Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels CUTARWA! P1 MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION ⚠️⚠️ *Ƙirƙirarren labari ne, duk abun da aka gani a ciki, yayi kamanceceniya da wani abu, na zahiri ko makamancin haka, arashi ne* *Haƙƙin mallakata ne, ban yarda a juya mini shi ta kowacce irin siga ba, sai da izinina" *BRIGHT PENS* (FREE BATCH). Gagarawa Jihar jigawa. Kasancewar wata ya nausa, domin kuwa watan jumada ula, ya kai kwanaki ashirin da biyar, wanda yake dai-dai da watan Nuwambar shekarar miladiya. Mislain ƙarfe biyu da rabi, dare ya tsala, duhu ya mamaye ko ina, baka jin sauti ko motsin komai, sai kukan ƙananan ƙwari, da sautin busassun ganyen bishiyu, da iska ke kaɗawa lokaci zuwa lokaci. A dai-dai wannan lokacin da kusan galibi mutane ke kwasar bacci, ni kuma har a lokacin idon ta tamkar an soya, babu alamar bacci a tare da idanun nata, sakamakon bushewar zuciya da raɗaɗi da take ji. Sai yau ta tabbatar da cewa, nutsuwar zuciya, da kwanciyar hankali, da ƙarancin tunani, suke haɗuwa su haifar da daddaɗan bacci, mai cike da annashuwa. A hankali ta tashi daga kan katifar da take kwance, na nufi tagar ɗakin, ta buɗeta, wani sanyi ya daki fuskarta, ta kalli ƙaton tsakar gidan, da baka iya gane komai a cikin sa, saboda duhu. Ta ɗaga kanta, ta kalli taurari, yadda suka yi wa sararin samaniya ado, ƙudura da iko na Ubangiji na riƙe da su a sama. Tayi ajiyar zuciya, tare da kamanta rayuwarta da wannan baƙin daren, mai cike da duhu, da ban tsoro. A lokacin da karin maganar bahaushe ya yi amsa amo, a tsakanin ƙabilar ta hausawa, na cewa dauɗar gora ciki ka sha ta, sai dai kash! Zamani ya zo mana da cigaba, ta hanyar nuna mana muhimmancin lafiyarmu. Duk da cigaban da aka samu, hakan bai hana a tauye ta ba, a shayar da ita dauɗar gorar ta ƙarfin tsiya ba, wanda hakan yake CUTARWA! Domin kuwa ya zame mata tamkar guba, domin ya zama silar sanya mata ciwon da take ta fama da shi, ta rasa maganin sa, wanda tun yana ɓoye, sai da ya fito yayi tsiron da mutane suke yi mata tambari da shi. Haka zalika, azancin hausawa na ciwon ƴa mace na ƴa mace ne, ya samu gindin zama a da yawa daga bakunan mata, sai dai ita a nata ganin, ciwon ƴa mace, na ta ne ita kaɗai. Wataƙila ko a cikin ta ta rayuwar ne Allah bai sa ta yi katari da waɗanda ciwon ƴa macen yake zama nasu ba. Duk iya ƙoƙarin da ta yi wurin haɗiye yawun bakinta, ta kasa, saboda bushewar da bakinta yayi, wani irin zafi zuciyarta ke yi mata, wanda ya haddasa numfashina fita cikin huci. A hankali ta furta "Me ya rage? Tun da duniya cike take da rikici, da tarin ƙalubale, kowa kansa kawai ya sani, kuma kuɗinka shi ne mutuncinka, tabbas! Tura ta kai bango, na ɗaura aniyar fito na fito da duk waɗanda suka cutar da ni. Tun da babu sani babu sabo, dole in fasa ƙwan da warinsa ka iya sanadiyyar tarwatsewar zumunci, idan ya so na gani, ko suma suna iya jure ɗaɗɗake dauɗar gorar a cikin su, kamar yadda suka yi mini, daga nan na ƙara gaba,, na basu wuri tare da gwagwarmayar nemawa kaina mafitar rayuwa. ***** La'asar sakaliya, wata matashiyar mace ce da ba zata gaza shekaru sha takwas a duniya ba, zaune a ƙaton tsakar gida, tana ta ƙoƙarin tsince waken da zata daka, ta zuba a cikin miyar yauƙin da take yi, cinyarta wata yarinya ce ƴar kimanin shekaru uku da rabi a duniya a kwance, ta saka babban ɗan yatsanta a baki ta na sha, hannunta ɗaya kuma tana wasa da cibiyarta. Idan ka kalli yarinyar sau ɗaya, sai ka sake kallonta, tare da son sanin daga wace ƙabilar wannan yarinyar take?. Baƙa ce sosai, mai ƙiba, tana da ɗan goshi, sai dai yalwataccen gashin girarta ya rage fitowar goshin nata, tana da manyan idanuwa farare, sai dai ƙwayar idonta brown ce, maimakon baƙa, bakinta ɗan cukul, sai dai laɓɓanta jawur, tamkar an saka mata jambaki. Babban abun da zai baka mamaki, bai wuce yadda take da dogon gashi ba, baƙi wuluk, mai tsayin gaske, ba curkukuɗaɗɗe irin na baƙaƙen fata ba, tamkar gashin larabawa, kalba aka yi mata guda biyu, amma ta saukko har cikinta, hancinta ba shi da wani tsawon kirki, saboda kumatu ya shanye su. "Wai Mariya ba zaki ajiye wannan gunsumemeiyar yarinyar ki mayar da hankali ki kammala aikin nan ba. Kawai kin ɗauki ƴa kin narka a cinya ƴa ba kaɗan ba ko nauyi ba kya ji? Na ga dai ba nono za ki bata ba" Mariya a ranta ta ce 'Ban da abun iya, ta yaya saniya za ta gaza da ƙahonta?' A zahiri kuwa cewa ta yi "Yanzu zan kammala iya" "To ki ajiyeta ta shiga cikin yara tayi wasa mana, wannan uwar matan ta zauna a cinya, kema ki haihu ki yi mata ƙani, kin naɗe kin ƙi haihuwa, kiyi ƙoƙari dai ki haifo wani, ko Allah ya sa a samu mai ɗan dama-dama, wannan ƴa muninta yayi yawa, Ko da yake can danginku ta kwaso wannan baƙin da muni, barebari ai haka ku ke baƙi kamar zunubin mutanen farko" Mariya ta sunkuyar da kai tayi shiru, ta na jin zafin maganganun nan, amma ba yadda ta iya, haka ta ƙaƙalo murmushin dole, ta ce "Hajiya iya kenan, jikar nan taki mamaki zata baki, idan ta tashi kawo miki siriki, mai maiƙo za ta kawo, wanda zai kai ki makka". Iya ta furzar da goron bakinta ta ce "Da wannan baƙin da munin? Maza na rububin farar mace, wa zai kwashi kayan muni, ai ko wannan idon nata, ya isa hanata auruwa, ido abun tsoro kamar ragowar maita, sai ido furi-furi kamar bururrun gawayi" Sake kwanciya yarinyar ta yi a jikin uwarta, tare da kawar da kanta gefe. Mariya ta shafa kanta ta ce "Ummina, ki tashi in haɗa abinci, kar yayyenki su dawo ban gama girki ba, ki tashi ki je ki yi wasa da su Auwwalu" Noƙe kafaɗa yarinyar tayi, tana tura ɗan mitsitsin bakinta, ta sake gyara zama ta mayar da hannunta baki. Sallamar da aka yi ne, ya sanya su haɗa baki wurin amsawa. Sai dai ba ƙaramar razana ta yi ba, da jin muryar mai sallamar, dan sai da tayi wani zillo ta tashi zaune, wani ɗan matashin saurayi ne, hannunsa riƙe da wata ƴar jaka. Iya ta ce "Ahh, idris ka dawo?" "Eh, an gama abinci ne?" "Ina fa, tana nan tana laƙai-laƙai tana fama da wannan jibgegiyar yarinyar, ita ba nono za ta sha ba, sai iskanci da taɓara dan sangarta". Ya kalli yarinyar ya ce "Ummi, zo mu je na sai miki biscuits, ki bari anty ta gama mana girki" Maƙale hannunta tayi, tana zazzaro ƴan idanunta, da tsoro ya bayyana ƙarara a cikin su. "Ummina, dan Allah ki bi yaya idris, in kammala aikin nan" Hawaye ya cika mata ido, tana kwantar da kanta a jikin mahaifiyarta. Ya miƙa hannu zai ɗauke ta, ta fashe da kuka mai kama da na shagwaɓa, amma a zahiri na tsoro ne. "Kai dalla ƙyale mata ƴar ta, dan ta samu za a ɗauke ta, ji iskancin da take, ita shagwaɓar ma ba kyau take yi mata ba, aba ba kyan gani kamar turotso". Ta ƙarfin tsiya ya saka hannu, ya ɗauketa, tana ta kuka, mariya kuwa cikin kara da kawaici, ta tashi tana cewa "rigimammiya sam ba kya girma". Ya fita da ita a kafaɗarsa, bai tsaya a ko ina ba, sai wani sashi na gidan, a ƙofar wani ɗaki da ba kowa a sashin, yanayin wurin zai nuna maka wurin ɗakin ƴan maza ne. Ya buɗe ɗakin ya shiga da ita, yana zuwa ya dungurar da ita a tsakar ɗakin. "Rufe mini baki, ko na shaƙe ki, ki mutu" cikin sheshsheƙa take ƙoƙarin danne kukan nata, gaba ɗaya ta burkice cikin matsanancin tashin hankali. Ya bankaɗa gefen wata katifa, ya ɗaukko almakashi, ya durƙusa a gabanta ya ce "Kin gaya wa mamanki ko?" Ta girgiza masa kai, hawaye na zuba daga idonta, ga ƙoƙarin haɗiye kuka da take yi tamkar zata shiɗe. "Kin faɗa ko baki faɗa ba?" Ta sake girgiza masa kai cikin razani. "Duk ranar da ki ka faɗa, sai na gutsutstsura namanki da almakashin nan, na zuba a leda na kaiwa karen namadi, ya cinye ki, kuma sai na saka ki a murhun da babarki take girki, ai kin taɓa ƙonewa kin san zafin wuta" Ba ta iya cewa komai, sai bin sa da ido, hawaye na zuba daga idonta. Ya ajiye almakashin, ya janyo ta, ya fara ƙoƙarin cire ƴar doguwar rigar jikinta. Sake fashewa ta yi da kuka, har da ɗan ƙara sauti, aikuwa ya zare mata ido, ya shaƙeta ya ɗaukko almakashin, ya saita tsinin a maƙoshinta, jikinta na rawa ta yi gum da bakinta. Kamar yadda ya saba ɗaukkota yayi mata, haka yau ma idris yayi mata, sai da ya gama abun da Allah ya nufe shi da yi, sannan ya ƙyale ta, sai dai bai taɓa gangancin ƙetara ta ba. Ya cigaba da yi mata kashedi, tare da firgita ta, a kan idan ta faɗa, sai ya sakata a murhu ya babbaketa. Ya bar ta a nan zaune, ya kintsa, sannan ya zo ya ja hannunta, da ƙarfi sai da ta ji zafi, amma ba damar yin kuka, tana tsoron kar ya babbakata a wuta ko ya yankata da almakshi. A wulaƙance, ya tafi da ita kanti, ya saya mata biscuit ɗin naira ashirin, da alewar naira biyar, ya sake fizgo hannunta ya nufo gidan da ita, sai tankaɗata yake yi yana masifar tayi sauri. "Ba zaki yi sauri ba, sai wani jagwab-jagwab ki ke, kamar tsohuwar talo-talo" tafiyar sa da tata ba ɗaya ba, mussman ita da ke da jiki, haka ya ja ta sai daf da zasu shiga gidan, ya sake jaddada mata, kar ta gaya wa kowa abun da yayi mata. Ya saɓata a kafaɗarsa ya shiga da ita gidan. "Anty mariya, ga rigimammiyar ƴar ki nan, uwar kuka, ta karɓe mini biskit, amma har muka dawo kuka take, saboda shegiyar ƙyuya". "Ohh, Ummi Allah ya shirya mini ke, an girma amma ke ba kya girma, kamar ba ƴan mata ba" gaba ɗaya ummi hankalinta baya jikinta, a tsorace take sosai da sosai, sai dai kasancewar ita kan ta mariyar yarinya ce, shekarunta sha takwas, a zaton ta kawai rigima ce, kasancewar ummi, yarinya mai azabar ƙyuya da miskilanci. A nan tsakar gida ta yasar da biskit ɗin, ta je ta rirriƙe mahaifiyarta, ana daf da sallar magariba, mahaifin ummi ya dawo, ya ɗauke ta yana juyi da ita a tsakar gida, yana faɗin "Ummi, waye ya taɓa ni ƴa ɗaya tilo, na ga kamar kin sha kuka? Ko dai kin daketa ne?" Yayi maganar yana kallon mariya. "A'a wallahi, ƙyuya ce kawai, ba zata yi wasa a cikin yara ba, ta maƙalƙaleni, dan idris ya ɗauke ta take kuka". "Ki daina ƙyuyar nan dan Allah, na zo miki da alewa daga kasuwa, da yalo ai kina ci ko?". But iya ta fito daga ɗakin ta, "Balarabe wannan ƴar ka sunkuta ka ke shillawa sama, sai ƙirjinka yayi ciwo tukuna ko?" Yayi murmushi ya ce "Iya guda nawa ummin take" "Ajiyeta dan Allah, duk a haka ku ke sangarta ta, tayi ta taɓara tana iskanci, ƴa sai ka ce teba" cikin jin nauyin mahaifiyar sa, ya ajiye ummi, yana murmushin yaƙe. "Ina alewa da yalon da na ji ka ce ka zo da su? Bani nan a rabawa sauran yaran gidan, ai ba ita kaɗai ce ƴa ba, nan idirs yanzu ya fita da ita ya kaso mata uban kuɗi, amma kai sai ka zo da abu ka hana sauran yaran? Saboda ka haifi gwal?" "A'a Inna, ina sayo da su suma, gani na yi ita ce ƙarama, kuma yau kasuwar sai godiyar Allah, tun da ba ranar kasuwa ba ce ba, ɗan kaɗan ne na zo da su ba yawa" yayi maganar yana nuna mata ƴar ledar hannunsa. Ta ƙaraso ta fizge ledar "To tun da ba ciniki, sai ƴar taka ta haƙura, kai dai balarabe kamar a kan ka, aka yi wahayin talauci, kullum kasuwa ba cigaba, kana kallon yadda ƴan uwanka suke ƙoƙari kowa da abun arzikin sa, kai kuwa ba ka ajiye komai ba, sai son mace da wannan mummunar yarinyar, daɗi aure ba zaka zage ka nemi arziki ba" shiru yayi ya sunkuyar da kansa, dan ba shi da abun cewa. Mariya kuwa ta mayar da hankali wurin kwashe tuwo, roba-roba. Malam Hashimu dodo, shi ne mijin iya, gidansu babban gida ne, da aka yi ittifaƙin babu gidan da ya kai su yawa. Da yayi aure ya ja nasa ɓangaren a cikin gidan su. Kasancewar gidan babba ne sosai, dan kusan duk garin babu mai girman gidan. Kowa ya san su, saboda galibi ƴan gidan manoma ne, sai masu taɓa kasuwanci, suna da rufin asiri dai-dai gwargwado. A hankali wasu suka din ga samun rufin asiri, suna watsewa daga gidan, malam hashimu yana sake shigar da wasu sassan nasa sashin. Daga baya ya auri iya, bayan matarsa ta ladan noma wato salamatu. Malam Hashimu mutum ne mai hidimtawa iyali, a lokacin boko ba ta yawaita ba, sai karatun allo, dan haka da shi da ƴan uwansa suna da ilimin soro. Bayan wani lokaci, salamtu ta mutu, ta bar yaranta huɗu, biyu mata biyu maza, iya ta cigaba da riƙon su, da nata ƴaƴan. Sai dai iya macece me shegen son abun duniya, tamkar ta yi ƙwace, ga ta da iya fuska biyu, a waje ta nuna ta Allah ce, amma na cikin gidan, su suka san gashin da suke sha. Ba ƴaƴan da aka bar mata ba, har facalolinta, da suke cikin gidan iya na azabtar da su, gwargwadon abun hannunka, da abun da ka ke bata, gwargwadon mutuncinka a idonta. Aka aurar da ƴaƴan salamatu mata, ɗayan kuma Yahaya, ya ce shi karatun boko yake so. Iya tayi ta sukar abun, amma malam Hashimu da suke kira da baba ya bashi goyon ba. Ƙaninsa kuma Ilyas, yana zaune a nan ƙauye, amma yana taɓa kasuwanci, nan da nan ya fara tara kuɗi, yayi wuf yayi aurensa, shima ya tare a cikin gidan. Yaran iya su biyar, biyu mata Shafa da zaliha, uku maza, Sagir, Saminu, sai Bashir wato balarabe. Duk wanda yake da kuɗi shi ne nata, hatta a jikokinta bambanci take nunawa muraran, sagir ne babba shine baban Idris da kuma Hashim suna ce masa magaji, saboda sunan malam ne da shi. Akwai tarin ƴaƴa da jikoki a gidan, bayan rasuwar iya ita ke tafiyar da gidan, saboda azabar faɗanta da iya masifa, hatta ƴan uwan malam tsoron ta suke ji, abun da ta dama shi ake sha. Saboda balarabe ba shi da kuɗi, wato baban ummi, duk gidan shi ne samunsa ba mai yawa ba, dan dako yake yi a kasuwa da ƴan buge-buge dan haka samun nasa galibi sai damina idan yayi noma, hakan ya sanya duk wata ɗawainiyar gidan ta wahala, iya ta sa matarsa mariya ce ke yi, wadda asalinta ƴar Maiduguri ce babarbariya ce, sun zo garin biki suka haɗu, har Allah ya sa suka yi aure. Tun da mariya tayi haihuwa ɗaya ta haifi, yarinyarta aka saka mata sunan mahaifiyarta, wanda yayi dai-dai da sunan uwar gidan malam, wato Salma ba ta sake haihuwa ba, tsawon shekaru uku kenan, iya ta ɗorawa yarinyar nan Ummi ƙahon zuƙa, da ba'a da cin mutunci, wai ta haifi wata halitta daban, da babu irinta a danginsu. Ba ita ba har yaran gidan, da sauran mutanen gidan, na yawan kushe halittar ummi, tare da tsokanarta, gashi ayi ta tankata, saboda baƙinta, da kuma ƙibar ta, ga kuma kalar idonta, sai dai kuma mutane na mamakin irin gashin kanta, dam idan mariya na gyara mata kai, ruf gashi yake rufe mata fuska, tamkar na larabawa. Allah ya albarkaci gidan malam Hashimu, da yawan yara maza a jikokinsa da ƴaƴansa, mata sam ba su da yawa, kuma da sun tasa ake aurar da su. Dan haka kusan ummi, ita kaɗai ce yarinya mace ƙarama a cikinsu, sai dai hakan ya zame mata babbar barazana ga rayuwarta!!! 08081012143                      *CUTARWA!* Watpad ayshercool7724 Arewabooks ayshercool7724 YouTube Cool hausa novels What's app 08081012143 BRIGHT PENS (FREE BATCH) P2 Yawan kyara da hantara, haɗi da kushe halittar ummi, ya sanya ta zama yarinya mara karsashi ko a cikin sa'aninta. Dan wasu har iƙrari suke ko mayya ce, saboda launin ƙwayar idonta da ta sha banban da ta sauran mutane. Wasu lokutan mariya duk sha'anin da za ayi na taron mutane, ta kan iya haƙura da zuwa saboda ummi, ba ta son mutane. Abubuwan da wasu daga samarin gidan suke yi mata ne, ya sanya ta sake tsorata da lamarin mutane, ta fara ganin tamkar ita ta ta duniyar daban take, dan idris ne kawai yake amfani da ita wurin biyan buƙatar sa ba. Mariya bata taɓa fuskanta ba, wasu lokutan har tsoron nuna wa ummi kulawa take yi, a gaban iya, saboda yanzu zata hau masifa da faɗa, wai tana nuna wa ƴar fari soyayya saboda ba ta da kunya. Ko yaya ummi ta ɗan sake a cikin yara, sai su fara cin zalinta, ko su din ga jan dogon gashin ta, ko jan kumatunta da suke tamkar doughnut ya ji yeast, ko yi mata dariya da ihun baƙar tukunya mai ƙyalli. Takurar yara ya takureta a gida, a gidan ma iya sashinsu, shi ma fitowa tsakar gida idan ba tare da mamanta ba, ba ta fitowa saboda hantarar da kyarar da iya take yi mata. Haka rayuwar gidansu ummi ta cigaba da garawa, iya kullum tana cikin haba-haba da ƴaƴa da jikokinta, masu kawo mata abun duniya. Yayin da ta tattara cin kashinta, a kan balarabe da iyalin sa, tamkar ba ita ta haife shi ba. Ummi ta ɗan ƙara tasawa, kusan kullum sai ta tambayi babanta, yaushe za a kaita makaranta. Ganin ta ɗan tasa, kuma idan tana tare da mahaifinta, ko mahaifiyarta, ta kan yi hira da su. Sai dai da tayi yinƙurin gaya musu, abun da su Idris ke yi mata, sai ta kasa ta tsorata idan ta tuna suna cewa za su yankata. Babanta yana bata lokacin sa, yayi wasanni da ita, har da ƴar tsere a tsakar gida. Da iya ta ganshi kuwa ranar ya shiga uku, da masifa da gori. Kasancewar garin sun ɗan samu cigaba da wayewa, yanzu ana yin karatu sosai, akwai makarantu, ya sanya balarabe ya kai Ummi makarantar gwamnati, aka saka ta a ECC. Ta din ga murna ganin an saka mata sabon uniform, fari da kore, ga jakarta baba na gode, an saya mata sababbin litattafai, sai washe fararen haƙoranta take yi cike da yarinta. Tun sha ɗaya da rabi, mariya ta cewa iya zata je ɗaukar ummi a makaranta, iya ta ce "Mariya wai meyasa ba ki da ta ido ne? Ni zan ƙarasa girkin kenan, ki bari ta biyo yara, ko idan su Auwwalu sun dawo sa ɗaukkota. Ni kaita makarantar ma, Allah ya sa ba asarar kuɗi ba ne ba, kar aje yadda fuskarta take haka ƙwaƙwalwar take, ayi biyu babu". Wani abu mai ɗaci ummi ta haɗiye, ta cigaba da kaiwa tana komowa, ta faki idon iya, ta ɗau mayafi ta fice ɗaukko ummi, duk da babu tazara sosai, amma yarinya ce ƙarama, ba ta san hanya ba. Sai dai da ta je ɗaukar ta, ba ta ganta tana wannan murnar kamar lokacin da za a kaita makarantar ba. Tayi zaton kawai ta gaji ne, dan da yawa yara na ɗokin makaranta, sai an kai su kuma, su ga ba abun da suke so ba, su ce ba sa so daga baya. Mariya tana cire mata uniform ta ce "Mamana, me aka koya miki a makarantar yau?" Cike da yarinta ta ce "Lemo aka zana mana" Tayi murmushi ta ce "sai kuma me?". "Bana son makaranta, ba zan sake zuwa ba?" "Subhanallah, ummina meyasa?" Ta yi maganar cikin kulawa. "Yala cu na ce mini baka" (Yara suna ce mini baƙa) Mariya ta yi ajiyar zuciya ta ce "Kar ki kula su Yarinyar kirki, ki din ga mayar da hankali a kan abun da malama take koya muku" "Ni bana son ana cewa baka" "Za su daina Ummi, yarinta ce take damun su" Ummi ta ce "To" Hargowar iya ta jiyo a tsakar gida"Sai ka ce mayya, kamar a duniya babu wanda ya taɓa haihuwa sai ke, ai ba a banza ba wannan kalar idon na ƴar ki, na fara zargin akwai masu lashe-lashe a danginku, dan baƙar masifa, sai da ki ka tafi yawon ɗaukotta, shafaffiya da mai" Mariya ta yi shiru ba ta ce komai ba. Sa'adatu matar Sagir, da tayi sallama a sashin ta tarar da iya tana ta zuba tijara, ta ce "Iya ke da wa kuma a tsakar ranar nan?" "Wacece idan ba mariya ba? Duniya kamar babu wani mai ɗa sai ita, in dai aka wannan mummunar yarinya ce, ba ta ji ba ta gani". "Iya kenan, mutum da ɗan sa ai sai Allah, sauran kunu na zo idan akwai in bawa yaro, ya fara yi mini kukan yunwa" "Shiga ciki ki duba, ni fita zan yi" tayi maganar tana saɓa mayafinta a kafaɗa ta fice. Sai da iya ta fita, sannan ta lallaɓa, ta fito yi wa ummi wanka. "Maman ummi, ashe ummi kuma an shiga makaranta" Mariya ta ce "Wallahi kuwa, ummi an shiga Ecc" "Masha Allah, Ubangiji Allah ya yi jagora, ya sa an shiga a sa'a" Mariya ta amsa da "Amin" Ummi ta ɗan samu sassauci, daga laluben da samarin gidan suke yi mata, saboda shigarta makarantar boko, tun safe sai sha biyu na rana, daga nan kuma ta kwanta tayi ta bacci, wasu lokutan yaran gidan da ƴan sa'anninta, su zo su tafi da ita makarantar allo. Duk da kuka wasu lokutan kuka take ba ta so, haka mariya ke tursasa mata ta tafi, saboda shi ilimi, dole a tsayawa yaro yayi shi, ko da kuwa ba ya so, mussaman ma na addini. Duk da a hakan wasu lokutan ba ta tsira ba, ba ya hana azo har sashin su a ɗauke ta, idan mariya zata hana, iya tayi ta masifa. *** Yau Mariya ta yi yamma wurin girki, tana ta aiki a tsakar gida, iya tana zaune a kan kujera ƴar tsuguno, ta kasa ta tsare, sai waƙe-waƙenta take yi na mutanen da, waƙoƙin daɓe wasu kamar na batsa,wasu kamar habaici. Wata mata ce tayi sallama, suka amsa baki ɗaya, matar ta gaida iya, Iya ta amsa mata cikin sakin fuska har da yi wa ɗan matar wasa. Mariya ta ce "Mai koko ke ce da yammacin nan? Bari na baki abun zama" Mai koko ta ce "Wallahi kuwa, haja na kawo miki" Mariya ta shimfiɗa mata tabarma ta ce "Haja kuma, to Allah ya sa ba ta fi ƙarfin talaka irin mu ba". Mai koko ta kwance kaya, kayan yari da sarƙa ne da mayafai a taƙaice dai kayan koli ne. Mariya ta yi ta ɗaɗɗagawa, kayan sun yi mata kyau sosai, ta san idan ta ɗauka baban ummi ba zai ce komai ba, amma ba ta son takura shi, dan haka ta ce "Mai koko muna da ɗan kunne, maɗaurin gashi na so saya wa ummi, sai dai wannan sun yi ƙanana ba zai riƙe gashinta ba, sai dai idan muna buƙata zan yi miki magana da yardar Allah" Ita ta ce "Ke ma dai mai koko, ke da ki ke neman arziki, ina ke ina kawo wa wannan kaya, ba su da komai sai tsiya da babu, ki kai sashin Sagir, ko gidan iliya, wannan ai da kin taɓa su babu". "Na ga alama kam, ban taɓa kawo kaya mariya ta saya ba, kullum sai aukin idan tana buƙata ta aiko ta saya". "Kema tun da aka yi ɗaya biyu, ai ba kya bari ayi uku ba, da dai hidimar ƴar ta ce, nan tafi kauri, ta kanainaye mini ɗa ta hana shi arziki" Tuni mariya ta tashi, ta koma kan aikinta. Mai koko ta ɗaure kayanta ta ce "Aikuwa iya ki dage da nema masa magani, ƴan uwansa duk suna da rufin asiri ban da shi, sa anjima" "Yawwa ki gaida gida" Ba ta sake bi ta kansu ba, kamar kullum yau da wuri ummi tayi bacci, bayan mariya ta kammala girki, ta ɗebi gawayi, ta goge wa ummi uniform ɗin ta, ta gama komai, tana jiran dawowar baban ummi. Kamar mai kiran kurma, Iya ta ƙwala mata kira, ta fito da sauri a ɗan razane ta ce "Iya gani" "Maza yafo mayafinki, ƴaron wurin iliyasu ne, ƙaramin ya haɗiye ƙaya, ku ɗauki yaron ki raka Sa'adatu ku je gidan sarkin suu, ya bashi magani" Ɗan jimmm mariya tayi, so take ta huta, tun safe take aiki a gidan kamar jaka, yanzu kuma iya ta tsiro da wani abun. Ba yadda ta iya, ta ce "To, bari na goya ummi, dan tayi bacci" "Wai ke wace irin mace ce, har yaron ya mutu baki gama goyon wannan buhun sumuntin yarinyar ba, ban da rashin kara, ai ke yakamata ki goya mata yaron, dan Allah ki hanzarta ku tafi, ina nan me zai samu ummin, hanzarta maza". Haka nan mariya ta ji gabanta yana faɗuwa, kamar wani abu zai faru idan ta tafi, ga Iya sai ɗaga mata murya take a kan tayi sauri. "Iya zan iya goya ummin, sai in ɗauki yaron a hannu" "Wai mariya meyasa baki da kunya, ina faɗa kina faɗa? Salon ki je ki kayar da yaron, ga wannan uwar ƴar ta ki, kaya guda a haka zaki ɗauki, yaron ba zaki hanzar ta ba, ko dan ba ɗan ki bane ba, ko da yake ina mai ɗa ɗaya ya san ciwon ɗa ma" Ta ce "To ko in kawo ta ɗakin ki, sai in kwantar da ita, idan na dawo na ɗauke ta?" "A'a ba zaki kawo mini ita ta yi mini fitsari ba, wannan samgartacciyar yarinyar, ɗuwawunta ba shi da saiti. Uban meye ma zai kamata a ɗakin, ki wuce ku tafi" Jiki a sanyaye mariya ta shiga ɗaki, ta ɗakko mayafinta, ta na ta kallon ummi, tana fatan Allah ya sa babanta ya shigo da wuri. Ta fito tsakar gida wasu daga cikin jikokin iya suka shigo, shigowar su bai sanya iya yin shiru ba, ta cigaba da yi wa mariya masifa. Duk mutanen da ke cikin gidan, iya ta rasa wanda zata saka yayi rakiyar kai yaron sai ita, saboda dai kar ta huta, kuma kar ta zauna lafiya. Suna tafe a hanya tana goye da yaron, sai kakari yake yi, saboda yadda ƙayar take sukansa. Ga gidan sarkin su da nisa sosai, haka suke tafe da fitila. Sai dai zuciyarta sai harbawa take yi da sauri, hankalinta yaƙi kwanciya, ji take tamkar ta juya da gudu, ta koma wurin ƴar ta. Sai wajen tara da rabi suka dawo, gudu-gudu sauri-sauri ta nufi sashin su, ba ta bi ta kan iya ba, ta nufi ɗakinta. Sai dai ta kai kai zata shiga ɗakin, shi kuma ya fito da sauri, jikinsa yana tsuma. "Me ka ke yi mini a ɗaki yanzu? Me ka yi?" Shiru yayi yana tsuma tare da kallon ta, ta hasken farin wata. "Me ka yi mini a ɗaki i yanzu? Me ya kai ka ɗakina?" Tayi maganar cikin ƙaraji. Iya ta ce "Wai lafiya kuwa? Kun dawo kenan ya jikin yaron?" Hankaɗe shi ta yi daga gabanta, ta shiga ɗakin da sauri, tana kiran sunan "Ummi" "Innalillahi wa Innalillahi raji'un. Iya! Iya! Zo ki ga? Iya zo da sauri" Da sauri iya ta taho da gudu tana cewa "Wai meye ne?" Ta shiga ɗakin, ta tarar da ummi a kwance, tana ta numfarfashi, jikinta sai rawa yake yi, an tura mata hularta a bakinta, ga wandonta a yashe a gefe gabanta duk jini. Iya ta dafe ƙirji ta ce "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'una, wace irin masifa ce wannan, me yaron nan ya zama, kar dai ki ce mini yaron nan ne?" Cikin kuka mariya ta cirewa Ummi abun bakinta ta rungume ta, cikin ɗaga murya ta ce "Haba iya, da idonki fa kin gani, kina gani fa, waye ya fita daga ɗakin nan idan ba shi ba, na shiga uku na lalace an cuce ni, an cuci ƴa ta" "Dalla ki rufewa mutane baki, idan kuma kururwar zaki cigaba, ki tonawa kanki asiri shikenan, idan ba wata ƙaddara ta Allah ba, waye ma zai aure ta, balle a san me ya faru da ita" sororo mariya ta bi iya da kallo, wanda hakan yayi dai-dai da sallamar baban Ummi. Iya ce ta iya amsawa, ya shigo ya same su, mariya rungume da ummi tana kuka. "Maman ummi, Iya meyafaru ne? Ummin ce babu lafiya?" Mariya ta ɗaga masa ƙafar ummi, tana kuka ta sanar masa da abun da ya faru. Salati ya saka ya durƙushe a wurin. Iya ta ce "Da ki ke ɗorarwa ke kin tabattar shi ɗin ne? Sai ki jirani in bincika in tabbatar ai". Ta tashi ta fita daga ɗakin. "Mariya, kina me? Garin yaya? Ya aka yi haka ta faru" Cikin kuka mariya ta ce "Wallahi iya ce baban ummi, iya ce na shiga uku an lalata mini rayuwar ƴa ta, ina zan saka kai na" Iya ce ta dawo riƙe da hannunsa, zuwa cikin ɗakin ta kalleshi ta ce "Uban wa ye ya yi wannan aikin? Me ka yi mata, ba sallama ka yi mini ka ce zaka tafi shagonku ba?" Jiki a sanyaye ya ce "Wallahi iya tsautsayi ne" A fusace balarabe ya tashi ya shaƙe shi, ya ce "Tsautsayin ka kasa sauke shi a ko ina, sai kan ƴa ta". "Zaka cika shi ko sai na ɗauke ka da mari? Ba ɗa yake a wurin ka ba kai ma? Idan ɗan ka ne ya aikata hakan, tona masa asiri zaka yi? Ko idan ka tayar da maganar wani abun hakan zai amfanar, aikin gama ya riga gama. Kuma bari ka ji in gaya maka, wallahi tallahi, muddin ku ka ɗaga maganar nan, wani ya ji ta, bayan mu ɗin nan, Allah ya isa ban yafe ba, kowaye sai na tsine masa. Ita dauɗar gora ai ciki ka sha ta. Idan baku rufa musu asiri ba? Waye zai rufa musu ko salon zumunci ya lalace? Ƙuruciya ce da ƙaddara da bai wuce kan kowa ba" Da wani irin mugun sauri zuciyar mariya ke yi, ƙuruciya ga yaron da har ya san, ya toshe mata baki da tsumma, ya keta mata haddi, shi ake kira da ƙuruciya. Jiki a sanyaye balarabe ya ce "Shikenan iya, duk ba za ayi haka ba, in sha Allah hakan ba za ta sake faruwa ba, an bar maganar da yardar Allah" Ta kalli saurayin yaron ta ce "Kai kuma wuce ka bani wuri, wallahi ka sake aikata makamancin haka, da kaina zan ci ubanka na hukuntaka. Wuce ka bar ɗakin nan". Ya fice sumi-sumi ya ci bulus. "Ke kuma ki daina wannan kukan, ki tashi ki dafa ruwa, ki sakata a ciki, kiyi haƙuri, ko ki cigaba da kuka baƙin ciki ya kashe ki" daga haka ta juya ta fice. Tana fita mariya ta kuma rushewa da kuka ta ce "Yanzu shikenan baban ummi, yaron nan ya ci bulus kenan? An lalata mini rayuwar ƴa, har iya na cewa wai babu lallai wani ya aureta, wane irin abu ne wannan?" Zuciyar sa fal takaici da ɓacin rai, saboda kar ya sake karya wa mariya gwiwa ya ce "Dan Allah kiyi haƙuri mariya, ki kwantar da hankalinki, kin ga iya uwata ce, ba yadda na iya, dan Allah ki yi haƙuri ki tayani yi mata biyayya, mu ɓoye sirrin nan, ko dan mutuncin ummi, kar abun yayi mata yawa. Dan Allah ki yi haƙuri mariya" Tashi tayi ta kwantar da ummi, ta fita tsakar gida. Babanta ya rungume ta, jikinta ya ɗau zafi, tana jin yadda hawayen sa ke ɗiga a hannunta. "Ummina sannu kin ji? Meye yake miki ciwo?" Tayi shiru ba ta yi magana ba, sai sheshsheƙar kuka. Mariya ta kawo ruwa a baho, ta fizge ummi daga hannun balarabe, ta saka ta a cikin ruwan ɗumin. Sai a lokacin ummi ta zabura ta fashe da kuka, ta ce "Mama zafi". Tana kuka ummi na kuka, ta yi mata wanka, ta saka mata kaya, ta nemi wuri ta kwanta, ta share balarabe. Kwana suka yi ummi na koke-koke, ko barci ya ɗan ɗauke ta, sai ta zabura tana turza ƙafarta tana ihu. Haka mariya ta kwana kuka, da balarabe ya kai hannu zai taɓa ummin, sai ta ɗauke ƴar ta, ta juya masa baya. Wayewar garin Allah, mariya ta saba zuwa ta gaida Iya, amma a ranar taƙi kula kowa, ta ƙi ɗora girkin gidan. Yara masu tafiya makaranta, duk sashin ta suke zuwa karɓar kunun safe, su sha su tafi makaranta, ranar shiru ba ta ɗora ba, kowa yazo sai ya koma. Balarabe ya din ga raragefe, ya rasa me zai cewa mariya, ya san ƙarshen cuta an yi mata, ba ma ita kaɗai ba, har da shi, sai dai ba yadda ya iya sawun giwa ya take na raƙumi, iya mahaifiyarsa ce ba yadda ya iya, dole ya bi umarnin ta. Yayi shirin sa zai fita kasuwa, jiki a sanyaye ya ce "Mariya, ko asibiti zamu kaita, na ga kamar da zazzaɓi ta kwana". "Dan Allah ka ƙyale ni da abun da ya dame ni, ka ƙyale ni bashir ka ƙyale mini ƴa ta, duk muninta daga jikina ta fito, ni na damu da ita, tun da a gurin kai da mahaifiyar ka, ba ƴa ba ce. Tun da baban sa yana da kuɗi dole ta ce dauɗar gora ciki ka sha ta, nayi imani da Allah da ɗan ka ne, yayi laifin nan, kowa sai ya ji" tayi maganar cikin matsanancin kuka. Lallai mariya ta kai ƙarshe a ɗaukar zafi. "Ki yi haƙuri mariya, ke kin san ina ƙaunar ƴa ta, ba yadda na iya ne, wallahi mariya ba ki fi ni shiga damuwa da tashin hankali ba, ki yi haƙuri dan Allah" Ba ta kuma kula shi ba, ta cigaba da shafa kan ummi, da ta ɗan samu bacci, tana zubar da hawaye. Da son ransa ne, ya wuni tare da su, ya cigaba da rarrashin ta, amma ya san idan ya ƙi fita, wani tashin hankalin zasu fuskanta daga Iya. Gaba ɗaya girkin ma taƙi yi, ummi kawai ta samawa abun da za ta ci, da ta tuna a yadda ta tarar da ummi, sai ta sake fashewa da kuka. Iya na son yin tijara, amma tana tsoron kar abun da ya faru ya tonu, dan sun haɗu da mariya a tsakar gida,ta hango tsantsar rashin mutunci da tashin hankali a idon mariya, wanda ba ta taɓa gani ba, dan haka ta ƙudurce a kan balarabe za ta juye. Haka kuwa aka yi, ana idar da sallar magariba, ya dawo, ya je gaishe ta, ta dira masa bala'i, tamkar ba ita ta haife shi ba, tare da jaddada masa muddin ko shi ko matarsa suka bari zancen nan ya fito, sai ta tsine masa kuma babu ita babu shi. Yayi ta bata haƙuri, sannan ya nufi ɗakin su, ya tarar da mariya tana goye da ummi kamar jaririya, tana jijjigata tayi bacci. Sallamarsa kawai ta iya amsawa, daga haka ba ta sake kula shi ba. "Ya jikin ummin?" "Ba sauƙi" ta faɗa kai tsaye. Ta je ta kwantar da ummi a kan katifarta da ke ƙasa, ta koma falo kan kujerar da ke ɗakin ta zauna. Da yake ɗakin babba ne sosai, suka raba shi biyu da labule ya zama kamar ciki da falo. "Ba sauƙi fa ki ka ce maman ummi?" "Ina sauƙin yake bashir? An yi wa ƴa ta rauni na har abada, waye zai auri ummi ya riƙe ta da amana, alhalin an binne gaskiyar abun da ya same ta tun a lokacin da ya faru, ɗan gata ya ci bulus, koda yake dama an ce ba zata auru ba, saboda muninta, da wanne ummi za ta ji? Wallahi ɗaukar ƴa ta zan yi na bar gidan nan, garinmu zan koma, ko kare Allah ya bani ina so, balle ɗan adam" Ta ƙarasa tana sheshsheƙar kuka. Ya ƙarasa ya zauna a kusa da ita, ya riƙe hannunta, idon sa ya tara hawaye ya ce "Haba maman ummi, ya zan yi, iya uwata ce, dole na yi mata biyayya, idan ki ka tafi da ummi ku ka bar ni, in zauna da wa? Ina son ku wallahi dan Allah kar ki yi mini haka, ummi kuma ba abun da zai hanata auruwa in sha Allah, dan Allah kar ki tafi ki bar ni" Kallonsa ta yi, har cikin zuciyarsa yake maganar, wani irin tausayin sa ya kamata, har ga Allah yana iya ƙoƙarin sa a kan su, mahaifiyar sa ce ta hana su zama cikin kwanciyar hankali. Ta kwanta a jikinsa tana kuka, rarrashinta ya din ga yi, yana yi mata magiyar, ta taya shi ya yi wa iya biyayya, ya san ba zasu taɓe ba, kuma rayuwar ummi ba zata wulaƙanta ba. Abun ka da mata da miji, haka ya lallaɓata ta janye batun yin yajin, har ya fara ƙoƙarin shiga wani abun daban. Iya ce ta faɗo ɗakin tana faɗin "Wai balarabe ba ka ji ana kiran salla bane, ka shige ka ƙule a ɗaka da mace" a razane mariya ta yi gefe, tana kare jikinta. "Eh iya yanzu zan tafi masallacin ma dama, dam..dama... Yanzu aka kira sallar" Ayshercool. 08081012143                             *CUTARWA!* Watpad ayshercool7724 Arewabooks ayshercool7724 YouTube Cool hausa novels What's app 08081012143 BRIGHT PENS (FREE BATCH) 3 Yanayin da suke ciki, bai sanya iya ja da baya ba, mussaman yadda suka rikice tamkar marasa gaskiya. "Ina jin duk abun da ku ke faɗa ai, idan ta tafi ta barka ka yi yaya, tun da ta fini a wurinka, kar Allah ya sa ta zauna ɗin mana, ta ƙara gaba, wataƙila dama ita ce ƙashin tsiyar da ta tokare maka ƙofofin arziknka, har ni zan gindaya umarni, ka zo kana lallaɓata? Ki tafin mana waye ya riƙe ki? Ke idan ƴar mutunci ce ina uwarsa har sai ya nemi shawarar ki sannan zai bi umarnina?. To ke idan ban isa da ke ba, na isa da ɗa na, dan haka ki san abun da yake yi miki ciwo, idan ƙabilar ku kun saba asiri ku mallake mazaje, to ni na yi wa kaina da ƴaƴana dafa'i, asirinku bai isa ya kama ni ba" Ba yau iya ta saba yi musu laɓe ba, dan haka yanzun ma mariya ba ta yi mamaki ba, dan idan da sabo ta saba. Iya ta sake jaddada musu duk wanda ya fasa abun da ta ce a rufe, bata yafe ba. Baban ummi ne ya yi ta bata haƙuri, mariya kuwa ta haɗe rai, wani abu mai ɗacin gaske na kaiwa da komowa a ƙirjinta, ji take kamar ta tashi ta ɗurawa Iya ashar, wanna ai shi ake kira da ga mari ga tsinka jaka, gaba ɗaya tsohuwar nan ba ta da imani, ba ta da mutunci, abu ɗaya take girmamawa a rayuwarta shi ne kuɗi. Bayan sun samu ta fita, ya leƙa ya tabbatar ta tafi, sannan ya dawo ya cigaba da rarrashin mariya, ganin ya shiga tsaka mai wuya, ya sanya mariya ce masa "Ka kwantar da hankalinka baban ummi, ba wanda zai ji maganar nan, ina fatan Allah ya yi wa ummi sakayya, ba wanda zan bari ya sani" Ya ce "Yauwwa, Allah ya yi miki albarka, in sha Allah zan san abun yi, zan yi ƙoƙarin neman fili a garin nan, na gina mana ko ɗaki ɗaya ne da makewayi, mu koma can, ko kema kya samu sassauci. Kallonsa kawai take yi, cike da tausayawa dan kuwa ta san tun da iya ta gama raina masa wayo ba shi da abun duniya, ba zata taɓa barin sa ya bar gidan ba, ko dan kar ta huta. A zahiri kuma ta ce "To Allah ya yassare" ya amsa da amin sannan ya tashi ya fita. *** Jujjuyar lokaci ya sanya abubuwa cigaba da gudana, wasu da daɗi wasu marasa daɗi, sai dai lokaci ya wuce ba tare da ɗaci da raɗaɗin abun da ya faru da ummi ya bar zukatan iyayenta ba. Kuma babu kunya, wanda yayi laifin ya cigaba da sabgoginsa hankali a kwance. Mariya ta ƙara tsananta kula da jan ummi a jiki, babanta ya kaita makaranta, ita kuma ta je ta ɗaukkota, ta daina barin kowa ya raɓi ummi. Mariya na zaune na ƙoƙarin koyawa ummi assignment a tsakar gida, kasancewar tana aji na uku a sakandare aka yi mata aure, ta iya karatu da rubutu. Iya na zaune suna hira da babarsu magaji da idris. Ummi taƙi mayar da hankali a kan karatun da mariya take koya mata, sai soshe-soshe take yi, tana ɓata fuska. "Mamana, wai ba zaki mayar da hankali ba, so ki ke anty ta zane ki?" "Mama ni bana son makarantar" tayi maganar hawaye na taruwa a idonta. Cikin damuwa haɗi da kulawa ta ce "Saboda me ummina" Cike da ƙuriciya ummi ta ce "Tsokanata ake yi, mama dan Allah ki mayar da ni fara, kuma ki rage mini ƙibata" Mariya ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Ummina, ke fa kyakywar yarinya ce, ai kin san sahabban manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam, da nake yi miki tarihi ko?" Ummi ta jinjina kai ta ce "Eh, Ina son tarihi" "Yauwwa ummina, mai kiran salla a zamanin Annabi Sallallahu alaihi Wasallam, sayyiduna Bilal radiyallahu an hu, baƙi ne, kuma Annabi bai taɓa ƙyamarsa ba, haka sahabbai ma" Ummi ta yi shiru ta ce "To mama kin ce in din ga son annabi, to masu tsokanata ba sa son annabi ko?" Shiru mariya ta yi, tana tunanin wane bayani za ta yi wa ummi, dan duk da rashin sakewarta da mutane, idan tana tare da mamanta, akwai surutu. Iya ta ce "Kin ga kar ki sakawa yarinya wani tunani daban, ki gaya mata gaskiya kawai, mummuna ce ko ki so ko ki ƙi" Babar su magaji ta kwashe da dariya ta ce "Iya wannan jika taki, ai tun yanzu yakamata a fara nema mata maganin farin jini, dan za ayi gwagwarmaya kan a samu mai so, dan ina jin Alhassan ranar yana cewa; da zai samu igiya da ya zargawa ummi, ya tafi tashe da ita a matsayin ɗan biri" tayi maganar tana ɓaɓɓaka dariya ita da iya, ba tare da tunanin, ya mariya zata ji a zuciyarta ba ko ita yarinyar, ummi tayi ƙuri tana kallonsu, duk da yarinya ce, ta san cin mutunci. Mariya ta ce "Biri kuma, ummin za a yi wasan biri da ita, kuma ki ke dariya, shikenan bakomai" tayi maganar cikin ƙunar rai, ta kama hannun ummi suka tafi ɗaki. "Mama, da gaske ni biri ce? M, for monkey na bayan littafina?" Mariya ta goge hawaye, ta ce "Ummina ke mutum ce, mai kyau sosai da sosai, kar ki sake haɗa kanki da biri kin ji ko? Kina da kyau sosai, kalli gashinki fa, duk garin nan kin ga mai irin gashinki?" Ummi ta girgiza kai alamar a'a. "Yauwwa ummi, idonki ma mai kyau ne, ina son idonki, duk garin nan babu mai irin idonki". Ummi ta taɓa idonta ta ce "Sai akuya ko?" "Akuya kuma?" "Eh, malamarmu ce ta faɗa, ta ce ni da akuya irin idonmu ɗaya, eyes sunan ido da turanci in ji anty" Mariya ta yi shiru tana kallon ummi, yarinyar na cikin taskun ƙalubale, daban-daban, har a kai ga malamarta na kamanta ta da akuya. Iya kuwa ta cigaba da hurawa balarabe wuta, da shi da mariya, cin kashin yau daban na gobe daban, har ƴan uwansa ma, ware shi suke a wasu abubuwan saboda ba shi da kuɗi, haka zalika mariya ta cigaba da yi wa iyalan gidan bauta, idan anjima su yi mata rashin mutunci, ko a ci zarafin ƴar ta a gabanta ba. Kusan kullum sai ummi ta ce ba ta son makaranta, dan kuwa abun da mariya ta fuskanta, ba iya ɗaliban ne ke tsokanarta ba har da malamansu a ciki. Dan idan ummi ta zo da aikin gida, tayi a gida, sai ta ce ba zata nuna wa malamarsu ba, idan ta tambayeta dalili sai ta ce "Malamarmu cewa take yi in fito gaban Allo, a tafawa ƴar baƙa saran daddawa, ayi mini dariya, ni kuma in yi ta kuka sosai, bana son ana tsokanata" Ba ƙaramin ɓaci ran mariya yayi ba, Dan haka da kanta ta je makarantar, ta roƙi headmaster, a kan ya taimaka ya tsawatar a kan abun da ake yi wa yarinyar, kar son karatun ya fita daga kanta gaba ɗaya. Yayi mata alƙawarin yin hakan, sai dai ba ta canza zani ba. Ummi na ta kaiwa tana komowa a tsakiyar ɗakinsu da safe, kasancewar yau ba makaranta, sai fama take da uban gashinta, taƙi tsayawa a gyara, mariya sai fama take da ita ta nemi wuri ta zauna. Ta kalli babanta da yake cin abinci ta ce "Baba kafi mama loma" tayi maganar tana dariya. "Eh mana, baki ga na fita girma ba?" Ummi tayi dariya ta ce "To ni kuma gaba ɗaya ƴan gidan nan, na fi su loma" Mariya ta ce "Ke ɗin, sai ka ce abinci ki ke ci" "Mama nafi duk ƴan yara girma fa" Babanta ya ce "Kin fi su lafiya ne, kuma kin fi su kyau shalelena" Ta kama kumatunta ta ce "Iya ta ce bani da kyau ai" "A'a ke kyakywa ce sosai" miƙewa ummi ta yi ta fita daga ɗakin, tana leƙa baƙon ɗan magen da yake wasa a tsakar gida. Mariya ta yi ajiyar zuciya ta ce "Baban ummi, kana ganin ummi zata iya samun miji tayi aure?" Ya kalle ta ya ce "Meyasa zaki faɗi haka? Kina mahaifiyar ta, kema kin fara biyewa surutun mutane na cewar ƴarmu ba ta da kyau mummuna ce?" "Ba haka bane ba, abun yana taɓa ni sosai da sosai, har malaman su ummi su da zasu tsawatar wai har da su a cikin tsokanarta, babar su magaji wai har da cewa Alhassan ya na kiran ummi da biri, kuma ta faɗa suna dariya" Jiki a sanyaye ya ce "Biri kuma? Cin mutuncin ya kai haka? Wallahi mariya ummi ba mummuna ba ce ba, tana dai da duhu ne, kuma ƙwayar idonta ce da ba irin tamu ba, amma ba mummuna ba ce ba" Mariya ta numfasa ta ce "Ni ba wannan ba, duk wanda ya ci zarafin ummi, na san bani na halicceta ba, amma abun da yake damuna, a zamanin nan yarinya ta kai mutuncinta ɗakin aure, ya ta ƙare ina ga idan ummi ta samu miji, gaya masa zamu yi ga abun da ya same ta? Idan muna gaya masa waye shaida babu tabbacin a lokacin dukkaninmu da muka sani muna raye. Idan kuma muka rufa, zai yi mata kallon mutuniyar banza, ummi ta san abun da ya faru da ita mummunan abu ne. Ina tausayawa yarinyar nan abubuwan da suka baibaye rayuwarta, ina tausayawa ƙalubalen da zata fuskanta wataƙila bana nan a lokacin balle na tayata kwasar raɗaɗin, amma ina tausayawa ummi, idan ba ta samu miji mai tawakalli ba, za ta fuskanci wulaƙanci, wa zai so mini ummi tsakani da Allah, ya karɓi ƙaddarar da ta same ta? Wallahi baban ummi ba zan yafe wa yaron nan ba, ya cuce ni ya cutar da rayuwar ummi, ko idan ta ƙara girma zata manta oho, haryanzu bata yadda na bar ta a ɗaki ita ɗaya, an cuce ni" tayi maganar kuka mai ƙarfi yana ƙwace mata. Balarabe yayi ajiyar zuciya, yana jin ɗaci a zuciyarsa ya ce "Wallahi mariya ni kaina abun nan yana ci mini zuciya, ba yadda na iya, mahaifiyata ta riga ta yi mini kandagarki, ƙetare maganar ta na iya shafar mu baki ɗaya, amma in sha Allah, ina sanya ran Allah ba zai wulaƙanta ummi ba, dan Allah kiyi haƙuri mariya, wallahi idan kina kukan nan, sai na ji kamar na bijirewa umarnin iya, na ɗau matakin abun da aka yi wa ummi". Ta share hawayen ta, ta ce "Kar ka yi haka, aikin gama ya riga ya gama, ko ka ɗau mataki, wannan wani miki ne a zukatanmu da ba zai taɓa warkewa ba". Yayi shiru ya zubawa mariya ido, shi kansa ya san mariya ba ƙaramin haƙuri take yi ba, zama da shi. Tsakaninta da shi babu wata matsala, amma azabar wahalar da take a gidan, duk ta rame ta yi duhu, soyayar kirki ba sa samun sakewa su nunawa juna, saboda azabar iya. Ihun Ummi suka ji, hakan ya sanya su yin rige-rigen fita tsakar gida da gudu. Ummi suka tarar da Alhassan ɗan wurin saminu, ya tattara gashin ummi, ya murɗe shi a hannunsa, jijiyoyin kanta sun mimmiƙe, duk ta gigice. A guje mariya ta ƙarasa, ta hankaɗe shi, ta ƙwace ummi da ke kuka. "Alhassan me ummi tayi maka ka murɗe mata gashi haka?" Cikin fitsara yaron ya ce "Ɗan magenmu take mana wasa da shi" A fusace mariya ta ce "Kuma saboda zalunci ka rasa me zaka yi mata, sai izaya da gashinta?" "To waye ya ce ta taɓa mana magenmu, ana ta nemansa?" Cikin zafin rai, mariya ta ɗauke Alhassan da mari. Sai da balarabe ya waro ido. "Tura ta fara kaiwa bango, wane irin zalunci ne haka? Ummi fa ƴa ce ba baiwa ba, wallahi duk wanda ya kuma dokar mini ƴa sai na ci ubansa. Dama a ciki nake da kai, na samu labarin kana ce mata matashiyar buranya, uwarka ce mai kama da buranya ba ita ba" "Wayyo Allahana iya, a taimake ni ta kashe mini ido" Alhassan ya wage baki yana kwarmato" Bakomai ya hana balarabe taɓuka komai ba, face sanin idan iya ta fito ba ƙaramar tijara zata yi ba, kuma ƙarshe su zata ɗorawa laifin". Buje a hannu iya ta fito daga banɗaki tana faɗin "Menene haka? Kashe yaron zaki yi me yayi miki?" Alhassan ya kwashe ƙarya da gaskiya ya gaya mata. Ta kuwa hau sababi "Balarabe kana tsaye take neman yin kisan kai, shikenan an taɓa ƴar gwal sai tayi yinƙurin cire masa ido. Duk ɗawainiyar da ubansa yake yi a gidan nan? Wace irin ɗawainiya ce ba yayi da ku, wasu lokutan ba har ciyar da kai yake ba da iyalin naka, da baka ganin kowa da mutunci sai su, saboda zuciyarka ta riga ta mutu, baka da amfani ka kashe zuciyarka ka auri mai ƙashin tsiya, baka da komai sai sokonci da son mace, wadda maganarta ta fi tawa, tun da tana baka abun da bana baka, to kayi ƙoƙari ta kashe masa ɗa, wallahi duk matakin da ya ɗauka a kanku, babu ruwana ko da kuwa wurin hukuma zai kai ku" Cikin takaici mariya ta ce "Wato iya saboda baban Alhassan yana da kuɗi shi ne ɗa, da idan aka ɗaukar masa mataki ba zaki hana ba, ummi ce da aka ketawa haddi ba ƴa ba? Iya Allah fa" cikin hanzari balarabe ya girgiza mata kai. Cikin ɗacin zuciya ta koma ɗakinta. "Ai da ka bar ta ta cigaba da gaya mini magana, ta tabbatar mini da bata da tarbiyya, kai ban da ina tsoron Allah da wallahi tuni na saka ka saketa, ko Allah ya sa ƙofar arzkin ka ta buɗe, idan ya so ka auro falla-fallan mata, mu samu ta haifa mana masu kyau, kadara irin arziki" Bai cewa iya komai ba, ya shiga ɗaki, ya tarar mariya ta rungume ummi, tana aikin kuka. Zai yi magana ta ɗaga masa hannu, ta yi masa alamar ya rabu da ita, haka ya ƙyaleta ya fice. Har ya tafi kasuwa tunani yake yi? Ko haya zai nema ya tashi ya bar gidan, ya san ba iya ce kaɗai ke da hakki a kan sa ba, iyalansa ma na da hakki a kan sa, kuma suna buƙatar walwala, amma iya ta takura su da yawa, kuma ya san ba zai iya biyan haya ba, kuma duniya zata zage shi, ya kasa zama da matarsa ya fifita iyalansa a kanta, haka yayi ta tunani, ba tare da samun mafita ba. Mariya ma wuni tayi tunani da zancen zuci, ita kanta ta san bata isa ta tafi gida ba, ta ce tayi yaji saboda takurar uwar miji ba, ba babanta ba yayyenta maza kawai sun ishe ta, babu mai goya mata baya, dan ko hirar take musu, idan ta je ganin gida, sai ace uwa ce a wurinta idan da kara da tarbiyya. Gidansu irin iyayen nan ne masu kashe ƴaƴansu su raya na wani a gidan aure, saboda dattaku dan gidansu gidan malamai ne. Kuma ko kusa ba zata iya gaya musu cewar an yi wa ummi fyaɗe ba, saboda ita kanta da take ta hayagagar rashin bi wa ummi hakkinta, tana yi ne saboda abun yana damunta, mussaman nuna wa da ake yi ƴar kamar ba ta da amfani, saboda babanta ba shi da kuɗi. "In sha Allah ummi sai ahalin nan sun kwanta a kafaɗarki, Allah ya nesanta ki da talauci, ya baki ikon cin jarrabawar nan da ni da ke baki ɗaya. Allah shi ya san dalilin da ya sanya yayi ki a haka, kuma ya jarrabeki Allah ya baki mai kula da ke, ko bana raye" haka ta wuni cikin kuka da damuwa. ***" Rayuwa ta cigaba da tafiya, umma ta cika shekaru shida a duniya, sai dai bata sauya zani ba, domin kuwa gorin yau daban na gobe daban, haka iya ke yi, a kan cewa balarabe ba ya iya tsinana komai, a gidan komai shi ne koma baya. Haka zalika balarabe, ya fara tunanin miƙewa ya nemi kuɗi, ko dan samawa iyalin sa farinciki da kwanciyar hankali, mussaman ƴar ƙaramar yarinyar nan, da aka mayar da ita tamkar wata halitta daban. Yau suna kwance da daddare tare da mariya ya ce "Maman Ummi kin san wani abu?" Ta ce "A'a" "Ina ga ƴan kuɗaɗena da nake tarawa, zan je birni in ga abun da zan iya yi, ko Allah ya sa na samo arziki" Mariya ta kalle shi ta ce "Baban ummi baka yadda da yadda Allah ya ajiye mu ba? Na san babu daɗi abun da iya take yi maka, amma dai ka yi haƙuri da barin garin nan, ka tafi yawon neman kuɗi, raba bawa da arziki sai mutuwa, dan Allah kayi haƙuri" Ya gyara kwanciyarsa ya ce "Maman ummi, tun da abun nan ya faru da ummi, ji nake tamkar ina kan wuta, gidan galibi duk maza ne tana cikin haɗari, sannan ki duba ki ga yadda ake yi mata a gidan nan, ɗazu fa suna tafe da yarinyar nan da take ɗaukarta ta tafi da ita islamiyya, yara suna tsokanarta baƙar tukunya mai ƙyalli, ba ki ji zuciyata ba, wallahi yanzu haka bani da burin da ya wuce tashi na bar gidan nan. Da nayi tunanin ko kano zan je wurin yaya hashimu idan da wata hanya da zai ɗora ni a kan kasuwanci, to kuma bana son na je na ɗora masa ɗawainiya, kuma kin ga shi ɗan boko ne, iya ta ce sai na bi su Rabiu kudu neman kuɗi, bana son yin nesa da ku, amma na fuskanci idan na cigaba da zama a haka, wahala zamu cigaba da sha". Mariya ta nisa ta ce "To, ni dai dan ta ni, wallahi baban ummi zan cigaba da haƙuri, komai lokaci ne, amma duk abun da ya shafi umarnin iya, babu ruwana a ciki, Allah ya taimaka ya bayar da sa'a, ummi kam za ta yi gwagwarmaya wadda sai dai mu bata gudunmawa ba zamu iya tare mata ba. "In sha Allah komai zai zo da sauƙi, kuma zai wuce umminmu zata rayu cikin farinciki" "Allah ya sa" Ya amsa mata da "Amin" Abu kamar wasa, Iya ta din ga yi wa balarabe kwarmato, a kan lallai ta yi magana da Rabi'u maƙwabcin su, lallai ya nemo kuɗi, ya bi shi lagos, ya ɗora shi a kan hanyar neman arziki. Bashir ba shi da kuɗin da aka ce ya tanada, dan kuwa rabi'u cewa yayi ya tanadi dubu ɗari, harkar fawa yake a lagos, ya je ya koya masa. Ya ce wa iya ba shi da halin kuɗin nan ta ce "Ai dama ba zaka yi su ba, Allazi babu wanda ya karɓo jakadancin talauci zuwa duniya, ka je ka tambayi ilyasu, ko sagir, ga saminu, ko Yahaya, tun da su masu zuciyar nema ne, kuma ba a rasa nono a riga, su baka aro. Bashir baya son dalilin da zai sanya ya keta billensa ya nemi alfarmar ƴan uwansa, saboda yadda ba sa yi da shi. Amma bisa ga umarnin iya, ya tambayi sagir aron kuɗi, amma ya kada baki ya ce "In ara maka kuɗi, ka biyani da me? Gaskiya ba zan iya ba, kuɗin nan masu wahalar samuwa, na baka in yi sadakar dole da ba niyya, kayi haƙuri kawai". Ya ji ciwon abun da yayi masa, amma ya dake ya gayawa maman ummi. Ita kanta mariya abun yayi mata ciwo, abun da iya take musu ya sanya ta tsane ta, duk da ita ta haifi mijinta, tattara samirun ta, har da zobenta da aka saya mata lokacin aure ta sayar, sai ganinta yayi da kuɗi, dan ita kanta wulaƙancin da ake yi masa yana bata haushi. Ya din ga yi mata faɗa a kan sayar da kayanta da tayi. Ta ce "Idan har tafiyarka zai sanya iya farinciki, a daina wulaƙanta mu, ka tafi kawai Allah ya tsare" Ya riƙe hannunta ya ce "Na gode mariya, Ubangiji Allah ya saka miki da alkahirin sa, ya ƙara miki haƙuri, kada Allah ya sa na ci amanarki, ko a yanzu ko a gaba, Ubangiji Allah ya kula mini da ku" haka ya din ga zuba mata addu'a kamar ta yaye masa gaba ɗaya matsalolin sa. Saura kwana ɗaya ya tafi, da ya shiga ya fita, sai yayi musu addu'a, ya sanya musu albarka da ita ummi. Da daddare mariya ta shirya masa kayansa a wata jaka, tana ta yi masa addu'a. Ya zura mata ido yana kallon ta. "Wai wannan kallon fa?" "Da za ace in nuna matar aljanna a duniya, zan nuna maman ummi" Tayi murmushi ta ce "Zaka fara ko?" "Allah ba wasa nake ba amaryata" ta kwashe da dariya ta ce "Ko ba amarya ba, da wannan ƴar tamu nake amaryar, in zo in fara tara kayan ɗakin auren ummi, wai wa ya ganni maman amarya ranar auren ummi ba zama". Yayi dariya ya ce "Kema ɗin yaushe aka yi naki auren ki ke hango auren ummina, in sha Allah sai ta yi karatu mai zurfi, Allah ya sa kan na tafi ɗin nan akwai rabo a cikin nan, ummi ta samu ɗan uwa" "Amin ya Allah, ni kaina ina son jariri wallahi" "To Allah ya bamu mai amfani, ya bani kuɗi na halal na wadata ku, mu rayu cikin farinciki" "Amin, amma yanzun ma Alhamdilillah, ai kuɗi ba su ne farinciki ba" sosai suka din ga hira, tana ce masa ban da kallon matan yarabawa idan ya tafi lagos, ya din ga yi mata dariya. Har ta yi barci, amma shi ya kasa bacci, ya tashi daga kan gadon, ya koma shimfiɗar ummi, da ta yi nisa a baccinta sosai. Ya kunna fitila yana kallonta, sam bai ga munin ƴar sa ba da mutane suke faɗa suna zuzutawa. Ya din ga shafa gashin ummi, yana kallonta. Mariya ta yi juyi ta hango shi, ta ce "Baban ummi, ko saka maka ita zan yi a jakar ka ku tafi, wannan ƙauna haka?" Yayi murmushi ya ce "Ko yara nawa zan haifa ummi ta daban ce a zuciyata, ina ƙaunar yarinyar nan" Mariya ta ce "To kar dai ummi ta mamaye ko ina a zuciyar, a rage mini wuri" Yayi murmushi yana cigaba da kallonta. Juyi ummi ta yi taga hasken fitila, ɗan razana ta yi, saboda haryanzu ba ta manta yadda aka yi mata fyaɗe ba, dan daren da aka yi mata fyaɗe ta tuna, da ƙarfe ta ce "Baba" Ya ce "Na'am ummina" "Kai ne" tayi maganar tana shafa fuskarsa. "Eh Ummina" Ta ce "To" ta cigaba da lumshe ido zata koma bacci. "Ina ƙaunar ki ummina, Allah ga ƴa ta da mata ta, Allah ka kula mini da su, ƴar kyakywar ɗiya ta" yayi maganar yana jan kumatunta. Ummi ta ɗora hannunta a kan nasa tana murmushi ta  cigaba da bacci. Washegari da zai tafi har soro suka raka shi, ji yake tamkar kar ya tafi, amma yana fatan idan har tafiyar ta sa zata zama silar walwalar iyalin sa gara ya tafi. Sai da iya ta fara maganganunta na rashin mutunci, a gaban mutane tana neman yi musu tijara, sannan suka rabu ya tafi. Kwanaki uku da tafiyar baban ummi, kewa duk ta ishi ummi da mariya, sai dai tafiyar ta sa bata sanya sun samu sassaucin jaraba da masifar iya ba da gore-gore, gashi a lokacin waya bata yawaita ba, dan haka ba wanda ya san halin da wani yake ciki. Bai fi sati biyu ba da tafiyar sa, abun da ya bar musu duk ya ƙare, gashi abu kamar wasa, muraran yara ke cigaba da cin zalin ummi, ga farmaki da Idris yake cigaba da kai mata, loka-lokaci da wasu daga samarin gidan, dan ma yanzu ta yi wayo sosai da sosai, da ta gansu sai gudu. Cin zali a wurin ƴan samarin yaran nan maza, tamkar sun samu sa'ar su, saboda tana mace, abu kaɗan sai a kai mata duka, ko ayi mata wata izayar ko a gida ko a makaranta, saboda ana ganin ummin tamkar sokuwa, kuma babu mai tare mata, da mariya tayi magana iya tayi kanta da tijara. Ɗan abun da ya rage a hannunta, ta fara fanken sayarwa, saboda ta samu abun juyawa, amma sai da iya ta cinye jarin da cin bashi, tare da tula mata ayyukan da zasu hanata sana'ar. Abubuwa fa suka fara yi wa mariya da ummi yawa, duka ko ta ko ina, wani ta iya karewa, wani ta kasa sai dai tayi kuka ta gaya wa Allah. Tana tsakar gida tana wanke-wanke, ta samu da ƙyar ta jiƙawa ummi garrin kwaki, bayan ta dawo daga makaranta tana sha, ta ji hayaniya ta yi yawa a waje. Bata damu ba ta cigaba da aikinta. Da gudu Alhassan ya shigo ya ce "Babar ummi Albishirinki?" Ta kalleshi ta ce "Albishirina kuma? Menene?" "Wai baban ummi ƴan fashi suka kashe a hanya, zasu taho gida daga ikko!!!" Ayshercool 08081012143                      *CUTARWA!* Watpad ayshercool7724 Arewabooks ayshercool7724 YouTube https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels What's app 08081012143 BRIGHT PENS (FREE BATCH) P4 Wani irin jifa mariya tayi da kwanon hannunta, ta miƙe a gigice jikinta na wata irin tsuma, zuciyarta na bugawa da saurin gaske amma ta kasa magana. Miƙewa ummi ta yi ita ma, tana bin su da kallo. Iya ta fito a gigice ta ƙundumawa Alhassan ashariya ya ce "Uban wa ye ya gaya maka haka? In ji wani ɗan iskan". Ilyas da saminu ne suka shigo, fuskokin su babu walwala. "Ku gyara wurin da za a shigo da balarabe, Allah ya yi masa rasuwa, tun safe muka tafi ɗaukko gawarsa" A gigice iya ta ce "Ƙarya ne ban yarda ba, ya za ayi ace ya mutu? Balaraben ne ya rasu? Waye ya kashe shi, ya aka yi aka kashe shi?" Sagir yayi sallama tare da idris, ya ce "A ina za a kwantar da shi idan an shigo ne? Ana jira fa" Mariya ji take abun kamar mafarki, addu'a take Ubangiji Allah ya sanya mafarki ne, Allah ya sa ba mijinta ne ya mutu ba, Allah ya sa ba baban umminta ne ya mutu ba". Magaji ya shigo da tabarma, ya shimfiɗa, aka yi sallama tare da ƴan sanda, da rabi'u da suka tafi tare, aka shigo da gawar bashir, tana ta ɗigar da jini. Nan da nan gida ya cika da jama'a, Iya sai ihu take tana kururuwa tana kuka, kai da gani ka san jahilci ya samu gidin zama a wurin iya, saboda yadda take ihun ta shiga uku ta lalace. Jiki na rawa mariya ta saka hannu ta buɗe mayafin da aka rufe gawar bashir, fuskar nan fayau kamar yana bacci, kamar wanda yayi wanka ya fito haka gawar take, ga ƙirjinsa in da aka harbe shi, jini yana ta zuba. "Innalillahi wa Innalillahi raji'un" shi ne abun da mariya ke ta nanatawa, tare da fatan Allah ya saukar mata da nutsuwa da dangana. Ummi ta shafa fuskar sa tana faɗin "Baba ka tashi, baba ka tashi daga bacci mama tana kuka" cikin haɗe rai sagir ya yi wa ummi tsawa ya ce ta tashi. Sa'adatu ta ce "Haba baban auwwalu, ka tausaya musu mana". Mutane suka cika gidan danƙam, saboda mutane sun san bashir sosai, mutum ne na mutane mai matuƙar haƙuri da girmama mutane. Sai ajiyar zuciya kawai mariya take yi, tana rungume da ummi, aka shiga da shi ɗakin Iya, aka yi masa sutura, sannan aka ce su je su yi sallama da shi. Har a lokacin mariya ta gaza zubar da hawaye, sai wata irin ƙuna da zuciyarta ke yi mata, abu kamar wasa bashir shikenan an yi an gama, rayuwar ta ƙare. Duk da yarinta ta ummi, amma ta san idan an mutu ba a dawowa, tayi kuka idonta duk ya kumbura, ta dinga taɓa shi tana "Baba ka tashi, ka ce zaka sai mini ƴar tsana in yi addu'a ka samu kuɗi, kullum ina yi maka addu'a" Mariya kam zubawa gawar ido kawai tayi, tana kallon ikon Allah, wai bashir ya mutu. Sa'adatu ta ce "Mariya ki riƙe yarinyar nan, za a shigo a ɗauki gawar" Mariya kamar sokuwa, dan kamar ma ba ta iya gane me ake cewa. Aka zo aka ɗauki gawar bashir, ana ta iface-iface, ummi ta riƙe ƙafar Saminu wan mahaifinta, da suka ɗaga gawar, tana wani irin kuka, amma babu tausayi ko imani, ya angije ta ƙasa suka yi waje. Allah sarki, ba ta karaya ba ta sake bin su, tana faɗin "Ku dawo da baban, zai tashi fa, bacci yake yi" Surayya, wadda take ƴar autar su bashir, ta riƙo hannun ummi tana kuka, ta rungume ta, tana ta rarrashinta. Gida ya cika da jama'a ana gaisuwa, mariya kuwa ta samu gindin bishiyar da ke tsakar gidan ta rakuɓe, tayi shiru ba ta cewa komai, ita kaɗai ta san azabar da zuciyarta take yi mata. Bata san hawa ba, ba ta san sauka ba, ta ji muryar iya na bala'i a cikin mutane "Dama ya za ayi mutuwar ta dame ta, ai dama ba dan Allah take zaune da shi ba, kalleta a ƙeƙashe ko kuka ba ta yi ba, alhalin ita ta takura lallai ya tafi neman abun duniya, ya zo ya wahalta mata, wallahi ban yafe miki ba" Daram! Gaban mariya ya faɗi, jin abun da iya ta faɗa na ƙarshe. Mutane suka shiga salallami, surayya ta ce "Haba iya, haba iya, baki san kukan zuci yafi kowanne ƙuna ba, gara ke kin yi kukan, ita kaɗai ta san me take ji a zuciyarta, da can ba ta ce ya tafi neman kuɗi ba, sai yanzu, dama Allah ya yi ajalinsa a can za same shi". Ai nan ta mayar da faɗan kan surayya, wanda hakan ya tilasta mata yin shiru, wasu suka goyi bayan iya saboda makira ce, wasu kuma suka goyi bayan mariya, kowa ya san kusan halinta ɗaya da mijinta, ba sawa ba fitarwa, akwai haƙuri da juriya, mussman a zamanta da iya. Yadda ta ga rana haka taga dare, abu goma da ashirin, ga raɗaɗin mutuwar mijinta, ga sharrin da iya ta ƙulla mata, wai ita ce silar mutuwar sa, ita ta hura masa wuta ya tafi neman kuɗi. Ta rasa me ta tsarewa iya, take yi mata wannan azababbiyar ƙiyayyar, saboda kawai tana auren ɗan ta, abun da ba haka take yi wa sauran sirikanta ba, kuma dukkansu babu wanda yake yi mata biyayyar da take yi mata, kawai ta camfata cewar ita ce mai farar ƙafar da ta toshe masa hanyar arzikin sa, ya kasa gaba ya kasa baya, gashi ya ɗauki son duniya ya ɗorawa mariya, yana matuƙar son ta da ƙaunarta. Ko fuskanta Iya tayi sun yi mu'amalar aure, ta ga sun yi wanka, to wunin ranar, haka zata wuni cikin ɓacin rai da tashin hankali, a wurin iya ta din ga ƙirƙirar mata laifi kenan tana ci mata mutunci, ta rasa wannan masifar, ga uwa uba ummi sunan kishiyar ta ne da ita, wanda hakan ya sa ta ƙara tsanar ummi, ga ƴaƴanta sun riƙe ta uwa, abun da ta dama suke sha, amma tana masifar kishi da uwar su. Washegari da azahar, dangin mariya suka dira a jigawa, suka zo gaisuwa, haka zalika Yahaya, yayan bashir da yake birni, shi ma ya zo ta'aziyya, ya ji mutuwar bashir ba kaɗan ba, abun ya girgiza shi, dan kaf cikin ƴan uwansa, ko wanda suke ciki ɗaya, basa shirin da suke yi da bashir, saboda biyayyar sa, yana matuƙar girmama shi. Yana son ummi, kasancewar sunan mahaifiyarsu ne shi ma da ita, marigayiyya uwar gidan malam hashimu. Ya tarar ana ta fama da ummi, ba ta ci abinci ba, sa'adatu da ba wani shiri suke yi da mariya ba, amma mutuwar bashir, da abubuwan da iya ke ta yi, ya sanya wani irin tausayin su ya kamata. Yahaya ya ga yadda ake fama da ummi, tana kwance a jikin mariya, ba wanda ya iya cin abinci a cikinsu. Duk da tana tsoron maza sosai da sosai, kuma shi baya yawan zuwa gidan, amma ta gane shi, dan yana kama da babanta sosai, kuma yana bata tsaraba idan ya zo. Ya ƙarasa ya ɗauketa, ya saka hannunsa a nata, ya ce "Mamana, ki din ga yi wa babanki addu'a, kuma ki din ga cin abinci, kuka ba zai yi magani ba" "Baba ba zai dawo ba ko, ya mutu wai?" Tayi maganar hawaye na zubo mata, kamar an kunna famfo. "Ba zai dawo ba ummi, amma zai ji daɗi idan kina yi masa addu'a" Cikin kuka ta ce "Na fi son ya dawo" ya din ga share mata hawaye, cike da tausayawa. Sai dai yayi mamakin yadda iya ke ta hantarar mariya, tana cikin alhinin mutuwar mijinta, ga ƴan uwanta a gida, amma iya na ta masifa da nanata ta kashe mata ɗa. Ya dubi Iya ya ce "Haba iya, haba iya da wanne za ta ji? Ya za ayi ta yi sanadiyyar mutuwar mijinta, mijin da suka yi auren soyayya, shekara bakwai tare, ko sulhu ba a taɓa yi musu ba, ki ce ita ta kashe shi, ga ƴan uwanta a gida ai babu daɗi" "Yahaya, ni fa nake zaune da yarinyar nan, ni na san abubuwan da take aikatawa, azabar son zuciyarta ya sanya ta hura masa wuta ya tafi neman kuɗi, gashi nan ya mutu a banza, yaron nan haƙurin zama yake yi da ita" Yahaya ya ce "A'a iya, idan na zo fa muna hira da bashir, a bar kaza cikin gashinta kawai banda tone-tone, amma batun ace mariya ce ta kashe mijinta bai taso ba, dan Allah ki bari ta ji da alhinin da take ciki" Kasancewar yana da abun duniya, domin kuwa lecturer ne shi a kano, kuma albashinsa da tsoka, dan haka yana yi wa iya sha tara ta arziki, a dole ta ja bakinta ta yi shiru. Wasa² magana har waje wurin maza, iya ta tubure tana cin mutuncin sirikarta, wai ita ta kashe mata ɗa. Yayan mariya har cikin gidan ya shiga, ya yi wa mariya wankin babban bargo. "Irin tarbiyyar da aka baki kenan dama mariya? Irin zaman da ki ka yi da mijinki kenan, ki kasa zama da shi a yadda yake, ki hura masa wuta ya tafi ajali ya riske shi, kuma gashi an ɗora miki, an ce ke ce sila. Mariya kin ɓata wayonki, wannan ba tarbiyyar gidanmu ba ce ba, kuma ahalinsa ba zasu taɓa mantawa da abun da ki ka yi ba". Kasancewar yana cikin manyan yayyenta, kuma tana bala'in tsoronsa, dan haka ba ta iya kare kanta ba sai kuka, ga shi a gaban mutane ya din ga yi mata faɗa, mariya ta rasa da wanne za ta ji. Iya kuwa ta samu damar cigaba da ƙullawa mariya sharri a wurin yayanta. Yahaya ya tsawatar, saboda shi ɗan boko ne, ya ce ba zai yiwu a saka mariya a gaba ace ita take aikata duk wannan laifukan ba. Idan ma haka ne tana matsa masa kan ya rasu yanzu yana ina? Kuma ai mijinta ne, tana da right na ya yi mata abun da take so. Ɗakinta ta shiga ta zauna, tayi kuka, tayi kuka, har zuciyarta ta fara raya mata ko kashe kanta zata yi ta huta da wannan azabar. Ummi ta zo tana kuka ita ma, dan tun ana yi mata faɗan nan ummi take tayata kukan, ta din ga share mata hawayen tana cewa "Mama ki yi haƙuri, ki daina kuka" ita kanta yayar mariya, ta san mariya ba za ta aikata haka ba, yadda iya ke yi wa mariya a gaban su, ba ƙaramin ƙular da ita yayi ba. Sai dai su al'adar gidan su, muddin ak kawo ƙararka daga waje, ba a taɓa goya maka baya, balle kuma a gidan aure, idan miji gutsurar namanki yake yana ci, sai ace ki je ki cigaba da haƙuri, wataran sai labari, kowa haƙuri yake yi. Maryam ta tambayeta ina samirunya, ta ga duk babu? Mariya taƙi gaya mata, ta shashantar da zancen. Bayan kwanaki uku da share zaman makoki, ƴan nesa suka watse, sai masu shigowa jefi-jefi gaisuwa, yayar ta ta zauna da ita, ta ɗan din ga ɗebe mata kewa, zuwa kwana arba'in, aga meye abun yi. Gaba ɗaya mariya ta gama fita daga hayyacinta, kai daka ganta ka san tana cikin alhini, ko abincin kirki ba ta iya ci. Salla kawai take iya yi, wanka kansa sai ta yi da gaske take iya yi. Daga kwanciya sai kuka, amma hakan bai sanya ta tsira daga tashin hankalin Iya ba, ga kyarar ummi da take yi kamar ba jininta ba, wanda hakan ya fara tunzura yayar mariya maryam. Kwanan bashir goma sha huɗu da rasuwa, rabi'u ya zo yayi sallama, suka amsa ya sake yi musu gaisuwa. Ya ce wa iya "Ina mariya, ina son zan yi magana da ku ne" Iya ta ce "Dole ne sai ta nan? In dai abun da ya shafi ɗa na ne, gaya mini kawai ina jinka" "Wane irin a gaya miki kawai? Ai tana da hakkin sanin menene ita ma, tun da mijinta ne" yaya maryam tayi maganar a zuciye kamar ta kife iya da mari, saboda a zamanta ɗin nan ta gane lallai mariya tayi zaman haƙuri. "Rashin kunya zaki yi mini?" "Ba wani rashin kunya, maganar gaskiya ce ai. Ke mariya fito za ayi magana" Jiki a sanyaye mariya ta fito cikin hijjabi, ta zo ta samu wuri ta zauna. Suka sake gaisawa da mariya, yayi mata gaisuwa, Sagir yayi sallama ya shigo suka amsa masa, shima ya samu wuri ya zauna. Rabi'u ya ce "Yauwwa, dama ni na yi masa magana tun da yana gida na ce masa ya shigo, Iya kamar yadda ki ka roƙi na tafi da bashir lagos, ya nemo arziki, to mun sauka Lagos lafiya". Maryam ta ce "Amma ki ka ce mariya ce ta ce lallai sai ya tafi neman kuɗi" Iya a fusace ta ce "Wai wace irin mara tarbiyya ce, ƙarya nake yi kenan, matsin da take yi masa ya sanya na yi masa magana, ya tafi da shi" Maryam ta ce "Amma ai ba haka ki faɗa ba, ki ka saka yayanmu ya din ga ci mata mutunci a gaban mutane, wallahi ki ji tsoron Allah" Rabi'u ya ce "Dan Allah ku yi haƙuri, ku saurare ni ku ji, bayan zuwanmu Lagos, mun fara sana'ar fawa da balarabe, kasancewar ba shi da account, yake tarawa a account ɗina, ya ce mini mariya ta sayar da kayanta, ta bashi kuɗin, amma shi a bashi ya karɓa, zai mayar mata da kuɗinta, dan haka ba laifi ya tara kuɗi, riba kawai kusan dubu sittin, uwar kuɗin sa da ribarsa da komai, kusan dubu ɗari biyu, basussuka da sauran su, duk na biya masa dubu ɗari da arba'in ne suka rage, mun taho gida da niyyar idan mun zo na cire kuɗin na bashi. A hanya ƴan fashi suka tare mu, suka ƙwace mana kaya, da kayan tsarabar sa, har sun yi gaba ya tashi kan su ƙarasa barin wurin, shi ne suka harbe shi a ƙirjin sa, kan ya rasu ya ce: kar a raba gado, sai an biya mariya kuɗinta na kayanta, da sauran kuɗin da take bin sa" Ya kalli ummi da ke zaune tana bin su da kallo, sannan ya kalli mariya ya ce "Ya ce; ki kula masa da ummi, sannan ki yafe masa" yana faɗar haka mariya ta sanya tafukan hannunta ta sake fashewa da kuka. "Ni bai ce maka komai a kai na ba?" Iya tayi maganar tana kallon rabi'u. "Yana cikin maganar yayi kalmar shahada, ummin dai ya fi nanatawa" Ta share hawayen da ke shirin zubo mata sannan ta ce "Ba wani zancen tana bin sa kuɗi, ni ban yi wannan maganar da shi ba, dan haka ka je ka ɗebo kuɗi ka kawo mini" Maryam ta ce "A kawo miki kuɗi kiyi me da su? Ai kuɗi na magada ne, kuma sai mariya ta gama idda za a raba gado, saboda a tabattar da babu ciki". "Ba dai ciki ba, shekara nawa rabonta da haihuwa, tun daga wannan mummunar yarinyar fuska kamar turotso, ba ta sake haihuwa ba, ba haihuwa take ba, dan haka ba ta da wani ciki. Wa ya sani ma ko balaraben baya haihuwa" "To me ki ke nufi, ummin ba ƴar ku ba ce ba? Wai ke matar nan anya musulma ce ke? Kin yi imani da Allah kuwa?" Sagir ya ce "Ke malama kar ki sake ki zagar mana uwa, na gaya miki" miƙewa maryam ta yi ta ce "Na zageta ɗin, ka yi abun da zaka yi. Azzalumar tsohuwa mara imani da tausayi, ashe ke ki ka ingiza ɗanki ya tafi neman kuɗi, amma kin saka yarinya a gaba, kina ta yi mata sharri, to wallahi dan kanki, ummi kuma idan ba ƴar ku ba ce, sai ki fita neman ubanta" nan da nan hayaniya ta ɓarke. Mariya ta tashi ta ce "Dan Allah yaya maryam ki yi haƙuri, in dai kuɗi ne, ni babu bashi tsakanina da baban ummi, na rasa mijina balle abun duniya? Tumunin takabar ma na yafe, a bawa ummi hakkinta, in ɗau ƴa ta in koma in da na fito dan Allah" tayi maganar cikin matsanancin kuka, tare da jan hannun ummi ta tafi ɗaki. Shi kansa rabi'u yayi mamakin rashin arzikin Iya, kawai ta ɗorawa mariya karan tsana. Ta sake jaddawa rabi'u ya kwaso kuɗi ya kawo mata, me balaraben ya mutu ya bari, da za a tsaya wani rabe-raben gado. Maryam kuwa da kanta ta tafi tasha, ya bayar da saƙo zuwa gida, a kan lallai a cewa yayansu ya zo, akwai matsala. Ko abinci ba a basu, maryam ita ta din ga cefane tana ciyar su. Yayan su mariya ya dira a garin, Iya sai da ta yi mamakin ganinsa, maryam ta ja shi, ta ce masa akwai matsala cigaba da zaman mariya a gidan nan, tana kallon irin zaman da mariya take yi a gidan, nan ta kwashe komai ta gaya masa. Abun ba ƙaramin ɓata masa rai yayi ba, wani irin tausayin mariya ya kama shi, karon farko da ya ji zai goyi bayan ƙanwarsa, dan haka ya yanke cewa kawai zasu ɗauki mariya da ummi su tafi. Dan haka ya je ya samu iya ya ce mata, washegari da safe zasu yi sammako su tafi Maiduguri, yaso su zauna su cigaba da gaisuwa, tayi takaba a ɗakin mijinta, amma wasu dalilai ya sanya sun yanke shawarar su tafi da ita gida kawai. Iya ta ce "Shikenan babu laifi" Mariya ta wani fannin ta ji daɗi zasu koma gida, wani ɓangaren wata irin kewar ɗakinta da mai ɗakik wato baban ummi, ta sake mamaye mata zuciya, har take jin anya ba za ta ce a bar ta a ɗakin nan ba, za ta cigaba da haƙuri da ita, kawai dan ya din ga gurbin da bashir yake dabdala. A daren Maryam ta taimaka mata, ta harhaɗa kayanta, abun da zasu buƙata, Maryam ta ce daga baya azo a sayar da sauran kayanta, dan ba zasu iya dakon kaya zuwa Maiduguri ba. Da sassafe maryam ta yi wa ummi wanka, suka yi wanka suka karya, ummi tana murna zasu tafi su bar gidan nan, tana fatan Allah ya sa idan sun je can babu yara masu tsokanar ta, ko dukanta. Sun fito maryam na ce mata, ta yi sallama da mutanen gidan, ta nemi afuwarsu, Iya na tsaye tana kallon su. Iya ya ce "Ummi zo mana mu yi sallama". Saroro ummi tayi tana kallon iya, ta ɗaga kai ta kalli mariya, mariya ta ce "Je ki Iya na kira" Ummi ta tafi sannu a hankali, ta ƙarasa gaban iya. Caraf iya ta sanya hannu ta riƙe hannun ummi, sannan ta kalli mariya ta ce "To, Allah ya raka taki gona, ummi dai ba da ita ki ka zo ba, kin san wannan, dan haka a sauka lafiya" Mariya tayi turus tana kallon iya, dan ganin abun take kamar almara. Maryam ta ce "Ban gane ba, yarinyar da ki ka ce ba taku ba ce ba" "Ɓacin rai ne ya sanya ni faɗar hakan, ba zan bayar da ita aje ayi mata gurguwar tarbiyya ba, ta tashi tana sa'insa da manya ba, dan haka ni zan riƙe ummi, ita kaɗai ya haifa, na rasa ɗa na, ina buƙatar ganin jinin sa a gabana". Cikin kuka mariya ta ce "Dan martabar Allah kar ki yi mini haka iya, ba zan iya jure zama babu ummi a kusa da ni ba, idan ma tafiyar ce na fasa, dan Allah ki bani ƴa ta". "A a, a kan me zan hana ki tafiya, haifarki na yi, na rasa ɗa na balle wata ke, Allah ya raka taki gona" Ƙoƙarin ƙwacewa ummi ta fara yi, tana kiran sunan mama. "Nutsu dan ubanki" Iya tayi mata tsawa. Yayansu mariya ya shigo, yana cewa su fito kar su yi rana, amma ya tarar da sabuwar dambarwa. Juyin duniya, Iya ta ce ba zata bayar da ummi ba. Mariya ta zube a kan gwiwoyinta, tana gursheƙen kuka, a kan iya ta bata ƴar ta, ta din ga cewa mutanen da suka taru, su saka baki iya ta bata ƴar ta, amma matar nan mirsisi taƙi. Ummi na kuka mariya na kuka, yayan su ya hasala ya kalli mariya ya ce "Ke tashi mu tafi, in dai ƴa ce su cinye, tashi mu tafi" "Yaya ka taimake ni, ba zan iya rayuwa babu ummi ba, dan Allah kar a rabani da ƴa ta, dan girman Allah ku yi mini rai, da wanne zan ji, na rasa mijina ƴar ma a ƙwace mini? Dan Allah ku bani ummina" "Sai dai kiyi kukan jini kuwa" A fusace ya daka wa mariya tsawa, ya ce ta wuce su tafi. Iya tayi tsaki ta ce "Aikin banza, ban da rashin tarbiyya, wai a kan ƴar fari take wannan abun" Idris ya shigo, Iya ta ce "Kai kuma mun yi magana ka ɓata mini lokaci, ɗauke ta ka tafi da ita in da na ce maka" Ya ƙarasa babu walwala, zai danƙi hannun ummi, ummi ya rirriƙe Iya, tana wani irin kuka, dan a rayuwarta, ta tsani ko haɗa hanya su yi da idris, ta ƙarfin tsiya ya danƙi ummi, tana kuka tana kiran mama, mariya ta bi bayansu da gudu tana kiran "Ka zo ka bani ƴa ta, ku bani ƴa ta ba ƙaunar ta ku ke yi ba, ku bani ƴa ta. Yaya maryam ki karɓo mini ƴa ta, ke shaida ce ba son ummi suke yi ba" Cikin tausaya maryam ta ce "Zaki kashe kanki ne? In dai ummi ce Allah zai kula miki da ita" shiru ta yi tana kallon maryam, ana gobe bashir zai tafi yake cewa Allah ga ƴa ta da mata ta Allah ka kula mini da su. "Wuce mu tafi, su je su cinye ta, kema kina da masu sonki" auwwalu ne ya bi bayansu da warin takalmin mariya, dan takalmi ɗaya ne a ƙafarta, hawaye ne kawai yake zuba daga idonta, can ƙarshen hanya ta hango ummi tana ɗaga mata hannu tana kiran mama cikin hawaye! Iya ta ce "Ba dai ke tsagera ba, daga ke har yayar taki dai-dai nake da ku, ummi ce dai tana hannuna, ba wani uban gado da za a raba, a baki ku cinye, gayyar tsiya arna a idi". *Page ɗin nan sadaukarwa ne, ga duk matar da ta rasa mijinta ko aurenta, kuma aka zo aka rabata da ƴaƴanta, we know is difficult to endure, ku yi haƙuri, ku yi haƙuri, ku yi haƙuri 🙏 Allah ya shiga lamarinku, ya kula muku da yaranku* Ayshercool 08081012143        *CUTARWA!* Watpad ayshercool7724 Arewabooks ayshercool7724 YouTube https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels What's app 08081012143 BRIGHT PENS (FREE BATCH) *BRIGHT PENS...* _suna mara ba da masu buƙatar a tallata musu kasuwancinsu, masu siyar da turarruka, kayan sawa, magani komai da komai, cikin sauƙi za a tallata musu a cikin duka littafan guda uku🤙🏼 *CUTARWA, MUNAFUKIN MIJI, YI WA KAI*_ Tsari👯🏻‍♀️ Duk page ɗaya 200 Duka littafin kuma 600 Shafi biyar a littafi ɗaya 1000 A littafai uku kuma 3000 Domin ƙarfin bayani sai a yi wa wannan number magana 08164069385🤙🏼👯🏻‍♀️🫶🫶🏼 P5 Har suka je tasha, jan ƙafa kawai mariya take yi, dan bata gane komai, hankalinta yana kan ummi, wace irin rayuwa ummi za ta yi a wannan gidan? Tana nan ma a ya aka cika, balle yanzu da babu idonta, kuma ya zamana ba ayi rabuwar arziki ba. "Allah ka kula mini da ƴa ta, Allah kar ka sanya ƴa ta ta lalace, Ubangiji Allah ka duba mini ita, ka tsare mini ita, Allah kai ka san dalilin da ya sanya, ka karɓi mahaifinta ka rabani da ita, Allah ka kula mini da ita. Haka ta din ga wannan addu'ar, jin abubuwan take tamkar a cikin nannauyan bacci, da take fatan ta farka. Har suka shiga mota suka kama hanya, duk wata nasiha da maryam ke yi mata, ba ji take ba, balle ta fahimta. Mariya ji take tamkar ta sauka daga cikin motar nan, ta koma ta rayu da ummi, ta san ummi wahala kawai za ta sha, dan iya ba ƙaunarta take yi ba. Tunawa da tayi da cin zarafin da aka yi wa ummi, ya sake karya mata gwiwa, ta sake fashewa da kuka mai sauti. "Idan ba zaki rufe mana baki ba, a tsaya ki sauka ki koma, ki je duk uban da za su yi miki, su yi miki, sai ka ce a kanki aka fara haihuwa, duk cin zarafin da suka yi miki bai isheki ba, ba dai ƴa ba ce su je su cinye ta, ai ta su ce da ma, dangin uba su ke da ɗa" tun da ya fara yi mata masifar ƴan cikin motar suka yi tsit, sai da ya gama ake bashi haƙuri. Maryam ta san abun da mariya ke ji, dan haka ta rungume ta tana rarrashinta, haka tana ji tana gani ta bar garin da duka goma da ashirin, ga rashin miji ga rashin ƴa. Ummi kuwa sai can daf da magariba aka saka yara suka rakata gida, dan can gidan wata ƴar uwarta ta sanya aka kai ta. Ta ci kuka ta ƙoshi, sai ajiyar zuciya take yi, ana zuwa gidan da sauri ta shiga ta nufi ƙofar ɗakinsu, sai dai ta tarar da shi da ƙaton kwaɗon da su mariya suka rufe ɗakin da shi. Ta nemi wuri ta zauna a ƙofar ɗakin, ta cigaba da rera kuka. Babu wanda ya saurareta, balle ya kula da ita ya rarrasheta. Sa'adatu ce tayi sallama, ta kawo wa iya tuwon dare. Ta ajiye mata suka taɓa hira, ta tashi fito, tana daf da shiga sashinta, ta ji ana bin ta a baya, ta tsaya ta waiwayo taga ummi. "Ke, lafiya ki ke bina?" "Dan Allah ina mama? Haryanzu ba ta dawo ba, ta buɗe mana ɗaki in yi salla, sanyi nake ji" Sa'adatu ta yi shiru tana kallon ummi, sam ba ta ga dalilin da zai sanya iya raba mariya da ƴar ta ba, ta san iya ba iya riƙe ta zata yi ba, saboda tsabar mugunta da rashin imani. "Ummi babarki ba zata dawo ba, ki tafi wurin iya ki je ki kwanta, gari da sanyi" "Ita ma maman ta mutu? Ba zata dawo ba kamar baba?" "Ba mutuwa tayi ba, nan kusa dai ba zata dawo ba, ki yi addu'a Allah ya sanya ta dawo ta tafi da ke, can in da aka kai ki kin ci abinci?" Ummi ta girgiza kai ta ce "Mama ta hana ni cin abinci a gidan mutane" Sa'adatu ta ce "Kenan wuni ki ka yi baki ci abinci ba, tafi na kai wa iya abinci, ki je ta zuba miki" ummi ta ce "To" Ta juya jikinta a sanyaye, ta koma sashinsu, ta zauna a ƙofar ɗakin su, tana kallon ƙofar ɗakin Iya, kuka take a hankali tana jin kewar mahaifiyarta, da yanzu mama ta yi mata wanka, ta shafa mata mai ta saka mata kayan sanyi. Tana nan zaune a ƙofar ɗakin, sanyi sai ratsata yake yi, ga ƙanan ƙwari na bin ta. Gani tayi an hasketa da fitila, ta saurin rintse idanuwanta, saboda hasken fitilar, bai ɗauke fitilar ba, har ya ƙaraso kanta ya tsaya. "Me ki ke yi a nan?" Jin muryarsa ya sanya ta tashi a razane ta ja da baya jikinta na rawa, dan ita duk wani namiji tsoro yake bata. "Me ki ke yi a nan?" "Mama nake jira ta dawo" "Kuma sai ki zauna a nan ga sanyi, ki tafi ɗakin iya ki jirata mana" Ta girgiza kai ta ce "Zan zauna a nan" "Wuce ki tafi dalla!" Yayi maganar cikin tsawa. Da sauri ta nufi ɗakin Iya, ya bi bayanta. Sai da iya ta ga ummi, sannan ta tuna ta ce da yamma a dawo da ita. Iya ta ce "Ke daga ina?" "A ƙofar ɗakinsu na ganta, wai mamanta take jira, a wannan sanyin, maimakon ta shigo nan ta jira ta". Iya ta ce "Ka ji munafuka, an tsotso a nono, amma a gaban idonki ai uwar taki ta tafi barki ko?". Hashim ya ce "Kamar yaya ina ta tafi?" Iya ta ce "Mhmm, ai mariya daga ita har ƴan uwanta ba su da mutunci, zuwa suka yi za su tafi da ita, shi ne zasu haɗa da ummi, na ce ba zai yiwu ba, in rasa ɗa na sannan ita ma su tafi da ita ba, na ƙwace ta" Yayi shiru yana kallon iya ya ce "Amma iya meyasa? Kin san bata shaƙu da kowa ba sai babarta, ga mahaifinta Allah ya karɓe shi". "Ba ka san rayuwa ba magajin malam, mariya sam ba ta da tarbiyya, ba zan rasa ɗa na kuma ta tafi da ƴar sa ba, ta koya mata mugun hali. Tashi ki miƙo mini kwanon can, ki zo in zuba miki tuwo". Ummi ta kawo kwano, iya ta zuba nata tuwon masara miyar karkashi, sai dai ummi ba ta son miyar karkashi. Ta jagwalgwala tuwon, ta cinye samansa, ta bar guntun cikin tsoro ta ce "Na ƙoshi". Iya ta kalleta ta, ta kalli kwanon tuwon ta ce "Ni zan cinye miki sauran da ki ka bari?" Ummi ta girgiza kai. "To maza cinye shi" duk ƙoƙarin da ummi tayi, ta kasa cin abincin nan. Iya ta din ga zaginta, ta ce ta rufe ta ajiye, zata yi maganin wannan sangartar da aka yi mata. Mariya ƴan uwa na ta tausaya mata abun da ya faru, da alhinin rashin mijinta ga muguntar uwar miji, da kuma rabata da ƴar ta. Dan sai da mahaifinsu ya so yayi faɗa, yayanta yayi masa bayanin abubuwan da suka faru, da ƙyar ya fahimta, duk da haka dan mariya tana cikin yaran da yake matuƙar so ne, tana da matuƙar haƙuri da biyayya. Ya ce in dai ƴa ce, tun da sun ƙwace ta, su ƙarata suma ba zasu sake bibiyar a basu ba, idan sun ga dama su din ga kawota, idan ba su ga dama ba su je su ƙarata, dan babban abun da ya baƙanta masa rai, bai wuce yadda aka ce Iya tayi iƙirarin mariya ce ta kashe mata ɗa ba, karo na farko a kan mariya, aka goyi bayan mace ko dan ba ƙara ta kawo ba, zahiri suka gani, dan maryam ta labarta musu komai, har da yadda ake muzanta ummi, da cewar da iya tayi, wataƙila ɗan ta ma baya haihuwa, saboda su kaf danginsu babu kalar ƴar, daga baya kuma ta ce ita zata riƙe ta. "Ai ban san mutanen kawai bane na basu ƴa ta, dattakun yaron da nutsuwarsa ce ta sanya haka, ina da yaƙinin zuriyata babu lalatacce, kar wanda ya kuma bi ta kan yarinyar, ku ƙyale su da ita, ke kuma idan kin gama takaba, Allah ya kawo miki miji nagari". A ɓangaren mariya ba ta ji daɗin wannan goyon baya da aka yi mata ba, mussaman yadda ƴan uwa suka goya masa baya, a kan yanke alƙarsu da in da ummi take, ita a ganinta hakan ba masalaha ba ce, ita da ummi meye nasu a ciki. Babu bakin magana, haka tayi shiru sai bin su da ido, ta ƙare ta shige uwar ɗaka, ta durƙushe a kan gwiwoyinta, ta din ga rusa kuka, ita ma meya rage mata na bashir da za ta kalla ta ji daɗi ban da ummin? Ta din ga kuka, zuciyarta na wani irin zafi, ji take kamar duniya babu wani abu da ya tage mata da zai sanyata farinciki, mahaifiyarsu ta rasu, yayyenta duk sun yi aure, sai ƙananan ƙannenta da matar babansu, dan ma mutuniyar kirki ce. Washegari da asuba, iya ta idar da sallar asuba, ummi na ƙasa a duƙunƙune a cikin hijjabinta a ƙasa, ko zani ba a shimfiɗa mata ba, ba wanda ya kai ta tayi fitsrai, ta saba sai mariya ta kai ta tayi fitsari, kan ta kwanta, dan haka ta yi wa iya fitsarin kwance. Kamar zata daki sa'anta, haka iya ta taƙarƙare ta ɗalawa ummi duka, a gigice ta tashi tana sosa wurin, saboda zafi. "Dan ubanki fitsarin kwance ki ka yi mini saboda sangarta?" Dubawa ummi tayi ta ga fitsarin tayi, ta yi shiru ta kasa magana, sai hawaye. "Au kuka ma ki ke yi mini, saboda sangarta da iskanci, zan yi maganinki, fita ki ɗebo ruwa a randa ki zo ki zuba" Da sauran duhun asuba, dan haka ummi tsoro take ji, ta fito waje ta tsaya tana kuka. "Ba zaki wuce ba, sai na zo" ta jiyo muryar iya. Cikin sauri ta je ta ɗebo ruwa, garin sauri ta koma ɗakin, ta faɗi sassanyar ruwan randar nan ya sheƙe mata a jiki. A gigice ta yi wata irin ajiyar zuciya, tana kyarma. Ta tashi da guntun ruwan a moɗa, ta shiga ta zuba a wurin, kamar yadda iya tayi mata umarni, ta dawo ɗakin ta tsaya. Iya ta kalleta ta ce "Munafuka, shi ne ki ka zuba ruwan a jikinki, sai ki cire kayan ki saka wasu, ga tsummokaranki can". Cikin rashin wayo, ta kwance kayan, ta saka uniform ɗin ta, dan ta san ranar monday ce, ta tattara kayan fitsarin, ta haɗa su a cikin masu kyan ta ɗaure, dan kuwa mama ta hanata zubar da kaya ko ina. Ta juya ta kalli gabas tayi salla, ba tare da tayi alwala ba, dan da ruwan ɗumi take alwala da mama tana nan, dan haka ta zata idan ba ruwan ɗumi, ba sai ka yi alwala ba. Gari yayi haske, ta je gaban murhu, ta saka hannunta ta dangwalo toka, ta cuccuɗa bakinta, ta kuskure ta koma ɗakin iya, tana jiran iya ta bata abinci. Aka kawo wa Iyan kunu mai zafi, amma ta kalli ummi, ya ce ta ɗauki tuwon jiya ya cinye, dan ba za a zubar ba. Miyar karkashin ce ba ta so, dan haka ta sake jagwalgwalawa, ta ajiye ta fito tsakar gida, tayi ta kallon ƙofar ɗakin su, ta ƙarasa ƙofar ɗakin tana ƙwanƙwasawa, wai ko mama zata buɗe, sai da ta gaji, kawai ta fita, ta kama hanyar makaranta, lokacin kusan tara da kwata, tana tafe iska na kaɗata, ga azabar sanyi jikinta babu rigar sanyi, sannan babu mai a jikinta, dan haka tayi busu-busu da ita. "Ke daga ina?" Malamar da take ajin su ta tambaye ta. "Gida" ta faɗa a taƙaice. "Yanzu ne lokacin zuwa makaranta?" Tuni hawaye ya cika wa ummi ido, saboda tana tsoron duka ta ce "Mama ce bata nan, ba ta dawo ba" "To kuma gidanku babu wanda zai ce ki taho makaranta da wuri? Kalli jikinki fa ko mai baki shafa ba, kamar wadda zata aikatau ba makaranta ba" ƴan ajin suka kwashe da dariya. "Silent" malamar ta tsawatar tana kallon ƙafar ummi, da kamar an ciro ta daga haƙa rami, ummi kuwa gwanar kuka, ta kama ƙasan farin hijjabinta, tana goge hawaye. "Wuce ki je ki zauna" Ta nufi wurin zamanta, can wuri ɗaya, ta cigaba da sheshsheƙar kuka, tana jin muryar wani yaro, cikin murya ƙasa² yana cewa "Baƙar tukunya, yau an shafeta da toka" Iya sam bata san makaranta ummi ta tafi ba, kawai sai nemanta ta yi ta rasa, hankalinta ya tashi, ta fito tana zagawa tana nemanta. Ummi kuwa da ƙyar ta koma gida, saboda azabar yunwa, har wani jiri take yi, tana ta Addu'a Allah ya sa tana zuwa ga mama, sai dai kash, tsakar gidan nan fayau, ko shara bai gani ba, ta kalli wurin murhu da maman ke ɗora girki, shi ma babu komai a wurin, ta kalli ƙofar ɗakin su, ɗakin dai a rufe. Ɗakin iya ta shiga, ta nemi wuri ta kwanta, ta fara kuka tana share hawaye, tana kiran sunan mama da baba. Bacci ya ɗauke ta, sai dai hayaniyar iya ta tashe ta, "Dan ubanki ina ki ka je, ki ka tayar mini da hankali, nake ta yawon nemanki, lungu-lungu kamar akuya. "Makaranta na je" "Uwar makarantar, kin gaya mini zaki je?" Ummi ta girgiza kai. "Kawai dan ki tayar mini da hankali, to ubanki ma bai ɗaga mini hankali ba, balle ke" ummi dai tayi shiru ba ta ce komai ba. Iya ta gama zaginta tsaf, sannan ta bata abincin rana, sai dai ba dan zai isheta ba, haka ta ci. Da yamma yarinyar da take tafiya da ita makarantar allo, na'ima, ta zo tafiya da ita, Naima ƴar ɗakin mariya ce, dan tana son ummi sosai, ita take tafiya da ita makarantar allo, kuma ta ji labarin mariya ta tafi, iya ta ƙwace ummi. Ta tarar da ummi a zaune tayi shiru, idonta duk hawaye. "Iya na zo tafiya da ummi makaranta" "Gata nan, sai kun dawo" iya tayi maganar tana nuna ummi a wulaƙance. Naima ta tambayi iya kayan ummi, ta gaya mata in da suke, ta ga jiƙaƙƙun kaya a ciki. Ta ce "Ummi, na ji kayan ki a jiƙe?" "Fitsarin kwance na yi ban sani ba" "To ki daina haɗa su da kayanki masu kyau, idan mun dawo daga makaranta, zan wanke musu" Ummi ta saka mata kuka ta ce "Yaushe mama zata dawo?" "Ki yi haƙuri, nima ban sani ba, amma za ta dawo" ta shirya ummi ta sakata a gaba suka tafi makaranta, tausayin ummi ya kama ta. Kwana ɗaya kawai, mariya ji take yi tamkar ta taka da ƙafa, ta koma gagarawa, ta ɗaukko ƴar ta, duk sallar da tayi, bata iya addu'ar komai, sai roƙon Allah ya kula mata da ummi, Allah ya dawo mata da umminta. A kwana a tashi mariya ta gama takaba, sai da tun bai fi watanni biyu da daowarta gida ba, ta fuskanci tana ɗauke da juna biyu, kuma ta ja bakinta ta yi shiru, ta din ga rashin lafiya, ba cin abinci, duk ta rame ta fita daga hayyacinta, maryam ta rakata asibiti, sai a lokacin da likita yake yi mata tambayoyi ta tabbatar musu da tana da ciki. Da suka koma gida, aka din ga yi mata faɗa, saboda ya zama dole a sanar da dangin su bashir maganar juna biyun nan. Watanni huɗu da barin ummi a hannun iya, Ummi ta gane shayi ruwa ne, dan duk da ba girma ne da ita ba, amma tafi samun sauƙi da sassauci, a lokacin da mariya tana nan. Gashi son makaranta ya shiga ranta sosai da sosai, idan ta yi wa iya laifi, sai iya ta hanata abinci, da ƙyar take iya zuwa makaranta, sai dai da ka ganta a cikin uniform ɗin nan, ka san babu kulawa, da babu wanda ya kai ummi tsafta a makarantar, amma wataran idan ka ganta, kamar ta shekara babu wanka, a wannan shekarun, ita take wanka da kanta, idan gari babu sanyi sosai tayi wanka da ruwan buta, idan da sanyi taƙi yi, dan wataran ruwan kawai take zubawa a jikinta. Man shafawa sai iya ta ga dama zata bata ta shafa, shi ma ba iya shafawar tayi ba, iya ta daina bata, wai tana yi mata ɓarnar mai. Wanki kuwa, sai idan na'ima za ta yi nata, sannan ya ta haɗa da na ummin, tayi ta goge mata, idan ba haka ba kuwa, sai dai tayi ta yawo cikin dauɗa. A wata ukun nan, ummi ta koma kamar rainon mahaukaciya, wannan uban gashin babu mai kula mata da shi, ga cin zali da yara suka cigaba da yi mata, tun ummi na saka ran dawowar mama, har ta haƙura. Saboda sabo, da sassafe idan ta tashi, sai ta ɗauki tsintsiya ta share sashin, ko da kuwa ba zai fita ba, saboda haka mama take yi, ta wanke bakinta da gawayi, ta jiƙa jikinta da ruwa buta ɗaya. Idan ba makaranta ta tafi ba, mutanen gidan wannan ya ja ya aika, wancan ya ja ya aika, kamar baiwa, masu aiken nata, wani lokacin idan sun yi abinci su bata, domin kuwa bata ƙoshi da wanda iya take bata. Duk ranar da tayi kuskuren yi wa iya fitsarin kwance kuwa, ko wani laifin, sai ta kira idris, ta bashi bulala, ta tuɓe ummi, ta ce ya zane mata ita. Ga shi ya cigaba da kawo mata farmaki, gashi ta yi girman da ba zai yiwu ya ɗauke ta ba, sai ya tsiro da salon aike, ya ce idan ta sayo ta kai masa ɗakin su. Yau idris ya kasa jurewa, ya aiketa sayen omo, ta dawo ta tsaya tana raɓe-raɓe, cikin ikon Allah sai ga naima, suka yi kiciɓis da ummi a soro ta ce "Ummi, tun ɗazu nake jiranki, ina kallon yadda malam babba ya zane ki, saboda makara, amma shi ne baki taho ba". "Yaya idris ne ya aike ni sayen omo, ya ce na kai masa ɗakin su". "Ɗakin su kuma? Ina laifin ya ce ki kai wa babarsa, kuma ina sauran yaran gidan? To wallahi ko da wasa, kar ki kuskura wani a mazan gidan nan, ya aike ki ya ce ki kai masa ɗakinsa, ko wani wuri da mutane ko da kuwa zasu dake ki" ta waiwaya ta ga awwalu zai shiga sashin mazan ta karɓi omon ta ce "Kai auwwalu, ka kai wa idiris aiken da ya yi wa ummi, wuce muje ke kuma" Suka tafi makaranta, ta saya wa ummi awara a hanya, da suka je ta zaunar da ita a makaranta ta bata ta ci. Suna tafe a hanya naima na sake jaddadawa ummi, kar ta kuskura wani ya aiketa, ya ce ta kai masa ɗakinsa a samarin gidan. Ta raka ummi har cikin gidan, tana shirin tafiya, Idris ya shigo yana yi wa naima bala'i. "Wacece ke a wurinta, da har zan aiketa ki hana ta kai mini aike?" Naima ta ce "kamar yaya, makaranta zamu tafi mun makara" "Dole tare zaku tafi makarantar? Har in aike ta ki hanata kawo mini saƙona?" "Amma dai da alama baka da gaskiya, ba dai an kai maka aiken ba, ya zaka din ga aiken yarinya ka ce ta kai maka ɗakin ka" nan da nan bala'i ya kaure abunka da gidan gandu, nan da nan aka taru, ya din ga kurarin zai yi mata dukan tsiya. Iya ta hau naima da masifa, har da cewa kar ta sake shigowa, tun da sharri za ta yi wa idris. Ita duk wannan abun ba shi ne damuwar ta ba, tausayin ummi take ji, ta kalli yadda ummin ta rakuɓe tana kuka. Naima ta ce "Ba abun da zai sake shigo da ni in sha Allah, amma dai wallahi idris ka canza hali, mutumin banza kawai" iya ce ta hana shi, da cewa yayi sai ya zane naima. Iya ta ce kowa ya watse, har ya nufi hanyar fita, ya dawo ya shaƙo ummi tare da luƙa mata wata irin ashar. Ƙara tayi tana kakari. "Dan ubanki, daga yau idan na sake aikenki, ki ka biya wani wurin, ko kuma na sake ganinki da wannan yarinyar, sai na kashe ki" ya jefar da ita a wurin, ta riƙe wuya tana tari, wani irin yawu mai kauri na wahala, na zubowa daga bakinta, ta cire hijjabin makarantar ta tana gogewa, gashin kanta kuwa, kalba biyu ce tafi wata, ita ma naima ce tayi mata. Mariya kuwa sallar magariba ake yi, kawai suka ga ta fito daga ɗaki, tana ƙoƙarin fita, mama wadda take matar babansu, ta riƙe ta, ta ce "Mariya lafiya ina zaki?" "Mama kukan ummi nake ji, kamar tana ƙofar gida fa" "Mariya ummi na jigawa, kina Maiduguri ta ina ki ka ji kukan nata?" "Iya wai ba kya ji ne? Ni kukan ummi nake ji" Mama ta ce "Iya kuma, nice fa mariya" Mariya ta yi ƙuri da ido, tana kallon mama, sai yanzu ma ta dawo hayyacinta, gaba ɗaya ta kasa gane menene yake faruwa, bacci take ko idonta biyu, ita dai kamar kukan ummi kunnunwata suke jiye mata. Ayshercool 08081012143                            *CUTARWA*              BRIGHT PENS             (FREE BATCH) Shiru mariya ta yi, tana bin mama da kallo, jiki a sanyaye ta ce "Ki yi haƙuri, na zata gaske ne, magungunan da na sha ne, bacci ya ɗauke ni na ga ummi" Mama ta ce "Mariya ki sassauta wa kanki a kan yarinyar nan, kar ki je ki haukace a banza fa" Mariya ta amsa da "To" "Ki din ga yi mata addu'a, Allah zai tsare miki ita" gyaɗa mata kai kawai ta yi, ta koma ɗaki. Ummi kuwa ta ci kuka kamar babu gobe, saboda zafin shaƙar da ta sha. Iya ta ritsuta a ɗaki tana tambayarta, ko wani abun take gayawa na'ima, ummi cikin kuka ta din ga girgiza mata kai, tana tsoron kar ta dake ta. Har gari ya waye, tana jin wuyanta babu daɗi, ta yi wanka, ta sanya cukurkuɗaɗɗun uniform ɗin ta, dan ma an yi sa'a a wanke suke, dama na'ima da yamma ta ce zata yi musu guga, aka yi uwar watsi. Iya bata kulata ba, dan haka ta yi sharar tsakar gida, ta ɗau kofinta, ta je sashin sa'adatu, da niyyar a bata kunu, sai dai ta tarar ta gama rabawa yaranta, suna sha zasu tafi makaranta. Ta juyo da kofin a hannunta, tayi karo da magaji. "Baki tafi makarantar ba ne?" Ta jinjina masa kai. Ya kalli kofin hannunta, babu komai a ciki. "Kunun ma baki samu ba? Iya bata baki ba?" Ta jinjina masa kai. Ya karɓi kofin, ya shiga sashin su na maza, ya fito ya miƙa mata kunun cikin kofi. Har ƙasa ta tsuguna ta karɓa, ta zauna a kan wani kututture, ta kafa kai ta din ga sha, saboda uwar yunwar da take ji. Ta shanye ya karɓi kofin, ya bata naira ashirin, ta karɓa ta ce "An gode" "Kiyi sauri ki tafi makaranta, kar su dake ki" ta ce "To" Ta kamar hanya ta tafi, jin ta a ƙoshe da kunu ya sanya ta tafiya cikin nishaɗi. Sai dai yau ma ta makara, a bakin gate discipline mistress ta fara zane ta, tare da ci mata mutunci saboda ƙazanta, jikinta bususu fuskarta duk busasshshen koko, ga sauran kwantsa a idonta. Ta tafi aji tana kuka, saboda zafin bulala. Ta je ta tarar ana yi musu darasi, ta buɗe jakarta da yanzu a baƙar leda take zuba su, duk sun zama shara da tarkace, fensirinta kuwa dama tsintar sa tayi, ya zama ɗan mitsitsi da ƙyar take iya riƙe shi ta yi rubutu. Head master ya shigo ajin, duk suka tashi suka gaishe shi, yayi musu umarnin su zauna. Ya dubi malamarsu ya ce "Malama, yara biyar zaki zaɓo mini masu ƙoƙari, zamu tafi da su gidan talabijin, za ayi wani shiri da su, a haska su" Malamar ta ce "Ok sir, yanzu kuwa" Ta tashi ta kira yara uku, ta huɗu ta kira sunan Salma Muhammad Bashir. Wani irin farinciki ya kama ummi, saboda  malamarsu ta zaɓeta a cikin wanda za a tafi da su gidan talabijin na jigawa, tana ta murna za ta ganta a talabijin, dan duk da rashin kulawar nan, ummi tana da matuƙar ƙoƙari, in dai aka yi darasi a gabanta, to ta ɗauke. "Ke!ke tsaya" headmaster ya dakatar da ita a tsakiyar aji. "Wannan kuma ina zata?" Malama ta ce "Sir, yarinyar na da ƙoƙari fa, ita ce take first position" "A hakan, wannan yarinyar da ya take karatun,? Ba ita ake kora ba ba ta biyan kuɗin PTA, da yaya take iya karatun" Ta ce "A haka, ita take ta ɗaya?" "Kai canza wata dan Allah, haba wannan tayi muni da yawa, wannan ko an saka mata camera ai ba za a ganeta ba, baƙi ƙirin da ita haka, ji uniform ɗin ta fa, tubarkallah ni wannan tayi baƙi samo wata mai ɗan kyan gani, ke koma ki zauna ba za a tafi da ke ba, ji kayan jikinta kamar ƴar ci rani" Tuntsirewa da dariya da yaran suka yi,hakan  ya bawa hawayen idonta ƙwarin gwiwar zubowa, ta tafi lungun aji ta zauna, tana share hawayen. Tana gani aka zaɓi wata daban, bayan malamar ta fita, suka ɗora da yi mata dariya da tsokanar ta, har da masu ja mata hijjabi, suna ƙazama ba ta wanka ba ta wanki, waƙar da aka saba yi mata a assembly idan an zo duban tsabta, har misali ake yi da ita, na ƙazamai. Ana tashi ta fita daga aji, ta nufi gida har da gudunta, dan kar ma ƴan ajinsu su taso, su tireta a hanya, ta ƙarasa tana ta numfarfashi. Sai da ta ɗan huta sannan ta shiga sashin su da sallama, muryar iya ta fara jiyo wa tana hayaniya, da muryar baba saminu, ba ta san dai faɗan me suke yi ba, ta kutsa kai ta shiga. Wan mahaifiyarta ta gani, a zaune suna ta jayayya da su iya. Hayaniyar da suke yi, ba ita ce ta dame ta ba, murnar ta Allah ya sa da mama suka dawo. Bai lura da ummi ba, sai da ta riƙe hannunsa, ya waiwayo ya kalleta ta ce "Ina maman take?" Yayi ƙuri da ido yana kallon ummi, sai ka ce ba ƴar mutane ba. Yadda mariya ke ƙalƙaleta, take kula da ita, amma ya ganta kamar an janyota daga ramin ƙasa. Ya ce "Baki gaishe ni ba" ta tsuguna ƙasa ta ce "Ina kwana" "Lafiya ƙalau, ya makarantar?" Ta ce "Lafiya lau, to ina maman take?" "Mama tana lafiya, ta ce; a gaishe ki" Ummi ta sake kallonsa ta ce "To zaka kai ni wurinta?" "Ke wuce ki je ki cire uniform, ki yi salla" Iya tayi mata tsawa. Yayi shiru ransa a matuƙar ɓace, bai taɓa tunanin ganin ummi a cikin wannan mummunan yanayin ba. Ta fito kanta babu ɗan kwali, gashin nan a cukurkuɗe, sai soshe-soshe take yi, saboda yadda ya addaba mata da ƙaiƙayi. Ya dubi iya ya ce "Shikenan, tun da kun ce cikin ba naku bane ba, baku san da shi ba, ni ba dan wani abun hannunku ya sanya muka zo muka sanar da akwai cikin ba, saboda a cika umarnin Ubangiji, amma tun da abun haka ne, Allah ya kyauta, mu mun ji mun gani, mun karɓa. Amma dan Allah ku bani ƴar ta in kai mata, mariya ta kasa zaune ta kasa tsaye, hankalinta yaƙi kwanciya, ku bata ƴar ta dan Allah" "Ba rashin ummi ne ya hanata nutsuwa ba, mugun abun ta ne yake koma mata kanta, hakkina da na ɗa na ba zai taɓa barinta ba, ya din ga bibiyar ta kenan" Ganin idan ya cigaba da zama, wannan jayayyar zata kai su ga maganar banza, ya sanya ya tashi tsam, ya ce "Shikenan babu laifi, Allah ya kyauta" Jin ya ce zai tafi, ya sanya ummi fitowa da gudu daga ɗaki, ta ce "Ba zaka tafi da ni, ka kai ni wurin maman ba?" Ya durƙusa ya shafa kanta ya ce "Ki yi haƙuri, in sha Allah nan gaba kaɗan, zaki koma wurin mamanki, Allah ya yi miki albarka" ya ciro kuɗi dubu biyar, ya bawa iya ya ce "Dan Allah a canza mata uniform, a saya mata wasu ƴan kayan buƙata" Ba kunya iya ta amshe, tana harare-harare. Ummi ta tsaya tabi bayansa da kallo har ya fice. Dukan da aka yi mata a kanta ne, ya sanya ta dawowa hayyacinta, ta firgita ta kalli Iya. "Duk wanda ya sake zuwa gidan nan, ki ka ce ya kai ki wurin uwarki, sai na saka idris ya zane miki jikinki, wato salon ace ba a kula da ke, saboda ƙwarewa a munafunci kin tsotsa a nono ko?" Tayi shiru ta sunkuyar da kanta ƙasa. "Munafuka, ga muni ga kinibibi, tashi ki wanke kwanukan nan na safe" sumi-sumi ta nufi wurin tara kwanukan wanke wanke, ta haɗa ta fara wankewa. *** Bayan sallar magariba, yaya garba ya je ya samu mahaifinsu ya sanar da shi cewa iya ta ce ba su san da ciki ba, dan haka a nemi ubansa. Malam yayi shiru, lamarin ya girmame shi ya ce "Haka suka ce?" "Wallahi, matar nan ba ta da mutunci ba ta da imani ko kaɗan, ba ka ga Yarinyar nan a halin da na baro bata ba, kamar ƴar jari bola saboda azabar datti da ƙazanta" "Ƙyalesu, yarinya kullum muna yi mata addu'a, in sha Allah babu wanda zai sake bi ta kansu, ita kuma Allah ya raba ta da ciki lafiya" Ya amsa masa da "Amin" *** Na'ima kuwa ummi na ranta, amma babarta ta ce mata ba ita ba ummi, dan kakarta ba mutunci ne da ita ba, kar ta yi mata wani sharrin. Sai dai ta kan ƙulle abinci wasu lokutan, ta tafi da shi makaranta ta bawa ummi. Yanzu babu mai yi wa ummi wanki balle guga, dan haka dauɗa kamar ka kankarota a jikinta. Ummi na iya ƙoƙarin ta wurin kaucewa haɗuwa da idiris, ga bala'in tsoronsa da take ji, saboda dukan da yake yi mata idan tayi laifi babu tausayi babu imani. Allah ya taimake ta, wasu lokutan magaji na taka masa burki a kan wasu abubuwan. Tsabar rashin gyara, ya sanya kwarkwata cika wa ummi gashi, kayan ta duk suka cukurkuɗe suka yi mata kaɗan, tana zaune har sakkowa kwarkwata suke yi daga kanta, suna bin ta, sai dai ta ɓuya tayi ta kashewa, ba ta son a gani. Ga wasu irin manyan ƙuraje da suka din ga fitowa a cikin gashin kan nata, suna ɗurar ruwa, suka ƙara bawa kwarkwatar nan damar hayayyafa babu ji babu gani. Banda zarnin fitsari da warin datti, babu abun da take yi, dan kuwa da kanta take yi wa kanta wankin kayanta, wando sai ya fi kwana uku a jikinta, ba ruwan iya balle ta ce cire ki wanke. Sa'adatu ce babar auwwalu, ta fara lura da wannan ƙurajen na kan ummi, ta kamata ta buɗe kan, ta ga ƙazantar da take cikin gashin. Ta nuna wa iya, Iya ta yamutse fuska ta ce "Taɓ gaskiya ba zan iya taɓa wannan kan ba, to gashi ne ba kaɗan ba, gaba ɗaya ba irin namu ba, kalar na mutanen ƙetare, shiyasa nake cewa anya ma kuwa tamun ce, duk zuriyar mu, babu irin wannan gashin, yanzu meye abun yi kar kan ya ruɓe ace ni ce ina kallonta, na bari ya ruɓe ji yadda wani mugun ruwa yake tsatstsafowa da ƙwayayen kwarkwata a ciki". "Aikuwa sai dai a aske kan nan, dan ban ga yadda za ayi maganin abun nan ba" Cikin ƙyanƙyami, sa'adatu ta sauke wa ummi gashin nan tsaf, ta koma sai ka ce namiji, ga hudar kunnenta ma, tana ruwa saboda tsufan ɗan kunne a kunnenta, ba a taɓa cirewa ba. Iya ta saka aka haɗa kanwa da gishiri, da omo aka wanke kan nan, ummi ta din ga wani irin masifaffen kuka, saboda azabar raɗaɗi, da bal'in zafi haka nan da ruwan sanyi aka tuɓe ta, aka wanketa a tsakar gidan, iya har tana cewa wannan baƙar fatar ba da dutsen goge faso za a wanketa ba kuwa?. Wata irin annakiyar dauɗa ta din ga zuba daga jikin yarinyar. Yara suka cika sashin danƙam suna kallon ummi, da tana ta ƙoƙarin rufe jikinta, amma azabar wahala da zafi ya sanya ta manta da tsiraicinta. Ummi na ji na gani, aka ɗaure gashinta a leda kaya guda da shi aka zubar, iya ta ce a sakawa kan ummi fiya-fiya, idan ba haka ba, sauran ƙwan zai ƙyanƙyashe kansa. Ba tare da tunanin wane hali zata shiga ba, suka shafe ƙwallon kan da suka saukewa sumarta da fiya-fiya, hakan ya sa ta din ga tari da atishawa, gaba ɗaya kanta ya juye, ta din ga jiri, kan dare zazzaɓi ya rufe ta da ciwon kai. Ba wanda ya kula ya saya mata magani, haka ta kwana tana rawar sanyi, da ta yinƙura ta tashi, sai ta tafi luuu zata faɗi. Da safe gwaggo ta bata, koko da ƙosai, sai dai ta kasa ci, ta cigaba da kwanciya tana burgima a ƙasa, kanta yana ciwo, ga tari da take ta faman yi. Cikin barccin wahala, ummi ta ji wani ƙamshin turare mai daɗi, ta ji magana sama-sama kamar muryar babanta. Da sauri ta buɗe ido, ta yi ƙuri da ido tana kallonsa, ga iya a gefe suna magana da shi. Yayi murmushi ya ce "Uwata ta kaina, kin tashi? Ƙaraso mu gaisa" sai yanzu ta lura ba baba bane ba, mutumin nan ne mai kama da shi. Tasowa ta yi da sauri, sai dai ta faɗi, saboda jirin da take ji. Da sauri ya tashi, ya ce "Iya ba ta da lafiya ne?" Iya ta taɓe baki, mussaman jin ya kirata da uwassa ta kansa ta ce "Eh zazzaɓi take". "Subhanallah, kuma ba a kaita asibiti ba?" Ya zaunar da ummi, ya sinsuna kanta ya ce "Ya na ji kamar kina warin fiya-fiya? Ya cire hular kanta, sai ga kai sol ba gashi, ga dagwalon gyambo a kan, ciwon duk yayi baƙi saboda fiya-fiya. A razane ya ce "Meye wannan? Iya meya sameta a kanta?" "Kwarkwata ce, da wasu ƙuraje, shi ne aka aske kan aka shafa mata fiya-fiya" "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, iya wannan ai ganganci ne, ina laifin a kaita asibiti, wannan ƙaramar yarinyar a saka mata fiya-fiya a ka, ai shi ya sanya mata zazzaɓi". "To ban da kai yahaya, ana ta abun da za a ci, waye yake ta wani asibiti, wa zai bayar da kuɗin kai ta wani asibiti?" Miƙewa yayi ya ce "Wannan abun kunya da yawa yake" Cak ya saɓa ummi a kafaɗarsa, yayi waje da ita, iya ta biyo shi tana tambayar ina zai kai ta?. "Asibiti zan kai ta, idan ta mutu ba makawa ku ne ku ka kasheta" yayi waje da ita. A mota ya kwantar da ita, ya ja suka tafi. Sosai likitoci suka din ga faɗa, dan ma asibitin kuɗi ne, aka sake wanke kan ummi, da magunguna, aka saka mata ruwa saboda zazzaɓin da ya rufeta, take ta rawar sanyi. Ya fita ya sayo kayan marmari, da ta farfaɗo zazzaɓin ya sauka, ya din ga bata da kansa. "Kana kama da baba" ta faɗa a lokacin da zaƙin kankana ya ratsa kwanyarta, wanda rabon da ta sha har ta manta. Yayi mata murmushi ya ce "Ai nima baba ne" "Ai an ce baba ba zai dawo ba, ya mutu yana cikin kabari". "Haka ne mamana, kina yi masa addu'a ko?" Ta gyaɗa kai alamar eh. "Yanzu me ki ke son na saya miki?" "Littafi" ta bashi amsa. "Littafin makaranta?" Ta jinjina masa kai alamar eh. Ya ce "To shikenan, zan sai miki in sayo miki kifi ko nama, wanne zaki ci?" "Nama" ta faɗa tana murmushi. Yayi mata murmushi shi ma, ya ce "To bari su sallame mu, sai na saya miki mu tafi gida" Har ummi ta ɗan murmuro, ya saya mata tsire a hanya, da babbar robar youghurt, ya sai mata litattafai, da sabuwar jakar makaranta. Babban abun da ya burgeta da shi, shi ne yadda take ta ce masa ta gode, a yanayin tattaunawar da yayi da ita, ya san baƙar azaba kawai take sha, bai ga dalilin da ya sanya iya riƙe ummi ba, kuma shi ma idan ya ce zai tafi da ita can gidansa, faɗa za suyi da Fauziyya matarsa, dan ya san ba zata karɓi ummi ba. Gashi shi bai san a ina mahaifiyarta take a Maiduguri ba, dan lokacin da balarabe yayi aure, yana kudu karatu. A mota ya sanya ummi ta ci, har ta ƙoshi, wani irin daɗi take ji, yau ta ci kayan daɗi, wataran tana kallo ake kawo wa Iya, bata sammata. A ƙofar gidan yayi parking, ya buɗewa ummi ta fito, ya riƙo ledar maganinta, ya riƙe hannunta suka shiga cikin gidan. "Baƙar randa, baƙin zunubi, an dawo jinsinmu na maza" Alhassan ya faɗa yana ƙyaƙyata dariya". Yahaya ya tsaya cak, ya kalle shi ya ce "Alhassan, wa ka ke cewa baƙin zunubi? Ummi ba ƙanwarka ba ce ba? Dan me zaku din ga aibata ta?" Alhassan ya yi shiru ya sunkuyar da kai. "Kai da ubanka na halitta, da zai halittoka  da wannan kunnuwan kan kamar zomo na zikiri, ga ƙaton kai kamar marmara?" Ya girgiza kai alamar a'a, nan yayi ta yi masa faɗa, ya shiga cikin gida nan ma ya ɗora, tare da yi wa iya ƙorafi a kan lallai ta sanya ido, a daina ci wa ummi zarafi, idan ba haka ba, zata dashi ba ta karsashi a cikin al'umma, saboda gudun kar a aibanta halittarta. Jin sa kawai Iya take yi, amma ba dan ta ji zata iya hana wani aibata ummi ba, dan ita ma aibata tan take yi. Yahaya ya kawo kuɗi ja bawa iya nata, kamar yadda ya saba yi mata alkhairi, ya sanya a ka kira masa magaji, ya bashi dubu goma ya ce "Ga dubu goma, dan Allah duk abun da Yarinyar nan take buƙata, ko na rashin lafiya, ko na makaranta ka cira ka saya mata, idan da damuwa zan rubuta lambar wayata, a kira ni a sanar da ni duk abun da take buƙata, zan biya. Zumunci bai ce haka ba, mahaifinta ya rasu, an rabata da mahaifiyarta, kuma aƙi tsayawa a kula da ita, dan Allah a kula da marainiya". Hashim ya ce "Ina sha Allah kawu, za ayi duk abun da ya dace" ya dubi ummi ya ce "Sannu ummi" Ta ce "Yauwwa" Yahaya ya miƙe ya ce "To iya, sai wani lokacin kuma, ayi ta haƙuri, Allah ya rufa mana asiri" Iya ta kwaɓe baki ta amsa da Amin. Da sauri ummi ta riƙe rigarsa ta ce "Baba yaushe zaka dawo?" "Da wuri in sha Allah ummi". "To ka ce ina gaishe da mama" Ya kalli iya, iya ta kawar da kanta gefe, ya ce "Iya yakamata a sanya lokaci a kaita ta ga mahaifiyarta, bai kamata idan ma wani abu ne a tsakanin ku da mahaifiyarta ya shafe ta ba" Iya ba dan ɗan abun duniyar da ya bata ba, da babu abun da zai hana, ta ɗura masa ashar. Sai dai ta yi masa shiru, ya ƙaraci maganarsa ya tafi. Hashim ya tafi raka shi, suna tafe yana sake jaddada masa, dan Allah a kula da ummi, babu wanda yafi ƙarfin Allah ya jarrabe shi da irin abun da ya jarrabe ta. Suka ɗan yi hira a kan karatun Hashim, yake gaya masa ai yayi jamb, ya ce duk yadda ake ciki, idan yana buƙatar wani taimako yayi masa magana. Suka yi sallama ya dawo sashin Iya, sai dai fa iya nata jibgar ummi da kara, Idris na tsaye yana kallonsu. Da sauri ya ƙarasa ya ƙwace ummi, ya ce "Iya daga asibiti fa aka dawo da yarinyar nan" "A'a daga mutuware aka dawo da ita, duk yadda nake ƙoƙari a kan yarinyar nan, bata da wani buri da ya wuce ta tozarta ni, ta nunawa duniya azabtar da ita nake yi" "To yanzu iya me tayi miki?" "Ban sani ba, tun da makaho ne kai, baka gani, munafukar yarinya, wallahi duk ranar da wani ya kuma zuwa gidan nan, ki ka yi masa zancen uwarki, sai mai shirin tafiya kabari ya fiki kwanciyar hankali, sai na casa ki, shegiya mai idon munafukai" Ummi ta cukuikuye rigar hashim tana kuka. Iya ta kalli Hashim ta ce "Kai ma ɗaya munafukin, bani kuɗin da ya baka, ai ba ita kaɗai ce ƴa a gidan ba, kuma idan bayarwar ne, ai ni yakamata ya bawa" Cikin takaici ya ce "Amma iya... "Rufe mini baki, ka bani na ce kan na ɓata maka rai" ya ciro kuɗin ya ajiye mata, ya fice. Ummi da sauri ita ma ta fita, jikinta na ciwo, ga zazzaɓi na sake son rufe ta. Ta koma ƙofar gida, ta samu in da rana take da saura, ɗumin yana ratsata. Auwwalu ya taho da tawagar abokansa, har ya wuce ta ya dawo ya ce "Yara baƙar randa ta koma baƙin namiji, aski aka yi mata fa" Ɗaya daga cikin yaran ya ce "Haba dai" Ya ce "Bari ku ga" ya tunkari ummi, yana zuwa ya fara ƙoƙarin ja mata hijjabi, ta rirriƙe hijjabin ta fara kuka. Ƙarasawa yaran suka yi, suka taya shi,  kasancewar maza ne, gashi ba ta da ƙwari ga rashin lafiya, suka kayar da ita, suka yage hijjabin. Ta saka hannu bibbiyu ta rufe kanta, tana kiran mama. Saboda mugunta irin ta yara, daga haka suka din ga kai mata duka a ka, wai sun ci ladan aski. Suka tuburbuɗata a cikin ƙasa, duk ta kurje jikinta, kan da aka yi wa dressing, duk suka cika shi da ƙasa. Mariya daga alhinin mutuwar miji da rabuwa da Ummi, mariya ta zarce da damuwa, ba ta hira ba ta walwala, sai dai kullum cikin wuni a ɗaki, duk lokacin da ta kwanta, ba ta da wani aiki sai mafarkin ummi, da kuma marigayin mijinta. Asibiti da maryam ke kaita awo, suka ce da zarar ta fara naƙuda, a kai ta asibiti ta haihu a can, saboda hawan da jininta yayi. Sai dai kusan kwanaki uku kenan, tana jin ciwo, kuma sai ta yi ta mafarkin gata ta haifi ummi tan jaririya, amma tayi shiru da bakinta, taƙi faɗa. Mama ta shiga ɗakin, da niyyar tashin mariya ta yi salla, ta tarar da ita tana jijjiga, sai datse harshenta take yi, tana mimmiƙewa ga kuma haɗe da jini na fita daga bakinta. Ayshercool 08081012143                          *CUTARWA!* BRIGHT PENS (FREE BATCH) arewabooks ayshercool7724 Watpad ayshercool7724 Subscribe my YouTube channel https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels P7 A guje mama ta koma tsakar gida, tana ƙwalawa malam kira, a kan ya zo ya ga abun da mariya take yi. Suka dawo a tare, ya tarar da yadda jikinta yake ta rawa tana jijjiga, ya fita da sauri, aka nemo maƙwabcin su, kasancewar yana da abun hawa, aka saka mariya a mota suka tafi asibiti. Can kuma hashim ne ya fito zai fita titi, ya hango yara sun yi dandazo, har zai wuce ya hango ƙafar ummi, ya ƙarasa da sauri, ya tarar da ita a kwance, yara sun yage mata hajjabi, ta sanya hannayenta biyu ta rufe kanta, sai kuka take yi. Wani irin baƙin ciki ya turnuƙe masa zuciya, ya rasa dalilin da ya sanya yara suka tsani ummi haka, kodayeke iyayensu suka gani suna yi, da sun tsawatar musu da tarbiyantar da su a kan girmama halittar ɗan Adam komai muninta, da ba su yi mata wani abun ba. Kai tsaye ya je ya tarwatsa yaran, yayi nasarar kama auwwalu, ya din ga kifa masa  mari, yana ball da shi, yayi masa dukan tsiya, sannan ya ɗaukko ummi ya shiga da ita gida. Gaban iya ne ya faɗi ganin yadda ya shigo da ummi, ta miƙe tana faɗin lafiya?. "Wallahi auwwalu ne ya tara yara, suka cire mata hijjabi suka yi ta dukanta a waje" "Saboda iskanci, me tayi masa?" "Oho masa" "Kema uban waye ya ce ki fita?" Tayi maganar tana kallon ummi, da take ta zirarar da hawaye. Ya ce "Dan Allah iya ki yi haƙuri, a jigace take, jikinta zafi rau da zazzaɓi" Ya karkaɗe mata ƙasar nan, ya samu ruwa ya din ga shashshafa mata a jikinta, ya kaita ɗakin gwaggo ya kwantar da ita. Iya kuwa mita take tana "Na rasa wannan baƙin jini na yarinyar nan, ƴa sai ka ce mujiya, ƴan uwanki yara ma gudunki suke yi, kodayeke ai dole a guje ki, wannan munin gaba ɗaya kalarki ba irin ta mutane ba" Hashim bai kula iya ba ya fice, saboda haushinta da yake ji, dan ya fara tsinkewa da lamarin son zuciyarta, gashi babu wanda zai iya tarar ta ya gaya mata gaskiya kowa tsoronta yake ji. Duk yadda likitoci suka yi ƙoƙarin ceto ran mariya da yaronta, Allah bai yi ba, yaron ya zo babu rai, kuma alamu sun nuna ya kwan biyu da mutuwa a cikin ta, saboda yadda fatarsa ta fara marmasowa. Sai dai har kusan kwana biyu da haihuwar ta, an kasa samo kanta yadda yakamata, da magani ya sake ta sai jini ya sake hawa. Sai suka shafe sati uku a asibiti, sannan aka sallame su, suka koma gida, sai dai abu idan ba ya zama dole ba, ba ta magana. Tunani kawai take yi, ko ta saci jiki ba a sani ba ta je ganin ummi, amma ta tuna wulaƙancin da iya ta yi wa yayyenta, ta san muddin ta je, ba abun da zai sauya, kuma hakan tamkar watsawa mahaifinsu da yayyenta ƙasa a ido ne. Ummi ba wanda yake kula da bata magani, sai idan magaji ya shigo sashin Iya, ya sanya ta a gaba ta sha, duk da iya ta ƙwace kuɗin da kawunsu ya bawa ummi, da kuɗinsa ya saya mata yadin uniform, ya canza mata nata da suka yayyage suka yi mata kaɗan. Ummi ta ji daɗi sosai da sosai, ga sabuwar jakarta dan haka cike da ƙwarin gwiwa take zuwa makaranta. Kafin kwana bakwai, tuni kan ummi ya cika da gashi, kamar ba ayi mata aski ba, kalar wanda ya fita kalar sa ne dai yake sake fitowa a kanta, ba baƙi ne wuluk ba. Duk wannan murnar da take yi na komawa makaranta, da tarin ƙoƙarin da ummi take da shi, ya zama a banza, saboda ko tambaya aka yi a aji, ba ta iya bayar da amsa, saboda gudun cin zarafi da tsokana da ƴan uwanta ɗalibai za su yi mata, koma malaman da kansu. Wujiga-wujiga ta dawo daga makaranta, saboda azabar yunwa, koko ne kawai a cikin ta, shima tun sha ɗaya da tayi fitsari, take jin kamar an sace mata kayan ciki saboda yunwa. Da ƙyar ta ƙarasa gida, tana zuwa iya ta ɗora mata kai niƙa, haka ta kuma kwasar rana, ta kai wa iya niƙan ta dawo, a wannan wahalen da take, wannan ya ja ya aika, wancan ya ja aika, har lokacin shiga makarantar allo yayi. Iya ta rage mata abincin rana, bai fi loma uku ba, a loma ɗaya da kaɗan ta cinye, ta tashi ta tafi makarantar allo. Naima ce ta hangota tana share hawaye da hijjabinta, ta ƙarasa in da take ta ce "Ummi, ya aka yi ki ka makara? Kuma kukan me ki ke yi?". Cikin kuka ta ce "Malam babba ne ya dake ni, na makara" "To meyasa ki ka makara?" "Iya ce ta aike ni" "Shegiyar mata, mai zuciyar kafirai" Naima ta faɗa a ƙule, ummi kuma ta kalli fuskar naima tana mamakin yadda take zagin babba kamar iya. Ta ja hannunta ajinsu, ta ɗaukko wani ɗan kwano ta bata abinci, aikuwa hannu baka hannu ƙwarya ummi take danna abincin. Na'ima ta dubi ummi ta ce "Ya jikin amma dai kin warke ko?" Ummi ta ɗaga mata kai alamar eh. "Gashin ya fara fitowa?" Ummi ta saka hannu ɗaya ta buɗe mata kan, Na'ima ta rufe mata ta ce "Masha Allah, ya fara fitowa, kin wanke kayanki na makarantar boko?" "A'a yaya magaji ya saya mini sabon uniform na makarantar boko" ta faɗa cike da jin daɗi. Na'ima ta ce "Alhamdilillah, Allah ya saka masa da alkhairi, na bayar a ɗinka miki atamfar bikina" Ummi ta kalleta ta ce "Biki, aure kenan?" Na'ima ta ce "Eh, aure zan yi ko in tafi da ke gidana?" "Eh yaya Na'ima zan biki dan Allah" Na'ima ta ciro ɗan ƙaramin tsumma a jakarta da ruwa a jarka, ta bawa ummi ta sha, sannan ta shiga goge mata hannu ta ce "Zan so ace za a bani ke na tafi da ke ummi, sai dai hakan ba zai yiwu ba, ki je aji idan an tashi ki jirani mu tafi tare, zamu je gidan mansura, an kawo mata takalma daga Kano, idan da wanda zai yi miki, sai na saya miki na biki" Ummi ta ce"Ba zaki tafi da ni ba?" "Ki yi haƙuri ummi, ba zai yiwu ba" "Kema tafiya zaki yi ki bar ni? Mama ma ta tafi taƙi dawowa" Na'ima ta yi ajiyar zuciya ta ce "Maza je ki ajinku, ga malam can ya tafi" ta miƙar da ummi tsaye, ummi ta tafi ajinsu. Naja da take ƙawar na'ima, ta ce "Ke dai ki na son yarinyar nan naima, gashi kin saka mata ran tafiya da ita" Na'ima da hawaye ya taru a idonta ta ce "Wallahi naja ina tausayin ummi sosai, wallahi da za a bani ita zan ɗauke ta, kakarta matsiyaciyar tsohuwa ce, ai babarta uwar ɗakina ce, mun yi mutunci sosai, baban ummi ya rasu, ta koma garinsu, Kakarta ta ƙwacw ta take azabtar da ita, ko a lahira na ganni gani g matar nan na san ban yi kyakkyawan ƙarshe ba" Duk da a ƙufule Na'ima tayi maganar, bai hana naja dariya ba, saboda maganar ta ta ƙarshe ta bata dariya. Bayan tashi daga makaranta, tare suka tafi da ummi, hannunta cikin nata suna tafe tana yi wa ummi hira, tana bugun cikinta, dan jin zaman da take yi, sai dai abun babu daɗi mussman da ta gaya mata abun da su auwwalu suka yi mata, da aka yi mata aski. Na'ima ta ce "Bakomai Allah ya isanki wallahi, duk wanda yayi nagari kansa,. Ki yi ta haƙuri kin ji ummi, duk tsanani duk yunwar da ki ke ji, kar ki bari wani a mazan gidan ku, manya ko yara, su kai ki wani wuri, su saka hannu a jikinki, kin ji ko?" Maimakon ummi ta amsa sai ta ɗaga kai tana kallon na'ima. Cikin sauri na'ima ta tsaya ta ce "Suna yi miki wasan banza ko?" Ummi ta girgiza kai ta ce "A'a" "Ki gaya mini gaskiya, suna taɓa ki ko?" Ummi ta girgiza kai ta ce "A'a" "Duk wanda ya saka hannu a cikin jikinki, kar ki yadda kar ki tsaya, ki yi masa ihu ki gudu kin ji ko" ta jinjina mata kai alamar eh. "Ko bayan na tafi, idan kina jin yunwa, ki je gidanmu wurin babarmu ta baki abinci" Da haka suka ƙarasa gidan mai takalmi, aka yi sa'a aka samu dai-dai ƙafar ummi. Na'ima ta ce "Zan ajiye a wurina, ranar bikina in yi miki kwalliya ko?" Ummi ta ɗaga kai tana murmushi, daga nan suka ƙarasa gida. Ummi ta shiga gida hannunta riƙe da wani kara tana wasa da shi "Ke!" Idris ya kwaɗa mata kira a wulaƙance. Ta juyo tana kallon sa. "Zo ki sayo mini sukari a kanti" yayi maganar yana watso mata kuɗi. Ta durƙusa ta ɗauka, ta je ta sayo masa, sai dai ta din ga tuna gargaɗin Na'ima na hanata zuwa ɗakin su idris. Ta nemi wuri ta zauna a ƙofar shiga wurin, ya gaji da jiranta ya fito. "Dan ubanki ina aiken da na yi miki?" Da sauri ta miƙe tana nuna masa sukarin. "Ba zaki shigo ki kawo mini ba saboda baki da mutunci, sai ki nemi wuri ki zauna?" Tayi shiru tana kallon sa, "Ba zaki kawo mini ba" ya sake yi mata maganar cikin tsawa. Ta ƙarasa in da yake cikin jin tsoro, sai dai ya ya haɗa da hannunta, ya ja ta cikin ɗakin. Kuka ta fara yi masa iya ƙarfin ta, yau ya samu damar da rabonsa da ita an daɗe, amma ta nuna masa tayi wayo yanzu, dan haka ta din ga yi masa kuka da ƙarfi, kamar yadda Na'ima ta gama gaya mata ɗazu. Wawan marin da ya kifa mata ne, ya tafi da ji da ganinta na wani ɗan lokaci, ta dafe kuncinta jikinta na wata irin tsuma, tana karkarwa. Wata sharɓeɓiyar wuƙa ya nuna mata ya ce "Ki ka cigaba da yi mini kuka, sai na yanka wuyanki" kallonsa take yi, kallo mai cike da tsoro da tsana, ya ajiye wuƙar tare da sanya hannayensa cikin rigarta, rigar da bakomai a ciki sai teɓa dan wannan dai ba nono bane. Ba ta karaya ba, ta fara kokowar cire hannayensa daga jikinta, tana kuka mai cin rai, iya ƙarfin ta. Bankaɗo ƙofar ɗakin aka yi, hakan ya razana shi, dan bai yi zaton zuwan wani a dai-dai wannan lokacin ba. "Idris meye haka?" Hashim yayi maganar yana kallon sa. "Kamar yaya meye haka, abun da ka gani" a fusace ya ƙarasa ya hankaɗe idiris, ya janye ummi, ya kalli idiris ya ce "Wani irin banza ne kai, ba zaka girma ba a rayuwarka, da me yarinyar nan za ta ji ne?" Wani uban tsaki idiris yayi, ya ce "Ka daina shiga sabgata ba ruwanka da ni". "an shiga sabgar taka, wallahi idan baka rabu da yarinyar nan ba, sai na ɗauki mummunan mataki a kan ka" "To ka ɗauka mana kar ka fasa" ya sake jan tsaki ya fice. Cikin ƙunar ran yadda ƙaninsa ya raina shi, duk saboda iya na goya masa baya, ya kalli ummi ya share mata hawaye, ya fito da ita daga ɗakin, shaidar yastun idiris kwance a kan baƙar fuskarta, da har idonta yayi taruwar jini. Ya zubawa ummi ido, da haryanzu jikinta yake tsuma, ga wata irin nannauyar ajiyar zuciya da take yi, har a lokacin a tsaorace take, kuma hawayenta ya ƙi tsayawa. "Ummi" ya kira sunanta, sai dai bata amsa ba, ta sake fashewa da kuka. Wani irin tausayinta ya ratsa zuciyarsa, ya din ga share mata hawayen, ya riƙe hannunta suka nufi sashin iya, tana ta dakan fura tana waƙe-waƙe. Tana ganinsu tare ta hau bala'in tun ɗazu take neman ummi, zata aiketa amma daga zuwa makaranta ta zauna. Magaji ya ce "Iya" "Ya aka yi" "Dan Allah idan ba za a iya riƙon yarinyar nan ba, a mayar wa da uwarta ita, idiris fa na kama yana neman haike mata a ɗakinmu, wace irin rayuwa ce wannan, kalli yadda ya mare ta, haba dan Allah" Iya ta dafe ƙirji ta ce "Shi idiris ɗin? Ita uban me ya kaita in da yake, me ya kaita ɗakin ku, ai ita ta kai kanta, amma shima zai zo ya same ni, da ni yake zancen. Kai kuma sai ka ce ba ɗan uwanka ba, ka ke ɗaga murya tona masa asiri zaka yi?" "Iya to zuba masa ido za ayi, idan abun da ba a so ya faru fa?" "Ba abun da zai faru sai alkhairi, jeka zai zo ya same ni, ke kuma canza kayan ki zo ki kai dusar nan gidan lami, ta bawa dabbobina" Hashim ya ce "Ni bani dusar na kai, kalli yadda take a razane" "Ba wani a razane, da a razane take ai da ba ta kai kanta ba, yarinya ƙanƙanuwarta da ita, ta san ta je wurin namiji" "Haba iya, me ummin ta sani da zaki faɗi wannan mummunar maganar a kanta?" Iya ta ce "Zaka zo ka kai mini dusar ko ta ɗauka ta kai mini?" Ya ƙarasa ya ɗauki dusar ya fita, zuciyarsa kamar ta tarwatse, tausayin yarinyar na damunsa sosai da sosai. Kwanaki biyu tsakanin abun da ya faru, sannan idiris ya shigo sashin Iya. Iya ta dube shi ta ce "Idris, kashedi zan yi maka a kan yarinyar nan, kar ka kuskura ka sake saka yarinyar nan a loko kana lalubeta, wallahi idan ka sake wani abu ya afku ba zan rufa maka asiri ba, kuma ba zaka janyo mini masifa ba, kai gashi ba sana'a ba balle ace ayi maka aure, in huta. Ina yi maka kashedi, wallahi wani abu ya faru ba zan saurara maka ba, na gaya maka" Cikin fushi ya ce "Me kuma na yi, magaji ne ya zo ya ce na yi mata wani abu?" "A'a ni banga magaji ba, bai gaya mini komai ba, fuskanta kawai na yi" Ficewa yayi ba tare da ya sake magana ba. Rashin samun biyan buƙatar sa a jikin ummi, ya sanya ya ji ya ƙara tsanar yarinyar, ko son ganinta ba ya yi, ita kanta ummi, har fargaba take yi a aike ta, saboda bayan iya ta yi masa wannan faɗan, sai da ya zane ta, saboda a zaton sa ita ta gaya wa Iya. Duk wannan cin kashin da ake yi wa yarinyar, daga ƴan uwan ubanta da suke ciki ɗaya, da wanda uba suka haɗa da matayen su, babu wanda ya taɓa shawartar iya a kan sassautawa ummi azabtarwar da ake yi mata, tamkar ƴar tsintuwar da ta faɗo daga sama. Azumi saura wata biyu, aka yi bikin na'ima, ta yi kuka sosai, ciki har da na rabuwa da ummi, dan har cikin zuciyarta take jin rabuwa da ummi. Mariya kuwa tun ƴan uwanta na ta tata, suna rarrashin ta, suna bata haƙuri, har suka zubawa sarautar Allah ido suka ƙyaleta, ta riga dai ta kamu da larurar hawan jini, a hankali kuma ciwon damuwa ya fara addabar ta, kullum tana ɗaki, daga bacci, kuka sai shiru. Yaya ɗan lami ya fara tunanin ko ta koma makaranta, amma yanayin da take ciki, ya tabbatar masa da ko an mayar da ita makarantar ba za ta iya mayar da hankali ba. Dama labarin haihuwar ta ta ko su iya ba a gayawa ba, dan gaba ɗaya sun fuskanci sabgar Iya babu Allah a cikinta. Yaya ɗan lami kuwa da suka ga mariya taƙi sakin ranta, ya ƙare mata cin mutunci, tare da tabbatar mata da muddin ta je wurin su Iya babu su babu ita, ƴa ce idan ta girma da kanta za ta neme ta. Watan azumin ramadana ya kama, wanda hakan ya sake jefa ummi tsaka mai wuya. Ba iya azumi take yi ba, dan haka babu mai kulawa ya bata abinci, haka za ta yi ta gararanba ta wuni a kwance, idan makaranta ta je, tana kallo yara na ciye-ciye, ita ba raɓar su take yi ba ma, balle ta yi musu kwaɗayi, ko kuɗin makaranta ba bata ake yi ba, dan haka bata saba da kashe-kashen kuɗi ba. Sai an sha ruwa take samu ta ci abinci, sai da hashim ya fuskanci ba ta samun abun da za ta ci da rana, shi ne yake rage mata abincin sa, da safe ya bata, da rana ya sai wani abun ya bata. A haka har aka ƙare azumi. Da salla kowane ɗa cikin kyakywar shiga mai kyau, ummi kuwa kayan bikin na'ima ta saka, da suka fara koɗewa, da takalmin makarantar da kawunsu ya saya mata, shi ta koma tana sakawa tayi yawo da shi a gari, saboda ko silifas ba ta da shi, wanda naima ta saya mata tuni ya lalace. Yara na ta shiga su na fita, ummi kuwa na ƙofar ɗakin mamanta, ta zauna tana wasa da duwatsun wurin. Hashim yayi sallama, ummi ta amsa cikin ƴar siriyar muryarta. Ya ƙarasa in da take zaune, ya ce "Kin je sallar idi ne?" Ta girgiza kai alamar a'a. "Me ki ke yi a nan wurin?" Ta ce "Bakomai" "Kin ci tuwon salla kuwa?" Ta ce "A'a iya dai ta ce zata bani" Ya miƙa mata hannu ya ce "Taso mu je" Ta saka hannunta a nasa, ya ja ta zuwa sashin mahaifiyar sa. Babansa ma, da ake cewa baba sagir, yana zaune yana cin abinci. Ummi ta durƙusa ta gaishe shi, ya amsa mata babu yabo ba fallasa. Ya ce "Yaya a zubawa ummi abincin salla dan Allah" Ta ce "Ga maimuna nan, ya zuba mata" ta kalli ummi ta ce "Ke ummi baki da kayan salla ne, ki ka saka wannan koɗaɗɗiyar atamfar?" Ummi tayi shiru tana kallon ta. Aka kawo wa ummi abinci, ya saka ta wanke hannunta, ta zauna ta saka tuwon sallar nan a gaba tana ci, tana yi tana kallon yadda yara suka yi kyau sosai a sababbin kaya. Ta gama ci ta hau tattara musu kwanukan wanke wanke, ta share musu tsakar gida. Hashim ya dawo sashin, ya tarar da ummi ta haɗa kwanukan wanke-wanke. "Me kuma zaki yi?" "Wanke-wanke zan yi". "Ke yara na can waje suna tsalle-tsalle, suna wasanni, amma ke kina nan ki na haɗa wanke-wanke, ki je ki yi wasanki sa yi wanke-wanken da kan su" "A'a bani da kayan salla, idan na fita tsokanata za ayi, su ce mini baƙa" tayi maganar tana ƙoƙarin jan kujera ƴar tsuguno tayi wanke-wanken. Shiru yayi yana kallonta, cikin tausayawa. Yana zaune yana kallonta, gata yarinya ƙarama amma ta riga ta saba da wahala, yadda yake wanke manyan kwanukan da aka ɓata da miyar abincin salla. Wata ragowar miya da ta rage, ta zuba mata ruwa zata zubar, idirisa ya kawo kai ta watsa masa a jikinsa. Ayshercool 08081012143                     *CUTARWA!* Watpad ayshercool7724 Arewabooks ayshercool7724 YouTube https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels What's app 08081012143 *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* BRIGHT PENS (FREE BATCH) P8 Tuni ummi ta zabura, ta jefar da kwanon hannunta, jikinta ya hau rawa, a fusace ya ƙaraso kan ummi, yayi ball da ita ta hantsila cikin kwanukan da take wankewa. A cikin azama hashim ya ƙarasa, ya hankaɗe idiris, yana faɗin "Idirs meye haka?" "Ban gane meye haka ba, ba kaga abun da ta yi mini ba? Dabbar ina ce? Ko makauniya ce?" "Kai za a cewa dabba,  ya za ayi ka shigo babu sallama, ya za ayi ta san da zuwan ka? Idiris zaluncin da ka ke yi wa yarinyar nan yayi yawa fa" Ummi kuwa karo tayi da ƙafar tukunyar ƙarfe, fiƙarta ɗaya ta karye, nan da nan bakinta ya rine da jini, kuka take yi sosai, saboda ciwon buguwar da tayi, har cikin kanta take jin azabar ciwo. Babarsu da ta jiyo hayaniya ta fito tana faɗin "Wai lafiya ku ke yi mini hayaniya da tsakar ranar nan?" Idonta ya sauka a kan ummi, da yawun  bakinta ya gauraye da jini". "Ita kuma wannan meya sameta?" "Ga wanda ya yi ball da ita cikin kwanuka nan" Hashim yayi maganar cikin takaici, yana nuna idiris. Nuna wa mahaifiyarsu kayansa yayi, da ummi ta ɓata da miya. Hashim bai tsaya jin abun da mahaifiyarsu za ta ce ba, ya ja hannun ummi, ya tafi da ita. Sun sha yawo sosai, kan su samu chemist, kasancewar salla ce, aka bawa ummi magani. Haka aka gama bikin salla, ummi ba kayan salla sai jinyar baki, da ya sanya ta ciwon kai sosai da sosai. *** Mariya na zaune a ɗaki tana ninkin kaya, fuskar nan kamar wadda aka yi wa mutuwa, tana jiyo hirar da mama, da jimmai maƙwanciyar su suke yi, wadda ƴar ta aka kai gagarawa, suka haɗu da balarabe suka yi aure. Tana bawa mama labarin ƴar ta mijinta ya samu sauyin wurin aiki zuwa ikko, sun bar gagarawa. Mariya ta yi shiru, tana tunanin ya aka yi ba tayi tunanin ta din ga bayar da abu, idan an samu mai zuwa gidan ƴar jummai a kai a bawa ummi ba. Sai dai ta tuna ba shiru suke yi ba, dan ƴar gidan jimmai, tana ganin tana auren mai kuɗi mijinta ɗan sanda ne, idan suka haɗu da mariya a hanya, kamar ba su san juna ba, saboda yadda take jin kanta. Tunaninta ne ya katse lokacin da ta jiyo jimmai na cewa "Ai nan asalamiyya ke bani labari, ƴar da mariya ta baro, wahala kawai take sha, ranar ta ganta ko takalmin kirki babu a ƙafarta, na ce ta ɗan din ga taimaka mata, to kin ga ma yanzu sun bar garin, na ce da kun je kun ɗaukko yarinyar nan" Mama ta ce "Da zai yiwu da anyi hakan ai, ba yadda ba ayi ba su bayar da Yarinyar sun ƙi, shiyasa muka ƙyalesu, ba su da mutunci ko kaɗan, da aka je musu da maganar cikin mariya, cewa suka yi ba nasu bane ba, shiyasa malam ya ce babu mu babu su, a ƙyale su idan yarinyar ta girma ta nememu" Jimmai ta ce "Ashsha! To Allah ya kyauta". Mama ta amsa da "Amin" Mariya ta ajiye ninkin, ta haɗa kai da gwiwa ta din ga kuka. Bayan tafiyar jimmai, mama ta shiga ɗakin, dan ta san mariya na jin su, ta ce "Mariya na san kin ji abun da jimmai take faɗa, amma haƙuri zaki yi ki kawar da kanki, ki sakawa zuciyarki salama a kan yarinyar nan, idan ba haka ba kuwa ciwo zai cigaba da cin jikinki, kin san dai ki na da hawan jini"  shiru mariya ta yi, ta cigaba da rera kuka, mai ƙona zuciya, tana ji a ranta ba zata taɓa yafe wa Iya ba. An doshi shekaru huɗu, da rasuwar Bashir, ummi ta cigaba da rayuwa ba tare da ta sake sanya idonta ana mahaifiyarta ba, tamkar baiwa a cikin gidan nan haka take rayuwa, babu gata babu kulawa, wahala ta yau daban ta gobe daban, ga Iya ta tsiri yi mata kunu ranar asabar da lahadi ta kai kasuwar garin, ta sayar mata, har ma wasu su yi abun sayarwar su a gidan su haɗa mata. Babu yadda Hashim bai yi da iya ba, a kan ta daina ɗorawa ummi tallar nan, azabar da take sha tayi yawa, amma iya ta zage shi tsab, ta ce idan ya cigaba da yi mata katsalandan, za ta ci mutuncinsa ta tsine masa. Babu kunya ba tsoron Allah, Iya ta saka aka ɓalle ƙofar ɗakin mariya, aka kwashe kayanta aka sayar, ta karɓe kuɗin, wai da su zata tarawa ummi kayan ɗaki, ɗakin ya zama wurin tara itace, hatsi da sauran shirgi. Ummi ta dawo daga makarantar boko, takalminta ya kusa rabewa biyu saboda tsufa ƙasansa kuwa ya huje, malaman su, sun gaji sun ƙyaleta, ƙafarta futu-futu. Ta tarar da Iya a tsaye tana jiran isowarta. Jiki a sanyaye ta ƙarasa in da Iya take, ta ce "Iya laifi na yi ne?" "Au tambayata ma ki ke yi, saboda tsabar kin shahara, nan gaba makami zaki fara nuna mini, ki yi mini ƙwace, kuɗina zaki bani da saminu ya zo jiya da daddare, ban gan su ba, kuma daga ni sai ke a ɗakin" Gaban Ummi ya faɗi, ta girgiza kai ta ce "Wallahi iya ban ɗauka ba, ki sake dubawa". "Ni ki ke gaya wa na sake dubawa? Ƙarya zan yi miki kenan? Ki zo ki bani kuɗina kan jikinki ya gaya miki" Ummi kawai tayi shiru tana kallon iya, dan ta rasa me za ta ce mata ma, ta san kawu saminu ya bata kuɗi jiya, amma ba ta san ma a ina ta ajiye su ba. "Au saboda kin mayar da ni ƴar iska ki ka tsaya kina kallona, ba zaki bani kuɗina ba?" Ummi ta sunkuyar da kai, dan gaba ɗaya kanta ya kulle. Iya ta saɓa mayafi ta fice, jiki a sanyaye ummi ta ƙarasa cikin ɗakin iya, ta hau duddubawa, ko za ta ga in da Iya ta ajiye kuɗin. Maganar Iya ta jiyo da idris ta ce "Ka tambayeta ina ta kai mini kuɗi, ka yi ta dukanta, har sai ta faɗa" kan ummi ta ankara sai ganin idiris ta yi a kan ta, hannunsa riƙe da manyan reshen bishiyar darbejiya. Kafin ta yi magana, ya shiga shimfiɗa mata tsumagiyar nan a jikinta, gashi ya tare duk wata hanya da zata bi ta fita. Kasancewar dama haushinta yake ji, ya sanya ya zage duk wani ƙarfin sa, ya dinga jibgarta, har da taka ta da ƙafa. "Fito mini da ita daga ɗaki, ɓarauniyar banza da ta wofi, kuma daga yau kin bar kwanar mini a ɗaki" a ƙasa haka ya din ga jan ummi, ya fito da ita tsakar gida. "Ga ɗakin uwarta can da ake tara itace yanzu, rufe mini ita a ciki, ko abinci kin daina ci, sai kin bani kuɗina" Haka kuwa aka yi, idris ya rufe ummi a ɗakin mariya, da yanzu ake tara itace da hatsi a ciki, ya rufe ɗakin bisa umarnin iya. Ummi ta kwanta a ƙasa, jikinta sai zafi yake yi, hannunta da Idris ya din ga hauri da ƙafarsa, tamkar ba a jikinta yake ba, hannun yayi sanyi ga ciwo yana yi nata. Sai da ummi ta kwana ta wuni a cikin ɗakin nan, shima magaji ne ya ga baya ganinta, ya matsa da tambaya, su Alhassan suka ce masa ai Iya ta sacewa kuɗi dubu goma sha biyu, ta saka idiris ya zane ta, aka kulle ta a ɗaki. Hashim ya ji kamar ya ɗora hannu a ka yayi ihu, ya buge kwaɗon, ya tarar da ummi a zaune a takure wuri ɗaya, saman idonta ya kumbura, ko ina jikinta rauni ne. Dogon gashin nan duk ya kwashi datti da karare. "Ummi" ya kira sunanta, ta ɗago ta kalleshi ta sunkuyar da kai. "Da gaske kin ɗaukar wa iya kuɗi" Ta girgiza masa kai, ya ce "Na san ba zaki ɗauka ba ummi, yi haƙuri taso ki fito" Ta girgiza masa kai ta ce "Dan Allah yaya magaji ka ce Allah ya sa na mutu, bana son zama da iya, dan Allah ka kai ni wurin mama, wallahi zan mutu" tayi maganar tana sheshsheƙar kuka. Ya kalleta yarinya shakaf, amma tana iƙirarin ta mutu, "Ba zaki mutu ba, wuya bata kisa ummi, tashi kar wani abun ya cije ki" Da ƙyar ya fito da ita daga ɗakin. Iya kuwa duk ta gama barbaɗawa mutanen gidan ummi ta sace mata kuɗi. Ko kallonsu Iyan ba ta yi ba, ya nemo abinci ya bata, ya ce tayi wanka. Tana banɗaki, Hashim ya samu Iya ya ce "Iya dan Allah meyasa ba kya ƙaunar ummi ne?" "Kamar yaya, in haifi ubanta ka ce bana son ta? Tarbiyya nake bata, uwarta na tsana ne, bana ƙaunar uwarta ne, kuma alamu sun nuna halin uwarta ta yi" "Ba wannan ba, Iya kin duba ɗakin nan da kyau baki ga kuɗin ba? Ummi bata taɓa yi miki sata ba fa?" "In ji uban wa? Faɗa ne kawai ba na yi, amma sata kam ba yau ta fara ba, kamar ta sha nonon ɓeranya" Zai yi magana ummi ta fito daga wankan, tana ɗingisa ƙafarta. Bai cewa iya komai ba, ya tashi ya bata kujera ta zauna, ya kamo hannunta da ya kumbura, ya fara matsawa a hankali. Nan ta din ga yarfe hannu tana kuka. Fatar ummi duk wannan wahalar da take sha, jikinta tamkar auduga saboda taushi. Iya ta watso mata ƙullin kayanta, ta ce sai dai ta koma ɗakin itace ta cigaba da zama. Babu magiyar da magaji bai yi mata ba, amma ta ce bata san zancen ba. Da kansa ya share wa ummi ɗakin, ya samo buhu ya shimfiɗa mata, ya kawo tabarma ya shimfiɗa mata, ya din ga rarrashin ta, yana bata haƙuri, ji yake kamar ya zauna ya yi wa ummi kuka. Iya ta aika a kirawo mata Alhassan zata aike shi, ta ce ya duba ƙasan katifarta ya ɗaukko ɗari biyu, Alhassan ya fito da wata leda a hannunsa ya ce "Iya ba wannan kuɗin ki ke nema ba?" A razane ta karɓa tana ƙifta masa ido, gaba ɗaya ta manta ina ta ajiye su. Hashim yayi kamar bai ji me ta ce ba, haka ummi, sarai ummi ta ji Alhassan yana gaya mata kuɗinta, duk wasu kalaman rarrashi, sai da Hashim yayi amfani da su, wurin ba wa ummi haƙuri, saboda ƙarfin hali, har da Murmushin ta, tare da ƙoƙarin nuna bakomai. Da daddare ya sayo gyaɗa da rake, ya kai wa ummi, duk cikin son ya ƙara rarrashin ta, ya daɗe yana sake kallon ɗakin da zata kwana a ciki, babu ko fitila a ɗakin, kuma ba za a rasa ƙwari masu cizo a ciki ba. Ya kalli ummi ya ce "In sha Allah zan sayo miki fitila, sai ki din ga haskawa, sannan tun yamma ki din ga karkaɗe ko ina, ki tabattar babu wani abu a ɗakin kan ki kwanta". "To yaya na gode" ya jinjina mata kai ya fice. Iya tana kallonsa daga tagar ɗakin ta, yanayin yadda yake shishshigewa ummi, abun ya fara ƙular da ita, dan haka tayi ƙwafa, tare da aniyar ɗaukar mataki a kansa. Sai dai can ƙasan ranta, ta ji babu daɗi ganin kuɗin da aka yi, gashi ta riga ta saka an zane ummin, an rufeta a ɗaki kwana da wuni, ba tare da hakkinta ba. Haka nan abun ya din ga damunta, da safe ummi ta je har ɗaki ta gaisheta, da uniform za ta tafi makaranta. "Kin karya ne zaki tafi makaranta?" Ummi ta ce "A'a" "Ki je wurin sa'adatu ta zuba miki kunu idan ta dama" ummi ta ɗan yi shiru ta tuna yadda sa'adatun ke haɗe rai idan ta je karɓar kunun. Ummi ta ce "Na san idan na je ya ƙare" Iya ta bankaɗa ɗan tofinta, ta ciro naira ɗari, ta ajiye wa ummi ta ce "Gashi nan ki sai waina a hanya ki ci" Ummi ta kalli kuɗin, tana wani irin murmushi da ita kaɗai ta san ma'anarsa, ta miƙe tsaye idonta fal hawaye ta ce "Ki bar shi iya, idan na dawo na ci abincin" tayi waje. Tana jin Iya na zazzaga mata masifa, tana zaginta, amma tayi waje tana share hawaye. "Ƴar ƙanƙanuwarki da ke, kin san munafunci, to kin yi wa kanki, halin uwar taki da nake ta gudu sai da ki ka kwaso shi? To ki ci kanki, da ke da mugun halin naki" Haka iya ta cigaba da sababi da kame-kamen borin kunya. Ummi na tafe a hanya tana kuka, haka ta ƙarasa makaranta, suna ta shirye-shiryen shiga sakandare, sun kusa zana jarrabawar common entrance, shi ma kuɗin jarrabawar da ƙyar, ta biya, shi ma Naima ce ta zo gida, ta sa aka kirawo ta, take ta yi mata tambayoyi da ƙyar ta gaya mata batun kuɗin jarrabawar. *** Manema na ta zuwar wa mariya, duk da ba fita take yi ba, amma mariya tayi burus, mahaifinta ya kaɗa ya raya, amma taƙi tsayar da kowa, da yayi mata zancen auren ma sai ta hau koke-koke. Yayi ta rarrashin ta, a tunanin sa ko saboda tsohon mijinta ya sanya take jin ba zata sake yin aure ba, yayi nasihar, yayi rarrashin saboda kusan shekaru huɗu kenan rabonta da aure. Kuma shekarun nan huɗu cif, ita ba mai lafiya ba ita ba mara lafiya ba. Takura mata da maganar aure, ya sanya ta daina cin abinci ma, ta ƙara tsananta kaɗaice kanta, ga rashin barcci da ya sarƙafe ta, ta wuni ciwon kai dare yayi ta kasa bacci. Tsananin ciwon kai ya sakata a gaba, gashi tayi shiru ba wanda ta gayawa, abu kamar wasa tun tana daurewa har ta kasa, ta din ga burgima a ƙasa tana wayyo kanta. Sai a lokacin suka san ba ta da lafiya, aka kaita asibiti, sai dai babu cigaba, idan an kaita asibitin sai an tursasata shan magani, idan ta sha ɗin ma babu cigaba, wasu lokutan haka zata riƙe kanta tana ihu, tana kuka saboda rashin iya bacci, idan aka kaita asibiti sai dai su yi ta yi mata allurai. Ƙarshe aka tura su ganin likitan ƙwaƙwalwa, hankalin mahaifin mariya ya tashi da ƴan uwanta, jin an tura su ɓangaren likitan ƙwaƙwalwa. Likita ya duba ta sosai da sosai, ya basu shawarar a kula da ita sosai, saboda depression ne ya kamata, idam ba a kula da ita sosai ba, za a rasa hankalinta gaba ɗaya. Karo na farko da iyalan su mariya suka ji mahaifinsu yayi wa wani ɗan adam Allah ya isa, wanda sai da ya zubar da hawaye, yana matuƙar tausaya wa mariya, dan haka bai gaza ba, ya sake tashin yaya magaji, tare da Maryam, ya ce su je su bawa uwar mijin mariya haƙuri, ko sau ɗaya ta bayar da ummi, ta zo ta kwana biyu tare da mariya, ko a samu hankalinta ya kwanta. Yaya magaji ya ce "Baba, ka san matar nan ba zata bayar da yarinyar nan ba, sai dai a tafi da mariyar, ta je ta ganta mu dawo" Maryam ta ce "A hakan zamu tafi da ita? Ba zai yiwu ba ai, kana kallon abun da take yi, ai salon ta sake jin daɗi ne, dan matar nan ba mutunci ne da ita ba, kuma muddin aka bawa mariya ummi, ba zata bari a sake rabata da ita ba, a ganina kawai mu mayar da hankali a kan nema mata lafiya" Yaya magaji ya ce "Duk da haka, zan jarraba zuwa, duk da na san ba zamu wanyeta ƙalau ba, amma zan jarraba zuwa na ga yarinyar ma daga nan, Allah sarki ummi, na san yanzu ta yi wayo sosai. "Zata shekara goma zuwa sha ɗaya fa yanzu, ai ta zama budurwa" Suka bar maganar a kan cewa, yaya magaji zai je ya gano ummi, idan ya ga fuska ya sako zancen tahowa da ummi. Ummi ta daina zuwa ɗakin iya idan ba dole ba, saboda gudun kar ace ta yi wani abun, kullum cikin itace nan da buhhunan hatsi take kwana. Tsabar daka kuwa hannunta duk yayi kanta, yayi ta ɗurar ruwa yana fashewa, saboda tana da taushin fata sosai. Tana tafe tana yada hannu, saboda gajiya ga rana, yunwa da ƙishirwa duk sun addabeta, mutumin da ta hango a ƙofar gidan su ne tare da kawu Ilyasu, ya sanya ta tafiya a hankali, ta ƙarasa ƙofar gidan. Shi ma ƙuri yayi da ido, yana kallonta, ta ƙarasa ta durƙusa ta ce masa "Ina wuni?" Jiki a sanyaye ya amsa ya ce "Ummi kin gane ni?" Ta jinjina masa kai alamar eh. "To waye ni?" Maimakon ta bashi amsa sai ta ce "Ina mama?" "Haryanzu baki manta da ita ba?" Da sauri Ummi ta sake kallonsa ta ce "Da ita ku ka zo?" "A'a, na zo dai neman alfarmar na tafi da ke na kai ki wurinta, amma sun ƙi yarda" Kawu Ilyasu ya wani haɗa rai, cikin haushi kamar tsohon kare ya ce "Ke! Tashi ki wuce ki shiga cikin gida" Ƙafafuwanta suka yi mata sanyi, ta ji tamkar ba zasu iya ɗaukarta ba" "Ba zaki tashi ba?" Ya sake yi mata tsawa. Cikin rawar jiki ta tashi, yaya magaji ya kamo hannunta ya danƙa mata kuɗi, yana riƙe da hannunta ya kalli Kawu Ilyasu ya ce "Da ku da mahaifiyarku, ku shirya amsar da zaku bawa Allah, kalli wai wannan ƴar ɗan uwanku ce dan abun kunya, kalli kayan makarantar da suke jikinta, kalli ƙafafuwanta. Kun ce idan na tafi da ita babu ku babu ita, ku ba dangin mahaifinta bane ba, duk in da aka je aka dawo, da dangin uba ake ado, kuma ba zan cigaba da jayayya da ku ba, muna raba abun faɗa, Allah zai zama gatan marainiya" "Ummi ki kula da kanki kin ji ko? Ki yi ta yi wa mamanki addu'a, hankalinta yana kan ki, Allah ya yi miki albarka". "Wai ba zan sake ganinta ba?" "Zaki sake in sha Allah, Allah ya shiga lamarin ki" Rirriƙe hannunsa tayi tana kuka, tana yi masa magiyar ya tafi da ita. Da ƙarfin tsiya kawu Ilyasu, ya fizgi hannunta, ya angizata zuwa cikin gida. Tana kuka suka ƙarasa shashinsu, sai dai da munanan kalaman iya ta fara cin karo, tana ɗaga murya tana cewa "Ni dai azo a nema mini magani, a rabani da wannan dangin maitar da jaraba, sun kashe mini ɗa suna bibiyata saboda ƴar su na hannuna, ba dole mariya ta haukace ba, ai kaɗan ta gani, hauka bata ma fara shi ba, tun shekarun baya da na karɓi ƴar ba ta yi haukan ba sai yanzu, Allah ya ƙara tuburata, yadda ta rabani da ɗa na babu ita babu sukunin duniya!!". Bright pens fans group, da sauran masoya ummin Iya, ina ganin sharhinku, ina godiya sosai da sosai 🙏🙏🙏 Ayshercool 08081012143                          *CUTARWA!* BRIGHT PENS (FREE BATCH) arewabooks ayshercool7724 Watpad ayshercool7724 Subscribe my YouTube channel https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels P7 A guje mama ta koma tsakar gida, tana ƙwalawa malam kira, a kan ya zo ya ga abun da mariya take yi. Suka dawo a tare, ya tarar da yadda jikinta yake ta rawa tana jijjiga, ya fita da sauri, aka nemo maƙwabcin su, kasancewar yana da abun hawa, aka saka mariya a mota suka tafi asibiti. Can kuma hashim ne ya fito zai fita titi, ya hango yara sun yi dandazo, har zai wuce ya hango ƙafar ummi, ya ƙarasa da sauri, ya tarar da ita a kwance, yara sun yage mata hajjabi, ta sanya hannayenta biyu ta rufe kanta, sai kuka take yi. Wani irin baƙin ciki ya turnuƙe masa zuciya, ya rasa dalilin da ya sanya yara suka tsani ummi haka, kodayeke iyayensu suka gani suna yi, da sun tsawatar musu da tarbiyantar da su a kan girmama halittar ɗan Adam komai muninta, da ba su yi mata wani abun ba. Kai tsaye ya je ya tarwatsa yaran, yayi nasarar kama auwwalu, ya din ga kifa masa  mari, yana ball da shi, yayi masa dukan tsiya, sannan ya ɗaukko ummi ya shiga da ita gida. Gaban iya ne ya faɗi ganin yadda ya shigo da ummi, ta miƙe tana faɗin lafiya?. "Wallahi auwwalu ne ya tara yara, suka cire mata hijjabi suka yi ta dukanta a waje" "Saboda iskanci, me tayi masa?" "Oho masa" "Kema uban waye ya ce ki fita?" Tayi maganar tana kallon ummi, da take ta zirarar da hawaye. Ya ce "Dan Allah iya ki yi haƙuri, a jigace take, jikinta zafi rau da zazzaɓi" Ya karkaɗe mata ƙasar nan, ya samu ruwa ya din ga shashshafa mata a jikinta, ya kaita ɗakin gwaggo ya kwantar da ita. Iya kuwa mita take tana "Na rasa wannan baƙin jini na yarinyar nan, ƴa sai ka ce mujiya, ƴan uwanki yara ma gudunki suke yi, kodayeke ai dole a guje ki, wannan munin gaba ɗaya kalarki ba irin ta mutane ba" Hashim bai kula iya ba ya fice, saboda haushinta da yake ji, dan ya fara tsinkewa da lamarin son zuciyarta, gashi babu wanda zai iya tarar ta ya gaya mata gaskiya kowa tsoronta yake ji. Duk yadda likitoci suka yi ƙoƙarin ceto ran mariya da yaronta, Allah bai yi ba, yaron ya zo babu rai, kuma alamu sun nuna ya kwan biyu da mutuwa a cikin ta, saboda yadda fatarsa ta fara marmasowa. Sai dai har kusan kwana biyu da haihuwar ta, an kasa samo kanta yadda yakamata, da magani ya sake ta sai jini ya sake hawa. Sai suka shafe sati uku a asibiti, sannan aka sallame su, suka koma gida, sai dai abu idan ba ya zama dole ba, ba ta magana. Tunani kawai take yi, ko ta saci jiki ba a sani ba ta je ganin ummi, amma ta tuna wulaƙancin da iya ta yi wa yayyenta, ta san muddin ta je, ba abun da zai sauya, kuma hakan tamkar watsawa mahaifinsu da yayyenta ƙasa a ido ne. Ummi ba wanda yake kula da bata magani, sai idan magaji ya shigo sashin Iya, ya sanya ta a gaba ta sha, duk da iya ta ƙwace kuɗin da kawunsu ya bawa ummi, da kuɗinsa ya saya mata yadin uniform, ya canza mata nata da suka yayyage suka yi mata kaɗan. Ummi ta ji daɗi sosai da sosai, ga sabuwar jakarta dan haka cike da ƙwarin gwiwa take zuwa makaranta. Kafin kwana bakwai, tuni kan ummi ya cika da gashi, kamar ba ayi mata aski ba, kalar wanda ya fita kalar sa ne dai yake sake fitowa a kanta, ba baƙi ne wuluk ba. Duk wannan murnar da take yi na komawa makaranta, da tarin ƙoƙarin da ummi take da shi, ya zama a banza, saboda ko tambaya aka yi a aji, ba ta iya bayar da amsa, saboda gudun cin zarafi da tsokana da ƴan uwanta ɗalibai za su yi mata, koma malaman da kansu. Wujiga-wujiga ta dawo daga makaranta, saboda azabar yunwa, koko ne kawai a cikin ta, shima tun sha ɗaya da tayi fitsari, take jin kamar an sace mata kayan ciki saboda yunwa. Da ƙyar ta ƙarasa gida, tana zuwa iya ta ɗora mata kai niƙa, haka ta kuma kwasar rana, ta kai wa iya niƙan ta dawo, a wannan wahalen da take, wannan ya ja ya aika, wancan ya ja aika, har lokacin shiga makarantar allo yayi. Iya ta rage mata abincin rana, bai fi loma uku ba, a loma ɗaya da kaɗan ta cinye, ta tashi ta tafi makarantar allo. Naima ce ta hangota tana share hawaye da hijjabinta, ta ƙarasa in da take ta ce "Ummi, ya aka yi ki ka makara? Kuma kukan me ki ke yi?". Cikin kuka ta ce "Malam babba ne ya dake ni, na makara" "To meyasa ki ka makara?" "Iya ce ta aike ni" "Shegiyar mata, mai zuciyar kafirai" Naima ta faɗa a ƙule, ummi kuma ta kalli fuskar naima tana mamakin yadda take zagin babba kamar iya. Ta ja hannunta ajinsu, ta ɗaukko wani ɗan kwano ta bata abinci, aikuwa hannu baka hannu ƙwarya ummi take danna abincin. Na'ima ta dubi ummi ta ce "Ya jikin amma dai kin warke ko?" Ummi ta ɗaga mata kai alamar eh. "Gashin ya fara fitowa?" Ummi ta saka hannu ɗaya ta buɗe mata kan, Na'ima ta rufe mata ta ce "Masha Allah, ya fara fitowa, kin wanke kayanki na makarantar boko?" "A'a yaya magaji ya saya mini sabon uniform na makarantar boko" ta faɗa cike da jin daɗi. Na'ima ta ce "Alhamdilillah, Allah ya saka masa da alkhairi, na bayar a ɗinka miki atamfar bikina" Ummi ta kalleta ta ce "Biki, aure kenan?" Na'ima ta ce "Eh, aure zan yi ko in tafi da ke gidana?" "Eh yaya Na'ima zan biki dan Allah" Na'ima ta ciro ɗan ƙaramin tsumma a jakarta da ruwa a jarka, ta bawa ummi ta sha, sannan ta shiga goge mata hannu ta ce "Zan so ace za a bani ke na tafi da ke ummi, sai dai hakan ba zai yiwu ba, ki je aji idan an tashi ki jirani mu tafi tare, zamu je gidan mansura, an kawo mata takalma daga Kano, idan da wanda zai yi miki, sai na saya miki na biki" Ummi ta ce"Ba zaki tafi da ni ba?" "Ki yi haƙuri ummi, ba zai yiwu ba" "Kema tafiya zaki yi ki bar ni? Mama ma ta tafi taƙi dawowa" Na'ima ta yi ajiyar zuciya ta ce "Maza je ki ajinku, ga malam can ya tafi" ta miƙar da ummi tsaye, ummi ta tafi ajinsu. Naja da take ƙawar na'ima, ta ce "Ke dai ki na son yarinyar nan naima, gashi kin saka mata ran tafiya da ita" Na'ima da hawaye ya taru a idonta ta ce "Wallahi naja ina tausayin ummi sosai, wallahi da za a bani ita zan ɗauke ta, kakarta matsiyaciyar tsohuwa ce, ai babarta uwar ɗakina ce, mun yi mutunci sosai, baban ummi ya rasu, ta koma garinsu, Kakarta ta ƙwacw ta take azabtar da ita, ko a lahira na ganni gani g matar nan na san ban yi kyakkyawan ƙarshe ba" Duk da a ƙufule Na'ima tayi maganar, bai hana naja dariya ba, saboda maganar ta ta ƙarshe ta bata dariya. Bayan tashi daga makaranta, tare suka tafi da ummi, hannunta cikin nata suna tafe tana yi wa ummi hira, tana bugun cikinta, dan jin zaman da take yi, sai dai abun babu daɗi mussman da ta gaya mata abun da su auwwalu suka yi mata, da aka yi mata aski. Na'ima ta ce "Bakomai Allah ya isanki wallahi, duk wanda yayi nagari kansa,. Ki yi ta haƙuri kin ji ummi, duk tsanani duk yunwar da ki ke ji, kar ki bari wani a mazan gidan ku, manya ko yara, su kai ki wani wuri, su saka hannu a jikinki, kin ji ko?" Maimakon ummi ta amsa sai ta ɗaga kai tana kallon na'ima. Cikin sauri na'ima ta tsaya ta ce "Suna yi miki wasan banza ko?" Ummi ta girgiza kai ta ce "A'a" "Ki gaya mini gaskiya, suna taɓa ki ko?" Ummi ta girgiza kai ta ce "A'a" "Duk wanda ya saka hannu a cikin jikinki, kar ki yadda kar ki tsaya, ki yi masa ihu ki gudu kin ji ko" ta jinjina mata kai alamar eh. "Ko bayan na tafi, idan kina jin yunwa, ki je gidanmu wurin babarmu ta baki abinci" Da haka suka ƙarasa gidan mai takalmi, aka yi sa'a aka samu dai-dai ƙafar ummi. Na'ima ta ce "Zan ajiye a wurina, ranar bikina in yi miki kwalliya ko?" Ummi ta ɗaga kai tana murmushi, daga nan suka ƙarasa gida. Ummi ta shiga gida hannunta riƙe da wani kara tana wasa da shi "Ke!" Idris ya kwaɗa mata kira a wulaƙance. Ta juyo tana kallon sa. "Zo ki sayo mini sukari a kanti" yayi maganar yana watso mata kuɗi. Ta durƙusa ta ɗauka, ta je ta sayo masa, sai dai ta din ga tuna gargaɗin Na'ima na hanata zuwa ɗakin su idris. Ta nemi wuri ta zauna a ƙofar shiga wurin, ya gaji da jiranta ya fito. "Dan ubanki ina aiken da na yi miki?" Da sauri ta miƙe tana nuna masa sukarin. "Ba zaki shigo ki kawo mini ba saboda baki da mutunci, sai ki nemi wuri ki zauna?" Tayi shiru tana kallon sa, "Ba zaki kawo mini ba" ya sake yi mata maganar cikin tsawa. Ta ƙarasa in da yake cikin jin tsoro, sai dai ya ya haɗa da hannunta, ya ja ta cikin ɗakin. Kuka ta fara yi masa iya ƙarfin ta, yau ya samu damar da rabonsa da ita an daɗe, amma ta nuna masa tayi wayo yanzu, dan haka ta din ga yi masa kuka da ƙarfi, kamar yadda Na'ima ta gama gaya mata ɗazu. Wawan marin da ya kifa mata ne, ya tafi da ji da ganinta na wani ɗan lokaci, ta dafe kuncinta jikinta na wata irin tsuma, tana karkarwa. Wata sharɓeɓiyar wuƙa ya nuna mata ya ce "Ki ka cigaba da yi mini kuka, sai na yanka wuyanki" kallonsa take yi, kallo mai cike da tsoro da tsana, ya ajiye wuƙar tare da sanya hannayensa cikin rigarta, rigar da bakomai a ciki sai teɓa dan wannan dai ba nono bane. Ba ta karaya ba, ta fara kokowar cire hannayensa daga jikinta, tana kuka mai cin rai, iya ƙarfin ta. Bankaɗo ƙofar ɗakin aka yi, hakan ya razana shi, dan bai yi zaton zuwan wani a dai-dai wannan lokacin ba. "Idris meye haka?" Hashim yayi maganar yana kallon sa. "Kamar yaya meye haka, abun da ka gani" a fusace ya ƙarasa ya hankaɗe idiris, ya janye ummi, ya kalli idiris ya ce "Wani irin banza ne kai, ba zaka girma ba a rayuwarka, da me yarinyar nan za ta ji ne?" Wani uban tsaki idiris yayi, ya ce "Ka daina shiga sabgata ba ruwanka da ni". "an shiga sabgar taka, wallahi idan baka rabu da yarinyar nan ba, sai na ɗauki mummunan mataki a kan ka" "To ka ɗauka mana kar ka fasa" ya sake jan tsaki ya fice. Cikin ƙunar ran yadda ƙaninsa ya raina shi, duk saboda iya na goya masa baya, ya kalli ummi ya share mata hawaye, ya fito da ita daga ɗakin, shaidar yastun idiris kwance a kan baƙar fuskarta, da har idonta yayi taruwar jini. Ya zubawa ummi ido, da haryanzu jikinta yake tsuma, ga wata irin nannauyar ajiyar zuciya da take yi, har a lokacin a tsaorace take, kuma hawayenta ya ƙi tsayawa. "Ummi" ya kira sunanta, sai dai bata amsa ba, ta sake fashewa da kuka. Wani irin tausayinta ya ratsa zuciyarsa, ya din ga share mata hawayen, ya riƙe hannunta suka nufi sashin iya, tana ta dakan fura tana waƙe-waƙe. Tana ganinsu tare ta hau bala'in tun ɗazu take neman ummi, zata aiketa amma daga zuwa makaranta ta zauna. Magaji ya ce "Iya" "Ya aka yi" "Dan Allah idan ba za a iya riƙon yarinyar nan ba, a mayar wa da uwarta ita, idiris fa na kama yana neman haike mata a ɗakinmu, wace irin rayuwa ce wannan, kalli yadda ya mare ta, haba dan Allah" Iya ta dafe ƙirji ta ce "Shi idiris ɗin? Ita uban me ya kaita in da yake, me ya kaita ɗakin ku, ai ita ta kai kanta, amma shima zai zo ya same ni, da ni yake zancen. Kai kuma sai ka ce ba ɗan uwanka ba, ka ke ɗaga murya tona masa asiri zaka yi?" "Iya to zuba masa ido za ayi, idan abun da ba a so ya faru fa?" "Ba abun da zai faru sai alkhairi, jeka zai zo ya same ni, ke kuma canza kayan ki zo ki kai dusar nan gidan lami, ta bawa dabbobina" Hashim ya ce "Ni bani dusar na kai, kalli yadda take a razane" "Ba wani a razane, da a razane take ai da ba ta kai kanta ba, yarinya ƙanƙanuwarta da ita, ta san ta je wurin namiji" "Haba iya, me ummin ta sani da zaki faɗi wannan mummunar maganar a kanta?" Iya ta ce "Zaka zo ka kai mini dusar ko ta ɗauka ta kai mini?" Ya ƙarasa ya ɗauki dusar ya fita, zuciyarsa kamar ta tarwatse, tausayin yarinyar na damunsa sosai da sosai. Kwanaki biyu tsakanin abun da ya faru, sannan idiris ya shigo sashin Iya. Iya ta dube shi ta ce "Idris, kashedi zan yi maka a kan yarinyar nan, kar ka kuskura ka sake saka yarinyar nan a loko kana lalubeta, wallahi idan ka sake wani abu ya afku ba zan rufa maka asiri ba, kuma ba zaka janyo mini masifa ba, kai gashi ba sana'a ba balle ace ayi maka aure, in huta. Ina yi maka kashedi, wallahi wani abu ya faru ba zan saurara maka ba, na gaya maka" Cikin fushi ya ce "Me kuma na yi, magaji ne ya zo ya ce na yi mata wani abu?" "A'a ni banga magaji ba, bai gaya mini komai ba, fuskanta kawai na yi" Ficewa yayi ba tare da ya sake magana ba. Rashin samun biyan buƙatar sa a jikin ummi, ya sanya ya ji ya ƙara tsanar yarinyar, ko son ganinta ba ya yi, ita kanta ummi, har fargaba take yi a aike ta, saboda bayan iya ta yi masa wannan faɗan, sai da ya zane ta, saboda a zaton sa ita ta gaya wa Iya. Duk wannan cin kashin da ake yi wa yarinyar, daga ƴan uwan ubanta da suke ciki ɗaya, da wanda uba suka haɗa da matayen su, babu wanda ya taɓa shawartar iya a kan sassautawa ummi azabtarwar da ake yi mata, tamkar ƴar tsintuwar da ta faɗo daga sama. Azumi saura wata biyu, aka yi bikin na'ima, ta yi kuka sosai, ciki har da na rabuwa da ummi, dan har cikin zuciyarta take jin rabuwa da ummi. Mariya kuwa tun ƴan uwanta na ta tata, suna rarrashin ta, suna bata haƙuri, har suka zubawa sarautar Allah ido suka ƙyaleta, ta riga dai ta kamu da larurar hawan jini, a hankali kuma ciwon damuwa ya fara addabar ta, kullum tana ɗaki, daga bacci, kuka sai shiru. Yaya ɗan lami ya fara tunanin ko ta koma makaranta, amma yanayin da take ciki, ya tabbatar masa da ko an mayar da ita makarantar ba za ta iya mayar da hankali ba. Dama labarin haihuwar ta ta ko su iya ba a gayawa ba, dan gaba ɗaya sun fuskanci sabgar Iya babu Allah a cikinta. Yaya ɗan lami kuwa da suka ga mariya taƙi sakin ranta, ya ƙare mata cin mutunci, tare da tabbatar mata da muddin ta je wurin su Iya babu su babu ita, ƴa ce idan ta girma da kanta za ta neme ta. Watan azumin ramadana ya kama, wanda hakan ya sake jefa ummi tsaka mai wuya. Ba iya azumi take yi ba, dan haka babu mai kulawa ya bata abinci, haka za ta yi ta gararanba ta wuni a kwance, idan makaranta ta je, tana kallo yara na ciye-ciye, ita ba raɓar su take yi ba ma, balle ta yi musu kwaɗayi, ko kuɗin makaranta ba bata ake yi ba, dan haka bata saba da kashe-kashen kuɗi ba. Sai an sha ruwa take samu ta ci abinci, sai da hashim ya fuskanci ba ta samun abun da za ta ci da rana, shi ne yake rage mata abincin sa, da safe ya bata, da rana ya sai wani abun ya bata. A haka har aka ƙare azumi. Da salla kowane ɗa cikin kyakywar shiga mai kyau, ummi kuwa kayan bikin na'ima ta saka, da suka fara koɗewa, da takalmin makarantar da kawunsu ya saya mata, shi ta koma tana sakawa tayi yawo da shi a gari, saboda ko silifas ba ta da shi, wanda naima ta saya mata tuni ya lalace. Yara na ta shiga su na fita, ummi kuwa na ƙofar ɗakin mamanta, ta zauna tana wasa da duwatsun wurin. Hashim yayi sallama, ummi ta amsa cikin ƴar siriyar muryarta. Ya ƙarasa in da take zaune, ya ce "Kin je sallar idi ne?" Ta girgiza kai alamar a'a. "Me ki ke yi a nan wurin?" Ta ce "Bakomai" "Kin ci tuwon salla kuwa?" Ta ce "A'a iya dai ta ce zata bani" Ya miƙa mata hannu ya ce "Taso mu je" Ta saka hannunta a nasa, ya ja ta zuwa sashin mahaifiyar sa. Babansa ma, da ake cewa baba sagir, yana zaune yana cin abinci. Ummi ta durƙusa ta gaishe shi, ya amsa mata babu yabo ba fallasa. Ya ce "Yaya a zubawa ummi abincin salla dan Allah" Ta ce "Ga maimuna nan, ya zuba mata" ta kalli ummi ta ce "Ke ummi baki da kayan salla ne, ki ka saka wannan koɗaɗɗiyar atamfar?" Ummi tayi shiru tana kallon ta. Aka kawo wa ummi abinci, ya saka ta wanke hannunta, ta zauna ta saka tuwon sallar nan a gaba tana ci, tana yi tana kallon yadda yara suka yi kyau sosai a sababbin kaya. Ta gama ci ta hau tattara musu kwanukan wanke wanke, ta share musu tsakar gida. Hashim ya dawo sashin, ya tarar da ummi ta haɗa kwanukan wanke-wanke. "Me kuma zaki yi?" "Wanke-wanke zan yi". "Ke yara na can waje suna tsalle-tsalle, suna wasanni, amma ke kina nan ki na haɗa wanke-wanke, ki je ki yi wasanki sa yi wanke-wanken da kan su" "A'a bani da kayan salla, idan na fita tsokanata za ayi, su ce mini baƙa" tayi maganar tana ƙoƙarin jan kujera ƴar tsuguno tayi wanke-wanken. Shiru yayi yana kallonta, cikin tausayawa. Yana zaune yana kallonta, gata yarinya ƙarama amma ta riga ta saba da wahala, yadda yake wanke manyan kwanukan da aka ɓata da miyar abincin salla. Wata ragowar miya da ta rage, ta zuba mata ruwa zata zubar, idirisa ya kawo kai ta watsa masa a jikinsa. Ayshercool 08081012143                     *CUTARWA!* Watpad ayshercool7724 Arewabooks ayshercool7724 YouTube https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels What's app 08081012143 *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* BRIGHT PENS (FREE BATCH) P8 Tuni ummi ta zabura, ta jefar da kwanon hannunta, jikinta ya hau rawa, a fusace ya ƙaraso kan ummi, yayi ball da ita ta hantsila cikin kwanukan da take wankewa. A cikin azama hashim ya ƙarasa, ya hankaɗe idiris, yana faɗin "Idirs meye haka?" "Ban gane meye haka ba, ba kaga abun da ta yi mini ba? Dabbar ina ce? Ko makauniya ce?" "Kai za a cewa dabba,  ya za ayi ka shigo babu sallama, ya za ayi ta san da zuwan ka? Idiris zaluncin da ka ke yi wa yarinyar nan yayi yawa fa" Ummi kuwa karo tayi da ƙafar tukunyar ƙarfe, fiƙarta ɗaya ta karye, nan da nan bakinta ya rine da jini, kuka take yi sosai, saboda ciwon buguwar da tayi, har cikin kanta take jin azabar ciwo. Babarsu da ta jiyo hayaniya ta fito tana faɗin "Wai lafiya ku ke yi mini hayaniya da tsakar ranar nan?" Idonta ya sauka a kan ummi, da yawun  bakinta ya gauraye da jini". "Ita kuma wannan meya sameta?" "Ga wanda ya yi ball da ita cikin kwanuka nan" Hashim yayi maganar cikin takaici, yana nuna idiris. Nuna wa mahaifiyarsu kayansa yayi, da ummi ta ɓata da miya. Hashim bai tsaya jin abun da mahaifiyarsu za ta ce ba, ya ja hannun ummi, ya tafi da ita. Sun sha yawo sosai, kan su samu chemist, kasancewar salla ce, aka bawa ummi magani. Haka aka gama bikin salla, ummi ba kayan salla sai jinyar baki, da ya sanya ta ciwon kai sosai da sosai. *** Mariya na zaune a ɗaki tana ninkin kaya, fuskar nan kamar wadda aka yi wa mutuwa, tana jiyo hirar da mama, da jimmai maƙwanciyar su suke yi, wadda ƴar ta aka kai gagarawa, suka haɗu da balarabe suka yi aure. Tana bawa mama labarin ƴar ta mijinta ya samu sauyin wurin aiki zuwa ikko, sun bar gagarawa. Mariya ta yi shiru, tana tunanin ya aka yi ba tayi tunanin ta din ga bayar da abu, idan an samu mai zuwa gidan ƴar jummai a kai a bawa ummi ba. Sai dai ta tuna ba shiru suke yi ba, dan ƴar gidan jimmai, tana ganin tana auren mai kuɗi mijinta ɗan sanda ne, idan suka haɗu da mariya a hanya, kamar ba su san juna ba, saboda yadda take jin kanta. Tunaninta ne ya katse lokacin da ta jiyo jimmai na cewa "Ai nan asalamiyya ke bani labari, ƴar da mariya ta baro, wahala kawai take sha, ranar ta ganta ko takalmin kirki babu a ƙafarta, na ce ta ɗan din ga taimaka mata, to kin ga ma yanzu sun bar garin, na ce da kun je kun ɗaukko yarinyar nan" Mama ta ce "Da zai yiwu da anyi hakan ai, ba yadda ba ayi ba su bayar da Yarinyar sun ƙi, shiyasa muka ƙyalesu, ba su da mutunci ko kaɗan, da aka je musu da maganar cikin mariya, cewa suka yi ba nasu bane ba, shiyasa malam ya ce babu mu babu su, a ƙyale su idan yarinyar ta girma ta nememu" Jimmai ta ce "Ashsha! To Allah ya kyauta". Mama ta amsa da "Amin" Mariya ta ajiye ninkin, ta haɗa kai da gwiwa ta din ga kuka. Bayan tafiyar jimmai, mama ta shiga ɗakin, dan ta san mariya na jin su, ta ce "Mariya na san kin ji abun da jimmai take faɗa, amma haƙuri zaki yi ki kawar da kanki, ki sakawa zuciyarki salama a kan yarinyar nan, idan ba haka ba kuwa ciwo zai cigaba da cin jikinki, kin san dai ki na da hawan jini"  shiru mariya ta yi, ta cigaba da rera kuka, mai ƙona zuciya, tana ji a ranta ba zata taɓa yafe wa Iya ba. An doshi shekaru huɗu, da rasuwar Bashir, ummi ta cigaba da rayuwa ba tare da ta sake sanya idonta ana mahaifiyarta ba, tamkar baiwa a cikin gidan nan haka take rayuwa, babu gata babu kulawa, wahala ta yau daban ta gobe daban, ga Iya ta tsiri yi mata kunu ranar asabar da lahadi ta kai kasuwar garin, ta sayar mata, har ma wasu su yi abun sayarwar su a gidan su haɗa mata. Babu yadda Hashim bai yi da iya ba, a kan ta daina ɗorawa ummi tallar nan, azabar da take sha tayi yawa, amma iya ta zage shi tsab, ta ce idan ya cigaba da yi mata katsalandan, za ta ci mutuncinsa ta tsine masa. Babu kunya ba tsoron Allah, Iya ta saka aka ɓalle ƙofar ɗakin mariya, aka kwashe kayanta aka sayar, ta karɓe kuɗin, wai da su zata tarawa ummi kayan ɗaki, ɗakin ya zama wurin tara itace, hatsi da sauran shirgi. Ummi ta dawo daga makarantar boko, takalminta ya kusa rabewa biyu saboda tsufa ƙasansa kuwa ya huje, malaman su, sun gaji sun ƙyaleta, ƙafarta futu-futu. Ta tarar da Iya a tsaye tana jiran isowarta. Jiki a sanyaye ta ƙarasa in da Iya take, ta ce "Iya laifi na yi ne?" "Au tambayata ma ki ke yi, saboda tsabar kin shahara, nan gaba makami zaki fara nuna mini, ki yi mini ƙwace, kuɗina zaki bani da saminu ya zo jiya da daddare, ban gan su ba, kuma daga ni sai ke a ɗakin" Gaban Ummi ya faɗi, ta girgiza kai ta ce "Wallahi iya ban ɗauka ba, ki sake dubawa". "Ni ki ke gaya wa na sake dubawa? Ƙarya zan yi miki kenan? Ki zo ki bani kuɗina kan jikinki ya gaya miki" Ummi kawai tayi shiru tana kallon iya, dan ta rasa me za ta ce mata ma, ta san kawu saminu ya bata kuɗi jiya, amma ba ta san ma a ina ta ajiye su ba. "Au saboda kin mayar da ni ƴar iska ki ka tsaya kina kallona, ba zaki bani kuɗina ba?" Ummi ta sunkuyar da kai, dan gaba ɗaya kanta ya kulle. Iya ta saɓa mayafi ta fice, jiki a sanyaye ummi ta ƙarasa cikin ɗakin iya, ta hau duddubawa, ko za ta ga in da Iya ta ajiye kuɗin. Maganar Iya ta jiyo da idris ta ce "Ka tambayeta ina ta kai mini kuɗi, ka yi ta dukanta, har sai ta faɗa" kan ummi ta ankara sai ganin idiris ta yi a kan ta, hannunsa riƙe da manyan reshen bishiyar darbejiya. Kafin ta yi magana, ya shiga shimfiɗa mata tsumagiyar nan a jikinta, gashi ya tare duk wata hanya da zata bi ta fita. Kasancewar dama haushinta yake ji, ya sanya ya zage duk wani ƙarfin sa, ya dinga jibgarta, har da taka ta da ƙafa. "Fito mini da ita daga ɗaki, ɓarauniyar banza da ta wofi, kuma daga yau kin bar kwanar mini a ɗaki" a ƙasa haka ya din ga jan ummi, ya fito da ita tsakar gida. "Ga ɗakin uwarta can da ake tara itace yanzu, rufe mini ita a ciki, ko abinci kin daina ci, sai kin bani kuɗina" Haka kuwa aka yi, idris ya rufe ummi a ɗakin mariya, da yanzu ake tara itace da hatsi a ciki, ya rufe ɗakin bisa umarnin iya. Ummi ta kwanta a ƙasa, jikinta sai zafi yake yi, hannunta da Idris ya din ga hauri da ƙafarsa, tamkar ba a jikinta yake ba, hannun yayi sanyi ga ciwo yana yi nata. Sai da ummi ta kwana ta wuni a cikin ɗakin nan, shima magaji ne ya ga baya ganinta, ya matsa da tambaya, su Alhassan suka ce masa ai Iya ta sacewa kuɗi dubu goma sha biyu, ta saka idiris ya zane ta, aka kulle ta a ɗaki. Hashim ya ji kamar ya ɗora hannu a ka yayi ihu, ya buge kwaɗon, ya tarar da ummi a zaune a takure wuri ɗaya, saman idonta ya kumbura, ko ina jikinta rauni ne. Dogon gashin nan duk ya kwashi datti da karare. "Ummi" ya kira sunanta, ta ɗago ta kalleshi ta sunkuyar da kai. "Da gaske kin ɗaukar wa iya kuɗi" Ta girgiza masa kai, ya ce "Na san ba zaki ɗauka ba ummi, yi haƙuri taso ki fito" Ta girgiza masa kai ta ce "Dan Allah yaya magaji ka ce Allah ya sa na mutu, bana son zama da iya, dan Allah ka kai ni wurin mama, wallahi zan mutu" tayi maganar tana sheshsheƙar kuka. Ya kalleta yarinya shakaf, amma tana iƙirarin ta mutu, "Ba zaki mutu ba, wuya bata kisa ummi, tashi kar wani abun ya cije ki" Da ƙyar ya fito da ita daga ɗakin. Iya kuwa duk ta gama barbaɗawa mutanen gidan ummi ta sace mata kuɗi. Ko kallonsu Iyan ba ta yi ba, ya nemo abinci ya bata, ya ce tayi wanka. Tana banɗaki, Hashim ya samu Iya ya ce "Iya dan Allah meyasa ba kya ƙaunar ummi ne?" "Kamar yaya, in haifi ubanta ka ce bana son ta? Tarbiyya nake bata, uwarta na tsana ne, bana ƙaunar uwarta ne, kuma alamu sun nuna halin uwarta ta yi" "Ba wannan ba, Iya kin duba ɗakin nan da kyau baki ga kuɗin ba? Ummi bata taɓa yi miki sata ba fa?" "In ji uban wa? Faɗa ne kawai ba na yi, amma sata kam ba yau ta fara ba, kamar ta sha nonon ɓeranya" Zai yi magana ummi ta fito daga wankan, tana ɗingisa ƙafarta. Bai cewa iya komai ba, ya tashi ya bata kujera ta zauna, ya kamo hannunta da ya kumbura, ya fara matsawa a hankali. Nan ta din ga yarfe hannu tana kuka. Fatar ummi duk wannan wahalar da take sha, jikinta tamkar auduga saboda taushi. Iya ta watso mata ƙullin kayanta, ta ce sai dai ta koma ɗakin itace ta cigaba da zama. Babu magiyar da magaji bai yi mata ba, amma ta ce bata san zancen ba. Da kansa ya share wa ummi ɗakin, ya samo buhu ya shimfiɗa mata, ya kawo tabarma ya shimfiɗa mata, ya din ga rarrashin ta, yana bata haƙuri, ji yake kamar ya zauna ya yi wa ummi kuka. Iya ta aika a kirawo mata Alhassan zata aike shi, ta ce ya duba ƙasan katifarta ya ɗaukko ɗari biyu, Alhassan ya fito da wata leda a hannunsa ya ce "Iya ba wannan kuɗin ki ke nema ba?" A razane ta karɓa tana ƙifta masa ido, gaba ɗaya ta manta ina ta ajiye su. Hashim yayi kamar bai ji me ta ce ba, haka ummi, sarai ummi ta ji Alhassan yana gaya mata kuɗinta, duk wasu kalaman rarrashi, sai da Hashim yayi amfani da su, wurin ba wa ummi haƙuri, saboda ƙarfin hali, har da Murmushin ta, tare da ƙoƙarin nuna bakomai. Da daddare ya sayo gyaɗa da rake, ya kai wa ummi, duk cikin son ya ƙara rarrashin ta, ya daɗe yana sake kallon ɗakin da zata kwana a ciki, babu ko fitila a ɗakin, kuma ba za a rasa ƙwari masu cizo a ciki ba. Ya kalli ummi ya ce "In sha Allah zan sayo miki fitila, sai ki din ga haskawa, sannan tun yamma ki din ga karkaɗe ko ina, ki tabattar babu wani abu a ɗakin kan ki kwanta". "To yaya na gode" ya jinjina mata kai ya fice. Iya tana kallonsa daga tagar ɗakin ta, yanayin yadda yake shishshigewa ummi, abun ya fara ƙular da ita, dan haka tayi ƙwafa, tare da aniyar ɗaukar mataki a kansa. Sai dai can ƙasan ranta, ta ji babu daɗi ganin kuɗin da aka yi, gashi ta riga ta saka an zane ummin, an rufeta a ɗaki kwana da wuni, ba tare da hakkinta ba. Haka nan abun ya din ga damunta, da safe ummi ta je har ɗaki ta gaisheta, da uniform za ta tafi makaranta. "Kin karya ne zaki tafi makaranta?" Ummi ta ce "A'a" "Ki je wurin sa'adatu ta zuba miki kunu idan ta dama" ummi ta ɗan yi shiru ta tuna yadda sa'adatun ke haɗe rai idan ta je karɓar kunun. Ummi ta ce "Na san idan na je ya ƙare" Iya ta bankaɗa ɗan tofinta, ta ciro naira ɗari, ta ajiye wa ummi ta ce "Gashi nan ki sai waina a hanya ki ci" Ummi ta kalli kuɗin, tana wani irin murmushi da ita kaɗai ta san ma'anarsa, ta miƙe tsaye idonta fal hawaye ta ce "Ki bar shi iya, idan na dawo na ci abincin" tayi waje. Tana jin Iya na zazzaga mata masifa, tana zaginta, amma tayi waje tana share hawaye. "Ƴar ƙanƙanuwarki da ke, kin san munafunci, to kin yi wa kanki, halin uwar taki da nake ta gudu sai da ki ka kwaso shi? To ki ci kanki, da ke da mugun halin naki" Haka iya ta cigaba da sababi da kame-kamen borin kunya. Ummi na tafe a hanya tana kuka, haka ta ƙarasa makaranta, suna ta shirye-shiryen shiga sakandare, sun kusa zana jarrabawar common entrance, shi ma kuɗin jarrabawar da ƙyar, ta biya, shi ma Naima ce ta zo gida, ta sa aka kirawo ta, take ta yi mata tambayoyi da ƙyar ta gaya mata batun kuɗin jarrabawar. *** Manema na ta zuwar wa mariya, duk da ba fita take yi ba, amma mariya tayi burus, mahaifinta ya kaɗa ya raya, amma taƙi tsayar da kowa, da yayi mata zancen auren ma sai ta hau koke-koke. Yayi ta rarrashin ta, a tunanin sa ko saboda tsohon mijinta ya sanya take jin ba zata sake yin aure ba, yayi nasihar, yayi rarrashin saboda kusan shekaru huɗu kenan rabonta da aure. Kuma shekarun nan huɗu cif, ita ba mai lafiya ba ita ba mara lafiya ba. Takura mata da maganar aure, ya sanya ta daina cin abinci ma, ta ƙara tsananta kaɗaice kanta, ga rashin barcci da ya sarƙafe ta, ta wuni ciwon kai dare yayi ta kasa bacci. Tsananin ciwon kai ya sakata a gaba, gashi tayi shiru ba wanda ta gayawa, abu kamar wasa tun tana daurewa har ta kasa, ta din ga burgima a ƙasa tana wayyo kanta. Sai a lokacin suka san ba ta da lafiya, aka kaita asibiti, sai dai babu cigaba, idan an kaita asibitin sai an tursasata shan magani, idan ta sha ɗin ma babu cigaba, wasu lokutan haka zata riƙe kanta tana ihu, tana kuka saboda rashin iya bacci, idan aka kaita asibiti sai dai su yi ta yi mata allurai. Ƙarshe aka tura su ganin likitan ƙwaƙwalwa, hankalin mahaifin mariya ya tashi da ƴan uwanta, jin an tura su ɓangaren likitan ƙwaƙwalwa. Likita ya duba ta sosai da sosai, ya basu shawarar a kula da ita sosai, saboda depression ne ya kamata, idam ba a kula da ita sosai ba, za a rasa hankalinta gaba ɗaya. Karo na farko da iyalan su mariya suka ji mahaifinsu yayi wa wani ɗan adam Allah ya isa, wanda sai da ya zubar da hawaye, yana matuƙar tausaya wa mariya, dan haka bai gaza ba, ya sake tashin yaya magaji, tare da Maryam, ya ce su je su bawa uwar mijin mariya haƙuri, ko sau ɗaya ta bayar da ummi, ta zo ta kwana biyu tare da mariya, ko a samu hankalinta ya kwanta. Yaya magaji ya ce "Baba, ka san matar nan ba zata bayar da yarinyar nan ba, sai dai a tafi da mariyar, ta je ta ganta mu dawo" Maryam ta ce "A hakan zamu tafi da ita? Ba zai yiwu ba ai, kana kallon abun da take yi, ai salon ta sake jin daɗi ne, dan matar nan ba mutunci ne da ita ba, kuma muddin aka bawa mariya ummi, ba zata bari a sake rabata da ita ba, a ganina kawai mu mayar da hankali a kan nema mata lafiya" Yaya magaji ya ce "Duk da haka, zan jarraba zuwa, duk da na san ba zamu wanyeta ƙalau ba, amma zan jarraba zuwa na ga yarinyar ma daga nan, Allah sarki ummi, na san yanzu ta yi wayo sosai. "Zata shekara goma zuwa sha ɗaya fa yanzu, ai ta zama budurwa" Suka bar maganar a kan cewa, yaya magaji zai je ya gano ummi, idan ya ga fuska ya sako zancen tahowa da ummi. Ummi ta daina zuwa ɗakin iya idan ba dole ba, saboda gudun kar ace ta yi wani abun, kullum cikin itace nan da buhhunan hatsi take kwana. Tsabar daka kuwa hannunta duk yayi kanta, yayi ta ɗurar ruwa yana fashewa, saboda tana da taushin fata sosai. Tana tafe tana yada hannu, saboda gajiya ga rana, yunwa da ƙishirwa duk sun addabeta, mutumin da ta hango a ƙofar gidan su ne tare da kawu Ilyasu, ya sanya ta tafiya a hankali, ta ƙarasa ƙofar gidan. Shi ma ƙuri yayi da ido, yana kallonta, ta ƙarasa ta durƙusa ta ce masa "Ina wuni?" Jiki a sanyaye ya amsa ya ce "Ummi kin gane ni?" Ta jinjina masa kai alamar eh. "To waye ni?" Maimakon ta bashi amsa sai ta ce "Ina mama?" "Haryanzu baki manta da ita ba?" Da sauri Ummi ta sake kallonsa ta ce "Da ita ku ka zo?" "A'a, na zo dai neman alfarmar na tafi da ke na kai ki wurinta, amma sun ƙi yarda" Kawu Ilyasu ya wani haɗa rai, cikin haushi kamar tsohon kare ya ce "Ke! Tashi ki wuce ki shiga cikin gida" Ƙafafuwanta suka yi mata sanyi, ta ji tamkar ba zasu iya ɗaukarta ba" "Ba zaki tashi ba?" Ya sake yi mata tsawa. Cikin rawar jiki ta tashi, yaya magaji ya kamo hannunta ya danƙa mata kuɗi, yana riƙe da hannunta ya kalli Kawu Ilyasu ya ce "Da ku da mahaifiyarku, ku shirya amsar da zaku bawa Allah, kalli wai wannan ƴar ɗan uwanku ce dan abun kunya, kalli kayan makarantar da suke jikinta, kalli ƙafafuwanta. Kun ce idan na tafi da ita babu ku babu ita, ku ba dangin mahaifinta bane ba, duk in da aka je aka dawo, da dangin uba ake ado, kuma ba zan cigaba da jayayya da ku ba, muna raba abun faɗa, Allah zai zama gatan marainiya" "Ummi ki kula da kanki kin ji ko? Ki yi ta yi wa mamanki addu'a, hankalinta yana kan ki, Allah ya yi miki albarka". "Wai ba zan sake ganinta ba?" "Zaki sake in sha Allah, Allah ya shiga lamarin ki" Rirriƙe hannunsa tayi tana kuka, tana yi masa magiyar ya tafi da ita. Da ƙarfin tsiya kawu Ilyasu, ya fizgi hannunta, ya angizata zuwa cikin gida. Tana kuka suka ƙarasa shashinsu, sai dai da munanan kalaman iya ta fara cin karo, tana ɗaga murya tana cewa "Ni dai azo a nema mini magani, a rabani da wannan dangin maitar da jaraba, sun kashe mini ɗa suna bibiyata saboda ƴar su na hannuna, ba dole mariya ta haukace ba, ai kaɗan ta gani, hauka bata ma fara shi ba, tun shekarun baya da na karɓi ƴar ba ta yi haukan ba sai yanzu, Allah ya ƙara tuburata, yadda ta rabani da ɗa na babu ita babu sukunin duniya!!". Bright pens fans group, da sauran masoya ummin Iya, ina ganin sharhinku, ina godiya sosai da sosai 🙏🙏🙏 Ayshercool 08081012143                         *CUTARWA!* *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* BRIGHT PENS (FREE BATCH) P9 Gaba ɗaya Ummi ta ji ƙafafuwan ta sun yi mata sanyi, har suna neman gaza ɗaukarta, tayi ta maza ta ja jikinta ta shiga, kai tsaye ɗakin da take ta wuce, ba ta tsaya a in da Iya ke banbaminta ba. Wucewar ta bai sanya Iya jan baki tayi shiru ba, sai ma haƙiƙancewa da tayi, tana cigaba da masifa "Ni dai na gaji da wannan maitar da masifar, dole in miƙe in nemi tsari da bala'i da tashin hankalin wannan mutanen su daina yi mini sintiri da bibiyata, ba dole mariya ta haukace ba, hakkin ɗa na ba zai taɓa barinta ba, daga haka ma in Allah ya yarda sai ta fara yawo tsirara, ni bai dame ni ba, hakkina da na ɗa na ba zai bar ta ji daɗin rayuwa ba, hauka ma yanzu ta fara ba ta ga komai ba tukuna". Ummi ta ja ta tsaya a cikin ɗakin, tana ƙare masa kallo, kasancewar haddar yaro ƙarami, ba abu ne da yake gogewa cikin sauƙi ba, ya sanya take ummi ta shiga hasaso abubuwa da dama da suka faru a ɗakin nan. Yanayin jeren ɗakin, ƙamshin turaren wuta ɗan tsinke da mamanta ke yawan kunnawa, yadda take zama a kan cinyar mahaifinta ta ci abinci, yadda daren da aka yi mata fyaɗe ya kasance, ko ba komai ummi ke iya tunawa ba, ba ta manta yadda mamanta take iya ƙoƙarin ta wurin yi wa Iya biyayya, ta kalli yadda ɗakin ya zame mata a yanzu baƙi ƙirin, tamkar dajin da wuta ta cinye bishiyun da suke ƙawata shi. Durƙusawa tayi ta fashe da kuka tana sheshsheƙar kuka, tana jin Iya na cigaba da ci wa mahaifiyarta mutunci, tare da yi mata fatan masifa kala-kala da aibantata da sharruka. Ummi ba ta samu fitowa daga ɗakin nan ba, sai daf da la'asar, dan ma Allah ya taimake ta zuwa makarantar allo da take yi, ana horasu a kan kula da ibada, wanda dama ta samu wannan horon daga mahaifiyarta, amma dan ta Iya, ko za ta shekara ba ta yi salla ba, babu ruwanta da ita. Ta yo alwala ta dawo ɗakin tayi azahar da la'sar, ko tunanin zuwa makarantar allon ba ta yi. Tana jiyo yadda duk wanda ya shigo sai Iya ta gaya masa ai Mariya ta haukace, tana can an sakata a turu, hakkin rai yana bibiyar ta, ta fara bi bola-bola tana tsince-tsince. Ummi ta sha kuka, sai da idanunta suka kumbura, dan duk kukan da za ta yi idonta baya ja, sai dai ya ɗan sirka, kuma su kumbura. Ta kalli kuɗin da yaya ɗanlami ya bata, ta watsar da su a tsakar ɗakin, ta ƙanƙame jikinta, tana sauke numfashi hawaye na tsiyaya daga idonta. Ba tsammani ta ga magaji a kanta. "Ummi" ya kira sunanta a hankali. Ta ɗaga kai tana kallonsa. "Kukan me ki ke yi?" "Yaya magaji" "Na'am ummi". "Wai mamana ta haukace?" Tayi maganar wasu hawayen na gangarowa saman kumatunta. "Subhanallah waye ya gaya miki haka?" "Wanda ya tafi da ita ne yazo, shi ya bani wannan kuɗin" Hashim ya ce "Kar ki sake cewa ta haukace, bata da lafiya dai, tana ganin likitan ƙwaƙwalwa aka ce" "Likitan ƙwaƙwalwa? An ce sai mutum ya haukace fa ake kai shi wurin likitan ƙwaƙwalwa" "Ba haka bane ba" "To meyasa Iya take cewa mama ce ta kashe baba, ba hatsari yayi ba?". "Ki daina damuwa da maganar Iya, ki kwantar da hankalinki, ki ta yi wa mamanki addu'a Allah ya bata lafiya" "Dan Allah yaya magaji ka kai ni wurinta, ina son in ganta dan Allah" tayi maganar tana haɗe hannayenta alamar magiya, tana kuka. Cikin matsanancin tausayinta ya ce "Ummi Maiduguri ba nan ba ce akwai nisa, kuma ban san a ina mahaifiyarki take a Maiduguri ba, lokacin da aka aureta muna yara, kuma kin ga ba taɓa zuwa muka yi ba. Amma ki yi haƙuri ki daina kuka, zan bincika miki in sha Allah" "Gidan uwarka zaka bincika mata, munafukin Allah ta'ala, to kar ka fasa, wallahi magaji idan ba ka kiyaye ni ba, sai na hau kujerar tsiya na ci ubanka la'ada waje a kanta, kar ka fasa kai ta inda uwarta take, zaka ga cin mutuncin da zan yi maka, dai-dai nake da kai. Kema tsohuwar munafuka, halin uwarki haka halinki yake, duk wannan ƙoƙarin da nake yi a kanki ba kya gani, da ki ke hannunmu mutuwa ki ka yi? Kowa yazo sai ki ɓare baki, ke a kai ki wurinta, tun da namanki nake gutsura in ci, to ki cigaba kar ki fasa, amma ki sani nayi alwashin yadda mariya ta rabani da ɗa na, ke da ita har abada, sai ta ɗanɗani abun da ta ƙunsa mini, wannan kuɗin na meye?" Tayi maganar tana nuna kuɗin da ummi ta watsar a wurin. Hashim ya ce "Yayan babarta ne ya bata" "Tattaro mini su ki miƙo mini" ummi ta tarkata kuɗin ta miƙa mata. Ta karɓe ta kalli Hashim ta ce "Zaka tashi ka fita ko sai na ɓata maka rai, kuma daga yau na yi maka tsakani da ita, tun da kai ne ka ke zigata, shashashai kawai" Hashim ya tashi zuciyarsa na yi masa zafi, muddin ya buɗe bakinsa, zai iya ɗurawa Iya ashar, dan haka yayi shiru ya bar ɗakin. "Tashi ki fice ki auni dawa ki surfa mini, tun da baki je makarantar allon ba" Haka Ummi ta ja jiki ta fito, ta fara ƙoƙarin aikin da Iya ta saka ta, ƙasan zuciyarta tana fatan, ina ma Maiduguri babu nisa da guduwa za ta yi, ta tafi wurin mamanta. Kayan da yaya ɗanlami ya kawowa Ummi kuwa, Iya ta tsince wanda zata tsince ta ce a fita da sauran, ba ta ƙaunar duk wani abu da ya shafi Mariya. Duk salla sai ummi ta yi addu'ar Allah ya jiƙan babanta, ya bawa mamanta lafiya, ya sa ta dawo ta ɗauke ta. Tun wannan tafiya da yaya ɗanlami yayi, wani daga danginsu, bai sake waiwayo in da Ummi take ba, suka mayar da hankalinsu a kan lafiyar ƴar uwar su. Dan abun na mariya gaba ya din ga yi, babu sauƙi ko sassauci, yanzu tana zaune lafiya idan aka jima, sai ta hau kuka tana burgima tare da surutai, irin na masu taɓin hankali. Ummi kuma ta cigaba da karɓar gashi a gidansu, tsangwama da kyara a cikin yara a makaranta ko kuma a gida. Iya ta sanya ido sosai a kan magaji, ɗan taimakon da yake yi wa ummi, ta tasaya tsyin daka ta hana shi. BAYAN SHEKARU BIYU!. Sauri-sauri ta kammala tulin wanke-wanken da ke tsakar gidan, ta warewa kowane sashi kwanukansu ta kai musu. Duk in da ta faki ido ta tsaya, sai ta yi soshe-soshe, dan itakaɗai ta san me take ji. Guntun omon da ya ragu, da shi ta wanke kayan makarantar bokonta, duk hantsar wandon ta fatattake, sun koɗe sun jeme, ƙafar wandon duk ta ɗage ta tattare, gwiwar duk a farfashe. Kasancewar lokacin rani ne, rijiyoyi duk sun ƙafe, ta ɗau bokiti ta samo ruwan wanka, ta ɗauki ledar omon da babu komai a ciki, ta faɗa banɗaki wanka, da sosonta na buhu. Ta daɗe a tsaye tana fargabar ta ina zata fara? Tun safe a makarantar boko take jin fitsari, ta riƙe shi bata yi ba, saboda azabar da take sha. A hankali ta cire kayan jikinta, ta ware gashin kanta, ta nannaɗe shi ta tufke, ta kawo tsumma da take ɗaure kan da shi, ta ɗaure yadda ba zai jiƙe ba. Ta cire wandon da yake jikinta, subhanallah, wani irin ragargazajjen wando ne, kusan da shi gara babu, duk roba-robar jiki ta zaro, har da in da aka yi ɗinkin zare da allura a jikin phant ɗin, haka ta rataye shi a jikin ƙofar banɗaki, sai tsami yake mara daɗi. Ta koma gefe ɗaya, ba tare da ta tsuguna ba, ta fara sakin fitsarin da ya cika mata mara fam, a tunanin ta hakan zai sanya ta kaucewa faruwar abun da take gudu. Sai dai kash! Tamkar ta zuba ruwan barkono a gabanta, wani irin raɗaɗi da azabar zafi, ya ratsata tun daga kanta har ƙafafuwanta, ta toshe bakinta tana jin zafi kamar ana kekketa mata wurin, ga mararta da ta ƙulle kan fitsarin ya fita. Ta shafe tsawon lokaci, kan ta motsa, saboda tsananin azaba da wahalar da ta shiga. A hankali ta motasa, ta tsuguna wani irin ƙarni mai haɗe da wari ya daki hancinta, ta ɗebo ruwan nan da sanyinsa da komai, ta zuba a wurin ta fara wankewa, wani irin ruwa mai ƙarni mara daɗi ya din ga fitowa daga jikinta. Zuba ruwan sanyin da tayi, ta ji tamkar ta zuba karara a wurin, wani irin ƙaiƙayi kamar ta kurma ihu, duk yadda ta so ta daure, ta kasa ta din ga sosawa, ƙurajen da suka feso a gabanta suka yi jawur, tun tana jin daɗin susar sai da ta koma jin zafi, dan da gask take yi iya ƙarfin ta, saboda azabar ƙaiƙayi, sai da ta yi wa kanta rauni, har da jini. Ta yi shiru ta jingina da jikin bangon banɗakin tana tunanin haka kowa yake yi? Ko ita kaɗai ce take fama da wannan masifar da bala'in, to idan ma haka ne wa zata tambaya? Da ƙyar ta samu ya lafa, ta zuba ruwa a cikin ledar omon nan, ta zuba a jikinta tayi wanka, sai dai a ƙarshe ta rasa yadda za ta yi ta wanke wandonta, dan babu omo, dan haka ta wanke shi a haka, da zallar ruwa, ta yarfe shi ta mayar shi jikinta a jiƙen, ta fito daga wankan tana tafiya a hankali, tana ɗan buɗe ƙafarta, saboda raɗaɗin da wurin yake yi mata. Man kaɗanyarta da na'ima ta aiko mata, shi ta shafa abun ta, ta sanya uniform ɗin ta, ƙungun wandon saboda rashin roba, da leda take kama wani sashin ta ɗaure, hakazalika takalminta ma, kasancewar ya mutu dan a tsinke yake, ta samu leda shi ma ta yi masa cunan leda, ta ɗaure shi da shi, ta saka. Haka ta tafi makaranta tana kaffa-kaffa da jikinta, ko yaya ta saki jiki za a iya ganin tsiraicinta, saboda yadda kayanta suka mutu. Ga wannan bala'in da take ciki, na sanyi da yayi mata mugun kamu. Iya kuwa hankalinsu yana kan bikin Idiris da za ayi, ana ta shirin biki a gidan, shi yaƙi karatun boko yaƙi na islamiyya, ya ce shi aure yake so, Hashim ya kaɗa ya raya, ya ce shi ba zai iya wannan wahalar banzar ba. Kawu Yahaya ma sai da yayi mitar idiris ɗin nawa yake, da har zai ce zai yi aure me yake da shi? Iya ta goya masa baya, ta ce su haɗu su yi masa aure. Aka kama masa hayar wani gida mai ɗaki biyu da kitchen da banɗaki, ginin ƙasa ne dai, amma an yi floor, da plastar ƙasa an shafa farar ƙasa. Wata yarinya ya nema a can gaban unguwarsu, yake ta yi musu sintiri yana son ta, babanta ya ce idan da gaske yake ya fito, shi ne ya zo ya saka Iya a gaba, lallai shi aure yake so, aka je aka nema masa auren ƴar mai suna Hindu. Kawu yahaya ya ce lokacin auren, yayi dai-dai da lokacin zuwansa umara, ba zai samu zuwa ba sai dai matarsa za ta zo, ya kuma aika musu da gudunmawa mai tsoka. Albarkacin bikin Idiris, Iya ta sayawa ummi atamfa, da takalmi na kayan fitar biki, ummi duk da ba shiri suke yi da idiris ba, ta ji dadin zai yi aure ya bar gidan ko ta samu ta sarara. Ana ta shirye shiryen biki, gida ya ɗau harama, ƴan uwa na nesa tuni sun fara zuwa, ummi na ta aiki kamar jaka, ɗan wannan idan yayi kuka a bata rarrashi, ɗan wancan yayi kashi ta wanke, haka dai ba ta da sukuni. Yau kusan tun bayan azahar, yanayi ya nuna akwai matsala, duba da yadda Iya ke ta shiga tana fita ita da mahaifin su magaji, kasancewar ba abun da ya shafi ummi bane, ya sanya ko a jikinta, ta cigaba da sabgoginta. Shi kansa yanayin Idirs ya nuna hankalinsa a matuƙar tashe yake, alamu suka tabattar da akwai matsala. Ba a tsaya da shirye-shiryen biki ba, dan magana ake ta bai fi saura kwana huɗu a shiga hidimar biki ba. Da yamma hashim ya shigo, ya tarar ummi na cikin mutane ana ta aiki, yayi mata nuni da ta zo. Ta wanke hannunta ta bi shi, ya kalleta ya ce "Ke ina naki shirin bukin, ki ke ta fama da aiki haka, ko gajiya ba kya yi?" Murmushi ta yi masa, sai da fararen haƙoranta suka haska fuskarta, fiƙarta da ta karye tana nan a yadda take, sai ƴar siriryar wushiryarta ta ce "To yaya magaji wani shiri zan yi? Ina da atamfata sabuwa da takalmin da zan saka" "Ke ba zaki yi ɗan lallen da ake yi na zamani ba?" Ta kalli hannunta, ta ɗan rausayar da kai ta ce "Bana so, ba zai yi mini kyau ba" Ya kamo hannunta ya ce "Jan nan da ake yi tafin hannunki fari ne masha Allah, ko kitson ma ba ayi miki ba, kin cukurkuɗe gashi kin ɗaure" Yayi maganar yana kallon yadda ɗankwalin kanta yake cike fam, ko ba a gaya maka ba, ka san wannan uban gashin nata ta ɗaure. "Ai ka san ni ba a iya yi mini kitso, duk sanda na cewa yayi mini kitso, sai ya ce wai bs zai iya ba kaina ba zai yi ba, lalle kuma ai sai an biya ɗari biyu huwaila take yi hannu da ƙafa" tayi maganar cikin yanayinta na shagwaɓa da Iya take cewa sangarta. Ya ce "To shikenan, da safe zan baki kuɗin lallen, kitson kuma sai na yi miki" Tayi dariya ta ce "To mata ne kawai suke yi wa mata kitso ban da maza" Ya ce "Shikenan, je ki sai goben in Allah ya kaimu" Cikin murna ta tafi ta cigaba da aikin, tana matuƙar son lalle, amma rabon da ayi mata, tun kan na'ima tayi aure, da take yi musu, yanzu yaran na'ima biyu a gidan miji. Da magariba Saminu baban su Idris ya shigo hankali a tashe ya ja hannun Iya suka fita, wata duhuwa ya ja ta ya ce "Iya muna cikin tashin hankali da masifa, Idris ya zubar mana da mutunci" Cikin kaɗuwa ta ce "Menene? Meyafaru?" "Ban da masifa da bala'i, saura ƴan kwanaki a ɗaura maka aure, a ganka kana watsewa da wata, saboda rashin mutunci" Iya ta ce "To ba mun gama wannan maganar ba? Har wurin maude mai babban carbi na je, ya yi mini aiki ya ce maganar an bar ta har abada, ba zata fasu ba, ko ta fasun ne?" "To yanzun nan ƙanin baban yarinyar da zai aura ɗin, ya dawo da kuɗin auren, sun ce aje a karɓi kayan auren gobe da safe, ba za su bawa mutumin banza ƴa ba" yayi maganar yana nuna mata kuɗin. Iya ta dafe ƙirji ta ce "Mun shiga uku, amma mutanen nan basu da mutunci, basu san tsautsayi ba?" "Koma menene ai shi ya janyo wa kansa, da bai yi ba wa zai ce yayi, ni wannan mutanen da muka tara ne, ban san ya zamu yi da su ba" Iya ta ce "Ni kuma tashin hankalina, garin Allah ya waye a dawo da kayan nan, kowa ya ji abun da ya faru, da sassafe ka je da kanka ka karɓo kayan, ka kai mini gidan kuluwa". "Ni kuma Iya? Ni zan je ɗaukko kayan?" "To kar ka je tsaya asirinmu ya tonu, sai ka ji daɗi, santolo kawai". "To Shikenan zan je in sha Allah " "Kai ka ga idan da hali, ka tafi yanzu cikin daren nan, ka tafi da babur ba wanda ya ji balle ya gani" "To bari sahu ya ƙara ɗaukewa, amma Iya yaya zamu yi da wannan mutanen, ta yaya zamu ce musu an fasa auren nan?" Iya ta ce "Nima shi nake tunani, dama ga akuyarsa tayi kuka a dangi, dan ma ana tsoro na ne, ya sanya ba a magana, amma jeka na san abun yi " "Meye abun yin to?" "Ka tafi na ce, idan ka dawo sai ka ji" ya jinjina mata kai ya tafi. Ɗakin samarin ta shiga, neman Idris, amma ba ta tarar da shi ba, dan haka ta juya ta tafi. A daren saminu yayi yadda Iya ta ce, ya je ya karɓo kayan a daren. Sosai Saminu, ya din ga yi wa idiris faɗa, a kan tashin hankalin da ya sanya su a ciki. Washegari kamar yadda Hashim ya yi wa ummi alƙawari, ya bata kuɗi ta je aka yi mata lalle. A ƙofar gida ta gan shi ya karɓo kayan guga, tun daga nesa take ɗaga masa hannu ta ce "Yaya ka ga lalle na?" Yayi murmushi ya ce  "Inyee an sha kyau, lalle yayi kyau, ki yi sauri ki shiga gida, Iya ta fara faɗa ana nemanki" Cikin faɗuwar gaba ummi, ta ce "Bari na yi sauri" ta yi cikin gida da gudu. Cikin damuwa Saminu ya kalli Iya ya ce "Iya kina ganin babu matsala, ba fa son yarinyar nan yake yi ba, kuma shekarar ta goma sha uku ne kawai" "To yaya ka ke son mu yi? Asirinmu da nasa ya tonu, idan ba haka ba kawo wata mafitar" Ya girgiza kai ya ce "Ba ni da wata mafitar". "To na yanke hukunci, ya auri ummi dan mutuncinmu ba zai zube ba, a sakamu a bakin duniya da wannan iskancin da yayi ba kamar ɗan taure" Ayshercool 08081012143.                       *CUTARWA* MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION *BRIGHT PENS (FREE BATCH)* Mafaka gidan ƙamshi, na da kyakywan albishir ga amare uwar gida, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi. Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku Oll types of Turaran wuta Sandal Halut Irik Difur Gab Gab Kajiji Habil Nabak Humra Kulakcha Dilke da kalta Kayan Garan jiki Muna turara Kaya Kujerar garan jiki Kannada Madarorin turare masu kamshi  Man garan gashi  Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702   08025453921 P10 Saminu ya numfasa ya ce "To shikenan, Allah ya sanya alkhairi" Iya ta ce "Yauwwa ka turo mini shi, ko kuma ya jira ni a ɗakinsu, zan same shi" "To shikenan, bari na je na nemo shi" Hashim kuwa dariya yake yi wa ummi, yana cewa ta tafi a hankali, saboda yadda ta kwasa da gudu cikin tsoro. Da Iya tayi karo, iya ta kalleta ta ce "Daga ina ki ke?" A tsorace ta ce "Dan Allah kiyi haƙuri, huwaila ce ba ta yi mini lallen da wuri ba" "Yenyenyen da an yi magana, dan Allah ki yi haƙuri, ki wuce ki nemi wuri ki zauna kar ki sake fita". Ummi ta ce "to" dan ba ta yi zaton Iya ba zata yi mata tijara ba. Iya duk ta bi ƴaƴanta da ta haifa da na riƙonta, ta sanar musu da halin da ake ciki. Ilyas ya ce "Amma Iya naga yarinya ce ƙarama sosai, girman jiki ne kawai ba zata iya jure ɗawainiyar aure ba" "Yarinya kuma? Ni ma shekarata sha uku aka yi mini aure, uwarta ba sha huɗu aka auro ta ba? Da ta shiga bulunbuƙui za ta yi, yaran yanzu da sun san komai, to idan ba haka ba ya zamu yi?" Sagir ya ce "To ai Iya ba a shirya ba, da wani kayan ɗakin za ta tare?" "Wani shirin za ayi? A sayo mata katifa a gidan dillalai, tsohuwa ba sabuwa ba, mai biyar mai goma ku yi karo-karo, ku  haɗa a saya mata buta, murhu tukunya da ƴar tabarma, ina da tsofaffin labulaye, da abun da ba a rasa ba, a saka mata kowa da haka yake farawa ai, rufin asirin ɗan uwanta ai na ta ne" Gaba ɗaya suka amince a kan haka, baiwar Allah ummi sam ba ta san wainar da ake toyawa ba, tamkar ba mace mai ƙananan shekaru ba, ita take ta ɗawainiyar aike da girkin abincin gidan bikin, ko nauyin jikinta ba ta ji, saboda tsabar sabo da wahala, ba ta san zama wuri ɗaya bata aikin komai ba. Idiris kuwa tun da aka gaya masa, hukuncin da Iya ta yanke, wanda da kanta ta gaya masa, ya kada baki ya ce "Allah ya kiyaye, uban ne zan ci da wannan baƙar yarinyar mummuna ragowa, ni wallahi bana son ta". Mahaifinsa ya ce "Rufe mini baki, ko na mangare ka, shashasha mara hankali, kai ka isa ka yi jayayya da maganar Iya? Ba kai ka janyo koma menene ba, aure ne babu fashi sai an yi shi wallahi, dan ba zamu ji kunya a idon mutane ba" Iya cewa take "Bi shi a hankali saminu, na sani ba son ta ka ke yi ba, muni kam akwai shi amma ka yi haƙuri, tun da kai ka janyo komai, mun riga mun tara mutane, idan muka ce an fasa dole za a so jin ba'asin abun da ya faru uban me zamu ce musu? Ko kuma gaya musu abun da ka aikata zamu yi?". Cike da iskanci, da rashin ɗa'a ya ke kumbura baki yana masifar, shi fa baya son ummi, hindu yake so. Iya ta fusata ta ce "Uwar hindu ka ke so ba hindu ba, ɗan iska mara mutunci, ba gata aka yi maka ba? Ka je ka yi abun da ka ke ganin zai fishsheka" Suka tafi suka bar shi, yana wani irin huci da takaici, yarinyar da aka gama lalubewa, wanda yana da tabbacin ba shikaɗai yake yi mata ba, ga baƙi ga muni, ace ita zai aura dan an raina masa hankali, ga hindunsa ƴar fara mai kyau, ace wai ya auri ummi, za ta ci ubanta kuwa, da ƙafarta zata gudu. Magaji ne ya shiga ɗakin su da kayansa da ya karɓo daga guga, ya kalli idiris ya cika yayi fam, yake ta tsaki da ƙanan maganganu. "Gunagunin me ka ke yi haka ne?" "Ba dole in yi gunaguni ba, saboda an tsane ni, za a cuce ni a kassara rayuwata da ta yaran da zan haifa" "Wai ka da waye ne? Me kuma aka yi maka?" "Iya mana" ya faɗa a fusace. "Too iya kuma? Duk kusancin naku, yau a ganku a rana?" "Ba wani kusanci, za a zalunce ni, wai dan an fasa aurena da hindu, wai sai an ɗaura mini aure da wannan buranyar yarinyar, mummuna wai ni za a aurawa ummi, wai ba zasu ji kunya ba, wannan jakar yarinya mai kama da mayu, ita fa iyan da kanta take faɗar baƙin halin uwarta, kuma za a liƙa mini" Sakin kayan hashim yayi, bakinsa na rawa ya ce "Wace ummin?" Idiris yayi masa mugun kallo ya ce "Wace ummin ban da wannan baƙar yarinya, da goshi kamar tsinin jirgi, mummuna ido kamar na kyanwa wallahi ni an cuce ni, kuma wallahi ko an yi auren sakinta zan yi" Bai bi ta kan kayan ba, ya fita da sauri, ya nufi sashin mahaifiyar su, wanda nan ma ya ɗau harama da mutane, uwar ɗakin mahaifiyarsu ya shiga, ya tarar da ita tana ƙirga kuɗi. 'yaya" ya kira sunanta. Ta kalleshi ta ce "Ya aka yi?" "Wai da gaske Idris ummi, za a aura masa?". Ta ce "Mhmm nima haka na ji" "Amma yaya meyasa?" "Kafi kowa sanin ai abun da ya aikata, Iya ce ta kawo wannan shawarar, mu ma rufin asirinmu ne ai" Kamar Hashim zai yi kuka ya ce "Amma yaya kin san yadda Idris yake da yarinyar nan, gata yarinya ƙarama,a haka zaku bari ayi auren nan?" "To ni na isa in hana ne? Kai ka san babu mai ja da maganar Iya ai ko?" Bai sake cewa komai ba ya fita, ya nufi sashin iya, a ƙofar ɗakinta ta hange shi, yana tsaye yana kallonta, fuskarsa babu walwala. Cikin azama ta fito, dan kar magajin ya faɗi wata maganar banzar, a cikin mutane ya tona musu asiri. Ta ce "Menene?" "Iya wai kin ce a aurawa idiris ummi, saboda an fasa auren sa?" "Eh sai yaya?" "Amma Iya kin san ba son ummi yake yi ba... Ta katse shi ta hanyar cewa "To ina ruwanka, ku yaran zamani ku kuka san wata soyyaya, mu duk bamu santa ba, idan ya aureta ko daga baya ya saketa, ba shikenan ba in dai asirin ya rufu, ai ba ana nufin yayi ta zama da ita bane ba din-din" Galala yake kallon Iya, idan dai-dai ya ji, kamar ta ce ko daga baya ya saketa, wato rufin asirin kawai suke nema, ko da hakan yana nufin tarwatsa rayuwar marainiyar. "Amma iya" "Kai rufe mini baki, bana son ƙauli da ba'adin banza, sai in ci maka mutunci yanzun nan, fice ka bani wuri" zuciyarsa na wani irin tafasa ya bar sashin na iya. Shikenan saboda ummi bata da gata kowa ya goyi bayan Idris, ummi ko ƴar tsintuwa ce, ya ci ta ci albarkacin ita ma ɗan adam ce a kula rayuwarta, balle ita ma cikakkiyar ƴa ce a gidan, yadda idiris yake cika yana batsewa yana masifa, ka sam babu Allah a ransa kuma babu abun da ba zai iya yi ba. Suka cigaba da shiri, sai washegari da safe, Iya ta kira ummi, da ta sha uban wanke-wanke. Ta hura wutar kunu, ƙanwar Iya nata yabonta tana cewa taje ta huta. Iya ta kira Ummi, ta kalleta ta ce "Ki je ki duba a tsummokaranki masu kyau ki wanke su, an fasa auren Idris da ke za a ɗaura, ki wanke kayan da zaki tafi da su, idan ya so daga baya a ɗinka wasu daga kayan auren da aka dawo da su a kai miki, atamfarki da na saya miki ki sakata gobe ɗaurin aure" Sai da numfashin ummi ya kusa ɗaukewa, na wucin gadi, ta haɗiye wani irin yawu da taji tamkar tana haɗiye wuta ta ce "Iy..Iya aure kuma?" "Kurma ce ke ba ki ji me na ce ba?" Karon farko da ummi tayi yinƙurin yin musu da Iya ta ce "Iya makarantar fa? Kuma yaya idiris dukana yake yi, dan Allah kar ayi mini aure da shi, ko da wa aka yi mini auren na yarda amma dan Allah ban da yaya Idris, wallahi dukana zai yi" "Ke dalla rufawa mutane baki, ba taimakonki ma za ayi ba, da wannan munin uban wa ye zai aureki ya zauna da ke? Ai idiris taimaka miki zai yi, kamata yayi ki yi mana godiya, idan ma bai zauna da ke ba, ai an samu asiri ya rufu, da mu da ku baki ɗaya, ita dauɗar gora ai ciki ka sha ta,  ki je ki tsami kayanki ki wanke" Kuka ne ya ƙwacewa ummi, ta juya ta tafi ɗakinta, ta kalli viva da take zuba kaya a ciki, ina wasu kaya ma suka banda tarkacen tsummokara, kuka kawai take tare da tabattarwa da kanta kashinta ya bushe. Karo na farko da ba ta taɓa neman taimakon kowa, wurin gaya wa wani matsalar ta ko damuwarta ba, amma ta fito cikin tashin hankali, ta tunkari sashin su Hashim tana nemansa, da ta rasa shi a gidan, ta fita waje a can ta samo shi wata majalissa da suke zama, ba kowa a wurin sai shi. Ya miƙe tsaye ya taro ta, jikinsa ya bashi wataƙila ummi ta samu labari, cikin dakiya ya ce  "Ummi lafiya?" "Yaya magaji" "Na'am Ummi" "Yaya magaji, wai iya ta ce ni yaya Idris zai aura?" ta riƙo hannunsa ta ce "Dan Allah mu je ka bata haƙuri, dukana zai din ga yi, ya ce ya tsane ni a rayuwarsa dan Allah mu je ka bawa iya haƙuri, dan Allah kar a aura mini shi". Hawaye take tsiyayarwa daga idonta, kamar an kunna famfo. "Ummi ki yi haƙuri, ƙaddararki ce a haka, na yi iya yi na, sun ƙi fahimta ta, ki yi haƙuri" Ummi ta ɗora hannu a ka ta ce "Shikenan na shiga uku, wallahi kasheni zai yi da duka, Innalillahi wa Innalillahi raji'un, na shiga uku" tayi maganar jikinta har rawa yake yi saboda tashin hankali da kiɗimewa. "Ki yi haƙuri ummi, ki cigaba da addu'a, babu abun da ya gagari Allah, idiris bai isa yayi miki abun da Allah bai yi miki ba" Kasa magana tayi, sai kuka tana jin yadda fargaba da tsoron idiris ke ƙara shigar ta. Muryar Hashim ta ji ya na cewa "Ki tafi gida, kar ki su yi ta nemanki, ki ja wa kan ki matsala" Ummi ta jinjina kai, ta tafi hannunta a tana zubar da hawaye, gaba ta yi ta bar cikin gari, ta samu wani wuri tayi zamanta, ta din ga kuka, idanuwanta suka haye suka kumbura sosai da sosai. Har azahar ta yi bata da niyyar tashi, sai da rana ta take sosai da sosai, sannan ta tashi ta tafi gida, daga nesa take hangen gidan, gabanta ya sake faɗuwa, tayi kwana ta tafi gidansu na'ima. Maman na'ima ta tarar a tsakar gida tana girki, ta na yi mata magana, amma ba ta iya tankawa ba, kawai ta shige cikin ɗaki ta kwanta. "Ummi ko ba lafiya ne?" Ummi ta girgiza mata kai, kanta na yi mata wani irin ciwo, ta hau bacci. Ƴan biki suka din ga tambayar Iya, ba za aje gidan su amarya kamu da suaran al'adu ba? Iya ta ce musu ba sai an je ba, gidan su amaryar malamai ne, ba sa gabatar da al'adun aure, sai ɗaurin aure da tariya kawai. Iya bata farga Ummi ba ta nan ba sai la'asar, hankalinta ya tashi aka shiga nemanta, nan da nan Iya ta kawowa ranta ko guduwa ummi ta yi, to ta gudu ta je ina? Aka din ga nemanta, har tasha aka je, amma aka ce ba a ga ummi ba. Hashim hankalinsa ya tashi sosai da sosai, saboda shi ya yi wa ummi ganin ƙarshe, dan sai da iya ta rutsa shi tana tuhumarsa a kan ko shi ne yayi wani abu, ya ɓoye ummi ko makamancin haka. Ummi kuwa bayan ta tashi, tayi salla, maman na'ima ta bata abinci, ta ci kaɗan kanta na cigaba da sara mata. Sai dai ƙememe ta ƙi yi wa maman su na'ima magana, balle ta gaya mata abun da yake faruwa. Har aka yi sallar magariba tana gidan, tayi sallar magariba, sannan ta cewa maman ta tafi. Ko da ta shiga gida, da yawan an watse, an tafi yawon nemanta, dan haka kai tsaye ta tafi ɗakinta, duk an baje itace a ɗakin, ta tutture su ta kwanta a kan buhunta. Iya ta dawo afujajan, saboda tashin hankali, ta din ga tsinewa ummi, da mariya tare da aibata mariya da cewa duk baƙin halinta ne yake gudanawa a jinin Ummi. Ummi na jiyo ta, tana jin wani abu mai ɗaci ya tsaya mata a ƙirjinta, da ta kasa haɗiyewa, ta sake ƙudindinewa tana kuka, tana wata irin ajiyar zuciya mai ban tsoro. "Laaa, ummi, nan ki ka zo ki ka kwanta ana ta neman ki?" Matar tayi maganar tana haske ummi da fitila. Iya ta ce "Wace ummin? A ina?" "Gata a nan a kwance" Iya ta ƙarasa ta leƙa, ta ga ummi ta dunƙule wuri guda. "Shegiya matsiyaciyar yarinya, ina ki ka tafi ki ka tayar mini da hankali?" Ummi ta tashi zaune, amma ta kasa magana, ta sunkuyar da kanta ƙasa. "Ba magana nake yi miki ba, sai na zo na hau ruwan cikinki? Wurin wani ɗan iskan ki ka je? Wurin maza ki ka tafi ko?" Ummi ta yi shiru tana tunanin ta je wurin maza tayi me?. "Dan ubanki tun safe, da yake ba mutunci ne da ke ba, ki ka saka ƙafa ki ka fice, ba zaki gaya mini in da ki ka tafi ba, tsinanniya ƴar matsiyata" salati wasu suka din ga yi,  suna hana Iya tsinewa Ummi. "Ku rabu da ni, ba ku san mugun halin yarinyar nan ba, riƙonta kawai nake yi, baƙin cikinta ya kusa kasheni, ku kalli ina yi mata magana ta yi mini banza, balle in san in da ta tafi, kuna ji ina tambayarta tayi shiru". Hawaye wani na bin wani a fuskar ummi, amma ta kasa magana, kawai iya ta rarumi itace, ta sauke mata shi a kafaɗarta, gantsarewa tayi saboda zafi da ciwo, amma ta kasa guduwa, aikuwa ta cigaba da kwaɗa mata duk in da ta samu, da ƙyar ƴan biki aka hanata. Wata ƴar yayar Iya ta ce "Haba Iya, yanzu wannan ƴar yarinyar da baki ki goya ba a bayanki, ki ke rafkawa wannan itacen, wannan ai mugunta ce. Ni tun da na zo gidan nan, wallahi ban ga yarinyar nan tayi wani abun ashsha ba". "Bar ni marka da hatsabibiyar yarinyar nan, baƙin cikin uwarta bai kasheni ba, na ta zai kasheni, ni na fara tunanin ko dai ba jinina ba ce, dan kaf zuriyarmu babu wannan munin kamar baƙar buranya". Aka yi ta bawa Iya haƙuri, ummi kuwa tayi mursisi ta kwanta, ta cigaba da kuka, tana jin kamar bayanta ya karye. Ƙaiƙayin nan ne ya cigaba ta taso mata, duk yadda ta so ta daure, kasawa tayi, ta din ga soshe-soshe, kamar za ta zaee. Da aka yi sallar magariba, ta tafi banɗaki tayi fitsari, ba tare da wurin ya tsane ba, ta tashi ta fito da jiƙaƙƙen wando, aikuwa ƙaiƙayi ya sake tasowa, ta kasa zaune ta kasa tsaye, ganin wurin da duhu, ya sanya ta kai hannu ta fara sosawa, wanda har ta shagala saboda azabar zafi da ƙaiƙayi. "Ai dama na faɗa, na faɗa wurin maza ki ke zuwa ko ummi, wurin maza ki ka je tun safe ba kya nan" zabura ummi tayi, ta girgiza mata kai, saboda yadda Iya ta haske ta da fitila. "Uban me ya kai hannunki gabanki, ki na  soshe-soshe a duhuwa? Na faɗa wurin maza ki ke zuwa, kina sakarci, an ƙi yadda, na ce ayi miki aure, sun ce kin yi ƙanƙanta, yanzu meye Wannan?" rasa amsar da zata bata tayi, Iya ta din ga yi mata kwarmato, a cikin mutane da duk wasu kalaman cin mutunci da muzantawa, kunya baƙin ciki duk suka cika zuciyar ummi. Saboda azaba a zaune ta yi salla, da ta motsa sai ta ji kamar ana yayyanka naman gabanta da reza, saboda wurin duk ya kwailaye. Ummi haka tayi kwanan baƙin ciki, ta rasa yadda za ta yi, saboda abubuwa kashi-kashi, da wasu ma ko sanin kan su ma ba ta yi ba, da yawa wasu daga maganganun Iyan ba ta san in da suka dosa ba, amma abun da ta fahimta kawai shi ne, ta san cin mutunci ne maganganun Iyan, uwa uba kamata da ta yi tana susa take yi mata kwarmato, da cewa tana zuwa wurin maza, to ta je ta yi me?. Hashim kasa bacci yayi, tsananin tausayin ummi na cin zuciyarsa, mussaman yadda ya ji Idiris ya na alwashin cin mutuncin ummi, da kuma azabtar da ita, da duk iya ƙarfin sa. Duk yadda ya so yi wa idiris nasiha, yayi mursisi yaƙi ganewa, ya din ga kumfar baki tare da muzantar halittar ummi. Bayan sallar asuba, Ummi ba ta fito ba, sai da Iya ta zo ta sakata a gaba, aka ce tayi wanka, da yawa sai a lokacin suka san cewa wai Ummi ce amarya. Da yawa akwai magana a bakin mutane, sai da ana jin tsoron Iya, babu wanda zai iya tofawa. Sai a lokacin Iya ta bata sabon kaya ta saka, ta nemi wuri ta zauna kamar gunki, kan nan a ƙasa tana aikin kuka. Ƴan uwan Iya suka din ga tambayar, ina dangin mariya, duk ba su zo ba?Iya ta ce "Ai auren ne ba shiri, wancan Yarinyar iyayenta sun raina ƙoƙarin idris, shiyasa aka fasa auren na ce ya auri ummi, ƙara zumunci, dan haka daga baya zasu zo". Ƙanwar babar idiris ta ce "Amma idiris yayi jihadi, na ji kin ce yarinyar ba ta ji, kina iƙirarin tana zuwa wurin maza". Kowa ya din ga faɗar albarkacin bakinsa, a kan auren, wasu suka din ga cewa idiris ya samu yarinya ƙarama mai nutsuwa da ƙoƙarin aiki, wasu kuma sun hau maganar Iya sun zauna, suna yi wa ummi hukunci da shi. Da azahar aka ɗaurawa ummi aure da Idris, a kan sadaki naira dubu takwas, mutane aka din ga yi wa ummi nasiha, ana ta cewa ta yi haƙuri, aure ɗan haƙuri ne. Abun da ummi ta kawo a ranta shi ne, ashe sun san halinsa dukanta zai din ga yi, amma aka aura mata shi. Cikin matsanancin tashin hankali, babar na'ima ta shigo gidan, dan tabattar idan da gaske ummi aka yi wa aure, aikuwa ta samu dahir, an riga an ɗaura aure ma. Galibi maƙwabtan su, sun girgiza da jin wai ummi aka yi wa aure, ummin da guda nawa take, da kuma mutum kamar idris, da ba wanda bai san shi a fagen iya rashin mutunci ba. Tsohuwar katifar ce dai da tabarma, katifar tsirarta, babu ko zani, gefenta duk ɓera yayi kalaci da ita, domin kuwa tsohuwar katifa ce, a gidan dillalai aka sayo ta, aka sakawa ummi a ɗaki, sai tsofaffin labulaye na Iya, labulayen nan sun sha jiki, dan ita ma kwancensu aka bata, daga baya ta samu wasu ta cire su, kitchen daga tukunya babba da ƙarama, sai ƴan tasoshi, da kofunan silba kamar bazawarar ƙauye. Bayan sallar magariba, aka bata wasu kayan, ta saka, aka tafi kai ta. Da ƙafafuwan ta, har gidan Idris!. Ayshercool 08081012143                        *CUTARWA!* *BRIGHT PENS (FREE BATCH)* Mafaka gidan ƙamshi, na da kyakywan albishir ga amare uwar gida, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi. Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku Oll types of Turaran wuta Sandal Halut Irik Difur Gab Gab Kajiji Habil Nabak Humra Kulakcha Dilke da kalta Kayan Garan jiki Muna turara Kaya Kujerar garan jiki Kannada Madarorin turare masu kamshi  Man garan gashi  Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702   08025453921 P11 Haka a ka kai ummi, mata suka gama surutansu, wasu daga cikin maƙwabta da suka san irin rayuwar da ummi take yi, suka din ga tsinewa iya, mussaman ganin ɗakin da aka kai budurwa, da tsohuwar katifa, ko zanin gado babu. Aka din ga ƙananun maganganu, sai dai babu wanda ya isa ya iya tunkarar iyan, ya gaya mata hakan, saboda iya bala'inta da tashin hankali, haka kowa yayi maganganun sa ƙasa-ƙasa. A hankali kowa ya watse aka bar ummi, ƴan matasan yaran da aka bar ta da su, suka gaji da zama, ango bai shigo ba, suka watse suka bar ummi ko fitila babu. Wani irin tsoro ya mamaye ta, da ta ji motsi kaɗan sai ta razana, shiru-shiru babu idiris babu dalilinsa. Ji ta din ga yi a ranta, kamar ta tashi ta koma gida, dan wani irin tsoro take ji, kamar ace kyat ta zura da gudu, saboda duhun da ya mamaye ilahirin gidan. Dare ya cigaba da yi, duhu ya sake mamaye ko ina da ko ina, ta yadda ko tafin hannunta ba ta iya gani, tun tana jin motsin mutane sama-sama, har gari ya koma yayi tsit, sai kukan ƙanan ƙwari. Cigaba da kuka ta yi cikin firgici, ta tashi a hankali ta leƙa tsakar gida, ta hango ƙofar gidan a buɗe, tsakar gidan kuma sai ta yi ta ganin abubuwa na yi mata gizo, saboda a tsorace take, kuma ga duhu. Da sauri ta koma can ƙuryar ɗakin ta takure, bacci take ji sosai da sosai ga gajiyar aiki, ga ta biki, ga tashin hankali ga kuma dukan da ta ci jiya da daddare a wurin Iya. Babu tsammani ta ji rugugin hadari, da walƙiyya ko ta ko ina, fashewa tayi da kuka, tana son tashi ta fita da gudu ta koma gida, amma tsoro ya hanata. Tana nan zaune ruwa ya kece ya din ga zuba kamar da bakin ƙwarya, ta tashi da nufin ta rufe ƙofar ɗakin, amma ƙarfin zubar ruwan, da kuma tsawar da ake yi, ya sanya ta koma ta zauna tana cigaba da kuka. Ruwa ya din ga feshi cikin ɗakin, wani irin sanyi ya mamaye garin. Ruwa ya shigo ɗakin sosai ya jiƙe, sai dai bai kai kan katifarta ba. Kasancewar bacci ɓarawo ne, ya kwashe ummi a nan zaune ba tare da ta shirya hakan ba. sai da gari ya waye ya fara haske, sannan ta tashi a razane. Ruwan da aka yi duk ƙasa ta shanye, ta zama taɓo, wani kofi ta gani a tsakar gida, ya cika da ruwan da aka yi, tayi alwala da shi, ta koma ɗakin tayi sallar asuba. Tana nan zaune cikin zullumi da fargaba, aka yi sallama, wasu daga cikin ƴan biki ne suka zo, hakan ya sanya ta ji daɗi. Suka din ga rafsa guɗa, ummi dai da ido kawai take bin su. Suka kawo mata abun karyawa, ake tambayarta ina angon? Tayi shiru ba ta ce komai ba, dan kuwa ba ta san me za ta ce ɗin ba. Suka ƙara yi mata ƴan gyare-gyaren da zasu yi mata, suna ta hira suna yi mata nasiha, da azahar suka ce za su tafi. Ummi ta ɗau hijjabinta ta ce za ta bi su. "Ki bi mu ina? Ai ko ƙofar gida ki ka fita babu iznin mijinki, Allah zai ƙona ki a wuta, ki koma ki zauna, shima yana ango amma safiyar fari ya fice, har azahar bai dawo ba?" Cewar wata dattijuwa. Ƙanwar Iya ta ce "Bar mara mutunci, ai da alama ba son auren nan yake yi ba, haɗin Iya ne kawai, kodayeke ai ma ya furta, tun da hama ta yi masa Allah ya sanya alkhairi, ya ce ba amin ba, ba ya so" "Too ikon Allah, ai dama idiris ba mutunci ya cika ba, har ta bani tausayi, sannu kin ji ummi, Allah ya baku zaman lafiya ya baki juriya" suka gama salallaminsu suka tafi. Ta dawo tsakar gida, ta haɗa takalmanta ta zauna, ta zubawa hanyar ƙofar gida ido, in da Allah ya taimaketa, baƙin da suka zo, sun saka yara su je gida, sun ɗaukko bokiti, an cika mata shi da ruwa, da haka ta samu na alwala. Da la'asar aka turo ƙanin idris ya kawo wa ummi, abinci ta karɓa ta ce masa dan Allah ya tayata zama kar ya tafi, tsoro take ji. Cikin ikon Allah bai tafin ba, ya tayata zama, har suka ci abinci tare, sai magariba ya tafi ya bar ta ita ɗaya ƙwal kamar mayya. Hashim ya rasa in da zai sanya ransa, damuwa ta din ga sassaƙar zuciyarsa, gashi tun da aka ɗaura aure, bai saka idiris a idonsa ba, yana son zuwa gidan ummi, amma yana tsoron yaje ya tarar da abun da ba shikenan ba, da zai ɗaga masa hankali. Baban su Idris ya samu Iya yake tambayarta, ya za ayi da dangin mahaifiyar Ummi, yakamata a sanar musu. Iya ta ce "Rabu da su, gayyar tsiya ko an gaya musu uwar mai za su tsinana, talakawan banza, ba su ajiye komai ba sai buzu da tawwada sai allo, ai a haka aka tsaface mini ɗa, aka shanye shi ba ya moruwa sai abun da take so, yanzu idan suka sani tsaf za su yi wata ƙulla-ƙullar, a bari sai komai ya lafa, an kwana biyu sai a aika musu da goro da alewa ace na aurar da jikata, shikenan" Saminu ya ce "Amma Iya za su ga kamar ba a kyauta musu ba fa" "Ita abubuwan da tayi mini kyautawar ta yi? Can su ƙarata yarinya ce dai na aurar da ita" Saminu ya jinjina kai, amma dai ya san abun da aka yi ba a kyauta ba, ko ba komai suna da hakki a kan ummi, tun da ƴar su ce ta haifeta. Ummi haka ta sake kwana a gidan nan, ita kaɗai babu idris babu alamarsa, haka ta sake yin kwanan tsoro da tashin hankali. Sai dai wayewar garin Allah, babu wanda ya tuna da ita balle ya aiko mata da abinci. Babar idiris ta fara ƙorafin, tun da aka kai ummi, Idiris bai zo ya ko gaishe su ba, har maganar ta je kunnen iya, ita ma tayi maganar a ranta, amma kasancewar sai a ranar baƙi suka gama watsewa, abun ya dawo kanta. Rai a ɓace ta aika Alhassan, ta ce ya je gidan ummi, ya ce Idris ya zo tana nemansa. A hanyar ƙofar fita, ya tarar da ita a zaune, tana kallon masu wucewa. "Ke ummi, kina amarya kina zama a hanyar ƙofar gida kina leƙe?" Duk da ba shiri suke yi ba, ummi ta ce "Tsoro nake ji, nikaɗai ce a gidan" Ya ce "Taɓ, ina yaya idiris, Iya ta ce yaje tana nemansa" Ummi ta ce "To ai bai taɓa zuwa gidan nan ba, ni tun da aka kawo ni ban ganshi ba" Ya waro ido ya ce "Ke da gaske!? Ke kaɗai ki ke kwana a gidan nan?" Ta ɗaga masa kai alamar eh. Ya ce "Sannu da ƙoƙari, kuma ki ka zauna? Kodayeke idan ma ki ka ƙi zama kin san sauran, bari na je na gaya wa Iyan" Hankalin iya ba ƙaramin tashi yayi ba, da jin cewar wai tun da aka kai ummi bai taɓa kwana a gida ba. Ta ɗau mayafi ta tafi gidan ummi, a nan tsakar gida suka tarar da ita a zaune. "Ke ummi, ashe tun da aka kawo ki, Idiris bai kwana a gidan nan ba?" Ummi ta ɗaga mata kai alamar eh. "Kuma dan ubanki ki ka ja baki ki ka yi shiru baki faɗa ba? Har sai da na aiko, ke da na nemeki na rasa haka na yi miki, ba yawon nemanki na tafi ba? Wato baki damu da shi ba ko?" Ummi dai ta yi shiru ba ta ce komai ba. Iya ta yi ta mata masifa, sannan ta fita, daga gidan, ta saka aka tafi kasuwa aka kirawo babansa, da sagir aka ce musu, ba a ga idiris ba. Iya ba ta damu da tsawon kwanakin nan, ya ummi take ba, ta ci abinci ko ba ta ci ba, bata bi ta kan hakan ba. Aka din ga yawon nemansa, wurin abokansa da sauransu, da ƙyar aka gano shi, can wurin wani abokinsa ya koma, a can yake kwana. Iya ta same shi ta din ga zaginsa, ta in da ta shiga ba ta nan take fita ba, mahaifinsu ma kamar zai kai masa duka, saboda takaici da ɓacin rai. Hashim kallon su Iya yake yi, yana tausaya musu ranar da hakkin ummi zai kama su baki ɗayan su, babban abun da yake ƙara bashi mamaki, irin yadda ba wanda yake iya yi wa musu a kan duk wani son zuciyarta. Ummi ba ta san me yake faruwa ba, sai ma tunanin Allah ya sa Idris yana lafiya, tun da an ce tun ranar ɗaurin aure ba a sake ganinsa ba. Da ƙyar tayi sallar la'asar, saboda yunwar da take ji, cikinta sai ƙugi yake yi, har wani jiri take ji idan ta tashi, ban da ruwa ba abun da ta sha, tana son fita nemawa kanta mafita, amma an ce idan ta fita ba da izinin Idris ba, Allah zai ƙonata, gashi kuma tana son komawa makaranta, amma ba ta ganshi ba balle ta tambaye shi. Sallamar yaro ta ji, tayi sauri ta fito daga ɗakin, wani yaro ta gani da kwano, ya ce mata "Gashi in ji mamanmu" saboda ƙuruciya da yarinta, ummi ba ta tambayi daga ina ba, ta karɓa ta ce ta gode. Dafaffen rogo ne, da ƙuli-ƙuli, ko wanke hannu ba ta yi ba, ta hau rogon nan da ci, saboda yunwar da take ji. Ta gode wa Allah bayan ta kammala, duk da ba ƙoshi tayi ba, saboda ɗan kaɗan ne aka zubo shi a kwano. Ta fito da kwanon tsakar gida, ta saka ruwa tana girgijewa, dan ba ta da ko omo. Kamar wanda aka cillo, ta ga idiris ya shigo, babu ko sallama, hannunsa riƙe da jakar kayansa, wata irin nannauyar ajiyar zuciya ta yi, saboda faɗuwar gaba da tsorata. Babansa da yake bayan sa yayi sallama, ummi ta amsa ta tsuguna ƙasa ta ce "Baba ina wuni?" "Lafiya ƙalau, ya gidan?" Kai a ƙasa ta amsa masa da "Lafiya lau". "Gashi nan, duk ranar da bai kwana a gidan nan ba, da safe ki je gida ki sanar da ni, zaka ga yadda zan yi da kai, mutumin banza wanda bai san abun da yake yi masa ciwo ba, an lallaɓa abun nan a rufawa juna asiri, ka daina ɗaukko mana magana, amma kana ƙoƙarin tona mana asiri" mahaifinsa yayi masa kaca-kaca, sannan ya tafi. Ummi ji ta yi kamar tabi bayan sa, dan ta wani fannin zamanta ita kaɗai babu Idris shi ne rufin asirin ta. Ta ajiye kwanon da take ɗaurayewa, ta nemi wuri can a tsakar gida ta zauna, tana ta addu'a a zuciyarta. Idris kuwa ya cika yayi fam! Kamar ya fashe saboda tsabar baƙin ciki da takaici, fuskar ummi kawai idan ya kalla, ji yake kamar ya shaƙeta ta mutu, me zai yi da wata ummi, mummuna kamar ba bil'adama ba, aba kamar bayan garwa. Tsaki yayi ya fito zai sake fita, aikuwa ta sake razana, kai tsaye inda take ya nufa, ta fara ƙoƙarin miƙewa tsaye, ya sanya ƙafarsa ya tankaɗata ta faɗi ƙasa. "Shine ki ke je ki ka gaya musu bana kwana a gidan nan ko? Idan na kwana a gidan uwar me zan yi miki?" Da sauri ta girgiza kai ta ce "A..aA'a iya ce ya aiko nemanka, wallahi ba faɗa na yi ba" tayi maganar cikin rawar murya. "Rufe mini baki"  yayi maganar yana dukanta a ka da hannunsa. Ta saka hannu bibbiyu ta dafe kanta, saboda jin zafin dukan da tayi, dan ma Allah ya taimaketa, tudun gashinta bai bari ta ji zafin sosai ba. "Idan ki ka kuskura ko da wasa, ki kai ƙarata, sai na yanka ki, kuma azabar da zan gana miki, sai kin gudu da ƙafarki, ke baki san yadda na tsaneki ba ko? Zaki gani yanzu ai, banza mai kama da dabbobi" Kame jikinta take sake yi, saboda gudun kar ya kuma dukanta, aikuwa sai da ya sake takata da ƙafarsa, sannan ya fita. Sai da ta tabattar ya fita, sannan ta iya ɗagowa a hankali, ta bi hanyar da ya fita da kallo. Ta kalli jikinta, da ya ɓata mata da ƙasar takalminsa, tun da tazo gidan sau ɗaya tayi wanka, shi ma ba soso babu sabulu. Kayan jikinta tun wanda ta zo da su ranar da aka kawota, Iya ta ce za a aiko mata da kaya, amma shiru. A hankali ta saka hannu ta karkaɗe ƙasar, tana takaicin yadda ya ƙasƙantar da ita ta hanyar takata da takalminsa mai datti da taɓo. Tayi shiru tana ta saƙe-saƙe a zuciyarta, ta haɗe gwiwoyinta, ta kifa kanta, ta nemi hawayen ma ta rasa, sai zafi da ƙunar zuciya. Yaya Hashim bai zo ya ganta ba, maman na'ima ba ta zo ba, tayi ta lissafin mutanen da take sanya ran su zo su ganta, amma basu zo ba. *** A ɓangaren mariya kuwa, tuburan depression ya zame mata hauka, ga ta dai a nutse, sai dai babu cikekken hankali, wasu lokutan sai hankalin ya dawo, ta yi ta harkokinta, amma da abun ya juyo, sai daina cin abinci, ta daina magana. Duk wanda ya shigo da ƙaramin ɗa gidan, sai ta ce sai an bata umminta, ko ta ɗauki fulo tana yi masa wasa, ta ce ummi ce. Idan ƴan yara mata suka shigo gidan, suma sai tayi ta kiransu da sunan ummi. Ta ce "Yaya ɗanlami, kalli yadda ummina tayi wayo ta girma". Ya amsa mata da "Tubarkallah, ki yi ta yi mata addu'a, Allah ya ƙara rayata" Ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Ba ummi ba ce, ummina baƙa ce mai kyau, bari in tashi in zuba ruwa in yi mata wanka, na goyata garin nan da sanyi" Yayi saurin tashi, ganin da gaske tana ƙoƙarin kama ƴar mutane ta yi mata wanka, ya ce "Ki yi haƙuri in anjima sai ki yi mata wankan". "To ai bana son babanta ya dawo ya tarar da mu, ba mu yi wanka mun yi kwalliya ba, kaga yana son turare da lallen da nake yi masa, baban ummina har kayan kasuwa yake sayo mana" haka tayi ta gwamutsa masa zantuka. Yayi shiru yana kallonta, ba zai manta zuwan ƙarshe da yayi gidan Iya ba, da yaje da maganar neman alfarmar ɗaukar ummi, ko na ƴan kwanaki ne, dan hankalin mariya ya kwanta, ta fara samun matsala a ƙwaƙwalwa, amma ta kada baki ta ce Allah ya ƙara, hauka yanzu ta fara da yardar Allah sai ta din ga bi bola-bola hakkin ran ɗan ta ne. Tun daga nan yayi alwashin ummi ko ƴar gwal ce ba zai kuma zuwa da niyyar a bashi ba. Mama ta fito ta taya shi lallaɓa mariya, suka mayar da ita ɗaki, sai surutai take, tana basu labarin baban ummi da kuma ummi, sai dai ko da wasa ba ta zancen Iya, ko sauran mutanen gidan sai ummi da babanta. Ummi ta sakankance idiris ba zai kwana a gidan ba, dan haka har ta hau kan tsurar katifar ta kwanta, sai dai ta kasa rufe idonta tayi bacci, saboda tana jin tsoro, ga gari hadari na ta haɗuwa, sai addu'a take Allah ya sa kar ayi ruwan sama. Sai da hadarin ya haɗo gaba ɗaya tare da iska, kawai ta ga hasken tochlight a tsakar gida, inuwar Idris ta hango, ya tunkaro ɗakin. Ta runtse idanunta, tana fatan Allah yasa ba shi bane ba, sai dai ta ji ya mayar da ƙofa ya rufe, hakan ya tsananta bugun zuciyarta. Ba ta san me yake yi ba, saboda ta rufe idonta, ƙafafuwanta ya taka ya ce "Ke dalla tashi" yayi maganar a matuƙar kausashe cikin rawar jiki ta motsa, ta tashi zaune, me zata gani Idris a tsaye a kanta tsirara kamar mahaukaci. Ihu ta saki, ta runtse idanunta ta dafe kanta da hannayen ta. "Dalla malama rufe mini baki, ki tashi na ce, uban meye baki sani ba? Munafukar banza da ta wofi, maƙaryaciya an cuceni an haɗani da saura, har da zuwa ki gaya musu bana kwana a gida, ai na san kin san komai kin saba". Kyarma ta fara yi, taƙi motsawa, aka kece da wani irin ruwan sama mai ƙarfin gaske, ba ka jin komai, sai sautin zubarsa da ƙarfin gaske a kan kwano. Ganin za ta ɓata masa lokaci, ya sanya ya jefar da fitilar hannunsa yayi kanta, kamar zararre. Ayshercool 08081012143 *CUTARWA!* *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* BRIGHT PENS (FREE BATCH) P12 Kamar mai shirin tarayya da dabba, haka yayi kan ummi, ya fara yage suturar jikinta, yana ja tana ja, tana ihu tana bashi haƙuri. "Ba zaki rufe mini baki ba?" Yayi maganar cikin fusata. Warin bakinsa ya daki hancin ummi, kai ka ce an buɗe masai. Sai dai ba ta gama shaƙe warin bakinsa ba, warin gashin kanta ya daki hancinsa, gashi ne fal Allah ya bata shi, sai dai kasancewar babu gyara babu tsafta, ya sanya yake wani irin tsami mara daɗin shaƙa. Sai da ya ware gashin ya sauka bayanta, warin ya ƙaru har wani gafi gashi gashin yake yi, saboda tururin warin dauɗa da ƙazanta. Ƙyale gashin yayi, ya cigaba da ƙoƙarin rabata da suturar jikinta, sai dai nan ma jikin ummi, warin dauɗa yake yi, da tsamin gumi, saboda rashin wanka da kula. Har ɗauke numfashin sa yake yi, ita kanta ummin warin hammatar idiris ɗin ya hanata sukuni, yafi ƙarfinta nesa ba kusa ba, amma ba ta gaza ba wurin ƙoƙarin kare kanta. Duk da a duhu ne bai hana shi, kifa wa ummi mari ba da dukkan ƙarfinsa, Allah ya sa hannunta ya samu ba fuskar ba, amma sai da ta gigice. Marin da yayi mata ya sanya ta saka kataɓus, har ya cimma in da yake burin zuwa, sai dai wari da ƙarni mai haɗe da zarni ya bugi hancinsa sai da yayi baya, take ya ji cikinsa ya yamutsa masa, kamar zai yi amai, nan da nan zuciyarsa ta fara tashi. Duk yadda ya so ɗauke numfashin sa ya kasa, wani irin baƙin ciki da takaici ya ninku a zuciyarsa, ya laluba ya ɗaukko fitilarsa ya hasketa, ta kare jikinta sai kuka take yi. Ya tashi ya rufeta da duka, abun da ta fi tsana, ya din ga takata da ƙafarsa, sannan ya janyota ya hankaɗata waje ana wannan ruwan saman, ba tare da imani ko tausayi ba. Kuka take iya ƙarfinta, tana danna ƙofar ɗakin, amma ya saka sakata ta ciki. Tsakar gidan ya shaƙe da ruwa, saboda rashin magudanan ruwa a unguwar. Jikinta duk ya yage mata sutura, kuma a haka tsirara ya hankaɗota waje cikin ruwan sama. Ga wani irin tsoro take ji, balle ta tafi ɗaya ɗakin, haka ruwa ya din ga dukanta tana kuka. Tun tana saka ran ruwan zai ɗauke, har ta zubawa sarautar Allah ido, ƙafafuwanta suka gaji saboda tsayuwa, ruwan saman nan ya ƙarasa zuba a kanta. Ta din ga buga ƙofar ɗakin a hankali ta na cewa "Dan Allah yaya idiris ka buɗe mini na ɗauki kayana, sanyi nake ji dan Allah" tayi bugun har ta gaji, jikinta ya din ga wata irin karkarwa saboda sanyi. Ruwan, bai gama ɗaukewa ba, ta fara takawa a hankali ta na ƙanƙame jikinta saboda ƙyanƙyamin ruwan da ya kwaso dagwalon unguwar ya shigo ya taru a gidan. Ɗaya ɗakin ta nufa, sai dai kasancewar ba taga babu ƙofa, a buɗe yake, shima ta tarar ya malale da ruwa, babu in da za ta zauna, ta samu wuri ɗaya ta raɓe tana cigaba da kuka. Har garin Allah ya waye ummi na tsaye, babu wurin da zata raɓa ta zauna, saboda an yi ruwa ba ɗan kaɗan ba. Gari ya fara haske tana sanya ran ya buɗe ƙofa ta suturta jikinta, amma bai buɗe ba, ta din ga fargabar kar a zo gidan a tarar da ita jikinta babu sutura. Sai da gari yayi haske tar, sannan ya zare sakata ya fito ya shiga banɗaki, tana hangen sa ta taga, ganin ya shiga banɗaki, ya sanya ta fita ta shiga ɗakin, ta kwashi kayanta da duk ya yayyaga, ta saka, jikinta sai wata irin tsuma yake yi, saboda sanyi, ga ciwo da jikinta yake yi mata da ƙafafuwan ta. A gurguje ta yi alwala, ta koma ɗakin yin sallar asuba, duk a ɗarare take cikin tsoro take yin ta. Aikuwa a raka'a ta biyu ya dawo ɗakin, bai damu da salla take yi ba, ya hankaɗeta, saboda wata irin tsanarta da yake ji a cikin zuciyarsa. Ta miƙe ta cigaba da sallar, ya tsaya a kanta yana kallon ta yana huci, da ta idar da sallar, ta miƙe zata bar masa ɗakin, amma ya janyota ta baya, ya sake hankaɗata ƙasa. Wata irin ashar da yayi mata sai da ta kalleshi a firgice, ya din ga ɗura mata ashar yana cin mutuncin ta da na iyayenta, har da mahaifinta da ba ya raye a duniyar, har da kiranta da ƴar iska lalatacciya. Ummi ta yi shiru ta sunkuyar da kanta ƙasa, ta nemi hawayen ma gaba ɗaya ta rasa. Har zai fita ya dawo, ya din ga dukanta hannu da ƙafa, cike da tsana da jin haushin ta. Ya gama rashin mutuncinsa ya fita, ta tashi a hankali, ta koma gefe tayi zuru da ido. Sai a lokacin kuma ta samu damar yin kuka, jikinta sai ciwo yake yi, ga yunwa tana ji, gashi haryanzu sanyi take ji, ta kwanta a wurin, ta hau bacci. Sallamar da Iya take kwaɗawa a tsakar gida ne, ya sanya ummi farkawa, ta fito da sauri, ta ga Iya tare da yaya, mahaifiyar su Idris. Murmushi ummi ta yi ta ce "Iya sannu da zuwa, yaya ina kwana" "Ai kya bari mu shigo mu zauna ko" Ta basu hanya suka shiga ɗakin, suka zauna, yaya tayi ƙuri tana kallon ummi, Iya ta ce "Ke lafiya na ga kayanki a yayyage?" "Ba komai" "Kamar yaya ba komai, kamar wadda ta yi dambe" hawaye ne ke shirin taruwa a idon ummi. "Kuma dan ƙazanta tun da aka kawo ki baki canza kaya ba, yau wurin kwana biyar". Ummi ta buɗe baki za ta yi magana, ta kasa hawaye suka riga maganar fita. Yaya ta ce "Menene na kuka kuma ummi?" Iya ta ce "Sangarta mana, idan zaki yi wa kanki ƙiyamullaili ki zauna ki daina wannan kukan shikenan, idan ba zaki daina ba, sai ki yi ta yi, ga kaya nan na ɗebo miki a kayan auren da aka kaiwa waccan, abun bai yiwu ba, sauran an sayar an bashi kuɗin yayi muku cefane, sadakin ki kuma, na bayar a sayo akuya a bayar da kiwo". "Dan Allah iya ki mayar da ni gida, bana son zaman nan" "Ki kiyayeni ummi, tun kan na ɓata miki rai, bana son shashanci, ki tashi ki yi wanka ki canza wannan kayan" Tashi ummi ta yi tana kuka, ta fita tsakar gida, suma fitowar suka yi, wai har tafiya za su yi. Ummi ta tsaya tana kallonsu, suka fice, wai wata unguwar zasu je, to da me za ta yi wankan, ko ruwa ba ta da shi? Ta koma ɗaki ta zazzage lesar vivar da Iya ta kawo mata, atamfa ce kala uku, sai sabulun wanka uku, man shafawa ɗaya da soson wanka. Sai kuma 'yar tsala, a ƙulle a leda, ummi ta ture kayan ta kwanta, wani irin zazzafan zazzaɓi ya rufeta, saboda dukan ruwan sama. Sai da ummi ta kwana biyu tana zazzaɓin nan, babu abun da ya shafi Idris, da ya dawo zai koreta daga ɗakin, bayan ya gama ci mata mutunci da zaginta, wasu lokutan sai yayi mata dukan tsiya ma, duka na cin mutunci, haka take kwana a ɗaya ɗakin da babu ko ƙofa a ciki, idan aka yi ruwan sama, haka zai sameta a ɗakin nan. Ƙarshe ma ya watso mata kayanta da ga ɗakin da katifa take, ya ce ta koma ɗaya ɗakin. Da ya tuna ƙarin da ya ji tana yi, da kuma yadda suka din ga lalubeta tana yarinya, sai ya ji ya ƙara tsanarta, da ganin an bashi saura. Dama abinci ba a magana, ba bata yake yi ba, wasu lokutan ne idan yaran gidan su za su zo, babar Idiris ɗin kan zuba mata abinci a kwano a kawo mata. Tana kwance a ɗaki tana numfarfashi,  zazzaɓi da ciwon kai sun ƙi sauka, fitsari ya dameta, ta tashi da ƙyar, ta je ta yi, tana shirin komawa ɗakin, ta ji an ce "Ummi" Tana waiwayawa taga Na'ima, ai sai ta nemi ciwon ta rasa, cikin wani irin zafin nama, ta rungume Na'ima ta fashe da kuka. Ita ma Na'iman kuka take yi, ta ɗago ummi ta kalleta ta ce "Ummi ba ki da lafiya ne? Na ji jikinki zafi?" Ta jinjinawa na'ima kai. "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, yanzu ummi a rasa wanda za a aura miki sai wannan ɗan iskan, dukan ki yake yi kenan? Kalli shaidar yatsu a fuskarki" Ummi dai ta yi shiru, daga baya ta ce "Mu shiga ɗaki" Saroro na'ima ta bi ɗakin da kallo. "Ummi kar ki ce ba su yi miki kayan ɗaki ba?" "Suna can ɗakin, koro ni yayi nan shi ne yake kwana a ɗakin" Na'ima ta zauna tayi kuka mai isarta sannan ta kalli ummi ta ce "Wai ke ba ki san in da mamanki take ba? Anya ma kuwa sun san halin da ake ciki?" "Yaya Na'ima nifa tun da aka tafi da mama ban sake ganinta ba, dan Allah idan kin san in da take ki kaini, na gaji, wallahi yaya Idris dukana yake yi, duk jikina ciwo yake zai kasheni" Ta rungume ummi, ta din ga rarrashin ta, ta ce "Kiyi haƙuri ummi, ban ma san an yi miki aure ba, mama ce ta aika ƙanin mijina ya gaya mini, Allah yana sane da ke ummi, bari na je gida na kawo miki abubuwan da na kawo miki, sai na kawo miki tabarma da labule, a kafa a ɗakin, tabarmar ki din ga kwana a kai" Ummi ta yi ta mata godiya, ta bata abinci, ta aika ƙannenta suka sayo mata magani, aka kafa labule, ta shimfiɗa tabarma, sai ɗakin ya ɗan yi kyan gani. "Yaya na'ima, dan Allah idan Allah ya yassare miki, ki saya mini wando, nawa ya ƙarasa lalacewa, ba zai saku ba" "Ummi meyasa ba zaki din ga zuwa wurin mama kina gaya mata ba? Ya za ayi ki rayu da wando guda ɗaya, abun da a ƙalla a rana ana so ki canza biyu" Ummi ta yi shiru, tana wasa da yatsun hannunta, yanzu ma dan ta ƙure ne ta nemi alfarmar na'ima, dan idris ya ƙarasa shi, wandon har da in da ta kama take ƙullewa. Ta ji daɗin zuwan na'ima, ta bata abubuwa da yawa, har da kuɗi, sai bayan la'asar ta tafi, kuma Allah ya taimake ta, Idiris bai dawo ba a lokacin. Duk yadda ummi ta so ta yi wa naima bayanin halin da take ciki, kasawa ta yi, ta ji abun yayi mata girma ta faɗa, dan haka ta yi shiru da bakinta, ta samu ta saya mata wanduna guda huɗu, har da ribbon. Duk in da idris ya haɗu da abokansa, suka yi masa kirarin ango, da tambayarsa yaushe za su cin girkin amarya, sai ya hau masifa yana basu labarin halin da ummi ke ciki, na mummunan ciwon sanyi da yadda take bugawa, da ƙazanta tare da ƙorafin ragowa ce aka haɗa shi da ita, su yi ta masa dariya, suna ce masa angon ɗoɗɗoya. Tare da tabattar masa, idan bai yi da gaske ba, sai ya kwashi ciwon. Sai dai ko sun tambaye shi dalilin fasa auren sa da Hindu, sai ya ɓoye musu gaskiyar zancen. Haryanzu kuma bai rabu da hindu ba, yana lallaɓawa su haɗu a wani wurin na daban, duk da tarin kashedi da mahaifinta yayi mata a kan idiris. Na'ima kuwa a ranar  zata koma gidanta, suka haɗu da magaji a hanya, suka haɗu suka gaisa. Ta ce "Yaya magaji ashe aure aka yi wa ummi babu labari?" Hashim ya ce "Ke dai bari na'ima, abun ne yazo babu shiri, ni kaina ban san da zancen ba sai ana gobe ɗaurin aure". Na'ima ta gyaɗa kai ta ce "Amma, ka yi haƙuri da abun da zan ce, wallahi ku din ga gaya wa kakarku da ɗan uwanka gaskiya, ya za a katsewa ummi karatunta, kuma a haɗata aure da wanda baya ƙaunarta, dama ita ba bi ta kanta za ayi, aji ko tana son sa ba, gaba ɗaya a firgice take a cikin gidan nan, jikinta duk shaidar duka, ya korota daga ɗaki, ɗakin da na tarar da ita, ba ƙofa babu taga, babu abun zama, ba ya bata abinci, wace irin rayuwa ce haka? A gidanku ba ta huta ba, an aurar da ita, ta buɗe sabon babi na ƙalubale, sai yaushe za ta huta kenan? Meyasa Iya ta tsani ummi ne, kamar ba a cikin jikokinta take ba?" Hashim ya numfasa, cike da damuwa da takaici ya ce "Biyayyar da iyayenmu ke yi wa Iya, ta samo asali ne ga wasiyyar mahaifinmu, na lallai su yi mata biyayya. Bayan haka ban san dalilin da ya sanya bayan biyayyar suke rufe idonsu a kan gaskiya ba, su kasa nuna mata hanyar da ta dace ba. Nayi iya yi na a kan auren nan, sai dai sun fi ƙarfina, ni dama ba wani shiri muke yi ba, saboda bani da kuɗi, Idris kuma sunan mahaifinta ne da shi. Ƙiyayyar ummi kuma, dama ba ta son mahaifiyar ummi, saboda kawu Magaji yana matuƙar son ta, har wasu lokutan baya iya ɓoye son da yake yi mata, bugu da ƙari, baban ummi ba shi da komai, bai mutu ya bar komai ba, duk da haka dai, ban san dalilin da ya sanya ta tsananta ƙiyayyar ummi haka ba. Zan cigaba da yi wa idiris nasiha, duk da ba jin shawara yake yi ba, zan kuma biya ta gidan yanzu, in ga halin da take ciki". Jiki a sanyaye na'ima ta ce "Yakamata kam, ummi na buƙatar kulawa da jaba jiki, har ga Allah ina jin tausayinta sosai da sosai, dan Allah yaya magaji ka din ga zagayata". "Kar ki damu, in sha Allah, ba zai gagara ba, ina godiya sosai da gudunmawar da ki ke bawa ummi". "Bakomai yaya magaji, ummi ƙanwata ce, ba zan manta karamcin iyayenta a gare ni ba, da yadda suke girmama iyayena ba" "Haka ne, ki gaida gida, da maigidan" Suka yi sallama, kowa ya tafi. Kasa wucewa gida magaji yayi, ya wuce gidan Idris da bai taɓa zuwa ba. Sallama yayi ya tsaya a waje, ummi ta leƙo, tana ganinsa tayi murmushi ta ce "Laa yaya magaji, shigo baka zo ba sai yau" Ya kalleta duk da tana da duhu, amma ga shaidar mari nan a gefen idonta. Ta yi gaba ta ce masa ya shigo, ya ce "A'a bani abun zama, na zauna a nan" Ta shiga ta ɗaukko masa tabarma, ta shimfiɗa masa ta ce "Yaya yaya na'ima ta zo fa" Ya ce "Haba?" "Wallahi, duk ta sai mini kayayyaki ta bani, ita ta bani tabar nan ma" "Masha Allah, Allah ya saka mata da alkhairi" Ta ce "Amin" Ya ɗan dube ta, ya ce "Ummi babu wata matsala? Komai lafiya ƙalau?" Ta jinjina masa kai ta ce "Eh". "Na san ko baki faɗa ba, akwai matsala ummi, amma dan Allah ki kwantar da hankalinki, komai zai wuce in sha Allah" "Yaushe zai wuce yaya? Gobe ko jibi?" Tayi maganar idanunta na tara hawaye. "Lokaci ne ummi, zai zama tarihi" Tuni idanuwanta suka fara zubar da hawaye. "Ki dake ummi, ki ƙarfafi zuciyarki, na san a cikin matsala ki ke, ki yi haƙuri ummi, ki share hawayenki, zai zama murmushi wataran" goge hawaye take yi, sai dai tana gogewa wasu suna zubowa. Idiris ne ya bankaɗo babu ko sallama, yadda ummi ta zabura kawai ya isa ya baka tausayi. Ko kallonsu bai yi ba, ya shige ya buɗe ɗakin da yake kwana, ya shiga. Hashim ya tashi ya bi bayansa, ummi ta karkaɗe tabarmar, ta ɗaukko tsintsiyar da na'ima ta bata, ta yi shara, hayaniyar hashim ta din ga ji, da idris. Hashim yana ce masa "Ka ji tsoron Allah wallahi, idan ka cigaba da biye wa Iya, wallahi Allah ba zai barku ba, kuna ta azabtar da marainiyar Allah ba gaira babu dalili". "An azabtar da ita ɗin, ni na ce a aura mini ita? Ko na ce ina son ta ne, kai meya hana a aura maka ita? An bani saura ƙazama mummuna, Wallahi ba zan zauna da ita ba, sai ta gudu da ƙafarta". "Amma ita ma ai ba cewa tayi tana sonka ba, haɗin Iya ne, ita tayi haƙuri, kai me zai hana ka yi haƙurin?" Idris ya ce "ba zan yi haƙurin ba, ka fita daga harkata, ko kai ma na karta maka rashin mutunci" Haka suka yi baran-baran, hashim ya fito, ummi tana ce masa kai gaida gida, kai kawai ya jinjina mata ya tafi. Yana fita, Idris ya dirar mata da duka da zagi da cin mutunci kamar yadda ya saba, yana iƙrarin ƙararsa ta kai wurin magaji. Maƙwabciyar su da ta kasance dattijuwa, yau ta kasa jure ihun ummi, ta shigo kawo mata ɗauki, ta din ga bashi haƙuri, amma mursisi ya ce ta fita ta bar masa gida, ganin idiris bai yi kalar mutunci ba, ya sanya ta fita ta bar gidan tana tausaya wa ummi. Tun daga ranar ya ƙara tsananta azabtarwar da yake yi mata, gashi ya tula mata wankinsa, ya ce tayi masa, idan tayi bai fita ba, ya kamata ya zane ta, ban da zagi da cin mutunci. Abinci kuwa ko tumatir bai taɓa kawowa ba, sai dai ta aika wa iya, Wataran ta bata, wataran ta ce ba ta da shi. Ƙarshe sai da iya tayi ta mata faɗa, wai ba zata iya rufawa Idris asiri ba, ta san dai ba wata cikakkiyar sana'a ce da shi ba, ranar da ya kawo su ci, idan ba shi da shi ta din ga haƙuri. Dattijuwar matar nan ta fuskanci halin da ummi take ciki, ta ɗauki ragamar ciyar da ita, idan ta cewa ummi ta gudu ta je gida ta kai ƙarar abun da yake yi mata, sai ummi ta ce ko ta je dawo da ita za ayi. Da ya kalli ummi, ya tuna a yanayin da ya sameta, sai ya ƙara ƙaimi wurin cutar da ita, haɗi da zaluntar ta. Idan aka zo ana sallama da shi abokansa, sai ta jiyo suna kiransa da angon ɗoɗɗoya, ba ta kawo komai a ranta ba, sai ranar da ta jiyo suna tambayarsa ina amaryarsa ɗoɗɗoya, ya ce musu kar su sake haɗa shi da wannan jakar yarinyar. Duk da ƙarancin shekarun ummi, a lokacin ta fuskanci asiri ya tona mata a wurin abokansa, hakan ya sanya ta yin kuka da har kanta ya yi ciwo. A haka a wannan baƙar azabar, tayi wata guda cir a gidan sa, tun tana tsoronsa har ta fara dakewa da duk abun da zai yi mata yayi mata. Yau ta tashi da wani irin zazzaɓi mai zafin gaske, wanda baya rasa nasaba da dukan ruwa da kuma azababben sauron da yake cizonta a wannan ɗakin. Ga gudawa da take zugawa babu ƙaƙƙautawa, jikinta duk yayi weak. Bankaɗa labulen yayi, ya tarar da ita a kwance, ya watsa mata kayansa ya ce ta wanke masa. Shiru tayi ba ta motsa ba, ya daka mata tsawa ta ce "Yaya bani da lafiya" "Ina ruwana, dalla fito" Ta janyo jikinta ta kwaso kayan ta fito, ya fita sayen omo, ta kwanta a kan kayan, tana jin ɗumin ranar dake ratsata, wanda hakan ya sa zazzaɓi ƙara rufeta. Azabar zafin dukan da yayi mata da ƙafarsa yasa ta tashi da sauri, tana riƙe hannunta. "Bacci na ce ki yi?" Shiru tayi tana sunkuyar da kai. Wani irin yawu ya haɗiye, yana ƙare wa ummi kallo, duk baƙin fatar nan ta ta fatar tana da ɗaukar ido. A wurin yayi yinƙurin sake afka mata, sai dai ba ta sauya zani ba, duk da ta samu sassauci, na ciwon saboda yanzu sau biyu take sauya wando a rana, kamar yadda Na'ima ta gaya mata. Amma duk da haka tana wannan ƙarin mara daɗi, duk da jikinta baya wari yanzu, saboda ta samu sabulun wanka. Zura masa ido kawai tayi, saboda a galabaice take da ciwo Wata mummunar ashar yayi mata, yana zubar da yawu, ya ɗagota ya din ga kifa mata mari. Kukan ma ba ya iya fita, saboda azaba da masifar idiris, da yake abu kamar dabba ba ɗan adam ba. Ya din ga tsine mata albarka, da ita da iyayenta, dan har Iya sai da ya zaga. Ƙarshe ma ya danƙara mata saki a wurin. Ƙafarta ko takalmi babu, ta gyara suturar jikinta ta fice daga gidan a haka, ta tafi gida ga hannunta ɗaya kamar ba a jikinta yake ba, saboda takata yayi a hannun. Iya da ke iza wuta ta miƙe tana faɗin "Ke lafiya?" Kan ummi ta yi magana, jiri ya ɗebe ta ta faɗi ƙasa. Da sauri Iya ta ƙarasa kanta ta ce "Ke, menene wai?". "Iya zan mutu, yaya idris zai kashe ni, dan Allah kar ki mayar da ni, ya ce ya sake ni" tayi maganar cikin gunjin kuka. Ta taɓa jikin ummi ta ji zafi, ga fuskarta shaidar yatsun Idris kwance a fuskar ta har idonta yayi taruwar jini. "Lallaɓa ki tashi ki shiga ɗaki ki zauna, daga yin aure ba a kashe shi ba, bari dai ya zo mu ji me ki ka yi masa" Iya ta tashi ta fita. Kuka ummi ta din ga yi, tana jin dama ta mutu ta huta, idan aka mayar da ita gidan idris ta san sai ya kashe ta. Da ƙyar Hashim ya nemo idris, aka nemo babansu, domin jin menene yake faruwa. Sai dai daga mugun kallon da yake yi wa ummi, ka san babu Allah a ransa. Babu zato babu tsammani sai ga kawu yahaya ya dira a gidan, kuma bai tsaya ko ina ba sai sashin Iya. Sai dai babu walwala ko fara'a a tare da shi, suka gaisa da Iya da ɗan uwansa, da su Hashim. Sannan ya kalli Iya ya ce "Iya dan me za a aurar da ummi, ba tare da na sani ba? Sai shekaranjiya magaji yake gaya mini?" "Saboda kai ne ubanta? Uban waye ma ya ganka balle ya gaya maka, tangarɗa aka samu da wadda zai aura, na saka aka yi da ita dan rufuwar asirinmu". Ummi da baccin wahala ya ɗauka, kamar a mafarki ta ji muryar kawu yahaya, miƙa hannu ta fara yi ta ce "Kawu" Cikin azama ya nufi ummi ya ce "Na'am mamana" "Dan Allah ka kai ni wurin mama, idan na koma gidan Idris kashe ni zai yi" ganin tana ƙoƙarin tashi ta kasa, ya sanya ya ɗago ummi. "Innalillahi wa Innalillahi raji'un" ya faɗa a razane. Fuskar ummi ya gani a kumbure suntum, ga hannunta ɗaya ma ya kumbura ba ta iya motsa shi sosai. "Meyafaru haka?" "Dukana yake yi kawu, dan Allah kar ka bani a nan wallahi mutuwa zan yi, idan baka san in da mama take ba, ko gidan marayu ka kai ni, ko idan akwai makarantar almajirai ka kai ni, zan mutu wallahi " tayi maganar tana wani irin gigitaccen kuka. "Kar ku ce mini shi yayi mata wannan dukan?" Iya ta ce "Ka ga Yahaya, ba abu ne na tashin hankali ba, abun da muke shirin sasantawa kenan, kai me take yi maka ne?" Cikin fitsara da rashin kunya ya ce "Haba Iya, kin san ni ba son ta nake yi ba, yarinya da take saura ce, ai kin san komai aka liƙa mini ita, ga sanyi ya kasheta ban da wari da ɗoyi ba abun da take yi, an liƙa mini na kwashi masifa gaskiya ba zan iya ba, jikinta kamar an buɗe masai, nima ba iya zama zan yi da ita ba". Tsit suka yi, babu wanda ya zaci fitowar wannan maganar daga bakinsa, baƙin ciki da takaici ya rufe Hashim. "Madalla, ka iya rubutu ai ko?" Ya jinjina kai. Kawu yahaya ya ciro takarda da biro ya ce "Sakar mini ƴa ta" Iya ta fara "A'a Yahaya, ai dauɗar gora ciki ka sha ta " "Ba wata dauɗa iya, koma menene ya samu ummi laifinki ne, kina me sanyi yayi mata wannan kamun? Da dauɗar gorar ciki ke shan ta, shi ya kasa rufa mata asiri ya nema mata magani, ya tona mata asiri haka, shi mai ya hana ya sha dauɗar gorar?, laifin waye idan ba naki ba, ya saki ummi, da ita zan tafi, abun da yayi kansa ya yi wa, ƴar shekara sha uku aure wata ɗaya ya rabu, In sha Allah ba zata wulaƙanta ba, na yi imani da Allah balarabe ba zai bari iyalinmu su wulaƙanta bayan bamu ba" yayi maganar ƙasan zuciyarsa yana jinjina girman hukuncin da ya yanke, dan ya san da badaƙala idan ya je da ummi gidansa. (Ina godiya da tarin comments da ake yi a kan litattafan bright pens, cutarwa, munafukin miji, yi wa kai, masu ƙorafi a kan littafin cutarwa, ayi haƙuri da yadda labarin yazo, ina ganin sharhi da ƙorafe-ƙorafe ina godiya sosai 🙏) Ayshercool 08081012143                                        *CUTARWA!* *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* BRIGHT PENS (FREE BATCH) P13 Iya ta ce "A'a Yahaya, kar mu yi haka da kai, wannan abu ne na cikin gida da yakamata a sasanta shi, wannan ai sai asirinmu ya tonu, duniya ta zage mu" "Iya zagi na nawa kuma? Kalli jikin yarinyar nan fa, baiwar ubansa ce ita? A gabanki a gaban ubansa yake aibata ta yake cewa baya son ta, baya ƙaunarta, wallahi dole ya saketa, zan je da ummi ta cigaba da karatunta". "Gaskiya ban lamunta ba yahaya, ba zaka ɓata zumunci ba da abun da na ƙulla dan ƙarfafa zumunci ba". Hashim da bai yi niyyar sanya baki ba, sai da ya ga abun na iya yaƙi ci ya ƙi cinyewa ya ce "Iya wane zumunci kuma banda wanda aka ɓata?" "Rufe mini baki dan ubanka, ai duk kai ne munafikin da ka kunno kowacce wuta, ban yadda a tafi da ummi ko ina ba, ko auren ya mutu, muna nan a bar mini ita". Yahaya ya kalli Iya ido cikin ido ya ce "Wallahi iya idan ki ka hana ni tafiya da ummi, zan ɗebowa idiris hukumar kare hakkin ɗan Adam, su bi mata hakkinta, kuma idan suka tashi, har ke ba zasu bari ba, da duk mutanen gidan nan, na farko ga child abuse, by forced marriage, kun mata auren dole da ƙanan shekaru, ga dukanta da ci mata mutunci, deformation of character ɓata mata suna, ta hanyar yaɗa larurar da take fama da ita a cikin mutane, wanda duk ya zo kunnena tun kan na zo nan na samu lanari, kuma mariya ma zata iya shigowa cikin lamarin nan, ƙwace mata ƴa babu dalili da ki ka yi, dan dai suma ba su san ƴancin su bane, da sun haɗa ki da hukuma, da sai kin basu ƴar su". Saminu ya ce "A'a yaya yahaya, ba za ayi haka ba" Cikin rikicewa Iya ta ce "Yahaya ni zaka kai ƙara hukuma ka saka a rufe ni?" "Ba ƙararki zan kai ba, ƙarar wannan sakaran zan kai, idan kuma na kai ƙararsa su hukuma zurfafa bincike zasu yi, ina gaya miki abun da hakan ka iya haifarwa ne, kai kuma ɗauki takarda da biro, ka sakar mini ƴa, ko daƙiƙancin naka bai bari, ka iya rubutun ba?" Cikin kumbura baki ya ɗauki takarda da biron, ya rubutawa ummi saki biyu. Kawu yahaya ya karɓa, ya kalli ummi ya ce "Tashi in tayaki ki haɗo kayanki mu tafi" Magaji ya ce "Bari na tayata" a hankali ta ce "Ai kayan suna can gidan, sai kuma kayana da ke ɗakin itace" Kawu Yahaya da kansa ya tashi, ya je ɗakin itacen, ya ɗaukko vivar kayan ummi, sai dai ya ga tsummokara ne kawai, dan haka ya ce ba za su tafi da su ba. Iya ta din ga harar ummi, amma ummi tayi kamar bata gani ba, magaji ya kawo kayan ummi. Jama'ar gida suka taru, suna kallon ummi za ga tafi birnin kanon dabo gidan kawu yahaya, wasu na tausaya mata, wasu kuma na yi mata murna. "Yahaya" Iya ta kira sunansa. Ya amsa mata, ta ce "Ka yi mini alƙawarin ba za ka kai ummi wurin mariya ba, dan idan haka ta faru, abun da zai biyo baya ba zai yi mana daɗi ba". "Abu ɗaya na sani, na ɗauki ummi tsakani da Allah dan inganta rayuwarta, ni ban san a in da mahaifiyar ta take ba, amma akwai lokacin da lallai dole a nemi dangin mahaifiyar ummi, ta gansu, dan babu in da shari'a ta ce a yanke alaƙa tsakanin uwa da ɗan ta, ko da kuwa kafura ce, abun da yake tsakanin ki da mahaifiyar ta daban, kuma bai kamata ya shafi ummi ba" Iya tayi muƙus, dan ba ta son yi wa kanta sagegeduwar ɗan abun duniyar da yake bata. Sosai kawu yahaya ya yi wa ƴan uwansa ta tas, a kan abubuwan da suka faru a kan ummi, kasancewar shi ne babba suna girmama shi, duk da kaf ɗin su sun riga shi yin aure, dam su ba karatun boko suka yi ba, wasun su ma shakara sha tara suka yi aure, amma suna girmama shi sosai mussaman da yana da abun duniya. Magaji ne ya riƙo ummi, sai layi take saboda yunwa da kuma rashin lafiya. Magaji ya ce "Ummi shikenan sai tafiya, in Allah ya yarda wahala ta ƙare, sai jin daɗi da kwanciyar hankali, ki kula da kanki, ki yi karatu da kyau". Ummi ta ce "To yaya, kai ne ka gaya wa kawu halin da nake ciki?" "Eh ummi, aron waya na samu, na kira shi, idan ba haka ba, bani da wata mafita da zan taimake ki". Ummi ta yi ajiyar zuciya ta ce "Allah ya sa kar iya tayi ta yi maka faɗa, dan Allah idan ka ga yaya na'ima ta zo ka gaya mata bana nan, ba zan iya zuwa yi wa mama sallama ba, jikina ba ƙwari ba zan so ta ganni a haka ba" Ya ce "To shikenan, in sha Allah" "To zaka din ga zuwa kanon muna gaisawa?" Yayi murmushi ya ce "Zan din ga zuwa, ai kema zaki din ga zuwa muna gaisawa ko?" Ta yi saurin girgiza masa kai ta ce "In Allah ya yarda ni da gagarwa har abada, ba zan sake zuwa ba, dan Allah idan ka samu labarin in da mama take, ka gaya mini" Sak yayi jikinsa yayi sanyi yana kallon ummi, jin abun da ta faɗa, sai dai bai kamata ya ga laifinta ba, an azabtar da ita azabtarwa mai munin da dan ta faɗi hakan, ba ta yi laifi ba. Kawu yahaya ya tsaya suna magana da kawu Ilyasu da sagir, wanda yanzu suka zo riski zasu tafi. Kawai Idris ya tsinci kansa da dawowa, dan ya tabbattar da gaske tafiya za ayi da ummin? Ko kuwa ba gaske bane ba?. Hannun hashim ya gani a cikin na ummi, ya riƙota sun tsaya suna magana, wani zazzafan abu mai raɗaɗin gaske, tamkar sukar kibiya, ya soki ƙirjinsa. Taɓe baki yayi tare da jan tsaki, hashim suka ƙarasa gaban motar, ummi ta shiga ta zauna tana kallon hashim da ƙofar gidan da nan ne tushenta, amma azabar cikinsa ko zamanin bayi sai haka. Yaran gidan har da mata, da maƙwabta sun yi dandazo suna kallon tafiyar ummi. Kawu yahaya suka gama magana, ya shiga ya kunna motar Ummi ta sauke idanuwanta masu kama da na mage a cikin na Idris, idanun da suka kumbura saboda duka ɗaya yayi taruwar jini a cikin sa, wani irin kallo take yi masa mai kama da na ka saurari dawowata, zaka girbe abun da ka shuka. Hanyar kano suka kama, suna tafe kawu yahaya yana yi wa ummi nasiha tare da rarrashin ta. Ya kalli ummi ya ce "Idan mun je, kar ki kuskura ki gaya wa wani kin taɓa aure, kin ji ko?" Ummi ta jinjina masa kai alamar to. Suna tafe tana amai, kasancewar baya son su yi dare a hanya, ya sanya ya tsaya ya saya mata ruwan gishiri da suga, da kuma maganin zazzaɓi, suka cigaba da tafiya, ya tanbayeta ko za ta ci wani abun ne? Duk da yunwar da take ji, cikinta babu daɗi, dan haka ta ce masa ba ta buƙatar cin komai. Tsayawa yayi ya saya mata kankana, ya ce ta sha, kaɗan ta ci ta kashingiɗa, tana tuna wulaƙanci da cin zarafin da idiris yayi mata, da yadda ya tona mata asiri a gaban mutane. Ko da suka isa kano, wani asibiti ya fara wuce wa da ummi, aka yi mata teses, sannan aka rubuta mata magunguna, har za su tafi, kawu yahaya ya cewa ummi, ta yi wa likitan bayanin ɗaya matsalar ta ta. Sai dai ummi ta sunkuyar da kai, ta kasa magana saboda tsananin kunya da ganin kamar tozarci ne bayanin wannan matsalar ta ta ga wani. Ganin taƙi magana, ya sanya likitan tura su wurin wata nurse, tun da mace ce, za ta fi iya sakin jiki tayi mata bayani. Sai dai ba ta sauya zani ba, nan ma ummi kasa magana ta yi. Nurse ɗin ta kalli kawu yahaya ta ce "Yallaɓai me yake damunta ne? Ta ƙi magana". Ya ce "Kina ji ƴa ta ce wannan, a ƙauye take hannun mahaifiyarmu, aka yi mata aure na je na tarar da matsala mijin ya ce ba ta da lafiya, sanyi yayi mata yawa, auren ma dai ya mutu" Nurse ɗin ta kalli ummi sannan ta kalle shi ta ce "Bawan Allah kai gaka wayayye, ya zaka bari a yi wa wannan yarinyar ƙarama aure a yanzu, kalli fuskarta ma kamar shaidar duka, ni wannan yarinyar ai ba ta fi in saka zani in goye ta ba". Ganin za ta fara yi masa faɗa, saboda yadda ta ɗau zafi, ya sanya ya yi mata bayanin komai. Jikinta duk yayi sanyi, tana jinjina lamarin, gaba ɗaya tausayin ummi ya kamata, wannan ƴar ƙaramar yarinyar ita ce aka yi wa aure, har ya mutu. Ta kalli ummi ta ce "Gaya mini menene yake damunki a wurin?" Ummi ta sunkuyar da kai tare da jin ta a takure. Ta kalli kawu yahaya ta ce "Ɗan bamu wuri" ba musu ya fita waje. Ta haɗe rai ta kalli ummi ta ce "Ke dan gidanku ki gaya mini nan asibiti ne, idan baki warke ba haka zaki yi ta aure yana mutuwa, saboda wannan matsalar". Ummi murya ƙasa-ƙasa ta ce "Ƙaiƙayi yake yi mini". "Tun yaushe?" "An daɗe" "Ya aka yi aka daɗe, wasa ki ke da wurin?" Ummi ta girgiza kai alamar a'a. "To ya aka yi yake ƙaiƙayi, kafin ayi miki auren ya fara ko bayan an yi mikk auren?" "Kafin ayi mini ne?" Nurse ɗin ta numfasa ta ce "Sau nawa ki ke canza wando a rana?" Ummi ta kalleta ta ce "Kan ayi mini?" Auren ne ba zata iya faɗa ba, tana jin nauyin haka. Ta ce "Eh, kan ayi auren" "Wandona ɗaya ne, idan na wanke sai na saka" Tayi ƙuri da ido tana kallon ummi, da ta ji ta ce wando ɗaya. "Yaya ki ke tsarki?" Amsar da ta bawa nurse ɗin ta girgiza ta, dan ciwon sanyin ummi, yana da alaƙa da rashin iya tsarki, da tsugunawa a banɗaki barkatai, da kuma rashin kyakywar kulawa na uwa da wurin bai samu ba. Ta dubi ummi ta ce "Daga yanzu, wando sau uku zaki din ga canzawa a rana, kuma idan ki ka yi bayan gida, sai kin fara wanke wurin fitsarinki, sannan ki wanke wurin bayan gida, ba haɗe tsarkinsu. Kar ki kuskura ki yi fitsari kina ɗigar da ruwan tsarkin, ki mayar da wando jikin ki, ko ki saka jiƙaƙƙen wando, ki samu ɗan tsumma mai kyau, ki din ga wankewa kina ajiyewa a banɗakin da ki ke, idan kin yi tsarki, ko kin yi wanka, ki din ga tsane wurin kan ki saka wando. Idan fitsari ya kama ki a wani wuri daban ba gida ba, ki yi fitsarin a tsaye, idan kin gama sai ki wanke ƙafarki, da jikinki, ki daina shiga banɗaki barkatai" ta din ga yi wa ummi bayanin yadda za ta din ga kula da tsabtar wurin, dan babu wanda ya taɓa zaunar da ita yayi mata wannan bayanin. "Kin fara al'ada ne?" Ummi ta ce "A'a" Nurse ɗin ta a aika ummi ta kira kawu yahaya, ta ce masa "Yallaɓai gaskiya sanyi ya yi mata yawa, kuma na lura rashin tsabta da kula ne ya haddasa mata hakan, dan haka dole ku kula, tun da yanzu ka ce ta dawo hannunka. Ku dawo ranar lahadi akwai gynea doctor ɗin da yake zama, sai ka kawota ta ganshi. Na so ace da mace ku ka zo, sai ta fi fahimtar bayanina, amma kai ɗin ba ta ɓaci ba, ai uba ne kai. A yanzu, abu na farko a sama mata isasshen wanduna, a ƙalla shida zuwa dozen. Sai kuma a sama mata flask mussaman na ruwan zafi, na ta ne ta din ga kama ruwa da ruwan ɗumi. Banda tsarki da sabulu, a samo mata ganyen magarya, a tafasa shi  ta din ga kama ruwa da shi. Kuma ka san shi ciwo ne mai naci, dan haka a kula sosai, sai kuma ku nemi kanumfari, tafarnuwa ba mai yawa ba, da namijin goro, a jiƙa su a robar ruwa mai murfi, ta din ga tsiyaya tana sha, ta yawaita amfani da kanumfarin nan. Sai kuma a samo saiwar zogale a din ga tafasa mata da jar kanwa, ta yi amfani da ko guda ɗaya kafin ku zo ku ga likitan, zata samu sauƙi in sha Allah. Wannan na ɗan gaya muku ne dabarunmu na cikin gida na gargajiya, kafin Allah ya sa ku zo ganin likitan". Ya ce "To shikenan, na gode sosai da sosai, Allah ya saka miki da alkhairi" Ummi ta bi bayansa suka fito, suna tafe a hanya yana jaddada da mata ta riƙe abubuwan da aka gaya mata, ummi kuwa gaba ɗaya jikinta sanyi yayi, wata irin kunyarsa ta rufe ta. Shi kansa yayi mamaki da nurse ɗin ta ce masa ummi ta ce wando ɗaya ne da ita. "Ummi" Ta amsa da"Na'am" "Ki kwantar da hankalinki, magnunnan nan zan saya miki zuwa gobe in Allah ya kaimu, har kayan da zaki yi amfani da su, duk zan yi miki har makaranta zan mayar da ke da yardar Allah, ke dai ki nutsu ki manta da komai, ban yi miki alƙawarin gidana babu ƙalubale ba, amma na san bai kai na ƙauye ba. Ki dage ki yi amfani da shawararin da ta baki kin ji ummana" Ta ce "To na gode sosai" Ya shafa kanta ya ce "Yauwwa Allah yayi miki albarka" Can gagarawa kuwa, Hashim ya sha zagi da cin mutunci da wulaƙanci a wurin Iya, ba Iya kawai ba, har da mahaifinsa suka ƙare masa tas, a kan ya kasa rufa wa ɗan uwansa asiri, da har ya iya sanar da kawu yahaya halin da ake ciki. Shi dai yayi shiru bai ce komai ba, amma har cikin ransa yake jin wannan abun da yayi shine mafita ga rayuwar ummi, kuma hakan da yayi bai saɓawa shari'a ba. Sirikan iya wasu sun jiye wa ummi rabata da gidan nan, saboda azaba da masifar iya ga ummi. Iya kuwa ta ji baƙin ciki da takaicin ɗauke ummi da yahaya yayi, dan yanzu ta san abu ne mawuyaci idan asirinsu da take ta ƙoƙarin  rufuwa bai tonu ba. Shi kansa Idris tun da aka tafi da ummi, bai dawo gidan ba, dan ya san zai sha faɗa a wurin Iya da iyayensa, shi kuma har ga Allah, ya tsani yarinyar nan hakan da yayi shine dai-dai. Horn yayi, wani matashin yaro, da zai ɗan girmi ummi ya zo ya buɗe gate ɗin, ummi ta san yaron amma da daɗewa dan wasu lokutan ya kan zo da shi gagarawa. Ya shiga da motar harabar gidan, ba laifi harabar mai ɗan girma ce, dan aƙalla za a yi parking ɗin motoci uku a ciki. Wasu ƴan mata ne ƙanana su biyu farare tas da su, an yi musu kitson ƙari, ɗaya tafi ɗaya girma, suka nufo motar suna faɗin oyoyo Abba. Ya buɗe motar ya fita ya rungumo su, sannan ya juya ya buɗe wa ummi motar ta fito. Duk da duhun magariba ya fara yi, hasken fitilar da take harabar gidan, ta basu damar tsayawa suna ƙarewa ummi kallo. Ya buɗe bayan motarsa ya cewa yaran su ɗaukko wa ummi kayanta. Ba laifi gidan mai kyau da shi, ummi sai kallon gidan take yi. A falo ya kalli yaran ya ce "Intee ina maama ne?". "Ta fita da muka dawo daga tahfee, bamu tarar da ita ba" Ya ce "Ok, ga sister ɗinku nan, sunan ta Salma, amma ummi ake ce mata, you can call her yaya ummi, ku nuna mata toilet ɗin ku ta yi alwala". Cikin ƙyama intee ta bi ummi da kallo, sannan ta yi gaba, ummi ta bita a baya. Ummi ta yi salla ta idar, tana ta kallon ɗakin, da gani na ƴan matan ne, kowacce da gadonta, ga ƙatuwar wardrobe, ga shoe rack ɗin su ɗauke da takalmansu na makaranta da na fita, duka-duka babbar da ake kira da intee ba ta fi shekara goma ba, ɗayar kuma bakwai. Ummi ta fito daga ɗakin, ta koma falo ta zauna a ƙasa. Ya shiga kitchen da kansa, ya haɗowa ummi tea mai kauri, ya saka intee ta dafawa ummi noodles ta ɗora mata ƙwai uku a kai. Duk da yanayi na rashin lafiya, ummi ta ɗan ci, dan bata taɓa cin indomie ba, duk da ta na burgeta. Yaran suka kunna tv suna kallo tare da mahaifinsu, ummi ma kallon take yi, suna ta yi wa babansu surutu, yana ta ƙoƙarin saka ummi a hirar, ta dai yi shiru ba ta cewa komai. Bayan magariba sosai sannan wata mata tayi sallama, ita da wata matashiyar budurwa. Ya amsa ya ɗaga kai yana kallonsu, yaran kuma duk suka tashi suka nufeta. Cikin iyayi ta ce "Abba ka dawo kenan?" Tayi maganar tana zama da tsohon cikinta. "Eh" ya amsa mata a taƙaice. Ummi ta kalleta ta ce "Ina wuni?" Ta bi ummi da kallo, ta ce "wannan fa?" Ya ce "Ki fara amsa mata gaisuwar mana" "Lafiya ƙalau" ta amsa a ɗan yatsune. Ya kalli su inteesar ya ce "Abdul, intee,  shalele ku bi anty rahama maza, ummi ki bisu ki samu ki huta, a haɗa mata ruwa tayi wanka" "Wai ban gane ba, ita wannan ɗin wacece?" Ya ce "Kya tsaya na yi miki bayani ai, yanzu dai daga ina ki ke?". "Gidan gana na je, wata ƴar aikin nake so ta samo mini, saboda su intee wahala tana yi mini yawa". "Amma ba kwanan nan ki ka rabu da wata ba, kina ta surutun tayi miki laifuka ba, shi ne zaki sake rakito wata?". "To Abba yaya zan yi? Ga tsohon ciki, da na haihu zan koma school, ga ayyukan gida ba zan iya ba wallahi. Ka yi haƙuri kawai ni dai". "Shikenan, amma kar ki kuskura ki zo kina ce mini an yi miki kaza an yi miki kaza" "Na ji wacece waccan yarinyar da ka haɗa mini da yara?" "Dama na san ba saninta zaki yi ba, tun da ba zuwa ki ke yi ba, Ƴar wurin marigayi ce bashir?" "To me zata yi a nan ɗin?" Ya gyara zamansa ya ce "Eh, na ɗaukko riƙonta ne na dawo da shi hannuna, a nan za ta zauna da mu" A fusace ta ce "Amma yaya zaka yi mini haka, ya zaka ɗaukko yarinya ban sani ba ba shawarata kawai ka ce in riƙe? Saboda me? Abba meye amfanin kawo bare ka haɗa a cikin iyalinka". "Ƴar ɗan uwan nawa ce bare kuma?" "Bare ce mana, ki ka haifeta? Naga ai ba cikinku ɗaya da ubanta ba, gaskiya ban yarda ba, ka mayar da ita in da ta fito wallahi ba zan iya ba, dama dinginku sun tsane ni, shi ne aka haɗoka da ita ta zo ta saka mini ido, wallahi ba zan riƙe ba". Ya dubeta ya ce"Well, ummi bare ce, amma ko ba komai ƴa ce a wurina, idan har ummi za ta bar gidan nan, ki tabattar rahama ma sai ta bar mini gida, dan bani da wata alaƙa da ita, dan ina aurenki ba dole ne na riƙe ki na riƙe ƙanwarki ba, tun da baki san mutunci ba, a gobe in Allah ya kaimu rahama ta bar mini gida na gaya miki". "Yahaya, ni ka ke gayawa ƙanwata ta bar gidan nan?" "Tun da ki ka iya kallona ki ka ce, ƴa ta ta bar gidan nan, to rahama ma sai ta bar gidan nan tun da ko ban riƙeta ba, bani da laifi a wurin Allah, ummi kuwa dole ne riƙonta a kaina" ya tashi fuuu ya nufi ɗakin su intisar. Ummi na zaune a ƙasa rungume da kayanta, tana kallonsu, suna zaune a kan gadonsu, sun sakata a gaba suna ta dariya, saboda yanayin ƙauyanci da yake tare da ita da kuma baƙar fatarta. Sallamar babansu ce ta sanya su tashi a razane, suka daina dariyar. "Ina ruwan wankan da na ce a bata?" Intee ta ce "Anty rahama ba ta haɗa ba" "Wannan ban isa da ita ba, ku na isa da ku, ki haɗa mata ruwa ki nuna mata yadda ake amfani da toilet ɗin" Ta jinjina kai, ya juya ya fita dan tafiya masallaci sallar isha'i. Cikin ƙyama take nunawa ummi banɗakin, ƴar ƙarama da ita, amma ta iya wulaƙanci. Ta cewa ummi kar ta kuskura ta taɓa musu sosunan wankansu, ta je ta ɗaukkowa ummi sabulun wanki, ta bata wai tayi wankan da shi, ta kuma nuna mata iya in da zata tsaya, tayi wakan. Ummi ta jinjina mata kai, sai dai ta tsaya tana kallon banɗakin yadda ya ƙawatu. "Rahama kina ina, wai ni yahaya ya ɗaukkowa ƴa a ƙauye na riƙe, wai idan ba zan riƙe ba kema ki bar masa gida" Rahama ta kalleta ta ce "In bar gidan nan wai? To me ki ka ce masa". "Wallahi ba zan riƙe ba, kuma ba in da zaki je, shi ya isa ma, wallahi yayi kaɗan, zai gane kuskurensa". Rahama ta ce "Anty ke da ki ke neman ƴar aiki? Gashi kin samu a ɓagas, ba dai gida ne ba, ta zauna mana iya ka idan bala'i ya isheta ta gaji ta bar gidan nan, ki rabu da shi, sai dai karki saurara mata wallahi, idan ma sa ido aka turo ta ki ci ubanta, ki rabu da shi kawai" Ta ce "Kuma fa haka ne rahama, haka za ayi, ɗakin mai aiki kawai zata koma, na samu baiwa zata ci ubanta kuwa, sai ta koma in da ta fito dan ba zan zauna da ita ba wallahi. Nifa gaba ɗaya ban yarda da yarinyar nan ba, lokacin da muka je gaisuwar babanta, ina jin kakarta na ta ce mata kamar mayya, ke kin ganta baƙa ƙirin ƙwayar idonta kamar mage". Raham ta ce "Idan ma mayyar ce ta ci kanta, dan wallahi mun fi ƙarfinta, to ma ina uwarta da za a kawo miki ita? Gaskiya baban Abdul yana da matsala wallahi". "Oho masa, sai ta bar mini gida dai wallahi, amma na san yadda zan yi da shi". Ayshercool 08081012143                          *CUTARWA!* *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* BRIGHT PENS (FREE BATCH) (Ku garzaya YouTube channel ɗina na COOL HAUSA NOVELS, KU YI SUBSCRIBING, AN FARA ƊORA LITTAFIN ƘANWAR MAZA NA SAURARO) P14 Har kawu yahaya ya dawo daga sallar isha'i, suna tattaunawa ita da rahama, suka gama ƙulle-ƙullensu, sannan farida ta baro ɗakin rahama. Yahaya ya tafi ɗakin yaransa, in da suke ta tsalle-tsalle a ɗakin, ummi kuma na ta gyangyaɗi a zaune a ƙasa. Suna ganinsa suka tsagaita da tsallen da suke yi, ya kalli babbar ya ce "Ke intee, ku yi squating da kausar a kan gadonki, yaya ummi ta kwana a kan ɗaya gadon. Turus suka yi suna bin mahaifinsu da kallo, cikin tsawa ya ce "Ba ku ji me na ce ba ne?". Intee ta ce "To" ya kalli ummi da ta buɗe ido ya ce "Ummana, ga gado nan tashi ki kwanta kin ji" Ummi ta ce "To na gode" Ta tashi ta hau gadon nan ta kwanta, wani irin laushi, ga ƙamshin room freshner mai daɗi kayan shimfiɗar suke yi, tun kan ya bar ɗakin bacci ya fara kwasarta. Inteesar ta kwashe wa da kausar da dariya ta ce "Shikenan bedsheet ɗin ki zai kwashi baƙi, kamar an ciro a buhun gawayi". Kwaɓe fuska kausar tayi za ta yi kuka, intee ta cigaba da dariya, ganin kausar ta fara kuka ya sanyata cewa "Bari idan abba ya daɗe da tafiya, sai mu tashe ta, ta saukko". Haka kuwa aka yi, intee har da leƙawa, ta tabattar da ya tafi, sannan ta dawo, ta hau dukan ummi a ƙafa. Ummi ta buɗe idonta tana kallonsu. "Saukko mana daga kan gado, kausar zata kwanta" Kasa magana tayi ta cigaba da bin su da kallo. "Ki saukko zata kwanta, dan ba zata kwana a gadona ta matseni ba" babu musu ummi ta saukko, ta koma ƙasa ta sake tada kai da kayanta. Kausar ta watso kayan kan gadon nata, har bedsheet ɗin da komai, wai saboda ummi ta kwanta a kai. Wajen ƙarfe ɗaya na dare, ummi ta ji ana haurinta da ƙafa, ta tashi firgigit, dan ji tayi kamar a gidan idris za ta buɗe ido ta ganta, dan shi yake yi mata irin wannan wulaƙancin, na haurinta da ƙafa. "Tashi malama, in nuna miki in da zaki din ga kwana, dan ba zaki kwanar mini a cikin yara ba, ban san irinki ba" Kai ka ce sokuwa, haka ta tashi, ta ɗaukko jakar kayanta, ta bi bayan farida. Ɗakin ƴar aiki da yake farkon falon, ta nuna mata ta ce ta shiga a nan zata kwana. Ba ta damu da a yaya ɗakin yake ba, ta je ta kwanta, saboda yanayin jikinta ga rashin lafiya ga gajiyar tafiya, dan haka duk a gajiye take. Washegari da safe, kowa ya fito falo, rahama ce ta haɗa breakfast, yaran duk sun shirya cikin uniform na makarantar boko. Abba ya fito ya kallesu ɗaya bayan ɗaya babu ummi, rahama ta gaishe shi ya amsa sama-sama. Ya kalli farida ya ce "Kawo mini abincina nan" Haushi ne ya kama ta, yana ganin yadda take fama da ciki, amma ya sakata aiki, bayan ta kai masa kayan abincin ɗaki. Bayan ta tafi ɗaukkowa, ya kalli intee ya ce "Kirawo mini ummana" intee tayi saroro tana kallon shi. Ya ce "Ummi nake nufi" Tunawa tayi da safen nan, ta ji maama da anty rahama suna zancen a ɗakin mai aiki ta kwana, har take gaya musu abun da suka yi mata jiya da daddare suka din ga dariya. A zaune ta tarar da ummi, ita ummi ɗakin ba ƙaramin kyau yayi mata ba. Duk da ba wani abu a ciki na burgewa, amma ɗakin ya yi mata kyau. "Ki zo in ji abba" yarinyar ta faɗa cikin fitsara. Ummi ta tashi ta bi bayan ta, sai dai farida na ganin ummi kamar taga kashi, ta haɗe rai. Daga in da suka fito falon, ya fuskanci a in da ummin ta kwana. Ummi ta durƙusa ƙasa ta ce "Abba ina kwana?" "Lafiya ƙalau ummana, ya jikin naki, ina fatan baki kwana da zazzaɓin ba?" Ta ce "Eh da sauƙi". Ya ce "Masha Allah, baki gaisa da maman naki ba, gata nan sunan ta farida, yara na kiranta maama, kema zaki iya kiranta da hakan, ga ƙanwarta nan anty rahama, ga Abdurrahman Abdul, ga inteesar, ga kausar, sai kuma muna jiran unborn baby da maama zata haifa mana. Abdul, intee, kausar kamar yadda na gaya muku jiya, yayarku ce, duk da kai Abdul ka girmeta, amma ku girmamata, ku zauna lafiya. Ummina duk abun da ki ke buƙata, ki sanar da ni, ko maama gidanku ne ki yi zamanki ki kwantar da hankalinki". Cikin ladabi ummi ta ce "To Abba" ta kalli farida ta ce "Ina kwana" banza tayi da ummi kamar ba ta ji abun da ta ce ba, ba ta damu ba ta kalli rahama ta ce "Anty ina kwana" Ba yabo ba fallasa rahama ta amsa mata, abun da farida tayi, ba ƙaramin ƙular da shi tayi ba, bai ce komai ba da kansa ya haɗa wa ummi abun breakfast a abincinsa, ya bata. Wanda hakan ba ƙaramin tunzura farida yayi ba, cikin ƙulewa take tuna masa yara zasu makara a makaranta, amma ya kada baki ya ce "Ƴaƴanki ne ai ki tarar musu abun hawa ya kai su, ƴa ta zan kai asibiti" Tsit suka yi suna kallonsa, aka rasa mai magana, ya jira ummi ta gama, ya sakata a gaba suka fice. Sai da ta kusa kuka, abun ka da mai ciki dama ga zuciya a kusa. "Rahama ki na kallo daga kawo yarinyar nan, ni zai yi wa wannan wulaƙancin, ya fifita bare a kan yaransa". "Kema anty farida you over react, a gabansa ta gaishe ki, ki ka shareta, ai kisan mummuƙe zaki yi mata". "Yanzu kwana ɗaya tal a gidan nan ta fara haɗa ni da shi? To wallahi da sake ba zai yiwu ba" Ran farida yayi matuƙar ɓaci, ta din ga cin alwashi kala-kala na mugunta a kan ummi. Ya tafi da ita wurin aikinsa, ya kulleta a office ɗin sa, ya je ya gabatar da lectures ɗin da zai yi, wajen ƙarfe sha biyu na rana, ya tafi da ummi kasuwa. Ya sai heater da nurse ɗin nan ta ce ya saya, ya sai mata phants dozen ɗaya, ya saya mata soso sabulu, brush, manyan jakar omo. Ya saya mata sababbin kaya wasu ready made wasu kuma sai an ɗinka, kasancewar yana da yara mata, kuma shi yake sayen komai na gidan sa, dan haka duk wani abu na ɗawainiyar yara mata ya sani, hatta ɗan kunne sai da ya saiwa ummi, under wear vest duk ya saya mata. Ya ce suje mota ta zauna ta huta, ya ƙarasa sayayyar, wani irin farinciki ummi take ji, saboda kayan nan da aka saya mata, gani take kamar a mafarki, wai duk wannan kayan nata ne, har da su ɗan kunne da ribbon, ga takalmi mai kyau, ta din ga kwarara masa addu'a a cikin zuciyarta. Wurin masu sayar da kayan ƙamshi yaje, domin haɗa magungunan da aka gaya masa a yi wa ummi. Sai dai wasu abubuwan duk ya manta yadda aka gaya masa, mai kayan ya tambaye shi, mai zai yi da su, yake gaya masa ai maganin sanyi za a haɗa. Kasancewar mutumin sana'arsa ce, sai ya haɗa masa komai da yadda ake amfani shi. (Previous page, na bayar da magungunan in breif, wasu sun biyo ni suna so, yanzu zan rubuta full yadda ake amfani da su) _Kanumfari _Tafarnuwa ƴar kaɗan ba mai yawa ba, saboda idan tafarnuwa ta huda jikin mace, tana sanya warin baki, na jiki har da na al'aura ma, sai dai maganin sanyi ce sosai. _Tumeric (yellown kur-kur) _Namijin goro _Citta mai yatsu _Lemon tsami Kowanne za a zuba shi in a moderate amount, lemon tsami babba guda ɗaya mai ruwa ya isa, namijin goron ma za a iya daddatsa shi, yana da ɗaci sosai, tafarnuwa one clove, sai citta mai yatsu madaidaiciya guda ɗaya, sai 1 table spoon of tumeric, sai a zuba ruwa kamar 2cups, a dafa su a din ga sha, za a iya zuba zuma, saboda yana da ɗaci, za kuma a iya haɗe su a mazubi guda, a jiƙa su, su jiƙu sosai a din ga tsiyaya ana sha. Idan wannan bai samu ba, ana iya jiƙa kanumfari, a din ga sha yana maganin sanyi sosai, amma sai an juri sha. Sai kuma ana samun saiwar zogale, a ɗaurayeta da ɗan gishiri, a tafasa ta da jar kanwa, a din ga sha, salam yake babu ɗaci, amma yana maganin sanyi sosai. Sai kuma kama ruwa da ruwan magarya da bagaruwa ba da yawa ba kaɗan a haɗa su a tafasa, ana kama ruwa da shi, ganyen magarya yana gyara jikin mace, mussaman bayan gama al'ada, ayi shaving a din ga kama ruwa da shi, kuma a din ga ɗiga farin miski a kan phant, ba a jiki ba, yana kawar da ƙarni ko wani wari mara daɗi, but mark you ba kowane wari ne yake fita a gaban mace na infection ba, akwai bacterias ɗin da suke wurin wanda ba masu cutarwa ba ne ba, suna haifar da wannan ƙarnin wasu lokutan. Galibi na infection ko na ƙazanta ya fita daban mussman idan ya haɗa da ƙaiƙayi ko ƙuraje shi ne na infection. Shi ma wannan warin, ana iya amfani da apple cider vinegar, ruwa kal da hausa, ana zuba tablespoon ɗin sa biyu, a ruwa cikin kofin shan shayi a din ga sha, yana magance warin gaba. Sai dai dole a kula da abincin da ake ci, domin cin abinci mai ƙarni, ko wari kamar kifi, albasa ko tafarnuwa suna da tasiri a gumin mu da sauran fluids da muke fitarwa a jikinmu. Kawu yahaya duk ya haɗowa ummi abubuwan da suka kamata, suna tafe yana sake yi mata bayanin yadda zata yi amfani da su. Sai azahar suka koma gida, sai dai matar gidan bata nan, da kansa ya bi ummi ɗakin masu aikin, ya dudduba abun da babu ya ce zai sayo mata. Tamkar yar da ya haifa a cikinsa haka yake jin ummi,kuma haka yake burin ta samu lafiya daga wannan ciwon, dan ya san illarsa da hatsarinsa, dan ya san halinsu maza bakomai suke iya jurewa su kawar wa da kai ba. Ya nuna mata yadda za ta din ga amfani da heater, da sabon flask ɗin ruwan zafi. Da kansa ya tafasa magungunan, ya zuba mata a jarka, na kama ruwan ya zuba mata a cikin flask ɗin shayi, ya ɗaukko tsintsiya ya taimaka mata wurin gyara ɗakin saboda an kwana biyu ba a gyara shi ba. Ya je ɗakinsa ya duba bedsheet ɗin da shi ya saya da kuɗinsa, har da bargo ya kawowa ummi. Ya bata babban gwangwanin turare a cikin nasa ya ce ta din ga fesawa. Kallonsa kawai ummi take yi, cikin jin daɗi da annashuwa, yadda ya zage yake ta ɗawainiya da ita, daga jiya zuwa yau, idan ta ce ya bari tayi da kanta, sai ya ce mata ai bata da lafiya, kuma cikin barkwanci ya ce mata albarkar ummansa yake nema. Haka nan ummi ta din ga murmushi tana yi masa godiya. Ya ce "Yauwwa ummina, Allah yayi miki albarka, saura makaranta ita ma in sha Allah sati mai kamawa, zaki koma makaranta ki manta da duk abu da ya faru, iyaka dai kar ki sake ki gaya wa wani kin taɓa aure kin ji ko?" Ta jinjina masa kai ya ce "Good, yi wanka ki yi salla, a cikin kayan nan akwai gurasa ki ci kiyi kwanciyarki ki huta" Murmushin kawai da ya gani a fuskar ummi, ya sanya shi cikin farinciki, kullum yaje ƙauye sai dai ya tarar da ita cikin kuka, sai kuma Murmushin yaƙe. Hatta yadda zata din ga amfani da banɗaki, sai da ya nuna mata komai. Fitowa yayi daga ɗakinta, a zuciyarsa yana tawasalli da farincikin da ya saka marainiya yana addu'a Allah ya biya masa buƙatunsa na alkhairi. Ba yau farida ta fara fita yawonta ba, tun yana faɗa har ya gaji ya daina yi. Ummi kuwa tun daga kama ruwan da tayi, ta ji daɗin jikinta, ta tsiyayi maganinta ta sha bayan ta ci gurasar nan, ta ɗauki sabon phanta ta canza. Wani irin daɗi take ji da nishaɗi, ta sake bubbuɗe kayan da ya saya mata tana jin daɗin hakan. Ko da wasa ba ta yi gangancin fitowa daga ɗakin nan ba, dan ta fuskanci ƴan gidan ba ƙaunar ganinta suke yi ba. Ana kiran sallar la'asar ta yi salla, ta cigaba da zamanta a ɗakin. Kamar an watso su, taga farida da rahama a ɗakin, hakan ya sanya ta tashi a razane. Farida ta ce "Tashi munafuka, ai ba zama ki ka zo yi ba" a zabure ummi ta tashi tana rarraba ido. "Ba dai kawo ki aka yi leƙen asiri da saka mini ido ba, zaki ci ubanki sai kin bar mini gida da ƙafarki" idonta ya sauka a kan ƙatuwar ghana must go sabuwa fil. Ta ce "Rahama janyo mini jakar nan ki zazzageta, wato zuwa yayi ya kashe mata kuɗi, wallahi ba zai yiwu ba ya daidaita da ƴaƴana, kar ta san kar ai". Rahama ta janyo jaka, suka zazzageta, farida har da ashar, farida ta saka farida ta tsitstsince mata kayan, phants ɗin ma duk ta kwashe ta bar mata uku, Allah ya taimaketa, tana da sauran wanda ta zo da su, da na'ima ta saya mata. Cikin ikon Allah, Allah ya taimaketa basu lura da ƙullin kayan maganin da ke bayan katifar ɗakin ba, heater da flask ɗin kuma suna cikin banɗaki. Hatta omo da sabulun da ya saya mata, sai da suka kwashe ta bar mata ɗai ɗai. Sannan ta sake dubanta a wulaƙance ta ce "Ki buɗe kunnenki da kyau ki saurareni, nan gidana ne, abun da na dama shi ake sha, shima kwana biyu na sarara masa ne, amma tun da haka ya zaɓa zan yi maganinku duka. Ki saka a ranki ke ƴar aiki ce kawai a gidan nan. Kullum da yamma idan yara suka taso daga makaranta, zaki wanke musu uniform ki goge musu shi tas, wanke-wanke da duk wani aiki a gidan nan ke zaki din ga yin sa, idan ki ga dama ki gaya masa babu abun da zai iya yi a kai, bari in gaya miki ƙiri-ƙiri idan ki ka sake kiransa da Abba sai kin bar gidan nan, dan bai haife ki ba. Kuma wanki ba na yara kawai ba, kaya ko na waye sai kin wanke a gidan nan, tashi mu je ma ki fara aikin ki daga yanzu. mummunar banza kawai". Rahama ta kwashe da dariya ta ce "Ni wallahi fuskarta ma dariya take bani, wannan baƙi kamar a dangwala". "Rabu da ita tashi ki wuce" ummi kaf maganganun su babu wanda ya ɓata wa ummi rai, dan ba yanzu aka fara yi mata ba, ƙwace mata kaya yafi komai ɓata rai. Sai dai wata zuciyar ta ce da kin san zaki samu ne?. Saboda tsabar mugunta akwai injin wanki a gidan, kuma akwai mai guga, amma farida ta tula wa ummi kayan makarantar su Abdul, na boko da islamiyyar su, kusan kowanne nasa set uku, daga na makarantar boko har na islamiyya. Ummi ko a jikinta, ta durƙusa ta fara wankin kayan nan. Tas ummi ta wanke su, kasancewar ta riga ta saba da wahala tun a gaban Iya. Bayan ta gama cike da mugunta, rahama ta ja ta kitchen, ta sakata sassauke kwanukan da sun fi wata shida ba a saukko su an yi amfani da su ba, ta ce ummi ta wanke. Babu ƙyuya ko ƙosawa ummi ta wanke su. Duk yadda suka wahalar da ummi a yammacin nan har zuwa bayan isha'i, ko da wasa bata nuna musu gazawarta ba. Kwanaki uku da zuwanta gidan, rashin mutunci da kyara, haka babar su Abdul suke yi mata, da yaranta da ƙanwarta, kuma wasu lokutan a hana ummin abincin. Sai dai lokaci ɗaya kawun nata ya rage bata wannan kulawar da yake bata da farko, hakan sam bai damu ummin ba, dan gani take duk wahalar da zata sha, ba zata kai ta gidan Iya da idris ba. Ranar lahadi suka koma ganin likita, sai dai ummi ta ji daɗin amfani da magungunan nan, dan kuwa sosai yayi mata sauƙi ba kamar da ba. Likita ya dubata, ya rubuta mata magunguna, Allah ya sa kawu yahaya bai yi ƙwauron baki ba, ya sanar masa magungunan da take sha, likitan ya ce ta ajiye su ta gama shan na asibiti, idan suka ƙare ta cigaba da waccan. Yayi masa godiya suka tafi gida, suna tafe yana rarrashin ummi, yana yi mata nasiha. Sai da ummi ta yi sati biyu cif a gidan, baban su Abdul ya cewa farida zai kai ummi makarantar su Abdul, amma ta ce ba ta yadda ba, sai dai ya nemi wata mai arha ya kai ummi, dan ba zai dai-daita ta da yaranta ba. Staff school ya saka ummi, ta nan makarantar da yake lecturing, makarantar islamiyya ma, wata daban ya saka ummi, sai dai makaranta ce mai kyau sosai ana karatu, dan akwai ƴaƴan manya a makarantar. Duk wanda ya shigo gidan nan ya ga ummi, sai farida ta ce musu ummi sabuwar ƴar aiki ta yi, su yi ta yaba ƙoƙarin ummi, yarinya ƙarama amma ba ta jin jikinta. Ko da ummi ta fara zuwa makaranta, a nan ɗin ma bata sauya zani ba, saboda ba ta tsira daga cin zarafi daga ɗalibai ba, saboda launin fatarta da ta idonta. Wahala ta ƙara ƙaruwar mata a ka, ga zuwa makaranta, ga kuma aikin gida tamkar jakarsu. Hatta rahama idan ta dawo daga makaranta, har wankin phant da brezia haka take watsowa ummi, ƙarewar wulaƙanci har da wando mai jini, sai ta cire ta bawa ummi ta wanke mata. Iya shege da rashin kunya kuwa a wurin su intee, ba a magana, sai ta gyara wuri su ɓata, idan suka ci abinci sai ta bi ta ɗauke musu kwanuka, sai dai kawu yahaya baya iya magana, yana ji yana gani farida da ƙanwarta suka mayar da ummi baiwa, ban da cin mutunci da wulaƙanci da muzanta halittarta. Dan har haramta mata zaman kan kujerar falo aka yi, wai kar ta shafa baƙi a jikin kujerar. Abdul ne ma ruwansa da ita, dama shi ba wani magana ya cika yi ba sosai. Yau ma farida ta tafi gida wai suna biki, ga tsohon ciki, amma kamar akuya saboda gantali, gashi tana cikin watanta na haihuwa. Daga ummi sai Abdul, sai kuma kawu yahaya da yake gida. Tana ta aikace-aikace, cikin tausayawa kawu yahaya ya ce "Sannu da aiki ummina, ki samu ki je ki kwanta ki huta". Tayi murmushi ta ce "Kawu na kusa gamawa ai" "Ummi kin daina kirana da Abba dai sai kawu ko?" Tayi shiru tana murmushin yaƙe. Bayan ta koma kitchen, ya numfasa ya ce "Yaya" Abdul ya ɗago ya ce "Na'am Abba". "Yanzu muna tare muna rayuwarmu, gwanin sha'awa kuna rayuwa tsakaninmu cikin jin daɗi, hakan yana yi muku daɗi ko?" Yayi murmushi ya ce "Sosai makuwa Abba". "Allah sarki, kamar haka idan Allah ya so, a kowane lokaci zai iya raba mu, muna raye ba tare da wani ya mutu ba, amma zai iya rabamu, kamar yadda ya ɗauke mahaifin ummi, ya rabata da mahaifiyarta, ya kawota zama a cikinmu. Ina kallon duk abun da mamanku take yi wa yarinyar nan, da ita da ƙannenka, ko ban ce komai ba, Allah yana kallon komai, dan Allah ko daga ɓangaren ka ne ta samu sassauci, ba dan Allah baya son ta ya ɗauki mahaifinta ba, ya kawota cikinmu ba, zaka so ayi treating ɗin ƙannenka kamar yadda ake treating ɗin ummi?". Jiki a sanyaye Abdul ya girgiza kai. "To dan Allah ka din ga nunawa ƴan uwanka, ummi mutum ce, kuma ƴa ce kamar ku, muzanta ta da bautar da ita, ba shi da wata fa'ida" ya din ga yi wa Abdul nasiha, sai duk jikinsa yayi sanyi. Sai dare sannan suka dawo, suna dawo gidan kamar sun dawo da dauɗa, suka cire kaya suka zubar, suka ci abinci suka baje kwanuka. Abdul ya tarar da ita a kitchen, tana ta wanke kwanukan da suka ci abinci, ya kalli ummi ya ce "Ki je ki kwanta, yakamata ki huta". Ummi ta ce "Kwanukan nan zan ƙarasa wankewa" Ya ce "Bari na tayaki" "Maza basa wanke-wanke" Tun da ta zo gidan nan, maganar kirki bata taɓa haɗa su ba, ba ruwansa da ita, dan haka yau tayi mamakin cewa da yayi zai taya ta aiki. Shi dai tun da Abba yayi masa wannan nasihar ɗazu, gaba ɗaya sai tausayin ummi ya kama shi. Kallonsa take yi tana mamaki, yadda yake kikkife mata kwanukan, ummi sai cewa take yi ka bar shi fa yaya Abdul. "Uban me ka ke yi a kitchen ɗin nan?" Rahama tayi maganar tana shigowa hannunta riƙe da indomie. "Aiki nake taya ta". Ta watsawa ummi indomie, ta ce idan ta gama, ta dafa mata guda biyu. Ko da wasa ummi babu alamar gazawa a fuskarta, ta dafa mata indomie, Abdul yana biye da ita, ta gama yayi zaton kwanciya ummi za ta yi, amma ta kwaso uwar guga ta hau yi, kayan su na babarsu da na rahama. Abdul ya zuba mata ido, tana ta sauri ta kammala gugar, dan tana da assignment, tana yi yana ƙoƙarin yi mata hira, amma kasancewar ba sabawa suka yi ba, ya kasa ya saukko ya ce bari ya taya ta. Ba iya gugar yayi ba, ummi tana nuna masa yadda zai yi, sai dai bisa tsautsayi Abdul ya ƙona rigar babarsa, ta lace babban lace ba ƙarami ba. Hakan yayi dai-dai da fitowar rahama, ta gansu a tare Abdul da dutsen guga. Ta buɗe murya ta ce "Anty farida, zo ki ga bariki, aikin da ake sakata take rabawa da ƴaƴan gida". Abdul ya ce "Ni ne na ce zan tayata fa" Farida da ƙyar ta ƙaraso falon, saboda ciwon baya da mara da take yi. "Uban me ka ke yi a nan a wannan daren?". Ya ce "Bakomai". "Tashi ka wuce ka je ka kwanta" ya tashi ya nufi hanyar ɗakinsa. Idonta ya sauka a kan rigar leshinta, da sawarta uku an ƙona rigar. Ashar ta lailayo, ta ɗago rigar ta ce "Rigar ta wa ki ka ƙona mini? Dan ubanki dan baki da mutunci ba ki da hankali?" "Anty dan Allah ki yi haƙuri, tsautsayi ne, ban san zata ƙone ba" "Wallahi sai na ƙona ki da iron ɗin nan, ke wallahi sai na fanshe rigata, kut lallai baki da hankali" Miƙews ummi tayi, ta fara kuka tana bata haƙuri, amma rahama ta danƙota, ta danne ta farida ta sake jona iron ɗin ya ɗau zafi, ta nufo ummi. (*Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ina amfani da wannan dama wurin miƙa saƙon ta'aziyyata, ga ɗaukacin marubuta, na rashin ƴar uwa marubuciya, maryam nasir marsad, dan girman Allah duk wanda ya karanta page ɗin nan, muna barar ƙulhiwallahu ƙafa uku, Ubangiji Allah ya yi mata rahama, ya kai haske kabarinta ya sanya bakin wahalarta kenan, idan ta mu ta zo ya sanya mu cika da kyau da imani Amin*) (MASU NEMA DAGA FARKO, KU DUBA A WATPAD PLEASE 🙏) Ayshercool What's app only please 🙏 08081012143.                             *CUTARWA!*     *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* BRIGHT PENS FREE BATCH P15 Ihu ummi take yi, tana yi musu magiya su yi haƙuri, amma cike da mugunta da zalunci, rahama ta danne ummi a ƙasa, ta cusa mata ɗan kwali a baki, ta yadda sautin ihunta ba zai fita sosai ba, ta ɗage wa ummi riga, farida ta din ga nana mata iron ɗin  nan a cikinta da zafinsa da komai. Wata irin miƙa ummi take, saboda azabar da ta ratsata, take ta saki fitsari, saboda azabar zafi da ya ratsa ta. Abdul har ya je ɗakinsa ya tuna ya ƙona rigar maama, kuma ƙila ummi zata hukunta, dan haka ya juyo da sauri, ya dawo falon. A gigice ya ƙarasa wurin, ganin bala'i da izayar da ake yi wa ummi. "Maama dan Allah ku bari, ba a yi wa mutum azaba da wuta". Fitsarin da ummi ta saki, ya sanya rahama cikata, ta rufeta da duka, saboda ta ɓata mata jiki da fitsari, ta fizge hijjabi da hular kan ummi, a take dogon gashin ta mai matuƙar santsi ya zubo har fuskarta. Rahama ta ce "Kut, wannan gashi ko attach" tayi maganar tana jan gashin ummi da ƙarfin gaske, ummi jikinta ya din ga rawa, ta kasa ihun saboda azaba, ta riƙe gashinta da rahama ta cika hannu da shi. Abdul ya fara ƙoƙarin ture rahama daga kan ummi, farida ta kai ƙafa zata daki ummi, ta zame da ruwan fitsarin da ummi tayi, ta faɗi. Wani irin ihu ta kurma, rahama ta ɗaga ummi, ta nufeta a gigice, ummi ta samu ta lallaɓa ta tashi da gudu, ta tafi ɗakinta. Banɗaki ta shiga, ta cire rigarta ta din ga zuba ruwan famfo a cikinta, tana jin tamakar wurin ci yake yi da wuta, ga wani irin azaba da kanta yake yi, har wani jiri take ji. Kan ka ce kwabo jini ya fara zuba daga jikin faruda, jikinta ya fara kakkafewa, rahama ta ce "Abdul yi sauri ka je ka taso abbanku" Abdul ya tafi da gudu ɗakin da mahaifinsa yake ta bacci, saboda a gajiye yake sosai, duk wainar da ake toyawa bai sani ba. "Abba, Abba ka tashi maama ta faɗi ƙasa" Da ƙyar ya buɗe ido, ya kalli Abdul ya ce "Meyafaru?" "Maama ce ta faɗi a falo" agogo ya kalla, ɗaya saura na dare, me ta je yi falo a yanzu?". Ya saukko daga kan gadon, suka fito falon tare, falon sai ƙauri yake yi saboda iron da aka bari a jone. Jini take zubarwa sosai cikin gushewar hankali, da sauri kawu yahaya ya ɗaukko mukullin motarsa, da ƙyar suka ɗaga farida, saboda nauyin cikin ta suka bar Abdul a gida suka tafi asibiti. Ummi ba ta san abun da ake ciki ba, tana can tana jinyar cikinta da suka ƙona da dutsen guga. Ta zauna ta yi shiru tana ta tunanin, me ta aikata da ya sanya kowa ba ya son ta ji daɗi, kowa babban burinsa shi ne ya ga ya cutar da ita ta yi kuka? Ta ɗauki vasaline ta shafawa wurin, duk da haka sai da ya fara ɗurar ruwa, duk fatar cikin ta tashi. *** Idiris a tunaninsa tafiyar ummi, shi ne samun sassauci a gare shi, ya yar da ƙwallon mangwaro ya huta da ƙuda. Hashim kuma Iya ta sako shi gaba da cin mutunci, ko gaisuwarsa ta daina amsawa, saboda haushin gayawa kawu yahaya abun da ake ciki da yayi, ya sanya yahayan yana yi musu kallon azzalumai. Idiris ya lallaɓa ya cigaba da zuwa wurin hindu, yana son ya hilace ta su aikata alfasha, tun da iyayenta sun ƙi ya aureta. Gulmace-gulmace suka din ga yawo, a kan azabtarwar da Iya ta yi wa ummi, da wanda idris ya yi wa ummin, tare da ƙoƙarin bankaɗa asirin dalilin da ya sanya aka fasa auren idiris da hindu, ana ta zaginsu a unguwa, aure wata ɗaya ya mutu. Haka nan sai ummi ta din ga yi wa Idris gizo, idan ya je gidan da suka zauna. Ko kuma yayi ta mafarkinta tana yi masa mugun kallo tana kuka. Gashi duk wannan abun da ya faru, ya kasa daina jin sha'awar ummi, ya kuma kasa manta yadda jikinta ke da matuƙar taushi kamar auduga. Tun da yake leƙe-leƙnsa, bai taɓa taɓa mace mai laushin fatar ummi ba, gashi dai ko man shafawar kirki ba ta da shi, amma fatarta har wani irin santsi take yi. Ya din ga tuhumar kansa, da ganin wautar sa na kasa daurewa ya sauke abun da yake damunsa game da ummin kan su rabu, amma da ya tuna annakiyar dauɗar da ke jikinta, da kuma warin da take yi sai yayi tsaki. A rashin ummi ya cigaba da ƙoƙarin hilatar hindu, yayi lalata da ita, hindu yarinya ce ƴar shekara goma sha shida, gidan su suna da tarbiyya sosai, dan haka sai wahalar da Idiris take, taƙi bashi haɗin kai, sai dai tana matuƙar ƙaunar idiris. *** Likitoci suka rufu a kan farida, ana ta ƙoƙarin ceto ranta, sai dai jini yaƙi tsayawa, ƙarshe aka ce tiyata za a shiga da ita da gaggawa a cire mata cikin, dan ta fara jijjiga ga jini ya ɓalle. A daren aka shiga da ita tiyata, aka ciro ƴa mace, sai dai ba ta san in da kanta yake ba, har aka fito da ita. Ita kanta yarinyar taƙi yin kuka, aka yi ta fama, sai dai tayi kaɗan tayi shiru, ga rashin isashiyar oxygen a jikinta sai da aka saka mata oxygen. Rahama ta din ga kuka, tare da ɗora zargin hakan a kan ummi, sai dai ta yi shiru ba ta gaya wa baban su Abdul abun da ya faru ba. Abdul kuwa a gida aka bar shi, ya kasa zaune ya kasa tsaye, mussaman yadda ya kasa manta ganin jini na zuba a jikin. Ummi bacci sai ɓarawo ya kwasheta, shi ma a rigingine ta kwana. Da asuba ta tashi tayi salla, fatar cikinta duk ta ɗaga tayi wani iri, saboda ƙuna. Bayan ta idar da sallar, ta lallaɓa ta fito falon, ta tarar da wurin duk jini, ga kayan gugar duk a watse a wurin, tsaf ta gyara wurin ta kwashe kayan gugar, ta shiga kitchen, ta ɗora ruwan shayi, sai lallaɓa jikinta take yi, saboda raɗaɗin da take ji a cikinta. Ta sake fitowa falo, ta tarar da Abdul a tsaye yana kallonta. Ta kalleshi ta ce "Yaya Abdul". "Na'am, ya jikin wurin ya ƙone?" Ta ce "Eh, amma ba sosai ba". Ya ce "Maama fa a asibiti ta kwana" Zaro ido ummi tayi ta ce "Meya sameta?". "Faɗuwa tayi" yayi maganar cikin damuwa. Sai a lokacin ummi ta tuna taga farida ta zame ta faɗi, ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, to yanzu ya jikinta?". "Nima ban sani ba, tun da suka tafi basu dawo ba". Ummi ta ce "Allah ya sa tana lafiya". Ya amsa da amin. Suna tsaye suna jajantawa, sai ga Abba yayi sallama, duk suka zura masa ido suna yi masa sannu da zuwa. "An yi wa mamanku aiki, an ciro baby girl, sai dai dukkannin su, they are under special care, duk basu da lafiya" Ummi ta ce "Subhanallah, Allah ya basu lafiya". Ya amsa da "Amin, ummina na san kin yi breakfast, ki zuba wani a flask a kai musu asibiti, ku shirya na ajiye ku a makaranta, ina su kausar?" "Ba su tashi ba" "Kamar yaya, ƙarfe bakwai saura, ba zasu makaranta bane?" A fusace ya nufi ɗakinsu, ya taso su da bulala. Ƙarshe dai sai da suka makara, jin mamansu na asibiti, ya sanya suka din ga kuka, haka ya kai su makaranta ya wuce asibiti. Gumin da ummi take ta yi, ya din ga taɓa wurin ƙunar nan, ga kuma rigar makaranta, hakan ba ƙaramin takurata yayi ba. Sai dai duk da abun da farida da ƙamwarta suka yi mata, tunaninta yana kan yaya jin faridan yake. Kasancewar rahama ce a can asibiti tare da farida, sai ya zamana kusan kula da ragamar gidan yana hannun ummi, kai ba ka ce babu mace a gidan ba, duk aikin gida ita take yi, har kawunta sai da ya yabawa ƙoƙarin ta tare da jinjina mata, dan hatta abincin da za a kai asibiti ita take dafawa. Gefe guda Abdul ne yake takawa su intee burki, dan tana yi musu wahala amma ba sa gani, dan sai suka tsiri cewa ai anty rahama ta ce musu, ummi ce ta saka mamansu ta faɗi, su yi ta yi mata rashin mutunci da wulaƙanci. Kwanan farida biyu a asibiti, aka samo kanta da ƙyar, kawu yahaya ya ɗauki su ummi ya tafi da su asibitin dubata. Sai dai yanayin kallon da ƴan uwan farida ke yi mata, ya sanya ta sha jinin jikinta, dan ko sannun da tayi wa faridan ba ta amsa ba. Tana kwance jaririyar a kusa da ita, ana ƙara mata jini. Sai dai kasancewar babansu Abdul yana wurin, ba su iya ce wa ummi komai ba. Ummi fa ƙuna ta din ga jagwalewa, ga ƙaiƙayi tana yi mata, ta tuna ta taɓa ƙonewa a ƙafarta lokacin tana ƙauye, na'ima ta din ga shafa mata zuma, dan haka ta cewa baban su Abdul, ya sammata zumar da yake shan shayi. Yayi murmushi ya ce "Zumar da gata nan kaya guda, ai ba sai kin tambayeni ba ummana" ta samu abu ta tsiyaya take amfani da ita a ƙunar, dan har wurin cibiyarta ta ƙone. Kwanan farida biyar a asibiti aka sallamo su, babu tsammani ummi ta dawo daga makarantar boko ta dawo ta tarar an cika gidan. Ta ƙarasa falon ta durƙusa tana gaishe su, sai dai basu amsa ba, rahama ta janyo hijjabinta har tsakiyar falon ta ce "Kun ganta nan azzaluma, ita ta kusa kashe anty farida, ita ta kayar da ita" "To ai da farida cewa tayi mai aikinta ce". "Ba ƴar aiki ba ce ba, ƴar wan maigidan nan ce". Ƙanwar babansu farida ta ce "Kuma shi babu matakin da ya ɗauka?" Farida na daga kwance ta ce "Wane matakin zai ɗauka, kin ga faman da nayi a kan ba zan zauna da ita ba ya dage, ni kuwa na samu ƴar aiki" "Aikuwa idan baki yi hankali ba ta kashe ki wataran". Ummi tayi shiru ta sunkuyar da kai, wata yayar su ta dunƙule hannu, ta ɗirka mata duka a tsakiyar ka ta ce "Wallahi da kin kasheta, sai kin yi prison daga ke har ubanki". Rahama ta ce "An ce ubanta ya mutu ai". "Matsiyaciyar yarinya da ya bar wata tsiyar, da ba a ganki a nan ba, har ki ke ƙoƙarin kashe mana ƴa, ni wannan anya ma ba mayya bace ba, kalli ƙwayar idonta fa". Wata a gefe tayi caraf ta ce "Wace iri ce? Turo mini ita nan, ai ni ina gane maye" Matar ta ja ummi kamar tana jan shara, ta dungurarwa da ɗaya matar ita, tuni ummi ta fara kuka, ga zafin duka ga na cin mutunci. "Ke ɗago idonki na gani" Ummi ta sunkuyar da kai ta kasa ɗagowa. "Ba zaki ɗago ba sai na mareki" ummi ta kasa ta sake fashewa da kuka. Aikuwa matar nan babu tsoron Allah, ta sauke wa ummi yatsunta a fuska iya ƙarfinta, sai da ta hantsula gefe. "Wallahi zata iya yiwuwa mayya ce, tun da ta kasa haɗa ido da ni, shegiya ga baƙi kamar ƴar maƙera". Suka ciwa ummi mutunci son ransu saboda abun kunya, da yawansu zasu haifi ummi, amma kasancewar ba ƴar su ba ce ba, suka din ga muzanta ta suna aibata ta. Tayi kukan da tun da aka kawota gidan ba ta yi irin sa ba, har ta fara tunanin ko roƙon kawu yahaya za ta yi, ya mayar da ita ƙauye. Sai dai gabanta ya faɗi, da tuna irin azabar da ta sha a ƙauye, da sauri ta girgiza kanta, har da istigfari, ta fara ƙoƙarin auna zaman nan da na can wanne yafi sauƙi. Duk zaluncin iya, ba ta taɓa ƙonata da wuta ba, illa iyaka duk laifin da tayi jikinta zai gaya mata. Nan kuma duk rintsi, ko ba a bata abinci sau uku ba, ba zata kwana da yunwa ba, kuma tana da kayan makaranta da na sawa duk da babu yawa, kuma tana da takalmi da sauran abun da ba a rasa ba. "Mama meyasa ba so na ne? Laifin me nayi, meyasa idona yake ba kalar na mutane ba? Duk abun da nayi mutane sai sun tsaneni, ko a gida ko a makaranta?" Tayi maganar tana ganin fuskar mariya a idonta, tana jin tamkar ta ga mamanta ta bayyana. Tayi kuka ta gaji, ta duba sabulun wankanta ya ƙare, tayi wankan a haka, ta shirya islamiyya, ta fice ba tare da kowa ya sani ba. Dama kuɗin motar zuwa islamiyyar ma, idan kawu yahaya yana nan, yana bata ko ya bawa farida ta bata, idan ta ga dama ta bata, ko taƙi bata wanda zai ishe ta shima saboda ta na biyawa ɗaukko su intee daga ta su makarantar islamiyyar, dan Abdul ba lokaci ɗaya suke tashi ba, sai ƙarfe shida, su kuma tun huɗu da rabi ake tashin su. Dan haka ummi tafiyar ƙafa ta sha, kan ta je makarantar, nan ma da ta je sai da aka daketa dan ta makara. Zama tayi, tayi shiru a ajin, dan kamar yadda ta saba, bata da ƙawaye, dan ba ta son shiga cikin su su tsokane ta. Haka kurum ta ɗan shagala da kallon yarinyar da take jin tsoro a ajin, mai suna maryam saboda hantararta da take yi tana kyararta, da nuna mata tsana ƙarara a fili. Tubarkallah maryam fara ce sol, irin fulnin nan masu dogon hanci, sai azabar iyayi da iya gayu, da yawa ƴan ajin na tsoronta, saboda azabar masifarta da rashin son rai ni. Ba tsammani ummi ta ji ta ce "Ke lafiya ki ke kallona kamar zaki cinye ni?" Da sauri ummi ta ɗauke kanta tare da cewa "Yi haƙuri" "Da haƙurin ta mutu sadakar nawa ki ka bayar? Bana son kallo" "Ai na ce kiyi haƙuri" ta faɗa a sanyaye. A ranta ta ce 'Dama nima fara ce, wataƙila da ba za a tsane ni ba. Amma ai akwai baƙaƙe da yawa da ake son su, ni meyasa ba a sona?' ta tambayi kanta, wasu hawayen na rige-rigen zubowa. Maryam ta zauna a kusa da ummi, ko a jikinta ganin ummi ta kifa kanta. Sai da malami ya shigo ajinsu sannan ta ɗago kanta, ya yi musu karatun da zai yi musu, sannan ya basu class work. Sai dai fa maryam ba ta iya komai ba, ta din ga rarraba ido, ga malamin ya jaddada cewar duk wanda ya faɗi sai ya zane shi. Ganin lokaci ya kusa cika, ya sanya ummi buɗe mata takardarta ta ce "ki kwafa ya kusa karɓa" babu kunya maryam ta kwafe duk abun da ummi ta rubuta. Lokacin sallar la'asar yayi, ɗalibai na ta ƙoƙarin fita daga ajin, ba tare da tuna alkhairin ummi ba, maryam ta hankaɗeta zata fita, bisa tsautsayi ummi ta faɗi ta fama ƙonuwar da take cikinta. Ƙara ta saki, tana girgiza kanta, duk ɗaliban suka tsaya suna kallon ummi, ganin jini yana tsatstsafowa a rigar uniform ɗin ta. Maryam a tsorace ta ce "Na shiga uku" ta durƙusa ta ɗago ummi, a zaton ta ko cikin ummi ne ya ɓule. Ummi sai yarfe hannu take yi tana kuka, ɗalibai suka taru a wurin, malamin da ya fita daga ajin ya dawo ganin ɗalibai a wurin yana tambayar meyafaru, aka gaya masa maryam ce ta hankaɗeta ta faɗi. Cikin tashin hankali ya ce a kai ummi ofishin malamai, ita ma maryam ta bisu sai an hukunta ta. Cikin tashin hankali malamai mata suka ɗaga rigar ummi, ana ƙoƙarin gano menene yake jini a cikinta, sai dai ba kyan gani, suka tarar da ƙonuwar ta jagwale, ga ruwa ga jini ya dame da zumar da take sakawa. Maryam na ganin haka ta fashe da kuka, ta zata duk faɗuwar ce ta janyo haka. Shugaban makarantar ya dubi Maryam ya ce "Wato maryam ba kya ji ko? Zaki gane kuskurenki, sai kin daku yau ɗin nan, makauniya ce ke da zaki tureta ta faɗi". Malamin ya dubi ummi ya ce "Ke ya aka yi ki ka zo da wannan ciwon makaranta, meya sameki haka?" "Ba maryam ce ta ji mini ciwon ba, dama na ƙone a gida" "Da me ki ka ƙone, kuma an kai ki asibiti?" Ta ce "Eh an kaini" "A'a wannan da an kai ki asibiti, da ba ta jagwale haka ba, kuma da ba a bari kin saka kaya ba, ki gaya mini gaskiya da me ki ka ƙone?" Malamin yayi maganar cikin zare ido. "Da ruwan zafi" "Mamanki ta san kin ƙone?" Ta girgiza kai alamar a'a. "Meyasa baki gaya mata ba?" Cikin kuka ta ce "Ai ban san in da take ba" "A'a to ina mutanen gidan da ki ka ƙone ɗin, ba ƴar gidan dr. Yahaya bace ne?" Ta ɗaga kai alamar eh. "Malama zuhra, a nemo abun hawa a kai yarinyar nan asibiti a dubata, ke kuma maryam mu je office ɗina sai na hora ki" Maryam ta fashe da kuka tana magiya, cikin ƙarfin hali ummi ta ce "Malam dan Allah kayi haƙuri, ba ta san ina da ciwo ba, na yafe mata ai" Ya ce "To zan duba, tashi a kai ki asibiti, daga nan a mayar da ke gida". A asibitin ma, ma'aikaitan sun yi faɗa sosai a kan sakaci da lafiyar ummi, dan da ƙunar zata iya zama infected ta taɓa sauran sashin jikinta, bayan ta zama gyambo. Suka ce lallai a kula da ummi, a samu ƙunar ta warke, kuma a zurfafa bincike dan wannan ƙunar ba tayi kama da ta ruwan zafi ba. Ummi ta sha kuka, saboda yadda aka dirje ƙunar nan tas, aka saka magani, aka bata magungunan sha. Sai dai da malama zuhra ta ce ta kwatanta musu gidansu a mayar da ita ta ce "A'a a mayar da ni makaranta, idan aka tashi zan ɗaukko ƙannena daga islamiyya" "A haka da wannan ciwon" malamar tayi maganar tana kallon ummi. Ummi ta jinjina mata kai. "A'a ba zai yiwu ba, mu je gidan naku, a saka wani ya ɗaukko su". Kuka ummi ta fara tana yi wa malamar magiya, a kan ta ƙyaleta a tashi ta ɗaukko su daga makaranta. Ba ta da zaɓi, suka koma islamiyyar ta gaya wa shugaban makarantar duk abun da ya faru. Suka yi waya da kawu yahaya, suka tattauna, ya ce a mayar da ummi gida, zai yi waya makarantar yaran, su jira yayansu sai su taho tare. Da ƙyar ta yadda da hakan, saboda tana tsoron abun da ka iya biyo bayan rashin ɗaukko su daga makarantar. Cikin sa'a malamar ta fuskanci yanayin da ummi take ciki na tsoro, dan haka a ƙofar gida suka yi sallama ummi ta shiga. Har ta tafi ɗakinta ba wanda ya san ta dawo, saboda ana ta hada-hada a gidan, ƴan barka na shige da fice. Ta kasa fitowa daga ɗakin, saboda tsoron kar su kuma dukanta. Sallamar kawu yahaya ta ji a ɗakin, ta tashi da sauri, tana gaishe shi. "Ya jikin naki?" "Da sauƙi" "Mu ga ciwon" a hankali ta ɗaga masa cikinta ta ƙonu sosai da sosai, ya zubawa ƙunar ido sannan ya kalleta ya ce "ya aka yi ki ka ƙone?" "Da ruwan zafi" ta faɗa tana ƙiƙƙifta ido, saboda ta san ƙarya tayi. "Meyasa baki gaya mini ba?" Tayi shiru ba ta ce komai ba. Wannan ƙunar ba ta yi kama da ta ruwan zafi ba, ki gaya mini gaskiya. "Da gaske nake..." Ba ta ƙarasa ba ya ce "Shaidar iron tayi, kalli yadda shape ɗin ƙonuwar ya tafi, ki gaya mini gaskiya". Ta ɗan yi jimm sannan ta ce "Idan na gaya maka ba zaka gaya wa maman su Abdul ba?" "Ba zan gaya mata ba" "Ina guge Abdul ya ce zai tayani, ya ƙonawa mamansu riga, ta zata nice shi ne anty rahama ta danneni, suka ɗora mini iron. Dan Allah Abba ka gaya musu bani na saka anty farida ta faɗi ba, sun ce ni na kusa kasheta wallahi ba ni ba ce, fitsari na yi da na ji zafi, shi ne ta zame ta faɗi" tayi maganar tana sheshsheƙar kuka. Ayshercool 08081012143 What's app only please 🙏                          *CUTARWA* *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* BRIGHT PENS (FREE BATCH) P16 PAID ADVERT!. Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi. Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku Oll types of Turaran wuta Sandal Halut Irik Difur Gab Gab Kajiji Habil Nabak Humra Kulakcha Dilke da kalta Kayan Garan jiki Muna turara Kaya Kujerar garan jiki Kannada Madarorin turare masu kamshi  Man garan gashi  Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702   08025453921 *TALLA!TALLA!TALLA!* *INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*. *BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU* *MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA* BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI P16 Ƙurriii kawu yahaya ya yi wa ummi da ido, abun ya girmame shi, bai taɓa zaton mugunta da zaluncim da farida za ta yi wa ummi zai kai haka ba. Ya sauke numfashi da ƙyar ya ce "Ya isa haka ki share hawayenki, ki daina kukan ya isa ba zan gaya mata ba, kuma na san ba zaki taɓa iya cutar da kowa ba, duk wanda ya cutar da ke, shi ma Allah ba zai bar shi ba, ki yi haƙuri ummi, in sha Allah gobe in Allah ya kaimu zamu koma asibiti, tun da yau an yi dressing ɗin. Mun yi magana da malaman islamiyyar ku, na biya kuɗin maganinki, sannan sun ce ki zauna a gida sai kin warke". Ummi kamar ta ce masa gara ta cigaba da zuwa a haka, dan ta san zamanta a gidan nan ba hutawa za ta yi ba, amma ta dake ta ce "To kawu na gode sosai" "Kar ki damu, Allah ya ƙara miki lafiya da nisan kwana ummana" Murmushi ummi tayi, tana so ta ji ya kirata da ummana ko ummina, hakan yana yi mata daɗi, kuma yana tuna mata da maman da babanta. Ya ce "Au, na manta ban gaya miki ba, mun kusa komawa sabon gida fa, bamu taɓa zuwa kin gani ba ko" Ta faɗaɗa murmushin ta ta ce "Allah ya nuna mana, wannan wa za a barwa, na ga shima mai kyau ne" "To ko in bar miki, tun da kin fi son nan?" Murmushi ta yi ta ce "Ai ni macece ba zan iya zama a gida nikaɗai ba, amma ina son gidan nan" "Can yafi kyau ai, idan muka koma zaki gani" "To Allah ya sanya albarka, to nan su iya ne za su dawo su zauna?" Sai da ya ƙara kallonta da sauri, ya ce "Su iya kuma?" Ta ce "Eh, su baro ƙauye su shiga makarantar islamiyya, makarantar mu har da matan aure da tsofaffi suna zuwa asabar da lahadi" Bakomai a ranta ta faɗi hakan, kawu yahaya yayi murmushi saboda magana tayi cikin magana mai ma'ana, ba zaka san ummi na magana ba, sai ka zauna da ita, a haka kamar ba ta magana. Sai kuma ta sake cewa "Kawu, kaga da ka san in da mama take ita ma zaka ɗaukkota ka dawo da ita nan? Sai mu zauna ni da ita a gidan nan sai ku koma sabon gida" Tausayin ummi ya kama shi, ya ce "Ki na kewarta ko?" Ta jinjina masa kai alamar eh. "In sha Allah zan nemo in da take, zan haɗa ki da ita, sai dai ba zan so na kawo ta nan ita ma ta din ga shan wahala kamar yadda ki ke sha ba" "To ai ba zan bari ta sha wahala ba, ni zan din ga yin duk wani aiki, idan na iya sana'a na din ga saya mata abubuwa, idan ka gano ta dan Allah kar ka kai ta wurin Iya, Iya ta ce ba ta son ta, wai mama mayya ce..." "Ummi ya isa haka, ki daina tuna abubuwan da suka shuɗe wanda za su dinga ɓata miki rai, ki yi karatu sosai yadda maman idan ta gan ki za ta yi alfahari da ke" Ta gyaɗa masa kai ta ce "In sha Allah" kai da ganin yadda ta ɗan kwaɓe fuska, ka san akwai tarin abubuwa cunkushe a zuciyarta da take burin amayar da su, sai dai babu wanda zai tsaya ya saurareta, to wa ma ya damu da ya zauna da ita balle aji matsalarta. Cikin son kawar mata da wancan tunanin, ya yi murmushi ya ce "Ki na buƙatar wani abu ne ummana?" "A'a bana son komai" Ya ajiye mata ɗari bibbiyu guda biyar, ya ce "Gashi idan kina buƙatar wani abun ki yi amfani da shi". Kallon kuɗin ummi take yi dan da yawa a wurinta, kan tayi magana ya tashi ya fita, zuciyarsa na yi masa zafi. Ɗakin farida ya wuce kai tsaye, ya tarar da ita tana saka kaya a gaban mudubi, ta ɗago ta kalleshi ta ce "Ya dai?" A take ya nemi karsashinsa da zafin zuciyar da ya zo da ita ya rasa, duk yadda ya so yi mata magana a kan ummi, sai ya kasa kawai ya tsaya yana kallonta. "Kana buƙatar wani abu ne?" Kawai ya girgiza mata kai ya juya ya fice, yana jin baƙin cikin kasa yi mata magana a kan cin zarafin da ta yi wa ummi. Duk da ƙonuwar cikin ummi, haka ta cigaba da yin aikace-aikacen gidan, kuma muddin ta fito ƴan uwan farida suka ganta, sai sun ci zalinta, ko sun aibata ta. Hatta makarantar boko, kawu ya hanata zuwa, ya ce sai ta samu sauƙi tukuna. Dan haka, a hakan take naɗe rigar ta, ta bar wurin ƙunar a waje tana shan iska, tana aikinta. Abdul ne kawai yake tausaya mata yake yi mata sannu, dan shi har ga Allah yake jin matuƙar tausayinta. Mopping kuwa a rana a gidan nan, sai tayi sama da sau sha biyar, wanke-wanke kamar gidan da ake rabon sadaka, banda ɗorawa da saukewa da kula da yaran baƙi, tana yi ana zaginta. Wani lokacin haka zata fama ƙunar tayi ta kuka. Kawu yahaya ya din ga kai ta dressing, Allah ya taimake ta ƙuna ta fara warkewa. Tana matuƙar son ta ɗauki jaririyar da antyn ta haifa, sai dai an ƙi bata damar hakan, daga nesa take hangen ƴar, zuciyarta har raya mata take ta ce a bata ta ɗauketa, amma da ta tuna hakan na iya haifar mata da cin mutunci, sai ta haƙura. Farida ta je ta tarar da mijinta a bedroom ɗin sa, yana ta aikin takardu. Ta zauna tana cika tana batsewa ta ce "Dr. Wurinka na zo" Ba tare da ya ɗago ba ya ce "Ina jin ki" Ta ɗan taɓe baki ta ce "Jibi in Allah ya kaimu ne fa suna, haryanzu baka ce mini komai ba, baka bayar da kuɗin hidimar suna ba, kuma wuri nake so a kama ka sani, amma ka ƙi magana". "A wannan karon babu suna, sauran ukun da aka yi Allah ya amfana, idan Allah ya kawo wata a gaba ayi". A fusace ta ce "Ban fahimta ba?" "To ki jira daga lokacin da ki ka fahimta, sai ki tashi ki bani wuri" Ta miƙe tsaye ta ce "Yahaya ni zaka wulaƙant, na gama gaya wa mutane da taron suna ka ce ba za ayi ba" "Hakika kawai zan yi, za a kawo raguna biyu manya, ayi hakika na sanyawa yarinya mariya, sai ki koma ki gaya wa mutanen babu suna" "Mariya kuma? Wace irin mariya ana zaune ƙalau, sunan uwar waye mariyar da zaka sanya wa ƴa ta, haka muka yi da kai? To ba gara Salman da na ce bana so ba, a kan wata mariya, kamar dattijuwa" Ya ɗaga kai ya kalleta ya ce "To ki koma ki bibiyi tarihin fiyayyen halitta, zaki gane suna ne mai daraja da ma'ana". Aikuwa ta hau ta din ga surfa bala'i, duk yadda ya yi ƙoƙarin sanar masa da cewa, hukuncin zaluncin da ta yi wa ummi ne, ya sanya ya hukunta da haka ya kasa, saboda tuni ta kai sunansa wurin malamai, a kan ko ya mayar da ummi, ko kuma duk izayar da zata yi mata ba zai iya magana ba, yarinyar ta gaji ta bar gidan. Tun a haihuwar inteesar, ya so saka mata sunan mahaifiyarsa Salma, farida ta ce ba ta san zancen ba, ba ta so, aka saka sunan ta ta uwar, haihuwar khausar ma, ta ce sunan yayarta da ta rasu za a saka, wannan ma suna ta kai ruwa rana a kan ita gaskiya ya bari sai wani lokacin a saka Salman, tun da sanyan wa ƴaƴa sunan iyaye ba wajibi bane ba, wai Jidda za a sakawa yarinyar, tana son sunan. Shi kuma ya sanyawa yarinyar mariya, sunan mahaifiyar ummi, wanda ita Farida sam hankalinta bai kai kan cewa sunan babar ummi bane ba. Ya fice daga ɗakin ya bar ta tana ta sababi da kumfar baki, ya zo falo ya tarar da ƴan uwan farida na ta cin abinci da lemuka da nama zuƙu-zuƙu. Ga ummi da ɗagaggiyar riga, tana ta mopping, tare da haɗa kwanukan da suka ɓata, sai ta kwashe zata tafi, sai a kirata a jefa mata wani kwanon. Gyaran muryar da yayi ne ya sanya duk suka juya, mai neman gyale nayi su rufe jikinsu, masu gyara zama na yi. "Yauwwa, ina godiya ga Allah subhanahu wata'ala, da kyautar haihuwar mace da ya bani, ina kuma godiya a gareku wurin tsayawa tsayin daka, wurin kula da ƴar uwakku, duk da hakkina ne. Ina godiya sosai, dan Allah idan kun gama cin abincin, zaku iya tafiya gida, rahama zata iya cigaba da kula da ita. Ba za a yi taron suna ba, ga yanayin rayuwa, gara a tattala kuɗin tayi jego mai kyau, kuna iya tafiya idan kun gama kan magariba dan Allah, sunan jaririya mariya, za a dinga kiranta da noor" Gaba ɗaya turus suka yi suna kallonsa, tun da suke zuwa gidan, su yi duk hauka da rashin hankalin da suke so, bai taɓa yi musu magana ba, sai yau, dan maganar tasa ta wani fannin kamar cin fuska. Ummi kuwa washe baki tayi, jin an sakawa jaririyar mariya, duk da ba ta san dan sunan mahaifiyarta ya saka sunan ba, amma wani irin daɗi da farinciki ya ratsa ta. A hankali ta ce "Allah ya raya noor takwarar mama" Daga in da yake ya hango farinciki a kan fuskar ummi, yayi murmushi ya fice, yana tawasalli da farincikin da ya sanyata yana neman biyan buƙatunsa a wurin Allah. Farida ta sha kuka, da yin alwashi kala-kala a kan yahaya, saboda yadda ya wulaƙanta ta, ya tozarta ta a gaban ƴan uwanta. Suka din ga rarrashinta, tare da bata shawarwari daban-daban. Babbar yayarsu ta xe "Duk sakacinki ne, waye ya gaya miki ana barin namiji haka, kyakywar mallaka zaki nema, ta mai da ɗan gida bawa, ki juya shi yadda yake so, kar ki yi bori da yawa, ki girgiɗe auren, duk cikinmu babu wanda yake cikin rufin asiri da kwanciyar hankali kamar ke, kar ki yi mana sagegeduwa, amma dole mu zage damtse". Suka din ga zigata, ƙarshe kan sallar magariba suka watse daga gidan sai rahma, rahama kuma ba wani abun kirki take yi mata ba, saboda shegen son jiki ne da ita. Bayan watsewar ƴan gidansu, ta ƙuduri aniyar ƙuntatawa dr. Ta hanyar nuna halin ko in kula ga yarinyar, gashi mutum ne mai mugun son yara, baya son ya ga ƙaramin yaro cikin damuwa. Yarinyar shegen kuka ne da ita, ba ta taɓa ɗa mai kukanta ba, idan tana kukan sai ta yi banza da ita. Yayi ta maganar ta kula da ita amma ta share shi. Ranar da aka yanka hakika kuwa, ummi ce ta zage ƙwanji, tsaf ta gyara hanjin nan, dan kuwa rahama ƙin fitowa tayi kan naman, ga rana na dukan kayan kitchen. Abdul ne ma ya kama mata wasu abubuwan, ta kunna murhu ta ɗora sai ka ce babbar mace. Sai azahar yayenta suka zo da ƙanwar babanta, suka tarar da ummi a akan aikin, suka din ga yi wa rahama da farida faɗa, wai dan me za su bar ummi ta yi aikin naman, sai ta sace ta cinye tukuna. Abdul ne ya fusata ya ce "Yaya ummi ba ɓarauniya ba ce ba, ba ta taɓa ɗaukar abun da ba nata ba" "Rufewa mutane baki kan in mareka, mara kunya fitsararren banza" Ummi da jikinta yayi sanyi ta ƙyale musu aikinsu. Suka gama aikin nama suka kwashe wanda za su kwashe, suka bar saura suka tafi, dr. Ya dawo ya tarar da farida da yaranta suna ta cin naman, ya leƙa ɗakin ummi tana zaune tana ta tilawar Alqur'ani ga gida ya buɗe da ƙamshi, ya shiga ɗakin farida ya ciko leda da nama, ya kai ya bata. A gaban yara ta rufe shi da masifa, a kan ko dai ummin nan kishiyarta ce ba ta sani ba. Ganin cin mutuncin da take yi masa a gabansu, ya sanya Abdul tashi ya bar wurin. Cikin miyagun maganganun da take yi masa, har da gugar zanar ko wani abu ne tsakanin sa da ummi, da ya sanya shi bawa al'amarinta muhimmanci har haka. Ta dire noor ta tashi ta bar masa falon. Ummi kuwa da sauri ta wanke hannunta, ta hau naman nan da ci, dan tun ana suyarsa ƙamshin ya cika mata ciki, ranta ya biya. Sai tayi aikin abinci  da nama ba adadi, da ta gama rahama ta shiga ta raba abincin, ta kwashe naman ta hanata, koma ta bar da ɗan kaɗan sai dai ta haɗa da ƙanzo, dan haka nama tana kallo ba za a bata ba. Ta fito falo, dan samun tsinken sakace, ta tarar da kawunta rungume da jaririya tana ta tsala uban ihu. Da sauri ta ƙarasa in da yake ta ce "Kawu bani ita, ban taɓa ɗaukarta ba". Ya miƙa wa ummi ita ya ce "Gata nan mai sunan mamanki, ina fatan ita ta so ki, kuma ta din ga ɗebe miki kewar mamanki" Da sauri ta ce "Amin ya Allah, Allah yasa" ta karɓi yarinyar ta ce "Mamana ki daina kuka, mama tana da haƙuri, kawu ta zama kakarka kenan? Maman mama ko?" Sai da ya ɗan dara ya ce "Tsohuwa ce kenan?" Ummi ta ɗorata a kafaɗarta, tana jin soyayyar yarinyar a ranta, da aka saka mata sunan mamanta. Haka ummi ta din ga zagaye da ita a falon, tun tana tsala ihun har tayi bacci. Dr. Ya ce "Lallai ummana kin iya raino, tun da har gashi kakata tayi bacci, kawota ki je ki kwanta" Ta bashi ita, tana kallon fuskar yarinyar, gashinta har goshi, jawur da ita. Ya kalli ummi ya ce "Na ga ƙunarki da sauƙi, in sha Allah ranar monday zaki koma school gaba ɗaya" Ta ce "To Allah ya kaimu" "Amin, ki je ki kwanta sai da safe" ta juya ta nufi hanyar ɗakinta, kamar ta ce ya bata ƴar su kwana tare. Ranar Litinin ta koma ta cigaba da zuwa makaranta, ranar da ta je islamiyya, Maryam ce ta fara ganinta, da sauri ta tashi ta nufi ummi ta ce "ya jiki?". Ummi ta ce "Na ji sauƙi" "Kin warke duka ƙonuwar ta warke?" Ummi ta jinjina mata kai alamar eh. Ta ce "Alhamdilillah, dan Allah ki yi haƙuri, tun ranar da abun ya faru na kasa mantawa, kuma ban san gidanku ba, na gaya wa mamanmu ta din ga yi mini faɗa, ba ina sane na tureki ba ta ce in nemi yafiyarki". Ummi ta yi murmushi ta ce "Ai bakomai, na samu sauƙi". "Amma ya aka yi ki ka ƙone a ciki da ruwan zafi?". Ummi ta ce "Zubo mini yayi". "To Allah ya ƙara afuwa" Ummi ta amsa da "Amin". Maryam ta liƙewa ummi, sai dai ummi sai ɗari-ɗari take yi da ita, saboda ba ta son wani abu ya haɗa su tayi mata tijara da tashin hankali, saboda ita bata iya faɗa ba, maryam kuwa dage ce, akwai masifa. Ga maryam da azabar kashe-kashen kuɗi, banda kayan ciye-ciye da take zuwa da su. Komai za ta ci sai ta bawa ummi, ummi kuma ta ce ba zata ci ba. Tun tana ɗan ɗari-ɗari da ita, har ta ɗan fara sabawa da ita kaɗan. Can gida kuwa kawu yahaya ya sanar musu matarsa an yi mata aiki, an ciro ƴa mace, sai dai likitoci sun ce sai matar ta huta sosai za azo dubiya. Saboda yana gudun su zo barka, Iya ta faɗi wani abun, da zai yi wa ummi mummunan tabo a nan. Dama kuma gashi ba shiri suke yi da farida ba, dan ita da Iya kar ta san kar ne, iyan za ta iya zuwa ta bar ta a falo ta cigaba da sabgoginta ba tare da ta bata ko ruwa ba. Ummi ta ɗauki soyayyar duniya ta ɗorawa jaririya noor, idan uwar ta yasar da ita, sai ta ɗauke ta ta goyata, tayi ta jijjigata tana aikin gidan da ita a bayanta, dan ko da yarinyar ta fara dariya ummi ta fara yi wa. Duk wannan soyayyar da ummi ke nunawa ƴar farida, bai sanya ta sassauta mata daga baƙar azaba da mugunta ba, da ita da ƴaƴanta da ƙanwarta, dan ummi ba sabon abu bane a wurinta, kaiwa ƙarfe ɗaya na dare ba ta kwanta ba, saboda azabar aiki. Ga wani sabon salon zalunci, har maƙwabta sai su aiko ummi ta je, a sakata aiki, har wankin labulaye da carfet, sai a sakata, gyaran kaji da fige su, sai a saka ummi. Makaranta kuma maryam na ta sake shishshigewa ummi, sai dai ummi ta fuskanci maryam ɗin na ƙoƙarin mayar da ita ƙarƙashin ta ta din ga mulkata ta zama kamar ƴar korenta, ummi ta cigaba da janye jikinta, maryam ta kasa samun damar hakan, saboda ummin na da mugun gudun abun hannunta. Wasu lokutan haka ummi za ta zo ba ta ci abinci ba, maryam ta zo da abinci na alfarma amma fafur taƙi ci. Kusan wata uku da haihuwar noor, kawu yahaya ya ce idan suka tashi suka koma sabon gida, sai su iya su zo, su ga noor, kuma su ga sabon gida. Dan yana tsoron Iya ta zo ta saki baki ta faɗi wani abu da zata ɓata ummi, dan ya ƙudurce a ransa sai ya je yayi mata kashedi a kan ummi kan su zo, kuma gashi ba jituwa suke yi da iyalinsa ba, duk zuwa sai Iya ta ce an yi mata laifi, duk zalamar iya da son abun duniyarta ba ta ƙaunar zuwa gidan yahaya, wannan karon ma shi kawun ne ya takura su zo, kar abun ya zama surutu, an yi mata aiki ba su zo ba, ga kuma tariya a sabon gida. Ɓangaren ummi kuwa sumul ta samu lafiya, kamar ba ta taɓa yin larurar sanyi ba, kuma lokaci zuwa lokaci, kawu yahaya ko bai sayi abu ya bata ba saboda matarsa, ya kan ɗan bata kuɗi ta sai abun da take buƙata. Suka fara shirin tashi daga gidan, dama ƴan kayan ummi ba su da yawa tuni ta tattare su ta ƙulle. Hatta su intee ummi ce ta haɗa musu kayansu, sannan ta koma ta haɗa na rahama, ga yau noor sai koke-koke take yi zazzaɓi na damunta, kai ka ce ummi ce ta haifeta, ta bata magani ta haɗa madara ta bata, sannan ta cigaba da aikin da ita a bayanta. Suka gama haɗa kaya cif, washegari tun safe mota ta zo ta kwashi kayan su, zuwa sabon gida. Gidan da suka koma, ƙato ne yafi wancan girma da kyau, a ɗan gaban unguwar da suke da yake, ƴan uwan su farida suka cika gidan, ummi na ganinsu suna ta binne-binne. An canza furnitures, duk ta rabawa ƴan uwanta tsofaffin, ummi kuwa da tsohuwar katifarta ta dawo gidan, sai dai hakan ko a jikinta, ɗakinta shi ne na farko, baya cikin ainihin falon da zai sadaka da sashen kowa, Abdul sashinsa daban ba a cikin falon ba, da kitchen ɗin sa da banɗaki, a can gefe ɗaya. Gidan ya ƙawatu yayi kyau matuƙa, ko ina ya sha flowers, sai ƙamshin sabunta yake yi. Hatta ɗakin su intee kamar ɗakin wata amaryar, dr. Yayi ƙoƙari sosai da sosai, dama mutum ne mai hidimtawa iyalinsa sosai da sosai. Bayan magariba ummi ta gaji matuƙa, har wani jiri take ji, ga ciwo da mararta take yi, wanda tun da take bata taɓa jin irin ciwon ba. Tana ta ƙoƙarin gyara nata ɗakin, dan kuwa ba ta gyara komai ba, tana ta fama da aiki, da rigimar noor. Ƴan uwan farida suna ta cewa ta karɓe ƴar ta daga hannun ummi, kar ta shafa mata baƙi da muni. "Ke!" Ummi ta waiwayo ta kalli rahama da ke tsaye. Ta ce "Bani kuɗin nan da zobena" Ummi tayi saroro ta ce "Wane kuɗin?" "Ba ke kika haɗa mini kayana ba?" "Eh nice" ummi ta amsa. "Kuɗin da suke cikin wardrobe ɗina, kuɗin anty farida ne" Ummi cikin faɗuwar gaba ta ce "A'a anty rahama, ban ga kuɗi ba wallahi, kayanki kawai na haɗa miki a cikin akwatin da sauran kayanki a cikin jakunkunan da ki ka bani, dubu biyun nan ce kawai kuma kin ɗauketa, amma ban ga kuɗinki ba". "Ke rufe mini baki ko na dalla miki mari, kuɗin anty farida ne dubu hamsin" "Wallahi wallahi anty rahama ban gani ba, ki cajeni ki caje kayana, wallahi ban ɗauka ba" ummi tayi maganar jikinta yana rawa tana tuna irin tozarcin da aka yi mata lokacin da iya ta ce ta yi mata sata. "Rahama ina kuɗin ne? Ta baki?" "A'a fa sai kin zo da kanki, ta ce ita ba ta ɗauka ba". Farida ta ce "Ke, ina kuɗina?" "Anty ban ɗauka ba" ta faɗa kamar numfashin ta zai ƙwace, saboda fargaba da tashin hankali. Ashar ɗin da farida ta yi mata cikin tsawa ya sake gigita ta, ta ma rasa me za ta ce. Shaƙeta rahama ta yi tana zazzaro mata ido ta ce "Zaki faɗa ko sai na kashe ki" girgiza kai kawai ummi take yi. Farida ta ce "Rahama ƙyaleta, kar ta ja miki bala'i, ta riƙe miki kurwa kamar yadda ta yi mini, wallahi sai ya biyani kuɗina, kuma a wannan karon ko ubanta zai fito daga kabari ta din ga yawo da shi, sai ta bar mini gida ta koma in da ta fito, ba zan zauna da ɓarauniya ba, ga sata ga maita ba zai yiwu ba". "Antyn dan Muhammadurasulillah ki yi haƙuri, dan Allah kar ki mayar da ni ƙauye, wallahi ban taɓa sata ba, ban san menene maita ba" "Zaki santa yau, ɗaukko ƙullin kayanki ki wuce, ba zai yiwu ba" Suka hankaɗo ummi waje, duk attention ɗin mutanen gidan ya dawo kansu, noor da ta fara dariya, tana hango ummi ta hau dariya tana ɗaga mata hannu. "Lallai farida an haɗaki da masifa, satar kuɗi kuma, wannan wataran sai ta ganki a makara hankalinta zai kwanta" a tsakiyar falon suka zazzage mata kayanta, sai ga dubu ɗaya sabuwa fil wadda kawunta ne ya bata. Rahama ta ce "Anty ta fito da sauran, suna wurinta wallahi, kalli dubu ɗaya fa a ina ta samu". Inteesar ta ce "Tashi a caje ki, olay" kausar ta ƙyalƙyale da dariya tana maimaita olay. Dr. Yayi sallama tare da Abdul ya tarar da ummi a durƙushe, tana ta gursheƙen kuka, noor sai zillo take ummi ta ɗauke ta. "Lafiya kuwa?" "Dr. Ni fa na gaji, da abun da yarinyar nan take yi mini, daga bawa rahama ajiyar kuɗi ta kwashe, ta bani kuɗi tun da girma da arziki amma taƙi". "Shi ne zaki ajiyeta a gaban mutane kina tozarta ta haka? Idan yaranki ne haka zaki yi handling ɗin su? Nawa ne kuɗin?" Cikin mamaki ta ce "Au haka ma zaka ce?" "Na ce nawa ne kuɗin?" "Dubu hamsin" ta bashi amsa tana riƙe ƙugu. "Sana'ar me ki ke yi da har ki ka tara dubu hamsin? Idan ma akwaita na san a jikina aka sameta, zan biya na kashe maganar nan daga yau, kuma daga yanzu. Ummi ba ɓarauniya ba ce ba halin ta bane". Ta yinƙura za ta sake magana ya tari numfashin ta ta hanyar cewa "Na ce na kashe maganar nan" Ya dubi ummi ya ce "Ummana, tashi kiyi tafiyarki" Ba tare da ummi ta yi zuciya ba, ta dubi yarinyar da take ta zillo tana kuka, ta ƙarasa ta ɗauketa, ta nufi ɗaki da ita. Abdul ya durƙusa yana kwashewa ummi kayanta. "Farida anya maganin nan yayi kuwa? Kin ga fa abun da yayi miki". Farida ta kasa magana saboda takaici, yau ta ƙuduri aniyar ummi ta bar mata gida, tun da yau sun yi sababbin ayyuka a gidan. Ummi kuwa zuruuu tayi da ido, tana kallon noor da ke ta ɓangale baki tana yi mata dariya. Cikin kuka take yi wa noor surutai, ta ce "Mamana, kin gani ko, tun tafiyarki ban taɓa kwanan farinciki ba, dan Allah mama ki dawo, ko ina ne ki tafi da ni, mama kamar in sha guba in mutu" tayi maganar tana kifa kanta a kan ƴan ƙafafuwan noor, tana wani irin kuka mai sauti" FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK. https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends Masu neman free books ɗina, da free pages duk akwai a kan watpad account ɗina. Irinsu Abduljalal Wata kissar sai mata Wuta a masaƙa Cutarwa Ƙanwar maza Gaba da gabanta Aƙidata Ruɗin ƙuruciya Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata. 08081012143. And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link. https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels Ayshercool. Ayshercool 08081012143                               *CUTARWA!" *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* P17 FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK. https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends Masu neman free books ɗina, da free pages duk akwai a kan watpad account ɗina. Irinsu Abduljalal Wata kissar sai mata Wuta a masaƙa Cutarwa Ƙanwar maza Gaba da gabanta Aƙidata Ruɗin ƙuruciya Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata. 08081012143. And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link. https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels Ayshercool. PAID ADVERT!. Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi. Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku Oll types of Turaran wuta Sandal Halut Irik Difur Gab Gab Kajiji Habil Nabak Humra Kulakcha Dilke da kalta Kayan Garan jiki Muna turara Kaya Kujerar garan jiki Kannada Madarorin turare masu kamshi  Man garan gashi  Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702   08025453921 *TALLA!TALLA!TALLA!* *INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*. *BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU* *MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA* BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI P17 Shiru noor tayi, tamkar tana jin abun da ummi take faɗa. Sosai ummi ke kuka, tamkar za ta shiɗe, duk da ba wannan ne karon farko da aka yi mata ƙazafin sata ba, amma na yau yayi mata zafi da ciwo ba kaɗan ba. Ji tayi an dafa ta, ta ɗago da sauri dan ba ta ji shigowar mutum ba. Abdul ta gani a bayanta da kayanta a hannunsa, cikin damuwa ya ce "Dan Allah yaya ummi kiyi haƙuri, na san ba zaki yi sata ba, amma ki yi haƙuri dan Allah ki daina kuka, kar kanki yayi ciwo". "Yaya Abdul, ya aka yi kai ka yadda ba zan sata ba, amma anty farida da rahama suka ɗora mini sata? Suka ci mutuncina a gaban mutane?" ya durƙusa ya ce "Na san babu daɗi, kiyi haƙuri dai dan Allah" Ta jinjina masa kai, dan kuwa tana ganin mutuncin Abdul sosai da sosai. Ya ɗora da cewa "Kar ki ga ɗakinki a haka, mun yi magana da abba ne, ya ce a bari mu tare ya ga ɗakin da maama zata baki, sai ayi miki furnitures, kar a saka miki ta hanaki ɗakin". Ummi ta girgiza kai ta ce "Dan Allah kar ka bari yayi mini, ya kashe kuɗi da yawa, ni katifata ta isheni, duk kyan furnitures ɗin da za a saka mini, ƙarshe a tsakiyar ƙasa za a binne ni, hakan ma ya isa" Shiru yayi yana kallon ummi, ta kwanta a kusa da noor, ta sanya hannunta ta riƙe ɗan ƙaramin hannun jaririyar. Abdul ya tashi ya fita yana waiwayenta, duk abun da aka yi mata, bai sanya tayi zuciya taƙi kula noor ba. Kasancewar a gajiye take, wani irin nannauyan bacci yayi awon gaba da ita, baccin da rabon da tayi makamancinsa har ta manta. Kwanki uku da tarewarsu, aka kawo wa ummi ƙatuwar katifa, da wardrobe mai biyu, sai ɗan mudubi da stool. Ba ƙaramar murna ummi tayi ba, tare da wani farinciki, wai duk wannan nata ne abun mamaki. Kawu yahaya ya fara deciding zuwa ƙauye, ya gaida Iya, dan haka ya tambayi ummi ko za ta bi shi, ta je a gaggaisa. Amma tayi shiru ba ta ce komai ba. "Ummana baki ce komai ba" "Kawu ka ce ina gaishe su, ba sai na je ba" tayi maganar tana addu'a a zuciyarta, kar ya matsa ya ce sai ya tafi da ita, saboda tana tsoron ya tafi da ita, Iya ta sake cewa ba zata biyo shi ba. "Ƙauyen ne ba kya son zuwa ko ummana?" Ummi ta gyaɗa masa kai alamar eh. Yayi murmushi ya ce "Kwantar da hankalinki kyakywar uwa, abun da ki ke so shi za a yi, zan sanar da su saƙon gaisuwarki, ko ni ba zan so ki je ba, sai kin zama cikakkiyar mutum, da babu wanda zai tursasaki yin abun da ba kya so a rayuwarki". Kawu yahaya da kansa ya je ƙauye dan ya ɗaukko iya, ta zo ta ga sabon gidansa da jaririya, amma ta ce ba zata ba, saboda matarsa ba ta da mutunci. Hashim kuwa yana ganin kawu yahaya ummi ya fara tambayarsa. Ya ce "Ummi na nan lafiya ƙalau Alhamdilillah, tana nan tana karatunta duk ta ce a gaishe ku" "Allah sarki ummi, muna amsawa". Iya ta ce "To wai yaushe zaka dawo mini da ita ne?" Kawu yahaya yayi murmushi ya ce "Ai Ummi sai Allah ya kaimu lokacin aurenta zamu gayyace ku, ba zata sake zuwa gagarawa ba". A ɗan hasale ta ce "Saboda me?" "Saboda babu abun da za ta zo tayi muku" "Kai yahaya bana son sakarci, zumuncin fa? So kake ka raba mini kan iyali?" Ya girgiza kai ya ce "Ba haka bane ba, na nemi iznin zuwa da ita, ta ce in gaishe ku, saboda makarantar ta" "Innalillahi wa Innalillahi raziƙuna, ita ummun ce ta faɗi haka? Ta fifita boko a kaina?" Magaji ya ce "Iya wa Innalillahi raji'un ake cewa ba raziƙuna ba" "Zan ci uwarka idan na sake magana ka tsoma mini baki, tun kan a haifi uwarka haka ake faɗa, ba damar mutum ya motsa sai ka ce zaka ci gyaransa?" Ganin Iya na son dasa faifan cin zarafin ummi da iyayenta, ya sanya shi bawa Iya abun da zai bata ya tashi ya ce zai tafi. Har mota hashim ya raka dr., Ya ce a cewa ummi yana gaisheta, tayi karatu da kyau. Kawu yahaya yayi alƙawarin isar da saƙonsa ga ummi. Kasancewar fitar sassafe yayi, yana gama abun da zai yi ya dawo kano, a falo ya yada zango, ummi tuni ta gama girki tayi shirin tafiya islamiyya, ya tsareta a falon yana bata labarin saƙon ƴan gidan na gaisuwa a gareta. Ganin yadda ummi ta ɗan sake da kawu yahaya, har tana tambayarsa wasu daga mutanen gidan, ya sanya farida yi mata tsawa, ta ce ta tashi ta tafi makaranta. Abdul ya shigo da noor a hannunsa, ummi tayi saurin karɓarta, ta ɗan ɗagata sama ta ce "Mamana tafi ta kowa" noor kuwa ta buɗe baki tana dariya. Wata irin zabura farida tayi, tun da ummi take kiran noor da maman wasu lokutan, ba ta taɓa kawo sunan mahaifiyar ummi bane ba sai yanzu, tayi wata irin zabura ta ce "Dr. Sunan matar ƙaninka ka saka wa noor? Babar ummi?". Kai tsaye ya ce "Yes" "Saboda me? Meye alaƙata da ita? Ita tayi mini cikin? Ko ita ta haufa mini, wai tsaya meye alaƙarka da ita?". "Alaƙar da ki ka faɗa mana, na kawo miki amanar yarinya kina ta wulaƙanta ta, gashi tana ta yi miki bauta kamar baiwar da ki ka sayo da kuɗinki, dan haka na saka mata sunan mahaifiyarta, atleast ta samu ƴar uwa, kuma wadda zata din ga kallo tana jin daɗi". "Yahaya gaba ɗaya na kasa gane kanka, na rasa in da ka dosa a kan yarinyar nan yanzu saboda tsabar wulaƙanci da rashin mutunci, matar da ban sani ba kawai ka saka wa ƴa ta sunanta? Ni wai wace irin alaƙa ce tsakanin ka da ummin nan, ko zagata ka ke yi ne ban sani ba, da a duniya kullum abun da zai faranta mata kawai ka saka a gaba?". A fusace ya ce "Wace irin maganar banza ce haka farida" "Ba wani maganar banza, maganar gaskiya dai, to ga noor ɗin nan na bar mata, ta je ta raine ta na bar mata, tun da sunan uwarta ne ba na uwata ba". Duk da ummi a tsaorace take rungume da noor, jin kawu yahaya suna faɗa, sai dai jin abun da farida ta faɗa, ya sanya cikin wauta da ƙuruciya, ta risuna ta ce "Anty na gode Allah ya saka da alkhairi, Allah ya jiƙan magabata na gode in sha Allah zan kula da ita, a bani kayanta da abincinta na gode" a zaton ta da gaske ta bar mata noor. Kawu yahaya duk da a fusace yake, sai da yayi dariya, aikuwa cikin ɓacin rai farida tayi kan ummi, ta fizge noor ta ce "Ai ba uwarki ce tayi mini naƙudar ba" Kawu yahaya ya ce "Ummana, jeki makarantar ki kin ji" ta ɗauki jakarta, ta fita cikin damuwa. Ummi ba ta cika makara ba, dan haka da wuri ta je makarantar islamiyya. Zama tayi ita kaɗai, tayi shiru tana tunani, tana son sake yi wa kawu yahaya maganar ya gano in da mamanta take? Sai dai ta kasa tana jin nauyinsa, shi ya ce mata ta bashi lokaci, dan haka ba ta son cigaba da takura masa. "Ummi" maryam ta kira sunanta. "Na'am" ta amsa a taƙaice. "Taso ga mami can ta zo, ita ta kawo mu, ta ce yau dai tana son ta ganki" Jin mahaifiyar maryam ce ke son ganinta, ya sanya ta tashi da sauri, dan duk in da aka ce wannan babba ne mussaman sha'anin uwa, ummi na bashi girma sosai da sosai. A ƙofar makaranta suka tarar da mamin a wata zuƙeƙiyar mota, suka ƙarasa gaban motar, ta buɗe ƙofar motar tana murmushi. Ummi ta durƙusa ƙasa ta ce "Mami ina wuni" Matar ta ƙarewa ummi kallo, sannan ta yi murmushi dariya na neman suɓuce mata ta ce "Lafiya lau ummi, ya gida ya makaranta?" "Lafiya ƙalau, Alhamdilillah" "Yau Allah yayi na ga ummi, kusan kullum sai tayi zancenki a gida" Ummi tayi murmushi tare da sunkuyar da kanta ƙasa. "To Ubangiji Allah yayi muku albarka baki ɗaya, ina fatan wataran kuma zaki kawo mini ziyara gida" Ummi ta ce "To, zan tambaya idan aka bar ni zan zo in sake gaishe ki" Tayi murmushi ta ce "Masha Allah, ku koma aji to, Allah ya yi albarka" Ummi ta amsa da "Amin ya Allah na gode, Allah ya tsare hanya" Maryam ta ce "Bye bye mami, drive well" Ta amsa mata da "Thank you dear" A haƙiƙanin gaskiya maryam bata da aiki sai bayar da labarin baƙin ummi, da gidadancinta da rashin wayo, da yadda take kullum cikin kuka, abu kaɗan sai ta hau kuka, da irin yadda malamai kan yi mata ba'a, ko yadda su kan su ɗaliban ke attacking ɗin ta, amma ba ta iya cewa komai. Babban abun da ya burge mamin da ummi, shi ne nutsuwarta, da kuma gudun duniya da ta gani yau da wanda take jin labari a wurin Maryam. **** Yau babban burin Idris ya cika, dan kuwa ya hilato hindu shagon wani abokinsa, ya aiwatar da abun da yake muradi a kanta. Hindu tayi kuka kamar ranta zai fita, sai dai ya zuba mata ido, a tunainsa yanzu hankalinsa zai kwanta, sai dai ina, kasancewa da ummi kawai yake burin yi. Duk da babu abun da ya shiga tsakaninsa da ummi, yana jin kamar akwai wani abu na musamman da ummi ke da shi, da baya tunanin ya samu a tattare da hindu. Iya taushin fatar ummi ya isa saka mutum annashuwa, ya daɗe yana jin haushin kansa, da har suka rabu da ummi, bai amfana da ita ba. Kukan hindu ne ya dawo da shi hayyacin sa, ya din ga lallaɓata yana bata haƙuri, tare da yi mata alƙawarurruka kashi-kashi irin na yaudara. Tun da farida ta san sunan babar ummi, aka saka mata, ya sanya ta ƙara tsananta ƙiyayyarta ga ummi, azabtarwa iri-iri. Rayuwa ta cigaba da garawa, sai dai al'amura sun tsananta ga ummi, lokacin da dr. Ya samu canjin wurin aiki, daga Kano zuwa kaduna, wasu lokutan sai yayi wata guda bai zo gida ba, wasu lokutan kuma ya kan zo weekends. Idan ummi ta karaya ta ji kamar ta mutu ta bar duniya ta huta, sai kuma taga wahalarta ta tashi a banza kenan, ba ta yi acheiving komai a rayuwa ba. Ko ina babu daɗi, gida azaba da wahala, makarantar boko, ba'a, cin zarafi daga ɗalibai har ma da malamai wasu lokutan, sukan aibata ta ko su muzantata da halittarta. Sai da ta kai ta kawo, kuɗin makaranta idan dr. Ba ya gari, idan ya turowa farida, ba zata bawa ummi nata ba, har korota ake yi daga makaranta. A ci mata mutunci, Saboda rashin biyan school fees, sai da ta kai Maryam ta saka babansu biya wa ummi kuɗin makaranta. Shugaban makarantar ya hana malamai korar ummi, a duk lokacin da ba ta biya kuɗin makaranta ba, sai ya yi wa kawu yahaya waya, sai a lokacin dr. ya san abun da yake faruwa game da kuɗin makarantar ummi da yake bawa farida ba ta bata, daga nan har makarantar boko, direct transfer yake yi musu. Duk wani aiki ko aike da yakamata namiji yayi ga Abdul, ummi ce za ta yi shi, sayen fetur, cefane, refilling ɗin gas, duk ummi ce ke yin sa, intee da kausar babu abun da suke tsinanawa a gidan nan, ko ɗauke cokali kuwa a kan hanya, saboda azaba har tayar da inji sai da ummi ta iya. ƙawayensu intee idan suka zo, su yi ta nuna musu ummi a matsayin ƴar aikin gidan su. Allah ya taimaki ummi, aka sakawa rahama ranar aure, ta din ga murna ta san ko ba komai ta ɗan samu rangwame. Gefe guda soyayya da shaƙuwa mai ƙarfin gaske ta shiga tsakanin ta da noor, noor komai ummi, kai ka ce ummin ce ta haifeta ba farida ba, dan ita ce ta yaye noor ma. Ummi na ta aiki a kicin da safe, ta je ɗakinta ta dawo, ta zo ta tarar da ƙwai guda biyu a kan drower kitchen, ita dai ba ta ajiye ƙwai ba, dan haka ta kai hannu ta ɗau ƙwan tana duddubawa, rubutu ne a jiki, an zana wani hatimi da sunan wanda rahama za ta aura, har da zanen kan ƙwarangwal. "Ke!" Tsawar da farida ta daka mata, ya sanya ta zabura ta saki ƙwan ya faɗi ya fashe, maimakon ruwan ƙwai ya fito, sai jini da wani baƙin abu ya tsiyaye. "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wai wace irin karfa ce ke ne?" Cikin magiya ummi ta din ga bata haƙuri, amma tsabar mugunta matar nan ta ɗauki muciya ta din ga bugawa ummi. Abdul yana falo yana video game, ya shigo kitchen ɗin da sauri ya tarar da ita tana ta bugawa ummi muciya, tana ƙoƙarin karewa. "Maama lafiya, meyasa ki ke dukanta da muciya" "Dalla rabu da ni, na gaji da abubuwan da yarinyar nan take yi mini" "Amma maama bai kamata ki dake ta da muciya ba, idan kuma ki ka ji mata ciwo fa?" Cikin ko in kula ta ce "Na daki banza" Tayi maganar tana sake kwaɗawa ummi muciyar iya ƙarfin ta. "Maama dan Allah ki daina cin zalin anty ummi, wannan CUTARWA! ce, maybe tsautsayi ne ya sanya ta yi miki laifin" A fusace ta ce "Ni ka ke gayawa ina cin zalinta?" Tayi maganar tana nufo shi. Babu tsoro ko fargaba ya ce "Idan ba CUTARWA! ba ce dai-dai ne Allah ya sa a yi wa intee ko kausar abun da ki ke yi mata" sak tayi tana kallon Abdul, ba ta taɓa zaton wannan maganar daga bakinsa ba. Ta ji jikin ta ya yi sanyi, ta jefar da muciyar ta fice. Ya girgiza kai shi ma ya fita, dan kunyar ummi ma yake ji, bai san me zai ce mata ba, saboda abun da mahaifiyar su take mata. BAYAN SHEKARU BIYU *** Ummi na tsaye a gaban mudubin ɗakinta, tana ta aikin taje gashin ta, ta nemi wuri ta zauna tana kallon kanta a mudubi, gashin duk ya rufeta, ta sunkuya tana cire gashin da yake jikin comb ɗin, ta tare shi a gefe sannan ta nannaɗe gashin kanta ta tufke shi. Ta sanya doguwar rigar shadda brown, ta kawo dogon hijjabi milk ta saka, ta ɗauki niƙabinta ta sanya. Ta shashshafa turare, tafin hannunta har ɗaukar ido yake yi, saboda tafin hannunta fari ne ƙal, kamar mata jini a jiki, kuma aka ɗora mata jan lalle a kai. Ta ɗauki ƴar ƙaramar jakarta ta fito, Abdul ya ce "Inyee ka ga amaren sauka" Kawu yahaya ya dube ta cikin fara'a ya ce "Congratulations dear, Ubangiji Allah ya sanyawa karatunki albarka, ya ƙara hasken makaranta" ta risuna ta ce "Amin kawu, na gode sosai da sosai" Ya kalli farida da ƴan matanta da suke ta sabgoginsu, kamar ba su san da zaman su a falon ba ya ce "To mu mun tafi wurin saukar" "Allah ya tsare" ta faɗa a yatsune. Kawu yahaya yaji babu daɗi, da yaransa ko mutum ɗaya babu wanda yayi saukar nan, idan baya nan sai sun ga dama suke zuwa makaranta, dan kuwa farida wurin koyon kwalliya ma ta sama musu, maimakon zuwa makarantar. Ummi gaba ɗaya bakinta yaƙi rufuwa, kaf a ƴan saukar ita ce ƙarama, danma tana da jiki ne, dan ko Maryam shekara biyu ta bata, itakaɗai ce mai shekaru sha shida a cikinsu, maryam na da sha takwas. Aka gabatar da abubuwan da suka kamata, sannan aka fara raba musu alluna. Ana bata nata ta nufi rumfar iyaye maza, har da gudu, wurin kawu ta ƙarasa ta durƙusa a gabansa tana cewa "Kawu ka ga" Ya karɓi allon yana murmushi ya shafa kanta ya ce "Allah ya sanya albarka ummana" "Amin kawu na gode" tayi maganar cikin tsantsar farinciki. Abdul ya ce "Rufe bakin mana" Ta kalleshi ta ce "Ta ina ka san bakina a buɗe yake a cikin niƙab". "Yadda ki ke magana ne ya sa na gane" Ta ce "Bari Yaya Abdul, Alqur'ani da daɗi wallahi". "Wannan gaskiya ne ummana, kalli baƙin ki na waccan rumfar" ummi ta waiwaya ta ɗaga kai. Wa zata gani? Yaya Magaji da auwwal, har da su Alhassan. Maimakon ta yi murna sai gabanta ya faɗi, ta kasa magana, dan fatanta Allah ya sa babu Idris suka zo, dan bata ƙaunar ganinsa. Sunanta aka din ga kira a speaker, ta zo ta karɓi kyautarta ta ɗaliba mai hazaƙa. A hankali ta tashi ta nufi in da ake kiranta, tafiya take cikin nutsuwa, shugaban makarantar ya ce "Ƙaramar su babbar su, Salma Muhammad Bashir, kun ganta nan duk ita ce ƙarama a ƴan sauka, amma babu ɗalibar da ta kai ta cin maki lokacin screening" Ummi ta karɓi kyaututtuka daban-daban, na hazaƙa, ladabi da biyayya da sauransu. Mamin su maryam ummi ta hango, ta tafi wurin da take, dan jan lallen da aka yi mata ma, gidan su maryam ta je, mamin ce ta biya. Mamin ta rungume ta tana faɗin "Allah yayi albarka ummi, Allah ya sanya wa karatunku albarka" Ta risuna ta ce "Amin ya Allah" Sau ɗaya ya ɗaga kai ya kalleta, ya lura da yadda ko iya haɗa ido da mamin ba ta yi, saboda tsananin tarbiyya da girmama manya, ya so ta ɗaga niƙabin ya ga ainihin fuskarta. Ya dubi Maryam ya ce "Ke ba uban da aka baki? ba na ƙoƙarin, babu na ɗa'ar" yayi maganar yana sake gyara zaman face mask ɗin sa. Cike da tsiwa Maryam ta ce "Ina ruwanka da ni? Ba a bani ɗin ba sai ka ƙwace allon saukar ma gaba ɗaya, mami ki rabani da shi wallahi, ai da yake ma ba gayyatarka na yi ba, waye ya ce ka zo?" "Rufen baki kan na ɓarar da ke a wurin nan" Ummi dai murmushi kawai take yi, duk ta san yayyen Maryam, wannan ne dai bata sani ba, kuma da alama maryam ɗin ta raina shi. Aka tashi daga filin sauka, su yaya magaji suka nufo su, "Ummi masha Allah, kin ga yadda ki ka girma?" Magaji Yayi maganar yana kallon ta. Alhassan ya ce "Ummi har kin yi sauka anya ba zuƙu ba ce ba?". Ummi ta yi murmushi ta ce "Ai makarantar nan ba a saukar zuƙu" Suka rankaya zuwa gida, suna komawa gida ta tarar da Iya, sai da ta ɗan ci burki, domin kuwa ba ta zaci Iyan za ta zo ba. Ta ɓoye mamakinta ta ce "Iya sannu da zuwa, dama zaki zo?" Ta harari ummi ta ce "Eh, da ki ka ce ke ba zaki zo in da nake ba, kar na yanka ki na cinye ko?" Ummi ta girgiza kai ta ce "A'a makaranta ce take hanani zuwa, ya gida ya kowa da kowa?". A ciki Iya ta amsa mata da lafiya lau. Dai-dai gwargwado kawu ya yi wa ummi ƙoƙari, dan naman kasuwa ya sayo fal, ya bata tayi girkin da zata rarrabawa mutane da ƙawayenta. Ita ummi ma kasancewar ba ta da ƙawaye, sai maƙwabta ta babbawa, sai su Iya da suka zo. Sam farida ba ta bi ta kan Iya ba, ummi ce take ta ɗawainiya da su, suna ta hirar makaranta da su magaji, sai dai ko da wasa, ba ta nuna musu tana shan wahala a gidan ba ko kaɗan. Kawu yahaya ya ji daɗin yadda ummi ta samu sakewa yau cikin ƴan uwa, tana hira ba kamar da da kullum a rakuɓe take ba. Iya kuwa ba dalilin saukar ummi ne ya kawota ba, balli ne ya tashi, Idris ya mayar da hindu tamkar matar da ya aura, tun bata saba ba har suka saba da sheƙe ayarsu. Kwatsam ciki ya bayyana a jikin hindu, suka rasa yadda za su yi da cikin, har sai da iyayen hindun suka farga. Dan haka zance ya fasu a gari, sai faɗuwa ta zo dai-dai da zama, domin kuwa iyayen hindu sun ce sai ya auri hindu, shi kuma ya ce ba ya son ta. Dan kuwa zance ya fara fasuwa, an fara zunɗensu a garin. Baban hindun kuma ya dage ba za a zubar da ciki ba, sai an haifi wannan ɗa ya riƙe, kuma sai ya aureta. shiyasa Iya ta lallaɓo wai kawu yahaya ya ɗauke shi ya sama masa sana'a a nan Kano, a mayar da aurensa da ummi!!! Iya a ɗakin kawu yahaya ta same shi, ta kora masa wannan jawabin. Yayi ƙuri da ido yana kallon Iya, har ta gama jawabinta. Kasancewar ummi na wurin, gabanta yayi wata irin mummunar faɗuwa, kawu yahaya ya kalli Iya ya ce "Amincewar ummi zaki nema, ni ba zan yanke mata hukunci ba, abun da take so shi nake so". "Zancen banza kenan, wane irin sai ta yarda ko ba ta yarda ba? Ba ɗan uwanta bane ba, rufin asirinmu ba nata bane ba, idan shi ma ya baro garin, suka neme shi suka rasa ba shikenan ba, asiri ya rufu, ai rufa masa asiri za ta yi,  ai umarni nake bayarwa ba shawara ba, dauɗar gora ai ciki ka sha ta!" Ayshercool 08081012143. WHAT'S APP ONLY PLEASE 🙏 18 Kan ka ce kwabo, hawaye ya wanke wa ummi fuska, har wata irin sheshsheƙar kuka take yi, dan kuwa da ace ta koma gidan Idris, gara a yanke mata hukuncin kisa, dan tana kyautatawa Allah zato a dukkan lamuranta, tayi imanin za ta dace da rahamar sa. Iya cikin masifa ta ce "To kukan uban me ki ke yi, ba taimaka miki zai yi ba? ke a wannan munin naki uban waye zai aure ki? Kalli fuskarki fa kamar buredi ya ƙone ƙurmus, har wani zaɓi ne da ke? Ke gaki nan ba ke ba mutum ba ke ba aljana ba". Kawu yahaya ya ce "Iya, lokacin da Allah ya halicci ummi fa, bai yi shawara da kowa ba, balle ace laifinta ne, ko wani abu ne ya sanya ubangiji yin halittarta a haka, halittar ummi hurumin ubangiji ne, dan haka bai kyautu a din ga ci nata fuska ba, kuma wallahi ummi ba ta da muni". "Ka ga ni kar ka yi mini wa'azi, ai maganar gaskiya ce, tun da Allah ya sa ita ba wata mamora ce da ita ba, balle ace za a samu mai kwasa ai duk sai a manta da abun da ya faru a baya ko? Tun da har da kansa ya ce ta dawo ɗin, sai a ja masa kunne" Dr. Ya kalli in da ummi ke zaune tana ta sheshsheƙar kuka ya ce "Ummana, jeki ɗaki abunki kin kwaso gajiyar sauka" ummi ta tashi zuciyarta na harbawa da sauri, ta tafi ɗakinta tana kuka, tare da adduo'i kala-kala a zuciyarta, tana fatan Allah ya sa kar kawu ya amince da abun da iya take faɗa. Dan har ta mutu ba za ta manta da azabar da ta sha a gidan idris ba, ko maƙiyinta ba ta fatan yayi rayuwa irin wadda ta yi a gidan idris. Noor ta bita ɗakin tana kiran sunanta. Kawu ya kalli Iya ya ce "Iya, ko ummi ta amince ko bata amince ba, ba zan sake bawa Idris ita ba, yaron nan gaba ɗaya jahili ne, wallahi da mutumin kirki ne, idan ta gama sakandare sai a mayar da auren, amma ni ba zan goyi bayan a cuci ɗan wani ba, yadda ya yi wa ƴar mutane ciki, ku je can ku nema masa mafita, dan baban yarinya bai yi laifi ba. Iya kin manta lokacin da ya din ga terere da ummi, yana tona mata asiri ga larurar da ke damunta? Shi meyasa ba a tursasa shi ya shanye dauɗar gorar ba, sai ummi? Allah da ya halicceta a haka in dai muna raye, zai bata abokin rayuwa na gari, haka zalika ba zan riƙe ƙato da bai san ciwon kansa kamar idiris ba, can ƙauye ya gagareku balle ni a nan, dan Allah kiyi haƙuri a bar wannan zancen. Ummin ma da kanta ta nuna ba ta so, dan haka dan Allah dan annabi a bar wannan maganar. Kuma ina baku shawarar mayar da idris makaranta kan a kuma bashi wata matar ya aura, dan kuwa jahilci ke ɗawainiya da shi". Cike da takaici iya ta kalle shi ta ce "Haka ka ce?" "Ba faɗa na yi dan na ɓata miki rai ba, amma gaskiya ce" Iya ta yi ƙwafa ta ce "Shikenan na tabattar da uwarka ce ba zaka tsallake umarninta ba, kuma da cikin ku ɗaya da baban Idris ba zaka so asirin sa ya tonu ba". Ya girgiza kai ya ce "Iya ai kin san mu kallon uwa muke yi miki, amma kowa ya ɗebo da zafi bakinsa, kin riga kin sangarta Idris, komai yayi ba zaki bari duniya ta hora shi ba, sai kin kare shi, kema yakamata ki hutawa ranki, ba shikaɗai ne ɗa a dangi ba". Ba ƙaramin takaici Iya ta kwasa ba, yadda ƙiri-ƙiri yahaya yayi burus da maganarta, ya zaɓi tonuwar asirin su. Dan haka ta ce masa babu ita babu ummi, tun da haka suka zaɓa, ya ce bakomai, Allhan da ya yi ummin zai kula da ita. Ko zama ba ta sake yi ba tun da ta tashi, ta ce magaji ya samo musu mota a tasha, kawu yahaya ya biya kuɗin motar, ya basu kuɗin kashewa, suka tafi. Ummi sai da tayi sujjadar godiya ga Allah, ga saukar Alqur'ani mai girma, ga kuma fasa mayar da aurenta da idris da aka yi. Duk da kuɗin da yahaya ya bawa Iya sun saka ta ɗan sassauta fushinta, amam ta sha takaicin rashin amincewa ya ɗauki Idiris a mayar da aurensa da ummi, ta din ga zagin ummi tana tsine mata, tamkar ba ita ta haifi baban ummi ba, tare da janyo mata jafa'i kala-kala. Ko da suka koma gida ta sanarwa Idris da babansa cewa yahaya ya goya wa ummi baya, yaƙi yadda da magabar da ta je masa da ita. Hankalin Idris ya tashi, dan kuwa baban hindu ɗan bala'i ne, ya ce ba zai yadda ba, ba za a zubar da cikin jikin hindu ba, sai ta haife shi, kuma sai sun karɓa sun riƙe, hindu na da wani yaya da yake soja, kurtu nema a cikin sojojin, amma ya zamewa su Iya barazana, dan kuwa shi ma cewa yayi sai ya saka bomb a gidan su iya, ko ya kama Idris ya harbe shi, tun da aka taɓa ƙanwarsa. Magaji ya san duk barazana ce, babu ɗaya da zai faru, amma yayi shiru da bakinsa, saboda sun cancanci koma menene ya same su, dan da idris bai taɓa ƴar mutane ba, babu mai ɗaga musu hankali, kuma ya danganta hakan da alhakin ummi Babu yawon da Iya ba ta yi wurin malamai ba, a kan a rufe bakin baban hindu, da ita kanta hindun da yayanta, amma abu ya ci tura, dan har barzanar kai su gaban hukuma baban hindu yayi idan suka cigaba da takura masa a kan maganar cikin nan, ko kuma ya saka ɗan sa ya ɗauki duk matakin da ya ga dace a kan su. *** Tafiyar rahama daga gidan dr., Bayan an yi mata aure bata sauya zani da komai ba, daga wahalar da ummi take yi, dan har undeas ɗin su intee ba zasu wanke ba, sai a haɗa mata a kayan wanki, duk ta haɗa ta wanke su. Sai dai tun ba aje ko ina da tafiyar rahaman ba, ta fara sintirin kawo ƙara wurin kawu yahaya, dan dama mahaifinsu ya rasu, duk wani abu na jin daɗi da ta sanya ran samu a gidan mijin, sai ta ga akasin haka, yana da hali ba bashi da shi ba, amma hatta shinkafa da man da za ta ci, sai ya ƙulla mata, ba yadda da zuwan baƙi gidansa ba, sai an kira shi ya bayar da iznin a zo, idan bai bayar ba kuwa babu mai zuwa. Kawu yahaya ya kira shi, dan a samu masalaha amma ya nuna shi tsarin gidansa ne a haka, dan haka dole a bar shi yayi yadda yake so. Haka nan kawu yahaya ya ce sai dai tayi haƙuri, yace shi tsarin gidansa ne a haka. Tun da shekaru goma sha shida, samari suka fara bin intee, hakan ba ƙaramin farantawa farida yayi ba, tana ganin intee mai goshin arziki ce, shekara goma sha shida, samari sun fara sintiri, dan ma dr. Yana korarsu ya ce yarinyarsa tayi ƙanƙanta sai ta fara karatu idan ma auren zai yi mata. Lokacin da ummi ta fara period babu wanda ta gayawa, dama ta riga ta san shi tun a karatuttukansu na makarantar islamiyya da na boko ana gaya musu shi, sannan an koyar da su tsabta a lokacin da mutum yake cikin jinin  haili. Dan har wata ƙungiya ta je makarantar su suka wayar musu da kai, a kan jinin haila da tsafta, dan haka babu wanda ta gayawa da ya same ta. Ta samu kayanta da suka ɗan kwana biyu, ta yayyanka ɗankwalin, take amfani da shi. Idan kuma Allah ya sa dr. Ya bata kuɗi, babu abun da take fara saya sai pad, tana iya haƙura da kowace irin buƙata ce da ita, ta sai pad ɗin da za ta yi amfani da ita da kuma farin muski. Sintirin samari zuwa wurin intee, ta din ga wani iyayi tana yauƙi, ya sanya aka fara yi wa ummi gori da habaici, domin kuwa babu wanda ya taɓa zuwa ƙofar gidan ya ce yana sallama da ita, ko a hanya ma babu wanda ya taɓa biyota ya ce ya na so. Su yi ta yi wa ummi wulaƙanci, wai farar mace Alkyabbar mata, baƙar mace bolar maza. Kodayake bolar akwai wadda ake iya recycling, wata ta riga ta zama waste gaba ɗaya bata da mamora. Ko sai sun ga ummi su fara wankan baƙi asarar ruwa, ko yayi ma kamar bai yi ba, blaki kalar dauɗa, su din ga yi suna tuntsura dariya. Ummi kuwa sai ta yi kamar ba ta ji ba, ta cigaba da sabgoginta, duk da a ƙasan zuciyarta kalaman na su na tasiri a cikin zuciyarta, tana jin babu daɗin cin mutuncin halittar ta da suke yi. Haka Maryam ma, kasancewar ta kyakykyawa, kullum ba ta da aiki sai bawa ummi labarin saurayinta kaza yayi mata kaza, ko ya bata abu kaza. Ba maryam kawai ba, ƴan ajinsu ba su da aiki, sai hirar samari, ita kuwa da ta san ba ta da kowa, ta rungumi litattafanta yadda yakamata. Idan suka so yin dariya kuwa, sai su yi ta zungurar ummi, suna tambayarta wai ita waye nata saurayin, ta gaya musu fari ne ko baƙi, dogo ko siriri. Kawai sai tayi murmushi ta yi musu shiru, taƙi kula su. Maryam ce ta fara bata shawara "Ummi, yakamata ko ɗan mayukan nan na zamani ki ɗan din ga shafawa, ko kema kya yi haske, maza ba sa son baƙar mace, ummi kin yi duhu da yawa, duk kwatancen baƙin da za ayi a makarantar nan da ke ake yi, idan ki ka shafa mai ki ka ɗan yi haske, ko yaya zaki samu saurayi, ko zaki ji daɗi duk mu yi aure mu bar ki? Ni fa mami ta ce ina candy aure za ayi mini, na cigaba da karatu a gidan mijina, amma ke kullum kin ƙi wayewa, ga uban hijjaban da ki ke sawa, ba kya kwalliya kamar mu, bayan hijjabi har da wani uban niƙab, to waye zai ce yana son ki, kalli ranar da muka je barkar gidan su Saratu, kowa yayi kwalliya amma ummi ke kin zunduma over size hijjab fisabilillahi. Ranar da babu school, ki zo gidanmu akwai wata mai mayukan gyaran jiki, muje ta haɗa miki mai sai na biya" Ummi shiru tayi tana ƙoƙarin haɗiye wani abu mai ɗacin gaske, da yake yi mata kai komo tsakanin maƙogwaronta da ƙirjinta, wannan shawara maryam take bata ko ci mata fuska. "Ina magana kin yi mini shiru" Maryam ta yi maganar a ɗan hasale, dan daga abun da maryam ta tsana a halin ummi bai wuce miskilanci da shariya ba. Wanda ba wai miskilancin bane kawai, tana gudun shiga harkar mutane, kar tayi wani abun da za aci mata mutunci. Ummi ta ɗago ta kalli maryam, hawaye har ya zagaye cikin fararen idanuwanta, ta ɗan juya brown ɗin ƙwayar idonta ta ce "Maryam, I won't bleach my skin, ko a so ni a haka, ko a ƙyale ni, banbancin fari da baƙi a wurin Allah, wanda yafi tsoronsa mu ƴan adam mune muke ɗorawa kanmu". Cikin ƙuluwa maryam ta ce "Au dan na baki shawara ina nema miki mafita, shine ki ke kuka, har ki ke nema ki kafirta ni? To ki ƙarata ummi, amma zaki ce na gaya miki, wallahi babu wanda zai aureki da wannan baƙin da gidadancin" Ummi tayi murmushi mai ciwo hawayen na zubowa ta ce "Ba ke ki ka fara faɗar haka ba maryam, an daɗe da gaya mini ba zan auru ba ni mummuna ce, dan haka ban sa aure a ka ba dama, nima na san maza farare suke so masu kyau, in dai ubangijina yana sona shikenan maryam" tayi maganar cikin sanyin halinta. Sai kuma jikin maryam yayi sanyi, ta ce "Am sorry please, ba ina nufin na ɓata miki rai ba ummi, mafita nake nema miki" Kawai ummi ta tashi ta bar ajin, domin kuwa an kaɗa ƙararrawar tashi. Kai tsaye gida ta nufa, tana tafe tana hawaye ta cikin niƙabinta. *** Babban mutum ne zaune mai cike da nutsuwa da kamala,kallo ɗaya zaka yi masa ka san a cikin hutu yake, falon da yake zaune kawai ya ƙawatu dai-dai gwargwado. A hankali yake zuƙar tea ɗin da yake hannunsa, yana kallon ƙatuwar plasma tv da ke manne a jikin bango, sai dai kana gani ka san ba kallon yake yi ba, zancen zuci yake yi. "Alhaji ya dai?" Wata mata tayi maganar tana ƙoƙarin zama a kusa da shi. "Bakomai" yayi maganar yana murmushi. "A'a da komai mana, zancen zuci ka ke yi, shekaru sun ja, yakamata a din ga rangwatawa kai, kar wani ciwon ya kama ka" Ya ajiye cup ɗin hannunsa ya ce "Da ciwo zai shigeni saboda tunani, da tuni ya shige ni hajiya. Lokaci yayi da yakamata na huta, huta nake buƙata amma ki duba ki ga haryanzu ban huta ba, ni nake fama da harkar kasuwancina, gaba ɗaya yaran nan basu saka komai a gaba sai shashasha. Na tara dukiya, suna ta bushashasha, gaba ɗaya babu hankali ko nutsuwa a cikinsu da zai tallafe ni yanzu, su karɓi ragamar kasuwancin ni na huta. Ko kartun kirki babu wanda ya tsaya ya kammala a cikinsu, duk da tarin kuɗin da na kashe musu da sun yi karatu, amma kalli duk shashanci suke yi, suna manya amma duk babu mai saiti a cikin su. Matan ne kawai nutsatsu a cikin su, su kuma duk matan wasu ne, ragamar babban kasuwanci irin wannan ma ai ba na mace bane ba. Jiki a sanyaye ta ce "Na sani Alhaji, ka yi haƙuri, ka ɗan ƙara musu lokaci, mu cigaba da addu'a, kuma a cigaba da jan su cikin harkar kasuwancin" "Eh su ƙarasa ni ba. Wane lokaci zan ƙara musu? Salim na da shekara talatin da ku san biyar, dukkansu babu yaro a cikinsu, wane lokaci zan basu banda wanda na basu a baya. Zan yanke hukuncin da nake ganin ya dace kawai". Ta ɗan gyara zamanta ta dube shi ta ce "Wane hukuncin kenan?" "Zaki gani idan na yanke" yayi maganar yana sauya channel da remote. *** Ummi kuwa tsaye take a gaban mudubin ɗakinta, tana ɗaure da zani kasancewar daga wanka ta fito, ta shiga ƙare wa kanta kallo a jikin madubin. Ta saki gashin nan a bayanta, ta din ga kallon ƙwayar idonta, da take brown sosai, cikin idon kuma fari ƙal, ta gangaro kan fatarta da take jiƙe da ruwa, baƙa mai ɗaukar ido. Ta kalli gashin ta, ta ɗan shafa shi a hankali, tana tambayar kanta wace irin halitta ce ita haka. Ita kanta ta san ba ta taɓa ganin mai irin halittarta ba, a ƙasar hausa duk wanda take haɗuwa da su, ba ta taɓa ganin mai irin gashin kanta da kuma ƙwayar idonta ba. A hankali ta murza fatar jikinta, tana tuna maganganun su kausar masu sosa rai, wai wankan baƙi asarar ruwa. Baƙar mace bolar maza, irinta kuma bolar da ko recycling ba za a iya yi ba. "Da gaske ba zan yi aure ba, saboda maza ba sa son baƙar mace mai duhu kamar ni? To haka zan cigaba da zama a gidan kamar baiwa? Ko kuma zasu mayar da ni ƙauye daga baya, saboda ban samu miji ba? Dama Iya ta ce babu wanda zai aureni, saboda munina. Idan ma na yi aure zai iya ƙara aure ya daina kula ni, saboda ni bani da kyau, to wa ma zai ce yana so na?. Ko dai maryam da gaske take hijjabin da nake sakawa, da kuma munina ba zai bari a aureni ba?" Ta dubi ƙirjinta, da tudunsu ya ɗaga sosai. Ta girgiza kai ta ce "Ni ba zan iya bari a ga jikina ba, kuma ba zan saɓawa Allah ba, idan na yi bleaching na raina halittar da yayi mini kenan. Ya bani lafiya bani da wani mummunan ciwo da yake hanani sukuni, sai jarrabawar rayuwa da tsananinta bai sanya na rabu da rai na ba" Istigfari ta hau yi, duk hawayen idonta ya kasa daina zuba. "Yaya ummi" ta jiyo muryar noor. Tayi saurin share hawayenta ta ce "Na'am ƴar gidan anty ummi" "Ki ɗora ni a kan mudubin na taɓa gashinki" Ummi ta yi murmushi, ta ɗora noor a kan mudubinta, noor ta saka hannu biyu ta kama gashin tana dariya. Can sai ta ƙurawa ummi ido, ta ce "Kuka ki ke yi?" Ummi ta girgiza kai ta ce "A'a mama". Noor ta kai hannunta ta shafo sauran hawayen ta ce "Kuka ki ke yi, maama ce ta dake ki? Ko su anty intee ne?" Ummi ta ce "A'a mura nake yi ne, zauna a kan katifata na saka kaya" tayi maganar tana ajiye noor a kan katifar. Noor ta din ga tsalle a kan katifar tana waƙe-waƙenta na yarinta. *** Iya da idris fa sun haɗu da wanda suka fi su tashanci, dan mussaman uwar hindu ta din ga tatsarsu kuɗi, wai hindu ba ta da lafiya, za a saya mata magani, yadda ake kula da kowacce mace mai ciki, dole a kula da Hindu, tun da da bai yi abun da yayi ba, da hindu ba ta samu ciki ba. Dama akuyancin sa ne ya hana su bashi hindu, dan haka tun da ya hilaceta ya ɓata ta dole ya kula da ita, saboda sun san ƴar su ba lalatacciya ba ce ba a baya. Yadda baban hindu yayi alƙawari, sai da ta haihu, ta haifi santaleleliyar jaririya, cibiya kawai aka yanke, aka naɗo jaririyar a zani, har da mahaifarta suka kai suka direwa Iya a tsakar ɗakinta, sai tsala ihu take yarinyar. Mutane kuma suka taru a gidan, ƙarshen tonon asirin dai da asiri ya tonu, domin kuwa rana tsaka ƙanwar babar hindu suka zo suka kawo jaririyar, sannan suka sanar da iya cewa, sun saka yara sun kama wani ƙaton rago da iya ke kiwo a waje, an kai shi can gidan za a yankawa mai jego bayan kwana bakwai na ƙauri an sakawa jaririya sunan Iya wato Hajara. Ayshercool 08081012143.     *CUTARWA!* *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* P19 FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK. https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends Masu neman free books ɗina, da free pages duk akwai a kan watpad account ɗina. Irinsu Abduljalal Wata kissar sai mata Wuta a masaƙa Cutarwa Ƙanwar maza Gaba da gabanta Aƙidata Ruɗin ƙuruciya Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata. 08081012143. And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link. https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels Ayshercool. PAID ADVERT!. Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi. Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku Oll types of Turaran wuta Sandal Halut Irik Difur Gab Gab Kajiji Habil Nabak Humra Kulakcha Dilke da kalta Kayan Garan jiki Muna turara Kaya Kujerar garan jiki Kannada Madarorin turare masu kamshi  Man garan gashi  Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702   08025453921 *TALLA!TALLA!TALLA!* *INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*. *BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU* *MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA* BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI. P19 Tun da Iya take, ba ta taɓa cin karo da tashin hankali irin na yau ba, gida ya cika da mutane, ana ta salallami, yayin da Idris ya kulle kansa a ɗaki ya kasa fitowa saboda kunya. Tabbas da yana da kuɗi babu abun da zai hana shi guduwa, kodayake yayan Hindu yayi masa kashedin muddin ya gudu sai ya ɗaure babansa. Yarinya ta din ga tsanyara ihu, a tsakiyar ɗakin Iya. Su kuma suka wanda suka kawota suka gama tijararsu da rashin mutunci, suka fice suka bar gidan. Iya ta ce a ɗauki ƴar a kai wa babar Idris, dan ita ba ta san ya za ta yi da jaririya ɗanyen goyo haka ba, ita ko nonon ma yanzu babu sun suɗe sai fata, dan haka sai dai uwarsa. Babar Idiris kuwa ta ce "Iya ke yakamata ki riƙe wannan ƴa ba ni ba, tun da dama sunanki suka sawa yarinyar, ba yadda ban yi ba na bawa yarona tarbiyar da ta dace, amma ki ka ƙi saboda yana da sunan mahaifinki, kin ɗau son duniya kin ɗora masa. Ko laifi yayi na yi masa faɗa, sai ki ci mini mutunci. Dan haka Iya ke zaki kashe wannan wutar, wallahi ki ka bani jaririya ban san yadda zan yi da ita ba". Cikin fusata Iya ta ce "Ni ki ke gayasa haka lami?" "Iya ba rashin kunya ba ce gaskiya ce, da kin bari na bawa ɗa na tarbiyya da haka ba ta faru ba". "Rufe mini baki, har wata tarbiyya ce da ke da zaki bawa wani? Ke ɗin a yaya ki ke? Ki zo ki ɗauke yarinyar nan ki san yadda zaki yi da ita" Lami ta ce "Ban gane ba iya, ni na yi mata cikin, wallahi ba zan ɗauka ba" "Lami uwata ce take faɗa kina faɗa?" Lami ta ce "Maganar gaskiya ce fa, in ɗauki ƴa in yi yaya da ita? Ta in da aka hau ta nan za a sauka ai" Iya ta ce "Rabu da ita, na san maganinta, yanzu abun da ya fi dacewa shi ne ka je, ka ce musu mun amince a ɗaura auren nan su karɓi ƴar nan. Amma wallahi Idiris ya cuce mu, ya janyo mana masifa da abun kunya, ga ragona da nake son sayarwa lokacin sallar layya, sun tafi da shi, ku san yadda zaku yi ku karɓo mini ragona". Ilyasu ya ce "Iya yanzu waye yake ta rago, muntuncinmu ya gama zubewa" Baban su Idris ya ce "Ina ga kawai mu je mu samu iyayen nata, ina sa'adatu ta zo ta yi wa yarinyar wanka, a saka mata sutura, mu je gidan su Hindun" Sa'adatu ta ce "Taɓ ƴar gaba da fatihar? Wallahi ba zan taɓa ƙazanta ba, sai dai uwarsa ta wanketa, haka kurum in taɓa masifa" Sakin baki Iya tayi tana cewa "Wai me yake damun matan nan ne? Ƙaddara ce fa, kowa zata iya faɗa a ka" Sa'adatu ta ce "A'a irin wannan ƙaddarar Allah ya tsayar da ita a kan wanda ta sama" Haka dai gida ya yamutse, kamar ayi yaƙi. Da ƙyar babar Idris ta yi wa yarinyar wanka. *** Yau lahadi, ummi sun yi hutun makarantar islamiyya, sai dai ta kasa zama wuri ɗaya ta hutawa ranta, dan kuwa ta san babu wanda ya bata wannan damar. Dan haka wuni tayi tana kaiwa tare da komowa, wurin yin kwalema da tsabtace ko ina na gidan. Tana sanye da dogon hijjabinta, da ya zame mata tamkar uniform, duk zafi ko sanyi, ko a cikin gida, da hijjbi take yawo, dan ko da ta fara ƙirgar dangi, tsananta rufe jikinta tayi, balle yanzu da take aji biyar na sakandare ta ƙara cika sosai. Dan idan tana girki, wuta ta sha kamo mata hijjabin, ko ta yi ɓarna a kitchen, farida ta ci mata mutunci, amma hakan bai sanya ta daina sawa ba. Hijjabin jikin nata ya sha jiki ya koɗe, sai dai kasancewar a goge yake, muninsa ya ragu. Tana mopping noor na biye da ita suna hira, ta saki jiki tana biyewa noor, suna shiririta. Ƙamshin turaren da ya cika falon ne, ya sanya ummi ɗaga kai, aikuwa tayi tozali da intee ta fito, sai taku take ɗaya-ɗaya. Ta sha doguwar rigar abaya, ƙamshin kansa ummi ta kasa tantance wane iri inteesar take yi. Tayi light make up, sai wani yatsuna fuska take yi. Ummi a ranta ta ce "Tubarkallah masha Allah, kyau yana in da yake" ba iya kyan da inteesar tayi ne ya burge ummi ba, doguwar rigar jikinta ma ta tafi da ita, ta ji ina ma ita ma tana da ita ta saka, taga ya zata yi a ciki, dogayen riguna irin haka suna burgeta". "Ke! Kalli gabanta kar ki kama mini kurwar ƴa" farida tayi maganar cikin tsawa. Ɗan zabura ummi tayi, ta cigaba da aikin gabanta. Kausar kuwa ta kwashe da dariya, yadda ummin ta ɗan shagala da kallon yayarta kamar shashasha. Farida ta yi murmushi ta ce "Farar mace.... Caraf kausar ta ce "Alkyabbar mata" "Farar mace kalar kyau, kalar babban gida da manyan motoci, kalar hutu da jin daɗi farar mace mowar mata" Inteesar kamar kanta ya fashe, saboda kirarin da mamanta ke yi mata. Ta dubi ummi ta ce "Baƙar mace borar gida". Farida ta amsa da "Idan ta samu mijin ba" "Idan ba ta samu ba kuma ta dauwwama ƴar wanke-wanke" Ummi tayi burus, ta cigaba da hirarta da noor, tana jin zuciyarta na wani irin zafi. Intee ta yamutsa fuska ta ce "Maama bari na je, ya kirani a waya, ya zo". "To shikenan, a kula sosai, a iya karairaya da jan hankali" "Kar ki damu maama, ammm ummi kin kammala girkin da na saki?" "Na gama" "Ok, ki shirya mini komai a tray, in the next few minutes ki kawo mana" Kallon ƙasan ido ummi tayi mata, ta yi mata girkin tarar saurayi, kuma ita za ta kai musu. Tayi ajiyar zuciya, tare da ɗan girgiza kanta. Farida ta ce "Ke ummi in tambayeki mana" Ummi ta ɗago tana kallonta. "Wai dan Allah ina babarki ne?" Ummi ta ɗan yi jimm, dan ba ta zaci wannan tambayar ba. "Ban san in da take ba" "Kamar yaya baki san in da take ba?" Ummi ta ce "Ai tun ranar da ta tafi, Iya ta hana a tafi da ni, ban sake ganinta ba, sau kusan uku ƴan uwanta na zuwa su tafi da ni, amma ta ƙi bayar da ni". "Kuma saboda rashin lissafi, ba ta sake neman in da ki ke ba, daga ita har ƴan uwanta, yau shekarar ki nawa a gidan nan, ko kare daga dangin majaifiyarki ba wanda ya nemi in da ki ke, wace irin uwa ce wannan? Ko suma ba sa buƙatar ki ne, an rasa mai riƙe ki, aka liƙa mana, anya babu lauje cikin naɗi a game da ke, ta hanyar aure aka same ki kowa yake gudunki?" Tuni idon ummi ya fara tara hawaye, cikin ƙoƙarin kare mahaifiyarta ta ce "Ai an ce ba ta da lafiya, tun da aka ƙwace ni, ta haihu ɗan babu rai, ta samu matsalar ƙwaƙwalwa" "Mahaukaciya ce kenan?" Kausar ta faɗa kai tsaye. Farida ta ce "To ai mahaukaci ya san ɗan sa, jahilci kawai da rashin sanin ciwon kai, idan ita ba ta da hankali, ƴan uwanta fa?" Ummi ta yi shiru, ta kasa magana. Farida ta shigo falon a fusace ta ce "Wai ke ummi me ki ke taƙama da shi ne? Cewa fa na yi ki kawo mana abinci, amma dan wulaƙanci kin shanya ni, bana son rashin mutunci" Ummi ta jingine mopper ba tare da ta ce komai ba, ta je ta ɗauki tray, ta kai wa saurayin intee. Kallo ɗaya ummi ta yi masa ta sunkuyar da kai, gaba ɗaya bai yi kalar mutane masu ɗa'a ba. Tunanin abun da farida ta faɗa ya ɗarsu a ran ummi, idan an ce mamanta ta samu matsalar ƙwaƙwalwa, to ƴan uwanta fa, yakamata ace sun nemeta, ta san da a hannunsu take, ba za su wahalar da ita sosai ba. Sakawa tayi a ranta a wannan karon idan kawu ya zo gida, za ta tuna masa alƙawarin da yayi mata na binciko maata in da mamanta take, dan ita ba ta taɓa jin ko sunan garinsu wani ya faɗa ba. *** Can gida gagarawa kuwa, an samu da ƙyar da siɗin goshi, su hindu sun karɓi jaririya, babanta ya ce idan ta yi arba'in, su zo su kawo kuɗin aure, kuma yadda ake auren budurwa komai da komai, haka za a haɗo mata, kuma shayarwa da hindu, za ta yi, sai an biyata kuɗin shayarwa ko su dawo musu da jaririyar. Kan su dawo gida, sai da babanta ya caje su kuɗi masu yawa, sannan suka dawo, suka sanar da Iya abun da babanta ya faɗa. Iya ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wannan wane irin matsiyatam mutane ne? Sai an yi mata komai kamar auren budurwa ba ta riga ta haihu ba, har wani kuɗin shyarwa suke nema, a gidan ubanwa aka taɓa haka, ai da an dawo da ƴar a din ga bata nonon akuya". "A'a iya, a samu a lallaɓa mu rabu da mutanen nan lafiya, kowa ya ɗebo da zafi ai bakinsa, gobe ba ya ƙara ba". Da labari ya iske idiris kuwa, masifa ya fara yi, yana baloƙoƙon shi fa ba ya son Hindu, ban da zalunci yarinyar da har haihuwa ta yi, tayaya za a ce wai ayi mata kaya kamar budurwa, saboda son zuciya. Cikin tsananin fusata mahaifinsa ya ce "Rufe mini baki, ko na turmushe ka a wurin, mara mutunci, muna zaman zamanmu ka janyo mana masifa, ka sanya kowa a tashin hankali, kuma wallahi ko ka so, ko ka ƙi sai ka auri yarinyar nan, ka ƙarata can bayan auren" yayi masa ta tas ya tafi ya bar shi. Magaji yayi murmushi ya ce "Allah sarki ummi, baiwar Allah yanzu idan na ce hakkinta ne ya fara bibiyarku, sai ace ƙarya ne a hayayyaƙo mini, da ka yi haƙuri da ummi, ka nema mata magani tsaf zata warke ku zauna lafiya, amma ka din ga muzanta ta, kana yamaɗiɗi da ita a kan larurar da ta same ta, har abokan ka suna ce maka angon ɗaɗɗoya saboda zunzurutun wulaƙanci da tozarci, ka saketa bayan ka gama azabtar da ita, saboda ka na taƙama da kai ɗan iska ne. Kai ma gashi Allah ya tozarta ka, gara nata tarihi zai iya shafe shi, naka kuwa har gaban abada ba zai goge ba, kuma kaɗan ka gani, ba dai bariki ba sai ma ka auro wannan ɗin, zaka san ka yi asarar mace". Duk wannan faɗan da magaji yake yi masa, bai iya cewa komai ba, saboda ya san ba shi da gaskiya, kuma yanzu yana cikin tashin hankali da tunanin menene mafita. *** Ummi tana ta dakon zuwan kawu, tare da fatan Ubangiji Allah ya sanya ya samo in da mama take, gara ta tattara ta koma can wurinta, dan da ta san in da take da ta daɗe da barin gidan nan, ko bola take bi za ta din ga bin ta. Sai da aka shafe kusan sati uku, sannan dr. Ya zo gida, bayan yayi kwana biyu ya ɗan nutsu ya huta, ummi ta same shi shikaɗai a falo, ta gaishe ta samu wuri ta zauna. "Ummana, ya aka yi ne?" "Dama ba wani abu bane kawu, dama tambayarka zan yi ko ka gano in da maman take?" Tayi maganar kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta. Ya ɗan yi shiru yana nazarin ta, sannan ya ce "Akwai matsala ne?" Ta girgiza masa kai alamar a'a. "Na san ba zaki faɗa ba dama, rabonki da yi mini wannan zancen an kwana biyu, na san a takure ki ke ummi, amma ki yi haƙuri, ina nan ina ta ƙoƙari a kai, ba yadda ban yi da Iya ba, ta ce mini ita ba ta sani ba. Ƙanin babanmu da yayi masa walicci ma ya rasu, su ilyasu sun ce basu san sunan garin ba, su dai kawai an zo da mota an kai su, na san faɗa kawai suke yi, Iya ce ta hana su faɗa. Amma ina nan ina ta bincike, ina da hotunanta biyu, da aka yi mana bayan bikin da na je gida, ina ta bincikawa, na samo sunan garin, ainihin yankin da take a garin ne ban sani ba, ana ta bincikawa ummi, ina sane ban manta ba, ki cigaba da addu'a da kula da karatunki, komai zai warware in sha Allah". Ummi ta risuna ta ce "Na gode sosai da sosai Allah ya saka da alkhairi". Ya ce "Amin ummana, baki ce Allah ya yi mini albarka ba" Rufe fuska ummi tayi tana murmushi. Ya ɗora da cewa "Kwanaki an ce mini ɗan uwan mamanki ya zo ganinki, Iya taƙi gaya masa in da ki ke, ta ci mutuncin sa ya tafi. Amma dai in sha Allah ina nan ina ƙoƙari a kai". "To kawu na gode" Ta tashi ta nufi ɗakinta, tana sake jinjina ƙiyayyar da Iya take yi wa mahaifiyarta da ƴan uwanta. Kasancewar maryam gaba take da ummi dama, dan haka ta riga ummi candy, tun kan ta yi candy aka kawo kuɗin aurenta, dan haka an yi candy babu daɗewa bikin ya tinkaro. Maryam ba ta tsaya saurarar ummi ba, ta sayi anko ta bawa ummi duk kyauta, sai dai da ƙyar farida ta bar ummi ta je rana ɗaya bikin, shi ma da ta je kasa sakewa tayi, dan wareta ƴan makarantar ma suka din ga yi, dan haka nan da nan ta koma gida ta bar wurin. Satin Maryam biyu a gidanta, mijin ya tafi da ita can wurin aikinsa, kasancewar soja ne babba. *** Kwanci tashi asarar mai rai, iyayen hindu suka din ga tatsar su Iya kuɗi, har sai da ta yi watanni shida cif a gida, sannan aka ɗaura auren Idris da hindu, saboda babanta dagewa yayi a kan sai an kai kuɗin aure da duk wani abu na al'ada da ake yi. Tare da cigaba da yi musu barazanar cewa, zasu dawo musu da ƴar su. Abun kunya dai da ake gudu, ya riga ya gama watsuwa a cikin gagarawa, na abun kunyar da jikan Iya ya tabka. Gidan da ummi ta zauna, aka sake kama haya, kansancewar ba kowa a ciki, aka ƙara gyara gidan, aka kai hindu da jaririyarta. Ko kallo hindu ba ta ishi idris ba, haka ita ma ba ta kansa ta bi ba, ta cigaba da sabgoginta da ƴar ta, sai dai cikin dare yarinyar nan ta tashi, ta din ga tsala ihu kamar za ta shiɗe. A fusace ya tashi ya ce "Dalla malama ki ɗauki ƴar ki saka tayi shiru, ta cika wa mutane kunne da kukan banza". "To kai mai zai hana ka saka tayi shirun, na ga kaima ƴar ka ce" "Ƴar gaba da fatihar? Kar ki sake haɗani da ita". "Ko ƴar gaba da meye uban waye yayi cikinta, ai ba ita tayi kanta ba, ka ga wallahi ka ce zaka takura mini, ko ka ɗaga mini hankali sai na koma gida na gaya musu. Kai ba ma ka da kunya, ni ka ke gayawa ƴar gaba da fatiha ce, uban waye ya lalata ni?". "Iyayenki dai suka ja miki, da ba aurenki zan yi ba, suka hana ni". Hindu ta yi shewa ta ce "To uban wa ye zai baka auren ƴa? Kana ɗan iska?" "Eh ina ɗan iskan amma ai gashi an liƙa mini ke" "Oho kai ka sani dai" Ta dubi ƴar da ke ta tsala ihu ta ce "Ke hajara tsohuwar banza, ubanki ya ce ki yi masa shiru, ƴar gaba da fatiha" Idiris ya ce "Tsohuwar banza, kakata ki ke zagi kenan?" "Eh to, idan ka tsargu hakan ne" haka suka din ga faɗa kamar kaji, a tsakiyar daren nan maƙwabta na jin su. Abdul ne yayi sallama a kitchen, ummi na girki, suna ta tilawar Alqur'ani ita da noor. Raino ummi take yi wa noor da kulawa, bacci ne kawai yake raba su, baccin ma wataran a ɗakinta take yi. Tun kan noor ta shiga makaranta, ta iya azkar da karatun Alqur'ani, dan ba ta yi pre nursery ba, kai tsaye nursery 1 aka kaita, saboda ta har rubutu ta fara iyawa. Sai dai noor masifaffiya ce, ba ta taɓuwa a wurin yayyenta, dan baki ne da ita sosai da sosai. Ba ta jin maganar farida, kamar yadda take jin maganar ummi, fitsara da rashin kunya kuwa ba a magana, ummi da Abdul kawai take ɗagawa ƙafa, ƴar mitsitsiya da ita ga azabar taurin kai, ummi ce kawai take iya sarrafa ta yadda take so, dan haka ba wani shiga shirgin noor suke yi ba, tayi maka rashin kunya ka jibgeta ba za ta yi kuka ba. Ummi tayi ta mata faɗa, dan ita kanta tana mamakin rashin kunyar noor. "Yaya ummi" Abdul ya kira sunanta. Cikin haɗa baki ita da noor suka ce "Na'am yaya Abdul" Abdul ya tsuke fuska ya ce "Da ke nake?" Ta girgiza masa kai tana ɗan murguɗa baki. Ummi ta kalli Abdul ta ce "Yaya Abdul yaya ake ciki? Ka dubo mini" Ya miƙo mata envelope ya ce "Eh to, congratulations you got nine credits including maths and English, i know you can do it ai" A take ummi tayi sujjadar godiya ga Allah, noor ma ta durƙusa tayi, ummi ta ɗago tana Alhamdilillah. Noor ta ce "Wai menene? Me aka yi?" Abdul ya ce "Yaya ummi ta ci jarrabawa, dan haka ita ma very soon zata shiga jami'a" Tsalle noor ta din ga yi tana ihu, ba tare da ta san ma menene cikakken bayanin ba. Kausar ta shigo kitchen ɗin tana tambayar lafiya. Noor ta ce "Yaya ummi ta ci jarrabawa, za ta shiga jami'a". Tsaki kausar ta yi ta ce "Shi ne kuma ki ke yi mana ihu?" "Eh ɗin, yeeee yaya ummi ta ci jarrabawa " tayi maganar tana tsalle ta fita daga kitchen ɗin. Kausar ta yi tsaki ta fice, Abdul ya ce "Yaya Ummi, kina zaune an haifi mai tare miki faɗa" Ummi ta ce "Ni mamana saliha ce, amma mama ƙarama ta fiye tsiwa" suka yi dariya, ummi na sake godewa Allah a kan wannan gagarumar nasara da ta samu. Takanas saboda ummi dr. Ya dawo gari, saboda shirye-shiryen nema mata admission, Abdul yana level 2 a BUK yana karantar Agric. "Dr. Wai ya na ganka a gida a tsakiyar sati haka? Kuma na ga baka daɗe da tafiya ba". "Abdul yayi mini magana a kan waec ɗin ummi, ina son in ƙarasa mata abubuwan da yakamata kar ayi mini ba dai-dai ba". "Shi ne ba zaka wakilta wani ba, sai ka dawo da kanka?" "Ki na da damuwa da hakan ne?". Haushi ne yakamata tayi masa banza, duk iya ƙoƙarin ta a kan cire hankalinsa daga kan ummi, ta kasa nasara ɗari bisa ɗari. Ta sake kallonsa ta ce "Wai ni dr. Zuwa yaushe zan cigaba da jerawa da ummi a gidan nan, intee tana gama secondary, nake son a aurar da ita, yaron ya matsa, ita kuma tana nan shirin tafiya jami'a ma take yi, gaskiya ina son privacy a gidana, ba zan cigaba da jerawa da gandamemiyar budurwa ba". "Intee ke ki ka takura a karɓi kuɗin aurenta, ba dole na yi muku ba, ni kuma a ƙyale mini ƴa tayi karatu. Guda nawa ummin take da ki ke wani zancen gandamemiyar budurwa, yanzu fa za ta shiga jami'ar". "To wai ina uwarta, a mayar da ita wurinta mana". A fusace ya ce "Wai a kan ki ummin nan take ne?". Muryar noor ce ta katse shi, tun daga wajen ɗakin take ƙwala masa kira. Ya ce "Na'am shalelena" "Kalli littafina, uncle ya saka mini 10 over 10, assignment ɗin da anty ummi ta koya mini". Ya ce "Wow masha Allah, congratulations baby". "Thank you " ta faɗa cikin iyayi sannan ta ce "To nima tunda na ci jarrabawar, zan shiga University?" Ya kwashe da dariya ya ce "From primary one to university?" "Eh, ba anty ummi ma ta ci jarrabawa zata shiga university ba?" Yayi dariya, ya biye mata ta gama shirmen ta, ta tafi, sannan ya kalli farida ya ce "Farida wai zuwa yaushe zaki daina planing ɗin nan, noor tayi girma yakamata ace kin sake haihuwa, 4yrs fa". Farida ta yamutsa fuska ta ce "Nifa na gama haihuwa, yaushe Allah ya amfana guda huɗun". "Amma da bani da yadda zan yi na riƙe ne, sai ki faɗi haka, Allah ya yassare mini yadda zan kula da yarana, meyasa zaki ce kin daina haihuwa?". Ta miƙe tsaye ta ce "Ka auri ummi ta haifa maka!". Wani irin damm ƙirjinsa yayi, ya bita da kallo, saboda munin maganar da ta faɗa. Ya girgiza kai kawai, domin ba shi da abun da zai faɗa gaba ɗaya. Iya ƙoƙari kawu yahaya ya yi wa ummi, a kan harkar makarantar ta, dan ma farida na ta yi mata mugunta a kan wasu abubuwan. Yayi mata komai sai dai ɓangaren sutura ummi na fuskantar barazana, domin kuwa ummi ba ta da suturar kirki, duk da ma'abociyar hijjabai ce, su kansu hijjaban nata duk sun mutu su yi haske. (Kowane ƙalubale ummi za ta fuskanta a jami'a? Bright pens na godiya sosai 🙏) Whats app only please. Ayshercool 08081012143    *CUTARWA!* *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* P20 FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK. https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends Masu neman free books ɗina, da free pages duk akwai a kan watpad account ɗina. Irinsu Abduljalal Wata kissar sai mata Wuta a masaƙa Cutarwa Ƙanwar maza Gaba da gabanta Aƙidata Ruɗin ƙuruciya Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata. 08081012143. And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link. https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels Ayshercool. PAID ADVERT!. Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi. Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku Oll types of Turaran wuta Sandal Halut Irik Difur Gab Gab Kajiji Habil Nabak Humra Kulakcha Dilke da kalta Kayan Garan jiki Muna turara Kaya Kujerar garan jiki Kannada Madarorin turare masu kamshi  Man garan gashi  Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702   08025453921 *TALLA!TALLA!TALLA!* *INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*. *BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU* *MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA* BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI. 20 Ummi ganin al'amuran take yi kamar a mafarki, duk da tsanani da matsi, haɗi da ƙalubale daban-daban yau ga ta a makarantar jami'a, lallai lokaci yana sauri. Hakazalika ta na ta shirye-shiryen haɗa saukarta ta biyu, domin kuwa bayan ta yi sauka ta cigaba da zuwa makaranta, ƴan ajinsu galibi duk sun yi aure, dama duk sun girme mata. Wuri ɗaya ta samu ta zauna a ajin, jikin window ne in da take, hakan ya bata damar kallon shige da ficen ɗalibai, tsofaffi wanda sun kusa fita ma, da masu rawar kai wanda yanzu suka shigo jami'a. Shigowar wani babban mutum ajin ne ya sanya ɗaliban ajin nutsuwa, tare da gaida mutumin. Ya amsa musu, tare da gabatar da kansa a matsayin HOD ɗin su, ya nemi da kowanne daga cikin ɗaliban, ya tashi ya gabatar da sunansa da kuma garin da yake. Haka nan gaban ummi ya faɗi, dan kuwa ba ta son mutane, da duk wani dalili da zai sanya a takurata da kallo. Ɗalibai suka din ga gabatar da kansu ɗaya bayan ɗaya, kan azo kan ummi gaba ɗaya jikinta yayi sanyi, sai wata irin fargaba take yi. Da ƙyar ta iya miƙewa tsaye, fuskarta sanye da facemask, malamin yayi mata alama da ta sauke facemask ɗin. Gabanta ya sake faɗuwa a karo na biyu, hannunta har rawa yake yi, ta sauke facemask ɗin tana jiran jin ƙanan magana kamar yadda ta saba, sai dai ba ta ji hakan ba. Sai dai ta kasa magana, sai da ta ɗan sauke numfashi, sannan ta ce "My name is.... Sai dai ta kasa ƙarasawa, saboda yadda gaba ɗaliban suka juyo suna kallonta. Ummi na da murya mai matuƙar ɗaukar hankali, duk wanda bai santa ba, idan har tayi magana dole zai waiwaya domin ganin mai muryar. Ko a islamiyya idan ana musaffa, Alla-Alla suke yi a zo kan ummi, saboda ta iya ƙira'a mai daɗin sauraro. Ganin ta diririce saboda kallon da ake yi mata ne ya sanya malamin takowa zuwa gabanta, ta ko ƙara sunkuyar da kanta ƙasa, tare da wasa da yatsun hannunta a cikin hijjabinta. "Kin manta sunan naki ne?" Ta girgiza masa kai. Ya sake cewa "Ko ba turanci ne?" Nan ma ta sake girgiza masa kai. "Oya ya sunanki?" "Salma Muhammad Bashir" Yayi murmushi ya ce "What a beautiful name, na ga duk a tsorace ki ke, but mark you, this is university idan malamai suka gane kina jin tsoron magana a public, za su yi ta takura miki da tambaya, ke kina jin tsoron amma ki ka zaɓi aikin jarida? Ai harkar jarida na masu baki ne. But you can do it when you overcome your fear" Ta ɗago a hankali ta ce "Thank you sir" "Ƴar wace ƙasar ce ke?" "Jigawa" tayi maganar muryarta na ɗan rawa. "Ƙasa fa" Ta ce "Au Nigeria" "Are you sure? Ko dai ta ɓarauniyar hanya ki ka shigo mana ƙasa? Kin yi kama da baƙaƙen larabawan Afrika" Ummi a ranta ta ce 'Amma kuwa an cuci larabawa, ko kuma ni aka cuta, maybe ba'a yake yi mini' Ƴan ajin kuwa dariya suka hau yi, ya ce "Kalar idonta da complexion ɗin ta, ba irin na ƴan Nigeria bane, dan haka zamu bincika idan baki da lasisin zama a Nigeria mu mayar da ke ƙasarku" yayi maganar cikin zolaya. A dole ummi ta ƙaƙalo murmushi. Ya ce "Yi zamanki, Allah ya yi albarka" kan ta zauna ta risuna ta ce "Na gode sosai Allah ya jiƙan magabata" ya ɗan ƙurawa ummi ido, yadda take amsa masa magana ma, kawai ya isa ka gane tana da tarbiyya sosai. Ya ce "Amin" sannan ya suce gaba. Yayi musu nasiha sosai da sosai, a kan kula da ilimi da kuma tarbiyarsu, da ba su shawarar su riƙe addinansu, kar su lalace saboda kawai sun ga sun shiga jami'a. Kowa harkarsa yake ba ruwan wani da wani, dan haka ummi ta ji daɗin hakan, da babu wanda ya matseta balle ya takura mata. Baki har kunne ta koma gida tana murna, duk da tana zuwa gidan ta tarar da uban kwanukan wanke-wanke, da wankin kaya, kuma an cinye abinci tas, kuma ana jiran ta ɗora na dare. Hijjabi kawai ta canza ta hau aiki, noor ta din ga bin ta, tana tambayarta "Anty, kin yi magana a gidan radiyon?" Ummi ta ce "A'a mamana, sai an kwana biyu tukuna" "To ta ina zaki din ga shiga radion kiyi magana?" Sai dare yayi kin yi bacci, zan buɗe gurin batirin in shiga ta ciki. Noor ta buɗe baki cikin mamaki, sannan ta ce "To zaki shiga da ni nima?" "Sai kin ƙara girma sosai tukuna, noor ta dinga tsalle tana murna. *** "Bilki, ki kira Bauchi ki gaya musu ba fa haka muka yi da su ba, ni fa ba bar musu ɗa na na yi ba, haba sun riƙe mini ɗa ko leƙo ni baya yi". Ta kalleshi ta ce "Taɓ, ba ruwana kun fi kusa, ka kira su ka gaya musu mana" Yayi murmushi ya ce "Shima zan gamu da shi ne, ko a waya baya nema na" Ta ɗan yi murmushi ta ce "Wai ɗazu da ina bacci, da wa ka ke magana ne, ka ke ta faɗa?" Ya ɗan ja guntun tsaki ya ce "Salim mana, wai zuwa yayi na bashi kuɗi zai yi gyaran mota". "To meyasa ba ka bashi ba?" "A kan me zan bashi? Duk iya ƙoƙarin da zan yi na yi wa yaran nan, dan su zama na gari, amma abu ya gagara. Yanzu daga shi har ɗan uwansa da a nutse suke, da yanzu yaushe zan din ga wannan zirga-zirgar?" Bilki ta ɗan yi ajiyar zuciya ta taɓe baki ta ce "Laifin babarsu ne, da ta bari suka lalace". Yayi saurin girgiza kai ya ce "No, Hajiya na iya ƙoƙarin ta a kan tarbiyyar yara, dan har ta fiki tsanantawa ma wasu lokutan" Ta tsuke fuska ta ce "Eh, nice mai sake da tarbiyya kenan?" "A'a mai gado ba haka nake nufi ba, ai kin ga matan duk lafiya ƙalau, gashi duk sun yi aurensu suna zaune lafiya, su ɗin ne dai, kuma shima na san jarrabawa ce, ba a barin ɗan Adam haka". "Allah ya kyauta, amma nikam ba zan bari auta ya riƙa ba yazo na kasa contrilling ɗin sa ba, aure zan yi masa yana dawowa" "To hakan ma yana da kyau, Allah ya zaɓa abun da ya fi alkhairi mai gadon zinari" yayi maganar yana jan hancinta. "Ba wata mai gadon zinari, ka koma wurin dattijuwar matarka" Kwashewa yayi da dariya, ya ce "Bilkisu, hajiyan ce dattijuwa Allah ya sa ta ji ki, ai shekarunta ba sa nunawa, saboda gayunta, kuma ni bana ganin girmanta, ba ta fi fifty fihe ba, amma idan ta ɗaura ɗankwali kamar ƴar 30yrs. Ai da yake ni na mayar da ita tsohuwar, ganinta nake kamar ƴar 16 lokacin da na aurota, hajiya ba ta tsufa" Wani irin haushi ya kama bilkisu, ta yinƙura za ta tashi ta bar masa wurin, ya riƙeta yana dariya ya ce "Danne kishin nan kar ki bari ya fito". Alhaji Tahir kenan, tsohon ɗan boko, kuma babban ɗan kasuwa, da yake juya naira yadda yake so. Mutum ne mai sauƙin kai da matuƙar son iyalinsa, mussaman ƴaƴansa, dan mutum ne mai biyewa ra'ayin yaransa, duk abun da suke so muddin bai saɓawa addini ba, zai yi musu shi, yana bawa iyalansa ƴancin yin abun da suke so, ba tare da ya takaura musu ba. *** Rashin wayar hannu, yana daga manyan abubuwan da suka zama barazana ga ummi, a harkar karatunta, gashi ita ba kowa take raɓs ba, balle idan an bayar da assignment ko class work tayi, idan assignment ne ta gwammace ta kai yamma a makaranta, ta je Library ta yi. Gashi farida ta tsiro da sababbun hanyoyin muzguna mata, ta hanyar ƙirƙirar mata abun da za ta sanya ta makara, wataran har ma ta rasa lectures baki ɗaya. Daga baya ne take iya roƙon Abdul aron wayarsa, tayi assignment da ita. Abdul ne ya gaya wa dr. Yakamata a saya wa ummi waya, saboda makaranta. Da ya tashi dawowa ya taho mata da sabuwar waya, mai kyau da tsada, amma farida ta ƙwace ta bawa kausar, kuma ya kasa magana a kai. Ba waya kawai ba, hatta undeas ummi na fuskantar matsala a kan su, sai dai idan ta tara ƴan kuɗi da ƙyar, idan farida ta aiketa kasuwa ta sai na gwanjo. Daga baya Abdul ya saya mata wata ƴar ƙaramar waya, gionee take amfani da ita. Makaranta ma da nata irin ƙalubalen, domin kuwa ƴan ajinsu, akwai yaran masu kuɗi, akwai ƴan ƙarya da yaran talakawa masu jin cewa su wasu ne. Gani suke ummi ba tsararsu ba ce da za su yi mu'amala da ita, mussaman ganinta babu suturar kirki, kullum cikin hijjabi, hijjaban nata da guda biyu ne take zuwa da su, sai takalminta ɗaya ɗan wambai. Banda masu zunɗen halittar ta, ko tambaya za ayi a aji, idan za a tanbayeta, sai malami ya  ce dark skin girl. Ummi ta sanya a ranta babu wani ƙalubale, da zai sanya ta kasa haƙuri ta cimma burinta. Yunwa da tafiyar ƙafa a kan karatun nan suka zamewa ummi jiki, ko lissafasu ba ta yi a cikin wahalar rayuwa, handout kuwa ba kowanne take iya saya ba, wataran idan har zata sayi handout, sai ta yi trecking, domin samun kuɗin sayen handout. Ta wuni a makaranta ba cin abinci, ta koma gida ta ci uban aiki, a ƙarshe ba godiya sai zagi da muzantawa. HOD kuwa ba ƙaramin mutunta ummi yake yi ba, saboda idan ta ganshi sai ta kai ƙasa take gaishe shi, idan ta ganshi da jaka, sai ta bishi ta karɓa. Yana jinjinawa tarbiyyar ta, da bayar da misali da ita, dan shi rabon da yaga ɗalibi mai biyayyarta tun a zamaninsu, shima zamanin na su ba kowa ba. Ummi ta dawo daga masallacin makaranta, tana ta sauri ta ƙarasa aji, saboda malamin da zai shiga, ko da minti ɗaya ya rigaka shiga aji, ba zaka shiga ba. Abun da kunnuwanta suka jiyo mata wani ɗan ajinsu ya faɗa ne ya tayar mata da hankali matuƙa. "Kai ishaƙ, ka yi sauri mu tafi kar malamin nan ya rigamu shiga, ga gorillar ajinmu can na ta sauri". Kalmar gorilla! Ta daki ƙirjin ummi, hakan ya haifar mata da wata irin mutuwar jiki, munin nata har ya kai a kira ta da gorilla? Zuciyarta ta din ga bugawa da sauri-sauri, tamkar zata kifa ƙasa ta shiga ajinsu tana wani irin kuka, wane irin abu ne wannan?. Ishaq ya kalli abokinsa ya ce "Kai Nura kamar fa ta ji ka" "Ahha haba dai?" "Tana kusa fa ka faɗa" Nura yayi tsaki ya ce "To sai me?". Ishaq ya ce "A'a nura, zuciya ba ta da ƙashi, cin fuska ba shi da daɗi, tuntuni na gaya maka ka daina kamanta ta da dabba, yarinyar so silent ba ruwanta da kowa bai kamata ba wallahi" "Ka ga kar ka isheni, jokes ne" "Ai gaskiya ce, ba wani jokes wallahi, ko kusa yarinyar nan ba ta yi kama da abun da ka ke misalta ta ba, hidden beauty ne da ita, baƙinta da rashin gayu ke hana kyanta fitowa, amma ba ta yi kama da abun da ka ke faɗa ba". Suka tafi aji, yana ta yi masa faɗa, suna shiga aji kuwa, kan ummi a ƙasa da alama kuka take yi. Gaba ɗaya jikin Ishaq yayi sanyi ya ce "Ka gani ko? Kuka take wallahi". Shigowar malamin ya sa kowa ya nemi wuri ya zauna, ya fara gabatar da abun da ya kawo shi. Sai dai yana lectures yana ganin yadda ummi ke sharɓar hawaye. "Ke are you ok? Meyake damunki ne?" Ta kasa magana ta tashi tsaye tsam, ta ɗauki jakarta cikin kuka ta ce "Sir dan Allah ka bani iznin tafiya gida" Duk da zafin malamin da rashin son wargi, amma kukan da ummi take yi, yana nuna akwai tsantsar damuwa a zuciyarta. Kamar yadda ake son malami ya kasance cikin kulawa ya ce "Babu damuwa, amma zaki iya tafiya? Ko ki na da ƙawa ta raka ki gidan?" Ta girgiza masa kai ta ce "Zan iya tafiya" "Kin tabbata?" Ta jinjina masa kai alamar eh. Ya ce "To shikenan, ki tafi a hankali ki yi ta Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ta jinjina masa kai ta risuna masa ta yi masa godiya sannan ta fice ta tafi gida. Ta daɗe ba ta yi kuka mai yawan na yau ba, tun noor tana rarrashinta, har ita ma ta fara kukan. Ta rarrashi noor, ta aiketa kitchen, ta mayar da ƙofar ɗakin ta rufe, ranar ba irin bugun da farida ba ta yi ba, a kan ummi ta buɗe ta zo ta yi mata aiki, amma mursisi taƙi buɗewa abun za ba ta taɓa yi ba kenan. Ta san ƙarshen abun dai, zagi ne za ta sha shi da cin mutunci a wurin farida. Tayi shiru tana tunani kala-kala a zuciyarta "Ko zan ji daɗi a rayuwata? Ko zan huta, ko kuma a haka zan cigaba da rayuwa, sanin gaibu sai Allah. Idan ina da rabon hutawa da jin daɗi, Allah ka kawo mini su da wuri, ba dan na gajiya da karɓar jarrabawar ka ba, ni'imominka gareni sun ninka jarrabawar, Allah ka shiga lamarina" tayi maganar a bayyane cikin kuka Sai da ta jera kwana biyu ba ta je makarantar nan ba, ranar da ta je, malamin da a period ɗin sa ta tafi gida, ya kirata ofishin HOD, suka din ga tambayar ta meyake damunta, dan malamai da yawa sun fuskanci kamar tana da social fear. Kukan da ta kasa riƙewa a gaban su, ya tabbattar musu da tana da damuwa sosai da sosai. Duk yadda suka matsa ta, ba ta gaya musu abubuwan da suke damunta ba, duk da tana da abubuwa da dama a ranta, da take son tattauna shi da wani, amma ta kasa samun wanda zuciyarta za ta nutsu da shi, su tattauna sosai, ko ba ayi mata maganin damuwar ba, atleast ta furta abun da yake damunta. Suka nemi zasu zauna da mahaifinta, amma ta din ga yi musu magiya, a kan kar su yi hakan, dan a ganinta idan aka yi hakan tamkar ƙure babanta kawu yahaya ne, domin kuwa yana iya ƙoƙarin sa a kanta. Nasiha suka din ga yi wa ummi, tare da bata ƙwarin gwiwa, a kan muhimmancin mayar da hankali a kan karatunta, da shanye ƙalubale, wanda ba ƙaramin jin daɗin nasihar ta su yi ba. A ƙarshe HOD ya cigaba da tsokanar ta, da cewar ba ta da visa baƙar balarabiya ce ta shigo musu ƙasa. Ɗaya malamin yake ce mata, tun da ƴar jarida ce ita, kuma an san su da neman suna, idan ta mutu yana son idonta zai saya da tsada, ta shiga kundin tarihi. HOD ya ce "Allah ya kiyaye, wannan idon na larabawa ne a Nigeria Masha Allah, in dai wannan tarihin ne mun yafe, ko Salma" Ummi ta sunkuyar da kai tana murmushi. Ummi ta ji daɗin mutuntawar da malaman da take wa kallon iyaye suka yi mata, da nuna damuwarta kamar ta su, nasihohin su, sun shige ta sosai da sosai. HOD yaje ajin su ummi, ya yi musu jirwaye mai kamar wanka, ta hanyar gugar zana a kan wulaƙanta ɗan Adam, da muhimmancin girmama ɗan Adam. Ta samu sassauci daga jin wani abu mai nauyi da yake damun zuciyar ta. Sai dai ta kasa manta kalmar gorilla, noor da Abdul suna falo suna kallon film ɗin king Kong, ummi har ta wuce ta dawo, ta ce "Yaya Abdul" Ya ɗaga kai ya ce "Na'am yaya ummi" "Dan Allah wai ina kama da gorilla?" Wani irin banzan kallo yayi mata ya ce "Wace irin magana ce wannan?" Cikin son ɓoye abun da ya faru ta ce "Amm, dama kawai na tambaya ne, dan na ji ana cewa ni mummuna ce" "Kuma sai ki haɗa kanki da biri, haba ummi, ke tsakani da Allah idan aka ce ke mummuna ce sai ki yarda? Ki ƙarewa kanki kallo, a kan me zaki yadda ke mummuna ce? A halittar Allah babu mummuna, duk wanda ya ce miki mummuna ki ce ubansa ya sassaƙo kamar ki" Noor ta ce "Maama kenan za a gayawa, itama tana cewa yaya ummi mummuna, kuma fa yaya ummi gashinta har nan, tafi fa maama gashi" "Tashi ki bar nan wurin kan na tatsileki, baba suda" yayi maganar yana kallon noor. Ummi kuma ta ce "To shikenan yaya Abdul, na gode sosai " "Dan Allah kar ki kuma faɗar haka " "Ba zan sake ba in sha Allah" sai dai a ranta tana jin har ta mutu ba zata manta da Nura ba, ya shiga cikin jerin mutanen da take yi wa wani irin kallo a zuciyarta. Ƴan ajinsu ummi ba su tashi mamaki ba, sai da result ya fito na first semester, ummi ta ja magana, GPA ɗin ta 4, wanda kaf ajin babu mai wannan grade ɗin. Kasancewar ɗabi'a ce ta ɗan adam, mu'amala domin cikar muradi, ya sanya suka fara lallaɓowa, domin shiga jikin ummi, amma fafur taƙi ta cigaba da rayuwar kaɗaici. *** Gidan Idris kuwa, kamar masu zaman bariki, saboda faɗa zagi yana zagin hindu tana ramawa, tana kiran sunan uwarsa da ubansa tana zagi, idan yayi gangancin dukanta kuwa, ta dinga wawurar abubuwa tana kwaɗa masa kenan, dambe da zage-zage har ƙofar gida kamar dabbobi, maƙwabta suna raba su. Sulhu kuwa an yi musu shi babu adadi, amma abu ya ci tura. Sam ba ta ganinsa da mutunci, shi ma kuma haka, taje gidansu ta gaida Iyayensa kuwa ba ta wannan, saboda ta ce ba zata je gaida tsohuwar banza ba, ta ji labarin zaman da yayi da matarsa ƴar uwassa, ita ba zata lamunci cin zarafi ba. Ya gaji da iskancinta, ya kamata yayi mata tulus da duka, ashe tana da juna biyu, ta yanke jiki ta faɗi, ƙarshe dai sai da iyayenta suka rufe Idris a police station, aka wulaƙanta shi aka kai ruwa rana kafin a sake shi, banda kuɗin magani da aka saka ya biya. Kwana biyu da dawowar sa daga hannun ƴan sanda, ya je ya samu hashim a kan ya bashi shawara, so yake a lallaɓa kawu yahaya da ummi, a dawo da auren su. Hashim ya ce "Haba Idris, lokacin da na din ga ankarar da kai ai kasa ganewa kayi, ummi tafi ƙarfin ka yanzu, wace irin azaba ce ba ka yi mata ba, tun tana ƙaramar yarinya. Yanzu ta sauke Alqur'ani har sau biyu, ta shiga jami'a tana karatu, ka ce ta dawo, to tayi maka me? Kai da ko kwalin sakandare baka da shi". Idris ya waro ido ya ce "Ummin ce a jami'a, kai waye ya gaya maka?". Hashim ya ce "Muna waya da ita, bautar ƙasa nake son na gama, idan Allah ya sa na samu aiki, zan nemi auren ummi". Idiris yayi masa wani mugun kallo ya ce "Amma dai ka ci kai, matar da na saki zaka aura? Bazawara ce fa kai kuma baka taɓa aure ba. Haryanzu bana son ummi, ban taɓa jin ƙaunarta a raina ba, amma ina da muradi a kanta, idan har ba ta dawo mini ba, idan ina raye baka isa ka aureta ba". Hashim ya yi murmushi ya ce "Zamu gani ai" Idris ya tashi fuuuu ya tafi. Idris yayi shiru yana tunani, tun da mahaifinsu ya takura masa da maganar aure, ya gaya masa ga ƙudurinsa, Iya ta ce bai isa ba, ba zai auri bazawar da ƙaninsa ya saki ba, kuma ta riga ta cire ummi daga jikokinta tun da ta ƙi yarda a rufawa Idiris asiri!. Babansa kuma ya ce Idan ya sake ɗaga maganar nan, zai yi masa abun da bai taɓa tsammani ba. Duk son ummi da islamiyya, haka ta haƙura, saboda yanayin makaranta, ta samu wata makarantar, a nan unguwarsu, take zuwa asabar da lahadi ɗaukar karatu. Sai dai ganin ummi tana da ilimin addini dai-dai gwargwado, idan aka yi mata ƙarin nata karatun, sai a haɗata da aji tayi musu ƙarin Alqur'ani da wasu litatafan. Duk da ayyuka sun ƙara yi mata yawa, hakan yayi mata, saboda tana zama busy sosai, tana hana zuciyarta tunane-tunane da sukan jefata cikin damuwa. Ga bikin Intee ya matso kusa, sai gori take sha a gidan nan, wai ta zama guzuma, babu mashinshini a haka za ta dauwwama wanke-wanke da shara. Kawu yahaya yayi rawar gani, ya yi wa inteesar kaya na kece raini, ya so ace ta fara makaranta kan yayi mata aure, amma ta dage soyayya ta rufe mata ido, ta ce ita fa aure take so, dan haka ba yadda ya iya ya ƙyale ta. Sagir ya danƙaro mata uban kayan lefe, kaya ba na wasa ba, ya ciko akwatuna da kaya, sai iyayi take tana rawar kai. Albarkacin auren inteesar, a wannan karon da kawu yahaya ya yi mata ɗinki, farida ba ta ƙwace ba, har da sabon takalmi, farida kuma ta bata tsohon mayafi, kalar kayan. Ranar party, farida ta ce ta zauna a gida, ta kula da baƙi masu shige da fice, kuma ta tsaya a kan girke-girken da za ayi. Ummi ta zage ana can ana party, tana gida suna aikin girki, dan ita ta jagoranci aikin abincin bikin. Ranar wuni ya kama ranar da za'ayi ɗaurin aure, dan haka da wuri motoci suka kawo ƴan gagarawa. Su Idris da babarsa, su magaji kafatanin ahalin Iya. Lokacin ummi ba ta gidan, suna can tana ta hidima da ƙawayen inteesar, ana yi wa inteesar kwalliya. Ummi ta yi wanka, ta yi wa noor, ta saka kayan ankonta da ita da noor. Sai da inteesar ta kalli ummi ganinta babu mayafi, dan zata iya ƙirga rabonta da ta ga ummi babu hijjabi. Tayi ture ka ga tsiya, ta kanannaɗe gashinta a ƙeyarta, ɗaurin ya zauna cas a kanta, ga ɗinkin ma dai-dai jikinta. Ta shafa man leɓe, ta yafa mayafinta a kanta, ta rufe jikinta sosai, ta kama hannun noor, suka fice. Wani irin farinciki ya kama ummi, ganin ƴan gida gaba ɗaya sun zo, dan rabonta da su tun da ta baro gagarawa. Duk bin ummi suka yi da kallo, yadda ta girma ta zama budurwa. Cikin su ummi ta shiga tana gaishe su, Iya sai wani hura hanci take yi. Ta ce "Ina yaya magaji?" Sa'adatu ta ce "Sun tafi wurin ɗaurin aure". Ummi ta karrama su da abinci, dan matar gidan ba ta ta su take yi ba, ta kai su ɗakinta, ta yi ta ɗawainiya da su. Bayan azahar su Hashim suka dawo daga wurin ɗaurin aure, ummi baki yaƙi rufuwa saboda duk ƴan uwan mahaifinta sun zo. Ɗaya bayan ɗaya ta din ga gaishe su, suna mamakin yadda ta girma, ta zama cikakkiyar mace, sai dai ko kusa bata kalli in da Idris yake ba. Farida sai bin ummi take yi da kallo, dan ba ta taɓa tsayawa ta kalli ummi sosai cikakken kallo ba sai yau, rashin gyara ne ke ƙara munanta ummi, idan ka kalleta sau ɗaya sai ka sake kallonta, mussaman yadda take kokowa da mayafin, kasancewar ita ba ma'abociyar ta'amalli da shi ba ne ba. kasancewar hashim shi ne mutumin ummi, can harabar gidan suka koma, suna ta hira. Ya dubeta ya ce "Ummi, kawu yayi miki magana kuwa a kan batun nemo mamanki?" Cikin sauri ta ce "A'a, ya ake ciki?" "Subhanallah, ya ce dai kar na kuskura na gaya miki saboda wani dalilinsa, amma dai idan bai ganta ba yana daf". "Ya salam, bai gaya mini ba, ko maganar zan yi masa?" "A'a, dan ya yi mini kashedin kar na gaya miki, ki kwantar da hankalinki duk abu zai haɗaku". Cikin karaya ta ce "Yaushe hankalina zai kwanta, tana raye amma rabona da ita kusan shekara goma sha, ina son ganinta". Idiris kuwa wani abu ne ya din ga yi masa zillo a maƙogwaronsa, ganin ummi tare da Hashim, gashi ta gayar da kowa, amma ko sashin in da yake ba ta kalla ba, balle ta gaishe shi. Kasa daurewa yayi, ya nufi in da suke zaune. Sai dai ummi na hango shi, ta miƙe tsaye ba tare da ta gama maganar da take yi da Hashim ba. Cikin zafin nama ya sha gabanta, ya kalleta ya ce "Ina zaki je? Saboda wulaƙanci ki ka gaida kowa baki iya gaisheni ba, kuma na taho da ki ka ga nan zan zo, shine ki ka tashi". Cikin ƙwayar idon Idris ta kalla, wani abu mai kama da wuta yana zafi a ƙirjinta. Tuni idanunta suka tara hawaye ta ce "Cikin abun da bana ƙaunar sake gani a nan duniya har da lahira, har da fuskarka, ka matsa ka bani hanya, ko kuma in yi maka abun da baka taɓa zato ba!" Whats app only please 🙏 Ayshercool. 08081012143   *CUTARWA!* *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* P21 FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK. https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends Masu neman free books ɗina, da free pages duk akwai a kan watpad account ɗina. Irinsu Abduljalal Wata kissar sai mata Wuta a masaƙa Cutarwa Ƙanwar maza Gaba da gabanta Aƙidata Ruɗin ƙuruciya Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata. 08081012143. And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link. https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels Ayshercool. PAID ADVERT!. Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi. Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku Oll types of Turaran wuta Sandal Halut Irik Difur Gab Gab Kajiji Habil Nabak Humra Kulakcha Dilke da kalta Kayan Garan jiki Muna turara Kaya Kujerar garan jiki Kannada Madarorin turare masu kamshi  Man garan gashi  Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702   08025453921 *TALLA!TALLA!TALLA!* *INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*. *BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU* *MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA* BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI. 21 Mamaki ne ya cika shi, har sai da ya bayyana a kan fuskarsa, bai taɓa tunanin ummi za ta iya furta abun da ta gaya masa ba, saboda tun fil azal tamkar sokuwa take ba ta da wani karsashi balle ta yi faɗa. Bai gama nazarin ba, ta angije shi tayi wucewarta tana tsaki, abubuwan da suka faru a baya, suna sake dawo mata tamkar yanzu suke faruwa. Ƙarshen cin mutunci da tozarci yayi mata a garin nan, wanda yana daga dalilan da ya sanya ba ta ƙaunar sake zuwa gagarawa, haryanzu baƙin ciki da mugun tabon da take da shi a garin, yana damunta. Dan har cikin zuciyarta tana fatan a gidan duniya, Allah ya yi wa Idiris abun da ya yi mata kafin ya koma ga Allah, ba ta sani ba ko a gaba ta iya yafe masa, amma har zuwa wannan lokacin, ba ta ji alamar manta abun da yayi mata ba, balle ta yafe masa. Ranar da ya fara kwana a ɗakinta, ya korota waje, ta kwana cir a tsaye ruwa yana dukanta, saboda mugunta da zalunci. Tayi iya ƙoƙarin ta wurin danne hawayen da ke ta ƙoƙarin zubo mata, ana ta hotuna, angon inteesar sagir, da kansa ya ce ummi ta zo ayi musu hotuna. Idiris ya jinjina kai, tare da tabattarwa da kansa zaman birni, da kuma zuwa jami'a ne ya sanya ummi lalacewa, domin kuwa an ce dama ƴan matan jami'a ba su da mutunci lalacewa suke yi. Duk in da ummi tayi sai ya bita da kallo, tamkar wani shashasha, hindu da yake yi wa kallon wayayyiya kyakykyawa, yanzu duk ta tararraɓe, haihuwa uku tayi, har da waccan mai sunan Iyan, ƙirjints da yake ɗaukar hankalinsa, duk sun zube, kullum daga ciki sai shayarwa. Amma yanzu ummi komai nata a tsaye kyam, dai-dai da jikinta, duk da tana ta rufe jikin nata da mayafi. Bayan la'asar suka ce zasu yafi, dan ba su zo da niyyar kwana ba dama, saboda sanin halin farida. Duk lalacewar naka naka ne, ummi ta ji daɗin zuwansu sosai da sosai, tayi ta yi musu fatan alkhairi har suka tafi. Idiris kuwa kamar maye, saboda azabar kallo, har suka ɗauki hanya suka tafi. Kallo ɗaya zaka yi wa rahama da yaronta, ka san ba a kwanciyar hankali take ba, ga dai kuɗi miji yana da shi, amma yarkace-yarkace hak take, dan hatta kayan sawa wasu lokutan farida ke bata ko ta sayawa ɗan, duk wannan ƙafafar da ikon babu shi, duk ta zama so silent. Taro ya watse, aka kai amarya, ummi kuma ta sake cin uban aikin gyaran gida, ranar monday kuma ta tafi makaranta. Gaba ɗaya jikinta a mace yake, da ƙyar take tafiya ma duk jikinta ciwo, saboda azabar aikin da ta sha, ba ta samu damar hutawa ba, a haka a tafe har gajiyar ta ware. Karatun ummi yayi nisa, kuma haryanzu ba a samu wanda ya doke point ɗin ta ba, duk da ba ta fasa fuskantar ƙalubale ba. Dan haryanzu farida da kausar ke cin ƙaniyarta. *** Tana zaune ta duƙufa tana ta aikin shirin dutse, ɗanlami yayi masa jagora har cikin ɗakin da take zaune. Ɗakin tsaf da shi, sai ƙamshin turare yake yi, kai ba ka ce mara lafiya ce a ɗakin ba. Ta ɗaga kai ta kalleshi, ta sunkuyar da kanta ta cigaba da aikin gabanta. Ya ɗan ƙare mata kallo, shekaru sun ɗan ja, ta girma yanzu, amma tsaf da ita, tana samun kyakywar kulawa. Ya dubi ɗanlami ya ce "Ɗan uwa, kuma a haka ba ta da lafiya?" Yaya ɗanlami ya ce "Babu lafiya, wasu lokutan dai hankakin yana dawowa, wasu lokutan kuma sai ciwon ya dawo tayi ta shirme. Amma a hakan nan da take, za ta yi wanka, tayi shara tayi kwalliya ga shirin dutse nan ma gashi ka ganta tana yi, likita ne ya ce a samo mata abun da zai din ga ɗebe mata kewa. Ka ga yanzu tafi sati ba ta yi magana ba, ba ta duka ba ta zagi, kaga daga mutuwar mijinta, ga rabata da ummi, ta zo ta haihu ɗan ba rai, tayi jijjiga depression yakamata sai kuma dai ta samu matsala gaba ɗaya. Ban taɓa tunanin wani daga dangin baban ummi zai biyomu ba, dan mun yi alƙawarin ba zamu sake zuwa ba, irin jafa'i da mugun bakin da mahaifiyar ku tayi wa ƴar uwarmu, ya sanya muka ce gara mu yanke alaƙa da ku kawai". Dr. Yayi ajiyar zuciya ya ce "Tun da na ɗauki yarinyar nan, nake fafutukar neman ina ku ke, ni ban san garin nan ba, ainihin in da kuka zauna aka aureta, mun je aka ce ba kwa nan, abubuwa dai duk ba su yi daɗi ba, sai fatan Allah ya kyauta". Mama da yaya maryam da suke gefe suka amsa da amin, dan maryam ta zo gida yau, babu tsammani suka ga kawu yahaya. Maryam ta ce "To ya ummin take? Ba ka zo mana da ita ba?" Ya girgiza kai ya ce "Ba yanzu ba, ummi na nan a jami'a". Yaya maryam ta ce "Dan girman Allah, ummin?" Yayi murmushi ya tashi ya ƙarasa gaban ta ya zauna yana kallonta, ba tare da ta ɗago ba tayi murmushi ta ce "Baban ummi" Ya ce "Na'am". "Jigidata da ka tsinka mini nake gyarawa" Sunkuyar da kai suka yi cike da jin kunyar abun da ta faɗa, dan tafi sati ma ba magana. Yayi murmushi ya ɗebi dutsen da take ta shiryawa ya ce "Gaskiya ban kyauta ba, ki haɗa wata maza". Ta sake yin murmushi ta ce "Da na san zaka dawo, ai da na yi kitso, an yi mini lalle, kaina ba kitso, bana son kitso tun da ka tafi bana son kitso" tayi maganar tana cire hular kanta, gashin kanta baƙi wuluk ya bayyana. Yaya maryam zata yi magana, ya ɗaga mata hannu tare da girgiza mata kai, ya ce "To tun da na dawo yanzu sai ayi ko?". "Ba zan yi ba, tun da ka tafi ka bar ni, ka ƙi ka dawo, Iya ta ƙwace mini ummi, ɗa na ya mutu ka ƙi ka zo ka ganni kuma bani da lafiya" tayi maganar tana kuka wiwi. Ya ce "To ki yi haƙuri, ki yi haƙuri ba zan sake tafiya naƙi dawowa ba" Ta riƙo hannunsa ta na cigaba da kuka ta kwantar da kanta a hannunsa ta ce "Baban ummi" Ya amsa mata da "Na'am" Ta ɗaga kanta ta kalleshi ta ce "Ka je ka karɓo mini ummina, Iya ba zata din ga yi mata wanka ba, ko idan yamma ta yi ta saka mata kayan sanyi, ba ta son ummi, dan Allah baban ummi ka karɓo mini ummi, kaga katifata ta ishemu ni da ita, idan ka sai mana gida sai in dawo gagarawa ko?" Ƙura mata ido yayi, cike da matsanancin tausayinta, lallai yana daga horon da za ka yi wa uwa, ka rabata da ɗan ta, duk da tana cikin hauka, amma ba ta manta da ƴar ta ba. Yayi ajiyar zuciya ya ce "To shikenan, ki daina kukan ya isa haka, mayar da hularki, kiyi haƙuri" ta ɗauki hularta ta saka. Ta ja bakinta ta sake yin shiru. "Zan kawo miki ummi in sha Allah, amma ba yanzu ba". Yaya maryam ta ce "Saboda me? Abun da ta daɗe tana jira kenan, ka taimaka". Ya ce "Ina da dalilina, kuyi haƙuri dan Allah" "To amma mu ai ka bari muje in da take". Kawu yahaya ya ce "Da ina da ƙudurin rabaku da ummi, da ba zan neme ku ba, ina da hujja mai ƙarfi sosai. Zan cigaba da shiga lamarin nemawa mariya magani in sha Allah, komai zai daidaita kuma zai wuce". Ba haka suka so ba, amma ba su san takamaimai menene dalilinsa na ƙin haɗa su da ummi ba. *** Hangen dala ba shiga birni ba, domin kuwa inteesar tayi zaton soyayyar da suka sha da sagir a waje, ita za aje a cigaba da yi a gidan, sai abun da take so shi zai din ga yi mata, amma ina. Ya nuna mata shi namiji ne, mage mai kwanciyar ɗaukar rai, a gida ta saba ba abun da take yi, ummi ce take komai. Yanzu kuma ya ce shi ba zai ɗauki ƴar aiki ba. Dan haka sai komai ya din ga bata wahala, asubar fari zata tashi ta haɗa masa breakfast, gashi su yi ta faɗa dan abincin nata ba daɗi, ga almubazzaranci kamar ba mace ba. Ga rashin kunya da rashin iya magana, gashi ɗan uwan mata, yana da tarin yayye da ƙanne mata, ga uwarsa mai shegen sanya ido. Sai ƙannensa su zo gidan su fi sati, gasu manya duk sun girmeta, su yi ta yi mata rashin mutunci, idan tayi magana su ce za su yi mata dukan tsiya. Abun duniya ya damu inteesar, ta dawo gida tana kuka, ta gayawa mamanta. Farida a zatonta zata iya maganin abun, ta kira Sagir tana masifar dan me ba zai tsawatarwa ƙannensa ba? Ya ce mata ba zai iya ba, baya son ya saɓawa mahaifiyarsa. Abu kamar wasa aka fara jamb, kawu yahaya ya turawa inteesar kuɗi, ya ce taje tayi jamb, a nema mata admission. Amma sagir ya ce ba yanzu ba, sai ta haihu, domin kuwa a lokacin ma laulayi take yi. Kawu yahaya bai matsa ba, farida ta din ga masifar dan me ba zai dage sai inteesar ta fara makarantar yanzu ba? Ya bata amsa da "Yanzu ya fi ni iko da ita, shiyasa tun tana ƙarƙashin ikona, na so ta fara makarantar, yadda bai isa ya hana ba, amma ku ka dage, dan haka ni ba abun da zan ce". *** BAYAN WANI LOKACI!. Kasancewar tsakiyar damuna ne, an ɗan kwana biyu ba a yi ruwan sama ba, dan haka ana tafka zafi, ga uwar rana da ake ƙwalawa. Tamkar ba ita ranar ke duka ba, haka take tafiya sannu a hankali, tana ratsa layukan unguwar, sannu a hankali take tafiyar, tamkar tana tausayin ƙasa, kamar mai rangji haka take tafiyar kamar tana tausayin ƙasa. Ta cikin niƙabinta take kallon dogon layin, tare da lissafa sauran tafiyar da ta rage mata, ta isa in take fatan zuwan. Layin shiru, sai lokaci lokaci, ababen hawa ke giftawa, manyan gidajen layin ko ina a rufe. Ƙarar babur ta ji, kasancewar gefen hanya take bi, ya sanya ko a jikinta, dan ko waiwaya wa ba ta yi ba, ashe layin da yake gabanta yake ƙoƙarin shiga. A ɗan fusace ya ce "Ke, kurma ce ne? Sai mutum ya tureku, ace bai kyauta ba, ba ki ji ina horn bane?" Ta tsaya cak, ta ɗan ja wasu seconds, sannan ta juyo ta kalleshi ta cikin niƙab, sai dai ba ta ce komai ba. Maimakon ya wuce ya tsaya ya ji me za ta ce, idan rashin kunya za ta yi masa, ya ƙare mata ta tas. A hankali ta ce "Sorry, ga hanya wuce" tayi maganar tana ɗan ja baya ta bashi hanya. Fuskar ta a rufe da niƙabi, amma muryarta ce ta saka shi ƙara kallonta. "Malama idan zaki ware murya ki ware, da na bugeki ai ba zaki maƙale murya ba". Ta ce "Ikon Allah, me muryata kuma tayi maka, ai na ce ka yi haƙuri ka wuce" Tsaki yayi ya ja babur ɗin sa ƙirar lifan, ya yi gaba. Ita kuma ta yi ajiyar zuciya, ta cigaba da tafiya. A ƙofar ƙaton gate ɗin gidan ta tsaya, mutum biyu ta tarar sanye da uniform na security, suka dubeta suka ce "Gurin wa zaki je?" Ta ce "Habu baka gane ni ba?" Jin muryarta ya sanya shi cewa "Ahha wata sabon gani, ke dama kina duniyar nan?" Ta ce "Ina nan mana, ya aiki ya kwana biyu?". "Alhamdilillah, gaba ɗaya tun da ƙawarki ta bar gidan nan muka daina ganinki" "To ai gashi na zo wanke laifina yau, ina fatan mami na nan?". Ya ce "Eh tana ciki" Ta ce "Yauwwa na gode" ya buɗe mata ƙaramar ƙofar gate ɗin, ta shiga ciki. Ɗayan ya kalleshi ya ce "Ka barta ta shiga? Baka kira hajiya bilkin ba, kuma ba ta ɗaga niƙabinta ba". Habu ya ce "Ai ƴar gida ce, ƙawar maryam ce, tun da tayi aure ne ta daina zuwa". Ya ce "Ok, na so ta ɗaga niƙabin naga fuskarta, muryarta tayi mini daɗi". "Ji ɗan wahala, ka sani ko yanzu tayi aure, ka shiga hankalinka". Ummi kuwa sashin mami ta nufa, fasalin gidan yana nan yadda yake, amma yanayin fentin da aka sassauya masa da wasu abubuwan zaka san arziki ya fi na da. A falo ta tarar da mai aiki, duk da ƴar bata san ƴar aikin ba, suka gaisa sannan ta tanbayeta ko mami tana nan. Mai aikin ta ce "Eh, tana falon sama" "Ki ce mata ummi ce ta zo" mai aikin ta jinjina kai ta nufi ƙafar benen ummi kuma ta zauna. Bai kai mintuna biyar ba, mai aikin ta saukko, ta ce wa ummi ta shiga. Ummi ta tashi ta bi bayan ƴar aikin. Da sallama ummi ta shiga, mami ta waiwayo tana cewa "muryar wa nake ji ne haka? Gaskiya koma nayi fushi" "Tuba nake mami" Sai dai tana zagayowa, ta tarar da na kan babur da ya kusa tureta da lifan, yana zaune ya barbaje ƙafa a kan centre table, sai yanzu ta gane a in da san shi. Sai da ya ɗan sake ɗaga kai ya kalleta shi ma. Nan suka gaisa da mami, mami nata mitar ummi ta ɗauke ƙafa ta daina zuwa tunda maryam ta bar gidan. Ummi ta kalleshi ta ce "Ina wuni?" Ya basar ya ce "Lafiya ƙalau" Mami ta ce "Laaa ka amsa kuwa? Kema meyasa ki ka gaishe shi? Ƙaninku ne fa, ƙanin maryam ne Raihan ne. Kai kuma ka amsa kamata yayi fa ka gaisheta" ya wani basar. Ummi ta ce "Ƙyaleshi mami, ai dama su Allah ya bawa girman" tayi maganar tana ɗaga niƙabin fuskarta. Sai yanzu shima ya ganeta, ranar saukarsu da maryam a makaranta. Mami ta ce "Ya wani je ya tara gemu, yafi kowa girma kai ka ce wani babba ne, ni wannan gemun ina tantama idan ba mai ya shafa ya fito ba, dan ga gemun nan dai, amma hankali da saura". Ummi ta yi murmushi ta ce "Girma ya riga hankali kenan" sai da ya ɗan buɗe baki jin abun da ummin ta faɗa. Mami ta ce "Eh mana, ya  makaranta ummi?". Ummi ta ce "Mami makaranta muna jiran result" "Masha Allah, lokaci ba wahala har kin gama ummi, Ubangiji Allah ya sanya alkhairi, to ya batun aure kuma? Ko invitation ki ka kawo mini?". Ummi ta sunkuyar da kai, tayi murmushin yaƙe ta ce "Tukuna dai mami" Mami ta ce "Ya salam, Allah ya kawo nagari ummi, yanzu fa maryam kusan shekarar ta bakwai da aure, ke kuma shiru duk ƴan islamiyyar ku sun yi aure, saura ke, amma kar ki damu komai lokaci ne" Ummi ta ce "To mami, bari na yi alwala dan Allah" Mami ta ce "To shikenan ba damuwa, je ki yi" Ummi na tashi raihan ya kalli mami ya ce "Dan Allah mami fisabilillahi meye na tambayar invitation ta kawo miki? Da shi ta kawo miki ai ba sai kin tambaya ba, kin ce shekarar maryam bakwai da aure ita ba ta yi ba, kin dawo kin ce tayi haƙuri lokaci ne, kamar fa kin mari mutum ne kina sane sannan ki ce yayi haƙuri". Mami ta ce "To uban tsari, ai da tausayi yakamata ace ita ma ta tashi haka, in da take tana shan wahala, matar yayan babanta ke wahalar da ita, shiyasa nake tambayarta ko auren ne ya zo, ta huta". "Matsalarku kenan mata, kune maƙiyan kanku, ladan ake rubutawa mace idan ta azabtar da ɗan wani? Kuma duk tausaya matan da ki ke, tun da dai ba ki samo mata mijin nan ba, ai sai ki yi mata addu'a, is like an insult at times, ka tambayi mace maganar aure, ni idan mace ne faɗa za ayi da ni" Mami ta ce "Kai,tashi ka je mini aike na uban tsari". "To ɗaukko kayan, ki haɗo da kuɗin shan mai". "Duk kuɗin da babanka yake baka, sai ka damfareni dan zan aikeka, to ba zan bayar ba". Ya kashingiɗa ya ce "Mami idan kina son aiken nan a kan lokaci, ki bayar da cin hanci " tashi mamin tayi tana hararsa. Hakan yayi dai-dai da fitowar ummi, fuskarta a jiƙe da ruwa, gaban gashinta duk a kwance, gashin girarta ma tamkar za su haɗe. Fararen idanuwanta suka bawa brown ɗin ƙwayar idonta fitowa sosai da sosai. Ƙwayar idonta yake son kalla, domin tabattar da kalarta, sai dai bata bashi damar hakan ba, dan mayar da niƙabin ta rufe fuskarta, ta tayar da salla. Mami ta dawo falon da ATM ɗinta, tana yi wa Raihan kashedin ya je ya dawo da wuri. Ya karɓi ATM ɗin yaƙi tashi, ummi ta idar da sallar, tayi Addu'a ta cewa mami za ta tafi, tashi yayi ya riga ummi fita. Mami ta ce sai ta tsaya ta ci abinci, amma ummi ta ce sauri take yi. Ta ajiye wa mami kyautar kwalbar turaren humra. Kuɗin motar da ta bawa ummi ma, ƙin karɓa ta yi, kuma da ganinta ka san tana buƙata amma mursisi taƙi karɓa ta tafi. A babban falo ta tarar da shi, yana taje sumar kansa. Har zata fita ya ce "Ki tsaya mu tafi tare na ajiyeki ko a titi ne" Ummi ta girgiza kai ta ce "A'a na gode sosai, zan ƙarasa" bai kuma ce mata komai ba ta fito daga falon. Ta fita harabar gidan, hakan yayi dai-dai da fitowar wata babbar mace, ta sha ado da lace blue, hannunta da wuyanta duk gold. Wani matashi yana biye da ita, kai da ganinsa ka ga ɗan shaye-shaye. Da sauri ummi ta ƙarasa in da matar take, ta ɗaga niƙabinta ta durƙusa ta gaisheta. Matar ta faɗaɗaɗa murmushinta ta ce "Ummi yau kece a gidan, ba dan Allah yasa na fito ba tafiya zaki yi bamu gaisa ba?" "Ba haka bane hajiya, a gurguje na shigo ne, kusan kullum ta hanyar nan nake bi, shiyasa na ce yau dai bari na shigo" "Eh amma zaki tafi bamu gaisa ba ummi, ya gida ya makaranta?" Ummi ta amsa da Alhamdilillah. Hajiya ita ce uwar gidan mami, tun lokacin maryam na nan, tana son mu'amala da ummi saboda nutsuwarta, amma ummi ta janye jikinta ta daina zuwa gidan ma, saboda ba a ga maciji, tsakanin mami da Hajiya. Ummi ta gaida Salim da suke tare da hajiya, ya amsa mata sama-sama. Hajiya ta ce "Ummi kin yi aure ne?" Ummi ta girgiza mata kai. "Ai da kin yi aure ban sani ba, sai mun yi faɗa". Kamar an jefo shi, ya dafo kafaɗar hajiya yayi ƙasa da murya ya ce "Ku daina yi wa mutum irin wannan tambayar babu daɗi" Hajiya ta yi murmushi ta ce "To babban mutum". "Biki zaki je kenan?" Ta ce "Eh, ƴar set ɗinmu ke auran ɗa" Raihan ya ce "Shiyasa ki ka sha kwalliya, kamar ƙawar amarya mu ga jakar" ya karɓi jakar hajiya ya zuge. Ya girgiza kai ya ce "Allah sarki Alhaji, an ɗebi kuɗinsa za aje ayi liƙi, to nima bari na ɗebi rabona" ya zura hannunsa ya ɗebo kuɗi ya zura a aljihunsa. "Raihan abun har da gori, sai ka gayawa duniya kuɗin babanka ne" Yayi dariya, ya ce "A dawo lafiya" Ummi ma ta ce "Hajiya bari na tafi, a dawo lafiya " Hajiya ta ce "A'a ummi, shigo mu fara aniyeki, sai mu ƙarasa wurin bikin" Ummi ba za ta iya jayayya da hajiya ba, dan haka ta ce "To na gode" Har ummi ta juya zata bi su ya ce "Eh ba shakka, ba zaki hau babur ba sai mota shikenan ai". Lokacin suna Islamiyya, Maryam bata da aiki sai bayar da labarin Muhammad Raihan, barkwancinsa da kuma tsokana, tsokanar ma irin mai cika cikin nan. Dan haka ummi ba ta waiwayo ba, tayi murmushi ta bi bayan su Hajiya. Ayshercool 08081012143 Whats app only please 🙏     *CUTARWA!* *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* P22 FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK. https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends Masu neman free books ɗina, da free pages duk akwai a kan watpad account ɗina. Irinsu Abduljalal Wata kissar sai mata Wuta a masaƙa Cutarwa Ƙanwar maza Gaba da gabanta Aƙidata Ruɗin ƙuruciya Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata. 08081012143. And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link. https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels Ayshercool. PAID ADVERT!. Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi. Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku Oll types of Turaran wuta Sandal Halut Irik Difur Gab Gab Kajiji Habil Nabak Humra Kulakcha Dilke da kalta Kayan Garan jiki Muna turara Kaya Kujerar garan jiki Kannada Madarorin turare masu kamshi  Man garan gashi  Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702   08025453921 *TALLA!TALLA!TALLA!* *INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*. *BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU* *MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA* BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI. 22 Raihan ya nufi in da babur ɗin sa yake, ya ɗauka ya fita daga gidan. Suna tafe suna taɓa hira da ita da Hajiya, duk da ta kasa sakin jiki da hajiyar sosai, saboda yadda take matuƙar jin nauyinta. Har kan layinsu suka kai ta, ummi ta yi ta musu godiya, sannan ta sauka ta nufi gida. A harabar gidan ta tarar da Abdul hannunsa riƙe da waya. Yana ganinta ya tsaya yana jiran ƙarasowarta. "Yaya ummi ina ki ka shiga ne?". "Na ɗan biya wani wuri ne, meyafaru?" Maama sai faɗa take yi, intee ce aka dawo da ita,  wai ta kuma yin ɓari, zasu tafi asibiti zata bar miki sallahu baki dawo ba. Ummi a ranta ta ce 'Ga kausar a gidan, ita ba za a bar mata sallahun ba' A zahiri ta ce "Subhanallah, ubangiji Allah ya bata lafiya". Ya amsa da "Amin, Allah ya taimake ki sun tafi, yanzu na dawo daga kaisu, kafin su dawo na san ta huce ba za ta yi miki faɗa ba". Ummi ta ce "Haka ne, bari na yi sauri na shiga ciki" Ta ƙarasa ɗakinta, ta yi wanka a gurguje, ta canza kaya ta saka hijjabinta na zaman gida, ta nufi kitchen. Ta tarar da noor tana wanke-wanke a kitchen. "Mama aiki ki ke yi haka?" Noor ta ce "Eh, rage miki aikin nake yi, na san a gajiye zaki dawo, na ɓoye miki abincinki a ƙarƙashin dining, kar a cinye ba ki ci ba" tayi maganar cikin iyayi. Ummi ta yi murmushi ta ce "Na gode sosai mama, bari na je na ci abincin, in zo mu ɗora abincin dare" Noor ta ce "Kije ki yi bacci ma ki huta, zan yi miki greating kayan miya, na yi miki mopping" Murmushi ummi kawai take tana kallon noor, soyayyarta da noor gamon jini ce. Bayan magariba Rayhan ya dawo yana zaune a falon mami, yana ta bawa ƙannensa umarni, duk barkwancinsa idan yana nan basa wani sakewa saboda akwai dealing. Mami na zaune a gefe tana cin abinci, tana kallon citruss. Ya kalleta ya ce "Mami kin san ina ta yi wa baƙuwar ɗazu kallon sani, sai daga baya na tuna a wurin saukar su Maryam na san muryarta, dan ban ga fuskarta ba ranar" Mami ta ce "Auu wai ummi, yarinyar kirki". Ya ce "Tana da tarbiyya sosai tun ranar da na ganta a wurin saukar nan, tubarkallah idonta mai kyau, ban taɓa ganin irin idonta ba". Mami tayi dariya ta ce "Kaga iskancin da su maryam suka din ga yi mata suna Islamiyya, saboda fatarta da idonta, duk in da maryam ta zauna sai ta bayar da labarin baƙin ummi. Gashi uwar riƙonta na azabtar da ita, ai ainihin ƙawancensu ma, maryam ce ta ture ta, ta faɗi ashe ƙonuwa ce a cikin ta, ta dinga zubar da jini, uwar riƙon ta ƙonata da dutsen guga a ciki, shima da ƙyar ta gayawa malaman ƙunar duk ta jagwale" A razane raihan ya tashi zaune, ya ce "Ta ƙonata da dutsen guga fa ki ka ce?" "Wallahi kuwa, maryam ta ce kusan kullum cikin kuka ummin take, kuma bata magana sai ta ga dama, duk yadda za ayi da ita, ba zata faɗi ga abun da yake damunta ba, sai kuka". Ya murza goshinsa a hankali ya ce "Mami kuma babu wani abu da ki ka yi, ki taimaka mata a wannan lokacin?" "Rufa mini asiri, ai yanzu ba a wannan shishshigin, na so dai na din ga taimaka mata financially, amma yarinyar nan ba a bata kyauta ta karɓa, halint sai ita" Ya dinga kaɗa ƙafarsa a hankali yana tunani, gaba ɗaya kalar ummi ba mai hayaniya bace, hasali ma fuskarta kalar tausayi ce. To wani laifi za ta yi wa mutum, har a ƙonata da iron a ciki, ita kuwa wannan wace irin azzaluma ce. Labarin da mami ta bashi tana dariya, bai ga abun dariya ba a ciki, na cewa yara na tsokanarta saboda tana da duhu da kuma ƙwayar idonta, meye a baƙar fata duk halittar Allah ce, kuma idanunta meye aibunsu, ai abun a hukunta su ne a wancan lokacin, ga child abuse a gida, makaranta ga takura daga abokan karatunta, Allah ka ɗai ya san the hardship she goes through. Dan bai manta yadda Maryam ke bashi labarin abun da ake yi wa ummi ba, da yadda take kwatanta masa baƙinta, sai duk iya ƙoƙarin sa wurin gano muninta shi bai gani ba. Fuskarta kawai yake hangowa, ko ɗazu da suka yi faɗa kan ya shigo bashi da gaskiya, amma ta bashi haƙuri, komai nata simple ne. Ya miƙe tsaye ya ce "Mami sai da safe, bacci nake ji" yana gama maganar ya fita. *** Ko da farida ta dawo sai da ta ci wa ummi mutunci, duk da ta san ummin wurin aiki take zuwa, domin kuwa bautar ƙasa take a lokacin a wani gidan jarida, daily news. "Maama dan Allah ki daina yi wa anty ummi faɗa, ba gashi nan duk mun gama yi miki aikin gidan ba". Cikin tsawa ta ce "Idan ina magana ki na saka mini baki sai na yi ball dake" tayi maganar tana nuna noor da yatsa. Ta mayar da idonta kan ummi ta ce "Dan kan ki, gaba ɗaya kin mayar mini da yarinya fitsararriya mara ɗa'a kamar ke, zaki haifa ne kema. Sakwara zaki daka, da jar miya, kije Abdul ya kai ki asibiti ki kai wa inteesar ki kwana da ita asibiti, kausar ta dawo gida". Daga auren inteesar zuwa yanzu, tayi ɓari ba adadi, dan kamar har mijin nata ya fara ƙosawa da hakan. Ummi ta je kwana da ita, ta tarar ana yi mata ƙarin jini, duk ta rame, ƙannen mijin suna zazzaune, suna ta hirarsu ko a jikinsu da halin da take ciki, kausar ce a kusa da ita a zaune, ita ma kuma danna wayarta take yi. Ko da ta ga ummi ta wani haɗe rai ta yatsine fuska ta ce "Dan wulaƙanci, tun kan mu taho asibitin nan ake jiranki, amma ki ka ƙi dawowa kin bar mutane da yunwa, kuma kin san dai ba iya cin abincin sayarwa muke ba" Ummi ta ja wuri ta zauna ba tare da ta kulata ba, suka gaisa da ƙannen mijin inteesar. Babu kunya suka ja kwanon sakwarar nan suka buɗe, suka ci abin su, suka gama suka ƙara gaba. Sai da inteesar ta yi sati a asibiti, ummi ce ke sintirin kai abinci da ɗawainiyar kwana da ita, amma duk basa gani sai rashin mutunci da hantara, gashi idan ta kwana kan wani yazo daga gida ta koma ta shirya ta tafi in da take SIWES, sai ta makara sosai da sosai. Idan ta je wurin aiki, shima ayi ta yi mata faɗa a kan makara. Farida ta cewa sageer ya bata inteesar su tafi gida, ta ɗan kwana biyu ta huta. Inteesar ta ji daɗin hakan, dan kuwa azabar ƙannen mijinta sun isheta, mijin suna zaune lafiya sai abun da ba a rasa ba, amma fa ƙannensa ba sa laifi, dan akan su har zaginta yake yi, ya ci mata mutunci tayi ta musu bauta. *** A ƙalla ummi ta shafe mintuna goma sha biyar a tsaye a bakin titi, tana ƙoƙarin tsallakawa, amma ta kasa saboda tarin ababen hawa da ke kaiwa suna komowa. Ga rana gashi ta gaji matuƙa, ta gaji da tsayuwa. "Tsallaka titin ma sai kin yi masa yanga Yaya?" Sai da gabanta ya faɗi, dan kuwa ta tsorata sosai. A hankali ta waiwaya tana kallon fuskar sa. Idon da yake son gani ya samu yana kallo, dan yau ba niƙab ta saka ba, facemask ne. Sai dai bai kalla yadda yake so ba ta janye idonta, tana ajiyar zuciya. "Na tsorata ki ne?" Ta ce "Na tsorata ne, ina wuni?" Ya dawo gefenta ya tsaya ya ce "Yini yana gidan biki, Ai mami ta ce ki daina gaisheni, ni ƙaninki ne, dama kin ce girma ya riga hankali zuwa" Murmushi ta yi ta sake cewa "Ya mamin da kowa da kowa?" Raihan ya ce "Suna nan ƙalau, ke na hango na tsaya a tsallake, morethan 20minutes, kin kasa tsallaka titi ki na yanga" A ɗan marairaice ta ce "Eyya ba yanga nake yi ba, kasa tsallakawa na yi ne" Ya jinjina kai ya ce "I see" Ya ce "Taho mu tsallaka" Gaba ya fara yi, tabi bayansa a hankali, sai da suka je tsakiyar titi, ta juya zata koma da gudu saboda motar da ta taho da gudu. Hanata hakan yayi, ta hanyar danƙo hannunta yayi suka yi gaba suka tsallaka. Ƙoƙarin cire hannunta take daga nasa, amma ya riƙe gam ya ce "Ke haka ki ke tsallaka titi? Gaba ɗaya kin tsorata kanki? Nutsuwa ake yi idan za a tsallaka titi" Ta sunkuyar da kai, tana cigaba da ƙoƙarin cire hannunta daga nasa. Ya kalli hannayensu nasa fari tas, na ummi mai duhu, sai dai nata hannun yafi nasa kyau sosai da sosai, nasa da gani kaga hannun namiji, duk a murɗe ga uban jijiyoyi, nata kuma ɗan madaidaici, ɗauke da dogayen yatsu, tafin hannunta fari tas, haka faratanta farare ƙal dogwaye gwanin sha'awa, ga hannunta tamkar auduga dan taushi. Ya zare nasa ya basar ya ce "Mu je na ajiye ki a gida" Ta ce "A'a kar ka damu, wannan ma na gode sosai da sosai, Allah ya saka da alkhairi" Raihan ya ce "Ai ba babur bane, yau mota ce, tun da ba kya hawa babur sai mota". "A'a ba haka bane wallahi, kar ka damu, yanzu zan tafi na gode sosai". Sai ka ce ubanta haka ya haɗe rai, ya ce "Mu je in sauke ki, bana satar mutane ai, ki daina haka" Haka nan ummi tayi tsuru-tsuru, dan da ya haɗe rai sai yayi mata kwarjini, ya nufi tsaleliyar motar da yayi parking ɗin ta a gefen titi, glasanta baƙaƙe wuluk, sai sheƙi yake, da gani ka san ba a daɗe da fara hawanta ba. Ya buɗe wa ummi gaban motar, gaba ɗaya ji tayi kamar zata aikata zunubi, ko da wasa bata taɓa hawa motar wani ba, idan ba ta kawu yahaya ba. Wani sanyi ne haɗe da ƙamshi mai daɗin gaske ya baƙunceta a cikin motar. Ya zagaya ya zauna, ya rufe motar, ya ɗaukko robar ruwa da lemo, ya miƙa mata ya ce "Ga ruwa ki sha, kin daɗe a rana". Fuskar sa ta kalla, ta karɓa ta ajiye a kan cinyarta. "Ina zaki yi ne?" "Gida" "Gida ina?" Ta kwatanta masa, ya ja motar ya fara tafiya. Ta gefen idonsa yake kallon yadda duk tayi tsuru-tsuru kamar ba ta da gaskiya, gaba ɗaya a takure take, kamar wadda ke zaune a kan ƙaya. Tunani yake ta yi a zuciyarsa, this innocent looking lady, ace an azabtar da ita har haka, to wane irin laifi zata yi, da zai saka ayi maka haka?. Ɗan satar kallon sa tayi, kamar ba shi ta gani wancan lokacin ba, yana barkwanci da wasa da dariya ba. Ya ɗaukko wayarsa ya nemo lambar Maryam, ya saka a hansfree. "Ke yane?" Ta amsa da "Normal, ya aka yi?" "Guess what?" Ta ce "I have no idea, menene?" "Na sake haɗuwa da ƙawar nan taki, da na ce miki tazo gida gaida mami" Ta ce "Allah sarki, ummi?" "Eh ita" "Wallahi bani da numbernta, ban sani ba ko tana da waya ma?" "Baki da kirki, maybe tun da ki ka yi aure baki sake neman ta ba". "To a ina zan ganta, ban son zuwa gidansu, antynta ba ta da mutunci" Ya ce "Ai shikenan, a gaida yaran" "Za su ji in sha Allah". Ya ajiye wayar, ya mayar da hankali sosai a kan tuƙinsa. "In da na ɗauko ki aiki ki ke ne a wurin?". Ummi ta ce "SIWES" "Me ki ke karanta ne?" Ummi ta ce "Mass communication" "Mass communication, ai karatun masu baki ne, ke kuma kamar ba kya magana ma" Ita dai tayi shiru ba ta ce masa komai ba. Ya bata wayarsa ya ce "Saka mini lambar ki, sai na turawa maryam, ku dinga gaisawa, zumunci abu ne mai kyau". Wayar ta sa zuƙeƙiya mai kyan gaske, ta saka masa lambar ta miƙa masa. Ya ce "Masha Allah, to nima za a din ga zumuncin da ni? Tun da ƙaninki ne ni?" Ummi ta yi murmushi ta ce "To" "To yaya ummi na gode sosai, sunana Muhammad Raihan" Ta ce "Ai na sani" "Ai tuna miki na sake yi, ranar da muka haɗu mun kusa yin faɗa, ashe kin sanni nine ban gane ki ba" Tayi murmushi tana sake gyara zaman facemask ɗin ta. "Ki rage saka niƙabin nan da facemask, idan ba haka tayaya mutum zai gane ki, you are lucky ina da saurin gane mutane ma, da mask ɗin na gane ki" Ummi dai ba baki, dan dama can ba mai hayaniya ba ce, sai murmushi da take yi. A bakin titi ta ce masa zata sauka. Ganin ya takura mata, ya sanya ya ƙyaleta, ta buɗe motar ta waiwayo ta kalle shi ta ce "Na gode sosai" "Nima na gode ki gaida gida" yana kallonta cikin dabara ta ajiye masa ruwa da lemon da ya bata ta fice. Raihan ya taimaketa da ya ɗaukkota, ba dan haka ba, sai ta ci uwa tafiya, kafin ta hau mota, dan kuɗin motarta ba yawa a jakar. Har ta shiga gida, jikinta ƙamshin turaren raihan yake yi, kasancewar gaba ɗaya motar ma ƙamshin turaren take yi. Yana zaune a motar ya kira lambar ummi, tana sauri zata shiga gida, wayarta ta fara ringing, ta ciro wayar ta ɗaga tana hello. Kashewa yayi jin muryarta ce, yayi saving number da brown eyes. Ummi ta shiga gida tana fatan Allah ya sa ba wanda ya ganta ta sauka daga motar raihan. Bayan sallar isha'i maryam ta kira ummi a waya, tare da yi mata ciwon bakin bata nemanta. Sosai suka fara hira da ummi, sai dai hirar ta daina yi wa ummi daɗi, lokacin da maryam ta fara yi mata zancen ita yaushe za ta yi aure? Ummi ta ƙarƙare hirar suka yi sallama. *** GAGARAWA Masifa da bala'i a gidan idris, kamar karnuka tun maƙwabta na shiga cikin lamarin, ana ƙoƙarin sasant al'amura, abu ya gagar a gaban yaran suke faɗa, suyi ta zage-zage da ashar kamar maguzawa. Yarinyar sa ga fari kuwa, tun da aka je da ita family house, aka yi mata gori, Hindu ta wanke ƙafa taje har gidan tayi musu tijara da rashin mutunci. Babu wanda hindu take saurarawa a dangin Idris, tun daga kan Iya har sauran mutanen gidan. Dan haka Idris ya fara tunanin ƙara wani auren, ko ya samu sassaka daga masifa da bala'in hindu, gashi kamar tayi masa asiri, duk tijara da bala'in da zata yi masa ba zai iya sakinta ba. Hashim kuwa ya kasa samun nutsuwar samun matar aure, saboda gaba ɗaya hankalinsa a kan ummi yake, sai dai iya tayi masa kandagarki, dan ta riga ta ce ba ta lamunce ba, dan haka ya san ko giyar wake ya sha, tun da iya ta furta ba ta so, babu mai goya masa baya. *** Ƙarfe kusan goma na dare, Ummi ta yi wanka tana shirin kwanciya bacci, dan washegari asabar ce, za ta je islamiyya da safe ta koyar da yara, dan haka da wuri take son kwanciya dan ta kammala aikinta da wuri ta tafi da safe. Kallon baƙuwar lambar take yi, sannan ta ɗaga tayi sallama. Ba ta ɗau muryarsa ba da farko, dan haka gabanta ya faɗi, ko bisa tsautsayin wrong number, wani namiji bai taɓa kiranta ba. Sai da ya ce "Yaya ummi" sannan ta ɗau muryar. Ta ce "Au babban mutum, yanzu na ɗau muryarka ai". "Ke, Alhajinmu ne fa kawai yake faɗar sunan da ki ka faɗa, sai Hajiya, waye ya gaya miki wannan sunan?". Ummi ta yi murmushi ta ce "A bakin maryam na ji, kuma ai sunanka babbane, ba a faɗarsa anyhow" "To sai ki ce Raihan ai" "To shikenan, ya mami da su Hajiya?". "Suna lafiya, ta kira ki kuwa?" "Eh mun yi waya da ita, ka kyauta ai". Ya ce "To Allah ya haɗamu a ladan baki ɗaya" Ta amsa da "Amin ya haiyyu ya ƙaiyyum" "Ya aikin?" "Aiki Alhamdilillah" Ya ce "Masha Allah, kiranki nayi na kwashi gaisuwa kawai, tun da mun yarda mu yi zumunci, tun da maryam ba ta nan, sai mu mu din ga yin zumuncin. Dama bani da abokai na yi ƙawa, ƙawar yayata ta zama ƙawata". Ummi ta girgiza kai ta ce "Mace da namiji ba sa ƙawance ai, ƙanina ne kai". Yana daga kwance ya tashi zaune ya ce "To shikenan, muje a haka yaya ummi" Tayi murmushi ta ce "Sai da safe". Ya ce "Allah ya tashemu lafiya yaya, sweet dreams". Ummi ta ajiye wayar tana cigaba da murmushi. Ta bi wayar da kallo, ƙanne suna da daɗi, ta so ta rungumi su intee kamar ƙanneta, amma suka nuna mata ba haka ba, shima Abdul alaƙarsu farida ta saka musu ido, da ta gansu tare sai zagi da cin mutunci. Ɓangaren Raihan ma, wayarsa ya bi da kallo, yana kallon lambar ummi da ya sakawa brown eyes, sanyin halinta ya burgeshi, abun da mami ta gaya masa game da ita, ya sanya masa tausayinta, dan haka yake jin ko na ƙanƙanin lokaci ne, zai shiga rayuwarta ya fahimci ta ina zai taimaketa, kuma zai yi mata addu'ar samun miji nagari mai ƙaunarta. A rayuwarsa ummi ce mace ta farko da ya ji yana son shiga rayuwarta, idan ba iyayensa ba sai ƴan uwansa mata, ba ruwansa da shiga harkar kowacce yarinya, duk da suna yi masa shishshigi, saboda Raihan kyakykyawa ne kamar maryam, kamar sa ɗaya da mahaifinsu. Washegari tana makarantar islamiyya, tana fama da ɗalibai, kusan ƙarfe goma da rabi, ta sake ganin kiran Raihan. "Ina kwana yaya" "Lafiya ƙalau, ka tashi lafiya?" "Lafiya ƙalau, ya nake jin hayaniya kina ina ne?". "Na je islamiyya, ne ina tare da ɗalibai" . Ya ce "Ok, ashe sayyada ce, mu yi waya idan kun tashi, dama kira na yi idan kina lafiya" Ta ce "To godiya nake, Allah yayi albarka" Yayi murmushi ya ce "Dan Allah ki saki muryarki ki daina iyayi" Dariya ce ta kamata, ta ce "Ka cuci iyayi kuwa" "Am serious, na yi recording wayar nan, zan tura miki ta what's app ki ji yadda ki ke magana, sai anjima take care" yayi maganar a hankali. Ayshercool 08081012143     *CUTARWA!* *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* P23 FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK. https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends Masu neman free books ɗina, da free pages duk akwai a kan watpad account ɗina. Irinsu Abduljalal Wata kissar sai mata Wuta a masaƙa Cutarwa Ƙanwar maza Gaba da gabanta Aƙidata Ruɗin ƙuruciya Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata. 08081012143. And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link. https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels Ayshercool. PAID ADVERT!. Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi. Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku Oll types of Turaran wuta Sandal Halut Irik Difur Gab Gab Kajiji Habil Nabak Humra Kulakcha Dilke da kalta Kayan Garan jiki Muna turara Kaya Kujerar garan jiki Kannada Madarorin turare masu kamshi  Man garan gashi  Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702   08025453921 *TALLA!TALLA!TALLA!* *INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*. *BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU* *MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA* BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI. 23 Murmushi ummi ta yi ta sauke wayar, tana sake gazgata maryam da take yawan faɗar Raihan rigiamamme ne. A ɓangaren sa shima ajiye wayar yayi yana murmushi.  Ya sauka daga kan gadon sa, ya shiga banɗaki ya yi wanka yayi brush, ya sanya kayansa ya fita. Sashin mami ya nufa, duk ba su tashi ba, ya duba kan dining an ajiye masa kayan breakfast da masu aiki suka girka. Ya buɗe foodflask, ya tarar da doya ce da ƙwai, sai kayan tea, doyar ta ja mai sosai da sosai. Yayi guntun tsaki, ya fice ya nufi sashin Hajiya, sai dai kai tsaye ɓangaren mahaifinsu ya wuce. Yana zaune yana shan tea, gefen sa ƙaton tray ne, ɗauke da kayan marmari yana kallon labarai. Ya ɗaga kai ya kalli raihan ya ce "Dama kana gidan nan?" Raihan ya ƙarasa kusa da shi ya risuna ya ce "Barka da safiya" "Yauuwa barka babban mutum, ka tashi lafiya?" Alhamdilillah, ya amsa yana zama a kusa da Alhajin. Ya ce "Alhajin Allah kana sararawa, ka bar mu a nan ka je ka huta ka dawo, ka ƙara fresh sosai" Sanin halin raihan, na zolaya ya sanya shi yin murmushi ya ce "Ina wani hutu Raihan? Ina can ma aiki nake yi, haryanzu ban huta ba, zuwa yanzu yakamata ace ku kuke kula da komai, amma sai dai nayi da kaina, yayyenka sun fi mayar da hankali a kan shashashanci". Cikin kulawa raihan ya ce "Ka yi haƙuri, ka daina damun kanka, kai ka ce ƙuruciya ce take damunsu, za su daina". "Zuwa yaushe kenan? Idan ƙuruciya ce kai meyasa ba ka yi?" Raihan ya ce "Haka ne, amma dai kayi haƙuri ka kwantar da hankalinka, abun da su Yaya Salim suke yi, ka ɗauka jarabta ce daga Allah. Kalli shekarunka sun ja, ba hawan jini, ba ciwon suga, ga mu Allah ya baka, ga tarin dukiya da al'umma suke amfana ga Hajiya ga mami dukkan mu naka ne, idan ka duba wannan ni'imomin sai ka ga abun da suke yi bakomai bane ba, dan Allah kar ka saka damuwa a ranka wani ciwon ya kama mana kai". Kallon Raihan yake yi, cikin tsananin soyayya da kulawa, ya tsiyayo tea cup, ya bawa raihan sannan ya ce "Madalla da yaron kirki, nasiharka na ratsa mini zuciya, in sha Allah zan cigaba da yi musu Addu'a" Raihan ya ce "Yauwwa father like no other, we are proud of you, ka cigaba da yi musu addu'a in sha Allah zai zama labari" Alhaji Tahir ya ce "Mahaifiyarka na ganin kamar laifin Hajiya ne ya sanya su lalacewa, amma kamar hajiya na iya ƙoƙarin ta a kan tarbiyya". "Haba Alhaji, kar ka ɗorawa kowa laifi, Hajiya ba ta da sakaci ko kaɗan". "Haka ne, ina son na roƙeka wata alfarma ne". Raihan ya gyara zamansa ya ce "To Alhaji, Allah ya bani ikon yi". Ya ce "Yauwwa, lissafin da muke yi na shekara shekara da manager, da kai nake so ku yi, a fitar da zakka, a fitar da wanda za a biyawa umara, harajinmu na nan gida da sauran ƙasashe, da duk wasu gyare-gyare da zamu yi, idan ku ka gama sai ka kawo mini na duba" Raihan ya ɗan yi shiru yana nazari, "Ya dai na ji ka yi shiru?" Raihan ya ɗago ya ce "Babu damuwa in sha Allah za ayi, zan je na same shi". Alhaji Tahir yayi murmushi ya ce Yauwwa "Babban mutum, ka ga atleast na sake na huta sosai da sosai" Raihan yayi murmushi yana cigaba da zuƙar shayi, nauyi ne mai girman gaske Alhajin ya haɗa shi da shi, dan aiki ne ba ƙarami ba. Ya shanye shayin, ya miƙe tsaye ya ce "Bari na ƙarasa wurin Hajiya mu gaisa" "To shikenan babu laifi" A sanyaye Raihan ya tashi ya nufi sashin hajiya, ba zai iya cewa mahaifinsu a'a ba ne ba, amma wannan aikin kamar yayi masa yawa, ba zai iya jajircewa ya yi shi, kamar yadda shi Alhajin zai yi ba. "Babban mutum ya dai, na ga kana tafiya a hankali, ko yunwa ka ke ji ne?" Ya zauna yana faɗin "Eh, ina ɗan jin yunwa ma, me ku ka yi?". "Ka san halinsu, kowa dafe-dafensa yayi, ni kuma tuwo na saka a ɗumama mini na sha da tea" "To ni ma zan ci tuwon" Ta ce "To bari a kawo, har da man shanu kuwa da yajin daddawa, mai ɗan karen daɗi" Yayi murmushi ya ce "Hajiya kenan, ina su Yaya Sagir?" Ta ɗan rausayar da kai ta ce "Ba su tashi ba". Ya jinjina kai sannan ya ce "Yauwwa Hajiya, kin tuna yarinyar nan ummi? Ƙawar maryam?" Ta ce "Eh, ya aka yi?". "Yauwwa Alhamdilillah, dan Allah me ki ka sani a kanta?" Hajiya ta ɗan yi shiru tana nazarin sa, sannan ta ce "Meyafaru da ita? Me ka ke son sani a kanta?". "Ba wani abu bane ba, mami ta fara faɗa mini abubuwa a kan ta, so ina son sanin if their is way, we can help her, like she's not socially ok" "To ai kaga ƙawar maryam ce, ni kuma ba wani son shiga harkata suke yi ba, amma dai ina ganinsu tare da maryam, yarinya ce mai matuƙar haƙuri da biyayya, kamar babanta ne ko babarta ce ɗaya daga ciki ya rasu, yayan babanta yake riƙonta, matarsa take maltreating ɗin ta, gaskiya i don't know much about her. Na so ace a cikin yaran nan akwai nutsatstse, ai da na haɗa su aure, tarbiyyar ta na burge ni sosai da sosai" "Kin san meya ja hankalina, har na tambayeki?" "A'a sai ka faɗa". "Yadda maryam take yawan bani labarinta, da irin abubuwan da suka din ga yi mata na wulaƙanci suna makaranta, gidansu an yi maltreating ɗin ta, makaranta yara sun yi maltreating ɗin ta, wai wasu lokutan har da malamai, abun bai yi mini daɗi ba wallahi Hajiya" Hajiya ta ce "Shiyasa nake yinka babban mutum, akwai hangen nesa da zurfafa tunani". Cikin damuwa ya ce "Hajiya, kowace halitta da Allah yayi, tana da muhimmanci da kuma amfani, sosai nake jin zafi idan na tuna abun da maryam ke faɗa a kan ta, gaba ɗaya yanayin ta kamar a tsorace take da mutane ma, kuma ni banga muninta ba, baƙa ce kawai, meye abun aibata mutum a kan abun da baka da ikon yin sa?" "Babu kam" "Amma Hajiya kina ganin zan iya taimaka mata?" "Me zai hana? Idan har da ɓangaren da zaka iya supporting ɗin ta, go ahead nima zan yi farinciki da hakan" Raihan ya sake gyara zaman sa ya ce "Wallahi na so maganarki ta farko ta tabbata, ina ma akwai nutsatstse a cikin su yaya salim, da ɗaya daga cikin su, ko shi ko yaya sagir da wani ya aureta" Cikin damuwa ta ce "To ya zan yi, sun ƙi karatu, sun ƙi kasuwa sai shirme, sai addu'a kawai" "Kar ki damu Hajiyarmu, lokaci ne, zasu daina ne in sha Allah, ayi tayi mana Addu'a" Hajiya ta ɗora hannunta kan na Raihan ta ce "Addu'a kullum cikin yi muku ita ake ai, ubangiji Allah ya tsare mana ku" Ya amsa da Amin. Sai da ya ci ya cika cikinsa, sannan ya tashi ya fita. Har ummi ta koma gida, Raihan bai sake nemanta ba, tayi ta duba wayar amma bai kira ba. Dr. Yan gari, yana ta ƙoƙari a kan kausar ta samu admission ita ma, domin kuwa a wannan karon, Farida ta ce ba zata sake aurar da ƴa ba, sai ta fara makaranta, saboda kar a sake kwata irin yadda aka yi a kan inteesar. Suna falo suna kallo, dr. Ya ce lallai ummi ta fito falon ita ma, dan baya son duk suna tare a falo, amma ta din ga ware kanta ita kaɗai a ɗaki. Ummi dai ta zo gefen kujeru ta zauna a ƙasa, tana kallon, wanda a son ranta tafi son zaman kaɗaicin a ɗakinta. Noor ta hana su yin kallon, sai tsalle take a tsakar falon, tana karanta ayar Allahu nooro samawati wal ardi. Abdul ya ce "Noor, dan girman Allah ki zauna wuri ɗaya ki yi karatun nan a nutse". Sai ta koma hawa kan kujera tana dirowa. "Ke dan ubanki ki nutsu" Kausar tayi mata tsawa. Noor ta ce "Babanmu ɗaya" Dr. Ya ce "Lafiya ce wannan tsalle-tsallen da take yi. Farida ta ce "Duk ta bi ta ishi mutane da karaɗin tsiya". Noor ta koma kusa da dr. Ta zauna ta ce "Dr." Ya ce "Na'am shalelena, yau kuma a dr. Na nake" "Ka san me? Wata a ajinmu, babansu ya auro kishiya, yanzu mamanta biyu kenan". Yayi dariya ya ce "Masha Allah, to Allah ya sanya alkhairi ya basu zaman lafiya". Ta gyara zama ta ce "To Abba ni bani da wata maman sai maama, ita kuma ba ta so na" "Tana sonki mana". "Abba dan Allah muma ka auro mana kishiya, nima mamana ta zama guda biyu" Ashar ɗin da farida ta yi mata sai da duk suka razana, ta zaburo zata make noor, amma noor ta tashi da gudu, tana murguɗa kwankwasonta tana dariya, ta tsaya daga can ƙarshen falon ta ce "Wallahi Maama idan ki ka kuma dukana, sai na ce Allah ya sa Abba ya auro kishiya" Farida ta dafe kai ta ce "Na shiga uku da wannan yarinyar, anya nikaɗai aka yi wa tiyata a ɗakin nan ba ayi mini musanye ba, anya yarinyar nan tawa ce? Gaba ɗaya ƴa ba ta da mutunci sai iskanci da rashin mutunci. Kodayake ba laifinta bane ba, tun da aka saka mata sunan bare da babu dangin iya babu na baba, kuma ana koya mata yadda zata wulaƙanta ni". Tsam ummi ta miƙe, dan ta san ƙarshe faɗan kanta zai dawo. Ta tarar da noor a ɗakinta, ta haye wa ummi kan katifa, ta yaye mata zanin da ta shimfiɗa. "Mama" ta kirata kamar yadda take kiranta. Noor ta ɗago ta kalleta. "Meyasa ba kya jin magana ne?" "Me nayi?" Tayi maganar cikin tura baki. "Ban hanaki yi wa maama rashin kunya ba?" Noor ta ce "Ba kya nan jiya ta dakeni, tayi ta zagina". Ummi ta ce "To ai ke ɗin ce ba kya ji mama" "Ina ji mana, ai in dai ta dake ni, cewa zan din ga yi Allah ya sa Abba ya auro kishiya" "Au ba ki ji faɗan da nayi miki ba ko? Zaki ga a auro muku kishiya, idan aka auro wadda zata din ga hanaki abinci, tashi ki bar mini ɗaki tunda ba kya ji" Noor ta ɗan marairaice ta ce "Dan Allah ki yi haƙuri, na daina" Can falo kuwa, ganin farida ta haƙiƙance tana ta bala'i, ya sanya dr. Bar mata falon shi ma. Ya rufe ƙofar ɗakinsa, ya zauna ya ciro wayarsa, ya danna wata lamba, ya kara a kunnensa. Amsa sallamar ya yi, sannan ya ce "Barka da yamma, kuna lafiya?". Yaya maryam ta ce "Lafiya ƙalau ya iyali?" Ya amsa da "Lafiya lau Alhamdilillah, ya mai jikin kuma?" "Jikinta da sauƙi Alhamdilillah, zasu sallame mu ma yau, ta warware zazzaɓin ma babu" Ya amsa da masha Allah "Ranar monday ne appointment ɗin ta na ganin psychiatric doctor ɗin nan ko?" "Eh in sha Allah" "To, ko zaku bari ta ƙara warwarewa daga zazzaɓin, kafin ku je ganin likitan" "To shikenan, ana samun cigaba sosai da sosai, domin kuwa shekranjiya take cewa ita fa kamar ka zo, kamar ta ganka ko mafarki take yi". Dr. Yayi murmushi ya ce "Masha Allah, da haka da haka, in sha Allah zata warware gaba ɗaya, a cikin watan nan zan shigo in ga jikin nata in Allah ya yarda". Yaya maryam ta ce "Ubangiji Allah ya kawo ka lafiya, muna ta godiya Ubangiji Allah ya saka da alkhairi, ya jiƙan magabata". Ya amsa da Amin. Yana ajiye wayar farida na shigowa, ta cigaba da yi masa bala'in idan ma yana da burin ƙara aure ne, to ya san abun da yake ciki, dan taga kamar ya ɗau maganar noor serious. Gaba ɗaya ma dariya ta bashi, dan haka ya shareta ta cigaba da banbaminta *** Haka nan ummi ta ɗan damu, kwana biyu shiru ba Raihan babu labarin sa, ya daina nemanta a wayar ma, kamar za ta damu, kuma ta basar ta manta, ta cigaba da sabgoginta. "Hi dear" taga message ta what's app ɗin ta, what's app ɗin da ta fi ƙarfin sati uku ba ta buɗe shi ba saboda rashin data, sai yau da ta samu ta saka ɗari biyu. Baƙuwar lamba ce, ba ta san waye ba, dan haka tayi replying da Assalamu alaikum. Ta tsaya ta ƙurawa message ɗin ido, hi dear, dear kalma ce da ake iya gaya wa kowa, amma mussman wanda yake da muhimmanci. To ita akwai wani wanda take da muhimmanci a gare shi, da har zai ce dear. Tayi guntun tsaki da ta tuna, akwai mutanen banza a what's app, wanda ba su sanka ba, amma su yi maka maganar banza. Ta cigaba da shirinta na tafiya wurin aiki, ba ta taso ba sai ƙarfe huɗu da rabi, a hankali take tafiya, sai dai wata mota ta cika mata kunne da horn. Ta matsa gefe amma ya cigaba da yi mata horn. Gefe ta koma ta bar wa motar hanyar, ta cigaba da tafiyarta. "A wannan yangar da iyayin naki, sai kin fusata mutum ya ture ki" cak ta tsaya, ta waiwayo da mamaki ta ce "Laa raihan, yi haƙuri ban san kai ne ba". "Eh shi ne ki ka bar mini hanyar, wato na ci kaina, ban isheki kallo ba" Ummi ta ce "Eyya ba haka bane ba, ban san kai bane" tayi maganar tana kallon sa, idonsa yayi ja, kamar daga wani wurin yake. "Wucewa na zo yi, na san sai yamma ki ke tashi, na tsaya ki fito mu tafi". Ɗan shiru ta yi tana kallon sa, ba ta son shiga motar nan tasa, kar a fara zargin wani abu. Ya ɗan marairaice ya ce "Nayi awa a wurin nan ina jiranki, dan Allah kar ki ce a'a". Ta ce "To" tabi bayansa, suka nufi motarsa. Suna tafe a hanya, har lumshe ido take yi, saboda gajiya. "Yaya ummi kwana biyu ko ki neme ni, anya za ayi zumuncin nan da ni kuwa? Na yi busy sosai kwana biyun nan, ko waya bamu yi ba, kuma baki nemi in da ƙanin naki yake ba". "Yi haƙuri ba haka bane ba, zan din ga kiranka in sha Allah". "Allah ya sa, ya karatu ya ɗalibai?" Ta amsa da"lafiya ƙalau Alhamdilillah" "Masha Allah, nima kwana biyu Alhaji ne ya sakani aiki, ya ga ina sararawa bana aikin komai, ina ga gani yayi sharholiya ta yi mini yawa, ya sani aiki ko cikakken lokaci bani da shi, duk na rame na zama baƙi" Ummi ta ɗan yi murmushin yaƙe, cikin fargabar abun da ka iya biyo bayan maganar sa, wataƙila cin zarafin kalar fatarta. Bai damu ba ya cigaba da maganar sa, "Ni fa yunwa ma nake ji, ko mu tsaya mu ci abinci?" Tayi farat ta ce "A'a, na ƙoshi ma ai, a ƙoshe nake ai" "Yaya ummi kenan, da abinci ki ke zuwa kenan? Tun safe fa kina wurin nan, to idan kin zo da abincin ki din ga ci kina rage mini, dan ni yau tun da aka kirsheni a wuri ɗaya tun ina ganewa har na daina, bari na yo takeaway a wannan wurin abincin". Ta ce "To". Ta kai mintuna sha biyar a motar, sannan ya dawo da manyan ledoji, ya tarar ta sauke facemask ɗin ta. "Sannu na bar ki kina jira ko? Tuwo na so in samu, babu sai shinkafa ni kuma damuna take yi" Tayi murmushi ta ce "Kana cin tuwo kenan? Abdul ɗin gidanmu baya son tuwo" "Haba dai, ai yaya tuwo abun so ne, ni a bauchi na saba, Alhajin Bauchi da shi yake karyawa, ga kwanonsa ga nawa, amma shima fa tuwon bana jera kwanaki ina ci yake isata" Tayi dariya ta ce "Ka fi son dai a din ga ccacanzawa" "Yauwwa, ba kullum abu ɗaya ba" Yau dai yayi sa'a, ta ɗan saki jiki kaɗan, dan yau har da dariya. Ya ƙarewa hijjabinta kallo, duk yayi fari takalmin ƙafarta ma ya tsufa. "Ummi" Ta ce "Na'am" "Me ya fi burgeki a rayuwa? Wanda yin sa yake yi miki daɗi, ko samunsa, abun da dai yake saka ki farinciki?" Tayi shiru tana tunani, oho, ita akwai wani abu da take jiran samuwar sa ya sanyata farinciki ne? Duk abun da ya zo mata a rayuwa kawai, karɓa take yi. "Babu" "Ban gane babu ba? Kawai haka ki ke rayuwa ba farinciki?" Ta sunkuyar da kai ta yi shiru. "No dole akwai, ki tuna sai ki gaya mini" "Babu" ta sake bashi amsa. Bai sake ce mata komai ba suka cigaba da tafiya, in da ya ajiyeta wancan karon, ta sake cewa ya ajiyeta. Ya yi parking sannan ya kalleta ya ce "A nan zaki sauke, ba zaki bari na ga gidan ba?" Ta hau wasa da yatsun hannunta bata ta kula shi ba. "Bayan ƴan uwa let's be true friends ummi, ki tuna abun da yake saki farinciki ki gaya mini, mu zama ƴan uwa kuma abokai saboda Allah" "To in sha Allah" Yayi murmushi ya ɗauki leda ɗaya, ya ce "Ungo naki" ta kalleshi zata yi magana, ya ɗora yatsansa a kan laɓɓansa ya ce "Shhh". "Idan zan wuce gobe in Allah ya kaimu zan jira ki mu tafi tare" ta jinjina kai, ta fice daga motar. Addu'a take yi, tana fatan Allah ya sa kar wani ya ganta, cikin ikon Allah babu wanda ya ganta, har security gidan yana banɗaki, ta wuce ta shiga har ɗakinta ba ta haɗu da kowa ba. Ta sauya kaya ta fito, ta dudduba gidan babu kowa, ta koma ɗakin ta duba ledar da Raihan ya bata. Rabin kaza ce guda a cikin ƙatuwar roba, sai shinkafa da salad. Jikin ummi har rawa yake, duk wannan kazar ita kaɗai?. Sai kuma ta yi shiru tana tunani, anya ba ta zura jiki ba? Kasa ci tayi ta tashi ta shiga aikin gida. Abdul ne ya shigo yana waya, ya kammala ya tsaya yana mita. Ummi ta ce "Yaya Abdul kana nan dama?" "A'a yanzu na shigo, wani ɗan rainin hankali ne ya kirani, wai babansu ne ya buɗe shago a tal'udu, suna neman casheir, wanda zai din ga zauna musu da safe zuwa azahar, ko azahar zuwa magariba". Ummi ta ce "Dan Allah yaya Abdul zan yi, ina so" Ya kalleta ya ce "Zaman jiran shagon, shagon furnitures ne fa da kayan kitchen" "Eh yaya Abdul dan Allah, dama na gama SIWES, kawai dai sun buƙaci na cigaba da zuwa ne, dan Allah zan yi" Abdul ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Zan yi magana da Abba, idan ya yarda shikenan". "Yauwwa zai yadda ma in sha Allah" tayi maganar tana addu'ar Allah ya sa Abba ya amince, ita ko kuɗin babu yawa tana so, atleast ta din ga samun na sayen wasu abubuwan da take buƙata. Ta kasa zaune ta kasa tsaye da kazar nan a ɗaki, dr. Gidansa ba ya rabo da nama da kaji, amma tsaf ummi za ta yi aikinsu, farida ta karɓe idan ta ga dama ta sanmata idan ba ta ga dama ba, sai ummi ta zo wanke-wanke ta ɗan tsinci sauran hanta, da diddiga ta lasa abun ka da zuciya. Hankalinta bai kwanta ba, sai da ta saka noor a gaba, ta gaya mata yadda aka yi, kamar sa'arta. Noor ta din ga murna ta ce "Yaya ummi kar ki gaya wa kowa mu cinye abunmu". Ummi da noor suka cinye takeaway tare, suna ta murna, dan kuwa ummi ba ta taɓa cin kaza mai yawan haka ba. Masu nema daga farko dan Allah ku duba a watpad Ayshercool 08081012143     *CUTARWA!* *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* P23 FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK. https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends Masu neman free books ɗina, da free pages duk akwai a kan watpad account ɗina. Irinsu Abduljalal Wata kissar sai mata Wuta a masaƙa Cutarwa Ƙanwar maza Gaba da gabanta Aƙidata Ruɗin ƙuruciya Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata. 08081012143. And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link. https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels Ayshercool. PAID ADVERT!. Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi. Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku Oll types of Turaran wuta Sandal Halut Irik Difur Gab Gab Kajiji Habil Nabak Humra Kulakcha Dilke da kalta Kayan Garan jiki Muna turara Kaya Kujerar garan jiki Kannada Madarorin turare masu kamshi  Man garan gashi  Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702   08025453921 *TALLA!TALLA!TALLA!* *INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*. *BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU* *MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA* BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI. 23 Murmushi ummi ta yi ta sauke wayar, tana sake gazgata maryam da take yawan faɗar Raihan rigiamamme ne. A ɓangaren sa shima ajiye wayar yayi yana murmushi.  Ya sauka daga kan gadon sa, ya shiga banɗaki ya yi wanka yayi brush, ya sanya kayansa ya fita. Sashin mami ya nufa, duk ba su tashi ba, ya duba kan dining an ajiye masa kayan breakfast da masu aiki suka girka. Ya buɗe foodflask, ya tarar da doya ce da ƙwai, sai kayan tea, doyar ta ja mai sosai da sosai. Yayi guntun tsaki, ya fice ya nufi sashin Hajiya, sai dai kai tsaye ɓangaren mahaifinsu ya wuce. Yana zaune yana shan tea, gefen sa ƙaton tray ne, ɗauke da kayan marmari yana kallon labarai. Ya ɗaga kai ya kalli raihan ya ce "Dama kana gidan nan?" Raihan ya ƙarasa kusa da shi ya risuna ya ce "Barka da safiya" "Yauuwa barka babban mutum, ka tashi lafiya?" Alhamdilillah, ya amsa yana zama a kusa da Alhajin. Ya ce "Alhajin Allah kana sararawa, ka bar mu a nan ka je ka huta ka dawo, ka ƙara fresh sosai" Sanin halin raihan, na zolaya ya sanya shi yin murmushi ya ce "Ina wani hutu Raihan? Ina can ma aiki nake yi, haryanzu ban huta ba, zuwa yanzu yakamata ace ku kuke kula da komai, amma sai dai nayi da kaina, yayyenka sun fi mayar da hankali a kan shashashanci". Cikin kulawa raihan ya ce "Ka yi haƙuri, ka daina damun kanka, kai ka ce ƙuruciya ce take damunsu, za su daina". "Zuwa yaushe kenan? Idan ƙuruciya ce kai meyasa ba ka yi?" Raihan ya ce "Haka ne, amma dai kayi haƙuri ka kwantar da hankalinka, abun da su Yaya Salim suke yi, ka ɗauka jarabta ce daga Allah. Kalli shekarunka sun ja, ba hawan jini, ba ciwon suga, ga mu Allah ya baka, ga tarin dukiya da al'umma suke amfana ga Hajiya ga mami dukkan mu naka ne, idan ka duba wannan ni'imomin sai ka ga abun da suke yi bakomai bane ba, dan Allah kar ka saka damuwa a ranka wani ciwon ya kama mana kai". Kallon Raihan yake yi, cikin tsananin soyayya da kulawa, ya tsiyayo tea cup, ya bawa raihan sannan ya ce "Madalla da yaron kirki, nasiharka na ratsa mini zuciya, in sha Allah zan cigaba da yi musu Addu'a" Raihan ya ce "Yauwwa father like no other, we are proud of you, ka cigaba da yi musu addu'a in sha Allah zai zama labari" Alhaji Tahir ya ce "Mahaifiyarka na ganin kamar laifin Hajiya ne ya sanya su lalacewa, amma kamar hajiya na iya ƙoƙarin ta a kan tarbiyya". "Haba Alhaji, kar ka ɗorawa kowa laifi, Hajiya ba ta da sakaci ko kaɗan". "Haka ne, ina son na roƙeka wata alfarma ne". Raihan ya gyara zamansa ya ce "To Alhaji, Allah ya bani ikon yi". Ya ce "Yauwwa, lissafin da muke yi na shekara shekara da manager, da kai nake so ku yi, a fitar da zakka, a fitar da wanda za a biyawa umara, harajinmu na nan gida da sauran ƙasashe, da duk wasu gyare-gyare da zamu yi, idan ku ka gama sai ka kawo mini na duba" Raihan ya ɗan yi shiru yana nazari, "Ya dai na ji ka yi shiru?" Raihan ya ɗago ya ce "Babu damuwa in sha Allah za ayi, zan je na same shi". Alhaji Tahir yayi murmushi ya ce Yauwwa "Babban mutum, ka ga atleast na sake na huta sosai da sosai" Raihan yayi murmushi yana cigaba da zuƙar shayi, nauyi ne mai girman gaske Alhajin ya haɗa shi da shi, dan aiki ne ba ƙarami ba. Ya shanye shayin, ya miƙe tsaye ya ce "Bari na ƙarasa wurin Hajiya mu gaisa" "To shikenan babu laifi" A sanyaye Raihan ya tashi ya nufi sashin hajiya, ba zai iya cewa mahaifinsu a'a ba ne ba, amma wannan aikin kamar yayi masa yawa, ba zai iya jajircewa ya yi shi, kamar yadda shi Alhajin zai yi ba. "Babban mutum ya dai, na ga kana tafiya a hankali, ko yunwa ka ke ji ne?" Ya zauna yana faɗin "Eh, ina ɗan jin yunwa ma, me ku ka yi?". "Ka san halinsu, kowa dafe-dafensa yayi, ni kuma tuwo na saka a ɗumama mini na sha da tea" "To ni ma zan ci tuwon" Ta ce "To bari a kawo, har da man shanu kuwa da yajin daddawa, mai ɗan karen daɗi" Yayi murmushi ya ce "Hajiya kenan, ina su Yaya Sagir?" Ta ɗan rausayar da kai ta ce "Ba su tashi ba". Ya jinjina kai sannan ya ce "Yauwwa Hajiya, kin tuna yarinyar nan ummi? Ƙawar maryam?" Ta ce "Eh, ya aka yi?". "Yauwwa Alhamdilillah, dan Allah me ki ka sani a kanta?" Hajiya ta ɗan yi shiru tana nazarin sa, sannan ta ce "Meyafaru da ita? Me ka ke son sani a kanta?". "Ba wani abu bane ba, mami ta fara faɗa mini abubuwa a kan ta, so ina son sanin if their is way, we can help her, like she's not socially ok" "To ai kaga ƙawar maryam ce, ni kuma ba wani son shiga harkata suke yi ba, amma dai ina ganinsu tare da maryam, yarinya ce mai matuƙar haƙuri da biyayya, kamar babanta ne ko babarta ce ɗaya daga ciki ya rasu, yayan babanta yake riƙonta, matarsa take maltreating ɗin ta, gaskiya i don't know much about her. Na so ace a cikin yaran nan akwai nutsatstse, ai da na haɗa su aure, tarbiyyar ta na burge ni sosai da sosai" "Kin san meya ja hankalina, har na tambayeki?" "A'a sai ka faɗa". "Yadda maryam take yawan bani labarinta, da irin abubuwan da suka din ga yi mata na wulaƙanci suna makaranta, gidansu an yi maltreating ɗin ta, makaranta yara sun yi maltreating ɗin ta, wai wasu lokutan har da malamai, abun bai yi mini daɗi ba wallahi Hajiya" Hajiya ta ce "Shiyasa nake yinka babban mutum, akwai hangen nesa da zurfafa tunani". Cikin damuwa ya ce "Hajiya, kowace halitta da Allah yayi, tana da muhimmanci da kuma amfani, sosai nake jin zafi idan na tuna abun da maryam ke faɗa a kan ta, gaba ɗaya yanayin ta kamar a tsorace take da mutane ma, kuma ni banga muninta ba, baƙa ce kawai, meye abun aibata mutum a kan abun da baka da ikon yin sa?" "Babu kam" "Amma Hajiya kina ganin zan iya taimaka mata?" "Me zai hana? Idan har da ɓangaren da zaka iya supporting ɗin ta, go ahead nima zan yi farinciki da hakan" Raihan ya sake gyara zaman sa ya ce "Wallahi na so maganarki ta farko ta tabbata, ina ma akwai nutsatstse a cikin su yaya salim, da ɗaya daga cikin su, ko shi ko yaya sagir da wani ya aureta" Cikin damuwa ta ce "To ya zan yi, sun ƙi karatu, sun ƙi kasuwa sai shirme, sai addu'a kawai" "Kar ki damu Hajiyarmu, lokaci ne, zasu daina ne in sha Allah, ayi tayi mana Addu'a" Hajiya ta ɗora hannunta kan na Raihan ta ce "Addu'a kullum cikin yi muku ita ake ai, ubangiji Allah ya tsare mana ku" Ya amsa da Amin. Sai da ya ci ya cika cikinsa, sannan ya tashi ya fita. Har ummi ta koma gida, Raihan bai sake nemanta ba, tayi ta duba wayar amma bai kira ba. Dr. Yan gari, yana ta ƙoƙari a kan kausar ta samu admission ita ma, domin kuwa a wannan karon, Farida ta ce ba zata sake aurar da ƴa ba, sai ta fara makaranta, saboda kar a sake kwata irin yadda aka yi a kan inteesar. Suna falo suna kallo, dr. Ya ce lallai ummi ta fito falon ita ma, dan baya son duk suna tare a falo, amma ta din ga ware kanta ita kaɗai a ɗaki. Ummi dai ta zo gefen kujeru ta zauna a ƙasa, tana kallon, wanda a son ranta tafi son zaman kaɗaicin a ɗakinta. Noor ta hana su yin kallon, sai tsalle take a tsakar falon, tana karanta ayar Allahu nooro samawati wal ardi. Abdul ya ce "Noor, dan girman Allah ki zauna wuri ɗaya ki yi karatun nan a nutse". Sai ta koma hawa kan kujera tana dirowa. "Ke dan ubanki ki nutsu" Kausar tayi mata tsawa. Noor ta ce "Babanmu ɗaya" Dr. Ya ce "Lafiya ce wannan tsalle-tsallen da take yi. Farida ta ce "Duk ta bi ta ishi mutane da karaɗin tsiya". Noor ta koma kusa da dr. Ta zauna ta ce "Dr." Ya ce "Na'am shalelena, yau kuma a dr. Na nake" "Ka san me? Wata a ajinmu, babansu ya auro kishiya, yanzu mamanta biyu kenan". Yayi dariya ya ce "Masha Allah, to Allah ya sanya alkhairi ya basu zaman lafiya". Ta gyara zama ta ce "To Abba ni bani da wata maman sai maama, ita kuma ba ta so na" "Tana sonki mana". "Abba dan Allah muma ka auro mana kishiya, nima mamana ta zama guda biyu" Ashar ɗin da farida ta yi mata sai da duk suka razana, ta zaburo zata make noor, amma noor ta tashi da gudu, tana murguɗa kwankwasonta tana dariya, ta tsaya daga can ƙarshen falon ta ce "Wallahi Maama idan ki ka kuma dukana, sai na ce Allah ya sa Abba ya auro kishiya" Farida ta dafe kai ta ce "Na shiga uku da wannan yarinyar, anya nikaɗai aka yi wa tiyata a ɗakin nan ba ayi mini musanye ba, anya yarinyar nan tawa ce? Gaba ɗaya ƴa ba ta da mutunci sai iskanci da rashin mutunci. Kodayake ba laifinta bane ba, tun da aka saka mata sunan bare da babu dangin iya babu na baba, kuma ana koya mata yadda zata wulaƙanta ni". Tsam ummi ta miƙe, dan ta san ƙarshe faɗan kanta zai dawo. Ta tarar da noor a ɗakinta, ta haye wa ummi kan katifa, ta yaye mata zanin da ta shimfiɗa. "Mama" ta kirata kamar yadda take kiranta. Noor ta ɗago ta kalleta. "Meyasa ba kya jin magana ne?" "Me nayi?" Tayi maganar cikin tura baki. "Ban hanaki yi wa maama rashin kunya ba?" Noor ta ce "Ba kya nan jiya ta dakeni, tayi ta zagina". Ummi ta ce "To ai ke ɗin ce ba kya ji mama" "Ina ji mana, ai in dai ta dake ni, cewa zan din ga yi Allah ya sa Abba ya auro kishiya" "Au ba ki ji faɗan da nayi miki ba ko? Zaki ga a auro muku kishiya, idan aka auro wadda zata din ga hanaki abinci, tashi ki bar mini ɗaki tunda ba kya ji" Noor ta ɗan marairaice ta ce "Dan Allah ki yi haƙuri, na daina" Can falo kuwa, ganin farida ta haƙiƙance tana ta bala'i, ya sanya dr. Bar mata falon shi ma. Ya rufe ƙofar ɗakinsa, ya zauna ya ciro wayarsa, ya danna wata lamba, ya kara a kunnensa. Amsa sallamar ya yi, sannan ya ce "Barka da yamma, kuna lafiya?". Yaya maryam ta ce "Lafiya ƙalau ya iyali?" Ya amsa da "Lafiya lau Alhamdilillah, ya mai jikin kuma?" "Jikinta da sauƙi Alhamdilillah, zasu sallame mu ma yau, ta warware zazzaɓin ma babu" Ya amsa da masha Allah "Ranar monday ne appointment ɗin ta na ganin psychiatric doctor ɗin nan ko?" "Eh in sha Allah" "To, ko zaku bari ta ƙara warwarewa daga zazzaɓin, kafin ku je ganin likitan" "To shikenan, ana samun cigaba sosai da sosai, domin kuwa shekranjiya take cewa ita fa kamar ka zo, kamar ta ganka ko mafarki take yi". Dr. Yayi murmushi ya ce "Masha Allah, da haka da haka, in sha Allah zata warware gaba ɗaya, a cikin watan nan zan shigo in ga jikin nata in Allah ya yarda". Yaya maryam ta ce "Ubangiji Allah ya kawo ka lafiya, muna ta godiya Ubangiji Allah ya saka da alkhairi, ya jiƙan magabata". Ya amsa da Amin. Yana ajiye wayar farida na shigowa, ta cigaba da yi masa bala'in idan ma yana da burin ƙara aure ne, to ya san abun da yake ciki, dan taga kamar ya ɗau maganar noor serious. Gaba ɗaya ma dariya ta bashi, dan haka ya shareta ta cigaba da banbaminta *** Haka nan ummi ta ɗan damu, kwana biyu shiru ba Raihan babu labarin sa, ya daina nemanta a wayar ma, kamar za ta damu, kuma ta basar ta manta, ta cigaba da sabgoginta. "Hi dear" taga message ta what's app ɗin ta, what's app ɗin da ta fi ƙarfin sati uku ba ta buɗe shi ba saboda rashin data, sai yau da ta samu ta saka ɗari biyu. Baƙuwar lamba ce, ba ta san waye ba, dan haka tayi replying da Assalamu alaikum. Ta tsaya ta ƙurawa message ɗin ido, hi dear, dear kalma ce da ake iya gaya wa kowa, amma mussman wanda yake da muhimmanci. To ita akwai wani wanda take da muhimmanci a gare shi, da har zai ce dear. Tayi guntun tsaki da ta tuna, akwai mutanen banza a what's app, wanda ba su sanka ba, amma su yi maka maganar banza. Ta cigaba da shirinta na tafiya wurin aiki, ba ta taso ba sai ƙarfe huɗu da rabi, a hankali take tafiya, sai dai wata mota ta cika mata kunne da horn. Ta matsa gefe amma ya cigaba da yi mata horn. Gefe ta koma ta bar wa motar hanyar, ta cigaba da tafiyarta. "A wannan yangar da iyayin naki, sai kin fusata mutum ya ture ki" cak ta tsaya, ta waiwayo da mamaki ta ce "Laa raihan, yi haƙuri ban san kai ne ba". "Eh shi ne ki ka bar mini hanyar, wato na ci kaina, ban isheki kallo ba" Ummi ta ce "Eyya ba haka bane ba, ban san kai bane" tayi maganar tana kallon sa, idonsa yayi ja, kamar daga wani wurin yake. "Wucewa na zo yi, na san sai yamma ki ke tashi, na tsaya ki fito mu tafi". Ɗan shiru ta yi tana kallon sa, ba ta son shiga motar nan tasa, kar a fara zargin wani abu. Ya ɗan marairaice ya ce "Nayi awa a wurin nan ina jiranki, dan Allah kar ki ce a'a". Ta ce "To" tabi bayansa, suka nufi motarsa. Suna tafe a hanya, har lumshe ido take yi, saboda gajiya. "Yaya ummi kwana biyu ko ki neme ni, anya za ayi zumuncin nan da ni kuwa? Na yi busy sosai kwana biyun nan, ko waya bamu yi ba, kuma baki nemi in da ƙanin naki yake ba". "Yi haƙuri ba haka bane ba, zan din ga kiranka in sha Allah". "Allah ya sa, ya karatu ya ɗalibai?" Ta amsa da"lafiya ƙalau Alhamdilillah" "Masha Allah, nima kwana biyu Alhaji ne ya sakani aiki, ya ga ina sararawa bana aikin komai, ina ga gani yayi sharholiya ta yi mini yawa, ya sani aiki ko cikakken lokaci bani da shi, duk na rame na zama baƙi" Ummi ta ɗan yi murmushin yaƙe, cikin fargabar abun da ka iya biyo bayan maganar sa, wataƙila cin zarafin kalar fatarta. Bai damu ba ya cigaba da maganar sa, "Ni fa yunwa ma nake ji, ko mu tsaya mu ci abinci?" Tayi farat ta ce "A'a, na ƙoshi ma ai, a ƙoshe nake ai" "Yaya ummi kenan, da abinci ki ke zuwa kenan? Tun safe fa kina wurin nan, to idan kin zo da abincin ki din ga ci kina rage mini, dan ni yau tun da aka kirsheni a wuri ɗaya tun ina ganewa har na daina, bari na yo takeaway a wannan wurin abincin". Ta ce "To". Ta kai mintuna sha biyar a motar, sannan ya dawo da manyan ledoji, ya tarar ta sauke facemask ɗin ta. "Sannu na bar ki kina jira ko? Tuwo na so in samu, babu sai shinkafa ni kuma damuna take yi" Tayi murmushi ta ce "Kana cin tuwo kenan? Abdul ɗin gidanmu baya son tuwo" "Haba dai, ai yaya tuwo abun so ne, ni a bauchi na saba, Alhajin Bauchi da shi yake karyawa, ga kwanonsa ga nawa, amma shima fa tuwon bana jera kwanaki ina ci yake isata" Tayi dariya ta ce "Ka fi son dai a din ga ccacanzawa" "Yauwwa, ba kullum abu ɗaya ba" Yau dai yayi sa'a, ta ɗan saki jiki kaɗan, dan yau har da dariya. Ya ƙarewa hijjabinta kallo, duk yayi fari takalmin ƙafarta ma ya tsufa. "Ummi" Ta ce "Na'am" "Me ya fi burgeki a rayuwa? Wanda yin sa yake yi miki daɗi, ko samunsa, abun da dai yake saka ki farinciki?" Tayi shiru tana tunani, oho, ita akwai wani abu da take jiran samuwar sa ya sanyata farinciki ne? Duk abun da ya zo mata a rayuwa kawai, karɓa take yi. "Babu" "Ban gane babu ba? Kawai haka ki ke rayuwa ba farinciki?" Ta sunkuyar da kai ta yi shiru. "No dole akwai, ki tuna sai ki gaya mini" "Babu" ta sake bashi amsa. Bai sake ce mata komai ba suka cigaba da tafiya, in da ya ajiyeta wancan karon, ta sake cewa ya ajiyeta. Ya yi parking sannan ya kalleta ya ce "A nan zaki sauke, ba zaki bari na ga gidan ba?" Ta hau wasa da yatsun hannunta bata ta kula shi ba. "Bayan ƴan uwa let's be true friends ummi, ki tuna abun da yake saki farinciki ki gaya mini, mu zama ƴan uwa kuma abokai saboda Allah" "To in sha Allah" Yayi murmushi ya ɗauki leda ɗaya, ya ce "Ungo naki" ta kalleshi zata yi magana, ya ɗora yatsansa a kan laɓɓansa ya ce "Shhh". "Idan zan wuce gobe in Allah ya kaimu zan jira ki mu tafi tare" ta jinjina kai, ta fice daga motar. Addu'a take yi, tana fatan Allah ya sa kar wani ya ganta, cikin ikon Allah babu wanda ya ganta, har security gidan yana banɗaki, ta wuce ta shiga har ɗakinta ba ta haɗu da kowa ba. Ta sauya kaya ta fito, ta dudduba gidan babu kowa, ta koma ɗakin ta duba ledar da Raihan ya bata. Rabin kaza ce guda a cikin ƙatuwar roba, sai shinkafa da salad. Jikin ummi har rawa yake, duk wannan kazar ita kaɗai?. Sai kuma ta yi shiru tana tunani, anya ba ta zura jiki ba? Kasa ci tayi ta tashi ta shiga aikin gida. Abdul ne ya shigo yana waya, ya kammala ya tsaya yana mita. Ummi ta ce "Yaya Abdul kana nan dama?" "A'a yanzu na shigo, wani ɗan rainin hankali ne ya kirani, wai babansu ne ya buɗe shago a tal'udu, suna neman casheir, wanda zai din ga zauna musu da safe zuwa azahar, ko azahar zuwa magariba". Ummi ta ce "Dan Allah yaya Abdul zan yi, ina so" Ya kalleta ya ce "Zaman jiran shagon, shagon furnitures ne fa da kayan kitchen" "Eh yaya Abdul dan Allah, dama na gama SIWES, kawai dai sun buƙaci na cigaba da zuwa ne, dan Allah zan yi" Abdul ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Zan yi magana da Abba, idan ya yarda shikenan". "Yauwwa zai yadda ma in sha Allah" tayi maganar tana addu'ar Allah ya sa Abba ya amince, ita ko kuɗin babu yawa tana so, atleast ta din ga samun na sayen wasu abubuwan da take buƙata. Ta kasa zaune ta kasa tsaye da kazar nan a ɗaki, dr. Gidansa ba ya rabo da nama da kaji, amma tsaf ummi za ta yi aikinsu, farida ta karɓe idan ta ga dama ta sanmata idan ba ta ga dama ba, sai ummi ta zo wanke-wanke ta ɗan tsinci sauran hanta, da diddiga ta lasa abun ka da zuciya. Hankalinta bai kwanta ba, sai da ta saka noor a gaba, ta gaya mata yadda aka yi, kamar sa'arta. Noor ta din ga murna ta ce "Yaya ummi kar ki gaya wa kowa mu cinye abunmu". Ummi da noor suka cinye takeaway tare, suna ta murna, dan kuwa ummi ba ta taɓa cin kaza mai yawan haka ba. Masu nema daga farko dan Allah ku duba a watpad Ayshercool 08081012143 *CUTARWA!* *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* P24 FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK. https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends Masu neman free books ɗina, da free pages duk akwai a kan watpad account ɗina. Irinsu Abduljalal Wata kissar sai mata Wuta a masaƙa Cutarwa Ƙanwar maza Gaba da gabanta Aƙidata Ruɗin ƙuruciya Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata. 08081012143. And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link. https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels Ayshercool. PAID ADVERT!. Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi. Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku Oll types of Turaran wuta Sandal Halut Irik Difur Gab Gab Kajiji Habil Nabak Humra Kulakcha Dilke da kalta Kayan Garan jiki Muna turara Kaya Kujerar garan jiki Kannada Madarorin turare masu kamshi Man garan gashi Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921 *TALLA!TALLA!TALLA!* *INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*. *BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU* *MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA* BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI. 24 Ummi ta kalli noor ta ce "Dan Allah noor kar ki gayawa kowa kin ji" Noor ta ce "Yaya ummi ina da wayona fa, ba wanda zan gayawa wallahi, kazar nan tayi daɗi sosai" Ummi ta yi murmushi ta ce "Yauwwa maman". Raihan kuwa tun da yaje gida, ɗakinsa ya wuce ya samu ya kwanta ya huta, ana kiran magariba ya fice, da aka idar da sallar isha'i, ya tafi gym domin motsa jikinsa. Bai sake komawa gida ba sai wajen ƙarfe goma, ya shiga sashin mami. "Wai yau ina ka shiga ne, tun safe ban sake saka ka a idona ba?" "Kasuwa na je" ya bata amsa tare da ɓoye mata aikin da Alhajinsu ya sanya shi. "Aikuwa ka kyautawa kanka, Allah ya taimaka" ya amsa mata da "Amin" Washegari da sassafe, raihan ko karyawa bai yi ba, ya ɗauki mota ya fita, dan yaje ya ɗauki ummi kar ta makara, dama yau zai zauna da cheif accountant na mahaifinsu su cigaba da aikin da ya saka shi. Ƙarfe bakwai da rabi, ummi ta ga kiran raihan. Ta ɗaga wayar tare da yin sallama. Ya amsa mata ya ce "Ina waje, idan kin shirya ki fito mu tafi" Ummi ta ce "Eyya, sai takwas da rabi nake fita ai, kayi tafiyarka wallahi bakomai, na gode sosai " Raihan ya ce "No, ina jiranki, idan kin kammala sai mu tafi, na zaci da wuri ki ke fita sosai, shiyasa ko karyawa ban yi ba na fito". "Amma ai zaka gaji". "Bakomai take your time" A gurguje ummi ta kammala duk abun da zata yi, saboda kar ta bar shi yana jira, ta juyo abincin breakfast ɗin ta, a flask, lokacin farida ko tashi ba ta yi ba, ta riƙo niƙab ɗin ta a hannu ta fice. Yana zaune a cikin mota, ya kashingiɗa yana danna wayarsa, ta buɗe ta shiga ta zauna. "Raihan, ka yi haƙuri dan Allah, na barka kana jira, na ce ka yi tafiyarka ka ƙi". Ya gyara zamansa ya ce "Ai na ce ki yi a hankali ki shirya a tsanake, shi ne ki ka fito a haka kamar an koro ki?" "Ai bana son in barka kana jira ne, jira babu daɗi, ina kwana ya su mami?". "Lafiya ƙalau, duk suna lafiya, ya gida?". "Alhamdilillah" tayi maganar tana ƙara kintsawa, ya kalli jakarta data buɗe, kamar jakar wanzamai, duk ta tsufa, daga ƴar ƙaramar robar Vaseline sai turare ɗan ɗuri, da tarkacen kuɗin da idan ka tattare su ba su fi naira ɗari da hamsin ba. "Me ma ki ka ce sunana?" Ta ce "Raihan" "Ba rayyan sunana ba fa, raihan" A ɗan marairaice ta ce "Ai haka na ce" Ya ce "Sake faɗa to" Ta ce "Raihan" "Idan na ce iyayi yayi miki yawa ki ce ba haka ba, Kamar rain kamar rayyan ki ke cewa fa" Ummi ta yi murmushi ta ce "Ni dai bana wani iyayi". "To sake cewa raihan in ji" "Ba zan faɗa ba" tayi maganar tana dariya, har dimples ɗin ta suka lotsa. Ya sanya seat belt yana murmushi, ya ce "Meye a cikin flask ɗin nan ne, ƙamshinsa ya cika mini hanci?" Ta ɗago idonta ta ce "Kai na zubowa abinci ka ce baka karya ba, kunun alkama ne da ƙosai, ban sani ba ko zaka iya ci?" "Saboda me ba zan iya ci ba?" "Abincin gargajiya ne, na ƴan ƙauye zaka iya ci?" Juyowa yayi yana kallon idonta, "Ke ƴar ƙauyen ce da ki ke iya ci?". "Eh mana, ni ƴar ƙauyen gagarawa ce jihar jigawa". "Ban ga alama ba, na gode sosai, dan aikin nan ko cikakken abinci bana iya ci, na kasa nutsuwa sai mun kammala, Alhaji ya ga sharholiya tayi mini yawa ya haɗani da aiki, ashe aikin ja ne ba ƙarami ba". "Allah sarki, Allah ya baka ikon yi, ni ko a mintuna goma da zan sake ganinsa ya sakani aikin da na so, sai dai ba zan sake ganin baba ba, Allah yayi masa rahama" Cikin kulawa raihan ya ce "Eyya, Amin ya Allah, Allah ya jiƙansa" Ta amsa da amin na gode. "To mama fa, tana raye?" Ta ce "Ina ga tana raye" "Kamar yaya kina ga? Tana ina ita?". "Rabona da ita tun ina shekara bakwai da baba ya rasu, ban ƙara ganinta ba". "Amma meyasa?". "Bakomai" ta faɗa tare da ƙoƙarin haɗiye wani abu mai ɗaci a ƙirjinta. Ta ɗaga hannunta tana ƙoƙarin sanya niƙab ɗin ta. "Wai shi wannan niƙab ɗin meye amfanin saka shi, kullum ke ko gajiya ba kya yi ne?" Ummi ta ce "Ai saboda idona". "Meye da idon naki?". "Bana son mutane su din ga tanka mini ido, ko fatata, shiyasa idan na saka shikenan ba wanda ya gani, ana cewa idona irin na akuya, ko na mage, duk bana so shiyasa bana son a din ga gani" tayi maganar a ɗan shagwaɓe da take ɗabi'arta, wanda ita a zahiri cikin damuwa ta yi maganar. "Ummi" "Na'am" "Meyasa zaki bari surutun mutane ya yi tasiri a zuciyarki? Ke ki ka yi kanki, duk wanda ya tanka ki, kice masa tubarkallah idan yana da dama ya sauya abun da Allah ya yi miki. Idanunki me kyau ne masha Allah, meye da kalar fatar ta ki, dan Allah idan dan haka ki ke saka niƙab ɗin nan ki daina". Murmushi kawai ta yi, irin ba zaka gane ɗin nan ba, hakan yayi dai-dai da ƙarasowarsu ƙofar gate ɗin wurin aikin su ummi. Ummi ta ajiye masa kayan abincin, ta ce "Na gode sosai, sai anjima" "Idan an tashi ki jirani, saura ki tafi" ba ta ce komai ba, ta buɗe ta fita. Ya daɗe yana nazarin, ta ina zai taimakawa ummi, babanta ya rasu, ba ta san in da mamanta take ba how? Kuma yau ta ɗan sake da shi fiye da da, lallai idan ya cigaba da lallaɓata har ya ƙara saninta sosai da sosai, dan ya fuskanci akwai abubuwa na damuwa sosai da sosai a cikin rayuwarta. Kiran wayar accountant ne ya dawo da shi hayacinsa, ya ja motarsa ya tafi. A motar ya gama karyawa, sannan ya tafi babban office ɗin su, in da suke aikin lissafin. Aiki raihan suke yi, suna ta aikin lissafi, amma rabin hanakalin raihan yana kan ummi. Da suka tashi ma daga aikin, a waje ta tarar da shi, ya zo yana jiranta ya ɗauke ta ya mayar da ita gida. Washegari da safe ummi na ta ɗawainiyar sallamar kowa, masu tafiya makaranta su tafi, ta gama abun da take yi, ita ma ta fara nata shirin, Abdul ya sameta a kitchen hannunsa riƙe da waya. Ya ƙarasa ya miƙa mata wayar, ta karɓa ta kara a kunnenta. Muryar dr. Ta ji ya ce "Mamana" "Na'am kawu ina kwana?" "Lafiya ƙalau, ina ta kiran wayarki baki ɗaga ba" "Caji take yi ina kitchen ne" Ya ce "Ok babu laifi, mamana Abdul ya zo mini da wani batu, wai kina son aikin jiran shago, me zaki yi da wani aikin zaman shago ummi, idan kina da wata buƙata ai gara ki gaya mini, amma zaman shago ba mutuncin ki bane a matsayin ki na mace" Jiki a sanyaye ta ce "To kawu" "Dan Allah ayi haƙuri da maganar nan" "To, in sha Allah an barta" Abdul ya karɓe wayar ya ce "Hello Abba". "Na'am Abdul" "Abba ka san ummi ba za ta ce maka a'a a kan hukuncin da ka yanke ba, amma wallahi tana so, ta gama SIWES, amma sanin ba ta da wurin zuwa ya sanya ta cigab da zuwa, wataran ko kuɗin mota sai na bata, zamanta a gidan nan ba abun da zai ƙara mata sai damuwa da rigima da maama, dan Allah Abba ka ƙyaleta tayi. Kuma ba wani abun fa zata din ga yi ba, tana zaune a wuri ɗaya, dan Allah ka bar ta tayi. Kaga ba ta iya zuwa ta ce na yi mata wani abu". Abba ya ce "Haka ne, to Ubangiji Allah ya yi jagora, na amince amma ka je wurin ka tabattar babu wata matsala, dan nima zan je da kaina na ga wurin, a satin nan zan shigo kanon". "To shikenan Allah ya kawo ka, Abbanmu maganin kukanmu" Ya kashe wayar ya kalli ummi da jikinta yayi sanyi, ya ce "Abba ya amince, zan je na ga wurin, na ce musu zaki yi, sai mu je tare ki ga wurin kema" Ummi ta ce "Alhamdilillah ala kulli halin, na gode yaya Abdul, Allah ya saka da alkhairi" "Bakomai, Ubangiji Allah ya kawo miki babban rabo na alkhairi" tayi murmushi tana sake hamdala. Gaba ɗaya ranar sallar daren da tayi, Allah take yi wa godiya, tare da roƙonsa ya kawar mata da duk wani abun ƙi a lamarin. Washegari Saturday ce, dan haka ba su haɗu da raihan ba sai waya. Da yamma Abdul ya ɗauketa a motar da dr. Ya saya ya ajiye musu saboda zuwa makaranta ko unguwa. Katafaren shago ne, na kayan kitchen da furnitures, manager wurin ya yi wa ummi tambayoyi, Abdul ya sanar masa ummi degree ne da ita, yanzu suna jiran result ne ma. Manager yayi murna ganin tayi kalar haƙuri sosai da sosai. Ya ce mata wurin sabon buɗewa ne, dan haka salarynta dubu goma sha biyar ne. Abdul ya raina dubu sha biyar, ya ce za su je su yi shawara, suna tafe yana mita, ya ce "Yaya ummi ki yi haƙuri, zan samo miki wani wurin in sha Allah, amma wane irin 15k kamar wasan yara" "Dan Allah yaya Abdul ka barni ina so, ko dubu biyar ce zan yi" Ya kalleta ya ce "Haba ummi, you are degree holder fa, kuma a cikin 15k har ki yi kuɗin mota da buƙatu?" "Eh zan yi in sha Allah, Allah ya sanya mata albarka" Yayi ajiyar zuciya ya ce "Amin, bari sai na kira su na gaya musu, na ji yaushe zaki fara zuwa" "Yauwwa yaya Abdul, na gode sosai da sosai" Yayi murmushi ya ce "Sai ka ce na baki kyautar wani abun, Allah ya taimaka". Suka je gida tana ta tunanin da wa zata yi sharing wannan abun farincikin, na samun aiki, ita ba ƙawaye ba, kuma ba abokin hira ba, tayi tunanin ko ta gaya wa raihan, amma sai ta ga hakan kamar ta zaƙe, dan haka ta share shi bata gaya masa ba. Ranar litinin, ta ga kiran wayar raihan ya zo su tafi, wanda ranar zata je ta yi sallama da ƴan wurin aikinsu, ta fara zuwa wancan kanti na furnitures. Tun da ta nufo motar yake kallonta, sannu a hankali, tafiyar ma cikin nutsuwa da yanga take yin ta. Maimakon ta shiga ta zagaya ta in da yake zaune ta ce "Ina kwana?" "Lafiya ƙalau, ina shirin aikin?" "Sai 9 zan je idan Allah ya kaimu, zan yi musu sallama, na samu aiki a wani sabon shago, MIKIYA GALLERY, can zan koma zuwa" Yayi shiru yana kallon ta, ya ɗan rausayar da kai ya ce "Rashin muhimmancin nawa har ya kai abu ya faru ki ƙi gaya mini?". "A'a ba haka bane ba, abun ne bai tabatta da wuri ba" "Shikenan na gode, Allah ya taimaka" yayi maganar ransa a haɗe. "Raihan haushi ka ji, walla.... "Shhhh, na fuskanci na fiye shishshigi, am sorry" yayi maganar yana kunna motar. Ummi ta yi saroro ta kasa magana, ba ta son ace tayi laifi a rayuwarta, mussaman raihan da yake ta ɗawainiya da ita, ba ta zaci za ji haushi ba. "Matsa zan ja motata" A hankali ta ja da baya, ya ja motar, yana kallonta ta mirror, ta tsaya kamar sokuwa tabi motar da kallo. A hankali ya furta 'Lets see, if it will works' Jiki a sanyaye ta din ga gudanar da al'amura ranar. Ta je sabon wurin aikinta, sai dai hankalinta baya jikinta, ta din ga kiran wayar raihan, amma yaƙi ɗagawa. Whats app ta koma, ta yi masa message nan ma bai amsa ba, sai dare sannan ya kirata. "Raihan dan Allah ka yi haƙuri, ban san zaka ji haushi ba, ka yi haƙuri mana". "Yaya ummi ba sai kin bani haƙuri ba, laifina ne da nake yi miki shishshigi, duk da yanayinki na rashin son mutane". "A'a ba shishshigi ka ke yi mini ba, ka yi haƙuri mana" Ya wani hura hanci ya ce "Ok, Allah ya taimaka". Ta ce "Yauwwa na gode, zan din ga gaya maka abu idan ya faru" Ya ce "Promise?" "In sha Allah " "To shikenan, abu na daɗi ko akasin haka, kar mu ɓoyewa juna" Ummi ta ce "To" "Good dear, gobe in Allah ya kaimu zan zo na ga wurin" Tayi murmushi ta ce "To Allah ya kawo ka" "Amin, goodnight" suka yi sallama tana jinjina daru irin na raihan. Status take kallo, ta kai kan status ɗin raihan, yana tsaye a gym, ya tsaya a jikin mudubi yayi hoto, daga shi sai gajeren wando, ya ɗaga wani ƙarfe jijiyoyin jikinsa duk sun ɗaga, ga cikinsa ya rabu kashi shida (six packs) ga ƙirjinsa kwance da gashi har saman cikin sa. Tayi reply da "Babban mutum meye haka?" "A ina?" "Ka saka hotonka babu kaya, ba mutunci a haka, dan Allah ka cire" Ya amsa mata da "Ai ni ba mace bane" "Duk da haka, manya ba sa haka, a cire dan Allah 🙏" Yana daga kwance yake murmushi, ya ce "To shikenan, an gama babbar yaya, in sha Allah ba zan sake sakawa ba". "Yauwwa babban mutum, Allah ya yi albarka ya kula da rayuwarka" "Amin ya rabb yayata, godiya nake Allah ya kula mini da ke" "Amin tare da kai" ta ajiye wayar tana murmushi. Washegari har shagon ya je ya tarar da ummi, sai dai ya ji daɗin ganinta a kauwwame a wuri ɗaya, ba wani aiki take na wahala ba. Ya samu wuri ya zauna suka gaisa da manager, ya hau yi wa ummi hira. Da farko a ɗan tsorace take, ko manager zai ce tayi laifi, amma yaga bai ce musu komai ba, har lokacin tasinta yayi, yana wurin. Da suka fito ya kalleta ya ce "Wai nawa zasu din ga biyanki ne?" Cikin murna ta ce "Dubu sha biyar duk wata" "Me?"yayi maganar yana yatsune fuska. "Dubu sha biyar" ta maimaita masa. "Share-share zaki din ga yi ne? Ki zo ki wuni a dubu sha biyar, duk girman shagon nan dan son kai". Ummi ta waiwaya ta ga babu wanda yake jin su ta ce "Kayi a hankali, dubu sha biyar ina laifi, da waye ya bani?". "Degree holder da aikin dubu sha biyar a wata, me 15k zata yi miki a wata, mussman ku mata masu tsarabe-tsarabe, ni fa a wata data da katin waya na dubu ashirin nake sawa zuwa sama" Ummi ta buɗe baki tana kallon sa, saboda abun ya ɗaure mata kai, har ya kaita gida mita yake yi, yana nanata dubu sha biyar ta yi kaɗan, tayi masa shiru taƙi kula shi. Dan in dai shariya ce ummi ta ƙware a wannan fannin. "Ni ki ka share ko, wato idan na gaji na yi shiru?" gyara zamanta tayi tana cigaba da kallon window. A hankali ya ce "Miskili ka fi mahaukaci ban haushi". *** Misalin ƙarfe goma sha biyu da rabi na dare, raihan da mahaifinsu, chief accountant da sauran accountants mutum biyu, lawyoyin Alhaji Tahir su biyu, sai kuma manajojinsa, zaune a wani katafaren office, ko ina fitilu kamar rana, kowa gabansa da ruwa da lemo, gefe ga flask na shayi, gaba ɗayansu raihan ne kawai yaro a cikinsu. Ɗaya bayan ɗaya kowa ya din ga gabatar da bayaninsa n shekara a kan ɓangaren da yake jagoranta. Suka kammala tsaf, sannan raihan ya tashi, ya yi connecting system ɗin sa da projector, ya fara bayanin abubuwan da ya tattara daga bayanan su, ribar da suka samu a shekarar, ya tabbattar wa da mahaifinsu duk sun bibiyi shige da ficen kuɗi na shekarar, kuma sun yi dai-dai da bayanan da abun da kowane accountant yayi presenting. Ya ware harajin da zasu biya, na ciki da wajen Nigeria, ya ware kuɗin zakka, kuɗin abun da ake rabawa ma'aikata na riba bayan albashinsu, abubuwan da suke buƙata, kuɗin duk wani abu da ya shafi sadaka da makamantansu, da kuma kuɗin umara na mutum goma, kamar dai yadda Alhajin ya umarce shi. Tafa masa Alhaji Tahir ya hau yi, ya ce "Ƙaraminsu babbansu, am so much proud of you, ban zaci zaka iya ƙoƙari haka ba, saboda na san aikin ba ƙarami bane". Chief accountant ya ce "Ni kaina ya bani mamaki, yayi ƙoƙari sosai da sosai, na bi duk abubuwan da yayi, kamar dai yadda ka saba ne, yayi iya yin sa, kuma da alama zai kamanta adalci kamar dai kai, sai dai rigimamme ne" Alhaji Tahir ya yi murmushi ya ce "Ai na san halin kayana" suka yi dariya baki ɗaya. Suka ƙarasa tattaunawa, da bibiyar abubuwan da Raihan ya gabatar, daga bisani Alhaji Tahir ya ce kowane ɓangare su rubuto abun da suke buƙata, na gyara ko makamancin haka, raihan zai duba, shi zai je hutun taƙaitaccen lokaci. Duk suka gamsu da abubuwan da aka tattauna, tare da yi wa Alhaji Tahir addu'a saboda mutum ne mai farantawa ma'aikatansa, dan ya ce abokan nemansa ne, bayan iyalansa ba shi da sama da su. Dirver ya ɗauke su zuwa gida, a hanya raihan ya ce "Alhaji" "Na'am babban mutum" "Tsakani da Allah aikin nan da wahala, kuma ko murmurewa ban yi ba, ka ce a kawo mini duba wani abu, ni fa ban san komai ba, dan Allah a kaiwa su yaya sagir, gaba ɗaya ƴan kwanakin nan saboda aikin nan, ko bacci bana yi sosai" ranƙwashin da Alhajin yayi masa ne ya sa shi yin shiru yana kallon sa. "Kana da nasibi a kan harkar kasuwanci raihan, amma wasa da shiririta sun yi maka yawa, da aikin kashe-kashen kuɗi, office zan baka a head branch, a din ga baka salary" Cikin sangarta ya ce "A'a dan Allah, shagona fa da nake ta processing, ka fa bani jari rance, ka manta, kayana sun kusa zuwa fa". "Na sani raihan, akwai abun da nake targeting ne" Raihan ya ce "To, Allah ya taimaka, amma ba sai na sake duba wani abun ba ko? Kuma ba sai na yi maka aikin ba ko?". "Sai fa ka yi, gara ma ka shirya" Raihan ya kifa kansa ya ce "Wayyo mami, dama ban dawo kano ba" Alhaji Tahir yayi dariya ya ce "Ko ina ka tafi, i know how to deals with you, Munnir ya sangarta ka, kashe kuɗi kawai ka iya, baka iya nema ba" yayi maganar yana murɗe masa kunne. Raihan ya ɗago da sauri ya ce "Ka tambayeshi ka ji, na sayar da agoguna, na sayar da takalma, kuma na tara kuɗi" Alhaji Tahir dariya kawai yake yi wa raihan, so yake dole sai ya zame, kuma ya san dalilin sa na yin haka, dan raihan akwai biyayya in dai abu zai faranta masa rai zai yi, da mamansa ne ma suke faɗa wasu lokutan ba su fiye shiri ba, idan ta zo da abu na son zuciya, ya ce ba zai yi ba. Duk da ummi ta ɗan girmewa Raihan, sannu a hankali ya nuna mata shi namiji ne, domin kuwa yafi ummi wayo nesa ba kusa ba, dan bata ankara ba, suka yi wani irin mugun sabo da ita da shi, duk ɗari-ɗarinta da shi, ta sake jiki da shi, dan barkwancinsa kawai nishaɗi yake saka ta. Kullum a wurinta yake karyawa, da safe sai ta tafi masa da abinci, kuma cikin ikon Allah babu wanda ya sanya mata ido ya lura da shige da ficenta. Shi kansa raihan a tarayyarsa da ummi, ya san tana da baki dan tana magana tana tsoron yi ne, saboda yanayi na yadda al'umma suke karɓar ta. Idan suna hira, wasu lokutan manager sai ya kalleta ya ce "Wai ummi dama kina da baki haka?" Sai ta yi shiru ta daina maganar cikin jin kunya. Gaba ɗaya ta daina jin nauyin raihan, haka kurum sai ya zame daga office, ya taho wurin aikinta, manager har tambayarsa yake "Wai kai Raihan baka sana'a ne? Kullum kana liƙe a wurin ummi?". Kasancewar manager matashi ne, da kaɗan zai girmewa ummi, ƙanin mai shagon ne, dan haka Raihan ya ce "Eh ni bani da sana'a, zaman banza nake a yanzu, shiyasa kullum muke tare da ita". "Ta ce Abdul yayanta ne, kai kuma ƙaninta, anya ba ka girmeta ba kuwa? Ka yi ta mata wayo, ta zo da ɗan abincinta, ta ajiye maka ka zo ka cinye, ka hanata sakat da surutu, ka zo in baka aiki kaima". Raihan ya ce "Allah ya kiyaye in yi aiki ku biyani dubu sha biyar, dan wayo, dan kun ganta saliha, ai ta kusa daina aikin nan". Manager ya ce "Ai tawakalli ta fika, shiyasa take aikin, kai ka raina sana'a, kullum kana liƙe da ita, ka cinye mata abinci, kuma kana jiran a biyata ka karɓe mata kuɗi". Raihan ya ce "Wai manager abincin nan daga gidanka ake kawo wa ne? Ina ruwanka ne ka dameni fa" Idan suna abun su shi da manager, sai dai tayi ta dariya, kamar sako da sako manager komai sai yayi magana, shikuma raihan baƙar magana da neman tsokana. Ummi na jin daɗin aikinta a wurin nan, ko albashin farko ba a bata ba, amma manager yana daga cikin mutanen da suke mutuntata, bai taɓa nuna mata ƙyama ba, kuma tana iya ƙoƙarin ta wurin kula da coustomers ɗin su, idan ta je da wuri ba ruwanta, har share-share yi take yi tayi mopping gaba ɗaya ba ta da damuwa. Zamanta a wurin yana rage mata damuwoyi da yawa. Yanzu ma tana ta bawa raihan labarin rigimar noor, ba ta da wata hira sai ta noor. Cikin nishaɗi take hirar, Raihan yana kallonta, ya ce "Ya aka yi haƙorinki ɗaya ya ɓalle ne? Ko dai da kina yarinya kin yi rashin ji ne?" Ta yi murmushi tana dariyar yaƙe, da tuna yadda aka yi haƙorin ya ɓalle ranar salla ta ce "A ƙaddara bana jin magana ne, na taho da gudu ranar salla, na faɗa cikin kwanuka na buge baki da tukunya, haƙorin ya ɓalle" tayi maganar tana tuna yadda idiris yayi ball da ita ranar. Raihan yayi dariya ya ce "Ai da alama, kuma fa da ya ɓalle ɗin yafi kyau, amma dai mijinki sai ya rage sadaki, saboda ɓallewar haƙorin nan, duk da ta wani fannin sai ya ƙara, tun da kina cikin matan da malaman fiƙhu suka ce a ƙarawa sadaki". Basar da zancen tayi, saboda jin zai ɗaukko wani babban karatu mai nauyin gaske, ita ina ta ga ko saurayi balle ayi zancen ƙari ko ragin sadaki, ita da tun da take, ba wanda ya taɓa cewa yana sonta?. Raihan yayi mugun sabo da abincin ummi, kusan kullum a wurinta yake karyawa, ba tare da ya san abincinta take sadaukarwa ta bashi ba. Suna tafe a hanya ta ce "Raihan, manager ya ce a satin nan fa za a biya salary" "Dubu sha biyar ɗin ki ke wa wannan washe bakin?" "Eh mana, idan Allah ya saka mata albarka zaka sha mamaki". Ya ce "Oho dai, amma dubu sha biyar ya fi kuɗin mayukan da zaki shafa a sata" ta ware ido ta ce "Ni ɗin? To wallahi vaselin nake shafawa ko man kaɗanya" Yayi murmushi ya ce "Amma zaki kai ƙaninki shopping ko? Muje ki yi mini sayayya" "Me ka ke so in saya maka?" Raihan ya ce "Sai mun je sai in zaɓi abun da nake so" Ta ce "To shikenan, in sha Allah idan aka biya sai mu je, nima na je shopping ban taɓa zuwa ba fa, to ina zamu je?" "Ki yi tunanin in da ki ke so mu je" ta jinjina masa kai tana ta murmushi, wai duk saboda dubu sha biyar take wannan farincikin. "Yauwwa, ya ake ciki da aikin Alhaji kuwa?" Ya ce "Hmm kin san ya kuma haɗa ni da wani, alhakin fitar da zakka, da mutanen da zai biyawa umara da aikin hajji" Ummi ta ɗan yi shiru ta ce "Masha Allah, sai ka tsaya ka ji tsoron Allah, kar ka bari son rai ya shiga lamarin, wataƙila ya yi hakan ne dan ya gwadaka, ka bawa wanda suke buƙata kayi adalci" "Haka ne ya sayyada, shiyasa ban so ya sakani ba, kin san ina da yayye, kamar ba zasu ji daɗi ba tun da su ne manya, tunda ki ka ce ina ma zaki sake ganin baba ya saki aiki, zaki yi farinciki, sai na sha jinin jikina, komai lokaci ne, wataran da kuɗi nima zan nemi na ganshi ya sakani aiki, ba zan ganshi ba" Ummi ta ce "Wannan haka yake, Allah ya ƙara masa lafiya da nisan kwana, ya yalwata arzikinsa" "Amin ya Allah sayyada" *** Kamar kullum sai da ya mayar da ita gida, sannan ya koma office ya cigaba da ayyukan sa, bayan la'asar ya koma gida. Mami na ganinsa ta hau murmushi, wanda har hakan ya bashi mamaki, ya ce "Mami na ga kina ta fara'a" Ta ce "Ashe kai Alhaji ya saka duba mutanen da za a bawa zakka, da wanda za a kai umara bana, har da aikin hajji mutum uku?" Ya kalli mami ya ce "In ji wa?". "In ji ubanka, da baka gaya mini ba, ai ni mijina ne ya gaya mini" Ya ɗan yi miƙa ya ce "To shikenan tun da ya gaya miki" Mami ta ce "Ohh, Allah dai ya cika mini burina, to su wa ka zaɓa? Dan ina da vacancies". Ya dubi mami ya ce "Vacancies kuma, na me?" "Ahh wanda za a bawa zakka mana da wanda za a kai umara har ma da aikin hajji". Raihan ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Amma ni mami, duk a gidanku su Anty Saude, ba wanda ba a kai aikin hajji ba wasu umara, ƙawayenki kuma duk suna da rufin asiri, to wa kuma za a baki? Ai gara a kai waje wasu ma su amfana" Ta ce "Kai dalla yi mini shiru, nima na san waɗanda suke da buƙata, ka bani vacancies, da kuma kuɗin da zan bayar nima, duk shekara Alhaji yana bani, maganar ma na yi masa ya ce kai ya bawa wannan damar". Raihan ya ɗan ɓata fuska ya ce "Haba mami, dan Allah me zaki yi da kuɗi? Zan baku vacancies huɗu, ke biyu Hajiya biyu shikenan, kuɗin zakka kuma gaskiya ba zan iya baki ba, an ware percentage ɗin share ku fa, a ribar da aka fitar ta shekara za a baku" Mami ta shiga tafa hannu, ta ce "Raihan, wai tsaya ni da hajiyar nan muka yi naƙudarka, da komai sai ka daidaitani da ita, kuɗin mijina ka ce ba zaka bani ba Raihan, shikenan ba zan kyauta ko sadaka ba nima?" Ya miƙe yana zumɓura baki ya ce "Dan Allah mami kiyi haƙuri, nifa ba haka muka yi da Alhaji ba, what if gwadani yake yi, wallahi kin fi Hajiya yawan ci masa kuɗi ma, haba mami dan Allah" sai ta kasa magana ta bi shi da kallo, gashi dai ita ta haife shi, amma idan ya botsare, wasu lokutan kasa magana take yi, dan bata san dalilin da ya sa yake yi mata kwarjini ba wasu lokutan, idan ta yi ba dai-dai ba ɓaro-ɓaro yake gaya mata. Manager ya kira ummi a waya, ya ce ta turo account number zai tura mata kuɗinta na albashi. Bata da account number, dan haka ta kira raihan jikinta yana rawa dan farinciki ta ce "Raihan, manager ya ce na tura account number, zai turo mini salaryna, amma bani da account, ka bani naka na bashi" Yayi dariya ya ce "Gaskiya banki za su rufe mini account ɗina idan aka saka dubu sha biyar, ni kuɗi idan bai kai dubu ɗari ba, basa shiga account ɗina". Ta ce "To ko kawai in bari sai da safe idan Allah ya kaimu, idan na je sai ya bani a hannu kawai ko?". "Ina da lambarsa zan tura masa, amma dan Allah kar ki kasa bacci saboda dubu goma sha biyar, kuma kar ki manta kin yi mini alƙawarin zaki kai ni shopping". Ayshercool 08081012143 What's app only please 🙏        *CUTARWA!* *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* P25 FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK. https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends Masu neman free books ɗina, da free pages duk akwai a kan watpad account ɗina. Irinsu Abduljalal Wata kissar sai mata Wuta a masaƙa Cutarwa Ƙanwar maza Gaba da gabanta Aƙidata Ruɗin ƙuruciya Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata. 08081012143. And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link. https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels Ayshercool. PAID ADVERT!. Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi. Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku Oll types of Turaran wuta Sandal Halut Irik Difur Gab Gab Kajiji Habil Nabak Humra Kulakcha Dilke da kalta Kayan Garan jiki Muna turara Kaya Kujerar garan jiki Kannada Madarorin turare masu kamshi  Man garan gashi  Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702   08025453921 *TALLA!TALLA!TALLA!* *INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*. *BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU* *MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA* BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI. 25 Cikin murna ummi ta ce "Ban manta ba, in sha Allah zamu je, nima ina son mu je". "To kin zaɓi in da zaki kai ni ɗin?". "A'a ai ni ban san wuraren ba, ko ina ne ma kawai sai mu je" Yayi dariya ya ce "To shikenan, amma dai dan Allah ki kwantar da hankalinki, ki yi bacci a nutse kar ki kasa bacci saboda 15k, you are not ɗangote yet, kar ki kasa bacci saboda 15k dan Allah" Ummi cikin halinta na yanga da ita ba ta gani ta ce "Kar ka dameni fa, ce maka aka yi ba zan iya bacci ba, kuma ko naira goma ce tunda ita ce gumina ai ita ce arzikina dole na yi murna" "Ahaaf, ai na san ba iya bacci zaki yi ba saboda dubu sha biyar, to dai ki nutsu da ƴar 15k ɗinki kin kasa rufe baki". "Ai kuma sai ka yi, ba kula ka zan cigaba da yi ba" Sosai yake yi mata dariya, noor ce ta shigo ɗakin ta ƙure ummi da take dariya da ido. Cikin diriricewa ta ce "Raihan sai da safe". "Akwai matsala ne?" Ta ce "A'a zan yi wani abu ne" ta katse wayar tana kallon noor. Noor ta ƙarasa ta zauna ta ce "Yaya ummi da wa ki ke waya ne?" Ummi ta ce "Amm ɗan ajinmu ne" Noor ta waro ido ta ce "Ke fa ki ka ce ƴan ajinku ba sa kulaki, kuma ba kin daina zuwa makarantar " "Kai maman ƙarya nake yi kenan?" Noor ta ce "A'a, to amma me ku ke cewa na ga kina dariya, ban taɓa ganin kina waya kina dariya haka ba, ko kema saurayin ki ka yi?" Da sauri ummi ta girgiza mata kai alamar a'a. "To me ku ka ce a wayar" Ummi ta ce "Noor kin fa isheni, magana muke za a bani salary ne, shi ne nake dariya, ai kiwa yana son kuɗi, ko ke ba kya so?" Noor ta ce "Ina so mana, zamu ci daɗi ashe" "Sosai ma" ummi ta yi maganar tana murmushi. "Kin san me yaya ummi?" Ummi ta ce "Sai kin faɗa maman" "Inteesar ce ta zo fa yanzu" ummi ta ɗan waro ido, ta kalli agogon wayarta ƙarfe goma da rabi na dare. Ta basar ta ce "Inteesar kawai ko? Ba na hanaki ba, ba zaki ce mata anty inteesar ba?" "Kema ai ummi take ce miki, kamar fa kuka take yi, sun shige ɗaki ita da maama, na je in ji meyafaru wai in fita har da ce mini munafuka". Ummi ta kwantar da noor ta ce "Shhh maza yi bacci, kar in sake jin bakinki, hakan gulma kenan kuma haramun ne babu kyau" Noor zata sake magana, ummi ta riƙe mata baki, tayi murmushi ta lumshe idonta kamar zata yi baccin. Ummi ta kashe musu fitila, ita ma ta kwanta, amma noor ta tashi ta lallaɓa kunnen ummi ta ce "Wai mijinta ne zai auro mata kishiya, uncle sagir" ta sauka daga kan katifar ummi ta fita da gudu. Sai da gaban ummi ya faɗi, ta san akwai tashin hankali kenan, tun da aka ce za a yi wa ƴar gwal kishiya, tayi saurin kawar da tunanin daga ranta dan ba huruminta bane ba. Maganar raihan ta tuna, wai kar ta kasa bacci, saboda dubu goma sha biyar. Dariya abun ya bata, ta gyara kwanciyarta ta shiga karanto addu'oin kwanciya bacci. Aikuwa da safe da ta tashi, ta ga inteesar a gida, idanuwanta sun kumbura alamar ta sha kuka, kuma ba ta samu isasshen bacci ba. Ummi ta gaisheta, ta amsa mata sama-sama. Daga haka ummi ba ta sake shiga sabgarsu ba, dan ta ga alamar ƙiris suke jira tayi wani abu, su huce a kanta, dan haka ta kama kanta, ko sallama ba ta yi musu ba ta fice. Ɗan halak yana in da suka saba haɗuwa yana jiranta. "Ina kwana" ta gaishe shi, sai dai maimakon ya amsa ya ce "Inye ka ga attajirar garin nan, ke fa yau jin kanki ki ke yi daidai da kowa, saboda kina da 15K" Ummi ta ce "Ka cigaba, tuwo ne yau a cikin flask ɗin nan, wannan kuma kunun tsamiya, ka cigaba da tsokanata ba zan baka ba" Ya kwashe da dariya ya ce "Aikuwa sai na ci abincin nan, kuma ba zan daina tsokanar ki ba" "Sai ka ci in gani ai" Raihan ya kunna motar ya ce "Girmata fa ki ka yi, ba fin ƙarfina ki ka yi ba, ƙwace abincin nan ba wahala zai bani ba". Ummi ta ce "Idan ya zube shikenan ba". "Kar dai ki manta kuɗinki account ɗina za a tura su, attajirar duk duniya". Ummi tayi dariya tana kallon window. Suna zuwa wurin aikin ummi, raihan ya ce a wurin zai ci abincin, idan ya tafi da shi ba zai ƙoshi ba. Suna shiga wurin bayan sun gaisa manager ya ce "Ummi, an saka miki kuɗin nan fa" Raihan ya ce "Eh, sun shigo sai ka ce wasu kuɗin kirki, gaskiya manager a ƙara kuɗin nan, haba 15k yafi ta sai man shafawa da cingam". Ummi ta kalli raihan ta girgiza masa kai ta ce "Manager na gode sosai da sosai, Allah ya ƙaro mana coustomers, dan Allah kar ka damu da abun da raihan yake faɗa, Allah ya sanya musu albarka ka san yaro ne, sai a hankali" tayi maganar tana kawar da kanta gefe tana dariya. Manager ya kwashe da dariya ya ce "Ai shiyasa bana biye masa, baƙinciki yake yi miki, shi yana zaman banza, wallahi ko kati kar ki saka masa". Kallon ummi raihan yayi ya ce "Me ki ka ce mini yanzu?" Juyawa ta yi tana dariya, ta nufi wurin da take zama, tayi aiki. Aikuwa ya bi bayanta, yana sake cewa "Maimaita me ki ka ce mini yanzu?" Ta ce "Na yi magana ne?" Ya ɗan tsuke fuska ya ce "Ki maimaita". Ummi ta kalli raihan ta ce "Yaro, ko ba yaron bane?" ta sake maganar tana yi masa dariya. Kyau ya ga tayi masa dariyar da take yi, haƙoran nan sun haska fuskarta sosai, ga laɓɓanta pink shar, dimples hagu da dama a kumatunta. Yadda ya tsaya yana kallonta, ya sanya ta zata, ko haushin yaron da ta ce ya ji, dan haka ta sake cewa "Lokacin da ka ke tsokanata, daɗi ka ke ji ai, nima yanzu is my turn". Yayi wani irin murmushi ya ce "Wai shekara nawa ki ka bani ne? Na san dai maryam ta girmeki". "Ba za a lissafa ba, koma dai yane kawai na girmi mutum, kuma idan kana son ka yi albarka ka din ga yi mini biyayya ka daina tsokanata" Ya ja kujera ya zauna, har cikin ransa yake jin daɗi idan ya ga ummi ta sake da shi tana dariya, saɓanin da da kullum kamar a tsorace take da mutane, da farkon haɗuwarsu ne, ko haɗa ido ba za ta iya yi da shi ba, amma yanzu da confidence take gaya masa abu. A ransa ya ce 'Irin wannan confidence ɗin nake son ki samu, a cikin mutane" Manager ya ce "Kai raihan, ka wani je ka gurfana a gabanta, zaka kalallame ta ka cinye mata kuɗi, to ahir ɗinka" Raihan ya ce "Manager, idan na waiwayo kanka ba zaka ji daɗi ba, yau ka sa an kirani da yaro, duk girman nan nawa, the whole me aka ce mini yaro, ke kuma ai shikenan ban abincina in ci, shima dan ba zan iya fushi da abincinki ba, da yasin ba zan ci ba" yayi maganar cikin sigar shagwaɓa. Ummi ta yi ƙasa da murya tana kallonsa ta ce "Haba kar aji kanmu ayi mana dariya, ci abincinka ko manager kar ka yi wa bisimillah" "Dama shi ya isa?" Ummi ta tashi tana ta  ɗawainiya da coustomers, raihan yana cin abinci, suna yi suna faɗa da manager. A hanya ummi take yi masa faɗa kuma ta haɗe rai kamar wata babarsa "Raihan, ka ce Alhaji ya baka aiki, amma sai ka zo wurina ka yi zamanka ka ƙi yi masa aikin, ko office ɗin fa baka zuwa, meyasa?". "Haka aka ce miki bana zuwa?" "To yau ka je ne? Zama fa kawai ka yi a wurin aikina, yakamata ka kammala yi masa aikin nan on time, sai shiririta ka ke yi" Raihan ya ce "Nifa ba shiririta nake yi ba" "To aikin ka ke yi? Banda surutun ƙwallo, me ku ka yi kai da manager? Gobe in Allah ya kaimu ka je office ka yi aiki, idan ba haka ba, ni da kai ne, ba zan kai ka shopping ɗin ba, kuma na daina bin ka mu tafi aikin tare" Raihan ya ce "Gidanmu dai ni ne autan maza, kuka zan tayi miki, kuma ke da Alhajinmu kin saka babban mutum kuka" Ummi ta ce "Ai bulala zan samu, na zaneka ka yi kukan da dalili, Alhaji ba zai ce komai ba" "Wallahi ummi ina iya ƙoƙarina, Alhaji ashe aiki yake tuƙuru ba kaɗan ba, dare nake bi in yi, bana son zaman office ɗin ne saboda kowa sai ya kawo mini abun da suke buƙata, na son zuciya, na rasa yadda zan yi musu, ni ba Alhaji bane cewa nake ba zan yi ba, kuma sai su zagaye su kai ƙarata. Sai wahalar da ni ake yi, wallaahi ji nake kamar na lallaɓa na gudu bauchi, amma kawai mun riga mun wani saba, ba zan iya tafiya na bar ki ba, ba zan din ga cin irin abincinki ba" Ƙuri ummi ta yi da ido tana kallonsa, wai yau ita ce a rayuwa wani zai ce yayi sabo da ita, da ba zai iya nesa saboda ita ba, babu dangin iya babu na baba, Allah sarki. "Ki ke kallona ki bani shawara mana" Tayi ajiyar zuciya ta ce "Kamar yadda na gaya maka a baya, kar ka nuna wa Alhaji gazawarka, ka yi haƙuri ka daure, da haka zaka san zafin nema, kuma kar ka kuskura ka yi zalunci dan ka farantawa wani rai, ka yi abun da ka ke ganin ya dace, amma dan Allah ka janye maganar guduwa bauchin nan" "Saboda me?" Ta ce "Kawai, Alhaji ba zai ji daɗi ba" "Shikenan, ranar da ki ka tashi da wuri, zaki rakani zagaya ƙananan branches ɗin mu, daga nan sai mu je sayayyar, kamar jibi in Allah ya kaimu ko gobe yayi?" Ta ce "Eh, Allah ya kaimu, amma dan Allah a cikin kuɗin ka bani ko dubu ɗaya ce idan ban takura maka ba, na sai kayan miya da kaina in yi wa kawu girki, yau zai dawo na saya wa mama noor chocolate, idan ya so ranar da muka je sayayyar sai in siya wa kawu wani abun, da ƴan gidanmu ko?" "Eh har da gori zaki yi mini, saboda kina da 15k, dan kuɗinki yana wurina, bari a samu POS na baki kuɗinki kan ki tara mini jama'a". "Ni ba haka nake nufi ba fa, to yi haƙuri, sonake kawai na farantawa kawu" "Albashin naki har nawa ne da zaki yi ta rabo? Daga kawu sai noor da ni zaki sayawa abu, idan aka kuma biya sai ki sayawa sauran, kuma ni duk wata sai kin saya mini abu". Ba musu ta ce "To" "Me zaki dafa wa Kawun ne?". "Haryanzu ban gama tsarawa ba, amma ina ga alkubus zan yi masa, da miyar ganye yana so sosai". "To nima zan ci". "To shikenan, idan na gama zan kiraka a waya, amma kar ka ƙaraso gida ka kira ni a waya, sai na kawo maka". "Meyasa ba zan ƙaraso gidan ba?" "Amm, saboda kar a ganka ace wani abun" Raihan ya ce "Saboda ni ciwo ne?" Ummi ta ce "A'a ba haka bane ba" "Salma" ya kira sunanta kai tsaye abun da bai taɓa yi ba" wani yarrr ta ji a jikinta yadda ya faɗi sunan. Ta waro ido ta ce "Salma kuma?" "Ba sunanki ba ne?" "Kuma sai ka faɗa gatsal, ina yayan ni ka daina kirana haka, yaya ummi zaka ce" Yayi dariya ya ce "Eh to sannu uwar son girma, ba za a faɗa ɗin ba". "To ba zan yi alkubus ɗin da kai ba". "Kuɗinki kuma suna wurina ba, in sai data da kuɗinki" "To ai ba damuwa zan yi ba idan ka yi hakan". "A'a kar ki zo kina yi mini kuka". Sai kuma ya ce  "Amma ummi kamar akwai matsala yanayin zamanki a gidanku ko?" Bata amsa masa ba ta kalleshi. "Ba sonake na ji sirrinki ba, mun wuce wannan zuwa yanzu, yadda wasu abubuwan suke gudana, duk da ni yaro ne ina fuskanta, dan Allah duk wani abu da zan yi idan zan janyo miki matsala ki gaya mini, kar a ɓata miki rai saboda ni ba zan ji daɗi ba" Bai jira amsarta ba, ya canza hirar har ta ware. Suna tafe suna hira suna dariya, suka tsaya wurin masu kayan miya, ta sayi abubuwan da take buƙata ya biya, a tunaninta a cikin kuɗinta ne. Tana zuwa gida ta tarar da kawun a gida, ummi ta ce "Kawu, na ɗauka sai yamma fa zaka dawo, na yi cefane zan yi maka abincin dare" Yayi murmushi ya ce "Mamana ta kaina, dawowa ce ta kamani da wuri". Ummi ta risuna ta ce "Kawu an biyani salary, shi ne na yi cefanen alkubus" "Allah dai yayi miki albarka, amma cefane nawa ne ummi, ki riƙe kuɗinki ki yi buƙatunki kar ki ce zaki din ga kashewa a gidan nan". "Kawu ka sanya albarka" tayi maganar tana murmushi tana jin ƙwarin gwiwar yin magana kamar tana tare da raihan. Dr. Ya ce "Allah ya yi albarka" "Amin na gode sosai " ta miƙe ta nufi kitchen, farida kuma sai kwaɓe fuska take yi tana hararar ummi babu dalili. Bayan sallar magariba ta gama girkin da ta yi wa dr., Ta zubawa raihan na sa a flask, ta buɗe data ta yi masa message ya zo ya karɓa, za ta bawa maigadinsu, da ya zo ya ce masa shi ne raihan, zai bashi. "Sai ka ce wani me ma zance ne? Idan ba ke zaki fito ki bani ba, na ƙoshi". "Haba raihan, ba lallai a barni na fita, kuma zan iya samun matsala, wai kai idan ba ka yi rikici da gangan ba ba ka jin daɗi?" Ya ce "Soryy don't cry Salamatu, zan zo in karɓa in sha Allah" "Salamatu ko?" Ya katse wayar yana dariya Shima bai samu zuwan ba, direba ya aika, ya karɓo masa, babu ƙarya raihan yana sarawa ummi wurin iya girki, dan sosai ya saba da abincinta ya rage yawon restaurant cin abinci, dan cewa yake ƴan aikin gidansu jagwalgwalo suke yi. Yana cin alkubus ɗin ya kirata yana ta zuba mata santi yana koɗata. Da safe ummi ta ji abun da ba ta taɓa tunani ba, dr. Ya kan yi faɗa wasu lokutan, duk da yana da kawaici amma yau ya ɗau zafi da yawa. Farida yake zazzagawa bala'i, a kan lallai inteesar ta koma ɗakinta. "Wai dan Allah dr. Meyasa ka ke haka? Ba zaka tsaya ka ƙwato wa yarinya ƴancinta ba? Ai ba haihuwa ne ba ta yi ba, ɓari take yi bayan ya hanata karatu, ga wulaƙancin danginsa kuma yanzu ace an bashi ƴa zai ƙara aure haka ake yi?" "Shut up farida, ki daina cusa mata wannan banzar aƙidar taki, bai hanata ci da sha da muhallin zama ba, a kan useless excuse ɗinku, ba zan kira yaron nan muna musayar yawu mutuncina ya zube ba, karatu kume ku ka janyowa kanku, dan haka dole inteesar ta koma ɗakinta a yau ba sai gobe ba, ke kuma" yayi maganar yana nuna kausar da yatsa. "Abun da ki ka aikata a makaranta kin kyauta mini kenan, kuma kin kyautawa kanki? Carryover shida a courses goma sha ɗaya, uban me ki ke yi a makarantar? Duk uban kuɗin da na kashe? Kuma baku gaya mini ba HOD ɗin su ne ya kirani ya gaya mini, haka ki ka ga ummi tayi ko Abdul? carryover shida fa, courses shida ki ka faɗi a sha biyu, ba ma ɗaya ko biyu ba balle ace tsautsayi ne, me hakan yake nufi? In cigaba da asarar kuɗina? Idan auren ki ke so kema sai ki yi mini bayani ki fidda miji" "Kaga duk ba a kai ga wannan maganar ba, tsautsayi ne bai kuma wuce kan kowa ba, ita ummin kana da tabbacin ƙoƙarinta ne ba satar amsa" "Ki yi mini shiru farida kan na yi miki rashin mutunci, ƴa ta tafi ƙarfin ta yi satar amsa, dan haka zaɓi biyu zan baku, ko dai in ga canji next semester ko kuma ta fitar da miji, in yi mata aure ta bar mini gida, ta daina tara mini ƙarti a ƙofar gida tun da hankalinta a kan su yake ba karatun ba". A harzuƙe farida ta ce "Waccan guzumar yakamata ka bawa wannan zaɓin ba kausar ba? Da ta gaji da balaga ta riƙe a gida taƙi fitar da miji, ita ma sai a saka mata wannan dokar, ai an yi na Allah, an riƙeta tayi karatu, ko ta fitar da mijin aure ko a san yadda za ayi da ita, dan wallahi nima sai ta bar mini gida ba zan cigaba da zama da zabgegiyar mace a cikin gida ba, kuma kana sakawa ƴaƴana doka ba, wallahi ita ma sai ta bar gidan nan " Ganin da ya yi idan ya yi magana komai na iya faruwa, ya sanya ya ɗauki mukullin motarsa ya fice, ummi tana jin abun da yake faruwa ta dake, ta fito daga kitchen ta ɗaukko takalminta tana gogewa za ta fita. "Ke ummi! Da ke nake na san kin ji komai ai" ummi ta yi shiru ta sunkuyar da kanta ƙasa. "Na gaji da zama da ke a gidana, ina buƙatar space nima, tun da komai ke ce ki ka iya, ƴaƴansa ba su iya ba, duk in da miji yake ki nemo shi, sai kin bar mini gida ko kuma wallahi ki koma ƙauye in da ki ka fito" Kausar da take kuka ta ce "Wallahi maama ta bar mana gida, banza mummuna ko kuma koma waye a aura mata, ta rabamu da ubanmu ji yadda ya ci mini mutunci" Inteesar ma ta fito falon tana faɗin "Ai wallahi maama ki tarka mata tsummokaranta baya nan, ta bar mana gida, tuntuni ki ke cewa sai ta bar gidan nan, idan ki ka cigaba da zama da ita wannan dai ba auruwa za ta yi ba, idan ba sadakarta za ayi ba, sadakin ma shi Abba ya biya ba, ko a mayar da ita can ƙauyen ta samu dai-dai da ita". Ummi ta saka takalmanta, ta tashi zata tafi, farida ta zabga mata wata irin ashar ta ce "Dawo nan ina magana zaki wuce, sai na tsinke ki da mari tukuna, ƴar ƙauyen banza daga zuwa cin arzki kin zaƙe, baya ganin kowa da gashi sai ke, zan yi maganinki, in dai ina numfashi wallahi sai kin bar mini gida. Ya kai ki duk in da zai kai ki, tun da su dangin mahaifiyarki da ƴan ƙauyen naku ba su da hankali, da ma neman maraba suke yi da ke". Ummi ta danƙe wayarta da take vibrating na kiran raihan, zuciyarta na wani irin zafi, idanunta suka cika da hawaye, yanzu meye laifinta a saɓanin da suka samu yau ɗin, da har aka huce a kanta haka da cin mutunci. Sai da farida ta gama, sannan ta juya ta kamar hanyar fita, ta goge hawayen da suke shirin zuba, saboda kar raihan ya gane, ya matsa mata da tambayoyi. Kallo ɗaya ya yi mata ya kawar da kai, dan ko gaishe shi ba ta yi ba, kawai ta zauna, tana ta murza yatsunta. Ya kunna motar sannan ya ce "Yau kin shanya ni fa, ga kuma kulolinki na abinci na gode sosai, Allah ya ƙara zaƙin miya". "Amin" ta faɗa a hankali. Tsit har suka kusa zuwa ya gaji da shirun yana ta son ya tsokane ta, amma gaba ɗaya ko in da yake taƙi kallo, waje take kallo, tana fargabar kar Allah ya jarrabeta da abun da zai mayar da ita gagarawa. Unexpected taga har sun je tana can tana tunani, ta kalli gefe ta ce masa thank you. Ta fara ƙoƙarin buɗe motar, amma ta ga ya saka lock, ta waiwayo ta sanya idonta cikin nasa, bai ce komai ba ya zuba mata ido. Idonta fal hawaye ta ce "Zan sauka" "Are you ready to tell me?" Yayi maganar very serious. Ta ɗan sake yin shiru, tare da sunkuyar da kanta ƙasa. "Salma" ta saci kallonsa sannan ta sauke idonta, tana ta kokowa da hawaye kar su zubo. "Yanayinki ya bayyana komai, kuma kin saka ni a damuwa nima, dan Allah gaya mini, idan ba haka ba zan yi ta kokwanto". Kawai hawaye ya fara gangarowa daga fararen idanuwanta, wani na bin wani. Tun tana yi a hankali, har sautin kunkan nata ya fara fita sosai da sosai, ta sanya tafukan hannayenta, tana wata irin sheshsheƙar kuka mai ƙona zuciya. Ji ya din ga yi ina ma kowace irin damuwa ce, ya ɗauke mata ita duka, idan ba zai iya ba su raba damuwar biyu. Ya saka hannayensa ya sauke nata, ya zira hannu a aljihunsa ya ɗaukki handkerchief, ya saka mata a hannunta ya ce "Ya isa haka, goge hawayenki" Ya kira manager a waya, ya ce masa ummi ba ta da lafiya, ba zata shiga shago ba yau. Ummi ta kalleshi, ya ce "Mu je yau ki tayani aiki a namu office ɗin yau" Za ta yi magana ya ce "Mata shhh" ya ja motar ya bar wurin. Ta ɗan yi shiru tana kallon hanya, ta rasa dalilin da ya sa ba ta iya yi wa Raihan musu. "Mu je ki ga wurin aikina, sai mu je shopping ɗin, daga nan zaki gaya mini meyasaki kukan?" Tayi ajiyar zuciya tana kallon fuskar sa, "Ko haryanzu ban kai in san damuwarki ba?" Ta girgiza kai alamar a'a. "To idan kin huce, sai ki gaya mini" Suna tafe yana ta ɗan jan ta da hira, ta fara sakewa. Ummi ta sha mamakin ganin wurin aikin su raihan, kuma nan kawai babban office ne na gudanar da ayyukan kasuwanci, ba wurin da suke gudanar da kasuwanci ba. Yadda raihan ya wani maze, ake ta girmama shi, har mamaki ya bata, kamar ba raihan ɗin da suke hira da wasa da dariya ba, ya wani maze. "Raihan wai me ku ke sayarwa ne?" "Mutane, da masu kukan banza, da matsorata, da ragwaye, sai kuma mun kai sai kawunan mutane mu sayar, kin ga kamar ke ɗin nan, na ajiye ƴan china zan sayar musu da idonki ne, da ƙafafuwan ki a cire a saka mini" handkerchief ɗinsa da yake hannunta ta kwaɗa masa, yayi gaba yana dariya. Sagir suka tarar a cikin office ɗin a zaune, yana jiran zuwan Raihan. Ummi ta gaishe shi ya amsa, raihan ya ce "Yaya ya na ganka a nan kuma, lafiya dai ko?" "Kai haka ka ke yi sai ka ga dama zuwa wuri kake zuwa? Ka shanya mutane suna jiranka?" Ya jefa masa takarda ya ce "Signing zaka yi mini" Raihan ya ƙarewa takardar kallo ya ce "Wannan Alhaji yakamata ka bawa yayi maka". "Shi ya turo ni wurinka" "Amma yaya meyasa zan yi Signing ka fitar da wannan kuɗin haka? Me zaka yi da su?" Abun ka da mai shaye-shaye a kusa, ya daki tebur ya kalli raihan ya ce "Wai kuɗin nan nake ne? Ina ruwanka ne, ya gani ya ce in zo ka saka mini hannu, business zan fara, kar ka ɓata mini lokaci" Raihan ya juya takardar ya ce "Sana'ar me?" "Ban sani ba" ya bashi amsa. "Ba zan saka hannu a wannan takardar ba yaya ka yi haƙuri, sai dai ka zo mu yi aiki tare a din ga biyan mu, sai ka tara kuɗin da ka ke buƙata, amma yana shan wahalar tara dukiyarsa bai kamata a din ga yi masa ɓarna ba". Kan kace kwabo, sagir ya shaƙe raihan, yana zazzaga masa bala'i. Nan da nan ummi ta rikice, saboda ba ta son faɗa ko tashin hankali, take ta fara kuka, tana basu haƙuri. Yinƙuri ɗaya Raihan yayi, ya hankaɗa Sagir, sai da ya kai ƙasa. Ya ɗauki takardar ya yayyaga, ya watsa masa cikin kurari da zafin rai ya ce masa "Get out" ya ɗaga murya ya ce "Idan da wani a waje, ku kirawo mini security su fita da shi". Ummi ta ce "Raihan yayanka ne fa, ya zaka yi masa haka?" Kallon da ya yi wa ummi ne ya sanya ta jan bakinta ta tsuke, dan gaba ɗaya tsoro ya bata jikinsa har tsuma yake yi, kamar wani zaki. *Khadija ƴar gatan mama, ina gaisuwa 😂 Autar manya tamu ta gargajiya, Allah ya bar zumunci, ɗaukacin jama'a masoya littafin CUTARWA! ubangiji Allah ya bar ƙauna* Ayshercool 08081012143.                    *CUTARWA!* 26 *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK. https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends Masu neman free books ɗina, da free pages duk akwai a kan watpad account ɗina. Irinsu Abduljalal Wata kissar sai mata Wuta a masaƙa Cutarwa Ƙanwar maza Gaba da gabanta Aƙidata Ruɗin ƙuruciya Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata. 08081012143. And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link. https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels Ayshercool. PAID ADVERT!. Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi. Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku Oll types of Turaran wuta Sandal Halut Irik Difur Gab Gab Kajiji Habil Nabak Humra Kulakcha Dilke da kalta Kayan Garan jiki Muna turara Kaya Kujerar garan jiki Kannada Madarorin turare masu kamshi Man garan gashi Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921 *TALLA!TALLA!TALLA!* *INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*. *BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU* *MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA* BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI. 26 Sagir ya miƙe cikin zafin rai ya ce "Ni ka yi wa haka raihan?" "Na yi maka ɗin, da na lallaɓaka meyasa ka kai ni bango? Ai sai ka bari na kammala masa aikinsa na bar office ɗin, sai ka sake rubuta masa wata takardar shi ya sanya hannu ba ni ba". Cikin zafin rai Sagir ya nuna kansa da yatsa, yau shi raihan ƙanin ƙaninsa ya yi wa wannan cin mutuncin. "Zaka ga abun da zan yi maka, komai ya faru ka kuka da kanka" Raihan ya ce "Get out from here, ko na sanya security su fitar da kai". Ummi ta ce "Dan Allah raihan kar ka yi haka, zaku zubarwa da mahaifinku mutunci a gaban ma'aikatansa, kuma kar hakan ya shafi zumunci da mutuncinku" Sagir ya fice daga office ɗin rai a ɓace, Raihan ma rufa masa baya ya yi, ummi ta bishi da sauri za ta yi magana, ya ce "Ki jira ni a nan" ya fice shi ma. Zama ta yi zuciyarta babu daɗi, tana ta tunani, yanzu ace ƴan gida ɗaya ciki ɗaya suna wannan abubuwan, abun da mamaki. Sai kuma ta tuna ba abun mamaki bane ba, duba da yanayin na su familyn suma. Ummi har ta fara gajiya da jiran raihan, ta kira shi a waya, amma ta ga wayar ta sa a office ɗin tana ringing. Ta sauke hannunta a hankali, tana cigaba da kallon hanya, Raihan ya dawo office ɗin, hannunsa ɗauke da leda, ya ajiye a kan table ya kalleta ya yi murmushi ya ce "Afuwan na bar ki kina ta jira, bari mu ci wani abun" Miƙewa ummi ta yi ta ce "Tafiya zan yi, ka rakani na samu abun hawa na tafi" Cikin mamaki ya kalleta ya ce "Meyasa?" "Au tambayata ma ka ke yi? kamar ba yanzu ka gama hantarata ba, daga gaya maka gaskiya, dama ina cikin wata damuwar ka ƙara mini wata" tayi maganar a shagwaɓe tana kai hannunta fuskarta, ya zata da wasa take yi, kawai ya ga ta fara zubar da hawaye. Da sauri ya ƙarasa gaban ta, ya kai hannu zai sauke mata hannunta yana faɗin "Am sorry please, let me explain.. Ta ja da baya ta ce "Kar ka sake taɓa ni, ni tafiya zan yi" "To shikenan, na yi kuskure amma dan Allah ki yi haƙuri". Ummi ta sauke hannunta ta ce "Na ji, amma ka mayar da ni" Raihan ya ce "Dan Allah ki zauna ummi, mu yi magana ki yi haƙuri Please " Yadda yake ta marairaicewa ne ya sanya ta ga idan ta cigaba da yi masa musu, ba ta kyauta ba, dan haka ta zauna, shima ya ja kujera ya zauna. Ya kalleta ya ce "Am sorry ummi, this is the raihan you don't know, ina da haƙuri amma idan aka ƙure ni bani da kyau, mutum ne ni mai zafin zuciya da fushi, amma da wuri nake sauka. Yaya Sagir da Salim, su ne manya, kuma mahaifinmu yayi iya ƙoƙarin sa a kan inganta rayuwarmu, sai dai sun ƙi makaranta, sun ƙi sana'a kullum sai ɓarnar kuɗi a kan mata da shaye-shaye. Ban taɓa tunanin haka mahaifinmu ke shan wahala a kan dukiyarsa ba sai yanzu, a haka ma fa aikin da ya sakani iya gida Nigeria ne, yadda yake zirga-zirga sai kin tausaya masa. Sana'arsa ba ɗaya ba ce ba, mutum ne mai nasibi a harkar kasuwanci, muna shigo da kayan gini daga ƙasashen ƙetare, ana bamu kwangilar kayan gini, na ofisoshi, manyan ma'aikatu na gwamanti da na ƴan kasuwa, kuma muna rarraba wa kamfanoni da yawa kayanmu a Nigeria da ƙasashen maƙwabta. Ya kunna system ɗin gabansa, ya shiga nuna mata kayayyakin da suke sayarwa, kama daga ƙofofi, furnitures, kayan banɗaki, da sauran kayan alfarma na ƙawata gini. "Ɓangare guda, mahaifinmu babban dealer ne na shige da ficen kayan masarufi, sai dai an fi saninsa da harkar kayan gine-gine, iya kano muna da shaguna sun kai goma sha biyu a wurare daban daban ban da sauran garuruwa. Mahaifinmu duk shi yake kula da ayyukan kasuwancin sa, sai ma'aikatansa wasu lokutan a cuce shi a karkatar da kuɗaɗen sa, babu mai taimakonsa a cikinmu sai dai ya nemo mu kashe. Wannan shi ne babban ofishinmu na ƙasa, duk da ya ce zai mayar da shi Abuja, duk da haka mukan tafka asara wasu lokutan, amma hakan ba ya sanya mahaifinmu shiga hakkin ma'aikatansa, idan an samu riba da yawa kuma, ya kan ƙara musu domin farincikin su da mu baki ɗaya, to kuma duk da wannan abun sai azo da son zuciya mu ƴaƴa cikinsa mu din ga cutarsa duk ƙoƙarin da yake yi mana?" Ummi ta yi ajiyar zuciya ta ce "Raihan, na ji duk abubuwan da ka faɗa, ka na da gaskiya, amma still ka yi kuskure, ba dan Allah ya fi sonka ya sanya ka zama shiryayye ba har Alhaji yake janka cikin al'amuransa ba. Yayyenka na buƙatar kulawarka da tausayawa, a wannan halin suna sama da kai, amma ace sai ka yarje musu yin wani abu, ka yi tunanin yaya za su ji? Ka na da gaskiya, amma kamata yayi ace ka yi ƙoƙarin dannewa kun rabu lafiya, abun da ka yi masa bai kyautu ba gaba ɗaya. Raihan komai lokaci ne, ina sake jaddada maka, ranar da ba sa doron duniya sai ka din ga ina ma ace, ni ba gani ba, sha'awa ku ke bani, mahaifina ya rasu, mahaifiyata ban san in da take ba, bani da wa, ba ni da ƙani, haka nan kawai dai rayuwa nake yi. Duk da ka ce yayyenka basa ji, but they are blessing to you idan ka kallesu ƴan uwanka ne, ban ce ka ƙyale su su yi abun da bai kamata ba, amma gaba suke da kai, su yakamata ace a wannan position ɗin, amma Allah ya ƙaddara kai ne ba su ba, haba Raihan, why are you kind to me, amma brother's ɗin ka ka yi musu haka?" Gaba ɗaya jikin raihan yayi sanyi ya ce "Haka ne, na yi kuskure kuma na fahimce ki, in sha Allah zan kiyaye gaba ba zan sake ba, raina ne ya ɓaci sosai, kuma na yi ƙoƙarin dannewa amma yayi pressing ɗin na" "Yauwwa dan Allah ka daina, ba ka ' sanin muhimmancin wasu abubuwan a rayuwa, sai ranar da ka rasa su, wani rashin idan ka yi sai ya tafi ya barka da rauni mai raɗaɗin da har ka koma ga Allah ba zai goge ba, kamar dai ni da na rasa babban masoyina babana, da barinsa duniya ya yi wa rayuwata giɓi" tayi maganar hawaye na kwararowa daga idonta, har jijiyar goshinta ta tashi. Raihan ya matsa kusa da ita ya ce "Ummi, dan Allah ki daina koke-koken nan haka, Addu'a ita ce abun da mahaifinki ya fi buƙatar mu yi masa". Ta jinjina masa kai tana share hawayen ta, ya ce "Ga lemo na sayo mana, na san is hardly idan kin karya, yau ba ki zo mana da abinci ba" "Na ƙoshi, ba zan iya cin komai ba" Cikin damuwa raihan ya ce "Ni gaya mini menene ya saka ki kuka ma tun farko, kin ce zaki gaya mini" Ta ɗan yi shiru sannan ta ce "A bar wannan zancen kawai" "Ba za a bar shi ba, sai mun yi shi, ai alƙawari ki ka yi mini" "Ai ba zaka gane ba". Raihan ya ce "Zan gane, ko ta ina ne yi mini bayani, ina cin maths a aji ai" yayi maganar yana ɗan murmushi. Ta ɗan tsura masa ido, har cikin zuciyarta take jin yardar da ta yi wa raihan, ba ƙarama ba ce ba, saboda sosai take jin sa a ranta, mutumin da yake ta ƙoƙarin fuskantar matsalolin ta. "Ina ƙarama mahaifina ya rasu, kakata ta karɓi riƙona daga hannun babata, nikaɗai kuma suka haifa, mama ta koma garinsu, ƴan uwanta suka yi ta zuwa a basu ni, amma kakata ta hanasu ni, aka ce mamana ta haihu ɗan babu rai, ga damuwar rabamu, ta samu larurar ƙwaƙwalwa, amma aka hana su ni, har ƴan uwan mama suka yi fushi, basu sake zuwa sun ce a basu ni ba. Abubuwa suka ɗan faffaru, har kawu yahaya, ya ɗaukkoni daga gagarawa ya dawo da ni nan, tun da ya kawo ni, ake ta samun issues da family ɗin sa, Allah dai yayi sai na zauna a gidan, yanzu ma dai wata rigimar ce ta taso, matar kawuna ta ce zan bar gidan na koma ƙauye, ni kuma bana son komawa garin nan wallahi, mamana nake son gani, wallahi ko ba ta warke ba ko bola take bi, zan bita bolar mu rayu tare da dai in koma wannan garin da ko sunansa bana son ji, Raihan aƙalla na kai shekaru goma sha takwas rabona da mama, kuma ban ji labarin ta rasu ba, kowa yaƙi gaya mini sunan garinsu abun da na sani kawai a Maiduguri take. Ba wanda yake kulani, duk wanda na raɓa sai ya tsangwameni, an ce mini mummuna, an ce mini mayya, an aibata ni, to wai ya zan yi nema? zuciyata ta kusa fara ciwo, ban ma san ina na dosa a rayuwata ba, tun a kan cinyar mama nake ganin bala'i da tashin hankali, raihan tafiya kawai nake yi amma na san zuciyata na ciwo, ƙwaƙwalwa ta kuma kamar  na haukace nima, abubuwa suna damuna, ba wanda yake zama na gaya masa ya zan yi?" Wata irin karkarwa ummi take yi, tana magana ba comma babu full stop, wani ɓoyayyen abu ne da yake cin zuciyarta da ba ta taɓa zama ta faɗe shi ba, once in her life, yau ta samu chance. Babu tsammani ta durƙushe a ƙasa daga kan kujerar, tana kuka mai sautin gaske. Raihan bai san lokacin da ya durƙusa, duk da dauriya da dakiya irin ta raihan, yau da aka zo gaɓar da yake jira a zo, ya ji wacece ummi, ya ji sai dai zuciyarsa ta gaza ɗauka, zuciyarsa ta karye, ashe da ba tausayinta yake ji ba, kallonta kawai yake yi bai san meye a ƙunshe a zuciyarta ba, a hakan ma ba wai buɗa masa rayuwar ta tayi ba. Shekara sha takwas, ba ta sanya mahaifiyarta a idonta ba, alhalin duk suna raye, bama ta san in da take ba. Ya sanya hannun sa cikin tattausan hannunta, yana murzawa a hankali amma ya kasa magana, sai saurara sautin kukanta, da yake ƙara bugun zuciyarsa. Danƙe hannunsa tayi sosai a cikin nata, tana ƙara pressure kukanta. "Is ok salma, ya isa haka" ta girgiza masa kai ta ce "Allow me, idan na yi kuka ina jin sauƙi". Ya ɗora hannunsa ɗaya a kafaɗarta, amma ya kasa magana. Ganin kukan nata ba mai ƙarewa bane, ya ɗago fuskarta yana share mata hawayen da suke ta kwarara ya ɗan tura baki ya ce "Nima kin sani kuka, ya isa haka please" yayi maganar yana cigaba da goge mata hawayen. Kallon raihan take yi, da girmanta ko Abdul bai taɓa kai hannu jikinta haka ba, tana da taka tsantsan da kanta, wa ma ya damu da ita balle yayi yinƙurin kai hannunsa jikinta? Amma rarrashin nan da Raihan yake yi mata, ji take yi kamar ɗan uwanta da suke ciki ɗaya ne yake yi mata. "Waye ya ce ke mummuna ce?" Ta ɗan ja numfashi ta ce "Mutane" tayi maganar cikin tura baki Hannunsa a kan fuskarta, yana goge mata hawayen ya ce "Kuma kin yarda?" Ta jinjina masa kai alamar eh. Ya girgiza mata kai ya ce "Kar ki sake sakawa kanki cewa ke mummuna ce, i understand that you are traumatized by what people are saying about you, this is common among us. Ke fa malama ce ummi, kin fi kowa sanin Ubangiji gwani ne, kuma ba ya kuskure. Kin manta cikin suratul mu'iminun, aya ta goma sha huɗu, bayan Allah ya yi bayanin yadda yake tsara halittar ɗan Adam da kansa ya yabi kansa ya ce fatabarakallahu ahsanul kaliƙin? Ubangiji da ya yi ki ya yabi kansa, kuma sai ki sawa ranki cewa ba haka ba saboda surutun banza na mutane, as from today duk wanda ya ce miki mummuna, ki tabattar kin gaya masa maganar da gobe ba zai ƙara ba, fight for yourself ke ba mummuna ba ce". "Har gorilla fa wani ɗan ajinmu ya ce mini" tayi maganar wasu hawayen na fitowa daga idonta. Wani abu mai zafi ya soki zuciyar raihan, banda tsabar rashin mutunci ya za a haɗa mutum da biri?. Amma ya maze ya ce "Sai kuma ki ka din ga kuka ko?" Kamar mara wayo, ta jinjina masa kai. Raihan ya ce "Meyasa baki tsinka masa mari ba" Ummi ta zare ido ta ce "Haka kurum ya dake ni, ni bana faɗa" "Ai shiyasa mutane suka rainaki ai, da kin guara masa mari, gaba ba zai ƙara ba ai" Ta girgiza kai ta ce "Ni ban kula shi ba, muna level 3 ma aka kore shi daga makaranta ya yi satar amsa, duk abun da zan yi mutane ba za su daina ce mini mummuna ba" tayi maganar a raunane. "Sun gano weak point ɗin ki ne, shiyasa suke amfani da hakan suna yaƙarki. Ki kwantar da hankalinki na san kawu ba zai taɓa bari ki koma ƙauye ba, and ki ƙara tuntuɓawa ko zaki samu wani information a kan in da mama take, zan yi iya ƙoƙarina na gano miki ita". Ummi ta zabura ta ce "Dan Allah raihan da gaske?" "I promise you salma, wannan kukan nake son na daina gani sai farinciki a fuskar ki" "Nifa abubuwan da suke sakani kuka da yawa, ka san alfarmar da nake so ka yi mini?" "Sai kin faɗa". "Dan Allah ka manta na taɓa baka labarin nan, ban taɓa yin irin wannan hirar da wani ba, kai ne mutum na farko da na ji na nutsu da kai, na yi maka kuka, na rage abun da nake ji a raina, dan Allah kawai ka manta da labarin babu wani abu mai daɗi na tunawa a rayuwata, amma for now ka manta da shi, na gaya maka ne saboda na yi maka alƙawarin gaya maka abun da ya sani kuka" Idanuwanta yake bi da kallo, ya kasa amsa mata maganar, muninta kawai yake so ya gani, amma har ga Allah ya kasa, kawai dai baƙa ce, kuma baƙi dai ba muni bane ba. "Kayi magana mana" tayi maganar a ɗan shagwaɓe. "Zan yi, amma ba yanzu ba, mu karya ko, zuwa azahar mu yi salla sai mu je siyayyarmu ko?" Ummi ta ɗan ɓata fuska ta ce "Ko kawai mu canza rana, kaga yau duk sai godiyar Allah". Ya jingina da jikin tebur, ya ce "Kin sani kuka ba, marainiyar Allah, Allah ya ƙara kulawa da ke". "Amin amma ba na ce ka manta ba". Ya shafa sumar sa ya ce "Kema dai kin faɗa ne kawai, tashi in nuna miki aikin da zan kai wa Alhaji na gama" Ta miƙe suka koma kan kujera, yadda ya rarraba bayar da zakka, da kujerun umara da na hajji da zasu bayar, da ƙarin da za a yi a ɗan bawa ma'aikatan na riba da sauransu. Ummi a ranta ta jinjina dukiya tana nan a in da take, kuma yadda raihan ke gudanar da lamarinsa, ba zaka ce ɗan mai kuɗi ne haka ba, Maryam ce ma dai uwar jin kai, da jin ita wata ce. Sai da suka yi sallar azahar, sannan suka nufi tafiya, a mota take tambayarsa ina za su je, ya ce mata zata gani. Ya ja ɗan guntun tsaki ya ce haƙarƙarinsa a riƙe yake, zai fara koya mata mota, ya gaji da aikin direba ba a biyansa. "Ai ba ni na ɗauke ka aikin ba, kai ka ɗauki kanka, amma ba faɗuwa ka yi ba ka ke ciwon haƙarƙari?" "Ina fa, coach ɗina ne na gym, ya sakani ɗaga wani ƙarfe, haƙarƙarina ya amsa". Ta kalleshi ta ce "Wai sai ka ji wa kanka ciwo tukuna, meye na zuwa gym kai ba ƙiba ba?" Ya rausyar da kai ya ce "Waye ya ce dan a rame ake motsa jiki, bari na nuna miki ƙarfen da na ɗaga a Instagram" ya buɗe mata wayarsa ya bata. Suna tafe tana mitar ƙarfen yayi girma, daga bisani ta cigaba da yi masa taɓe-taɓe a wayar. Suka shiga go slow, yana jiran a basu hannu, ya ɗan leƙa wayar, ya ga ta nutsu, kallon dogwayen riguna kawai take yi tana liking ɗin su, da takalma da jakunkuna. Ya ɗan yi murmushi, aka basu hannu suka tafi. Katafaren kantin saye da sayarwa, suka shiga, ummi kamar ƴar ƙauye, sai kalle-kalle take yi. "Ta ina zamu fara?" Ummi ta ce "Ko ta ina ne ma". Sannu a hankali suke zagayawa, suka fara zuwa wurin turarruka, ya saka hannu ya ɗauki wani, ya jefa a cikin trolley. Ummi ta waro ido ta ce "Raihan, dubu sha takwas fa aka rubuta, ka manta kuɗin dubu sha biyar ne?" Ya kashe mata ido ɗaya ya cigaba da ɗaukar kaya. Tayi ta magana, amma yayi mata shiru, suka je wurin kayan kwalliya ya kalleta ya ce "Me ki ke so a nan?" "To ai kuɗin sun ƙare" "Ke ina ruwanki ne, ɗauki abun da ki ke so kawai" Comb ta ɗauka sai ribbon da coacoa butter, dan man yana burgeta ta ce sun isa. "Wai ke ba kya kwalliya ne, ga su hoda da kayan mata" "Ni bana wata kwalliya" ta bashi amsa tana ɗan kalle-kalle. Ya ɗaukko ɗaya wayar ta sa, yana dube-dube, ya ɗaukko wasu mayuka ya koma kan mayukan gyaran gashi, suma ya ɗauka. "Wannan me zaka yi da su?". "Budurwata zan saiwa lefe zan fara tarawa". Ummi ta yi dariya ta ce "Riga malam masallaci, za ta kwashi kayan shiririta" "Ni ne ma shiriritar ko? Son kowa ƙin wanda ya rasa da ni ɗin nan, ɗan kyakkyawan matashi mai gemu, kin san maza masu gemu muna da tsada". "Ai mami ta ce mai ka shafa ya fito" "Wallahi ban shafa mai ba, girma na yi gemu ya fito" "Muyi sauri kar na makara komawa gida" Ita dai ummi ta zuba wa sarautar Allah ido, ta san dai abubuwan da raihan ya ɗauka, sun fi ƙarfin kuɗinta nesa ba kusa ba. A wurin biyan kuɗi aka yi billing ɗin sa kuɗi masu yawa, ya basu ATM suka cire. Gaba ɗaya ummi ta manta da damuwar da ta baro a gida, jin zuciyarta take fes, yau ta faɗi abun da yake ci mata zuciya tsawon shekaru, kuma ta samu ta yi kuka, an saurareta. "Raihan" ya ɗago ya kalleta "Na gode sosai da lokacinka, Allah ya saka da alkhairi, ya ja kwanan Alhaji da mami" Ya ce "Da kuma Hajiya" tayi murmushi ta ce "Amin, kuma dan Allah da ka je gida, ka yi haƙuri ka danne zuciyarka, ka bawa yaya Sagir haƙuri dan Allah" "Zan yi in sha Allah" "Allah ya yi maka albarka" Kasa amsa mata yayi sai murmushi, ƙasan zuciyarsa na hango masa ita tana kuka ɗazu. Suka isa bayan layin su ummi, ta buɗe motar ta sauka har ta fara tafiya ya ce "Ke wannan alkunyar taki tayi yawa, maimakon ki ce "Malam bani kayana, ko kin bar mini  dubu sha biyar ɗin taki?" Ta waiwayo ta jinjina masa kai alamar eh. Ya fito daga motar, ya ɗaukko kayan yabi bayanta, ta tsaya cak ta waiwayo ta ce "Ina zaka ne?" "Gidan zan biki na kai miki kayan" A rikice ta ce "A'a dan Allah" "To karɓi kayanki" "To ya zan yi da su, idan aka tambayeni.... "Ki ce da salarynki ki ka saya, ba wasu kaya ne masu yawa ba fa, ya kamo hannunta ya danƙa mata ledar ya ce "Zan je gida na cika alƙawarin da na yi miki" ya juya ya koma motarsa ya tafi. Cikin mamki ummi take kallon kayan, wai duk wannan nata ne? Amma uban kuɗin da raihan ya kashe, dubu ɗari da sha takwas, kayan mai turare da ciye-ciye. Cikin matsananciyar fargaba ta shiga gidan, kasancewar ɗakinta ne a farko, ba ya cikin main safe contain na gidan, shiyasa ba sa sanin shige da ficenta. Ta kalli agogo ta san noor tana makarantar islamiyya, da ta kirata ta gani. Tayi alwala ta yi sallar la'asar, ta zauna ta din ga kallon kayan, wannan mayuka masu uban tsada, ita za ta shafa a fatarta. Wai har da hoda, to ita mai za ta shafawa hoda ma? Ta ɗau turaren tana shaƙar ƙamshinsa mai sanyi da daɗin gaske. Ga roll on, kusan kala huɗu, wanda kullum cikin dabaru take na haɗa alumun, ko ta jiƙa gishiri bayan yi wanka ta shafe jikinta, saboda kar ta yi wari. Wata envelope ta gani a cikin kayan, wadda ba ta san da ita ba, ta ɗauka ta buɗe taga kuɗi a ciki sai takarda. "Assalamu alaikum, brown eyes, this is your first salary, given to you 15th April, spend it well, ga additional na 15k making 30k, ki lallaɓa na ji daɗi na kuma gode da shopping, Allah ya ƙara arziki ummita. Raihan" galala take bin takardar da kallo, Raihan ya mayar da ita sakarya ma. Wurin Alhaji ya fara zuwa, ya tarar da mami, da kuma Hajiya tare da Alhajin. Cikin damuwa mami ta ce "Raihan sannu da zuwa, ba abun da ya sameka dai ko?" Ya ce "A ina?" "An ce mini Sagir yaje har office, ya yi yinƙurin dukanka, na kira wayarka baka ɗauka ba, na zo in ji ba'asi". Raihan ya haɗe rai ya ce "In ji wani munafukin ne ya faɗa?". Alhaji ya ce "Bai yi maka komai ba dai ko?" "To aini Alhaji ban gane yayi mini wani abu ba?" Sagir yayi sallama, suka amsa banda mami da take sababi tana faɗin "Wallahi dole ka ɗau mataki Alhaji, kar a kassara mini ɗa a cuceni" Cikin dakiya Hajiya ta miƙe ta ce "Sagir, uban meye ya kai ka wurin raihan, ka yi yinƙurin dukansa?" Yayi shiru yana kallon Hajiyan. Alhaji ya ce "Yi masa a hankali, ni na tura shi wurinsa, ban san kuma haka zata faru ba, zo ka yi mini bayanin meyafaru?" Cikin fusata hajiya ta riƙo rigar Sagir ta ce "Ba magana nake yi maka ba? Zuwa ka yi kayi rashin mutunci a gaban mutane ko sagir? Idan baku yi abun da za a ce baku kyauta ba ba kwa jin daɗi ko?" Raihan ya cire hannun Hajiya daga jikin Sagir ya ce "Duk fa baku fuskanta ba, ya zaku ɗauki zafi a kan abun da ba a gabanku aka yi ba? Ni ne mai laifi abun da na yi wa yaya Sagir yana gaba da ni ban kyauta ba, kuma da niyyar ba shi haƙuri na dawo, bai kamata ba yadda na yi treating ɗin sa, dan Allah ka yi haƙuri yaya Sagir" wani irin mugun kallo Sagir yayi masa, tare da tunanin wata shiryayyiyar ce Raihan da babarsa suka shirya, kawai ya juya zai tafi, Hajiya ta bishi a zafafe, Raihan ya riƙeta ya girgiza mata kai, kawai ta fashe da kuka zuciyarta na yi mata zafi. "Jarrabawa ce mai buƙatar juriya Hajiya, ki daina yi masa kuka" raihan ya faɗa da sigar rarrashi. Mami kuma sai rashin mutunci take yi, tana yaɓawa Hajiya magana, Raihan ya dafa kafaɗarta ya ja ta suka bar falon yana rarrashinta. "Gaskiya Alhaji ka saka baki, yaranta ba za su lalace kuma ta din ga nema ta ƙwace mini ɗa ba, alhalin yaranta na barazana ga rayuwar Raihan ba. Ummi ta yi ta kiran raihan a waya, amma sai ta ji busy, bama ta shiga gaba ɗaya, haka ta haƙura ta ajiye ta tafi kitchen dan yin sanwar dare. Farida ta daka mata tsawa, ta ce kar ta kuskura ta shigar mata kitchen, ba ta buƙata, domin kuwa barin gidan za ta yi. A karo na farko da ummi ta ji ko a jikinta, yau ta samu hutu. Alhaji Tahir ya kira meeting na gaggawa na iyalansa, da manyan manajojinsa da lawyoyinsa gidansa, bayan sallar isha'i. Suka din ga mamakin hakan, dan kuwa ba su san dalilin hakan ba, dan bai taɓa yi ba. Raihan yana maƙale da Hajiya, dan tun ɗazu da suka bar falon, sashinta ya koma ya tare yana rarrashinta. "Bakomai ne ya sanya na taraku a halin yanzu ba, sai dan gabatar da wani hukunci da na yanke, wanda na daɗe ina nazarinsa kafin yanke shi. Daga yanzu Raihan zai riƙe office ɗina, na tsawon shekara guda, ni kuma zan koma gefe ina monitoring ɗin ayyukan sa, duk hukuncin da ya zartar kamar ni na yi ne, duk mai buƙatar wani abu, zai yi a rubuce ya kai masa, yana da damar sallama ko ɗaukar ma'aikata, kar wanda ya zo ya sameni ya sani in yi masa wani abu, wurinsa za aje. Aikinka tuƙuru shi zai tabattar da kai a kan wannan kujera mai nauyi, Allah ya tayaka riƙo Muhammad Raihan sabon MD na Tahir and Son's Limited. Wata irin razana raihan yayi yana kallon mahaifinsu, yayin da Mami ta rangaɗa guɗa tana faɗin "Ƙaraminsu babbansu, ka ga ɗan ƙaramin sauro mai hana giwa bacci" Hajiya da yake zaune kusa da ita ta yi murmushi ta shafa sumar Raihan ta ce "Allah ya tayaka riƙo babana, Allah ya tsare mana kai" Raihan kuwa miƙewa yayi ya bar falon, zuciyarsa babu daɗi ko kaɗan Allah ya gani baya so, kuma ya ƙudirci a watse ya samu Alhaji. Ayshercool 0808012143 What's app only please 🙏                       *CUTARWA!* *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* P27 FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK. https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends Masu neman free books ɗina, da free pages duk akwai a kan watpad account ɗina. Irinsu Abduljalal Wata kissar sai mata Wuta a masaƙa Cutarwa Ƙanwar maza Gaba da gabanta Aƙidata Ruɗin ƙuruciya Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata. 08081012143. And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link. https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels Ayshercool. PAID ADVERT!. Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi. Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku Oll types of Turaran wuta Sandal Halut Irik Difur Gab Gab Kajiji Habil Nabak Humra Kulakcha Dilke da kalta Kayan Garan jiki Muna turara Kaya Kujerar garan jiki Kannada Madarorin turare masu kamshi Man garan gashi Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921 *TALLA!TALLA!TALLA!* *INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*. *BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU* *MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA* BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI. 27 Mami har ta yinƙura za ta bi bayansa, amma Alhaji ya hanata, mami tamkar ta taka rawa, tana kallon fuskar Hajiya, ko zata ga damuwa ko ɓacin rai a fuskarta. Amma sam bata ga hakan ba, sai ma fatan alkhairi da take ta yi wa raihan ɗin, su kansu su Salim ko a jikinsu, sai dai Salim ya ɓata fuska ya kalli Alhaji ya ce "Yanzu idan muna buƙatar wani abun sai mun je wannan yaron ƙanin bayanmu ya yarje mana, ni bani da matsala da koma me ka bashi, amma wallahi ba zan je wurinsa neman abu ba, a nemi wani abun kawai" Sagir ya ce "Balle kuma ni, da yayi niyyar dukana, sai dai ace na daina morar komai a gidan nan, da dai ace in je in sake neman wani abu a wurinsa wallahi" "Sagir.... "Shhhh" ita ma Alhaji ya hanata yi masa magana, duk ya ce su rabu da su. Raihan wuri ya samu yayi zamansa, gaba ɗaya ransa babu daɗi, saboda sam bai yi farinciki da wannan al'amarin ba. Har kusan sha ɗayan dare, babu wanda ya san in da raihan ya yi, Alhaji kuma yana falo yana jiransa, dan ya san a daren dole zai dawo ya neme shi. Aikuwa sai ga shi yayi sallama ya dawo, da ya tabattar kowa ya watse. Alhaji bai ɗago ya kalli raihan ba, har ya zo gabansa ya zauna, a hankali ya ce "Alhaji" "Ka dawo ka ce mini ba zaka yi aikin bane ko? Ba ka so na nemi wani, kaima da nake jin daɗinka zaka fara bujure mini" Jiki a sanyaye raihan ya girgiza kai ya ce "Ba haka bane ba Alhaji, yayi mini nauyi da yawa, ba zan iya ba wallaahi kaima ka san na yi ƙanƙanta da wannan al'amarin, kuma nine ƙarami kar yayyena su ji babu daɗi a kan hakan" "Raihan" "Na'am". "Ba lokaci ɗaya kuma kai tsaye na yi assigning ɗin ka a kan wannan matsayin ba, na yi addu'a, kuma na jarrabaka ta kowane ɓangare, kai ɗin ne dai zaka iya, yara nawa Allah yake ɗaukakawa wanda suka kai ka, da wanda basu kai ka ba ma? Wani a waje bare ka ke so na ɗaukko na danƙa masa ragamar dukiyata da kula mini da ku? Ko kuma wannan yayyen naka da ba su san ciwon kansu ba? Ka sani ko takaicin abun da na yi musun, ya sanya su shiryu? Hajiya ce ta bani wannan shawarar, kuma na ga hakan ne ya dace" Raihan ya kalleshi da sauri, ya ce "Hajiya ce ta ce ka bani ragamar kula da harkokinka?" Alhaji ya jinjina masa kai, raihan ya yi shiru yana tunani, ya san da mami ce sai dai ayi mutuwar kasko kowa ya rasa, da dai ta yarda ko ta bayar da irin wannan shawarar. Maganar Alhaji ce ta dawo da shi daga tunanin da ya tafi "Babban mutum, kar ina yabonka salla ka kasa alwala mana, kar ka watsa mini ƙasa a ido, i will always be by your side, duk abun da ba ka gane ba, ko abun da ka ke buƙata i will assist you like a ghost" yayi maganar yana dariya, wanda raihan ma yayi murmushi. "Alhaji ka ɗaureni da jijiyoyin jikina, kana faɗar maganar nan na ji kamar ka sakani a kurkuku". Yayi dariya ya ce "Ba wata kurkuku, ka san babban abun da ya burgeni? Da ka yi offending ɗan uwanka, ka dawo ka bashi haƙuri, ka hana abun da ya faru yin tasiri a cikin gidan nan, da kuma tsakanin iyayenku mata". Raihan ya jinjina kai ya ce "Ummi ce ta bani shawarar yin hakan ai, ba idea ta ba ce". Alhaji ya sake dubansa ya ce "Wace ummi kuma?" "Baka santa ba, ƙawata ce bari ne je na kwanta Alhaji, idan na yi bacci wataƙila kaina ya daina ciwon". "To Allah ya bamu alkhairi, zan saka ranar yi maka walima tare da abokan hulɗarmu da ma'aikata, da gabatar da kai a matsayin sabon MD". "Alhaji riƙon ƙwarya fa ka ce, ko dai wayo ka yi mini?" "Tashi ka tafi sai da safe" kamar soko raihan ya tashi ya bar ɗakin ya nufi ɗakinsa. Wayarsa ce ta fara ringing, ya tsaya ya ɗaga. "Ƙaraso sashina ina son ganinka" ya sauke hannunsa shi ko son yin wata maganar baya yi. Ya koma ya nufi sashin mami, tana falo tana jiransa, "Mami, baki yi bacci ba?" "Ya za ayi na yi bacci, zaka yi mana sagegeduwa, ai bacci bai kama ni ba, dole na din ga bacci da ido ɗaya. Uban me ka je ka cewa Alhaji?". Kai tsaye raihan ya ce "Ce masa na yi ya taimaka ya saukeni daga muƙamin nan". "Saboda ba ka da hankali ko? Allah ya ƙwaci abun ya baka, sai ka ce ba ka so saboda shashasha ne kai raihan?" Bin mami kawai yake yi da kallo, ta haƙiƙance ta din ga yi masa faɗa, shi dai yayi shiru bai ce mata komai ba, babban abun da ya bashi mamaki, irin huɗubar tsiyar da ta din ga yi masa, har ta yi ta gama bai ce mata komai ba, ya tashi ya tafi, yana mamakin halin mami da tunanin yaushe zata sauya. Ta kafa wa Hajiya ƙahon zuƙa, gashi dai hajiya ta tarar a gidan, amma tun tasowarsu mami ta kanainaye komai, gashi kishi take da hajiya kamar abokiyar gabarta, ta haɗe kai da yaranta mata duk sun saka Hajiya a gaba, dan ma duk an yi musu aure saura Nihal da ke karatu a ABU zariya, ba ta fiye zama a gidan ba, shikaɗai ne a ƴan ɗakinsu suke shiri da hajiya, dan shi har ga Allah bai ga aibun matar ba. Ummi kuwa daga ita sai noor suka san da kayan nan, ummi ta ɓoye su a cikin kayanta, tuni ta yi wanka ta fara shafawa, sai dai fa kayan kwalliyar ne ba sa gabanta, ita turarukan da mayukan sun fi ɗaukar hankalinta. Tayi ta kiran Raihan, daga baya tana ta shiga amma baya ɗagawa, tayi wankanta ta shafa mayukanta da turare, tana sake kiran wayarsa farida ta shigo ɗakin. Gabanta ne ya ɗan faɗi, ummin na zaune a kan katifa, babu hijjabin nata na gado, ta saka skirt kawai da vest ga hijjabin a gefe, fatarta tana ta ƙyallin man da ta shafa, ga ƙamshi da ɗakin yake yi, ta saki gashin kanta ta sunkuyar da kai tana danna waya. "Ke!" Ta daka mata tsawa, ummi ta ɗago da sauri, ta ja hijjabi ta saka. "Dalla ki tashi ki wuce ki ɗora mana abincin dare" kallonta ummi take da mamaki, ɗazu taje tayi girkin ta koreta ta ce ba ta buƙata, yanzu kuma ta ce wai sai ta taso ta yi. Da "To" ta amsa, ta tashi ta tafi kitchen. Ga alamar an yi girki, amma duk an jibgeshi an ƙi ci, ta duba tukunya wata jallof aka yi ta shinkafa ta yi jagab kamar da shinkafar tuwo aka yi ta, ta kai bakinta ta ɗanɗana, da sauri ta fuzar an zabga uban gishiri da attaruhu, ga mai male-male a kai. Hakan ba aikin kowa bane sai kausar, dan farida ta ce ummi ba zata sake shigar mata kitchen ba, ta ƙuduri aniyar ƙuntata mata, kausar ta yi girki ya ƙi ciyuwa. A daren ta tuƙa tuwon semovita, ta sallami kowa sannan ta koma ɗaki. Missed calls ɗin raihan ta tarar, da message "Call me when you are available" Ba ɓata lokaci ta kira shi, ya ɗaga da sallama, ta amsa masa sannan ta ce "Ka kyauta raihan". "Da na yi me?" "Ka fi kowa sanin me ka yi mini ai, sannan ka kashe wayarka, daga baya ka ƙi ɗaga wayata, mun yi da kai muje mu yi sayayya, in saya maka abu sai ka sai abun da ya fi ƙarfin kuɗina, kuma ka dawo mini da kuɗina har da ƙari, kafi ƙarfin abun hannuna ko?" "A'a ba haka bane ba, dan Allah kar ki yi mini wata fassara daban". "Haka ne mana, ni bani da abun da zan baka ko? To ka zo ka karɓi kuɗin nan and am serious" Ya gyara kwanciyarsa ya ce "Ni fa a cikin damuwa nake, kaina har ciwo yake yi, zaki ƙara mini damuwa" Sai kuma ta nutsu "Wace irin damuwa kuma?" "Ba maganar waya bace ummi, zan zo in sameki" Ummi ta ce "Amma dai komai lafiya ko? Kar ka sa hankalina ya tashi fa, ka fara gaya mini" "A'a ba abun tashin hankali bane ba, ki kwantar da hankalinki gobe in sha Allah zan zo" "To Allah ya kawo ka lafiya, ko menene ka fawwala wa Allah ka ji?". "In sha Allah, sai da safe" suka yi sallama, ta gyara shimfiɗarta, ta kwanta tana jin ta kamar wata ta daban, ƙamshin da yake tashi a jikinta sai nishaɗi take yi. *** "Anty Rakiya, ai in gaya miki da ƙyar na yi barci daren jiya, tun da Alhaji ya faɗi wannan sanarwar da ƙyar na yi barci saboda murna, shi ɗan naki da yake ba kan gado ya cika ba, ya je ya samu uban wai ba ya so" Rakiya ta ce "Kin ga raihan da rigima, Allah ya kawo dama yayi fatali da ita, kar ki kuskura ki yarda, ai ke lalacewar ƴaƴan can gaba ta kai ki Bilki". Mami ta ce "Can gaba ma, kuma ƙoƙari zan yi duk mai yiwuwa in saka masa ido, dan tun a jiyan na kirawo shi na ƙare masa ta tas, yanzu abun da ya rage zan yi, dole in jajirce kar ruɗin kuɗi ya sanya shima ya fara biye-biye in yi biyu babu, shima ya lalace aure zan yi masa yaya, ai zai iya riƙewa" Yaya rakiya ta ce "Ke bilki" "Wallahi yaya rakiya, kar in je ya lalace mini in shiga uku, idan na yi masa aure, sai ma yafi mayar da hankali a kan kasuwancin uban, ya san yana da nauyi a kansa, duk da ba ma'abocin kula mata bane ba, amma kin san kuɗi, yadda ya samu wannan babban matsayin yakamata ace yana da cikar kamala ta aure kuma" "Wannan gaskiya ne, to da mai zai hana ki haɗa shi da Safiyya, ayi ƴar gida kawai" Mami ta ce "Wallahi kuwa, tuwona naina sai dai kin san shi, ba a iya masa, zan tuntuɓe shi da zancen idan har ya amince bani da matsala, amma dolensa yayi aure, hakan zai ƙara sanya ma'aikatan su girmama shi" Suka cigaba da hira, Anty rakiya na ƙara ziga mami, da yadda za ta ɓullowa lamarin hajiya, ta kankane komai, da kuma muhimmancin aurar da raihan, mussman idan suka haɗa shi da Safiyya, dan ƙarafafa zumunci. *** Ƙurii raihan ya yi wa ummi da ido, yadda take ta yi masa dariya. "Ni ko? Ni zan gaya miki damuwata ki saka ni a gaba kina dariya, wasu abubuwan duk shawararki na bi, ƙarshe na rufta kuma kin zo kina dariya" "To ai kai ɗin ne, yadda duk ka tashi hankalinka dole ka bawa mutum dariya. Ni da na zata wani abun da ba a so ne, da farko dai congratulations mai girma MD" hararta yayi yana kallon wayarsa. "Attention" tayi maganar tana kallon sa. Ya juyo yana kallonta shi ma "Ka saurareni, mu ajiye wasa da komai a gefe, zan yi magana a matsayina na yayarka ne" ya haɗa hannyensa biyu ya yi tagumi ya zuba mata ido. Ummi ta ce "Ba bakina zaka kalla ba, ka saurareni da kyau, a matsyinka na mutum mai muhimmanci da ba zan manta da shi ba, ina fatan Allah ya haɗa ni da kai a aljanna a majalisar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam, kuma duk mai son ya tashi da annabi Sallallahu alaihi Wasallam sai ya kiyaye cin hakkin mutane. Kai mutumin kirki ne raihan, kar ka bari kuɗi da shugabanci su yi wasa da imaninka, ka ji tsoron Allah, ka ji tsoron Allah ka riƙe gaskiya da amana, kar ka cuci kowa kar ka ƙasƙantar da kowa, yayyenka ƙannenka ma'aikatanka da duk wani na ƙarƙshinka, ka kula da su bisa amana, kar ka yi son zuciya, kuma kar ka saka a ranka lallai sai kowa ya soka, kawai ka yi dan Allah. Abu na gaba, dole ka rage wannan jin kaɗe-kaɗen, ka mayar da hankali a kan azkar, da addu'a Ubangiji ya dafa maka yayi maka jagora, ya rabaka da dukkanin abun ƙi. Sannan idan Allah ya sa ka tashi yin aure, a yanzu ko a gaba, ka samo mace ta gari, wadda abun da ka ke da shi, ba zai rufe mata ido, ta ja ka ga hallaka ba, danmu mata mutane ne masu kanmu da yawa, tsaf sai wata ta yi yinƙurin mallakarka da dukiyarka ta rabaka da kowa, kar ka auri mace dan kai kana sonta kawai, ka duba makomar zuriyarka da ahalinka, kai mutumin kirki ne zaka iya babban mutum, ka yawaita saurara tarihin salihan bayi da yadda suka gudanar da rayuwarsu mussaman ta fuskar shugabanci, hakan zai ƙara sanya maka tsoron Allah, Allah ya tayaka riƙo Muhammad Raihan" Jikinsa gaba ɗaya yayi sanyi, kalaman ummi maimakon su kwantar masa da hankali, tayar masa da hankali suka sake yi, tare da jin tamkar ta sake ɗaure shi da jijiyoyin jikinsa. "Ummi wallahi an scared, ba zan iya ba, jagoranci abu ne mai wahala" "Haba madubina, kai kake ƙoƙarin koya mini jajircewa, kai kuma in ga gazawarka? A'a kar ka watsawa Alhaji ƙasa a ido, zaka iya ka ji" Yayi shiru bai ce komai ba. Ta ce "Ka ce to mana" "Ba zaki gane a yanayin da nake ba ne". Ummi ta ce "Eh ba zan gane ba kam, karɓi kuɗinka" tayi maganar tana ajiye masa envelope ɗin da ya saka mata kuɗi a kan tebur. "Ɗauke tun kan ki fusata ni, na yi miki rashin mutunci a gaban mutane" Da mamaki ta kalleshi ta ce "Amma raihan idan ka yi mini haka ba ka kyauta mini ba, kuma ba zan ji daɗi ba" tayi maganar muryarta na rawa, dan tuno shi tayi ranar da suka je office ɗin su, da ya burkice sai da ya bata tsoro. Ya tashi tsaye ya ce "Bari na ƙarasa office, idan na samu kaina zan zo mu tafi gida, idan kuma aiki yayi mini yawa zamu yi waya" ko amsarta bai jira ba, yayi waje ya barta da kuɗin. Sai da ya fita manager ya ce "Ummi, me aka yi wa mutumin ne na ga yana cika yana batsewa?" Ummi ta ce "Rigima kawai yake ji" "Ai nima na ga alama, shiyasa ban kula shi ba". Abu kamar wasa, aka yi ta shirin yi wa raihan liyafa, ya so ummi ta je, amma ta ce ba zata ba. Abokan hulɗar Alhaji Tahir wasu sun ga wautarsa, na bawa raihan jagoranci babban business irin wannan, matashi mai shekaru 23 dan ma yana da siffar kwarjini da girman jiki, amma kallo ɗaya zaka yi masa ka san yaro ne. Sai dai ko a kalamansa na godiya, da na kama aiki, sun tabattar wa da mutane ƙaraminsu babbansu ne, kamar yadda Alhaji Tahir yake faɗa, wanda wasu maganganun ummi ce ta gaya masa abun da zai ce, dan Alhaji Tahir ya sanar masa ya shirya kalaman da zai faɗa ranar liyafa. Aka yi taro aka watse, ya turawa ummi hotunan abun da aka yi, ta ɗauki hotonsa guda ɗaya ya sha coat, ƙuruciyarsa ta fito sosai, sai dai ya tsare gida babu fara'a, ta saka shi a status da caption na "Allah ya tayaka riƙo ƙanina, MD Muhammad Raihan" Ta kai awanni biyu da yin status ɗin, da ta buɗe what's app ta tarar da saƙonni, na tambayar waye shi, ciki har da yaya magaji, babban wanda ya fi bata mamaki shi ne message ɗin maryam, tun da raihan ya haɗa su, suka yi magana maryam ba ta sake kulata ba, idan ta yi mata magana ma, sai ta ga tana shareta, dan haka ita ma ta daina kulata, sai yanzu taga message ɗin ta, wai ya aka yi ki ka sani?. Ummi ta yi mata reply da "Shi ya gaya mini". Maryam ta ce "A ina ku ka haɗu ya gaya miki?" "Muna gaisawa idan zai wuce ta wurin da muke aiki ne". Ta yi reply da "Dan Allah ki cire shi, ba kowa ya sani ba, kar azo hakan ya bashi matsala" Ummi ta daɗe tana jujjuya message ɗin, ita mutum nawa ne ma a what's app ɗin nata. Ta ga ita kanta maryam ɗin, ta saka hotunan sun fi goma, kodayeke wata kusan ta fi wata, dan haka ummi ta goge. Tamkar jira yake ta goge, ya ce "Meyasa ki ka goge status ɗinki?" "Bakomai". "Akwai dalili mana, saboda Maryam ko?". Abun ya bata mamaki, kan ta yi magana ya sake turo wani saƙon ya ce "Muna tare take nuna wa mami status ɗin naki ai, ita take saka miki data da zata ce ki cire abu kuma ki cire? Ina ruwanta, ko haifarki tayi da zata bani umarni ki bi? Akwai mutane a wurin ne ya san na ƙyale maganar, ƙarewa gobe in Allah ya kaimu hira za ayi da ni a wani gidan jarida. Dan Allah ki daina bari ana raina mini ke bana so" Karanta saƙon nasa ta din ga yi, tana ƙoƙarin bawa saƙon damar yin tasiri a zuciyarta, amma ta kasa. "Dan Allah ki sake duba wani hoton, ki ɗora ni ki yi mini addu'a, tun da ba ki je taron ba Please". "Yanzu ka gama cewa a daina sani abu in yi, ai ba kai ka saka mini data ba" ta tura masa tana dariya. Emojin dariya ya tura mata ya ce "Ta kaina zaki fara kenan? Ni ki ka raina ko?" "Kai ka mayar da ni haka ai, ina salihata ka koya mini surutu". "Dama can kin iya abinki" "To na ji, sai da safe bacci nake ji" " ya kaimu" ya rufe data ya ajiye wayar, ya lumshe ido yana tuno moments ɗin su tare, ba zaka taɓa cewa ummi na magana ba, dama ce kawai ba ta samu ba, amma tana da baki sosai". *** Alhaji Tahir kallon mami yake yi, bayan ta gama kora masa bayanin abun da take so. Ta kalleshi ta ce "Wai ya ka yi shiru kana kallona ne?" "To ai abun ne na ji shi banbarakwai, guda nawa raihan ɗin nawa yake zaki ce ayi masa aure yanzu? Daga ɗora masa wannan ɗawainiyar sai kuma ki ce ayi masa aure?". "To ai shine cikar kamalarsa, ya samu matsayi ya zamana yana da iyali, dole zai nutsu ya mayar da hankalinsa, ko so ka ke na saki jiki shima ya lalace? Ni dai dan Allah ka taimaka ka amince" Alhaji ya ce "Ai ni bani da damuwa, in dai ya amince yana so shikenan, Allah ya sanya alkhairi" "Yauwwa, dan Allah ka tayani shawo kansa, ka san ko budurwa ba shi da ita, ko zancen na yi masa sai ya sha kunu, dan Allah ka tayani lallaɓa shi, ko da Safiyyar Anty rakiya a haɗa shi" Ya kashingiɗa ya ce "Wannan ba hurumina bane, kin san takura wa ɗa ba ya cikin tsarina, ku tattauna kawai" Tayi ajiyar zuciya ta jinjina kai. Mami ta din ga fargabar tunkarar raihan da maganar, haka nan ta dake da safe ya shiga gaisheta zai fita office, ta ɗaukko masa zancen, aikuwa ya haɗe rai, ya ce "Dan mami ki daina wannan zancen, abokaina kowa ba wanda yayi aure sai ni, kawai na tsufa da wuri, kuma matar ma ki rasa wa zaki zaɓar mini sai wannan marar kunyar, ni ba zan auri matar da ba zan iya tanƙwarata ba, yarinyar da bata da kunya, ni bana so". "Raihan, cikar kamalar mutum iyali, ace kana da wannan matsayin baka da aure, ai sai a rainaka, kuma ganin kai baka da ko budurwa ya sanya na zaɓa maka, aure yana ƙarawa mutum kamala" Ya ce "To mami na ji, amma dan Allah ki ƙyaleni, idan lokaci yayi zan yi miki magana zan yi auren, amma ni yanzu wallahi ban yi niyyar yin auren ba, kuma da kaina zan samo budurwa da zan aura, ummi ta ce in nutsu in samo mace ta gari". Cikin mamaki mami ta ce "Wacece ummi kuma?" Ya miƙe tsaye ya ce "Kar ki damu mami, ni dai ki bar wannan maganar" "Wallahi ba zan barta ba, dole ka yi aure dan ba zan zuba ido ka lalace a banza ba, ko wata ta lallaɓa ta lalataka ba, wato ni nake yi maka kallon salihi, har mai baka shawara ce da kai a waje?". "You should thank God, shawarar kirki take bani, ita ta saita ni a hanyar da na ci jarrabawar Alhaji" daga haka ya fice ya bar falon. Abu kamar wasa, raihan har ba ya son shiga sashin mami, dan ta fara hura masa wuta, shi ko zancen ba ya so. Yanzu Ummi haɗuwa da raihan yana bata wahala, saboda yadda aiki ya saka shi a gaba, ba shi da cikakken lokacin kansa. Yau ya kirata a waya ya ce mata zasu fita, zai zo ya ɗau excuse a wurin manager. Da azahar ya zo ya sameta, lokacin ta gama aiki, tana ta tsokanarsa MD, yayi mata shiru yana hararta. Ta bashi wayarta ta ce "Raihan, dan Allah ka buɗe mini Instagram" "Me zaki yi da shi?" Ta ce "Kallon abubuwa zan din ga yi" "Wai wannan wayar taki, da ke da ita waye ya girmi wani? kalli yadda ta ci ƙaniyarta" "To sai ka bani taka ai" tayi maganar tana hararsa. Ya ce "Kin samu, ciro mini layukana ki ɗauka" "Ni da wasa nake yi, ka buɗe mini dan Allah na kasa buɗewa". Raihan ya ce "Ke Instagram ba zai hau wannan dattijuwar wayar taki ba, ai na ce ki ɗau tawa, ba abun da zaki ce na baki na hanaki" "Da wasa nake yi maka, ka buɗe mini" tayi maganar tana miƙa masa wayar tana ɓata fuska kamar ƴar yaye. "Da gaske na bar miki wayata ummi, kawo wayar taki mu yi exchange na layukan". "So kake ace na fara sata ko? Me nake sayarwa da zan mallaki wannan wayar?" Ya ce "Sai ki ce ke ƙawar MD ce" "A'a nice ma MDn, tun da ba zaka buɗe mini ba shikenan" ya karɓi wayar ta ta yana dubawa, ya ce. "Tashi muje mu dawo da wuri" "Ina zamu je?" "Budurwata zan sai wa wasu kaya, mu je ki tayani saya, za ta yi ki a jiki, bana son na sai mata wanda zai yi mata yawa". Ta harare shi ta ce "Kuma saboda ka raina ni, da ni zaka gwada? Daga baka muƙami ka fara kule-kule, guda nawa ka ke da ka fara yin ƴan mata" wani irin kallo yayi mata, tayi shiru, ta zata maganar da tayi ne, ta ɓata masa rai. Shi kuwa hoton da ya gani ne ya bashi mamaki, hotonta da noor, gashin kanta kamar aljana. Sai dai yayi tunanin ko sakawa tayi, amma ina ummi take da wata wayewar saka gashi. "Tashi mu je" ta tashi tabi bayansa, a ranta tana fatan Allah ya sa ba haushi ya ji ba. Ita kanta mamakin kanta take yi, yadda take bin raihan duk in da ya ce suje, ba tare da musu ba, yanzu ta daina fargabar shiga motarsa, kodayeke zuciya na son mai kyautata mata, kuma bai taɓa yi mata wani abu na rashin ɗa'a ba. Suna tafe a motar, ta ciro leda a jakarta ta ce "Gashi, dama ina ta jira mu haɗu, kuma saura ka ce baka so, sai ka je gida zaka duba" Ya amsa mata da "To babbar yaya" Wani ƙaton shagon sayar da kayan sawa suka je, suka shiga raihan suka gaisa da matar da ke shagon. Ya nuna mata ummi ya ce "Yauwwa hajjaju, ban san size ɗin da take sakawa ba, amma ga wata mun zo tare da ita, ki bata ta gwada, idan dai ta yi mata dai-dai, ita ma za ta yi mata. Matar ta ce "Masha Allah, bisimillah, muje to ka zaɓa sai ta gwada". Tarin abaya ne a wurin da suka je, kala-kala na kece raini. Ya kalli ummi ya ce "Zaɓo ɗaya wadda za ta yi mata kyau sosai". "To ai ban san ya take ba, ko wanda ta fi so ba, fara ce ko baƙa?" "Ina ruwanki da kalarta? to black beauty ce" Ta tsaya ta kalleshi ta riƙe ƙugu ta ce "Daga baka office, ka fara kashewa ƴan mata kuɗi ko? Alhaji ya sani?" Raihan shima ya riƙe ƙugu ya ce "Yau nake ganin ikon Allah, ke ina ruwanki ne? Wai ce miki aka yi ɗan zaman banza ne ni? Ɗauki muje akwai in da zamu je". Wata blueblack ta ɗaukko mai matuƙar kyau, matar ta nunawa ummi in da zata shiga ta gwada rigar. Tsayawa ta yi a gaban mudubin ɗakin, tana ƙarewa kanta kallo sanye da rigar, yau dai sau ɗaya a tarihin rayuwarta, ta saka doguwar rigar abaya da take matuƙar burgeta. Ta riƙe ɗan kwalin rigar a hannunta, ta zubawa mudubin ido, ta tafi tunani, ta zubawa mudubin ido, tana hango rayuwarta ta baya a ciki, cike da tozarci da ƙasƙanci, da rashin galihu kamar mara amfani, shigowar raihan rayuwarta ya bata lokacinsa, duk hankalinsa saboda kawai ya sakaya farinciki. A ranta take addu'a 'Allah idan ina da rabon yin aure a duniya, Allah ka kawo mini miji na yi aure, kar na yi aure na kasa rabuwa da raihan' saboda sosai take jin sa a jikinta. Ummi bata san adadin daɗewar da ta yi a tsaye ba, saboda gaba ɗaya ta bar cikin hayyacinta. Raihan gajiya yayi da zaman jiran ummi, kawai ya ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin amma shiru, kawai ya tura ƙofar da sallama. Kamar gunki ya ganta a tsaye hannunta riƙe da ɗan kwalin rigar, hawaye ya wanke mata fuska. Sandarewa yayi a tsaye, ta saka siririn ribbon ta ɗaure gashin, ta sake shi har tsakiyar bayanta. Ganin raihan ta cikin mudubi daf da ita ne, ya sanya ta dawo hayyacinta a razane, kokowar rufe kanta ta fara yi. A hankali ya saka hannu ya ɗaure zaren rigar ta baya. Ya saka hannu ya kamo gashin da ya sauka a bayanta, tsigar jikinta ce ta tashi, ta waiwayo da sauri, ƙare mata kallo yake yi. Rigar ta yi cif a jikinta, dirarriyar mace ce ta gaske, baƙar fatarta kawai mutane suke kallo, amma daga ƙirjinta zuwa ƙugunta komai dai-dai jikinta, kasa daina kallonta yayi, karo na farko kuma da yau ta kalli raihan a wani abu daban ba ƙaninta da take yawan faɗa ba. (Team a bamu daga farko, ku yi Allah ku din ga dubawa a watpad Please 🙏) Ayshercool 08081012143 What's app only *CUTARWA!* *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* P28 FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK. https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends Masu neman free books ɗina, da free pages duk akwai a kan watpad account ɗina. Irinsu Abduljalal Wata kissar sai mata Wuta a masaƙa Cutarwa Ƙanwar maza Gaba da gabanta Aƙidata Ruɗin ƙuruciya Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata. 08081012143. And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link. https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels Ayshercool. PAID ADVERT!. Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi. Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku Oll types of Turaran wuta Sandal Halut Irik Difur Gab Gab Kajiji Habil Nabak Humra Kulakcha Dilke da kalta Kayan Garan jiki Muna turara Kaya Kujerar garan jiki Kannada Madarorin turare masu kamshi Man garan gashi Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921 *TALLA!TALLA!TALLA!* *INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*. *BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU* *MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA* BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI. 28 Ajiyar zuciya ya sauke, ya sanya hannunsa a aljihunsa, ya ciro wayarsa. Ya shammaceta ya fara ɗaukar ta hoto ta cikin mudubi. Haɗe rai ta yi ta ce "Meyasa zaka shigo mini ba izini? Ni ka fita" "Na yi knocking, na kuma yi sallama, duk baki amsa ba, kin bar ni a tsaye ina ta jiranki, kin shigo kina kuka, idan ma dan in bar miki rigir ne ki ke kuka, ba zan baki ba, fito mu tafi" Ba tare da ta saki fuska ba, ta ce "Ni ka fita na cire rigar" Ya basar ya ce "Ki batta a jikinki, ki zo mu tafi". "Dan Allah ka fita na cire" tayi maganar a raunane tana ɓoye jikinta. A hankali ya taka ya nufi hanyar fita, ya sake waiwayo wa, tana tsaye jiran ya fita ta canza kayan. Ya fita ya koma reception. Ba ƙaramar kunya ce ta kama ta ba, ganin da yayi mata a haka, gashi dai doguwar riga ce, amma ta kasa manta irin kallon da yayi mata, da ya sanya ta shiga wani yanayi da ba ta san menene ba, gaba ɗaya sai ya canza mata, kamar ba raihan ɗin da ta sani ba. Ta mayar da hijjabinta, ta fito da rigar a hannunta, matar ta kallesu ta ce "Rigar ta yi?" Ya ce "Eh, bamu wasu kalolin a haɗa da wannan, su zama biyar sai takalmi uku da zai shiga da kowacce" komai da ummi aka gwada, kuma ba ta kawo komai a ranta ba. Ɗan nazarinta ya din ga yi, ko fushi take yi da shi, amma ya lura kawai ta tsorata ne, ta kasa sakin jiki ma tayi masa magana, dan abu ne mawuyaci ka ga ummi ta yi fushi, dan zai iya cewa bai taɓa ganin tayi ba, idan ma abu bai yi mata daɗi ba, sai dai ta yi shiru. Suna tafe a hanya ya cigaba da yi mata hira, kamar bai ga komai ba, yana koɗa kyan da kayan suka yi. Sai dai gaba ɗaya shima jikinsa yayi sanyi, basarwa kawai yake yi. Wani restaurant suka je, yayi reserving VIP, aka kawo musu abinci kala-kala, amma ummi ta ce ba za ta ci ba, ya gama kawai su tafi ita hankalinta yayi gida. "Amma mussman saboda baki je walimar nan ba na shirya mana wannan" "Sai ka ce wani film, ni ka yi sauri mu tafi, kar na je gida na kasa kare kaina". "Da na san zaki watsa mini ƙasa a ido, da ban kashe kuɗina ba, i did all this because of you" Ta ɗan kalleshi ta ce "Ni ban taɓa cin abinci a waje ba, dan Allah ka yi haƙuri" Raihan ya ce "Zan fita na baki wuri ki ci, amma idan ki ka yi mini haka ba zan ji daɗi ba". Ƙarshe dan kar ya ji haushi, da ƙyar ta cakala ta ci, suka tafi gida. A hanya yake ta ce mata tayi ƙoƙarin rarraba CV ɗin ta, ko Allah zai sanya ta samu wani aikin da ya fi wanda take yi. Ta ce masa zata jarraba yin hakan. Raihan ya dage sai ya mayar da ummi ƴar gayu, ta hanyar kaita wurare da zasu ɗebe mata kewa, ba tare da ƙetare iyakar addini ba. A ɗan fitar nan da ummi suke yi, take ganin mata kala-kala, masu dressing kala-kala, ba ta sani ba ko rashin shiga cikin mutane ne ya sanya ita duk ba ta iya wannan abubuwan ba, hatta ɗaurin ɗan kwalin da ta kan gani a kan mata yana burgeta, amma ita ba yi take yi ba, daga aikin gida sai makaranta ba ta da wani hope balle tayi tunanin wata kwalliya. Da Raihan yaje gida ya duba ledar da ummi ta bashi, sabon agogo ne kar, da links sai littafin azkar babba, da carbi counter. Ta yi rubutu kamar haka "Allah ya taya riƙo mai girma MD, wannan ce gudunmuwata, ban san me kake buƙata ba, amma ina fatan ba zaka raina kyautar yayarka ba, Ummi" Ya yi murmushi a hankali ya ce 'Kin rama kenan, a taƙaice kin dawo mini da kuɗina' Ya kirata a waya, sai dai wayar a kashe. Ya kashingiɗa yana tuno ummin, mussaman ɗazu da ta saka doguwar rigar abaya, tayi wani irin kwwarjini da kyau, daga cikin abun da ya ɗau hankalinsa dogon gashin ta har tsakiyar bayanta, ya fara tunanin anya ummi ba ta haɗa dangi da wani ahali na yankin ƙasashen ƙetare ba? Idonta da gashinta, sun nuna hakan. "You are beautiful fa ummi" ya faɗa a fili ba tare da ya shirya yin hakan ba. Dubu talatin ɗin nan da ya bata, dubu biyu ce tayi saura, dan sai da ta saya wa kawunta turare, ta saya wa Abdul, sai ƴar ɗakinta wato noor, har da su farida, amma kausar ta yatsuna fuska ta ce Allah ya kiyaye ta shafa wannan abun kamar ƴar bori, suka bar ta da abun ta. Duk da abun da suka yi mata, ummi ta ji daɗin murna da addu'a da dr. Yayi mata, hakazalika Abdul ma yayi mata addu'a sosai, mutuniyarta kuwa kasa zama wuri ɗaya tayi, dan ƴar tsana ta saya mata. Ummi ta yi mamakin yadda aka yi kuɗin ma suka isheta, ba ta taɓa tunanin haka yi wa mutum kyauta yake da daɗi ba, ayi ta yi maka addu'a. Kwanaki biyu da fitar su ita da raihan, tana ɗakinta tana tilawa Abdul yayi sallama, ta kaste karatun tare da amsa masa. Ya miƙa mata ledar hannunsa, ta karɓa tana kallonsa bakinta fal tambaya. Kan tayi masa tambayar ya ce "Wani guy ne muka haɗu a waje ya ce na baki, wani ɗan dogo mai haske" gaban ummi ya faɗi, ta san ba wani bane face raihan. Abdul bai sake yi mata wani bayanin ba, ya fita daga ɗakin. Jikinta na rawa ta hau duba kayan, dogwayen riguna nan ne da suka sayo, har takalman da komai. Da sauri ta tashi ta leƙa ƙofar ɗakin, ta tabattar babu kowa, me raihan yake nufi ne? Wannan kayan idan aka tanbayeta ta ce a ina ta samu? Layinsa ta fara kira, ya ɗaga a nutsensa tare da amsa sallamar da tayi masa. "Raihan, shine ka bawa Yaya Abdul wannan kayan ya kawo mini, idan aka tuhume ni a ina na samu me zance? Kar ka janyo mini matsala fa" "Kar ki ji komai ki ce ni na saya miki, saboda na fuskanci kina so, budurwa ce ke ba tsohuwa ba, dan haka mace sai da kwalliya, ni ina da yayye da ƙanne mata, duk in da mace take tana buƙatar kulawa, a kan buƙatunta na yau da kullum, kar ki ji komai yayata, ki yi kwalliyarki dai-dai da addinin musulunci, Allah ya kawo mana abokin rayuwa na gari" maganar sa ta ƙarshe, da yayi addu'ar sai ya ji wani abu mara daɗi a ƙasan zuciyarsa. Ya kashe wayarsa, ummi ta bi kayan da kallo, ina ma zata iya amfani da kayan nan, ta tashi ta kulle ƙofar ɗakin, ta ɗauki kayan tana gwadawa ɗaya bayan ɗaya, karo na farko da ta ɗauki jambakin da yasa mata wancan karon, ta ƙara tisa shi a kan jajayen laɓɓanta, ta saka kwalli a idonta. Ta ƙurawa kanta ido a gaban mudubin, ta din ga juyi a tsakiyar ɗakin, wai yau ita ce ta saka wannan kayan masu tsada, ta kalli takalmin ƙafarta mai tsini, ta din ga kaiwa tana komowa a ɗakin. "Allah ya ƙaro maka arziki mara yankewa, ya yalwata maka duniya da lahira" hakanan ta ji ina ma ya ga kayan a jikinta, har da janbaki ta saka yau, abun da yake so ya mayar da ita ƴar gayu. *** Gaba ɗaya farida ta kasa sukuni, tun da mijin inteesar ya ce zai ƙara aure, suke yawon neman asiri, amma babu abun da ya sauya, ga azabar takura daga dangin miji, da gori na cewa ita juya ce. Da ya ce kan ya ƙara auren zai canza mata gida da furnitures, amma babarsa ta ce bata yadda ba, da wanne zai ji, kuɗin da zai kashe yayi wani auren, ko kuma wanda zai kashewa juya, da ma tana haihuwa ne da sauƙi. Gefe ga kausar dr. Ya ƙara hura mata wuta, a kan lallai ko tayi karatu, ko sai ta fitar da miji. Farida kuma ta yi alwashin, sai ummi ta koma ƙauye ta bar mata gida, ko kuma ta fitar da miji itama, dan ba zai yiwu ya takura wa ƴar ta ita kaɗai ba. Ga noor wani irin rashin ji take yi, ba ta shakkar farida ko kaɗan, tsagera ce ta gaske, ummi ce kawai sai dr. Suke iya tanƙwarata, dan ko Abdul sai ta ga dama take jin maganar sa, dan ta ce faridan ba ta sonta, su inteesar kawai take so, ita kanta ummi tsagerancin da noor take yi da ƙanan shekarun nan, yana bata tsoro, amma babu yadda ta iya, tana yi mata addu'a, tare da yi mata fatan shiriya. Gashi farida ta ɗora laifin hakan a kan ummi, wai ita take zigata, take hurewa ƴar ta kunne. Kamar a baya da duk abun da za ayi ummin ba magana take yi ba, haka yanzun ma, ba wani abun take cewa ba, duk abun da za ayi sai dai tayi shiru. Babban abun da ya ɗaga mata hankali, bai wuce kawu Yahaya da ya je gagarawa, ya dawo da katin bikin Yaya magaji ba, kuma ya tabbatar mata da ita za su je bikin nan, kuma a yadda yayi maganar umarni ne kawai ba wai neman yardarta ba. Ta amsa masa da to, amma ƙasan zuciyarta wani irin lugude take yi da fargaba, da fatan Allah yasa ba da sun je za a baro ta a can ba, dan kuwa farida ta ƙara matsa lamba sosai da sosai, ta addabi ummi da gorin rashin aure da kuma ƙara tabattar mata da barin gidan. Gefe guda kuma, abokin shawarar ta ta, ya zama very busy, wataran sai su wuni ma basu yi waya ba, ga tafiye-tafiye da suka sako shi a gaba, saboda importing na kayansu, nan da nan kuwa ya fara rama, duk ranar da zai dawo gari, sai ya yi wa ummi waya tayi masa abinci, ya aika a karɓo masa ba zai ci na gida ba. Alhaji Tahir ya sha suka da caccaka, a kan yadda ya ɗauki ragamar babban kasuwanci kamar wannan, ya danƙawa raiha, a matsayinsa na ƙaramin yaro, Alhaji Tahir ya toshe kunnensa, dan kuwa bai ji zai canza ra'ayi ba. Abunka da mata da miji, mami tayi ta lallaɓa Alhaji, har ya amince da maganarta a kan raihan yayi aure, amma ya ce ba ruwansa da zaɓa wa raihan ɗin matar aure, balle auren  yaƙi daɗi ace laifinsa ne. Shima Alhajin yayi iya ƙoƙarin sa wurin fahimtar da raihan muhimmancin ace yana da iyali yanzu, tun da ya samu matsayi. Raihan ya ce "Wai Alhaji da wanne zan ji?, tsufa zan yi da wuri, ka manta nauyin da ka ɗora mini?" Alhaji ya ce "Ni meyasa ban tsufa da wurin ba?akwai riba a cikin yin aure da wurin babban mutum, aure ba takura bane ba, kwanciyar hankali ne da nutsuwar zuciya ka yi tunani a kai". Raihan ya ce "To Alhaji zan yi, zan yi shawara da hajiya" Alhaji ya ce "Ba maminka ba?". "A'a Hajiya" "Ɗan gidan Hajiya, ni ba zan bayar da shawara ba sai Hajiya kenan? Ai shikenan babban mutum". Gidansu ummi kuwa yau gaba ɗaya jikinta babu daɗi, ta gaji sosai da sosai, dan farida baƙi tayi, kan ummi sai ciwo yake yi, kamar za ta yi zazzaɓi da ƙyar ta lallaɓa ta yi aikace-aikace. Sai da ta jera kwana biyu ba ta zuwa aiki, ta sanarwa manager ba ta da lafiya ne, haka islamiyya ma, kwana biyu zazzaɓi ya sakata a gaba da matsanancin ciwon kai da na ciki. Dama Ummi ba ta saka ran wani ya bata kulawa ba, ita da noor kawai suke jinyar, noor ta yi wanke-wanke da abun da zata iya, a daddafe ummi take aikin gidan, farida ta lura da hakan, amma ko a jikinta dama da dr. Yana nan ne ya fuskanta zai kaita asibiti. Raihan kuma ba sa iya waya, sai ta what's app, dan kuwa baya ƙasar gaba ɗaya, dan haka bai san halin da take ciki ba. Tun ƙarfe shida ummi ta ga farida sun  ɗauki mota da ita da kausar sun fice, Abdul kuwa aiki yaƙi samuwa, dan haka a wani kamfanin sarrafa taki, dr. Ya samar masa aiki, shima farida ta din ga kushewa, da nuna ɗanta ya fi ƙarfin wannan, amma Abdul ya ce yana so zai yi. Ganin da noor tayi ummi babu lafiya sosai, ya sanya ta karya da buredi ta tafi tahfeez, ummi ta din ga burgima a ɗakin ta, ga amai kuma cikin ta babu komai. Wayarta tayi vibrating ya fi sau shida, da ƙyar ta ɗaga ta yi sallama. "Baccin safe ki ke yau kenan, ko islamiyyar baki je ba? Na shigo gari jiya da daddare, abincinki nake son ci, kuma in ganki". Cikin ƙarfin hali ta ce "Dan Allah ka yi haƙuri, bana jin daɗi amma zuwa yamma in sha Allah idan na gama zan kira ka". Bai san lokacin da ya tashi tsaye ba ya ce "Ummi kamar fa haki ki ke yi, kina Asibiti ne?". "A'a ina gida ne, zan warware in sha Allah" tayi maganar da ƙyar kanta na sarawa. "Bani 20minutes gani nan" kan ta sake magana ya kaste kiran, ya fita da sauri. Ummi ba ta sake sanin in da kanta yake ba ma, sai da ta ji ana buga ƙofar ɗakinta. A hankali ta ce "Waye?". "Mai gadi ne, kin yi baƙo ne, yana sallama" Ummi ta ce "To" maimakon ta tashi, sai ta cigaba da bacci na rashin lafiya, a ƙalla maigadin ya zo sau uku, kan ta iya fitowa. Hankalin raihan ba ƙaramin tashi yayi ba, da ya ga ummi, idanuwanta duk sun yi waje. Tana ƙarasawa ta nemi wuri zata zauna a ƙasa, ya hanata hakan ya saka ta shiga motar. Tun da ya ja motar yake faɗa a kan wasa da lafiyarta, oho ba ta ma san takamaiman zahiri ne ko mafarki ba saboda zafin zazzaɓi. Ba a samo kan ummi ba, sai bayan ta sha ruwa roba biyu, sai dai a halin da take ciki, hankalinta yana gida, kar wani ya dawo a tarar ba ta yi girkin rana ba. Likita ya din ga yi mata tambayoyi cikin harshen Ingilishi, dan ba ya jin hausa, da ƙyar take iya amsawa saboda ciwo, kuma hankalinta yayi gida. Ya ce "Akwai ciki ne?" Sai da ummi ta kalli likitan, amma ta kasa magana. Raihan ya ce "Babu". "Ka tabattar? When last ta yi period?" Maimakon raihan ya ce ba ta da aure, sai ya kalleta ya ce "Yana tambayar ki". Likitan ya ce "Kai baka sani ba ne? Are you not couples? Na ji ka ce babu ciki" Raihan ya wani gyara tsayuwa ya ce "Ai da yake bana gari, shiyasa ban riƙe ba, ummi ki gaya masa" ta sunkuyar da kai ta yi shiru, kamar ta buɗe ido ta ga ta ɓace, raihan ya gama da ita gaba ɗaya. Raihan ya ce "She can't recall, but she's not pregnant" Aka yi wa ummi teses, malaria da typhoid sun yi mata mummunan kamu. Likita ya ce a bari ta kwana ɗaya a asibitin, ummi ta ce ba ta san zance ba, ta sha faɗa a wurin raihan kan rashin kula da lafiyar ta, tare da yi mata kashedin saura ta je gidan a sakata aiki tayi. Ji yake tamkar ya samu wani kauwamammen wuri, ya ajiye ummi ya din ga kula da ita, kulawa ta musamman. Ta so ace zata iya abun da raihan ya ce, taƙi yin aikin gidan, dan a galabaice take, amma da cin mutuncin da za ayi mata, gara aikin gidan. Tayi ta yi wa Allah godiya, har suka dawo bayan azahar su farida ba su dawo ba, dama noor sai la'asar zata dawo. Haka ta lallaɓa take aikin, lokaci-lokaci sai raihan ya kira ummi, ya tambaye ta ya take ji a jikinta, gaba ɗaya ya kasa nutsuwa hankalinsa ya ƙi kwanciya, dan babban fatansa ace a kwance take ko ruwa za ta sha, a ɗaukko a bata. Babban abun da ya bawa ummi mamaki, bai wuce yadda headmastern makarantar islamiyyar su ya zo dubata ba, har da kawo kayan dubiya, headmaster yana daga cikin mutanen da su kan hantari ummi, mussman idan ta je a makare, gashi ita kuɗin makaranta take biya, wurin ɗaukar nata karatun, ita kuma koyarwar da take yi, ko sisi basa bata, dan raihan har mita yake yi, a kan hakan ya ce yakamata ko ba yawa a din ga biyanta. Amma ga mamakinta sai ga headmastern ya zo dubata, ba ta kawo komai a ranta ba, tayi masa godiya ya tafi. Saboda rigimar raihan, ummi ta lallaɓa ta koma aiki, dan kuwa idan ba ta yi wasa ba, a sintirin da yake yi, sai an san da alaƙarsu, alaƙar da ba ta san ta yaya za ta yi bayaninta ba. Har wurin aikin yake bin ta, ya tabbattar ta ci abinci ta sha magani. Ta sanar masa da batun zuwa gagarawa, da yadda take cikin damuwar hakan, kar idan ta je a riƙeta a can. Raihan ya ce "Ki kwantar da hankalinki, babu abun da zai faru sai ikon Allah, kuma babu wanda zai rabaki da garin nan, abun da nake so da ke, ki yi iya ƙoƙarinki ki sake samo information a kan mama idan kin je, zan san ƙoƙarin da zan yi a kan hakan, da wallahi suka riƙe ki a garin nan, ba abun da zai hana ni binki" Ɗan buɗe baki ta yi tana kallon sa, da gaske har cikin zuciyarsa yayi maganar. "Raihan wai ranar da na yi aure, yaya zaka yi ne?" "Yaya zamu yi dai? A ƴan uwanmu zan samo miki miji nagari, ni kin san kuwa mami ta sakani a gaba, wai tun da Alhaji ya bani ragamar kasuwancin nan, wai sai na yi aure" Ummi tayi dariya ta ce "Daɗina da mami hangen nesa, wallahi kuma da gaskiyarta" Ya girgiza kai ya ce "Ba zaki gane bane yanzu haka kawai ganina ki ke yi, bana son yawan takura miki, amma sai kin tayani da addu'a, akwai ƙalubale sosai a harkar kasuwancin nan, kuma kamar yadda ki ka faɗa, akwai buƙatar yadda ki ka gaya mini, ina buƙatar mace ta gari to assist me, wallahi ummi ban taɓa budurwa ba, kuma bana son auren haɗi, ni ba zan auri matar da bana so ba" Ummi ta yi dariya ta ce "Za a sha ƙiriniya, amaryar ka za ta sha fama da ƙuruciya" Kallonta yayi ya ce "Kin rainani da yawa fa, idan na fita kin ga yadda nake tsare gida kuwa a waje, a man of 24yrs, ki ke cewa za a sha ƙuruciya" Ummi ta waro masa idanunta ta ce "24 kuma, ka ji tsoron Allah raihan, yaushe ka kai 24yrs kuma?" Ya ce "Wallahi na cika 24yrs" Da suka yi lissafi, watanni goma sha huɗu ummi ta bashi. Ya ce "Da na san ba wani girmata ki ka yi ba, ba zan bari ki raina ni ba, ashe ma sa'ata ce na ma fa fiki girma ummi, daga yanzu ma ni ne yayanki yaya zaki din ga ce mini" Ummi ta ce "To meye a ciki Han? Ai duk in da namiji yake jagora ne, mai girma MD, sai dai ba a canzawa tuwo suna, ni yayarka ce" Yayi dariya yana shafa sajensa, ya na bin ta da kallo, ya kasa gane a wane bugire ma ya ajiye ummin ne a yanzu. "Me ka ke kallo ne?" "Your eyes, masha Allah i like them, ina son idanunki" Ummi ta rausayar da kai ta ce "Idan ka faɗi haka kana tuna mini da babana, idan na ce masa baba wai idona irin na akuya ne da mage? Sai ya ce A'a, idonki mai kyau ne, ina son idonki ummina" Raihan ya ce "Allah sarki, Allah ya jiƙan baba da rahama" "Amin Yaya Han, ina godiya sosai da sosai" Yayi murmushi ya ce "Han sai ka ce sunan ƴan china, amma duk yadda ki ka faɗa zan amsa, ki kula da kanki sosai a garin idan kin je, zamu din ga waya har ku dawo" Ummi ta ce "To, in sha Allah" Ummi na son nunawa raihan hotunan da ta yi da rigunan nan a wayarta, amma ta kasa, shi kuma bai takurata da tambayar bai taɓa ganin ta saka kayan da ya bata ba. Ummi ta lura kamar babu jituwa tsakanin dr. Da farida tun wancan karon da ya koma aiki, har wannan dawowar tasa, sai dai kasancewar ummi ba huruminta bane ba, ya sanya ta cigaba da sabgoginta. Ranar tafiyarsu gagarawa na ƙaratowa, adadin tashin hankalinta, da fargaba na ƙaruwa, sai dai ta na ta addu'a a kan Allah ya kare faruwar dukkan wani abun ƙi. Ta ɗauki ɗaya daga cikin dogwayen rigunan wurin raihan, da abun da ba a rasa ba, ta haɗa kayan da zata yi tafiyar da su. Dr. Ya ce har da noor zasu tafi, noor ta din ga murna, tana jin daɗi. Suna tafe a hanya, adadin fargaba da tashin hankalinta, yana ƙaruwa, tana tuna irin azabar da ta sha a gagarawa, ta din ga fatan ina ma har ta je ta dawo, ba zata haɗu da wasu mutanen ba, dan ko ambatar sunansu na sanyata cikin damuwa. Kwantsin yaran gidan ne suka firfito, suna shelar ga kawu Yahaya ya zo, yaran da galibi duk ba ta san su ba, dan da yawansu bayan ta baro garin aka haife su. Kallon gidan ummi take, zata iya cewa wannan gidan shi ne kurku mafi azaba a tarihin rayuwarta. Da yawa yaran basu san ummi ba, dan haka suka din ga bin ta da kallo. A tsakar gida sashen iya, mata nata hada-hadar shirin biki, sallamarta ce ta janyo hankalin matan. Wanda suka santa, suka din ga zuzuta girman da tayi, ta ɗaga kai ta kalli ɗakinsu, ɗakin mai ɗauke da ɗumbin tarihi, alamu ya nuna akwai mutane a ɗakin, amma ba ta san suwaye a ɗakin ba. Ɗakin Iya ta nufa, ta tarar da Iya zaune a tsakar ɗakin ta, tana ta bayar da umarni. Saroro ta bi ummi da kallo, cikin ƙarfin hali ummi tayi murmushi tana gaida Iya. "Yau Allah ya kawo ki wurin mayu kenan, wanda za su cinyeki?" Ummi ta yi shiru tana sunkuyar da kai. Noor dai ta kame tana kallon kowa ɗaya bayan ɗaya. Dr. Ya shigo shima yana ta gaisawa da mutane, da ya isa ɗakin iya, ko gaisawa ba su yi ba, ta fara masifar ya bar ummi ta balage ba aure, kodayeke dama ya za ayi ta auru, ai dama tun da tun farko taƙi amincewa da rufin asirin aure, ya goya mata baya, haka zata riƙe a gida ba aure. Aikuwa kawu yahaya ya haɗe rai ya ce "Iya dan Allah ya isa haka, haba ummin guda nawa take? Ke ba ki yi farincikin ganinta tayi ilimi, a nutse a kame ba, ni na zaci wannan abubuwan duk sun wuce tun a baya?". Ummi ta sha mamakin yadda Iya ba ta canza ba, tsawon wannan lokacin. Tun a daren yaya magaji ya zo wurin ummi, sun daɗe suna hira, tare da murnar ganin sauyin da ummi ta samu, ya din ga gaya mata irin yadda abubuwa suke ta kwaɓewa a cikin dangin nasu. Abubuwan duk babu daɗin ji, mussaman gidan Idris, yarinyar su ta gaba da alfatiha, ƙalubalen da take fuskanta ya sanya ta fara fanɗarewa ita ma. Al'amarin bai yi wa ummi daɗi ba, wanda jahilci ke taka muhimmiyar rawa a rayuwar mutanen gidan. Washegari ɗaurin aure, bayan ummi da noor sun yi wanka sun shirya, ta ja noor suka fita gidansu na'ima, amma ta tarar maman na'ima ta rasu, ƙannenta duk sun yi aure. Doguwar riga ummi ta saka ta wurin raihan, sai dai tana jin ta kamar ba ita ba, saboda jin ta take a takure a cikin kayan, dan ma rigar isashiya ce, sai dai fa ta zama a bar kallo a cikin gidan, duk in da tabi sai a kalleta. Iya ta din ga nuna wa mutane ummi, ga ƴar wurin bashir, da Idiris ya aura taƙi zama, ta bi kawu yahaya gashi haryanzu ta gama balagewa ta riƙa ba aure shi yanzu yana da yara biyar. Idiris kuwa tun da ya ga ummi kamar maye, saboda azabar kallo, sai dai ga mamakinsa ummi tayi masa kwarjinin da ko magana ya kasa yi mata, gashi dai ba wani abun ta canza ba, kamaninta suna nan, sai dai ta girma ta cika, kai ba ka ce tana fuskantar ƙalubale a in da take ba. Ko in da Idris yake bata kalla ba, balle ya sanya ran za ta gaishe shi. Su Alhassan ma duk sun girma, da su auwwalu, sai dai babu wani cigaba su ma, dan kuwa auwwalu ma ya zama ɗan shaye-shaye sosai da sosai, dan har prison yayi, babu sana'ar kirki ya zama criminal. Alhassan ma babu sana'ar kirki, sai kamasho da ƴan buge-buge. Raihan kuwa yana ta kiran ummi a waya, da jin ko komai lafiya ƙalau. Ana dawowa daga ɗaurin aure, kawu yahaya ya ce zasu koma gida, sai dai ummi ta sha surutun mutanen gidan na rashin aure. Suna tafe kawu yahaya yana yi wa ummi nasiha, a kan ta kwantar da hankalinta a kan rashin aure, saboda lokaci ne, shi aure ba gaggawa ba samun nagartaccen miji da gidan aure mai cike da farinciki shi ne abun fata. Ita dai ummi ganin sun taho daga gagarawa ya fi komai faranta mata rai. Tashin hankali ba a saka masa rana, bayan su ummi sun sauka a kano gida, ummi ta tarar da ɗakinta a garƙame an saka masa mukulli. Falo ummi ta tafi, ta samu Farida ta ce "Anty ke ki ka kulle ɗakina?" "Eh ni na kulle, saboda ba gidan ubanki bane ba? Dan mun riga mun yi da shi ba zaki dawo mini gida ba" Saroro ummi ta yi tana kallon fareeda, dr. Ya fito yana faɗin "Wai farida bamu gama wannan maganar ba? To wallahi idan ki ka cigaba da matsawa, sai dai ke ki bar gidan, kema ki koma naku gidan" Farida ta duba wajen dining, ta ɗaukko kaya ta watso su tsakar falon ta ce "Sai ka tambayeta a ina ta samu wannan kayan? Wallahi dole ta bar mini gida, kan ta lalace ta lalata mini yara" Ummi tabi kayan da kallo, kayan mayukanta ne, na wurin raihan da kayan sawa. "Wannan kayan sun fi ƙarfin na dubu ɗari, sai ka tuhumeta a ina ta samu, kuma gidanka ba zan bar shi ba, dan na ci gida"..... Ayshercool 08081012143 [4/20, 7:20 PM] Authoresses: *CUTARWA!* *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* P29 FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK. https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends Masu neman free books ɗina, da free pages duk akwai a kan watpad account ɗina. Irinsu Abduljalal Wata kissar sai mata Wuta a masaƙa Cutarwa Ƙanwar maza Gaba da gabanta Aƙidata Ruɗin ƙuruciya Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata. 08081012143. And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link. https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels Ayshercool. PAID ADVERT!. Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi. Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku Oll types of Turaran wuta Sandal Halut Irik Difur Gab Gab Kajiji Habil Nabak Humra Kulakcha Dilke da kalta Kayan Garan jiki Muna turara Kaya Kujerar garan jiki Kannada Madarorin turare masu kamshi Man garan gashi Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921 *TALLA!TALLA!TALLA!* *INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*. *BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU* *MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA* BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI. 29 Wata irin tsuma jikin ummi ya fara yi, dan ba ta san ta ina zata fara bayani ba, bata taɓa tunanin farida za ta shiga ɗakinta, tayi mata bincike ba. Dr. Ya bi kayan ɗaya bayan ɗaya da kallo. Cikin haƙilo farida ta ce "Sai ta yi maka bayanin in da take samun wannan kayan, idan ba wani mugun abun take aikatawa na rashin gaskiya ba" Tsulum noor ta tsoma baki ta ce "Kai, yaya raihan ne fa ya saya ya bata, ko yaya ummi?" Kamar gunki ummi ta sake sandarewa, dan ba ta san ta aka yi noor ta riƙe sunan raihan haka ba ma. Dr. Ya durƙusa ya tsince kayan, ya mayar cikin ledarsu, ya miƙe tsaye ya kalli farida ya ce "Bani mukullin da ki ka rufe mata ɗaki" "Ban gane ba, me ka ke nufi?" "Abun da ki ka gani, ba budurwa ba ce ba? Ke abubuwan da ake kawowa kausar cikin gidan nan zama ki ke ki tuhume ta?" "Amma tsakani da Allah ka taɓa ganin wani yayi sallama da ita da sunan yana sonta, da zai saya mata wannan kayan masu tsada?" Ya wuce ɗakin farida, tabi bayansa tana cigaba da masifa, ya ɗaukko mukullaye, ya dubi ummi ya ce "Mu je" Tabi bayansa hawaye na zuba daga idonta, ya buɗe ɗakin nata, duk an hargitsa shi. Ya ajiye mata kayan, ya kalleta ya ce "Mamana, na yarda da ke ɗari bisa ɗari, na san ba zaki aikata wani abu na Allah wadai ko a bayan idona ba, goya miki baya baya nufin, ki aikata abun da bai dace ba, ba zan matsaki a kan lallai sai na san me ki ke ciki ba, ni uba ne, kuma malamin makaranta, na san yadda zan tafiyar da tarbiyar yarana. Kin mai munzalin da bin diddigin rayuwarki, ba shi ne mafita ba, amma dai ina sake yi miki tuni, da ki ji tsoron Allah, ki kuma kare mutuncinki, amma har ga Allah ni bana zargin ki, ki goge hawayenki ki samu ki huta, ni ban gaji da zamanki da mu a gidan nan ba, saniya ba ta taɓa gazawa da ƙahonta, dan haka ki kwantar da hankalinki komai mai wucewa ne, kuma in sha Allah zaki sha mamakin abokin rayuwar da Allah zai zaɓa miki, ke dai ki cigaba da tsare mutuncinki" Ummi ta jinjina masa kai, ya fita daga ɗakin, ta zauna a hankali tana kallon kayan, tayi shiru tana nazari, idan har zargi zai shiga zuciyar dr. Game da ita, gara ta nemi duk mai yiwuwa ta rabu da raihan. Tabbas kaya ne masu tsada da ta cancanci a tuhumeta a kansu, da kawu ya matsa ta ina zata fara yi masa bayanin wannan alaƙar ta su, da ba kowane mai hankali ne zai sanyata a gurbi mai ma'ana ba. Ya zama dole ta nesanta kanta da raihan, duk da abu ne mai wahala a wurinta, daga haɗuwarsu zuwa yanzu, ya gina wani tarihi da ba zai rushe ba a rayuwarta, raihan na daga cikin mutane masu muhimmanci da ba zata taɓa mantawa da su ba, zuciyarta ta saba sa shi, ta shaƙu da shi, ya bata ƙarfin gwiwa daban-daban, ya sanya ta jin ita cikakkiyar mace ce ɗan Adam da zata iya gogayya da kowa, tabbas raihan ya cancanci a kira shi ƙaraminsu babbansu, domin kuwa a manyan ba kowa ne za a samu da irin qualities ɗin sa ba. A hankali ta tattare kayan, ta gyara ɗakinta, ta rama sallolin da suka tsere mata, ta cigaba da tunani. Ta ɗaukko wayarta ta duba, missed call ɗin sa duk a wayar, har da saƙo yana tambayarta meyafaru ba ta ɗaga wayarsa?. Ta kashe wayar gaba ɗaya ta ajiye, tana son fara koyawa kanta janye wa raihan. Ta yinƙura ta fito daga ɗakinta, amma ta jiyo hayaniyar kawu da farida, kuma duk a kanta, jiki a sanyaye ta koma ɗakinta, da tana da wurin zuwa da zata bar wa farida gidanta, ko kawu ya samu sassauci daga wulaƙancin da farida ke yi masa. *** Anty Rakiya ta cigaba da matsa lamba, da ƙarfafa mami, a kan lallai a haɗa auren nan na zumunci, ita kuma mami ta cigaba da matsawa raihan, tare da ziga Alhaji a kan lallai a takura raihan yayi aure. Abun ya fara damun raihan, dan haka ya samu hajiya da maganar, Hajiya ta ce "Babban mutum, menene a ciki dan ka yi aure, gaskiyar maminka ne shi ne cikar kamalarka ai". "To hajiya sai in yi aure su yaya ba su yi ba, kuma nema ake fa a sakani na auri wadda ba na so, ni bana son yarinyar nan" "Raihan, dan ka riga su Salim aure babu laifi a ciki, bujirewa umarnin mahaifiyarka ba shi da fa'ida, ko ba ka auri wadda take so ba, ka yi ƙoƙari kai ka kawo musu wadda ka ke so" Yayi shiru yana nazari, sannan ya kalli hajiya ya ce "Shikenan hajiya na gode sosai da sosai" Ya tashi ya fita, yana nazarin maganar Hajiya. Gefe guda kuma yana mamakin kasa samun ummi a waya, har ta what's app, ya fara tunanin ko dai wani abun ya sameta ne. Yaje wurin aikinsu Ummi, ya tambayi mai yi musu shara, ya ce masa ba ta je ba. Ita ma ummi a lokacin da take ƙoƙarin ƙauracewa kiran raihan, headmastern su ya kunno kai, sai ya din ga kiranta a waya, wai su gaisa, wannan satin har da bata dubu biyu wai ta hau mota, saboda ɗawainiya da take yi da ɗalibansu. Hankalinta ba a kan wannan yake ba, kamar ta fi raihan azabtuwa da ƙauracewar da ta yi masa, gashi pressure cikin gidansu, ta ƙara yawa, dan kuwa farida kullum cikin masifa da tashin hankali take a cikin gidan nan. Babu tsammani dr. Ya samu ummi ya ce mata "Mamana, wani mutum ya zo wurina, ya ce mini yana sonki, kuma babu daɗewa yake son ayi auren, na bashi damar ya zo ku gana, sai dai ba ina nufin lallai sai kin aure shi bane ba, bana son yi masa karambani, ganin babban mutum ne, amma duk yadda ku ka yi sai ki gaya mini" Ummi ta amsa masa da to ne, amma ta shiga cikin fargaba da zullumi, tare da tunanin, waye wannan? Kai tsaye ya tafi wurin dr.? Abun yayi ta bata mamaki, sai dai sam ba ta ɗokin abun, domin kuwa bayan saka wayarta a flight mode, sai ta koma tana duba messages ɗin raihan. Gaba ɗaya ummi ta manta da dr. Ya ce za ta yi baƙo, saƙon raihan na ƙarshe ya tsaye mata a rai. "Ummi na bincika kina lafiya, amma you are avoiding me, ban sani ba ko nayi miki laifi ne, idan na yi miki laifi ne dan Allah ki yi haƙuri ki yafe mini, ina cikin damuwa sosai wallaahi, ban zaci shaƙuwarmu ta kai in shiga damuwa haka ba, dan Allah ki yi mini reply ummi, zan tafi italy gobe in Allah ya kaimu da asuba, dan Allah ki yi mini magana" Ajiye wayar ummi tayi, idonta na cika da hawaye, "Ban kyauta maka ba raihan, amma yanzu ko na yi maka bayani ba zaka gane ba, buyagi zaka yi mini" tayi maganar a hankali, tana sake kallon wayarta. "Yaya ummi, wai baƙonki ya zo" noor tayi maganar ba tare da ko sallama ta yi ba. Ummi ta jinjina mata kai, tare da jin matsananciyar faɗuwar gaba, dan wannan ne karon farko da zata tsaya tayi zance da wani, da sunan yana sonta, gashi alamu sun nuna da gaske yake, tunda ya biyo ta wurin dr., Duk da abun da take ta addu'a a kai kenan, idan tana da rabon aure, Allah ya kawo mata miji nagari, sai dai gaba ɗaya ba ta murna da lamarin a yanzu, kuma ta rasa dalili. Sai dai ta tsinke da al'amarin, ganin headmastern su a gareji, wai shi ya zo wurinta, kenan shi ne baƙon? Suka gaisa suka zauna a kan fararen kujeru, tana bin sa da ido, dan ba ta gama yadda da shine baƙon ba. Yayi gyaran murya ya ce "Wato ummi na san zaki yi mamakin ganina, da dalilin zuwana, duk da nasan mahaifinki yayi miki bayani. To ni dai ummi ba wani abu ne ya kawo ni wurinki ba face alkhairi, na daɗe ina sonki, tun ranar da na ga kin cire hijjabi kina alwala, watannin baya baki ganni ba ke amma, to a lokacin gidana mata huɗu ne, amma yanzu Alhamdilillah mun rabu da ta ukun, dan haka akwai gurbin mutum ɗaya, ya sanya na ce tun da naga alamar babu tsayayye bari ni na tsaya, mu dai-daita mu rufawa juna asiri, dan yanzu kin san maza tsada muke yi" yayi maganar yana murmushi yana kallonta. Ummi dai sama-sama take jin sa, ƙasan zuciyarta lissafi take yi, ta yi wa raihan reply ko ta ƙyale shi, ta san duk daɗewa idan ya dawo sai ya nemeta. Dan haka sama-sama take jin maganganun headmastern. "Ba zan takuraki yanzu ba, amma dai ki yi tunani, dan kuwa da wuri nake son ayi auren nan, bana son ɓata lokaci, kuma za ayi abu ne dai-dai talaka da tsarin addini, ba wani ɓarnar bidi'a, in kawo abun da Allah ya yassare ayi" Ummi ta yi ajiyar zuciya ta ce "To malam, idan na yi tunanin sai mu yi magana" Ya ce "Yauwwa ummi, Allah ya wuce mana gaba " ta amsa da Amin, ya tashi ya tafi, ita kuma ta dasa sabon zama tana nazari da tunani. Sai da ta ji sauron wurin na neman halakata, sannan ta tashi ta koma cikin gida. Kitchen ta nufa ta zubo abinci, zata fito farida ta tare ta ta ce "Ubanki ne ya kawo abincin?" Ummi ta girgiza kai. "To ajiye ki fita, mayya mara zuciya, ai si ki je wurin waɗanda ki ke bi ku watse su saya miki kaya, su saya miki abincin, wallahi takura da masifa yanzu ki ka fara ganinta, sai ranar da ki ka bar mini gida, ko ki yi aure, ko ki koma in da ki ka fito ko ki bi duniya " Salin alin ummi ta ajiye abinci, ta bar kitchen ɗin. 'Tabbas! Tura ta kai bango, yakamata na yi wani abu na matsa daga gidan nan, na fuskanci ƙalubalen da ke gaba, zaman gidan nan yana neman fin ƙarfina" tayi maganar a zuciyarta. Abokin kukan nata ga ƙoƙarin da take yi a kansa, ta nesanta kanta da shi. Abubuwa suka cigaba da ɗaukar zafi, dan da kawu zai koma aiki, sai da ya gindawa farida sharaɗi, a kan muddin ya dawo ya tarar ummi ba ta nan, sai ya saketa. Farida har mamaki take yi, yanzu asirin ya daina kama dr. Al'amari in dai ya shafi ummi, ba ya saurarawa. Ummi ta din ga sallar dare tana kai wa Allah kukanta, amma a ƙasan zuciyarta ta ji ta amince da auren headmaster, no matter what wahala ba yanzu ta fara shigar ta ba, tarwatsewar gidan dr., Da kuma alƙarsu da raihan su ne manyan barazanar ta a yanzu, idan ta yi aure ta san ta rage kaso mafi yawa daga matsalolinta. Raihan ya sha mamakin burus da ummi ta yi da shi, ba dan ba ta ganin saƙonninsa ba. Gajeren saƙo ta tura masa "Baka yi mini komai ba raihan, tarayyarmu na barazana ga kwanciyar hankalina, da jefa zargi a zuciyar mariƙana, ka yi haƙuri da hukuncin da na yanke" Message ɗin ya nuna blue tick, alamar ya ga saƙon amma yaƙi reply, tun ummi na jiran yayi reply, har ta sare, sai kuma abun ya dame ta ta rasa sukuni, ga headmaster ya matsa mata kamar maye, ita har mamaki take yi, duk lokacin da suka shafe, bai ji yana son ta ba, sai watannin baya da ya ganta tana alwala, mata huɗu sun rabu da ɗaya zai aureta, kodayeke wannan duk bai dameta ba, wutar gabanta take ƙoƙarin kashewa, dan haka ta ce masa ta amince. Tamkar ya goya ummi, saboda murna da nishaɗi, ta amince da aurensa, ya ce mata zai zo wurin kawu su yi maganar kawo kuɗin aure, ta ce masa baya nan sai ya dawo. Ya fara yi wa ummi huɗubar shi talaka ne, dan haka kuɗin sadaki, da na lefe da na aure, zai bayar dubu ɗari, dan Allah ta ce ta yarda a haka, ko da babanta zai ce ba yadda ba. Ummi ta amsa masa da to, dan ba ta da burin da ya wuce ta ɗaga daga gidan nan, ita ma tana burin ta ganta a ɗakinta, ko ta samu sauƙin gorin da take sha. Kullum cikin duba wayarta take, taga raihan yayi mata reply na message ɗin da tayi masa, amma yaƙi yin reply, wasu lokutan tana kallon sa online, amma bai yi responding ba. Tunani ta din ga yi hanyar da ta bi tana neman maraba da raihan tayi musu tsauri daga ita har shi, amma ta san idan tayi masa bayani, ba zai taɓa tsayawa ya fuskanceta ba, dan akwai shi da kafiya wasu lokutan. Noor tana ta gyara wa ummi kan mudubin ta, tana jera mata mayukanta tana faɗin "Ai yaya ummi ba sai kin cigaba da ɓoyewa ba, kawai ki jera abun ki, dama na san dr. Ba zai yi miki faɗa ba" ta lura hankalin ummi baya kanta, dan haka ta ce "Wai yaya ummi me ki ke jira a wayar ne, ko salary ki ke jira ne?" "Noor raihan ya daina kulani" Noor ta ɗan waro ido ta ce "Faɗa ku ka yi? Innalillahi yaya raihan ɗin namu?" Ummi ta ce "Ni na fara daina kula shi, noor bana son zargi ya shiga ran kawu a kaina ne, kuma aure nake son yi, bana son na yi aure mu kasa rabuwa". "To yaushe zaki auren?" "Malam ya ce idan kawu ya dawo zai zo su yi magana ya kawo kuɗin aure, sonake ya kawo kan raihan ya dawo" Noor ta kwaɓe bakk ta ce "Wai wani malam, ni fa bana son malam ɗin nan, Astagfirullah bari dai na yi shiru, amma dan Allah kar ki auri wani malam, ki auri raihan mana" ummi ta zare ido ta ce "Ke ƙanina ne fa, kamar ɗan uwa yake a wurina, malam ya ce zai bayar da dubu ɗari kuɗin komai da komai, kar a wuce wata uku, amma ban san yadda za su yi da kawu ba". Kamar shashasha noor ta kalli ummi ta ce "Wai ke yaya ummi, ni na rasa me zance, shikenan ke ba za a kawo miki lefe ba? Matansa fa uku, gashi tsoho, to kina son sa ne?" "Mama ƙyaleni, surutun nan naki ma ya fara damuna". "Hmm, Yaya raihan yayi fushi da ke fa, har makarantarmu ya je, bayan mun dawo daga gagarawa, ya tambayeni idan tare muka dawo kuma lafiyarki ƙalau, na ce masa eh. Ya jinjina kai ya tafi" Cikin tsananin mamaki ta ce "Ya aka yi ya san makarantar ku har ya je? Sau biyu fa kawai kuka taɓa haɗuwa, Kin ga dalilin da yasa nake son mu rabu, raihan ya iya rigima fa" Noor ta ce "Eh amma yana da kirki sosai ai, tun da ya taɓa bani kuɗi, wannan malam ɗin gaskiya talaka ne, ko kuma wayo, dubu ɗari fa ba ta da yawa sosai, shikenan ke ba za a kawo miki akwatuna masu yawa ba, kamar na inteesar" Ummi kawai ta kwana ta yi wa noor shiru. Ta cigaba da kallon wayar, a ranta ta ce 'Haba babban mutum, manyan ba sa haka fa' ta cigaba da duba chats ɗin su na baya. Headmaster ya kira dr. A waya, yana tambayarsa yaushe zai dawo, so yake da ya dawo, ya kawo kuɗin, dr. Ya ce masa baya son gaggawa ya jira shi tukuna. Wasa-wasa kusan sati uku kenan, raihan da ummi ba su yi magana ba, ba kuma dan hakan yana yi wa kowanensu daɗi ba. Ummi ta kira direban da yake aikowa ya karɓar masa abinci, ta tambaye shi ko raihan ya dawo, ya ce mata a'a. Yanayin sintiri da nacin da headmaster yake yi mata, abun har mamaki yake bata, kamar ya ɗauketa ya kaita gidansa ya ajiye. In da Allah ya rufawa ummi asiri, aikin nan nata, tana ɗan samun salary, idan tayi girki ta gama farida sai ta hanata abinci, tayi ta janyo mata masifa da bala'i da miyagun alkaba'i, tare da fatan ta sha wahala a rayuwa kamar yadda ta wahalar da ita a gidan aurenta. Ummi a ranta ta ce 'Wahala waccece ban sha ta ba, kuma ban cutar da ke ba a zamanmu ke ki ka cutar da ni!" Tun da dr. Ya zo gida, headmaster yake sintiri, a kan zai kawo kuɗin, dr. Ya ce ya ɗan ba shi lokaci tukuna. Hatta wurin aiki manager ya lura yanayin ummi ya sauya, kamar wani abu na damunta, amma dai yayi shiru bai ce mata komai ba. Dr. Ya kira ummi ya tambayeta ko tana son malam Isa, ummi ta ce eh. "Ummi, kar takura ko damuwa ta sanya ki kai kanki ga halaka, rauwar aure ba rayuwar gida ba ce da babu nauyin kowa a kanki, kar ki kai kanki in da zaki yi dana sani, mutumin nan babban mutum ne, kar ki zo daga baya azo a samu matsala, ki dai je ki sake tunani" ummi ta amsa masa da to, ba dan ta so ba, ita fatanta kawai dr. Ya amince. Kasancewar yau babu coustomers, ummi ta bar reception ta koma in da take zuwa ta yi salla ta ci abinci ta kwanta, tana cigaba da duba chat's ɗin su da raihan. Ƙamshin turaren raihan ne ya fara yi mata sallama, ta zaci hallucinating kawai take yi, sai dai ba ta gama tunanin ba, ta ganshi a tsaye a kanta. A zabure ta tashi zaune, tana bin sa da kallo. Wani irin kwarjini ta gani a tare da shi, wanda ba ta taɓa gani a tare da shi ba, fuskarsa a matuƙar haɗe, kamar ba ya dariya. "Raihan" ta kira sunansa a hankali. Ya nemi wuri ya zauna, ya ƙura mata ido sannan ya ce "Salma wannan shi ne tukuicina daga gareki ko? Ko rabuwa ki ke son mu yi, yanke alaƙa da ni kai tsaye ba tare da wani dalili ba kina ganin shi ne mafita? Bafa a rana ɗaya muka gina alaƙar nan ba, ummi dama zaki iya wulaƙanta ɗan Adam har haka kamar yadda ki ka yi mini?" Cikin rauni ta ce "A'a raihan, ba haka bane ba, dan Allah ka fahimce ni" nan ta gaya masa bayan dawowarta gida abun da ya faru, yadda farida tayi mata bincike ta nuna wa dr. "Raihan wulaƙanci ba halina bane ba, ina ma naga ƙarfin gwiwar da zan iya wulaƙanta wani? Raihan ba kowa zan yi wa bayanin alaƙarmu ya kalli abun da idon basira alaƙar ta yi masa ma'ana ba, bana son zargi ya shiga ran dr. Duk da ya goya mini baya, amma ban san ta yaya zan wanke kaina ba, kafi ƙarfin wulaƙanci a wurina raihan, ban yi haka dan wulaƙanta ka ba" Ya girgiza kai ya ce "Ban yadda ba ummi, duk a ƙoƙarinki na guje mini, ki ke shirin kai kan ki ga halaka, zaki auri shugaban makarantar ku ko? Malam isa" A zabure ta kalli raihan, ya aka yi ya san wannan maganar? "Mamaki ki ke yi ma? Ni zaki juya baya rana tsaka ummi, har ki yi shirin aure ban sani ba? Ina bibiyar rahuwarki fiye da yadda ki ke tunani, gani nake ko yaya na kawar da kai a kanki wani abu zai faru da ke, rabuwa da ni ba mafita bane" "Raihan haka ne kawai mafita a wurina, matar gidanmu ta matsa mini da yawa, ƙalubale ko ta ko ina, ba zaka gane a mawuyacin halin da nake ba... Ya katseta da cewa "Kuma sai ki kai kan ki ga halaka, mutumin da ya saki mata sun kai biyar, ya saki wata ke ma zai aureki ya biya buƙatar sa ya sake ki, ba irin wannan mijin nake roƙa miki ba" Ta ce "Raihan alkhairi nake fata" "Yi mini shiru" yayi maganar a hasale, galala take bin sa da kallo. "Yakamata mu daina yaudarar junanmu, daga ni har ke, idan saboda ki rabu da ni ne, ki ke ƙoƙarin yin wannan auren, kin riga kin makara, ba za ayi shi ba. Ban damu da koma me wani zai yi zargi ba, ba zaki iya rabuwa da ni ba, kin riga kin makara. Ke banda rashin lissafi ma me zaki yi da wannan dattijon, shekarunsa nawa ke naki nawa? Me zai tsinana miki, ko ke ba kya wannan lissafin, ko an ce miki ci da sha ne kawai aure? Kodayeke ai kin san me nake nufi" kai ka ce gunki haka ummi ta koma, yau raihan ya zama wani abu na daban. "Salma, ki yi haƙuri ba zan iya barin wani ya aureki ba, saboda ni nake sonki" Tamkar ya jona mata shocking ta zabura ta ja da baya tana kallon fuskar raihan, yadda farar fatarsa ta koma ja, da irin kallon da yake yi mata, ya sanya ta tabattar da ba ƙarya yake yi ba. "Ummi ki yi tunani, wace irin alaƙa ce a tsakani na da ke?" Kamar zata fashe da kuka ta ce "Raihan, ni fa ƙanina na ɗauke ka, ƙanin ƙawata ce kai, mutum ne kai mai muhimmanci ne a gareni, amma ba irin wannan alaƙar ba". Tashi yayi ya taka, ya je gabanta ya durƙusa, ya ɗan tsura mata ido ya ce "Bamu haɗa alaƙa da ke ba, ta uwa ko ta uba ba, kuma tarayyar mu da muka yi da ke ta wuce yadda ki ke tunani, ta kuma wuce gurbin da ki ka ajiyeta. Salma son juna muke yi. Lokacin nan da muka ɗauka ba ma tare, ki ka yanke alaƙarmu, kin sani a mummunan yanayin da yakamata ki ce na yafe miki, na shiga matsananciyar damuwa" Da sauri ta girgiza kai ta ce "A'a Raihan, ina ganin mutuncinka, babu wannan maganar a tsakanin mu dan Allah a barta, kar ka sake yin ta bana so" Ya shafi gefen fuskarsa, yana jin zafi a zuciyarsa, ya kalli ummi ya ce "Na gode Salma" ya tashi ya fice daga wurin. Ummi ta takure tana ajiyar zuciya. "Salma, ki yi haƙuri ba zan iya barin wani ya aureki ba, saboda ni nake sonki" shi ne abun da ya din ga yi mata kai kawo a zuciyarta. Manager ne ya biyota yana tambayarta me ta yi wa ƙaninsa ya ga ya fita rai a ɓace, ummi ta ce masa babu komai. Kwanaki biyu a tsakani, headmaster ya daina kiranta a waya gaba ɗaya, messages ɗin ma da yake tura mata ya daina. Sai dai ko a jikinta, tunanin ya raihan yake yafi tsaya mata a rai. Gashi ya ce halin da ta saka shi a ciki, yakamata ta nemi yafiyarsa. Ganin ba ta da mafita, ya sanya ta neme shi a waya, amma shiru ba ya ɗagawa. Tana cikin jimamin lamarin, dr. Yayi sallama a ƙofar ɗakinta, ta amsa sannan ya shiga. Ya nemi wuri ya tsaya, sannan ya dube ta ya ce "Ummi, baya fa ta haihu, mutumin nan malam Isa ya kirani a waya, ya ce mini ya janye maganar aurenku, kuma hakan yayi mini dai-dai, dan kuwa ko bai janye ba, ba zan bashi aurenki ba, binciken da na yi a kansa bai yi mini daɗi ba, dan haka ki cigaba da addu'a, Allah ya kawo mafi alkhairi" har kawu yahaya ya fita, ummi na tunanin me raihan ya yi wa headmaster ya fasa aurenta, kenan da gaske yake yi sonta yake, ba zai bari kowa ya aureta ba!? Gabanta ya faɗi tare da tabattarwa da kanta ba ta ga ta zama ba, idan ba raihan da rigima ba, ai ya san zaren ba kalar yadin bane ba, ina shi ina ita? Kyakkyawan matashi kamarsa me zai yi da ita, ga uwa uba ta girme shi, dole ta lallaɓa shi su rabu lafiya. Sanin baya ɗaga wayarta, ya sanya washegari da ta shirya, ta tafi office ɗin su raihan. Sai dai ba a bari ta shiga ba, sakataren shi yayi mata sannu da zuwa, tare da tambayarta raihan ya san da zuwanta?. Ta ce "A'a, amma ace masa ummi ce" Sakataren ya tashi ya shiga cikin office ɗin raihan, ya dawo ya ce mata ta jira, zai neme ta. A ƙalla ta shafe awanni biyu tana jira, bai fito ba, ba kuma dan yana abun da ya fi ganinta muhimmanci ba, sai dan ya sanya ta yarda da alaƙarsu soyayya ce. Yana office ɗin sa, ya kira waya ya saka aka kai mata ruwa da lemo da snacks. Ya koma ta window ya tsaya yana kallonta in da take zaune, fuskarta duk ta faɗa, tana ta wasa da yatsun hannunta. Ji yayi ya kasa jurewa, ya nufi ƙofa ya fita, tana hango shi ta tashi ta tsaye, sakataren ya fara yi masa bayanin ita ce baƙuwar da take son ganinsa, ta daɗe a wurin. Buɗar bakin raihan sai cewa ya yi ta rubuta a rubuce tana son ganinsa, idan yayi approving ya bata date da time ya fice ya bar ummi. Ayshercool. 08081012143 [4/20, 7:21 PM] Authoresses:                          *CUTARWA* *BRIGHT PENS* (FREE BATCH) MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH. Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe. FOLLOW AND SHARE AYSHERCOOL 08081012143 MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH. Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe. 31 Har raihan ya bar harabar gidan bayansa ummi take kallo, ko sau ɗaya bai waiwayo ba, ita kuma ba ta daina zubar da hawaye ba, gani take kamar kallon ƙarshe take yi masa, ba zai sake dawowa rayuwarta da sunan yana son ta ba. Ta tashi jiki babu ƙwari, ta tafi ɗakinta, ta rufe ɗakin ta saka sakata, saboda kar noor ta zo ta isheta da surutu. Ta zauna ta din ga kuka, ta ma rasa kukan me take yi. Ta yi shiru tana tuno irin rayuwar auren da ta yi a gidan idiris, ta kasa manta irin wulaƙantar da ta yi a gidan idiris, irin tozarcin da ya yi mata, tamkar ya auri mushen dabba ba ɗan Adam ba, kuma ɗan Adam ɗin ma ƴar uwarsa. Ta tuna yadda abokansa suke zunɗensa da angon ɗoɗɗoya, ba zata manta tonon asiri da wulaƙantarwar da Idiris yayi mata ba. 'To idan kuma haryanzu ban warke ba fa'?" Ta tambayi kanta. Ta dafe ƙirjinta tana zancen zuci, ita dai tun da Allah ya sa kawu yahaya ɗaukkota, yayi ta ƙoƙarin saya mata magunguna, cikin ikon Allah ba ta sake jin wannan matsalar ba, ko maƙiyinta ba ta fatan Allah ya haɗa shi da bala'in da yake cikin larurar sanyi. Tun da farida ta dawo daga gidan inteesar, tamkar ita za ayi wa kishiya, kamar za ta yi hauka, domin kuwa da ita da wasu daga ƙannenta suka dawo gidan, suna ta bata haƙuri, a kan sai ta daure ita ma, idan ba haka ba inteesar ba zata kwantar hankalinta ba. Sun cika falo suna mayar da yadda aka yi, noor kuma na ta kokowa da remote tana ƙara volume ɗin tv. "Wai ke noor baki da hankali ne? Ba ni san meya samu yayarki Inteesar ba ne?" Noor ta juyo ta kalli mai maganar ta ce "Mutuwa ta yi ne?" "Wane irin mutuwa, ke ko gidan nata ma baki je ba, balle a haɗu a rarrasheta da ke, kina kallon mahaifiyarku hankalinta a tashe, ita ma can muka baro ta tana kuka, amma ke kina nan kina ƙure wa mutane kunne da ƙarar tv" Noor ta taɓe baki ta ce "To tun da dai ba mutuwa tayi ba ai barkanta, wanda ba shi da kunya ai dole ayi masa kishiya, haka wata malama ta ce rannan a tv, na ce ashe saura maama" "Ke uwar taki ki ke cewa ayi wa kishiya?" Kausar ta ce "Mama hadiza, ki ƙyale yarinyar nan kar ta saka hawan jininki ya tashi, ba isasshen kai ne da ita ba, yanzu sai ta yi miki rashin kunya, kuma ba kowa ne ke zigata yana koya mata wannan iskancin ba, ban da ummi, idan ba haka ba ta yaya ɗa zai yi fatan a yi wa uwarsa kishiya, banda shashasha mara hankali" "Ni dai ban saka da daƙiƙi a maganata ba, mutum ya bari ya fara gane karatu" kausar ta ja bakinta tayi shiru, idan ta cigaba da tankawa noor, sai noor ta kunyata ta a gaban mutane. Nan kuma akalar hirar ta koma kan ci wa ummi mutunci, da ziga farida a kan lallai yakamata ummi ta bar mata gida, tun da ta tsofe a gidan babu aure. Suka gama soko burutsunsu, suka bar gidan. Ummi kusan kwanan zaune tayi, tayi ta salloli tana kaiwa Allah kukanta, wayarta kuwa ta dubata babu adadi, amma babu saƙon raihan ɗaya da ya sake shigowa cikin wayarta. Ƙasan zuciyarta ya shiga tabattar mata da sun rabu da raihan kenan. Bayan ta idar da sallar asuba, message  ya shigo wayarta, wani website da raihan ya saka ta shiga, ta yi submitting cv ɗin ta, an kira su screening ciki har da ita, wani sabon gidan talabijin da ba a daɗe da fara shirye-shirye a cikin sa ba. Yau da safe aka ce su je wurin, ba ta ga saƙon ba sai yanzu, cikin sauri ta tashi ta haɗa credentials ɗin ta, agogo ta kalla, muddin ta ce za ta jira ta yi musu girki, to fa zata makara, dan haka ta dudduba jakunkunanta, ta samu kuɗi ta fito, ta turawa Abdul message na in da ta tafi. Ko da ta je wurin ta tarar da mutane da yawa, haka nan ta fara bin layi ita ma, ta din ga duba wayarta tana tunanin raihan, shi ne mutum na farko da yakamata ta kira, ta sanar masa da an kirata screening, sai dai ba ta da wannan damar a yanzu. "Dama na sani, babu lallai ka dawo gareni raihan, amma duk da haka ba zan ga laifinka ba, ina yi maka fatan alkhairi a duk in da ka ke". Farida tamkar ita aka yi wa kishiyar, ko bacci gagararta yayi, ta taso da nufin ta tarar da abincin safe, Abdul ya shigo ya sanar da ita saƙon ummi, tana fara zage-zagenta, ya fice ya bar mata falon. Raihan yana zaune yana ta juyi a kan kujera a office ɗin sa, ya kasa taɓuka komai, ya juya kai nan ya juya kai can, in aka jima sai ya ciro wayarsa ya duba ya mayar ya ajiye. Ya kifa kansa a kan teburin gabansa, yana jin yadda kansa yake masa wani irin zafi. Jin motsin an buɗe ƙofa ya sanya shi ɗaga kai ya ga me shigowar, babu tsammani ya ga safiyya, tana sanye da doguwar riga straight gown, sai mayafinta a kafaɗa da jakarta, ta shigo bakinta ɗauke da sallama. Ya amsa mata tare da mayar da kansa ya kifa. "Yaya raihan, barka da rana?" "Yauwwa sannu" Ta nemi wuri ta zauna ta ce  "Gidan su wata ƙawata na je, a nan tsukin ne, na ce bari na biyo mu gaisa" Yayi shiru bai ce mata komai ba. "Are you ok?" Tayi maganar tana kai hannu goshinsa, ganin yana gumi duk da akwai sanyi a office ɗin. Rau ta ji goshin nasa ya ɗau zafi, ta ce "Subhanallah, yaya raihan baka da lafiya ne? Jikinka zafi" Ya ɗago a hankali ya ce "Safiya, ki tafi gida Please, ki ƙyale ni" "Amma ya zan tafi na barka a wannan halin?" Kallonta yake yi, yana tunanin dama ummi ce a zaune a gabansa take yi masa magana yanzu. "Ki tafi na ce" yayi maganar a ɗan hasale, tare da jin haushin yadda ya ta tsare shi da ido, saɓanin ummi da ba ta iya ƙura masa ido haka, sai tana yi tana kawar da kai. Safiyya ba ta fi shekaru goma sha tara ba, ummi ta girmeta sosai, sai dai shegen iyayi da rawar kai, duk in da ta zauna ba ta da aiki sai hira da samari a waya, ga shegiyar kwalliya kamar ƴar tsana. Ta razana da tsawar da yayi mata, ta tashi da sauri, har ta kusa fita ya ce "Kar ki sake biyo ni office, office wurin aikina ne ba shirme ba" tayi sauri ta fice tana waiwayensa. Ummi kuwa ta galabaita a ranar, dan bayan screening, aka ce su jira aka tura musu waɗanda suka yi nasara a waya, ciki har da ita, aka ce su jira ayi musu interview. Kuɗin hannun ummi ba zasu kai ta ci abinci ba, ga yunwa ta isheta, haka nan suka cigaba da jira. Ba a zo kan ummi ba, sai kusan biyar na yamma, da farko bayan shigarta studion aka fara yi mata interview, a ɗan tsorace take, ga yunwa tana ji, ɗaya daga cikin masu interview yana cewa masha Allah muryarta mai daɗi. Ɗayan ya ce "Jin ta ya fi ganinta, wannan da radio ce irin su ne masu sauraro ke ɗokin gani" Shugaban wurin ne ya shigo, ma'aikatan suka din ga gaishe shi, yana hura hanci, ya dubi ummi ya ce "Wannan fa?" "Sir tana cikin wanda suka tsallake screening, interview ake yi mata" "Wannan ɗin?" "Eh sir" "Dan Allah ku zaɓo wanda za su yi attracting ɗin mutane, ba wanda sai mun yi ta faman sanya filter muna fafutuka kan mu haska su ba, wannan shirin talabijin ne, ba na gidan rediyo ba!" Tsit mutanen wurin suka yi, ba wannan ne karo na farko ba, amma a duk lokacin da aka yi mata, jin abun take kamar sabo, sum-sum, ta tattara kayanta, tayi waje, duk suka tsaya suna kallon ummi, shi kuma ko a jikinsa ya cigaba da maganar sa. Ita ba ta san ma yadda aka yi ta isa gida ba, abubuwa daban-daban cunkus a ranta, ta ɗaukko gajiya da baƙin ciki, tana zuwa gida farida ta dira mata nata tashin hankalin. "Raihan ka gani ko?, ka kori wanda zai aureni, kaima ka tafi ka bar ni, komai yayi mini zafi" Tayi kuka-kuka iya yin ta, har ta gaji tayi shiru. Ta wuni da yunwa, haka ta kwana da wata. Kwanaki huɗu rabon raihan da ummi, yayi ƙoƙarin sanya abun da ta gaya masa a matsayin hujjar da za ta rabu da shi, amma shi sam bai ji hakan a matsayin hujja ba, dan damuwa yake ƙara shiga na rashin ta, ya zuba mata ido ya ga iya gudun ruwan ta, ko za ta neme shi, amma ya ji shiru. Hakan ya sanya ya fara zargin anya ba da gaske take ba ta son sa ba, tun da ta iya gaya masa cewar su rabu, kwanaki huɗu amma ba ta sake nemansa ba, dan haka tsoro ya sake shiga zuciyar sa, ummi ba ta son sa. Ƙasan zuciyarsa yana mamakin yadda ta ce masa ta taɓa aure, shi ba auren ta ne ya dame shi ba, meya kashe auren? A yadda ummi take har ace namiji ya sake ta?. Daurewa yayi, ya sake bawa ummi kwana ɗaya, ya zamana kwanaki biyar, amma shiru ba ta neme shi ba. Kwana na biyar, da yamma ya koma gidansu ummi, sai dai ya kira wayarta amma ba ta shiga. Yana tsaye sai ga motar dr. Raihan ya risuna ya gaishe shi, dr. Ya amsa masa, yayi parking a waje, ya shiga cikin gida. Raihan ya dudduba, mai gadin gidan ma baya nan, yayi ta kiran lambarta amma shiru ba ta shiga. Ya samu wuri ya zauna a ƙofar gidan, yana cigaba da dannan wayarsa. Dr. Ya sake fitowa,  ya ga raihan, ya kalli raihan ya ce "Yarona wa ka ke nema ne? Ko wurin Abdul ka zo?" Raihan ya ce "A'a Abba, wurin Ummi na zo" Dr. Ya ce "Too, ummi kuma lafiya dai ko?" "Eh lafiya ƙalau, wurinta dai na zo, na kira wayarta ba ta shiga ne" "Amma wani abun tayi maka ne?" Ya girgiza kai ya ce "A'a, ba ta yi mini komai ba" Dr. Ya jinjina kai ya ce "Yaron kirki, ai babu lallai ummi ta tsaya ta saurareka, a yanzu mijin aure ne ya dace ya zo wurinta, ba wanda za a yi soyayya ba kawai, wannan idan ba ku yi sa'anni ba, ba zaka girmeta da yawa ba. Ka yi haƙuri ka ji ɗana. Cikin girmamawa raihan ya ce "Abba ummi ta sanni, akwai alaƙa tsakani na da ita, wallahi abba ba ɓata mata lokaci zan yi ba, aurenta zai yi, ina son ta wallahi". Dr. Yayi shiru yana kallonsa, sannan ya yi murmushi ya ce "Meye matakin karatunka?" "Na yi degree a ɓangaren Business administration, a ATBU" "Idan da gaske ka ke zaka aureta, ranar lahadi ka turo mini mahaifinka mu yi magana da shi" Raihan ya washe baki ya ce "To Abba, in sha Allah zan gaya masa, na gode sosai da sosai" Dr. Yayi murmushi yayi gaba, a tunaninsa yayi maganin raihan, dan ya zata irin yaran nan ne marasa ji, amma duk da haka nutsuwa da kamalar raihan ɗin. Raihan tafiya yayi yana murmushi, yana ganin abun kamar a mafarki, yau ya tsinci dami a kala, abun kamar a shirin film, wai ya tura Alhajinsa a nema masa aure? Kai tsaye gida ya tafi. Sai dai ƙasan zuciyarsa yana tunanin, ummi za ta amince ko kuwa za ta cigaba da gardama ne? Dan ya ga kamar ta raina shi ne a matsayin mijin aure, yayi mata ƙanƙanta. Yana zuwa ya tafi sashin Alhaji, dan kwanakin nan kusan kullum Alhajin yana gida, ya daki sa'a shikaɗai ya tarar a sashin nasa. Alhaji Tahir ya gyara zaman tabaran sa, ya ce "Ya aka yi ne? Yanayin farinciki haɗe da damuwa a fuskar babban mutum" Raihan ya je ya zauna a kusa da shi, ya ce "Kowanne akwai Alhaji" "Bani labari" Ya ciro wayarsa, ya nemo hoton ummi da yayi mata, lokacin da suka sayo dogwayen riguna, ya ce "Alhaji ka ga wannan" Alhaji ya karɓi wayar, ya ƙare wa hoton kallo ya ce "Na gani, meyafaru?" "Alhaji tana da kyau?" Ya ce "Masha Allah, very beautiful kuwa, da gani kuma tana da kunya" "Ita nake son aura Alhaji, zaka nema mini aurenta?" Alhaji Tahir ya kalli raihan yayi murmushi ya ce "Babban mutum wannan ai matar manyan ce, anya ba ka yi tsaurin ido ba kuwa?" "A'a Alhaji, ai nima babban mutum ne, dan Allah tayi? Wallahi mutuniyar kirki ce" Alhaji ya yi shiru ya ce "Ai ni kallon sani nake yi mata ma" Raihan ya ce "Eh, ƙawar maryam ce, amma ita ba ta girme ni ba, shekrunmu ɗaya da ita, kuma mutuniyar kirki ce ka tambayi Hajiya ma ka ji" Alhaji Tahir ya dafa kafaɗar raihan ya ce "Easy my dear, in dai kana son ta tayi mini, za a nemi aurenta in dai za a bamu" Raihan ya washe baki ya ce "Babanta ya ce ranar Sunday wai ka je ku yi magana, gani yake yi kamar ba aurenta zan yi ba, Alhaji tana bani shawarari masu kyau, tana da kirki sosai" "Allah ya kaimu lahadin, zan je in sha Allah, ko a lokacin suka ce sai a ɗaura, Ubangiji Allah ya sa abokiyar zama ta gari ce" Raihan ya sosa kai ya ce "Alhaji saura abu ɗaya" "Ok to ina jinka" Raihan ya ce "Dan Allah kar ka gaya wa mami sai maganar ta faɗa, ban san yadda za ta karɓi maganar ba. I really have to marry her, Alhaji rayuwar ummi akwai ƙalubale da ban tausayi, dan Allah ka tsaya mini" Alhaji Tahir ya jinjina kai ya ce "In dai ni ne ka san baka da matsala da ni, ko tsohuwa ka ce kana so, zan wuce maka gaba in dai tana da tarbiyya, kuma ko a hoto, ni yarinyar ban ga aibunta ba, ko ta girmeka in dai kana son ta shikenan, ai soyayya ba ƙarya ba ce raihan, mune muke barin al'ada na rage mana jin daɗin abun da addini ya halatta mana. Allah ya sanya alkhairi ango" Raihan ya sunkuyar da kai yana murmushi, wani irin farinciki na ratsa zuciyarsa. Dr. Ya manta da batun haɗuwarsa da raihan, dan ko ummi ma bai nema da maganar ba, sai dai ya rage ganin gilmawarta ko a gidan, ya bar hakan a wataƙila takurar farida ce ta saka ta ƙara takura kanta. Washegari raihan ya tafi wurin aikin Ummi, amma manager ya ce "Ai ummi yau kusan kwana uku ba ta zo ba, ni ban sani ba, ba ta da lafiya ne ko ya aka yi ban sani ba, kawai ta ce mini za ta je screening, tun ranar ba ta sake zuwa ba, na zata ma ko ba ta gama ba ne ba". Raihan ya yi shiru ya ce "kira ta a waya ka ce ko ta dawo aiki, ko zaka koreta". Manager ya zare ido ya ce "Yayarta ka za a kora? Idan ban koreta ba ni ai yayana ya kore ni, ka san yadda yake yabawa ƙoƙarin ta, da yabawa amanarta" Raihan ya ce "Dan Allah ka bar wannan maganar, kawai ni dai taimakon da zaka yi mini kenan, ka ce lallai ta dawo aiki. "Ba zan yi ba, ba kun fi kusa ba" Raihan ya sassauta murya ya ce "Haba manager, dan Allah ka taimaka Please" "Da ka ce ba ka ji? Zan yi mata magana, amma ba dan halinka ba, kuma ba zan ce zan wani koreta ba, zan dai yi ƙoƙarin ta dawo ɗin" Raihan yayi dariya ya ce "Allah ya bar mini manager" Manager kawai yayi murmushi, ya cigaba da aikin da yakamata ace ummi ce ta yi. Sai dai manager bai kai ga yin hakan ba, washegari sai ga ummin ta zo aiki, sai dai ta rame sosai, kallo ɗaya zaka yi mata ka san akwai tashin hankali a fuskar ta. Manager ya kira raihan a waya, ya gaya masa ummi ta zo. Bai ja dogon lokaci ba, ya daidaici lokacin tashin ta ya kusa, sannan ya tafi. Ta fito daga wurin aikin, yana nesa kaɗan da ita yana kallonta, tana tafe a hankali kamar mara lafiya. Zuwa yayi ya sha gabanta da motar, ta tsaya tana kallon motar, ya sauke glass ɗin motar suka haɗa ido, sai da ta ɗan razana, ya buɗe mata motar ba tare da ya ce mata uffan ba. Jikin ummi ya yi sanyi sosai da ganin raihan, dan ba ta taɓa tsammani ba, kamar mai jin tsoro haka ta ɗosana ta shiga motar. "Ta tabatta dai ba kya so na ko ummi? Kina iya rabuwa da ni, baki damu da halin da zan shiga ba, kin ce mu rabu, ko nema na baki sake yi ba, rashin muhimmancina har ya kai haka kenan ko Salma?" Ta girgiza masa kai alamar a'a. "Shikenan, ni gashi na sake biyo ki ai, ranar lahadi Alhaji zai zo wurin dr." A razane ta kalleshi, tana ƙifta ido. "Eh, mun haɗu da dr. Shekaranjiya, na zo wurinki kin ƙi ɗaga wayata, mun yi magana ya ce Alhaji ya zo su yi magana" "Wai da gaske aurata zaka yi?" Tayi maganar cikin matuƙar rauni. "Gashi ina gaya miki, kin zata da wasa nake yi? Na san wataƙila ba ni ne irin mijin da ki ke so ba, na san zaki ga na yi miki yarinta da yawa, amma har cikin raina nake jin zan iya aurenki na riƙe ki da kulawa da girmamawa". "Raihan zaka aureni ina bazawara" "Kar ki sake kawo mini maganar kin taɓa aure, zuciyata zata fashe, ummi kina wasa da son da nake yi miki kina ganin kamar wasa ko? Hubban shadidan na kira shi, ban taɓa jin damuwa da takura a kan son wani abu ba kamar ke, kawai in ganki a kusa da ni, shi zai kawo mini cikakkiyar nutsuwa" Tayi shiru tana wasa da zoben hannunta. "Meya rabaku da tsohon mijinki?" Tayi ajiyar zuciya ta ce "Kakarmu ce ta haɗa auren, ba ya so na, an kai kuɗin aurensa aka fasa, shi ne ya aure ni" Ya ce "Ya yi wa kansa, ni ina so. Ki saka aurenmu a addu'a salma, in sha Allah zai yi albarka, wata nawa ki ke so a saka na ji kin ce a matse ki ke ko?" "Ai wannan maganar dr. Ba tawa ba" Ya ce "Haka ne, nima na matsun ne, in ga kin zama tawa" ummi dai ta yi shiru tana tunanin ko dai ba da gaske raihan yake ba. "Na ga gidan tv nan sun kira screening, manager ya ce mini kin je, ya ku ka yi da su?" Ta ɗan rausayar da kai ta ce "Kyawawa suke so, ba wanda sai an ta saka musu filter ba" "Kamar yaya kenan?" "Haka mai wurin ya ce" Kawai ta ga yayi parking ɗin motar, ya kalli ummi ya ce "Ke kuma ki ka ce masa me?" Tayi shiru tana kallon sa. "Magana nake yi miki?" "Ni ban ce komai ba" Raihan ya ce "Sai ki ka tsaya kina kuka ko? Gwanar kuka" Ta ce "A'a ai ban yi kukan ba" Ya danƙo kunnenta ya ce "Wallahi ummi, duk wanda ya kuma kushe mini ke, ki ka tsaya kina kallonsa, baki ɗau wani mataki ba, sai na huce a kan ki, kamar na fi ki jin takaici idan aka kushe mini ke. Ke kina da baki, amma ba zaki iya magana ba? Tun da ba aikin zai ɗauke ki ba, sai ki wanke shi tas ki bar wurin, atleast ai kya ce masa Allah ya sa kyawawan su durƙusar da tashar, ko ki ce masa ya koma islamiyya a karanta masa Allah ne mahalicci" Sosai ya riƙe mata kunne, ta kai hannu ta riƙe hannunsa da ya riƙe mata kunnen cikin muryarta mai cike da iyayi da shagwaɓa ta ce "Babba ne fa" Ya sakar mata kunnen ya ce "Babban banza ba, tun da ba shi da hankali" Sai kuma ya kwantar da murya ya ce "My wife" Ta ce 'Na shiga uku" "A'a ko ɗaya baki shiga ba, ko ba ni ki ke so ba, dan Allah ki yi haƙuri mu karɓi ƙaddara a yadda ta zo mana, bamu san dalilin da Allah ya sa ya haɗa mu ba, kar taurin kanki yayi delaying zuwan wasu bayin Allah duniya" tayi burus kamar ba da ita yake magana ba. "A haka kamar saliha, nan kuwa taurin kai a cikin ki kamar me". Ranar lahadi gaba ɗaya dr. Ya manta da batun zai yi baƙi, dan ya faɗi maganar ne dan ya kori raihan, ummi ma ta kasa zaune ta kasa tsaye, dan raihan ya tabattar mata da ranar lahadin Alhajinsu zai zo. Ƙarfe sha ɗaya na safe, Abdul ya je ya sanarwa dr. Yayi baƙi. Ya fita ya ga manyan mutane a manyan motoci, suka gaisa, Alhaji Tahir ya ce "Ka manta zaka yi baƙi ne? Kodayake ƴan boko sai kun bawa mutum lokaci yake zuwa, Tahir ne baban sirikinka Muhammad da ka ce kana son ganina". Dr. Ya ce "Subhanallah, Allah sarki bisimillah ku shigo"  suka bi bayan dr. Zuwa cikin gida. Har cikin falo, ya fita da sauri ya samu Abdul ya bashi kuɗi, ya ce ya sayo musu ruwa da lemuka. Sun daɗe suna hira da Alhaji Tahir, da wasu mutane su biyu ɗaya ƙaninsa ɗaya abokinsa. Dr. Ya sha mamakin jin waye raihan, tare da yi wa ummi fatan, Allah ya sa ƙarshen wahalarta ne ya zo. Nan Alhaji Tahir yake gaya wa dr. Tuni ya saka an gama yi masa bincike a kan ummi, kuma ya ji daɗin sakamakon binciken, dan haka ko yanzu aka ce su bayar da kuɗin aure dr. Ya yanka za su biya, idan kuma shima zai yi bincike a kan su tukuna shikenan. Dr. Ya ce "Eh to, ina son a bani damar binciken tukuna, sannan kamar nan da sati biyu zan yi magana, saboda in kira wasu daga ƴan uwana a karɓi kuɗin auren" Alhaji Tahir ya ce "Babu laifi, Allah ya kaimu" Ba tare da wata alkunya ba, suka ci abin da dr. Ya gabatar musu, suka yi masa godiya suka tafi. Farida ta din ga bin sa tana tambayarsa suwaye wannan baƙin, amma yaƙi gaya mata ko suwaye. Ummi ta sha mamaki, ba ta zaci da gaske ba, sai da ta ga su Alhaji Tahir sun zo. Alhaji Tahir ya koma gida, ya kira mami sashinsa, Hajiya na tare da shi, sai dai bai gaya mata ba ita ma, sai da Mami ta zo, ta tarar da su ta wani haɗe rai tana harare-harare. Alhaji Tahir ya ce "To ke fa abun arzki ya same mu, ban sani ba ko mun yi laifi" Mami ta ce "Meyafaru?" "Babban mutum ya zo mini da magana, ya je zance an ritsa shi an ce in je in gabatar da kaina idan da gaske yake, dan yau ma daga can nake da ni da su Alhaji Hamza, nan da sati biyu zamu koma mu kai kuɗin aure" "Ikon Allah, kuma shi ne ba a saka ni a maganar ba sai yanzu?" Hajiya ta ce "Masha Allah lallai babban mutum an girma, Ubangiji Allah ya sa abokiyar arziki ce, Alhaji a ina take zan yi shishshigi" Alhaji Tahir ya ce "Au kema babbar aminiyar ta sa bai gaya miki ba? Wai wata yarinya amm.. ammi ne sunan nata ne ko ummi ne, wai ƙawar maryam ce dai". Hajiya ta ce "Laaa ko dai Ummi, Ummi dai da suka yi islamiyya tare?" Ya ce "Yes of course haka ya ce mini" Cikin tsananin mamaki da takaici mami ta ce "What! Wannan kwazgwamar yarinyar baƙa ƙirin?" Ayshercool 08081012143 FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK. https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends Masu neman free books ɗina, da free pages duk akwai a kan watpad account ɗina. Irinsu Abduljalal Wata kissar sai mata Wuta a masaƙa Cutarwa Ƙanwar maza Gaba da gabanta Aƙidata Ruɗin ƙuruciya Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata. 08081012143. And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link. https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels Ayshercool. PAID ADVERT!. Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi. Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku Oll types of Turaran wuta Sandal Halut Irik Difur Gab Gab Kajiji Habil Nabak Humra Kulakcha Dilke da kalta Kayan Garan jiki Muna turara Kaya Kujerar garan jiki Kannada Madarorin turare masu kamshi Man garan gashi Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921 *TALLA!TALLA!TALLA!* *INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*. *BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU* *MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA* BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI.                          *CUTARWA* *BRIGHT PENS* (FREE BATCH) MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH. Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe. FOLLOW AND SHARE AYSHERCOOL 08081012143 MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH. Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe. 31 Har raihan ya bar harabar gidan bayansa ummi take kallo, ko sau ɗaya bai waiwayo ba, ita kuma ba ta daina zubar da hawaye ba, gani take kamar kallon ƙarshe take yi masa, ba zai sake dawowa rayuwarta da sunan yana son ta ba. Ta tashi jiki babu ƙwari, ta tafi ɗakinta, ta rufe ɗakin ta saka sakata, saboda kar noor ta zo ta isheta da surutu. Ta zauna ta din ga kuka, ta ma rasa kukan me take yi. Ta yi shiru tana tuno irin rayuwar auren da ta yi a gidan idiris, ta kasa manta irin wulaƙantar da ta yi a gidan idiris, irin tozarcin da ya yi mata, tamkar ya auri mushen dabba ba ɗan Adam ba, kuma ɗan Adam ɗin ma ƴar uwarsa. Ta tuna yadda abokansa suke zunɗensa da angon ɗoɗɗoya, ba zata manta tonon asiri da wulaƙantarwar da Idiris yayi mata ba. 'To idan kuma haryanzu ban warke ba fa'?" Ta tambayi kanta. Ta dafe ƙirjinta tana zancen zuci, ita dai tun da Allah ya sa kawu yahaya ɗaukkota, yayi ta ƙoƙarin saya mata magunguna, cikin ikon Allah ba ta sake jin wannan matsalar ba, ko maƙiyinta ba ta fatan Allah ya haɗa shi da bala'in da yake cikin larurar sanyi. Tun da farida ta dawo daga gidan inteesar, tamkar ita za ayi wa kishiya, kamar za ta yi hauka, domin kuwa da ita da wasu daga ƙannenta suka dawo gidan, suna ta bata haƙuri, a kan sai ta daure ita ma, idan ba haka ba inteesar ba zata kwantar hankalinta ba. Sun cika falo suna mayar da yadda aka yi, noor kuma na ta kokowa da remote tana ƙara volume ɗin tv. "Wai ke noor baki da hankali ne? Ba ni san meya samu yayarki Inteesar ba ne?" Noor ta juyo ta kalli mai maganar ta ce "Mutuwa ta yi ne?" "Wane irin mutuwa, ke ko gidan nata ma baki je ba, balle a haɗu a rarrasheta da ke, kina kallon mahaifiyarku hankalinta a tashe, ita ma can muka baro ta tana kuka, amma ke kina nan kina ƙure wa mutane kunne da ƙarar tv" Noor ta taɓe baki ta ce "To tun da dai ba mutuwa tayi ba ai barkanta, wanda ba shi da kunya ai dole ayi masa kishiya, haka wata malama ta ce rannan a tv, na ce ashe saura maama" "Ke uwar taki ki ke cewa ayi wa kishiya?" Kausar ta ce "Mama hadiza, ki ƙyale yarinyar nan kar ta saka hawan jininki ya tashi, ba isasshen kai ne da ita ba, yanzu sai ta yi miki rashin kunya, kuma ba kowa ne ke zigata yana koya mata wannan iskancin ba, ban da ummi, idan ba haka ba ta yaya ɗa zai yi fatan a yi wa uwarsa kishiya, banda shashasha mara hankali" "Ni dai ban saka da daƙiƙi a maganata ba, mutum ya bari ya fara gane karatu" kausar ta ja bakinta tayi shiru, idan ta cigaba da tankawa noor, sai noor ta kunyata ta a gaban mutane. Nan kuma akalar hirar ta koma kan ci wa ummi mutunci, da ziga farida a kan lallai yakamata ummi ta bar mata gida, tun da ta tsofe a gidan babu aure. Suka gama soko burutsunsu, suka bar gidan. Ummi kusan kwanan zaune tayi, tayi ta salloli tana kaiwa Allah kukanta, wayarta kuwa ta dubata babu adadi, amma babu saƙon raihan ɗaya da ya sake shigowa cikin wayarta. Ƙasan zuciyarta ya shiga tabattar mata da sun rabu da raihan kenan. Bayan ta idar da sallar asuba, message  ya shigo wayarta, wani website da raihan ya saka ta shiga, ta yi submitting cv ɗin ta, an kira su screening ciki har da ita, wani sabon gidan talabijin da ba a daɗe da fara shirye-shirye a cikin sa ba. Yau da safe aka ce su je wurin, ba ta ga saƙon ba sai yanzu, cikin sauri ta tashi ta haɗa credentials ɗin ta, agogo ta kalla, muddin ta ce za ta jira ta yi musu girki, to fa zata makara, dan haka ta dudduba jakunkunanta, ta samu kuɗi ta fito, ta turawa Abdul message na in da ta tafi. Ko da ta je wurin ta tarar da mutane da yawa, haka nan ta fara bin layi ita ma, ta din ga duba wayarta tana tunanin raihan, shi ne mutum na farko da yakamata ta kira, ta sanar masa da an kirata screening, sai dai ba ta da wannan damar a yanzu. "Dama na sani, babu lallai ka dawo gareni raihan, amma duk da haka ba zan ga laifinka ba, ina yi maka fatan alkhairi a duk in da ka ke". Farida tamkar ita aka yi wa kishiyar, ko bacci gagararta yayi, ta taso da nufin ta tarar da abincin safe, Abdul ya shigo ya sanar da ita saƙon ummi, tana fara zage-zagenta, ya fice ya bar mata falon. Raihan yana zaune yana ta juyi a kan kujera a office ɗin sa, ya kasa taɓuka komai, ya juya kai nan ya juya kai can, in aka jima sai ya ciro wayarsa ya duba ya mayar ya ajiye. Ya kifa kansa a kan teburin gabansa, yana jin yadda kansa yake masa wani irin zafi. Jin motsin an buɗe ƙofa ya sanya shi ɗaga kai ya ga me shigowar, babu tsammani ya ga safiyya, tana sanye da doguwar riga straight gown, sai mayafinta a kafaɗa da jakarta, ta shigo bakinta ɗauke da sallama. Ya amsa mata tare da mayar da kansa ya kifa. "Yaya raihan, barka da rana?" "Yauwwa sannu" Ta nemi wuri ta zauna ta ce  "Gidan su wata ƙawata na je, a nan tsukin ne, na ce bari na biyo mu gaisa" Yayi shiru bai ce mata komai ba. "Are you ok?" Tayi maganar tana kai hannu goshinsa, ganin yana gumi duk da akwai sanyi a office ɗin. Rau ta ji goshin nasa ya ɗau zafi, ta ce "Subhanallah, yaya raihan baka da lafiya ne? Jikinka zafi" Ya ɗago a hankali ya ce "Safiya, ki tafi gida Please, ki ƙyale ni" "Amma ya zan tafi na barka a wannan halin?" Kallonta yake yi, yana tunanin dama ummi ce a zaune a gabansa take yi masa magana yanzu. "Ki tafi na ce" yayi maganar a ɗan hasale, tare da jin haushin yadda ya ta tsare shi da ido, saɓanin ummi da ba ta iya ƙura masa ido haka, sai tana yi tana kawar da kai. Safiyya ba ta fi shekaru goma sha tara ba, ummi ta girmeta sosai, sai dai shegen iyayi da rawar kai, duk in da ta zauna ba ta da aiki sai hira da samari a waya, ga shegiyar kwalliya kamar ƴar tsana. Ta razana da tsawar da yayi mata, ta tashi da sauri, har ta kusa fita ya ce "Kar ki sake biyo ni office, office wurin aikina ne ba shirme ba" tayi sauri ta fice tana waiwayensa. Ummi kuwa ta galabaita a ranar, dan bayan screening, aka ce su jira aka tura musu waɗanda suka yi nasara a waya, ciki har da ita, aka ce su jira ayi musu interview. Kuɗin hannun ummi ba zasu kai ta ci abinci ba, ga yunwa ta isheta, haka nan suka cigaba da jira. Ba a zo kan ummi ba, sai kusan biyar na yamma, da farko bayan shigarta studion aka fara yi mata interview, a ɗan tsorace take, ga yunwa tana ji, ɗaya daga cikin masu interview yana cewa masha Allah muryarta mai daɗi. Ɗayan ya ce "Jin ta ya fi ganinta, wannan da radio ce irin su ne masu sauraro ke ɗokin gani" Shugaban wurin ne ya shigo, ma'aikatan suka din ga gaishe shi, yana hura hanci, ya dubi ummi ya ce "Wannan fa?" "Sir tana cikin wanda suka tsallake screening, interview ake yi mata" "Wannan ɗin?" "Eh sir" "Dan Allah ku zaɓo wanda za su yi attracting ɗin mutane, ba wanda sai mun yi ta faman sanya filter muna fafutuka kan mu haska su ba, wannan shirin talabijin ne, ba na gidan rediyo ba!" Tsit mutanen wurin suka yi, ba wannan ne karo na farko ba, amma a duk lokacin da aka yi mata, jin abun take kamar sabo, sum-sum, ta tattara kayanta, tayi waje, duk suka tsaya suna kallon ummi, shi kuma ko a jikinsa ya cigaba da maganar sa. Ita ba ta san ma yadda aka yi ta isa gida ba, abubuwa daban-daban cunkus a ranta, ta ɗaukko gajiya da baƙin ciki, tana zuwa gida farida ta dira mata nata tashin hankalin. "Raihan ka gani ko?, ka kori wanda zai aureni, kaima ka tafi ka bar ni, komai yayi mini zafi" Tayi kuka-kuka iya yin ta, har ta gaji tayi shiru. Ta wuni da yunwa, haka ta kwana da wata. Kwanaki huɗu rabon raihan da ummi, yayi ƙoƙarin sanya abun da ta gaya masa a matsayin hujjar da za ta rabu da shi, amma shi sam bai ji hakan a matsayin hujja ba, dan damuwa yake ƙara shiga na rashin ta, ya zuba mata ido ya ga iya gudun ruwan ta, ko za ta neme shi, amma ya ji shiru. Hakan ya sanya ya fara zargin anya ba da gaske take ba ta son sa ba, tun da ta iya gaya masa cewar su rabu, kwanaki huɗu amma ba ta sake nemansa ba, dan haka tsoro ya sake shiga zuciyar sa, ummi ba ta son sa. Ƙasan zuciyarsa yana mamakin yadda ta ce masa ta taɓa aure, shi ba auren ta ne ya dame shi ba, meya kashe auren? A yadda ummi take har ace namiji ya sake ta?. Daurewa yayi, ya sake bawa ummi kwana ɗaya, ya zamana kwanaki biyar, amma shiru ba ta neme shi ba. Kwana na biyar, da yamma ya koma gidansu ummi, sai dai ya kira wayarta amma ba ta shiga. Yana tsaye sai ga motar dr. Raihan ya risuna ya gaishe shi, dr. Ya amsa masa, yayi parking a waje, ya shiga cikin gida. Raihan ya dudduba, mai gadin gidan ma baya nan, yayi ta kiran lambarta amma shiru ba ta shiga. Ya samu wuri ya zauna a ƙofar gidan, yana cigaba da dannan wayarsa. Dr. Ya sake fitowa,  ya ga raihan, ya kalli raihan ya ce "Yarona wa ka ke nema ne? Ko wurin Abdul ka zo?" Raihan ya ce "A'a Abba, wurin Ummi na zo" Dr. Ya ce "Too, ummi kuma lafiya dai ko?" "Eh lafiya ƙalau, wurinta dai na zo, na kira wayarta ba ta shiga ne" "Amma wani abun tayi maka ne?" Ya girgiza kai ya ce "A'a, ba ta yi mini komai ba" Dr. Ya jinjina kai ya ce "Yaron kirki, ai babu lallai ummi ta tsaya ta saurareka, a yanzu mijin aure ne ya dace ya zo wurinta, ba wanda za a yi soyayya ba kawai, wannan idan ba ku yi sa'anni ba, ba zaka girmeta da yawa ba. Ka yi haƙuri ka ji ɗana. Cikin girmamawa raihan ya ce "Abba ummi ta sanni, akwai alaƙa tsakani na da ita, wallahi abba ba ɓata mata lokaci zan yi ba, aurenta zai yi, ina son ta wallahi". Dr. Yayi shiru yana kallonsa, sannan ya yi murmushi ya ce "Meye matakin karatunka?" "Na yi degree a ɓangaren Business administration, a ATBU" "Idan da gaske ka ke zaka aureta, ranar lahadi ka turo mini mahaifinka mu yi magana da shi" Raihan ya washe baki ya ce "To Abba, in sha Allah zan gaya masa, na gode sosai da sosai" Dr. Yayi murmushi yayi gaba, a tunaninsa yayi maganin raihan, dan ya zata irin yaran nan ne marasa ji, amma duk da haka nutsuwa da kamalar raihan ɗin. Raihan tafiya yayi yana murmushi, yana ganin abun kamar a mafarki, yau ya tsinci dami a kala, abun kamar a shirin film, wai ya tura Alhajinsa a nema masa aure? Kai tsaye gida ya tafi. Sai dai ƙasan zuciyarsa yana tunanin, ummi za ta amince ko kuwa za ta cigaba da gardama ne? Dan ya ga kamar ta raina shi ne a matsayin mijin aure, yayi mata ƙanƙanta. Yana zuwa ya tafi sashin Alhaji, dan kwanakin nan kusan kullum Alhajin yana gida, ya daki sa'a shikaɗai ya tarar a sashin nasa. Alhaji Tahir ya gyara zaman tabaran sa, ya ce "Ya aka yi ne? Yanayin farinciki haɗe da damuwa a fuskar babban mutum" Raihan ya je ya zauna a kusa da shi, ya ce "Kowanne akwai Alhaji" "Bani labari" Ya ciro wayarsa, ya nemo hoton ummi da yayi mata, lokacin da suka sayo dogwayen riguna, ya ce "Alhaji ka ga wannan" Alhaji ya karɓi wayar, ya ƙare wa hoton kallo ya ce "Na gani, meyafaru?" "Alhaji tana da kyau?" Ya ce "Masha Allah, very beautiful kuwa, da gani kuma tana da kunya" "Ita nake son aura Alhaji, zaka nema mini aurenta?" Alhaji Tahir ya kalli raihan yayi murmushi ya ce "Babban mutum wannan ai matar manyan ce, anya ba ka yi tsaurin ido ba kuwa?" "A'a Alhaji, ai nima babban mutum ne, dan Allah tayi? Wallahi mutuniyar kirki ce" Alhaji ya yi shiru ya ce "Ai ni kallon sani nake yi mata ma" Raihan ya ce "Eh, ƙawar maryam ce, amma ita ba ta girme ni ba, shekrunmu ɗaya da ita, kuma mutuniyar kirki ce ka tambayi Hajiya ma ka ji" Alhaji Tahir ya dafa kafaɗar raihan ya ce "Easy my dear, in dai kana son ta tayi mini, za a nemi aurenta in dai za a bamu" Raihan ya washe baki ya ce "Babanta ya ce ranar Sunday wai ka je ku yi magana, gani yake yi kamar ba aurenta zan yi ba, Alhaji tana bani shawarari masu kyau, tana da kirki sosai" "Allah ya kaimu lahadin, zan je in sha Allah, ko a lokacin suka ce sai a ɗaura, Ubangiji Allah ya sa abokiyar zama ta gari ce" Raihan ya sosa kai ya ce "Alhaji saura abu ɗaya" "Ok to ina jinka" Raihan ya ce "Dan Allah kar ka gaya wa mami sai maganar ta faɗa, ban san yadda za ta karɓi maganar ba. I really have to marry her, Alhaji rayuwar ummi akwai ƙalubale da ban tausayi, dan Allah ka tsaya mini" Alhaji Tahir ya jinjina kai ya ce "In dai ni ne ka san baka da matsala da ni, ko tsohuwa ka ce kana so, zan wuce maka gaba in dai tana da tarbiyya, kuma ko a hoto, ni yarinyar ban ga aibunta ba, ko ta girmeka in dai kana son ta shikenan, ai soyayya ba ƙarya ba ce raihan, mune muke barin al'ada na rage mana jin daɗin abun da addini ya halatta mana. Allah ya sanya alkhairi ango" Raihan ya sunkuyar da kai yana murmushi, wani irin farinciki na ratsa zuciyarsa. Dr. Ya manta da batun haɗuwarsa da raihan, dan ko ummi ma bai nema da maganar ba, sai dai ya rage ganin gilmawarta ko a gidan, ya bar hakan a wataƙila takurar farida ce ta saka ta ƙara takura kanta. Washegari raihan ya tafi wurin aikin Ummi, amma manager ya ce "Ai ummi yau kusan kwana uku ba ta zo ba, ni ban sani ba, ba ta da lafiya ne ko ya aka yi ban sani ba, kawai ta ce mini za ta je screening, tun ranar ba ta sake zuwa ba, na zata ma ko ba ta gama ba ne ba". Raihan ya yi shiru ya ce "kira ta a waya ka ce ko ta dawo aiki, ko zaka koreta". Manager ya zare ido ya ce "Yayarta ka za a kora? Idan ban koreta ba ni ai yayana ya kore ni, ka san yadda yake yabawa ƙoƙarin ta, da yabawa amanarta" Raihan ya ce "Dan Allah ka bar wannan maganar, kawai ni dai taimakon da zaka yi mini kenan, ka ce lallai ta dawo aiki. "Ba zan yi ba, ba kun fi kusa ba" Raihan ya sassauta murya ya ce "Haba manager, dan Allah ka taimaka Please" "Da ka ce ba ka ji? Zan yi mata magana, amma ba dan halinka ba, kuma ba zan ce zan wani koreta ba, zan dai yi ƙoƙarin ta dawo ɗin" Raihan yayi dariya ya ce "Allah ya bar mini manager" Manager kawai yayi murmushi, ya cigaba da aikin da yakamata ace ummi ce ta yi. Sai dai manager bai kai ga yin hakan ba, washegari sai ga ummin ta zo aiki, sai dai ta rame sosai, kallo ɗaya zaka yi mata ka san akwai tashin hankali a fuskar ta. Manager ya kira raihan a waya, ya gaya masa ummi ta zo. Bai ja dogon lokaci ba, ya daidaici lokacin tashin ta ya kusa, sannan ya tafi. Ta fito daga wurin aikin, yana nesa kaɗan da ita yana kallonta, tana tafe a hankali kamar mara lafiya. Zuwa yayi ya sha gabanta da motar, ta tsaya tana kallon motar, ya sauke glass ɗin motar suka haɗa ido, sai da ta ɗan razana, ya buɗe mata motar ba tare da ya ce mata uffan ba. Jikin ummi ya yi sanyi sosai da ganin raihan, dan ba ta taɓa tsammani ba, kamar mai jin tsoro haka ta ɗosana ta shiga motar. "Ta tabatta dai ba kya so na ko ummi? Kina iya rabuwa da ni, baki damu da halin da zan shiga ba, kin ce mu rabu, ko nema na baki sake yi ba, rashin muhimmancina har ya kai haka kenan ko Salma?" Ta girgiza masa kai alamar a'a. "Shikenan, ni gashi na sake biyo ki ai, ranar lahadi Alhaji zai zo wurin dr." A razane ta kalleshi, tana ƙifta ido. "Eh, mun haɗu da dr. Shekaranjiya, na zo wurinki kin ƙi ɗaga wayata, mun yi magana ya ce Alhaji ya zo su yi magana" "Wai da gaske aurata zaka yi?" Tayi maganar cikin matuƙar rauni. "Gashi ina gaya miki, kin zata da wasa nake yi? Na san wataƙila ba ni ne irin mijin da ki ke so ba, na san zaki ga na yi miki yarinta da yawa, amma har cikin raina nake jin zan iya aurenki na riƙe ki da kulawa da girmamawa". "Raihan zaka aureni ina bazawara" "Kar ki sake kawo mini maganar kin taɓa aure, zuciyata zata fashe, ummi kina wasa da son da nake yi miki kina ganin kamar wasa ko? Hubban shadidan na kira shi, ban taɓa jin damuwa da takura a kan son wani abu ba kamar ke, kawai in ganki a kusa da ni, shi zai kawo mini cikakkiyar nutsuwa" Tayi shiru tana wasa da zoben hannunta. "Meya rabaku da tsohon mijinki?" Tayi ajiyar zuciya ta ce "Kakarmu ce ta haɗa auren, ba ya so na, an kai kuɗin aurensa aka fasa, shi ne ya aure ni" Ya ce "Ya yi wa kansa, ni ina so. Ki saka aurenmu a addu'a salma, in sha Allah zai yi albarka, wata nawa ki ke so a saka na ji kin ce a matse ki ke ko?" "Ai wannan maganar dr. Ba tawa ba" Ya ce "Haka ne, nima na matsun ne, in ga kin zama tawa" ummi dai ta yi shiru tana tunanin ko dai ba da gaske raihan yake ba. "Na ga gidan tv nan sun kira screening, manager ya ce mini kin je, ya ku ka yi da su?" Ta ɗan rausayar da kai ta ce "Kyawawa suke so, ba wanda sai an ta saka musu filter ba" "Kamar yaya kenan?" "Haka mai wurin ya ce" Kawai ta ga yayi parking ɗin motar, ya kalli ummi ya ce "Ke kuma ki ka ce masa me?" Tayi shiru tana kallon sa. "Magana nake yi miki?" "Ni ban ce komai ba" Raihan ya ce "Sai ki ka tsaya kina kuka ko? Gwanar kuka" Ta ce "A'a ai ban yi kukan ba" Ya danƙo kunnenta ya ce "Wallahi ummi, duk wanda ya kuma kushe mini ke, ki ka tsaya kina kallonsa, baki ɗau wani mataki ba, sai na huce a kan ki, kamar na fi ki jin takaici idan aka kushe mini ke. Ke kina da baki, amma ba zaki iya magana ba? Tun da ba aikin zai ɗauke ki ba, sai ki wanke shi tas ki bar wurin, atleast ai kya ce masa Allah ya sa kyawawan su durƙusar da tashar, ko ki ce masa ya koma islamiyya a karanta masa Allah ne mahalicci" Sosai ya riƙe mata kunne, ta kai hannu ta riƙe hannunsa da ya riƙe mata kunnen cikin muryarta mai cike da iyayi da shagwaɓa ta ce "Babba ne fa" Ya sakar mata kunnen ya ce "Babban banza ba, tun da ba shi da hankali" Sai kuma ya kwantar da murya ya ce "My wife" Ta ce 'Na shiga uku" "A'a ko ɗaya baki shiga ba, ko ba ni ki ke so ba, dan Allah ki yi haƙuri mu karɓi ƙaddara a yadda ta zo mana, bamu san dalilin da Allah ya sa ya haɗa mu ba, kar taurin kanki yayi delaying zuwan wasu bayin Allah duniya" tayi burus kamar ba da ita yake magana ba. "A haka kamar saliha, nan kuwa taurin kai a cikin ki kamar me". Ranar lahadi gaba ɗaya dr. Ya manta da batun zai yi baƙi, dan ya faɗi maganar ne dan ya kori raihan, ummi ma ta kasa zaune ta kasa tsaye, dan raihan ya tabattar mata da ranar lahadin Alhajinsu zai zo. Ƙarfe sha ɗaya na safe, Abdul ya je ya sanarwa dr. Yayi baƙi. Ya fita ya ga manyan mutane a manyan motoci, suka gaisa, Alhaji Tahir ya ce "Ka manta zaka yi baƙi ne? Kodayake ƴan boko sai kun bawa mutum lokaci yake zuwa, Tahir ne baban sirikinka Muhammad da ka ce kana son ganina". Dr. Ya ce "Subhanallah, Allah sarki bisimillah ku shigo"  suka bi bayan dr. Zuwa cikin gida. Har cikin falo, ya fita da sauri ya samu Abdul ya bashi kuɗi, ya ce ya sayo musu ruwa da lemuka. Sun daɗe suna hira da Alhaji Tahir, da wasu mutane su biyu ɗaya ƙaninsa ɗaya abokinsa. Dr. Ya sha mamakin jin waye raihan, tare da yi wa ummi fatan, Allah ya sa ƙarshen wahalarta ne ya zo. Nan Alhaji Tahir yake gaya wa dr. Tuni ya saka an gama yi masa bincike a kan ummi, kuma ya ji daɗin sakamakon binciken, dan haka ko yanzu aka ce su bayar da kuɗin aure dr. Ya yanka za su biya, idan kuma shima zai yi bincike a kan su tukuna shikenan. Dr. Ya ce "Eh to, ina son a bani damar binciken tukuna, sannan kamar nan da sati biyu zan yi magana, saboda in kira wasu daga ƴan uwana a karɓi kuɗin auren" Alhaji Tahir ya ce "Babu laifi, Allah ya kaimu" Ba tare da wata alkunya ba, suka ci abin da dr. Ya gabatar musu, suka yi masa godiya suka tafi. Farida ta din ga bin sa tana tambayarsa suwaye wannan baƙin, amma yaƙi gaya mata ko suwaye. Ummi ta sha mamaki, ba ta zaci da gaske ba, sai da ta ga su Alhaji Tahir sun zo. Alhaji Tahir ya koma gida, ya kira mami sashinsa, Hajiya na tare da shi, sai dai bai gaya mata ba ita ma, sai da Mami ta zo, ta tarar da su ta wani haɗe rai tana harare-harare. Alhaji Tahir ya ce "To ke fa abun arzki ya same mu, ban sani ba ko mun yi laifi" Mami ta ce "Meyafaru?" "Babban mutum ya zo mini da magana, ya je zance an ritsa shi an ce in je in gabatar da kaina idan da gaske yake, dan yau ma daga can nake da ni da su Alhaji Hamza, nan da sati biyu zamu koma mu kai kuɗin aure" "Ikon Allah, kuma shi ne ba a saka ni a maganar ba sai yanzu?" Hajiya ta ce "Masha Allah lallai babban mutum an girma, Ubangiji Allah ya sa abokiyar arziki ce, Alhaji a ina take zan yi shishshigi" Alhaji Tahir ya ce "Au kema babbar aminiyar ta sa bai gaya miki ba? Wai wata yarinya amm.. ammi ne sunan nata ne ko ummi ne, wai ƙawar maryam ce dai". Hajiya ta ce "Laaa ko dai Ummi, Ummi dai da suka yi islamiyya tare?" Ya ce "Yes of course haka ya ce mini" Cikin tsananin mamaki da takaici mami ta ce "What! Wannan kwazgwamar yarinyar baƙa ƙirin?" Ayshercool 08081012143 FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK. https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends Masu neman free books ɗina, da free pages duk akwai a kan watpad account ɗina. Irinsu Abduljalal Wata kissar sai mata Wuta a masaƙa Cutarwa Ƙanwar maza Gaba da gabanta Aƙidata Ruɗin ƙuruciya Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata. 08081012143. And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link. https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels Ayshercool. PAID ADVERT!. Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi. Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku Oll types of Turaran wuta Sandal Halut Irik Difur Gab Gab Kajiji Habil Nabak Humra Kulakcha Dilke da kalta Kayan Garan jiki Muna turara Kaya Kujerar garan jiki Kannada Madarorin turare masu kamshi Man garan gashi Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921 *TALLA!TALLA!TALLA!* *INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*. *BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU* *MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA* BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI.                         *CUTARWA* *BRIGHT PENS* (FREE BATCH) *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH. Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe. FOLLOW AND SHARE AYSHERCOOL 08081012143 MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH. Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe. 32 Alhaji ya ce "Meye kuma na wata kwazgwamemiya baƙa? Ba mutum ba ce ba?" "Ban gane ba mutum ba ce, ta girme shi fa ƙawar maryam ce?" Ya ce "To shi ne me? Idan har shi zuciyarsa ta nutsu da ita ba shikenan ba, ni na yaba da tarbiyyar gidansu" "Wallahi da sake, tun wuri ma dole a janye wannan maganar. Na zaɓa masa yarinya ya ƙi sai ya jajibo wannan mummunar yarinyar? Gidan da take zaune ai ba gidansu bane ba, zaman boranci ta yi a gidan kamar ƴar aiki" "To kin ga kya samu lada ma, idan ya aureta ya kula da ita" Kamar zata kama da wuta dan bala'i ta ce "Wallaahi ba zan lamunta ba, shi ne dan munafunci ni bai gaya mini ba, kawai sai yau ka zo mini da wannan zancen, a'a wallahi" Alhaji ya ce "Ni dai in kin ga na fasa zancen auren nan, sai dai in shi ne ya dawo ya ce mini ya janye ya fasa, amma ba zan zama mutumin banza ba, shima sai dai in yi masa jagora ya je ya samu ubanta ya ce masa ya fasa" Hajiya ta ce "Banda abun ki, ai ummi yarinyar kirki ce, nutsatsiyar yarinya ce, shi kyau ba shi ne abun dubawa ba, nagarta ake da cancanta ake dubawa" "Kin ga malama ki rufa mini baki, ban saka da ke ba, idan nutsatsiya ce, ki haɗata da makakkun yaranki mana, sai ɗa na dama na san wannan duk kitumurmurarki ce, ke ki ka shirya wannan abun aka yi ban sani ba" Hajiya ta ce "Allah ya baki haƙuri, nima ban san zancen ba sai yanzu, kuma su makakkun ƴaƴa ba laifi na yi wa Allah ya bani ba, jarrabawa ce, kuma da da nutsatstse a cikin su na yi sha'awar sanya ɗaya ya aureta" Har mami za ta yi magana, Alhaji ya yi mata wani mugun kallo, hakan ya sanya ta yin shiru tana huci. Hajiya kuwa tuni hawaye ya cika mata ido, tana jin zafin gori da cin mutunci da mami ke yi mata a kan yaranta, gani take yi kamar dabarar ta ce ta sanya Allah ya bata shiryayyun yara. Alhaji ya kalli mami ya ce "Tun da kin saka mini mata kuka, sai ki bani wuri zan kula da ita" Maganar ta sa ba ƙaramin fusata mami tayi ba, ta tashi ta ce "Haɗiyeta ƙarewar soyayya" tayi waje fuu rai a ɓace. Ya dubi hajiya da hawayen fuskarta suka fara zubowa, ya rungumota jikinsa a hankali ya ce "You are brave woman, kar ki karaya, ki yi haƙuri ke ce fa mai Kwantar mini da hankali da rarrashina, ki yi haƙuri in sha Allah zaki ga tanadin da Allah ya yi miki sakamakon haƙuri" Ɗan ƙara sautin kukan nata tayi, hawayenta ya ɓata masa riga, amma bai damu ba ya cigaba da rarrashin ta. Kira uku raihan ya yi wa ummi sannan ta ɗaga, tayi masa sallama. "Meyasa baki ɗaga ba, missed calls uku fa na yi miki" "Ina aiki ne a kitchen, wayar tana ɗaki" Raihan ya gyara kwanciyarsa ya ce "To ya ki ke sweetheart" wata irin kunya ce take kama ummi, idan ya ce sweetheart ɗin nan, wai raihan ke ce mata sweetheart abun da kunya. "Ba zaki amsa ba?" "Ina lafiya" ta amsa a taƙaice. "To yaya, su Alhaji sun zo ko? Na ga ya dawo ɗazu ina jiran ya kira ni ne" A sanyaye ta ce "Eh sun zo" "Yauwwa masha Allah, daga nan zuwa kowane lokaci zaki zama matata baby" Ummi ta ce "Dan Allah ka din ga ce mini ummi kawai ko salma" Raihan yayi murmushi ya ce "Ba kya son babyn saboda me? Ba daga bakin yaro kamata ki ke son ji ba ko? Kar ki yanke mini hukunci a yanzu, ina da kyakywan tanadi a kanki da rayuwarki ummi, zaki ji daɗin zama da ni sosai da sosai ki yi ta yi mana addu'a kin ji my Salma". Ta amsa masa da "To" amma tunanin yadda za ta yi rayuwar aure da raihan take yi, ita yanzu gaba ɗaya ma kunya yake bata. Faɗowar mami afujajan ɗakin ya sanya shi tashi zaune, ya ce "Zan kira ki" sai dai kan ya katse wayar ta ce "Sannu shashasha, ni zaka je ka aurowa wannan mummunar yarinyar?" Kan ya katse wayar ummi ta ji me mami ta ce. "Mami meyafaru ne?" "Uwarka da ubanka ne suka faru, in ce maka ga safiyya ka aura amma ka yi burus, ka je ka kwaso wannan yarinyar uwar mata ka yi yaya da ita? Ta girmeka ba sa'arka ba kawai saboda baka da hankali ko dan ba ka da mafaɗi?". Raihan ya ce "Mami, dan Allah ki kwantar da hankalinki, duk fa ba abun ɗaga hankali bane ba. Ke ki ka gabatar mini da ita da kyawawan halayenta, na ji ina jin tausayinta. Ki ka kawo mini maganar aure na ga ita ta dace da ra'ayina, idan kowa ya ce ba zai aureta ba mummuna ce shikena sai ta rayu a haka, ba tausayawa babu kulawa?" Rufe mini baki kan na daki bakin naka ya fashe, kai ne ɗan sarkin taimako, wani ya taimaketa mana a waje, ta girmeka ba sa'arka ba ce ba, ita ba ƴar uban kowa ba, kawai ka jajibo mana ita, to wallahi idan ma wannan matar ce ta zigaka dai-dai nake da ku. Kuma umarni nake ba ba shawara ba, ka je ka samu mahaifinku, ka janye wannan maganar da zancen auren nan da komai, dama ai ni na kawo maganar auren to safiyya na zaɓa maka, ita kuma ummin na san yadda zan yi da ita" Cikin sauri ya ce "Dan Allah mami kar ki yi wa ummi komai, ni zaki yi wa ni na ce ina son ta, dan Allah kar ki sakata a damuwa, dan Allah mami ki yi haƙuri" Galala ta saki baki tana kallon sa, "Au kar in sakata a damuwa? Har abun naka ya kai haka kenan? Dole na san abun yi" Ta juya ta fita. Ummi kuwa a hankali ta sauke wayar hannunta, fes abun da ta ji mami ya faɗa yake dawo mata, tabbas! Ta san a rina ta san zata fuskanci wannan ƙalubalen, tayi ta ƙoƙarin ankarar da raihan, amma bai gano ba, ta san yanayin mami ƴar ƙarya ce, mace ce mai iyayi da son nuna isa, ta san dama abu ne mai wuya mamin ta amince. Dr. Ya yi sallama a ƙofar ɗakin ummi, ta amsa masa ya shiga, ya kalleta cikin farinciki da kulawa ya ce "Ummana, ke ashe ɗan manya ki ka samo mini siriki, ai ni gatse na yi wa saurayin naki, ganin yayi yarinta da yawa, na ce ya turo mini babansa ni na ma manta, kin ga sai ga su sun zo" Ummi ta yi shiru ta sunkuyar da kai, tamkar ta ce wa dr. Dan Allah ya warware maganar. "Alhamdilillah, ina jin labarin Alhaji Tahir ashe babban mutum ne, mutumin kirki ne, kamar ba mai kuɗi ba, yayi mini bayanin komai, na ɗeba musu sati biyu, zan ne na yi bincike a kansu da yaron, in dai lafiya ƙalau nan da sati biyu za su kawo kuɗin auren, Ubangiji Allah ya kusa kawo miki ƙarshen zaman gidan nan, Allah ya baku zaman lafiya, ya kawar da fitina. Dama wani jinkirin alkhairi ne, ki kwantar da hankalinki ummi, kar ki ga yaro ne ƙarami, ki saka a ranki Allah ne ya duba ki, ya kawo miki miji. Ita nagarta ba a shekaru take ba ko tarin dukiya, babban fatan Allah ya tabbattar da alkhairi, dama ke mai biyayya ce, dan haka ki ƙara dan sa'anki ne kar ki ce ba zaki bi shi ba, Allah ya sanya muku dukkan alkhairi" Ummi a ranta ta ce "Ji kawu da wata magana, har da nasiha kamar an ɗaura auren, akwai ƙura fa' sama-sama take jin sa, ya gama nasiharsa ya fice. Farida kuwa har Abdul ta tambaya, ko ya san suwaye baƙin dr., Amma ya ce mata shi ma bai sani ba. Bayanin da Alhaji ya yi wa raihan ne ya rage masa damuwar abubuwan da mami ta yi masa. Ya ɗora da cewa "Mahaifiyarka ta fara tutsu, a kan ba ta san lamarin, idan har da gaske kana son yarinyar kana son tainakonta, ka tsaya a kan hakan, ka cigaba da addu'a, ni dai yarinyar ta yi mini, ban ga aibunta ba, wani muni wani waye hotonta da ka nuna mini ban gani ba, ban sani ba ko dan kana sonta ba ka ga munin bane ya sanya nima ban gani ba. Ka je ka cigaba da shirye shiryen ka, a duba fili ɗaya ka gina abun ka yadda ka ke so, ba wata matsala in sha Allah" Cikin girmamawa raihan ya ce "Na gode sosai Alhaji, Allah ya ƙara maka lafiya da nisan kwana" "Amin babban mutum" Hajiya ta yi sallama hannunta ɗauke da tray, da kayan shayi a kai. Tana ganin raihan ta ce "In fara guɗa tun yanzu ne, ko in ɗan jira?" Murmushi raihan ya yi yana sosa ƙeya. Hajiya ta zauna tare da faɗin "To kai raihan daga ganin ummi, har ce maka fa na yi wa ina yi wa yayanka kamu, kawai sai ka lallaɓa" Ya ce "Wallaahi hajiya tausayi take bani a lokacin, na din ga damunta har muka fara sabawa. Hajiya ummi na da matuƙar kirki da tarbiyya" Hajiya ta ce "Sosai kam, ina fatan Allah ya sanya alkhairi, na yi maka murna raihan, in dai mace ta gari ake nema, aka samu ummi to a gode Allah. Sannan shekarun da ke tsakanin ku ba abun damuwa bane, shekaru lambobi ne kawai, ka riƙe ta ka kula da ita, ni dai ina son ta saboda Allah, tun tana zuwa gidan nan lokacin maryam tana nan, akwai ɗa'a da ladabi" Raihan ya ce "Kuma wallahi ta iya girki sosai hajiya, ba ki ga yadda take bani abinci ba, ban taɓa cin abinci mai daɗin nata ba" Alhaji ya dungure masa kai ya ce "Sannu ciki muka kawo duniya " suka yi dariya gaba ɗaya, gaba ɗaya sai ya manta da damuwar da yake ciki. Ummi na zaune na tilawar litattafanta na addini, wayarta ta fara ringing, baƙuwar lamba ce, tayi zaton ko raihan ne, dan akwai canza lambobi. Sai dai tana kai wayar kunneta, tayi niyyar sallama, ta gimtse sallamar jin uwar ashariyar da aka lailayo mata. "Sannu asararriya ƴar wahala, baƙin kunurci, saboda asara da taɓewa kana da rashin kyakykyawar makoma, ummi ki rasa wa zaki ce zaki aura sai ƙanina ummi, na yi dana sanin saninki, saboda kin zama guzuma muni yayi miki katutu shi ne ki ka yi wa ƙanina asiri, saboda zalamar abun duniya, to wallahi ummi ki kuka da kanki, ko ki janye wannan maganar ta auren raihan, ko kuma in ƙasƙanta ki a idon duniya, in muzantaki kin san zan iya" Jikin ummi yayi sanyi matuƙa, ta kasa magana, har maryam ta yi tijararta a waya ta gama, ta kashe wayar, kamar shashasha ummi ta bi wayar da kallo. *Sweetheart, ki yi bacci cikin aminci da salama, zan so kiranki in ji muryar ki, amma na san wataƙila kin yi bacci, ki kula mini da kanki, ina son ki* message ɗin raihan ya shigo wayarta. Ta miƙe ta tafi gaban mudubin ɗakinta, tana ƙarewa kanta kallo. 'to shi raihan ya aka yi baya ganin munina ne? A wajen ina munin nawa yake da yake ɓuya a idonsa baya gani?'. Abu kamar wasa, mami ta sako raihan a gaba, ta daina amsa gaisuwar sa, ta daina shiga sabgarsa ta ce lallai sai ya je ya cewa Alhaji ya fasa auren nan. Duk taurin kan ɗa, fushin uwa masifa ne, hakan ya sake jefa shi cikin damuwa da wasi-wasi, idan ta ce ya rabu da ummi, sai ya ji kamar ta ce ya raba jikinsa da rai. Gefe Hajiya da Alhaji suna ta ƙarafafa masa gwiwa a kan auren ummi. Ga lokacin kai kuɗi na cigaba da kusantowa, ga pressure office, ga ummi gaba ɗaya ta canza ta koma masa kamar wata baƙuwa, taƙi sakin jiki da shi, kamar ma ƙara nesanta kanta da shi take yi. Yanayin aiki ya ƙara takura raihan, dan haka ko wurin aikin bai fiye samun damar binta ba, ga yawan barin ƙasar da yake yi. Gefe guda maryam ta saka ummi a gaba da cin mutunci da zagi na cin zarafi kala-kala, ban da saƙonni da kuma barazana da take yi mata, ummi ta rasa in da za ta saka kanta, daga kuka sai addu'a, dan ta rasa yadda za ta yi da al'amarin gaba ɗaya. Duk da mami ba ta shiga harkarsa, hakan ba ya hana shi zuwa in da take, da la'asar bayan ya dawo daga aiki, yayi niyyar zuwa yau ya je ya ga ummi, ya nufi sashin mami ya je ya tarar da maryam ta zo gidan. Sanin halinta ya sanya ya tsuke fuska, dan ya san ba wai zuwan Allah da annabi ba ne ta yi shi haka. "Mami barka da yamma" banza ta yi masa, daga baya kuma ta ce "Kar ka sake zuwa gaishe ni, muddin ba ka aiwatar da umarnin da na baka ba, bana buƙatar ganinka a sashina ma gaba ɗaya" Maryam ta kalleshi ta ce "Wallaahi ka bayar da maza raihan, me aka yi aka yi ummi? Meye da ita meye abun burgewa a tare da ita? Sannan menene aibun Safiyya, amma na lura kamar ba a hayyacinka ka ke ba, wannan annakiyar baƙin zaka ɗaukko ka kawo mana mugun iri cikin family, wannan yarinyar da mujiya..... "Dalla malama dakata!" Ya yi wa maryam tsawa. "Islamiyyar da ki ka yi ba ta amfane ki da komai ba, da baki san daraja karramawar da Ubangiji ya yi wa ɗan Adam ba, ki tsaya iya matsayinki, idan mami tayi matsayinta ne, ke kuwa ko kusa ko a nesa ba ki da alaƙa da aurena, dan haka ki zuba ido idan zaki iya idan ba zaki iya ba ba zan juri cin zarafin matata ba, idan kin yi mata a baya ba ta da bakin ramawa, ni dai-dai nake da ke" A tare suke shiga karanto "Innalillahi wa Innalillahi raji'un" Mami ta ce "Au raihan har ta zama matarka ma ashe? Yanzu a gabana ka ke gaya wa ƴar uwarka haka saboda yarinyar da ba ka aureta ba ma? A wayance kana nuna mini babu gudu ba ja da baya kenan sai ka aureta" raihan ya yi shiru yana huci. Maryam ta ce "Taɓɗijan, akwai ƙura mami, ita ma munafuka na kirata a waya ta ƙi magana, da yake ba ta da gaskiya, munafuka uwar son abun duniya, sumi-sumi da ita garin yayime-yayime na, na yayimo mana masifa" Cewar ta kira ummi ya fi komai ɗaga masa hankali, ya san dole sai ta yi wa ummi rashin mutunci. Juyawa yayi da sauri ya fice, ya tafi ɗakinsa ya sauya kaya, ya ɗau babur ɗin sa ya fita. Gidansu ummi ya tafi, ya yi sa'a security yana nan, ya ce masa ya yi masa sallama da ummi. Jin ana sallama da ita, ya sanya farida kallon ummi da take ta aiki a falo. Farida ta kwaɓe baki, haka ma kausar, kausar ta ce "Ohh su mujiya an yi abun arziki, kowane mai tsautsayin ne? Na ga dai wancan tsohon ya ce ya fasa" Farida ta ce "Oho dai, ni dai ayi a tattara a bar mini gida" A gaggauce ummi ta gama, ta je ɗakinta ta shirya, ta fito harabar gidan, ya mayar da hankali a kan wayarsa yana dannawa. Ƙamshin turaren wurinsa da take yi, ya sanya shi ɗagowa, ya zuba mata ido. Duk ta yi wani iri, alamu sun bayyana ƙarara a cikin damuwa take. "Sannu da zuwa" ta faɗa a hankali. "Yauwwa, ya ki ke ya gidan?" "Lafiya ƙalau" ta amsa tana murza yatsunta. "Kwana biyu ayyuka sun yi mini yawa sosai ban samu na zo na ganki ba, zuciyata duk a takure" Ita dai ummi ta yi masa gumm, taƙi magana. "Yaya ummi" ya kirata da sunan da ya saba a baya. Ta ɗago ta kalleshi, ya ce "Meyafaru ne? Duk kin canza mini, kamae an canza mini ke, meyafaru ne?" Kamar ya soso mata in da yake yi mata ƙaiƙayi, ta ce "Dan Allah, ka taimaki rayuwata ka fasa auren nan raihan, wani ƙalubalen ne yake tinkaro ni, kamar ba zan iya ɗauka ba, Astagfirullah idan ka aureni kamar sabon babin ƙaddara zan buɗe, da alama kai kaɗai ka ke so na, gidanku ba zasu karɓe ni a matsayin sirika ba" Ya jinjina kai ya ce "Eh, thank God tun da ina son ki ni, na san akwai ƙalubale, maryam na san ta kira ki, haka zalika na san mami kin ji abun da ta ce ranar, amma duk ba matsala ba ne ba. Salma ki canza rayuwarki ki koyi tsayawa a kan ra'ayinki da abun da ki ke so duk tsanani duk ƙalubale. Ke kin san ko mata huɗu na ce ina so za a bani a garin nan, amma na tsaya kai da fata na ce sai ke, ni meyasa zaki watsa mini ƙasa a ido? Ummi ba wasa nake yi ba da nake nanata miki ina son ki, ni kaina fa a cikin ƙalubalen nake, amma na ji zan jure saboda ke. Dan Allah ummi kema ki koyi tsayuwa a kan ra'ayinki ba ra'ayin wani ba, ita maryam ɗin waye ya hanata auren wanda take so, sai ke? Dan Allah ki manta da wani ƙalubale mu tsara rayuwar mu, jarrabawa ba ta ƙarewa a rayuwar mumini. Ai ki na so na ko? Tayi shiru tare da haɗe rai. "Ba kya so na saboda na yi miki yarinta ko? Headmaster ki ke so?" Ta ɗaga kai alamar eh. "Ko gidan tsohon mijinki ki ke son komawa" yadda ya ga ta razana ne abun ya bashi mamaki. Ya kawar da zancen ya ce "Ni a wani bugiren ki ka ajiye ni?" Bai yi tsammanin za ta bashi amsa ba, ya ɗora da cewa "Ƙanin ki ko, wanda ki ka raina da aure?" Zumɓura baki ta yi, tana juya ƙwayar idonta a hankali. "Ummi wai meyake damunki ne? To mu yi hira ta yaya da ƙanwa kamar yadda muka saba" Ta ce "To, ya gida ya office?" murmushin yayi ya ce "Ita ce hirar da ki ka fi so take yi miki daɗi kenan?" Ta jinjina kai alamar eh. "Office aiki ya yi yawa ba hutu" "Ina su Yaya sagir? Kun shirya kuwa?" Raihan ya ce "Mun shirya, amma ba ya kulani" "To kai ka din ga kula shi mana ai kai ne ƙarami" Ya ɗan shafi sajensa ya ce "Gayen nan ɗan wulaƙanci ne fiye da tunaninki, yanzu sai ya yarfa ni, har gara Salim wasu lokutan" "Ai gani za su yi kamar idan suka sakar maka fuska zaka raina su, ka cigaba da jan su a jiki, kar ka nuna musu ƙyama saboda abun da suke yi watarana sai labari, ka gayyace su cikin ayyukan kamfaninku, ko ba ka sakar musu komai ba, ka ja su a jiki sosai". Ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Gaskiya ne, sai ma kin ga hajiya, ta fi bani tausayi wallahi, tana iya yin ta a kansu, amma kullum kamar ana tura su dawa, amma zan yi ƙoƙari in yi abun da ki ka ce in sha Allah" "To Allah ya baka iko" Ya amsa da amin, "Bari na je, zani wani wuri zo mu je ki karɓi saƙon ki" Ya tashi ya yi gaba ta bi bayansa, a jikin babur ɗin sa suka tsaya, ya kalleta ya ce "Alhaji ya ce na zo na fara gini, a wace unguwar ki ke son mu zauna? Sannan wane irin gida ki ke so, flat ko mai bene?" "Kowanne ka yi shikenan, Allah ya yassare" "Salma kenan, haryanzu kina doubting idan ni zan aure ki, kuma ko zan iya riƙe ki, abun da muke shirin yi ba zunubi bane ba, hasali ma yana da asali a addinin musulunci, dan haka ki manta da batun al'ada da surutun mutane kin ji sweetheart" Ta jinjina masa kai, tana wasa da hannun babur ɗin. "Salma" ya kira sunanta a hankali, ta ɗaga ido ta kalle shi. "Ina sonki sosai saboda Allah" tsigar jikinta ta tashi, ta kawar da idonta gefe. "Ko sau ɗaya ki gaya mini wani abu mai daɗi da zai bani ƙwarin gwiwar cigaba da gwagwarmayar neman aurenki, dan nima ina fuskantar ƙalubale" Jiki a sanyaye ta ce "Dan Allah raihan ka yi abun da zaka zo ka cutu daga baya, ka ƙara tunani a kai". "Ni na riga na roƙi Allah a kan lamarin nan, kuma shi so baya bayar da ƙofar tunani, ba abu ne da yake bamu damar yin shawara ba, ki tausaya mini ummi" jikinta yayi sanyi, wani irin tausayin su ya kama ta. "Ban san me zan ce ba, zan yi mana addu'a iya yi na, Allah ya zaɓa mana abun da ya fi alkhairi" Ya ce "Amin ya haiyyu ya ƙaiyyum. Gobe in Allah ya kaimu ki yi mini girki dan Allah, zan biyo ta wurinku na ci" "Me ka ke so" tayi maganar tana murmushi. "Ke nake so" Ta yamutsa fuska ta ce "Ina nufin me zaka ci?" Yayi dariya ya ce "Abinci mana, ko me ki ka dafa zan ci da yardar Allah" yayi maganar yana miƙa mata ledar hannunsa ya ce "Ki koma gida ki huta, duk da ban gama ganinki ba, zamu yi waya, dan Allah kar ki kashe waya kin ji baby" Ta karɓi ledar ta juya tana murmushi. Sabuwar waya dalleliya raihan ya gwangwaje ummi da ita, irin wayar da ba ta taɓa zaton zata riƙe irinta ba, bakinta ya ƙi rufuwa sai da ta kira shi ta yi tayi masa godiya, ya ce shi ba godiya yake so ba, kawai ta ce masa tana son sa shi zai sa ya ji daɗi ya tabbatar da ta ji daɗin kyautar da yayi mata. Aikuwa ta yi gumm, ta kasa magana. Da kuɗinta tayi cefane, washegari da safe ta sheƙa masa girki, bai kira ta a waya ba, sai fita tayi ta ganshi a waje yana jiranta. Suna tafe yana yi mata normal hira, tare da nuna mata yadda za ta yi amfani da wayar da ya saya mata. A mota ya ci abinci, yana ci yana yi mata hira, ta buɗe ruwa ta bashi, ta duba jakarta ta ɗaukko tissue, ta warwro masa ta bashi ya goge hannu. Yayi murmushi ya ce "Ka ga mace ta gari, ta fara aikinta tun yanzu". Ta haɗa kan kwanukan ta ta ce masa "Sai anjima, Allah ya kiyaye" "Amin ya rabb, yakamata mu koma ayi siyayya, mayukan nan kamar sun karɓe ki, na ga kina ta glowing" Da sauri ta ce "Fari na yi?" "A'a kyau ki ka ƙara, ban sani ba ko idona ne" "Kar ka saka mu makara, sai anjima" ta fice daga motar, ya zuba mata ido, har ta shige shagonsu, sannan ya ja motar ya tafi. Duk wata hanya da mami za ta bi, ta rusa maganar auren raihan, abu ya gagara ta kaɗa ta raya, amma raihan ya dage, ya samu goyon baya ɗari. Dr. Ya sanar da su kawu Ilyasu, zai karɓi kuɗin auren ummi, dan haka mutum biyu daga cikin su su zo ranar juma'a. Hatta kayan soye-soye da zai karɓi baƙi, daga waje ya yi order abun sa, dan sai saura ƴan kwanaki, sannan ya gaya wa farida. Farida ko a jikinta, tana ganinsa yana ta shige da ficensa shikaɗai, ya shirya komai. Kafin sallar juma'a, su kawu Ilyasu suka zo gidan, bayan sallar juma'a, su Alhaji Tahir suka zo. Bayan gama tattaunawar da duk yakamata, dr. Ya gabatar da su kawu Ilyasu ga su Alhaji Tahir, tare da gaya musu matakin karatun ummi, tare da tabattar musu da binciken da yayi a kan Raihan, bai samu wata matsala ba. Alhaji Tahir ya sake gabatar da kansa ga su kawu Ilyasu. Sannan ya kalli dr. Ya ce "Ban sani ba ko kun yanke kuɗin aurenta da sadakin?" Dr. Ya ce "A'a, duk abun da Allah ya sa ku ka bayar, zamu karɓa fatanmu ubangiji Allah ya sanya alkhairi" Alhaji Tahir ya jinjina kai, sannan ciro kuɗi a aljihunsa ya ajiye kuɗi dami guda a tsakiyar falon, ya ce "Ga su nan, dubu ɗari biyar ne, mun saka watanni huɗu idan Allah ya sa zamu gani, amma idan kuna ganin mun saka da yawa kuna iya ragewa". Dr. Yayi murmushi ya ce "Bamu nemi ƙari ba ma nemi ragi? Allah ya nuna mana" Kawu Ilyasu ya ce "Amma ranka ya daɗe har naira dubu ɗari biyar, kun kuwa san yarinyar nan bazawara ce? Kuma auren da ba a tsauwwala almubazzaranci ba yafi albarka, bazawara ce ta taɓa aure shekarun baya". Ayshercool 08081012143 FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK. https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends Masu neman free books ɗina, da free pages duk akwai a kan watpad account ɗina. Irinsu Abduljalal Wata kissar sai mata Wuta a masaƙa Cutarwa Ƙanwar maza Gaba da gabanta Aƙidata Ruɗin ƙuruciya Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata. 08081012143. And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link. https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels Ayshercool. PAID ADVERT!. Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi. Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku Oll types of Turaran wuta Sandal Halut Irik Difur Gab Gab Kajiji Habil Nabak Humra Kulakcha Dilke da kalta Kayan Garan jiki Muna turara Kaya Kujerar garan jiki Kannada Madarorin turare masu kamshi Man garan gashi Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921 *TALLA!TALLA!TALLA!* *INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*. *BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU* *MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA* BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI.                           *CUTARWA* 33 *BRIGHT PENS* (FREE BATCH) *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH. Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe. FOLLOW AND SHARE AYSHERCOOL 08081012143 MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH. Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe. 33 Tsit suka yi gaba ɗaya, suna jiran abun da Alhaji Tahir zai ce, dr. tamkar ya nutse saboda takaicin abun da kawu Ilyasu ya yi. Alhaji Tahir ya yi murmushi ya ce "Ɗan uwa, ita bazawara ba mutum ba ce ba da ba za a kyautata mata ba? Shi ya ga yana son ta ai, ni mutum ne mai matuƙar ƙaunar ƴaƴana duk abun da suke so, sai ya saɓa wa addini ne zan ce a'a, amma dan bazawara ce ba shi yake nufin a aureta a wulaƙance ba" Kawu Ilyasu ya ce "Ai dama kar ku ga an rufe ku ne, ku kallemu a matsayin mutanen banza, shiyasa na bayyana komai ko ba gaskiya ba? Kar ku zo a saka yaro yayi ta kashe kuɗi, tun da an ce shi bai taɓa aure ba, kar ya narka dukiya a auren bazawara ya zata budurwa ce, amma dubu ɗari biyar sun yi yawa a kuɗin auren bazawara, kar a cutar da shi" Alhaji Tahir ya gyara zamansa ya kalli kawu Ilyasu ya ce "Ka san da wa ka ke magana kuwa? Bana alfahari da fariya, amma ko yafi haka ya bayar in kawo zan kawo, ba bazawara ba ko da tsohuwa ce kuwa, ka kuwa san wa ƴar ku zata aura ne? Da alama dr. Shikaɗai yayi binciken nan yakamata ya faɗaɗa muku bayanin waye Muhammad Raihan Tahir, zuriyarmu mun gaji yi wa iyali hidima. Ai ni da raihan ya ce mini mahaifiyar ta ƴar maiduguri ce, na yi zaton zaku yanka mana sadaki ne da sisin gwal, dan an ce auren ƴaƴanku sai jarumi" yayi maganar cikin barkwanci. Dr. Da kunya kamar ya nutse ya ce "Ai kamar yadda na gaya maka, mu ƴan jigawa ne gagarawa, mahaifiyarta ce ƴar maiduguri" "Allah sarki, to ace wa sirikata ina nan ina jiran turaren wuta, dan mutanen barno akwai ƙamshi" Kawu Ilyasu ya ce "Kuma akwai ta'addanci da surkulle ba, ai da yake ma babartata ba wanda ya san a in da take yanzu, shekarun baya aka ce mana ta haukace ma" Alhaji Tahir ya yi masa banza ya ce "Yanzu kun amince a kan watanni huɗun?" Dr. Ya ce "Ubangiji Allah ya nuna mana, ya sa zamu gani" Suka kammala, suka tashi suka tafi, suna tafiya dr. Ya dirar wa Iliyasu da bala'i. "Wane irin mutum ne kai mara mutunci, ka ke tozarta yarinya a gaban sirikanta, wannan ai ba daidai bane ba" "A'a yaya yahaya, haka shi ne kankaro mutuncinmu da kimar mu, haka kurum su gano daga baya, su ga mun zalunce su ai gara mu faɗa" Kawu Saminu ya ce "To yanzu da ka faɗa ɗin me ya sauya?" Cikin takaici kawu yahaya ya ce "Auren na ta na fari, ba a gabanku Idiris ya saketa ba, ko kusantarta bai taɓa yi ba ya ce saboda larurar da take fama, ya tozarta ta da bakinsa ya faɗa, da na taho da ummi daga gagarawa na kaita asibiti a kan larurar da take damunta, shi ma da bakinta ta tabattar babu mu'amalar aure a tsakanin ta da idiris ba ta da iddarsa. Idan ka tona wa ummi asiri meye ribar ka? Sigar yadda ka faɗi maganar salon tozarci ne kawai, In da na gode wa Allah mutumin wayayye ne, kuma magana ake ta zunzurutun ilimi, kuma wannan maganar duk mun yi ta da shi, na gaya masa ummi bazawara ce ta taɓa yin aure, ya ce mini in dai ɗan sa yana son ta, shi ba shi da matsala da ita, kuma ɗaukakace kuna raye sai ummi ta yi ta, dan yaron manyan mutane ne, in sha Allah sai yarinyar nan ta huta. Ya ciri dubu hamsin a aljihunsa ya ce "Ga wannan, ku bawa Iya dubu goma, ku ɗau goma-goma sauran ku rabawa dangi an saka ranar ummi" Kawu Saminu ya ce "Amma yaya, a bayar da kuɗi har dubu ɗari biyar amma ka bamu dubu hamsin, a duba lamarin nan mana" "Da nake raye na yi auren ƴa ta nawa ku ka bani gudunmawa? Sai ummi da ba ta da gata sai Allah sai ni, yarinyar da ku ka son tozartawa zan baku kuɗin aurenta, a kuɗina ma na baku dubu hamsin ɗin nan, kuɗin aurenta sisi ba zan taɓa ba, kayan ɗaki zan yi mata na alfarma" Haka suka rabu baran-baran dutse a hannun riga. Suna tafe a hanya kawu Saminu ya ce "Ilyasu meyasa ka yi haka? Kai ina ruwanka?" Ilyasu ya yi tsaki ya ce "A gidanka ko a gidana meyasa ba a samu irin wannan ba, fin ƴaƴanmu kyau ta yi, kaf sirikanmu babu wani mai maiƙo, amma kalli ya kawota birni zai aura mata mai kuɗi, su haɗu su yi ta ci Allah ya isa wallahi" "To yanzu da wa ka ke Allah ya isan?" "Kai ba zaka gane ba, yarinyar nan idan ta samu daula, za ta iya aikata rashin mutunci, ina laifin a samo mata miji dai-dai ita, wai kuɗin aire kawai dubu ɗari biyar, wai ya zata sisin gwal za a yanke musu, a'a sisin uwarsa, sai wani baza babbar riga yake wai shi ga attajiri, shi kuma wannan banzan sai ƙaryar turanci, ƴaƴan mu ba su samu haka ba, sai wannan galmashurar yarinyar" har suka isa gagarawa bakin Ilyasu bai rufu ba yana bala'i. Su Alhaji Tahir ma suna tafe, abokinsa Alhaji Sabo yake cewa "Tahir mutumin nan fa da gaskiyar sa, yaya za ayi ka bari raihan ya auri bazawara kuma ya kashe mata wannan kuɗin haka?" Alhaji Tahir ya ce "Saboda ɗa na kowa ne, kuma dukiya ɗazu ce, muddin na bari yayi abun da mutuncinmu zai zube tun yanzu, to raihan ba zai taɓa kima a idonta ba, ina fatan ko bayan raina, nima Allah ya kawo masu kula da bayana, labarin nagartar yarinyar da na ji, ko tsohuwa ce ta kai a bayar da hakan" Ƙanin Alhaji Tahir ya ce "Gaskiya ne wannan, Allah ya wuce mana gaba, amma daga yadda wannan kawun nata yake zaƙewa kawai na ji ta bani tausayi, Allah ya sanya musu albarka" Suka amsa da Amin. Tsananin ɓacin rai da farinciki, ya sanya dr. Gaya wa ummi abun da kawu Ilyasu ya yi, a ƙa'ida farida yakamata yayi zancen ya ji sanyi, amma ya san sai ta sake yin wani abun da zai tunzura shi, dan haka ya zaunar da ummi yana gaya mata, tare da nuna mata kuɗin, ya tambaye ta wani irin kaya take so. Jiki a sanyaye ta ce "Duk abun da ka yi mini na gode kawu, Allah ya saka da alkhairi ya jiƙan magabata" Ya amsa da "Amin ummana, ki yi ta addu'a kina haƙuri kin ji ko? Nasara ba ta zuwar wa bawa daga kwance babu jarrabawa"ta jinjina masa kai ta ce "In sha Allah" Iya tayi mamakin jin abun da kawu Ilya suka ce mata an kai wa ummi, ta riƙe baki ta ce "Shi kuwa wani asarren ne zai kwashi wannan mummunar yarinyar mara fasali, har da kashe mata maƙudan kuɗi haka?" Kawu Ilyasu ya ce "Oho musu, kuma yaron ma wai bai taɓa aure ba, amma an cuce shi gaskiya" "Ai ba zai wuce yahaya shi yake ƙuƙƙula wannan abubuwan ba, kuma zai zo ya sameni har in da nake" Magana ta cika gagarawa, cewar ummi ta samu wani hamshaƙin attajiri a kano za ta aura, kuɗin aurenta kawai naira dubu ɗari biyar. Aka din ga surutu da yayata zance, har da masu zuwa yi wa iya Allah ya sanya alkhairi. Kasancewar Alhaji Sabo da suka kai wa raihan kuɗi, matarsa ƙawar mami ce sosai da sosai, bayan gama bawa matarsa labarin abun da ya faru, ta ɗauki waya tana yi wa mami mitar duk ga ƴaƴan su amma raihan ya tsallaka waje zai auri bazawara. Mami ba ta gane zancen ba, sai da ta yi mata dalla-dalla, hakan ya ƙara tunzura mami, ta tafi sashin Alhaji kamar za ta kama da wuta. "Alhaji Tahir" ta kira sunansa kai tsaye. "Na'am Bilkisu ya aka yi ne?" "Wallahi raihan ba zai auri bazawara ba, ba zai yiwu ba, wai ka san yarinyar da zai aura bazawara ce?" "Na sani, ba shi ya ce yana so ba?" "Kuma ka kwashi kuɗi har 500k ku ka kai, to wallahi sai dai ayi wadda za ayi, auren nan ba za ayi shi ba, ban lamunci auren fari ya auri wata bazawara ba, lallai yarinyar nan munafuka ce macuciya, har aure ma ta taɓa yi" "A irin wannan ƙadamin, idan ɗa namiji yana son abu ba ya ji ba ya gani, ba ya ganin aibun abun, ki bi a sannu kan yaron nan ya fara bujure miki, na so ace matar Alhaji Sabo ba ta yi gaggawar gaya miki ba, da kaina zan gaya miki, amma tun da ta riga ta gaya miki shikenan " "Ba wani baka yi niyyar gaya mini ba, to idan shi ba shi da hankali, ni ina da shi" Ya girgiza kai ya ce "Hankalin nan dai ban ga alama ba da saura bilki, baki san rayuwa ba haryanzu " "Ni ka ke cewa bani da hankali?" Ya tashi tsaye ya riƙo hannunta da ƙarfi ya ce "Ni da ke duk musulmai ne, da aka haufa a cikin musulunci gaba da baya. Kuma muna koyi da rayuwar annabi sallalahu alaihi Wasallam ne, idan kuwa haka ne, sunna ce mai ƙarfi raihan zai yi koyi da ita. Bilki yaranki Allah ne ya shirya miki su, ba wai dan kina da techniques na yadda ake tarbiyar yaran ba, mutane da yawa na ganin bai dace biye wa yarana da nake yi a kan abun da suke so ba, ina tunatar da ke zamani ya sauya, ka yi wa yaranka tarbiyya dai-dai da zamani sai a zauna lafiya. Wannan baloƙoƙon da ki ke kamar a zamanin da, ba abun da zai haifar miki, illa bijirewar yaron nan, shawara nake baki kar ki matsa da yawa, dan yana wani stage ne da ba ya ji ba ya gani, cikar muradi kawai yake fata, amma idan kin ƙi ji gaki nan ga shi" kamar ta shaƙe Alhaji Tahir haka take ji, tare da jinjina tsantsan rashin hankali da wauta irin na raihan, da ma ba ta ce za ta yi masa aure ba, ta bar shi a haka, kawai daga cewa za ta yi masa aure, ya jajubo wannan ina da munin wai ita zai aura. Raihan ya fito daga Masallaci sallar la'asar, Ummi ta kira wayarsa, ya samu wuri ya tsaya tare da ɗagawa "Hello my love" Cikin sassanyar muryarta da yake cewa iyayi ta ce "Barka da yamma" "Yauwwa barka, kin wuni lafiya?" "Lafiya ƙalau Alhamdilillah, ya su mami?" "Duk suna lafiya, ina noor ɗina?" "Tana tahfiz" ta faɗa a hankali. Ya ce "Kirana ki ka yi ki ji muryata love?" Ta ɗan yi murmushi ta ce "Muryartaka ba gata nan a what's app ɗina ba? Su Alhaji sun zo ɗazu" Yayi murmushi ya ce "Shiyasa na ji bakin ki yaƙi rufuwa, zaki yi wuf da ɗan kyakykyawa yaron da ki ka raina" Ta ce "Hmm amma kuɗin da su Alhaji suka kawo, har da kayan lefe ko?" "Yaushe muka yi haka da ke?" "Ba muyi ba tambayarka kawai na yi, kuɗin da yawa ka manta na taɓa aure ne?" "Ke ki ka san kin taɓa auren ai, ni ban sani ba, kuma ke ina ruwanki da abun da zan yi, ke da ba kya so na, ina ruwanki idan zan yi lefen koma ba zan yi ba" "Yi haƙuri" ta faɗa a sanyaye. Ya gyara tsayuwarsa ya ce "Ummi ke malama ce, annabi Sallallahu alaihi Wasallam, mutum ne mai hidimtawa iyalinsa, kuma rayuwarsa ce abun koyi a garemu, haka zalika mahaifina mutum ne mai hidimtawa iyalinsa sosai haka na tashi na ga yana yi, kuma babana mudubina ne, bana cikin maza masu nakasashiyar zuciya duk abun da na kashewa wadda zan aura ribata ce, kin san tsare hakkin iyali yana ƙarawa namiji kima da kwarjini a wurin iyalinsa. To balle ni da nake yaro kuma ba a so na, dole sai na yi aiki tuƙuru tukuna, dan saya wa kaina kima a wurin matata" Ummi ta numfasa ta ce "In dai kai Allah ya ƙaddara ka zama mijina, ba ka buƙatar wahalar da kanka, zan yi maka biyayya iya yi na, ban yi wayo sosai da mahaifiyata ba, amma mama mace mai matuƙar biyayya ga babana" Cikin yanayi na nishaɗi ya ce "Allah ya sakawa iyayenmu da mafificin alkhairi ummi, ya nuna mana auren nan lafiya" Ummi ta yi shiru ta kasa amsawa. Hira suka yi sosai, sannan suka yi sallama. Raihan yana zaune a ɗakinsa yana danna system yana shan lemon kwali, Salim ya yi sallama a ɗakin. Raihan ya amsa yana mamakin ganin Yaya salim a ɗakin nasa, dan sai ya shafe shekara bai shiga ɗakin sa ba. Kamar wanda yayi baƙo raihan ya tashi yana faɗin "Sannu da zuwa yaya" Salim ya jinjina masa kai ya zauna, ya kalleshi ya ce "Yanzu muke magana da hajiya, ashe yau an yi maka engagement? Ubangiji Allah ya sanya alkhairi babban mutum, girma zai ƙara hawa kanka, Allah ya sanya alkhairi" Duk in da ɗan uwa yake ɗan uwa ne, maganganun ummi suka din ga dawo masa, ya dubi Salim ya ce "Na gode sosai da sosai yaya, Allah ya saka da alkhairi, Allah ya sa ayi naka kafin ayi nawa" Salim yayi murmushi ya ce "Sai ka ce wasan yara? Allah ya baku zaman lafiya, ace ina gaisheta" yayi maganar yana shafa sumar raihan. Salim shi ne babba, aƙalla ya kai shekaru talatin da huɗu, ya fi Sagir sauƙin kai, ba shi da magana, sannan mutum ne mai son kaɗaici, amma akwai abokan banza, dan su suka koya masa shaye-shaye. Raihan ya ce "Za ta ji, amma ita tana yawan cewa a gaishe ku, da kai da Yaya sagir" Ya ɗan kalli raihan ya ce "Ta sanni ne?" "Eh, ummi ce ai ƙawar maryam, ta sanku, sannan ina yi mata zancenku" Ya ce "Ohh that dark lady, mai brwon eyes ko? Wow na yi maka murna she's decent and good lady" "Amm yaya dan Allah da gaske ummi mummuna ce? Mami tana ta complain a kan hakan" Salim ya ce "Ita wannan mamin naka, ra'ayi idan ba nata ba, kowa bai iya ba, just go ahead, ita kuma mamin ka yi ta sakata a addu'a, Allah ya kwantar maka da hankalinta shikenan kawai" Raihan ya riƙe hannun Salim ya ce "Na gode sosai Babban yaya, Ubangiji Allah ya baka kujerar MD Tahir and Son's" Salim ya ce "You are not serious, kai dai Allah ya tayaka riƙo, ya sanya maka albarka, take care" ya fice daga ɗakin. Raihan yayi shiru, babu shaƙuwa sosai a tsakaninsu, saboda shi raihan a Bauchi ya ƙarasa girma, gidan yayar Alhajinsu Hajiya Aisha, mijinta da ita da Alhaji duk cousin's ne, shi kuma su Salim suna nan kano, kuma mami ba ta da aiki sai gaya masa yayi a hankali da Hajiya da yaranta ba sa ƙaunar su, kuma kar su Sagir su koya masa shaye-shaye. Sai dai shi bai ga alamar hakan ba, hasali ma ba sa wani shiga shirgin sa, dan ba sa'aninsa bane ba, har gara Sagir ma suna faɗa da raihan sosai. Hajiya kuwa kamar ɗan da ta haifa haka ta ɗauki raihan da ma duk ƴaƴan mami, amma matan duk mami ta hure musu kunne. Farida ko a jikinta, jin an kawo kuɗin auren Ummi, dan kawai jikinta bai bata ummi wani mutumin kirki za ta aura ba, dan da an kawo abun arziki da jiki na rawa dr. Zai gaya mata, sai dai yayi mata shiru bai gaya mata me aka kawo ba, kuma wa za ta aura ba. Noor ta kasa nutsuwa saboda murna, sai tsara yadda bikin zai kasance take yi, har da cewa sai dr. Ya ɗinka mata sababbin kaya guda hamsin har da irin na amarya da ango. Saboda tsokana ta je ta samu kausar tana bata labarin yadda raihan yake, ta koreta amma ta ƙi tafiya ta cigaba da cewa "Kin ganshi kuwa? Wallahi duk saurayinki babu mai kyan sa, fari ne fa sosai da sosai, wallahi motarsa ta fi biyar, masu kyau ɗan bala'i, idan yana magana yana ɗage girarsa guda ɗaya, me kyau da shi" kasancewar hankalin kausar ba a kan noor yake ba, ya sanya sam ba ta fahimci me noor ɗin ke faɗa mata ba. Mami ba ta nemi raihan ba, sai yau da safe ya je karyawa, tayi masa shiru, ya gaisheta ta amsa masa, ya kammala cin abinci, ya tashi zai fita, ta janyo hannunsa da ƙarfi ta tankaɗa shi har ɗakinta ta mayar da mukulli ta rufe, ta dawo ta ɗauke shi da mari har kashi biyu. Sai dai ya tsaya yana kallon mami da mamaki, ba tare da kuma ya yi yinƙurin kare marin ba. Ta ɗora da ɗura masa ashar, amma ya sunkuyar da kansa ƙasa yana kallon tiles. "Ashe ba ka da hankali raihan, ba ka da mutunci ba ka san abun da yake maka ciwo ba, ashe yarinyar nan bazawara ce, ka je zaka auri bazawara sauran wani, da ƙuruciyarka da komai, ashe baka san me yake yi maka ciwo ba? To ai dama ni na ce zan yi maka aure ko? To na janye na fasa, ba zaka yi auren yanzun ba, sai ranar da ka fuskanci kai mutum ne da daraja da girma. Dan haka umarni nake baka ba shawara ba, ka je ka janye maganar auren nan. Saboda hauka tana bazawara ga muni da rashin gata, amma ka ɗauki kuɗin aure har dubu ɗari biyar, ka bayar a kai, to baka isa ba wallahi, idan har ni na haifeka ka ka je ka gaya wa mahaifinka ka fasa auren nan, ba zaka aureta ba dan kai kaɗai ne kawai zaka gaya masa haka ya yarda, idan ba haka ba zaka fuskanci abun da baka taɓa tununi daga gareni ba, na gaya maka. Ka wuce ka je ka same shi ka ce masa ka fasa yanzu ba anjima ba. Matar da na zaɓa maka ita zaka aura, duk matan garin nan masu kyau da aji, ba ka ga kowa ba sai wannan cilakowar?" Tuni fuskar raihan ta yi jawur, jijiyoyin kansa suka mimmiƙe, saboda tashin hankali da ɓacin rai, ya buɗe ƙofar ya fice, yana gazgata maganar ummi da ta taɓa ce masa su mata mutane ne masu masifar son kansu, bai yi mamakin hakan daga mami ba, duba da yanayin halinta kuma gashi jiya ya ga Anty rakiya ta zo gidan, ya san ita zata sake ziga mami, amma ita bazawara ba mutum ba ce?. Zuciyar sa na wani irin tafasa ya tafi sashin Alhaji, Alhaji tashin sa kenan, yana ta shiri za shi Abuja, ya ga raihan, bai yi wa raihan magana ba, Raihan ya ce "Na fasa auren ummi, na janye, ka karɓo kuɗin auren, amma idan aka karɓo kuɗin auren nan an karɓo kenan aure sai dai in ga ana yi, babu ƴar da za a sake kaiwa kuɗin aure da sunan zan aureta" yana gama maganar ya juya ya fice. Alhaji bai yi niyyar dakatar da shi ba, dan ko magana bai yi masa ba, ko raihan bai yi masa bayani ba, ya san bilki ce ta kunno shi, dan raihan akwai ladabi, idan ya je bango kuma akwai taurin kai, dan haka Alhaji ya ƙyale shi, da nufin idan ya huce sai su yi maganar. Ummi na wurin aiki tana ta shigar da sabbin price a computer, ta ga raihan ya shigo, fuskar sa babu walwala. Bai ce mata uffan ba, ya zagaya ya zauna a kujerar kusa da ita. "Baka gaya mini zaka zo ba, ai da na dafo maka wani abun, baka da lafiya ne?" Ya girgiza mata kai ya ce "Bauchi zan tafi daga nan, na zo mu yi sallama ne, babu lallai na dawo nan kusa" Da sauri ummi ta ce "Saboda me?" Ya kalleta wani abu mai ɗaci na kaiwa na komowa a zuciyarsa, ga wani irin tausayin ummi da yake ji, idan ya fasa aurenta bai yi mata adalci ba sam. "Ka gaya mini mana, menene meyafaru gaba ɗaya ka yi wani iri, me aka yi maka ne?" Tayi maganar cikin rauni sosai, saboda ba ta fiye ganinsa a irin wannan yanayin ba. Kasa magana yayi, ya tashi ba tare da ya ce mata komai ba zai tafi, karo na farko ta riƙo hannunsa a nata ta ce "Ka zauna ka gaya mini menene, ka ɗaga mini hankali ka gaya mini menene?" Ya zauna a hankali ya ce "Ummi, ban san me yake shirin faruwa ba, daga yanzu zuwa ko yaushe abu mai daɗi ko akasin haka ka iya faruwa, dan Allah ko me ye ya faru, ni dai ki saka a ranki ina son ki sosai da sosai ummi, kuma ba zan daina sonki ba, ki tsananta yi mana addu'a, ko da ke ba kya so na, ni ina sonki ummi" "Raihan, dan Allah idan a kaina ne, kar ka samu matsala da ƴan gidanku, ahali sun fi komai daɗi, ni daga baya ka sanni, zaka iya canza ni, su kuwa fa, in dai nice babu komai zan fahimceka amma ahalinka na da muhimmanci a rayuwar ka, ni tsangwama da kyara na saba da su" "Amma ba zaki dauwwama a cikin su ba, akwai hatsari mai girman gaske a rabani da ke, ko kin auri wani ba ni ba, ba zan iya rabuwa da ke ba, zan tafi bauci wataƙila zan shafe tsayin lokaci, amma zamu din ga waya in sha Allah, take care am going to miss you dear" yayi maganar yana shafar gefen fuskarta. Ya tashi ya fice. Haka kurum gabanta ya tsananta faɗuwa, a duk lokacin da ya ce ko tayi aure ba zai iya rabuwa da ita ba, sai ita ma ta din ga jin irin haka a zuciyarta, kamar itama ba zata iya rabuwa da shi ɗin ba. Jikinta duk yayi sanyi, har ta kammala aiki ta tashi, bayan ta koma gida tana ta neman layukansa, amma shiru ba ta samunsa a wayar. Sai washegari ya kirata da wata lambar daban, ya ce mata yana bauchi cikin ƙoshin lafiya, da wannan lambar za ta din ga kiransa. Jin muryarsa wasai ya sanya ta cewa "To amma yanzu zaka dawo ko?" "Ko zan dawo ba yanzu ba, kewarki ce kawai take damuna" "Dan Allah ka dawo ka ji babban mutum, manya ba sa haka, idan laifi muka yi mutanen kano, tuba muke yi kar a hora mu da yi mana yaji, ka san menene zan dafa maka abinci mai daɗin gaske, na san abun da ya saka bar garin zuwa yanzu ka huce ai ko? Zan yi maka girki" Raihan yayi dariya ya ce "Matar raihan, kirarin nan kawai ya ƙara sanyaya mini zuciya, kar ki saka na ɗaukko mota na taho mana. Ke dai ki yi ta addu'a kamar yadda na ce miki kin ji ko?" "To shikenan, amma dai ka yi tunani a kan lamarin nan". Can gida kuwa Alhaji Tahir ya saka mami a gaba da masifa, tare da cewa duk in da ɗan sa yake sai ta fita ta nemo shi, dan ba a samun sa a waya, baya gida kuma baya office. Abu kamar wasa, hankalin mami ma ya tashi, ba ta yi zaton raihan zai yi haka ba. kwana kusan biyar, babu raihan babu dalilinsa. Dr. Ya samu ummi ya ce mata ta shirya kayanta, washegari za su yi tafiya ta kwanaki uku, ta sanar a wurin aikinta. Ummi tayi ta mamakin, ina za su je haka afujajan babu cikekken shiri babu komai. Ba ta matsa masa da tambaya ba, ta shirya kayan kamar yadda ya umarce ta. Mami kuwa, Anty rakiya ta bata shawarar ta je har gida ta ci mutuncin ummi, kuma ta tursasata ta gaya mata in da raihan yake, dan ba zata kasa sani ba. Alhaji Tahir ya shigo a fusace ya ce "Kin yi naki role ɗin, barkana tun da na san in da ɗa na yake, amma bari na gaya miki wani abu, idan har kin cigaba da dagewa ba za ayi auren nan ba, to ki tabattar da zan kawo yarinyar nan matsayin matata ta uku, dan ba zaki zubar mini da mutunci a idon duniya ba" Gabanta ne yayi wata irin mummunar faɗuwa, wayarta ta fara ringing, cikin rawar jiki ta ɗaga. Saboda kura ta san gidan mai babban sanda bijirewa ɗaga wayar ka iya jefata cikin matsala. "Bilki, ashe baki da mutunci baki da hankali? Ashe wayewar ta ki ta ƙarya ce, saboda wulaƙanci da rashin mutunci ke da ba a aure, da zamu bari Tahir ya aureki ne? Ke kin san auren zumunta muke yi, da matarsa ƴar uwassa tana son shi yana son ta, ya auro ki, mu a cikinmu waye ya hanakk zaman lafiya? Saboda rashin kunya yaro ya kawo mace yana so ki ce a'a, saboda wulaƙanci idan shima ya faɗa shaye-shayen ki ce me? Bar ganin ke ki ka haifi raihan, wallahi ba zamu lamunci son zuciya ba, ko tsohuwa ya ce yana so, zamu bashi goyon baya, ba dan Allah ya sa ya taho nan bauchin wurin mu ba, wani wurin yayi ba, to ahir ɗinki wallahi idan ba haka ba da ni ki ke zancen, kuma bauchi ya zo kenan, ku nemi wanda zai riƙe muku kasuwancin naku, tun da kin hana shi auren". Cikin tsuma Mami ta ce "Dan Allah Hajiya Aisha ki yi haƙuri, in sha Allah hakan ba zata sake faruwa ba" "Oho miki ta cigaba da faruwar ma, kin ce ya fasa aure, ai ke uwa ce yayi biyayya ya janye, amma ya ce a gaya miki, shi da aure har abada, sai kuma ki shirya idan ya kawo miki ɗan gaba da fatiha ki karɓa ki riƙe tun da ba ki da hankali" ta kaste wayar. What's app only please, masu so daga farko su yi joining channel ɗin nan. 08081012143 FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK. https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends Masu neman free books ɗina, da free pages duk akwai a kan watpad account ɗina. Irinsu Abduljalal Wata kissar sai mata Wuta a masaƙa Cutarwa Ƙanwar maza Gaba da gabanta Aƙidata Ruɗin ƙuruciya Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata. 08081012143. And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link. https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels Ayshercool. PAID ADVERT!. Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi. Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku Oll types of Turaran wuta Sandal Halut Irik Difur Gab Gab Kajiji Habil Nabak Humra Kulakcha Dilke da kalta Kayan Garan jiki Muna turara Kaya Kujerar garan jiki Kannada Madarorin turare masu kamshi Man garan gashi Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921 *TALLA!TALLA!TALLA!* *INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*. *BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU* *MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA* BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI.   *CUTARWA* *BRIGHT PENS* (FREE BATCH) *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH. Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe. FOLLOW AND SHARE AYSHERCOOL 08081012143 MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH. Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe. Wani irin gumi ne ya dinga gangaro wa mami, duk da yadda sanyin AC ke ratsa ko ina a falon. Raihan ƙararta ya je ya kai wa wannan masifaffiyar yar uban nasa kenan? tuno maganar Alhaji Tahir, da tuni ya bar falon da yayi ya sanya ta jin wata muguwar gudawa, saboda yadda cikinta ya murɗa mata. Afujajan ta fita ta nufi sashinsa, har da tuntuɓe. "Wallahi Baka isa ka gaya mini maganar da zata hana ni sukuni ka fice ka bar ni ba, kai yanzu saboda abun kunya goɗai-goɗai da kai sai ka auri yarinyar da ɗan ka ya ce yana so?" Alhaji Tahir ya ce "In dai haka shi ne mafita a gareni me zai hana? Ku mata ku kuka san wani abun kunya, mu maza abu in dai mu yayi mana ba ruwanmu da abun kunya, kuma ina sake tunatar da ke, bana magana biyu, wallahi da gaske nake, sai dai idan na aureta wanda ba zai iya zama da ni ba ya ƙara gaba, shawara ta rage ga mai shiga shiga rijiya" ya ƙarasa maganar tare da ɗaukar wayarsa ya fita. Kamar wadda ta zare, haka ta sake kwasa har da gudu, ta tafi ta kira Anty rakiya a waya. Rakiya na ɗagawa mami ta fashe da kuka, "Anty rakiya na shiga uku na lalace" "Wane irin kin shiga uku, meyafaru ba yanzu muka gama waya lafiya ba?" "Ashe raihan bauchi ya tafi, ya je ya haɗo ni da wannan masifaffiyar matar yayar babansa, kin ga yadda ta ci mini mutunci kuwa? shi kuma Alhaji wai idan ban bari an yi auren ba, wai shi zai aureta ya kawota gidan nan a matsayin matarsa" Anty Rakiya ta ce "Kai haba, dalla rabu da shi, barazana ce kar ki fasa wallahi, kar ki yadda a kawo miki bazawara a matsayin sirika" "Anty Rakiya waye ya gaya miki Alhaji Tahir yana barazana ne? Magana ɗaya yake yi ko ta yi maka daɗi, ko kuma akasin haka, har rantsuwa yayi mini, na shiga uku, kuma wai raihan ya ajiye aikin nan ina na kama?" Anty Rakiya ta ce "Taɓ, lallai raihan ba shi da hankali, to wallahi idan ki ka zuba masa ido, haka zai aurota ya fi ƙarfinki, tun da har ya san yayi miki yaji, ki kira shi ki ce lallai ya dawo dan ubansa" Mami cikin takaici ta ce "Lamarin fa ya wuce yadda ki ke tunani, kin san taurin kan raihan kuwa? To cewa tayi wai ba zai dawo ba, ya bar aikin kenan, ya kuma ce idan aka karɓo kuɗin auren nan, shi da aure har abada, ga babansa ya ce idan aka fasa zai aureta, na shiga uku ina na kama? Kin ga suna nema su haukata ni, raihan kafiya da taurin kai kamar ubansa, idan ya ƙi aure ya lalace yaya zan yi?" Anty Rakiya ta ce "Ai kawai ki dage ki samu ya dawo tukuna, ki kira shi a waya" "Wayoyin da duk ya kashe su, ina zan yi?" "To ki koma ki samu babansa ki lallaɓa shi, ya dawo da shi kar a rasa wannan damar kuma ta kasuwancin nan " Mami tayi ajiyar zuciya ta ce "Shikenan, zan kira ki mayi magana anjima" ta katse wayar ta ajiye tana wani irin haki, ita ba mai asma ba. *** Dr. suna tafe a mota da shi da ummi, ya ce "Mamana zaki ga zamu yi doguwar tafiya, ba sayar da ke zan yi ba abun alkhairi ne" Ummi ta yi murmushi ta ce "Idan sayar da ni ɗin ma ka yi ai na saidu kawu" Yayi murmushi ya ce "Idan na sayar da uwata ina na kama? Yakamata ace kin yi azumin farinciki kan mu yi tafiyar nan" "To Ubangiji ya tabattar mana da dukkanin alkhairin da yake cikinta" Ya amsa mata da "amin" Ummi ta gaji da zaman motar nan sosai da sosai, sai dai tun da taga symbols da sunan borno, jikinta ya fara sanyi, har ta rasa tunanin me ma za ta yi ne?. Kawu kuma ya mayar da kai sosai a kan tuƙinsa, sai lokacin salla ya tsaya suka yi salla, ya saya mata abinci. Ta tuno lokacin da ya ɗaukkota daga gagarwa a wahale, ba sutura ga ciwo, ko ba komai ta samu alkhairi a dalilin riƙonta da yayi A ranta ta ce "Allah sarki kawuna, baba ya tafi amma ya bar mini Allah, Allah kuma ya bani kai, Allah ya kula da kai da zuriyarka". Duk da ba ga saba baccin mota ba, gajiya ta sanya wani irin nannauyan bacci yin awon gaba da ita. "Mamana tashi mun zo" a hankali ummi ta motsa tare da buɗe idonta, har suka fito daga cikin motar, ba ta iya cewa komai ba, sai bin wurin da kallo. Ƙofar wani gida suka tsaya, dr. Ya ciro wayarsa ya ɗan daddana ya kara a kunnensa ya ce "Gamu mun zo" Wani matashin saurayi ya leƙo ya durƙusa ya gaida dr. Sannan ya ce su shiga. Suka shiga cikin gidan, ummi ta zubawa dattijon da suka tarar a tsakar ido, yana zaune a kan buzu, da Alƙur'ani bugun warshi a gabansa. Dattijon ya miƙe tsaye yana yi musu maraba, tare da bin ummi da kallo, ba ta ɗaga niƙabin fuskarta ba, sai dai ta shagala da kallon sa ta san shi, amma a ina? Ta kasa tunawa. Yayi musu jagora har wani matsakaicin falo, yana ta yi musu sannu da zuwa. Suka gaisa da dr. Ummi ta gaishe shi, ya amsa mata cikin kulawa, sai dai bai tambayi wacece ba, kuma ya kasa daina kallonta. Dr. Ya ce "Ina mutuniyar kuwa?" "Wai sun fita barka a nan bayan layi, jikin ne ma ya ɗan motsa, amma Alhamdilillah mun gode Allah, bari azo a ɗora muku girki, ai bamu san zaku zo ba" Dr. Ya ce "Ai alƙawarin da na ɗauka na zo cikawa, zuwan babu cikekken shiri, bari mu yi salla kafin su dawo". Ya ja dr. Suka fita, bayan nuna wa ummi banɗaki, tayi alwala ta yi salla, ta nemi wuri ta kashingiɗa tana hutawa, saboda gajiyar da tayi. Ummi ta ɗan jima a zaune, sannan dr. Ya shigo, shigowar ta sa yayi daidai da shigowar matashin da ya yi musu iso, ya kawo musu nono mai sanyin gaske, da nama fal malam ya ce a kawo musu da ruwa, dan azo a ɗora sanwa. Ummi dai ta kasa sakewa ta ci, dr. Kuma sai hira suke yi da malam. Dr. Ya ce "Malam ba ka ganni da baƙuwa ba ne? Baka tambayeni wacece ba" Malam yayi murmushi ya ce "Tun da baka gaya mini ba, bai kamata na yi shishshigi ba ai, na ma zata ko mai ɗakinka ce, shiyasa ban yi magana ba, kuma na ganta sanye da niƙabi" Dr. Yayi murmushi ya ce "Aishikenan, mama malam ne fa, baki gane shi ba?" Ummi ta ce "Na sanshi amma na manta a ina?" "To ki cire niƙabin ko zai gane ki" Ummi ta jinjina kai tana ƙoƙarin cirewa, aka  yi sallama. Bayan matar farko ta biyun ma tayi, a nan take ummi ta daskare, ƙirjinta ya buga da ƙarfin gaske, ta ji tamkar numfashin ta zai bar ƙirjinta, wata irin tsuma ta ji ta fara yi, amma ta gaza motsawa. Malam ya ce "Daga zuwa barka kun yi zamanku, gashi kun yi baƙi tafiyayyu daga kano" Ta ce "Baban ummi ne?" Malam ya ce "Eh shi ne, tun da shikaɗai ki ka sani a kanon ba" Shigowa suka yi tare, tana riƙe da mayafinta a hannu, hannunta kamar amarya an yi mata lalle yayi jawur. Ba ta kalli baban ummi ba, kai tsaye ummi ta zubawa ido, yayin da ummin ma ta zuba mata ido, tana jin yadda ƙirjinta ke lugude. Gaba ɗaya suka zuba musu ido, kai tsaye ta nufi ummi ta zauna a gabanta, tana cigaba da kallon ummi ta niƙabinta. Ta miƙa hannu a hankali ta ɗaga niƙabin ummin, tayi tozali da fuskar ummin da a duniya bata ganin kyan komai, kamar yadda take ganin kyawun wannan fuskar. A gigice ummi ta yi mata wata irin runguma ta fashe da matsanancin kuka, saroro mariya tayi, ta kasa taɓa ummi sai hawaye da ya fara zuba daga idonta. Mama ta miƙa hannu tana faɗin "Ki yi mata a hankali ba ta da cikakkiyar lafiya" Mariya ta buge hannun maman da ƙarfi, ta ruƙunƙume ummi, tana wata irin ajiyar zuciya kamar za ta fita daga hayyacinta. Ta miƙa hannu ta warware mayafinta, ta lulluɓe da ummi da shi, ta ɗaukko mafici kuma tana yi mata fifita tana kuka. Sai a yanzu suka gane wacece, malam ya sunkuyar da kai yana hawayen tausayin ƴar sa. Ya zura hannu a aljihunsa ya ɗaukko wayarsa, ya kira Maryam a waya da kuma yaya ɗan lami. "Ummina, kina cin abinci kuwa? Naga duk kin rame, iya tana yi miki wanka? Ko dai zazzaɓi ne a jikinki?" Tayi maganar tana ɗora hannu a goshin ummi. Wasu irin jijiyoyi suka ɗaɗɗaga a goshin ummi, wani irin riƙo take yi wa mariya, tana jin kamar an sanyata a wata ni'ima. Sun fi mintuna talatin a haka, sun ƙi sakin juna, mariya sai kakkare ummi take yi, kar wani ya taɓa mata ita. Dr. Yayi gyaran murya ya ce "Yau na cika alƙawari ko?" Ta jinjina masa kai, tana kuka ta ce "Wallahi ba zan taɓa yafe wa iya ba, Allah ya saka mini zaluncin da ta yi mini, ta ƙwace mini ummi bayan ba son ta take yi ba, ta ce ni na kashe mata ɗa, kalli yadda duk ummi ta rame, haka zan kwanta in yi ta mafarkin ummi tana kuka, tana cewa na zo na tafi da ita" Ta ɗago ummi tana goge mata hawaye ta ce "Ki daina kuka kin ji ummana, ba zan sake bari a mayar da ke wurin iya ba, na san ba ta sonki ba ta ƙaunarki, ban san me ki ka yi mata ba, wallahi ba zan yafe mata ba, yaya ɗan lami yaƙi dagewa ya karɓo mini ƴa ta, kullum sai na yi kuka saboda ummi, yaya maryam ma ta hantare rannan wai kamar nikaɗai ce me ƴa, ki daina kuka kin ji ummina, da kaina zan din ga yi miki wanka, ina baki abinci, katifata zata ishemu mu din ga kwana tare, ba zan sake bari a kai ki wurin iya ba kin ji mamana" Ummi ta ƙura mata ido, yadda mama ke wannan surutan daga wannan zuwa wancan tare da kasa gane ummi ta girma yanzu, ya tabbatar wa da ummi cewar mariya bata da lafiyr ƙwaƙwalwa. Ta miƙa hannu ta ɗaukko ledar pure water, ta buɗeta ta saka wa ummi a baki tana faɗin "Na san ƙishirwa ki ke ji ummi, sha ruwa kin ji" Babu wanda tausayin ummi da mariya bai kama a wurin ba, uwa kenan duk da ciwon ya motsa ba ta hayyacinta, amma hakan bai hanata gane ƴar ta ba, duk da shekarun da suka shafe basu haɗu ba. Dr. Yayi gyaran murya ya ce "Alhamdilillah ala kulli halin, na gode Allah da ya sanya ummi da mahaifiyar ta suka haɗu, ba tare da ta Allah ta kasance ba. Ummi na yi miki laifi, kuma na yi muku duk da ina godiya da fahimta ta da ku ka yi. Ummi ban ƙi sada ki da mahaifiyarki dan baƙanta miki ba, a lokacin da na ganota, tana cikin halin larura sosai, ba komai take ganewa ba, na yi fargabar haɗuwarku ba za ta yi daɗi ba, idan ku ka haɗu ta kasa gane ki, abu na gaba kuma ina tsoron halin da ki ke ciki, ya sanya ki ƙi zama ki dawo wurinta, alhalin kina tsaka da karatu, dan duk wanda yake ruwa, ko takobi aka miƙa masa zai kama, dan haka a matsin nan da ki ke, duk da kasancewar ki mai biyayya, zaki iya bujirewa ki zaɓi dawo wa gaban mahaifiyarki, ba tare da kin yi acheiving wani abu ba. Wanda a lokacin babban burina da fatana, ki samu nagartaccen ilimi, da zaki iya tsayawa da ƙafafuwanki, ina fatan zaki yafe mini daga ke har mahaifiyar ki" yayi maganar a sanyaye. "Ai dama kai na yafe maka, baka cuceni ba, amma iya iya iya, ban san me na yi mata ba, amma za ta maimaita a gaban Allah, amma wallahi ba zan yafe ba, na ji labarin azabtar mini da ummi ta yi, amma yaya ɗan lami ka ƙi dagewa ka karɓo mini ummina" Dr. Ya ce "Haba maman ummi, ki yi haƙuri abun da ya wuce ai ya riga ya wuce, ki yi haƙuri dan Allah" yayi maganar yana haɗa hannayensa. "Ai kai na ce na yafe maka, tun da ka kawo mini ummi, kuma kana saya mini magani da abun da nake so, har yaya ɗan lami na yafe muku, amma ban da iya da wanda suka ci zalin ummina, bani da abun da zan gani na tuna da bashir sai ummi, amma ta ƙwace mini ita dan ta wulaƙanta ni" Dr. Ya ce "Ba gani a gabanki kina kallona ba?" "Yaya Yahaya ne fa ba Bashir ba, na gane ka yau" yayi murmushi ya fahimci memoryn na ta yana yi yana seizing ne. Sun sha mamakin yadda ummi ta girma, ummi kuma kallon mamanta take yi, kamar ba ita ta haifeta ba, haryanzu shar da ita, gashi gaba ɗaya ba sa kama, sai kaɗan, kamar ya da ƙanwa ba uwa da ƴa ba. Dangin mama kamar su cinye ummi, a yamamcin nan suka din ga zaryar ganin ummi, sai dai ta ɓoye ummi a bayanta, kowa ya zo sai dai ya hango ummi daga nesa wai kar a ɗauketa a mayar da ita wurin Iya. Ummi ta ga ƙauna da soyayya, mariya ta din ga zuba mata hira, wata tana ganewa, wata ba ta ganewa, ummi space take son samu, ta kira raihan a waya ta sanar masa. *** Raihan yana zaune a falon hajiya Aisha yana kaɗa ƙafa, yana danna wayarsa cikin damuwa, ya kasa samun ummi a waya. Falon ta shigo cikin takunta na ƙasaita, ta samu wuri ta zauna ta kalli raihan ta ce "Kai, babanka ya kasa samunka a waya, yana ta ƴar murya a lallaɓoka ka koma fa" Raihan ya gyara zamansa ya ce "Wallahi ko dan saboda Alhaji ban so na taho ba, mami ce taƙi tsayawa ta fuskance ni, na rasa yadda zan yi da ita wallahi, taƙi fahimta ta kuma anty rakiya ce take zigata" "Kai dalla can, na kirata mun yi magana da ita, ba abun da za ta sake yi a kan maganar, ita ba a auren aka aureta? Mu ba auren zumunci ake a danginmu ba, babanka shi ya fara karya mana wannan ta'adar, ya aurota daga nan kowa ya samu ƴancin yin hakan, sai yanzu ita kuma ta ce ba za a auro wata ba?" Raihan ya ce "Abun kuma har da gori?" "Eh an yi mata gorin, da ai ba ayi ba, siyama na nemanka wai ka je ta girka maka menene oho mata" Yayi murmushi ya ce "Nifa yanzu abincin kowa ya daina yi mini daɗi sai na matata" "Ka ga fitsararre, amma dai da namun ka ke ci ko? Wai wani matarka ka ga idan ba ka rage rawar kan nan ba a kak yarinyar nan, haka zaku yi ta faɗa da babarka" Raihan ya miƙe ya ce "Ni kaina na sani, ina ƙoƙarin ragewa wallahi, amma hannun ummi akwai maggi ta iya girki sosai" Hajiya Aisha kawai ta yi murmushi ta girgiza kai, tana sake jinjina wautar mami, a irin wannan stage ɗin, ba a saka pressure wurin cewa lallai sai an tanƙwara namiji, sai nasiha da rarrashi idan ma so take ta soke auren. Da daddare mariya da kanta, ta gyara katifarta, ummi ta kwanta, ta kawo abun rufa ta lulluɓe ummin, sannan ta rungumeta. Sai da ta tabattar da mariya tayi bacci, sannan ta tashi zaune ta kira wayar raihan. Aikuwa a take ya ɗaga ya ce "Ina ki ka shiga ne? Tun safe nake kiran wayarki amma shiru" Ummi ta ce "Albishirinka" "Goro fari ƙal" "Na haɗu da mama" Yana kwance ya tashi tsaye, ya ce "Wace maman?" "Mamana mahaifiya, ashe kawuna ya san in da take, wai dan kar in gudu in ƙi zama na yi karatu ya sanya ya ɓoye mini" Adduoi na nuna godiya ga Allah ya din ga jerowa, yana hamdala can kuma ya ce "Congratulations to both of us ummi, dan wallahi da al'amarin nake kwana nake tashi, ina tunanin ta ina zamu fara nemanta, Alhamdilillah Ala mun gode wa Allah" Tare suka din ga murna da raihan a waya, suka gama ta ajiye wayar, ta rungume maman tsam a jikinta, tana tuno irin rabuwa da suka yi, da irin so da ƙaunar da maman nata ta nuna mata. Bacci suka yi sosai da sosai, babban abun da ya burge ummi, ya ƙara sanyata nutsuwa, duk da rashin lafiyar da maman take fama, tana yin salla, sai dai wasu lokutan akwai kura-kurai sosai a sallar ta ta, amma duk da haka tana kamantawa. A washegari kawu ya ce zai koma Kano, nan da sati biyu zai dawo ya tafi da ummi. Yaya maryam ta ce "Dr. Ka tafi da ita kuma, kusan shekara goma sha takwas, ba sa tare kuma ace nan da sati biyu za a zo a ɗauketa a tausaya mana dan Allah" Dr. Ya ce "Eh ai ban gama maganar bane ba, abu na farko ummi tana aiki, in da take aikin kuma sun jin daɗin zama da ita, abu na gaba kuma an saka mata rana watanni huɗu, kun ga za ta yi shirye-shirye ita da mijinta, daga kano ace ya din ga zuwa maiduguri yayi masa nisa, duk da dole zai zo ya gaisheku" Anty maryam ta yashe baki tana faɗin "Masha Allah, Alhamdilillah" Malam ma ya din ga murmushi yana sanya albarka. "To amma, akwai ɗan shirye-shiryenmu da muke yi wa yaranmu na aure, ai da an bar mana ita mun yi mata" Dr. Ya ce "Nan da watanni biyu zuwa uku sai ta dawo nan, ku yi duk shirye-shiryen ku a tsanake" Yaya ɗan lami ya ce "Amma ba za a ƙara mana ko wata ɗaya ko biyu ya zama nan da wata shida ba, mu gama shirinmu mu ma" "A'a kar ka damu, in sha Allah babu wani abu da zai gagara, manyan mutane ne, idan muka ce a ƙara zasu ga bamu kyauta ba, hakan ma in sha Allah babu abun da zai gagara" Suka kammala tattaunawa, suna ta yi wa kawu godiya, ya kama hanya ya koma kano. Ummi taga gata da ƙauna, babu kyara, babu hantara babu cin zarafi, duk ba a rasa wanda sukan yi maganar cewa ummi ba ta kama da mariya, mariya ta fita kyau da haske, maryam ce ma a tsaye take faɗan kar wanda ya sake yi musu wannan zancen. Ummi murmushi kawai tayi, dan da ta san abun da tayi going through, da wannan bai ɗaga mata hankali ba. *** A ka yi bikon raihan da ƙyar ya koma kano, Alhaji sai tsokanarsa yake "ni zaka yi wa yaji ko? Zamu gauraya da kai ne". Hajiya ta ce "Raihan ba a fushi da iyaye, nan gaba kar sake aikata abu makamancin haka" Raihan ya ce "Hajiya ba fushi na yi ba, na tafi ne dan na je na samu nutsuwar zuciya, amma in sha Allah hakan ba zai sake faruwa ba" Cikin tsananin fargaba ya tashi ya nufi sashin mami, ba addu'ar da bai karanta ba, saboda ya san dole ne zuwansa ya tarar da sabon ɓacin rai. A bedroom ɗin ta ya tarar da ita a zaune, cikin ladabi ya durƙusa ya ce "Mami barka da gida" Maimakon ta amsa sai ta ƙure shi da ido, da har sai da ya fara tsarguwa. "Ai gara in ƙare maka kallo, in tabattar da ni na haifeka kuwa? Ba matar ubanka ce kuwa ta haifeka ba ko har ubanka? In haifi ɗa a cikina ya janyo mini zagi da cin mutunci, raihan kana son gamawa da duniya lafiya kuwa? Ka sani sarai matar nan ba ƙaunata take yi ba, ka je ka sameta ka kai ƙara ta ta kira ni ta ci mini mutunci" "Wallahi mami ba ƙararki na kai ba" "Yi mini shiru tun kan na fasa maka baki, ka kyauta ba dai wannan mummunar yarinyar ba ce ba, ka je gaka nan gata, amma ka sani babu yawuna babu saka hannuna a aurenka raihan, kuma bayan ka aireta sai ka auri safiyya. Kuma ban lamunci ka yi mata kayan lefe ba, tun da bazawara ce, dubu ɗari biyar ɗin ta isa komai da komai" Cikin damuwa raihan ke ƙoƙarin yin magana, amma ta dakatar da shi, tare da bashi umarnin ya bar mata ɗaki. Kansa har wani sarawa yake yi, wai ita safiyyan nan dole sai ya aureta kamar wahayi? Baya son ta ba ya ƙaunarta amma an dage sai ya aureta, ga kuma wata magana, wai ba zai yi wa ummi kayan lefe ba, to iyayenta ne zasu saya mata sutura da kayan kwalliyar da za ta yi masa a gidansa? Kuma a wannan marrar nawa dubu ɗari biyar take, da har za ta isa ayi wa ummi kayan lefe, nauyin ai sai ya yi wa iyayenta yawa, shi abun kunya ne ma a gare shi ace bai yi wa ummi kayan lefe ba. Haka yayi ta wasi-wasi yana nazarin abun a ransa. Farida ba ta damu da in da ummi take ba, sai dai tana tambayar dr. Tana fatan ummi ta tafi kenan, amma yayi mata banza ya ƙyale ta. Noor kuwa sai bin sa take tana tambayar sa, wai yaushe ummi za ta dawo, ita fa gidan babu daɗi idan ummi ba ta nan, ya ce mata zata dawo nan ba da daɗewa ba. Ummi a gabanta aka fara haɗa kayan turarukan wutanta, wai akwai turarukan da sun fi shekara a binne a ƙasa ana tsuma su. Yaya maryam ta kasa zama, kullum tana yawon kasuwa ita da mama, matar malam wurin yi wa ummi sayayyar kayan aure. Ita babban abun da yafi faranta mata, bai wuce kasancewar ta da babarta ba. Mami ta ƙara matsanta wa raihan, ga gefe guda kuma, Safiyya sai ta wani kira shi wai za ta gaishe shi, duk rashin son wulaƙanta ɗan Adam irin na raihan, ƙarshe sai da yayi blocking ɗin ta, dan ta daina damunsa da kira. Ya cewa ummi zai zo Maiduguri ya ganta, ya kuma gaida mama, amma gudun matsala ya sanya ta ce masa ya bari ta kusa dawowa. *** Sai da ummi tayi sati uku cif, sannan dr. Ya koma ɗaukar ta, kamar ta ce masa dan Allah ya barta a nan, amma sai ta ji nauyin hakan ta kasa, kayanta ƙwaya biyu da ta je da su, sai da aka ɗinka mata kusan kala goma a can, kuma tuni suka haɗa kayan gyaran jiki masu haɗe da turarrruka, ummi ta fara amfani da shi. Yaya maryam sai jaddada mata take yi, kar ta yi wasa da kayan gyaran da aka ba ta ta yi, da sabulan da aka haɗa mata. Mariya ta kalli dr. Ta ce "Ka yi mini alƙawarin ba wurin Iya zaka mayar da ita ba?" Yayi murmushi ya ce "Ai aronta na ce ki bani, ba zan kai miki ita wurin Iya ba" "To ai zaka dawo da ita ko?" "In sha Allah" "To dan Allah ka kula mini da ita sosai da sosai, kar ka bari ta yi kuka" "In sha Allah zan kula da ita sosai da sosai" Ta kalli ummi ta ce "Kar ki yi musu kuka kin ji ummi, ban da ƙyuya da kuka, ba ruwanki da yara, kar ki je su din ga dukanki kin ji ko?" Ummi ta riƙe hannunta ta ce "To mamana, me ki ke so na taho miki da shi idan zan dawo?" Ta ɗan yi jimm sannan ta ce "Bakomai, ni dai kawai ki dawo, ba dan ina jin kunyar kawu yahaya ba, ba zan bashi ke ba" Ummi ta cigaba da kallon mariya tana jin daɗi. Da ƙyar suka rabu suka nufo hanyar Kano. Duk rashin surutun ummi, haka ta sake ta din ga yi wa kawu hira tana bawa kawun labarin mamanta. Bayan azahar suka sauka a kano, noor kamar ta mayar da ummi cikin ta, dan murnar ta dawo. Ummi ta shiga har falo, ta ce wa farida sun dawo, ta amsa mata a yatsune, sai dai fuskar inteesar kawai ta kalla ta san matsala ce ta kawota gida. Ummi ta koma ɗakinta, suka din ga hira ita da noor tana bawa noor labarin mamanta. Noor ta ce "Kuma ki ka yadda ki ka dawo, wallaahi idan ni ce ba zan dawo ba, amma na san saboda yaya raihan ki ka dawo ko?" Ummi ta ce "Ban sani ba" Suka din ga dariya, noor ta ce "In gaya miki, Inteesar mijinta ya ɗauki amaryarsa sun tafi umara, shi ne take kuka wai ba a tafi da ita ba" "To waye ya tambaye ki?" Noor tayi shiru tana ƙifta idanu. Haka nan take murna, ta san yau za ta ga raihan, ta rasa dalilin da ya sanya take murna. Haka nan ta samu kanta da yin shirin haɗuwa da shi. Ta ɗauki kayan tsaraba da ta zo da su, har da su kayan turaren wuta ta kai wa farida, ta karɓe ba tare da godiya ba. Bayan sallar magariba ummi ta saka rigar atamfa bubu, tana ta fama ta ɗaura ɗankwali, abu ya gagara saboda ba ta saba ba, ƙarshe noor ce ta ɗaura mata da ƙyar, shima gashin ya ƙi rufuwa, sai da ta saka hula sannan aka ɗaura ɗan kwalin. Ta yafa mayafi, tana ta rufe-rufe tana tunanin anya za ta iya fita a haka? Kiran wayarsa ta gani, ta tashi ta kalli noor ta ce "Anya in fita a haka kuwa?" "Wallahi kin yi kyau, kin rufe ko ina kuma" Da ƙyar ummi ta iya fita, tana ta kare jikinta, ta ƙarasa in da yake. "Oyoyo sweetheart, long time" Tayi murmushi ta zauna, tana kawar da kanta gefe. "Congratulations once again, ya ki ka baro mini maman?" Ummi ta yi murmushi ta ce "Tana lafiya ƙalau" "Kin bata labarina kuwa?" Ummi ta ce "Idan na yi mata babu lallai ta gane ma" Ya ce "Ba ki yi niyya ba dai, zan je da kaina mu gaisa ai" "Ka gama yajin?" Yayi murmushi ya ce "Ke ma haka zaki ce?" Ummi ta ce "To ba yajin ka yi ba, ko kunya ba ka ji ba?" Yayi dariya ya ce "Na samu mafita ai, kin yi kyau sosai da sosai wallahi, Allah ya nuna mana ranar nan lafiya babyna" ummi ta yi shiru tana sunkuyar da kanta. Kausar ce ta nufo in da suke zaune, dan haka yayi shiru yana kallon ta. Cikin mamaki take kallon raihan, yanzu wannan ne zai auri ummi? Wannan yaron, amma kuwa tayi asara, ko kuma shi yayi asarar kyakykyawan matashi kamar wannan ya auri ummi. Ta yi maganar a zuciyarta Cikin gadara ta ce "Ke ki zo maama tana kiranki, wa ki ka barwa yin abincin daren da haryanzu baki ɗora ba," tayi maganar cike da son wulaƙanta ummi a gaban raihan. Raihan ya ce "Tana magana da mijinta ne, idan kun matsu ku ci, ku dafa, tana buƙatar hutu, tun da yau ta dawo daga tafiya, kuma ina buƙatar yin magana da ita" Zare ido ummi tayi ta ce "Na shiga uku, raihan" "Shhh" ya ɗora yatsansa a kan lips ɗin sa yana zare mata ido. Ya sake kallon kausar ya ce "Ki koma ki ce ba za ta yi ba" Ayshercool 08081012143.                          *CUTARWA* *BRIGHT PENS* (FREE BATCH) *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* 34 MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH. Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe. FOLLOW AND SHARE AYSHERCOOL 08081012143 MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH. Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe. Wani irin gumi ne ya dinga gangaro wa mami, duk da yadda sanyin AC ke ratsa ko ina a falon. Raihan ƙararta ya je ya kai wa wannan masifaffiyar yar uban nasa kenan? tuno maganar Alhaji Tahir, da tuni ya bar falon da yayi ya sanya ta jin wata muguwar gudawa, saboda yadda cikinta ya murɗa mata. Afujajan ta fita ta nufi sashinsa, har da tuntuɓe. "Wallahi Baka isa ka gaya mini maganar da zata hana ni sukuni ka fice ka bar ni ba, kai yanzu saboda abun kunya goɗai-goɗai da kai sai ka auri yarinyar da ɗan ka ya ce yana so?" Alhaji Tahir ya ce "In dai haka shi ne mafita a gareni me zai hana? Ku mata ku kuka san wani abun kunya, mu maza abu in dai mu yayi mana ba ruwanmu da abun kunya, kuma ina sake tunatar da ke, bana magana biyu, wallahi da gaske nake, sai dai idan na aureta wanda ba zai iya zama da ni ba ya ƙara gaba, shawara ta rage ga mai shiga shiga rijiya" ya ƙarasa maganar tare da ɗaukar wayarsa ya fita. Kamar wadda ta zare, haka ta sake kwasa har da gudu, ta tafi ta kira Anty rakiya a waya. Rakiya na ɗagawa mami ta fashe da kuka, "Anty rakiya na shiga uku na lalace" "Wane irin kin shiga uku, meyafaru ba yanzu muka gama waya lafiya ba?" "Ashe raihan bauchi ya tafi, ya je ya haɗo ni da wannan masifaffiyar matar yayar babansa, kin ga yadda ta ci mini mutunci kuwa? shi kuma Alhaji wai idan ban bari an yi auren ba, wai shi zai aureta ya kawota gidan nan a matsayin matarsa" Anty Rakiya ta ce "Kai haba, dalla rabu da shi, barazana ce kar ki fasa wallahi, kar ki yadda a kawo miki bazawara a matsayin sirika" "Anty Rakiya waye ya gaya miki Alhaji Tahir yana barazana ne? Magana ɗaya yake yi ko ta yi maka daɗi, ko kuma akasin haka, har rantsuwa yayi mini, na shiga uku, kuma wai raihan ya ajiye aikin nan ina na kama?" Anty Rakiya ta ce "Taɓ, lallai raihan ba shi da hankali, to wallahi idan ki ka zuba masa ido, haka zai aurota ya fi ƙarfinki, tun da har ya san yayi miki yaji, ki kira shi ki ce lallai ya dawo dan ubansa" Mami cikin takaici ta ce "Lamarin fa ya wuce yadda ki ke tunani, kin san taurin kan raihan kuwa? To cewa tayi wai ba zai dawo ba, ya bar aikin kenan, ya kuma ce idan aka karɓo kuɗin auren nan, shi da aure har abada, ga babansa ya ce idan aka fasa zai aureta, na shiga uku ina na kama? Kin ga suna nema su haukata ni, raihan kafiya da taurin kai kamar ubansa, idan ya ƙi aure ya lalace yaya zan yi?" Anty Rakiya ta ce "Ai kawai ki dage ki samu ya dawo tukuna, ki kira shi a waya" "Wayoyin da duk ya kashe su, ina zan yi?" "To ki koma ki samu babansa ki lallaɓa shi, ya dawo da shi kar a rasa wannan damar kuma ta kasuwancin nan " Mami tayi ajiyar zuciya ta ce "Shikenan, zan kira ki mayi magana anjima" ta katse wayar ta ajiye tana wani irin haki, ita ba mai asma ba. *** Dr. suna tafe a mota da shi da ummi, ya ce "Mamana zaki ga zamu yi doguwar tafiya, ba sayar da ke zan yi ba abun alkhairi ne" Ummi ta yi murmushi ta ce "Idan sayar da ni ɗin ma ka yi ai na saidu kawu" Yayi murmushi ya ce "Idan na sayar da uwata ina na kama? Yakamata ace kin yi azumin farinciki kan mu yi tafiyar nan" "To Ubangiji ya tabattar mana da dukkanin alkhairin da yake cikinta" Ya amsa mata da "amin" Ummi ta gaji da zaman motar nan sosai da sosai, sai dai tun da taga symbols da sunan borno, jikinta ya fara sanyi, har ta rasa tunanin me ma za ta yi ne?. Kawu kuma ya mayar da kai sosai a kan tuƙinsa, sai lokacin salla ya tsaya suka yi salla, ya saya mata abinci. Ta tuno lokacin da ya ɗaukkota daga gagarwa a wahale, ba sutura ga ciwo, ko ba komai ta samu alkhairi a dalilin riƙonta da yayi A ranta ta ce "Allah sarki kawuna, baba ya tafi amma ya bar mini Allah, Allah kuma ya bani kai, Allah ya kula da kai da zuriyarka". Duk da ba ga saba baccin mota ba, gajiya ta sanya wani irin nannauyan bacci yin awon gaba da ita. "Mamana tashi mun zo" a hankali ummi ta motsa tare da buɗe idonta, har suka fito daga cikin motar, ba ta iya cewa komai ba, sai bin wurin da kallo. Ƙofar wani gida suka tsaya, dr. Ya ciro wayarsa ya ɗan daddana ya kara a kunnensa ya ce "Gamu mun zo" Wani matashin saurayi ya leƙo ya durƙusa ya gaida dr. Sannan ya ce su shiga. Suka shiga cikin gidan, ummi ta zubawa dattijon da suka tarar a tsakar ido, yana zaune a kan buzu, da Alƙur'ani bugun warshi a gabansa. Dattijon ya miƙe tsaye yana yi musu maraba, tare da bin ummi da kallo, ba ta ɗaga niƙabin fuskarta ba, sai dai ta shagala da kallon sa ta san shi, amma a ina? Ta kasa tunawa. Yayi musu jagora har wani matsakaicin falo, yana ta yi musu sannu da zuwa. Suka gaisa da dr. Ummi ta gaishe shi, ya amsa mata cikin kulawa, sai dai bai tambayi wacece ba, kuma ya kasa daina kallonta. Dr. Ya ce "Ina mutuniyar kuwa?" "Wai sun fita barka a nan bayan layi, jikin ne ma ya ɗan motsa, amma Alhamdilillah mun gode Allah, bari azo a ɗora muku girki, ai bamu san zaku zo ba" Dr. Ya ce "Ai alƙawarin da na ɗauka na zo cikawa, zuwan babu cikekken shiri, bari mu yi salla kafin su dawo". Ya ja dr. Suka fita, bayan nuna wa ummi banɗaki, tayi alwala ta yi salla, ta nemi wuri ta kashingiɗa tana hutawa, saboda gajiyar da tayi. Ummi ta ɗan jima a zaune, sannan dr. Ya shigo, shigowar ta sa yayi daidai da shigowar matashin da ya yi musu iso, ya kawo musu nono mai sanyin gaske, da nama fal malam ya ce a kawo musu da ruwa, dan azo a ɗora sanwa. Ummi dai ta kasa sakewa ta ci, dr. Kuma sai hira suke yi da malam. Dr. Ya ce "Malam ba ka ganni da baƙuwa ba ne? Baka tambayeni wacece ba" Malam yayi murmushi ya ce "Tun da baka gaya mini ba, bai kamata na yi shishshigi ba ai, na ma zata ko mai ɗakinka ce, shiyasa ban yi magana ba, kuma na ganta sanye da niƙabi" Dr. Yayi murmushi ya ce "Aishikenan, mama malam ne fa, baki gane shi ba?" Ummi ta ce "Na sanshi amma na manta a ina?" "To ki cire niƙabin ko zai gane ki" Ummi ta jinjina kai tana ƙoƙarin cirewa, aka  yi sallama. Bayan matar farko ta biyun ma tayi, a nan take ummi ta daskare, ƙirjinta ya buga da ƙarfin gaske, ta ji tamkar numfashin ta zai bar ƙirjinta, wata irin tsuma ta ji ta fara yi, amma ta gaza motsawa. Malam ya ce "Daga zuwa barka kun yi zamanku, gashi kun yi baƙi tafiyayyu daga kano" Ta ce "Baban ummi ne?" Malam ya ce "Eh shi ne, tun da shikaɗai ki ka sani a kanon ba" Shigowa suka yi tare, tana riƙe da mayafinta a hannu, hannunta kamar amarya an yi mata lalle yayi jawur. Ba ta kalli baban ummi ba, kai tsaye ummi ta zubawa ido, yayin da ummin ma ta zuba mata ido, tana jin yadda ƙirjinta ke lugude. Gaba ɗaya suka zuba musu ido, kai tsaye ta nufi ummi ta zauna a gabanta, tana cigaba da kallon ummi ta niƙabinta. Ta miƙa hannu a hankali ta ɗaga niƙabin ummin, tayi tozali da fuskar ummin da a duniya bata ganin kyan komai, kamar yadda take ganin kyawun wannan fuskar. A gigice ummi ta yi mata wata irin runguma ta fashe da matsanancin kuka, saroro mariya tayi, ta kasa taɓa ummi sai hawaye da ya fara zuba daga idonta. Mama ta miƙa hannu tana faɗin "Ki yi mata a hankali ba ta da cikakkiyar lafiya" Mariya ta buge hannun maman da ƙarfi, ta ruƙunƙume ummi, tana wata irin ajiyar zuciya kamar za ta fita daga hayyacinta. Ta miƙa hannu ta warware mayafinta, ta lulluɓe da ummi da shi, ta ɗaukko mafici kuma tana yi mata fifita tana kuka. Sai a yanzu suka gane wacece, malam ya sunkuyar da kai yana hawayen tausayin ƴar sa. Ya zura hannu a aljihunsa ya ɗaukko wayarsa, ya kira Maryam a waya da kuma yaya ɗan lami. "Ummina, kina cin abinci kuwa? Naga duk kin rame, iya tana yi miki wanka? Ko dai zazzaɓi ne a jikinki?" Tayi maganar tana ɗora hannu a goshin ummi. Wasu irin jijiyoyi suka ɗaɗɗaga a goshin ummi, wani irin riƙo take yi wa mariya, tana jin kamar an sanyata a wata ni'ima. Sun fi mintuna talatin a haka, sun ƙi sakin juna, mariya sai kakkare ummi take yi, kar wani ya taɓa mata ita. Dr. Yayi gyaran murya ya ce "Yau na cika alƙawari ko?" Ta jinjina masa kai, tana kuka ta ce "Wallahi ba zan taɓa yafe wa iya ba, Allah ya saka mini zaluncin da ta yi mini, ta ƙwace mini ummi bayan ba son ta take yi ba, ta ce ni na kashe mata ɗa, kalli yadda duk ummi ta rame, haka zan kwanta in yi ta mafarkin ummi tana kuka, tana cewa na zo na tafi da ita" Ta ɗago ummi tana goge mata hawaye ta ce "Ki daina kuka kin ji ummana, ba zan sake bari a mayar da ke wurin iya ba, na san ba ta sonki ba ta ƙaunarki, ban san me ki ka yi mata ba, wallahi ba zan yafe mata ba, yaya ɗan lami yaƙi dagewa ya karɓo mini ƴa ta, kullum sai na yi kuka saboda ummi, yaya maryam ma ta hantare rannan wai kamar nikaɗai ce me ƴa, ki daina kuka kin ji ummina, da kaina zan din ga yi miki wanka, ina baki abinci, katifata zata ishemu mu din ga kwana tare, ba zan sake bari a kai ki wurin iya ba kin ji mamana" Ummi ta ƙura mata ido, yadda mama ke wannan surutan daga wannan zuwa wancan tare da kasa gane ummi ta girma yanzu, ya tabbatar wa da ummi cewar mariya bata da lafiyr ƙwaƙwalwa. Ta miƙa hannu ta ɗaukko ledar pure water, ta buɗeta ta saka wa ummi a baki tana faɗin "Na san ƙishirwa ki ke ji ummi, sha ruwa kin ji" Babu wanda tausayin ummi da mariya bai kama a wurin ba, uwa kenan duk da ciwon ya motsa ba ta hayyacinta, amma hakan bai hanata gane ƴar ta ba, duk da shekarun da suka shafe basu haɗu ba. Dr. Yayi gyaran murya ya ce "Alhamdilillah ala kulli halin, na gode Allah da ya sanya ummi da mahaifiyar ta suka haɗu, ba tare da ta Allah ta kasance ba. Ummi na yi miki laifi, kuma na yi muku duk da ina godiya da fahimta ta da ku ka yi. Ummi ban ƙi sada ki da mahaifiyarki dan baƙanta miki ba, a lokacin da na ganota, tana cikin halin larura sosai, ba komai take ganewa ba, na yi fargabar haɗuwarku ba za ta yi daɗi ba, idan ku ka haɗu ta kasa gane ki, abu na gaba kuma ina tsoron halin da ki ke ciki, ya sanya ki ƙi zama ki dawo wurinta, alhalin kina tsaka da karatu, dan duk wanda yake ruwa, ko takobi aka miƙa masa zai kama, dan haka a matsin nan da ki ke, duk da kasancewar ki mai biyayya, zaki iya bujirewa ki zaɓi dawo wa gaban mahaifiyarki, ba tare da kin yi acheiving wani abu ba. Wanda a lokacin babban burina da fatana, ki samu nagartaccen ilimi, da zaki iya tsayawa da ƙafafuwanki, ina fatan zaki yafe mini daga ke har mahaifiyar ki" yayi maganar a sanyaye. "Ai dama kai na yafe maka, baka cuceni ba, amma iya iya iya, ban san me na yi mata ba, amma za ta maimaita a gaban Allah, amma wallahi ba zan yafe ba, na ji labarin azabtar mini da ummi ta yi, amma yaya ɗan lami ka ƙi dagewa ka karɓo mini ummina" Dr. Ya ce "Haba maman ummi, ki yi haƙuri abun da ya wuce ai ya riga ya wuce, ki yi haƙuri dan Allah" yayi maganar yana haɗa hannayensa. "Ai kai na ce na yafe maka, tun da ka kawo mini ummi, kuma kana saya mini magani da abun da nake so, har yaya ɗan lami na yafe muku, amma ban da iya da wanda suka ci zalin ummina, bani da abun da zan gani na tuna da bashir sai ummi, amma ta ƙwace mini ita dan ta wulaƙanta ni" Dr. Ya ce "Ba gani a gabanki kina kallona ba?" "Yaya Yahaya ne fa ba Bashir ba, na gane ka yau" yayi murmushi ya fahimci memoryn na ta yana yi yana seizing ne. Sun sha mamakin yadda ummi ta girma, ummi kuma kallon mamanta take yi, kamar ba ita ta haifeta ba, haryanzu shar da ita, gashi gaba ɗaya ba sa kama, sai kaɗan, kamar ya da ƙanwa ba uwa da ƴa ba. Dangin mama kamar su cinye ummi, a yamamcin nan suka din ga zaryar ganin ummi, sai dai ta ɓoye ummi a bayanta, kowa ya zo sai dai ya hango ummi daga nesa wai kar a ɗauketa a mayar da ita wurin Iya. Ummi ta ga ƙauna da soyayya, mariya ta din ga zuba mata hira, wata tana ganewa, wata ba ta ganewa, ummi space take son samu, ta kira raihan a waya ta sanar masa. *** Raihan yana zaune a falon hajiya Aisha yana kaɗa ƙafa, yana danna wayarsa cikin damuwa, ya kasa samun ummi a waya. Falon ta shigo cikin takunta na ƙasaita, ta samu wuri ta zauna ta kalli raihan ta ce "Kai, babanka ya kasa samunka a waya, yana ta ƴar murya a lallaɓoka ka koma fa" Raihan ya gyara zamansa ya ce "Wallahi ko dan saboda Alhaji ban so na taho ba, mami ce taƙi tsayawa ta fuskance ni, na rasa yadda zan yi da ita wallahi, taƙi fahimta ta kuma anty rakiya ce take zigata" "Kai dalla can, na kirata mun yi magana da ita, ba abun da za ta sake yi a kan maganar, ita ba a auren aka aureta? Mu ba auren zumunci ake a danginmu ba, babanka shi ya fara karya mana wannan ta'adar, ya aurota daga nan kowa ya samu ƴancin yin hakan, sai yanzu ita kuma ta ce ba za a auro wata ba?" Raihan ya ce "Abun kuma har da gori?" "Eh an yi mata gorin, da ai ba ayi ba, siyama na nemanka wai ka je ta girka maka menene oho mata" Yayi murmushi ya ce "Nifa yanzu abincin kowa ya daina yi mini daɗi sai na matata" "Ka ga fitsararre, amma dai da namun ka ke ci ko? Wai wani matarka ka ga idan ba ka rage rawar kan nan ba a kak yarinyar nan, haka zaku yi ta faɗa da babarka" Raihan ya miƙe ya ce "Ni kaina na sani, ina ƙoƙarin ragewa wallahi, amma hannun ummi akwai maggi ta iya girki sosai" Hajiya Aisha kawai ta yi murmushi ta girgiza kai, tana sake jinjina wautar mami, a irin wannan stage ɗin, ba a saka pressure wurin cewa lallai sai an tanƙwara namiji, sai nasiha da rarrashi idan ma so take ta soke auren. Da daddare mariya da kanta, ta gyara katifarta, ummi ta kwanta, ta kawo abun rufa ta lulluɓe ummin, sannan ta rungumeta. Sai da ta tabattar da mariya tayi bacci, sannan ta tashi zaune ta kira wayar raihan. Aikuwa a take ya ɗaga ya ce "Ina ki ka shiga ne? Tun safe nake kiran wayarki amma shiru" Ummi ta ce "Albishirinka" "Goro fari ƙal" "Na haɗu da mama" Yana kwance ya tashi tsaye, ya ce "Wace maman?" "Mamana mahaifiya, ashe kawuna ya san in da take, wai dan kar in gudu in ƙi zama na yi karatu ya sanya ya ɓoye mini" Adduoi na nuna godiya ga Allah ya din ga jerowa, yana hamdala can kuma ya ce "Congratulations to both of us ummi, dan wallahi da al'amarin nake kwana nake tashi, ina tunanin ta ina zamu fara nemanta, Alhamdilillah Ala mun gode wa Allah" Tare suka din ga murna da raihan a waya, suka gama ta ajiye wayar, ta rungume maman tsam a jikinta, tana tuno irin rabuwa da suka yi, da irin so da ƙaunar da maman nata ta nuna mata. Bacci suka yi sosai da sosai, babban abun da ya burge ummi, ya ƙara sanyata nutsuwa, duk da rashin lafiyar da maman take fama, tana yin salla, sai dai wasu lokutan akwai kura-kurai sosai a sallar ta ta, amma duk da haka tana kamantawa. A washegari kawu ya ce zai koma Kano, nan da sati biyu zai dawo ya tafi da ummi. Yaya maryam ta ce "Dr. Ka tafi da ita kuma, kusan shekara goma sha takwas, ba sa tare kuma ace nan da sati biyu za a zo a ɗauketa a tausaya mana dan Allah" Dr. Ya ce "Eh ai ban gama maganar bane ba, abu na farko ummi tana aiki, in da take aikin kuma sun jin daɗin zama da ita, abu na gaba kuma an saka mata rana watanni huɗu, kun ga za ta yi shirye-shirye ita da mijinta, daga kano ace ya din ga zuwa maiduguri yayi masa nisa, duk da dole zai zo ya gaisheku" Anty maryam ta yashe baki tana faɗin "Masha Allah, Alhamdilillah" Malam ma ya din ga murmushi yana sanya albarka. "To amma, akwai ɗan shirye-shiryenmu da muke yi wa yaranmu na aure, ai da an bar mana ita mun yi mata" Dr. Ya ce "Nan da watanni biyu zuwa uku sai ta dawo nan, ku yi duk shirye-shiryen ku a tsanake" Yaya ɗan lami ya ce "Amma ba za a ƙara mana ko wata ɗaya ko biyu ya zama nan da wata shida ba, mu gama shirinmu mu ma" "A'a kar ka damu, in sha Allah babu wani abu da zai gagara, manyan mutane ne, idan muka ce a ƙara zasu ga bamu kyauta ba, hakan ma in sha Allah babu abun da zai gagara" Suka kammala tattaunawa, suna ta yi wa kawu godiya, ya kama hanya ya koma kano. Ummi taga gata da ƙauna, babu kyara, babu hantara babu cin zarafi, duk ba a rasa wanda sukan yi maganar cewa ummi ba ta kama da mariya, mariya ta fita kyau da haske, maryam ce ma a tsaye take faɗan kar wanda ya sake yi musu wannan zancen. Ummi murmushi kawai tayi, dan da ta san abun da tayi going through, da wannan bai ɗaga mata hankali ba. *** A ka yi bikon raihan da ƙyar ya koma kano, Alhaji sai tsokanarsa yake "ni zaka yi wa yaji ko? Zamu gauraya da kai ne". Hajiya ta ce "Raihan ba a fushi da iyaye, nan gaba kar sake aikata abu makamancin haka" Raihan ya ce "Hajiya ba fushi na yi ba, na tafi ne dan na je na samu nutsuwar zuciya, amma in sha Allah hakan ba zai sake faruwa ba" Cikin tsananin fargaba ya tashi ya nufi sashin mami, ba addu'ar da bai karanta ba, saboda ya san dole ne zuwansa ya tarar da sabon ɓacin rai. A bedroom ɗin ta ya tarar da ita a zaune, cikin ladabi ya durƙusa ya ce "Mami barka da gida" Maimakon ta amsa sai ta ƙure shi da ido, da har sai da ya fara tsarguwa. "Ai gara in ƙare maka kallo, in tabattar da ni na haifeka kuwa? Ba matar ubanka ce kuwa ta haifeka ba ko har ubanka? In haifi ɗa a cikina ya janyo mini zagi da cin mutunci, raihan kana son gamawa da duniya lafiya kuwa? Ka sani sarai matar nan ba ƙaunata take yi ba, ka je ka sameta ka kai ƙara ta ta kira ni ta ci mini mutunci" "Wallahi mami ba ƙararki na kai ba" "Yi mini shiru tun kan na fasa maka baki, ka kyauta ba dai wannan mummunar yarinyar ba ce ba, ka je gaka nan gata, amma ka sani babu yawuna babu saka hannuna a aurenka raihan, kuma bayan ka aireta sai ka auri safiyya. Kuma ban lamunci ka yi mata kayan lefe ba, tun da bazawara ce, dubu ɗari biyar ɗin ta isa komai da komai" Cikin damuwa raihan ke ƙoƙarin yin magana, amma ta dakatar da shi, tare da bashi umarnin ya bar mata ɗaki. Kansa har wani sarawa yake yi, wai ita safiyyan nan dole sai ya aureta kamar wahayi? Baya son ta ba ya ƙaunarta amma an dage sai ya aureta, ga kuma wata magana, wai ba zai yi wa ummi kayan lefe ba, to iyayenta ne zasu saya mata sutura da kayan kwalliyar da za ta yi masa a gidansa? Kuma a wannan marrar nawa dubu ɗari biyar take, da har za ta isa ayi wa ummi kayan lefe, nauyin ai sai ya yi wa iyayenta yawa, shi abun kunya ne ma a gare shi ace bai yi wa ummi kayan lefe ba. Haka yayi ta wasi-wasi yana nazarin abun a ransa. Farida ba ta damu da in da ummi take ba, sai dai tana tambayar dr. Tana fatan ummi ta tafi kenan, amma yayi mata banza ya ƙyale ta. Noor kuwa sai bin sa take tana tambayar sa, wai yaushe ummi za ta dawo, ita fa gidan babu daɗi idan ummi ba ta nan, ya ce mata zata dawo nan ba da daɗewa ba. Ummi a gabanta aka fara haɗa kayan turarukan wutanta, wai akwai turarukan da sun fi shekara a binne a ƙasa ana tsuma su. Yaya maryam ta kasa zama, kullum tana yawon kasuwa ita da mama, matar malam wurin yi wa ummi sayayyar kayan aure. Ita babban abun da yafi faranta mata, bai wuce kasancewar ta da babarta ba. Mami ta ƙara matsanta wa raihan, ga gefe guda kuma, Safiyya sai ta wani kira shi wai za ta gaishe shi, duk rashin son wulaƙanta ɗan Adam irin na raihan, ƙarshe sai da yayi blocking ɗin ta, dan ta daina damunsa da kira. Ya cewa ummi zai zo Maiduguri ya ganta, ya kuma gaida mama, amma gudun matsala ya sanya ta ce masa ya bari ta kusa dawowa. *** Sai da ummi tayi sati uku cif, sannan dr. Ya koma ɗaukar ta, kamar ta ce masa dan Allah ya barta a nan, amma sai ta ji nauyin hakan ta kasa, kayanta ƙwaya biyu da ta je da su, sai da aka ɗinka mata kusan kala goma a can, kuma tuni suka haɗa kayan gyaran jiki masu haɗe da turarrruka, ummi ta fara amfani da shi. Yaya maryam sai jaddada mata take yi, kar ta yi wasa da kayan gyaran da aka ba ta ta yi, da sabulan da aka haɗa mata. Mariya ta kalli dr. Ta ce "Ka yi mini alƙawarin ba wurin Iya zaka mayar da ita ba?" Yayi murmushi ya ce "Ai aronta na ce ki bani, ba zan kai miki ita wurin Iya ba" "To ai zaka dawo da ita ko?" "In sha Allah" "To dan Allah ka kula mini da ita sosai da sosai, kar ka bari ta yi kuka" "In sha Allah zan kula da ita sosai da sosai" Ta kalli ummi ta ce "Kar ki yi musu kuka kin ji ummi, ban da ƙyuya da kuka, ba ruwanki da yara, kar ki je su din ga dukanki kin ji ko?" Ummi ta riƙe hannunta ta ce "To mamana, me ki ke so na taho miki da shi idan zan dawo?" Ta ɗan yi jimm sannan ta ce "Bakomai, ni dai kawai ki dawo, ba dan ina jin kunyar kawu yahaya ba, ba zan bashi ke ba" Ummi ta cigaba da kallon mariya tana jin daɗi. Da ƙyar suka rabu suka nufo hanyar Kano. Duk rashin surutun ummi, haka ta sake ta din ga yi wa kawu hira tana bawa kawun labarin mamanta. Bayan azahar suka sauka a kano, noor kamar ta mayar da ummi cikin ta, dan murnar ta dawo. Ummi ta shiga har falo, ta ce wa farida sun dawo, ta amsa mata a yatsune, sai dai fuskar inteesar kawai ta kalla ta san matsala ce ta kawota gida. Ummi ta koma ɗakinta, suka din ga hira ita da noor tana bawa noor labarin mamanta. Noor ta ce "Kuma ki ka yadda ki ka dawo, wallaahi idan ni ce ba zan dawo ba, amma na san saboda yaya raihan ki ka dawo ko?" Ummi ta ce "Ban sani ba" Suka din ga dariya, noor ta ce "In gaya miki, Inteesar mijinta ya ɗauki amaryarsa sun tafi umara, shi ne take kuka wai ba a tafi da ita ba" "To waye ya tambaye ki?" Noor tayi shiru tana ƙifta idanu. Haka nan take murna, ta san yau za ta ga raihan, ta rasa dalilin da ya sanya take murna. Haka nan ta samu kanta da yin shirin haɗuwa da shi. Ta ɗauki kayan tsaraba da ta zo da su, har da su kayan turaren wuta ta kai wa farida, ta karɓe ba tare da godiya ba. Bayan sallar magariba ummi ta saka rigar atamfa bubu, tana ta fama ta ɗaura ɗankwali, abu ya gagara saboda ba ta saba ba, ƙarshe noor ce ta ɗaura mata da ƙyar, shima gashin ya ƙi rufuwa, sai da ta saka hula sannan aka ɗaura ɗan kwalin. Ta yafa mayafi, tana ta rufe-rufe tana tunanin anya za ta iya fita a haka? Kiran wayarsa ta gani, ta tashi ta kalli noor ta ce "Anya in fita a haka kuwa?" "Wallahi kin yi kyau, kin rufe ko ina kuma" Da ƙyar ummi ta iya fita, tana ta kare jikinta, ta ƙarasa in da yake. "Oyoyo sweetheart, long time" Tayi murmushi ta zauna, tana kawar da kanta gefe. "Congratulations once again, ya ki ka baro mini maman?" Ummi ta yi murmushi ta ce "Tana lafiya ƙalau" "Kin bata labarina kuwa?" Ummi ta ce "Idan na yi mata babu lallai ta gane ma" Ya ce "Ba ki yi niyya ba dai, zan je da kaina mu gaisa ai" "Ka gama yajin?" Yayi murmushi ya ce "Ke ma haka zaki ce?" Ummi ta ce "To ba yajin ka yi ba, ko kunya ba ka ji ba?" Yayi dariya ya ce "Na samu mafita ai, kin yi kyau sosai da sosai wallahi, Allah ya nuna mana ranar nan lafiya babyna" ummi ta yi shiru tana sunkuyar da kanta. Kausar ce ta nufo in da suke zaune, dan haka yayi shiru yana kallon ta. Cikin mamaki take kallon raihan, yanzu wannan ne zai auri ummi? Wannan yaron, amma kuwa tayi asara, ko kuma shi yayi asarar kyakykyawan matashi kamar wannan ya auri ummi. Ta yi maganar a zuciyarta Cikin gadara ta ce "Ke ki zo maama tana kiranki, wa ki ka barwa yin abincin daren da haryanzu baki ɗora ba," tayi maganar cike da son wulaƙanta ummi a gaban raihan. Raihan ya ce "Tana magana da mijinta ne, idan kun matsu ku ci, ku dafa, tana buƙatar hutu, tun da yau ta dawo daga tafiya, kuma ina buƙatar yin magana da ita" Zare ido ummi tayi ta ce "Na shiga uku, raihan" "Shhh" ya ɗora yatsansa a kan lips ɗin sa yana zare mata ido. Ya sake kallon kausar ya ce "Ki koma ki ce ba za ta yi ba" Ayshercool 08081012143. FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK. https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends Masu neman free books ɗina, da free pages duk akwai a kan watpad account ɗina. Irinsu Abduljalal Wata kissar sai mata Wuta a masaƙa Cutarwa Ƙanwar maza Gaba da gabanta Aƙidata Ruɗin ƙuruciya Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata. 08081012143. And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link. https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels Ayshercool. PAID ADVERT!. Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi. Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku Oll types of Turaran wuta Sandal Halut Irik Difur Gab Gab Kajiji Habil Nabak Humra Kulakcha Dilke da kalta Kayan Garan jiki Muna turara Kaya Kujerar garan jiki Kannada Madarorin turare masu kamshi Man garan gashi Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921 *TALLA!TALLA!TALLA!* *INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*. *BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU* *MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA* BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI. *CUTARWA* *BRIGHT PENS* (FREE BATCH) *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* 35 MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH. Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe. FOLLOW AND SHARE AYSHERCOOL 08081012143 MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH. Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe 35 Galala kausar ta buɗe baki tana kallon raihan. "Ko ba ki ji me na ce ba ne?" Yayi maganar yana kallon kausar. Ta kalli ummi, ta ce "eh lallai, zaki shigo zaki haɗu da maama" Raihan ya ce "Idan ta shigo kar ku bar ta da rai" kausar ta juya fuuu ta tafi. A rikice ummi ta ce "Raihan, meyasa zaka yi haka? Ka san me zaka jan yo mini ne?" Ya ƙare mata kallo ya ce "Idan kin koma gidan, ki tsaya ki zuba musu ido su illata ki, ummi ba fa kowanne lokaci ne haƙuri yake maka amfani ba, meyasa da ba a ce sai kin yi girkin ba sai da na zo? Dole ki rage wannan shirun naki, kuma ki shirya tsaf, domin akwai ƙalubale a zaman da zamu yi, zaki fuskanci challenge daban-daban dole ki din ga ƙoƙartawa, a yanzu dai duk abu ba zaki daku ba, dan haka kar ki bari wani abu ya baki tsoro, idan ma dukkan ne ki rama, ki daina zama ana cin kashi a kanki, tun da kin kusa bar musu gidan" Ummi ta yi shiru tana nazarin matsalar da raihan ya jefa ta a ciki. Ya basar ya ce "Baki bani labarin Maiduguri ba, ya ki ka ga garin, ya kuma ki ka ji da ki ga mama?" Duk da a tashin hankali take, sai da ta yi murmushi, ta ɗan saki jiki, ta bashi labarin yadda ta ga garin, da abubuwan da suka faru. Har ta fara mantawa da matsalar da raihan ya jefata a ciki. Da zai tafi ya zura hannu a aljihunsa, ya ajiye mata kuɗi, ya ce "Na san ba zaki rasa buƙatunki ba, sannan ranar monday zamu je banki a buɗe miki account, zan saka miki kuɗin kayan lefenki a ciki" Ta kalli tudun kuɗin da ɗan yawa, ta ce "Ka bar kuɗin nan mana, hidima ce a gabanka sosai" Ya girgiza kai ya ce "Kar ki damu, ai ba wani kyautar kuɗi nake yi miki ba, kina buƙatar kuɗi kuma na san ba tambayata za ki yi ba, abu na gaba kuma shi ne, saura ki shiga cikin gidan nan, su yi miki magana ki zauna kina kuka, ina da cid na kin sani, idan ki ka bari noor ta ce mini kin zauna kin yi kuka, ni da ke ne, ki kula mini da kan ki amaryata" Ummi ta yi zuru da ido tana tunanin irin tashin hankalin da zata iya fuskanta. Kausar kuwa jiki na tsuma ta je ta sanar wa farida abun da raihan ya ce, babu kunya a gaban ƴaƴanta ta kuza ashar ta miƙe tsaye jikinta yana tsuma. "Wai wani ɗan iska ne ma wanda za ta aura ɗin? Wani matsiyacine ne, bari in je in ga ɗan gidan uban waye na ci mutuncin sa daga shi har ita". Kausar ta tare ta ta ce "Wallahi wani ɗan yaro ne, dan dai yana da jiki ne, amma wallahi ba ki ganshi ba" "A'a bari na ƙarasa na je na ga wani shegen ne, ita ma ba ta isa ba balle shi" Kausar ta ce "A'a maama, ba mutuncinki bane ba ba girmanki bane, ai kin fi ƙarfin haka, dan Allah kar ki je, ki jira ta shigo ki ci ubanta" Noor ta ƙyalƙale da dariya, har da tuntsurawa, ta ce "Hmm wallahi maama baki san yaya raihan ba, ba fa matsiyaci bane da ki ka faɗa, ranar da aka kawo kuɗin auren anty ummi, kin ga motar babansu kuwa?" "Rufe mini baki kan na zo na tatsile ki, munafuka kamar na saka da ke" noor ta tura baki tare da yin shiru. Sai da ummi ta nufo shigowa cikin gida, ƙirjinta ya tsananta bugawa, wani irin tsoro ya shige ta, ta din ga tunanin yaya za ta yi. Ganin har ta shiga ɗakinta babu wanda ya ganta, ya sanya ta rufe ƙofarta ta ciki, tana fargabar abun da hakan ka iya haifarwa. Farida na zaune na jiran shigowar ummi, dan ta san dole za ta shigo ta ce za ta yi girkin, dan haka ta yi niyyar wulaƙanta ummi, sai dai shiru babu ummi babu dalilinta. A fusace farida ta kasa jurewa, ta tafi harabar gidan, kausar tana riƙeta tana ƙoƙarin hanata. Sai dai suka tarar da kujerun babu kowa, ta tambayi mai gadi, ya ce mata tun ɗazu suka shiga cikin gida. cikin zafin rai da zage-zage ta nufi ɗakin ummi, tana wani irin bugun ƙofar kamar za ta hau iskokai. Noor ta fito ta ce "Maama maƙwabta fa suna jin ki, kina ta ɗaga murya" Banza ta yi wa noor, ta cigaba da bugun ƙofar ɗakin ummi, tana ɗura mata ashar kamar bamagujiya. Ummi kuma wani irin tsoro ya kamata, ta kasa buɗewa tsoro take ji, ba ta san me faridan za ta iya yi mata ba idan ta buɗe. Sai da farida  ta ji ƙarar motar dr. Sannan ta saurara da bugun tana huci, dr. ya ƙaraso ya tarar da su a tsaitsaye, ya ce "Lafiya kuwa?" Farida ta ce "Ina fa lafiya? wallahi na gaji, wai ba wurin uwarta ka kaita ba, meye na dawo da ita gidan nan, to wallaahi barin gidan nan za ta yi, ko a kan bola uwarta ta take, ta je su ƙarata" Dr. Ya ce "Wai meyafaru ne?" "Sai ka yi magana ta buɗe ƙofar ɗakin ka tambayeta ka ji, tun da kai ka isa da ita, ni tana ganin sa'arta ce" Dr. Ya bubbuga ƙofar ɗakin ummi ya ce "Mamana ni ne buɗe ƙofar" Cikin tsoro da fargaba ummi ta buɗe ƙofar, kallo ɗaya yayi mata ya san a tsorace take. "Meyake faruwa?" Ya sake tambaya. "Dole ka ce meyake faruwa tun da ta riga ta raina ni, wallahi ba zan cigaba da zama da yarinyar nan ba, ka mayar da ita wurin uwarta wallahi ba zan cigaba da zama da ita ba" Cikin zafin rai ya ce "Dan Allah ki nutsu ki yi mini bayani, ummi ba ta taɓa yin haka ba, me ki ka yi mata?" Cikin takaici farida ta ce "Au tambayata ma ka ke yi me na yi mata?" "Dr. Maama ce fa ta aika anty kausar, wai ace ummi ta zo tayi girki alhalin yaya raihan ya zo, aikuwa ya ce ba za ta zo ba, anty kausar ta je ta yi girkin, ko su kwana da yunwa" Gaba ɗaya suka tsaya suna kallon noor, da ke wassafa abun da aka yi. Ummi ta yi saurin cewa "Dan Allah anty ki yi haƙuri, wallahi ba ni na faɗa ba, kuma tsoron abun da ya faru da rashin sanin abun da zan ce miki ya sa na rufe ƙofar, kunya ma nake ji, dan girman Allah ki yi haƙuri" Dr. Ya ce "Ummi wuce ki je ki kwanta, Allah ya yi miki albarka" Ya kalli Farida ya ce "Ai gara da ya nuna miki ɗan zamani ne shi, kuma gaskiya ya faɗa miki, idan ba zaku girka ba ku zauna haka, dan ba baiwar ku ba ce ba, banda zubar da kai da son nunawa duniya rashin sanin ciwon kanki, su ƴaƴanki haka ki ke yi musu, shikenan yarinyar nan babu damar ta huta, har a gaban mijin da ta aura sai kin yi yinƙurin tozarta ta? Meye na wani ta zo ta yi girki, a bari ta dawo mana" Babu kunyar idon ƴaƴansu farida ta din ga zuba wa dr. Rashin mutunci a gaban yaransa. Yayi ƙoƙarin danne zuciyarsa ya shareta. Har da iƙrarin ummi ba zata sake shigar mata kitchen ba, tun da ya fifita ummi a kan ta, sai ya ware mata kitchen ɗin ta ya raba musu kwana kuma. Sosai ummi ta yi kuka, ba kowa ya ja wannan abun ba sai raihan. Tun daga ranar takun saƙa mai zafin gaske ya shiga tsakanin ummi da farida, idan ta taho kausar ta taho, sai ta bangajeta, sabon wulaƙanci da tozarci iri-iri. Farida har da iƙrarin in dai dan ta samu mijin aure ne, ta fara take-taken iskanci, sai gidan mijin ya zame mata gida mafi azaba da tashin hankali. Ummi ta mayar da hankali a kan addu'a, tare da yaƙinin ko da raihan zai wulaƙanta ta bayan, ba zai kai yadda Idris ya ci zarafinta ba, tun da shi mutum me mai ilimi. Can gida ma raihan Mami ta sake sako shi a gaba,  duk ta in da ya motsa idonta na kansa, gashi sai cigaba da tura masa safiyya take yi, ɓangaren anty rakiya da safiyyan ma sun riƙe wuta sosai da sosai. Ummi kullum sai sun yi waya da mama da su yaya maryam, maryam tayi ta gaya mata shirye-shiryen biki da suke yi, ummi sai dai ta yi murmushi ba ta iya cewa komai saboda kunya. Ana tsukin wannan tashin hankalin, jami'ar bayero suka kori kausar daga makaranta, saboda rashin kawo points ɗin da ake buƙata, ga Inteesar gidan miji ya ƙara yi mata tsanani, saboda abokiyar zamanta ta samu ciki, da mijin da danginsa duk sun juya mata baya ta amarya suke yi. Hakan ya saka ummi ta ɗan samu sassauci, kamar yadda farida ta ce ta daina shigar mata kitchen, abinci sai ta ɗan sai abu ta ci, da ta ga babu sarki sai Allah idan an yi girki ba ya ciyuwa, sannan ta ce ai ita da yaranta ba bayin ummi ba ne, ita ce yakamata ta zama baiwa, tun da tana cin albarkacin su, dan haka dole ta fito ta yi musu girki su ci. Duk wannan abun bai damu ummi ba, dan ko a jikinta, farida ta shiga cikin tashin hankalin yadda za su sanar da dr. An kori kausar daga makaranta. Wani irin kyau da sheƙi fatar ummi ta din ga yi, tayi kyau sosai da sosai, ga wani irin ƙamshi na mussaman da yake ratsata. Raihan daga ya dawo daga office, sai mami ta tsiri kirshe shi ta hana shi fita,wai dan kar ya je wurin ummi, abun da ba ta sani ba shi ne, yana tsaka da aikin ma idan ya so ganinta sai ya ajiye yayi tafiyarsa wurinta. Ummi ta dage a kan cewar, raihan ba zai saka mata kuɗin lefe a account ba ita tsoro take ji, yayi yayi da ita taƙi yarda. Hajiya Aisha ce ta din ga kiransa tana tambayar sa ya batun lefe, ya ce mata sai sun yi aure zai yi mata, yanzu akwai matsala. Hajiya Aisha ba ta takura masa a kan sai ta ji matsalar ba, ta san ta mecece dan haka ta ƙyale shi. Amma ta ce masa dole ya yi wa ummi kayan fitar biki na gani na faɗa, ya amince da hakan ya ce mata su ba zasu yi wasu bidi'oi ba, sai an ɗaura aure juma'a zai yi reception da abokansa da ƴan uwansa, ita kuma su yi taronsu Saturday a kaita. Lokacin biki ya cigaba da ƙaratowa, dr. Shikaɗai yake faɗi tashin sa, babu mataimaki sai Allah, babu wani wanda zai ba shi shawara, shi yake ta ƙoƙarin playing both roles ɗin, ya kira raihan ya tambaye shi ya yanayin gidan da zai ajiye ummi, saboda ya san me zai saya, raihan ya ce masa kar ya takura kansa yayi iya abun da zai iya yi. Ummi ta sanar da dr. Abun da raihan ya ce mata a kan kayan lefe, dr. Ya ce "Ummi, ba kayan lefen ba, zaman aure mai ƙarko dan dai kayan da zaki saka, ni zan yi miki kar ki damu" Ummi ta ce "Dama ba damuwa na yi ba, gaya maka dai kawai na yi" Ya ce "Yauwwa mamana, na san ba zaki damu ba dama, Allah ya yi miki albarka" Ta amsa masa da amin. Dr. Kallon farida kawai yake yi, dan tuni ya san an kori kausar daga makaranta, amma taƙi gaya masa sai gaba da take yi da shi ma, a kan abun da ya faru tsakanin ta da ummi. Message ɗin da ummi da tayi tozali da shi a wayarta ne ya girgiza ta, ta duba lambar ba ta maryam ba ce ba, dan ta daina ɗaga kiran maryam, idan tayi mata message kuma gogewa take yi. Ta duba lambar a Truecaller ta ga an rubuta safiyya. Shiryayyen zagi ne na cin mutunci da cin zarafi ta shiryowa ummi mai zafin gaske, tare da tabattar wa da ummin cewa ita ce matar da aka zaɓa masaya aura, dan haka ko ta aure shi tamkar zaman haya za ta yi a gidansa. Ran ummi yayi mummunan ɓaci, ta sake duba message ɗin, sai ga kiran wayar lambar ya shigo wayarta, kamar kar ta ɗaga, sai kuma ta ɗaga ta saka a kunnenta ta yi sallama. "Na san zuwa yanzu kin ga message ɗina ko? To kina magana da safiyya matar da raihan zai aura, tun wuri idan ki na son kanki da arziki, ki fita harkarsa, domin kuwa babarsa ba son ki take yi ba, mummuna da ke har zaki ce zaki aure shi kin yi masa asiri dan mugunta, to wallahi raihan nawa ne kuma sai na aure shi, ke ban da mugunta ma kina bazawara ni kuwa budurwa ce, ba zaki haɗa kanki da ni ba, mummuna kawai" gaba ɗaya kalaman yarinyar ya tabattar wa da ummi yarinya ce. Ummi ta yi murmushi ta ce "To meye a ciki safiyya? Namiji ba mijin mace huɗu bane ba? Sai ya auremu duka mu yi zamanmu, da matar so da matar shige, sai a cika bakin bazawara da budurwa, ai ni bani da damuwa ki tambaye shi ki ji, lafiya ƙalau zamu zauna da ke, in dai wannan alfarmar ki ke nema, na yi miki ƙanwata Allah ya bamu zaman lafiya" Ta katse kiran ƙirjinta na bugawa da sauri-sauri, dan ba ta tunanin daga ƙuruciyarta zuwa yanzu, ta taɓa tsaya wa ta mayar wa da wani martani ba. Ƙasan zuciyarta kuma wani irin tafasa yake yi mata, da tuna yadda take ce mata wai ita ce matar da aka zaɓa masa, lallai akwai aiki a gabanta kamar yadda yake gaya mata, to meyasa bai gaya mini ba?' ta tambayi kanta. Kiran Safiyya ne ya cigaba da shigowa, amma tayi banza ta ƙi kula wayar, har magariba tayi ranta a ɓace yake, da ta tuna maganganun Safiyya sai wani irin haushi ya kama ta. Tana kallon kiran raihan da ta yi saving lambar da MD, amma ta yi burus da shi, taƙi ɗaga kiran. Abun ya bashi mamaki, dan haka da safe ya zo har gidan, ya duba ko bata da lafiya ne. Amma ya ga ta fito da shirinta na zuwa aiki, har ya fara murmushi, kawai ya ga ta yi gaba, ba ta nufo in da yake ba, kan ya bita ga shige lunguna, ta ɓulla titi ta haye napep ta yi tafiyar ta. Nan da nan raihan ya kiɗime, ya fara tunanin laifin me yayi mata? Da take share shi haka? Ya rigata isa wurin aikin na ta, ya tarar mai gadi ya buɗe wurin yayi shara. Ya shiga ya zauna, yana jiran isowarta, da ta iso ɗin ma, tana kallonsa ta ajiye jakarta ta shiga hidimomin ta, kallon ta kawai yake yi, ya zuba mata ido yana son gano meyake damunta, ko me yayi mata, amma ya kasa gano komai. Ana ta kirnaa a waya, ana jiransa amma yana zaune yana jiran ummi ta gama jan ajin ta saurare shi. Shi yadda ta share shin, take abubuwan ta ma, burge shi yayi, da alama fushi take yi. Ga wani irin kyau da ta yi kamar ya sace ya ya gudu, ta yi kyau sosai da sosai, ta ɗan washe sai sheƙi fatarta take yi. Ta zo ta zauna, ta kunna computer ta, za ta fara aiki, ya zuba mata ido, duk da a takure take da kallon, amma ta wani maze. Dukan teburin yayi da ɗan ƙarfi, sai da ta razana, ya ce "Yaushe zaki saurare ni ne?" "Ba rana ta bashi amsa tana harararsa" a ransa ya ce "Wow, ta fara iya tsiwa" Ya kwantar da murya ya ce "Ayi haƙuri dan Allah, laifin me na yi ne? Kina kallona har ki ka share ni ki ka yi tafiyarki?" "Ai na zata ɓatan kai ka yi ai, gidansu Safiyya zaka je" Wani irin shock ya ji da abun da ta faɗa, wani irin shu'umin kallo yayi mata, sannan ya ce "Wacece Safiyya kuma?" "Ka fi ni sani ai, idan ka san an haɗaka da wata a gidanku, ni me zaka yi mini?" "Ke a ina ki ka santa?" A ɗan ƙule ta ce "Wace irin tambaya ce wannan? Kirana ta yi a waya" tayi maganar tana tura masa wayarta. Ya ɗauki wayar yana dubawa, kawai ya kwashe da dariya. Ta zuba masa ido tana kallon sa, ya ce "Kina da haƙuri da kawaici a kan komai, amma banda kishi kenan? Aishikenan gaskiya ne Safiyya ita ce wadda ake son haɗa ni da ita, ni kuma ke nake so, shiyasa na ce miki akwai ƙalubale, ko ba komai safiyya ta saka na gane in da ki ka dosa, yanzu zaɓi ya rage naki sweetheart, ki kula da ni sosai kar Safiyya ta ƙwace miki ni, kin san zuciya na son mai kyautata mata, ke kin ce ba kya so na, safiyya kuma tana so na, ki zage damtse kar ki bari a ƙwace ni, i so much love you baby" Ɗaga ido tayi ta kalleshi, ya ga kamar hawaye ne yake shirin taruwa a idon ummi, ya tashi tsaye ya ce "Bari in tafi wurin safiyyan, tun da ita take so na, na san zata yi mini, idan kin tashi ki kirani" "Idan ka je kar ka dawo, a ɗaura muku aure yau" Gwalo yayi mata ya ce "Ki gama iyayin da tsiwar, raihan ɗin dai ki ke so". Ayshercool 08081012143 FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK. https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends Masu neman free books ɗina, da free pages duk akwai a kan watpad account ɗina. Irinsu Abduljalal Wata kissar sai mata Wuta a masaƙa Cutarwa Ƙanwar maza Gaba da gabanta Aƙidata Ruɗin ƙuruciya Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata. 08081012143. And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link. https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels Ayshercool. PAID ADVERT!. Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi. Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku Oll types of Turaran wuta Sandal Halut Irik Difur Gab Gab Kajiji Habil Nabak Humra Kulakcha Dilke da kalta Kayan Garan jiki Muna turara Kaya Kujerar garan jiki Kannada Madarorin turare masu kamshi Man garan gashi Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921 *TALLA!TALLA!TALLA!* *INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*. *BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU* *MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA* BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI.                         *CUTARWA* *BRIGHT PENS* (FREE BATCH) *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* 36 MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH. Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe. FOLLOW AND SHARE AYSHERCOOL 08081012143 MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH. Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe. AFUWAN BAN YI EDITING BA 36 Ya fice daga shagon yana murmushi, ta iya ɓoye fushinta da damuwa, amma ta gaza ɓoye kishinta. Yana tuƙi yana tuno fuskarta, wai har da yin fushi saboda shi, fushi sosai kishinta ya fito. Ya shafi gemunsa ya ce "Ina sonki sosai salma, in sha Allah idan na aureki ba zaki sake yin kukan damuwar rashin wani abu ba" Ummi kuwa, tayi shiru tana tunani, tare da ganin kamar tayi wauta raihan ya gano tana kishinsa, tayi guntun tsaki za ta cigaba da aiki, kawai sai Safiyya ta faɗo mata. Sai gabanta ya faɗi, gaskiya ne akwai banbanci tsakanin budurwa da bazawara, amma ita babu abun da ya taɓa haɗa ta da Idiris har suka rabu, a take kuma tunaninta ya sauya da tunanin kar matsalar da ta faru da ita a farko ta sake faruwa da ita. Tayi shiru tana tunani menene mafita? Ita ba ƙawaye ba, mamanta kuma ba lafiya ba su yaya maryam kuma ba sabawa suka yi ba, ko da sun saba ma, ba zata iya gaya musu wannan lamarin ba. Ta din ga saƙe-saƙe a ranta, ta tuna duk da tsanar da Idiris yayi mata, larurar nan ta ƙara taka muhimmiyar rawa, wurin kashe mata aure, dan da ya samu abun da yake so, da sai ya gama moreta kan ya saketa, ta tuna yadda ya din ga ƙoƙarin haike mata tana yarinya, take ta kawar da tunanin, dan a duk lokacin da ta tuna har kuka take yi, yadda Idris ɗin yake lalubeta, ba ta jin a duniya ko zata yafewa kowa za ta iya yafewa Idiris, ba ta riƙe CUTARWA! idan an yi mata amma cutarwa irin ta iya da Idiris ba zasu goge a tarihin rayuwarta ba cikin sauƙi. Ta cigaba da tunani a irin wa'azin da take bibiya, mussman na malamai daban-daban da sauran shirye-shiryen gidajen rediyo, domin kasancewar ta ƴar jarida, ya sanya tana yawan sauraren Radio, da bibiyar labarai, ta fuskanci cewa duk soyayyar da namiji yake yi wa mace, idan aka samu naƙasu akwai matsala, ƙila ba lallai raihan ya jure ba ya auro safiyya su juya mata baya, kamar yadda aka yi wa inteesar. Sai kuma kawai ta ga abun banbarakwai, wai ace raihan ya aureta shi ne mijinta, ta haɗa shimfiɗa da shi, goɗai-goɗai da ita, kawai ta ji wata kunya ta sake kamata. A ƙarshe ta yanke shawarar yin haɗin da malamar asibitin nan ta taɓa bata, na kanumfari, citta, namijin goro da tafarnuwa, tun da maganin sanyi ne sosai. Aikin ma dai ta kasa mayar da hankali a kansa sosai, sai saƙe-saƙe, rayuwar aure rayuwa ce da ke buƙatar a zaunar da mace a karanta mata darussa daban-daban, ba kuma wai sai lokacin da aka kawo kuɗin aure aka saka mata rana ba, yakamata mace ta san wasu abubuwan, amma ummi ba ta da wani da zai zauna da ita ya buɗa mata, duk da daga ita har mijin nata ba wani mai yawan shekaru sosai. *** Yaya maryam ta kira dr. A waya,suna yi masa tunin ya kawo musu ummi, suka cigaba da shirye shiryen su na al'ada, ga mariya ma duk ta ishesu, har da koke-koke a kan a dawo da ummi. Ya ce mata so yake ƙarshen wata, tayi sallama da wurin aiki ya rage saura wata biyun sai ta dawo. Ya gaya musu yadda aka tsara bikin, ta ce a matsayin su na dangin uwa, zasu gabatar da nasu bukukuwan a nan maiduguri, sai su taho da ummin kano, suma su yi nasu. "Amma ina ganin kar ɗawainiya tayi muku yawa, ba sai kun yi ba, ku bari duk ayi a kanon" Ta ce "Haba baban ummi, ƴar mariyar ƙwaya ɗaya tal mu kasa bajinta a bikinta, a'a ka bari zamu yi mata bikk na gani na faɗa, sai mu taho da ita, da mu da abun da Allah ya yassare mana" Ya ce "To shikenan, in sha Allah zan kawota da kaina, amma saura sati biyu biki, zan zo na kaita gagarawa, ta je ta yi musu sallama, ta kuma basu katin bikinta" Yaya maryam ko sunan garin ba ta ƙaunar ji, balle wani abu da zai sake haɗa su da garin, ta kasa jurewa ta ce "Amma ba a iya aika musu ba, dole sai ta je" Dr. Ya ce "Na san abun da yake cikin zukatanku, amma ba a canzawa tuwo suna, dangin mahaifinta ne dole ku yi haƙuri" Ta ce "To shikenan, Allah ya kaimu ƙarshen watan, sai kun zo ɗin" Ya amsa mata da Amin. Raihan daga shi sai Hajiya da kuma Hajiya Aisha suke ta shirin bikin, sai Alhajin sa, tausayin ɗawainiyar da yake ta yi, ya sanya Salim ɗan shiga lamarin, yake taimaka masa da shawarwari, dan shi abokansa duk sun yi aure, raihan kuwa age mate ɗin sa wasu ma ba su kammala makaranta ba. Saura watanni biyu bikin ummi, dr. Ya ce ta haɗa kayanta, zata tafi maiduguri kamar yadda ya yi alƙawari. Ummi murna kamar ta taka rawa, dan dama jin ta take yi a matse a gidan nan, farida ta sakata a gaba da masifa iri-iri. Ta rubuta takarda ta kai wa manager na barin aiki, manager kamar yayi kuka, saboda sun saba da ummi sosai da sosai, kuma suna jin daɗin aikinta, ba ƙyuya babu ganin ido komai na ta tsakani da Allah, sai dai sun yi mata fatan alkhairi sosai da jin ummi za ta yi aure. Tana ta shirin tafiya maiduguri, raihan ya kirata a waya, ya ce mata manager yana nemanta, tayi mamakin yadda aka yi manager bai kirata ba, ya kira raihan, kai ka ce shi ma ma'aikacin su ne. Ko da suka je, manager ya ce yayansa ne yake son ganin ummi, su ɗan jira shi zai zo. Manager sai cewa yake "Shikenan tayi aurenta ta huta da nacinka, ko gidan nata zaka din ga bin ta kana takura mata?" Raihan yayi wani irin murmushi ya ce akwai wanda ya isa ya raba ni da ummina ne? Kullum ina gidanta, ko kuma ka bani ƙanwarka na aura a haɗa mu biyu" Manager ya harare shi ya ce "Aikuwa da mijinta ya zaneka saboda hayyatarka, in baka ƙanwata kai wa zai maka aure yanzu? Raihan da kana ganin ka fi ni girma gani ka ke kai wani babba ne ko? In sake jin ka yi maganar auren nan, sai na zaneka" Wata irin kunya ta kama ummi, ta san da kunya idan ya bayyana raihan za ta aura, dan manager ya ɗauka kawai ɗan uwanta ne, irin sako da sakon nan. Raihan kuwa ya din ga dariya, ya ce "Zan baka mamaki kwanan nan" Shugaban wurin ne ya yi sallama, da yaransa suka amsa masa, ya samu wuri ya zauna suka gaggaisa, ya ɗan yi musu raha kasancewar sa mutum mai barkwanci. Ya ce "Ummi yanzu haka zaki tafi ki barmu, mijin ba zai bari ki cigaba da zuwar mana ba?" Ummi ta sunkuyar da kai tana wasa da yatsunta. Raihan ya zuba mata ido ya ji me za ta ce, amma tayi shiru. Ya yi ta yi wa ummi nasiha a kan zaman aure, ba tare da sanin da angon a wurin ba, sai dai raihan ya fara jin haushin yadda manager ya tsare ummi da ido, yana yi mata faɗan kamar mai rarrashinta. Bayan sun gama ya ce ya bawa ummi kyautar sabon fridge babba, da kuɗi dubu hamsin da certificate na karramawa saboda gaskiya da riƙon amana, da kuma ƙoƙarin da tayi wurin cigaban wurin. Raihan cikin girmamawa ya ce "Masha Allah, mun gode sosai da sosai, Ubangiji Allah ya saka da alkhairi, ya sa afi haka" Ummi ma godiyar take yi masa, ta san kuɗin fridge ɗin nan ba kaɗan ba ne ba, ga kuma kuɗi da ya bata. Manager ya ce wa raihan "Ka gani, haƙuri mai tarar da rabo, da ba ta raina 15k ba, ga rabon da ta tarar nan, ka canza hali raihan. Ko kuma tun da ta tafi kai ka zo mu baka aikin" Ya harari manager ya ce "Ba zan yi ba" Har da masu kai fridge ɗin aka haɗa ummi, masinjojin su. Ummi ta kira dr. Ta gaya masa, ya din ga murnda sanya albarka ya ce zai je yayi musu godiya. Ana gobe ummi za ta tafi maiduguri, raihan kamar yayi mata kukan ba ya son ta tafi, saboda zai daina ganinta a kai-a kai, sai dai yayi mata alƙawarin zuwa ya gaida mama. Haka zalika ya tura mata kuɗi a account ɗin ta, ya ce idan ya tashi zuwa maiduguri zai taho mata da kayan fitar biki. Suna zane suna hirar, wayar ummi ta fara ringing, ta ɗaga wayar, sai ya ga ta yi shiru tana kallon sa, amma ba ta ce komai ba. Kawai sai ya tsargu, ya karɓi wayar ya saka a hansfree. Muryar Safiyya ya ji, tana ta zazzaga rashin mutunci, da kalaman muzantawa ga ummi. Jin ummi ba ta ce komai ba ya sanya safiyya cewa "Malama ba magana nake yi miki ba?" "Da raihan ɗin ki ke magana ba ummin ba" hankali a tashe ta kashe wayar, tana salatin Allah ya rufa mata asiri. Ya kalli ummi ya ce "Dama haka take kiranki tana ci miki mutunci ba ki gaya mini ba?" Ummi ta ce "To me zan ce, kullum sai in ƙare a kan ƙara, ni ba zan iya ba tun da ka ji yanzu da kanka shikenan, dan Allah idan zaka aureta ka aureta amma ni ta daina zagina" Ya jinjina kai ya ce "Ina fatan dai ba shiru ki ke yi mata ba?" "Ni mu bar wannan zancen bana so" tayi maganar tana zumɓura baki, ya ɗan ƙura mata ido, kishin ne yake damunta, dan haka yayi mata shiru kawai. Daga wurin ummi da niyyarsa ya je gidan su safiyya, sai dai ya fasa ya tafi gida kawai. Ummi ta tattara muhimman kayanta, ranar tafiya ta je yi wa farida sallama, amma ta ka da baki ta ce mata Allah ya raka taki gona. Mami na ta sake maimaitawa raihan idan ya kuskura ya kashe kuɗi sosai a harkar auren ummi, sai ta ci masa mutunci fiye da yadda yake zato. Kwana biyu da tafiyar ummi maiduguri, Raihan ya je gidan su safiyya, anty rakiya har ta fara yashe baki, tana cewa "Babban mutum barka da zuwa, yau kai ne a gidan namu?" Ya ce "Eh, safiyya fa" Ta ce "Ahh wurin mutuniyar aka zo kenan, to bari na yi mata magana" Kasancewar Safiyya ta san abun da ta aikata, ya sanya gabanta faɗuwa ta ce ba zata ba. "Dan ubanki abun da muke neman zaki ce ba zaki ba?" Kamar za ta yi kuka ta ce "Ni fa tsoro nake ji, na gaya miki abun da ya faru" "To sai ki bari kanki ya kulle, ba mace ba ce ke? Guda nawa raihan ɗin yake banda ma ya jajibo aure? Tashi ki je dalla" Har ta shiga falon tv yake kallo, bai ko ɗaga kai ya kalleta ba, sai da ta zauna ta fara gaishe shi ya amsa, ya tambayeta ya makaranta ta ce masa lafiya ƙalau, sannan ya kalleta ya ce "Safiyya na san kin san abun da ki ka aikata, to ki sani, ba zuwa na yi bin ba'asi ba, kuma ba wani ya gaya mini ba, ta gaya mini na farko na kawar da kai, ban zaci irin wannan zagin ki ke yi mata ba, to ba sa'arki ba ce ba, kuma hakan da ki ke yi ba zai canza komai na batun aurena da ummi ba, wallahi idan ki ka sake kira mini mata ki ka ci zarafinta sai na gwada miki waye raihan, ba ruwana da wani zumunci sai na ɗaureki an ci tarar ki, na gaya miki. Ni ba ƙyale-ƙyale nake bi ba, mutunci, tarbiyya da soyayyar da nake yi mata ya sa zan aureta, kalli jikinki kowa ya gama gani, ba shigar mutunci a tuninki wannan ce wayewa safiyya? Dan an ce miki matar da zan aura kidahuma ce, ni a wurina hakan ne wayewa, kar ki bari abun da ki ka yi ya taɓa zumuncinmu, dan bana magana biyu, idan kuma Anty na da kuɗin belinki ki cigaba da kiran Salma kina ci mata mutunci tun da baki da kunya" bai ko tsaya yin sallama da anty rakiya ba, ya tashi yayi tafiyarsa. Aikuwa kan ya je gida, tuni sun sanarwa da mami, yan zuwa ta dirar masa da masifa tare da kashedi iri-iri, ciki har da barazanar sanyawa a fasa auren sa da ummi, tare da jaddada masa cewar aurensa da safiyya ba fashi. Ummi kuwa yadda su yaya maryam suke kula da ita da gyarata, har gajiya ta fara yi, a murza mata wancan, a shafa mata wannan, gashi aka hanata aikin komai, kullum tana kauwwame a wuri ɗaya, daga ci sai sha, banda kayan magungunan gyaran da ake ta yi mata. Tulin turarukan wutan da ake ta haɗawa kuwa, kai ka ce ci za ayi, ga uban kayan kitchen. Ummi har hawayen daɗi tayi, saboda irin so da ƙaunar da dangin mahaifiyarta ke nuna mata, gashi dai ba wani ƙarfi ne da su ba, amma sai zuciya da ƙoƙari. Ga isasshen lokaci da ta samu tare da mama, ga isasshen abinci mai kyau, komai na ta daban. Saura wata guda biki, raihan yana ta shirin zuwa maiduguri, yana zaune suna shawara da hajiya, a kan yadda abubuwa zasu gudana, ya haɗa akwati guda na kayan fitar biki kawai. Salim yana zaune sai dai bai tsoma musu baki ba. Sai daga baya ya ce "Wannan akwatin ɗaya kawai zaka kai sai ka ce tsiya, ba zaka yi lefe ba?" Cikin sanyin jiki ya ce "Mami ta hana, ta ce bazawara ce, wai kuɗin auren da aka kai ya isa, shi ne na ce bari na yi mata kayan fitar biki, lefen idan ta je gidana na yi mata, amma kalli kayan ka gani masu kyau ne fa" yayi maganar yana buɗe masa akwatin. Tabbas manyan kaya ne sosai da sosai na alfarma. Salim ya yi ajiyar zuciya ya ce "Idan ka kai musu sai dai ka yi musu bayani, na ji ka ce maiduguri zaka kai mata, ana yi wa iyaye akwati fa su ma, dole ka yi ƙoƙarin fitar da su kunya, aurensu da tsada sosai" Hajiya ta ce "Kai a ina ka sani?" Ya amsa mata da "Abokina umar ɗan can ne ai, kuma ƴar can ya aura, ni da shi muka din ga shirin bikin ai" Cikin marairaicewa raihan ya ce "To ka taimaka mini mana nima" Ya girgiza kai ya ce "Bana son babarku ta zo ta ce ba a kyauta ba" Hajiya ta ce "Ba ƙaninka bane ba? Babu abun da za ta ce" Haka kuwa aka yi, dan sai da suka sake sayen akwati, aka zuba atamfofi da shadda, wanda ake yi wa iyaye, sannan ya gaya masa zai bayar da kuɗin turaren wuta. Gwiwar raihan ba ta yi sanyi ba, dan shi a ganinsa komai zai kashe wa ummi bai faɗi ba. Yadda raihan ɗin ya din ga yi wa salim biyayya, ya sanya da Hajiya ta lallaɓa shi ta ce su tafi tare maidugurin bai yi musu ba. Can Maidugurin ma da ummi ta ce musu raihan zai zo, aka din ga shirye-shiryen tararsa, dan bai gaya mata da Salim zai zo ba ma. Mami ta so hana tafiyar nan, amma Alhaji ya taka mata burki, ya ce babu abun da zai hana raihan zuwa maiduguri, tun da matarsa a can take. Kasancewar ana idar da sallar asuba suka tafi, ƙarfe sha ɗaya na safe suka sauka. Suka bi adress ɗin da ummi ta basu har gidan suka je. Kasancewar sun yi shigar kamala, daga shi har Salim, hakan ya ƙara musu kima a wurin ƴan uwan ummi. Sai rarraba ido kawai yake yi ya ga ummi, aka kawo musu abinci na alfarma. Sun kai a ƙalla awa guda, yaya maryam ta tsare ummi, ta hana ta zuwa, sai daga baya ta shirya cikin lafaya mai kyau, sai ƙamshin turare take yi, hujin hancin da suka yi mata, ta saka barimar azurfa, sai ƙyalli take yi a kan baƙar fuskarta. Da tayi sallama tare suka ɗaga kai suka kalli ummi, babu kunya raihan ya kafe ta da ido. Salim ya jinjina kai a ransa ya ce "Lallai yaron nan akwai tsaurin ido" Ummi ta wani ƙara cika sosai, ga wani irin ƙamshi da ya cika ɗakin. "Oyoyo sweetheart" yayi maganar cikin sanyin murya. Durƙusawa tayi har ƙasa ta gaida Salim, ya amsa mata fuskarsa babu yabo ba fallasa. Ta juya wurin raihan ma ta gaishe shi, ya amsa yana washe baki. Ya ce "Tun da ga yaya salim, akwai kuɗi a jikina, sai a ɗaura yanzu kawai" hararsa tayi ta samu wuri ta zauna. Salim ya mayar da hankali a kan wayarsa, kamar bai san suna wurin ba, raihan kuwa ya rasa control ya din ga zuba a gaban Salim, ummi kuma kunya kamar ta nutse. "Baby me mama take baki ne? Kin ƙara ƙiba, kalli skin ɗinki" "Ni fa bana son ƙibar nan" ta faɗa a hankali. "Ni kuma ina so, baki ga kyan da ki ka ƙara ba, kin ji ƙamshin da ki ke yi kuwa? Anya zan iya jiran lokacin nan, Innalillahi kin ganki kuwa? You look take away, ko dai in yi zamana a nan" Dukan da Salim yayi masa a ƙeyarsa ne, ya sanya shi yin shiru yana sosa kai. Ummi ta yi masa gwalo, ta ce "Bari na je n yi wa mama magana, mu shiga ku gaisa" ta tashi ta fita. Tana fita Salim ya ce "Kai dan ubnka a gidan sirikai fa ka ke? Wannan da bamu zo tare ba me zaka yi?" Raihan ya ce "Bakomai" Yayi ƙasa da murya ya ce "Zaka ƙara da kuɗin gyaran jikin da ake yi mata, kara fa aka yi maka da duk ba ta tambayeka ba, zaka saki bakin aljihu tun da ɗiyar ƴan maiduguri zaka aura" Raihan ya ce "To ai duk ba ta gaya mini ba" Salim ya ce "Ni yanzu na gaya maka, kuma wannan ginin da ka ke yi, ka je ka ce wa Alhaji ya saya ko ka bashi jingina, ka samu gida mai kyau ginanne ka saya" Raihan ya ce "To ai ina son gidan sosai " "To ka ce wa Alhaji ya baka gudunmawar bikin, ka ƙarasa" Raihan ya yi dariya ya ce "Haka za ayi yaya" Ya ɗaga masa gira. Ummi ta ce "Bisimillah ku shigo" Suka tashi suka shiga, suka din ga gaisawa da mutanen gidan, ummi tana gabatar musu da kowa. A ɗakin mama suka yi sallama, suka zazzauna, ta din ga murmushi tana amsa musu gaisuwar. Ta kalli yaya maryam ta ce "Yaya, wannan suwaye?" "Sirikanki ne, wannan ne zai auri ummi" Sai tayi dariya ta rausayar da kai ta ce "Ummin za a yi wa aure yanzu? Ai tayi ƙarama da yawa" Maryam ta ce "Wai ke ummin haryanzu a kan cinyarki take ne tsawon shekaru ba ta girma ba?" Ta kalli raihan ta ce "To kai ba ka ga munin na ta ba? Iya ta ce mummuna ce babu mai aurenta" Raihan ya ce "Haba mama, ummi ba mummuna ba ce ba, kalleta fa ki gani tubarkallah masha Allah" Ta ce "Yauwwa, da ma na faɗa, wani zai ce yana son ummi a haka, amma iya ta din ga yi wa ummi ba'a, har sauran yaran gidan, su yi ta ce mata mummuna ko wasa da yara ba ta yi, kuma duk iya ce ta janyo, da ta tsawatar ai ba za su yi mata ba ko?" Raihan ya ce "Gaskiya ne, amma ummi ai mai kyau ce, ga ilimi da tarbiyya, ta cancanci a so ta" Yaya maryam ta ce "Dan Allah ki daina zancen nan da ya wuce" Salim ya ce "Kamar tana jin daɗin hirar, ki ƙyaleta" Mariya ta sake cewa "Ka san har malaman makarantar su ummi, wai su yi ta ce mata baƙa, na yi ta kuka, ko ace idonta irin na mayu, da ta fita yara su yi ta cin zalinta, shiyasa ni da babanta mu yi ta sonta, ba ka ga yadda yake son ta ba" Raihan ya ce "Allah sarki, mu ma muna son ta sosai" Ta kalli Salim ta ce "Ka ga yadda kakarta ba ta son ta ko? Amma bayan mutuwar baban ummi, matar nan ta ƙwace mini ummi, ba fa iya kula da ita take yi ba, an ce sun azabtar mini da ummi sosai da sosai" tayi maganar tana share hawaye. Salim ya ce "Ki yi haƙuri ki daina kuka dan Allah". Ta kalli raihan ta ce "To ka ga dai yarinya ce, dan Allah ka kula da ita sosai, ka din ga ba ta abinci, idan magariba tayi a saka mata kayan sanyi, cikin dare ma a tashe ta tayi fitsari" Ya ce "Duk za ayi mama, ai ummi yarinya ce kyakkyawa, duk za a din ga kula da ita" "Eh, to amma ban bar maka ita ba fa, zaka dawo mini da ita" Mama ta din ga zuba, suna hira da raihan da Salim, duk rashin sakin jikin salim, suka din ga hira da mama, wani abun idan tana gaya musu, sai tayi kuka, wasu abubuwan ma duk ummi ba ta san sun faru ba. Har da tambayar maryam, wai anya Salim da raihan ba su ne jaririn da suka haifa ba aka ya ce ya mutu. Gashi dai ba ta da cikakken hankali, amma a nutse take, malam kakan ummi, ya din ga yi musu nasiha, tare da gaya musu muhimmancin riƙe addu'a. Salim suka ba su kayan da suka zo da su, Malam ya ce ai ba su suka riƙe ummi ba, dan haka babu buƙatar kawo wannan kayan. Malam akwai kwarjini, ya kasa magana, Salim ne ya tausasa harshe tare da nuna masa cewar ba su takura ba, duk abun da suka yi wa ummi ta cancanta. Kuɗin turaren wuta da na gyaran jiki, suka danƙawa yaya maryam masu kauri. Mama har bakin mota ta raka su, suna cigaba da hira. Ummi ta ji daɗin karamcin da suka nuna wa mama, mama har da tambayar yaushe zasu kuma zuwa? Su faɗi abun da zata dafa musu. Yaya ɗanlami ya ce "Ban da larura ma, yaushe mutum zai zauna ya yi ta zuba da sirikai" Su raihan suka koma kano, cikin farinciki da tausaya wa mama da irin abubuwan da ta din ga faɗa game da rayuwar ummi. Har suka je gida ummi na kiransu na jin yaya suka je gida? Mama sai zancen su raihan take yi, ko sunansu ba ta sani ba, tun da Allah ya sa ta haɗu da ummi, bakinta ya buɗe tayi ta surutu amma da ummi take yi, sai kuma su Salim da suka zo. Da daddare bayan su raihan sun sauka kuwa, ya takurawa ummi da waya, dan duk taka tsantsan ɗin sa sai da ya kusa kauce hanya, sai dai ummi ta yi masa shiru. Kwana biyu da komawar raihan kano,  Salim da kansa ya samu Alhaji ya tsutsiye shi, wai me zai bawa raihan na gudunmuwa. Alhaji ya ji daɗin kulawar da Salim ya bawa raihan a kan aurensa, kuma ya lura raihan ɗin ne bai canza masa daga biyayyar da yake yi masa ba, duk da yana da wani muƙami ba. Alhaji ya ce "Ni za a yi wa solidarity?" Ya ce "A'a ginin da saura ne, kuma saura wata guda biki, za a kai mahaifinta ya ga gida, kuma da kai da hajiya bamu ga gudunmawarku ba" Alhaji ya yi murmushi ya ce "Na tsaya na ga iya gudun ruwan sa ne, kuma yayi ƙoƙari sosai da sosai, kuma babban abun da ya burgeni, duk faɗi tashin da yake yi, bai nemi taimakona ba, bai kuma ci amanar da na bashi ba, ya ɗaukar mini kuɗi babu izinina ba, dan haka za a san abun yi, kar ka damu" Ya ce "Ok, mun gode, dan Allah a bashi da kauri sosai" "Za a duba, Salim na ji daɗin ƙoƙarin da ka ke yi masa, ka yi playing role ɗin ka na babban wa, saura kuma kai ma ka nutsu ka yi naka auren" Salim ya ce "Raihan, duk da wasu abubuwan da mahaifiyarsa take yi, ina kallon yadda yake ɗawainiya da mahaifiyarmu, duk da yadda muke ɓata mata rai wasu lokutan, shi sanyin idaniyarta ne, yana ƙoƙari a kan mahaifiyarmu sosai, amma a cigaba da yi mana addu'a" bai jira me Alhaji zai ce ba, ya fita. Alhaji ya ce "Tabbas raihan babban mutum ne, amma akwai dattaku kam" Da Alhaji ya tashi, a account ɗin Salim ya tura masa kuɗin gudunmuwar auren raihan, kuɗi masu kaurin gaske. Nan da nan aka ƙarasa ginin raihan, suka kai Alhaji tare da Dr. Rana ɗaya suka gani. Jikin dr. Yayi sanyi, gado biyu ya yi wa ummi, da dining da kujeru saiti ɗaya. Sai dai falukan ummi uku, bedroom huɗu, sai kitchen da sauransu. Alhaji ya ja dr. gefe ya ce masa "kar ka damu, ka saka abun da Allah ya yassare maka, zan ƙarasa ba tare da kowa ya sanu ba, ai ana ƙoƙari sai godiyar Allah" Saura sati biyu biki, Raihan ya koma maiduguri ya kai wa ummi katin biki, ya ce ko akwai wanda za ta rabawa a kano ta ce ita ba wanda za ta bawa. Raihan ya tafi da kwana ɗaya, dr. Ya je, ya ɗauki ummi zuwa gagarawa, ta kai musu katin bikin da kanta, in da ta ji daɗi, sai ya tafi da  noor. Kamar kullum, tarbar da ta saba samu ita ta samu, sai dai sai kallon ummi suke yi, ta yi kyau sosai da sosai, a nan dr. Ya gaya wa iya cewar ya gano garin su mariya, kuma ummi tana can, sai da suka yi faɗa sosai da iya a kan hakan. Ummi suna zaune, wata yarinya ta shigo za ta yi sa'ar noor, kallo ɗaya ummi tayi mata ta gane ta, saboda kamar da take yi da hindu matar Idris. Iya ce ta hau zagin yarinyar tana tambayarta daga ina take?. Cikin fitsara yarinyar ta ce "Tasha na bi sajida sayar da shinkafa da wake na tayata ta san mini" "Saboda matsiyaciya ce ke, sai kin tona mana asiri?" "Tun da aka bar ni da yunwa, ba a ƙaunata dole na ciyar da kaina". Ganin da Yarinyar ta yi ummi na kallonta, ya sanya ta ce wa ummi "Ina wuni?" "Lafiya ƙalau ya ki ke?" Ta ce "Lafiya ƙalau" Ummi ta ce "Zo mana" ta ƙarasa gaban ummi ta durƙusa. Ummi ta ciro kuɗi a jakarta ta ce "Ungo, yo cefane sai mu yi girki mu ci, amma ki daina zuwa tasha ba mutuncin ƴa mace bane, kamata yayi ace kina makaranta duk da an yi hutu" Yarinyar ta ce "Ni da bana zuwa makaranta, ko abinci basa bani, sai idan babarmu ce ta bani, kowa ya tsane ni, ni ya zan yi ni na ce a haife ni haka?" Yarinyar tayi maganar tana kuka, duk da ba ta san ummi ba, amma ta ji hankalinta ya nutsu da ita. Ummi ta fuskanci in da zancen ya dosa, ta ce wa noor "Rakata ku yi cefanen, sai ayi girki kowa ya ci" Iya na kallonsu ba ta kula su ba. Kusan mintuna talatin, ummi ta tayar da salla, ta ji sallamar su noor, sun dawo, sai dai suna shigowa ba daɗewa Idris ma yayi sallama, kuma bai yi wata-wata ba, ya hau yarinyar ta sa da duka. Ihu take yi tana neman taimako, ummi ta yanke sallar ta fito da sauri, ya saka itace yana ta jingar yarinyar, har bakinta ya fara kumfa. Ummi ta hankaɗe shi, ta riƙo ta, bai san wacece ba, ya kuma kawo itacen yana ƙoƙarin janye yarinyar, a fusace ummi ta tsinka masa mari, da ya sanya shi ɗaga ido ya ga wacece. "Jahilin ina ne kai? Azzalumi mara imani, ƴar ta ka ma baka ƙyale ba, dabban ina ne kai idris?" Ayshercool 08081012143                            *CUTARWA* *BRIGHT PENS* (FREE BATCH) *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* 37 MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH. Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe. FOLLOW AND SHARE AYSHERCOOL 08081012143 MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH. Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe. *Alhamdilillah ala kulli halin, ina amfani da wannan damar, wurin isar da ɗimbin godiyata ga ƴan uwana marubuta, tarin masoya makaranta, da sauran al'ummar da suka yi mini ta'aziyyar rashin kakata, ina fatan Ubangiji Allah ya jiƙan magabatanmu baki ɗaya, ya kuma bar zumunci, yayi mana jagora a rayuwa baki daya, Allah ya sanya kaburburan magabatanmu ya zama dausayi daga aljanna, idan tamu ta zo ya sanya mu cika da imani* 37 A razane yake kallon ummi daga sama zuwa ƙasa, iya kuma ta miƙe tsaye da sakakken baki ta kasa magana. Ummi ta durƙusa ta ɗago yarinyar da take zubar da wani irin yawu daga bakinta, saboda wahalar duka. Noor kuwa na gefe tana tsuma, duk da basu saba ba, tare suka yo cefane, har noor ta bata shawarar su sayo taliya sai tafi sauri, tun da ummi ba ta gaya musu me zasu sayo ba. Suna tafe a hanyar ta kalli noor ta ce mata "Ya sunanki?" "Sunana mariyatul kibɗiya, ana ce mini noor" "Masha Allah, sunanki me daɗi" Noor ta ce "To ke ya sunanki?" "Wai hajara, sunan kakata aka saka mini, ni kuwa na ce wallahi bana so, na canza suna ake ce mini Nana" "To meyasa ba kya so, ba kakarku ba ce? Au kamar sunan iya ne ai ko?" Nana ta ce "Eh mana, baki ga yadda ta tsane ni ba, ni ma kuwa na tsaneta, yauwwa idan kuɗin yayi ragowa muka sayi kifi, ba za ta ce komai ba?" Noor ta ce "Ai idan ma kifin ki ka saya da duka kuɗin babu abun da za ta ce miki, yaya ummi fa babu ruwanta" Nana ta ce "Na gani, kin san wani abu, wallahi ta burgeni, ga muryarta mai daɗi, a nutse take komai, sau ɗaya na taɓa ganinta sun zo da kawu yahaya, ƴar sa ce?" Noor ta ce "Ke, ni ma fa ƴar sa ce, iya duk kakarmu ce kenan? To ya aka yi ban sanki ba" Noor ta ce "Ni ba kakata ba ce ba, kakana ta haifa dan haka babu abun da ya yi mini zafi da ita" Wani yaro suka haɗu da shi a hanya ya ce "Nana, ana ta nemanki a gida, wallahi ki je gida baba yana nemanki" "Ba zani ɗin ba, in je a jibgi jaka, gidan iya zan je, tayi baƙi za a dafa abinci, sai na ci na dare zan dawo gida" Mamaki ya kama noor, jin amsar da ta bayar, da aka ce babanta yana nemanta. Sai dai sun shiga sashin iya sun yi sallama babu jimawa, Nana ta fara ɗaukko kwanukan da zasu yi amfani da su su yi girkin, Idris yayi sallama da itacensa a hannu, ya fara jibgar Nana. Marin da ummi ta yi masa ba a kan sa hankalinsa yake ba, face shaiɗan da ya shiga ƙawata masa ummi, hijjabi ne a jikin na roba, dan haka ya kwanta a jikinta, gaba ɗaya tamkar ƙibarta ta koma ƙirjinta, haka da ta juya baya ma, kamar an aunata an dasa mata ƙugunta. "Ke yanzu lalacewar taki har ta kai haka ummi, Idris ɗin ki ka mara?" Duk da jikin ummi tsuma yake da tashin hankali da tsoro, dan ko a mafarki ita kanta ba ta taɓa zaton aikata abu makamancin haka ba. Amma ta ji zuciyarta ta bushe, ta ce "Iya yaushe zaki bari kanmu ya haɗu a matsayin iyalanki ne? Kalli fa dukan da yake yi mata? Mutum ba dabba ba" Cikin ƙwarin gwiwa, da son ɓoye halin da ya faɗa ya aro jarumta ya ce "Ni zaki mara? Kin san abun da ta yi ne?" "Ina ruwana da abun da tayi maka? Barewa za ta yi gudu ɗanta yayi rarrafe ne? Abun mamakin daga haɗuwata da yarinyar yau, har ta fara faɗar irin damuwar da take ciki, look at her, just an innocent kid like me before" Tayi maganar cikin matuƙar rauni, hawaye na zuba daga idonta, tana share wa yarinyar hawayenta da wannan yawun, da daƙalƙallen hijjabin da yake wuyan yarinyar, sautin kukan na ta ma ya kasa fita sai sheshsheƙa, santaleleliyar yarinya kai da ganinta ka san fara ce, azabar datti da rashin kula duk ya dafar da ita. Bilhakki ummi ta rungumeta tana kuka, wanda kukan na ta yana da alaƙa da tuna irin baƙar rayuwar da ta yi a baya. Iya kuwa ba ta taɓa zaton ummi ta yi kilewar da zata iya gaura wa Idiris mari har haka ba. Hashim ne yayi sallama tare da matarsa, ya ji labarin ummi ta zo, ya ce bari ya zo tare da matarsa su gaisa, dan ba su taɓa haɗuwa ba. Amma ya tarar da mutane cirko-cirko, ga Idiris a gefe yana ta huci, ummi a durƙushe da yarinya tana kuka. Ya kalli mutanen ya ce "Lafiya kuwa? Meyafaru ne?" "Ai magaji ba lafiya ba, ƴar daba ta zo mana gida, ashe bayan lalacewa a birnin ina ga ko dai shaye-shaye ko daba ta fara, wai ace ummi ta ɗaga hannu ta zabge Idris da mari" Saroro yayi ya ce "Wane irin mari kuma ana zaune ƙalau?" Iya ta ce"Au to ƙarya zan yi maka, ba gata nan a zaune ba?" Hashim ya ƙarasa gaban su ummi, ya ce "Ummi meyafaru ne?" Ummi ta kasa magana sai kuka. Ya ce "Nana meyafaru?" Cikin kuka yarinyar ta ce "Ƙawata na raka tasha, na tayata sayar da abinci, da ta gama ta bani na ci, shi ne babanmu ya biyoni yana dukana da itace" tayi maganar tana kuka. Magaji ya ce "Tabbas abun da ya baka tausayi, watarana zai iya baka tsoro, Allah ya kyauta, kuma wannan tsayuwar da ku ka yi duk ba mafita ba ce ba, dan Allah kowa ya watse " haka sai hashim ya sallami kowa. Suka gaisa da matarsa da ummi, ummi cikin kuka take yi wa hashim ƙorafin abun da yake faruwa a familynsu, na muzanta wanda wata ƙaddara ta same shi, ko kuma a ɗorawa mutum tsana babu dalili. Ya ce "Ummi, wannan abun da zan iya maganinsa, da tun a kan ki na yi, lamarin yafi ƙarfina, kuma har da sakacin iyayenmu, da son zuciya irin na iyayenmu. Ba irin nasihar da ban yi masa ba a kan kula da yarinyar nan ba, amma yaƙi. Ƙarewa ba ya kula da su da uwarsu, aka korota daga makaranta, uwar ta koma ɗora mata talla, aka tasamma lalata ta, idan ma an lalata tan ban sani ba, duk in da tayi sai tsangwama, na ce ya bani ƴar ya hanani, idan aka ɗora mata tallan sai ta sayar ta kashe kuɗin su yi ta rigima, abubuwan dai duk babu daɗin ji" Ummi ta dafe kai, tare da faɗin "Innalillahi wa Innalillahi raji'un" muddin ba a takawa wannan lamarin burki ba, ƴaƴa da yawa za su cigaba da shan wahala a gidan, idan har basu zo a yadda ake so ba. Ummi ta bata kuɗi, ta sayo sabulu ta yi wanka, ta bata kuɗin omo ta ce idan ta je gida ta yi wanki, ta ce washegari ma kan su tafi, ta zo ta karɓi kuɗin abinci. Nana ta din ga yi wa ummi godiya, ummi ta roƙi Hashim a kan dan Allah azo mata da Nana kano lokacin bikinta, yayi mata alƙawarin da yardar Allah za a taho da ita. Faranti ɗaya suka ci abinci da ummi, da Nana, nana na ta basu labarin irin azabtarwar da ubanta mahaifi yake yi mata. Ummi a ranta ta ce "Mugunta idan kana yi, ba ka yi wa kanka ba, ai baka iya ba' ta rubuta wa Nana lambar wayarta, ta ce gashi nan ta ɓoye, idan tana buƙatar wani abu, ta saka wani ya kirata. Iya ta din ga bugun cikin ummi, sai ta ji yadda suka haɗu da raihan, da kuma sana'arsa amma ummi ta ƙi gaya mata. Sai dai da dare yayi, Nana ta ce a wurin Ummi za ta kwana, idan ta je gida babansu zai sake zaneta, buɗar bakin Iya sai cewa tayi ba zata kwana da ƙazanta a ɗakinta ba, sai dai ta tafi gidan ubanta ta kwana. Cikin tsiwa Nana ta ce "Sai ka ce wata tsiyar ce a ɗakin, ba dan anty ummi ba nima ba zan ce zan kwana a ɗakin nan ba, kuma in sha Allah sai ɗakin nan yayi gobara, kin ƙone a cikin sa" Iya ta ce "Laaa, ki gani a kan uwarki, tsinanniya" Nana ta ce "Wanda yayi zagi a kasuwa ya san da wanda yake" Ummi kasa magana ta yi, jin mummunan alkaba'in da ƴar ƙaramar yarinyar da ba ta fi sa'ar noor ba, ko sha huɗu ba su cika ba, take ja wa iya. "Oho, idan ma baki ƙone a ciki ba, ko dai ɗakin nan ya zama kabarinki, ko kina ji kina gani zaki barshi tun kina raye" Noor ta ce "Taɓ girma ya faɗi" Ummi ta ce "Shut up noor" "Ai ban ce komai ni" Ummi ta ce "Nana, iyan ki ke gaya wa haka?" "Kina ji fa yadda take tsine mini, ni me na yi mata take ce mini ƙazanta? Ba fa yau ta fara yi mini ba, In sha Allah kina raye sai kin ga ƙazanta a jikinki kuma ba zaki iya gyarata ba" Nana ta yi maganar cikin ɗaga murya tana kuka. Abun duniya ya ishi ummi, ta yi dana sanin zuwa gagarawa. Idris kuwa marin da ummi tayi masa bai yi masa zafin da abun da ya bijiro masa yake damunsa a kanta ba. Yana zuwa gida ya tarar da Hindu a zaune tana tankaɗe, ta saki nono tana shayar da yaro kamar akuya, duk sun zuɓe sun suɗe, ya ja uban tsaki ya shiga ɗaki yana zage-zage. Sai da ya shiga ɗaki ya tsaya ya yi shiru, wai ummi ce ta mare shi a kan ƴar sa, ummin da ya din ga cin ubanta a baya, wai yau ita ce da ƙwarin gwiwar tsinka masa mari. Hindu ba ta kula shi ba, ya hau zage-zage yana ci mata mutunci da ita da Nana. Da abun ya isheta ta ce "Kaga ni fa ban yi maka komai ba, ba zaka din ga zagina ba, Nana kuma ka je can ka nemeta, ni ma ban san gidan uban da ta tafi ba, dan haka ba zaka huce a kaina ba" "Ai koma menene ke ki ka ja, a can gidan Iya na sameta, ta ja mini mari shegiya watsatsiya" Hindu ta ce "kai ne babban watstste da ka kawota duniya, kuma ko waye ya mareka, Allah ya saka masa da alkhairi" suka din ga faɗa, ba ganin mutuncin juna, balle kima. Nana kuwa da ta je gidan, idiris ya kuma yinƙurawa zai daketa, ta fita da gudu, ba ta kwana a gidan ba. Dama dr. Yana garin, cikin gari ya tafi ya samu hotel ya kwana, da niyyar washegari ya mayar da ummi maiduguri sannan ya koma kano, a ganinsa haka shi ne ƙa'ida duk da abun da ya faru a baya, yakamata ace da kansa ya kai ummi gagarawa su kai musu katin aurenta. Da sassafe ummi da noor suka shirya, sai ga Nana da farar safiyar nan, dan a gidan iya tayi sallar safiya kamar yadda take cewa. Ummi ta yi ta mata nasihar ba a salla da safe, ta ce "Ai ba a gidanmu na kwana ba, babanmu ne zai sake dukana na gudu na tafi ƙasan teburin wani mai tireda, na kwana" Ummi ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un" tabbas idan ba a tsaya a kan yarinyar nan ba, to zata gagari kowa. Har ƙasan zuciyarta ummi take jin damuwa a kan Nana, kyakywar bafulatanar yarinya kamarta ɗaya sak da mahaifiyarta, amma ba kula. Tana kallon iya tana kallonta, amma ko kallo iya ba ta isheta ba. Ummi ta dafa musu tea har da madara, ga bredi da ƙwai, duk da cin mutunci da Iya tayi musu, bai hanata cin abincin da ummin ta sayo da kuɗinta ba. Gidan babu wanda bai san zancen marin nan ba, aka din ga surutu a kai. Allah ya taimaki ummi, da wuri kawu ya zo, dan kuwa tuni kawu Ilyasu ya kira shi ya sanar da shi abun da ya faru. Sai da Iya tayi ta faɗe-faɗen maganganu, tare da gaya masa ƙarya da gaskiya, amma ya basar da zancen, dan shi yanzu abun da ya dame shi, yadda zai samu sauran kuɗi, ya cika ya ƙarawa ummi kujeru. Suna tafe a hanya, yake bata labarin gidanta da raihan ya kai shi, ummi ta ce "Kawu kar ka wahalar da kan ka, ka yi abun da Allah ya yassare maka kawai" Ya ce "Haka ne, amma dai duk da haka dolena ne na fitar da ke kunya" "Na gode sosai kawu, ubangiji Allah ya ƙara arziki" Ya amsa mata da "Amin" Aka jima ya ce "Ummina, meya haɗaki da idris har ki ka mare shi? Na dai ji zancen ne amma ban yadda ba" Ummi ta sunkuyar da kai ta ce "Wallahi kawu ban yi tsammanin hakan za ta faru ba, ƙoƙarin ceton yarinyar nake yi, abun ya taɓa mini zuciya sosai da sosai, amma na yi dana sani sosai wallahi" Dr. Ya jinjina kai ya ce "Na fahimce ki ummi, amma ki kula sosai". "In sha Allah, amma kawu shikenan kowane family suna zamansu gwanin sha'awa, mu kuma shikenan idan ka zo ba a yadda ake so ba, sai a tsangwame ka, yarinyar nan zuciyarta a bushe take fa, za ta iya lalacewa" tayi maganar idonta na tara hawaye, dan sosai take jin abun a ranta. "Ummi, duk al'ummar da zata zauna cikin jahilci, dole a din ga samun irin wannan, bayan jahilci kuma har da son zuciya, sai dai fatan ke da nake saka ran Allah ya ɗaukaka, Allah ya sa ki zama silar gyaruwar komai" ta jinjina masa kai. Haka kawu yahaya yayi ta ɗawainiya, dan bai koma kano ba sai cikin dare, kuɗinsa duk sun ƙare, a harkar bikin ummi, iya labulayen da zasu isa gidan ummin, sai da aka yi masa estimating kusan dubu ɗari biyar, ya dage baya son daga ɓangaren raihan ace sun ƙarasa wani abun. Da safe yana zaune a falo, bayan ya karya yana waya, zai sayar da wani filinsa ya ƙara wa ummi kujeru, bayan ya gama wayar, Farida ta kalleshi ta ce "Wasu irin kujeru ne da sai ka sayar da filinka, ga ƴaƴa kana da su? Ba ka ce ka gama komai ba?" Dr. Ya ce "Ke ina ruwanki? Ke ki ka saya mini filin? Falonta uku na riga na yi kujera set ɗaya, dole zan nemi yadda zan ƙara mata" Waro ido tayi kamar za ta faɗi daga kan kujerar ta ce "Ban gane falo uku ba, ɗan wa za ta aura haka? Anya ka yi binciken sana'arsa kuwa?" Dariya yayi, yana kallon yadda hassadar ta, ta kasa ɓuya ta fito fili, ya ce "Ai ummana, Allah ya gwangwaje ta da miji, ni na san sana'ar sa kuwa, sai fatan Allah ya sanya alkhairi" Can maiduguri kuwa, noor ta sake sosai, tana hidimominta, gashi kasancewar mariya na son yara, kuma ta ji sunansu ɗaya, ya sanya noor da mariya jonewa, komai tare suke yi. Raihan yana ta turawa da ummi kuɗi, a ciki ta yi wa noor ɗinkuna ita da Nana, da kayan fitar biki, shi ma raihan ya na ta samun gudunmuwar biki, duk da ba wani babban biki ya ɗaukko ba, amma ya kashe kuɗi sosai da sosai. Ita kanta Ummi ta san ta gyaru, ta sha kulawa da gyara kala-kala daga wurin dangin mahaifiyarta. Aka shiga satin biki, suka din ga shagulgulansu a maiduguri, har ummi ta gaji, daga wannan sai wancan, aka yi aka gama, ana gobe ɗaurin aure, ranar Alhamis, suka taho kano. Sai dai dr. Ya aika Abdul, ya ce ya kai su tsohon gidansa, ya saka an gyara, a can za su zauna, su yi nasu taron bikin, saboda sanin halin farida. A yammacin da suka zo, raihan ya zo, suka kuma gaisawa da su mama, kamar ya sace ummi, tana magana tana lumshe ido saboda azabar gajiya. Ya ce "Madam, tun yanzu har kin gaji har haka?" A ɗan raunane ta ce "Ba zaka gane ba MD, a gajiye nake sosai wallahi" "Kar ki damu, akwai kulawa ta mussaman jibi in Allah ya kaimu da zan baki" tayi masa shiru. "Babyna am talking fa" taƙi kula shi. Ya sake cewa "Ina fatan da ki ka je gagarawan babu wata damuwa? Kuma ba ku haɗu da tsohon mijinki ba?" Ta ce "To meya kawo wannan maganar kuma?" "Saboda ina kishinki fiye da yadda ki ke tunani, duk da ɗan uwanki ne, ba zai sake saka ki a idonsa ba" "Saboda me?" "Saboda haka na ce" yayi maganar cikin isa, tare da tsareta da ido, sai da ta ɗan sha jinin jikinta. Ta tura baki ba tare da ta ce masa komai ba. Ya ɗora da cewa "Gobe in Allah ya kaimu da wuri mai yi miki kwalliya za ta zo, duk in da huɗu tayi, ki kammala shirinki, zamu zo ɗaukar ki". "Tom Allah ya kaimu" "Gobe in Allah ya kaimu i yanzu, kin zama matar Muhammad, inyeee babyn ba" zolayar raihan ta yi yawa, sai da ya sakata murmushi tana rufe fuska. Ya ce "Bari na tafi, ki je ki huta, ki ci abinci sosai da sosai" ta jinjina masa kai suka yi sallama. Washegari da sassafe ƴan gagarawa suka isa kano, sai dai babu Iya, dan cewa tayi ba zata je ba. Ranar juma'a tun sassafe, su Yaya maryam suka je kafin kaya, sai dai sun riƙe baki da ganin gidan ummi, gida ya haɗu sosai da sosai, ya ƙawatu kai da gani ka san an kashewa gidan kuɗi ba kaɗan ba. Ba ƙaramin murna ummi ta yi ba, ganin an zo da Nana, ƴan gagarawa a gidan dr. Suka sauka, su mama kuma suna ɗaya gidan. Bayan sallar juma'a, aka ɗaura auren Ummi da raihan, a kan sadaki naira dubu ɗari biyar. An sha surutu shi ma a kan sadakin nan, mussaman ƴan gagarawa, har da cewa dr. Zai aurar da ummi ga ɗan yankan kai, tana bazawara ana wannan bushashasha haka a aurenta. Manager yayi mamakin ganin wai raihan ne mijin da ummi za ta aura, dan ko da ya ga katin ma, bai kawo shi ne ba, dan Muhammad Muhammad Tahir aka saka a katin bikin. Duk in da ummi ta yi, noor da Nana ne ke biye da ita, su ne ƙawayen nata, can gidan su raihan Hajiya ce take hidima da jama'ar da suke ta shiga suna fita. Wani irin danƙareren leshi da raihan ya saya mata ta saka, ɗinkin doguwar riga, da mayafi, ba wani make up aka yi mata ba, komai dai-dai kalar fatarta. Idan ba an gaya maka ba zaka ce mama ba ta da lafiya ba, ta sha kwalliya cikin atamfa ita ma, tayi kyau sosai da sosai. Ƙarfe huɗu da rabi raihan ya aika motocin da zasu tafi da waɗanda zasu je walimar da za ayi. Daga baya kuma motarsa ta je ɗaukar ummi, ta yi kyau sosai da sosai, cikin tausaywa da soyayya yake kallon ummi. Ta shiga cikin motar da sallama, tuni ƙamshin turaren ta ya cika motar, ta sunkuyar da kanta ta ce "Ina wuni?" "My wife, legally sealed you now belongs to me Salma" yayi maganar yana riƙe hannunta. Tayi murmushi ta ce "Ka rabani da headmaster ko... Ba ta gama ba, ya riƙe hannunta da ƙarfi ya ce "Ki sake maganar wani a gabana ki gani, da kin aure shi in ba sai ya gaji ya sakar mini ke ba, idan na din ga sintiri a gidan ki har uwar ɗakinki" ƙunshe baki tayi tana dariya, haryanzu gani take kamar ba ita ba, wai raihan za ta aura, abun da mamaki. Babu mutane da yawa a wurin, an ci an sha sosai, sai dai duk da mayafi ne a jikin ummi irin na amare, daga sama har ƙasa, tana ta rufe jikinta, amma sai da raihan ya ji wani abu a ransa na kishi. Ana ta hotuna, a nan ƴan gagarawa suka ga mariya, tsaf da ita kamar ba ita ta haifi ummi ba, tsaf da ita gashi ta yi kyau sosai da sosai, shekara sha takwas rabon da a haɗu. Suka din ga gaisawa da facalolinta, ta kalli sa'adatu ta c "Ina Alhassan mai yi mini Albishir da mutuwar mijina?" Tayi tsuru-tsuru tana basar da zancen, dan ba su zaci ganinta a haka ba, sun ɗauka hauka take yi tuburan. Ana ƙoƙarin yin hoto, noor na ta ture Sagir, wai ya koma kusa da raihan shi ne ɗan uwansu, su kuma su ne ƴan uwan ummi, a kusa da ita za su tsaya. Zuwa sallar isha'i aka tashi daga wurin, noor da Nana suka shige motar Salim, noor ta ce "Bawan Allah dan Allah ka mayar da mu mukaɗai gida, kar ka ɗauki kowa, motar daɗi" kallonsu yake yi, har gara Nana akwai ƙauyanci a tare da ita, amma ya lura da noor, tun a wurin bikin tana da rawar kawai sosai da sosai. Ya kalli noor ya ce "Ke bana son surutu, ke ki shiga bayan mota, ke kuma dawo gaba" yayi maganar yana nuna Nana. "A'a ka barmu mu zauna a baya daukkanmu" "To ku nemi wani" Noor ta ce "A'a yi haƙuri, Nana ki koma gaban" suna tafe suna ta surutu ita da Nana. Nana tana magana tana fulatanci, Noor ta ce "Nana, Allah ya sa nima na auri irin yaya raihan, mai kyau kamarsa" Sai da Salim ya waiwaya ya kalli noor, ba ya tunanin ko fitsarin kwance ta daina take zancen wani miji. Suka yi ta surutu, ko gajiya ba sa yi, har ya kai su gida. Washegari aka yi wunin biki, da isha'i aka kawo motocin ɗaukar ummi, da mariya da yaya maryam da wasu daga ƴan uwan su, suka tafi da ummi gidan farida, domin yi mata sallama. Yaya maryam ta din ga yi wa farida godiya, saboda riƙe ummi da ta yi, sai wani cika take tana batsewa, ta zata za ta gan su ƴan ƙauye, sai dai ta ga sun sha dressing, sun yi kyau, tayi mamakin ganin babar ummi, ta ɗauka ita ma baƙa ce wuluk, amma ta ganta da haske kuma shar da ita. Dressing ɗin da aka yi wa ummi, ta din ga kallo, ita kanta a ƙasan zuciyarta ta san son zuciya ne ke sanya suke ce wa ummi mummuna, tana da baƙi ne dai kawai amma ba wani muni. Dr. Ya yi wa ummi nasiha sosai da sosai, ummi ta yi masa godiya tare da neman yafiyarsa, ya ce shi ba ta yi masa komai na laifi ba. Ƙarfe tara na dare, aka kai ummi gidan raihan, dr. Da kansa ya kaita a motarsa bayan yi mata nasihohi masu ratsa jiki, mutane sun yi santin gidan nan sosai da sosai, dr. Sai da ya cika ko ina, kitchen ɗin ta kuma su yaya maryam sun yi rawar gani, ga uban kayan turaren wuta duk an yi mata, komai nata sai masha Allah. Dangin mami da ta din ga ce musu ba ta da gata, sun ɗauka ba za a zuba mata kayan kirki ba, su samu na gori, amma suka sha mamakin kayan da dr. Ya zuba mata. Kowa ya watse, ummi idonta ko kuka ba ta yi ba, saboda ita a wurinta cigaba ta samu, ta bar wa farida gidanta, sai fatan Ubangiji Allah ya sassauta mata ƙalubalen gidan raihan. Sai sha ɗaya ya shigo, daga shi sai Salim da wasu mutum uku, da take kyautata zaton ƴan uwansa ne, suma suka yi musu nasiha, tare da addu'a zaman lafiya, suka watse suka bar su. Ya dawo ya tarar da ummi a zaune a in da ya bar ta, ya yi gyaran murya ya ce "Yaya" ta ɗago kai ta kalleshi yayi murmushi ya ce "Kin yi kyau fiye da kullum" ta sunkuyar da kanta ƙasa. Ya zauna a kusa da ita, ya miƙa mata hannunsa ya ce "Ɓalle mini" jikinta na rawa ta ɓalle masa maɓallan hannun rigarsa, ya cire babbar rigarsa, da ta cikin, ya shiga banɗaki yayi alwala, yayi mata umarnin yi ita ma. Bayan sun yi salla raka'a biyu, raihan ya daɗe yana yi musu addu'a, bayan ya kammala kuma, ya din ga yi wa ummi nasiha. "Salma, bayan gwagwarmaya daban-daban, Allah ya cika mini burina a kanki, ina da yaƙinin na kawo mace ta gari, kuma uwa ta gari ga ƴaƴana, ummi duk wani aure da nasa ƙalubale, amma in sha Allah, daga gareni babu ƙalubale, sai abun da ba a rasa ba, amma zaki yi haƙuri da wanda zaki fuskanta daga ƴan uwana, mu zama masu haƙuri da riƙe sirrin junanmu, kamar yadda na yi wa mama alƙawari, zan riƙe ki amana na kula da ke, in sha Allah zan yi iya yi na, Allah ya bamu zaman lafiya. Na san ba a za a rasa ɓacin rai a harkar auratayya ba, kin san halina wasu lokutan ina da zafi, amma ki zama mai yi mini uzuri, Ubangiji Allah ya bamu ikon kula da juna" ta amsa da Amin, ya tambayeta ko ta na da abun cewa ta ce masa a'a. Duk yadda yayi da ita ta saki jiki ta ci abinci, ummi fafur taƙi, shi yayi ciye-ciyen sa. Ita kuwa ummi wata irin fargaba da tsoro ne ya addabwa zuciyarta, abun da ya faru a aurenta na farko ne ya din ga ya dawo mata, tana ta fargaba da addu'ar kar ta sake cin karo da matsalar da ta faru a farko. Ya fita daga ɗakin, ya dawo da wasu kaya a hannunsa, ya ce "Ƙaraso" yayi maganar yana yi mata nuni da hannunsa. Ta tashi tana sinnewa ta ƙarasa, ya ɗaga mata wata doguwar rigar bacci, ja mai kyau, nasa kayan ma jajaye, ya ce "Ungo naki" Jikinta na rawa ta karɓa, wani irin girma da kwarjini ta ga raihan ɗin yayi mata. "Ki saka naki, bari na baki wuri" yayi maganar yana ɗaukar nasa kayan, ya fice daga ɗakin. Ta lura raihan yana son jar kala, ta din ga jujjuya rigar, a ranta ta ce "Taɓ ni zan saka wannan rigar kamar a turai, ba kunya kuma in kalle shi?' ta zubawa rigar ido, sam ba ta ji za ta iya sakawa ba, haka ya dawo ya tarar da ita, shi har ya saka nasa, kallo ɗaya tayi masa ta kawar da kanta, ya cika tasa rigar shirt ɗin cif, an rubuta i love you, a gaban rigar sai wandon ta ja 3quater. "Ya baki canza ba?" Yayi tambayar yana kallon ta. Tayi shiru ba ta ce komai ba. Ya ƙarasa gabanta ya ce "I understand, bari na taimaka miki" yayi maganar yana janyo mayafinta. "A'a dan Allah, yi haƙuri" tayi maganar kamar ta yi kuka. "Oya ki canza ina jiranki, dare yana yi" Ya juya ya sake ficewa, bayan wasu mintuna ya dawo, ta saka rigar amma ta yafa mayafin kayanta. A ransa ya ce 'Lallai aurenki na fari mijinki yayi fama da taurin kai' rigar iya gwiwar ta, tayi kyau sosai, bai takura mata sai ta sauke mayafin ba, ya kama hannunta suka bar ɗakin. Suka ratsa falo suka shiga wani ɗakin daban, an yi wa ɗakin ado na musamman, duk da a cikin fargaba take, ɗakin ya yi mata kyau sosai, ya yi wa komai adon jar kala. "Sai ka ce ɗakin amaryar indiya" tayi maganar a hankali. Yayi dariya ya ce "Duk wani abu na soyayya ummi, ba sai a wurin wasu ba, mu ma zamu iya idan har bai saɓawa addininmu ba, bai burge ki ba?" Ta ce "Yayi kyau sosai" ya yi murmushi, suka ƙarasa gaban gadon ya zaunar da ita, ya tashi ya kashe fitilar ya dawo da plate ya zauna a kusa da ita ya ce "Ki na buƙatar isasshen abinci sweetheart, ba zan bari ki kwana da yunwa ba, na kashe fitilar tun da kunyata ki ke ji, dan Allah ki ci" Sai a lokacin ummi ta tuna aurenta na fari, ko fara Idris bai shigo mata da ita ba, yau kuwa kazar da ta gani a ƙalla ta kai biyar, ban da kayan marmari da lemuka. A hankali yake lallaɓata yana ba ta a baki, kai ka ce wani babban mutum ne mai shekaru. Duk da ba da yawa ta ci ba, ta ji daɗin hakan, dan dama tana jin yunwa, hira ya ɗan din ga yi mata, kan ya bata damar ta kwanta. Sai dai ummi tamkar zuciyarta ta tsaga ƙirjinta, ta faso saboda tsananin tsoro da fargaba, da zunzurutun tashin hankali, duk da kulawar da ƙoƙarin kwantar mata da hankalin da yake yi. Shi har mamaki ta bashi, kamar wadda ba ta taɓa aure ba. Raihan ya nuna mata banbancin ilimi, da zunzurutun jahilci, banbancin dattaku da tarin wauta, banbancin wayewa da kuma ƙauyanci. Komai na shi cikin nutsuwa da aji yake gudanarwa, ba kamar yadda Idris ya yinƙurin haike mata, tamkar wani jaki ko mahaukaci ba. Ya nuna mata ita mutum ce, mai ɗauke da zuciya mai rauni a ƙirjinta, da ke buƙatar tausasawa da kuma kulawa tare da tarin soyayya, ba abar wulaƙantawa da cin mutunci ba. Yau ta san meye aure, ba auren Idris ba, dan auren Idris ta bar shi a matsayin wata ƙaddara da dole sai ta faru da ita. Raihan ɗin da take yi wa kallon auren sa abun kunya, haka tana kallo ta zama cikakkiyar mallakinsa. Babban abun da ya razana ummi, tare da ɗaga mata hankali bai wuce yadda raihan bai ce mata komai ba, hasali ma ya juya mata baya yayi shiru. Hakan ya ɗaga mata hankali, tare da tabattar mata da an samu matsala a wannan karon ma. Ayshercool 08081012143 PAID ADVERT!. Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi. Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku Oll types of Turaran wuta Sandal Halut Irik Difur Gab Gab Kajiji Habil Nabak Humra Kulakcha Dilke da kalta Kayan Garan jiki Muna turara Kaya Kujerar garan jiki Kannada Madarorin turare masu kamshi  Man garan gashi  Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702   08025453921 *TALLA!TALLA!TALLA!* *INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*. *BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU* *MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA* BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI.                        *CUTARWA* *BRIGHT PENS* (FREE BATCH) *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* 38 MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH. Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe. FOLLOW AND SHARE AYSHERCOOL 08081012143 MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH. Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe. 38 Ƙirjin ummi ne ya cigaba da bugawa, tare da sallama cewa, a wannan karon ma an samu matsala, wataƙila shi ma raihan ya ci karo da matsalar ta, ta farko. Ta zubawa bayansa ido, duk da ɗakin ba haske, sai dim light na kan side bed. Ko wane hukunci zata karɓa a wannan karon a hannun raihan? Allah ne ya bar wa kansa sani. A hankali ta ga ya motsa yayi miƙa, yana gode wa Allah, ya tashi tsam ya nufi toilet. Duk Addu'ar da ta zo bakin ummi yi take, saboda ita sam ba ta ga al'amuran sun faru kamar yadda take karantawa ko sauraro a littatafan soyayya ba, a zaton ta tun da abun da take tsammani bai faru ba, an sake samun matsala, tun da babu wanda ya zaunar da ita a nasihar da aka yi mata, aka yi mata bayanin menene gundarin auren. Tana tufaka da warwara, da adduo'i, ya buɗe ƙofar ya fito, ba ta iya ganin me yake yi daga in da take, amma ta ji alamar ya buɗe wardrobe ya rufe. Bai ɗauki lokaci da yawa ba, ya kunna fitilar ɗakin, hakan ya sanya ta sake shigewa cikin bargo tana jiran irin hukuncin da zata karɓa a wannan karon. A hankali ta ɗago kai jin shiru, ta ganshi a tsaye a kan ta, ƙugunsa ɗaure da towel jikinsa da sauran ruwan wanka, ya yi murmushi ya ce "Ya ki ke sake shigewa cikin bargo, taso mana" yayi maganar yana miƙa mata hannu yana murmushi. Jin maganar sa ya saka ta ɗaga kai ta kalli fuskar sa, ta ga me za ta iya ganowa, amma ba ta ga komai na damuwa ba, ko ɓacin rai ba. "My love, ba fa canza miki ni aka yi ba, naga kamar wani abu ki ke son ganewa, yaron nan ne dai ki ke cewa ba zaki auri ƙaninki ba" Ta sunkuyar da kai cikin matsananciyar kunya. Ya ce "Ok, let me help you" yayi maganar zai ɗaga bargon amma ta riƙe ta ce "Ka bani hijjabi" "Ai nan babu hijjabi, sai dai na baki towel sai ki yafa mayafinki" haka kuwa aka yi, ta ɗaura towel, ta yafa mayafinta, ya rakata har toilet, ya dawo kan gadon ya sake gyarawa, sai dai abubuwa na ta kai komo a ransa, duk da bai san dawan garin ba, amma ya san akwai banbanci tsakanin budurwa da bazawara, to ita ummi mecece? Budurwa ko bazawara?. Yana tsaka da wannan tunanin, ta fito ya tashi da sauri ya nufe ta yana jera mata sannu, kamar wadda ta yi hatsari, sai raɓe-raɓe take tana tafiya a hankali. Ya rungumota jikinsa ya kai ta bakin gado, ya zaunar da ita, cikin dabara ya zare mayafin, ya shiga tsane mata dogon gashin ta da yake jiƙe da ruwa da shi. "My love, gaskiya yakamata mu tambayi mama, anya asalinku ƴan Nigeria ne? Ni fa ban taɓa ganin bahaushiya mai irin gashin ki ba" Ta ce "HOD ɗinmu ma haka ya ce, wai ƙwayar idona ba irin ta ƴan Nigeria ba ce" "Shi kuma saboda sa ido, har ya zuba miki ido ya gano ƙwayar idonki ba irin ta ƴan Nigeria ba ce?" Ta tura baki ta ce "To ai ana ganina ake ganewa ba baƙa ba ce" Ya ce "Idan na tashi dole a nemo hand drier, saboda tsane gashin nan, kar yawan wanke shi ba a busar ba, ya din ga saka ki mura ko ciwon kai" Ummi ta ce "Ai ban damu da yawan wanke shi ba ma, saboda wahalar bushewa, na yi ta fama, duk ya dame ni, sai ... Sai kuma ta yi shiru. Ya kwashe da dariya ya ce "Yanzu kuma wanke kai ya ganki, ba dare ba rana daga ɗaya zuwa sau ba adadi a rana" yayi maganar yana dariya, ta ja bakinta ta yi masa shiru. Yadda yake ta tattalin ta, da nuna mata kulawa kawai ya ga hawaye na zubowa daga idonta, tun daga kan auren Idiris ba ta taɓa zaton zata samu miji da zai nuna mata kulawa ba, hakan ba ƙaramin tayar masa da hankali ba. "Sweetheart na yi miki wani abu ne da ba dai-dai ba? Dan Allah ki gaya mini menene me na yi miki? Ko abum da na yi ne ya ɓata miki rai?" Ummi ta share hawayen ta ce "Bakomai fa, wani abu na tuna ne kawai" "Dan Allah kar ki sake tuna abun da zai saka mini ke kuka please, kar ki ɓata mana farincikin da muke ciki mana, abun da ya wuce ki bar shi a baya, yanzu sabuwar rayuwa zamu gina baby, dan Allah ki daina" yayi maganar yana share mata hawayen fuskarta, ya rungumeta suka kwanta. Sai yanzu yake yi mata abun novel ɗin da take tunani, yana ta yi mata magana mai sanyaya zuciya, wasu maganganun ma kamar ta toshe kunneta dan kunya, dan a duk rashin jin raihan, ba ta yi zaton jin wasu maganganun daga bakinsa ba. Can gida kuwa ƴan gagarawa na koɗa gidan ummi, dan sai da kausar ta je gidan, kuma sai da ta ɗaukko wa babr su videon komai, ta zo ta nuna mata. Nan ɓangaren su mariya ma haka ne, ana ta santin gidan ummi, da irin maƙudan kuɗin da mijinta ya kashe a kan aurenta. Mariya ta ce "Yaya maryam kin gani ko? Ina da kyakywan yaƙinin ummina ba za ta tozarta ba, na yaba sosai da nutsuwar mijin nan nata" Yaya maryam ta ce "Shiyasa kullum nake cewa ki din ga yi mata addu'a, yawan damuwar ba shi ne ba, ke dan ma baki je kin ga gidan ba, zuwa gobe in Allah ya kaimu kafin mu tafi, sai mu je ki gani" Mariya ta yi murmushi ta ce "Yaya Maryam kenan, mai ɗaki shi ya san in da yake yi masa yoyo, ba zaku fahimci halin da na shiga ba a kan raba ni da ƴa ta" "Eh dama ya za ayi mu gane mara kunya, ƴar farin ki ke wa haka" mariya ta sunkuyar da kai tana murmushi. Kiran sallar farko, Raihan ya tashi, da ƙyar ya yaƙi shaiɗan ya saukko daga kan gadon, ya je yayi alwala ya gabatar da nafiloli, sai da aka kira sallar asuba, ya tashi ummi shi kuma ya fita masallaci. Kafin ya dawo ta yi salla, ta koma kan gado, saboda gajiya da kuma bacci da take ji. Jin motsinsa a kan gadon ne ya sanya ta farka ta buɗe idonta da ƙyar. "Kin yi sallar ne?" Ta jinjina masa kai tare da cewa "Good morning" cikin kasalalliyar muryar bacci. "Morning honey, duk gajiyar ce ne, ake yi mini shagwaɓa" murmushi ta yi tana ƙoƙarin juyawa, amma ya riƙe ta ya sumbaci goshinta, ya gyara kwanciyarsa shima a gajiyen yake, dan haka bacci duk yayi awon gaba da su. A hankali ya yi juyi, ya nemi ummi ya rasa, kamar aljana, ya daɗe a kwance yana miƙa, sannan ya saukko ya fito, can ɗaya falon ya ganota, tana ta zazzagawa tana kallon ko ina, ta saka dogon hijjabi abun ta. Fito yayi, hakan ya ɗan razanata ta waiwaya. "Me ki ke nema ne?" Ta ce "Bakomai, kawai na gaji da kwanciyar ne na tashi" Ya ƙaraso falon ya ce "Sai ki ka tashi ki kar bar ni? Ni fa yunwa ce ta taso ni ma, bari na kira hajiya a kawo mana abun karyawa kan mutane su fara zuwa" Ta ce "Da in girka mana, kar a wahalar da su" ya girgiza kai ya ce "No, kina buƙatar hutu, kuma gidan bakomai na masarufi, ban sayo ba tukuna bari na kira ta, akwai sponge da sabulu da toothpaste a drower mudubin ɗakin da muka kwana, ki shirya kan mu fara baƙi". Ta ce "To" A ƙalla ta kai awa guda, sannan ta dawo falon, yana kwance a kan doguwar kujera, yana danna wayarsa, ya ɗaga kai ya kalleta cikin dogon hijjabinta, ya girgiza kai tare da yin murmushi ya ce "Wane irin wanka ne haka fiye da awa goma?" Ta ce "awa goma tun jiya kenan fa" "Ai kin daɗe ne, ƙaraso mu gaisa mana amaryata" Cikin matsananciyar kunya, ta ƙarasa gaban sa, ya tashi ya zauna, tare da zaunar da ita a kusa da shi, ya ce "Kin tashi lafiya?" "Lafiya ƙalau" "To ya jikin naki? Are you ok now?" Ta sunkuyar da kai, tana murza yatsun hannunta, da ya zame mata ɗabi'a idan ba ta da amsar bayarwa ga tambaya. Cikin son ƙureta ya sake cewa "To ya daren jiyan?" Mutsu-mutsu ta hau yi, za ta tashi ta tafi, dan raihan ɗin ya wuce tunanin ta, kamar an canzo wani. Riƙeta yayi ya ce "Ba in da zaki fa, yanzu dai bari in rama dukan da ki ka yi mini jiya, poor me kin kusa karya mini ƙashi, you even bite my tongue daga kiss" "Zan je ɗaki in yi abu" tayi maganar cikin rauni. Yana dariya ya ce "Koma menene yi a nan, amma sai na rama" wayarsa ce ta fara ringing, ya ɗaga yayi sallama, daga bisani ya ce "Ok" Ya katse wayar ya ce "Bari na karɓo mana abincin, hajiya ta aiko" ta jinjina masa kai ya tashi ya fita. Tayi ajiyar zuciya tana bin bayansa da kallo. Shiru ta yi ta tuna irin cin zarafin da idiris yayi mata, ta kwana a waje tsirara cikin ruwan sama, saboda kawai ya same ta da larura, ta girgiza kai abun kamar ba zai wuce ba. Raihan ya yi sallama da ƙaton kwando, ta tashi ta karɓe shi, suka iso falon suka zauna. Sai dai ita ta kasa sakewa ta ci abinci, sai cakala take yi, ya ci ya ƙoshi, ya hau kan kujera ya kwanta sai bacci. Ummi ta lallaɓa ta bar masa falon. Sai azahar sai ga su yaya maryam da mama, dan a washegari za su koma maiduguri, ummi ta ji daɗin zuwansu, kamar ba jiya suka rabu ba. Suka kawo mata soyayyayiyar miya ta sha kaji, har da kayan gara, sun kai ruwa rana da dr. A kan kayan garar nan, ya ce ba addini ba ce ba, idan ma sai an yi su bari a kwana biyu shi zai yi mata da kansa, suka ce sun riga sun zo da ita, sai dai ya yi haƙuri. A nan wasu daga dangin su raihan ma suka zo, suka tarar da su, wanda ba su samu damar zuwa ganin gida ba, ciki har da wasu daga ƙannen mamin raihan. Kallonta suke suna zunɗen ummi, ganin yadda take tafiya a takure, kamar mara kuzari. "Ji munafuka, kowa fa ya san bazawara ce, amma ji salon kinibibi da iskanci, wai a dole sai ta nuna wa mutane budurwa ce" suka yi ta surutun su, ummi ba ta ma san suna yi ba. Da za su tafi, mariya ta kama hannun ummi, tayi ƙasa da muryarta ta ce "Mamana, kin shiga sabuwar rayuwa, duk da baki da wayo sosai lokacin da na yi rayuwar nawa auren, amma aure ba soyayya ba ce kawai, kowane aure da kalar jarrabawarsa, ni na samu soyayyar miji, ƙalubale na danginsa ne. Ki riƙe Allah ki ji tsoron Allah, babu abun da ya gagari Allah, kar ki bari ki yi nesa da Allah, babu abun da zai yi galaba a kanki, sai abun da Allah ya ƙaddara. Ki riƙe mijinki domin Allah, banda yaji ko kan ƙara, matar da ta isa a ɗakinta take yi wa miji yaji, ayi haƙuri, ayi haƙuri da juna" sosai mariya ta yi wa ummi nasiha, sai dai a ƙarshe ne kuma ta koma shirme. Da za su tafi ummi ta je ta kira shi, sai dai bai ji daɗin garar da suka kawo ba, yaya maryam ta ce masa ai su normal ne al'adar su ce. Bayan tafiyar su ummi ta dudduba kayan da suka kawo mata, ta je kitchen ta jera wanda za ta jera, kayan miya, busasshshen kifi, man shanu da sauran su. Kasancewar raihan ba ya ɓangaren da take, kuma duk baƙin sun tafi, ya sanya ta ɗan sake, tana ta ɗan gyara in da aka ɓata. Tana ta gyara abun da bai yi mata ba, tana yi wa kawu addu'ar samun buɗi da alkhairi mara yankewa a duniya da lahira, kamar an ce ta ɗaga kai, ta hango raihan a tsaye yana kallonta. Ta miƙe tsaye ta ce "In zo ne, kana buƙatar wani abu?" Ya ɗaga mata gira. Ta nufi in da yake tana takawa a hankali, cikin tafiyarta da yake cewa yanga ce tayi mata yawa. Ta ƙarasa ta ce "Gani" Ya riƙo hannunta ya ce "Dama kin tambaye ni ina buƙatar wani abun ne, mu je daga ciki to, sai na gaya miki me nake buƙata" danƙarewa ta yi a wurin taƙi yin gaba. "Ya haka kuma? Ke fa ki ka tambaye ni" "A'a to na janye tambayar" ta yi maganar tana son ƙwace hannunta. Raihan ya yi dariya ya riƙe hijjabin jikinta ya ce "Ummi nan fa ba muhallin hijjabi bane yanzu, aure muka yi, dan Allah ki cire shi na din ga ganin kwalliyar ke ko zafi ba kya ji" Ummi ta ce "To, zan din ga cirewa" "Ai yanzu nake son ki cire" yayi maganar yana cire hijjabin daga jikinta. Doguwar rigar material ta saka, sai ƙamshi take yi, ya cire mata ribbon ɗin kanta, gashin ya sauka a jikinta, ya gyagygyara mata zaman gashin ya ce "Masha Allah, what a beautiful creature" yayi maganar yana murmushi. Tura baki tayi tana ƙoƙarin karɓar hijjabinta daga hannunsa. Ya riƙo ƙugunta yana ƙare mata kallo daga sama har ƙasa, tabbas ba dan ummi ta kasance ma'abociyar suturta jikinta ba, da babu shakka mutanen banza su din ga bin ta, saboda duk in da ake fasalta mace mai diri, Allah ya yi wa ummi dirin jiki mai kyau da ɗaukar hankali. Suka koma falon suka zauna, sai dai ya hana ummi sakat da tsokana kala-kala, kuma ya riƙeta a jikinsa. "Komai na ki perfect baby, da headmastern nan ya yi gardama, da na yi masa abun da ban taɓa yi ba" Ummi ta ɗaga kanta ta kalleshi ta ce "Wai dan Allah me ka ce masa ya fasa?" Raihan ya yi murmushi ya ce "Dubu ɗarin da ya ce zai baki kuɗin aure, na bashi uku, na ce aje a mayar da wadda aka saka a kula da iyali na gida, ya bar mini ke, jikinsa na rawa ya bar mini ke, dama na gaya miki na fi kowa sonki" yayi maganar yana haɗa fuskar sa da ta ta yana murmushi. "Cin hanci ka bashi dan ya bar maka ni, cin hanci ba kyau" "A nan ya halarta" yayi maganar yana dariya. Raihan na ƙoƙarin ɗaukar su zuwa wata duniyar, wayarsa ta fara vibrating, sunan mami ne a kan screen ɗin wayar, ya ɗaga tare da yin sallama. "Raihan har ka fi ƙarfin ka zo in da nake ka gaishe ni ko?" Ya san a rina, ya kwantar da ummi a jikinsa sannan ya ce "A'a ba haka bane mami, zan zo ne" "Zaka zo sai yaushe? Har an yi ƙulle-ƙullen da zaka kasa zuwa ka gaisheni?" "Mami, wallahi a gajiye nake ne sosai da sosai, na kira ki ma da safe baki ɗaga ba, but an ce mini gida haryanzu da mutane, na ce bari na ƙyale ki, sai da daddare, amma in sha Allah a satin nan dole na  na zo gaishe ki, na gaji ne sosai.... "Dalla rufe mini baki, nusari shashasha. Yaushe aka yi daren da gari zai waye?  Lallai lallai ka zo gida ina son ganinka, yarinyar nan safiyya ma na kwance babu lafiya duk saboda kai, kar ka bari ka fusata ni" Raihan bai yi mamaki ba, ya san a rina, amma shi bai ga haɗin rashin lafiyar safiyya da shi ba, asibiti zai kai ta ko me zai yi mata? Kodayake ba abun mamaki bane ba idan mami na jin rigima. "Shikenan mami, zan zo in sha Allah" sai dai tun da aka ambaci Safiyya, yana jin yadda bugun zuciyar ummi ya ƙaru a ƙirjinsa. Ya saka hannu ya ɗagota, amma taƙi kallonsa. "Sweetheart, an fara kiran sallar magariba, bari na yi alwala na tafi masallaci" ba ta kula shi ba, ta tashi ta nufi ɗaki, ya bi bayanta da kallo, zubin manyan mata sosai. A hankali ya ce 'Haba mami, is too early for that'. Bai je kiran mami a ranar ba, dan ya san idan ya je da mutane a gidan, kuma sai ta yi wani abun da zata ci mutuncin ummi, a gaban mutane dan haka ya ƙi zuwa. Kwanan ummi uku a gidan raihan, ta fara girkin abinci, sai dai rigimar raihan har mamaki take bata, baya zuwa ko ina sai salla, yana maƙale da ita kamar cingam, ga wani irin mugun kunyarsa da take ji, ta kasa sakewa da shi, kusan kullum cikin ƙorafin saka hijjabin nan yake, ta kasa daina yawo da hijjabi. Kwana na ukun da daddare, Raihan ya je gida, sai da ya je wurin Hajiya yayi mata bangajiya, Alhaji dama baya nan, washegarin ɗaurin aure ya tafi umara. Sai dai cikin fargaba ya isa sashin mamin. Ya tarar da ita ta hakimce, gefe ga Nihal a zaune, sai Safiyya da ke kwance a kan doguwar kujera. Yana shiga suka gaishe shi, ya amsa musu, sannan ya je gaban mami ya risuna yana gaisheta. "Sai yau Allah ya nufe ka da zuwa? Har ka sallami kanka na yi maka waya ka zo raihan amma ka ƙi" "Ba ƙi na yi ba mami, wallahi bana iya zuwa ko ina, zirga-zirgar bikin nan na gaji ne wallahi" "Uwar zirga-zirgar bikin, ka fito fili ka faɗi uban abun da ya hanaka fitar, na yi dana sanin cewa zan yi maka aure ina ganin mafita ce, ashe ruwan dafa kaina ne, ka kwaso bazawara da ta tafi ƙarfin ka, wallaahi ka shiga hankalinka, ka san abun da yake yi maka ciwo" Ta din ga yi masa faɗa na babu gaira babu dalili, ƙarshe ta rufe da cewar, watanni uku ta bashi, yazo ya nemi auren Safiyya. Ya ji ta da kunne kawai, ta gama ya ce zai tafi, ta ce ba zai tafi a lokacin ba. Ummi kuwa na gida na ta duba agogo, dan be gaya mata zai je wani wuri ba. Har ƙarfe goma saura shiru bai dawo ba, ta kasa jurewa ta kira wayarsa. Bai ji nauyin mami da ke zaune tana kaɗa ƙafa cikin isa ba, ya ɗaga wayar ya ce "Hello dear". "Ina ka tafi tsoro nake ji" Yayi murmushi ya ce "Gani nan, babu dodo a gidan fa" "Dan Allah ka yi sauri, tsoro nake ji sosai ko falo na kasa fita". Mantawa yayi da mami a wurin, yayi dariya ya ce "To yi ta addu'a kan na dawo? Kin ci abinci ne?" "A'a" Ya ce "But you are not hungry ko?" Ummi ta ce "Eh" "Ok ki jirani, in sha Allah yanzu zan taho" Muryar mami ta jiyo tana cewa "Zaka ajiye wayar nan ko sai na ci ubanka mara kunya" a rikice gaban ummi ya faɗi, ta kashe wayar ba ta san gidan ya je ba da ba zata kira shi ba. Mami ta tashi ta shiga ɗaki, raihan ya ɗau mukullin motarsa ya fice da sauri. Abun da raihan yayi, ba ƙaramin mamaki ya bawa mami ba, dan mugunta ta shirya yi, ta zaunar da shi har sha biyun dare, daga nan ta ce dare yayi ba zai fita ba sai da safe, bisa ga miyagun shawarwarin da Anty rakiya ta bata, sai dai abun da raihan ɗin yayi ya bata mamaki. Ta din ga kiran wayarsa amma a kashe. A bedroom ya tarar da ummi, kai da ganin ummi ka san a tsorace take, ya ajiye kayan hannunsa ya ce "Sorry dear, yi haƙuri" "Ban haƙura ba" ta yi maganar cikin shagwaɓa. "Yi haƙuri, ayi mini afuwa" ba ta nuna masa ta san in da ya je ba. Ya cika cikinsa da abinci, yana ta yabonta tare da santin abincin. Ya koma ya hana ummi sukuni, ya gama tara mata gajiya, suna kwance babu tsammani ta ji ya ce "Salma, me ki ka yi wa mijinki na farko ku ka rabu?" Gyara kwanciyar ta tayi, ta ce "Meyasa ka tambayeni?" Ya kalli fuskarta ya ce "Am just curious about it" Tayi ajiyar zuciya ta ce "Labarin babu daɗi, auren huce takaici aka yi masa da ni, saura kwana uku aurensa, ba ya so na, ranar da ango ya tare a tsakar gida na kwana cikin ruwan sama, ba ya so na, tuntuni ni mummuna ce kuma ya rasa wadda yake so yayi niyyar aure. Auren watanni biyu ne dai bai kai uku ba ma, watanni mafi tashin hankali, marasa daɗin tunawa, na tozarta sosai a aurena na fari ko tunawa bana son yi" tayi maganar tana zubar da hawaye. Ya rungumota jikinsa yana share mata hawayen, ya ce "Is ok, you are much more than special, ke ta daban ce, kuma ya yi wa kansa, ni kuma ya taimakeni irin sosai ɗin nan fa" yayi maganar yana ƙoƙarin zolayarta. Da safe da ya kunna wayarsa, da kiran mami ya fara cin karo, ya ɗaga ta ƙare masa zagi tsaf, amma ko a jikinsa, shi kasancewar sa da ummi, mantar da shi komai yake yi. Duk da kunyarta har ta yi yawa. Abu kamar wasa, raihan ya shafe sati biyu cirr a gida, ummi ba ta da aiki sai ɗorawa da saukewa, abokan aikinsa su ka zo ummi ta yi musu girki, har da ƴan china. Raihan ba ya jin duk wanda zai zo gidansa, saboda matarsa ta iya girki. Haka zalika ga rigimarsa da ba ta ƙarewa. Gidan farida kuwa, tun da Allah ya sa ummi ta bar gidan, komai ya taɓarɓare, kausar mugun sok jiki, ba ta iya aikata komai, noor ce ma mai ƙoƙartawa, ita ma idan ta gaji, sai ta watsar da aikin ta ce ta gaji, idan aka tursasata kuma, tayi abun da ba a so. Uban wankin da ummi ke yi musu, babu wanda zai yi yanzu, mopping gyaran ɗaki, da kuma girki duk abubuwan sai a hankali, girkin ma ba daɗi yake yi ba. Farida ta ce sai an samo ƴar aiki, dr. Ya ce babu mai kawo masa ƴar aiki, idan aka kawo ta kuwa sai dai ta din ga biyanta, babu yadda za ayi ga kausar a gida, ba aure ba karatu, ace an ɗaukko ƴar aiki. Dr. Ya kira ummi ya tambaye ta me take so ayi mata da kuɗin sadakinta, ta yi tunanin wata sana'ar, ya bata jari sauran ya cika ya saya mata kadara. Ummi ta tuntuɓi raihan, amma ya ce a wannan lokacin, ba ta buƙatar sana'a a saya mata kadara kawai. Duk yadda mami ta so yin abun da za ta ƙure raihan, ta shiga hakkin ummi, raihan sai ya zille, ta yi masa faɗa ta zage shi, ko a jikinsa. Babban abun da ya ba ta takaici, bai wuce tana tsaka da duba saƙonni, ta ga raihan yayi status da special whats app ɗin sa, da ba kowa ne ya san shi da shi ba, galibi family ne kawai ke da lambar. Hoton Ummi ya saka, tana zaune a kan dining, ta naɗe kanta da mayafin doguwar rigar jikinta "My perfect woman, khairun nisa'i, Allah ya ƙara miki lafiya" Ya sake rubuta "Goodnight ƴar aljannata" A fili ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, bazawarar wannan mummunar" Hankalin Safiyya ne ya koma kan mami, dan kuwa mami ta sanya safiyyan dawowa gidan da zama. "Mami menene?" Ta miƙa mata wayar, bayan ta nemo status ɗin raihan. Gaban Safiyya ya faɗi, duk yadda ake koɗa munin ummi bai kai nan ba. Mami ta din ga zage-zage, tana cewa an asirce mata ɗa. Sai da ta jera kwana biyu tana kiransa ya je tana nemansa, amma ya ce mata ai aiki yayi yawa a office, baya samun isasshen lokaci, alhalin rabonsa da office ɗin tun saura sati biyu bikinsa. Asabar ce suna baccin safe, kiran Alhaji ya tashe su, raihan ya ɗauka cikin jin nauyinsa. "Ango ka sha ƙamshi" "Alhaji ka dawo kenan?" "Eh na dawo, baka nema na ko?" Raihan ya ce "Haba dai wane ni" "To yaya ƴar tawa?" "Gata nan tana jin ka, ta ce a gaisheka kan mu zo" "To dan Allah ace mata ina roƙon arziki, a taimaka a bar mini kai ka koma office, ana ta kirana a waya ana nemanka" Raihan ya ce "To za a gaya mata, amma na zata saura sati biyu sannan na koma" Alhaji ya ce "A'a babban mutum, a duba mini lamarin nan" Raihan ya ce "Zan shigo in anjima in sha Allah, sannu da zuwa" Alhaji ya sauke wayar yana murmushi ya ce "Lallai babban mutum, ka ci gidanku da sati biyun" Mami da ke kusa da shi ta ce "Kana nufin ba ya zuwa aiki dama?" "Da sabon auren zai fita aiki? Lallai wato ni ya mayar shashasha, idan na ce ya zo sai ya ce mini wai aiki ya yi yawa". Alhaji ya kalleta ya ce "Ya zo yayi miki me? Ango ne fa" A fusace ta ce 'Angon banza, bazawarar?" "Ba mace ba ce? Ke ina ruwanki ne, Bilkisu ki kiyayi shiga shirgin yaran nan kin ƙi ko? Zaki yi ta fama da takaici kuwa" Haushi ne ya ishi mami, tare da yi wa kanta alwashin, dole ta san abun yi a kan raihan da ummi, tun da tun ba aje ko ina ba, kansa yana rawa. Ummi sai magiya take yi wa raihan, ya tafi da ita ta gaida Alhaji, ya ce mata sai an kwana biyu. Ta ja gefe ta kashingiɗa a kan kujerar da suke ta ce "To ka tashi ka je ka yi masa sannu da zuwa" "Sai anjima" yayi maganar yana ɗora ƙafafuwan ta a kan cinyarsa yana matsa mata. Ta buɗe datar ta, taga messages da yawa sun shigo, ta din ga mamaki dan ita wanda take chatting da su ba su da yawa. Group ta ganta a ciki, na ƴan makarantar islamiyyar su ne, kuma ta ga ana ta tagging ɗin ta, banda messages da ta gani ta private. Voice messages ta fara buɗewa, ta din ga jin saƙonnin zagi da ashar, wai saboda ta auri ƙanin maryam, ana ta cewa ta yi asara. Kashewa take ƙoƙarin yi, ta ajiye wayar, ya karɓe wayar, ya cigaba da saurarar abun da suka ce, tare da duba messages ɗin duk da suka yi. Tun tana jure jin, har ta karaya ta fara kuka, saboda cin zarafin yayi muni. Wayarsa ya ɗaukko, ya danna ya kara a kunnensa. "Zan turo maka wasu lambobi, ayi tracking ɗin su duk in da suke dan Allah, zan biya ko nawa, zan turo maka wani abu" Ya ajiye wayar ya kalleta ya ce "You don't need to cry anymore, zan yi dealing da duk wanda ya ce zai saka ki kuka ko waye shi" daga haka ya tashi ya fita. Gaba ɗaya jikin Ummi yayi sanyi matuƙa, zagin da suka yi mata yayi mata zafi, tun da suka bar islamiyyar suka yi aure babu wadda ta sake neman ta, sai yanzu da suka sakata a group na makarantar suka ci mata mutunci, da dawo da abubuwan da suka faru a baya, wai tana yawo duk da dauɗa ga muni, dan son zuciya ta auri ƙanin ƙawarsu. Hankali kwance raihan ya je gida, ya shige wurin Alhaji, Alhaji ya din ga ce masa yayi ƙiba ya ƙara kyau. Nan suka tare a sashen Alhaji, har da Hajiya da Salim. Mami ce ta kira shi hankali a tashe ta na tambayar sa yana ina. Ya bata amsar yana sashin Alhaji. Ko mintuna uku ba ayi ba sai gata, ba ta damu da su hajiya da suke zaune ba, ta nufi raihan tana neman ta kai masa duka. Alhaji ya miƙe ya ce "Bilki meye haka?" "Aure hauka ne? A kan me zai sanya ƴan sanda su kama matan mutane? Maryam ta kira ni tana kuka, an kama su an kira shi a waya yaƙi ɗagawa, uban me suka yi maka?" "Matata suka zaga babu dalili, tsakani nake so ayi musu, kar su zagar mini mata, ba tayi abun kunya ba dan ta aureni" "Ni ka ke gaya wa haka raihan?" "Mami ba da ke nake ba, ba kuma da wata manufa na faɗa miki ba, ni na saka ummi ta aureni, idan na zuba ido ana cin zarafin ta, ban yi mata adalci ba". Hajiya ta yi murmushi ta ce "Allah mai ƙudura, ɗan so ya faɗa hannun matar so, ko dai ki bi a hankali ko ki rasa shi gaba ɗaya" Ayshercool 08081012143 PAID ADVERT!. Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi. Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku Oll types of Turaran wuta Sandal Halut Irik Difur Gab Gab Kajiji Habil Nabak Humra Kulakcha Dilke da kalta Kayan Garan jiki Muna turara Kaya Kujerar garan jiki Kannada Madarorin turare masu kamshi  Man garan gashi  Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702   08025453921 *TALLA!TALLA!TALLA!* *INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*. *BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU* *MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA* BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI.    *CUTARWA* *BRIGHT PENS* (FREE BATCH) *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* 39 MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH. Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe. FOLLOW AND SHARE AYSHERCOOL 08081012143 MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH. Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe. *Alhamdilillah ala kulli halin, ina amfani da wannan damar, wurin isar da ɗimbin godiyata ga ƴan uwana marubuta, tarin masoya makaranta, da sauran al'ummar da suka yi mini ta'aziyyar rashin kakata, ina fatan Ubangiji Allah ya jiƙan magabatanmu baki ɗaya, ya kuma bar zumunci, yayi mana jagora a rayuwa baki daya, Allah ya sanya kaburburan magabatanmu ya zama dausayi daga aljanna, idan tamu ta zo ya sanya mu cika da imani* 39 Alhaji ya ce "Jidda ya haka ne? Wace irin magana ki ke yi kuma?" Hajiya ta ce "Kaga ƙyale ni na faɗa, ai a baya ban taɓa yi ba, sai mu gani idan dabarar mutum za ta ƙwace shi, me aka yi da maza ko sati uku ba a rufa ba fa? Baki ga komai ba" Mami kuwa kumfar baki ta din ga yi tana cika baki, Salim ya tashi tsam ya fice, dan baya son hayaniya, hajiya ma ficewa tayi ta bar ɗakin. "Ka gani ko ka ga abun da ka janyo mini ko?" Kamar raihan zai fashe da kuka ya ce "Mami me kuma na yi?" Alhaji ya ce "Raihan bai yi miki laifin komai ba, ke ki ke ƙoƙarin koya masa rashin gaskiya, da kuma raina ki, wuce ka jirani a mota, mu je a kashe wancan case ɗin da ka ɗaukko" Raihan ya fita yana satar kallon mami. Alhaji ya sake mayar da idonsa kan mami ya ce "Gaskiya hajiya ta gaya miki, na sha gaya miki mu maza idan muna kan wannan gigin da rawar kan, ba a cewa za a tanƙwaramu ta ƙarfin tsiya, ko da kuwa iyayen da suka haifemu ne, ke meye ban yi ba a kanki? Ko kin manta yadda na ɗauke ki, na bar ƙasar sama da wata uku na bar hajiya, na toshe kunnena, na ƙi saurara kowa sai yanzu dan abun ya zo kan ɗanki ki ce ba ki san zancen ba? Shiyasa a kowane ƙadami ake so ka zama mai adalci, ko dan gaba, baki nuna mini illar abun da na din ga yi ba, sai daga baya da na gane kuskurena dan kaina, ka kwanta da mace kawai ba shi ne aure ba, wannan abu ne na lokaci, managarciyar mace mai tsoron Allah, da kuma biyayya ita ake fata. Amma idonki ya rufe dan ɗanki ya auri bazawara, sai me qualities ake dubawa ga mutum mai hankali, ba wai abun da ku ke tunani kawai quality na mace ba" da farko faɗa yake yi mata, daga bisani kuma ya koma nasiha, ya gama ya fice daga ɗakin ya bi raihan. Ko kaɗan mami ba ta ji nasihar Alhajin ta shige ta ba ma, babban burinta a yanzu kawai, shi ne raba ummi da raihan tun kan ta kanainaye shi gaba ɗaya. Ba dan tare da Alhaji raihan suka je station ba, da sai raihan ya ja case ɗin, dan kuwa babbar headquarter hukumar ƴan sanda yasa aka kai su, kuma ya tafi da wayar ummi a matsayin shaida. Alhaji ya ce wa raihan, ya kai shi gidansa, yana son yin magana da shi da ummi gaba ɗaya. Suna tafe yana yi wa raihan nasiha. "Babban mutum, na son kana son matarka, amma ka yi ƙoƙari ka din ga ɓoyewa saboda mahaifiyarka da bakin sauran mutane, ka san kishin mata ba lallai sai tsakanin kishiyoyi ba, su ba sa raina abun yi wa kishi, sannan ka yi ta haƙuri kana cigaba da addu'a komai zai wuce, amma matarka ka riƙe ta sosai ka kula da ita" Raihan ya jinjina kai, suka ƙarasa gidan sa, tun da raihan ya kirata ya ce mata tare za su zo da Alhaji, ta gama girki, amma ta shiga ƙoƙarin ƙara wasu abubuwan. Tun da ya zo kanta a ƙasa yake, saboda tsananin kunya, ko sau ɗaya ba ta yadda sun haɗa ido ba, shi duk yadda ake zuzuta muninta shi bai gani ba, sai tsantsar tarbiyya da nutsuwa, kuma tubarkallah shi bai ga wani muni ba. Yayi musu nasiha sosai da sosai, ya ce raihan ya mayar da shi gida. Ummi ta ce "Baba na gama abinci, bari na kawo maka" Alhaji ya ce "Kar ki damu ƴar albarka ta, sauri nake kuma a ƙoshe nake, Allah ya yi muku albarka, ayi ta haƙuri kun san irin auren nan naku, society ɗinmu sun ɗauke shi, kamar wani zunubi, amma tun da bai saɓawa addini ba shikenan. Da ƙyar ya sha lemo ya tashi, sai dai lemon yayi masa daɗi sosai da sosai, lemon cucumber ne da lemon tsami. Da ƙyar wannan tarzoma ta lafa, sai dai aka saka ƴan islamiyyar su ummi ba ta haƙuri, kuma suka rubuta takardar ban haƙuri, suka yi signing ba ruwansu da ita ya taho da ita gida. Bayan ya nuna mata takardar ta jujjuyata ta ce "You go far MD, da duk ba ka yi musu haka ba" Ya ce "No, abun da na yi dai-dai ne, ba zai yiwu su ɗarsa miki wani abu mara kyau game da aurenmu ba, alhalin halataccen aure muka yi ba, kuma gaba ba za su sake yi wa wani hakan ba". Ta ce "To Allah ya kyauta. Alhaji bai ci abincina ba" tayi maganar a shagwaɓe. "Bani in haɗa da nawa da nasa na cinye" "Wai ba ka gajiya da cin abinci ne, ka daina zuwa gym ɗin ma, idan ba ka yi wasa ba, sai ka kasa wucewa ta ƙofar falo" "Eh na ji bakomai, hakan ma normal ne" Ummi ta ce "Sai na saita maka cin abincin ka, ba zan je da kai unguwa ka bani kunya ba, ace ba ka ƙoshi" ya kwashe da dariya, ya ce "Yanzu ba zan gane wannan ba, sai cikina ya cika tukuna". Ranar litinin kuwa, ummi ta sha fama da raihan kan ya tashi ya tafi aiki, aikuwa da ya je ya sha aiki sosai da sosai. Tun da raihan ya koma aiki, sai gidan ya yi wa ummi girma, ba ta aikin komai, duk sai kaɗaici ya dameta. Gashi baƙin da sukan shigo, duk sun daina zuwa. *** Anty Rakiya ce a zaune tana kallon fuskar mami me ɗauke da zunzurutun damuwa. "Ke yanzu Bilki har matar nan ta samu bakin yi miki rashin mutunci, yaushe ta waye?" "Anty Rakiya ni ba wannan ne ya dame ni ba, kar bakinta ya tabatta yarinyar nan ta ƙwace raihan na shiga uku, ta ji daɗin yi mini dariya, shi ne babbar damuwata da tashin hankali" "To wai kin bi shawararin da na baki kuwa?" "Wallahi na bi, kin san raihan da taurin kai, ban gaya miki ranar da na kirshe shi ba, daga shiga ɗaki ya gudu ba. Ya ce mini ya koma aiki ashe duk ƙarya yake yi, yarinyar nan sumi-sumi, kar in je ta ƙwace shi, tun da sa'arsa ce kuma bazawara wayo za ta yi masa na shiga uku Anty rakiya". "Ba ki shiga uku ba, ai wanda ya rigaka kwana sai ya rigaka tashi, dole ki samu hanyoyin muzgunawa yarinyar nan, kuma ki fara matsa masa a kan auren safiyya" Mami ta yi ajiyar zuciya ta ce "Shikenan, in sha Allah zan cigaba da ƙoƙari". Ranar asabar raihan yana ta murna zai wuni a gida tare da ummi, tana kitchen tana shirya musu breakfast, yana ɗaki yana bacci mami ta kira shi a waya wai ya je. Tamkar ya fashe da kuka, haka ya ji, ya ajiye wayar, yana tunanin meyasa mami take yi masa haka, lallai sai ta shiga rayuwar aurensa da ummi. Ya lumshe idonsa, ransa babu daɗi, ummi ta shigo ta kunna turaren wuta a ɗakin. Ta shiga banɗaki ta haɗa masa ruwan wanka, ta je kan gadon tana ɗan dukan filonsa ta ce "MD, ka tashi ka yi wanka mu karya" juya mata baya ya yi, ya ce "Wake me up in romantic way" Ta ce "Like how? Ba gashi yanzu ka tashi ba" Ya juyo ya kalleta ya janyota jikinsa, yayi kissing ɗin ta a goshi ya ce "Wake up sweetheart" irin haka nake so. Ta ce "Ashe ba zaka tashi ba idan haka zan yi maka, yadda nake fama da kai ka tashi, da ƙyar ka ke tashi fa" Ya ce "A'a idan ki ka yi mini haka sai na fi saurin tashi ai" ya ƙare mata kallo ya ce "Ni gaskiya a daina tashina da irin wannan kayan, ni dressing zaki din ga yi mini yadda ba za ace ki na jin hausa ba ma" Ummi ta ce "Innalillahi, wai dama haka ka ke, mutum sai tsaurin ido, duk a ina ka san wannan ne?" Wata irin dariya ta bashi, ya ce "Ai tsaurin ido ya riga ya ƙare tsakaninmu, tun da ni da ke yanzu kin san waye boss, fita fa zan yi" Ta ɗan ɓata fuska ta ce "Cewa fa ka yi a gida zaka wuni" "To ya zan yi fita ta kamani, ki yi haƙuri kin ji baby" Ummi ta kalli fuskar sa ta ce "Yaushe zaka kai ni gida na gaida su mami ne? Kuma ban je na yi wa Kawu da su anty bangajiya ba". Ya ɗan sosa kai ya ce "Haka ne, amma for now ban ji zan iya bari ki fita ba" Ta marairaice ta ce "Dan Allah" "Na ji amma da sharaɗi" Da sauri ta ce "Menene sharaɗin?" "Sai kin ce mini baby"  tayi turus tana kallon sa. Ya ce "Yauwwa ai na san lagonki, and ki roƙe ni in a romantic way, a guje zan barki". "Dan Allah baby ka bar ni na je na gaida su mami, na je gida na yi wa kawu bangajiya" Ya girgiza kai ya ce "Ba haka ba, idan kin koyo sai ki tambaye ni, yanzu dai tashi mu je ki tayani wanka" sai da ta ɗan matsa daga kusa da shi ta ce "Wanka kuma?" Ya ɗaga mata gira. "A'a zance maka babyn dai" sauka yayi daga kan gadon ya ce "Kina da sauran aiki Salma, ina son soyayya sosai ban sani ba ko dan ban taɓa yi ba sai a kanki, amma ina son gidana ya fi ko ina samar mini farinciki, kar ki saka na fara leƙe-leƙe" ya ƙarasa maganar yana shigewa toilet, a daidai lokacin da ƙirjin ummi ya buga da maganar sa ta ƙarshe. Shi ya ma manta da ya faɗi maganar, ummi kuwa duk ta shiga damuwa, ya gama cin abincin sa ya fice. Ummi ta zauna ta yi shiru tana tunani, abun duniya ya isheta, tana son yin abun da za ta faranta wa raihan rai, sai dai haryanzu tana tsananin jin kunyarsa. Ta buɗe wayarta ta shiga YouTube, tamkar sun san halin da take ciki, ta ci karo da wani video, malamar tana ta bayani a kan kula da miji. Malamar take cewa "Ƴan mata nawa ya tsallake bai aure su ba, ke ya auro ki ya kai ki gidansa, ko da ya kasance mai kule-kule ke ɗin dai ke ya zaɓa, dan me zai kai ki gidansa ki din ga yi masa gidadanci, ba ko yaushe kunya take da muhalli a aure ba" ummi ta shagala tana kallo, malamar har da demonstration na yadda za a yi wa miji kissa. Ji ta yi ana danna bell ɗin ƙofar falon, ta ajiye wayar ta tashi ta buɗe. Ta faɗaɗa murmushinta, ganin wata babbar mace da wata. Tayi musu maraba zuwa cikin falon, tana ta jera musu sannu da zuwa. Matar ta kalleta ta ce "Kin gane ni ne?" Ummi ta yi murmushi ta ce "Na gane ki, maman bauchi ce, ai ya nuna mini a hoto" Hajiya Aisha tayi murmushi ta ce "Lallai kin yi kyan kai, ina can ya aike ni bana ƙasar, ban samu zuwa bikinku ba, na je umara daga nan na tafi aiken raihan" Ummi ta yi murmushi ta kawo musu ruwa, da lemo. Ta ce "Daga baucin ku ka taho?" Hajiya Aisha ta ce "Daga can muke, tun safe muka taho ai" Ummi ta ce "Be gaya mini ba, ai da na ɗora muku girki tun kan ku ƙaraso" "Be san zamu zo ba shi ma, amma yana gida ai ko?" Ummi ta ce "A'a ya fita tun ɗazu" Ta kawo musu kayan tea, ta shiga kitchen ta ɗora tukunya. Siyama ta kalli Hajiya Aisha ta ce "Mummy, ga fa kairun nisa'i in ji raihan, ki ga rashin mutuncin da yake yi mini a kan matar nan, wai duk matan ƙarshen zamani ita suka rako" Hajiya Aisha ta yi dariya ta ce "Raihan ne fa, haka nima yake ce mini duk ranar da na zo gidansa na ci girkin ummi, wai sai na koma bauci ba yatsu saboda daɗi, hannunta akwai maggi" Suka yi ta dariya, nan da nan ummi ta din ga yi musu hidima, ta kawo wannan ta kawo wancan. Duk rashin son sakewa da mutane irin na ummi, ta ɗan sake da hajiya Aisha, suna ta hirar duniya. Hajiya Aisha ta kira raihan a waya tana faɗan ina ya tafi weekends, ta zo baya nan. Ya ce mata yana gida, ta ce ita ba zata kwana a kano ba, ya dawo za ta tafi. Dama duk a takure yake, kiransa kawai ta yi ta zaunar da shi, Safiyya na ta kaiwa tana komowa tayi kwalliya, sai dai ko kallo ba ta ishe shi ba, hankalinsa yana kan wayarsa yana kallon hotunan ummi. Idan ya kalli safiyya sai ya ganta wani iri, shi dai a wurinsa ya fi ganin kyan ummi nesa ba kusa ba, ita baƙinta ke hana a ga kyawunta, kuma yanzu ta washe ta ƙara kyau. Duk da yana complain da kunyarta ta yi yawa, amma yana jin daɗin wuninsa a gida tare da ita, ya ci abinci da ita, ya shaƙi daddaɗan ƙamashin turarukan ta, uwa uba lallausar fatarta da ba ya gajiya da taɓawa, jikinta tamkar jikin tarwaɗa, ko kuma wata fulawa. Shi komai na ta burgeshi yake yi. Raihan ya kalli mami ya ce  "Maman bauci tazo tana gidanmu tana jirana" "Saura ka je ka gaya mata wani abu, ta zo ta cika mini kunne da masifa". Mintuna arba'in sai ga raihan ya dawo. Aikuwa hajiya Aisha ta din ga masifar weekend ya zauna a gida da matarsa, amma ya fita yawo, idan ya je wurin mamin shayar da shi take ko kuwa?. Shi dai bai ce komai ba ya ce "Ayi haƙuri na daina, amma kar a juya mini baya a koma wurin ummi" Ta ce "A'a ni fa na yi ƴa, ga iya girki ga mutunci, kalli yadda ka yi ƙiba fa, ummi ta iya kiwo, ya ma sunan da ka ke gaya mata" Ba kunya raihan ya ce "Khairun nisa'i" Ummi kuwa kamar ta nutse, ta tashi ta tafi kitchen tana wanke kwanuka. Ya sameta a kitchen ya ce "Madam sannu da ƙoƙari, Mummy na ta yaba miki, ina godiya sosai da sosai" Hararsa tayi ta ce "Baƙina ne ai ba naka ba" Ya ce "To ai shikenan, zo ku yi sallama" Ummi ta ce "Har tafiya za su yi?" "Wallahi kuwa, ta ce ko gidanmu ba zata ba bauchi zasu koma, gashi ba su taho da direba ba, kar su yi dare". Ta ce "To yi gaba zan taho" "Saboda me?" "To kawai sai kuma a ga mun jero tare?" Danƙo hannunta yayi suka yi waje, turus ummi ta yi ganin iyayen akwatuna a falo. Hajiya Aisha ta ce "To ga kayanku nan, ku duba abun da bai yi miki ba, sai a canzo, ko kuma ma yi waya kawai, tafiya zamu yi" Ummi ta ce "Mummy ki bari ki kwana mana" Hajiya Aisha ta ce "Taɓ mijina yana gari, wa zai kula mini da shi, sai mun yi waya" Cikin sauri ummi ta tafi ɗaki, ta ɗebo turaren wuta, na gashi da na jiki, ta din ga haɗo kaya a leda, ta bawa Siyama ta ce musu ba yawa. Hajiya Aisha ta yi musu nasiha, tare da fatan alkhairi suka tafi. Nan raihan ya zauna a falon, yana bubbuɗe akwatunan, ummi kawai ta zuba masa ido tana kallon uban kayan da ko a mafarki ba ta taɓa tunanin mallakar su ba. "Ki saukko ki gani mana sweetheart" ta saukko ta zauna a kusa da shi tana kallon kayan. Ganin tayi saroro kamar sokuwa ya sanya ya ce "Ko kayan ba su yi miki bane ba?" Kawai ya ga hawaye na bin idonta, gaba ɗaya ya rikice ya ce "Menene kuma? Ko Mummy sun yi miki wani abun da ya ɓata miki rai ne?" Ta girgiza masa kai alamar a'a. "To menene? Bana son kukanki ummi, gaya mini" Ta ƙara matsawa kusa da shi, ta rungume shi tana kuka. Ya saka hannunsa ya tallafo fuskarta, cikin kulawa ya ce "Gaya mini menene?" "Na gode" tayi maganar wasu hawayen na zubo mata. Raihan ya ce "Haƙƙinki ne fa ummi, meyasa zaki yi kuka?" Ta sake kwantar da kanta a jikinsa, ta ce "You mean a lot to me, na tuna lokacin da na shekara biyu babu kayan kirki, yau ka gwangwaje ni da wannan uban kayan, ni wallahi ban san ma me zan ce ba, kamar kalmar godiya ta yi kaɗan, Allah ya suturta ka duniya da lahira, ya yalwata arzikinka, na gode MD" Jikinsa yayi sanyi sosai, duk da bai san cikakken tarihin ummi ba, amma alamu sun nuna ta sha gwagwarmaya da rayuwa. "To ki daina kukan haka, in sha Allah in dai ina raye, sutura sai dai ki ɗauka ki bawa wani, sutura ba zamu yi ta ɗinka ta muna sawa". "Na gode MD, amma dan Allah kar ka takurawa kanka yi mini abun da ba ka da shi, ni dai na gode sosai" "To ba zaki kirani da wani suna na soyayya ba, sai MD" "MD my dear" ta faɗa tana murmushi. "Wow ashe duk tsawon wannan lokacin, am your dear ban sani ba, barakallahu fik baby" Ɗaɗɗaga mata kayan ya cigaba da yi, kaya sun haɗu masu tsada har da gwal. Sai da ya zo kan akwatin ƙanan kaya, ya din ga ɗaɗɗagawa yana cewa ba ƙaramin kyau zaki yi a ciki ba. Ummi ta ce "Ai kai a nan ka fi kauri, ni bari na je kitchen abincina kar ya kama". Idan ummi ta kalli raihan ta kalli kayan nan, sai ta rasa me ma za ta ce masa, ya baje yana ta aiki a system gefen sa ga biro da takarda. Dogon matashi cikakke, dai-dai gwargwado raihan kyakkyawa ne, kuma duk kyawawan mata babu wadda ya gani ya ce yana so, sai ita kuma yake ta wahala da ita. "Ya dai madam?" Ta tashi ta ce "Bakomai, zan je wancan falon na gyara shi kan magariba". Ya ce "Yauwwa, ni kuwa na ce ko ƴar aiki za a samo miki ne? Ta din ga taya ki aikin nan, yayi miki yawa". Ummi ta ce "Aikin gidan nan guda nawa yake, zan iya abuna" "Faɗi gaskiya dai, ko abun ne ya motsa, dan kar a aure ni" "To a aurekan mana, duk wadda za ta iya zama da ni ta shigo" Ya kwashe da dariya ya ce "Eh lallai kin yi baki baby". Ummi ta ɗauki hoton kayan, ta turawa su Yaya maryam, suka din ga murna tare da sanyawa raihan albarka. Iya ƙoƙari ummi take yi, wurin rage kunyar raihan da take ji. Dan haka a yau tayi iya yin ta tayi irin shigar da yake so. Aikuwa daga kallon da ya din ga yi mata, ta gane ya ji daɗin hakan sosai da sosai. Ya sha mamaki sosai da sosai, dan kuwa tayi masa kyau sosai da sosai, Allah ya taimaki ummi raihan ba shi da abokan da zai yi zaman majalisa da su. Duk a kunyacen take, amma ta dake kar sokoncinta ya sanya shi fara kalle-kallen. "Baby zaka kai ni gaida su mamin da su kawu". Ya ce "Wow, shagwaɓar nan taki tana burgeni ummi" Maganar Iya ta tuna, da take ce mata 'Tana shagwaɓa da fuska kamar kashi' Ya amince da zuwanta gaida su mami, amma ya ce sai ranar juma'a da daddare. Washegari ranar asabar kuma sai ya kai ta gidansu. Ummi ta yi ta murna, raihan ya ce "Ai in dai zaki din ga abun da nake so, zan zama mijin hajiya Salma. Wata irin soyayya raihan yake nuna wa ummi, da take fatan ta ɗore har abada. Ranar juma'a tun safe, ummi take aikin yin sinasir da miyar agushi, wanda za ta kai gidan su raihan. Tun sallar magariba ta shirya take jiran raihan, ya dawo ya ƙare mata kallo ya ce "Gaskiya kin yi kyau da yawa, ba zan tafi da ke a haka ba, sai ƙamshi kuma ki ke yi, am jealous ki rage kyan nan" "Daga ni sai kai fa zamu tafi a mota mu dawo, dan Allah ka shirya mu tafi" Sai da ummi tayi da gaske, sannan ya shirya suka tafi. Tambayarta ya din ga yi a kan wannan kulolin restaurant za ta buɗe ne?. "Eh in dai zaka yi patronizing ɗina" "To ɗan buɗe ki san mini abun da ki ka dafa ɗin" "Aikuwa ba za ka ci ba" "Suna tafe suna faɗansu irin na masoya". Karɓar da mami tayi mata kawai jikinta yayi sanyi, ko kallo ummi ba ta isheta ba. Safiyya kuwa tun da ta ga ummi jikinta yayi sanyi, ana ta ummi mummuna ce, amma ta ga ummi dirarriyar mace, muryarta kawai idan ta yi magana sai ka so ganin waye yake yin maganar, gashi komai na ta a nutse. Duk da dare ne amma duk wanda ya ga ummi ya santa a da, ya san ta canza sosai, fatar nan ta ƙara kwanciya tayi fresh sai ƙamshi take yi. Ko gaisuwar ummi taƙi amsawa. Raihan ya ce "Mami zuwa muka yi ta gaishe ki, ta yi muku bangajiya" "Na ce maka ina nemanta ne, tun a farko ban gaya maka babu yawuna a maganar aurenka ba? Ka nema mata wata sirikar bani ba. Muguwa kawai, sumi-sumi da ke na zata ta Allah ce, ashe mutuniyar banza ce, kuma da ni ki ke zancen. Ɗa na ne dai wallahi sai kin bar shi, zan yi masa irin auren da nake so, kuma ina nan dawowa kanki" Raihan ya tashi ya ce "Ummi mu je mu gaida su Alhaji mu tafi kar dare yayi" Ta tashi kanta a ƙasa, ta ɗauki kwandon da suka zo da shi, ta ajiye wa mami na ta food flask ɗin. Mami  ta ce "Kwashe tsiyarki, ba abun da zan yi da abincinki" Raihan ya durƙusa ya ɗauka ya ce "Bari a ƙarawa mami da shi" Ta buɗe baki tana kallon raihan. Bayan fitarsu Nihal ta ce "Taɓ mami dama haka matar yayan take? Gaskiya babu lallai ya saurari safiyya, kin san halin sa ba komai yake burge shi ba, amma idan ya ce yana son abu ya dage, canza shi sai Allah. Kalli dirarriyar mace ga iyayi". "Ke dalla rufe mini baki, tashi ki bar falon nan" Can kuwa ummi jikinta yayi sanyi, amma karɓar da ta samu a wurin Alhaji da Hajiya, sai ya mantar da ita abun da mami ta yi mata. Sai gashi sun shantake, har goma na dare suna gidan, sun sha nasiha da sanya albarka daga bakin Hajiya da kuma Alhaji. Alhaji da kansa ya kira Salim da Sagir a waya cewa yana nemansu, bayan sun zo, ya sake gabatar musu da ummi. Tun ummi na nan suka fara cin abincin su, suna santi ana koɗa girkin nata, wanda hakan ya yi wa ummi daɗi sosai. Goma da rabi, sannan suka tafi gida, raihan bai yi mata maganar abun da mami ta yi ba, ita ma ba ta yi masa ba, sai dai ta damu da ganin safiyya ya ɗaga wa ummi hankali, ganinta yarinya kuma kyakykyawa. Haka ta kwana tana wasi-wasi daban-daban, ta ƙuduri aniyar sake zage damtse a kan raihan, yadda ko zai yi wani auren, ba za ta rasa soyayyar sa ba. Ta nemi iznin sa, tana son ɗaukar wani abu daga lefenta tayi kyauta da shi, ya ce nata ne, babu buƙatar ta tambaye shi. Washegari  ta yi girke-girken ta, ya kaita gidan dr. Suna hanya take ce masa "MD, yakamata ka koya mini mota, sai in din ga kai ka wurin aiki, ina ɗaukko ka" Yayi dariya ya ce "Matata direbata" "Eh mana, kaiman ka din ga hutawa" "Kawai ki ce a saya miki mota" Ta waro ido ta ce "Wace ni? Ba haka nake nufi ba da wasa nake yi maka". A ƙofar gidan yayi parking, ya ciro 10k ya miƙa mata ya ce "Wannan ki bawa dr. Ki ce in ji ki amma, ni idan na zo ɗaukar ki, zamu gaisa da shi" Kissing ɗin raihan ta yi a kumatunsa ta riƙe hannunsa ta ce "Thank you baby.. ya kalli idonta ta ƙarasa babyna. Dariya yayi yayi kissing ɗin ta a baya, yana maimaita mata i love you. Farida kasa ɓoye mamakinta tayi, ta bi ummi da ido, ummi kuwa ta shagala suna murnar ganin juna ita da noor. Kallo ɗaya zaka yi wa ummi, ka san hankalinta ya kwanta, leshin jikin ummi kawai take kallo, da yake wasu kayan a ɗinke a ka kawo mata, ta sha kwalliya duk da mayafinta a ka ta ɗora shi. Dr. Ya fito yana faɗin "Oyoyo mamana, amarya ba kya laifi" Ummi ta durƙusa tana gaishe shi, ya amsa mata cikin kulawa. Ya ce "Mamana, kin ga yadda ki ka yi kyau kuwa? Lallai aure ya karɓe ki, kin ganki kuwa? kunya ta rufe ummi. Da kausar ba tayi niyyar fitowa ba, amma dai ta fito ganewa idonta ikon Allah, ummi an sha to match, har da wani agogo mai ɗan karen kyau. Noor ta bubbuɗe kwanukan da ummi ta zo da shi, miya ta sha kaji zuƙu-zuƙu ga snacks, abun da inteesar ba ta taɓa yi ba. Sun yi hira sosai da dr. Har take gaya masa cewar raihan ya yi mata lefe. Dr. Ya din ga sanya masa albarka. Da azahar da zai fita, ummi ta kawo kuɗin nan ta bashi dubu bakwai, ukun kuma ta ƙara biyu ta bawa farida biyar. Sai dai farida ba ta so yadda ta ga ummi ba, ta kasa ɓoye hassadarta baƙin ciki ya bayyana ƙarara a kan fuskarta, kausar ma sai wani zumɓura baki take yi tana hura hanci. Ummi ta ce wa noor "Yaushe zaki zo ki ga kayan da MD ya saya mini, ki zo ki ɗauki abun da ki ke so" Noor ta ce "rana ita yau, zan diro ko ta katanga ne, zan zo ki haɗa mini akwatu guda" ummi kamar wurin noor ta zo, tare suke ta hirarsu. Ummi ta miƙe ta hau gyare-gyaren gidan, duk gidan yayi ƙazanta saboda ba ta nan. Tana nan Abdul ya dawo, shi ma ya yi farinciki sosai da sosai da ganin ummi, sabuwar shadda ta bashi yadi goma, ta ce ya ɗinka musu shi da dr. Ana sallar magariba raihan ya zo tafiya da ummi, suka gaisa da dr. Yayi wa dr. Alheri, ya sha sanya albarka sosai daga wurin dr. Ya ɗauki matarsa suka tafi. *** Watannin ummi huɗu a gidan raihan, mami ta matsa lamba a kan lallai sai ya auri safiyya. Sai dai juyin duniya, fafur raihan ya nuna mata ba zai iya auren Safiyya ba. Ta je ta samu Alhaji da maganar, ya ce ta bari, za su yi maganar da Raihan. Raihan ya amsa kiran da Alhaji yake yi masa, ba tare da sanin dalilin sa ba. Bayan Alhaji ya sanar masa da buƙatar mami, sai ya ga ya ɓata fuska. "Babban mutum ba ka ce komai ba" "Alhaji me zan ce? Kwata-kwata yaushe na yi auren da zan ƙara wani? Ni wallahi ummi ta isheni, mami ba za ta iya samo mini mace mai qualities ɗin ummi ba, ni dai dan Allah ka bata haƙuri, ka san plan ɗina Alhaji wallahi ina son ummi, yayi wuri in yi mata kishiya, kuma wallahi idan na auri wata ba zan iya adalci ba, na fi son ummi" Alhaji ya yi murmushi irin nasu na dattawa ya ce "Shikenan, jeka ba sai ka je wurinta ba, tafi gida abun ka". Sai da daddare da mami ta zo wurin Alhaji, tayi masa maganar ya ake ciki, yaushe za a kai kuɗin auren Safiyya" Alhaji ya ce "Bilkisu, ina son ki fuskanci wani abu, ki ƙyale yaron nan da matarsa hankalinki da na su su kwanta, kar ki saka ƴar mutane a wahala, idan ba ki bi a hankali ba yaron nan zai iya gaya miki abun da zaki gaza haɗa ido da shi, ya ce ba zaki iya samo masa mace irin matarsa ba, ko ya auri wata ba zai yi musu adalci ba, idan kin gane shikenan idan kuma sai ranar da yayi miki hansfree shikenan. Na manta ban gaya miki ba, this coming Friday, za su tafi China tare da matarsa maganar auren nan ki bar ta for now. Ayshercool 08081012143 *Alhamdilillah, sai kuma Allah ya kaimu salla da rai da lafiya, Ubangiji Allah ya karɓi ibadunmu, ya sanya mu cikin ƴantatun bayinsa*                          *CUTARWA* *BRIGHT PENS* (FREE BATCH) *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* 40 MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH. Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe. FOLLOW AND SHARE AYSHERCOOL 08081012143 MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH. Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe. 40 Kamar ya gaya mata ranar mutuwarta, ta ce "Ban gane ba, da ita zai tafi china, a kan me?" "A kan matarsa ce, kuma ya isa" A fusace ta ce "Wai meyasa ka ke haka ne? Wallahi ko bangon duniya zai je, sai an yi maganar aurensa da safiyya". Alhaji ya yi murmushi yayi shiru, ya ƙyaleta ya cigaba da abun da yake gabansa. Ummi da raihan Kuwa suna zaune a toilet, yana ta murza mata dilka a bayanta, ita kuma tana shafawa a fuskarta. "Salma" ta ɗaga kai ta kalleshi ta ce "Salma kuma?" "Ba ke ki ka ce in din ga kiranki da sunanki ba?" Cikin shagwaɓa ta ce "To ba da ba ne?" Yayi murmushi ya ce "Lokacin ba kya so na ko? Yanzunma ina doubting" Shiru ta yi masa ta mintsine shi a gashin ƙafarsa, ya janye ƙafar yana dariya. "Wai wannan abun ba zafi da nake murza miki kuwa?" Yayi maganar yana leƙa fuskarta. "Ai ba ka murzawa ma sosai fa" "To ai gani nake zai ji miki ciwo, meye amfaninsa ne?" "Laushin fata yake ƙarawa" ta bashi amsa. "Ban da wannan laushin wanne ki ke nema kuma, idan ba so ki ke a ji miki ciwo ba?" Ta tashi ta ce "Zauna saura kai, kai ma yi maka zan yi" "A'a ni ba na so, ba zaki bani wahala ba" Ta riƙe hannunsa tana shafa masa a fuskar sa, tana murza masa tana dariya ta ce "Sonake kai ma ka yi kyau, in ga ka na glowing" "Duk wannan kyan bai yi miki ba" dariya take yi duk ta shafa masa a jiki. Ta gama ta ɗaukko wata roba, an rubuta annur glowing scrub, ya kalleta ya ce "Wannan fa?" "Scrub ne, homemade, na saya zan gwada, ka san mutanenmu suna da skills, amma mun fi son sayen na ƙasashen ƙetare, amma yana da kyau sosai komai na ciki natural ne" (Ga mai buƙatar mallakar scrub ɗin nan, domin su yi glowing tare da ummi, mijinta ya zame mata kamar raihan GA ANNUR GLOWING SCRUB, kuma ku saya ku jarraba, ba iya nan suka tsaya ba, har da maganin gyaran gashi, wanda amosani, karyewar gashi, ko ƙarfin gashi ya dama, sun tanadar muku maganin matsalar da ingantattun kayan haɗi natural, kuna iya tuntubar su kai tsaye a wannan lambar wayar 0907 820 9905) Raihan kallon ummi yake yi, yadda take yi masa bayani, yayi murmushi ya ce "Ki wanke mini fuskata, wannan abun ya dameni, duk ya maƙale mini a gemu" Ta wanke masa fuskar, ya tsaya yana kallon mudubin toilet ɗin ya ce "Kamar na fara glowing ɗin ko?" Tayi dariya ta ce "Daga yi sau ɗaya, sai ka kwana biyu kana yi sannan zan fara tantance? to ka tafi zan yi wanka, dilkata ta bushe" Yayi mata wani irin kallo ya ce "Ban gane in fita ba?" Ta ɗan kwaɓe fuska ta ce "Eh wanka zan yi" "Ina zamana ki ka ce na zo na shafa miki abu, yanzu kuma ki ke korata?" Ummi ta ce "To ai dama iya shafa mini nake son ka yi, hannuna ba ya kaiwa tsakiyar bayana". Raihan ya ce "Tun da na shafa miki ni zan ɗauraye ki, nima kalli yadda ki ka ɓata mini jikina da wannan abun, sai na sake wanka" yayi maganar yana cire vest ɗin jikinsa, da duk tayi yellow. Raihan a rayuwar sa yana matuƙar son soyayya da kulawa, sai da ya auri ummi ma ja gane hakan, dan shi da duk hakan ba ya gabansa, kuma a hankali ummi na rage wannan kunyar ta sa da take ji. Bayan sun fito daga wankan, ya zaunar da ita a gaban mudubi, yana shafa mata mai, ya jona hand dryer, zai busar mata da gashi. Ta cikin mudubi ya kashe mata ido ya ce "Ya dai? Wanka da miji ya fi lada fa, sai wani ɓata rai ki ke yi, kuma kin fi fita fa da na wanke ki?" Yayi maganar yana murza fatarta yana murmushi. "Au da bana fita?" "Gaskiya dai, ki din ga biyana ina yi miki wankan, na shafa miki kayan shafe-shafen naki, kuma in yi miki wanka, ki din ga biyana, idan ina yi miki sai kin fi fita" Ummi ta ce "Hmm kalli agogo, sai makara ka ke yi, kuma sai na kira Alhaji na gaya masa wasa ka ke yi da aiki, ba ka fita da wuri" Yayi dariya ya ce "Sai in ce masa ke ki hana ni fita, ki ka tsare ni da soyayya, na kasa fitowa" miƙewa tayi ta ce "Kai ba ka jin kunya fa ko?" Kamar ba za su rabu ba, haka ya shirya suka fita falo, ta raka shi har gaban motarsa ya tafi. Ta koma ciki tayi ta fama da aiki, dan kaf ɗakunan gidan nan, kullum sai ta shiga kowanne ta gyara. Wajen ƙarfe sha biyu ta kammala aikinta, ba ta karya ba sai a lokacin ta yi farfesun kifi da dankali, ta koma falo ta zauna tana karyawa, ga ƙamshin turaren wuta yana tashi, ga Tv tana yi. Ta ƙarewa falon kallo, ta kalli kwanon hannunta, ta yi murmushi ta ce "Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabatta gareka, tsarkakken sarkin da babu wani kafinsa kuma babu a bayinsa, Sarkin da ni'imarsa da yalwarsa ba su da iyaka" ta furta hawaye na taruwa a idonta, ba ta taɓa tunanin irin wannan rayuwar ta ƴanci ba. Ta ɗaga wayarta ta kira maiduguri, sun daɗe suna gaisawa, bayan sun gama ta kira raihan. Sun daɗe suna waya, suna hira sai da ya ce mata zai shiga meeting sannan ta katse wayar. Kasancewar kifin da ta ɗiba tayi farfesu da yawa raihan ya kawo, dan haka ta tsiri yin girki da kifin, a cewarta a kai wa dr. Wani wani kuma a kai gidan su raihan. Dan raihan ya riga ya bata damar duk lokacin da take son yin alkhairi, ya baga dama ba sai ta tambaye shi ba. Tun la'asar da raihan ya dawo gida ya ci abinci, take lallaɓa shi ya kai abincin nan, amma sai yawo yake yi mata da hankali. "Dan Allah MD ka kai abincin nan kar yayi sanyi" Ya ce "Zan kai, yauwwa tafiyarmu fa sai next week in Allah ya kaimu" Jiki a sanyaye ummi ta ce "Ka gaya wa mamin zancen tafiyar ne?" "Meyasa ki ka damu ne? Zan gaya mata in sha Allah, kar ki damu ba wata matsala in sha Allah, zan kai abinci da daddare yanzu so nake na kasance da ke, wuni muka yi fa ba ma tare" Ta yi shiru ba ta ce komai ba, ya fuskanci ta na tsoron abun da ka iya biyo baya idan ya sanarwa da mami zai tafi da ita china, dan ita a so samunta kawai ya ƙyaleta shi yayi tafiyar sa. A booth ɗin mota ya tafi da abincin sallar magariba, bayan ya idar ya fara zuwa gidan su ummi, sannan ya tafi gidansu. Bai san Alhaji ya gaya wa mami zancen tafiyar ba, ya fara shiga sashen hajiya, suka gaisa ya ajiye mata abincin, dan ya san idan ya kai wa mami, ba burgeta zai yi ba ƙarshe ta ci zarafin Abincin ma. Bayan sun gama gaisawa, ya shiga sashen mami, sai dai yanayin fuskarta  ya nuna masa akwai matsala. "Ina wuni mami?" "Nemi wuri ka zauna" tayi maganar ba tare da ta amsa masa ba. Ya zauna yana satar kallonta. "Ni na haifeka ko waccan mummunar yarinyar?" "Wace irin tambaya ce haka mami, me kuma tayi?" "Yanzu raihan ka yi riƙar da zaka tsallake maganata ka ce zaka ɗauketa ka tafi china, tawa maganar ka banzantar da ita ko?" Raihan ya ce "Wallahi mami Alhaji ne ya shirya tafiyar, ba laif.... "Rufe mini baki ina magana kana magana, na kusa kawo ƙarshen auren nan, na fuskanci ba haka suka ƙyaleka ba, tun da ka fara bijire mini, kama aure kai da Safiyya babu fashi,  umarni nake baka ba shawara ba, na soke tafiyar nan" yayi mata shiru, ta ci masa mutunci daga shi har ummi, tare da aibata ummi yadda take so, tayi ta gama bai tanka mata ba, ya tashi ya bar falon. Bayan fitarsa Nihal ta fito ta ce "Mami, dan Allah ki din ga sassauta adawa da auren nan, kina gani fa kin gama banbamin ki, ko amsa bai baki ba ya tafi" Mami ta ce "Shi ya isa, ban haifi ɗan da zai bijire mini ba a kan mace wallahi" Nihal ta kalli mami ta ce "Idan kuma safiyyan ma yayi mata haka fa, ya so ta kamar yadda yake yi wa wannan? Tun da kin ga yanayin halinsa ɗaya da Alhaji" Mami ta ce "Gara safiyya wannan ai tawa ce, ba wani abu" Nihal ta numfasa ta ce "Mhmm to mu kuma fa? Wasu fa zamu aura, mu ma ayi mana yadda ki ke yi mata kenan?" Cikin mamaki ta ce "Au goyon bayan sa ki ka fara kenan ya wulaƙanta ni?" Nihal ta yi murmushi ta ce "Ahh haba dai, kawai dai wani hasashe nake yi ne, Allah ya kyauta" Ummi kuwa ta sha kwalliyar dare, tana jiran dawowar raihan, amma yanayin yadda ya shigo ya tabattar mata da akwai matsala, ko kallon in da take bai yi ba, ya wuce wani bedroom ɗin. Jikin ummi yayi sanyi sosai, ta shiga tunanin ko ta yi wa raihan wani laifin, amma ta ga lafiya ƙalau suka rabu, hakan ya tabattar mata da ba ita ta yi laifin ba. Bayan mintuna talatin, ta je ta leƙa ɗakin da ya shiga, ya kwanta yayi ruf da ciki, ta na son shiga amma idan yayi irin wannan burkicewar tsoronsa take ji, dan haka ta ƙyale shi. Da safe ma ko karyawa bai yi ba, dan tana kitchen ya tayar da motarsa ya fice, sai ta ji gaba ɗaya duniyar ta yi mata zafi, kamar ta ɗora hannu a ka tayi ihu. Raihan kuwa ga damuwar abun da mami tayi masa, ga tausayin ummi yake ji, har cikin ransa yake jin idan ya auri Safiyya ba zai yi mata adalci ba, dan jin ummi yake yi a kowanne sashi na zuciyarsa, haka zalika ma yaushe ya auri ummi, da har za ace ya kawo wata?. Ya ji ba zai iya cewa ummi ya janye tafiyar su ba, hakan kamar zubar da kimarsa ne tare da kimar ita kanta mamin da ta kasa gane hakan, dan haka ya ji bai zai iya cewa ya fasa tafiyar nan ba da ummi, ya san duk abu Alhaji zai tsaya masa. Sai ƙarfe huɗu na yamma ya dawo gida, ya kwaso gajiya sosai da sosai, sai dai kamar mai aljanu ya koma normal har yana ce mata gajiyar da ya yi kamar yayi gudun kwana biyar. Ta biye masa ya gama cin abinci, ya koma falo zai yi kallo, amma ta bar falon ta koma bedroom. Ya bita ɗakin ya tarar da ita ta fito da kayan wardrobe tana gyarawa. A ɗan shagwaɓe ya ce "Yanzu fisabilillahi ba ki yi aikin bana nan ba, sai yanzu da na dawo, sonake ki zauna a kusa da ni mu yi hira" ta ɗago da idanunta ta kalleshi, ta kawar da kanta tana tura baki ta cigaba da aikinta. Ya ƙarasa gabanta yana cewa "Wai madam ya ne? Me na yi miki ne?" Cikin rauni ta ce "Kai zan tambaya me na yi maka? Kawai ka share ni, har da canza ɗaki kuma ni ban san me na yi maka ba, sai yanzu zaka din ga yi mini wasa ba zan yi hirar ba" tayi maganar har muryarta na rawa saboda shagwaɓa. "Ohhh sorry kairun nisa'i, ba ki yi mini laifi ba, ba na son laifin da ba naki ba ya shafe ki ba ne, kin san idan ina fushi sai a hankali yanzu ba gashi na saukko da kaina ba, ai idan ke ki ka yi mini laifi ke zan yi wa, bana son in ɓata miki rai ne alhalin ba ke ki ka yi laifin ba". "Ni ba ruwana da kai, har da wani canza ɗaki, to ka tafi kenan kwaso maka kayanka zan yi na mayar maka ɗakin da ka kwana, nima na huta" Ya kwashe da dariya ya rungumota jikinsa ya ce "Ke idan wani ya gaya miki wannan tatsuniyar zaki yarda? Raba ɗaki da ke, ke ko a baki ya yi miki ma'ana? Iya wuya muna tare sai dai ki yi ta haƙuri. For now dai a yafe mini laifina" Ta ɗaga kai ta kalleshi ta ce "Bribe me tukuna" "Da me?" Cikin nutsuwa ta ce "Ka fasa tafiya da ni, saboda hankalin mami ya kwanta bana son ta yi mini fushi da kai" Yayi saroro yana kallonta, ya maze ya ce "Ba na ce miki zan kula da komai ba? ba zata ƙi ba ai" Tayi murmushi ta ce "Na san a kan maganar ne ka yi fushi jiya, idan damuwarka ta wurin aiki ce ina ganewa, haka idan da mami ne dan Allah ka yi haƙuri, wallahi ba wani abu ka je ka dawo". Raihan ya ce "Ba yadda ki ke tunani ba ne, za ta amince fa, honeymoon zamu je" Ta waro ido ta ce "Wane honeymoon kuma? Me ya rage kuma wani honeymoon zamu je, ai ka gama honeymoon ɗinka a nan" "A'a fa, ga aiki ga stress, gara muje mu samu cikakken lokacin cin soyayyarmu ba hayaniya" yayi maganar yana sumbatar bakinta. *** An kai ruwa rana sosai da mami a kan tafiyar nan, Alhaji ne ya tsaya tsayin daka a kan tafiyar, ya ce idan raihan ya dawo ayi zancen auren safiyya. Duk da farida ta san sirikar ummi ba ta sonta, amma ba ta zaci ummi za ta samu kwanciyar hankali da nutsuwa haka ba, Ummi ta je ta yi musu sallama a kan tafiyar su china. Duk wanda ya san ummi a baya ya ganta yanzu ya san a cikin ni'ima take, iya kyan da fatarta tayi ka san tana samun kulawa. Noor ta din ga murna, jin ummi za ta je china har da cewa ta gaisar mata da su bursuli. Kwanciyar hankalin ummi ya tsayewa farida a rai, tare da jin cewar kausar ce yakamata ace a cikin wannan kwanciyar hankalin, inteesar dai ga ta a cikin daular, amma mijinta ba ya ɓanɓaruwa, gashi ya juya mata baya. Ashe tun kan aure ya kai ta aka yi mata allurar family planning, wai yafi son su gama cin amarci kan su tara yara, babu wanda ta gaya wa daga baya kuma abun ya bata matsala ciki yaƙi zama, wadda ya auro kuma ta samu ciki sai wulaƙanci take fuskanta iri-iri. Ga kausar ba makaranta ba mijin aure duk da ga kyau ga kwalliya. Abdul kuma babu ƙwaƙƙwaran aikin yi. Saura kwana uku tafiyar, Ummi da raihan suka je maiduguri ma, Mariya kamar ta haɗiye ummi, suma sun yi farinciki ganin ummi, raihan yayi musu alkhairi sosai da sosai. Suke gaya mata har a lokacin bayan bikinta, dr. Yana zuwa ya kawo musu sha tara ta arziki, tare da duba lafiyar Mariya. Hakan ba ƙaramin daɗi ya yi wa ummi ba, karamcin kawu yahaya ya sanya ba ta taɓa mantawa da shi a cikin Adduo'inta, kuma a duk lokacin da ta samu abun alkhairi take kai masa da iyalinsa. Jin mami ta matsa a kan maganar auren raihan, ya sanya jikin ummi yin sanyi, a baya tana ganin babu wani abu idan raihan ya ce zai ƙara aure, amma a yanzu fargaba ta shige ta da tsoro. Dan a gabanta mami ke kiransa ta jaddada masa maganar auren, ko ma safiyyan ta kira shi wai zata gaishe shi, tana iya kokarinta wajen kar ta nuna masa wani abu na ɓacin rai, dan tana ganin idan ta yi masa haka ba ta yi masa adalci ba. Ta ji gaba ɗaya tafiyar ma ta fita daga ranta ba ta so. Sai dai suna barin ƙasar, ta ɗan samu nutsuwa, mussman da kullum tana tare da raihan tana shan soyayya da kulawa kala-kala a wurin matashin mijinta. Sun samu zuwa wurare masu matuƙar kyau da ɗaukar hankali, ƙarƙashin jagorancin ɗaya daga manyan manajojin su raihan, da suke kasuwanci tare. Shi yake kula da komai nasu kama daga masauki zuwa abincin su da sauran buƙatu. Ummi ba ta taɓa tunanin ganinta a ko da airport ba, sai gashi ta keta hazo, ta bar ƙasa Nigeria. Babban abun da ya bawa ummi mamaki, bai wuce yadda ba ta ga mutanen ƙasar na muzanta halittarta ba, sai ma bayan shirya musu wani cin abinci da managern yayi, da iyalansa da wasu daga abokan kasuwancin su, suke cewa ba su taɓa ganin baƙar fata mai kyan ummi ba. Da aka fassara mata da turanci abun da suka ce, saboda galibi ba su iya turanci ba, mamaki abun ya bata, wai idonta mai kyau da fatarta, har ta fara tunanin ko ba'a suke yi mata, suka din ga layin hotuna da ummi. A duk lokacin da suka fita shaƙatawa, sai mutane su yi ta kallonta, har wasu su nemi su ɗauki hoto da ita, suna yi musu tambayoyi mussaman idan ta yi shigar hausawa, duk da ta fi saka rigunan abaya a kan kayan hausawa. Duk da ummi na ƙoƙarin kare mutuncin aurenta, da matan su kawai take gaisawa tayi hotuna, sai da kishin raihan ya kasa ɓuya. Sun fita baki wani ruwa da daddare shan iska, take  tambayar raihan "MD dan Allah mutanen nan da gaske suke, ko zagina suke yi da suka ce ina da kyau?" Ya ja hancinta ya ce "Idan na faɗa ai ba kya yarda, you are beautiful baby" Ta saka hannu ta shafi fuskarta ta ce "An ce fararen fata suna ƙyamar baƙaƙe, amma ni har ƴan uwana baƙaƙen ƙyamata suke yi" Ya kwantar da muryarsa ya ce "Mutanen china suna da ƙarancin nuna wariyar launin fata, su kuma mutanenmu son zuciya ne kawai, da rashin bawa abun da muke da shi muhimmanci". Ta sake jan numfashi ta ce "Ni fa bayan baba da mama, kai ne kawai ka ke cewa ina da kyau, sai noor gani nake duk Nigeria na fi kowa muni" Ya ɓata fuska ya ce "Ban hanaki faɗar irin wannan maganar ba? Me ki ke nema a yanzu da Allah bai yi miki ba? Ubangijin da ya yi ki yana sonki, mama na sonki nima ina sonki to me ki ke nema kuma?" Ummi ta girgiza kai ta ce "hmm MD kenan, idan aka ce ina da kyau wallahi sai in ji kamar zagina ake yi, saboda na fi sabawa da jin kalmar cin mutunci " "Ni kuma wallahi a duniya, a yanzu dai ban sani ba ko a gaba, amma wallahi ba ki ga yadda ki ke yi mini kyau ba Salma, komai naki son shi nake, wallahi duk macen da na gani, sai in ga ba ta kai ki ba. Ina kaucewa auren Safiyya ne saboda a yanzu dai na ƙara aure ba zan iya adalci ba son da nake yi miki daban ne, a ƙasan zuciyata nake jin ki, bana son wani abu na rashin daɗi ya raɓe ki, ban san ya zan misalta miki ba ki gane ummi, kawai ni dai ki yadd ki saka a zuciyarki ina sonki, kuma wallahi ban taɓa ganin muninki ba ko sau ɗaya. Kawai ji nake duk matar da zan aura ba zan samu biyayya da kulawar da nake samu a wurinki ba, mutane kawai suna ganinmu ne, amma ba za su gane tarin baiwa da Allah ya yi miki kala-kala ba, su muninki suke gani, ni kuma abubuwan da nake gani game da ke ba zasu lissafu ba. Ina sonki kariun nisa'i" Sanyin iskar wurin, da daɗin kalaman raihan, ya sanya wani irin shauƙi ya kama ummi, tare da jin ta a sama, kalaman na raihan suka sanya ta ji kamar a duniya babu wadda ta fita sa'ar miji. Abu kamar a mafarki ita da ake cewa ba zata auru ba, sai dai a taimaka a aureta saboda muninta, amma yau gashi Allah ya gwangwaje ta da miji na kere wa sa'a, kalaman na raihan ko ƙarya yake yi mata sun yi mata daɗi. Ta rungume shi sosai ta ce "Allah ya barmu tare har aljanna Zaujul janna, kana cikin mutane masu muhimmancin da suka haska fitila a rayuwata mai cike da ƙalubale kala-kala, dan Allah kar ka daina sona, ko zaka yi aure a gaba ko ka so wata, dan Allah kar ka daina so na, ko da ka daina sona ka ɓoye mini dan Allah, kulawarka tayi tasiri a rayuwata idan na rasa soyayyarka da kulawarka komai nawa zai koma farko, kai kaɗai ne hope ɗina yanzu, an ce wataran ana gajiya da juna dan Allah kar ka gaji da ni" ta ƙarasa maganar kamar mai magiya. Ya saka hannayensa biyu yana shafa bayanta, yana jin yadda take kuka. "Soyayyar da aka gina da tubalin toka ita ke gushewa, tamu kuma da tubalin dutse muka gina ta, ni da ke har aljanna babyna" ya ƙarasa maganar yana ɗago fuskarta yana share mata hawaye. Tausayin ummi ya cigaba da mamaye masa zuciya, tare da jin zai jure kowane ƙalubale ummi ta samu farinciki. Kwanakin su ummi takwas a ƙasar, ɗaya daga cikin waɗanda suka ci abinci tare da su ummi, ta nemi iznin ummi a kan tana son ɗora videonsu da suka yi ita da ummi, a YouTube, babu tunanin komai ummi ta ce mata to, saboda yadda ta san da shigarta ta mutunci a jikinta a ka yi videon. Sai dai kwana ɗaya take nunawa ummi adadin views ɗin da videon ya samu, ya tafi viral da yadda mutanen ƙasar har ma da wasu suke sharhi a kan ummi. Communication da mutanen yana bawa ummi wahala, dan su ba su iya turanci ba, ita kuma ba ta jin yarensu. Amma duk da haka mutane ne masu tambaya, wasu lokutan har live videos suke yi da ummi, suna yi mata tambayoyi a kan mutanen Afrika, a gaya mata tambayar da turanci, ta basu amsa da turanci a fassara musu. Raihan sai dai ya kalle su yayi dariya, ya san suna takura ummi, dan ba son mutane take yi ba, gashi kuma kamar tsoronsu ma take ji. Sai dai ya ƙyalesu ne, saboda wataƙila a dalilin haka ummi ta samu wani cigaba a rayuwarta, da zai tabattarwa da duniya musamman masu nuna cewa ita mummuna ce, ba za ta yi acheiving wasu abubuwa a rayuwa ba saboda kalarta. Har tambayarta suke yi a kan ƙabilar hausawa, da Nigeria baki ɗaya, duk da akwai masu tambaya cike da izgili ga ƙasar sai dai cikin hikima da dabara ta aiki ummi take basu amsa. Sai da ummi ta fara damuwa da yadda adadin masu zuwa ganinta da hotuna da ita ke ƙara yawa kamar wata halitta ta daban, ga kuma kyaututtuka da ake ba ta. A daddafe suka yi wata ɗaya, fatarta ta ƙara kyau, duk da daga ita har raihan abinci ba kowane iri suke iya sakin jiki su ci ba. Ummi ta tara kyaututtuka sosai, ranar da zasu tafi ƙawarta da suke video ta ba ta kyaututtuka, ɗan zaman da suka yi sun saba da ita, suka yi ta tambayarsu yaushe za su dawo, raihan ya ce musu sai wani lokacin. A jirgi ya din ga yi wa ummi mitar daga zuwa ƙasar mutane ta zama cele, shi fa haushi yake ji yadda ake sakata a social media. Cikin damuwa ta ce "Meyasa baka gaya mini ba ka so ba? Ka bari muke yi, ni bana son su ga kamar na yi musu wulaƙanci ne" Yayi murmushi ya ce "Sweetheart, komai yana da sila, tsakani da Allah zuciyata kamar ta fashe, ana talla da matata, amma sai na tuna ke ƴar jarida ce tun ainihinki ma, kuma ban san alkhairin da zaki iya samu a sanadin hakan ba, ina fatan ko iya haka a ranki zaki ji cewa ke ta mussman ce, kalli dubban mutanen da ke bibiyar live ɗin da ku ke yi, ba kuma wai dan kina wani abu na musamman ba, kalarki da irin halittarki da mutanenmu suke kushewa, su ita ta ja hankalinsu" Tayi shiru ba ta ce komai ba, ta cigaba da wasa da yatsun raihan da ke hannunta. Ko da suka dawo ya hanata gaya wa kowa sun dawo, ya ce sai sun gama hutawa. Ita kuwa ba ta zauna hutun ba, saboda ganin yadda gidan yayi mata ƙura da yawa. "Dan Allah ki zauna ki huta, aikin nan yayi miki yawa, ki yi da kaɗan-kaɗan, an ce a samo miki ƴar aiki kin ce ba kya so". Ta ce "Bana son in ga wurin da datti ne, dan Allah ka yi haƙuri" haka ya ƙyaleta ta yi ta share-sharenta. Sai da suka kwana biyu da dawowa, ya je gida, ya gaida su mami. Alhaji ya din ga mitar meyasa bai zo da ummi ba. Raihan ya ce "Ta gaji ne sosai, ba ta saba doguwar tafiya ba, kamar ma dai ba ta jin daɗi shiyasa na baro ta a gida". "Allah sarki, with time za ta saba ne in sha Allah" ya samu kyakkyawar karɓa daga Hajiya da Alhaji banda mami, da ke masa abu kamar agola ba ɗanta ba. Ganin shirun yayi yawa ya sanya ya miƙe zai tafi, da mamaki mami take kallonsa kamar yanayin ko in kular da take yi masa baya damunsa balle ya saduda. "Ya maganar mu?" Ya ɗan yi turus ya ce "Wace maganar?" Ta ce "Tambayata ma ka ke yi?" "Mami ki dubi girman Allah ki yi haƙuri, wallahi ni bana son yarinyar nan, ummi ba ta yi mini laifin komai ba, watanmu shida fa da aure har kuma sai na ƙara aure, da ƙanan shekaruna in tara mata" "Raihan ni ka ke gayawa ba ka son safiyya? Kuma da ka ji maganata tun farko ai da haka ba ta faru ba, kuma wallahi ka cigaba da bujire mini sai na kashe auren nan a kwanakin nan dan bana ƙaunar yarinyar nan". "Mami, dan Allah ki taimaki rayuwata, ki ka rabani da ummi, ba zaki iya sama mini matar da zata maye mini gurbinta ba!. Ayshercool 08081012143                       *CUTARWA* *BRIGHT PENS* (FREE BATCH) *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* 40 MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH. Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g AYSHERCOOL 08081012143 MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH. Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g 41 Galala mami ta buɗe baki tana kallon raihan, ba ta taɓa zaton wannan kalaman daga bakinsa ba ko a mafarki, ta rasa wace amsar ma yakamata ta bashi, ganin ba ta da abun cewa ya sanya jiki a sanyaye ya fice, zuciyarsa na wani irin zafi. Har ya nufi motarsa ya ji an riƙe hannunsa, ya waiwaya ya ga Salim. Ya gyara nutsuwarsa cikin girmamawa ya ce "Yaya ina wuni?" "Meyafaru ne?" Raihan ya kalleshi ya ce "A ina?" "Dambe ka yi ne? Ba ka ga yadda ka ke gumi ba, idonka ma yayi ja?" Ya girgiza kai ya ce "Bakomai, dama mun dawo ne na zo gida mu gaisa ban zaci ma kana nan ba" Salim ya kama hannun raihan ya wuce da shi ɗakinsa, Sagir na kwance a falo yana kallon tv suka shigo, sallamar su kawai ya amsa ya cigaba da abun da yake yi. Ya zaunar da raihan a kan kujera, shima ya mayar da hankali a kan kallon ba tare da ya cewa raihan ɗin komai ba. Sun shafe a ƙalla mintuna talatin a haka, sannan Salim ya numfasa ya kalli raihan ya ce "Are you ok now?" Ya jinjina masa kai ya ce "Yes, na gode sosai" Salim ya sake tattara nutsuwar sa a kan raihan ya ce "Me yake faruwa? Kar ka ɓoye mini" raihan ya yi shiru yana yi wa Salim kallon mamaki, dan sam ba mai shiga abun da bai shafe shi ba ne ba. Kamar ya san me raihan yake tunani a kai ya ce "Na san zaka yi mamakin tambayarka da nake yi, na samu labarin matsin lambar da ake yi maka a kan ƙara aure a wurin Hajiya, kuma daga dawowarka ba zai yiwu ace har  wani abun ɓacin rai ya faru da za ka shiga cikin tashin hankali ba, in dai ba a kan maganar ba ne ba. Ka san meyasa na titsuyeka nake tambayar ka?" Raihan ya girgiza masa kai alamar a'a. "Alƙawarin da muka ɗaukko wa mahaifiyarta da ni da kai, Allah ya sani ina tausayin baiwar Allah nan sosai, kuma kai ka bani labarin irin wahalar da take sha a rayuwa, idan har ka rabu da ita, ka yi wa mahaifiyarka biyayya haka ake son ɗa na gari amma ka sa a ranka ko da ranka ko bayan ranka sai wani ya auri ƴar ka ya saketa!. Haka zalika idan ka auri wannan yarinyar ka zalunci ummi, ko ita wadda zaka aura ɗin, shi ma ka shirya kare kanka a gaban Allah" Gaba ɗaya raihan ya sake rikicewa ya ce "Wallahi yaya na rasa yadda zan yi, ina son ummi muna zaune lafiya tana kyautata mini, me zai saka na saketa ko ace sai na yi wani auren? Ni ba na son safiyya a matsayin matar aure, kuma bana son saɓa wa mami" Salim ya kaɗa ƙafa ya ce "Am sorry to say, iyayenmu mata wasu lokutan na da gajeren tunani, iyayenmu da suke aure fa, ba daga sama suka faɗo ba, su ma ƴaƴan wasu ne. Anyway Allah ya kyauta, na kira ka ne dama dan na yi maka tuni a kan amanar da ka ɗaukko, kayi ƙoƙarin gyara tsakanin ka da mahaifiyar ka, ba tare da wani ya cutu ba". Raihan ya jinjina kai ya ce "Na gode sosai yaya da tunatarwa, zan yi iya ƙoƙarina in sha Allah" yayi musu sallama ya fice. Sagir ya bi bayansa da kallo, yana wani tunani a ransa na kowa da irin jarrabawar sa, shi da yake mai biyayya babarsa ta saka shi a gaba, su da suke sai a hankali su suka saka tasu uwar a gaba, kuma ya san su ta su uwar ba za ta taɓa yi musu haka ba, amma tabbas da shi ne a matsayin raihan, ba wanda ya isa ya tursasa shi yin abun da ba ya so. Mami kuwa hankalinta ya gama tashi, tare da tabattar wa da kanta, ummi da danginta sun haɗu sun mallake mata ɗa, dama ance irin su ba sa zaman aure haka sai sun yi asiri. Cikin rashin dabara, ta kira yayarta da ke yi mata baƙi jagoranci, ta zayyane mata komai, aikuwa ta ƙara zigata a kan ko dai ta raba raihan da ummi, ko kuma maganar Hajiya ta zama gaskiya, ɗan so ya auri matar so!. Raihan ya koma gida, yana ta saƙe-saƙe, amma tunda ya ci ya ƙoshi, suka shiga soyayyarsu da ummi sai ya manta, ta hau bashi labarin aikin da ta sha na gyara gidan jikinta sai ciwo yake. Ya yamutsa fuska ya ce "Ki daina gaya mini kin wahalar mini da kanki, tun da dai ba kya jin magana". Tayi murmushi ta ce "Zaujul janna, wata alfarma nake nema dan Allah" Ya ce "Yau Allah ya yi kenan, tun kan mu tafi nake ganin alamar akwai magana a bakinki, kin ƙi faɗa ne kawai. Ina jinki" Ta ɗan yi jimm tana jujjuya maganar sannan ta ce "Dan Allah idan ban takura maka ba, dan Allah so nake idan da ɗan space a taimaka a ɗauki yaya Abdul aiki dan Allah, amma idan babu shikenan bakomai" Kawai ya zuba mata ido, dama wannan maganar take ta yi wa kwana-kwana. Ya maze ya ce "Ki rubuta a rubuce ki kai mini office" hararsa tayi ta ce "zaka sake kenan ko?" Yayi dariya ya ce "Ashe baki manta ba?" "Ya za ayi na manta, waccan ranar sai da na yi kuka" "Koma me na yi miki ai ke ki ka janyo, handsome guy kamar ni, a wanke hannu a taɓa ɗan kyakykyawa da ni, wai ki ka rufe ido ba zaki aureni ba, wai ni yaro ne ko?" Ta tura baki tana kawar da kanta gefe. "Kuma yanzu ko kunya ba kya ji, kin kwanta a jikin yaro kina shagwaɓa, ko kuma yanzu na girma ne?" "Wai kai abu ba ya wucewa?" Yayi dariya ya ce "Ina zai wuce, memory ne mai girman gaske da ba zai shafe ba" yayi maganar yana kai bakinsa na ta, ta lumshe idonta ya ce "To buɗe idonki na fasa, ai ni yaro ne, ba ma a yaye ni ba, ki ke wani lumshe ido" Ta buɗe idonta tana kallon sa, ba ta ce masa komai ba, tayi murmushi, dan ta fuskanci tsokana yake ji, ta shammace shi ta yi kissing ɗin sa. "Eh lallai kin waye baby, ke da ko kallon mutane ba kya iya yi" "Ba zan kula ka yanzu ba, zan rama ne" ya rungume ta ya ce "Ai ba zaki iya hukunta ni ba, duk laifin da zan yi, ki tura mini CV Abdul ta email ɗina, i will find a position that will suit him, ko akwai wani position da ki ke so a bashi ne?" "A'a kowanne ka bashi yayi, na gode sosai Allah ya saka da alkhairi" "Never mind sweetheart, ko wa ki ka kawo ki ka ce na yi masa abu zan yi masa, wannan dolena ne kar ki ji komai, gobe in Allah ya kaimu zan cigaba da koya miki driving, na ga kina da saurin gane abu, motarki ta kusa zuwa in sha Allah, da ke da mami da yaya Salim" Ummi ta ce "A'a ni a naka ka bani ɗaya, sai ka canza wata kar mami tayi maka faɗa" kamar bai ji ba, ya bar maganar suka shiga wata. Bayan sallar asuba cikin bacci ya ji ummi na ƙwala masa kira a banɗaki, yana zuwa ya tarar da ita a tsaye jini yana bin ƙafafuwan ta. A kiɗime ya ce "Lafiya kuwa?" Cikin kuka ta ce "Kawai marata na ji tana ciwo, sai kuma jini yake ta zuba da yawa, ba haka na saba yin period ba" Ya girgiza kai ya ce "Wannan ai ya fi ƙarfin period, asibiti zamu tafi" Nan da nan ya taimaka mata ta kintsa jikinta suka tafi asibiti. Aka yi wa ummi gwaje-gwaje aka tabattar musu da cewa ɓari ne, kuma sai an yi mata wankin ciki dan da saura bai faɗi duka ba. Hankalin raihan ya tashi sosai, dan daga shi har ita babu wanda ya san da cikin, sai kuma ya ji matsanancin ƙaunar cikin, ya aka yi be san da cikin ba?. Yana nan tsaye yana jira aka fito da ummi daga wurin wankin cikin, fuskarta kawai ya kalla ya san abun babu sauƙi. Aka kaita ɗakin da za ta huta, aka ɗebi jininta dan yin gwaje-gwaje aka saka mata ruwa. Ya zauna a gaban gadon ya riƙe hannunta yana yi mata sannu. Can ya numfasa ya ce "Salma ya aka yi ba ki gaya mini ki na da ciki ba?" Ta ɗaga ta kalleshi ta ce "Nima ban san da shi ba" "Abu a jikinki ki ce ba ki san da shi ba? Ke fa ki na da zurfin ciki, abu har wata uku baki sani ba? Ba ki ga kin daina period ba?" Ummi ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Wasu lokutan ina yin irregular periods, kuma ni ban yi rashin lafiya ba, ban san da shi ba" Raihan yayi ajiyar zuciya ya ce "Shikenan, Allah ya mayar mana da alkhairi. Wataƙila ma wannan aikin da ki ka din ga yi ne ya zube, kin ƙi yarda a samo mai tayaki aiki, gashi kin yi mana asarar baby" shiru ta yi masa taƙi kula shi. "Ina magana ki ka yi mini banza?" Kamar za ta fashe da kuka ta ce "To me zan ce maka? Kana kallon na sha wahala kuma kana yi mini faɗa, ka ga ƙarafunan da aka saka a jikina kan ayi wankin cikin? Gashi wai wataƙila a ƙara mini jini, amma kana yi mini faɗa" tayi maganar har da hawaye. Ya zuba mata ido yana kallon fuskarta, sarai ya gano ta fake da haka ne dan tayi kukan zubewar cikin. Yayi ƙasa da murya ya ce "Is ok na yi laifi ba zan sake ba, na daina yi miki faɗan, have some rest" yayi maganar yana shafa gashin kanta. Raihan ne kawai a wurinta, ya din ga kaiwa yana komowa duk abun da aka buƙata shi yake kawowa, sai wurin la'asar ummi ta ɗan warware, dan jiri ta din ga yi da farko saboda jininta da ya yi ƙasa. Yana cikin ba ta abinci Alhaji ya kira shi a waya, yana son ganinsa, ba ɓoye-ɓoye ya gaya wa Alhajin suna asibiti ummi tayi ɓari. Cikin kulawa da tausayawa Alhaji ya jajanta wa raihan, tare da nanata masa ya rarrashi ummi, sannan su yi fatan Allah ya basu mai amfani, zai gaya wa mutanen gidan azo a duba ummi. Ummi ta dafe kai tayi shiru cikin matsananciyar kunya, sai da ya gama wayar ya kalleta ya ce "Ya dai?" "MD dan Allah kai ba ka jin kunya, ka cewa Alhaji ɓari na yi" Cikin ko in kula ya ce "To menene?" "Haba dan Allah, tayaya zan iya haɗa ido da Alhaji, kuma sai azo duba ni, da ka yi shiru ba wanda ya sani sai mu biyu shikenan" Raihan ya yi murmushi ya ce "Kunya ki ke ji ace kin yi ɓarin cikin ƙaninki" yayi maganar yana wani irin miskilin murmushi. Murguɗa masa baki tayi, shi kuma ya din ga dariya, ganin duk yadda ta damu. Ko awanni biyu ba ayi ba, sai ga Hajiya tare da Alhaji har da abinci, suka zo duba ummi. Raihan ko a jikinsa, ita kuwa ummi kamar tayi fuka-fukai ta gudu dan kunya. Bayan sallar magariba aka sallame su, suka koma gida. Washegari da safe sai ga Abdul tare da noor, dan raihan ya gaya wa Abdul. Sai dai duk zuwa dubiyar nan, ko da wasa farida ko a waya ba ta yi wa ummi sannu ba. Abun ya din ga damun ummi, tare da jinjina irin ƙiyayyar da farida take yi mata, da ma ba ta saka ran ganin mami ba ma. Dr. Kuwa dama yana uganda, ya je yin wani course a ƙoƙarin sa na zama professor. Sai da noor ta kwana uku a gidan ummi, sannan ta koma gida. Abun da ya ƙara bata kunya da Salim ya zo dubata shi ma, gashi raihan a gabansa yake nuna irin soyayyar da yake yi wa ummi. Duk wanda ya zo duba ummi ya san tana samun kulawa daga mijinta. Cikin ikon Allah ummi ta warware, sai dai kullum sai raihan yayi zancen dama cikin nan bai zube ba, kuma sai ya roƙi Allah ya kawo musu wani. Sai dai a wannan halin mami ba ta ɗaga wa raihan ƙafa ba, wurin cigaba da ƙwarzabarsa a kan yin aure, tare da barazanar raba shi da ummi. Duk da mami mahaifiyarsa ce, ya ji takaicin rashin jajanta wa ummi abun da ya same ta, ko ba komai a sanadin ɗanta lafiyarta ta taɓu, ko asarar jininta da ta yi ya ci ayi mata sannu, amma mami ba ta nuna hakan ya dameta ba, balle tayi mata sannu. Kasancewar weekends ne, raihan yana gida, ummi ta sha kwalliyar ƙananan kaya, tana aiki a kitchen tana waya da Abdul tare da sanar masa cewa raihan ya ce ya je main branch ɗin su na Kano, game da batun bashi aiki. Abdul ya ce "Ummi ina fatan ba takura masa ki ka yi ba, kuma kar hakan ya cigaba da haifar miki da matsala tsakaninki da sirikarki" "Kar ka damu yaya, ya ce ba wani abu, ai ban taɓa roƙonsa wani abu makamancin haka ba" "To shikenan ummi, zan je in sha Allah, Allah ya saka miki da alkhairi" "Haba yaya meye na godiya kuma, ka ce wa noor da an yi hutun makaranta ina jiranta dan Allah ta zo mu zauna" Yayi murmushi ya ce "Zan gaya mata, ina ji tana cewa idan aka cigaba da takura mata za ta bar musu gidan ta dawo gidanki, kin san mutuniyar taki" Ummi ta yi dariya ta ce "Zuma ga zaƙi ga harbi ba" suka yi dariya sannan suka yi sallama. Har ta ajiye wayar, ta ji kamar ana kallonta, tana waiwayawa ta ga maryam a tsaye tana yi mata wani irin mugun kallo. Ras! Gabanta ya faɗi, dan tun da ta auri raihan ba su haɗu ba, mijinta a kudu yake aiki, suna can tare. Cikin dakiya ummi ta ƙaƙalo murmushi, duk da ba ta ji daɗin yadda maryam ɗin ta ganta ba, yanayin shigar jikinta mijinta kawai yakamata ya gani. "Babbar baƙuwa ce haka yau ta sauka, ba sanarwa balle in yi shirin karɓar ki" "Dalla rufe mini baki, asararriya tun da ba gidan ubanki bane kin isa na sanar miki da zuwa na gidan ƙanina, wadda ta bawa abun kunya gaba ba baya ba" Ummi ta ce "Haba Maryam me yayi zafi?" A hasale maryam ta ce "Ban sani ba, kwaɗayyiya mayyar abun duniya, kodayake barewa ba ta gudu ɗan ta yayi rarrafe, na samu labarin a garin mugun son abun duniyar babarki, babanki ya mutu, ita kuma ta hukace" Ummi ta girgiza kai ta ce "Cin mutuncin har ya kawo kan iyayena, Allah ya baku haƙuri maryam daga ke har mami, aurena da raihan ba shirina bane, Allah ne.... Maryam ta ɗaga mata hannu ta ce "Yi mini shiru, ba ki da wata magana da zaki kare kanki malama, kalleki dan Allah wai raihan ƙanin bayanki, shi ki ka aura wai saboda shi ki ka yi wannan shigar ko? Kuma saboda baƙin abun kunya har ki ɗau cikin raihan, saboda tsabar abun kunya raihan fa, ni ban ma san yadda aka yi ki ka yi wannan gogewar ba, ko rantsuwa zan yi ba zan kaffara ba, bokaye ki ka bi ki ka aure shi, kuma wallahi tun da na zo garin nan kin shiga uku, sai kin gudu da ƙafafuwan ki, mummuna dangin kwaɗayi da asiri, kuma ba zaki taɓa haihuwa ba ki haifo mana mahaukata da munana ba" Ummi ta yi murmushi mai ciwo, ta tattare gashin kanta, ta mayar bayanta, tare da goge hawayen fuskarta, ta din ga tuno maganganun raihan na ƙwarin gwiwa da ƙoƙarin kare kanta a duk lokacin da wani ya ci zarafin ta, ta kalli maryam ta ce "Maryam! Da aurena da naki duk sunansu aure, wataƙila nawa ya ɗara naki, tun da ke da ki ke kyakywar ma ba a baki sadakin da aka bani ba. Kuma cikin raihan yanzu na fara ɗauka sai na tarawa raihan zuriya, ko zaki mutu, dama na shiryawa arangamata da ke, idan kin isa maryam ki saka raihan ya sake ni, ki zo ki aure shi. Batun bin bokaye kuma kema da zaki samu irin bokana na tabatta zaki bi, dan wasu sai su shekara suna asirin bai ci ba" Buɗe baki maryam tayi tana tunanin anya wannan ummin da ta sani ce? Yaushe ta waye tayi baki, ummi ta fice ta barta a wurin. Tana shiga ɗaya falon ta tarar da raihan ya fito da dogon wandon bacci a jikinsa fari, yana ganinta ya rausayar da kai ya ce "Ke na fito nema, baki tashe ni in karya ba" Ba tare da ta nuna masa wani abu ba ta ce "Na fara shirin ɗora abincin rana ne, barka da fitowa maigidana na kaina" ta nufe shi, ya buɗe hannayensa ta shiga jikinsa ta rungume shi. Ya saka hannunsa ɗaya ya riƙe ƙugunta, ɗaya kuma ya shafa kanta ya ce "You look cute baby" sai dai bai kai ga aikata abun da yayi niyya ba, maryam ta faɗo falon. Mamaki ne ya kama raihan, dan bai san ta zo ba, ummi ma ta yi pretending da ba ta san da zuwanta ba ta juya da sauri tana kallon in da maryam take. "Maryam, wannan ai saɓa dokar addini ce, ai a main falo yakamata ki tsaya ki nemi izini, kawai sai ki faɗo mana haka babu ko sallama?". "Sallama, ni ka ke gaya wa haka raihan, saboda wannan mummunar yarinyar da ka aura, me ka gani a jikin ummi da babu a jikin matan garin nan ka aureta dan asara?" Raihan ya sosa kai yana murmushi ya ɗago ummi daga jikinsa ya ce "Abubuwa da yawa mana, next time karki sake shiga wurin ma'aurata anyhow please, ba girman ki bane" Ummi ta yi murmushi ta ce "Sannu da zuwa Maryam, yau ina da babbar baƙuwa" "She ruin my enjoyment" yayi maganar a taƙaice. Maryam kuwa ta ɓarke da masifa ta babu gaira babu dalili, tana alwashin sai ta raba auren nan, dan asiri ummi ta yi wa raihan. Ummi ta yi shiru, zuciyarta na yi mata zafin cin zarafin da maryam ke yi mata, kuma ta ƙi ɗaga jikin raihan. A hankali ya ce wa ummi "Go and get some rest, kin san baki gama warkewa ba" ta jinjina masa kai, ta nufi ɗaki. "Dubeta dan Allah, ko kunya ba kya ji"  sai dai abun da Maryam ba ta sani ba, har da hassada ta kamata, gidan da raihan ya saka ummi ya fi nata haɗuwa, kuma gaba ɗaya yau ta nemi munin ummi ta rasa, a dire take ba abun da wata ƴa mace za ta nuna mata. Ga wani irin ƙamshi da take yi, yau ta ga ainihin kyawun surar da Allah ya yi wa ummi. Dan da ta juya baya ma tana tafiya, ga gashin ta ya kwanta a bayanta, kamar ba bahaushiya ba, dole yaro ya rikice ta faɗa a ranta. Ummi na barin wurin ya haɗe rai ya kalli Maryam ya ce "Idan har kin san zaki zo gidana ki ci mutuncin matata kar ki sake zuwar mini gida ki ɗaga mini hankali, Mami idan tayi ta isa ne, ke kuwa kin yi kaɗan duk rashin mutuncin da na yi miki ke ki ka saya". "Ni ka ke cewa kar na sake zuwar maka gida? Kodayake ba laifinka bane ba, an kai sunanka gaban bokaye an mallakeka" "Bakomai, ni bokan ya taimakeni da ya mallake mata ni, kar ki sake zuwar mini gida ki ɗaga mata hankali, definitely na san sai ta yi kuka cin mutuncin da ki ka yi mata". Maryam ta ja numfashi ta jinjina kai ta ce "Bayan cin mutuncin da ta yi mini, kai ma ka ɗora naka, sai na nuna wa Salma haryanzu kanta a kwano yake, yarinyar da na taimakawa a baya mara galihu irint... "Kema ta taimaka miki, dan a irin daƙiƙancinki, ba dan taimakon nata ba asarar kuɗin tara za ayi a banza, dan haka juna ku ka taimaka" suka yi wa juna kaca-kaca suka yi faɗa ta tafi ta bar gidan. Ummi kuwa ta din ga saƙe-saƙe a ranta, tabbas yanzu tun da har ta riga ta yi aure ta bar gida, raihan ne kawai ya rage mata source of happiness, idan ba ta yi da gaske ba, Maryam za ta iya aikata abun da ta ce, dan ba mutunci ta cika ba, dan haka a wannan karon ba ta tunanin za ta iya ɗaga wa maryam ɗin ƙafa. Raihan ya bi ta ɗaki ya din ga rarrashin ta. Sai dai ta kasa daurewa, sai da ta din ga yi masa kuka yana rarrashinta. Wayarsa ce ta fara ringing, ya duba ya ga sunan Yaya Salim, ya ɗaga suka gaisa, Salim ya ce "Ina waje" Raihan ya ce "Yaya ka shigo falo, gani nan" ya ajiye wayar ya ɗauki jallabiyarsa ya ce "Yaya ne ya zo, ki wank fuskarki ki zo" "Allah ya sa ba laifi na yi masa ba" Ya girgiza kai ya ce "Haba dai, yaya Salim ya ce ke ƙanwarsa ce, da ya karɓo amanarta a wurin mama, idan ban kula da ke ba, ni da shi ne" Ummi ta yi murmushin yaƙe, ta sanya kaya suka fito. Sai dai tun da suka fito yake bin su da kallo, suka zauna ummi ta gaishe shi, ya amsa tare da cewa idan ina ganinku taren nan, sai na ji kamar nima na yi auren nan. Da sauri Raihan ya ce "Yaya da gaske, dan Allah ka yi" Salim yayi murmushi ya ce "Ya ƙarfin jikin naki" raihan ya ce "Ta ji sauƙi sosai" "Kai na tambaya?" Raihan ya ce "Allah ya baka haƙuri". "Meyafaru ne? Na ga kamar fuskar ku da damuwa, mussaman ummi". Ummi ta ce "A'a yaya, komai lafiya ƙalau" Salim ya gyara zamansa ya ce "Yadda ku ke ɗin nan gwanin sha'awa yayi wuri ace kun fara samun saɓani, duk da ma bana tunanin hakan ne, na san akwai abubuwa marasa daɗi a ƙasa, amma ku yi haƙuri da juna". Raihan ya ce "In sha Allah babban yaya" Ya ce 'Masha Allah, dama zan wuce ne na ce bari na zo na sake dubata, amma Maryam ta zo gidan nan ko?" Gaba ɗaya suka kalle shi a tare. Raihan ya ce "Eh ta zo" "Tun da na ganta a gida jiya na san za ta zo, kuma yanayin ta ya nuna mini ba zuwan arziki tayi ba, ta yi miki wani abu mara daɗi ko?" Ummi za ta yi magana raihan ya ce "Haka ne yaya, amma in sha Allah i can handle it" Salim ya miƙe ya ce abun da nake son ji kenan, bai sake ce musu komai ba ya fice. "MD meyasa zaka gaya masa haka?" "Wai dan kin ga yana shiga sabgar aurenmu? Idan na yi masa ƙarya a gabanki zai zageni, ba a ayi masa musu, na gaya miki kallon ƙanwa yake yi miki,ko na ɓoye masa idan ya gano na kaɗe" Ummi ta ce "Ni dai duk da haka da baka gaya masa ba, ai na san da ta tafi shikenan. Salim kuwa fitar maryam ya gani a mota, ya samu nihal ya ritsata ya tambayeta ina maryam ta tafi daga zuwanta jiya? Ba ta ɓoye masa ba ta gaya masa gidan raihan ta tafi. Maryam kuwa bayan komawarta gida, ta samu mami ta zayyane mata abun da ya faru da wanda bai faru ba, wanda hakan ya ƙara tunzura mami, mussaman da maryam ta gaya mata baƙaƙen maganganun da ummi ta faɗa wanda suka ba ta mamaki. Bayan la'asar Salim ya shiga sashin mami, wanda rabonsa da sashin, yayi shekaru. Mami na cin abinci maryam kuma na kallo yaranta na ta wasa a falon. Ya tsaya a kan Maryam ya ce "Zuwa na yi nayi miki gargaɗi, idan ki ka sake taka ƙafarki a gidan raihan, ki ka ci zarafin matarsa wallahi sai na casa ki, ba soja ba ko bindiga ki ke aure tun da ke mahaukaciya ce" Mamk ta miƙe tsaye ta ce "Saurara kai a wa?". "Ni a wanta, wanda na isa na saka na isa na hana, wallahi ba zan yi kaffara ba, na sake jin labarin kin je masa gida kin yi masa hauka, sai na ci.... Ya ɗirka mata ashar mai zafin gaske. "Shaye-shayen ka yi zaka zo ka sauke iskancinka a nan?" Salim ya ce "Ras nake, sai dai da sannu zaki gane manufata, let her make another scene zaku gani" fuuu ya fice kamar zai tashi sama. "Yaushe yaron nan ya samu kusanci da raihan, har yake shiga cikin lamarinsa haka?" Maryam kamar tayi kuka ta ce "Mami ƙarata suka kai masa kenan? Mami raihan ya fifita matarsa a kaina, mami ki yi wani abu a kai tun kafin raihan yafi ƙarfin control ɗinki". Babu tunanin komai, ta hau kan maganar ta zauna. Ummi tana sallar magariba a bedroom ɗin ta, ta ji yo hayaniya a falo, wanda ko tantama ba ta yi muryar mami ce, mamin da tun da aka yi bikinsu ba ta taɓa takowa gidan ba. Bayan ta idar da sallar, cikin tsananin fargaba da tashin hankali ummi ta fita falon, raihan yana ta ƙoƙarin shawo kanta daga masifar da take yi. "Mami sannu da zuwa" riƙe sannu da zuwanki, idan kin so ma ki kirani da bilki, dan ban haifeki ba, saƙon da ki ka bawa maryam na ji, na zo kuma in nuna miki na isa da ɗa na, kai kuma ka aiwatar da abun da na ce" "Mami dan girman Allah ki yi haƙuri, mai zai sanya na aikata haka babu wani dalili". "Ni ka ke gaya wa haka? To ka saka a ranka zaka canza wata uwar bani ba, kai ba ka isa ba ma, wallahi sai ka saketa raihan na riga na rantse maka, ko in yi maka abun da ba ka zata ba" tayi maganar tana watsa masa biro da takarda. Tuni jikin ummi ya fara rawa, ta ji numfashin ta kamar zai ɗauke, da sauri ta bar falon, ta tafi ɗaki, lallai tsuguno ba ta ƙarewa rayuwarta ba. Ta ɗauki ƙaramar akwatin ta, ta zuba kayanta, ta buɗe wurin da raihan yake zuba kuɗi ta ɗiba ta zuba a jakarta ta ɗauki ATM ɗin ta ta fito, tana zubar da hawaye. Ta tarar da raihan a zaune ya dafe kansa, cikin tashin hankali bai yi zaton mami zata aikata masa haka ba. Tana ganin ummi ta ce "Ita akwatin ai na san ba daga gidan ubanki ki ka zo da ita ba, dan haka ajiyeta" ummi ta durƙusa ta kwashe kayanta ta ajiye akwatin. Raihan ya miƙe yana kiran sunanta. "Wallahi ka taka ka bita ban yafe maka ba!!!. Ummi ko waiwayawa ba ta yi ba ta fita. "Kuma ka san duk yadda zaka yi ka kareni a wurin babanka, wallahi ka kuskura ka gaya masa umarnina ne ka rabu da ita sai na saɓa maka, ba zan zuba ido ka zama soko ba" Zuciyar sa na tafasa ya ce "Mami kina ganin wannan hukuncin shi ne farincikin ki ko? Ni kuma kin ƙuntata mini, shikenan tun da haka ki ka yanke kin isa ne, na gode" Ƙura masa ido ta yi ta ce "Raihan kuka zaka yi dan na rabaka da masifa" ya kalleta hawaye na gangarowa daga idonsa, ya san komai zai ce mata ba zata fuskanci irin son da yake yi wa ummi ba. A falon gida ummi suka yi karo da farida, da ita da kausar da alama ba su daɗe da dawowa daga unguwa ba. Ta ƙarewa ummi kallo da kaya a hannu ta ce "Lafiya?" "Ya sake ni ne" ta faɗa a hankali. Kawai farida ta rafsa guɗa ta ce "Har an yi an gama? Soyayyar da ɗaga hancin ya ƙare? To wallahi ba zan riƙe bazawara har karo biyu ba, ki nemi wurin zuwa ba dai nan gidan ba!!!. Ayshercool. PAID ADVERT!. Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi. Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku Oll types of Turaran wuta Sandal Halut Irik Difur Gab Gab Kajiji Habil Nabak Humra Kulakcha Dilke da kalta Kayan Garan jiki Muna turara Kaya Kujerar garan jiki Kannada Madarorin turare masu kamshi  Man garan gashi  Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702   08025453921 *TALLA!TALLA!TALLA!* *INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*. *BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU* *MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA* BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI.                        *CUTARWA* *BRIGHT PENS* (FREE BATCH) *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* 42 MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH. Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g AYSHERCOOL 08081012143 MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH. Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g 42 Cikin sanyin jiki ummi ta ce "Dan Allah anty ko zuwa da safe ne, sai na tafi in sha Allah" "Wallahi ba ki isa ba, ba zan sake zama inuwa ɗaya da ke ba, ai ni ba zan manta cin kashin da dr. Ya din ga yi mini saboda ke ba, a samu ki auru da ƙyar sannan ki dawo mini, bana maimaita kuskure, haka Allah ya yi ki da baƙin jini, kamar mai hatimin jaɓa duk in da ki ka je sai an tsaneki an kore ki" Ummi ta yi shiru ta rasa abun da yake yi mata daɗi, ina zata tafi ga duhun magariba. Kausar ta nufo ummi gadan-gadan da niyyar ta hankaɗata ta koreta, ummi ta ja da baya ta kalli kausar ta ce "Kar ki kuskura, akwai banbanci tsakanin da da kuma yanzu, ko da aurena ya mutu da yardar Allah na fi ƙarfin komawa baya, ba sai kin hankaɗa ni ba, zan tafi". Duka suka kalli ummi, yaushe bakinta ya buɗe har haka da take mayar da martani. Ta juya ta fita, ta ɗan yi nisa kaɗan sai ga noor, sanye da uniform ɗin islamiyya. "Yaya ummi, da tafiya zaki yi ban dawo ba, to Allah ya kama ki" tayi maganar tana murmushi. Sai kuma ta yi saroro tana kallon ummi, ganin ummi a saɓule. "Ya na ganki a haka? Ina yaya raihan ɗin?". "Ya sakeni noor" ummi ta samu kanta tana gaya wa noor. Ta dafe ƙirji ta ce "An shiga uku, saki? Me ki ka yi masa? Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ashe da gaske maama take idan Abba yayi mata laifi ta ce namiji ba ɗan goyo bane ba, ashe da gaske ne me ki ka yi masa?" Ummi ta dafa kafaɗarta ta ce "Kul ki ka sake faɗar haka, mata mukan yaudari kanmu da ɗorawa maza kaso mafi yawa na zaluntarmu, alhalin a zahiri mu ne azzaluman kanmu, mu yi ta ciwon ƴa mace na ƴa mace ne, amma a zahiri kowace mace ciwonta na ta ne ita kaɗai, noor maza ƴan goyo ne, kuma iyaye ne, ɓata garin cikin su ba zai sanya ayi musu kuɗin goro ba. Mami ce ta saka ya sake ni, ba laifin sa bane ba, ni duka da na san baƙin cikin ɗa namiji a rayuwata, amma maza sun tallafi rayuwata fiye da yadda mata suka yi". Tuni noor ta fara kuka ta ce "To ina zaki je? Ba dai gagarawa ba ko? wannan garin da ba sa sonki, me zaki je ki yi musu, ki zo mu tafi gida kawai" Ummi ta girgiza kai ta ce "A'a ai ni in da ba a so na da yawa noor, ki yi maza ki tafi, magariba ta yi" "To ina zaki je?" "Ke dai kar ki damu, zan dawo maza ki ƙarasa gida". Noor ta tafi gida da gudu, sai dai ta tarar farida suna sake tattauna abun da ya faru, a nan ta ji korar ummi suka yi, suka ce ba zata zauna a gidan ba. Duk da ƙarancin shekaru na noor, sai da ta jinjina mugunta irin ta mahaifiyarsu. "Maama yanzu idan wani abu ya sami yaya ummi a hanya fa, dare ya fara yi ki ka ce ta tafi gida? Idan Abba ya ji fa?" "Idan ina magana kina saka baki, sai na murɗe miki wuya, tun da ita ta haife ki, duk irin cin kashin da aka yi mini a gidan nan saboda ita ke ba kya gani, saboda ita aka saka miki sunan uwarta ban haɗa dangi da ita ba, ki cigaba da saka baki a kan irin wannan maganganun ki ga yadda zan yi da ke". Noor jikinta a sanyaye ta ce "Malaminmu ya ce; duk wanda ya shuka alkhairi ana yi wa ƴaƴansa ko ƴan uwansa, haka ma sharri, ni dai tun da ban yi aure yanzu ba, Allah ya sa a rama a kan anty inteesar ko kausar tun da dama ku ne kuke cin zalin yaya ummi" gaba ɗaya sai suka kasa magana, wata maganar idan noor ta yanko ta, sai ka kasa ba ta amsa. Farida ta yi ƙarfin halin cewar "A gidan Ubanki aka zalunceta?" Tayi shiru ta rungumi jakarta ta shiga ciki. Raihan yana zaune din ga jujjuya takardar a hannunsa. Mami ta zuba masa ido tana kallon ikon Allah, duk zafin ciwo ko na mutuwa raihan ba ya kuka, amma yau saboda ta raba shi da ummi, har da hawaye. Nan ta ƙara tabattarwa da kanta cewa ummi asiri suka yi wa ɗan ta. Ta miƙa hannu za ta karɓi takardar hannunsa, ya janye takardar. Saki nawa ka rubuta a jiki?" Tayi maganar tana kallonsa. "Dan Allah mami ki yi haƙuri ki ƙyale ni, ai na rubuta" "Kar ma ka rubuta, kuma ka tabattar a yau ba sai gobe ba, ka bi ta da takardar nan, kuma bana buƙatar sake wata alaƙa a tsakanin ka da ita. Abu na gaba shi ne zan je na nema maka taimako a warware sihirin da suka yi maka, azo ayi maza² a yi bikin nan". Bai ce mata ƙala ba, ta gama surutun ta tafi, ji take kamar ta yaye wa kanta wata babbar damuwa da ta hanata sakewa. Tana tafiya raihan ya shiga ɗaki ya ɗauki wayarsa ya tura wa ummi saƙo. "Salma, ki jirani a gida komai ya lafa, zan zo na ɗauke ki, dan Allah kar ki gaya wa kowa, ban rubuta komai ba, ban sake ki ba, zan dai-daita komai. Ki kwantar da hankalinki da safe in sha Allah zan zo" Bayan ya aika mata saƙon, ya ajiye wayar ya shiga yayi alwalar magariba. Sai dai hankalinsa ya kasa kwanciya, ji yake kamar ya bi ummi, amma da ya tuna gargaɗin mami sai ya kasa bin ta. 'Ban kyauta ba salma, am very sorry, baki cancanci haka ba' haka ya din ga sintiri yana surutai. Kasa jurewa yayi, ya ɗauki wayarsa ya kira tata, sai dai ba ta ɗagawa, tun yana saka ran za ta ɗaga har ya fara sarewa ya sanyawa ransa ummi ta yi fushi da shi. "Haba ummi, meyasa ki ke tunanin zan iya sakinki? Ba zan iya ba wallahi ban sake ki ba" ya din ga surutai yana kiran wayarta. Ummi kuwa ƙarfe goma na dare, tana cikin motar haya, ta nufi gagarawa, tana ta lissafi kala-kala a zuciyarta, yanzu shikenan lissafin rayuwarta ya koma baya?. Ta san zaman gagarawa ba zai kai ta ba, to sai ta tafi maiduguri daga yin aure ace ya mutu, ga mama ba cikakkiyar lafiya ba, suna murnar sun aurar da ita, kuma ta koma ta zaune musu a gida yau da gobe sai Allah. Ta share hawayen ta a hankali ta furta "Mami ba ki yi mini adalci ba raba ni da ɗakina da mutumin da nake matuƙar ƙauna" tayi maganar tana ƙunshe kanta a hijjabinta tana kuka. Ƴan cikin motar sai ba ta haƙuri suke yi, ba tare da sanin dalilin kukan na ta ba. Sai sha ɗaya da kusan rabi ta shiga family house ɗin su na gagarawa. Duk an rufe wasu ƙofofin wasu duk sun kwanta, jiki a sanyaye cikin tsananin fargaba ta shiga sashin iya da sallama. Iya ta amsa daga ɗaki tana tambayar waye, ummi ta shiga tana amsa mata da ni ce. Kamar sokuwa iya ta kalleta, ta ɗau fitila tana haskata. "Lafiya zaki shigo mana gida a tsakar daren nan kamar wata ƴar fashi?". Ummi ta ce "Lafiya ƙalau" "Kamar yaya? Ki rasa lokacin da zaki zo sai a wannan tsohon daren, yahaya dai an ce ba ya ƙasar nan me ki ka aikata ki ka gudo nan, ba zaki kwaso masifa ki yo nan ba, dan na san ba alkhairi ne ya kawo ki ba a daren nan dai" Ummi ta yi ajiyar zuciya, ga gajiya ta kwaso kanta har ciwo yake, ga uban kuka ta sha ga tuhumar wulaƙanci daga iya, kodayeke ba yau ne farko ba, dan haka ta ce "Mun rabu ne" "Da wa?" "Ya sake ni" ta faɗa a taƙaice. "Kuma da ya sake ki ki rasa ina zaki zo sai gagarawa? Garin da ki ka ce ba zaki sake zuwa ba? Amma ke dai an yi mai ƙashin tsiya, a yadda ki ke Allah ya rufa miki asiri ki auru da ƙyar ki kaso auren? Kodayeke kin gaji tsiya da rashin arzki a wurin uwarki, wallahi sai dai ki koma can wurin yahayan, ko ki koma wurin uwarki ba ki da wuri a gidan nan, ke ko kunya ma ba ki ji ba?" Ummi ta ce "Dan Allah iya ki yi a hankali, ki rufa mini asiri ko sati na yi zan yanke shawara idan bai mayar da ni ba shikenan, ba a san ransa ya rabu da ni ba, na san zai neme ni da..... "Dan Allah ki rufe mini baki, kin manta iskancin da ki ka din ga zubawa saboda zaki auri mai kuɗi? Wallahi sai kin bar gidan nan" Kasancewar dare ne, tuni kwaroroton iya ya sanya wasu tasowa, suka taho sashin iya dan jin ba'asi. "A daren nan fa zaki bar gidan nan" Babar auwwalu ce ta fara roƙon iya "Haba Iya, ko korarta zaki yi, ki fara bari gari ya waye mana, a daren nan ina za ta je yanzu?" "Ta koma in da ta fito, irin tsiyar da yarinyar nan ta shuka, idan tana da mutunci ba zata sake waiwayar gidan nan ba, ta koma in da ta fito, dama ba kowa take gani da gashi ba". Ana tsaka da bawa iya haƙuri, ummi ta nufi ɗakin da mamanta ta zauna, da kayanta a hannu, ba tare da ta tankawa kowa ba. Iya ta biyo ta ta riƙe ta, "Babu in da zaki je, tun da ba ɗakin uwarki bane ba yanzu, amaryar ilyasu ce a ciki yanzu, sai fa kin bar gidan nan". Ummi ta ƙwace hannunta ta ce "Ban damu ba ko ɗakin waye, abun da na sani shi ne akwai gadon ubana a cikin gidan nan, dan haka dole a sama mini wurin zama. Tabbas yau tura ta kai bango, na gaji, na gaji Iya shekara ashirin da shida ban yi ƴanci daga ƙangi da ƙuncin da ki ka jefa ni ba, na ɗau layin da ki ke son na hau, babu ragowar mutunci ko kimar ki da nake gani a yanzu, tun tuni yakamata na yanke alaƙa da ke, saboda tsanar da ki ke yi mini da mahaifiyata, amma kullum ina duba mahaifina ki ka haifa, nake baki girmanki saboda haka. An zo kunyar ƙarshe, ba zaki taɓa canzawa ba, zan bar gidan nan amma ba a yanzu ba" Tayi gaba ta shige ɗakin amaryar kawu ilya, ta ajiye kayanta. Daskarewa iya tayi a wurin, ummin da ko buɗe baki ba ta iya yi idan za ta yi magana, amma yau ita ta yaɓawa maganganu haka. "Iya ki rufawa kanki asiri a ƙyale yarinyar nan zuwa safiya" suka yi ta lallaɓa iya suna ba ta haƙuri. Ummi ta yi alwala ta yi salla, ko yunwa ba ta ji saboda baƙin ciki da tashin hankali. Amaryar kawu Ilyasu ta rasa me za ta ce, haka ta shiga ɗakin ta tarar da ummi ta haye mata kan katifa ta kwanta. Raihan bai gaji ba, ya cigaba da kiran wayar ummi, kawai ya ga wayar a ɗakin kwanansu a ƙasan pillow. Hankalinsa ya tashi, ya ɗauki wayar ga tarin missed calls ɗin sa da ya yi mata, ya ajiye wayar ya zauna, kansa yana wani irin sarawa sosai. Gidan ya ƙara yin shiru, bayan gama hayaniya a kan ummi. Ko kusa ko alama, bacci bai yi yinƙurin ɗaukarta ba, ta din ga tunanin ita kuwa meye laifinta haka, da kowa yake gudunta sai ka ce annoba?. Ta tashi a hankali ta tafi tagar ɗakin, ta buɗe tagar, wani sanyi ya daki fuskarta, ta ɗaga kai tana kallon sararin samaniya, tana tuna abubuwan da suka wakana a rayuwarta. Tabbas zamanta a gagarawa ba zai yiwu ba, akwai matsala, sai dai kan ta bar gagarawa sai ta amayar da abun da sai dai zumuncin ya watse, ta lura wannan duniyar kowa yayi ta kansa kawai, kar ka ce lallai sai ka dogara da wani, ko sai kowa ya so ka, kamar yadda raihan yake yawan gaya mata. Ummi ta ƙara ƙaryata azancin hausawa, na ciwon ƴa mace na ƴa mace ne, da ya samu gindin zama a da yawa daga bakunan mata, sai dai ita a nata ganin, ciwon ƴa mace, na ta ne ita kaɗai. Wataƙila ko a cikin ta ta rayuwar ne Allah bai sa ta yi katari da waɗanda ciwon ƴa macen yake zama nasu ba. Duk iya ƙoƙarin da ta yi wurin haɗiye yawun bakinta, ta kasa, saboda bushewar da bakinta yayi, wani irin zafi zuciyarta ke yi mata, wanda ya haddasa numfashitna fita cikin huci. A hankali ta furta "Me ya rage? Tun da duniya cike take da rikici, da tarin ƙalubale, kowa kansa kawai ya sani, kuma kuɗinka shi ne mutuncinka, tabbas! Tura ta kai bango, na ɗaura aniyar fito na fito da duk waɗanda suka cutar da ni, da masu baƙin cikin ganina cikin walwala. Tun da babu sani babu sabo. Zan aikata abun da zuciyata ke raya mini, ko da zai yi sanadain tarwatsewar zumunci, idan ya so na gani, ko suma suna iya jure ɗaɗɗake dauɗar gorar a cikin su, kamar yadda suka yi mini, daga nan na ƙara gaba, na basu wuri tare da gwagwarmayar nemawa kaina mafitar rayuwa. Raihan, tabbas ina sonka amma dole zan ɓacewa duniyarka, tun da zamana da kai barazana ne gareka da mahaifiyar ka, duk wanda ba sa buƙata ta, zan gusa daga rayuwarsu. Yadda ta ga rana haka ta ga dare, haka ɓangaren raihan ma, tun da ta idar da sallar asuba take zaune a wurin da ta yi salla, tana tufka da warwara. Mami tun da ta koma gida kuma ta fara fargaba da addu'a Allah ya sa kar raihan ya tona mata asiri, gashi Alhaji sai tambayarta yake yi ya aka yi ya ganta kamar mara gaskiya, ko wani abu na faruwa ta ce masa babu komai. Ƙarfe bakwai raihan ya ɗauki mota ya tafi gidan su ummi, ya kira Abdul a waya. Mintuna kaɗan Abdul ya fito suka gaisa, Abdul ya ce "Ka zo da kanka, ai mun yi magana da ummi, ta ce ka ce na je, jira nake dama kamar ƙarfe takwas na zo na sameka". Raihan ya ce "Abdul ba wannan ba tukuna, yanzu ina ummi take? Dama dr. Ba ya ƙasa ai ko?" Cikin rashin fahimta ya ce "Ban gane ba, ummi kuma a gidan nan?" "Eh, jiya ba nan ta zo ba?" Abdul ya ɗan yi shiru ya ce "Ai ni ban ga ummi a gidan nan ba" Kamar raihan zai yi kuka ya ce "Dan Allah ka duba mini" Abdul ya jinjina kai, ya shiga cikin gidan, noor tana ta shirin makaranta, ya kalleta ya ce "Noor, wai ummi ta zo gidan nan ne? Ga raihan can a waje" Noor ta ce "Jiya ta zo, a waje muka haɗu ma, ta ce mini wai yaya raihan ya saketa, ina ga su maama korarta suka yi, wai ba zata zauna a gidan nan ba". Abdul ya ce "What! Saki kuma, sai kuma a kore ta daga gidan nan? Ina ta tafi to?" Noor ta ce "Nima ba ta gaya mini ba" Abdul ya fita da sauri, ya tarar da raihan na ta zagaye motarsa. Yana ganin Abdul ya ce "Yauwwa tana ciki ko? Ka ce ta zo mu tafi" "Me ummi ta yi maka zaka saketa? Ba abu ne da za a iya sasantawa ba? Har ta kai ga saki? Ka bani kunya raihan" "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ce muku ta yi na saketa? Abdul ban saketa ba" "Ba ka sake ta ba, me ta zo yi gida?" "Ba ta fahimci meyafaru bane? Ka tsaya ka ji, wallahi ba laifina bane ba" Abdul ya ce "To, koma laifin waye ummi ba ta gidan nan" "Ba ta zo ba? Ina ta tafi?" "Ta zo, amma a jiya ta bar gidan nan ban ma san ta zo ba" Raihan ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ummi meyasa zaki yi mini haka? To ina ka ke ganin za ta tafi, ko gagarawa?" Abdul ya ce "Bana tunanin ummi za ta je gagarawa, tun da ba shiri suke yi ba, sai dai ko maiduguri" "Maiduguri ta tafi a daren jiya? Meyasa ta bar nan gidan? Wallahi ban sake ta ba. Dan Allah Abdul ka yi mini wani taimako mana". "Ina jinka" "Dan Allah kar ka gaya wa dr. Halin da ake ciki zan nemo ta, dan Allah kar ka gaya masa" Sai tausayin raihan ya kama Abdul, lallai akwai maƙarƙashiya, sai dai ya san idan dr. Ya ji to ba raihan ba, har maama tana cikin matsala korar ummi da ta yi. "In sha Allah ba zan gaya masa ba, zan saka a bincika gagarawa, amma ka kira wayarta?" Raihan ya ce "Wayar a gida ta bar ta" Abdul ya ce "In sha Allah tana nan lafiya, zan kira gagarawa ka tuntuɓa can maidugurin". A rikice raihan ya juya ya koma mota, yana salati tare da tunanin in da ummi ta tafi. A cikin motar ya kira Anty maryam ta can Maiduguri suka gaisa, sai dai yanayin yadda suka gaisa ɗin ya tabattar masa da ummi ba ta je maiduguri ba. Abdul kuwa da ya koma cikin gida, ya tarar mami ta fito, ya gaisheta sannan ya ce "Mami wai jiya da gaske ummi ta zo?" "Eh" ta amsa a taƙaice. "To tana ina?" "Na koreta, dan ba zan riƙe bazawara har a karo biyu ba, ta koma gidan ubanta". Ya kalli farida ya ce "Haba maama, da ki ka koreta ina za ta je, ina take da shi da ya wuce nan?" Farida ta ce "Ta koma gidan ubanta, ko wurin uwarta ta barni na huta a gidan mijina na sake, kuma kar sake yi mini maganarta, kan ranka ya ɓaci" bai sake cewa komai ba, ya fito ya ɗau wayarsa ya kira yaya Hashim can gagarawa. Suka gaisa sannan ya tambaye shi ko ummi ta je. "Ai ka san ni yanzu na bar cikin gagarawa, ina dutse ina koyarwa a wata makaranta, har matata muna can, su kuma gagarawa ba kowa yake da waya ba, masu wayar ma sai ka yi ta kira ba ta shiga, saboda rashin caji, amma zan yi duk mai yiwuwa na tuntuɓa na ji, ina fatan dai lafiya ko?" Abdul ya ce "Eh lafiya ƙalau, na gode sai na ji ka" ya kashe wayar. Ko da Abdul ya kira raihan ya gaya masa halin da ake ciki hankalinsa ya tashi, ya ce wa Abdul zai je gagarawa da kansa. Abdul ya ce "Muddin ka je idan ba ta can, dr. Zai iya sanin halin da ake ciki duk da ba ya ƙasar, ka bari mu ji mu tabattar ta je". Da ƙyar ya lallaɓa raihan. Gashi a iya tunanin sa, ummi ba ta da ƙawaye ko wasu ƴan uwa da za ta je gidan su. Yana cikin wannan taradaddin, managern su ya sama musu masauki a china, ya kira raihan yake sanar masa, da ummi ta samu kuɗi saboda wannan videos ɗin da suka yi, kuɗi masu yawa. Raihan sam ba fahimtarsa yake yi ba, ya kashe wayar. Yana kallon kiran mami a wayarsa ya share, ya cigaba da tunanin ina zai ga ummi?. "Ai garin Allan ya waye ko, sai ki fito ki kama gabanki" Iya ta riƙe ƙugu tana huci. Ummi ta ƙarewa iya kallo, ta tsufa sosai sai dai zuciyarta babu Allah sam. "Iya wai me zamana a gidan nan zai rage ki da shi ne?" "Kar ki sake ki yi mini rashin kunya, ki zo ki fice, ai yanzu kin san in da uwarki take" Tana cikin maganar sai ga Idris yayi sallama, dan ya zo ya ganewa idonsa da gaske idan ummi ta dawo, an ce masa aurenta ya mutu. Ita ɗin ce kuwa, kar da ita gwanin sha'awa. Nana ce ta yi sallama ita ma, tana ganin ummi ta fara murmushi ta ce "laaa ashe ke ce ki ka zo?" Ummi ta ƙaƙalo murmushi, ga zafin maganganun iya da take ta yaɓa mata babu ƙaƙƙautawa. Tana dawo da abubuwan da suka wuce, tana sake nanata cewar son zuciyar mariya ne ya kashe bashir ta haukace. "Ke a duniya har ki na da bakin da zaki cewa wani yana son abun duniya iya? Duk wannan tsanar da ki ke yi mini ta samo asali ne saboda mahaifina ba shi da abun duniya, ki ka riƙe ni da zalunci, ki cutar da ni da dafin harahenki, jikokin ki suka yi mini zalunci kala-kala, ki ka danne ni aka yi mini ɗurar dauɗar gora da ki ke cewa ciki ka sha ta. Iya kema sai na ɗura miki dauɗar gorar nan na ga ko zaki iya shanyeta. Na yi miki uzuri a rayuwa, duk da zaluncin da ki ka yi wa uwata da wanda ki ka yi mini. Banda zaluncin da jikanki yayi mini, duk ba su isheki ba iya, wallahi tura ta kai bango babu ɗaga ƙafa tsakanina da duk wani mahaluki da yake ganin ni abar banza ce, zan bar gidan nan amma zaki ga abun da zan iya, kuma ba zan bar gidan nan ba sai na kammala abun da na yi niyya, tun da akwai gadon ubana a gidan nan, a da na so in mayar da komai ba komai ba amma a yanzu komai ji nake ya dawo sabo, wallahi iya ki rubuta ki ajiye zalunta ta da ki ka yi da ke da Idris wallahi ba zan taɓa yafewa ba haƙurina ya ƙare mara mutuncin da ki ke so na zama". Baban su idris ya ce "Ke ummi, shaye-shaye ki ka fara ne? iyan ki ke wa Allah ya isa". "Lokacin da ɗanka ya keta mini haddi me ta ce, kai me ka yi a kai? Ina da ƙanan shekaru lokacin, abun ya din ga zuwar mini a mafarki na rasa wane irin mafarki nake yi, Iya da bakinta ta goranta mini, ƙarewa da ku ka je karɓar kuɗin aurena har wannan maganar ku ka ɗaukko, kuma dan rashin imani, kun san abun da ya faru bayan na auri Idris ya din ga wulaƙanta ni, baku gaya masa cewar ɗan uwansa Hashim ne ya keta mini haddi ba, duk da yaya magaji yayi iya ƙoƙarin sa dan ya wanke wancan laifin da ya yi. Kuna ina na kwana a waje tsirara ruwa yana dukana, da duk sauran zaluncin da aka yi mini? Wallahi ba zan yafe ba, kuma na shirya tsaf dan aikata abun da ba kwa tunani, sai na tagayyara ku, ba dai kuɗi da son abun duniya ki ka saka a gaba ba, zaki gani" Tsit aka yi a wurin, dan da yawa ba su san wasu abubuwan sun faru ba, ta yi wa Iya wankin babban bargo. Haka Ummi ta zaune wa amarya a ɗaki, taƙi tafiya, Iya bata fasa cigaba da cin zarafin ummi ba, duk da irin abubuwan da ummi ta yi mata, ta cigaba da aibata ummi, da cin mutuncnta. ranar kwanan amarya ya zagayo, ummi ta bar ɗaki ta ce ba zata bari ba". A kwana na uku, Yaya magaji ya zo gidan, sai dai bai tarar da ummi ba, dan asubar fari aka ce ummin ta bar gidan ba ta yi wa kowa sallama ba. Gaba ɗaya raihan ya fita hayyacinsa, kwanaki huɗu ba ummi ba labarinta, ya ƙi zuwa gida ya daina zuwa wurin aiki, Alhaji ya kira shi yana tambayarsa ko lafiya ya ce masa ba shi da lafiya ne. Tun da ummi ta tafi, kullum da ciwon kai yake kwana yake wuni, gashi ba ya iya cin abinci duk ya fita hayyacinsa, kai da ka ganshi ka san baya cikin nutsuwarsa. Ummi ba ta yi wa ƴan gagarawa sallama ba, sai nemanta suka yi suka rasa. Kwananta uku da barin gagarawa, wanda yayi dai-dai da kwananta bakwai da barin gidan raihan, aka kaiwa su kawu Ilyasu sammaci daga kotu, ummi ta yi ƙararsu a kan raba gadon kakanta a fitar da na babanta, sannan a bata na ta gadon, da tumunin takabar mahaifiyarta!!! (Tofa! Ummi ta zama boss😂) I hit the jackpot with PalmPay! Join PalmPay with my link or my code 'XWPK6722' within 72 hours to help me get my gift! >>https://link.palmpay.com/uwyy6 Team Ummi wanda ba su taɓa cike palmpay ba, dan Allah ga refaral ɗina a bi link a cike mini. Ayshercool. 08081012143 PAID ADVERT!. Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi. Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku Oll types of Turaran wuta Sandal Halut Irik Difur Gab Gab Kajiji Habil Nabak Humra Kulakcha Dilke da kalta Kayan Garan jiki Muna turara Kaya Kujerar garan jiki Kannada Madarorin turare masu kamshi  Man garan gashi  Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702   08025453921 *TALLA!TALLA!TALLA!* *INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*. *BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU* *MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA* BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI.                     CUTARWA! AYSHERCOOL (BRIGHT PENS) MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g 43 PAID ADVERT *Hajiya ina zaki? Saurin me ki ke yi haka? Ɗan bani aron mintuna biyu kacal, na gaya miki albishir ɗin da na zo miki da shi. Shin ko kin san sirrin sheƙin fatar ummi, da ya sanya ta kama zuciyar MD raihan ta hana shi sukuni? Kai ba ma skin care ba, har da sirrin gyaran gashi, ina masu fama da amosani, karyewar gashi ko kuma sanƙo, jan gashi ne da ke? Ko taurin gashi kamar soson ƙarfe. Idan matsalar ki budurwar fata, tare da rashin glowing, Annur skin scrub da hair bliss sun shirya tsaf domin magance muku kukanku, me ku ke jira ku tuntuɓe su a kan lambar wayar su dan ƙarin bayani 07045971194 ko 08140450950* 43 Magaji ya sake duba takardar da aka kawo sammacin ya ce "An ya ummi ce ta kai wannan ƙarar?" Iya ta ce "Za ta aikata, dan ba ka ga rashin mutuncin da ta tafka a cikin gidan nan ba" Kawu Ilyasu ya ce "Yanzu ba wannan ne abun yi ba, kai magaji kai ne ka yi boko, yanzu meye abun yi ta yaya zamu shawo kan matsalar nan?" Kawu Saminu ya ce "meye abun yi magaji?" Ya numfasa ya ce "Tun jiya nake kiran wayarta a kashe, kamata yayi a fara ganin ummi, amma me aka yi mata har ta kai ga ta aikata haka, ummi da take saliha?" Babar auwwalu ta ce "Ai ummi ta fetsare, dan ba ka ga rashin mutuncin da ta yi ba, har cewa ta yi ka yi mata fyaɗe iya ta ce ayi shiru da maganar, dauɗar gora ciki ka sha ta, da iya da idris da kai duk ba zata yafe muku ba". Yayi turus, gabansa yayi mummunar faɗuwa ya ce "Ni kuma? Yaushe na aikata?" "Oho muku dai, ta ce Iyan ce da kanta ta gaya mata" Ya kalli iya ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Iya ni kuma? Yaushe? Ban san zancen ba fa sai da na nuna miki ina son auren ummi, ki ka gaya mini cewar ragowa ce, an taɓa yi mata fyaɗe tana yarinya, na ce ina son ta a haka, tun da tana yarinya ne, ki ka ce ba ki yarda ba. Nayi-Nayi ki gaya mini waye yayi mata ki ka ƙi, za ki aura mata idris na ce ki gaya masa abun da ki ka gaya mini, ki ka ce idan na faɗa zaki tsine mini, sai da zaki aurawa Idris ita na ce bai kamata ba ki ka ce dama shi yayi mata, amma ki zagaye ki ce mata ni na yi mata fyaɗe tana yarinya, duk saboda ki kare wanda yayi? Baki yi mini adalci ba, tsawon shekaru ummi kallon macuci take yi mini kenan?" Iya ta ce "Ni fa ba haka na ce mata ba, na gaya mata hakan ne dan ta yarda da auren Idris a karo na biyu, kar ta auri wanda za ta aura amma kuma taƙi, kuma na yi haka ne dan Idris ya samu dama ta biyu a daidaita zumunci" Hashim ya ce "Kuma ki ka ce mata ni na yi mata fyaɗe Iya, amma an yi abu ba ta sani ba har ki ka gaya mata? Wace ribar ki ka samu a kan hakan? Kawai ki cuce ni ki ɓata ni a idon yarinya saboda ki kare Idris? Iya meye dalilinki na fifita wani sashe a kan wani a cikin iyalanki ne?" Tuni idonsa yayi jawur, ya jefar da takardar sammacin ya ce "Ku je ku san yadda zaku yi ni ba ruwana" Kawu Ilyasu ya ce "Idan ka tafi gidan ubanwa zamu koma? Yaya zamu yi da wannan abun? Ta ina za a fara rabon gadon shekara talatin da wani abu baya?" "Wallahi baba ba saka hannuna, ba zan shiga maganar ba" yayi ficewarsa. "Iya baki yi mini adalci ba, kin rarraba mini kan yarana kamar yadda ki ka rarraba kan naki yaran saboda son rai, ƙiri-ƙiri babu jituwa tsakanin Idris da magaji saboda ke, ashe wanda ki ke zaluntar da yawa, gashi kin zo kin sake damalmala lamari" cewar babar su Idris. Kawu Ilyasu ya daka mata tsawa ya ce "Rufe mana baki, da can baki ga hakan ba sai yanzu? Uwar ta mu zaki ci wa mutunci " "Na faɗa ɗin, tsawon shekaru muna yi mata biyayya ashe cutar mu take yi, ƙiri-ƙiri ta din ga muzgunawa mariya da ƴar ta muna ganin mu take so da ƴaƴanmu ashe zumuncinmu take yi wa illa tana kassaramu, ba ayi mini adalci ba" haka gida ya kacame da hayaniya kamar za a bawa hammata iska. 4YEARS BACK (SHEKARU HUƊU DA SUKA GABATA) Iya ta kalli ummi ta yatsuna fuska ta ce "Au ke yanzu a yadda ki ke ɗin nan, har wani zaɓi ne da ke? Kin san  dai mutum a hayyacinsa ba zai ce zai aureki ba, dan mazan yanzu fararen mata suke so kyawawa" Ummi da kanta yake sunkuye ta yi shiru ba ta ce komai ba. "Hmm ai duk da Idris ya ce ba abun da ya taɓa haɗa ku, ai ba a canzawa tuwo suna, kuma Idiris ɗin da ki ka guda shi ne rufin asirin ki, dan yadda ki ke ganin cewa an zalunceki da ki ka aure shi ai shi aka zalunta ya rufa miki asiri, tun da fanko aka kai masa, gaki fanko ga larura, duk namijin da zai aure ki ko dai a bazawara ko wadda ta zubar da mutuncinta tun a waje" ummi ta ɗaga kai tana kallon iya. "Eh mana, ai ba ki kai budurci gidan Idris ba, tun kina shekara uku da watanni aka kawar da shi, dan an ƙetare ki" Gaban ummi yayi mummunar faɗuwa, jikinta na tsuma ta ce "Fyaɗe kenan?" "Ƙwarai fa, da ki ka fara tasawa ma ai cigaba da biye-biyenki ki ka yi, Idris shi ne wanda ya rufa miki asiri, amma an buɗe ki tuni, dan haka wani zaɓe² ba naki bane, kuma dole a wannan karon ki sake auren Idris" Ummi ta kalli iya cikin ƙunar zuciya, Idris ɗin da ya kwatsawa duniya cewar ba budruwa ba ce ita, ga kuma ciwon sanyi ya cinye ta, kenan shi tuntuni ya san an yi mata fyaɗe. Sai a lokacin ta tabattar da cewa mafarkin da take yawan yi gaskiya ne. Tana kwance tana bacci a ɗaki, fitilar ƙwai na ci a cikin ɗakin, jin motsin wani abu ya sa ta buɗe ido, ba ta iya ganin fuskar waye, ya rage hasken fitilar ɗakin, daga nan ba ta iya tuna komai sai muryar iya tana cewa dauɗar gora ciki ka sha ta, duk wanda ya tona wannan sirrin Allah ya isa ban yafe ba, ɗan uwanta idan ba a rufa masa asiri ba, zumunci sai ya lalace. Ummi cikin wani irin gigitaccen kuka ta ce "Iya dama a gaske abun ya faru, ba Idris ɗin ne ba dai, ina ganin abun a bacci, kuma na yi biye-biye na bi wa?" Iya ta yi mata wani irin mugun kallo ta ce "Uban waye ya ce miki Idris ne? Shekara uku da rabi ki ke a duniya lokacin, uban me zaki tuna?" Ummi ta yi shiru sannan ta ce "Dauɗar gora ciki ka sha ta, duk wanda ya tona wannan sirrin ban yafe masa ba, ba haka ki ka ce ba a lokacin? Mama ta din ga kuka a lokacin da daddare, Idris ne mana iya" Iya ta dafe ƙirji ta ce "An shiga uku, dama na daɗe ina faɗar kina da alaƙa da maita, tayaya zaki tuna abun da ya faru kina shekara uku da rabi? To ba Idris bane ba magaji ne" Ummi ta girgiza kai ta ce "A'a Iya Idris ne, dan haryanzu ban manta irin barazanar da yake yi mini ba, da ƙoƙarin sake haike mini, yaya magaji ne yake ƙwatata" "Sai kuma ki yi, Idris godiya yakamata ki yi masa, dan taimakon ki yayi" Ummi ta yi kuka kamar ranta zai fita, ta ji zafi da baƙin cikin mummunan labarin da iya ta gaya mata, daga Idris ɗin har hashim wata irin tsanarsu ta shiga ranta, amma ƙasan zuciyarta ya kasa amince mata da yaya magaji zai aikata haka, ta yi ƙoƙari ta din tuna alkhairin sa, hakan ya sanya yin ƙoƙarin ɓoye masa abun da yake ranta game da shi. Gashi babu wanda za ta tattauna Maganar da shi, dan haka ita kaɗai tayi kukanta ta sha baƙin cikinta, haka zalika maganganun iya ba su yi tasiri a zuciyarta ba, ta ji za ta iya yafewa Idiris zaluncin da ya yi mata ba. Iya ta faɗa mata haka ne, saboda zafin rashin amincewa da auren Idris a karo na biyu, da kuma yadda Hashim yake ta son nuna shi yake son ya auri ummi lokacin da suka je saukar. Sai dai hakan bai yi tasiri a zuciyarta ta ji zata sake iya auren Idris ba, shi ne zuwan da suka yi har dr. Ya ce sai an nemi iznin ummi. Ummi ta ɓata darare da dama tana kuka, tana tunanin babu wani abu mai kama da farinciki da zata samu a rayuwa. Yana ɗaya daga cikin dalilin da ya sa ta ƙara tsananta gudun Raihan. CIGABAN LABARI. Raihan kamar zai zare saboda neman ummi, duk iya tunaninsa yayi amma ya rasa ina ta shiga. Gagarawa kuwa Abdul suka kira suka sanar masa da halin da ake ciki, wai sun nemi lambar dr. Sun rasa su zo su kawo musu ɗauki, ummi ta kai ƙarar su kotu. Abun ya bawa Abdul mamaki, Abdul ya tambayi ina ummin take, suka sanar masa ai ta bar gidan ba su san in da ta koma ba, ya cigaba da matsawa da bincike, dan ya san ummi ba zata aikata irin wannan ɗanyen aikin ba, ya kira Yaya magaji, magaji ya ce an yi haka, amma Iya ce ta kori ummi. Ya tambaye shi ko ya san in da ummin ta koma, ya ce masa bai sani ba. Abdul ya tabattar da lallai an kai ummi bango da har ta fara da irin wannan hukunci mai girma. Kawu Saminu ya din ga nanatawa Abdul, lallai ya sanar da dr. Kan ranar da za a fara shari'ar domin, a kashe maganar. Abdul ya ce "Kawu ka manta baya ƙasar, babu abun da zai iya yi a kai, kuma yanzu a fara mayar da hankali a samo in da take tukuna, sai a yi wa tufkar hanci, tun da in dai ba ita ta janye ƙarar ba, ba zai yiwu a kashe maganar ba" "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, amma wannan yarinyar an yi sheɗaniyar mara mutunci, maimakon iya mu ta gaya mana ta ce a raba gadonta a bata, sai ta kaimu kotu?" Ummi kuwa ana gobe za ta bar gidan su Iya, ta karɓi aron wayar amaryar kawu Ilyasu, ta aika nana ta sayo mata kati ta kira yaya magaji. Suka gaisa ya ce "Ummi layi ki ka canza ne?" "A'a yaya, akwai matsala ne, ina so ka taimaka mini ina gagarawa yanzu haka" "Subhanallah, matsalar me kuma?" Ummi ta ce "Aurena ne ya samu matsala, can gidanmu anty farida ta ce ba zan zauna ba, nan ma Iya ta ce sai na tafi" Hashim ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, mutuwa auren yayi?" "Eh, mamansa ce ta saka ya sake ni, ba na son zuwa maiduguri in ɗora musu nauyi daga yin aurena, ga dr. Ba ya gari" "Kin san menene, ni yanzu ina dutse ni da matata, ki saurara da kyau, zan yi miki kwatancen gidana, akwai mukulli a maƙwabta, zan kira su su baki, ki buɗe ki shiga ki zauna, ki bani account number ki in turo miki kuɗi, ko zaki buƙaci wani abun, amma Abdul ya kirani ana nemanki, basu san in da ki ke ba, ai ban san kina gagarawa ba". Ummi ta ce "Dan girman Allah ko ya sake kiranka kar ka gaya wa kowa ina gagarawa, kuma ba wanda zan gayawa ina gidanka, dan Allah kar ka gayawa kowa idan ku ka dawo zan yi maka bayanin komai" Ya ce "To shikenan, ki turo mini account number" "Kar ka damu, akwai isashshen kuɗi a hannuna". Ana idar da sallar asuba, Ummi ta ɗebi kayanta ta bar gidan iya, sai dai ba ta bar gagarawa ba sai da ta je ta shigar da ƙara a kotu, sannan ta tafi gidan magaji da ba a cikin gagarawa yake ba. Ko da magaji ya dawo ummi ta kwashe komai ta gaya masa, sai dai ya ji zafin kora da wulaƙanci da Iya ta yi mata, sai dai ba ta gaya masa batun kai ƙara kotu ba, dan haka da ya je gagarawa bai nuna musu ya san meyafaru ba. Sai dai tun da ya ji ta'asar da Iya ta aikata, ya kasa komawa gidansa, saboda damuwa da fargaba, ya kasa komawa gidansa ya kalli ummi, ashe duk tsawon lokacin nan kallon da take yi masa kenan?. Ganin ba shi da wani zaɓi, ya sanya ya koma gidan, ya tarar da ummi da matarsa suna hira. Kamar baƙon munafiki haka yayi sallama idonsa yayi jawur. Ummi ta ce "Yaya menene? Wani abun suka yi maka?" Ya girgiza kai ya ce "Ashe kin kai ƙara kotu?" Ummi ta ce "Eh, dama ina son zan yi maka bayani, na san zaka fuskance ni" Ya ƙarasa gaban ummi ya zube a kan gwiwoyinsa, sai ga hawaye ya ce "Wallahi! wallahi! wallahi ummi ban aikata abun da Iya ta gaya miki ba, bani bane ba ummi, ban taɓa sanin abun da ta gaya miki ba kenan, dama da abun ki ke kallona? Wallahi ummi Idris ne, nima ban san an yi ba sai lokacin da za ta yi miki auren huce takaici da shi, na nuna mata illar yin hakan, saboda kina da ƙananan shekaru kuma ba ya ƙaunar ki, amma ta gaya mini ga abun da ya faru shekarun baya, aurensa shi ne rufin asirin ki, wanda a kan haka sai da ta haɗa ni da babanmu kamar zai tsine mini, kuma still bayan auren da ya zo yana faɗar maganganu a kan an bashi ragowa na tuna masa koma menene shi ya fara, ya je ya gaya wa Iya ta sake ci mini mutunci da barazanar na sake ɗaga maganar sai ta tsine mini, ina ji ina gani yayi ta yamaɗiɗin ragowa aka bashi ke, ga kuma larura kina da ita, ba yadda na iya, amma ko Alqur'ani aka bani zan rantse wallahi ummi bani bane ba" Ummi cikin sheshsheƙa ta ce "Ka yi haƙuri yaya magaji, nima zuciyata ta daɗe tana yi mini wasi-wasi a kan hakan, amma ba yadda na iya tura ta kai bango, na gaji da abun da Iya take yi wa rayuwata, shiyasa na zaɓi fesar da abun da yake zuciyata ko da kuwa zumuncin zai tarwatse. An cutar da ni da yawa me nayi da na cancanci haka yaya magaji?" Yayi ajiyar zuciya ya ce "Ummi ba zan hana ki ba, ba zan dakatar da ke ba, Iya ita ta rusa duk wani tubalin soyayya da ƙauna da tarwatsa kan iyalanta, ta hanyar fifita wasu a kan wasu saboda zunzurutun tsagwaron son zuciya da abun duniya, ta yi miki CUTARWA ma fi muni wallahi kowane mataki zaki ɗauka ba ruwana, ni dai ki yafe mini wallahi bani bane ba" Ummi ta share hawaye ta ce "Ni yakamata na nemi yafiyarka yaya, amma ba zan ɓoye maka ba har iyayenmu dr. Kawai na cire amma suna kallon yadda rayuwata ta wulaƙanta cikinsu ɗaya da mahaifina saboda bai mutu ya bar mini komai ba, aka rasa wanda zai kula da rayuwata, aishikenan" Cikin sanyin jiki matar magaji ta ce "Ummi abun da haƙuri bai bayar ba, akasin ba zai bayar ba ki yi haƙuri ki yafe musu mana" Ummi ta ce "Ai da fari na yafe musun, sai na ga idan ba rayuwata ce ta ƙare ba, ba za a daina cutar da ni ba. Mijina yana yawan gaya mini in tsaya da ƙafata a rayuwa in fuskanci kowane irin ƙalubale". Yayi nisa a zurfin tunani, ya ji ana bugun ƙofar falo kamar za a karyata, babu shiri ya tashi ya je ya buɗe a fusace, sai dai ganin Mami a tsaye ya sanya shi haɗiye masifar da ya ƙunso ya saukewa mai bugawar. "Raihan, meye haka? Amai da gudawa ka yi ne kayi wannan mummunar ramar?" Ya girgiza mata kai tare da shigewa falon. Ta bi bayansa, tana ƙare masa kallo. "Ya aka yi na je office ba ka je ba? Me ka ke yi a gida?". "Mami ba a san fa in da Ummi take ba" "Shi ne me? Ƙaramar yarinya ce ita? Saboda haka ne nake ta kiranka a waya kashe wayoyinka?" Yayi shiru bai ce komai ba. "Alhaji yana nemanka, za ku yi magana a kan kai kuɗin Safiyya, kuma a yau ba sai gobe ba, ka je ka ji me take buƙata na shirin biki, kuma idan ka kuskura ya san na saka ka saketa sai na yi mummunan ɓata maka rai" bai ko ɗaga kansa ba, balle ya tanka mata, tayi ta gama ta tafi. Me zai yi da wata safiyya? Ya tuna yadda take yawo da wani ɗagaggen mayafi tana gantsare-gantsare kamar an banƙare kaza, gaba ɗaya baya ganin kyan kowa idan ba Salmansa ba. Bai san lokacin da ya ja wani guntun tsaki ba. Gaba ɗaya gidan yayi ƙura saboda ba ummi, ya tara wanke-wanke a kitchen, da ƙyar yake iya yi. Daga baya ma sai dai ya sayo fruita ya ci duk ya zubar a wurin. Yayi wanka ya shirya ya je gida ya samu Alhaji. Shi kansa sai da ya tambayi raihan ko ba shi da lafiya ne? Ya ce masa lafiyarsa ƙalau. "To kai babarka ta ce wannan juma'ar kai kuɗin aure, ni ban ganka ba. Ka zo ka kawo mini kuɗin, da sauran shirye-shirye amma ba ka ce komai ba, na san ba so ka ke yi ba amma ka daure ka yi mata biyayya". Raihan kamar zai yi kuka ya ce "Ni fa bani da kuɗi" Alhaji ya ce "Kai babban mutum, ba ka da kuɗi kuma? A auren Salma ne ka ke da kuɗi kenan?" Yayi shiru. Alhaji ya kira mami a waya, ta zo ta same su, ya sanar mata raihan ya ce ba shi da kuɗin ƙara aure a yanzu. Mami ta ce "Duk dan ya kaucewa umarnina ne, ni ina da kuɗin zan bashi" Alhaji ya ce "Dakata tukuna, me za a yi wa ƴa ta wanda zai kwantar mata da hankali? Ba zai yiwu watanni takwas da yin aure, ba dan ta gaza ta ko ina ba ace za a ƙara mata kishiya ba tare da yi mata wani abu da zai kwantar mata da hankali ba". "Alhaji me kuma za ayi mata? Ta ci nata rabon ai" Alhaji ya katse ta da cewa "Da ki ka hana ayi mata lefen sai ta ɓarauniyar hanya ya yi mata? Ke ma da ban bayar da kayan faɗar kishiya ba, duk da Hajiya na da haƙuri, da ba ki shigo ta daɗin rai ba, gara ita ta daɗe na aure ki? Wannan fa?. Na gargaɗe ki kar ki yi abun da zaki zo ki na dana sani, amma kin ƙi. Kar ku jefa yarinya a halaka ƙiyayyar ɗa namiji masifa ce, kin ƙi ai shikenan" Ta ɓata fuska ta ce "Ba wata ƙiyayya, iskanci ne kawai da kuma asiri da yake ɗawainiya da shi" Alhaji ya kalli raihan ya yi murmushi ya ce "Ba wani asiri, ta iya kiwo ne kawai, ke ba abun alfaharinki bane a. Mallake ɗanki ana kula da shi, nan ya zo ana bani labarin hannunta akwai maggi, ta iya girki, nima shaida ne ta iya girki. Dan haka ko dai a samu wadda ta fita ko kai ɗaya da ita idan ana son zaman lafiya, amma shawara ce na bayar. Babban mutum, me zaka bawa ummi da zaka kwantar mata da hankali?" Raihan ya ji kamar Alhaji yana shiga zuciyarsa yana karanto damuwarsa ne. "Alhaji ban san kan abun ba, ban san me ake bayarwa ba". "Eh to, ka ga recently kun fita waje, amma wannan cikin honeymoon ɗinku ne, kyauta zaka yi mata ta bajinta, ka gane me nake nufi ai kyauta mai sunan kyauta. A samu danƙareriyar mota a bata, idan da hali gidan da ke ciki a bata takardunsa, ita amaryar sai a nema mata haya a wani wurin, gidan ya zamana nata ne" Cikin tashin hankali mami ta zabura ta ce "Alhaji wannan kyautar ai sai kai? Idan ya bata gidansa shi shikenan ko oho? Wai meyasa kamar goya masa baya ka ke yi ya bujire mini ne?" "Yanzu ya ce ba shi da kuɗin aure kin ce zaki bashi, ita wannan saboda ba ƴar ki ba ce ba, kin hana a bata kyauta, ta samu kwanciyar hankali, ba zan so raihan ya rabu da gidansa ba, amma muddin kina so na tsaya yadda yakamata ya ƙara aure, sai an yi balancing, tun da ba shi da kuɗi, ke ki biya masa kuɗi yayi aure, ni kuma zan yi mata kyautar da zata sanya hankalinta ya ɗan kwanta ya rage mata zafin kishi". Raihan yayi murmushi ya ce "Alhaji na gode sosai da sosai" "Wallahi ba zai yiwu ba, ƙarya yake yi yana da kuɗi, kuma sai ka fito da su" "To ya rage naku dai, ni dai idan aka yi wa Ummi kishiya, in sha Allah zan yi mata kyautar ban mamaki, sirikata ba ta yi laifin komai ba, marainiyar Allah ba zan bari a cutar da ita ba" Duk maganar da yake yi, yana observing ɗin raihan da ita kanta mamin, dan yana sane yake faɗar wasu abubuwan. Ya sake nisawa ya ce "To duk kun yi shiru, kai babban mutum ka fito da kuɗi mana, kuɗi fa akwai su" Raihan ya karkace kai ya ce "Dan Allah Alhaji a bar maganar auren nan yanzu, nifa ba ni da lafiya ma" Gaba ɗaya suka kalle shi. Mami ta ce "Kamar yaya ba ka da lafiya?". Ya ce "Ba zan iya ƙara aure ba, a bari na nemi magani" ya bata amsa kansa tsaye. Alhaji ya sunkuyar da kai kamar ya kece da dariya, raihan ba saiti wasu lokutan. Ya maze ya ce "me yake damunka?" Ya sosa kai ya ce "Ai kawai muna zaune ne da salman, magani nake nema" "Amma ba dawowarku aka ce tayi ɓari ba?" Tayi maganar a hasale. Ya ce "Eh, amma bani da lafiya, dan Allah idan ba asirina ki ke son ya tonu ba, dan Allah mami ki bar maganar auren nan na samu magani" Yadda raihan ke tsara maganar kawai Alhaji ya san ƙarya yake yi, yayi wani irin ƙasaitaccen murmushi na manya ya ce "This is serious, dole a jinkirta maganar nan, dan wannan ba issue ne ƙarami ba" Ba tare da mami ta ce komai ba, ta hau zancen zuci, da ƙoƙarin gane ƙarya raihan yake yi, ko kuma da gaske? To me za ta cewa su Safiyya? Amma ba shi da lafiya ummi ta yi ɓari". "Kin ga bilki, ki tashi ki je zamu yi magana da shi" Ummi ta yi wa raihan wani mugun kallo, amma yaƙi kallonta. Bayan ta fita Alhaji ya yi ƴar dariya ya girgiza kai ya ce "Ɗan zamani da uwar zamani, tashi ka je Allah ya shiryeka babban mutum" ko a jikinsa ya tashi ya bar falon, dan dama haka yake so, kuma ya ƙudirce idan mami ta cigaba da uzzura masa sai ya gaya wa safiyya da Yaya rakiya ba shi da lafiyar da zai auri safiyya ummi ma rufa masa asiri take yi. Ganin ya kwantar da tarzomar wannan maganar, ya sanya ya sake tatara hankalinsa a kan neman ummi. Ya ɗauki wayarta yana duddubawa, ya tarar da gmail a wayarta, wani babban gidan talabijin na jamus, suna son bawa ummi aiki. Idan tana da buƙata ta tura takardunta ayi interview da ita. Tsaki yayi ya ajiye wayar ya dafe kansa yana tunani, ko a gidan ubanwa ma suka san ummi oho. Managern su ne ya faɗo masa, dan ya gaya masa yadda ummi ta ɗauki hankalin mutane. Ranar da aka fara shari'ar su ummi, ba ta je kotu ba sai lawyernta, kasancewar ATM ɗin ta na hannunta, kuma raihan yana saka kuɗi a cikin account ɗin ta, ya sanya ta saki kuɗi. Alƙali ya bi komai tiryan-tiryan, tare da neman a kawo duk wani abu da aininhin kakan su ummi ya mallaka, da yayyensa suka hau suka turmushe, a zama na gaba. Su kawu Ilyasu suka cigaba da kururwar neman agaji, suna kiran Abdul a waya, ya ce shi ba abun da zai iya yi, tun da ba a san in da take ba. Sati ɗaya aka koma kotu, Aka je da komai na kakansu ummi. Gidan da suke ciki, aka ce ba zai rabu ba, saboda wasu sun rasu sai ƴaƴansu, wasu duk sun ja wuri sun yi gini a ciki, sai dai a yi wa gida kuɗi, a raba a fitar da gadon ummi, da tumunin mahaifiyarta, sai su biya su. Duk wannan abun, ƙarƙashin jagorancin lawyern ummi ake yin sa, dan ko sau ɗaya ba ta je kotun ba. Aka shafe wata guda da sati biyu, ba ummi babu labarinta, har Abdul sai da hankalinsa ya tashi, wurin neman ina ummi take?. Mami ta ce zata saka raihan a gaba ta nema masa magani, ya ce mata shi yana zuwa wurin likita ana duba shi, dan ta san komai za ta yi ba zai sha maganin hausa ba. Amma duk da haka ba ta haƙura ba, ta cigaba da saka pressure sai da aka kai kuɗin nan! Raihan duk yayi baƙi ya lalace, gashi kwatsam! Dr. Yayi masa magana a what's app cewar ba ya samun ummi a waya, shi ma tasa wayar ce ta lalace amma kwana biyu ba ta gaishe shi ba. Raihan ya yi masa ƙaryar ita ma ta ta wayar ta lalace amma zai haɗa su. Duk wannan abun, Salim bai kuma tsoma baki a kan lamarin raihan da ummi ba, gashi bin ƙwƙƙwafin da Alhaji yake yi, yana daf da gano ummi ba ta nan, dan kuwa yana ta cewa raihan kwana biyu fa bai kawo sirikarsa sun gaisa ba Gagarawa kuwa, da ummi da mariya aka yi ƙiyasin suna da naira miliyan uku da rabi a gidan, dan haka Alƙali ya ce  ko su kawo wannan kuɗin su fitar da ummi da mahaifiyar ta, ko Alƙali ya saka gida a kasuwa a sayar, a sallame su, kuma aka basu wa'adin sati biyu. Sun san ko giyar wake suka sha, ba su da wannan kuɗin, ga kotu ta saka an yi wa sauran gonakin su kuɗi, za a cire gadon bashir, sannan a cire na ummi da mariya. Alƙali ya ce su haɗa su biya su ummi, sai su riƙe gida da gonaki. Raihan yana office baya gane komai, wayarsa ta fara ringing, ya ɗaga a hankali ya kara a kunnensa. "Barka da rana" tayi maganar cikin sassanyar muryarta. A zabure ya tashi tsaye yana faɗin "Ummi, kina ina? Ina ki ka shiga haka?" "Ina nan cikin ƙoshin lafiya" ta bashi amsa. "Haba Salma, kin san yadda ki ka tayar mini da hankali kuwa? Kina ina ki tsaya na zo na ɗauke ki". Ummi ta ce "Ka zo ka kawo mini takarda ta dai. Dan Allah wani abu nake son ka yi mini, family house ɗinmu na gagarawa kotu za ta saka a kasuwa nan da sati biyu, dan Allah da an saka a kasuwa idan kana da hali, ka sai gidan ka basu short notice su tashi, da k yi haka zan gaya maka in da nake a Maiduguri ka zo ka kawo mini takardata, kar kuma kayi tracking ɗina, sannan bana gidan mama, naira miliyan goma sha huɗu aka yi masa kuɗi burina kawai ka sayi gidan ka tashe su!" Turus raihan ya yi yana kallon wayar, me zai saka ummi ta yi haka? Lallai akwai wani abu a ɓoye, amma idan har zai ganta kuɗi ko na Alhaji ne zai ɗiba ya sai gidan kamar yadda ta buƙata, duk da bai san dalilinta na yin hakan ba! Ayshercool 08081012143. I hit the jackpot with PalmPay! Join PalmPay with my link or my code 'XWPK6722' within 72 hours to help me get my gift! >>https://link.palmpay.com/uwyy6 Team Ummi wanda ba su taɓa cike palmpay ba, dan Allah ga refaral ɗina a bi link a cike mini. Ayshercool. 08081012143 PAID ADVERT!. Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi. Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku Oll types of Turaran wuta Sandal Halut Irik Difur Gab Gab Kajiji Habil Nabak Humra Kulakcha Dilke da kalta Kayan Garan jiki Muna turara Kaya Kujerar garan jiki Kannada Madarorin turare masu kamshi  Man garan gashi  Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702   08025453921 *TALLA!TALLA!TALLA!* *INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*. *BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU* *MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA* BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI.                       *CUTARWA* *BRIGHT PENS* (FREE BATCH) *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* 44 MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH. Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g AYSHERCOOL 08081012143 MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH. Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g 44 Yayi ajiyar zuciya ya ce "Amma meyasa ki ka yanke wannan hukuncin?" Cikin nutsuwa ta ce "Saboda na zama abun da ake so na zama" "Me kenan?" "Zaka ji daga baya" ta bashi amsa. "Zan saya, amma dan Allah ummi kina ina, duk hankalina a tashe, Alhaji na daf da gano gaskiya ba ma tare, idan ya gano ina cikin matsala dan girman Allah kina ina?". Ummi ta ce "Kai da zaka yi sabon aure, meye na damuwa da ni? Idan komai ya kammala ka tabatta ka taho mini da takardata, da zan nuna wa dr. Shaida, sannan ban ce ka gaya wa kowa mun yi waya ba, ka yi shiru da bakinka" "Ummi.... Ta kaste wayar ta sakata a flight mode, dan kar ma ya sake kiranta. Ta ƙurawa wayar ido, tabbas tana kewar raihan ɗin ta nesa ba kusa ba, ji tayi kamar ta yi kuka wannan abun da ta yi masa, gaba ɗaya zuciyarta babu daɗi amma dole ta ƙaurace masa dan samun cikakkiyar nutsuwa dan ta san da ya lallaɓata shikenan ba zata iya taɓuka komai ba. Raihan yayi ƙoƙarin bin ummi, amma ta ƙi shiga wayar. Ya zubawa wayar ido yana lumshe ido, a hankali ya furta "Alhamdilillah, tun da kina lafiya" Su kawu Ilyasu hankali ya ƙi kwanciya, saboda kuɗi babu su babu dalilinsu, gashi ba su san in da ummi take ba, balle a lallaɓata a rarrasheta su bata haƙuri, ba su taɓa zaton zata aikata abu makamancin wannan ba, yarinyar da suke wa kallon ko yatsa aka saka mata a baki, ba za ta iya cizawa ba. Iya kuwa ta tsinewa ummi da mariya babu adadi, ta zageta har ta gaji, ba tare da ta ji alamar ta huce daga takaicin da ummin ta sanya su ba, ba ta taɓa tunanin ummi za ta aikata haka ba. Rana ba ta ƙarya, sai dai uwar ɗiya ta ji kunya, wa'adin da kotu ta ɗibarwa su kawu ya cika, ba su da kuɗin da za su fitar da su ummi, dan haka aka saka gida a kasuwa, kuma Alƙali yayi musu faɗa sosai a kan illar jinkirta rabon gado komai ƙanƙantarsa. Kamar yadda ummi ta buƙata, babu tunanin komai ko neman shawarar kowa ba, Raihan ya aika wani yaronsa gagarawa, ya ce zai sayi gidan, ba tare da wani ɓata lokaci ba, aka koma kotu, aka kai kuɗi Alƙali ya rarraba, aka bawa kowa nasa. Sai dai duk ƙoƙarin da raihan yayi wurin samun ummi a waya, ya kasa ga gefe mami ta isheshi da ƙwarzaba a kan Safiyya. Ga ayyyka sun yi masa yawa, suna ta ƙoƙarin buɗe katafaren branch ɗin su na Abuja, hankalinsa ya rarrabu kashi-kashi. Aka bawa su Iya notice na sati uku su tattara su bar gidan nan. Saboda tsabar tashin hankali, ta yanke jiki ta faɗi aka tafi da ita Asibiti, aka yi ta sassaka mata ruwa. Kowa ya fara tunanin bazama ya kama haya, sai dai aka rasa wanda zai ɗauki Iya, dan duk wanda aka ce ya ɗauketa, sai iyalinsa su ce su ba zasu iya da jaraba da masifarta ba. Ana ta wannan badaƙalar ummi ta kira waya, kawu Saminu da fari bai ɗauki muryarta ba sai daga baya, tana cewa ita ce ya hau bala'i "Ashe ke ba ƴar arziki bace ba? Gidanmu da ubanmu ya mutu ya bar mana, ki saka aka sayar dan ki tagayyara mu?" Ummi ta ce "A'a kawu, wataƙila da kun sama mini matsuguni a gidan, da duk haka ba ta faru ba, na ji iya har kwanciya ta yi a asibiti, idan ta warware ina buƙatar gidana, sonake a rushe shi gaba ɗaya, na daina ganinsa ko zan manta da baƙinciki da bala'in da na gani a gidan". Cikin tashin hankali ya ce "Ki ka sayi gida? A ina ki ka samu kuɗin sayan wannan gidan? Yanzu ummi ko kunya ba ki ji ba yadda ki ka tozarta mu, gari ko ina ya ɗauka?" "Kuma ba ku ji kunya ba lokacin da ake tozartani, gari ya ɗauka ku yi haƙuri kawu nima ba haka na so ba, duk ku ne sila" Nan fa zance ya sauya, magana ta sake ɗaukar zafi, saboda yadda ummi ta yi musu mummunar shammata. Abdul yana gida a falo, aka kira shi daga gagarawa aka sanar masa da abun da ummi ta yi, na ta saye gida ta basu kwanaki ƙalilan su tashi, a take ya ce "Anya kawu? Ina ummi ta ga kuɗin sayen wannan uban gidan?" "Abdul zamu yi maka ƙarya ne? Kuma wai nan kusa take so mu tashi mu bar gidan, ina zamu saka kanmu ga ƴaƴa ga jikoki mun zuba" Abdul ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, shikenan zan san abun yi" ya kaste wayar ya ce "Gaskiya akwai wanda ya tsayawa ummi take wannan abubuwan, kuma na tabattar tura ce ta kai bango, dama mai haƙuri bai iya fushi ba, anya ba zan sanar da Abba halin da ake ciki ba?" Yayi maganar yana kallon farida. Farida ta ce "To ni ina ruwana? Ka daina sakani a sabgar da ba ta shafe ni ba" Ya ce "Maama ta shafe ki, dan ke ki ka ɓallo aikin nan? Amma ban sani ba ko kina da abun da zaki gaya wa Abba, da ki ka koreta daga gidan nan da aurenta ya mutu, ki ka ce ba zata zauna ba" Noor ta ce "Taɓ, lallai yaya ummi ta zama jan wuya, wallahi maama tun da ta fara da ƴan gagarawa da alama ɗaukar fansa take yi saura ke, Allah kaɗai ya san me za ta yi miki" "Ita ta isa, sai dai dangin uban naku ƙauyawa, gidana  nawa ne babu mai sake zaun mini, ya takura mini rayuwa, kai kuma kar ka kuskura ka gaya masa ka ɗaga masa hankali su je can su ƙarata" Shi kansa Abdul ya shiga tsaka mai wuya, bai taɓa zaton ummi za ta aikata haka ba, amma dama mai haƙuri bai iya fushi ba, kusan kullum sai an kira shi daga gagarawa. Babu zato babu tsammani, raihan ya duba wayarsa ya ga ummi ta turo masa adress ɗin in da take a can Maiduguri, gashi a washegari zai tafi Abuja, ga tarin ayyuka a office, ba shiri ya soke ayyukan da zai yi ya shirya ya ɗauki mota ya tafi Maiduguri. Tiryan-tiryan ya bi adress ɗin, babban abun da ya ɓata masa rai, bai wuce adress ɗin hotel bane ba, sai dai yayi iya ƙoƙarin sa ya danne fushinsa, har ya ƙarasa full address ɗin. Ya je har ɗakin, yana tura ƙofar ƙamshin turaren ta, da sanyin AC suka dake shi, hakan ya rage kaso mafi yawa na ɓacin ran da yake ciki. Tana zaune a gefen gado, kanta babu ɗan kwali, duk da ta rame amma ta yi fresh da ita, gashin kanta ya sha gyara, sai ƙyamli yake yi. Jiki a sanyaye ta tashi tsaye, ya rufe ƙofar ya kalleta ya ce "Ummi me ki ke yi a hotel da aurena?" "Kana zargina ne? Ban taɓa zuwa ba, wannan shi ne last option ɗina, babu yadda na iya, ina fatan ka taho mini da takardar sakin" A ƙule ya ce "Ni na furta na sake ki ne? Ni ban rubuta miki saki ba, na dai karɓi takarda na yi rubutu, amma ai ban baki ba, kuma ban furta ba, amma ki ka yi tafiyar ki, kalli yadda ki ka din ga wahalar da ni, duk na shiga tashin hankali kowa na tambaya bai san in da ki ke ba saboda ina matuƙar sonki shiyasa ki ka zaɓi ki wahalar da ni? Kuma a ƙarshe ki rasa a ina zan ganki sai a hotel da aurena kuma a kan ki, kin yi mini adalci kenan?" Ya hasala matuƙa, sosai yake yi mata faɗa" ta ƙare masa kallo babu ƙarya ya rame sosai da sosai, sai dai ta san fushi ba nata bane ba a wannan yanayin, da ya shiga mood ɗin da ba ta so da yake ba ta tsoro, duk da ta ji kamar zuciyarta ta yi ƙeƙashewar da ba ta jin tsoron, sai dai girman miji mussaman nagartacce kamar raihan, kwarjininsa daban ne a idon iyalinsa. A hankali ta taka daf da shi, ba tare da ta ce masa komai ba ta kwanta a jikinsa, ta zagaye hannayenta a bayansa ta ce "Da gaske MD ba ka sake ni ba? Ranar kasa jurewa na yi in kalli rabuwata da abun da nake matuƙar ƙauna, in ga ka rubuta mini saki, zai shiga jerin abun da ba zai taɓa gogewa a rayuwata ba. Na je gidanmu, Antynmu ta ce ba zata riƙe bazawara har karo biyu ba, na je gagarawa kakata ta ce bani da wurin zama a gidan, tun da na bar gidan na riga na bar shi, ba gidan ubana bane ba. Dangin mahaifina sun saba yi mini haka, idan na je wurin mama tayaya zan fara yi musu bayanin mutuwar aurena, suna yi maka kallon mutumin kirki, ko baka da laifi sai sun tsaneka. Kwata-kwata yaushe na koma rayuwarsu, da zan fara yi musu sintiri da matsala? Ga mama ba cikakkiyar lafiya, duk da ta fara warkewa, ina tsoron ɓacin rai ya sanya ta sake rasa lafiyarta. Duk wannan lokacin ina gagarawa, gidan yaya magaji, babu wanda ya sani sai shi, yayi iya ƙoƙarin sa a kan in yadda ya kiraka a tattauna ya sasanta na ƙi, saboda bana son ka samu matsala da mami, idan ka mayar da ni zaku cigaba da samun saɓani, daga baya na dawo Maiduguri, ina gidan su mama, na yi niyyar gaya musu na kasa, ga zuciyata na ta azabtuwa da rashinka, wallahi yau ne na zo nan, saboda ba na son su mama su sani, bana son soyayyar da suke yi maka, da mutuncinka da suke gani, ya ragu a idonsu. Ban yi haka dan na ɓata maka rai ba, rashin gata ne ya sanya hakan faruwa. Dan Allah ka yi haƙuri MD na, ka yi haƙuri ka daina fushi da ni, na wahala da yawa Please" ta ƙarasa maganar tana fashe masa da wani marayan kuka. Gaba ɗaya sai jikinsa yayi sanyi, ya ƙanƙameta a jikinsa yana shafa gashinta zuwa bayanta. A hankali ya ce "Is ok sweetheart, kukan ya isa haka" ya ɗagota yana share mata hawayen fuskarta sannan ya ce "Duk da kin neme ni da haka ba ta faru ba, amma ki ka ƙaurace mini gaba ɗaya haba Salmana" "To ka ce baka sake ni ba, kuma na riga na ce ka sake ni" "Baki da shaida ai, dan haka ni ban sake ki ba, takardun gidan suna mota ta, amma kina ganin babu matsala abun da ki ka sa na yi? Ina za su koma su zauna?" Ummi ta ce "Cewa aka yi bani da masauki a gidan, ba gidan ubana bane ba, tun da bana ubana bane ba, yanzu na mijina ne, sonake a rushe gidan ma ya zama tarihi na daina ganinsa saboda na manta mummunar rayuwar da na yi a cikinsa". Ya ce "Mu bar wannan maganar for now, i so much miss you sweetheart, abinci babu daɗi, ko san tunkarar gida bana yi, saboda babu ke a cikinsa" Ta kwaɓe baki ta ce "Ba amarya zaka yi ba? Meye na damuwa da ni" "Salma kin fa san komai, kuma waye ya ce miki zan yi aure? Kema kin san ba so nake yi ba". Ta harare shi ta ce "Ni zaka yi wa daɗin baki, duk wadda take ganin za ta iya kishi da mummunar mace kamar ni, bisimillah" Raihan ya ce "Innalillahi, wai ummi anya ba canza mini ke aka yi ba? Dan Allah mu bar wannan zancen i so much miss you kairun nisa'i" yayi maganar yana ƙara ƙanƙameta. "Na kusa gama idda, kar ka ɓata mini iddata" "A'a takaba ki ke yi ba idda ba" Nan suka shiririce, suka manta da duk wata damuwa da suka shiga a ƴan kwanakin. Tare da nuna wa juna tsantsar soyayya da yadda suka yi missing ɗin juna. "My" "Na'am sweetheart" "Meye abun yi yanzu?" "A ina?" "Ban gayawa kawu abun da ya faru ba, ban sani ba ko ya sani, ina ga dai wurin mama zan koma na zauna dole" Raihan ya ce "Ke a tunaninki zan bari ki sake kufce mini ne? Gobe in Allah ya kaimu da sassafe zamu tafi Abuja" "Amma mami fa? Kuma ga aure zaka yi, kar ka kuma samun saɓani da ita" "Ke ina ruwanki da aurena ne? Kin san wani abu?" Ta ce "A'a" "Har cewa su Alhaji na yi, bani da lafiya ba zan iya ƙara aure ba, kema haƙuri ki ke yi da ni" A zabure ummi ta kalleshi ta ce "Amma da wasa ka ke yi ko?" "Wallahi da gaske nake" "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wai kai ba ka jin kunya ne?" "In dai a kan ki ne bana jin kunya, a wurinki ne kawai nake da lafiya" haka suka manta da damuwa da matsalolin da suke ciki. Washegari da sassafe, suka shirya suka tafi Abuja da shi da ummi. Ya danƙawa ummi takardun gidan gagarawa ba tare da ya cigaba da takura mata a kan me za ta yi da gidan ba. Sai dai ta ce masa ya ajiye mata. Raihan ɗin da sai da Alhaji yayi ta fama da shi a kan tafiya Abuja, amma daga baya ya ji raihan shiru, ya tafi babu ko sallama. Ummi har mamakin irin son da raihan yake yi mata take yi, kullum fatanta da Addu'arta Allah ya sa kar ya daina sonta. Ummi ji take za ta iya ɗaukar kowace kasada dan ta cigaba da rayuwa da mijinta, dan sai dai ta bar gidansa ta ƙara tabattar da ɗakinta shi ne rufin asirin ta, dan sai da ta yi wa maryam Allah ya isa. A gidan su wani abokin raihan suka sauka, gidan babu kowa a ciki, kuma kafin su je an gyara gidan komai akwai a cikin gidan. Cikin dare suna bacci, raihan ya farka ummi na jikinsa, sai dai jikinta ya ɗau zafi sosai. Ya haskata ya ga baccinta take yi hankali kwance, washegari da safe da ta tashi, idonta ya ɗan yi wani iri. Ta dube shi ta ce "Good morning" "Sweetheart, wai ba ki da lafiya ne? Jiya da daddare na ji jikinki ya yi zafi?" Tayi murmushi ta ce "Duk cikin murnar ganinka ne, amma lafiyata ƙalau" Ya rungumeta a jikinsa ya ce "Anya kuwa, idonki kamar wadda ba ta da lafiya" wayarsa ce ta fara ringing, ya kai hannu ya ɗaga yayi sallama. Muryar Safiyya ya ji ta ce "Yaya ina kwana?" "Lafiya lau" "Dama mami ce ta ce na kiraka, maganar kuɗin party, sannan kuma kayan da zan yi fitar biki". Raihan ya ce "Ai dama auren na mami ne, dan haka ita zaki tambaya bani ba" Ya katse kiran, ya kalli ummi da take ta sauke numfashi. "Salma ya dai?" Ƙoƙarin tashi take yi daga jikinsa, ya riƙe ta ya ce "Meyafaru ne?". "Dan Allah idan kana sonta, kar ka yi pretending dan ka kwantar mini hankali, dan Allah ka yi aurenka". "Haba ummi tun yanzu? Kin fara karaya ni ya zan yi to? Dan Allah kar ki ce zaki daina kulawa da ni, wallahi banda tursasawar mami, ni babu agender ƙara aure a gabana, wannan ɗin ma da yaya aka yi ana cewa na yi ƙanƙanta?" Ummi ta yi masa shiru, dan wani irin zafi ƙirjinta yake yi mata. Ya tashi zaune ya ce "Me zan yi mana order mu karya, zan fita da wuri ne" Ta juya masa baya ta yi shiru. Sai a lokacin ta ji ashe ƙarya take yi, da take cewa ba zata ɗaga masa hankali idan zai ƙara aure ba. Ya leƙa fuskarta ya ga yadda ta haɗe rai. Bai ce mata komai ba, ya tashi ya shiga banɗaki, har ya gama shirinsa ya fita ba ta sake kula shi ba. Sai dai fitarsa ke da wuya ta fashe da kuka, yayi wuri ace za ayi mata kishiya tana tsaka da karɓar kulawa da soyayya daga wurin mijinta, an hanata samun cikakkiyar nutsuwa tare da shi. Ya dawo da takeaway, nan ma ta ce ya ci nasa ba yanzu za ta karya ba. Haka ƴan kwanakin yayi ta fama da ummi, ita kanta ba ta san tana da azabar kishi har haka ba, sai yanzu dan ta fara zancen ita maiduguri za ta koma. Ta addabi kanta da zuciyarta ko abincin kirki ba ta iya ci, idan baya nan sai ta zauna ta sha kuka kamar ƙaramar yarinya, idan ya dawo babu ruwanta da shi, ko shimfiɗarsu ya je, sai ransa ya ɓaci. Ga kiran waya da mami take babu ƙaƙƙautawa a kan maganar auren sa. Yau da ya kai ƙarshen ƙulewa da halinta, ya hau zazzaga mata bala'i. Tayi masa shiru abun da ya fi komai ɓata masa rai. "Ai gara na yi auren, tun da kin gaji dani kin daina tausayi na, ina ta taki kina wahalar da ni". Kai tsaye ta ce "Da ka huta dama kana son abun ka a ranka" Sai da ya sake ɗaga kai dan ganin ko ba ummi ce ta yi maganar ba. Janyota yayi da ƙarfi yana fuskantar ta, zai sake balbale ta da faɗa, ya ji tana sheshsheƙar kuka, sai kuma jikinsa yayi sanyi. "Ummi wai meye haka? Gaba ɗaya kin canza". "Dan Allah ka bari na koma maiduguri na zauna, ka je ka yi aurenka" "Ummi ni ɗin ne ba kya so kuma yanzu?" Cikin kuka ta girgiza kai ta ce "Ba fa abu ne mai sauƙi ba, wallahi ba zan iya jurewa ba, kishi zai kashe ni, ba zan iya pretending ba ɗan aljannata, i so much love you sweetheart, ba zan iya pretending ba, kullum zuciyata da sauri take bugawa idan na tuna zaka zama namu ni da wata, ka yi haƙuri ba dan in ɓata maka rai nake yi ba, ban san haka kishin yake ba, na ɗauka ba shi da wahala" ta ƙarasa tana ƙanƙame hannunsa tana kuka mai ratsa zuciya. Tausasan kalamanta sai suka sanya tausayinta ƙara shigarsa. "Na san babu sauƙi, amma ki jure dan Allah na samu na yi wa mami biyayya ko na gama da duniya lafiya, idan ina ganinki a haka zan iya bujirewa, ki daure Salmana ki yi haƙuri na san da ciwo" ya din ga rarrashinta tana wata irin ajiyar zuciya, da sai da ta din ga bashi tsoro kar wani abu ya sameta. Cikin dare jikinta yaƙi daɗi, dama tana zazzaɓinta a tsatstsaye, idan ta ci abinci tayi ta amai, ba abun da yake zama a cikin ta, sai dai na yau ya tsananta, da har sai da raihan ya gane, tun tana iya zuwa banɗaki yin aman har ta kasa. Ranga-ranga ya tafi da ita asibiti, a karon farko gwaje-gwaje suka tabattar da ciki ne da ita. Raihan kamar yayi tsalle dan murna. Tun da tayi ɓarin nan ba ta ƙara yin period ba. Aka din ga saka mata ruwa, sai dai zazzaɓi ba ya sauka, kuma ko ta ci abinci ko ba ta ci ba sai tayi amai. Tausayinta ya cika raihan, ga zafin laulayi ga kishi, sai da likita ya zo dubata ne ma take gaya masa ta fi wata tana zazzaɓi a kaɗan-kaɗan. Raihan yana saka ran a sallame su, amma likita ya ce sai sun riƙe ta, saboda low bp, ga jininta ma yayi ƙasa, sai an ba ta kulawa ta musamman. Kwananta biyu a asibiti, da sassafe ya dafa tea zai kai mata, ya fito daga motar sa, sai ga kiran wayar Alhaji. Ya ɗaga yana gaida Alhaji sai dai yanayin muryarsa ya tabattar masa ba lafiya ba. "Kana ina?" "Ina Abuja Alhaji lafiya?" "Ban sani ba, ina ummi take?" Gaban raihan ya faɗi ya ce "Tana gida?" "Ni zaka yi wa ƙarya? Ashe baka da hankali ba ka da mutunci raihan? Jiya da daddare babanta ya kirani cikin damuwa ashe sakar masa ƴa ka yi, kuma an nemi in da take an rasa, ga wani case can a familynsu ma ana ta nemanta, ka gaya mini ka sakar masa ƴa? A baka yarinya cikin girma da mutunci amma ka wulaƙanta ta, yarinya mai tarbiyya da nutsuwa, bilki ce ta saka ka saketa ko?" Raihan ya girgiza kai ya ce "A'a ba ita ba ce ba". "Koma waye ya saka ka, ka cuci kanka, kana ina? Kuma ina ƴar mutane" Raihan ya ce "Muna tare a nan Abuja" "Uban me ka ɗauketa ka yi mata a abujan bayan ka saketa?" "Alhaji ba sakinta na yi ba, rashin fahimta ne" A fusace ya ce "Kai ka sani, baka ma da kunya, in anjima zan shigo garin Abujan, ka bani ƴar mutane da takardarta na danƙawa mahaifinta ita, kai kuma tun da mutumin banza ne ka je ka ƙarata, am so disappointed on you!. 08081012143 PAID ADVERT!. Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi. Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku Oll types of Turaran wuta Sandal Halut Irik Difur Gab Gab Kajiji Habil Nabak Humra Kulakcha Dilke da kalta Kayan Garan jiki Muna turara Kaya Kujerar garan jiki Kannada Madarorin turare masu kamshi  Man garan gashi  Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702   08025453921 *TALLA!TALLA!TALLA!* *INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*. *BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU* *MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA* CUTARWA! AYSHERCOOL (BRIGHT PENS) MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g 45 PAID ADVERT *Hajiya ina zaki? Saurin me ki ke yi haka? Ɗan bani aron mintuna biyu kacal, na gaya miki albishir ɗin da na zo miki da shi. Shin ko kin san sirrin sheƙin fatar ummi, da ya sanya ta kama zuciyar MD raihan ta hana shi sukuni? Kai ba ma skin care ba, har da sirrin gyaran gashi, ina masu fama da amosani, karyewar gashi ko kuma sanƙo, jan gashi ne da ke? Ko taurin gashi kamar soson ƙarfe. Idan matsalar ki budurwar fata, tare da rashin glowing, Annur skin scrub da hair bliss sun shirya tsaf domin magance muku kukanku, me ku ke jira ku tuntuɓe su a kan lambar wayar su dan ƙarin bayani 07045971194 ko 08140450950* 45 Raihan ya rasa ta ina zai fara kare kansa ma, haka yayi shiru Alhaji ya gama faɗan ya kashe wayarsa. Kamar wanda aka gayawa saƙon mutuwa, haka ya ƙarasa cikin asibitin, ya taimakawa ummi ta wanke baki, ya haɗa mata tea da dankali yana bata. Cikin ɗari-ɗari take ci, dan ta san ƙarshen abun ta amayar da abun da ta ci, ga yunwa tana ji sosai. "MD ka ga wancan cikin ban san ma da shi ba, ban yi laulayi ba wannan kuwa sai wahala nake sha" Yayi murmushi da ƙyar ya ce "Wancan kin ci bonus" "Wai ya na ganka duk wani iri ne? Na san zaman asibiti da gajiya, ba daɗi shiyasa gara ka mayar da ni maiduguri" Raihan ya ce "No, ba gajiya na yi ba, da ke da babyna kuna buƙatar kulawata. Ai gazawa ce in ce ki koma gida dan baki da lafiya, ni zan yi abun da ya dace na kula da ku" Tayi murmushi ta ce "To aikin fa?" "Shima duk zan iya" "Ɗan Aljannana, Allah ya saka maka da mafificin alkhairi, ya barmu tare har aljanna" Ya amsa mata da Amin, ƙasan zuciyarsa yana fargabar hukuncin Alhaji, dan daga ji ya ɗau zafi sosai. Yadda ta gama cin dankalin nan, sai da ta amayar da shi gaba ɗaya, abun har tsoro yake bawa raihan, duk ta rame saboda laulayi. Yana nan zaune tare da ita, har ta samu bacci, bayan wasu awanni ta din ga jin hayaniya kamar a mafarki. Ta buɗe idonta, ta ga Alhaji a ɗakin tare da Salim, ga raihan a gefe ransa a haɗe sai kuma likita a tsaye da file. A hankali ta tashi zaune, tana mamakin zuwansu ta ce "Alhaji sannu da zuwa" Ya dubi Ummi ya ce "Sannu ya jikin? Dan Allah kalli yadda duk ta bi ta ƙare ta rame, meke damunta ne? Ko kuma duk tsiyataku da rashin mutuncinka ne ya sanya ta rame" Yayi maganar yana kallon raihan. Likita ya ce "Ahh ba wani abun damuwa bane, laulayi ne na mata, ba ta iya cin komai shiyasa muka ajiyeta mu ke ta saka mata ruwa" Alhaji ya ce "Ka rubuta mata sallama, gida kano zamu tafi, za a cigaba da kula da ita a can" Ya mayar da idonsa kan ummi ya ce "Banda abunki ummi, gani menene amfanina? Ko dr. Ba ya nan wani abu ya haɗaku sai ki zo ki gaya mini, ni ƴa ta ce ke ba sirika ba, kawai sai ki biye masa ki tafi wani wurin ace ba a san ma in da ki ke ba? Kuma dan baka da kunya ka lallaɓa ka mayar da ita ka taho da ita nan ba wanda ya sani, hankalin mahaifinta na can a tashe bai san ina take ba, ka bani kunya" daga ummi har raihan aka rasa mai magana, ummi ba ta taɓa zaton Alhaji ya iya faɗa haka ba, saboda kullum fuskarsa cikin murmushi yake. Haka aka sallami ummi, suka nufo kano, raihan ya sha faɗa a wurin Alhaji,kuma yayi shiru bai ce komai ba ummi gaba ɗaya ta ji babu daɗi. Asibiti suka zarce da ummi, aka cigaba da ba ta kulawa ta musamman, saboda suna tafe a hanya ma tana amai. Alhaji ya kira dr. A waya ya sanar masa ya gano ummi, tana tare da raihan a maiduguri. Dr. Ya ce ya haɗa shi da ummin a waya, Alhaji ya ce masa ba ta da lafiya, ba za ta iya amsa waya ba. Dr. Ya ce a cikin satin zai shigo Nigeria, dan hakan yayi dai-dai da lokacin zuwansa hutu. Ya karɓi kwatancen asibitin, ya kira Abdul a waya, ya ce su je asibiti da shi da noor, su duba masa jikin ummi. Ko da suka je, sai da Abdul ya yi wa raihan ƙorafin, meyasa bai gaya masa ba ya ga ummi. Babban abun da ya bawa ummi mamaki, bai wuce yadda Salim da noor suke yi wa juna murmushi ba, kamar sun saba. Kuma a iya sanin ummi ba shi da fara'a ko kaɗan. Noor ta ƙarasa gaban gadon ummi ta na yi mata sannu. "Yaya ummi shi ne ki ka tafi aka neme ki aka rasa ko? To ƴan gagarawa ne suka samo wani abokin Abba, suka saka ya kira musu shi, aka gaya masa abun da ki ka yi, ya bi ba'asi ban san dai me suka ce masa ba, ya kira waya yana faɗa ya cewa yaya Abdul ya je gidanki ya duba masa ke dama ba ya samunki a waya, aikuwa dai ya gaya masa gaskiya, amma fa mun sha faɗa saura ke idan ya dawo dan ransa ya ɓaci" Salim ya ce "Ba ki ga bata da lafiya bane?" Ta ce "Au, haka ne fa, zumuɗi nake na ganta, ba ka san yadda na shiga tashin hankali ba da aka ce ta ɓata". Yayi murmushi ya ce "I see" Alhaji ya ce "Ai daga ita har shi, sun yi laifi, kuma ba zan matsa da bincike ba, sai dr. Ya dawo, amma fushi dole ayi fushi da su" shi dai raihan ya rasa menene yake yi masa daɗi, ga rashin lafiyar ummi, ga faɗan Alhaji da yaƙi saurarensa. Salim ya ɗauki Alhaji suka tafi gida, tun da yaje gida yake cigaba da faɗa a kan abun da ya faru, hankalin mami yayi mugun tashi, dan yadda ransa ya yi mummunan ɓacin nan, zai iya aikata komai dan kamar ƴar cikinsa aka yi wa haka ɗauki lamarin da zafin gaske. Ta din ga kiran raihan tana jaddada masa, kar ya kuskura ya gaya wa Alhaji ita ce ta saka ya saki ummi. "Mami na ji, ni ba zan faɗa ba, amma ummi fa?" "Au kai sai ka bari ta faɗa ɗin?" "Mami ya zan yi, tayaya? Zan yi mata dole ne, tana kwance muna fama ba ta da lafiya, ba zama ta fahimci me nake nufi ba" mursisi raihan ya nuna wa mami ba zai tursasa ummi ba. Bayan ya kashe wayar ya kalli wayar ya ce "Mami ina fatan zaki fahimci cewa, ɗan adam duk ƙin da ki ke yi masa wataran zai iya yi miki rana, ko ki nemi alfarma a wurinsa. Kwana biyu ummi ta ɗan warware, ranar dr. Ya dawo, Alhaji dai tare da Salim suke zuwa asibiti, haka Hajiya ma take sintiri. Tun da raihan yayi aure, Alhaji da Salim suke ɗasawa saboda Alhaji ya jinjinawa Salim yadda yayi playing role ɗin sa na babban yaya ga raihan ba tare da wata adawa ba. Kuma a hankali ya lura da ya rage fitina sosai da sosai, dan ko fita baya son yi suna tare da Alhaji. Alhaji ya kasa shiru, sai da ya tambaye shi, dalilin canzawarsa lokaci ɗaya yayi murmushi ya ce "Alhaji kenan, ai ko dabba idan kana mutunta uwata zata so ka, balle ɗan Adam ni dama wasu lokutan babarsa ke sanyawa nake ja baya da shi, duk abun da yake faruwa ina sane da yadda mutunta da girmama mahaifiyarmu. Da na raka shi maiduguri ma, yadda dangin matarsa suka din ga yaba kamalarmu na ji daɗin hakan sosai, na ƙara yadda da zama mutumin banza ba shi da wata fa'ida. kuma ƙanina zai yi aure very soon zai fara tara zuriya, kuma yaransa namu ne, abun kunya ne a garemu yaranmu su taso su ganmu a irin wannan yanayin. Ina ta addu'a kuma ina jan hankalin Sagir ma. Abu na gaba rayuwar raihan da matarsa ta burgeni, da har na ji nima ina son yin aure, amma na san za a iya hanani aure saboda halina, duk ruɗin abokai ne dama, amma yanzu Alhamdilillah ina ta ƙoƙarin gyara kuskure na na baya, a cigaba da yi mana addu'a". Alhaji ya ji daɗin kalaman Salim ya din ga saka masa albarka, tare da alwashin duk yarinyar da yake so ya sanar masa, zai nema masa aurenta, tun da matar na tuba ba ta rasa miji. Daga haka ya ƙara janyo shi a jikinsa,  da cigaba da rarrashin sa da yi masa nasiha. Murna ta saka sai da ya bawa Hajiya labari, Hajiya ta din ga murna ta ce "Aini auro ummi cikin familyn nan ya zame mini alkhairi mai tarin yawa, ba abun da zan cewa Allah sai godiya, Allah ya ƙara musu zaman lafiya da kwanciyar hankali, ya ƙara haɗa kan zuriyarmu". Yadda ummi ke ƙara girmama shi, yaya sama yaya ƙasa, mutuntawa ta kowane fanni, ga yadda ita ma ta ɗora da kyautatwa mahaifiyarsu, dama can kuma kan a aurota, ya san yadda take mutunta kowa a gidan, hakan ya sanya shi ma yake girmamata da jin nauyinta. Dan wasu lokutan ta kan tsokane shi, da shi ne ɗan uwanta da mama ta faɗa, lokacin da suka je maiduguri, babu wasan ƙanin miji tsakaninsu sai girmamawa da mutunta juna. A falon gidan dr. Kuwa, ga raihan, ga ummi, ga dr. Da Alhaji, sai Abdul da Salim. Alhaji ya kalli raihan ya ce "To ayi ta ƙeƙe da ƙeƙe a gaban mahaifinta ka faɗi saki nawa ka yi mata? Tun da dama abu kan ya faru ake magance shi, da ka sanar akwai matsala ne sai a sasanta ku, kan a kawo nan amma tun da aka zo nan, sai ayi ta ta ƙare. Raihan ya yi shiru bai ce komai ba. "Ba magana nake yi maka ba?" Kamar zai yi kuka ya ce "Alhaji wallahi ban saki matata ba, idan ma na saketa a na mayar da ita" "Rufe mini baki, abun da na ce shi zaka yi tun da har ka yi ƙwarin sakin mace, tun da ka ke ko tafi gidanku ka ga na taɓa cewa wata a matana?" Ganin Alhaji zai sake rufe raihan da faɗa ya sanya ta ce "Alhaji ka yi haƙuri, ba laifinsa bane ba laifina ne, rashin fahimta ne na zata sakina zai yi shi ne na tafi" "A'a ban yadda ba, ƙoƙarin kare shi ki ke yi, babu yadda za ayi ki tafi ba tare da izininsa ba" Dr. Ya ce "Ni bama haka ba, banda abunki ummi, da lamarin ya faru maimakon ki taho gida, sai ki yi wani wurin, ayi ta nemanki ba a san in da ki ke ba, haka ake yi? Ba ki taɓa ɓata mini rai kamar a wannan karon ba, ummi kuma saboda rashin neman albarka gidanmu na gado na iyaye da kakanni, ki ka sayar da shi haryanzu ina tantama idan ke ki ka aikata haka, kin bani kunya kuma fushi nake yi da ke" Alhaji ya ce "A'a dr. Ban tari numfashinka ba, a fara jin ta bakinta" "Haba Alhaji Tahir, ai komenene hanzarinta abun da ta aikata yayi muni, iyayenta ne fa a ciki har da babarmu, wane irin abu ne wannan? An ce mini ma ke ki ka yi sayi gidan, a ina ki ka samo kuɗin sayen gidan?" Ummi ta fashe da kuka, sai kuma nadamar abun da ta yi ya ziyarci zuciyarta, ta ga lallai ta yanke mummunan hukunci cikin fushi. Raihan ya ce "Dan Allah kawu ka yi haƙuri, ka yi mana afuwa mun yi kuskure, ba laifin ummi bane ba, ni ne na sayi gidan, saboda ta dawo, dan Allah ku yi haƙuri ku yafe mana mu koma gida ba ta da lafiya" Salim ya girgiza kai, ana ƙoƙarin gyara abu, shi ta a koma gida yake yi, kuma sai ƙumbiya-ƙumbiya suke yi, sun ƙi magana sai kare juna. Ummi ta ƙarasa gaban dr., Tana kuka ta riƙe ƙafarsa ta ce "Dan Allah kawu ka yi haƙuri, fushinka a gareni fitina ne, na yi laifi na yanke hukunci cikin fushi, na yi haka ne dan rage raɗaɗin da yake zuciyata, wallahi dr. Wanda ku ke so na a duniyar nan ba afi a ƙirga ku ba, shikenan ranar da babu ku haka zan tagayyara?. Na zo gidan nan, Anty ta ce ba zan zauna ba, ba zan sake zaunar mata a gida ba, na je gagarawa iya ta kore ni, wai bani da mutunci babu gadon ubana a gidan, tayaya zan koma maiduguri daga yin aurena ace ya mutu, ai sai su tsane ni, na rasa yadda zan yi na kasa tunanin komai, zuciya ta ɗebe ni na yi abun da na aikata dan Allah ka yi haƙuri kawu" Cikin takaici ya ce "Faridan ce ta kore ki daga gidan nan?x ummi ta jinjina kai alamar eh. Raihan ya ce "Dan Allah kawu ka yi haƙuri, mun yi laifi ". "Rufewa mutane baki, duk da baka saketa ba ya za ayi haka ta faru, kuma kema ummi waye ya gaya miki dr. ne kawai babanki, ni meyasa baki zo wurina ba? Ina da masaukin da zan ajiyeki ko da ba kwa tare da raihan, tun da ba shi da kirki bai san halacci ba". Salim ya yi gyaran murya ya ce "Raihan ka yi haƙuri da abun da zan faɗa, Alhaji da raihan da ummi, duk ƙannena ne, kuma stll ina da ƴan uwa mata, da ba zan so su tozarta a gidan aure ba. Ummi da raihan suna zaune lafiya da junansu, mami ce ta saka ya saki ummi" gaba ɗaya suka kalli Salim. Bai damu ba ya cigaba da cewa "Na je gidan Raihan maigafi ya ce mini kwananta biyu ba ta gidan, kawai na ji jikina bai bani ba, mussaman tun da na ga maryam ta zo gida, da kuma saɓanin da suka samu. Na zo nan gidan, na yi sa'a na haɗu da noor, ita ta gaya mini raihan ya saki ummi, kuma mami ce ta saka shi, nan gidan kuma matar gidan ta ce ba zata zauna ba. Na koma gida na ritsa Nihal ta sake tabattar mini da hakan. Na je garinsu can gagarawa, na haɗu da ummi kan ta bar gidan, ta gaya mini abun da ya faru, da yadda ta koma gidan yayanta ta zauna. Na yi ta zuba ido in ji ko raihan zai faɗi abun da ya faru amma shiru bai yi magana ba" Tsit falon yayi, raihan ya ɗaga kai yana kallon Salim, kenan duk wannan wahalar ya san in da ummi take, amma bai gaya masa ba?. Dr. Ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un" Alhajin ma Innalillahi wa Innalillahi raji'un ɗin yake maimaitawa "Wai mata wane irin tunani ne da su haka? Har ki saka ya saki yarinya saboda wulaƙanci me tayi mata?" Raihan ya yi farat ya ce "Wallahi ban saketa ba Alhaji, ban ba ta takarda ba, ban faɗa mata da baki ba kawai tafiya ta yi" "Rufe mini baki, tun da nake banbamina ka gaya mini abun da ya faru?" Raihan ya sunkuyar da kai. "Kema kuma ummi baki faɗa ba duk ku ka yi shiru ko?" Salim ya ce "Alhaji, dan Allah duk ku yi haƙuri aikin gama ya riga ya gama, tun da dai ya ce bai saketa ba, ayi haƙuri su koma gidansu" Raihan ya ce "Eh Alhaji, ayi haƙuri dan Allah, kawu dan Allah ayi haƙuri dan girman Allah" Dr. Ya ce "Shikenan, ɗauki matarka ku tafi, Allah ya kiyaye gaba" Alhaji ya ce "Da dai ka bari an hukunta shi daga shi har ita" Raihan cikin zumuɗi ya cewa ummi ta tashi su tafi. Daga dr. Har kawu sun ji takaicin abun da ya faru, sun daɗe suna tattaunawa sannan suka yi sallama. Sai dai Alhaji ma ya yi wa Salim faɗa sosai na ɓoye masa abun da ya faru. Sai dai danne fushinsa yayi, dan ba ƙaramin takaici da kunya ya sha ba, da aka ce wai Bilki ce ta saka raihan ya saki ummi. Dr. Bai cewa Farida komai ba, dan haka ba ta kawo zai ce mata wani abu ba. Daga ƙauye sagir ya kira dr. A waya, kamar zai fashe da kuka yana yi masa magiya a kan ya dubi Allah ya yi wani abu a kan lamarin nan, sun rasa yadda za su yi ba za su iya haya ba. Dr. Ya ce "Sagir ai aikin gama ya riga ya gama, sun riga sun sai gida, sai ku yi magana da su, ko ku din ga biyanta haya ko kuma ku bar mata ni ban san yadda zan daidaita wannan al'amarin ba" "Yanzu haka zamu tagayyara da mu da mahaifiyarmu?" "To Sagir ya zan yi? Ku kuka nuna wa yarinyar nan ƙiyayya, kuna ina iya ta koreta daga gidan waye yayi magana a cikinku? Ko kana tunanin za ta manta wahalar da ta sha tana yarinya babu wanda ya iya jiɓantar lamarinta? Nima da fari na ɗau zafi amma daga baya na fahimce ta, kuma yanzu ummi ba a hannuna take ba, mijinta zaku tuntuɓa shi ne ke da alhaki da ita yanzu" Haka dr. Ya yi ta artabu da ƴan gagarawa, fafur ya ce ba ruwansa. Alhaji yana zuwa gida, kai tsaye ya wuce sashin mami, tana zaune tana waya da Anty rakiya, a kan shirin auren Safiyya, yadda Alhaji ya shigo ya sanya ta ɗan tsorata ta ajiye wayar ta ce "Alhaji lafiya?" "Ban sani ba, biliki wace irin mace ce ke ne? Ina iliminki da tunaninki suke? Saboda tsabar wulaƙanci da rashin mutunci, ki je ki saka raihan ya saki matarsa? Ki zubarwa da kanki kima ki zubar mini? Na zo miki da zancen ya saketa ba a san in da ta tafi ba, ki ka nuna mini baki san zancen ba, ashe ke ce kanwa uwar gami ki ka raina mini hankali? Lokacin da na aureki bilki sa'an aurenki ne ni? Ban taɓa yi miki gori ba amma yau zan yi ke kin san idan nasabar dukiya ce ke ba sa'ar aurena ba ce, idan kyau ne na fiki ta ko ina, soyayya ce ta saka na aureki ke ba auren na aure ki, na zauna da ke nake kyautata miki? Ke ba a auren aka auri naki ƴaƴan? Kin tsiro da zancen yayi aure yana ta ƙoƙarin kaucewa, kina ta wasu abubuwa ashe ke kin je kin saka ya saketa. Wallahi bilki idan ba ki shiga hankalinki ba, idan baki bar yaron nan ya zauna lafiya da matarsa ba, kema zaki koma naku gidan, tun da ke ba mutuniyar kirki ba ce" A razane ta kalleshi ta ce "Alhaji ni ce zan koma gidanmu, da girmana da komai?" "Eh ke ɗin, zama dake ai ba dole bane ba, tun da ba ki da girma kema" yayi mata ta tas ya fice a fusace. "Lallai yarinyar nan, wato sai da ta faɗa kenan? To wallahi da ni take zancen, ɗa na ne sai ta rabu da shi in dai ina raye". Raihan kuwa cigaba da tattalin matarsa yayi, yana rarrashinta. Kwanan ummi uku da komawa gidan raihan, dr. Ya saka noor ta koma gidan ummi ta ɗan zauna da ita saboda rashin lafiya. Ƙarshe Alhaji ne ya sake tafiya Abuja, wurin sabon kamfaninsu, saboda gaba ɗaya raihan hankalinsa ba ya jikinsa, saboda ummi kamar ba za ta yi rai ba, saboda wahalar laulayi. Sai dai mami ba ta daddara ba, sai da ta je har gidan raihan, ta sake yi wa ummi wankin babban bargo, ta zageta tsaf raihan baya nan, noor kuma ta tafi makaranta. Har ta yi ta gama cin mutuncin ta, ummi ba ta tanka mata ba, dan ita ciwon da take fama ya isheta. Sai dai maganganun da ta gaya mata na cin mutunci sun yi mata zafi, amma ta shanye. Share² da girki duk noor ce take yi wa ummi. Da azahar raihan yake cewa ummi, dr. Ya ce zai zo, dan haka da kanta ta lallaɓa ta shiga kitchen ta taya noor suka yi girki. Bayan la'asar sai ga dr. Da ƴan uwan babanta na gagarawa, har da yaya magaji. Suka gaisa, ƴan mazan nan da ba su taɓa zuwa gidan ummi ba, suka din ga mamaki ganin uban gidan da ummi take ciki. Suka fake da yi wa ummi ya jiki, sannan kawu Ilyasu ya ce "Ummi, dama zuwa muka yi mu nemi afuwarki a kan abubuwan da suka faru a baya, dan Allah ki yi haƙuri, iya ma ta ce a baki haƙuri, sannan dan Allah ki taimaka mana da batun gidan nan, wallahi idan muka tashi bamu san in da muka dosa ba". Dr. Ya ce "Neman yafiyarta ku ka zo ko kuma neman alfarma?" "Duka, dan Allah yaron kirki ka saka baki, dan Allah a dube mu mun yi ƴaƴa da jikoki, bamu san ina zamu je ba, a taimaka mana dan girman Allah" Hashim ya yi murmushi ya sunkuyar da kai, ya tuna lokacin da mariya idan iya ta guma mata tayi kuka, ta ce in Allah ya yarda sai sun nemi alfarmar ummi. Raihan ya ce "To ai ni bani da ta cewa, ni da na sai gida, ummi na sayawa ba kaina ba, dan haka gida nata ne ba nawa ba, kuma ni ban san me ku ka yi mata ba, ba zan tursasa mata ba" "Ummana, ki yi magana mana" dr. Yayi maganar yana kallon ta. Hawaye ya ƙwace mata ta ce "Kawuna duk abun da ka yanke shikenan" "A'a Ummi, ba zan takura miki ba, ki samu lokaci ki yanke hukuncin da ki ke ganin ya dace sai ki tuntuɓe ni, alfarma ɗaya zan nema musu, a bar su a gidan kan ki yanke hukuncin" Ta jinjina masa kai, tana share hawaye. "Ke mai haƙuri ce da juriya, kuma haƙurin ne ya kawo ki wannan matakin, ni shaida ne an zalunce ki ummi, kin fuskanci ƙalubale a rayuwar ki mai tarin yawa, amma ki yi haƙuri, ba a canza tuwo suna, ko ba kya so dangin mahaifinki ne, ki yi haƙuri ko kin ɗauki fansa ba zaki huce ba" ta jinjinawa dr. Kai cike da borin kunya, suma suka cigaba da ba wa ummi haƙuri. Sun raka su za su tafi, dr. Ya ja ummi gefe, ya ƙara yi mata nasiha sannan ya ce "Mamana zaki iya tuna wata magana da ki ka gaya mini shekarun baya, da zamu tashi daga tsohon gidanmu?" Ummi ta ɗan yi shiru ta ce "Wace maganar kawu?" "Da ki ka ce ina ma na gyara tsohon gidan, in an ga in da mamanki take ku zauna tare a ciki" Ummi ta yi murmushi ta ce "Kawu lokacin ai har da ƙuruciya" Yayi murmushi ya ce "Yanzu fa?" "An girma" tayi maganar da ƴar dariya. "What if, hakan ta kasance?" Ummi ta ɗan rausayar da kai ta ce "Da na yi murna mara misaltuwa, ni kaina da zai yiwu da na dawo da ita gidana, amma ga yanayin yadda nake zaune da uwar mijina kar na janyo mana gori". "No ba wannan ba, auren mamanki nake son yi, zan gyara mata tsohon gidana na sakata a ciki" Ummi ta waro ido tana kallon dr. "Ya dai mamana, ko baki ji daɗi ba?" "Kawu, amma...Anty fa?" "Babu ruwanki da ita, abun ne ya faɗo mini na ce bari na ɗan tuntuɓe ki" Ummi ta faɗaɗa murmushinta ta zube a kan gwiwoyinta ta ce "Kawu da ka gama yi mini komai, dawo da mama kusa da ni, Na amince ɗari bisa ɗari, Allah ya sanya alkhairi " Ya ce "Tashi maza, bana son wani ya san me ake ciki, ai lokacin da na ganota ma, na yi niyyar hakan iya ta hana, amma a wannan karon abun da farida tayi miki, ya sanya na ƙara ganin muhimmancin hakan. Na fara magana da baba ma, da kuɗin aure da sadaki da komai rana ɗaya za a kai a ɗaura, ina ga da ita zan tafi Uganda, in ƙarasa karatun tana tare da ni" Idan ummi ta fahimta dai-dai, kamar da haka dr. Yake son hukunta farida. "Allah ya ba da iko kawu, Allah ya biya maka buƙatunka na alkhairi, na gode sosai da sosai" Dr. Ya ce "Menene na godiyar kuma? Duk abun da ya dace za a yi wa gidan, zan turo miki kuɗi ki yi sayayya a zuba a ciki kan mu dawo, a sati biyun nan da suka rage mini, za'ayi komai da yardar Allah" Ummi ta din ga murna, take duk wata damuwarta ta ji babu ita, saboda tsabar zumuɗi ta iske raihan a bedroom ta rungume shi tana murna. "Ikon Allah, daga kuka zuwa farinciki bani labari, meyafaru?" Nan ta kwashe komai ta gaya masa, ya taya ummi murna sosai da sosai. Yadda Alhaji ya ɗauki zafi, yayi fushi da mami, har tsoron tunkararsa take yi, da maganar auren raihan, ya daina kulata ya daina cin abincinta, kuma ya hanata zuwa ɗakinsa. Tana kitchen tana tsiyayar tea, ta rasa abun da yake yi mata daɗi, kawai ta ga Salim a kitchen ɗin. Sai da ta razana dan bai taɓa yi ba. "Na ji kin je har gida, kin sake cin mutuncin matar raihan, kina zaton ita ta gaya wa Alhaji kin saka an saketa, to ba ita ba ce ba, ni na gaya masa, dan tun bayan lamarin ya faru na sani. A yanzun ma ba ita ta gaya mini ba, ina da CID na da ke gaya mini komai, kin san wani abu kuwa, duk kasancewata makakke kamar yadda ki ke faɗa duk wanda yake mutunta uwata mutum ne mai kima a idona. Dan haka ba zan bari ɗan uwana ya cutu ba dan kina babarsa, kuma ba zan bari yarinyar da ba ta ji ba ba ta gani ba ta cutu. Kin san wani abu, ina amfani da raihan, wurin rama cin mutuncin da ki ke yi wa uwata, na fuskanci a duniya masoyinki ba ya gaban raihan, kamar yadda yake ji da wanda yake ƙaunar matarsa, dan haka zan taya ɗan uwana son abun da yake so, idan kuma ki ka cigaba da matsawa zaki yi biyu babu, gargaɗi nake yi ba shawara ba" sakin baki mami ta yi tana kallon Salim, me yake nufi da biyu babu. Kamar ya san me yake zuciyarta ya ce "Zaki rasa soyayyar ɗanki, dan a yanzu yana yi miki kallon wadda ba ta son farincikin sa, kujerar da yake kai ma zaki yi masa dalilinta, dan na san yadda ki ka ƙallafa rai a kanta, raihan ya ɗauki kuɗin Alhaji ya sayawa matarsa gida, idan ki ka cigaba da takura yarinyar nan, za ta yi abun da ba kya zato" ya juya ya fice daga kitchen ɗin. Jikinta har rawa yake yi, ta fara tunanin da gaske raihan ya ɗauki kuɗi ya sai wa ummi gida ba tare da izinin Alhaji ba?. Bazama ta yi sashin Alhaji, yana tare da Hajiya ta shiga babu ko sallama ta ce "Alhaji, da gaske raihan ya ɗauki kuɗi babu izininka ya sai wa matarsa gida?". Alhaji ya kalleta ya ce "Eh" "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ka ga abun da nake gaya maka ko? Shiyasa na ce fa ya rabu da ita" "Rufe mini baki, ba ke ki ka sanya ya saketa ba, ke ai gashi kin ce ya ƙara aure ya ce ba shi da kuɗi ya sai wa matarsa gida, kuma kuɗi nawa suka ɗauka ba ruwanki da wannan, kuma ban ce ki saka baki a kan maganar ba, tun da ni mai kuɗin ban yi magana a kai ba" Kawai Hajiya ta kwashe da dariya. Farida tana ta murna, dr. Bai ce mata komai ba tsawon kwanaki, ya sanya ta saki jiki ta cigaba da sabgoginta, noor kanta ta san zancen auren dr. Amma ta yi shiru ba ta gaya wa farida ba. Da daddare ta shirya tana jiran dawowarsa, tun safe tana kiran wayarsa shiru bai ɗaga ba, tun da ya fita da safe bai dawo ba. Shigowa yayi cikin manyan kaya, da gani ka san a gajiye yake, ta bishi ɗaki tana tambayar sa ko lafiya. Ya zube mata goro da alawa, ya ce "lafiya ƙalau ga wannan an ɗaura mini aure yau a Maiduguri" Ayshercool 08081012143 PAID ADVERT!. Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi. Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku Oll types of Turaran wuta Sandal Halut Irik Difur Gab Gab Kajiji Habil Nabak Humra Kulakcha Dilke da kalta Kayan Garan jiki Muna turara Kaya Kujerar garan jiki Kannada Madarorin turare masu kamshi  Man garan gashi  Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702   08025453921 *TALLA!TALLA!TALLA!* *INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*. *BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU* *MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA* BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI. CUTARWA! AYSHERCOOL (BRIGHT PENS) MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g 46 PAID ADVERT *Hajiya ina zaki? Saurin me ki ke yi haka? Ɗan bani aron mintuna biyu kacal, na gaya miki albishir ɗin da na zo miki da shi. Shin ko kin san sirrin sheƙin fatar ummi, da ya sanya ta kama zuciyar MD raihan ta hana shi sukuni? Kai ba ma skin care ba, har da sirrin gyaran gashi, ina masu fama da amosani, karyewar gashi ko kuma sanƙo, jan gashi ne da ke? Ko taurin gashi kamar soson ƙarfe. Idan matsalar ki budurwar fata, tare da rashin glowing, Annur skin scrub da hair bliss sun shirya tsaf domin magance muku kukanku, me ku ke jira ku tuntuɓe su a kan lambar wayar su dan ƙarin bayani 07045971194 ko 08140450950* 46 Wata irin zabura farida ta yi, ta fizgo babbar rigar dr. Ta ce "Ni! Ni yahaya wai da gaske ka ke ko wasa?" "Na taɓa yi miki irin wannan wasan ne? Na yi aure kamar yadda na gaya miki" Girgiza kai ta yi ta ce "Ni zaka ci wa mutunci, wallahi idan bacci ka ke gara ka farka, dan baka isa ba, da can da ƙuruciyata ba ka yi mini kishiya ba sai yanzu? Wallahi ba zai yiwu ba ba a gidana ba" Ya fizge hannunta ya ce "Ni nake aurenki ba ke ki ke aurena ba, farida rashin mutuncinki da wulaƙancin da ki ke yi mini, ya sanya na yi miki koma menene. Aikin gama ya riga ya gama, zan gyara tsohon gidana na sakata a ciki, nan da sati ɗaya zuwa sama idan visarta ta zama ready zan tafi da ita uganda. Zan saka miki dubu ɗari biyu da hamsin a account ɗinki, kya sayi wani abun" "Dubu ɗari biyu da hamsin ɗinka ta banza da ta wofi, wallahi ba zai yiwu ba" Ya girgiza kai ya ce "Ya riga ya yiwu ma, ba wata ba ce na aura a waje, mariya ce mahaifiyar ummi, abun da yakamata na yi ne tun a baya, ban samu dama ba, sai a yanzu" Farida ta ce "Ka rasa wadda zaka auro a matsayin kishiyata sai mahaukaciya, wallahi yahaya kai butulu ne azzalumi wallahi ba zan zauna da mahaukaciya ta kashe ni a banza ba, kai ba zai taɓa yiwuwa ba ma wallahi ni zaka tozarta?" Ya tsaya ya ƙare mata kallo ya ce "Farida, duk abubuwan da suke faruwa a baya, kallonki kawai nake yi, tsantsar zaluncin da ki ka yi wa yarinyar nan a zamanta da ke, ina kallonki, saboda ba ki da mutunci kin mayar da ni ɗan iska da son nuna wa duniya ban isa da gidana ba, auren ummi ya samu matsala ta zo gidan ki koreta ga dare, saboda baki da hankali kin san yadda nake jin yarinyar nan a raina kuwa? Ita kaɗai take babu wa ba ƙani, ki yi mini alfarma ki riƙeta da mutunci ki ka gaza, bayan ni na riƙe taki ƴar uwar babu cuta babu cutarwa? Wannan dalilin ne ya sanya na ga lallai yakamata ummi ta ƙara shigowa cikin iyalina in sama mata farinciki ta hanyar auren mahaifiyarta, na san kome zai sameta a rayuwa ba zata taɓa korarta ba" Tayi wata irin shewa mai cike da takaici ta ce "To ayi mu gani? Wannan dai ba abun da zata tsinana maka, ba uban da zaka tsinta a tare da ita, ka ce auren na ramuwar gayya ne? To ka yi mu gani, wallahi sai ka yi bankwana da farinciki da kwanciyar hankali har abada". Ya nufi gadonsa yana faɗin "Allah ba zai gwada mini rashin kwanciyar hankali ba, in sha Allah auren nan alkhairi ne a gareni" *** Cikin mamaki da takaici mami take kallon hajiya, da take yi mata dariya cike da son tura mata takaici. Ta ce "Wato Alhaji a duniya mace ta samu nagartaccen miji irin raihan, to ta ɗaga hannu ta godewa Allah ta haye, yaron kirki Allah dai ya ja zamanin babban mutum" "Hauwwa babu ruwanki da ni, da sabgar iyalina ban saka da ke ba, ashe shiyasa ki ka turo makakken ɗanki ya ci mini mutunci yana gaya mini maganar banza, wallahi ki shiga hankalinki babu ruwanki da ni" Hajiya ta ce "Ko ba makakke ba, ai gara makakken ƙwaya, idan ƙwayar ta sake shi zai iya dawowa daidai, wanda yake cikin mayen soyayya kuwa ko za a shekara dubu ba zai farfaɗo ba, dan haka akwai banbanci ko dai ki nutsu ki yi playing role ɗinki na uwa, ko kuma idan yarinyar nan ta waiwayeki, ki ka cigaba da saka mata ƙiyayyar ki, sai ganin ɗan naki ma ya gagare ki, ɗan ɗaya tilo da ki ke alfahari da shi shiryayyye ta rabaki da shi". Alhaji ya ce "Hajiya wai kwanan nan meyake damunki ne? Ban sanki da irin wannan abubuwan ba, idan tana yi a baya ba kya mayar mata da martani, amma yanzu duk kin canza" Ta ce "Duka yau duka gobe shi yake sanya baƙin ba'auzine tawaye, kuma komai girman gona akwai kunyar ƙarshe, sai a wannan karon Allah ya kawo ni lokacin ramawa da mayar da martani, ko kun manta ɗigimin da ku ka din ga yi da ka aureta, sai da na ji kamar mu rabu na huta, Hajiya Aisha tayi ta bani haƙuri, matar nan ta din ga yi mini gorin zafin kishi zan kashe aurena ita tafi ƙarfin goga kishi da ni, ka din ga yi mini halinku na maza? To Alhamdilillah koma menene abun kunyan da na yi, bai kai naki ba da ki ke kishi da matar ɗanki, duk da zafin abun da ki ke ji, bai kai wanda na ji ba da ki ka auri mijina. Anyway, Alhajin Allah zan shiga in yi wa sirikata ɗan abun da zan tafi mata da shi na dubiya, ka san mace mai ciki bakomai take iya ci ba, idan ana ƙinta ni ina yinta tun ba yau ba, dan gara munin fuska da munin hali, duk da Alhamdilillah ba ta da muni" Alhaji kuwa sakin baki yayi yana kallon Hajiya, ta gama cashe musu ta fice. "Ciki kuma? Ba cewa yayi ba shi da lafiya ba? A ina ta samu ciki kuma?" A ƙule Alhaji ya ce "Kin ga dan Allah jeki ki bani wuri, kar saka mini ciwon kai" kamar ta fashe da kuka yau ita Alhaji yake kora, tamkar mahaukaciya ta fice daga sashin nasa tana tuntuɓe, tana tafe tana tambayar kanta ciki a jikin ummi, ƙarya yake yi kenan lafiyarsa ƙalau?. Raihan yana ta shirin fita aiki, ummi ta lallaɓa ta dafa masa tea, ta dawo ta kwanta a falo, aka ƙwanƙwasa ƙofar falon. Raihan ya tashi ya buɗe sai ga noor, ya kalleta ya ce "A'a kin gama gudun namu kin dawo?" Noor ta ce "Ai na ga zamana a nan ya fi alkhairi, gidanmu kamawa da wuta yake neman yi" Ta shigo falon tana yi wa ummi sannu. Ummi ta ce "Noor wace irin wuta kuma? Meyake faruwa a gidan?" "Wai Abba ne yayi aure, ya kawo mata alewa da dabino take ta masifa da bala'i da tashin hankali, daga na ce in ci dabinon kin ji zagin da tayi mini? Ni kuwa na ɗebo na haɗo kayana na dawo, dama sai da ku ka ce kar na tafi na ce sai na tafi. Gidanmu yana nan yadda ki ka san rasha da ukrain" Ummi ta harari noor, saboda yadda take ta zuba, a gaban raihan. Amma cikin mamaki Ummi ta ce "Amma aure kuma?" Noor ta ce "Eh mana, ashe jiya maiduguri ya je mamanku ya aura, dama na daɗe ina ce masa dama ya ƙaro mana anty" Ummi ta ce "To baba suda na ji ya isa haka" Noor ta sake cewa "Kin san Allah anty ummi, na daɗe ina tausayin Abba, dan ba kya gidan ba kya ganin yanzu abubuwan da suke faruwa, tayi ta ɗaga masa murya, amma kin ga takwarata ai saliha ce a hankali ma take magana" Raihan ya ce "Lallai dr. Ya shamamce mu, Ubangiji Allah ya sanya alkhairi, tun da gaki kin zo, bari na tafi aiki" Bayan tafiyar sa aiki, ummi ta din ga yi wa noor mitar yadda ta saki baki a gaban raihan. Noor ita ba ta ga abun laifi ba, dan a ganinta yanzu ai sun zama ɗaya da raihan. Sannan ta kira can gida maiduguri, suka tabattar mata da hakan. Cikin mamki ummi ta ce "Amma anty maryam, mama ta gama warware ne?" Anty maryam ta ce "Jikinta fa da sauƙi sosai da sosai, ai kuna waya ki ji, ya ce wai can wurin da yake karatu zai tafi da ita, amma ni matarsa nake ji ye mata tsoro" Ummi ta duba taga noor ta tafi kitchen, sannan ta ce "Babu abun da zai faru sai ikon Allah anty Maryam, kuma in sha Allah mama ta shigo gidan nan kenan, dr. Mutum ne managarci, kuma zan tsaya iya yi na hakan ya tabatta, babu wanda zai cutar mini da uwa, kuma da ba a aure ita ma da ba a aureta ba" "To ki dai ta yi musu Addu'a" "In sha Allah" Noor ta dawo falo da plate, da ƙaramar wayar ummi a hannunta ta ce "Yaya ummi, ga mutuniyarki indomie mai yaji da kifi, Yaya salim ne za su zo" Ummi ta kalleta ta ce "Wane Salim ɗin?" "Yayan MD mana" Cikin mamaki ta ce "Ya aka yi ki ka sani" Sai kuma ta ɗan diririce ta ce "Yaya raihan ne ya gaya mini" Ummi ta ce "Allah ya kawo su lafiya, me zamu girka musu?" Noor ta ce "Zan yi musu abinci, amma ki koma ɗaki ki kwanta, kar ki ce warin girkin zai saka ki amai" Ummi ta tashi tana murmushi ta ce "Yauwwa ta wajena, shiyasa nake son ki ummana, bari na je na yi wanka na kintsa kan su zo, kar su zo su same ni a haka, kalli kaina ko taza babu na fi kwana uku ban taje ba, MD jiya har ya jona hand dryer zai taje mini na ce bana so da zafi, ya ƙyale ni" Noor ta ce "Ohh, yaya ummi soyayya da daɗi ko? Ke ban da wannan abun da ya faru na ga yana sonki ba kwa faɗa, amma anty intee da wayona fa lokacin da mijinta Salim yake zuwa suke shan soyayya amma yanzu kullum cikin faɗa kamar abokiyar gabarsa" Ummi ta ce "Waye ya ce miki bama faɗa? Babu wata soyayya da za ayi zaman aure ace babu saɓani, sai dai danganta da yadda aka gina soyayyar, idan har ta gaskiya ce kuma an fahimci juna, ko saɓani yazo za a warware cikin sauƙi. Ni kaina MD ba dan yana sona ba, kuma mutum ne mai fahimta ba da laifukan da na yi masa a kwanakin nan wani zancen ake yi ba wannan ba, shiyasa ko mun samu saɓani nake duba alkhairnsa bana taɓa yi masa hukunci da laifin da ya yi mini". Noor ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ni wallahi soyayyar da ba a faɗa nake so, idan muka yi faɗa kuka zan yi" Ummi tayi dariya ta ce "Sai ki tafi littafi ko film, ko kuma tatsuniya, a nan zaki samu wadda ba a faɗan. Bari na shiga daga ciki" Noor ta yi shiru tana ta zancen zuci, ita har ga Allah ta fi son ayi ta soyayya babu faɗa. Ummi daga yin wanka ta ji sanyin Ac, ta kwanta ta hau bacci a ɗakinta. Noor ta zage tana ta gyara gidan, ta iya aiki sosai da sosai saboda zama da ummi. Ta gama aikin ta shiga ta yi wanka ta saka wata ƴar doguwar riga da ɗan kwali, ta dawo falo tana shan lemo mai sanyi. Ba ta daɗe da zama ba a ka buga ƙofar falon. Ta tashi ba tare da tambayar waye ba, ta buɗe ƙofar, kallonsa ta tsaya tana yi tana murmushi, hannunsa ɗauke da manyan kulolin abinci,  ta ce "Sai yanzu ko? To koma mun yafe" alama yayi mata da ido, ya tura ƙofar hajiya ta gani a bayansa. Da sauri noor ta nutsu, ta durƙusa tana gaishe ta, saboda ta shaidata, ta karɓi kayan hannunta suka ƙarasa cikin falon. Hajiya ta ce wa noor "Kamar na so na gane ki" Salim ya ce "Ƙanwar ummi ce" ya kalli ummi ya ce "Ga hajiya, in faɗa mata me ki ka ce a kan ta?" Noor ta kalleshi da sauri tana zare ido, ta girgiza masa kai. Hajiya ta kalleshi ta kalleta, ta ce "Laifi na yi mata?" Yayi murmushi ya ce "Hotonki ta gani a wayata, ta ce na sanki, na ce eh ƴar uwammu ce ke, wai ranar bikin su raihan tana ta kallonki, wai kwalliyar ki tayi kyau, gashi kin iya turanci, kina magana kina turanci, har gwada maganarta ki ka yi ko ba ayi ba?" Noor tamkar ta nutse a wurin nan, ta sunkuyar da kai tana hararsa ta ƙasan ido. Hajiya ta yi dariya ta ce "To ai da sauƙi tun da ba laifi na yi mata ba, ina ummin ne?" Duk da noor ta san ummi bacci take yi, ta tashi da sauri ta ce "bari na kirawo ta" har noor ta bar falon kallonta yake yi yana dariya. Hajiya ta ce "Wai ya aka yi har ku ka saba haka ne?" Ya gyara zamansa ya ce "Ina ganinta a nan gidan, sai kuma lokacin da aka samu matsalar nan na su raihan, da na je gidansu ita ta gaya mini. Ta wurinta na din ga samun information ɗin da na samu ummi a can garinsu. She's very funny ne kawai tana bani dariya. Hajiya ma ta yi murmushi, noor ta dawo falon amma ta laɓe ta bayan labule ta ce "Na duba bacci take yi" Ta gudu ta koma kitchen, ta haɗa musu ruwa da fruit, amma ta kasa fitowa tana jin kunya, sai a yanzu ta fuskanci hajiya mahaifiyar Salim ce dan suna kama sosai, saɓanin da ya ce mata ƴar uwarsu ce. Da ƙyar ta dawo falon tana sunkuyar da kai. Hajiya ta ce "Ya sunanki ne?" "Mariya, amma ana ce mini noor, maman ummi aka yi wa takwara aka saka mini sunanta" Hajiya ta ce "Masha Allah noor, kar ki damu da abun da ya faɗa rabu da shi, bari mu tafi ga abinci muka zo wa da ummi, na zo na ƙara duba jikinta" Noor ta ce "Dan Allah kar ku tafi, bari na tashe ta" Hajiya ta ce  "A'a ba sai kin taso ta ba" Muryar ummi suka ji tana cewa "Hajiya sannunku da zuwa, wallahi bacci ne ya kwashe ni" Hajiya suna can suna hira da ummi, Salim ya fita, noor ta bi bayansa. Yana tsaye yana waya ya ji muryarta ta ce "Allah ya kama ka" Ya waiwayo ya ce "Da na yi me?" "Ashe mamanku ce" Ya ce "A'a ƙanwar Alhaji ce" Noor ta ce "To wallahi mamanku ce, shi ne ka gaya mata abun da na ce, duk na ji kunya". Salim ya yi dariya ya ce "Last born" Ta ce "Ba wata last born, wallahi ka bani kunya sosai" Yayi dariya yana kallonta, ƴar ƙarama da ita sai baki. "Ka san me? Babanmu yayi aure fa, ya auri babar su yaya ummi, mamanmu sai fitina take yi a gida, ni kuwa na yi tahowata nan" Ya ce "Kin kyauta, ba kyau kallon manya idan sun samu saɓani" Kawai ta saka hannu a aljihun rigarsa, sai ga kwalin sigari. Ta ce "Ba ka daina ba ko? Ka ce mini fa ka daina" Ya haɗe rai ya ce "Meyasa ba ki da kunya ne? Dan kin ga ina yi miki dariya har ki ka saka hannu a aljihuna?" Noor ta ce "To ai ba kuɗi na ɗaukko ba, kuma ka ce mini ka daina" Hannu ya kai ya karɓa, ya mayar da kayarsa cikin aljihunsa, ya juya ya tafi. 3 MONTHS BACK Salim ya je gidan raihan, amma maigadi ya sanar masa raihan ya ce duk wanda ya zo ace masa baya nan. Ya tambayi maigadin dalili, ya ce bai sani ba, amma tun da hajiya bilki ta je, ummi ta tafi tana kuka da kayanta a hannu, amma bai san meyafaru ba. Tun daga nan jikinsa ya bashi akwai wani abu, da safe neehal za ta fita suka haɗu, ya tambayeta meyafaru a gidan raihan da mami ta je, ta ce masa ba komai, sai da ya zageta sannan ta gaya masa abun da ya faru. Da azahar ya wuce gidan su ummi  dan jin meyafaru, ya haɗu da noor a hanya za ta je makarantar islmaiyya . "Ke!" Yayi maganar yana sauke glass. Ta tsaya ta ce "Sunana mariya wato noor" tsyaawa yayi yana kallon ta ya ce "Kin gane ni?" "Eh, na ganeka ɗan uwan su yaya raihan" "Yauwwa, ummi na gida ne?" Ta ce "A'a tana gidanta" Ya buɗe motar ya ce "Ba ta can ki gaya mini gaskiya " Ta ce "Eh ta zo gida, mamanmu ta ce wai ba zata zauna ba, ba a san fa in da take ba, yaya raihan ya zo ana ta nemanta, sakinta fa yayi". Salim ya ce "Ina ta tafi yanzu?" "Gaskiya ba zan gaya maka ba, islamiyya fa zan tafi, kar na makara". Salim ya ce "Shigo mu tafi na kai ki islamiyyar " "A'a ni ba zan hau motar wanda ban sani ba" Ya ce "A'a ai ni kin sanni, yayan raihan ne ni" Ta ce "Bari na gaya maka dai, duk da ta ce kar na sake na gaya wa kowa, gagarwa ta tafi, can garinmu a jigawa, amma kar ka gayawa yaya raihan, ta ce kar na faɗa, jiya kan ta tafi ta gaya mini". Salim ya ce "Na gode sosai da ki ka gaya mini, daga gagarwan ina za a yi aje gidan" Ta wassafa masa komai, kwatancen gidan tun daga tasha, da yake ba ɓoyayye bane ba, ya yi wa noor godiya ya tafi. A yammacin ya tafi gagarawa, bai jira sai washegari ba, yayi sa'a ya tarar da ummi, kuma ta sanar masa duk abun da ya faru, da shawarar da ta yanke, ta kuma roƙe shi a kan dan Allah kar ya gayawa kowa in da take. Bayan wata guda, ya haɗu da noor ta je gidan yayar farida, a sharaɗa, shi kuma ya je wurin wani abokinsa. Suka gaisa, yake bugun cikinta ko an ga ummi, ta ce masa ba a ganta ba, ta nuna masa yadda take cikin damuwa, rashin sanin in da ummi take. Ta saki baki tayi ta bashi labarin zaman da ummi ta yi a gidansu, da yadda ake yi wa ummi gorin ta auri yaro ƙaninta. Ta ce "Yauwwa ka ce kai yayan yaya raihan ne, amma ba mamanku ɗaya ba ko?" Ya ce "Eh" "To wallahi in gaya maka mamansa ce ta saka ya saketa, ba ta sonta wai mummuna ce ta auri yaro, dan Allah ai auren yaro ba haramun bane ko? Kuma ai yaya raihan babba ne yana da gemu fa" Ya ce "Eh gaskiya ba laifi ba ne, in dai mutum yayi gemu ba yaro bane" Message ya shigo wayarsa, ta kalli lock screen ɗin sa, da hoton hajiya ne a kai, ta ce "Laa ka san wannan matar?" Ya amsa da "Eh, ƴar uwanmu ce" "Innalillahi, ta burgeni lokacin bikinsu yaya ummi, ta iya wanka, gashi ta iya turanci" Yayi dariya ya ce "Gaskiya ne" Noor ta ce "Wallahi duk ƙarfin hali nake yi, rashin yaya ummi har kuka nake yi, rayuwarsu tayi ta bani sha'awa da MD ba sa faɗa, amma kawai ya saketa na zata auren saurayi ya fi daɗi, amma na fasa" "Tsoho zaki aura kenan? Ai shi ma yana sonta ba laifinsa ba ne" Ta ce "A'a ba tsoho nake so ba, me dai gemu kamar naka, wai dan Allah da ka je gagarawa ba ka ga yaya ummi ba?" Abun da ta faɗa na farko ya bashi dariya, ya ce "Da na ganta ai da na gaya miki, amma me zaki bani na nemo miki ita?" Noor ta ce "To ai bani da kuɗi" Ya ce "Ba kuɗi zaki bani ba, zan gaya miki amma sai na nemo miki ita" Tun daga ranar suka saba da Salim, lokaci-lokaci ya kan bi unguwarsu, dan ya ganta, saboda yana son surutunta. A haka ta gane yana shan sigari, tayi ta masa mita, ya ce idan ya nemo mata ummi, zai daina sha. Haka nan yake jin daɗin mu'amalarsa da ƴar yarinyar da da yayi auren wurin zai haifeta. CIGABAN LABARI. Hajiya sun daɗe tare da ummi, kuma ummi ta samu ta ci abincin da hajiya ta kawo mata sosai ta ƙoshi, kuma Allah ya taimaketa ba ta yi amansa ba. Bayan tafiyar Hajiya, Dr. Ya kira ummi a waya, bayan sun gaisa ya ce "Noor tana gidanki ko?" Ta ce "Eh kawu" "Na san ta riga ta gaya miki komai ma,  bayan mun zo gidanki mun yi wannan maganar, na yanke shawarar yin abun cikin gaggawa, saboda kar wani abun ya kutso ya hana. Na kira baban maiduguri, muka yi magana da shi, da na tabattar da ya amince, kawai da muka je jiya, na tafi da sadaki aka ɗaura, dan hatta ƴan gagarawa ba su sani ba, sai da aka ɗaura na san za a iya samun matsala ko daga gare su ko wani ɓangaren. Nan da sati ɗaya idan komai na ta ya zama ready, zan ɗaukkota ta yi miki kwana ɗaya ko biyu sai mu wuce". Ummi bakinta ya kasa rufuwa, ta ce "Alhamdilillah ala kulli halin, Allah ya cigaba da faranta maka kamar yadda ka ke yi mana kawu, Allah ya saka da alkhairi na gode sosai da sosai" Dr. Ya ce "Ba komai ummi, yi wa kai ne". Can Maiduguri kuwa, mariya na zaune ta yi shiru tayi zurfi a tunani, mama ta ce "Mariya, wai menene? Ko abincinki fa baki taɓa ba" Ta yi ajiyar zuciya ta ce "Wallahi mama tunani nake kawai" "Tunanin me?" "Auren nan mana, ni fa banda baba ya matsa ba zan yi wani aure ba, ido ya mutu kwalli ba zai farfaɗo da shi ba, kuma idan ina tuna wahalar da na sha a hannun iya, ko a mafarki bana fatan sake yin aure" "Ashsha, mariya ba a fitar da rai da rahamar Ubangiji, kuma ke ba tsohuwa ba, haryanzu da sauranki, babu wanda zai ce kin haifi ummi, gashi albarkaci auren har jirgi zaki hau" ta ƙarasa maganar cikin zolaya. Mariya dai ta rausayar da kai ta ce "Wallahi mama ba na ƙaunar abun da zai sake haɗa ni da iya, auren nan ya sake mayar da ni jikin su" Mama ta girgiza mata kai ta ce "Akwai banbanci, tsakanin Bashir da Yahaya, Kuma ai ba wuri ɗaya zaku zauna ba" mama tayi ta lallaɓata tana kwantar mata da hankali. Can gidan dr. Kuwa Farida kamar za ta kama dr. Ta daka, saboda azabar kishi da bala'i, sai dai fafur ya mayar da ita kamar mahaukaciya ya ƙi saurarenta. Yanzu da safe Abdul ya kawo kai zai shigo falo, ya ji yo muryarta tana ta ɓaɓatu, tare da amfani da kausasan malamai wurin ci masa mutunci. Dr. Ya fito ya fice, ba tare da ya ce mata uffan ba, Kausar na ta ba ta haƙuri, Abdul ya shigo rai a ɓace ya kalli farida ya ce "Maama wannan abun da ki ke yi ba mutuncinki bane ba, duk maƙwabta na jinki, wannan zubar mana da mutunci ki ke yi" "Haba yaya Abdul, ka san menene kishiya kuwa? Kuma kishiya da mahaukaciya ku baku san komai a kan wannan lamarin ba" Farida ta ce "Rabu da shi, baƙin ciki ya kasheni, sai su ci duniya da tsinke da ubansa, bands butulci da zalunci irin na ɗan Adam, duk halaccin da na yi masa ya rasa da mai zai saka mini sai wannan rashin mutuncin, maimakon ya auro cikakkiyar mace da zan yi kishin na gaske da ita, sai ya ƙare a mahaukaciya, ai da ƴar tata ya aura shi ne ƙarshen soyayya" Abdul ya ce "Koma wa ya auro, hakan dai zaki yi maama, wallahi Abba ba ma bin sa bashi, shi ne yake bin mu, menene bai yi mana ba na kulawa a rayuwar nan, shekara sama da ashirin yana ƙarar da ƙarfin sa saboda mu, kuma lokaci ɗaya duk sai mu haɗu mu goya miki baya mu rabu da shi? Bamu yi masa adalci ba, kuma wataƙila da baki kori ummi ba, da bai ce zai ƙara auren ba". Muguwar ashariyar da ta luluƙa masa ya sanya shi waro ido, ba shiri ya fice ya bar su da kausar. Ta kalli kausari ta ce "Ki shirya ki je gidan ta, ki dawo mini da ƴa ta, idan ta ƙi ki ci uban noor ɗin, tun da ba mahaukaciyar uwarta ce ta haifeta ba, sannan ki tabattar kin ci mata mutunci da sai ta zubar da hawaye" Kausar ta ce "Zan yi, amma dan Allah ki kwantar da hankalinki, kin ga fa yadda ki ke haki" gaba ɗaya farida sai ta fi kama da mahaukaciyar tuburan. Noor kuwa ta miƙe abun ta a gidan ummi, ummi ta fara samun sauƙin wasu abubuwan saboda noor, ita take bata kuɗin motar zuwa makaranta boko da islamiyya. Ummi ta ce mata yakamata ta biya gida, su gaisa da su farida, amma ta ce ita ba ta son ta je gidan ta tarar da su Abba suna faɗa. Ɓangaren mami ma abubuwa sun yi mata zafi sosai, dan haryanzu Alhaji fushi yake yi da ita, ga ɓangaren su safiyya sun hura mata wuta, dan zuba ido suke yi, a danƙaro musu kayan lefe. Sai dai zancen nema yake yi ya shiririce, dan Alhaji ma ya ce kar ta sake yi masa maganar auren raihan, shi na fari da ya yi masa, shi ne hurumin sa. Kuma sanin halinta ya sanya yayi mata gargaɗi na gaske, a kan gidan da raihan ya saya wa ummi. Kausar kuwa da ta je gidan ummi, hankali kwance ta tarar da su har da raihan suna kallo, babu abun da ya dame su. Sai duk ta kasa sakewa ta yi rashin mutuncin da ta ƙullo, duba da yadda raihan yake muzurai. Hankali kwance ummi ta karɓeta, ta karrama ta. Ta ce "Dama maama ce ta ce noor ta koma gida" Raihan ya ce "Saboda me?" "Haka dai ta ce" Raihan ya ce "To ai ni mun yi magana da dr. Ya ce tayi zamanta, ta din ga zuwa makaranta daga nan, amma noor kin ji abun da mamanki ta ce" Noor ta tura baki ta ce "Ni na tambayi Abba ya ce na zauna, zan koma amma ba yau ba" juyin duniya, noor ta ce ba in da za ta je, ita fa maama ba son ta take yi ba, dan kullum cikin yi mata faɗa take da zaginta. GAGARWA. "Kai auwalu, daga kai har Alhassan kun kashe zuciyarku, kalli yadda rana ta take, sai baccin asara ka ke yi ba zaka tashi ba?" Tayi maganar tana dukan ƙofar ɗakinsa. Amma ya ƙi tashi, ta gama ɓaɓatunta yayi burus da ita, ta ƙyale shi, ta koma sashinta, ta ɗebi ruwa tana alwala. Ta ɗago za ta tashi, ta ji an yi ball da ita gaba, ta dungura. Cikin tangaɗi da maye, ya ce "Ke banzar tsohuwa, ban gaya miki babu ruwanki da ni ba? Ko in tashi ko kar in tashi ban hana ki shiga harkata ba" Iya da ƙyar ta motsa, wani irin jiri ya din ga ɗibar ta, taga gari yana jujjuya mata. Kan ta ankara, ya sake surarta yayi jifa da ita kamar tsummokara. Ta kurma uban ihu, amma ba kowa, ya din ga jifa da ita, tun tana ihu, ta koma kakari, jini ya fara zuba daga hancinta. Ya sake surarta yana tangaɗi ya nufi wawakekiyar rijiyar da ke tsakar gidan. Ayshercool PAID ADVERT!. Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi. Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku Oll types of Turaran wuta Sandal Halut Irik Difur Gab Gab Kajiji Habil Nabak Humra Kulakcha Dilke da kalta Kayan Garan jiki Muna turara Kaya Kujerar garan jiki Kannada Madarorin turare masu kamshi  Man garan gashi  Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702   08025453921 *TALLA!TALLA!TALLA!* *INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*. *BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU* *MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA* BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI. CUTARWA! AYSHERCOOL (BRIGHT PENS) MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g 47 PAID ADVERT *Hajiya ina zaki? Saurin me ki ke yi haka? Ɗan bani aron mintuna biyu kacal, na gaya miki albishir ɗin da na zo miki da shi. Shin ko kin san sirrin sheƙin fatar ummi, da ya sanya ta kama zuciyar MD raihan ta hana shi sukuni? Kai ba ma skin care ba, har da sirrin gyaran gashi, ina masu fama da amosani, karyewar gashi ko kuma sanƙo, jan gashi ne da ke? Ko taurin gashi kamar soson ƙarfe. Idan matsalar ki budurwar fata, tare da rashin glowing, Annur skin scrub da hair bliss sun shirya tsaf domin magance muku kukanku, me ku ke jira ku tuntuɓe su a kan lambar wayar su dan ƙarin bayani 07045971194 ko 08140450950* 47 Gadan-gadan ya nufi rijiyar yana tangaɗi. Amaryar kawu Ilyasu ta ƙwala ihu da salati, bayan ta shigo daga cefane. Bai kai ga rijiyar ba, ya sake yin jifa da ita. Ta tafi da gudu tana kiran sunan iya, sai dai jini sai zuba yake daga hancinta. Auwwalu kuwa cikin maye yake ta masifa "Sai da na gaya mata ba ruwanta da ni, amma taƙi ji, dama a ƙule nake da ita ta zagi babarmu jiya, duk ta tsane ni saboda bana ba ta kuɗi, ina kallo har kazata ta mara dan tana jin haushina, wallahi wiwina ta fiye mini wannan tsohuwar banzar" yana gama maganar ya juya yana tangaɗi ya fice. Da gudu amarya ta fita tana kururwar neman agaji, mutanen gidan suka fara shigowa, Iya na kwance ko motsi ba ta iya yi. Da ƙyar aka samo abun hawa, aka tafi da ita asibiti, daga can asibitin suka ce sai dai su je babban asibiti, ba zasu iya dubata ba. *** Can garin kanon dabo kuwa, ummi kamar ta taka rawa, saboda ranar dr. Zai ɗaukko mata mama daga Maiduguri, ita da noor sai aiki suke yi, ummi cikinta ya fito sosai ganin tudunsa a rigarta. Dr. Kuwa tun sassafe ya tafi maiduguri, domin ɗaukko mariya, da shi da abokinsa. Can Maidugurin ma, an shirya musu kayan abinci, an yi wa mariya lalle, ta sha gyaran jiki kai ba ka ce ta haifi ummi ba, ana gobe dr. Zai je suka ɗan gayyaci mutane da ƴan uwa aka yi walima a can maidugurin. Anty maryam ta kalli mariya ta ce "Wai duk murnar ganin angon ce haka? Bakinki ya ƙi rufuwa" Ta ce "Haba Anty Maryam, kin saka na ji kunya, kawai zan ga ummina ne, nake ta jin daɗi" "Kai mariya, ke sam ba ki da alkunya,  ƴar fari ce fa" Ta ɗan rausayar da kai ta ce "Shekarar mu nawa ba ma tare, sai in din ga jin tamkar ta koma ƴar karamarta, ƴar baƙar ƴa ta mai kyau, na gyara duk wasu abubuwa marasa kyau da suka faru da rayuwar ƴa ta, wallahi anty maryam haryanzu ina jin tausayin ummi, rayuwar da ta yi ya kasa zama tarihi a wurina, kuma zuwan da ta yi na ƙarshen nan, kamar akwai wata damuwa da take ɓoyewa, fatana Allah ya sa ba wata matsalar ce a gidan auren nata ba, Allah ya sa ta daina shan wahala" kan ta kai maganar gaba ɗaya hawaye ya wanke mata fuska. Mama ta ce "Mariya, ba zaki daina ɗorawa ranki damuwar abun da ya wuce ba ko? Ga bawan Allahn nam sun zo, ai sai su zata ko son shi ne ba kya yi" Sallama dr. Yayi tare da abokinsa, suka amsa suna yi masa sannu da zuwa. Suka shiga ɗakin da aka saba saukarsu, ya kalli maman ummi, ya tuna maganar Farida, ta yi shar da ita, sai dai yayi mamaki ganin tana kuka. Ya kalli mama ya ce "Mama lafiya kuwa take kuka?" Anty maryam ta ce "Daga yin zancen ummi, ta hau kuka ta ƙi ta bar abu ya wuce, kullum ta tuna rayuwar ummi sai ta yi kuka, abu ya riga ya zama tarihi" Mariya ta ce "Anty Maryam, tun tana kan cinya fa, aka ƙwace mini ita, kuma fa itakaɗai ce da ni" Mama ta ce "To da mutuwa ta yi ya zaki yi?" Da sauri ta ce "A'a ummi ba zata mutu ba, babanta ya mutu, ƙaninta ya mutu, idan ta mutu ya zan yi?" Dr. Ya fuskanci jikinta haryanzu da saura, kuma tuna rayuwar ummi, ke saka jikin ya motsa mafi akasari, dan haka ya ce "Shikenan ya isa haka, ke da zaki koma kano ma, duk lokacin da ki ke so zaki ganta, ku koma kusa da juna" Kamar ƙaramar yarinya take goge hawayenta ta ce "Ni sonake ta koma ƴar ƙarama kamar lokacin da iya ta ƙwace mini ita, in din ga goyata, idan na yi mata wanka na yi mata kwalliya, amma kawai iya ta ƙwace mini ita, ga zafin mutuwar mijina" Ya ɗan ƙura mata ido, ba a ƙasa ummi ta ɗaukko shagwaɓa ba, duk da ummi ta ninka mariya shagwaɓa nesa ba kusa ba. Ya kalli su Anty Maryam ya ce su ɗan basu wuri. Bayan sun fita ya matsa gabanta ya ce "Haba maman ummi, idan mijinki ya mutu yanzu ba gani ba". Ta kalleshi ta ce "Kai ba bashir bane, yaya yahaya ne, ba na so kai ma iya ta ce na kashe ka, wai iya ta ce ni na kashe baban ummi, ya za ayi na kashe shi?" Tayi maganar hawaye na cigaba da zuba. "Ki manta da maganar iya, yakamata ace memorynki, yana tuna abubuwa masu daɗi, idan baby ki ke so ki yi addu'a Allah ya kawo miki ƙannen ummi, ki yi ta goyawa ita yanzu ummi tana da mai goyata" Ta ɗan yi shiru kamar wadda ta farka daga bacci ta ce "Kai, ummi fa ta yi aure, kuma nima sai na haihu?" Yayi murmushi, ganin kamar tunaninta ya dawo. Ya ce "Idan ki ka cigaba da kuka, da tuna abun da ya wuce, ba zan tafi da ke ki ganta ba". Haka yayi ta rarrashin ta, dama tuni su mama sun haɗa mata kayanta, suka raka su har mota, suka kama hanyar kano. Gidan ummi, bayan sun gama aiki, noor ta ɗauki wayar ummi ta tafi ɗaki tana game. Ummi kuma na falo tana kallo, sai ga Farida ta zo gidan, gidan da tun da ummi tayi aure, kusan shekara ba ta taɓa takowa ba. Sai dai duk yadda ake kwatanta mata haɗuwar gidan ummi, sai yanzu ta tabattar da idonta ya gane mata. Kamar babu komai ummi ta tashi cikin fara'a, kamar babu wani abu a ƙasa tana "Oyoyo, yau na yi babbar baƙuwa, sannu da zuwa anty" wani irin mugun kallo take yi wa ummi, da mamakin iskanci ne ko rainin hankali ya sa take wannan washe mata bakin. "Ke saurara bana son karuwanci da iskanci, ni zaki yi wa bariki kina wani washe baki kamar bakin buhu?" Ummi ta shafa bakinta, a iya saninta dai ba ta da ƙaton baki, ji ta yi kamar ta yi dariya amma ta maze ta ce "Ai baƙonka annabinka anty, kuma akwai hadisin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam, da yake cewa wanda yayi imani da Allah da ranar lahira, ya girmama baƙonsa. Ki zauna bari na kawo miki ruwa". "Ki yi mini shiru ko na ɓarar da ke, ba ki da abun da zaki bani, ke da aka kawo mini ke cikin dauɗa da ƙazanta babu ko suturar kirki, har ke ki ke da abin bani, dan kin auri mai kuɗin da uwarsa ba ƙaunarki take yi ba, auren abun kunya, auren yaro ƙarami? Butulallaiya mara mutunci, wato abun da ki ka yi wa wancan ƴan ƙauyen shi ne nima ya biyo ta kaina, ki ka saka dr. Ya auri babarki, mahaukaciya da ba ta san ciwon kanta ba?" Ummi ta ce "A'a fa, ni ban bayar da shawarar hakan ba, dr. Ya zo mini da maganar na goyi bayansa ɗari bisa ɗari, ko ba komai na yi ramuwar gayya, kuma ba fata ba ko aurena ne ya mutu, ko wani abu ya faru ina da wurin zuwa. Da ki ke iƙirarin an kawo ni cikin dauɗa da ƙazanta, ai ba ke ki ka kula da ni ba, wan ubana ne, dan haka ke bai kamata a ji wannan gorin daga bakinki ba, ba ki isa ki yi mini gori ba a kan wannan, ko kin manta irin riƙon da ki ka yi mini?" Ummi ta ɗaga rigarta, gefen cibiyarta ya ɗan yi shati, ta ce "Na san wataƙila ke kin manta, kuma an yi sa'a jikina ba ya riƙe tabo, wannan ne kawai yayi saura kuma da shi zan koma ga Allah, har azaba da wuta ku ka yi mini ke da ƙanwar ki, wallahi da ramuwar gayya zan yi a kan ki, sai kin bar gidan dr. Kuma Alhamdilillah a yanzu dai Allah ya yi mini sutura da rufin asirin da ba kwa so, kuma wallahi ni Salma ina da abun da zan baki. Amma ba wannan ba, na zata bayan na yi aure komai zai wuce, na yafe komai ya wuce, amma na fuskanci hali zanen duste ne, ba zaki canza ba, tun bayan da ki ka yi mini korar kare da na je gida aurena ya samu matsala, dan haka mun saka ƙafar wando ɗaya da ke, za ki ga mahaukaciya ganin idonki, yadda na ke shimfiɗa mulkina ba boka ba malam a gidan mijina, sai uwata mahaukaciya ta shimfiɗa na ta mulkin ba yadda ki ka iya, zaɓi ya rage naki, ko ki kwantar da hankalinki ku zauna lafiya, ko kuma ki shirya yin fito na fito da ni, tsakanina da ke babu ɗaga ƙafa, kuma ki gaya wa rahama, idan har muna raye sai Allah ya jarabceta da wuta, kamar yadda ku ka yi mini azaba da iata, dan wallahi ban yafe ba! Ko zan yafe muku komai, banda wannan" Tirƙashi! Ummi ta shayar da farida ruwan mamaki, gani take kamar daga wani wurin maganar ke fitowa ba bakin ummi ba. Cikin dakiya farida ta ce "Yaushe aka yi daren, da har gari zai waye, ki ke iƙirarin shimfiɗa mulki a gidan miji? Ɗa namiji ne fa da bashi da tabbas". Ummi ta yi murmushi ta ce "Anty farida, ai daren yayi tsayi, ke ce ba ki farga ba, sai da garin ya waye. Duk da kina iƙirarin uwata ba ta da hankali, amma a hakan ta din ga yi mini nasihar, jin tsoron Allah, riƙe addu'a da biyayya a aure, idan har tsoron Allah, addu'a da yi wa miji biyayya na saka a ci ribar aure, da yardar Allah ni da uwata mun fi ƙarfin masu bin ƴan tsubbu, kuma zamu zauna dai-dai a gidan miji, namiji ba shi da tabbas, ya danganta da yadda ki ka ɗauke shi ne, nawa yana da tabbas, haka babana dr., Ke ce baki iya tattalinsa ba ki ke ganin ƴan tsubbu sun mallake miki shi, shiyasa ki ka ga bashi da tabbas". Farida ta saki baki, hangal tana kallon ummi, ba ta gama mamakin ba ummi ta ce  "Yauwwa tun da bani da abun baki, zaki iya tafiya, na ga kin yi mini aike noor ta koma, in dai noor ce, sai dr. Ya ɗauke ta ya ba wa mamana, saboda kin raini ƴar ki da ƙiyayyarki, saboda banzan dalilinki, na an saka mata sunan mahaifiyata, duk shaƙuwar ɗa da uwa, ta fi son babanta a kanki, cikin sauƙi zan sanya ya karɓe ta ya bawa mama ita, ba zan so ta tashi da rashin imani irin naki da su kausar ba, masu baƙar zuciya ba, tayi aure tana hali irin naki ba, idan kin fita ki rufe mini ƙofar falo, kar ƙuda ya shigo mini bana son ƙuda" ko jiran amsar farida ba ta jira ba, ta bar falon ta bi wata hanyar, ta tafi can bedroom ɗin da noor take, wadda ba ta san ma farida ta zo ba. Ƙarfe huɗun yamma, dr. Ya sauka, basu tsaya ko ina ba sai gidan raihan, ta rungume ummi suka din ga murna, kamar sun shekara ba su ga juna ba. Sam farida ba ta san ranar ma maiduguri ya je ba, yana komawa gida, ta dira masa bala'i tana gaya masa abun da ummi ta yi mata. Kai tsaye ya ce ƙarya take yi wa ummi, sharrinta ne kawai ummi ba zata aikata haka ba, tsabar kishi ne kawai, idam ma hakan ne meyasa da ba ta je gidan ummi ba sai yanzu da wannan lamarin ya zo. Abun duniya duk ya ishi farida, asirin tayi har ta gaji, ya shammaceta, da kan ayi ne da ta yi yaƙinin asirin zai kama shi, maganar ta rushe. Raihan ma ba ƙaramin daɗin zuwan mariya ya ji ba, tayi ƙalau da ita. Noor kuwa tun bikin ummi da suka je maiduguri, suka saba da mama, tun da dr. Ya gaya mata takwararta ce. Kuma aka yi sa'a ba ta manta ta ba, a ranar da daddare, sai ga Salim ya zo har da Sagir. Mariya ta din ga murna, duk idan tana magana wasu lokutan ta kan haɗa da shirme, amma a hakan take yi musu nasiha, tare da ƙara musu haske a kan rayuwa. Sagir ya din ga mamaki da aka ce ita ce maman ummi, ita da haskenta ma, ummi ce dai baƙa, sai dai idan tayi wani abun kamar ummin. Ta tsiro da batun cewa lallai, a kai ta su gaisa da babar raihan, da babansa sun gaisa da Alhaji, babar raihan ce ba su taɓa haɗuwa ba. Gaban raihan ya faɗi, amma ya basar ya ce zai kaita su gaisa. Su Salim sun daɗe sosai, duk da a zahiri bayan mama, noor ce ta riƙe shi, dan chatting suke a wayar ummi ba ta sani ba, idan suka gama sai ta goge. Ummi ta yi iya ƙoƙarinta, ta mantar da mariya, batun haɗuwa da babar raihan. Allah ya taimaki Iya, ba ta samu mumunan rauni ba, sai dai ta fasa kai, fuskarta duk ta ƙuje, sannan ta targaɗe ƙashin ƙafarta, da hannunta, gashi kuma kanta sai da aka yi mata ɗinki, kan ayi ɗinkin nan kuwa sai da aka sauke gashin kan gaba ɗaya, ga bakinta ya kumbura saboda wahala. Da ƙyar suka yi karo-karon haɗa kuɗin magani, likita ya rubuta hoton ƙwaƙwalwa, saboda kai da take ta kuka da shi, amma babu kuɗin yi, maganin ma ba duka suka saya ba. Suna tsaka da wannan gaganiyar, ana ƙoƙarin kiran dr. Suka samu labarin yayi aure, ya auri mariya. Gaba ɗaya sai suka manta da halin da iya take ciki, suka shiga salallami. Iya na daga kwance ta tuna yadda tun bayan ya gano in da mariya take, ya ce zai aureta, amma ta ce ba ta lamunta ba, tun da ya riƙe ummi shikenan, ba zai sake kwasota ya kawo musu dangi ba, saboda a cewarta mariya annoba ce, mugun abun ta ne ya sanya ta haukace. Su ummi suna airport, tare da dr., Ta wani ɓangaren ransa a ɓace, saboda tijarar da ya sha a wurin farida daren jiya, da ya ce yau zai koma uganda, tare da babar ummi. Har da zaginsa ta ƙare masa cin mutunci, abubuwa da dama yana duba yaransu ne ya sanya yake ɗaga mata ƙafa, kuma tun ainihi, shi mutum ne mai sanyi ba shi da hayaniya, shiyasa take yi masa duk abun da ta ga dama. Suna airport sun rako su dr. Mariya sai kalle-kalle take yi, da alama a tsorace take. Sai ga wayar kawu Sagir, dr. Ya ɗaga tare da amsa masa sallamar. "Yanzu yahaya tsakaninmu da kai abun har ya kai haka? Muna ƴan uwanka amma sai dai mu ji a gari ka yi aure? Abokanka sun fi mu kenan?" Dr. Ya ce "Ba abun ɗaga hankali bane ba, abun ne ya zo ba shiri, na ga akwai buƙatar tun ina raye ya zamana ummi tana da madogara ko bayan raina, dan yadda ba a kula da ita bayan ran mahaifinta ba, bayan raina ma ba za ta sauya zani ba, dan na san kun san wadda na aura, kuma da na neme ku, ba zaku bari ba, da kaina zan zo har gida na yi muku bayanu" "Aishikenan, ni ba ma wannan ba, ka ganmu fa a asibiti da iya" "Subhanallah me ya same ta?" "Wallahi dai tsautsayi ne, Auwwalu ne ya sha ta gaya masa ƙarya, ta yi masa faɗan rashin sana'a sai bacci, ya din ga tamaula da ita, saura ƙiris ya jefa ta a rijiya. Yanzu dai gamu a asibiti, magunguna an sayi wasu, wasu kuma ba a saya ba, ga hoton kai an rubuta shi ma ba kuɗin" Dr. Ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ka ga illar rashin mayar da hankali a kan tarbiyyar yara da iliminsu ko? Ina Auwwalun yake?" "Ya gudu ba a san in da yake ba". "To ka ga ni yanzu ina filin jirgin sama, zan koma makaranta, zan turawa Abdul kuɗi ya zo ya dubata ya baku, Ubangiji Allah ya sauwwaƙe" "Amin, amma dan Allah yayi sauri ana buƙatar kuɗin" Dr. Ya ce "Sai ya tura muku, idan ya so daga baya sai ya zo ya dubata" Kawu Sagir ya ce "To hakan ma yayi, bari na ga Idris yana da lambar banki, sai a turo ya saka kuɗin, an gode" bayan dr. Ya gama wayar suka din ga jajantawa, mariya kuwa ko Allah ya kyauta ba ta ce ba. Ummi har da hawayen murna, ganin mama tare da dr. Za su keta hazo tare, ko ba komai tana sanyawa mama ran samun kulawa daga dr. Kasancewarsa jajirtaccen mutum. A ranta ta ce "So so ne, amma son kai ya fi, in sha Allah a kujerun hajji da umaran da Alhaji yake rabawa sai kun samu, ko ban je ba ku je a tare hakan nan, ku yi mini Addu'a. Bayan jirginsu ya ɗaga, suka koma gida. A cikin jirgin ƙanƙame dr. Ta yi, saboda gani take kamar za su faɗo daga cikin jirgin. Dariya ya din ga yi mata, ganin yadda take a rikice gaba ɗaya, hakan ya bashi damar rungumeta a jikinsa, sai wani irin daddaɗan ƙamshi take yi. A hankali take tambayar sa "Baban ummi ba zamu faɗo ba kuwa? Tsoro nake ji sosai" "In sha Allah ba zamu faɗo ba, lafiya zamu sauka". Dr. Dubu hamsin ya turawa Abdul, ya ce masa ya tura wa su iya idan sun turo account number, shima ya ƙara dubu talatin ya tura musu dubu tamanin. Ummi bayan sun koma gida, raihan ne ya sakata a gaba, yana mammatsa mata jikinta a hankali cikin tsantsar soyayya da kulawa yake ce mata "Am sorry sweetheart, kwanan nan am very busy, kamar bana kula da ke sosai, kuma na san kina buƙatata" Tayi murmushi ta ce "Saboda jin daɗi yayi mini yawa ko? A cikin mata hamsin nawa ne suke samun kulawar da nake samu, idan suna da juna biyu, kana iya yinka aiki ne yayi maka yawa". Ya numfasa ya ce "Duk da haka dai, wallahi ummi wasu lokutan kaina kamar ya fashe, ina jinjinawa Alhaji yayi ƙoƙari, kin ga yakamata ace Yaya salim yana cikin system ɗin nan, tun da bamu muka tara dukiyar ba, mu kula mu tattalata ta haɓaka, ga branch ɗin mu na Abuja, ina ga a watan da zaki haihu za a buɗe shi, ban san ma ya zan yi ba, wa za a mayar can Abujan, atleast yakamata ace da wani daga cikin mu" Ummi ta ce "Mhmm ka lura zuwan yaya Salim gidan nan ya ƙaru sosai?" Ya jinjina kai ya ce "Magana ce kawai ban yi ba" "Anya nan gaba magana ba zata taso tsakanin sa da noor ba, shaƙuwarsu ta yi yawa" Cikin murna raihan ya ce "Wallahi sam ban kula ba, tun da ya ce ke ƙanwarsa ce na zata saboda ke ne, yana cigaba da bibiyata ne kar na yi miki wani abu. Amma kina ganin dr. Zai bashi ita? Kamar yayi mata tsufa kuma ga yanayin sa" Ummi ta ce 'Aikuwa yaya Salim ya shiryu, a kan lokacin da na san shi, ba abun da zai hana ya bashi ita, nima haka aka yi mini surtu da na aureka, in dai suna son juna ba shikenan ba" Ya jinjina kai ya ce "To Allah ya tabattar mana da alkhairi, Kairun nisa'i, wannan cikin naki kamar ya fi ƙarfin watanninsa, kafin mu koma awo, sai mu je ayi miki scanic kawai mu tafi da shi" Ummi ta shafa cikin ta ce "Nima na gani, kamar girman yayi yawa a wata biyar, amma sai a sake hoton" Sun jima suna hirarsu cikin nishadi, har ta nemi izininsa a kan zuwa duba Iya, an kai ruwa rana kan ya amince, ta ce idan Abdul zai tafi sai ta bishi ita da noor. Ummi tun bayan dawowarta, ta duƙufa Addu'a, da roƙon Allah ya sassauta mata mugun kishin da yake damunta. Babu dare ba rana, ta miƙe da yawan tasbihi da bayar da sadaka, tare da tawasalli da ayyukan alkhairin ta, tana roƙon Allah idan auren Raihan da alkhairi Allah ya tabattar ya rage mata kishi, idan babu kuma, Allah ya rusa abun, ya musanya da mafi alkhairi, yayi mata maganin duk wani abu da zai tayar mata da hankali, ko kawo cikas ga rayuwar aurenta. Sannan ta tsananta addu'a, a kan Allah ya ƙara qa raihan son ta, da ƙaunarta ita kuma Allah ya bata ikon yi masa biyayya. A hankali ta ji zafin kishin yana raguwa, bayan auren mamanta da dr. Ta din ga istigfari a kan ɗagawa raihan hankali a kan maganar auren sa, wataƙila da ta cigaba da matsawa, da ba ayi na mamanta ba. Lokaci ɗaya mami ta daina kira tana ɗagawa raihan hankali a kan auren nan a gabanta, kuma ta daina zuwa ci mata mutunci, dama tuni ta saka lambar maryam a blacklist. Gidansu raihan kuwa, rana tsaka babu notice, Hajiya Aisha ta dira a gidan Alhaji Tahir. Sai da yayi mamkin ganinta, ya ce "Ke hajjaju, zuwa ba sanarwa matan gidan babu wanda ya sanar mini zaki zo ai". "Ina na ga ta tsayawa jiran notice, ashe raihan zai ƙara aure, kuma daga ɓangaren uwarsa, haba Tahir, kuma kana kallo, yaushe yayi auren farin zaku ɗora masa ɗawainiyar auren matan biyu?" Alhaji ya ce "Ke daɗina da ke, ba kya ɗaukar abu da sauƙi a kan raihan, babarsa ce take son ya ƙara" "A'a ban lamunta ba, yanzun ma ba dan Salim ya gaya mini ba, ba zan sani ba kenan? Kuma a rasa wa zai aura sai wannan dangin masifa da bala'in, ashe har ƙarya yayi muku bashi da lafiya dan ku ƙyale shi, amma abu kamar bala'i, kuma saboda tumasanci irin na bilki har da sakawa ya saki ƴar mutane, to mu ba haka muke ba, ko da muka yi bore da ka aure ta, ka juyawa ƴar mu baya, bamu ce ka saketa ba, dan haka da kaina na zo na yi wa tufkar hanci, ba zai auri ƴar rakiyar ba". Alhaji ya ce "Ke ki daina yi mini faɗa kamar wani ɗanki mana, har kuɗi fa an kai". "Amma ai ya ce ba ya so, dole na yi maka faɗa, ba fa kowane lokaci yakamata ka din ga biye wa matanka da yaranka suna abun da suke so ba. Wallahi muddin ta ce sai yayi auren nan, sai dai ta nema masa wata sana'ar ta kafa shi, ya bar shugabancin kasuwancin ka, dan na san da shi take taƙama, idan ba zaka iya cewa an fasa ba, zan je na yi wa ita rakiyar magana, dama ni da ita kar ta san kar ne ai. Su riƙe kuɗin an bar musu, amma ƙara aure ba yanzu ba". Tana tsaka da masifar, Hajiya ta kawo mata abinci, ita ma ta rufeta da faɗa a kan, meyasa ba a gaya mata abun da yake faruwa ba, dan haka ta je ta kirawo mata bilki, kuma a kirawo mata Salim, dan ta tabattar mata shi ya gaya mata ba Raihan ba. Aikuwa ranar mami ta ga ta kanta, dan cin mutuncin da hajiya Aisha ta yi mata sai da ta yi kuka, sannan ta ɗora da cewa "Ke ma ki ji idan da daɗi abun da ki ke yi wa taki sirikar, saura maryam dan ubanta, zan iya wanke ƙafa na je har fatakol ɗin, ba a barikin soja ba, idan a cikin bindiga take na je na ci ubanta a kan matar raihan. Raihan ɗin sai ka ce wani ɗan gwal da ake ta wannan tsiyar a kansa, ita ba uwa ce tayi naƙuda ta haifeta ba? Da ki ke mata iƙrarin munin ke halitta ki ke yi, da hancinki kamar pipe ɗin ruwa. Mu danginmu bamu sabawa yi wa sirikai rashin daraja ba, dan haka ba zaki fara ba. Tun wuri ki samu rakiyar ki yi mata bayani, idan kuma ki ka bari na yi mata abun ba zai yi muku daɗi ba". Duk da haka sai da suka yi faɗa da Alhaji, yayi mata ƙorafin za ta mayar da su ƙanan mutane. Bayan su hajiya sun tafi ta ce masa "Yarinyar nake yi wa gata, na lura matar raihan irin matan nan ne da ba kowace irin mace za ta iya gogayya da su ba a kishi, ai ko ba ƙarara ba yana faɗa, kai ka sani, idan aka yi masa auren dole matar wahala kawai za ta sha, shi wannan dai da ake yi wa kallon mummuna ita ce tayi masa, da azo ya auri ƴar mutane ta wahala a banza ai gara ba ayi ba". Ya ce "Na nuna wa bilkin haka, amma taƙi ganewa, kuma uwar yarinyar ce take zigata, amma tun da ke tana tsoranki, ƙila ta ji. *** Dr. Kuwa kwanansu uku a uganda, dama akwai abokinsa da yake zaune a can yake lecturing, kasancewar babban gida ne sosai da gwamnatin ƙasar ta bashi, a wani sashe na gidan dr. Yake zaune. Kamar wanda ya auri yarinya ƙarama, haka yake jin kansa, ya tuna abun da farida ta ce na ba uwar da za ta tsinana masa, amma ya ga abun da bai yi tsammani ba. Tun ranar da suka je, take mugun jin kunyarsa, ko kallonsa ba ta iya yi, da safe idan ta gaishe shi, komai zai ce mata sai dai ta bashi amsa da ka, amma ba zata yi magana ba, kamar ya auri budurwar ƙauye. Shi gaba ɗaya ma dariya take bashi, jin sa yake hankalinsa a kwance ya samu nutsuwa da kwanciyar hankali, saɓanin idan yana tare da farida, da wani lokacin rashin mutuncinta ba ya motsawa, sai yana buƙatar ta, sai ta tsiro da na ta buƙatun, sai ya yadda zai yi, koma ya yi mata sannan ta yadda da shi, kamar masu zaman dadiro ba aure ba. Ya zuba mata ido, ta koma gefen kujera tana ta sinne kai, ya ɗaukko wayarsa ya duba ummi na online, ya kirata voice call. Mariya na jin muryar ummi, ta tattara hankalinta a kansa. Suka gaisa da dr., Yake tambayar ta ko sun je duba Iya, ta ce masa a'a sai cikin satin. Mariya ta ƙura masa ido, ya ce "Ko in baki ku gaisa?" Ta jinjina masa kai da sauri. Ta matsa kusa da shi ta karɓi wayar, ta saka a kunnenta ta ce "Ƴar baƙa kyakykyawa" Ummi ta yi dariya ta ce "Mama Amarya" Ta ɗan tsuke fuska ta ce "Zan ci gidanku" Ummi ta yi murmushi ta ce "To ya ugandan? Kin fara jin yaren su" Ta ce "A'a ni ban taɓa fita ba ma, amma daga nan gidanki ba nisa ko? Ai zan iya zuwa" Ummi ta ce "Haba mama, ba fa Nigeria ba ce ba, ba ki ga sai da ku ka hau jirgi ba" Ta ce "Eh to haka ne, to ya cikin naki ashe kin kusa haihuwa" Ummi ta yi sauri ta kashe wayar dan kunya, tun da mama tazo manyan riguna take sakawa da hijjabi, dan kar ta ga cikin, kuma har ta gama kwanakinta ba ta nuna mata ta ga cikin ba sai yanzu. Ta kalli dr. Ta ce "Ka ga na daina jin ta, ɗan dubo mini ita" Yayi dariya ya ce "Kunya ki ka bata ta kashe wayar, ina ruwanki da cikinta" yayi maganar yana matsawa daf da ita. "Ni mamaki ma nake yi, har ummi ce da ciki, ohh kwanci tashi asarar mai rai. Aka yi ta cewa ba zata yi aure ba, gashi ma har za ta haihu" Dr. Ya ce "Eh haka lamarin Allah yake, amma dai dan Allah ki daina guduna, ni ba dodo bane ba, yanzu saboda maganar ummi ce shi ne ki ka kula ni, bayan tun safe kin ƙi kulani" Ta sunkuyar da kai kamar ta yi layar zana ta ɓace. Ya ɗago haɓarta, amma ta ƙi kallonsa. Yayi murmushi ya ce "Zo mu tattaka, mu je kasuwa ki ga garin" ya riƙe hannunta ta tashi tsaye, suka nufi bedroom. Kusan kwana huɗu, da Abdul ya tura kuɗi, kawu Ilyasu ya kira Abdul yana tambayar sa, wai shiru fa ba su ga kuɗi ba, jikin Iya yana tsamari, za a sallame su ma saboda rashin kuɗin. Abdul ya ce "Ai tun a ranar na tura dubu tamanin, dr. Bai hau jirgi ba sai da ya tura mini kuɗin, ni kuma na ƙara na tura". "To ya haka? Idris ya ce ba su shigo ba". Abdul ya ce "A'a dai, ya sake bincikawa, dan ta application na tura kuɗin" Ya din ga mamaki, ya duba wayarsa har da receipt kuɗi sun fita. Washegari tun da safe suka shirya, raihan ya je Abuja, noor da Abdul sai ummi suka tafi Jigawa duba Iya. Sai dai da suka je asibitin, sai da ummu ta ɗan tsorata, Iyan duk ta zama abun tsoro, fatarta ta yamushe, gashi an aske gashi, duk an liƙe kan da bandeji, hannunta da ƙafrta ma haka, idonta yayi ja saboda azabar ciwon kai, ba ayi hoton ƙwaƙwalwa ba, balle a san menene yake faruwa. Noor ta ce "Kai na ga iya ta koma kamar simigul" Abdul ya galla mata harara, ummi ta ce "Sannu iya ya jiki?" Iya ba baki sai kallon ummi da take yi. Ta kalli amaryar kawu Ilyasu ta ce "Ga abinci mun zo da shi a bata, amma kunu ai ba zai riƙe ta ba". Suna nan zaune su kawu Sagir suka zo, aka gaggaisa, ake sake mayar da yadda aka yi, kuma ummi ta yi musu kwarjinin da suka kasa yi mata zancen auren dr., Sai magana suke yi mata da girmamawa. Ummi ta ce "To shi Auwwalun an kama shi an hukunta shi, ko kuwa?" Amarya ta ce "A'a ya gudu" Ummi ta ce "Kodayeke ba hurumina bane ba, tun da dauɗar gora ciki ka sha ta, da na saka an nemo shi, wannan dauɗar yakamata iya ta shanye ta, a rufa masa asiri ai ɗan so ne " Aka rasa wanda zai yi magana, Idris yayi sallama, suka amsa, sai dai hankalinsa ya tashi ganin su ummi. Ummi ma zaune har da ciki, kayan jikinta ya isa ya saye nasu gaba ɗaya har da canji. Sai gashi ya risuna yana gaida ummi. Abdul ya ce "Malam Idris, na turo kuɗi aka ce ba ka gani ba" Cikin kame-kame ya ce "Eh wallahi, ba su shigo ba" Abdul ya ce "Kawo wayar ta ka in duba balance" ga waya a hannunsa babu damar yin ƙarya, ya miƙawa Abdul. Yana duba messages, ya ga alerts, yadda Idris ya din ga cire kuɗi, ga tsohuwa a kwance a asibiti ciwo zai kashe ta!!! Ayshercool 08081012143 Masu neman daga farko, dan Allah ku yi haƙuri ku duba a watpad, ko ku tambaya a groups whats app ɗina ne yayi expire, bani da shi a what's app 🙏 Masu son a tallata musu hajar su a what's app channel ɗina, should contact me, ina godiya sosai da jimirin bibiyata. *TALLA!TALLA!TALLA!* *INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*. *BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU* *MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA* CUTARWA! AYSHERCOOL (BRIGHT PENS) MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g 48 Cikin tsananin takaici, Abdul yake kallon Idris da yake ta rarraba ido, kamar an kwashe wa karya ƴaƴa. "Amma ga alert ɗin da banki suka yi maka, na kuɗin, kuma sannan ga wanda suka yo maka kana ta cirar kuɗi, ga sunana da komai da sunan bankina". Nan ƴan ɗakin suka hau salati da salallami, iya ta ɗago idanunta da suka yi ja, saboda azabar ciwo da wahala, ta kalli Idris kawai ta sunkuyar da kai. Wata ƙanwar iya ta fara masifa ta ce "Amma Idris an yi mutumin banza, kana kallon yadda matar nan take kwana tana wayyo ciwo, an rasa kuɗin yi mata abun da yakamata, saboda kai azzalumi ne ka cinye kuɗi ka ce ba a turo maka ba, yanzu duk soyayyar da iya take nuna maka wannan ne sakamakon abun da zaka yi mata?" Yaya magaji ne yayi sallama, suka amsa masa, ya kalli yadda suka yi jugun-jugun ga dai iya a zaune, balle ya ce mutuwa ta yi suka jimami. Suka gaisa da kowa, suka gaisa da ummi cikin girmamawa, sai dai bai ko kalli in da Idris yake ba, dan tuni ya daina yi masa magana ba ya shiga harkarsa. "Wai lafiya na ga kowa ya yi shiru?" Kawu Ilyasu ya ce "Ɗan uwanka ne ya cinye kuɗin da aka turo masa ayi wa Iya magani, yayi magana ma ya ƙi yayi shiru" Hashim ya ɗan kwaɓe baki ko a jikinsa, dan gaba ɗaya yana danasanin kasancewarsa a tsatson iya.  Da ƙyar matarsa take tursasa shi ya zo dubata. Ya ce "To Allah ya kyauta, ai da sauƙi tun da shi ya ci ba wani ba, balle a tsine masa na hannun daman ta ne" Kawu sagir ha haɗe fuska ya ce "Wane irin iskanci ne wannan? Uwarmu na kwance ba lafiya kuna faɗar abun da ku ka ga dama" Ummi ta ce "A'a kawu, Allah ne ya kawo wa iya lokacin shan dauɗar gora, dan duk wanda zai sha barinta ne, ita da take yawan faɗa, kuma da sauƙi tun da shi ya ci ba wani ba, sai ta fi jin daɗin shanyewa" Abdul ya kalli ummi yana girgiza mata kai, amma tayi burus da shi, dan lokaci yayi da yakamata ta amayar da damuwarta, ayi mata fyaɗe amma iya ta ce a rufa dauɗar gora ciki ka sha ta. Duk wani abu in dai a kan Idris ne ko son zuciyarta, sai ta ce dauɗar gora ciki ka sha ta. Ita ma gashi Allah ya kawo nata lokacin. Kowa ya din ga tofa albarkacin bakinsa a kan Idris, yayi shiru ya kasa magana. Wata maƙwabciyar su idris, mai suna ɗahara ta zo duba iya, sai dai matar kamar ba ta da saiti, kamar wadda ta taɓa hauka, saboda yadda take magana take sakinta yadda ta ga dama. Cikin tsantsar ƙauyanci da rashin iya magana ta ce "Kai Innalillahi wa... me ye ma ƙarashen na manta, Iya haka ki ka koma? Wannan naɗai da aka yi miki a ka, kamar shugabar bokayen gagarawa? Rayuwa kenan, ai baban Nana, gidanka da na higa kan na taho, na ce wa Shindatu ta zo ta rakoni na duba gyatumar nan Iya, amma ta ce mini wallahi ba za ta zo duba tsohuwar banza da ba ƙaunarta take yi ba. Nana ta ce Allah ya sa daga Asibitin nan ba za a maidota gida ba, na ce ke Shindu ki ji tsoron Allah, da gyatumar ki ce a ba kya ce haka ba". Ta yi maganar tana dariya, kamar abun da ta faɗa ɗin ba wani abu bane a wurinta. Ta sake cewa "To dai jin abun da suka faɗa, ya sa jikina yin sanyi na taho, to Allah dai ya bata lafiya, ni dai idan ta warke to, idan ba ta warke ba dai dan Allah ina bin ta jaka ɗaya da muttala biyu kuɗin surfe na, gara a fara sauke mata nauyi tun tana raye". Hashim ya saka hannu a aljihunsa, ya ɗaukko ɗari biyar ya bata ya sallameta. "Amma dai ka kyauta, wallahi gara ku bincika, Iya akwai shegen cin bashi, kuma ba ta biya, sai dai wani ka yi mata Allah ya isa ka ga hakan kuma ai bai yi ba" Kawu Ilyasu ya ce "Ke dan Allah ki tafi ki bawa mutane wuri, mahaukaciya kawai" Ta soke ɗari biyar ɗin ta, ta fita tana dariya. Babansu ya kalli Idris ya ce "Ka ga illar bujirewa iyaye ko? Matar da aka aura maka, ka wulaƙanta ta bayan ka yi abun kunya, ga wadda ka ke so ɗin abun da take faɗa a kan kakarka, mun gode amma in Allah ya yarda zaka gani, kuɗin nan da ka cinye sai sun hanaka kwanciyar hankali " aka din ga bashi haƙuri, a kan kar ya yi wa Idris baki. Ummi ta ƙara tsorata da lamarin rayuwa, da yadda take tsoron Iya da Idris, abun ba a cewa komai, amma kallesu yanzu abun tausayi, da gari banza ne da iya tana nan tana ta zagin jikokinta tana tsine musu da sun motsa, ga tsinuwar nan tana ta tasiri a tsakanin su yanzu. Ummi ta tashi ta fita tana amsa wayar raihan, a ƙalla ta kai mintuna arba'in, sai ga ta dawo da receipts a hannunta. Ta miƙawa ƙanwar iya ta ce "Gasu nan, na biya duk abun da yakamata ayi mata, za su yi mata". Ta waiwaya ta kalli Idris ta ce "Kai kuma, daga nan zan je in kai ƙararka wurin ƴan sanda, duk in da kuɗin nan suke ka dawo da su, dan ba wanda za a ƙara tursasawa shan wata dauɗar gora, da ake shanye ta wasu a ƙi shan ta wasu, shi ma auwwalun duk in da yake sai an nemo shi" Kamar su shige cikin ummi, suka din ga zambaɗa mata godiya, Iya kuwa ta ƙure ummi da ido. Ummi ta zauna a kusa da ita, ta ciro kuɗi, ta saka mata a cikin hannunta ta ce "Na san da magana a bakinki iya, amma ki sani ban yi miki wannan abun, dan na burgeki ba, ko ki so ni, bana fatan ko da ƙiftawar ido na yi abun da zai saka ki so ni ko na burgeki, tun da wanda na yi a baya ma babu riba. Na yi miki ne kawai saboda zatin Allah, kuma saboda kin haifi mahafina, mutumin da ki ka azabtar kamar ba ke ki ka haife shi ba, saboda abun duniya, saboda waɗan nan" tayi maganar tana nunawa Iya kuɗin hannunta. "Yanzu dai ba ya duniyar, mummunar ƴar sa da baki tabattar ko daga tsatsonki take ba, cikin hukuncin Allah ya rufa mata asiri. In sha Allah ba zan bari ki yi wulaƙantcciyar jinya ba, saboda babana bai wulaƙanta mini uwa ba, ke ma ba zan wulaƙanta ki ba, amma ki sani hakkin zuriyarki da ki ka raba kansu da kanki ne, ki ka gama tsine musu yake bibiyar ki. Allah ya baki lafiya, duk abun da Allah ya yassare mini, zan din ga turawa yaya magaji" Kamar munafukai haka duk suka duƙar da kai, ta gama maganganun ta, ta tashi ta ce wa su Abdul su tafi. Idiris hankalinsa ya tashi da ya ji ta ce ƴan sanda, dan ya tsorata da lamarin ummi, tun da ta saye gidansu na gado. Abdul suna tafe a hanya, suna tattaunawa a kan yadda familynsu yake ƙara rushewa, saboda jahilci da rashin background mai kyau. Can uganda dr. Ya cigba da karatunsa, idan baya nan yaran abokinsa suna shiga su taya mariya zama. Duniyarsa kawai yake ci da tsinke, yana samun duk abun da yake so daga gareta, ba tare da fargabar tashin hankali ko abun da za a buƙata daga gare shi ba. Sai dai ƙasan zuciyarsa babu daɗi, yadda kausar da inteesar suka haɗe kai da babarsu, suka daina shiga sabgarsa, ko gaishe shi da suke yi a waya suka daina, daga noor sai Abdul sune suke ta tasa, sai kuma ummi. Dan ƙarewa ma farida blocking ɗin sa ta yi a what's app. Tun abun yana damunsa har ya watsar, ya cigaba da addu'a tare da rungumar amaryarsa hannu bibbiyu, ya ji hakam kamar samun salama ne daga rashin mutuncin farida. Ga mariya da tsantsar ladabi, dan haryanzu wasu lokutan abubuwan ta irin na da take yin su. Bayan tafiyar ummi, a ka yi wa Iya hoton ƙwaƙwalwa, cikin kanta lafiya ƙalau, sai dai tsananin damuwar abubuwan suke faruwa ya sanya jininta yin mummunan hawa. Likitoci suka yi iya bakin ƙoƙarin su, aka sallamota a kan magunguna. Bayan sun koma gida, aka kwantar da ita aka shiga jinya, saboda ba ta iya yi wa kanta komai, ita ma jinyar tun da aka yi mata ta marmari, aka fara ƙosawa. Idris kuwa ya din ga bin ƙannen babansa yana roƙonsu a kira ummi, a bata haƙuri kar ta kai shi wurin ƴan sanda. A ranar da ya koma gida daga asibiti, ya samu hindu ya din ga zaginta da ci mata mutunci, a kan maganganun da ɗahara ta ce ta faɗa a kan Iya. Hindu ta ce "Duk tsohon dai bai ji kunyar hawa jaki ba, jaki ba zai ji kunyar kayar da shi ba, tun da ba uwata ba ce ta je ta mutu ba abun da yayi mini zafi, matar da ba ta da mutunci. Wai kai har ka na da bakin magana ma, tun kan ka dawo har gida aka zo aka bani labarin ka cinye kuɗin maganinta, kai ba ka ga laifinta ba sai nawa, sai ka fara yi wa kan ka masifar ai" Kamar yadda suka saba, haka suka yi ta faɗa su na cece ku ce. *** Anty rakiya kuwa, ta samu mami ta din ga surfa mata bala'i, ta in da ta shiga ba ta nan take fita ba, wai ta biyewa tsoron dangin miji, za a raba musu zumunci. Ta ɗauki gaba da ita, gaba ɗaya ta rasa abun da yake yi mata daɗi, ta na ji tana gani raihan yanzu ya koma mata kamar wani baƙo, sam ba ya sakewa da ita, saboda kar ta yi wata magana a kan ummi, kusan abun da take gudu shi yake shirin faruwa, ummi ta mallake mata ɗa. Dan labari yana isheta cewar, kullum raihan status ɗin sa, yabon ummi ne tare da koɗata, dan ita ya riga ya rufeta daga gani. Ta fuskanci sam fushinta da shi ba ya tasiri a kan sa yanzu, dan ya fi zuwa wurin hajiya ma yayi al'amuransa, ga wata irin muguwar shaƙuwa tsakaninsa da Salim yanzu har ma da Sagir. Hakan ya ƙara mata tsananin tsanar ummi, da duk da abun da take yi wa ummin, ta kan kira waya ta gaisheta, tayi girki ko ta bayar da abu ta ce a bata, ta wulaƙanta amma tun da abun nan ya faru, ummi ba ta ƙara shishshigin raɓar in da take ba. Aka gama gyaran gidan dr. Da idan sun dawo za su tare da mariya, daga can ƙasar ya turowa ummi kuɗi, a kan ta yi mata sayayya ta haɗa da kuɗaɗen hannunta, ta din ga yi mata sayayya. Dan ba ƙarya hannun raihan a sake yake, kuma yana sakar mata yadda yakamata, kuma ita ma na ta hannun a sake yake. Tun da aka yi scanic aka tabattar wa su ummi, yara biyu ne a cikinta, raihan yake murna, kuma ya gargaɗe ta a kan kar ta kuskura ta gaya wa kowa. Suka yi ta shiri, tare da sayen kayan jarirai. Sai dai cikin yana wata bakwai, kamar ummi za ta durƙusa ta haihu, saboda girma, kullum cikin lissafin kwanakin da suka rage take yi, saboda yadda nauyin cikin yake damunta, idan ta zauna sai an ɗagota saboda girman cikin. Gefe guda kamar yadda ta yi alƙawari, tana tura wa yaya magaji kuɗi lokaci zuwa lokaci, saboda kula da Iya. Farida ba ta haƙura ba, wurin bin bokaye da malamai, a kan lallai sai an raba auren dr. Da mariya, kuma a sake mallake mata shi ta juya shi fiye da yadda take yi a baya. Sai dai abun da ba ta sani ba shi ne, duk da kallon mahaukaciya tuburan take yi wa mariya, a hakan ba ta wasa da addu'a, mace mai son addini sosai da sosai, dan yana ɗaya daga abun da ya sanya ta ƙara shiga ran dr. Sosai da sosai. Hajiya ita ta maye wa ummi gurbin sirika, dan kusan har role ɗin uwa take yi mata playing, kusan kullum tana tafe zuwa duba ummi, ko yi mata aike take, tana tausayin ummi sosai da sosai, saboda abu ne na fari ba ta san ya yake ba, tana yawan cewa ummi "Anya ummi ba zaki likitoci su ƙara caje cikin nan ba, girmansa yayi yawa tubarkallah" sai dai tayi murmushi, ba tare da gaya mata haƙiƙanin abun da yake cikin ba. Ummi ta daina fita ko ina, gashi ta ƙara zama mafaɗaciya, saboda damuwar ciki. Kasancewar Hajiya na gaya wa raihan sai yayi haƙuri da ummi, a wannan stage ɗin mata masu ciki na fuskantar saurin fushi, dan haka sam baya damunsa, shi tausayi ma take bashi. Duk tsaftar ummi, sai da zamana dogon gashin nan sai ya kwana uku babu taza, kusan kullum sai dai ta saka kaya masu sauƙin nauyi yadda iska za ta wadace ta, takalmi kuma idan ba over size ba duk haushin takalman take ji. Da safe ta fito, tana ta mita noor ba ta ɗumamata shinkafa ba, wai ita ba ta cin abun da ta dafa. Noor ta ce "Ke fa ki ka ce ba kya son warin shinkafa" Kamar tayi kuka ta ce "Haba noor, amma tun jiya na ce miki zan ci, yunwa nake ji, ina magana kina kallo kin yi mini banza" Noor ta ce "Ai Yaya ummi ban san yaya zan yi miki na burgeki ba, MD ne kawai yake iya miki, ni ba ni na ɗora miki nauyin cikin nan ba, amma ki yi ta yi mini faɗa. Kuma sai na koma gida tun da faɗa ki ke yi mini" Ummi ta marairaice ta ce "Haba noor, to ki yi haƙuri dan Allah kar ki tafi, wai ni ya ku ke so in yi?" Raihan da yake bayanta ba ta sani ba, ya kama dariya, ba wuya ta bayar da haƙuri, ba wuya kuma ta fara kuka. Ciki duk ya mayar da ita wata iri, sai dai bai sanya ta daina kyau a idonsa ba. Yayi gyaran murya ya ce "Ya aka yi ne yau ke da noor ɗin taki ku ke faɗa" A shagwaɓe ta ce "Wai tafiya za ta yi" Ya ce "Haba nooriya, uwa guda ki tafi ki bar ƴar ta ki?" Noor ta tura baki ta ce "Faɗa take yi mini, kai ma fa shaida ne ta ce ba ta son shinkafa, wai yau kuma shinkafa za ta ci, wai ta gaya mini jiya da daddare, ni ina na ganta jiya da daddaren?" Ummi ta ce "Ni duk kun tsane ni, baku san me nake ji ba, ko tausayina ba kwa ji" Raihan ya ce "Mu mun isa, mu kuwa muke ƙaunar ki, jeki ki yi wanka ki shirya, har noor tare zamu tafi office yau, kya ji daɗin jikinki" Ta juya tana hararar noor, noor ta kama dariya ta ce "Na fasa tafiyar yaya ummi" "Ki yi ta tafiyar ma, ina ruwana" suna lallaɓata suna yi mata dariya. Aka ba ta ɗunamen shinkafa ta ci hankalinta ya kwanta. Tare suka tafi wurin aiki, fitowar ta yi mata daɗi tana kallon titi. A can wurin aikin, suna zuwa a parking space noor ta ga motar Salim. Sun shiga take tuna masa wulaƙancin da ya yi mata, ta zo ganinsa. Yau bai biye mata ba, ya ce "Allah ya baki haƙuri, kar na tanka cibi ya zama ƙari" Ma'aikata na ta gaishe shi, yana amsa musu cikin mutuntawa. Wani mutum ya taso, ya tare su ya durƙusa a gaban raihan yana dan Allah maigida ka taimaka mini da aikin sharar nan ko masinja, nafi wata ina zuwa an hana ni ganinka, ina cikin mummunan yanayi na babu da fama da rayuwa, dan Allah ka taimaka mini. Ummi ta zubawa mutumin ido, raihan ya kalli ummi ya ce "ya dai? Kin san shi ne?" "Ishaq Abdulkarim magashi" ta faɗa jiki a sanyaye, mutumin ya ɗaga kai yana kallonta. A rikice cikin tashin hankali mutumin ya ce "Salma Muhammad Bashir, ke ce da ma ke ce? Kina nan dama" ya fara maganar cikin kame-kame. "A ina ki ka san shi?" Ummi ta ce "Ɗan ajinmu ne a University" Raihan ya ce "Ɗan ajinku? Amma yake neman shara?" "Wallahi yallaɓai korata aka yi daga makaranta, dan Allah ka taimaka mini" Raihan ya ƙare masa kallo ya ce "Kana cikin wanda ku ka din ga muzanta mini mata kuna makaranta ko?" "Dan Allah ka yi mini rai yallaɓai, lamarin Allah kenan, gashi yau ina neman alfarma a wurinta, na yi nadama dan Allah ki yi haƙuri ki yafe mini" Gwiwoyi a ƙasa yake yi musu magiya, ummi ta ce "Kar ka damu, ba ni nake ɗaukar aiki ba, ni abun da ya faru ya wuce a wurina, wannan wurin kuma ba ni da hurumin ɗaukar ka aiki, idan  ya baka haka nake fata, idan bai ba ka ba ka yi masa uzuri wataƙila babu vacancy ne" daga haka ta ja jikinta ta yi gaba zuwa office ɗin raihan. Ba ta san yadda suka ƙare ba, shima da ya zo office ɗin bai gaya mata yadda suka yi ba, noor ta ce "MD a ina yaya Abdul yake?" Raihan ya ce "Ai ba a nan branch ɗin yake ba, yana sharaɗa shi". "To ina first born?" Ya kalleta ya ce "Wa kenan?" "Yaya Salim mana, ba ka san last born yake ce mini ba, shi kuma first born?" Raihan ya yi dariya ya ce "Ni ina zan sani, baya nan" Noor ta ce "Na ga motarsa fa" Ummi ta ce "Kai noor, me zaki yi masa an ce miki baya nan" Raihan ya ce "Da gaske kin ga motarsa?" "Wallahi na ganta" Raihan yayi murmushi ya ce "Yaya hukuma sai da rarrashi, office fa na bashi, nake ta bin sa ina yi masa magiya, ofishin kula da ma'aikata da ladabtar da au na bashi, ya ce ba ya so ba zai yi ba wai wata sana'ar zai yi. Na ce Alhaji ya saka baki, amma ya ƙi shi ne yau ya zo ban sani ba, ko ma ya neme ni, bari na je office ɗin nasa na duba" Noor ta bi raihan har office ɗin da Salim yake, sai haɗe rai yake yi. Ya kalli raihan zai yi mita, sai ya ga noor a bayansa, sai kuma ya saki fuska. Raihan ya ce "Yaya ashe ka zo ɗin ban sani ba". "Eh da ka je ka haɗa ni da hajiyan Bauchi ko?" Raihan ya sosa kai ya ce "Tuba nake babban yaya, with due respect kuma kai ne mataimaki na zan ɗebo sauran ayyukan da nake gabatarwa, na kawo maka zuwa next few months kuma, i will step down ka yi taking over" Salim ya yi masa wani mugun kallo ya ce "Raihan ba ka da hankali ko? Tayaya makakke zai jagoranci wannan abun, kai da ka ke a nutse ma kana fama" Noor ta ce "Ahh ba ka daina ba? Ka ce mini ka rage sosai ai" Raihan yana ja da baya yana dariya ya ce "Yauwwa noor gaya masa dai" Kwanaki suka cigaba da tafiya, wasu rayuwarsu na daidaituwa, wasu kuma suna girbar abun da suka shuka. Ummi ta shiga watan haihuwa, dr. Suka dawo ya kammala karatun da zai ba shi damar zama professor. Duk wanda ya kalli mariya ya san ta samu kwanciyar hankali, shi kamaa dr. Ya canza. Bai sauka a ko ina ba sai tsohon gidansa, in da za su zauna da mariya, gida yayi kyau ummi ta gyara komai. Abdul ne ya ɗaukko su daga airport ma, farida sam ba ta san ma sun dawo ba. Ummi ta yi wa Allah godiya, ganin mama cikin ƙoshin lafiya da kwanciyar hankali. Dr. Ya ce noor ta kwana tare da mariya, duk da jikinta yayi sauƙi sosai da sosai, shi kuma ya tafi can gidansa, sai dai ko kallon kirki bai samu daga farida ba, balle karɓa mai kyau. Tana saka ran asirin da ta yi ya ci shi, ya biyo ta yana lallaɓata, amma ta ga ko ta kanta bai bi ba shi ma, yayi wanka ya shiga ɗakinsa ya hau bacci. Tsananin takaici da baƙin ciki ya sanya ta je ta tashe shi da masifa, har da iƙirarin sai ta kashe mariya, bayan ta gama ci mata mutunci da kiranta mahaukaciya. "Wallahi farida ban taɓa gaya miki ba, amma yau zan faɗa na yi dana sanin aurenki farida, baki da tarbiyya ko kaɗan. Suffar da ki ka mu'amalance ni daban kan na aureki, wadda ki ka nuna mini bayan auren daban. Wallahi na yi dana sanin rashin auren mahaukaciyar da ki ke faɗa tuntuni ta fiki sanin darajata. Wallahi ki ka kuskura ki ka yi mata wani abu, a shirye nake da kowa ya kama gabansa da ni da ke, ba zaki kashe ni ba wallahi" ta dafe ƙirji tana zazzaro ido "Da can ba ka san bani da tarbiyya ba sai da ka auri mahaukaciya?" "Na sani mana, kara nake yi miki ina yi miki kawaici, ke kuma ba kya gani, gara na fito miki a mutum, ina kuma jaddada miki, idan ki ka kuskura ki ka taɓa mariya kin taɓa igiyar aurenki, dan ba zaki cutar da abun da nake samun farinciki daga gare shi ba". "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, na shiga uku wallahi yahaya kai butulu ne, azzalumi ni ka ke gaya wa haka?" Dr. Ya ce "Ke ki ka so, ai ni ban san tuntuni kamar a kurku nake ba, sai yanzu na yi ƴanci ai. Ke ki ka janyo duk abun da na yi miki, ke ma kin san na yi haƙuri da ke, kuma bani da niyyar cutar da ke, amma halinki ya fara kaini bango" Gaba ɗaya farida ta ji duniyar tayi mata zafi, komai ne naman ƙwace mata. Washegari dr. Ya shirya ya tafi gagarawa duba iya, babu yadda bai yi da mariya ba, ta ce masa ita fa ko rasuwa iya ta yi ba za ta je ba. Sam mariya ba ta da zafi, amma tun da ta faɗi haka ya san abubuwan da iya tayi mata suna cigaba da ƙona mata zuciya ne, dan haka ya ƙyaleta. Ya je ya tarar an mayar da iya asibiti, babu wata kulawar kirki, babu jinya mai kyau tana iya magana amma ba sosai ba, sai ta yi zawo har ya fara bushewa a jikinta ba a ɗagata an gyara ta ba. A wannan karon mariya ta matsa sosai a kan lallai sai ta je sun gaisa da maman raihan. Raihan ya sanar da Alhaji, Alhaji ya ja wa mami kunne sosai a kan kar ta kuskura ta wulaƙantawa ummi uwa. Mai hali baya fasa halinsa, dan sai da tayi abun da mariya ta fuskanci akwai wani abu a ƙasa, Hajiya kuwa ta karramata sosai da sosai. Sai dai mami ta yi mamakin ganin maman ummi, sam ba baƙa ba ce ba ga dogon hanci har baka. Sati biyu da dawowar su dr., Ƴan maiduguri suka zo ganin gidan mariya, suka din ga murna ganin yadda ta yi ƙalau da ita. Bayan ummi ta koma gida daga gidan mariya, cikin dare naƙuda ta tayar mata. A cikin daren ita da raihan suka tafi asibiti, dan noor ta gudu wurin mariya, wia sai ummi ta haihu za ta dawo, yanzu ta zama masifaffiya. Da safe raihan ya kira waya ya sanar suna asibiti, sai dai haihuwa ta gagari ummi, ga ciwo amma labor baya gaba, duk ta galabaita, likita ya ce sai dai ayi mata aiki. Alhaji ya ce lallai sai mami ta je asibiti ita ma, ayi komai da ita ai matar ɗanta ce. Ummi ta tayat da hankalinta, ta din ga kuka tana cewa tsoro take ji, duk aka kewayeta ana rarrashinta. Noor kuma tana gefen ta tana tayata kukan. Ummi ta kalli mariya, ga mama matar kakanta, ga Anty maryam, ga hajiyar su raihan, ga Abdul ga raihan kansa har da Salim, ga Nihal ƙanwar raihan, ana rarrashinta. Duk da mami ita sai yatsuna fuska take yi. A ranta ta ce "Allah sarki, haka family suke dama? Kowa ya damu da kai" wani irin farinciki ya cika mata zuciya. Ta ce sai dai a shiga aikin har da raihan, idan mutuwa za ta yi ya riƙe hannunta. Mami ta ja wani uban tsaki, raihan kuwa ya riƙe hannunta yana ta kwantar mata da hankali. Raihan ya kasa zaune ya kasa tsaye, aka shiga da ummi, awa guda da wani abu, aka fara fito da jarirai, mace da namiji. Sai dai hankalinsa ba a kansu yake ba, Ummi yake jira a fito da ita. Yana nan tsaye aka turo ta a kan gado idonta a rufe, an rufeta da green ɗin yadi. "Salma" ya kira sunanta da ɗan ƙarfi. Ta buɗe ido tare da riƙe hannunsa ta ce "Ka yi magana a hankali mana, ban mutu ba" yayi dariya ya durƙusa ya sumbaci goshinta ya ce "Thank you very much sweetheart, Allah ya baki lafiya" Can waje kuwa ana ta murna an fito da jarirai, mami ta kallesu ta ce "Taɓ, wannan wane irin yara ne, mu kaf danginmu babu wannan kalar, meye wannan?" Ayshercool 08081012143. CUTARWA! AYSHERCOOL (BRIGHT PENS) MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g 49 PAID ADVERT *Hajiya ina zaki? Saurin me ki ke yi haka? Ɗan bani aron mintuna biyu kacal, na gaya miki albishir ɗin da na zo miki da shi. Shin ko kin san sirrin sheƙin fatar ummi, da ya sanya ta kama zuciyar MD raihan ta hana shi sukuni? Kai ba ma skin care ba, har da sirrin gyaran gashi, ina masu fama da amosani, karyewar gashi ko kuma sanƙo, jan gashi ne da ke? Ko taurin gashi kamar soson ƙarfe. Idan matsalar ki budurwar fata, tare da rashin glowing, Annur skin scrub da hair bliss sun shirya tsaf domin magance muku kukanku, me ku ke jira ku tuntuɓe su a kan lambar wayar su dan ƙarin bayani 07045971194 ko 08140450950* 49 Tsit kowa ya yi ya zuba wa mami ido, tana wani yatsune fuska. Hajiya ta ce "Amma meyasa zaki ce haka? Wannan ai ba magana ba ce ba" "Eh na faɗa, ko a dangina kin taɓa ganin irin wannan?, kalli kalar uwarsu ki kalli raihan ki kalli yaran". Jajawur yaran, haskensu ya wuce ace hasken raihan kawai suka ɗaukko, gasu manya sosai, kuma kansu ƙwal babu gashi, kuma ba su da gashin gira ko kaɗan sai alamarta. Mariya cikin jin kunya ta ce wa Hajiya "Bari na gansu" Aka miƙa mata yaran, ta zuba musu ido tana murmushi sannan ta kalli mami ta ce "Hajiya, ai yaran nan da babansu su ke kama, haka na haifi ummi, Iya ta din ga ce mata aljana, sai dai kwana biyu kanta ya cika da gashi ko anty maryam, sai dai ummi tun tana jaririya baƙa ce". Wani mugun kallo ta yi wa mariya ta ce "To ni danginmu babu irin wannan abubuwan, ni ban taɓa ganin jarirai a haka ba, danginmu dai kaf babu mai wannan farin" Nan da nan Maryam ta harzuƙa ta ce "To mu namu akwai, duk tsiya dai ai na ɗanki ne ba wani ba" "Ba ni da tabbas, ni ɗa na ma ba shi da cikakkiyar lafiya" Hajiya da ta fara fusata ta ce "Ke dai ya rainawa hankali, dan ya tsallake son zuciyarki" Mariya ce ta din ga basu haƙuri. Raihan kuwa yana can ɗakin da aka kai ummi, sai zuba yake yi yana yi mata kalamai masu kwantar da hankali da ƙwarin gwiwa. Likitan da yake yi mata allura ya ce "Maman twins ai ba Kya buƙatar maganinmu, wannan kalaman sun ishe ki warkewa" suka din ga dariya, sai da bacci ya ɗauke ta sannan ya tafi ɗakin da su Hajiya suke. Noor ji take kamar ta kwaɗawa mamin raihan mari, ko karar ganin idon mariya bai saka ta yi alkunya ba. Abdul da yake ɗakin ya tashi ya fita, Salim ma surutun ya ishe shi, ransa ya fara ɓaci. Mariya ta kalli Salim ta ce "Salim, dan Allah jariran nan ba da babansu suke kama ba, dan Allah kar ki saka zargi a kansu tun suna jarirai, su sha wahala kamar ummi, idan ta tashi ta ji, ba za ta ji daɗi ba". Salim ya ce "Mama, muna murna muna fatan Allah ya bawa ummi lafiya, mun gode wa Allah kyautar da ya bamu" ya ƙarasa maganar yana yi wa mami mugun kallo. Kamar daga sama raihan ya shigo ya ce "Hajiya ba ni su na gansu" Hajiya ta maze kamar babu abun da yake faruwa ta ce "Tun yanzu ka fara nuna wariya, ka tafi wurin matarka ko ɗaukar su ba ka yi ba" cikin washe baki ya ce "Tuba nake, dole in fara zuwa kanta, saboda su an yanka mini mata" yayi maganar ko a jikinsa yana ɗaukar su, wanda hakan ya sake ƙular da mami. Ya ce "Tubarkallah, Hajiya irin idon ummi ne da su, brown masu kyau masha Allah, yaya ka ga namijin kallesu duk farare. Alhamdilillah" yayi maganar yana kallon Salim. Farincikin da mariya ta gani a fuskar raihan, sai ya mantar da ita takaicin abun da mami ta yi musu. Sauran mutanen maiduguri da suka zo ganin gidan mariya, suka cika asibitin. Ana jimawa ma sai ga dr. Ga Alhaji. Raihan ya din ga sanar da ƴan uwa batun haihuwar. Tsabar takaicin yadda raihan yake rawar ƙafa, ya sanya ta tashi ta bar asibitin. Sai da ummi ta yi awa shida tana bacci, sannan nurses suka tasheta, suka ɗagata aka wanke ta, sannan aka bata abinci. Ta saka kaya tayi kyau, kamar ba ita ba, sannan aka turo ta a kan gado aka mayar da ita main ɗakin da take. Suka din ga murna ganin an fito da ummi ras da ita. Sai jerawa ummi sannu ake yi, aka miƙo mata yaran dan ta shayar da su, amma ta kasa saboda yadda ido ya yi yawa. Hajiya tare da Salim suka koma gida, ta yi wanka ta yo girki, suka dawo da Alhaji. Shi ma Alhaji baki buɗe yake ta murna, yana yi wa jariran addu'a, duk da babu wanda ya gaya masa abun da matarsa ta yi. Sai dai noor ta gaya wa ummi, abun da mamin ta ce, wanda ba ƙaramin ciwo yayi mata ba, sai dai ta basar saboda tana cikin murnar kyautar da Allah ya bata. Ummi ta ce "Mama, jikin yaran nan kamar jariran mage, basu da gashi kwata-kwata". "Me ki ke ci na baka na zuba? Zai fito in sha Allah" Dr. Ma da daddare ya zo ganin jariran, tare da yi mata sannu. Kusan kwanaki uku, ana ta shigowa ana fita duba ummi, a kwanaki ukun nan gashi ya cika kan yaran nan fal. Kwanan ummi biyar, aka sallame su daga asibiti, raihan ya ce bai yadda a ɗauki hoton yaransa ba a saka a waya. Saboda masha Allah kai ba zaka ce ummi ce ta haife su ba, dan sun fi kama da larabawa sosai. Su Hajiya Aishan bauchi, da sauran jama'arta, duk suna kano, sai da ummi ta yi kwana goma da haihuwa, sannan aka shirya gagarumin taron suna a wani katafaren event center. Sai ranar suna ƴan gagarawa suka zo, aka ci aka sha, ummi sun samu kyaututtuka sosai da sosai ita da yaran, manyan mutane abokan hulɗar Alhaji Tahir, da abokan aikin Raihan, ban da ƴan uwa da abokan arziki. Sai dai kan ranar sunan nan, yaran nan sun juye kalar larabawa sosai da sosai, gashi ya cika kansu da girarsu, kuma dukkansu brown eyes ne da su, namijin mai baƙin gashi, macen kuma irin na ummi. Sai dai sunan da aka sakawa yaran ya yamutsa hazo, dan kuwa raihan sunan ummi ya saka wa macen Salma, namijin ya saka masa Muhammad, wai ya yi wa kansa takwara, ya yi wa Alhajin su, kuma ya yi wa mahaifin Ummi, tun da duk sunansu Muhammad laƙanin ne daban-daban, aka yi musu laƙani da Iman da kuma Ayman. Ba yadda ummi ba ta yi da raihan ba, a kan ya canzawa macen suna, kar ya janyo mata magana a cikin dangi. Amma ya ce "Kome mutum zai ce ya ce, son da nake yi miki, dole na yi miki takwara dole duniya ta shaida ina son matata". Noor ta sha kwalliya, kamar amarya. Ta je ta saka salim a gaba, sai ya yi mata hotuna da iphone ɗin sa. Ya gama yi mata hotunan yana nuna mata, sai murmushi take yi, ya kalleta ya ce "Kin yi kyau kamar ranar bikinmu" a razane ta kalleshi ta ce "Bikinmu kuma?" "Eh mana, ko ba kya so na?" Ta ɗan sosa kai ta ce "Yarinya ce fa ni" "Ba kya son tsoho ko?" Ta girgiza kai ta ce "A'a kai ba tsoho ba ne" Ya ce "Tsoho ne mana a kan ki, am 37 you are just 15, dama so nake bayan suna in yi wa Alhajinmu magana, amma tun da kin ce haka shikenan, idan kin gama hotunan ki kawo mini wayar"sai kuma ta ji babu daɗi. Mami kuwa a ranar sunan sai da ta kira raihan, ta ƙare masa zagi da cin mutunci, wai ya ƙare a gidin mace, saboda asara har da saka wa ƴar sa sunanta, bayan uban kuɗin da ya kashe mata ita da yaranta. Shi dai yayi shiru bai ce komai ba, dan ya san duk abun da ya yi wa ummi bai faɗi ba, kuma ba zai yi hidimar da Alhajinsu yake yi wa iyalinsa ba. Da daddare ummi ta yi wanka ta saka kaya, Anty maryam ma ta wanke jariran, an samu sun yi bacci saboda sun gaji, sun sha kuka da jagwalgwalon ƴan suna. Raihan ya shigo yana yi wa ummi murmushi. "My MD, murmushin me ka ke yi ne?" "Kallonki kawai yana sani murmushi, amma murmushin na yau na musamman ne, guess what?" Ta girgiza masa kai ta ce "I have no idea" Ya kamo hannunta ya danƙa mata mukullin mota ya ce "Gashi in ji Alhaji, ya ce a baki ya riga ni" Ummi ta waro ido ta ce "MD mota Alhaji ya bani" ta rungume raihan tana murna, ta din ga zuba masa addu'a da shi da Alhaji. Da gudu ta fita falo, tana nuna wa su mama da ba su riga sun bar gidan ba, aka din ga yi mata murna. Noor ta ce "Yaya ummi baki ji zuciyata ba, na taya ki murna, amma ina son mu yi magana" Suka keɓe da noor, ta gaya wa ummi abun da ya faru tsakaninta da Salim. "Noor meyasa baki da wayo ne? To meye aibun yayan?" Noor ta ce "To ai ni yarinya ce, kuma ni bana son ayi ta yi mini surutu kamar yadda aka yi miki" "To sai me? Wataƙila da ina nan a gida ban yi auren ba, ai yanzu ki samu mai sonki tsakani da Allah shi ne. Shi da ake son ya yi auren ma, kin san da manyan ƴan mata nawa aka haɗa shi, duk ya ce ba ya so dan ya ce yana sonki zaki wulaƙanta mini yaya, to kin yi wa kanki" Noor ta ce "Dan Allah ki yi haƙuri" "Kin fi son ki koma gida kina jerawa da kausar kuna faɗa kenan? Ke ba kya son ki ganki kema a gidanki?" "To ai yanzu ba a gida nake ba, gidan mama zan koma, ni ba zan koma gidanmu ba, maama haushina take ji kamar ba ta son ganina ma" "A'a ba sonki ne ba ta yi ba, amma dai yaya Salim dai kin yi wa kanki" "Na shiga uku, yanzu ya zan yi?" "Ki ɗauki waya ki bashi haƙuri" Noor ta tura baki ta ta ce "Salon ajina ya zube" ummi ta ƙare mata kallo kawai tayi tsaki ta bar ɗakin. Ummi na komawa ɗaki ta kira Salim, suka gaisa sannan ta ce "Yaya ka ji Alhaji ya bani mota?" Yayi murmushi ya ce "Na riga ki sani ai, ina taya ki murna ƙanwata" "Na gode sosai yaya salim, Allah ya saka muku da mafificin alkhairi" "Amin ƙanwata, Allah ya raya mana su Iman" "Amin yaya. Yauwwa noor ta gaya mini shirmen da ta yi maka, abun duk ya dame ta, dan Allah ka rabu da ita, Alhaji ya samu dr. Da maganar". Yayi murmushi ya ce "Kin je kin takura mata ko? Bana son takura ta, daga baya nake ganin kamar na yi wauta nayi mata tsufa" "Dan Allah ka bar wannan maganar, tana sonka, duk ta damu fa" "Amma, kina ganin dr. Zai bani noor kuwa? Kin san ni ina da case" "A'a yaya me zai hana? Kuma dan kana da case sai a ƙyamace ka? Ai yanzu ka shiryu a kan yadda na sanka a da, dan Allah ka ƙyale shirmen noor yaya" Yayi murmushi ya ce "Auta danger, shikenan zan yi tunani, a bata lokaci" "Dan Allah yaya ka ƙyaleta, mun yi magana da ita fa" "To shikenan, sai da safe" "Yauwwa yaya, a yi wa su hajiya bangajiya" Suka yi sallama, ta din ga addu'a, Allah ya tabattar da alkhairi, dan tana fatan noor ta yi aure da wuri, tun kan farida ta ƙwace ta, ta siffantu da miyagun halayenta. Har dr. Ummi ta kira, ta sanar masa da abun alkhairin da Alhaji ya yi mata. Ƴan gagarawa sai da suka kwana uku a gidan ummi, da zasu tafi ta haɗa kayan suna ta basu suka tafi da shi. Ummi ta saka noor a gaba, ta bata waya ta kira Salim. Sai dai da ya ɗaga wayar ya ji murayarta, bai kashe ba suka gaisa. "First born" "Mmmm auta" "Fushi ka ke da ni ko?" "Me ki ka yi mini zan yi fushi da ke?" Ta ɗan sosa kai ta ce "Maganar da muka yi ranar suna". "Ai ta wuce auta" "Ba ka so na yanzu?" Yayi murmushi ya ce "Ke dai ba kya so na, an bar maganar bana son takura miki" "To yanzu na canza shawara ka yi haƙuri" "To" ta ɓata rai saboda yadda yake bata amsa a taƙaice da izza. Ummi ta girgiza mata kai, alamar kar ta yi fushi. "Yaya Salim" "Noor" "Idan muka yi auren zaka bar ni in yi makaranta, ka ga yaya inteesar mijinta hanata yayi daga baya". "Zan barki in sha Allah" "A'a rantse da Allah, kar ka canza shawara" yayi mata shiru, ummi ta dafe kai, saboda wautar da noor ɗin ke yi. Bayan sun gama wayar, ummi ta ce "Eh lallai akwai jan aiki a gabana, noor babban mutum yayi magana ki ce ya rantse? Ke fa baki da kai" "To ba ki ji yadda yake yi mini magana da gadara ba, da fa ba haka yake yi mini ba" "Ba aurenki zai yi ba yanzu? Dole yayi miki izza. Ke fa miji ba abun wasa bane ba" ta din ga yi mata faɗa. Ummi ta ƙara ɗaura aniyar, raba noor da Farida har zuwa lokacin da za a saka auren noor ɗin, saboda kar ta ɗorata a kan mummunar ɗabi'arta na raina miji da yin asiri. Ummi ta kira Alhaji a waya, ta din ga yi masa godiya, tare da yi masa adduo'i masu daɗi. Ummi ta tara kuɗi da suturu, da sauran abubuwa. Farida kuwa tayi watsi da dr., Shi ma yayi watsi da ita ya daina shiga sabgarta kausar ma ta biye mata ba sa kula shi. Yau yana gidanta, tana ta cika tana batsewa, ta same shi a fall ta tsaya a kansa ta ce "Malam yaushe za ka dawo mini da ƴa ta ne?" Ya ɗaga kai ya kalleta ya ce "Ke da noor, sai lokacin aurenta, ta bar gidan nan kenan na bawa mariya ita" "Wallahi ba ka isa ba, ai ba ita ta haifa mini ita ba, da zaka bayar mini da ƴa" "Ni ban isa na ƙwace miki ƴa ba, halinki da ki ke nuna mata ne, ya sanya ta guje ki ita ma" za ta yi magana wayarta ta fara ringing. Ta ɗaga wayar ta yi sallama. "Farida kina ina, ki yi maza ki zo asibitin murtala emergency, Rahama mijinta ya ƙonata da ruwan zafi da ita da ƴar da take goyo" Farida ta dafe ƙirji ta ce "Ruwan zafi me tayi masa?" "Wai faɗa suka yi, ta tafi tsakar gida tana girki, ya zageta ta rama, ya fito yayi balla da kurfotin gabanta da tafasasshen ruwa a kai, da garwashin duk ya watse musu a jiki ita da ƴar" "Innalillahi na shiga uku" tayi jifa da wayar tayi ɗaki tana salati. Kiran sallar la'asar ake yi dama, dr. Ya fice sallar isha'i, dan bai san me aka ce mata a wayar ba. Daga sallar isha'i, ya tafi gidan mariya. Ya tarar ta idar da salla tana zaune ta yi shiru. "Ya dai, na ganki sai a hankali, ina noor ne?" "Tana gidan ummi, ai noor ta gujeni saboda sun yi jarirai" Yayi murmushi ya ce "Noor an kusa girma, Alhaji Tahir ne yayi mini magana, wai su na riƙo Salim yana so, na ce zai sha shiririta" Mariya ta ce "A'a kar ka ce haka, abu namu ƴa ta wa ɗa na wa, za ta yi hankali in sha Allah kan lokacin" "Wane lokaci kuma, shekara ɗaya ne kawai fa, tana gama secondary school ne suke so" Mariya ta yi dariya ta ce "Allah ya sa zamu gani" Ya ɗan kalleta ya ce "Kamar akwai magana ko?" Ta jinjina masa kai alamar eh. "To ya aka yi?" "Dr. Tun muna waccan ƙasar kamar ban kuma al'ada ba fa" Yayi dariya ya ce "To me ki ke so in ce?" "Koma meye ka ce mana" Dr. Yayi dariya ya ce "Maman ummi rigima, kin fi ni sanin meyake faruwa ai" "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wai ciki ne da ni?" Dr. Ya kashingiɗa yana dariya, gaba ɗaya ta ruɗe "Haba dr. Ummi na jego nima a ganni da ciki, na shige su" "To laifina ne? Ni dai ina so ina murna Allah ya raba lafiya, kowa ya kalle ki fa zai gane kin ƙara haske sosai" gaba ɗaya ta rikice, wai abun kunya ne, shi kuma ya din ga yi mata dariya. Gaba ɗaya ya manta da a gidan farida. Ummi na ɗaki tana ta yi wa noor nasiha, a kan maganar salim, ta ce mata ita tana son sa amma tsoron auren take yi, ummi tana ta lallaɓata, dan sun yi magana da dr. Kuma ta san zai kira noor ɗin ya tambaye ta. Anty Maryam ta shigo ɗakin ta ce "Ummi, kin yi baƙuwa, sai wani harare-harare take yi, ban san me aka yi mata ba, amma da alama ƴar uwar mai gidan ce, suna kama da shi" Ummi ta yi murmushi ta ce "Anty ki ce ta shigo". Mintuna kaɗan sai ga Maryam ta shigo. Ummi ta ce "Sannu da zuwa, yanzu ki ke tafe?" Ta ja tsaki ta zauna. Noor ta ce "To, ikon Allah" "Noor kawo mata ruwa da yaran ta gansu" "Ai fa, an samu abun da ake so, an samu daular da ake kwaɗayi tashin farko an zubo yara biyu, yaran da aka ce babu kalarsu a danginmu" Ummi ta yi dariya ta ce "Ai abun alfaharinku ne, kun samu iri a dangi. Kuma ƴaƴa biyu sai matar so ba kwaɗayayyi ba, abun alfaharinku ne, ƙaninki akwai himma, ko kuma maybe daga ni ce" "Ummi ni ki ke gaya wa haka?" "Ke fa ki ka fara, wai kwaɗayi? Ke in kwaɗayi ne kawai ya kawo ni gidan nan, da ban kai haka a cikinsa ba" Noor tayi sallama, ummi ta amsa, ta miƙawa maryam yaran, maimakon ta karɓa ta ce "Ba shakka, dole mami ta ce akwai lauje cikin naɗi a wannan yaran, ba zata taɓa karɓar su a matsayin jikokinta ba" Ummi ta ce "Noor mayar mini da ƴaƴana wurin Anty"Noor na fita ummi ta ce "Kar Allah ya sa ku karɓe su a matsayin jikokin, ku mayar da su in da suka fito, tun da ubansu ya san nasa ne shikenan. Dama ni ban ce ta ƙaunace ni dole ba, tun da ba ku ku ka halicce ni ba. Ni yanzu a duniyar nan da a so ni da a ƙi ni duk uwar ubansu ɗaya. Babu yadda ban yi ba wurin yi wa mami biyayya, da girmamata amma ba ta gani, a gaban uwata saboda rashin ta ido, take cewa wai yara ba na ɗan ta bane, da yake uwata ba zuciya ce a ƙirjinta ba ko? Maryam da zan baki shawara da kun daina jayayya da ikon Allah, ni da raihan ajiyar Allah ne mutu ka raba. Idan ku ka cigaba da takurawa aurena ko kun raba aurena da raihan, zan cigbaa da rayuwar aure da shi ina haihuwa ko da aure ko babu, dan a yanzu ba wani ƙalubale ko abun kunya da ba zan iya fuskanta ba. Zaman gidan raihan, da zazzago ƴaƴa yanzu na fara, idan kin ga dama daga nan ki je wurin mami ki yi mini wani sharrin ke ta shafa da ke da ita" Maryam ta miƙe ta ce "Ummi, mamin ki ke gaya wa haka?" "Idan tsoho bai ji kunyar hawa jaki ba, jaki ba zai ji kunyar kayar da shi ba. Na yi iya yi na, na gaji, ba zan cigaba da cusa kaina in da ba a ganin kima ta ba. Kuma wallahi idan kuka cigaba da uzzura mini, hakkina zai fara bibiyarku ai ke ma mace ce, kuma a gidan wani ki ke aure, a sannu kema zaki haɗu da dai-dai ke". Ta fice ta bar ta a ɗakin a tsaye. Farida kuwa hankalinta ya tashi, saboda yadda ta je ta tarar da rahama, a asibiti, jikin yarinyar duk ya saɓule, haka na rahama cikinta, fuskarta da ƙafafuwan ta duk sun ƙone ƴan sanda sun kama mijin nata. Ta din ga kuka tamkar za ta zare. Ummi kuwa duk da furucin da Maryam tayi mata, ko a jikinta ta miƙe ƙafa ta cigaba da sabgoginta a gidanta. Hausawa suka ci idan kana da kyau, ka ƙara da wanka, ummi ta san in dai ɓangaren kula da mijinta ne, to tana da kyau ba a magana a ɓangaren kula da raihan. Amma duk da haka, maganar hausawa gaskiya ce, dan haka ba ta yi ƙasa a gwiwa ba, wurin lalubo lambar Amina Gachi, CEO beenad herbal center, mussaman ita da taɓa fama da ciwon sanyi, kuma galibi ciki ya kan tayar da ciwon, dan haka nemi Amina gachi, domin shiryawa koma wa ɗakin mijinta. (Bari na baku bayani, beenad herbal center, ba iya maganin sanyi suka ƙware ba, suna bayar da magunguna daban-daban dai-dai da matsalolin ku, damun kawo daidaito a gidajen auren ku. Suna da kaya kamar haka; Shedaniyar gumba Gumba mai saying Garin mai kabbara Mai dalalan miyau Wayyo dadi Zumar kwakwa Zumar ridi Zumar dabino Zuma mai ma'ul ijaba Farin jini Gumba kalla kalla da dai sauran su A BEENAD HERBAL suna da turarukan wuta da humrah kalla daban daban sai Wanda kuka zaba Ga kuma maganin slimming Gyaran nono Maganin hips Maganin Kara kiba Da dai sauran su. Kayan mu tested and trusted ne Suna maraba da masu siyan Daya ko sari Suna Nan cikin garin kaduna Kuma suna tura Kaya duk inda kike da yardar Allah AMINA GACHI 07034404975 CEO BEENAD HERBAL MEDICINE &INCENCE KADUNA Phone no 07034404975. Da labarin abun da ya faru da rahama ya zo kunnen ummi, hankalinta ya yi mummunar tashi, dan sai da ta yi kuka, dan yadda Abdul ya gaya mata abun babu daɗin ji, ummi ta ce raihan ya bar ta je ta dubata, ya ce ba zata fita ba sai tayi arba'in. Yaran raihan kamar ana hura su, dan baya wasa wurin kula da su, ummi na cin abinci mai gina jiki, da zai samar mata da ruwan nono, kunu masu kyau da kayan marmari, su kuma yaran ga isashshiyar madara yana saya, kan su yi arba'in suka cika ɓul-ɓul gwanin sha'awa. Can gagarawa, aka samu wani irin maimakon ruwan sama, kamar da bakin ƙwarya, ga ƙarfi ga kuma iska hakan ya sanya rufin ɗakin iya kwashewa. Dama dr. Ne ya bayar da kuɗi, a gyara mata ɗakin ta saka aka yi rufi ta karɓe sauran kuɗinta ta cinye, sai ledar ɗaki da ta saka. Iska ta yaye kwanon, ruwa ya din ga zuba a kanta, ruwa ya jiƙa tsohuwar ƙasar da aka yi ginin ɗakin da ita, ita ma ta zube wani ya danneta, ban da katakon rufi da ya din ga ƙwalo mata a ka. Gashi itakaɗai take kwana babu kowa a wurinta, dan haka babu wanda ya san abun da ya faru sai washegari. Babu wanda yayi zaton za a ciro iya da rai, haka aka kwashe ta aka yi asibiti da ita, tamkar an jiƙa kaza a ruwa, ga jikinta duk ƙazantar zawon wahala da tayi, kan nan kamar an suɗe ƙwallon giginya, duk ta zama abun tsoro. Su farida kuwa an kai ruwa rana, da su da mijin rahama a wurin ƴan sanda, dan kuwa ƴar kwananta goma sha ɗaya ta mutu, kasancewar uwarsa tana da kuɗi, sai kaiwa ta ke tana komowa a kan lallai sai an sake shi. Ana wannan ƙadamin, su Alhaji Tahir suka kai kuɗin auren noor, aka saka watanni tara watan da za ta kammala karatun sakandare, za a yi bikinta da Salim. Tun da aka saka auren nan, ummi ta dage wa noor da addu'a, tare da yi mata nasiha sosai a kan zamantakewa. "Noor, bani da burin rabaki da anty farida mahaifiyarki ce, kuma komai ta yi miki, mahaifiyar ki ce. Abun da nake so ki sani shi ne, kar ki yadda wani ya ɗauki wani abu na tsafi ya ce miki ki yi wa mijinki. Daga zarar abun ya karye, za ki ji kunya, kuma sai mushen kare ya fi ki daraja a wurinsa. Noor Allah bai halicci namiji dan ya bi mace ba, mace ita ce a ƙarƙashin namiji, gwargwadon biyayyarki, gwargwadon mallakarki. Idan ki ka kwantar da kai, ki ka yi addu'a ki ka miƙa lamarinki ga Allah ki nemi aljannar ki da gaske, zaki juya namiji yadda ki ke so. Wasu abubuwan sai lokacin auren yayi zan gaya miki, babu ruwanki da ɗaukar shirmen ƙawaye su gaya miki abun da ba zai amfane ki ba. Babu ke babu yi wa miji asiri noor, asiri ba ya tasiri, ko yayi na lokaci kaɗan ne. Namiji kullum shi ne a gaba, dan haka ban da ɗaga masa murya, kuma ki fara yi muku addu'a samun zaman lafiya tun yanzu". Noor ta jinjinawa ummi kai. Hajiya kamar ta taka rawa, ganin a wannan karon Salim ya yadda zai yi aure. Kuma ta ji daɗin zaɓar noor da yayi, ko ba komai ta ga misali a kan ummi, ahalin gidan dr. Suna da tarbiyya. Dr. Ya je gagarawa, ya duba Iya, sai dai aka tabattar masa da spinal code ɗin ta ya taɓu, ba zata ƙara takawa ba, komai sai dai ayi mata. Dr. Ya tsorata da yanayin da ya ga Iya a ciki sosai da sosai. Gashi babu wata cikakkiyar kulawa ta a zo a gani. Bayan ya koma gida, ya tarar an dawo da rahama gidansa, a nan za ta yi jinya, da kamar ya ce bai yadda ba, kawai ya ƙyale su. Ummi ta na ta Alla-Alla tayi arba'in, tana son ta je ta duba rahama, kuma ta duba jikin iya. Sai dai shi Yallaɓai MD, lissafinsa kawai tayi ta koma turaka. Da  dr. Ya gaya wa Farida batun karɓar kuɗin noor, bala'i ta hau bala'i taƙi nutsuwa yayi mata bayani balle ta ji waye. Hankalin kausar yayi mummunan tashi, jin an karɓi kuɗin auren noor, ita kuma ba ta ga tsuntsu ba ta ga tarko. Ummi tana jikin raihan, tana ta zuba shagwaɓa, ta kalli fuskar sa tana ƙoƙarin tashi ta ce "Malam cikani na tashi, yarana jarirai ne, ba zaka haɗa ni da ƙajaga ba ban gama warkewa ba, ka sakani konika" Yayi dariya ya ce "Ke matar so ita ce ke konika, ki yi wa duniya proving ɗin ke ɗin matar so ce ga raihan" "Ni zaka yi wa wayo? Ai na riga na gama yi wa duniya proving ni ɗin ɗaya ce a zuciyar mijina" "Wallahi faɗi ki ƙara faɗa, ni kyautar da Alhaji yayi miki ni na so yi miki ita, wata gigitacciyar kyauta nake son yi miki". "Ni ba na son kowace kyauta, wuri nake son ka ƙara gyara mini a zuciyarka na miƙe ƙafata" Raihan ya ce "Kin samu, ba kowa a ciki sai ke Salmana, Allah ya ƙara miki lafiya da nisan kwana, ya ƙaro miki lafiya, ki yi ta haifo mini ƴaƴa" Riƙe hannunsa tayi tana dariya ta ce "Ni zaka yi wa wayo, wai ba zuwa ka yi kana cewa ba ka da lafiya ba?" Ya kwashe da dariya ya ce "Duk cikin neman hanyar tsira ne, bani da lafiya idan har ba tare da ke nake tare ba, ni a idona duk wata mace idan ba Salmana ba ba zata taɓa zama ɗaya da ke ba. Ke daban ce a kowane fanni". Kalaman jinjina da girmamawae da yake yi mata, ya sanyata jin kamar ta fi kowace mace sa'a a rayuwarta. *** Idris da sasassafe yana ta shirin fita zuwa karɓar wani kuɗi, sai faɗa suke yi da hindu suna zage-zage kamar ƴan tasha a kan kuɗin cefane. Sallama aka yi a waje ya fita, ya tarar da ƴansanda a tsaye, ba su yi wata-wata ba suka cafke shi suka tafi da shi. Babu wanda ya san in da yake, dan babu wanda ya san kama shi. Sai da aka je wurin ƴan sanda, wai ana tuhumarsa da yi wa wata yarinya fyaɗe, an tsinci yarinyar a hanyar makarantar islamiyyar su, an yi mata fyaɗe an kasheta, wai shi ake zargi saboda hanyar wucewarsa ce, kuma an san halinsa na biye-biye yaran mutane. Farida na tsaka da jinyar rahama, ɗakin da take ƙonuwa sai wari take yi, duk da yadda ake kula da ita sosai. Inteesar ta shigo falon gidan, fuska duk a kumbure, idanunta sun yi jawur. "Ke inteesar lafiya meyafaru?" Ta miƙa wa farida takarda, tana kuka ta ce "Hajiyar sa ta saka ya sakeni, wai sun gaji da ciyar da ni sai dai na yi kashi babu haihuwa, alhalin ɗanta ne silar komai!" *Ina baku haƙuri, na san ina laifi rashin posting, ayyuka da bukukuwa ne suka yi yawa, ayi haƙuri dan Allah ina godiya da kulawa jama'ata ko in ce na ummi😡* Ayshercool 08081012143 CUTARWA! AISHA ADAM (AYSHERCOOL) (BRIGHT PENS) MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g 50 Jikin farida na tsuma, ta karɓi takardar ta duba, ga saki nan rangaɗa-rangaɗa guda biyu. "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wai meyasa duk maza halinsu ɗaya ne? Butulci kawai suka sani? Ita ma uwar ta sa shegiya mummuna mai baƙin hali. Ɗaukko mini wayata maza na kira babanku, na shiga uku ni farida wannan masifa hawa-hawa" ta kira wayar dr. Amma bai ɗaga ba. Ta dungurar da wayar ta ce "Ai na sani, ba zai ɗaga ba yana tare da wannan mahaukaciyar, na shiga uku ni farida". Dr. Kuwa sallama yayi ya dawo daga salla, mariya ta shirya masa abinci, ya lumshe ido ya ce "ƙamshin abincin kawai ya sa na ji na ƙoshi" tayi murmushi ta ce "Ka dai fara ci tukuna" Ta zuba masa faten wake doya, yana ci ya ce "Yauwwa, noor ta dawo ta zo ki fara koya mata irin abincin nan, kar tayi aure ba ta iya girki ba" "Waye ya ce maka ba ta iya girki ba? Idan ta zo gidan nan tana yi ai, noor ɗina ta iya girki sosai ta ce a wurin ummi ta koya" Dr. Ya ce "Ai tun da ummi tayi aure, na yi kewar abinci mai daɗi" "Son kai, saboda ƴar ka ce ko?" Yayi dariya yana kashe mata ido ɗaya. "Yauwwa ga wayarka, an kira ban ɗaga ba" Ba tare da ya karɓa ba ya ce "Ki na tsoron kar ki ɗaga ki ji budurwa ta ce ko?" Tayi dariya ta ce "Haba dai, ko ma budurwar ce na san ba za ta wuce maman ummi ba, maybe ko tana buƙatar wani abun ne, idan ka gama kar ka manta ka kira ta" ya ɗan ƙura mata ido. Ita har cikin zuciyarta tsakani da Allah take son su zauna lafiya da farida, wai ko ba komai ta riƙe mata ummi, daga baya ta haƙura ganin faridan ba haka ne abun a wurinta. Ya gama cin abincin, ta kawar da kwanukan, ta zauna tana matsa masa ƙafa ya lumshe idonsa. Ta ce "Baban ummi, ba ka ce mini komai ba a kan zuwa maiduguri" "A'a" ya faɗa a taƙaice. Ta sunkuyar da kai ta cigaba da abun da take yi masa. Ya ɗago haɓarta ya ce "Kin yi fushi ne?" "A'a, amma in anjima ma zan kuma tambayar ka, dan Allah baban ummi, ka san menene?" Ya ce "A'a sai kin faɗa" "Taron family aka shirya mana, wai an binciko tun farkon asalinmu, an gayyato mutane da dama da muke da alaƙa, ba tare da mun san mu ƴan uwa ba ne, dan Allah baban ummi" Ya ɗan yi murmushi ya ce "Na ji, amma ni kin ga bani da lokacin kai ki, bana son kuma ki hau motar haya, kin ga kina da juna biyu kar ki wahala" "Ai zan gaya wa ummi, idan ya barta sai mu tafi da Abdul da noor, dan Allah kar ka ce a'a" yanayin yadda ta kwantar da kai take lallaɓa shi ya sanya shi jin daɗi a ransa tare da jin kansa eh shi ne maigida. Saɓanin yadda farida ke yi masa magana gatse-gatse, wani lokacin ma sai ta yi abun da take so yake sani. "Shikenan, Allah ya kaimu lokacin, za ki je in sha Allah" Faɗaɗa murmushinta ta yi tana yi masa godiya. Sai magariba ya je gidan farida, dan duba su. Sai dai ta fara da yi masa ƙorafi, da zazzaga masa masifa, sannan ta miƙa masa takardar da inteesar ta zo da ita. Ya karɓa ya karanta, sannan ya kalleta ya ce "Na gani, me zan ce?" "Kamar yaya me zaka ce? Ba zaka kira shi ba a kan abun da ya aikata, ya wulakanta ƴar ka" Dr. Ya ce "Ƴar ki dai, ki nema mata wani uban da zai tsaya mata, ni da ban isheku kallo ba ke da su, ai na yi zaton wani uban ki ka canza musu, kuma ba wani abu da zan kira mijinta na ce masa, tun da ya riga ya saketa, in dai irin halin da ki ke yi, ta je tana yi dole a korota, yayi haƙuri ma. Idan baki riƙe tawa ƴar bazawara karo biyu ba, ga zaurawa biyu nan har da ƙarin budurwa Allah ya haɗa miki, kuma dolenki ki riƙe" ya fice ya bar mata gidan. Inteesar ta ɗora hannu a ka ta din ga rusa kuka, can gefe ma rahama kuka take yi, dan an saki mijinta, ya ƙwace mata sauran yaran, bayan aiko mata da tata takardar sakinta. Farida ta koma kamar mahaukaciya, ta rasa in da zata saka ranta. Kwanan ummi arba'in da biyar, ita da raihan da noor suka tafi yawon arba'in, a motar da Alhaji ya bata. Suka fara da zuwa gidansu raihan, da suka je gwiwa a ƙasa ummi ta durƙusa ta din ga yi wa Alhaji godiyar mota da ya bata. Yara sun cika hannu, sun ƙara kyau sosai, babu yadda za ayi ace yaran hausawa ne a yadda. Alhaji ya ce "Su wannan larabawan ba su fara dariya ba ne? Ko ni ɗin ne ba su gane ba" yayi maganar yana yi musu wasa. Har wurin mami suka je, sai dai Nihal ce kawai ta ɗauki yaran, tana hangen yaran abun ka da jini, zuciyarta na son ɗaukarsu, amma sharrin zuciya da ƙiyayyar ummi ta saka ta share su. Ana ta shirin bikin Nihal, saboda an kusa kawo kayan lefe, da an kawo kuma ba za a saka da yawa ba, za ayi bikin. Daga nan kuma ta ce su tafi can gidan farida, daga nan ma ta duba jikin rahama, tun da an ce a gidan take jinya. Raihan ya ajiye su, ya ce awa uku ya basu, zai dawo ya ɗauke su, su tafi gidan mama. A falo suka tarar da inteesar, kamar aljana ta rame, hasken nan babu shi, duk ta fita hayyacinta. Ummi ta zauna tana faɗin "Anty intee kwana da yawa, ya ki ke ya gida?" "Lafiya lau" ta amsa jiki a sanyaye, tana ƙarewa ummi kallo, da shigowarsu kawai ƙamshin kabbasar kayanta, ta gauraye ɗakin. Wata irin danƙareriyar lafaya ce a jikinta mai tsada, hannunta yatsu uku duk gold ne, haka kunnenta, har da chain na gwal a ƙafarta. Kai ba sai an gaya maka ba ka san ummi a hutu take. Noor ta ce "Anty intee baki da lafiya ne? Duk kin rame" inteesar ta girgiza kai. "Ina su Antyn su ke da rahama?" Da hannu kawai ta nuna musu ɗaki. Ummi ta kwantar da iman, a kan kujera noor ta ajiye aiman suka shiga ɗakin da sallama. Ɗakin sai warin gyambo yake, sai ɗan zani aka yafawa rahama, duk ta ƙone. A gigice ummi ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Anty rahama sannu ya jiki" rahama ta sunkuyar da kai sannan ta amsa. Ta kalli farida ta ce "Anty ina wuni, ya mai jiki?". "Dalla rufe mini baki, kin zo munafunci ki ga a wani hali nake ciki, ko na haukace na fara bin bola kamar babarki, to ina nan daram. Dangin maita bakin da ki ka yi mata ya kama ta. Jiki a sanyaye ta ce "Astagfirullah, ƙaddara ce daga Allah, kuma ke ki ka hasala ni, ɓacin rai ya sanya na yi wannan furucin. Sannu Anty rahama, yadda Allah ya jarabce ki da wuta a duniya, Allah ya haramta mata namanki a lahira, Allah ya baki lafiya da akwai wani abu a raina ba zan zo duba ki ba, Allah ya baki lafiya" Rahama ta riƙo hannun ummi ta ce "Ummi ba zan musa ba, idan aka ce alhakinki ne ya kamani, na san mun azabtar da ke, wallahi tun da na yi aure ko amarci ban gama ci ba, na fara shan wahala har yau ban samu kwanciyar hankali a gidan aure ba. Dan Allah ki yafe mini" Ummi ta shafa hannun rahama ta ce "Na yafe miki wallahi, Allah ya yafe mana baki ɗaya, Allah ya baki lafiya bari na je falon na ji kamar kukan aiman" ta miƙe ta fita. Farida ta kalli noor ta ce "Sannu sallalamammiya, ashe kin canza uwa ko?" Noor ta ce "Idan na yi miki laifi fa ce wa ki ke yi na nemi wata uwar, dama ke ba uwata ba ce, ki yi ta hantarata da zagina, ni kuma bana jin daɗi ni ki ka tsana ban san me na yi miki ba" sai jikin Farida yayi sanyi, ta tuna maganar ummi, ba ta taɓa zaton abun da tayi zai yi tasiri a zuciyar noor ba. Ta basar ta ce "Da uban wa aka saka miki rana ban sani ba?" "Yayan yaya raihan ne, yaya salim" Kausar da ke gefe tana danna waya ta ce "kutt wannan gandamemen mutumin, me yayi miki zafi?" "Ni kar ki yi mini hassada, haka kurum in tsufa a gida, ke da ki ke kyau ma baki yi aure ba, balle ni ba zaki zigani ba" suka hau faɗa kasancewar kwana biyu ba su haɗu ba. Farida ta tsawatar musu, sannan ta koma kan rahama da masifar, uban me suka yi wa ummi da take neman yafiyarta. "Ashsha! Yaya ki farga kema kan lokaci ya ƙure. Kin san mun azabtar da ita, ke ki ka gaya mini halin da Iya take ciki, ni dube ni wallahi hakki ne" "A'a ni ban ɗauki hakkin kowa ba, dan haka ba wata yafiya da zan nema, ta daɗe ba ta yafe ba". Ummi kuwa na komawa falo, ta tarar da inteesar tana zaune ta zuba wa yaran ido, ta saka hannu ta ɗauki aiman da ya tashi ya fara kuka. Tana ɗaga kai ta ga ummi ta ajiye shi, tana basarwa. Ummi ta yi murmushi, ta ƙarasa ta ɗauke shi, ta ajiye mata shi a cinyarta ta ce "Haba ɗan gidan babban mutum, mamanka ce da ba ka santa ba, ka buɗe ido ka kalleta" Inteesar ta saka hannu ta rungume shi, ta fashe da kuka. Ummi ta san kukan me take yi, ta dafa ta ta ce "Haba Anty intee, Allah ya baki rai da lafiya, kar ki yi masa butulci, rashin haihuwa jarabta ce, ki gode masa ki yi addu'a idan ki na da rabo, Allah ya baki naki kema. Zan taya ki Addu'a in sha Allah zaki ga ɗanki, Allah ya baki rabo a satin nan, ni na yi biyu ke ki yi uku, mu tarawa kawu abokan wasa" Cikin kuka ta ce "Aurena ya mutu ummi, uwar mijina ta saka ya sakeni, wai bana haihuwa sai ci da kashi. Sun wulaƙanta ni, sun tozarta ni, Abba ya ce babu ruwansa na ƙarata na nemi wani uban. Zuciyata za ta fashe ummi, gashi tun da na dawo kausar ta mayar da ni kamar maƙiyiyarta sai raini da wulaƙanci ita kanta maama tayi ta hantarata, wallahi ji nake kamar na sha guba na mutu" Da sauri ummi ta toshe mata baki, fuskar ummi ɗauke da hawaye ta ce "Haba anty inteesar, mutuwar aure ba kan ki aka fara ba, ba kuma yana nufin ƙarshen rayuwarki bane ba. Abba kuma kun yi masa laifi yana gaya mini, kun tafka kuskure da kuka daina kula shi, ko gaishe shi ku ka daina yi, dan ya auri mamana. Ku ka manta da duk ɗawainiya da hidima da ya yi mana a rayuwa. Ki kwantar da hankalinki, ki nemi afuwarsa nima zan taya ki roƙonsa, na san zai yafe miki. Abu na gaba kuma, ki yi ta addu'a da miƙa wa Allah lamuranki, idan ki ka gama idda, ki roƙi Abba ya bar ki, ki koma karatu, ko ki fita ki koyi wata sana'ar hakan zai rage miki lokacin da ki ke spending a cikin gida da su Anty farida, amma dan Allah kar ki sake cewa zaki kashe kanki" Inteesar ta kwanta a jikin ummi ta ce "Ba ki san me nake ji ba" "Na ɗanɗani fiye da abun da ki ka ɗanɗana, da ko maƙiyina bana fatan ya ɗanɗana. Sai da ta kai a duniya ina jin kamar nikaɗai aka tsana, na sha jin nima kamar na kashe kaina, a lokacin da bani da kafaɗar kashingiɗa na yi kuka, noor ce kawai take tayani kuka, sai zuwan Baban su iman rayuwata, ya nuna mini ita rayuwa yadda ka ɗauke ta, haka take zuwar maka. Dan Allah ki daina wannan kukan". Ummi ta yi ta rarrashin inteesar, Farida ta fito tana faɗin "Ke Inteesar kukan me ki ka yi mata?" Inteesar ta share hawayen ta, ta ce "Babu abun da tayi mini, miƙo mini macen na ganta" Ummi ta miƙa wa inteesar iman, ta haɗa su ta rungume, tana cigaba da zubar da hawaye. Duk yadda farida ta bugi cikin noor, a kan ta gaya mata shirye-shiryen da ake ciki a kan aurenta, amma tayi mursisi tayi shiru. Sai da suka yi faɗa, ta ce noor ba za ta bi ummi su tafi ba. Sai ga inteesar ta sake da ummi, tana ta bata labarin irin zaman da ta yi a gidan aurenta. Ummi ta ce "Babu auren da ba shi da ƙalubale" nan ita ma ta din ga ba ta labarin irin ƙalubalen da take fuskanta. Ummi ta din ga jaddada mata, ta nemi yafiyar dr. Raihan ya kira wayar ummi ya ce yana waje. Noor ta kwashi takalmanta da gudu, ta yi waje saboda farida ta ce ba zata bar gidan ba. Ummi ta je ta ajiye wa rahama kuɗi, suka yi waje. Inteesar ta raka ummi da jariran nan, kamar kar ta bawa ummi su, har ta yi wa ummi alƙawarin zuwa har gida ta yi mata barka. Daga nan suka wuce gidan mariya, tayi murna sosai da sosai da zuwansu, aka yi sa'a dr. Yana nan, ummi ta yi masa maganar inteesar. Ya ce "Inteesar tsakanina da su ai sai ido, ni da ban ishe su kallo ba" Ummi ta ce "Mun yi magana da ita kawu, dan Allah ka yi haƙuri, za ta baka haƙuri ma. Ta fara iƙirarin shan guba ta kashe kanta, dan Allah ka yi haƙuri ka ja ta a jiki dan Allah. Mun yi hira da ita sosai, ta fuskanci ƙalubale sosai a gidan aure, sai dai anty farida ba ta din ga ba ta shawara ta kirki ba" Ummi ta cigbaa da lallaɓa shi, har ya amince. Noor tun da aka saka ranar aure, take wani irin jin nauyin Salim, idan ya zo duk surutun ba ta iya yi masa. Kausar kuma hankalinta ya tashi, noor za ta yi aure ta bar ta, duk samarin nata babu na aure sai ƴan sharholiya. Mariya kuwa, Abdul ne zai kai ta maiduguri, ummi kuma da ita da noor, raihan ya tafi da su bauchi, daga can idan suka kwana biyu su tafi maiduguri. Hajiya Aisha ta din ga murna, dan dama raihan bai taɓa kai mata ummi ba. Ranar da suka sauka da magariba, Hajiya Aisha ta kira wata a waya, ta ce ta shigo yau ga matar raihan su gaisa. Ummi na zaune a kan sallaya tana lazumi, ta ji muryar da ko a mafarki ba zata manta mai ita ba. "Ina amaryar tamu, yau Allah ya yi zamu haɗu, na ji kunya ni ban je ba su gasu a garinmu" Raihan da yake bawa yaransa madara ya ce "Aikuwa dai kin ji kunya yasin, kuma na daina uwar ɗakin da ke" "Amma dai ka san uzurina, bama gari amma tuba nake, dolena na je Kano, Mummy ki taya ni bayar da haƙuri" Hajiya Aisha ta ce "Kun fi kusa ni babu ruwana". "Anty Na'ima" ummi ta yi maganar cikin rawar murya. Na'ima ta waro ido ta ce "Ummi, ummi ke ce" da gudu ummi ta ƙarasa jikin na'ima suka rungume juna, ummi na kuka" Na'ima ta ɗago ta ce "Ummi, dama zan sake ganinki? Kan rasuwar mama duk lokacin da na je gagarawa sai na tambayeki, ace mini ki na kano, bayan rasuwar mama na daina zuwa, ummi me ki ka zo yi nan, zan sake ganinki dama". Mummy ta ce "Ikon Allah, ai ita ce matar babban mutum" Na'ima ta waro ido ta ce "Alhamdilillah ala kulli halin, Allah kai ne abun godiya, ummi na san ba zaki wulaƙanta ba a rayuwa, raihan ummi ƙanwata ce, dan Allah ka ƙara riƙe mini ita da kyau, ta sha wahala a rayuwa" Raihan dai ya din ga bin su da ido, da ƙyar suka bar kukan. Na'ima yaron mijin Hajiya Aisha take aure, shi ne, shi ne babban yaronsa, dan shi ne babban manager, kuma lokacin da raihan ya zauna a bauchi, gidanta yake zuwa yawon cin ɗan wake, suna zaman mutunci sosai. Ummi ta fara basu labarin, gudunmawar da take iya tunawa, da Na'ima ta yi mata a gagarawa. Raihan ya ce "Salma, ku daina tuna abun da ya wuce, anty na'ima in dai ummi ce, ba zan sake barin tayi kukan wahalar rayuwa ba". Na'ima ta ce "Ummi ina Anty mariya?" Nan ummi ta bata labarin suna tare, da yadda gagarawa ta koma. Ai har kusan sha biyun dare, Naima suna tare da ummi, kuma ta yi wa ummi alƙawarin zuwa kano. Kwanansu biyu a bauchi, suka tafi Maiduguri. Mariya sai ɓoye-ɓoye take yi, dan kar a ga cikinta, ita kuwa ummi tuni ta gano ta. Gagarumin taron family aka shirya, ƙaton hall na gaske, da ya haɗa da manyan mutane daga sassan ƙasar nan, wanda suke duk ƴan uwa ne, ba tare da sun san ƴan uwa bane ba. Riahan ma yana wurin, noor ta ce "Yaya ummi, kin ga har da larabawa a ƴan uwanku". Aka rarraba musu sovenir, wanda a ciki yake ɗauke da littafi da ya bayar da asalin su. Asalin mahaifin kakan su mariya ta ɓangaren uba, balaraben ƙasar tunus ne. A yawon fatauci ya auri wata ƴar somalia, ya taho da ita Nigeria, yawon fatauci, jin daɗin zamansa a Nigeria, ya sanya ya cigaba da zamansa a Nigeria, ya auri wasu matan ya hayayyafa. Bayan rasuwarsa, galibi duk suka kama gabansu, ita ta somalia ta koma ƙasarsu, manyan ƴaƴanta da suka riga suka girma a Nigeria, basu bi ta ba suka yi auratayya a Nigeria, duk suna jin turanci, larabci da wasu yarukan na Nigeria. A taron har da ire-iren dangin su na tunusiyya, da wasu daga cikin dangin matar nan ta somalia. Kuma ɓangaren su ummi, suka faɗo a ɓangaren matar nan ta somalia. Ta ƙaton allon majigin da yake ɗakin taron, aka din ga nuna hotunansu, wanda da ka kalla ka san na da ne, sai dai da aka zo kan matar nan ta somalia, duk da tsohon hoto ne mai black and white, sai da na kusa da ummi suka juyo suna kallonta. Kamarta ɗaya da matar, sai dai shi mutumin, brown ɗin gashi ne da shi, haka zalika yaron hannun raihan aiman kamarsa ɗaya sak da mutumin. Raihan ya ce "Allahu Akbar, sweetheart ashe can ki ka tafi ƙarshen dangi, ki ka kwaso mana kamannin larabawa. Su Aiman ma haka" Ummi na zaune ta ga an fara zagayeta ana kallonta, sai larabci ake yi mata a ka. Aka kamo hannun ummi, aka fita da ita kan stage, tare da sake nuna hoton matar nan, a ƙalla kakarta ta huɗu kamanninta ta ɗaukko. Sai da mariya ta yi kukan daɗi, mussman idan ta tuna yadda aka din ga wulaƙanta mata ƴa, da iƙirarin cewa ba ƴar su ba ce ba. Galibin wanda suka zo taron daga somalia, duk brown eyes ne da su, irin na ummi. Sai taro da kallo ya koma kan ummi, aka din ga ɗaukar hotunanta, duk yadda raihan yake kaffa-kaffa da yaran nan da matarsa, haka ya zuba ido yau, dan sosai yaran suke kama da wannan mutumin na tunusiyya. Gaba ɗaya taro ya koma kan ummi, aka din ga basu kyaututtuka da ita da yaran, aka ce har gidanta za a bayar da wakilci, aje a ga in da take zaune, kuma za a bata muƙami a shugabancin jagorancin haɗa kai da tattaro kan sauran iyalan. Ba ummi ba har raihan da mariya sai da aka gabatar da su a wurin, aka gabatar da shi a matsayin MD na Tahir and son's. Ummi ta ga manyan mutanen da ba ta taɓa tunanin ganinsu ba. A matuƙar gajiye ummi suka koma gida, da a ranar raihan ya ce su koma kano, amma gajiyar da suka yi sai da suka bari su kwana. Labari har a gidajen jaridu da radiyo, aka haɗa hotunan ummi da na matar mai suna Alina, da kuma su Aiman da balaraben tunus, yadda yara suka ɗaukko kamanin kakansu na biyar. Kuɗi kuwa ummi ta same su, Alhaji Tahir suna kano ya kira raihan, yana gaya masa suna gida suka ga taron su ummi. Ummi dai a satin sai da ta zama cele, ko ina zancenta ake yi. Kamar yadda ummi ta buƙata, dr. Ya yafewa inteesar kuma ya ce ta cire tunanin tsohon mijinta daga ranta, ta gama idda, zai yi ƙoƙarin ganin ta koma makaranta. Raihan da kansa ya je gidan su, ya samu mami ya ce "Mami, ina fatan zuciyarki ta wanke daga zargin da ki ke yi, na cewar su aiman ba yarana bane ba" "Na ji, ni matarka ce ba na ƙauna, kuma ba zan taɓa ƙaunarta ba" Ya ce "Na sani, ita ma ta gaya mini na daina wahalar da kaina ba zaki taɓa ƙaunarta ba, amma ina roƙon kar hakan ya shafi yarana". Tayi masa banza ba ta kula shi ba. Na'ima sai da ta zo Kano, gidan ummi, har wurin mama suka je. Mariya ta ji daɗin haɗuwa da Na'ima sosai da sosai. An kawo lefen nihal, sai dai wasu abubuwan duk babu, tun da kuɗi ya bata ta haɗa abun ta da kanta, ya zo ya ɗauka ya kai gidansu aka kawo. Sai dai babarsa da yayyensa duk suka ciccire wasu abubuwan, ita kuwa ta ce masa ko dai a dawo da abubuwan da aka cire, ko kuma ta fasa. Ya je gida yana masifa, uwar sa ta ce idan ba sa so, ya je ya karɓo kayan, tun da ba ƴar gold ba ce ba. Aka din ga kai ruwa rana, Mami ta ce su zo su kwashi tsiyarsu. Alhaji ya ce ba za a mayar da shi ƙaramin mutum ba, neman auren ƴar sa a hannunsa yake ba hannunta ba, dan haka ba za a mayar da lefen ba, shi zai sayi abun da babu a saka. Hajiya kuwa suna ta shirin bikin Salim, ɓangaren ummi ma, ita da mariya ke ta shirin bikin noor, farida ta zama ƴar kallo. Rahama ta warke, sai dai ga zawarci, ga inteesar ga kausar duk a gabanta. Ummi da ta je ta ga Iya, ta tsorata. Gaba ɗaya kamaninta sun sauya, jikinta har saɓa yake yi saboda tsabar kwanciya, ba a ɗaga ta a gyara mata jikinta. Ga ɗakinta duk ya rushe, ga kuma abun da aka ce Idris yayi, ƴar sa nana ma ta gudu, babu wanda ya san in da take. Watan ƴan biyu shida, mariya ta haifi ɗanta namiji, murna a wurin dr. Ba a magana, aka saka masa sunan baban ummi. Ummi na ta shirin auren ƙanwa, kuma ƴar da ta raina, sai haɗeta ta take yi da kayan gyaran jiki kala-kala, tare da yi mata nasiha da addu'a. Noor da sassafe bayan raihan ya fita, ta samu ummi ta ce "Yaya ummi, kin san meyafaru?" "A'a" "Muna waya da shi da asubar nan, yake gaya mini wai yayar raihan, jiya da daddare ta dawo gida" Ummi ta ce "Maybe zuwa ta yi ganin gida" Noor ta ce "Akwai magana, gaya mini ne ba zai yi ba, ba ganin gida ta zo ba, ban tambaye shi ba ya fara gaya mini, bai kai ƙarshen labarin ba ya wani maze ya canza labarin. Ni ya fara bani tsoro ma" Ummi ta ce "Tafi can, ba wani tsoro kar ki yadda mijinki ya baki tsoro, abokin rayuwa ne, kuma aure tausasawa ce a ciki. Nima fa kan na yi aure sai da ya fara bani tsoro, yadda ya canza mini, amma daga baya komai normal" Sai dai da azahar bayan raihan ya dawo, yake gaya wa ummi cewar, Maryam ta kama mijinta da wata a gidanta, tayi magana ya kamata yayi mata dukan tsiya, jikinta duk jini ta ɗaukko mota ta taho gida. Ummi kuwa ta jajanta ta ce Allah ya kyauta. An kai ruwa rana sosai da sosai, maryam ta ce ba zata koma gidansa ba, ta daɗe tana zarginsa ba ta tabattar ba, sai da ta kama shi red handed. Ana tsaka da case ɗin maryam, aka yi auren nihal, sai dai a yanayin yadda aka yi bikin, zaka san iyayen mijin ba su da kirki. Aka jinkirta buɗe kamfanin su raihan na Abuja, sai an yi auren Salim. Alhaji ya yanke raihan ya koma Abuja, Salim ya riƙe Kano. Raihan ya ji daɗin hakan, saboda Ummi ta samu chance na reapplying aikin gidan jaridar, da suka taɓa gayyatar ta ya hana. Lokaci-lokaci inteesar na zuwa gidan ummi, ummi kamar babu abun da ya faru, haka za su yi hira su ci abinci, ta kawo alkhairi ta yi mata. Ta kan yi amfani da damar, wurin nemawa farida afuwar ummi. Ba yadda ƴan gagarawa ba su yi da ummi ba, da dr. Akan su taimakawa Idris, a fitar da shi sharri aka yi masa, ummi ta ce babu ruwanta. Dr. Ya ce kar wanda ya sake kiran ummi, ya ce tayi masa wani abu, ba zaman kanta take yi ba, a ƙarƙashin wani take. Tun ana ƙoƙari a kan case ɗin nasa, har aka ɓatar da file ɗin shari'arsa. Ummi da za ta bar kano, gaba ɗaya furniture's ɗinta, raihan ya canza mata. Ta ɗauki nata ta bawa mama, na mariya kuma masu kyau, ta bawa matar yaya magaji. Bikin noor ne kawai ya zaunar da ita, aka yi gagarumin biki, aka din ga taya Hajiya murna, an samu Salim yayi aure. Duk irin tarin miskilancinsa, da rashin son wargi, sai da yaba wa noor, dan ummi ba ƙaramin ƙoƙari ta yi a kanta ba. Farida tana ji tana gani, ga ta amma Abdul, inteesar, ko noor idan suka tashi neman shawara sai dai su nema a wurin ummi. Kuma su ka koma suna girmama mahaifiyarta, dan har gidanta suke zuwa. A danginsu da aka yi taron family, sai da suka cika alƙawarin zuwa gidan ummi, bayan ta koma Abuja. Ta samu aiki, a sashen hausa da turanci na gidan talabijin na Chinese da yake Abuja. Iya ta sha baƙar wahalar jinya, kafin Allah ya karɓi rayuwarta. Duk girman kan farida, sai da ta koma ta kwantar da kai, tana bin ummi, saboda rufin asiri da arziki da Allah ya yi wa ummin. Dan sai da Mariya ta je aikin Hajji ta kai dr. ta kai farida umara. Ta saka raihan ya mayar da Abdul Abuja, yayi aure a can. Maryam ta samu ta sake aure na biyu, babu kwanciyar hankali. Nihal ma haka ta din ga fama da nata dangin mijin. Barin ummi kano, har mantawa take yi da matsalar mami. Noor kuwa lafiya ta zauna da salim, ya nutsu kamar bashi ba,hajiya ma ta riƙi noor kamar ƴa. Ummi ta cigaba da hayyafa da raihan, shima kuɗi ya zauna. Mariya ma yara maza uku ta haifa wa dr. Ummi ta cigaba da rayuwarta hankali kwance, kamar babu wani abu mara daɗi da ya taɓa faruwa a rayuwar ta. Tammat bi hamdillah *DUKKAN YABO DA GODIYA, DA JINJINA DA KIRARI SU TABATTA GAREKA TSARKAKKEN SARKI, UBANGIJIN TALIKAI* *INA MIƘA TARIN GODIYA, DA JIMIRIN BIBIYATA DA KU KA YI A WANNAN TAFIYAR, INA FATAN DARUSSAN DA KE CIKI, ZA AYI AMFANI DA SU, AKASIN HAKA KUMA UBANGIJI ALLAH YA YAFE MANA BAKI ƊAYA, KUMA INA FATAN ZAKU YI WATSI DA SHI* *JAMA'AR DA SUKA BANI TALLACE-TALLACE INA GODIYA, MASU ADDU'A DA FATAN ALKHAIRI, KUMA INA GODIYA* *A MADADIN BRIGHT PENS, INA SAKE MIƘA GODIYATA GA AL'UMMAR DA SUKA BIBIYE MU, A LITATTAFAN CUTARWA! MUNAFUKIN MIJI DA KUMA YI WA KAI. INA FATAN ZAKU BIBIYE MU A SECOND BATCH, DOMIN JIN, ME ZAMU ZO MUKU DA SHI* *Ƙofata a buɗe take, dan jin darussan da ku ka ɗauka, in da littafin ya samu naƙasu da sauransu ina godiya sosai, taku har kullum Aishatu Adam (Ayshercool)* Ayshercool 08081012143 Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels