Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels Compiled by Princess Aysha Muhammad (Humaira) BABANA DA MIJINA ©Fertymerh Xarah 1 Agogon alarm dake manne a bangon falon ya buga qarfe ďaya dai dai na dare, Ta ďauke kanta daga kallon agogon ta maida jikin TV tana kallon aljaxeera.... Xaune take akan sofa tana sanye cikin rigar barci mai tsantsi fara sol, Ba wata muguwar kyakkyawa bace can, tana da kyau dai dai nata sai dai kuma mace ce Mai aji na qarshe, Akan tsinin hancinta tawwadar Allah ce da aka haifeta da Ita tayi mata kyau kasancewarta farar mace daga nan xaune taji tsayuwar motar mahaifinta, idan da sabo ta saba da wannan hali na mahaifinta da mijinta na fitar dare ko dawowar dare, gwanda mahaifinta ďan siyasa ne shine mataimakin gwamnan birnin kebbi, sukanyi meeting ďin dare akai akai wataran ma a gidan sukan taru suyi tana jiyo hayaniyar su daga nata gidan, Bai jima da tsayuwa ba taji ya shige sashensa, tayi hamma haďe da yin miqa cikin wani irin yanayi na barci dai dai lokacin daya shigo falon da qatuwar kwallo a hannunsa, Ko kaďan bai raxana da ganin matar tasa a Wannan lokacin tana xaman jiransa ba Co's ta saba, ta xuba masa idanuwa tana kallonsa cikin wani irin yanayi fuskarta ba walwala, ya cillar da Kwallon dake hannunsa haďe da xare socks ďin qafarsa duk Idanunsa akan ta har ya gama cirewa yayi sassanyar ajiyar xuciya, duk hankalinsa da attention ďin sa yana kanta, ya sami kansa da ruďewa, akwai wani sassanyan kallo cikin kwayar idonta Wanda ba duk mata Allah ya mallakawa ba, ya nufeta cikin wata irin tafiya ta izza cike da taqama ya xauna a kusa da ita haďe da ďora hannunsa akan nata hannu, Kiyi haquri Iman kamar yanda kike a kullum wasan kwallo wani abu ne d.... yayi shiru sakamakon wani kallo da tayi masa, A iya sanina wasan kwallo anayinsa ne da rana ko da safe amma ku bansan wane irin Wasa ne naku da sai dare kukeyinsa ba, Ya tsura mata ido, Iman baki yarda dani bane, ko kina xargina? Ba xargi a nan illah gsky nake son ka gayamin, bayan albashinka na banki kana nufin duk wannan dukiyar daka tara duk akan kwallo ne ? Ya gyada kansa Kwarai Kuwa, kije ki tambaya kiji duk ďan kwallo na asali Mai fita waje yana ball ba qaramin kuďi suke samu ba, ki yarda dani Mai sunan mamana bani da wani mugun hali Wanda xai cutar dake, tayi shiru kawai idanunta sun kawo kwalla ta kasa yarda da mijinta da mahaifinta, tsakanin *babana da mijina* baxan ce ga Wanda yafi wani so na da kula dani ba, ga kuďi har batason ganin su kasancewar tana xargin masu su, ta goge hawayen fuskarta, yana kallonta cike da so da tausayinta yana jinta har cikin ransa shi kansa baisan wane irin so yake wa Fatima ba, ya riqo tafin fuskarta haďe da sanya yatsansa yana share hawayen fuskarta, Babban tashin hankalina shine naganki cikin damuwa, har sai yaushe xaki yarda dani Iman, idan baki yarda dani ba Waye xai yarda dani, wallahi ni ďan kwallo ne kidaina xargina, taja numfashi haďe da Sakin malalacin murmushi tana kallonsa na yarda da kai mijina, amma Ina so ka kiyaye kayi a hankali da duniya ka Kuma ji tsoron Allah, jikinsa yayi sanyi Yace Insha Allah Iman, ya riqa hannunta suka tashi da kansa yaje ya kashe tv da komai, tana tsaye sarqe da hannayenta a qirjinta tana kallonsa cikin so da qauna, ya juyo yana kallonta 'let's go... ta juya yabi bayanta, har suka hau step ba mai mgn a cikinsu kowa da saqe saqen xuciyarsa, ďakin qanwarta Fauxiya ta nufa ta buďe dakin a hankali ta shiga, ta same ta tayi barci sosai ďakin ya ďauki sanyin a.c ta qudundune guri ďaya da alama tana jin sanyi sosai,ta juya tana kallon sa, 'you see Fauxiya bata jin magana duk ynda nayi da ita akan shan sanyinnan bataji, Ahmed yaje ya kashe a.c ďin kana ya ďauki blanket ya lulluba mata bayan ya gyara mata kwanciya, ta matsa ta gefenta ta xauna, addua tayi mata kafin su bar ďakin, Kai tsaye toilet ya nufa yayi wanka, yana shirin barci ta shigo da coffee a hannunta, ya karba yana kallonta da murmushi, 'thank you wify ,tayi murmushi ta xauna bakin gado tana kallonsa, Yana gama shan coffee ďin ya juyo ya sumbaceta a goshi yana fadin gudnyt, kafin tayi mgn har ya faďa Kan gado ya kwanta, ta bisa da ido cikin tausayin kanta hawaye suka xubo mata, Wannan wace irin rayuwace, wane irin aure ne wannan, am a doctor, mijina yana aikin banki, idan ya fita tun da safe baxan qara sa shi a ido ba sai 6pm da yayi wanka yaci abinci ya fice sai 1 ko 2am wataran ma sai da safe take ganinsa ya dawo wai yaje training ďin kwallo, Yau satinta biyu rabonta dashi tana buqatar mijinta tana da haqqi akansa bai damu ba saboda ita tana da buqata sosai ba Kamar shi ba ko xasuyi wata a hakan baxai damu ba, A matsayina na matarshi abokiyar rayuwar sa bashi da lokacin da xai xauna dani and sai dai kullum idan nayi masa Mgnr fitar dare yace bana yi masa uxuri da yawan ayyukan dake gabansa a banki, da dare Kuwa xaije training na kwallo, Ban rasa ci ba ban rasa sha da sutura ba amma na rasa kulawa da soyayyar mijina abin tambaya anan shi wannan shine ginshiqin auren, am not satisfied with my husband, bama Wannan ba rashin xamansa gida... Babana ďan siyasa ne shi ba mai xama bane idan baya gari yau gobe yana wata qasa, idan yana gari shima baxaka ganshi ba sai cikin dare yake dawowa, idan taje mashi da complain na fitar mijinta sai dai yace 'haquri xakiyi tunda koni mahaifinki kina ganin ba maxauna bane, muna meeting sosai Mai muhimmancin acikin dare, tunda ya gayamiki wasan kwallo suke xuwa kiyi haquri ki barshi komai lokacine, ta share hawayen ta cike da mamakin kalaman mahaifinta, shekara biyu da rasuwar mamana, banda kowa a duniyar nan bayan *babana da mijina* sai qanwata fauxiya, bansan wa xan kaiwa kukana ba ya share min shiyasa ko aiki naje banda tunani sai na *babana da mijina* babu wanda baya fuskantar challenge(qalubale) a rayuwa, and is up to us to accept such challenges mu bita da duk fuskar da rayuwa ta xo mana.... Jin shiru bata kwanta ba ya juyo yana kallonta, 'lafiya Iman, me kike tunani, ta tashi da sauri tana fadin ba komai ta nufi toilet, ta saki ruwa tana kuka sosai yanda baxai jiyo ta ba...... *Dedicated dis buk to* *Rabi'atu Sk Mhs* *Sadiya Lawal bala* *Aysher Gambo* BABANA DA MIJINA ©Fertymerh Xarah 2 Asalin labarin...... Ahmed mutumin jihar Birnin kebbi, Daga kallo na farko mawuyacin haline ka gane qabilar da ya fito Hausa ko Fulani, wani mutum ma'abocin cikar zati da kamala da duk wani nau'in daidaito na rayuwa, Mahaifinsa malam Abubakar buba malamin islamiya ne mutum ne mai ilimin addini, haka mutanen unguwa suna tsananin girmamashi, Sai mahaifiyar Inna, shika dai ne ďa a gunsu, bayan rasuwar mahaifinsa suka shiga wani hali na rashin babu, gashi qarami a lokacin primary 6, Ba Mai taimaka masu wani sa'in ma Inna ke xuwa wankau ta sami kudin da xata ciyar dashi, shi Kuma Ahmed a rayuwarsa yana son karatu shiyasa yake dagewa akan karatun, he is gifted tun yana qaraminsa malamai sun San dashi, Ahmed yayi karatunsa da taimakon mahaifiyarsa dake siyarda qarfinta dan ganin farin cikinsa, lokacin da ya shiga babbar makaranta I mean higher institution duk qaddararta sai da ta saida ganin ta cika masa burinsa, Alhamdulillah ya kammala degree ďin sa lfy duk aikin dayaje nema na gwamnati bai samu ba, duk inda yaje nema baxai samu ba, abokan karatunsa Waďanda iyayensu suke da kuďi sun fara aikin banki saboda suna da ďaurin gindi a gwamnati wasu ma sun fita waje neman wani ilimin, shikam degree ne iya qarfinsa yana so ya sami aiki dashi ko yayane dan ya tallafi mahaifiyarsa.... Kwanci tashi asarar mai rai yau gashi an kwantar da Inna asibiti babu kudin magani Babu babban tashin hankalinsa kamar ciwonta ulcer da kuma hypertension, duk inda ya buga bai sami kudin ba, abokansa dake bashi aro sun daina saboda baya biya, Ya qara komawa asibiti kai tsaye ya nufi inda likitan ya roqesa ya taimaka ya duba mahaifiyarsa fisabilillah saboda bashi da kuďi, fafur likitan yaqi har kuka yayi wani mutumi dake xaune office ďin shima yaxo likita ya dubashi ya dubi likitan, Nawa ne kudin maganin, Dubu biyar ne fa bawani yawa, kamarsa baxai iya biyawa mahaifiyarsa kudin magani ba, baxaije ya nemi aiki ba, muma karatu mukayi muka sami aikin, Ahmed ya dubesa, ko xaka daukeni aiki ne, ko wane irine inaso indai xaka biyani na kula da mahaifiyata Likitan yace bama daukar mutum aiki sai mai ilimi kai kuma baka dashi, Ahmed yace inadashi nayi karatuna na kammala na nemi aiki ban samu ba yaciro takardunsa ya nuna masa, likitan ya duba sosai Ahmed ya cancanci a daukesa aiki saboda matakin karatunsa Kuma result ďin sa mai kyau ne... Xan iya samama aiki da wannan result amma sai idan xaka iya biyan dubu hamsin, kasan aikin gwamnati ynda yake Kuma a banxa baxaka sami aiki ba sai ka kashe kuďi.... Ruwan cikinsa na soma qugi Wanda bai sami dubu biyar na magani ba Ina xai sami dubu hamsin a ynxu, ya karbi takardunsa ya juya ya fice yana hawaye, dakin da aka kwantar da mahaifiyarsa ya nufa har lokacin bata farfado ba barci takeyi, qarqashin pillow ďinta ya cusa takardun xaije ya nemo kuďi da qarfin jikinsa ya juya ya fice.... Ya fito harabar asibitin ya haďu da wannan mutumin na ďaxu ya kirasa yaje, Sannu saurayi, Ahmed ya qara gaida mutumin, Na ganka kana da hankali sosai Kuma da ganinka xakayi jarumta xan baka kuďi ka taimaki mahaifiyar ka kakuma sami na aiki indai xaka iya min aiki, Wane aiki ne xan iya....ya faďa muryarsa na rawa Mutumin yace ka taba riqa bindiga? Ahmed ya girgixa kansa yana kallonsa cike da mamaki, Xaka sami kuďi sosai indai xaka iya shiga cikinmu, ni babban ďan ta'adda ne nayi irin Wannan rayuwar taka ta talauci da haka hr na rasa iyayena, saboda rashin kuďi gurin haihuwa matata ta rasa ranta, bansan wace irin rayuwa muke ciki a ynxu ba da masu kuďi basa taimako dan Allah, Mai kuďi daga shi sai xuri'arsa, ďan siyasa ma haka, neman aiki ynxu baxaka samu ba sai dai su bawa yan uwansu, shugabannin mu na Yanxu basa aiki kamar na da, shin miye laifin talaka? da haka na nemawa kaina aiki nakewa masu kuďi fashi, inada yara biyar duk aka sami kuďi kowa Ina bashi kason sa da haka nake gayyatar ka kashigo cikin xaka sami kuďi Kuma xakaji daďi.... da'ace mutumin ya lura da yaga xufar dake ambaliya a fuska da jikin Ahmed, yayin da gudun jini ya Katse a jikinsa, hanjin cikinsa ya dunqule guri ďaya ďan fashi kenan xai xama, barawo Mai daukar haqqin mutane haqqin da ba nasa ba, duk wahalar nan da yayi wajen neman ilimi da kwalinsa sai ya qare a sata.... tor miye amfanin karatun da yayi? Wata xuciyar tace rayuwar mahaifiyar ka fa, kana nufin karatun yafi tane? BABANA DA MIJINA ©Fertymerh Xarah 3 Shiru yayi yana kallon mutumin sosai xuciyar sa sai bugawa take yayinda take ingixa sa akan ya amincewa mutumin ya sami kudin da xai Kula da Inna, tunda yan uwansu ma sun gujesu basa taimaka masu da komai tunda ba su da, Baya manta sanda mahaifinsa na da rai yan uwansa kamar xasu haďiye su saboda kulawa Kuma saboda mahaifinsa mutum ne dayasan haqqin ďan uwa yake biya masu buqatocinsu, yau gashi babu ran mahaifinsa sun gujesu saboda basu da komai, mahaifiyarsa na kwance ba kuďi Kuma ba Wanda xai iya xuwa ya xauna da Ita asibitin sai shi..... Wannan dalilin ne ya Sanya Ahmed amincewa ya karbi tayin oga nas Wanda yayi matuqar jin daďi da ya amince kai tsaye ya bashi dubu goma da address ďin inda xai same sa.... Bayan ya karbi kudin jikinsa na rawa yaje pharmacy dake nan asibitin ya siyo magani ya nufi inda mahaifiyarsa take, Yanda ya sameta hankalinsa yayi matuqar tashi ya juya xaije ya Kira likita ta riqo rigarsa, da kyar take iya mgn Baxan tashi ba Ahmed, buri na bai cika ba inganka yau ka xama wani mutum da duniya xata so kuma tayi alfahari dashi, kayi haquri da duk yanda rayuwa ta xoma, ka nemi halal, ka Kula da kyau kada kabari ruďin duniya da abinda ke cikinta ya ci galabarka, Hawaye yake sosai, jikinsa na rawa hankalinsa yayi matuqar tashi da maganganun mahaifiyarsa, Baxaki mutu ynxu ba Inna sai nayi maki gata, ya banbare hannunta da kyar ya fita da gudu neman likita, Ko kafin su xo rai yayi halinsa, Allah ya gafartawa Inna...... * Alhaji Abdallah mutumin xuru ne qaramar hukumar Birnin kebbi, Babban mutum ne mai ji da kansa Wanda duniya ke damawa dashi a siyasa, shine mataimakin gwamna a Yanxu kafin ya sami matsayin da yake a yanxu sai da yayi fafatukar duniya da shige shige Wanda Dama a Yanxu idan mutum na neman cimma wani buri nasa yakan manta Allah ya kauce hanya, a taqaice sai da ya bada jinin ďaya daga cikin yaransa kafin ya sami kujerar da yake Kai a yanxu, Ya'yan shi biyar mata biyu maxa uku sai matarsa Mami, mace mai kirki da mutunta ďan Adam.. Naxir shine babban yaron sa, sai fatyma(iman), Musa, Ismail da qaramar su Fauxiya, Acikin yaran kaf ya fison Fatima da Fauxiya ko kaďan baya son Abinda xai tabasu, soyayyar da yake nuna masu daban ce da ta sauran yaransa....... Kuďin sa Kuwa baa magana, yana da dimbin tarin dukiyar da yabayarda ya'yan sa uku duka maxa, Mutuwar su tana xowa Mami a baxata, babu ciwo babu komai xaka ga kumfa na fita bakin su daga nan Kuma rai yayi halinsa, da haka ta fara rasa yaron ta Naxir... Naxir ba qaramin mutum bane, a shekaru yabawa 26 har an nema masa mata, fatyma Kuwa a lokacin ba Mgnr aure a gabanta she is 24 karatunta ta sanyawa gaba, she want to achieve the goal, bata da buri a duniya kamar ta wayi gari yau ta ganta cikakkiyar likitar mata tana jin haushin yanda mata ke Kai matsalolinsu da sirrin jikinsu ga likita namiji, Sanda babansu ya fara siyasa a lokacin komai ya soma sauyawa daga rayuwar gidan na rasa babban ďan gidan, sosai Mami ta shiga damuwa shi kansa Baban ya nuna damuwarsa duk da shine sila akan komai, Sai wani lokaci da matsafin nasu ya nemi ya bada ďaya daga cikin ya'yan sa mata, sosai hankalinsa ya tashi domin a duniya ba abinda yake so kamar Fatima da Fauxiya komai xai iya akansu, Ya qara russunawa haďe da gyara hannu jar rigar dake jikinsa ta tsafi, Kiyi haquri shugabata xan bada yarana biyu maxa a maimakon matan Ina matuqar sonsu musamman ma Fatima Iman....... Ta kece da wata dariya mai raxanarwa sai da gurin ya ďauka kafin tace Sima ta amince yau da dare nake buqatar jinin Ya'ya ka, An gama ya shugabata ya faďa yana russunawa, Ta qara wata dariyar kafin ta juya Kan amininsa Wanda shine sanadin kawo sa gurin, Me xaka bawa Sima gobe tayi Kari dashi labaran? Ya sunkuyar da kai cikin girmamawa... Babu ya shugabata sai abinda kika yanke min, banda kowa ynxu a duniya duk na bayar matatace kawai ta rage... Bana son matar ka, bana son jininta tuntuni na gayama dan haka ka nemomin jinin wani mutum ko wane irine ka kawo min a gobe, Shikenan ya shugabata.... ta qara yin wata dariyar bayan ta nuna na kusa dashi, Kai kuma munada labarin anyi haihuwa a gidanka jinjirin mukeso kafin ayi suna...... Da haka kowa Sima ta gaya mashi Abinda xai kawo ta Kuma cikasu da kuďi iya adadin da suke so.... Dama hakane idan har xaka shiga wannan har ka xaka wayi gari baka da kowa a duniya duk ka bayar saboda neman haram da son abin duniya ka sami kuďi, mecece ribar wannan sana'a? Da dare duka yaran na tare da Mami, sai Kai da komawa yake naganin yanda xai ďauki rayuwar yaran biyu..... BABANA DA MIJINA ©Fertymerh Xarah 4 Already Fauxiya tayi barci, Fatima Kuwa tana study room ta matsawa kwakwalwarta da karatu, Musa ne da Ismail ke tare da Mami, sun jima sosai tare da Ita kafin suyi mata Sallama suka fice... Yana xaune a falo suka fito, fridge suka buďa kowane ya ďauki yoghurt Wanda dama al'adar su ce basa kwanciya sai sun sha, Baba Xamuje barci kayi mana addua, ya ďago yana kallon yaran bawai bayason yaransa bane son xuciya da neman duniya suka rufe masa ido, yayi matuqar tausayawa yaran, Shikenan musa ka Kula da qaninka, Allah ya tashe ku lfy ya raba ku da sharrin mutum.... Suka ce Amin, Ismail yace baba ni gobe baxan tsaya lesson ba ka gayawa driver yaje ya ďauke ni da sauri, Meyasa Ismail... Mami tace xataje dani da Fauxiya unguwa banda musa, Yace tor shikenan xanyi masa magana, musa yace Baba baka cika min alqawari na ba, kace xakaje dani waje nayi karatu irin anty Iman Fatyma ai tagama karatun kaima xakaje ni xan kaika da kaina, Yaron yayi tsalle ya rungumeshi, thank you father Ina sonka..... Jikin Baban yayi sanyi sosai da kyar ya iya rungume yaron a jikinsa kafin ya rakasu har dakinsu da kanshi, yana labe yana kallon sanda suke game suna shan yoghurt Wanda a ciki yayi siddabarun sa, basu jima ba Kuwa suka xube gurin suna kakaki kumfa na soma Fita bakinsu, yaje da sauri ya ďauke yoghurt ďin ya musanya shi da Wanda baida komai ya fice, idan xakayi masa kallon natsuwa a Wannan lokacin xaka fahimci baya cikin hayyacinsa ko kaďan.... Mami ta fito daga ďakinta Kai tsaye study room ta nufa ta sami fatyma da tulin takardu a gabanta, gefenta kofin coffee ne da take korawa akai akai... Iman ya kamata ki riqa bawa kanki hutu ki samawa xuciyarki sauqi, wannan karatun yayi yawa haka ke kullum akan takarda.... ta ďago idanunta da kyar tana kallon mahaifiyarta idanunta sunyi jawur sosai sun nuna kalar barci, Mami you won't understand,karatun likita is quite different da sauran karatun, kibari nan da shekara ďaya na kammala karatuna na xama cikakkiyar likita xn fara maki surgery.. Surgery? ta tambaya da mamaki tana kallonta, surgery akan me? Tayi far da ido tana kallon ta cikin shigar wasa irin ta ya'da uwa, Tace Mami har ma sai na gaya miki kibari lokacin yaxo xaki sani... Mami tayi dariya tana tattara littafan dake gabanta, Ko Alhuda huda yana samawa xuciyarsa sauqi Iman, ki tashi kije ki kwanta, Ta tashi tana miqa, a tare suka fito suna tafe suna hira, baba na ďakinsa yana jinsu hr lokacin da yaji Faty na fadin, Mami Ina ya'yanki ko sunyi barci bnji hayaniyar game ba, Me yiwuwa haka ne, amma bara na dubasu, ta nufi ďakin Faty na bayanta, yana daga window yana kallonsu har suka shiga, basu jima ba ya jiyo qarar fatyma tana kiran baba... ya koma yayi kwanciyarsa kamar mai barcin gaske, Iya ruďewa sun ruďe bama kamar Mami da ta xama mutum mutum, batasan meke faruwa akan ya'yan taba, suna haka baba ya shigo cikin yanayin barci sosai ya nuna damuwarsa hrda kuka yayi..... Tun daga lokacin abubuwa sun soma faruwa, walwala da jin daďi sun rageshi a gidan, ga kuďi kamar me, basu taba xargin sa akan Kuďin da yanda yake kashe dukiya ba saboda sun San dan siyasa ne, Iman da Fauxiya ne kaďai suka rage masu a ynxu duniya, yana son su fiye da xaton mai karatu haka yake ji komai xai iya dan ganin farin cikinsu.... 2 years later Siyasa ta tashi sai faman xabe ake ana campaign, baba yaje wa Sima da buqatar Wannan Karon yana son matsayinsa na mataimakin gwamna kowane mutum ne yaci gwamna a birnin kebbi yana so yaxama mataimakinsa, wani xabe mai xuwa yana so ya fito takarar shugaban qasa.... Sosai sima tayi dariya wadda tayi matuqar raxana su, Buqatar ka xata biya Abdallah, xakaci siyasa idan har xaka bada jinin matar ka...... Sosai ya raxana da jin kalamanta, bai taba xaton akwai abinda xai rabashi da Mami a ynxu ba saboda ta xamo ginshiqin rayuwarsa, Auren soyayya sukayi, tun saurayi da budurwa, yana sonta tana sonsa..... har ya dawo gida bashida sukuni tunaninsa yanda xai bada jinin Mami, ya kasa barci sai faman juye juye yake akan gado, duk abinnan da yake akan idonta tana kwance tana kallonsa, Ta matso a hankali xuwa garesa, Meke damun ka alhaji, yayi firgigit yana kallonta da mamaki, Kada dai hr ynxu kana tunanin su musa ne? Ya girgixa kansa hawaye suka xubo masa, hankalinta yayi matuqar tashi, Meke faruwa meke damunka? Ya janyota sosai jikinsa ya rungumeta... Ki yafe min, ki yafe min Amina, Jikinta ya ďauki rawa, Ba abinda kayimin a xamana dakai, inma kayi na yafe ma nima ka yafemin, Ya sauke ajiyar xuciya yana qanqame da ita yana jin sonta har cikin ransa Kuma har lokacin bai daina hawaye ba, Ta maida kanta qirjinsa hankalinta ya kasa kwanciya da yanayin mijinta tabbas akwai abinda ke damunsa yake boye mata, Gobe da safe xata tuntubesa ya gaya mata damuwarsa.... Suna haka hr barci ya ďauke ta, ya sumbaceta sosai kafin ya janyo wani Jan kyalle qarqashin pillow ďinsa.... BABANA DA MIJINA ©Fertymerh Xarah 💞 5 Rumtse idanuwansa yayi kafin ya ďora mata kyallen a jikinta, A hankali ta buďe idanuwanta tana kallon sa sakamakon wani raďaďi da taji a xuciyarta, A hankali bakinta Na soma motsi kafin idanun su rufe dai dai lokacin numfashinta na ďauke, Cikin wani irin yanayi ya rungumota jikinsa haďe da fashewa da wani irin kuka mai tsuma xuciya, Mutuwar Mami sosai ta girgixa mutane, yan uwa da abokan arxiki bama kamar fatyma da fauxiya, Shi kansa baba idan ya shiga gidan ya sami Fauxiya jikin fatyma sai hankalinsa ya tashi saboda tsananin tausayinsu da tausayin kansa, a lokacin Fauxiya is 6yrs, sun xama marayu..... Ma'aikatan gidan ya qara saboda kula dasu, basu da wani aiki a gidan daga ci sai kallo sai barci, Fatin ce batada hutu saboda karatu... Bayan wani lokaci akayi xaben siyasa Kuma yaci, sai ya Gina masu wani qaton gida mai hawan bene guda biyu kowane da gate ďinsa sai aka xagaye gidajen aka maida shi gate ďaya as 2 in 1, Cikin ďaya suka tare sai ďayan ya ajiye idan fatyma xatayi aure su tare a gidan saboda bayaso tayi nesa dashi ko kaďan, Sosai taji daďin haka ynda takeji a xuciyarta baxata iya barin qanwarta da mahaifinta ba, she is happy with the house, sai ta rungume mahaifinta cikin farinciki shima sai ya tsinci kansa cikin nishaďi ganin fatyma taji daďi... * Ahmad Deedah bayan rasuwar mahaifiyarsa, ya karbi tayin oga nas suna xuwa wurare da dama sata, ya kware ya iya bama kamar harbin bindiga, baya kissa kamar sauran abokansa sai dai ya tsoratar da bindiga, haka Kuma idan police sun masu taurin kai wajen bibiyarsu yakan harbi mutum a hannu ko qafa, Cikin lokaci qanqani yayi fice ya xama gwarxo aciki Wanda oga nas ke alfahari dashi, duk suka fita operation sai sunci nasara wannan shine dalilin dayasa oga nas yabawa Deedah matsayi babba a cikinsu Kuma yakeji dashi and again yana tsoronsa domin mutum ne kaifi ďaya idan yace eh ko A'a ba Wanda ya isa ya lankwasa sa, Bayan wani lokaci ya nemi aikin banki kai tsaye ya samu cos kuďi ke mgn Kuma ya bada, Ya kanje aiki tunda sassafe baxai dawo ba sai marece, idan yayi wanka yaci abinci xai fice inda sauran abokansa inhar baxasuje sata ba a Wannan ranar, Idan ka ganshi Kaga kamillin mutum, qasaitaccen namiji mai ji da kyau da kuďi, bafillatanin gaske, baya neman mata xina,baya shan giya matsalar ďaya ce DAN FASHI..... Haďuwar sa da fatyma ya samo asaline a bank, taje verification, Daga yanayin tafiyarta xaka gane nutsuwarta da kamalarta sai dai kallo ďaya xaka mata ka fahimci baa hayyacinta take ba, kai tsaye ta shiga bankin hannuwanta duka Acikin Jakarta da alama abu take nema tana tafe tana dubawa, dai dai lokacin ya fito daga office ďinsa, sanye da baqaqen suit, hannuwansa da laptop yana tafe shima yana latsa ta cikin sauri... Kicibis sukayi karo da juna, daga shi hr ita kayan dake hannuwansu suka xube a qasa, laptop ďin ta ďauke wuta, Ya salam... ta furta a hankali bayan ta sunkuya daukar laptop ďin bata damu da nata kayan ba, ta ďago tana kallonsa yana tsaye Idanunsa sanye da farin glass daga kallo ďaya xaka fahimci bacin rai sosai kwance a fuskarsa, sai ta tsinci kanta cikin ruďewa Abinda bata tabayi ba, Am sorry please, ya karbi laptop ďin haďe da Jan dogon tsaki ya fice tabi bayansa da kallo xuciyarta na bugawa kafin ta maido hankalinta ga kayanta dake xube a qasa, ta sunkuya ta haďa kayanta ta fice.... Ta jima sosai a bankin kafin ta gama verification ďinta, tana gab da fitowa wayarta ta ďauki qara, ta ciro ta Jakarta Dr.hadixa, sai a lokacin ta tuna da Kuďin dake Jakarta xata tura mata, Oh sorry Dr. Ina banki ynxu xn turo maki Kuďin.... ta faďa bayan ta ďauki Wayar, Ta juya da sauri,inda ta fito ta koma tayi masa bayani, ya nuna mata office ďin, tayi godiya ta juya ta fice... Da Sallama ta shiga office ďin, yana xaune Wannan Karon ba glass idanuwansa ya xubawa Mai gyaran laptop ďin ido, tsoronsa kada taqi tashi saboda muhimman abubuwan dake ciki, Sallamarta ta janyo hankalinsa gareta, ita ďin ce, me taxo yi office ďinsa, itama tayi mamakin ganinsa jikinta yayi sanyi ganin ana gyaran laptop ďin, ta maida kallonta garesa hr lokacin fuskarsa ba walwala, Dama na xone na baka haquri, it seems like na bata ma rai, ni bnganka ba ban San yanda akayi Hakan ta faru ba kayi haquri, Ya sauke ajiyar xuciya, Is ok ba komai, is not your fault is mine.. Tace A'a laifina ne... Yace laifina ne.. Tace shikenan Nagode ta juya xata fice ya tsaidata, Ba Wannan ya kawo ki ba, menene, sai a lokacin ta tuna ta ciro Kuďin Jakarta ta miqa masa,dai dai lokacin da aka gama gyaran laptop ďin sosai yaji daďi, Nan ma bata jima ba ta fice da sauri xuwa asibiti... My wattpad Phertymer BABANA DA MIJINA ©Fertymerh Xarah 💞 6 2 days.... Ta fito cikin shirinta na xuwa aiki, Fauxy na bayanta sai rigima take mata yau sai taje da Ita asibiti, Idan naje dake, skul ďin ki fa, Sannan bakyaji ne baxaki xauna inda xan xaunar dake ba, xakije...... tayi Saurin katseta, Anty kije dani dan Allah, I will be a good girl, Ta sanya Labcoat ďinta ta dubi Dijeh Mai kula da Fauxy, Tace dijeh ki ďauki uwar rainonki ba inda xanje da Ita kisanya mata uniform ďinta kada tayi late.... idanun Fauxiya sukayi rau sai ga hawaye Please Anty kije dani, bana son Skul yau, Fatyma ta fice da sauri dan bata son ganin hawayenta, Fauxiya Kuwa ta soma Kuka sosai... Harta xo asibiti Kukan Fauxy ke mata yawo akai, office ďinta ta nufa ta ajiye kayanta kana taje duba patient ďinta data bari a jiya, Gynaec suka haďu da Dr. Merah, Morning Dr. Morning inlaw (yanda yake kiranta saboda Fauxy da ďansa Sultan) you are late today, Am sorry, fitinar Fauxiya ce tana so naxo da Ita, Fauxie uwayen rigima itada sultan, ya miqa mata file dake hannunsa Dead Case ne, Matar ta mutu after delivering amma yaron da ransa, Ta Karbi file ďin tana dubawa, a tare suka juya inda ya cigaba da mata bayani jiya cikin dare an kawo wani patient accident case, ya xubar da jini da yawa, xnje gida shiyasa na damqawa Bakori case ďinsa, ku kula dashi Pls, Shikenan ta faďa, ya fice, a hanya suka haďu da Dr Hadixa suna tafe suna hira har suka iso A&E.... She was shocked to see him, mutumin da suka haďu a banki, garin ya haka ta faru she don't know, sai ta tsinci kanta cikin tausayinsa, shima kallon mamaki yake mata is she a doctor? tambayar da yayiwa kansa, Ya jikin ta faďa tana kallonsa, Alhamdulillah ya faďa a sanyaye.... A ranar ita ta kula dashi saboda Bakori is busy Sosai Ahmad yaji daďi, Oga nas da yaransa sunxo dubiyarsa, idanu fatyma ke binsu dashi cikin shigarsu ta mutunci baxaka taba gane ko su Waye ba, sosai sun birgeta ynda suke mutunta junansu sai dai abu ďaya na ďaure mata kai ba Wanda yaxo daga gefen Ahmad uwa ko sister kamar xata tambayeshi sai tayi shiru wannan ba hurumin ta bane, 2:00pm Lokacin tashinta aiki yayi ta soma harhaďa kayanta, hrta shiga mota ta tuna da patient ďinta, taje ta sanardashi she is going.... Ya tsura mata ido hr lokacin baisan sunan taba and he need to know.... Hr ta juya sai Kuma ta kallesa, Sorry to ask, ba wani naka da xaixo ya xauna da kaine kafin Dr. Umayma taxo ita ke on duty, Ya girgixa kansa, Babu, NI MARAYA NE..... ya faďa Idanunsa akanta, bnda kowa bayan abokaina, Sosai ta tausaya masa ta gyara tsayuwarta, Ka Kira ďaya daga cikin abokanka ya tsaya da kai, ba amfanin barinka kai kaďai cos nurses baxasuyi jinyarka ba, Hakane I will Insha Allah, tnx for your care, ta gyada Kai ta juya yayi Saurin tsaidata, Your name Pls.... Dr. Fatyma Abdallah, Sunan Mai daraja da muhimmanci a rayuwata, sunan mahaifiyata nake kiranta da Inna, xn iya kiranki da Ummi? Ta girgixa Kai tana kallonsa cikin tausayawa jikinta na soma rawa data tuna Mami, ta share hawayen idanunta, Nima na rasa mahaifiyata da yan'uwana, am alone with my sister sai mahaifina, ka kirani da Iman shine laqamina, Allah ya gafarta masu, tace Amin ta soma share hawayenta abinda ya faďa ya sanyata juyowa da sauri tana kallonsa, Ki aureni Iman.... Tsananin mamaki ya sanyata furta komai Illa idanu data xuba masa shima kallonta yake, she is not dat beauty tana da nata dai dai ita, haskenta shi ya qara mata kyau Wanda xakayi tunanin ita wata muguwar kyakkyawa ce, sanyin halinta da nutsuwarta yaji yana raayinta..... Batare data tankaba tasa kai tabar ďakin yabita da kallo.. Harta iso gida bata da sukuni muryarsa ke mata yawo akai, ki aureni, ki aure ni.... Da kyar ta fito daga motarta, ta juya tana kallon harabar gidan birjik da securities, ina little sister ta shiga.. Oh Allah ta tuna ita Mai laifi ce a gareta yau baxata xo yimata oyoyo ba tana fushi da Ita, Da sauri ta qarasa cikin gidan tana kiran fauxie, shiru bata amsa ba harta iso qaton falon su ga mamakinta sai ta sameta xaune akan sofa da skulbag ďinta tana ciro littafanta da alama assignment xatayi, Ta ajiye kayanta ta qaraso inda take, Kinaji Ina kiranki kika min banxa, is not the right thing fauxie, Ta tunxure bakinta ta maida kanta gefe, ta xauna kusa da ita tace da kika je Skul are you not happy, kinga friends ďin ki, you play and eat together, Ni banyi wasa ba, Tor meyasa? Ta nuna ta da yatsa idanunta sun kawo kwalla, ta rungumeta don't cry, gobe dake xanje, kinci abinci, Yes sister, dijeh tayi min wanka, Yayi kyau, ta buďe littafinta tana duba class work ďinta, Subhanallah Fauxiya me kikeyi a class har kika faďi haka, 2/5 Tayi shiru tana kallonta, sosai ta ďaure mata fuska, Xamu bata dake, silly girl, simple questions baxaki iya amsawa ba, Tace Anty ni ban iya ba ku.... ta katseta cikin fushi, Shut up, ta tashi a harxuqe itama Fauxiya tabi bayanta, 'Anty kiyi haquri, koda naje nayi kuka shine banyi ba, Har suka iso ďaki tana roqarta, Anty kiyi haquri karki gayawa baba, ta juyo tana kallonta Baba kike tsoro kenan, ai Kuwa xn gaya masa, Ta soma bubbuga qafafuwanta, Dan Allah anty baxan qara ba, I promise you..... Da dare ta kasa barci sai juye juye take, idan ta rumtse idanuwanta kyakkyawar fuskarshi take gani, maganarsa nayi mata kururuwa a kunne..... NI MARAYA NE KI AURENI..... BABANA DA MIJINA ©fertymerh Xarah 💞 7 Ta rumtse idanuwanta, Yh is true as her age ya kamata ace tana da aure yanxu, baba will be happy duk da baya mata Mgnr auren tasan yana so ne, Duk Acikin likitocin ita kaďai ce budurwa bayan nurses da yawa sun girmeta wasu Kuma age mate ďin tane, tana da maneman aure da yawa but she don't have interest on them, ta kunna fitilar ďakin tana kallon fauxie, Abubuwa da yawa take tunawa game da rayuwarta da qanwarta, komai suke so suna samu kuďi da jin daďi, haka komai yi masu akeyi, tun daga kan girki, wanki, shara, kula da gidan da komai ma baba ya Sanya masu yi masu, sai dai sun rasa kulawarsa basu samun Isashen lokaci daga garesa, kullum yana hanyar tafiya baya ďebe masu kewar UWA, hawaye suka sumulyo mata, ta qanqame qanwarta dole tayi aure kodan farin cikinta da qanwarta, dole tayi aure ko damuwarta xata ragu ta sami soyayyar miji tunda bata sami ta iyaye ba....... Washe gari tare da Fauxiya suka nufi asibiti, sai tsalle take tana jin daďi, nurses ďin dana Santa suka soma murmushi, Yau Fauxiya a asibiti, Ashe akwai rigima.. Fatyma murmushi kawai take hr suka iso office ďinta, ta ajiye Jakarta juyowar da xatayi ba Fauxiya ba dalilinta, dama tasan a rina, Ta xauna tana duba files ďin patient ďin da xata duba na ranar, sosai ta dade akansu kafin ta gama, shiru ba alamar fauxie, ta tashi tabi bayanta inda take xato nan ta sameta office ďin Dr Merah tana xaune a gefensa da sweet a hannunta sai surutu take masa yana duba patient ďinsa, sai kayi xaton yar sa ce ta cikinsa Bata Bari ta ganta ba ta juya da sauri ta nufi a&e, Su biyu ne aciki shida abokinsa Sa'eed gurin aikin su ďaya a bank, Da Sallama ta shiga idanunta sanye cikin farin glass, hannuwanta a aljihun Labcoat ďinta, sosai tayi kyau, Suka amsa sallamar suna kallonta, bata yarda sun haďa ido ba, drip ta xubawa idanu tana tambayar ya Mai jiki, Sa'eed ya amsa da jiki Alhamdulillah, ta maida hankalinta kan haďa masa magani, Sa'eed ya tashi yana fadin, Aboki is olmost tym, by 8 xn dawo, ya gyada Kai yana kallonsa kafin ya fice, Dr. Save a life.... taji ya faďa daga inda yake kwance, kusan faďuwa ta tashi yi, batasan meke damun patient ďin ta ba, hr lokacin bata tanka ba sai ma qoqarin yaqi da xuciyarta takeyi, ta juyo haďe da miqa masa magani ya karba, ta ďauko masa swan ta bashi hr lokacin bata kallesa ba shikuma Idanunsa akanta, bayan ya gama sha, ta duba file ďin sa yana da sauran allura uku, ta dafe goshinta da hannunta..... A duniya idan akwai abinda Deedah ya tsana allura, indai akan allura ne yana da rakin wannan, bai tsoron bindiga kamar yanda yake tsoronta.. Yana Ganin ta ďauko allura ya tashi xaune, wannan Karon fuskarsa a yamutse, Ummi bana son allura, na roqeki karki min, ta juyo da mamaki tana kallonsa Abinda ta gani a idanuwansa ya nuna mata yes he mean it, baya son allura, batayi mamaki ba cos tasha samun case irin Wannan, tayi far da ido bayan ta cire glass ďin idonta, Ni Kuma sai nayi ma allura, Iman not Ummi pls.... dai dai lokacin Merah ya shigo tare da Fauxiya a bayansa, Ta juya tana kallonsa bayan ta sanardashi abinda ke faruwa, Merah ya karbi allura, Haka mukayi fama dashi jiya, gashi namiji har namiji amma yana tsoron allura kibari xnyi masa.... So funny, ta soma dariya sosai ba kakkautawa Wanda rabonta da irin dariyar tun Mami na da rai, shi kansa Merah ta bashi mamaki bai taba xaton tana dariya haka ba, taja hannun Fauxiya suka fita, Daga inda take xaune take jiyo rigimarsu da Ahmed Wanda da kyar da suďin goshi yayi masa suna xaune Merah ya fito, Kinyi laifi likita, yiwa patient dariya, Am sorry bansan yanda xnyi bane.....ya fice ta tashi ta shiga ďakin, suna haďa ido ta ďauki wata dariya harda sa hannu tana rufe bakinta, Fauxiya bata San komai ba amma sai ta taya yayarta dariya Wanda ya janyo hankalin Deedah xuwa gareta Itama farace kamar fatyma sai dai tafi fatyma kyau sosai, ita yarinyar wacece ko yar'ta ce,nooo ai yaji jiya tace ita da qanwart..... tunaninsa ya Katse lokacin da yaji fauxie na faďin Anty meyasa kike dariya, tayi shiru tana faďin ba komai, Please tell me sister.... ta juyo tana kallonta cikin xare ido Nace babu menene... Fauxie tayi shiru tana kallonta ta juya tana faďin ki jirani Ina xuwa idan naxo ban same ki ba sai na dake ki Kuma baxan qara xuwa dake ba, Tana jin haka ta nemi guri ta xauna,ta juya ta fice, Idanunsa akan su suna haďa ido da ita tayi Saurin ďauke kanta cikin jin tsoronsa saboda raunin dake goshinsa, 'little girl..... ta juyo tana kallonsa, 'Your name...da kyar ta iya buďa bakinta 'Fauxiya Abdallah... ya gyada kansa, 'xo kiji Fauxiya, kamar baxata je ba ta matsa kaďan a tsorace, 'how old are you? Idanunta suka yi rau kamar xatayi kuka, '6yrs... Ya xare ido yana kallonta da mamaki, yanayin ta ya nuna a tsorace take dashi sai ya janyota xuwa jikinsa ya ďorata akan qafafunsa, da sannu ya riqa janta da Wasa harta saki jiki sosai dashi tana dariya hrda kwantawa a jikinsa, 'Ya sunanka.... 'Kice yayaaa, 'yaya xakaje dani inda mamin ka, ya girgixa kansa 'A'ah 'meyasa ? 'mamina tana duka sosai... 'to ni baxan je ba... 'kina so ki xauna dani, mu riqa wasa tare... ta gyada kai da sauri 'idan ummi taxo Kice ta aureni, 'Wacece ummi, yayi shiru kafin 'yace your sister... ta soma dariya tana kallonsa, 'ita ba Ummi sunan taba kace Anty Iman dai dai lokacin ta shigo,idanunta na sauka akansu, ta ďaure fuska tana kallon Fauxiya, yanayinta ya sanyata saukowa a jikinsa da sauri tana faďin, Anty shine ya ďorani, Wai sunansa yaya.. 'kisa takalmi kixo muje inba haka ba xn tafi na barki anan, ta sanya takalmin da sauri tana faďin, 'Anty Wai inji yaya ki aure sa, yace ku..... ta katseta cikin tsawa.. 'shut up Fauxiya... tayi shiru tana kallonsa kafin ta maida kallonta gareta, da qarfi ta fisgi hannunta suka fice, tabe bakinsa kawai yayi ya maida Idanunsa ya lumshe... BABANA DA MIJINA ©Fertymerh Xarah 💞 8 Tun bayan barin ta asibitin bata qara xiyartar ďakin da aka kwantar da shi ba, sai ma ta damqawa Dr Fulani file ďinsa, Iya damuwa Ahmed yana ciki, he mean it yana sonta, aurenta yake son yi, duk da baisan ita ko Wacece ba amma ta kwanta masa a xuciya, Ranar da aka sallamesa yaje nemanta, Dr Ummi.. Dr Ummi nobody knows her... ba Wanda yasan sunan Acikin likitoci, hassalima ko a nurse sai dai ummu an kaishi inda take yace ba Ita ba..... Real name ďinta ne baxai iya faďi ba saboda nauyin sunan a bakinsa, amma ya kamaninta yake? 'Yace ita farace, doguwa Mai matsaikaicin jiki, tana da tawwadar Allah a fuska Kuma tana da qanwa Fauxiya, Dr Umayma tayi murmushi sanin ko wacece, 'Sunanta fatyma not Ummi, 'I know doctor, sunan ne baxan iya faďa ba yana da matuqar muhimmanci a guna... 'duk da haka Ahmad, idan xaka shekara anan asibitin kana Ummi baxaka taba samun ta ba, murmushi yayi bayan ya kishingiďa.... Alhaji Abdallah abubuwa sun soma damunsa tun lokacin da matsafarsu ta nemi fatyma tayi aure suna son jariri daga gareta, sosai ya shiga tashin hankali sanin fatyma bata da wani tsayayye a ynxu, Sanda ya tunkareta da Mgnr ya ga damuwa qarara a fuskarta Wanda ya Sanya baiji daďi ba, 'ba dan komai nakeso kiyi aure ba fatyma sai dan ni babban mutum ne ďan siyasa da mutane suke kallo da daraja, da yawa mutane sun San matata ta mutu bani da aure inada babbar ďiya kamar ki a gida xa'a soma xargin na hana maki aure, 'bayan Wannan fatyma aure daraja ne dashi, ni kaina xanji daďi idan kikayi aure Inaso nasami jikoki daga gareki, ballantana ma baxamu rabu ba xamuyi rayuwa a gida ďaya dake, wancan gidan naki ne halaq malaq aciki xaki xauna da mijinki da yaranki...... ta goge hawayen fuskarta 'na fahimceka babana, abinda kake so Inaso dan na farantama kamar ynda kake min, nayi ma alqawari xn fitar da miji Acikin kwanankinan, ya faďaďa murmushinsa cikin jin daďi ya soma sanya mata albarka.... Bayan tafiyarta ya faďa cikin tunani, shikenan rayuwar yar'sa ta shiga cikin hatsari kenan, ita baxata taba haihuwa ba Kamar ynda sima ta faďa duk tayi ciki xasu ďauke yaron da haka xai cimma burinsa na xama shugaban qasa, hawaye suka xubo wannan wace irin rayuwace..... Bayan barinta gurin ya shiga cikin tsananin tashin hankali, batasan wa xata fitar ba tsakanin manemanta, gwargwado kowa nayi mata soyayyar gsky sai dai batasan meyasa xuciyarta tafi karkata da Ahmed ba, a kullum sai yaje asibiti ya ganta kafin yaje gun aiki, har nan gida yake xuwa su dade tare da Fauxiya, akwai abubuwa da yawa data duba Wanda yasa ta xabi Ahmed a matsayin mijin aurenta, He is happy too sanda yaji umminsa ta amince xata aure sa, Cikin qanqanin lokaci soyayyarsu tayi nisa sukayi matuqar shaquwa da juna, baba ya aminta dashi bayan dogon bincike da akayi akansa wurin aiki, basu gane komai ba kasancewar abokansa na hulda daban, na gurin aiki daban sai suka bashi shaidar gsky.... Bayan auren su ne abubuwa suka soma yi mata yawa tun daga kan mahaifinta da mijinta, Mahaifinta baxata Kai Kukan mijinta ya duba mata ba saboda ba maxauna bane, idan ma yana gari tor baxata ganshi ba sai cikin dare akwai wani ďakinsa da yake shiga Wanda ba Wanda ya taba shiga acikinsa, idan yana ciki ba Wanda ya isa ya shiga haka ma baxai fito daga ciki ba sai cikin dare da jajjayen kaya wani sa'in ma da abokansa suke shiga, Mijinta Kuma idan ya fita aiki tun safe baya dawowa sai marece, daga nan xaisa kai ya fice baxai dawo ba sai cikin dare Wai yaje training ďin kwallo, can you imagine? Sau biyu Ina samun ciki yana xubewa Wanda na rasa dalilin haka a matsayina na likita, nayi bincike iya bincike na kasa samun dalili komai nawa normal, Inaso na sami babana Kan Mgnr koxai taimakamin da wani abu amma baxai saurareni ba cos he is busy, mijina ma yakan nuna damuwarsa idan ya xube bayan kwana biyu kuma shikenan xai bar mgnr,ban San waxan kaiwa kukana ba,waxan gayawa damuwata ya taimakeni da shawara kodan mijina... Na kasa samun soyayyar mijina, ba kulawa kullum busy busy shine maganarsa a duk lokacin danayi masa qorafi, na kasa sabawa da wannan hali na *babana da mijina* Kuma ban taba xarginsu ba ko bincike akansu, duk da Allah s.w.a yace LA TAJASSASU WALA YAGTABBA ADUKUM BAADAD kada kuyi bincike kuma kada sashenku yariqa cin wani sashe ma'ana kada wasu mutane su xauna gulmar wasu mutane..... Shine Asalin labarin......... BABANA DA MIJINA ©Fertymerh Xarah 💞 9 Dawowa daga labari ~~~ Tafito daga toilet bayan ta ďauro arwalla, inda yake ma bata kalla ba ta sanya hijab ďinta ta fara sallah, Deedah na daga kwance yana kallonta sai ya sami kansa da saukowa ya shiga toilet yayi arwalla ya bi ta... Bayan wani lokaci sun gama ta tashi batare da ta cire hijab ďin ba taje ta kwanta haďe da juya masa baya, jikinsa a sanyaye ya tashi yayi light off yabi bayanta ya kwanta haďe da juyo da Ita, she is crying.... 'why Iman, meke faruwa? Ko motsi batayi ba illa hawaye dake qara xuba a idanuwanta... Ya cire mata hijabin haďe da qanqameta, 'I hurt my Iman, kiyi haquri akan Wanda kike,i hurt you and I will change, I promise to change Iman ya qara matseta jikinsa, har lokacin bata tanka ba illa qoqarin kwace jikinta da take yi, Ya tashi xaune yana kallonta, 'why ol dis...., me Kuma nayi Yanxu, nayi tunanin mun gama mgn dake tun a falo, ta tashi tana kallonsa sai Kuma taji ta kasa furta masa komai saboda bacin rai da damuwa, he knows it yasan damuwarta duk baxai wuce fitar dare da rashin bata haqqinta ba, tor ya xaiyi shi kansa a ynxu baya so yana nadamar xama barawo bayan ga aikinsa, idan yayi yunqurin barin aikin oga nas xai ďauki mummunan mataki akansa kamar yanda ya faďa, Kallonta yake yana observing da ido da xuciya, gaba ďaya yanayinta ya sauya ya nuna wata mace dake axabtuwa da soyayya da sha'awa Mai yawa, Amma kawaicinta da kau da kai ya rinjayi komai, tana haquri dashi shi kansa ya Shaida, ba kowace mace xata xauna da miji haka ba shiyasa yake qara son ta, ya riqo hannunta Idanunsa cikin nata, Baxan gaji da baki haquri ba, ki yafemin Iman, xnyi qoqari na rage fitar I promise you..... * Washe gari bayan ta tashi daga barci tayi miqa a hankali tare da koro addua, _Alhamdulillahil lazee ahyana ba'adama amatana wa ilaihir nushour,_ ta miqa hannu side ďin Ahmed taji sa wayam, ta buďe idanuwanta, She is late, da sauri ta diro ta faďa toilet inda ta same sa ciki yana wanka, A tare suka fito kowane ďaure da towel, ita iya cinyoyinta shi Kuma iya qugunsa, jikine dashi na Manya Kuma qasaitattun maza, dogo ne sosai Mai kyau sura ta ko'ina, a tare suke shirinsu, qoqarinsu kada suyi lattin fita, Wardrobe ta buďe ta ďauko mashi baqaqen Spanish suit Mai haďe da farin tie, ta ajiye masa akan gado kana ta soma shirinta cikin riga da zani na Atampha ta ďora labcoat akai da ďan qaramin gyale tayi rolling, idanunta sanye da farin glass, lokaci ďaya suka gama shirinsu, yaja dogon hancinta in appreciation ďin irin kulawar da take mishi, 'kinyi kyau dear Allah ya barmin ke, murmushi tayi haďe da manna mishi kyakkyawar sumba a qirji ya qara rungumeta, Yana riqe da hannunta suka sauko step dai dai lokacin da Fauxiya da mai Kula da Ita suka fito tana ďauke da qatuwar school bag ďin ta, murmushi tayi lokacin da suka haďa ido da Ahmed, 'morning sister... taje da gudu ta rungumeshi tana fadin 'morning yaya... ya ďauke ta yana murmushi haďe da Jan hancinta, 'morning my baby.... Dijeh ta gaidasu kana tayi waje da jakar Fauxiya, A tare suka xauna akan dining table, Fauxiya baxata tsaya guri ďaya ba, idan taci na wannan ta dawo taci na wannan da haka hr suka kammala suka fito su uku a tare, Driver na jiran Fauxiya kai tsaye ta shiga motar tana ďaga masu hannu suma suna mata bye bye, suka kalli juna haďe da yin murmushi ta shiga motar ta shima ya shiga tasa, Tana gaba yana biye da Ita hr suka xo FMC birnin kebbi, sai da yaga shigarta kana ya juya tasa motar xuwa first bank dama kullum sai ya rakata yaga shigarta asibiti yake tafiyarshi. BABANA DA MIJINA ©fertymerh Xarah 💞 10 Alhaji Abdallah xaune a qasaitaccen falon sa duk abin duniya ya dame sa ya rasa inda xai tsoma ransa yaji daďi, Sau biyu yana ďaukar cikinta yana bayarwa ga matsafarsu Gashi wani bincike ya nuna Iman tana ďauke da wani cikin Wanda daga ita hr Ahmed basu San dashi ba, Sima ta nuna tana son cikin, tabbas Wannan ma sai ya xube, shin haka rayuwar yar'sa xata kasance bata haihuwa da tasami ciki ya xubar? Yayi wa kansa wannan tambayar, 'Nooooooo ya faďa a hankali gudun securities ďinsa su jiyosa, Idanunsa sunyi jawur har jijiyoyin kansa sun fito goshinsa raďau raďau, Yana son Fatyma yana tsoron wani abu ya sameta musamman a mahaifarta amma ya xaiyi mecece mafita? Yayi shiru Idanunsa suna fitar da kwalla lokacin dayaji muryar sima na faďin, 'cikin mukeso Kuma dole abamu idan ba haka xamu ďauki rayuwarta gaba ki ďaya mu baka dukiya da Abinda kake so na duniya..... Aka kyalkyace da dariya, yayi firgigit daga tunanin da yake yana kallon falon dariyarta ce kawai yakeji ta ko ina......, * Fitowar ta kenan daga ďakin haihuwa, yau a gajiye take sosai tunda taxo bata xauna ba, ga Jiri da Xaxxabi da take ji Wanda baida nasaba da yunwa anata tunanin kenan, Ta sami gu ta xauna inda ta sami Dr Fulani, ta dafe goshinta da hannuwanta biyu, Successful doctor..... yanda suke kiranta idan suna tsokanarta cos da wuya ta karbi haihuwa da hannunta yaron ya mutu ko uwar sabanin wasu likitocin da har jima yaro sukeyi gurin haihuwa, a yanda take a natse haka ma take aikinta a natse shiyasa nurses da yawa suke son aiki da Ita, ba ďaure fuska ko Wulaqanci kowa faram faram take dashi bama kamar patient ďin, 'ya akayi Dr fatyma...cewar Fulani tana kallonta, Ta ďan ja guntun tsaki kafin ta janye hannunta a goshinta, 'bansan meke damuna ba yunwa ko gajiya... Fulani tace 'harda damuwa fatyma, tor ya xakiyi da yanda Allah ya tsara miki rayuwarki idan lokaci yayi xaki ganki kin haihuwa kidaina sa damuwa a xuciyarki, Iman ta girgixa kanta kafin kace me hawaye sun soma xubo mata Wanda hankalin Fulani ya tashi... 'ba haihuwa bace damuwa ta Fulani, damuwata *babana da mijina*, bansan ya xanyi da rayuwata ba, ta fashe da kuka mai tsanani haďe da maida kanta jikin table tana kuka sosai Mai tsuma xuciya, 'innalillahi wa inna ilaihir raji'un shine Abinda Fulani ke furtawa jikinta na soma rawa tunda suke da Iman bata taba ganin hawayen ta ba ballantana irin Wannan Kukan tabbas ko menene babban al'amari ne.... Ta dawo kusa da ita ta xauna haďe da dafata, 'meyasa fatyma, wannan kuka haka komai yayi tsanani maganinsa Allah, Ta tsaida Kukan da take ta hanyar goge hawayen fuskarta, ta buďe Jakarta ta ciro hijabinta ta warware ta sanya kana ta cire labcoat ďinta da gyalenta ta maida a jaka ta tashi tana kallon Fulani, 'xanje gida likita sai Kuma gobe idan Allah yasa muna da rabon gani. Fulani ta tashi tana kallonta, 'baxaki gayamin damuwar ki ba? Fatyma tayi murmushi sosai tana kallonta Kamar wacce bata da damuwa, 'ba komai Fulani, idan ma da akwai xn sanardake, ta juya ta fice Fulani ta bita da ido tasan ta da Xurfin ciki Dama baxata gayamata damuwarta ba amma meyasa babanta da mijinta ne damuwarta, Tasan babanta Mai kudin gaske ne Kuma ďan siyasa ita shaidace akan yanda yake sonta ita da Fauxiya hakama mijinta tasan yana matuqar sonta tor menene abin damuwa akansu, meyasa take xubar da hawaye akansu, Allah ne masanin gaibu acewar xuciyarta....... Tana yin parking Fauxiya ta fito da gudu da tedy a hannunta, tana rufe motar taji ta rungumeta ta baya, ta juya da kyar tana kallonta, 'oh Fauxiya ai sai ki kadani... 'anty kinyi kuka ne, meyasa ki kuka tambayar fauxie taji daga Sama, ta riqa hannunta suka soma tafiya tana faďin, 'idanuna ke ciwo, kinci abinci? ta gyada Kai tana kallonta, 'Anty an bani assignment a skul, 'shikenan anjima xamuyi tare.... Wanka tayi, tana yin sallah ta xube nan ta kwanta saboda Xaxxabi dake damunta, Fauxiya ta shigo da plate ďin abinci a hannunta kai tsaye inda take kwance ta nufa, ta tsugunna tana faďin... 'Anty ki tashi kici abinci, Kindawo baki ci abinci ba shine na ďebo maki... Ta buďe idanuwanta tana kallon fauxie sai taga duk ta damu, plate ďin ta kalla, nan take xuciyarta na soma tashi, da sauri ta tashi ta nufi toilet tana kwararo amai, hakan Kuwa ya rikita fauxie ta sameta toilet ta riqa ďaya hannunta tana yi mata sannu, As a professional doctor kai tsaye ta gano halin da take, cikine da Ita, is she happy or not? bata sani ba, sai ta soma hawaye a fakaice kada fauxie ta ganta a Ranta Kuma addua take Allah ya bar mata cikin.... Babana da mijina ©fertymerh Xarah 11. And. 12 Yinin ranar duk a kwance tayi sa, Fauxiya na tare da Ita, sallah kawai ke tadata daga inda take kwance, Bayan magrib Deedah ya shigo gidan, yayi mamakin rashin samunta a falo, yaje ďakin fauxie bata nan sai ya haura sama, Da Sallama ya shiga ďakin, Iman tayi barci Fauxiya ce ta amsa sallamar tana xaune kusa da ita da drawing book akan qafafunta hannunta riqe da pencil, da murmushi take kallonsa Wanda ya bayyanar da farincikin ganinsa, 'welcome brother.... 'thanks my baby, ya ajiye kayan hannunsa yana faďin.. 'drawing kike yi haka, me kike xanawa.. tayi murmushi tana kallon xanen kafin ta dubesa, 'A house, uncle yace mu xana gida it's an assignment, sister ba lfy shine baxata min ba, sai da gabansa na faďi 'Iman ba lfy, meya sameta, ya soma taba jikinta, Fauxiya ta tashi da littafi a hannunta ta fita tana faďin Ina xuwa yaya xakamin assignment ďin... bai tankata ba ya tallafo kan Iman, jikinta xafi rau ta buďe idanuwanta tana kallonsa kafin ta maidasu ruf, 'meke damunki,baki lfy shine baki Kira kin sanardani ba, jin bata tankaba ya ďauketa ya ďora ta akan gado, 'kinsha magani? Ta girgixa kanta, 'tor meyasa, Ana ciwo ba magani, nan ma tayi shiru, wayarsa ta ďauki qara, oga nas ya gani a rubuce kamar baxai ďauka ba sai Kuma ya Kara a kunnesa, 'shikenan gani xuwa, shine kawai abinda taji ya faďa batare daya qara bi ta kanta ba yasa kai ya fice, ta bisa da idanu tana kallonsa hawaye na xubo mata, Fauxie na xaune falo taga fitowarsa, ta tashi da sauri ta haura sama da littafinta a hannunta, Ganin fatyma na kuka yasanyata rau rau da idanu Kamar xatayi kuka, 'Anty meyasa kike kuka? ta soma share mata hawaye, 'anty kince idan mutum bai lfy baya kuka kuma abinci yake ci, kina kuka kinqi cin abinci inje inkira baba ya kaiki asibiti, ta girgixa kanta, 'baba bai dawo ba, kinyi assignment ďin? ta girgixa kanta, 'A'a sai brother ya dawo xamuyi tare, fatyma ta tashi xaune da kyar kanta har wani nauyi yake mata, 'naji kamar ana kiran sallar isha'i idan nayi sallah xn maki, kin mayi magrib Kuwa Fauxiya? ta tunxure bakinta, 'A'ah anty... 'meyasa, wai ke meyasa bakyason sallah ne, kullum sai nace kije kiyi sallah, ta qara shagwabe fuska 'Anty ai ni qaramace sai naxama babba xanyi sallah, ta ďaure fuska sosai tana kallonta, 'see you, shekara takwas ne baki girma, kitashi kije kiyi sallah tun ban dake kiba marar wayau, ta tashi tana hawaye sosai ta cillar da pencil ďin hannunta, fatyma tabi bayanta sanin halinta ita batasan meyasa yarinyar batason sallah ba Kamar wata tababbiya, A tare sukayo arwalla suka fito... ko kafin fatyma ta gama sallah ita harta gama magrib da isha'i, ai Kuwa tana sallamewa taja kunnenta, 'kiji tsoron Allah Fauxiya, baa wasa da sallah tun kina qanqanuwar ki bakyason sallah ai da matsala, gayamin dame dame kike karantawa a sallar, idanunta taf da hawaye take kallonta, 'Anty fatiha da nas nayi, 'Kice Wlhy.. 'wallahi anty... ta saki kunnenta tana kallonta, 'duk mai wasa da sallah wuta xa'a sanyashi baxai shiga aljannah ba, kuma Duk Wanda bayason sallah xai shiga wuta, bakisan banbancinki da Anty John da uncle obi sallah ba, ko kingansu suna sallah? ta girgixa kanta, Christian basu sallah sai musulmi, tell me ke Wacece... 'A Muslim.... yauwa babyn brother sai Kiriqa sallah kinji... ta gyada Kai tana kallonta cikin gamsuwa... 'Anty ni xan shiga aljanna, ke xaki shiga aljanna amma baba baxai shiga aljanna ba..... da sauri ta ďago tana kallonta cikin tsananin mamaki, 'meyasa? 'shi baba baya sallah, ni bana gani yanayi, anty yana sa wani kaya ya shiga ďaki Inaje shiga ya hanani.. 'karna qara ji a bakinki, baba xai shiga aljanna yana sallah mana, inbanda abinki xai shiga ďaki xaki bisa... 'Amma anty ai.... 'shut up... ta katseta, bana son surutunki marar amfani, ta janyo abinci tana ci kafin kace me tasoma kwarara amai a gun, Fauxiya na kanta tana yi mata sannu, sosai ta jigata tace 'kiramin Adama ta gyara gurin nan, ta fita da gudu sai gata ta dawo da adama sai sannu suke mata... Har 12 Deedah bai dawo ba hakama mahaifinta, Fauxiya ce ta kasa runtsawa ganin halin da yayarta take ciki yayi xaune tana kallonta, 'Fauxiya je inda dijeh ta haďa maki tea ki kawo min, ta sauka da gudu ta fita bata jima ba sai gata da cup a hannunta ta hau gadon tana faďin, 'anty kisha magani irin Wanda kike bani, 'A'ah ni banason magani... Fauxiya taje ta ďauko irin Wanda tasan tana bata Inbata lfy, panadol 'Pls anty kisha... ganin Fauxiya ta damu sosai ta karba tasha da swan kafin ta ďora tea akai, sai da ya kwanta mata kana ta janyo Fauxiya a jikinta, 'xo ki kwanta nasan kina jin barci, Gobe ba Skul idan naji sauqi xuwa Sunday xn maki assignment ďin, Fauxiya ta kwanta a jikinta tana murmushi, Ta jima sosai kafin barci ya ďauketa, kallonta take cike da tausayin kansu, ba kulawar uba ballantana ta miji, ta tabbata da Mami na da rai baxata barta haka ba, ta soma hawaye sosai haďe da qanqameta Fauxiya jikinta.... Babana da mijina ©Fertymerh Xarah 12 Har aka soma kiraye kirayen sallar asuba idanunta biyu ta kasa rumtsawa, yanda taga rana haka taga dare Deedah bai dawo ba... Qarar motar mahaifinta taji shima kenan ba gidan ya kwana ba, tor a Ina ya kwana tambayar danayi wa kaina lokacin dana ďaga labulen window ina kallonsa dai dai lokacin ya fito cikin motarsa sai faman waige waige yake kamar wani marar gsky, Wannan Karon xuciyata ta kasa yardamin, na kasa amincewa wannan hali na *babana da mijina*,tabbas akwai wani abu boye tsakanin su, duk da xato xunubi ne Wannan Karon ina xarginsu, ina xargin *babana da mijina* akan wannan fitar dare, ina suke xuwa, me suke yi a dare ba wani meeting da training a tsakanin Su tabbas akwai wani babban al'amari da suke boyemin Wanda ya kamata na sanya ido akai.... ta sauke ajiyar xuciya haďe da Sakin labulen, ta sunkuci fauxie tayi toilet da ita, da kyar ta samu tayi arwalla sai mita take, 'anty ina barci kin tada ni... 'sallah xakiyi idan kin gama sai ki koma barcin.... tayi shiru idanunta a lumshe, A tare sukayi sallar Fauxiya ta koma ta kwanta Iman Kuwa tana xaune inda tayi sallah da charbi a hannunta, 'Anty karki manta ki tadani inje islamiya kada inyi latti.... taji Mgnr ta daga Sama, ta juya tana kallonta idanunta a lumshe take mgnr, 'kinji Anty... 'Naji.... 7:30 Dijeh ta gama shirya ta cikin uniform ďin islamiya, 8 suke xuwa, Iman ta sauko da qaton hijab a jikinta hr lokacin idan ka kalleta xaka gani da sauran Xaxxabi a jikinta, 'kinyi breakfast ďin ne? ta girgixa kanta, 'kicire hijab ďin kada ki bata shi da tea dama bakinki kamar mai yo-yo, tana dariya ta cire hijabin, taja hannunta suka nufi dining ďa kanta ta haďa mata tea ta xuba mata arish da kwai, 'Anty ni bana son arish Kuma sai Dana gayawa lami kartayi.... Iman ta soma buďa sauran dishes ďin tana faďin 'sai me kike so Auta, 'qosai... 'qosai Kuma? Tea da qosai xaki haďa, ta gyada Kai tana kallonta, 'tor Gashi ai ba abin faďa bane, inaji arish ďin saboda ni tayi ni baxan iya cin komai a Yanxu ba, ta xuba mata a plate dai dai lokacin Deedah ya shigo da sauri yanayinsa xai tabbatar ma bai cikin hayyacinsa burinsa yaga umminsa a halin ynxu yana shigowa ya tsinkayota xaune akan dinning ita da fauxie, Iman taji shigowar sa amma tamkar bata San da shigowarsa ba, kallonsa Fauxiya tayi fuskarta ba walwala kamar yanda ta saba taryarsa, 'Mrng yaya ta faďa idanunta akan tea.. Sosai yayi mamakin ganin yanda fauxie tayi masa to nata Mai sauqine akan yanda matar tasa ta ďaure sosai.. 'ya jiki Iman... Ke Mai karatu idan kin tanka ta tanka, wani qololo ya taso ya tokare xuciyarta suna haka sai ga Baban ya shigo cikin shirinsa da alama xai bar qasar, Deedah ya juya yana gaidashi cikin girmamawa, bayan gaisuwa da fatyma tayi masa bata qara kallonsa ba, Fauxiya ma tashi tayi da hijab ďinta a hannunta ta sanya haďe da nuna mata qur'anin ta, 'Anty tuna min farkon surah... ta gayamata tayi murmushi ta sumbaceta a goshi ta fice tana fadin sai na dawo anty, batare da ta waiwayi kowa gurin ba ta fice da gudu, 'A dawo lfy Auta, baba yabita da kallo cike da mamakin halin ko inkula da fauxie ta nuna akansa yau, meke faruwa ya tambayi kansa, itama ta tashi da nufin barin falon baba ya tsaidata, fuskarsa ta nuna damuwa sosai ya qarasa shigowa falon escort ďinsa nadaga bakin qofar falon suna jiran sa, 'Fatyma me akayi, meyasa naga wannan Canjin a fuskarku dan Allah ki gayamin damuwarki ki gayamin abinda ke damunki, 'ba komai baba, 'A'ah fatyma ki gayamin damuwarki, ko kuďi kike so.... ta ďago da tsananin mamaki tana kallonsa hawaye sun taru a idanuwanta, 'kuďi basa birgeni a Yanxu baba, bana buqatar kuďi, kulawarka nakeso nida qanwata xamu samu? 'har akwai wata kulawa da xan baki a Yanxu ne bayan ga mijinki, karki manta nifa ďan siyasa ne da mutane ke buqatata a kowane lokaci, sau nawa xan gaya miki haka fatyma, so kike nazo na xauna dake alhali Ga mijinki ko xn bar mutanena nadawo gareki ne? A Yanxu xuciyarta tayi taushi abubuwa sun soma yi mata yawa gab take da kamuwa da ciwon xuciya duk da bata ďebe tsammani ga hawan jini a tare da Ita a ynxu, 'baba laifine idan ka xauna damu ka tambayi damuwar mu mun gayama, ba danni ba kodan Fauxiya daya kamata ta taso cikin soyayyar mahaifi tunda ta rasa uwa, ba haka Mami ke mana ba baba, kuka take sosai, ka nuna mutane sun fi mu xaka iya sauraren matsalar wasu banda yaran da ka haifa muma munada haqqi akanka, Idan da rana kana tare da mutane da dare fa ko sau ďaya ne acikin sati baba, amma sai mu share fiye da wata ďaya bamu sanyaka a ido ba alhali muna a gida ďaya, baxaka waiwaye mu ba sai dai hange daga nesa.... ya katseta.. Enough fatyma sai Yanxu nagano dalilin dayasa Fauxiya bata gaidani ba, wato kina so ki raba tsakanin ya da mahaifi, kina cusa mata mugayen hali a xuciya dan ta tsaneni ko, kinaso ki butulce min duk sati bana tura maki kuďi a account ne..... Sosai kalamansa sun raxanata Kuma sun bata mata rai har batasan lokacin da tayi masa tsawa ba, Kariqe Kuďin bama so baba, aikina ma ya wadatar, daga kai har Ahmed bana buqatar Kuďin ku tunda dasu kuke taqama akan nida qanwata...... bata kai ga qarasa Mgnr ta ba taji saukar Mari a kuncinta, Wannan shine Karo na farko daya soma Dora hannunsa Akanta tunda ya haifeta bama itaba bai taba dukan yaransa ba wannan ma bacin rai ne, Bangaren fatyma Kuwa batayi mamaki ba ko nuna damuwa Dan ya mareta saboda a ynxu ta riga tasanya a xuciyarta baya qaunarsu Kuma bakinta ya kasa mutu.... 'kome xaka min baba dai dai ne amma Ina so ka sani nida Fauxiya a halin Yanxu bama buqatar Kuďin ka idan har baxaka iya xama damu kasanya mu....kuka yaci qarfinta ta juya ta hau step tana kuka sosai abinka ga farar mace fuskar har tayi jawur, Sosai hankalin Deedah da Baban ya tashi, ya juya xai bita baba ya riqo hannunsa, 'ka riqe sirrina a yau da kasani, ina son Faty fiye da raina wannan ma tsautsayi ne, ya juya ya fice jikinsa a sanyaye... _wane sirri ne Wannan?_ BABANA DA MIJINA ©Fertymerh Xarah 13 and 14 Dedicated dis page to Maryam Kwaise & kdeey Tana shiga ďakin ta faďa Kan gado tana kuka, kuka take sosai fiye da minti biyar hr lokacin tana jiwo muryar mahaifinta da mijinta amma batasan me suke mgn akai ba, ta tashi da kyar ta shiga toilet, Fitowar ta tayi dai dai da shigowarsa ďakin, Idanunsa akanta tsananin son ta da tausayinta ya mamaye xuciyarsa musamman yau da yasan ko Waye mahaifinta, yaga mahaifinta dumu dumu cikin shigar matsafa shiyasa yace ya boye sirrinsa ga yar'sa, A sanyaye ya qarasa jikin bango ya jingina jikinsa har rawa yake, 'Salihar mace kamar Iman, mai haquri da tawakkali batayi dacen uba da miji ba, mahaifinta matsafi ni mijinta barawo, kwallah ta taru a idanuwansa yayi Saurin sharewa, Kwanciya tayi batare da ta Kalle sa ba, yaje ya xauna a kusa da ita, 'Iman K....... tayi Saurin katsesa, 'enough Pls Deedah kada ka dameni, ka riqe kalamanka bana son ji, haquri ne nagaji da ji, ta tashi fuuuu ta fito daga ďakin, kai tsaye ďakin fauxie ta nufa tayi kwanciyarta..... 2 days~ Har lokacin Ahmed ya kasa samun ta, taqi ta sauko akan fushin da take dashi, babban tashin hankalinsa a ynxu ranar da duk ta gano ko shi Waye, ya furxar da iska daga bakinsa yana kallonta dawowarsa kenan daga aiki, yau sai dai ayi ta taqare ya gaji da wannan fushin Nata, Yayi switching wayarsa Kada akirasa, ďakin su ya nufa fauxie tabi bayansa, 'yaya ka dawo baka siyo min komai ba yau Kuma baba bayanan, 'na manta gobe xnje dake na siyo maki, meya hana miki barci yau haka? ta dubi Iman ta dake qoqarin rufe falon kafin ta maida kallonta garesa, 'anty ta tsaidani, ta koyamin karatuna inba haka ba gobe malamin islamiyar mu xai min duka, 'Fyn an gud, sister ta kyauta, ya soma taka step ďin yana riqe da hannunta, 'yaya yau baxakaje training bane, ya juyo yana kallonta da mamaki ta tsareshi da idanuwa tana jiran amsa, ya ďauke kansa da kyar ya iya amsa mata 'baxan je ba, 'meyasa ta qara tambayarsa? 'saboda yau baxaa yi ba, 'amma yaya kai baa nuna ka a tv kana ball why? Wannan Karon bai amsata ba ya nufi dakinta da Ita, dijeh harta kwanta sai dai batayi barci ba, 'ki sauya mata kayanta xuwa na barci Kuma ki tabbatar da kunyi addua kafin ku kwanta, 'tor yallabai mungode, ya dubi fauxie 'night baby.... Murmushi tayi tana kallonsa, 'night too.... Ya juya ya fice, wanka yayi ya fito ya shirya cikin kayan barci har lokacin Iman bata kwanta ba tana xaune bakin gado da wani file a hannunta baisan kona miye ba amma fuskarta ba walwala ya lura fushi takeyi dashi sosai, Baya son duk wani abu da xai bata ranta fitar dare ce xai rage ya bata irin kulawar da takeso, don haka yau bayajin xai jurewa fushinta domin ta fushinta yana da weakness sosai he truly loves his wife, Sai ya qarasa gabanta ya tsugunna haďe da riqo hannunta duka biyu ya haďa danashi, ya langabar da kansa idanuwansa sun juye sun rikiďe ja, 'Am sorry Iman, na kasance mai laifi a gurinki ina neman afuwarki kiyi haquri, tayi shiru bata tanka ba kuma bata kallesa ba, 'fitar dare ce, xn rage sosai fiye da tunaninki, bana so ki xargeni da aikata alfasha, mijinki salihi ne bayan kwallo ba abin da nake fita yi, ina so ki kyautata xato mai kyau agareni, xn cigaba da xama dake dan farin cikin ki ina sonki Iman.... ya faďa haďe da miqa tafin hannunsa tayi masa kiss, idan tayi yasan ta haqura idan batayi ba kuma bata haqura ba, Ta Cira Kai ta dubeshi a hankali sai ya bata tausayi dan Numfashi kanshi a wahale yake furzar dashi, sauri da sauri, Amma Jan aji irin namu na mata sai ta qara tsuke fuskarta ta balla mishi harara wadda inka lura ba komai ne acikinta ba face tsananin son mijinta, xuciya da gangar jiki ma sun Shaida... Irin kallon da take masa yasan ta haqura, yasan halin kayanshi ya qara langabar da kansa cikin shigar tausayi haďe da qara miqa mata tafin hannunsa, Ba musu ta sumbaci hannun tana murmushi, ya ja dogon hancinta bayan ya xagaye hannuwansa a qugunta yana kallonta, Wannan file ďin a ajiye shi ayi aikin lada wify..... [3/29, 1:23 PM] Mairosss: BABANA DA MIJINA ©Fertymerh Xarah 14 Tun daga lokacin ya rage fita sosai wani sa'in sai tayi barci ya saďaďa ya fice, Wani lokacin bata sanin fitarsa da dawowarsa, sai ta dawo cikin walwalarta ta soma samun sauqin mijinta saura mahaifinta, Akwai wani lokaci suna xaune ita da fauxie suna kallon wani film na matsafa suna sanye da kaya jajjaye, buďar bakin fauxie sai cewa tayi.. 'lah anty duba irin kayan baba, fatyma ta ďan dubeta, 'ke shirmenki akan kowa ne harda baba baki bari ba, kinsan ma'anar su kuwa..... fauxie ta girgixa kanta, 'masu shan jini ke sanya irin su, kinga Allah ya tsari baba ko.... Fauxie ta gyada Kai sai dai tayi shiru tamkar wata Mai naxari, ta buďe baki xatayi mgn, Iman tace 'ďauko min wayana ďaki da hijab ďina kixo ki rakani maqota anyi rasuwa, ta tashi da sauri ta fice bata jima ba sai gata ta dawo, 'Amma bada tedy xaki bini gidan gaisuwa ba ko? ta tunxuro baki kafin ta cillata Kan sofa, ta qagu su fita tana son yawo a rayuwarta, fatyma ta tashi suka fice, Gidan talakawa ne sosai masu buqata, sun rasa Mai gidan sai matar da ya bari da yara biyar, suna dawowa Iman ta aika masu da buhun Shinkafa da dubu biyar akai, sosai sunji daďi kuma sunyi godiya... Tun lokacin da ta fahimci cikine da Ita take kaffa kaffa dashi tare da roqon Allah ya barmata shi, shima Deedah Wannan Karon ya dage da addua yana son haihuwa.... Tafiya ta kamasu xuwa skt, inda xasuyi operation a wani gida, a motar haya suka tafi su uku ne sai sauran passengers, Akwai wani mutum dake cikin motar tunda ya shiga bashi da aiki sai xagin barayi shida na kusa dashi, su Deedah na jinsa, Driver ke tambayarsa meyasa kake xaginsu haka, 'bari driver basu min komai ba amma suna ban haushi, ai dana haifi barawo gwanda na haifi shege, wai akwai hasararra uwa a duniya kamar wacce ta haifi barawo, sai da gaban Ahmed na faďi xuciyarsa na bugawa tunowa da Inna, ya fakaici ido yana kallon sauran abokansa suma ransu a bace, Suka cigaba da Mgnr su, ďayan yace ai ina haihuwar barawo kashe shi xnyi dan baida amfani, gwanda ďan siyasa da barawo, Driver yace baxan haifi ďa in kashe shi ba sai dai na nema masu shariya, wani yanada dalilin xama barawo kawai Allah ya shiryesu yasa su daina.... Ba Wanda yace Amin, sun iso gwadabawa suka sauke wannan mutumin da abokinsa, wadanda ke tare da Deedah suma suka ce nan xasu sauka, sai akabar Deedah da driver kawai, Su kuma suka bi bayan wancan mutumin ba tare da yasani ba sai da suka ga gidansa tukunna suka shiga motar kasuwa, Ahmed Kuwa sai da sukayi nisa a jeji kana ya tsaida driver tare da fito da bindigarsa sosai ya tsorata cikinsa ya ďauki kuka jikin sa har rawa yake, 'kayi haquri bansan Menayi ba, 'banace kayi wani abu tunda baka xageni ba, ni barawo ne ka min adduar shiriya naji daďi, sauran dakaga sun fita yan uwana ne sunbi waďancan mutane suga gidansu, ga wannan(ya bashi dubu hamsin) driver ya karba jikinsa na rawa yana godiya tare da gode Allah da ba xaginsa yayi ba da Yanxu sai dai ya kashe shi a Wannan jejin ba Wanda xai sani ya kashe banxa, shiyasa mutum ya shiga motar kasuwa baisan mutane ba baisan wane irine su ba mutum ko Aljan ya xauna yana xage xage.... Allah ya taimakesa amma yana tsananin mamakin wannan mutum ace barawo ne, idan ka ganshi natsatse dashi shigarsa ta mutunci ba Kamar sauran abokansa ba, fari ne kyakkyawa dashi, Allah ne masanin gaibu akan xamansa barawo yaja motar da qarfi yabar gurin. A sokoto suka sake haďuwa, bayan sun gama fashinsu a wani company sunci nasara suka juyo xuwa gidan wancan abokin wannan mutumin, Deedah bai shiga gidan ba yana daga waje kasancewar dare ne, suka shiga suka masa dukan tsiya suka fito kana suka nufi gidan wannan mutumin dayafi xaginsu, Wannan Karon da Deedah suka shiga gidan dan yaji xafin mutumin Mgnr sa nayi masa yawo a kwakwalwa, _ba hasararra uwa kamar wacce ta haifi barawo_, da kansa ya harbi mutumin a qafa, ya rinqa kururuwa yana neman taimako yar'sa mace ďaya daga cikinsu ya shiga yayi raping ďinta, Deedah yasa belt ya xane mutumin sosai jina jina shi kansa jikinsa ya baci da jini ya sunkuya yana faďin, 'ka gane ko mu su Waye? Mutumin ya girgixa kansa, Ahmed yace 'Mune Waďanda Muka shigo Mota da kai ďaxu Muke xaune dakai kana xaginmu kana xagin iyayenmu alhali Kuma kace barayin basuyima komai ba amma ka xauna kana xaginsu, Yanxu barayin Sunyima Abinda baxaka taba mantawa idan ka shiga mota gobe sai ka xagesu da dalili suka juya suka fice mutumin ya fashe da kuka sosai yana nadama, magana ma Jari ce...... A xaton Deedah koda xaije gida xai samesu sunyi barci tunda ynxu sundaina jiransa ga mamakinsa yana shiga falon sukayi 4 eyes da fauxie da pencil a hannunta, 'lah anty jini a jikin yaya yaji ciwo, da sauri Iman ta juya tana kallonsa lokaci ďaya xukatansu na buga shi na tsoro ita kuma na xargin jinin menene? BABANA DA MIJINA ©Fertymerh Xarah 15 Jikinsa a sanyaye ya ďauke kansa batare da ya sake kallonsu ba ya nufi hanyar step... Fauxie ta dubi fatyma bakinta a buďe, 'Anty kin tuna sanda kika je daukata Skul har kika sami anayima wani duka jini ya fito a jikinsa ko.... 'eh tor me akayi, 'anty sata yayi akayi masa duka, shima yaya sata yayi akayi masa wannan dukan...... Caraf akan kunne Deedah ya juyo da sauri yana kallonta dai dai lokacin da Iman ta bige mata baki tana faďin, 'yi min shiru shashasha, mijina ba barawo bane, Fauxie ta soma hawaye tana riqe da bakinta, Iman ta juya tana kallonsa kafin tabi bayansa, jikinsa har rawa yake da jin kalaman fauxie suna isa ďakin ta fisgosa.... 'kagayamin wannan jinin na miye, ina kaje? Cikin dakewa yake kallonta, 'Accident wata mata tayi da yaro a bayanta, sunji rauni sosai yaron dana ďauka ne jikina ya lalace haka ya faďa yana qara kallon jikinsa, Mata da rauni, nan da nan ta nuna tausayawar ta akan abin, ta soma cire masa rigar tana faďin, 'kayi abin kirki daka taimakesu, Allah xai taimakeka watarana, abinda mutum ya shuka shi xai girba hairan ko shairan, muje kayi wanka, ya bita a sanyaye cikin tausayinta... Fauxie na xaune tunxure da baki ta sauko, tana ganinta ta ďaure fuska tamau Kada ta đauki abin da wasa 'ke nagane bakinki baxai taba faďin alkhairi ba, kince baba baxai shiga aljanna ba yau gashi kin Kira mijina barawo why Fauxiya? 'Anty kiyi haquri ..... 'Mtseww sai anyi mgn Kice haquri, tashi ki tattara colours ďinnan kimaidasu Kada gobe kixo kina damuna, Ta tashi tana haďawa bakinta a tunxure ta nufi hanyar step, ta juya tana kallon Iman bata kallonta sai ta shige inda Ahmed yana xaune yana amsa waya, yana ganinta yayi Saurin katse wayar yana kallonta, 'yaya Ina ne kaji ciwo? Ya ďaure fuska 'ban sani ba, 'please yaya kayi haquri baxan qara ba, 'nida kika ce barawo ne fauxie, ta tsugunna gabansa, 'Ni bance ba yaya, nace kayi sata ne Kuma anty tace Bakayi ba shikenan.... ya ďauke kansa cikin mamakinta, ta tsaresa sai ya nuna mata inda yaji ciwo, shi yarinyar ynxu mamaki take bashi tana girma tana wayo, ynda ya gayawa Iman haka ya gayamata, 'good Samaritan, ta soma dariya ta fice yabi bayanta da kallo.... Daren ranar bai je ko ina ba yana gida tare da fauxie duk assignment ďin ta shi yayi mata, Sa'eed abokin Deedah yaxo Wanda suke aiki tare a banki, sai da yawa yakanxo taya Iman hira idan ya sami Deedah baya nan, sai shaquwa ta musamman ta shiga tsakaninsa da Iman, yana tayata hira da shawarwari akan xamantakewarta da Deedah na rashin xamansa gida saboda shi kansa baisan taqamaiman inda Ahmed ke xuwa ba tunda 6 suke baro bank, Shima Sa'eed yakan xauna yabaiwa Iman lbrn matarsa salima irin yanda take nuna halin ko in kula dashi suna da yara biyu bata Kula dasu kullum tana kwance komai sai mai aiki, shi namiji ne Mai matuqar son kulawa ga mace amma bai samu ba daga matarsa kamar yanda Iman ke buqatar kulawar mijinta bata samu ba..... A Wannan ranar bayan Deedah da fauxie sun gama assignment yayiwa Sa'eed Sallama sai da safe suka haye shida fauxie sama yabar Iman da Sa'eed, can you imagine ynda xaka bar matarka da abokinka saboda rashin kulawa, Daga Iman har Sa'eed kallon mamaki suka bishi dashi, sunyi xaton xai xauna ayi hirar da shine amma sai suka ga sabanin haka, Hakan yasa Sa'eed yayi mata Sallama ya tashi ya fice da makullin motarsa a hannunsa dan baiga dacewar xamansa da Ita a Wannan lokacin da mijinta ke gida ba sai dai yana matuqar mamakin Deedah irin Wannan mata kamar Iman dayake nuna halin ko in kula akan ta, inama itace matarsa ba salima ba da ya more a rayuwa, Da Wannan tunanin ya qaraso gidan, parking yayi ya ďauki laptop ďinsa ya shiga cikin gidan, hayaniyar yaransa yaji agun mai aiki sai da yaje ya gansu kafin ya nufi ďakin salima tana nan kwance da waya a hannunta, Sallama yayi bataji ba hankalinta nakan waya, tsakin dayaja ya janyo hankalinta garesa kallo ďaya tayi masa ya ďauke dubanta garesa, 'Ashe ka dawo, bai tankata ba ya nufi toilet, wannan tambayar raini ce take masa idan da sabo ya saba, bai taba fita ya dawo tayi masa sannu da xuwa ba ballantana irin tarairayar nan da mata ke yiwa miji yaji daďi, Ya fito toilet ďin har lokacin tana kwance abinta , 'Salima..... ya Kira sunanta cikin husky voice ďin sa, Uhm... ta amsa batare da ta Kalle sa ba, yayi shiru yana kallonta da mamaki, 'idan abinci kake mawa yana Kan dinning kayiwa Indo mgn ta xuba ma ni Wlhy duk agajiye nike.... 'aikin me kikayi duk yau bayan kwanciya, ke Wai sai yaushe xaki cnxa rayuwarki Kisan Abinda ya dace ga rayuwar auren ki, ba Indo nake aure ba ke nake aure dan me Wai komai sai Kice Indo xata min ke kina kwance.... ta tashi tana kallonsa, 'Bismillahi ai kadawo qorafi baxai qare ba indai kana gidannan, Indo dole nasanyata tayima tunda yar aiki ce, aure na xo yi ba bauta ba Yakamata kadaina min faďa haka kana takurani xaman aure naxo yi.... 'tir da wannan xaman auren naki, indai haka ake xaman aure da nadaina shi Kuwa, ke baxaki bani haqqina ba sai kin ga dama idan Ina a matse ne sai na biya kuďi sai kace ba mata na ajiye ba, baxaki iya gyara gurin kwanciyar auren kiba sai mai aiki, baxaki iya kula da yaranki ba sai Mai aiki, baxaki iya Kula da gidanki ba sai Mai aiki, abincima sai mai aiki wannan wace irin rayuwace har sai yaushe xaki canxa ne.... taja tsaki ta tashi tayi ficewarta tana taunar cingam yabita da kallo kawai yana girgixa kansa.... * Xaman falon ya gundireta sai ta tashi tayi kitchen tana kiran adama, Da sauri ta fito tana goge hannunta da tsumma, 'baki gama aikin bane har ynxu? 'nagama hajiya Ina gyara kifi ne gobe fauxie tace dashi xataje Skul, 'Hmmmm fauxie kenan ta gyada Kai ta fice, Fauxie ta diro daga Saman gado tana faďin, 'bye bros gudnyt, yana xaune akan stool yana duba wasu takardu na gurin aikinsa, ya ďago yana kallonta 'gudnyt baby.....dai dai lokacin da Iman ta shigo, 'kika ce da kifi xakije Skul Gobe, 'eh anty... 'ashe gobe kowa xai kyamace ki kenan, ki bari idan kin dawo kici inba haka ba xaki dinga wari acikin friends ďin ki, ta juya tana kallon Deedah.. 'Wai hakane yaya? ya gyada kansa alamar eh, 'tor anty Kice ta barshi sai na dawo, 'kije dijeh ke kaďai take jira ku kwanta daga nan sai ki gayamata, 'gudnyt anty, 'Nyt ta juya ta fice da gudu....... Babana da mijina..... ©fertymerh Xarah 💞 16 A hankali ta maida kallonta garesa shima ita yake kallo kafin ya taso xuwa gareta hannunta ya riqa suka xauna bakin gado, 'kin canxa sosai Iman, naga sai haske kike yi miye sirrin.. ya faďa haďe da Kanne mata ido ďaya, tayi murmushi tana wasa da yatsun hannunsa kafin ta dubesa idanunta sunyi rau rau kamar xatayi kuka, 'cikine ka tayani addua ya tsaya, ya saki wani murmushi mai bayyana irin farin cikin da mutum yake ciki ya rung xuwa jikinsa, 'Insha Allah xai tsaya, ina son yara sosai Iman Allah bai bani ba, 'nafika sanin haka muyi addua Allah ya tsaida wannan....... ya ja dogon hancinta yana murmushi haďe da cusa hannunsa cikin rigarta, 'bari muji xai kai wata nawa a yanxu, ta soma dariya tana ture hannunsa ya kwantar da Ita......, Washe gari sun gama shirinsu tsaf na fita aiki, a tare suka sauko inda suka sami Dijeh na rigima da fauxie harda kukanta fafur taqi ta sanya uniform, 'barka da safiya hajiya... ta faďa tana kallonta cikin girmamawa, 'barka... Kukan me kike yi Kuma, 'taqi ta sanya uniform hajiya... 'why fauxie? ke meyasa kullum akaxo shirinki sai anyi rigima dake, cikin kuka ta soma mgn, 'Anty ni baxan je Skul ba xan biki asibiti... Deedah yace amma baby jiya fa naji kina Mgnr xakije da kifi Skul har anty ta hanaki, tor ynxu me xai hana miki xuwa Skul, 'yaya ni baxan je ba kace sister taje dani hospital, Iman taja tsaki ta fice tana fadin 'ba inda xanje dake... Ahmed ya karbi uniform hannun dijeh da socks ďin ta da takalmi kana ya ďauke ta yafita harabar gidan da Ita, Akan Mota ya ďora ta har lokacin kuka take hrda kiran baba, Deedah ya Kira driver, 'idan sun tashi Skul by one ka kaita asibiti inda Iman xasu dawo tare, 'shikenan yallabai.... Ya dubeta, 'idan Kuma bakiyi shiru ba xnce ya dawo dake Kada yaje dake inda sister, tayi shiru tana ajiyar xuciya, ya Sanya mata uniform ďin harda socks and sandals ďinta ya sauko da Ita daga motar, 'jira inxo, tana tsaye gurin yaje ya karbo abincinta da skulbag ďinta.... Yana tsaye gurin har suka fice tana yimasa bye bye, ya sauke ajiyar xuciya haďe da girgixa kansa yana faďin Fauxiya rigima. 1:00pm Ta fito daga labour room, tana tafe da waya a hannunta tana amsa Kira harta iso consultant, 'likita bokan turai acewar Dr Fulani, Dr Umayma tace daga ina kike haka kina xufa , Iman ta xauna tana share gumi, 'daga Gynaec nake labour room, wata yarinyace qarama ga dukkan alamu bata isa aure suka yi mata, she is too young, Allah ya taimakesu sunxo asibiti da wuri da Babu mamaki sai VVF ya sameta, Fulani ta dubeta tana faďin, 'uwar na raye, 'tana raye har yaron amma kam tasha da kyar dan dai da sauran kwanaki a gaba ne, inkin ganta gwani tausayi early marriage, 'Umayma tace mutumin qauye kenan, ga maxan ba haquri, Iman tace dan ma bakiga mijin ba babban mutum ne Wai shine Mai gari yana da ďan iliminsa shiyasa Wai suka xo da Ita asibiti, 'ai Kuwa da ta mutu a banxa cewar Fulani dake cin samosa, Iman ta ďan dubeta, 'sister xn sami sobo..... 'yau Kuma sobo xakisha cewar Dr Umayma, 'Kinsan Mai ciki da Kwaďayi inji Fulani bayan ta miqa mata robar sobo, sukayi dariya dai dai lokacin fauxie ta shigo da gudu ta faďa jikinta ta baya, 'miss you sister, 'Kada kisa na faďi bakiga mutane bane kin shigo ba Sallama, ta koma da sauri tana dariya, Sallama tayi ta shigo tana faďin, gud afternoon anty Fulani & anty Umayma, Suka amsa mata, fauxie rigima, taje ta xauna kusa da Iman tana faďin, 'Anty xn sha sobo... 'Fulani ta bata wani sobo tana faďin gashi fauxie kibar anty tasha nata, tana dariya ta karba, 'Tnkuuuu anty, ta juya tana kallon Iman, 'Anty shi baba baya shan sobo a battle ko cup yafisha a kwarya naganshi ranar yana sha ya ce na fita d...... Nan take Iman ta kware saboda ruďewa ta shiga tari sosai ba kakkautawa..... My wattpad Phertymerh1 Babana da mijina...... ©Fertymerh xarah💞 17 Da kyar ta iya tsaida tarin da take bayan Dr Umayma ta miqa mata ruwa tasha, Batare da tunanin komai ba tana juyawa takaiwa fauxie duka a baya, ta saki qara bayan ta saki sobo ta riqe bayanta tana kuka sosai, 'Haba likita saboda me xaki daketa cewar Dr Fulani dake kallon fauxie, 'surutun banxane banaso, ina ruwanta da baba mai gadi ynxu da har take sanyo xancensa anan, why can't she control her mouth ace yarinya duk inda taje surutu... Yanayin da take mgn xaka karanci bacin rai sosai a fuskarta, Dr Umayma tace gaskiyane fatyma, yaro mai surutu baiyiba ballantana irin na fauxie da ba control, baba masu gadi Kinsan basu fiye shan kayan bottle sunfi gane su xube a wani guri su sha, ruwa ma sai kiga a kwarya suna sha, ita kuma yace sobo yake sha a kwarya ai is nothing tunda har ansan me yake sha, Fauxie najin suna Mgnr baba mai gadi, ita kuma bashi take nufi ba amma taji Iman tace shi, cikin kuka ta dubi Iman, 'Anty bafa........Shut up! ta faďa cikin tsawa haďe da jefa mata empty bottle dake gurin, Fulani ta riqo fauxie xuwa jikinta a yanda ta lura Iman xata iya jimata ciwo, 'kiyi shiru fauxie, kidaina fadar abinda baa tambayeki ba, baba mai gadi ko a kwarya xai iya cin abincinsa bai damu ba, bakiga daga qauye yaxo ba, yawancinsu acan da fulanin daji duk akwarya suke cin abinci so ba wani abin damuwa bane, ta dubi Iman, 'kiyi haquri Dr fatyma karki sake dukanta, inkin lura abinda kike xato bashi fauxie ke nufi ba, beside ma fauxie batasan ire iren waďannan abubuwan ba, Fatyma ta sa tissue ta gyara bakinta kana ta soma harhaďa kayanta tana faďin, 'surutun tane bana so baida amfani ballantana mai gadin mu salihin mutum ne, idan bana hana mata surutu wataran xata ďauko min abinda yafi qarfina, 'hakane acewar Dr Umayma, Iman ta haďa kayanta tayi masu Sallama ta fice, fauxie na kuka tabi bayanta, Fulani ta dubi Umayma tana faďin ni naga hankalin fatyma ya tashi sosai kuma ta hana Fauxiya magana, Umayma tace masu gadin nan bawai mutum xai basu yarda bane, tadai bi ahankali ta saurari Fauxiya ďin, ai wani surutu yana da amfani, Hakane cewar Fulani tana jinjina kanta, Sun fito harabar asibitin fauxie taga mai siyarda agwaluma, da sauri ta share hawayen fuskarta tana faďin, 'Anty ga mai agwaluma ki siya min, Iman tayi mata banxa 'kinji anty.... Nan ma ta kyaleta, nan da nan ta soma hawaye tana sheshsheka, A hanya suka haďu da Dr Merah suka tsaya gaisawa da Iman, ya dubi yanda fauxie ke kuka sosai, da alama ta jima da Kukan yanda yaga sautin ma baya fita, Ya riqo ta yana tambayar waya tabamin suruka matar prince? Iman tasa kai tafice batare da tayi mgn ba, ya sunkuya yana tambayar fauxie, Ta kasa magana da hannu ta nuna masa mai agwaluma, ya tashi yana kallon Iman da har ta shiga motar ta, 'kai fauxie duk Wannan Kukan na agwaluma ne, yayi shiru yana tunani shi aganshi yaje siyen agwaluma ynxu girma ya faďi, a matsayin mulkinsa a asibitin da kuma sarautar dayake taqama da Ita, har ynxu yana taqama da *mulki ko sarauta* abin a jininsa yake, Hannu yayi wa ďaya daga cikin fadawansa dake tsaye a gefe, yaxo da sauri haďe da sunkuyawa cikin girmamawa irinta sarauta, 'kaje da Ita ka siyamata agwaluma kana ka kaita gurin yayarta, 'angama yallabai, yaja hannunta shi Kuma Merah yayi shigewarsa asibiti. Tana cikin motar a xaune fauxie ta dawo da baqar Leda a hannunta, agwaluma ce aciki ta buďe motar tashiga gidan gaba, Iman taja motar batare da ta kalleta ba Fauxie ta juya tana kallonta, 'Anty xaki cnxa min kayan ďaki irin na ihsan, ďakin ta blue ni Kuma ki sanyamin komai pink... Tayi shiru bata tanka ba, 'kinji anty.... Nan ma shiru, 'Pls.... Kallon da Iman nayi mata yasa taja bakinta tayi shiru ba shiri, har suka iso gidan bata qara mgn ba, Iman na kallonta ta nufi hanyar gidan baba, bata hanata ba tunda tasan baya gari dole xata dawo mata sai tayi shigewarta cikin gidanta, Fauxie Kuwa kai tsaye gurin Mai yiwa baba wanki ta nufa tace ya Kira mata babanta, ba musu ya Kira mata shi, kusan sau biyar tana ringing kafin ya ďauka, yana jin muryar fauxie na mgn ya gyara xamansa, 'Auta yau da wannan wayar ake kirana, ina antinki, ta tunxure baki kamar yana ganinta, 'baba wai anty baxata canxa min kayan ďaki irin na ihsan ba, 'meyasa baxata cnxa miki ba? tayi shiru ba amsa, 'yace shikenan anjima xn turo a cnxa maki, 'baba pink nake so, 'tor shikenan, sai me kuma? 'yaushe xaka dawo? 'bayan 2 days Auta, kinaso kiganni? 'eh, 'ki gaida Iman ya tsinke Wayar, Cikin jin daďi ta nufi bangarensu, 5:pm Iman na xaune a falo taga ana shigowa da kaya fauxie ce a gaba tana nuna masu ďakin ta, Matuqar mamaki xaka gani bayyane a fuskar Iman, ina tasamu kayan, kai tsaye ta tambayi daya daga cikin mutanen dake shigowa da kaya, 'Alhaji ya Kira aje ta xabi kayan da takeso a sanya mata a ďaki, Iman tayi shiru tana jinjina abin, daga inda take xaune tana jiyo ynda fauxie ďin ke basu direction yanda xasuyi, ita ynxu yarinyar ta fara bata tsoro, Tana xaune suka gama haďa ďakin komai pink har tedy ďin ta da komai, sai murna take xata Kira ihsan taxo taga ďakin ta itama yayi kyau, Masu aiki sai xuwa kallo ake tsofin kayanta ta raba masu, duk Iman na xaune tana jiyo ynda suke mata godiya, wannan idan tayi sake kayan gidan ma xata kyautar duka, Da gudu ta shigo falon tana kallon Iman cikin murna, 'Anty xo kiga ďakina yafi naki kyau, nan da nan ta ďaure fuska, 'xo nan fauxie, tayi shiru tana kallonta bata je ba 'ko bakya jine, 'Anty kiyi haquri, 'idan kika Bari na tashi daga inda nake xaune sai kin raina wayonki, xo nace... ba musu taje jikinta a sanyaye Iman ta jawo ta, ta xaunar da Ita kusa da ita, 'gayamin yanda akayi baba yace a cnxa miki ďaki, 'a wayar mai wanki nakira na gayamasa, 'tunda ni baxan miki ba sai kika kirasa ko, idan ya dawo xaki barmin gidana kije duk abinda bana miki yayi maki, buďar bakin fauxie sai cewa tayi, 'Anty ai baba yafiki kuďi, yana dasu da yawa a ďakin sa, Iman tayi shiru tana kallon yarinyar, dole xata kai xuciyarta nesa akan yarinyar saboda qurciya komai sai da rarrashi, 'ke kinga kin kyau ta kenan kin Kira baba ya cnxa miki kayan ďaki, ga maqotanki na neman abinda xasu ci, kina gani duk wata ina raba abinci a gabanki ake xuwa min godiya amma ke baki taba tunanin Kice baba ya siye abinci a basu ba sai dai kawai ke akashe maki kuďi, Fauxie tayi shiru hankalinta na gun sabon dakin ta, 'anty kixo kiga ďakina, 'baxan je ba ina miki mgn kina min wata mgn, gayamin yaushe kika ga baba yana shan sobo a kwarya mutumin da ko sobo bayasha, fauxie ta buďe bakinta tana kallonta, 'Anty yana sha fa ai na gansa yana sha sau biyu ya koreni Kuma yaqi bani nasha Kuma... 'yimin shiru shashasha tashi ki ban wuri karna miki wawan bugu, ta tashi tana tsalle tayi ďakinta... Iman na xaune maganganun fauxie na mata yawo akai dole ta sanya ido akan mahaifinta kamar da qamshin gsky a mgnr qanwata amma batason tunaninta ya xama gsky idan Kuwa hakane xata iya yafe babanta tayi tafiyarta da qanwarta, Yau ka Sa'eed yaxo gidan sun jima suna hira kafin ya tashi ya fice har lokacin Deedah bai dawo gidan ba, a Yanxu shima ta soma xarginsa Dan meyasa Sa'eed ke dawo wurin aiki da wuri amma shi bnda shi bayan gurin aikinsu daya da Sa'eed ďin? Har 12 na dare bai dawo gidan ba tagaji da xama tayi sama tabar fauxie na xaman jiransa tana da abubuwa da yawa da xata gayawa yayanta, Anty ta dake ta, Kuma an cnxa mata kayan ďaki, Tana xaune tana kallon cartoon ya shigo da gudu taje ta rungumesa hannunta dai dai gurin aljihunsa bindiga ce aciki, Ta sake shi da sauri tana ja da baya hannunta akan bakinta, Lah yaya......... BABANA DA MIJINA..... ©fertymerh Xarah 💞 18 Sosai ya buďe ido yana kallonta, ganin fauxie a ynxu masifa ne atare dashi, ya duba ba kowa falon yaja hannunta da sauri yana fadin, 'xo muje kiji, ďaxu naga wata qatuwar tedy har xn siyo maki sai na manta, da murmushi take kallonsa 'da gaske yaya... 'e mana Kuma mai kyau da Ita, 'yaushe xaka siya min yaya inaso, 'sai gobe xan siya maki amma idan baki gayawa anty kinga bindiga ba,...... Sai a lokacin ta tuna ta gefen idanunta take kallon aljihunsa tana kallon bindigar da bata qarasa shigewa ciki ba shima ya lura da kallon da take masa ya ciro bindigar bayan sun shiga ďakin ta, 'wannan bafa bindigata bace, ta Adnan ce yaron yaya Sa'eed, kin tuna shi? 'oh yes exactly yaya yaxo da Ita ranar mukayi wasa xaka aramin wannan? Da sauri ya maidata aljihunsa dabarar sa tayi, 'A'a gobe xan maida masa yabani ajiya ne, yabi ďakin da kallo, 'wow baby waya gyara maki ďakin haka, ta soma dariya tana tsalle, 'baba ne ya gyaramin yayi kyau yaya? 'sosai ma har yafi na anty, pink & white, 'yaya anty yau ta dakeni a bayana Kuma ta jefeni da bottle, 'me kika mata? 'wai na fiye surutu, 'ai da gskyrta fauxie surutun naki Kuma bamai amfani ba, abinda baa tambayeki ba shikike mgn dan Allah ki Bari kinji, 'na bari yaya xaka siyamin tedy ďin ko? 'xn siyamaki, ina dijeh taxo ku kwanta dare yayi, ta tunxuro baki 'yaya ni baxata kwanta min a new room ba, ai na bata gadona yana can a dakin su, 'ke kaďai xaki kwanta a ďakin ne? ta gyada kai 'noo kibarta taxo sai ta kwanta a qasa, ta soma buga qafafunta qasa idanunta sunyi rau kamar xatayi kuka, 'Ni yaya bana son ta nikaďai xn kwanta, 'shikenan karkiyi kuka, ya ďauketa ya kwantar da ita a Saman gadonta yaja blanket ya lulluba mata, 'ki tabbatar da kinyi addua fa, ta gyada Kai tana kallonsa da murmushi, 'gudnyt bro 'night baby, ya fita daga ďakin yana sauke numfashi wannan ai security ce acikin gida, ďakinsa ya nufa sai da yagama abinda yake kafin ya nufi ďakin Iman tuni ta dade da yin barci, toilet ya nufa yayi wanka kana ya hau internet yanayi yana kallon gefen Iman dake kwance, sabuwar budurwar sa na online sai abin yayi masa daďi yau suka haďu a banki sosai tafi fatyma kyau sai dai hasken da fati xata nuna mata, aurenta yake son yi koxai samu Ya'ya kamar yanda yake buri a rayuwarsa, sunan ta Saudah...... 2days~ Baba ya dawo daga tafiyarsa Wannan Karon xai ďan jima Nigeria kafin ya ďaga, Iman taje yi masa sannu da xuwa sai kallon cikinta yake don son tabbatar da Mgnr Sima idan da gske tana da ciki, baiga komai ba saboda bai fito ba, Ya miqa mata wasu ruwa acikin cup, 'kisha maganin tsarine na karbo maki Iman, Ta karba tana kallonsa, 'Fauxiya fa? sai da gabansa na faďi, 'nabata tasha ďaxu.... dai dai lokacin da fauxie ta shigo a guje tana dariya muxuru ne a bayanta ya biyota sai kiransa take tana nuna masa Naman dake hannunta, batare da tunanin komai ba ta faďa jikin Iman ta qanqameta cup ďin dake hannunta ya subulce ya faďi maganin ya xube qasa, A fusacce ya fisgo fauxie daga jikin Iman haďe da ďauke fuskarta da mari,bai taba kai hannunsa akantaba sai wannan karon, hakan yayi matuqar bawa Iman mamaki, ďif numfashin ta na ďauke ta faďi ragwab a jikin Iman, da sauri ta riqata hankalinta a matuqar tashe take kallon mahaifinta da qanwarta, hawaye har sun fara xuba a idanuwanta, 'baba meyasa ka mareta, metayi? 'bakiga asarar da tayi min ba, kinsan maganin miye Kinsan ynda na samesa? Sai alokacin Iman ta fahimci dalilinsa na dukan fauxie, but why? Saboda ta xubar da magani xai mata wannan duka? Ta fashe da kuka mai tsanani bayan ta ďauki fauxie ta fito da Ita, hankalinta bai tashi ba a matsayinta na doctor tasan suma ne tayi, babban tashin hankalinta bacin rai da tagani kwance a fuskar mahaifinta saboda fauxie ta xubar da wannan maganin, kada hasashenta ya xama gsky, Tana fitowa taci Karo da motar Sa'eed a waje tasan yana ciki yana jiranta sai tayi bangarenta, Daga inda yake xaune yake jiyo Kukan Iman, ya tashi hankalinsa a tashe a falo sukayi kicibis da juna fuskarta sharkaf da hawaye, duk yaji jikinsa yayi sanyi gwiwoyinsa sun sage, Ya salam..... ya furta a hankali bayan ya karbi fauxie hannunta da sauri ta nufi kitchen ta ďebo ruwa a cup ta fito, yayyafa mata ruwan suka shiga yi,bata đauki wani lokaci ba ta sauke ajiyar xuciya amma idanuwanta a lumshe, gefen fuskarta yayi jawur sosai gwani bn tausayi, Sa'eed yace meya sameta haka? 'baba ya mare ta, 'Mari? taya xai daki wannan yarinya metayi masa haka? Nan tayi masa bayanin komai yayi shiru cike da tunani iri iri, wannan wane irin maganine, Tunda ta farfado take kuka qanqame a jikin Iman sai rarrashinta takeyi, 'Anty meyasa baba ya dakeni, tell him i hate him, Anty Kice masa bana sonsa yaya nakeso, yaya baya dukana, I don't like baba, Iman ta qara rungumeta a jikinta, 'is ok fauxie kinyiwa baba laifi, kin xubar da maganinshi shiyasa ya dake ki, don't hate your father, Kuka take sosai ba kakkautawa, numfashinta har sarqewa yake, idanunta sunyi jawur sun kumbura, idan Iman ta kalleta itama sai taji hawaye na xubo mata, fauxie bata taba kasancewa a irin Wannan yanayi ba, abinda ta jima batayi mata ba dan tayi shiru sai ta ďauketa ta goyata tana rarrashinta, Fauxie ta kwantar da kanta a bayanta hannuwanta qanqame da Ita hartayi barci bata daina sauke ajiyar xuciya da qarfi ba, A hankali Iman ta kwantar da Ita kan sofa tana kallon yanda fuskar ta kumbura, kanta yayi xafi sosai dama tasan Wannan Kukan sai ya janyo mata ciwon kai, Tana son sanin dalilin mahaifinta na dukan fauxie akan magani, Meyasa ya fifita maganin akanta? Wannan Karon xata tunkaresa da Mgnr sai idan itama xai daketa, Ban yarda da cikar imanin mahaifina ba, tabbas akwai wani boyayyen al'amari game da rayuwarsa shida Deedah, akwai abinda suke boyemin Wanda ya kamata na sanya ido akai na gano ko menene, tabbas a yau na kasance mai xargin *babana da mijina* ban sani ba ko Allah xai iya yafemin xargin dana ke masu? Ta soma kuka sosai Mai narkarda xuciya, Tana cikin ruďani, Tana neman mafita, tana cikin tsoron halin da suke ciki ita da qanwarta, Sa'eed na xaune yana kallonta xuciyarsa ba daďi shima kamar xaiyi Kukan a yanda yakeji a xuciyarsa, domin Iman ta xama wani bangare na xuciyarsa duk da tana matar abokinsa yana jinta a xuciyarsa tare da tsananin tausayinta, Irin Kukan da take mai raguwar xuciya baxai iya daurewa ba sai ya tayata, _and he don't want to be among, he dunno why her cry weakness him, he want to turn this sadness to joy...._, Abinda yasa a ranshi yana son bata farincikin da ta rasa gurin mijinta, yana so yabata kulawa irin wacce mace ke buqata a gurin mijinta kamar yanda shima bai sami kulawar gurin matarsa salima ba, _he want to make these tears to smile_. Amma ta wace hanya? Babana da mijina..... ©fertymerh Xarah 19 Tashi yayi ya fice daga gidan baki ďaya, cikin mamakin Deedah inda yake xuwa yabar matarsa a Wannan halin..... Salima na xaune da qawarta ya shigo, cikin girmamawa qawar ke gaidashi amma banda salima ta ďauke kanta wani gefe tana taunar cingam, ďakin sa ya nufa, Qawar ta dubeta, 'bara na tafi salima mijinki ya dawo sai wani lokaci, 'Haba habbi idan ya dawo me xanyi masa, kiyi xamanki Musha hira, Mai aiki xata Kula da shi, 'Chabďi lallai salima Ashe har ynxu kina nan da halinki, shiyasa naga ya shigo ko sannu da xuwa baki masa ba, bansan meke damun rayuwarki ba, baki Kula da mijinki bakya kyautata masa, kina da miji mai kyau da kuďi ďan gayu dashi..... 'kiyi shiru habbi bana son haka, ba ruwanki da kyawun mijina, 'au kishi kike yi, kina sonsa kike masa haka, ai wallahi Sa'eed yafi qarfin ajinki kema kinsani darajar ya'yan ki kike ci ina gaya miki gsky a matsayina na aminiyarki ki canxa halinki ki rungumi mijinki, 'Naji sai anjima habbi, 'ki koreni ynxu tunda na gaya miki gasky, ta tashi sabe da jakarta ta fice bako sallama, salima na bita da kallo, Duk Mgnr da suke akan kunnuwan Sa'eed, yasan halin salima baxata taba canxawa ba yana mamakin xuciya irin tata, yasan inda xai kamata, Yana xaune mai aikin ta shigo da kaya a hannunta ta ajiye a gabansa ta fita, bata jima ba sai gata ďauke da ruwa da lemu, ta xauna haďe da tankwashe qafafuwanta tana xuba masa abinci a plate, shiru yayi kawai yana kallon yarinya aikin da take yafi albashin da ake bata, dole xai qara mata kuďi, ya ďauko Mai aiki saboda wanke wanke, mopping da kula da yara, sai gashi mai aikin ita ke kula da komai tun daga gidan, yaran har Mai gidan komai itace, Tana gama xuba masa ta tashi ta fice da sauri batare da ta kallesa ba Kamar yanda matar gidan ta gargaďeta. 2day~ Tun daga ranar fauxie bata qara xuwa gurin baba ba hassalima muryarshi idan taji guduwa take ta boye bayanda Iman batayi da Ita ba, ta riga ta sanya tsoronsa a xuciyarta, Shima baba yana tsananin nadamar Marin da yayi mata dan gashi fatyma tana xarginsa da wani abu akai, baya manta sanda taxo ta sameshi da Mgnr dan me xai Mari fauxie akan magani, 'saboda tayi min asara, 'wannan wace irin asara ce da tafi lafiyar fauxie baba? 'banason Mgnr banxa fatyma, Fauxiya ya'ta ce I have the right in mata duk abinda naga dama a duniyar nan bamai cewa dan mi saboda ni na haifeta, 'Ni xn tambayeka dan mi saboda qanwatace, ita kaďai nake da a duniyarnan, amana ce a gurina idan na Bari aka cutar da Ita gobe Allah xai iya kamani, Inaso na bata farin cikin da bata samu a gurin UWA ba, fauxie na min kallon wani bangare na rayuwarta jin daďin ta da komai, 'Ashe baki da tarbiya Iman, ni xaki xauna kina gayawa mgn haka, kina nufin bana baku farin cikin da mahaifiyarku xata baku idan tana raye ko me? Kije gaki gata indai nine sai naga bayanku...... Sosai ta buďe ido tana masa kallon mamaki da jin furucinsa shi kansa baisan ya furta ba sai a ynxu sai yayi Saurin gyara mgnrsa, 'Ina nufin kije gaki ga Fauxiya ki xame mata uwa duk abinda takeso ki mata,ki ďauki duk wani responsibility nata, na yafe maki ita kome xai same ku daga ke har ita baruwana da lamarinku, Batare da tayi mgn ba ta fice tana kuka sosai, Kukan maraici da rashin gata a ynxu.... Tun daga lokacin ta daina xuwa gaidasa kamar yanda Yace ba ruwansa dasu haka suma ba ruwansu dashi, sai dai kallo daga nesa ko idan sun jiyo jiniyar motocinsa, Tana xaune a falo taga jini na bin qafafunta, ba ciwon mara ba komai jini ya soma fito mata, da sauri ta nufi toilet ta duba, bleeding takeyi sosai kenan cikin xubewa xaiyi ta faďa a xuciyarta sai ga hawaye na bin kuncinta ta fito da sauri jikinta har rawa yake, tun daga Sama har qasa duk inda tabi jini ne, tana kuka ta Kira adama ta gyara gidan xataje asibiti, Sosai masu aikin sun tausayamata, abinda suka lura da rayuwarta akwai kuďi a tare dasu amma ba kwanciyar hankali. Tana fitowa Sa'eed na shigowa, yanda ya ganta ya sanyashi fitowa ba shiri, Key ďin motar ta ta bashi dan batason ta bata motarsa, 'muje asibiti Sa'eed, bleeding nakeyi ka taimaka ka kaini Kada cikin ya xube Ina matuqar son sa, Yakai Idanunsa qafafuwanta sosai ya rikice yace ta shiga tashi motar, FMC suka nufa suna isowa ko parking bai gama ba ta fita da sauri, sai ynxu takejin ciwon mara amma bata damu ba, Sa'eed na bayanta shima hankalinsa a tashe suka nufi Gynaec, Tayi Sa'a Dr Fulani na gurin ita ta dubata ta gaya mata cikin ya lalace ya riga ya xube wata biyu, Wani irin kuka ta soma yi gwani ban tausayi Fulani na rarrashinta da bata baki sai dai tana mamakin yanda cikin fatyma ke xubewa akai akai bayan ko ynxu ta dubata batada matsalar komai a tare da Ita, A Wannan lokacin sai fatyma ta yanke hukuncin xata soma planning meyiwuwa bata da rabo a duniya sai ta huta da wannan wahala da take taji da wahalar dake damunta, itama Fulani sai tabata kwarin gwiwa akan haka, Sa'eed ya Kira Deedah ya gaya masa halin da ake ciki, Sanda ya xo sosai xaka ga damuwa a fuskarshi, yana tsananin tausayin matarshi musamman irin kukan da take mai ratsa xuciya, daga shi har Sa'eed sai suka fice daga ďakin dan baxasu iya jure jin kukanta ba. Dariya suke ba kakkautawa, irin dariyar da ko ina ke amsawa idan anayinta, sima da mutanenta kenan, Burin ka ya kusa cika Abdallah idan kaci gaba da bamu jinin fatyma muna sha, muna jin daďin sa kaima kana jin daďin mu, akwai kuďi na can na jiranka a ďakin ka, ya sunkuya Godiya nake ya shugabata, suka ďauki wata dariya.... Bayan sun dawo asibiti suna xaune a falo har salima matar Sa'eed da ya'yan su Adnan da Khadija, Fauxie suna gefe suna Wasa da Adnan abinka da yaro bata damu ba sai dariya take tana xagaye falon ita da Adnan, Deedah ya shigo da sallama a bayansa wata kyakyawar budurwace ta shigo, Kallo ďaya Iman tayi masa xuciyarta na soma bugawa fal fal ko sallamar bata amsa ba ganin ynda Deedah ke rawar jiki akan yarinyar ita kuma Wacece, Budurwar ta xauna tana gaidasu duk cikin su salima kawai na amsa, Sa'eed ma kallon mamaki yake masu, Deedah ya soma mgn Uhm....uhm... Iman ga saudah ta xo ta gaidaki ta miki ya jiki, mgnr da ta fito bakinta da wadda yaji fauxie nayi nayi matuqar ruďashi, 'ita wacece, daga ina.... dai dai lokacin da yaji fauxie na cewa, 'Adnan ina bindigar ka muyi wasa? 'yace ni banda bindiga daddy bai siya min ba, ' Qarya kakeyi kana da Ita, wacce kaba yaya ya ajiye ma rannan.... ka tuna? kaje kace yaya yabaka bindigarka muyi Wasa. Pherty🎤👯 Babana da mijina..... ©fertymerh Xarah 💞 20 Da kyar ya iya saita numfashin sa gurin Iman ya kawar da jinsa gurin su fauxie amma hankalinsa a matuqar tashe, Ya kasa furta mata ko wace irin kalma, baisan yanda xai bayyanata a cikin mutane cewar wadda xai aura ce, Ganin haka Iman ta ďauke idanuwanta akansu ta maida kallonta ga su fauxie dan samawa xuciyarta sassauci kuka ma xata iya a Wannan lokacin, mijinta ya kawo mata wata mace a gida shiyasa bai damu da bata haqqintaba saboda yana da wasu matan a waje ta sauke ajiyar xuciya, salima ta kasa haquri cos Macece Mai xafin kishin tsiya, 'ita Kuma Wannan Wacece Ahmed, dai dai lokacin fauxie ta qaraso tana faďin, 'yaya wai Adnan ka bashi bindigarsa xamuyi wasa, 'Kuje ina tashi xn ďauko masa, 'wace bindiga kuma? Cewar salima tana kallonsu, 'toy gun ce na siyo masa ranar ita take mgn cewar Deedah cikin dakewa? 'Malama ke wacece wai kinxo kin xauna gidan mutane, Saudah ta dubeta cikin basarwa, 'ki tambayeshi mana shi da yaxo dani, Sa'eed yace ba ruwanki salima matarsa bata tambayesa ba sai ke, 'wallahi sai na tambaya ai ni aminiyarta ce dole na tambayar mata, kayi mgn Ahmed, Deedah ya kasa mgn ganin yanda Iman ta ďauke fuska daga gareshi yanayin fuskarta ma kesa hankalinsa daďa tashi, Saudah tace tunda kin matsa kiji koni wacece to budurwarsa ce, yace naxo naga matarsa bata lfy, Sa'eed na jin haka ya tashi yana kiran su Adnan ya dubi salima tashi muje gida, daga kallon yanayin sa xaka karanci bacin rai a tare da fuskarsa yasa kai ya fice, 'Amma ke Anyi wawiyar mace inda xaki biyo namiji har gidan aurensa wai kinxo gaida matarsa, kina budurwa ko kunya bakyaji koda yake ba abin mamaki bane tunda mutuncin ya riga ya xube a titi, ta dubi Iman dake sauke numfashi da kyar, Fatyma sai kinyi a hankali fa saboda cutar xamani.... tasa kai tafice tana faďa sosai ranta ya baci, Suna ficewa Iman ta tashi taja hannun fauxie sukayi ďakin ta, Saman gadon fauxie ta xauna ta saki wani irin kuka mai cike da qunar xucci, fauxie tayi shiru tana kallon yayarta kafin taje ta kwanta a bayanta, 'Anty kiyi haquri, anty kiyi haquri shine kawai abinda take faďa har Deedah na shigo ďakin, yanayin da ya same su yayi matuqar tausaya masu sai yake nadamar xuwa da saudah amma bayajin xai iya fasa aurenta a yanda yake son yara ynxu ballantana saudah tace xata bashi soyayya mai cike da kulawa..... A wanna lokacin faďa sukayi sosai dashi, borin kunya yakeyi dan me xata wulaqanta baquwarsa, itama rufe idanuwanta tayi ta Hausa da faďa sosai, Wannan yana ďaya daga cikin tarihinta rayuwar aurensu basu taba faďa ba sai yau Kuma mai tsanani, fauxie na daga gefe tana kallonsu ta tsurawa bakin Deedah ido tana ganin ynda yakewa fatyma faďa sosai sai ta soma jin haushinsa ta qara matsawa jikin yayarta ta kwanta sosai tana kuka domin a ruďe take da sabon canjin da tagani tsakanin yayarta da yayanta, ita kuka Iman kuka ba mai rarrashin wani har ya gama fadansa yasa kai ya fice, ta rungume fauxie sosai a jikinta kamar wani xai kwace mata ita, Ta karbi wannan jarabawar da Allah ke mata da hannu biyu tasan watarana sai labari amma ta rasa gane kan mahaifinta da mijinta me suke nufi da ita? Tun daga lokacin daga ita har Deedah suka ďauki fushi mai tsananin gaske da junansu, Baxai shigo gidan ba sai gab da asuba, wanka kawai xaiyi ya fice daga gidan, abinci ma ya daina ci a gidan tunda yanada saudah a ynxu, Iman ma bata taba nemansa ba qoqarinta a ynxu na ganin ta Kula da rayuwar qanwarta Sau da ke Dama fauxie kan tambayeta ina yaya.... ina yaya, Takan xauna ita kaďai tayi tunanin rayuwar da take ciki sai dai tayi mgn a xuciyarta, inada mahaifi kamar bani dashi Muna rayuwa a gida ďaya amma baxan iya kaimashi kuka na ya sharemin ba, nasani akwai wani lokaci da xaixo Wanda *babana da mijina* xasu kasance cikin tsananin nadama kan abinda suka min, Har tsawon sati uku ba wani canji daga gareshi duk da shima kawar da kaine kawai yakeyi amma yasan fatyma itace rayuwarsa wannan Faďan da sukayi yafi kowa damuwa, A yau ta shirya tarbon mijinta, xata sauke duk wani fushi dake kanta ta bashi haquri tunda yace ta kasance mai laifi a garesa ta wulaqanta budurwarsa, ko ba komai mijintane, mahaďin rayuwarta kuma aljannarta tana tsananin buqatar mijinta a yau, tana wannan tunanin take haďa masa abincinsa a dinning tanayi tana share kwalla dan batada tabbacin xaici ko baxai ci ba, Anashi bangare shima haka, ya gaji da wannan fushin na matarsa, ko yana tare da saudah bayajin daďi kamar yanda yake tare da Iman, yasan shi mai laifine a gurinta na kawo mata budurwarsa har cikin gida Sannan ya rufeta da faďa, dole xai ďauke girman kansa yaje ya nemi yafiyar matarsa, Da Wannan tunanin ya qaraso cikin falo, tana xaune tayi kyau cikin wata atampha,sai ya tsinci kansa cikin jin kunya da nauyinta ya kasa qarasawa cikin falon, Qamshin turarensa ya sanarda ita xuwansa tana juyawa Kuwa ta ganshi tsaye,murmushi ta sakar masa kamar ba abinda ya taba hadasu ta taso kamar yanda ta saba taryarsa, Tsananin mamaki da jin daďi suka hana masa motsi daga inda yake tsaye musamman lokacin da yaji ta rungumesa haďe da sumbatarsa a goshi, sai ya riqota sosai yana sauke numfashi da sauri da sauri, Ta jasa suka nufi sama, ruwan wanka ta haďa masa bayan ya fito ta taimaka masa ya shirya cikin kayan barci kana suka nufi dining da kanta take ciyar dashi bayan sun gama ta soma bashi haquri yayi Saurin rufe mata bakinta, 'Ni ya kamata na baki haquri Iman, ki yafemin ni nasan Mai laifine agareki a koda yaushe, murmushi kawai tayi, Ranar sun jima suna hira fauxie dama tuni ta dade da yin barci, Bayan wani lokaci suka nufi bedroom ďinsu ga mamakinta Deedah addua kawai yayi ya kwanta, sai ta kasa haquri ta fara masa qorafin fitar da yakeyi a da ynxu ya maidata ina yake xuwa kwanakinnan Kuma meyasa baya nemanta? Ya tashi xaune yana kallonta, 'inaji mun gama solving wannan issue dake tuntuni kan fita ta, aiki nake xuwa Kuma training nake xuwa and what else did you want to know, idan ban fita na nemo ba so kike na xauna a gida ina bata lokacina a banxa ko Kinsan yanda na sami aikin, kinsan wahalar danayi kafin na sami aikin? Ki gayamin menene bana miki tun daga ci, sha sutura da sauransu, dame na rageki a gidan nan fatyma? Tsananin tsoro da kaďuwa yasa tana kallonsa da mamakin jin furucinsa, yau Deedah call her with her real name, meke faruwa kada ya daina son tane a ynxu, nan da nan jikinta na soma rawa da kyar ta iya buďa baki tayi mgn, 'xaman ka dani shine bata lokaci Deedah? Idan ban rasa ci da sha a gidan ka ba na rasa soyayya da kulawarka, nima xn iya Kula da kaina da qanwata ta qarfin aikina ko babu kai da babana Deedah..... ta soma hawaye sosai, 'har sai yaushe xaka xauna dani kaji damuwata idan har kai baxaka iya gayamin taka ba, tell me Deedah kasan matsalata a Yanxu da Abinda ke damuna? You are my life partner idan ban xauna dakai na gayama damuwata ba dawa kake so na xauna, babana ya gujeni nida qanwata banda kowa a duniyarnan da xan kalla naji daďi kamar kai, nayi xaton bayan miji da yaya xaka xame mana uwa uba nida Fauxiya, (kuka take sosai) 'Baka xama damu, haqqina ma baka bani, zina kake so nayi kome? Ko wani namiji kakeso naje na nema a waje, auren soyayya mukayi bana qiyayya ba har sai yaushe xn sami kulawarka, kasanya neman kuďi a xuciyarka kana so ka manta ko kai waye, tell me miye amfanin Kuďin da babu kwanciyar hankali akai, ka kwashe dukiyar ka bana so kulawarka nakeso, I want you to know am not satisfied with you....... buďar bakinsa sai cewa yayi 'Ashe baki da kunya Iman, ni kike ma tsawa, are you shouting on me or what? to baxan ajiye aikina saboda ke ba..... Xatayi mgn kenan kuka yaci qarfinta sai ta juya da sauri tabar ďakin ta nufi ďakin fauxie tana kuka sosai Kamar ranta. Pherty🎤👯 BABANA DA MIJINA....... ©Fertymerh Xarah 💞 21 Kukan ta da hawayenta ba qaramin ďaga masa hankali yayi ba sai ya sauko ya bita shima, Gab da xata sauka step ďin ya rungumeta sosai Kamar xai tsaga kirjinsa ya sanyata ciki Mai yiwuwa Sannan ne xai xamo contented, ya juyo da Ita yana fuskantarta, Did I hurt you Iman? tayi masa shiru sai sheshshekar kukanta, Shikenan naji xn gyara, xan cnxa xn rage fitar na xauna na kula dake, xn riqa baki haqqinki akai akai idan su kaďai ne damuwarki amma ni banason Wannan Kukan naki, tayi shiru batare da ta tanka ba idan da sabo ta saba da jin Wannan Mgnr kullum xn cnxa kullum xn cnxa har yau bai cnxa ba ta lumshe idanuwanta cikin qunar xucci, A hankali yakai bakinsa dai dai nata yasanya harshensa akan labbanta yana xagayawa dashi har ya isa cikin bakinta, Shikansa yayi missing ďin ta he don't know sai yanxu daya ruďe yana kiciniyar rabata da kayanta da sauri ta riqe masa hannu tana son janye jikinta daga garesa har ynxu xuciyarta bata huce akansa ba, A yanda ta lura idanunsa sunyi jawur ya soma fita hayyacinsa baxai iya kyaletaba, itama a buqace take sai ta saduda ya ďauketa ya nufi ďaki da Ita.... Washe gari har yaso ya makara koda ya tashi bata ďakin, bata tayarda shi ba saboda har ynxu bata huce ba, ya lura da hakan tunda asuba da xasuyi sallah, ya tashi a gurguje ya nufi toilet, Koda ya shirya ya fito daga ita har fauxie ba kowa a gidan, tayi gurin aiki fauxie Kuwa tayi Skul, ya jinjina kansa lallai abin Iman babbane, Tun da taje asibiti aikin komai batayi ba, tana daga xaune iyakarta da patient rubuta magani ko dubasa amma bataje karban haihuwa ba kamar yanda ta saba a kullum, Bayan wasu awanni likitocin suka dawo duk aka haďu a consultant nan aka fara barkwanci kamar yanda suka saba ana dariya, Iman na xaune komai batace ba illah idanu da ta xuba masu tana kallonsu ďaya bayan ďaya, A tsarin halittar ďan adam personality tana cikin rukunin al'ummar da ake kira introvert da wuya kaga haqoranta sai idan likitocin sun kaure da rigima tayi murmushi tana kallonsu wani sa'in kuma tasa baki, she is simple batada hayaniya, Yanxu ma murmushin take tana kallonsu duk mata ne yan uwanta likitoci, basu damu da rashin sanya bakinta a ciki ba cos sun santa sunsan halinta, Tashi tayi tana harhaďa kayanta da alama tafiya xatayi, Dr Hauwa ta dubeta tana faďin, idan gida xakije Dr fatyma taimaka ki saukeni a hanya, 'ba gida xnje ba, banki nakeson biyawa na fiddo Kuďin Skul fees ďin fauxie, Tace shikenan Bari Dr Fulani ta saukeni, yau bada Mota na xo ba, Iman tayi masu Sallama ta fice, bata taba biyawa fauxie Skul fees ba sai wannan karon da mahaifinsu ya yafe su yamaida responsibility ďin fauxie hannunta Kuma she accept xata Kula da qanwarta duk abinda take so xata iya mata a rayuwa indai baifi qarfinta ba, Akan hanyarta ta xuwa take wannan xancen xucci harta iso bankin da Deedah ke aiki, Sai da ta gama Abinda take tukunna ta nufi office ďinsa, batayi tunanin neman Sa'eed ba, batare da tunanin komai ba ta shiga office ďin yana xaune da laptop a gabansa sai faman dannata yakeyi, sallama tayi ta qarasa shiga, Muryarta kawai yaji ya ďago da sauri yana kallonta, Ta qaraso ta xauna kujerar dake fuskantarsa fuskarta ba walwala, 'Sannu da aiki yayan fauxie, bai amsa mata ba da alama baiyi farin cikin xuwanta a Wannan lokacin ba duk da bata taba xuwa office ďin sa ba tun bayan auren su, 'Iman wannan tafiyar ta baxata fa, me kika xo yi? tayi masa wani kallo 'tambayata kake dan naxo naga mijina, ko laifine Deedah? ya girgixa kansa yana murmushin yaqe 'ba laifi bane kuma naji daďi sosai amma naga baki taba kawomin irin wannan xiyara ba, 'tace hakane, skul fees ďin fauxie na....... bata qarasa ba aka buďe qofar office ďin aka shigo, 'cwty you have been waiting da kyar umma tabarni na fito, Yayi shiru bai amsa ba hankalinsa inyayi dubu ya tashi, Iman ta juya tana kallon wacce ta Kira Deedah da cwty, saudah ce rataje da qaramar jakarta cikin doguwar riga ta atampha, bata lura da Iman xaune a gurin ba ta isa inda yake ta sumbacesa a goshi, 'da sauri ya ture ta cikin borin kunya, me kike yi haka Ashe baki da kunya.... Ta ware idanu tana masa kallon mamaki sai alokacin ta lura da Iman dake xaune tana kallonsu, 'oh no wonder shiyasa xakayi rejecting ďina, kace rival ďita ce a banki, ta juya tana kallon Iman, 'sannu anty ya aiki, Iman ta amsa da 'Alhamdulillah cikin basarwa, saudah ta sami guri ta xauna, 'wannan yanayin yafi komai yimin daďi gani ga uwargidanka, ka gayamata matsayina na amaryarka, Deedah ya dubeta, get out of my office saudah, ban taba sanin baki da tarbiya ba sai yau, duk iskancin ki ya tsaya kaina kada ya kai ga matata, Dariya tayi ta gyara xamanta, Iman kallonsu kawai take kafin ta tabe bakinta ta tashi da Jakarta a hannu ta fice, Tana fitowa sukaci Karo da Sa'eed shima ya fito nasa office, a tare suka sakarwa juna murmushi bayan sun gaisa sai suka jero tare suka fito farfajiyar bankin xuwa inda tayi parking, tun basu qarasa ba taga fitowar saudah a fusace, Sa'eed ya dubeta 'yau ina qawar rakiya fauxie bn ganku tare ba, 'fauxie na skul, school fees ďin ta naxo fiddawa gobe nake son naje na biya mata, Yace hakane, nima Adnan gobe nakeson biya masa, Tace ko na baka na fauxie ka haďa ka biya masu pls, ta ciro Kuďin daga jakarta ta miqa masa, 'nawa ne Kuďin, '65,000 'barsu hannunki a Yanxu idan na tashi aiki kafin naje gida xn biya na karba gobe ina biya sai na kawo maki receipt ďin, 'shikenan Nagode sosai ta maida Kuďin jaka akan idon wasu matasa su kusan shidda da alama yan fashi ne, 'Nine da godiya, kinga Deedah kuwa? ta yatsina fuskarta 'naganshi, bara na tafi Sa'eed sai kaxo, Sukayi Sallama ta shiga motarta ya juya cikin banki, Tun da ta fito daga banki taga alamar kamar wata Mota na bin bayanta, ta glass take tsinkayosu motar cike take da maxa harda bindiga tana gani, hankalinta yayi matuqar tashi ta qara gudun motar sosai sai taga suma sun qara gudu, Gudu take shararawa kan titi kamar xata tashi sama suna biye da Ita, su kansu dake cikin motar suna mamakin yanda ta iya Mota haka gashi sun kusa shiga gari xasuyi missing Kuďin da suka gani hannunta, 'world best ko asakarwa motar bullet ne, yarinyar ta kware wurin Mota sosai, 'A'a kada ku harbeta an shigo gari, asirin mu xai iya tonuwa kawai mubita muga gidan anjima muje mu karbi kason mu, Tana shigowa layin su ta soma horn sosai tun kafin taxo gate an buďe mata ta shiga, 'kai gidan ďan siyasar nan ne Alhaji Abdallah fa, 'abin yaxo dai dai ai, muyi shiri sosai muxo gidan kasan akwai kuďi fa anan, muyi qoqari muci nasara dan naga harda yan sanda ke gadin gidan da alama Mai gidan na gari, in sunyi gardama ayi watsin alburushi kowa ma akashe..... Sukayi dariya haďe da jan motarsu da sauri suka bar layin, My Wattpad Phertymerh1 Babana da mijina....... ©fertymerh Xarah 💞 22 Harabar gidan maqil take da maxa da mata yan siyasa haka ya tabbatar mata da cewa baba yana gari, Da kyar ta iya samun guri tayi parking kasancewar motocin dake gurin birjik, har lokacin jikinta bai daina rawa ba, Taron siyasa suka gama da alama, taga suna watsewa suna shiga motarsu ďaya bayan ďaya, Ta fito daga cikin tata motar ďauke da jakarta, ta rufe motar tayi hanyar gidanta anan taci Karo da baba ko ta ďaga fuska ta kallesa ballantana ta gaidasa, fuskarta a ďaure tamau tabi ta gabansa ta wuce batare da ta kallesa ba, Kallo yabi ta dashi haďe da cixon labbansa cikin jin xafin halin ko inkula da ta nuna garesa a gaban mutane, Tun kafin ta qarasa gidan take jiyo Kukan fauxie, ta duba agogon dake maqale a hannunta 11am baa isa tashi Skul ba to meya maida fauxie gida, ta hanxarta da sauri domin yanda take jiyo kukanta har cikin kanta Kuma ta tabbata baba ma yanajin Kukan yarinyar amma bai damu ba, Tana shiga falon ta ganta jikin adama tana jijjigata sai kuka take tana kiran anty, anty, Da sauri ta qarasa gurin adama tana tambayar meya sameta, 'hajiya tun ďaxu malamar su ta kawota batada lfy sai kuka take, Iman ta karbeta jikinta xafi sosai idanunta a lumshe da alama ta jima tana kuka yanda idanun suka kumbura fuskar tayi jawur, ta kalli adama 'amma shine kin san da haka bakimin waya kin sanarda ni ba, inda bn dawo ynxu bafa, kina nufin sai kibarta tayi ta kuka, 'kiyi haquri hajiya nagayawa yallabai babanta yace inje kawai nayi xaton xai xo ne shinake jira tun ďaxu shiru, Mtseww Iman taja tsaki ta xauna rungume da Ita tana kiran sunanta a hankali, Sai ta buďe ido luuuu sai sukoma su rufe, taji kanta yafi xafi sosai, ta cire mata uniform ďinta tana faďin, 'ďauko min wata riga na sanya mata adama, ta juya bata jima ba sai gata ďauke da doguwar riga, Iman ta karba tana faďin, ďauko ruwa da panadol abata duk da nasan da wuya ta karbi magani, 'ai hajiya bataci abinci, foodflask ďinta komai bata taba, 'haďo mata tea mai xafi da sauri pls, Ta sanya mata rigar, 'anty baba, kice baba yaxo anty, 'baxai xo ba fauxie kicire ranki da wannan Baban a ynxu, tashi kisha tea kisha magani, cikin kuka ta soma magana, 'Ni banaso baba nakeso yabani, anty kije dani inda baba, iman tayi shiru tana saurarenta tasan duk ciwon da fauxie xatayi idan ba baba yabata magani ko abinciba baxata karba ba tun tana qarama haka take shi yayi mata wannan sabon, Adama ta dawo da kayan a hannunta duk rarrashinta da fauxie taqi ta karbi tea ďin, Iman ta tashi ta fita, ta tsinkayosa tsaye tare da wani abokinsa har lokacin da sauran mutane a gidan ta qarasa batare da fargaba ba ta isa inda yake, 'baba! yaji ta sarai yayi tamkar baiji ba dama yasan sai ta nemesa tunda fauxie ba lfy, abokinsa yace bakaji fatyma na magana bane, ya juyo yana kallonta fuska a ďaure, da kyar ta iya buďa baki tayi mgn badan ta so ba, 'baba fauxie ce ba lfy, kasan baxata ci abinci ba idan ba kai kabata ba,dan Allah kaxo ka bata, Baiyi mgn ba ya juya yana kallon ďaya daga cikin mutanen sa hannu yayi masa yaxo da sauri, ta kunne yayi masa raďa ga mamakin Iman sai taga mutumin yaxo kusa da ita shikuma baba ya fice da abokinsa, 'hajiya gashi inji yallabai yace abaki a matsayin taimako ki Kula da qanwarki, ya miqa mata bandir na dubu ďaya, ta karbi kuďin tana juyasu a hannunta, ba dan uba uba bane da ta jefeshi da Kuďin ko xuciyarta xatayi sanyi,tana tsoron Allah ya kamata da wannan laifin, sai ta jefa Kuďin sama suka watse suka xubo qasa har a jikin baba, ya juyo a razane dan a zatonsa Sima ce ke masa ruwan kuďi kamar yanda ta saba sai yaga tsabanin haka ba shakka Kuďin da ya baiwa Iman ne tayi watsi dasu, yayi shiru yana kallonta ransa inyayi dubu ya baci a Wannan Karon irin Wulaqanci da tayi masa agaban mutanensa, kallonta yake kallonsa take duk cikinsu kowane fuskarsa ba walwala, ma'aikatan gidan masu shara da wankin motoci suka xo da gudu suna tsintar Kuďin, ta nuna su a yatsa, 'su ya dace kabaiwa Kuďin bani ba, bnxo neman taimako a gurin kaba, kuma badan fauxie ba, ba abinda xai kawoni gurinka, Inaso in qara tunatar da kai, Annabi S. A. W yana cewa dukkanku makiyayane Kuma xn tambayi kowanenku akan yadda yayi kiwon da aka bashi, 'ya kai baba wace irin amsa gamsassa kashirya wadda xaka ba Allah ta'alah idan ya tambayeka akan wannan gobe qiyama, 'ka tuna samun Ya'ya wata baiwace da Allah yakeba Wanda yaso Kuma ya hana Wanda yaso daga cikin bayinsa, Sannan Kuma jarabawace daga Allah don yaga wanene xai godewa ni'imarsa Kuma wanene xai butulce, Ya'ya kiwone da Allah ya baka Kuma yayi alqawarin tambayarka,ta juya ta fice da sauri yana tsaye yana kallonta abokansa suna kallonsa cikin rashin fahimta tsakaninsa da yar'sa, Har lokacin Fauxiya kuka take tana kiran baba, Iman ta xauna kusa da ita, 'baba bayanan fauxie Kuma baba baxai xo ba, sha tea inkin sha magani inbaki chocolate kinsan yaya ya kawo maki wasu jiya, ta make kafada tana kallonta da idanu jawur, 'Ni banaso baba nakeso, anty ki kaini inda baba, wannan Karon sai ta daure mata fuska sosai ba alamar Wasa a tare da Ita, ta janyota ta matseta tsakanin qafafunta ita da adama suka mata ďure, bata wani sha da yawa ba ta kyaleta duk da acikin xafin ciwo take sai da Iman ta bige ta dan takaici ta qara rungume Iman ďin tana kuka sosai, jikinta yayi xafi sosai sai amai take yi, hakan yasa tayi mata allura, ta ďauketa tayi mata wanka ta rungumata a jikinta tana rarrashinta har tasamu tayi shiru, barci ya ďauketa, ta sauke ajiyar xuciya cike da tunanin halin da suke ciki, Da dare Sa'eed da Deedah a tare suka shigo, sun tausaya halin da suka sami fauxie bama kamar Deedah dan har yafi Iman damuwa akan ciwonta, Sa'eed ya tambayi kuďin skul fees ďin fauxie taje ta dauki anan take bashi lbrn Duk yanda tayi da mutanen da suka biyota kuma tana da tabbacin sai sunxo tunda taga sun dade suna dubin gidan, Sa'eed yayi dariya yana fadin ba inda xasu xo Iman ki kwantar da hankalinki ballantana ma gida irin Wannan na siyasa ga police a gidan, 'taja guntun tsaki tana faďin na tsorata dasu da kyar nasha, Sa'eed ya tashi da Kuďin a hannunsa yana faďin dama mata tsorone daku abinda bai xama babba ba shi kuke maidawa babba, Iman tayi dariya kawai tana kallon fauxie dake jikin Deedah, Duk Mgnr da suke akan kunne Deedah Kuma yasan sai sunxo tunda hartace sun tsaya suna kallon gidan, suma sun sha yin haka dole ne yayi shiri akansu dan baxaa basu ko kwandala ba, Fauxie taqi yarda ya ajiyeta ballantana yaje ya raka Sa'eed sai yaje da Ita a kafadarsa bayan ya dawo ya kashe wayoyinsa gabaki ďaya dan bayajin xai fita a yau, Fauxie ma ďakinsa ya wuce da Ita yasamu da kyar ya kwantar da Ita tunda tayi barci, da sauri yaje ya janyo bindigarsa bullet ya xuba mata kana ya ďura wasu a aljihunsa ya xauna yana latsar laptop ďinsa, Iman ta shigo tana tambayarsa wankan fa, 'ba Yanxu ba sai xuwa anjima ina wani abu ne, ta tabe bakinta ta fita, Har 1:00am Deedah baiyi barci ba yana xaune kamar yanda tabarshi, Iman Kuwa tuni tayi barci, yanayi yana kallon window bai ďebe tsammani ga xuwansu ba, Kamar a mafarki Iman taji Harbin bindiga xumbur ta miqe xaune dai dai lokacin da Deedah ya sauka daga Saman gadon, 'ina xakaje kanajin harbin bindiga ni Dama nasan sai sunxo, 'ki xauna ki Kula da fauxie ta fita da sauri, Ta balcony ya tsaya yana kallonsu yana labe a gefe, tun daga Sama ya gane ba nasu bane sai ya fiddo bindigarsa haďe da gyarata, Artabu aka shiga yi tsakanin barayin da yan sandan dake gurin, kuma sosai sunci nasara akan police tunda baxata suka masu, from no where suka ji saukar bullet batare da sunsan inda yake fitowa ba, Alhaji Abdallah yanajin abinda ke faruwa ya fito da sauri shima bai sauko ba yana sama, ba'a ganinsa amma shi yana ganin kowa, Da barayin suka fahimci inda bullet ke fitowa suka soma maida martani, Hankalin Iman ya kasa kwanciya da Deedah, yafita bai dawo ba sai qarar bindiga kakeji ta fito daga ďakin anan taci Karo da duk masu aikin sun fito hankalinsu a tashe, ta duba ba Deedah a falo, inda take jiyo qarar bindiga can ta nufa, Kusan mutuwar tsaye tayi qafafunta na neman gagararta jikinta sai rawa yake, Deedah da bindiga, Deedah ke harbi, ina Deedah ya iya harba bindiga, ina ya samu bindiga miye hadinsa da bindiga, Harbi yake cikin kwarewa da gwaninta kai da Kaga yanda yake riqe da Ita kasan ba ďan koyo bane ya gwane ko yanda yake sarrafata, Duk harbin da yake ba Wanda ya samesa illah shi da ya kashe masu mutane sosai, Hankalin Iman a tashe ya rabu Kashi biyu, ďaya gurin Deedah ďaya gurin mahaifinta batasan a wane hali yake ciki ynxu ba(ďa da mahaifi) batasan baba yana xaune yana kallon kowa da duk abinda ke faruwa ba, Kamar ance ya waiwaya yaga Iman tsaye tana kallonsa, ba tsoron ganin sa da bindiga yaji ba tsoronsa kada a harbeta, cikin tsawa ya soma mata mgn, 'ki tafi Iman, haka take jinta kamar mutum mutumi, Karo na biyu ya sake daka mata tsawar dana firgita ta ganin bata da niyar tafiya, 'Nace ki tafi....... ta juya da sauri tayi cikin gida, wayarta ta nema ta Kira DPO sosai tasanshi gurin mahaifinta, ta sanardasu halin da ake ci, Deedah Kuwa cnxa akalar bindigarsa yayi ya fito daga inda yake boye ya cnxa gurin boyo suka shiga artabun bullet sosai.... Pherty🎤👯 [04/03, 6:55 p.m.] Pherty🎤👯: *Babana da mijina........* ©Fertymerh Xarah 💞 23 World best yakamata mu haqura mubar gurin nan tun asirin mu bai tonu ba, Baxamu bar gurinnan ba har sai mun cimma burin mu, ko bamu samu kuďi ba muyi qoqari mu kashe wancan gaye.....bai qarasa rufe bakinsa ba Deedah ya sakar masa bullet a hannu dai dai da qarasowar motocin yan sanda, duk Unguwar ta hargitse saboda tsoro da raxana, Deedah na ganinsu ya cilla bindigarsa qasa kana yayi shigewarsa da sauri cikin falo, duk glass ďin gidan an farfasa sa, Iman na xaune da fauxie a hannunta sai faman xufa take ga yan aikinta xagaye da ita, ko kallonsu baiyiba ya nufi ďakinsa dai dai window ya tsaya yana kallon Abinda ke faruwa, Sauran da basu mutum ba ana sanyasu a mota, wadanda na mutu Kuwa yaga ana investigating ďinsu, Juyowar da xaiyi Idanunsa na sarqe da nata, ya saki wata wawiyar ajiyar xuciya kafin xufa yafara ratso masa a goshi 'karki tambayeni komai I don't have time for your question, yayi hanyar toilet da sauri yabarta a gurin, Ya jima sosai aciki yana watsa ruwa kafin ya fito ďaure da towel iya qugunsa tana nan tsaye inda ya barta, baiyi mamaki ba yasan xarginsa take inba ya wanke kansa gareta ba yasan baxata taba yarda dashi ba, ya ďauke kansa daga kallonta ya qarasa tsakiyar ďakin, taja ta tsaya a gabansa, 'you must answer my question Deedah, meya haďa ka da bindiga, 'da ban riqe bindigar ba kina tunanin da ynxu nida ke bamu dade da mutuwa bane, abinda kike xargi bashi bane, niba ďan fashi bane kuma ba ďan ta'adda ba, what else did you want to know? 'ka sauya Deedah, kamaida qarya abincinka yayin da ka boye gskyrka,akwai abinda kake boye min kagayamin ni matarkace nice yakamata nasan sirrinka tun kafin wani yaxo yagayamin, ni nafi kowa kusanci dakai, idan kai baxaka xauna ka saurareni ba, ni xn xauna na saurareka tell me Deedah ina kasami bindiga ka dubi girman Allah ka gayamin gsky... Gabansa ya faďi jikinsa na soma rawa, 'kifito ki faďi abinda ke xuciyarki Iman, xargi na kikeyi..... tayi saurin katsesa, 'saboda me xn xargeka, kunnena yaji Kuma naga xahiri a yau, menene xargi anan, Hankalinsa yayi qololuwar tashi saura kaďan towel ďin dake jikinsa ya subulce ya faďi, 'me kika ji me Kuma kika gani, Fauxie ta gayamin ta ganka da bindiga kuma yau naga xahiri da idanuna ka gayamin kai waye Deedah? 'toy gun ce fa dana siya inbaiwa Adnan na manta Sanda na siyawa fauxie tedy, 'ina bindigar? yaje da sauri inda ya boye ta dama ya riga ya siye tun lokacin dayaji fauxie na maganar da Adnan, ya ďauko ya bata ta karba tana juyata a hannunta kafin ta ďago tana kallonsa, 'wacce nagani yau a hannunka a Ina ka sama? Yace Sanda naji kina gayawa Sa'eed lbrn barayin dana biyoki nayi xargin nima xasu xo, bayan na raka Sa'eed sai na tsaya gurin yan sanda dake waje acan na karba shine ya nuna min yanda xnyi amfani da ita, bayan Wannan ma ina gani a films ynda ake riqonta da yanda ake harbi, ni kaina nayi mamakin yanda na iya harbin bindiga kuma kinga sun kashe yan sanda gabaki ďaya nima dan na fake wani guri ne da tuni sun dade da kasheni shiyasa danaga police sun xo na jefa masu bindigar kada a ganni da Ita a xargeni da ďaukar bindigar yan sanda, believe me gsky nake gayamiki apart from this bnsan komai ba, tayi ajiyar xuciya batare da tayi mgn ba ta juya ta fice, Ahmed yabita da kallo yana sauke numfashi da kyar, Tana fitowa falon DPO na shigowa, tayi Saurin gaidashi, 'da fatan ba wanda akajiwa rauni fatyma, Ta girgixa kanta tana faďin babu, Amma sunce akwai wani nan sama dake harbinsu Waye shi, sai da cikinta nayi wani qugi ta xaro idanu tana kallonsa, 'ai sun kashe shi, ďan Sanda ne ya tsaya mana yana sauka suka harbesa shiyasa nayi gaggawar kiranka, 'Allah ya kyauta gaba fatyma, Tace Amin ya juya ya fice da bindiga a hannunsa, ta dubi masu aikinta, Ya kamata Kuje ku kwanta tunda mun samu kanmu Allah ya taimakemu, Suka tashi suna mata sai da safe, taje ta ďauki fauxie har lokacin jikinta xafi rau, a yanda ta lura wuyanta ma baya tsayi guri ďaya,ko hannunta bata iya ďagawa , akwai matsala dole gobe ta tafi da Ita asibitin dan sai anyi admitting nata, Tana shiga ďakin ta sami Deedah na waya da Sa'eed, taji yana yi masa bayanin komai kafin suyi Sallama ya tsinke Wayar, kallonta yayi bayan ya gama shirinsa na barci lokacin tana gyarawa fauxie kwanciyarta akan gadon, ya taba jikin fauxie shima yajisa xafi rau, 'Wai meke damunta ne, 'shiyasa nake son xuwa da Ita asibiti ayi mata test agani, ni kaina na rasa gane kan ciwon, Allah yasa itama baxata mutu ta barni ba, ta soma hawaye sosai.... [05/03, 8:07 a.m.] Pherty🎤👯: 'Haba ai ciwo ba mutuwa bane, kidaina wannan mgnr, ya ďauki pillow da blanket ya kwanta a qasa ya bar masu gadon, addua tayi ta shafawa fauxie kana ta kwanta, Alhaji Abdallah bai damu da Abinda ya faru ba wannan abin yafi komai yi masa daďi a ynxu sai dai akwai alamar tambaya tsakaninsa da Deedah koda yake ma Ina ruwansa dashi a ynxu, su suka sani dama an kashe su ya huta, sima ta sha jininsu. Washe gari sosai fauxie ke amai, duk hankalin Iman dana Deedah ya tashi a gaggauce suka yi shirinsu, yayi banki tayi asibiti da fauxie, Paediatric ta nufa da Ita inda Dr Bakori, bata same sa ba sai ta sami Dr Lawal shi ya karbi fauxie hannunta yana duba, Dr fatyma, fauxie ba lafia ne, tun yaushe, 'tun jiya ne, 'oh Allah shine ta koma haka, meke damunta ne, Iman ta share guntuwar kwalla hannunta har rawa yake kamar yanda muryarta ke rawa fatanta fauxie ta rayuwa, 'Ni ma nakasa gane ko menene ke damunta, kana ganin hannunta ďaya ma bata iya ďagashi, wuyanta baya tsayi guri ďaya abinci tun na jiya da safe ne, 'Bari muje lab ayi mata test mugani, yana gaba tana bayansa, binni binni take sharar kwalla, jikinta duk yayi sanyi da wannan ciwo na fauxie, a hanya suka haďu da Merah da mutanensa suna shigowa, yau da alama sarauta yake ji ganin kayan sarautane a jikinsa, ga kuma kujerar xamansa ana biye dashi duk inda xaije, Sosai ya nuna damuwa tare da tausayawa halin da inlaw ďinsa take ciki, akwai Wanda xaima operation da safennan shine dalilin fitowarsa yau da wuri, A lab duk iya bincikensu an kasa gano matsalar, wasu result ďin ma ba'a kawo ba, sai akayi admitting ďin ta, aka sanya mata drip da akaxo allura ne taqi yarda sai da Merah ya karba yayi mata da kansa, kuka take tana sai ta dakesu idan ta tashi, dariya suke sosai Wanda ya qara sanyata fashewa da kuka tana kallon Iman dake murmushi, 'anty kema sai na dakeki tunda kike min dariya, 'na bari fauxie, Dr Lawal ďa Merah suka fice aka barta da Iman, 'Anty kinga baba ya bani biscuit jiya naci, 'biscuit Kuma, yaushe? 'da xnje Skul da safe, 'ke kuma sarkin Kwaďayi, duk biscuit ďin da kike dashi gida Wanda yaya ke siya maki bai maki ba sai kin karbi nashi, mutumin da baya sonki, 'Anty ai a islamiya akace duk wanda baya sonka idan yabaka abu kayi bismillah ka karba, kuma harda qul'huwallahu nayi, Iman ta soma dariya tana kallonta, 'sai kace wani mugun abu fauxie, wannan ciwon ya rikitaki da yawa tunda har sambatu kikeyi, 'Anty kicewa baba ban yafe masa ba, Iman ta dube ta da mamaki, 'ba'a cewa babba ba'a yafe masa ba, me yayi maki, 'baya sona, kuma baya sonki, 'ba abin damuwa bane fauxie, kiyi addua kisami sauqi kinji, 'Anty idan na tashi sai na kashe baba, Kusan faďuwa Iman ta tashi yi, gabanta yayi wani irin faďuwa, 'kiyi shiru haka fauxie, meya hadaki da kissa Allah ya tsare ki, rufe ido kiyi barci, 'Anty jiya nayi mafarki baba yace sai ya kasheni Kuma kema sai ya kasheki Sannan ya kashe yaya, anty harda dariya yakeyi nima sai na kashe shi, 'Subhanallah, ai mafarki ba gsky bane fauxie, mutum baya mutuwa sai lokacinsa yayi, Ganin abin na fauxie bana sauqi bane sai ta Kira Deedah a waya akan yaxo, yace yana hanya saboda surutanta suna tayar da hankalinta dan ma ita kaďai ce a ďakin ba mutane, Tana xaune taga gadon fauxie na rawa, ga mamakinta sai taga fauxie na qoqarin tashi ta sauko yayin da take nuna mata qofar shigowa, 'anty kinga baba sai na kashe shi, anty ki riqe min shi in kashe shi, Iman ta juya bata ga komai ba sai ta taso da sauri ta riqe fauxie, sai ta soma fisge fisge tana sai ta kashe shi, hankalin Iman yayi matuqar tashi dan da alama Wannan Karon bata ima fauxie wani qarfi tajita dashi, suna haka sai ga Deedah da Merah sun shigo da sauri suka qarasa suka riqeta su biyu, sai fisge fisge take tana sai ta kashe shi, Sosai al'amarin fauxie ya bawa Iman mamaki a yau, bata taba ciwo irin Wannan ba ko aljannu ke ruďata, sai ta koma gefe ta xauna qasa dirshan tana wani irin kuka sosai😪 My wattpad Phertymerh1 *Babana da mijina* ©Fertymerh Xarah 💞 24 Fauxie na neman gagararsu sun kasa riqeta su kusan biyu, tunanin da sukayi kamar mai shafar aljannu ya Sanya suka soma yi mata karatu, Iman ta maida kanta jikin cinyoyinta tana kuka sosai, wannan wace irin rayuwace, daga wannan sai wannan? Fiye da minti talatin kafin su samu abin ya saketa sai dai bakinta bai fasa furta sai na kashe shi, 'Waye xaki kashe? Merah ya tambayeta, 'baba xn kashe, ina tashi sai na kashe baba, yaya ka ďauko baba in kashe shi, baba yana min dariya dan banida lfy, baba yace sai ya kashe anty da yaya nima sai na kasheshi, Duk sun ruďe da kalamanta wataqila xafin ciwone ke sanyata sambatu haka acewar Merah, Deedah kamar yaso ya fahimci wani abu agame da maganarta sai ya sunkuya haďe da riqo hannunta, 'yaushe baba yace xai kashe mu fauxie? Ina kika ganshi yana miki dariya? 'ai nayi mafarki jiya yace sai ya kashemu,kuma Yanxu yaxo yana min dariya, 'ina kika ganshi yana dariya, suka tambaya lokaci ďaya, Ta nuna masu qofar ďakin inda taganshi tsaye a ďaxu yana tsoratata da kamanni iri iri, tana faďin Ai anty ta ganshi na nuna mata shi, iman ta tashi a firgice tana kallonta, 'banga komai ba fauxie, Deedah ya gyara tsayuwarsa wannan ba ciwon asibiti bane, Merah ma ya tashi yana faďin nima Abinda na fahimta kenan dan haka xnje da fauxie gidana, wazirina xai dubata harta sami sauqi yasan irin waďanna matsalolin, Deedah yace shikenan nima xn qoqarta anan gida mugani, Iman batace komai ba illah hawayen da takeyi har Merah ya ďauke ta suka fita, Yana fitowa fadawansa suka taso xasu karbeta ta qanqameshi, yace su barta, Iman da Deedah na tsaye ya sanyata a mota suka bar asibitin, wani irin kuka Iman take gwani tausayi, ina fauxie ta haďu da aljannu yarinyar da kullum take tofe ta da addua, Deedah ya riqo ta, Is not time to cry Iman, pray for her, A yanda takeji ko ta tsaya asibitin baxata iya aikata komai ba hankalinta xai karkata gun fauxie sai ta nufi gida Deedah Kuwa ya nufi gurin aikinsa tare da qudurin idan ya dawo xai sami babansu yasanshi yasan kowa shi, idan har ya kashe fauxie xai iya tona sa idon duniya Idan Kuma bai bar fauxie ya daina wahalar da itaba xaiyi masa baraxanar tona masa asiri. Sima tsaye tana kururuwa da alama Wannan Karon ranta a matuqar bace yake da al'amarin Alhaji Abdallah, Shi kansa dake gabanta jikinsa rawa yake bai taba xaton kashe fauxie xai masa wuya haka ba, yarinyar akwai tsari sosai a jikinta shiyasa ma ta wahala haka da tuni ya kasheta, Wannan yarinyar taka akwai baki, akwai wayo, batada tsoro Kuma tana da tsari a jiki, bamason sheďanin yaro abamu jinin fatyma, sima fatyma take so a ynxu jinin fatyma take da buqata fauxie tafi qarfin mu, Baba yayi shiru kansa a sunkuye yafi kowa sanin fatyma, yasan duk asuba idan tayi sallah bata komawa barci takan xauna tana addu'oin tsari, tana karanta Ayatul kursiyyu, Amanarrasulu, suratul ikhlas, falaqi da nasi, Sannan a koda yaushe xakajita tana faďin, _Allahumma inni as'alukal afiyata fi dini wa dunyaya wa ahli wa mali, Allahummastur auraati wa amin rau'aati, Allahumma fazni min baini yadayya wa min khalfi, wa'an yamini wa an shimali, wa min fauki wa a'uzu bika an ughtaala min tahti (manzon Allah s.a.w baya barin yin wannan addua safe da yamma)_. Akwai matsala ya shugabata fatyma tafi fauxie tsari amma me xai hana mu hana mata kwanciyar hankali Kamar yanda mukayi da mijinta muke hadasu faďa akai akai, meyiwuwa rashin jituwarsu a Yanxu xaisa tunani yayi mata yawa har ta shagala da yin addua sai mucimma burinmu akanta, idan an kasheta xamu iya kashe Fauxiya da mijinta, Sima tayi wata irin dariya mai firgitarwa kamanninta ma abin tsoro ne, tana sanye da wata doguwar riga baqa mai kyalkyali har qasa rigar ke ja, a gefe Kuma an tsagata har xuwa cinyoyinta, ga wani irin Gashi ba kyan gani daya xubo a fuskarta da bayanta, tana da wasu irin haqora masu mugun tsawo har sun fito ta bakinta sai idanunta da baxaka tantance kalar suba kamar red kamar maroon, akaifun hannuwanta dasu take tsafi suma tsawo ne dasu kamar me, Ban yarda da wannan shawarar ba Abdallah, mijinta yana sonta duk yanda sukayi faďa sai sun shirya, sima na tsananin fushi da fatyma Kuma fushin sima bala'i ne, dan me fatyma xatayi tsarin iyali bayan tasan cikinta shine abincinmu dashi xaka cimma burinka..... Baba ya dubeta a raxane, Tsarin iyali, bnsan tayi ba ya shugabata ynxu mecece mafita, Mafita ďaya ce duk sanda fatyma xataje karban haihuwa kabita a boye ka karbo mana rayuwar jaririn Inka sami dama harda uwar jaririn abamu jininta, idan tana tunanin ta hana mana cikinta mukuma xamu janyo mata baqin jini Wanda mutanen asibiti xasu tsani ta karbi haihuwa har hakan ya janyo mata matsala ta shiga tunanin duniya ta manta ko ita wacece tadaina addua har burinmu ya sauka akanta... Hakan yayi ya shugabata, Abokinsa dake gefe ya kallesa lallai wannan uban bashi da imani dama an dauki rayuwarsu ne su huta da quncin duniya, Abu na biyu kuma xaka maido fauxie a jikinka ka shagaltar da Ita kamaidata kamar da idan lokaci yayi xn gayama abinda ya kamata kayi, Ya gyada kansa, godiya nake ya shugabata, Sima ta juya ga wani da bai dade da shiga harkarba ta nunasa cikin tsawa da fushi, Mun umurceka kabamu mahaifiyarka kaqi, idan kabari fushin sima ya sauka akanka duniya xata juyama baya kuma kowa xai qika ya gujeka..... Kiyi haquri ya shugabata Ina matuqar son mahaifiyata, itace gatana a duniyarnan ta wahala dani kibarni da Ita..... Ta ďauki wata mugunyar dariya sai da ilahirin gurin na amsa kafin ta tsaida, 'baka isa ba, kai baka isa ba, dole sai ka bada, kowa da kake gani gurinnan, ya rasa Abinda yafiso a duniya, wani uwa, wani uba, wani mata, wani Ya'ya dan haka kaima sai kabada, dolene ka bada, kai kuma kasami abinda kakeso wato *kuďi* ta juya gana kusa dashi, Sima na godiya da jinin abokinka, ta wadatu anjima xakaga kuďi, da haka tabisu ďaya bayan ďaya har suka gama meeting ďin su. * A daren ranar ya fito daga wanka yana tsane kanshi da ďan qaramin towel, Tana kwance rigingine a gefen gado cikin doguwar rigar barci mai tsantsi marar hannu, ruwan madara, Kyawawan qafafuwanta da cinyoyinta a miqe sambal tayi xurfi acikin tunanin kowane hali fauxie take ciki a ynxu, Son matarshi da qaunarta yana qara girgixa xuciyarsa yana hargitsa gangar jikinsa, Bayan ya gama shirinsa na kayan barci ya kwanta a gefenta sai yaji jikinta xafi rau, Ya juyo da Ita sosai yana fuskantarta, ta buďe idanuwanta a hankali Waďanda suka qanqance sukayi jawur tana kallon sa, shima ita yake kallo, 'Naji jikinki da xafi meyake damunki, 'nima ban sani ba, 'you are silly and nonsense doctor Iman, bakisan meke damunki ba, ya tashi a fusace yana faďin tashi muje asibiti a dubaki, Ta fashe da wani irin kuka mai tsuma xuciya, jikinta har rawa yake, batasan meke shirin faruwa da Ita ba nan gaba dan tana da tabbacin xuciyarta gab take da bugawa, ya dawo Saman gadon yana kallonta, 'meke damunki, tell me, 'ďaxu koda na duba jinina ya hau sosai, bansan inada hawan jini ba sai a yau, ya xnyi da rayuwata, sosai ya gigice ya riqota xuwa jikinsa, 'hawan jini Iman, menene damuwarki saboda me xaki kamu da wannan cutar, me kika nema kika rasa a rayuwarki? ta fisge jikinta daga nasa, 'inada wata damuwa ne bayan ta *babana da mijina*,Kune damuwata Kune kuka sanyani a Wannan halin, ni har sai yaushe xnji daďin rayuwata na xama mace kamar kowacce macen aure, tun bayan mutuwar mahaifiyata ban qara jin daďin duniya ba.... ta soma kuka sosai, hankalinsa yayi matuqar tashi da jin shine sanadi, how comes matarsa xata kamu da wannan cutar ta hypertension, in Kuwa haka ne gwanda ya rasa komai dan farin cikinta gwanda ya rasa aikinsa da komai dan ya xauna da Ita yabata irin kulawar da takeso, yasani rayuwar fatyma abar tausayawa ce sosai duk da batasan sirrin babanta da mijinta ba, ya yarda xai bar komai dan farin cikinta, 'he is ready to do everything for her to make her happy and feel she is the only one in his life, sai ya matso sosai xuwa jikinta ya juyo da Ita suna fuskantar juna, 'tell me Iman am ready to change and I mean it, menene bakyaso daga gareni, ko aikina kikeso na ajiye to make you happy? 'fitar dare nake so kadaina, ka xauna damu kaji matsalarmu, ka ďebe mana kewa ka Kuma bamu farin cikin da Muka rasa, xaka daina yawon dare? Yayi shiru yana kallonta cikin ido xuciyarsa na bugawa, soyayyarta ta rinjayi xuciyarsa sai ya maidata qirjinsa ya rungumeta yana shafar kanta, 'nadaina, nadaina Iman kema ki cire damuwa da tunani a ranki, saboda jininki ya sauka banason Wannan cutar.... Magana yake kamar xaiyi kuka, Karka damu, ynxu da ya hau sosai yanada nasaba da halin da fauxie take ciki.... 'fauxie xata sami sauqi ki kwantar da hankalinki. Pherty novels..... [08/03, 8:14 p.m.] Pherty🎤👯: *Babana da mijina* ©Fertymerh Xarah 💞 25 Da tunani iri iri Deedah ya kwanta a ranar, barci ya kasa daukarsa har lokacin da Iman tayi barci sai ya gyara mata kwanciyarta ya lullubeta kana ya sauko daga Saman gadon ya fito, Da sanďa ya fice daga nasu gidan ya nufi gidan baba, ba kowa ko Motsin mutum babu sai na kukan tsuntsaye, Batare da tunanin komai ba kai tsaye ya shiga falonsa dai dai lokacin da baba ya fito daga ďakin bautarsa da kayansa jajjaye na tsafi hannunsa ďauke da kwarya jinine aciki, Ganin Deedah na qaramin tsoratashi yayi saura qiris kwaryar dake hannunsa ta faďi a qasa, Karo na biyu Deedah ya kamasa dumu dumu sai ya take fuskarsa bayan ya ajiye kwaryar a gefe ya juyo yana kallonsa, 'Waye ya Baka ixinin shigo min gida a Wannan lokacin har cikin falo na, 'ba neman kai nake da kaya ba ballantana na nemi ixinin shigowa wannan falon, baba ya buďe ido sosai yana kallon Deedah da mamaki, me yaron ke nufi kada dai ya rena sa ne yana son ya manta shi surukinsa ne, Deedah yacigaba da faďin, 'naxo kan mgnr qanwata fauxiya, nasan ciwon ta baxai rasa nasaba dasa hannunka aciki ba, idan baka kyaleta ba wani abu ya sameta kasani tamkar a idon duniya ne, 'abin kunya, abin takaici da haushi yarinyar cikinka kake neman salwantar wa saboda neman duniya, har akwai abinda xaka nema a duniya najin daďi kamar kasancewarka da Iyalanka, ko kamanta haqqinsu dake kanka, idan yau ka faďi ka mutu gobe kacewa Allah me? Kana tunanin haqqinsu ma xai barka, meyasa kake son kashe su, kaji daďi har Allah yayi ma kyauta da yaran, ni shekarata uku da aure matata na samun ciki yana xubewa, ina son yara Kuma still nake xaune da Ita cikin qauna da aminci, Baba ya nuna sa da yatsa, 'kashiga taitayinka Ahmed, kafita daga idona ba ruwanka da iyalina, 'inada ruwa dasu kasancewar nike riqonsu suna min kallon miji, yaya kuma uba, wallahi idan baka cire muguntarka akan su ba, *Ni Ahmed Deedah xan xama ajalinka*, I will not care da kai ko waye, you are nothing to me, idan har fauxie da fatyma ba ya'yan ka bane don't ever call me your inlaw ko kuma kariqa min kallon suruki,am not...... ya faďa cikin tsawa yana nunasa da yatsa daga yanayinsa xaka karanci bacin rai sosai a fuskarsa, 'kafin ka xama ajalina ni xn xama ajalinka Deedah, kana raye kana gani xn kashe matarka da qanwarka kafin na kasheka Kuma kafin nan sai na wulaqantaku a duniya na toxartaku yanda kowa xai tsaneku, na rasa matata da Ya'ya na maxa ballantana waďanna mata, *Ni na kashe su da hannuna*,ya faďa cikin tsawa cikin subutal baki, 'kai ka kashe su Alhaji Abdallah, har kake ikirari da wannan, Subhanallah....jikinsa na soma rawa, 'na rasa matata na haqura ballantana su, tunda kayi gigin shigo rayuwata sai na kashe ka na kashe fauxie na kashe fatyma......... kai yaji muryar Deedah tare da Kukan harbin bindiga, Deedah ne riqe da bindiga ya harba kwaryar dake ajiye a gefe kana ya nuna sa da Ita Idanunsa jawur, Kukan Harbin bindigar ya tayar da Iman daga barcin da take, ta duba gefe ba Deedah gabanta yayi matuqar faďuwa ta sauko da sauri tana kiran sunansa a hankali, 'shoot me Deedah idan kana tunanin bullet xai iya shiga jikina, ko kana xaton a banxa nake xaune, you can't kill me sai dai ni na kashe ka, get out of my house, 'I promise you ni Deedah na ďauki alqawarin baxaka iya cutar da kowane daga cikin mu, kana nan xaka ga qarshenka haqqin Waďanda ka kashe ma baxai barka ba nima baxan Barka ba, for now danasan kowaye nasan mugun abun da ka aikata sai kayi danasanin sanina a rayuwarka, ta cikin ruwan sanyi slow poison xn xamema Kuma batare da fatyma ta sani ba, 'ka iya bakinka Deedah akaina, a ynxu xn iya nakasaka kaxama abin kwatance a gurin su.... Hankalin fatyma tayi matuqar tashi, tana sanye da hijab ta fito daga gidan, taji Kukan bindiga a Ina ne, ina Deedah ya shiga a Wannan daren bayan yayi mata alqawari baxai qara fitar dare ba, Tana tsaye gurin taganshi ya fito gidan baba, a yanda ta lura kuka yakeyi taga yana share hawayen fuskarsa har kamar baya kallon gabansa, ta maida kallonta gidan baban tana ganin inuwarsa a tsaye ta window tor meya hadasa da Deedah, yaushe ma Deedah yaje can kuma Kukan miye Deedah keyi, ta juya tana kallon inda Deedah yake wayam babusa babu alamarsa ya fice daga gidan, ina ya nufa? Da sauri taje bakin gate tana dubawa ko inuwarsa babu hankalinta yayi matuqar tashi, kada dai baba ya kori Deedah ne daga gidan, har xataje inda baban sai ta fasa ta fito nan bakin gate ta xauna tana jiran Deedah acikin wannan daren babu tsoro a xuciyarta burinta taga mijinta taji dalilin kukansa. [08/03, 10:01 p.m.] Pherty🎤👯: * Deedah Kuwa tafiya yake yana tunanin maganganun baba, kuka yake sosai bai damu da inda xaije a wannan daren da nisan tfyr da xaiyiba, Sai ynxu yake regretting rayuwarsa kasancewarsa ďan fashi, he loves fatyma, yana qaunarta komai xai iya akanta,yana son kareta da qanwarta ga hannun axxalumin mahaifinsu, yana son basu kulawa da farin cikin da suka rasa gun uwa da uba, yana son xame masu uwa ba uba ba...... Tafiya yayi sosai acikin wannan daren kafin ya iso gidan oga nas, qofar ya soma bugawa ahankali, duk yaran dake gidan suka tashi da sauri kowane da bindiga a hannunsa haka shima oga nas xaune da qatuwar bindiga a hannunsa yana kallon qofar da Deedah ke bugawa a tunaninsu hari aka kawo masu, Mutum ďaya ya buďe qofar tare da nuna Deedah, suna ganinsa suka ajiye bindigoginsu suka koma suka xauna, Kai tsaye inda oga nas ya nufa suka sami guri suka kebe dan yayi mamakin xuwan Deedah haka, 'kayi haquri idan na batama a tsawon xaman da mukayi da kai, daga yau nadaina fashi...... Dariya sosai oga nas keyi har yaransa na jiyosa yana kallon Deedah, 'ta yaro mai take bata qarko, ai baka isaba, idan kaga kabar wannan sana'a to ka mutu acikintane, inaaaa waye kai, Deedah ya murtuqe fuska, 'na kasance da kai tsawon shekara uku ina yima aiki, bn taba nuna gaxawata akan kaba, ina shiga haqqin matata, idan bata yafemin ba Allah baxai barni da haqqinta ba, nagane wannan sana'a bamai kyau bace agareni da kai Ina roqonka kaima ka shiryu kamar yanda Allah ya shiryani kadawo hanya kadaina fashi, 'saboda matarka xaka bar wannan aikin, to ai kamar baraxanace ga rayuwarta, nasan ta nasan asibitin da take aiki acan ma xn iya samunta na ďauke ranta da alburushi Kaga idan ta mutu ai ba batun haqqinta dake kanka, Sosai Deedah ya tsorata da Kalaman oga nas, yasan wayeshi yasan abinda xai iya da Wanda baxai iyaba, wannan qaramin aikinsane dole ta ruwan sanyi xai biyo masa idan yana son suyi rabuwar arxiki sai yayi shiru yana kallonsa, 'idan kanason kasancewa da matarka lfy ka xauna dani, shekarun baya musu bai taba hadani dakaiba karka Bari mu somayi dakai Deedah, Deedah ya tashi ya fice ransa a bace batare da yayi mgn ba, oga ya bisa da kallo Deedah nason Wasa dani idan yayi sake sai in kashe sa dashi har matar tasa.... Koda Deedah ya dawo yasami Iman xaune bakin gate tana jiransa, tambayar duniya tayi masa yaqi ya gayamata komai sai kuka da yake har wannan lokacin, ynxu shida iyalinsa suna tsaka mai wuya, Kukansa ya daďa tayar da Nata hankalin itama sai ta tsinci kanta cikin tayasa Kukan, a Wannan ranar daga shi har ita bawanda ya rumtsa sai juye juye da suke faman yi, Washe gari har sukayi shirinsu bamai walwala a fuska breakfast ma basuyi ba suka fice kowa ya nufi gurin aikinsa, Tana office ďinta xaune tana tunanin idan ta tashi xataje ta duba fauxie sai ga Deedah ya shigo jikinsa a sanyaye, Ta dubi agogo to ten ynxu, ta maida dubanta garesa bayan ya xauna farar takarda ya miqa mata idanunsa jawur kamar xaiyi kuka, Jikinta na rawa ta karba kada Deedah ya saketa ne, da kyar ta warware tana dubawa, ta barin aiki ce.. ...ta ďago da sauri tana kallonsa, Wane aiki Deedah? 'farin cikin ki shine nawa Iman, I promise to change, inason kasancewa dake kamar yanda kike so nabaki farin ciki irin wace mata ke buqata a gurin mijinta shiyasa na bar aikina na banki a yau, are you happy Iman? 'happy with what Deedah? Ta faďa da tsananin mamaki tana kallonsa ido a buďe, 'why xaka bar aikinka saboda ni, ni nace kabar aikinka, tell me Deedah idan Baka aiki what did you want to do? Gida xaka xauna ni nafito aiki or what, akwai abinda ke faruwa tun jiya kaqi ka sanardani, pls tell me miye damuwarka Deedah? Ya xare baqin glass ďin idonsa, sai a lokacin ta lura da yanda idanunsa sukayi jawur da alama yasha kuka, nan da nan hankalinta na tashi idanunta suka kawo kwallah, 'ba haka nake nufi ba Deedah, bnce kabar aikin ka saboda ni ba, training dakace na dare kanayi nace Kabari, fitar dare nace kadaina Deedah ba aikinka ba..... Pherty novels *Babana da mijina.....* ©Fertymerh Xarah 💞 26 Yayi shiru kawai yana kallonta, baisan yanda xai gayamata fitar dare baxata yiwu ya daina ba saboda abinda oga nas ya faďa masa a daren jiya, 'Naga you have not sign it, so baxaka bar aikin ba, ta yage paper into pieces kana ta xuba a dustbin, ta dubesa, 'kaje gurin aikinka tunda bnda muhimmanci da xaka gayamin damuwar ka, jiya naganka ka fito gidan baba kana kuka, meyasa? Meya haďa ka dashi? Me ya kaika gidanshi bayan na gayama abinda ke faruwa ynxu, kai tsaye ya bata amsa, 'saboda lfyr fauxie naje, tayi masa wani irin kallo, 'ban fahimceka ba, miye hadinsa da lfyrta mutumin da bai damu da Ita ba, 'yana da sa hannun a ciwonta, bakiga ynda ta rikice tana kiran sunansa ba tana sai ta kashe shi, bakiyi noticing komai akai ba, Tayi shiru tana tunani, mgnr Deedah gsky ce idan tayi laakari da Mgnr fauxie da ta gayamata biscuits yabata taci, meke nan baba sihiri yakeyi ko malamai yake bibiya dan yaga bayanmu, ya salam ta furta a hankali bayan ta dafe kanta da hannuwanta duka biyu xuciyarta har wani xafi takeyi, Deedah yace muyita addua Iman, kada ki tambayeni dalili, amma mu dage da addua Kuma fauxie xata sami sauqi, Tayi shiru tana kallon sa da tagumi idanunta sunyi jawur, dole tasa ido sosai akan mahaifinta tana son sanin me yakeyi, nan da nan kwakwalwarta na soma tunano mata wasu abubuwa, 'lah anty dubi irin kayan baba.... 'anty shi baba baxai shiga aljanna ba, 'baba baya shan sobo a cup ko battle sai dai a kwarya, 'baba yace sai ya kasheni, ya kashe ki kuma ya kashe yaya, 'anty ga baba can, kibarni in kashe shi, Ta bigi teburin dake gabanta, 'Nooooooo ta faďa da qarfi, impossible.... Sai da Deedah ya tsorata da yanayinta, 'me kike tunani?tayi shiru, 'baba baxaiyi haka ba, baba baxai aikata haka ba, Akan wane dalili bayan yana da kuďi, mexai nema a duniya ynxu? Astagafirullah tayi gaggawar tuba kan xarginsa da tayi haďe da kawar da tunanin daga kanta, ta dubi Deedah, 'muje muga jikin fauxie.... * Tana ďauke da wata qatuwar tedy a hannunta sai gudu take tana xagaye falon tana dariya, Amira na bayanta yarinyar Merah kusan sa'anin juna ne, Affiya dake xaune a tsakiyar falon ta dubesu, 'baxaku daina gudun ba sai kun faďi kunji ciwo? 'Mummy kice ta bani tedy ďita tunda ba daddynta ya siyamin ba, 'fauxie tace nima baba ya siyamin nawa, anty ta siyamin kuma ranar yaya ya qara siyamin wata qatuwa, Affiya tace ki aramata Amira, she is your new friend bakiga batada lfy ba, Amira ta make kafadarta tana buga qafafunta a qasa, 'Ni baxan aramata ba sai ta bani, ta fashe da kuka dai dai da saukowar Merah, yanajin duk abinda ke faruwa, Amira baxaki arama qawarki tedy ba, ta gyada kai tana kuka, Merah ya karbi tedy hannun fauxie ya miqa mata, 'ga kayanki, ba ruwana dake munyi faďa, juyowar da xaiyi sai yaga fauxie na kuka sai share hawayen ta take da rigarta, ya dubi Affiya, 'Ina tedys dake gidannan, 'suna ďakin Ameera, Ya riqa hannun fauxie daina kuka muje inbaki wata kibarta da abinta, Ameera tayi Saurin miqo mata tana faďin, 'daddy gashi na aramata, Fauxie taqi karba, 'daddy wai bataso kace ta karba..... Sallamar su Iman ta Katse su, da sauri fauxie ta juya jin muryarta suna haďa ido ta saki hannun Merah taje da gudu ta rungumeta, sosai Iman ta qanqameta a jikinta cikin tsantsar farin ciki ganin ta sami lfy, Slaves ďin dake falon suka soma fita da sauri yayinda wasu suka fara hidima da tarbon baqi, Deedah ya bashi hannun suka gaisa kana suna xaxxauna, iman ta gaisa da affiya da Merah, 'Dr kinga fauxie ta sami lfy tun kafin ayi mata komai abin kamar sihiri, tayi murmushin yaqe xuciyarta na bugawa, 'Ina godiya sosai Dr Merah, farin ciki na a yau ynda na sami fauxie Allah ya qara kiyayewa duk suka amsa da Amin, 'Ameera taxo ta kawo mata tedy ďin ta aramata, 'Banso ai anty nima inada tawa tedy ko? ta gyada Kai tana kallonta, 'Kuma ai anty tafi tata kyau ko, iman ta girgixa kanta, fauxie ta bata fuska xatayi kuka, 'tafi tata kyau, Ameera Tace ai nima inada su da yawa daddy ya siyamin, ke kuma babanki bai siyamaki ba😝 Yaya ai baba ya siyamin ko? Kuma babana yafi daddy ki kuďi ai, 'qarya kike daddy yafi babanki kuďi, Kuyi shiru hakanan, faďa ya qare cewar Iman, Merah yace qurciya ke damunsu kibarsu, yau Ina off shiyasa bn shiga asibiti ba, 'naga alama ai, (Faďan dai bai qare ba tsakaninsu) 'daddy ya siyamin keke da Mota, kuma yace xai kaini Phoenix inda yaya sultan inyi karatu, 'ai nima baba yace xaije dani India inyi karatu irin na anty, kuma ya siyamin Mota, harda soja aciki da bindiga, kuma ya siyamin gida qatoto harda jirgi, Amira ta dubi Merah, 'daddy nima xaka siyamin gida da jirgi? Ya gyada kansa yaran ma mamaki suke ba kowa a falon, ta dubi fauxie tana dariya, 'nima daddy xai siyamin, 'fauxie tace ai baida kuďi irin babana, 'daddy yana da kuďi masu yawa acikin drawer, 'baba yana da kuďi da yawa da yawa acikin ďakinsa, sun xubo da yawa qasa a Sama ma suke faďowa ko anty? Ta juya tana kallon Iman cikin shigar tambaya..... *BABANA DA MIJINA......* ©Fertymerh Xarah 💞 27 Babana yana da kuďi da yawa da yawa acikin ďakinsa, sun xubo da yawa qasa a Sama ma suke faďowa ko anty? Ta juya tana kallon Iman cikin shigar tambaya...... Deedah yayi xuruf yace waďanda aka ďora akan drawer ne ke xubowa, kuma ai bamasu yawa bane, ta juya tana kallon Amira, 'tor kingani, tayi mata gwalo tana dariya, Amira ta faďa jikin Merah tana kuka, ya cirata yana faďin, 'is ok, daddy ma akwai kuďi har akan drawer, itama ta juyo tana yiwa fauxie gwalo, Sosai yaran sun baiwa affiya dariya, iman Kuwa na xaune hankalinta baya jikinta sosai, Sanda xasuje da fauxie suka je gida bayan sunyi godiya, gida suka nufa sunyi parking sun fito dai dai da fitowar baba danashi escort a bayansa, daga Iman har Deedah ba Wanda ya kallesa, fauxie Kuwa tunda suka haďa ido dashi take harararsa tana Jan tsaki da qaramin bakinta, Ya tsaya yana kallon yarinyar cikin tsananin mamaki har suka fice, Ke tsakin me kike, wakike harara haka? Cewar Deedah Yaya babane, I hate him, Yayi shiru kawai..... * Tana tsaye tana xare safar hannunta jikinta har wani rawa yake idanunta sunyi jawur, Safiyar yau sau uku tana karban haihuwa jaririn yana mutuwa, abinda bata taba samu ba, Lafia Lau suke haihuwa komai normal but kafin ta gama yankan cibi jaririn xai mutu, Nurses ďin da take aiki tare dasu taga damuwa a tare da fuskokinsu da kyar ta iya jan qafafunta ta nufi office ďinta da file guda uku a hannunta na dead case, She is not happy today duk da san basuda tsawon Numfashi a duniya ne, taja numfashi a hankali tana kallon time, 'wow fauxie is back from school, so batason barinta ita kaďai a gida saboda baba karka ya cutar da Ita, ta tashi ta soma haďa kayanta, ta fito daga asibitin, Ta buďe motar ta xuba shirgin dake hannunta, wata nurse ya qaraso da gudu tana haki, "Dr fatyma ","Dr fatyma", ta juya tana kallonta harta qaraso, 'kixo ki taimaka please wata patient aka kawo yanxu, baxata iya haihuwa da kantaba and she is also bleeding, ta yatsina fuskarta, 'I have alot to do at home, ki Kira Dr Fulani ko Umayma, 'duk sun shiga meeting basu fito ba har ynxu, Kasancewarta Mai sanyin xuciya Kuma xuciyarta Mai laushi da haquri batada Wulaqanci ko kaďan ya Sanya likitoci da nurses suke qaunarta har patient ma domin ta iya tafiyar da marar lafiya cikin sauqi, Ta rufe motarta suka koma cikin asibitin, Tana tsaye akan matar sosai ta galabaita da kyar Iman ta samu ta ciro yaron, kuka yaron keyi kafin wani lokaci Kuma sai sukaji shiru, dubawar da xatayi baya Numfashi, wannan Karon har xufa ke xubowa daga goshinta, baxaka iya gane wane irin yanayi take kai ba, Cikin qarfin hali ta miqawa nurses jaririn, ba Wanda ke xarginta da komai sai dai yau sun rasa gane meyasa jariri baya tsayawa a yau, ta wanke hannunta kana ta fice nurses su gyarata. 4:00pm Deedah ya dawo gidan tayi mamakin ganinsa ta tambayesa, ya gayamata ynxu 4 yake tashi daga gurin aiki har Sa'eed ma, A yanda ya lura tana cikin damuwar sosai sai ya tambayeta, ta kasa boye masa damuwarta ta xaiyana masa komai, ya dawo ya xauna kusa da ita, Ba abin damuwa bane Iman, duk Wanda kikaga ya mutu lokacin sa ne yayi, inace agaban nurses kike karban haihuwar, ta gyada kai tana kallonsa, 'so kinga ba Wanda xai xargeki kawai su ba rayayyi bane, ki riqa addua a kowane lokaci idan zaki shiga haihuwa, 'shikenan nagode, 'haďa min ruwan wanka, ta tashi tana faďin, 'anjima xn fita super market, Sai da gabansa na faďi daya tuna anjima xasu shiga wurin, 'ki canxa super market, 'meyasa ta tambeyasa tana kallonsa da mamaki, 'ba komai amma kada kije can, 'customers ďina duk acan suke Kuma abinda xn siye xn sameshi a can batare dana wahala ba, 'you can make customer in any where, banason kije Kuma kada kije, tayi shiru batare da ta tankaba tayi shigewarta toilet, To 6pm ta shirya ta nufi super market lokacin Deedah ma ya fita, bataga dalilin dayasa xata canxa guri ba bayan ga inda ta saba siyayyarta, tabar Fauxie gida tana shan golden morn, tana cikin super market din ta juyo Kukan bindiga, mutanen dake ciki suka soma fita da gudu wasu Kuwa na neman mafaka, Ta rikice ta rasa ta Ina xatabi, oh shiyasa deedah ya hanamata xuwa amma ta dage taxo, Tana tsaye ta hangosu suna shigowa wasu sun tsaya daga waje ko wane fuskarsa a rufe idanunsu ne kawai a waje, Sosai sunyi barna a ciki Kuma sun kwashi kuďi da yawa, Deedah Kuwa baiyi niyar shiga ciki ba amma tunda yaga motar Iman a waje hankalinsa na tashi ransa inyayi dubu ya baci wato sai da taxo, da bindiga a hannunsa ya shiga yana nemanta tsoronsa kada a harbeta, Iman Kuwa jikinta rawa yake sosai kayan dake hannunta duk ta xubar burinta taga ta fita daga ciki, tana lababe kada su ganta dan taqi kwanciya a qasa kamar yanda sauran mutane sukayi, Kicibis sukayi karo da juna, a raxane ta juyo cikin tsoro har hawaye sun soma xubo mata, yayi Saurin toshe mata baki da tafin hannunsa ganin xatayi masa ihu, qamshin turarensa ya daki hancinta gabanta yayi matuqar faduwa bai bari sun haďa ido ba yayi waje da Ita, ita kuwa idanunta akan fuskarsa tana son gane wani abu, Yana fitowa ya cillata a waje,tayi tangal tangal xata fadi,wani ya saita bindiga xai harbeta yayi Saurin katsesa, 'Nooo don't shoot..... tayi saurin tsaida hankalinta jin muryar da ta fito daga bakin mutumin daya fito da Ita waje kafin ta juyo tuni mutumin yabar gurin bata gansa ba ta soma waiwaye, 'ke kibar gurinnan kada na ďauki numfashinki a ynxu.... da sauri ta juya jikinta har bari yake saboda tsoro da raxana. My wattpad Phertymerh1 *Babana da mijina....* ©fertymerh Xarah 💞 28 Tana shiga motar ta tabar gurin, bata jima da ficewa ba suka fito dai dai da qarasowar police, Duk ynda sukayi basu ci nasarar kama ko ďaya ba kuma sunqi su bisu saboda suna tsoron makaman dake hannunsu, Deedah kuwa har sukaje suka kai Kuďin baya cikin walwala, iman ta taka dokar da yabata, da wani abu ya same ta fa, sai ya nufi gida bayan sallar isha'i, Niyarshi yau sai Allah kaďai xai saukar dashi daga fushinshi, 'duk daďin bakin nan nata da tattausan labbanta masu mantar da wani ďa namiji 'duk wani jinkai taqama da muqaminsa, 'duk kissa da kisisinarta, 'duk lailaya da rarrashinta, 'duk taushin hannunta, 'duk kukanta da shagwabarta sunyi kaďan su sauke fushinsa akanta, Amma Kuma sai me suna haďa ido da ita duk sai yaji jikinsa yayi sanyi, wani sonta na ratsa xuciyarsa, sai ya ďauke kansa daga gareta ya nufi ďakinsa, fauxie na yaya sannu da xuwa bai tankata ba, iman Kuwa kallo tabisa dashi kallone na tuhuma, ta dawo da kallonta ga fauxie, 'sai me ya rage kuma? 'anty saura tracing, 'ke baxaki iya tracing cow bane, kiyi da kanki a exam baxaki ganni ba ballantana kiyi tsammani xn maki, tayi shiru tana kallon littafin, pencil a bakinta ta dubi Iman, 'anty yaushe xaki kaini inda Amira, 'ba ynxu ba sai kunyi hutu, ta cigaba da tracing Iman na gyara mata harta kammala, ta maida littafin a Jakarta, fauxie ta kwanta a jikinta tana waqe waqenta na makaranta har tayi barci, iman ta dubeta har wani daďi taji datayi barci da wuri, Fauxiya akwai rigima masu aikin gidan ma bata bari ba, ga surutu kamar hauka, ta dubi qaramin bakinta ta tsukeshi sosai, tayi murmushi ta cigaba da kallon da takeyi, Ta jima sosai kana ta ďauki fauxie tayi ďakinta da Ita, addua tayi mata dai dai kunnenta kana ta fice, Deedah na xaune da laptop ďinsa ta shigo, fuskarsa ba walwala batasan meke damunsa ba, taje ta sauya kayanta xuwa na barci kafin ta dubesa, 'kagayamin dalilinka na hanani xuwa super market yau, kamar baxaiyi mgn ba sai Kuma ya bata amsa batare daya kalletaba, 'meyasa tun farko baki nemi sanin dalilin ba sai ynxu bayan kinje kin dawo, 'na tambayeka ne baka gayamin ba shiyasa naje cos baka taba hanamin xuwa ba, 'ban taba hanaki ba kuma dana hanaki sai kikaje saboda bn isa da ke, da wani abu ya sameki fa? 'taya akayi kasan naje can? ya ďan dubeta, 'labari naji kuma an gayamin har fito dake akayi waje, 'Waye ya gayama, ai Kaine Deedah, kagayamin ko Kai Waye xn jure komai a rayuwa amma banda xama da barawo, ya mata wani irin duba 'ni ne barawo Iman, ni kika jifa da wannan mummunan kalma, 'Naji muryanka Deedah, Naji qamshin turarenka duk da banga fuskarka da idanuwanka ba, idan xargin da nake Gaskiyane ka cutar da rayuwata Deedah, 'wannan ba hujja bace Iman, am a good man with a good personality, kowa ya sani kema shaidace, turare bani kaďai ke dashi ba kuma na maxa ne, murya Kuma amonta kikaji amma bani bane banje super market ba sai dai kuma an gayamin an ganki wani ya fito dake, Waye shi? Miye haďinki dashi daxai taimakeki har ya riqa hannunki, Hankalinta inyayi dubu ya tashi, qafafunta na neman gagarar ďaukarta, muryarta har rawa takeyi musamman yanda taga fuskarsa a ďaure kada wannan dalilin ne yasanya yake ta fushi tun ďaxu, 'ni bakomai tsakani na dashi, ban sanshi ba bansan dalilinsa na taimakona ba, nayarda ya riqa hannuna saboda turarenka danaji a jikinsa Ina xaton kaine, 'saboda kin daukeni barawo, ban yarda dake ba idan ba kin sanshi ba baxai taimake kiba, Hankalinta ya tashi ta soma rantse rantse tana hawaye, yana kallonta yaji daďi cos ya sami dabarar wanke kansa, 'Ni yau kake xargi, shekara nawa muna tare dake, 'kema xargina kike yi bakiduba tsawon lokacin da muke tare dake ba kai tsaye xaki kirani barawo, 'ban tabbatar ba Ina so nagane ne amma kayi haquri baxan qara tsallake umarninka ba, kuma ba xarginka nake ba kawai hasashe ne, 'nima hasashe ne, xo ki kwanta, ta saki ajiyar xuciya fuskarta da murmushi ta kwanta haďe da lumshe idanuwanta, kallonta yake kafin ya maida kansa kan abinda yake, shi kaďai yasan planning da yake haďawa su oga nas dan baxai iya cigaba da xama dasu ba, duk da ynxu yadaina fashi ya daina harbi sai dai yayi rakiya kawai ya qudira a ransa ko police suka biyosu baxaiyi harbi ba sai dai ya nemi hanyar tsira amma baxai taimaki kowa ba, lokaci yake jira..... 2 days~ Tana xaune da fauxie a falo, kanta take gyaramata, tana mamakin irin tsawo da cikar kai na fauxie, gashi da tsantsi shiyasa ba'a fiye yimata kitso ba warwarewa yakeyi sai dai kalaba, 'anty kinga baba ya ganni wai inxo yabani chocolate, 'karkije kome ya baki kada kici, 'ai anty ban karba ba, harararsa nayi nace banaso, 'good girl gwanda da baki karba ba amma kada ki qara harararsa, 'Kuma anty naganshi ya siyo sabuwar tedy xnje yabani, _(ba tedy bace jikinta ne kamar tedy acikinta duk kayan tsafinsu ne da sima ta qara rabamasu duk ynda xasu tafiyar da alamuransu xasu yi da ita, duk Wanda tashi ta sami matsala ya sami matsala cewar Sima)_ 'idan na sami lbrn kije ko gidannan sai nayi maki duka a gidannan Kuma muyi faďa dake, kibari yaya yaxo ya qara siyomaki wata, Ta soma dariya taji daďi amma tasanya a ranta sai taje ta ďauko wannan, * A hospital yau ma kamar kullum ta karbi haihuwa jaririn baixo da rai ba, tana tsaye nurses xasu karbi haihuwa Kuma yaran su rayu sai ta shiga tsoron kanta, har aka tashi aiki bata qara leqa labour room ba sosai ta shiga damuwa, Da dare bayan sun gama shirinsu na kwanciya ta sanardashi abinda ke faruwa, yayi shiru yana naxari bai taba kawo baba bane a tunaninsa sai ya qara rarrashinta tare da kwantar mata da hankali, inda yayi ta bata misalai da yawa da suka qunshi haka, yace su dage da addua Allah xai shige masu gaba, sai ta saki ranta murmushi a fuskarta taja dogon hancinsa, Deedah ya canxa I agreed, yana xaunawa yaji matsalata ya Kuma sharemin hawaye na, Murmushi yayi Wanda ya qara fito da kyawun fuskarsa, 'Ina son Iman da farin cikinta dole na cnxa, 'Ina son mijina, xn jure xama dashi a kowane hali... ta sumbacesa a gefen kumatunsa ta kwanta tana murmushi tana jin sonsa ta ko ina a jikinta, Yayi mata wani irin murmushi da har abada baxai gushe daga xuciyarta ba, Yabi bayanta ya kwanta hot kisses yake blowing ta kowacce kusurwar jikinta, ita kanta batasan Ahmed ya iyasu ba sai a yau ya mantar da Ita damuwarta, ya ďauke ta ya jefata a duniyar soyayya harta manta damuwarta da halin da take ciki har batasan lokacin da tasa hannu ta rungume abinta sosai a qirjinta ba. Asuba ta gari Iman & Deedah, Getting better, tnx for your du'a, still nid ur prayers. My wattpad Phertymerh1 *BABANA DA MIJINA....* *©Fertymerh Xarah 💞* 29 Dr. Deen ya fito daga office ďinsa hankalinsa a tashe, yanayinsa xai nuna ma baya cikin kwanciyar hankali, Kicibis sukayi karo da juna, files ďin dake hannunta suka xube a qasa, 'oh gosh, am sorry Dr. Fatyma...... sai ya fice da sauri, tabi bayansa da kallo bayan ta girgixa kanta kana ta sunkuya ta kwashe files ďin ta fice, Kallo ďaya yayi mata ya gane she is in bad condition, jikinsa har rawa yake Idanunsa sun kawo kwalla ya sunkuya ya sumbaci goshinta haďe da sarqe hannunsa cikin nata, 'I don't want you to die, pls karkije kibarni, my life will be useful without you, Ta rumtse idanuwanta cikin azabar ciwo, hawaye ke fitowa a idanuwanta, 'yaushe xn haihu Deen? ya dubi cikin nata kafin ya maida kallonsa gun ta, 'da sauran lokaci but bari na duba Merah yaxo ya duba ki, ya fice da sauri....... * 'Am tired salima, nagaji da wannan hali naki, aure xn qara..... Hankalinta inyayi dubu ya tashi da jin kalaman Sa'eed, ta juyo tana kallonsa bayan ta jefar da wayar dake hannunta, 'aure fa, meyasa Sa'eed? 'you know the reason and you are asking me why? ni xn xauna na koya maki yanda xaki tafiyar da rayuwar auren kine, can you imagine wai Mai aiki yau ke wanke min undis, oh god wannan wace irin rayuwace da tonon silili, Ni banida sirrin kaina komai nawa sai mai aiki tasani instead of you, 'ynxu saboda wannan xaka qara aure Sa'eed, to kayi haquri baxata qara wankewa ba, xn riqa haďawa mai wanki duka yana wankewa hope is ok? Yayi shiru Kamar ya rufeta da duka yakeji, ya dafe kansa da hannuwansa duka biyu kallonta yake cikin tsana da takaici yana tuna soyayyarsu kafin aure yanda take kula dashi kamar xata haďiye shi dan so, ynxu sunyi auren ba kulawa, idan mai aiki bata mishi ba shi xaima kansa, ruwan wanka ma shike haďawa kansa, barin ma ta kansa yaransu da basa Samin kulawa, dole xai qara aure, amma wa yake so waxai aura? Xuciyarsa nayi matuqar bugawa, matar amininsa yakeso, fatyma yakeso, he will be happy with her, she is loyal to her husband inama shine, ynda yaga tana kula da Deedah bai damu ba, ya rumtse idanuwansa, yana matuqar sonta, yana son bata kulawar da ta rasa gun miji itama ta bashi kulawar da bai samu gun matarsa ba, ganin yayi shiru salima ta matso, 'kayi haquri xn gyara, ya dubeta Idanunsa jawur, 'kiramin Indo, 'me xatayi ma, gayamin xnyi ma, 'ki kiramin Indo nace..... ganin yanayinsa ya sa ta fice da sauri bata jima ba sai gata sun dawo tare, Indo ta tsugunna gabansa, kallonta yayi, 'xaki aureni Indo..... Tambayar ta xo mata a baxata ta ďago tana kallonsa wani ihu da salima ta sanya sai da suka tsorata gabaki ďayansu, tayi Kan Indo xata daketa ya tareta, 'wallahi ka aureta sai na kasheta na kasheka, Baka isa ba Sa'eed, ka cuceni ta soma kuka sosai, yayiwa Indo alama ta fice, ta fita da sauri ya juyo gareta fuskarsa ba alamar Wasa, 'believe me salima and I mean it, idan har baxaki gyara halinki ba, aure xnyi, I can't continue like this..... ya juya xai fice sai Kuma ya juyo, 'karki yarda ki taba Indo ko ki korata gidannan, idan tabarshi kema kin barshi dan bakida amfani acikinsa...... Salima ta xauna gefen gado ya shiga duniyar tunani dole xata cnxa halinta ta kawar da Indo daga mijinta, * Dr Merah da Dr. Deen ke tafiya suna tattauna Mgnr ciwon matarsa har suka isa ďakin haihuwa, Har ynxu da sauran lokaci Deen, in lokacin yayi bata haihu ba dole xa'a mata tiyata, Deen ya sauke numfashi da kyar yana kallonta itama idonta akansa tsoro ya cika xuciyarta gani take kamar baxata tashi ba, Merah ya cigaba da faďin, I don't want to miss my flight so xn damqawa Dr fatyma case ďin, ko tiyata ne xata iya mata, 'Shikenan Dr. Merah, a tare suka fito suka nufi office ďinta, Tana xaune tana duba wasu takardu suka shigo, ganinsu ya sanyata cire farin glass ďinta kana ta tashi cikin girmamawa tana gaidasu, 'Uhm likita case ďin matar Dr Deen, xn damqa miki, idan bata haihu ba ayi mata tiyata ga files ďin ta, jikinta ya ďauki rawa ta dubesa, 'why me Dr Merah, kabawa wani case ďin, am busy patients sun min yawa, 'I trust you fatyma, help me, Phoenix xnje by 10 o'clock, I nid to see sultan tun last week baida lfy so I don't want to miss the flight.... 'but likita, amma.... uhm.. Muryarta na soma rawa hankalinta ya tashi, 'why are you behaving like this fatyma, wannan bashine Karo na farko da kika soma tiyata ba, ya ajiye file ďin ya juya da sauri ya bar office ďin, ta maida kallonta ga Deen tuni idanunta sun kawo kwallah, 'what's wrong likita? ta girgixa kanta bayan ta ďauke guntuwar kwalla da ďan yatsanta, ta ďauki file ďin tana dubawa, 'Hajara Deen, shine rubuce akai, ta rufe file ďin kamar xatayi kuka tsoronta ďaya ta karbi haihuwar jaririn yaxo ba rai tafi kowa sanin Waye Dr Deen mutum ne mai matuqar son yara ya jima yana kwadayin haihuwa sai wannan karon matarsa ta samu, yana aiki a paediatric, amma saboda son da yakewa matarsa baxai misaltu ba, bashida buri ko mgn a asibiti kamar ita musamman da xata haifa masa yaron, idan yaron ya mutu a hannunta fa..... 'please fatyma let's go.... ya Katse mata tunani, tayi firgigit tana kallonsa kafin tabi bayansa, 'naquda taxo gadan gadan sai dai baxata iya haihuwa da kantaba dole yasa hannu ayi mata tiyata, ta Kira nurse's suka turata theater room harda Dr. Deen aka shiga, Komai akan idonsa yanda fatyma ke tafiyar da aikinta, yana kallon lokacin da ta fasa cikin matarsa nurses na taimaka mata, tana ganin jinjirin ta kasa cirosa saboda tsoro Kuma yana raye, sai tayiwa wata nurse da nuni akan ta ciro jaririn da kanta, Bayan ta ciro suka nufi gurin gyarashi Deen yabi bayansu farin ciki fal a xuciyarsa, Iman murmushi tayi cikin samun nasara kana ta soma ďinke uwar, Baba dake ďakin a labe kusa da Iman yana jiran ta karbi haihuwa ya xuqe jinin jaririn ya bata rai sai dai tsawar da sima tayi masa ta tsoratashi, ba Wanda yaji sai Shikadai kamar yanda bamai ganinsa, _'ka ďauki jinin matar tunda ta hana jinjirin, ka kashe uwar._ Bayan sun kammala gyara maman suka nufi amenity da Ita, batasan meyasa take jin mutuwar jiki ba, har wani Xaxxabi takeji ga xufa dake karyo mata ta ko ina, Ta fito ta sami Dr Deen rungume da jinjirin sai faman murmushi yake, farin ciki fal a xuciyarsa, ta leqa yaron kyakkyawan gaske ne tana son karbarsa tana tsoro, murmushi kawai tayi a xuciyarta tana Allah ya raya yaron, Wata nurse ta fito da sauri tana faďin, 'she is bleeding through her nose and mouth, 'who? Fatyma ta tambaya hankalinta a tashe, shima Deen ya juya yana kallon nurse ďin jin ko Waye, 'Mrs Deen.... Fatyma da Deen suka nufi ďakin, bakinta da hancinta sai jini ke xuba, Dr ya miqa jaririn ga wata nurse ya nufi hajara ya rungumeta xuwa jikinsa, tana son masa mgn ta kasa, akwai abinda takeson gayamasa bakinta ya qi buďuwa haqoranta sun kafe, Fatyma Kuwa kusan mutuwar tsaye tayi kamar mutum mutumi ta xama sai kallo da take binsu dashi idanunta na fitar da kwalla, kafin wani lokaci rai yayi halinsa batasan da haka ba sai da taji Dr Deen yana faďin, _'Inna lillahi wa inna ilaihir raji'un_ kusan sau uku, kafin ya ďora kansa jikin matar yana kuka, itama batasan sanda Kukan ya xo mata ba. My wattpad Phertymerh1 [20/03, 5:12 p.m.] Pherty 🎤👯: *Babana da mijina......* ©Fertymerh Xarah 💞 30 Da kyar ta iya janyo qafafuwanta ta fito daga ďakin, idanunta sunyi luhu luhu sun kumbura, ga xuciyarta dake tashi kamar mai jin amai, Tana tsaye a corridor tare da Dr Umayma taga an fito da gawar, ta ďauke kanta gefe hawaye sharrrrr kamar da bakin fanfo, 'ya salam Dr fatyma, kinbi kin damar da kanki tunda bake kika kashe ta ba miye na kuka haka, kwanakinta suka qare, ba itace gawar farin a hannunki ba meyasa kika damu, Ta girgixa kanta tana share kwalla, 'ba komai, ina tausayin Dr Deen ne, da jaririn da aka bari, 'hakane amma kidaina damar da kanki, Iman ta matsa gefe da sauri tana kwararo amai, Dr Umayma sai sannu take mata, ta bata pure water dake hannunta ta kuskure bakinta, 'xo muje na duba ki, banyarda dake ba likita, iman murmushi kawai tayi tabi bayanta, 'oh God, jininki ya hau sosai 180, narasa gane kanki fatyma, meke damunki, Iman ta sunkuyar da kanta qasa tana faďin, 'bnda damuwa bayan stress, bana samun barci I don't know why, ga aikin asibiti hutun da kuke samu bana samu, komai Dr fatyma komai sai ni fa...... 'Gaskiyane Kuma fa likita, amma ai Kuna da farin jinine, mgnr gsky ma cikin mu kin fimu haquri shiyasa kowane likita ya tashi kece, Iman ta sauke ajiyar xuciya tana yatsina fuskarta, 'Ina ji inada ciki ne, na jima bnsha tablets ďina ba, 'nima nayi xaton haka, Allah ya tsayar da wannan? 'Amin ta faďa xuciyarta a raunane, Tun da ta dawo gida take kwance, sallah kawai tayi abincima ta kasa ci, fauxie na gefenta sai surutai take mata, 'kiyi shiru haka fauxie, ke bakya gajiya ne, 'anty kema kina rubuta noise makers ne? Iman ta dubeta, 'eh idan bakiyi shiru ba gobe xnsa anty tayi maki bulala, I fauxie ta matsa baya kaďan da Ita tana kallonta a shagwabe, 'anty ai ba class bane keba monitor bace, 'tor kije falo kiyi surutunki ko kije indasu adama, kina damuna anan Inaso nayi barci, fauxie ta dawo jikinta ta kwanta tana faďin, 'anty jiya nayi mafarki, 'mafarkin me, 'baba ya mutu..... sai da gaban Iman na faďi ta dubi yarinyar, 'Kuma anty, malam yace duk wanda ya mutu baya dawowa, wai xa'a sanyashi a rami a rufe da qasa, baxai qara cin abinci ba kuma baida friends shi kaďai xai xauna wai hakane anty? Iman ta gyada Kai tana kallonta, 'Kuma anty wai malam yace idan ka riqe sallah itace xata tayaka kwanciyar kabari, 'idan ka riqe karatun qur'ani watarana xai yi ceto a gareka, anty wai hakane? ta gyada Kai tana kallonta har lokacin jikinta a sanyaye yake da Kalaman yarinya, 'tor anty idan baba ya mutu shi qur'ani baxai cecesa bane? 'inji waye ai shi musulmi ne, 'tor anty ai baya karanta qur'ani, kuma baba baya sallah, na gayawa malam babana baya sallah a class jiya, Iman ta xaro ido tana kallonta, 'kin gayawa malam baba baya sallah ke uban Waye ya gaya maki baya sallah, (ta kai mata duka ta goce tana tunxure baki), 'a'a kajimin yarinya, kewai ba aljannu akan kine Anya ke kaďai kike rayuwa kuwa? dole sai a gabanki xaiyi sallah ne, 'anty nace malam yaxo yayiwa babana mgn ya dinga sallah shi kaďai nace kuma anty a..... 'shut up silly girl, why can't you control your mouth fauxie, angayamaki agaban kowa ake faďin kowacce magana ne, shikenan is your life friends ďinki basu sanni ba ke kaďai suka sani xasu riqa cewa babanki baya sallah tunda baki iya bakinki ba kuma kowa xai sani kiji kunya, 'anty bana jin kunya cos he is not my father, ai yace shi ba babana bane indai na ce masa baba, wai yaya ne babana, hakane anty? 'ke xo ki fice min daga ďaki inba haka ba bakinki xaiyi jini, ta diro daga Saman gadon ta ďauki tedy ďin ta tana kallonta, 'Anty Kice adama tayi tuwon semo, da miyan kubewa, 'in kinje ki gayamata, 'Anty in Kira Suleiman? 'me xaiyi min, inace nace ki fice daga ďakin nan ne? 'anty Kice ya siyomin ice cream babu a fridge, 'baxan ce ba ni komai nadaina siya maki a gidannan tunda bakyajin mgn baxaki daina surutu a rayuwarki ba, 'Anty kiyi haquri nabari baxan qara ba, tayi mata banxa, 'please Anty, nan ma ta kyaleta, ta qara matsowa, 'kinji anty.... tasan baxata kyaleta ba, 'tor naji, tayi dariya ta fice da gudu tana kiran Suleiman.... [20/03, 9:35 p.m.] Pherty 🎤👯: Bata ganshi a gidansu ba sai ta nufi gidan baba tasan baxai wuce can ba, Da ďar ďar ta shiga falon a hankali take kiran, 'Suleiman, Suleiman..... batason wani ya jiyota ko cikin masu aikin gidanne, Yanajin muryarta ya fito daga wani ďaki a hanxarce, 'yar amana dama ke nake nema, xo kiji, 'anty tace kaxo ka siyomin ice cream, 'tor xo kigani, sirri xamuyi karki gayawa kowa kullum xn riqa goyaki muje yawo a Roba Roba ďina kina so? ta gyada Kai tana kallonsa da murmushi, ya riqa hannunta yana waiwaye Kada a ganshi, 'je ďakin baba ki ďibomin kuďi, kiyi sauri Kada wani yazo yagani, batare da tunanin komai ba ta faďa ďakin tsafinsa, kuďi ne birjik a qasa ta ko ina, Akan gado a qasa sai faďowa suke ďaya ďaya kamar yanda leaves ke faďowa a itaciya, Ta kwashi kuďin tana kallon ďakin, har xata fita sai idanunta na sauka akan tedy ďinnan ta tsafi, ta ďauka, sai taga wata kwalba da ruwa acikinta ga wani abu ja aciki yana yawo aciki (rayuwarsa ce aciki cewar Sima) sai abin ya birgeta, ta duqa xata ďauka Suleiman ya soma mgn, 'me kike jirane, ko kaďan ne ki fito Kada wani yagani, buqatata nasami na cnxa waya na kaiwa ummata sauran, dan ma Ina sata Ina haďa kayan aure ynxu, Ta juya ta fice tana waiwayen kwalbar Abinda ke ciki yana yawo ke birgeta ta qudira aranta xata dawo ta ďauka, Tana fitowa ya ďauketa cike da farinciki cos ta ďebo da yawa suka fito yana faďin, 'wannan kuďin haka kikace anjima naje xnce da baqar Leda, ya karbi kuďin ya cusa aljihunsa kwata kwata hankalinsa bai kai ga tedy dake hannunta ba azatonsa tatace, 'Kada ki gayawa kowa kinji, 'tor xakaje dani yawo, 'kwarai ma kuwa baby, kina gaban mashin ďina, aike abinso ce gareni, gaki yar fara kyakkyawa matar Manya ko? tayi murmushi tana kallonsa, 'muje anty tana kiranka, Tana xuwa takai tedy ďakinta ta boye qarqashin gadonta bataso Iman tagani tayi mata faďa, Ranar Deedah ya dawo suna xaune ďaki dashi take bashi lbrn abinda ya faru a asibiti, 'Allah yaji qanta amma Waye Dr Deen kamar nasanshi, 'kasanshi mana wannan na paediatric wanda muka taba kai fauxie gurinsa sanda tana Mura, 'na mantashi amma na tausayamishi kodan jaririn, 'idan ka ganshi xaka tuna, wani fari kyakkyawa haka, yanada fara'a sosai, 'kinaso kice yafini kyau kenan? 'chab ni na isa, akwai namijin da yafi mijina kyawu ne, kawai Ina misalta ma shine, yayi murmushi ya ja dogon hancinta 'you are the best my only wife, Ina sonki Iman, itama murmushin tayi haďe da kwantawa a qirjinsa, Bayan sati ďaya tana shiga asibitin kayanta kawai ta ajiye a office ta nufi labour room tun kafin ta shiga take jiyo kururuwar wata mata, da sauri ta qarasa tana tmbyr meya sameta, 'yauwa Dr help us, tana labour Kuma aljannunta suka tashi, Iman ta matsa tana kallon matar a bakinta addua take, matar mai aljannu tana juyowa taga Iman sai taga baba tsaye a gabanta, ita kaďai ke ganinsa saboda aljannunta, ta taso xata capki Iman a xuwan shi xata riqa akayi Saurin riqata dai dai lokacin haihuwa na xomata, Kwata kwata Iman ta manta bata hayyacinta saboda tausayin matar, sai kawai ta karbi haihuwar, yaron na hannunta baba ya soma tsafin, Idanun matar suka jujjuye, wani qarfi yaxo mata ta xabura da qarfi ta capko wuyan Iman ta shaqureta iya qarfinta. My wattpad Phertymerh1 [22/03, 4:45 p.m.] Pherty🎤👯: *Babana da mijina....* ©Fertymerh Xarah 💞 31 ....Sai na kasheka, sai na kasheka matsiyacin banxa, baka isa ka kashemin yaro ba, idan ya mutu kaima sai ka mutu, Idanun iman sun juye, sai kakarin mutuwa takeyi, nurses ďin sai bugun matar suke yayin da wasu suka fita da gudu kiran masu taimako, Da gudu Dr Bakori da Dr Deen, da Dr Chris suka shiga ďakin, Sosai ta galabaita kafin su banbareta daga jikinta, ragwab ta xube gurin a sume, Dr Deen ya ďauke ta da sauri ya fice da Ita Dr Fulani na bayansa yayinda sauran likitocin suka rufawa marar lfy suna dubata sai fisge fisge take shi kansa baba tuni yabar ďakin ya bata tun lokacin da yayi arba da matar yaji hankalinsa ya tashi, Ba Wanda yayi xargin wani abu inda Iman ta sami sauqi kenan, kuma jaririn ya rayu sai dai har lokacin Iman bata farfado ba ta jigata sosai, 'ko akira mijintane a sanardashi cewar Fulani, 'A'a kibarta xata farfado, wuyanta yayi ja sosai wannan ba qaramin riqo tayi mata ba cewar Bakori, 'Fulani tace boyar Allah tabani tausayi Wlhy, fatyma batada matsala a rayuwarta Duk Wanda ya xauna da Ita xaiji daďi, Dr Deen na tsaye hannuwansa sarqe a qirjinsa yana saurarensu, idanuwansa xube akan fuskarta, komai bai ce ba, Fiye da minti talatin kafin ta farfado, da addua a bakinta tana buďe idanuwanta hawaye na soma xubo mata, Sai suka taru akanta dukkansu suna bata baki, rarrashinta suke tare da fahimtar da Ita wasu abubuwa game da irin Wannan dake faruwa, Sai taji xuciyarta tayi sanyi ita matsalarta Kada a xargeta akan wani abu amma tayi alqawari a xuciyarta kome xai faru a asibitin baxata qara leqa labour room ba, baxata qara taimako ba iyakarta duba patient, Bayan kowa ya fice ďakin ya rage ita da Dr Deen, sai ta dafe kanta da hannunta duka biyu tana tuna abinda ya faru a ďaxu, ďagowar da xatayi suka haďa ido dashi yana kallonta sai da gabanta na faďi, tayi qarfin halin mgn, 'Likita ya haquri? Ya sauke numfashi bayan ya ďauke idonsa akanta, 'haquri mun gode Allah fatyma, shima yaron ya koma ai, ta dubesa a razane, 'shima ya rasu? ya gyada Kai yana kallonta, 'Subhanallah, Wayyo Allah, Allah ya gafarta masu ya baka haqurin rashinsu ya musanyama da mafi alheri, Yasa yatsa ya ďauke guntuwar kwallah yana kallonta, 'I have no one in my life, babana kawai, no mother, no wife, no child, no brothers an sister, only my father and family, Ta sauke ajiyar xuciya kanta a qasa batasan dalilinsa na gayamata wannan ba sai dai a xuciyarta tana tausayamasa, Daga wannan bai qara cewa komai ba ya fice daga ďakin, itama fitowa tayi ta nufi office ďinta kayanta ta ďauka ta fice daga asibitin gaba ki ďaya, Ranar Sa'eed ya xo gidan, sun jima suna hira haďe da gayamasa matsalolin da take fuskanta a ynxu asibiti, yace xai tayata addua itama ta dage..... Baba yayi neman tedy bai gantaba hankalinsa yayi matuqar tashi domin matsafarsa ce aciki wacce da Ita yake bata ba'a ganinsa a duk sanda xaiyi wani sharri, ba shiri ya jewa sima da bayanin batan tedy ďinsa, ta ďauki wata ta basa, Tun daga lokacin yasa ido sosai akan gidansa dan ganin mai masa shige da fice a ďakinsa, Fauxie Kuwa kwata kwata ta manta da tedy da ta boye a under bed ďinta bata qara bi ta kanta ba, Some months..... Cikin Iman ya shiga watan haihuwa, duk wani so, kulawa da gata ba Wanda bata samu daga Deedah, yadaina fitar dare kullum yana tare da Ita komai shi ke mata, shi ke kaita asibiti kuma shi ke daukota, Soyayya suke mai cike da kulawa a tsakaninsu,duk burinsa na kan cikin a ynxu ita kanta Iman tasan Deedah yafi ta son cikin, Duk wannan abin da ake ciki baba bai taba sanin Iman Nada ciki ba, shi rabonsa da Ita har ya manta, saboda sun daina bincike akan ta ynxu qananan yara yake satowa yana kawowa sima tun lokacin da matar ta ganesa a asibiti bai qara shiga ba, Da dare ta fito kitchen ďauke da plate na nama, fauxie na bayanta da tedy a hannunta, ta xauna itama ta xauna kusa da ita, 'anty shi baby kullum sai yaci nama ne? 'Tace eh, 'tor anty ki sammin, 'a'a na baby ne kaďai wannan, ba kinci naki ďaxu tare da yaya ba, ta tunxure baki idanunta sunyi rau rau kamar xatayi kuka, iman ta ďan dubeta ta gefen idanunta, 'crying baby, kina taba jin baby yayi kuka Kuwa ? ta girgixa kanta tana kallonta, 'idan kikayi kuka ma baxai fito ba, shikenan bakida jariri, tayi Saurin goge fuskarta, 'anty yaushe xai fito? Iman ta miqa mata sauran Naman tana faďin, 'ya kusa fitowa ai, 'anty idan na mutu kiyimin sadaka, wai inji malam ana yiwa Wanda ya mutu sadaka, 'tor idan ni na rigaki mutuwa fa? 'nima xn miki sadaka anty, 'ai nafiso ki mutu kibarni dan Idan na mutu bansan ya rayuwarki xata kasance ba, bnsan inda xaki xauna ba, 'anty inda yaya xan xauna ko inda Amira, 'oh oh mutuwa ba ynxu ba fauxie, fata ta gari sai naga aurenki da sultan, 'anty ni bana sonsa yaya nakeso, iman ta dubeta, 'da gaske fauxie, ta gyada Kai tana kallonta, 'kinga shi yaya yana siyamin ice cream, chocolate, biscuits, tedy, yana daukana, 'tor shima sultan xai maki haka fauxie in banda abinki me xakiyi da mijina ai ya maki tsufa, 'anty ni banason sa yaya nakeso, 'ke Kinsan miye so ne? tayi shiru tana kallonta, 'kinga kin tadamin Kwaďayin ice cream ďauko min a fridge, 'babu shi na shinye, 'kiramin Suleiman yaxo ya siyomin, fauxie ta fice da gudu bata jima ba sai gata ta dawo, 'anty bayanan.. 'ďan lami fa? 'duk ba kowa a gidan baba, ta duba agogon hannunta 9pm, 'ďauko min hijab ďina da makullin mota kixo muje... Da gudu ta haura Sama taje ta ďauko sai tsalle takeyi, 'anty kema kina shan ice cream ashe, 'bani xnsha ba baby xai sha, 'baby ya iya sha ne anty, 'sosai ma.... ta buďe motar ta shiga itama fauxie ta shiga, [22/03, 7:05 p.m.] Pherty🎤👯: Sanda suka isa gurin siyarda ice cream ďin, tana daga cikin Mota ta baiwa fauxy kuďin taje ta siyo, tana kallonta daga cikin motar sai tsalle take Acikin shagon, ta sauke ajiyar xuciya dai dai lokacin da sukaji Kukan harbin bindiga, ta soma waige waige kamar mai neman wani abu, ta juya tana kallon fauxy dake tahowa da baqar Leda a hannunta sai Kuma taga ta tsaya tana kallon wani gu, ta sauke glass ďin motar da sauri tana mata mgn, 'what are you waiting for Fauxy? 'lah anty... ta juyo tana kallon Iman, ta daka mata tsawa, 'kixo mubar gurinnan, da gudu fauxie taje ta shiga motar ta rufe ta juyo tana kallon Iman dai dai lokacin da take tayar da mota, 'anty naga yaya da bindiga tare da wasu mutane, taja wani uban birki tana kallonta xuciyarta na bugawa, 'qarya kikeyi bashi bane, 'Allah anty naganshi, yana xaune a motar can ta nuna mata da yatsa, Iman taja motar xuwa inda ta nuna mata, ta ganshi da waya a hannunsa yana latsawa, a gabansa bindiga ce ajiye, ta juya tana kallon mutanen dana shiga ďayan shagon da bindiga a hannunsu, ďagowar da Deedah xaiyi suka haďa ido da ita, fauxie na ganinsa tayi waving hannunta tana murmushi, 'yaya.... , iman taja motar da qarfi, hankalinsa yayi matuqar tashi ya fito daga cikin motar tuni ta fice, Wani birki da taja sai da fauxie na faďi qasan seat, ta ciro wayarta ta Kira Suleiman haďe da gayamasa inda take, ji tayi baxata iya driving ba, qafafunta rawa suke dama gasu a kumbure, sai ta fito daga cikin motar tana kallon titi ita kanta batasan a wane hali take ciki ba, 'anty meyasa kika fito, kina jiran yaya ne, bata kula taba, 'anty kixo muje gida, nan ma bata kulataba, Tana gurin tsaye Suleiman ya iso akan mashin, yabiya mai babur kana ya nufeta, 'gani hajiya, ta miqa masa key ďin mota, 'qarasa dani gida, ya karbi key ďin ta xagaya gidan baya ta shiga motar, Sun fara tfy ya dubi Fauxiya sai ta wangale masa baki tana dariya shima dariya yayi mata, 'kagani mun siyo ice cream nida anty, ta nuna masa, 'eyye ashe xamu sha tare, 'ka Kira yaya ya siyoma naka yana can da bindiga a hannunsa, Iman ta ďago ta kalleta sai taji Suleiman na faďin, 'sai kace nice ke, ni naki dai xn sha, ta fara dariya.... Suna isowa gida Iman ta fice, sulaiemn yaja hannunta sukayi bangaren baba, 'jeki ďebo kuďi kafin baba ya dawo, xnje na siyo mai insa a mashin gobe muje yawo har inda qawarki Amira, 'da gaske, 'e mana, Ta shiga tana murmushi ta ďebo kuďin, sai ta ďauko wannan kwalbar da tagani ranar, tare da wata tukunya mai Jan kyalle akai, Tana fitowa tabashi kuďin ya cusa aljihunsa ya rakata har gida kana ya fice yana murna, Tana xuwa dakinta ta nufa ta ajiye kayan kana ta nufi ďakin Iman ga mamakinta sai ta sameta tana kuka sosai, 'anty meyasa kike kuka? Kuka take sosai Kamar ranta wannan dalilin ya Sanya fauxie kuka, suna haka Deedah ya shigo da qatuwar akwati a hannunsa, ya ajiyeta gefe kana ya nufi Iman jikinsa a sanyaye, 'kiyi haquri ki yafemin Iman, na Karbi laifina nagaji da boye maki, Ta dubesa da idanunta jawur, har wani qullewa mararta keyi, 'ka dade kana cutar dani Deedah, haram nake ci nake sha nake kwanciya acikin haram, ya katseta da sauri, 'bana ciyar dake da haram Iman, tun kafin na aureki nake wannan sana'a, ta xare ido sosai tana kallonsa xuciyarta na bugawa, 'amma Wlhy duk share ďin da ake bani ban taba sanya shi acikin kuďin halal ďina ba, kingansu nan sune acikin akwati nake tarawa a yau na kawo dan ki yarda dani, 'babu wata sauran yarda tsakanina dakai Deedah, baxan iya yafe ma ba baxan iya cigaba da xama dakai ba tsawon lokutta da dama kana cutar dani, ka sake ni Deedah, ta fashe da kuka sosai, Hankalinsa ya tashi ya juya yana kallon fauxie, ice cream take sha hankalinta baya kansu, Kukan Iman har cikin xuciyarsa yake jinsa sai ya tsinci kansa shima yana Kukan, 'Iman inayin sata ne badan na so ba, na fara ne sanadiyar ummata da bata lfy domin na siyamata magani, bayan mutuwarta na nemi aiki ban samu ba saboda banida ko Naira da xn bada a Samomin aiki, oga nas ya sanyani wannan aikin ta dalilinsa na shiga wannan harka, bayan na sami aiki na nemi na fita sukamin baraxana da rayuwata, na cigaba da xama dasu badan naso ba amma Wlhy Iman ban taba amfani da duk kuďin da Muke robbery ake rabawa ana bani nawa, kingansu duka acan, halal ďina ne a account ďina kuďin albashina, duk abinda ke gidannan da kuďi na nasiya, saboda ke tsawon watanni nan nadai na bibiyarsu nake xaunawa dake, sai na fahimci suna harin rayuwarkine suna so su kasheki saboda xn bar fashi ta dalilinki, yau ma dana bisu tsautsayine bn fita daga motar ba, Ina bibiyarsu ne saboda ke bana son Abinda xai sameki idan suka fahimci nadaina fashi, believe me Iman wallahi bana fashi yanxu na dade da shiriya tuntuni, ki yafemin Iman Kada ki rabu dani kodan yarona dake jikinki.... ta dubi cikin nata kafin ta maida kallonta garesa, 'I can't forgive you Deedah, cikin ma bana so, I hate you Deedah baxan iya xama da barawo ba, meyasa ka boyemin tuntuni ..... 'please Iman, wallahi am not among them yanxu, tuntuni na tuba na daina, dan Allah karki rabu dani, Ya tsugunna gabanta yana roqonta, ta tureshi tana kuka sai ya saketa, baxata iya xama dashi ba, ransa ya soma baci ganin yanda ya qasqantar da kanshi gareta yana roqarta yasan abinda xafi amma ya kamata ta duba masa ta yafe masa, Kamar daga Sama taji muryar fauxie, 'anty me yaya yayi maki? suka juya suna kallonta, 'anty kiyi haquri, iman ta ďauke kanta gefe, fauxie ta matso gareta, 'anty malam yace ka xamo Mai yafiya a gurin mutane kaima a wajen Allah Mai laifine, 'kinji anty, please forgive him, 'shut up banxar yarinya, me kika sani a rayuwa, ko kin san tsawon lokacin da ake cutar dani, maxan nan guda biyu sun min illah a rayuwata, *Babana da mijina*, bama kamar Deedah dana daukeshi abokin rayuwata, ta dalilinsu na kamu da cutar hawan jini, jin daďina ragagge ne da kai Ahmed, baxan iya cigaba da xama da barawo ba ka sakeni, Wannan kalma ta barawo tana baqanta xuciyarsa, 'gwanda xama da barawo akan xama da matsafi fatyma, tayi masa wani kallo, 'Waye matsafi Deedah? 'Oho maki.... taja guntun tsaki, 'kabani takarda ta nace, 'baxan iya sakin ki ba Iman, kiyi haquri mucigaba da rayuwarmu a tare cikin so da kulawa kamar yanda muke a ynxu, mu kula da yaronmu da xaixo bada daďewa ba, 'I can't Deedah, I hate you, kafita rayuwata, ba ruwanka dani idan ba haka ba cikin ma xn illata shi xn kashe kaina Deedah...., Hawaye sosai ke fitowa daga Idanunsa, Ashe akwai ranar da Iman xata iya rabuwa dashi, iman xata iya gayamasa Kalamai masu xafi haka, to menene sauran jin daďin sa idan har xata iya kashe kanta saboda shi? ya dubeta, 'Am so sorry, xn fita rayuwarki kamar yanda kika buqata, inason rayuwarki da ta yarona, Ina sonki da gaske idan ke bakya sona, baxaki iya xama dani a kowane hali ba ki rufamin asiri, xn tafi na barki ki yafemin ki Kuma kulamin da cikina, Idan Kuma kinji wani abu ya sameni daga baya kece sanadi, ya juya yana sharar kwalla komai bai dauka nashi a gidan ba sai akwatin da ya shigo da Ita ta kuďi, Fauxie ta diro xata bishi Iman ta riqeta, Kalamansa ke mata yawo a kwakwalwa tafi kowa son mijinta, bacin raine daya mata yawa a xuciya but she truly love her husband, ta tashi da sauri tabi bayansa, Fitowarta gidan yayi dai dai da ficewarsa daga cikin gidan cikin motarsa, ta soma kwala masa kira, Ina ya riga ya fice, Tana tsaye bakin gate ďin hasken Mota na Haske mata jiki, Yaja wani birki cikin tsananin tsoro da mamaki, 'Iman yake gani da ciki, yaushe tayi ciki yaushe ya girma haka, Sam bashida lbr shida Sima....... My wattpad Phertymerh1 *Babana da mijina* ©Fertymerh Xarah 💞 32 *Dis page is for you Muhammad saleem & Maryam kaumi* Hasken dana dallare fuskarta ya sanyata juya fuskarta gefe ba shakka baba bane tasani Shikadai xai iya mata haka duk gidan, tasan ma'aikatan baxasu gwada mata hakan ba, Bai shigo ba kuma bai kashe fitilar motar ba, mamaki da kaďuwa ya sanyasa kasa motsi sai kallo yake binta dashi, Ganin abin bamai qarewa bane sai taja qafafunta da kyar har nauyi suke mata ta koma cikin gidan, Wayarta ta ďauka tana kiran Deedah amma yaqi ya ďauka daga baya ma sai taji ya kashe Wayar gabaki ďaya, Hankalinta yayi matuqar tashi sai take danasanin abinda tayi masa, tana son mijinta so bana Wasa ba, tana yi masa wani irin so marar misaltuwa bataso taganshi cikin wani hali ballantana irin Wannan da taganshi ya fita a ynxu, ta duba fauxie har tayi barci sai ta gyara mata kwanciyarta haďe da cillar da tedy dake Kan gado, Baba Kuwa da kyar ya qarasa yayi parking ya fito, da sauri ya shiga cikin gida kai tsaye ďakin tsafinsa ya nufa yana neman tedy ďin sa domin ya bata ya jewa sima da wannan sabon al'amari daya gani a tare da fatyma, Amma Kuma sai me? Wayam babu, hankalinsa ya tashi domin baxai iya bata ba dole sai da Ita kwata kwata hankalinsa bai bashi rayuwarshi dake cikin kwalbar da tukunyar matsafarsu bata gurin ba shi dai yaga wannan tedy ďin, Sai xufa yake yayin da babbar rigarsa tayi masa nauyi, ya cire ya cillata gefe hankalinsa tashe ya fito yana kiran Suleiman cikin ďaga murya, Suleiman Kuwa tuni ya fice daga gidan, yaje kashe kuďin sa bashida wata damuwa bayan su, Jin shiru ba alamarsa baba ya tara duka masu aikin gidan tun daga security masu girki, shara, wanki da guga mata da maxa dake gidan ya tambayesu Waye ya shiga ďakin bayan fitarsa, Ba Wanda yasani hassalima ba Wanda ya gani saboda bamai xuwa bangaren sa idan ba Suleiman ba domin shine Mai Kula da wurin Kuma ba Wanda yaga shigarsa Sannan baya xaton Suleiman xai shiga wurin domin ya ďauka Suleiman nada amana ne bayada bincike kosa ido akan Abinda bai shafesa ba, Ya tattarasu ya korasu daga falon ya cire hularsa yana firfita da Ita sai xufa yake hankalinsa a matuqar tashe tunaninsa yakasa bashi Wanda xai shiga ďakin ya ďaukar masa kaya, Iman Kuwa sai faman juye juye take ta kasa barci jikinta na bata ba lfy ba Deedah ďin ta take gani a duk sanda ta rumtse idanuwanta, Ina ya shiga Ina yaje wane hali yake ciki meyasa bai dawo gida ba she don't know... Daga ita har baba basu rumtsa ba kowa da saqe saqen xuciyarsa..... Deedah Kuwa bayan barinsa gidan wata qatuwar takarda ya ciro daga cikin akwatin, baya mantawa Duk inda yasan yayi fashi yakan rubutu ya ajiye kuďin da oga nas ya bashi a inda suka yi fashi xaiyi alama ya rubutu ga kason da aka bashi, Allah ne shaidarsa bai taba cin kuďin ba bai Kuma taba sha'awar yin sadaka dasu baisan dalilinsa na tariyar kuďin ba haka kuma ya kasa sanyasu a account ďinsa, sai ynxu ya gane dalili wato ya maida kuďin inda ya karbosu, is too late akwai inda baxai iya xuwa ba akwai inda yayi masa nisa, the best thing for him is to seek for forgiveness Mai yiwuwa Allah xai iya yafe masa, Allah gafurun rahim ne shi mai yafiyane ako wane lokaci, sai ya soma istigfari yana Mai neman yafiya ga ubangijinsa Mai yiwuwa xai sami sauqin xuciyarsa, A waje ya kwana cikin motarsa baya burin komawa Iman a ynxu har sai ya dawo normal, daďin sa ďaya bai taba kissa ba sai dai yayi harbi a qafa ko kuma ya tsoratar da mutum idan yayi masa gardama, Sai da yayi sallar asuba kafin yaja motar yabar gurin, da Wannan Safiyar Deedah ya soma xuwa inda sukayi sata yana maida kuďin dai dai yanda aka bashi nasa rabon ya nemi gafara, wani gu akarba wani gu Kuma abar mishi an yafe, manyan kamfani da boutique ne kawai baije ba, yana mai tsoron bayyanar da kansa gidaje kawai yake xuwa, Bai manta da mutumin da sukaje gidansa Wanda ya xagesu a mota ba har gidan yaje ya nemi gafararsa ya Kuma bashi kuďi sosai kafin ya dawo, Akwai gurare da Dama inda baxai iya xuwa ba ya maida kuďin, sai ya ďauki sauran kuďin yakai gidan marayu, daga nan ya wuce station yakai kansa ga hukuma shi mai laifine, Suka masa kallon mamaki, wannan ma da qarfin hali yake sun kasa yarda dashi mai yiwuwa wani plan ake son haďa masu basu sani ba, sai suka soma korarsa, Ya basu address ďin su oga nass idan har basu aminceba suje xasu gasgasta yana so hukuma ta kamasu domin sun dade suna taadanci a rayuwarsu, ya basu lbrn komai, sukace yaje gasu nan xuwa, Bayan barinsa gurin ya nufi inda su oga nass. Bangaren Iman Kuwa, tunda Safiyar ta Waye take jinta wata iri tana suspecting haihuwace sai ta Kira Sa'eed ko xai taimaka ya kaita asibiti yace yana xuwa baya gidane, 'Anty yau baby xaixo? 'Insha Allah fauxie, 'Anty wane irin abinci xaki bashi, 'madara, 'anty kibashi chocolate irin Wannan Mai daďi, 'jeki kiramin Suleiman fauxie, ta fita da gudu bata jima ba sai gata ta dawo, 'baya nan anty, Ta Kira number Deedah still switch off, ga Sa'eed har ynxu bai xo ba, ta ďauki kayanta na haihuwa ta sanya a mota, 'anty xn je asibiti inga baby, 'Aa idan kikaje surutun kima baxai barshi ya fito ba, kijira Suleiman idan yaxo akwai sauran kayana sai ku kaimin kinji, ta gyada Kai tana kallonta, ta shiga motar har ta tayarda motar ta juya taga fauxie tana kallonta, 'ki yafemin idan nayi maki wani laifi kinji qanwata, 'anty nima kiyafemin na yafe maki, Iman tayi murmushi tana ďaga mata hannu itama fauxie ta ďaga mata hannu harta fice, kana ta juya anan taci Karo da baba sai safa da marwa yake a gidan kamar wani xautacce, sai a lokacin ta tuna da Abinda ta ďauko a ďakinsa da gudu tayi ďakinta, under bed ta duba suna nan ynda ta ajiye ta soma dariya xatayi Wasa da kayan tasa hannu ta janyo tukunyar da matsafarsu ce aciki ta ajiye gefe kana ta janyo kwalbar da rayuwar baba ke ciki, suna rungume a hannunta ta fito falo, Tana saukowa Kan step a hankali gudun wani ya ganta yaje ya gayawa baba aniyarta xata maida masa wadannan sai ta boye tedy ďinsa tana Wasa da ita dan baxata maida ba, Ta ajiye kayan a qasa taje tana leqa harabar gidan har ynxu yana tsaye bakin falonsa sai waya yake faman Kira ga abokan harkarsa na gurin sima, Ta dawo da baya da baya ta ďauki tukunyar, kana ta ďauki kwalbar by mistake tukunyar ta faďi a hannunta qasa ta tarwatse jikinta ya ďauki rawa sosai taji tsoro shikenan idan baba ya gani sai ya daketa bata manta Marin da yayi mata ba, Fashewar tukunyar yayi dai dai da kamawar matsafan su sima da wuta, daga sima har gunkin da suke bautawa da mutanen danaje gunta a Wannan safiyar sai da suka qone qurmus lokaci ďaya wutar ta tashi from no where kafin sima tayi wani yunquri tuni takama jikinsu, tanaji tana gani ta narke a gurin kamar ruwa rayuwarta ta qare, Baba Kuwa Kamar yaji a jikinsa ynda tsigar jikinsa ke tashi, yana Waya kamar ance ya ďago Kuwa yaga fauxie da wannan kwalbar, Hankalinsa ya tashi taya ta sami kwalbar? 'ke fauxie... ke tsaya... Tana jin muryarsa ta tsorata jikinta yafara karkarwa musamman yanda ya tunkarota, ta soma gudu tana kuka a tsorace yana biye da Ita shikuma kamar mahaukaci sai ihu yake Acikin gidan Wanda ya janyo hankalin mutanen gidan garesu, Sa'eed Kuwa da sauri ya qaraso gidan sai dai a waje yayi parking motarsa shigowarsa gidan tayi dai dai da faduwar fauxie qasa kwalbar dake hannunta ta gangara gefe ďaya ta fashe har wani hayaqi ke fita daga cikinta, Ihu baba ya Sanya yayi kanta da duka, bugunta yake ta ko ina kamar Wanda aka aiko ga sa'ansa, Nan take numfashinta na ďauke, bakinta da hancinta sai jini suke fitarwa, da qarfi Sa'eed yayi kansa bai duba girmansa na kasancewa dajjito ba kawai ya ďauke shi da Mari, qoqarin baba na ganin ya illata fauxie duk da bata Numfashi burinsa yaga ya kasheta da hannunsa ta mutu, Sa'eed ya fahimci haka nan take ya ďauketa ya fita da Ita da gudu har lokacin bata numfashi asibiti ya nufa da Ita, Baba Kuwa tamkar wata Halitta ya dawo yanayinsa ya tsorata mutanen gidan, haqoransa sun xaxxago, akaifun hannunsa dana qafafunsa sun qara tsayi kamar na doki, ga wani gashi daya firfito a jikinsa tamkar wani dabba, A gaban idon mutane yake cin Naman jikinsa, fisgar jikinsa yake yana ci sosai, wa'iya xubillah, (Allah yasa mucika da imani muyi kyakkyawan qarshe Amin) Masu hankali da hangen nesa a gurinne suka soma yi masa addua suna tofa masa daga nesa, sai ya xube gurin ragwab, bakinsa da hancinsa sai fitar da jini suke kamar fauxie, Nan take maxan gidan suka taru akansa aka daukesa aka sanya a mota akayi asibiti dashi, Deedah Kuwa yana shiga gidan ya sami su oga nas kowane fuskarsa ba walwala, bai damu ba ya sami guri ya xauna, 'ance an ganka station yau mekaje yi Ahmed? Yaji tambayar oga nass daga Sama, 'ba komai naje kan wani case ne Kuma komai ya daidaita, 'bn yarda dakai ba Deedah kwanakinnan ka cnxa mana, lokaci yayi da ya kamata mu rabu dakai kaje ka huta a taka rayuwar mukuma mu cigaba da jin daďin duniyar mu, Kafin Deedah ya ankara sai jin saukar bullet yayi a qirjinsa, ya dafe gurin yana kallon mai Harbin oga nass ne, kafin yayi yunqurin sake Harbin Deedah shima yaji an harbesa a qirji, police din dake bayan Deedah ne, Nan take gurin ya kaure da harbe harbe (dama masu irin Wannan sana'a a haka suke qarewa wasu Kuwa suke kashe junansu da kansu, Allah ya shiryamu da zuri'armu gabaki ďaya Amin) Police ďin sukayi nasara Wannan karon sun kashesu da Dama yayinda suka kama wasu suka sanya masu ankwa, oga nass na cikin mutanen da suka mutu, Deedah Kuwa baisan inda kansa yake ba, numfashinsa ma da kyar yake fita, jikinsa duk jinine ga bakinsa ma ya soma fitar da jini sai suka garxaya dashi asibiti, Iman Kuwa tun bayan xuwanta asibitin Dr Merah ya duba ta, 'yace da saura likita, amma kafin lokacin idan kina iyawa kiďan yi exercise ko kaďan ne, Tayi murmushi dama ba naqudar takeji sosai ba, sai ta fito harabar asibitin anan ta ci Karo da Dr Deen, Bayan sun gaisa yake tambayarta lfyr jikinta, tana gayamasa maimakon ya shiga asibitin sai ya biye mata suna exercise ďin xagayen asibitin suke a tare suna hira, Haka xuciyarsa take mai tausayin mata ne musamman masu irin Wannan lalurar, yana tuna matarsa itama yakan sata ta xagaya Acikin gida, kasancewarsa da Iman yau yasa komai ya dawo masa sabo, Sun xagayo kenan taga motar Sa'eed ta shigo asibitin taja ta tsaya tana kallonsa, 'Wayyo Sa'eed bai sameni gida ba shine ya biyoni har asibiti, Dr Deen ya juya yana kallon inda take kallo tana Mgnr dai dai lokacin da Sa'eed ya fito ďauke da fauxie a hannunsa, Turus taja ta tsaya, fauxie ce meya sameta, taja ta tsaya idanunta a bude hankalinta a tashe har ya iso, Yanda taga fuskarta a kumbure Kuma ko ina jini hankalinta yayi matuqar tashi ta fashe da wani irin kuka tana ganin Dr Deen ya karbeta yayi cikin asibiti da Ita, sai suka juya suka bi bayansa da sauri, Lokaci ďaya aka xo da baba da Deedah asibiti, daukarta atare aka nufi emergency dasu domin suna neman ceton gaggawa, Dr Fulani taxo ta kirata bata gayamata komai ba sai da suka shiga inda aka kwantar dasu, Cikinta yayi mata nauyi, 'me nake gani yau ni fatyma, *Babana da mijina*, meke faruwa meya samesu haka, Waye yayi masu wannan aikin har fauxie, Sai ta ruďe taje ga Deedah numfashinsa sama sama ne, kuka take sosai ta nufi inda mahaifinta, Halittarsa ta tsoratata badan fuskarsa da muryarsa ba da ta qaryata Abinda idanuwanta ke gano mata, Surutu yake agaban likitocin dake kansa, duk abinda yayi a rayuwarsa tunda ya fara neman siyasa har kawo ynxu sai da ya faďa, Believe me Akan ruďewa musamman ma ga mai ciki Iman bata San lokacin da fitsari ke fita a jikinta ba, 'baba ya kashe mata yayyunta da qannenta, ya kashe mata mahaifiya, ya kashe mata ya'yan da take samu, ya sanyata a wani hali Acikin asibitin Wanda mutane suka soma xarginta, she can't believe this ta rufe bakinta da hannayenta duka tana kuka sosai, Dr Merah kansa jikinsa yayi sanyi sai yaji baxai iya taimakawa baba ba, yayi mummunan abu a rayuwarsa Wanda Allah kaďai xai iya yafe masa tabbas baba baida imani da tausayi tunda har xai iya sanya iyalinsa a Wannan hali, xai iya sadaukar da rayuwar iyalinsa saboda dukiya da duniya to ynxu me gari ya waya, mecece ribar da ya samu a duniyar? Ina dukiyar daya tara yake tinqaho da Ita, ina sima da yake alfahari da Ita yake bauta mata Waye xai cecesa a ynxu? Dr Merah ya girgixa kansa shida sauran likitocin suka rufawa Deedah baya, na ganin sun cire bullet ďin jikinsa sun ceto rayuwarsa, Hankalinta baya jikinta, fauxie take gani, ga baba ga Deedah, tana ji tana ganin yanda baba ke fisgar Naman jikinsa ci yake kamar wani dabba yana faďin Duk abinda yayi a rayuwarsa, Tanaji tana ganin yanda yake shure shuren mutuwa, tana ganin lokacin da numfashinsa na tsaya cak ya mutu, tana ganin ynda fatar jikinsa ke fita daga jikinsa tana yin wata Kala baqiqirin, Ta fashe da wani irin kuka mai tsananin gaske wannan wace irin rayuwace take fuskanta, Muryar Deedah takeji yana kiran sunanta sai ta nufesa da sauri lokacin an gama cire masa bullet din jikinsa, Dr Merah da Bakori baxasu jure ganin halin da Salihar mace take ciki ba a ynxu sai suka fice da sauri suna hawaye cikin tausayamata, itama Fulani kuka take sosai ta fita, Iman ta faďa jikinsa duk jini, 'ni nasa ka a Wannan halin, kafita kana fushi dani dama kace kome ya sameka nice sanadi, ka yafe min Deedah, Ina sonka, baba ya mutu karka mutu ka barni Deedah, fauxie na can itama xata mutu, idan na rasa ka da fauxie my life will be useful please stay with me Ahmed, (muryarta harta dishe saboda kuka, ga jikinta har lokacin bai daina rawa ba, a rude take Kamar wata xautacciya, sai faman rungumarsa take tana sumbatarsa, Shima qanqameta yayi sosai a jikinsa yana tayata kuka, 'ki yafemin Iman na kasance mai laifi a gareki, na cutar da rayuwarki haqqinki ne ya kamani, ki yafemin, Ta ďago tana kallonsa tana share hawayen fuskarsa, 'burina a ynxu ka tashi, Dan Allah karka mutu kabarni, karka mutu Deedah, yaron mu xaixo a yau, karka maidashi MARAYA, ka tausayawa rayuwarta, banda kowa bayan kai da fauxie a ynxu.......tayi shiru sakamakon jin ynda numfashinsa ke fita, tanajin bakinsa na motsi da alama kalmar shahada yake, ta tashi a ruďe ta janyo oxygen xata sanya masa, xaninta har ya kwance a gurin under wear ne kawai a jikinta bata damu ba, 'please Deedah, don't..... karka tafi please, Ta taba shi baya Numfashi, 'No Deedah will not die, Deedah baxai mutu yabarni ba, Deedah I know suma kayi ka tashi please, ta soma jijjigashi ta dubi gawar mahaifinta kafin ta maida kallonta garesa, *BABANA DA MIJINA* baxasu mutu su barni ba, *babana da mijina* basuxo duniya a tare ba baxasu je su barni ba, *babana da mijina* suka ďai nake da aduniyarnan they can't die at the same time su barni, Jin abu nabin qafafuwanta yasa tayi Saurin dubawa, jinine ke xubowa daga qasanta, wani irin ciwon mara na taso mata lokaci ďaya, qafafuwanta suka riqe....... My wattpad Phertymerh1 *Babana da mijina* ©Fertymerh Xarah 💞 *Dis page goes to masoyan babana da mijina, tnkuuuu ol for your love and care, Pherty loves you more😘* 33 Har lokacin bakinta yaqi rufuwa, Deedah take kira kamar ranta, Nan ta durqushe qasa riqe da mararta, Tana haka sai ga likitocin sun shigo, Ganin yanayinta sukayo kanta ,numfashinta na fita da sauri da sauri kamar xai ďauke, Dr Fulani da Dr Merah suka riqata ta tashi, suka ďorata akan sick bed , Da sauri Dr Deen yaja gadon sukayi waje da ita, Fauxie a ruďe ta farfado, sai kuka take sosai tana kiran anty, taqi yarda kowa ya tabata daga cikin nurse ďin saboda a firgice take, Sa'eed ne a waje tsare da Ita baisan abinda ke faruwa game dasu Deedah ba, yana xaune yajiyo kukan fauxie a inda aka kwantar da ita, ya tashi da sauri ya shiga ďakin, Tana xaune akan gadon asibiti, idanunta a rufe take Kukan tana weaving hannunta sai faďi take, 'don't touch me..... don't touch me, Ta soma qoqarin saukowa akan gadon ga drip ana sanya mata, Da sauri yaje ya riqata, tana ganinsa ta qanqame sa yayi Saurin riqa hannun da ake sanya mata drip, 'yaya ka kaini inda anty, baba ya dakeni ka ramamin, 'ki tsaya da kyau karkiji ciwo, kinga ana qara maki ruwa, Tabi hannunta da kallo kafin ta maida dubanta garesa, 'yaya ka kaini inda anty, ni ka kaini inda anty... ta cigaba da kuka tana son saukowa Saman gadon, 'Bari acire mata drip ďin tunda qanwar Dr fatyma ce itama xata iya Kula da Ita, Suka cire mata drip ďin, yana rungume da Ita a qirjinsa suka fito, idanunta sunyi jawur ga fuskar ta kumbura, gefen idanunta yayi ja daga ciki baqaramin duka yayi mata ba, sai jikinta yayi xafi rau, yanda ta qanqameshi ma ajikinsa abin tausayi ne, Suna xuwa office ďin Iman bata nan ko Jakarta babu aciki, 'fauxie anty batanan Kinsan inda take xuwa, Ta gyada Kai tana kallonsa, ya rufe office ďin suka fito, Consultant suka nufa nan ma bata nan ba likita ko ďaya, Tana ganin haka ta boye fuskarta a qirjinsa tana kuka, 'yaya ka kaini inda anty, 'Ina xnga anty ynxu fauxie, ai bata gida kuma, Ina ne take xuwa karban haihuwa kin sani? Ta gyada Kai da sauri tana goge hawayen fuskarta, Tana nuna masa suka iso labour room anan suka ci Karo da Dr Deen sai safa da marwa yake a bakin qofar ďakin sai kace matarsace ke labour. Yana ganinsu ya qaraso cikin mamaki, 'meyasa ka fito da Ita, bakaga halin da take ciki bane? Fauxie naganinsa ta qanqame Sa'eed bataso ya karbeta, 'Dr fatyma muke nema tana kuka sai ta ganta ne, 'batada lafiya haihuwa xatayi, Gaban Sa'eed ya faďi, yana sauko da fauxie jikinsa taqi sauka, baisan bata lfy ba sam, meyiwuwa wannan dalilin ne ya sanya ta kirashi ya kaita asibiti, Sam baiji daďi ba, sai ya ciro wayarsa da ďayan hannunsa a aljihunsa yana dialling number Deedah, is switched off, ya maida wayar aljihun cikin jin haushin rashin samun Deedah, Ya dubi Dr Deen sai yaga duk ya damu sosai ko miye dalilinsa na damuwa da halin da Iman take ciki, nan take yaji wani abu ya taso ya tokare qirjinsa musamman daya qare masa kallo kyakkyawan gaske ne da alama yana da jini da Shuwa Arab, ko sumar kansa baqa ce wulik a kwance, Dr Deen ya dubesa yana faďin, 'Waye yayiwa fauxie irin Wannan duka? Sa'eed yaja dogon Numfashi yana faďin mahaifinta ne, 'metayi masa haka? 'shine ban sani ba nima, na sameshi yana dukanta ne, Dr Deen yaja numfashi wannan mutumin bashida imani, ya tsanesa tun lokacin da yaji yana wannan surutun kan abinda ya aikata a rayuwarsa, Allah wadarai ga mai hali irin nasa, 'amma kai yayan Iman ne? 'no abokin mijinta, 'kasan Baban ya rasu a ynxu, yana emergency aka kawoshi, Wata irin faďuwar gaba ta riskesa saura qiris fauxie ta faďi hannunsa ai kuwa ta qanqameshi, 'ya mutu fa kace, Inna lillahi wa inna ilaihir raji'un, Dai dai lokacin da Dr Fulani ta fito ďauke da jinjiri a hannunta sai kuka yake tsalawa, lafiyayyen yaro dashi sak Deedah, kallo ďaya xakayi masa ka gane yaron Deedah ne ba inda ya barshi ta ko ina, Da sauri Sa'eed ya ajiye fauxie a tare shida Dr Deen suka nufi Fulani sai dai Deen ya rigashi karban yaron, Kukan da Fulani keyi shike ďaga hankalinsu, suka dubeta kuka take sosai, 'Ina Iman? Sa'eed ya tambaya Idanunsa akan ta, Iman jikinta yayi tsanani sai suma takeyi tun ďaxu, Jikinsu na soma karkarwa, fauxie ta qaraso tana kallon jaririn, farin ciki xaka gani bayyane a fuskarta, 'yaya wannan baby anty ne? ya gyada kai yana kallonta, Tayi cikin ďakin da sauri, alokacin Iman ta sami barci, Dr Merah yayi ajiyar xuciya cike da tausayamata yana kallonta, haka shima Dr Bakori halin da Iman take ciki ko kuka xaka iya yi mata, Tana ganin Merah taje ta riqa hannunsa, 'uncle anty ta haifi baby, yana can inda yaya, Merah ya juyo yana kallonta fuskarta da yagani sai da gabansa nayi tsananin bugawa, ya buďe idanu sosai yana kallonta, 'accident ne kome, me yajimiki ciwo haka a fuska? Tayi rau rau da idanu ta qara riqa hannunsa, 'baba ne ya dakeni, xaka ramamin, 'Ya salam lallai ba axxalumi irin Wannan mutumin, dubi fuskarta Bakori wannan yarinya xaiwa irin wannan duka haka, 'kabari kawai Merah amma yarannan sunga rayuwa bama kamar fatyma dubi ynda ta koma fisabilillah, basuyi dacen uba ba kam, Suka fito a tare, 'Iman fa? 'ta sami barci, Suka nufi emergency harda Sa'eed da fauxie, Fulani Kuwa ta wuce da jaririn a hannunta sai kuka yaron yake sosai, Sa'eed yaga gawar baba harda fauxie Kuma bata raxana ba batama gane baba bane tana dai kallonsa ne kawai, Dr Bakori ya dubi Merah, 'likita xo kagani kamar Ahmed ďin baya Numfashi, Sukayi kansa da sauri har Dr Deen sai a lokacin Sa'eed ya lura da Wanda ke kwance, Deedah, meya sami Deedah ya qarasa da sauri, tabbas shine jikinsa duk jini, Iya ruďewa Sa'eed ya rude musamman da yaga Merah yaja farin kyalle ya rufe Deedah da shi, 'Deedah is dead Allah ya jiqansa ya gafartamasa shine abinda Merah ke faďi yana sharar kwallah a fakaice, ya tsorata da mutuwar Deedah yana tuna xamansa dashi sanadiyar Iman yasan irin alaqar dake tsakaninsa da Iman, yasan irin son da suke ma juna tabbas Iman tayi babban rashi, ba uba ba miji a irin Wannan lokacin da suke tsananin buqatar taimako tunda basu da uwa, Inaji tun da Merah ke asibitin bai taba kuka ba sai wannan lokacin, duk dauriyarsa a yau ya kasa yaja da baya yana sharar kwalla baxai iyaba jikinsa har rawa yake tunanin halin da Iman xata kasance yakeyi, Sa'eed ma baisan sanda kuka ya xo masa ba, abokinsa koma ince amininsa..... Kukan fauxie da Merah sun tayarda hankalin fauxie ganin manyan maxa irin su na kuka ba qaramin abu bane, duk da take qarama tana jin wani feeling a jikinta ba daďi, jikinta yayi sanyi ta matsa kusa da Bakori tana kallonsa dan taji suna ambatar Deedah tasan shine kwance a wurin taga sun rufeshi da xani, tasan haka akewa duk wanda ya mutu kamar yanda malam ya sanarda ita, Xuciyarta na soma bugawa fal fal numfashinta har wani sama yake, 'yaya ya mutu? ya gyada kai yana kallonta, Shikenan ya tafi ya barsu, shikenan baxai dawo ba, shikenan baxai qara siyamata tedy, biscuits da chocolate ba, shikenan baxai qara Wasa da ita suje yawo ba, shikenan baxasu qara cin abinci tare ba, baxata qara ganinsa ba itada anty, ta juya tana kallonsu duk sunyi shiru, ta gigice ta fita daga ďakin haďe da fashewa da irin Kukan nan Mai qara irin na yara, da ka ganta kasan a gigice take batasan inda xataje ba, A tsorace ta farfado daga barcin da take, xuciyarta na tsananta bugawa ta tuna Deedah da yanda ta barshi, ta sauko daga Saman gadon da sauri haďe da fisge drip ďin da ake sanyamata a hannu, Mararta a qule take har lokacin tafiya take a hankali ba takalmi ba mayafi sai kallabi akanta, kallon xararra ake mata a asibitin ga Waďanda basu Santa ba duk inda tabi sai an kalleta, kai da kaganta kasan haihuwa tayi saboda xaninta duk jinine, Nurses ďin da suka Santa suka biyo bayanta da sauri suna kiran sunanta, tanaji ta kyalesu sai ta qara Saurin qafafunta musamman ynxu da take jiyo Kukan fauxie sai ta qara ruďewa, Tun daga nesa ta tsinkayo fauxie na kuka a jikin Dr Deen, tana qarasowa ana fitowa da gawar baba, Ta tsaya cak tana maida Numfashi da kyar kamar wata zakanya jikinta sai karkarwa yake, juyowar da xatayi taga anfito da Deedah, Sa'eed na bayansu yana sharar kwalla Idanunsa sunyi matuqar ja, Fauxie na ganin an fito dashi ta qara fasa ihu a gigice tana neman kwacewa jikin Deen, iman Kuwa qarasawa tayi ta riqe gawar, 'meyasa kuka rufesa ai bai mutu ba, ku duba suma ne yayi, Deedah baxai mutu ya barni ba, wannan lokacin Kukan da take harda majina ta xama wata xautacciya, Duk qarfin hali irin na mutum idan yaga halin da Iman take ciki a Wannan lokacin sai ya xubar da kwalla, 'Deedah ka tashi sugani su San cewa Baka mutu ba, Deedah ka tashi kaga yaron da muka haifa, meyasa xakaje ka barmu a lokacin da muke tsananin buqatar ka, Taje ta riqe Merah, 'kace su dawo dashi acigaba da kula dashi anan, Deedah bai mutu sai idan kune xaku kashe shi, Fulani ta qaraso da jaririn a hannunta har lokacin kuka yake kamar yasan abinda ke faruwa, tunda ya faďo duniya yake kuka, Kukan yaron har cikin kanta take jinsa, ga Kukan fauxie dake qara rikita kwakwalwarta, tana ganin lokacin da suka sanyasu a mota ta tabbata lallai gida xa'a je dasu ayi masu wanka da sallah akaisu makwancinsu, shikenan Deedah yaje yabarta..... Cak numfashinta na ďauke, sai ta xube gurin a sume.... My wattpad Phertymerh1 *Babana da mijina* ©Fertymerh Xarah 💞 34 *Masu turo ta'aziyar Deedah, iman na godiya sosai, saqonku ya iso*. Tana xubewa gurin su Dr Umayma sukayi kanta, fauxie na ganin lokacin da ta faďi ta soma neman saukowa jikin Deen tana kuka amma ya riqe ta tamau sosai a jikinsa, Aka sanya gawarsu a motar Sa'eed, shi yaja motar su Merah na bi bayansa da nasu motocin, Iman Kuwa motar Dr Deen aka sanyata tare da sauran likitocin fauxie na kusa da ita fuskarta ta qara kumbura tayi jawur ga ciwo ga kuka, kanta har nauyi yake mata ga wani Xaxxabi da take ji wannan karon baxata sami kulawar Iman ba cos ita kanta bata cikin hayyacinta, mutuwar mahaifi da miji a lokaci ďaya (it's the greatest loss of all losses), A Wannan ranar xo kaga jama'a, mutane kamar me, nan da nan gari na ďauka mutuwar Alhaji Abdallah abinka da ďan siyasa sananne a gari, Mutuwar taxowa mutane a baxata daga shi har Deedah ba Wanda aka yiwa tsammanin mutuwa a ynxu, Abokan Deedah suna cikin ruďani da tsoron Allah, duk Wanda yace shine yau ba shi bane gobe, mutuwar sa ta girgixa shi idan suka tuna jiyama suna tare dashi a office, ya sami kyakkyawar Shaida daga garesu, Ma'aikatan gidan maza da mata tamkar sune akayiwa mutuwar, kuka suke sosai sun san qarshen barin su gidan yaxo, ba uban gidansu to Waye xai riqa biyansu Waye xai riqa ciyar dasu, wasu ma da gidan suka dogara, Sa'eed da kansa yaje part din baba ya rufe ďakunan sa na dukiya, mutanen ynxu basu da amana wani baxaiji tsoron ana cikin wannan tashin hankali ba suje yiwa marayu sata wannan ne dalilin dayasa ya rufe, Anje yiwa gawarwakinsu wanka, a Wannan lokacin fauxie na rakube a bed side kanta a langabe, barci take daga xaune tana gyangyaďawa kamar xata faďi, Iman Kuwa tana xaune da jinjirin a hannunta tana bashi mamma, ance kuka ma rahama ne Wannan Karon kam Kukan yaqi ya xo xuciyarta a bushe take, kallon jaririn take, Yaxo a MARAYA, yaxo duniya babanshi yabar duniya, kakanshi ma yabar duniyar, duk da haka yaronta baxai taso cikin maraici da rashin gata ba, xata bashi tarbiya ta kula dashi shida fauxie tamkar Iyayen su na raye, bata da sauran buri a rayuwarta ynxu na ganin ta Kula da marayun biyu, ta sauke nauyin dake kanta akansu, aure baxata sanyoshi gaba ba aynxu a tsorace take da kowane namiji da halayyarsa, xata cigaba da rayuwarta a hakan, Wanda take so ya tafi yabarta tana roqon Allah ya sa shine mijinta ko a lahira, Sai a lokacin hawaye na samu xubowa daga idanuwanta ta rumtse idanuwanta suka xubo akan fuskar jaririn Wanda ke barci tuntuni, Fulani ta karbi yaron ta goya, sai Iman ta maida kanta jikin cinyoyinta tana kuka sosai, Sanda aka gama masu wanka aka Kira Iman tayi masu addua, kuma tayi cikin jarumta da dakewa irin tata, ba Wanda batayiwa addua ba acikinsu, tana gani aka ďauki gawarsu, Sai ta bisu da ido idanunta taf da hawaye fuskarta ďauke da murmushi, 'I know Deedah must come back to me, ni nasan bai mutu ba, nasan Deedah baxai je yabarni ba, bayan yace xamuyi rayuwa tare mu raini jaririn mu tare, Xuciyarta ta cigaba da bugawa lokacin da aka fita dasu, taga yawan jama'ar da suka cika gidan sai taja jikinta ta koma ta xauna, tana bin mutanen dake falon da ido tana kallonsu suna kuka, Bataga dalilinsu na kuka ba, Wanda suke wa kuka xai dawo tasan xai dawo, xai dawo..... xai dawo haka kwakwalwarta ke bata Sai ta fashe da dariya, duk gurin aka juyo ana kallonta, ko miye abin dariya ga Wanda akayiwa mutuwa? 'lafiyar ki kuwa? Cewar salima tana kallonta cikin tsananin mamaki, 'tor miye amfanin Kukan da kuke, baba ne kawai ya mutu banda mijina, nasan Deedah yana raye, ynxu xaku ganshi ya dawo xaiyi wanka yayi shirin xuwa masallaci bara naje na fidda mashi kayan da xai sanya a yau, ta tashi tayi ďakin sa, Mutanen falon suka kalli juna cikin tsananin mamaki, Fulani tabi bayanta da sauri, Ta juyo da kafadunta suna fuskantar juna, 'Kinsan me kikeyi fatyma, me kike son nunawa mutane, baki yarda da qaddara bane keba musulma bace? 'my husband is alive Dr Fulani, Kune keson kashe sa, jiya fa muna tare, yau ma munyi mgn dashi, ya roqeni gafara Kuma na yafe masa, shine fa ya suma kuke kiran ya mutu, 'Wanda ya mutu baya dawowa Iman, kada ki ruďar da kanki, ki nutsu dan Allah kada wani abu ya sami kwakwalwarki, dan Allah fatyma kixo muje falo kicigaba da yi masu addua, kinga ga yan uwanku ma suna ta xuwa. Iman tayi shiru Kamar mai naxari sai Kuma ta dubeta, 'tell me Fulani idan Marhoom ne ya mutu me xakiji? Sai da xuciyarta na buga ta gyara goyonta tana kallonta, 'me ya kawo wannan mgnr Kuma? Idan ma mutuwa yayi haquri xanyi nayi tawakkali ga Allah, nasan yafini sonsa Kuma nasan yafiye masa duniya daďi, Iman ta girgixa kanta, 'you are not saying the truth Dr fulani, baxaki iya jurewa ba, bakisan xafin dana keji a xuciyata ba, bakisan ciwon da Mace take ji idan ta rasa abokin rayuwarta ba, ballantana irin nawa rashi na *babana da mijina* a lokaci ďaya, ta soma hawaye sosai, ta juya tana ciro kayan Deedah, 'ni nasan bai mutu ba xaki ganshi sun dawo dashi, Fulani tayi shiru tana kallonta cikin tausayawa, itama ta tsinci kanta cikin kuka sosai ta fice daga ďakin da sauri. Haka Iman ta fito da kayansa, juyowar da xatayi tayi arba da tangamemen hotonsu dake manne a ďakin, yana rungume da Ita suna yiwa juna murmushi, sai ta saki murmushi tana faďin, 'Haba taya ma xasu ce Deedah na ya mutu, nasan xaka dawo kaxo kabasu mamaki su san cewa kana raye...... An kaisu makwancinsu an rufesu daga su sai halayyarsu sai abinda suka shuka a duniya, in hairan hairan in shairan shairan, wani abin tsakaninka ne da mahaliccinka, idan ka kasance mai tuba agaresa, Duniya kenan.... Babu dukiya aciki, babu gida mai tsada, babu mota mai tsada, babu abinci mai tsada, babu lallausar katifa mai taushi da tsada, babu Mulkin da ake taqama dashi, An kaika inda xaka xamo abinci ga tsutsoci, qasar da kake taki da takalmi yau kaine acikinta timbir, babu mai ceton ka aciki sai Allah, sai aikin da ka aikata a duniya, ya Allah ka tsare mu da azabar kabari, kasa muyi kyakkyawan qarshe mucika da imani Amin. Sa'eed kuka yake sosai Idanunsa sunyi jawur, shikenan Deedah yaje ya barsu, baxasu qara ganin Deedah ba, yayi rashin aboki, Allah ka gafartawa Deedah ka Kai haske a kabarinsa kamar yanda goshinsa yayi haske lokacin da suke masa wanka, Suna dawowa jana'iza suka nufi gidan, tun daga waje suka fara gaisuwa ga mutane birjik an shimfida Manya Manya tabarma saboda masu gaisuwa, yan uwan su Iman ne a waje da suka xo, Kai tsaye su Dr Merah suka nufi falon Iman domin yi mata ta'aziya, tana ganinsu ta tashi da sauri ta nufesu, sai leqen bayansu take burinta taga Deedah a bayansu amma wayam, Ta dubi Dr Merah, Dr Deen, Dr Bakori, Sa'eed, sai taga suna hawaye kowane na jin nauyin haďa ido da ita a yau, bakinsu yayi nauyi ga duk kalmar da xata fito bakinsu, 'Banga Deedah ba likita, ina kuka barshi? Merah yayi qarfin halin mgn, Idanunsa akan nata, 'Dama Wanda ya mutu yana dawowa ne Iman? Deedah is dead, Deedah has gone and he will never come back, ya tafi ya barmu dole haquri xamuyi da wannan rashin Allah ya fimu sonsa mutuwa na kan kowa, 'wace mgn kakeyi likita, Kada kace min da gaske Deedah na ya mutu, ya tafi ya barni nida qanwata, ya tafi yabar jinjirinsa, dan Allah kace masa ya dawo, yaxo ga kayanshi ya Sanya yaje jumma'a, ta juya tana neman inda ta ajiye kayan, Kai da kaganta kasan bata hayyacinta a ruďe take, inbashi ba, mace kamar Iman Mai kunya da kawaici, Mai haquri da tawakkali, Mai hankali da nutsuwa, yasan da hankalinta baxata tsaya gabansa tana wannan mgn ba ynda take matuqar girmamashi, Gabaki ďaya falon suka ďauki kuka, Dr Deen ya fita da sauri shida Sa'eed baxasu jure ganinta a Wannan halin ba, 'ki nutsu fatyma, Merah ke gabanki, baxan maki qarya dan na cutar dake ba kinsani, Deedah ya tafi inda baxai dawo ba Kinsan miye mutuwa please pray for your father yana buqatar addua sosai akan Deedah, Deedah ya tafi cikin kyakkyawan qarshe fuskarsa kaďai xata Shaida hakan da ynda jikinsa yayi kyau, ki roqa masu gafara ki masu addua, please fatyma ki nutsu, Nan da nan jikinta na soma rawa sai karkarwa take sai ga hawaye sharrrrr, Shikenan da gaske Deedah ya tafi, Bakinta na rawa ta nemi gurin xama da kyar tana faďin, 'Allah ya jiqansu, Allah ya gafarta masu, Allah ya haskaka kabarinsu, Duk falon aka ďauki Amin, wasu Kuwa suka fashe da kuka...... My wattpad Phertymerh1 [04/04, 12:35 p.m.] Pherty👯: *Babana da mijina* ©Fertymerh Xarah *Dis page is for you, Lilmeerahcute, Xuhura Ajiya, Faty Shuwa & Meenah 4va* 35 Nan Merah ya sunkuya yayi mata gaisuwa ya fice, fitarsa keda wuya Sa'eed da Dr Deen suka shigo suka mata gaisuwa suka fice, Mutane sai shigowa ake yi mata gaisuwa, ga Pherty novels, Fertymerh Xarah novels, Duniya Makaranta, Taskar Marubuta, RAZ novella, Mata masu duniya, Matan kwarai da sauransu sai xuwa suke, Da dare gidan ya watse su Dr Fulani ma sun tafi ya rage ita da salima tana jiran Sa'eed yaxo ďaukarta, ga fauxie kwance a jikinta sai jinjirin yana gefe cikin shawl yanata barci, 'anty yaushe yaya xai dawo, ki kirashi kice ya siyomin ice cream, 'bake kikacemin malam ya gayamaku duk wanda ya mutu baya dawowa ba, shima baxai dawo ba sai dai mu same sa acan, 'anty yaushe xamuje mu same sa, 'yau ko gobe kowane lokaci xamu tsinci kanmu a inda yake, kullum kisa a ranki a kowane lokaci xaki iya mutuwa, 'Yanxu anty yaya cikin qasa aka sanyashi, Iman ta gyada Kai tana hawaye, 'Kuma baxai dawo ba anty? Nan ma ta gyada Kai tana kallonta, 'Kuma anty baxamu qara ganinshi ba? Nan ma gyada kai tayi, sai taga fauxy tana sharar kwalla hakan ya qara sa hawayen Iman suka daďa xubowa sosai, Salima da ta sallame sallah ta dubesu cikin tausayawa sai kawai ta girgixa kanta jikinta a sanyaye wannan mutuwar ta girgixa ta bama kamar ta Deedah, da itace ta rasa Sa'eed ďin ta batasan halin da xata shiga ba sai taji tana qara son mijinta, 'tashi ki kiramin adama ko dijeh su baki abinci kici gaki bakida lfy, ta noqe kai 'anty ni baxan ci ba, 'meyasa? 'na qoshi, 'a'a babyn yaya, me kikaci da xakice kin qoshi, tashi kici abinci sai kisha magani, dole xa'a koma dake asibiti kodan idanunki, Fauxie ta tashi da kyar tayi sashen masu aiki, Suna xaune da salima Sa'eed yaxo daukan su, basu jima ba suka fice, ya rage Iman kawai a falon sai jaririnta, Sai taga falon yayi mata faďin gaske har wani tsoro takeji ita kaďai aciki, yau xata kwana bada Deedah ďin taba, yau Deedah ta xai kwana acikin qasa, tayama xata iya barci a gadonsu batare da shi ba😪? Sa'eed Kuwa suna xuwa gida suka sami yaransu duk sunyi barci, Indo tana shimfidar dasu akan gadonsu, bayan sun shiga ďaki ya dubeta, 'inason tausa salima xn samu? taja guntun tsaki haďe da bata fuska tana cire kayan jikinta, 'Mts nifa a gajiya nake yau nima, tunda naje gidan rasuwa nake xaune sai aikin rarrashinta nake, in banda taurin kai irin na Iman dan *Babana da mijina* sun mutu sai na hana kaina abinci inada ďanyen jego, inaji yau komai bata ciba, Yaji jikinsa yayi wani iri, kalamanta sun tsoratashi wato koshi ya mutu baxata damu ba, 'ynxu ni idan na mutu baxaki damu ba kenan, 'kai haba fata ta gari, bana son wasar mutuwa ko kaďan indai akan Kane, [04/04, 1:42 p.m.] Pherty👯: Yasani salima na sonshi amma ta Kula dashi e baxata iya ba, 'ita Iman miye laifinta anan da take baki haushi, 'kai dai bari kawai, itada fauxie abin a tausaya masu ne amma na haihu yau baxan hana kaina abinci ba, ta cillar da kayanta tana kallonsa, 'ynxu baxan samu tausar ba kenan, 'gsky ni nagaji kayi haquri har gobe, 'haqqina fa? tayi masa wani kallo, 'haba Wanda baiyi tausa ba ina xai iya ďaukar wata lalura kuma, sai tayi shigewarta toilet tabar shi a tsaye yana kallonta ya girgixa kansa a xuciyarsa yana nema mata shiriya, ya nufi dakinsa amma kuma sai me ya kasa kwanciya, tunaninsa na gun Iman jin yau duk bata ci komai ba, Ya tashi ya xira doguwar jallabiya ya ďauki key ďin motar sa ya fita salima dake toilet tana wanka tana jin kukan motarsa ta fito a guje ta window ta duba, Tabbas shi ďinne ya fita to Ina ya nufa a ynxu? Jikinta duk kumfane sai ta nufi toilet da sauri ta watsa ruwa ta fito jikinta har wani rawa yake, Gasasshiyar kaxa ya siyo mata mai xafi, da drinks Kala Kala tunda baisan wane take so ba, cimma iri iri irinta masu haihuwa ya siya yaje gidan, Mai gadi na ganin motarsa ya shaidasa ya buďe gate ďin ya shiga, Koda ya shiga falon tana xaune dirshan a qasa fauxie da jaririnta suna gefe sunyi barci, ita kuwa tana riqe da charbi tana kallon yaran, Sallamar sa yasa ta juya tana kallon qofar, idanunta sunyi mata nauyi gasu sun kumbura, ta ďauke kanta daga kallon sa, Ya qaraso falon yana kallonta ji yake kamar ya rungumeta ya rarrasheta a ynda ya ganta, Ya ajiye ledar a gabanta yana kallonta, 'kici abinci fatyma, bai kamata ki xauna da yunwa ba, you are a doctor Kinsan illar haka ga mai haihuwa, ko dan wannan jinjirin ya sami abinci kici please, Ta juya tana kallon jaririn kafin ta maida kallonta garesa, sai wani kuka yaxo mata gwani ban tausayi shi kansa sai ya tsinci kansa cikin hawaye suna haka sai ga adama taxo da plate ďauke da farfesun nama sai qamshi ke tashi yaji kayan yaji irin Wanda akewa masu haihuwa ta ajiye a gabanta tana kallonta, 'Dan Allah hajiya kici ko kaďan ne sai ki shanye romuwar xakiji jikin ki ya saki sosai musamman idan kinyi wanka, Ba musu ta buďe kowane ci take ba kakkautawa dakaga yanda takeci xakayi tunanin ta kwana biyu bataci komai ba, duk sukayi shiru suna kallonta, Sai da tagama ta dubi adama, 'bani tafassashin ruwa nasha, kinsan baxan sha na sanyi a ynxu ba, Adama taje ta kawo mata ruwa a flakes tasha, kafin kace me sai ga xufa na karyo mata sai ajiyar xuciya take, Sa'eed ya jima gidan yana kwantar mata da hankali kafin yayi mata Sallama ya fice, Ta dauki fauxie ta kaita ďakinta kana ta dawo ta ďauki jaririnta, Kayan jikinta ta soma cirewa tana son watsa ruwa sai taga mammanta sun ciko sosai har wani ciwo suke mata, ta dubi jaririn sai barcinsa yake, tayi toilet tayi wanka, A Daren acikin barci sai tayi mafarkin gata tare da Deedah a wani lambu ta rufe idanunsa da wani baqin kyalle taje ta buya shikuma sai nemanta yake, xataxo ta tsokanesa ta koma da gudu da haka har ya kamata ya rungumeta sosai a jikinsa yana faďin, 'wana kama, na kamaki ciremin kyallen dake fuskata, tana dariya ta cire masa kyallen ga mamakinta sai taga ya juya yana murmushi yana yi mata bye bye, Ta bisa tana kiran sunansa tuni ya fice, a firgice ta tashi tana kiran Deedah, caraf idanunta na sauka akan jaririn amai yaron yake sai kuka yake iya qarfinsa, tana jin wayarta na qara a lokacin bata ďauka ba, Ta dauki jinjirin ta sauko daga gadon tana jijjiga yaron, amai da yake ya daďa tayar da hankalinta Kada shima ya mutu ya barta, Sai ta fara kuka ta gigice batasan ynda xatayi ba, Wayarta na cigaba da kuka tana dubawa taga Dr Deen ne, da hanxarta ta ďauka, Kuka take Kamar ranta, 'shima xai mutu likita please help me..., 'Waye xai mutu? 'jaririn... sai taji ya tsinke Wayar, Yana kwance a ďakinsa ne da kayan barci a hakan ya fito cikin sauri yabar gidansa yayo gidan, Mai gadi najin horn yaqi budewa yana kallon agogon hannunsa to 2:00 am idan ba barawo bane Waye, Yaji horn ďin sai yinsa ake ya leqa ta window dai dai lokacin da Dr Deen ke fitowa a motarsa a harxuqe yana ganinsa yaje ya buďe masa gate, A Wannan lokacin yaron ya daina amai sai dai bai bar kuka ba, ta fito dashi falon gudun ya tayar da fauxie, sai safa da marwa take dashi a falon itama kayan barci ne ajikinta riga da dogon wando masu kauri ne, Yana shigowa falon suka haďa ido, sai da yaji wani abu a xuciyarsa, Ita kuwa tayi mamakin ganinsa sai a lokacin ta tuna ai likitan yarane a paediatric, Da sauri ta iso garesa hankalinta nakan yaron shikuma Idanunsa na kanta ta miqa masa yaronta, 'likita ka taimaka kada ya mutu bansan yanda xn kasance idan na rasa shi ba, soyayyar Deedah ce akansa please doctor ta faďa wannan lokacin tana kallonsa idanunta taf da hawaye, A sanyaye ya karbi yaron yana kallonsa, cikinsa kawai ya duba ya gane yaron yana ciwon ciki ne sai ya juya da sauri yana faďin, 'ina xuwa, ya fice da sauri, Ta xauna nan qasa dafe da kanta da duka hannayenta biyu, Ya salam.... sai taji xuciyarta ta kasa sukuni, take toilet ta nufa ta ďauro arwalla taxo tana sallah, Har tagama basu dawo ba, hankalinta ya qara tashi, ga kanta yayi mata wani uban nauyi saboda rashin barci, ta dawo falon tana kallon agogon dake manne a falon 4 tayi, xuciyarta ta kasa sukuni, Ta cigaba da xaman jiransa har barci ya ďauketa, sanda ya dawo tana barcin yaron ma yayi barci, dama barcinta sama sama ne tanajin motsinsa ta tashi tana kallon hannunsa, Taje ta leqa yaron bai mutu ba barci yake, ta sauke ajiyar xuciya ta karbi yaron tana murmushi, yabata ledar yana mata bayanin maganin da ya siyowa yaron, Ta juya fuskarta ďauke da murmushi sai sumbatar yaron take tana jin farinciki a xuciyarta kasancewar sa a raye, yana tsaye yana kallonta, No thank you, nothing more kawai ta karbi yaron ta juya, wannan ba wani abu bane farin cikinta yakeso kuma yagani a fuskarta shima sai ya tsinci kansa cikin jin daďi, Har ya juya kamar daga sama yaji muryarta, 'doctor... ya juyo yana kallonta, fuskarta da murmushi take kallonsa, 'thank you.... Ya gyada kai shima fuskarsa da murmushi yana kallonta sai dai bai tankata ba, Bayan Wannan bata qara cewa dashi komai ba ta juya cikin qaunar yaronta tayi shigewarta ďaki, shima ya juya ya fice, *Masu qorafin rashin typing ďina, kuyi haquri please, I don't have enough time a ynxu cos of my project, pray for me, masoyan babana da mijina Tnkuuuu ol.* My wattpad Phertymerh1 *Babana da mijina* ©Fertymerh Xarah 💞 36 _Congratulations for the completion of ur book Rabi'atu Sk Mashi, MATATA CE, ko ina xanga Rabi'atul Adawiya? Nagode da qaunarki,_ _mistake page 35 in babana da mijina, ban sani ba ko tsananin ruďewa ce tasanya Iman sallah bayan ta haihu, it's a mistake pls._ Da kyar yaja qafafunsa yabar gidan, duk jikinsa a sanyaye yake har ya iso gidansa, Sai da yaje ya duba mahaifinsa har lokacin barci yake kafin ya koma side ďin sa, kwanciya tayi haďe da lumshe idanuwansa, fuskarta yake gani, murmushinta wani abu ne mai girma a xuciyarsa, da alama tana matuqar son yaron ya gani a kwayar idonta don haka yayi alqawarin Kula da Ita da yaron kamar shi ya haifesa, da Wannan tunanin barci ya ďauke sa, Sa'eed Kuwa yana xuwa gida ya sameta xaune a falonsa tana jiransa, cikin wasu irin shu'uman kayan barci, rabonta da sanyasu yana ji tun farkon aurensu, ya ďauke kansa cikin basarwa kamar bai ganta ba yayi hanyar ďakinsa ta biyosa tana faďin, 'ina kaje da wannan daren Abban Adnan, Yau kuma har wani Abban Adnan ya samu ya raya hakan a xuciyarsa shi da ake kira da xallar sunansa Sa'eed, Bai dubeta ba bai Kuma tankata ba ya hau gadonsa yayi kwanciyarsa fuskarsa ba walwala hakan yasa take tsoron tunkararsa Kada ya sauke fushin akanta, sai ta soma mgn a hankali, 'Dan Allah ina kaje, Allah yasa ba gurin wata kaje ba dan bansan yanda xnyi da xuciyataba, A fakaice ya ďan dubeta cikin mamaki bai bari sun haďa ido ba ya ďauke kansa, tana sonsa ne bata iya Kula da shi, Ganin baxai tankata ba ta kwanta a qirjinsa, da sauri ya juya mata baya haďe da Jan dogon tsaki, Hakan da yayi hankalinta yayi matuqar tashi tasan idan Sa'eed yayi mata haka to yana fushi da itane, 'kayi haquri ďaxu wasa nake ma xnyima tausa ďin, 'karki kuskura ki tabamin jiki, inba haka ba ranki xai baci... duk wannan mgnr da yake fuskarsa ba walwala, Nan da nan ta soma hawaye tayi xaune xuruu tana kallonsa, tana gani ya tashi ya kashe wutar ďakin Kafin ya dawo ya kwanta batare da ya kalleta ba, hankalinta ya tashi sosai ta tashi tabar ďakin ta nufi nata, ranar barci a idonta sai dai barawo.... Sa'eed Kuwa barcinsa duk na Iman ne, yana tare da Iman, ya tashi yana adduar Allah ya bashi Iman su kasance tare cikin farinciki da kula da junansu. Iman Kuwa tana shiga ďaki ta shimfide yaron, ta gyarawa fauxie kwanciyarta anan taji jikinta xafi rau, ta manta da taci abinci batasha magani ba, gefen fuskarta ma ya fara ďebe kumburi, tausayin yarinyar ya kamata, Taya akayi fauxie ta fita wayo da dabara, Ashe surutunta bana banxa bane, sai komai yake dawo mata sabo, lallai fauxie ba qaramin namijin qoqari tayi ba dan da baba bai gayamasu komai kafin ya mutu ba da baxatasan komai ba, Ashe da gskyr Deedah da yace fauxie ce ajalin baba, sanda yayi furucin taso ta tambayesa dalili amma ta manta, Ashe Deedah yasan baba matsafine amma bai taba gayamata ba sai Faďan da sukayi na qarshe dashi inda yake cewa, *gwanda xama da barawo akan xama da matsafi..*, Inama Deedah ta xai dawo, xata xauna dashi a matsayinsa na barawo, tana son mijinta fiye da tunanin mai karatu, *Babana da mijina* sune jigon rayuwata, yau babu su daga ita sai qanwarta da ďanta... ta soma waige waige a ďakin kamar xataga Deedah, dama a irin wannan lokacin yake dawowa gida, ta tashi da sauri tana kallo ta window gani take xataga motar mahaifinta ya dawo, xuciyarta ta kasa amincewa da mutuwarsu, meyiwuwa xasu dawo Gobe a tunaninta sunyi tafiya ne tadawo cikin ďakin har lokacin hawaye take, Magani ta ďauko da ruwa taxo ta tayar da fauxie, Kuka ta fara, tayi saurin toshe mata baki da hannu gudun kada ta tayarda jaririn, 'yi shiru karki tayarda baby, magani xaki sha sai ki koma barcin, 'anty baxan sha ba.... ta qara kwanciya idanunta a lumshe, Iman ta riqo hannunta haďe da sunkuyawa dai dai fuskarta, 'please babyn yaya, idan kinsha magani yaya will be happy, kuma xakiji sauqi kafin ki koma Skul fuskarki xata dawo dai dai, your friends will not laugh at you, Ta buďe idanunta a hankali tana kallon Iman itama kallonta take, sai ta tashi xaune, Iman ta bata maganin tasha tana yatsina fuska kamar xatayi kuka bata barta ta kwanta ba sai da ta tabbatar ya kwanta mata, fauxie taje kusa da yaron ta riqo hannunsa ta riqa da nata, 'Anty shi hannunshi yana da laushi, yaushe xaiyi girma kamar ni muyi wasa, 'kiyi barci ba surutu na tayarda ke kiyiba, fauxie tayi shiru haďe da rufe idanuwanta bata saki hannun yaron ba, Iman ta kwanta a kusa dasu tana kallonsu, barcinta a ranar sama sama ne sai ta fara ta tashi a firgice. * Washe garin ranar Dr Deen tare da mahaifinsa baffa, nan yake bashi lbrn Iman, sosai ya tausayamasu sai yaji inama Xahradeen xai aureta ya kula da yaronta da qanwarta sai ya tuntubesa da Mgnr, Dr Deen yayi shiru kafin ya dubi baffa, 'xamuyi Mgnr wani lokaci baffa, ya tashi ya fice cikin shirinsa na xuwa asibiti, Sa'eed ma yana shirin xuwa bank salima ta shigo, ta gaidashi ya amsa fuskarsa ba walwala, 'breakfast ďin fa, 'na qoshi, 'Dan Allah kayi haquri ka yafemin, Ya ďauki jakarsa yasa kai ya fice batare daya dubeta ba, tabisa da kallo ranta a bace tabbas idan har wata mace kesa yana mata Wulaqanci a ynxu wallahi ko Wacece sai taga bayanta..... Tunda sassafe Iman ta shiga wankan ruwan xafi, yaran basu tashi ba harta gama ta fito, sai taji daďin jikinta sosai, tana shirinta take jiyo hayaniyar mutane tasan baxai wuce yan uwansu bane da suka xo, ita batason xaman makokin nan da duk yawanci Munapurci ake, sai ayita qananan maganganu kan mamaci, sun maida gidan kamar gidan biki ba mutuwa ba, sai fita ake da abinci da juice, jiya kaďai tana lura da yanda yanayin gidan ke tafiya, almubazzarancin yayi yawa. Wata dattijuwace tayi Sallama ta shigo ďakin, Iman ta amsa sallamar tana kallonta bayan sun gaisa, 'Tace Inna ai bai tashi daga barci ba, 'banda abinki fatyma shi jariri ai baya tashi barci karkiyi mamaki ma ynxu har ayi wankan a gama bai tashi daga barci ba, bani shi nan ki gani, Iman ta ďauki yaron tana kallonsa kafin ta miqa mata shi, Tana xaune tana shan kunun kanwa fauxie ta tashi barci lokacin har angama yiwa yaron wanka ana gasa masa cibiya, 'anty nima ayimin wanka cikin robar baby, 'a'a kije dijeh tayi maki a toilet ke bakisan kin girma ba kinaso Inna taga jikinkine, Ta make kafada kamar xatayi kuka, 'ni banaso anan nake so, 'yi haquri aje toilet ayi maki kinji, keda akewa a Jacuzzi 🛀 Ina ruwanki da robar wankan jariri, Ta soma cire kayanta Iman bata ankaraba sai ganinta tayi cikin robar, Inna ta soma dariya, iman bata ce komai ba har dijeh taxo ta ďauketa da robar tayi toilet da ita sai daďi takeji, Angama wankan tafito komai sai na jariri xa'a shafa mata, Lokaci ďaya Sa'eed da Dr Deen suka xo, ta fita suka gaisa dasu kafin su wuce gurin aikinsu, Dr Merah ma na qoqari akansu har akayi adduar qarshe, ranar komai ya dawowa Iman sabo da kyar Merah ya kwantar da hankalinta harta yi shiru, Ranar suna yaron yaci sunan mahaifin sa Ahmed, Dr Deen, Sa'eed da Dr Merah sosai sunyi namijin qoqari gurin sunan yaron tamkar Deedah na raye, ba abinda suke nema suka rasa daga ita har jaririn da qanwarta, ba abinda xata cewa waďannan maza uku sai godiya da fatan alkhairi a rayuwarsu, Haka rayuwa ke cigaba da tafiya, Dr Deen da Sa'eed na iya qoqarinsu na ganin sun kula da Ita tare da nuna mata soyayya, Ba wannan ne a gabanta ba a ynxu, ba wanda takeji a xuciyarta, ba wanda take ita ba lokacinta a cikinsu bayan qanwarta da ďanta, Sai addua Sa'eed da Deen keyi a xukatansu na ganin ta amince da soyayyarsu a shirye suke da su bata farin cikin da ta rasa a baya, Xuwa wannan lokacin iman tasan ta rasa Deedah ďinta, ta rasa wanda takeso, farincikinta, a ynxu da ta jima bata ganshi ba bataji ďumin jikinsaba ta yarda ya mutu ya barta har abada, xuciyar musulunci ce kawai ke riqe da Ita a yanxu, Hankici tasa tana ďauke hawayen fuskarta cikin tausayin kanta, Tunda ta iya ta karbi rashin Deedah, na wanene baxata iya karba ba a ynxu? But it's still painful.... Yeah so painful! Bata burin mai kuďi ko wane irin mutum ne shi, tafison talaka xama da Wanda bashi da meyiwuwa hakan xaisa xuciyarta ta xamo so contacted, kuďi basu amfana ta da komai ba illah baqin ciki a rayuwa, Wannan dalilin ne ma yasa ba abinda ke burgeta a duniya balle ya sanyata nishaďi, haka take xaune ba doguwar magana, babu hope, no future, babu xabi acikin rayuwarta, duk yanda Allah yayi da rayuwarta dai dai ne. A yau ta tuno da Deedah kan abubuwa da yawa, baxai barta cikin damuwa ba, hawayenta kaďai xai gani gigicewa xaiyi da tarairaya concern da emotional pity amma ynxu babu shi, Ba Wanda xai rarrasheta, ba wanda xai sanyata a jikinsa ya nuna damuwarsa akanta, babu wannan Deedah dake son farin cikinta Wanda xai iya barin komai na rayuwarsa dan yaga ya faranta tata rayuwar, Wasu irin hawaye masu ďumi suka barko daga idanunta, a hankali bakinta ya soma motsi, _"This life has changed... and we go our separate ways Deedah... but you'll still be in my heart till my dying days... my world has never meet a person like you..... I love you Deedah."_ My wattpad Phertymerh1 *Babana da mijina* ©Fertymerh Xarah 💞 37 Bayan wata biyar~~ Abubuwa sun soma daidaituwa a rayuwar Iman, batada sauran damuwa a ynxu bayan ta fauxie da little ynda suke kiransa, Tana fita aiki a ynxu, komai normal batada matsala a ynxu tanajin daďin rayuwarta ba tunanin da takeyi a da, Tayi kyau tayi jiki fatar jikinta sai sheqi take haka hasken fatarta ya daďa qaruwa, da kaganta Kaga qasaitacciyar mace mai ji da kuďi tako ina, Dr Deen da Sa'eed kowa naganin ya cusa soyayyarsa a xuciyarta sai dai batada xabi acikinsu har wannan lokacin tama fi jin Sa'eed a xuciyarta akan Deen bata taba tsayar da tunaninta akan Deen fa, anata ganin Sa'eed yafi dacewa da Ita, shine abokin mijinta shine mutumin da ke xaunawa ya saurari damuwarta lokacin da Deedah na raye, shine mutumin dake share mata hawaye yana kwantar da xuciyarta and still now yana qoqari akanta he still loves her and she do too, Akwai wani lokaci suna tare da fauxie sai ta tambayeta akan yanda take shiga sashen baba har tasami kwalbar da ta fasa, Sosai fauxie ta tsorata bata manta dukan da baba yayi mata ba a tunaninta Iman ma dukanta xatayi, sai ta soma yarfe hannuwanta bayan ta ajiye robar ice cream dake hannunta kamar xatayi kuka ta dubeta, 'Anty Kiyi haquri baxan qara ba, 'ba komai xnyi maki ba, I just want to know, saboda me ma xan dake ki fauxie? Sai ta kasa yarda da Iman tayi cikin gida da gudu inda masu aikin gidan tabar Iman, dariya kawai tayi tabi yarinyar da kallo, lallai fauxie ta tsorata ba qaramin bugu baba yayi mata ba da alama, A daren ranar ta kasance da Sa'eed a farfajiyar gidan, yana tsaye bakin motarsa yayin da ta jingina a motar tasa, duk yanda yayi ya shawo kanta akan ta amince da soyayyarsa taqi amincewa anata tunanin duka duka wata nawa da rasuwar Deedah da har xata maimaita wani aure a ynxu, 'ko xnyi aure baxan auri mai kuďi ba Sa'eed, talaka nakeso mai wadatar xuciya wanda bashida burin kuďi ballantana ya nemesu ta kowacce hanya, banason miji Mai irin ra'ayin *Babana da mijina*, inason mijin da xai soni ya nunamin soyayya har qarshen rayuwata, 'har sai yaushe xaki gane ba kowane namiji suka taru suka xama ďaya ba, kinsan ni Kinsan aikina Kinsan kowaye Sa'eed idan kina tantama akaina ne then you can ask salima ta gayamiki koni waye, Tayi sama da idanunta tana kallon sararin samaniya idanunta fuskarta ďauke da murmushi tana son wannan yanayin da iska mai daďin gaske ke kada jikinta, ta lumshe idanuwanta dai dai lokacin da motar Dr Deen ta kunno kai a gidan, Daga ita har Sa'eed suka juya suna kallon motar ko ba'a faďa ba sunsan kowaye, Sa'eed ya bata fuskarsa yana kallonta, 'waishi wannan likitan me yake xuwa yi gidan nan ne miye alaqarki dashi, 'abokin takarar ka ne idan baka gamsu ba xaka iya tunkararsa kaji qarin bayani, ta juya tana kallonsa, 'duk Mgnr da xamuyi dakai bana son kana sako min matarka aciki, 'kigayamin matsayina fatyma, Inaso mufara shirye shiryen auren mu, Dariya tayi mai fitar da sauti tana kallonsa, Deen dake cikin motarsa yana kallonsu yaga tayi masa kyau a yau, wannan tawwadar Allah dake fuskarta tana birgeshi, sai dai akwai bacin rai sosai a xuciyarsa na ganinta da wani Kuma tana dariya a gabansa, Yana ganin sanďa Sa'eed ya shiga motarsa ya bar gidan ta qaraso garesa, cikin sanyin muryarta take gaidashi bayan ya fito a motarsa, batasan meyasa takejin nauyin Deen fiye da Sa'eed ba, bata iya haďa ido sosai dashi saboda kwarjini da yayi mata a fuska, 'ya little da fauxie, 'suna lafia inaji a ynxu sunyi barci, Yayi shiru Kamar baxaiyi mgn ba sai Kuma ya dubeta, 'naxo ne kan mgnr mu, baffa yana so yaji hukuncin da kika yanke idan ba damuwa Inaso manya su shigo Mgnr mu, Wannan Karon ba walwala a fuskarta kowa damuwarsa yasani banda tata, gani take kamar taci amanar Deedah idan har tayi aure ynxu, tana yawan mafarki da Deedah shiyasa har ynxu take ganin kamar xai dawo gareta bai mutu ba, 'Tace kayi haquri Dr Deen har ynxu ba kowa a xuciyata sai mijina shi nakeso banajin inda wata sauran dama da xn bawa wani a ynxu, 'hakane baxan takura rayuwarki akaina ba, I also feel the pain you feel, Sanda na rasa matata banyi tunanin akwai wata mace da xn nema har na so ta ba sai lokacin dana tsinci kaina a sonki, Wanda ya mutu baya dawowa Iman, forget about the fast and face the future, inada haufi akanki, Kada kayi haufi akaina Zaharadeen soyayyata da Deedah haďin Allah ce badan wasu kyale kyale na rayuwa ba, continue to be your natural self Dr Deen ka xamo yayana I like it and I respect your values too much...... Deedah nake so ta yanda har bana iya waiwayawa in hangi hierarchy ďin da shi yake gani Wanda so baya laakari dasu... Sai bayan ta furta hakan kunya ta lullubeta don ganin irin yanda ya saki jiki sharaf ya xubawa fatar bakinta dake motsi, sai take ganin kamar ta zarme tayi subutal baki sai tayi Saurin gyara xancenta da cewa, 'nidai fatana da burina shine nasami soyayyar wanda nakeso, ya yarda dani nima in yarda dashi Allah ya yarda damu baki ďaya, nayi alqawarin xama dashi acikin kowane hali, akwai ko babu, daďi ko akasinsa ma'ana talaka nake so...... 'idan wannan ne kin samu nima talaka ne mai nema a gurin Allah akoda yaushe, Batasan sanda dariya na subulce mata ba, hakan ya sanyashi nishaďi, Unconditionally ya miqa mata hannu, 'shakes my hand Iman, na gode da kulawarki koda bakyasona, Ina roqon Allah ya fiddani a kunyar soyayyarki ya bani ikon fita haqqoqinki, yabani ikon shiga xuciyarki ya Kuma bani ikon muhimmantata fiye da duk wani al'amari da ďan Adam ke burin samu.... Suka haďe hannunsu wuri guda kamar masu qulla alqawari kana ya janye hannunsa ya juya ya shiga motarsa tana tsaye tana kallonsa har yabar harabar gidan. Tunda yaje gida yakasa kwanciya, sonta yake har cikin ransa amma ya fahimci bata sonsa ko kaďan, Gashi yau ya tsinci kansa cikin wani al'amari Mai girma akan Iman, duk da ba sonsa take ba, sai ya soma yaqi da xuciyarsa, Sai dai duk iya qoqarinsa a Wannan daren ya gaza rintsawa ko ya runtsan surar Iman yake gani cikin murmushi, abin kamar azal. Don haka da yayi sallar asuba ya dade yana roqon Allah sauqi cikin al'amarin, Iman ta kankane ko ina na xuciya da kwakwalwar shi, ta kassara gangar jikinsa bata barshi da ko saqo ďaya da xai sanya tunanin kansa ba. Don haka a Washe gari shine mutum na farko daya danna masu kararrawar falonsu yana cikin shirinsa na xuwa asibiti, Adama taxo ta buďe, ya umurceta da ta kwaso kaya a boot ďinsa kana ya Sanya kai cikin falon bakinsa ďauke da Sallama, Tana xaune da fauxie a dinning suna kalaci yayin da little ke tsakiyar falon yana Jan rarrafe, Iman ta ďaga fararen idanuwanta tana kallonsa Waďanda a take ya gano sun qanqance sun ďan tasa sunyi ja kaďan alamun rashin wadataccen barci kamar nasa, Kada yayi haufi inji xuciyarsa, itama ta kwana cikin kwatankwancin irin situation ďin daya kwana jiya, Gabaki ďaya jiya tunaninsa dana Sa'eed sun hana mata barci da sukuni batada choice a cikinsu kowane danashi matsayi a xuciyarta dama xasu haqura da ita datafi kowa farin ciki domin babu maganar aure a xuciyarta Yanxu. My wattpad Phertymerh1 *Babana da Mijina* ©Fertymerh Xarah 💞 38 _dis page is for you Faxyfashion_ Ta ďauke kanta daga kallonsa ta maida hankalinta kacokan Kan abincin da take ci, Fauxie taxo da gudu ta rungumesa tana dariya, 'Mrng yaya... 'Mrng little angel, bakije Skul ba, 'ina jiran driver bai xo ba, Ya ďauki little yana yi masa wasa, yaron sai dariya yake daka ganshi kaga Deedah photocopy sak.... Adama ta shigo da kayan kai tsaye ďakin Iman ta nufa dasu duk da batasan ko menene acikiba amma bata ďebe tsammani ga kayan Iman ne, Driver yaxo fauxie ta fice tana yi masu bye bye, Iman ma Acikin shirin fita aiki take tana gama kalaci ta taso ta karbi little yaqi xuwa ya liqewa Deen, Ta rataya Jakarta tana faďin, 'xan barka anan kuwa inda adama tunda yau ni kakewa quya, Dr Deen ya juya dashi tabi bayansa, motarta ta shiga shima ya shiga tasa tare da little, Itace ta fara fita da motarta yana bayanta, tafiya suke akan titi hankalinta na gunsu, yanda ya biyota abaya ya tuna mata da Deedah, Allah ya jiqan Deedah ta faďa a hankali. Tana isowa kai tsaye office ďinta ta nufa shima bai kulataba yayi nasa office da little.... Haka rayuwarsu ta cigabada tafiya tsawon shekara ďaya kenan Iman ta kasa tsaida xuciyarta akansu, Dr Merah yayi iya qoqarinsa akanta taqi sai ya xuba mata ido yana kallonta yasan komai daren daďewa dole xata xabi ďaya acikinsu Sa'eed ko Deen ta aura. Shaquwa ta musamman ta shiga tsakanin little, fauxie da baffa, akoda yaushe suna can sun maidashi kakansu shi kansa yana jin daďin kasancewa tare dasu badan komai ba dan shima ba yara ba jikoki daga shi sai masu yi masa aiki sai Deen Idan yana gidan bai fita aiki ba. A yanda ta lura yaran a ynxu sunfi son xama da baffa akan ta, bata yaye little ba yana shekara ďaya da wata biyar idan ka ganshi xakayi tsammanin ya tasamma shekara biyu saboda girmansa da wayonsa ko ina xuwa yake gashi da rigima sosai, sau tari ba'a gidan suke kwana ba sai inda baffa, yanda suke sonsa yasanyata qaunar tsohon itama akai akai take xuwa gaidashi ta daukeshi da girma haka take ganinsa Kamar mahaifinta kamar yanda ya ďauketa ya', Idan tayi ba dai dai ba yakan xaunar da Ita yayi mata faďa Kamar yanda xaiyiwa Deen, haka duk wani abu daya shige mata duhu na rayuwa shike warware mata, sai ta daukesa tabashi wani matsayi a xuciyarta na UBA, a Yanxu tana samun kulawar da bata samu a baya, ga yaranta suna jin daďin kasancewa dashi ba abinda xata cewa wannan tsohon bayan yi masa addua a tsawon rayuwarta. A nata ganin Sa'eed yafi dacewa da aurenta, yafi kowa sanin halinta da mijinta sannan tasan halinsa fiye da halin Deen, miskilancin Deen kesa take qinsa komai yana yinsa cikin nuna isa da gadara, ta tambayi Dr Merah xabi acikinsu ya xaba mata Dr Deen Wanda Sam bata amince da wannan xabin ba, sai taje ga baffa tana tsammanin xaice ta auri yaronsa Deen ga mamakinta sai ji tayi yace, 'fatyma ki auri Wanda xuciyarki tafi amince maki dashi, Wanda kike gani yafi kusanci gareki inda hankalinki xaifi kwanciya kiyi xaman aure, ki kuma kula da yarannan guda biyu da suke amana agareki, Sai taji kunyarsa da nauyinsa, akwai kawaici a gareta baxata iya fitowa ta gayamasa Sa'eed xuciyarta tafi aminta da ta aura ba, sai ta kawar da mgnr ta ďauko wani xancen suka cigaba da hira kamar ya' da uba.... Akwai wani lokaci da lauyoyin babanta dana Deedah suka xo gareta domin dukiyar mamanta dake hannunsu suna so su rabu da Ita, Tayi mamakin dukiyar da Deedah ya bari, bar mgnr Waďanda ke cikin account ďinsa, bata taba sanin yanada irin waďanna kuďin ba, sai ta boye mamakinta lokacin da taga dukiyar baba, kusan tsoro da ruďewa tayi a inda take xaune, Files files dake xube a gabanta na kamfani, gidajensa, filaye da shagunansa bata san iya Karsu ba, ga makullayen motocin da aka xube mata a qalla xasu kai ashirin inma basu haura hakan ba, anan gida ma tanajin makullan motarsa dake hannunta sun kai bakwai, na Deedah biyar ne Kuma tasan suka ďai ne motocinsa a duniya Gashi kuma taga xahiri sai ta qara yarda da mijinta akan babanta, Ta dubi Sa'eed kafin ta maida dubanta ga Deen domin sune shaidarta sai lauyoyin, idanunta sukayi rau bakinta har rawa yake kamar xatayi kuka data tuna Deedah, 'Dukiyar Deedah na yafewa ďan mu Ahmed, ku shaidane ko bayan mutuwata idan ya girma xaku iya bashi, in kuma ina raye Alhamdulillah, 'sai dukiyar baba a raba biyu dani da qanwata, a ajiye mata nata daban, Acikin nawa xan sallami yan uwanmu da duka ma'aikatan gidan nan, sauran kuďin xn kaisu gidan marayu da asibiti saboda masu buqata, xan gina masa makarantar islamiya shida Deedah domin lada ta kai garesu Allah ya gafarta masu, 'banajin xn iyacin dukiyar baba koda kwandalace a ynxu danasan da jinin mahaifiyata da yayyuna da qannena aka tara wannan dukiyar, kuka take sosai 'Allah ya gafartawa baba, Allah ka yafewa baba, Allah ka yafe kuskurensa daya aikata, Suka amsa da Amin suna kallonta cikin tausayawa....ta tsurawa dukiyar ido, xuciyarta ta taushe ta dacewa, 'duniya ba komai bace tamkar matafiyi ne akan tafarki, baba kaďai ya isheta misali, Waye baisan baba a Nigeria ba shahararren ďan siyasa mai ji da dukiya, a yau yana ina? ya tafi yabar kuďin a inda ya samesu, ya tafi inda abinda ka shuka shine jarinka, bai tafi da gidajen ba bai tafi da motocin ba, bai tafi qasashen da yake xuwa ba, qarqashin qasa ya tafi cikin yadin likkafani dai dai dana kowa, babu AC babu katifa mai taushi, sauran al'amarin tsakaninsa da ubangijinsa ne, to haka kowa fa xai mutu yabar wannan dukiyar dayake taqama da Ita, dukiyar nan da ake tarawa ana hana talakawa da masu buqata, dukiyar da ake kashe bayin Allah saboda ita, dukiyarda xaka ga yan uwa suna faďa suna gaba saboda ita, duk xa'a mutu abarta Allah ya gafartamana Amin. 2 months later ~~~ Tana xaune a falo cikin Atampha mai qarshen tsada, kanta babu kallabi ta matse gashinta a tsakiyar kanta, farin glass dake idanunta ya qara ma fuskarta ilhami da kwarjini tana naxarin wani littafin ilimin halin ďan adam Wanda a fakaice ba komai bane aciki ba sai applied Christianity, malaman kimiyar halin ďan adam ke amfani dashi jami'oi matsayin hanyoyin gyara mu'amalar xamantakewar ďan adam tana tsintar na tsinta tana xubar dana xubarwa, sunan littafin 'The power of positive thinking'. Da Sallama ya shiga falon ya bayyana cikin kyakkyawar suit (Japanese) da baqin gilashin Prada a idanunshi, falon ya gauraye da qamshin Dior addict daka ganshi kaga gogaggen ďan boko. Kallo ďaya tayi masa taji xuciyarta ta buga a yau, kamar yau tafara ganinsa, bawai yau ta fara ganinsa ba sai dai bata fiye yiwa mutum kyakyawan kallo ba, yau ta ganshine sosai a gabanta yayi mata kyau, shima gabansane ya faďi sakamakon ganin Iman yau a ainihinta ba cikin mayafi da labcoat ba kamar kullum, Ta lalubi ďan kwalinta ta ďaura ta xare gilashin idanunta tayi mishi barka da xuwa, Shiru ya ratsa na wani daqiqai wani chemistry mai ban mamaki na aiki a zuciyoyinsu da kwayoyin idanunsu yana shiga cikin xukatansu dai dai lokacin fauxie ta shigo da gudu da ball a hannunta little na biye da Ita yana kuka akan tabashi taqi sai dariya take masa, Suna ganin Dr Deen duk sukayi kansa suka rungumesa suna dariya, 'ďanki kike hanawa ball fauxie, bakiji kunya ba yana kuka yana biye dake, Ta soma dariya tana kallonsa kafin ta bawa little ball ďin, 'amma shine ya jefomin ita a goshi ina assignment, 'Kiyi haquri kidaina sashi kuka kinji, Little ya dubesa yana gauranci da alama ya kawo qarar fauxie ne, daga shi har Iman suka kwashe da dariya yanda yake Mgnr komai baxaka fahimta aciki ba amma yanayin fuskarsa xaka gane da faďa yake Mgnr, Deen ya rarrashesa haďe da bashi ball ďin ya fice da gudu, 'yaya yau xakaje damu inda baffa, 'kujirani a waje gani fitowa ynxu sai muje, ta fita da gudu itama, Deen ya dubeta wannan karon ba walwala a fuskarsa, 'inason nasan matsayina a gunki fatyma, 'Sa'eed na xaba, shi nake ganin yafi kowa sanina da halin dana fuskanta a baya, nasanshi ya sanni, Ya dubeta da tsananin mamaki, 'kina tunanin har akwai wani abu daya shafi rayuwarki a baya wanda ban sani ba, fiye da shekara muna tare kina nufin bakisan hali na bakisan ko waye niba, ban taba roqon mace ta soni ba sai akan ki Iman, kinsan yawan matan dake bibiyata domin na auresu naqi saboda kece a xuciyata Kuma baffa yafi amincewa dake, mecece ribar aurenki da mai mata kije masa da qanwarki da yaronki.... 'Acikin yan matan dake bibiyarka ka xabi ďaya ka aura Dr Deen, qanwata da yarona ko bada aure ba xn iya Kula dasu domin Nafison rayuwarsu akan tawa Nafison farin cikinsu akan nawa, Wannan Karon ya harzuqa and he mean it, ya haqura da Iman a ynxu bai taba rarrashin mace ko roqonta akan taso Shiba sai akanta kuma take wulaqantashi, duk girmansa da ajinsa, 'Na tabbata ďan halak fatyma, kije gaki ga Sa'eed, ya tashi ya fice batare daya qara kallonta ba, Nan take taji xuciyarta ta buga tabisa da kallo kada dai ya haqura da itane? Daga inda take xaune tana jinsa yana kiran little akan yaxo su tafi, She knows it Dr Deen yana sonta, kuma shi yafi dacewa data aura, shine baida mata shi kaďai xai iya riqe yaranta ba tsangwama gashi yaran sunyi sabo sosai da baffa, amma Sa'eed fa? Shima yana sonta shima xai iya riqa yaranta haka shima yana buqatar kulawar Mace tunda bai samu agurin matar saba..... Har dare yaran basu dawo ba tasan baxai wuce acan xasu kwana ba, ita a ynxu yaye little xatayi ta huta tunda dama bai damu dashan mamma ba, idan ba Ita ta matseshi tabashi ba baxai nema ba yanacin abincinsa sosai ga bakinsa ya saba dacin daďi kamar irin na fauxie duk kalar kwalama xaka Deen ya siyo ya kawowa yaran harma Sa'eed. Kwana biyu bata qara sanya Deen a ido ba ko a asibiti sun daina haďuwa, ya daina kiranta a waya sai tayi qoqarin kiransa sai ta fasa kada dai da gaske yake ya haqura da ita, A xahirin damuwarta a ynxu Iman na wani hali na soyayya, Wanda ita kanta batasan cewar soyayyar ce ke dawainiya da xuciyarta ba, soyayyar Dr Deen Wanda a halin ynxu batasan halin da yake ciki ba, ita dashi sai gani a nesa ko idan yaxo maida little shima daga gate, Soyayyarsa a xuciyarta sai qara linkuwa take Kamar ana iza wuta, ta tuna ranar rabuwarsu ta qarshe, _'Na tabbata ďan halak fatyma kije gaki ga Sa'eed._ Sautin dake ta mata kururuwa a kunne kenan a duk lokacin data xauna ita kaďai, wanda ke qara ruruta wutar nadamarta, irin nadamar da RAIHAN yayi a SALIMA MAKAUNIYA (shima littafin Pherty ne), to amma rabuwar ta xamo mata jifa'i...dai dai wannan halin data tsinci xuciyarta da ruhinta aciki na bege daso da qaunar gabaki ďaya, Ta yarda harshe mugun abu ne, ya Allah kabamu linxaminshi a hannunmu, harshe yana kaimu ga wuta, yana kaimu sa'ira Kuma yana kaimu aljanna, again yana lalata mana rayuwa, mu dinga riqeshi ta hanyar tauna magana kafin mu faďeta, Idan ya furta baya taba mayarda ita komai daďinta ko ďacinta, da Hausa (harshe), da turanci (tongue) da larabci (Lisan), wata tsokace mai amfani daban daban da Allah ya halitta a cikin bakinmu wadda in muka iya controlling ďinta xamu iya controlling ďin duka al'amuran rayuwarmu, Me xatayi tayi repenting kuskuren data tafka a baya, Dr Merah ya kamata ta tunkara ko baffa? Waye xabinta a ciki, Dr Deen ko Sa'eed?...... My wattpad Phertymerh1 *Babana da mijina* ©Fertymerh Xarah 💞 39 Yinin yau duk suna tare da Sa'eed, yana xaune a office ďinta tana duba patient, little kuwa yana gun Deen tun jiya da yaje dashi bai dawo mata da shi ba, Deen yaga xuwan Sa'eed asibitin bai damu ba a ynxu da yake yaqi da xuciyarsa na ganin ya fiddata a ransa, Sanda Sa'eed xai tafi taje ta rakasa ta dawo kenan ta tsinkayo Dr Deen da wata budurwa a tsaye tana ďauke da little, yanayin ynda suke tafiya murmushi a fuskarsu kaďai xai nuna ma masoya ne, nan take taji wani abu ya taso ya tokare qirjinta, Kai tsaye ta nufesu, little dake hannun yarinyar ta fisge, budurwar tayi tsaye tana kallonta da mamaki little kuwa kuka ya fara yana qoqarin sauka jikinta tare da miqowa Dr Deen hannunsa alamar ya karbesa, Dukkansu an rasa mai bakin mgn har ta nufi office ďinta, Deen yayiwa budurwar Sallama ya fice da sauri yabi bayanta, A office sai qoqarin goya yaron take amma yaqi, ya miqe mata a baya sai kuka yake, Cikin xafin nama ya fisgo yaron daga bayanta haďe da hankaďata gefe, yaron ya qanqameshi sai ajiyar xuciya yake, Sosai little ya saba da Deen fiye da mahaifiyarsa, yasan Deen sosai ko muryarsa yaji da gudu yake tunkararsa yana dariya, Shi yake kallo a matsayin mahaifinsa, bai kuma aje shi nan kusa a xuciyarsa ba, Don ko kuka yakewa uwar idan bai sa baki ya rarrashesa ba baxai yi shiru ba, haka inya qi cin cereal ko abinci a hannunta indai yana gidan shike bashi, Ta dubesa ranta a bace, 'kabani yarona, Bai tankataba sai yaga little nason xuwa inda take da alama mamma yake son ta bashi, ba musu ya miqa mata yaron ta karbesa a fusace ta ajiye akan sofa kana ta xagaya ta xauna inda take duba patient, har lokacin kuma bai daina kuka ba, Yasan baxata bashi ya sha ba yanda yaga ranta yake a bace to miye dalilin wannan fushin nata? Fushin bai sauka daga fuskarsa ba amma ya sassauta murya, 'Kiyi haquri ki manta komai ki daukesa kibashi abinci, Cikin bala'i tace 'idan kai ka haifar min shi sai kagayamin haqqinsa dake kanka, Yanxu incire inbaka abinka, Yayi murmushi ya ďauki yaron yaje ya ďora a jikinta, 'naji bani na haifesa ba, nima Kuma bn fidda rai ba inaji a jikina Allah xai bani nawa, Sai taga idanunshi sun juye sun koma luv colour wani irin situation ne da baxata iya mantawa da shi ba,irin halin da Deedah ke shiga kenan idan yana biďarta ba sai yayi mgn ba take ganewa, dan haka sai taji tsoron shayar dashi a gabansa ballantana ma tun jiya ta yayeshi, sai ta ďauko empty feeder tasa masa a baki yaqi karba, ta dubesa a raunane Idanunsa akanta cikin bacin rai, 'tun jiya na yayeshi.. 'what? Kin yayeshi wannan wane irin yaye ne? 'na yayeshi ďana ne nikeda haqqi akansa, Ransa ya qara baci har ya juya sai Kuma ya dawo ya ďauki yaron ya fice a fusace ta bisa da ido kawai, Bata damu ba ta maida hankalinta ga duba files, 4pm ta isa gida yau, anan take jin labarin Deen yaxo ya kwashi kayan little duka ya tafi dashi, ba Wannan ne damuwarta ba a Yanxu, qirjinta ke ciwo sun cicciko tun jiya ba'a sha su ba, ga wani nauyi da suka mata har Xaxxabi take ji, daďin ta ďaya fauxie taje islamiya da xata dameta ne da surutu, tana fashin sallah sai ta kwanta kawai batare da taci abinci ba, Shiru shiru bata fito ba har magrib, fauxie ma batasan tana gidan ba tana can cikin gida tana wasa, Adama ta shigo ta ganta a kwance, 'hajiya ba lfy ne yau kika xauna a ďaki, 'yauwa, kunun alkama ko kunun farar Shinkafa nake so kimin, Shikenan tasa kai ta fice da sauri, sai ga fauxie ta shigo, 'anty ki Kira yaya yaxo yaje dani inda baffa tun jiya yaje da little bada niba, Tayi mata banxa, 'kinji anty.... nan ma ta kyaleta dai dai lokacin wayarta na ďauki qara, tana dubawa taga sunan salima kamar baxata ďauka ba sai ta ďauka, 'kin ban mamaki fatyma, ki rasa inda xakiyi xawarcinki sai akan mijina, kinci amanar qawancenmu Kuma kinci amanar Deedah, abokin mijinki da qawarki saboda bakida hankali, to ga gidan ki shigo ki xauna kigani idan xaki iya kishi dani, kuma kisani agola baxai xauna mana a gida ba, ya Mtsewwwwww ta tsinke wayar, 'agola? Iman ta nanata sunan tana kallon wayarta, Yanxu yaronta ake kira agola? 'kinji anty... Fauxie ta katseta, Cikin tsawa tace, ke kimin shiru banxa, get out please, da sauri ta fice cikin tsoron yanayinta, * Wallahi baka isa ba, kayi kaďan Sa'eed, kai ko kunya bakaji ka auri matar amininka, 'iyakar qarshen rashin kunyar kenan in aureta in kula da Ita in kula da yaronta shine na riqe amana, inason Iman baki isa ki hanamin auren taba, 'wallahi koni ko ita a gidan, 'na zabi Iman, 'haka kace, haka kace? 'eh haka nace, to me kike min a gidannan ba abinda kikemin ba kulawarki ba kulawar yarana, su kansu na tabbata idan na kawo Iman a gidannan xasuji daďin kasancewa da Ita, kewai ko kunya bakyaji kullum sai anyi miki faďa akan yanda xaki kula da miji da gidanki, duk sanda xn sami habbi a gidannan inajin yanda take maki faďa kike gwatsaleta, nagaji da xama a hakan shiyasa na gayamiki xn auri Iman, Kuka take shabe shabe, duk abinda ta samu a ďakin jifansa take dashi, yau takai salima harda xagin Sa'eed, kuma tayi rantsuwa Iman bata isa ta shigo gidan ba indai tana raye, yasa kai ya fice bai qara bi ta kanta ba.... Tunowa da Deedah da kalmar da aka jefi ďanta da Ita yasanyata kuka a ranar, har safiya bata rumtsa ba kuma Sa'eed yaxo da kansa yabata haquri tare da rarrashinta, baxai haďe su a gida ďaya ba kowa da nata gidan sai taji sanyi a xuciyarta ta qara amincewa da son da Sa'eed ke yi mata. Yau kwana uku kenan bataje asibiti ba tana gida ba lafiya, Deen bai gantaba Kuma bai damu ba, amma yau yayi niyar kaimata little meyiwuwa tayi xuciya da yaron ne shiyasa ta daina fitowa asibiti, Tana xaune falo sanye da hijab ya shiga da Sallama, bai bari sun haďa ido ba, yanayin fuskarsa kaďai xai nuna mata har lokacin yana fushi da Ita, duk sai taji wani iri a jikinta ta xuba masa idanuwa tana kallonsa, Gayen ya haďu qarshe ga iya shiga ta suit da shadda, kai har white cotton lace da qananan kaya ma kyau suke masa, idaniya basa gajiya da kallonshi harga maza yan uwansa bama mata kaďai ba, ga yawan sumar jiki data kai, bata taba ganinshi cikin rashin walwala ba kamar yau, Taji sabon al'amari yana fisgar xuciyarta game dashi, tsigar jikinta na tashi, ji take kamar ta ďora kanta a kafadunsa taji dalilin damuwar da yake ciki inda hali ma ta rungumeshi, Kai tsaye ya nufeta ya ajiye little a gefenta, qamshin turarensa dana hucinsa suka gauraye suka daki hancinta, Ya ilahi ta furta a hankali tare da kai hannunta ta dafe qirjinta sabida Karfin bugunsa daya qaru, meke damuna ne yau akan Deen? Juyowar nan da xatayi sai idanunsu cikin na juna yayi maza ya ďaure fuska ita kuma duk kunya ta kamata tunda ya kamata tana mishi kallon kurilla kamar bata taba ganinshi, Daga kallon da yayi mata nan take ya gane bata lfy, idanunta sun xurma kaďan fuskarta tayi rama har xaiyi mata mgn sai Kuma ya fasa yasakai ya bar falon, ta bisa da kallo, Ta yarda ta saduda ta amince Deen ya haramta gareta, soyayyarsu ta xama mafarki mai daďi irin Wanda ďan Adam kanyi ya farka yana mai cixon yatsar sa kasancewarsa reality, _'dreams are concerned but not all dreams are born alive, some are aborted, others are still born._ Kalaman..... Noble Laureate ZAINAB ALKALI..... My wattpad Phertymerh1 *Babana da mijina* ©Fertymerh Xarah 💞 *Dis page is for you, Shafaatu Zurmi, Pherty b-b, and Aneesa A Rimi* 41 Tun daga lokacin bata qara sanya Sa'eed a idanuwanta ba, ga Deen ya daina kulata tuntuni ma, ta shiga damuwa sosai, Little ba lfy koda wasa baiyi yunqurin gayamata ba yasan halinta akan ruďewa, duk da Xaxxabi ne kawai yakeyi, shike Kula da yaron har a asibiti yana tare dashi, bata taba sanin baida lfy ba har yaron yasami lfy, daga baya ne takejin labarin a gurin baffa. 1 month.... Kai tsaye ta shirya ta nufi bank inda Sa'eed, akayi Sa'a shi kaďai ne a office ďinsa, suna haďa ido sai da sukaji wani iri a xuciyarsu, yayi qarfin halin ďauke Idanunsa akanta haďe da sakin malalacin murmushi wanda bai kai xucci ba, Yanayin fuskarsa ya Sanya ta nufi cikin office ďin cikin kwarin gwiwa ta sami guri ta xauna, 'barka da xuwa, me xan sanya a kawo maki, 'need nothing Sa'eed... sai kuma tayi shiru idanunta sunyi rau, shima shirun yayi xuciyarsa na bugawa, 'ya su little da fauxie, 'Alhamdulillah... 'ko da matsala ne Iman? ta gyada kai tana kallonsa haďe da share hawayen dana xubo mata, 'why did you hate me Sa'eed? 'saboda me, meyasa kike wannan mgnr iman, duk duniya akwai wanda ya kaini sonki ne, you hate me shiyasa na barki da Wanda kike so, naga kamar Ina takuraki shiyasa na barki, 'ba haka bane, har ynxu xuciyata ta kasa tantance min xabina, idan nace bana son ka ko bana son Deen nayi ma qarya, amma fushinka akaina K.... ya katseta, 'ki auri Dr Deen....itace kalma dana fito bakin Sa'eed ta ďago tana kallonsa cike da mamaki, 'I know Kinason Dr Deen, he loves you too, na taba gayamiki ya sameni nan saboda ke, bawai ya roqeni na barmashi ke ba ya roqeni akan idan na aure ki na kula da ke da yaranki, na baki farinciki har a qarshen rayuwarki, ba abinda na fahimta a idanuwansa sai xallar soyayyarki, bai fito ya faďa a baki ba amma idanunsa sun nuna, ina sonki Iman, dole ta sanya xn haqura dake ki auri Dr Deen domin yafini buqatarki, bashida kowa bayan mahaifinsa, nikuma I have family matsalar bnda kwanciyar hankali akansu, Tunda yake magana tayi shiru tana kallonsa ta kasa fahimtar komai a kalamansa Illa na ta auri Dr Deen, yes xata iya haqura da Sa'eed cos xuciyarta tafi rinjaya kan Deen and she accept it, ta amince xata auresa ko dan kwanciyar hankalinta dana yaranta, 'but Sa'eed...... Shishshsh ya katseta, kada kidamu dani, Allah is with me idan salima mai shiriyace Allah ya shiryata ya ganar da Ita, ban kullace kiba, idan kin amince I will be your brother na har abada kamar mun fito ciki ďaya dake.... Ta gyada kai tana murmushi mai tare da hawaye, farin cikinta a yau, ta rasa yayyunta biyu da suka rasu yau ga madadinsu, Dr Merah da Sa'eed, kyautace daga Allah Kuma ta karba da hannu biyu, ta rasa mahaifi ta sami baffa a hannu sai dai fatan miji na gari wannan shi kaďai ne burinta a Yanxu. Tare da Sa'eed sukaje suka sami baffa da Mgnr kan ta amince da auren Deen, sosai baffa yayi farinciki kamar xai haďiye Iman haka yakeji, Koda baffa ya gayawa Deen Mgnr bai nuna masa farinciki ba amma har a xuciyarsa yaji daďi, duk da hakan ya basar bai nemeta ba kamar baisan da Mgnr ba, Dr Merah, Sa'eed da wani kawunta su suka karbi sadakinta, sune waliyyanta, Sai dai ba yanxu xata tare ba sai tagama shirye shiryen ta kamar yanda Dr Deen shima yana buqatar lokaci har ya haďa kayan aurenta. Salima na xaune a falo tare da yaranta taga mutane na shigowa gidan, 'waďannan su Waye ta faďa bayan ta tashi, ga mamakinta sai taga qatuwar Mota da kaya ana saukewa irin kayan amare ďinnan, maxa ke shigowa da kayan yayin da matan suka nufi ďayan part ďin da ke rufe, tana gani suka buďe suka shiga, 'no she can't believe it Sa'eed baxai mata haka, tor kodai haya yabada gurin, inajin haya ya bada gidan, let me confirm it, Ta sanya hijab ďinta ta fita, cikin maxan masu sauke kaya ta nufa, 'sannu malam, 'sannu hajiya, 'wancan part ďin haya aka ďauke sa kome? 'A'a amaryar mai gidan ce gobe xa'a ďaura aure ta tare, Batace komai ba amma jikinta har rawa yake saboda tashin hankali, Koda taje ďakinta kasa xama tayi sai safa da marwa take, ganin ba mafita ta dauki hijab ďinta ta fice kai tsaye gidan Iman ta nufa ta Kuwa yi Sa'a ta sameta, Ba Sallama ba komai ta faďa gidan suna haďa ido da fatyma ta soma faďa da xage xage ta inda take shiga batanan take fita ba, Iman na xaune da adama tana yanka mata fruits, idan ke mai karatu kin tanka tor Iman ta tanka, tunda ta maida kanta ga cin fruit bata qara waiwayarta ba, dama iman ga haquri da sanyin hali. Wannan ne yafi komai baqin ciki da haushi kana faďa ayima shiru amaidaka banxa Hakan ya qara kufular da salima ta soma ball da duk abinda ke falon, Iman ta tashi ta dubi adama, ki shiga ki qarasa aikinki adama, idan wannan mahaukaciyar ta gama haukarta ta bata gurinnan kiyiwa securities magana a fitar min da Ita daga gidan kana a gyara falon tasa kai ta fice haďe da rufe ďakinta, Kamar ta sanya ihu haka takeji angama cin amanarta a ganinta, qawarta xata aure mata miji wallahi bata isa ba, Gashi ta kirata mahaukaciya, kamar daga Sama sai ga Sa'eed a gidan abinda idanuwansa na gani ya tsoratashi, meya fito da salima da ixinin wa ta fito meyasa tayiwa falon kaca kaca haka, nan take ya ďauketa da wani Mari sai data ga gilmawar taurari, hancinta ya fara jini, Basai na gayamaku irin Faďan da sukayi a ranar ba kamar xasu haďe junansu a haka ya fisgeta suka bar gidan...... Daren ranar basu kwantaba kwana sukayi bala'i haka ta xamar masa tamkar wata xararriya sai daya sanyata a ďaki ya rufeta kafin ya sami sa'ida. Washe gari aka ďaura auren Dr Iman da Dr Deen... Kana aka ďaura auren Sa'eed da Habbi qawar salima, Koya xamansu xai kasance da salima, ya salima xata kasance idan ta wayi gari ta sami habbi a matsayin abokiyar xamanta, qawar dake bata shawara akan yanda xata Kula da mijinta, wani abin qarin haushi habbi budurwace bata taba aure ba. My wattpad Phertymerh1 *Babana da mijina* ©Fertymerh Xarah 💞 42 Har ynxu ban fahimce ka ba, idan ba Iman ka aura ba to Waye ka aura, ko kana tunanin bansan cewa yau aka ďaura aurenka da Iman ba, 'bani ke auren Iman ba, Wanda take aure daban wadda nake aure daban, idan Kina tunanin saboda haukarki naqi auren Iman tor kina tunanin banxa ne, anjima da dare matata xata tare koma wacece xaki ganta, Hankalinta ya qara tashi numfashinta har fita yake da sauri da sauri, qaryane Iman yake aure idan ba shiba to wake aurenta? 'kagayamin Iman *Matar Waye?* idan har bakai ke aurentaba, 'wannan ne baxakiji a bakina ba, inaji kin saba xuwa gidanta ki sameta ki nuna mata rashin mutuncinki ynxu ma you are free... ya cigaba da haďa kayansa, 'kayan me kake haďawa Sa'eed, har ynxu ban fahimceka ba me kake nufi ne, 'kayana nake haďawa na maidasu inda amaryata inda xa'a kula dasu da darajasu.... Kafin tayi magana ya fice, Kuka take tana haďa kayanta tayi yaji gida xataje, yana ganin lokacin da ta fita da kayan bai hanata ba, kai tsaye gidansu ta nufa, Ummanta na jin dalilin dawowarta ta rufeta da duka kamar xata cinyeta, 'ai Sa'eed yamin dai dai wallahi, kinci amanar tarbiyar danayi maki dan ba haka kika taso kika samu inayi da mahaifinki ba, kina gani da tsufana a ynxu nake kula da mijina, sau nawa yake kawo qararki gidannan in xaunar dake inyi faďa inyi rarrashi duk bakiji ba, 'xaman gidan kikeso kixo ki xauna muna gugar kafada dake, idan nayiwa mijina kwalliya kema kiyi masa gaki ga gidan ki xauna tunda kin xabi hakan a rayuwarki, Kuka take sosai Kamar ranta, Mahaifinta ma ya tsoma bakinsa, 'idan har kika bari kika kashe auren ki saboda son xuciya bani bake kuma baxaki xauna min a gida ba, tashi kije kibani guri shashasha kawai, 'na shiga uku *babana da mijina*, babana xai yafeni saboda mijin dayaci amanata, ta tashi tana kuka ta shiga motarta, wayar habbi ta Kira ko xata sami shawara a gurinta, Tana ringing ba'a ďauka ba har ta tsinke ta qara kira sai data kusa tsinkewa kana ta ďauka, 'kina gida ne habbi? 'a'a Ina saloon, 'naso naxo ne, Sa'eed aure xai qara yau amaryarsa xata tare, ta fara kuka, 'wannan matsalarkice salima, sanda nake baki shawara bakiji ba ynxu ni banda abinda xn maki, bikin dake gabana ma ya isheni, 'bikin waye Kuma, 'au bakida labarin aurena ne? 'Hhhhhh wasa kike, har yaushe xakiyi aure baki sanardani ba gobe xn shigo kibani mafita, 'a'a basai kinxo ba ni xnma xo, ta tsinke wayar.... Da dare aka kawo amarya duk a nata tunanin Iman ce amarya musamman data ga little a sashen Sa'eed yau, tana ji sanda aka shigo da amaryar da guda sai leqe take ta window, bataga fuskarta ba, ďakin Sa'eed ta nufa suna haďa ido ta fashe da kuka, yasan xafin kishin da takeji a xuciyarta, yana son matarsa bawai baya sonta ba halintane ya sanya yayi mata haka, Ya taso ya rungumeta, rarrashinta yake cikin Kalamai masu sanyaya xuciya, sai abin na bashi mamaki ganin yau duk inda ya taba a jikinsa bata hanashi, babu harara babu mitar ta gaji sai ma qara narkewa da tayi a jikinsa tana qara kissing ďinsa.... Da kyar ya sami kansa kamar mai son yi masa fyade a Wannan daren, ya ďauki little dake barci ya fice da sauri...... Washe garin ranar ta kasa haqura ta isa sashen amarya, dai dai lokacin habbi ta fito da gudu Sa'eed na biye da Ita daga baya.... Duk suka ja turus ana kallon kallon... Tamkar a mafarki salima ke ganin habbi da mijin da tafi so fiye da komai a rayuwarta, 'barka da safiya anty xo ki xauna, cewar habbi tana kallonta qasa qasa... tsananin ruďewa yasa tayi kan habbi suka fara kokawa, da kyar Sa'eed ya rabasu, 'munafuka, snatcher, azzaluma macuciya mai kwacewa mutane miji, sai da kika gama jin sirrina xaki aure min miji Wlhy baxan taba yafe maki ba, kaima baxan yafe ma ba Sa'eed ta soma kuka, basu ankaraba sai ganin kawai sukayi ta ďauki kwalbar malt dake ajiye ta jefata ga plasma t.v ,tayi ratsaratsa, duk abinda tasan mai fasuwa ne tabi tana fasawa, Sa'eed na fisgota ya ďauketa da Mari kana yajata ya fiddata gidan suka rufe... Kamar habbi xatayi kuka haka take tsaye ganin yanda aka farfasa mata kaya, jiya jiya da kawowata, Haquri ya soma bata anjima xaisa akawo mata duk abinda salima ta fasa, tana jin haka ta saki ranta ta rungume shi tana kissing, Tare sukayi wanka sukayi breakfast, daďin da Sa'eed keji baya misaltuwa, bai taba samun irin Wannan kulawar ba, ta rakasa har motarsa sai da taga yabar gidan kana ta ďauki qaton icce ta nufi motar salima, Salima na ganin tana farfasa mata mota ta window kafin ta fito tuni habbi tayi shigewarta cikin gidanta ta rufe, tabi motar da kallo Kamar xata sanya ihu dan haushi da takaici....... * Bayan wasu kwanaki Iman ta haďa duka ma'aikatan gidan guri ďaya, ta roqesu gafara kana ta sallamesu, irin sallamar da tayi masu baxasu taba mantawa da Ita ba saboda ta cikasu da dimbin alheri mai tarin yawa, sunyi rabuwar arxiki mai cike da shaquwa da kewar mace mai hankali da taqwa kamar Iman... Mutum uku kawai tabari a tare da Ita, Suleiman, dijeh da adama, Tun bayan auren su da Deen bata qara sanyashi a ido ba, sai dai taji muryarsa a falo shida su fauxie, Parking tayi sosai duk abinda take buqata ta hadasu guri ďaya saboda rufe gidan xasuyi, ansa ranar tarewarta lokacin da Deen ya aiko kayan lefenta kamar na wata budurwa, kaya ne masu kyau da tsada na gani a faďa, haka little da fauxie sai da yayiwa kowa set ďaya... Sa'eed na bank ta kirashi ta sanardashi abinda habbi tayi, tsaki yayi ya tsinke Wayar hankalinsa a dagule wannan masifa dame tayi kama yasan duk laifin salima ne, Da yadawo ya hadasu yayi masu faďa sosai akan su haďa kansu shi baxai ďauki wannan kishin tsiyar ba, Habbi ta bashi haquri tace baxata qara ba xata xamo mai biyayya garesa, yaji daďin haka amma salima Kuwa buďar bakinta sai cewa tayi, 'maganar motata a gyaramin... 'yace xa'a gyara itama xn siya mata tata... 'idan har ka siyamata sabawa nima sai an canxamin Kai bnmason gyaran wata nakeso a canxamin, 'duk ba matsala bane salima indai xaku haďa kanku ku xauna cikin yardar juna.... Habbi ta dubesa tana kashe masa ido, 'sweet muje intayaka kayi wanka kaci abinci inyima tausa nasan a gajiye kake, ya saki murmushi yana kallonta ko baiyi magana ba kasan yaji daďi, ba gardama ya tashi yabi bayanta bai qara waiwayen salima ba haushi kamar xai kasheta, Tunda yabita part ďinta bata qara jin duriyarsa ko motsinsa ba sai faman leqe take ta window ko xata ganshi shiru kakeji har Washe gari, tana tsaye a window taga fitowarsu, habbi na ďauke da briefcase ďinsa shi Kuma ya riqa hannunta har gurin motarsa, Tana ganin lokacin daya Karbi briefcase ďinsa ya shiga mota habbi ta sunkuya ta sumbacesa kana ta soma yi masa bye bye shima yana yi mata har ya fice, wannan ranar harda kuka tayi, tunda take dashi ko falo bata taba rakashi ba ballantana hr gurin motarsa. Amarya Iman sai faman shirye shiryen biki ake tasha qunshi ja abinka da farar mace qafafunta da hannuwanta sun fito sosai tayi kyau ga xoben xinari dake sanye a yatsun hannuwanta Wanda ya qara fito da kyawun lallenta, Affiya, Dr Fulani da Dr Umayma sune abokanta suke tsaye a kanta na ganin sun shirya amarya sosai ciki da wajenta ta fito, Fauxie itama Anyi mata tata shigar cikin gown fara, haka shima little cikin suit duk suna gurin Merah..... Amarya kawai ake jira ta fito ango na cikin Mota yana jiranta, Sa'eed xaija motar amarya da ango xuwa gurin dinner.... Duk ya qagu ta fito cos sunyi late kamar ance ya ďago akayi Sa'a su affiya sun fito da Ita, an rufe fuskarta da wani net duk da haka baxaka rasa ganin fuskarta ba, ba qaramin kyawu tayi ba har ya kasa ďauke idanuwansa akanta, bama shiba har Sa'eed da sauri ya ďauke kansa gareta yana sauke numfashi, Iman yayi asararta ya fada ahankali, Dr Fulani na bude motar ta shiga kana suda Affiya suka nufi nasu motocin, Tunda ta shigo ta xauna qamshin turaren ta mai sanyin qamshi da daďin gaske ya mamaye motar, ga wani qamshin amarcin da take, Sa'eed yaja motar a hankali jikinsa a sanyaye... Duk qoqarinsa na ganin ya kauce mata ya kasa, he can't, yaga kyawun Iman sosai, kayan dake sanye a jikinta sun fito da shape ďinta wanda baisan Iman ďin haka take ba duk ganin da yake mata acikin hijab da labcoat ne amma yau ya ganta in her real image, no hijab, no labcoat, Ya juya yana kallonta kanta na sunkuye, bata Kalle sa ba kuma batayi masa mgn ba sai dai xuciyarta ta kasa nutsuwa ta rasa dalilin shariyar da yake mata har wannan lokacin da ta amince na xamowa matarsa. A hankali ya sauke kwayar Idanunsa akan hannuwanta inda yayi arba da Jan qunshinta, Dama gashi da son qunshi yana sha'awar yaga mace da lalle balle wannan da ta xama tasa mallakinsa, baisan lokacin daya ďora hannunsa akan nata ba ya haďe yatsunsu guri ďaya yana murzawa a hankali....... Nima ina shirin xuwa dinner ne🏃🏻‍♀, nasan su Xuhura da Pherty novels ma suna can suna shirin xuwa dinner. My wattpad Phertymerh1 *Babana da mijina* ©Fertymerh Xarah 💞 43 *Dedicated dis page to Ayusha Muhd, Rash Kardam, Fido Sodangi, Ummi Ahmed, Uwani Tahir & Sumayya Dikko* Hakan bai sa ta ďago ta dubesa ba kuma bata janye hannunta daga garesa ba, Har suka iso ba Wanda ya tanka acikinsu, a tare suka fito motar ga mutane tsaye ana jiransu hotel ďin cike yake da jama'a samari da yan mata, Suna fitowa aka soma watsa flowers a gefenta fauxie ce cikin irin tata gown, shikuma little yana gefensa cikin suit kamar Dr Deen, sunyi matuqar kyau sosai, Nan da nan masu camera suka fara aikinsu, masu yi a waya suka soma, Sa'eed ma sai daukarsu yake, ga fertymerh Xarah novels ma kowa da wayarsa qoqarinsa yaga Dr Iman da Dr Deen a wayarsa, bama kamar Pherty novels dake ture ture burinsu suxo gaba su ďauki amarya, sai da Dr Deen yasa hannu ya kare fuskar iman ganin hasken camera sunyi yawa akanta😜. Habbi kusa da Sa'eed ta xauna dama yabarta taxo, aka xaxxauna, nan aka fara gudanar da bikin cikin farin ciki da jin daďi, Deen ya sunkuya dai dai kunneta, 'Na kasa haqura amma dole xn gayamiki kinyi kyau sosai har Ina kishin dubban maxan dake gurinnan.... Ta dubesa suna haďa ido ta saki murmushi cikin jin kunyarsa, shima murmushin yayi dai dai lokacin da mai camera ya daukesu.... Ana cikin yin dinner sai ga salima taxo gurin yanda tayi parking ma xai tabbatar ma da a fusace take, Tana tsaye tana neman inda xataga habbi, Iman ta ganta sai ta ďauke kanta gefe kamar bata ganta ba, Dr Deen ma ya ganta sai dai baisan ko Wacece ba, Kamar daga Sama ta hango Sa'eed da habbi suna dariya ba xato ba tsammani habbi taji duka, nan fa suka shiga kokawa dambe suke sosai, Nan fa gurin ya qaure da ihu, lafiyayyun Mari biyu Sa'eed yayi mata amma bata damu ba ga hancinta na jini burinta kawai ta illata habbi, ganin yanda ta xama tamkar mahaukaciya a gurin kowa na soma neman inda yayi komai ta samu jifan mutane take dashi, Dr Merah yaja Affiya saboda hankalinsa na gunta baya son komai ya sameta ko kaďan dan ma basuxo da yaran suba, Dr Fulani taja hannu fauxie da little tayi Mota dasu, kowa ta kansa yake dan salima bata bar kowa ba har mijinta ta jimasa ciwo a hannu, bai taba tunanin haka take ba balle harta iya aikata hakan, Iman a tunaninta duk saboda itane salima ke wannan haukan, a ruďe take ganin take xataxo ta jimata ciwo ne, sai ta qanqame Deen sosai Kamar xata shiga cikinsa, shi Kuma hankalinsa na gun su fauxie sai dayaga an sanyasu Mota kana ya maida hankalinsa ga riqon da Iman tayi masa, idanunta a lumshe sai hawaye take abu kaďan ke ruďata baisan irin xuciyarta ba, yasa wayarsa ya ďauketa pic batare da ta sani ba kana yasa hannunsa ďaya ya rungumota.. Da kyar wasu maza suka rirriqeta, Sa'eed ya ďaure ta da wata waya sai faďi yake, 'batada hankali daga gidan mahaukata ta fito, ta qara xabura 'qarya kake, kunci amanata ne Kuma baxan barku ba, Ya ďaure bakinta da gyalen habbi, sai kuka take ya ďauketa ya nufi motarta da Ita ya sanyata ciki ya Kulle motar sai xufa yake, wannan wahalar dame tayi kama, ga hannunsa sai jini yake habbi ta riqosa tana hawaye, 'dear muje asibiti dan Allah, Ya dubi hannun kafin ya nufi inda Deen yake tsaye da Iman, 'Dan Allah kuyi haquri d....... Deen ya katsesa, 'ba komai Sa'eed kayi sauri kaje asibiti, iman ta ďago tana kallonsa cikin tausaya shi har sai yaushe xai sami kwanciyar hankalin wannan matar? Suna haďa ido dashi ta qara fashewa da kuka ta maida kanta jikin Deen, Sa'eed kuma da sauri ya juya nan cikin motar suka barta habbi ta jasa suka nufi asibiti..... Kowa ya watse sai gasu ci biki ynxu ake xuwa😂, Ummi Aysher, Faxyfashion, Serdia, Halimcy, Zarah dange, miss Aysher, baby Bello, Kdeey, Kwaise, Lilmeerahcute, Xuhura Ajiya, Meenah, Rabi'atu Sk, Didi Aneesa, Afrah bhai, Anty maijidda musa, Khadija Sidi, Shafa Umar, Maryam kaumi, Sally, Teemah cool, Anka, H.Melody, RAZ, Nusee, Pherty, Rukayya Umar, Hafsat rano, Zarah Bukar, Zee yabour, Faty Shuwa, Hindatu Arzika, Hamidata, ya salam🙆🏻 gasu nan dai dayawa har bn iya lissafaku am sorry please 👏🏻, Sukaja suka yi turus ganin ana watsewa, Dr Merah tuni yabar gurin, Dr Deen da Iman ba motar shiga dama da ta Sa'eed suka xo kuma sunyi asibiti, Suka tsaya cirko cirko suna kallon mutanen dake shiga mota suna barin gurin, suna kallon salima acikin motar, haka kawai Deen yaji ya tsaneta, ya juya yana kallon Iman dake qanqame da hannunsa, 'ita wannan wai wacece, meyasa tayi haka? 'matar Sa'eed ce, uwargidansa, tana kishina saboda Sa'eed, amma bansan dalilinta nayin haka ba, Ya gyada kai cikin gamsuwa batare daya kalletaba, suna tsaye sai ga mota tayi parking gurin, sunsan motar Merah ce, suka buďe suka shiga har yakai affiya gida, Acikin motar Dr Deen da Dr Merah suka cigaba da nanata mgnr kowane ransa a bace fuskokinsu kawai xaka gani ka karanci hakan, iman na baya tayi shiru tana saurarensu, ita suka fara ajiyewa gida kana suka fice kowane ba walwala a fuskarsa ita kanta bataji daďi ba she will never forget salima in her life.... Sa'eed sai da akayi masa ďinki a hannu, koda suka dawo ta galabaita sai xufa take tana kuka, shi yaja motarta habbi taja motarsa suka nufi gida, suna xuwa gida ya fito da Ita motar ya cillata gefe ďaya ta faďi, ya nunata da yatsa ransa a matuqar bace, 'kije na sake ki saki ďaya.... ta buga wani ihu a harabar gidan har yaranta suka fito, 'wallahi baka isaba, kayi kaďan ka sakeni saboda wannan yar iskar, ba inda xanje nida kai mutu ka raba, tana kuka ta nufi cikin gidanta..... Sa'eed yaje ya bawa Iman haquri sosai, ta nuna masa ba komai, suna xaune Deen ya shigo gidan yanda ya gansu a falo su kaďai xaune sai dayaji wani kishi, fuskarsa kadaran kadahan suka gaisa da Sa'eed, Iman ta karanci yanayin fuskarsa sai taji jikinta ba daďi, Sa'eed ya qara bawa Deen haquri duk ya damu ba daďi ace matarka ce sillar duk wata matsala dake afkuwa, Deen ya nuna masa ba komai kana ya ajiyewa Iman wata alkyabba mai kyau da tsada sai qamshi take wadda xata sanya anjima idan anxo ďaukar amarya, baiyi mata mgn ba ya fice ta tashi tabi bayansa har gurin motarsa ya dubeta, 'kin fito kuma kinbar baqonki, Ashe bakida karamci.... xuciyarta na buga tasan mgn ya gayamata ta dubesa, 'ya xone fa kan mgnr salima, bayan wannan Sa'eed is a brother to me a ynxu, Ya tabe bakinsa batare da yayi mgn ba yaja motarsa.... Da dare amarya tayi kyau cikin alkyabba, manyan motoci suka xo ďaukar amarya harda yan karere irinsu Pherty novels motarsu daban, Motar Merah amarya ta shiga tare da Fulani, sauran qawaye da abokan arxiki da yan uwa suka shiga sauran motoci, kana aka ďauki hanyar gidan Dr Deen....... My wattpad Phertymerh1 *Babana da mijina* ©fertymerh Xarah 💞 I like the novel Badakala👌🏼 45 Tayi juyi a hankali ta buďe idanuwanta wadanda ke cike da barci da gajiya suka haďa ido kunya ta kamata, Deen ďin sai ya qara lumshe mata idanu, ta sunne kanta cikin yalwatacciyar sumar data cika qirjinsa, xuciyarta fal da so da qaunar mijinta Wanda ya siye duk wata soyayya da Allah ya halittawa ďan Adam cikin xuciyarsa a dare ďaya kacal, Ta lumshe idanuwanta cikin tunanin Deedah, bata taba tunanin kasancewarta matar wani bayan shi ba, hawaye suka xubo mata, ko ba'a faďa ba yasan tsohon mijinta ta tuna ta qara rungumeta a qirjinsa tare da gayamata kalamai masu sanyaya xuciya...... Bayan ta gama wanka tayi sallah ta nufi kitchen, anan ta samesa yana kiciniyar ďora breakfast har lokacin yana sanye da kayan barci, ta fashe da dariyar dana janyo hankalinsa gareta ganin ynda yake fere arish duk ya xubar da rabin a banxa, ya juyo yana kallonta, murmushi kawai yayi ya ďauke kansa, ta qarasa kicin ďin haďe da riqe wuqar dake hannunsa, 'daka bari ai xn fito nayi, da can danakeyi bakama sani ba, ya sakarmata wuqar ya xagaya ta bayanta haďe da sumbatarta a wuyanta, ya kwantar da kansa a kafadunta, 'na yau daban ne dana kullum, jiya na ďora miki gajiya nasan baxaki iyaba, 'a naka tunanin kenan, na hutar da kai wannan ba aikin ka bane, kaje kayi wanka ka shirya dan idan na shirya baxan jirakaba, baiyi mgn ba sai kallonta yake tasa hannu cikin nasa ta ciro arish ďin tana kallonsa, 'ko ina kaga ana fere dankali haka, fauxie ma baxatayi wannan ba.... Duk ynda tayi dashi yaqi tafiya dole a tare sukayi aikin, miqo wannan ajiye wannan, duk shine sunayi cikin farin ciki da qaunar juna abinda bata taba samu a gurin Deedah ba, ba irin Wannan kulawar da shaquwa tsakaninta da Deedah, *wani hani ga Allah baiwa ne*, sai taji Deen ya sami matsayin babba a xuciyarta, A tare suka haďa komai a dinning ta ďauki nasu baffa ta kaimasu shikuma ya shiga wanka.... Soyayya ruwan zuma gangariya ake gudanarwa a gida da asibiti cikin yan kwanakinnan da suka biyo baya, a mota ďaya suke xuwa asibiti, idan ta rigashi gama aiki shike maidata gida ya dawo wani sa'in Kuma tare suke tashi, Kallo ďaya xakayi mata kaga kwanciyar hankali da jin daďi a tare da Ita, ta canxa har wata yar qiba tayi, Sa'eed yaji daďin ganin ynda Iman ta sami kwanciyar hankali a gidan mijinta hakama Merah, baffa ma na qoqari akansu ya maye masu gurbin baba, basu da kamarshi a ynxu suna darajashi sosai, Yau ma tare suka fita asibiti bayan sun gaisa baffa, fauxie tuni an wuce skul, little yana jikin baffa bai damu da suba a ynxu yafi sabawa da baffa, A asibiti binni binni xaka ganshi Gynaec yaxo dubinta, 'mekike so, kina buqatar wani abu, akwai matsala? sai ta girgixa kanta tana kallonsa da murmushi, 'need nothing just only you..... idan da mutane a office ďin sai dai yayi murmushi ya fice idan ba kowa sai ya sumbace ta ya fice ta bisa da kallo fuskarta da murmushi, kowa nayi masu kallon birgewa...... Karfe biyu ta tashi daga wurin aiki yau kai tsaye office ďinsa ta nufa, yana ganinta ya taso ya rungumeta, ta dubesa da murmushi a fuskarta, 'natashi aiki xnje gida saboda girki nasan baffa yana jirana, 'banason kina wahalarda kanki, akwai adama ga dijeh xasu Kula da girkin, ki jirani nan da 2hours xn kammala sai mutafi tare, Ta ajiye Jakarta haďe da cire labcoat ďinta, ta cire agogon hannunta tana faďin, 'Olryt bari nayi sallah, ta nufi hanyar toilet ďinsa kafin ta fito har ya shimfida mata darduma.... Shi da yace 2hours sai gasu har bayan isha'i patient suka masa yawa, tana xaune akan sofa da laptop ďinsa a hannunta tana kallo, da kyar ya samu ya kammala suka fito, yana ďauke da jakarta da labcoat ďinta, ta dubesa tana dariya, 'Yanxu sai ace ďan kwali yaja hula, baka kunyar mutane musamman abokan aikinka, idan na qasa dakai suka ganka da jakar mata a hannunka ai girma ya faďi, Ya ďan dubeta yana yatsina fuskarsa, 'Dama mata sun fiye sa ido, inba wannan ba miye damuwarki da duk wanda ya ganni, jakar matata na ďauka ba budurwata ba, ni bn yarda dake ba kin tsaya bayana kina min dariya shiga gaba, Tayi dariya ta wuce tana gaba yana biye da Ita har gurin motarsu, ita ta buďe masa ya shiga ta rufe kana ta sunkuyo tana murmushi, 'your excellency, Iman na godiya, 'idan kika qara mgn xn tafi in barkine, Kuma xakije a qasa ba lift ba napep.... tayi dariya haďe da sumbatar kumatunsa ta xagaya da sauri ta shiga motar ya bita da idanuwa yana kallonta har ta xauna ta rufe kana yaja motar, sunyi Rabin tafiya yayi parking ya fito, 'ni nagaji bayana ke ciwo kixo ki qarasa, ina driving sai kallona kike kamar yau kika fara ganina, tayi murmushi ta karbi key, ya shiga motar ta xagaya taja, sai da suka xo bakin gate tayi horn Maigadi ya buďe gate ďin ta soma qoqarin fita ya riqo hannunta, 'Ina xakije... 'ni na gaji, bayana ke ciwo, ina driving kana kallona kamar yau kafara ganina, 'yi haquri nadaina kallonki, ki qarasa ladarki, ya ďauke kansa gefe tayi murmushi taja motar. Sashen baffa suka fara xuwa yana xaune da qur'ani a hannunsa fauxie na gefensa danata a hannu yana koya mata karatu, tana ganinsu taje ta rungumesu tana masu sannu da xuwa, Deen ya ciko chocolate masu yawa a aljihunsa ya xuba a tafin hannuwanta, 'ki ajiye wa little nasa idan kika shanye *Ni da ke* a gidannan, ta karba tana dariya ta dubi Iman, 'kefa anty me kika siyo min, 'komai sai gobe, Sukayi masu sai da safe, suna isa falonsu bai bari ta koma takawaba, ďaukarta yayi bai diretaba sai a lafiyayyen gadonsa, da kanshi ya haďa mata ruwan wanka, tsugunnawa yayi dai dai gwiwoyinta, ya cire mata sarqa da yan kunne ya ajiyesu a gefe, ya tayata rage kayan jikinta ya rage daga ita sai shimi, 'get ready maman little, taja dogon hancinsa idanunta akansa, 'get ready too Baban little, ta tashi ta nufi toilet. Kitchen ya nufa ya duba cikin microwave, kaza ce gasashiya taji yaji albasa da tumatir, ya dorata akan tire, ya ďauki chips and Scottish salad da ruwa da juice ya nufi ďakinsa, Ya samu harta fito tana Shafa'i da wutri, ya ajiye agabanta bayan ta sallame, ta ďago ta dubeshi idanunta taf da barci ga gajiya, 'sannu da qoqari, bai bata amsa ba illah murmushi da yayi ya soma ci yana faďin, 'kici da kanki baxan baki ba nagane wayon harda min wani sannu, Itama dariya tayi ta janyo tiren gabanta, 'ni xn baka, sai ta soma bashi a baki, Wannan kulawa da kyautayi ga babban mutum irinsa ya taba xuciyarta shiyasa take qara sonsa take ganin ba wani kamarshi a duniyarta, Bayan sun gama ta jasa toilet da kanta ta cuďasa suka fito sukayi shirin kwanciyarsu a tare bayan sunyi light off. Suka buďa sabon shafin soyayya, gabaki ďaya Deen ya gigitata, haka ya cigaba da shayar da Ita mamaki cikin fannonin qauna da soyayya daban daban daba duk maza Allah keyiwa baiwarsu ba, ita kam ta yarda tayi miji a ynxu loving and caring husband irin Dr Zaharadeen...... My wattpad Phertymerh1 *Babana da mijina* ©Fertymerh Xarah 💞 *Dedicated dis buk to Rabi'atu Sk Mhs, Serdia Lawal bala & Aysher Gambo* 46 A gurguje Rayuwa ta miqa, so da shaquwa sai daďa qaruwa take tsakanin Su, Xuwa Yanxu Iman ta gama sanin ko Waye mijinta Zaharadeen , ta yarda ita kaďaice a xuciyarsa, Mutum ne dayasan ciwon kansa, ya kuma San mutuncin ďan Adam da kuma darajar aure, Haka Kuma mutum ne da ya San soyayya mai tsayawa mutum a qoqon rai, barta kyawun halittarsa Deen is Classique da kowacce ďiya mace da tasan ciwon kanta xata yiwa kanta burin mallakarsa, Xuwa ynxu soyayyar mijinta ta ratsa kowacce jijiya mai gudanar da jini a jikinta ta ratsa qashi da bargo, Duk dukiyar da suke da bai damu ba, ba ruwanshi da dukiyarsu burinsa ya sauke haqqinsu dake kanta, Iman knows her husband for now, tasan waye shi tasan aikinsa, ta bashi amana da yarda 99% tasan baxai cutar da rayuwarta ba, Daga Deen har mahaifinsa tafisu kuďi amma basa barinta taba dukiyarta sai dai suyi amfani da tasu, hankalinta da xuciyarta sunfi kwantawa a ynxu she loves Deen tana masa wani irin son da bata taba yiwa wani namiji irin sa ba, A da ta ďauka Deedah kaďai ne a xuciyarta, Deedah kaďai xata so har qarshen rayuwarta, Deedah ne masoyinta amma ynxu Deen ya mamaye wannan gurbin na Deedah, idan tana tare da Deen harta Kan manta kanta da wani Deedah, sai dai idan ta kalli little tayi masa addua, Ko a ynxu xata iya shaidawa duniya she have the best father and husband a ynxu, mutanen nan biyu tana alfahari dasu a ko ina and she will never forget them in her life, presently *Babana da mijina*, tayi murmushi tana kallon baffa dake tsokanar fauxie, 'matar sultan, matar sultan, yarinya tun tana qarama anyi mata kamen miji... 'ni ba matar sa bace baffa, bana sonsa..... ya soma yi mata dariya, 'shikenan irin auren nan da akeyi a da shi xa'a yiwa wata, Wayyo bata san mijinta ba sai dai a ďauketa akai masa, kinma ji daďi xakije gidan sarauta, akwai Wanda yafiki Sa'a Kuwa na kasancewarki surukar Dr Merah, Kuka take sosai ta faďa jikin Iman, daga baffa har iman dariya suke mata ganin da gaske kuka take suka kyaleta, akwai bidiri kenan a *Sultan Merah*, Ko ina kuka hango min salima🤔 Salima Yanxu ta xama cikakkiyar mace wace ko wane namiji yake alfaharin samun irinta, Believe me Sa'eed har cewa yake da haka take tun farko da ba'a abinda xai sanyashi auren habbi, duk da haka baya regretting na auren habbi itace sanadiyar shiriyar salima, Xama suke na amana duk da baxaa rasa irin kishin nan namu na mata ba, (kamar Serdiyer Lawal bala) suna ďan tattatabawa watarana amma ba kullum ba, Kowace tana kula da mijinta da ganin ta kyautatamasa, kowacce tana son tafi yar uwarta a xuciyar mijinta, yana sonsu Kuma yana kwatanta adalci tsakaninsu gwargwado iyawarsa..... Ta fito sanye da doguwar riga ta shadda, cikinta ya turo sosai Kamar yau xata haihu, Deen na bayanta da plate ďin sinasir ďayan hannunsa juice ya riqo, rarrashinta yake akan taci abincin taqi, duk inda tayi yana biye da Ita, Suna isowa falon ya ajiye kayan ya juyo yana kallonta lokacin take qoqarin xama, 'har sai yaushe xaki daina wahalar dani, idan baki ci abinci ba taya kike tunanin nima xn iya cin nawa, ta tsuke baki tana kallonsa, ya xauna kusa da ita haďe da ďora hannunsa akan nata hannu, 'Bari na baka kaci tukunna, bana son kana xama da yunwa saboda ni likitana, all I have is you.... taja dogon hancinsa tana murmushi, yayi murmushi ya janyo sinasir ďin yana kallonta, 'sai kinci xnci, kina so baby na ya xama raggo baida kuxari ko, to baxan yarda ba ďure xn maki a ynxu, ta kwanta a kafadarsa tana murmushi, 'Baban little kana so ka nuna min kafison babyn dani... yayi shiru bai tanka ba ya soma cin sinasir ďin, 'kinga ni ki Kyaleni Kada ki dameni tunda baxakici abinci ba kuma ba ruwanki dani munyi faďa, Dariya tayi haďe da sanya hannunta a plate ďin suka soma ci tare.... Watan haihuwar ta na shigowa suka ďauki annual leave a asibiti sukayi Dubai, acan ta haihu ta sami baby girl, Rayuwa suke mai daďi wacce aka gina ginshiqin ta da soyayya ta gaskiya da amana, irin wacce tayi qaranci a Wannan xamanin, rayuwace mai cike da qauna da soyayya yarda da girmama juna, babu abinda suka sanya a gaba daga aikinsu, sai Kula da yaransu da kuma junansu, Kwanciyar hankali da jin daďi tare da Iman a ynxu, ko yaushe xaka ganta fuskarta da farinciki sabanin da, bata da damuwa ynxu ko fargabar rayuwa, Dr Deen shi ya taimakamata wajen ganin ta gina qatuwar islamiya mai ďauke da sunan baba da Deedah, adduarta ladar ta isa garesu a koda yaushe kuma Allah ya yafe masu kurakurensu, Lokaci lokaci take masu sadaka, bata manta da waďannan mutanen biyu masu muhimmanci a rayuwarta ba komai kin daďin da take ciki, suna nan maqale a xuciyarta Kuma tana yi masu addua a koda yaushe, Allah yaji qan maxan jiya ta faďa fuskarta da murmushi tana kallon Deen, Ya amsa mata da amin, yana cigaba da danna laptop ďinsa, ta kwanta ta bayansa haďe da lumshe idanuwanta, 'Ina son mijina, ina alfahari da mijina, ko a ynxu xan iya bawa duniya labarin *Babana da mijina*, ba abinda xance sai Allah ya saka masu da gidan aljanna, 'wannan adduar tare dake fatyma, bani da mata a aljanna sai ke da hajara, kun bani farinciki a rayuwata bn taba dana sanin auren ku ba, the best wife's in the world, proudly to have you, Ta qanqameshi sosai, 'my husband is the best too.. Suka rungume juna cikin tsantsan farin ciki da qaunar junansu. Masha Allah lakuwwata illah billah!, Anan na kawo qarshen littafin *BABANA DA MIJINA*, kuskuren dake ciki Allah ya yafemin, Ina Godiya ga duk makarantar littafan *Pherty*, Allah ya sada mu da alherinsa Amin. Kuyi haquri da yanda qarshen littafin ya xo maku, a gurguje nayi komai exam Monday.... Sai mun haďu a *Sultan Merah* dan jin qarshen rayuwar fauxy, *Sultan Merah* yana referring kowanne motion ďin sa akan *Mulki ko Sarauta* kamar mahaifinsa Dr Merah, ko ya rayuwarsu xata kasance tsakaninsa da fauxie? *love you all* My wattpad Phertymerh1 Compiled by Princess Aysha Muhammad (Humaira) Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels