bayan exam Suna da Wasa(game)da zasu buga anan London Kuma har dashi a cikin Yan wasan da makarantan ta zaba zasu buga Mata,bayan fitar su paper aka Soma iska Mai karfi sosai hadari gabaki d'aya ya game garin yayi bakikkin sai yayyafi da aka Fara ganin haka yasa Ade cewa shi gaskiya zai zauna a makaranta ga yamma tayi ga iska ga ruwa taima ma ya kwana a dakin abokan sa na hostel"gaskiya Ade nikam Zan tafi saboda nabar Yar mutane babu abincin dare gashi Bata gani Kuma ita kadai gaskiya bazaiyu ba nikam Zan tafi" Duk yanda Ade yaso Lahab ya tsaya a tsagaita ruwan ki yayi ya fita wajen makaranta daker ya samu taxi da zai kaisa Hawa yayi,ruwan ya zuko da karfi dole tasa drivern fakawa Yana jiran ruwan ya tsagaita saboda dokane ba'a tuki in ana ruwa Mai karfi,agogon hannun sa ya duba karfe kusan 7 na dare ya gota Koh sallan mangariba baiyi ba ga isha'i ya gabato,magana Yama driver Koh zai tada motar su tafi yanuzn tunda ruwan yadan tsagaita,ki baturen yayi haka suka zauna sai wajen 8 na dare kafun ruwan ya tsaya amma akwai yayyafi Kam sosai, parking baturen yayi a kofar block in su Lahab sauka yayi Yana tafiya da Sauri ya hau floor in lokacin yayyafin ya jikasa sosai don har kayan jikinsa sun jike,da gudu ya bude leta ya hau,sauka yayi a daidai kofar dakin su hannu yasa ya bude kofar ya Shiga tare da maidawa ya rufe Yana kakkare jikinsa da ruwa ya jika. d'akin su ya Shiga da Sauri yana kwalama Nnenna Kira amma shuru bata amsa ba bin dakin yayi ganin babu kowa yasa shi nufar toilet Nan ma ba mutum da Sauri ya fito daga dakin ya nufi na Adewale shima Yana budewa yaga wayan toilet ya bude Nan ma wayam kiranta ya somayi da Sauri Yana fitowa falon........................... *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 08084453785 tare da shaidan biyan ki* *BUZHUWA EmphireπŸͺπŸͺ* Assalamu Alaikum,Barkanmu da wannan lokacin ,Sannun mu da shigowa Halarar mu na buzaye.... Albishirin ku matan AureπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ BUZUWA EMPIRE ta taho maku da sirrika na MALLAKAR mijin ki yar uwa a hannun ki ba tare da boka ko malam ba. Matan da yawa na fuskatan matsalolin su da maxajen wato kalubalen a gidan auren mu...kuma irin wannan maganin matan Asha tabaje...mene wani shirme wani gayinan dai ,bashi ne ba... Ina macen da daga zarar mai gida yy sallama gaban ki keda yara ya hau fadi?. Ina macen da mijin ta kullum idanun shi na akan matan banxa?. Ina macen da ga kudin mijin yanada amma babu ci sai dai duniya suci yy kyautan riya? Kai duk wani matsalan ki na gidan Aure kizo taskar BUZUWA EMPIRE. zata baki mallaka ta hanyar sirorin kur'ani da dai sauransu. Mallaka ta hanyar kwai Mallaka ta hanyar nama ,madara ,kifi , yan shila da dai sauran su.. Ga kuma mallaka ta hanyar suratul yusuf . Mallaka ta hanyar jauhara. Mallaka ta hanyar Yaseen Mallaka ta hanyar fatiha umul qur'an. Mallaka ta hanyar turaruka da dai sauran su... Ina Yammata marasa farin jini ?πŸ’ƒ Kuzo kuma da naku ,sai kaji ana gata mummuna baka kirin amma sai farin jinin manyan alhajazai masu jifa jifai kome take dashi oho..!! Kuji ita tasan inda tazo ta taho taskar BUZUWA EMPIRE . sai kin taho yar uwa gaba daya sirrin nan na farin jini dana mallaka 5k ne duka . Idan kuma mallaka ne kadai munayin na 2k da kuma 3k. Na farin jini kacal 3k ne ,gamasu bukata zasu tuntu6a wannan number 08081202932 09061466409 amsawa Nnenna tayi daga cikin kitchen da Sauri ya nufi kitchen in da mamaki ya tsaya ganinta sai girki take cikin fada yace"meye haka Zaki shigo kizo ki kunna gas bakiga halinda kike ciki bane Wai"?d'an murmushi tayi tace"Naga dare yayi ga ruwa kuma baku dawo ba shine Zan d'aura muku girki"kwace spoon in hannun ta yayi ya Kama hannun ta hade da kashe gas in Yana cewa wuce muje daki in ruwan ya tsakaita sai na fita na sayo Mana abinci"ah ah nidai ka bari na girka karka fita kazo ka samu Mura Kuma"sosai Suka shiga muhawara Lahab yace sai tabar girki ita Kuma tace alafatau bazata bari ba zatayi girki,karshe dai sai da yarjejeniya Lahab zaizo ya Fara girkawa ita Kuma zata tsaya tana gaya Masa abubuwan da zaina sawa rigan jikinsa ya Kwabe Mai sanyi ya makala a kofa ya matso kusa da bojuwan Suka Soma girkin"sai kusan 9 na dare ya kammala dafa taliyarsu dafa duka da wake yasa kifi a ciki rufe abincin yayi yashiga daki da ita a hannun sa ajeta yayi yayi wanka yazo ya Soma Rama sallan da ake binsa Saida ya kammala yayi nafila kana ya taimaka Mata ta shiga toilet itama tayi wanka kayan bacci ya bata tasa wando da riga sai hula. Shima Lahab sanye yake da kayan baccin mikewa yai ya sassauke labule kana ya koma kitchen in plates na taliyan ya d'auka da ruwa ya shigo dakin ajewa yayi a kasan carfet kana ya riko hannunta suka zauna abincin sukaci kana sukayi brush hawa Kan gadon Nnenna tayi ta kwanta Lahab Kam na zaune Yana duba littatafansa sai kusan 12:00am ya mike daga Kan table in ya nufi Kan kujeran kwanciya yayi sai Kuma ya mike saboda sanyin da ake bargon sa yayi niyar d'auka a cikin wardrobe sai Kuma ya dafe goshin sa da karfi tunawa da yayi aima ya bada wankin bargon daman guda biyu ne d'aya nasa daya na Nnenna,bincike yayitayi Koh zai samu zani Koh abin rufuwa amma Ina bai samu ba,matsowa yayi kusa da gadon yasa hannu a hankali Yana zame blanket in jikinta harya ciresa gabaki d'aya a jikinta. Yamotsa fuska tayi irin sanyi ya shigetan Nan tana harhada jiki,maida Mata bargon jikinta yayi ya lulluba Mata shima ya hau Kan gadon a hankali ya kwanta Yana lumshe Ido rabonsa da gado tun a naija sai yau ya sake Hawa kanta,lullubuwa yayi kansa ne kawai a waje ya daura kansa a filo lumshe idanunsa yayi Yana jinsa uncomfortable,d'an matsowa yayi kusa da Nnenna har Yana Jin numfashinta dake sauka, hannu yasa ya kunna bedlamp in Yana bin fuskarta da kallo sosai ya zubawa lip's nata eyes Yana Jin wani mugun sha'awar ta na taso Masa a hankali ya matso sosai kusa da ita zai manna bakinsa a nata da Sauri Kuma yaja baya, ganin ta waro manyan idanunta masu kyau gaske. tana bin saitin da yakejin numfashinsa a wajen,sai Kuma yaga ta maida idanunta ta rufe a hankali,baiyi wata-wata ba ya damko lip's nata da Sauri Yana wani irin tsotsa da Sauri-Sauri hannu yasa ta karkashin wuyanta Yana shafawa hade da kamo kanta ya Kara mannata kusa da kansa,da Sauri ya birgino ya hau kanta d'aura gwuwarsa yayi akan dollof in yayi ya manna hannunsa akan nata duk da bai kwanta akanta ba amma Yana manne da ita hot and romantic kiss yake watso Mata cikin soyayya. A hankali yasa hannu Yana warware igiyar rigan bacci dake jikinta da Sauri tasa hannu ta riko nasa lokacin idanunta a rufe,a hankali ta Soma magana muryarta na sarkewa matso da kunnensa yayi saitin bakinta Yana Jin abinda take cewa"pls ka Bari karmuyi abinda zai jaza Mana matsala dan .......bai bari ta karasa ba yayi saurin sake manna bakinsa a wuyanta Yana kissing nata a hankali ya zame rigan d'an dagowa yayi ya ciresa gabaki d'aya a jikinta,ya rage daga ita sai vest kama hannun vest in yayi ya xamesa gabaki d'aya ya cire Mata shi da Sauri tasa hannu ta kamo keyarsa dake d'auke da gashi Mai yawa,mikewa yayi a kanta da Sauri ya zame rigan dake jikinsa komawa yayi ya kwanta akanta kirjinsa babu Kaya Kamar yanda nata babu mannata yayi sosai da jikinsa yana Mai cikin tsananin bukata. "Lahab Lahab stop it pls"shine abinda take maimaitawa Kara masowa gareta yayi ya kwantar da kansa a kirjinta tanajin yanda bugun zuciyarta ke gudu da sauri-sauri har wani huruwa na shanunta suke"bazan iya ba"amsar da ya bata kenan Yana Kara ja musu bargo,rumtsa Ido tayi da karfi Jin yanda yasa kafa Yana gyara Mata kwanciya a hankali,d'an zabura tayi sai kuma ta maida kanta Kan pillow ta lumshe idanunta hawaye Nabin gefen idanunta Yana sauka akan pillown, motse Mai kyau bata Kara ba gabaki d'aya ta sakar Masa ragamar rayuwarta ta barsa Yana Inda yaga dama da ita ba tare da tayi tirjiya Koh nuna gajiyawa ba don Lahab agunta yafi karfin haka hannunta dake bayan wuyansa ya Kama da Sauri ya maida Kan katifar yasa nasa tafin hannun a nata ya Danna da karfi gabaki d'aya hankalinsa a tashe yake kome yanayine cikin kuzari da Kuma mugun tsoro sosai shima zuciyarsa yake bugawa baisan haka aure yake ba shidai diran makiya yama aure amma yau gashi Yana Jin wani Kalan d'adi da ni'ima da baisan da irinsa ba a duniya. da karfi Lahab ya Kara damke hannunta ya danna a katifar zufa sharkaf yayi har diddiga yake har zuwa lokacin idanun Nnenna a kulle Bata bude bama bare tasab halinda yake ciki gabaki dayansu zufa Suka had'a duk sanyin AC da na damuna baisa zufar yankewa ba,a hankali yasa hannu Yana share Mata zufar da take a hankali ya zame daga ronkwafar da yayi a kanta ya kwanta akanta Yana maida numfashi da Sauri-Sauri har ya dawo Yana saukewa a hankali hankali,ya sake sa hannu ya kamo gashin kanta daya jika jakaf da zufa,harhada Mata gashin yayi waje d'aya a hankali ya mike a kanta cikin wani irin tsananin kunya da bai tabaji ba sai yau Wai shine yau ya sadu da mace shi lahab?da Sauri ya zame bakin gadon,gajeren wandon sa dake yashe a kasa yasa hannu ya d'auka tare da zurawa a jikinsa cikin toilet ya shiga ya tsaftace jikinsa wallahi yama rasa Ina zaisa kansa kunyarta ma yakeji baisan Yana da kunya irin na yau ba,d'aure da towel ya fito toilet in Yana tafiya Kamar Wanda kwai ya fashewa a ciki. Matsowa yayi kusa da bed in ya kunna lamp,haske yadan haska dakin,Kai dubansa gareta yayi har war lokacin idanunta a rufe suke haka zalika idanunta har lokacin Bai saya daga zubda hawaye ba,hannu yasa a hankali ya Kama bargon da niyar yayewa da Sauri tasa hannu ta rike bargon amma bata bude idanunta ba"kiyi hakuri so nake na taimaka Miki"girgiza Kai tayi alamun bataso,bai kulata ba ya dagota duka da bargon ya nufi toilet da ita ajeta yayi sannan ya had'a Mata ruwan zafi tunda ita ba musulma bace basai tayi wankan tsarki ba fita yayi a toilet in yazo yad'au zanin gadon ya aje a gefe ya Kuma rasa wani abin zai lullubawa katifar tsayawa yayi sai Kuma ya fita a dakin da zanin gadon dakin Adewale ya shiga zanin gadon Ade guda daya ya dauko ya dawo ya shimfida Mata harda blanket in Ade ya shimfida Mata Kaya ya Ciro ya aje Mata da Sauri yadau xanin gadon da Suka batan ya fita dakin da Sauri Jin motsenta tana kokarin fita a dakin,dakin Ade yaje ya wanke zanin gadon ya matse sosai ya aje a boket kwanciya yayi a Kan gado yayi shuru a cikin bargo har lokacin zuciyarsa Bata bar luguje ba,so yake yaje yaga ya take amma ya kasa a hakan har bacci ya daukesa. Jiki da jini duk da bai kwanta da wuri ba amma asuba nayi ya farka Alwala yayi ya tada sallah yana idarwa ya mike ya sanya Kaya da wurwuri yadau boket na zanin gadon ya bude kofar balcony nasu ya Haura shanya kayan yayi yadau wayarsa ordern abinci yayi musu ta waya abinka da turai kafun 7 yaji knocking karban abincin yayi ya koma ciki aje laidan yayi a hankali ya bude dakin nata lekawa yayi ya hangota kwace akan gado,da Sauri ya fita a gidan pharmacy yaje yayi-yayi su Saida Masa magani sukaki sukace sai yazo da shaid'an likita basa Saida magani barkatai dolensa ya dawo gida shiga dakin nata yayi a hankali Yana tafiya Yana tsaibi Harya karaso kusa da gadon nata sauke ajiyar zuciya yayi ganin ta tana bacci. Laidan abincin ya aje Mata kusa da gado tare da note a paper yasa hannu ya shafa Kan nata da yayi zafi sosai ya fita,dakin su ya shiga yayi wanka Koh abinci ya kasa ci ya d'au school bag nasa sai makaranta,Koda yaje makarantan yau gabaki d'aya ya Zama wani silent dashi tuni nutsuwar aure ya shigesa sai ka gansa ya zauna yayi sugudun dashi waje d'aya kasa hakura Ade yayi Saida ya tambaye sa Koh baida lafiya ne. Sun kammala lecture tun 2 na rana amma Lahab yaki yarda su dawo gida har yamma Saida Ade yace zai tafi ya barsa kafun ya yarda su koma don daman shi wallahi yafison sai dare haka su kuma lokacin da Suka kusa Isa kawai sai yace a saukesa ya manta Suna da training zai koma school da mamaki Ade yake kallon sa amma baice kome ba aka saukesa don daman ya riga yayi order abinci za'a kaima Nnenna, Adewale lokacin daya Isa gidan shuru ya tarar da gidan bai Kuma nemeta ba ya wuce dakin sa. Lahab yawo yayi-tayi a garin London Saida dare yayi kafun ya nufo gidan zuwa lokacin ya samu ya sayo Mata maganin zazzabi da ciwon jiki,don shima asibiti yaje kafafunsa na ciwo ga baya duka na ciwo tun daren jiya daurewa kawai yake da aka basa magani shine ya d'auko zai kawo Mata,shigowa gidan yayi da sallama Ade ne zaune a falo Yana cin dinner ya amsa Masa ba tare da ya dago ba kasa Zama Lahab yayi a falon gudun karta fito ta gansa dakin Ade ya shiga shidai Ade idone nasa baice Masa kala ba. 10:20am Ade ya fito toilet sanye da kayan bacci kallon Lahab yayi dake kwance akan gadonsa Yana waya da Rahab,Zama yayi akan kujera Yana jiran ya gama wayar,ganin baida niyar gamawa yasa Ade mikewa ya dawo Kan gadon ya kwanta tare dama Lahab nunu da hannu yabar Masa daki. Kin tashi Lahab yayi sosai suka ringa rikici karshe dai Ade haka yayi hakuri badon ransa yaso ba ganin dai kawai anfi karfinsa ne,Kuma bai tambayi dalilin dawowar Lahab dakin ba,da misalin karfe biyu na dare Lahab ya mike lekawa yayi ya duba Ade na bacci kafun yadau magani a hankali ya fita a dakin, dakin nata ya Shiga duhu ne mamaye da dakin,hannu yasa ya kunna wutan dakin maganin ya aje akan drower ya matso kusa da ita har Kan gadon,hannu yasa ya taba jikinta sosai jikin yai zafi jau Kamar garwashi"am sorry Labiba am so so sorry wife"shine abinda yace Yana tofa Mata Addu'a ya sauka agadon ya kashe wutan ya fita,bude idanunta tayi hawaye ne cike a cikin su tunda Lahab ya shigo dakin ta farka kawai motsene batayi ba bare ta nuna Masa ta tashi Harya fita,Mikewa tayi a hankali ta kunna hasken tadau maganin da ruwa tasha ta koma ta kwanta. Washe gari da safe kafun su tashi har Lahab ya shirya ya gudu makaranta,kawai farkawa ade yayi ya tarar Bayanan,lokacin da yaje makarantan Yana tambayar sa dalilin zuwan sa da sassafen, kawai cewa yayi Yana da class ne da wuri Wasa Wasa Saida Lahab ya shafe sati guda bai Bari Nnenna ta gansa ba a tasa tunanin kenan, amma baisan cewa duk lokacin da ya shigo dakin dubata farkawa take kawai Bata nuna Masa ne duk dare zai shigo ya dubata haka ma asuba zai aje Mata maganin gargajiya dana asibiti ya tafi da wuri tun Ade na hakuri Harya kasa ya tambaye Lahab Koh lafiya har yanzun bai koma dakin su ba sannan meyasa yake fitan sassafe, Nnenna idanunta sun bude ras ta dawo gani amma Basu hadu da Lahab Koh Ade ba don Bata fita a dakin sai sun tafi makaranta zata dau abincin da sukayi order taci tayi wanka ta kwanta Koh tayi kallo intaji sha'awar girki ta girka nata taci tunda su kullum abincin waje ake kawo musu. ************** Su Lahab sun kammala exam lafiya an kammala shirya musu tafiya game Inda zasuje Kuma akallah zasuyi sati biyu Koh daya,shirye shiryen tafiyar ya Fara ba tare da sun sake haduwa ba don wallahi duk lokacin da yayi tunanin abinda ya faru sai yaji wani mugun kunya ya kamasa,gobe ne tafiyar su,sauke su taxi yayi a block nasu suka sauka agogon sa ya duba karfe 1 ne na Rana Ade ya damesa Wai sai yazo su tafi,tura kofar yayi ya Shiga daidai lokacin Nnenna dake sanye da dogon rigan kanti Kai Koh dankwali babu ta fito cikin kitchen in had'a Ido sukayi da Sauri ya hau eiiieiiina Yana Shirin juyawa zai koma Ade dake bayansa hankad'asa yayi da karfi ya shigo shima hade da maida kofar ya rufe da Sauri Lahab ya nufi dakin ade jawosa yayi ya dawo dashi baya ya d'aga Ido ya kalli Nnenna sau d'aya sai Kuma ya Kara kallonta ganin Kamar tana kallo tunda kwayar idanun Mai kallo dana Mara kallo daban yake. Kin Soma kallo ne"shine tambayar da ya jefo Mata cikin turancin sa daya Fara sajewa Dana turawa,gyada Kai tayi ba tare da ta kallesa ba ta nufi daki da Sauri Ade yace"Nnenna meya had'aku da Lahab ne Kuma garin Yaya Kika Soma ganine Wai"magani nake sha"shine abinda tace masa ta Shiga daki,Lahab mikewa yayi haryana buge kafarsa yabar wajen baiyi wani mamakin warakar nata ba,dakin su ya shiga babu abinda ya d'auka sai system nasa don kome akwai a team nasu Kama daga sports wear da abinda zasu bukata naci dana Kaya, wasika na bankwana da Kuma tafiyar ya aje Mata da dare bayan ya Shiga dakin,washe gari ya wuce makaranta daga Nan suka wuce Inda zasuje su buga ball in. Adewale na dawowa yacewa Nnenna ta had'a kayanta kala biyar wani bag ya bata madaidaici don shi bazai iya Zama dagashi sai ita a gidan ba in Kuma yaje dakunan abokan sa ita kadai a gidan Bai Dace ba shiyasa zaibi Lahab suje suga wasan da zasu bugan tunda shima student na school nasu ne, amma bai gaya Masa ba,don daman bazasu koma najeria ba sai karshen shekara Kuma yanzun watan su biyar a London. Washe gari Suka d'auki hanya,Lahab baisan dawan garin ba kawai yana fita a fili Kamar ance ya d'aga idanunsa ya hangi Ade zaune da Nnenna sanye suke da rigan ball na team nasu, waro Ido yayi sai Kuma yayi saurin fitowa,wajen su ya nufa Yana mamakin zuwan su hannun Ade ya rike har Suka fita a wajen kafun ya Soma masifa akan me zai dauko Masa Mata ya jawota cikin arna haka"in baka da hankali Ni Ina dashi Kuma insu arna ne nima Arne ne Bai Kamata ka barta dani a gida d'aya ba harna tsawon kwanaki"ganin ran Ade ya baci yasa Lahab sauka ya basa hakuri sanann suka cigaba da Wasan. Ana tashi Ade hotel Inda ya Kama yaje ya barwa Lahab Nnenna abinka da kasar turawa babu gulma babu sa Ido dakinsa Lahab ya wuce da ita har lokacin bai yarda sun had'a Ido ba tana Zama ya kawo Mata abinci,kafun ya Shiga yayi wanka ya sauya Kaya cikin t-shirt Mai kyau da wando dogo roba sai p-cap ya daura akan gashin kansa ya Yama wata arniyar aski, haraman fita yayi da sauri ta Mike ba tare da tayi magana ba kallonta yayi suka had'a ido,yayi saurin kauda nasa Yana magana cikin eiiieiiina yace"ya dai"? "Zan bika"d'an zaro Ido yayi yace"muje Ina"Inda zaka"shuru yayi sai Kuma yace toh shirya muje mikewa tayi tayi wanka fita yayi a dakin ya zauna a kujera a kofar dakin Yana jiranta,wando tasa pencil Baki sai ta dau riga ta sanya ta kawo jacket ta d'aura akai gashinta ta daure ta sanya socks da boot nata,ta daura agogon hannnu ta daura, fitowa tayi a dakin wannan karon ma again Suka Kara had'a Ido dashi,kallonta yayi wannan Karo sosai sai itace ta kauda tata fuskar mikewa yayi ya koma cikin dakin sai gashi da veil medium baki matsowa yayi kusa da ita har Suna had'a numfashi da yake tana da tsaho tsakanin su babu nisa sosai amma dai yadan fita sosai,Yana kakkauda fuska yafa Mata yayi akai yayi rounded nasa a fuskarta ya gyara Mata tayi kyau kafun ya juya ya Soma tafiya binsa ta Soma a hankali a baya. Motar wani abokin aikin su Lahab ya karba Suka wuce hotel insu Ade, daukar da sukayi daga nan Suka fita cikin gari sosai Suka ringa yawo a hankali-hankali Lahab da Nnenna suka dan sake jiki da juna har waya Lahab ya baiwa Ade yayita d'aukar su hoto da vedio duk Inda sukaje,sunje har cikin kankara, Suna ta hotona su kayi ciya ciye gashi Lahab ya Fara Zama popular yanzun suk Inda ya Shiga sai kaga ana Kiran sunan sa wasu su basa memo Koh wani Abu ya musu sign,Basu Suka dawo ba sai dare. Daman sun riga sunyi dinner a waje Suna isowa wanka sukayi dukansu Suka sanya kayan bacci da yake daki d'aya ne babu yanda ya iya haka ya hau gadon ya kwanta itama kwanciyar tayi Suka bar space Mai yawa a tsakanin su a hankali bacci ya dauke Lahab,da misalin karfe 1 Lahab ya farka tare da dan juyawa zai gyara kwanciyar sa sai Kuma ya dan bude idanunsa da kyau ganin wajen Kamar ba mutum hannu yasa ya taba wajen kwanciyar ta Nan ma babu Nnenna,mikewa yayi zaune ya kunna hasken dakin. Zaune take a kasan tiles ta tasa laidan da suka ci abinci Suka rage tun kafun su fita, ta lasheshi tass harda drinks in kana ta zauna tayi tagumi gabaki d'aya daga ka ganta kaga Wance take cikin damuwa hannu yaga tasa ta share hawaye da Suka saukomata a kumatun mikewa yayi a hankali ya sauka a gadon har lokacin bata San ya farka ba a hankali ya Soma taka kafafunsa a tiles in Yana nufar Inda take da Sauri yaga ta juya Suna had'a Ido ta Mike tsaye cikin kunya tana tattara kwalaye da laidodin abincin zata bar wajen,hannu yasa ya kamo nata Yana kallon ta sosai kana yace......................... *Banyi Alkawarin na dare ba Amma Inna samu lokaci zanyi* *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 08084453785 tare da shaidan biyan ki* Wai menene haka don Allah meyake damunki"?girgiza Kai tayi tana kokarin kaucewa zata aje laidodin sake Mata hannu yayi ya kwace laidan yaja hannunta ya Kamota Zama yayi da ita a bakin gadon shima ya zauna kana yace"Wai meke faruwa ne na ganki cikin damuwa Kuma kincemin babu kome"?matsa Mata yayi lalle saita fada Masa meke damunta kuka ta fashe dashi sosai cikin Sauri ya rungumeta gam a jikinsa ya koma baya-baya ya kwanta da ita a jikinsa,Yan@ kwance a dollof ita tana kwance a kansa,hannu yasa ya kashe wutan. Labiba"ya Kira sunan ta a hankali kin amsawa tayi har lokacin hawaye bai tsaya a fuskarta ba,a hankali ya manna bakinsa a kumatunta hawayen Nata yake lashewa,lumshe Ido tayi tana d'an sake jikinta a nasa sosai ya lashe hawayen tas Kuma hawayen ya daina zuba,dan Jan lips nasa yayi a fuskarta har zuba gefen lip's nata sannan ya tsaya Yana bin fuskar da kallo,idanunta a lumshe suke jira kawai take taji saukan lips nata a nasa amma taji ya tsaya cak,dan bude idanunta tayi sai Kuma da Sauri ta kauda nata saboda tsayuwa da yayi kawai Yana kallon ta,"kin koshi da abincin Koh a kawo Miki wani"?girgiza Kai kawai tayi batace kome ba,sakin murmushi yayi a hankali ya zamar da ita a jikinsa ya kwantar tare da gyara Mata rufuwa shima ya rufu tare da kamo hannunta ya rike Yana bin fuskarta da kallo kawai. A hankali ta matso kusa dashi tare da manna jikinta a nasa,waro Ido yayi da mamaki sai Kuma yasa hannu ya dagata jabal ya daura a kansa,lip's nata ya Kama amma bai tsotsa ba kawai mannawa yayi da nata,dan Jimm tayi sai Kuma ta Kama lips nasa na kasa cikin sanyi ta tsotsa,Kama nata yayi Suka hau bawa juna hot kissing sosai salon wasan ya chanja duk wani kunya kunya gabaki dayansu ajesa sukayi a gefe sosai Lahab ke sarrafa matarsa yayinda ita Kuma ke basa goyon Baya dari bisa dari,lokacin da kome ya kankama Lahab yasha mamaki matuka Kuma ya rude don dadin da yaji na yau ya d'ara na Ranan dadin da yaji sosai. Lokacin da nutsuwar sa ta samu kokarin tashi yake a kanta da Sauri tasa hannu ta Kama waist nasa gam,Wanda hakan ya fahimtar dashi cewa itama tana bukatar nutsuwarta duk da akwai mutuwar jiki da gajiya a jikinsa hakan baisa sa kasa tallafawa matarsa ba sosai ya tallafeta har ta samu natsuwa,mikewa yayi a hankali ya d'auki towel NASA wanka yaje yayi kana ya fito mikewa tayi itama ta shiga toilet in kafun ta dawo Harya chanja zanin gadon ya kwanta,tana fitowa Zama tayi daga ita sai towel,shuru shuru yaji Bata hau Kan bed in ba kallonta yayi kana yace"lafiya bazaki kwanta ba kinsan karfe nawa yanzun"?shuru ta Masa Bata hauro Kan gadon ba,shima Bai Kara magana ba ya gyara kwanciyar sa so yake ya samu bacci kafun asuba don gobe Suna da training da sassafe,amma kasa baccin yayi ya sauka akan gadon d'aukarta yayi gabaki dayanta yazo ya kwantar akan gadon ba tare da ya damu da towel in jikinta ba ya lulluba Mata blanket. ************ tashi tayi ta zauna again Wanda hakan ya saka sa sake tashi agogo ya gani kusan 2:30 na dare tsaki kawai yayi yace"Wai don Allah wannan ai d'aukar alhakine ya Zaki kasa bacci ki hanani nima"?a fusace tace"toh ninace maka karka kwanta ne"toh Taya Zan kwanta kina zaune"a hankali tace"yunwa nakeji"wani kallo ya Mata sai Kuma ya tashi tsaye hannu yasa ya taba jikinta Jin sanyi babu zafi yasa sa komawa ya kwanta abinsa Bai Kara magana ba ya barta a zaune bacci barawo yayi awun gaba dashi. da asuba Lahab daya farka da mamaki Nnenna ya gani d'aure da towel Kamar yanda ya kwanta ya Barta idanunta biyu da mugun mamaki yake tambayar ta Wai Bata kwanta ba?kin amsa Masa tayi yasa hannu zai tabata kawai ta turesa Saida ya koma Kan katifa ya kwanta,bata Kara magana ba shima gyada Kai yayi irin lallai innan ma, ya mike Alwala yayi yazo yayi sallah duk tana zaune,Kaya ya chanja ya fita waje da asuban amma shuru babu kowa shaguna duk a rurrufe dakin wani makwancin sa ya shiga yadau fresh milk guda biyu ya kawo Mata kin karba tayi Wai tayi fushi daker ya samu ta karba tana Sha Koh aje goran batayi ba ta Soma amai Kamar zata amayar da hanjin cikinta sosai tayi aman lokaci d'aya wani irin zazzafi ya rufeta,daukarta yayi ya Kai toilet tare da wawwanke Mata jikinta ya fito da ita, Kaya ya sanya Mata ya kwantar da ita akan gado kafun yazo ya gyara wajen da ta batan. Wanka yayi da misalin karfe 6 zuwa lokacin wani irin bacci yayi gaba da ita so yake suje asibiti Kar ciwon yayi tsananin amma ganin tana bacci tunda bata samu na daren jiya ba sai yayi tunanin bari ya barta sai ya dawo,kayan ball yasa wando da riga sai takalmi ya fita a dakin, direct training ya wuce basu Suka bar wajen ba sai kusan 9 na safe daga wajen wajen Saida abinci ya wuce kaza yasai musu sai kayan ciye ciye na laida Incase kada ta bukace Abu lokacin da bazai samu ba shiyasa ya sama Mata irin su cake su pizza duk ya sassaya sosai ya Mata sayayya. Lokacin da ya dawo ya samu ta farka zaune take gabaki d'aya ta jirkita ganinsa da laida Koh barin ya ajiye batayi ba ta kwace tare da budewa cake Inda ta gani a ciki shita warware da Sauri ta Soma ci ci bana Wasa tama cake in ba,shidai Lahab idone nasa ba bakin magana amma yasan tabbas Bata da lafiya wallahi irin wannan haukan cin Kamar Wanda ta shekara da yunwa,Kamar d'azun da asuba tana gama ci sai amai,ganin haka yasa Lahab cewa ta tashi su tafi asibiti amma kai da fata Nnenna tace ita lafiyarta klau babu Inda zata,taba jikinta yayi yaji babu zafi Kamar d'azun, tambayar ta abinda zataci yayi tace apply,mikewa yayi yaje ya jido apply kwali guda fresh dasu yazo ya jera Mata a daki Aiko shikenan Nnenna ta samu abinci Bata da aiki saicin apply tunda kome taci amai yake sata Amma Banda shi. Lahab yaga ikon Allah gabaki d'aya Nnenna ta sauya ta Zama mabukaciya don tun tana kunyarsa tana jiran shiya Fara tabata Harya kasance ita ke nuna tana sonsa a aikace ba'a bayyane ba,shima Yana iya bakin kokarinsa wajen sauke nauyin da Allah ya daura Masa akanta Koh da kuwa baya mood,ga cin apply ga fad'a fushi da mita duk yanzun Nnenna ta koya cikin satin da sukayi harta chanja Sosa ga yawan zazzabin asuba da kuma yamma, sai yace su tafi asibiti tace bazata ba suyita fada Harya hakura ya kyaleta. Sun samu nasara sosai Lahab Yayi bajinta a wasan da suka buga yasha musu sosai,hakan yasa sa daukaka sosai,sun koma gidan su,sannan team nasu sun basa kudi sama da million biyu cikin abinda Suka samu saboda bajintarsa cikin kudin ya baiwa Ade have million sannan ya turawa Rahab 300k ya baiwa uzaifa 200k tunda Sunsan Inda kudin ya fito lokacin da ya tura musu basuki amsa ba account ya Kai Nnenna ta bude ya zuba Mata kudin da shayibu ya basa nata kana ya Kara Mata 100k a ciki,Lahab a sannu sannu ya Fara Zama sannan ne a fagen kwallon kafa don sosai ya iya buga wasa hakan yaja Masa farin jini da daukaka har yasa wasu team Fara daukar sa haya Yana buga musu Wasa ba tare da sun damu da kankantar sa ba kudi kuwa sosai ya Soma damkarsu sosai Kuma Alhamdulilah Lahab mutum ne da baida gyashi kome ya samu sai ya tsamma Rahab dake India da uzaifa haka zalika zaisa wa Nnenna a account nata duk da Bata cin Koh sisi haka zalika Adewale don yanzun tuni Suka bar gidan da suke lahab ya Kama musu gida Mai zafi wadacece Suka koma ciki don wani sa'in sai afi wata Ade Bai hadu da Nnenna ba waje d'aya sai in ya shigo part nasu Lahab ga moto Lahab ya saya ya saima Ade duka rayuwa tayi Dadi bana Wasa ba tuni papan Ade yayi sanyi lokacin da ya kawowa Ade ziyara yaga yanda Allah ya daukaka Lahab Kuma Yana taimakon dansa har dawainiyar makarantan Ade yanzun Lahab keyi,Amma tuni ya manta da zancen wani Nabeel don tunda yazo kasan Bai taba kiransa ba saidai in Suna waya da Ade in Yana gun shine inya tambaye shi sai Ade yace gashinan su gaisa. Lahab sun koma makaranta tuni har semester yayi nisa yaso yasa Nnenna a makaranta Amma babu Hali tunda Bata da shaid'an takardun Gama secondary,ga rigimar da take fama da ita nata na masifa ga yawan ciye ciyen kayan fruit don yanzun tabar apply ta koma kankana da mangoro Koh Kuma abarba. Lokacin da labarin Lahab ya Fara zaga katsa tuni Yan nageria Suka Soma Jin labarin sa wani Dan naija best footballer Kuma very young a turai gashi da farin jini bana Wasa ba duk channel na sport ba'a rasa nasa a ciki,lokacin da labari ya Fara riskan Mami tunda ba kallon kwallon take ba sai Yan uwa ke kiranta Suna cewa sunga Lahab na ball a TV koransa tayi tana Masa fada akan an turasa karatu yaje ya Kama abinda bazai amfane saba Bata yarda ba,Aiko waya yayiwa Abbu ya sanar dashi dare da Masa Alkawarin insha Allah zai kammala karatunshi tare da sakamako Mai kyau daker dai Abbu ya sauko ya baiwa Mami hakuri ya cigaba da Wasa tunda sunga kokarin da yayi a karatu. tun safe Lahab ya fita Bai dawo ba saboda Wasa da suke bugawa Mai zafin gaske bashi ya dawo gida ba sai kusan 2 na dare,shigowa falon yayi ba tare da ya kunna wutan ba ya wuce sait nasu bude dakin su yayi ya shiga da sallama,dan waro Ido yayi ganin wutar dakin a kunne ga Kuma Nnenna kwance a bargo"Kai amma yarinyar Nan bakiji taya Zaki kwanta da wuta a kunne"kashe wutan yayi ya zaro tafkeken wayarsa dake bag dake bayansa ya kunna hasken waya aje bag in yayi yadau towel ya nufi toilet wanka yayi kana ya fito,daure da towel in kayan bacci yasa ya fita a dakin kitchen ya wuce ya tare coffee nasa Mai zafi ya zauna a dinning dake cikin kitchen in ya Soma Sha Saida yasha Rabin cup kafun ya mike. d'akin ya shiga tare da matsowa kusa da gadon hannun sa yasa ya warware blanket Inda ta lulluba zai kwanta da Sauri ya sake blanket in, saboda turirin da yaji ya fito daga cikinsa har yanajin wucin numfashinta Mai zafi Ashe idanunta biyu sai rawan d'ari take hannu yasa ya tabata da Sauri yaja baya zafi jikinta jaujau"subhanallah Labiba tun ba yauba nasan baki da lafiya amma rashin jin da Kika kakkabawa kanki yanzun ya hanaki Bari muje hospital"?kasa amsa Masa tayi bakinta ya bushe sosai hakoranta har haduwa suke da juna,mikewa yayi da sauri ya nufi wardrobe nata budewa yyi ya dauko Mata wando da riga amma irin bujennan masu Fadi yasa Mata hijab ya dauko cikin Wa'inda ya sai Mata duk da ba amfani yake dasu ba Kuma hijab in irin have Sunnah ne. A daren nan Lahab ya dauketa sai Wani hospital Mai tsada, a cikin daren Nan aka amsheta zuwa lokacin zazzabine yaci karfinta sosai ruwa Suka daura Mata tuni tayi bacci sai gwaje gwaje da aka mata,a asibitin Lahab ya kwana tare da ita tana farkawa da safe ta Fara Neman abinci Kuma ta tashi garau abinta,fita yayi ya sai Mata abinda zataci taci kana aka sake daura Mata ruwa. 8:21pm zaune Lahab yake a Kan kujeran dake dakin dayake kowani mutum d'aya dakinsa ne guda ba'a had'a wani da wani zaune take ta tasa kaza a gaba tana ci hannun ta d'auke da ruwa a makale, don Koh barin a cire batayi ba ta Soma ci shi Kuma Lahab ya Barta Bai Kira nurse ba gudun kada ace ya kawo cinnedu amusu dariya,wayarsa ne yayi Kara zarowa yayi yayi picking up"Lau Ade Labiba ce babu lafiya Muna hospital amma karka damu fa jikin da Sauki sosai"yayi shuru Yana sauraran abinda Ade ke cewa sai Kuma yace"no ka tafi school kawai yauma sukace zasu sallame mu basai kazo ba sai Kuma ya katse wayar"Kara kallonta yayi ganin tana tauna kashin kaza"Amma wallahi kin chanja haba Dan Allah kece ci Kamar me Amma Baki karuwa sai ma rama da kikeyi sai haske amma dai ba kome hips da breast sun ciki"? Kala batace Masa ba dan yanzun Sam babu irin kunyan da a tsakanin su bare taji kunyar sa Koh kunyar abinda yace"amma dai da ace bakicin nama har yanzun da anyi babu ke tsabar dadi har kashin cinya kike tumurmusawa,dan Allah kici Naman dake gefen plate in kibar kasusuwan Nan in Naman ya Kare Zan sayo Miki wani amma ace mutun ya aje nama ya kamacin kashi salon wani ya shigo muji kuny..................bai karasa ba aka bude kofar dakin da Sauri Nnenna ta sake kashin hade da boye plate in gudun Kar aga taunannun kasusuwan data aje a ciki. Dariya kawai Dr tayi ta karaso cikin dakin,hade da turo kujera d'aya ta zauna kusa da Lahab kana ta kalli Nnenna ta kalli Lahab tace"Kamar u look familiar"dan murmushi yayi yace"Hassan Lahab the footballer"?oh oh really great footballer nice to meet,am Dr jeme John by name"hannu lahab ya Bata sukayi musabaha, don tsohowace ba yarinya ba,had'a fuska Nnenna tayi amma batace kome ba kallon ta again Dr tayi tace"gaskiya ya Kamata ki fito da abinki kici gaba daci,ba kunya ta dauko plate nata taci gaba dacin Naman Amma Bata tauna Kashi, kana tacewa Lahab wacec ita Nnenna a wajen sa"? dan shuru yayi sai Kuma ya cije yace matarsa ce, waro Ido baturiyar tayi ya nuna Nnenna yace matar ka?gyada Mata Kai yayi, shuru tayi don ita duk zatonta Koh yar'uwa Koh friend ne Koh girlfriend,tunda taga irin kyau da Nnenna kedashi gashi zaman turai ya karbeta sosai tayi fresh da ita sai Kuma ta d'aga kafada kana tace,ok anyway congratulations ur wife is pregnant. Ji kake karaaararam plate na nama ya Fadi a hannun Nnenna saiga hawaye Shar mikewa tsaye Lahab yayi da karfi yace"what?........................... da mamaki Dr tace yes she is pregnant bakace wife nakace ba"?komawa Lahab yayi ragob akan kujera gabaki d'aya yanayin sa sun sauya sabanin Nnenna da tayi shuru tana dai zaune a Bakin gado ba yabo ba fallasa ta sanya hannayenta ta cikin rigan tana shafa cikin,da Sauri Lahab yace"how many months ne Dr,Mika Masa result na hannunta tayi jikinsa a mace ya karba yayi Sai Kuma ya rumtsa idanunsa da karfi cikine na wata uku da sati uku,kallon Nnenna yayi sai yanzun yaga irin chanjawar da tayi amma dai ckinta Na nan a shafe Kamar babu halitta a cikinta. Shuru yayi Bai Kara magana ba haka zalika itama Nnenna batace kome ba har ruwan ya Kare aka sallame su tare da bude Mata file na zuwa Ayo a wajen su,haka suka Kama hanyar silently Suka koma gidan yayi parking budewa yayi ya fita ba tare da yajirata ba itama binsa tayi a baya hannu yasa ya bude kofar flat nasu, Adewale dake zaune a falon tun safe mikewa yayi Yana tambayar Lahab Ina Mai jikin,bai rufe Baki ba sai gata ta shigo,wucewa dakin sa Lahab yayi ya maida kofar ya rufe ba tare daya baiwa Ade amsa ba sai Nnenna data tsaya Suka gaisa ya tambaye ta jikin nata kana itama ta wuce dakin ta. Tura kofar dakin Lahab yayi ya Shiga zaune ya gansa yayi tagumi,tsayawa yayi a bakin kofar ya harde hannu don har lokacin Lahab baisan ya shigo ba,matsowa yayi ya dafa shi sai a lokacin ya dawo hayyacin sa ya kalli Ade sai Kuma ya sake tsaki"Wai Lahab lafiya meke faruwa ne wai me akace Yana damunta donni Karan kaina Naga Rama a tattare da ita Kuma kace tanacin abinci sosai"?Mika Masa paper kawai Lahab yayi Baiyi magana ba"amsa Ade yayi ya duba sai Kuma ya sake murmushi yace"daman irin wannan Rana nake guje maka Lahab shiyasa tun farko na nuna maka illan wannnan sure da zakayi" "Wallahi Ade nayi auren Nan bada niyar a waye gari tayi ciki ba"oh kana nufin ka aure tane don ka ringa sex da ita karta haifi Y'ay'a Kamar kowace mace"?bazaka gane ba Ade taya Zan dau ciki Koda nakai nageria a matsayin nawa kasan Abune Mai girman gaske" Cikin mamaki Ade yace daman tunda ka Fara kwanciya da ita baka tanadi abinda zaka fadawa gidan ku ba akanta nufinka Randa zaka koma gida rabuwa zakuyi Koh yaya"Koh saboda yanzun ka zama celebrate shiyasa bazaka iya Zama da ita da ciki ba"?da Sauri Lahab yace Ade bazaka gane abinda nake nufi ba wallahi Koh sau daya ban taba tunanin rabuwa da Labiba ba Amma Ina Jin tsoron kada mu tafka kuskuren da bunayya da muwaddat(Aisha bagudu)sukayi"Aiko ku kunma fiso tunda su Koh banza iyayen su Sunsan da auren jama'an garine Basu sani ba dasu kansu ma'aurantan Saida Suka tafka aika aika Amma daga karshe duk da haka an Kira cikin ta da shege bare kaida babu Wanda yasan zance. Yanzun Ade menene mafita"mafita dayane Lahab ta haihu ka tattarata ku koma nageria Kama danginka bayani insun amince ai shikenan"wani kallo Lahab ya Masa kana yace karfa ka manta bari na tuna maka Nnenna suspect ce a naija komawarta yanzun bazaiyu ba haka zalika tinkaran iyayena yanzun matsala ne babba kawai Ni na yanke shawara za'a zubar da cikin kawai muyi planning sai lokacin da Zan koma nageria Inna kammala karatu saimu koma daidai lokacin case nata ya mutu" Kai Lahab kana da hankali kuwa an gaya maka Nan nageria ne da zubar da ciki ya Zama abin sauki cikin ma na wata uku Yana kokarin shiga na hudu Koh kunyar halinda yarinyar mutane zata shiga bakayi toh wallahi karka kuskura karka Fara abinda zaija maka matsala a kasan Nan kaji na gaya maka" "Koh baka fada Masa ba Ni bazan amince ba"juyawa dukan su sukayi wa zasu gani Nnenna ce Wance ke tsaye rike da kofa ga dukkan alamu ta Jima a wajen,sai hawaye kebin kumatunta bata taba tsammanin hakan daga wajen Lahab ba Wai zubda ciki"mikewa yayi yace"ciki Kam tunda Ni nayi nace a zubar Koh y'ay'a d'ari kike so daga baya mu Haifa Amma Banda yanzun kwata kwata shekaruna nawa da Zan kakkabawa kaina yaya"? "Lahab bazan taba zubar da cikin Nan ba,domin shikadai ne ya ragemun Wanda Zan daga hannu na nuna nace ga dangina nan Banda kowa nawa sai shi Taya Zan zubar in Kuma Banda rabon wasu cikin a duniya fa sai wannan fa Kai kana da daman aure amma Ni har abada ka cuceni"Zan rike duk abinda na Haifa Koda kuwa baka so ni Mai iya cewa ba d'anka bane,Ni Zan zamo Masa uwa da uba bazanji kunya ba,amma wallahi banda zancen zubarwa Ina son jinina Ina son cikina Koda kuwa kowa zai gujeni"mikewa Lahab yayi Yana nuna kansa kana yace"Ni kike gayawa haka"an gaya maka Lahab na gaya maka indai akan cikin Nan ne"toh nace bana bukatar cikin"Ni ina ruwana Kuma daga yau Ina so ka manta cewa akwai sure a tsakanin mu da Kai haka zalika bazan Kara cin abinda ya zamo naka ba muddin dai zanci yaron cikina ya rayu" Juyawa tayi tabar dakin tana kuka,kallon sa Ade yayi cikin tausayin su duka don wallahi sun basa tausayi yace"Lahab karka kuskura ka sake zancen zubda cikin Nan itace uwa ita keda ra'ayin haihuwa Koh ah ah don haka ka zamo Mai adalci,karfa ka manta Koh a addinin ku haramun ne abortion ka kula da ita Lahab ka tausaya Mata,daga haka shima yasa Kai yabar dakin,har yamma Lahab na dakin sa,mangariba nayi yayi sallah mikewa yayi ya shiga toilet,wanka yayi ya fito ya sanya Kaya fita yayi a dakin ya leka kitchen yaga kome net babu alamun ma Nnenna ta dau wani Abu a ciki. Fita yayi ya sayo musu abinci laida biyu bude kofar dakin nata yayi ya shiga zaune take da kayan da Suka dawo asibiti Koh chanjawa batayi ba idanunta jawor da gani tun kukan safe da tayine Suka rine,shigowarsa baisa ta motsa daga inda take ba aje laidan yayi ba tare da yayi magana ba ya fita a dakin,washe gari da safe Kamar yanda ya aje Mata laidan haka yazo ya gani da mamaki yake kallon ta sai Kuma ya kasa hakuri yasa hannu ya dago blanket in, kwance take amma Bata dago ba"meya hanaki cin abinci"?ba abinda ya shafeka bane"abinda ya shafeni ne Mana kina ikiraren kinason abinda ke cikin shine kikeson kasheshe da yunwa" Wani kalllo ta Masa sai Kuma tace"babu ruwan ka daya mutu Koh yayi Rai aikai farin ciki ya Kamata kayi sai Kuma ta Mike ta shiga toilet tare da banko Masa door,fita yayi a dakin ya wuce flat na Adewale zaune ya samesa Yana karyawa abincin gaban nasa Lahab ya Iba da yawa kana ya koma dakin Nnenna ya aje Mata yabar gidan,haka Suka cigaba da rayuwa kwata kwata Nnenna ta d'auke wuta fadan Mai ciki Bata shiga harkan Lahab abinci ma badon karta mutu da yunwa ba da bazataci ba gashi inta dafa da kanta baya Mata Dadi a Baki amma dataga uwar Bari ci take shi Kuma Bai fasa kawo Mata ba,tun tana dari dari karya sa Mata maganin zubda ciki harta cire tunanin abin a ranta amma Sam Bata yarda sun sake kwana daki d'aya ba ta tatttarasa ta watsar duk lokacin da taji sha'awa na taso Mata saidai ta shiga ruwan dumi shima Bai wani shega harkan nata iyakansa bata abinci akan kari yazo ya duba yanda ta waye gari. ************* Wasan Lahab ya Fara gaba gaba don yanzun Yana iya barin kasan America ya tafi har wata kasa ball sai dai duk lokacin da zai tafi zai barwa Ade nauyin kula dacin Nnenna Kuma ba laifi shima Yana iya bakin kokarin sa,yau Monday Nnenna ce ta fito daga dakin ta sanye da siker da riga ta dau jakanta ta rataya a kafada sai takalmin ta flat gashinta a sake har gadon baya fitowa tayi daga part nasun ta fito compound na gidan,Lahab dake zaune a waje Yana Shan iska mikewa yayi ganinta tsaye a bakin titi. Ina Zaki"?kauda fuska tayi ba tare da tayi magana ba,"ba magana nake Miki ba"?Nan ma shuru ta Masa ta tare taxi zata Shiga hannu yasa ya fizgota saura kad'an ta buge da marfin data bude janta yayi Suka koma ciki cikin bacin Rai yace"har zanna tambayar ki kina rainamin wayo Ina Zaki a hakan babu lullubi"kaga Lahab baison surutu da ranan Nan akan me Zan fada maka Inda zani,maganan lullubi Kuma Ni ba musulma bace"dagata yayi sama Suka koma ciki hijab karami ya d'auka ya saka Mata tare da kwace jakan budewa yayi ganin takardun asibiti ne hannunta kawai ya Kama ya rike jakan a daya hannun sa Suka fita daga gidan. Asibiti Lahab ya wuce da ita aka Mata awo ba karamin shauki ya shiga ba lokacin da likita ke sanar dasu tagwayene a cikin Nnenna amma Bai wani nuna murna a fili ba,wayarsa ya d'auka ya d'auki hoton na'ura daya nuna yaran baro baro Suna kwance gasunan mitsitsi dasu yan 6 month's,kana ya dauketa tana zaune akan gado lokacin likita na Mata bayani ya had'a harda likitan dashi ya d'auki hoto likita sai dariya take don wallahi ita abin ma dariya ya Bata don kwata kwata Basu wuce 19year's ba a lokacin,Suna fitowa Suka samu wata Mata da miji zaune Suna jiran su fita Suma su shiga cikin matan ya girma don zaikai wata 8 sai kallonsu Mata da mijin Suke shidai Lahab baice kome ba ya Kama hannunta Suka fita, saloon ya kaita aka wanke Mata Kai da kafa ya biya duka,don lokacin cikin nata har ya fito ras dashi kowa ya ganta yaga Mai ciki ga jiki data juga Kamar me wuyanta har wani guru guru yayi na jiki ga haske Wanda Bai sani ba zai tsammaci bata had'a dangi da bakaken fata ba. ********************* Su Lahab an kammala exam na karshen shekara Kuma na chanja aje sun samu dogon hutu na karshen shekara tunda Yan nageria sukaji kammala exam nasu suke sauraron ranan da uban gayyan zaice zasu kamo hanya,Lahab yayi kudi iya kudi yanzun Harya mallake gidan kansa a turai da mototi,sai dai har gobe Basu dawo normal da Nnenna ba lokacin da yaji bukatar matarshi ya tasashi a gaba yaje neman hakkinsa tace batasan zancen ba,shikenan shima ya ajeta a gefe yasa karatu a ga Kuma Alhamdulilah abinda ake tsammani shiya samu yau sati guda da kammala jarabawan,zaune yake a falo shida Ade Suna hiran wasan da Lahab a buga anan Ade ke kawo Masa zancen komawar su gida"gaskiya Ade kayi tafiyarka kawai wallahi Ni bazan iya zuwa Koh Ina ba" da mamaki Ade yace saboda me"saboda bazan iya tafiya nabar Labiba da cikin 8 month's a jikinta fa,karfa ka manta dogon hutu Muka samu akallah mukai 2 to 3 months a chan nasan halinda zata Shiga bayan babu mu Ina wallahi ah ah"kaga Lahab Bai Kamata ka musu haka ba nasan kana da uzuri a gaban ka amma fa ka sani Suma Suna da hakkin akan ka,Mamu shekara guda Bata saka ka a idanunta ba haka ma Rahab tuni sun koma nageria Kai ake jira"Wai Ade da wani yare Zan maka bayani ka fahimta ne nace maka bazan iya tafiya nabar Nnenna ba" Amma Lahab tunda Allah ya hore maka why not ka samu wata dattijuwan baturiya ta zauna ta kula maka da ita ko haihuwarce ya tashi ai akwai wata a kusa"wani banzan kallo Lahab ya Masa irin na baka da hankalin Nan"Ade taya Zan bar matata a hannu bayahudiya salon a haifamin yara biyu ta sabe daya ta gudu Koh ace sun mutu saboda da Bata da tsayaye gwara Ina Nan"shuru Ade yayi h?ar Lahab ya gama surutun sa kafun yace"toh nidai Ina kewar kasata Kuma zanje Naga iyayena"Allah ya bada sa'a babu Inda zani harsai Naga gudan jinina a doron kasa"yanzun me zakace musu a matsayin excuse naka" Cewa zanyi Muna da wasa a France kawai"uhmmmm shine abinda Ade yace Suka cigaba da Hira Nnenna dake cikin kitchen tanajin duk abinda ke faruwa sosai taji zuciyarta tayi sanyi Jin Lahab har yanzun ya damu da lafiyar ta Koda yake ai ya damu da lafiyar ta ya bai damu da lafiyarta ba ai da ta Jima bata gidan sa,ta yarda Lahab na sonta baba Wasa ba. Allah sarki Lahab bai sanar da gida bazai dawo ba har Saida Adewale ya koma nageria kafun ya sanar dasu sosai ran Mami ya baci tayita fada Akan wasan banza zaiki dawowa hakuri kawai ya Bata,yau tun safe lahab Suka shirya dashi da Nnenna zasu hospital cikin Nan gashinan tirim a gaba sanye take da polon wando sai riga bankacece har gwuwa Mai dogon hannu cikin Nan a gaba gyale tayi rafen nasa a kanta,ta sanya boot a kafarta,Lahab ma sanye yake da kananu kaya,motar ya bude Mata ta shiga Suka wuce hospital,Suna Isa facemask ya d'auka ya sa gudun kada mutane su Soma daukarsu hoto a watsa a duniya ya shiga uku tunda yanzun shima ya Zama popular Koh Ina ya Shiga hotuna ake masa,yauma anyi sa'a sun hadu da mutumin da suke yawan haduwa dasu in sunje asibiti awo matar sa mai ciki Amma ayau sun hadu dasu ne lokacin da suke Shirin shiga mota sai ga Matar da mijinta sai wata tsohowa da baby a hannunta daga gani haihuwa matar tayi Kuma an sallame su,Suka nufi motar su Suma ba tare da sun kula dasu Lahab ba duk da daman duk haduwar su basa magana duk da bakaken fatane sai dai su ringa kallon su Lahab shikuma kallon ke hanasa musu magana tunda barikine kowa zaman kansa yake ba irin Naija bane mutun zaice wane ya ganni Bai gaisheni ba" Shiga Nnenna tayi Lahab ya shiga Harya tada motar bayan ya zare facemask in fuskarsa sai Kuma ya tsaya ganin motar gayen Taki tashi gashi lokaci d'aya aka Fara yayyafi fitowa sukayi daga motar zasu koma cikin hospital in,da Sauri Lahab ya fito a motarsa hade da musu sallama,da mamaki mijin ya amsa hade da basa hannu Suka sake gaisawa,kafun Lahab yace in babu damu suzo su shiga ya rage musu hanya,tsohowar taso ki amma data ga Nnenna a cikin motar saita amince suka shiga baya gabaki dayan su Lahab yaja mota. "**************** Kamar nasan fuskar nan taka in ban manta ba Kamar Hassan Lahab Koh?"gyada Kai kawai Lahab yayi,wow gaskiya naji dadin haduwa dakai Ni Sunana Muhammad Auwal wannan iyalina ce Hauwa amma ana kiranta da jidda sai mamata gata ?"nima haka" shine abinda Lahab yace,shuru mutumin yayi ganin Kamar Lahab baison hiran,tsohowar Kam kasa hakuri tayi tace"yaro wannan Yar uwarka ce"saboda ita haka kawai taji ta Kosa Taji menene a tsakanin su tunda matar d'anta tace Mata ai Suna haduwa dasu a hospital sa'i da lokaci Suna zuwa"har Lahab ya bude Baki zaice matar sane Nnenna ta rigashi da cewa"kaninta ne"wani kallo Lahab ya Mata amma baice kome ba yaji matar na hausa da d'anta don a zatonta ko su Nnenna basajin hausa don Basu Mata Kama da Yan nageria ba Nnenna tafi Mata Kama da Yan Ethiopia harda Lahab in ma duk da bakine amma kyakkyawa ne sosai,gulmansu ita da matar suka Fara tana cewa ai wallahi itama Saida tayi tunanin Koh Yan uwane amma meyasa kullum Lahab ke rakota,da Sauri mijin yace"gaskiya mama ya Kamata kuyi shuru babu Dadi Kuma cikin mutane kuma yare zasu tsargu bare Kuma wa'innan da kuka jefawa tambaya. Murmushi Lahab yayi don yasan Nnenna ba wani fahimtar hausan take ba"mata tsohowan ne tasake jefowa Nnenna tambaya tace"aiko gaskiya yayi tsawon kafa dubeshi Kamar wani yayanki amma ku Yan Ethiopia ne"?haba dan Allah mama kiyi shuru Mata"yaron ya tareta da Sauri Lahab ma juyowa yayi yadan kallesu kana yace"munata tafiya Baku fadamin address naku ba"fada Masa sukayi da mamaki yake kallonsu don kuwa gidan sane manne dana mutumin amma baice musu Suna waje daya ba don baya fatan yayi makwantaka da tsohowar Nan sarkin surutu. Wuce kofar gidan sa Lahab yayi ya tsaya a kofar gidan mutumin bude kofar sukayi Suka fiffito mikawa tsohowar laima Lahab yayi dake cikin motar sa gudun sanyi kada ya Kama babyn,sai a lokacin ya musu barka da samun haihuwa itama Nnenna ta musu barka harda karban baby tayi ta kalla kafun ta maida musu, number Lahab mutumin ya karba Yana ta godiya kana Suka shiga ciki Lahab Kam reverse yayi ya nufi nasu gidan. tunda cikin Nnenna ya shiga wata tara shikenan Lahab ya tattara wasan kwallo ya aje a gefe ya koma zaman gida tunda babu makaranta Suna jiran lokacin haihuwarta,yau tun safe lahab yace Nnenna ta shirya bayan sunyi breakfast shiryawa sukayi ita dashi Suka fito zasu fita sayyayyan kayan yara da zasu sayo yayi-yayi ta Masa list yaje shi kadai tace shida baya kaunar yaran yake ba tasan bazai sayo Abu Mai kyau ba,lokacin da Suka fito compound ganin da gaske zata bisan yasa da tsayawa yace"Amma so kike kije ki haihu a hanyane Koh"ai Dr yace saura 2 weeks"da dariya yace waike kin amince da maganar Dr Koh yau in Allah ya nufa Zaki haihu"da masifa tace koma me zakace kace sai make"abinka da gidan turawa na wancan gidan na kallon na wannan kawai cikin magana sukaji an kwala Masa Kira Yana juyawa da mamaki ba kowa bane sai tsohowar Nan tsaye a baranda tana murmushi tare da tafa hanneye daga nesa yaji muryarta Kamar Ansa lasfika tsabar karfi tana cewa"daman Nan ne gidan ku D'an ball ban sani ba ai dana ringa shigowa na huta da zaman kadaici, Kanna kowa saina ringa zuwa wajen mamanka............................... *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 08084453785 tare da shaidan biyan ki* *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 08084453785 tare da shaidan biyan ki* Wai menene haka don Allah meyake damunki"?girgiza Kai tayi tana kokarin kaucewa zata aje laidodin sake Mata hannu yayi ya kwace laidan yaja hannunta ya Kamota Zama yayi da ita a bakin gadon shima ya zauna kana yace"Wai meke faruwa ne na ganki cikin damuwa Kuma kincemin babu kome"?matsa Mata yayi lalle saita fada Masa meke damunta kuka ta fashe dashi sosai cikin Sauri ya rungumeta gam a jikinsa ya koma baya-baya ya kwanta da ita a jikinsa,Yan@ kwance a dollof ita tana kwance a kansa,hannu yasa ya kashe wutan. Labiba"ya Kira sunan ta a hankali kin amsawa tayi har lokacin hawaye bai tsaya a fuskarta ba,a hankali ya manna bakinsa a kumatunta hawayen Nata yake lashewa,lumshe Ido tayi tana d'an sake jikinta a nasa sosai ya lashe hawayen tas Kuma hawayen ya daina zuba,dan Jan lips nasa yayi a fuskarta har zuba gefen lip's nata sannan ya tsaya Yana bin fuskar da kallo,idanunta a lumshe suke jira kawai take taji saukan lips nata a nasa amma taji ya tsaya cak,dan bude idanunta tayi sai Kuma da Sauri ta kauda nata saboda tsayuwa da yayi kawai Yana kallon ta,"kin koshi da abincin Koh a kawo Miki wani"?girgiza Kai kawai tayi batace kome ba,sakin murmushi yayi a hankali ya zamar da ita a jikinsa ya kwantar tare da gyara Mata rufuwa shima ya rufu tare da kamo hannunta ya rike Yana bin fuskarta da kallo kawai. A hankali ta matso kusa dashi tare da manna jikinta a nasa,waro Ido yayi da mamaki sai Kuma yasa hannu ya dagata jabal ya daura a kansa,lip's nata ya Kama amma bai tsotsa ba kawai mannawa yayi da nata,dan Jimm tayi sai Kuma ta Kama lips nasa na kasa cikin sanyi ta tsotsa,Kama nata yayi Suka hau bawa juna hot kissing sosai salon wasan ya chanja duk wani kunya kunya gabaki dayansu ajesa sukayi a gefe sosai Lahab ke sarrafa matarsa yayinda ita Kuma ke basa goyon Baya dari bisa dari,lokacin da kome ya kankama Lahab yasha mamaki matuka Kuma ya rude don dadin da yaji na yau ya d'ara na Ranan dadin da yaji sosai. Lokacin da nutsuwar sa ta samu kokarin tashi yake a kanta da Sauri tasa hannu ta Kama waist nasa gam,Wanda hakan ya fahimtar dashi cewa itama tana bukatar nutsuwarta duk da akwai mutuwar jiki da gajiya a jikinsa hakan baisa sa kasa tallafawa matarsa ba sosai ya tallafeta har ta samu natsuwa,mikewa yayi a hankali ya d'auki towel NASA wanka yaje yayi kana ya fito mikewa tayi itama ta shiga toilet in kafun ta dawo Harya chanja zanin gadon ya kwanta,tana fitowa Zama tayi daga ita sai towel,shuru shuru yaji Bata hau Kan bed in ba kallonta yayi kana yace"lafiya bazaki kwanta ba kinsan karfe nawa yanzun"?shuru ta Masa Bata hauro Kan gadon ba,shima Bai Kara magana ba ya gyara kwanciyar sa so yake ya samu bacci kafun asuba don gobe Suna da training da sassafe,amma kasa baccin yayi ya sauka akan gadon d'aukarta yayi gabaki dayanta yazo ya kwantar akan gadon ba tare da ya damu da towel in jikinta ba ya lulluba Mata blanket. ************ tashi tayi ta zauna again Wanda hakan ya saka sa sake tashi agogo ya gani kusan 2:30 na dare tsaki kawai yayi yace"Wai don Allah wannan ai d'aukar alhakine ya Zaki kasa bacci ki hanani nima"?a fusace tace"toh ninace maka karka kwanta ne"toh Taya Zan kwanta kina zaune"a hankali tace"yunwa nakeji"wani kallo ya Mata sai Kuma ya tashi tsaye hannu yasa ya taba jikinta Jin sanyi babu zafi yasa sa komawa ya kwanta abinsa Bai Kara magana ba ya barta a zaune bacci barawo yayi awun gaba dashi. da asuba Lahab daya farka da mamaki Nnenna ya gani d'aure da towel Kamar yanda ya kwanta ya Barta idanunta biyu da mugun mamaki yake tambayar ta Wai Bata kwanta ba?kin amsa Masa tayi yasa hannu zai tabata kawai ta turesa Saida ya koma Kan katifa ya kwanta,bata Kara magana ba shima gyada Kai yayi irin lallai innan ma, ya mike Alwala yayi yazo yayi sallah duk tana zaune,Kaya ya chanja ya fita waje da asuban amma shuru babu kowa shaguna duk a rurrufe dakin wani makwancin sa ya shiga yadau fresh milk guda biyu ya kawo Mata kin karba tayi Wai tayi fushi daker ya samu ta karba tana Sha Koh aje goran batayi ba ta Soma amai Kamar zata amayar da hanjin cikinta sosai tayi aman lokaci d'aya wani irin zazzafi ya rufeta,daukarta yayi ya Kai toilet tare da wawwanke Mata jikinta ya fito da ita, Kaya ya sanya Mata ya kwantar da ita akan gado kafun yazo ya gyara wajen da ta batan. Wanka yayi da misalin karfe 6 zuwa lokacin wani irin bacci yayi gaba da ita so yake suje asibiti Kar ciwon yayi tsananin amma ganin tana bacci tunda bata samu na daren jiya ba sai yayi tunanin bari ya barta sai ya dawo,kayan ball yasa wando da riga sai takalmi ya fita a dakin, direct training ya wuce basu Suka bar wajen ba sai kusan 9 na safe daga wajen wajen Saida abinci ya wuce kaza yasai musu sai kayan ciye ciye na laida Incase kada ta bukace Abu lokacin da bazai samu ba shiyasa ya sama Mata irin su cake su pizza duk ya sassaya sosai ya Mata sayayya. Lokacin da ya dawo ya samu ta farka zaune take gabaki d'aya ta jirkita ganinsa da laida Koh barin ya ajiye batayi ba ta kwace tare da budewa cake Inda ta gani a ciki shita warware da Sauri ta Soma ci ci bana Wasa tama cake in ba,shidai Lahab idone nasa ba bakin magana amma yasan tabbas Bata da lafiya wallahi irin wannan haukan cin Kamar Wanda ta shekara da yunwa,Kamar d'azun da asuba tana gama ci sai amai,ganin haka yasa Lahab cewa ta tashi su tafi asibiti amma kai da fata Nnenna tace ita lafiyarta klau babu Inda zata,taba jikinta yayi yaji babu zafi Kamar d'azun, tambayar ta abinda zataci yayi tace apply,mikewa yayi yaje ya jido apply kwali guda fresh dasu yazo ya jera Mata a daki Aiko shikenan Nnenna ta samu abinci Bata da aiki saicin apply tunda kome taci amai yake sata Amma Banda shi. Lahab yaga ikon Allah gabaki d'aya Nnenna ta sauya ta Zama mabukaciya don tun tana kunyarsa tana jiran shiya Fara tabata Harya kasance ita ke nuna tana sonsa a aikace ba'a bayyane ba,shima Yana iya bakin kokarinsa wajen sauke nauyin da Allah ya daura Masa akanta Koh da kuwa baya mood,ga cin apply ga fad'a fushi da mita duk yanzun Nnenna ta koya cikin satin da sukayi harta chanja Sosa ga yawan zazzabin asuba da kuma yamma, sai yace su tafi asibiti tace bazata ba suyita fada Harya hakura ya kyaleta. Sun samu nasara sosai Lahab Yayi bajinta a wasan da suka buga yasha musu sosai,hakan yasa sa daukaka sosai,sun koma gidan su,sannan team nasu sun basa kudi sama da million biyu cikin abinda Suka samu saboda bajintarsa cikin kudin ya baiwa Ade have million sannan ya turawa Rahab 300k ya baiwa uzaifa 200k tunda Sunsan Inda kudin ya fito lokacin da ya tura musu basuki amsa ba account ya Kai Nnenna ta bude ya zuba Mata kudin da shayibu ya basa nata kana ya Kara Mata 100k a ciki,Lahab a sannu sannu ya Fara Zama sannan ne a fagen kwallon kafa don sosai ya iya buga wasa hakan yaja Masa farin jini da daukaka har yasa wasu team Fara daukar sa haya Yana buga musu Wasa ba tare da sun damu da kankantar sa ba kudi kuwa sosai ya Soma damkarsu sosai Kuma Alhamdulilah Lahab mutum ne da baida gyashi kome ya samu sai ya tsamma Rahab dake India da uzaifa haka zalika zaisa wa Nnenna a account nata duk da Bata cin Koh sisi haka zalika Adewale don yanzun tuni Suka bar gidan da suke lahab ya Kama musu gida Mai zafi wadacece Suka koma ciki don wani sa'in sai afi wata Ade Bai hadu da Nnenna ba waje d'aya sai in ya shigo part nasu Lahab ga moto Lahab ya saya ya saima Ade duka rayuwa tayi Dadi bana Wasa ba tuni papan Ade yayi sanyi lokacin da ya kawowa Ade ziyara yaga yanda Allah ya daukaka Lahab Kuma Yana taimakon dansa har dawainiyar makarantan Ade yanzun Lahab keyi,Amma tuni ya manta da zancen wani Nabeel don tunda yazo kasan Bai taba kiransa ba saidai in Suna waya da Ade in Yana gun shine inya tambaye shi sai Ade yace gashinan su gaisa. Lahab sun koma makaranta tuni har semester yayi nisa yaso yasa Nnenna a makaranta Amma babu Hali tunda Bata da shaid'an takardun Gama secondary,ga rigimar da take fama da ita nata na masifa ga yawan ciye ciyen kayan fruit don yanzun tabar apply ta koma kankana da mangoro Koh Kuma abarba. Lokacin da labarin Lahab ya Fara zaga katsa tuni Yan nageria Suka Soma Jin labarin sa wani Dan naija best footballer Kuma very young a turai gashi da farin jini bana Wasa ba duk channel na sport ba'a rasa nasa a ciki,lokacin da labari ya Fara riskan Mami tunda ba kallon kwallon take ba sai Yan uwa ke kiranta Suna cewa sunga Lahab na ball a TV koransa tayi tana Masa fada akan an turasa karatu yaje ya Kama abinda bazai amfane saba Bata yarda ba,Aiko waya yayiwa Abbu ya sanar dashi dare da Masa Alkawarin insha Allah zai kammala karatunshi tare da sakamako Mai kyau daker dai Abbu ya sauko ya baiwa Mami hakuri ya cigaba da Wasa tunda sunga kokarin da yayi a karatu. tun safe Lahab ya fita Bai dawo ba saboda Wasa da suke bugawa Mai zafin gaske bashi ya dawo gida ba sai kusan 2 na dare,shigowa falon yayi ba tare da ya kunna wutan ba ya wuce sait nasu bude dakin su yayi ya shiga da sallama,dan waro Ido yayi ganin wutar dakin a kunne ga Kuma Nnenna kwance a bargo"Kai amma yarinyar Nan bakiji taya Zaki kwanta da wuta a kunne"kashe wutan yayi ya zaro tafkeken wayarsa dake bag dake bayansa ya kunna hasken waya aje bag in yayi yadau towel ya nufi toilet wanka yayi kana ya fito,daure da towel in kayan bacci yasa ya fita a dakin kitchen ya wuce ya tare coffee nasa Mai zafi ya zauna a dinning dake cikin kitchen in ya Soma Sha Saida yasha Rabin cup kafun ya mike. d'akin ya shiga tare da matsowa kusa da gadon hannun sa yasa ya warware blanket Inda ta lulluba zai kwanta da Sauri ya sake blanket in, saboda turirin da yaji ya fito daga cikinsa har yanajin wucin numfashinta Mai zafi Ashe idanunta biyu sai rawan d'ari take hannu yasa ya tabata da Sauri yaja baya zafi jikinta jaujau"subhanallah Labiba tun ba yauba nasan baki da lafiya amma rashin jin da Kika kakkabawa kanki yanzun ya hanaki Bari muje hospital"?kasa amsa Masa tayi bakinta ya bushe sosai hakoranta har haduwa suke da juna,mikewa yayi da sauri ya nufi wardrobe nata budewa yyi ya dauko Mata wando da riga amma irin bujennan masu Fadi yasa Mata hijab ya dauko cikin Wa'inda ya sai Mata duk da ba amfani yake dasu ba Kuma hijab in irin have Sunnah ne. A daren nan Lahab ya dauketa sai Wani hospital Mai tsada, a cikin daren Nan aka amsheta zuwa lokacin zazzabine yaci karfinta sosai ruwa Suka daura Mata tuni tayi bacci sai gwaje gwaje da aka mata,a asibitin Lahab ya kwana tare da ita tana farkawa da safe ta Fara Neman abinci Kuma ta tashi garau abinta,fita yayi ya sai Mata abinda zataci taci kana aka sake daura Mata ruwa. 8:21pm zaune Lahab yake a Kan kujeran dake dakin dayake kowani mutum d'aya dakinsa ne guda ba'a had'a wani da wani zaune take ta tasa kaza a gaba tana ci hannun ta d'auke da ruwa a makale, don Koh barin a cire batayi ba ta Soma ci shi Kuma Lahab ya Barta Bai Kira nurse ba gudun kada ace ya kawo cinnedu amusu dariya,wayarsa ne yayi Kara zarowa yayi yayi picking up"Lau Ade Labiba ce babu lafiya Muna hospital amma karka damu fa jikin da Sauki sosai"yayi shuru Yana sauraran abinda Ade ke cewa sai Kuma yace"no ka tafi school kawai yauma sukace zasu sallame mu basai kazo ba sai Kuma ya katse wayar"Kara kallonta yayi ganin tana tauna kashin kaza"Amma wallahi kin chanja haba Dan Allah kece ci Kamar me Amma Baki karuwa sai ma rama da kikeyi sai haske amma dai ba kome hips da breast sun ciki"? Kala batace Masa ba dan yanzun Sam babu irin kunyan da a tsakanin su bare taji kunyar sa Koh kunyar abinda yace"amma dai da ace bakicin nama har yanzun da anyi babu ke tsabar dadi har kashin cinya kike tumurmusawa,dan Allah kici Naman dake gefen plate in kibar kasusuwan Nan in Naman ya Kare Zan sayo Miki wani amma ace mutun ya aje nama ya kamacin kashi salon wani ya shigo muji kuny..................bai karasa ba aka bude kofar dakin da Sauri Nnenna ta sake kashin hade da boye plate in gudun Kar aga taunannun kasusuwan data aje a ciki. Dariya kawai Dr tayi ta karaso cikin dakin,hade da turo kujera d'aya ta zauna kusa da Lahab kana ta kalli Nnenna ta kalli Lahab tace"Kamar u look familiar"dan murmushi yayi yace"Hassan Lahab the footballer"?oh oh really great footballer nice to meet,am Dr jeme John by name"hannu lahab ya Bata sukayi musabaha, don tsohowace ba yarinya ba,had'a fuska Nnenna tayi amma batace kome ba kallon ta again Dr tayi tace"gaskiya ya Kamata ki fito da abinki kici gaba daci,ba kunya ta dauko plate nata taci gaba dacin Naman Amma Bata tauna Kashi, kana tacewa Lahab wacec ita Nnenna a wajen sa"? dan shuru yayi sai Kuma ya cije yace matarsa ce, waro Ido baturiyar tayi ya nuna Nnenna yace matar ka?gyada Mata Kai yayi, shuru tayi don ita duk zatonta Koh yar'uwa Koh friend ne Koh girlfriend,tunda taga irin kyau da Nnenna kedashi gashi zaman turai ya karbeta sosai tayi fresh da ita sai Kuma ta d'aga kafada kana tace,ok anyway congratulations ur wife is pregnant. Ji kake karaaararam plate na nama ya Fadi a hannun Nnenna saiga hawaye Shar mikewa tsaye Lahab yayi da karfi yace"what?........................... . *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 08084453785 tare da shaidan biyan ki* Cike da damuwa ya Kara Kiran Adewale amma sai ya danna Masa user busy,baiyi zuciya ba ya tura Masa message dan Allah ya d'auki wayar sa daker dai ya samu Adewale ya dau wayar sannan ya amince zaije ya dubo Nnenna amma daga wannan kada ya sake sakasa a shirgen Nnenna babu ruwan sa,katse wayar Lahab yayi Yana hamdala sannan ya koma cikin dakin har lokacin Rahab na zaune yana jiran sa,yana fitowa ya Mika Masa hannu wayan nasa ya basa sannan ya maida ruwan jikin sa ya kwanta. da daddare Koh abinci Lahab ya kasa ci sai tsumayen Kiran Adewale yake amma shuru sai kusan 8 na dare Adewale ya Kira Rahab Rahab ya kawo Masa wayar amsa yayi da Sauri ya tashi Kamar d'azun ya shiga ban dakin Kara wayar yayi a kunne ya Soma mita sai yanzun Adewale zai kirasa tun d'azun Yana zaune Yana tsumayen Kiran nasa amma shuru"?yanzun zaka tsaya na fada maka abinda na ganone Koh zaka tsaya min mita na kashe wayata"?da Sauri Lahab yace toh kayi hakuri fadamin inji meya faru"? Ajiyar zuciya Ade yayi yace ka duba WhatsApp na tura maka hoton ta kaga halinda naje na sameta a ciki zuciyar Lahab Saida ta buga cikin tsoro yace meya sametan,baidai basa amsa ba kawai ya katse wayar,jikinsa har rawa yake ya bude data ya shiga WhatsApp zubewa yayi a kasa ya zauna tabas saban shock Nnenna ya gani kwance Kamar gawa Ido a rufe jikinta gabaki d'aya ya sauya daga fari zuwa yellow sosai ga bakinta yayi jajer dashi rabin fuskarta har wajen wuyanta jijjiyoyine bakekkerin Suka fito rudu-rude jikinsa ne ya cigaba da rawa ya fita da Sauri wayar Ade ya Kira Yana d'auka ya Soma Masa magana"Adewale mutuwa tayi ne meya sameta"kaga Lahab karka sa kanka a matsala nidai goggoji tacemin yau kwana biyu kenan da Fara ciwon Nan nata sun tsorata ainun don numfashin tane kawai zai tabbatar maka tana da rai"innalilahi wa'inna'ilahu raji'un kawai Lahab yace ya katse wayar da gudu ya fito daga ban dakin wardrobe ya bude ya fito da kayansa sakawa yayi ya zaro takalmi zai sa yaga Rahab ya shigo da mamaki yace"Lahab sai Ina zaka a haka Kuma"? "da Sauri Lahab yace fita zanyi"fita fa kace wani irin fita kake nufi Koh ka manta ne baka da daman fita a gidan Nan yanzun"da Sauri shima Lahab yace Ina da Kai Koh ka manta ne dan Allah Rahab kaje ka kwanta a matsayi na Ni Kuma na fita a madaden ka ka taimaka min wallahi akwai babban matsala"wani kallon tuhuma Rahab ya Masa sannan yace wani irin matsala kenan? Nidai ka taimaka min kin taimaka Masa Rahab yayi daker ya samu ya shawo kansa kafun ya amince kwanciya yayi akan katifar Lahab yayin da Lahab Kuma yasa Kai yabar dakin Yana zuwa compound na gidan nasu security Suka tashi shiga mota yayi Suma Suka shiga aka jasu suka Soma tafiya gidan ya jafar Lahab yace a kaisa Suna Isa yace su tsaya a kofar gidan basai sun Shiga ba bude kofar yayi ya shiga gidan da Sauri ya nufi falo gashi yammane Kuma goshin mangari ba falon ya bude da sauri ya Shiga babu kowa sashen su Majid ya nufa Yana bude kofar yaga babu kowa Kamar falo sai kida dake tashi a dakin Majid bude dakin yayi da Sauri Majid ya juyo ya kallesa sai Kuma ya juya yaci gaba da rawansa. Xama Lahab yayi a hankali yasa hannu ya kashe mp in a kufule Majid yace"kaga Rahab banson surutu tashi kabar min daki da Allah"Majid Lahab ne"zaro Ido majid yayi yace kana nufin kaida aka sawa Mari Kaine ka fito"?nidai ba wannan ba taimakona zakayi security na kofar gida so nake ka taimaka nabar gidan Nan ba tare da sun sani ba"kallon sa Majid yayi da mamaki yace"so kake nayi fiffige da Kai mu tashi ta samane Koh yaya Ni ta Ina Zan iya fiddakai"? "Shuru Lahab yayi sai Kuma yace back door ka taimaka min"d'an dakata Lahab nifa karkazo ka sani a matsala munddin aka nemeka aka rasa Ni za'a zarga karka kiramin ruwa babu ruwana wallahi"dan Allah Majid ka taimaka min Dan Allah nace fa"dan shuru yayi sai Kuma yace Ina zuwa fita yayi a dakin Bai Jima ba sai gashi ya dawo da key yana cewa Lahab ya bari a Shiga sallan mangariba. Ana shiga sallan mangariba backdoor Lahab ya nufa da Majid bude Masa yayi ya fita harda waya Lahab ya karba a wajen sa Yana barin layin Adewale ya Kira akan ya fito gida Yana bayan GRA,Bai wani Jima ba saiga Adewale daga Nan gidan su goggoji Suka nufa da yake darene babu Wanda ya gane Lahab Shiga gidan sukayi har dakin da Nnenna ke kwance abin tausayi gabaki d'aya kammanin ta sun sauya ta chanja hannu Lahab yasa ya bude kwayar idanunta Saida ya koma baya da Sauri saboda yanda jini ya taru a idanun tim goggoji ya tambaya garin Yaya ta Soma ciwon"wallahi Lahab kwana uku batacin abinci a kwana na hudun ne na matsa Mata akan saita d'anci abinda na kawo daga gidan ku daga saka abinci a Baki Koh hadeyewa bata gama yiba Naga ta damke makogoronta tana amai harda jini a ciki shikenan ta yanke jiki ta Fadi Ido ya rufu har yanzun bata budewa kwana biyu kenan. Mikewa yayi da Sauri ya nufi kofar gidan Keke napep ya tare sannan ya dawo gidan da Sauri ya ciccibi Nnenna da jikinta ya bushe ta sandare,da Sauri Ade dasu goggo Suka Soma tambayar sa lafiya Ina zaije da ita gudun kada a ganeta a Kamata,kala baice ba yayi kofar gidan da Sauri Ade da goggoji Suka Shiga keken Suma aka bar faruq a kofar gida a tsaye,wani private hospital na kudi Lahab ya kwatantawa Mai keken directly Suka karasawa asibitin ya d'auketa sai ciki ganin halinda take ciki yasa likitoti rufuwa a kanta. da misalin karfe 12:30am na dare Lahab da goggoji ne a asibitin don Ade tun 9 na dare papa ya kirasa yanata masifa akan ya dawo gida,likitane ya Kira su vayan sun shiga office nasa ya Soma musu tambaya Koh akwai abinda ke damun tane daya shafi iska-iska girgiza Kai goggoji tayi shidai Lahab shuru kawai yayi Yana Jin abinda Dr ke cewa Wai Basu gane Kan cutar ba sun saka Mata ruwa ma ruwan baya gudu haka Allurar ma sun saka amma ruwan yaki shiga a jikinta,su d'auketa kawai jinyan Nan bana asibiti bane,mikewa Lahab yayi da gudu yayi dakin da aka kwantar da ita Yana zuwa kuka kawai ya fashe dashi ya zauna a bakin gadon hade da kamo hannun ta Yana hawaye. Goggoji ce ta turo kofar ta shigo ta zauna akan kujeran tana kallon Lahab sai Kuma tace"Lahab yarinyar Nan ta Fara bani tsoro gaskiya mezai Hana ta koma wajen danginta kaga halinda take ciki fa"hawaye ya share sanann yace"gaskiya goggoji bazan iya barinta a halinda take ciki ba gaskiya tunda yace abar musu hospital nasu da safe sai mu kaita wani"? Kaga Lahab Kai suspect ne haka ma ita nasan dai ba kowa bane zai gane Nnenna tunda ita gabaki d'aya jijiyoyin fuskarta sun sauya Mata kamanni bai Kamata ana ganinka haka barkatai ha bugu da Kari Kuma halinda yarinyar Nan take ciki bana asibiti bane gobe in Allah ya kaimu sai muje nida faruqu kauyen mu akwai wani babban malami acan gaba da kauyen, insha Allah koma menene zai kawo karshen sa,d'an shuru Lahab yayi sannan yace"muje dai tare goggoji shi faruq ya zauna a gida bai Kamata na bar Miki d'awainiya haka ke kad'ai ba" amma Lahab baka gani akwai damuwa na barin gari yanda tsaro yayi yawa a kankan Nan"?karkiji kome goggoji Allah ya kaimu goben"ameen ta amsa,washe gari tun asuba Lahab Suka bar cikin gombe Kuma cikin hukuncin ubangiji Basu samu wani matsala a tafiyar tasu ba,haka zalika baibi takan Kiran da Majid keta danna Masa ba sosai suke ta shiga cikin kauyuka wasu kauyukan ma da machine suka shigesa kafun su Isa kauyen da zasu Saida Suka hau kuran shanu kafun Suka iso wani rugan Fulani. Zaune suke a gaban wani dattijo ne babba sosai tsohone ga farin gemun shi,Lahab da goggoji ne a gabansa a cikin bukkan sai Nnenna da aka shimfidar akan wani taburman kaba,magana ya Fara a hankali cikin nutsuwa yace"Alhamdulilah Ramatu naji dadi matuka da yanda Kika taimake wannan baiwar Allah Nan ba tare da kinsan wacece ita ba haka zalika Kai Lahab kayi matukar kokari Allah ya saka maka sannan ya kalli goggoji yanzun Ramatu inaso ki sanar dani menene ya faru da ita Koh Kuma me tayi ta Soma ciwon"a hankali goggoji ta rusuna tace abinci kawai na takura Mata taci"wani irine abincin"?shinkafa ne da Miya"a nutse yace dakwai nama a ciki"?gyada Kai tayi ganin haka yasa Lahab saurin cewa ai batacin nama"da mamaki goggoji tace Koh shiyasa Inna Bata abinci Mai nama sai takici amma Bata taba fadamin ba ranan ma nina matsamata taci bata gama hadewa ba abin ya faru. Mikewa tsohon yayi ya nufi Kan Nnenna masowa yayi sosai yasa hannu ya bude kofar idanunta"sai Kuma ya girgiza Kai tare da d'auko wani magani ya bude xamxam ya juye a ciki ya zuba magani Addu'a yayi sosai ya tofa sannan ya Kira goggoji taxo ta Kamata ya bude bakinta ya Soma zuba Mata maganin tana Sha wasu na zuba sai kawai sukaga ta zabura ta Mike ta Soma aman jini babu gaggautawa harda guda-guda sai Nishi take amai tayi bana Wasa ba,har lokacin idanunta a rufe komawa tayi ta kwanta shi Kuma ya mike ya d'auko magani ya kwaba da man shanu yace ta shafa Mata aduk Inda jijiyar ya fito,Dole tasa Lahab ya fita waje shida dattijon don jijjiyar daga fuskarta ya gangara har wuyanta har Kan kirjinta na hagu ya sauka har kafarta na hagu,fita sukayi goggoji ta gama shafa mata kafun Suka dawo gaushi aka kawo a kasko ya zuba magani a ciki maganin na turnuke dakin Nnenna ta Mike tana wani irin ihu da surutai da Sauri goggoji ta Fadi kasancewar tana da marabai,ya aike Lahab ya Kira wasu sukazo Suka fita da ita shi Kuma ya cigaba da fama da Nnenna Harya samu ta natsu sannan ta koma ta kwanta Lahab kam na bare a waje duk abin duniya ya damesa ya kasa nutsuwa yasan war haka ana neman sa. *************** Bayan sati d'aya Alhamdulilah jikin Nnenna yayi sauki sosai amma har yau Bata dawo hayyacinta ba gashi idanun nata yadan washe daga jini-jinin zuwa fari tass amma Bata tashi ba jinya dai ake Mata sosai goggoji ta koma cikin gombe tabar Lahab a kauyen su,duk sati faruq na zuwa ya dubasa sannn Yana kawo Masa labarin irin Neman sa da ake Kamar me,dayake garin babu Network Sam tsawon sati d'aya kenan isheshen bacci Lahab baya samu sosai,zaune yake a kusa da ita hannunsa d'auke da kwaryar no-no Wanda aka dama da magani,iba take a ludayi Yana sanya Mata a baki a hankali in Kuma ya gangaro sai ya dau tsumman gefensa ya goge mata Inda ya gangaran a haka ya samu tadan sha kad'an,sai Kuma yaga ta Soma tari sosai tana kwarewa mikewa yayi ya dagata zaune ya jinginar da ita take ta Soma kwarara amai sosai take aman bakikkirin, kaman bakin Mai sosai tayi aman duk ta bata jikinta ta bata Masa jiki babu kyankyami ya Kamata harta gama kafun a hankali ya maidata kwance ya mike yadau babban tsumma ya goge wajen ruwa ya ibo ya wanke abinda ta batan ya Shanya ya had'a da kayan jikinsa ya wanke kayan jikinta matar malam ne tazo ta canja Mata don malam yace haka zatayi tayi ta aman har sai ta dawo aman abinda tasha wato in tasha no-no tayi aman nono. A kallah Lahab yakai wata yanzun a kauyen Suna jinyar Nnenna Kamar kullum Yana zaune kusa da ita Qur'an ne a hannun sa Yana karanta mata,Kamar a mafarki yaga tana dan motsa hannunta Bai wani yi mamaki ba tunda dai ta Saba motse kawai dai Bata hayyacinta ne,sai Kuma yaga tana d'an bubbude idanunta harta budesu tar a hankali ta Soma magana Wanda yasa Lahab rufe Qur'an in ya matso kusa da kunnen ta Yana sauraron abinda take cewa Jin yanda take Kiran sunansa yasa sa damko hannunta jikinsa har rawa yake yake ce Mata"Nnenna ki kalleni ganinan kusa dake kinji Labiba"? Hawaye ne ya Soma bin kumatunta da Sauri tasa hannu ta daura a jikinsa tare da jingina a kafadunsa tana kuka take cewa Lahab bata gani ya Bata glass nata da Sauri ya mike tsaye Jin tace bata gani kuka ta fashe dashi itama ta Mike tsaye tana lulubar hannnun sa kamo hannun nata yayi da Sauri ta damke hannun har tana kokarin faduwa na rashin kuzari,kamota yayi Yana cewa ta koma ta zauna amma Ina tace karya tafi ya Barta Dan Allah karya sake barinta"shigowa malam yayi sai Kuma ya tsaya Yana kallon su kauda fuska yayi yace Lahab ya zauna,Zama Lahab yayi itama ta zauna tana rike Masa hannu sai Kuma tambayar da ta jefo Masa"Lahab inane muke waya shigo dakin Nan? bana kallo Lahab bana kallo fa?Ina goggoji ta Miki min glass nawa. Ki natsu shine amsar da malam ya Bata natsuwar tayi Lahab yadau wulan Fulani dake gefe ya aza Mata akai don gabaki d'aya gashin nata duk sun wargaje sunyi datti,kallon ta malamin yayi babu Wasa a fuskar sa yace"Zan tambaye ki Kuma Ina so ki ban amsa babu karya a ciki abinda Zaki cemin"jikinta har wani rawa take tasa hannu ta rike rigan Lahab da karfi ta gyada Masa Kai"ganin yanda ta rikice yasa Lahab sa hannu ya riko hannunta Yana dan Mata magana a hankali"ki natsu Mana babu abinda zai Miki kawai tambayar ki zaiyi fa"shuru tayi tana Jin abinda malam yake fada Mata. Koh Zaki sanar dani sunan ki"Sunana Nnenna obinna"ke wace kabila ce"a hankali tace Igbo"toh tambayar da Zan Miki yanzun shine menene halakarki da Mafi'a(secret code)"zaro Ido Lahab yayi sai Kuma yace"haba malam ya zaka..........d'aga Masa hannu malam yayi yace"karka kuskura na sake Jin bakinka a cikin tambayar da Zan Mata karka kuskura"shuru kawai Lahab yayi Nnenna Kam jikintane ya tsoma rawa a hankali ta Soma hawaye sai Kuma ta fashe da wani irin kuka ta koma da baya timmm kakeji ta yanke jiki ta Fadi tayi wani irin sandarewa"salati Lahab ya sake yayi Sauri ya matso gareta ya tallafo kanta Yana Kiran sunan ta amma shuru bata amsa masa ba. Mikewa malam yayi ya dauko wani magani yazo ya Shaka Mata a hanci saiga jini ya Fara bulbulowa Kamar bakin fanfo Kara Lahab ya sake Yana kuka yana cewa a taimaka Masa karta mutu"Kai ka kwantar da hankalin ka wannan jinin dake fita a jikinta warakane a gunta ka natsu sosai,natsuwa yayi aka maidata Kan shinfidar da ta tashi ,fita malam yayi yace Lahab ya biyo bayan sa bayan sunfita Zama yayi a kasan bishiyar tsakar gidan Zama yayi a gefen sa,magana malam ya Soma Masa Kamar haka"Lahab a gaskiya yarinyar Nan tana cikin gagarumin hatsari bana Wasa ba wanda in aka cigaba da hakan zata iya rasa ranta gabaki daya Dan soyayya ya Fara tasiri a zuciyarta. Waro Ido Lahab yayi yace"mutuwa fa kace malam dan Allah ka taimakamin kada ta mutu don Allah fa"tabbas Lahab zata iya mutuwa in ba dai wani ikon Allah ba muddin ba'a samu ta dawo hayyacinta ba hakan Kuma bazaiyu ba harsai ta samu wani muharraminta kusa da ita wato miji muddin aka d'aura Mata aure karfinta a kungiyar su zai raunana rauninta zaisa ta samu sassaucin ciwon da take ciki in ba haka ba naman daya wuce cikin tannan zai iya Zama ajalinta...................... *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 08084453785 tare da shaidan biyan ki* πŸ€ *By Ruqeenjalal* πŸ€ da mamaki Dr tace yes she is pregnant bakace wife nakace ba"?komawa Lahab yayi ragob akan kujera gabaki d'aya yanayin sa sun sauya sabanin Nnenna da tayi shuru tana dai zaune a Bakin gado ba yabo ba fallasa ta sanya hannayenta ta cikin rigan tana shafa cikin,da Sauri Lahab yace"how many months ne Dr,Mika Masa result na hannunta tayi jikinsa a mace ya karba yayi Sai Kuma ya rumtsa idanunsa da karfi cikine na wata uku da sati uku,kallon Nnenna yayi sai yanzun yaga irin chanjawar da tayi amma dai ckinta Na nan a shafe Kamar babu halitta a cikinta. Shuru yayi Bai Kara magana ba haka zalika itama Nnenna batace kome ba har ruwan ya Kare aka sallame su tare da bude Mata file na zuwa Ayo a wajen su,haka suka Kama hanyar silently Suka koma gidan yayi parking budewa yayi ya fita ba tare da yajirata ba itama binsa tayi a baya hannu yasa ya bude kofar flat nasu, Adewale dake zaune a falon tun safe mikewa yayi Yana tambayar Lahab Ina Mai jikin,bai rufe Baki ba sai gata ta shigo,wucewa dakin sa Lahab yayi ya maida kofar ya rufe ba tare daya baiwa Ade amsa ba sai Nnenna data tsaya Suka gaisa ya tambaye ta jikin nata kana itama ta wuce dakin ta. Tura kofar dakin Lahab yayi ya Shiga zaune ya gansa yayi tagumi,tsayawa yayi a bakin kofar ya harde hannu don har lokacin Lahab baisan ya shigo ba,matsowa yayi ya dafa shi sai a lokacin ya dawo hayyacin sa ya kalli Ade sai Kuma ya sake tsaki"Wai Lahab lafiya meke faruwa ne wai me akace Yana damunta donni Karan kaina Naga Rama a tattare da ita Kuma kace tanacin abinci sosai"?Mika Masa paper kawai Lahab yayi Baiyi magana ba"amsa Ade yayi ya duba sai Kuma ya sake murmushi yace"daman irin wannan Rana nake guje maka Lahab shiyasa tun farko na nuna maka illan wannnan sure da zakayi" "Wallahi Ade nayi auren Nan bada niyar a waye gari tayi ciki ba"oh kana nufin ka aure tane don ka ringa sex da ita karta haifi Y'ay'a Kamar kowace mace"?bazaka gane ba Ade taya Zan dau ciki Koda nakai nageria a matsayin nawa kasan Abune Mai girman gaske" Cikin mamaki Ade yace daman tunda ka Fara kwanciya da ita baka tanadi abinda zaka fadawa gidan ku ba akanta nufinka Randa zaka koma gida rabuwa zakuyi Koh yaya"Koh saboda yanzun ka zama celebrate shiyasa bazaka iya Zama da ita da ciki ba"?da Sauri Lahab yace Ade bazaka gane abinda nake nufi ba wallahi Koh sau daya ban taba tunanin rabuwa da Labiba ba Amma Ina Jin tsoron kada mu tafka kuskuren da bunayya da muwaddat(Aisha bagudu)sukayi"Aiko ku kunma fiso tunda su Koh banza iyayen su Sunsan da auren jama'an garine Basu sani ba dasu kansu ma'aurantan Saida Suka tafka aika aika Amma daga karshe duk da haka an Kira cikin ta da shege bare kaida babu Wanda yasan zance. Yanzun Ade menene mafita"mafita dayane Lahab ta haihu ka tattarata ku koma nageria Kama danginka bayani insun amince ai shikenan"wani kallo Lahab ya Masa kana yace karfa ka manta bari na tuna maka Nnenna suspect ce a naija komawarta yanzun bazaiyu ba haka zalika tinkaran iyayena yanzun matsala ne babba kawai Ni na yanke shawara za'a zubar da cikin kawai muyi planning sai lokacin da Zan koma nageria Inna kammala karatu saimu koma daidai lokacin case nata ya mutu" Kai Lahab kana da hankali kuwa an gaya maka Nan nageria ne da zubar da ciki ya Zama abin sauki cikin ma na wata uku Yana kokarin shiga na hudu Koh kunyar halinda yarinyar mutane zata shiga bakayi toh wallahi karka kuskura karka Fara abinda zaija maka matsala a kasan Nan kaji na gaya maka" "Koh baka fada Masa ba Ni bazan amince ba"juyawa dukan su sukayi wa zasu gani Nnenna ce Wance ke tsaye rike da kofa ga dukkan alamu ta Jima a wajen,sai hawaye kebin kumatunta bata taba tsammanin hakan daga wajen Lahab ba Wai zubda ciki"mikewa yayi yace"ciki Kam tunda Ni nayi nace a zubar Koh y'ay'a d'ari kike so daga baya mu Haifa Amma Banda yanzun kwata kwata shekaruna nawa da Zan kakkabawa kaina yaya"? "Lahab bazan taba zubar da cikin Nan ba,domin shikadai ne ya ragemun Wanda Zan daga hannu na nuna nace ga dangina nan Banda kowa nawa sai shi Taya Zan zubar in Kuma Banda rabon wasu cikin a duniya fa sai wannan fa Kai kana da daman aure amma Ni har abada ka cuceni"Zan rike duk abinda na Haifa Koda kuwa baka so ni Mai iya cewa ba d'anka bane,Ni Zan zamo Masa uwa da uba bazanji kunya ba,amma wallahi banda zancen zubarwa Ina son jinina Ina son cikina Koda kuwa kowa zai gujeni"mikewa Lahab yayi Yana nuna kansa kana yace"Ni kike gayawa haka"an gaya maka Lahab na gaya maka indai akan cikin Nan ne"toh nace bana bukatar cikin"Ni ina ruwana Kuma daga yau Ina so ka manta cewa akwai sure a tsakanin mu da Kai haka zalika bazan Kara cin abinda ya zamo naka ba muddin dai zanci yaron cikina ya rayu" Juyawa tayi tabar dakin tana kuka,kallon sa Ade yayi cikin tausayin su duka don wallahi sun basa tausayi yace"Lahab karka kuskura ka sake zancen zubda cikin Nan itace uwa ita keda ra'ayin haihuwa Koh ah ah don haka ka zamo Mai adalci,karfa ka manta Koh a addinin ku haramun ne abortion ka kula da ita Lahab ka tausaya Mata,daga haka shima yasa Kai yabar dakin,har yamma Lahab na dakin sa,mangariba nayi yayi sallah mikewa yayi ya shiga toilet,wanka yayi ya fito ya sanya Kaya fita yayi a dakin ya leka kitchen yaga kome net babu alamun ma Nnenna ta dau wani Abu a ciki. Fita yayi ya sayo musu abinci laida biyu bude kofar dakin nata yayi ya shiga zaune take da kayan da Suka dawo asibiti Koh chanjawa batayi ba idanunta jawor da gani tun kukan safe da tayine Suka rine,shigowarsa baisa ta motsa daga inda take ba aje laidan yayi ba tare da yayi magana ba ya fita a dakin,washe gari da safe Kamar yanda ya aje Mata laidan haka yazo ya gani da mamaki yake kallon ta sai Kuma ya kasa hakuri yasa hannu ya dago blanket in, kwance take amma Bata dago ba"meya hanaki cin abinci"?ba abinda ya shafeka bane"abinda ya shafeni ne Mana kina ikiraren kinason abinda ke cikin shine kikeson kasheshe da yunwa" Wani kalllo ta Masa sai Kuma tace"babu ruwan ka daya mutu Koh yayi Rai aikai farin ciki ya Kamata kayi sai Kuma ta Mike ta shiga toilet tare da banko Masa door,fita yayi a dakin ya wuce flat na Adewale zaune ya samesa Yana karyawa abincin gaban nasa Lahab ya Iba da yawa kana ya koma dakin Nnenna ya aje Mata yabar gidan,haka Suka cigaba da rayuwa kwata kwata Nnenna ta d'auke wuta fadan Mai ciki Bata shiga harkan Lahab abinci ma badon karta mutu da yunwa ba da bazataci ba gashi inta dafa da kanta baya Mata Dadi a Baki amma dataga uwar Bari ci take shi Kuma Bai fasa kawo Mata ba,tun tana dari dari karya sa Mata maganin zubda ciki harta cire tunanin abin a ranta amma Sam Bata yarda sun sake kwana daki d'aya ba ta tatttarasa ta watsar duk lokacin da taji sha'awa na taso Mata saidai ta shiga ruwan dumi shima Bai wani shega harkan nata iyakansa bata abinci akan kari yazo ya duba yanda ta waye gari. ************* Wasan Lahab ya Fara gaba gaba don yanzun Yana iya barin kasan America ya tafi har wata kasa ball sai dai duk lokacin da zai tafi zai barwa Ade nauyin kula dacin Nnenna Kuma ba laifi shima Yana iya bakin kokarin sa,yau Monday Nnenna ce ta fito daga dakin ta sanye da siker da riga ta dau jakanta ta rataya a kafada sai takalmin ta flat gashinta a sake har gadon baya fitowa tayi daga part nasun ta fito compound na gidan,Lahab dake zaune a waje Yana Shan iska mikewa yayi ganinta tsaye a bakin titi. Ina Zaki"?kauda fuska tayi ba tare da tayi magana ba,"ba magana nake Miki ba"?Nan ma shuru ta Masa ta tare taxi zata Shiga hannu yasa ya fizgota saura kad'an ta buge da marfin data bude janta yayi Suka koma ciki cikin bacin Rai yace"har zanna tambayar ki kina rainamin wayo Ina Zaki a hakan babu lullubi"kaga Lahab baison surutu da ranan Nan akan me Zan fada maka Inda zani,maganan lullubi Kuma Ni ba musulma bace"dagata yayi sama Suka koma ciki hijab karami ya d'auka ya saka Mata tare da kwace jakan budewa yayi ganin takardun asibiti ne hannunta kawai ya Kama ya rike jakan a daya hannun sa Suka fita daga gidan. Asibiti Lahab ya wuce da ita aka Mata awo ba karamin shauki ya shiga ba lokacin da likita ke sanar dasu tagwayene a cikin Nnenna amma Bai wani nuna murna a fili ba,wayarsa ya d'auka ya d'auki hoton na'ura daya nuna yaran baro baro Suna kwance gasunan mitsitsi dasu yan 6 month's,kana ya dauketa tana zaune akan gado lokacin likita na Mata bayani ya had'a harda likitan dashi ya d'auki hoto likita sai dariya take don wallahi ita abin ma dariya ya Bata don kwata kwata Basu wuce 19year's ba a lokacin,Suna fitowa Suka samu wata Mata da miji zaune Suna jiran su fita Suma su shiga cikin matan ya girma don zaikai wata 8 sai kallonsu Mata da mijin Suke shidai Lahab baice kome ba ya Kama hannunta Suka fita, saloon ya kaita aka wanke Mata Kai da kafa ya biya duka,don lokacin cikin nata har ya fito ras dashi kowa ya ganta yaga Mai ciki ga jiki data juga Kamar me wuyanta har wani guru guru yayi na jiki ga haske Wanda Bai sani ba zai tsammaci bata had'a dangi da bakaken fata ba. ********************* Su Lahab an kammala exam na karshen shekara Kuma na chanja aje sun samu dogon hutu na karshen shekara tunda Yan nageria sukaji kammala exam nasu suke sauraron ranan da uban gayyan zaice zasu kamo hanya,Lahab yayi kudi iya kudi yanzun Harya mallake gidan kansa a turai da mototi,sai dai har gobe Basu dawo normal da Nnenna ba lokacin da yaji bukatar matarshi ya tasashi a gaba yaje neman hakkinsa tace batasan zancen ba,shikenan shima ya ajeta a gefe yasa karatu a ga Kuma Alhamdulilah abinda ake tsammani shiya samu yau sati guda da kammala jarabawan,zaune yake a falo shida Ade Suna hiran wasan da Lahab a buga anan Ade ke kawo Masa zancen komawar su gida"gaskiya Ade kayi tafiyarka kawai wallahi Ni bazan iya zuwa Koh Ina ba" da mamaki Ade yace saboda me"saboda bazan iya tafiya nabar Labiba da cikin 8 month's a jikinta fa,karfa ka manta dogon hutu Muka samu akallah mukai 2 to 3 months a chan nasan halinda zata Shiga bayan babu mu Ina wallahi ah ah"kaga Lahab Bai Kamata ka musu haka ba nasan kana da uzuri a gaban ka amma fa ka sani Suma Suna da hakkin akan ka,Mamu shekara guda Bata saka ka a idanunta ba haka ma Rahab tuni sun koma nageria Kai ake jira"Wai Ade da wani yare Zan maka bayani ka fahimta ne nace maka bazan iya tafiya nabar Nnenna ba" Amma Lahab tunda Allah ya hore maka why not ka samu wata dattijuwan baturiya ta zauna ta kula maka da ita ko haihuwarce ya tashi ai akwai wata a kusa"wani banzan kallo Lahab ya Masa irin na baka da hankalin Nan"Ade taya Zan bar matata a hannu bayahudiya salon a haifamin yara biyu ta sabe daya ta gudu Koh ace sun mutu saboda da Bata da tsayaye gwara Ina Nan"shuru Ade yayi h?ar Lahab ya gama surutun sa kafun yace"toh nidai Ina kewar kasata Kuma zanje Naga iyayena"Allah ya bada sa'a babu Inda zani harsai Naga gudan jinina a doron kasa"yanzun me zakace musu a matsayin excuse naka" Cewa zanyi Muna da wasa a France kawai"uhmmmm shine abinda Ade yace Suka cigaba da Hira Nnenna dake cikin kitchen tanajin duk abinda ke faruwa sosai taji zuciyarta tayi sanyi Jin Lahab har yanzun ya damu da lafiyar ta Koda yake ai ya damu da lafiyar ta ya bai damu da lafiyarta ba ai da ta Jima bata gidan sa,ta yarda Lahab na sonta baba Wasa ba. Allah sarki Lahab bai sanar da gida bazai dawo ba har Saida Adewale ya koma nageria kafun ya sanar dasu sosai ran Mami ya baci tayita fada Akan wasan banza zaiki dawowa hakuri kawai ya Bata,yau tun safe lahab Suka shirya dashi da Nnenna zasu hospital cikin Nan gashinan tirim a gaba sanye take da polon wando sai riga bankacece har gwuwa Mai dogon hannu cikin Nan a gaba gyale tayi rafen nasa a kanta,ta sanya boot a kafarta,Lahab ma sanye yake da kananu kaya,motar ya bude Mata ta shiga Suka wuce hospital,Suna Isa facemask ya d'auka ya sa gudun kada mutane su Soma daukarsu hoto a watsa a duniya ya shiga uku tunda yanzun shima ya Zama popular Koh Ina ya Shiga hotuna ake masa,yauma anyi sa'a sun hadu da mutumin da suke yawan haduwa dasu in sunje asibiti awo matar sa mai ciki Amma ayau sun hadu dasu ne lokacin da suke Shirin shiga mota sai ga Matar da mijinta sai wata tsohowa da baby a hannunta daga gani haihuwa matar tayi Kuma an sallame su,Suka nufi motar su Suma ba tare da sun kula dasu Lahab ba duk da daman duk haduwar su basa magana duk da bakaken fatane sai dai su ringa kallon su Lahab shikuma kallon ke hanasa musu magana tunda barikine kowa zaman kansa yake ba irin Naija bane mutun zaice wane ya ganni Bai gaisheni ba" Shiga Nnenna tayi Lahab ya shiga Harya tada motar bayan ya zare facemask in fuskarsa sai Kuma ya tsaya ganin motar gayen Taki tashi gashi lokaci d'aya aka Fara yayyafi fitowa sukayi daga motar zasu koma cikin hospital in,da Sauri Lahab ya fito a motarsa hade da musu sallama,da mamaki mijin ya amsa hade da basa hannu Suka sake gaisawa,kafun Lahab yace in babu damu suzo su shiga ya rage musu hanya,tsohowar taso ki amma data ga Nnenna a cikin motar saita amince suka shiga baya gabaki dayan su Lahab yaja mota. "**************** Kamar nasan fuskar nan taka in ban manta ba Kamar Hassan Lahab Koh?"gyada Kai kawai Lahab yayi,wow gaskiya naji dadin haduwa dakai Ni Sunana Muhammad Auwal wannan iyalina ce Hauwa amma ana kiranta da jidda sai mamata gata ?"nima haka" shine abinda Lahab yace,shuru mutumin yayi ganin Kamar Lahab baison hiran,tsohowar Kam kasa hakuri tayi tace"yaro wannan Yar uwarka ce"saboda ita haka kawai taji ta Kosa Taji menene a tsakanin su tunda matar d'anta tace Mata ai Suna haduwa dasu a hospital sa'i da lokaci Suna zuwa"har Lahab ya bude Baki zaice matar sane Nnenna ta rigashi da cewa"kaninta ne"wani kallo Lahab ya Mata amma baice kome ba yaji matar na hausa da d'anta don a zatonta ko su Nnenna basajin hausa don Basu Mata Kama da Yan nageria ba Nnenna tafi Mata Kama da Yan Ethiopia harda Lahab in ma duk da bakine amma kyakkyawa ne sosai,gulmansu ita da matar suka Fara tana cewa ai wallahi itama Saida tayi tunanin Koh Yan uwane amma meyasa kullum Lahab ke rakota,da Sauri mijin yace"gaskiya mama ya Kamata kuyi shuru babu Dadi Kuma cikin mutane kuma yare zasu tsargu bare Kuma wa'innan da kuka jefawa tambaya. Murmushi Lahab yayi don yasan Nnenna ba wani fahimtar hausan take ba"mata tsohowan ne tasake jefowa Nnenna tambaya tace"aiko gaskiya yayi tsawon kafa dubeshi Kamar wani yayanki amma ku Yan Ethiopia ne"?haba dan Allah mama kiyi shuru Mata"yaron ya tareta da Sauri Lahab ma juyowa yayi yadan kallesu kana yace"munata tafiya Baku fadamin address naku ba"fada Masa sukayi da mamaki yake kallonsu don kuwa gidan sane manne dana mutumin amma baice musu Suna waje daya ba don baya fatan yayi makwantaka da tsohowar Nan sarkin surutu. Wuce kofar gidan sa Lahab yayi ya tsaya a kofar gidan mutumin bude kofar sukayi Suka fiffito mikawa tsohowar laima Lahab yayi dake cikin motar sa gudun sanyi kada ya Kama babyn,sai a lokacin ya musu barka da samun haihuwa itama Nnenna ta musu barka harda karban baby tayi ta kalla kafun ta maida musu, number Lahab mutumin ya karba Yana ta godiya kana Suka shiga ciki Lahab Kam reverse yayi ya nufi nasu gidan. tunda cikin Nnenna ya shiga wata tara shikenan Lahab ya tattara wasan kwallo ya aje a gefe ya koma zaman gida tunda babu makaranta Suna jiran lokacin haihuwarta,yau tun safe lahab yace Nnenna ta shirya bayan sunyi breakfast shiryawa sukayi ita dashi Suka fito zasu fita sayyayyan kayan yara da zasu sayo yayi-yayi ta Masa list yaje shi kadai tace shida baya kaunar yaran yake ba tasan bazai sayo Abu Mai kyau ba,lokacin da Suka fito compound ganin da gaske zata bisan yasa da tsayawa yace"Amma so kike kije ki haihu a hanyane Koh"ai Dr yace saura 2 weeks"da dariya yace waike kin amince da maganar Dr Koh yau in Allah ya nufa Zaki haihu"da masifa tace koma me zakace kace sai make"abinka da gidan turawa na wancan gidan na kallon na wannan kawai cikin magana sukaji an kwala Masa Kira Yana juyawa da mamaki ba kowa bane sai tsohowar Nan tsaye a baranda tana murmushi tare da tafa hanneye daga nesa yaji muryarta Kamar Ansa lasfika tsabar karfi tana cewa"daman Nan ne gidan ku D'an ball ban sani ba ai dana ringa shigowa na huta da zaman kadaici, Kanna kowa saina ringa zuwa wajen mamanka............................... *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 08084453785 tare da shaidan biyan ki* Murmushi yake Lahab yayi Aiko da Sauri Mata Kam ta zagayo daga cikin gidan su zuwa nasu Lahab tana washe baki, tace"Ina zakuje ne Koh asibiti ne"?Ah ah mama zamuje sayyayyan kayan babies ne"Nnenna ta Bata amsa Kama Baki tayi tace yanzun da cikin Nan Zaki fita wani sayayya ai saidai kuzo na rakaku muje ki zauna Ina zabar Miki"Lahab baiso ba Amma ba yanda ya iya haka matar Nan ta bisu tafiya suke sai surutu tane musu Kamar me Suna Isa mall Nnenna ta nemi waje ta zauna tsohowa da Lahab ne Suka Soma jidon Kaya"mama kayan tagwaye Zaki d'auka kome bibbiyu ganin ta Soma zaban suturan sawa"toh tace ta Soma d'aukan na jarirai biyu amma kayan da mace Koh namiji zai iya sawa shopping Lahab yayi sosai kama daga gadon yara kayan su bargo set na feeder duk abinda jarirai zasu bukata sai da Lahab Suka saya ya kashe kudi kusan million daya a kayan yara kad'ai sai Yan suturu daya sayawa Nnenna kala goma tsohowar ma ya sai Mata kayan yara yace ta kaima jikokinta inta koma nageria Aiko taji Dadi ainun sosai, yawo sukayi bana Wasa ba,sai kusan yamma ligis Suka kamo hanyar gida. Mama na baya Nnenna na gaba da Lahab tunda Suka nufo layin Suka hango Yan Sanda a tsaye Suna magana da Muhammad da matarsa duk Suna waje da gani dai a cikin tashin hankali suke tunda motar ta nufi kofar gidan su suke binsu da kallo,bama Kamar lokacin da mama ta bude kofar da Sauri Muhammad ya nufeta Yana tambayar ta"mama Ina Kika shiga kinsa hankalin mu ya tashi haba mama dan Allah Nan fa ba nageria bane,fitowa Lahab yayi ganin yanda ran Muhammad ya baci sosai don mama kam bude boot na motarsu tayi tadau laidan da Lahab ya sayo Mata tana Masa godiya tayi cikin gidan tabar su tsaye a waje. Hakuri Lahab ya baiwa Muhammad tare da fad'a Masa dalilin da yasa ta bisu,sai anan Muhammad ya sake ransa tare da cewa babu kome yasan halin mama sarai,sallaman yan Sanda yayi tunda anga Wanda ake nema,cikin gida Lahab ya shiga, Nnenna daker take taka kasa ta fito a motar kafafunta sunyi mugun kumbura Kamar me,takawa take a hankali harta shiga falon,kayan Lahab ya ringa daukowa one by one Yana ajewa yaje ya dawo Saida ya kwashesu tas kana ya rufe motar ya shigo gidan,har lokacin Nnenna na zaune a falo Bata tashi ba,dakinsa ya Shiga yayi wanka tare da daura Alwala yayi sallan mangariba,ya fito a dakin har lokacin tana zaune a falo sai had'a zufa take,matsowa yayi kusa da ita Yana tambayar ta lafiya"kafafuna kemin ciwo ga kirjina nauyi"toh ba Dole ya Miki nauyi ba Labiba Saida na hanaki fita Amma saboda tsabar taurin kai Saida Kika fita"ita dai batace kome ba hannu yasa ya zame wandon jikinta yajashi kasa cire Mata wandon yayi ya rage daga Ita sai polon riga don ta riga ta cire gyalen,takalmin kafarta ya cire ya zare socks duka,dukawa yayi ya d'auketa. Ajeta yayi a bathroom ya had'a Mata ruwa wanka kana ya zare rigan nata da under wear itama Bata Masa musu ba don jikin nata gabaki d'aya batajinsa normal,rigan jikinsa ya zare ya rage daga shi sai dogon wando wanka ya Soma Mata,yana gamawa ya daura Mata towel kana ya ajeta,ruwan zafi ya had'a a baf ya dauko kafar yasa a ciki Yana dannawa,sosai ya dumama kafan kafun ya d'auketa sai cikin daki,ajeta yayi a Kan gado yadau pillow babba ya daura kafarta akan cream ya d'auka Yana shafa Mata Koh zataji saukin kafan,duk abinda yake matan Nan basu Koh ga maciji shurune kawai Kamar wasu kurmaye. Mikewa yayi ya dauko kayan baccinta dogon riga saka Mata yayi kana ya kwantar da ita ya sanya mata socks na bacci,ya tashi zai fita a dakin hannu tasa ta Kama nasa amma batayi magana ba sai Kuma tace"idan abinci zaka sayo ka Bari kawai a koshe nake banajin yunwa"zame hannunsa yayi yace"na sani inna kawo kada kici"yasa Kai ya fita a dakin. Yana fita falo ya waro Ido ganin tsohowar Nan dake falo ta wani rungume kuloli a hannu,dan kallon sa tayi sai Kuma tace"Dan ball Aina Jima a falon Nan naku nayita sallama shuru shine nace taima sallah kuke Bari na jiraku,Lahab Kam d'an kunya yaji ganin babu riga a jikinsa da Sauri ya bude kofar dakin sa ya Shiga riga ya d'auka ya dawo falon Zama yayi Yana gaidata amsawa tayi kana ta aje kulan hade da cewa"wannan abincin garin mune,tuwon masara miyan lawashi da kifi harda gyada kasan lokacin da akace min hauwa'u zata haihu duk Saida na tanadi abincin masu jego na tawo dashi,shine nace Bari na zubawa yayarka mema sunan ta"?dafe Kai Lahab yayi yace"Labiba"Labiba Kuma sunane wani irin sunane haka Ina ma laifin a karasa da Habiban ta ai yafi"mikewa yayi yadau kulan kana yace Mata sun gode sai Kuma ya juya zai bar falon. Am nace ba Ina mamar taku Ina Mai cikin"mama duk Suna bacci ne"bacci Kuma haka da isha'innan Koda yake nasani Koh Yan gayune ku"shuru yayi Yana cigaba da tafiya da abincin yasa hannu zai bude kofar dakin daidai lokacin Nnenna ma ta bude kofar zata fito Jin surutai kad'an kad'an a falo"lai kin tashi"mama tace cikin farin ciki karasowa falon Nnenna tayi tazo ta zauna a kasan carfet da Sauri mama tadau pillown kujera tana cewa maza ta tashi tasa Mata bakyau tana Zama dabas haka a kasa. Shidai Lahab na tsaya da kula a hannu Nnenna nata Hira da mama mikewa mama tayi ta nufesa hannu tasa ta kwace kulan tazo ta aje a gaban Nnenna babu tambaya ta nufi kitchen Wai zata dauko plates,kallon Nnenna yayi yace"kiyi taka tsamtsam da wannan Mata kinji na fadamiki"shuru ta masa har mama ta dawo Iba Mata tuwon tayi da Miya Nnenna Kam sosai ta zage tayita cin abinta Suna Hira rabonta dacin irin wanann abinci ai anfi shekara. Lahab na daki a kwance Yana Jin surutansu a falo,har kusan 10 na dare mama Bata koma ba,ya zubawa sarautan Allah ido yaga iya gudun ruwan su, knocking na kofa yaji akayi,da Sauri ya mike ya fito falon kallon mama yayi Wance ta kwanta akan kujera harda filo ana ta Hira,bude kofar yayi Muhammad Ne nan dai Muhammad ya tasata a gaba suka bar gidan duk da ranta baiso ba,washe gari da safe lahab na gida da gangan ya sawa kofarsu key gudun kada mama ta sake dawowa,da misalin karfe uku na yamma ya tafi airport dauko Ade. Da dare zaune suke dukan su a falo ana hiran yaushe gamo anan Ade ke Basu labarin nageria jakansa daya shigo falonsu dashi ya jawo budewa yayi ya dauko laida babba Bakin laidan ya bude ya fito da maganin kulli kulli Yana cewa"ga wannan gogojice ta ban Wai inji malam Nnenna tana Sha a shayi Koh kunu sai Kuma wannan yace na wankan Kane wa'innan Kuma yace Wai in ta haihu a baiwa yaran susha kafun a Fara Basu nono,a had'a musu da ruwan zamzam"da mamaki Lahab yace"ya akai malam yasan tana da cikine Wai"wallahu alamu shine abinda Ade yace sai Kuma ya dauko wani laidan yace gashi inji mubeena abaka"dariya Lahab yayi yace lallai big Aunty gabaki d'aya na manta da ita wallahi Amma yanzun tayi aure koh"girgiza Kai Ade yayi yace batayi ba. "Toh ya maganar soyayyar ku"kaima dai Lahab Wasa kake Koh aini inaga na hakura kawai wannan karon ma wulakanci na Tara Saida nazo Mata bankwana na samu fuskar da tacemin na kawo maka sako"bude letter Lahab yayi gaisuwa ne sai Kuma number ta data aje Masa a karshe tare da fatan Alkhari, murmushi kawai yayi lokacin da ya Gama karantawa Yana dago Kai sukayi Ido hudu da Nnenna dake hararansa da Ido Kamar zasu bullokuto waje mikewa tayi cakal cakal irin saurin masu cikin Nan ta nufi daki" Kallon juna kawai Ade sukayi sai Kuma Lahab yadau laidan maganin ya bita cikin daki,zaune ya sameta ta had'a gabas da yamma Zama yayi a bakin gadon da mamaki yake tambayar ta meya Bata mata rai"tura hannunsa tayi a jikinta ta kwanta hade dajan bargo Bata Kara magana ba,aje magangunan yayi ya fita a dakin,da misalin tagwas na dare Nnenna mikewa tayi Jin Karan bude kofar da rufewa fita tayi a dakin Lahab directly ta wuce budewa tayi ta Shiga sannan ta shiga dube duben abinda take nema da Sauri ta dau lettern dake Kan gadon ta warware kana ta Soma karantawa,cikin haushi ta yayyaga paper tana Jan tsaki,daga Ido da zatayi sukayi four eyes da Lahab dake tsaye harde da hannu. "Meyasa Kika yaga"shuru tayi Bata ce kome ba"meyasa Kika shigomin daki Ina mun riga mun raba daki bake bane?"Nan ma shuru ta Masa"nuna Mata kofa yayi"fita"a hankali ta Soma takawa sai Kuma ta fashe da kuka tana dafa bango da Sauri ya matso gareta Yana tambayar ta lafiya kasa amsa Masa tayi sai kokarin dukawa da tayi,da Sauri ya tallafota akan cinyarsa Suka zauna,yamutsa fuska ta somayi tana Dan juya Kai a hankali hankali tashe yake cewa meke damunta Amma shuru babu amsa sai lip nata na Kasa data Kama da karfi tana taunasu,mikewa yayi ganin jini ya biyo sahunta da Sauri ya Soma sanati hade da ciccibarta suka fito daga flat nasu da Sauri ta bude motar ya sata tare da zagayowa ya shiga yaja da karfi tunkan ya Isa hospital in ya Kirasu akan Suna zuwa ya sake kiran Ade ya sanar dashi,Suna Isa hospital aka shiga da ita labour room,iya wahala Nnenna Tasha Amma haihuwa shuru Kamar zata mutu tace a Kira Mata mijinta ya yafeta karta mutu Yana Jin haushinta, lokacin da Lahab ya shigo dakin kuka kawai ya Soma Nnenna na kuka tanacewa ya yafe Mata mutuwa kawai zatayi,shi Kuma sai cewa yake bazata mutu ba. Dr cewa yayi Lahab yasa hannu za'a Mata operation,saboda kasa haihuwa da tayi da kanta ga karfinta ya Kare,hannun Lahab na rawa yayi sign cikin fargaba sai Addu'a yake Allah ya sauketa lafiya,fitowa yayi a dakin Yana hawaye da Sauri Ade dake zaune a waje tuntuni ya mike zuwa yayi ya Fara basa Baki akan yayi hakuri,insha Allah zata sauka lafiya ya Mata Addu'a shitafi bukata. Zaune suke gabaki dayan su hankalin su a tashe yake cikin damuwa, fitowa nurse tayi ta ce Lahab ya shigo,mikewa yayi yabita har dakin da aka kwantar da babies in tunda yasa hannu ya daukesu kuka kawai ya fashe dashi ya mannasu a kirjinsa mace ne Dana miji aka Haifa yara farare tass Kamar mahaifiyarsa,Saidai fuskar sak na ubansu ne,kuka yake hawaye shabe shabe dagasa nurse in tayi tana cewa kukan ya Isa haka yaran sa kyawawane don ita Bata taba ganin Miji ya kawo matarsa Yana kuka haka ba sai yau tunda daman sun riga Sunsan Lahab da Nnenna yanzun basa mamakin auren nasu,,kiss ya manna musu a kumatun kana ya kalli nurse in"Ya jikin nata?sunkuyar da Kai tayi sai Kuma tace am sorry ka kwantar da hankalin ka muna iya bakin kokarin mu Amma jininta ya tsinke yanzun ma jini ake sa Mata jini na zuba a jikinta sosai ka Mata Addu'a zataji sauki amma maganan operation anyi nasara sai na tsayuwar jini,zaro Ido Lahab yayi yace"tsinkewar jin.......???? Bai karasa ba yaga nurse tasa hannu ta amshi yaran hannun sa tana Kiran Jesus ganin numfashin yara na sarkewa akai akai dukan su biyu................................................ *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 08084453785 tare da shaidan biyan ki* Salati Lahab ya sake da karfi itama nurse hankali tashe ta kwantar da yaran tare da Kiran likita da telephone Inda ke manne a dakin Koh minutes biyu ba'a Yi ba saiga Dr ya shigo harda gudun sa Suka Soma bawa yaran taimakon gaggawa oxygen Suka saka musu a hanci har lokacin numfashin su Bai daidaita yanda ake so ba,Allah sarki d'a Mai dadi Lahab Bai tabajin yanason wani Abu farar d'aya Kamar yanda yaji wani irin kaunar yaran Nan ba, hankalin sa sosai ya tashi Wanda yasa likitoti koransa waje,Ade Karan kansa ya shiga tashin hankali bare da Lahab ya shiga dakin da Nnenna ke ciki yaga yanda ta jirkita laidan jinine hannu biyu aka saka Mata tsaban irin zuba da jini keyi a jikinta" Kamar an mintsine sa da gudu ya fita a hospital in gida ya koma ya Soma neme nemen maganin da Ade ya kawo Masa saban tashin hankali daker ya gane maganin fitowar sa kenan a gida zai Shiga mota saiga Muhammad anan Suka gaisa yake sanar dashi d'azun mama tayita zuwa gidan su a rufe lafiya Kam,a damuwan ce lahab yake cewa haihuwa Nnenna tayi tana hospital babu wani kawaici Muhammad yabi Lahab hospital lokacin da ya tsinkawo lamarin sosai ya tausaya wa Lahab don shi Karan kansa yasan tashin hankali daya Shiga lokacin haihuwar matarshi,bare Lahab da aka ma Matarsa tiyata ga tsinkewar jini ga yara babu lafiya Kuma sosai yasha mamakin kasancewar su couple Bai taba tsammanin hakan ba. D'akin matar sa ya Fara Shiga lokacin ta fita ma a hayyacinta Bata masan wake kanta ba lokacin da yadau maganin zai Bata bayan kammala tofi da yayi a ciki,likitotin sukace afatau bazai Bata ba ai hanjinta a nade yake bazataci abincin yanzun ba haka zalika in yasan zai Bata traditional medicine meyasa bai mata a gida ba Suka kawo ta hospital, Lahab yabuga ya buga sunki daga karshe dai Saida ya musu hauka kafun Suka barsa maganin ya shafa Mata a Kai da fuska kana ya zuba Mata kad'an a Baki ta hadiya,da Sauri Kuma ya nufi dakin yaran balla roban zamzam yayi ya juye a kofi duk abinda yake innan jikinsa rawa yake karkar Kar don shi kadai aka bawa daman ganin su,zame oxygen in yayi ya bawa yaran ruwa da Sauri namijin ya Soma tsotsa Yana hadiye wa,kwantar dashi yayi yadau macen itama ya Bata baima mayar musu a oxygen in ba Yana dai rike dasu a hannunsa sai Addu'a yake shafa musu gabaki d'aya yau yaga abinda ake Kira tsinkewar Rai,a sannu sannu numfashin su ya Soma daidai ta sai Kuma ya sama sauka Normal,bacci ya daukesu kwantar dasu yayi Yana Mai Addu'an fatan gamawa da duniya ga malam,da Sauri ya nufi dakin Nnenna Alhamdulilah jini ya tsaya ya Soma zuba kad'an kad'an Wanda sosai abin ya baiwa likitoti mamaki Basu tsammaci hakan ba. Alhamdulilah jikin Nnenna yayi sauki na ban mamaki har an chanja Mata daki an had'ata da yaranta waje daya lokacin da ta farka taga Lahab rungume da yaran ba kunya tace saiya aje mata yaranta Aiko Lahab bai biye mata ba tana ta masifa har Saida Dr yazo ya Mata allura don su sun dauko irin farkawar Nan ce da mutun yakeyi da shirme, Muhammad ya koma gida ya sanar da mama Aiko Nan ta musu girki Mai kyau da dare ta tattara kayanta a jaka ta biyo Muhammad hospital lokacin Nnenna Bata farka ba,anyi anyi ta koma gida tace ita Ina da Nnenna zata zauna kafun maman su Lahab tazo,anan Muhammad ke sanar da ita ma'aurata ne ba Yan uwa ba,aiko gyara Zama tayi tace babu Inda zata gashi asibitin basason mutum ya wuce daya Mai jinyar Mara lafiya dole Lahab badon yaso ba yabi su Ade suka koma gida. Washe gari tunda ya idar da sallan asuba yayi wanka tare da ibawa Nnenna magangunan su,ya fita a gidan ya wuce mall zai sai Mata kayan shayi amma ya samu Basu bode ba babu yanda ya iya haka ya jirasu har kusan 6 kafun ya sassayi kayan karyawa duk da yasan da wuya taci wani Abu yau,da abinda zata bukata na yau da kullum ya jido musu,7:30 ya samesa a hospital in,lokacin da ya tura kofar ya shiga mama ce zaune da hijab da gani sallah ta idar bata tashi a Inda ta zauna ba,Kai dubansa yayi ga matar tasa bacci take,matsowa yayi kusa da gadon yaran hannu yasa a hankali zai dagasu sai Kuma ya tsaya Jin gyaran murya da mama ta Masa dan juyowa yayi suka gaisa kana tace"kaga bawan Allah karka dagasu don daren jiya bamuyi bacci ba sai koke koke suke,Kai Koh kunya bakaji Yan farine fa xaka dagasu a gabana"? Koh sauraranta baiyi ba waishi da yaransa za'a ma iyayi xama yayi a bakin gadon ya dagosu duka ya rike sosai ya kurawa fuskokin yaran Ido yanajin kaunar su na kara nutso a ransa, Addu'a ya tofa musu a ruwa ya ibi maganin ya basu,kana ya musu huduba daidai lokacin akayi knocking na kofa Adewale ne da Muhammad Suka shigo sai jidda dake d'auke da kula,karasowa sukayi duka Suka zauna ana gaggaisawa Ade ya zaro wayansa ba tare da ya bari Lahab ya gane ba yayi musu hoto dukan su dashi da yaran harda Nnenna dake bacci,kana ya maida wayar sa Aljuhu"malam zaka bamu yaran mu rikene Koh yaya"?inji Ade ganin Lahab baida niyar Basu yaran. Mikewa yayi yazo ya mikawa Muhammad daya ya baida jidda daya kana ya dau yarinyar Muhammad ya koma ya zauna,Kai Masha Allah yara Kam sak ubansu tabar kallah yara Kamar larabawa Allah ya rayasu ta farkin musulunci"jiki a sanyaye duka Yan dakin Suka amsa da ameen zuciyar Lahab Saida ya amsa sai yanzun yake tuna makomar yaransa shin ya zaikaya dasu yau Suka girma Suka tarar da uwarsu Bata sallah shin a matsayinsa na uba zai iya da tarbiyar su ta farkin islama shi kadai babu sa hannun uwa a ciki,tabbas ba auren ahlil kitab bane tarbiyar addinin ka shine babba tunda ita ke tare dasu kullum a matsayinta na uwa,Hira Yan dakin suke a hankali har Nnenna ta farka,Suka Mata ya jiki kana Ade da Muhammad Suka wuce makaranta ya rage sai jidda da mama sai Lahab. **************** Kwanan Nnenna hudu aka sallamota zuwa gida saboda jikin nata yayi sauki Alhamdulilah abinka da tiyatan waje Koh na gida ma baya wuce haka a yanzun,mama gabaki dayanta ta tattaro ta dawo gidan Lahab tana kula da Nnenna sosai tayi musu goma Sha ita ke kula da yaran dan Saida Suka kwana uku kafun ruwan no-no yazo Lahab ya koma bangaren Ade Suna kwana tare Kuma har yau babu shiri a tsakanin su don tunda Nnenna ta haihu ta dau son duniya ta daurawa yaranta Kuma bai Isa ya taba yaran Nan ba sai sunyi rigima da ita Saidai ya aje Mata yara. Bayan sallan isha'i da sallama Lahab ya shigo falon nasu,zaune Nnenna take akan pillow a kasa,tuwo takeci miyan ganda yaji pepper sosai sai jaririn dake kwance akan kujera idanunsa biyu amma ba kuka yake ba dan Sam yaran Basu da yawan kukan banza sai in dare yayi su Hana uwan su bacci,amsa Masa tayi ciki-ciki bata Koh daga Ido ta gansa ba takalmin sa ya cire ya aje laidan hannunsa ya zauna akan kujeran da babyn ke kwance tare dasa hannu zai daukesa da Sauri Nnenna ta daukesa Bata damu da hannunta akwai Miya ba,"ke Wai me kike nufi ne Ya ni da y'ay'ana ki hanani sakar Koh a garin gaba-gaba naji irin wannan"suwaye yaran naka"wani banzan kallo ya Mata kafun yace"au yaran ne Baki san nawa b"? Nidai wa'innan nasan nice uwarsu amma bakaine ubansu ba"me kike nufi banine ubansu ba"kwarai ma kuwa koka manta ne"ai wallahi baki Isa ba? da Allah bani yarana"hannu yasa ya fizgo d'ansa da karfi tayi tagal tagal zata Fadi da Sauri ya tarota hade da saurin rungumarta ya had'a da babyn duka a kirjinsa,kokarin banbare jikinta take amma yaki Bata daman haka a hankali ta Soma zamewa shima ya bita Suka zauna akan kujeran tare da zare babyn ya daura Mata akan cinya Jin yaron ya Fara kuka,hannu yasa zai daga Mata riga da Sauri ta make Masa hannu,Aiko yasa hannun nasa duka ya Kama nata ta baya ya rike kana ya zame rigan tare da fitar da breast in ya baiwa yaron da Sauri ya amshi abinsa ya Kama Sha,sosai kirjinta Suka dad'a cika Suka kumbura dam dam,dan zamewa yayi ya kwantar da kansa akan kafadar ta. "Labiba Labiba"bakin sa biyu Yana kiranta Bata amsa Masa ba illa tallafar d'anta da tayi da kyau tana feeding nasa,"duk fushin Nan na menene"?ya Kara tambayarta again Bata Masa magana ba"hhhhh shine da Kika ga Zaki mutu a dakin haihuwa kike ta cewa a kirani na yafe Miki"Nan ma shuru ta Masa Bata basa amsa ba,in akan abinda ya farune kiyi hak..............Bata Bari ya karasa ba tasa hannu ta rufe Masa Baki hawaye na cika Mata Ido ta Soma magana a hankali"baka cancanci ka bani hakuri ba,bakamin abinda zaka bani hakuri ba,Niya dace na baka hakuri Lahab"?da Sauri ya mike zaune yace"hakurin me Zaki bani alhali Kuma nine Banda gaskiya"?Mata a wajen mijinta kullum ita ke daukar hakuri ai bare nida ka zame mini kome Kaine kadai Wanda Zan daga hannu na nuna a matsayin nawa sai Kuma wannan kyauta Mai girma da tsada da ka bani"ta nuna yaran, bani na Miki kyauta ba Allah ne ya Baki Ni Kuma na Zama suka, Amma duk da haka Kuma shine kike fushi Dani"murmushi tayi tana kokarin sauka a Kan kujeran Zama tayi ta Soma cin abincin shima zaman yayi yasa hannu suka Soma ci kafun tace"duk abinda namaka nayi ne bawai Dan Ina Jin haushin kaba sai don kada ka sake zancen zubar da ciki"gaskiya da nayi nadama har karshen rayuwata da nayiwa kaina wauta wannan kyautar da Allah yamin nasa subi flushing ga zunubi" "Yanzun kana sonsu kenan"?Nnenna ta tambaye sa"ke yanzun harsai na fada miki"nasani Koh ganin idon mutane kake nuna........................................Bata karasa ba saiga mama ta fito daga dakin nasu d'auke da yarinyar alamu wanka ta Mata sai cinyara kuka take"ah ah angon karni Kaine"eh mama mum wuni lafiya"?lafiya Alhamdulilah,ke ungo bata no-no tasha sai Kuma take"hannu Lahab yasa ya dau namijin dake Kan cinyar mama tasa Mata macen Aiko Nan na mijin ya sanya kuka da karfi da Sauri mama ta had'a Madara ta baiwa Lahab ya kafa Masa a Baki shuru kakeji yaran sun natsu. Zama mama tayi tana kallon su sosai taji sun burgeta yaro karami da Mata da yara Kamar babba bayan Kuma koshi ba'a gama rainon sa ba"Wai d'an ball ya sunan yaran ne in ban mantaba yau kwanansu biyar a duniya Koh"?gyada Mata Kai yayi kana yace"eh nazeefi da nazeefa"ah ah tabar kallah ubangiji ya musu Albarka"Ameen mama ga wannan ya dauko laidan daya shigo dashi ya Mika Mata amsa tayi ta bude nama ne da yawa gasasu,Hira sosai suke sai kusan 11 na dare ya musu sallama ya wuce flat na Ade. Ana gobe Suna kasa hakuri mama tayi ganin babu wani daga dangin Lahab Kona Nnenna da yazo yasa ta aje Nnenna ta Soma Mata tambaya"Wai Yar Nan in tambaye ki Mana"?Ina jinki mama Nnenna tace tana ninke kayan yara da mama ta wanke"kin daukeni a matsayin uwa Kamar yanda na daukeki"?barin abinda take tayi ta juyo tana kallon mama Jin tambayar da ta Mata alamu dai abinda zata fadamata Mai muhimmaci ne"sosai ma mama"shikenan tunda kin daukeni a matsayin uwa Ina so ki fadamin tsakanin ki da mahalicin ki?gyada Mata Kai Nnenna tayi"shin keda yaron Nan Anya aure kukayi kuwa"? Waro Ido Nnenna tayi sai Kuma taji ranta ya baci wato ma kokonton zaman nasu ake kenan"mama wani irin magana ne haka"kiyi hakuri yata in maganar ta Miki zafi Naga tunda nake daku Banga wani naki ko nasa dayazo kasar nan da sunan zuwa duba yara ba haka zalika babu Wanda ya bugo waya a idanuna"kuka Nnenna ta Fara ahankali sai yanzun tunanin yazo Mata lallai Suna da Kura a gaban su shin Menene makomar yaranta,mama Kam shuru tayi Bata Kara magana ba har Nnenna tayi kukan ta ta gaji. Washe gari Suna babu kowa a gidan sai Muhammad dasu Lahab da iyalinsu sune Suka hadu sukaci abinci tare da gifts da Suka baiwa yaran,bayani Suna Lahab ya cigaba da zuwa makaranta haka ma ball ga Mama na zaune Masa da matar sa tana baiwa yaran kulawa sosai da gyara Masa Mata kome ya daidai ta a tsakanin su sun koma Kamar da ana Raha Wasa da dariya yaransu na samun kulawa na ban mamaki,a sannu sannu kwana na tafiya har Nnenna ta kammala wankan jegon ta Lahab ya koma dakin matar sa yayin da mama ta koma kasar nageria da tsaraba Mai yawa da Lahab ya mata,badon ranta yaso ba sai don Kiran da tsohon mijinta ke Mata akan taje ta zauna a tsakiyar yara,yanzun rainon yara ya koma wajen Nnenna da jidda da Suka kasance makwanta kawaye Kuma masu zumunci sosai,don wani lokaci in Lahab yabar kasar sai jidda ta dawo gidan Nnenna su zauna suyi girki su wuni sai dare ta ibi abinci a kula ta wuce gidanta dashi. Yaran Lahab sun girma sosai yara kubul kubul dasu Kamar yaran turawa ga haskensu sosai ya karu fuskar Nan Kamar na mahaifinsu, don yanzun har tafiya Suna Yi babu Inda bada gudu Lahab ya Zama cikekken mutun magidanci Dan shekara 20 a duniya da yara Yan shekara 1, Nnenna tayi kiba ta waye duk Wanda yasan ta a Nnenna obinna a kauyen su inya ganta yanzun ba lallai ya gane ta ba,su Lahab sun samu hutun karshen shekara yanzun haka sun kammala part 2 saura musu shekara daya su kammala digree nasu anyi hutu Adewale yayiwa Lahab zancen tafiya nageria Amma Lahab ya murza Ido yace sai ya kammala makaranta zai je nageria,babu irin yanda Ade baiyi dashi ba yace bazashi yabar matar sa da yaransa ba. Yau Ade baije Koh Ina ba kwanton Lahab yake yabar gidan Amma Ina dayake yau baida Wasa Koh training Yana gida da iyalan sa don haka yake in baida abinyi baya fita in Kuma zai fita toh da family sa,Jin motse a compound yasa sa mikewa yazo bakin windown sa ya bude labulen,Lahab ne tsaye da Nnenna Suna sanye cikin kananan Kaya gabaki dayan su jeans ne da t-shirt sai yaran su dake sanye da Kaya irin daya Lahab na rike da daya Nnenna na rike da daya ya sanya facemask a fuskar sa don haka yake indai zai fita da family sa sai ya rufe fuska gudun kada a daukesu hoto a yada a duniya ya Shiga uku,tsaki Ade yayi ganin sun shiga motar sun bar gidan tsake labulen kawai Ade yayi Yana mamakin halin Lahab nason Kai ace mutun nason yayan sa da matar sa haka Amma bazaiyi tunanin ya tasa mahaifiyar take kewar sa ba a zatonsa in Lahab yaga yaransa zaiyi hankali ya Fara natsuwa Amma baiga alamu ba Sam. Washe gari lahab ya fita training hakan yasa Ade nufar kofar lahab ring na door ya Danna kana ya tsaya Yana jira ta bude Saida ya Jima sosai Harya juya zai tafi sai Kuma ya tsaya Jin an bude kofar"ah ah Uncle in twins Kaine sannu da zuwa shigo Mana"tace tana matsa masa,shigowa yayi da fara'ar sa ya karaso falon Zama yayi da sauri nazeefe dake zaune a kasan phalorn Yana Wasa ya mike da gudu Wai zaizo wajen Ade sai Kuma ya Fadi take ya sanyara Kara da Sauri Ade ya mike ya dagasa yana rarrashen sa"ba rawan Kai ba haka yake a Rana saiya Fadi sau uku ma"dariya Ade yayi Jin abinda tace yace"kin manta jinin Lahab ne in baiyi ba sai Allah ya tambaye sa"had'a fuska Nnenna tayi tana tafiya kitchen tace"gaskiya Uncle bazamu shirya dakai ba husband nawa kake fadawa haka"?sai Kuma ta shiga kitchen abinci ta ibo Masa ta dawo falon aje Masa tayi da drink's,Jin nazeefa tana sanyara Kara a daki Daman bacci take yasa Nnenna mikewa ta shiga daki jawo abincin Ade yayi ya Soma ci Yana baiwa nazeefi dake ta sa hannu a plate in Wai zai Iba Daman gashi yayi hakori hudu. Fitowa Nnenna tayi da ita ta zauna akan kujera tana Bata Madara a feeder,ture plate na gaban sa yayi ya kalleta"mun wuni lafiya maman twins"? lafiya klau"Masha Allah Daman akwai wata magana da nake son muyi dake ne in ban takuraki ba"babu kome Ina jinka Allah yasa lafiya"? Gyara Zama yayi yace lafiya kalau kawai dai aKan mutumin ne nace bari nazo ta wajen ki Koh Allah zaisa kisa baki,wallahi Nnenna Lahab baida hankali tunda mukazo kasar Nan waya wannan in ba Yan nageria ne suka kirasa ba sai sa'i da lokaci yake Kiran su,wancan shekara akayi hutu yace bazai koma ba saboda cikin ki daya girma toh ga wannan shekara yace bazashi ba,abinda Ni nagani Kamar abinda yake Bai Dace ba ace shekara biyu baka koma gida ba bayan Kuma kana da dama,hakan zai jefawa family sa cikin tunanin Abu biyu"na farko ko don Lahab yayi kudi shiyasa yake kokarin zame kansa a cikin su Koh fifita aikin sa akan su hakan Kuma zai iya saka manyan yayunsa sa Ido akansa a cikin kasarnan tunda Suna kudi ba Basu dashi ba, Kinga za'a gane kome akanku,Abu na biyu Kuma mundin aka gano kina tare dashi ne za'a daurawa alhakin rikon nasa Akan ki,Kuma daker su barku tare tunda sunga yanda ya iya Zama dake ba tare da yayi tunanin gida ba Wanda ada ba haka yake ba,don haka nazo na Baki shawara ki sa Baki Koh Allah zaisa yaji naki tunda yanzun kun riga kun Zama daya"? Ajiyar zuciya Nnenna tayi ita kanta tana tsoron randa asirinta zai tonu"yanzun Ade kana ga duk Randa family sa suka San da auren mu zasu barmu tare kuwa wallahi bazan iya rayuwa babu shi ba"?uhmmm kedai kiyi Addu'a kawai shine abinda yace Yana mikewa da nazeefi a hannun sa,Aiko da Sauri nazeefa tasa kuka ganin zasu bar falon Wai itama a dagata"dawowa yayi ya ciccibeta da boron madaran su harda feeder da flasks a ciki na ruwan dumi karami ya bar falon dasu duka. Goshin mangariba Lahab ya Isa gida tura kofar falon yayi ya shiga da sallama falon tsabtsab sai kanshi dake tashi Nnenna ce ta fito kitchen hannunta d'auke da kuloli tana jerawa a dinning,sanye take da guntun siket da riga karami kannan nata yasha gyara sosai wallahi mutun ya ganta zai zaci Koh Bata had'a jini da kasar bakaken fata ba,saukowar tayi Akan steps biyu dake wajen dinning in,ta karaso kusa da mijinta dake zaune akan kujeran falo tsungunawa tayi tana warware Masa igiyoyin dake makale a takalmin ball dake kafar sa ta zare dogon socks in,kana ta Mike ta sabe jakan sport nashi ba tare da tace Masa kome ba ta haura upstairs,binta yayi da Ido harta Haura saman Ya shafa kansa yana mamakin wannan cicin maganin da take innan fa yasan dai lafiya suka rabu, gashi yaga yau sama ta haura alhalin Kuma tunda yaransa Suka Soma tafiya yace Mata bayason amfani da upstairs gudun kada yaransa suce zasu hau Koh a hau dasu suce zasu sauka suje su illata a banza a wofi. Mikewa kawai yayi ya bita saman dakinsa na saman ya bude ya shiga a gyara yake Kamar Yana kwana a ciki alhalin Kuma sai yafi wata bai hau sama ba,Jin motsinta a bandakin yasa sa tura kofar ya shiga,wanka ya fito daure da towel kana daya na hannunsa yana goge ruwan dake kansa,mikewa tayi tazo ta karbi na hannun nasa shi Kuma ya zauna ta Soma goge masa,kafun ya tashi ta Mika Masa zallabiya da wando Yasa ta shimfida Masa sallaya ganin lokacin sallan mangariba ya kusa calbin sa ta sauka ta dauko a dakin kasa ta kawo Masa lokacin Harya Fara sallah ta aje Masa a gefe,ta koma ta zauna akan kujera ta jawo wayar sa tana dannawa. Yana idar da sallan Addu'a yayi kana ya d'aga Ido ya kalleta sai Kuma yace"Wai Ina yaran Nan ne tunda na dawo Banga su ba Koh bacci suke kuma kinsa nace Miki banason kina barin yaran Nan Suna baccin yamma bashi da amfani kwata kwata Kuma baida kyau"bafa bacci suke ba Kuma tunda kace bakason Suna baccin yamma nadaina barin su Suna bacci Koh sunyi ta dasu nake"gyada Kai yayi"in kawo maka abincin Nan ne"?no Zan sauka naci a dinning Amma Baki bani amsa taba Ina suke kinsan banson yaran Nan kina kaisu gidan Muhammad da sunan barma jidda raino fa"? Mtwsss ikon Allah waika ka fini son yaran Nan ne Inka tashi sai kayita min fada Kamar nika Haifa Basu ba,kafasan Ni na girmeka baikamata kana min magana haka ba"wani zabura Lahab yayi ya tsaya Yana Mata wani kallo kana yace"keee niii Kika girma inji wani makaryacin.............................. *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 08084453785 tare da shaidan biyan ki* dariya Nnenna ta sake da karfi ganin yanda Lahab ya had'a gabas da yamma don shi a duniya Kam ya tsayi yaji kalmar girma daga wajenta,mikewa tayi a guje ganin yayo Kan gadon da niyar kamota,da gudu ta sauka ta nufi kofar amma kafun ta Isa har Lahab ya Kamata d"agata yayi da karfi ya maka akan gado tsorata tayi ta kwala Kara duk da kadon Mai laushine Dan Saida katifar ta lotse ta Kara tashi da ita binta Kan katifar yayi ya danne kana ha had'a fuskokin su waje daya Yana wuci Kamar wani kumurci,fuskar tasa take bi da Ido tana kallon mijin nata sai Kuma tasa hannu a hankali ta shafa gemun sa daya cika dam da gashi,buge hannun yayi irin bayason Nan yace"wallahi wallahi daga yau Kika Kara min maganar girma Zan Baki mamaki,yaushe Kika girmeni a gidan uban wa"? "Hhhh ka manta Naga date of birth naka nafa baka wata biyu"wallahi karyane babu wani wata da Kika bani Kuma Kika Kara cewa kin ban banyafe ba wallahi"ganin fad'an nason Zama babban magana Kuma gashi taga ya hau zuciya,a hankali ta Kama lips nasa ta tsotsa lumshe Ido yayi sai Kuma ya zame lips nasa a bakin ta ya Kara maidawa shiya Kama nata Yana tsotsa duk lokacin da ta yunkura zatayi amshi nasa sai yayi saurin Zame nasa a nata inta yunkura zata kama sai Kuma ya d'aga kansa a nata"hannu tasa ta kamo Kan da karfi hade da capkar dan tsukekken lips in nasa ta hau tsotso. dan zame jikinta tayi a nasa ganin abin nason wuce gona da iri ajiyar zuciya ya sauke kana ya d'aga Ido ya kalleta ganin tana kokarin maida riganta jikinta"ya haka"kaga"ta nuna Masa agogon bango tace"isha'i yayi ya Kamata ka tashi kayi wanka kayi sallah kaci abinci"hararanta yayi yace wankan da nayi kafun nayi mangari ba fa"?hhh ai wani zaka sake wancan ya baci"kana ta Mike ta bar dakin,zaune suke akan dinning Suna cin abincin ya Kara tambayarta a Karo na uku Ina yaran sa"Suna wajen Ade kasan yaran Nan tun azahar har yanzun banji duriyan su ba"tura abincin hannunsa yayi Baki kana yace"ai su indai da Madara baka da matsala dasu"? "Gaskiya ne Kam",bayan sun gama cin abinci Lahab ya zauna a falo tare da kunna TV Yana kallo,zuwa tayi ta zauna akasan cafert in dake kusa da kujeran,hannu tasa ta d'aga kafarsa ta daura akan cinyarta ta Soma matse Masa kana ta Soma magana Kamar haka"mijinta"daga Ido yayi ya kalleta Suka had'a Ido sai Kuma ya d'aga Mata gira daya"?akwai maganar da nake so muyi da Kai"uhmm Ina jinki"akan maganar koma warka nageria ne gaskiya banji dadi ba Kuma banso abin ya faru ba kwata kwata"meya faru Wanda Baki so ba"ya tambaye ta Yana kwace kafarsa daka Kan cinyar ta" "daman akan maganar tafiyarka nageria ne a ganina bai Kamata kaki zuwa ba kodon abinda zaije ya dawo dear baka tunanin randa asirin mu ya tonu kada ace saboda Ni kaki komawa gida"had'a fuska yayi kana yace"watoh karana Ade ya kawo Miki kenan? ke kuma gaki uwata"kayi hakuri ba karanka ya kawo ba yadai zo ya ban shawara akan abinda ya dace ne, Kuma kaga duk duniya wallahi bana tunanin zaka samu abokin da yakai Adewale tsakani da Allah yake sonka Kuma Yana so maka abinda yake sowa kansa"shuru Lahab yayi na dan wani lokaci kafun ya kalleta yace"toh shikenan in Allah ya kaimu Rana ita yau zamu tafi nageria Amma fa ki sani zanyi kewar ku"dariyan yake ta Masa itama tace"ai Suma sunyi kewarka"? Amma fa innaje sati biyu zanyi na dawo"waro Ido tayi tace shekaran ka biyu kaje ka musu sati biyu ka musu 2 months dai kawai"Kee in tafi in bar yay.................... knocking in door shiya hanasa karasa maganar sa mikewa Nnenna tayi sanin wake bugawar ta shiga daki,Lahab bude kofar yayi ade ne d'auke da yara harda bag nasu ya shigo falon fuskar Lahab Koh walwala babu ya koma ya zauna,fitowa Nnenna tayi sanye da hijab Kamar yanda Lahab yace Mata ta daina Zama da mutane babu hijabi shiyasa haryau su Muhammad basu San ba musulma bace ita,"uncle sai yanzun gaskiya sannunka da kokari wallahi"tana karasa maganar ta ciccibesu sukayi daki,Zama Ade yayi Yana dariya kana yace"daga gani dai hajiya ta bada umurnin tafiya ne" Shuru Lahab ya Masa shikam Koh a jikinsa haka ya zauna Yana Masa hira daga baya Lahab ya sauko sukayita Hira har Suka Saida ranan tafiya. *************** After one week,yau ne ranan tafiyar Lahab tun safe yake zaune a dakin sa Nnenna nata shirya Masa Kaya haka yaransa Suna manne dashi ya d'aga wannan ya aje ya dauke wanan ya Goya haka Yan nageria yau ba karamin farin ciki suke ba especially matasa The great footballer zai ziyarce kasar sa na haihuwa, ayau ga Family ma gabaki d'aya Suna cikin annashuwa Kiran waya Kam Lahab Harya gaji dashi Wanda abokai ke Kira su Kara tabbatar da zuwan nasa a yau ne,shigowa dakin Nnenna tayi ta Shiga toilet ta had'a Masa ruwan wanka kana ta fito tana cewa Koh Ta fasa tafiyar ne,lokaci nata tafiya baida niyar tashi yayi wanka. Mikewa yayi ya shiga ban dakin wanka yayi ya fito ta taimaka Masa ya sanya tsadadden wani sport wear wando dogo na roba sai riga a ciki ya Kara da jacket,boot ya sanya a kafarsa ya dau hulan sanyi ya rufe Arnen askin dake kansa irin na Yan ball,kallon matarsa da yaransa dake Kan gadon yayi tana zaune tana kallon sa,masowa yayi ya manna Mata kiss a kumatu,d'an hararansa tayi tace"sai ka makara Koh? Ade na jiranka a falo tun d'azun na fitar maka da bag's naka tunda baka son akwati"nafasan zakiyi kewata Koh ince kin Fara ma tun yanzun"hawaye ne ya gangaro Mata da Sauri tasa hannu tana kokarin gogewa Kama hannun yayi ya manna lips nasa a fuskar ta ya tsotse hawayen"duk lokacin da kikayi kewata ki kirani ban yarda kimin asaran hawayen kiba"? Gyada masa Kai tayi kana ta Mike tsaye sanya hijab tayi da Sauri ya kalleta yace"Ina Zaki Kuma"?zamu rakaka airport"no basai kinje ba kinsa ansan Zan bar kasarnan yau so dole zamu Hade da Yan jarida don haka ki zauna kawa"da Sauri ta dau nazeefi shi Kuma yadau nazeefa tace"muje na rakaka Koh compound ne toh"fita sukayi a dakin Ade Suka samu a falo sai duba agoge yake ganin su yasa sa mikewa tsaye ya fita waje Suna binsa a baya Muhammad da jidda ne Suka Shigo Suka musu sallama kana Lahab ya baiwa matarsa nazeefa hade da shafa Kan yaran ya shiga mota Ade yaja Suka bar gidan cike da Kewan juna. NAGERIA 5:30pm jirgin su Lahab ya sauka,bag's nasa guda biyu ya d'auka ya goye daya a baya ya rike daya a hannu kana Ade na d'auke da nasa kowa ya gansu yaga zaratan samari masu ji da naira da tashen kurunciya,sauka Lahab Suka Soma daga steps Yana sanye da bakin glass a fuskar sa ga gemun Nan ya cika yasha cum taku suke da Ade a hankali Suna saukowa,Aiko Nan hasken camera ya Soma haskasu ji kake rass rass kess kess,hannu Lahab yasa a hankali ya dan Kare fuskar tasa sai Kuma ya sake hannun nasa Yana kallon jama'ar da aka Bari suka shigo filin saukar jirgin,,tunda yake a rayuwar sa Bai taba zaron zai Zama wani haka ba. Fitowarsu waje tuni Yan jarida Suka rude da jefo musu tambayoyi shidai Lahab Koh daya Bai amsa ba sai jifa jifa Ade na Basu amsa kasancewar abotar dake tsakanin su yasa duniya tasan da Ade na hannun daman Lahab ne"d'aga Ido Lahab yayi Nan ya sauke akan Anmar da Shareef harma da umaima dake ta washe Masa Baki da Sauri Shareef ya nufesa jakan sa ya karba shi Kuma Ade ya nufi papa daya nufosu gaisawa sukayi cikin mutunci da Lahab kana Ade yabi mahaifan nasa shikam Lahab duk rungumar yayan dan uwan nasa yayi cikin farin ciki da kaunar juna Suka rungunsuma sai unguwan su. Hira kawai ke tashi a motar kowa na zuba Inka cire Lahab da in sukayi magana sai dai yayi murmushi kawai Shareef sai cewa yake Ashe da rabon Lahab zaiga bukin sa shidai Lahab nasa murmushi ne,kawai surutu da tsokana irin nada duk sun ragu kad'an sai fara'a ga wani irin chanjawar da sukaga bawan Allan nan ya musu gabaki d'aya Lahab ya cika ga Kiran karfi naira da wayewa sun Kara ratsashi sosai,tunda aka nufo layin nasu yakebin koh Ina da kallo babu abinda ya sauya sai abinda baza'a rasa ba,horn Anwar yayi Mai gadi ya bude gate in Suka Danna mota ciki, fara'ar sa ta Kara fadada ganin ahlinsa gabaki d'aya sun fito tsakar gida Suna tsumayen isowar sa sauka yayi a motar a hankali idanunsa suka fada ana Mami dake ta murmushi,da gudu yaji an rungumesa ta baya Yana juyowa yaga dan uwansa Kara rungumar juna sukayi Sosai very tight na yaushe gamo. Zazzaune suke a falo sun tasa lahab a gaba Addayiya Kam sai kuka take gwanin tausayi,tunda Lahab ya shigo gidan saboda wani irin change da yayi gabaki d'aya kamannin su da Rahab yaja baya kad'an yanzun mutane zasu iya Ganeshi saboda d'aga karfe da buga ball da Lahab keyi jikinsa ya fi nadan uwan sa ciki,mikewa Lahab yayi yazo ya rungume Addayiya sosai Yana Jin kaunar tsohowar har cikin ransa,hannu yasa Yana share Mata hawaye yace"Wai Baki murna ne tsohowa na dawo Anya kinaso Inna koma na sake dawowa Kuwa? tunda kuka kike,da Sauri tace"ah ah kukan murna ne Kuma bazan Kara ba"?dariya kawai Yan falon Suka sake Mami kauda hawayen idanunta tayi cikin happy. Lahab bayan ya fito wanka masalanci ya wuce shida sauran mazan dake gidan,Yana dawowa aka zauna cin abinci ana ta Hira gawanin ban sha'awa ga umaima da baby boy nata dan shekara kusan biyu da watan Ni haka ma Aisha yarta ta girma,Yusuf in Mami ma an girma Allah sarki dayake Rahab na dawowa hutu shiyasa Bai wani ki Lahab ba. Kwance Lahab yake da Rahab a daki sai Hira Rahab ke Masa ya Masa na wancan ya Masa na wannan shima Lahab ya sake jiki sai Hira yake har bacci ya dauke rahab,wayarsa Lahab ya zaro ya kunna ganin karfe 12 na dare ne yasan zuwa yanzun safiya ne Kiran ta yayi da sauri ta d'auka vedio call Suka ringa Hira ta jera Masa yaransa a screen ya kalle su kafun sukayi sallama lokacin har 2 na dare yayi ya kwanta bacci ya dauke sa,washe gari da safe bayan dawowar su sallah Lahab bacci ya koma bashi ya tashi ba sai kusan 10 na safe ya fita ya karya tare da gaida jama'ar gidan. da yamma ligis Lahab na kwance a falo sai Jin surutan samari yake a kofar gida ba'a Jima ba saiga Mai gadi Wai dandazon yaran dake team nasu Lahab ne suka had'a zuga sunji Hassan Lahab ya shigo kasa amma Mai gadi ya hanasu shiga Koh tsakar gidan,mikewa Lahab yayi ya sauya Kaya ya fito Aiko Yana turo gate in wani irin ihu matasan Suka sake har Saida suka cika unguwan da muryoyinsu Wanda yasa wasu Mata masu gulma fiffitowa su baiwa idanunsu abinci. Kudi Lahab ya zaro ya mikawa wani babba a cikin su yace a raba Aiko zo kaga Kura shikam tuni ya wuce cikin gida ya barsu Suka gaba gurnanin su suka watse. Lahab ya zaga cikin dangi sosai babu Inda Bai zaga ba har wajen mama yaje(maman Muhammad) Kuma duk inda yaje sai ya Mika musu wani Abu duk da suna da arziki Amma akace Mai baka yanaso a basa haka Mai arziki baikin kyauta duk dukiyar sa, Adewale yazo wajen Lahab Yana tambayar sa Koh Nabeel yazo wajen sa, amma Lahab yace ah ah baizo ba,Ade yayi yayi dashi akan suje su gaida Inna amma Lahab yace bazashi ba,sai ya zauna sosai yake kewar matar sa don a kalla Suna waya sau biyar a Rana wani lokacin in Bai samu lokaci ba cikin dare ma suke waya. Satin Lahab daya a nageria ya tada maganar komawa Nan Abbu yace waneshi Bai Isa ba sai ya kammala hutun sa duka amma Lahab yace shikam gaskiya zai tafi Yana da wasa,Mami ta rantse bazai koma ba sai yayi wata biyun nan,anyi auren Shareef a idon Lahab Kuma Alhamdulilah biki anyi an gama lafiya satin Lahab yanzun uku da zuwa nageria,kawai su Abbu suka waye gari babu Lahab ya tattara yanasa yanasa ya gudu basuma San da zancen ba sai da suka ga Bai kwana a gidan ba,ran Mami ya mugun baci bana Wasa ba lokacin da Rahab ya sanar da ita,Kuma ta kudiri aniyar Lahab na kammala karatu bazai cigaba da Zama a wajen ba. Nnenna Karan kanta Bata san da zancen dawowar sa ba kawai cikin dare ta gansa ya diro ba karamin mamaki Tasha ba,da ta tambaye sa lafiya yace lafiyar kenan kewarta yayi. Babu Wanda ya Kira Lahab daga gida akan gudun nasa haka zalika shima Bai Kira kowa ba sai dan uwan sa hatta Ade baisan da maganar guduwar sa ba sai bayan ya tafi,Kuma Bai kirasa ba. Adewale ya kammala hutun sa lafiya ya dawo sun cigaba da karatun su yaran Lahab sai girma suke dad'awa da wayo. ***************** Yau tunda Nnenna ta tashi takejin zuciyarta na tsinkewa Wanda Bata San dalilin ba, breakfast suke a dinning su biyu sai yaran su dake zaune a falo Suna Wasa,kallon ta yayi yace"Wai wife meke faruwa ne tunda Muka tashi da safe Naga Koh kuzari Baki dashi wanka wannan yau Nina ma yaran Nan gabaki d'aya na ganki lagwas"?gashi yanzun ma tunda muka zauna breakfast na kusan tada plate nawa ke Koh spoon biyu Mai kyau bakiyi ba"?Dan ajiyar zuciya ta sauka kana ta zame tagumin dake kumatunta tace"wallahi dear tunda na tashi yau nakejin wani irin faduwar gaba da damuwa Wanda Ni Karan kaina bansan dalili ba"? Uhmmm toh Allah ya rufa asiri kinsan wani lokaci shedan ma na haka sai ya saka maka faduwar gaba"gaskiya ne amma wallahi na rasa peace of mind Ina ji Kamar wani Abu na Shirin faru..........."kul karki Soma babu abinda zai faru damu sai Alkhari"gyada masa Kai tayi Suka cigaba dacin abincin badon hankalinta ya kwanta ba mikewa Lahab yayi bayan ya goge bakin sa ya dau school bag nashi Yana Mata sallama Harya sa hannu zai bude kofa yaji anyi knocking,budewa yayi da mamaki Muhammad ne da gani Kuma hankalin Sa a tashe yake"Lahab kana da labarin abinda ke faruwa kuwa? da Kai kuwa a nageria"rass rass haka gaban Lahab ya Fadi amma yayi ta maza yace"subhanallah meke faruwa"? rike baki Muhammad yayi yace"Ina wayar ka"a fusace Lahab yace wani irin Abune haka in zaka gayamin ka fadamin Ni wayata tun daren jiya da aka damen da Kira cikin dare na kashesa Kuma yanzun makaranta zani"uhmmmm wayar sa Muhammad ya zaro ya daddanna kana ya mikawa Lahab,amsa Lahab yayi sai Kuma ya zare Ido sosai Yana kallon screen in, a hankali ya koma baya-baya ya Mannu da jikin kofar falon wani irin zufa na karyo Mata a hankali ya Soma furta kalmar innalilahi wa'inna'ilahu raji'un,tare da sulalewa ya zauna Muhammad ya karasa Masa"Adewale ka cuceni"shine kalmar da ya Fara fitowa daga bakin Lahab ransa yayi mugun baci har jijiyoyin fuskarsa Suka tashi baro baro. da gudu ya fito daga flat nasa ya nufi nasu Lahab hannun sa d'auke da waya cikin tashin hankali turus yayi ganin Lahab zaune dabas a kasa ga Muhammad a tsaye a kansa,nufar Lahab yayi Yana cewa"mun shiga uku Lahab kasan cewa................kasa karasa maganar yayi saboda wani irin mugun kallo da tunda yake da Lahab bi taba tsammanin Yana da irin Saba,shiya maka Masa tare da mikewa ya cakumo kwalarsa da karfi.......................................... *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 08084453785 tare da shaidan biyan ki* Adewale meyasa zakamin haka meyasa"sakeni Lahab muyi magana wallahi kaji na rantse maka Ni bansan yanda akai hotunan Nan suka fita ba"in baka sani ba toh waya fitar kenan waya fitar kenan"?Kaine dai ka d'auke hotunan Nan Kuma a wayar ka suke wazai fitar"? Muhammad sai kokarin kwace kwalar Ade yake a wuyan Lahab amma Abu ya gagara Jin ihun tsawar Lahab shiya saka Nnenna saurin fitowa,da gudu ta nufesu tasa hannu tana ma Lahab magana akan ya sake Ade amma Lahab yaki data shiga tsakani suma bangajeta yayi harta kusa faduwa"don Allah Lahab ka sakeni a zatona jimawar da mukayi Koj Wani akace maka nama haka bazaka yarda ba Kuma zaka tsayamin akan gaskiya ta amma yau Ni nake rantse maka ka kasa yarda har kana rikemin kwana"Ade yace cikin damuwa don shi yasan dai bbu Wanda ya nunawa hoton Nan. Jikin Lahab yayi sanyi a hankali ya sake Masa kwalar sa ya koma ya zauna anan bakin baranda ya rike kansa"tambayar abinda ke faruwa Nnenna tayi? wayar hannun sa Ade ya Mika Mata,amsa tayi"hoton sune ita dashi lokacin da take da ciki Suna tsaye a tsakar gida sai Kuma wanda aka d'auka a hospital ranan da ta haihu duk su biyu da yaran su, sai Kuma Wanda aka d'auka Suna zaune a falo Koh wata biyar hoton baiyi ba, posted nasu akayi tare da dogon sharhe Kamar haka"shahareren dan wasan kwallon kafan Nan Wanda akafi sani da Hassan Lahab mazaunin America a yanzun an gano yana tare da wannan makashiyar Nnenna obinna tsohowar class mate nasa Wance aka taba kamasa akanta na zargi, Suna zaman dadiro harda yara biyu ba tare da sanin iyayen su ba. Kuka Nnenna ta sake da karfi shikenan abinda suke gudu ya faru amma Koda sunan Wasa Bata taba tunanin ta wannan tsigar asirin nasu zai tonu ba"matsowa yayi kusa da Lahab tasa hannu ta rike nasa a hankali ta Soma magana"Lahab ka sani daman irin wannan Rana na zuwa duk boye boyen mu Koh guje gujen mu amma nima banji dadi datazo ta wannan tsigar ba,amma ka sani dai-dai da Rana daya ban taba kawowa raina Ade zai aikata Abu makamancin haka ba,wata kil wani ne ya aikata hakan saboda ya shiga tsakanin ku karfa ka manta ba kowa keson ka da Ade ba bugu da Kari Ade ya riga ya zamo wani bangaren naka bai cancanci haka ba" Tsungunawa Ade yake da niyar yi zai baiwa Lahab hakuri da Sauri Lahab ya tarosa hade da rungumarsa Yana bubbuga bayan sa a hankali yace"kayi hakuri abokina raina ne kawai ya baci amma tabbas nasan Wanda ya aikatamin wannan Abu Kuma na Jima da gane sa, fuska biyu garesa shiyasa na yakiceshi a cikin rayuwata amma wannan Karo Zan basa mamaki"da Sauri Ade yace"waye kenan"girgiza Kai Lahab yayi ya sake Ade ya Shiga cikin falon binsa sukayi a baya zaune suke dukan su Muhammad da kansa ya kulle tambayar su yayi daman ba aure Lahab sukayi ba?,anan Adewale ke warware Masa kome sosai yayi mamakin abinda Lahab yayi Kuma sosai ya Masa Nasiya akan rashin Jin da yake dakin Jin maganar magabatan sa,haka zalika ya basa shawara akan boye boyen Nan ya Kare ya tinkare iyayen sa da maganar kawai Kai tsaye ya fad'a musu gaskiya. Amma Muhammad kana ga babu matsala kuwa kasan fa ita Nnenna zargin kisane akan ta komawar su nageria babban hatsarine fa gwara ya zauna anan maganar tayi sayi kafun Nan,hakaKo akayi Muhammad sosai ya musu wa'axi jikin Lahab yayi sanyi sosai haka itama ta shiga damuwa wayarsa Kam Sam Bai kunna tanaba daren ranan Koh bacci Bai samu ba washe gari ya tashi da zazzabi Mai zafin gaske da ciwon Kai duk yanda taso suje clinic ki yayi yace bazashi ba. Magana tayi girma a nageria Koh Ina ka leka zancen ake, ashe daman Lahab da yarinyar Nan Suna tare amma yayunsa sukayi tsayuwar daka da naira aka sakesa magana sosai tayita karade Koh Ina da Koh Ina,abinka da nageria babu Inda zaka zaga babu hoton Lahab da family sa,ga case in Nnenna ya Zama sabo, nageria ta Mika bukatar ta ga America na son kamo Lahab a dawo dashi amma Suka kasa samun daman hakan saboda matukar amfani da Lahab yake dashi agunsu haka zalika sukace au Basu da kundin laifinsa Koh daya haka Kuma su a wajen su haihuwa ba tare da aure ba ba abin tashin hankali bane,dole nageria ta hakura yau kwana uku da faduwar abin Lahab Kam ciwo yaki ci yaki cinyewa zazzabi yaki sauka da ciwon Kai ga nazeefa ma na fama da ciwon ciki amma Ita Nnenna ta kaita hospital Kuma jikin nata da sauki sosai. daren yau Kamar bazai Kai safiya ba saboda yanda ciwon ya tasar Masa ga amai duka, hankalin ta ya tashi Kuma ta tsorata da ciwon nasa don duk yabi ya rame, tunda abin ya faru Koh abinci baya ci sai ruwa,kuka ta sanya Masa da asuba akan kin zuwa hospital da yayi gashi Yana tashi zaije yayi Alwala ya Fadi a toilet,gari na wayewa ta sanya Sabon kuka tare da Kiran Ade yazo tare da ita da Ade Suka basa Baki daker ya yarda Ade zai rakasa suje hospital in,Kaya ya sauka Suka tafi,lamarin kasar turawa su abinda ya faru bai wani Zama abin magana ba Koh labarin abin ba'a Yi,daga isan su Lahab aka kamasa a gado tare da daura Masa laidan ruwa da allurar bacci saboda tsawon kwanaki daya d'auka Bai rimtsa ba. Sai yamma lis aka sallamo sa daga hospital in Suka nufo gida,tunda Suka tinkaro gidan nasu yakejin wani irin mummunan bugawar zuciya,kamar zatayi tsalle ta fito daga kirjinsa amma sai Kara maimaita kalmar innalilahi wa'inna'ilahu raji'un kawai yake Yana dafe da kirjin,a hankali ya malle marfin motar ya fito a sannu yake takawa Kamar zai Fadi da Sauri Ade yasa hannu ya bude Masa kofar falon yana binsa a baya da laidan magani,turuss yayi ya Lahab ya tsaya a tsakar falon tare da durkusawa daga tsayen da yake zuwa zaune,saboda mutanen da ya gani a falon"Mami ce da wata kawarta Mara mutunci,ga Nnenna zaune akasa Kamar wata marainiya ta wufi y'ay'an ta a gaba Kamar kace kit ta ruga da gudu"karaso bakin munafuki algungumi d'an iska"Mami tace tana mikewa tsaye cikin kakkauran murya tayi maganr babu Koh dogon sassauci a cikin furucinta. Hawaye ne ya cika a kunyan idanunsa amma ya kasa daga kafarsa daga Inda yake"bazaka karaso bane Koh Sai Nina karaso"?mikewa yayi a hankali ya taho gareta dukawa yayi akan kneel nasa ya riko kafarta kana ya bude Baki da niyar baiwa mahaifiyar tasa hakuri ji kake kauuuukauuuukauuuuu Mami ta wankesa da wasu irin razanannun Maruka masu gusar da tunani take hancin Lahab ya fashe saiga jini Shaaa,Bai damu da jinin ba ya sake yunkurin Kama kafafunta kafar tasa ta hankad'asa gefe. Sai da ya buge da center table,da gudu yaransa suka nufi uban nasu Suna kuka tun ihun farko da Mami ta daka Masa, Suka tsorata suka Soma kuka, Nnenna ma da gudu ta nufi mijin nata rigan nazeefa ta cire tana tare jinin dake biyo hancin sa,mikewa Mami tayi da Sauri ta Shiga kitchen saigata ta fito da wuka gadan-gadan tayi Kan Nnenna lura da hakan yasa Lahab zabuda da Sauri ya ture hannun Nnenna daga jikinsa ya turata gefe har Saida ta Fadi da ita da yaran akan rashin sani ta sauka a hannun nazeefi wani irin kukan azaba yaron ya sake Wanda Koh tantama babu kariya ya samu a hannu"nuna Nnenna Mami tayi da wukar tana zare Ido tace"wallahi summa tallahi Kika kuskura Kika Kara tinkarar yarona Koh inuwar sa saina daba Miki wukar nan Inga waye ubanki,Yar iska karuwar mayya kinzo kin likema yarona Yana mutuwa akanki harda haifan shegu toh wallahi badani ba kaf zuriyana dana ubansa babu shegu baza'a Fara akansa ba. Lahab da hankalin sa ya tashi da Sauri ya nufi nazeefi don ganin meya faru dashi"wallahi tallahi Inka Kara taku daya a wajen saina tsine maka albarkan jikinka Lahab,karkaga kowa ya zuba maka Ido kafi karfin kowa toni uwarka Zan nuna ikona,tsayawa Lahab yayi Bai Kara Koh taku daya ba yanajin wani irin zafi a ransa Jin kalar kukan da dansa yake itama nazeefa tana tayasa Nnenna sai faman girgizashi take amma yaki shurun,shima Lahab baisan lokacin da kuka ya kubuce Masa ba, Adewale dake tsaye a tsakar falon har yanzun wani irin kukane ya tawo Masa da Sauri ya fita a falon ya wuce flat nasa dakin sa ya shiga ya kulle Yana sakin kukan tausayin yaran sai Kuma ya sake fitowa ya koma falon, karasowa yayi yasa hannu zai d'au nazeefi da niyar kaisa hospital yaji Mami tace"toh bakin munafuki d'an arna dakai da yar'uwar taka kunzo kun likewa d'ana, waya sani ma Koh kaika Mata cikin......haba Mami haba Mami wannann wani irin magana ne Taya zakina shegantamin yara tass tasss Mami ta sake wanke fuskar sa da Mari kana ta nuna Adewale"Kai aje yaron Nan"? Mami ciwo yaji fa a hannu"uwarka nace uwarka dan iska kawai sakeshi ya mutu ma Mana dan ubansa"keee ta nuna Nnenna mike maza ki tattara shegunki kubar ma d'ana gidan sa Koh a mafarki karki sake tunanin Zaki Kara rayuwa dashi shegiya mayya makashiya Ashe kina Nan kina like da dana ya makale Miki baya ji baya gani toh wallahi daga yau kome yazo karshe indai Nina tsunguna na haifi Lahab,mikewa Lahab yayi da gudu ya nufi Mami dukawa yayi ya Soma wani irin kuka Yana Bata hakuri akan dan Allah kada ta koreta dan Allah wallahi ya tuba yabi Allah bazai Kara rashin ji ba,tsawa Mami ta bugawa Nnenna tare da nuna Mata kofa"dan Allah mama kiyi hakuri Bari naje daki na dau kayana"Nnenna tace hawayen tausayin kanta dana yayanta harma da mijin nata Yana ratsata ga yayanta sai kuka suke. Waye uwarki Allah ya tsareni da had'a zuriya da mayu,Kuma Uban me kika zo dashi gidan Nan bare har Zaki dau Abu?babu abinda Zaki d'auka karuwa kawai"rumtsa Ido Lahab yayi yanajin kansa na wani irin juyawa Jin sunan da mahaifiyar sa ta Kira matar sa dashi"ah haba hajiya Amina ki barta ta dau Koh suturun su ne,da Visa tunda Kinga tana tare da yara"kawar Mami da jikinta ya gama sanyi ta fada don harga Allah sun Bata tausayi. Babu abinda zata d'auka taje ta mutu da yaran, Khadija bazaki fahimci yanda nakeji a Raina bane da ace wani nakine yayi abinda Lahab yayi da wallahi baza kice haka ba,tafiya Nnenna ta Fara a hankali zata fita a falon da Sauri Ade ya matso kusa da Mami ya Soma Bata hakuri akan ta bar Nnenna ta dau wasu abubuwan daker de aka samu Mami ta yarda zuwa lokacin har Nnenna ta fita a gidan da gudu Ade ya kirata ta dawo dakin ta shiga ta aje yaran akan gado sai kuka suke nazeefi har hannu ya kumbura yayi dam dashi jajazer kuka ta Soma a hankali ta jawo akwati ta bude, Madaran yaranta ta Soma sanyawa a ciki sai pampas nasu da kayan su dasu flask kayanta Koh kala daya Bata d'auka ba na yara take sawa, ta Shiga Neman visanta don ba ita ta aje ba Yana hannu Lahab. Har lokacin gwuwowin sa na kasa hawaye baibar zuba ba mikewa yayi a hankali ya nufi dakin da Nnenna ta shiga Mami dake zaune sai huci take tsawa ta daka Masa tana tambayarsa Ina zaije namamajo duk ya Kare a gindin karuwa"dan dakatawa yayi sai Kuma yace dan Allah Mami kiyi hakuri na dauko Mata visan ta don Bata San Inda na aje ba"wani uwar harara ta watsa Masa,kawarta tace yaje,da Sauri ya shigo dakin daidai lokacin tana zuge zip na akwatin karasowa yayi bakin gadon da Sauri yasa hannu ya d'auki nazeefi tare da d'aga hannun aiko Nan yaro ya Kara karfin kukan har wani kwarewa yake gabaki d'aya sun cika dakin da kara,aje yaron yayi ya nufi Nnenna da tunda ya shigo dakin bata d'ago Ido ta kallesa ba rungumar ta yayi a hankali kana yace"dan Allah Nnenna kada ki tafi,sai Kuma ya mike da Sauri ya fita a dakin,sai Kuma ya dawo dauke da wani envelope ya shigo dakin Mika Mata yayi yace"gashi visan ki na ciki da ATM card nawa kidau yaron Nan kuje hospital a duba hannun sa,kome ya Kama kiyi kawai sannan dan Allah karkibar London ki zauna daidai kome ya daidaita ga wayarki zamuna communication"? d'aga Ido tayi ta kallesa sosai jikinta yayi sanyi ya bata tausayi ita Karan kanta tasan Lahab na sonta so na gaskiya bana Wasa ba"Lahab kayi hakuri amma wannan karon ya Kamata nayi abinda ya dace"zaro Ido yayi yace"meya dacen kenan kike nufi"?dafa sa tayi a hankali Suka zauna a bakin gadon yasa hannu ya dau yaronsa Yana girgizawa"Lahab banason Inga an cigaba daga inda aka saya ya Kamata wannan Karo na yankewa kaina abinda ya dace Koh na zauna dakai toh bani da kima a idanun dangin ka kallon karuwar Nan har abada shi zasuna min,don haka Ni Zan tafi ban maka Alkawarin Zama a London ba amma na maka Alkawarin jiran ka har karshen rayuwa ta mundin tsawon Rai Zan jiraka wannan *ALKAWARIN MASOYA* ne. "Wai me hakan yake nufi kina nufin tafiya zakiyi ki barni"?Lahab ya Zama dole,kana ta karbi evalope in ta d'au ATM nasa ta Mika Masa ya karba,kudin dake cikin account nawa ya Isa in Kula dasu"no ki amsa in kika ki karba bazan ji dadi ba,maidawa tayi cikin akwatin kana ta dau macen ta Goya da majanyi hannu tasa zata karbi namijin,da Sauri Lahab ya mike tsaye Yana kallon ta kana yace"Wai da gaske tafiya zakiyi"Dole na tafi lahab"amma dan Allah kada kiyi nisa dani zamuyi waya ki Kama gida cikin tsohon unguwa da Muka Bari zanzo na sameki agun ki kular Mana da yaran mu sannan dan Allah inaso yarana su tashi cikin addinin musulunci Ina son su kasance musulmai ki Basu tarbiya daidai gwargwado,na Miki Alkawarin insha Allah kome zai daidaita wata rana ga wannan"ya Mika Mata wani golden box Mai sheki hannu tasa ta karba kana ta dau akwatinta a hankali sai Kuma ta tsaya tare da Mika Masa daya hannun ya bata yaron ta amma Lahab bai Mika mata nazeefi ba Kuma har lokacin yaron baibar kuka ba da ajiyar zuciya. Lahab na maka ALKAWARIN yaran ka zasu tashi cikin musulunci Zan Basu tarbiya daidai gwargwado Zan sasu a makaranta da ake koyar da ilimin addinin ka,Koda Allah yasa bamu Hade yanzun ba, haka zalika Zan jira ka tsawon Rai amma bana tunanin zamu cigaba da rayuwa Nan kusa,nima inaso Koh bayan babuni dan Allah ka ringajin maganar iyayen ka Kama mahaifiyarka biyayya duk abinda tace maka kayi mata,kaga nida bani da iyaye wazai min Holo innayi ba daidai ba koh kuskure?babu bana dashi" amma Labiba taya zakice bazamu ray..............bauuu kakeji an turo kofar da karfi mami ce ta shigo"toh karuwa an nuke da yaro a daki ana kitsa Masa magana ke Koh kunya bakiji ki rasa zaki bi sai wannan yaro"?Koda yake daman Ina Arne Ina kunya"maza shege ki fita tunda ba gidan ubanki bane,aje a nemi wani daderon bada d'ana ba,anga yaro yayi kudi ana Shirin d'auke Masa hankali"Mika Mata shegen ta ta Kara gaba dashi kin mikawa yayi da Sauri Mami ta karaso cikin dakin ta fizge yaron ta wurgawa Nnenna da karfi,saura kad'an yaron ya subuce baiwar Allah ta canke abinta salati Lahab y sake ya rumtsa idanunsa donshi a tunanin sa yaron ya Fadi akan tiles,a gaba Mami ta tasa Nnenna Kamar wata Shaniya tana zaginta tana turata da karfi ita da akwatin nata,Lahab na binsu a baya shima hawayen yake Yana rokonta. Har wajen compound Mami ta fita da ita da Sauri Lahab ya sake kneel down batare da gajiyawa ba yahau baiwa uwar tasa hakuri amma Mami ta rantse bazata hakura ba"wallahi Lahab kaji yau sai rantsuwa nake ba? toh bazanyi a banza ba Koh bayan Raina hajiya Khadija ki shaida ban yarda ya Kara rayuwa da yarinyar Nan ba,haka zalika Inka sake Koh magana ya hadaka da ita Koh neman Inda take Koh a bayan idanunsa ne,Allah ya Isa Lahab Allah ya Isa,Kuma saina d'aga maka no-no in yaso kabi duniya,wani irin daskarewa Lahab yayi Yana tsaye harta fita a gate in,da gudu Ade yabi bayanta da niyar ya bita cakumosa Mami tayi tana zaginsa tana cewa babu Inda zaije wato zai bita su hadawa danta munafurci Koh? ai daman Arne bai iya samun waje ba"Lahab dai na tsaye Kamar gunki da Sauri Ade ya samu ya b'anb'are kwalarsa ana Mami da gudu ya nufi kofar gidan amma abin mamaki babu Nnenna Babu Mai Kama da ita,haka ya wuce hospital dake unguwan nasu amma Bata Nan,duk wani bus stop daya sani yaje amma Babu Nnenna. ***************** Yayyafin aka Soma da karfi Mai hade da iska a hankali Lahab ya zame ya zauna akasan compound in Yana wani irin kuka maicin rai,sosai yaji tsoro ya darsu Masa a ransa kada Nnenna tashiga wani matsalar Kuma gashi baisan ya lafiyar dansa ba Ashe haka Y'ay'a suke da dadi? Mami tuni Suka shiga ciki Suka barsa a wajen tunda ya kafa idanunsa a gate tun fitarta har yanzun bai kauda ba,ruwa aka Soma dakarfi haka ruwan nan ke sauka akan Lahab amma Koh gezau ko alamun tashi baiyi ba,yanzun Kam kukan ma ya tsaya hawaye ya bushe,fitowa kawar Mami tayi tana cewa Lahab ya taso a wajen Kar wani ciwon ya kamasa"ki barsa inyaso ya mutu a wajen da irin wannan yaro ai gwara baka haihu ba"abinda Mami tace kenan taja kawarta Suka sake komawa ciki so take ta nunawa Lahab true colourn ta yanda gaba bazai Kara yunkurin tafka wannan kuskure ba. Ruwan sama na kusan 2 hour's kaf suka Kare akan Lahab daman ba isheshen lafiya bane dashi gashi yaki rufe idanunsa har lokacin idanun nakan gate na gidan ruwa ya shishiga cikinsu sunyi jazur dasu,turo gate in akayi a hankali Adewale ne ya Shiga jikinsa a jike shima a hankali ya Soma nufo wajen da Lahab ke zaune a hankali lahab ya dago idanunsa ya kalle Adewale irin kallon Nan na tambaya?girgiza Masa Kai Ade yayi watoh baiganta ba, lumshe idanunsa Lahab yayi a hankali,kawai sai Ade yaga Lahab na sulalewa a hankali da Sauri ya tarosa da hannayen sa gudun kada kansa ya sauka da kasa,amma Ina Lahab Kam gabaki d'aya ya zube a jikinsa baya Koh motse. A hankali ya Soma bude idanunsa sai Kuma ya maida ya rufe kirim ganin wani irin duhu daya mamaye dakin,Jin ana Kiran sunan sa a hankali yasa sa Kara bude idanun nashi dishi dishi ya Soma kallon sama sai Kuma ya Wulla idanunsa ga wajen da yaji ana Kiran nasa,Abbu ne da uncle muzammil sai Mami,maida idanun yayi ya rufe Koh tantama bayayi a gadon asibiti yake,toh amma yaushe su Abbu suka zo?Jin an rike hannunsa yasa sa Kara bude idanun,ya saukesa akan Addayiya dake zaune abakin gadon da yake,bude baki yayi a hankali yana Mata magana amma saboda dishewar da muryarsa yayi yasa Addayiya bataji abinda yake cewa ba matso da kunnenta tayi Kan bakinsa"Addayiya kwana na nawa anan"? A hanakli Addayiya tace"yau kwanan ka uku Lahab a gadon asibiti"?..................... *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 08084453785 tare da shaidan biyan ki* Lumshe idanun nasa yayi ya koma ya kwanta,matsowa kusa dashi muzammil yayi yasa hannu ya taba wuyansa sai Kuma ya fita a dakin bai Jima ba sai gasa ya dawo tare da Dr, ta basa Dr yayi Lahab yaki bude idanun sa tambayar sa yayi akwai Inda yake Masa ciwo?girgiza Kai yayi a hankali ruwan Dr ya cire masa kana yace ya wanke Baki ya samu yasa Abu Mara nauyi a cikin sa,sannu Yan dakin Suka Soma wa Lahab shidai gyada musu Kai yake kansa na kasa don wani irin kunyar yayun nasa yake daman Mami Kam Koh kallon Inda yake batayi ba. Kamasa muzammil yayi a hankali ya mike tsaye sai Kuma yace uncle ka sakeni Zan iya zuwa toilet in da kaina sakin sa muzammil yayi Aiko saura kad'an Lahab ya zube a kasa ya tarosa Yana cewa ba bayaji ba shiyasa ya barsa yaga gudun ruwan sa mutum kwana uku a kwance har Yana da kuzarin cewa zai mike ya taka,Kai muzammil ka bisa a hankali Mana kafun yaji saukin tukunna"Addayiya tace tana mikewa tabi bayan su cikin toilet in ruwa ta hadawa Lahab yayi wanka ta basa Sabon toothpaste da brush ya wanke bakinsa Sabon uniform na hospital in da aka aje musu a goge Addayiya ta dauka ta basa ya sanya Wanda ya ciren Kuma aka saka a basket. dawowa Lahab yayi ya zauna a bakin gadon gabaki d'aya ya zube,ya Kare kowa ya gansa yaga Wanda yakejin jiki,tea Addayiya ta had'a Masa tare da Mika Masa,gizgiza Kai yayi kana yace"Addayiya banajin yunwa bazan iya Sha ba"aiko Dole kasha Taya zaka zauna babu kome a cikin ka har kwana uku Allah yaso ma ana daura maka ruwa"duk yanda Addayiya tayi Lahab yaki Shan tea Nan gajiya Mami tayi ta daka Masa tsawa akan ya karbi shayin yasha hannu Lahab yasa ya karbi shayin bawai don tsawar data buga Masa ba sai don kudurin da ya daukarwa kansa akanta,tunda ya kafa kofin shayin Bai sauke ba Saida ya karar duka Yana aje kofin amai ya tasar Masa kafun ma ya Isa toilet tuni ya kwarara a tsakar dakin. Sai da Lahab yayi kwana biyar a hospital kafun aka sallame su Kuma abinda ya bawa kowa mamaki shine,tunda ya farka baiyi zancen rashin ganin Ade ba Koh Kuma zancen Nnenna asalima Lahab gabaki d'aya ya sauya inya zauna ya lumshe idanun sa sai yakai awa uku Koh hudu Bai bude ba sai ka gama surutun ka akansa bai d'ago ya kalleka ba,indai ba Mami bace ta Masa magana Koh Abbu Koh muzammil wannan Kam Koh Bai Basu amsa ba yanayin abinda sukace Koh abinci Suka basa Koh baison ci ci yake inyaso amai ya biyo baya,bazai hanasa sake ci ba. Gabaki d'aya jikin dangin sa yayi sanyi yau aka sallame sa,zaune yake Akan gadon hospital in ya chanja uniform nasu zuwa kayan sa kallon sa Addayiya tayi, guri daya ya kurawa Ido zuru magana take Masa Amma baimasan tanayi ba hannu tasa ta tabasa,da Sauri ya zabura sai Kuma ya kauda fuska,shigowa dakin Abbu yayi yace ya tashi su tafi an sallame sa,mikewa kawai yayi kansa a kasa har Suka fita,mota Suka hau sai gidan Lahab. Suna Isa anan Lahab yaga sauran yayun nasa sunzo ya jafar da addan sa matar sarkin katsina duk Suna tare a falon ga Ade ma zaune yake Wanda rabonsa dashi tun Randa akai ruwa,nuna Masa waje Abbu yayi ba musu ya zauna Yana bin falon da kallo wasu abubuwan na dawo Masa kunyar kansa,Mami ce ta shigo falon da mijinta Suka neme waje Suka zauna har lokacin Lahab bai cewa kowa kome ba haka zalika Bai daga Ido yaga kowa ba,gyaran murya Abbu yayi kana ya Soma magana Kamar haka"Lahab ka gan mun Nan kaf namu badon kowa Muka taru anan ba sai don Kai Muna so ka Mana cikekken bayanin da zamu gansu,shin mun taba maka wani Abu daya sa kaji cewa bamu cancanci kayi shawa damu ba"?hawaye ne ya cika idanun sa sai Kuma ya girgiza Kai"magana zakayi ba body language ba"ya jafar yace"ah ah baku taba ba"toh meyasa kayi abinda kayi kasan kana tare da yarinyar Nan ka samu muka tashi tsaye ka fito daga hannun hukuma sannan kazo ka zauna da ita kana Zina Lahab Zina fa yanzun abinda zaka saka Mana dashi kenan saika tara yaran da bata hanyar aure aka samesu ba ka Mana daidai a matsayin mu na marikanka? "Wallahi Yaya banyi haka don in zubar muku da mutunci ba Kuma ba Zina na aikata ba"da Sauri Mami tace toh Meka aikata nace Meka aikata Koh ba'a gidanka nazo na sameta ba ka samu Sabon uwa"? d'aga Mata hannu muzammil yayi rai a bace yace"Kinga Amina ki rufe Mana Baki karki sake saka bakinki a maganar Nan sai ansaki"Kai muzammil bazan rufeba ya za'ayi kace sai an sani a ciki Zan Shiga d'ana ne fa"? Kallon ta sumayya tayi tace"Ke da Allah ya Isa ke duk abinda aka sakaki a ciki sai anga rikici tun farko ai Saida akace ki hakura da zuwa London ki jiramu mu shirya Amma dayake idanunki sun rufe kikazo kikayi abinda ranki yakeso Kika dagula kome sannan zakizo kina nuna ma mutane Isa"ke dakata sumayya karki kuskura ki sake saka bakinki a magana ta badake nake ba Kuma Babu abinda na dagula wato so kuke na zauna a likawa yarona sharrin shegu. Wani irin sharri wani irin sharri Koh makaho ne ya shafa hoton yaran Nan yaga jinin mu,Kuma Koh yaran Nan shegune mu bazamu kasa rikesu ba Kuma bazamu ji kunyar nunawa duniya su ba,tunda keda kike uwarsa bazaki iya ba" "Dan Allah ya Isa haka Dan Allah nace, kaina zai fashe"shine abinda Lahab yace Yana kuka a hankali mikewa yayi zai bar falon da Sauri Abbu yace Masa ya koman ya zauna"Lahab baka bamu amsa ba menene dalilinka na aikata wannan d'anyen aiki Kuma riban me kacin ma"? Share hawayen sa yayi a hankali ya Soma magana"wata Rana da safe a makaranta.......................................tsab ya zayyana ma Yan uwan sa dalilin haduwarsu har abubuwan da Suka faffaru har kawo abinda Mami ta Masa kwana biyar daya wuce Yana karasa labarin Yana hawaye, girgiza Kai Abbu yayi Yana cewa"haba Lahab haba Lahab meyasa baka tinkare da zancen Nan ba meyasa tun farko baka sanar Dani ba kayi gaban kanka Lahab kayi kuskure yanzun dame zamu gansar da Jama'a da dangi akan auren ka bamu da wani shaida"? Zaro wayar sa Ade yayi ya mikawa Abbu vedio dauren aure ne gabaki d'aya falon Saida kowa ya kalla Mami kam tabe Baki tayi, gaskiya Amina abinda kikayi bai dace ba kwata kwata hukuncin da Kika yanke yayi tsaurin yanzun kikasan halinda yaran Nan zasu shiga Koh irin hannun da zasu shigo Koh irin riko da zata musu"?don haka ki janye furucinta akan Lahab kana musa a nema Mana yarinyar Nan inyaso mu amshi yaran a hannunta in ma rabasu za'ayi gwara a karbi yaran mu murike namu itama ta Kama gaban ta,tunda zargin kisane akan ta" Mikewa Mami tayi wallahi bazai sa'u ba Akan me za'a amshi yaran maganata Kuma bazan canja ba duk lokacin da Lahab ya nemi yarinyar Nan Allah ya Isa"waike Amina hankalinki daya Kuma Anya kanki daya kuwa menene haka Wai meyasa bazaki chanja bane Infa Rai ya baci hankali Bai gushe ba"Alhaji sulaiman ya fad'a ganin rashin kunyar da matar tasa take zubawa"kaga Babu ruwan ka ai Dole kace kaina ba daya ba,tunda ba danka mahraz bane Dole kace na natsu kaga ma tsaya kada ka sake sa bakinka a maganar Nan"? Haka kikace Amina?kwarai ma kuwa ta basa amsa Kade rigansa yayi yabar falon gabaki d'aya yabar gida mikewa muzammil yayi yace"zakiyi iko da d'anki Amma mu zamu nemeta mu karbi jinin mu"a karata lafiya"shine abinda Mami tace tana bin bayan mijin nata don Daman tunda yazo tabar gidan Lahab,sauran Yan falon duk mikewa sukayi Suka shishiga dakunan da Suka sauka a cikin gidan, shima Lahab mikewa yayi a hankali Yana tafiya yana kallon dishi-diahi,dakin ta ya shiga a hankali ya maida kofar ya rufe tare dabin dakin da kallo Yana tuna abubuwan da dama da suke gudanarwa a ciki bude wardrobe nata yayi kayantane a jere tsaf ya rufe tare da Zama a bakin gadon idanunsa suka sauka akan hoton su da Suka d'auka su hudu hannu yasa ya dau hoton Yana kallo sai Kuma yaji hawaye ya tarun Masa a idanu hannu yasa ya shafa hoton"Dan Allah Labiba karkiyi nisa dani bazan iya jurewa ba"sai Kuma ya mike da Sauri wayansa ya d'auka da hanzari messager ya Shiga yaga babu alert na alamun bata cire Koh sisi daga cikin account nasa ba wayar tata ya Kira Amma yaji a kashe dukawa yayi a kasa ya Kama kansa da karfi. turo kofar akayi Adewale ne ya shigo Amma Lahab Bai d'ago ya kallesa ba matsowa yayi kusa dashi kana yace"Lahab kayi hakuri da duk abinda ya faru sannan ka cire wannan damuwa da take ranka duk da bansan dadin d'a ba Amma Bai Kamata kasa kanka a damuwa har haka ba? zakaje ka daurawa kanka cuta Nnenna Kuma insha Allah Allah zai kareta indai kayi Imani da ubangijinka"tabbas haka ne Ade duk da Kai ba musulmi bane Amma kafi wani musulmin sanin ya Kamata,Allah ya muku albarka abinda Addayiya tace kenan ta aje kwanukan hannunta abinci ta Iba ta mikawa Ade Amma yaki amsa tare da cewa shi zai wuce Daman yazo Yama Lahab sallama ne"d'ago Ido Lahab yayi ya kallesa da tsigar tambayar Ina zashi"Dan yake Ade yayi yace"Lahab yanzun bana cikin gidan Nan na Kama gida a waje inaga hakan zaifi"gyada Kai Lahab yayi don yasan Daman irin zagin da Mami Tama Ade ba lallai bane ya Kara Zama a gidan fita yayi bayan sunyi bankwana da Addayiya. *************** Haka Lahab ya cigaba da rayuwa cikin kadaici da damuwa inya tasa hoton yaransa a gaba saidai kawai yaji hawaye na zuba ba tare da sanin Saba duk Inda su Abbu suka shiga aka Kai bincike ganin Nnenna ya gagara anje airport an bincika amma akace Babu jirgin da Nnenna ta hau,rayuwa tama Lahab daci karatu da ball in duk baya tabuka musu kome Yama ajesu a gefe Daman Yana exam na final year nasa abin ya faru gashi yai missing na wasu paper dolen sa yayi losing na one year,family sa sun hakura sun koma nageria Addayiya ce ta cigaba da Zama dashi tana kula dashi don Babu Inda yake zuwa yanzun gabaki d'aya Lahab ya sauya daga Lahab nashi zuwa wani sabo. Rahab yaji labarin abinda ya faru Kuma hankalin Sa ya tashi yaso zuwa London Amma jarabawan ya tsaidashi da Kuma Mami"Alhamdulilah Rahab da Ade sun kammala digree nasu cikin yardan Allah tare da sakamako Mai kyau, yanzun Rahab cikekken accountant ne da kwalin digree nasa, Adewale Kuma engineer,Rahab na karban result nashi gudu yayi ya dawo London Suka zauna tare da Addayiya Suna kula da lafiyar Lahab gudun kada ya samu wani ciwon Kuma daban, masters Rahab ya nema a school nasu Lahab kana yasa Lahab ya koma makaranta da lallama yaje ya karasa final nasa dayayi losing,Ade ma ya join suka cigaba da bawa abokin nasu kulawa duk da yanzun Ade baya zaune dasu gida daya,haka Mami Bata sake zuwa London ba Kuma Bata takura Lahab yazo NAGERIA ba kasancewar zargi na kansa Kuma Koh yau ya dawo magana zai sake tashi sabo,labarin Nnenna Babu shi har gobe ba'a San Inda ta shiga ba. Lahab ya kammala digree nasa Amma zancen kwallo ya aje gefesa a gefe su Rahab ma Suna shirye shiryan had'a masters nasu shida Ade,yau tunda safe lahab ya tashi da zazzabi Mai zafi Yana kwance Adewale da Rahab sun tafi makaranta sai shi da Addayiya ne da har yanzun Taki komawa tana zaune dasu tare,tana kula dashi,turo kofar dakin nasa ta shigo karasawa tayi bakin gadon tasa hannu ta yaye blanket in a hankali kwance yake gabaki d'aya sai had'a zufa hake,Kai innalilahi wa'inna'ilahu raji'un Lahab zaka kashe kanka a banza Lahab duk nasiyar da nake maka bazaka fawwalawa Allah lamuran kaba kayi hakuri da kaddarar ba"sanin bazai amsa Mata ba yasata mikewa ta shiga toilet ruwa ta Iba a baf ta saka towel a ciki tazo ta Kwabe Masa riga dagashi sai 3quiter ta Soma matse towel in tana goge Masa jiki Koh zazzabin zai sauka don sun gaji da jagelen asibiti. da yamma da Rahab ya dawo daukar Lahab yayi sukaje hospital aka Masa allura da magani kana suka dawo gida kwance yake a falo Rahab na matse Masa jiki Yana Masa hira wani ya amsa wani yaki amsawa a hakan de suke hiran Addayiya nasa musu baki,door bell aka danna kallon juna Lahab sukayi sai Kuma Rahab ya mike Yana cewa"taima order danayi ne ya karaso"kallon sa Lahab yayi yace wani order Kuma bayan Banga kayi ba"Kai d'azun wayanka na d'auka nayi Mana order abincin dare Addayiya yau na hutar dake"ah ah Rahab bana bukata bazan iya cin abincin turawan Nan ba gudawa yake sani garamin na dafa abuna da kaina. Murmushi Lahab yayi Wanda Rabon yayi irinsa tun ranan da Nnenna tabar sa,dukan su kallon sa sukayi sai Kuma Rahab ya hau dariya ya nufi kofa zaikarbo abin Yana cewa"in bazakici ba ai nida kanina zamuci,mikewa Lahab yayi da gudu yadau pillow yabi Rahab Wai zai buga Masa duk da ba karfin jikinsa yakeji ba Amma haka kawai yau yakejin kaunar Dan uwan nasa sama da da, yaji baida buri daya wuce ya gansa cikin happy shiyasa yana mikewa ya Soma bin Rahab dariya Rahab ya Fara Suka ringa zagaya falon Addayiya Kam sai magana take sun bar mutum tsaye a kofa,sosai Lahab ke gudu Yana bin Rahab shima gudun yake Yana kakkaucewa da Sauri ya bude dakin su ya Shiga Yana kokarin rufe kofa,Lahab ya turo kofar da karfi Aiko Nan yasa Kara yayi Kan gadon binsa Lahab yayi ya dannesa kana yad'au filon Yana ta buga Masa Yana cewa"nine kaninka ni"?da Allah kayi hakuri toh ba Kai bane haba"d'an sayawa Lahab yayi yace toh kacemin Yaya"da Sauri Rahab yace Yaya dan Allah gani ka matsemin hannu fa zafi yake min,mikewa Lahab yayi shima ya mike zaune Yana duba hannun nasa,hannu Lahab yasa ya rike hannun dan uwan nasa Yana dubawa. Kallon sa Rahab yayi yace"ya Allah ka dauwamar da zuciyar d'an uwana cikin gaskiya da aminci"d'ago Kai Lahab yayi ya kallesa tare da amsawa da Amin"Lahab ka rame sosai kayi hakuri da kaddarar aduk yanda tazo maka Mai kyau Koh Mara kyau kayi hakuri kome ya faru jarabawa ne daga ubangiji zanji dadi Inka kasance cikin happy Kamar rayuwarka tada"girgiza Kai Lahab yayi kana ya zame ya kwanta a cinyan Rahab Yana cewa"Anya kuwa wannan geben zai cika abinda ya wuce ya wuce bazai taba dawowa ba, Rahab yanzun Kaine kad'ai farin ciki na Kuma nawa dake kusa dani"shafa kansa Rahab yayi yace toh inka waye gari babu Ni ya zakayi bazaka iya hakuri ba kenan"? d'ago Kai Lahab yayi da sauri yace"banason haka karka karamin wasa irin wannan banason ai duk Randa Babu Rahab Babu Lahab Koh ka manta Abu dayane mu guda biyu"?haka ne Lahab Allah ya baka hakuri kaji"nuna min hoton yaran namu na Kara gani naji ance Suna Kama damu Niko sai Inga Kamar sun fimu kyau"da Sauri Lahab ya mike system nasa ya d'auka ya mikawa Rahab Aiko Nan Rahab ya kwanta Lahab ma ya kwanta tare da daura Rabin jikinsa ana Dan uwan nasa,kallon hotonan Rahab yake Yana yaba kyawon yaran da tsamtsam kamannin su dasu sai dai yaran farare ne"smma sunan da ka sawa yaran baimin ba Ina laifin kamin tagwara Lahab"? Kasan fa sunan mu sunan iyayen mune kana nima na sake sawa yarana haba abin yayi yawa shiyasa nasa Musu nazeefi da nazeeefa Ni sunan yamun Kuma Ina Jin dadin sa"kyebe Baki kawai Rahab yayi Yana cewa lallai masu yara manya Allah nifa dariya kake bani Inna ganka na tuna Wai yara biyu gareka,make sa Lahab yayi shima yasa hannu ya hambare Lahab in Saida ya Fado daga Kan gado zuwa kasa,turo kofar Addayiya tayi hannunta d'auke da laidan ordern ajewa tayi tana cewa Kai ga abin naku nidai bazanci ba"mikewa Rahab yayi yazo ya amshi laidan ya koma Kan gado ya zauna bude laidan yayi ya dau roban takeAway in ya mikawa Lahab amsa Lahab yayi shima Rahab ya dau sabo ya bude sai Kuma ya kalli na Lahab ya kalli nasa. "Yaya dai haka"?tsaki Rahab yaja yace nace takeAway uku biyu shinkafa daya gasheshen nama Kuma Ni Naman nafiso fa"kallon takeAway gabansa Lahab yayi sai Kuma ya dauka ya mikawa Rahab Yana cewa"anything for u brother gashi daman Ni nama bai wani dameni ba yanzun ban shinkafan naci,Mika Masa Rahab yayi sai Kuma yadau takeAway Naman ya aje a gabansa ya ibi guda bakwai ya sama Lahab a cikin shinkafan sa,iba a spoon Lahab yayi zaikai Baki haka kawai sai yaji abincin ya fita akan sa yaji baya kaunar cin abincin sauke spoon in yayi Yana kallon Rahab dake ta cin nama Yana kada Kai irin ya Masa dadin Nan,had'a Ido sukayi Rahab ya d'aga Masa gira daya"? A hankali Lahab yace"Rahab na rasa meyasa nakejin wani iri a jikina Kamar Zan rasa abinda nafi so"?amsa Rahab ya basa,sai kayita astagafurullah na rasa meyasa Lahab ka kasa hakuri da abinda ya faru yanzun dai kaci abinci tukunna sai muyi magana dan Ni yunwa nakeji"shuru Lahab yayi Yana ta kallon dan uwan nasa"bazakaci bane Lahab girgiza Masa Kai yayi da sauri Rahab ya cire hannusa a naman Yana tambayar sa meyasa Koh Naman yakeso ba shinkafa ba sai Kuma ya tura Masa Naman duka a gabansa"toh gashi karba kaci"hawayen da Lahab baisan na menene bane ya cika masa Ido yace"nima bansan meya faruba haka kawai nake jina incomplete wallahi" Murmushi Rahab yayi sai Kuma ya yamutsa fuska kana Kuma ya Fara tari a hankali Abu Kamar kiftawar Ido saiga Rahab ya rikice da wani irin mugun tari,hankali tashe Lahab ya mike Yana Masa sannu a zatonsa Koh kwarewa yayi,Amma Ina Rahab tari yake Yana sarkewa wani hararwa da yayi ya yunkura zaiyi amai Aiko sai gani Lahab yayi gudan jini bakki Kirin ya Fado daga bakin dan uwan nasa a rude ya mike Yana salati Yana kamasa ganin ya Soma wani irin aman jini Yana wani irin mimmikewa,ihunsa da salati shiya shigo da Addayiya cikin dakin a rikice. Salati ta sake hade da kamo Rahab in Lahab saban rikita rasa ma mezaiyi yayi da gudu ya fitoh cikin dakin sai Kuma ya koma da Sauri waya ya d'auka ya Kira ambulance sai kuma ya kasa hakuri yadau keyn mota ya dauka yazo ya ciccibi Rahab daya sandare baya Koh motse sai Kuma kunfa dayake fitowa a bakin sa bayan jini ya tsaya,gudu yake Yana kuka Koh takalmi babu a kafarsa ya fita tsakar gidan motarsa ya bude yasa Rahab Addayiya daga ita sai dankwali itama Shiga tayi yaja motar da karfin gaske ya fita a gidan da mugun gudu,daidai lokacin Adewale ya shigo arean ganin yanda Lahab ya fito gidan yasa sa bin bayan sa da motarsa shima......................... *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 08084453785 tare da shaidan biyan ki* gudu kawai Lahab yake shararawa Addayiya na baya ta daura kan Rahab a cinyar ta tana tofa Masa duk Addu'an da yazo bakinta"ruwa ruwa zansha ruwa"shine kalmar dake fita a bakin Rahab cikin magagin fitan Rai wani irin Jan birki Lahab yayi da gudu ya balle marfin motar don Babu ruwa a ciki kafa Koh takalmi Babu ya Soma gudu Akan kwalta saura kad'an wani Mai mota ya kadesa shagon wata Mata ya Shiga Babu magana ba kome kawai ya bude freezer ya dau ruwa ya fita da gudu cikin motan ya dawo ya shiga baya Kan d'an uwan nasa ya kama ya balle marfin Goran ya kafa Masa,gadai ruwa ya cika bakin sa Amma Koh kad'an Bai wuce ba sai dawowa da yayi Yana zuba,adaden ruwan da ubangiji ya rubuta Masa zaisha a duniya ya kare,ganin haka yasa Lahab ya Soma kuka,zai fita a sit in ya koma driver sit,sai Kuma yaji an rike Masa hannu da Sauri ya kalli hannun sai Kuma yace"sakeni Rahab sakeni muje asibiti babu abinda zai sameka. "Lahab kayi hakuri da rayuwa kome yayi farko yana da karshe tabbas nikam ajalina yazo amma nagode Allah daba kaci abincin Nan ba da yanzun dukan mune a cikin wannan hali"kayi shuru sakeni mu tafi kaji Babu abinda zai sameka dan uwa ka manta tare aka haifemu tare zamu rayu Kuma mu mutu tare"?girgiza masa Kai Rahab yayi cikin azaba yace"wannan tsarine na ubangiji duk abinda ya tsara shine daidai Allah ya riga ya rubuta iyakacin rayuwar da zanyi a duniya kenan,naso kafun nabar duniya na Kara ganin mamina amma Dan Allah in tazo bayan babuni kuce ta yafemin duk abinda tasan na Mata Wanda nasani da Wanda ban sani ba kuce Mata Ina sonta,Kamar yanda nakeson ka kaida Addayiya Ina maka fatan Alkhari a rayuwar ka zan kwanta cikin salama mundin na mutu Lahab baka zubda hawaye ba,banason ganin ka kana kuka,sai wata rana"Yana karasa maganar yahau sassakewa la'ilaha'illahlah la'ilaha'illahlah............ Addayiya ta Soma cewa cikin kuka cikin yardan Allah Rahab ya karbi kalmar shahara"la'ilaha'illahlah Muhammadu rasulilah sallalahu allaihi wa sallam,wannan shine kalmarasa ta karshe daya furta a duniya Rai yayi halinsa. Wani irin kafewa Lahab yayi a cikin motar jijiyoyin kansa kwayar idanunsa wani irin tashi sukayi suka zazzaro saiga jini ya Soma bulbulowa a hancinsa amma Babu Koh digon hawaye Sam babi hawaye a idanun sa, Addayiya kuka take tana maimaita innalilah wa'inna'ilahu raji'un, police ne suka matso kusa da motar ganinta a no packing matsowa sukayi daidai lokacin Adewale ya karaso fitowa yayi a motar shima ya nufi motan su Lahab in,kansa police yasa ta glass ganin wa'inda ke ciki yasa da Sauri ya Soma tambayar lafiya"?Addayiya na kuka ta musu bayani a take sukace Bari su dau Rahab akai hospital girgiza Kai Addayiya tayi tana cewa wani irin hospital Kuma bayan Rai yayi halinsa,Kinga ma wannan babban case ne gubafa yaci,daukar Rahab akazoyi Amma Lahab na damke da hannun dan uwan nasa anyi anyi a banbare yaki sai hakuri ake basa zuwa lokacin zama'a sun cika makil an zagaye motan daker da Nasiya Lahab ya sake dan uwansa da jagoran Yan Sanda aka kaisa asibiti,Lahab na zaune a kofar dakin da aka shiga da dan uwan sa gabaki d'aya kamannin sa ya sauka sai jini dake zuba a hancin sa anyi anyi ya shiga likitoti su dubasa yaki yace a barsa in ma mutuwa zaiyi ya mutu amma yaki kula kowa. Abin mamaki da Yan Sanda Suka koma gidan don duba abincin wani shago aka saya Amma abin mamaki gidan a bude Suka samu Daman su Lahab Basu rufeba anyi Neman duniya ba'a ga abinci ba sai jinin da yake zuzzube a kasa da Kan gadon na Rahab,waya Ade ya d'auka ya Kira Abbu Yana sanar dashi abinda ke faruwa hankalin Abbu a tashe ya Kira ya jafar da mijin Mami ya sanar dasu akan zasu hau jirgin yawo zuwa London Amma kada ya sanar da Mami abinda ke faruwa harsai sunje London in sun dauko gawan sun dawo hatta jama'an gidan Abbu bai fada musu ba. Alhaji sulaiman daman Suna falo da matarsa tunda ta tashi da safe Koh abinci bataci ba haka kawai take yawan cemai zuciyar ta na tsinkewa,shiyasa Bai fada Mata ba yadai ce Mata zashi emergency meeting a kwara state,dashi dasu Abbu suka wuce London a ranan sai washe gari Suka Isa zuwa lokacin Lahab duk Mai Imani inya gansa sai yaji tausayin sa gashi Dr yace sai an Nemo babba namiji zaiyi magana dashi ganin su gaba daya kuka suke Inka cire Lahab daya zamo mutum mutumi. Lokacin dasu Abbu suka Isa anan likita ke sanar dasu cewa poison yaci Kuma a take ya tsintsinka Masa hancin cikinsa Allah ya Masa rasuwa innalilahi mutuwar mahaifinsu sabuwa ya zame musu yau sosai mutuwan yasasu tunawa da baban su,ya jafar har hawaye Saida yayi bincike aka shiga gadan gadan don sunki bada gawan sukace a tsaya ayi bincike amma su Abbu sukace Ina su zasu tafi da gawar kasarsu amasa sallah a binne sa. CCTV camera dake gidan Lahab da Kuma cikin area aka bibiya tabbas anga wani da masks bayan fitansu Lahab ya shiga ya dau laidodin abincin saidai ba'a ga fuskar sa ba an bibiye camerori harna motar daya saukesa da Kuma Wanda ya dauke sa bayan ya fito a gidan haka zalika an dau wayar Lahab an dudduba anan aka ga shagon da akayi order anje shagon amma Waiter dayakai abincin ance tunda yakai ma su Lahab abinci Bai dawo ba bincike yayi bincike karshe aka rufe shagon kwata kwata magana tayi girma a garin sosai. Su Lahab sun dau gawar zasu dawo nageria anan yayun sa sukace ya zauna a London bai Kamata ya dawo nageria yanzun ba Amma Lahab Koh amsa Bai Basu ba kuma Bai fasa Shirin binsu ba sufa abin nasa ya Fara basu tsoro tunda Rahab ya rasu shikenan Bai Kara furta Koh eh a bakin Saba sai dai kayi magana ya baka amsa a aikace. ***************** Allah sarki uwa abinka da social media tuni zance ya karade Koh Ina ba Wanda baiji mutuwar Rahab a jikinsa ba Babu ma Kamar na kusa dashi wa'inda Suka San halinsa bazakaji wani ya aibata bawan Allah Nan ba sai dai kaji ana fadin Alkharin sa,Mami kan tunda taji labarin faduwa tayi a take marabanta da tun tana budurwan rabon dasu dashi toh a ranan sun tashi kame kame akayi da ita wallahi duk Wanda ya ganta saiya tausaya Mata ana samu iskan ya sauka sai Kuma ta kom Suma Kan Suma akayi asibiti da ita. Dirowan dare su Lahab sukayi cikin NAGERIA duk da dare ne gidan su Lahab makil da Yan uwa na nesa da kusa sun cika gidan tab, shimfidasa akayi a falon Abbu,a daren Abbu ya Soma ma mamacin wanka Lahab na falon Yana taimaka Masa Suka shirya dan uwan nasa har lokacin idanunsa gangataran a bushe, Qur'ani yayun Suka d'auka duka Suna karantawa shima Lahab Yana rike da nasa karatu yake,kwanan ketso da akai Saida Suka sauke Qur'ani cip kafun safiya. Jama'a sun cika gidan nasu da unguwan gabaki d'aya jama'a ne, a ranan Koh mutum baisan Lahab ba in yaji labarin su sai kaji yace zaije zana'ida Yan garin gombe Basu taba ganin mutuwa Mai jama'a a yanzun ba irin Wanda suka gani a mutuwan Rahab,Mami dake hospital tana farkawa za'a sake Mata Allura ta ringa kuka da magiya akan a barta taje taga gawan danta ta Masa addua ta Masa kallo na karshe, Dr yaso yaki amma sulaiman yace a barta,da taimakon sa aka baro hospital in da ita,tunda ta fito daga cikin mota wasu Mata suka fashe da kuka ganin yanda Amina ta koma Rana daya sai kaji ana ga mahaifiyar mamacin Allah sarki. Kasa karasowa Kan gawar tahi sai da Addayiya dake gefe tayi kuka harta rasa Inda zata da kanta ta Mike ta Kama Mami Kamar makauniya ta ajeta a gaban gawan,hannu na rawa tasa ta bude fuskar sa Allahu Akbar kamar ka kirasa ya amsa fuskar nan tsab dauke da annuri,ya Allah kaji Kan wannan bawa naka ka Masa Rahama ka gafarta Masa, na yafe maka duniya da lahira d'ana baka tabamin abinda na kwana dashi a Raina ba yaro Mai biyayya,shekaran jiyan Nan ya kirani cikin dare Yana cewa na yafewa Dan uwan sa na daina fushi dashi,Ashe da rabon bazamu sake gamawa ba innalilahi wa'inna'ilahu raji'un Allah kaji kansa da Rahama ubangiji ka haskaka kabarin sa da rahamar ka ka bani hakurin rashin sa da dangana a cikin raina"ameen Ameen Yan falon suke cewa one by one yayun sa sukazo Suka Masa Addu'a. Mikewa Lahab yayi a hankali Yana takowa kusa dashi Zama yayi ya Soma Masa Addu'a Yana nema Masa Rahama a wajen mahaliccin mu,kana aka dauko gawan a makara Lahab da Abbu sai muzammil da jafar su Suka rike sa aka Soma fita dashi Mami kuka ta fashe da karfi sai Kuma aka ga ta sulale a wajen Addayiya Kam salati take tana Allah ya jikan ka Allah ya maka Rahama yasa can yafiye maka Nan,Lahab Suna fitowa ana Basu hanya kofar gidan su Lahab yayi kad'an masallacin juma'ar unguwan aka wuce dashi don yafi fili Inda kasan sallan edi haka jama'a Suka taru. Aje makaran sukayi daman an riga anyi Alwala aka Soma daidai ta sahu,juyawa da Lahab zaiyi saiya hange Ade acan gefen wani gida Yana zaune nesa dasu amma Yana hango duk abinda ake ga hawaye nabin gefen kumatunsa Yana sharewa juyawar da Lahab zaiyi wazai gani Nabeel ne tsaye a sahu wani irin super Lahab yayi yasa kafa ya taka kirjin Nabeel har Saida ya koma baya baya ya bugu da kasa ji kake Tim salati jama'a Suka Fara don a zaton su Koh hauka Lahab ya Fara fuskarsa cikin fushi har wani rawa Naman fuskar cikin rawan muryar sa daya kwana uku baiyi magana bane ta ratsa jama'ar cikin yakini da tsananin tsana ya nuna Nabeel kana yace"wallahi tallahi in baka bar wajen Nan ba zanyi ajalinka Kuma ka sani dan uwana Bai mutu a banza ba bakaci banza ba na rantse da sarkin daya busamin numfashi bazan barka ba. Hayaniya aka Fara ana tambayar lafiya mikewa Nabeel yayi ya karkade jikinsa kana ya juya ya barwajen bisa umurnin wasu don an zati matsalan rashin Rahab yasa sa haka juyawa yayi ya shiga sahu aka tada sallan gawa,ana kammalawa aka d'auki gawan sai makabarta,Lahab da hannunsa ya Kama gawar aka saka a Rami lokacin da aka tura daidai lokacin jini ya Soma zuba ta hancin Lahab har Saida ya zuba a bakin Ramin a hankali ya d'ago sai Kuma mutane Suka soma salati ana cewa yayi Sauri yaje hospital wannan jini yafi karfin habo,kin zuwa yayi ya tsunguna aka binne dashi kana ya tsunguna agefen kabarin yanama Dan uwan nasa Addu'a gabaki d'aya jini ya Bata gaban rigansa Amma Bai damu ba. Suna fitowa daga makabarta Lahab ya yanke jiki ya Fadi,Saida aka kwana biyar da mutuwar Rahab kafun ya farfado Mami duk tayi laushi tayi kuka tayi kuka harta gode Allah rashin lafiyar Lahab ya Kara daga Mata hankali Kai bama ga ita kadai ba har dangi sun tsorata kada tarihi ya maimaita kansa akan yaran nan,bare da akace Lahab ya samu heart attack shiyasa jini yake fita a hancin sa Kuma sun bada shawa Koda ya farfado don Allah kada aringa abubuwan da zai daga Masa hankali don zai iya rasa ransa gabaki d'aya haka zalika baza'a Kara basa abinci Mai Kara jini ba,farfadowar sa gabaki d'aya saiya chanja shi baya magana baya cewa kome ba uhmm ba uhm uhm sai dai kaga ya sunkuyar da Kai,toh baya Kara dagawa sai yaji Kiran sallah zai tashi yaje yayi Mami Kan intaga Lahab cikin irin wannan yanayi sai kaga ta fashe da kuka,ita a yanzun burinta Lahab nata nada ya dawo tafi kaunar ganin sa cikin walwala inyaso ana kawo Mata karansa tana Masa fada yafi Mata wannan shurun nasa so dubu duniya kenan waya taba tunanin wata Rana Lahab zai zama haka. A cikin satutuka da Suka gabata kowa na dangin kokari yake yaga yasa Lahab farin ciki Amma Ina Lahab baisan anayi ba Adewale ma wuni yake tare dashi Yana Masa hirarraki amma Lahab Bai dagowa bare yasan anayi, sau uku Inna da mubeena suna zuwa dubasa,Allah sarki mubeena kallo daya zaka Mata ka gane ba karamin damuwa take ciki ba a rayuwar ta, watan su Lahab biyu a hospital aka sallame sa ya dawo gida, Adewale haka zaizo tun safe suna tare da Lahab Yana Masa hiraraki abubuwa, duk da Lahab baya ce Masa kalallahu sai dare yake tafiya abinci wannan Lahab sai anyi da gaske yakeci so daya a rana yawan tasa hoton su Wanda suka d'auka da Rahab yasa aka kwashe duk hotonan Rahab aka boye,sai Kuma ya koma tsayawa a gaban Miro tayita kallon fuskar sa Kamar tababbe. Zaune yake a garden na gidan su, Ade na gefen sa sai kokari yake yaga Lahab yaci Koh wani Abune amma Lahab yaki,bude gate na gidan Mai gadi yayi sai ga mota baka kirim guda daya ta shigo gidan mutane uku ne suka fito a ciki Suka nufi cikin flat na gidan ba'a Jima ba saiga Addayiya dasu Abbu tare da mutanen sun nufo garden in,wani irin zaku tafi dashi meya muku gashi Yana under medical don haka koma menene bazaizo ba sai yaji sauki"am sorry sir Dole zamu tafi dashi munso tafiya dashi tun bayan mutuwar da akayi amma mukayi hakuri har yakai iyau" Toh Wai me yayi ne"?wannan Kuma sai kin biyomu zakuji"Kai officer dakata wani irin wulakanci ne wannan da baza'a Mana bayani ba toh wallahi Babu Mai tafiya dashi"muzammil yace don haryau Bai koma ba,gyada kai dayan yayi kana yace"yayi alwashi ga wani yaro Nabeel na ikirarin ganin bayan sa,kana case in kisan da aka taba shariya dashi ya taso sabo iyayen yaro sun daukaka Kara don haka zaku bamushi dole"kaga dakata officer wannan yaro Nabeel da ake magana kowa yasan Nabeel da Lahab haka zalika Lahab bazai taba cutar dashi ba zafin mutuwa ne yasashi furta wannan kalaman maganan case na Abraham Kuma yanzun baida isheshen lafiya so bazamu badashi ba har sai yaji sauki" Mika musu hannu Lahab yayi baiyi magana ba tsawa Abbu ya buga Masa Yana cewa"Kai Lahab kanka daya kuwa koka haukace ne da zakayi surrender"dan Allah yaya kayi hakuri ku Bari su tafi Dani Kamar yanda doka ta umurta Kuma a shiga kotu na amince da duk wani hukunci da za'a yanke a kaina" Abbu ya wankesa da Mari daidai lokacin Mami ta shigo gidan don itama yanzun kullum cikin zuwa take saboda farin cikin d'anta,har cewa tayi ta yafe Masa duk lokacin da Allah ya bayyana yarinyar zata karbeta hannu bibbiyu,Kuma ta basa dama yanemeta,amma Lahab a lokacin da tayi maganan Nan Koh annuri bataga ya wanzu a fuskar Saba bare ya d'ago Kan nasa daga duke. Karasowa tayi tana tambayar lafiya shikam Lahab gaba yayi yaje ya Shiga motar tasu aiko sunga hauka Mami bala'i babu Wanda batayi ba Amma Koh kulata basuyi ba haka Suka shiga Suka tafi da Lahab.. ************** Wata sabuwa inji dan caca,zance ya karasa gari akan abinda ya faru kowa zagin Nabeel ya Fara aka abinda ya aikata wasu Kuma Suna cewa ya musu daidai,Abbu yadau lauya akan case na Abraham zancen Nabeel an ajesa gefe dan karamine shikam,in an shiga shariya duk lokacin da akayi zaman kotu Lahab baya magana sai lauya yayi jawabi in ance hakane Koh ba haka ba anan zaice musu hakane babu Koh musu abinda ya Kara Kona ran family sa kenan don sun fahimci so yake ya mutu shima,Mami da Addayiya sunyi kuka harsun godewa Allah jarabawar da Allah ya jarabcesu kenan dashi a shekaran nan Suna Addu'an Allah ya Basu ikon cinyewa. RANAN TONON ASIRI Ayau akayi Zama na karshe Babu Wanda Bai hallanta a kotun Nan ba harda peace (Mai aikin su Nnenna da aka Kai prison)family Lahab danasu Nabeel ganasu Abraham Kai jama'a a kotu makil Adewale ne kawai Babu shi Inna sunzo da mubeena Kuma tasa Nabeel ya janye Karan daya daukaka Akan Lahab don shima yanzun yayi kudi sosai Wanda ba'a San daga Ina ba,jinsa yake daidai da uban kowa shiyasa Koh Zama aji ya gagaresa"badon ransa yaso ba ya janye sai don kuka da Inna ta sanya Masa tana cewa zata tattara kayanta ta gudu ta barsu kafun ya janye zancen aka Kama na Abraham kawai,an gama gabatar da shaidu da hujoji Kuma Lahab ya amsa laifinsa na cewa dasa hannun sa aka kashe Abraham kamar yanda ake zargi. "Abisa duba da hujojin da lauyoyi Suka gabatar, da amsa laifinsa damai laifin yayi wannan kotu Mai adalci ta yankewa Hassan Al'hassan dogo Mai naira hukuncin........................................Ina daja ya Mai shariya"kattafanin kotun sukaji Amon muryar mutumin daya shigo cikin kotun ga Adewale na binsa a baya"mikewa tsaye Alhaji sulaiman yayi jikinsa na wani irin Bari sakamakon ganin Wanda ya shigo cikin kotun yace"kaiiii buba meya kawoka nan haka mukayi dakai baka tashi bayyana ba sai a irin wannan Rana tsawon shekarun nan.......................................... *Naga complain na mutane akan mutuwar Rahab Amma fa kuyi hakuri littafina na riga na tsarasa akan hakan ne,Kuma Inna bite na cire wannan bar wannan daga baya Zan rikice ne kawai in ban mantaba shekaran jiya nayita samun magana akan character in Lahab wasu sunce zasu bar karantawa saboda Babu Wanda Lahab yakejin tsoro kaza kaza kana jiya ance kunci zaima Lahab yawa* 🀧🀧🀧 * *Kunga ai Inna sake nawa na Kama naku karshe nazo na makale a hanya Ina zare ido Daman shi rayuwa ba kome akeso ake samu ba Daman haka rayuwa take aka rasa uwa ma Kuma mutum ya hakura* *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 08084453785 tare da shaidan biyan ki* Wani irin murmushi Lahab ya sake yana gyada Kai ganin Wanda ya Jima yanason gani ya bayyana a bayan Ade wato abokinsa Barrister khamal najib,tsawa alkali ya buga da guduman sa don da yawa sun mike tsaye cikin su harda ummu da Addayiya,natsuwa kotun ta danyi kad'an kafun sulaiman ya mike Wai hawan jininsa ya tashi zai koma gida hanasa fita akayi a ciki code in ganin Kamar akwai bayani a bakin Wanda ya shigon,Koh zaka sanar da kotu Kai wanene da Kuma dalilin shigowarsu a irin wannnan lokaci ana tsaka da Sharia"Zama Ade yayi mutumin da sulaiman ya Kira da buba sai Brr daya gabatar da kansa a matsayin lauya Mai zaman kansa Kuma mataimakin lauyan dake Kare Wanda ake zargi,kotu sosai yayi tsit sai ummu dake da zufa sai yanko Mata yake"Kara natsuwa khamal yayi ya gyara zaman rigansa kana ya nemi izinin Fara gabatar da hujojinsa na Kare Wanda ake tuhuma"an baka dama"shine abinda alkhali yace"nagode ya Mai shariya sai Kuma ya juya yace"Kiran buba yayi ya fito ya tsaya a inda masu bada shaida Koh masu laifi ke tsayuwa tambaya Brr ya Soma Masa Kamar haka"Malam Koh zaka iya sanar da kotu cikekken sunan ka"eh Sunana Adamu ja Amma anfi kirana da buba ja"Masha Allah Koh zaka sanar da kotu menene alakanka da family dogo Mai naira da Kuma son halartar shariya tayau daka nema"? Kamar yanda nace Sunana bubaja Ni ainahin dan nijar ne kamar yanda kowa ya gani Ni buzune,Neman kudi ya kawomu NAGERIA nida iyalina,bamusan kowa a kasar Nan ba tunda mukazo wahala mukesha sai dai mu samu bayan shago Koh gida mu rabe mu zauna muna kwana Ni Kuma Ina Saida shayi. A hakan wata Rana Allah ya hadani da Alhaji Alhassan Harya daukeni aikin gadi a gidan sa nida iyalina mun koma gidan sa da Zama Kuma Babu abinda Muka nema muka rasa rayuwa ta Mana dadi dayake matar Alhassan macece Mai fada Amma tana da kyauta hakan yasa Muka kashe zuciyar mu dagani har matata Muna cin harziki harda yaron mu. Nafi shekara ishirin Ina gadi a gidan Alhaji hatta makarantan d'ana shike biya,mun Zama Kamar Yan uwa,yayansa sun giggirma har wasu sunyi aure. Bayan wasu shekaru zuwa lokacin gidan ya Kara cika ga aure da Alhaji ya Kara ya auro Amina,tunda Alhaji ya auro Amina kullum sai sulaiman yazo kofar gate yayiita min magiya Akan na Kira Masa Amina Koh Kuma ga wasika na Kai Mata amma Koh daya ban amince ba duk yanda yayi ta hadani da Allah naki,ana haka sai kanwarsa ta Fara zuwa gida tana baiwa Amina wasika daga baya Allah ya tona asirin abin Alhaji ya ganosu shikenan sai yasa security a gidan tsaro ya ninka nada. Shikenan tun daga lokacin bankara ganin sulaiman ba Ni harnama manta da labarin sa,kwasam wata rana saiga yarona ya shigo gidan da gudu ya Kama hannu na Dana mahaifiyarsa Muka nufi sashin mu don yanzun mun Jima da barin bakin gate,hankalin mu ya tashi da abinda ya sanar damu kwata kwata bamu taba kawo hakan a ran mu ba cameran daya dau kome ya bani kana yace in nunawa Alhaji,Kuma ya Kamata mu gudu mubar gidan don Sun gansa dumu dumu Yana musu vedio"shin yanzun kana tare da kemeran ne tsahon shekarun Nan Koh yaya Kuma ya Kamata kama kotu bayani dallah dallah suwa dan naka ya gani"? Eh dama Yana karatun jarida ne da Alhaji yadau nauyin sa yace min wata Rana sun fito makaranta Suka biya gidan abokin su zai dubasa kutsam sai yaga Khadija(ummu)ta shiga wani gida dake unguwan shikuma yayi zaton Koh gidan Yan uwantane yace Bari ya shiga ciki ya gaidasu saiya bita cikin gidan Yana kokarin bude kofar dakin ya shiga sai ya Fara Jin magana na tashi Nan ya zagaya ta window yasa hannu ta baya ya bude labule wa'inda ya gani a ciki yasa sa daukar camera sa yayi record na kome Yana tsaka da daukane Mutumin ya gansa harma da matar suka bisa shine ya fito a cikin gidan. A ranan yarona yabi ya rikice akan mubar gidan nace Masa Ni sai na nunawa Alhaji Kuma na Masa sallama bazaiyu nabar gidan baby sallama ba kuma in Muka koma nijar Banda sana'a Koh wani aiki Amma hakan yaron Nan yace sai dai mu tafi shi haka kawai yaji tsoron Zama a gombe,mahaifiyar sa tace ya shirya kayansa zata tafi dashi in yaso inya samu natsuwa sai su dawo in Kuma Basu dawo ba Nina bisu,haka Koh akayi a ranan Suka bar gidan,nayita jiran ganin fitowar Alhaji Amma bansamu ganawa dashi ba Ina zaune Khadija ta dawo tazo ta shiga gidan. Washe gari abin mamaki saiga Alhaji ya tashi da ciwon kafa hankali na ya tashi naso naje na sanar dashi Amma Kuma saina kasa Koh shiga cikin falon gidan a hakan yayita ciwo wata da watan Ni duk lokacin da na yunkura Zan sanar dashi sai na kasa, har Allah ya dauke rayuwar sa, a Randa ya rasu na tattara kayana bamma kowa bankwana ba nabar gombe na koma kasarmu Amma abin ciwo iyalina Basu zo kauyen muba na tsorata sosai hakan yasa na dawo cikin gombe Babu irin yawo da banyi ba Amma bansame suba duk Inda nasan Zan gansu na duba Amma bangansu ba hakan yasa na Kama shago Ina xama a ciki Ina dan sana'a,maganan camera Kuma memory na saya Ina chanja record na vedio duk bayan shekara biyu duk abin kallo daya fito na yayi saina saya na tura a ciki na aje don nasan wata Rana xai min matukar amfani. Kusan a Yan kwanakin Nan sai na ringa mafarki akan yarona Yana cewa na nemi gidan Alhaji naje nakai abinda ya bani,Koh bayan shekaru darine indai Ina da Rai unguwan bazai bace min ba saidai Kuma na kasa gane gidan dayake anyi gine-gine na zamani Kuma masu kyau don ashekarun baya kaf unguwan gidan Alhaji ne Mafi kyau sauran duk na talakawa ne Amma yanzun Naga ba haka bane,kutsam wata Rana Allah ya hadani da wannan yaro Adewale nake Masa kwatance gidan yace min yasan gidan don dan gidan abokin sane saidai babu lafiya don yaron gidan yasha guba Allah ya Masa rasuwa Nan yake bani labarin abinda ke faruwa,haka kawai naji hankali na ya tashi Kuma naji yaron ya kwantamin a rai anan nake basa labarin abinda ya kawoni,amma yace gaskiya zuwana gidan yanzun akwai hatsari, Inna yarda dashi muje ya nemamin gida na zauna zasu daukaka Kara akan lamarin ayi kome a gaban Sharia abi musu hakkin su, salati jama'ar dake code in suka sake,buga guduman sa Alkali yayi kowa ya nutsu,Neman ganin vedio akayi Mika musu wayan sa yayi aka zare memory,had'a kayan kallo akayi babba yanda kowa dake zaune acikin code in zai gani,ummu Kam sharkaf tayi da zuba,haka uzaifa hankalin sa ya tashi, wato mutumin da ya nuna baya kaunar wani Koh ance yama wannan Abu baza'a Yi mamaki ba da ace Mamu ce Babu Wanda zaiji dar don ansan Bata son mami Amma Wai ummu mikewa tayi ta Soma rantse rantse,malama Khadija Nan kotune ki kiyaye komawa tayi ta zauna hankali a tashe. Haskene irin na films in da Babu colour amma ras ake ganin fuskar mutane,falone irin na da Alhaji sulaiman na tsaye sai Khadija daken zaune akan kujera cikin dari dari Suna magana"gaskiya kaf duniya Babu Wanda na tsana irin Amina"Kuma Zan iyayin kome don Naga bayan ta"gyada Kai Alhaji sulaiman yayi sai Kuma yace"karki damu nida kike ganina innan tsohon saurayin tane amma ganin Mai kudi yasa ta auresa ta barni don haka nima fansa nakeson d'auka a kanta Kuma Koh nawa Zan iya kashewa don ganin bayanta Ni aguna kudi ba kome bane"gyara Zama Khadija tayi tace watoh yanzun ka nemenine dan mu had'a hannu dakai mu raba auren nasu Koh yaya don nidai kome Zan iya Amma Banda kisa bazan iya kisa ba" Karkiji kome Ina dai kin amince Zaki had'a hannu Dani"eh na amince"toh ke mekike so ayi Mata"Ni bani da buri daya wuce Naga Babu ita a cikin gidan, haka cikin dake jikinta babu shi shine burina,itace tazo a baya sannan tana kokarin mallake kome na gidan Kuma Ni na tsaneta so nake mu Kulla Mata sharri Wanda zaisa Alhaji da kansa yaji ya tsaneta Kuma ya saketa tabar gidan cikin jikinta Kuma so nake ya zube Babu shi"an gama karkiji kome basai an Mata sharri ba ni Ina da malami Kuma harma yamin aiki akanta,waro Ido Khadija tayi tace malami Kuma nida nace ayi Abu na sharri Kuma a samu maganin zubda ciki"? Karkiji kome wannan zaifi yin aiki farat daya sai Kuma ya shiga daki ya fito hannunsa dauke da wani laida fito da wani yadi yayi ya Mika Mata Amma ba'a ganin wani kalane saboda Babu colour a vedion Amma sunajin tambayar da Khadija ta Masa"wannan Jan Kellen fa malam"?Mika Mata wasu layu uku yayi again bai Bata amsa ba ya sake Mika Mata wani sweet"karba tayi tana jujjuyawa a hannunta kana ta sake jefo Masa tambaya"wannan Jan sweet in ki tabbatar Alhaji yasha shi Koh a abinsha Koh a hakansa wannan kelle Kuma Zaki shimfida ne a kasan zanin gadon da zai kwanta saiki jera wannan layun duka uku a kasan filonsa ki tabbatar Babu Wanda ya kwanta akan shimfidar Koh Shan abinnan sai shi kadai" Toh meye ma'anan hakan Kuma Ni a zatonsa ai Amina ce za'a ma magani ba Alhaji ba"wannan kikayi abinda nace Miki toh shikenan kaf duniya Babu Wanda Alhaji zaiji ya tsana sama da kome a duniya...............sai Kuma Sukaga Alhaji ya juyo ya kalle window Yana cewa waye a wajen sai Kuma Sukaga camera na gudu Yana haska kasa shikenan Kuma saiya dauke"innalilahi na shiga uku salati kawai ke tashi a kotu sannan lauya ya nemi ganin Khadija fitowa ummu tayi sai hawaye take tazo ta tsaya tambayar da aka jefo Mata yafi kome daga Mata hankali"watoh menene gaskiyar alakarsu da sulaiman Kuma zargin da ake gaskiya ne abinda sulaiman ya sata shita aikata washe gari Alhassan ya tashi da ciwon kafa"? Tabbas nasan irin wannan Rana na zuwa shiyasa tun farko naso na sanar da hakikanin gaskiyar abinda ke damun Alhaji tun kafun yabar duniya amma sulaiman yayimin barazana da rayuwata mundin na furta ainahin abun saiya ga bayana"kotu ta tambaye ki hakikanin Al'amarin batace ki kamo wata jawabi ba"shin Menene alakarki da sulaiman? gaskiya bamu da wata alaka a tsakanin mu asali ma wata Rana Dana fita a gida ya tareni yace Yana so muyi magana naji tsoro ainun Amma lokacin da naji yacemin saurayin Amina ne nada, Kuma aiki yake so muyi tare zai biyani kudi masu makudan yawan gaske Jin zancen kudi yasa na amince muka saka rana da waje Muka hadu a Randa muka zauna muna tattaunawa yaron bubaja ya ganmu Kuma muka gansa munso ya tsaya amma haka yaki tsayuwa ya gudu hankali na ya tashi shiyasa nace Nina fasa aikin Amma yace Dole nayi abinda ya sani zancen d'an bubaja Kuma in zuba Ido zancen Nan babu Wanda Zai sani. dana dawo gida nayita dari-dari dasu bubaja gani nake Kamar zasu tonamin asiri Amma hakan bai hanani narkar da sweet Inda sulaiman ya bani a shayin surkina ba haka zalika na shimfida Kellen Nan da laya a daren na langwabe da sunan rashin lafiya na dau uzaifa na kaiwa Addayiya a daren ta kwana dashi don nasan tabbas ba kwanan Amina bane Kuma Amina bazata yarda ta karbi uzaifa a hannun Addayiya ba Kuma haka zalika Addayiya bazata kwana da uzaifa ba daki d'aya da mijinta duk da lokacin yarone karami,Aiko hakata ta cimma ruwa washe gari ya tashi da ciwon kafa Amma haka ya d'aure yaje masallaci daman Ina fakonsa Yana fita na shigo sashen nasu Alhamdulilah Babu Wanda ya ganni harna Shiga na Ciro abinda nasa Masa sauran shayin ma na zubar a toilet,lokacin da nazo fita a dakin karaf Muka hadu da Addayiya Nan na Soma Kame Kamen Mara gaskiya kana nace Mata nazo duba uzaifa ne Yaya kwana"dayake ita Bata kawo mummunan Abu a ranta ba Kuma Bata tambaye ni Jan Kellen dake hannuna a nannade ba tace min in zanzo duba yarona Saida asuba zanzo uzaifan dan yayene,kana ta daukesa ta bani nabar sashen su. Hankali na ya tashi lokacin da Naga surkina sai ciwa ce ciwa ce yake tun ranar dana saka Masa abubuwan Nan, hankali tashe na koma wajen sulaiman anan yake cewa ai maganin haka yake Nan da wata uku zanga abinda zai faru Aiko Nan da wata uku Alhaji ya rasu, hankali tashe naje na samu sulaiman akan gaskiya Ni Zan tona asirin gaskiyar abinda ya faru kudi sulaiman ya bani bana Wasa ba Kuma ya rantse da Allah Ina fadan gaskiya sai yayi ajalina,Ni Kuma haka na amshi kudin nazo naci gaba da rayuwata na watsar da kome Amma daga baya na fahimci dalilin amfani dani da sulaiman yayi watoh saboda Amina ta dawo garesa. Uhmmmm ummu na gama bayani lauyan su Adewale ya mike Yana cewa" ya Mai shariya wannan Sharia da muke da Wanda ake yanzun Yana da banbanci an shigar da Sharia ne cikin shari'a Babu alakar kisan Abraham da Kuma wannan gabatar da shaidu da ake,gyada Kai Alkali yayi yace a tsare Masa sulaiman kana a cigaba da shari'an su Lahab shin lauya nada hujoji dazai Kare Wanda ake zargi"kwarai ma kuwa Ina dasu,toh Bismillah ka gabatarwa da code hujojinka"Kiran Nabeel lauya yayi dam dam haka zuciyar sa ta amsa mikewa yayi a dake yazo ya tsaya a Inda aka tanada"code zataso sanin cikekken sunan ka"Sunana Nabeel Muhammad"zaka iya sanar da kotu alakar dake tsakanin ka da Wanda ake tuhuma dasa hannun sa a kisan Abraham"abokina ne"abokin ka nada Koh na yanzun"Kamar ya nada Kona yanzun"calw down Mana Nabeel Wai nace abotar taku har yanzun anayi Koh an daina"? Kaga Brr karka kawo wata manufa ta daban kawai in zaka min tambaya kamin abinda ya shafe kaina ba wani ba"kotu ta bashi dama kuma tana umurtar ka daka amsa Masa duk tambayoyin da zai jefa maka"a gaskiya Ina bukatar lauya nima Mai girma Mai shariya a d'aga shariyar Nan harsai na d'auki lauya" da murmushi brr yace"haba Nabeel tambaya ce fa Kamar yanda akama Khadija haka za'a maka ka koma ka zauna kaima toh, menene na d'aukan lauya Kuma"?dan shuru yayi sai Kuma yace eh abokina ne har yanzun. a ranan............. Koh zaka iya sanar da kotu a wannan dare a Ina ka kwana"?dan rikicewa Nabeel yayi kafun yace kamar ya bangane a Ina na kwana ba"?eh a wannan daren dai a Ina ka kwana"gaskiya bazan iya tunawa ba don ya Jima sosai"toh shikenan tunda kace ya Jima sosai bari na tuna maka a ranan baka kwana a gidan ku ba Kama iyayen ka karya da sunan zaka kauyen su mahaifiyar ka zaka je ka gaida kakan ka ta wajen uwa sai Kuma da misalin karfe 1:23am na dare ka fito daga cikin gidan Godwin dake saman layin ku Kuma a daidai lokacin aka kashe Abraham Koh zaka gayawa code meya kaika gidan a daidai wannan lokaci? Wallahi karyane Babu Inda naje Ina gidan mu wallahi karya ake min wannan ai kazafine"malam Nabeel ka kiyaye a kotu kake"shuru Nabeel yayi cikin tashin hankali ganin wankin hula nason kaisa dare,Dr Colin's kutu nason ganin ka don amsa wasu tambayoyinta mikewa wani magidan cin Cristian yayi yazo ya tsaya"Koh zaka sanar da kutu hakikanin abinda ka gani a wannan rana"kwarai ma kuwa a wannan Rana bayan na taso daga aikin dare da aka kirani na nufo gidana dake kusa da gidan Godwin tunda na sharo kwanar layin mu wutar mota ta ta haskamin mutum Kuma akwai hasken nepa duka, ya fito daga gidan hankali tashe jiki duk jini fuskarsa a rufe nayi matukar tsorata hakan yasani niyar juyawa na koma Inda na fito sai Kuma motar ta mutu yaki tashi wutar motar ma ta d'auke Nan nayi ta kokarin kunnata amma na kasa Saida yazo daf dani cikin duhu kawai saiya gwaru da motar tawa ba tare daya kula akwai mota a wajen ba Nan ya buge kafarsa da Sauri ya tsunguna Yana mammatse kafar Kana ya mike yabar wajen Saida yabar wajen nayi Sauri na bude motata na sauka Nan na kunna wayata Zan haska hanya na wuce gidana kawai saina ga wayarsa a kasa ya Fadi da Kuma mask na fuskar sa alamu ya cire mask inne,da banyi niyar d'auka ba amma daga baya saina d'auka kawai nayi gida tunda na koma gida haka na kasa natsuwa kwata kwata Saida na kunna wayan Nan amma wayar da lock a ciki sai dai screen in wayar akwai hoton shi Nabeel da Kuma yayarsa sun dau hoto tare Kamar ranan sallah ne ma hoton aka daukesa,lokacin dana ga hoton saina aje wayar da yakinin taima ya Kira yanason wayarsa,washe gari da safe saiga labari ya karade gari an kashe Dan Godwin babu Wanda naji ina zarginsa a Raina sai Nabeel amma Ina tsoron karna sa kaina a rikici bani da gamsheshen hujja Kuma naji tsoro Kar wani bincike yasa a bi diddigin layinsa,na kashe wayar gabaki daya,wata sabuwar labari danaji shiya dagamin hankali shine Wai Nnenna da Lahab su ake tuhuma sai dai ba'a Kama yarinyar ba har Shiga code nasu Lahab na farko naji labari da Kuma fitarsa Lahab na fita da kaina naje gidan su da sunan musu Jaje nace Ni malamin sune na makaranta anan Muka kebe da Lahab na basa wayar Nabeel Kuma na Masa bayanin ta Inda na samo wayar,Nan yamin godiya amma yace bazai iya kaiwa hukuma wayar ba,Koh bayani ba don Koh Nabeel ne yayi kisan Nan bazai iya tona Masa asiri ba" tuni code ya kidime da hayaniya da Al'ajabin abinda ke faruwa kankace me jama'a sun Fara tofa Albarkacin bakinsu,bayani kotu ta natsu aka Kara tambayar Nabeel amma Nabeel ya karyata yace sai dai in sharri akeson lakaba Masa tabbas wannan wayan sane amma an saceta bai gani ba tun da Jimawa ganin Nabeel nason bawa lauya ciwon Kai aka dauko record na CCTV camera dake wani gidan shahararren dan kasuwa dake kallon gidan Godwin Nan aka haska tabbas gashi Nan Nabeel ya fito daga gidan awannan rana sabar toshiwan basira abinda yasa ya rufe fuskar tasa Yana fita kofar gidan ya cire Kuma camera ta d'auka dayake kofar gidan mutumin akwai hasken wuta radau. Kuka Nabeel ya sake cikin tashin hankali"Muna sauraron ka malam Nabel"tabbas anyi haka nasan Koh naki Koh naso yaune ranan tonon asiri duk wata boye boye yau bazai boyeni ba"tabbas Nina kashe Abraham da hannu na"Inna Kam faduwa tayi a kasa sumemmeya take aka dauketa akayi waje da ita itama mubeena da Sauri tabi wa'inda Suka dau innan tana Kuka don dukan su Sunsan tabbas a ranan Nabeel baya gida,kenan gaskiya ne Nabeel dan uwanta kwalli d'aya a duniya Kamar tsokar nama daya a Miya shine yayi kisan Kai innalilahi wa'inna'ilahu raji'un..................................................... *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 08084453785 tare da shaidan biyan ki* Menene Abraham ya maka da harka kashesa Wanda a iya bincike da kotu tayi akanka Babu wani sanayya a tsakaninku"?share hawayen sa yayi bai iya daga Ido yaga jama'ar dake zaune ba tunda Inna ta Fadi gabaki d'aya yaji duniyar ta Masa zafi"tunda Muka taso da Lahab bani da abokin kishi irin sa saboda Ni Ina da bururruka a rayuwata masu yawan gaske amma abin takaici kullum Lahab shike nasara akan burina saiya samu Ni Kuma naci alfarmar sa wannan yasa na Fara Jin tsanar sa a raina tun Muna kanana,kokari ya fimu a makaranta tare Muke kin zaman class amma abin mamaki duk lokacin da zaiyi jarabawa sai yafimu samun Makin da Average Mai yawa"ban Kara Jin tsanar Lahab ba sai lokacin dana kyalle Ido na gansa da Nnenna yarinyar da kyawonta gabaki d'aya ya tafi dani naji duniya kaf babu Wanda nakeso sama da ita amma kafun ma na ganta Lahab Harya shiga rayuwar ta. Na ringa bibbiyar ta harna gano gidan su Kuma naje nace Mata ta rabu da Lahab bata Mata rayuwa zaiyi amma budan bakinta sai tace bani da matsala da hakan sosai nayita shishige Mata a boye amma ta nuna bana kaunar Koh ganin fuskata abin yamin ciwo bana Wasa ba duk da nasan Bata sanar da Lahab abinda ke faruwa,gashi mu uku Muke abota Amma Lahab yafi sirri da Ade duk da Yana kokarin boye hakan a gabansa Amma Ni na sani, sai Kuma aka soma zancen jarabawan weac Karo na farko Lahab Bai bawa jarabawa na hankalin sa ba Koh zancen biyamin kudi bayayi lokacin sama bana samu sosai,hakan yasa na Soma binciken sa anan na gano yana tare da Nnenna naji tsoro kada shigowar ta rayuwar sa yasa ta kwace min shi. Wata Rana Ina zaune a cikin gida aka turo yaro Yana kirana Ina fita abin mamaki farida(budurwar Anwar) na gani cikin mota Kuma daman na riga na santa nasan zancen fasa auren ta,shiga motar nayi taja mukabar layin,wani gida Mai tsananin kyau Muka Shiga har lokacin bata sake cemin kome ba faka motar tayi ta bude ta fito nima fitowa nayi Ina tambayar ta lafiya tace na Shiga mota Kuma zata kawoni Nan"?Mena gaggawa in mun Shiga zaka ga Koh menene ai,Koh tsoro kake ne"?girgiza Mata Kai nayi muka shiga cikin gidan,abin mamaki dadyn mahraz ne zaune Yana jiran mu Zama nayi na gaidashi anan yake cemin fatan na gane sa nace kwarai ma kuwa abinda ya biyo baya a zancen sa shine"yasan cewa Ina matukar jin tsanar Lahab Koh"?don ya lura Adewale ne kadai ke zaman tsakani da Allah da Lahab nikam zaman abin hannun sa nake dashi"da fari maganar daya fadamin ya batanin Rai saidai magana ta biyu taja hankali na"shine Wai zamu had'a hannu muyi aiki amma fa Zan samu kudi zai ban kudi kusan 10 millions. Hankali na ya tashi Jin makudan kudin da ake zancen za'a bani Nan naji cewa Babu abinda za'a sani na kasa Yi akan kudin Nan anan yake sanar dani cewa kisan Kai zai sani nayi"Abune da ban Saba ba ban Kuma San dalilin dayasa ya zameni a matsayin makashi ba,amma kudin Nan bazan Bari ya kubuce min ba"nunamin farida yayi yace wannan yarinya fansa takeso ta d'auka akan Lahab Kuma ta gano Lahab ba karamin kaunar Nnenna yake ba don haka daurawa Nnenna sharri ba karamin broken na heart nasa zaiyi ba,daman ba kaunar Lahab nake ba hakan yasa banyi wani gardama ba anan Muka shirya plan namu,farida ita taja ra'ayin Abraham kamar yanda Muka tsara a club kwaya ta basa masu karfin gaske kana ta hada Masa dana tada sha'awa Mai tsanani Kuma tace Masa yaje dakin Nnenna tayi Masa waya tace yaje su Kwana tare,dayake ya bugu da kanta ta maidashi har kofar gidan su ta saukesa ya fita da layi ya Shiga cikin gidan nasu cikin tsakar daren Nan"daidai lokacin nima na shiga cikin gidan saidai ban shiga flat in ba Zama nayi a bayan window Nnenna, Inajiran abinda zai faru Aiko Kamar yanda Muka tsara haka yagudana,tabbas Nnenna buga masa lamp tayi ihunsa shiyasa ja hankalin y'an gidan Wanda yasa Nnenna tsorata ta bude window ta dirka Kuma duk abinda take Ina labe Ina kallonta tana fita dayake karnukan sun Saba da ita basu Mata haushi ba. Window data bude shina bi na Shiga dakin nata wuka na d'auka na caka Masa a ciki kafun na fita dakin da gudu a lokacin karnukan Suka Soma Bina Suna haushi Wanda yaja hankalin Yan gidan suka zaci Koh Nnenna ne,suka zagayo.......................... "toh Nabeel Koh zaka sanar damu abinda Rahab ya maka ka kashesa bayan sharri dakasa aka ma Lahab meye Rahab ya maka shida babu ruwan sa baida wata alaka dakai saita mutunci amma ka bisa har London ka kashesa Kuma camera ya tabbatar da shigarka layin nasu a wannan Rana"?tabbas naje London Amma kafun naje na cikawa farida aikinta watoh na d'au wayar Ade a ranan danaje gidan su lokacin daya dawo hutu,bayan nace Masa Ina so ya kawomin abinci sai kawai nadau wayarsa bincike nayi sosai harda chatt nasu Nan na gano Lahab har aure yayi nayi farincikin haka na tura hotonan a wayata,na turawa farida ita Kuma ta yad'a,kudin da Alhaji sulaiman yamin Alkawari ya cikamin yaban kudaden Amma yace Dole Zan dan Kama sana'a Wanda zai d'au hankalin mutane karsu zargi kudin danayi dare daya. duk da aikin farko da mukayi bamuyi nasara ba amma ana biyu munyi nasarar da tasa gabaki d'aya family su Lahab a damuwa amma Kuma sai naji hakan bai wada ceni ba ganin d'aukaka da Allah Yama Lahab sosai abin ya tsayamin a wuya naji Babu Wanda na tsane cigaban sa sama da Lahab,nida farida mukaje London Muka had'a Baki da Waitern dasu Lahab ke ordern abinci a wajen su,munfi wata biyu a London muna jiran randa za'a Yi order amma shuru Lahab baya ordern kome,kutsam saiga shi ranan yayi,sam ban kawowa raina Rahab bane zaici harga Allah duk da nasan gida daya suke amma tunani baizomin kila Rahab Koh Addayiya suci ba Muka saka poison Mai hatsarin gaske Rahab yaci ya mutu" Aiko Nan code ta cika da mamaki aka hau salati bana Wasa ba ganin waje yaki natsuwa yasa alkali wanke peace tare da bimata hakkin ta ga Kuma tara da Nabeel zai biya ta. lokacin da aka juyo za'a Kama Alhaji sulaiman wayam kamar walkiya ba'a gansa ba,babban magana su dai police dake gadi basuga wucewar Saba,Nan aka Soma kus kus Ashe Dan kungiyan asiri ne, Nan aka d'auki ummu da Nabeel aka wuce dasu tare da d'aga shariya sai Nan da sati biyu kotu ta bada belin Lahab zai iya komawa gida, mutane da yawa sun babbawa peace kyautar kudi masu mugun yawa ana Kuma tsinewa su Nabeel Sunsa yarinya zaman yari harna shekara biyu cip ba tare da hakkin taba dady shima hankalin sa ya tashi baisan a wace duniya Nnenna ta Shiga ba ya kasa riketa a matsayinta na Yar dan uwan sa Wanda ya turota wajen sa gashi yanzun baisan Inda zai sameta ba,Mami Kam saida aka fitar da ita don kasa fita tayi sai kuka take tana ta Cuce kanta. Kutu ta bada umurnin kafun shariya ta gaba tanason a durkusar Mata da Alhaji sulaiman da Kuma farida a kotu a duk Inda Suka Shiga Yan Sanda su Nemo su. Mami Saida ta kwanta a gado gabaki daya ta gama rikicewa sai cewa take ta cuci kanta ta ruguzawa yaronta rayuwarsa ta rabasa da matar sa da yayansa Anya Allah zai yafe Mata kuwa sulaiman ya cuceta,ana ta Bata hakuri shidai Lahab ba uhmmm ba uhmmm uhmm Amma dai yaje ya dubata sai cewa take Hassan ka yafe min ban maka adalci ba a matsayina na uwa shidai kansa a kasa harta gama surutun ta ya mike ya fita. Yaje wajen Inna gaskiya halinda ya ganta ita da mubeena ya saka sa a damuwa sosai Inna ke fama da ciwo bana Wasa ba asibiti ya chanja musu zuwa Mai tsada yadau d'awainiyar jinyar ta ita dai mubeena duk lokacin da ta gansa sai dai kawai mutum yaga tana kuka. Cikin sati biyun Nan abubuwan da dama sun faru ciki kuwa harda rasuwar Inna da Kuma kamo farida da akayi amma Alhaji sulaiman ba'a Yi nasarar Kama sa ba haka kotu ta yanke mutu hukunci daidai da abinda Suka shuka Allah sarki mubeena Suma Kan Suma ta ringayi ta rasa dame zataji da mutuwar Inna ne ko da rabuwa da Nabeel dan hukuncin kisa aka yanke Masa ta hanyar rataya shida farida ita Kuma ummu a bisa lura da akai Bata da niyar kashe Alhaji Kuma bata San zai mutu ba a dalilin abinda ta saka Masa, yasa aka sassauta Mata hukuncin zaman gidan yari na shekara bakwai,ga maraicin rashin uwa da uba,lokacin da yazo Kan gawan Inna zai Mata bankwana ba karamin kuka yaci ba ya nemi yafiyar mubeena duk da yaso ace Inna na ra'ayi yazo ya nemi tata yafiyar amma sai ya kasance shine ajalinta,tabbas duniya budurwar Wawa ce shikam tasa ta Kare,duniya tama mubeena zafi jau yayin da Mami ma ke fama da rashin lafiya Wanda hakan ya Hana Lahab komawa London. Mubeena maraici ya Mata yawa sosai yanzun tana gidan bappa Ado ana fama da rayuwa amma kwata-kwata rayuwar ta baya Mata dadi kwata-kwata tana cikin bakin ciki da damuwa bama Kamar inta tuna saura kwana kaza a rataye dan uwan nata. Mami taji sauki kana ta tattara ta koma gidan da ta sayawa mahaifiyar ta da yaranta donta rantse bazata Kara Zama a gidan sulaiman ba yaran ma badon badon ba da dangin sulaiman zata mayarwa suje can su karata amma data tuna Y'ay'a dai nata ne Kuma itace gatansu hakan yasa ta rungume abinta,Lahab ya taso da zancen komawa London Wanda Mami ta nuna Bata son hakan ya zauna a Nigerian in ma karatu zai cigaba yaci gaba anan don ita yanzun kaf duniya Babu Wanda takeso a kusa da ita irin Lahab yanda taga ya chanja gabaki d'aya dabi'arsa da halayen sa Suka sauya, hankalin ta atashe yake gabaki d'aya yaron ya koma Kamar wani baki a cikin familyn sa baya sakewa da kowa magana wannan bayayi sai yaga dama yake,Kuma duk a dalilinta ta rabasa da duk wani yakini nasa akanta,da ciwa yarinyar da bataji ba bata gani ba mutunci,yanzun burinta Bai wuce aga Nnenna ba. ***************** Abbu ne yace bata Isa ba Lahab ya koma ya jona masters nasa yaci gaba da karatu in ma ball inne yaje yaci gaba da bugawa Allah ya bayyana Masa iyalansa,bazasu sake Bari Mami ta karasa shiba a banza, inya zauna a gidan ma hankalinsa bazai kwanta ba tunda kullum tunani yake matarsa na kasar,haka Koh akayi Lahab ya tattara yanasa yanasa yabar NAGERIA shida Adewale don Ade Yama samu aiki a London yanzun Kuma har gobe ba'a ga sulaiman ba. ********************* BAYAN SHEKARA GOMA Ihune ya cika cikin stadium in dake kasar Egypt,Wasa ne ake bugawa tsakanin NAGERIA da EGYPT Kuma a lokacin wannan gorzon footballer yayi winning nasu Yan NAGERIA dake zaune tuni suka mike Suna ihu ana Kiran"Hassan Lahab Hassan Lahab gabaki d'aya sunan ne ya cika stadium in Mai girman gaske dake dauke da dandazon Al'umma na kasashe daban daban,jarumi Kuma sadauki shiya bayyana a tsakar filin Yan uwansa bakaken fata kuma Yan team nasu sun dagasa sama ga coach nasu dake ta murna hannun sa d'auke da wani tafkeken cup an Masa Ado a ciki sai walwale yake Golden colour,kowa ka gani indai bakin fatane fuskarsa a washe yake sabanin Wanda yaci kwallon babu alamun fara'a Koh alamun Jin dadi a fuskar sa Wanda jama'a basu damu da hakan ba don Inda sabo sun Saba da wannan dabi'ar tasa,Saukesa akayi a hankali ya Soma tafiya sanye take da kayan ball wando da riga damtsen hannun sa d'aure da shaid'an Captain na Yan Wasa, Yana fita a stadium kwata-kwata mutum ya gansa bazaiyi zaton Yana da wannan kuzari na buga kwallo ba sai dai Yana dauke da manyan 6pack ga muscle nasa masu girma sosai tafiya yake kansa daya sha aski irin na Yan kwallo Yana duke a kasa Bai dagowa bare yaga Yan jaridu dake binsa Suna jefo Masa tambayoyi,matashi ne a kalla bazai wuce shekara 30 zuwa 31. Zaune yake a cikin hotel Inda aka Kama musu shi kadaine a dakin sa a zaune ya zubawa waje daya Ido,turo kofar akayi amma Bai wani dago ba,wani kyakkyawan matashi brown colour dashi kudi dajin Dadi sun ratsa shi sosai fuskar sa d'auke da farin ciki ya shigo dakin cikin Jin dadi baiyi wata wata ba Koh shakkan Wanda ke zaune fuska a hade ba yazo ya rungumesa da karfi,amma Koh gizau bawan Allah nan baiyi ba. Haba Lahab yaufa ranan murna ce dan Allah ka sake fuskar Mana friend"?hannu Lahab yasa ya ture Wanda ke bayan nasa har Saida ya kwanta akan gado kana ya dago kansa ya kallesa sau daya ya sake kauda fuskar tasa,shikam dayeke ya Saba da halin Lahab Bai wani Bata Rai ba sai mikewa da yayi ya zare P-cap dake kansa take yalwatancen gashin kansa ya bayyana harma da tabon sallah da yayi radau a goshin sa yayi bakikkirin Wanda ya Kara haska annurin fuskar sa"ya sake kallon Lahab in yace"kaga lokacin sallan mangariba ya kusa ya Kamata ka tashi kayi wanka mu tafi masjid time na wucewa" Kin mikewa Lahab yayi tsungunawa guy in yayi ya kamo takalmin ball in kafar Lahab ya zare ya zare socks in, wandon ball in waist in Lahab yasa hannu zai zame wani irin damko hannun sa Lahab yayi hankali tashe cikin muryarsa Mai amo da girma yace"Kai Adewale a u out of ur sense"?kyalkyalewa da dariya Ade yayi haryana kwanciya kana yace"toh bagashi nasaka kayi magana ba ace mutum tunda ya tashi da safe banji yace kome ba"?tsaki kawai Lahab yayi ya mike ya Shiga toilet in bai Jima sosai ba sai gashi ya fito da towel lokacin Ade baya dakin. Sanye yake da jallabiya fari sai hulama fari tas takalmi ya sanya kana ya fita a cikin hotel room in,laft ya hau ya saukesa kasa,fitowa yayi haraban Hotel in gabaki d'aya larabwa ne ke shawagi a wajen duk Inda ya wuce sai kaga ana nuna sa da hannu Koh ana kallon sa masallaci ya shiga anan ya hadu da Ade a ciki. Bayan an idar da sallah har mutane sun watse lahab Bai fita ba hakan yasa Ade tashi ya fita sai da akayi isha'i kusan karfe 8:00 na dare lahab ya mike yabar masallaci,Yana Shiga cikin dakin nasa ya samu Ade zaune agaban system Yana dannawa amsa Masa sallamar yayi bawai don yaji sallamar ba sai sanin da yayi yayi kafun ya shigo dakin, Kwabe jallabiyar yayi ya kwanta akan gado,ga abincin Kanan ninaci nawa"Ade yace kala Lahab baice ba Kuma bai Mike ba shima Ade bai Kara magana ba har kusan 9:00 na dare Suna dakin bawai Hira suke Koh wani abuba ah ah Lahab na kwance Ade na aiki a system,d'an d'ago kai yayi ya kalli Lahab kana yace"Wai friend kasan gobe zamu bar kasar Nan Koh pls wannnan Karo kabi Yan team naku ku koma NAGERIA Mana shekara da shekaru ka bar kasa, Kai an zuba maka Ido ma bakasan anayi ba" Shuru Lahab yayi again amma ya Kara tamke fuskar Nan tasa tamau Babu Koh digon fara'a"maganar gaskiya nefa Lahab wannan Karo ya Kamata ka d'aure muje naija Mana Kai baka gajiya da zaman London da sauran wasu kasashe amma baka tuna kaifa cibinka a naija yake"?karkaga shuru da Mami da Abbu Suka maka kazaci Koh Basu damu da Kai bane Koh basa sonka a kusa dasu Dan Allah ka musu adalci mana" "Adewale gaskiya bazan je naija yanzun ba daga Nan Libya Zan wuce"da mamaki Ade yace"Libya Kuma Lahab wani wasan kake dashi ne a can don Ni na gaji da London Nan so nake na leka nageria"?MAXHEAL pharmaceutical's(Libya)Ltd, industry akwai wasu pharmacist da akeso nayi aiki dasu acan Suna so mu had'a hannu ne da industry nasu akwai wasu magunguna da sukeso su bugane"gyada Kai Ade yayi cikin happy Jin yanda Lahab yayi dogon magana yau kana yace"toh Allah ya bada sa'a amma Ni gaskiya Ina ga Zan wuce London daga Nan Zan wuce naija"? Gyada Kai Lahab yayi ya koma ya kwanta abinsa shi Kuma Ade ya sake cewa"Wai Lahab bazaka ci abincin bane"?Nan ma Bai basa amsa ba ya juya ya gyara kwanciyar sa........................ *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 08084453785 tare da shaidan biyan ki* Washe gari da safe Yan team in su Lahab sukayi bankwana dashi zasu dawo gida yayin da Ade ma yabi jirgin London ya rage saura shi kadai washe gari shima ya d'aga daga Egypt xuwa Libya,saukar sa kenan daga jirgi yaji wani irin duka da kirjinsa yayi haka kurum yaji wani irin kwanciyar hankali da natsuwa daya tako kasar,sunan sa da yaga an rubuta a jikin wani karamin board a hannun wani balarabe yasa shi d'aga hannu Yana nufar wajen mutumin da Sauri mutumin ya gyara tsayuwar sa Lahab na fitowa ya Kama bag na kayan sa sai sannu da zuwa yake Masa Suka fita daga cikin airport in,mota Mai zafin gaske baka ya budewa Lahab ya Shiga shima ya shiga Yaja motar Suka bar airport in. Babban gidane Mai shegen kyau Wanda Industry ta basa ya zauna a ciki har su kammala meeting Inda ya kawosa akwa kome na bukatar dan Adam a ciki ga masu aiki Kota Ina,Suna Isa wanka yayi Suka Soma jajjera Masa abinci kad'an yaci ya kwanta,sai Kuma ya zaro wayar sa number Abbu ya Kira Suka gaisa Yana tambayar sa ya kafar Addayiya don kwana biyu ance Masa batajin dadi ba kafarta na ciwo sannan ta kirata itama. washe gari da safe dayake meeting in Suna dashi ne karfe 10 na safe shiyasa bai tashi ba sai kusan 9 na safe wanka ya Shiga ya shirya cikin wani Arnen suit wando Baki sai rigan ciki fari kana ya daura baban rigan akai,ba karamin kyau yayi ba kannan nasa ya tajeshi sosai kana ya dau bakin glass ya kwaba a fuskar sa Sabon labcoat nasa ya d'auka ya rike a hannu kana ya bude kofa ya fito haraban gida da gudu drive yazo ya bude Masa mota shiga Lahab yayi da Bismillah gateman ga bude gate Suka bar gidan ,tafiya suke hankalin sa nakan wayar sa Yana dannawa Koh xai samu sukuni don kwata kwata yau ya rasa sukunin sa. Suna ssa industry sosai yake bin wajen da kallo bawai kallon kauyanci bane ah ah sai kallon naira tayi kuka daya Mata, labcoat in ya sanya kana ya gyara zaman glass nasa ya sauka a mota,yayi cikin meeting room in dake cikin wajen. Zazzaune suke akan kujerun a kalla pharmacy da Kuma pharmacology da likitoti akallah sun Kai ishirin Amma gashi goma da wani Abu yayi na safe an kasa Fara meeting in adalilin mutum daya dabai iso ba Wanda Lahab baisan Koh wanene ba guntun tsaki yaja don shi a duniya ya tsane African time bare har zaizo yana jiran mutum d'aya,mikewa yayi da niyar barin dakin hakuri manyan ma'aikatan suka Soma bashi akan yayi hakuri Wanda ake jiran ma ta karaso,ransa ne ya Kara baci Ashe ma macece ya tsaya Yana jira badon yanajin kunyar idon mutane ba yau Babu abinda zai sashi cigaba da Zama a wajen Nan,komawa yayi ya zauna yasha mur dashi. Turo glass na kofar akayi da Sauri gabaki d'aya jama'ar dakin suka juya Dan ganin Mai shigowa sabanin Lahab da kansa nakan wayarsa Yana dannawa Yi yayi Kamar baisan da halinta ta shigo ba,wow Masha Allah taku take daya bayan d'aya macece Mai cikar Kamala natsuwa da haiba ga wani irin kyau dake tattare da ita Mai sanyi da sanyaya zuciya farace Sol Kuma tass dogowa Mai jiki daidai fuskar ta d'auke da medicate glass, suit na Mata ta sanya ruwan toka wando da riga ta daura lab coat akan kayan ta farin hijab data sanya karami iya wuyanta Wanda Harya bata daman da gashin gaban koshinta kwantattu Suka dan leko,kafarta sanye da takalmi Mai tsini kujerar da aka tanadar dominta ta zauna ta Soma gaggaisawa da sauran jama'ar dakin,muryarta ta dan makale kad'an lokacin da idanunta sukaci Karo da Lahab Wanda ya sata kasa karasa gaisuwar data Mika Masa shikam kansa har lokacin na kasa Yana Jin duk abinda ke gudana amma bai dago ba. Jawabi aka Soma da tattaunawa kowa kokari yake ya zuba bajintar sa Kuma ya nuna kwarewarsa a harkar sanin magunguna,Deyana Abbas Ali shine sunan da Lahab yaji an ambata da sunan ta mikewa tayi a hankali ta Soma jawabi sai a lokacin ya d'ago ya kalleta had'a ido sukayi a tare dukansu suka kauda idanun su ana juna, meeting yayi zafi kowa mikewa yake Yana jawabin sa,har aka zo Kan Lahab. 1:20 cip aka tashi meeting in a hankali aka Soma fita one by one abinka da cikakkun Yan boko wa'inda suka San abinda Suke Babu wani hayaniya Koh ture ture Lahab da Deyana duk Basu mike ba sai da jama'an dakin Suka fifita saura bai wuce mutum biyar ba Suma Suka mike a tare kamar haden Baki,itace a gaba yana baya Suka Soma tafiya sosai ya zubawa jikinta Ido Yana kallon duk wani taku da take,yayinda ita Kuma kafafunta sai hardewa suke na rashin sabo. Suna fitowa haraban wajen yaga wasu manyan bodyguards a kallah sunyi goma manyan maza majiya karfi sai Mata guda biyu,d'ayar ta bude Mata mota zata shiga kenan ya ratsa tsakanin su, ba tare da yayi magana ba yasa hannu ya Kama nata hannu tare da juyar da ita da karfin sa"tamkar wasu mayunwatan zagi haka Suka yunkura Masa da Sauri ta d'aga musu hannu,Kuma sukabi umurnin nata Suka tsaya, kallon hannun nata tayi fari tass dashi ta Kara d'ago idanunta ta kalli fuskar sa"irin kallon Nan na tambayar dalili"?ganin baice Mata kome ba yasa ta fizge hannun ta ta juya ta Shiga motar aka ja Suka barsa a wajen a tsaye da Sauri yaji an dafasa,dagowa yayi ya kalli mutumin a kalla zasuyi sa'o'i Kuma ya shaidaishi Yana daya daga cikin likitotin da sukayi meeting yare"kaga bawan Allah kada ka wahalar da kanka aka baiwar Allah Nan ba irin naci daban nuna Mata ha amma Koh kallo ban isheta ba tsawon shekarun Nan Koh haduwa mukayi nunawa take bata taba kallo na ba alhalin Kuma a hospital d'aya muke aiki"kala Lahab baice Masa ba ya juya shima yabar wajen. Yana Isa gidan sa waya ya d'auka ya Kira Ade Ade na d'auka yace Masa"duk abinda kake ka bari pls kazo Libya Zan turo maka address na wajen da nake yanzun"keet ya kashe wayar ba tare daya jira abinda Aden zai fada ba"tsawon kwana uku Lahab na sintirin neman information akanta Amma ya kasa samun hakan Adewale yazo amma Lahab baice Masa kome ba, sosai yaji haushi sai masifa yake ma Lahab shidai Lahab baice kome ba sai visan sa daya dauka ya boye,yau tunda Suka tashi da safe ya shirya ya tafi meeting Inda za'a sake, yau sai xuba Ido yake ya ganta amma har aka tashi batazo ba. Jikinsa a sanyaye ya dawo gidan tura kofar falon yayi ya shiga Ade ne zaune da wani balarabe Suna hira,ganinsa da Bako yasa sa bude muryarsa yayi sallama amsa Masa sukayi dukansu kana ya karaso falon nufar bedroom yayi da Sauri balaraben ya mike Yana sake gaidashi dawowa Lahab yayi ya zauna akan kujeran wajen Nan balaraben ya gabatar da kansa amasayin sa na coach khamaludeen saboda kaunar da suke Masa shiyasa Suka had'a Wasa dan Allah Suna so ya hallarta wasan ya buga da yaran su in Basu takurasa ba zasuyi farin ciki inya amince,da fari yaso yaki zuwa Saida Adewale yasa Baki sosai yayita basa Baki akan Bai Kamata mutane su nuna Masa kauna sannan Yana banzarar dasu ba hakan yasa sa hakuri suka saka Rana da venue. Monday afternoon Lahab ne sanye cikin kayan ball farare tass har takalmin kafar nasa farine,sai Adewale dake rataye da sport bag na Lahab, shikam sanye yake da kananan Kaya,mota Suka shiga a tare driver yaja Suka bar gidan. **************** Stadium cike yake da larabawa especially yara matasa sun cikane makil har wajen Zama yama wasu kad'an,shigowar Lahab filin wasan wani irin ihu wajen ya d'auka ana Kiran sunan sa,karasowa yayi ciki gurin da aka tanadar na zaman Yan Wasa Zama yayi Nan Yan Wasn Suka ruga wajen sa wasu suna sanye da Jan jese wasu Kuma Kamar na jikin sa watoh fari kenan, Nan suka Masa caaa kowa nason su musaba'ha dashi hannu kawai yake Basu Suna musaba'ha. Wasa aka Fara cikin nishadi sosai su Lahab ke Shan yaran Wasa duk da yaran ma na bugawa iya kokarin su don sai su Lahab sunyi da gaske suke Shansu,an tashi Wasa su Lahab nada 3 goal yayin da yaran Suka tashi da 1 ihu wajen keyi da karfi ana Lahab Lahab Lahab da gudu wata balarabiyar yarinya sanye da jese sak na jikin Lahab sai dogon wandon roba pencil shima fari kanta dauke da hulan sanyi Babu Koh hijab a jikinta a kallah zata Kai shekara 13 don harta Soma Zama budurwa ga kirjinta cike da no-no tsallakowa tayi Kamar namiji ta hayo inda aka saka tsakanin Yan Wasa da Kuma yan kallon Wasa rugowa tayi da gudu duk kokarin tareta da ake kin tsayawa tayi ta nufi Lahab da gudu cikin larabci tana cewa akheeeeeeeeeee. Da Sauri security Suka kamota sai kokuwa take dasu su barta ta Isa wajen Lahab sai cewa take ita fan nasa ne,so take suyi photo dan dakatawa Lahab yayi Jin Amon muryarta daya cika wajen muryar so familiar to him waro Ido yayi lokacin da Suka had'a Ido da yarinyar,nuna wa security yayi da hannu su barta ta karaso,Aiko Suna saketa da karfin cin tuwo ta ruga ta nufi wajensa shidai tsayawa yayi kawai Yana ganin ikon Allah a casa'in, kafarta kawai yake kallo dake cikin boot tana zuwa har zata rungumesa sai Kuma ta saya cikin fara'a tace"Ni Ina daga daga cikin fans naka ne Koh da yaushe Ina kwallon wasan ka ba Wanda yake wuceni dan Allah muyi hoto,gyada Mata Kai yayi da Sauri tasa hannu zata dau wayarta a Aljuhunta sai Kuma ta zaro Ido ganin Babu waya,Fara dube dube tayi Wanda hakan yasa Lahab yafito Ade dake tsaye nesa dasu tashi Ade yayi ya shigo wajen dan tsayawa yayi Yana bin yarinyar da Ido sai Kuma ya waro Idon ya kalli Lahab. Zaiyi magana Lahab ya girgiza Masa kai hannu kawai yasa ya amshi bag NASA budewa yayi yadau wayarsa ya Mika Mata gashi toh ki dau hoton da wayata in yaso inkinga taki saiki tura ki bani tawa,da Sauri ta amshi wayar tsayawa tayi sai Kuma ya mikawa Ade tace"pls brother Amana hoto"amsar wayar Ade yayi Yana murmushi yayi musu kala biyu Suma Yan jarida sai daukar moments nasu suke,juyawa yarinyar tayi tabar filin,shikam Lahab na tsaye harta mule Masa. *************** lahab na Shiga motar sa Adewale ma ya shigo harsunyi nisa Lahab ya amshi wayar Ade ya Kira wayar sa Saida yayi five miss call kafun ta d'auka cikin ihu take magana Hello bamai wayar bane tace cikin larabci"Hassan Lahab ne nace kin koma gidane ya maida Mata maganar da turanci"da Sauri yaji tace ba ma fito a cikin stadium in ba"ok toh ga munan a waje kizo"sai Kuma ya yanke wayar kallon driver yayi yace ya koma baya"shidai Ade Bai Kara yunkurin magana ba. Aiko tun daga nesa Suka hangota tana dube dube,tsayawa motar tayi a gabanta Dan ja baya tayi sai Kuma ta matso kusa da motar ganin Lahab a ciki kawai ta bude motar ta Shiga shima Lahab baice kala ba yace direban yaja,tafiya suke yarinya Koh a jikinta wayar sa dake hannun ta take daddan nawa saiji tayi sunyi parking kallon Inda suken tayi sai Kuma ta waro Ido cikin zazzakar muryarta tace"ah Ina ne Nan Kuma Nan fa ba gidan mu bane big brother"?kala baice Mata ba ya bude motar ya fita shima Ade budewa yayi ya fita itama budewa tayi da gudu ta nufi gate na gidan da niyar barin gidan da gudu Kamar giftawar Ido Lahab ya damkota kamo hannun nata yayi duka biyu,ihu tasa tana cewa ya saketa itakam gida zata koma daman ummen ta bata San ta fita ba ya rufa Mata asiri ta had'asa da Allah koh sauraronta baiyi ba fiiiiiiiiiiii ya jata tare da bude kofar falon ya turata ciki fuska Babu walwala. Saura kad'an ta Fadi sai Kuma ta fashe da kuka ta zauna a kasa tana cewa"nifa fan's naka CE wallahi daman tunda Aunty Esha ta ganka a TV tace da gani Kai mugune Ashe shiyasa Al'ameen baya kaunar ka Kuma yace shi ba Fan's naka bane,baya sonka"shut up rufemin baki nonsense kawai"shine abinda Lahab yace Mata cikin tsawa Yana shigowa falon,Ade na bayan sa,kuka ta Kara fashewa dashi da karfi da Sauri Ade ya shigo falon Jin kalan kukan da take Kamar an yankata dagata yayi daga zaunen da take tana ihu duk ta cika gidan da kara...................... *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 08084453785 tare da shaidan biyan ki* Keee rufemin baki Koh yanzun na Saba Miki"? jiki na rawa ta rufe bakin Nata maida kofar falon yayi ya rufe da key kana ya matso kusa da su don har lokacin Ade na kusa da yarinyar fizge wayarsa yayi ya nufi daya daga cikin dakunan,mikewa Adewale yayi yabi Lahab cikin daki zaune ya samesa ya tallafe kansa"Lahab mekake ne haka"?uhmmm Adewale don Allah don annabi ka kalli shigen dake jikin yarinyar Nan ace yarinya tana by this age a barta babu suturan kirki haka mukayi da Labiba?don ita Bata sallah nace ta barmin yara haka kara zube ne"? Waro Ido Ade yayi cikin mamaki yace"Wai Lahab ban gane ba daman kasan yarinyar ne Koh me"?wani banzan kallo ya maka Masa cikin haushi yace"yanzun Kai fisabililahi saina fada maka Kai daga ganin yarinyar Nan baka ga alama ba"cikin danne dariyan sa Ade yace"alaman me ranka ya dade"?tsaki kawai Lahab yayi ya mike ya fita a dakin yana Jin zancen da Adewale ke Masa Akan ya Kamata a maidata gida Kar hankalin iyayen ta ya tashi,shi kuma Lahab ya Kulla Niya a ransa sai uwarta ta duri ruwa yau,yana fita tsawa ya daka Mata hade da karbo abinci ya Mika Mata yace taci ba musu ta karba ta Kama ci da mamaki yace yanzun ci take bataji tsoron cin abin hannu mutane Koh Kuma damuwa na rashi komawa gida ba?abin haushi amsar da ta basa shine ai kwara ta mutu a koshe data mutu tana Jin yunwa. Fita yayi Bai Jima ba ya dawo da Kaya dogon rigane na Arab gown sai hijab ya Bata yace ta canja na Jinkin taje tayi sallan mangariba, masallaci yaje ya dawo yace ta tashi tayi sallah a idon sa ya gani,tana kunkuni ta tashi sosai ya yaba da ibadar nata ajeta yayi ya zauna shima Yana cin abinci Yana Mata tambayoyi ta fannin addinin koma sosai yaga alamu yarinyar ta samu koyarwar addini,sunan ta ya tambaye ta Wai sunan ta "Meera Hassan Lahab Amma Sunana na gaskiya nazeefa Kuma in gaya maka saban sonka da nake har cewa ake Wai Muna Kama shiyasa nakewa yaran ajin mu karya nace Kai yayana ne"gyada Kai yayi yace meyasa bakice musu Ni Abien ki bane"? Wani kallo ta Masa sai Kuma ta rufe fuska tana dariya hararanta yayi ba Wasa yace toh dariyan me kike Kuma ke kin sannni kuma"ah ah kawai dai dariya nake Taya zance wa kawaye na Kai abie nane D'an wannan dakai"ai gwara uncle Usman shidai Zan iya cewa babana"murmushi Ade daya karaso wajen yayi ya zauna kana ya jefo Mata tambaya"toh ke Ina baban ki tunda wannan abie ya Miki kadan"uhmmm babana dai Bayanan Koh rasuwa yayi Koh guduwa yayi Ni ban sani ba ummi batason mu Mata tambaya a kansa kullum ai tace Mana wata Rana zaizo Kuma haryau baizo ba"Aiko Kisha kuruminki yazo Kam"waro Ido tayi da kyau tacewa brother ka sanshi ne"? Gyada Mata Kai yayi Nan fa tadi ya barke a tsakanin su shidai Lahab nasa Ido har kusan 11 na dare kafun Suka kwanta amma Lahab ya kasa bacci bini-bini saiya mike ya fita a dakinsa yaje ya leka yaga Koh tayi bacci gabaki d'aya gani yake Kamar inya kwanta zai farka yaga mafarki yake Koh ya tashi yaga ta gudu. Washe gari da safe suna karyawa yarinya gabaki d'aya ta sake jikinta dasu Babu wani tsoro Koh kewan gida abin Yama Lahab ciwo gani yake kamar Nnenna bata Basu tarbiyar daya dace ba,mace ace tabar gidan su tun jiya amma Bata damu ba,Suna kammala karyawa Lahab ya tasata agaba Suka nufo gidan su Meera harda Adewale,tunda Suka nufo unguwan suke jinjina kudin da mamallakan gidajen kedashi wani hamshakin gida Suka nufa Wanda Meera ta nuna musu a matsayin gidan su gidane Mai kyaun gaskiya,horn Suka danna wani security yazo ya leka ganin Meera yasa shi saurin bude gate in Suka kusa Kai ciki. Akallah gidane da za'a Kira unguwa guda Mai girman gaske dauke da part part masu zafi Kuma iri daya a kalla security dake kewaye da gidan sunfi hamsim ga police da Suka gani a gidan sai jama'ar dake tsattsaye Suna magana da police in sun Kai su Sha biyar gabaki dayan su Suka juyo Suna fuskan tan motar su Lahab bude motar Meera tayi da gudu tana Kiran ummi ta nufi wajen jama'ar,matar da Lahab ya gani a wajen meeting ita yaga ta Mike cikin tashin hankali fuska a kumbure alamun kuka Tasha bana Wasa ba ta nufi yarinyar da Sauri,yarinyar na Isa ta rungume ta fizgo yarinyar tayi ta wanketa da Mari Mai zafi ba Wasa a fuskar ta tana cewa zata kasheta ne tasan halinda ta sata a ciki yanzun inta Bata me zata cewa mahaifin.................makalewa sauran maganan yayi ganin Lahab da Ade da Suka sauko a motar. Gabaki d'aya mutane tsakiyar gidan da mamaki suke kallon Lahab,maza samarin kam tuni Suka matso kusa Suna basa hannu, sake fuskar sa yayi ya duka har kasa yana gaida mutanen dake wajen,sai Kuma sukace ya shigo falo sai ayi magana a ciki,binsu yayi Suka shiga ciki zazzaune suke akan kujera Lahab Kam Yana zaune a kasa sai Deyana data shigo hannun ta damke cikin na Meera tazo zata giftasu kwala Mata Kira Jaddu(kakan Nnenna ta wajen uba) yayi yana cewa Ina zata tazo ta zauna maganar daya shafeta ne suje Ina bayin Allah Nan Suka same ta"girgiza Kai kawai tayi tabar wajen. Shigowa wani kyakkyawan balarabe yayi fari tas dashi sak Deyana(Abbas Ali)Zama yayi Lahab ya Kara gaidashi da murmushi ya amsa kana yace Hassan Koh"ba mamaki Lahab ya amsa don yasan yanayin aikin sa shiyasa mutane ke yawan sanin sa"Masha Allah yace kana ya nuna Lahab wa Yan falon a hankali yace"wannann shine mahaifin Abulkhari da Meera"da Al'ajabi jama'ar falon Suka Soma mamaki Suna cewa daman dan wasan kwallon nageria da suke gani a TV kullum shine mahaifin su Abulkhari Ashe ba abanza Meera keson sa ba,sun Kuma nemi dalilin kin fada musu da ba'a Yi ba sai yanzun Suka sani, Kuma sunsha mamakin ganin dan 31 dauke da yara Yan 13 year's,ana tsaka da maida magana saiga wani babban mutum a kalla zaikai 40 hannun sa rike dana wani yaro fari kyakkyawa Kamar dai Meera sun shigo daga ganin su hankalin su ba'a kwance yake ba dukan su biyu. Yauwa Usman kaga Meera Kam an ganta Allah ya had'ata da mahaifin ta,dam dam haka Usman yaji zancen Nan,shikam Abulkhari da Sauri ya matso kusa da tsohon Yana tambayar sa Ina mahaifin nasu,nuna Masa Lahab dake sunkuye yayi Baiyi wata wata ba yazo ya rungume sa Yana cewa laii Abien mu Ashe ba tshoho bane . Bayan an natsu Adewale ya maida musu yanda akai suka hadu,anan dai Jaddu yace su Lahab suyi hakuri gaskiya zancen auren sa da Deyana bamai daurewa bane don yanzun Yana bukatar jikansa a kusa dashi bazai iya barinta daga Nan har nageria ba tun tana yarinya batasan menene dadin iyaye ba bazai iya saketa sakaka ba, mahaifan Deyana(Nnenna)Basu so haka ba don su harga Allah Sunsan yarsu nason mijinta amma ka'ida ne a danginsu sai abinda babba ya yanke, kasa hakuri mamar Nnenna taso ta nausar da jaddu amman yace a Kira ita Deyana da kanta, shigowa falon tayi kanta a kasa ta zauna tambayar ta akai Nan tace itakam duk abinda suka yanke shi takeso daman kin raba auren da tayi Ada tayine don ta cika Masa ALKAWARIN data d'auka don haka duk abinda ya yanke yanzun daidai ne. Adewale yasha mamakin chanjawar Nnenna zuwa Deyana duk da abubuwa da dama sun chanja shekaru sunja amma dai yayi mamakin Ina ta samu sabbin iyaye har Suna ikirarin diyarsu bazata koma naija ba sun manta irin wahalar da Lahab yasha da ita,Koh sun manta Nnenna Yar nageria ce kasa hakuri yayi ya tambaye su ta Ina Nnenna ta Zama diyar su"?nan jaddu ya Soma basa labari cewa shekaru 30 da wani Abu daya wuce sun kasance Suna da arziki sai dai rikicin akida sun musu katuntun sun hanasu sakar wata Rana kawai aka tashi da rikicin akida a Libya fada ya barke bana Wasa ba sun matukar tsorata,Daman a lokacin bakaken fata na shigowa wajen su Neman aiki na aikatau,cikin masu aikin gidan sune da mijinta ta damkawa Deyana tun tana jinjira ta Kuma Basu kudi tace su bar kasar da yarinyar ta don ita a lokacin ta zaci zata mutu ne kasancewar tunda aka Soma rikicin Koh asibiti ba'a budewa akallah an kashe family su kusan mutum ishirin, gashi tafara ciwo Wanda gabaki dayan mu Muka tsorata da ciwon nata tamkar bazata tashi ba Saida ta bada yarinyar kafun daga baya Muka sani na shiga tashin hankali bana Wasa ba na Kuma Yi takaicin daga karshe na fawwalawa Allah kome. Kutsam Allah ya bayyana mana ita a London bayan ta hadu da Najib(Wanda Suka hadu lokacin Yan fashi Suka taresu a gombe har ta dau jaririn sa Yan uwansa na gombe suka Bata 500k)Ashe Dan uwan tane Kuma cikin yardan ubangiji yazo ganin gida Muka hadu da ita Allah ma yasomu Wai ashe da Bata sallah Saida ta zauna dasu ta fara"jinjina lamarin Allah Adewale yayi sai Kuma ya Soma zancen rashin dacewan raba auren amma Suka kekace babu Inda zata koma kawai in zai dawo ya zauna a Libya Bismillah in Kuma ba haka ba Saida ya sallame ta ita shi Kuma Lahab yace bazai bar kasansu saboda mace ba,harga Allah mahaifiyar Nnenna bataso hakan ba Amma batace kome ba,mikewa Lahab yayi a hankali ya musu sallama tare da juyawa zai bar falon a hankali Nazeefi(abulkhari)yace"Dady Zan bika"wani irin shaukine ya cika Lahab a karon farko yaji wani irin shauki da iyaye keji in aka kirasu da suna iyaye. Da Sauri ya yafito yaron Aiko da saurin sa ya mike ya Kama hannun uban nasa,da mamaki nazeefa(Meera)tace Abul tafiya zakayi ka barni ne? Ai kema jiya tafiyar kikayi Kika barni "ai da Sauri itama tace nima Zan Bika dady gabaki d'aya yaran Suka Kama hannun uban nasu,kuka Deyana(Nnenna) ta sake don a zatonsa tafiya nageria zaiyi dasu,ganin haka Yasa jaddu(kakanta)tambayar Lahab shin Ina zashi da yaran Lahab yaso ya juya yace Masa ai yayan sane Koh bangon duniya zashi dasu Babu Mai bashi permission,Amma darajan tsohon yasa sa kasa magana sai Ade ne yace masa aiki sukazo insha Allah kafun su koma zai dawo dasu zancen makarantan su Kuma karsu damu zai iya kaisu daga nan,. ********************** Suna komawa gida ba karamin masifa Lahab ya sake ba Yana cewa wallahi in Nnenna ta manta waye Lahab sai ya tuna Mana zai Mata bakin aiki harshi za'a nuna wa iko zasuga iko don wallahi daukar yaran sa yayi,washe gari yakaisu aka musu visa makarantan ma basa zuwa haka zai wuni dasu Suna Hira suna basa labari anan dai yaji labarin Yan gidan su Labiba Wai Usman cousin nata ne kuma son ummin su yake amma ummi Bata sonsa yasha zuga jaddu akan a raba auren a kotu kawai ta daina Zama ita ba aurareyya ba ita ba sakakiya ba karshe Saida ya gwabe Meera kafun ta dakata da labaran ta,yace baison gulma maganar ta Isa don kwata kwata nazeefi ya fita natsuwa. ran sa ya Kara baci hakan yasa sa kuduri aniyar barin kasar da yaran wallahi sai dai ita ta nemosa,haka Koh akayi ya kammala kome nashi Kuma washe gari da safe zasu bar Libya,da misalin karfe uku na yamma kwance suke a falo Suna Hira Ade ke Basu labarin abotar su da Lahab tun yaranta hotonan su dake cikin system in Lahab ya d'auko Yana ta nuna musu, yaran sosai suke Jin dadi da marmarin zuwa NAGERIA don ya sanar dasu gobe insha Allah zasu tashi. Knocking na door in akayi,bada izinin shiga Ade yayi Mai gadi ne yace wata ce tazo tace a Mata sallama da Lahab, balance Lahab yayi don haka kawai jikinsa ya basa itane kallon sa Ade yayi ganin baida niyar magana gamai gadi a tsaye yasa sa cewa a ce Mata ta shigo,da sallama ta bude kofar mikewa yaran sukayi suna Mata oyoyo bude hannayen ta tayi ta rungume su da karfi sannan Suka Karasa ta zaune akan kujera a hankali ta ce"Ina wuni Adewale"?dariya ya sake kana yace"nifa yanzun Sunana Nabeel kawai mijinki ke kirana da Adewale Dan Allah kekam ki Bari da Nabeel Kinga yaran Nan na samu Suna kirana uncle Nabeel karkusa su koma cemin uncle Ade Mana"kai Ade Naga dai sunan Kane bana wani ba don haka nikam dashi Zan kiraka"Kuma ai bakai bane Nabeel Ina Nabeel inne"? ganin Ade Bai Bata amsa ba,Mikewa Lahab yayi yabar falon dakin sa ya shiga ya kwanta Bai fi 20 minutes ba yaji an turo kofar daga Ido yayi ya kalleta sai Kuma ya maida idon ya rufe Yana girgiza kafarsa,karasowa tayi a hankali ta nemi bakin gadon ta zauna"Ina wuni"?kin amsawa yayi batayi fushi ba ta sake cewa"daman nazone na dau yaran mu koma gida Naga yau kusan 1 week basa zuwa makaranta malaman su na complain zasu Fara jarabawa"Nan ma Bai Bata amsa ba haurawa tayi Kan gadon a hankali tasa hannu ta taba kafarsa"maganafa nake maka' wani irin mikewa yayi da karfi ya fizgota da iya karfinsa ya makata akan gadon kana yayi gaggawa hayewa kanta zaro Ido tayi tana kallon sa sai Kuma ta kalli kofa da Sauri bai koyi gizauba illah fuskar ta dayake bi da kallo kawai cikin Al'ajabi tace"in yaran Nan Suka Shigo fa"? Sai suga abinda uwarsu da ubansu suke"shine abinda yace mata Yana sauke numfashi cikin haushi"harni Zaki nuna wa iyaka ta watoh kinyi kudi kinyi ilimi har kina da bakin da Zaki ce in sake ki Koh?gaji Mai dangi"watoh Ada saboda rashin kowa yasa kike biyayyar Dole badon kina sona ba Koh?toh wallahi zanyi maganin ki in an hanani ke ai baza'a hanani yarana ba"?hawaye ne ya taru a idanunta kana tasa hannu a hankali ta shafa fuskar sa cikin sanyi Hali tace"ka Kara girma sosai dear"? Make hannun nata yayi sannan a hankali ya kwantar da kansa a wuyan ta wani irin unexpected kiss ya sake Mata Wanda ya sata mikewa da Sauri shima ya maidata kwancen yayi ya danne,Yana cewa wallahi bakin ce na sakeki ba watoh ke aure Usman Koh"? da Sauri ta girgiza kanta tana maida numfashi a hankali saboda yanayin kwanciyar nasu ba karamin cinnata yake ba"kawai dai Ni yanzun kaga a NAGERIA Ni Mai laifi ce duk da a yanzun Ina da karfin gwuwar tinkarar shariya,Kuma dangin ka basa kauna ta tunda har mahaifiyar ka tayi ikirarin kasheni ai babu wani zancen cigaba da zaman aure da Zan sake a kasarku,tunda Alhamdulilah yanzun na samo asalina". Duk wannan maganar meya hadashi da auren mu wannan alakar dake tsakanina dake Zaki tsaya akai bawai akan zancen dangina da kasata ba in Kuma akace duka sun chanja ra'ayi a kanki fa"gaskiya Ni yanzun na maka girma Kuma ma Taya Zan iya cewa Wai Kaine mijina wa mutane gaskiya da kunya wallah.........a hankali ya danna bakinsa a nata a hankali ya Soma kissing nata irin kiss Nan ne da ake cewa ci da zuciya watoh cikin zafin Rai da haushi zame bakinsa yayi a nata kana ya tashi akan nata,ganin haka da Kuma yanayin sa yasata rarrafawa da Sauri zata d'auka akan gadon kafafunta farere tass ya Kama tun daga bakin gado ya jata fiiiiiiiii har tsakar gadon jikinsa na rawa ransa sosai ya baci ya Soma magana yana cewa"ki kace kin fi karfin zaman aure Dani koh.......................... *Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 08084453785 tare da shaidan biyan ki* dan Allah kayi hakuri karka min haka"tace cikin tashin hankali ganin ya danne kafafunta da nasa kafafun ya Soma Kwabe riga"kaga dan Allah ka maida riganta karfa ka manya yaran mu na falo"zare wandon jikinsa yayi Kara tayi a hanakli ta fizgo jikinta a nasa tana kokarin sauka akan gadon kamota yayi da karfi Yana cire Mata kayan jikinta had'asa ta somayi da Allah amma Saida ya zare dogon rigan jikinta a hankali"yana bin hips nata da kallo ganin yanda kwata kwata yanzun ta sauya Kamar ba Nnenna ba ta Kara cika ta Zama babban mace" "dan Allah ka bari wallahi ban shirya d'aukan ciki a gidan mu ba dan Allah dai"?au aikin fi karfina ne yanzun Koh kikace"ah ah dan Allah kayi hakuri ka bari banaso dan Allah dai kokawa Suka Fara a hankali ta koma ta kwanta tana hawaye ganin da gaske yake son kasancewa da ita,yayin da ita Kuma bata shirya karbar sa a wannan lokacin ba,sallama da ake kwad'awa a bakin kofar shiya dakatar da Lahab daga abinda yake,a hanakli ya mike zaune gabaki d'aya jikinsa Babu kuzari mirginawa yayi ya kwanta agefen ta. Itakam murna fal cikinta mikewa tayi kayanta ta sanya da Sauri ta bude kofar dakin,nazeefa ce Wai Uncle Nabeel(Ade) yace Lahab yazo su tafi masallaci ana Kiran mangari ba"nufar hanya tayi tare da cewa su mike suzo su tafi kin binta sukayi kai da fata,karshe dai haka ta tafi Babu Shirin don Bata son Lahab ya fito ya sameta mikewa Ade yayi ganin ana kokarin tada sallah Lahab bai fitoh ba har lokacin gashi nazeefi yayi Alwala shi kawai suke jira dakin ya shiga anan ya gansa kwance har lokacin bai mike ba girgiza Kai kawai Ade yayi tun lokacin da yaga kwayar idanun sa sunyi mugun rinewa gashi gadon kaca-kaca shiyasa shi juyawa kawai yabar dakin. Washe gari Lahab Suka nufi NAGERIA Koh sanar dasu Abbu basuyi Suna zuwa ba Rabon Lahab da NAGERIA an Jima sai yau lokacin da suka iso ba karamin mamaki familyn Lahab Suka Sha ba gashi gidan ya Zama daga Abbu sai Addayiya data tsofa sosai sai Mamu don ummu tana fita a gidan yari Abbu ya sallame ta, yara kuma kaf nasu sunyi aure hatta zulai auta itama ta Jima da auren ta. dangin Lahab sunyi matukar farin ciki na ganin walwalan Lahab ta dawo kowa na dangin su Saida Suka zo kallon yaran Nan kowa yazo, saiya Yaba da tarbiyar yaran ga saurin Shiga Rai,Mami lokacin da tazo kuka ta sake don yaran sun tuno Mata da d'anta Rahab Allah sarki da shima yanzun yayi aure kila. Lahab ya mayar musu da yanda akai harma dakin auren su da dangin Nnenna basayi Kuma suka nuna akan bazata dawo dakin taba,Abbu da kansa shida Mami sukaje har Libya amma jaddu yace Ina zance dai d'aya ne Nnenna bazata dawo nageria ba an buga an buga Abu yaki haka Suka hakura Suka dawo,shikam Lahab makaranta yasa y'ay'an sa suka cigaba da karatun su shima ya zauna a kasarsa abinsa Yana kula da yaran sa Babu abinda Suka nema Suka rasa. Esha(cousin na Nnenna) Adewale ya Fara soyayya da ita yarinyar bazata wuce 17 ba ba karamin mamaki Lahab yasha ba ganin tsawon shekarun Nan Adewale baya zance wata mace Saida ya hadu da eshat Ashe shikam tuni sun Soma tsula soyayyar su lokacin daya tare sa da zancen mubeena budar bakin Ade yace yanzun mubeena tafi karfin sa rai bace Lahab yake cewa shida yake da Mata age mate nasa meya samesa, Kuma a haka Yana son suci gaba da rayuwa tare Bai taba Jin sha'awar wata ba. Amsar da Ade ya bashi shine aisu sunci kurucciyar su shifa? Kuma da ace shima mubeena ta nuna Masa so da har gobe bazai kalli wata ba Ada yayi hakuri Amma Banda yanzun Kam, murmushin takaici kawai Lahab yayi don yasan har gobe mubeena na zuciyar abokin nasu don yayi bincike sosai ya gano Adewale yaci gaba da biya Mata makaranta harta kammala karatun ta har matakin digree aikin da take ma shiya nema Mata kuma duk wata sai ya tura Mata da sakon Kaya Koh wani Abu,amma da sunan Lahab yake amfani Wai Lahab ke Mata sako, don tuni ya gane Wanda mubeena keso shiyasa shima ya sanyayawa zuciyar sa hakuri ya Zama Yana kyautata Matane saboda Allah da Kuma abotar su. Lahab yadau yaransa har wajen mubeena ya kaisu Allah sarki so ranan sosai tayi Kuka bama kamar daya ce Mata zai aureta don ta matukar basa tausayi gabaki d'aya unguwan su Babu macen data kaita girma a budurwan sai ita kadai,gaskiya so bala'i ne wani lokacin. Auren Adewale da eshan ya tashi wannan Karo jaddu yace bazai bada eshan ga tubabbe ba Amma eshan tayi fito na fito da jaddu iyayen ta Kuma suka Goya Mata baya don jaddu kakan tane ta wajen uwa Nnenna Kuma ta wajen ubane,Yan uwan Ade Cristian ne shiyasa su Abbu suka tsaya Masa a zancen auren nasa sai dai duk abinda ake anayi ne da izinin iyayen sa papa girma yazo Kuma Ade ba karamin kudi yake dashi ba don yanzun gidan su ma abin kallo ne ga kauyen su daya koma yana d'aukan yara Yana zuwa Yana sasu a makaranta wasu boarding Koh day Suna karatu sosai,wa'inda suka kammala karatu ba aiki duk Yana nema musu aikin yi hakan yasa kiyayyar da suke Masa a dalilin musuluntar sa tuni ya washe a idanun su daman akace kyautatawa tana rage kiyayya. Zacen auren Ade daya tashi Saida mubeena ta kwanta ciwo sosai ta gane kuranta a rayuwar tayi kuka tayi kuka daga karshe tafawwalawa Allah kome Kamar yanda ta Saba,don zaman gidan bappa Ado ba dadi ne dashi ba sai d'an Karen bakin ciki, yanzun Addu'a take Allah ya Bata Miji komai ruwane(garuwa) tayi aure ta huta itama ta samu zuriyar da zasu debe Mata kewa,Allah sarki mazan jiya su Nabeel(real)an Zama tarihi da farida rayuwa kenan duk abinda ka shuka shi zaka girbe Inka biyewa zuciya zata kaika ta baroka kayi Wasa da Daman ka na rayuwa. *************************** An daura auren eshan da Ade Ade sai rawan Kai yake an aure balarabiya lokacin da akazo za'a d'auki auren eshan mutanen NAGERIA guda bakwai ne Suka je maza uku sai Mata biyu d'aya goggon sa dayar kuma goggon su Lahab sai ango da abokan sa uku cikin su harda Lahab sai su Abbu da Suka karbi auren,a lokacin jaddu yace Deyana ta tashi tabi mijinta Allah ya Basu zaman lafiya Kuma yaji dadin biyayya data masa ubangiji ya Basu zaman lafiya Kai ranan nan Deyana tayi kuka Kam bana Wasa ba kafun Suka rabu da iyayen ta daman yaranta tuni suna nageria Lahab baki har kunne aka karkato naija. Hadadden dinner aka had'a a washe garin ranan da Suka dawo da daddare Ade yaso Lahab ya shiga cikin dinner ayi dasu amma Lahab yace dashi da matar sa sun girma, Addayiya ma daker tabar Nnenna (Deyana) taje dinner don tace baza'a tare ba sai Lahab yamata Sabon gida gidajen sa na naija sun tsufa Nnenna tafi karfin su Kuma ya Mata lefe. Zazzaune ake akan kujerun ga jama'a Kamar me an cika Hall in dam Adewale ne Akan floor da Amaryar sa Esha kyakkayawar yarinya ajin farko, saidai fa Bata Kai Deyanan muba,Lahab na zaune a Inda aka tanadar wa Baki shida matar sa sai yayan su dake zaune kusa dashi daman table ne Mai daukar mutane hudu abokan su tunna secondary school duk sun hallara harda na London duka,hall innen yayi shuru sakamakon sanarwa da MC (Dj) yayi ayi shuru akwai wani abin mamaki da za'a nuna musu,yaye labulen dake jikin gidan hall in akayi. Farin kyelle ne ya bayyana sai Kuma abinda mutane bazasu zata ba hoton Lahab ne tsaye da Rahab sunyi ne a cikin gida su a wancan shekarun,Nan wa'inda Basu San Lahab tagwaye bane suka Soma tambaye wannan Kam shine dan uwan sa kenan,hoton ne ya bace aka nunu na Lahab sanye da uniform sai Nnenna da itama tana sanye da uniform a jikinta tsaye suke a unguwan su Basu ma San anyi hoton ba,sai Kuma hoton Lahab da Adewale da Nabeel na ainahi,sai Kuma hoto na gaba shine Randa Suka kammala secondary school sukayi hotuna dukan su da mate nasu harma da coper dasu Lahab Suka duka. Abin Al'ajabi sai ganin vedio dauren auren Lahab akayi sai Kuma aka Kara nuna hoton Nnenna da Lahab again lokacin da take da ciki,kana aka sake Nuno hoton su dayaransu harda Ade a cikin hoton,sosai mutane ke jinjina soyayyar dake tsakanin su, Ada sai gulmar su ake tunda Suka zauna Amma tunda aka ga hoton sai jikin mutane yayi sanyi hotona sosai aka yita nuna wa, mubeena da tayi karfin Hali tare da ma kanta ALKAWARIN insha Allah zata zo bikin Ade Koh don d'awainiya da yayi da ita a boye don taje ta samu Mai kawo Mata kudi da sauran abubuwa tsawon shekarun nan tace ya fad'a Mata tsakani da Allah wake d'awainiya da itan Nan yace Mata Adewale ne. Hawaye ne ya cika idanunta a hankali ta Mike tana kuka ta fita a Hall in Babu Wanda ya hankalta da fitar ta sai Lahab shima baisan tana hall in ba Saida tazo fita ya ganta,a hankali ya mike tsaye tare da cewa Nnenna Yana zuwa fita yayi a hall in Yana bin bayanta ganinta yayi zaune ta kifa kanta tana kuka,sosai jikin sa yayi sanyi gabaki d'aya ya rasa meyasa yanzun ya damu da lamarin mubeena sosai ya damu akan lamarinta ace mace har 33 Babu aure gaskiya abin a tausaya Mata ne,tsaye yake akanta yafi minti goma amma mubeena bata sani ba a hankali yasa hannu yad'au purse nata data Yar a kasa daga Ido tayi Suka had'a Ido murmushi yayi kana yace inkin gama kukan ki goge hawayen naki ya Isa haka mubeena kiyi hakuri da rayuwa aduk yanda tazo Miki nasan tabbas kina Jin ciwo a ranki amma hakuri ake kome zai wuce. Dole nayi kuka Lahab Dole ne rayuwar da nake ciki a yanzun ban taba tsammanin Koh hasashen Zan taba shige ta ba,Babu duka Babu zagi sanan Ina da albashina Mai tsoka sai dai rashin aure yamin cikas ka duba fa ka gani Ranan kawai Na fito gida saiga Yar Ahmad (14year's)Wai hartana nuna Ni Wai ga budurwar baban ta har yanzun batayi aure ba sai Kuma ta sake kuka da karfi don harga Allah yanzun so take tayi aure Amma tunda aka ganoo abinda Nabeel ya aikata ta nemi manema ta rasa. tashi muje na kaiki gida"girgiza kanta tayi a hankali tana cewa"no basai ka kaini ba nida kaina Zan koma ka koma wajen iyalinka"girgiza Mata Kai yayi a hankali yasa hannu ya rike nata ya Soma magana"mubeena ki manta da kome daya wuce a baya mu fuskance gaba Koh da Inna Koh Babu Inna mun riga mun Zama Yan uwa pls feel free with me kinji big Aunty"? A hankali ta gyada Kai tana share hawayen idanunta sake Mata hannu yayi kana yace suje ya maidata 9:00 na dare yayi tuntuni, tafiya suke Lahab Kamar ance ya d'aga Ido kawai ya had'a Ido da Nnenna dake tsaye a bakin hall in tana Masa wani irin kallo da Bai taba ganin ta dashi ba haka kawai yaji mugun shakkanta ya shigesa,amma ya basar bude motar sa yayi mubeena ta shiga kana shima ya Shiga yaja Suka bar wajen,har unguwan su ya kaita lokacin da zasu rabu kudi kusan 100k ya Bata Amma mubeena taki karba yayi yayi taki. Lahab na dawowa yaga wani kallon harara da Ade ke aika Masa,kallon yaran nasa yayi yace su taso su tafi Nnenna kin tashi tayi har Saida nazeefi ya Kara Mata magana kafun ta tashi Albarkacin yaron nasu kada ya fiskanci akwai wani abu,shikad'an sa yake Hira da y'ay'an sa itakam bakinta kus Kama wata hanyar taga yayi hakan yasa ta kalle sa Amma batayi magana ba,gidane Mai kyau Kuma kerarre bude kofar sukayi dukan su Suka shiga haurawa upstairs yayi da yaran Koh wannen su ya nuna Masa dakin kwanan sa Babu abinda Babu a dakin nasu Kama daga man shafawa zuwa sutura duk ya tanadar musu. A ranan bacci ma Lahab basuyi tare da Nnenna ba saboda masifar data yitayi Masa akan mubeena harda cewa in son mubeena yake bazai burgeta ba sai taga ya aureta abu dai baiyi dadi ba ranan. *************** Washe gari da safe Addayiya ta turo ma yaran kayayyakin su don ta fahimci Lahab Kam ya Kai matar sa dakin tane sun koma gidan su,Yan uwan Nnenna da suka zo aure dukan su sunzo sunga gidan ta Kuma gaskiya sun yaba wa Lahab,Mami tazo tayi ta Neman gafarar Nnenna amma Nnenna tace Mata Babu kome yanzun kome ya wuce ai Suma da laifin su a wancan lokacin,vedion auren Ade da aka had'a dana Lahab Sosai mutane suka ringa tofa Albarkacin bakin su. Bayan aure bai Jima ba saiga Usman (cousin in Deyana)daga kasar su ya taso har NAGERIA gidan su Lahab yazo da hoton mubeena Wanda a cikin hotonan biki aka d'auka Bata ma sani ba tana zaune akan kujera ga hawaye cike a idanunta,yace fa shi duk duniya yaga matar aure ta tafi dashi,ai ba karamin dadi Deyana(Nnenna) taji ba Koh hankali ta zai kwanta saboda yanda Lahab ke shiga harkan mubeena abin na jaza musu rikici akanta. Anyi bikin mubeena bukin da d'angi da jama'ar gari basu taba tsammani ba tabbas sunga ikon Allah daman akace Mai hakuri na tare da riba Allah ya kawo wa mubeena Miki balarabe Kuma saurayi ba magidanci ba,bugu da Kari Yana tsananin sonta da kaunar ta a bikin su ba karamin bajinta Lahab yayi ba duk da su basa kayan aure Koh gara Amma bikin yayi armashi kudi yayi kuka kome daya shafe mubeena Lahab ne yadau nauyin sa har aka kammala biki lafiya aka dagata daga naija zuwa Libya. Iyayen Deyana sunzo bikin don haka Basu koma ba Suka nemi dady(baban Abraham) Wanda kunya ya hanashi Koh zuwa Inda Deyana(Nnenna)take,haka zalika momy itama tayi dana sani sosai,dady shiya dau iyayen Nnenna ya kaisu har Enugu daga nan Ya wuce dasu Edo state duk da dangin papa(marikin Nnenna daya rasu )Basu rike Nnenna ba amma iyayen ta sun musu goma na arziki wa'inda Nnenna ta sani da wa'inda Bata sani ba duk an musu abin Alkhari anan Nnenna take Jin labarin matar papa data rasu Ashe tunda ta dawo Libya da yarinyar(Nnenna)Kuma tace yarta ce ta Fara kudi Kamar na hauka yaranta data tafi Libya ta barsu su uku kaf Suka mutu saura Nnenna kawai Kamar tsafi saiga arzikin matar papa ya Soma karewa wata Rana kawai aka waye gari gidanta da ita ya Kama da wuta ta mutu murus Amma Nnenna Babu abinda ya sameta duk da kuwa tana cikin gidan wannan ne musabbabin rikon Nnenna ya dawo hannun papa,Kuma da iya gaskiya suka rike Nnenna Babu Wanda ya taba tsammanin ba yarsu bane. Papa yasha tsangoma da tsana akan Nnenna saboda lakaba Mata maita da ake Amma Bai hanasa cigaba da rikon taba. Bayan tafiyar iyayen Deyana Lahab yaje London ya tattaro duk wani Abu nasa dake can Mai amfani ya dawo nageria ball ma yace yanzun yayi girmeta bazai cigaba da bugawa ba ya barwa yara shi yanzun uban matasa ne, hospital babba ya budewa Deyana tana aiki ga yaran sa na zuwa makaranta duk karshen hutu zasu koma wajen Mami su Mata kwana biyu Su karasa sauran kwanakin a wajen Addayiya. Labarin Alhaji sulaiman kutsam aka samu wata Rana,sakamakon wani tsoho daya kawowa Yan Sanda rahoto Kuma ya musu jagora,lokacin da aka shiga gidan dake dukar daji sulaiman aka samu rashe rashe dashi da Yan kungiyar su Suna Shan jinin jariri ga gawar yaron a kwance akan table nasu dukan su sanye da jajayen Kaya abin d'aga hankali Amma su Bako Imani, kamosu Yan Sandan sukayi a haka aka fito dasu cikin gari a kallah sun Kai su 10 Kuma dukan su Babu karamin mutan a cikin su, masu kudine sosai d'aga mazan har matan. Makasu akayi a kotu a ranan dubun al'umma Suka shaida fuskokin mugaye da siffan mutanen kirki Mami tayi kuka bana Wasa ba lokacin da sulaiman ya Fadi dalilin sa na tsanar su Lahab Ashe tun lokacin da Al'hassan ya aure Mami yayi Alkawarin ganin bayan sa da duk abinda Mami zata Haifa Kuma saita Zama mallakin sa,amfani kawai yayi da kiyayyar su Lahab a zuciyar farida da Nabeel yasasu wannan aiki Wanda haka ya bayyana cewa Mami tafison y'ay'an Al'hassan akan nasa y'ay'an shiyasa yayi niyar kashesu yaga Koh in Babu su zata fi son y'ay'an sa sama da kome Daman tuntuni yayi niyar kashesun. Zancen Nnenna Kuma Ashe kungiyar sune,asalin matar papa tana da mukami Mai tsoka a kungiyar don ta riga sulaiman shiga kungiyar tasu don shi sulaiman wani abokin sane dayaje service inyamuri suka hadu shine ya kawosa kungiyar,bayan matar papa ta dawo Libya kungiya ta bata mukami Mai girma sakamakon yaranta data bayar har uku,Saida Kuma rikici ya barkene lokacin da kungiya ta bukace,ta bata jinin Nnenna anan tace Nnenna Amana ce aka Bata bazata taba cutar da ita ba iyayen ta sun Mata halacci an buga an buga Abu yaki ta kafe akan bazata taba data jininta ba. Hakan ya fusata shugaba su ya Aiko Mata da annoba Rana tsaka ya Kama gidan ta don duk barazanan da zasu Mata sun Mata amma ta nuna musu saidai tabar kungiyar akan ta bada Nnenna, amma abin Al'ajabi babu abinda ya samu Nnenna cikin yardan Allah saboda marabai dake jikinta sosai suke Bata kariya Amma da izinin Allah (tunda malam ya Bata magani shikenan Bata tare dasu yanxun)bayan mutuwar matar papa, sun gano jinin Nnenna ba karamin karawa kungiyar su shahara zatayi ba duk wani hanya da Suka San zasu bi suga bayanta sun bi Allah baya Basu sa'a lokacin da ta girma sai Suka Soma janta zuwa cikin kungiyya a nufin su ta gaji karagan mulkin matar papa Kuma ta dalmaya dasu saboda Karin shahara da daukaka da zasu samu amma sun rasa meyasa Nnenna tafi karfin su karshe ma duk lokacin da Suka yunkuro Mata sai sunga tashin hankali shiyasa suka sanya Mata kaunar Kule Kuma suka hadata da kiki Yana gadinta. Jin wa'innan labaren ya d'aga hankalin jama'ar NAGERIA Inda wasu gaggan matasa Suka bankawa motar su sulaiman petur da wuta lokacin da aka fitar dasu daga kotu Basu ma Bari shariya ta kare akan su ba,mutuwar su Babu abinda jama'a ke tofawa sai Allah ya Kara nauyin kasa,mahraz da kannen sa harma da Mami ha karamin kuka sukasha ba uba ubane Koh yaya mutum zaiji zafin abin a ransa. Su Lahab sun koma rugan su malam Inda Suka tarar Allah Yama malam rasuwa Lahab ya d'auki dawainiyar matar malam nayau da kullum ya gyara Mata gidan ya koma na zamani haka zalika ya kaita haji duk wata Kuma sai ya turo Mata da kayan abinci,mama da Muhammad Ashe iyalan bubaja ne mama ta sake aure ne,lokacin da Suka hadu ba karamin kuka mama tasha ba shima bubaja ya Barta da Sabon mijinta don yaji matukar dadi daya hadu da gudan jinin sa,sannan mijinta ya rike dansa Kamar na cikin sa,ashe lokacin da Suka fita a gidan haka kawai Suka manta da kome da kowa nasu sai mutuwar su sulaiman ne abubuwan Suka dawo musu. Rayuwa ta koma sabuwa sai abinda ba za'a rasa ba daman shi dan Adam kulum cikin jarabawa da tawakkali yake yau dadi gobe akasinsa,mubeena Amarya ta haihu Allah ya azurta ta da samun ya mace,haka zalika matar Ade ma ta haifi namiji,amma Deyana shuru kake ji har yara sun gima kusan 15years kafun Allah ya saukar Mata da rabon ta,itama ta Kara haihuwar namiji yaro yaci sunan Rahab duk da ba tagwaye bane amma Lahab yasa Masa Hussain Kuma ana Kiran sa da Rahab,saboda har lokacin Kewan Dan uwan sa da har gobe yake damun sa Bai barsa ba, Y'ay'an Mami kaf sunyi sure Yusuf autane kad'ai ya rage shima ya Zama saurayi. Abotar Adewale da Lahab sai Kara gaba gaba yake har Kuma lokacin iyayen Ade basu musulunta ba sai dai hakan baisa eshat da yaranta sun guje jinin ubansu ba haka suke zuwa wajen kakanayen nasu Kuma Alhamdulilah Suma Suna kaunar y'ay'an d'an nasu(jikokin su) Kamar me ga yara Kamar larabawa kamannin uwar su Suka d'auka hatta launin fatar su. Yau tun safe gidan Lahab ke cikin farin ciki ata dalilin bakin da zasuyi daga Libya,ba karamin shirya gidan Nnenna da nazeefa sukayi ba Lahab de na kwance a daki don kwata kwata yau da mutuwar jiki ya tashi shiyasa ya Shiga daki yayi kwanciyar sa sai yaran da mamar sune keta murna,wayar sane yayi ringing amma ya kasa d'auka turo kofar akayi Dr Deyana ce ta shigo dakin nasu kallon Lahab tayi sai Kuma ta girgiza Kai kawai,wayar tasa daya tsinke ta d'auka ganin miss call in waye yasa ta bin Kiran,sai Kuma ta matso kusa da mijin nata ta manna Masa a kunne amma tana Jin duk abinda na cikin wayar ke cewa. Waro Ido tayi Jin muryan Ade na dariya Yana cewa sai dai fa suyi hakuri su mubeena a gidan sa Suka sauka yanzun haka ma Suna Kan dinning ita da Usman Suna cin abinci da yaran sh,"what wallahi basu Isa ba Suka sani tun safe Ina Kan kafata kana suzo suce Wai sun sauka a gidan sa"tace cikin Jin haushi dariya kawai Lahab yayi ya katse wayar da Sauri ta Mike bude wardrobe nata tayi ta dau hijab bata saurare tambayar ta da Lahab yake Ina zata ba ta fito falo kallon yaron nata tayi tace"Kai Rahab maza mike,kee nazeefa fito a dakin Nan kwalliyar ta Isa haka kizo ki dau Abdul-Rahim mu tafi gidan big uncle naku,sai Kuma ta dakata tana cewa Kai nazeefi d'au kulolin abincin Nan muje baza'a sani asara ba,shidai Lahab fitowa yayi Yana kallon abin mamaki Nnenna ta tasa kuloli da yaranta a gaba suka fita a falon gidan......................... *ANAN NA KAWO KARSHEN LABARIN KUSKUREN DAYA YI A CIKI ALLAH KA YAFE MIN MASOYA INA MANA FATAN ALKHARI* *Alhamdulilah Alhamdulilah Allah nagode maka daka nuna min Rana ta yau jumma'a 25/2/2022 Na kammala labarin ALKAWARIN MASOYA godiya Mai tarin yawa gareku Fan's na ALKAWARIN MASOYA nagode da kaunar da kuka nunamin ubangiji ya Kara bude Aunty's masu cewa har yanzun ba update me toh yau dai Zan kwanta sakayau Dani Babu tunanin update,duk da naso labarin yafi haka tsawa saidai Alhamdulilah hakan ma nagode wa Allah daya bani iko da basiran kammalawa lafiya Bissalam* πŸ€ *By Ruqeenjalal* πŸ€ Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels