Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM GODIYA YA TABBATA GA ALLAH DA YA BANI IKON FARA WANAN NOVEL DIN A CIKIN KOSHIN LAFIYA YADDA MUKA FARA SHI LAFIYA UBANGIJI YA BAMU IKON GAMAWA LAFIYA. DA FATAN SAKON DAKE CIKINSA ZAI ISA GA INDA YA KE BUKATAN ZUWA GURIN MATA YAN UWANA ALLAH UBANGIJI YASA MU ANFANA DASHI WANAN PAGE DIN FREE PAGE NE DAGA SHIMFIDAR LABARIN MAI SO ZATA IYA TUNTUBANA DON YIN REGISTER SHIGA GROUP DIN NAGODE TAKU HAR KULLUN ZAINABUN KU Hasken farin watan daya haski taurarin da suka zagaye shi masu fitar da kyalli daga ganin su, Wanda hakan yasa sun kayata gari matuka hadi da sanya zukatan bayin Allah a nishadi Wanda mafi yawan zukata mutane musan man na kauye inda babu wutan lantarki a garesu cikin jin dadi da walwala. Ga iska mai dadi da yake dan kadawa lokaci lokaci gami da kamshin kasa dake tashi gwanin dadin shaka. Ga yara dake jin dadin yanayi duk da dare yayi amma suna waje suna wasan su don babu duhu da zai sa ashige gida a lokacin Tafe take da sauri iskana dan kada ta hannuta rike da farar roba mai marfi da ta dauko nikan awara da zasu soya da safe kafin ta tafi makarantan boko. Tafe take cike da nishadi a zuciyar ta wanda yanayin yake saka ta jin dadi har tana lumshe idunuwan ta. Tana tafe cikin sauri bata da wani guri daya wuce taga ta isa gida ta tatace markaden wanken da ta dauko daga gurin nika. Wasu mutane ne zaune wanda magidanta ne dabian su shine duk dare a shimfida katon tabar kofan wani gida su dinga yan ciye ciye kafin su shiga gida gurin iyalinsu da aka bari da tuwo da miyar kuka bakifi ko nama a cikin sa haka mace zata rufe idon ta taci har sun saba. Basu da wani aiki idan idan sun zauna sai tsirko da sa ido idan mace tafito zuwa unguwan dare zasu fara cewa wance ce matar wani ko diyar gidan wani ne waccan. Idan akwai abin da naki jini a rayuwana shine na wuce wanan bakin daban na yan gulman shiyan mu. Don duk mutuncin da kai masu baka taba tsira a gurin su sai sunyi gulmanka idan kaba da baya. Ina kawo gurin kamar na wuce na share su amma hakan baiyuyuwa don hasken farin watan dake akwai a lokacin. Ina kawowa gurin su na dan duka ina fadin ina aunin ku suka amsa kusan a tare da lafiya kalau. Nasa kai na wuce su nasan cewa ba tsira zanyi ba nima daga kaidin su lokacin. Sauri nakeyi ba abinda ke raina kamar naga nashiga gida na idar da abinda ke gabana lokacin. Ina shiga gida da sallama na samu su Inna zaune tare da yan uwayena suna cin abincin dare mahaifina shima ya dawo gida a lokacin. Gaishe su nayi inna ke cewa dani kin karbo nikan ne nace da ita eh inna. Ban tsaya bana na tube zanin jikina kada ya baci na daura wani kodaden zani nawa duk dashima wanda na cire din kodadde ne sosai amma wanda na daura yafi kodewa sosai. Nafara tatsan kullun wanke dake cike fam ga roba ina jin suna hiran su na manya har nagama abinda nakeyi sai a lokacin na samu saidan kaina. Kwanon tuwo na najawo na tasa a gabana don naci amma ina kallon tuwon naji banajin cin sa sai kallon tuwon masaran kawai nake yadda yai sanyi kalau a kwano har ya fara bushewa daga sama. Muryan mahaifiya na naji tana fadi wai Rahama bazaki ci abincin nan ki tashi ba ? Kin saka tuwo a gaba haka kina kallo yanzu zaki iyacewa yai sanyi bazaki ci ba ki kwana da yunwa. Jin maganan ta yasa na dan kai hannu ga kwanon na fara tsakura a hankali nasan cewa idan naci sai ya tayar min da zuciya na don haka nake tuwo mai sanyi baya bani lafiya. Gashi kuma Allah ya hallice ni a gidan tallakawa tallakan ma na kwarai don ko a kauyen mu mahaifana basu dashi ko kadan. Hakane yasa muke cikin wahalan rayuwa sai nayi dan talla zamu samu abinda mukai lalurar rayuwan mu dashi. Duk da hankan da muke zance Alhamdullahi don munajin dadin rayuwan da muka tsinci kan mu a hakan. Idan na dawo boko zan dauki tallan abubuwa iri daban daban nayau daban na gobe daban. Tun daga kan awara da safe idan na sayar na wuce boko idan kuma na dawo na dauki shimkafa da wake dafafa zuwa yamma wani lokaci na dan je islamiya wani sain kuma na kara fita da tallan gujiya ko rogo ko marau, marau wani lokaci har kwai dafafe nake dauka ina yawata dashi. Duk wani abinda za, a dora min sai Allah yaban sa, a na sayar na dawo a cikin lokaci. Da haka muke samun dan abin rufin asirin mu bamu zama da yunwa a gidan mu. Akan ce talla yana bata yarinya ni dai zance sai dama an tarar da halin baci ga yarinyar don bana tsayawa wasa da maza balle har akai ga min maganan banza. Ko hannu namiji ya rike min zan tsaya nai mai cin mutunci da gobe bazai kara ba ma. Ganin yadda Allah yake ban sa, a ga sana, ata har wasu iyayyen sukan min kazafi wai kila loko ake tsayawa dani aimin juye abani kudi ko suce akwai wanda na lakanta da ke bani kudi na cas. Abin basu san daga Allah bane sa, a yake na saka a raina nema wa mahaifiyata zaman lafiya a dakin ta. Kishiyar Inna ta takan ta faman sake magana da diyan ta don su basu da irin hazakana ta ko ina. Duk da ba wani issashen karatu nake samun yi ba amma kuma Allah yabani kokari ga karatuna na boko da na mahammadiya din. Don ba, a taba mayar dani baya ba ga karatuna shiyasa ko yaya ne nake dagewa naga naje kowani don na dan samu. Duk da mahaifin mu baison tallan mu dole ne yasa yake bari don idan yai magana yasan amsan da zai samu gun uwayen mu akan tallah. Wata rana an kawo mai kara hafsat diyar kishiryar innata yashigo gida rai a bace yana fada sai cewa Mama tayi. Yo idan basuyi tallaba kan mu zamuci mayye amfanin diya mace a gare mu idan ba tallaba damay zamu tara masu kauan aure ga lalurorin da baka iya tsare muna. Ka kwaso mu ka cika a gida kamar zaka kai kurmi sai diya muke zubawa ba wani tallafi a gurin ka. Baba yace amma saboda Allah ko ban iya tsare maku komai ai baikamata ace har an kawo karan yaran nan ba gareni kan talla. Mama tace idan baka son suyi talla sai mu gani a kasa kaga sun huta muma mun huta. Su yan gulman da sukazo fada maka ga aibun su ina duk karkaran nan ba gidan da yaran su basu talla. Murmushi yayi kawai yace lauratu wata rana zaki gane magana ta gaskiya ne, idan yaro yayi ba daidai ba har kasamu mai fada maka gaskiya kamata yayi ka tsaya ka duba baka hau fada ba. Tace ai dole na hau fada tunda anzugaka kashigo zakai mun tujara a tsakar gida haka. Ba lawisa ce kawai ke tallaba a gidan nan amma don ana hassada da ita andauki tsana an sakawa yarinya ita kadai. Fita yayi daga gidan don baida tacewa don mama ba wani power yake dashi ba agurin ta. Mahaifiyana ma haka take zaman hakkuri da ita tana binta don azauna lafiya kawai. ****** ********* ****** Na dawo daga makaranta ke nan ina kokarin cire uniform dina naji murya sanusi dan gidan mama Altine makwabciyar mu yana sallama. Tsarabane ya kawo gidan mu yana fadin gashi inji maman shi tace yakawo muna wai anty Sa,ade tazo daga birni. Sabulun wanki ne clean da biscuits a cikin wani roba aka sako mai kunsan halin yan kauye da kara ko yaya abu yake sai makwabci ya san ma makwabcin shi idan yana da dan yawa. Da sauri na daga labulen dakin jin sunan wace akace tazo daga birni yar gayu ce ta karshe don ko maganan ta abin sha, awane gata da son mutane bata kyaman yan kauyen mu ko kadan. A yadda naji wai diya take ga mama altine yar kaunata ce ta birni da ta rasu su biyu ne a gurin iyayyen su shine da mahaifiyan ta ta rasu ta mayar da mama Altine kamar uwar cikin ta. Da sauri na daga labule ina cewa anty Fara tazo sanusi ? Yace tazo har ta haihu da yar ta maikyau da sauri na juya na jawo tsohon hijjab dina na saka na suri yan tsufin takalmana da duk sun sude gurin yawon talla ba asai min wasu ba nafice daga gidan mu. Ina jin Inna ta kwada min kira da ke ke don bata kiran sunana saboda ina yar fari gurin ta. Ban tsaya ba don nasan kiran akan dafafan gyadan da aka dafa min ne nazo na fita dashi. Ina shiga gidan na samu ta dauko buta zatai alwala sai naja na tsaya don kunya. Saboda ina matukar jin kunyan ta haka kawai tun ina karama idan tazo ina like da ita kafinta tashi zaka gane don ina shan kwalliya da kitso irin na yan birni kalakala akaina. Don Allah ya yalwantani da yawan gashi mai santsi da tsawo gashi baki amma bai samun gyara don ba lokacin yin hakan gare ni saboda busy akan talla tun ina yar ficiciya ta. Idon ta yakai gareni tace cikin murmushi a, a wa nake gani haka kamar yar Rama rama na ? Nabi bango ina karasowa inda take duke zata fara alwala a lokacin mama altine tafito daga dakin ta na bunu take cewa itace mana. Ba ta girma ba yanzun kuma kunyar ki take ji tagama maki fitsari a kwance nace kai haba mama ai dane wannan. Ida mama take tsaye rike da yarta na karasa nace mama diyar anty ne wanan ? Ina mika hannuna ina kokarin karban yarinyar dake dauke a hannuta nace mama yar anti ne wanan mai kyau haka ? Yarinyar sai kamshi takeyi kamar kamfanin turare a jikin ta nace kukan kunji dadin ku komai naku na birni ji yar nan mama kamar baturiya. Dariya magana ta yaba anty dake alwala batai magana ba sai da ta gama alwala tana mikewa take cewa ni dai Rama baki gaishe niba fushi nake dake ai. Nace don Allah anty kiyi hakkuri idan kinyi fushi dani ai na bani. Dariya ta karayi har hakoran ta na makka ya dan baiyya na a fili tace kai Rama har yanzun dai kina nan da shirmay ki ashe . Yanzu Rama na kece kiga girma haks idan wani guri na ganki ai bazan ce kece ba haka. Kunyan maganan ta naji mama ce tace ga ta saura aure ta girma abinta fa bakiga har ta wuce kidan dangiba komai acan acan da ita. Don ma Asiya tana azama mata talla ba hutu gareta ko kadan ta samu yarinyar ta mayar kamar injin. Mama bata rufe baki ba sai ga kani na Nura yashigo yana cewa Rahama Inna tace kizo wai gyadan da kika bari wa zai fita mata dashi ? Mama tace bakaji ba maganan da nake fada maki ni nasan ba, a rasa abin fitarwa ai yanzun haka. Nace kace gani tafe zan ga antyna ne tukun kafin nazo yaron ya juya yana fadin wallahi zanje nace kince bazaki zo ba. Ban damu da zancen shi ba nabi bayan anty zuwa cikin dakin mama dauke da yarta a hannu na. Na zauna nan na shantake gurin kallon yarinyar ina mamaki irin kyaun da Allah yai mata haka. Har ta idar da sallah ina zaune mama tana waje tana dan aiyukan ta na tsakar gida. Tana idarwa ta juyo gareni bayan ta shafa tana cewa Rama ke nan kinga yadda kika girma kuwa ? Na kara jin kunya ina sune kaina ajikin yarta wace nake jin dadin kamshin ta sosai har cikin raina. Tace ina fatan dai kina karatun ki ko har yanzu baki daina ba ? Nace lah anty banayi maki alkawarin zanyi karatu ba kince fa idan nai karatu watarana zan kai ki nima. Tace kwarai kuwa Rama kilama har kifini haka muke fata insha Allahu nace cikin dago kaina ina mamakin abinda tace. Anty wane ni, ni dake kauye kullun talla bani da hutu idan ba dare yayi ba na kwanta. Tace to kin san abin Allah ne ? Nace kamar wata babba cikin girgiza kaina da a, a amma gaskiya da wuya hakan ya kasan ce. Tausayin yadda yanayina ya kasance da nake maganan taji har a cikin ranta ga yarinya har yarinya amma babu wadata ga kauyanci zai illanta ni. Gafara dai masu gida muryan mama Laure ne kishiyar inna ta tayafo tabiyo ni da cin mutunci har gidan mama altine. Sun gaisa sama sama da mama Altine take cewa halan mutumiyar taki tana ciki ko ? Da hannu tai mata nuni da dakin take cewa tana ciki kuma kun san tunda Sa,ade ta sauka garin nan kuda samun hankalin Rahama kuma sai baba yagani sai saade tabar garin nan. To in ba shedana irin na Rahama ba ace uwarta ta dafa mata sana,a amma tanajin ance saade tazo ko minti daya bata kara ba ta suri takalman ta tayo nan. Daga cikin daki ina jin ta na balai akaina akan an aiko nazo naki zuwa na lake a nan, na dan turo bakina nace ni ba inda zan tafi ina nan yau da Anty ina zan tafi nabar wanan yar mama altine dama ko goyo bata iya ba tabarta a kasa. Kai Rama yanzu mama din ne bata iya goyo ba ni waya goyani har nakai haka yanzu ? Lokacin mama altine da mama suka shigo dakin mama tace wai mai take fadi ne ? Dariya ya kama anty sai kyalkyala takeyi nan dai suka gausa da mama laure ta hauni kuma da fada. Muryan anty ne ya katse fadan ta tana cewa wai gyadan har na nawa ne mama ? Tace kai yana da yawa fa kin san sherin Rahama yawa gare shi idan ta tashi amma ta yaya uwarki tayi sana, a zaki zo nan kiyi zaman ki. Maimakon na tashi ga mamakin mama ko har tai min zan bar duk abinda nakeyi na kama wanda ta sani amma yau sai gani zaune ko gezau ban yi ba. Rahama wai ba dake nake magana bane mama ta kara nanatawa cikin hasala. Anty Saade tace gyadan na nawane mama ? Tace zaikai na jakka biyu fa idan taso sayarwa ko da dan kai sama. Mikewa tayi zuwa inda hand bag dinta yake ta dauko kudi a ciki dubu daya mikakan ta tana cewa ina gashi da na yau da gobe don Allah abar min Rama na ta huta mama. Harara mama laure ta watso min daga gurin da nake tana cewa dama haka kike so ai. Ji fa mama ita da ko yaushe take cikin kyashewa tallana shine wai take fadin haka don taga kudi. Ta juya tafice daga gidan tana zuba magana tana fita nace lah Anty aida baki bata ba baki san halin mama laure ba ko ? Yanzu bai wuce tabawa mamana jakka daya tace ai shi kika bada, daga inda mama altine take tace karamin aikin Laure ne hakan. Tace to bari idan zaki wuce nabiki a boye sai kikai wa inna ta rike a hannun ta bashi ke nan ba. Aiko kamar na sani hakan tayi don tana shiga gida dakin ta ta fada ta dauko jakka daya da rabi tabawa Inna na wai inji anty Sa,ade tace arabawa yara gyadan ta saye sana,ata na kwana biyu. Inna tace kai ita bata gajiya da dawainiya ne da yarinyar nan idan tazo gari ko yaushe cikin dawainiya take. Allah ubangiji ya bar zumunci baki mama ta tabe tace kwadayi dai madudin wahala ne karamar yarinya tasan ta lakewa masu hannu da shuni tun tana kara ma idan ta gan su gashi har girma abin yabita Allah dai ya kyauta kawai. Ban shigo gida ba sai da magariba koshi don nasan baba idan ya dawo ban gida zai min fada ne shiyasa. Don mu kadai yake da ikon yaima fada a zauna lafiya a gidan batare da anyi tada jijiyan wuya ba. Nashigo ina dan rabe rabe na samu suna sallah don haka nima suri buta na wuce zuwa alwala. Na idar da sallah Inna tana zaune tana addua nace Inna nawa mama ta kawo maki dazun. Tace ina ruwan ki ai a gaban ki aka bata takawo min ko don naji nai saurin cewa eh jakka biyar ba sabuwar ta fil a mike. Humm din da naji Inna tace yasa nagane anyi cuta ke nan kai mama dai ba, a girma wallahi na fadi a raina. Kudin da anty taba sabbi fil ban ko tsaya kidayawa na fitar daga haban zani na dana kulle nace ma inna ta Inna gashi inji anty tace na kawo maki. Don na fada mata mama bazata baki su duka ba dazun shine tabani wanan nakawo maki. Bakina Inna takaiwa duka tana cewa kika aibanta uwarki agaban bakuwa aiko yaya take dai uwarki ce ita din. Bakin nawa da Inna ta daka na dafe cikin jin zafi amma hakan bai hanani kokarin mika mata kudin ba da nakeyi. Takarba da mamaki tare da kirgawa ta dago da sauri tana cewa ke yar nan har jakka hamsi ne fa tabaki ? Nace ban kirga ba ta daice na kawo maki kiyi amfani dasu kafin ta wuce na fara talla. Take cewa ikon Allah ita din aikin may takeyi haka har ta samu wanan kudin masu yawa take kyauta dasu ? Nace Inna ba, a birni take ba ance kudi abirni banza ne duk wanda yaje fa sai yai kudi a can. Tace ke rufa min baki da maganan wautar ki can a ina kika samu wanan labarin karyan haka ? Idan da banza ne may zaisa wasu suje su dawo tsula yadda suka tafi ? Mahaifinku sau nawa yake zuwa birni bai samo ba da zaki fadi hakan. Nace to inna kin sani ko baiso ne shi yafi son zaman mu haka ? Kallon takaici tai min tace ke kan ban san ranan da zakiyi wayau ba wallahi. Nace killa sai na girma ko Inna ? Wani irin takaici na kara bata tace to ai sai ki tsaya har ki girma din sai kiyi wayon. Sai dan shiru da ya biyo baya a dakin can tace ki saurare ni da kyau kiji abinda zan fada maki. Na gyara zama ina fuskantar Inna na tace banda kwadai banda roko don yafi komai zubar da mutuncin mutum da sauri. Ki kawar da idon ki ga abin duniya sai ki zauna da kowa lafiya a duniyan nan. Allah ne ya hada ki da ita jinin ku ya hadu haka don haka ni bazan hanaki hurda da ita ba don ban taba jin wani abin assha daga gare ta ba banda alherin ta da nake ji a gurin uwarta ko yaushe. Don haka ki kama mutuncin kan ki don Allah ki rufa min asiri ni da mahaifin ki. Inda sabo na saba jin nasiha irin haka ko yaushe a bakin Inna ta don haka wanan ba bakona bane sai ma cewan da nayi. Ai ina dazun da mama altine ta dafa mata kaza tace nazo naci nace da ita na koshi. Tace kin daiji na fada maki don ke har yanzu naga ba wayo ne dake ba. Haka ya kasance tsakanina da Inna ta har mahaigin mu ya dawo daga kasuwan kauye da yake zuwa tallan buhun shi na saka kayan masarufi aciki. Lokacin Inna ta fita don itace da girki ranan idan tana girki dakin mama laure nake kwana haka ma idan mama laure ce da girki dasu Lawisa muke kwana a dakin Inna ta. Ba zancen awara da safe don haka na fito daga dakin Inna ina gaida baba da dawowa. Yace a, a Rahama yau ba atafi kai nikan bane nace baba ai bazan yi tallah ba har kwana biyu. Yace ikon Allah damay ya faru kuma sarkin tallah ? Nace baba Anty Sa,ade ta zo na gidan mama altine itace ma tace na zauna gida har sai ta koma. Yace a, a kice min uwar dakinnki ko uwar goyon ki har yanzu ashe ana tare ke nan ? Mama na zama take cewa kai kwadai bayi ba wallahi yanzu kaida kan ka kake koya mata harkan kwadayi ? Ashe bari nabar ganin laifin uwarta ita kadai abin ruwan dare ne ashe Allah ya kyauta. Muna nan maji magani wai an bizzine tsohuwa da ranta. Yanzu may ye abin kwadai a furin nan ina dai jinin sune ya hadu da yarinyar nan tun tana karama suke tare ? So kike nace ta daina kulata ko may kike son nayi Allah ne fa ya hada jinin su. Yara nawa ke garin nan wakikaga ta mama idan ba ita ba da Allah ya hada jinin su. Yanzu dai ni may nace kuma wanan ai koyawa yaro kwadaiyin abin duniya ne ba akidar alheri bane . Baba bai kara mata magana ba yajawo turen abincin shi kawai ya soma ci ranshi a bace Da dare na shiga kwanciya har na kwanta a saman dan keson tabar da nake zuwa kwana dashi naji mama laure tana tashina tace ke Rahama tashi muyi magana. Wallahi idan naji kin fadawa sokuwar uwarki ko nawa aka bani gidan Altine sai rayuwan ki ya baci a gidan nan kin dai san halina wallahi ko. Nace ni mama ai ban san ma ko nawa tabaki ba balle na fadi tace munafuka kece baki san kudi ba ? Kin dai ji abinda na fada maki saina lahira yafiki jin dadi wallahi ko. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU MARICCIN KAN DUTSE, , , WANAN LITTAFIN NA KUDI NE CIGABAN SHI SAI DAI ZAKI FARA KARANTA FREE PAGE DINA A KYAUTA YAR UWA IDAN KINA DA RAAYIN HAKAN. Yau da sauri na shirya zuwa makaranta tunda ba tallan safe gareni ban tafi ba sai da na leka gidan mama Altine tukun. Ita kadai ce a tsakar gida tana yan aikace aikacen ta muka gaisa nace ina baki tace wai ke ma kin san ai basu tashi da wuri haka. Tace yau da wuri haka za, a bokon ? Nace mama kin manta anty ta saye tallen nawa sai hutu yanzu tace humm hakane fa na shafa sam. Duk da ance suna barci bai hanani lekawa ba dakin nasu suna kwance saman gadon mama da yasha shimfidan sabon zanin gado. Barci suke hankalinsu a kwance na dan dade tsaye a kan su ina kallon su cikin sha, awa komai nasu gwanin ban sha, awa dashi. Najuya nafito mukaci karo da mama zata shigo dakin tace ai har ina batun shiga na samay ki kada ki tayar dasu da ga barci. Nace kai haba mama, may zai sa na tayar dasu suna hutun gaji tare da su. Nace zan tafi mama sai na dawo muryan ta ne naji tana cewa yaki Rahama. Najuyo zuwa inda take tsaye tana kokarin kwance haban zanin ta data kulle kudi a cikin sa . Naira ashirin ta miko min tana cewa karbi wanan kyaci tara dashi indan kin tafi can. Take fuska na ya sauya nace cikin marairaicewa mama da kibar shi wallahi yau ai Inna ta tabani Naira biyar zai isheni na sha ruwa a can. Tace ruwa kawai Rahama bayan nasan ko karyawa bakiyi ba kika fito daga gida? Nace dimamay mama laure tace baida yawa don haka su dake gida zasu ci abinsu wai idan naje can ban rasa abinda zanci. Mama Altine tace shine kuma ita Inna ki ta baki Naira biyar kacal ki sai mai da naira biyar din. Muryana na tausa kada wani yaji ni nace mama kin san idan tabani da yawa mama fada take mata wai tana lalatani da yawa shiyasa mama ta kafa doka wai Naira biyar kawai za, a dinga bani ya isheni . Kai amma dai laure takai muguwa wallahi nace mama barin tafi kada na makara yau ina son naga assymbly don na manta yaushe rabo da ayi shi dani. Najuya ba tare da na karbi ashirin din hannun nata ba nafice daga gidan da sauri tana kirana amma bai sa na tsaya ba . Koda na isa makaran ta nayi dace da abinda nake son gani ina shiga ana kada kararawan assymbly yau ba duka gare ni zan kuma ga assymbly din mu. Kowa ya ganni sai mamaki daga dalibai har malamai suna cewa, sarkin late yau lafiya kuwa ? Sai dai nayi masu murmushi kawai na wuce haka muka zauna nai matukar jin dadin samun darasin safen da nayi yau. Allah Allah nakeyi a tashi daga makaranta na koma gida na samu anty na yar birni don ni gaskiya ban gajiya da kallon ta ita da yarta mai kyawo. Har zuwa lokacin tashi ranan saurin da nayi har yafi wanda nakeyi zuwa daukan talla na a kullun. Na shigo gidan mu da hakki alaman nayi gudu ko sauri a lokacin sai dai may na samu a gidan mu mama lauratu na sana,an fadan ta da ta saba yi idan fitinan ya motso mata. Duk da har taci ta sude babu mai biye mata indon ta inna tace zata iya kwana tanayi bata tanka mata ko uffan. Sai dai idan baba yana gida ne wani lokacin zaibi ta kanta suyi ta tonon asiri a junan su. Wanan haushin da naji tayi yayi dalilin da na fasa shiga cikin gidan namu na dan daka ta ina sauraren ta don naji akan may take fada kuma. Daga inda nake sauraren fadan nata na fahinci fitina take da Inna na wai akan kudin da aka bani inna bata nuna mata ba taba babana ya dan kara jarin shi. Sai zuwa can naji muryan Inna tana cewa yaya kiyi hakkuri dan Allah ni bawai na nuna bakece kika haifi Yarinyar nan ba . Naga kin san da zancen ne tunda boyar Allah nan a gaban ki ta furta cewa ta dauke ma yarinyar nan yin sana,an ta. Ai fa yanzu sai kiyi kwana nawa ne idan bakin ciki kikeyi dani akan ki zai kare Asiya don wucewa yar gidan Altine mai kuli zatayi. Kuma kowa komawa zaiyi ga turken shi mai cabo ai har kudin nawa ne da suka rufe maki ido haka ? Maimakon na shiga yadda nai niyar yi da farko sai kawai naja na juya zuwa gidan mama altine mai kuli. Tafiya nake kamar banda lakka a jiki Allah ya taimake ni naga kanina zai shiga gida na mika mai jakkar makaranta na nace ya kai min dakin mu. Da sallama na shiga gidan suna zaune su biyu ga kwanon dan wake da mai da yaji tana ci cikin irin cin abincin su na yan gayu. Mama altine ne tace a, a yar gidan anty har andawo bokon ke nan nace eh mama cikin kada kaina. Zama nayi tare da gaishe su naci gaba da tunane a cikin raina wai yaushe ne Inna ta zata samu saukin rayuwa ne agidan mu? Duk abinda tayi batayi daidai ba gurin mama, damu da ita duk bamu da wani yancin kan mu sai abinda mama laure tace. Na sauke ajiyan zuciya ina fadi a raina yaushe ne wai muma zamukai ga namu yancin kan ne agidan mu , ? Jin ajiyan zuciyar dana sauke karama dani yasa hankalin su ya dawo gare ni mama altine da anty sa,ade har suna hada baki ita mama na cewa may kuma ya faru yar gidan anty ita kuma nacewa Rama na duk gajiyan ce haka wai ? Nace a hankali mama ni halin mama laure ne yake min ciwo ace kullun duk abinda Inna tayi ita a gurin ta ba daidai bane ? May kuma ya faru yanzu? Nace mama bakiji haushinta bane har nan gidan wai akan kudin da anty ta bani shi ne Inna nasan tabawa baba kudin ne ga Mama can ta saka inna a gaba da masifa akan may tabashi kufin bata bata ba. Ikon Allah waiko laure na da hankali kuwa mama altine ne ta fadi hakan. Nace mama akullun wanan halin na mama ya damu na inna sam bata da sukuni a gidan mu. Wanda kinga abin har muma ya shafe mu muda ita bamu da incin kan mu ko kadan. Nan kata tunanen yaushe ne wai muma zamu zauna kamar kowa agidan. Nace mama fa har ikirari takanyi da cewa sai dai mu zauna a haka mu da uwar mu don bazata zauna tana ganin ita da mijin ta ba wasu banza can suzo su shige mata gaba. Duk da Inna tana hakkuri da ita kalamanta badu damunta nake gani amma baisa mama ta watsar da wanan halin nata ba har zuwa wanan lokacin. Wai mama kin kuwa san duk saba, an da nakeyi kudin mama laure ce ke karbe su a gurin Inna da sunan wai zatai min tari ko kuma tace wai ta ara. Kuma bawai zata biya bane sannan ni har yau banga wani tari da ake min ba agidan. Wani lokaci idan tace abata kudin na hana don sai yakai ma bamu da jarin da zamu juya awataran. Data gane ina hanawa yanzu shine take cewa idan ina ganin nai wayo ne na kama kaina don dagani har uwana da uban nawa bamu fi karfin ta ba don haka in ina shiga hankalina mu zauna da ita lafiya nayi . Idan bazan iya ba wallahi ko yaushe kofa a bude yake mina dagani har Inna muyi gaba. Anty ce tace kai ashe haka take ina ganin ta a hakan ? Mama tace wa laure da kike gani bata da dama komu makwabta sai munkai zuciyar mu nisa da ita ake zaunawa lafiya. Nace muma hakan muke zaman takura da tsangwama a tare da ita kullun sai ta kirkiri sabon jidalin da ta dora akan Inna don dai ayi fitina kawai. Anty tace kuma shi mahaifin naku duk yasan da haka Rama ? Nace cikin kada kai kamar wata babba dani yasani mana anty may zaice tunda baya iyayin musu kullun da ita baya kuma jayayya da ita sai abinda tace don azauna lafiya. Sai idan abin ya ishe shine yake magana kuma maganan ba amfani zaiyi ba ai. Balle ma yanzu nagane baba yana matukar gudun bacin ran mama sosai sai abinda takeso akeyi agidan mu. Don kinga kan tallah mu ba yadda baba baiso mu bari mu kama boko da islamiya ba amma mama ta hana. Don dai kawaiba zauna lafiya a gidan da ita ko kwanaki an kawo karan Lawisa amma mama ra hana yayi magana dole yai shiru ya kyale ta hakana. Anty tace Allah ya kyauta ni dama zai ban ke mu tafi birni muyi zaman can ki shiga bokon ki yadda kike so daya kyauta min. Nace wai anty idan na tafi birni na zauna waye zai kulla min da Inna ta ko kudin sayen sabulu kawai ya isheta ai. Mama tace balle ma laure bazats bari ba dakike ganin ta na tunda ba yayan tane zaki dauka ba. Ai duk wanan fitinan da kikaji tanayi da ace tare da yarta kike da baza, a ji shi ba sam. Halin Laure sai ita dubi yadda Asiya ta koma kamar ba ita bace ta tashi a garin nan abin sha, awa ga kowa. Amma mahaifinta ya hana ta zabi yacs sai malam Abubakar zaiba don zumuncin dake tsakanin shi da mahaifan ta. Yarinya da gatan ta amma dubi yadda duk ta zuke takoma kamar ba Asiya ba, lokacin da tai yan matancin ta babu wanda zai ganta bai kyasa mata ba. Yanzu gashi tun auren ts gidan nan dubi duk yadda ta tsiyaye babu komai gajikin ta sai tarin hakkuri da zaman sunnu kawai. Anty tace mama ashe mahaifiyan ta takwaso gurin kyau ke nan ? Kai wane ita da kyaun Asiya wanan da bata gyara kai zaikai wata biyu ba kitso kafa ba lalle kamar ba matashiyar budurwa ba da ita ? Nace kai mama duk wanan gyaran da nakeyi zakice haka ina wanka fa sau uku ko biyu a sati 😆 Dariya ne sosai ya kumshe anty tace kai Rama na wankan ma har sai an kidaya kwanakin yin shi kuma ? Nace anty ai nayi kokari bakiji har ana yaba tsabtana ba don fa ina da tsabata wasu ke sayen sana, ata sosai. Dukan su dariya suke min akan maganata niko ko ajikina ban damu ba sai mama ce tace nidai bari na zubo maki abinci kici da wanan bakin surutun naki haka ? Na gyara zama ina ta kawo min dan wake ranan har da ruwan goran da anty ke sha nasha azatona yana da zaki amma sai naji shi salaf kamar ruwan rijiya. Ina gamawa na gyatse dama nasan ko naje gida tuwo ne zai tare ni don haka ban rage komai ba harda sude kwanon nayi. Anty tana ganin haka tace dani ko a karo maki ne idan baki koshi ba nace sai zuwa anjima Anty yanzun kan Alhamdullahi. Tace oya zo na banye maki kanki nai maki kitson shi duk da take na manta ko yaushe rabona da yin kitso a duniya. Ina bude kaina saida tai wani irin ihu tace Rama subbahanallahi kanki ne haka nace shine anty yayi yawa ko ? Tsuki naji taja tace haba Rama kamarki kuma kinkai har secondary ace baki gyara jikin ki sai yaushe zaki koyi gyaran jiki kuma ? Haka zaki dingayi agidan mijin ki idan kinyi aure ki dinga zama da kazanta yace kina wari. Kunya maganan ta yabani na tsune kaina akafa nace aure Anty ina nai aure wazai zauna da inna ta yana taimaka mata da diban ruwa da tallah kuma ? Kinaji na idan kina son mu shirya dake daga yau duk sati ki dinga kitso da kunshin da mama tace idan ba haka ba wallahi wanan kazantan zai sa mu bata dake. Nace insha Allahu anty zan dinga kitso bani son mu bata dake ko kadan a rayuwana. Tace dakin kyautawa kanki haka taci gaba da sance kan har wani gari ke zuba a cikin don dankarewan dayayi. Dama asalin haduwan mu da ita shine yawan gashin da nake dashi. Watarana tazo garin inna takaini an min kitso ya sauko har bayana taga mun shigo gidan mama Altine sayen mangyada take cewa kai wake wanan fine girl din a kauyen ga kyawon yarinyar na ace a birni kika fito da kinsha gyara yarinya. Tace zo nan ban mata kiuya ba nazo ta rugumay tana cewa kina so na na kada mata kai alaman eh. Tun rana muka shaku da ita da zan koma ta saya min biscuit da sweet naje dashi gida amma mama tana gani ta kwace ta rabawa yayan ta lokacin ni kadai ne a gurin inna ta ban da kanne baya na. Wassh nace don jin zafin kan da anty taja min da karfi tace yaya akayi kuma nace babu komai idanuwa na sun ciko da hawaye da zata gani kila zata barni don akwaita da tausayi sosai. Tana gamawa ta sa asayo mata clean ta wanke min kan tas dashi sai da naji wani iska yana shiga na sosai acikin kaina. Mun zauna tafara min kitso ke nan sai ga Rakiya diyar mama tashigo babu ko gaisawa tace to akwadaita mama tana kiran ki. Nace cikin daure jin zafin kitso kice kitso ake min gani nan zuwa idan angama min. Tace mama tace tana kiran ki shine zakice wai ana maki kisto ne barin je na fada mata kince bazaki zo ba. Anty tace bari na sake maki idan kin dawo sai mu karasa ko ? Nace taci gaba don nasha zafi daya yanzu idan na tafi bazata bari nadawo maza ba. Ban tafi ba Rakiyan ma bata dawo ba daga sakon har aka gama min kitsona nai wanka wasu kaya daga cikin tufafin ta sun min yawa sosai amma haka tasa na saka su na fito wata shar dani. Sai da na gama komai na kama hanya na nufi gidan mu nan na tar da balain dake jirana na mama. Ina sallama tako haukaina da balainta tana fadin mai kwadai baji dadi ba wallahi yanzu don kina isar sa ke kinga gurinci shine na aika kizo kikace ace min bazaki zo ba sai kin gama kwadayin ki ko. Bari mahaifin naki ya dawo gida yau ai ayita akare don wanan abin baku kadai da uwarki za, a zaga ba harni sai an hada dani an muna suna indai kauyen gane. Kuma ki tafi ga diban ruwa can yana jiran ki tunda babu bawan ubanki da kika aje da zai debo maki ruwa ai aiki dashi. Ban tanka mata ba don nasan ko na fada mata yadda mukayi da Rakiya ba yarda zatayi ba. Kayan jiki na na cire na daura tsuman zanina na fara diban ruwan don nasan idan banyi har inna ranan sai ta yabawa ayya zaki. Saida na cika mata randunan ta na fara cika na Inna na don ban isa na fara zuba a namu ba naja bala,i kuma. Ban koyi rabin randan mu ba sai ga Lawisa tafito da roba tana diban ruwan rabi a cikin roba rabi a kasa . Kasa daurewa nayi nace haba lawisa wanan ai hainci ne idan ma zaki dibane ai ki tara roban dakyau mana amma kina diba kina zubarwa akasa don baki san wahalan diban ruwan ba ko ? An zubar din ko zaki hanani amfani da ruwan ne kuma tunda wuyanki yai kwari yanzu ya isa yanka don kina ganin kina hurda da yar birni ana hure maki kunne kiwa mutane rashin kunya. Nace ashe hurda da yan birni isa ne ai ban san kina hassada da hakan ba sai da kikai magana yanzu? Kafin tabani amsa sai ga mama tafito daga dakinta tsagal tace eyye Rahama lalai kuwa ashe wuyan ki ya isa yanka yanzu yarki kikewa shamaki akan ruwa don ta diba. Saboda kina kurin kece kika debo ko may ai kafinki fara diban ruwa su suka fara kuma akai amfani dashi. Kamar ince bako ga Inna ta ba don da wayo na akai fadan ruwa agidan mu wai don may babana yake debowa innata ruwa. Kuma alhalin ita bata bari yaranta su diban ma Inna ruwa anata randan haka inna zatai ta zama ba ruwa koda kuwa girkin gida ne zatayi. Tun ranan baba bai sake diban wa inna ta ruwa ba sai dai ta dinga tarataran yaran mutane suna dibo mata. Tun ban kai munzalin iya jan ruwa arijiya ba dole haka na fara zuwa bakin rijiya wanda yaga Allah ya taimaka ya zuba min har na samu Inna ta dan samu na aikin ta. Muryan mama ne ya katse min tunane na tana fadan ta da cewa yanzu don kinga kin girma kin iya hassada da kyashi irin na uwarki shine zaki hana ai amfani da ruwan ko ? Ni dai ban kara magana ba na fita raina bace daga gidan sai magariba na gama diban ruwan a gurguje na shiga naiwa anty sai da safe. Tana ganina a jiki cikin tsuma babu dadin gani tace yaya haka kuma Rama na ? Na turo baki gaba nace ba mama bace saida tasa na cika duk kayan ruwan dake gidan mu kuma ban gama ba Lawisa tana diba tana zubarwa nai magana kuma ta hauni da zagi wai don naga ina hurda dake ne nake wa mutane rashin mutunci. Kai ikon Allah yanzu har nima na samu shiga cikin ran mama daga zuwa na ko ? Nace ai har yaranta bakin ciki suke da ke wai don naga kin fito daga birni nake lake maki ina kwadayi. Allah sarki ni may nake baki da zasu ce haka Allah dai ya rufa asiri wallahi shaf na manta da zancen ki da sun ga aikin gaiyya kuwa. Nafita da sauri na koma gida kada aga na dade inna tai min fada don ni ko tallah naje bani kai magariba koda kuwa ban sayar ba ne. Sai bayan sallah ishai baba ya dawo daga kasuwan kauye yana jaye da wani dan karamin rago da yasayo daga can kauyen da yatafi. Baya ya daure ragon wanda ya cika muna gida da kuka irin na dabbobi kowa yasan an shigo da dabba. Mama tafito daga dakinta tai mashi shimfida inda yake zama yaci abinci ya huta idan ba zai fita ba hiran dare wanda shi ba kasafai yake fita ba don yafi fita ne idan suna siyasa ko wani abu mai muhinmanci a garin. Bayan ya zauna muka dinga fitowa muna mashi sannu da zuwa wanda zance kusan mu yan dakin mu ne keda wanan halin. Sai nice nafito karshe don ina sallah koda ya dawo lokacin na gaishe shi na juya zan wuce ne naji Mama tana fadin dama kai nake jira ka dawo tun dazun. Yace to ai gani kuwa Allah ya dawo dani lafiya cikin ku tace dama akan Rahama ce . Don dakai da uwarta kun daure mata gindi akan bakuwar birni da tazo don kunga kudi idanuwan ku sun rufe . Shine take ganin kowa tana iya takawa ta zauna lafiya yanzu wai har na aika don ta samu daurin gindi daga uwar ta tace min wai bata zuwa tana kitsone. Ni zata gwadawa kitso tunda tun uwarta bata san duniya ba nakeyi a kaina. Yanzu dai may tayi baba ya katse dogon sharhin data fara cikin tambayan ta ba, asi don baison suyi jidali daita gashi ranan itace da girki a gidan. Yasan idan yaja zance cikin shi tayi don daren shi ke nan zai kashe a ranan. Tace ruwa fa zata debo bayan tasan cewa itace da alhakin diban ruwan gidan nan akanta amma uwarta najin amsan da ta aiko min bai sa ta dauki mata ki ba jifa ? Yanzu ita Asiya da taji abinda tace bata dauki mataki ba akai ? Tace ta dauka ran yar gwal din ta ya baci ita ma nata ya baci, yanzu ta debi ruwan ko bata debo yar kwal uba ?. Tace ta debo amma kuma sai rashin mutunci yabiyo baya nan tai muna tas nida Lawisa wai don may tana wahala ana zubarwa jifa wai aikin gidan ubanta ne wahala ? Ina daga daki daga ni har Inna ta muna sauraren maganan da mama keyi karya da gaskiya . Cikin bacin rai ya kwala muna kira ni da Inna ta bamu dauki lokaci ba muka fito inda yake zaune. Tambayan dalilin dayasa Inna tanajin sakon rashin kunyan da na aikowa mama dashi taki daukan mataki a lokacin. Cikin murya mai sanyi Inna ke magana tana cewa haba malam yanzu don ban da kunya zan saka baki ga maganan yarinyar nan da maman ta ? Aikuma sai ace nayi rashin kunya kuma baba yace ke nan kina nufin karya Lauratu tai mata ba amsan banza ta aiko mata dashi ba ke nan? Inna tace ni bance karya yaya tayi ba dakai da ita sai ku dauki hukuncin daya dace akanta basai kun fada min ba. Au to haka ma zakice ke nan ko ? Inna tace idan ba haka zance ba ni may kake so nace yar tace tana iya daukan matakin daya dace akan ta duk sanda taso. Mama tai karaf tace wace ni na dauki mataki abi gari dani ana nazalunci uwa da yar ta don cin amanan dana iya Sai ranan naji Inna ta ba da amsa mai ingaci da tace uhumm zalunci kan ai sai dai kada a kara don kullun a cikin sa muke raye, sai ranan da mai ramawa zai rama muna idan ba yafewa mukayi ba. Ai Inna ta na fadin haka da ga baba har mama sukoyo cikin ta da masifa kamar zasu cinye ta danya a ranan. Wai tayi masu Allah ya isa shi da mama ke nan take nufi akan yar ta na suka sakata gaba da wullakanci kowa yana fadin albarkacin bakin sa. A take naji jikina yahau tsumi ina ta dan karkarawa daga inda nake a tsugune kamar na tsoma masu baki ga zancen su wata zuciya ta haneni da hakan. Na rasa yadda zanyi a inda nake yadda ake ciwa uwata mutunci yau akaina gaba daya kwanakin nan baba ya karkare birkicewa akan mama a gidan. Duk abinda ta fada ya zauna ke nan daram ba canji cikin sa . Nasan idan na saka bakina ga zancen abin zai kara muni gashi yau alama ya nuna inna ta fara gajiya da halinsu har takai ga fara bada amsa da bakin ta . Don haka na mike tsam na juya zan tafi daki muryan mamace ke cewa dani ina zaki rasa kunya an sallamay ki ne ? Bari ta nuna min ta isa mana tunda uwarta ta daure mata gindi inji baba yake fadin haka. Ke maza shiga daki kada ki dawo gurin nan kinji na fada maki so kuke da ni da ita ku turke mu kuyi muna wankin babban bargo don bamu dagata kuke gani ko? To bari kuji gatan muni dayara na Allah a gidan nan da duniyan nan kai nagaji da wanan halin cin amana kullun mune dai masu laifi a gidan nan ku bakwa yi. Idan wani laifi ne ai babu dan da baya laifi ni dan wa nataba kawowa kara duk da urin kuncin rayuwan da ake min a gidan nan ina sa kafa ina takewa daga haka ta juya tabi bayana zuwa daki. Ranan daga ni har Inna babu wanda yaci abincin dare ba, a ma taya muna balle muci. Shekaruna da kurciya na bai hanani fahintan ranan Inna tana cikin kunci da bakin ciki akan dalilina. Daga inda nake zaune takure bakin gadon karfen ta na mike zuwa inda take zaune saman tabarman sallah ta na tsunguna nace. Nace Inna don Allah kiyi hakkuri duk nice na jawo maki wanan bacin haka da ba don ni ba bazaki shiga wanan bacin ran ba yau. Batai magana ba sai na kara cewa don Allah Innan mu kiyi hakkuri ki yafe min. Tace ke nagaji ne da irin cin kanshin da ake min a gidan nan don may har in suna ganin kinyi laifi ne bazasu hukuntaki ba sai sunkirani don raini sun hada dani. Saboda yana son gyarawa matar raine zai dinga min wullkanci a duk lokacin da ya bushi iskan shi ko may ? Nagajine wallahi ni may ye yaran yaya basuyi min a gidan nan waya taba jin nayi magana balle nace itace ke daure masu gidin sai ni da aka raina za aiwa cin fuska yadda akaso. Shiru shiru aiba tsoro bane don sunga ina basu girman su shine zasu dinga takani yadda sukaso. Inna na kaiwa nan sai ga baba ya daga labulen dakin mu yana fadin ke Rahama daga yau sai yau kada na kara ji ko ganin kin kara hurda da bakuwar birnin nan don ba yar uwarki bace ban san dalilin ki na manne mata ba to na hana wanan hurdan daga yau. Yana fadi haka a cikin daga murya nasan yana fadi ne don mama taji ya yanke alakata da Anty. Abinda take muradin gani daji don tasan zamana da ita babban alheri ne ga rayuwan mu idan bata hana ba. Zama guda ta kashe min kudi haka har jakka sittin ba gaira ba dalili akaina. Yana gama fadin haka ya juya ya cuce a cikin hasala babu wanda ya tanka mashi yabar dakin dama yayi ne kawai don dadin ran mama takuma ji dadin. Sai bayan tafiyan shi Inna ke ce wa an daiji kunya wallahi mutum har mutum amma baida ta cewa a cikin iyalin shi sai yadda akace mai. Hakkuri na kara ba Inna don nasan yau kan ancin ma rashin hakkurin ta a gidan. Duk da karancin shekaru na ina iya fahintar wasu al, amuran da akeyi a gidan mu wanda ko kadan bai dace ace anyi shiba a tsakanin iyali. Amma gashi da karancin shekaruna yakai har na fahinci hakan a gidan mu, kai bani kadai ba duk yaron dake gidan mu yasan irin zaman rayuwan da akeyi a gidan. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , , IDAN KIN BIYA KIKA BA WA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH YAR UWA, , , Tafe nake da robar talla na yau doya ce dafafa gishiri sai kuli, kuli da yaji aciki wana nake barbadawa mutum idan ya saya. Daya daga cikin tufafin da Anty ta bani na saka wasu material ne masu walkiya walwal idan kana tafiya da su. Tafe nake nayi irin digirgire din kaya a saman kai din nan hankalina a kwamce nake tafe . Kai kai kai da sauri dayan mutumin da suke zaune a tare ya juya yana kallon gurin da nafarkon mai magana yake kallo, Da sauri suka kawar da kan su daga kallo na don na kusa karasowa inda suke a zaune. Dama yarinyar nan haka take da kyau ashe kamar wata matar gwauna haka da ita ? Wai may ne ne haka salla ni duk ka cika ni da zancen yarinyar nan yace wallahi ranan da kuke zamcen ta bani kusa sai yanzu nai mata kallon tsab ai. Garbati idan kana son abinka kawai ka shige kai tsaye nan ai babban iri ne ga wanda ya samu. Allah na tuba ko kyawawan yaya ake haifa wa mutum a gida ai ya wadatar akan su. Ni fa ko da kukaji nai magana a ranan ba wai har zuci nake zance na ba amma naga kuna gidada abin haka ku ? Garbati kada kaiwa kan ka salalalan tsiya walahi in har kana so kasa kai kawai na fada maka kada ka tsaya garin kallon ruwa wani yai maka tsalle. Kaga dama ina ga ba ai mata wani matsayi ba zuwa yanzu yan uwan tane kawai nake gani suna fitowa hira da dare amma banda ita. Wanda ake wa fadancin ake kuma zuzuta shi a kaina sai yanzu yai magana yace. Kai salla, banki ta naku ba fa akan maganan yarinyar nan sai dai gaskiya a yadda shekaru na yakai yanzu sai nake gani ai na wuce tsayawa koda akan yyayyenta ne da kake magana balle ita. Sannan kaga yarinyar ga ta dai karama ce amma akwaita da kwarji a fuskanta kamar ba karamar yarinya ba. Gashi kuma bata bada fuska kamar sauran mata ko yaushe fuskan ta a daure yake ba fara, a agare ta. Sau tari da yawa nakan so na dan mata magana koda na wasa ne amma da na dumfare ta sai naji gabana yana faduwa tana matukar yi min kwarjini sosai a idona. Salla yace assha Garbati kada ka zama ragon maza mana yanzu kuma manya mata ma mun sha gaban su babu gezau balle wanan yar ficiciyar karamar yarinyar zata kayar maka da gaban ka. Don haka idan har kana ciki ka bari zan maka iso har gida na gabatar dakai tun wani bai riga ka ba. Da zaran nema iso a gidan su insha Allahu komai zaizo daidai koda baka zo tadi ba gurin zance sai kawai ayi yadda za,a a daure aure batare da kowa ya farga ita din taka ce ba. Kai haba salla yaushe rabon da ai irin wanan neman auren yanzu da kai ya waye wa mutane. Sallah yace kai dai in har kana ciki ce min eh kawai kasha mamaki indai har zaka bude bakin aljihun ka komai zai tafi daidai insha Allahu. Har na kawo daidai gurin da suke zaune suna zance na ban ko gaida dasu ba don rabin hiran su ya dan zo a kunne na naji. In ba gulma irin ta mutanen yau ba ina ni ina su Lawisa da koda aka haifesu ba, a auri uwata ba a gidan. Don an kawo sadakin auren su zasu yi aure aiba abin mamaki bane hakan idan anyi la, akari da irin girmuwan da sukai min. Ban saka zancen dattijan banzan nan a raina ba don nasan ba abu bane wanda zai yiyu suke magana don jin dadin fatan bakin su ne kawai sukeyi. Nikan inda naji zance tsofin banzan kamar yadda na sa masu suna a gurin na bar zancen. ****** ********* ****** Sai bayan kamar kwana biyu da zancen ne da dare na dawo daga tallah nayi diban ruwana da wuri na dauko littafaina ina bita don mun kusa zana jerabawan mu na fita tunda na samu an min jummping a school bana zan kare karatun secondary dina. Ina jin lokacin da baba ya shigo gida bai jima da shigowa ba akai mai sallama yafita. Ya dan dauki lokaci a waje kafin ya shigo ina jin mama na mitan wai abincin shi yana sanyi bai shigo yaci ba. Ya dawo cikin gidan yanayin da ya shigo dashi kawai zaka kalla kasan yana cikin damuwa. Sai da ya zauna yagama cin abincin shine sa, an nan ya umurci lawal yaron mama karami ya kira mai Inna. Bata jima ba tafito ta samay su zaune da mama a saman tabar ma guda itama ta samu guri ta zauna don tasan magana ce mai muhinmanci zai yi dasu. Bayan ta zauna ne ya dube su yace ina Asiya tace gani gaban ka ai malam ina sauraren ka. Yace Asiya wani sha, ani ne ya taso gamay da yar ki Rahama. Jin haka da yace yasa Inna ta kara natsuwa tana sauraren shi tunda taji yace yar ta Rahama tasan ba abin alheri bane zai fada mata a lokacin. Don indai lafine a gidan dama bai wuce yaran dakin ta ko yaushe mussan ma ita Rahama din da take kamar ta tsone makowa ido a gidan. Shiru baba yayi na dan lokaci kamar yana shakkun fadin abinda yake son fada masu a lokacin. Sai zuwa can ya dan nisa yace dama wani mutum ne yazo yana son auren ita Rahama din . Nikuma har na bashi saboda naga dacewan hakan don haka na bashi dama akan yazo yaga yarinyar. Inna tace idan da Alheri a ciki Allah ya tabbatar da alherin sa . Baba yaji dadin hadin kan da Inna raba shi ba tare da tsayawa jayayya ba akai ko wani kwankwanto. Tana kokarin mikewa tabar gurin yace idan kin shiga ki turo min ita Rahama din. Inna tace to kawai ta mike tabar gurin ran ta a bace sai dai su basu gane ba. Bata kai ga shigewa ba taji mama na fadin ai ma an mata gata koma waye tunda har yau babu ko karen da ya taba sallama mata gidan nan. Tana shiga daki ta samay ni nabar karatun da nakeyi ina sauraren maganan su. Tana fada min sakon baba na saka hijjab dina nafito gurin da suke zaune tare da mama din. Na durkusa tare da gaida baba ta amsa min a kasalance cikin wani yanayi mara dadi. Sai da ya dan kalle ni Yake cewa Rahama nace uwarki ta kira min ke ne saboda ina son sanar dake Garbati ya gane ki yace yana son ki kuma da aure. Ni kuma naga dacewan hakan na bashi ke ina son ki zama yarinya mai ladabi da biyayya kibi umurni na don dama nice da alhakin zaba maki mijin da ta dace dake. Wani irin mugun faduwan gaba naji tare da wani irin jiri a lokaci daya kila badon ina a tsugunne ba dana fadi a lokacin. A hankali na dago kai nace baba wani garbati ke nan kuma a gatin nan ? Mama ta tare da cewa ungo nan Garbati nawa kika sani a garin nan Garbati dai mana mai arzikin garin nan dai . Kasancewa na ya mai tarbiya ga iyayyena da sanin darajan su tare da sanin hakkin aurena ya rataya a garesu don sune ga kaidan musulunci dama ya dace su zaba min miji aure na fari a rayuwana yasa nai shiru. Amma kuma duk da haka ace kuma Garbati Garbatin da a girmay ya girmay ma baba ba kadan ba. Gaskiya wanan zance na baba da yanayin sa sun bani mamaki matuka ganin cewa duk yan uwana mata zabin kansu ake basu su aura tun farko. Bayan haka aiga Lawisa da Rukkaiyya a gidan duk sun girmay min a shekaru don may su ba za, a basu shi ba sai ni da aka rainawa kurar uwata dani. Ni da ko yaushe nake hango kaina da a mainasara nake ga rayuwana zan tsaya tsayin daka naga nayi karatu mai tsawo a gidan mu, shine zan buge ga auren wani tsoho wanda ma ya girmay ma mahaifina ga shekaru sosai don dai yana da dan abin hannun shine ba, a gane shekarun shi ko may ? Ko kadan bazan iya yiwa babana mussu ba gama yadda naga mama ta gwagwafe ta tsura min ido tana son taji wani rashin mutunci ya fito daga guri na ko inna a lokacin. Na sunnkuyar da kaina a kasa murya a tausashe na ce baba na gode Allah ya tabbatar da abinda yafi zama Alheri . Yace insha Allahu hakan shine alherin ki Rahama tunda kikaga babban mutum haka yazo neman auren ki. Don haka sai ki shirya don zai fara zuwa zance gurin ki duk da yace shi ba irin na yara zaiyi ba zai dai zo koda saudaya ne kuga juna dashi. Ki kwantar da hankali ki kada kika kamar shi ba yaro bane kice zaki ta da hankalin ki akai na tabbatar da zakiji dadi a gidan sa don in kiyi la, akari duk kauyen nan babu maihalinsa ga kuma kula da iyalin sa da yakeyi. Bake ba har mu nan nasan zamu amfana da auren ki dashi insha Allahu. Take naji gabana ya yanke nace a raina watau auren kudi ne baba zai yi dani ke nan ko tunda har ya soma fadar haka. A take naji jikina yai min wani irin sanyi a lokaci daya sai faman sake sake nake a raina wanda daga karshe ma banji abinda yake fadi ba sam. Sai muryan shi naji yana cewa shike nan zaki iya tashi ki wuce Allah yasa mu dace. Da kyat na iya mikewa tsaye sai kace wace kwai ya fashewa a ciki nabar gurin zuwa dakin mu . Nan nake jin muryan mama tana cewa dama may na fada maka tunda makwadaitane daga ita har uwar ai yarda zasuyi. Ina shiga daki inna tace a zaune ta rafka uban tagumi da hannu daya dagani tana cikin tashin hankali ita ma. Zama nayi a kusa da mahaifiyan tawa cikin muryan kuka nace Inna kinji irin abinda yayi da rayuwana ? Inna tace cikin jan dogon ajiyan zuciya, naji yarinya yaya zamuyi tunda shi ya haife ki ? Kuma kin san yadda gidan nan yake da gani ba ra, ayin kasa bane saka shi yin haka akayi don kawai muyi magana ta zama muna abin gori da fade a tsakar gida. Don haka abinda nake so dake shi kada ki sawa kanki damuwa akan zancen nan ko kadan mu bar wa Allah al, amarin shi don yana sane da komai. Na dan dago na kalli Inba nace shi ke nan inna nabarwa Allah din komai kamar yadda kikace. Ina fadin haka na dunkule a saman tabar man da nake kwana zuciya tab da tunane rayuwan da zan fada ciki. A iya sani na dai gidan Garbati babban gida ne don har da sarakan shi zaune a gidan suke. Mutum ne mai mai neman kudi yana noma yana kiwo da kuma hadawa da kasuwanci. Gwargwado akwai kulawa za, ace ga iyalinshi a kauyen mu don baka ganin su a cikin kazanta kamar sauran matan garin. Amma ina yarinyar yar shekara goma sha biyar za, a aura min tsohon mutum kamar Alhaji garbati. Haka na kwana ina mutsutsuri saman tabar mana cikin tunane ga matan shi dukka uku bazasu rasa yara sama da takwas ko tara ba ni Rahama yaya zanyi zama cikin wa yan nan kakanin nawa a matsayin kishiyoyi ? Ashe abinda mu bamu sani ba ta gurin mama suka fara biyowa da zancen itace ma ta hurewa baba kunne akan maganan don yaso yaki maganan. Amma ra kawo mashi kabbali da ba, adi har yaji yagamsu da maganan ta ya yarda akan zai badani ga garbatin. A yadda ya nuna ma baison a dauki lokaci ba ai auren ba don kada a hure min kunne. ****** ********* ****** Washegari dagani har inna ta babu wani mai sukuni a gidan mu sai mamace da yaran ta suke gadan su a tsakar gida. Ina jin Rukaiyya tana wanki tana waka kamar haka yarinya ancuce ki an hada hadaki da tsoho, tsoho wari kakan ki shine kika aure ga hurhura gyamu kamar na kucaki. Inna tace min kada ki kulata Allah yafiso idan da hannun uwar su fa alamarin nan Allah zai saka maki yarinya. Dayake ba makaranra a ranan ban yi sana, a ba don bazan iya tallah ba a halin da nake ciki. Da kyat na iya diban ruwa a randa na tafi na watsowa jikina ko zan danji dama. Na zauna nai kwalliya na tare da saka tufafi a jikina inna tace na fita na gyara mata gurin girkin su kafin ta fito. Mama dake zaune saman tabarma tana sauraren redio kaduna ana zabi kanka na yamma. Ta izo daurin dan kwallinta a gaba kamar wata magajiya da ruwa yakarewa. Ina fitowa tace kayya kyau da kwalliya ya kare kuma a gidin tsoho atafi akarata can a iske su sabuwa muna nan za, a bamu labari mu dai. Wasu hawaye ne naji sun zubo min dana duka na fara shara ashe tagani sai cewa tayi ai idan mutum yace kwadayi ne yakai kashe yanzu kam. An iya shiga lungu da mazan banza sunawa mutum juye ana muna takama wai sa, an talla kega mutum yau ga inda sa, an yakare a gidin tsoho tukuf. Yo Allah na tuba kodai ni din nan tsuhuwa akace za, a hada da garbati ai sai inda karfina yakare to abinka da wanda ya saba da maza ko gezau babu. Daga kofa na dago zan ba wa mama amsa naga inna a tsaye kai da kada min alaman kada na soma na tanka mata. Har muka gama aiki da Inna tana zaune sai maga take sakewa ita da diyan ta a tsakar gida. Bayan sallah na samu guri a dakin mu na shige ban fito ba har lokacin da naji shigowan baba gida. Ya zauna don cin abincin dare Inna na gurin shi don itace da girki. Sai murya wani yaro naji yai sallama ya gaidasu yace wai ana sallama da Rahama . Gabana yai wani irin mugun faduwa daga inda nake zaune a dakin mu naji baba yana cewa waye ? Yaron yace ina ganin kamar Alhaji garbati ne da wani a wajen. Baba yace kace su jira gata nan fitowa daga inda yake zaune, yake cewa ke Rahama kina dai jin ana sallama dake ko ? Na jawo hijjab dina dake gefe na nasaka tare da yan silifas dina da anty ta saya min nafice daga gidan. Suna zaune a gidin iccen durumin dake kofan gidan mu inda wani lokaci samari ne ke zama suna hiran dare idan sun dawo daga gurin neman kudinsu. Su biyu ne bazan iya sheda dayan ba tunda akwai duhu a lokacin sosai. Sai kamshi turare suke irin na yan kauye mai hawa kai ya saka mutum ciwon kai a lokaci daya. Na karso inda suke zaune tare da sallama suka wani amsa min kamar wasu kananan yara dasu. Tare da cewa barka da fitowa hajiya Rahama insha Allahu kila badi dake za, a sauke farali indai kin amince. Dan gajeren murmushi nayi bayan na fahinci mai magana baba sallah ne dan uwan mama. Nace baba ina wunin ku ? Yauwa barka dai Rahama . Kin wuni lafiya dai ko ? Na ansa a fili a gajarce da lafiya kalau. Amma azuciyata cewa nayi ina fa na wuni lafiya bayan bakin cikin da kukajawa rayuwana ? Baba salla ne ya fara magana yace ba sai mungabatar maki da kan mu ba dai tunda naga alaman babaki da Lauratu sun gudanar da komai yadda ya kama ? Na dan kai durkushe a gaban su cikin ladabi nace haka ne kan. Yace yauwa ashe bazamu samu matsala ba ke nan yadda muke tsanmani ? Malama Rahama ga abokina nan kuma amina na yaganki ya yaba da tarbiyan ki shiyasa yaji yana son kasan cewan ki daya daga cikin iyalin shi. Don haka yanzu yakike gani ?. Nace kamar ya fa ? A yadda nai magana tankar ban fahince su ba nayi. Sai shi baba sallah din yace kamar na amincewa da shi amin nawa ga bukatan shi a gare ki ? Nai wani gajeren murmyshi da har ya baiyyana sukajini a fili danayi shi. Nace lah ni na Isa na ketare maganan mahaifina aida ban fito duya ta gari ba mai tarbiya ga iyayyen ta ba ? Nace ai babu komai sai dai Allah ya tabbatar da abinda yafi zama alheri ga rayuwan mu. Sun nuna sunji dadin magana na yadda suke fadin to Alhamdullahi alama ya nuna ke diyace mai tarbiya tun yanzu. Sai lokacin shi garbatin yai magana da cewa na ji dadi kwarai Rahama da kika amince da bukatana haka da sauri don ban taba zaton hakan ba a gare ki. Nace to yaya zanyi tunda umurni ne daga mahaifana ai dole nayi biyayya garesu. Ai ko ban amince don ra, ayina ba dole ne na amice don biyayya ga mahaifa na tunda sune masu iko dani bani ce keda ikon kaina ba. Cikun wani jin dadi garbatin yake cewa. Duk da umurni ne iyayyen ki akaina naji matukar dadi da amincewan ki haka ba tare da wani matsala ba. Insha Allahu kada kiji komai zakiji dadin zama da iyalina don zan kafa masu doka akanki don ke karamace sosai a cikin su. Sukace zasu tafi sai na kara jinsu dama sunzo ne su tabbatar da idon su halin da ake ciki. Kuma Alhamdullahi a yadda suka samu taro a gurina sunji dadi kuma sun gode. Yanzu dai kinga mu ba yara bane don haka bazamu dinga zuwa ko yaushe ba don gujewa idanun jama, a akan mu. Kindai sai komai a kauyen nan yanzu ana ganin mu labari sai yasha banban kuma. Bakar Leda ne baba sallah yake miko min yana cewa fa wanan dan tsaraban rano ne da muka shiga dazun mukazo maki dashi. Na girgiza kaina tare da cewa da kubarshi aiko haka ma nagode kwarai. Haba haba ayi haka kuma diya ta ki karba kawai wanan ai ba komai bane idan mun samu hadin kanki yadda muke so ? Nace kada muyu haka daku baba idan ina karban kayan maza Innata fada take min . Da alama sun gamsu da bayani na yadda naga sunyi sun fahinci dai a karkashin controling din iyayyena nake ba kamar sauran yaran da suka sani ba . Baba sallah ne yace duk da gaka dai diyata ki daure ki karba zan wa mahaufin ki bayani yadda zai gamsu. Kinsan kin karban kayan mosoyi wani alama ne na kiyayya kuma. Haka dai na daure na karba tare da masu godiya na juya nashiga gida raina a bace . ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , , IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH YAR UWA, , , Shiru mukayi dakin akan hukucin da mahaifi na ya yanke ta alakata da anty birni, yanzu baba akan su mama ya rufe idon shi ya yanke wanan hukunci haka duk da yasan mutunci ne ya hada ni da ita ba wai kwadayin da suke ikirari bane. Muryan Inna ce take ce min kin dai ji may ya fada don haka sai ki san yadda zakiyi da shiga gidan mai kuli. Waahegari ban tafi makaranta ba sai da na faki idon mutane na leka gidan mama Altine muka gaisa dasu na wuce. Haka ma da na dawo ban shiga gida ba sai da na fara shiga gidan gurin su . Hakana wuni ina fakin idon mutanen gidan namu ina fita zuwa gurin anty sama sama. Ganin haka yasa suka fahinci akwai matsala na fito zan tafi diban ruwa na shiga gudu gudu gidan. Nan ne mama take tambaya na ko may ke faru ne yau na kasa tsayawa kamar kullun. Ban boye ba na fada masu komai da ya faru a gidan mu har baba ya hana ni shigowa gidan su. Mama ce tace to babu laifi ki natsu ki zauna gidan ku kada kuma ta sa aiwa Innan ki wani abin. Kin san ance mai hakkuri dama bai iya kai karshe ba sun kai ta karshe ne tunda ta fara basu amsa yanzu. Allah ya taimake ni aahe mama ta saka ido sosai a kaina kozan tafi gidan mama altine a wunin nan. Ganin ban fitaba yasa ta fara sakin magana a tsakar gida tana cewa ai na dauka ko ba abin dokar mune inwa uwa da diya dukan tsiya yau a gidan nan. Idan shi ya kafa doka ba,abi ba ni dole na kafawa mutum ko baiwa Allah dole ko abi. Ke a dole wai ga yar gwal ba, a tabaki uwar ki ta shigan maki ba kunya ba tsoron Allah. Inda ma mutum nada wani asalin kwarai ne har zai muna yanga da kyau yo ina kyaun ma yake don dai haske fatan da ake kuri dashi kawai bayan shi din sai may kuma ? Inna dai bata tanka taba sai ci gaba take da masifan ta tana cewa ni za, a gwadawa rashin mutunci ni da mutunci ya ganni ya gudu. Idan kace zaka shiga tsabgata wallahi sai inda karfi na ya kare a kan mutum duk da haka kana doso ni da rashi mutunci in kama mutum in mashi dukan tsiya a gidan nan inga uban da zai ramawa mutum. Mu dai muna daki abin mu muna jin ta tana faman haushi tana neman mai tanka mata ta sauke mai. Da babu wanda ya tanka mata sai ga lawisa ta dawo da kayan sana, an da mama ta dora mata batai ciniki ba. Nan mama ta juye fadan kan yar ta tace shiyasa ake ganin daman ku ana maku yadda rai yaso harda sheri. Ko da yake kubaku iya shiga lungu ai maku juye ai abinda akeso da ku ba a baku kudi. Mama tana nugin nice mai shiga lungu da maza da sana, ata ana min juye idan anyi lalata dani. Ban san lokacin da na ce Allah ka isar min ban yafe ba sai Allah ya , , , Marin da Inna takaiwa bakinane yasa naja nai shiru ban karasa fadin maganan da nake fadi ba. Tana cewa kul na sake jin kina jawa babba Allah ya isa sai na fasa bakin nan naki. Duk wajawo min wanan bake da ban isa na tsayar dake inda naso ba da kin dauki sana,an ki kin tafi wa zai ganki a gida yai maki maganan banza haka. Kamar nace Inna aiko bani gida mama zata fadi hakan ne a kaina don bayau ta fara fadin hakan ba. Da dai tagaji da fadan naji tana cewa ai tunda abin haka ne wallahi mu zuba da mutum a gani. Inna tafito yin alwalan la, asar ne mama take cewa kada ta dibi ruwan randan ta don dashi take son yin wanka don randan ta ba ruwa a cikin sa. Inna bata saurare ta ba ta duka tana diban ruwa ne ta ji saukan duka a bayan ta daga gurin mama din. Yaya abin yakai harda duka tace na doke ki ko zaki rama ne mara mutunci kawai. Ta sake daga hannu zata kai wa Inna duka ina tai cikin ta Allah ya bata sa, a ta kwashe kafan mama tai kasa tim, ta bita ta haye taita dukan ta. Ga mama babu ko dan buje a jikin ta sai tsiraicin ta da ya baiyana a fili lokacin. Jin haya niyar sau yasa mukayo waje gaba dayan mu muka shiga ihu don bamu taba gani ba. Ganin haka su Lawisa suma suka far wa Inna da duka ina ganin haka nai kan lawisa sauran suka biyo ni suna duka Allah yaban sa, a na jefa ta a randan ruwan su saida ya fashe. Ta samu targade ta yanka wani irin ihu kamar ranta zai fita a lokacin ganin haka Isa ya dauko tabarya yai kan Inna dashi bai kai ga buga mata ba ni rike shi yai baya yafadi kasa shima sai da yaga wani wuta ya gifta mai. Wani ihu suke kurma wa na neman taimako mama tace shigiya mai karfin doki wace ta san ma diyan ta mugun abu. Su mama altine da wasu makwabtane suka shigo don jin kururuwan da yai yawa a gidan. Da kyat aka banbare Inna ajikin mama sai zagi da ashar mama ke faman sakewa aka bata zanin ta, ta daura. Inna tace sakariya kawai wawiya wacd bata riki darajan ta ba balle na uwargidancin da bai amfana mata komai sai zalunci an fada maki shirushiru tsoro ne dama. Mutane sai fadi suke asha Lauratu mai yakai wanan taasan haka bayan karfi ba daya ba ? Gaskiya wanan abin dai kan baiyi dadi ba wallahi yarinyar nan tana maki biyayya yadda ya kamata karami yai wa babba amma sai da yau kika kaita bango. Makwabta kowa na fadin albarkancin bakin shi abindai kan baiyi dadi ba wallahi don babu wanda bai san halin da gidan mu ke ciki acikin su. Har da anty Sa,ade sai da tashigo gidan dauke da yarta a hannun ta tajani gefe tana min nasiha yadda ya dace. Jinya sosai mama tayi a ranan har dare suna daki ita da yaran ta da sukai tangarde tana jiran dawowan baba. Tun a hanya yan unguwa suka tare baba suka fada mai tare da bashi shawaran ya saka ido ga halin da iyalin shi suke ciki don babh inda akejin wai kishiya don samun guri ta daki kishiyar ta koma wacece bazata kyale ba . Haka yasa koda baba ya dawo gida bai dauki wani matakin da mama taso ya dauka ba. Ganin baba bai dauki matakin da taso ba na farwa inna ta da duka ya rama mata ba ita da diyan ta. Wanan zance yasa har saida Iyayen mama suka ziyarci gidan mu nan suka zauna kowa ya mayar mai da bayanin kan maganan. Nan dai suka taru suka bawa mama rashin gaskiya yadda ya dace akai masu nasiha da suci gaba da zaman lafiya. Tun daga wanan ranan mama ta kwashe kayan ta na aiki dake a tsakar gida ta boye kuma wasu ma da kudin sana, ata aka saye su. Nice nake labartawa anty da mama take anty tabani kudi tace kada na koma gida naje na sayo wa mama duk abinda bata dashi komai da yakamata na aikin mu saida na hado shi kamar wata babba can dani. Aiko mama tana ganin haka hankalin ts kuma ya tashi ta fara sabon habaici tana fadi sai dai haka dama an samu kayan banza ana amfani dasu. Take cewa wai na dauki kaina na saka a cikin kishin su ai tasan magani na indai itace. Wanan kalamin na mama da takance wai tasan magani na kullun na rasa wani maganin me zatai min wai ? Mu dai bamu biye mata ba haka zaman ya koma na doya da manja a gidan na mu. Naji dadin zuwan anty Sa, ade a wanan lokacin don ko ba komai ta fitar min da uwata a kunya. ****** ********* ****** Ban san da zancen tafiyan anty ba sai dana dawo daga school nashiga don nagan su. Sai mama ce kawai na samu a gidan cikin karaji nace mama ina antyna ? Idona yana gurin da kayan ta suke a dakin mama, murmushi mama tai min tace yar gidan anty ai yau anty ki tai muna na baki. Dazun mijinta yazo ya dauke ta suka tafi sun koma birni inda suka fi wayo in ma ba don Saade yarinyar kirki bace ina zata iya zaman garin nan har tsawo sati daya haka? Inda kinga irin daulan gidan iyayyen ta da na mijin ta ai bakyace zata iya ko zama ba anan din. Duk wanan maganan da mama take bana jin ta don nayi nisa ga tunane ina fadin yanzu shike nan anty ta tafi tabarni zan koma ga turke na mai cabo ke nan na talla. Gashi dan kwana biyun da nayi bana talla har na dan yi kyau na koma wata wayayiya dani. Ashe anty tasan zata fi a yau shiyasa jiya tasa na sance kaina tai min wani sabon kitso a kaina duk da wancan na farkon da tai min bai tsufa ba? Muryan mama ne ya katse ni tana cewa ga sakon nan ta bayar abaki tace kiyi hakkuri idan ta samu hannu na gari zakiga sakon ta. Dakin ta shiga ta dauki min wasu kaya tufafi ne na anty da na santa dasu na jikin ta, ta bani. Sai sauran tarkace irin su sarka takalma da gyale da sauran su ta bani nai amfani dasu. Haka na karbi kayan jikina duk a sabule na juya jiki ba lakka zuwa gidan mu inajin kamar na kurma ihu a lokacin. Mama tabi bayana da kallon tausayi tana mamakin wanan irin shakuwa dake tsakanina da yarta tun ina karama. Don itama antyn ta tafi dani a baki tana fadin Allah sarki wallahi mama da mahaifin Rama zai yarda dana wuce da ita kano taje can tayi karatun ta . Mama tace raba kan ki da zancen yarinyar nan Sa,ade iyayyen ta basu da mutunci don basu san haka ba. Wanan dalilin yasa taja bakin ta tai shiru ba don ranta yaso ba ta kyale zancen. Nan na dawo kan sana, ata ban ko tsaya Inna tai min umurni ba na dauki wake na wanke nakai nika da sauran abinda ya dace inyi. Ganin ina wanke wake yasa mama take cewa yau kuma karya ta kare wa buddari ne za, a koma inda akafi wayo. Ban dai kulata ba naci gaba da abinda nakeyi don na nasa a raina washe gari bazan shiga makaranta zan zage naiwa Innata sana, a ne don nagane shine kawai rufin asirin mu a gidan. Na dade a zaune ina kwalliya irin ta mu na yan kauye idan zamu fita nacewa inna na dauki kayan da anty tabani ne na saka. Tace ba naki bane idan zaki saka sai kin tambaye ni na jawo ledan kayan da tunda nashigo dasu ban bude ba tun jiya sai a lokacin nan. Na fara budewa naga emvlove a ciki a mike a hankali na bude kudine yan duba a cikin har dubu ashirin sai yar guntuwar takardan da ke ciki. Da mamaki na dauki kudin na kiraga duba ashirne cif din su sai na dago kai na kalli Innata data kura min ido. Takardan na bude na fara karantawa ga abinda tace a cikin takardan kamar haka. Rama na nasan lokacin da zaki samu takardan nan nakai kano kiyi hakkuri ban fada maki yau zan tafi ba don kada ki fasa zuwa makaranta da fatan zakiyi hakkuri ki kula min da kanki. Ga kudi nan daga ciki nakine kibawa Inna bana son kina wanan tallan a rayuwa na idan sun kare insha Allahu zakiga sakona. Kada kiyi wasa da karatun ki kidage sosai don watarana ki samu ki taimakawa Innan ki don tana bukatan taimakon ki sosai saboda halin da kuke ciki a gidan ku. Dafatan zaki fahinci abinda nake nufi naki antyn ki Saade sa, adu rano. Kifewa nayi ina kuka a gurin wanda ban san dalilin yin kukan nawa ba a lokacin ko na may nenw? Sai da nayi mai isata na fita na wanke fuskana na dawo na shirya na fice daga gidan dauke da roban tallan wara na. Ina fitowa mutane suka fara tambayana ko nayi tafiya ne kwana biyu sun daina ganina a garin. Ba wani cikakken amsa da nake basu sai kawai ina nan boko nake zuwa shiyasa. Saura kadan ya rage min a roba don haka nai haraman komawa gida don nasan yanzu diban ruwa yana can yana jirana ko karfe nawa zan kai a wajen tallan. Ina tafe bugujan buganjan dani a cikin sauri naji muryan dattawan nan dake zama a gindin cidiyar uguwar mu suna fadin ke mai wara kawo wara mu dan taba. Ban ja ba na juya zuwa gurin su inda suke a zaune tare da durkusawa na fara gaida su tare da aje roban a wara a gaban su. Nawa nawa ne dayan ya tambaya nace mai biyar ashirin yake yace to kiba kowa na ashirin anan. Na shiga saka masu na ashirin a leda ina mika masu daya bayan daya suke karba. Don ina gurin bai sa su fasa hiran da sukeyi ba na matan su sai faman dariya suke a tsakanin su. Muryan dayan naji yana cewa ka samu daidai wanan ka saka a gida ai damana da sanyin bana lafiya ga mutum. Sai suka fashe da wani irin dariya fuska na a daure daidai lokacin da na gama mika masu a sanyaye nake cewa na gama zan tafi. Dari biyu ya miko min ina kokarin banye kudi na bashi canji naji yana cewa a, a ki bar canji kawai ki tafi dashi ai gobe ma ma hadu ko ? Cikin sanyin murya nake cewa Inna ta ta hanani rike kudin maza a guri na don haka ga canjin ka na aje mai a gaban shi ashirin uku na mike tare da daukan roban tallah na bar gurin cike da jin takaicin su. Ina ba da baya naji daya na fadin ga yar gutsun uwa arziki na binki kina ki dan shashanci kawai. Daya ce bata san arziki bane in bashi ba aiko yaro mara hakori yasan sa, a a yanzu balle ita da tafito cikin rana nema. Mai kudin yace ku kyale ta in kunga haka tarbiyan da uwarta tai matane take bi dagani danya ce shatab. Sai duk suka sa dariya a lokaci daya dayan yace yaya dai mutumina sai naga kamar fa ka kyasa Allah ? Yace ko na kyasa may wanan yar shilar zatayi dani da hurhura na har a mugun guri. Cab di ai sai dai idan ka tsuke aljihunka ne za, ace ba, ayi dakai zamanin nan amma ina wani hurhura can kawai watarana sai ka nema ka rasa kana kwasan kurciya gurin yar yarinya ka huta da wa yan nan tsufin kwaman kwana biyu. Ayi haka ga yara ina zan kai wanan yar shilan cikin wanan dabin iyalin nawa ai sai su farwa yar mutane tun dai ban ce ma kaciya ba ? Aff ina ruwan ka da wanan mace ce ma fa ita kada kaji mamakin ka shigo gida wataran kasamu ta zage tana masifa a kan ka. Dariya sosai suka kwashe dashii har nai nisa ina jin sautin dariyan su na shige gidan mu abina tafe nake a cikiin sa, a na akoda yaushe haka Allah yai min baiwa ni. Abinci na dan tsakura na kwabe kaya na tafi diban ruwa marance da nakeyi. Sabbin robobin da na sayowa inna ta saida na cika su taf da ruwa na kawo marafan su na rufe su akofan mu. Shine yaba mama haushi sosai tace wai karama dani na iya bakin makirci kamar wata tsohuwar mace. Da baba ya dawo ina ta tare shi da zance wai bata san inda muke samun kudi ba da inna na yanzu ya duba yaga irin kayan da muka saye ? Idan ba dai maza na fara bi ba ina kawowa Inna ta kudi muna shagalin mu a daki ba wanda yasani.? Ita ba don komai tai magana ba don zama tare ne kada wani abu yazo ya samay ni ace tana gidan ta sa ido. Baba ya hasala da zancen sai gashi ya daga labulen dakin yana cewa ke Asiya kki fada min gaskiya gidan uban wa kuke samun kudin da kuuke wanan bushashan haka agidan nan keda yar ki ? Shiru inna tayi har saida ya kara maimaita tambayan shi gareta ba dake nake magana ba ne wai ko bakiji may nace bane ? Iinna tace bada amsa baida amfani don ko na fada ba yarda zakayi ba tun da an fada ma sheri. Ni dai nasan kulba dade kulba jima Allah yana tare da mai gaskiya komai dadewa kuwa. Yace to yayi kyau ya juya ya fita da daren nan Inna ta shiga gidan mama altine da kudin da anty tabani na karatuna. Bayan sun gaisa tai mata godiya take cewa mai kuli nazo gurin ki ne don ki bani shawara akan kudin nan. Kinga kudi bazasu aju ba don haka nazo neman shawaran ki da na aje kudin nan a guri na sai naga kamar na baki su ki sayowa yarinyar nan kayan tari ki barsu anan gurin ki kamar zaifi. Don ko na barsu ban san ranan da zan sake samun irin su ba haka sai ma mu dinga zara da guda da guda har mu kashe su ga banza. Idan kuma yaya ta gane karshe ma rance su zatayi tace zata juya muna don ni ko malam ban son yasan da zancen kudin nan yanzu. Mama Altine tace kin kawo shawara mai kyau Asiya nima sai da nai tunanen haka tun farko. Amma sai na bari naga hankalinki da fun tunii kike wanan dabara da tallan yar nan da yanzu ansan abinda aka aje mata ai. Amma kin bari ana maki wayo kullun ana karbewa baku aje komai ba sai bakin wahala ke a wahalce ita yarinyar a wahalce. Inna tace to ita yarinyar takice indan anyi maganan haka sai tace ita karatun boko zatayi mai zurfi irin na anty ta. To ke kyabi tana ta ballantana a kauyen nan yaushe karatun bokon ya mace ke zurfi suma ainaga sun jima suna karatun don tana son abin. Yanzu da miji yazo zakiga afitar da ita karatun ya tsaya ke nan cak ba ci gaba sai wahalan aure ya biyo baya. Ai mai kulli mukan kauye ana kwarar mu wallahi kai wahalaa dan ka a wahala shine rayuwan mu kawai. Tun wanan lokacin Inna take daukan dan riban da muka samu ga tallah bayan ta cire na amfanin mu take kaiwa mama altine ba tare da sanin kowa ba. Zancen da mama tayi na zuga baba ina samo kudi ba asan inda nake fitowa dashi bane yasa aka kafa min doka akan talla sau daya a wuni. Haka yasa har na mayar da hankali ga karatuna daga baya ma sai na kirkiro sana, ata a kofan gidan mu anan nake suyan warana shima din nan a take na sayar da abina na shigo gida. Hakan kuma sai ya jawo sabon fitina gurin mama again take cewa wai maza nake tarawa a kofan gidan mu ana abinda bai dace ba. Shima baba yai fadan shi har yagaji baida yadda zaiyi ya hanani talla ne da yahana ni yadda ya sha zugi gurin mama din. Ina aji hudu akai min jumping a school din mu don kokarina don munyi debet na sa school din mu tayi nasara na samu wanan daukakan haka. Nan ma mama tace ai inba ina tare da malaiman ba babu yadda za, ai min hakan ni kadai don banfi kowa a school din ba. Nan ma baba ya hau ya zauna akan zance haka ya jawo mama tasawa karatun nawa kahon zuka sai da a ka dakatar dani daga karatun boko na ga baki daya hankalinta ya kwanta. Tsayawa fadin irin bakin cikin da naji alokacin bata bakine gurin fada. A makarantan mu sun samu labarin babana ya fitar dani daga makaranta haka yasa suka tausaya min sukazo har gida suka samay shi kan zancen. Amma yace suyi hakkuri abar zancen da suka matsa mai yace a bari sai yayi shawara tukun. Badakowa zaiyi shawara ba nasan da mamacd idon itace kuma babu yi ke nan na sani. Daya tunkare ta da zancen cewa malam mu ne sukazo akan zancen dakatar dani daga kararu sai cewa mama tayi dama may na fada maka ? Tare take dasu yanzu sunga basu samun ganin ta su kwakwaleta shine suka biyo sawun ta har gida. Nan baba ya kara turjewa bazan koma karatu ba idan mana samu miji aure zai min kowa ya huta. Jifa ga Lawisa ga Rukaiyya da Naja wai amma nice baba ke maganan aure na. Ganin za, a cuta min a gida yasa shugaban makarantar kai karan babana a gidan maigari. Kan zasu cutawa rayuwana kasancewa ta yarinya mai kwazo ga karatu ya kamata ace ko dai secondry din ne na gama ai. Da kyat baba ya yarda koshi sai da maigari yai mai jan ido ya yarda don yasan idan yadawo gida akwai matsala tsakanin shi da mama idan taji zan karasa karatuna a shekaran nan. Haka kuwa akayi don ranan ba karamin tashin hankali akayi ba tsakanin baba da mama. Take cewa ai dama har dashi cikin cin kudin da mazan dake lalata dani suke bani. Idan bashi ba don may zaice sai na karasa karatuna may ye amfanin karatun diya mace na boko da za, a kare shi a gidan miji. Tana kurin tana karatun boko watafi kyau da za, a nace kan sai nayi boko nakai wasu can daban Ni dai tunda naji baba yace na shirya gobe na koma makaranta nake cikin farin ciki da zumudi don ina gani kila ina da rabo ne a duniya. Washe gari tun da safe na bar gidan duk da na saba idan zan tafi sai na sallami kowa na gidan kafin na fita. Yau ma dana shirya munyi sallama da inna na nufi kofan mama tun ban karaso ba tana hangoni take cewa za, a yawon tazubar din ko akuyan daure ta samu saki. Duniya ce dai ayi ta a sannu don maza ba abin goyo bane da sun gama yayin ka su ka hango wata kai kuma ka tashi aiki ke nan. Ni dai ban biye taba nace mama ni na tafi kafin ma naji amsan da zata bani har na fice daga gidan ko. A kofa na hadu da babana da zai shigo gida na dan rabe gefe nai mashi ina kwana yabini da harara yana cewa har zaki tafi ke nan ? Nace eh baba yace Rahama ki kula da rayuwan ki kada ki ja min abin kunya a garin nan. Duk dai har yau babu wanda ya taba kawo min karan ki na assha amma dai kuma maganan maman ku abin dubawa ne. Don diya mace ba, a saka mata ido tayi yadda take so dole sai da tsawatawa akai. Nace nagode baba insha Allahu zan fake na tafi ina tunanen halin baba idan mama bata kusa zakaji ya dan sanyaya ma al, amarin mu . Amma da zaran yaga idon mama damu da makiyan shi duk daya muke gare shi kamar zai yanka mu da ran mu. Bani ba har yan kanne na biyu hakan ya shafa don dai kawai su maza ne basu zama gida su. Ina isa makaran ta ban tsaya ba sai office din malam Mudi don nasan shine kadai zai iya min wanan kokarin. Na samay shi yana shirin fita na duka nagaida shi cikin ladabi nake cewa kuma malam nazo ne nai ma godiya don nasan kaine da wanan kokarin. Yace hakane Rahama don haka kema ki kula da rayuwan ki don ban san dalilin yin hakan ba ga mahaifinki. Ko da yake mun samu labarin cewa takurawan kishiyar mahaifiyan ki ne akan ku ya shafe ki. Ki kula ki mayar da hankalin ki wata rana sai labari idan kin dage Allah zai kawo maki mafita da yardan ubangiji. Nai mashi godiya tare da sallama na koma class sai sheri yan uwana dalibai suke min wai ta fudu ta dawo. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , IDAN KIN BIYA KI KA BAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH YAR UWA, , , , A haka na juya zuwa cikin gida jiki a sabule min ina dauke da ledan da suka bani a hannu na. Har lokacin Inna suna gurin zaune da babana nazo na wuce su zuwa cikin dakin mu. Tafe nake ina tunane a zuciyata sam bana cikin natsuwa ko kadan a lokacin zuciya bata kwanta ba da wanan hadin da ake son yi min. Sam garbati bai min ba gashi dai dattijo a gurina na ni yar sha biyar tsoho kutuf nake ganin shi, Koma da ace lokacin kuruciyar shi yake nidai bai mun ba don bakine wulluk kakaura dashi sai dai ba can kwarai ba. Ga fuskan shi duk ya bar gemu a ciki baje baje wai shi sunnan kauye babu dai wani abin armashi a cikin sa ko kadan. Sai dai ban da wani zabi ga gakan tunda ba zan iya bijirewa hukuncin mahaifina ba akaina. Duk da har lokacin ba wai ma na fahinci may ye zaman aure ba tunda a gidan mu ba wani zaman auren dadi naga anayi ba ma balle na koya. Nasan irin rayuwan da inna ta tayi na zaman bakin cikin rayuwa ni ma dai din shi zan je naitayi gidan nawa auren ke nan. Ban da wani zabi a hakan don ban isa na bijirewa zabin mahaifina ba haka zan ta kokarin tursawa zuciya na kaunan shi koda kuwa zuciyan nawa na barazanan kamuwa sa ciwo ne. Ganin yanayin da na dawo gidan yasa bayan na dan shiga da yan mintoci Inna ta mike daga inda take zaune ta biyo ni dakin mu. Nan ta samay ni nayi zaune nayi tagumi ga ledan da nashigo dashi na tasa a gabana. Tocilan hannun ta ta haska ledan da shi sabulai ne sai clean manya biyu sai turare fesawa na passition da turmi zani guda biyu sai kudi wai kudin dinki dubu uku. Baki Inna ta ta rike tana cewa kai anya Alhaji garbati bai dauko hanyan riya ba ga alamarin nan kuwa ? Yanzu ace duk yawan iyalinshi zai iya binsu da makamancin kayan nan haka ne ? Gaskiya ni ban son abinda tun ba, aje ko ina ba zai shafa maki bakin jini akai . Duk wani abinda zaiyi a gidan nan tamfar a kunnen iyalin shi ne don dai yaya tana hurda da sabuwa da can baya. Daukan ledan tayi wai zata kai wa babana da mama dake waje da sauri na tura hannu ciki na kwashe kudin don nasan idan ankaisu mamace zata kwashe su da wani dadin bakin ta. Inna dai bata ce min komai ba ta juya ta fice daga dakin ina jin su baba yana cewa kai kaya haka kamar za, a kai lefe ? Mama sai faman binciken ledan take da sauri nasan kudi ne take nema a ciki gashi ta wani tsuke fuskan ta tamau da ganin kayan. Can taja tsuki tare da tura kayan a gaban babana tana fadin kaiyya sai dai tsiyan abin duk wanan gatan tsoho ne. Da yaro ne shine za ai farin ciki da nuna rawan kai amma tsoho ga karamin yaro may za, a gane ciki haka. A, a lauratu inji babana kon san da haka kikace nai maki alfarma na bada ita gare shi tunda da dan uwanki akazo neman ta ? Idan kin san haka ne may yasa kika sakani gaba saida na furta na bada ita yanzu zaki zo min da wanan sabon zance kuma ? A, a ni yanzu may nace kuma ai gaskiya na fada yanzu ba ga abin arziki ya fara sauka maka ba har kuna murna. Cikin mamaki yace murna kuma kamar yaya lauratu akan wanan kayan ne zanyi murna da rayuwan da yata zata shiga ? Nifa don ki na yarda naba Rahama ga wanan mutumin may naci nasa da zanji nauyi shi a baya ? Ashe ke nan ke da wata manufa kika sa na bada Rahama gare shi ke nan ? Manufar may kuma malam banda abin arzikin da na hada ni idan bashi din ba akwai wanda ka taba jin yazo ya sallama akanta ne a gidan nan bayan duk ta gama zubar da mutuncinta ga samarin gari. Daga inda nake ina sauraren su na hade wasu yawun bakinciki a raina tare da hawayen da yazubo min. Koma may zan tarar a gidan gara na tafi na huta da kullin sherin mama da yaranta hakana nida inna ta akaina. Jin hayaniyar tasu zai yi karfi ne yasa na fito waje inda suke don mama ba komai bane hassada ta nuna min karara . Tayi min hakane don ta jefa rayuwana dana mahaifiyata a kunci ne kawai. Basuyi aune ba sai ganina sukayi a waje durkushe a gaban su ina cewa baba don Allah kabar wanan magana haka. Indon nice na yarda da kaddaran da Allah ya kawo min na auren garbati bazan bari kayi kunya ba a kaina insha Allahu. Tausayi na bashi yai shiru tare da yi min wani irin kallo na ban tausayi yagane manufata bazan bari yai magana biyu ba yace eh yadawo yace kuma a, a daga baya. Yace shike nan Rahama Ubangiji ya tsare mun ke a duk halin da zaki riski kan ki a gidan shi nace amin baba na share kwallan da suka zubo min na mike na koma dakin mu. Ina jin mama bayan sun gama hayaniya ta juya dakin ta bata dade ba ta rufo kofan ta hakan ya nuna ranan bazata yarda na kwana a dakin ta ba ke nan. Inajin Innata bata shigo daki ba da taga haka dakin da suke aje shirgin su har bunun dakin ya zabbace ta gefe daya don wahala ta dan gyara min gefe daya tace na kwana a can ko naje gidan mai kuli na kwana. Nace dare yayi Inna bari kawai na koma can na kwanta yanzu mama ta rufe gidan ta nasani. Baba tana ganin haka ya nufi dakin mama ya na bugawa tace daga ciki wai lafiya kake dukan min kofa haka kuma may kuma zan maka ? Yace ki bude Rahama ta shigo ta kwanta tace ai kaba uwar ta daki ka bani don haka ku kwanta tare da ita mana tunda ta zama yar gwal matar Alhaji yanzu. Dole ya juya ya barta zuciyar shi na tir da Allah waddai da halin mace ba haguwa irin ta. Sai ta kaika ta baro kuma ta tsira ma sabon fitina dama wanda ya kaucewa Allah dole ya fuskanci kalubali irin haka a rayuwan shi. Hakana na kwana dakin ga sauro ga beraye suna ta hawa min jikina ba dadi ko kadan dakin don yawan shirgin kayan aikin su dake cikin dakin. Kwana biyun girkin Inna haka tayi shi a cikin kunci a gidan rai a bace mata duk nabi na damu ga bacin ran da mahaifiya ta take ciki ga zancen auren da ake son yi min na dole. Haka nake zaune a takure ga mama ta saka mu gaba da gori ita da diyan ta duk mun kasa sukuni a tare da mu. Na dai yanke shawara zuwa yamma na shiga gurin mama altine ko zan dan sarara a tare da ni. Nan samu mama tana dan aikace aikacen marance na shigo da sallama na na karbi tsintsiyan da take shara a hannun ta na karasa mata sharan. Na dawo gurin da take zaune tana gyara geron da zatayi birbisco dashi na abincin dare na karba ina gyara mata. Kallon yanayi na tayi abinka da babban mace ta fahinci babu dadin rai a tare da ni lokacin. Take cewa lafiya kuwa yar gidan anty na gan ki yau wata iri dake haka ? Maimakon nayi magana sai hawaye ne suka biyo baya tace subbahanallahi may ke faruwa ne Rahama ? Sai da nayi kuka mai isata nake cewa mama baki ji kaddaran daya fada akaina bane halan innata bata samu shigowa ta fada maki komai ba ? Tace Asiya ta kwana biyu bata shigo gidan nan ba gaskiya may ya faru. Ina kuka nw nake labarta mata komai da ya faru a gidan mu akaina cikin kuka tace waye shi wanda aka baki din ne ? Nace Garbati cikin rike kirjin ta tace wani garbatin ba dai Alhaji garbatin dan bida ba dana sani ? Nace a sanyaye shi mama. Tace subbahanallahi yanzu shi mahaifinki da ranshi da lafiyan shi zau dauki ya kamar ki ya mika wanan gidan na sa, an nin kakan nin ki ko may ? Nan ta haufada tana cewa idan Salihu bai yi hankali ba sai Lauratu ta kona shi tun a cikin duniyan nan wallahi ko. Fada sosai mama tayi tare da kara kwantar min da hankali take cewa zan tafi gurin anty ki ance min ita ma bata jin dadi ga abokan zaman ta ba kirki ne dasu ba. Kin san kishin yan birni ba irin namu ne ba na kauye kishi suke suna hadawa da yahudanci aciki. Rayuwan ne na kowa tasa ta fishe shi akeyi wai suna ganin su wayewa ne a gare su. Inbashi ba dan uwan ka baida lafiya ina zaka kawar da kai gareshi haka kana tsabagan gaban ka. Nace mama Anty na bata da lafiya ne ?. Tace ina fa taga lafiya tunda tazo din nan take fada min wai bata da lafiya ajikin ta har zasu tafi kasan waje da maigidan a dubata. Allah yaba anty na lafiya nace tace amin Rahama ita nake gani ta tuna min da mahaifiyar ta don dan uwan ta shi namijine baidamu damu ba kamar yadda ita take kula mu. Na sake cewa mama dama anty tana da abokan zama ne tace tana dasu mana har biyu ma. Ai anyi aurenta ba a kokai shekara ba uwar mijin tasa ya auro yar uwarta shima mahaifin shi wai akwai yar abokin shi da yake son hada shi dashi tun farko shima yasa ya auri yarinyar. Zoki ga irin yadda suka saka min yarinya a gaba da fitina suna ganin itace bare a cikin su sai abinda suka ga dama suke mata a gidan . Allah dai yasa shi mijin yana son abin shi haka yasa basu samu yadda suke so ba akanta. Yanzu ga ciwo yazo ya sakata agaba haka wama yasani ko ije ne aikai mata ya hanata jin dafin rayuwan ta. Nace mama ije kuma may nene ije ? Tace baka ji maganan ba keda zaki shiga kishi cikin tsofon mata Rahama baki san ije ba kuma sai may. Nan tashiga yi min irin kissan ije da dalilin da ke sa aiwa mutum asiri idan anga hankalin miji nagareshi da yaran shi. Nan nai mutuwan zaune nace na shiga uku mama koma don ai min ne yasa mama ta tura baba ya kaini wanan gidan akashe ni kowa ya huta dani kamar yadda take fadi. Har na dawo gida duk yadda mama taso ta fahintar dani hakan bai samu ba daga gare don na kasa fahintar dongon sharfin da take min akan ije wai shirin kishiya . Ko da na dawo gida na samu ranan har baba ya dawo daga kasuwa ko suna zaune da mama yake tambayana daga ina nace na shiga gurin mama altine ne na taya ta aiki . Bai yi magana ba sai bina da yayi da harara har na shige dakin mu ban dade da shiga ba Inna ta kamala abinda takeyi sai ji kawai nayi ta rufo kofan dakin ta garam. Nace ashe yau akwai tsiya a gidan nan ke nan don Inna zata rama abinda akai min ne kwana biyu na barina na kwana dakin shirgi ni kadai sai bera ye. Lawisa ce tashigo gidan daga gurin hira ta fara zuwa dakin mu don ta kwanta taji shi a kargamay. Ina jin ta lokacin data juya zuwa inda iyayyenta suke tana fadin wai Asiya ta rufe kofan ta don haka suke kiran Inna da sunan ta gazatsau ba sayawa. Mama tace kamar yaya ta rufe kofan ta a ina take son ku kwana yau din ? Nace a raina jifa mama da son kai ta manta abinda tai min ni . Ban dai ji baba ya tanka masu ba har lokacin tasowa mama tayi ta shiga dukan kofan mu da karfi amma ko motsi Inna batayi ba ga wani katon dutse da tasa ta kare kofan dashi. Ranan inna tasha zagi gurin mama shima baba yazo ya buga amma taki budewa ban san ya suka karasa ba da yarasu yan so a gidan mudai basu kwana ba a dakin mu. Haka na kwana da wanan damuwan a rana washe gari tun da farar safiya na fito daga dakin da nake mu dana kwana. Ina alwala naji mama na tayar dasu Lawisa wai su fito kada beraye su kashe su a dakin wai sun kwana suna ihun bera. Dariya ya kumay ni daga inda nake nace farau da dadi ramuwa da ciwo ke nan tai min taji dadi yanzu an mata wai taji zafi. Baba da ya dawo daga sallah dakin mu ya fado yanawa Inna fada wai bata kyauta ba da ta rufe dakin ta inda yake shiga ba nan yake fita ba. Har ya gaji ya juya ya fita daga dakin don kan sa ba wanda ya kula shi. Na fito ina shara naga fitowan Inna daga dakin saye cikin zumbudeden hijjab din ta na sallah idanuwan ta yana fitar da hawaye. Kai tsaye na fahinci manufarta da sauri na yada tsintsiyar dake hannuna na nufe ta tare da shan gaban ta na riko mata hijjab din ta. Allah ya taimake ni duk suna daki a lokacin nace inna ina zaki ? Inna ta juyo idon ta yana zubar da hawaye cikin raunaniyar murya take ce min. Yarinya bari na tafi gidan mu na gaji da wanan tauye incin da ake min a gidan nan haka. Take nawa idanuwan suka kawo ruwa a lokaci daya ganin yadda Inna ke zubar da hawaye ga nata idon. Nace Inna may zai sa ki tafi a lokacin da nafi bukatan ki a kusa dani ? Hannun ta na kama sai naga bata mussa min ba na jata muka koma dakin mu ni da ita. Sai bayan mun shiga naji motsi a tsakar gida ashe mama ce tafito don ta hura wutan kunu. Nace haba Inna may zai sa ki bari shedan ya rude ki a daidai lokacin da mukafi bukatan zaman ki a gidan nan a tare da mu. Don Allah inna kiyi hakkuri hakan mama ta dade tana son gani daga gareki. Inna sai kuma da komai ya kusa kai karshe zakice zaki fice kibar mata gida taji dadin gallazawa rayuwan mu yadda take so. Kiyi hakkuri Inna wata rana sai labari insha Allahu. Kallona Inna take yadda karama dani nake jero mata wanan maganan haka. Zama naga tayi bakin gadon ta sai da ta share hawayen dake fuskan ta hakan ya nuna min tayi taushi ga magana na. Tace haba yarinya da za, a daina da zuwa yanzu yaci su daina sai abu yai dan sauki sai kuma abu ya sake dawowa sabo. Ni wallahi nagaji nagaji wallahi duk haihuwan da nayi a gidan nan nayi shi ne bisa rantsatsen rabo kawai amma ba da son raina ba. Nace cikin sanyin murya inna ki dai yi hakkuri ko dan darajan mu don Allah. Cikin fushi tace dani yarinya ina son na kwaci inci mune a gidan nan daga ni har ku an mayar damu kamar wasu bayi can a gidan nan bamu da incin kan mu ko kadan. Nace ki dai dan kara hakkuri inna don Allah komai da sanin ubangji akeyin sa baki san tana din da Allah yai ma hakkurin mu ba. Shiru tayi tana nazari niko ina tsaye na kura mata ido cikin tausayi nasan Inna tana matukar hakkuri agidan mu sosai. Na share hawaye nace inna ki saki ranki kamar komai bai damay ki ba zakiga mama abin ya kuma koma mata ciki. Ai ance mace ko a dakin ta tana yaji ko ? Gashi naga kin fara daukan wa kanki fansa a gare su ai basu taba tsan manin zaki iya masu haka ba da kikeyi yanzu. Nan dai nai ta bata hakkuri har na samu ta sauko naga ta dan sake jikin ta muryan mama ce ke cewa ina mai sharan nan take ne kin bar shara iska zai kwashe. Sai ji nayi Inna na fadi aiki take min a daki a sa wasu su share ba ita kadai bace ai a gidan. Nace a raina taufa ance mai hakkuri dama bai iya fushi ba mama zata kai inna ga bango ke nan. Muna nan zaune wani dabara ya fado min a raina na saurin daukan hijjab dina nace wa Inna ta ina zuwa na fice daga gidan. Kofan gida na koma na tsaya ban dade ba naga baba ya fito gaidashi nayi yana kallona yace Rahama may kike a wanan gurin da sanyin safiyan nan haka ? Nace baba kai nake dako kafito akwai maganan da nake son muyi dakai ne. Kallon mamaki ne yai min nakai durkushe a gaban shi nace don Allah baba alfarma nake nemawa inna ta akan zaman su da mama a gidan nan. Duk zaman da suke na kishi a tsakanin su baba ba wai lalai bane sai ka saka bakin ka a ciki tunda kai ba mazauni gida bane baka san waina da ake toyawa ba a bayan fitan ka. Kallona yake cikin mamaki yace Rahama har ankai lokacin da za ki tari gabana akan maganan uwayen ki. Nai saurin cewa baba ba hakana bane yaune naga inna har ta shirya wai zata bar gidan bata iyawa ta gaji da abinda ake mata shine nace bari nai magana. Yanzun haka wallahi inna batasan zan yi wanan maganan da kai ba ma hakkuri dai nake baka baba ko dan darajan mu a tsakanin ku ka rangwanta ma rayuwan ta hakana. Shiru yayi kamar mai nazarina can yace naji amma ita Asiya ne yau har tai niyar yaji ? Nace kwarai kuwa baba Allah ya gyara ni kadaine a waje na tare ta data fice daga gidan. Yace to jeki naji Allah yai maki albarka idan nadawo zanga ita innar taki zamuyi magana da ita na fahinta nace baba nagode Allah ya kara rufa asiri. Ya wuce na juya na shiga gida zuciyana fes na san ko ba komai killa Allah ya kusa kawo muna saukin al, amarin mu ne a gidan. ****** ********* ****** Tun daga wanan lokacin da mukai magana da babana ta fahinta naga al, amura sunyi wa inna sauki sosai ba inna kawai ba har ma diyan ta da akewa kahonzuka a gidan mun dan samu saida sosai. Ya zuwa yanzu ba karamin alheri Garbati yake kawowa ba gidan mu wani naci wani kuma dangin tufafi ne duk ba, a tabawa sai gurin mama altine ake boyewa. Cikin hakane na roke shi yai hakkuri har na zana jerabawa na na karshe kafin ayi bukina dashi. Da kyat na samu ya amince min wanda zuwa lokacin har labarin zancen aure na dashi yabi gari wanda mama ce da diyan ta suke yada zancen a gari. Don mama har iyalin shi sai da ta fada masu irin alherin da yake kawo muna gidan mu . Wai yanzu duk neman shi a kaina yake karewa komai kawo muna yake dani da uwata idan anga yadda muka koma wasu bulbul damu don mun samu ya rike muna kan maciji muna wasa da bindin shi. Haka yasa matan shi suka tayar da hankalin su su basu yarda ba ya dauko masu yar jikan su a matsayin kishiyar su mafarin nazo ina masu rashin kunya a cikin gida. Yace shi ra, ayin shi ke nan mai zama ta zauna wacce bata iyawa hanya a bude yake mata. GNin da gaske yakeyi yasa suka kama kan su bayan ya saka masu waigi ga zancen da cewa. Kada yaji wani ko wata yaiwa yarinyar nan ko iyayyen ta wani sheri zai dauki mumunan mataki akan ko waye a gidan. Dole suka saka mai ido ba yadda zasuyi namiji idan yaso abu kunya fice mai yake a idon shi. Mama altine ta tafi birni ganin anty da tadawo daga waje ganin likita akan matsalan ciwon ta. Sai washe gari bayan ta huta anty ke tambayan ta wai mama ina Rama na take tana nan tana karatun ko ? Mama tace wani karatu Sa, ade Raman ki kan aure zatayi bada dadewan nan ba. Haba mama wani aure yarinya kamar Rama kuma ? To ai sai kiyi Rahama kan har an kawo sadakin ta itace ma ta hudu a gidan mijin ta. Anty dake kwance tace what ? Mama wai da gake kike ko wasa tace ina wasa dake ne balle na fada maki wasa. Uban ta yaba da ita ga wani tsohon maikudi na garin mu aure yanzu haka karatun data kwallafawa raine ya hana ayi bukin kin san ta samu sa, a don kokarin ta an kaita gaba yanzu bana zata fita daga makarantan ma. Ran anty yai matukar baci dajin wanan labarin da tayi na zancen aure na nan dai mama ta koro mata komai akan zancen. Na bata matukar tausayi tace mama in ba abin kauye ba ko mu da mukai aure da girman mu yaya muka kwashe da kaidin kishiya balle yarinya karama akaita cikin guzamay mata haka ? Mama tace mu a kauye ai hakan ba komai bane gare mu amma duk da haka Rahama tayi kankanta kwarai agidan nan. Da mama zata dawo sakon zannuwan gado da sauran kayan aiki dasu kudi anty ta bayar akawo na shagalin buki na wanda baifi wata biyu ba ayi yanzu. Harda yan din kuna kala biyar da sauran abubuwa duk ta hado min tace aba Inna hakkuri saboda jikin ta bata samun zuwa bukin . Amma idan ta samu lafiya zata zo taga dakina daga baya insha Allahu. Mama tace kice wanan tafiyan na Rahama ne nayi ai taso ta biyoni sosai amma nasan mahaifinta ba zai yarda ba shiyasa na bata hakkuri. Da mama ta dawo daga birni sai washe gari muka shiga taron ta don da dare ta iso garin. Ai nan ta baje muna sakon anty na muna kallo wani abin ma ni ban san yadda za, ai amfani dashi ba agidan. Ban san lokacin da na dunkule na fara kuka ba da kyat mama ta lalashe ni na wanke fuska na. Sai da naje gida nake labartawa Inna ta abinda ya faru ta rike baki cikin mamaki tana cewa kai wanan boyar Allah ni ban san abinda zan saka mata dashi ba a duniyan nan ? Mama ko sai gori take sake muna da habaici wai rana bata karya sai dai uwar diya tai kunya. Daga uwar har uban sai kudi ake ci amma ko roba ba asai wa yarinya ba na aure . Su dai gasu gani wai an bizzine tsohuwa da ranta suga yadda za afita kunya duk tallan da nayi Inna ta kasa saye min wani abin kwarai. Dama tayi haka ne don ta kure inna don tasan ba, a aje min komai na aure ba a yanzu tunda mun sakakance cewa ni boko zanyi ba aure ba yanzu. To yanzu ga aure ya taso suga ta tsiya tasan dai gidan su Inna ba wata tsiya zasu barkata min ba don suma nema sukeyi. Magana duk yabi gari inna bata aje min komai ba ga aure ya taso ba abin kaiwa gidan miji. Lokaci ko kamar jira yake sai kara matsowa yake niko sai karatun jerabawa na dake gabana nakeyi kawai. Ba abinda yai min tsinanen zafi akan maganan mama da diyan ta a gidan mu. Garbati yasa aka gina min daki mai girma da fadi yadda zai isheni aka kewaye shiyan daban cikin na iyalin shi can gefe daya an shafa farar kasa yaji sai kyali yakeyi. Haka ya kara bankantawa iyalin shi rai sosai har suka so tayar da hankalin su. Amma da ya basu dan wani abu suma suyi gyara sai baki ya mutu murus kowa ta shiga sha, anin gaban ta da diyan ta amma kishin yana nan daram a ran su. Duk inda yabi sai ba, a ake mai na ya fado gari ya zarta maza zai bare yarinyar dalleliya a ledan ta sai ya washe baki cikin jin dadi yana dariya. Mama ko sai auki fadawa mutane karya da gaskiya takeyi akan zancen bukin tana zunden inna ta. Inna ta duk tabi ta ramay sai dan wuya daga ita sai uwar dakin ta mama altine suke shirin bukin sai yan uwan su tsiraru da sukaji suka gani. Ko su ba wai sun san shirin da Inna da mama altine sukayi min bane haka ake tafiyan a dunkule. Gaba daya daga inna har baba babu wani mai kwanciyan hankali dama ma inna dake nuna halin ko in kula da bukin. Idan ka cire mama da yaran ta wanda su ko a kwalar rigan su bai shafe su ba. Ta dai zuga shi ya zugu yanzu kuma ta saka mai ido yaji kunya dan kudin sadakina da aka kawo dashi ne yake kokarin sayen komai. Na dan gadon katakon da za, a sai min ma ya gagara daga karshe ganin haka tasa inna dabaran cewa yaba mama altine kudin ta shiga birni ko na hannu ne ta sayo min. Tayi hakane don idan kudin ya shiga hannun su sai su san dabara mama altine ne ce ta koya mata wannan dabaran. Baiki shawaran Inna ba tamika masu dan abinda ya saura takaiwa mama altine ta shirya sai birni da kudin daga karshe anty ce ta cika aka sayi min saitin gado da dan wardrove da katifa har da karin tarkace. Wanan matar ba abinda zamuce mata sai dai Allah ya bata lafiya ya shirya mata zurian ta da albarkan sa kawai. Ganin babu komai a dakin inna ta yasa mama ta samu baba da zancen da yamma bayan ya dawo gida take cewa. Yanzu malam kana ganin haka zaku kai yarinyar na aure babban gida irin haka babu komai da uwarta ta tana da mata na fita kunya kaima sai nake ganin a furin ka hakan ne ? Baba da yanzu ya fahinci mama so take taga wallen shi kuma tasan sirin abin sai ya boye mata ba su mama kudin sadakin da yayi yace anyi auren ne ko kikaga uwarta ta kaita hakana ? Haka yasa taji haushi taja bakin ta ta tsuke ta bar zancen sai ido tana cewa ni dama taimakon ku naso nayi ko mu tafi gida tumba dillaliya adan samu abinda aka tsintar mata gurin ta in yaso bayan bukin abinda aka samu sai abata kudin ta. Baba yace ko tabarma Allah ya hore mata daga gare ni sai na kaita dashi . Yafice abin shi gidan ya barta nan tana mashi dariyar mumuke ta baya tana an daiji kunya wallahi anyi shigewa ai ciki amma ba, a iya fitar da yarinya kunya. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE , , IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA KINCI AMANAN ALKAWARI DON ALLAH ZAI TAMBAYE KI HAKKINA NAYI HAKA A KAN KI DON SAI DA NA ROKE KI KADA KI FITAR MIN DA NOVEL DINA DON ONLINE NOVEL NE BA NA SHAGO BANE WANNAN DA FATAN ZAMU JI TSORON GAMUWAR MU DA UBANGIJIN MU ALLAH RANAN GOBE KIYAMA AMANA YAR UWA IDAN BAKI IYA RIKE AMANA KIYI MAGANA NA BAKI KUDIN KI DON BA ZAN YAFEWA HAKAN BA MUJI TSORON ALLAH KADA MU BARI SHEDAN YA RUDI ZUKATAN MU PLEASE, , , , Haka rayuwan zaman sabon gurina ya kasance min agidan mijina kuma babana uwayen gidana da sukai jika dani. Manyan diyan shi maza ko matan su sun kusa haihuwa na don haka mazan nake kiran su da yaya matan su da anty. Haka ya jawo min saukin zama gidan don sun kula ban zo masu da fitsara ba ko kadan. Bani kuma kyashin taya mutum aiki koda na sana, an shi tare dani za, ayi shi har a gama kuma da zuciya daya. Wanan dalilin nee yajawo min sasauci sosai a gaare su gashi zan sha aiki idan an bani naci bana ci don ban saba da irin ciye ciye haka ba barkatai. Wankin kayan Alhaji daya cire kafin ya tashi na kwasa na wanke sai dai ya sake wasu wanka kuma ya zama kullun sabanin da da sau daya ko sau biyu zaiyi wanka a sati. Ga maclean da brushe da yakeyi akai akai yanzu yake wanke baki dashi wanda na kula shi kan shi alhajin zuwa yanzu yana jin dadin sauyin rayuwan da ya samu. Don ko wa yagan shi cikin sati dayan da nayi a gidan yasan ya samu sauyi sosai a rayuwan shi. Don nakan ji matan shi suna mashi ba, a wai auren yarinya yasa shi ya sauya ga abinda basu san shi dashi ba a baya. Sai ya basu amsa da nata sallon ke nan ke ai baki min ba a lokacin ki dana sauya din tun can. Ranan da na cika sati daya ne agidan har lokacin ba wani abinda ya taba shiga tsakani da shi ban maga alaman hakan ba daga gare shi. Ina kasa ya na saman gado kwance da ya kwanta kuma sai barci mai nauyi ya dauke shi sai safe. Amma a gurin mutane suna ganin akwai abinda ke shiga tsakani na dashi a cikin dare don nakan ji sabuwa na cewa dashi ya daiyi a hankali kada ya takura karfin shi kan karaman yarinya yaje yajawa kan shi matsala kuma ? Dariya yakan yi mata yace ai yafi son haka don lokacin ta ne abar ta tayi nata zamanin. Sauran matan ba ruwan su da sha, ani na sai girmamawa amma sabuwa kan kullun sai tayi kokarin sake min magana a tsakar gida wanda zai bata min rai. A banza don wani zancen ma ban san wai dani takeyi ba har ta kare haukan ta. Idan ina zaune wani sain nakan ce ashe haka shine aure ba takura ba matsi ba tsangwama irin na mama a gidan mu ? Gashi duk Alhaji zai shigo sai ya dan sayo min dan abin tabawa watarana ma har kayan shayi da biscuit da su sweet zai bayar akawo min . Haka yasa na sake jikina sosai dasu wani sain har yar hira mukan yi dashi kafin yai barci sai dai hiran tamu nakan ga yana dariya sosai idan ina shirmay na. Ranan ya dawo daga kasuwa ya tara mu a dakin mama Hausi uwar gidan shi kusan nice ta karshen shigowa dakin inda suke zaune. Ina shigowa na samu guri na durkusa tare da gaida su gaba dayan su suka amsa min ina nan dai durkushe sai cewa mama tayi. A, a Amarya samu guri mana ki zauna ai ina ganin magana Alhaji zaiyi da mu. Nace mama har dani ? Tace kai amarya ke ba matar shi bane yanzu har da ke mana. Shi dai murmushi yayi kawai yana sauraren mu can bayan mama Hausi na koma na takure kamar uwata. Can dai yai gyaran murya alaman zai fara magana ke nan a lokacin don haka naga kowan su ta natsu. Yace to Alhamdullahi yau dai amarya ta gama satin ta daya kamar yadda sharia ya tana da. Don haka yau ne zan koma dakin wace keda girki a cikin ku don haka ina rokon alfarma gurin ku. Wanan yarinyar da Allah ya kaddari zaman ta a cikin mu da kuji tsoron Allah ku rike ta amana kamar yar cikin ku. Yar cikin mu kuma Alhaji kishiya ce zan rike kamar yar cikina ta kwana da kai in kwana da kai kuma in rike ta kamar ya ta ? Wanan maganan baiyi ba gaskiya ka dai sake wani maganan inji sabuwa dake magana a hasale a lokacin. Murmushi yayi yace sabuwa ke nan ba laifi yadda kika dauke ta a tafi a haka sai dai saukin abin Allah yasa bake kadai nake aure ba. Kuma bake ce uwar gidan gidan nan ba kinga ashe ba wani matsala ga hakan. Ita Rahama har wani kishi ta sani a yanzu bayan daukan ku uwayen ta da takeyi tana maku bauta may kuma kike so a gare ta. Eh yanzu kan hakane a/a idan ta goge ai babu shegu nan gaba kamar mu, balle yadda naga kana rawan kafa haka a kan ta wai kai ka samu yar jikan ka ka saka a daki kana abinda bai dace ba da ita. Haba sabuwa wai may yasa baki da hakkuri ne ke inji mama Kulu matar shi ta biyu. Yai murmushi tare da cewa ai ba rashin hakkuri bane gani takeyi abinda tazo gidan a lokacin tana maku rashin kunya shine itama yar mutane tazo dashi zatai maku. Sai dai ki sani alama ya nuna tarbiya ba daya ba wallahi don ke ko kwana ba, ayi ba kika fara sakani ga fitina. Amma yanzu ki duba karamar yarinya tasan daraja na tasan naku hakama na iyalina baki daya. Au to kana nufin ta fini ke nan yanzu maji magana ai gara da ka fito fili ka fada min kowa yaji. To bari kaji Alhaji wallahi duk ranan da yarinyar nan tai gigin shiga harka na sai dai uwarta ta haifi wata don ko ban halaka ta ba zaka dawo ka samu ankaita jiya gidan su. Yace ke ko da kin kwana a gadirom rana wallahi da karshen zaman ki gidan nan yazo sabuwa da kinyi nadama mara adadi a rayuwan ki. Yace naga abin naki ba wasa bane yanzu wallahi duk ranan da kikai gigin taba lafiyan yar mutane sai na lahira yafiki jin dadi a garin nan. Lalai ma ba, ayi ba yanzu aka soma ke nan don kayi dandane haukace ka zauce kamar wanda bai taba jin dadin bujen mata ba ko ? Yai murmushi yace kaiyya a fili tare da girgiza kan shi yace ashe kin gane wani bujen yafi wani buje ke nan. Ranta yai matukar baci bata karasa ba taji yace dama abinda yasa na tara ku nan shiine ke hausi ke ce babba ke zan roka alfarma don Allah. Ina son yarinyar nan ku dauke mata nauyin girki a gidan nan don kunga karfin ta bai gama kaiwa ba don Allah a dan sahirta mata wanan aikin har ta dan kara tasawa nan gaba idan Allah ya ce. Cabdijam ba ta iya aiki amma tana iya shigewa da kai daki tai shiru har safe ko ? Kai sabuwa inji mama kulu tace waban bai dace ba gaskiya shi fa ke da gidan shi balle ma wanan yaushe zata iya tuka tuwon gidan nan haka ? Ai dama nasan duk da hadin kan ku don ai min bakin ciki kuka hada baki akawo ta gidan nan idan hakane bazatayi girki ba sai dai nima na dinga yi ni da yarana kawai wallahi. Isan kinyi hakan ma daidai ne inji Alhajin amma ki sani cikin ki tayi don su nan duk suna da sarakai da zasi girka masu ba sai sunyi ba kece mai yara kanana da yawa kuma. Tace koma maye na dai ji muddin wanan yar mussan da ka kwaso baitai girki ba nima bazan yi ba wallahi yace har da shan wallahii tace eh na sha. Mama hausi ta bude baki zatai magana ya dakatar da ita yace Hausatu kada kice komai hakan ma yafi min komai dadi daga yau kowa ta girka nata da diyan ta ita kuma Rahama ta girka wanda zataci can shiyan ta. Dama ba yau ba kike min korafin sai nasa sarakaina suna girkin gidan nan naki biye maki amma yanzu tunda haka kike so hakan yai min dadi wallahi. Sai dai kada ki manta ba leken tallen kowa ba kuma wani zancen na wance yafi nawa na kashe wanan korafin a gidan nan. Yarinyar na kuma ba ruwan ki da ita ko irin habaicin da nake ji kinawa yar mutane kada na kara jin shi a gidan nan. Idan ba haka ba wallahii rai zai baci don haka ke Kulu da hausi ga amanan wanan yarinyar gare ku da diyan ku na danka maku don Allah ku tayani bata tarbiya yadda ya dace. Sukace insha Allahu Alhaji mu yarinyar nan bata tsare muna komai ba wallahi har yaran mu tunda tasan darajan mu. Ko yaran nan suka dawo kasuwa har kofan su takee binsu tai masu sannu da kasuwa yaran su kuma tana haba haba dasu . To yaron da yasan haka may zakace akan shi kuma sai fatan alheri yadda muma muka haifa itama Allah ya bata nata tasaka a cikin mu ba shi ke nan ba. Yace nako gode dama nasan bazaku ki duk wani abinda na koso ba gidan nan indai har alheri ne da jin dadi na don haka Allah yai maku albarka suka ce amin a lokaci daya. Yace ke kuma Rahama tarbiyan nan da iyayyen ki sukai maki ina son kici gaba dashi don shine tubalin zaman ki gidan nan. Can sabuwa tace muma da ba a saka muna ba Allah yai muna shi sannan yaya zancen namu kayan dakin daka saya mata. Cikin mamaki yace kayan daki kuma nine ma na saya mata kayan dakin nata ke nan. Tace idan ba kai ka saya mata ba uban waya basu kudin sayen wanan kayan haka giredi masu kyau ? Yace toni wallahi ko ku yarda ko kada ku yarda ban san komai ba akan wanan zancen. Ita bata da mahaifa ne da zasuyi mata ban san lokacin da nace nikan anty na ta birni ce tai min komai ba wani ba. Yace to kinji tai wani irin murguda baki tace haka dai akace kawai amma wata anty gare ta na birni da zatai mata wanan. Yace to yanzu dai kowa yaji kowa ya tsaya a matsayin shi babba ya rike girman shi karami ma ya rike nashi. Yace ku tashi ku tafi na gama magana na ni ban son wani abu kuma ya biyo baya. Bayan fitan su sai ni ban fice daga dakin ba mama tace Rahama tashi zuwa dakin ki kinji. Nace mama ni anan zan kwana tsoro nake ji ni daya a dakin nan kada sabuwa ta kashe ni. Subbahanallahi inji su suna hada baki ita da mijin ta yace kin gani ko ta riga da ta tsorata a gidan nan da sabuwa. Mama hausi tace kinga tashi na sa zuwaira ta tayaki kwana a dakin naki ba shi ke nan ba. Daga ranan muka fara kwana ni da zuwaira a dakina kafin mu kwanta mukan yi hira na ta karanta muna labarai a littatafai. Idan nace ina da wani matsala kuma nai karya girkin abinda zanci ma sai na so don idan su mama sunyi nasu suna saka min wani lokaci naci wani sain kuma nace na koshi. Gashi ban gajiya gurin kama masu aiyukan su tun suna hanawa har sun gaji sun kyale ni ina yi da zuciya daya don yadda uwa da yar ta suke haka nake dasu su biyun. Idan girki ya zo kaina a dadafe cikin takura nakeyin shi don Alhaji kan min nauyi a dakina har yanzu na kasa sake jikina dashi. Sai ma kwana da zuwaira yafi min ace shine zai kwana a dakin duk da ba komai yake min ba sai lalashi da ban hakkuri wanda ni ban fahinci na maye ba. Nayi kyau dani haskena yafito har dan kiba na kara gani shar fes dani idan kin gan ni. Har kirjina dake a shafe sun fara tasowa yanzu sai dai duk wanan dadin da nake ci hankalina yana gurin Innata ko yaushe don yanzu ban san wake dibar mata ruwa ba wake mata talla wake mata aiki don kanni na duk yan maza ne. Kaunata mace yar karama ce sosai ita aka yaye ba a haifi wani ba bayan ta ko may yasa inna bata kara haihuwa ba oho ? Sallaman wani yaro ne a kofana rike da dakwalen kaji guda biyu a hannun shi sai kayan miya a wani leda mai yawa yace Alhaji ne yace ya kawo min. Na karba yaron zai tafi nake cewa ya tsaya nazo na shiga daki na dauko mai biscuit na bashi har ya fara tafiya yace. Amarya Alhaji ko na tsaya na taya ki gyaran kajin ? Nace to shi ke nan dauki kaje a yanka bari na sa ruwan zafi kafin ka dawo ya juya dasu yafita. Daidai lokacin da sabuwa tafito daga daki yaran ta sun fada mata an kawo kaji a sashe na yanzu sai ko ga yaron tafe dasu za, a yanka. Tabi kajin da kallo har yaron ya fice daga gidan tanisa tace hum, umm ashe akwaita ke nan ? Tare da yaron muka gyara ya kama min nayanka na zauka na shuga jajagen kayan miya kafin wani lokaci har guri ya dauki kamshi. Miya ya kammalu na sauke na dora tuwo duk tare da yaron nan da yace min sunan shi habib ne dan gidan mai faci. Sai yamma Alhaji ya shigo gidan daga shiyana ina zubawa yaron abinci naji muryan sabuwa tana cewa yau wani sabon cin amana ne da muna funci ya taso a gidan nan kuma ?. Kamar yaya kuma ya tambaya tace duk munafuncin da kake a gidan nan nabawa yarinyar nan kayan dadi taci don ta yarda dakai ta kwantar da hankalin ta ka murje ra yadda kake so nagane ka. Mu sai ka tura muna tuwo ita ko daga shinkafa sai taliya kake bata bata taba cin tuwo a gidan nan. Ga kowa yai cirko cirko yana sauraren ta yace cikin daka tsawa ke sabuwa ban son sheri ni kike kira da munafuki yau. In ma har munafunci ne ai ake nakeyi don ke ce munafukan kullun a gidan nan ba mai bani bani sai ke, ke, kenan kullun yin karya da ciwon yara ba ranan da zan fita baki karbi kwabona ba a gidan nan karyan yau daban na gobe daban. Kaji kuma na sayo mata don itace mai girki su nake son ci shiyasa na sayo ke ranan da zan sayo bacewa kikiyi wai nabaki kufin ba ki sayo da kanki dana baki na dawo cewa kikayi n sace kudin ai. Nawa nake ba wanan yarinyar a gidan nan ko bata nayi yadda nake bata sai dai tace na sayo mata duk abin da ya dace idan na fita. Sabuwa nan ta hau borin kunya akan wai Allah dai ya kama ka yau kila ma har gashin dare kake kawo mata kai a dole gaka mijin yarinya ko ? Sabuwa yau dai na gaji da sherin ki a gidan don haka na fada maki akan yarinyar nan zan iya saba maki kifice min daga gida. Ahayye nanaye abin kunya wai aure da mara kwabo yace balle da kwabona ko kin manta kwabon kika gani a baya kika lake min da aike da komai har na yarda kika shigo gidan don haka yau ko wayai maki tsaye a gidan nan wallahi baki kwana min a gida. Maimakon ta ci gaba da gudan da takeyi sai kuma jikin ta yai matukar sanyi sosai don tasan takan mashi fiye da haka amma bai taba yanke irin wanan hukuncin ba a kan ta sai yau kuma akan yar karamar yarinya. Nan dai mama hausi ta saka bakin ta tace asha Alhaji da baka biye mata ba halin sabuwa ne kuma bako a gare ka yau. Yace bari hausatu nagaji da sherin yarinyar nan yau ta kaini kat ne ita bata ji kunyan yaudara na ba sai nine zanji kunyan ta. Ina kazan nan a kowan ku da yai girki sai da na saya mai aka girka min naci amma don wanan yarinyar na da girki na sayo zatai min sheri tace ai ba biyu ka saya muna ba kamar nata. Bai kula ta ba ya shige dakin ta da kan shi ya kwaso kayan shi na kwan ciya ya fito daga dakin nata. Hankali yai matukar tashi sosai a lokaci don nasan halin kauyen mu yazu labari zai sha banban ace daga shiga na na fara watsa matan gidan da na samu. Hakana jiki ba kwari na dinga aiken wanan yaron da Allah ya hadani dashi yau yana kai wa kowa miyan duk sai da na kusa rabe naman don yawan gidan. Mama hausi dake zaune tare da sarakan ta matan diyan ta su uku ta ce kungani ba yanzu ga naman ma karshen ta duk ta rabe shi gare mu. Har ya fita zuwa sallah ya dawo bata bar gidan ba kamar yadda ya bukata haka yasa shi zuwa har kofanta ya daga labulen dakin yace. Sabuwa may kike jira ne a gidan nan wai ai tunda gidan nan bana ubanki bane yau na fada maki wallahi baki kwana min a gida ki tafican gidan ku kikarata can. Idan kuma kin ki fita yanzu na turo masu karfi aja min ke da karfin tsiya har waje. Ganin haka tasan kuma da gaske yake yi yasa ta fara tattara kayan ta tana kuka wai saboda karamar yarinyar da kokwai bai aje da ita zai koreta gidan shi ita dake da yara bakwai a gidan. Haka tafice daga gidan bakin ta bai mutu ba ta nufi gidan su a cikin dare kowana na kallon ta a wullakance. Sai bayan tafiyan tane na fahinci ashe halinta ya ishi kowa agidan sai fadin aibunta kowa keyi. Nan naji abubuwa da dama akan halinta ashe shiyasa take ganin an auro ni zan karbe mata power da take dashi a gidan da gurin mijin su. ****** ********* ****** Washegari tunda safe na shiga gurin mama bayan na gama aikin da nakeyi na kwashi kayan wankin ta sai aune tayi dani ina wanke tufafin ta. Ta saka salati tana cewa haba amarya ai sai kina ace muna bautar dake ko iyayyen ki suka samu labari bazasu ji dadi ba gaskiya. Nace daidai danta babba yana shigowa gidan dauke da dan karamin yaron shi a kafadan shi haba mama don nai maki wanki shine za, ace kina bautar dani kefa uwatace mama ba kishiya ba kamar yadda naji ana fada. Ko a gida nike wankewa su innata har da mama kayan su idan yai dauda don wanan kayan da baida yawa ma. Girgiza kan shi yayi yana cewa a ranshi ikon Allah yanzu baba wanan karamar yarinyar daya kwaso kurciya zalla haka may zai gane a gurin ta ne wai. Nan dai dole uwar ta barni da wankin na wanke su fes na shanya na koma dakina ina jiran su bushe na kwashe mata. Yaron nata mai suna yaya sani ya shigo dakin mahaifiyar tashi ya samu guri ya zauna daga gefen ta yace. Mama dazun sai nake jin ki da amaryan ku a bakin rijiya kuna gaddama kuma akan wanki. Tace bari kaidai ni kurciyar yarinyar na ya fara daure min kai wallahi bata tasan kyashi ba ko hassada a rayuwan ta komai haka zata zage tayi shi tsakani da Allah. Yace haka naji nima sai dai mama gaskiya sai kunyi da gaske gurin rike amana tun da dai ba sanin ciwon kan ta tayi ba yarinyar gashi uwarta tai mata tarbiyan da ya dace duk uwa ta gari taiwa yarta. Tace insha Allahu haka nake kokarin ganin nayi yo har ma may mutum zai cuta a wanan gurin kuma ? Nan dai sukai ta zancen su har suka fado kan maganan sabuwa da irin hallin gallaza masu data dinga yi a zamanin ta a gidan. Mama hausatu tace don yaran ai ayi hakkuri ta dawo dakin ta gashi kuma bazan so ace don wanan yarinyar tabar gidan nan ba. Kada azo a shafa wa yar mutane labbo bata ci ba tasha akama zarginta ga banza kasan haln mutanen yanzu da dauka su dagwarawa kan su maganan da bata shafe su ba. Dan nata yace hakan yana da kyau mama indai wanan mara mutuncin ne aiko ta dawo ba dainawa zatayi ba. Gara dai tadawo dakin ta din zaifi don kaga yanzu idan tafice gidan nan nauyin diyan ta duk akaina zai dawo gasu ba tarbiya ke garesu ba. Yadda mama hausatu tai shawara da danta haka akayi da yamma da Alhaji yadawo gida ta sanya shi a gaba tana bashi baki akan yayi hakkuri ya daure sabuwa ta dawo dakin ta hakana ko don yaranta. Yace wai hausatu ke ce ke auren ta ko ni da zaki isheni naje nayo bikon ta ina indai sabuwa ce koke bata bari a gidan da tsufanki kuwa ? Mama hausatu tace kadai yi hakkuri Alhaji kodan yaran ta ta dawo taci gaba da duba abinta. Yace yara ai bada su tazo ba anan ta samay su kuma a gidan iban su suke ko ? Ya ja tsaki ya dauki buta ya fice daga gidan. Gaba daya yaran Sabuwa sun ishi matan gidan da rashin kunya idan ka cire shi Alhajin da basuyi a gaban shi don tsaye yake akan iyalin shi. Don haka shi zaman su ma babu uwar su a gidan ko a kwallan shi bai taba damuwan shi ba don dan ficewan ta har ya samu natsuwa tare dashi. Satin ta daya shiru babu labarin dawowan ta gidan har wanan lokacin ganin maganan wasa zai zama gaskiya yasa. Mama hausatu samun wani dan uwan Alhaji kuma amin shi akan zancen sabuwa din don yaran sun ishesu ba hutu gareta. Bayan sun gaisa ne tayi mashi bayanin komai akan matsalan da ake ciki tsakanin sabuwa da Alhajin. Malam shehu yace a gaskiya ba yau ba Alhaji hakkuri yake da al, amarin sabuwa ke ma kin sani . Don ko jiya muna tare nan dashi yake min bayanin komai don iyayyen ta da yan uwan ta sun damay ni da zariya agida. Amma tunda kinzo ba komai insha Allahu anjima zan samay shi muyi magana idan ya dawo. Mama tace don Allah malam a taimaka a sa baki ga alamarin a gyara tun bai baci ba kodon yara. Daga haka sukai sallama ta tafi tana godiya don sun saba dashi sosai akan matsalar gidan su. Duk yadda ya raya da Alhaji akan yai hakkuri Sabuwa ta dawo dakin ta yaki yarje mashi. Don haka ya kyale shi malam shehu ya nemi wani amin shi da magariba suka shirya sai gidan wan sabuwa inda take zaune. Lokacin da suka isa gidan sun samu wan nata baya gida dole suka dan jira shi don ba nisa ya tafi ba. Bayan sun gaisa ne suke cewa da shi dama mun biyo bayan sabuwa ne don Allah ayi hakkuri ta koma dakin ta hakana. Don sabani akasamu kuma yanzu kowa ya gane kuresa don ko tsakanin harshe da hakori ana samun sabani balle mutum da mutum don gaskiya iya hakkuri kukan ku kun sani Alhaji garbati yana iya hakkurin shi da sabuwa a gidan shi. Yayan nata yace hakane amma naso ace shi Alhajin ne yazo nan da kan shi don na kara bashi hakkuri saboda nima dan zaman ta cikin iyalina nasan yana hakkuri sosai. Malam shehu ya jinjina kan shi yace hakane amma da zuwan Alhajin da namu duk kusan guda ne don a madadin shi muka zo mu. Koma may nene ai yanzu ta san ta fara kaishi bango don baka kallon babban mutum kamar Alhaji garba tsakiya iyalin shi tace mai munafuki. Yayan nata yace don Allah akara bashi hakkuri kafin nazo har gidan na bashi. Yayan yace kafin ku tafi bari na kirata taji da kan ta don ku kara ja mata kunne mace da girman ta kamar Sabuwa ace wai ta saura yaji don rashin hakkuri irin nata. Bai jima ba suka fito a tare yana gaba tana bayan shi ta samu guri daga gefe ta tsugun na. Yayan nata yace sabuwa ga malam shehu nan sunzo bikon auren ki a madadin maigidan ki. Ta dukar da kai cikin kunya da nauyi zatayi magana malam shehu yace da ita. Haba Sabuwa yanzu lokaci yayi da za, a san girma ya kama a daina wasu halaiya kuma. Don Alhaji ya auro wanan yarinyar bai kamata ace daga gareki ne ba a samu zaman lafiya ba idan kin yi tunanen irin zaman da kukayi ke dashi har takai kina ci masa mutunci a tsakiyan sarakan shi hakana. Don haka idan kin koma dakin ki da fatan komai zai sauya daga gareki yanzu shiga ki dauko kayan ki basai gobe ba mutafi na mayar dake dakin ki. Zatai magana yayan nata dake zaune a gefe yace ya katseta cikin bacin rai da cewa . Kin sani sarai bana son tashin tashin kije ki shiryo ku tafi. Ba don taso ba ta tashi ta shiga ciki can sai gata tafito da lulubinta dauke da dan ledan kayan ta suka kama hanya. Ko da suka iso gidan sun samu Alhaji a kofan gida shi da baba salla zaune suna hira. Yacewa Sabuwa shiga gida ta shige simi simi ciki shi kuma ya tsaya wajen su Alhaji dake kallon shi a cikin mamaki. Nan ya zauna ya dinga bashi baki akan yayi hakkuri ya taushi zuciyar shi akan iyalin shi. Yace babu komai tunda taci albarkacin shi zai kula ya saka ido ga komai a gidan insha Allahu. Muna zaune kofan mama gaba dayan mu gidan ga hasken farin wata ya haske ko ina anyi gungu gungu ana hira. Sai ganin shigowan ta kawai mukayi gidan da kumshin kayan ta babu ko sallama. Kowa ido ya saka mata wasu sun gane cewa itane musanman ma yara ta da suka hau ihu eh mama mama da murnan su. Nan dai duk da batai sallama ba aka shiga gaida ita tana amsawa cikin basarwa ta shiga dakin ta. Ganin akwai duhu a dakin sai gata tafito tana cewa mama yaya ara min fitilar ki na haska naga guri don Allah. Mama tace a dauko mata ta amsa fuuuu ta juya zuwa dakin nata daya daga cikin sarakan mama tace bisimillahi Allah matsala ta dawo ke nan kuma. Kowa nan suke fadin albarkacin bakin su akan dawowan nata kuskus kus daya bayan daya muka watse gurin kowa ya kama gaban shi. Da daddare can sai gashi ya shigo gidan dakina ya nufo don nice da girki a ranan. Ya samu kujeran da yake zama kafin ya kwanta ya zauna na gaida shi da dawowa yace. Amarya kinga wanan fitinanan ta dawo gidan ko ? Nace wa wai maman Suwaiba ? Yace ita , Don haka abinda nake so dake kikama kan ki daga gareta daga ita har yaranta ba tarbiya ne dasu ba. Nace insha Allahu zanyi kamar yadda kace Alhaji bazan shiga tsabagan taba ko na diyan ta a gidan nan. Ashe sabuwa tun shigowan shi gidan tana hankalece wai ita a zaton ta tunda ta dawo ranan a dakin ta zai kwana don haka takeyi wa sauran matan nashi a baya. Tana ganin ya wuce zuwa dakina wani tukukin bakin ciki da kishi ya rufe mata zuciyar ta a lokaci daya. Don haka tafito fuuu zuwa dakin mama hausatu tafada mata daki tana haki tace yaya kinga wanan mutumin baya son a zauna lafiya a gidan nan ko ? Mama tace da akayi may kuma Sabuwa ? Tace amma ai yasan na dawo amma ya iya wucewa ko dakina bai leko ba yana nufin cewa yarinyar nan itace zatai girki ko may ? Ke sabuwa wai yaushe zakiyi hankali ne ke ki san jiya ba fa yau bane ? Idan mu dacan kin samu kina muna yadda ran ki yaso yanzu baki tunanen cewa wata tazo gidan ne. Gara ki rufawa kan ki asiri ki zauna dakin ki ki dubi yaran ki zai fi maki sauki wallahi . Aiko da dakike muna hakan idan kin dawo kema kin san ba hakkin ki bane yin hakan don dai a zauna lafiya muke saka maki ido kawai. Yanzu kuma wata tazo yarinya danya sharaf kice zaki tauye mata nata incin kinga haka zaiyuyu kuwa. Gara ki kama kan ki da mutunci ki a gidan nan tun bakija wa kan ki raini ba ga yar diyar cikin ki da ko uwarta kin girma ga haihuwa. Nan dai taga ba ci idan tace zata ja gashi da kyat ta samu tadawo dakin ta tun ba, a kwana ba kuma ace wani matsala ya taso a gareta haka ? Ta juya cikin kwafa zuwa dakin ta tana faman mita da ace tasan zaman da muke da mijin nata da take ganin na anshe mata data bawa kanta lafiya. Don idan tace taja wani fitina da daren nan wani sabon tonon asirin ta ne zai a bainan jama, a don yanzu maigidan nasu akan yar karamar yarinya baijin ass. Don a dole banda yadda zanyi nake zaune gidan gashi har takai iyanzu na saba da komai ina zamana hankali a kwance tunda ba takura. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE NA FADA IDAN BAKI BIYA BA KIKA KARANTA MIN NOVEL NA BARKI GA ALLAH. IDAN KIN BIYA KIKA TURA MIN NOVEL WANI GROUP KO KIKA BA WA WANDA BAI BIYA BA KE MA NA BARKI GA ALLAH DON KINCI AMANATA ALLAH ZAI SAKA MIN A KAN INSHA ALLAHU WACE TASAN BAZATA IYA RIKE AMANA BA DON ALLAH TAI MAGANA NA BATA KUDIN TA TAFITA MIN GROUP DON AMANA NAUYI GARE SHI ABINDA KA RAINA SAI YA HANAKA KETARE SIRADI GOBE KIYAMA ALLAH YA BAMU IKON RIKON AMANA A TSAKANIN MU. DON NAGA NOVEL DINA A WANI GROUP KUMA NASAN WACE TA FITAR DON BATAI MAGANA BA NA BARTA GA ALLAH DON ALLAH SHEDA NE GA ALKAWARIN MU DA KU, , Ranan da na zana jerabawan karshe na na secondarya rana ce da ya kamata nai mafarin ciki a raina don kowa ka gani a cikin mu yana cikin farin ciki da jin dadi a ran shi. Sai dai ni a gareni sabanin hakane don ya kasance min kamar rana na bakin ciki a gare ni. Lokaci daya yanayi na ya sauya min naji duniya tai min kunci a raina komai ganin sa nake yai min baki a raina a dalilin tunawan da nayi wanan jin dadin rayuwan ya kusa yanke min. Don wanan auren jarabtan da na tsinci rayuwana dashi na auren tsoho da mahaifina zai min a lokaci daya haka, batare da yai la, akari da irin rayuwan da zanje gidan miji na tarar. Wanda yau baifi saura kwana goma ba naje gidan Alhaji garbati a matsayin matar auren shi nima a gidan. Juyawa nayi zuwa staff room don nai sallama da malam mutumin da yai tsaye a kaina har nakai wanan matsayin na yau a gare ni. Malam yana ganina yace a, a Rahama an kanmala ko ? Maimakon na nuna farin ciki na sai na kai durkushe a gaban shi na fara kuka yace subbahanallahi Rahama lafiya dai ko ? Cikin kuka nafara cewa malam nazo ne nai maku godiya akan tsaya min da kukayi har na kai ga wanan ranan ga karatuna. Sai dai kuma gashi guri na ba zai kai na zama likitan da nake son zama ba na taimakawa yan garin mu kamar yadda nake da gurin haka a rayuwana. Mahaifina ya yanke min wanan gurin nawa ta bayar dani aure ga wanda yaso yau saura kwana goma ayi bikina akaini. Subbahanallahi inji malam yace yaushe haka ya faru kuma Rahama waye kuma miji ? Sai na dan kakaro murmushi a fuskana nakw cewa malam an kwana biyu da hakan ba kuma kowa bane mijin sai Alhaji Garbati dan bida na garin nan. Shi da sauran malamai da suke saurare na cikin tausayi sukace garbati dai garbati wanan tsohon mutumin da muka sani ? Nace shi malam , Malamai suka ce kai amma mahaifin ki ya cuce rayuwan ki Rahama ga wanan tsohonbzai bada ke dan kwadayi ko don may ? A hankali nace nima ban sani ba malam na mike ina masu godiya na ke masu sallama na tafi, Nan na barsu da mamaki kowa na fadin albarkacin bakin shi a kaina na nufi gida. Na shiga gida da sallama na na gaida da su mama da na samu tana raba abinci a tsakar gida. Nan na shige dakin inna na kwabe uniform din jikina fita nayi na debi ruwa don na watsa naji dadi jikina. Mama ta bini da harara wai dan ruwan da zasuyi aiki dashine kuma zan kwashe nai wanka don ni nafi kowa tsabta ko may ? Ina ban daki na fara watsa ruwa ne naji mama tana rafka salati haka yasa nasan ba lafiya ba ke nan. Nai saurin watsa sauran ruwan a jikina na fito da sauri nan na samay su tsaye cirko cirko sai fada mama takeyi ita kadai Inna ta tana tsaye a bakin kofan ta itama fuskan ta a cikin damuwa yake. Na karaso inda take ina fadin Inna lafiya ko may ya faru kuma ? Kafin mama ta bani amsa take cewa dani wai angon ki ne ba lafiya gashi can an kwashe shi zuwa asibitin birni yanzu. Gabana ne naji ya yanke ya fadi min ras ras nace shi Alhaji garbatin ne da kan shi baida lafiya ? Mama tace idan bashi ba da uban ki ko bakiji may nace bane ni. Allah ya sauwa nace na watsa ruwa a kafana dana rage a sauran roban da na fito dashi ban daki da nai wanka. Nashige dakin mu kawai na fara sallah bayan na idar ina jin mama tana karasa aikin ta sai faman mita takeyi akan zancen ita kadai a tsakar gida. Na juya inda inna take zaune cikin damuwa nace inna may ya samay shi ne ? Take cewa dani yanzu nima nake jin zancen a gurin yaya wai ya kwana biyu yana irin wanan ciwon dama. Allah ya sauwaka nace, naci gaba da kwalliya na ba abinda ya damu raina ko kadan. Sai bayan dawowan babane muka samu labari wai ashe ya kwana biyu yana irin wanan lalurar . Fitsari ne ke mai wahalan fita idan zaiyi sai kuma yanzu da suka tafi asibiti ake cewa harda hawan jini yana da shi. Mama sai cewa tayi Allah ya cece mu ga farar kafa mu kan ? Kamar yaya farar kafa kuma baba ya tambaye ta hakanan ? Tace to yau saura sati a saka lalle haka ya kasance dashi ai sai ace yar mu ce zata shiga da farar kafa gidan shi . Ki kadai fadi yanzu inji baba lalurar da kowa yasan ashe yana dashi dama shine zaki fadi haka ? Tace ai idan ni ban fada ba iyalinshi su fada tunda koda yake dashi duniya basu sani ba sai yanzu . Lauratu wai may yasa baki son a zauna lafiya ne ke duk abinda zai kawo fitina a tsakani kin san yadda zaki jawo shi. Idan da yar cikin ki ce za, a kai gidan ai baza, ki fadi haka ba akan ta. Allah ma ya tsare ya ta da wanan rayuwan gaskiya ne baka son a fadi kuma in ni ban fada ba duniya zasu fada ai. Baba yace yanzu na gane may kike nufi akan yarinyar nan mutane suna fada min ban yarda ba amma yau na yarda da hakan. Nan dai suka fara halin nasu na sa in sa a tsakanin su wanda ba mai shiga don ko mutum ya shiga sai yai kunya don ajima kadan zakaga sun shirya ne. Bayan an sallamo Alhaji garbati ne daga asibiti ya turo kiran babana yana son magana dashi. Baba baiyi nauyin kafa ba ya tafi amsa kiran da Alhaji Garbati yake mai a kofan gidan shi inda akai mai shimfida mutane suna zuwa gaida shi da jiki baba ya samay shi. Bayan sun gaisa yai mashi yaya jikin shi da sauran iyalin shi ? Ya bukaci da sauran mutanen dake gurin yana son ganawa da babana akan wani magana sun san alakal dake a tsakanin su don haka suka basu guri. Alhaji garbati ya sake gaida babana yake cewa ya aika a kira shi ne don su yi magana akan zancen auren shi dani. Yace bai san ko don matsalan da ya samay shi za, a iya daga bukin har zuwa lokacin da Allah zai bashi lafiya sai ayi. Baba yace haba Alhaji ai kowa yasan lalurar ciwo inda yin ba zai zama matsala ba sai ayi din a wuce gurin. Alhaji yace amma duk da haka da a shawarci yarinyar da uwarta aji ta bakin su don kada azo ayi daga baya kuma a zo a samu matsala ya biyo baya. Baba yace hakan ma shawara ne zai je yayi shawara da ni da uwata yaji ra, ayin mu ga hakan. Nan dai sukai sallama baba yai mai fatan samun lafiya ya tafi ya barshi a gurin da ya samay shi a zaune. Baba ya dawo ya samay ni da inna ta a daki muna hiran mu cikin jin dadi tai muna sallama ya shigo daga ciki. Nan ya samu guri ya zauna ya na mike zan bar dakin yake cewa dawo ki zauna magana zamuyi daku. Na koma na zauna cikin natsuwa a inda nake yace dama akan zancen auren Rahamane yanzu Alhaju garbati ya kira ni gidan sa mukai magana. Jin abinda ya fadi yasa muka natsu daga ni har inna ta muna sauraren shi muji may zai fada muna. Kaf yadda sukayi da Alhajin ya fada muna tare da tambayan mu may ye ra,ayin mu akai mu ? Inna tace to malam ko dai an daga bukin nan ai ba fasawa za, ayi ba ko ? Don may ba, a ayi a haka ba kowa ya huta da kace nace akai asan ayi an gama ta zaunu a dakin ta. Baba yace ke Rahama may kika ce shiru nayi ni may zance tunda bani ce da ikon kaina ba. Baba ya sake maimaita tambayan shi a gare ni a hankali nace baba abinda Inna ta fada gaskiya ne ayi kowa ya huta kawai. Baba yace to madalla Rahama Allah yai maki albarka yasa haka shine alheri a gare ki. Sai kiyi ta hakkuri da halin rayuwan da zaki tsunci kanki a gidan don kin san manyan mata zaki sama a gidan. Idan kin je masu da taushi yadda na san ki sai kiji dadin zama dasu har iyalin su. Amma idan kince zaki nuna masu halinku na diyan yau sai ki samu matsala dasu har iyalin su. Mama da taji muryan baba a dakin mu ta kasa zaune ra kasa tsaye akan tana son jin may akeyi a dakin wanda ba, a son ta sani. Sai ta hau fadin tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa ka doka ai wanda yaci shi ka biya don dai nasan bai wuce ance garbati yace a mayar mai da komai nasa ba ya fasa. Wanan rufa rufan wa za aiwa shi wa zai kwashi mai farar kafa ya jefa a cikin iyalin shi . Baba dai ya fito bai kula ta ya fita da dare ya koma ya fadawa garbati yadda sukayi da iyalin shi. Shiru yayi yana nazari maganan baba na irin halarcin da sukai mai don shi a rayuwan shi yana son kasancewa da wanan yarinyar a rayuwan shi. Don haka ba, a fasa komai na shirin buki ba akaci gaba da gudanar da shirin da za, ayi. Mama a zaton ta an fasa ne ne sai da taga yan uwan Inna suna shige da fice ta fahinci akwai zancen bukin ke nan. Nan kuma hankalinta ya tashi ta sulale har gidan garbati taje a cikin dare ta gana da matan shi take fada masu mugun kalamai na batanci akaina da uwata. ****** ********* ****** Ranan kamu aka saka ni a lalle kamar yadda akewa ko wace budurwa kamu. Duk wanda ya ganni ko inna ta yasan bamu a cikin walwala ana dai sha, ani ne kawai na bukin ba cikin dadin rai ba. Gidan mama altine nake zaune da kawayena don a gidan mu babu fili ga magan ganun mama da basu da dadin ji. Ya kasance washe gari daurin aure nan mama ta dora a tsakar gida ga dakin Inna tab da yan uwan ta sai cewa mama take ita bata gane ba fa. Ace har yanzu ba, a fito da kayan amarya ba aje zuwa jere ko sai mutane sun watse ne za, a tafi jeren kamar marasa gaskiya. Wata daga cikin yan uwan Inna ta fito tana bata amsa da cewa in ma mutane sun watse ai ko wasuwasun mu zamu iya gyara dakin yar mu. Ballanta na rana muke jira yai sanyi mu tafi don bamu fada gidan mutane da rana tsaka ba kamar mun gaji da yar ta mu. Dole mama taja bakin ta tai shiru ta kyale su dai gani ai duk abin da akewa taratara din ake boyo yau rana ce da bata karya sai dai uwar diya tai kunya. Sai zuwa karfe biyar mutane suka fara shiga gidan mama Altine suna kwaso kayan da aka saya min na aure. Wata daga cikin kawayen mama da ta gaiyyata suzo saka ido ta shigo tana cewa mama. Ke laure wai kayan da naga ana fitowa dasu gidan mai kuli na waye ba dai kayan yar taki bace haka? Ni duk garin nan ban taba ganin yarinyar da akaiwa kaya haka ba ? Kinko ga kayan kamar ma na kamfani ne fa don a cikin ledan su ma suke, ga wasu irin manyan zannuwan gado da na fani kamar na makka dasu didin didin dasu. Gaban mama ya fadi tace ke haule wai da gaskiya kike ko ba, a baki ga komai nakai gida ba tace idan karya nake fita ki ganewa idon ki ai. Mama bata saya ba taja wani raggan zani dake shaye a igiya ta nufi kofan gida da saurin ta. Aiko tana lekawa tai tozali da kujerun da ake fitowa dasu tace kan uban nan ni za, aiwa munafunci ke nan. Watau malam yana da kudin yin wanan kayan haka wa yar shi. Shine ya barni da yara a zunbule a daki sun kai sun kawo ga girma kuma ba manema suka rasa ba. Da kyat kawayen ta suka samu ta natsu suka jata zuwa cikin gida dakin ta suna tausan ta akan idan tai haka taba da kan ta. Nan dai aka shiga shirin buki ba wanda ya tsaya kula mama da haukan ta da takeyi ta kasa boye hassadan ta a fili. Bayan sallah jumma, a aka daura aure duk dai ba wani shagali akayi ba tunda ba auren saurayi da budurwa bane, amma an ci ansha an koshi. Da yamma aka dauke ni sai gidan Alhaji garbati gida ne babban gida mai cike da iyali fiye da arbain a gidan. Sai da aka kaini dakina na dan zauna na yan mintina akace na taso akaini dakin uwayen gidan. Dakin uwargidan mama salla aka fara kaini dattijuwa ce sosai don ta manyanta sosai ba sai an fadi ba itace ta wanke shi ya wanke ta. Nan iyayyena suke fada mata cewa ga amanan yarsu nan sun kawo masu da fatan zata rike masu ni amana idan nayi ba daidai ba don Allah ta tsawata man. Tace kada suji komai ai da na kowa ne da fatan nima zan masu biyayya yadda ya dace karami yai wa babba. Suka ce insha Allahu in wanan ne baza, a samu matsalan komai ba a kaina. Nan dai suka mike suka bar dakin ina biye a bayan su sai dakin mai bi mata itama dai acan ba matsala sai cewan da tayi na daiyi hakkuri don su yara ne da su sa, a na dama wa yanda suka girmay ni. Mun bar dakin zuwa dakin wacce nake biwa ita ma din tana zaune da mutane da yaran ta bayan an gaisa aka fada mata zaman lafiya ake nema a gare mu. Sai cewa tayi haba zaman lafiya a tsakanin kishiya da kishiya ai sai dai zama na ki goga in goga tasan gidan da ta shigo ai har ta yar da ra kutso kai don kwadai ita da iyayyen ta. Ai babu wani zaman lafiya illa tazo ga tukunya nan lamba ashirin ta tuka mu tuka da ita don yau an zama daya. Daya daga cikin yan uwan mama tace to shi ke nan Allah ya bata ikin iya tukawa kamar yadda kowa keyi a gidan. Muka bar dakin muna jin ta tana yadda bakaken magana wai haka kawai an koso yarinya karama don jaraba an kawo masu a g raino a gida ace wai an basu amana. Dakina aka mayar dani aka zaunar dani a saman gadona da ya sha gyara nan aka shiga jero min nasiha na zaman lafiya har sai da na rasa na kamawa. Sukai min sallama suka fice gidan suka bar ni ni kadai a daki nai tsuru tsuru dani kamar manya. Ban san lokacin da wani kukan bakin ciki yazo min ba ga daki har daki amma ba ango a gurin ba gidan zaman lafiya a nan. Ina nan zaune a takure ni kadai a dakin naji sallama muryan mama naji uwargidan garbati na amsa mata sallaman ta a sanyaye. Tana dauke da wani zani kamar bargo na rufa da tocila a hannun ta na mike tsaye ina cewa sannu mama. Tace a, a Rahama ke kadai ce a dakin ashe to ga kayan kwanciyar angon ki na kawo maki idan kin kare girkin ki zakikaiwa wace zata karbi girki kayan ita ma a dakin ta. Bayani take min amma gabana sai faduwa yake min a lokacin na rasa fahintar komai da take fada min har ta fita tabar dakin ban fahince ta ba. Na kalli kayan data aje min a bakin gado tare da kura masu ido ina nazarin su. Na koma daga can kuryan dakin na zauna sama kujera tare da kara bin dakin wanda yake mallakina da kallo. Sai faman tunanen irin rayuwan da zanyi a gidan nakeyi ga maganan Sabuwa da ya tsorata ni da tace wai ni kishiya nake a gare ta. Baifi minti sha biyar ba da fitan mama din uwargidan shi sai na ji motsi alaman za, a shigo dakin nawa. Mamace again tare da maigidan nasu tana mashi jagora kallo daya zakai mai kasan baida cikkaken lafiya a tare da shi don yanayin tafiyan shi ma kawai ya nuna hakan. Da sallama ta shigo dakin yana biye a bayan ta ban iya amsa sallaman ba don girman su da nake gani. Tace Rahama ga anginki na kawo maki kin san dai yanayin da yake ciki da fatan zaki lalaba muna shi dai. Murmushi naji yayi ta juya ta fice daga dakin na mike daga inda nake na durkusa kasa nace a cikin sanyin murya ina wuni baba . Murmushi yayi yakai zaune a inda na tashi ya dan kalle ni yace yaya hidimar buki amarya ? Ban iya cewa komai ba sai sada kaina da nayi a kasa kawai babban rigar dake jikin shi naga yana kokarin cirewa tare da aje hular kan shi a gefe daya. Da alaman dama kayan sun ishe shi a jikin shi yake cewa dani sai kuma ga angon naki da matsala amarya. Sai lokacin na dan kalleshi naga duk ya ramay ya fada sosai ga yadda na san shi da farko. Dan tashi mana amarya ki miko min kayan can na saman gado na sauya ko ? Gurin da kayan suke na kalla tare mikewa zuwa daukowa na kawo mai na durkusa tare da bashi kayan. Ganin da nayi yana kokarin sauya kayan ne a gabana yasa nai saurin fita daga kofana na tsaya sai dana tabbatar da ya gama na shiga dakin. Yace yauwa zo ki zauna ko dauko ledan can ki dan samu kici wani abu daga ciki don nasan kina tare da yunwa. Nace a koshe nake baba sai da Inna ta tabani abinci naci kafin na baro gida dazun. Yayi shiru yana kallo na tare da nazarina sai kuma fuskan shi da na dan ga yanayin sa ya sauya a lokaci daya. Yace amma wanan din hakkin ki ne na yau da ya dace na baki ai na kawo maki. Nace a koshe nake shiyasa. Yace to ni miko min na danci kafin na kwanta ko ? Duk a takure nake a lokacin don yanayin yadda ya ke zaune cikin doguwar rigar jallabiya yasa nake kara jin nauyin shi sosai. To zo mana ki zauna nan amarya gaki tsaye kin kasa sukuni ko ? Gabana yai mumunan faduwa nace a raina wanan tsohon may yake nufi nazo na zauna zaman sa, a da sa, a dashi ko may ? Nayi maza na juya can daga gefe nakai zaune a kasa tare da dukar da kaina kasa ina wasa da yan yatsun hannuna cikin dan lankwasa su. Zuba min ido yayi a inda nake a zaune yana kallo na kafin ya bude baki yace Rahama yau gaki Allah ya kawo ki gidana cikin iyali na amatsayinki na mata tata. Yace don haka ina son ki kasance yarinya mai ladabi da biyayya ga wa yanda kika sama a gidan. Idan kinyi min haka kinyiwa kanki da nima adalcin rayuwa. Don bazan taba jin dadi ba a rayuwa idan har wani rashin mutunci ya fito daga gare ki a zaman ki na gidan nan. Idan kinyi haka kin min komai a rayuwana wanda hakan zai sakiji dadin zama dani bama ni kadai ba har ma kowa da zaki sama a gidan. Nace insha Allahu zaka samay ni kamar yadda kake tsanmani a rayuwana yace to Allah yai maki albarka ya tashi kata kata ya mike tare da nufar gadon da yasha shimfida yana cewa ki dai yi hakkuri da yanayi har na dan wani lokaci amarya. Daga haka naji yana bissimillah yabi lafiyayen gadon ya kwanta tare da mimikewa a sama yana sauke ajiyan zuciya. Can yake cewa idan kin gama zaki kwanta sai ki rufo muna kofan dakin daga ciki kinji. Nayi maza nace mashi tau ba, a dauki lokaci ba ina daga inda nake zaune naji ya fara nasari alaman barci ya dauke shi ke nan. A hankali na mike na nufi kofan na rufo kamae yadda ya umurce ni da nayi idan zan kwanta. Na koma kasa na kwanta ban dade ba sai barci dama jikina da gajiyan jigilar dana sha na jama, a atare dani. Bani na falka ba sai asuba ana kiraye kirayen sallah naji motsin shi haka yasa na falka tare da mikewa zaune zubur yace a kasa kika kwanta Amarya ? Ya dauki buta zuwa bandakin da akai min a kusa da dakina basai na shiga na taron gidan ba sai bayan ya fito ne na shiga nai tsarki na dauro alwala na shiga dakin. Bayan nayi sallah ban kwanta ba tunda na saba a gida bana kwanci sai aikin gida idan na tashi na gyara gadon daya kwanta tare da sharo dakin har zuwa kofana inda aka kewaye min shi nagyara ko ina tsab. Na fita zuwa tsakar gidan duk girman shi sai dana share shi kafin gari ya karasa waye, Na hada kayan wanke wanken da na gani birjit ko ina na gidan na fara wankewa . Sai lokacin matan gidan da yaran su ke fitowa daga barci duk wace ta ganni sai ta tsaya tana mamaki hakan . Ina gaishe su daya bayan daya suna shigewa dakunan su da yaran su. Ina gamawa na juya zuwa dakina na debi ruwa na shiga na watsa na saka wani lace mai laushi dashi cikin kayan da anty ta aiko min dashi. Duk da ban san kudin shi ba nasan mai tsadane kwarai ga dinkin yai matukar karban jikina kamar an auna ni kafin a dinka min shi. Can na fara jin hayaniyan matan gidan suna fitowa tsakar gida daya bayan daya haka yasa na gane cewa sun tashi ke nan na yafa gyale a kaina na fito na fara zuwa sashen mama tana kokarin fitowa daga dakin ta tana ganina tai murmushi take cewa a,a amarya baki huta ba gaki da gajiya kika fito kikai wanan aikin haka? Hutun may zatayi bayan dama an saba da komai tun a waje muryan sabuwa ce dake bayan mu hannun ta rike da wani karamin roba kore. Na durkusa na gaida mama da ina kwana mama tace lafiya kalau Rahama yaya dare yaya angon naki ? Sabuwa ta kara cewa dare kan ai kinga inda alaman shi ya nuna ba a wahala ba don ansan komai. Haba sabuwa wai may yake kawo wanan magana hakan ga wanan karamar yarinyar kuma ? Wanan ai ba sa, an yin ki bace may ta sani akan zancen ki dakikeyi yanzu sai muryan maigidan mukaji daga bayan mu lokacin ina durkushe a gaban mama yana cewa. Sabuwa ki kiyaye ni wallahi a gidan nan don zan iya saba maki akan yarinyar nan a gidan nan fiye da tsanmanin ki. Idan ba hauka ba irin naki yanzu wanan yarinyar zaki titsiye a gaban ki kina fada mata wanan magana haka ? Ina yatinyar take tashige daki ta kwana da kai ta fito kemaymay da ita har kake kiranta yarinya. Yarinya kan na bayan uwar ta ai wace bata san shigewa daki da namiji ta kwana ba kuma ta tashi lafiya tarmazazai haka ?. Ganin dayar matar tana cewa kai haba tunda wanan farar safiyan haka za, a tusa muna wani fitina a gida. Na mike daga gurin mama na nufe tare da durkusawa har kasa nace ina kwana mama ? Tace a,a amarya ni ba mamakin bace zaki iya kira na da yaya ko maman Aisha. Nai murmushi na kara gaishe ta ta amsa fuskan ta ba yabo ba fallasa cikin sa dacewa yaya daren Amarya ya angon naki koda yake gashi nagan shi ya samu lafiya ai a gaban mu. Inda sabuwan take na nufa itama na gaida ita a cikin ladabi sai cewa tayi ke tashi da kili bibin ki idan ban kwana ba zaki ganni ne nan ? Yace uhumm kaji ba ke abinda baki taba yiwa yan uwan ki an maki kuma kina jin haushi yanzu . Ni dai ina ganin sun rikice na juya zuwa dakina ban tsaya sauraren su ba. Sai zuwa can naji ya shigo dakin shima dai gaida shi nayi tare da mai yaya jikin yace jiki da sauki sosai. Zuwa can naji anyi sallama ya amsa wata budurwa ce daga cikin diyan shi dauke da kwanon kunu da kosai taje cewa baba ga abin karyawa inji mama akawo maku. Yace kice ana gaida ita da aiki ko inda nake bata kalla ba tafita daga dakin har takai kofa naji ya kirata yace suwaiba kun gaisa ne da sabuwar umman taki ? Tace baba ai ban gan ta bane tabashi amsa murmushi tayi tace ina kwana . Nace mun tashi lafiya yaya gida bata tsaya ba tabar dakin yace taso ki dibi kunun da kosan mai isar ki kisha. Nace sai zuwa anjima bani karyawa da safe haka ai yace to injin ku yan boko ne ?. Da naji alaman suna aiki na fito na samu ashe kowa ce ta fito tana aikin sana, anta da takeyi a gidan . Na kama wa mama dama kokon da takeyi za, a fita mata dashi nan da nan muka gama. Sai mai bi mata dake dafa shinkafa da wake itama na karbi wanke shinkafan na wanke mata tas na zuba tare da gyara wutan da icce ya jaye na hura wutan sai gashi ya kama. Ban koma daki ba sai dana kwashe mata shi a kwano na gyara yadda za, a fice dashi na koma daki na. Na samu maigidan ya shirya zai fita yace ina kika shige ne Amarya nace ina gurin da ake aiki ne. Yace to ni zan fita sai na dawo zan dan leka waje nagani ko akwai abinda zan iya yi a can na neman kudi. Kin san angon naki dan bida ne ba mai zaman gida bane ni. Na durkusa nace Allah yasa a dace Allah yaba da nasara a dawo lafiya baba. Yace kai ni fa wanan baban ba son jin shi nake a bakinki ba da dai za, a canza min suna ko Alhajina akirani dayafi min alheri. Nace to Alhaji Allah yaba da sa, a yasa a fita a nasara yace amin yar amarya ta yaushe rabon da naji anmin fatan alheri haka a rayuna. Nan yasa kai yafice ni gyara dakin na dan zauna sai barci ya kwashe ni afurin mai nauyi ban sani ba. Muryan yan gidan mu ne da suka shigo ganin kwanana ya tayar dani daga barci. Na mike zubur ina masu sannu da zuwa idanuwan su fes a kaina suna kallona ban san may suke son fahinta ba daga gare ni. Na gaidasu daya bayan daya tare da tambayan sauran mutanen gida. Da yake iya yan uwan inna ne sai kadan daga dangin babana sai cewa sukayi kowa lafiya sai maman ku ne dai da ta saka muna hauka wai sai baban ku ya fada mata inda ya samo kudin da yai maki hidima haka na fita kunya. Duk rantsuwan da yai mata ba yarda dashi ba wai idan bashi ya yi ba mijinkine yaba da kudin aka boye mata. Nace cikin murmushi tare da zama kan makarin kujera na kai mama ho yaushe zata bar wanan halin nata ne na hassada da bakin ciki. Ita da tace da tabar za, a kawo ni yanzu da taga sabanin haka shine kuma ta tayar da hankalinta. Rabu da mahaukaci wacce bata son azauna lafiya iji kauna babana ta fadi hakan. To yaya kuka kwashe da matan gidan naku yau da safe da fatan babu wani matsala dai ko daga gurin su. Nai dan murmushi nace babu komai mama batare da na fada masu abinda ya faruba da safe akaina a gidan. Sai dayan mama tawa tace ai ina ganin indan dai ta iya binsu zata samu sauki ga biyun mata wanan dai da take biwa ce matsala nake gani sai yaran su kuma don naga yaran a tsaye suke suma. Nan dai sukaci ga ba da yi min nasihohi na in zauna da zuciya daya dakowa na basu girman su tunda duk sun haifeni baki dayan su. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WASU MUN BARKI GA ALLAH YA BI MUNA HAKIN MU A KANKI YAR UWA DA FATAN ZAMU JI TSORON ALLAH MU RIKE AMANA DON AMANA GIRMA GARE SHI. Dawowan Sabuwa gidan yasa yanzu na rage fita gidin darbejiyan da matan gidan suke fita hira ko yaushe. Idan ma na dan fita bani daukan lokaci a gurin don gujewa shiga tarkon ta don ko yaushe ita a cikin fitina take. Gata irin figagan matan nan ne marasa jiki komai nata dan kyamn, ne a fige sai bakin fitina da mita ga yawan haihuwa a yadda naji matan gidan suna fadi wai bata yayewa take samun ciki. Ganin na rage fitowa ne yasa ranan mama hausatu take tambayana dalilin kumshewa na daki yanzu murmushi kawai nai mata batare da na bata amsa ba. Sai cewa tayi Allah ya kyauta halin sabuwa sai ita don mai hali baya barin halinsa komu nan ba barin mu tayi ba ai da girman mu gaban diyan mu da sarakan mu sai taci muna mutunci ba komai bane a gurin ta. Jin da nayi yarona abokin hirana dan makwabbcin mu habib yana da kwazo ga karatu addini gashi karami amma Allah yai mai baiwa gurin garatu. Yasa na ke zama dashi muna karatun mu a shiyana muyi karatu idan mun gama muyi ta shiriritan mu kamar yada kauna muke dashi. Don dan abinda yake samu a gurina gashi na rike shi da zuciya daya shima hakan nake gani a gare shi don bai taba min abu sai ya roke ni . Wasa wasa sai na fahinci ba karamin karuwa nakeyi ba da karatun da nakeyi a gurin habib din. Hakane ya bani daman tunanen na roki Alhaji idan zai yarda na rika zuwa makarantan islamiyan dake kusa da gidan mu. Don akwai daya daga cikin sarakan gidan da kullun ita sai tafita zuwa daukan karatu. Da naiwa Alhaji magana yace haba amarya kofa wata uku baki kai ba da zakice zaki fara fita ? Dole na hakkura naci gaba da karatuna tare da habib din amma abin yana a raina. Dama nayi nisa tun a gida haka yasa na samu saukin karatun a yanzu wani lokaci kuma littafaina na boko na kan dauko nai tabi ina dubawa ni kadai a daki na. Mama Hauwa tana aikin fura sai dai ba kullun takeyi ba daga shiyana nake jin harshen ta tana fada da yarta mai mata talla wai sunyi rana ga aikin kuma yarinyar ta tsaya tana shiririta ga aikin. Na mike tare da shiga daki na sauya zanin jikina na jawo kofan dakin da kuma kofan shiga shiyan nawa don akuyoyin gidan masu bakin barna. Na samu ga gari aje ga aikin gida da yasha mata kai don ita ce da girki ranan. Ina zuwa nai mata sannu na karbi rariyan dake hannun ta na shiga tankade da gyaran garin. Na fahinci su kamar mama lauratu na gidan mu suke don basu damu da koyawa yaro aiki ba a gida. Yar ta Amina tana fitowa ta ganni a zaune ina tankade tace wai har naji dadi amarya dana ganki don yanzu dana fita tunda kin saka hannu ga aikin nan zaki ga na sayar da furar nan a take. Kai ji wani batu daga can kofan mama hausatu Zuwaira tace mama ai ba karya ta fada ba mun gane idan amarya ta taba kayan sana an mu a take muke saidawa idan mun fita. Hannun ta yana da albarka sosai wallahi a kaji min yara da sabon surukulle kuma ? Inji mama hauwa take fadi tana dariya tace muma wallahi zuwaira ta fara lurar damu haka dakuma muka duba muka ga ai hakan gaskiya ne. Nan dai sauran matan gidan aka taru ana wanan zancen ana dariya ni dai akina nake ban yi magana ba. Daga can kofan ta sabuwa ce ke cewa daurewa karya gindi ke nan ita waye da zaku ce haka ko watafi sa, a kuke kara zugata tana ganin ta kai wata aba a cikin mutane ji wani sabon tsurkun da kuma kuka camfa mata don taji dadin iya shege. Ni dai wanan aikin jagwalgwalen badani balle a camfani ni kishiya bata fini ba balle na sa a kaina. Wanan abar ce zaku tsaya kunawa wanan camfin kamar wata babban mace can da ita. Nan daya da kacin sarakan mama ta cafe da cewa ai ba camfi bane dama can a garin nan kowa yasan irin sa, an dake ga Rahama ai gurin talla don komai ta dauka sai kudin shi. Eh hakane dama tunda tana da tsifin dake mata juye subata kudi ta kaiwa uwarta ana cewa sa, a ne yanzu ai gaskiya ya tabbata don mungani koshi Alhajin ba ragowa ne ya kwaso muna ba Allah mudai ya cece mu da daukan ciwon sanyi wallahi. Shiru gurin yayi don jin inda ta biyo da zancen can mama hauwa tace wanan kuma sabon kake ne don ban taba ji bani kan abin garin nan da ba a boye yake ba. Tace kece baki sani ba kuma dole ne sai kin sani ba tunda idon ku ya rufe don kawai ai min sheri a hada min kai a gidan nan aga bayana nida Alhaji ko mutu ka raba. Sai lokacin mama hausatu uwargida tai magana tace kai haba sabuwa in an girma asan an girma mana yanzu wanan yarinyar dako hankalin kanta bata gama mallaka ba zaiyi wanan sheri a matsayin ki na uwa. Ke ma fa gakin nan dasu a gaban ki indai yaran ne ai ba uwar da zata so aiwa yarta sheri haka ? Au to yaya abin yakai can baki zakiyi wa yarana kuma? Ai dama ba yau ba nasan sun kai maku ko ina a gidan nan saboda hassada aiko tashiga bakin ta harshen ta har waje ana jin ta. Daidai lokacin ne mukaji gyaran muryan maigida yana tafe tare da dan shi babba a baya da mai bi mashi. Tun a kofa yake fadin wai yaya ne kuma may kuma ya faru haka da rana tsaka. Ledan dake rike a hannun shi na vaco na je na karbo da sauri yayin da sauran matan ma suka karbi na hannun mazajen su idan ta akan ledan dana karbo take fada. Na nufi dakin mama hausatu da ledan don itace ranan da girki sai yamma zata fita sabuwa ta karba don girkin namu a jere yake muna. Ina nufin shigewa dashi dakin ta yace dawo dashi nan mikawa hausatu a raba abakowa nata ta shiga dashi ya juya yana fadin tambaya nakeyi mai ya faru wai ake wanan fada murya har kofan gida. Shiru kowa yayi babu ma magana a cikin su sai Amina yar shi ce ta shiga koro mai da zancen abinda ya kawo rigiman haka. Ya kalli inda sabuwa take yace kai amma dai sabuwa ke mutumiyar banza ce wallahi. Kina zaton yadda kike watsatsa haka kowa ma yake a rayuwan shi tashinki a garin nan aike ce kika so bata tarbiyan yaran garin nan kaf don ke kka zo da wanan halin ko don su nan basu sani ba har kika samu bakin yiwa wata sheri kuma ? Haba nan ta juye bala,in ta kan shi sai da yai saurin saka mata waigi ta dakata don tasan abin da yake nufi zai iya aikata shi da gasken a kan ta. Malam wanan kuma Yaya za, a yi dashi tana kokarin fitar da gorunan man shanu daga cikin ledan tana jerawa a kasa. Ya dan juyo gare ta yana tsuki abinda ya dakatar da su daga fitinan da suka dauko yi da sabuwa ke nan. Yace ai gora hudu ne ko kibawa kowa nata ke Amarya ya duban gurin da nake ina gyara wutan huran da muka nasa yana zabarbaka daga tukunya. Jeki ki karbi gorunan ki bawa kowa nata kason ta dauka da sauri na nufi gurin mama hauwa din na fara kaiwa mama hausatu ta zaba na mikawa mama hauwa na ta,na dauki daya zuwa gurin yaya sabuwa da nata goran . Tun kafin na karaso na ji tace may kike nufi wai ke yar wayo ko kin zabi mai kauri kn kawo min mai ruwa ko ? Da sauri na juya inda dayan goran yake na dauka na kai mata ta zaba sai da ta karba ta jijiga ta kara juyawa sama da kasa sai ta miko min wanda na aje da farkon na juya don duk a tsorace na ke a gaban ta kada ta make ni. Kaiyya inji mijin su daga gurin da yake zaune saman wani dutse dake tsakar gidan. Yana na kallon yadda muke kwasa da ita kan man shanun da ya sayo muna daga kauyen da suka tafi. Tace ana dai rabon son kai a gidan nan ace da may iyali da mara iyali duk kaso daidai za,ayi shi wai haba wanan ai dul cikin zalumci ne wallahi Allah ko. Zaki soma ko ? Wai ke Sabuwa baki ba kanki lafiya ne ki rufawa kanki asiri ne haka wai ?. Kin manta da yadda aka kwasa a baya ko da kyat fa na samu malam shehu yai bugun gaba yaje ya dawo dake . Au to kina son fada min cewa kece kika tura biko na ko may ? Daga inda yake zaune yace ke dama kina daukan cewa zata canza halinta ne ai mai hali baya barin halin sa. Yace ke hausatu dauko min tsimayn nan nawa na dan sha don banjin alaman dadin jikin nan. Nan dai kowa ya watse ya kama gaban shi muma muka gama hura kusan nice nai aikin huran don na iya dama tun a gida. ****** ********* ****** Kamar yadda mata idan sun taru sai zancen mazan su hakane ke kasancewa yanzu a gurin maza. Taron da akeyi na fadanci a kofan gidan na Alhaji garbati wanan karon ma sun hadu ana fadanci don dan abin da suke samu daga gare shi. Baba salla ne ya fara cewa aikai Alhaji sanyin babana lafiya lau kake ga amarya ga sanyi . Ko ba a fada ma jikin ka ya nuna ka samu lafiya ga hakan nima dai kukewa zanyi naga na samu koda bazawara ce mai dan dama na kawo gida ko zan samu dan gurin hutawa bana. Jin zancen su kawai yake amma zancen yana tsuma shi sosai haka yasa ya yanke cewa zai gwada ya gani dai ko ya samu lafiya shima ya fara murzan amarci da yar amaryan shi. Ranan da akai wanan zancen a dakin sabuwa yake dama ta ishe shi da mitan ita a bukace take fa. Bayan ya shigo gurin ta ya kokarta yaga ya samu gamsuwa amma ya kasa hakan gashi ta isheshi da minta wai ai da amarya ce inda yake kare karfin shi gurin yar karamar yarinya dan yai bajinta ta gani. Shiko ya na samun kanshi daga gareta ya fara wani irin nishi yana jin kamar ranshi zai fice mai a lokacin. Da kyat yaga safiya sabuwa ce ta tayar da mutanen gidan don neman taimako a kan shi. Ba,a bata lokaci ba da safen nan aka nufi asibiti dashi hankali a tashe duk kowa gidan ya koma jigun, jigun abin babban gida take a kashiga tsegumi ga Sabuwa. Wasu suce kila wani mugun abin tai mashi har taso halaka shi, wasu kuma suce dama ba lafiya gare shi ba kila bakar jarabanta da ta sabane ta matsa mashi har ta so halaka shi. Nidai da yake akwai kurciya a tare dani ba fahintar zancen su nakeyi sosai ba amma na shiga halin damuwa don ance sabo turken wawa ne. Dan zama na gidan ko ba komai yana bani kulawa yana tattalina yadda ya dace ayi. Sai zuwa karfe biyu suka dawo tare dashi yaji sauki sosai kamar ba shine aka fita dashi gidan da taratara ba.. Sun tara mu duk kan mu matan shi a dakin mama hausatu sun muna bayani cewa likita yaba da doka kan cewa mahaifin su har yanzu bawai yaji saukin lalurar shi bane don haka akula don Allah kada a dinga matsa mai kancewa lalai sai yayi wani abu da watan mu a bishi a hankali. Ni dai na fahinci suna magana suna yawan kallon inda nake zaune ni da sabuwa ne amma ba wai na gane manufan su bane. Sai da yai mata kwana biyun ta ya dawo dakina kamar kullun idan nice zanyi girki na kammala komai da nakeyi wanda ba sai na fita tsakar gida nayi shi ba. Don ni ai fadan sabuwa zance gaba ya kaini don Allah ya rabani da tuwon taro komai a dan karamin shiya na da aka kebe min nake abina wanda hakan yakaiwa Sabuwa ko ina. Tayi mita akan itama sai ya kebe mata nata shiyan daban kamar yadda ya ke be min nawa ni kadai nake kwamacala na ba wanda ke ganina sai wanda ya shigo inda nake. Girki dai Alhamdullahi don tun a gida nakeyin abina tun mama nacewa wai Innata tana sa ina masu jagwalgwale har ta gaji ta sa ido ranan girkin inna ta idan na dawo tallah da wuri kafin naje diban ruwa zan tsaya na taya ta aikin girki da gyaran gida. Haka yasa yanzu ban sha wani wahala ba a gidan auren nawa da na tsinci kaina a ciki da rana tsaka. Yau da yake ba fita hira yakeyi ba sai gashi ya dawo gurina tunda magariba, anan yai sallolin shi kofan daki inda yasa nai mashi shimfida. Nakawo mai abinci na koma daki na zauna ina ciki naji ya kirani yana cewa fito mana Amarya ki barni kuma ni kadai a waje ina maki gadin kofa. Haka yasa na fito daga ciki na samu gefen tabarman da yake zaune na zauna can dan nisa kadan dashi. Ya soma cin abinci koda na fito yace wai ke waya koya maki girki haka ne yar karama dake amma kin iya girki haka. Nace Lah inna ta ce ai nice ke mata girki idan ina gida, yace kai amma gaskiya ta kyauta min sosai. Yaushe rabon da na dinga cin girki haka acan acan mai dadi a gidan nan ? Cikin shirmay yara nace kai haba Alhaji ga mama hausatu ga mama hauwa ga kuma yar barayan ka duk kace baka cin girki mai dadi ?. Yace ai sunayi amma nakin yafi dadi ne Amarya da ina da lafiya ai wanan girkin da kika iya da na more ma hannun ki . Don ance yadda mace ke aikin ta ko mai nata haka ake samun shi nace to kila magi ne basu sakawa kamar yadda nake sakawa a nawa ? Murmushi kawai naga yayi min yace to ke naga bakici komai ba mana ko har kinci naki ne ? Sai da na dan tabe baki can nake cewa nifa ko a gida tuwo bawai ya damay ni bane nafi son naci shimkafa komai rashin dadin shi ko abu mai dan ruwa. Shiyasa ma mama takan ta fada da inna ta wai itace take koya min rashin cin tuwo gani diyar tallakawa dani sai karya. Nace kuma fa Alhaji babu laifin Inna a ciki nice dai bana so idan an matsa min naci sai na amaye shi kaf. Yace ikon Allah abin naki halita ne ke nan nace haka naji Inna ta tana fadi shiyasa koda zanyi auren nan maganan inna ta ko yaushe shine kada nai sakaci da kunnu don shine abincina. Yace to ashe sai na dinga sawo maki shimkafa kawai kina sarafawa kina ci ko ?. Nace a, a kada ka wahal da kanka ai na saba da hakan don ni abinci bai damay ni ba. Yace ashe shiyasa man shanun da na sayo maku ke naki kamar ba, a amfani dashi tunda baki cin tuwo ? Muna cikin haka dashi sai ga mama tashigo gaidashi tace a, a ango da amarya ake hira ashe Sabuwa na bayan ta tafe. Sai ji mukayi tace ai abinda yakeyi ke nan yana biye mata kullun jiya wa yau abu yaki ci yaki cinyewa an kwaso muna mai farar kafa tana batun mayar damu marayun dole. Haba Sabuwa may yakawo wanan magana haka kuma a gurin nan wanan yar cikin taki ne zaki tsaya yiwa wanan magana haka ? Tace Allah ya raba yata da wanan bakin jaraba na wanan yarinya dubaki gani don tsaban rashin kunya wai zaune take shimfida daya da Alhaji adole ita wai ga mace ? To yin haka laifine kuma mace da mijinta ana raba su zama ga shimfida daya tunda anriga da anzama daya ko ? Dama yaya kune masu daurewa karya gidi ai take gani kamar ta kai mace ? Kai yauko ga wata magana ga sabuwa uku gareki uke ke gareta to mayye banbanci a nan. Ya dakatar da ita da cewa yanzun dai may ya kawo ki nan din don ina fama da kaina ban son fita ? Tace dama zuwa nayi naima yaya jiki sai na samu kana ma a cikin raha ne ashe kai ? Yace eh kin san ina gurin da ake kwantar min da hankali kamar yadda nake bukata ko yaushe. Ai naga alama sai ayi a sannu don kaji dokan likita idan da son samune ma kabar gurin yarinyar nan har ka samu lafiya don nasan kana ganin ta ba kyaleta zakayi hakana ba ? Yace shi likitan ne yaba da dokan na kauracewa iyalina din ? Kada na basu kulawan da ya dace dasu sai na nisance su ko ? Kadai yi a hankali don ko banza ita a ganiyar kurciyar ta take yanzu tunda jarababban yarinya ce ta na iya saka yin abinda bashi ba ? Yace kamar yadda kika sani yin dole shekaran jiya ko kika tashi kashe ni ke nan ? Idan ban kashe ka ba ai wanan mai ido tsakiyar kai zata kashe ka ita. Ta juya ta wuce abinta yace sakariyan banza kawai mara hankali da tunane. Nan mama dake sauraren su tun zuwan su ta nisa tace kai halin sabuwa sai ita kullun ba a girma. Yace ina girma ga sabuwa anan bakin kishin yarinyar da bata ma san tanayi ba yana batun kashe ta don ita kanta kawai ta sani a duniya. Sai lokacin nace mama ina batun zuwa gaida ke da wuni sai gaki kuma kin shigo yanzu tace to na hutar dake ai nazo duba jikin maigidan ne dama. Yace jiki Alhamdullahi da sauki sosai yanzun ma nake batun shan magani na da likita ya ba ni ai. Tace to amma malam a tsaya ga na likita kawai ba a dan gwadawa dana gargajiya agani kuma ko a dace. Yadda aka fita dakai a gidan nan fa shekaran jiya ya tayar wa kowa da hankali sosai. Yace ai ina kan gwadawa ke ma kin sani al,amarin ciwo ne yanzu idan ya kama sai a hankali fitan shi. Ta nisa tare da cewa haka ne kuma Allah dai ya kawo sauki kawai za, a ce . Ta juyo inda nake na dukar da kaina ina wasa da kafana dana ke kadawa a hankali, take cewa to mu kwan lafiya Amarya. Nace mama Allah ya bamu alheri tace amin ta juya tafice tare da rufo min kofan shigowa sashen nawa. Yace bari na koma daga ciki sai ki samu ki shige da kayan nan ciki ko ? Nan ya mike da kyat zuwa cikin daki ni kuma naci gaba da kawar da kayan da yai amfani dasu a gurin. Haka a dadafe yai kwanakin da zaiyi a daki na ya koma gurin sauran matan shi can. Ranan naji shakat a raina don nan yake zaune duk wanda yazo gaishe shi ciki zai shigo su gaisa dashi. Haka yasa na kasa sake jikina a gurin nawa don yawan manyan mutanen kauyen mu da ke shigowa gaida shi. Shi ko na lura yana jin dadin azo a samay shi a gurin nawa da yake acan acan ko yaushe a cikin gyara da kamshi. Don ina manejin dan kayan kamshi da anty ta turo min dashi daga birni saboda mama altine ta kashe lokaci gurin yi min bayani a kan kamshin dakin mace. A ranan da ya koma dakin mama washe gari sai ga Iyyaye na sun samu labarin rashin lafiyan nashi sunzo gaida shi. Ina dakina ban san shigowan su ba ashe har sun dan jima da shigo sai mama Altine ne ne kewa ni banga diyata ba fa ? Lokacin mama ta tura a kirani ana fada min na taso da murna na nazo dakin inda suke da zuwa ina ganin su maimakon nai murna sai kawai na fashe da kuka kawai. A, a ashe da mun san haka zakiyi muna da bamu zo ba sai dai mu tsaya daga kofa mu gaidashi mu koma. Da kyat suka samu nai shiru mama altine tace ashe har yanzun yar tawa bata daina wanan tabaran nata ba ? In banda haukanki ai sai a dauka ko wani mugun hali ake maki gaki kinyi kyaunki bulbul dake daki ya karbe ki. Na kara shigewa jikin mama altine ina cewa wallahi mama nayi fushi ace idan ita Inna ta taki zuwa ta dubani har dake mama bazaki zo ki gan ni ba sai kace nai maku wani laifi ? Yanzun baga mutanen gidan ku masu kirki da karamci suna kula dake ba duk halin da kike ciki fa muna da labari. Mama altine da dayan makwabciyar mune kawai suka bini zuwa dakina ita Inna ta taki zuwa nan ta zauna dakin mama hausatu har su fito daga guri na su tafi. Narasa irin taron da zan masu don murna nace mama ni nama rasa may zan baku wallahi tace, ba mu ruwa ya wadatar damu tunda munsha a dakin yar uwarki amma zamu sha naki. Ruwan randan kasa na da yai matukar sanyi har naso bayan randan ke bayarwa don sanyi. Na debo masu suka kinkima sosai nan muka kara gaisawa dasu suna ta yaba kyaun dakin danayi. Nace mama yaya wajen anty na kuna da labarin ta ko ? Tace Anty ki Alhamdullahi don ta samu lafiya sosai har naji tana cewa tana son zuwa ta duba mu ma nan. Nai murna kwarai dajin wai antyna zata zo garin duba mu mun jima da su mama muna dan hira sukace zasu koma sai ga yarona habibb da leda wai Alhaji yace abawa bakin da sukazo suyi hakkuri. Ban tsaya duba ko may ke cikin ledan ba na mikawa makwabciyar mu ledan sukace ashe mu dawainiya muka kawo maku kuma mu da mukazo duba lafiyan maigidan. Kafin su barni su kara jamin kunne nayi hankali da Sabuwa da diyan ta a gidan don gujewa makircin su. Ban sani ba ashe bayan tafiyan su fitina ya tashi tsakanin Alhaji da Sabuwa wai don may zai ba su mamana leda da abuba ciki ? Wa nafi da zai fifita uwaye na akan su ai itama matan gidan su suna zuwa gaidashi amma bai taba basu komai ba sai ni za , abawa iyayyena. Da kyat aka samu wutan ya mutu bayan kakausan kashedin da yai mata yana hurta sai ya sake ta wanan karon. Jin kalman saki yasa ta ja bakin ta tai shiru tasan tunda ya furta hakan zai aikata ne don bai taba hurta mata kalma na saki ba a duk rikicin da sukeyi tsakanin su. Sai gashi yau akaina yana furta mata cewa ta ishe shi da fitina a gida ai itama wasu ta samu a gidan kuma ba abinda bai mata ba lokacin da take ganiyar amarcinta har zuwa yanzu. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , , IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WA WANDA BAI BIYA BA ALLAH NA GANIN KI DON AMANA NE, , , Izuwa yanzu komai na gidan ba matsala saboda kakausar kashedin da manyan diyan Alhaji suka taru a tsakar gida sukayi. Kan abar masu mahaifin su ya samu lafiyan shi don yawan futinan da aje saka shi zai iya jawo mai wani sabon matsala kuma. Sunyi barazanan daukan mataki akan duk wace take kawo masu yawan tashin hankali a gida. Wanan dalilin yasa gidan ya samu kwanciyan hankali na kwana biyu. Gashi dai zan iya cewa Alhaji yana cikin mazan dake kokarin ganin yaba iyalin shi kulawa don bai make aljihun shi ga iyalin shi. Kwanciyan hankalin da na samu ba fitina ba tsangwama yasa na sake murjewa nai kyau nai haske sosai. Nan kan kula da yanayin Alhaji idan yana dakina sai naga ya tsura min ido kawai can naji ya sauke ajiyan zuciya a sanyaye. Ban daukan wanan a komai sai dai naga kamar wani abune ya shige mai a duhu yake saka shi a tunane. Ban sani ba ashe tausayina ne yake ji yana ganin kamar ya shiga hakkina da yawa. Yakawo ni gida ya girke ba biyan bukatan komai a kaina bai san ni haka wani gata ne Allah yai min ba da hakan. Allah bai barin bawan shi mai hakkuri ya tabe banza a duk inda yake watarana sai kaci riban hakkurin ka insha Allahu mudfin kayi shi da zuciya daya. Ranan na tashi da safe na shiga nai wanka bayan na gama yan aiyuka na sai ganin nayi jini yana zubo min a gabana. Tun ina bini bini kewayawa na wanke har tsoro ya fara kamani gashi naki sakin jikina ko cikin gida naki shiga na taya su aikin komai a ranan. Sai bayan sallah azahar da naji kowa ya shige dakin shi na idar da sallah na nufi gurin mama hausatu. Na samu ta idar da sallah tana zaune tana lazumi ita kadai a daki tana ganina tai dan murmushi a fuskan ta tana cewa Amarya . Yanzun fa nake zancen ki a zuciyana yinin yau banga kin fito ba tun safe da muka gaisa nake cewa ko dai lafiya kuwa ? Nakai zaune tare da cewa wallahi mama yau banda lafiya akwai matsala shine nazo na fada maki. Cikin sauri tace subbahanallahi may ya samay ki kuma yar nan ? Shiru nayi ban san may zance da ita ba a lokacin sai dai kaina dana sada a kasa kawai. Tace may yafaru amarya gaya min mana nifa ban dauke ki a kishiya ba matsayi diya ta ta cikina nake daukan ki. Na kara dukar da kaina a kasa nace mama dama sai nai shiru can kuna na dago na kara cewa a sanyaye dama yaune naga jini kawai yana ta zuwa min a karkashina tun safe da na tashi ga marata sai ciwo yake min. Nace barin fada maki ko zanga likitane tun cutar bai min yawa ba ? Tace cikin mamaki ikon Allah Rahama dama baki fadi bane sai yan zu ? Na dago kai da sauri na dan kalle ta tace wanan ne karo na farko da kikaga haka ko may ? Nace mata a sanyaye eh mama. Tace to ki saurare ni kiji da kyau wanan abin da yazo maki zan iya cewa ba cutane ba kuma cuta bane alama ce ta girma yazo maki da hankali da samun natsuwa. Duk ko wace mace da kike gani tana yin wanan abin a rayuwan ta wace bata yi kuma to tana da matsala kuwa babba. Wani irin ajiyan zuciya na sauke taci gaba da fadin kada ki tsorata da hakan nan tafara yi min bayanin yadda zan kama kaina a lokacin da nake cikin wanan laluran na fashin sallah. Kamar yadda uwa zatai wa yarta bayani haka ta zauna tai min bayani sai daga karshe tace da zaran kin gama zakiyi wanka kamar yadda kike yin wankan janaba. Nace wankan janaba mama tace eh idan kin kwana da mijin ki ba kikan yi wankan tsarki ba ? Nace eh kawai ba tare dana fahinci may take nufi ba tace to shima hakan zakiyi sai dai gurin niyya ya banbanta ne wacan janaba zaki ce wanan kuma haila. Nan dai ta kara koyar dani komai nace nagane mama a makarantan boko dana islamiya duk an koya muna shi na kuma rike. Nace mama dama wanan jinin shine jinin hailan da ake nufi tace shine amarya sai jinin haihuwa shima tai min bayani da kwanakin da ake son mace tayi ta fara yin tsarkin shi. Na gamsu sosai da bayanin mama akarshe take ce min sirina ne daga ni sai mijina kawai daya zama dole ya sani ake son ya sani idan ma ina fashin sallah naga kowa ya tafi sallah na shige daki nima kada na zauna a waje kowa ya fahinci ban salla don siri ne babba ga mace. Nai mata godiya tare da mikewa na wuce zuwa dakina na kimtsa jikina kamar yadda tai min bayani nayi. Ina fita na bata tausayi sosai sai dai bata ga laifina ba sai na iyayyena dake da alhakin haka akaina. Gashi yar karama dani a wanan zamanin an min auren cushe ga miji, mijin kuma babban mu kamar alhaji gashi ashe ko hankalina ban gama mallaka ba. Kamar yadda mama ta fadakar dani hakan ne nayi na gyara jikina tsab mai makon na ma dinga shiga mutane sai kawai na dinga nisanta kaina da jama, a baki daya gani one two one ta na kewaya na gyara jikina. Da maigidan ya shigo gida ne mama ke fada mashi cewa ashe amarya sai yanzu ta fadi yau ta samay ni cikin damuwa take fada min don bata san kaiba. Shima yai mamaki kwarai jin sai a lokacin na fadi ashe kuma ban san komai ba akan faduwa hakan na nufin ke nan har yanzu ina a matsayina na cikakkan budurwa as a virgin . Tausayi na ne ya kara kamashi a lokacin ne yai daya sani shiga rayuwa na da yayi da wuri haka nan. Ke nan zancen da kishiyar mahaifiyana ta fada mai nacewa gara ma da yazo nema don ni watsatsace ban da kamun kai na san maza ko zan iya zama dashi ai ban ganin tsufan shi tunda maza nake so a rayuwana. Wanan magana babu inda ya hango kamshin gaskiya a cikin sa don dai halin rayuwa na ya nuna mai ta ko ina ni yarinya ce mai mutunci da kima nasan darajan kaina da iyayyena. Don haka dole ne yai min adalci akan zaman da nake dasu don ya fahinci yarinya ce ni sharaf ban san komai ba na duniya. Wanan dalilin ne yasa ya kara jawo ni jikin shi sai naga yana haba haba dani fiye ma da farko da yake min. Mutanen gidan ganin kwana biyu bana yawan fitowayasa suke shigowa daya bayan daya suna tambayana may ke faruwa dani ne wai ? Sai cewa masu nake banda lafiya ne bana jin dadin jikina na ne shiyasa. Su daukan su na samu cikine, wai, sai naji suna cewa Allah ya ingata ya kawo muna mai albarka. Jin haka yasa Sabuwa ta fara dan sake magana tana fadin an dai ji kunya wallahi . Karshen muna funci ya baiyyana ace muna ba, a da lafiya amma sai ga shi an iya labewa da karamar yarinya har ana dirka mata ciki. Abin kunya girma ya zube kamar wanan yar yarinyar za, a ce wai ta samu ciki da mutum irin Alhaji wanda kewa iyalin shi ikirarin baida lafiya bai iya komai da mace amma ya takure a gidin yarinya karama to ga abin boye ya fito fili ai kowa ya gani yanzu gaskiya ya baiyyana. ****** ********** ****** Tun lokacin da na fara period naga gaba daya na sauya wani girma ya zo min ga kayan dadin da nake samu ina ci iri iri gwagwadon halin yan kauye irin dadin su na kauye. Wani lokaci sai nayi kyauta da wani abin ma na rabawa yaran cikin gida su ci don ban iya ci ni don ban saba da yawan ciye ciye ba a rayuwana. Zaune nake a saman kujeran dakina nayi tagumi da hannuna na hagu na zurfafa ga tunane. Sai ganin shi nayi ya shigo dakin na bishi da idanu kamar shima yadda ya bini da kallo don ganin yanayi na a cikin damuwa. Guri ya samu ya zauna a bakin gado yana kokarin cire babban rigar dake jikin shi. Yace may kuma ya faru na gan ki haka amarya, murmushin kake nayi wanda bai kai ciki ba a fuska na. Yake cewa wai may ke faruwa ne ko anyi wani abin ne kuma bayan fita na ? Nace babu komai tashi yayi daga inda yake ya dawo kusa dani ya zauna saman kujera two seater dani kai a zaune. Yake cewa fada min mana may akayi ne wai naga yanayin ki ya nuna min kina a cikin damuwa. Nace ba komai Alhaji tunane Inna ta kawai nakeyi. Yace wani abu ya samu inna din ne kuma ? Kai na girgiza mai alaman a, a. Murmushi yayi tare da riko min hannuwa na wani irin yar naji har cikin zuciyana tare da jin nauyin shi na ganin ya taba min jikina karo na farko zamana dashi. Ban kai ga karasa mamakina na ba naji ni ya kwantar dani a saman jikin shi yana dan shafana a hankali. A take naji yanayina na neman gagarana zama a gurin da nake zaman tsara dashi. Yace ki kwantar da hankalinki insha Allahu akwai shawaran da nakeyi akan ki idan har nakai karshe wata kila ma zaki koma gurin Inna din da zama na dindindin. Da sauri na dago kai ina duban shi yace ki dai kara hakkuri kinji Rahama dan bani lokaci kadan. Nace ni ban son komawa gidan mu gurin inna ta, zama na nan yafi muna komawa gidan su Inna yanzu hankalin ta a kwance yake don mama bata gani na balle ta tayarwa Inna da hankalinta . Ni nan zan zauna gurin ka kana kula dani fiye da Inna ta da baba na ban cikin matsin mama kuma yanzu. Dukar da kan shi naga yayi a kasa sai naga hawaye suna zubo mai sannu a hankali. Cikin mamaki nai zubur na mike daga inda nake a zaune tare da dawowa gaban shi na tsugun na ina cewa . Don Allah Alhaji idan har na fadi wani abinda ba daidai bane kayi hakkuri kayafe min naji zan koma gidan mu gurin Innata muyi ta hakkuri da rayuwan da zamu tsunta agurin mama. Ji nayi ya tallafo ni daga gurin da nake a tsugune zuwa jikin shi ya rugumay ni yana dan shafa min bayana tare da fadin ya isa haka kiyi shiru babu inda zaki tafi kina nan tare da mu insha Allahu. Wanan ranan ne muka fara kwanciya saman gado daya da Alhaji sai dai yana gefe ina gefe a kwance har gari ya waye . Abinda ban sani ba ranan shi gare shi ko runtsawa bai yi ba sai faman tunanen duniya yakeyi. Ya so it a mayar dani gidan mu gurin iyayyena don yana ganin yana kuntatawa rayuwa na sosai, amma kuma sai gashi ni da bakina nake fadin wanan zaman yafiye min zaman gidan iyayyena dadi. Haka yasa ya fahinci daga ni har innata muna wani rayuwa ne na zaman ukuba a gidan. Dole yabar wanan yarinyar yaga abinda Allah zaiyi akai don Allah kadai yasan dalilin wanan auren don shi baki sa,ata ba ko wace tafini shekaru bai da nufin karawa a rayuwan shi. Sai gashi a lokaci daya Allah ya jarabce shi da kara aurena auren kuma yazo da kaddaran rayuwa gare shi. Yadda na samu kwanciyan hankali na mirje nai kyau dani haka yasa Sabuwa tayar da hankalin ta duk ta fige tayi wani baki da ita. Gashi ta sa a ranta cewa cikine a jikina yasa na koma haka dani lokaci daya. Akwana a tashi hasaran mai rai yau nakai wata takwas da aure har lokacin ban sheda nayi aure ba a rayuwa na. Iyakata naci na sha na kwanta nai kwana idan naso na shiga na taya matan gidan aikin su. Ba mama da mama hauwa ba kawai nake tayawa aiki har sarakan su idan aiki yai yawa nakan kama masu. Ban hakkura da zancen zuwa islamiya ba na kara tunawa Alhaji da kyat na samu ya yarda na tafi sai gashi ya sawo min hijjab har uku maya har kasa da nikaf na rufe fuskana. Ranan da zan fara fita nasha sheri gurin matan gidan wai ni yar izzala ce shiyasa nake da mugun tsabta ashe. Na dai yi murmushi nai masu sai na dawo nafice daga gidan dama Alhaji ya riga yai min register komai a school din. Don haka ban sha wani wahala ba na gane ajina gwajin farko ya fahinci na dan yi nisa aka mayar dani ajin manya. Sosaina dage ga karatu na ba wasako a gida nake banda abinyi sai karatu da yan aiyuka na. ****** ********* ****** A bangare Alhaji ya samu sauki sosai don tsare dokokin da yayi na likita har anfasa zancen yi mashi aikin da akace za, ayi da farko. Hakan da yake ji yasa yake ganin ya samu sauki ya shiga kokarin gwada sa,anshi ya gani . Ranan a cikin barci na dinga jin wani bakon al,amari ya na ziyarta na idan dai ba mafalki nakeyi ba to zan iya cewa kirjina, watau dukiyan fulani na ne kejin ana taba min a lokacin. A hankali na zubura zubur daga mafalki kamar zan fasa ihu sai jin muryan shi nayi yana ce min kamar rada yi shiru amarya nine Alhaji ba kowa bane. Na gyada kaina alaman na gamsu sai naji yana sauke ajiyan zuciya naji yana ci gaba da saukewa a hankali. Bai kuma fasa abinda da hannayen shi keyi a saman kirjina ba har lokacin. Sai faman rintse idanuwa na nakeyi don irin bakon yanayi da nake ji a lokacin. Kama an fisge shi naji ya juya da sauri tare da rike maran shi da hannayen shi yana wani irin nishi kamar kugi a hankali. Shiru nayi ina sauraren yadda yake fitar da sauti daga bakin shi cikin yanayin ban tausayi . Can a kasan makogwaron shi naji yana kiran suna na a hankali da kyat sautin maganan shi ke fitowa a lokacin yana fadin naje na dauko mai ledan maganin shi da ya bari a dakin sabuwa. Ban ki ba haka na daure cikin wanan Uban daren hana na wucw gurin mama hausatu na buga mata kofan dakin ta tare da cewa maganin shi yace na karbo mai a gurin mama Suwaiba. Ita da kanta ta tafi dakin ta buga mata take cewa miko min ledan maganin Alhaji da ya bari a nan ta tambaya da sauri injin dai lafiya yaya ? Lafiya kalau ya manta bai sha bane yace a dauko mashi ya sha ta karbo ta mika min na juya na bar dakin simi simi dani. Nakai mai sai da ya hada ya sha zuwa can ya dan samu relief sai barci mai nauyi ya dauke shi nima na koma na kwanta zuciya na fam da tunanen abinda ya faru yan mintina da suka wuce a tsakanin mu. Wanda har lokacin ina dan jin dan matashin kirjina yana dan min radadi. Washe gari na tashi ina matukar jin nauyin shi da kunya akan abinda yai min a daren jiya gashi alama ya nuna yana dan jin jikin shi . Amma haka ya daure yafita daga gidan zuwa gurin neman kudin shi daya saba yi. Bai jima ba a waje jikin ya tsanan ta mai ya dawo gida ya kwanta min a daki gashi kunya da nauyi nake ji har lokacin ban iya hada ido dashi. Haka yasa shi fahinta halin da nake ciki daga inda yake kwance na shigo dakin ne naji ya kira sunana. Na amsa sai naji yace na gode daren jiya fa ko ba komai na dan more daga ni,iman da Allah yai maki ya fadi hakan cikin dan lumshe idanuwan agi a hankali. Shi kadai yasan irin halin da ya tsinci kan shi a daren jiya sai dai yana gap da biyan bukatan shi a gare ni ne yaji maran shi ya rike mai sosai a lokacin. Hakan ne yasa shi dole neman magani ya hadiye don samun saukin abinda yake ji. Tambayan kan shi yake a zuciyar shi yayin da idanuwan shi suke a rufe yaushe ne zai samu ya more niiman da Allah ya hallata mai ga wanan yarinyar ? Irin yanayin da ya tsinci kan shi da ace shi mai lafiya ne yasan cewa a daren jiya din Allah ne kadai zai kare bai kai ga mayar da ni cikakkan mace ba kamar yadda yake gurin yin haka a gareni a kullun. Ganin da nayi jikin shi ya matsa mai yasa naje na fadawa sauran matan nashi halin da yake ciki. Ba bata lokaci dakin nawa ya shiga ganin yan zuwa yi mashi sannu da jikin shi. Nan sabuwa ke cewa Alhaji kana son matsawa rayuwan ka akan sai kaga ka burge wanan yarinyar a koda yaushe. Idan baka bi sannu ba zaka halaka kanka da kan ka furin budurwan zuciya. Sai ka dinga farwa yar karamar yarinya akoda yaushe yaushi zaka ganewa lafiyan ka tunda kaki na tsuwa da girman ka a koma ana taratara da kai kamar karamin yaro har may kake nema ne gareta wanda baka samu ba a baya. Yana jin ta sai dai halinda yake ciki bai iya bata amsa a lokacin don jin zuciyar shi yake yana mai tafasa . Ga zancen ta na kara kona mashi zuciyar shi akoda yaushe. Shima laifi ne ga maganan sabuwa da take yawan nanata yana yawan kusantar Amaryan shi ne yasa matsalan shi ke yawan tashi koda yaushe. Shi dai a gare shi yadauka kawai wanan wani jerabawa ne daga Allah kawai. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , , IDAN KIN BIYA KIKA BAWA WACCE BATA BIYA BA ALLAHNA GANIN KI DON AMANA NE A GARE KI YAR UWA, , , Sannu sannu sai gashi lokaci yana ja a wanan lokacin duk wani dan matashin yaro dake gidan idan dare yayi muma shiyana muna karatu, wanda suke jin dadin hakqn anan zamuyi ta shirmay har dare kowaya watse. Bayani nake masu sosai yadda zasu fahinta gakaratun da suke dan tsinta a gurina. Wani lokaci kuma novel zan samu mai dadi da ma,ana da koyar da wani abinda ya shafi fannin rayuwan dan adam. Zan dafa abinci na zuba a babban tire nan zamu taru muna ci muna hira muna dariya abin dai na kurciya zallah kawai. Har zuwa wanan lokacin zama na da maigidan kamar kullun ne ya kan yi iya bakin kokarin shi don yaga yadda zai yi ya dan samu gamsuwa. Sai dai hakan bai yuyu ba a gare shi don da alama matsalar shi tana nan mai bai gushe daga gare shi ba. Don idan yaso ya kai gare ni sai naji yana zufa yana wani irin kugi mai fitar da wani sauti na ban tausayi. Ni kaina nakan matukar jin tausayin shi idan ya shiga wanan halin don haka zai wayi gari ya wuni a wahalce dashi dashi. Na fara fahintar wasu abubuwa duk da dai wayo na baikai na fahinta ba a lokacin amma sai nake fahintar ba gani kadai hakan ke faruwa ba har ga sauran matan shi musanman ma dai sabuwa. Idan ya kwana a dakin ta zanga ya tashi wani lokaci ba dadi har aka fara dan rade radi a gidan abinka da gidan yawa. Ranan mama da kanta take bugun cikina akan zancen take cewa dani wai amarya kuna dai biyewa wa maigidan yaki natsuwa har ta samu lafiya komai ya zama daidai ko ? Nace mama na daina zama ne idan yana daki kike nufi? Ta kama baki tace wane ni da fadar haka amarya rufa min asiri tace ni dama cewa nayi kawai ki dan kaurace mai ga shimfida irin ki dan rika ba da lokaci din nan . Kin san shi namiji kullun a bukace yake da mace ba ruwan su da lafiyan su koda hakan kuwa zai masu illa ne. Nace mama kina dai nufi idan yana daki na fito waje na barshi ya huta ya samu hutu sosai ko. Nan dai ta gane shirmay na bai bari na fahince ta sai ta fito min fili tai min bayanin komai a baiyyane. Cikin canza fuska nake ce mata gaskiya mama ni Alhaji bai taba nuna min wanan abin ba a tsakani na dashi sai mutunci kawai. Kan ta ya daure ba don ta yarda ba don tasan hakan ma ba zai faru ba koda kuwa ace ni ba yarinya bace yaya zan zauna har wanan lokacin. Karshe dai sai cewa tayi dani ki daiyi a hankali kinji kada ki yarda ace an samu wani matsala a kan ki kinji ya ta. Nace to mama nagode Insha Allahu zan kula kamar yadda kikace din. Sai gurin karima sarakuwan tane ranan take kara fayyace min yawan hasashen da ake mun a gidan kan lafiyan Alhaji. Muna hanyan makarata ne take fada min komai tare da jamin kunne akan na kara kulawa sosai. Tun ranan ban yarda ko dan tabanin da yake ya samu relief din da yake yi na daina bari yanzu. Har abin ya fara dan damun shi da yai min magana ban boye mai komai ba na fara kuka ina fada mai abinda akace ina yi mai. Ya gane anja min kunne ne akan haka yasa ya daina kada ya jamin bakin jini ga iyalin shi don su a ganin su nice ban bari ya samu sauki. Ranan dakin mama hauwa yake ciwo ya murtuke shi a cikin dare aka kwasa sai asibiti. Nan suka fara fahintar cewa ciwon ne dai bai bar jikin shi ba ba yadda suke hasashe bane. Koda aka dawo dashi gida wanan karon andai dawo ne amma yana matukar jin jikin shi sosai. Don yakai idan zaiyi fitsari ma kusan zakaji yadda yake faman nishi da kugi kafin fitsari yazo mai. Wasa wasa ciwo sai gaba gaba yake mai ya ramay yai baki sai dan wuya takai ma yanzu bai fita kamar yadda yakeyi a baya. Cikin haka ne ranan aka aiko babana yai faduwan mashi a hanyan shi na dawowa daga kasuwan kauye da yake zuwa. Alhaji ya samu labari don haka yana dakin sabuwa yasa a kirani nazo na dan rusunna daga kofan dakin nata don ban yarda na shiga daga ciki ba don ta cikin dakn zaune a lokacin. Yake cewa dani yanzu nake jin labarin abinda ya faru da mahaifin ki jiya shiyasa na kira ki. Ki shirya sai zuwa ta rakaki ki dubo shi amma kada ku wuce goma ku dawo gida. Nace na gode cikin murana wanan ne karo na biyu bayan aure na da naje gaida mahaifana. Na farko tare dashi muka tafi ban ko kai minti talatin ba baba ya matsa min nafito muka koma gida. Sai wanan daya bani bako mu tafi da zuwaira na dubo jikin mahaifina ko shi nasan don baya jin dadi ne da tare zamu tafi dashi. Tsab na shirya cikin katon hijjab sai nikaf dana dora akai duk d dare ne amma na saka nikaf din na tare fuskana da shi. Har mu uku muka tafi don Aisha ta biyo mu da taga zamu fita tare da zuwaira din. Da sallama muka shiga gidan a tsakar gida muka samay su suna shan iska tare da baba. Nan muka durkusa muka gaida su tare da mai yaya jikin shi da Allah ya sauwaka ya tsare gaba. Sai can yake cewa wai Rahama ke ce ai ban gane kiba ikon Allah ya kuke ya gidan duk kuna lafiya ? Yaya shi maigidan naku da na sa jikin dafatan ya samu sauki ko don ance jikin nasa ba dadi kuma ? Bayan mun gama gaisawa da baba ne da tambayoyin da ya jero min na juya inda mama take tayi tsit tare da kura min ido. Ko may take kallo hakana ban sani ba daga jikina na daiga duk da dare ta kura min idanuwan ta a kaina. Nace mama mun samay ku lafiya yaya gida ashe baba kuma wani kaddarane ya samay shi haka? A cikin basarwa take amsa min gaisuwa na a tsatsaye na gaida Inna ta dake zaune a gefe tana motsa kunu mai zafi data dama ina ga na baba ne. Can na mike na leka dakin mama gurin su Lawisa suma ba wani karban arziki ne na samu a gurin su ba. Na fito na shiga dakin Inna ta na samu kannena zaune suna dan hiran su, suna gani na suka hau murna. Nace dasu ba wani bayan kun yadani ba ku zuwa gurina sai kace ba, a gari daya muke daku ba kamar wacce bata da yan uwa. Nasir yace kiyi hakkuri mama ce ta fadawa baba ranan nan da muka tafi gurin ki shine baba yace kada mu sake zuwa gidan ki. Lokacn Inna ta shigo dakin inda muke ta samay mu muka kara gaisawa da ita cikin mutunci. Nan ta zauna a bakin gadon ta ganin Inna ta shigo dakin yasa su zuwaira da muke tare mikewa suna fadin amarya zamu tsaya kofan gida mu jira ki. Nace haba ku zauna mana suka ce a, a muna dai waje har ki gama mu tafi ai. Bayan fitan su ne Inna ta nisa take cewa yaran suna da da, a da sanin ya kama ta ne. Nace cikin shagwaba Inna nikan dai yanzu ba kya sona nice kawai nake can cikin damuwa daku ? Tace da akai may kuma nace ina ko su Nasir an daina tura min nagan su sai na tara abu don a kawo maku amma babu yaron da zan ba ta kawo nan na ciro wani babban leda daga cikin hijjab dina ina mika mata. Kallon ledan takeyi tare da tambayan wanan may ne kuma a ciki ledan cike yake fam da tarkace iri iri dana tara don na kawo mata. Bayan ta gama dan dudubawa ne race yarinya kardai ince kayan mijinkine kika kwaso muna haka na amfanin ki ? Mijinki fa bai rage ni da komai ba yanzu don inba rashin lafiyan nan da ya kwantar dashi ba kusan duk sati da aiken da yake min daga gurin mamakin mai kuli. Ni ban san irin godiyan da zanwa wanan bawan Allah ba gashi ya rike min ke da mutunci kullun yana yabawa da halin ki na tarbiya a garesu. Ga kuma abin alherin da yake kawo muna don kinga yanzu banda talaucin dangin kayan miya sabulun wanka man shafi da sauran su. Watarana ma har kayan girki kamar shine ya aje mu zai kawo muna da kudi ga hikimar da yayi na bi ta hannun mai kuli ya kai muna ta gurin ta sai dai ta aika nazo ko ta kawo min idan uwar ku tafita daga gidan. Nisawa nayi nace mama shi Alhajin ne ke kawo maku wanan amma ni bai taba fada min komai ba wallahi. Tace shine alherin arziki gashi yanayi ke da yakeyi kanki ma baki sani ba sai yanzu. Nidai ko rike min ke da sukayi da mutunci ya wadatar dani wallahi tun har yau banji wani abin asha ba daga gare ki. Murmushi nayi nace haba Inna baki koya min yin haka ba aikuma bazaki taba jin shi daga gare ni ba ai. Nan dai nace Inna su Lawisa yaya nasu zancen auren ne naji shiru har yanzu ? Tace kin ga yadda baki san komai ba nima haka iyakata dasu ido a gidan nan bana shiga zancen su suma hakan. Sune ma ganina a wadace yake damun su kin san halin uwar taku da hassada da kyashi ai. Yadda taso ta kawar dake a gabana taga na wullakanta sai taga sabanin haka ga taimakon da Allah ya jefo mijin ki a rayuwan mu yake muna. Kedai kikara hakkuri akan wanda kikeyi mai hakkuri baya tabewa ga banza insha Allahu. Nace insha Allahu ina tace idan ma tayi muna hakane da wani manufa to yanzu mu hakan ya zama muna alheri. Don ya koma mata ciki kullun zaka ji ta tana sake magana da habaici a gidan nan. Gashi Allah ba ai mashi wayo ita nata diyan ko tsohon ma Allah bai kawo masu ba sai zaman sa,in sa suke a tsakanin su da ita. Muryan baba ne daga waje yake kiran Inna ta yana fadin ke Asiya bazaki sake yarinyar nan su tafi ba ga dare yanayi ko anan kike son ta kwana. Shine ya katse muna hiran mu da inna na mike ina cewa inna zamu tafi zan shiga gurin mama na gaida ita kafin mu tafi. Tace injin mijin naki yace ki shiga gurin nata don kada ki koyi wanan halin na matan yau da muke daukan hakan ba komai a rayuwan mu hakan ko shine babban koma a gobe kiyama. Sai kiji mace ta fita da sunan zuwa gida daya sai ta biya gida goma ba da bakin mijin ta ba. Nace Inna har na fito fa ya kirani yake cewa na, ratse na gaida mama altine din tace to tashi ku tafi kada dare yai maku. Naba kanne na dari biyar nace su karya dashi da safe suka shiga murna itama inna dubu daya na bata na fita naba babana dubu daya mama dari biyar. Sai sa min albarka baba da Inna sukeyi mama kan tun ce min da tayi an gode bata kara magana ba. Gashi ko ranan da haka zata kwana ba ko sisi a hannun ta don yanzu yaranta sunyi wayo suke rike kudin su a hannun su. Da kyat zata iya karban naira hamsin a gurin su don sai tasha mita kafin su bata wani abu. Mun shiga gurin mama Altine tai murna kwarai da ganin mu tana ta ina aka saka dani. Sai tambayana take yaya muke yaya abokan zaman nawa injin dai ba wani matsala ko ? Tace nayi hakkuri na dage gurin kyautatawa mijina da sauran abokan zamana kamar yadda nakeyi. Tace hakan da kikeyi shine samun kwanciyan hankalin ki a gidan don da kinje masu a tsaye ne ko shi mijin naku bazaki samu kan sa ba ai. Bamu jima ba mukai sallama muka koma gida ina jin zuciya na ba dadin rabuwan da zan sake yi dasu sai kuma wani lokaci mai tsawo kila na sake ganin su. ****** ********* ****** Wanan ganin da mama tai min ya matukar tayar mata da hankali sosai gashi don samun guri wai harda kyauta kudi nai masu har dari biyar. Wa ma yasan abinda nabawa uwata a daki don haka tun da safe tai sammakon barin gidan zuwa gidan aminiyar ta larai bamu da nisa sosai da ita. Tana shiga suka gaisa larai tana ganin ta tasan akwai abinda ya faru don duk tai mata sakko haka agida da akwai matsala ke nan gare ta. Tace may kuma ya faru mutumiyar tace bari kedai larai nai wa kaina abinda ya koma min ciki wallahi. A zato na na hada auren yarinyat nan da garbati don na kawar da ita da uwar ta daga farin cikin da suke ciki . Ashe ban sani ba na dauko wuka ne na dabawa kaina a ciki dana sani daya daga cikin wa yan nan shashashun yaran na cina mashi. Kin koga yadda yarinyar nan Rahama ta koma Larai ? Wai yau har Rahama ce da kanta tabani kyautan dari biyar cas kin gashi gashi nan . Ta baje tayi kyau ta wani murje ta kara haske da ita kamar mai aure a birni yanzu fa uwarta ma bata cikin matsalan komai a gidan nan don sai bushashan ta takeyi. Jin tai shiru larai tace da ita to ai baki san wani abuba ne Lauratu idan da yar taki kika bashi sabanin haka zaki gani fa. Da sauri take kallon Lairai don jin abinda tace tace eh haka nane mana don kinga halin su ba daya ba da ita Rahaman. Yadda nake jin labari fa ita yarinyar ce ta sai wa kanta zaman lafiya da kowa a gidan. Don ko sabuwa dake hauka da farko yanzu ta aje shi gefe don mutuncin yarinyar a kan su ta dauke su tankar iyayyen ta ne bata je masu a tsaye ba. Kin ga kuwa banga dan ki ko daya da zai shiga ya mayar da kanshi kamar bawa ba a gare su don a zauna lafiya. Dama hakane dan hakin da ka raina sai yazo ya tsone ma ido shiya sa tun farko da kika zo min da maganan wanan hafin nace dake kinyi babban kuskure amma alokacin har haushina kikaji don may na fadi haka. Kina ganin ke kin cuta masu ne baki san taimakawa rayuwan su kikayi ba ke . Tace bari larai sabon atamfane ma fa ta daura a jikin ta kuma bana cikin lafen ta ba ne don nasan kayan lefen nata. Gaskiya yaya sallah ya munafunce ni don da yasan akwai ci a wanan auren shine yaki jona daya daga cikin diyan shi. Nan dai sukai ta kulle kullen su har take cewa duk yadda zatayi ta goga min bakin jini a gidan nan sai tayi don bazata bari tana kallo ina cikin daula ba dani da uwa ta. Da tasan hakane da bala mai faci zata hada aurena dashi naje ko abincin ci ya gagare ni. Kamar yadda ta kulla haka ta samu wata aminiyar sabuwa take fada mata wai suna may suka saka min ido ina yadda naga dama a gidan Alhaji gashi sai dinke dinke yake min kullun kuma yanawa uwata aike ba kakautawa. Irin zancen da sabuwa ke so ke nan ranan da sakon ya samay ta nan ta haukacewa mutane a gida da masifa inda take shiga ba nan take fita ba ga miji kwance a daki ba lafiya amma ta tayarwa mutane da hankali. Haka yasa shi daurewa yafito katakata dashi yana cewa ke Sabuwa kin ishe ni da masifa da tashin hankali a gida. Ke lokacin da kika zo gidan nan haka wa yanda kika sama a gidan su kai maki ne shi ? Don haka daga yau na sake jin hayaniyar ki a gidan nan kowa yaya ne nai alkawarin sai kin bargidan ko akan waye haba kin ishe ni Sabuwa kin kai min ko ina. Ba a kan ki aka fara kishiya ba ke ba wasu ne kika zo kika sama a gidan bane wai ko su ba mata bane da basu daga hankalin su ba ga shigowa cikin su. Duk abinda ke fadan wai nayi wa yarinyar nan nayi mata sabuwa sai kizo ki kwata ke ma in na karfi ne ? Ya juya zai koma daki ya yanke jiki ya fadi tun take mata da yaran gida aka saka kururuwa a gidan aka kwasa sai asibitin birni Kwanan shi biyar a ka dawo dashi ba hannu ba kafa tare dashi abu kuma ya koma kasa sabo. Wanan faduwar ya dawo da ciwo sabo gare shi hawan jini yazo ya shiga ciki kuma da sauran ciwar wukan zamani da ba, a rasawa. Aiko yaran gida da matan su suka saka ta a gaba sai tabar gidan nan ko suyi mata dan karen dukan tsiya su kora ta. Ganin zasu iya mata abinda suka furta a kan ta yasa ta sulale ta bar gidan baki alaikum tun basu illanta ta ba. Haka ya sa suka dan sarara mata don ficewan ta gidan ya dan rage masu zafinta da suke ji a lokacin. Kusan kwanan kin da tayi bata gidan duk fama da jikin Alhaji akeyi don jikin yaki mai dadi sosai a lokacin. Haka nan ko yaushe cikin jike jike da dafe dafen magani ake mai wani ai mai tausa wani kuma dafa mai yasha. Muna faman sintiri yi mai sannu a duk dakin da yake haka za, a kwashe shi tara tara zuwa dakin. Ranan sai ga Sabuwa ta dawo wai iyayyenta ne suka zo suka bada hakkuri akai. Washegarin da ta dawo ne ina dakina ina barcin safe misalin karfe sha dayan rana na gama dafawa mama hausatu shimkafa da wanken sana an ta. Shine na dan kwata don na huta a raina can a cikin barci na nake jin ana sallama a daidai kofan dakina. Firgigit na falka ina amsa sallaman tare da fadin shigo daga ciki ina kokarin saukowa a saman gado. Lokacin suka shigo dakin Anty Sa,ade na ce daga birni tayi shigan ta na yan gayu ga kamshi na tashi daga jikin su. Tana tare da wata yar matashiyar budurwa tare da ita sai diyan ta biyu da take tafe dasu. Ban san lokacin da na yanka wani uban ihu ba na makale mata a jikin ta ina cewa wai ni Rahama yau ina zan saka kaina. Sai kuma na fashe da kuka a lokaci daya na durkushe a kasa daidai kafan ta ina rusa kuka gwanin ban tausayi. Naji tace yau ga tsiya taron da zakiyi min kuma ke nan Ramana daga gani na kuma sai ki saka kuka haka ? Tace wa budurwan da suke tare maryam tashi mu tafi wanan bata son zamana a nan. Da sauri cikin kuka nace anty don Allah kiyi hakkuri na daina ina kokarin share hawayen dake fuskana a lokacin. Nashiga daukan yaran ina cewa kai Fatima kece kika girma haka na taba hannun babban dan ta sai ya jaye daga gare ni. Nace baka san ni ba ko kokaga na zama wata bakauya dani ko ina fadi ina dariya tare da kallon fuskan yaron. Nan muka shiga gaisawa dasu cikin murna da jin dadi ina tambayan ta yaushe tazo garin namu ? Tace ikon Allah Ramana ke ce yau haka a dakin auren ki gaskiya naji mamaki da mama ke fada min wai aure zakiyi sai ko gashi na tabbatar da hakan yau da nazo dakin ki na gani. Murmushi nayi tare da fita daga dakin da sauri na fita zuwa bakin randan ruwa na na kasa na debo masu run shi a cikin kofin silver mai marfi. Nakawo masu ba laifin sun karba sun dan kora ruwan suka aje kofin amma yaran su sunki shan ruwan sai turanci suke da uwar su da dayan budurwan da suka shigo da ita gidan. Tambaya na take ina maigidan naki ne mama tace muna yana fama da jiki wai Allah ya sauwaka ya bashi lafiya. Mun dan taba hira dasu wanda akan karatuna ne nake mata ina fada mata cewa nawa karatun ya rushe ke nan tunda zaman gidan nan da nakeyi ba fashi a cikin shi. Tace komai ai na Allah ne baki san ko watarana zai yarda kije gaba ba ai nace cafdi anty bako a gidan nan ba. Tace muje kikaini na gaidashi da sauran abokan zaman naki ko ? Ban bata lokaci ba na mike muka nufi dakin mama hauwa inda yake kwance a ranan. Kwance yake yana ganin mu yake kokarin mikewa zaune sai dai bai iyawa dole ya koma ya kwanta yana masu sannu da zuwa. Kusa dashi naje ina cewa Alhaji anty na ce ta birni da nake baka labari tazo ganin mu yau. Hannu yake daga mata alaman yana masu sannu da zuwa yai matukar bamu tausayi gaba dayan mu a dakin. Gashi dai ya na son yin magana amma babu halin yin haka a gare shi sai in maganan ya zo mai yake samu yayi shi. Muryan anty ce ke fadin an kaishi asibiti kuwa a hakan da yake kwance a daki ? Mama tace an kai shi sai dai ba wani babban likita ne suka samu gani ba suka dawo wai akwai tsada ga ganin likitan. Haba komai tsadan shi ai sai a kashi a ji halin da yake ciki yafi wanan kumshe shin da akayi haka a gida yana wanan wahalan haka. Tace yana da yara manya ne maza suka ce mata eh tace idan suna kusa ina son magana dasu don Allah. Daga haka muka fita na kaisu dakin mama hausatu tabata dubu biyar dakin sabuwa ma haka da mama hauwa. Ai sai aka shiga saka mata albarka kwando kwando a ranan muka koma dakina kafin su yaya Hadi suzo gidan. Tace gaskiya Ramana mijin ki ya bani tausayi mutum yana wahala haka an kunsheshi a gida ba wani maganin kwarai gare shi. Kiyi hakkuri kinji duk wanan jerabawa ne daga Allah kici gaba da biyayyan dakike yi Allah ba zai bari ki tabe ga banza ba a rayuwan ki. Muna cikin maganan ne sai ga yaya Hadi babban dan Alhaji yana sallama daga kofan shiya na. Na fita naga shine nace mai ya iso itama na fada mata zuwan shi nan tafita daga waje gurin shi suka gaisa. Take cewa dama tana so ne idan sun yarda sai akaishi asibitin can birni don zata koma ga jibi kunga sai ku isa ina can amma sai abinda kuka gani ga hakan. Yai godiya yace sun gode zai yi shawara da sauran yan uwan shi takawo dubu hamsin taba shi tace ayi amfani dashi idan zasu zo din. Da zata tafi tabani dubu ashirin wai na dinga amfani dashi tunda mijina da zai bani baida lafiya yanzu. Sau mutanen gidan ta basu dubu goma wai su raba haba sai gida ya kaure da bakin albarka kowa na saka mata albarka agidan suka wuce muna kallon su. Basu ki ba bayan shawaran da sukayi sun yake cewa tunda za, a taimaka masu gara su kaishi su gani kawai zaifi . Haka su ka yanke shawara bayan kwana biyu da tafiyan ta suma suka take mata baya sai garin kano ganin likita. Basu sha wahala ba don ta basu lanban wayan ta idan sunzo su kirata don ta sani. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH DON AMANA NE SHIGAN KI GROUP DIN MU, IDAN BAZAKI IYA BA KIYI MAGANA MU BAKI KUDIN KI YAR UWA, , , Taro na mutunci suka samu a gurinta ba bata lokaci ta wuce dasu asibiti inda saboda sanin ta gurin ba a dauki lokaci ba suka ga likita. Nan likita yai ta fada don may zasu aje shi a gida haka har tsawon wanan lokacin basu zo dashi asibiti ba. Hakkuri suka shiga bashi ya duba shi aka bashi gado har na tsawon sati biyu . Duk anty Sa, ade ce ke kokarin haka dasu gashi tana yawan zuwa duba su akai akai har zuwa lokacin da ya samu sallama daga asibitin. Sunyi da likita nan da wata hudu zasu dawo dashi lokacin ya kara murmurewa za, a ai mashi aiki a gaban shi. Itace taba da mota aka dawo dashi gida cikin iyalin shi da abinci masu gina jiki da zai dinga ci don lafiyan shi. Muna nan muka ji dirin mota sai ganin su mukayi yana tafiya da kan shi ba kamar yadda aka tafi dashi ba da farko alaman sauki ya samu ke nan gare shi. Mun ga yan zuwa gaida shi daga ko ina na muna barka da arziki suko su yaya hadi sai labarin irin karamcin anty sukeyi baki sake. Suna fadin sunga inda daula ya yanke saka a gidan su sai kace ba a kasan nan ba mutum yake sun yaba da halarcin ta kwarai da gaske. Sosai yake samun kulawa yadda ya dace abashi nan kuma aka koma yawon bin daki dashi duk wace keda girki za a kawo shi dakin ta yai kwana biyu kafin ta fita daga girki ya koma wani dakin kuma. Ranan ina zaune ina kwalliya yana dakina nikan na mayar da hankalina ga shafan mai da nakeyi . Ashe yana daga bayana ya falka ya kura min ido yana kallona a cikin tausayawa. Shi kadai yasan abinda yake ji a ran shi a lokacin gamay dani yana ganin ya kuntatawa rayuwa na ya zama wajibi idan ya dan kara samun sauki ya sallamay ni naje na auri yaro wanda ya dace da ni. Ban ankara ba sai jin sautin kukan shi nayi daga bayana yana tashi a hankali. Ban lokacin da na shuri da kayan shafan nawa ba na isa gurin shi cikin tashin hankali nake tambayan shi ko jikin ne na kira mutanen gida suzo. Yace dawo ki zauna Amarya lafiya na kalau wallahi tausayin ki ne kawai ya kamani ni san ban maki adalci ba a rayuwan ki. Bazan iya biya maki bukatan ki ba amma na ajeki a hakana ina kallon ki gashi sai kara cikowa kikeyi shine nake ganin anya ban shiga hakkin ki da yawa ba kuwa nan da wani dan lokaci dole tun baki fahinta har kizo ki fahinci maynene sirin aure ke da kanki zaki fara son hakan a rayuwan ki. Kinga duk halin da kika fada ciki nine da alhakin hakan a kaina ba wani ba don nine na ajeki batare da biya maki bukatunki ba. Nace haba Alhaji bayan wanan kokarin da kake min may na rasa a gidan nan ni wallahi nagode kuma har gobe ina gode ma sai idan ban nufashi zan daina gode ma. Na sa hannu na dan share mai hawaye nace kayi hakkuri Allah zai baka lafiya kamar kowa da yadda Allah. Ajiyan zuciya naji ya sauke yake cewa ba komai zan dai san yadda za, a yi akan wanan ala, amarin naki nan gaba. Haka yai min kwana biyu na ya koma wani dakin wasa wasa sai wanan halin ya zama mai jiki duk yake dakina da wuta bai zubar da kwalla ba a kaina wanda ni ban san ko na may ye ba. Haka muka zauna dashi watan shi uku da dawo asibiti yaji sauki sosai ya murje har ya dan fara fita kofan gida yana shan iska waje tare da jama,a. Ranan ya dawo dakina naga yana muku mukun ciro abu daga Aljihun shi na taimaka na ciro mai sai naga kudi ne masu yawa a ciki ya kira da yawa yace min yaki nan . Nazo kamar yadda yace kusa dashi na durkusa yace ungo wanan kikai wa Innan ki asamu wani sana, a a dinga juya maki kudi suna dan shigo maki kina samun na kashi. Don kinga yanzu ni ba fahita nake ba balle na dan dinga samo maki dan abin kwallam kina tabawa. Gashi duk wani motsina idon mutane yana akaina ba halin nai maki wani alheri mai tsoka a gani. Har lokacin da yake bayanin kudin suna a hannun shi ban karba ba sai da ya kara cewa cikin daure fuska karbi mana nace maki. Nasa hannu na karba tare da godiya yace gobe sai ki shirya idan nabar dakin ki kije gida kikaiwa Inna ki ayi shawaran abinda za, ai maki dasu nace nagode. Nan na duka gefen shi nai kuka mai isata tare da fatan Allah ya bashi lafiya. Washe gari kamar yadda yace na shirya sai gidan mu na kebe da Inna ta nai mata bayanin komai kamar yadda yace min. Tace to sai dai naga mamanki Altine don tafini dubura sai na barmata ta dinga juya maki su don nasan gurin ta sisin kwabo bai ciwon kai a cikin kudin nan. Da haka na dawo gida na shige dakina ita kuma taga mama Altine tai mata bayanin komai suka yanke shawaran yadda za, a dinga juya min su Mai hali baya barin halin shi ranan ya bamu dubu biyu biyu yace mu rike a hannun mu muyi amfani dashi. Nan Sabuwa ta shiga fadawa wai ba, a adalci don may damay iyali da wanda baida za, a basu komai daidai. Sau daya ya iya cewa ke Sabuwa daga haka kuma sai maganan ya tsaya mai ya dan dukar da kan shi. Wasa wasa yana fadin yana jin kamar masasara ya kama shi nan suka kira wani nurse yazo yai mashi yan allurai a gida. Sati biyu da yin wanan a tsakanin mu ina barci tsakar dare naji an fasa wani irin kuwa a gidan. Duk wanda yaji wanan kuwan yasan muryan Sabuwa ce gaba daya mukayo waje sai ihu take tana fadin Alhaji Alhaji babu shi. May kikace Sabuwa tace wallahi Alhaji ne daga yace na bashi ruwa yasha sai kawai naji ya sarke shike nan sai naji shiru. Nan aka fada dakin amma ina yariga da ya tafi sai addua kuma din rai yayi halinsa ko a gare shi. Hadi ya shiga yafito ya fasa wani irin kuka yace baba ya riga mu mama baya yarasu ko . Daga inda nake tsaye nace da karfi Alhaji ya rasu yaya ? Ban kara sanin inda nake ba sai dai na falka naga mama Altine da mama Asabe makwabciyar mu a kaina ina kwance saman gado dakina. Ina iya jiyo hayaniyan mutane suna koke koke a tsakar gidan na tunkura zan tashi mama ta rike ni tace haba Rahama. Kiyi hakkuri ki dangana Allah daya hada ki da Alhaji ya karbi abinshi sai hakkuri kawai. Wani sabon kuka na fasa ina fadin mama da gaske Alhaji ya rasu shike nan bazan sake ganin shi ba. Tace ya tafi Rahama adduan mu kawai yanzu yake bukata tashi takare shi yau ya koma ga mahaliccin mu sarki Allah. Kuka sosai nakeyi haka gari ya waye muna cikin tashin hankali a gidan kafin wani lokaci har an hada shi za, a kaishi gidan shi na gaskiya. Aka ce muzo muyi ban kwana dashi kafin afita dashi daga gidan mama tace min ki daure kada ki fara kiyi mashi kuka Rahama. Ina rike ga hannunta muka shiga dakin da yake kwance an shirya shi cikin fararen kayan shi na tafiya kayan da kowa ke jiran ranan sawan shi tazo mai. Nan mukai mai addua muna waje aka fito dashi aka fice dashi daga gidan nan gida ya barke da sabon kuka kuma. Daga ranan muka shiga takaba sai tambayana ake zuwa yi wai banda komai tare dani ko ? Sai dai nai masu murmushi kawai ba amsa don ban san may zan ce dasu ba ni don mama tai min dalla dalla akan tambayan da ake min. Sai da aka watse an tafi sallah nake cewa da ita mama nifa ba wa abin da ya taba shiga tsakanina dashi irin haka. Tace ke don Allah rufe muna baki da wautan ki keda kwanaki akewa radw radin ciki sabuwa har da yaji tayi kan haka zakice wai ke ba abinda ya taba shiga tsakanin ki dashi. Kada na kara jin wanan zancen ko ga wani balle ai maki daukan mahaukaciya. Haka dole naja bakina muka shiga takaba ni da sauran matan shi a gidan inda nake zama da mama Altine da wata tsohuwa cikin yan uwan Inna ta. ****** ********* ****** Tunanen makoma na yadda zan koma gidan mu cikin ukubar mama ya fara damun zuciya na. Har nakaiga furtawa ga mama tace to yaya za, ayi ya zama dole yanzu kan ki koma gidan ku gaban iyayyen ki tunda nan baki da kwai baki da dunge a gidan to zaman may zakiyi masu a gida kuma ? Hakana muke wankan a dadafe ranan da ya cika sati biyu ne yar gurin sabuwa ta zo ta kwashe min ruwan randana nai mata magana cewa bata ganin yanzu sai na sayi ruwan tunda banda mai debo min. Daga can kofan uwarta ke cewa ke ma dai baki jin magana wallahi may yakai ki gurin wanan mai farar kafan ki debo min tsiya. Ga uban ku nan tun ranan da ya tsiri auren wanan matsiyaciyar yarinyar bai kara lafiya ba sai da ya kwanta daman shi. Shine ni zakije ki debo min tsiya kikawo min har ana maki kwakwazo akai kan ruwa. Mama Altine ce tafi ban ko sani ba tace boyar Allah maida yukan ki kube yau ina wanda kuke fadan a kan shi ya kwanta daman shi. Ke har wani dadi kikaji kina cikin wanka kike sababi haka kamar wacce abin bai dama ba. Aiko ta juya kan mama da masifa wai mama ta kama girman ta kada yanzu ajisu da ita. Karya ta fadi banice na jawo masu masifan rayuwa ba kala kala don iyayyena suna makwadaita aka cinna mai karfen kafa. Allah yasa yaya Hadi yana shigiwa lokacin ya taka mata waigi da cewa ke sabuwa kin fa ishe mu a gidan nan dama don baba nake daga maki kafa. Yanzu ke ba, ace kin kashe muna mahaifi ba sai wanan yarinyar da kullun baba cikin saka mata albarka yake har ta bar duniya keko fa daidai da rana daya banji makamancin wanan kalman ba daga gareshi a kanki. Don mu har wasiya ya bar muna akan yarinyar nan kan ko bayan ranshi mu kula mashi da rayuwan ta kada mu bari ta shiga wani hali na wahala. In ma kashe baba ne badon kada mu bata mai gawan shi ba ai sai muce kece kika kashe muna uba. Don matsalanki ya kara jefashi ga ciwon da yayi na ajali karshe ma bamu san may kikai mai ba sai gawan shi muka gani a dakin ki. Cikin wani irin tashin hankali take cewa yanzu Hadi ashe sherin da kuke kulla min agidan nan ke nan ku da muna fukan uwayen ku ban sani ba. Tsofin dake gidan suka fito sukai mata caaa akai suka ce fitinan ta ya ishe su idan kin matsa zamu mayar dake gidan ku ne. Tace wani gida ga gidan mijina da dakina da ya mutu ya barni a cikin sa ai yanzu kuma sai ido don jini ya riga ya gauraya da ruwa ko. Fitinan sabuwa ne yasa diyan shi suka hadu kan a hada gadon daya bari a raba aba kowa nashi kowa ya kama gaban shi gashi ita yaran ta duk yan mata ne har su bakwai ras gare ta a gidan. Nan akai kasafi basu yarda sun barta a cikin gidan su ba aka bata wani gida na Alhaji karami ita da yaran ta ranan sukace bazata kwana masu gida ba sai ta fice ta basu gurin su. Da kyat aka lalashe su su bari a gyara gidan tafice masu daga gidan su. Ban san Alhaji na da arziki haka ba sai wanan ranan nima na samu gida daga kason na na wanka da gona sai dai ba babba ga shanaye dana samu a ciki da kudi tare da sauran tarkace. Iyayena suna ganin yadda aka kwashe da sabuwa suka roka abasu ni su tafi dani gida na karasa wanka a can amma aka hana. Suka ce idan sun min hakana basu rike amanan da mahaufisu yabasu ba nawa ayi hakkuri kwana nawa in ga rai ga lafiya zan gama wanka na koma gida. Mama Altine kwana arbain tai min ta barni cikin su banda wani matsala tare dasu sai na kewan Alhaji kawai wanda bani kadai ba har yaro karami dake gidan yana yi don halin shi na alheri ga iyalin shi. Ban da rashin komai in ban da na maigidan don komai suna wadatar min dashi duk da an raba an ba kowa kason shi amma su yaya Hadi basu barina haka na cikin su. A dadafe na gama wanka a gidan ranan da muka fita tun safe sai ga su Rukaiyya wai mama tace suzo su fara rage min kayana zuwa gida. Mama hausatu ne tace haba sai kace zaman da akayi cikin bacin rai aiko zata koma a bari har a dan natsu sai ta koma gidan ko ? Haka suka juya suka koma suna fada mata ta haufada wai ko ni nafi kowa son gidan miji yanzu ai dole na dawo gidan ubana tun da dadi ya kare anga guri anbaje ana cin dadi yanzu ko dole na dawowa turke na mai cabo yana nan yana jirana karya ya kare da sallon auren mai kudin gari gare ni. Ban dawo gida ba sai da na cika sati biyu ranan mutuwan ta sake dawo muna sabo a gidan . Ina kuka sunayi aka kwashe min kayana zuwa gidan mu su mama ne suka raka ni har gida da dare sai fadin alherina sukeyi suna fadin zasu sha kewa dai kan a gidan. Yarinya karama amma bata san zafin jikin ta ba ko kyashi irin na yaran yau komai da zuciya daya zatai maka shi. Mama jin su kawai take tana fadi a ranta ai dole kuce haka tunda kun samu boya to muma nan mun fiku bukatan ta ai yanzu. Suka tafi suka barni ina kukan bakin cikin rabuwa dasu danayi na shige dakin Inna ta na kwanta a saman gadon ta na lafe. ****** ********* ****** Ban fito ba tunda na kwanta haka gari ya wayw min sai juyi nake ina tunane banyi barci ba mai dadi. Sai bayan nayi sallah ne na samu barci ya dan dauke ni mai dadi har ban san inda nake ba a lokacin. Can cikin barci naji muryan Inna ta tana tayar dani wai na tashi mama tana kira na a waje. Nai mika tare da juyawa na mike na sauko saman gadon tare da jan hijjab dina na saka a jikina. Na nufi waje inda nake jin mama tana kwada min kira harshe sama na amsa da na,am mama . Tace to kin shige daki kin mimike kafa wa kike jira ya debo maki ruwa da za, ai aiki da shi. A hankali na dago kai na kalle ta nace ruwa mama ? Tace eh ruwa ko kinfi karfin diban ruwan ne ke da bazaki ba kike nufi ko may , don ban san uban da kika aje da kike son yaje maki rijiya ba ai. Ko har yanzu mulkin auren gidan mai kudin ne a saman kan ki muji ? Ban yi magana ba sai juyawan da nayi zuwa dakin mu na koma na zauna a bakin gadon dana tashi. Inna dai tana jin mu batai magana ba sai aikin ta takeyi kawai a tsakar gida. Can dai taji ni shiru ban fito ba ta kara kwala min kira karo na biyu daga dakin na leko kaina ina fadin mama ni ba zan fita ba gaskiya don kunya nake ji wallahi. Eyya su kunya manya ke nan ke gaki matar Alhaji ko to Alhajin ma ina yake yau ko diyan shi da matan shi na kwarai sun kama kan su yanzu haka. Balle ke da ba kowan kowa ba a gari kice wai ke kina jin kunya anganki a bakin rijiya. Nace ciki ciki gaskiya mama ba zan je ba fa don wallahi ban san yadda zan kalli mutane ba da idona. Eh lalai kuwa kin kai Rahama aure dadi idon ki ya bude don yanzu abinda na sani kin riga kin san shi shiya har nake fadi kina fadi ko ? Nan ko ta hau fada ban san lokacin da wani kukan bakin ciki yazo min ba atake na shiga rera kuka. Sai ga baba gidan kamar an jefoshi yayi mantuwa ya dawo gidan. Tun daga kofan shigowa gidan yake jin muryan mama sai kuma sautin kukana dake fitowa daga cikin dakin mu. Kai kai wai yaya hakane kuma may ke faruwa ne wai kuma yanzu fa na bar gidan nan na fita shine har zan dawo na samu gida ya rude may ke faruwa ne wai tambaya fa nakeyi ? Tace isashiyar yar ka mana wai taje ta debo ruwa shine ba kunya wai har yarinyar nan ta kalli idona tace min ita bazata ba kunya take ji. Baba yace haba lauratu wai har yaushe yarinyar nan ta dawo gidan nan da za, a fara jin ku da ita. Yanzu koke ce kikaga ta dauki abin diban ruwa ai ki mata fada lauratu don haka bai dace ba gaskiya. Tau ashe abin naku dama hadin bakine kukayi kun riga da kun shirya yar lele ta dawo gida ko ? Baba yace kaji haukan ki ke nan ke wallahi yanzu don duniya su zage ni lauratu yarinyar nan jiya jiya da dawowan ta ace wai yau da safe har ta fara fita diban ruwa a rijiya. Ki tuna fa mijin ta mutuwa yayi ba wai rabuwan dadin rai sukayi ba dashi da har haka zai kasance da ita. Ya tako har kofan inna yana cew ke kama min bakinki ruwa dai ne nace bazaki diba ba su zauna haka ba ruwa in sai kin fita diban masu shi. Maganan baba yasa na dan sasauta kukan da nakeyi tare da share hawaye na zuciyata yai min wani kololon bakin ciki dashi. Mama tace aiko zaku ga tsiya a gidan nan don wallahi daga ita har uwarta ba yaron da zai debo min ruwa su taba shi. Can bayan ta dan lafa fadan ta naji sallama a kofan dakin mu take na sheda muryan mai shi nace wa nake gani kamar habib. Yace nice Anty naje can gidan shine akace min wai kin dawo nan yakarasa shigowa dakin yana zama tare da dan share hawayen shi dake zubo mai. Nima kukan nake sai da mukayi mai isar mu wanda kowa da abinda ke damuwan zuciyar shi wanda idan mun hada damuwa guri daya zai dawo akan sanadin rashin Alhaji a tsakanin mu. Nice na fara kawar da shirun da cewa yau habib ka tashi ka fita idan ka samu mai ruwa ka kira min na saya ina son nai wanka yace bari dai na debo maku anty. Wanan randunan ne za, a cika ko na waje ? Nace zaka iya kuwa Habib don rijiyan na da zurfi fa sosai yace zan iya mana anty ai kayan ba yawa ya dauki abin diban ruwa yafita daga gidan. Lokacin mama tana nan ta hake ruwan da aka debo mata mayawa uku tana jiran mu taba tai muna cin mutunci akan shi. Don daren jiya bata bar komai ba a randunan Inna ta don tsaban mugunta dama gadan zare ne ta shirya muna. Sai ganin Habib tayi yana cika muna kayan ruwan mu gashi da kwazo nan dana ya cika komai na kofan Inna ta da ruwa. Naje nai wanka nafito na shirya naji shi muka fice zuwa gidan mama Altine don bazan iya zama gidan mu na wuni tare da Mama ba a gidan. Tana ganina ta shiga nuna jin dadinta na ganina sai dai kallo daya tai min ta fahinci nayi kuka a ranan . Take cewa haba yar nan yanzu har yau baki daina wanan kukan ba gaki da manyan idanuwa kada kijawa kanki illa fa. Na kai zaune ina murmushi nake cewa mama ba kukan Alhaji nayi ba. Nan dai na kwashe yadda mukayi da mama da safe na fada mata komai take cewa kai amma anyi mutumiyar banza wallahi. Yanzu ita bata tausaya ma halin da kike ciki sai ma nina halin ko in kula zatayi , Da tasan ciwon kan ta da ta tausaya maki don itama ai uwace tunda tana da yaya mata mata zaune a daki. Habib dake jin mu yace anty kada ki damu nai maki alkawari kullun safe da yamma zanzo na cika maku randunan ku na ruwa insha Allahu. Mama tace kinga ma Allah ya kawo maku sauki ta wanan hanyan kuma ba. Can muka ci muka sha sai lokacin zuwa makaranta yace min zai tafi sai ya dawo. Ban shigo gidan mu ba sai da akai kiran magariba ashe wai mama takiba su Inna abincin rana a gida sai dan dabara mama tayi tabawa kanne na sukaci. Kamar wace ke jiran shigowa na sai ta hau bakin ta tana cewa ni dama nasan ai asoye da mutum wanan mutuwar don gashi har an fara yawon zawaeci ko. Bamu kulata ba muka shige daki sai da dare ya dan yi na kwanta abina na barsu nan suna harkokin su. Washe gari ban shiga gidan mama ba sai da na hada kayan Innata dana kanne na na wanke su fes na shaya na bar gidan. Ganin har kwana biyu mama ta hana ma inna ta abinci yasa na fito da kudi dake hannuna na aiki habib ya sayo muna kayan abinci a kasuwa. Nai sa,a mama bata gida muka shige da abin mu daki muka boye nace wa inna ta daga yau basai kin tsaya jiran na gida ba ki girka abinki kuci ke da yara kada yunwa ya illanta ku. Da yake mama bata da kunya da inna tai abincin ta ta kwashe bata tsaya tambayan na gida ba ranan. Don gurin mama Inna ta take karban komai na girki kamar yadda wasu matan hausawa sukeyi komai sai dai mace ta karba a hannun uwar gida idan zatai girki. Haka ranan mama ta hake mama tazo karban kayan girki tai mata wullakanci yadda ta saba yi mata. Amma sai taji shiru bata zo ba kuma gashi tayi girki kamshi ya bure ta ko ina dama kuka ne da dadddawa sai magi take karba gurin mama din . Amma yau mama kamshin lafiyayyen girki take ji tana mamakin haka ba dama kuma ta tambaya don tasan akwai magana jiran baba ya dawo takeyi. Inna ta sa yaran ta daki tabasu abinci suka ci suka koshi tai masu wanka suka shige ciki. Itako bata girka ba wai ala dole Inna ce da girkin gida itace zata girka masu suci ita da yaran ta takwas. Shigowa na gida daga gidan mama Altine dana taya ta aikin kuli kulin ta yai daidai da dawowan babana daga kasuwa. Yake tambayana Rahama daga ina haka da wanan magariban nace ina gidan mama altine muna aikin kuli kuli da ita. Yace hakan yana da kyau don zai rage maki kewa ai da zaman gidan da zakiyi na kwana biyu kafin Allah ya kawo maki mijin aure. Muna nan zaune inna tana labarta min yadda mama take ta leken ta da take girki sai muryan baba mukaji yana kiranta ta kawo mai abinci. Ba bata lokaci ta dauki tuwon masaran da tayi da miyan danyen karkashi ciki takai mai. Ya zauna ke nan zai fara ci sai ga mama ta uso gurin tana zuwa ta jaye kwanukan abincin a gaban shi cikin hasala ya dago kai yana cewa yaya haka kuma ? Tace ni za, a kawowa barkado a gida anshirya makirci ni na dama mutum na shanye indai gurin barkado ne. Yace da akayi may tace wanan makiran matar taja bata girka tabamu ba duka gida shine kai zata girka ta baka daga kai sai diyan ta kawai iya bakin ku. Mu may take nufi damu da bata bamu namu abincin da zamuci ba sai kai. Kafin baba yai magana Inna ta take cewa kamar yadda kwana biyu kika hana min ni da yara na muci musha a gidan nan don kina bakin ciki da zaman mu cikin ku haka nima yau na girka na hana maki. Lauratu may yai zafi haka da har zaki hana masu abinci a gidan nan ita da diyan ta. Sai mama tace saboda ba yar aikin su nake ba nan ruwa a debi ka daurewa karya gindi wai Rahama bazata dibo ruwa ba waye dan aikin su. Tsaki yaja yace amma anyi babban kwabo ke kan baki san girman ki ba wallahi ko . Ashe ke kika fara an maki kuma kice kinji zafi tace zafin may abinci dai ne idan bamu ci baka cin shi kai ma indon ka akayi shi dama. Inna tace idan kin hana mijin ki ci ki bani abinci na na mayar daki don kada ki fara ki ce zaki taba min abinci ko yanzu duk a rikice a gidan nan. Tasan bata in ma Inna ta kuma tunda taji ta fadi akwai tsiya ke nan ranan don Inna ta hau. Tace sai dai ki dauke shi amma bai cin shi Inna tace ai tunda yaci naki wanan ma kamar ya gama cin sa ai. Ina daki ina sauraren draman su nace oh ni ko yaushe iyayyena zasu daina wanan kishin kauyen nasu haka ? Gidan Alhaji da nai zama sabuwa ce kawai mai irin wanan matsalan a gidan ita kuma anfi karfinta bata samun yadda take so tayi a gidan. Nan naji Inna ta tana cewa indai ni zan girka kuci keda diyan ki a gidan nan daga yau na kashe yi sai dai mu zauna da yuwan idan Allah ya bani abinda zamuci sai muci. To, wooo yanzu nagane da kyau watau makiran diyar ki ta dawo gida irin mulkin da taje gidan Garbati ta kafa tasa aka raba talle shine tadawo muna dashi nan kuma yanzu ko.?. Don kuji dadin cin karen ku ba babbaka ko ta baki isa ba wallahi Asiya. Inna tace idan ma na usa ko ban usa ba ai yanzu ki gani na gaji da wulakancin ki gidan nan abu ba abu ba sai kice zaki horani da yara da yunwa to nagaji wallahi. Baba yace ku dakata ni kan banda karfin raba maku tukunya nakawowa wanan nakaiwa waccan idan zaku gyara ku gyara yafi maku sauki. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH DON CIN AMANA NE YIN HAKA, , , Sanye take a cikin kayan sanyi irin na kasan turawa rigan yakai kusan gwiwan ta hakanne ga mijin nata kamar yadda tasaka kayan tare tsananin sanyin da akeyi a garin. Yana rike da ita a kafadan shi suke saukowa daga matakalar benen gidan nasu wayan shi ce dake aljihun shi ta ruri a lokacin yadan tura hannun shi cikin aljihun shi ya ciro ganin wacce ke kiran shi a layin yasa shi daukan wayan nata. Sai da ya sauke wani irin ajiyan zuciya yake cewa yaya akayi ne zulfa ? Jin sunan wacce ya ambata yasata zare jikin ta daga nashi a hankali, tafara tafiya tako biyu zuwa bakin dayan kujeran dake falon. Ta zauna tare da tsura mai ido daga inda take a zaune daga jin yadda yake magana ta tsigan lalashi ta san fitina ne ake da shi ga wayan. Can taga yayi dan murmushi a fuskan yana cewa ke ma ai uwarsu ce zulfa don haka kiyi yadda ya kamata dasu mana. Kofa likita bamu samu gani ba tukun ki ke wanan zance haka idan mun gama ai zamu dawo ne ko. Bataji may tace dashi ba sai dai murmushin da taga yayi a fuskan yake cewa wata rana kema ai zaki bar naki a gurin ta ko ? Don haka ki yi hakkuri kifitar da komai a ranki ina diyana diyan ki ne kema koda ba, a gida kike ba. Can taji yace kwarai da gaske zulfa aiko ita kun san dalilin zuwan namu wannan lokacin ko. Shiru ya dan ratsa falon yana sauraren mai maganan ta waya har ta taji shi yana cewa ok shike nan sai mun yi waya anjima ke nan. Ya kashe wayan tare da dago kai yana kallon inda take zaune, ya dan yi murmushi . Ya zauna gap da ita yana cewa yaya tafi mana ko kin kuma zauna anan ? Ta dago idanuwan ta fuskan shi a cikin damuwa take cewa dashi akan yaran take magana ko ? Bai bata amsa ba don yasan ranta zai kara baci ne ga banza yace tashi mu tafi ko ? Da kyat ta mike tsaye ga dan matashin cikin dake a jikin ta ya turo a cikin rigan dake jikin ta. Rai bace take magana tana fadin kaga abinda nake gudu ke nan tun farko nace ka bari na kai su gurin hibba su zauna har mu dawo amma kace wai a barsu su zauna agida tunda akwai mutane. Ya jawo hannun ta yana fadin ke ma dai kin san bazan lamunci ina da gida da iyalina a ciki kuma na dauki diya na zuwa wani gurin ba. Tace idan baka yarda an kaisu wani wurin ba ai gashi kana shan korafi akai ni dai tsorona kada a cutawa yaran da basuci ba basu sha ba kan zancen mu. Haba Sa,ade Zulfa ce zata cutawa yarana kuma kada ki manta fa a matsayin yar uwa take a gareni fa. Tace a da ke nan yanzu kan ai a matsayin diyan kishiya take daukan diyan ka gare ta. Kofa ya bude masu suka fito daga gidan wani sanyi ne ya daki fuskan ta amma ba yadda ta iya dole haka zasu fita duk da tsananin sanyin da akeyi a garin Don fitan ya zama masu dole sai sunyi shine dole zai sata fita a hakan. Bayan sun gama da asibiti ne suka wuce zuwa wani shago nan ta dan yo sayayan abubuwan da ya dace ta tsinta har da tufafin yaran ta dana yaran abokan zaman nata. Ko da suka dawo gida a gajiye take don bata da kuzarin da zata dinga tafiya haka mai nisa a jikin ta. Zama yayi kasa a daidai kafan ta ya dan fara matsa mata su a hankali tana jin dadi hakan har cikin ranta ta dan fara lumahe idanuwan ta a hankali. Haka yasa ta samu saukin yadda take ji a ran ta a lokacin sai bata samu wani matsala komai ba ga yadda take zato. Washe gari ta riga shi sauko wa kasa don ta karya saboda yace yana son ya dan kara barci. Har sai bayan ta gama ne sai gashi yau sauko kasan a lokacin har yai wanka yana saye a cikin kananan kaya a jikin shi. Sau daya ta daga kai ta kalleshi taci gaba da duban wayan ta da takeyi tana murmushi a fuskan ta. Da alama hiran da takeyi yana mata dadi a ran ta lokacin ya iso inda take yana cewa madam yaya jikin naki ? Ta dan dago kan ta a hankali ta dube shi tana cewa Alhamdullahi ya kokari bai amsa mata ba sai da yakai zaune yace kokarin yiwa kaine ai nidai gurina naga Alllah ya rabaki da wanan cikin na jikin ki lafiya. Sai lokacin tabar abinda take a wayan ta ta dago kan ta ta dube shi inda ya zauna sai suka hada ido dashi tayi saurin kawar da idon ta cikin nasa . Yace No no no kada ki soma yi min wanan kukan naki dake tayar min da hankalina please ? Yace cikin kamo hannun ta zuwa na shi cikin girgiza mata kai yake fadin ki dinga sakawa zuciyar ki dangana Allah daya baki ciki a cikin wanan halin da kike yasan dalilin yin haka a gare ki. Don haka ki zamo cikin bayi masu rugumar kaddaran ubangijin su ako da yaushe. Wanan tayar da hankalin da kikeyi zai iya kara jefa ki a cikin wani sabon tashin hankali kuma har mu dake tare dake abin ya shafi zukatan mu. Ajiyan zuciya ta sauke tace dole na daga hankalina idan na tuna da lalurar dake tare dani sai ga shi kuma wanan cikin yazo ya shiga again. Murmushi yayi tare da jawo ta ajikin shi yana dan shafa bayan ta yake cewa lafiya lau zaki haihu insha Allah ai ciwo ba mutuwa bane. A hankali tace dashi abin ne ke bani tsoro sosai sai yake hanani sukuni a raina. Ya girgiza mata kai yace ai abin bada ga nan bane heartbeat ke dai Allah ya kawo muna sauki ga al,amarin. Sai da ya tabbatar ta kwantar da hankalin ta ya mike yana cewa zai dan fita amma ba zai dade ba indan ya fita. Nan ya fice ya barta zaune zuciyan ta cike da tunanen yan diyan ta biyu dake gida Nigeria gurin kishiyan ta. Tun ba akai ko ina ba gashi ta fara jin Zulfa din ta bugo waya tana korafi akan rikon yaran nata gashi zasu iya share wata uku basu koma gida ba. Shine dalilin da tun farko taso zuwa da yaran ta ko tabar su gurin yar uwarta amma sai ya nuna mata rashin yardan shi ga hakan . Don shi mutum ne mai matukar son iyalin shi a kusa dashi akoda yaushe haka ne yasa akwai shakuwa sosai tsakanin shi da italin shi don yana fitarwa kowa da hakkin shi yadda ya dace. Wanan zuwan da sukayi dashi ba itace ya dace tabiyo shi ba amma saboda dalilin rashin lafiyan ta yazo da ita din. Wanda kafin su zo saida akakai ruwa rana da sauran kishiyoyin nata akan basu yarda da hakan ba don acewa su yafi nuna kulawan shi akan Sa,ade da yaran ta bisa gasu. Don har kara suka kai shi gurin iyayyen su kan abinda yake shirin yi masu. Ita bata da ko labari sai dai ta fahinci ya dauki zafi da sauran matan nashi a lokacin. Ita da ake abin akan ta sai daga baya ta fahinci rigiman akan tafiyan su ne akeyin sa. Haka ne ya dan haifar mata da rashin natsuwa a tare da ita don haka ta bukaci da ajaye tafiya sai taga likitan ta na nan gida Nigeria. Amma amma mijin tana yaki janye zancen ba irin rokon da bata mashi ba kan ya barta amma sai yaki yarda da bukatan ta. Karshe ma cewa yayi da ita idan ke lafiyan ki bai damay ki ba ni ya damay ni tunda bake ce keda hasara ba ai . Hakkuru ta bashi don yadda taga ya hau tasan itama zata iya samun nata rabon fitina a ciki don haka taja bakin ta ta tsuke tai shiru har lokacin tafiya yayi suka wuce. Don makaran ta ne kawai yasa ta bar yaran ta a hannun kishiyoyin ta ba don taso ba don tana nan ma yaya aka kwashe da su balle bata kusa. Ko ita Zulfa ba don Allah ta rike yaran ba don sai daya zube mata kudi masu yawa ta yarda zata zauna dasu din. ****** ********* ****** Na gama aikin da nake taya mama altine na kwashi kayan na aiki tare da kaisu bakin kwata na wanke komai fes na mayar na kife mama na zaune ta zuba min ido daga inda take zaune ta motsa furan data dama ta sha. Ina yarfar da ruwan dakw hannu na bayan na dauraye kafana take cewa sannu Rahama ai kin huta ke bakajin kiyuyan aiki ko kadan. Da ace uwarki lauratu ta gane haka ta nemi zaman lafiya dake a gidan dan wanan zaman da zakiyi a gida aida ta more maki sosai. Na dago kai da sauri ina kallon mama nace kai mama matar da tun ina yar kankanuwa na fahinci bata kaunana yaya zan zauna da ita ta more min haka. Ni fa yadda mama bata kaunana a sannu nima haka kiyayyan ta ya shiga har kasan raina wallahi. Mutumin da zai iya maka sheri da kazafi aiko kasheka yana iyayi mama. Bata kashe ki sai dai sherin ta ya koma mata baga diyan ta nan ba babu mashinshini a tare da su duk fa cikun mugun halin ta ne amma ita bata ganewa ne kawai. Ki debi abinci kici kada yai sanyi gashi da zafin shi nace ba yanzu ba mama sai anjima kafin na kwanta don tunda na dawo gida idan Innata ce da girki a gidan mama altine nake kwanci na don nasan Mama bazata yarda da na kwana a dakin ta ba yadda muke din nan yanzu kamar annabi da kafiri ni da ita. Muna nan muka ji sallaman dan wurin mama yana cewa Rahama wai kizo inji baba . Nace yau baba lafiya ya dawo gida haka da wuri don nasa sai yamma lis da magariba yake dawowa gida. Ban bata lokaci ba na figi hijjab dina zuwa kiran baban nawa da yake min ko da na shiga yana alwala zaiyi sallah na nufi inda yake zaune saman dutse na gaishe shi da dawowa. Na samu guri daga gefen shi na tsugunna ina fadin baba gani . Yace dan dajan ta min na rarage alwala na mike na koma gefe ina jiran idarwan shi har lokacin daya gama ya mike tsaye. Sai naji yana kiran Lauratu lauratu, lauratu fa da dan karfi ta amsa daga daki da saurin ta tafito tana gyara daurin zanin ta. Tana cewa lafiya dai malam wanan kira haka kamar zaka tsaga min kunne dashi. Yace to ke ce din idan ba haka aka kiraki ba sai ki kyale mutum tsaye wani zubin. Yace ina ita Asiya take inna dake bakin murhu tana kashe wutan da tai girki tace gani. Yace to dama ba wani abu bane yasa nai kiran ku ku duka ukun sai akan Rahama gata nan. Allah ya kawo mata mai nema a cikin sauki ba ko wani bane sai Malam Jatau na hayi dotse abokin maigidan ta marigayi. Shine ya aiki min yau da safen nan akan yana son ta da aure ya hada ta cikin iyalin shi. Don ya yaba da zaman ta gidan aminin nashi da tayi kwadayin hakan yasa yake sha, awan auren ta. Wani irin dariya gami da guda mama ta ranga tare da cewa yarinyar tayi tagomashi ga tsofin gari. Wani irin dam dam naji kirjina yaba da a lokaci guda cikin raina nace wani malam Jatau kuma can ai gara ma Alhaji garbati marigayi din shi a tsaye yake kyam ba irin malam Jatau ba dake tafiya a duke. Gashi da dan banzan kazanta da rowa ko kiyashin gidan shi sun san shi da rowa da mugun halin. Mama sai da ta gaji don kanta san nan ta tsagaita dariyan ta tana cewa injin ka bashi dai. Yace ban amsa mai ba sai naji shawaran ku tukun akan zancen kafin na basu amsa ta. Lalai ma malam yo may zaka tsaya jira da ita Allah ya kawo mata mai so da wuri haka ? Yace ai komai sai a hankali akeyin sa tunda yanzu ita ba budurwa bace kin ga zama dan bata zabi ai ko? Zabin may har nawa Rahama take da za, a tsaya neman wani zabin ta kudine dai akwaishi kaga sai taje taciwo muna nashi kasuwan kuma. Ban san lokacin da bakina ya kufce ba nace ai kina da tan mata zuka zuka har uku a dakin ki kibashi mana. Salati ta saka tare da saka kuka wai naci mutuncin ta a gaban uwaye na ai ba ita bace tasamin farin jinin tsofi balle naci mutuncin ta bakin halina ne dani da uwata ke bibiyan mu. Da kyat baba ya lalashe ta ta koma dakin ta nikuma yai min fadan haka kaca kaca ya fice gidan. Dakin Inna ta muka shiga kowan mu bakin ciki yana cin sa a rai da wanan sabon fitinan dake neman bullo muna kuma. Nace wa Inna ta ni wallahi wanan karon ko kashe ni baba zaiyi ba zan yi auren nan ba ai bani kadai ce diya ba a gidan da zaita badani ga tsufin gari haka. Inba tace kidai bi sannu ke ma kin san idan uwarku ta kafe sai ya bayar dake ko bakya so hakan. Daga daki muna jin mama da yaran ta suna bidirin su cikin jin dadi har da shewan su. Don su burin su dama shine suga bakin cikin mu nida uwata a gidan ga kuma wani dama ya sake samuwa gare su again. Washegari koda na je gidan mama na kasa fada mata komai sai dai ta fahinci ina cikin yar damuwa a lokacin. Ta tambaye ni nai mata yake kawai da cewa ba komai mama don ba ko wani sirin gidan mune zan dinga fada mata ba din yanzu girma yazo min na san wasu abu ba kowane zaka fadawa ba. A kai sallama a kofan gidan mu lokacin baba ya fice zuwa kasuwa ba yara gida mama ta yafa ta fita. Malam Jatau ne a cikin wani tsohon babban rigan shi daya takure don tsufa ga dauda taf ga kayan sai tsohon hular dake kan shi don tsufa har zaren hullan ya fara zarewa daga jikin shi sai shafin dauda daya kwanta akai. Suka gaisa tana washe baki take cewa , a, a Alhaji Jatau ne sannu da zuwa . Ai kuwa ba kunya mama take cewa har an fara zuwa zance ne gashi maigidan ya fita amma ba matsala bari a kira ma yarinyar ai tunda ina nan. Ya washe bakin da duk goro ya bata shi yake cewa ikon Allah ashe kun san da zancen ke nan wallahi yabawa da halaiyar yarinyar don marigayi yana yaba hankalin ta. Hakan yasa nai kwadayin saka ta a cikin nawa iyalin ko banza na taimakawa shi marigayin ga nauyin da ya bari ai. Mama take cewa gaskiya ka kyauta muna sosai ga wanan jahadin don kaga dama yanzu auren ta sai mai dan hannu da shuni tunda ta saba da daula a can. Ya kara washe bakin shi yana dariya tare da fadin kada aji komai zan rike ta amana yadda shima ya rike ta a gidan shi. Mama ta wuce shi zuwa gidan mama Altine inda nake ina dakin mama na dan kwanta don ranan bamu aikin komai. Sai muryan mama Lauratu muke ji yana tashi tun kafin ta kawo kwanan shigowa cikin gidan. Rahama Rahama wai ina mara kunyar yarinyar nan ta shiga ne haka ana kira kamar bata ji. Daga inda nake kwance ina jinta sai mama Altine ce kecewa injin dai lafiya wanan kiran irin haka ? Cikin takaici take cewa ina wanan yarinyar take ne wai ana kira tana kyale mutane to ki fito ga bazawarin ki yazo gurin ki. Bazawari kuma mama Altine ta tambaya cikin mamaki tana kallon mama lauratun dake wani haki. Tace basu fada maki zancen malam Jatau na hayin dutse dake son auren ta bane ko may ? Takara cewa ai kinga matsalan su basu bar kowa ba a gurin kilibibi har dake uwar dakin nasu sai sun gwadawa halin su. Daidai lokacin na fito daga dakin mama ina mata kallon takaici nace. Mama ina tun ranan na fada maki ra, ayina akai ke ma may yan mata uku a daki da basu taba aure ba ai su gwada sa, an su sugani gareshi ko don naga sunfi dacewa dashi bani Rahama ba. Daga haka na shige daki abina na kwanta na barta nan waje tana sallami da zagina sai inda ta tsaya ta fita tana cewa Jatau din kyale jairan yarinyan nan sai an fito mata tabayan gida. Koshi Alhaji marigayin ai ba kasafai ya samay ta hakana ba sai da muka hada kai dashi komai yazo daidai gareshi. Kokai sai mun kai ga hakan in har kana son ta da gaskiya dole sai kayi wani abu don na shiga na fita a samo maka kan ta. Ya gyara tsugun ni shi yace to wo hakane abin yake to yanzu kina ganin kamar nawa zamu kashe ke nan.? Mama ta samu yadda take so takara dan matsowa kusa dashi ta kashe murya tana dan kuskus tare da shi cikin rada. Badon abinda yake muradin samu bane da babu yadda mama zata iya cin naira guda nashi daga aljihun shi komai dabaran shi kuwa. Nan dai sukai sallama da ita tai mashi alkawarin zata san yadda ta shiga tafita aka samu kaina a cikin sauki. Bayan fitan ta gidan mama Altine ne ta saka ni gaba da tambaya ina kuka ina sharan hawayen bakin ciki da takaicin dake cina ne ina fada mata kan maganan. Tace amma ko halin malam baiyi ba wallahi don dai wanan karon in har da adalci bai kamata yai maki haka ba. Abune dai na sunw iyayyen ki ban da iko akan ki da sun ga tsiya wanan karon. Kuma ai ba karya kika fada ma tana da yara dakin ta in har yarinya yake son aure ta bashi daya. Mama ko tana shiga gida sai zagin Jatau takeyi tana cewa kaga matsiyaci ko kudin share kasa wanan yana isa ne balle na wani aiki can a haka dai komai rowan ka sai naci abin ka ta wannan fannin. Baba na dawo wa gida ina jinta tana mayar mai da yadda mukayi da Jatau da ita. Daga can naji yana kirana babu tsoro ko kadan a raina na fito amsa mai kiran. Nan ya hauni da fada inda yake shiga banan yake shiga ba yana fadin ba zai lamunci ina wa mama rashin mutunci ba a gidan shi in har nace ban auren Jatau to nafito da wanda nake so yai min aure don shi ba ai mai dogon zawarci a gidan shi. Inna tana daki tana jin duk yadda muke kwasa da babana a tsakar gida na shigo daki ina kuka ina cewa ban san abinda naiwa baba da mata suka tsaneni ba haka ? Inna tace bake suka tsana ba yarinya nice suka tsana a gidan nan har ya shafe ki an riga an dasa mashi kiyayyan mu a ran shi tuntuni. Nace Inna irin wanan abinda baba yake min wani lokaci har tunane nakan yi nace anya kuwa shine mahaifina kuwa ? Tayi shiru ranta a bace yana mata suya da takaici cikin bacin rai tace dani idan bashi bane uban ki waye yarinya ? Tsaban rashin tsoron Allah da makoma ne dai ke damun su daga shi har ita din. Karasa wacce zaka dinga kuntatawa sai yar cikin ka ko yaushe ita yaya nata haukan kishine ya rufe mata ido take haka akan mu. Don kullun burinta shine taga bacin raina a gidan nan idan taga haka shine farin cikin ta a gidan nan. Ki dai yi hakkuri ko yaya yake mahaifin ki ne daga su har mu bamu isa muja da ikon Allah ba idan kuma Allah ya kaddara shima wanan din mijin ki ne babu tsimi babu dabara sai kin aure shi. Yanzu abinda nake so dake shine ki daina wanan rashin kunyan da kika dauko mata kici da yi mata biyayya a matsayin ta na uwa a gare ki don matar uban ki ce kullun ina fada maki haka. Ina zaune ina jin duk nasihan da Inna ta take min naso na daure amma kuma kukan da nake dan newa ya tsanan ta min zuciyana ya kasa daurewa ita kanta Inna ganin yadda nake kuka gwanin ban tausayi bata san sanda kukan ya kwabce mata ba. Can dau inna ta daure take ce min yarinya yanzu ba kuka ne abin yi ba gare mu dole ne musan mafita ga wanan zancen naki. Muryan baba ne mukaji yana cewa duk abinda zakuyi sai dai kuyi dana ai nasan kece mai daure mata gindi tanayiwa mutane iya shige a gidan nan. Inna tana jin haka tamike tafito daga dakin tana cewa ai dama nasan duk maganan yarinya idan ya taso akaina yake karewa a gidan nan don rashin adalcin da ba ai muna. Idan bani da ita ba wa ake wa wanan ikon haka a gidan nan ya kyale sai dai mu da aka raina muna kuran mu kawai. Baba ya dinga kallon Inna da mamaki yasan duk lokacin da ta va da ansa ga zance a gidan to abin yakai karo ke nan ba dadi. Ido kawai ya tsura mata ya kasa tabuka komai a kan ta sai muryan mama ne daga bayan su take cewa ai har da daurin gindin ka da suke samu suke ganin kamar wuyan su ya isa yaka yanzu a gidan In bashi har yau Rahama take da zatace wai ga zabinta bayan wanda kai mata don ta samu dauri daga uwarta ko ? ****** ********* ****** Da sassafe sai ga Larai kawar mama ta shigo gidan wurin mama lokacin Inna tana dama muna koko da zamu karya dashi don ina daki dun kule har lokacin bana jin dadin jikina. Da dariyan ta suka gaisa da mama take cewa a, a lauratu kice min kuma yar ki ta kara maku babban kamu ne agidan kuma ? Lalai kun iya jefa fatsa a ruwa ko yaushe sai manyan kifin garin kuke kamawa, yarinya ta zama ma uwarta jari a gari don ko shi wanan din kada ku bari ya sullube maku. Don nasan yo Allah na tuba ai kaman wancan din za, ayi tunda shima sai a hankali kinga kun kara samun wani gadon kuma ku haye ai. Da farko Inna taso tai banza da su da suka taba ita da mama sai kuma taga indan tai shiru ta kyale su sun sha da ita. Don ko gobe dawowa zatayi ta kara gasa mata wani don taci riban na farko din da tazo tayi. Inna ta dago kai inda suke ta dube su tana murmushi ace hakane fa kedai Larai. Kuma kin sab jahili shike gagawan yanke hukunci amma shi mai ilimi kullun yana kyautata zaton sa gurin ubangijin sa ne domin shine mai azurta bawan sa a duk lokacin da yaso hakan. Tunda fatsar mu ya iya kama babban kifi ko yaushe idan kamu banza ne wasu sukama koda karami ne mugani . Don ita killa wanan karon kifin da zata kama ba irinsa a wanan ruwan sai na gaba zata kamo. San nan ku sani shi sheri kare ne don mai shi yake bi hassada ga mai robo ko yaushe ai taki ne da ace ko wancan din ansan haka zai zama muna alheri da wasu sun kai nasu sunci. Amma daya abin rabone daga Allah sai sheri ya juye muna alheri a rayuwan mu. Sai gashi a filin Allah an dawo ana hassada akan mu kinga ko ai bamu ga kaico ga kamun manyan kifi don isa ne wani ko uwar ruwa yajefa fatsan shi ko kwai bazai kamo ba. Take suka hasala matuka gaba dayan su don sun fahinci inda maganan Inna ya dosa gare su don kowa na da manyan yan mata a dakin shi. Don idan baki yasan abin fadi baisan ansan da zai samo ba sai suke ji kamar Inna ta watsa masu ruwan zafi ne da safen nan. Nan suka kama masifa da kumfan baki gareta sai ashar da mugun kalamai suke watsowa ita dai inna ta shige daki abinta tana dariya. Bata san baba na gida ba sai muryan shi taji yana cewa haba haba Laira wanan ba girman ku bane kizo har gidan mutane kina masu shagube. Idan ma an kaiki gurin maigari baki da gaskiya anan din babu ruwanki cikin zancen kishin su. Nan suka juya kan baba da fadan suna fadin dama ai baka taba ganin laifin su kamar Asiya ce har zatai muna gori wai namu diyan ko samarin kirki basu dashi. Dama ai nasan duk munafunci ne kokai baka kaunan wanan zancen akan ta sai in yai dadi ne kake fin kowa cinyewa. Idan ma asirin su ne da suka iya yaka ma ka sai dai ya tsaya a kan ka don ni bazasu iya komai dani ba. Yace maza Larai ta fice mai a gidan shi tunda ba alheri ne ke kawo ta ba gidan sai hadin hasumi a tsakanin iyalin shi. Simi simi larai ta juya tabar gidan tana fadan karya inda tasan yana gidan lokacin da batai gigin shigowa ba lokacin. Tana fita ne baba ya juya gurin mama yana cewa ke kuma in kina kama girman ki ki kama don wanan ba halin arziki bane gareki. Mama dai sai faman haushi takeyi wai tana fada an mata gori ita da diyan ta a gidan. Indai don auren tsofin da nakeyi ne inna take ganin kamar wani fin diyan ta nayi su zuba haka zan kare rayuwana a wahalce gidan Jatau. Don duk yadda zatayi shige da fice sai tayi ko bama so sai na tafi gidan nan nai masu bauta su ma kamar yadda na saba yi a gidan garbati bakin ciki shi ya dade bai kashe Inna ba dani. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE. IDAN KIN BIYA KI RIKE AMANA YAR UWA KADA KIBA WA WANDA BAI BIYA BA PLEASE DON AMANA NAUYI GARESA, , Shirin kwanciya sukayi tana saye cikin kayan barcin ta sun matukar karban jikin ta sai hullan da ta saka a kan ta don kariya. Har wanan lokacin mijin ya fahinci tana cikin damu wanda bai wuce nasaba akan yaran ta ne da zaman su ke hannun kishiyan ta. Tsaye yake saitin window dakin yana waya daga inda take kwance tana kallon shi. Tun yana wayan a hankali har yakai ya fara daga muryan shi yana cewa. Wai ke mahaukaciyar ina ce haihun ki nawa a gidana don a sani na ai kina haihuwa har ma yaushe ne kika haihu wai ? Bata ji may ake cewa dashi ba don ba handfree wayan shi yake ba a lokacin ta fahinci indai zaiyi waya bai saka handfree ba da kishiyoyin tane yake waya wani lokacin. Muryan shi taji yana fada a hasale yana fadin wai ke hindatu wata irin mace ce wacce a kullun sai ta fito da sabon sallon tashin hankali a rayuwan ta kada dai a zauna lafiya. To ki sani na fada maki banda kudin zuwa Germany ganin wani likita kan neman ciki duk shekaran yar ki nawa da zaki tayar da hankalin ki kan wai neman ciki yar just three years take nema fa yanzu. To ki sani duk abinda kikaga dama kiyi amma amma ni bada kudina ba cikin wanan shirmay naki. Daga haka ya katse wayan tare da jan tsuki ya nufo gadon don ya kwanta shima. Yana kwantawa yaji muryan salihan matar nashi mai son shi da kaunar shi tsakani da Allah na fadin. Hindatu ce ko ? Yace a hasale itace mana. Anya kishin hundatu ko akwai imani a cikin sa heartbeat ? Yace nima abinda nake tunane ke nan ko dai tana da matsalan kwakwalwane . In ba haka ba yaya da ganin wata da ciki duk tabi hankalin ta ta tayar ga banza ? Ta manta cewa Allah ne ke bayarwa ba mutum ke badawa ba da kan sa. Tace to ai ba fada zakai mata ba tunda abinda take so ne sai ka lalashe ta a wuce gurin. Yace oho na tsaya mata sanya ta ci gaba da min rashin hankali da ta saba ke nan ko ? Tace ba haka bane hankalinta ne ya tashi bata cikin natsuwa ne yakawo hakan . Yace matar da bata damu da damuwan kowa ba kan ta kawai ta sani ita a rayuwan ta. Tace hakkuri dai zakayi ka rarasheta kada ta jefa kan ta cikin wani hali kuma na daban. Yace na fada maki ki bar wanan yarinyar kawai samun daurin gindi tayi a gurin daddy shiya sa take min abinda taga dama. A can kuma gida Nigeria inda Hindatu take zaune gaban mahaifiyan ta tana rusa kuka. Mahaifiyan nata tace na fada maki kibi a hankali kin san halin mijin ku da murdaden hali baida saukin fahinta ko kadan. Maza ki kirashi ki kara bashi hakkuri tun bai ce zai dauki wani mataki ba a kan ki. Uwar tace maza kira min shi nai magana dashi don nasan yanzu yana can hasale duk inda yake. Mama yanzu fa dare ne a can wata kilama sun kwata a lokacin nan ko. Dama dai baki son zaman lafiya aike baki san maza sai da lalashi ba kina ganin komai dole daddy sa ya sa shi dole a kanki. Sai dana fada maki kada ki kirashi yanzu kiyi hakkuri har su dawo don sai ya fahinci kan wanan matar tashi kike wanan haukan haka? Mama ni kunyan kiran sa fa nake ji na fada maki kin kuma ji amsan daya bani har da ce min wai ni mahaukaciya ce. Kira min shi kibani shi nace maki aini dole ya ta tsaya ta saurare ni ko. Dole Hindatu ta kira layin mijin nasu har wayan ta katse ba a dauka ba . Uwar ta rude iya rudewa don tana gudun mahaifin hindatun yaji yai masu tsiya. Sake kira min shi inji uwar cikin kidimaywa taje magana fuskan ta kan yarta. Dole hindatu takara kiran shi yana ji yaki dagawa sai Saade ne ta daga kiran tare da mika mai wayan ya kalla cikin hasala tare da kara mai a kunnen shi. Mama ya dauka Hindatun tace tana mikawa uwar wayan Muryan mahaifiyarta yaji a wayan yasa shi dan gyarawa cikin muryan ladabi yana cewa Yusuf nice a layin, Yace na gane mama kuna lafiya yaya mutanen gida tace duk muna lafiya. Yusuf dama kan zancen da kukayi da yarinyar nan ne nake son maka magana . Yace mama idan wanan zancen ne ni na gama magana na ba hannuna acikin wanan magana. Har yaushe ta haihu da zata dauku tashin hankali tasakawa ranta haka ? Uwar tace na sani Yusuf nasan da haka ai rigimane kawai irin na yarinyar nan don shi ciki ai rabo ne. Don haka kayi hakkuri abar wanan zancen don bana son ko mahaifin ta ya san da wanan zancen haka. Don Allah kayi hakkuri kasan halin kowa da irin nashi tunanen hakan yana damun tane yasa take wanan haukan haka. Inji Saade ke bashi hakkuri bayan sun gama wayan da mahaifiyar hindatu din. Yace ba komai bane ke jawo min haka sai wullakancin da sukaga daddy da hajiya suna min akan su amma yarinya zata gane kuren ta wallahi. ****** ********* ****** Mama ce daki da baba cikin tausan murya take cewa yanzu malam haka zaka bari wanan daman ya wuce mu a gidan nan. Allah ya rufa maka asiri sai masu hannu da shunin gari ke zuwa neman yar nan don sa, an ta. Amma ita da uwarta basu fahinci nasaran haka ba don basu da fahinta akai. Wancan auren da tayi da suka samu dadin su da wasu kaci ko wanna ma idan yai dadi ai sune zasu ci abinsu muna kallo. Dadin baki mai ratsa zuciya mama kewa baba kullun akan maganan tun bai yarda ba har takai ya amince da zancen ta ya shiga zuciyar shi ya zauna daram ya kafe zai ba Jatau ni. Ko ina so ko ban so dole ne na amince da zabin shi tunda shine keda Alhakin zaba min miji ai. Ranan da baba ya koma dakin Inna sai gashi ya fito mata da zancen wai maganan Rahama da Jatau fa yana nan don haka sai ku fara shiri akan aure nan bada dadewa ba za, ayi. Take ran Inna ya baci idanuwan ta sun sauya launi cikin bacin rai take cewa . Malam da ba dakai na haifi yarinyar nan ba sai nace kana hassada da ita ko kiyayya don irin kiyayyan da kake gwadawa yarinya yai matukar yawa a gidan nan. Yanzu kai ko kunya baka ji garin nan aji zaka kara aurar da yarinyar nan ga wani tsoho don kudi don abin hannun su kukewa kwadai. Yanzu Asiya ni kike kallin idona kice saboda kwadan abin hannu nake aurar da yarinyar nan. Inna ta ma rasa may zata ce da shi saboda takaicin daya rufe ta a lokacin. Cikin bacin rai take cewa ai ba karya na fadi ba don duk wanda ma yaji haka yasan abinda kukewa ke nan. Yanzu wancan auren abinda ta samu wa ya amfana dashi ba kai ba ina gidan ne kawai kila zata tsira dashi. Don haka wallahi wanan karon bazan yarda da cin zalun din yarinyar nan da ake muna ba. Har nawa yarinyar nan take da za, a dinga mata haka ina ga yayyin ta nan zube a gida su ko zancen su ba ayi. Yace to tunda kin isa da ita duk matakin da zaki dauka kan wanan zance sai ki dauka mu gani tunda kin isa ke . Wasa wasa magana har takai ga daga murya tsakanin su sai ga mama da ta dade tana sauraren su ta saka baki daga waje tana fadin Malam kada ka biye mata kasan va hankali ke ga Asiya ba don son abinda yarta ke so ya rufe mata ido bata hangen abinda kaje ya dawo. Cikin fushi baba yace mata ki kyale ni da ita Lauratu wallahi Asiya kin yi karya dake da yarki ku mai dani mutumin banza a gari. Duk iskancin da budewan idon ku da kuke ganin kuna dashi yanzu baku kai ni ba don haka ku ci gaba da min rashin da, a ke da yar ki ku gani a gidan nan. Indan kunce haka kuka dauko sai kun kwammace rashin zaman ku gidan nan dani. Kallon shi Inna tayi shekeke tace dashi ai kasan kaine keda rayuwan mu a hannun ka . Indai kan wanan zancen ne sai dai ajimu don nai magana akan hakkin ya ta ai ba haramun bane ko ? Kuke samun riban auren da takeyi shi yasa kuke son kara tursasa mata sai tayi wanan din taje ta ciwo maku kasuwa gidan. Duk masifan baba yana ganin ta haukace mai sai jikin shi yai sanyi yasan duk yadda akayi akwai abinda ta digora dashi take hakan don ba halinta bane haka. Aikin banza inji mama tace may ye bamu sani ba wani dare ne kuma jemage bai gani ba. Auren da sai anyi kifi kowa zakewa da jin dadi shine har za, a tsaya ana muna tijara akan shi. Malam ka kwantar da hankalin ka kana nan zakaga yadda take rawan kafa da jiki ita a dole yarta ta samu gurin zama. Idan ni ban yi rawan kafa ba ai ke sai kiyi tunda ke ma kina da yaya dakin ki sai ki bashi daya daga ciki a wuce gurin. Tana fadin haka ta koma ta kwanta abinta tare da watsawa baba harara tana fadin don an mayar dakai haka bari a turo ka kai min cin mutunci ko. Tun ranan da akai fadan nan ina wuta mama da baba su jefa mu ni da Innata. Duk wani kule kulle da makirci shi mama take kullawa akan zancen sai cin kudin Jatau takeyi tana bushashan ta a cikin gida ita da diyan ta kawai. Duk wani hanya da baba zai fahinta mama ta toshe shi har yakai ta fara dan fita zuwa gurin malaman ta wai a kulle muna baki duk mu ukun sai abinda tace kawai za, ayi. Haka Inna take cikin tashin hankali kan zancen don ta fahinci idan bata yi da gaske ba babu makawa sai anyi wanan auren gamin gan bizan dani da Jatau. Kullun tana hanyan gidan mama Altine kan magana daya duk tafita hayacin ta. Gashi mama taci kudin shi yakai dubu ashirin da biyar tana karba wai tana bani tana kuma kamun kafa da sauran. Bata san cewa komai nashi a lissafe yake mai ba don ba mutun ci ne dashi ba akan dukiyan shi ko kusa bai taka kafan Alhaji Garbati ba gurin tara abin hannun shi ba. Amma mutane don baya ci sai suke gani yafi garbatin ma tara dukiya a garin. Wata rana ina fitowa zan shiga gidan mama sai ganin shi nayi a kofan gidan mu don kusan a nan yake wuni. Yana gani na ya fara washe baki ya na dan soshe soshe kamar mara gaskiya. Ya dan tafo duduke kusa dani yana cewa a, a mutumiyar barka da fitowa ashe yau nazo a sa, a zan gan ki ashe ? Wani kallo nai mai nace yauwa sannu baba . Yayi dariya hakoran shi da wanda babu da rinanun sauran dake cikin bakin shi suka baiyyana a fili. Cikin dariya yake cewa ai ni yanzu ba babane gurin ki zaki dai iya kira na da ango ango mai shirin shan mai ko ? Nace tau ikon Allah baba aure ne zakayi halan ? Kallon mamaki yai min yace kamar yaya kike tambayana haka kamar baki san da zancen ba kuma. Na dan fadada fara, a na nace ban ko sani ba baba a ina kasamu matar ke nan ? Yace ikon Allah gaki tsaye a gabana kike min wanan tambaya kuma ai ni yanzu nan da kika ganni jira kawai nake a shafa a tsakanin mu don har dukiyan aure na biya ko jiya. Nace amma bakasan wace ka biya dukiyan akan ta ba ko don bani bace kake zance akai. Ya sake kallona cikin mamaki yace ai ko ke din ce nan da sati biyu insha Allahu zaki tare a gida . Dadai kin dan tsaya mun fahinci juna naji dan naki tsare tsaren don kin san shi marigayi garbati ya riga ya shagwabaki so sai. Ban tsaya sake sauraren shi ba kada ya kara jefani wani sabon damuwa na shige gida abina na barshi nan yana kwala min kira kamar wani tsohon maye. Na samu inna ta a waje ganin yanayin da na shigo gidan ciki yasa ta barin abinda takeyi tabini daki. Ta samay ni zaune nayi tagumi sai hawaye nake zubarwa a idona babu sautin kuka. Hankali a tashe take tambayana ke kuma da kika fita yanzu cikin dadin rai may ya dawo dake gidan haka ne kuma ? Na dago idanuwa dake zubar da hawaye ina cewa Inna kinji mutanen nan ashe wai har sadakina baba ya karba hannun Jatau. Cikin mamaki Inna tace yaushe akai hakan bamu da labarin komai akai nan dai ina kuka nake fada mata yadda mukayi da Jatau din dana fita. Inna ta zuba min ido cike da tausayina domin tasan irin zafin da nake ji a lokacin take cewa. Yarinya ki kwantar da hankalin ki insha Allahu ba a wanan auren idan kinga anyi shi sai dai bana raye. Bari yanzu naje naga mamakin mai kuli musan abin yi tun kan mu makara akai. Koda hakan na nufin rabuwa na da mahaufin ki ne sai dai mu rabu amma ba mai maki dole akai indai ina raye . Na gaji da wanan mulkin mallakan da ake muna a gidan nan ya Isa hakana wallahi zasu gane basu da wayo wanan zubin. Gidan mama ta fada muka shiga kusan tare a lokaci daya yadda mama ta gan mu tasan ba lafiya ba. Nan Inna ta shiga zaiyano mata duk halin da ake ciki itama dai fada ta shiga yi da tsinuwan mama lauratu tana cewa. Wanan karon saidai abinta ya koma mata amma Allah bai basu ikon yin hakan a kanki. Mafita daya ne idan zaku iya da dare muje gidan maigari mu samay shi mu fada mai abinda ke faruwa don asaka ma abin waigi tun wuri. Inna tace may zai hana ni zuwa indai zaki kaimu mai kuli ai mu mafita muke nema tako wani hanya indai hakan zai samu. Kamar yadda suka shirya dare nayi Inna tace zata shiga gidan su ta gaida wanta da baida lafiya. Lokacin ni dama ban dawo gida ba ina gidan mama Altine don anan zan kwana Akai sa, a baba bai hana ba don dama yana son zasuyi magana da mama kan zancen auren gashi kuma kafa ya samu. Inna na zuwa muka wuce zuwa gidan maigari mun samay shi yana cin abinci muka gaisa dashi da iyalin shi cikin mutum ci. Sai da ya idar muka isa gurin shi nan mama Altine ta koro mai duk halin da ake ciki dani. Ya kurkure baki tare da watsar da ruwan gefen shi yana cewa kai amma malam Audi baiyi ba wallahi. Don ma dai Allah ya hada shi da yar aziki ne ya samu tai mai biyayan akan na farko yanzun kuma shine yake son lakaka mata wani. Kada ku damu dama mun samu wanan dokan daga birni cewa babu auren dole ga yarinya ko yaro yanzu wanda kuma ya karya doka tara mai tsanani a kan shi. Don haka kutafi gida gobe da safe insha Allahu zan nemay shi muyi magana dashi. Mukai sallama dashi muka barshi yana fada yana cewa wasu mutane basu san ciwon kan su ba wallahi ko. Ina jatau ina yarinyar nan ina zai kaita duk yadda zan fahintar da mahaifin ta illan abinda hakan zai haifar zanyi idan ya kiya kuma nai karan shi. Hakan matan shi suka ci gaba da bashi labari akan zaman da Inba take a gidan dafin karfin ta da mama take a gidan tana mata mulki kama karya. Tun da farar Safiya ake kwasa sallama a kofan gidan mu baba ya fita ganin ko waye ? Sai yaron mai unguwa yagani nan yake fada mai ana neman shi a fada hankalin shi yai matukar tashi sosai don idan akwai abinda dan kauye yaki jini shine kiran maigari. Yashigo gida hankali a tashe yana fadin zashi gurin mai gari yanzu yaron mai unguwa yazo yace ana neman shi gidan mai gari shida mai unguwa. Mama hankali tashe take cewa to may kuma ya faru ko anyi wani abin ne kuma. Bai tsaya bata lokaci ba yafita gurin amsa kiran inda mai uguwan mu yai mashi jagora har gidan. Bayan an gaisawa ne maigari ya gabatar mai da zancen karan shi da aka kawo kan yana son yiwa yar shi kuma bazawara auren dole da Jatau. Sai da wani uban zufa ya karyowa baba yana gyara zaman shi cikin kwantar da murya yake cewa. Rankaidade ba haka na bane ba wai auren dole nake son yi mata ba ita da uwarta ne dai basu fahince ni ba. Take dattawan fada suka katse shi da cewa shin yarinya ta yarda ko bata amince ba akan auren. Sai baba ya dukar da kan shi kasa yace a gaskiya ba ra, ayinta bane nawane dana iyayyen ta hakan. Iyayyen ta uwar da ta haife ta ko wa kokai da yan uwan ka ke da wanan danyen hukuncin akan ta haka ? Shiru baba yayi don ba amsa sai lokacin maigari ya karba dacewa ko wancen auren na farko dakai mata mun so mu hukunta ku amma sai muka duba shi garbati mutumin kirki ne zai iya rike maka ita amana. Amma Jatau ko mutumin banza mutumin da bai san darajan kowa ba a garin nan sai kansa. Babu wanan zancen yarinua dai bazawara ce abarta ta yi zabinta da kan ta dan doka yanuna yanzu ko budurwa ce idan bata son aure kada ai mata dole balle bazawara da tasan ciwon kan ta ko. Fada sosai akai wa baba ya baro fada sai dai maigari ya boye mai cewa Inna ne da kan ta ta kawo karan shi yadai ce makwabtane suka zo suka fada mai wanan labarin . Shiko a matsayin shi na maigari yana da ikon karewa yaro da babba hakin su idan za, a cuta masu. Wanki nake yi kafin na shiga gidan mama Altine ina dan rarage kayan daudan mu ni da kanne na da Inna baba yadawo. Kana ganin shi kasan babu lafiya tare dashi lokacin Inna ko har ta shirya tana jiran cin mutuncin da baba zai dawo mata dashi daga gidan mai gari. Yana shigowa mama najin sallaman shi tai but tafito daga daki tana fadin malam lafiya dai ko wanan kira haka tunda sassafe haka ? Yace lokacin da yake zama saman dutsen dake tsakar ana alwala a saman shi bari ke dai Lauratu munafunci baiyi ba wallahi. Wai yanzu aka samu munafuki a cikin uguwan nan yakai karana kan auren yarinyar nan da Jatau gurin maigari. Gaban mama yai mugun faduwa tace kara malam wake da wanan aikin haka yace wayasani yadai ce daga uguwar nan namu ne akai karana gurin shi. Affan malam wa zaiyi karan ta inba ita da uwarta ba kaiwa kake tsamanin zaiyi haka waya damu da damuwan su anan balle ya kula al, amarin su. Umm, umm lauratu daga nan ne dai aka fadawa maigari amma ai mace bata ganin mai gari kai tsaye wane ita nan. Nan suka shiga dura ashar har mama na ikirarin ai ba maigari ne ya haifa mashi ya ba da zai mai iko akan gidan shi. Baba yace Lauratu na rabaki da wanan zancen kada ki dauko min wani sabon rigima kuma don ni yanzu tsoron mutane nake ji su labe ta baya suna sauran ki. Mama tace duk mai fadi yaje ya fadi amma aure ba fashi sai anyi shi tunda bashine ya haifa muna diya ba ba kuma cin shi a gidan mu. Baba ya katse ta da cewa kina da kudin biyan taran da za ai min ke nan ko da kuma dauri kan na shiga hakkin diyata bada son ran ta ba. Cikin mama ya duri ruwa sai da ta kewaya ban daki tafito ta samu baba a gurin yana fada har lokacin. Nidai ina wanki na tare da hamdalla a cikin rai na don maigari da mama Altine sun ceci rayuwana ko ba komai sun kwato ni da shiga bani. Inda nake ina buga zanin da zan shaya mama ta kalla tare da cewa tir dake Rahama kinyi hasara wallahi tunda akan yi yau akai karan mahaifin ki har gurin mai gari sukutum. In yar arziki kike kin haihu cikun malam yau kije kice wa maigari da miyau bakikin ki za ai wanan auren. Ban kula ta ba illa idon da suka sako min daga ita har baba din a lokaci daya. Ganin bazan taka masu ba ne baba yace ai in taki wanan auren nikan ba dai gida na ba wallahi don ba zan zauna da ita ba haka ina ganin bakin ciki a raina. Fat naji muryan Inna a bayan mu tana fadin a hayye nanaye wanan hukuncin yau yafi nono fari a gare mu don na dade ina jiran anan ranan dama. Idan baka zauna da ita ba a gida don tana bazawara ai zaka zauna da gandan gadan din yan mata suna maka manne da dare a bayan katanga da samari. Aure dai ne Allah ya kawo muna saukin shi cikin dadin rai Allah kuma yaiwa wanda yakai kara albarka. Ikon Allah zamani yanzu Asiya bakiji kunyan wanan maganan ba a duniya ana jinki kina guda akan yar farinki don baki da kunya ga idon ki. Kunya kunya fa kace malam ai kunya ya kaura ba yau ba ga idon Asiya don ka sani don baku so haka ba. Gida kuma in kace yarinya bata zama maka gida sai dai dani da ita mubar maka gidan ka a tare don ni ban san zaman da zanyi ba kuma ? Lalai Asiya kin haihu cikin fulani yau kin sheda min kun bar rugga da dadewa tun da idon ki ya kyakyashe haka kan yar farin ki. Mu zuba dake a gidan duk inda zaku tafi ku tafi badai gidan Audi ba wallahi ba mai min gori kan abinda na fi karfi yazo yafi karfina a gida na. Inna tace haka yafi nono fari wallahi yanzu kuwa ba sai anjima ba zamu bar maka gidan ka sai ka zauna da wa yanda kake so kajika kasha. Magana har takai ga makwabta sun shigo gidan namu suna tambayan ba, asi nan baba ya shiga zagin mu dasu yana cewa wai duk munafukaine mu dasu afice a bar mashi gidan shi. Hijjab dina na jawo daya bushe na saka nafice daga gidan inajin mama nace indai baki auren Jatau daga wanan fitan kin fice daga cikin mu ke nan. Nasa kai abina na fice ko waigen ta ban tsaya yi ba sai gidan mama Altine ina shiga take cewa dani Allah mun godema da ya kawo muna saukin al, amarin nan. Ni yanzu damuwa na shine wanan rantsuwan da mahaifanki ke yi sai kinbar maigidan shi ita kuma Inna ki ta rantse kina barin gidan itama ta bari ke nan. Nace mama nima shine ke damuna wallahi don bazan so ace saboda ni Inna ta bar dakin auren ta ba akaina. Zafin raine ke damun su dukan su daga ita har malam Audi din suna cikin bacin rai ne. Muna nan muna magana sai jin hayaniya mukayi ya kaure a kofan gidan mu da sauri mama ta yafa tafita daga gidan. Jatau ne yazo ya zauna yana cin mutunci wai kamar shi za, a tozarta a gari ai karan shi don yace yana son . Indai har ban son shi nafito na bashi kayan shi da naci don shi bai gaji hasara ba akan shi. But nafito daga gidan mama nace dashi dakata malam ga mutane sun taru wasu har a zanan gida matan aure ke lekowa ta kafan zanan gidan su don gulma. Nace tsakani na dakai ko uwa ta ka taba ba mu ko kwandalan ka a hannun mu idan dai ka taba ka fada min yanzu na biya ka abinka. Sai yadan washe baki yace ni da zaki yarda ki amince ai da babu zancen biya a tsakanin mu. Amma ace ba a bani mata kuma a ci min dukiya na ga banza shine ba zan lamunta ba gaskiya. Nace to kayi da wanda kaba kudin ka don ni ban san ka raba bani komai ba, muryan mama Lauratu naji daga ta cikin gida tana cewa tau mara kunya idan ke baki ci ba ai mu iyayyen ki munci don nai amfani dashi gida kowa yaci. Nace kin dai ci ni tundana dawo kin taba girka abincin ki kika bani a gidan nan ko kiba kanne na sai naji tayi shiru nan mutane suka saka salati yan gulma suka hau bakin su. Aka shiga zuga shi na shige cikun gida abina na barshi nan yana haukan shi shida yan kallin shi. Nasa kafa zan karasa ciki naji muryan mahaifina cikin kakausar murya yace dakata nan Rahama badai gidana ba wallahi nai maki itaka da gida na daga yau duk inda zaki kije nayafe ki. Inna dake daki tagama hada kayan ta naga tana fitowa da buhuhuwan data dura kayan ta a ciki. Nan na duka nafara rusa wani sabin kuka zuciyata tana raya min nace kawai na amince da wanan sabon kaddararen auren akaina kada uwa ra ta shiga wani hali saboda ni. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , , IDAN KIN BIYA KADA KI TURAWA WANDA BAI BIYA BA KI TUNA DA AMANA NE HAKAN A TSAKANIN MU , , , , Ina duke a gurin naji an dafa ni mama altine ce a bayana take fadin taso daina kuka haka zo mu shiga gida wanan tonon asirin haka da may yai kamane wai ? Ban kiba namike na bita sai ga yara na shigo da kayan inna ta gidan buhu har uku duk na komatsen ta ta hada ciki. Ba a jima ba tashigo gidan ran ta abace sai dai kana ganin idon ta kasan ranan ba sauki sai na Allah. Nan mama ta shiga bata hakkuri akan ta zauna amma tace indai ba zai barni gidan shi itama may zata zauna yi a gidan. Dama don ni da kanne take zama badon wani abuba don haka bazata koma ba sai idan nima ya mayar dani gidan. Nan dai abu ya yamutse daddatawan unguwa duk sun taru suna ba baba na baki amma ya kyakyshe kasa yace bai san zancen ba tunda mama da tai jagoran ci muke son tozartawa. Magana zabban kunya yadda baba ke magana kai daji kasan an fi katfin shi. Shi dai jatau anbashi hakkuri akan cewa ya bari a sulhunta maganan nan da sati daya za, a nemay shi insha Allahu. Sai dare Inna ta nufi gidan su can taiwa mutanen gidan su bayani suka ce ta zauna suma halin gidan ya ishe su haka na. Magana har gurin maigari ya koma kan fitinan gidan mu aka kira babana aka bikon Innata amma yace shi ba zai tafi ba kuma zancen Rahama ya yafe ta cikin zurian shi. Ba, a watse gurin ba sai ga Jatau yazo kan zancen kudin shi yace yai lissafi har sadakin shi dubu sittin yaba mama din. Akace wa babana to kai kaji abinda ya fadi sai da baba ya share zufan dake karyo mashi yake cewa baida wanan labarin . Amma abari yaje gida ya tambayi mai dakin shi yadda akayi haka don shi dai bai san komai ba akai. Sadaki kawai ta nuna mai kuma suna hannun ta tace zataiwa yarinya sayaya da su ne ya bar mata a gurin ta . Nan yabar fada maimakon suji haushin shi sai tausaya mashi sukayi don sun san baida tacewa a gidan shi don mama tafi karfin shi. In bashi sadaki da maza ke karba ina mace ina karba sadaki hannun mijin yarta. Washe gari da aka sake tuntuban shi kan zancen Inna sai cewa yayi suje ya sauwaka mata . Wanan labarin yai matukar tayar muna da hankali sosai dayazo muna kowa na ma baba kaico da rabuwa da Inna dayi. Don yayi hasaran macen rufin asirin shi a duniya gashi tana haifa mai diya kyawawa masu tarbiya yace ta tafi da kanne na maza biyu duk ya yafe mata don mama tace bata rika su. Sabon tashin hankali na shirya ni da mama sai gidan su Inna ta a yadda nai tsanmanin na samay ta cikin damuwa sai naga sabanin haka don dan kwana biyun da tayi har ta dan murmure sosai abinta. Nan hankalina ya dan kwanta muka ba juna magana take ce min indai naga zaman bai min gurin mama na dawo nan na zauna tare da ita a gidan su. Nace inna banda matsala gurin mama ko kadan tabkar a furin ki nake zaune a gidan ta don haka zan zauna gurin ta kusa da babana watakila idan yana gani na ya sauko ga fushin shi a samu ku shirya dashi. Tace Allah sarki yarinya idan har kina hasashen komawa na wanan gidan to kina kaunan mutuwa na ke nan. May zai mayar dani gidan Audi kuma indai ba wani ikon Allah ba kuma ai na bar gidan shi har abada insha Allahu. Banji dadin hukuncin Inna ba nashiga damuwa take cewa dani na kwantar da hankalina gurin mama in Allah yakawo min manemin da hankalina ya kwanta dashi a daura min aure na nima na huta. Cabdijam ni zawarci uwata zawarci dawani ido mutanen gari zasu kalle ni dashi ace auren uwata ya mutu akaina ko may. Cikin tashin hankalin da na wuni ke nan a gidan su innata ina lalashinta ko zata sauko in baba ya huce ya aiko bikon ta ta koma dakin ta amma fir inna tace badai ita ba kan. Haka na dawo gida da dare gidan mama ban gane komai ba a gurin Inna sai hakkuri da kwantar min da hankali da tayi. Ina shigowa gida na samu mama tana waya ga alwal mai wayan sadawa tsaye kofan gida uana jiran tagama abashi kudin shi ya tafi. Ko ban tambaya ba nasan da yarta take waya a lokacin don yadda naji suna magana na fahinci hakan. Don naji tana cewa yanzu haka ma rikicin auren ta ake a gari don uban ta ya kara jajibo mata wani tsohon wai ta aura har kai tashin hankalin daya sauwaka wa uwarta tabar gidan nasu. Banji may tace ba sai cewa tayi abani waya naji mama tana ce min karbi wayan anty ki ce daga birni ke magana dake. Nakarba muka gaisa da inta take ce min ashe abinda ya faru ke nan Ramana ? Sai na sa kuka take cewa nayi shiru na saurareta zata dawo wani sati in Allah ya yarda da tadawo zata turo a dauki mama sai mu taho tare da mama na huta da kauyen nan idan ba a ganni ba aibabu mai saka ido a kaina kuma. Nan dai tai ta bani magana har na gamsu da maganan ta mukai sallama muka awal wayan shi da kudin shi yatafi yana godiya. Mama tace min kin dawo a lalace na amsa mata tare da neman guri na zauna ina cewa ehmama. Tace ga abincin ki can dauko kici nace da ita mama na koshi kunu kawai nake son na dan sha na kwanta. Ina cire kayan jikina ne naji mama nace kinji abinda yar uwar ki ta fada ko akan ki. Nace naji mama amma ai al, amarin babane da wuya don nasan mama bazata bari ba idan taji tace nima hasashen da na keyi ke nan Allah dai ya haushe mu kan ta. Mun bar zancen don ko inna ta ban fadawa maganan ba kada hankalin ta ya tashi sai in abin ya tabbata zataji. ****** ********* ****** Bai fadawa kowa dawowan su kasar ba bayan sun gama ganin likita haka ita ma yace bai son ta bugawa kowa waya zasu dawo. Taja bakin ta tai shiru bata fada ga ranan da zasu dawo ba gidan har suka shigo b Nageria ba wanda yasan da zuwan su. Karfe goma sha biyun rana suka sauka gida kano ya daukan masu shatan taxi din airport sai gida. Alama ya nuna matan gidan basu gida a lokacin duk da weekend ne ranan hutu don motocin su baya gida. A can kan hawa step din gidan ne ya hango Nasir a zaune yayi tagumi sai Amira dake tsaye bayan dan uwan nata tana wasa tsaletsalle akan steps. Tun hango yaran ya sauke ajiyan zuciya yaran basu damu da tsayawan mota ba a haraban gidan nasu sai harkan gaban su sukeyi kawai. Muryan mahaifiyar su ne sukaji tace Sweethearts da sauri yaran suka yo kan su cikin murna da jin dadi nan ta durkusa tare da rungumay su zuwa jikin ta sai kuma ta sake kuka. Ya gama sallaman mai taxes yazo inda suke shima suka rungumay shi cikin murna yake tambayan su ina anty ta tafi yaran sukace tun safe bata tare da mu sunfita da yasmin a mota. Ciki suka shige da kayan su wanka ta fara yiwa yaran tare da canza masu kayan jikin su tabasu abinci sukaci don sunce yunwa suke ji a lokacin. Har tagama abinda takeyi bata ga shigowan shi ba gurin su haka yasa ta tsamani ko ya kwanta ne a lokacin don ya huta. Dakin shi ta nufa don taga halin da yake ciki zaune ta samay shi a saman kujera yayi tagumi da hannayen shi biyu ta hayan rike haban shi dasu. Sallaman ta yasa shi dago kai yana kallon ta yake cewa har kinyi wanka kin dai ci abinci ko ? Tace munci nida yara kaine dai naga baka zo kaci ba shine na biyo ka nagani ko ka kwanta ne ? Yace No banci ba kuma banjin ci din . Haba dai saboda my kuma heartbeat kai dake da gajiya tare da kai ka tashi kai wanka kaci wani abin ko ? Yace zan dai yi wankan amma bazan iya cin komai ba gaskiya yanzu sai zuwa anjima . Wankan yayi duk tana zaune tana jiran shi har yafito ya shirya suna dan hira jefi jefi sai dai bai sako mata zancen matan gidan ba itama batai mashi ba tafice daga dakin nashi ta koma gurin yaran ta. Har goma da rabi na dare sai lokacin ne Zulfa ta dawo gidan da yarta daka gansu kasan a gajiye suke tafe lokacin. Wutan falon dake a kashe take kokarin kunnawa a lokacin don akwai dan duhu gurin haske wutan waje ne ke shigowa kawai. Tana kunna wuta sai ganinin shi tayi zaune a falon ya harde kafafuwan shi yana kallon ta yace kashe min wuta ki wuce ciki bayan ya gama kallon wayan hannun shi don diba time. Simi simi ta shige part din ta hankalin ta a tashe don tasan bata kyauta ba bata rike mai amanan da ya barmata ba na yaran shi. Bayan yai bugun gaban ita yar uwar shice tajini yabar mata yaran shi amana suka tafi ganin likita da matan shi a Uk. Shadaya da dan kai sai ga hindu ta parker itama alokacin kamar yadda zulfa tayi hakane tana fada tana cewa don iskanci sai abi wutan ma akashe don sallon mutum ya fadi yaji ciwo ke nan. Gashi a zaune fuska a daure yasa ta cewa dear saukan yaushe babu ko waya a shirya ma dawowan ka. Ido kawai ya tsura mata tare da kallon agogon bangon dake manne a falon . Itama agigon ta kalla cikin firgici yace miko min baby nan ki koma inda kika fito. Tace kamar yaya nakoma inda nafito kuma gida fa na fito yace will you do as i said ? Babu sauki a fuskan shi ta bude baki zata ce dear kayi hakk, , , , ya dakatar da ita cikin daga hannu yace please tun raina bai baci ba nai maki abinda baki zata ba ki aje min ya ta kibar gidan ? Ganin ba wasa yasa tai mai yadda yace yarinyar dake barci a kafadan shi ta aje mai a saman kujera ta dan juta sai kuma taja ta tsaya ya nuna mata hanya da hannu dole tasa kai tafice gidan. Gidan su ta nufa shi kuma yasa maigadin shi ya rufe mai get kada ya fara ya budewa koma waye yazo da daren nan. Yace angama ranka ya dade kamar yadda kace haka za, ayi ban bude gidan nan sai gobe da safe. Yana shiga dakin Hindatu ya nufa ya samu tana tsaye tagama saka rigan barcin ta a jiki tana shirin kwantawa. Daga kofa ya tsaya tana ganin shi ta mayar da hankalinta gare shi yake cewa da ita abinda yasa ke bazance kibar gidan nan yanzu ba kamar yadda naiwa Hindu shine koda kin bar nan nasan gidan Daddy zaki nufa da nan da gidan daddy duk daya ne a gare ki don haka gobe karfe takwas na safe ki tabbatar da kin bar gidan nan baki alaikum. Hankalin ta ya tashi tana shirin mashi magana ya fice dakin nata ran shi a bace ya koma part din shi ya kwanta. Haka suka kwana rayukan su a bace ranan kowa da abinda yake ji a ranshi sai Sa, ade ne tai barci a tsakayin yaran ta hankali kwance cikin jin dadi. Kafin ya kwanta sai da ya shigo dakin nasu ya samu sunyi barci ga wuta a kunne basu kashe ba ya kashe masu yafice daga dakin . Washe gari haka ta tashi ta gyara yaran tare da abin karyan wasu duk lokacin bata san matan gidan basu gidan ba ma ita. A zaton ta ko wace na dakin ta kwance ne don halin su ne hakan ta koma ta kwanta don agajiye take. Hayaniyan da take ji yai yawa a falo yasa ta fitowa dakin ta sai gani sarakan ta tayi a zaune suna magana sai dai babu maigidan cikin su ga Hindu a gefe zaune cikin damuwa. Hajiya ce ta kalle ta a lala ce tace a, a matar iko matar mulki matar so anga daman fitowa ke nan. Hajiya ban ji shigowan ku bane gidan ina barci yanzu naji magana nafito nagani. Bashi na tambaye ki ba ai duk abinda kukayi don kanku ke dashi in cin amana abin yine sai ku matsa kuyi tayi ni dai na fada maki in ma wani abin kukai mashi don ku rabani dashi Allah yafi ku ke da iyayyen ki. Murmushi tayi tare da fadin ayi hakkuri hajiya kamar kullun maganan ta ke nan tsakanin ta da uwar mijin nata. Shi mijin naki ance ya bar garin ko da yake yasan abinda ya shuka na rashin gaskiya. Tace ya tafi nw ko ? Hajiya tace rufe min baki mara gaskiya kawai ai bakin ku daya dashi. Bayan kun tafi shakatawan ku kun bar yarinya da dawainiyar yara kuma zaku dawo ku saka mata da sheri. Ai duk inda yaje zai dawo ne ya samay ni gidan ba inda zai gudu min ko ? Ke kuma koma ki zauna dakinki har ya dawo muji hujjan shi na maki wanan danyen hukuncin haka. Don yana dan wullakanci yabi wayoyin shi ya kashe don kada a samay shi balle ai mashi magana ko ? Hindatu tace yanzu maigadi da zamu shigo ya bani wanan takardan inji shi yace abani. Hajiya da yar uwanta gurin hada baki suke cewa takardan may ? Tace a, a cewa yayi kada na fara na zauna mai a gida har sai ya dawo in ba haka ba a bakin aure na. Salati suka saka hajiya tace lalai yaron nan ya kai dan rainin wayo na gaske yar uwarta tace yaya tunda ya furta haka kada ta zauna tazo mu koma tun abu bai lalace ba. Hajiya tace babu inda zata zama zatayi inda ya dawo in ya isa ya sake ta mu gani. Hajiya ai wanan maganan dayayi a matsayin sakin yake in har ta zauna maigida aure ya kare a tsakanin su ke nan. Inda Sa, ade take ta kalla tana cewa tsohuwar banza kawai kin samu yara kina masu wayo yadda kike so. Shiyasa tun farko ban so wanan bakin auren naku ba don ke sam ba sa, an auren shi bane. Fin karfi na kawai akayi amma wanan da nake gani da wuya in bata girmi dogon sarki ba Hajiya mu tafi tunda baya gari har ya dawo sai asan abinyi don yanzu bata lokacin muke a hanka don ba komai zamu gane gurin wanan ba in ma mun tsaya. Haka suka fita suka bar gidan suna sababi inda suke shiga ba nan suke fita ba akan zagin Saade. Suna fita takai zaune tare da dafe cikin ta da taji yana mata motsi take cewa haba heartbeat yaya zakai min haka ashe yasan abinda ya shuka ke nan yace na shirya yaran su tafi makaranta idan sun dawo kuma anan zasu zauna tare dani. kanta girgiza kanta cikin takaici may yasa ko yaushe yake abinda zai ja min zagi ga mahaifiyan shi ne bayan yasan irin zaman da nake gidan da hajiya. Maigadi ne ya shigo ya katse mata tunanen ta lamban waya ya bata yace inji maigidan wai yabata idan ta tashi barci. Gurin maigadi take ji wai iyayyen hindatu ma sunzo neman shi ya bata takardan da yace a bata kamar yadda yaba Zulfa na ta. Layin shi ta kira ya dauka ba bata lokaci zai fara magana ta tare shi tana cewa heartbeat may yasa ko yaushe kake jawo min abin zagi ga yan uwanka da iyayyen matan ka ne ? Yace ke ki saurare ni kada ki fara kiba kowa nomban wayan nan idan bani nace ba tace kai kana ina ne yanzu ? Yace yanzu na sauka Abuja zan wuce office ke nan ki kula da shan maganin ki a kai kafin na dawo don da na dawo zamu tare sabon gidan mu da yardan Allah. Allah ya kai mu tace yace kada ki manta da zancen zuwan mama na kauye da kikace zata zo ta zauna dake sai ki tura Hamza driver idan yakai yara gobe yaje yazo da ita. Sukai sallama ya barta da mamaki don yaki bari ko suyi wani magana sa ya shafi zancen matan shi da ya tura gidajen su. Suna gama wayan ta kira Awal mai waya ya sada ta da mama din lokacin ina zaune na saka lalle a kafana naji sallaman shi kofan mu. Ya kawo wa mama waya sukai magana kan gobe driver zaizo ya dauke su don haka su shirya da wuri kafin yazo. Mama tace tun ranan da mukai magana dake mu a shirye muke take cewa kiba mahaifin Rahama dubu ashirin hakama mahaifiyar ta dubu ashiri hamza driver zaizo dasu insha Allahu. Suna gama wayan awal ya karbi kudin shi ya tafi mama ke cewa dani kumshinki yazo a sa, a gobe ne tafiyan mu in Allah ya yarda. Zanje na samu mahaifinki muyu magana dashi inji ta bakin shi akan tafiyan ki in ya yarda sai mu tafi idan kuma yaki yarda sai ki koma can wajen Innan ki har lokacin da na dawo. Tunda ta kafe bazata dawo gidan ku ba har abada tabar gidan ke nan , Allah dai yai mata sauyi da mafi alherin sa. A sanyaye na amsa da amin badon naso don dai kawai addua ce ta alheri tai mata. Da yamma da baba ya dawo kafin ya shiga gida cikin hikima mama Altine ta samay shi a waje da zancen don zancen bai yuyuwa a cikin gida don mama lauratu. Bayan sun gaisa sama sama dashi don haushi mama yake ji da ta barni gidan ta duk da gidan dan uwan shi ne amma yana jin takaicin haka don yaso tabarni na bi uwata can mukarata gidan su. Mama acikin hikima takw mai magana tace to Audi dama zancen wanan yar ne Rahama dake gurina. Don gobe zan tafi birni ganin diyata kuma zan kwana biyu shine nake son zuwa da ita don kaga babu kowa a gida idan ka yarda da hakan. Yace Altine na fada maki ba yau ba ki rabani da zancen yarinyar nan a rayuwana na riga na gama magana akan Rahama. Ba kano ba duk inda zata ita dade bata tafi ba babu ruwana a cikin harkan ta na fada maki ko. To shike nan tunda haka kace mu Allah ya bamu ikon rike maka ita amana kamar yadda ka bar muna ita din. Yace indai wanan irin tsiyane ai kice nace maki watarana akan ta mama tace ba amin ba tunda mun gama maganan ta ko dakai. Ta banye kudi a haban zanin ta tana mika mai kallon kudin yake a cikin mamaki yake cewa na maye wanan din tace dama yar tawa ce tace a baka kayi hakkuri dashi ba yawa. Sai da ya dan juya yana kallon kofan shiga gidan shi baiga kowa ba yai sauri ya karba yana fadin an gode ya shige gida har yai dan nisa mama ta juya zata shiga gida taji yace ki dai ja mata kunne ta kula da rayuwan ta a can Allah ya tsare tace amin nagode da karamancin da kai min. Da tashigo ne take fada min yadda sukayi da baba nake cewa Allah sarki baba abin nashi akwai daure kai a ciki wallahi yana son iyalin shi amma tace ta raba shi dasu da karfi da yaji. Mama tace ba abinda ya bani dariya sai waigen da yakeyi kada angan shi yana karban kudi yasan idan ta gani yau basu kwana aljihun shi. Da dare muka tafi sallaman inna ta nan mama tai mata bayanin komai mama tace wa inna ta ina rokon ki Asiya ki bari yadda mahaifinta ya bari ta tafi ke ma kibarta Allah kuma yasa hakan shine Alheri ga rayuwan ta. Don ni zaman ta gurin Saade zaifiye min zamata a kauyen nan ko bazan ta kara sanin duniya. Inna tace ni na isa in hanaki yadda kike so da yarinya tsakanin mu dake sai fatan alheri da neman gamawa da duniya lafiya. Allah yasa yarinyar nan gurin ta na karatun da take son yi ya cika ta wanan hanya. Mama tace zata barni mu dan gana na kwana a gurin ta don sai zuwa gobe da rana zamu tafi in Allah ya yarda taima mama godiya takawo sakin Inna rabata tana godiya. Bayan tafiyan mama inna sai faman nasiha take min na kama kaina na zama ya ta gari abin alfahari ga kowa nan gaba don wata rana sai labari. Naji matukar dadin nasihan Innata ga albarkan da take ta saka min yafi a kirga Kwana nayi ina tunanen yaya rayuwana zai kasance a gurin anty Saade ko baba zai yarda ya barni nakai ga samun cikan burina a rayuwa. Da safe na shirya zan tafi gida gurin mama inna takawo adduoi tabani tace na fake na kula da yin su ko yaushe don suna da falala da faida nai godiya naiwa kakannina sallama nafice gidan tare da jaddawa Innata zancen karatun kanne na kada a bari ya dakata masu. Shiko baba sai da zai bar gida ne washe gari yake fadawa mama cewa kinji wai Altine zata birni da yarinyar nan. Wani uban ashar ta lailayo ta watsa ma mama Altine tana cewa munafuka makira dama ta fahinci duk itace mai hura muna kunne akan halin da muka tsira yanzu ni da uwata . Da sauri tace kai may kace mata kan magan tafiyan da ita ? Yace may zance da ita banda Allah yakai lafiya idan na barta nan din wani abu zatai min ban da karin bakin cikin da zata jefani ciki kawai. Jin haka tace malam kakoyi tunane kafin ka bada bakin tafiya da ita birni tana nan ma bamu inmata ba balle rashiga birni idon ta ya bude ai watarana ma sai tace bakaine ubanta ba don raini. Don haka wanan magana ajeye shi babu zancen tafiya gare ta ba inda zata tafi tana nan cikin mu dadi da wuya haka zata zauna garin nan. Yace yanzu kan sai anjima in na dawo nai mata bayani don na makara kada mota ya wuce ni na rasa. Abinda ita dashi basu sani ba yaune tafiyan mu zuwa burni sai dai baba ya dawo ya samu labarin tafiyan mu kawai gurin jama, an unguwa. Komai na amfani mama ta dauka takai makwabtan ta boyo kayana dake gidan ta tasa an kwashe ankaiwa inna ta gurin su. Haka yasa na fahinci tafiyan namu mai dadewa ne don ban taba ganin haka ba wani bako ta dauko da matarshi da suke yawon neman gida tace ya zauna a dayan dakin dake gidan da iyalin shi. Sha biyu da rabi na Rana hamza driver na kofan gidan mama ba bata lokaci muka kama hanya. Da zamu shiga mota yara sun fadawa mama lauratu sunga motan birni kofan gidan mama Altine sai gata tafito daidai mun fito zamu shiga mota. Nan ta buga kasa tana fafin ba inda mama zata dani don ubana ya hana tafiya dani mama tace da ita kin makara don ni ubanta ya riga ya sallama min ita kamar yadda kika bukaci yai masu ita da uwarta to tun jiya mun gama magana dashi ko. Nan taje har da tare gaban mota ta baje hannayen ta wai sai taga yadda za, a tafi dani birni. Tana jin hamza driver yasa giyan mota tsoro ya kamata ta ruga da gudu gefe tana Allah ya isa tsakanina dake mai kuli kuli. ****** ********* ****** Mota na tashi nabi kauyen mu da kallo hawaye na zubo min a idona una tuna rabuwana da mahaifiyata da yan uwan haihuwana. Biyu da rabi shaf muna cikin garin Kano ta Dabo jalla babban hausa yaro koda may kazo anfi ka . Sai bin garin nake da kallon mamakin ikon Allah gine gine kamar ba mutane ne sukayi shi ba da hannuwan su. Abin hawa tun ina girgawa har bakina da zuciyana suka daina aiki sai binsu da kallo kawai nakeyi. Mutacan mu wuce nan driver na ta aikin tukin shi sai ga mu wani katon unguwa mai gine ginen zamani kala kala. Muryan mama ce ke cewa dani ikon Allah Rahama yau gaki birni a kanon dabo tunbin giwa yaro ko da may kazo anfika. Nace mama harda maita da sata sunfi kowa tace yarinyar sawasa kin ganki mayan ka. Nace aiko har na koma gida bazan taba fitowa waje ba balle a sace ni tace ce Allah kin tuba fita kan ai sai randa babu rai kuma. Wani irin katon gida ne naga driver ya karya kwana ya shiga damu yai horn maigadi ya wagale kofan muka shige. Daidai lokacin ne na sauke wani irin ajiyan zuciya mai karfi mama tace barka da arziki yar nan Allah ya rabaki da rigiman uwarki lauratu da masifan jatau kin huta. Mun fito da yan kayan mu dake cikin ghana most go don sai dana cika jakata da tufafina masu kyau tsufin nabarwa Inna ta su a gida. Anty tana zaune a mamakeken falon su kafata harde a cikin daya ga remote din tv rike a hannun ta tana jin sallama mu ta mayar da hankalinta gare mu. Tana fadin lale marhabin da Ramana yau gani ga Ramana a gidana Allah nagode maka daka nuna min wanan ranan gare ni. Da gudu na naje na rugumay ta naji tace waisshi Allah yi a hankali anty taki rubabace na dago kai nace wayo sannu anty ta dafa min kai tana cewa Sannu Ramana sannun ku da zuwa. Dukawa nayi da kaina sai hawaye shar tace da sauri subbahanallahi ko baki son zuwa ne aka rabo ki da gida ? Sai lokacin ne ta dago kai tana cewa sannu mama mama take cewa ai dole na tsaya har ku gama shirmayn ku ko. Wani bata son zuwa shirmay ta daine wai taji dadin ganin ki ke nan take wanan kukan haka. Nan muka zauna a falo tare da ita tace bari ta dauko muna abinsha kafin abinci ya sauka. Mama tace ina yan aikin naki kuma keda baki jin dadi tace cikin murmushi wai mama yaushe rabo ai duk an watsa su saboda fitinan matan gidan nan. Gulma yai yawa ga fitina yaki ci yaki karewa dole aka sallami kowa daga mu sai halin mu yanzu a gidan. Mama tace naji gidan shiru ina sauran yan uwan zaman ki da maigidan kuma murmushi tayi ta mike da kyat zuwa kitchen sai gata da kayan sanyi da sauri na mike naje na karbo mata kayan na kawo gaban mama na dire su. Sanyi lemon ya hanani sha Anty ta kalle ni tace kisha mana Rama nace sanyi anty sai ya huce zan sha suka sa min dariya ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , , IDAN KIN BIYA KI RIKE AMANA DON AMANA NAUYI GARE SHI YAR UWA DON ALLAH MU KULA PLEASE, , , Zan iya cewa tun dawowan matan gidan har zuwa yau kwana biyu ke nan da cewa sun dawo gidan amma banji duriyan su ba har wanan lokacin Ni dai a bangaren mu zan iya yiwa anty na aikin komai da duk wani abinda yaka mata na kula dashi. Sauran matan gidan sai mamaki sukeyi yadda suka samu yaran su ga kuma gidan a gyare tsab kamar yadda da farkon shigowan su gida . Kafin zaman gidan nasu ya canza kala, don ko wace daga cikin su tana ji da kanta bata iya gyara gida in general sai dai ta gyara daidai part din ta kawai ba ruwan su da sauran part din gidan haka zai dauki lokaci a cikin datti. A da suna da mai aiki har mutum biyu da tsohuwa da yar matashiyar budurwa sai ya kasance gulma yai yawa kowan su na kokarin jaye mai aiki ta koma katkashin shi haka ya kawo fitina mai karfi har ya kai maigidan ya sallami duk yan aikin ya ce. Yau da safe anty ne ta shigo dakin mu ina zaune ina gyara kayan yara ina ganin ta na gyara zamana da kyau tare da gaishe ta don nasan ba kasafai take shigowa dakin ba, dakin da muke ni da yaran nata. Bayan na gama gayar da ita ne ta samu guri a bakin gadon Nasir ta zauna tana cewa na fa gane kunfi dasawa da Nasir gidan nan Rama. Murmushi nayi mata kawai nace anty ai shi na daban ne a gurina yana bukatan a ja shi a jiki sosai. Baki ta tabe tana cewa wanan ai halinsa sai shi don baida yadda sam wallahi ina mamaki ma yadda ya amince dake haka da sauri. Tace cikin dan sake, tsaki tare da cewa dama nazo ne naga idan baki aiki ki shirya ki rakani wani gurin don fitan ma dole ne zanyi shi, su Amira ya damay ni na je ni tun jiya yake damuna na akan maganan. Ban bata lokaci ba gurin shiryawa don anty dama da shirinta tazo dakin namu don mu tafi a lokacin. Mun nufo kofan fita daga gidan na hango wata mace shigowa daga ciki kai tsaye yadda nagan ta tafe yasa na fahinci watace daga gidan don yadda take tafe a gadarance. A karo na farko da na fara saka daya daga cikin matan gidan a idona ke nan tun bayan dawowan su gidan daga yajin da suka sha. Wace nagani doguwa ce yar fara ba can ba tana shigowa gidan sabale da gyalen ta a kafadan ta tana kada yan makullaiyan motar ta a hannnun ta. Waya take a cikin sakin fuska amma tana hango mu take annurin fuskan ta ya gushe mata ta hade rai a lokaci guda. Tana ganin mu ta wani bata fuska tare da kawar da kai gefe daya ta nufo mu gadan gadan babu alaman kauce muna gare ta. Hakan yasa naga anty ta dan kauce gefe daya gudun kada su hade su buge junan su. Kai tsaye kamar ban ma san da ita a tafe ba saida kafada na da nata ya gogi juna ko gezau ban yi ba itace ma naga ta dan yi kamar zata tangada don buguwan da junan da mukayi. Kam kaza tace tare da juyawa tana fadin, ke wata irin bagidajiyar ina ne wai kina tafe kamar dabba dake baki iya kaucewa mutane ? Kamar ba dani take magana ba don ban juya inda take tsaye ba a lokacin. Don idan na tsaya zan gwada mata ni yar tallah ce a kauye a baya don bani shayin uban kowa inda ta ganni. Kada na tsaya bata amsa na batawa anty farin cikin ta yasa na dake na wuce ban bata amsa ba don da taji amsa daga bakina sosai. Motan anty muka shiga batare da tace dani komai ba din ban ma yi zaton taga abinda ya faru a tsakani na da hindatu kishiyar ta din ba a lokacin. Tafiya mu kadan yi mai dan nisa kadan daga uguwar su sai gamu a wani irin katon gida mai wani irin wawakeken get mai girma. Horn tayi har sau biyu sai ga wani mutum daga ciki ya bude kofan ta danna kan motar muka shiga daga ciki. Abinda idona ya gane min ban san lokacin dana sauke ajiyan zuciya ba har sai da anty ta dan juyo inda nake tana murmushi Wani guri na hango an tara motoci har kusan hudu sai sheki suke suna walkiya kamar an tara dawakai kosassu a gurin. Ta juyo inda nake tace dani bisimillah ko Ramana fito mu shiga daga ciki mu duba ban tsaya ba kamar yadda ta fita nima haka na fita daga motan. Ko kasan gidan ma abin kallo ne a lokacin don ko ina yaji grass carpet a gurin kore shar da shi gwanin ban sha,awa. Direct wani kofa muka nufa sai gamu a wani katon fili da ya raba sassan gidan kashi biyu ga wani katon part a tsakiya dake nuni hawan bene ne gurin. A hankali muke tafe muka fara shiga side din dake left hand din gidan part biyu ne manya kowani dauke da bed room uku uku a cikin shi mayan an saka gadaje da kujeru baban daban sai muka fito zuwa sashen dayan sai naga ai kamar kayan shi yafi haduwa har dakunan gurin kamar sun dan fi girma sosai part din gaskiya ya hadu. Muka dawo wani katon falo da yasha gyara sosai a gidan da gani shine main falo na gidan na kowa da kowa banda wanda ke cikin ko wani part. Anan muka zauna don ta huta saboda ta gaji sosai a lokacin sai da ta dan huta take cewa dani Ramana yanzu zabi ya saura akan mu cikin gidajen nan biyu da muka shiga wani kike gani zamu zaba a matsayin namu a ciki. Cikin mamaki nake cewa Anty wanab ne sabon gidan naku da zaku tare a cikin sa ?. Cikin sakin fuska take cewa dani shine Rama baban su Amira ne ya matsa min sai nazo na zaba kuma kin san may? Wai fa yau din nan yake so mu tare a gidan nan don haka wani kike gani zamu dauka a matsayin namu shiyan ni daku da yara. Don yace su biyu a dayan part din zasu zauna kowace dana ta ai kin ga ba mai ganin wani a tsakani yanzu kowa yaci gashin kan shi kawai ne. Ta kara tambayana na rasa ma wani zan zaba daga cikine wai farat nake cewa da ita ni sai nake ganin kamar wanan na ka shen da muka shiga yafi haduwa ai anty don haka shine zamu zaba. Tace ashe tunanen mu yazo daya dake Rama don nima ya burgeni gaskiya sosai gashi da girma ga shi komai nashi purple ne da milk colour . Bamu jima ba take cewa mu koma mu fara shiri don haka muka juya zuwa gida . Kamar yadda mijin ya umurce ta tayi hakan tayi don bamu kwashi wasu kaya ba masu yawa muka koma gidan ranan laraba da dare don girman gidan duk a daki daya muka kwana gaba dayan mun cikin shiyan da ta zaba a matsayin nata a gidan. ****** ************ ****** Sai washe gari sauran mutanen gidan suka tare don ina ganin basu san da zuwan mu ba a daren jiya sai washe gari ne suka ga ana kwasan kayan anty ga wa yanda taba ma kyau cikin yan uwanta marasa karfi. Suke tambayan mijin yake cewa dasu ai ya fada masu cewa kowa ya koma can tun two days ago. Suna zuwa suka saka balai wai basu yarda da part din da anty ta zaba ba wai sun zabe shi a matsayin nasu tun farko da suka gane shi. Mijin nasu ya nuna masu basu isa ba don basu zasu fara zaben guri ba sai anty dake matsayin babba a gare su a gidan. Hakan bai masu ba sai da zulfa ta daga waya takira hajiyan shi tana kuka take sheda mata wai ana yawan take masu gakkin su a gidan nan don ko yanzu da suka dawo sabon gidan su gurin da ta zaba da farko nan Saade ta shige da yaranta. Ran hajiya mama mahaifiyar maigidan nasu yai matukar baci ta shiga fada tana neman layin dan nata don taji ba, a sin maganan daga bakin shi. Can ta lalabo lamban shi da kyat don balain da take kan yi yana dauka yaji ta haushi da masifa tana fadin wai mai sunan Alhaji may kake son mayar da kankane wai. Mace daya figaga da ita ta hanaka samun sukuni da iyalen ka ta hana ka shakat don son kai irin nata. Yanzu har wanan gidan ma da kuka koma sai da tai maka iko irin nata data saba don ita bakin hali irin nasa na gado da suka saba. Yadda take takaman ita matarka ce haka su ma suke a matsayin matan ka ba wai finsu tayi ba Shi bai kashe wayan ba shi kuma bai bata amsaba don ya san koma ya mata bayani ba sauraren shi zata yi ba. Suka kashe wayan ya ci gaba da harkokin shi don a lokacin baya gida yana gidan gonan shi. Washe gari muna part din mu duk muna falon anty din bamu faye zama a dayan part din da tace shine zamu zauna ni dayaran ba amma kayan mu yana ciki sai dai mu dan shiga mu fito mun fi zama a gurin ta. Babu sallama sai ganin an fado muna kawai mukayi a shiya anty da ke kwance ga cikin ta da yai girma ya tana shirin shiga watan ta na haihuwa tai zubur ta mike tana yan kamay kamay tare da fadin hajiya sannu da zuwa. Dakata ke ta bata amsa ba gaisuwan ki nazo nema ba zuwa nayi don inji dalilin ki na saurin daukan wanan part dina matsayin naki? Shiko ke kina ganin cewa su sauran ba mata bane sai ke kadai ce macen auren a gidan nan don kina takama kinfi har mijin naku shekaru zaki iya mai wayo yadda kika saba. Anty dai tana duke yayin da mama Altine dake ballan goro ta dakata tana sauraren hajiyan. Idan ba kaddara ba ke har yaushe Alhaji karami zai auro sa, auroki a matsayin matar shi ya aje a gida haka tsofai tsofai da ke. Baba inda yaran nan zasu tafi suna gidan nan daram kamar yadda baki so shigowan su gidan ba sai ki ta zama ke kadai a dole kin samu gida kin mike kafa daga ke sai diyan ki a gida. Ni dai ban san yaya akayi ba ko maganan matar ne yai min yawa a zuciya ta yadda take faman aibanta min Anty na. Sai ji sukayi nace kai amma dai wasu girma kawai sukafi mutum ba wayo ba. Duk babban da bai gyara tsakanin maurata ba baikamata kuma ya bata ba har mutum ya zauna ya na aibanta macen aure wai dama yin haka shine wayewa ? Ni na dauka ai duk abinda dan ka ya dauko yazama naka tundai ga uwaye mata . Abin danka naka ne ba bambanci tsakanin matan shi sai dai kai babba ka hada hankalin iyalin danka ka nuna ma babba matsayin shi haka shima karami yasan matsayin shi shine girma. A ko wani gida wanda aka san tarbiya da mutunci ansan uwargida itace kan gida dole itace mai fara zaban abu kafin na baya su zaba. Kamata yayi uwa ta godewa Allah idan ya bata dan da yasan shimfida adalci a tsakanin iyalin shi bai kauce wa addini. Amma wanan magana ba girman ki bane da darahan ki ba hajiya ace kina zuwa gurin matan dan ki kina raba daya biyu a tsakanin su don suna karkashin ki kawai kema fa uwa ce hajiya tunda nasan kina da diys don haka, , Tau ke kuma fa karamar mara kunya daga ina haka ke kuma wacece a gidan nan da dan tsugunin ki zaki tsaya ki dubi fuska na kina fada min magana ba kunya ba tsoron Allah. Nace hajiya ba haka bane ni naga ke uwace a gurin mu ba girman ki bane da mutuncin ki yadda kike hajiya ace aji wanan irin kalamin na aibanta matar dan ki daga bakin ki. Mutuncinki da kimarki yafi karfin aji haka a gare ki koda ace tsohuwar ce yake aure ai bai dace ba ke aji daga bakin ki kina aibanta abinda yake mallakan danki ne kuma abinda yake so. Cabdi Sa,ade a ina kiia debo wanan fitsararar yarinyar haka mara mutunci mara kunya da ita ? Wai ma waya baki ikon aje ta a cikin gidan nan ne har take ganin ta samu guri da kamar wanan yar zata kalli tsaban idona tana fada min maganan da wani mahuluki bai taba tsayawa a gabana ya fadi ba. Anty saade na fadin hajiya yi hakkuri yarinyar ce shiyasa , Hajiya sannu da zuwa mukaji ance daga bayan mu ashe maigidan ne tunda nake magana da hajiya yana tsaye a kofan daki. Ya karaso yana fadin hajiya kaunan Saade ne tazo kuma kinga abinda nakewa gudu ke nan a koda yaushe idan kina fadin magana na aibanta Sa,ade kada ya fada a kunnen yan uwan ta. Gashi kuma yau karamar yarinya tana mayar maki da martanin maganan ki na kullun akan saaden. Ke nan ran ka bai baci ba ga abinda tai min ba ke nan a gaban ka yace hajiya ai wanan maganan ku ne na mata ni bai shafe ni ba. Yanzu ma nazo fitane naga motan ki a waje shine yasa nasan kina gidan na biyo ki nan don nasan kina nanan din. Tace eh ina nan din don nazo ne kan zancen shiyan da ta mamaye na yan uwan ta. Mu hadu a falo a hajiya nan akwai mutane a gurin sai muyi magana a tsanake. Ba taki ba suka kwasa zuwa falo gaba dayan su har anty sa,ade din tabi bayan su don jin may za, a fada a falon. Zaune suke kallo daya zakai masu ka fahinci kowan su a falon a cike yake a lokacin. Cikin fushi hajiyan ta ke magana tana cewa ka taramu ka barmu a zaune ko kuma wani sabon wulkancin ne yin hakan. A fusace ya ke don daya dago fuskan shi gaba dayan su sai da hankalin su ya tashi don ganin yanayinsa. Sai da yakai kamar minti uku kamar yana nazarin wani abu can yace ina son na fara da tambaya anan ? Don Allah ko a cikin ku gurin nan akwai wanda yasan yadda na samu aiki har na kai ga tara abinda ke gare ni a yanzu har nai wanan ginan da muka shigo. Shiru sukayi gaba dayan su ba wanda yai magana sai hajiya ce can tai karfin halin cewa . Don bamu san yadda ka samu ba shine zai hana mu yin magana idan kayi rashin adalci ko may ? Yace hajiya may ye rashin adalci anan don na bawa uwargidana zabi akan girman da Allah ya bata a gidana. Nakuma bata zabi amatsayin ta wacce ta taimaka ma rayuwana tun ban san ko mai ba na hanyan neman kudi har yakai ta fara lurar dani yadda zan zamo mai dogaro da kaina har zuwa wanan lokacin. A fusace hajiyan shi, take cewa kace ma da kudin ta ka zama haka a yau. A gadarance yace kusan hakane gaskiya don kudin ta da nawa ne muka hada nasai form na sai sauran abubuwan da ya sace nayi kafin na samu na kai ga appointment dina. A lokacin hajiya ke kin sani Abba bai yarda da zancen aikin da nake nema ba yafi da son na kama kasuwanci kawai. Ashe don haka hajiya yau komay nai ma sa,adatu kaman ma ban mata komai bane daga cikin gudun mawan da tai min a rayuwana. Don haka yau hajiya a gaban ki ina son kowacen su ta sani cewa Sa, ade da suke gani ba abin da zanyi wasa ko sakaci da ita bane arayuwa na. Don haka wace zata iya zama dani da mata ta zauna don a tare kuka gan mu da ita auren mu va zai sa na watsar da mata na mai tausayina mai sona da kauna na wace ta san zafina da tausayawa rayuwana. Hajiya ta cabe da cewa ai ka karasa kace wace ta haife ka ta san zafin cikin ka da goyon ka. Aa hajiya bata kai can ba amma dai ina son su fahinci darajan ta a guri na yafi karfin yadda suke tsanmani a yanzu don naga suna son su wuce limite din su agidan nan. Duk wace bata iya zama a gurin da na ajeta hanya a bude yake gareta zata iya komawa inda tafito don babu dole a gareta. Matata dai ce ba zan taba wullakanta taba akan ko wacen su insha Allahu. Kuma ina son ku sani hajiya da kuke kai karana kona matana a gare ta ga hajiya ga ku duk wace ta kara kai karan dayan mu gurin hajiya a gidan nan kan al,amarin da ya shafe ni ko Sa,ade. Mace ta sani kuma ta rike a kanta zan bata mamaki kwarai ga irin matakin da zan dauka akan ko wacece a gidan. Haka ya isa please ban san may kuke so dani ba kowacen ku nan tasan zamana da matana tun farko haka kuma kuka amince da zaku iya zama damu a hakan da muke ban auro ku don na wulakanta matana ba don ina son abina kowan ku kuma ta sab da hakan ta amice don haka yanzu kune kma kuke son bi ta hanyan mahaifiyana don ku cuta mata kuma cutawa mahaifiya don Alhakin yarinyar mutane ya haukan magaifiyana. Saboda may zakuyi muna wana mugun sakkaiyan hakan kuna amfani da mahaifa na don ganin an cutatawa yar mutane saboda hakkurin ta. Kada kuyi tsanmani ban san abubuwan dake gudana a gidan nan ba na bar kowa tana abinda ta ga dama a gidana. Akwai watarana yaba tafe ranan da zan dauki mataki daidai da laifin kowan ku amma dai ina mai kara ja maku kune ga abu biyu zuwa uku. Na farko shine mai son zaman lafiya ya bar hadani da matata da iyayye na fada. Sai kuma ina gargadin ku da ku daina shiga harkan Sa,ade ku barta taji da lalurar da Allah ya jarrabe ta da shi. Don haka zance shiya da kuke cewa ta zaba ta bar maku wanda bakwa so zaku iya komawa can dakunan ku da kuka fito don yau idan Sa, ade tace min bata bukatan zama da kowacen ku a cikin gidan nan ya ya tabbata hakan a gare ni. Aiko na hajiyan shi ta amshe da cewa tau issahe akan wanan figagan matar naka mutu kwakwai rai kwakwai kake wanan magana. May yarinyar nan tai maka hakane har idon ka da zuciyar ka ya rufe yau a gabana kake wanan magana. Lalai Sa,adatu kin gwada min ki kai kin kai matakin daba naki ba a gidan nan tunda har yau Alhaji karami ya rufe idon shi a gabana yake wanan magana haka. Hajiya ya kamata ki sani yau idan haka ya kasance a gidajen auren yan uwan mu mata ba zaki ji dadi haka ba, muma ba zamuji dadi ba don may hajiya ba zaki daina wanan halin ba ko don kwanciyan hankalin diyan ki mata dake gidan mazajen su suna aure. Au to lalai abin har yakai zakaiwa yan uwanka mata baki akan matar son ka duk ka haukace min yau don na taba ko. Ai kafin kayi naka, naga wata fitsararar yarinyar da matar ka ta dauko ta aje a gidan don isa da mallaka ra fara nuna min fitsara don samun wuri. Ta juya gurin antyna tana cewa ban son ganin wanan yarinyar a gidan nan ta gagawan barin gidan nan tun ban dauki mataki ba a kan ta ? Hajiya wanan yarinyar yar uwar Saade ce nina bada bakin ta dauko ta nan don ta samu mai taimaka mata ga halin da take ciki tana bukatan taimako ? Kafin suci gaba da magana sai ga maigidan ta ya kirata yana tambayan ta tana inane wai.? Ta kasa bashi amsa don tasan ya hanata zuwa gidan dan nata saboda wanan halin da take zuwa tayi. Kwata kwata bata kaunan zaman Sa,ade da danta don acewan ta kullun wai ta girmay wa mijin nata shi yasa take masu wayo. Ta manta cewa itama tana da diya mata dake aure a wanu gidan har su uku bata tunanen cewa abinda take wa yar mutane zai iya faruwa akan diyan ta. Mata bamu tunanen cewa mu uwaye ne masu diya duk abinda ka shuka shine kake girma a rayuwan ka. Muryan mijin nata ne ke fada mata cewa tazo gida ga Aisha, yar su ta dawo gida da matsala. Wanan maganan da taji ne yasa ta dafe kirjin ta tana cewa zata tafi amma zata dawo don bata karasa maganan da ya kawo ta ba. ****** ********* ****** ****** Tun da farar safiya muryan Jatau ne ya tayar da mutanen gidan da balain da yazo masu. Yake cewa mama tafito bazai yarda ba tasan yarta honko ne ta dauka takai mashi gidan shi don an raina shi. Shi za, aiwa wullakanci ko may da za, a dauko honkon akawo maigida don an mai dashi tsoho. Gaban mama ne yai mugun faduwa haka ta daure tafito zani na faduwa mata gashi har mutane sun fara taruwa don gulma. Tace a ranta bari ta rufe ido tai mai na mahaukaci kawai a wuce gurin gaba daya. Ta na lekowa take cewa kai Jatau kada ka dauka ko tsoron ka ake ji duk haukan da kakeyi kyaleka na keyi. Mata kace kana so mata kuma na baka banga dalilin da zaka taso tsofai tsofai dakai ba kazo muna kana wanan magana abin kunya. Tace ankai maka honko din sai ka turo min yata yau din nan na fasa auren bazata zauna ba a gidan ka. Da Jatau yaga mama ta fishi iskanci da hauka dole ya kwantar da nashi haukan yace baki da hurimin daukan min mata, don mata zamana take yanzu. Matar ka da kace honko ce ai daga yau ta gama zama dakai a gidan ka don dama kudin bazawara ka biya bana budurwa ba. Yace a shekeke yo ina budurwan take anan kin kai min hinkon diyar ki aiko sai ga su Rukaiyya sun fito daga cikin gida. Mama ta juya garesu tana cewa maza kuje kuzo min da Lawisa gidan nan yanzun nan. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , , IDAN KIN BIYA KI RIKE AMANA DON NAUYI GARESHI YAR UWA KADA KI TURAWA WANDA BAI BIYA BA DON GIRMAN ALLAH, , , , , , Da taimako na muka kanmala aikin girkin rana da muka samu anty ta dora don muna cikin hira na mike don jin kaurin abinci danaji. Kofan danaga ta nufa dazun dauko muna abun sha na nufa sai dai ina shiga kaina ya daure yadda naga kayan girkin zamani ya cika kitchen din ta ko ina. Na rasa yaya zan duba abincin da naji yana nuna alaman ya dahu a lokacin. Gurin gas din na nufa da tsoron tabawa fal a zuciya na don ban taba amfani dashi ba sai dai cikin karfin hali na bude tukunyan dake saman wuta. Na samu abincin har ya tsotse na sauke sai dai ban iya kashewa ba ganin kayan miyan da tai blandinga cikin blander na juya na dora a wutan sai kamshi ne ya ziyarci hancin su a falo lokacin kuma suka fahinci bani falon tun dazun da sauri anty ta mike zuwa kitchen din ta samay ni a tsaye. Cikin mamaki take cewa dani Rama dama kin iya girki da gas ne ? Kaina girgiza mata tare dacewa yau ma na fara ganin shu ai, tace min kiyi a hankali nan take min bayani kan komai na kitchen din muna aiki a tare da ita har muka karasa tana gwada min komai sannu a hankali har na fara fahinta har muka gama aikin na zubo ma mama dani , mukaci mukasha muka koshi. Suna hira da mama nake fahintar akwai matsala a gidan nasu yadda naji tanawa mama bayanin komai dake faruwa. Na bu gidan da mamaki gashi da girma da kyau babu ne kawai babu a gidan amma wai zasu bar gidan bada dadewa ba. Ganin ina zaune a takure na kasa sake jikina yasa ta kallon inda nake tausayi nake bata matuka idan ta kalle ni yadda rayuwa yazo min ina yar karama da ni. Anty ke cewa na taso ta gwada min dakin da zamu zauna a part din ta nan na kwashi kayan mu na kai dakin sai da na tsaya na gyara shi tas na shiga nai wanka tare da yin sallah. Don a kauye na tashi amma ina da matukar tsabta sosai naki jinin ganin daki a ya mutse ko kadan. Kafin wani lokaci nai ma gidan kwal don dama gyara yake so bai samu ba ita gashi tayi tafiya sauran matan gidan kuma ba zama sukeyi ba a gida koma sun zauna basu iya gyara ko kadan don son jiki. Tun wanan ranan da na zo anty tasan ta rage matsala ta wanan fannin sai misalin biyar saura yaran gidan suka dawo daga makaranta su hudu na gani uku mata daya namiji. Na sheda yaran anty daga cikin su, don na sansu kwanaki da taje dasu ina gidan garbati. Biyun yan matan ne ban san su ba sai ranan na fara ganin su don haka nake kyautata zaton diyan maigidan ta ne su din, don akwai dan kama na jini tsakanin su da diyan anty din. Nan suka kewaye ta suna mata hiran makaranta sai can anty tace bakuga Grandma tazo ba da Anty Rahama. Gaba dayan su yaran suka juyo inda muke muna masu kallon sha,awa da namijin ne ya juya yana kokarin cire school bag din shi dake goye a bayan shi cikin rashin damuwa da abinda uwar tace mai. Duk da yara ne an koya masu gaisuwa sai yaran da ba nata bane suke muna wani irin kallon mamaki. Nasir baka gaida Anty Rama ba fa ya dan juye fuska a daure yace ina wuni ? Muka amsa mai a tare da mama lokaci daya sai dayan yarinyar ta dan kwanta gefen hannun kujerar da anty ke sama tace mummy are they going to stay with us ? Gaba daya yaran suka juyo suna son jin amsan da uwar tasu zata bayar a kaina maman tace dasu i think so, cikin jin dadi suka saka ihu lokaci daya suka samu waje suka zauna suna surutu. Kamar yadda nake wa kannena a gida idan sun dawo school zan sa su tube uniform din jikin su na kwasa na wanke na basu abinci kafin su wuce islamiya. Tsab na mike daga inda nake na ce da Amira oya Amira zo na cire maku uniform kuci abinci. Duk sukayo kaina suna rige rigen zuwa gare ni cikin jin dadi a tsakanin su, anty tai murmushi daga inda suke zaune da mama suna kallon mu tace dani ku shiga daga ciki dayan dakin kayan su yanan an kowa ta nuna maki nata aini kin ceceni yau wallahi. Komai na gama masu har abinci a sama sukace zasuci don haka can na hau dashi sukaci muka gyara gurin kamar basu bata ba. Cikin kwana biyun da nayi a gidan na dan fahinci abubuwan rayuwa na gidan yadda take gudanar dashi a tsarin ta. Kaman tashi da wuri da safe a girka abincin yan makaranta ai masu wanka a shirya su a hada masu abincin zuwa makaranta sai rakiya har bakin motan da zai kai su school. Haka yasa ta samu sauki sosai a dan zuwan da mukayi da nayi motsi kadan zata fara cewa wai Rama na nagode nagode kinji idan naji ta fadi hakan. Sai dai nayi murmushi nace kai haba anty wanan har wani aiki ne mai yawa ? Nikan a guri na ai wanan ba wani aiki bane don banga abin wahala ba a cikin sa amma ita sai take ganin babu taimakon da yakai wannan tunda gashi tana samun hutu da yin barci da safe wadattace yadda ake bukata a gareta. A kwana biyun da mukayi kawai shakuwa ne sosai ya shiga tsakanin yaran matan gidan dani sai Nasir ne har yanzu bai sake jikin shi dani. Sosai nake mayar da hankali ga taimakon rayuwan anty a gidan ko ina na gidan sai walkiya yakeyi don yana samun gyara. Idan yara sun tafi zan gyara falo har kitchen na dora abincin rana sai na koma part din anty na hada mata ruwan wanka na dan zauna da ita muna hira har ta mike ta shiga tai wanka sai nai saurin gyara mata dakin kafinta fito daga wanka na koma kitchen gurin girkin rana, kafin wani lokaci na gabatar masu da abincin rana ko. Kafin mu cika sati daya komai na kan gidan nasan yadda akeyin shi zan kuma yi mata shi tsab haka yasa suke samun hutu daga anty har mama sun dan canza a wanan lokacin. Duk wani abinda nasan bata so ko zai bata mata rai da yaran ta basu so, zan gujewa wanan abin . Na zomo mai kafa kafa a kan komai na gidan bana shiga shirgin dabai shafeni ba don ko yaushe ina busy ne. Ganin yadda yanayi na yake bana jin kiwar ko kyashin aiki komai idan ina yi, yawan shi bai damuna don ni a gare ni yar kauye tashin kauye har ina aikin yake anan bisa ga namu na kauye mai wahala sosai. Sai dai ita anty ko yaushe cikin yi min fada take wai na dinga hutawa sai dai nayi murmushi kawai idan ta fadi hakan mama kan ce ai gareta wanan ba aiki bane. Tana matukar bani kulawa ta bangaren ta sosai don tana nuna min kamar cikin mu daya da ita idan tana nuna min so. Yau ma zaune take falo ta mike kafa saman dan stol din katakon dake gefen kujera wanda ta jawo zuwa gaban ta, dauke da waya take hannun ta tanayi tsawon minti goma da fara wayan ta kamar ba kudi ake akashewa ba. Sai tv ke ta aiki shi kadai a falon don mama da suke zaune tare gyangyadi take yi lokacin a zaune ba kallo ba, ai dole mama tayi gyangyadi, taji sanyin AC na ratsa mata jini yanayi ya sauya sai barci duk inda ta zauna. Ferfeson kodan kaza zalla tace nai masu yaji kayan yaji don hadin kauye nai masu take kamshi ya gauraye ko ina na gidan . Na zuba mata shi mai yawa tare da dorawa ga ture da goran ruwa sai dai ba mai sanyi ba nazo gaban ta inda take waya na aje mata kayan abincin naji tunda safe tana cewa tana son cin bread da shi ferfesuf irin dai kwazaban mace mai ciki abinda, bai yuyuwa tace shi take so. Sai ganin na hado mata shi komai kamar yadda take muradin son cin shi kusan kwana biyu ke nan da take marmarincin hakan. Ta manta waya takeyi sai cewa tayi kai masha Allah Ramana Allah yai maki albarka duniya da lahira ya kare ki daga sherin masheran ta. Yanzu abinda nafi kusan wata ina son nayi na zauna naci kamar may shine daga kinji na fada kika hada min yadda nake so. Murmushi nayi ina gyara aje mata kayan abincin da kyau take cewa anya Ramana idan mutanen gidan nan suka dawo zasu gane ni kuwa wanan irin kulawa dana samu a yan kwanakin nan haka. Sai da taji dan murya cikin waya yasa ta tuna waya take tun farko abincin dana shigo mata dashi ya katse ta. Daga cikin waya ake tambayan ta wacece take zukawa albarka haka ne wai ? Tace bari kai dai heartbeat sister na da suka zo da mama ne ta hada komai na gidan nan ta hutar dani daga barci sai ci sai wanka sai ko kallo. Yace good da kyau amma ko na gode mata wallahi tayi min maganin ki tace wallahi kamar ka sani, kafin duk na gama barci na, zan samu komai is ready yarinya karama bata jin nauyin jikin ta ko kadan. Yace kai amma wanan yarinyar ta kyauta min wallahi ki min godiya gurin ta tunda ta kula min da bugun zuciya na. Dago kai tayi inda nake duke ina zuba mata ruwan miyan a plate tace Ramana kinji ana maki godiyan kula dani ko ? Murmushi kawai nai mata na fara kokarin zubawa mama nata na mika mata, lokacin kamshi ya tayar da mama dake zaune tana gyangyadi a saman kushin. Yaran da yake weekend ne na sauko dasu cikin hikima nazuba masu suka zauna ci don abinci bai damuwan su sai dai kayan kwadai kawai shine abincin su. Ganin Nasir yaki saukowa yasa na diban mai nashi zanje nakai mai murya anty ne dake shan ruwan miya da cibi take tambayana da cewa wanan na waye ? Cak na ja guri daya na tsaya tare da juyowa gare ta da hannuna dake dauke da kayan plate dana shirya. Nace anty na Nasir ne yana kwance bai taso ba shine zan kai mai nasa a dakin su. Tace cikin tabe baki Allah yasa ya karba waban yaron halinsa sai shi wallahi ya faye yawan bakin rai zakace bani na haife shi ba. Ni dai juyawa kawai nayi zuwa dakin koda na shiga dakin yana kwance rub da ciki da littafi a gaban shi yana rubutu a ciki. Abincin na aje na dawo gefen shi ta gaban shi na zauna na dan shafo kan shi nace Nasir tashi kaci abinci kaji rana yayi. Ban ci yace batare da ya dago kai ba nace haba Nasir ka tashi ko kadan ne kaci kaji kada mummy tai muna dariya dama tace min bazaka ci ba nace idan na baka zaka ci don ni abokiyar ka ne. Dago kai yayi ya kalleni sai ya duka yaci gaba da abinda yake a littafin, nace ni kasan duk cikin ku nafison ka don halinka na da kyau nasir baruwan ka da rigima. Kaga ko dole na soka na kuma damu dakai gaka yaro mai kirki da kai ko anty ma ta fada min kana da kirki sosai shiyasa take son ka ita da daddy. Sai ya sake dago kai ya kalle ni nace cikin daga kai hakane yace ba ai kazanta ba ga abincin ? Banyi magana ba sai bude mai plate din nayi kaman mai tunane sai naga ya mike zaune tare da jawo plate din a gaban shi ya dan diba kadan yakai a bakin shi sai ya fara danci a hankali amma hankalin shi na wurin littafin shi. Ruwan da nazo dashi na tsiyaya mai na mika mai ya karba ya dan yasha. Ina zaune tare dashi ban daga ba har sai da ya turo min plate din a gabana a raina nace kai lalai maganan Anty ne wanan yaron akwai miskilanci gare shi. Na mike tare da kwashe kayan nace dashi na gode Nasir ya bini da kallo har na fice. Ina fitowa da kayan zan kai kitchen ta bini da kallon tace ai na fada maki ba zaici ba daga inda nake tsaye nake cewa da ita yaci. Na shige da kayan sai dana wanke su komai da aka bata ina yi ina tuna kalamin Nasir watau kazan ta na cikin abinda bai so ke nan yaro dan kimanin shekara shidda wai yasan kazan ta haka. Sai da na gyara komai na fito daga kitchen din na nufi daki direct gurin kayan Nasir na nufa na gyara mai komai nashi tsab yanayi yana kallo na. Na fahinci rashin hayaniya hhalin yaron ne haka hallita ne mai haka Allah yayi shi amma ko ma maye a sannu zan gane komai nasa. Abincin dare na girka nagama da wuri na sa a kula ganin yaran na waje suna lesson yasa nace da Anty nima ina son zuwa na saurara. Anty tace kaman kin shiga raina dama ina son magana da lesson teacher din akan ki don nasan karatun kauye ba wani waya ta dauka kafin na fita tai mashi bayani a kaina. Cikin sati daya na fara fahinta da yake na dan san wasu abubuwa dama don haka ban sha wani wuya ba gurin fahintan karatun. Gashi dan zamana dasu na fahinci halin ko wani yaro ina kuma jan su a jiki sun sake dani sosai. Wanda hakan na fahinci yana matukar yiwa anty dadi a ranta niko a guri na naga ba komai ba ne hakan don tafi haka a gurina ni. Banda abin su na masu hali ni banga wani aiki da take yawan cewa yai min yawa ba amma gashi ita ko wani lokaci sai gode min takeyi. Sosai yaran suke sake jiki dani gashi har Nasir na dan fahinci halayen shi haka yasa yauma tun dawowan su na fahinci yaron bai jin dadin jikin shi amma ya kasa fadawa kowa sai kwanci yake yana mika. Mun dawo lesson nake cewa dashi Nasir bari na hada ma ruwa mai zafi ka gasa jikin ka dashi bai ce dani uffan ba har na hada ni da kaina nai mashi wanka na gasa shi da ruwa mai zafi na shirya shi har da robb na shafa mai na rufe shi da bargo. Na fahinci yaji dadin yadda nai mashi don naji ya sauke ajiyan zuciya dakin anty na nufa don karbo mai magani. Na tura kofan na shigo da sallama tana zaune saman gadon ta ta baje kanta babu dan kwali akai. Tana gani na take cewa dani cikin murmushi maman yara kin samu kanki ko kin gama komai. Nace eh anty yanzu ma nazo ne in da magani ki bani naba Nasir. May ya samay shi kuma nace ina ganin zazzabine ke dan satan shi amma ba wai ya fada min bane nan dai nai mata bayanin komai. Tace wanan yaron sai kinyi hakkuri halinsa sai shi wallahi don ni halinsa na rasa ina ya samo shi. Ta nuna min inda magani yake na miko mata tace Allah yasa yasha don miskili ne wallahi. Murmushi nayi nace haba anty ba kudai fahince shi bane amma yana da saukin kai ai idan abin shi a sannu. Tace ai yanzu kunfi kusa dashi Allah yasa dai ya sha maganin don bai son magani sam. Nashiga dakin na samu yana kwance yadda na barshi da farko na dafa goshin shi jikin ya dan yi sanyi a lokacin ya bude idanuwan shi yana kallona. Nace Nasir dina tashi ga magani ka sha kada jikin ya matsa ma sai naga ya ya mutsa fuskan shi nace ko na jika mane ? Sai ya gyada min kai alaman eh yana son haka na dawo da cup da ruwa a hannuna a gaban shi na jika na nasa spoon na juya na bashi sai ya karba yasha yana ya mutse fuskan shi na bashi ruwa yasha. Ina gyara mai kwanciya sai ga uwar tasu ta shigo dakin tana tambayan yasha ko akai shi asibiti yaga likita nace ya sha anty. Matsowa tayi ta zauna a bakin gadon da yake kwance sai take bin dakin da kallo komai na dakin tsab dashi. Tun dai gurin kayan Nasir komai a natse yake tace dani kai ashe ba karamin aiki kisha ba dakin nan ne haka Rama ? Nace kin san zama da kazanta ba kyau anty gashi yara ne sai anyi hakkuru ana gyara masu dakin nasu. Kakarin amai yaron keyi yasa hankalin mu ya koma gare shi kama shi nayi amma kafin na dago shi har ya bata min jiki da aman . Nan uwar ta haushi da fada tana cewa haba Nasir wanan sakaci ne ai zaka batawa Anty jiki da amai kuma ni ba batun kaina nake ba sai kokarin kamashi muka shiga bandaki yai amai sosai a ciki na gyara shi muka fito har lokacin tana zaune inda muka bar ta. Nace bari na canza mai zanin gado tace haba goge gurin kawai ya kwanta mana. Nace bari dai na canza mai tunda wanan din ya baci yaron cikin san murya da nuna fushi a fuskan shi yace kai mummy please go now. Tace cikin dariya dama abinda yake so ke nan shegen tsabta gare shi kaman ba karamin yaro ba. Sauran yaran ne suka shigo dakin suna cewa anty is time for prayer mun zo muyi sallah ne tare da ke nace tau ayi alwala. Tace masha Allahu ashe har jam,in sallah ake a dakin lalai an samu ci gaba. Suka ce anty ta fada muna cewa idan bamu sallah za, a kona mu ne wai da wuta. Tace gaskiya ta fada maku oya aje zuwa alwala kafin anty tazo nan suka shige bandaki kafin su fito na fitar masu da hijjab din su. Anty ke cewa idan mun koma wancan gidan zakuji dadin shi don yafi wanan girma sai dai aikin zai karune don haka nace a samo min wata yar dattijuwa mai dan dama don akwai dakuna da yawa sosai a kowani part gidan babbane kwarai. Nace cikin mamaki anty yakuma fi wanan girma da kuk ciki tace babban gidane sosai Rama sai in kin gani zaki sheda . Ba karamin kudi ya kashe ba gurin gina gidan don har ginan yaso ya taba mai aikin shi da kasuwan cin shi don mutane nata magana akai. Nace ashe harda babban gari akwai tsegumi kamar mu kauye tace inane babu gulma yanzu haka duniya ya koma fa. Ranan itama a dakin mu tai sallah tana kallo yadda muke sallah da yaran sai sun kalla sun ga abinda nayi zasu kwaikwaya suma suyi hakan. Muna gamawa taji mun fara karatu duk sun haye min jiki na amma haka muke karatun tai mamaki jin har mun kai kulhuwallahu da yaran don tare muke hadda dasu da baki. Abin yai matukar bata sha, a take cewa lalai munyi kure dole a samo malamin mai koyar da addini koda da dare ne sai yazo a dan taba. ****** ********* ****** Fitina yakai fita don Jatau ya saka mama da baba a gaba daya samu labarin bani garin. Haka magana har takai gidan maigari dole sai da aka kira mama taje da kanta. Nan dai ya koro bayani mama tai tsuru tsuru sai kamay kamay takeyi tarasa na cewa gashi babu kudi don har kudin sadakin ta kashe wai tayi sayayya dasu na aure. An basu sati biyu kacal su kawo mai kudin shi ko su dauki hukunci kan ta nan suka bar gurin kan wanan magana. Suna dawowa gida ta saka baba a gaba kan sai dai ya tafi birni yazo dani a daura aure akai ma jatau don bata san inda zata samo mai kudin shi ba cikin sati biyu. Yana gama sauraren ta yace amma kina da wani magana ni ina zanje cikin kano na dauko Rahama ? Altine ce tasan inda ta kaita kuma suna can tare ban san wanda zan tambaya inda suke ba yanzu don ba wanda yasan gidan yan uwan nata. Hankalin mama ya kara tashi sosai har gurin Inna ta taje cikin kwantar da murya take cewa a tsaya a fahinci juna kada abin yakai ga bacin rai. Inna tace rai shi ya dade baici ba ita ko kano bata taba zuwa ba balle ta ce tasan inda muke. Su dai da suka ci kudin shi sai su tafi can su karata dashi ita babu ruwan ta cikin wanan magana kuma daga yau su fitar da rai ga tinanen zasu hada ni aure da wani jatau a yanzu. Mama ta bar gidan cikin bacin rai take cewa yadda ba, a so sai ankai ga yin hakan Inna tace to bissimillah kuma tai mata kashedi akan zuwa gurin ta don babu hadin kifi da kaska yanzu. Haka ta dawo gids cikin tashin hankali ga kwanaki sai matsowa sukeyi tace idan baba ba zai je nemo mu ba ita zata shirya taje kano da kanta ai mai tambaya baya bata sai ta gano inda muke a kano ta dawo dani an mata aure. Yace bissimillah gaki ga hanya nidai banci komai na Jatau ba balle ya damay ni. Haka tashirya ita da Larai kawar ta suka tafi kano tun shigan su garin hankalin su ya fara tashi duk wanda suka gani a bakin tasha sai su tsayar dashi suce don Allah ko yasan wata Rahama tare da Altine mai kulli kulli. Wasu suyi masu daukan mahaukata wasu kuma su tsaya masu tambayan a wani unguwa sukace daku suke ? Basu sani ba sai a barsu a tafi sun koma kamar mahaukata suka dawo gida cikin dare hankali a tashe. Ko sannu baba bai mata ba shiya tayar mata da hankali ke nan ta haufada tana cewa munafuki dama ashe tare dashi aka hada baki don aga bayan ta ai tasan zaman ta dashi. Hankalinsu har baba ba, a kwance yake ba gashi gidan ya fara yi wa baba tsamin har ya fara kewan Innata a lokacin sai dai yana gundu yanuna yaji masifan mama. Har bakon da mama Altine ta aje gidan ta da iyalinshi sai da mama ta tayar mai da hankali tace yasan inda mama Altine take inba haka ba may zai sa ta aje shi gida bata sanshi ba. Nan sukayi tas da mutumin ya nuna mata yafita kwaya dole ta fita batun shi ta kyale shi don yace idan ta sake shigowa ta tayar mai da iyalin shi hankali kan abinda bai shafe shi ba sai yai mata tsinanen dukan da sai an kaita asibiti ta kwanta. Gidan Lairai taje neman shawara nan dai suka kasa kai mafita ga maganan sai larai ne ke cewa nifa ina ganin mafita daya ne a gareki yanzu shine ki daure ki bashi daya daga cikin yaran nan a zauna lafiya. Cikin mamaki mama tace wa kawar nata Larai yaushe kika fara hassada na a garin nan ban sani ba Jatau ne zan dauki yar cikina naba aure ko may ? Larai tace to may ye a hakan ba mafita muke nema ba ko kina da jakka dari da tamanin da zaki ba jatau ne kudin shi. Nu naga haka shine mafita kawai cikin wanan magana ki samu a zauna lafiya don kin san dai Jatau bai daukan kaddara shi. Aiko mama tai cikin Larai da masifa suka dinga tonon asiri a tsakanin su kaca kaca sukayi tabar gidan Larai a hasale kowa ya kama gaban shi daga ranan. Duk wanda yaga mama a lokacin yasan tana cikin tashin hankali sosai don ko ba, a fada ba duk ta ramay ta fita hayacin ta fa fitinan yaran ta da yai mata yawa. Don babu ragowa ko kadan tsakanin ta dasu sai cin mutunci kamar ba uwarsu ba. Ana cikin haka akace an kama Rukkaiya da mai nama a shagon shi suna lalata wanda dama ba ranan ne farkon yin haka ba a gare su. Nan wani sabon magana ya bi gari kwaaa ga kauye da iya daukan magana ko karami ne balle irin wanan. Da labari yaje wa Inna tace ita kan dai ta godewa Allah da yaraba ta salin alin da wanan fitinanen gida a wanan lokacin. Ranan komawan su gurin maigari yazo dole ba don taso ba ta hada dubu goma da kyat koshi sai da ta sayar da yan kaddarorin ta ta samay su. Bayan ta gabatar da kudin da tazo dasu ne aiko Jatau ya buga kasa yace bai san da haka ba shi kudi shi minamina yake so don ba zai dauki hasara ba baiga mata baiga kudin shi. An kai ruwa rana so sai a gurin dole aka bata zabi idan babu kudi a turasu kotun birni ko kuma ta samu mafita ta bashi kudin shi. Maiunguwa ne ya kebe da ita gefe ya bata shawara ta bashi yarta daya a wuce gurin don idan ta bari aka tafi kotu daure ta za, ayi can babu kuma may sanin inda aka kaita. Kuka ta saka ma maiunguwa tana cewa ya cece ta yai mata rai ita bazata iya ba Jatau yar ciki ta ba yadda yake din nan gashi kazami fa tsufa ga rowa da cin mutunci. Maiunguwa yace ni wanan shawaran shine nake gani kawai mafita a gurinki a wuce gurin don gujewa shigan ki gidan yari. Bata da zabi dole da wanan shawaran suka koma tabarman mai gari nan mai uguwa ya gabatar da shawaran da sukayi da ita. Baba dake zaune yace idan haka zai kashe maganan shima ya aminta da hakan . Aka tambayi Jatau idan ya yarda da hakan yace sai dai yayi maneji don dai shi ba cikin su yaso ba. Mama naji ta dago kai ta kalli Jatau mutum haka a kazance har yake kiran wai maneji zaiyi da yarta. Muryan mai gari taji yana tambayan su daga cikin diyan wacece zata bayar. Nan wani sabon tashin hankali yazo mata to ita wa zata bashi don duk yaran nata ba mutunci ne dasu ba ai. Babu wace zata fahince ta ta fitar da ita wanan kangin da take ciki cikin ruwan sanyi. Sai bude baki tayi tace kai kai Rahama Allah ya isa tsakani dake da uwar ki da kika jefa ni wanan halin haka. Maigari ya matsa mata tace a bashi Rukaiyya nan jatau yace wa shi Allah ya sauwaka mai yarinyar da ta zama ba gari dadi zai aura yagane may gurin ta. Ran mama ya kara baci tai cikin shi da masifa karshe dai da aka kai ruwa akai rana yace sai dai Lawisa dan dama dama zai laba da ita hakana. Haka a kawatse kan za a daura aure nan da sati daya ta tare dakin ta mama ta dawo gida cikin bacin rai ta isa gida har da suma sai da tayi hankalinta ya tashi baci ba sha ta shiga wani hali na tashin hankali. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , , IDAN KIN BIYA KI RIKE AMANA DON NAUYI GARE SHI YAR UWA KADA KI TURAWA WANDA BAI BIYA BA DON GIRMAN ALLAH, , , , Muna nan jikin yaron yaki dadi dole anty ta kira mahaifin shi a waya take sheda mai yau Nasir jikin ba dadi don har da amai yayi sau biyu Yace yanzu zai turo hamza driver yazo yakai shi asibiti amma ni yanzu na sha magani ba zan iya fita ba gsskiya. Yace ko da mama ce ta kai shi mana asibitin tace ba damuwa tana gama wayan lokacin ina tsaye na rike hannun shi sai cewa tayi ki shirya shi ku tafi asibiti yanzu driver zai zo. Da sauri na dan kalle ta nace asibiti gabana ta fadi na farko ga dare yayi na biyu ban taba shiga ko asibitin garin mu ba balle na birni irin kano san nan ma ni a wurina dan wanan ciwon ne za, a kai har asibiti. Ganin nayi shiru tace dani ko akwai matsalane naga kaman kina tunane akai ? Dan dariyan yake nayi da bai kai ciki ba, kawai nake cewa da ita ba komai anty. Amma gabana sai faduwa yakeyi sosai haka na shirya driver na zuwa muka fito don tafiya asibitin. Can naji tana cewa da driver ya tabbatar da bai barmu mu kadai ba don ni ba kuwa ce ban san gariba sai lokacin nadan ji sanyi a raina. Tafiya mukeyi yayin da Nasir yake kwance a jikina jikin shi yai zafi radau. Amma ni sai faman kallon yanayin garin nakeyi ga kwan haske wutan lantarki ya haske ko ina na garin. Wani katon guri muka shiga naga motoci an parker iri iri a gurin nan ya samu guri shima ya parker tamu motar. Ya bude don ni ban iya bude motan ba ma muka fita ina rike da yaron shine ya karbo family file din su muka bi layin ganin likita. Sai baza ido nakeyi ina kallon yanayin mutanen birni yadda suke harkokin su ba ruwan wani da wani na lura ba mai ko gaida wani sai dan wanan yabi can wancan yabi nan. A haka har aka kira mu Hamza driver yace na shiga da yaron ciki shigan mu office din ya dawo mun da burina na son zama likita ko nurse. Komai na office din a tsare yake nan ya nuna min kujera muka zauna yai muna yan tambayoyi akan ciwon yaro na bashi amsa. Bayan ya gama yan rubutun da zaiyi a cikin takardan ne ya miko min tare da cewa muje lab da yaron. Nafito Hamza ne ya kai mu akai koma suka gane maleria ne kawai ya kama shi nan akai mai allurai muka juyo zuwa gida. Sosai yaron ya samu kulawa a gare ni haka shine ya jawo mun shakuwa dashi fiye da duk sauran yaran da nake dawai niya dasu nata. Shakuwan da yaron da bai yarda koda iyayyen shi yasa anty matukar mamaki take cewa lalai Rahama kinci sunan ki wanan mara yardan ne har yake manne dake haka ko yaushe. Ai Nasir da kike gani tun yana goye baya da yarda sam da kowa ko yaushe yana like dani. Da ya fara wayo ne kuma koni din baruwan shi dani kullun yana make gefe daya shi kadai. Nace anti baku fahince shi bane akwai abubuwan da baya so kuma hallitan shine hakan. Na fahinci ita anty irin rayuwan turawa gare su nabawa kowa freedom din shi don har yaran sai abinda suke so ake masu. Ni kan ai a gare ni ya kwana gidan sauki dama ina da son yara don haka sai nabiye masu amma cikin hikima nake gyara mata tarbiyan su. Ganin yadda ta ya mutse ne a yadda na san ta yar gayu a baya ranan nake cewa da ita Ina son nayi kitso kaina yana damuna. Tace kinga sai mu tafi tare a gyara muna kai ni dai ba kitso zanyi ba sai dai a wanke min kaina kawai. Tace shirya da azahar mu fita mu leka saloon din don kiga guri. Ni dai ban san ina ne saloon ba na dai ce da ita to ne kawai na shirya kamar yadda tace din muka fita. Ita da kanta take jan motan ina ta kallon ikon Allah ashe dama ta iya tukin mota mace da ita. Wani katon shago naga mun tsaya sai mata ke shige da fice a gurin an rubuta a gurin saman wani katon abu da rubutu mai launi tare da hoton mace da gashi dogo da akaja. ASSAMA,U SALOON waje ne dake cike da manyan mata masu fada aji yanayin masu aikin gurin ba namu bane don shigan matan kasan larabawa ke jikin su. Na kara ganin wani guri an rubuta haka PEDICURE & MANICURE Anty tace zo mu fara shiga nan muna shiga na fahinci ba bakuwa take a gurin ba don naji suna cewa a hajiya kwana biyu baki leko mu ba ko lafiya ? Ta dan yi murmushi tace kin san jikin ne sai a hankali yanzu ni tace a fara yiwa ina ta faman kalle kallen abinda akeyi a gurin. Gaba daya naji yan gurin nata faman yaba kyauna da dadawa ni dai bangani ba sunce na kalli mirro amma na kasa don kunya. Har kai na sai da aka yarfa min kitso masu kyau kanana nai mamakin irin saurin mutanen Da akai wa anty sai naga gaba daya ta canza min ta koma kamar wata yar karamar budurwa da ita sai ka rantse da Allah ba itace muka shigo ba a ya mutse. Haka muka dawo gida shar damu tun shigiwan mu mama ke fadi kai kai kai wai ko Rahama ce nake gani ko gizo idona ke yi min. Falo muka zauna sai naga ta baje rigunan da muka sayo a kusa da ita tana fitarwa daya bayan daya ta sake duba su tare da yaba kyawon su. Gaba daya ta miko min su gaba na tana cewa a kashe lafiya sai na samu lokaci akwa wanda zan kara duba maki a cikin kayana sai ki kara. Daga yau bani son ki kara saka komai da kikazo dashi daga kauye don matan gidan nan yan rainin wayo ki dinga kwalliya kamar kowa a nan kina gyara jikin ki a kai akai. Kafin nakai ga godiya ta daga min hannu alaman a, a bata son haka shigowan yaran da suka dawo ne yasa muka mai da hankalin mu gare su baki dayan mu. Yau da kuka Amira ta shigo wai Nasir ne ya buge ta a mota anty tace oya kije gun anty Rama ta cire maki uniform. Kallon mamaki naga yaran na min ai dayan yar gurin zulfa take cewa wanan anty Rahama ce mummy. Gaba daya dariya akasa anty ce a to sunga yau kin sake masu kin zama wata yar birni dake haka nake son kowa yaga yar kauna nawa ya yaba maki don badai kyau ba kan sai dai wani abin kuma. Muka kwasa dani da kayana dasu muka shige ciki a tare gaba dayan mu. Bayan shiga na ne mama ke cewa ikon Allah watau gyara shine mutum mutumin kauye da ta gyara akafi watau. ****** ********* ****** ****** Yau tun safe dana tashi banji duriyan ta ba sai ni da mama ne ke faman dawainiya da yaran har suka gama shiriritan su suka wuce school. Lokacin ne nake cewa mama yau ban ga anty ta fito ba don takan fito su gaisa da mama wani lokaci ma a falo zata dan zauna har sai yaran sun fice daga gidan amma yau shiru banji duriyan ta ba. Dakin nata na nufa a hankali na tura kofan dakin don na dubata na hangota rufe a cikin bargo tana rawan sanyi. Da sauri na karasa gurin ta ina cewa anty lafiya kike kuwa maganan ta baya fita don haka na bude bargon da take rufe a cikin sa. Gabana ne yai mugun faduwa don duk ta fita yacin ta cikin murya mai makyarkyata nake cewa anty jikin ne ? Da kyat ta iya cewa Rama taimaka min miko min wancan abin maganin nawa kibani na sha, ga wani irin numfashi da takeyi kamar zata shude a lokacin. Da sauri na dauko abin maganin tana nuna min na juya zuwa waje don na dauko goran ruwa tasha. Hankali tashe nake fadawa mama halin da Anty ke ciki naga hankalin ta yai matukar tashi sosai tabi muka koma dakin tare. Na bata maganin tasha da kyat ganin yadda jikin nata yake nace da ita ko akwai taimakon da zan iya maki anty ? Na tambaye ta cikin dukawa kanta ina son inji may zata ce dani sai alama taimin na rufa mata bargo a jikin ta. Haka muke a kanta cikin tashin hankali yadda naga tana shan wahala yasa na fita daga dakin dakin mu na koma na takure kaina ina faman kuka. Ba abinda nake tunane sai irin taimakon da boyar Allah nan take min yanzu idan wani abu ya faru da ita aiko diyan ta sai na fisu shiga uku. Muryan mama ne naji tana kiran sunana shi yasa ni fitowa daga dakin da sauri da kaga idanuwa baisai amfadawa mutum na darji kuka bane. Mama take tambayana ina kika shige ne tundazu kije Saade na neman ki a dakin ta da sauri na karasa dakin ba laifi na samu ta yaye bargon dana rufa mata a jikin ta. Ba laifi don tabar rawan sanyin da take yi da farko murya a wahale take magana dani. Ramana don Allah taimaka min ki matsa min kafafuwan nan ko zan samu ya sauka min gaba daya. Ba musu na gyara yaye bargon a kafanta na shiga tausa mata kafan ta a hankali ina jin yadda take sauke ajiyan zuciya a hankali. Sai ce min takeyi ta gode jin banyi magana ba yadda muka saba da ita yasa ta dago kai ta kalle ni. Yanayin idanuwa na ne ya nuna mata kukan da sha tace subbahanallahi Rama kuka kikayi ne ? Allah sarki ai wanan ba komai bane don yazo min ma da sauki ai don Allah ya kawo min ke da wuri kin bani magani nasha. Dan fitan nan da mukayi jiyane nasan ya tayar min da ciwon haka amma ya kwana biyu bai motsa min ba da yake na samu hutu yadda ya dace. Tun dare ya fara min gashi ban iya tashi na dauko magani inda yake ke kuma baki da waya a hannun ki. Yakama ta nasai maki waya ki rike don irin haka idan ya taso kina sani nace waya anty tace eh nace ban san yadda ake amfani dashi ba ai. Zaki sani ai baida wuya da ankoya maki zaki gane yadda yake tun ban gani ba nace da ita na gode. Babu wanda ya sake magana cikin mu sai zuwa can a zatona ma ta samu barci ne sai take cewa. Gobe baban su Nasir zai dawo don munyi waya dashi yanzu yake fada min haka. Don haka ina son ki gyara gida da kyau kamar yadda kika saba sai kiyi abincin da zamu tare shi. Amma shi yafi son yaci abinci mai nau,in gargajiya idan zai samu sai ki duba kiga wani yafi maki saukin girkawa a tanadi abinyi. Taci gaba da cewa sai dai idan ya dawo fitinan gidan nan zai dan karu don matan shi zasu dawo don a matse suke ya dawo din daga su har iyayyen su. Don haka abinda nake so dake a gidan nan ki tsaya a inda na aje ki don ba mutunci ne dasu ba. Gabana ya fadi don jin may tace dani tace ina ga ai shike nan zaki iya tafiya ki huta kafin yan rigima su dawo. Sai yamma lis ta samu tafito falo ta zauna har lokacin alama ya nuna bata jin dadin jikin ta sosai ga yanayin ta duk ya dan sauya ko don gyaran jikin da akai mata ne nake ganin canji a jikin ta haka. Aiki nake amma tunane nake a raina don gaskiya ina ganin za, a takurawa rayuwan mu ne idan sauran masu gidan sun dawo. Tunda yadda na fahinta sam babu zaman lafiya a gidan da sauran mata ga alama ya nuna maigidan kamar fitanane yadda yai karfin halin tura mata biyu gidan iyayyen haka kai tsaye kuma aka tsaya ga sai yadda yace za, ayi. Ni dai komai mugun halin su mudfin ina gidan nan bazan bari su kawowa Anty na rashin mutunci ba a gabana ina gani na kyalesu sai dai ayi wanda za, ayi din. Tuwon farar shinkafa na tuka mai da miyan kuka yaji kayan yaji kamshin dadawa yakeyi sosai sai kassan maman rago da nai amfani dashi cikin miyan. Nai ferfesu kayan cikin rago da ban shima hadin hausa nai mai don ban sa kayan an gayun su ba ga miyan. Daga gidan har abinci na kammala gyaran su tsab na koma gurin anty dake daki a kwance na samayta nake fada mata na kammala komai yadda ya dace take cewa kin gama a cikin sa,a don yanzu ya bugo min waya wai sun sauka garin. Su ma matan nashi ina ganin yau zasu dawo gidan don naji yana tambayana ko sun shigo. Nace to anty ki tashi mana ki dan shirya kada a amay ki haka ko ? Murmushi tayi tace kai kaji Rama da wani zance waye bako na a cikin su idan sun samay ni a hakan ? Nace su duka ai tunda sun kwana biyu basu gidan ya kamata su samay ki a shiri ke ma. To yanzu yaya kike son ayi na ce bari na duba maki mai saukin sawa sai ki saka. Duk wanda na ciro sai tace yai mata nauyi da yawa ga kaya shake a wadrove amma bata damu da sakawa ba ita. Sai wani dogon riga light blue mai shara shara baida nauyi tace na miko mata shi ta saka. Rigan yai mata matukar kyau a jikinta sosai gashi dama ta yi gyaran jikin ta sai kyaunta na asali ya fito sosai. Falo ta koma ta zauna nace mata ina zuwa na shige ban dade da shiga ba naji hayaniya a falon amma hakan bai sa na fito ba a lokacin don ba, a nemay ni ba in ba gulma ba may zan fito yi kuma. Duk da dai ina so ganin waye mijin na anty mai irin wanan dukiyan haka mai yawa haka da yai sa, an samun mace ta gari mai halarci irin Anty Sa,ade. Daga kitchen nake jin muryan wata dadtijiya yana tashi da alama fada takeyi don sai na kasa kunne na dakyau naji tana cewa. A kan wanan tsohuwar da ka aje a gida zaka kwaso diyan mutane kuna cuta masu sai abinda tace shine akeyi don ta mai she ka bi can. Dakai da ita Sa, ade duk zan yi maganin ku ne kwanan nan yadda ta hure maka kunne ka tunkuda keyan yaran gidajen su itama haka za, a tunkuda ta tafi nasu gidan. May ma wai kagane ga auren wanan wannan mutu kwakwai rai kwakwai ne wai ni banga abinda kagani jikin wanan maikama da kyankyaso din. Wanan wanan da kake gani bani mussu idan ance ta girmay maka don kana ganin ta haka a fige ne kake mata daukan yarinya karama. Ni dai daga inda nake ba na jin muryan mijin nasu amma matar dake fada naji tana cewa in har tace bata zama da yaran nan don bakin kishin tsiyan ta sai dai ita ta fita tabar masu gidan mai bakin halin tsiya. Yau ko kinki ko kin so duk zasu dawodakun nan su kuma su kwana a gidan nan jarababban baza kawai mai bakin kunatan tsiya. Zuwa can na bar jin hayanitan su haka yasa na fahinci masu fada kila sun tafi ne don naji shiru kamar babu kowa falon. To amma kuma wacexe mai ma anty wanan mugun zagin haka har take kiran ta da tsohowa na ji dai tana fadin wai ta girmi mijin nata shi mijin wani iri ne wai badai yaro ne zai iya tara wanan abinda nake gani ba haka ? Har nagama abinda nakeyi ban ji duriyan kowa ba na koma daki na shige sai da yara suka shigo muyi sallah ne naji suna cewa wai sun raka daddy su sharada gidan su grandma. Ina shirin kwanciya don yau ba fita falo kallo gare mu tunda mai gidan yana gari suna falo da iyalin shi mama kuma har tayi barci a inda tai sallah. Sai ga Nasir ya shigo inda nake yana cewa anty wai mummy kizo ku gaisa da daddy. Nace to tsaya mu tafi tare kaji Nasir na jawo hijjab dina da nai sallah har na nade shi na saka akaina. Nabi bayan yaron muka fita zuwa falon inda iyayyen nasu suke zaune tare da sauran yaran gida baki dayan su. Da sallama na na shigo falon yana zaune saman dan karamin carpet din dake tsakiyan falon nasu, Ya mike kafafuwan shi tare da dora daya akan daya yana rike da wayan shi yana dubawa. Da alama abinda yake a wayan yai matukar dauke mai hankalin shi sosai a lokacin Anty ce na hango ta kishingide a saman dayan kujeran da yake zaune jingine akai. Tana amfani da remote a hannun ta gurin canza channels din tv dake aiki shi kadai a falon da alama tagaji da inda yakai ana news . Kallo daya nai ma inda yake zaune ban iya kara daga kai na koma kallon shi ba, saboda tsaban kwarjin da yai min a idona ga kuma hallita mai cikar zati a tare dashi. Zaka rantse da Allah kace shi din ko saurayine bai ma taba aure ba balle har tara mata har uku haka a gidan shi. Jin na shgo falon yasa anty dago kai tana murmushi take cewa Ramana ga baban su ku gaisa ko. Tun dazu da ya dawo bai samu zama ba sai yanzu ya samu kan shi, gashi yaci abinci sai faman satin tuwon ki yake yi wai ya dade bai ci tuwo mai dadi haka ba. Murmushi nayi nace kai anty kila ma bai yi dadi bane kike zolayana ko ? Fuskan shi a dake duke ya dago kai yana murmushi tare da kallon inda nake lokacin har na kai durkushe ina fadin sannu da dawowa daddy. Yace cikin murmushi yaya na samay ku ? sannu da fama fa ina tajin labarin ki ta waya wurin yara kullun idan muna gaisawa dasu. Sunce yanzu anty tana masu sallah kullun kuma kuna hadda a tare da su don sun karanta kuma na gamsu sosai da karatun su. Na murmusa tare da dukar da kaina kasa ina wasa da yan yatsun hannuna a hankali nace Alhamdullahi. Yace ban da abinda zance dake sai godiya don kinyi matukar kokari gurin taimakawa iyalina da bana nan. Cikin murmushi nace ai yiwa kai ne balle ma ai ba wani aiki don yaran na da saukin kai sosai. Ya dan murmurmusa karo na biyu tare da juyawa inda matar shi take zaune yace lalai wanan anty kan akwai sa,a ance harda nasir ta san yadda take zama dashi ai kinyi kokari. Na mike tare da cewa Allah ya hutar da gajiya yace Allah yasa na juya tare da fara tafiya zuwa ciki. Muryan anty ne kewa dani Rama dawo ki kwashe kayan nan ki shiga dasu ciki cup ne da goran ruwa da akasha. Muryan shi naji yana fadin ashe ba wata babba bace yadda na dauka wanan ta ma kai 18 kuwa ? Tace yanzu dai take seventh don ko da ta gama makaranta kasan irin karatun su na kauye ne ai pushing din mutun din nan don kokarin shi. Ni dai nai simi simi na kwashe kayan zuwa cikin kitchen na barsu nan suna magana a kaina. Yace wa matar nashi yanzu yar wanan abar ce kike nufi an tabawa aure ? Tace sosai kuwa mutuwa mijin yayi don ba yaro bane zai haifi sa, ata ma gaskiya. Ikon Allah wani magana sai kauye ba tausayi ba sanin human right ko kadan a kauye. Anty tace ina son na mayar da ita makaranta taci gaba da karatun ta don tana son karatu a rayuwan ta. Yace dakin kyauta gaskiya don yarinyar na da hankali na gani tace ai Rama akwai hankali sosai wallahi. Sai da safe dana shiga gaida anty bayan tafiyan yara take fada min wai matan gidan ai sun dawo jiya cikin dare. Da maki na ce da ita ashe sun dawo gidan ya cika kake nan yanzu? Tace kin san su da naci kamar masu jiran saukan shi sai ga kowace an dawo da ita daga gidan su a cikin dare. Har uwar yesmin tazo cikin dare don fitina wai a bata yarta a gurin ta zata kwana sai da maigidan ya tsawata mata. Ni dama ya bari na bata yar ta tun daren kowa ya huta haka ko kwasa fitsari ai ya ishi mutane ma. Ni ba don Allah ya kawo min ke ba da ban san yadda zan kwashe da rigiman yaran nan da ya bar min ba. Yasan kuma ba lafiya ke gareni ba gashi fitinan su ya hana ko yar aiki a bar muna a gidan ko mutum yaji dan sanyi. Don haka don Allah Rama kafin su dawo ki hadawa kowa na ta ya na ta su koma wurin iyayyen su kema kya huta ai, da wanan wahala tunda su basu san wahala suka barwa mutane ba ma. Inda sune ai ba zasu dibawa mutum nashi ba kamar yadda yaran ke samu kulawa a nan yanzu. Nan take bani labarin tafiyan ta da yadda ta dawo ta samu yaran ta hannun su tace shine take ganin dalilin barin su gidan da sukayi. Ta tabe baki tare da komawa ta kwanta tana cewa nasan shine dalilin jin haushin da yasa tazo cikin dare wai a bata yar ta ta tafi da ita gurin ta. Nace ai da abari ta tafi da abinta ba shike nan ba kowa ma ya rike nasa a zauna lafiya. Tace wallahi fa kedai Rama ba su da mutunci fiye da tsanmanin ki don sun samu daurin gindi a gurin sarakkan mu ne. Dazu bakiji yadda hajiya tazo tai min tas ba a gidan nan saboda sune kuma tai min haka. Ai indai kina gidan nan zaki gani don kullun aikin ke nan su basu laifi sai nice bare a cikin su nice mai laifin don Allah ya jefani cikin su. Nace anty dama yan uwan shi ne yake aure ? tace eh kusan hakane don ita hindatu yar uwan hajiyan shi ce. Ita kuma zulfa diyan amininahaifin shi ne da suka dade suna tare tun kurciya suke tare kinga ke nan ai sai ace duk yan uwan shi su biyu din. Nace cabdi amma kina fama gaskiya anty tace bari ke dai to yaya na iya da raina Rama ? Ganin ta kwanta na juya zan fice dakin take cewa dawo kiji, da sauri na juyo ban tafi ba tace daga yau wanan girkin wahalan ya kare koda yake ma ina ganin nan da two days zamu bar gidan nan kowa ta kama part din ta daga ita sai nata babu mai ganin wani cikin mu Amma dai duk da haka yau abinda zamu ci kawai anan ni daku zaki girka muna yau din. Nace to anty na juya na fita tare da rufo mata kofan dakin don nasan barci zatayi kila. ****** ********* ****** ****** Mama Lauratu ne zaune da yaran ta dukkan su uku sai baba da ke gefe daya zaune saman tabar ma yana sauraren abinda zata fadi. Can ta sauke ajiyan zuciya tare da cewa ina son ku saurare ku fahinci may nake son fada maku a gurin nan. Bawani magana ba sai maganan kaddaran da ya samay mu a gidan nan wanda ba kowa ne ya jawo muna shi ba sai Rahama da uwarta don sune suka cuce mu haka? Haba mama in zaki magana da kika tara mu kiyi muna amma ki bar kawo muna zancen mutanen da basu san arziki ba a rayuwan su. Rukaiyya ce ke wanan magana cikin hasala tana kokarin dakatar da uwar tasu da ta fara masu dogon sharhi. Mama tace cikin sanyin murya na dauko maganan ne yadda zaku fahince ni da kyau amna tunda baku so bari naje kan maganan da nake son fada maku. Ke Lawisa dai yau Allah ya nufi auren ki da Jatau na hayin dutse don haka Allah ya kadda, , , , Kafin ta karasa Lawisa tai but tace wata Lawisan mama ba dai ni Lawisan ba kan ? Daga inda baba yake zaune ya karba da cewa ke ko Lawisan don an daura auren ki da Jatau bisa ga sadakin da uwar ku ta karba a hannun shi da niyan bashi Rahama Allah bai yi ba. Baba na shirin ci gaba da maganan shi ai Ihun da Lawisa ta sake ne ya hana shi ya karasa zancen shi. Lawisa ta dinga kuka tana durawa iyayyen ta ashar tana bata ga dan kazan abu kaza ba da ya isa ya daura mata aure da Jatau ba. In gaskiya inta mama ta kashe auren ta ita da taci kudin shi taje ta aure shi mana. Amma ita don ba a sonta shine za, a cuce ta a hada da wanan kazamin tsohon ace wai shine mijin ta. Nan suka shiga lalashin ta amma ina kamar kara zugata sukeyi ai a lokacin. Suma su Rukkaiya nan suka shiga fadawa iyayyen bakar magana son ran su ba wanda ya iya magana a cikin su sai sadda da kai kasa da sukayi kawai. A take baba ya tuna da auren da sukai min na Garbati bani so amma dani da uwata ba wanda yaji bakin mu haka aka kai ni salin alin mun danne zuciyan mu dani. Yau gashi diyan mama diyan da yake son su kamar may a ran shi gashi yadda suke masu cin mutunci a bainan jama, a kowa naji don har sun fara tara masu makwabta a gidan don ihu da Lawisa ta yanka ya jawo hankalin mutanen shiya. Basu kai ga ci gaba da magana ba sukaji dir mota sai ga wasu mata biyu sun shigo gidan suna fadin sun zo daukan amarya ne Jatau ne ya turo su don su yan uwan ango ne Jatau. Nan su Rukkaiya suka shiga zagin bakin suna masu rashin mutum ci sai da kyat ranan baba ya gwada masu ta maza haka suka shuga daki da ita tana shiri tana kuka. Ga shi mama sunyi fada da aminiyar ta Larai babu wanda zata nufa a makwabta takai kukan ta. Mama ta shiga daki cikin sanyin jiki tana cewa Lawisa kiyi hakkuri nasan amanane ya koma muna akan ki tun ba aje ko ina ba gashi Allah ya nuna min abinda naso yiwa yar wata ya fada kaina. Nasan na cuce ki na cuci rayuwan ki abinda Allah ya kaddaro muna gani ke nan wanan daren a kan ki Ki daure kije gidan nan don rufin asirin mu da na ki don kin san Jatau ba mutunci ne dashi ba. Kan kudin nan yana iya ya daure ni har uban ki ko ya sayar da dan gidan nan da muka mallaka a duniya. Muryan daya daga cikin matan da suka shigo daukan amarya ne ke cewa ayi a fito da amarya mai akori kura yace zai tafi jigilan shi ne. Yau abinda mama ke son gani a gare sai gashi a kanta burin mama shine ko yaushe tagan mu ni da mahaifiyata a cikin kuncin rayuwa. Idan ta gan mu a haka takan ji duniya yai mata dadi kamar ta zuba ruwa kasa tasha ta kanji a lokacin. Haka aka fito da Lawisa zabban tausayi tana kuka tana tirje tirje aka kada ta a mota sai tabarma da filo da mama ta bayar aje mata dashi tace daga baya zata sayo mata kayan aiki a kawo mata. Aka fito da ita sai guda yara da manyan uguwa suke yi yan gulma suka shiga motan zuwa kai amarya gidan mijin ta. Lawisa sai kuka takeyi a gaban mota zuciyata fam da bakin ciki tausayin kan ta takeyi yadda zatayi rayuwa da tsoho irin jatau a matsayin mijin ta. Haka aka isa gidan da ita tana matsanacin kuka suko mata sai guda da shewa sukeyi yayin da Lawisa take jin kanta kamar tana cikin kabari ne a lokacin. Allah ke nan yadda sukai min sai gashi ya mayar masu da abin su tun a nan duniya sunga kayan su. Har gara nawa akwai rashin sanin ciwon kai da kurriciya a tare dani lokacin kuma gara nawa mijin sau dubu da nata ita. Wani rubaben daki daya gyara mata shi nan aka saka ta daga ita sai yar tabarman kwancin ta don ko katifa bata samu ba a lokacin. Yan uguwa sukai mata nasiha yadda manya keyi idan an kawo amarya yi nayi bari na bari a zauna lafiya kiyi biyayya ga mijin ki da matan shi sai a zauna lafiya da kowa. Daga can kofa sukaji wata tace kada Allah ma yasa tayi mu ai nan ko da may tazo mun fita gidan Jatau ne fa ta shigo. Ashe daya daga cikin sarakan gidan ne tazo ganin gulma taji ana wanan nasihan ta cabe da bada amsa. Su dai basu tanka mata ba suka fice gidan suka barta zaune saman yar tabarman ta ta hade kai da gwiwa tana rusan kuka sai Allah ya isa take aikawa mama da baba a lokaci daya ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: A Lokacin ne,,,, IDAN BAKI BIYABA KADA KI KARANTA YAR UWA DON HAKKIN WASU NE,,, Zaune take a kofan dakin ta tai tagumi sai faman tunane take tana kulawa tana warwarewa ita kadai a gidan don mijin ta ya fita tun safe zuwa gurin aikin saukalen da yakeyi gurin manyan motoci , Sai idan ya dawo ne suke dora girkin abinda zasuci kullun a haka suke wanan rayuwan wahalan ita da iyalin ta, Yanke shawara tayi a inda take zaune gara ta hada kayan dakin ta ta,sayar ta,dan samu koda tsohon fridge ne ta,saya tana sana,an kayan sanyi ko zata samu kobo yana dan shigo mata a hannun ta, Ba bata lokaci da mijin nata ya,dawo gida batai nauyin baki ba tafara fada mai shawaran da ta yanke, Shiru yayi tare da nisawa inda yake zaune saman tabarman shi, da yake shan iska a kai, yace Halima banki shawaranki ba gaskiya amma ni a nawa tunanen da kiyi hakkuri ki zauna da kayan ki don wanan lokacin da muke ciki lokaci na lahaula ga kowa ba masu kudin ba ba tallakawan ba kowa wiwi yake yi da wanan karnin, Koda kin sayar da kayan dakin ki don kiyi sana,a ina mai tabbatar maki rayuwa bazai bari ka mayar da ko kwatankwancin abinda ka rasa ba a baya kinga hasara da dana sani sai ya hau mutum, Ke dai kawai ki bar kayanki tunda Allah bai hana muna dan abinda zamuci ba a rayuwan mu to ai alhamdullahi komai yanzu sai hakkuri don ba kowa ke samun yadda yake so ba, Matar tanisa tace ni dai gaskiya nayi niyya da kabarni kawai na sayar a samu, dan gurin rage wani hanyan kuma. Ya fahinci bazata dauki shawaran shi tayi hakkuri da jarabbatar talaucin da suke ciki ba don haka sai ya kyale ta tayi yadda take so kawai. Don yanzu ba matan birni ne kawai ke bijirewa girmama wa dokan mazan su ba har ma da matan kauye haka suke don yadda zamani ya juya a lokaci ne muke ciki, Bai gida washe gari baya gida takira dillaliya sukai cinikin kayan dakin ta tazo ta kwashe akan dan kudi kalilan tabar mata su, Ba bata lokaci ta hada kudin tana jiran dawowan maigidan ta ta fada mai ya barta taje ta dan samu abin da tai niyar saye da kudin, Bai mussa mata ba don yasan kudin ta ne don haka ya kyale ta tayi yadda take so da abinta don yana gudun yai magana ta ga kamar yana son wani abune daga cikin kudin, nata. Bata tsaya bayan sallah magariba ta shirya sai gidan wata dillaliya mai sayar da kayan hannu, inda tai sa,a tasamu fridge har guda uku a gidan da akasa a kasuwa nan sukai ciniki ta samu dan babban wanda bai tsufa ba sosai ta saya da kudin nata, Suna barin gidan ta turo mai baro ya daukan mata shi zuwa gida zuciyar ta fam da farin ciki a ran ta, Da mijin nata,ya,dawo yai mata fatan alheri da,daukaka a cikin al,amarin. Tun daga wanan lokacin ne tafara dan sana,a da fridge din nata tana dan samun kwabon kashewa ta fannin ta ita ma, Hakan ne ya kawo mata saukin yan damuwan yau da kullun da take ciki don tana dan samun kudin kashewa a wanan fannin nata. ****** ********* ****** Safiyane duk jama,an gari sai faman zirga zirga suke kowa harkan ga ban shi yake yi ba mai kama hannun yaro daga cikin su. Sai faman sallama ake a gidan gwago Asmau da manyan kuloli gurin sayen masan da take soyawa tun da farar safiya. Gwago Asmau taji dadin kasancewar Bintu da ita a yau din don ba karamin taimaka mata takeyi ba. Komai cikin natsuwa Bintu takeyi ga tsabta sai ta wanke hannu da da kayan aiki kafinta taba shi, Sannu sannu tafara gyara ma gwago aiyunkan ta sabanin yadda take aikin ta a baya in local way, Bintu taba gwago shawaran cewa ta mayar da masan ta na zamani don yanzu akasarin mutane suna fama da lalurar ciwa gyambon ciki watau ulcer, Gwago Asmau tai mamakin yadda Bintu karama da ita tasan wanan dubara gashi kuma daga kauye take zaune, Don Bintu ta bata shawaran cewa yanzu da safe zasu dinga kai nika kuma su toya shi, a lokacin, Gwago Asmau tace kai haba Bintu ni kada ki jawo min hasaran kudi yaya zaki ce na kai nika ranan kuma na soya masa a ranan, Bintu tace wallahi gwago ki gwada masan ki zata samu karbuwa sosai wallahi don duk masu tsoron cin masa don tsamin shi zakiga sun fara sayen shi, Gwago tace yaya zan yi wanan aika aikan haka Bintu na, Bintu tace gwago zamu wanke shimkafan mu fara sai mu barta a jike cikin ruwa ta kwana da safe zamu tsamay mu hada da dan falawa dai yadda muke son shi sai mu hada da dafafan shinkafa da yis da baking powder, Sai a kai nikan shi ayi muna kullun shi na ruwa amma kada a cika ruwa da yawa gurin nikan shi idan an dawo sai k8 dan kara gurorin dafafan shikafa da kaurin shi yadda kike bukatan shi, Sai kawai a fara soyan shi kamar yadda ake masa a koda yaushe, Kai yan nan akwai ki da dabara kamar wata babban mace ke a ina kika koyo wanan masan kuma, Bintu tai murmushi har dan dimple din ta ya lutsa kadan tace nima a gurin wata makwabciyar mu dake masa a bauchi sukai zama, naga tana hakan. Yadda Bintu ta fada hakan sukayi sai dai gwago Asmau sai Allah Allah take kada abin ya bashe su sai da taga zubin farko masa yafito da kyau hankalin ta ya kwanta, Nan da nan masa ya kare masu washe gari masu sayen masa sai yaba dadin masan jiya sukewa gwago Asmau, suna cewa kai masan jiya ga taushi ga dadi wallahi babu tsami ko kadan, don har miyan sai da bintu ta sa aka dan zuba mai dan baking powder kadan, Nan da nan labarin dadin masan gwago Asmau ya dan kewaye shiya, don dadin shi. Daga gidan malam Habu aka aiko asai masan dubu da dari biyar sai aka samu akasi babu canji a gurun gwago don haka aka ba su masa kawai, sun biyo canjin . Sai da yamma ne gwago ta ba Bintu canji ta kai gidan rayuwan Asmau bai so ba don bata son dabi,ar shiga gidajen mutane ita. Haka yasa tun zuwan ta garin bata je gidan kowa ba, tana cikin gida gurin gwagon ta kawai sai nikan da tafita da,safe tabi almajirai, don taga yadda za,a nika masu kullun masan su. Hijjab din ta ta saka tare da sa dan sifas din roban ta sai gidan duk da dai kwatancen gwago tabi don shiga gidan, A hankali tai sallama daga kofan farko na shiga gidan babu kowa sai flawer a shuke daga can nesa ta hango wani saurayi a duke yana sa takalman kwallo a kafan shi da alama shigar shi ya nuna cewa gurin wasan kwallon kafa zai tafi. lna wuni tace tare da dan duka mashi har kasa batai tsanmani ya amsa mata ba sai cewa tayi don Allah ina hanyan da zan shiga cikin gida canji na kawo na masa. Fuska a murtuke ya nuna mata da hannun shi, ba tare da yai magana ba, Inda ya nuna mata ta nufa a hankali sai dai tana shiga duk ta daburce don gina ne na part din mata hudu ko wace da nata daban, Yanzu ni ina zan nufa ta fadi a ranta batare da tasan wanda zata kaiwa canji ba. Tana shiga tai tsaye tana ta faman kwada sallama ita ka dai a tsaye shigowan wata mata gajera fara mai kiba yasa ta mayar da hankalinta ga matan, Ina wuni take ce mata cikin ladabi matar ta,amsa a,dadare da fadin lafiya, Bintu tace canji aka ce na kawo daga gidan hajiyan masa, kamar yadda ake kiran gwago Asmau, dashi a uguwar, Cikin wani irin kushe fuska take cewa isa mana ki tambaya ciki tun nan ta fahinci akwai kishiya a gidan ke nan , Tanan tsaye sai sake, sake, take a zuciyar ta, tana niyar juyawa ta koma ne taga wata mata baka, tafito daga wani shiya dake daga can gefe tsabare da sauran shiyan , Hannun ta dauke da bukiti da mopa da tsiyatsiya da alamar da ga shara take futowa matar. Itama dai cikin ladabi ta gaida matar da ta gani ta amsa mata cikin sakin fuska. Tana cewa sannu ko kina neman wani ne ko Bintu cikin murmushi don taga fuska, tace dama canji ne akace in kawo inji Hajiyar masa, Au daga gidan hajiyan masa kike ne, ? Eh a nan nake tana kokari miko canjin dari biyar din dake hannun ta din, A shigo mana daga shigowa har zaki tafi zo shigo daga ciki kinji ba mussu Bintu tabi bayan ta zuwa part din da matar ta nufa. Suna shiga dakin taga ashe daga ciki a kwai dakuna da kuma kitchen, a cikin su. Kujeran dake a falon gidan ta nuna mata ta zauna tare da kara gaisawa da ita, Amira Amira matar ke kira daga falo, sai ga wata yarinya doguwa zata dan girmay ma Bintu tafito daga dayan dakin dake part din, Tana ganin Bintu zaune sai kallon ta take da mamakin ko wacece ita, gaida yarinyar mai suna Amira Bintu tayi. Maji gani inji Amira din tana mai kallon uwarta, don son jin mai zata ce mata. Karbi canjin nan jeki sauran dakuna ki tambaya wa hajiyar masa take bi canji dazun da safe, Amira ta turi baki gaba tana cewa ni wallahi in ba dole ba ban sin shiga gurin kowa a gidan nan don dai kawai da mutum ya shiga yanzu za,ace ga abinda yayi kuma. Aiken ki fa nayi Amira kika tsaya mai da naki ba,asin son raki haka Amira taja kafa ta,wuce zuwa sauran sassan gidan, Inda Bintu take zaune maji ta dan kalla tana fadin yi hakkuri kinji har ta dawo muji ko canjin waye, Andan jima kadan sai ga Amira ta dawo tana konkwami tana fadin wai, maman su Hadiza tace takawo ta aje ko na baba ne amma taki bata ga kudin tana kokarin mikawa mahaifiyar ta kudin hannun ta, Amira mai yasa baki bata ba da kika dawo da kudin nan may zanyi maki dashi a nan , Maji cewa fa tayi wai zata ajewa Baba ni kuma nasan ba,bashi kudin zatayi ba shiyasa nace mata tabari na tambaya sauran shiya muji in ba nasu bane, Yadda maji take magana da yar ta acikin lumana ba daga harshe ya ba Bintu shawa sosai sai faman bin su da kallo take yi, na sha,awa. Yadda uwa takewa yar ta magana a cikin kwantar da hankali da fahinta, Inda Bintu take a zaune Maji ta,waiga tana fadin inaga canjin Alhajine idan ya dawo zan tambaya muji in har ba nashi bane zan sa su dawo mata da kudin. Bintu ta mike don fita daga dakin a daidai lokacin da Umar ya shigo dakin ke nan babu ko sallama. Sai cewa yake ni zan tafi ball kada kuma ace ban fada ba natafi , yana,wani cicin magani cikin dakewa, Haba babana kai wai yaushe ne zaka girma zaka shigowa mutane daki babu ko sallama kana wani shan kamshi da cin magani. Kamar wan da zai tafi gurin wani abin arziki wai ball, ball din mai zai tsinana maka a rayuwanka ne wai, Maimakon ya tsaya yaji karshen maganan ta,sai juyawa yayi kawai ya fita daga dakin, A hankali maji ta sauke ajiyan zuciya tana furta Allah ya shirye ka babana, Bintu dake tsaye ta amsa da Ameen Mama sosai har cikin ran maji taji dadin Ameen din da Bintu ta amsa mata dashi. Mama ni zan tafi sai anjima ke nan zan fada mata yadda akayi, to kin ji yar albarka ki gayar min da Hajiyar masa din kinji , Bintu takai kofa Maji tace may ye sunan ki ne bakuwar hajiya ? Cikin murmushi Bintu ta amsa da Bintu nake mama Allah sarki sunan mai kyau sunan mahaifiyar maigidan nan ke nan ai. A waje ta samu wanan mai bakin ran yana tare mashin zai hau ko kallin shi batayi ba don tsoro ma yake bata, ita, ****** ********** ***** Kida ke tashi daga cikin waya daga daki yayin da uwar ke daga gurin wanke wanke tana wanke kwanukan da suka ci abinci dashi na daren jiya, Ganin hankalin uwar yana ga aikin da takeyi yasa Raiha mikewa a hankali zuwa gurin da ta boye kayan harkan ta a ciki ta jawo wani kwalba ta kwankwada son ranta tai wani jan iska da tsuke bakin ta a hankali. Ta koma saman gadon da ta tashi a kai, ba bata lokaci sai barci ya dauke ta a gurin. Uwar na shigowa daki taga yadda ta kwanta daidai da ita, a hankali uwar ta kada kan ta don takaici tana dan kiran sunan ta , Ke Raiha Raiha fa wai bazaki tashi ki yi abinda zakiyi bane ki kwance haka galala tun safe kamar mara lafiya. Cikin murya irin ta mashaya Raiha tace kai haba mama please easy please easy barci nake ji fa. Ikon Allah barci dai barci dai kamar wata malalaciya sai kin tashi ki ce wai ke yunwa yunwa kamar zaki hadiye mutane, lokaci guda. Nan uwar ta barta ta,tafi tana mita a kanta a lokacin ta gyara kwanciyar ta da kyau taci gaba da barcin ta. Bata farka ba sai yam lis ta farka sai bandaki tafada tana sauri don fitsari da kashin da take ji a lokaci daya. Bayan ta dauki lokaci tafito ne daga ban dakin shine ta debi ruwa a randa ta watsa don ta dan ji jikin ta ya sake mata don nauyin da yai mata a lokacin. Tsab ta shirya cikin wasu kananan kaya ta,dauko hijjab din ta tayafa a kan ta kamar wata ta kirki can. Inna ni zan fita tace a gadarance uwae tace ina kuma zaki yanzu ana batun yin magariba kuma ? Ba nisa zan tafi ba zan dan je can kasan layin mu ne na,dawo . To ki daiyi sauri kafin mahaifinki ya dawo bai samay ki ba. Yanzun ai zan dawo ba dadewa zanyi ba Inna, tana fita ta tare mashi sai wani uguwa da ke da yawan mutane akasarin su duk matasa ne maza da mata birjit a gurin. Kutsawa tayi itama tashige gurin can wani dan lungu wani gaye ne ta nufa yana zaune tsakiyan su sai busa hayaki yake, Yana saye da,riga blue mara hannu a jikin shi duk mozuqu din shi sun fito wahe sosai. Yana ganin ta tace yar halas yanzu fa nake zancen ki a,raina nace ko kayan basu kare bane har yanzu don tun shekaran jiya baki leko mu ba nagani, Ina tafe ai na tsaya ne har na karasa sauran wanda ya dan rage min don gudun kada na tara kwalabe a dakin namu yai yawa. Kasan gyatumar ba sanin kai tayi ba har yanzu bat da sau nake mata koda ta rutsani nakan ce mata maganin mura ne nake sha ai, Shegiya baby watau dai a kwana kike sakata ke nan dai ko? Kai ma kagane ke nan ai don abin sai da kwana don ba,a,bari ai saurin sani abin. Nawa kiia zo dashi don kin san ranan ma na biyo ki canji dai ko? Nawa ka biyoni brosha ina dari uku ne dai kawai ko? To dari uku ba kudi bane dasu ne ai muke karawa muna business din ga,shegun kwalawan nan kullun sai kokari suke suga,sun kama mutane don kawai su caji mutum dan canjin kashi badon a,daina harkan ba. Ni dai kaji miko min kaya na natafi don yau ba dadewa zanyi ba ina sauri ne. Wasu kala za,a baki akwai fa,sabbin fitowa masu aiki sosai wallahi tace cikin tsiwa bani dai wanda ka saba bani kawai na,wuce na biya shagon Samuel na kara dan kwalabe a can, Daidai lokacin Umar yazo baiyi magana ba,sai kudin da ya miko mashi yace kaibani nabar gurin nan don ban son sa ido da yawa. Brosha amma kasan sai ka sallameni zaka sallami wani can ko? Umar yana daga gefe ya harde hannayen shi a kan chest din shi ya zuba masu ido yana sauraren abinda sukeyi kawai. Sanin ko waye Umar yasa brosha fara hado mai kayan shi don yana kai wata biyu baizo gurin ba yafi aikowa a,saya mashi, Yana kokarin miko mai canji tare da kayan shine fam cike da leda, yaji muryan Umar yana fadin ka bata da sauran canjin sai wani lokaci kuma ya juya yatafi a bin shi bai tsaya jin may zasu ce ba, Binshi da ido Raiha tayi tana,mamaki mutum haka ga alheri ga kuna ta hango jin kai a tare da shi. Mtwee tace tare da juyawa tace kai bani na,wuce kaji ban son bata lokaci nace ma, Aike yau kin taka sa,a wallahi haka yake in har yazo sai yai wa wani alheri a gurin nan, sai dai kuma ba kullun ne yake zuwa ba, Tana karba ta juya tabar gurin don zuwa chemist ta sayo sauran abubuwan ta. Tana fitowa yana,shigewa mota ya harba yabar erea din don gudun wani ya ganshi idon sani yasa yake zuwa wanan uguwar sayen kayan mayen shi can nesa da gida. Ko da Raiha ta isa gida lokacin har takwas da rabi na dare. A lokacin mahaifinta har ya dawo daga kasuwa sai dai yana daki shi yana rage kayan jikin shi. Hakane ya bata daman shigewa ciki batare da yasan dawowan ta ba gidan. Ganin ta kawai mahaifiyar ta tayi don haka hankalinta ya kwanta don tasan da zaran mahaifinta ya ji bata gidan matsala ya faru ke nan. Tafito daga dakin mahaifiyar ta,a,daidai lokacin da mahaifinta yake kokarin zama a,saman tabarma a kofan dakin shi tana cewa baba sannu da,dawowa kawai ta,sa kai ta shige abinta, Ashe tana gidan ai yanzu nake batun nace wai tana ina ne banji motsin ta ba uwar tace tana ciki ai tundazun, (Uwa ke nan,) Nan ya zauna yana cin abinci suna hira da mahaiyar Raiha cikin so da kauna a tsakanin su, ****** ********* ****** Yaro ne daga kofan gida yake kwada,sallama yana cewa abani ruwan pure water, na naira goma. Da sauri Hanne tafito daga dakin ta tana cewa shigo ka karba kaji ta bude dan fridge din ta ta dauko mai ruwa leda biyu ta bashi ta karbi kudin zuwa dakin ta, Ba,ajima ba wata yarinya tashigo itma ta saye haka mutane suka gane cewa tana sayar da,ruwa ana dan shigowa gida ana,saye. Nan tai shawaran ta fara dan kayan sanyi irin zobo da kunun ayya tana hadawa dashi ko zata kara cabawa ga samu, Kudin ta bayar aka,sato mata kayan zobo da na kunun ayya ta hada. Ba bata lokaci aka ganeta mutane suna shigowa,saye tun dai da,zafin ranan da,ke yawa a garin don ko baiyi sanyi sosai ba ana saye hakana. Ance rai da kwadai don haka Hanne tafara shawaran canza fridge din ta zuwa wanda yafi wanda ke gare ta girma don ta kara bun kasa sana,an ta dashi. Da maigidan ta yadawo ta fada mai ahawaran da tayi shiru yayi don baida na fadi, don baida na fadi saboda yasan cewa shi kan shi yana amfana da wanan sana,an data samu tana dan yi yanzu. Saboda yana tare masu gurare da dama na yau da kullun a gidan har ma,da wanda bai zata ba don yan zu a lokaci ne muke inda mata suke bada nasu gudun mawa a gida fiye ma da yadda ba, zata ba a rayuwa ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: A LOKACIN NE BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAIJIN KAI, ALLAH NAGODE MA DAKA BANI WANAN DAMA NA RUBUTA WANAN LABARIN DA KE DAUKE DA YADDA RAYUWAN ZAMANIN NAN NAMU MATSALOLI DA ILLOLIN DAKE CIKIN WANAN RAYUWAN NA WANAN LOKACIN DA MUKE CIKI ALLAH KA BAMU IKON AMFANI DA FADAKARWAN DA ZAMU TSUNTA A CIKIN WANAN GUNTUN LABARIN,,, IDDAN BAKI BIYABA DAN GIRMAN ALLAH KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE BADA YARDANA BA,,,,,, Zaune take saman sallaya a gurin da ta idar da sallah hannun ta ya na dauke da farar tasbaha tana ja a hankali sai dai a zahiri ne hakan a can cikin kasan zuciyar ta tunane fam a ranta tana tunanen ko a halin yanzu ina dan ta Umar ya shiga, Kadan kadan tana daga kanta tana kallon agogon dake manne a,bangon dakin ta a hankali, Karfe goma,sha daya na,dare saura agogon ya nuna mata a lokacin hankane ya kara sa hankalin ta, tashi sosai don tana tsoron kada ya shigo mata kamar yadda take zargin ganin shi Tarasa gane wani haline dan nata yake kokarin jefa kan shi a ciki, ga yawan surutun kishiyoyi dake damun ta a a kullun, Maimakon ace sun taimaka mata gurin kara bashi tarbiyan da suke ganin baida shi issashe sai kawai suka buge da gulma da kara mugun zance a kan dan nata wanan al,amarin ne ya ke kara sa jefa Maji a cikin tashin hankali, da damuwa a rayuwan ta gashi dai ita a nata fannin bata kasa da nasu yaran ba, gurin daukan su har a cikin zuciyar ta a,tsakani da Allah take masu komai, Kara daga ido tayi takai duban ta ga agogon bangon dake manne a bangon dakin nata, Karfe sha biyu saura yan mintina na dare ta gani haka ya kara tayar mata da hankalin ta, Bata kai karshen tunanen taba taji an turo kofan dakin ta, da karfe inda sabo da hakan tasaba tasan ba mai mata wanan halin sai maigidan su, Ba sallama sai cewan da yayi a hasale wai ina danki ya tafine ? Shiru Maji tayi don ta saba da wanan kalman na danki a bakin maigidan nasu, Kefa nake tambaya yakara fadi daga inda yake tsaye daga kofan daki rike da labulen dakin nata, A hankali Maji ta dago kanta zuwa kalkon shi tace cikin yar murya siririya ban san ina ya shiga ba ba nima tun dazun nake zaman jiran shigowan shi don yaci abinci, Wani wawan kallo ya watsa mata daga inda yake tsaye yace ai dama nasan da yardan ki yake wanan mugun rayuwan da take don ke ce kike daure mai gidin yake kara lalace wa ai kowa yasan hakan, Hmmm kawai tace tare da fadin Allah ya kyauta malam amma ta yaya zan goyawa Sadauki baya ya dinga abinda yake alhalin nasan ba alheri yake koyawaba a rayuwan shi, Wanan kuma ke kika sani don ke ce da hasara saboda ni ba shi kadai ke gareni ba ai, Yana fadan haka ya gaura kofan dakin da karfi yafita daga dakin nata rai a bace, A hankali maji ta sauke ajiyan zuciya, zuciyan ta yai mata wani tauri saboda kalamin da mijin ta ya fada akan dan tilon danta namiji guda da Allah ya bata a gidan sai yan kannen shi mata da ke bayan shi su uku rak Allah ya bata a gidan mijin nata, Yayin da sauran kishiyoyin ta suke da yara fiye da nata a gidan Maji itace mace ta uku a gidan malam habu dan kasuwa ne shi, sai uwar gidan su mama hauwa mai yara bakwai a gidan,tana aikin a women center, Sai mummyn Asiya, wace itace Maji ke biwa, tana da yara biyar a gidan, tana aikin koyarwa sai amaryan su Anty Kubura da ke da yara hudu ita ma aikaciyar jinyace a wani asibitin gwaunati, Daga cikin su maji ce bata wani aiki kwakwara don ita batai boko mai zurfi ba tana aji hudu secondary malam habu ya auro ta don haka bata da aiki sai yan buga bugan kasuwanci irin na mata da take a gida kawai,, Da farko malam Habu yana matukar son Maji da kuma tausaya mata don bata da ilimi mai zurfi, sosai, Amma yanzu matsalar dan ta, Umar ya wanda takewa lakani da sadauki don kasancewar shi sunan shi Umar faruk, kuma a matsayin shi na dan farin ta yasa take kiran shi da haka, Rayuwan da Umar yake ciki a yanzu yafara kawo matsalar a tsakanin malam habu da matar shi Maji mai suna maimuna,, Matsalar farko dai daga irin yanayin shigar shi na tufafin shi, don sam baya iya saka irin tufafin diyan hausawa na al,ada a jikin shi, Sai kuma gashi ya bullo da dabi,ar son wasan kwallo a rayuwan shi don duk abinda yake da zaran time din zuwan shi filin wasan kwallo yayi dole yabar koma maynene zuwa gurin wanan wasan a duk safiya da marance, na kulli yaumin, Malam habu yayi iya kokarin shi gurin ganin Umar yabar wanan wasan kwallon kafan da yake yawan fita tun yana dan karamishi, Amma abin ya faskara duka zagi da bakar magana ga mahaifiyan shi bai sa Umar ya daina wanan wasan kwallon kafan ba da yakeyi Yan uwan Umar duk yan kasuwa ne sai masu aikin gwaunati daga cikin su amma shi ba ruwan shi da shiga harkan kowan su Iyakar shi yai wanka yafuta gurin abokai sai kuma zuwa wasan ball, da yake a gaban shi, Maji tai nasihan rana taina dare amma bai sa Umar ya daina wanan halaiyar nashi ba Fitan malam Habu daga part din Maji suka hade da Umar wanda ke shigowa gidan a lokacin wani wawan kallon da tsana ya watsawa Umar din, Sannu Baba ina wuni yakai har kasa yana gaida mahaifin nashi a cikin ladabi da biyayya wanan gaisuwan yaran dakin maji ke da wanan tarbiyan a gidan kawai, Uwaka na ce uwaka tare da kara mika mai dakuwa da hannun shi na dama yace yaron banza yaron wofi kawai mai ladabin shegu, Da ban wuni ba zaka gan ni haka ina ka shige haka tun safe sai yanzu zaka shigo min gida, kana wani ladabin shegu haka dakai, Baba bafa ko ina naje ba ina gurin training tun dazu yanzun kuma da zan dawo na tsaya gurin dantani mai shago muna hira a majalisasr su, Training din uwar ka na ce training din tsiya jeka ai tunda rayuwan da kazaba wa kanka ke nan ni ba ruwana inka samo wahalanka kada ma kace ni Ubankane, Umar dai yana duke a gurin da yake baidaga ba yana sauraren kalaman mahaufin nashi, Malam habu ya wuce ciki fuuu yaba ta faman sababi da bambami akan umar din, Daga kai yayi ya kai kallon shi ga kofan dakin mahaifiyan shi wace yasan daga gurin ta mahaifinshi yake yagama zazzaga mata tsiya ke nan a kan shi don haka yasa tafasa shigan da yai niyar yi gurin ta a lokacin, Don yasan yanzu tana can ranta a bace akan rashin ganin shi da batayi ba yini guda zur ga kuma baba ya je yanzu ya zazaga mata balain shi da ya saba,, Yashige part din shi ya fara dan rage kayan jikin shi, daga shi boxe din shi irin ta maza ya rage a jikin shi, Dukawa yayi kasan gadon shi ya jawo wasu kwalabe cikin wani leda mai karfi daga karkashin gadin inda ya balli wasu kwaya dake cikin ledan ya bude wani kwalban syrup ya hade su tare ya shanye, a lokaci guda, ya fada saman kujeran shi tilo daya dake dakin, A hankali ya fara zukan syrup din har sai da ya shanye duk ruwan maganin dake cikin kwalban gaba daya, ya wurga kwalban a kasan carpet din dakin, Nan saman kujeran ya dan fara lumshe idanuwan shi a hankali yana rufe su ko may ya tuna sai kuma ya mike daga inda yake zaune zubur ya dauke kwalban daga inda ya aje su ya mayar gurin da ya dauko su, Nan yaja jiki zuwa saman kujeran da ya fara zama ya kara zubewa sama da karfi har saida kujerar yai, dan kara don fada mashi da karfi da yayi, Nan barci ya kwashe shi babu bata lokaci a gurin baifi mintuna ba sai ga Maji wacce ta kasa barci ta shigo dakin ganin ko ya dawo daga yawon da mahaifin shi yace ya tafi, Maji ta dade tsaye a kan shi tana kare mashi kallo cikin mamaki tayi tayar dashi amma bai tashi ba dole tafita daga dakin tabarshi a hakana, Zuciyar ta fam da kunci sai kuna dan zargi da ya fara darsuwa a zuciyar ta a hankali, A haka ta kwana ranta babu dadi a cikin sa sai faman tunanen da takeyi har dare ya raba sosai a lokacin, ****** ********* ****** Zaune take a f gaban mahaifin ta a cikin natsuwa take sauraren shi, yana mata zance akan zuwa birnin da zatayi gur8n kaunan shi dake can tana aure don ta matsa a kan Bintu tazo mata hutu ta dan kwana biyu a gurin ta, Sam Bintu bata,son wanan tafiyan don dai babu yadda zatayi ne da umurnin mahaifinta da gaskiya bataje ba, Don tafi son ta,zauna a kauyen su tare da mahaifinta don koda take mace ce itace kamar jagoran gidan nasu duk da kasancewar Bintu karamar yarinya , Haka take yawan aikin wahala a kan su samu dan abinda zasuci a gidan su kasancewar mahaifin nata ba,wani mai abin hannun shi bane, Itace zuwa icce itace suyan awara da rana da safe kuma tana koko da kosai kafin ta dawo zuwa makarantan bokon da yake a ranta, Yanzu gashi gwagonta ta birni ta matsa sai tazo gurin ta wai hutu wanda ita bata san dalilin da ya sa,duk tazo sai tai zancen zuwan Bintu gurin ta hutu ba, Yan kayan ta,already ta,shirya su a dan jakar ledan ghana most go karama duk jakar ta tsufa sosai don har ledan jikin jakar ta dan tashi ya,wani dan takure daga jikin shi, Kudi mahaifinta ya ciro daga aljihun shi dubu daya ya mika mata tayi kudin mota dashi, Kallon kudin take tana mamaki inda ya samo har dubu daya yabata wai tai kudin mota dashi, Hannu biyu Bintu ta mika ta karbi kudin cikin ladabi tare da fadin na gode Baba, Bayan ta karba ne yake cewa tau Bintu ki saurareni kiji abinda zan fada maki da kyau, Ki sani dai rayuwar birni daban yake da,tamu irin na kauye don haka kiyi taka tsatsan da duniya ki kama kanki , Ki kawar da idon ki ga duk abinda,bai shafeki ba a rayuwan ki ki tsaya inda gwagon ki ta tsayar dake duk da yake ke yarinyar ce nnatsatsiya amma nasan zakiga abin mamaki da zai iya canza maki rayuwan ki a can, Don haka kiyi taka tsatsan da duniya baki dayan ta a yanzu babu gaskiya ki tsaya a matsayin ki na yar talkawa kamar yadda kika samu rayuwar mu, aciki tun farko, A hankali Bintu tace insha Allahu baba zan tsare kamar yadda kace zaka kuma samayni da kiyayyewa insha Allahu, Yace Allah yai maki albarka Bintu Allah ya tsare min ke da tsarewar shi ta karba da amin Baba idanuwan ta sun kawo hawaye kamar zasu digo dag idanuwan ta, Shi da kan shi ya rakata har tasha inda zata samu motar da zai kaita, garin Sokoto, Tana zuwa motar ta cika suka kama hanya sai Sokoto zuciyar ta fam da kunci a cikin sa, Sai karfe biyu suka shigo gatin na sokoto a lokacin mutane suna ta haramar yin sallah azahar a garin, Mai yar mashin ta dauka kamar yadda akai mata kwatance tace a kaita Sama road, a bakin shagon dantani mai yar mashin ya tsaya da ita, Shi ta tambaya gidan Gwago Asmau mai masa ya nuna mata da kwatance tabiya mai mashin kudi ya tafi ta dauki yar jakar kayan ta zuwa gidan da akai mata kwatance, dashi, Da sallama a bakin Bintu ta shiga gidan ta samu gwago zaune a tsakar gida tana gyara kayan yin masan ta, Tana ganin Bintu ta fara fara,a tana cewa a,a,a wanake gani yau garin namu kamar Bintu, Maraba da yar gwago sannu da zuwa sannu da zuwa tana mata maraba cikin jin dadi da ganin ta, Daki ta nunawa Bintu ta,shiga da kayan ta daga cikin dakin tare da,samun guri ta dan zauna a takure daga gefe guda, Gwago ta,shigo, dakin dauke da kwanon abinci a hannun ta a rufe ta aje a gaban Bintu, tana fadin zauna ki ci abinci sai mu gaisa, Cikin yar muryan ta take cewa gwago sallah nake son nafara yi tace tau Bintu ga bayi can jeki ki kewaya, Sai bayan ta idar da,sallah ne ta fito inda gwagon ta take zaune tana gyaran alaihu tana kokarin karba daga hannun ta, A,a haba Bintu jeki ki ci abinci mana daga zuwanki zaki buge ga aiki haka jeki kawai ki ci abinci kinji Bintuna, Kamar yadda gwago tace haka din Bintu tayi ta koma daki ta zauna tare da lankwashe kafafuwanta a hankali ta bude kulan dake gaban ta shimkafane da,wake da mai da yaji a cikin kulan abincin da gwago ta aje mata,sai salad da tumatir da aka yanka daga saman shi, A hankali take ci a cikin natsuwa har ta kare cin abincin nata wanda ko rabi batayi ba ta mayar da kulan ta rufe wai ta koshi, Bata zauna ba a,tare sukai aikin masa da gwago ranan ba bata lokaci suka kammala komai da wuri, Nan suka samu guri suka zauna,suka,fara hiran mutanen gida gwadabawa, ****** ******** ****** Hasken ranan da ya haska dakin ne ya haska dakin abinda ya farkar dashi daga nauyayan barcin da yake ke nan, Zubur ya mike gami da salati a bakin shi, yana cewa subbahanallahi da sauri ya dan dago daga kwance sai dai jikin shi ya dake mai sai wani nauyi da ciwo yake mai kamar yai wani aiki, Wanka ya fara shiga yafito da,sauri yake shiri don zuwa makaranta saboda duk abinda yakeyi bai wasa da al,amarin karatun shi ko kadan, Yana cikin shiri yaji cikin shi yana wani irin kugi na yunwa duk yai waban shaye shayen nashi da dare haka zai wayi gari yana jin cikin shi kamar yai kwana goma bai saka komai a cikin shi, Don haka da sauri ya shirya ya nufi cikin gida don ya dan samu abinda zai ci a ran shi don yasan cewa yanzu Maji nacan ta aje mai abin karyawan shi ko, Yana fitowa don zuwa part din mahaifiyar nashi ne yai karo da,daya daga cikin kannen shi diyan dakin mama maimuna, A guje yaron yake tafe bai ankara da Umar dake fitowa ba daga part din samarin gidan ba,sai ji yayi sunyi karo da junan su, ba,shiri UMAR yakai mashi nashi yana,fadin wanan wani irin iskanci ne haka zaka bangajeni ko kai makahone wai, Yaron bai tsaya ba don sani zafin zuciya irin na UMAR don yasan idan ya tsaya zai iya shan dukan tsiya yanzu da farar safiyan nan a gurin shi, Da sallama ya shigo falon mahaifiyar nashi Maji tana tsaye a tsakiyan falon tana magana da kaunar shi Amira, Shigowan shi ya sa Amira,saurin cewa ina kwana yaya Umar,? Lafiya kawai ya,ansa mata dashi a takaice ba wani dogon magana Maji dake tsaye jin muryan shi ya,sa ta,waigowa da,sauri tana kallon shi fuska a matse babu walwala, sai wani kallon takaici take mashi, Maji ina kwana ya kara fadi cikin dan dukar da kan shi kasa cikin jin nauyin mahaifiyar nashi, A dadare ta,amsa gaisuwa sai cewa tayi Amira dauko mashi abincin shi a kitchen kinji, Amira ta juya zuwa dauko ma yayan nata abincin nashi kamar yadda mahaifiyar su ta umarce ta da yi, Kujeran dake falon ya nufa don ya zauna wa saman kujera sai dai muryan Maji ne ke cewa ina ka shiga haka jiya Baba na har dare yayi sosai baka dawo gida ba alhalin kasan mahaifin ku bai son wanan bakin yawon har tsawon dare haka, Kafin ya bata amsa sukaji muryan Mummy tana fada tanacewa ina Farukun yake ne wai wallahi bari kaji ba,zan daukan maka dukan min yara ba iskancin ka ya tsaya iya kannen ka da uwarka ta haifa amma baga yarana ba wallahi don bazan daukan maka hakan ba, Ke kuma Hauwa wallahi kiyiwa danki fada yafita harkan yara na a gidan nan tun mu na,sheda juna dake, Tajuya fuuu tafita daga kofan falo ran ta a,bace sai lokacin ta juya gurin dan nata tare da sauke ajiyan zuciya, Tace Baba na kafita harkan yaran matan nan a gidan nan don ban son fitina a,rayuwana daka ganni nan, Dukar da kai kawai UMAR yayi yana kallon kasan dakin ran shi yana kuna don wanan wulakancin da akewa mahaifiyar shi bazai iya dauka ba dole ne ya dauki mataki, Dama yasan don dan wanan rakwashin da yai mai har uwar shi zataji haushi tazo har dakin uwarshi kafa sheda da da yai mai dan banzan dukan tsiya wallahi, Har ya gama cin abincin shi Maji bata tanka,mashi ba saboda ran ta ya baci sosai, dashi saboda yawan maganan da yake jawo mata a gidan nan yaiyawa gaskiya, Jin sallaman shi tayi kawai yana ce mata yatafi sai yadawo zai shiga school don gap yake yanzu da yakare karatun shi, a jamia mataki na biyu da yakeyi, Yana fita takai kalkon ta ga kayan da yaci abinci tana matukar mamakin yadda wani lokaci yake cinye yawan abincin da take aje mashi duk safe sai dai da rana bai wanan cin abincin haka, mai yawa sosai sai da,safe, Nan dai ta kwashe kayan zuciyar ta a cunkushe da bakin cikin dan nata, mai yawan jawo mata fitina a gida da,waje, Jiya da dare mijin su yai mata masifa a kan shi yau kuma da safen fari kishiyarta har daki tazo tai mata still a kan shi dai din guda Haba haba haba dai babana Allah dai ya shirya min kai kawai zan iya cewa don matsalar ka tai min yawa wallahi kowa dai kai kowa dai kai ya Allah kai min dauki akan halin wanan yaron, Ya Allah ka,shirya min su baki dayan su ka,shiryawa sauran kullimin musulmin Allah a baki daya,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,,, A LOKACIN MU KE,,,,, MAJI ce kwance a,saman dogon kujeran dake cikin falon dakin ta, ziciyar ta a cacushe yake mata da bakin da bacin rai ga radadi da zugin da yake mata. Bakomai ke damun zuciyar Maji ba sai irin halin rayuwan da Allah ya jarabi dan ta dashi. Wanda a da can baya ba haka rayuwan shi take ba sai yanzu da girma ya fara shigan shi ne bakon al,amarin ya fara shigan shi haka. Hayaniyar da take ji yana tashi daga cikin gida yasa ta sauri mikewa zaune da sauri, don ta saurara idan dai ba saudakine ya ja mata wani sabin maganan ba kuma a gidan. Aikuwa jitayi mama tana fada tana cewa wanan yaro ya dai zama muna masifa a gidan nan yanzu. Yaro guda ya zama alkakai acikin yan uwa wai mai saudauki ke son mayar da mutane ne haka wai, duk yaro abu ba abu ba ya kai mai duka bugu haka har na tsiya. Sai muryan dayar kushiyarta da take biwa tana cewa ni wallahi karan shi zanyi akan takalman banza zakaiwa yaro mugun duka haka har ka fasa mai baki. Anty watau amaryan su tace a,a kada ki karan shi kijira har shi mahaifin nashi da ya bata shi ya dawo ki fada mai muji ko muga abinda zai yi, Basu suja batashi ba da so sun dauki son duniya sun dora akan shi yanzu ai ga abinda so ya jawo masu sun gani. Maji dake daga daki takai zaune a hankali saman kujeran da ta tashi a kanshi tana maijin zafin maganganun su a ranta don dai ita tasan a iya yinta ba wani gatan da ta gwadawa dan ta, a baya fiye da sauran yan uwan shi. Amma babu yadda zatayi don ance dan kuka mai jawa uwar shi jifa don da bai shiga harkan yaran su kamar yadda ta hore shi da zafin zuciyar shi akan ya rage da bai ja mata yawan magana na habaici ba ga kishiyoyin ta. Wasu irin hawaye ne masu dumi suka fito daga idanuwan ta a hankali, a daidai lokacin Amira dake cikin daki kwance tafito falon nasu. Ganin yanayin uwar,su yasata karasawa kusa da ita ta zauna tanavmai kura mata ido tace yaya sadauki ne ko maji. Don Allah maji ki fita zancen su ki daina zubar mashi da hawaye malamin mu fa na islamiya yace muna ba kyau uwa tai kuka akan dan ta musan ma ma da namiji don Aljannar shi yana ga hannun ki mama don Allah ki yi hakkuri ai ya kamata ace kin saba da halin shi yanzu ki daina bata ranki a kan zancen shi hakana. Suma ai daukan magana ne mai yakai su ga kayan shi tunda sun san bai son raini shi. Baki maji ta bude da nufin tai magana sai kuma bacin rai ya hana ta iya furta komai sai taja bakin ta tai shiru, amma duk AmiraA yarinyace karama zancen ta ya shiga ran ta sosai don haka tai shiru kawai amma a zucuyar ta ba dadi sam wani kunci take ji sosai. Har dare sadauki bai shigo gidan ba don yasan abinda yaiwa kanin shi yana can ana jiran shi dashi cikin gida. Shi ko yanzu daidai yake jin shi dakowa don ya fahinci daga mahaifiyar su har su duyan ta ba mai kaunan su a gidan gaba dayan su. Sai yamma kamar kullun malam Habu yadawo gida ko hutawa ba,a bari yayi ba aka tare shi da zancen sadauki akan yaiwa Abdul mugun duka wai don kawai yasa mashi takalman shi na kwallo yafita dashi gurin wasa. Kai kawai malam habu ya kada yace wanan yaron wanan yaron ya kai min ko ina a rayuwana wallahi. Daidai lokacin Maji ta shigo dakin saye da hijjab din ta mai ruwa light green. Tana mashi sannu da dawowa amma bai karba mata ba,sai cewan da yayi Maijidda wallahi danki ya zama min masifa a rayuwana . Kullun har zullumin dawo gida nake daga kasuwa don nasan da zaran nadawo da,wuya ba,a tareni da zancen shi wanda zai bata min rai ba. Shiru maji tayi tana,sauraren kalamin maigidan nasu a gaban sauran kishiyoyin ta yana cewa ki fada mashi wallahi zanyi maganin shi don na lura kamar ma ya fara shaye shaye ne a rayuwan shi. Niko bari kiji in har hasashe na ya zama gaskiya to wallahi ba zan barshi a gidana ba ya bata min sauran yara na na kirki. Allah ya tsare ya kare Maji ta furta a fili aidama haka kawai zaki iya cewa bayan shi baki da,wani abin fadi ai, Bata ce komai ba,sai hadiyan bacin ran da tayi tare da juyawa tana fadin Allah ya kyauta. Malam Habu yace ai zai zo ya samay ni zan mu hadu dashi don ba zan yarda ya,sabauta min yara ba ga banza. Maji dai fita tayi daga dakin don tasan ko ta,tsaya,babu abin da,zataji banda bacin rai kawai. Din haka taiwa kanta kiyamallaini tabar dakin don bazata iya jure sauraren kalaman mijin nasu ba akan ita da dan ta. Tafiya take zancen mijin nasu gareta yana ci mata rai don zancen sadauki shi ne zance mafi muni dake hada ta,da maigidan nasu. Duk irin kwaram din da,aka,sha a,baya baya akan kishiyoyinta da ita a baya, baya tayar mata da hankali kamar zancen sadauki da ya taso mata a yanzu, Yanzu saboda shi tana ji tana gani duk wanda ya kwaso zancen shi akan tane zai yaba mata don halin dan ta kawai, A kulun kalaman maigidan ta ga dan ta yanzu yana kona mata zuciyar ta da jikin ta ba ma zuciyar ta kadai ba, Ita a,zaton ta ai wanan abin abinda ya shafe su ne baki dayan su bawai ita kadai za,a dorawa laifin ba don itace mahaifiyar shi ne kawai kowa ke ganin laifin ta ita kadai. Abin da ya kamata su taru su nuna bacin ransu a kai su tayata bakin ciki amma sai gashi kowa ya,zamay yabarta da laifi ita daya. Amma babu komai ta furta a,ranta tare da hade yawun bakin ciki a cikin ta, tana mai sauke ajiyan, zuciya kawai. Bata ankara ba,sai hawaye kawai taji yana biyo mata a idon ta. Gaskiya zancen Sadauki yana tayar mata da hankali sosai ta rasa wanda zata kai kukan ta gare shi ya tayata bata shawara a cikin gidan. Don duk yanzu suna matukar nuna mata kyama akan zancen shi gabadayan su gidan har shi maigidan kan shi. Shin may nayiwa Allah da yai min wanan mumunan jerabawan haka akan dan tilon da daya da Allah yabani namiji a duniya ? Ni dai nasan harga Allah ban cuci dan kowa ba a rayuwana da wanan jerabawan yafado a kaina. Duk da ni marainiya ce na riki maraici na ban kai kaina inda Allah bai kaini ba, ina zama a matsayina na mara galihu har a gidan aure na. A hankali ta kara lumshe idanuwan ta tana tuno rayuwanta na baya da kuma irin kokatin ba yaran ta tarbiyan da takeyi. Ba komai take kara tunawa ba,sai irin dafin bakin da maigidan su yake mata a,baya, Da yakan ce maijidda duk da ba komai ke gare ki ba,a,duniya ni ina sonki a yadda kike. Don kina da komai da nake bukata sabida ke ta daban ce acikin matana, ba zan iya jure rashin mace irin kiba . Kallo daya in nai maki yana wanke duk kan wata matsalar rayuwana don haka nake kwadayin samun zuri,a dake don nai alfahari dasu koda bayan rayuwana ne. Murmushi gami da hawaye ne yazo mata a lokaci guda ta furta namiji kanin ajali. ****** ********* ****** Akwana a tashi yau Bintu satin ta hudu gurin gwago Asmau a garin sokoto. Kullun sauraren take raji gwago na mata zancen zuwa gida amma shiru kake ji ba zancen, har ranan ta gaji tai wa gwagonta zancen komawan ta gida amma sai gwago take ce mata. Haba Bintu yanzu ke har kina sha,awan komawa gida gurin wanan bakar matan uban naki mai mugun nufi a kanki ko yaushe. Nifa da mahaifinki mun yanke shawaran kiyi zaman ki a nan don yace hankalinshi yafi kwanciya idan kina a guri na ko kiyi ni sa dasu kadan. Don haka ki kwantar da hankalinki kiyi zamanki a nan ba zancen komawa gida don hankalin mahaifinki ya kwanta. Badon Bintu taso ba dole ta yarda da zancen gwago din don tasan haka zancen yake. Kullun adduan mahaifinte ke nan akan Bintu Allah ya kawo lokacin da zaki bar gidan nan zuwa wani guri ke ma ki huta hakana wa rayuwan ki. Tunda mahaifiyarki ta barki bata damu da damuwar ki ba ko wani hali kike bata sani ba. Gaki yarinya natsatsiya duk halarcin da kikewa matar nan da diyan ta kina bauta masu dare da rana ba gani take ba. Amma kiyi hakkuri da irin rayuwan da kika tsinci kanki a ciki haka Allah ya kaddara maki taki rayuwan zai kasance a gidan uban ki. Hawayen da ya silalo mata ne ta dan sa gefen hannun ta ta share a hankali. Duk lokacin gwagon tana kallon ta a cikin muryan kuka ta dan dago kanta a hankali tace to gwago zancen karatuna fa ? Wanan ba matsala bane ai Bintu zan yi magana a,samo maki makaran tar jeka kadawo dake can kasan layin mu ta gwaunati sai kici gaba da zuwa ko? A hankali Bintu ta,daga kai alaman taji ta juya jiki ba karfi zuwa cikin dakin kwanan su don ta gyara masu saboda yamma yayi kuma,su basu sharan dare saboda ance baida kyau, yana kawo tsiya a gida. A kwana a tashi ba,wuya a,wurin Allah Bintu tafara zuwa makaranta kamar yadda gwago tai mata alkawari a baya. Da yake Bintu yarinya ce mai hazaka baiwanta daga Allah ne, sai bata sha wani wuya ba sosai a cikin karatun ta komai tana ganewa yadda ya dace. Yawan aiken da take mata gidan malam Habu yadan sa tasaba da Maji da yaran ta don a gurin su kawai take dan samun fuska a gidan ko su ba wani can sosai ba. Sai dai idan Maji ta aiko sayen masa in har Bintu ce a kan tandar suyan waina sai ta cika masu kula fam tace akaiwa maman ta. Haka yasa watarana Maji tasa su Amira su dan yi kwalemar kayan su su ba Bintu don taga tana da bukatan haka saboda rashin wadatan da basu dashi ita,da,gwagon nata. Gwago Asmau batai sanyi a kafa ba gurin shiga gidan don taiwa maji godiya ita da yaran ta, da suka ba yar ta kyautan kaya. Ta shiga gidan bayan sallah azahar lokacin Bintu ta dawo daga makaranta ke nan. Tare suka shiga ita da Bintu din, inda suka samu maji zaune a falon ta kasan tias din dakin nata tana gyara wani ganye da,alamar magani take hadawa dashi. Sallaman su yasa ta dan gyara tana mai ansa masu sallaman su da fara,a a fuskan ta. Sun gaisa da,gwago inda tafara zabga masu godiya tana mata fatan alheri akan alherin da sukai wa yarta, Bintu. Cikin murmushi Maji take cewa ai Bintu yarinyar kirki ce halin alherinta ne yasa sukai mata haka. Sun dan fara hira tsakanin gwago da Maji inda gwago ke cewa wallahi nakan so shigowa mu gaisa da ke, amma kuma yanayin gidan naku ne baida dadin shigowa don kowa idan ka,shigo sai ya,dinga ma kallon munafuki. Maji tace haba dai hajiyan masa ai ba yau muke dake ba koma sun zarge ki da hakan ai su ma mutanen arzikin su suna shigowa gidan nan amma ban damu dasu ba ni. Gwago tace ai babu komai insha Allahu zan dan dinga shigowa idan na,samu lokaci. Suka mike suna,wa junan su sallama nan gwago ke cewa ina Sadauki ya yashiga kwana biyu bana ganin shi dai. Murmushi Maji tayi tana cewa yana nan baidai zamane suna batun rubuta jerabawan su na karshe ne shi yasa ba,a ganin shi yanzu. Allah sarki inji gwago Allah ya taimaka Allah ya bada sa,a Allah ya tsare muna su daga duk wani abinki dana sheri a rayuwan su. Amin inji maji inda taji dadi sosai da addu,an mai masa da,taiwa sadauki wanda ta dade rabon da taji wani mahaluki yai mashi wanan adduan. Har,zasu fita Maji tace su dan tsaya tazo inda tashiga daki ta dauko masu dan sabulun wanki da clean cikin irin wanda mijin su yake kawo masu duk sati don wankin tufafin su. Gwago tana ta godiya da fatan alheri ga maji suka fito, a tsakar gidan nan suka hadu da amaryan su tana shigowa gwago na gaishe ta wani kallo ta,watsa mata na ke wacece ? Gap da zasu fita daga get din gidan suka hadu da sadauki yadawo ko kallon arziki basu ishe shi ba sai ma gwago ke ce mai Umar sanda mazan fama andawo daga bokon ke nan ? Ya wani sha toka fuska babu walwala ya ansa ciki ciki Maji dake tsaye daga bayan su data rako su take ce mai bakajin hajiyan masa tana gaida kai ne sadauki Yace cikin wani murya ai na amsa mata mana ya shigewan shi part din su na,samarin gidan. Allah ya shirya ka inji maji ta furta a fili sai gwago tai dan murmushi tace amin ke dai ai yaran yanzu sai addua kawai. Ke dai kibi abinki da,addu,a Allah yasa halin iya kurciya ne kawai . To Amin hajiyan masa halin wanan yaron sai shi wallahi haba bari fafin haka mana inji gwago ke zaki kara jan abinki ga jiki kina lurar dashi dasannu zai bari ai wanan kurciya ne Allah yasa takara fadi tai masu sallama ta tafi. Bayan sun tafi maji taga yadace tabishi dakin shi suyi magana tunda Allah yasa yashigo a gaban idon ta. Yana duke yana hada wayan tv tashigo dakin abinda yasa shi saurin dagowa ke nan daga inda yake duke. A hankali take bin dakin dake hargitse da kallo sai warin dakin irin na,samari ke tashi daga dakin. Cikin ya mutse fuska take ce mashi, yanzu kaiko inda kake kwana baka iya gyarawa babana ace dakin dan musulmi ne haka inda ake ibada? Wai may ke damun kane haka babana na zaci kaine mutim na,farko da za,ayi koyi da halin shi nagari a gidan nan sai dai kasshh ban samu hakan daga gareka ba sadauki. Naga alamar abinka ba mai yankewa bane, sai a lokacin yadago kai yadan kalli mahaifiyar tashi yana fadin may kuma nayi yanzu maji? Yanzu fa na dawo daga makaranta tun safe da nafita gidan nan . To babana shine baka iya,gyara muhalin ka haka dubi fa kagani ai wanan wani abin cutarwa ma yana iya shigo maka baka,sani ba. Zan gyara ya bata ansa a takaice don yasan duk lokacin da tai amfani da kalaman babana a,gars shi maganace ta kwantar da hankali da fahinta take nufi a gare shi. Don ba ko yaushe take amfani da kalman babana a gare shi ba tafi kiran shi da,Sadaukin da kowa a gidan yake kiran shi kamar yadda mahaifin shi yake kiran shi dashi tun yana karamin shi dashi. Ta,dan dade a,tsaye tana kallin shi a cikin tausayawa dan nata ga,irin rayuwan shi ta bahagon halin da ya,fada ciki. Hawaye ne ya,gangaro mata a,daidai lokacin da ya,dan dago kan shi ya kalleta don jin da yayi tayi shiru a,tsaye bata fita ba daga dakin. Shiru yayi yana kallon ta sai ya dan dukar da kan shi gareta, tace babana ban son ganin rayuwan ka haka . Wanan rayuwan da kake yi ba,shine irin rayuwan da na,soka dashi ba a,rayuwan ka. Don Allah babana ka canza rayuwanka a gidan nan ka koma kamar ko wani yaro na gidan nan. Ina son naga ka canza ka koma normal life din ka kamar kowa a gidan nan wanan halaiyar dakakeyi ba,rayuwan alheri bace a gare ka damu ma kan mu da muke naka. Katai maki rayuwanka saudauki ka canza halinka don Allah kazamo min abin alfahari a,duniya, gama kowa dake tare damu. Zan so ace na zamo uwa abin alfahiri ga duniya na nasamu da dan albarka a,rayuwana, kamar yadda sauran uwaye suke alfahari danasu diyan. Zan so ka,sasauta halaiyar ka akan wanda kake a yanzu don samun natsuwar hankalina dana mahaifin ka. A hankali maji ta fashe da kuka,wanda kuka ya sa ta kasa karasa maganan da take son ta fada mashi. Maji ya ce cikin sanyin murya nifa ban san wani hali da nake yi ba,wanda har zaisa ki zubar da hawayenki haka akaina. Kallon shi maji tayi a cikin mamaki don watau shi bai fahinci ma yana,da nakasu ba ke nan tare dashi. Tace kako san har mutanen gidan nan sun fara zargin wai kana shaye shaye ne, Ya,dago kai da,sauri ya,dan kalle ta sai kuma ya dukar da kan shi yace maji nifa wa yan nan mutanen sun fara isa ta,sun fara saka min ido har da bina da,sheri haka? Ni dai ka gyara halinka shine bukatana a,gare ka idan ka gyara babu wanda zai dora ma,sheri ai. Ta juya tana cewa Allah ya kyauta kaji bukatana gareka don naga yanzu guduna ma kakeyi baka son shigowa nasan lafiyan ka kamar yadda kasaba yi a baya. Bin bayan mahaifiyar shi yayi yana mamakin mutumin da,yafara gano likin shi a gidan don haka ya zama dole ya canza takon shi tun mahaifan shi basu tabbatar da,zargin su ba akan shi. Don yasan in hakan ya tabbata ba karamin tashin hankali mahaifiyar shi zata shiga ba har ma mahaufin shi din dake nuna yanzu babu ruwan shi da shi yanzu. ****** ******* ****** Zaune take ta tula kudi a gaban ta,sai faman kidayawa take a hankali don gudin tai kure. Sai da ta kirga su cif tajera a,faban ta tana kallo sannan ta,sauke ajiyan zuciyar ta. Yanzu abin da ya rage min na hada kudin fridge din nan saura dubu goma don haka bari na kara kaimi naga sun hadu na,samu kafin azumi na dauko babban fridge wanda zai isheni sana,a yadda nake so. Tashi tayi da sauri ta mayar da kudin inda ta ciro su ta boye, don gudun kada wani ya gani yasan inda ta,aje don tasan da,zaran maigidan ta ya kyala ido yaga kudin nan sunan ta sorry don yanzu zai mata dadin baki sai ya karbe su gaba daya su huta. Abinda bata sani ba shine shi maigidan nata sam hankalin shi bai ga,abin hannun ta ko kadan don asali ma,shi bai bukatan wanan sana,an wahalan da yaga tana saka rayuwan ta a ciki yanzu. Don da,ace yana,da,hali da iyalin shi sunji dadin rayuwa a gurin shi. Amma ina talauci kamar ya yanke saka ne a kan shi don kullun bida yake amma kamar ba,ayi yake sai dai Allah bai hanashi dan abinda zasuci ba agidan daidai gwargwadon hali. Mikewa tayi ta gyara dakin har zuwa tsakar gidan su don akwaita da,tsabta ko yaushe duk da,talaucin su zaka,samu gidan su tsab tsab dashi. Yaran tane suka fara dawowa daga islamiya inda tun a,waje tasan da zuwan su din saboda hayaniyar su da taji tun daga waje. Sannu da gida Umma suke cewa sai faman ce masu take kun dawo sannun ku da,dawowa , Yar karamar yar ta,take cewa mama yau a makaranta malam yai muna alwala mungani nima zan iya yadda yai muna nagani. Nanyaran suka shiga bata labarin yadda malamin su ya koya musu yadda ake alwala har lokacin da mahaifin su yadawo daga kasuwa suka juya gurin shi yana,alwala suna bashi labari n abinda yafaru a islamiyar su yau. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,, A LOKACIN MU KE,,,,,, Ya na fita daga waje ya,ci karo da,bucket din roban da mama ta,aje a tsakar gida shuri daya yayiwa bucket din din yai sama ya maku da,bango. Ji kake pappp karan fashewan bucket din da ya maku da bangon dakin mama Asiya ji kake tayau, Da sauri mama Asiya tafito daga dakin ta,tana ganin irin ta,asan da Umar yai mata tafara salati tana tafa hannayen ta cikin salalami da mamaki. Maijjidda fito fito kiga,ta,asan da,danki yai min, dan iskan yaro kawai mara mutunci, kawai bucket yana aje may ya tare maka don kawai kana haushina zakai min wanan aika aikan haka, Bari ubanka ya,dawo yau gidan nan akwai ta don sai an biyani kudin bucket dina a gidan nan. Haka mama Asiya taita faman masifa inda take shiga ba nan take fita ba sai yan kore da suka fito kara zugata tana hawa. Maji dai tana daki bakin ciki da takaici ya hana ta fita waje a lokacin. Sai dai duk abinda suke fadi a kunnuwan ta yake irin yadda suke kara aibanta mata yaro duk da ran ta ya baci amma bata da bakin magana dan kuka maija wa uwar shi jifa. Sadauki ya jawo mata wani sabon masifa don tasan yadda mama Asiya ta fadi sai an biya ta haka zancen yake sai an biyata din. Don haka ta mike tsam zuwa kuryan dakin kwanan ta ta dauko kudi, a take ta dauko kudi taba Amira wai ta sayo mata bucket. Haba maji don kawai tace sai anbiya ta basai taje gurin shi shida ya fasa mata taje gurin shi mana in ta isa, ya biyata abinta. Maji tace,ban son rashin kunya Amira ki tashi ki tafi inda na aike ki kawai. Bintu tace mama kawo naje yanzu zan dawo sai maji tace a,a Bintu yi zaman ki bari dai Amira din ta tafi. Mama barshi kawai ni na tafi anty Amira ta huta kawai ta duka ta karbi kudin daga hannun Maji ta saka silifas din ta dake ta kofa tafita daga dakin. Inda Amira ke zaune Maji ta dan kalla tace kin ga ikon Allah karamar yarinya haka da kaifin hankali, Don tafahinci baki bukatan zuwa yasa ta karbi kudin ita ta tafi, da sauri Amira ta daga kai ta kalli maji tace bance banzuwa ba maji , Allah dai ya kyauta Amira ina tsoron kada ke ma kizo ki zama min irin dan uwan ki nan gaba wallahi. Haba maji don Allah kibar fadin haka mana idan ranki ya baci kiyi hakkuri don Allah ta fadi a,dan marairaice, Allah ya kyauta ta furta a fili a cikin zuciyar ta kuma fadi take ya Allah ka shirya min yaran nan shiri irin na addinin musulunci. Wannan adduan ya zama kamar waka a bakin Maji don duk abinda take adduan ta akan zurian ta dana sauran yan uwa musulmai yake. Exactly kalar roban da ya fasawa mama Asiya Bintu ta sayo don ma saida tai yawo kusan shago uku ta samu roban. Gap da zata shiga gidan ne a daidai side din samarin gidan dake daga wajen haraban gidan ta hango shi zaune yai zaman kamar tsuguni saman dan dakalin dake gurin. Kamar ance ya dago kai ya hango bakuwar yarinyar da yake yawan gani dakin mahaifiyar shi yanzu tafe da buket din roba kalar dayai shuri dashi a cikin gida kuma tun kan ya karasa fita daga gidan yaji bambamin mama Asiya akan wai ya fasa mata buket wanda ba ma fashewa yayi ba. Daga hannun buket din ne ya balle hannu daya na bucket din ya balle daga jikin roban. Sauri take ta shige gidan sai taji muryan shi kamar daga sama yace. "Ke, Cak taja ta tsaya don balain tsoron shi take ji don ko yaushe fuskan shi babu rahama cikin shi, don har takanyi mamakin ace wai wanan mai siffan bugai yafito daga mace saliha kamar Maji. Zo nan yace mata inda ta dan taka a hankali kamar kwai ya fashe mata a ciki, har ta karasa gurin shi. Waya aike ki sayan wanan robar ya tambaya cikin daga muryan shi. Cikin dan in,in,niya take cewa, mamace tace na,sayo mata, A gatsale ya tambayeta, waye mama ? Don ya tantance ko wa ya aike ta sayen robar. Bintu tace mama ta dakin ku, kina nufin Maji ke nan, tace eh cikin daga kanta. Miko min bucket din kice mata na karba ya,fadin cikin dakewan fuska mika mashi tayi ta juya simi simi ta shige cikin gidan yabi bayan ta da harara yana fadin munafuka kawai. Maji tana zaune Bintu tashigo gidan tana dan kiukiu da idanuwar ta alamar damuwa a fuskan ta. A,a Bintu ba,a samu roban bane ko kudin shine baikai ba? Kafi Bintu tai magana Amira tace a,a ya za,ace ba,a samu irin roban ba kodai baki san inda ake sayarwa bane ? Harara Maji ta maka wa Amira da sauri taja bakin ta tai shiru tare da kawar da kan ta don tasan har yanzu Maji a kufule take da ita ke nan. Bintu tace na,sayo amma ya karbi bucket din a gurina. Shi wa ya karba ? Shi wanan yayan namu da ya,fasa roban yace na bashi roban dana sayo din . Sadauki ke nan ko ? Eh shi yace na bashi nace ya karba. Mikewa Maji tayi ta saka hijjab din ta ta nufi hanyan waje fuuu a cikin fushi da hasala. Ya na kulle kofan dakin shi zai fita ne Maji ta karaso gurin tana fadin miko min roban mara mutunci kawai. Wani kallo ya waigo yaiwa uwar sai kuma ya,dukar da kan shi kasa ya dan fara kokarin bude kofar dakin shi daya rufe. Yafito da bucket din yana cewa wallahi matar nan yar rainin wayo ne naso ne ki barni da ita, tun da tace yau akwai balai akan bucket din roba a gidan nan. Fisgan roban Maji tayi daga hannun shi ta watsa mai harara tana cewa. Duk abinda tace waja min ida baka taba kayan ta ba ai bazatai wanan fitinan ba. Ksi tayi sadauki tunda na fahinci kwanciyar hankalina ne baka bukatan gani a duniya. Maji ni fa ba haka nake ba ki barni kawai na wuce gurin kwallo na in huta da wanan munafukan matan. Anki a barka anan ma da kake yaya aka kare dakai balle ka sa kafa ka tafi wata duniyan da babu mai kwabon ka a can. Indai zaka gyara halinka ka gyara don bakai kadai bane yaro a gidan nan da kullun a ce sadauki dai sadauki. Ta juya zuwa cikin gida kamar yadda tafito a hasale daga gidan da farko. Maji bata shiga daki ba,saida takaiwa mama Asiya bucket din dakin ta takuma bata hakkuri akan ta yi hakkuri da halin sadauki din . Ba kunya mama Asiya takarbi bucket din tana zuba bakar magana tana cewa wallahi da ba,a,sayo min kayana ba da yau akwai magana a gidan nan. Da maji ta shigo lokacin Bintu da su Amira suna zaune a falon ta, Amira ce tace bai bayar bane maji ? Kamar yaya bazai bayar ba aiko ya sha giyar wake ne bai fara shi wallahi. Sai Amira din take cewa to Maji ina shi tsohon bucke din ai naga bai wani fashe ba fa . Amira ki fita idona don ni ba,sa,ar ki bace, don naga kina son raina ni. Shiru Amira tayi tare da kokarin mikewa tabar falon don gudun fadan Maji a kan ta don yanzu tana sauke mata haushin dan uwan ta a kan ta in batai hankali ba. Inda Bintu take Maji ta kalla tana cewa Fatima kinci abinci kuwa, cikin sauke ajiyan zuciya a hankali. A cikin natsuwa Bintu tace ina jiran su anty Amira ne muci tare dasu. Haba Bintu kada ki biyewa wa yan nan don su cin abinci a gurin su kamar shan zuma ne sai sunga dama suke ci. Tashi kici abinci kada gwagon ki ta dawo ta samu kin ramay kan wa yan nan mara sa kai. Haba mama aiko suna da kai adduan ku a gare mu shine takin mu akoda yaushe cikin murmushi da kwantar da murya Bintu tai maganan ta. Allah sarki Allah yai maki baiwa da kaifin basira karama dake Bintu amma kin san abinda ya kamata ko yaushe. Tashi jeki ki debi abinci kici mai isar ki kin ji diyata Allah ya bar muna ku. Bintu ta mike a hankali fon bin umurnin maji amma bafon ranta nason cin abincin ba ta shiga kitchen din su ta dan debo abinci dan kadan a cikin plate tare da ledan ruwan pure wata. Maji tabi abincin da kallo tana cewa haba Fatima wanan dan abincin may zai maki ashe shiyasa baki kiba don baki son cin abinci sosai. Ko har yanzun kina kewar gwagon ki ne kin ki sake jikin ki da mu. Murmushi Bintu tayi kawai tare da cewa a kunyace a,a mama ai ban damu ba. To dayafi maki don ko gwago ta dawo zance tabarki a nan don halaiyar ki ni dai yana min wallahi saboda yaran nan su dan kara daukan darasi a gurinki. Don duk irin halaiyar yaran gidan nan shine diba,ar su a rayuwan su basu san halin rayuwan duniya ba. Da,sauri Bintu ta dago kai tana kallon Maji sai kuma ta dukar da kanta tana dan juya abincin dake cikin plate a hankali ba tare da takai a bakin ta ba. Yadda maji take jin sha,awan Bintu yasa take so da kaunar yarinyar har cikin ran ta ganin zata takura mata yasa maji ta dan mike tabar falon zuwa waje. Bintu tana gamawa ta kwashe kayan zuwa inda suke wankewa ta wanke har ma da wanda tagani saura a gurin duk ta hada ta wanke su. Daidai zata shigo da kayan, maji ta ganta take cewa Fatima baki hutawa duk aiki bai baki wahala ke. Murmushi kawai tayi ta,shige da kayan ciki ta aje tana fitowa ta shiga wanka don magariba ya kawo jiki a lokacin. Tsab Bintu tafito cikin wasu kayan da aka bata na Amira an gyara mata sun mata matukar kyau kamar don ta aka dinka kayan dama. Maji dake zaune ta idar da sallah tana jan tasbaha takalle ta lokacin duk suna falo da yaran ta a zaune. Duk suka bita da kallo a lokaci guda ta,zo har inda Maji take zaune tana cewa ina wuni mama. Kai Maji dake lazumi ta kada mata tare da daga mata hannu Bintu ta mike zuwa bakin dayan kujeran ta zauna a kasa. Maryam ta kalleta tana cewa may yasa ke baki son hawa saman kujera ne Bintu bata ce komai ba sai dan halinta watau murmushi. Can suka fara jin dan hayaniya daga cikin gida yana tashi inda duk sukai shiru suna saurare don suji may ke faruwa ne wai. Maji daga inda take tai murmushi tana cewa Alhaji ya dawo ke nan nasan an fada mashi. Kai wanan matar batayi ba wallahi yanzu bayan an biya ta bucket din ta kuma,shine sai ta fadawa Baba zancen. Maryam tace ai in bata fadi yayi masifa wa maji ba hankalin ta baya kwantawa. Mikewa Maji tayi bayan ta shafa tafita daga dakin zuwa gaida Baba da dawowa daga kasuwa. Ta samay shi shi da mama da uwargidan su a falon shi zaune tai mashi sannu da dawowa,da yaya kasuwa. Ta juya zata wuce sai maigidan nasu ya ce maijidda yaya akayi dan ki ya fasawa Asiya roban ta da gangan? Shaye shayen nashi har yakawo a,cikin gida cikin iyalina kuma? Shiru maji tayi tana maijin kunan zancen baba a ran ta sai dai cikin dakiya yau karo na,farko tun da ya fara mata cin fuska a gaban kishiyoyin ta kan dan ta tace. Da na ko dan mu Alhaji ina bani kadai na samu yaron ba tare da kaine kuma a tare mukai mashi ladabi a cikin gidan nan gaba dayan mi daku. Don haka sai makiyin Allah zaice ban ba sadauki ingantaccen tarbiya ba a cikin gidan nan. Kawai dai Allah ne mai yin ikon shi akan duk wanda yaso ni kuma nasan bawai Allah yakini bane ya mayar da dan da yafito daga tsatso na haka a,rayuwa ba. Ai bazata bari a,fadi ba don kaga har roban ta,sayo ta mayar ma Asiya da abinta wai don ta nuna ita ta haife ta. Maji tace yaya Asiya ya kike son nayi kin face yau idan ba,a biya ki roban ki ba,akwai tsiya a gidan nan don babu mai rabaki da shrgiyar uwar shi sai Allah. Alhaji ya juya yana cewa ke ko Asiya haka kika ce mata don maganan maji yadan sa jikin shi yin sanyi. Ba dole ince haka ba tunda yana takamar shi dan iska ne har iskancin yakawo ga kayana tun yana dukan min yara yau kuma ya koma ga kaya na. Idan ko haka kikace gaskiya baki kyauta ba don dai kinga maijidda ba itace ke tura shi wanan aika aikan ba. Wai haka ma zakace Alhaji akan may zan zauna yaro kamar sadauki yana min cin fuska kala kala tsoron shi nake ji ko may da,zan kyale shi. Yanzun dai idan har ya kara takalar wata a gidan nan don Allah na rokeku da kuyi hakkuri har lokacin da na dawo sai na dauki mataki da kaina. Ke kuma Maijidda nasan kiyi hakane don kawar da fitinan don a zauna lafiya amma ba daidai bane ki biya Asiya roban ta don Sadauki ya fasa mata roba. To ayi hakkuri in har ban kyauta ba amma ni bada wani manufa na biya roban ba. Ai dan tane shi don haka ba zancen biya a tsakanin ku don dan wani yai wa,wani barna. Mama Asiya tace wa ni sadauki ne dana Allah dai yai min katangar tsari wallahi da wanan bakar haihuwa a,rayuwana. Ikon Allah Asiya a gabana kike wanan zancen haka ? Ai gaskiya na fadi don bani fatan haihuwan dan majiciji a rayuwana na haife shi ya kasheni. Allah ya kyauta inji Baba yafadi ciki kunar rai tare da mikewa yai shigewan shi daki kawai su ma mikewa sukayi suka watse daga dakin mama Asiya tana ta bakar magana. Maji tadawo daki zuciyar ta na mata kuna ta samu su Amira suna ta hiran su Bintu tana gefe zaune a makure bata tanka masu a hiran nasu. Suna ganin ta sun fahinci ranta a bace yake anyi ba dadi ke nan a can falon baba. Amira tai tsuki tana fadin wallahi yaya sadauki dai yana jawo muna matsala a gidan nan. Bintu tace sai ko mu bishi da addu,a don adfua makamin mumine ne tunda ba haka Allah ya halicce shi ba ai. Dago kai Maji tayi ta dan tsura wa Bintu ido sai kuma ta kawar duk yadda taso ta danne hawayen ta kada su zubo saida suka zubo mata. Hankalin yaran gaba daya ya tashi sai cewa Amira take halan mi sukace maki maji. Bintu tace haba Anty Amira maganan manyane fa sai su kawai dai mama tayi hakkuri tabarwa Allah al,amarin shi, ian Allah mai karban adduan bayin shine idan Allah ya tashi canza shi sai kowa yai mamaki a gidan nan. Hmmm Bintu ke nan baki san ko waye yaya sadauki ba ko a gidan nan ki barshi kawai kuyi yar nisa danisa dashi shine sauki wallahi. A,a anty Amira insha Allahu wata rana sai kunyi mamakin shi Allah dai yasa wanan halin na iya kurciyane kawai. Ikon Allah ke kin iya magana kamar tasbin kaka kamar wata babba van wallahi. To Antu ai ba abinda yafi karfin ubangiji nagani don shine maitin komai a lokacin kuma da yaso wanan fa jerabawa ne akan su mama da baba sai dai muce Allah ya basu ikon cinyewa kawai. Shiru dakin yayi suna nazarin zancen Bintu yarinya karama da babban magana kamar wata babba can. Jin sunyi shiru Bintu tace da zamu dage ko mu iya dakin ga mu dinga aiwatar da ibada akan shi kawai ba,wai mu tsaya muna magana kamar sauran mutane ba muna kuma yin sadaka akai insha Allahu ba,dadewa zamuga saukin al,amarin da yardan Allah. Don ni wallahi na yarda da addua takobin mumine sosai don da na roki Allah saiki ga an karba min. Dariya,suka saka mata kai Bintu wanan cika baki haka kamar wata,shirihiya can. Hmmm anty ke nan nifa tun ina karama Baba na ya kowaya min yin addua kin san ban tashi a gaban mahaifiyata ba. Da sauri maji wacce sai yanzuta sa masu baki a zancen su tun shigowan ta tana hawaye tace. Fatima ina mahaifiyar ki take Bintu tace tana can wani kauye tana aure sun rabu da Baba ance tun ana goyo na da ya auri kishiyar mamana. Shine da aka yayeni iyayyen ta suka dawo dani gurin mahaifina wai bazasuyi wahalan banza ba . Tayar dake shine suke gani wahalan banza Bintu tace cikin yar murya haka suke gani sai kawai ga kwallah ya zubo mata, Bata daina magana ba don kwallan sai cewa tayi, mama nasha wuya a gurin mama hausi sosai don har tsakar gida na kwana ni kadai tun ina yarinya na. Da kuma na girma abin ba,a cewa komai don ba irin wahalan da bata gwada min. Amma sai gashi duk yaran ta ba wanda ya kaini don mazan su da matan su duk sun lalace mata sai nice ma nadawo tana dan jin sanyi a gurina. Ina ganin ganin da Baba yayi aikin wahala zai kashe shine suka hada baki da,gwagona wai nazo nai mata hutun sati biyu na koma. Sai daga baya gwago take fada min cewa wai Baba na yace na zauna gurin ta kada na koma garin mu. Takarasa maganan cikin kuka tace ina kewan gida da yan uwana sosai da farko amma yanzu don rikon da gwago take min yasa na manta da komai gashi yanzu zama daku yakara sa hankali na ya kwanta sosai bisa ga zamana a can kauye don abubuwan da ban sani ba,a,rayuwa yanzu na,san su sosai. Tun ina shekara sha hudu na haddace alkur,ani maigirma yanzu tulawa nake sai dai akwai banbancin karatun mu na can da naku na,nan birni sosai. Kinga ashe na,dan san wani abu nima ga,addini ke nan don malamin mu yana gwada mu abubuwa siri sosai. Allah sarki ashe mahaifiyar ki bata tare da mahaifinki gaskiya wasu mata akwai ha,inci a tare dasu sosai wallahi. Shi yasa nake ta hakkuri tun farko da cin fuskan da ake min a gidan nan don yaran nan dake gabana don idan na fita na barsu cikin gidan nan wa kuke ganin zai rike min ku amma na cikin su, ina ciki ma yaya muka kare dasu balle na fita na barku. Duk shiru sukayi suna nazarin maganan Maji don sun san gaskiya ta fadi ba mai iya rike su amma kamar yadda suke rike yaran su. Kowan su tasan gaskiya Maji tafadi don ba mai iya rikon su amana suji dadi kamar yadda tace don haka sukaji tausayin uwar tasu ya kara shigan su sosai a gidan. ****** ********* ****** Salamu Alaikum wai ana sallama da Raiha sai mama dake duke a kitchen ta dago tana cewa kai waye da yamman nan ka ce bata nan. Kai tsaya Raiha dake fitowa daga bandaki tace wa yaron je kace gani tafe kaji. Raiha yanzu don baki da kunya zance zaki fita da rana haka kowa yana ganin ki kikau a kofan gida tsaye da namiji duk wanda ya wuce yai miki tir da halinki ko? To mama kin san ko waye da,zaki kore min mai shi mama bari naje naga ko waye nadawo, kawai sai ta shiga daki ta shiga gyara fuskan ta tsab ta saka hijjab din ta sai waje. Mama dake waje ta rike habar ta cikin mamaki sai cewa tayi ikon Allah yaran yanzu Allah ya kyauta kawai. Raiha tana fita taga gidan su tunfitowan ta ya kura mata ido yana kare mata kallo nan yasan yarinyar tayi mashi ga komai kuma,zai more mata sosai idan yai sa,a ta yarda da bukatan shi gare ta. Dan waige waige taks don bata ga mai neman taba a lokacin sai wani bakar mota mai tsada da ta hango, daga wajen gidan su, dan nesa kadan da gidan. Hon din da mutumin dake cikin motar yayi yasa tagane shine mai neman ta a lokacin. Raiha ta nufi gurin a cikin mamaki don ita duk iya sanin ta,bata da saurayin da keda koda karamar mota balle wanan dirkekiyar motan dake gaban ta. Mutimin da tagani a motar bata taba ganin shi ba,a,rayuwan ta don haka sai tai tsanmanin ba gurin ta yazo ba. Sai taji yace malama,Raiha ko ? Eh nice Bisimillah shigo daga ciki mana ko kina tsoro ne kuma. Tai wani irin har da idanuwan ta ce tsoron may zanji kawai dai ban gane ka bane dai. Bazaki gane ni ba,asalima baki sanni ba ni ne dai na,san ki ta hanyar gane gane na nahagonki kawai. Shine na biyo ki har nagane gidan ku ne nan sai yau na yanke shawaran nazo gurin ki dafatan zaki fahince ni ai. Wani kallo tai mai kamar bata yarda da,zancen shi ba sai tace mai a ina ka ganni ne ? Sai da yai murmushi sannan yace a gurin birthday din Salim murmushi tayi don tasan anyi hakan . To amma duk tsararun yan matan;dake gurin bai gansu bane sai ita zaizo gurin ta, sai kuma,wata zuciya tabata amsa dacewa kece kikai masa kawai a gurin. IkonnAllah tace a fili tare da,fadin shine kabiyo ni har gida kuma ? Yace eh mana ko nayi laifi ne tace bance ba yace to sunana Abdul amma ana kirana duwel ne don haka abokaina ke kirana dashi. Hmm tau nagode da,har ka zabi kazo guri na,dafatan lafiya kazo har gidan mu a,kaina. Murmushi guy din yadan yi tare da,cewa ai tunda kika ganni a gurin ki ke ma kin san alheri ne yakawoni gareni da,fatan zaki fahinci manufata a,gare ki batare da kin fassara min zance na ba. Murmushi Raiha tamayar mashi tana cewa da fatan zan samay ka mai cika alkawari nima. Nan suka tsaya suna dan kara fahintar da junan su kan shi tare da dan hira yana fada mata ko shi waye da inda yake aiki. Ganin yamma tayi sosai tasan mahaifinta zai iya dawowa a lokacin yasa ta yi mashi sallama ta,shiga gida da fara,anta. Tana shiga takasa boye farin cikin ta take cewa mama yau saura kiris ki kore min sa,a ta kin kuwa ga mutumin da yazo gurina ne. Uwar ta mayar da hankalinta akan yar ta tana sauraren bayan nin da takd mata akan bakon ta. Har saida mahaifinta ya shigo gidan suka bar zancen don gudun kada yaji zancen su. Tun daga wanan ranan suka hada alaka a tsakanin su ita da Abdul din guy din da ya tafi mata da imanin ta gurin son ta. Ba uwarta ba har mahaifin ta saida ya,san da zaman Abdul din don masifan son da Raiha take mashi. Wasa wasa Abdul ya fara dan test din Raiha da,wasu yan abubuwan da yake son sani ko tasan da su a sabon sallon so da matasan yanzu ke ciki yanzu. Bai samu matsala ba don ya samay ta yarinya ce yar rock sosai ba wasa don haka harkoki suka fara tafiya a tsakanin su ba bata lokaci. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,, A LOKACIN MU KE,,, Waya take sai ko mama dake kusa da ita bata iya jin may take fadi a,wayan , saboda matukar tausa muryan ta da tayi ga wayan. Sai yar dariyar da tayine yasa mama dake zaune saman kujera yar tsugunno dago kai tana mata kallon mahaukaciya. Ta dan dauki lokaci tana wayan cikin jin dadin abinda ake fada mata ga,wayan wanda babu maijin ta balle a san abinda su ke fadi. Mikewa,tayi zuwa cikin dakin su inda ta kwanta saman dan gadon katakon dake dakin mahaifiyar nata. Nan ta shige cikin katon hijjab ta rufe kanta sai dai hannunta na akan gaban ta zuwa kirjin ta a hankali take dan shafa,su don kada a gane may take a lokacin. Nan taci gaba da,wayan ta na tsawon lokaci mai tsawo sannan tai wani mike barci ya dauke ta. Haka mahaifiyar ta ta shigo dakin daga gurin girkin da take yi ta samay ta kwance tana barci, A fili ta furta kai amma,anyi malalaciyar yarinya gurin nan yanzu barci kikayi ashe ni ina jiranki ki min shara a,tsakar gida. Nan dai uwar dole itace ta karasa aikin ta,da kan ta inda Raiha bata farka ba sai bayan sallah azahar ko shi sai da kyat uwar ta,tayar da ita don tai sallah. Bayan ta gama cin abinci a lokacin har uwarta na zance dora girkin dare don yamma tayi sai ga Raihanatu tafito a cikin shiga na fita da katon hijjab din ta har kasa. Sai dai kassh da mutum zaiga mai ta sa a kasan ta da yayi tir da Allah waddai da irin shigar ta haka. A,a Raihatu ina kuma zaki a wanan lokacin bayan yamma ya riga da yayi ko? Mama dan wani guri ne zan tafi ba,wai dadewa zanyi ba yanzun zan dawo mama. Tana fita bata tsaya ba sai shagon sayen kayan mayen su wand kamar kullun gurin ya zama majalissan matasa yan maye kala kala. Duk da jami,an tsaro suna kawo masu samay akoda yaushe suna zuwa kama mata a gurin masu dabian shaye shaye. Can ta kutsa tashige daga ciki gudun kada wani yagan ta a gurin don gudun ganin idon sani. Brosha na ganin ta a lokacin yana mikawa Umar kayan harkan shi Umar wanda yake tsaye da bakaken kaya fuskan shi a murtuke. Burosha yana ganin ta ya fara washe bakin shi cikin farin ciki da ganin ta yana cewa A,a yau mutumiyar an shigo ke nan kayan aiki sun kare ke nan dai ko don ba,a ganin ku sai rana,tai zafi. Ya dauko canji zai mikawa Umar yake ce ko yau din ma,za,a barmata canjin ne dan wancan katon ma naga kai ka biya mata. Wani kallo Umar ya watsa wa Raiha yace cikin dakiya don Allah ka,sallamay ni don kasan ban son ina dadewa a gurin nan naku, Raiha cikin yatsune fuska tace aikowa ma,sauri yake don ba wanda yazo don ya tsaya . Kamar Umar ya bata amsa har ya dan bude baki da zuman yai magana sai kuma yaja bakin shi yai shiru . Borasha ya mika mai canjin shi yai gaba bai tsaya bin ta kan raiha ba balle ya kulata ma. Bin shi Raiha tayi da kallo tana fadin ji shi kamar wani mutumin kirki wai sauri yake bai son a gan shi. Brosha yace to ke nan fa wanan zubulelen hijjab da kika,sa wa zai dauka ba islamiya zaki a haka ba . Dallah gafara malam nagafa kafara saka min ido don tsokanarka ya fara yi min yawa fa. Dan sa ido kawai ina ruwan ka da shigata wanan nayi ne kawai don batar da sau amma a ciki ai shigar manya ne nayi sai ta dan daga mashi hijjab din ta inda ya hago wani matsatsen rigar da ta,sa duk nonuwan ta sun dan bultso a gaba sai dan guntun buje na zuwa part dakd saye a kunkurun ta iya cinya kawai. Kai brosha ya daga tare da fadin kai amma Raiha kin kai shu,uma irin wanan shigar haka sai ina? Don dai nasan da,akwai inda kike nufi zuwa da wanan shigar haka da kika boye cikin wanan katon hijjab din naki. Tai wani har da idanuwan ta tana cewa ashe ka gane ke nan mazan, yau casu gare mu har dare shiyasa na dauki kayan aikina don ya taimaka min a can, Tirka sa ki ce yau akwai babban harka ke nan raiha don nasan mutanen mu zasu hadu a gurin, Tace hakane amma ba,wai irin wa yan nan ba wanan gayu ne masu harka da kwalabe da manyan wa yan nan, Nima hanya akai min don naje naba idona abinci ko zanyi cafka a can don kasan ala,amarin sai da kwaskwarima ciki wanan lokacin don gamu nan birjit ko ina kowa na rabon ido yasamu mai cafkan shi. Gaskiyan ki Raiha nima nasan sai da haka al,amarin don abin ba,a cewa komai. Aje lafiya a dawo lafiya a yo muna kamu babban giwa mu sha shagalin mu muma ga,aljihun shi. Ta,wuce tana tafiya a cikin rangaji da layi irin nasu na mashaya da suka goge a fagen boyon kan su, don batar da kaman nin su ga mutane. ****** ********* ****** Guri ne mai kyau da,shuke, shuke ko ina bakajin komai sai sautin kidan dake tashi na turan ci na mawakan Afrika. Tana fita daga cikin napep din da ya kawo ta ta samu dan nesa kadan ta cire hijjab din dake a jikin ta tare da dan kara gyara tufafin dake jikin ta. A hankali take takon ta zuwa inda mutane sukai dan dazo akasarin maza da matan gurin zakace ko ba diyan gari bane. Don irin shigar su da kuma aakin kan su sai mutum ya rantse cewa ai a wata kasar arna ya ke ba cikin garin sokoto ba ma gari shehu usman dan fodio. Mutumin da yai gwagwalmaya akan addini a kasa da,watsa su har sauran kasashen duniya don amfanin al,umma. Amma,yau sai gashi a,kasan shi garin shi duniya da lokaci yasa matasan kasar kwaso akidar yahudawa suna yadawa da cusa shi ga,sauran masu tasowa na baya. Wanda ba,a sokoto ba kawai yanzu ko ina a kasashen hausaw a na samun wanan akido jin na koyan akidar wasu da,al,adun su. Allah ka tausaya muna ka,shirya muna al,umman mu yaran mu kan,nen da ma,sauran yan uwa musulmai baki daya, Da farkon shigan Raiha a guein ta dan sha jinin jikin ta don tana ganin abinda yafi karfin idanuwan ta. Sai da ta hadu da,wasu kawayen ta biyu haka yadan sata sake jiki dama can sune suka gaiyato ta gurin. Daga inda take a zaune tana bin mutanen gurin da,kallo a fakaice tana kallon irin shigar da mata da mazan gurin sukayi abin sai shukaran kawai. Don nata shiga ai mai sauki ne bisa ga na wasu yan matan yadda suka saka dan mitsitsin abu a jikin su abin ba dadin gani Raiha sai tarena kanta a guri don taga iyakar wayewa a gurin yan duniyan da suka fita iya duniyan ci sosai. Taro yai tsit saboda fara gabatar da bukin da,aka,soma wanda suka ce sunyi shi ne don tunawa da kafa gungiyar su mai shekara biyar da,kafuwa yanzu. Inda,wasun su sin mutu wasu kuma,sun dain harka suna wani kasar haka dai maigabatar wa yai ta bayane na,shirmay a guri a na ihu da,sowa irin na yan iskan matasan zamanin nan. Sai kuma aka fara rawa da da,zagaye duk wanda aka jefa a bu ya fada a kan shi dole ya fito yai rawa ko a ci mai shi taran kudi. Irin wanan jifan ne koda aka jefo sai abin yafada akan jikin Raiha wace ke can ta juya tana magana da kawar ta. Jin an sa ihu yasata juyawa don ganin may akewa ihu haka,sai jin kyalen rawan tayi a kan ta inda,zasuyi rawa da,wani sauri dan dogo fari dashi. Dole badon Raiha ta so ba ta mike tafita filin don bata da kudin biyan tara har dubu biyar idan bazakai rawan show ba. Fitowan ta yasa mutane da,dama gurin suka,san da,zuwan ta a,filin, inda aka sa masu kidan tausi watau cool music, Rawa na ban mamaki sukayi da saurayin a filin inda,suka bada show yaron ya,dinga juyata yadda ake rawan kidan na ai nahi. Wanan abin ne ya haska Raiha,a idon mutane don dama Raiha yarinya ce mai kiran mata duk wani abinda ake so gajikin mace ta mallake shi ko. Wani matashi wanda tun fara,event din ya kafa hular shi a gaban goshi kamar baya kallon abinda ke faruwa a gurin ya mayar da hankalin shi a kan raiha,sosai. Yarinyar ta,tafi da imanin shi don haka ya yanke shawara a,ran shi cewa dole ne ya nemay ta don ya gana da ita,yadda yake so. ****** ********* ****** Yanzu abubuwan sun dan yi sanyi wa Maji akan Sadauki don tun ranan da tai mafada sai ta dan samu sauki daga gare shi. Don haka shawaran hajiyan masa yai mata rana a gurin ta sosai maimakon fada na fitan arziki ga yaron yanzu nasiha da ban baki yafi komai sauki ga yaron yau. Don yanzu sam ba ruwan shi da kowa gidan kwata kwata yafita batun yaran su amma fa idan ka,shiga shirgin shi duk da haka bai ragawa mutum. Safiya ce matan gidan kowa sai harkan gaban ta takeyi ba,ruwan wata da wata a gidan kowa tasa tafisshe ta haka zaman su yake. Sallaman Bintu ya,dakatar da Maji daga aikin da takeyi daga cikin uwar dakin ta. Tafito suna gaisawa da maji a cikin mutunci da ladabi da tsintsiya a hannun ta Bintu sai take mika mata ledan da,gwagon ta, ta bata ta kawo wa maji din. Tare kuma da karban tsintsiyar dake hannun Maji Bintu ta karba duk da Maji ta so hanata amma yadda ta marairaice yasa Maji mika mata tsintsiyan sharan. Nan ta kara yabawa da hankali da tarbiyan yarinyar tana dama ace nice da haihuwar wanan yarinyar ma hankali da sanin ya kamata haka. Tas ranan Bintu taiwa dakin tare da kawar da komatsan dake a fili ta,shige mata dasu daga ciki don yanzu dama duk Maji ta sukurkuce bata da,wani kuzari a jikin ta saboda dafin bakin cikin dan ta ya fara tabata sosai. Bayan Bintu ta gama da gyara waje ta kofan part din Maji ne ta shigo dakin tana,saye da dan hijjab din ta mairuwan cingan . Tana cewa Mama na rarage ni zan tafi gida kada gwago taga na dade ban dawo ba. Nagode Fatima Bintu Allah yai maki albarka Allah ya albarkaci ruwan ki, Bintu ta amsa cikin yar muryan ta, da Ameen mama nagode. Ta fita daga gidan matan gidan sai binta da kallo suke da take aikin suna mamaki don dai su sun san yaran su basu iya wanan aiki da yar karamar yarinya tayi haka. Duk wanda ya,shigo ya,samu yadda Bintu ta gyarawa Maji guri sai yai maga suce kai Maji amma yau kan kun sha aiki sosai maji waban gyaran guri haka. Tace wa Ameera bani fa nayi shi ba yar gidan hajiyar masa ce ta gyara min shi haka ta shigo ta samu ina shara sai ta karba shine tai min wanan aikin haka, Yarinya yar albarka da ita da mutunci ga sanin ya kamata a yar karamar yarinya da ita haka. Amira tace ni dai yarinyar tana bani shawa wallahi don tasan girmama na gaban ta sosai. Har maigidan sai da yaiwa Maji magana dacewa yau shiyan nan naki yai min kyau ga kamshi na tashi sosai. Murmushi maji tayi tana cewa ya ta yar albarka tazo tai min wannan aikin yar gidan hajiyar masa na makwabtar mu A,a tayi kokari su wayan nan katar banzan may sukeyi ne da,bazasu iya gyara guri ba,sai wata tazo ta gyara masu. Maji tace halin yaran nan ai sai su don ko sunyi basuyin yadda wanan karamar yatinyar tayi. Tun wanan rana kwana bibiyu sai Bintu ta shigo gidan gurin maji ta dan yi mata aikin da ya kamata tai mata sai ta koma gida. Sannu sannu har Bintu tafara fahintar cewa Maji tana fuskantar matsala a gurin mutanen gidan don basu kaunarta sam. Ga fitinar dan ta da koyaushe ya shigo gidan tana jin yadda yake uwar ke fama da shi akan wasu matsalolin da bata fahinci aini cin yawan laifin da yakeyi ba ako da yaushe don maman nashi bata fitowa fili tafadi sai dai taganji tana cewa. Baba kaiwa Allah ka rufa min asiri ka,daina halin nan naka don girman Allah. Sai ya kan katse uwar da wani irin magana a gala baice da cewa ni mama mai nayi ne wai kullun ace wai mutum yai laifi. Sai yafita a kasalance yabar dakin zuwa waje maji kan bishi da kallo har yabar dakin ta sauke ajiyan zuciya tace Allah ya kyauta. Yawan ganin da Sadauki yakewa Bintu a gurin mama bai sa ya,sake da ita ba asalima dai shi yarinyar haushin ta yake matukar ji a,ran shi sosai. Don tafaye yin abu kamar muna fuka idan ta ganshi ta kama dan noke noke ke nan kamar taga dodo ko mugu bata jimawa zata bar dakin ta ce ita zata wuce duk yadda maji tayi ta tsaya bata yarda ta tsaya idan yana nan part din. Gwago tana son zuwa kauye don uzuri na tafiya ya taso mata zuwa gida shine taga bazata iya barin Bintu gida ita kadai ba. Don haka tazo da kanta gurin maji tana neman arzikin Bintu ta zauna a gurin su har ta dawa daga gida. Don babu damar ta tafu da ita a na cikin makaranta a lokacin ana karatu ne ba hutu akeyi ba. Da yar ledae kayan ta tazo gidan aka sauketa daki daya dasu Amira da maryam. Tunda gwago ta, tafi a takure Bintu take gidan su Amira din koda kowa yana falo Bintu tana daki ita bata fita zuwa ko ina ko kallo bata fitowa tayi a falon kamar yadda kowa keyi. Yau da ya dawo daga wasan ball ya samu maji a kwance bata jin dadi don haka tana ganin shi tasan cewa abinci ne ya kawo shi don haka daga inda take kwance ta kwalawa Bintu kira tazo. Mamakin jin tana kiran wani bakon suna daga ciki Umar keyi sai dai halin shi bai barin ya tambaya ko bakuwa,ce uwar tayi mai suna hakan. Bintu tafuto tana saye da dan farin hijjab din ta a jiki don dabiar tane bata zama jiki ba hijjab ko kadan. Mama gani inji Bintu duk da jin muryan ta da jin muryan ta da yayi ta shigo da sallama bai sa ya dago kan shi ba daga abinda yake a,wayan shi ba. Bintu don Allah kawo wa yayan ku abincin shi kin ji, Tau mama tace tare da juyawa zuwa dauko mai abincin dan lokaci kadan sai gata da ture ta ta dauko kayan abincin har ruwa duk a cikin ture din. Kujeran da yake zaune akai hankalin shi a,waya ta nufa, ya dora kafan shi daya saman daya. Ya mayar da bayan shi a makarin kujeran da yake sama zaune yana ta faman la tsan wayan shi. Bintu ta karaso gaban shi ta dire mai turen abincin a gaban shi ta juya da,sauri zata bar falon, Muryan shi taji kamar mai jin barci bayan ta juya yana cewa, "Ke, yace da dan karfi abinda yasa Bintu ta,tsaya guri guda cak ke nan bata daga kafa ba kuma bata juyo ba. Kizo ki zuba,mana zaki ajewa mutum abinci hakana kamar wata yar kauye can dalllah, Da hanzari Bintu ta juya don bin Umurnin shi ta duka tare da jawo plate tafara zubawa a plate din dake cikin ture din. Sai da Bintu ta shake plate din fam sannan take cewa nazuba tana shirin mikewa. Ke Uban wa zai ci wanan abinci haka kamar jaki ko an fada maki cewa kowa irin ki dan kauye ne. Kai Babana inji Maji wanan wani irin hali ne maka yarinya ta,dafa,ta kawo maka kuma cine kawai naka har kake kokarin kiran ta,da,sunan dabba. Ke wuce ki shige abinki kinji Bintu kar ki tsaya,sauraren shi da zancen banzan shi. Da hanzari Bintu ta juya zuwa cikin uwae dakin mama inda dakin su yake da,su Amira gaban ta yana faduwa irin yadda yai magana ya bata tsoro sosai. Tun ranan bata son taji koda muryan shi don tsoro yake ba bintu din idan ta gan shi. Da wani dare yashigo gidan sai wani lumshe idanuwan shi yake anyisa,a Bintu ma tana falon do Amira ta takura mata tafito suyi kallon wani hausa film sabon fitowa. Bayan ya,samu guri ya zau a suka,shiga gaishe shi daya bayan day suna mashi sannu da,zuwa, Ya zauna tare da mayar da hankali shi ga mahaifiyar su da ke zauns daga gefe saman salaya tana jan casbi ta a hannkali suka gaisa dashi daga gurin da take zaune , Sai dan wa lokaci ya dan nisa yanacewa Maji abinda yasa ta,dawo da hankalinya ke nan gurin dan nata don tasan magana yake son yi da ita. Yace dama nazo maki da wani magana ne akan al,amarn da ya,shafe ni. May kuma ya faru ne babana Maji dama ina son fada maki ne na,samu wani contarac akan zancdn ball din da nake yi wasu club suna son dauka na zuwa yi masu wasa. Cikin sauri Maji tace ban amince ba kaji na,fada maka kada ka,fara ka,tayar da,zancen nan har wani yaji ko mahaufin ku a gidan sai nai matukar bata maka rai wallahi kaji na fada maka gaskiya. Kallon mamaki yakewa mahaifiyar nashi don tabashi mamaki don shi a,zaton shi yai tsanmanin zatai farin ciki dajin wannan labarin tunda kullun gori take mashi akan wasan ball din da zaman banza bai zuwa shago kamar sauran yan uwan shi na, nagidan da,suke taya mahaifin su sana,a. Shiru yayi tare da,dukar da kan shi guri guda bai daga ba har tsawon wani lokaci . Tsam Bintu ta mike zuwa ciki don tsoro takeji naganin fushin wanan jarumin kada ya hada fushin shi dasu. Maji amma,wanan abin fa alheri ne sosai idan har anyi nasara akai don Allah ki bari naje. Bazaka banace na fada maka,gaskiyan magana ta ke nan har cikin raina . Nan ma da kake a gaban mu yaya muka kare dakai balle can inda babu kowa naka. Shiru yayi sai ya mike zuwa fita Maji tace abinci fa yace makoshi kawai yasa kai yafita daga dakin. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,, A gurin da suke zaune suna magana suke jin hayaniya daga cikin gida, shiru sukayi suna saurarawa. Labulen dakin tane ya,daga ko sallama babu ya fado masu dakin duk jikin shi yai futu, futu da kasa ga wandon shi kamar yai fitsari a ciki. Kara shigowa yayi daga cikin dakin ya fadi kasan ties din falon jagwab dashi sai kuma ya fara nasarin barci. Innalillahi Baba na may ke faruwa ne haka, may ya samay ka, may akai maka, wa yai maka wanan abin haka. Sai ta,sake wani irin kuka cikin wani murya mai ban tausayi da tsuma zuciyan mai sauraren ta. Innallilahi wa,inna alaihim rajium Baba kada dai ace da gaske shaye shaye kake yi haka. Cikin kuka take magana da tashin hankali, mai masa kin ga yaron nan yau yadda ya koma ikon Allah. Allah kataimake ni ya Allah wanan yaron yau may zangani haka da idona. Nashiga uku na lalace a rayuwata Sadauki may ka koma haka yaushe ne kafara wannan bakar rayuwan haka. Takara daga murya tana cewa Baba na badai shaye shaye kakeyi ba cikin gigicewa take maganan. MAJI bafa,,, abinda ya,samay ni just ,,,, relax ,, relax Maji,,, kawai,kawai dai ,,,, dan joy neeee,,,,, Sai ya mayar da kan shi kasa yaci gaba,da barcin shi, nashiga uku mai masa yau dan nan ya, jawo min magana babba a cikin kishiyoyi da al,umma. Baba da nasan wanan rayuwan zakayi a duniya da na barar da cikin ka na huta da ganin wanan bakar ranan da nagani yau a,rayuwa na. Haba haji ki daina fadin hak don Allah yanzun dai musan abin yi kafin abin yai mashi illa haka. Mai masa ai gara ace ya mutu da na zauna ina ganin shi a gabana haka. Umm,umm hajiya don girman Allah ki daina fadan haka wa dan ki Ai babu abinda ya gagari Allah ko? Kuka mai tsuma rai Maji takara sakawa cikin tashin hankali tana fadin da daya ke nan tilo namiji da Allah ya bani mai masa yau ga abinda ya zama min a duniya. Ba u komai Allah ya shirya muna shi dashi da ma sauran diyan musulmai masu wanan halin. Daga waje kofa tsakar gida kuma kishiyoyin maji a tsatsaye suna fadin ikon Allah yaukan mun ga abin mamaki a cikin gidan mu wanan bakar masifan ya,fado muna. Hmmm lalau akwai magana da,sake don dole a,dauki mataki ga hakan kafin a lalata muna yaran mu. Dayar kuma sai cewa tayi kai gurin bakar jaraba har an kwaso muna jikokin yan maye a gida yau ga abinda bakar jaraba ya jawo a gidan nan. Ace wai cikin gidan nan yadda muke da mutunci a cikin shiya an samu dan maye irin haka. Allah kai muna tsari da wanan bakar masifan ka kare muna yaran mu dama karshen so ke nan ga yaron da ba,a kwabo ai. Haba dai ai wanan ba daga nan ba inji amaryan su kowa dai yabi nashi da addua amma ai ita Maji ba itace ta turashi zama haka ba kudai kowa ya iya kan sa don wanan masifan ta shafi kowan mi a gidan nan, ba ita kadai ba. Ke don Allah ni ban son munafumcin banza ina ko ke bai bari ba indai sadauki ne a gidan nan. Haka sukai ta cacan bakin su daga kofan dakin Maji da suke daga ciki suna jin cacan bakin su. Mai masa kinji abinda nake fada maki ta fadi cikin kuka da tashin hankali. Ai basu kamar Allah ba don ba wanda ya wuce jerabawan ubangi daga cikin su. Ke dai kibi dan ki da adduan neman ashiryuwan daga Allah dan yanzu ke ce da matsala basu ba. Kara jajircewa ki koma haikan gurin ubangiji tare da nemar taimako, kina bashi koda baya so ki bashi ya shanye a gaban ki ba bayan ki ba. Insha Allahu nima zanyi kokari naga na taimaka da dan abinda zan iya gurin al,amarin. Don kinga shi aikin shedan shiga rai ke gare shi sai mutum yai kamar zai bari sai kuma shedan ya rude ka ka koma. Don haka yanzu ki yawaita jan shi a jiki ki kada ki biyewa maganan mutane kina nuna mai kyama ko hattara ,a,a ki jawo danki zuwa jikin ki don ki san damuwar shi. Shigowan Bintu dauke da dan wani kwanon glass na tangaran da cibi a cikin sa yasa sukai shiru baki dayan su. Su Amira duk suna tsa tsaye cirko cirko sai faman kuka sukeyi da tashin hankali. Gurin da yake kwankwance sharkaf dashi ta nufa inda ta durkusa tare da dora kan shi a cinyar ta suko duk ido suka saka mata. Amira na ganin haka ta fahinci may Bintu ke shirin yi masa don haka itama ta karaso tare da karban kwanon daga hannun Bintu. Haka maryam itama ta guso inda suke da taimakon su ta samu ta bude mai baki da kyat suka dura mai manja da girshirin da ta hada har kusan cibi uku, Sai ya fara wani irin tari ya bude idon shi da kyat tare da dan kara yunkurawa sai kuma bintu ta mayar da bakin shi da karfi ta rufe gam sai ko yai wani zabura tace ku danne min shi dan Allah. Maji dake gefe tana kallon su ta kara sakewa da wani sabon kuka sosai cikin tashin hankali. Yan mintina kadan saiko wani irin amai ya taso mai nan ya fara sharara amai kamar zai amaye kayan cikin shi a lokacin. Amai sosai Umar yayi a lokacin sai kuma ya koma barci dan gefen su kadan. Bintu ce ta kwashe amai don su sauran sai faman kuka suke tayi cikin tashin hankali. Dawowa tayi falon ta zauna a cikin damuwa da tashin hankali, Maji ce ta taso inda yake takai mai wani irin mari da duka mai gigita mutum abinda yasa shi bude idanuwan shi ke nan yana kallon ta. Yace cikin muryan maye Maji may nayi kike duka na haka? Uwar ka kayi dan banzan yaro mara mutunci kawai wallahi sadauki sai Allah ya,,,, Haba mama kiyi hakkuri dan Allah kada ki furta mai mugun kalami yafi kuma nan lalace maki don Allah dai kiyi hakkuri mama takarasa cikin kuka da tashin hankali. Mai masa tace haba hajiya watau baki dai ji abinda nake fada maki ba ke nan ko? Wallahi idan ma yafi nan ba tsira zakiyi daga zagin duniya ba don haka ki dawo da hankalin ki guri daya kiyi nazarin magana ta. Hannun ta ta cusa cikin aljihun shi don jin karar ledan da takeji daga cikin aljihun nashi. Fito da ledan tayi daga aljihun nashi sai wasu kwayoyi suka zubo daga ciki da yawa haka. Salati suka saka ita da mai masa a lokaci guda take cewa kinga abinda ya sha yafitar mai da hankali ko. Koma ki zauna saman kujera kada ki fadi kinji hajiya akwai Allah shine zai muna maganin abin. Ba,a san ko wacece daga cikin matan ta bugawa maigidan waya ba, sai kawai gashi yazo a sukwane gidan cikin tashin hankali shi da sauran yayyen sadauki. Dakin maji da akace masu ya na ciki suka shiga anan suka samay shi kwance sharkaf kasa yana barci. Nan suka samay shi da duka mai shuri na shuri mai mari yana mari saida ya farka daga barcin da yakeyi. Suna ganin ya tashi suka jashi zuwa waje kiiii sukaci gaba da dukan shi cikin tashin hankali. Ganin zasu halaka shine hajiyan masa ta isa gurin ta fada saman jikin shi tana tare dukan tana fadin haba Alhaji ai duka baya yi sai dai addua tunda abin yai muni ko? Cikin takaici da bacin rai Alhajin yace mai masa bari kawai mu kashe dan banza may zanyi dashi cikin zuria ta mara mutunci kawai. A dai yi hakkuri dan Allah abi al,amatin sannu tunda ya riga da ya aikata sai a san hanyan bi da shi kawai yafi. Amma duka ai kara hinjira shi kawai zakuyi ba wai gyara abin ba . Duk mutanen gidan suna tsaye tsakar gida cirko cirko sai amaryan su ce itama ta tako gurin ta kama mashi hannu zuwa part din ta duk da Alhajin yana ce mata wallahi ki barshi ya fito min gida ba dana bane wanan dan banzan yaron kawai. Bataji ba,sai kulle kofan part din ta da tayi dashi a ciki ta,zaunar dashi nan ta shiga lalashin shi da bashi magana tana mashi nasiha. A kan ya daina wanan muguwar akidar da ya sawa kan shi ko dan martaban iyayyen shi, Tace ka tausayawa mahaifiyar ka Sadauki yau ka san irin halin da uwarka zata kwana aciki ai babu abi mafi muni ace yau cikin dubu nakane lalattace. Dukar da kai UMAR yayi kasa tare da,wa i irin nadama ya,ziyarce shi a lokaci guda yake cewa mummy kuyi hakkuri insha Allahu zan daina bazan kara ba. Tace da ka kyautawa kanka,wallahi da ka cece mahaifiyar ka daga tashin hankali da masifa. Kuma kaje in komai ya lafa kabata hakkuri kai mata alkawarin baka sake shaye shaye har ma da mahaifinka. Shiru sukayi ya,sadar da kan shi a kasa can takara cewa, yanzun kai ko don irin zaman da ake a,wanan gidan kowa ya tunkaho dan shi wani abu ne bai saka kai zuciya ka zama wa uwarka dan kwarai abin musali ga sauran dangi. Maza tashi jeka kai wanka ka,tsabtace jikin ka don naji kamar sun fita daga gidan. A lokacin su Maji suna daki hajiyan masa na kara bata hakkuri da magana mai kwantar mata da hankali, har ta dan sauko tana daukan nasihan mai masa. Mai masa take cewa yanzu dai yana gurin kishiyar ki ta,saka shi a dakin ta ta rufe dashi nasan nasiha take mashi a can. Wa mummy Amarya ko wa ina ganin itace dai mai daki can kusa dake karshe. Itace maji ta fada a hankali don in ba itaba nasan indon su yayane sai dai a kashe shi ai. Sadauki yafito daga part mummy yana tafiya cikin dan gyasawa a hankali don dukan da yasha ya taba mai kafa har da baya duk jikin shi ya farfashe sosai don dukan da yasha gurin mahaaifin shi da yayyen shi. Wa yanda ke tsakar gida a zaune suka bishi da ido da bakar magana8 suna fadin andaiyi hasaran haihuwa wallahi. Yadago kai ya,watsa masu harara sai dai bai tanka masu ba ya shige yafice daga gidan kawai. Ranan Maji tayi kuka kamar ranta zaifita da,kyat mai masa ta samu tai shiru, tare da bata magana. Gwago mai masa ta sa Maji taje taiwa Amaryan su godiya kan halarcin da ta nuna mata kan dan ta. Maji ta shiga part din tana saye da hijjab mairuwan toka har kasa a jikin ta sai dai duk idon ta ya kumbura don kukan da ta yini yi ranan. Da sallama a bakinta tashiga dakin inda ta dan tsaya daga kofa tana sallama daga waje. Akai mata da iso da amsa sallaman da tayi hakan yasa ta daga labulen ta shiga daga cikin dakin. Bayan ba,tasan dakin ta tsaru kamar na yan boko dama don komai akwai cikin dakin nata. Amma da take ita ba ruwanta da bin dakin kishiyoyin ta,sai bata iya kaiyade abin dake cikin part din gaba daya. A,a hajiya maijjida kece tafe yanzun fa nake son nagama da wanan dan rigiman naje gurin ki sai kuma gaki cewa karamin yaron ta da ta yaye amma ya dan tasa yagirma. Ta kai kallonta ga yaron tace Amir kaine wai dan rigima aiko ba ruwan shi dai nagani. Cafdi baki san komai ba ke na wanan ai fitinanne na karshe wallahi. Yanzu fa nake zancen zuwa gurinki na kara baki hakkuri akan abinda yafaru dazun don abin ba dadi gaskiya saidai hakkuri da addua kawai Allah ya shirya muna su baki daya. Maji tace nazo ne nai maki godiya kan irin halarcin da kikai nuna dazun din. Nagode Allah ya saka da,alheri Allah ya kara bamu hakkurin zama da junan mu yasa wa zuria albarka. Habba hajiya maijidda ai shi da na kowa ne danki fa da nane kamar yadda nawa suke naki. Ke fa mutum ce mai kokari da sanin ya kamata duk irin halarcin dakike min kan nawa yaran aina sani. Don ko dawowa sukayi ban dawo ba,daga school gurin ki ne kawai suke samun fuska a gidan nan har nadawo na,samu sunci abinci hankalin su a kwance. Don may yau zanga naki cikin wani hali na kasa nuna bakin cikina akan hakan abin baiyi dadi ba gaskiya amma ayi hakkuri don Allah. Hawaye ne suka zubo wa Maji daga idon ta take cewa hajiya, kubura ban san yaya zanyi da,wanan yaron ba a,rayuwa ta duk yadda ake ba yaro tarbiya nasan ina ba sadauki shi a,rayuwa amma a karshe duk ya,watsar dasu ya zabi wanan harkan na,shashan ci. Hmm abin fa yanzu sai addua don ya fara zama ruwan dare ga matasa sai dai wanda Allah ya kare kawai shine ya tsira. Na san zafin wanan tun a gida don ina da kani mai irin wanan rayuwan amma cikin ikon Allah yanzu ya daina ya koma normal mutum din shi kamar kowa. Wani abinda baki sani bama shine abin fa ba mazane kawai ba harda ma mata wallahi mata ma ba,wai yara ba manyan mata hamshakai wallahi. Ke dai kawai Allah ya gyara muna amma a lokacin muke da in kana da da namiji ko mace baka huta ba kowa da tashi irin matsalar. Ki dai yi hakkuri kada ki sa zancen a ranki harki jawa kan ki matsala babba yazo yai maki illa a,rayuwanki. Maji tai mata godiya inda hajiya Kubura ke cewa don Allah a dake da addua da rokon Allah kuma ki toshe kunnnen ki ga duk wani magana ko gorin da wani zai maki don ba wanda ya wuce hakan ai. Maji takara cewa nagode Hjy Kubura nagode kwarai Allah ya saka da alheri tabar dakin tana masu sai da safe. Ta kawo daidai tagan hjy Asiya taji tana cewa yaran ta wallahi kuyi hankalin da mashayin nan na gidan nan kunga ya fara haukacewa don haka duk wanda ya shiga tsabgan shi kun dai san ba,a shari,a da mahaukaci sai dai ace kuyi hakkuri an cuce ku. Shigewa tayi part din ta tana jin kamar ta hade ranta yadda zancen yake mata kuna a rai. Ikon Allah yau Sadauki dan cikina ake kirawa hauka da raina ikon Allah Allah ka taimakeni ka,shirya min wanan yaron ya Allah na rokeka. Hajiyan masa bata zaina ba da dare ma sai gata ta dawo gidan ta kara ba Maji hakkuri inda suka kara tattaunawa akan al,amarin tai mata alkawarin shiga da fita don suga ya daina wanan harkan. A nan tabar Bintun ta don dama ba yazo don ta,bane sai dai duk shiyan nasu ranan haka suka kwana cikin bacin rai babu maidadin rai daga cikin su. Washe gari ma haka suka tashi sukuku duk ran su ba dadi saida safe ne Alhaji yakira su gaba dayan su ya tarasu a falon shi. Inda ya kira sadauki da sauran yan uwan shi suka zauna don tattauna matsalar da,ya fada ciki. Bayan gurin ya natsune maigidan yafara magana kamar haka. Dama nataru kune nan don kowa yasan akan dalilin dana kiraku nan, batare da dogon magana ba ina son kowan ku yasani Umar gashi nan a gaba na daga yau na yafe shi daga cikin diya na. Don ba zan zauna da dan da zai jawo min abin kunya ba a gidana, na,wuce ana nunani ga mahaifin mashayin nan can. Kuma ka sani daga yau kada ka kara shigo min gida don kada ka bata min sauran yarana kimtsatu. Uwargidan su tace gaskiya wanan matakin yayi daidai wallahi don gaskiya nima tun jiya nake wanan tunanen don barin shi cikin mu gamu da yawa a gida yana iya sa wani yaron yai koyi da halin shi na banza. Mama Asiya itama ta tare zancen dacewa nima wallahi hakan yai min daidai don gaskiya barin shi a cikin mu babban hatsari ne don kada wata rana ya zo ya shawo ya kama mu da bugu. Wani irin zafi da dacin zuciya Maji take ji shiko sadauki kan shi yana duke don kunyan mahaifiyar shima yake ji ba nasu ba don yasan shine ya jawo mata wanan sukan da ake mata mai kama da an daba mata wuka a zuciyar ta. Assha Alhaji wanan maganan da kayi wallahi ba girman ka bane. Ka taba ganin inda hannun mutum ya rube ya yanke ya yar dashi, don Allah ya jarabi wanan yaron da wanan lalurar shine zaka yanke wanan danyen hukuncin haka akan shi. Wallahi baka kyauta masu ba ko kadan in kai masu haka daga shi har uwar shi. Idan bamu jashi a jiki muka nuna mashi illan abinda yakeyi ba kyau ba, watau ya tafi ke nan yafi nan lalacewa ko? Gidan kowa yanzu akwai matsala in hat gida babban gida ne amma kowa hakkuri yake yana boye abin shi yana jan kayan shi a jiki. Amma ya daina shigo maka gida dakace ita uwar shi a ina zata gan shi har tasan halin da yake ciki ta tsawata ma abinta. Da dai ka haife shi kuma jerabawa ya fado kan shi sai ayi hakkuri anema mashi shiryuwa ga Allah shine daidai. Kai ji hajiya kubura wallahi ni ban son al,amari da munafunci uwar ahi in tana son ganin dan ta taje gidan mashaya ta,samay shi mana inda yazabi zama. Umm,umm hajiya Asiya wallahi daji bai gama cin wuta ba ba aiwa kututure barka, kema fa uwace kamar hajiya maijidda don haka kii iya bakin ki. Tuff tuf wallahi bakin ki ya sari danyen kashi wallahi nikan ba,a cikin kayana ba wallahi, watau baki kike min akan diyana ko ? Ni ba baki nai maki ba gani nayi ko ita uuwar shi bataso dan ta da hakan ba, jerabawa ne dai daga Allah ya fada kan shi. Kaidon Allah ni ya,ishe ni ban kira ku nan ba don kuzo kuna min cacan baki kiran ku nayi don ku ji shawarana. To gaskiya Alhaji shawaran ka bai yi ba gara ka canza wani, wani irin huci Alhaji yayi yafitar da iska daga bakin shi. Yace naji amma idan ya ganin ni wallahi ya kama kan shi inba haka ba zamu sa kafan wando daya dashi a gidan nan kaji na fada maka yaron banza yaron wofi kawai. Tashi ka bani guri mara mutunci kawai mun sakafan wondo daya dakai a gidan nan wallahi ko. Allah dai ya,shirya muna shi kawai za,ace amma wanan fadan ai bayi ba,wallahi tana fadin haka tamike tabar dakin cikin bacin rai, sauran suka bita da kallon ke asuwa munafuka mun san sallon kishin ki ai. Ita ma Maji mikewa tayi tabar dakin tabarsu nan tafada dakin ta tana kukan bakin ciki da takaici. Yau dan ta yaja mata wullakanci ga kowa agidan saboda shi anzaunar da ita ana fada mata magana son ran mutum. Shiko Alhaji ya mutuwan son hajiya kubura badon yaso ba ya yarda da,shawaran ta don kawai kada su sami sabanine a gidan. ****** ********* ****** Tun da akai wanan case din sadauki bai kara,shigowa gidan ba yau kusan sati daya ke nan haka ranan abin da da mahaifi maji tatura maryam ta duba mata shi idan yana nan takira matashi don tana son suyi magana dashi. Itama hajiya kubura ko yaushe tana tambaya idan yadawo ko ya shigo sai maji tace mata bai shigo ba ai. Maryam ta samay shi a kwance dakin shi ya yi kwanciyar rigingine yana kallon saman dakin ta tsaya daga kofa tagaida,shi tafada mai sakon mahaifiyar su. Yace taje tace gashi nan zuwa, ta dawo ta fadawa maji abinda yace mata bayan kamar minti goma sha ya,shigo gidan sai dai bai shigo ba kamar yadda ya saba ya dan tsaya daga waje kadan ya tura wani dan kannin shi ya kira mai maji dakin ta. Yaron yashigo yana cewa yaya sadauki ne yace na kiraki yana daga waje wai. Amira tace bazai shigo ba ke nan bari naje na shigo dashi, maji tace ai kunya marin da ne . Amira na zuwa tace yaya Maji tace nace kashigo daga ciki mana ka tsaya nan . Yace look Amira ki fada mata bazan shigo ba gani nan dai tazo ina jiran ta, tausayin dan uwan ta ya kamata ta juya rai a bace takoma ta fadawa uwar nasu abinda yace mata. Maza jeki kice mashi nace bani son diban albarka shi da yai laifi ba,ai fushi dashi ba dai shine zai wa mutane zuciyan banza. Amira na fada mai sako sai gasu a tare sun shigo gidan da ita. Yana saye da farin shadda a jikin andanyiwa shaddan kwalliyan dan bakin kyalle a gaban rigar da fari. Ya shigo da,sallama ya koma kaman wani kamili dashi ya ramay yai dan dogon wuya sai dan bakin da yayi. Maji ina wuni kamar bazata amsa mashi ba tai shiru ya samu guri ya zauna a saman kujeran dakin. Tausayin mahaifiyar shi ne ya kama shi don ita ma ta,ramay ta,fada sosai da ka kalleta kasan tana cikin rashin kwanciyar hankali sosai. Yaya ina wuni muryan Bintu da ke mikewa zata shiga daga ciki ne ya katse mai tunanen shi a lokacin. Lafiya kawai ya amsa mata,dashi sai kuma dan abinda ya,faru ranan yafado mai a rai din ya dan iya tuna lokacin da ta bude mai baki kan shi yana samancinyan ta ta tura mai manja a ciki. Wani irin kunyane ya kama shi da nauyin yarinyar don yasan ta taimaka mai har sau biyu a rayuwan shi. Maji tace kai ba,ai fushi dakai ba shine kai zakiyi da mutane ko, da kai fushi kaki shigowa may kake nufi da yin haka. Maji ba,wai hakana bane kinji abinda baba ya fada ai shiya sa ni kuma naga gara kawai nabar shigo mashi gida kada na ja maki matsala. Matsala kuma na yaushe sadauki akwai maysalar da kuma yafi wanan din da ka jawo min ne a cikin gidan nan. Maji don Allah kiyi hakkuei wallahi kaddarace amma ban taba shan kwaya ba sai ranan koshi bacin raine na rashin barina nabi abokai na gurin kwallon da akayi yakaini ga hakan. Insha Allahu bazan sake hakan ba da yardan Allah don Allah dai kiyi hakkuri maji ya fadi cikin kwantar da muryan shi. Yanzu Baba na kana ga inin irin hanyan da ka daukar wa kanka shine daidai gareka gare mu ma. Kaiwa kanka fada,wallahi ka dibs ka gani saboda kai aka zaunar da ni kowa na fada min irin abinda yaga dama a lokacin. Inda ka gyara halinka duk gidan nan wa ya isa yai muna haka babu shi wallahi don ni ba ruwana da harkan kowan su. Amma sanadiyar abinda ka aikata ji irin yadda kowa ya takamu son rashin ana fada muna abinda aka ga dama. Maji kiyi hakkuri don Allah insha Allahu ba,zan sake ba da yardan Allah hakan ba,zai sake faruwa ba. Nan dai taita mashi nasiha tana cewa yanzu ashe badama su Amira su yi laifi na kawo maka karan su a matsayin ka na babba a cikin su. Ni hajiya kubura wallahi tai min komai don ta nuna min ita uwace a gareka kuma tasan ciwon kan ta ba kamar sauran iyayyen naka ba. Don haka wallahi kaiwa kanka fada kaceci kanka kace ceni ni uwarka da yan uwanka kafitar damu daga zagi mutanen duniya. Sun kai wani lokaci tace ya tasgi ya tafi take ce mai kuma daga yau ya tabbatar da ya dinga zuwa gida yana cin abinci bata son yana ci a waje inda batasan ko ina bane. Yai mata godiya ya mike yabar gurin tare da kara bata hakkuri yabada baya take cewa jika don Allah kamar wani mutumin kirki can ashe mutimin kawai. Murmushi yayi yace kiyi hakkuri maji don Allah bazan sake ba insha Allahu. Yana fita ta sauke ajiyan zuciya tare da cewa a filo Allah ka,shiyar mun da wanan yaron dama sauran yara masu halin shi na,wanan lokacin,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYABA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,, A LOKACIN MU KE,,, Murna sosai takeyi don ganin ta dauko sabon fridge dinta da ta dade tana gurin taga ta saye a rayuwan ta, don bunkasa sana,arta. Ta bude fridge din yafi a kirga tana duba ciki da wajen shi don tabbatar da lafiyan shi. Ba laifi don ta samu yadda take bukata saboda sanyi da kankara yake daga sama har kasan shi tsab. Wanan abin yasa ta yini tana farin ciki da wanan karuwan da ta samu na ci gaban ta. Ranan sai da ta aikawa makwabta da kankara tana fada masu idan suna son saye ta sai fridge mai kankara da ruwan sanyi, don haka su sa mata albarka a ciki. Wasu sun yaba, wasu kuma sun kushe don haka duniya take dama wani baka hada komai dashi ba amma yana bakin ciki da karuwan ka a duniya. Shima maigidan ta bawan Allah da ya dawo yai mata fatan alheri akan fridge din, tare da yar guntuwar nasiha akan sai tayi hakkuri da jama,a don mai saye da sayarwa sai hakkuri dama. Sai dai kassh matsalan hauwa shine bata da hakkuri don ta sawa ranta masifan son kudi sosai. Ta manta cewa zafin nema baya kawo samu sai in Allah yaso bawan shi da arziki yake arziki. Ba dama mutum yazo sayen kankara ya mayar mata koda yace bai kankareba sai ta hau masifa da fada taki canzawa mutum abinda yake so. Gashi duk samun da takeyi yanzu baisa mijin nata yakai idon shi ba ga kudin ta, don ko ba dadi sai yakawo masu dan abinda zasu dafa agidan suci. Yana da matukar kokari gurin ganin ya kare hakkin iyalin shi sosai a rayuwan shi. Amma daidai da rana daya idan dan wani abu ya kasa ga cefanen shi sai Hauwa tai mirsisi taki yi masu girki wai sai ya ciko ta girka masu. Don ita bazata yarda da akidar cikawa namiji kudun cefane ba saboda itama tana da nata bukatan ai da kudin ta don yanzu ta sa rai wai fili take son saye ta yarda kaddaran itama. Baida fushi hakan bai damun shi, dole sai ya samo ya cika mata sai ta girka masu inba haka ba su kwana da yunwa har yaranta. Wanan kuma ba komai bane sai zugin uwarta da kullun take mata hudubar shedan akanta. Na karta yarda da namiji don tana ganin ta ita kadai bai hana wata rana sai tagama kashe maijiki ya ce zai jajibo mata kishiya. Halin Rashi hakuri irin na hauwa yasa mutane suka dan rage shigowa sayen kayanta yanzu sosai sun kwammace suje wani guri su saye. Haka yasa ake barinta da kimin kankara a fridge har su narke tayi hasaran kudin ta. ****** ******* ****** Cikin mota suke a kofan gidan su Raiha yana yadda ranshi yaso da ita, a cikin rashin damuwa Raiha ta barshi yana juyata yadda yake so. Don son shi da kalaman shi ko yaushe suna kara tasiri ne a zuciyar ta don ta yarda dashi 100%. Daga nesa matasan dake zaune suna hira hankalin su yana gare su tun shigar Raiha motar, daya daga cikin matasan yake cewa kai yanzu dai mutane basu da tsoron Allah wallahi. Kadiba fa yarinyar can ina lura da ita tun dazun suke zaune a motar nan har takai motar tana motsi don kanta. Ashe bani daya nake lura da hakan ba inji dayan matashin yaba dayan amsa. Sai dayan da sai yanzu yai magana yake cewa ai wanan yarinyar batayi ba wallahi. Gaba daya haliyar ta baida kyau bata dauki kanta diyan tallakawa ba ko kadan takai kanta inda Allah baikaita ba ko. Ni yanzu Raiha tafita raina tunda abokina yake fada min cewa yagan ta uguwar su gurin sayen kayan maye. Kaifa Nasir ? Yace wallahi ranan daya ganta a uguwar nan yake ce min a uguwar nan take ne nace mashi eh. Shine yake cewa babba yar hannu ce sosai tana zuwa uguwar su gurin wani deler ta sayo kayan aiki masu karfi a can. Sai wanda yafara magana yake cewa kai amma ko udan gaskiya ne wallahi dole mu saka mata ido don kada ta kawo muna matsala ga sauran yan matan shiyan nan. Yanzu kai ya kake ganin zamuyi yace kokari zamuyi mu kamata a hannu sai mu dauki mataki daga iyayyen ta mana ko yaya kuka gani. Hakane sauran suka bashi amsa da,sauri suna cewa wallahi in har ba,a,dauki mataki ba zata iya gurbata wasu ba,a sani ba. To yanzu ita ina ta koyo wanan bakar akidar naga dai a uguwar nan ta tashi a gaban mu ai. Kai yanzu sai wani ya koya wa mutum hakane abin fa masifa ne kawai sa warai ne ai. Ni wallahi mamaki take bani yadda idon ta ya bude baki daya a lokaci guda haka. Kaidai bari ai yanzu haka kila a makaranta ko kuma wasu sabbin kawaye ne suka koya mata wanan harkan. Tana shiga gidan mu gurin kanne na zan shiga nai masu fada wallahi su rabu da ita tun bata lalata min kanne ba. Kaidai kawai Allah ya,sauwaka ita kuma Allah ya shirye ta don kaga ai mahaifinta mutumin kirki ne. Uwarta kuma bata ko magana shiru shiru mutumiyar kirki ce sosai don bakajin ance ga abinda tayi a uguwar nan na assha. Sai wani lokaci Raiha ta bude kofar mitar ta sako kafan ta guda daga waje, daga inda matasan suke zaune suna iya hango ta daga cikin motar tana gyara rigar ta da kuma saka hijjab din ta. Allah ya kyauta amma dole mu dauki mataki akan wanan fitsaran da ake muna da rana tsaka a uguwa. ****** ********* ****** Abin duniya ya ishi zuciyar Umar faruq ya rasa yadda zai shawo kan Maji ta yarda ta mara mai baya akan zancen tafiyan shi zuwa ghana kwallo kamar yadda yan club din su suke son yaje ya buga masu ball. Haka yasa yafara dirkawa cikinshi kwaya kala kala har takai ya shiga hali na maye sosai. Fatima don Allah zoki sayo min magani kafin duhu ya kara yi don yanzu dana aiki su Amira Alhaji yagan su fada zai min sosai. Kiyai sauri ki dawo da wuri kinji Fatima kada ki dade kinji Fatima dare ya soma sosai. Don takwas saura yanzu, ban son fitan dare ga diya mace haka koshi dole yasa zan aike ki don kaina ya matsa min da ciwo sosai wallahi. Bintu ta dauko hijjab dinta ta,saka ta fito ta karbi kudin maji tafada mata kalar maganin da take son a,sayo mata. Tana zuwa aka bata maganin ta juyo zuwa gida gap da zata shiga gidan ne taga mutum a kwance bakin get. Sai faman nasari yake harta dan raba shi zata wuce don tagane wanene a kwance gurin. Da,sauri ta dawo ta dan duka a kan shi a hankali tana fadin. Yaya sadauki ka tashi ka,shiga daga ciki kada wani ya gan ka anan haka. Da kyat ya bude idanuwan shi ya kalleta cikin maye ya nunata da hannu ya bude baki da kyat yana fadin, tare da nunata. "Ke zan _ci uban,ki idan baki ban guri ba walla_hi sai ya mayar da kan shi kasa. Innalillahi Bintu ta furta a fili ta mike tsaye kamar zata wuce sai kuma taji bazata iya ba don idan har wani ya gan shi a haka yashe a kasa cikin maye, yau bakwanciyan hankalin ga Maji dama gashi kanta tun safe take yana mata ciwo. Komawa tayi iya karfin ta ta dago shi daga kwancen da yake ta na cewa tashi yaya ka koma dakinka don Allah. Shegiya idan baki barni ba zan maki dukan tsiya wallahi, yafadi a cikin muryan dan maye. Bintu bata bi ta nashi ba sai kokarin mikar dashi take shiko sai ashar yake jefa mata. Cikin ikon Allah ta samu ta daga shi daga inda yake kwance ta kaishi daidai kafadan ta duk da yai mata nauyi amma haka ta daure ta ja shi zuwa dakin shi. Da kyat ta lalabo key daga jikinbshi cikin wandon shi na baya ta bude dakin tana,shiga wani wari ya daki hancinta, haka ta daure ta kaishi bakin katifan shi. Sai barci yake a kafadan ta cikin maye, tana son kifar dashi don duk tagaji saura kiris su zube tare sai ya kwararo mata amai da fitsari a lokaci guda duk ya bata mata jiki dashi. Haka ta daure ga,warin amai yana damun ta ta kifar dashi akan katifan dakin. Kallon hijjab din ta da ya lalace da amai da fitsari tayi tare da girgiza kanta tana Allah ya kyauta tajowo mai kofan dakin tare da dunkule hijjab dinta daya lalace da aman shi. Gap da zata shiga gida taji karan motar Alhaji habu dake dawowa daga kasuwa, shi da sauran yaran shi dake bin shi shago. Da,sauri ta karasa kada suga fitowan ta part din samarin gidan kuma dakin sadauki su fassara mata zance. A can cikin gida kuma Maji hankalinta ya tashi sosai ganin Bintu ta dade sai gata saidai a hargitse take don hankalinta ya tashi. Amira data kalleta yadda ta shigo gidan take cewa, ke lafiya kika dawo wata kala haka dake ji yadda jikin ki ya lalace. Saida Binta ta kalli jikin ta take cewa cikin sauri faduwa nayi gurin kwata da,wata mota tabiyo gefena. To amma ai ba kwata bane kamar amaine jikin ki tace gurin masu saida abincine gurin. Ta mikawa Maji maganin ta,shige ciki don duk a tsawale take da aman dake jikin ta dama. Saida tai wanka ta gyara jikinta tsab tafito falon inda suke ta zauna tana kallon shirin da ake a sokoto tv. Maji dai bata ce masu kalla ba don kanta da yake damunta da ciwo a lokacin. Sai da ta dauki lokaci bayan tasha magani sannan kan ya fara lafa mata don ranan bata ko fita zuwa yiwa maigidan su sannu da,dawowa ba. Wai ko yau yayan ku yadawo kuwa don banga ya shigo ba daukan abincin shi. Amira tace, waya sanan mashi kila yana can gurin yawon banzan shi sai baba yasan bai gidan yazo yaitawa mutane masifa akai. Bintu tace da zan shigo nagan shi zai shigo da leda da,ya,sayo doya soyayya gurin mai sayar wa nagan shi da zan wuce yana saye. Oho ashe shiyasa banga yashigo ba ya samu abinda zaici ke nan . Ai da yana jin yuwa da yanzu yashigo ya cinyewa mutane abincin su ko inji maryam. In baici abinci ba nan a ina kuke son yaje yaci ne maryam, ni dai idan zai shigo yaci a nan din ai zaifi min komai dadi. Bintu taji tausayin Maji ya kamata a zuciyar ta take cewa kai uwa uwace dai. Da yau maji zata san halin da dan ta yake ciki tasan da yanzu suna cikin tashin hankali da balai a rayuwan su a shiyar su. Amma dai yau Allah ya rufa wanan asirin an wuce gurin in ba,wani ikon Allah ba kuma. Tana jin su suna hiran su amma bata saka masu baki ba sai faman tunane take a ran ta. Shigowan baba a part din ya katse mata tunanen ta suka fara gaida shi suna mashi sannu da,dawowa. Bintu ce tafara mikewa tashige daga ciki sai Alhaji yabi su Amira da harara dole suka mike simi simi suka shige bayan Bintu. Yace marasa kunya kawai wai har bakuwa tafisu hankalin sanin ya kamata. Har yanzu gwagon yarinyar nan bata dawo bane ko kuwa dai? Bata dawo ba Maji taba shi amsa a takaice, takara da cewa ni ban ma son rabuwa da yarinyan don halinta na kirki yai min. Hmmm ki dai ji da na kanki kafinki kara jajibowa kanki sabon matsala ya bata amsa. Ai Fatima ba matsala bace zan ma iya cewa zaman ta ya zama min alheri don kaga yaran nan suna samu karuwa sosai a gurin ta ga ta yar karama amma akwai addini sosai a kanta. Ta godewa Allah da,ya bata wanan baiwan har takai ga samun yabo haka na alheri Allah muma ya shirya muna yaran mu. Ban ganki ba ne yasa nabiyo nagani ko lafiya don nasan ba halinki bane rashin zuwa yi min sannu da kasuwa. Maji ta dan ya mutsa fuskanta tana cewa wallahi tun safe nake fama da ciwon kai yanzun ma aka sayo min magani na,dan sha shine naji yadan fada min. Naso naje gaishe ka amma sai nai tunanen ko ka shige ne ko ai. Ki daina shan magani haka batare da likita ya baki umurni ba idan kinji kan ya matsa maki aida kin kirani nazo mun tafi asibiti ko . Naga ciwon kaine kawai shiyasa ban dauke shi wani babban ciwo da zani asibiti ba. Haka dai kikace a lokacin da ya karasa takon shi inda take zaune yana kai hannun shi akan wuyan ta don taba jikin ta yaji lafiyan ta. Kai haba Alhaji ai na samu sauki dana sha maganin nan yanzu, ki dai bar wasa da ciwo don ciwon da ka raina shike zama babba yanzu. Allah dai ya sauwaka inji maji tafada cikin dan sauke ajiyan zuciya. Ki dai bar tunane akan wanan yaro ki kai kukan ki ga Allah shine zai bamu mafita akan shi,insha Allahu. Allah yada inji Maji ta fadi voice din so soft don zancen Sadauki yana tayar mata da hankalinta sosai. Daga haka yai mata saida safe yabar part din nata cikin tausaya mata halinda take ciki yanzu kan lalurar dan ta wanda duk ta tayar da hankalin ta. Washegari sun tashi kowa na batun fita zuwa makaran ta sai Bintu ce a gida don ita yau basu zuwa makaranta suna hutu. Part din nasu yai shiru bakajin motsin kowa duk lokacin kowa yafita zuwa nashi tsabgan gaban shi don ci gaban rayuwan su. Wani irin yunwa ne ya farkan dashi daga nauyayen barcin da ya yi mai tsawo bai san inda yake ba. A hankali ya bude idon shi inda ya kurawa silin din dakin nashi ido, can yakai kallon shi ga agogon dakin a hankali yaga har tara da rabi na,safe. Da kyat ya iya mikewa zaune ya samu har yakai tsaye don yunwan da yake ji yai mai yawa sosai a lokacin. Wanka yashiga yana wankan ne abinda yafaru jiya da dare ya dan fara dawo mashi a,rai. Kai aiko na,shige su tunda wanan bakuwar yarinyar ta san da wanan zancen don yanzu nasan ta fadawa Maji halin da,ta ganni a ciki daren jiya. Aiko idan har ta fadi sai yai mata dukan da sai an kwantar da ita asibiti sai da ya shirya tsab yafito tare da kulle dakin shi ya nufi cikin gida don ya gaida Maji ya kuma karya saidai gaban shi na faduwa badon yana son cin abinci ba da bai shiga gidan ba a lokacin. Da sallama a bakin shi ya shiga part din nasu duk da ya hadu da mama a kofa amma bai mata magana ba ya shige abinshi tabishi da harara tana fadin mara kunyan yaro kawai tabbatacce. Maji dake zaune saman salaya tana lazumi ta karba mai sallaman shi tana cewa sai yanzu katashine babana kowa a gidan manya da yara sun kama gaban su ko. Yace cikin dan shafan kan shi wallahi Maji barci ne ya kara daukeni bayan mun dawo daga sallah. Ai jiya da,dare muna ta jiran kazo kaci abinci baka shigo ba har ana batun rufe gida sai Fatima ce ke fada muna cewa. Gaban shi yai wani faduwa ras ras kafin yaji ma yarinyar tafada wa maji din. Maji tace take ce muna ta gan ka,,, lokacin Bintu tafito daga cikin daki tana cewa Mama a canza zanin gado ne. Wani uwar harara ya,watsa mata saida ta kasa fadin maganan da zata kara fadi. Maji tace ashe jiya doya kaci ka kwata gata itace ke ce muna tagan ka kana,sayen doya da kwai da dare dana aike ta. Wani wawan numfashi ya sauke tare da dan sake fuskan shi yace eh wallahi maji shi nake son ci shiyasa na saya ai. Fatima dauko wa yayan ku abinci shi ya karya yafita shima don ban son zaman gidan nan kamar mace. Bintu ta juya inda yake tana cewa ina kwana yaya can kasan harshen shi ya amsa mata da lafiya kalau, Ta juya zuwa cikin kitchen ta dauko mai abin karin shi takawo mai gaban shi ta duka don ta aje mai ya faki idon Maji yana cewa kin kuru baki fadiba dana karyaki yau wallahi. Da sauri Bintu ta mike tabar falon don kada ya kara ce mata wani abin kuma don ko yanzu ta tsorace dashi don mashayi ba abinda bai iyayi shi. Sunaci suna hira da mahaifiyar nashi tana dan mashi hira maikama da nasiha sai cin abincin shi yake hankali a kwance abin shi. Daidai Bintu na shigowa taji yana cewa ni dai Maji don girman Allah ki yardan min natafi wanan wasa kiyi hakkuri ki gwadani ki gani idan ban canza ba kada ki kara bari na tafi don Allah maji. Daka ta sadauki na riga na fada maka cewa bazan yarda da zancen tafiyan ka ba,wani kasa can da babu kowa na gida a tare da kai, nan ma da kake a gaban mu yaya muka kwashe da kai? Bintu batasan yadda akayi ba tace mama yace don girman Allah ki barshi yaje insha Allahu zakiga canji a gare shi da yardan Allah ke dai adduan ki yake nema da yardan ki. Da har zai bude baki yace ke wayasa bakin ki zan balballaki yanzun nan, amma sai yaji maji tace . Fatima bar shi kawai ni nasan halin abina ke yarinya ce baki gane may nake nufi da zance na yanzu amma ba zancen tafiya a guri . Tafiyan ma fa wai na wasan kwallo haba sai kace uwar banza da batasan ciwon kan ta ba. Maji komai zamuyi saida adduan ku don haka kamara yayi kisawa zancen albarka ki mara mashi baya yakai ga kudirin shi. Don ba,a san mai gobe zai iya yi ba shiru maji tayi tace kai Bintu badai iya magana ba dai kam. Shiko Umar shiru yayi yana mamakin wanan yarinyar yadda ta iya magana haka kamar wata tsohuwa can. Fatima naji zancen ki sainai shawara ya dan dakance ni kawai nagama nazari nagani , Daga haka ya mike tare da cewa cikin murya ba dadi zan fita sai nadawo Allah ya tsare tace sai kadawo. Haka fita jiki ba karfi yabar dakin sai dai yaji dadin yadda wanan yarinya ta saka baki har Maji ta dan yi taushi sosai yagani ai. Tun lokacin da sukai wanan magana hankalin maji bai kwanta ba sai sakawa take ta walwalewa a ran ta daga karshe dai ta watsar da zancen ma kawai. A na cikin haka gwagon Bintu ta dawo daga kawai ta zo gidan bayan ta huta don ganin Bintun ta. Nan suka tare ta da murna sai bin Bintu take da kallon yadda gaba daya ta canza mata a fuskan ta ta kara haske da kiba, taiwani irin kyau da ita. Nan ta shiga yi wa Maji godiya da karamcin da tai mata akan rike mata yarta yar dan uwan ta da take hannun ta. Maji tace haba hajiyan masa ai Fatima mutun ce yarinya ce mai dadin zama da sanin ya kamata sosai. Naji matukar dadin zama da ita a gidan nan don ta taimaka min da abubuwa da dama a gidan nan Hakane ma yasa nace ko kin dawo bazan barta takoma gurin ki ba sai dai mu zauna nan da ita tunda danan da can guri ki ai duk dayane kuma a shiya daya muke dake. In dai har hakan bawai zan takura maki bane gwago tai godiya da karamcin Maji tana cewa nagode Hajiya dama ba zama nadawo nayi ba don jinya nake a can na yayata da bata da lafiya. Shine naga na barta a nan da suna sati biyu gashi har nai sati hudu a can baku da labarina, kada hankali ku ya tasbi na rashin jina da bakuyi ba na tsawon lokaci. Ai babu komai nasan tunda najiki shiru lafiya ne ai tunda kin san inda aka barta ai. Nan suka dan taba hira gwago tana bata labarin rashin lafiyar yar uwarta da take jinya a kauyen su. Da zata wuce ne ta bukaci da Bintu ta rakata ta dan gyara gida don kuran da yayi na rashin mutum a cikin shi na wani dan lokaci. Aiki sosai Bintu tayi a gidan harda girki saida tai masu don suci tanayi tana tambayan gwagon ta labarin mutanen gida. Sai da suka natsune Bintu takw fada mata irin rayuwan kawai cin data samu a gurin Maji da kuma irin matsalar da take ciki akan dan ta da baijin magana da bukatar shi a gurin mahaifiyar shi na son tafiya wani gari buga kwallo da yake son zuwa yi. Gwago tace kai amma ko hajiya da ta barshi don bata san ko shine mafitan ta ba arayuwa tunda har yai mata alkawarin canzawa idan ya dawo. Gwago tana fada irin ta manya tana fadin ai gara ta barshi ya tafi don batasan abinda Allah ya shirya ba a kan yaron. Suna ta zancen ita da gwagon ta har dai dare yayi don haka ranan a na gidan su Bintu ta kwana da,gwagon ta suna kewan junan su. Sai washegari da yamma ta shigo gidan cikin jin kunyan Maji da yaran ta, sai faman yi matasheri sukeyi taga gwago ta gudu masu. Maji tace yanzu Fatima haka zamuyi dake ni da nake fadin anan zaki zauna shine kina gani gwagon ki kika gudu gurin ta ko? Ko dama bakijin dadin zama damune dai kika boye muna hakan ? Da sauri Bintu takai kasa tana cewa ,a,a mama ba hakana bane kawai dai na tsaya ne na kara shirya mata kayan ta. Jeki ga abinci can a kitchen ki diba kici inji Maji tana mata magana cikin kallon fuskan yarinyar. Mama na koshi gwago tai muna gwaben ganye mun ci dazun mun koshi sosai ban jin yunwa yanzu. Sai dai anjima in Allah ya kaimu. Daga nan ta samu guri ta zauna tana kallon maryan dake dakilar wayan ta tana dariya ita kadai. Sun kai wani lokaci falon yana tsit kowa yana tsabgan gaban shi sai Bintu dake ta tunane kala kala cikin ranta yadda zata zauna a gidan nan dake cike da tarin matsaloli. Fada sukaji tsakanin mama Asiya da uwargida ya kaure sai cacan baki suke a kan yaran su. Maji bata fita ba tana zaune a falon ta har sukaci suka sude ko magana batayi ba, sai ma Amira da tace su daici kan su munafukan banza kawai kanku ake ji. Sai lokacin Maji tai magana dacewa Amira ban son rashin kunya fa iyayyen naki kike zagi da munafukai kuma. Kada na kara jin wanan kalamin a bakin ki ko kin manta cewa ke ma watarana uwace a wani gidan. Shiru Amira tayi don tasan in ta kara furta,wani abu yanzu Maji zatai cikin ta da masifa sosai. Har masu fadan suka kare cacan bakin su da tonon asiri ba,wanda yai magana a dakin daga dakin mummy Amarya ma ba tafito ba haka ma yaran ta. Don ita dama,yar i don't care attitude ce a,gidan harkan kowa bata shiga sai in abu yakai mata karo. Sai da yamma sosai gwago ta shigo gidan gurin Maji inda ta aika mata da abincin dare tace kada ta girka komai ta dinga bari akai mata daga nan gidan su. Shine gwago tashigo yin godiya gurin Maji din da,wanan irin halarcin da take gwada masu haka. Maji tace haba dai mai masa ai yiwa kaine ina laifi duk cikin shiyan nan baki aminta,da kibar yar ki a gurin kowa ba sai gurina, kika yaba da ni ai wanan ma wani mutuncine babba. Murmushi gwago tayi tana cewa Allah dai yabar daukaka da girma Allah kuma ya kara shirya muna yaran mu. Ameen inji Maji tare da sauke ajiyan zuciya a fili tace bari mai masa ba boyo a tsakanin nidake yanzu. Jin haka yasa Bintu tai saurin mikewa,zuwa ciki tabar su gurin ganin ta,shige yasa maji hararan su Amira dake zaund suma din mikewa sukayi suka shige suna zunburo baki gaba. Maji ta kara kwantar da muryan ta kasa, tana cewa hajiyan masa ina cikin matsala da,wanan yaron na,waje na. Yayan su Amira ke nan inji gwago maji tace shifa,wallahi sai tace cikin kariyan murya mai masa yaron nan yana son kashe ni wallahi. Maganar safe daban ta rana,daban ya zama wa kowa kaya a gidan nan balle ko banza kin san irin zaman da muke a gidan nan. Yanzu msi masa nifa har na fara,zargin ko yana shaye shaye ne don abinda yake abin ma bana kai sake bane. Subbahanallahi i ji gwago Allah ya tsare ya kare hajiya amma kada ki mashi mumunan zargi haka don Allah. Koma maye dai dole ke uwa hakkuri zakiyi kikara jan danki a jikin ki kina nusar dashi hanyan alheri har ya gane. Mai masa ni yanzu har abin yana son yafi karfina wallahi don kinga sam yaki zancen shago kamar kowa shi kuma ba,wani sana,a yaje zuwa yi ba yadda kowa keyi. Ina gani a gidan nan ko wani da yana kawo wa uwar n shi abin arziki daga shago amma ban dani sai ma shi Alhanin ne wani lokaci yakan ji tausayina ya dan taimaka min ko shi da kwankwami da komai yake min. Tunda kinga ba karfine gareni ba don ni banyi karatu mai zurfi kamar sauran matan gidan ba. Amma mai mas wanan yaron duk da haka bai zama min da ba wallahi takare da sake kuka wi, wi,wi a lokaci guda. Ba kuka zakiyi ba hajiya kamata yayi ki kara jajirce kina mashi addua da fatan alheri, kin fasan bakin uwa taki ga "yayan ta. Mai masa wallahi inayi sai dai kawai na kara akan wanda nakeyi don banda lokacin kai na ko yaushe sai na yarana tun bai zama haka ba ma, balle yanzu da al,amarin shi yai kamari sosai cikin gida. Yanzu ke hajiya baki fahinci ko akwai wani buri wanda yafison yayi abin ba akan kasuwan ci din. Saida Maji ta share hawayen da ke fuskanta take cewa, mai masa waifa shi ba komai bane gurin shi sai sha shanci wai kwallo. Kwallo yake da ra,ayin yi maigidan mu yayi fada har yagaji yanzu ya saka mashi ido yabarshi da kwallon. To hajiya wa ya,sani ko anan alherin shi yake ga wasan kwallon. Wasan kwallo kuma mai masa za,a samu wa i alheri a cikin sa ? To ba haka naji ana fadi ba wai suna samu ga harkan sosai kinga sai muyi mashi addua mugani ko anan arzikin nashi yake. Hmmm mai masa ni wanan ai abin kunyane a gareni ace wai cikin gidan nan da na yafita zakka wai bai kasuwanci sai kwallon kafa kawai. May zai samu a cikin wasan kwallon kafa kuma banda shashanci irin na sadauki kawai. A,a hajiya ban son ki na fadi haka fa kin daiga ki godewa Allah idan har zaiyi wasan ya jawo mai alheri da kintsuwa ai gara a arshi ya,tafi yayi abinshi kinga,zaki rage taahin hankali don kin san inda yake. Ni kuma nai maki alkawari insha Allahu zan taimaka maki akwai gurin malamin dazan tafi maki can kauyen mu sai yai muna istihara akan matsalarshi don muga may ke damun shi ne wai. Don kingafa gidan ku babban gidane gaki da kishiyoyi marasa imani da tsoron Allah. Don haka abu na farko shine mu fara,sani may ye nasabar wanan matsalar tashi ne wai ? Shin daga Allah ne ko kuwa,saka mashi hannu akayi din a danbala makishi yakoma haka. Hmmm mai masa ba,wanda ya saka mashi hannu shashancine kawai irin na yaran yanzu . Ya hadu da miyagun abokai sun sauya mashi tarbiyan dana bashi tun farko don rashin tausayi irin na dan yau. Kin taba zuwa akai maki istihara akanzancen ne ko kuwa dai haka kike gani ke ? Gaskiya ban taba zuwa ba mai masa ina dai hasashen hakan ne kawai a raina. Hajiya yanzu duniya tai nisa wallahi kibar mutum inda kika barshi kai kana kwana,wasu na maka hansari ne, Balle yanzu ba,a zama kan yara ko nawane gareka dole katashi masu tsaye gurin nema masu tsari da kuma addua. Gaskiya ni mai masa ban taba yin komai akan yaran nan ba gaskiya nidai nasan ina masu addua sosai wallahi. Hajiya wanan zamani ai ya,wuce ko gurin mutane don zamani ya lalata mutane da son kai, don A LOKACIN MUKE,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU, PLEASE,,,, Bayan gausuwa a tsakanin su sai kuma dan shiru yafara biyowa baya hakan yasa Maji cewa yaran ku bamu guri mana ko. A,a su zauna ai gara suji abinda zan fada da kunnuwan su don su fahinci maganan da zan fadi da kyau. Tsit yaran har Maji su ka yi a falon bawanda ya koda dan motsa sai gwago ce tafara magana kamar haka. Na tafi kauye ne gurin wani malami amma dan uwana ne can gaba da kauyen mu. Na samay shi akan zancen wanan yaron sadauki ne amma kuma sai wani magana ta daban tafito muna. Kin san yanzu mutane ba imani da tsoran Allah a tare dasu. Kin san yanzun muna a lokaci, ga imani a baki amma ba shi ko kadan a zuciyan bayin Allah. Wai kuma a haka kowa ke son shiga aljannane , ga son duniya ya rufewa mutane ido da zukatan su. Wanan duniyan da ba bakin komai take ba ga mai imani da tsoron Allah. Wai may kuma ya farune hajiyar masa inji Amira da take jin digon bayanin da hajiyan masa keyi yai mata yawa. Waiko kina da hankali Amira baki da kunya fa ke ko kadan ,ina ruwan ki da zancen mu ne wai. Hajiyan masa tace barta ai zancen ne taji shi kamar da,tsawo a zuciyan ta. Mai masa ina,sauraren ki kinji rabu da mara kunyar nan futsarara. A,a hajiya barta don Allah duk ba yin kan su bane ai ,abinda ke tafe dani shine. Yaran ki gaba daya wallahi an sa masu hannu, duk yadda kike fatan samun su gaskiya a yanzu abin zaiyi matukar wuya. Don gaba daya an lalata masu rayuwan su ta inda ma baki zata ba wallahi. Kai ni wallahi ban son irin wannan spercition believe din na,anyiwa wani wani abu wanan ai duk shirka ne. Hmm kawai mai masa tace tare da fadin kaiyya bazaki gane ba ke yar nan sai an makara ko? Tiryan tiryan yadda malam ya fada wa gwago haka ta fadawa Maji bata boye masu komai ba don taga basu da niyar yarda yaran. Tabbas kuwa hajiyan masa na tuna anyi hakan don abin nima ya tsaya min arai sosai. Don wata rana yaya babba ta ce wai kifine ta dafa wa yaran ta zaunar da sadauki wai ga nishi da ta aje mai saida ya cinye shi tas, Ya kusa gama cine sai ga babangida dan ta ya,shigo yana cew sadauki ya,raga mashi amma,babu kunya a gaban mu yaya take cewa wai a,shi kadai tayi kada yaba yaron, Amma dashi sadaukin ya mikawa dan uwan sauran da ya,raga sai tai wa yaron nata jan ido akan idan yaci sai ta bata mashi rai sosai wallahi. Daga baya ne tunane yazo min cewa may zai sa yaya ta hana babangida cin kifin bayan tace a tare ta dafa masu shi. Wallahi ko anyi haka don ba,a fi watanni ba yaron nan yafara birkice min na rasa gane rayuwan shi gaba daya a gidan nan. Shagon da suke fita gaba daya ma ya daina fita duk fadan Alhaji dole yasa mai ido ya bar shi don ba yadda za,a yi dashi. To kinji ke mai cewa wai duk sharce ne na malaman tsubo kawai ko ku din ai baku tsira ba nan ta fada masu abin da su ma suke ciki a rayuwan su. Haba gaskiya abin kan da ban mamaki inji maryam don cewa fa su Lawisa basu kai mutu. Komai ba amma kullun gidan nan sune da sabbin samari kai gaka zaune ko tsoho bai zuwa yace yana son mutum. Amma gaskiya duk wace tai muna wanan abin inji Amira sai Allah ya saka muna wallahi ko. Ai ko baki ce Allah zai saka maku don zai koma kan mai shi da yardan Allah. Yanzu dai ga,wanan yace na kawo maku ku fara sha nan da,sati biyu zan koma na karbo maku sauran hadin insha Allahu.tana kokarin sance ledan dake a hannun ta. Kuma yace da hannunki zakiba ko wani yaro yasha wanan rubutun, shikuma sadauki idan da hali yace nazo mashi da kashin shi akwai abinda zai yi dashi wanda zai sa ko warin kwaya bazai so ya sake ji ba a,rayuwan shi. Cabdi aikuma shine babban magana wallahi don nasan ba zai yarda ba ya bani saboda shegen tauri kai ne dashi inji Maji. Lalai nima nayi tunanen hakan tun a can amma dai yanzu yi kokari ba,shi wanan. Ta kara fito da wani kulli yace da nonon akuya zaki hada ki bashi ya,shanye yace idan har abin yai aiki zakiga kwana biyu yana yawan barci ki kyale shi maganin ne yake aiki a kan shi. Nan dai taba da harda wanda su Amira zasuyi wanka da hayaki dashi don makarun asirin da ke kan su harda shi gaiyar aikin. Mai masa nagode nagode kwarai wallahi, ban ma,san kalar godiyan da zanyi maki ba ni wallahi. Wai yanzu don Allah shi mutumin bai fadi wanda yai muna wanan irin aikin ba ne don mu sani. Yafadi bai fadi ba yadai ce min mata biyu ne sai namiji guda kuma ba,atare suke aikin ba kowa tashi tafishe shi ne. Yace shi bsi son tonon asiri bukatar shi dai aiki yayi kyau asamu biyan bukata don fadin zai kawo hadin hasumi. Ikon Allah yanzun ni mai na tarewa mutane har na samu makiya daga cikin su haka.. Mai masa may nakd dashi a gidan nan daya tsone wa mutane ido dashi har za aimin haka wai ? Nuna yaran mai masa tayi tace gasu kuwa abinda kika raina,shine ya dami wasu ai. Wallahi Maji nafi zargin su mama da Umma don sune basu kaunan mu a gidan nan. Kada kuyi zaton haka ya kasance basu bane din don zato zunubi ne koda ya zama gaskiya. Kada azo ana zaton wuta a masaka,asmay shi a makera. Hakane fa to amma gaskiya su sunfi nuna basu kaunan mu sam wallahi tun muna yara mun san da hakan. Yanzun dai abar wanan zancen don koma waye mu barshi ga Allah shi zai saka muna. Yanzu mai masa nawa zanba wanan bawan Allah ke nan don ni har ma na rude wallahi. Dole ki rude ai don wanan magan ba karamar magana bace saboda yanzu a lokacin muke kana barci ana maka nasari a kai. Nan dai suka dan taba huran lokaci tsakanin su tai masu sallama tabar su nan suna jimamay. ****** ********* ****** Da farko maganan bai so damuwan Maji ba amma da,dare yayi kasa barci tayi tana nazari akan irin zaman da take da abokan zaman ta a gidan. Wanda dai ita taga babu ruwanta da,hassadan ko dayan su balle zurian su , bata taba tunanen wai ta aikatawa wa dan ko dayan su wani mugin abu ba koda a,baki ne. Amma yau gashi ita an sakata gaba har yan yaran da ta haifa a gida ba,a barsu ba don hassada kawai. Ita dake da yara uku kawsi kacal amma wai sun tsone idon masu bakwai tara da hudu. Haba jama,a kishi haukane wai da har zaka salwantar da dan kishiyan ka kan bakar kishin da iyakar shi nan duniya sai kuma lahira inda,za,ai hisabi. Lalai yanzu lokaci yayi da kowa zai kama taka tsantsan da dan abinda Allah yaba,shi don gujewa sherin shedanu mutane. Gaskiya sai yanzu tasan tayi mugin sakaci akan yaran ta don ita ko goro bata taba basu ba da,sunan wai tsarin jiki. Musan ma ma,shi sadauki wanda ya tashi tun yana yaro da shiga idon jama,a. Don haka yake kamar dan larabawa ga kyau ga ilimi ga kunya gashi da miskilanci. Bai shiga harkan kowa ba,agida ba har gari baki daya, bazata iya cewa ga,ainihin abokin shi na kurciya ba balle ma yanzu da ya koma hakan. Tayi tayi ta san ko da wa yake hurda da har ya fara wanan shaye shayen amma ta rasa aini hin abokin shi. Dan dama dama,ma,yaron malamin da,sukai karatu a gurin shi na islamiya ana ce dashi Manir shi manir hae yanzu yana zama da mahaifin shi yana koyawa yara karatu a kofan gidan su. Don haka bata zargin Manir da wani harkan sha,shanci ko kadan sai ma jin dadin shi na aminin shi da take yi. Don tasan ko banza zai dan dinga mashi nasiha akan sabon halin da ya dauko ma rayuwan shi. Sai da dare ya shigo gidan har zuwa yanzu inka gan shi kamar natsatse yake sai dai gaskiya bai bari ba don bai jin zai iya barin sha gaskiya da,wuya. Amma dai yanzu shan da yakeyi na,tsanaki ne a ganin shi yana wayo ne don kada a gane shi. Abinda bai sani ba shine karfin adduan mahaifane ke tasiri a kan shi lokacin. Don Alhaji yaba bada kudi ana mashi addua yanzu sosai sabanin da can da yake daukan abin da,wasa. Ya fadawa wani amin shi a kasuwa irin halin da yaron na shi sadauki yake ciki. Mutumin yai murmushi yace Alhaji ke nan kai kama yi arziki yaro daya ke wanan halin. Ni wallahi har da yarana mata suka fada cikin wanan mugun rayuwan nayi nayi abin yafi karfina dole nasa wa sarautar Allah ido. Kasan sai mutum ya,daga hammatan shi ake jin wari amma yanzu duk wanda kagani yana da matsala akan iyalin shi sai dai mutum ya rufe kawai. Don abubuwane gasu nan ba iyaka da lokaci ya kawo muna,sai dai Allah ya kyauta kawai. Akwai wani malamina zan kaika gurin shi onda abinda abinda zai iya maka sai ya taimaka muna dashi. Don kasan kowa da irin abinda ya karbe shi mai yuyuwa ni banci nasaraba kai kaci. Abubuwa da dama Alhaji keyi akan Sadauki amma ba wanda yasani a gidan har ita mahaifiyar yaron ma kanta batasan yanayi ba. Don ita gani take ita kadai ce keda damuwa akan yaron kawai shi ai yana da,wasu. Bata san cewa shima abin kamar yafi damun shi ba, don shi ke fita yana ganin duk gari kowa yasan da dan shi mashayi ne. Yazama mutumin banza ke nan a idon mutanin gari ai. Suna hanyar su dawowa ne, wani abokin shi ya tare shi hanya yana ce mai bayan sun gaisa. Alhaji yaya akayine yaronnka ya samu abin arziki, amma kuma kukai sakaci da hakan. Ban fahince kaba ai wani dan nawa ke nan kake nufi daga cikin su. Yace U, F mana dan kwallon nan dake gidan ka ance an zo sayen shi yafita zuwa ghana buga kwallo amma baku yarda ba. Kana nufin Umar Faruq ke nan ko sadauki muke kiran shi ai shifa shi. Wallahi yaron ya iya kwallo sosai don hakane ma couch din su yai mashi hanyar fita amma wai baku yarda ba. Sai abokin tafiyan Alhajin ke cewa kai amma kuwa Alhaji baku kyata ba da kuka hana shi zuwa ai wani hanyane na samu nan ma. Abinda muke ganin yan kudu kawai keyin sa yau gashi ya kawo ga yaran mu. Don Allah kubar yaron nan yaci gaba da,wasan shi kada ku lalata mashi hanyar samun shi. Shiru Alhaji habu yayi don shi bai ma san da zancen ba a rayuwan shi don ba,wanda ya taba fada mai hakan. Yace cikin mamaki gaskiya banda masaniya,akan wannan magan ni in ba yanzu ba din bai taba samuna da,wanan zancen ba gaskiya. Amma zan bincika naji ko mahaifiyar shi ta san da zancen ita. Gaskiya a bincika don kaga har team din farko sun shiga gasu sun dawo da abin arziki mai yawa wallahi. Don Allah Alhaji kubar yaron nan ya tafi don akwai alheri so sai ga,wanan harkan don ba harkan banza bane gaskiya. Ga yaron naka yana samun yabo sosai a gurin abokan shi dama mutanen gari don haka abarshi kawai yatafi ko zai zama alheri a nan. Sunyi sallama da mutumin bayan sun kama hanya da abokin shine mutumin ke cewa kaga ikon Allah ko kai duk ka damu kanka gashi ashe mutane kallon mutumin kirki ma suke wa yaron. ****** ********* ****** Sadauki ya,gayar da Maji a cikin mutunci tare da tambayan ta lafiyan ta? Maji tabashi amsa a takaice da da sauki, Alhamdullahi dama ai kaine kaso kashe ni da raina. Murmushi kawai yayi irin nashi can saman fuska yace ayi hakkuri don Allah, insha Allahu na daina ai. Suna nan suna dan hira shi dai yana zaune baice komai ba kuma bai ma sauraren su hankalin shi na daga maganan Maji. Ke Amira dauko min ledan nan na,saman TV stand kikawo min ba mussu Amira ta mike ta dauko ledan take cewa kawo min ludayi a kitchen. Bayan an kawo ludayin ta bude roban maganin ta,zuba tana mai addua a bakinta cewa Allah yasa wanan maganin yai muna aiki a jikin mu baki daya. Babana zo nan tace tana zaune a saman salayan ta bai tsaya ba ya mike zuwa gurin uwar tashi. Mika mashi ludayin da maganin ke a ciki tayi tana fadin duko kasha duk da bai so bai musa mata ba ya karba ya,sha ta shayar dashi da hannun ta kamar yadda aka umurce ta da tayi. Haka taiwa Amira da maryam sai ga Bintu tafito daga cikin daki tace yaki ya ta zo ke maki karba kinji. Bintu ta karaso kamar yadda suka sha haka itama tasha maganin daga hannun maji Inda maji ta,shanye sauran maganin gabadayan shi da ludayin. Sai kuma ta hada wani nasha tace a mikawa sadauki wanda ke zaune ya kurawa Tv ido kamar yana kallo. Saida ta tabbatar yasha komai kamar yadda akace tace dauko mashi abincin shi kinji. Ana kawowa bai tsaya ba ya karba tare da mikewa maji tana fadin ina kuma zaka tafine wai ? ya ce dakin shi zai tafi yaci tace tau kadai ci abinci don naga kana,wani rama can. Sai da safe ne taje gaida mijin su yake ce mata ta dagata yana da magana da ita, haka yasa Hajiya Kubura tafita daga dakin . Yace dagata ai duk magan ta,shafe ku don ka sadauki ne zancen da zamuyi da ita. May kuma dan nawa yayi inji hjy kubura take tambayan shi da sauri. Baiyi komai ba wani magan ce dai aka tare ni da shi akan shi wai zancen kwallan ball din kafan da yakeyi. Oho Allah yasa alheri ce ta samay mu akan maganan t Tau kusan hakane dai don wai ashe sun bukace shi da yatafi ya buga masu ball a kasar ghana. Amma sai yace wai gida an hana,shi zuwa shine nace ni dai ban sa zancen ba amma kila ita uwar shi ta san da zancen? Eh na sani tabashi amsa amma kuma na fada mai hakan baiyoyuwa. Kada ma ya kara min zancen shine yake ta faman fushi a kwanaki ai har yaje yai wanan aika aikan. Kai amma hajiya maijidda baki kyauta ba gaskiya. Ai wanan abin alfahari ga kowan mu nan ace an samu haziki daga gidan mu . Amma may yasa ni ba a shawarce ni ba kika yanke hukunci ke kadai, maji tace Alhaji naga baka ra,ayin wanan kwallon da yakeyi ne. Sannan kuma yana nan ma a,tare da mu yaya aka kare ballw yatafi wata uwar duniya can, inda babu mai kwaba mashi. Haba kwabo fa daga Allah yake mu itakarmu dashi addua ne a duk inda yake, amma ai wanan wani babban abin alfaharine idan Allah yasa mashi hannu inji hajiya kubura. Nikan gaskiya sai naga kamar hakan zai kara jefashi cikin mugun halin da yasa kan shi a cikine. Alhaji yace yanzun dai idan ya shigo kafin na fita kice ina magana dashi don inji yaya zancen yake ne. Majibata,dade da barin gurin maigidan na suba sai ga sadauki ya,shigo don yau sammako zaiyi ya fita saboda yana process kan fita service din shi. Bayan sun gaisa ne maji take cewa yaya akayi Alhaji yasan zancen zuwa kwallon da kai min bayan na fada maka cewa ban ra,ayin hakan tun farko. Cikin muryan ahi ta,rowa yace wallahi Maji ban sani ba don bamuyi maganan da kowa ba a gidan nan. Ta ka godewa Allah da uwarka hajiya kubura don naga ta dauki abin haikan ita akan dole sai anbarka. Na ko san tunda tai magana Alhaji yarda zaiyi ba fashi amma ya,dai ce idan ka,shigo kasamay shi yana nemanka wai. Baba ke nema na maji tace eh ba,wanj abu bane wai yana,son jin kan maganan daga bakin ka ne. Sadauki bai tsaya ba ya mike don zuwa kiran mahaifin shi da yake mashi, Yana kaiwa kofa yaji muryan bakuwar yarinyar nan cikjn yar siririyar murya tana fadin Allah yasa baba ya,yarda yatafi wallahi. Juyowa yayi ya maka mata harara yafice daga dakin yarinya karama,sai bakin iyayi ina,ruwan ta dani ne Yarinyar nan bata,san halina,ba,sai watarana na gwada mata,zata gane kuren ta gidan nan. Yafita yana magana,shi kadai a ran shi yana fita hajiya kubura tana kulle kofan part din ta zata fita ya ke cew mummy ina kwana. A,a sanda sadauki sabda gagare ashe ana ganinka ni yaushe ma rabo dana saka a idona ne wai. Yai yar murmushin shi yace ban zama,sosai ne yanzu shi yasa ba,a gani na, Tace tau akula dai don Allah a daina rashin ji kaji Umar Allah ya tsare muna ku Allah kuma yai maka,albarka. Yace amin yabarta taba,ci gaba da,rufe kofan dakin ta shi dai matar batai mashi komai ba amma kuma ya kasa sakin jiki da ita, Dan dama,ma,yau har ya tsaya sundan yi dogon magana dashi ko shi don irin halarcin da ta nuna mashi ne ranan yasa yadan sake mata yau. Da Umma ya hadu tafito tana sauri don ta makara kauce mata yai nufin yi don kada,su hade amma sai cewa tayi wallahi haukan yaro yakawo gareni da,uwar yaro zanyi a gidan nan. Bai ko gaisheta ba ya,wuce abinshi gurin mahaifin nasu don amsa kiran da yake mashi. Ya samu yana gap da fita ya,shigo falon da,sallaman shi suka gaisa yake cewa hauwa ta fada maka ke nan ina neman ka ko. Don nasan inbashiba bazaka zo mu gaisaba ai anya Umar kana kyautawa kanka kuwa? Baba kayi hskkuri lokacin da nake fitowa sai na samu kafita ko kuma lokacin da zan fita baka fito ba tukun. Ba sanan ba idan maka gyara don kanka, yaya zancen dana ji na batun fita kwallon ku yake ne? Don ban son abinda zai je ya kara saka sha shan ci kuma a bayan idon mu, anan ma muna nan kafara haka inaga babu kowan mu. Baba insha Allahu ba,zanyi wani abinda zai bata maku rai ba ko martaban gidan mu, Hmm daga baya ke nan amma sadauki yaushe kuma,ai kayi waka an amsa maka ko. Don tunda harka bari kishiyoyin uwarka suka fahinci halin da kake ciki ai abu ya baci ko saidai Allah ya kyauta kawai. Nan dai sadauki cikin dukar da kai yai ma mahaifin shi bayanin komai yadda abinyake ya kuma fahince shi. Ga mamaki shi sai yaji Uban na cewa Allah yasa haka yafi zama maka alheri gare ka da ma muma iyayyenka. Ya amsa a sanyaye da Amin baba insha,Allahu alheri ne ma hakan da yardan Allah. Kadaikula don Allah ka kula,da rayuwan ka don mu shine adduan mu a gareka ko yaushe Allah yasa ayi a cikin sa,a Allah ya tsare ya kare. Yakara amsawa da fadi a sanyaye cikin farin ciki da jin dadi nagode baba yace tare da mikewa yabar dakin cikin farin ciki. Ya shiga dakin mahaifiyar shi da murna yana fada mata duk yadda sukayi da uban nashi. Yace maji don Allah ke ma ki samin albarka don in baki yarda ba gaskiya babu inda zan tafi ni kan. Sadauki Allah yai maka,albarka Allah yasa a,tafi a sa,a adawo lafiya cikin nasara. Har kasa ya kai yana fadin Maji nagode nagode maku dake da baba nagode ma Allah baiko tsaya cin abinci ba yafita daga dakin zuwa club din su ya,sheda masu yardan mahaifan shi akan tafiyan shi. Maji tabi bayan shi cikin tausaya mashi irin na da da mahaifi, tasan kwanaki akan bakin cikin rashin yardan su yasa shi zuwa ya sha manyan kwayoyi yazo masu gid a buge Yau tasan cewa duk abinda yaro ke ra,ayin yi indai babu illa acikin sa tauka kyale shi yayi sai dai kai naka kabishi da,adduan da fatan alheri shine mafita. Amma idan ka hana sai suga ba,a kaunar su bari kawsi su sha abin kawar da hankalin su ko zasu samu relief akan maganan. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,, Baby yaya zamuyi ne ina son ki rakani zuwa lagos don ina da seminar da zamuyi a can, kuma dake nakeson zuwa. Shiru Raiha tayi tana nazarin zancen shi a cikin ran ta don tasa abu mai wahala ya dauko mata. Yaya zatayi da uyayyen ta a gida may zata fada masu ina zata ce masu zata tafi. Muryan shi ne ya katse mata tunanen ta yana cewa naji kin yi shiru mana ko baki san rakani ne wai? Hmm ba,wai hakana bane kasan in da hali koma ina ne zan iya raka ka amma ban san yaya zanyi da iyayyena ba may zance a gida. Haba baby sai kace wata local can dan karya kawai zaki shirya masu mana kice zaki gurin wani dan uwan ki koda kauye ne kinga indan munje mun dawo sai na kai ki garin ko kwana daya kiyi sai ki dawo ko? Nan ma,Raiha shiru tayi tana tunanen akan zancen shi don tasan abune mai wuya abarta zuwa wani guri ita kadai. Gashi kuma tana son bin shi sosai a ranta don batajin yanzu zata iya rabuwa dashi ko na dan lokaci kadan ne. Sai cewa tayi zan yi shawara don nasan abinda zan yi akan tafiyan. Huci yayi don jin dadin yasamu yadda yake so daga gurin ta nan ya shiga yi mata abinda yasan tafi bukata daga gare shi har suka kai ga,watsewar su a hotel din da ya kaita. Da zasu rabu ne yake jadfa mata cewa next week ne fa sunday tafiyan su kuma da jirgi zasuyi tafiyan, don haka yana son yasan idan zata tafi ya sai tickets din su shida ita. Ba matsala tabashi amsa zansan yadda zanyi mu tafi din tare insha Allahu. Wani shu,umin murmushi ya,sauke tare da,shafan dogon fuskan shi ya na cewa dat is my baby shiyasa nake kara,son ki. Tun dawowan ta gida take ta faman sake sake a ranta sai kullawa take tana warwarewa ita kadai a ranta. Can wani dabara ya fado mata a rai tai wani murmushi daidai uwarta ta zo shigewa take cewa, mama ina fa son zuwa kamba gurin su kaka na dubo su. Kamba Raiha kedawa zaki tafi har kamba ? Raiha tace haba mama sai kace wata karamar yarinya ni ko makka ai ina iya zuwa ni kadai yanzu. Kai Raiha wai may kike daukan kanki ne yanzu har nawa kike da zakice zaki iya kai kanki makka. Yanzu dai mama da na shiga mota daga nan sokoto ba sai jega ba daga jega ga motocin zuwa garin kamba nan sai na,shiga kawai. Eh lalai ashe ko zaki iya aiko kin kyauta bari malam ya dawo na fada mai Allah yasa ya barki dai ki tafi din . Raiha cikin marairai cewa take cewa don Allah mama ki tayani rokon shi ya barni ba dadewa zanyi ba sati daya zanyi nadawo kawai. To shike nan bari yadawo din muji yadda za,ayi idan zai yarda sai ki shirya ki tafi aini wallahi kin kyauta min nasha kulla tafiya na dubo su amma sai abin bai yuyuwa. Yanzu kinga ai inkije sai ki taimaka min nasan halin da,suke ciki a can din. Sai da,dare bayan mahaifinta ya dawo ne take sheda mashi bukatar yarsu na,son zuwan ta kauyen zu garin kamba wanda ko anje kambadi sai an shiga mota ko mashin zuwa can. Haba nana yanzu kamar Raiha ne zamu saka a mota daga nan har kamba ita kadai a,wanan zamanin da muke ciki. Malam insha Allahu zata iya ai yanzu tasan hanya zata iya kai kanta ita kadai bada wani ba. Nan dai suka kama inyafito nan tafito mai nan abin mata da miji har ya yarda da zasu tafi ya bata kudi tayi sayayya da kudin mota wanda zai kaita. Sosai Raiha taji dadi a ranta nan take ta kira Nasir take sheda mashi halin da take ciki. Yai murna yaji dadin samun nasaran da sukayi don haka washe gari yaje yai saya masu ticket din tafiyan su. Bayan kwana biyu suka shirya sai air port inda suka tashi zuwa garin lagos ita da shi. A wani katafaren hotel ya sauke su ita dashi inda tun ranan ya fara nuna mata wane shi, don dama can ashe a sannu yake binta. Bata da hutu a gurin Nasir don kusan a kanta yake kwana har gari ya,waye. Tun tana iya jurewa halin Nasir har Raiha tafara raina kan ta da kanta don yanzu yakai bar ta baya yake ne manta. Da farko takiya amma da tasha duka a gurin shi dole ta yarde mashi yana yadda yake so da ita. Idan sun gama kuma ya dauko kayan maye ya dirka mata sai ta futa hankalin ta . Sati dayan da sukayi Raiha tagan shi kamar shekara daya ne na,wahala da ukubar zugubar namiji a gare ta. Sam babu tausaya tsakanin ta da nasir ko kadan kamar ba soyayya ce ta hada su ba don yi yake kamar ya samu boya. Saura kwana uku ta dawo ya shiga da ita gari shida wani abokin shi suka je zaga garin da ita. Yai mata sayayya sosai na abinda duk tagani tana so a fitan nasu taci kayan ciye ciye masu kyau sosai da tsada. Bayan sun dawo sai taga wanan dayan abokin nashi baida niyar tafiya kamar yadda tai zaton tafiyan shi. Ashe bata sani ba aun hada plain a tare shida Nasir zasuyi amfani da ita gashi shi ba ko musulmi bane dan uwan ta. Nan suka samay ta da ihu da komai suka kwana a kanta suna juyata yadda suke so. Tai kuka har tagaji tahakkura ta kyale su suka gama don kan su ka barta, abokin nashi yata yaba ma dadin ta har yana rokon Nasir da ya bar mashi ita for ever amma nasir din yaki yarda da hakan. Yake cewa Michael ai ba,addinin su daya ba don haka ba,zai yarda ya zauna da ita ba. Bai san bayan sunyi barci Michael ya dauki wayan Raiha ba ya saka layin shi yakira nan ya samu nomban ta. Sun dawo arewa kwanan su daya a garin sokoto takaita garin kakan nin ta ta kwana washegari ta dawo sokoto ita dashi dake jiran ta a birnin kebbi. Maman ta taga ta sake maimakon taje kauye tayi baki amma sai wani haske ta dan kara sai dai tayi dan rama amma fa tayi mata kyau a fuska sosai. Yanzu ke Raiha kada dai kinje kin cinye ma yan tsofi kajin su wanan irin haske da kikayi haka anya kuwa ba barna kikayowa tsofin nan ba. Raiha kuwa sai rankon barcin wahala takeyi don sai yanzu ta samu hutun wahalan da tasha gurin Nasir a can Iko. Sai dai shi bai sani ba ta riga da ta yanke a ranta cewa ta gama zama dashi ke nan don yai mata wullakanci a can dama lalaba shi tayi har ta samu su dawo arewa. ****** ********** ***** Ganin yanzun ba wani ciniki take samu ba sosai yasa ta yanke shawaran samun dan almajirin da zai dinga mata talla tana bashi abinci da dan kudin sabulu kamar yadda da yawan almajirai sukeyi yanzu. Duk almajirin da ya shigo zatai mashi tayin talla amma sai su zille suce malam ya hanasu yin talla ko kuma suce dama shara ne ko wanke wanke zasu yi amma ba talla ba. Sai wani yaro ne tasamu yace mata zai yi Allah ya taimaketa yaron yana da kan talla sosai don da yafita kamar ya kifar ne zai dawo ya kara wani. Haka yasa tagane fita da sana,a waje yama fi cikin gida sosai samun ciniki . Maigidan ta yaga almajirin yai mata magana akan ta dai kula da bashi hakkin shi don kada Allah ya tambaye ta akai. Amma,saboda dadin baki irin nata bata bari yakai karshen nasihan shi ba ta shiga bakinta akan zancen. Maigidan dai ido ya,sa mata baice mata komai ba sai cewa yayi bani abinci nashi kada na makara zuwa daukan karatu. Yana cin abincine yaran shi suka zagaye shi suna fada mashi makarantar su ance a,sai masu shocks da takalma. Yakai loma,a bakin shi yana cewa aiko sun dauko min aiki yanzu hada kudin safa da takalma ai aiki a cikin wanan daman da ya fara. Kuyi hakkuri insha Allahu zan sayo maku nan bada jimawa ba da yardan Allah. Yana gamawa bai tsaya jiran komai ba yafita zuwa gidan babban malamin shi inda yai karatun allon shi. A nan yake zuwa daukan karatu gurin malamin duk dare idan ya,dawo daga gurin neman kudin shi. Yana fita ymta jawo bankin kudin ta tafara lissafawa inda taga irin ribar da ta samu gurin tallan almajirin ta. Tayi murna kwarai don ba karamin cabawa tasamu ba ga wanan tsarin sai fadi take ai wallahi mama ta taimakeni da wanan shawaran nata. Don gashi kwana kadan na hada,waban uban kudin haka nan ta,ware nata ta cire ma,almajiran ta nashi. Har yaran sukai barci amma ita hankalin ta yana ga sakan zucin da takeyi itta kadai a lokaci, na ganin ta hada kudi ta sai fili da sunan nata. Sai karfe goma mijin ta ya dawo gida ya samu yaran saman shimfidan da ya tashi ga sauro na cizon su. Yacee haba maryama da wannan sauron kikabar yaran nan haka a cikin shi suns cizon su gani ba kudi gareni ba idan maleria ya kama su da,wani zanji. Sayen abinci ko sayen magani da zuwa asibiti gashi yanzu zazzabi idan ya kama mutum kamar ba zai barka,ba sai ka hada da,asibiti dole ko chemest. Nan ya shiga kwasan yaran zuwa cikin dakin kwanan su gaba dayan su saida ya kwashe su ya kaisu daga ciki. Maria na gama abinda take ta nemi guri ta kwanta don dama a ganiye take don tun safe bata huta ba tana gudun tai barci masu sayen ruwa ko wani kayan sanyi su shigo. A gaakiya ta godew haduwan ta da Muda almajirin ta don yaro ne ma hazaka gashi da amana. Koda gurin lissafi tai kure zai dawo mata da canjin ta, ya bata abinta, bai sa ta gode mai ba. Ko da daga gurin talla ya dawo bata barin ya dauki abinci komai yunwar da yake ji. Sai yai mata shara da wanke wanke, da yan sauran aiyukan gida kafin ta sallamay shi. Hakan ne ke batawa yaron Muda rai yana yawan yiwa yan uwan shi almajirai korafi sosai. Wanan shine matsalar da ke damun yaron mai mata talla koda zai makara ga karatun shine sai yai mata aiki bayan kuma akan talla sukai alkawari kawai dashi. Wata rana yana fita daga tallan ne sai gashi ya dawo jiki na makyarkyata yana jin sanyi ba lafiya. Maimakon Maria ta ji tausayin yaron sai cewa tayi shine baka sayar ba kadowa min dashi ya tsiyaye ga banza. Cikin rawan sanyi yaron ke fadin banda lafiya ne maman Abba sanyi nake ji sosai. A je katafi tunda yau baka son yin tallan ke nan nagani, maman abba in kina da magani don Allah ki bani nasha. Tace cikin tsawa banda shi kaje gurin malamin ku yabaka shida ya dauko ka mana. Yai shiru kamar mai nazari can yace don Allah ki taimakeni da koda cikin kudina ne na biya shago nasai magani. Babu su tafadi a cikin fada da,dan tsawa yaron yafita yana dan makyarkyatan sanyi don fever ya damay shi. Yana zuwa makaranta ya rabke da ciwo maleria ta kama shi sosai nan malamin su ke tambayan shi ina kudin tallan shi ya bayar a,sayo mai magani yasha. Da kyat yaron ke iya magana yake cewa na tambayi matar tace wai babu kudin. Malamin ya hasala yafito yana tambayan wayasan gidan da Madu ke talla ya aike shi. Suka yaran wasu sukace sun sani nan sukatafi gidan don su karbo kudin shi hannun maria. Amma sai tace a tafi ita babu kudi a hannun ta sai dai idan ta samu zata aiko mashi dasu. Almajiran basu fita ba suka tsaya yi mata tsageranci, akan sai ta bayar da, kudin sukai wa malamin su. Sun dade basu samu ba dole suka bar gida taki bayarwa kuma tabi su da zagi. Suna fadawa malamin yace kada wanda ya koma gidan subarta da Allah a bar maganan. Shi yakai yaron asibiti akai treating din shi ya biya kudi har yaron ya samu sauki. Bayan Muda yaji sauki yaki zuwa gidan ta nan almajirai yan uwan shi kewa makwaciyar ta hiran shi tace akawo shi ta dauke shi aiki. Ita ta rike yaron zaman amana kamar itace ta haife shi haka yasa Maria jin wani irin kishi kamar zatayi hauka ****** ******** ****** Kamar yadda mai masa taiwa Maji alkawari haka din ne don batai sanyi a,gwiwa ba ta shirya sai wani kauye can gaba da kauyen su gurin wani malami. Malami irin malamai na kwarai bai damu da wani kudi ba don a kauye yake kuma ita dashi yan uwane ta mahaifiyar su. Yana ganin ta ya shiga murna da nuna jin dadin ganin ta nan yasa ai mata girki na musan man kamar yadda yan kauye suke yi idan sun ga bakon birni yazo gurin su. Sai da dare suka samu kebewa dashi da ita suka kara gaisawa sosai, nan take, sheda mashi dalilin zuwan ta gurin shi. Ya jijiga kan shi yana cewa matsalar ku ke nan yanzu yaran birni don kwanaki akwai wani da yazo tun daga kano har nan gurina akan wanan matsalar. Amma yanzu ba abinda zamuyi sai dole munyi istihara don naga daga inda matsalar take, don kinga ba dama muzo muna aiki inda muka dosa daban abinda ke damun shi daban. Don haka ki bari sai zuwa gobe da safe sai nai maki bayani, mai masa tai mashi godiya sosai nan suka dan taba hira na yaushe rabo da junan su. Washegari tun da,sauran duhu aka kaiwa gwago ruwa masu zafi tai wanka tana fitowa ga koko mai zafi da kosai da masa irin tasu ta kauye da badin shi. Tace wani abu sai kauye mu a,birni ai yanzune ma,wata mace ke gyara kwanciyar ta. Sai da ta karya tashiga ko wani lungu na gidan suka gaisa da mutanen gidan sai ta dawo dakin da akai mata masauki . Ba a jima ba malam ya,shigo gidan ya shigo dakin da mai masa take ciki suka gaisa yai mata ban gajiyan tafiya da bakun ta. Can yace Asmau nayi duba akan matsalar ku amma gaskiya akwai yar matsala a cikin harkan. Don shi wannan yaron gaskiya akwai hannu ga harkan shi. Don tun yana karami aka soke shi don haka su abubuwan bayin kan sa bane. Yaron nagani yana da taurari masu haske sosai a rayuwan shi don hakane akayi kokari dakushe masa su don kada ya haska. Anje anyi tambaya a kan shi amfadawa wa masu shi cewa zai zama wani abu ga rayuwan shi shine suka,sa ai mashi wanan aika aikan. Kuma al,amarin ga yadda nagani ba wai mutum guda bane yai masa haka ,a,a suna da yawa kowa kuma da irin aikin da akai mai. Ga miyar kifi aka bashi wanan abin shaye shayen yaci shi. Matane da namiji guda sai dai ba zaso na fada maku su ba don gudun hadin hasu mi. Yanzun mu matsalar mu shine mu san mafita akan zancen mu san yadda zamu nemo makaru mu kara wanan asirin na jikin shi. Don muddin yana tare dashi ba,zai taba zama wani abin kwarai ba ga rayuwan shi. Kin ga yadda nagani matar tana da yara uku a,raye shine dana farko a gurinta. Su ma sauran diya matan nata biyu wallahi ba,a barsu ba don suma suna da nasu asirin sai dai suyi ta zaman gida ba aure. Koda ma an dace sunyi auren bazasu zauna ba zasu fito don zasuji auren ba dadi. Yan da zaai sha rubutu ne kinga sai na rubuta maki wani rubutu ki fara,zuwa masu dashi har uwar tasu tasha. Kafin kwana biyu nan da sati biyu ki dawo lokacin na,shirya,sauran abinda da zan baku. Gwago tace zai sha mana malam ai kasan wanan dolene asan yadda za,a bashi yasha. Yace kin san yanzu yayin izalar nan ta sa matasa basu son shan irin abubuwan nan. Kuma mutane ne basu gane ba ai shi a addini musulunci da kike gani kur,ani maigirma yazo muna da,warakan komai a cikin sa. Malam zai sha yace to amma fa uwar ce zata sha tabasu da hannun ta,suma su sha hakan zai dan kawo muna saukin abin insha Allahu. Zanbaki abu biyu zuwa uku kikai masu sufara yi insha Allahu idan sunyi badai samu ba in ma wani yakara kokarin yi masu sai dai ya koma ga maishi wallahi da izinin Allah bana mutum ba su dai kada suyi wa wani sheri a rayuwan su. Nan ya mike yaje ya hadowa gwago mai masa abubuwan fa,zai bata yace takaiwa Maji da diyan ta Allah ya sauwaka. Gwago bata tsaya ba ta juyo zuwa,sokoto a ranan sai dai cikin dare ta iso garin. Don haka ta wuce zuwa gidan ta da abubuwan sai washegari take da niyar takawo wa Maji su. ******* ******** ****** Washegari ba a zuwa makaranta don haka yaran kowa yana zaune falo tare da iyalin shi. Bintu tana daga ciki tana shiryawa don yanzu tagama gyaran guri don ita bata gajiya da aiki ko kadan, Idan kaga yadda part din maji yanzu yake kalkalkal zakace ba mutane a cikin sa da yawa. Wani lokaci har hajuya Kubura takanyiwa Maji ba,a tace hajjiya maijidda ki bani wanan yar taki mana. Wallahi ni dai yarinyar taimin bata,da kiuya ko kada,akwaita da tsabta ga ta,da kwai wallahi. Maji kanyi dariya,tace a,a kibar mi "ya ta,Allah ne yakawo min hutu ta hanyan ta . Bintu tafito falon duk suka bita da ido har maji din, sai maji ke cewa kun gani tai aiki kuma harta gyara jikinta kuko kuna nan kuna bakin shiriritan ku da kuka saba ace gari ya,waye mace bazatai wanka ba ba kuma komai kukeyi ba. Mutane suyi ta shigowa suna,samun ku a haka. Kai maji ko munyi kwalliya wa za muyi wa mutum ko saurayin kwarai baida. Au sai da,saurayi ake kwalliya mace fa da kwalliya aka san ta ko yaushe don abinda kuke yi anan shi zaku je gidan mazajen ku kuna yi. Bintu ta dan zauna daga kasa sai cewa maryam tayi kai Bintu ke kullun kamar bakuwa har yanzun baki saba ba ke. Kila dai tsoro take ji a,a bata da tsoro wallahi, don ranan fa itace tafara zuwa gurin yaya sadauki ta kama shi. Aini wallahi ranan Bintu ta bani mamaki sosai wallahi, don gaba daya na tsike ni a lokacin. Maji wacce zuciyar ta ya sosu da zance amma sai take cewa ai Bintu tai kokari wallahi sosai. Toke halan waya fada maki anabawa mutum manja da gishiri ya sha idan yana haka. Tace nima labari naji wata yar ajin mu tanayi cewa wai duk yadda mutum yasha maye idan aga yai mashi yawa abashi manja da gishiri sai ya amaye su su rage mai aiki a jikin shi. Ikon Allah inji maji tace Fatima shine kika gwada ke kuma gashi kuma na lura abin yai mashi amfani sosai don yasa yadan dawo cikin hayacin shi. Amira tace wallahi aini duk mamakin Bintu ya kamani a lokacin don ni ba karamin tsorata nayi ba don na dauka ma mutuwa zaiyi ai. Kai sadauki Allah dai ka,shirya kayan ka amma sadauki bai min da ba,wallahi. Yaro kai kadai Allah yabani namiji amma kuma kai ke sani kuka. Maji ki daina mashi kuka don Allah adaiyi ta addua inji Amira ta fadi cikin muryan tausayi. Ai inayi Amira Alla dai ya,sauwaka kawai don na lura fa abin nashi yai girma sosai ko ba yanzu yafara sha ba. Shin tsaya dai in tambaye ki Bintu wai dai ko ranan nan ma da kikace wai kin fada kwatane shine yai maki amai ga jikin ki wai. Da sauri Bintu ta dago kai sai kuma ta dukar da kanta kasa don bata iya karya ba. Da sauri maji ta dago kai tana kallon Bintu tace wai Fatima hakane ko kuwa? Tace hakane Maji nan ta fada masu duk yadda abin yafaru da yadda ta samay shi a kwance har shigowan ta gidan. Shiru sukayi dakin suna nazarin zancen Bintu kowansu yana yaba kaifin hankalinta. Maryam tace shine da kika shigo baki fadi ba Bintu? Haba Anty Maryam bayan nasan mama bata da lafiya shine zan fadi na kara mata ciwon kai. Bazan fadi ba gaskiya don ban son hankalin mama ya tashi, don ba karamin tashin hankali zata shiga ba. Baki gafa yadda yake bane nima da kyat na uya kai shi dakin shi kamar numfashina zai dauke nake ji a lokacin. Ikon Allah wanan yarinyar akwai ki da mugun karfin hali wallahi danice ai ihu zan dinga kantarawa sai kowa yafito a gidan nan. Da,sauri Bintu tace kai anty ai wanan rufin asiri ne ba abinda za,a bari wani yaji bane. Kinji ke mai cewa zakiyi ihu maji ke fadawa maryam hakana tace ai Bintu yarinya ce mai hankali wallahi. Ai kan inji Amira don akwai ta da dan banzan wayyo kun gan ta nan. Sallaman mai masa ne ya dakatar su suka,shiga gayar da,ita suna mata ina kwana. Maji tace a hajiyan masa ashe tafiyan naki ba mai dadewa bane har kin dawo ? Nadawo hajiya dama tafiyan nawa ai donki nayi shi ba tafiyan kaina bane nayi. Maji tagyara zama tana fadin ikon Allah ashe mu akaiwa tafiyan ke nan. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,, Ganin yanzu bata samun kasuwar sana,anta irin farko da Mud al,majiri ke mata talla yasa hankalinta ya tashi sosai. Saboda a yanzu ta saba da rike yan canji a hannun ta tana kadawa a bankinta na gida. Sai gashi yanzu da kyata zata hada naira dari daya ta kada a ciki ga wuni. Hakan yasa duk hankalin maria ya yai matukar tashi ga fridge yai ta haukan kankara shi kadai amma babu kasuwan saye kamar farko. Gurin mahaifiyarta taje da zanjen, budar bakin uwar tace shi,Aliyu ba zai iya dan fita maki dashi ba koda a cikin uguwar ku ne yana yawata maki dashi. Da sauri tace ,a,a,a Umma wallahi mahaifin su bai yarda sam idan yaji nasan ba karamin tashi hankali zamuyi va dashi. Ashe ke wawiya ce maria ke zaki bari yaji ne cewa yana talla. Mutumin dan in ya sa kafa yafita tun safe dai yamma yake dawowa, lokacin ai har kunci kasuwan ku ko kungama. Lalai Umma haka za,ayi nagode da wanan shawaran insha Allahu gobe zan fara aza mashi talla kuwa. Kafinta shigo gida,saida ta tsaya ta sayo ma yaron farin roban ruwa dan madaidaici irin wanda zai iya dauka. Washegari tun safe ta tsaya shininiki bata shirya yaran zuwa makaranta ba yadda ta saba tashi da wuri ta shirya su su karya su fita tare da mahaufin su, ya aje su islamiya sai ya,wuce gurin sana,ar shi. Da maigidan nata yai magana sai cewa tayi yau bata jindadin jikin tane shiyasa. Shi dai ya shirya yafita abin shi amma yana mata mitar tayi ta shirya yaran su tafi islamiya kafin su makara. Daga wanan ranan ta fara,azawa yaron talla duk da Aliyu kara mine sai da yai kuka yana fadin mama makaranta fa kada a wuce ni gurin bita fa. Amma sai hawan shi tayi da fada cewa indan baije mata tallaba wa yake son ta azawa. Ya dai ga duk almajirin da ta kira sai yace malam ya hana su yin talla yanzu. Kuma gashi yasan da dan kudin take samu tayi masu dan lalurori a gidan wa yake son ta azawa talla. Yaron haka ya dauka ranshi bai so ba ya tafi tallan ruwan yana turo baki harda kwalla a idon shi. Da yake bai iya tallan ba shiga farko da kyat ya samu yayi dan ciniki yadawo da saura gida duk yayi zafi wasu ma duk sun yoye a roba. Nan maria ta hau yaron da masifa da fitina har tana kirarin idan bai mayar da hankali ba yai mata, bazata sayi mashi komai ba da kudin ta. Dole yaron ya dan kara dagewa ya mayar da hankali gurin tallan duk da ba,wani girma yayi sosai ba. Ita uwar ganin yaron ya mayar da hankalin shi yanzu sai dadi take ji don har tana wa makwabciyar ta da ta rike almajirinta na farko habaici wai in an maka bakin ciki sai ka fashe haushi da naka tunda Allah bai hana maka,ba. Hakana yaron tin bai saba ba yana fita da kuka har yazo ya sake jikin shi yana shiga mutane talla. Ito ba abin da ya shille ta sai jin dadi take yi yana kawo mata kudi tana kadawa a bankin ta na gida kawai. ****** ********* ****** Raiha tun bata kula wayan Michael dake damun ta, da kiran akai akai har tazo tana daukan wayan shi. Da farko tana ganin kamar hada kai sukayi da Nasir a kanta si da ga baya ta fahinci bada sanin Nasir din yake kiran ta ba. Don yakan ce kada tai serving din nomban shi yadda Nasir zai fahinci cewa shine. Don baya son Nasir yasan shine ya rusa mashi plain din shi a kanta. Da lalashi da komai yasamu ta yarda ta tra mai da account number din da yasa ta ta,bude. Tashin farko kudin da ya turo mata saida hankalin ta ya daga don dubu dari biyu ya turo mata ga account din ta. Ta rasa yadda zata boye wanan kudin don haka ta fadawa mahaifiyan ta amma bata fada masu cewa ba musulmi bane shi, Ta daice a waya suka hadu dashi yace a lagos yake aiki hankalin mahaifinta ya tashi amma da sukai waya da Michael yace ba komai yadai bata ne kyauta don ya fahinci ita diyar tallakawa ne. Abinka ga kudi masu shiga rai sai mahaifin nata bai tsaya wani dogo n bincike ba kawai aka shiga harka dasu harda tayar da katangangidan shi daya zube badi guda. Bai san cewa katanga mai muhinman ci agare shine ya mugun zubewa ba kan kudin. Shiko Nasir ganin Raiha bazata samu ba yasa shi canza akalar sa zuwa gurin cigiyar wata sabuwar kamu da,zatayi daidai dashi. Sai dai Raiha ta riga ta rusa mashi plain din shi na,wanan shekaran kamar yadda ya tsara al,amarin nashi. Wata yammaci yafito ne daga ma,aikatar su sai ya hangi ra yarinya tsaye a,bakin titi daganin shigarta yar hannun ce don ta dan waye a fuska. Daidai inda take tsaye yai farkin din motar shi inda ya bude yafito har inda take a tsaye. Sun gaisa zakace ko yasan ta a bayane yake ce mata daga ina take haka ta tsaya rana yana bugun ta duk haduwan ta. Amsan da ta bashi yass shi gane cewa tana da,wayo don sai yayi da gaske idan har tafiyan su zaiyi daidai. Tun daga wanan ranan yafara dawai niya da yarinyar yana kashe mata masu gidan rana yadda ya kamata. Yarinyar irin wanda idon su ya riga da ya bude da kudi da maza ne sosai ya sa shi fara ganin indan baiyi da gaske ba ba zai samu yadda yake so ba. Tashin farko ya taya mata zuwa lagos kamar yadda yake a duk bayan wata uku don yin assignment din company su. Ba wahala ta yarda zata bishi su tafi amma sai ya bata wasu kudin da zata sai wasu abubuwan bukatun ta da zata da su. Kusan tare dashi suka tafi tasayo abubuwan da take so wa ranta a kasu da wani shago. Daga baya suka shirya zuwa lagos kamar yadda ya bukaci suyi tare dashi. Yaso yai mata irin yadda ya,saba yiwa mata don ya horar dasu amma sai ya fahinci kamar matafishi sanin bariki sosai. Ya samu Michael yana fada mashi irin matsalar da ya samu akan sabuwar kamun da yayi yanzu. Nan ya bashi shawara akan yabi yarinyar a sannu don mata yanzu suma sun yi wayo sosai. Haka suka dawo bai samu yadda yake son bata training ba don in ya tura ta turai kada a samu matsala sosai da ita. Bayan sun bar Michael ne ya bugo waya yana fadawa Raiha sabuwar yarinyar da abokin shi ya samu kuma yana son ya aiwatar da nufin shi a kan ta. Raiha taji a ranta yarinyar ta bata tausayi don haka dole ne ta taimakawa ko wacece. Sai bayan sun dawo ne ta samu wani abokin shaye shayen ta bashi kudi don yanzun bata da matsalar su ta ce yai mata bincike akan sabuwar yarinyar da Nasir yake target ga fitawar waje wurin safarar matan da yake a boye. ****** ********* ****** Tsaye ta hango wani guy a kofan gidan su kafar shi daya a cikin mota daya kuma ya daga waje ga waya a hannun shi. Ganin Amira da,zata shigo gidan yasa shi saurin samun ta ya tsare ta yana fadin, barka dai. Don Allah idan gidan nan zaki shiga ina son ki sallamo min Nafisat ne, wani kallo Amira tai mashi kamar zatai magana amma sai tace mashi kawai taji. Tana shiga gida ta fara haduwa da Bintu wacce ta sheko ta rugumay ta cikin so da kauna zakace yar uwarta ce tajini tana cewa Anty Amira sannu da dawowa ya makarata ya hanya tare da karbar wa Amira school bag din da ke rataye a hannun ta zuwa cikin dakin su. Mama Asiya suna waje da yaran ta sai tsaki suka ja suna fadin sai kace diyar wata, Harda zuwa don kisisinar yarinyar nan yar kauye zuwa yi mata sanni da zuwa. Wai ma mama may wanan yarinyar takeyi a gidan nan ne har yanzu, wallahi ban son ganin ta shegiya gata yar kauye amma ta iya ba mutun haushi da takaici gata aiki baya isan ta. Uwarta ce ina ga kamar a nan take zaune yanzu tare da su kin san su da shegen kwashe, kwashen tsiya ai da son asani komai basu aje ba. Dayar yar mama dake yankan akaifa tace may zasu bata banda wahala suma ta kan su sukeyi ai. Ni Alhaji ma yafi bani mamaki don da watace cikin mu ta ajeta da yanzu ya fara fada za,a kawo mashi bakuwa a gida cikin yaran shi ta bata mashi tarbiyan ta. Can kuma cikin daki da Bintu ta shiga da murnan ta tana fadin Mama Anty ta dawo. To yar gidan Anty sai kace wace ta dawo daga wani guri haka kina ta wani farin ciki dake. Mama ai duk wanda yafita ta dawo lafiya ai masa barka da arziki inji Bintu, kai Fatima ke kan halin ki sai ke wallahi. Amma a ran Maji dadi taji irin yadda taga Bintu tana matukar son diyan ta wanda a da can baya ba ruwan su da juna a dakin kowa kan shi daban basu damu da junan su ba. Amma zuwan Bintu cikin su yasa koda maryam bata kusa zata bita tana fara,a tana fafin Anty maryan antyn mu ta dawo.dole ta fito Idan kuma maryam ce ta dawo sai ta nemo Amira tana fada mata cikin jin dadi har takai suna barin abinda sukeyi suzo su tari junan su cikin nuna jin dadin su. Yau ma hakan ne don har baya taje tana fadawa maryam dawowan Amira inda maryam tazo da murna tana wa yar uwar ta sannu da zuwa Anty don ita bata fita ba. Nan suka zauna a falo Amira bayan ta cire kayan jikin ta tafito Bintu ta aje mata abincin da ruwa tafara ci suna hira a tsakanin su. Tana fadin kai yau wallahi akwai rana ga zafi duk dama na matsu na dawo na cire wanan kayan nasamu ruwan sanyi nasha. Maji tace aiko mu dake gida wanan zafin ya ishe mutun Allah dai yai muna Rahama kawai. Yaran suka amsa da Ameen ya Allah. Amma kila an kusa fara ruwan sama ne don zafin yau yai yawa mama Bintu ke fadi. Sai suka sa dariya gaba dayan su maryam tana kokarin cewa ke Bintu ai haka garin nan yake da shegen zafi walla,,,, Sai gani sukayi an daga labulen dakin kawai ashe Nafisa ce gaba daya suka juya don ganin waye haka bako sallama zai fado masu kai tsaye. Tau yar bakin ciki ashe anzo nemana shine don bakin ciki irin naku na gado kika ki fada min, to Allah bata ku ba. Wai dawa kike yi ne inji Amira take tambayan ta a cikin daga murya. Ke mana yar bakin ciki mai shegen kishin tsiya kamar na uwarta ni bani na hana azo a soki ba balle ki gwada bin bakin ciki karara a fili. Nafisa niba sa,arki bace balle don kin kwaso dan rashin mutunci irin ki yace wai ni na kiri mashi ke don rainin wayo. Ji yar rainin hankali oho sai yanzu ai na kara gane bakin cikin ki a fili wallahi don naga aikin hassada yau, To wallahi a haka zaku kare tanbade lalace sai bakin kitifi ku da uwar ku a daki dangin yan caca da shaye shaye. Kafin tace wani abu ba,wanda ya san Maryam har takai inda take tako shako wuyanta ji kake tas,tas, mari biyu masu lafiya ta kwashe ta dasu. Umma fito wallahi gasu Amira can sun tarar wa Anty Nafisa da duka inji karamar kaunarta take fadawa uwarsu. Haba gaba daya sukayo part din Maji hankali a tashe daidai duk su kuma sunyo waje inda Nafisa take tsaye da maryam. Maji tana fadin ke Inna Isa kyale ta haka na barta taitayi ita kadai. Daga nesa Umma ke fadin wallahi idan kuka kara dukan ta yau sai dai duk akai mu asibiti gidan nan . Kaji man marasa mutunci haukan ashe ba,a kan sadauki kawai ya tsaya du, dukan ku kenan ya shafa. Ke Nafisa may yakawo ki gurin wa yan nan matsiya ta ki jawa kanki tsiyan su irin ta gado ya shafe ki ke ma. Nan take fadawa uwarta duk abinda yafaru uwar take cewa barsu tsiyane da talauci yai masu katutu a kai shine bakin cikin su gare ki. Hassada ko sai dai su mutu dashi a gidan nan don babu mai kama kafar mu don mun riga mun masu nisa ko. A haka zasu kare daki tsiya tsiya kamar madallacin malam ba komai sai tarin raggaduda kawai ciki. Saurayi kuma sai sun ga har dan gidan gwauna a gidan nan gurin ku. Sai lokacin sadauki dake tsaye daga kofa shigowa gidan tun farkon fitina yana tsaye yana sauraren su. Ran shi yai matukar baci irin yadda yake jin ana zagin mahaifiyar shi da yan uwan shi a kan talauci. Su madai su Amira duk da Maji tana masu fada bai sa sun fasa mayar masu da amsan zagin da suke masu ba don harda mama Asiya ta shige tsagal cikin fitinan tana cewa ai wanan mutanen kune baku san sherin su ba dama da kowa bakin ciki sukeyi a gidan nan. Ke Amira shige daga ciki kada na kara jin muryan kowan ku yai tsaye yana nuna masu kofan dakin su da hannun shi. Ranshi a bace idanuwan shi sun kada saura kiris ya fashe irin yadda ya hasala. Yaran suka bi bayan uwar su da tafara shiga ciki ranta a bace yayin da ya juya inda taron mutanen gidan suke tsaye ya watsa masu jajayen idanuwan shi akan su. Zo mutafi kinji don wanan mahaukacin yanzu yana iya muna haukan shi akai. Gaba daya suka watse zuwa shiyan su a can suka yada zangon su yana jin sunci gaba da fitinar su ya shiga dakin mahaifiyar tasu. Tsawa yadaka wa su Amira akan suyi shiru hakana bai son hayaniya ya isa. To amma yaya don kawai an raina mu shine kowa ya kwaso sharan shi a kan mu zai yaba tsiyar shi. Nace ya isa haka ya fadi cikin tsawa hakan yasa gaba daya sukai shiru da maganan. Nan yakai zaune saman dayan kujeran da ya saba zama idan yashigo gidan, maimakon ya zauna yadda ya saba sai kawai yayi kwance tare da dora hannun shi daya saman kan shi daya na saman kijin shi. Ya kai wasu mintina a hakan gaba daya dakin ba wanda yai magana daga cikin su. Bintu ce ta mike don shigewa don dai ita gaskiya zaman ta a dakin duk a tsorace take dashi. Don gani take cewa kiris ya rage ya kamasu da dukan tsiya a dakin. Takai gaf da kofan zata shiga taji yana cewa "Ke kawo min abinci na na fita. Da,sauri ta juya zuwa kitchen inda ta hado mashi abinci kamar yadda ya saba hada mashi wanan karon har da spoon din da yace dashi yake ci. Bai masu magana ba ya mike zaune kamar zai dauki abinci sai kuma ya bude a,nan falon ya fara ci a hankali. Maji ki yace daidai zaikai spoon din shi a baki batare da ya kalleta ba kiwa yaran nan magana su daina shiga harkan mutanen gidan nan ana zagin ki a banza. Don bazan iya hakkurin wanan mugun zagin da ake maki ba a gidan nan haka. Talauci dai ba mune muka azawa kan mu ba Allah ne yayi mu a haka ba yin kan mu bane ai. Amma mutanen nan da,sun tashi da,wanan zasu zage ki ke da yaran ki, don tun ina karami nake jin wanan kalman daga bakin mama da Umma a gidan nan. Sai kuma ni da na ja maki wanan gorin na dan shaye shaye da kuma cacan da suka ce ina yi wai. To amma ba komai Allah na gani shida ya dora min wanan lalurar shine zai yaya min shi dakan shi aduk lokaci da yaso. Ke kuma Amira na roke ki da kuyi hakkuri da kowa a gidan nan don rayuwan mahaifiyar mu kin dai san ita ba mai son fitina bace a ranta. Haka ke maryan wanan zuciyar taki matsayinki na mace ki rage shi don gidan wani zaki tafi. Inda Bintu take zaune ya kalla tare da,watsa mata harara yace ke kuma da sauri Bintu ta dukar da kanta a kasa tare da mannewa jikin kujeran da Maji take zaune a kai. Yace kada ki yarda naji ance kinjawa uwar mu bacin rai a kanki a gidan nan zaki hadu dani. Sai lokacin Maji da takaici ya isa tai magana tace kai ku tsaya wasu,wasun ku amma kada ka hada da yar mutane da bataji batagani ba da kowa a gidan nan iyakarta imu a shiyan nan ba ruwan ta da kowa a gidan nan. Inda na tsayar da ita anan take bata taba saka kanta ga harkan kowa ba cikin gidan nan. Don haka tafita a ido ka kada kasa min "ya a cikin zancen ku wallahi kaji na fada maka gaskiya. Mikewa yayi ya ce kun daiji abinda na fada maku kowa ta kiyayyeni akan hakan. Barin dakin yayi kamar wanda aka tsakara baiko juya ba yafice abinshi har lokacin yana jin hargowan Umma daga part din su. Zancen bai kare ba don da maigidan yadawo an samay shi da zancen yana ji yace a kira mashi su Amira da maryam tun kan hajiya Umma tafita daga gurin shi har Nafisa din. Bayan kowar su tashigo tare da uwarta harda mama Asiya da yaranta yan mata, yana cin abincin shi hankali kwance ga hajiya kubura dake girki daga gefen shi suna zuba soyayyan su a cikin style. Alhaji kaifa kace a kiramu kuma kabar mu a zaune kana harkan gaban ka inji mama Asiya da kishi ya kumay a lokacin na irin yadda yakeyi da mummy. Mummy tace ke hjy Asiya ko so kike kuma yabar cin abincin ya tsaya shirmen kishin ku na kullun da baku san angirma ba har yara sun fara irin shi. Kada ki fara ki fada min maganan banza wallahi yanzu a jimu a gidan nan don ke baki da kunya kowa so kike yabi ki kamar yadda kika mayar dashi a gurin ki. Alhaji wanda yagama wanke hannun shi da hjy kubura ke zuba mashi ruwa yace ta mayar dawa wai ni ko wa ? Shiru tayi don tasan idan ta tanka yanzu zai iya watse ta a gaban kowa babu ruwan shi da yara na gurin. Gurin Amira ya juya yana cewa mamana yanzu Umman ku ke fada min wai kun taru kunwa Nafisa duka yau a gidan. Sai kuma ya juya gurin Maji yana fadin ina bakuwar yar ki ita bata zo bane don nasan ba,a dukan Nafisa bata sa hannun ta ba. Nafisa tai but tace wallahi danaci uban ta ko murmushi yayi tare da duban Umma yace kin dai ji tarbiyan ki ko ? Yace wa yar mama Asiya karama hauwa kira min yarinyar dake dakin maijidda tazo da sauri yarinyar ta mike zuwa kiran Bintu. Ta na shiga bako sallama Bintu da ke zaune hankali a tashe ta kurawa tv ido sai dai hankalin ta ba,a kallon yake ba sai ji tayi ance ke yar kauye baba na kiran ki. Tare da watsa mata harara tana yatsune fuska tare da bin dakin da kallon wulakanci ta juya da sauri bintu ta jawo hijjab din ta dake gefe har kasa tasaka. Tare da bin bayan yarinyar don bata masan falon baban ba duk zaman ta gidan da tayi ba ruwan ta da sanin komai. Saida tajawo kofan dakin Maji da zata fito tasaka key tabar dakin da key din a hannun ta. Inda taga hauwa ta shiga nan ta shiga itama tare da sallama dauke a bakin ta. Maji da hjy kubura sai Alhajin ne suka karba mata sallaman ta da tayi tare da samun guri ta tsugun na ta sunkuyar da kanta kasa tana fadin. Ina wuni Baba, cikin lada bi tare da sunkuyar da kanta a kasa, yace tare da nuna ta da hannu kun gani, Sannan ya karba mata gaisuwan nata yace ku diba ke Asiya da kika samay ni kan maijjidda ta dauko bakuwar yarinya takawo min gida. Kinga abinda tabi ta jawo ta a jikin ta tarbiya natsuwa da sanin ya kamata ga yar kauyen yar makwabtan da kika ce. Hajiya kubura dake gefd tace kai Allah dai ya sawaka idan kuma anyi magana ace wai wani ke hassada. Ke kubura wai may kike so ma dashi ne ki fada min don kin san daidai nake da ke wallahi. Ai kaji maganan ke nan yanzu ku dakata da wanan bashi nakiraku yi ba anan ina son nasan may yakai har ke Amira kuka taru kuka daki Nafisa yau a gidan nan. Anyi magana kuma uwar ku ta daure maku harda ita ta shiga zancen, ana haka kuma mahaukacin wanku shima ya shigo ya saya ya zama nashi. Nafisa ta tare zancen dacewa baba bakin cikine fa kawai don sunga ana zuwa gurina su ba,a zuwa kiran su kamar sauran yan mata. Alhaji yace a gidan har ake haka banda labari Nafisat ? Allah ya kyauta kawai yace tare da girgiza kan shi cikin takaici yana kada kafan shi irin na magidantan da abu ya daurewa kai. Yace ke tare da kallon inda Bintu take zaune yace mayye sunan ki ne ma ? Tace a hankali Bintu Baba, yai yar murmushin manya yace Fatima bintu ke nan ko? Eh Baba ta bashi amsa yace ki fada min abinda kika sani akan fadan da akayi a gidan nan yau. Shiru Bintu tayi na dan lokaci kamar ba zatai magana ba sai kuma can tace. Baba muna daki bayan anty Amira ta shigo gida nan tafara bashi labarin abinda ta sani da irin kalamin da kowa ya fadi har marin da Maryam taiwa Nafisat din. Amma maryam wallahi kin kyauta min inji hjy Kubuta tare da kallon gurin da maryam take zaune. Eh zaki fadi haka mana tunda ba yarki akaiwa hakan ba a gidan. Hjy Umma ce uwargidan su mahaifiyar Nafisa ta ke fadin haka din cikin bacin rai. Batare da Alhaji ya kalli gurin da take ba yace kubura ban son na kara jin bakin ki a zancen nan. Daga haka yai shiru bai kara cewa komai ba kuma again, ya juya gurin Umma yace to kinji ke maimuna zagin uwarsu tayi har dakin ta kuma tana zaune babu kunya don kawai an bata mata rai akan saurayin ta da yazo kiranta ba,a fada mata ba. Alhaji kada ka juya zancen nan fa dukan min ya akayi kuma shi nazo fada maka din ka dauki mataki a kai. Yace wani mataki zan dauka idan kece su Amira suka shiga gidan kike sukai maki haka a gaban ki wani mataki yaran ki dake gurin zasu daukan masu ?. Shiru Umma tayi yace ba amsa ke nan sunyi daidai dai din ke nan ko ? Tace yanzu mai kake son nace tunda na fahinci ka daure masu gindi akan abinda sukayi sunyi daidai. Yace kin taba gani mai kai takaka yayi nasara gurin maida magana balle harda cin mutuncin uwa a ciki. Ai ko ke ne suka kawo wa takaka akai masu hakan iya matakin da,zan iya dauka ke nan a kan su kinji na fada maki. Ke kuma Nafisa wani yaro ne yake zuwa gurin ki gidan nan ban sani ba har kike iya tsayawa kiwa yan uwanki cin muntunci akan shi don ya aiko kiranki ba,a fada maki ba ranki ya baci kibi yarki har daki kina zagin ta don samun guri. Shiru Amira tayi tare da dukar da kanta cikin tsawa ya daka mata tsawa yana fadin badake nake ba nace dan gidan uban waye ke zuwa gurin ki gidan nan har kofan gida na ? Sai ga Nafisa tana hawaye don daga ita har uwarta basu zaci abin zai juye masu haka ba a lokaci guda. Yace tunda aure kike so ba karatu ba sai ki turo min yaron yazo ai maganan aure dashi. Ya juya gurin hajiya Umma yace maimuna yanzun saboda Allah kin san yarinyar nan tana tara min samari a kofan gida haka shine baki fada min ba saboda Allah da girmanki ? Idan da da dan wani dakin ne yake haka dafa a gurin ki zan fara jin wanan labarin. Yanzun dai nafahinci ka juye maganan ya zama laifi akan mu, shike nan nida diyana bamu da shakat kan yan mayen diyanka a gidan nan. Duk abinda sukayi shine daidai mu bamuyi daidai ba indai duk wa yan nan marasa mutincin yaran Hauwa ne ka daurewa gidin ai suje suyi tayi. Ba sabon al,amari bane gasu nan daga dan maye sai yan iska data tara muna a gida. Ta mike fuuu, ta fita daga dakin inda shima yabi ta da kallon takaici mama Asiya ma mikewa tayi tana fita tana fadin babu dai adalci yanzu a gidan nan. A dakin mutun kuma ace wai shine bai da gaskiya don samun guri da daurin gindi kawai. Ya juya inda yaran suke ya kara masu fada akan baya son ya kara jin fitina daga gare su ko ya batawa mai shi rai suka mike suka mike suka bi bayan uwayen su rai a bace su ma. Suna ganin ba ai sharian gaskiya ba a gurin don sune da gaskiya amma mahaifin su ya danne masu gaskiyan. Bintu ma ganin yaran sun mike yasa ta mikewa tabi bayan su amma sai taji muryan Baba yana cewa ke Fatima sai ta koma ta tsuguna don taji may zai ce mata din. Yace ban son naji ance kin saka kanki a harkan cikin gidan nan kamar yadda ban taba samun labarin banza ba a kanki fon haka ki kiyayye kin ji . Ta amsa da to Baba nagode ta mike tabar dakin duk tsoro ya cika mata zuciyar ta ta samu su Amira suna jiran ta takawo masu key din kofan su data rufe masu. Hauwa kici gaba da hakkuri don ance dan kuka mai jawa uwarshi jifa yau duk yaran ki bugu daya ake masu akan danki daya daya samu matsala, Don haka saikin toshe kunnuwan ki don babba da yaro dashi zai zage ku duk wanda ya tashi a magana gudu zai fake ya harbe ki dashi. Sai kuma ya jijiga kan shi a cikin takaici da jin zafin sadauki a ran shi yace Allah ya kauyata. Sai lokacin hjy kubura tai magana tace rashin dai tunane ne ga mutane ai wanan matsalar ta shafi kowa a gidan nan don ba nata bane ita kadai. Amma hakkuri da addua bai bar komai ba Allah ya sauwaka ya kiyayye gaba kawai za,ace. Maji ta mike tare da cewa nagode Alhaji ranta babu dadi yabita da kallon tausayi kawai. Har takai kofa hjy kubura tace gobe dai ba aiki don Allah ki ara min yarki ta tayani gyaran daki na. Ta juyo tana cewa wai Fatima Alla ya kai gobe ai ita yaro ba kiuya ne bata jin nauyin jikin ta ko kadan. A daki ta samu su Amira suna dariya Bintu wai ta rufe kofa da zata, fita daga dakin. Tace ba dole ba don ni abin wallahi yanzu tsoro yake bani ma mutane haka ba tsoron Allah. ****** ********* ****** Sadauki yana fita jin shi yake kamar yana taka kaya don bacin rai, duk wanda ya yanzu ya tashi zagi akan shi akewa uwar shi gori. Ya madai godewa Allah da jiya bai sha komai da da yai niyar sha yasan da yau gorin da Maji zata sha akan shi Allah kadai yadan irin sa. Gashi saida ya zuba kwayan a bakin shi sai yaji kamar ance ya furzo su waje duk ya zube su a kasa suka narke yana kallon su. Har ya usa filin kwallo zuciyar shi sai faman sake sake take mai kan abinda zaiyi wanda zai sa Maji ta danji sanyi akan shi. Amma ya rasa mafita akan haka, haka ya samu guri ya zauna ranan yana kallon masu kwallo kawai ya kasa tsinanawa kan shi komai a lokacin. Sai faman kulawa da warwarewa yake shi kadai a ran shi abin duniya duk ya damay shi. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,, Tun bayan dawowan Raiha daga tafiya gaba daya bata son fita zuwa ko ina ko yaushe tana gida sai faman barci takeyi kamar wace tai wani aiki. Gaba daya ta kashe wayan ta kuma ta hana kowa ganin ta tayi hakane don gujewa Nasir kawai. Kusan sati biyu yana sintiri a kofan gidan su gashi tun dawowanta wayanta a kashe yake mata. Ranan da ta bude wayan ta bayan kaman minti goma kiran unknown nomba ya shigo mata layin ta. Da farko kyale kiran tayi har ya gaji ya tsunke don kan shi amma,sai gashi mai kiran bai hakkura ba ya kara kiranta again. Cikin kasala ta dauki wayan sai taji murya cikin turanci a na cewa hey, baby, It's me Michael, your friend from lagos, i hope you remember me now. Cikin wata murya tace you mean, Michael Nasir friend ? Yes it's me baby . I called your nomber several time is switch up what happen with you baby? Tsuki tayi tana fadin dan rainin wayo kawai har ma kana tambayana abinda ya samay ni ne wai? Sam batai tsanmanin ya taba iya hausa ba sai taji yace don Allah kiyi hakkuri nasan bamuyi maki adalci ba shi yasa nakira layin ki na baki hakkuri don ban son abinda zai dawo a gare ni wata rana. Maimakon tayo magana sai ta kama kuka dama gashi mahaifiyarta bata nan gida ta tafi makwabtan su . Cikin rudewa michiel kece tayi hakkuri ta,saurare shi yana son magana da ita ne. Da kyat ta dakatar da kukan ta yake cewa kina jina baby dama na dauki nomban ki ne batare da sanin abokina ba. Don kawai nakiraki saboda ya bani labarin irin abinda yake maki wanda banji dadin shi ba kuma ranan ban san cewa two in one zamuyi maki ba don mun shirya dashi ne ni kadai zanyi amfani dake. Wani abinda baki sani ba yanzun hakama yana nan yana planning din yadda zai fita dake waje, ne ya sayar dake ga turawa don ya tara kudi. Bake ce ta farko da yai wa haka ba akwai yan mata biyu da ya kai waje daga garin ku. Batan lokkacin da tace what da karfi ba cikin wani irin murya mai karfi. Yace cool down my friend, kin bani tausayi ne don naga ke yarinya ce karama. Kuma d way yadda naga kina kuka yasa kika bani tausayi, ba zan yarda ya yaudare ki ba shi yasa na kiraki na fada maki komai da fatan zaki rufeni bazaki bari yasan na fada maki komai ba. Godiya take mai tana fadin tagode tagode yace ba komai, sai dai idan kina da account ki turo min zanturo maki da kudin ki. Don shi ne ya hana na biya ki tun yana kuna nan yace free sex nayi dake ni kuma i can't dole ne na baki hakkin ki. No kabarshi kawai ba komai, nagode, sai kawai ta kashe wayan. Kifewa tayi saman dan katifan dakin ta ta,shiga gurzan kuka wi,wi tana cewa Nasir Allah ya isa tsakani na dakai wallahi. Sai kuma tai shiru tafara tunane na, son, datakewa,Nasir ya haukatar da ita ta kasa fahintar irin son da Nasir yake mata. Sai yanzu tafara tunanen lalai maganar Michael yana da kamshin gaskiya sosai don a wanan tafiyan ta fahinci wasu dabiun shi da bata sani ba. Baida tausayi ko kadan son kan shi yai yawa bai damu da damurta ba ko kadan, shi kan shi kawai ya sani. Gashi in ba dan sayayyan da yai mata ba bai bata komai ba haka ya barta tadawo gida sai dan dubu biyar dake a hannun ta. Gashi kayan da,ta,sayo ta rasa yadda zata fitar tai amfani dashi a gani a gida, a tambaye ta ina ta samo shi. Don har yanzun tana da sauran burbushin tsoron iyayyenta a ran ta. Maganan Michael yai matukar tsaya mata a rai sosai don duk da bata ga Nasir ba amma matukar tsoron shi take ji a ranta. Ko da Raiha tafara fita bata yarda ta hadu dashi ba sai guje mashi takeyi duk inda tasan zasu hadu bata yarda su hade dashi. Wata rana tana tsaye tana jiran taxi taga wata far mota ta tsaya a gaban ta. Bata tsaya kallon kan motar ba, sai kokarin tare mota take yi hankalin ta yana kan titi. Ya fito daga cikin motar yana saye da shedda kalar kakin soja tai matukar yi mashi kyau sosai da haka yake yaudaran yan matan gari. Don Allah yai mashi matukar kyau don duk shigan da yayi zai mashi kyau sosai ya karbe shi. Baby ya karaso yana fadi kamar bata ji shi ba tayi ta kawar da kanta tana kokarin shiga motan da ta tare. Da sauri ya karaso gaban ta yana cewa haba baby wai may ke damun ki ne don Allah na fa rasa gane kan ki. Wani kallon tai mashi kamar bata san shi ba ta na kokarin zaunawa a motan da zata shiga. Hannun ta ya riko da karfi yana fadin sunan for d first time sabanin baby da yake ce mata da, Ke Raiha wai may ke faruwa ne please ? Sake min hannu tace cikin wani zafafan muryan tare da kokarin kwace hannun ta daga rikon da yai mata din. Mamaki sosai abin yaba Nasir din don dai shi yasan lafiya suka dawo da ita daga tafiya. Look baby Raiha ki fada min idan wani abu ya faru ne please don ban san laifin da nai maki ba ni. Kawai ra,ayina ne hakan na nisan ta kaina dake don bakai min ba ni, maganar ta yasa shi murmushi yace to ni kin min ai. Ko ba shike nan ba ki tsaya please muyi magana mu fahinci juna kada ki tara min mutane please. Da,wasa ya dauki zancen amma sai yaga finfirin Raiha ta shige mota ta tafi abinta tabar shi nan tsaye. Gurin Brosha ta tafi don dama kayan aikinta sun kare gashi kuma tana son jinta a network sosai don kwana biyun da tayi bata sha ba duk wani kala take jin kanta. Shiko Nasir nan ta tafi tabar shi da mamaki don ya kasa fahintar abinda yai mata, saidai tunanen shi ya tsaya ne kodai yadda yai mata a lagos ne yasa tai hating din shi. Wanan yatinyar may take nufi sai da tafiya tai nisa take son ta bata min show dina wallahi bata isa ba. Don na riga da na fara shirin fita da ita waje gashi shegiya nasan ba karamin kudi zan samu a kanta ba don shegen dadi ke gareta. Koni don dai son kudine kawai da ya rufe min ido aida bazan iya rabuwa da ita ba. Gidan mahaifan shi ya nufa inda yan kannen shi suna ganin shi suka taso da murna suna mashi sannu da zuwa. Duk cikin subabu sa,an Raiha don suna girmay mata da shekara biyar ko hudu. Bayan ya gama gaisawa dasu ne yake tambayan Gaban hajiyan shi dake zaune saman kushin ya zauna yana mata ina kwana. Ta amsa cikin dakewa tana ce mashi lafiya yakara da tambayan ta ya gida da sauran al,amuran gidan, nan ma ta bashi amsa da Alhamdullahi. Sai dan shiru, can uwar tace ashe kadawo ban sani ba yace eh inna ai yau kwanana biyu da dawowa. Wani kallo tai mashi tace bayan Abdul yau kusan kwana biyar ke nan da yace min kun hadu dashi, zakace wai kwanan ka biyu da dawowa. Nasir ko kana son mayar da kanka mutumin kwarai kuwa ? Ka saki matar ka kakuma ki aure sai yawon kwasan yan mata kake a mota baka nan baka can dasu. Wallahi kayi hattara da cutan zamani don yawa gare su ko ba wanan akwai wancan. Dukar da kai yayi kamar wani mutumin kirki yana cewa Inna ai zanyi bandai samu wadda namu yazo daya bane har yanzu. Don ina gudun kada akara maimaita irin na wancan karon aza kuma ba,a dace ba. Kai din ma ai ba halin kwarai ke gare ka ba tunda baka iya zama kurum. Ga shaye shayen da ka sawa kanka don ban tsan manin ka daina yi yanzu. Girma dai ya kama ka in kanawa kan ka,fada kayi wallahi ni zan fitane kada kazo ka tare ni da surutun banza. Yace Inna ina zaki sai na sauke ki dayani tunda gani na shigo. Tace da sauri wa aganni da kai ace may ace har alfahari nake da irin halinka ina shiga mota da kai darana cikin gari. Murmushi kawai nasir din yayi duk da,zancen mahaifiyar tashi ya soshi zuciyar shi. Ya mike yana mata a dawo lafiya yafita inda kannen shi suke ya basu dubu goma wai su raba don yasan ko yaba inna ba karba zatayi ba don tace kudin da yake sayar da kwaya ne ita bata ci. Duk yadda yaso ya fada mata matar shi da suka rabu kazafi take mashi amma inna taki yarda da ba gaskiya bane. Abu daya tasan yana masu shine biyan kudin wuta da na ruwan fanfon gidan nasu tun bayan da mahaifin shi ya rasu. ****** ********* ****** Ranan da matan gidan suka samu labarin tafiyan da sadauki zaiyi zuwa kasan waje sunyi ta zuba bakar magana kamar tashin hankali. Inda suke cewa lalai maji bata san ciwon kan ta ba da har zata yarda ta barshi yafita zuwa wani guri wai ma kwallin kafa. Itako mama Asiya cewa tayi sai dai a kare da hakan a lalace wai wasan kwallo don tambadewa kawai. Umma sai da ta samu maigidan su da zancen tana cewa wai da gaske ne zancen da taji yara suna fadin sadauki zaifita waje wasan ball. Yace da gaske ne mana akwai illa ne ga hakan ko yaya ? Tace haba Alhaji yanzu kamarka da kimar ka da darajan ka,za,ace wai danka ne ke wanan abin. Shi kwallon kafan kuma yanzu mugun abune, da na barshi nan zaune gida yana tambadewa ai gara na san ya kama wani abun. Tace amma gaskiya Alhaji,,, ke yafa isa haka Rakiya don nasan abinda nakeyi sarai wallahi don haka na fada maki da yardana zai tafi. Cabdi ashe akwaita gidan nan ke nan don sunan ka bai lalace ba yanzun ne ake shirin yin ta. Ta fito fuuu, daga dakin tana zuba bakaken maganganu itakadai har zuwa dakin ta. Ba su hakkura ba sai washegari kuma suka kara,tayar da zancen. Lokacin haniya kubura tana kusa sai cewa tayi maye cikin wasan kuma ai wanan idan Allah yasa mashi hannu sai kiga an take akai. A sawan kwallon ko a shaye shaye wanan dai kawai an kara turashi ne yaje ya kara yin cos kan shaye,shayen shi kawai. Nikan wallahi idan ya dawo naga yakara haukacewa sai dai na bar ma su gidan shida uwar shi kawai don dama haka sukd so. Allah dai ya shirya muna shi amma ai ba kai wa dan wani mugun fatan mugun abu ya samay shi. Daya samay shi da farko ni nai mashi fata ko may kada fa mace ta daure ni da raina. Ni yanzun ma gani nake kamar ya koma ga shaye shayen shi ne don ko yaushe yana gida kwance kamar wani malalaci sai aukin barci kawai. Duk a kunnen maryam dake zaune a falon suke wanan hira da dane kafin maji ta hore su da rashin kunya da,tabasu amsa daidai da maganan su. Sai da ta,dawo daki take fadawa maji abinda taji suna fadi kan tafiyan na sadauki. Maji tace Allah ya sauwaka ai Allah yafi su ni dai ban wa dan kowa mugun nufi akan shi. Amira tace ai ba zasu so suga ya zama abin kwarai ba tunda ba haka suke son ganin shi ba dama. Ke kubar wanan magana duk ma abinda su ke nufi ni dai ga Allah na dogora. Sai lokacin Bintu da bata faye shiga maganan su ba ta sa baki tace ai in ba abin mutum ba ba mai son yaga nashi ya lalace su dai suyi mashi fatan alheri kawai. Ke kika san wanan amma ai su basu sani ba sunfi son ko yaushe su ganshi a hakanan inji Amira. Amma maji kafin ya tafi da ki sa ai masa saukan alkur,ani maigirma Allah ya kare shi a can inji Bintu . Ina da niyar yin hakan sai dai ban san wanda zan sa yai min ba tunda ba, baga hajiyan masa ba maji Amira tace mata da sauri. Lalaifa haka za,ayi zan mata magana da ta san yadda zata samu na Allah da zasuyi min. Amira tace ashe su ma wai har sun farga da wanan yawan barcin da yaya yake yi kwanakin nan Ba sa ido bane duk abinda mutum yakeyi idon su yana a kai kamar wasu mayyu can Mutane suce basu son suga dan uwan su a farin ciki ko kadan sai dai kullun aga kana wahalan tsiya kawai Ai yanzun haka duniya ya koma hassada da bakin ciki yai wa mutane yawa a rayuwan su inji maryam. Allah ai yafisu don duk abinda zasuyi Allah ya dai yana ganin su. Uwar dai tana zaune tana jin su kala bata kare ce masu ba ga hiran nasu. Duk zuciyar ta a jagule yake akan tafiyan da dan nata zaiyi a cijin wanan halin da ake ciki dashi. A kullun, zancen Maji kan sadauki shine ya taimaka idan ya tafi ya kama kan shi da rayuwan shi acan. Don Allah Baba na kada ka bamu kunya ni da mahaifin ka, sadauki yakan yi mata murmshi ne kawai yace kada ki damu maji insha Allah zan tsare kaina danan dacan kamar kuna tare da nine ai. Mai masa ta tafi kamar yadda Maji ta bukaci da ta taimaka mata akan ai mashi addua kafin yatafi inda tabada kudi cikin asiri ko yaran ta basu san da zancen ba. Da dare sadauki ya shigo gida inda ya samu maryam kaunan shi a tsaye gaban tsohon TV dakin su tana kwalan shi don ya tashi yai aiki don saboda tsufa ya gaji ya na tsayawa don kan shi. Sai yake cewa ke Maryam kina ta faman kwalan Tv haka idan ya fashe fa? Yaya idan ba dukan shi mukayi ba baya tashi sabofa ya tsufa da yawa sosai shi yasa muke dukan shi gashi za,ai program da karfe tara muna son muyi kallo. Wani irin ba dadi yaji a,ran shi inda ya kara jin tausayin uwar shi sosai a ran shi . sai ya tuna yadda yaga dakin hajiya Kubura a ranan, Komai akwaishi na,zamani a dakin amma su ga dakin uwar su kamar zaure ba komai a cikin shi sai yan tsofafafin kujeru da wanan tshon TV da maryam take kwalla. Wani dogon huci yaja a fili har yasa su dago kai su kalle shi kan shi ya mayar saman makarin kujera ta baya yana shafo fuskan shi kawai. Bintu tafito cikin wani dogon rigan atamfa wanda akaiwa dinki budade daga kasan shi. Maji tafara sallah ishai a lokacin don haka ta waiga inda yake kwance saman kujera taso share shi amma tsoron shi take matukar ji. Don haka takara waigawa still yana a yadda yake kamar mai barci, tace cikin daurewa yaya sadauki ina wuni. Tankar a cikin mafarki ya tsinkayi zazzakan muryan ta da take gaishe shi. Batare da ya,sauke hannun shi daya kare fuskan shi dashi ba ya amsa mata da kyat da lafiya. Tace akawo maka abincin ka ne yanzu kamar ba zai amsa mata ba sai can yace kawo min kawai. Ta juya zuwa kitchen don ta dauko mata yai daidai da ya dago fuskan shi sai ganin bayan ta yayi tana tafiyan ta a cikin natsuwa. Yace ke idan zaki fito ki zo min da ruwan sha daga nan, ta amsa mashi da tau kawai ta shige abinta. Tana kitchen sai faman tunane take barkatai tana cewa, shi wanan haka Allah yayi shi da mudaden hali ne wai. Girman kan shi da share mutane gami da nuna isa sunyi yawa don isa ma da izza wai ke yake ce mata. Shigowan da Amira tayi kitchen din shi ya tsayar mata da tunanen zuccin da takeyi. Amira tace abincin yaya sadauki ne zaki hada mai ta bata amsa a cikin ladabi da fadin eh nagan shi zaune nako san abinci ne ya kawo shi amma bai iya tambaya. Amira tai dariya tace kin san shi magana ma matsalace a gurin shi kafin kiji yai magana aiki ne gare shi, dan dama idan da maji suke magana zai iya dan kai lokaci yanayi. Tana hada abincin suke magana da Amira inda ta dauki abincin zuwa falon su inda yake zaune. Wanan karon ta samay shi a,zaune ya dauki kafa daya ya dora ga dayan kafan shi yana kallon yadda maryam ke bugun TV nasu da karfi. Daidai ta kusa karasowa inda yake taji yana cewa Please maryam kibar TV nan hakana idan ba zaiyi ba mana. Bintu ta,kawo abincin a gaban shi ta dire mai zata juya yakw cewa ke mai aka dafa don banga cibi ba. A tsorace tace mai tuwo ne shi yasa ban hado da cibi ba cikin jin tsoron shi take magana. Da hanzari ta juya zata bar gurin yace ke dauko min cibi dan Allah ko tuwo ne ba,aci da cibine akace maki bakauyar banza kawai. Simi simi Bintu ta juya zuwa kitchen din duk da zagin da yai mata yaci mata rai akan tai mashi abin arzikine kuma zakirata da bakauya. Kai inji Maji da data idar da nafila take cewa kada na karajin kakirata da bakauyan nan don ba gurin ka tazo ba. Ina laufin ta ta hado ma abinci don kai miskilancin ka bai bari ka tambayi mutane abincin ka. Mikewa yayi tare da dauka abincin nashi yana kokarin barin falon don bazai yarda a raina shi ba akan bakuwar yarinyar Maji da bai san inda tafito ba. A lokacin ita kuma Bintu tafito daga kitchen din dauke da cibin a hannun ta tana mika mai. Yace ke barshi dan Allah ya fice daga falon Maji taja tsaki tace shiyasa ake ce ma mahaukaci yaji ta amma bai tsaya ba yafice kawai abin shi daga gidan zuwa part din su ranshi a bace. Don shi bai son ai mashi fada a gaban yara kada su raina shi. Sai bayan kwana biyu ya shigo gidan duk lokacin yana fushi wai maji ta kunyatashi a gaban kannen shi. Jin gidan shiru sai maryam dake zaune falo tana karatu yace mata ina Maji tace mai tana ciki ta kwanta. Yai kamar zai fita sai kuma ya tsaya ya mayar da hankali ga maryam yace ke, Wai wanan bakuwar yarinyar da nake gani a nan daga ina tazo tace yaya sadauki kana nufin Bintu? Yace ina ruwana da sunan ta nace dai ita din wacece ? Tace diyar hajiyan masa ce makwaciyar mu Maji tace ta zauna nan don hajiyan yanzun bata zama tana jiyan yarta a kauye. Ya koma tambayan ta a nan makwabtan mu suke ke nan shine maji tace ta dawo nan kuma,? Tace eh daga kauye tazo karatu take kuma hajiyan masan bata zama yanzu. Wani irin tsuki yaja yace kai Maji da kwashe kwashe take wallahi shine har zata disgani a kan ta? Maryam duk ta kagu da tambayan da yake mata kada itama nata ya samay ta. Idanuwan shi sun yi ja sun kada sai take tsoron ko ya shawo ne a lokacin. Yana kokarin fita daga falon Maji tana fitowa tace ina jinka mara kunya dana kwaso ta akan ka nace ta zauna ko kuwa. Tana kallon shi ido da ido taga idanuwan shi yadda sukai mai ja sun kade kamar an watsa mai barkono a cikin su. Tace mashi kai mai kuma ka,shawo ne naga duk idon ka ya wani sauya haka. Sai lokacin yace kai haba Maji shike nan ni banda aiki sai sha harda rana haka. Kuna da lokacin shane tunda kun bushe filar ku baku jin kunyar kowa a wanan yanayin, Kamar zaiyi magana sai kuma yace ni ban sha komai ba kaina ne dai tun safe yake min ciwo. Ya juya yana fadin yanzun ma magani na sayo bari naje nasha na kwan ta, ya juta yafita daga dakin. Yana tafiya Maji ke fadin in ma dai ka koma shane wanan kuma ruwanka. Amma da yafita hankalin ta bai kwanta ba sai cewa take a ranta ko ya sha din ne ko kuma barin shan da yayi ne yake haifar mashi da ciwon kan oho. Maryam ce ta katse da cewa nima wallahi yadda naga ya shigo ya tsare ni da tambaya tsoro ya bani . Shiko yana fita sashen su na samari ya shiga kai tsaye ya nufi dakin su don da gaskiya kan shi din ke masa ciwo don rashin shan da baiyi ba kwana biyu. Ya fada kan katifan shi batare da yasha maganin da yace ba din, kwance yake kamar mai barci yana tunanen kodai ya dan hada ne yasha ko zai samu relief. Yana gurin a kwance sai faman sake sake yake a cikin ran shi kodai yashane ko ya bari. Sai wata zuciya tace mai idan kasha shike nan zancen tafiyanka ya lalace. Don ko kowa ya yarda Mani bazata yarda yatafi ko ina ba tunda ba bari yayi ba. Amma wata zuciya kuma tana ce mashi yasha koda kadan ne don ya dan samu sauki a ran shi. Mikewa yayi ya jawo ledan da yake aje kayan aikin shi a ciki yana kallon su sai faman sakan zuci yakeyi shi kadai a dakin. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYABA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,,,, A LOKACI MU KE,,,,,, Bintu bata da wani matsalar komai tsakanin ta da mummy da take zaune a shiyan ta. Don mummy dai irin wayyayun matan nan ne masu faraf faraf da mutane ba,a gane gaskiyan cikin su. Wata, yammaci da dare, Bintu tana kwance tana barci don yayi saurin kwanciya don ta gajiya sosai gashi bataci abinci ba da yunwa ta kwanta hakana. Cikin dare yunwa ya damay ta don haka ta bude idon ta don ta sauko saman gadon da take kwance akai. Tana son fitowa zuwa kitchen don dauko abincin ta da bata ci ba a daidai kofan dakin mummy take jin sautin muryan ta tana waya kamar haka. Wallahi ina fada maki yau kwanan ta uku bata gidan tana can garin su ana mugun a bu, Yanzun haka yarinyar da take gurin ta,da nake fada maki tana dakina ta barta ba,aje da ita ba. Wai kin san may wallahi ni kin san ba yarda nayi da su ba matan gidan nan baki daya. Kada taje can ta yi sa,a har ta samu galaba a kaina, don nasan kowan wansu ba wai ta zauna bane. Duk yadda za,ayi gobe ki je min gurin nan ya kasance duk abinda ma taje garin su ta kullo a lalata min shi baki daya. Bintu bata tsaya ta karasa jin komai ba ta juya a hankali ta koma dak8n da take ciki kwance, Jin motsin mummy tayi don haka tamike zuwa dakin da Binta take kwance a ciki tagani in itace take sauraren hiran ta, Jin motsin mummy tafito daga dakin ta yasa Bintu lafewa tankar mai barcin da yai nisa sosai. Mummy ta,dan duba da kyautaga barci takeyi abinta hankali kwance,tai wani irin sauke ajiyan zuciya tare da dafe goshin ta tana fadi Allah ya soni yau da kashina ya bushe wallahi. Komawa tayi taci gaba da wayan ta wanda babu wani abin arziki da take kullawa a cikin wayan sai kishi irin na kishiyoyin lokaci. Imani da tsoro duk sun rufe Bintu a lokaci daya na irin maganan da,taji mummy tanayi a,waya akan uwar dakin ta, Maji ke nan. Gaba daya kara tsanar gidan taji a ran ta kwata kwata babu mai imani da,tsoron Allah kowa kan sa yasani yanzu. Idabn da a hira wani kefada mata abubuwan da taji Mummy tana fadi akan Maji da sai inda karfinta ya kare gurin karyata maishi. Matar da duk gidan tafi nuna tausayin ta a kan Maj da yaranta yau kuma itace take wanan sake maganan a bayan idon mutane don tsaban iya kisisina na,zamani. Washegari haka Bintu ta,tashi ta kasa sake jikin ta,ga yunwan da ta kwana dashi harsafe tare da,bacin rai na abinda taji mummy na fadi. Ita ma dai yanzu gaba daya jin gidan takeyi duk yafita mata a,rai baki daya ba wanda ta yarda dashi dan dama maman ta watau maji ke nan. Don in ba kazafi zatai mata,ba,zata iya cewa tunda ta,zo zama dasu bataga wani anin assha ba daga gurin maji har yaranta sai dai matsalan shaye shayen sadauki shine kawai abin da zata ce tagani na assha a gurin su. Bintu tafito daga daki inda ta samu mummy zaune ta gaida ita acikin ladabi da biyayya. Sai ta mike tana cewa cikin kwantar da murya zan tafi na gyarawa mama gurin ta don ina,ganin yau zasu dawo. Kallon mamaki Mummy take mata tace Bintu yaki nan zo zauna muyi magana ta fahinta dake. Komawa tayi ta zauna kamar yadda aka bukace ta da yi din. Mummy sai da ta dan ja lokaci tace ba komai yasa na ce zanyi magana dake ba,Bintu sai ganin ki yarinya mai saurin fahinta,da sanin ya kamata. Ina,fatan maganan da zan gaya maki zaki fahince ni ba,tare da,wani manufa ba a,ranki. Murmushi Bintu tayiwa mummy kawai a lokacin sai da Mummy ta,dan yi shiru tace gaskiya Bintu a dan zaman da nayi dake na fahinci cewa ke yarinya ce mai mutumci da sanin yakamata. Irin yarinyar da,na,dade ina gurin samu a,raina a gidan nan na rike ta. Sai dai kuma,gashi kin zo min a ta,wani babban yanayi mai daure kai sosai, don zaman da hajiya maijidda zai ita kawo min akasi akan bukatana. Don haka nake neman hadin kai a gurin ki idan ta,dawo don Allah ki jajirce kice a gurina na zaki ci gaba da zaman ki. Kin daiga ni da ita,ba daya bane,don haka ki zabarwa kanki inda zaki zauna ki samu karuwa iyayyen ki, su ma su samu ta gareki, Don kinga ni kudi zan dinga baki duk karshen wata sabanin yadda maijidda ta aje ki sai bauta mata kikeyi bata baki komai dake da gwagon ki. Wani irin mumunan faduwan gaba ne ya daki zuciyar ta na wani dan lokaci inda tsoro da firgici suka ziyarce ta Kanta ta,dukar kasa inda mummy take cewa ke nake saurate fa, Murya kasa kasa take cewa mummy ai da nan da can duk dayane ni a gareni. Don duk mutunci ne ya hadani da kowan ku. Ok tau yanzu zabi ya rage naki sai naji shawaran da kika yanke wa kan ki. A cikin gatse tabata zuwa zabi don ta san bazata bar kudi ba da jin dadi ta koma inda uwa tsugunne diya a kwance ba dole zata dawo nan gurin ta inda ga dadi ga sutura masu kyau, ba second hand ba. Tasan dole ne ta dawo gare ta ma don ta kashe mata zuciya ko. Haka ta mike ta nufi part din Maji tana tafe tana nazarin maganan mummy matar da a da take matukar ganin ta da daraja da sanin ya kamata tana tausayin uwar rikon ta maji fiye da ma mijin da ya hadasu zama tare a gidan. Haka ta shiga gurin na maji tana aiki tana tunanen irin rayuwan wanan zamanin namu da muke cikin sa yanzu. Har girki sai da taiwa maji tare da kamsashe masu ko ina na gidan. Sai yamma Maji ta iso gidan da yaranta suna daukin ganin Bintu wace itama haka da murna suka tari junan su cikin jin dadi tsakanin su. Tun fitan da Bintu tayi part din mummy zuwa,taron su Maji bata kara leko part din mummy din ba har zuwa dare takwas saura sosai. Dan, ta mai bi ma na biyu ta tura wai a kira mata Bintu zata rufe part din ta. Sai ga yaron ya shigo duk muka juya gurin shi inda ya nufo gurin da Bintu take zaune direct yana cewa, Mummy tace nace ki zo zamu rufe kofan part din mu dare yayi wai. Kafin Bintu tai magana Amira ta,watso ma yaron wani fitinaneniyar harara yaron ya,noke yana cewa mummy ce tace nazo na kirata ya juya yabar dakin zuwa,part din su. Muryan Maji sukaji tana cewa,a,a Fatima tashi kije ku kwanta ko har kin gudo ne zaki mata halin yan duniya yau yau da dawowan mu. Tashi ki dan tafi tunda ta aiko maki da sako bai kamata ace baki je ba kinji diyata ta fadi cikin dan kwantar da,muryan ta. Shima yaron ai iyayi tsiyane dashi mai makon ya tsaya tun can yai sallama shine ya fado wa mutane daki haka. Ai shi yaro dan auke ne baida laifi, an aiko shi kuma ya fada ya tafi a binshi yanzu shawara ya rage namu. Maji takara yiwa Bintu magana da ta tashi taje ai yaune kawai gobe ta dawo dakin su. A zuciyar ta take cewa Allah sarki Maji da kin san abinda ke nan da,baki barni na tafi ba ko yau din nan ma. Ita ko mummy tana can dakin ta saikallon kofa take a kai akai tagani ko Bintu zata zo tabar Maji akan tayin da tai mata. Zuwa can sai ga Bintu saye da,dan hijjabin ta tashigo gurin mummy a,bisa Umurnin Maji. Sai dai ita kuma mummy tana ganin ai tayi nasara saye zuciyar Bintu da abin duniya shi yasa ta,dawo gareta. Bintu na fita Amira tace maji da ma kin bar Bintu don naga bada son ranta ta tafi ba wallahi. Allah ko ai ban san bata son zuwa ba da ban tura ta dole ba amma kuma,sai naga in munyi wa Kubura haka bamu kyauta,ba tunda har ta aikomata. ko da,ta shigo falon Mummy tabita da kallo tare da,sauke ajiyan zuciya a fili, har ta karaso tsakiyan falon nasu. Mummy ke cewa k8n wa kanki kiyamallaini yarinya don ba mai son wahala yanzu. Bintu da bata ce uffan ba tashige dakin da take kwana abinta tabar mommy da yaranta suna kallo zaune a falo. Tun shigan ta bata fito ba sai washe gari ta farka kafin kowa ya,fito tai ma mummy duk aiki kamar yadda ta,saba yi a kullun tare da,dafa ma,yan makaranta abinci. Bada,sanin kowa ba ta kwashe yan kayanta zuwa dakin maji tunda farar safiya. Koda Mummy ta tashiga gurin ta ta samay ta zaune sai cewa tayi kinga Bintu nasan kina jin kunyar Maijidda ne ki barni da ita zan san yadda nayi da zancen ta. Fitan mummy daga gidan Bintu ta kwashe sai part din Maji da farko taso ta boye damuwarta amma sai su Amira suka fahinci da damuwa a tare da ita. Da suka tambaye ta sai take cewa babu komai kanta ne kawai ke mata ciwo. Sai zuwa rana kowa na sha,anin gaban shi Kubura ta dan fakaici ifon su ta kwashe komai nata sai dan gidan gwagon ta ta bude ta shiga. Shiga da fitan ta duk akan idon sadauki wanda yake zaune kofan dakin shi sai dai furannin gurin sun boye shi ba za,a iya ganin shi ba. Sai bayan fitan ta ne daga gidan shikuma yamike yabi bayan sai yaga gidan su ta shiga. Nan yakoma ya zauna a inda yake zaune cikin tunanen irin nasihan da yasha gurin kamilin kakan shi dan matashin dattijo mai dan farin gemu a fuskan shi. Kubura ta gyara ko ina tsab tunda dakin kwanan su har tsakar gidan nasu ita kadai a gidan. Sai da Maji taji shiru bata ga fitowan yar amanan ta ba ta ce Maryam ta diba mata ita taga may takeyi. Da sauri Maryam ta,dawo tana fadin Maji Bintu fa bata gidan nan nake gani. Da sauri Maji tace kodai tana bandakine ki koma ki duba min mugani. Aikuwa har bandakin ta duba ta kuma duba gurin kayan ta babu komai nata a gidan. Da sauri ta dawo gurin Maji tana fada mata Maji har kayan Bintu babu a gidan nan fa. Hakali a tashe Maji ta mike zuwa dakin hajiya kubura sai dai a rufe dakin yake shima. Ikon Allah ta dawo dakinta nan ta samu yaran ta duk a cikin damuwa Maji tacewa Amira jeki gidan mai masa ki duba min ita da sauri. Shigowan sadauki yayi daidai da jan hijjab din Amira ganin yanayin su yasa shi kalkon su cikin mamaki yana tambayan su may ya faru ne wai. Bintu ce bami gani ba shine zan tafi na duba gidan su. Ke zauna naga fitan ts tana cikin gidan su don nan naga tashiga dazun da rana. A jiyan zuciya Maji ta sauke tare da cewa akwai matsala ke nan tunda yarinyar nan tai muna haka. Haba Maji wai may yasa kika damu da zancen wanan yarinyar ne haka bayan ita bata damu da ku haka ba. Kai ban son rashin mutunci Fatima a dan zaman da tayi damu ni nasan irin karuwar da nasamu da zaman ta nan din. To may akai mata da zata gudu bata fadawa mutane ba har zata kwashe tabar gida. Nifa na ganta ban yarda da ita ba yasa na tashi na bi bayan ta amma sai naga ta shiga gidan su. Yanzun haka ma da zan dawo naga gidan a bude da alaman tana ciki har yanzu. Amira maza jeki ki jiyo min ko may ke faruwa da ita har ta guje muna hakan nan. Amira da maryam suka fita zuwa gidan hajiyan masa lokacin Bintu ta idar da sallah tana zaune ita kadai ta hada kai da kujeran dakin gwagon ta inda tafi zama akoda yaushe indan tana gidan. Da sallama suka tura kofan shiga gidan inda tun a tsakar gida suka hango ta a zaune. Bintu na ganin su gaban ta ya fadi don in akwai abinda ta tsana shine ta koma gidan su mai tarin rikici a cikin sa. Maryam tun bata karaso ba take fadin haba Bintu may akai maki zaki tafo gida batare da sanin kowa ba kin tayar wa Maji da hankali yau sosai wallahi. In ba don yaya sadauki ba da ya shigo yana fadin yaga lokacin da kika dawo nan gidan. Amira tace Bintu nasan akwai abinda ya faru ki fada muna ba boyewa zakiyi ba a ranki. Don in har baki fadi ba ba,a san may yasamay ki ba balle asan ta inda za,a bullowa maganan. Maimakon Bintu tayi magana sai kawai ga hawaye sun fara zubo mata shar nan ta fashe masu da kuka mai tsuma zuciya. Duk yadda suka so tai magana Bintu taki fada masu komay ye matsalarta da har ta guje su haka a lokaci guda. Haka suka koma gida da sanyin gwiwa suna fada wa uwar su yadda suka yi da ita a can. Hakalin Maji yai matukar tashi si dai kuma gashi babu halin ta fita zuwa gidan don maigidan yana kasuwa a lokacin. Gashi kuma itace zatai girkin gidan ranan nan abu ya taru ya rikice mata akai. Itako mummy tana can hankalinta a kwance, don tasan yanzu bata da matsala don Bintu zatai mata komai kafin ta dawo gidan. Sai yamma lis ta shigo tare da yaranta da takai suka sayo abubuwa a wani shago. Ganin kofan ta a rufe yasa ta tunanen ko Bintu ta shiga gurin hajiya Maijidda ce sai take fadi a ranta dole nasan yadda na hana wanan yarinyar shiga gurin matar nan. Sai dai tana shiga taga ko ina tsab an gyara amma babu alamar an dafa abinci a part din. Don haka tafito da kanta har kofan dakin Maji tana fadin hajiya ina ya ta tashiga ban samay ta,ba a daki dana,dawo. Tun lokacin Maji tadan fara tunanen duk yadda akayi akwai wata magana a kasa. Maji tace hajiya ina yarda da fahinta yasa nabar wanan yarinya a gurin ki da zanyi tafiya. Eh haka ne amma kuma ai haka ba yana nufin yarinyar bata da yancin kanta da zata zabi inda take ra,ayin zama bane ko? Oho yanzun nagane inda matsala take ke nan ashe akwai abinda ke faruwa a gidan nan bayan tafiya na ban sani ba. Babu komai sai alheri inji hjy kubura tace kawai dai mun shirya da yarinyar zata dinga min aiki ina biyan su, aikin san babu boyo a tsakani na dake. Hmm tau Bintu dai bata gidan nan yanzun haka don ta kwashe kayan ta tabar gida ta koma gidan su. Kai amma ban zaci haka,ba daga gareki hajita maijidda. Ban taba zaton zaki yi min bakin ciki ba irin haka yanzun don kada yarinyar ta taimaka min kika kore ta a gidan nan. Hmm ke ma kin san hakan ba halina,bane ra,ayin kantane takwashe batare da,sanin kowa ba tabar gidan nan don kanta. Ikon Allah inji Mummy kamar zatai magana sai kuma ta juya a fusace tabar gurin zuwa part din ta ranta a bace wai Maji tai mata hassada. Kai duniya kan yanzun ba gaskiya babu tsoron Allah a cikin ta,wai ita da za,aiwa zargin rashin gaskiya amma itace ke ganin hakan akaimata. Maji nashiga daki Maryam tace amma kuwa Bintu munafuka ce yanzun saboda kwadayin duniya har ta uya yiwa mutane haka. Amira tace aini tabani mamaki wallahi.yanzun ita tana ganin taiwa mutane wayo ke nan ko. Aitazo indai Mummy ce dan abu kadan zatai mata sai duniya taji su . Matar da bata da,yarda ko kadan inba diyan taba ita batasan kowa ba aduniya shine kwadai zaikaita gurin ta. Maryam tace bataga daki yana kyalli ba kamar aljannan duniya dole ta gudu nan inda ba komai ai. Kai ya isa haka dan Allah kubari muga yatinyar muji may ke na kafi ku yanke hukunci ku fara zaginta. Da zata zauna da ita aida tun tuni tayarda da zugin da tai mata, ina jiya kince da kuka taje kwana dakin dana tura ta. Koma may nene duk nice najawa Bintu din haka don ni nakaita da hannu na cikin rashin sani. Maji dama aikin san mummy ba mutunci ne da ita ba don ita kanta kawai ta sani amma wanan rashin gaskiyan haka ai ya zama cin fuska. Da yamma da maigidan yadawo maji takai masa abinci lokacin ya tafi sallah sai tadawo dakin har in ya huta ta samay shi akan ya bari ta shiga gurin Bintu taji may ke faruwa. Amma tana zuwa gurin maigidan saita samu hajiya kubura tana mayar mai da magana akan karya da gaskiya. Wai taimata bakin ciki akan yarinyar shine har ta koreta bayan tafita daga gidan. Shigowan Maji ya sashi cewa madalla ga Maijiddan ai ta shigo ma dama yanzun nake nufin kiran ki. May ke faruwa ne akan yarinyar nan ta gurinki don hjy kubura ta samay ni da wani magana sai dai ban fahinta,ba. Murmushi maji tayi tace nima dai ban fahinci maganan ba sai takai zaune yayin da mummy tacika ta batse da Maji din. Nan ya kara tambayan ta ta fara fada mai tun farkon barin yarinyar da tayi a gurin mummy da kuma yadda jiya akayi kafin ta tafi gurin ta ta kwanta kamar yadda mummy ta bukata. Maji tace ni a zatona ko don a jiyadin muka dawo yasata cewa tazo ta kwanta. Sai yau tun safe yarinyar ke daki tana kuka dana tambaye ta take cewa wai kanta ke ciwo. Wallahi Alhaji dafa haka ban sani ba bayan nabata magani ashe ta faki idon mu ta kwashe duk kayan ta a gidan nan ta sulale ta fita ba wanda ya sani. Saidana tura yaran ban,suka ce tana gidan su dakin gwagon ta ita kadai a gidan. Subbahanallahi yanzun dai ina yarinyar take tana gidan su ita kadai a gidan. Yanzun nake batun na rokeka naje naji ko may ke faruwa da ita tai muna haka amma kuma sai dazun ga hajita kubura tazo tana wani maganan da ban san dashi ba mani. Yanzun dai ba,wanan ba ahin kun san hatsari ne abar yarinya karama kamar wanan ita kadai cikin gida babu kowa a wanan zamanin da muke ciki. Hakan yasa fa uwarta takawota gurinki don ki rike mata ita har lokacin da zata dawo. Don da kanta mai masa sai da taimin magana akan zaman yarinyar gidana shine ma dalilin da yasa na barta kowan ku bai sani ba. Amma kubura kin bani mamaki wallahi yardane fa yasa maijidda ta barta a gurinki. Yau ina wayon ki da iliminki ya tafi ina suka shiga da zaki turawa yar mutane wanan akidar na bijerewa. Alhaji nifa ba,a kyauta zan dauketa ba kudi zan bata ita da iyayyen ta don ina bukatan taimako. Wani irin tsuki yaja ya dauki wayan shi nomban Amira ya kira tare da babban dan,shi yace su zo yanzun falon shi. Ba,a dade ba sai gasu yake cewa ya raka Amira tazo da Bintu yanzun nan suce inji shi. Bintu har ta rufe gida da daki ammajin da tayi anata bugawa tare da kiran sunan ta yasa ta bude kofan tafito. Duk ta fyde ta ramay lokaci guda da ita ta canza don fitinan daya samay ta. A tsiwance Amira tace da yaya Imirana muke Baba ne yace muzo dake yanzun nan. Daga haka Amira bata sake cewa komai ba ta tsaya jiran ta ta shirya su tafi. Jin Alhaji da kanshi ke nemanta yasata dauko hijjab dinta zuwa amsa kiran inda tabiyo bayan su simi simi har falon Alhajin. Shikan Imirana bai san komaiba ya na cewa gata nan yajuya abinshi ya fita falon shida Amirah. Guri ta samu ta zauna a makure duk ta kode lokaci guda da ita fuskan ta duk ya wani kode mata. Gaba dayan su kallonta sukeyi take taba Alhaji tausayi yace Fatima may ke faruwa ne. Sai tai shiru ta dukar da kanta kasa tare da sako wasu hawaye masu dumi daga idon ta. Ganin bazatai magana ba tasa Alhaji cewa may kike a gidan ku ke kadai baki tsoron dare wasu miyagu bata gari su shigo maki ke kadai a gida karamar yarinya dake. Nan ma Bintu sautin kukanta takara batare da tai magana ba sai tsoron da ya kamata a cikin ran ta lokaci guda don ita batai ko tunanen hakan ba. Yace kin fadawa maijjida abinda ya faru tsakanin ki da hajiya kubura ne. Da sauri ta dago kai tare da cewa cikin kuka ban fadawa kowa ba Baba. Baki kyauta ba Fatima don kinga amana kike a gurinta agurin mu ma baki daya idan wani abu ya samay ki damu uwarki zatai kuka. Baba kuyi hakkuri amma ni na guji hafin hasumi ne akaina shiyasa na kona gida. Baki kyauta backe nan baki rike maijida a matsayin uwaba gareki tunda har zaki iya boye mata maganan ki. Da sauri tadago kai ta dan kalli maji tace ba hakana bane Baba ban son wani abu ya faru ne a tsakanin su don naga akwai yarda a tsakanin su. Inda mummy take zaune ya dan kalla yace kinga karamar yarinya ma tafiki tunane wai mai ya samay kine kubura da zaki wanan danyen hukunci wa kanki haka. Maganan nan ba abin kunya ne gare ku abokan zaman ku suji shi an yarda dake abaki amanan yarinya sai kuma ki mata wanan danyen aikin haka. Kituna fa kema kin haihu idan wani yaiwa yaranki haka zaki ji dadi bafa rashi gatane yasa kika ganta nan ba lalurace takawo ta gurin mu. To amma Alhaji aini naga ,,,,, dakata don Allah wallahi baki kyauta ba kuma kin bani kunya yau ace kece kikawai maijida haka a gidan nan. Ke tashi ki koma dakin ku kuma na kashe wanan zancen a gurin nan kada naji shi wani guri don ranku zai baci. Daga yau ke maijjida nabar maki rikon yarinyar nan a hannunki koda uwarta tadawo zanyi magana da ita kada na kara jin zancen nan ko nan gaba. Bintu ta mike jiki ba karfi tana fadin nagode baba cikin kuka tana fita taji yana cewa ke kuma kubura wallahi duk naji kin wa yarinyar nan wani muvun kallo gidan nan sai na saba maki ta yadda baki zata ba. Bintu tana shiga dakin da dan muryan sallama duk su Amira suka kalleta a wulakance bata gane masu ba. Bata jima da shiga ba saiga maji tashigo tana cewa Amira hado mata tea mai zafi tasha tasha magani. Nan taje mayar masu da yadda maganan yake sai ko suka shiga zagin hajiya kubura sai da ta tsawata masu. Ta juta kan Bintu tanacewa Fatima ashe baki dauke ni uwa ba da gar zaki iya biye min magana irin haka tunda badawo. Cikin kuka tace mama ban so kuyi fitina ne shiyasa naga gara kawai nabar gidan gaba daya. Nan maji tai mata fada sosai tare da kara bata shawara akan mutanen gidan gaba dayan su. Bintu a ranta tace nafiki sani komai yanzu ai mama nan dai su Amira ma sukai mata magana sosai akan zaman duniya. Duk yadda suka yi da mummy ta kwashe ta fada masu komai suka shiga tsinarta da kwashe mata,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,, A LOKACIN MUKE,,,,,, Nocking din kofan take a hankali yayin da take jin sautin kida ya na tashi daga dakin, sai dai ba a da niyan bude dakin a lokacin. Kara sautin nocking din da takeyi tayi sai ji tayi ana cewa wai waye please ke damuna haka. Mai dakin tana bude daki sai suka fara kallon kallo a tsakanin su don ba wanda yasan wani a cikin su. Kina neman wani please ? Har lokacin tana tsaye ta tare kofan dakin nata ta inda mutum zai iya shiga dakin. A,a gurin ki dai nazo. Ni kuma ta fadi cikin dan mamaki a fuskan ta tare da dan sake fuska tana dan kada idanuwan ta cikin mamaki. Eh duk da dai nasan baki sanni ba amma dai gurin ki din ne nazo ai. Ok tau shigo daga ciki mana ko ? A tare suka shiga dakin a lokaci guda suna nuna a jere da junan su. Kujeran dake dakin ta nunawa Raiha ta zauna inda Raihan ta gane nufinta ta ta zauna kamar yadda ta bukace ta da yi. Juyawa tayi zuwa ciki sai gata dauke da kwalin juice da cup a hannunta inda Raiha take zaune tazo ta aje drinks din tana cewa bisimillah. Raiha ko sai bin dakin take da kallo wanda dakin yai mata kama da ta mai zaman kanta ko kuma wace tazo karatu a garin. Idon ta ya kai akan kwalaben syrup din maye dake saman wani dan table can gefe guda. Kisha mana bisimillah ko sai takai idon ta akan kwalaben da Raiha take kallo, tace, Ko kema dai yar hannu ce na miko maki ki surka dasu ne? A,a barshi kawai ni sai dare nake sha idan zan kwanta yafi min caji don ina gudun mutane su gane ina wanan harkan. Dariya Nura tayi har fararen hakoranta suka haska daga bakin ta tana cewa. Kai har kin bani dariya wallahi ashe da sauran ki ke har yanzu dasha da rana da dare ai ni duk daya na dauke su a gurina. Haka dai kika ce amma akwai banbanci gaskiya baki dai ganewa ne kowa da nashi irin ra,ayin nake gani. Kurba biyu Raiha taiwa juice din sai ta aje cup din tana kallon Nura cikin murmushi. Nura tace ni kin barni a duhu ban fa gane kiba gaskiya har yanzu gashi kuma kince guri na kika zo. Raiha tace eh gaskiya baki sanni ba nima haka Sunana dai Raiha amma mutane suna kirana da Raihanatu musanman ma iyayyena. Ok ni Nura nake karatu ne yakawo ni wanan garin ina karatu a dan fodio university ne. A ran Raiha tace shikan karatu kikazo kika buge da harka ke nan a garin da ba,a sanki ba. Raiha tace cikin murmushi ko kin san Nasir Habbib mai aiki a sokoto cement ? Nura tace a ranta au budurwan Nasir ke nan ta biyoni don nai mata snatching din shi a gurin ta ko? Aiko yarinya kinzo gida wallahi don zan maki wankin babban bargo yanzun nan kuwa. Amma sai ta kyale a fili tana cewa nasan shi kuwa kwarai da gaske anjima kadan ma zaki ga yazo nan ai idan ya taso daga gurin aiki. Raiha tace good zan iya kiranki da Anty Nura don ko ba,a fada ba nasan kin girmay ni. Dafatan zaki saurari maganan da nazo maki da ita da kunnen basira batare da kin fassara min zance na ba da wani abu. Ok ke nake saurare ina jinki ai. Da farko dai kamar yadda na fada maki sunana Raiha kuma ni haifafan wNan gari ne muna zama a uguwar arkilla ne nida iyayyena. Sai kuma tai shiru tare da dan kallon saman silin din dakin zuwa dan wani lokaci, Nura tace ke nake saurare fa kada mu bata lokaci. Ba zancen bata lokaci ai don magana ce mai muhinmanci da zata amfane ki nazo dashi. Tace ok ai ina sauraren ki ko? Raiha tace kafin Nasir ya nemay ki ni Raiha ya fara nema amma sai Allah ya tsallakar dani daga mugun nufin shi a kaina. Kamar ya mugun nufi kuma Nura ta tambaya a cikin mamaki da son karin bayani ga Raiha din Raiha tace niyar shi na shigewa yan mata ya sace zuciyar su da so da kauna kamar yadda yake maki a yanzun haka. Amma fa daga baya zaki zo ki sha mamaki don ba nufin shi ke nan ba a kanki. Nura tace a gatsale Allah ko ? Hmmm Raiha ta dauki cup din drinks din da ta aje takara kaiwa a bakin ta tadan kurba kadan sai ta juya gurin Nura tace. Wallahi wallahi ifan bakiyi hankali ba a karshe zaiyi safaran ki ne zuwa kasa shen turawa ya tura ki karuwanci a can ya kuma karbe passport dinki duk gudin da zaki samu sai dai dila ya turo mashi ta account din shi. "Ke Kada ki maisheni karamar yarinya mana kedai kinzo da tsigar nabar maki Nasir don ki yaudareni da wanan magana naji tsoro nace ban son ki sai ya koma maki ko ? Allah sarki babu ko daya wallahi don idan da na yarda da yanzu nima nazama tarihi a gurin iyayyena da yan uwana a nemay ni a gari a rasa inda na shiga. Amma sai Allah ya kare ni da yake banda rabon wahala nasamu wani abokin shi ya tausaya min ya fada min ainihin gaskiyan abinda ke nan. Raiha ta mike tana cewa ni zan tafi tunda naga kamar baki yarda dani ba yanzu amma nasan watarana zaki tuna da wanan dan zaman da mukayi dake. Ni zan tafi kuma ban tsoron ki fada mashi cewa nazo gurinki don yanzu a shirye nake da na tona mashi asiri a harkan da yakeyi . Ta juya tare da daukan jakarta dake saman kujera tana cewa idan kin shirya saurarena sai ki nemay ni. Har Raiha takai kofa zata murda kofan Nura tace kinga dawo ki zauna ai bamu gama magana ba tukun ko? Baki da niyar saurare na shiyasa kina ganin kamar kishin Nasir na tare dake yasani zuwa gurin ki ko? Ba haka na bane amma akwai wasu yan tambayoyi da zan maki ina bukatan amsa daga gareki in naji su daidai kinyi gaskiya. Raiha ta dawo ta zauna tana kallon Nura ido da ido tace ina sauraren ki ko? Hmm wai ma ta ina zan fara tambayan ki ne duk kin sani a caji wallahi. Duk ta inda kika fara in na sani zan baki amsa insha Allahu. Ok tau dan Allah kunkai kamar tsawon wani lokaci dashi Nasir din a tare dashi. Ummm gaskiya mun kai kamar wata takwas muna tare inda a sannu ya fara koya min wasu abubuwa na rayuwa. Kallon ta Nura tayi da kyau tace hmmm lalai ma amma ce min yayi tunda matar shi suka rabu bai kara neman wata ba bayan ni. A,a karya yai maki don kafin ni akwai wasu da har yai galaba a kan su yanzun haka suna waje on behalf of him suna karuwanci a Spain. Kai wai da gaske kike da zancen ki ni yar uwa wallahi ba karya a magana ta sai tsabar gaskiya kawai. Ok ya taba zuwa dake tafiya ne ke dashi kubar garin nan zuwa wani waje? Tace kwarai mun je lagos da sunan yatafi aiki ashe yakaini ne gurin yan commuty din su sugan ni idan zan yi sai ya dawo ya shirya tafiya na. Mikewa tsaye Nura tayi tana fadin ikón Allah na ko yarda da zancen ki don duk inda muka tafi sai naji ana cewa she is ok, Very pretty you will get a high level on dis pretty, Sai da nai mashi magana ya daina kaini ana fada min hakana don ban son jin wanan kallaman daga bakin arna. Murmushi Raiha tayi tace a can bai nuna maki true color din shi ba ne ko ? Kamar yaya Nura ta tambaya. Murmushin takaici Raiha tayi tare da fara fada mata duk yadda yayi da ita a garin Iko din. Mikewa Nura takarayi tsaye tace umm ummm na yarda da zancen ki gaskiya don nima ya jawo wani abokin shi akan na tarda mu kwana tare dasu su biyu amma bai san ina jin lokacin da suke maganan haka ba sai na bijire mashi tun kafin dare nace period yazo min. Mikewa Raiha tayi tace nasan koke can akayi shiyasa nasa a saka min ido a kan shi nai alkawarin duk yarinyar da yai niyar batawa sai na kwatota daga halaka hannun mugu azzalumi mayaudarin banza macuci kawai. Nan suka zauna sukai ta hira akan yadda zasu dau mataki a kan shi don kada yaci gaba da abinda yakeyi. Tun wanan ranan suka kulla kawance da junan su inda ta rako Raiha tana mata godiya. ****** ********* ****** Tun daga kofa yake kwala wa mariya kira har zuwa cikin gidan, maria wace ke duke tana wanke wanke taji kiran a bazata yai mata yawa. Ta mike tana fadin gani nan babban Abba lafiya dai ko kira haka daga waje babu kakautawa. Yace cikin hasala yanzu naga malam a kasuwan mu yake ce min wai yaran nan yanzu basu zuwa makaran ta ko yaushe. Shi Abba ma sai ya makara kullun kafin yaxo in ma har yaje din yace yai magana yan uwan shi suka ce wai talla yake zuwa. Tace tallafa tallan may wani kallo yai mata na ban yarda dake ba fa. Tace ba gaskiya bane in zai yi talla ai ban dora mashi ban fada maka ba balle ma nasan ba yarda zakayi ba. Shi dai kila yara sunyi mai yawa yanzu bai gane zuwan su da rashin zuwan su shiyasa ya fadi hakan. Yanzu ina suke ya tambaye ta tare da tsureta da idanuwan shi tace sun tafi tin da karfe hudu suna can. Yace ai zan tafi nagani ko suna makarantan ya mika mata ledan ce fanen da yayo ya dauki buta zuwa ban daki. Nan ta samu tafa leken zaure ko Aliyu yana tafe saiko gashi ya sayar rataye da roban shi na talla a wuyan shi. Da sauri ta tare shi ta karbi roba da kudi tai mashi magana kuskus a kune yaron ya juya da sauri yabar gidan. Kafin maigidan ya fito ta boye roban da kudin da sauri a dakin kayan su ta kama aikin ta. Yafito daga ban daki yana fadin yanzu zan tafi nagani idan suna can ko kuma wasa suke tsayawa yi a hannya. Yafita tana ce mai a dawo lafiya bai amsa mata ba don a cike yake ran shi ya baci sosai. Don shi bai wasa da hakkin iyalin shi a kan shi don haka yake matukar saka ido akan al,amarin yaran shi dama ita kan ta matar tashi. Tun daga nesa ya hango su a zaune gaba dayan su don haka sai bai karasa kusa ba ya juya zuwa kasuwa ko zai dan kara samun wani abin tabawa a can. Kafin ya dawo yaran sun rigashi dawowa gida Aliyu da yuwan taci ta ishe shi abinci yafara nema yaci sannan yai wanka zakace bai tafi ko ina ba . Taja ma yaran kunne akan duk wanda yace Aliyu yana fita talla sai ta yankewa yaro kauna a gidan. Bayan maigidan ya dawo ne yake tambayan yaran inda suke tsayawa basu zuwa makaranta da wuri yanzu. Sai cewa sukayi suna zuwa andai canza masu ajine malam baiganin su yanzu. Haka yasa yaja bakin shi yai shiru ya yarda da maganan su tunda ya gansu dazun a makaranta sabanin yadda malamin ya fada mai. Haka Aliyu yaci gaba da zuwa tallan ruwan shi batare da mahaifin su ya fahinci komai ba tunda shi ba mai zaman gida bane ko yaushe. Haka yaron ke kawo mata dan kudi itako tana bunkasa bankin ta dashi kullun tana farin ciki. ****** ********* ****** Tun ranan da akai wanan rikicin a gidan hankalin Bintu a tashe yake da mutanen gidan baki dayan su. Ance babban gida babban magana ashe har da ita da take ganin ta kama kanta da kowa a gidan bata tsira ba ga matan gidan. Don har da zaman ta gurin Maji ya tsone masu ido sai yanzu tagane nufin maji na bata magani tare da sauran diyan ta a baya. Gashi yau Alhaji da kan shi yake fadin korafin da sauran matan shi sukayi a gidan kan zaman ta da Maji. Wanda ba komai suke wa kishi ba sai basu kaunan suga ta karu da komai kankantan abu a gidan, Wanan dalilin gitinan yasa damuwa ya dan fara yiwa Bintu yawa arai sai kafa kafa take da komai a gidan. Tun da har mai gidan yai mata warning din shiga harkokin mutananen gidan shi da kan, shi. Sai lokacin take mai jin zafin gwagonta hajiyan masa da tazo gidan mutane ta yar da ita kamar wata wacce bata da uba ko gata. Da uwarta da uban da ransu a duniya amma yau ta zama,marainiyar karfi da yaji a duniya. Ba don Maji mace ce mai halin alheri ba da bata san iya inda al,amarinta zai tsaya,ba a,rayuwa. Amma gashi Allah ya hada ta da mace tagari wace tasan ciwon kanta tasan zafin ta a rayuwa. Ta rike ta amana tankar itace ta haife ta ko kuma ince wata yar uwarta ta jini can daban. Yanzu Bintu ko falon maji bata son zama da yawa ko yause tana cikin dakin su a kumshe. Idan kuma aiki tafito yi zata yishi gudu gudu ta gaba ta kara komawa tashige daki wai ita tana taka tsatsan da kanta. A haka zancen tafiyan sadauki zuwa kwallon farko da zai fara fita ya buga yazo masu. Maji bata zauna ba sai faman karban taimako take akan dan nata akan shaye shaye da kuma na tsarin jikin shi. A cikin hakane maji tace wa yaranta su shirya sukaiwa kakan in su ziyara kafin yatafi don kada sai yatafi su samu labari baza suji dadi ba. Sadauki bai so wanan tafiyan ba amma ba yadda zaiyi ya zama dole yabi umurnin iyayen shi. Sai faman shiri suke amma Maji bataji duriyar Bintu ba don ko falo bata fito ba don ba,a shiga makaranta ranan. Da kanta tashiga dakin na yaran tun zuwan Bintu gidan ko yaushe zaka samu dakin tsab dashi ba wani datti a cikin shi kaman baya can da dakin yake motsutsu kowa na kyashin gyarawa . Kwance ta samay ta ta kifa kanta a saman filon da ta ke akai. A hankali maji takira sunan ta,da Fatima abinda ya dan sata firgita ke nan don bata san da shigowan Maji dakin ba a lokacin. Cikin dan firgita ta amsa da na,am mama tare da saurin kokarin mikewa zaune daga kwanciyan da take. Zama maji tayi daga gefen ta tare da dan kura mata ido tana cewa waiko lafiyan ki kalau kuwa Fatima? May ke damuwanki ne duk kwanakin nan kin koma,shiru kina kuma nisanta kanki da kowan mu? Dan murmushi Bintu ta kirkiro a fuskanta tana cewa ba komai mama kaina ne ke dan ciwo shine nadan kwanta. Tun yaushe kanki ke maki ciwo baki fada min ba fatima baki sha magani ba yaya zaki ji sauki. Shiru Bintu tayi tana fadin dama gashi zamuyi tafiya zuwa garin mu gobe tunda safe gashi kuma baki da lafiya. Don haka dole na barki nan har mu dawo don ba,a daukan ciwo akai kauye. Da sauri Bintu ta daga kai ta kalli Maji, sai kuma ta dukar da kanta don bata iya jure kallonta ido da ido haka. Maji da ta fahinci may Bintu take nufi sai tace kada ki damu ba,a nan zanbarki ba gurin hajiya kubura zan barki don kwana biyu zamuyi mu dawo insha Allahu.ko kuma guda yadda dai tafiyan namu ya kasance don wanan mai tafiyan. Bintu ta kara kallon Maji alaman ranta baizo hakan ba take cewa mama da abarni ko anan din zan iya zama ai. A,a haba Fatima yaya zanbarki karaman yarinya dake a daki ke kadai kuma gashi ko lafiya,bai isheki ba ma. Kada ki dmu nasan zata rike ki da kyau har mu dawo daga tafiyan, kamar Bintu tace taji sauki zata tafi amma kuma sai take cewa tau mama. Maji tamike tana cewa don haka saiki shirya kayanki wanda zaki dauka tun yau ki koma can. Bintu tanaji tana gani Maji da kanta ta dauki dan jakar kayan ta zuwa dakin hajiya kubura. Nan suka dan zauna suka taba hira a tsakanin inda tai mata sallama dacewa gobe asubanci zasuyi zuwa tafiyan su. Hakan akayi don koda gari ya waye har sun tafi ko don can ne kauyen Niger state iyayyen ta suka koma da zama don noma. Bintu bata farka,ba don maganin da tasha mai sa barci sai zuwa takwas na safe lokacin har hajiya kubura ta shirya zuwa gurin aiki tana cikin uniform din ta. Dakin da Bintu take ta leka tasamay ta zaune tana lazumi ta idar da sallah a lokacin. Kin tashi Binta ya jikin naki Bintu ta amsa a sanyaye da Alhamdullahi ga breakfast din ki a falo idan kinyi wanka sai kici ni zan fita sai na,dawo. Sai kindawo mummy ta bata amsa tare da kokarin mikewa da ga saman abin sallah da take zaune akai. Zuwa rana kadan ta dan samu sauki nan ta mike tafara gyaran part din sai da taima ko ina tsab a part din sai bedroom din mummy ne kawai da ke a kulle bata gyara ba. Tana gamawa tashiga tai wanka bayan tafito ne ta dan zauna sai kuma tai tunanen kada su dawo da yaran ta basu samu abinci ba. Kitchen din ta shiga inda ta samay shi sabanin na Maji don wanan komai na zamani ne a cikin sa. Ga kayan abinci na kala kala babu abinda babu cikin sa komai gashi kamar ba saye akeyi ba. Ta yanke shawaran tai masu tuwo don taga kullun yaran ta na zuwo rokon tuwo a gurin maji don ita bata da time din tukawa ko yaushe busy take. Nan ba bata lokaci ta girka tiemwon shinkafa da miyan agushi da manja tai amfani da naman da tagani a fridge din. Gashi ranan girkintane ta kwashe a wani kula da bai saurin sanyi takara hada masu pepper surp din kayan cikin rago da drinks din hannu na kayan fruit din data gani a kitchen din. Takara gyara gurin ya koma tsab takoma daki ta kwanta sai yamma mummy tadawo da yaran ta inda tun a,wajen part din ta soma ganin canjin yanayin shiyan nata. Tana shiga dakin gaba daya taga duk ya canza mata sai ta tuna da lokacin da take amarya a gidan komai nata tsab yake a lokacin. Ba irin yanzu ba da,bata da lokacin tsayawa gyara komai kamar yadda ya dace mace tana gida tayi. Yaran suna shiga daki suka fara ihun da murnan ganin yadda komai nasu ya canza a lokaci guda. Dan karamin sune yafara maganan abinci Bintu dake fitowa daga dakin da take ciki take cewa Anwar zo ga abinci can kazo kaci taja hannin yaron inda ta tsaya daga kofa tanawa mummy sannu da dawowa. Mummy tace Bintu ke da baki da lafiya kika sha wanan aiki haka sannu da fama nagode. Tana fitowa taga Anwar a hannun ta take cewa kaikuma may yafaru Bintu tace wai abinci zaici. Uwar tace kaida andawo kace zakaci abinci har yaushe muka dawo na girka maku abinci. Bintu tace a sanyaye mummy ai na yi girki tun dazun ma nagama bari na debo mai. Da mamaki uwar tace kinyi girki Bintu bayan wanan uban aikin da kikasha haka. Murmushi Bintu tayi ta juya rike da hannun yaron ta debo mashi abinci ta zauna tafara bashi. Saiga Mummy tafito daga daki idon ta ya sauka akan plate din da yaron ke cin abinci take taga mai Bintu ta girka masu. Wani irin dafi ne ya kumay ta tace kai amma wanan yarinyar Allah yai maki albarka. Nan tashiga kitchen ta samu komai tsab kamar ko ina mamakine ya kama yadda karamar yarinya kamar Bintu tai irin aiki haka mai yawa ita kadai. Gashi kuma,ba lafiya ne take dashi ba ajikin ta take taji kwadayin zama da yarinyar ya kamata don irin haka take son yaron ta dashi. Ba,wani abinda aka taba mata ko aka lalata hatta sharan da tayi bata zubar ba ta tara a wani roba har mummy din tazo tagani idan babu abinda take so daga ciki dai a zubar dashi. Haka mummy ta dinga jin dadin zama da Bintu kamar kada uwar rikon ta tadawo take ji. Suko matan gidan ai nan gulma ya fara tashi akan zaman Bintu gurin Hajiya kubura na kwana biyu kafin maji ta dawo don ance babban gida ba,a raina dan magana kadan,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,, A LOKACIN MU KE,,,, Washe gari da safe sadauki yana dakin Maji saman dogon kujera ya dan nade hannayen shi a saman kirjin shi idanuwan shi duk suna a lumshe, zakace barcin safe yau yake a falon mahaifiyar tashi. Duk zirga, zirgan da sisters din shi keyi yana jin su sai dai idanuwan shi a,rufe suke still zakace barci yakeyi. Maji ta,shigo dakin daga part din maigidan take, tana ganin Sadauki a falo tun da farar safiya haka sai taja tai turus tana kallon shi cikin mamaki. Ba tare da ya sauke hannun shi dake saman fuskan shi ba, ya ke cewa Maji barka da asuba, jin haka,ya,sata sauke ajiyan zuciya takarasa gare shi cikin yanayin mamaki. Yau kuma a,nan kazo ka,kwanta muna da,safe haka ko har yanzun kana kewar namu ne. Murmushi kawai yayi wanda har yakai ga sauke hannun shi da ya kare fuskan shi dashi da,farko. Maji bana son Baba ya fita bamu gaisa da,shi ba shiyasa na zo nan nake jiran ya,shirya sai na shiga gurin shi mu gaisa. Maji ta,karaso cikin dakin tana fadin a to tin dai jiya naji ya fara tambayan ka idan ka wuce yanzu za,a jiku dashi, Yace cikin kara kwantar da kan shi bama za,a jimu ba insha Allahu maji, Maryam ce ta katse su da fadin Maji tun dazun nake jira kizo sauran madaran da ya,rage shine Bintu ta dauka wai tana hadawa yaya tea dashi . Kai maryam baki da hakkuri wallahi jiyane fa kayan tean namu ya kare shine har kin fara raki haka. Sai a lokacin ya daga idanuwan shi da,sukai ja yake cewa No ni kubar shi bazan sha tea ba,sauran tuwo nake son ci ni. Yana kokarin tura hannun shi cikin aljihun wandon shi ya ciro kudi masu yawa yace wa marya karbi jeki sayo maku kayan tea ku karya kafin na,fita. Tana mika hannu zata karba ne, Maji ke fadi kai haba Sadauki na fada maka ka daina wanan kashin kudin haka. A hankali ya mike zaune da kyau yana fadin no maji ai wanan ba komai bane ki barta kawai ta sayo masu abinda zasu karya su fita. Anjima idan na fita zan sayo masu abinda ya dace a saya din yanzun dai tafi ki samo wanda zaku karya dashi Cikin mamaki yarinyar take cewa ai nan har dubu uku naga ka miko min yace baza su isheku bane ko yaya. Gaba daya suka mayar da hankalin su gare shi cikin mamakin yace a kashe dubu uku a lokaci guda kan breakfast kawai. Ke miko min kudin nan nan ki je ki sayo maku komai na dari biyu ki kawo canji wannan bai san ciwon kan shi ba. Ta juya gare shi yayin da take karban kudin hannun maryam tana fadin. Jiya kaje ka yi barnan kudi kunyi yadda ranku ke so yai kuma shine zaka wani ce wai su sayo kayan tea da wanan kudin haka masu yawa. Murmushi ya dan sauke yana cewa No maji ki bata kada ki damu don wanan kawai don Allah basu su sayo abinda suke son saya. Sauran sai su hau Napep da shi zuwa makaranta ya mike yana cewa Baba din yafito falo ne Maji tace yana falo na barshi yana karyawa ne. Shi kadai ne zaune a falin nashi yana karyawa da,sauran tuwon da aka gyara mashi, na,daren jiya, Bawai rashi yasa ahi cin abincin ba a,a ra,ayi dai ne kawai yafi son yaci dumamay da safe wai yafi rike mai cikin shi. Falon na,Baban nasu yana da,dan tsarin shi xon tsari irin na,falon maza masu dan abin hannun su irin na da can baya. Duk da zamani ya,sauya bai sa Baba canza tsarin falon nashi ba a hake yakw zama da abinshi duk da,akwai halin canzawan amma,bai canza ba. Sadauki ya, shigo falin da,sallaman shi ya samu guri ya zauna tare da,gayar da baban nasu cikin ladabi da,biyayya. Baba ya amsa tare da fadada murshin dake fuskan shi na jin dadin hango tarin natsuwa daga dan shi sadauki. Baba,yace cikin yar tsokana haba dan kwallo kai kuma sai kawai ka bace wa mutane daga dawowanka jiya. Ga shi tun jiya ina zaune ina jiran kazo nasha labarin yadda kwallon ta kaya maku a can don bamu da wani labari ko kunyi nasara ga tafiyan naku. Cikin dan murmushi Sadauki yake cewa Baba munyi nasara da yardan Allah mun samu shiga nida abokaina da mukaje, wanda basu samu shiga ba kadan ne kuma ba musulmai bane su. A to Alhamdullahi masha Allahu abu yai kyau gaskiya sosai haka muke son ji dama ai tafiyan nasara. Sadauki ya dan lumshe udon shi don jin yadda mahaifin shi yake farin ciki yau da,samun nasaran shi a fili. Shigowan su mama,Asiya da Umma da suka ga shigan sadauki gurin mahaifin shi shine suka shigo don suji kwam. Haka yasa fuskan Baba ya canza a lokaci guda daga fara,ar da suke shi da dan shi. Don yasan shigowan su a tare haka da biyune suka shigo don basu shiri sai gurin sheri. Ganin shigowan su fuskan mahaifin shi ya canza ya fahinci mahaifinshi bai ji dadin hakan ba, Don haka ba,tare da,sun tattauna komai ba kamar yaddaa sukaso yi ya mike yana fadin Baba ni zan fita adawo lafiya. Har yakai kofa sai Umma take cewa kai baka iya gaisuwa bane ko may ne koko zuwa kwallon kara zama dan iska ya mayar da kaine wai? Haba Maimuna a kulun kalamin ki akan yaron nan babu dadi wallahi yanzu may yai maki kuma kike kokarin yi mai wanan zagin haka. Tau fa ai na manta dan Baba dan masu gida na ke wa fada don Allah ayi hakkuri kada a zageni nima don na,zageshi. Hmmm Alhajin yace cikin murmshi tare da,girgiza kai yace bana son ki,da,wanan halin wallahi yaya ke nan yanzun fa kin san dan kwallo ne ba,a wasa da al,amarin shi kuma Umma ta lailayo wani ashar tace kwallon kaza kazan uba masu kwallo suna abin arziki ai an san inda suke ba masu zuwa tafe ba,a bayan fage. Daga Alhaji har sadauki dake kofa yana daura igiyar takalman shi a kafan shi sai da ya,dan murmusa kadan. Don jin abinda Umma tace mashi, Alhaji yace cikin murmushi a naku irin hasashen kuke ganin bai koyo komai ba, Amma aini Alhamdullahi don naga haske ga wanan tafiyan na sadauki a gidan nan jiyafa tare mukai sallah magariba dashi a massalaci. Mama,Asiya ta cabe da cewa mu dai yadda akaje haka aka dawo muna don haka bamu ga wani abin yiwa mutane rawan kai ba a nan. Mu dai in muga yaro ya kara lalacewa wallahi dole a,dauki mataki a gidan nan don ba,zamu zauna da irin mahaukata ba kullun hankalin mu a,tashe cikin gida. Maji dake bayan su ta shigo kwashe kayan abincin da takawo wa baba tana jun komai a kunnen ta. Har ta dauki kayan tabar dakin batace masu kalla ba sai ma dan magana akan kudi cefanen abinci ranan da zata girkawa Alhaji takeyi. Inda sai a haka take dan samu canji ya rage ta danyi wasu lalurar ta dashi. Anan tabar su suna wa Alhaji magana akan zuwan sadauki kwallo gari ya gari har ghana amma bai tsinano uwar kowa ba a can. A kofa shima ya hadu da hjy kubura dake bayan Maji gurin shiga part din mai gidan nasu. Hjy Kubura tana ganin shi sai ta fadada murmushin a,fuskan ta da dan fara,a takw cewa a,a mayan yan kwallon mu, ke nan ya gajiyan hanya yace Alhamdullahi mummy. Ta shige tana mashi wasa shikuma ya juya zuwa dakin mahaifiyan shi wanda bai dade da shiga ba ita ma tashigo dakin dauke da kaya a hannun ta. Koda Sadauki ya shigo falon mahaifiyan shi zama yayi tare da hade kai da gwiwa cikin damuwa. Bintu ce ta kai hankalinta gare shi ta karaso gare shi tana fadin yaya akawo ma abincin ne yanzu. Akwai kuma koko da kosai mai zafi an dama yanzun nan wa Baba sai a hado ma dashi. No ki barshi kawai ya bada,amsa tace tau ko a debo maka kunun kasha kawai don tasan kamar mahaifin shi yake gurin son koko da kosai da safe. Cikin nuna gajiya da tambayan ta yake bata amsa da fadin ke ban son komai please ki barshi nace ko. Maji dake daga bayan su take cewa haba ina laifin ta, don taga su kafi damuwa dasu shine take maka tayi mana. A hankali ya dago yana kallon inda Maji take yake cewa bana jin ci ne fa shiyasa kawai. Ya sadauki kaifa kace zakaci saura yanzu shine nace Bintu ta gyara maka Amira take fadin haka. Yaya halan anyi ma wani abu a falon Baba ke nan ko maryam ce take mai wanan tambayan. A sanyaye yace ba ai min komai ba maryam kawai dai gajiya ce ke damuna kawai. Yaya kun gaji da yawa kwallo ai ko na,wasa ne akwai gajiya balle irin naku na kuke na kuke sai anci. Yayi murmushi yace ai dama shi kwallo ba hutu bane motsa jikine kawai cikin shi. Bayan fitan yan matan daga gidan kowa ta tafi makaranta, matan gidan kuma sun futa aiki, ko haka yasa maji samun daman kebewa da dan ta don ta kara mashi nasiha akan irin rayuwan da yake dake jawo mata magana da gori. Sosai tai mashi nasiha mai ratsa jiki akan duk wani al,amarin dake gudana a gidan takw ce mashi bata taba sa al,amarin gorin arzikin dasu yaya suke yawan yi min shi ba,agidan nan a raina. Nabar wa Allah al,amarina don shi da ya halicce ni yasan dalilin da ya yi mu a haka. Dara daya idan Allah yaso sai a wayi gari si gan mu yadda ba su zata ba,a,rayuwan su yace hakane maji. Tace amma fa hakan ba,zai samu ba gare mu sadauki sai ka mayar da kan ka abin kwarai a,gurin Allah. Don kai yanzu kamar uba kake agare mu baki dayan, mu ni da yaran nan, sai dai kuma hakan ba,zau samu gare mu ba,sai ka,zama kamili, mai addini, gujewa sherin shedan akoda yaushe. Haka,zai sa mu cin wa manufar mu da muke fatan samu a,gare ka. Don Allah sadauki ka,tausaya min ka,taysayawa rayuwanka,ka mayar da kanka tsarkaken mumuni dan albarka a cikin al,umma idan kai haka,ni wallahi ka gama min komai wallahi. Yana zaune yai shiru yana sauraren hudubar da mahaifiyar tashi take mashi akan sanadiyar irin sake maganan da,ake ta,mata daga kishiyoyin ta,a,tsakar gida har da yaran su ma. Wanan nasihan na maji da tai mashi yasa shi jin wani irin sauki a zuciyar shi kodon kalman Allah yai maka,albarkan dataita nanata mashi ne tare da neman masu shiryuwa na,alherin a rayuwan shi da,daukaka mai albarka. Da,dare ba karamin farin ciki sadauki ya tsinci kan shi a ciki ba don duk wani abin da yake ji cikin zuciyar shi yanzu ya,kau mashi aran shi. Hakane ma ya bashi dama,daga kwance yake kasafin irin abinda yake son yaiwa mahaifan shi don su fara,alfahari dashi a,rayuwan su. Su dai mahaifan shi murnan su kawai suke da,farin ciki akan dan su yaje lafiya ya kuma,dawo masu lafiya yadda suke fata. Fatan kawai dama Allah yasa wanan wasan da Allah ya,nufe shi da,zaiyi ta nisanta,shi daga,akidar shi ta,shaye shayen da ya,fara nisa a cikin sa. Gashi kuma,da,alama Allah ya taimake su akan haka don dai ko bai bari ba ya dai rage kan don yanzu ya,dawo kamili salihi dashi ba kamar da can baya,ba da ko su sai sunyi da gaske akan shi zaiji. Wanan rashin nuna,damuwa da,abin duniyan da,ake tsanmani daga masu irin fita wanan wasan kwallin da mahaifan shi suka,nuna mai ya kara sa,shi sanin cewa shi din dan gatane na kwarai. Sabon halin da,ya,tsinci kanshi aciki ma shaye shaye shi ya kawar mai da gatan shi a gare su . Adinin mu da,al,adan mu duk sun kyamaci mai wanan irin halaiyar tashi ta shaye shaye. Wasu hawaye masu dumi ne suka dan zubu mashi daga idon shi yai saurin mayar dasu a inda suka fito. Nan dai ya yanke hukuncin duk wasu tdare tsaren da ya dade yana planning din su a ran shi yana ganin komai ya tafi mashi yadda ya dace. Kwanan shi biyar da,dawowa yafita daga gida tun safe bai ko shigo ya karya,ba. Haka yasa hankalin Maji ya dan tashi don tasan yanzu yana gida ko yaushe bai fita waje. Amma yau ga abin karyawan shi bai shigo yaci ba ga kuma na rana har ana batun kare girkin dare kuma again. Haka yasa ta kasa daurewa tana jin shigowan Imirah gida don shi ke fara dawowa daga kasuwa ko yaushe, da kayan cefane da dan abubuwan da,suka sayo na gida. Maji tafito inda yake tsaye yana,ba Umma sako tace a Imirana an dawo lafiya yaya kasuwan? Ya amsa da Alhamdullahi a takaice kawai, Maji tace don Allah Imirah ko dan uwan ka yana kasuwa ne tare da ku don bai shigo gida ba tun dazun da safe . Yace waye dan uwa na Maji? Duk da tambayan ya bata mata rai amma sai ta share ta,dake a ran ta tace mashi Sadauki. Kafin yaba da amsa Umma tace, dan uwan shi don Allah gyara hausan ki mana. Kada ki sa mashi bakin jini da zargi ga mutane, ace ko tare suke shaye shaye dashi. Imirah yace haba Maji, may kuma zai kai Sadauki gurin ni tunda harkan mu ba daya,ba dashi. Maji tace Allah sarki ai zatona yana tare da kune a can kasuwan, kasuwan kan ba gidan yan maye bane ai. Ba ta dai juyo ba ta koma part din ta inda dama daga itace sai Bintu su Maryam basu dawo ba tukun. Ba,a jima ba suka shigo dawowan su ke nan daga makarant alokacin, sai suka shiga neman abinci. Maryam da tafita waje ta samo ruwan sanyi don sai sun saye basu da fridge a part din su. Nan ta samu Umma nata fada dan may za,ace wai Sadauki dan uwan Imirah ne ganin maryam bai hana ta fadan da takeyi ba. Maryam na dawowa take cewa halan anyi wani abin ne wai naji Umma na tafada wai dan shaye shaye don rainin wayo za,ace dan uwan tane. Bintu ce tabata amsa tace kin san basu da tunane da mama take fada wai don ta tambayi yaya imiranah yaya sadauki da,bai shigo gida,ba tun da safe yau. Ikon Allah shine kuma abin fada inji Amirah cikin nuna mamaki karara a fuskan ta. Komai fadan su dai ai ba,a raba anta da jini ko? Don basu san cewa wata rana suma abin zai iya shafan su ba ko, Nan Amira take ta fada ran ta a bace basu san shigowan shi ba sai ji sukayi ana cewa wai kedawa ke fada haka ne Mira, Tace hmmm ashe ma ka dawo yaya nida su Umma mana da basu so a zauna lafiya. Nan take fada mai abinda ya faru shiru yayi baice komai ba suma dai din hakan ne. Maji tafito da alwala tana mashi kallin mamaki tace kai ina ka,shige yau haka ne. Yace maji wallahi ina cikin gari kayan mune ya iso shine naje nai clearing din su a gurin da ake saukewa. Kaya kuma wasu irin kaya ne haka yace cikin wasa yana wuce kayan yan kwallo mana maji. Kai kan da kwallo Allah ya inganta kawai, don ya zama maka jinin jiki ko? Fatima kawo mashi abinci kinji tun safe mutum bai karya ba yana gurin zancen kwallo kawai aranshi. No Maji gaskiya,abar abincin nan don sha dan drinks a can kada naji yunwa saidai anjima da dare zanci. Yaro ke fadin wai ana sallama da Umar UF a waje, inji wani mutum. Mikewa yayi yafita saida Maji tai mamaki take cewa a ranta yau kuma Sadauki akewa sallama a gidan nan. Allah dai yasa mutumin kirki ne ba abokan shashancin shi bane suka fara biyo shi su mayar dashi ruwa. Amira ce ta sako zancen abinda Umma takeyi na kokarin raba su da yan uwan su don ganin su basu da komai wanda yakai ace sun hada alaka dasu. To koma maye ai dai ai su yan uwanku ne kuma duniya ta sani to may ye abin damuwan kai a ciki uwar ta,basu amsa. Kafin tai magana sai ga sadauki ya shigo yana zama yake cewa Amirah gobe zaku shiga school ne da safe. Wani abin kake so ne yaya, ya na,gyara zama yake cewa bani amsa mana kafinki min halinku na yan Nigeria. Tace idan da abinda zanyi sai na bari sai jibi ko na shiga yace dana gode sai yai shiru daga haka bai kara magana ba suke tahiran su kan wata yar uguwar su. Dawowan Alhaji yasa Maji fita tabar su don zuwa gaidashi kamar yadda ta saba, Sai da ya mike, tsaye bayan fitar mahaifiyar su, yake cewa don Allah Amira gobe ku kwashe kayanan gaba daya kufita dashi kafin nine na safe. Amma kada ki fadawa maji yau sai goben kawai taga kuna kwasa please angama yaya tace mashi do ita kadaice a falon lokacin su maryam da Bintu suna ciki. Maji na,shigowa bata ga sadauki ba take cewa,a,a shi kuma wanan din ina,ya tafi ne wai,? Bai faci abinci ba yau gaba daya Amirah tace yako fita ina ganin saida safe ke nan, nan Maji tasawa maryam da Bintu kira tace su zo sukaiwa yayan su abincin shi a dakin shi. Tai hakane don tagani idan yana gidan ko yafita don in fita yayi to gaskiya zancen ya fara baci ke nan kuma. Zun dauki abincin zuwa part din samarin gidan tun daga,nesa,suka gane yana cikin dakin nashi don wutan dakin da yake kunne a lokacin. A hankali ta kwankwasa kofan don itace a gaba maryam hankalinta yana kan wayan ta. Sadauki wanda yake zaune dakin shi yana karatun wani littafi mai ban tausayi yaji nocking din kofan shi mamakine ya kama,shi don dama har ya rufe daki ko. Don haka ya taso ya bude don yaga wanda ke kwankwasa mai kofa a wanan lokacin haka. Daga shi sai yar singileti da gajeren wando irin da maza ke kwanci dashi da dare idan zasu shiga kwana. Bintu ce yagani da kayan abinci a hannun ta ya zuba mata ido baice mata komai ba. Ganin yadda yake yasata dukar da idon ta kasa tana cewa Mama ce tace mu kawo maka abincika nan. Dan guntun tsuki yaja yace banace na koshi ba shine sai an biyoni dashi har nan kuma. Bai sanda maryam suke ba,saida taimagana daga bayan Bintu tace kasan maji in bakaci ba hankalinta bai kwanci ai. Maryam na koshi wallahi yanzun na,rage yawan cin abincin nan sosai don gudun kada nai nauyi da yawa na,kasa yin wasa kuma. Yace shiga ki aje min daga ciki, yadan jaye mata a hanya Bintu ta shiga ta aje mai a bakin katifan shi da sauri tafito bata sab yana gap da ita ba sai ji tayi tayi karo dashi. Tsaki yaja yana fadin ke dai yar kauye ce wallahi ko baki ganine zaki tureni haka kamar baki da ido. Yi hannkuri ta fadi cikin dan muryanta kamar zatayi kuka shi dai ya kauce mata ta,wuce ta gaban shi yai tsaki yace yar kauye kawai da ita. Maryam dariya take take cewa kai Bintu ke dai matsoraciyace wallahi kamar wace za,a kama ko tai laifi. Har suka shigo gida Maryam tana mata dariya take basu Maji labarin abinda ya faru. Maji tace wallahi in yana kiramin yarinya da yar kauye sai na bata mashi rai Allah, duk wanan kokarin da yarinya ke mashi baya gani. Washegari kamar yadda ya umurci Amirah dayi haka,tayi don ta,tayar da Bintu suka,fara aiki don ita a,zaton ta fenti zai sa ai ma,shiyan nasu. Matan gidan kowa tana fita daga gidan daya bayan daya zuw gurin aikin su inda suke gulma a ran su cewa, kullun sharan daki kamar wani tsiyane cikin shi. Mani dai a zaton ta gyara kawai yaran keson yiwa shiyan don karan kan su kawai. Tara da yan mintina sukaji muryan sadauki yana cewa wasu mutane ku shigo dashi nan. Set ne na kayan gado tare da masu hakawa aka,shigowa Maji din dasu nan masu aiki sukansuka fara aikin gyaran guri kamar yadda ya dace. Labule sabbi, kujeri set masu dan karen tsada, fridge sabo dal dashi a kwalin shi, TV plastama babban size din sai center carpet mai laushi duk a falon. Dakunan ta duka ukku an saka sabbin gadaje a ciki don shi ana shigo da kayan ya fita abin shi waje, bai shigo ba,balle maji da imani ya cika ta tambaye shi inda wanan abinda bata taba mafarki ba ya fito masu. Kafin karfe biyu masu wanan aikin da yake aikin su ne har sun gama komai ko nan su Amira suka karasa sauran gyaran da yarage masu. Sai uku ya shigo gidan da ghana most go manya manya har guda hudu niki niki dasu aka zube su a falon Maji. Maji tace Sadauki zonan cikin damuwa da rudani take tambayan shi ina ka,samo wanan kaya haka. Ya lura cewa ta,shiga tashin hankali yasa shi zama kasa gap da kujeran da take yace Maji ko kin manta kin gura danki tilo guda sadaukar da ranshi wa kasanshi ne. Yace abinda kika yarda shine alherin shi ya fara zuwa maki a yau din nan duk abinda zan samu ga,wasan da nakeyi Maji nakine ke da yan uwana gasu nan. Sai mahaifina da kuna kakannina da suka nuna min hanya madaidaiciya da ta dace dani. Don haka kwantar da hankalin ki Maji dankine ya,fara kawo karfi lokaci yayi da zamu fara shiga mutane muma ayi damu. Maji yau ina matan gidan nan suke? Duk sun fita gurin neman na kasu da rufin asirin diyan su, amma ke kina gida kina masu bautan da basu gani har abada. Idan na samu bakiji dadin ba Maji ai ban haihu ba gare ki. Wasu hawaye ne masu dumi suka zubo mata don abin kamar a mafarki take ganin shi a ranta. Ji yayi ta dafo kan shi abinda ta dade batayi mashi ba tun yana yaro in zasu tafi makaranta take mashi haka. Takance Sadauki Allah ya tsare min kai Allah yabada sa,a Allah ya daukaka min kai Allah ya albarkace ka da arziki ta hanyar alheri. Yau ma da yaji ta dafa mashi kai yasan maka manci haka za,ayi sai yaji tace. Allah nagode ma daka azurta min Sadauki ta hayan daka zaba mashi a rayuwan shi. Ya Allah ka tsare min shi ka kare min shi daga duk wani abincutarwa da kuntatawa a,rayuwan shi Allah ka albarka ta min wanan yaron fiye da tsamanin mai tsanmani, Ya Allah ,,,,,,, sai kawai kuka mai karfi ya subce mata ta kasa karasawa abinda tai niyar fadi daga karshe sai a cikin ranta tafadi Allah ka,azurta shi da zuria masu albarka. Bintu ce mai karfin halin amsawa don duk kuka suke adakin gaba dayan su har ita Bintu din dake kallon ikon Allah. Saida sukaci kukan shi ne ya,fara yin shiru cikin su yake cewa Amira dauko jakarcan na baya ki bude. Tajawoshi dakyat zuwa gaban su inda ta bude turamay zannuwane irin na kasar ghana ciki makil dasu. Yacd tajawo dayan kuma shima dogayen riguna ne na yan mata acikin sa su takalma da hand bags, nan suka,rude suka shiga fitarwa, Dai dayan shadda ne ciki masu tsada suma dayan kuma kayan kantine nashi da yan kanneshi kana yasayo masu. Nan ya,ware wa kowa naahi kason kamar yadda yasayo su tun can ghana din. Maji tai matukar jin dadin haka a,ranta don yafara da yaddaya dace duk da nagari yayi yasamu yan uwa su sheda. Tasan Allah ya hore mata da nagari wanda yasan zafinta da darahan ta a idon duniya ke nan. Yace ban sayo maki kayan kitchen ba don ban san kayan da kuke so ba sai a saya a nan kawai. Maji tace a,a dakata ko wanan ma sun isa haka wallahi. Saidai banji ka fadi may kaiwa mahaifin ku ba har yanzu don baiyuyuwa ace ni kai min haka amma shi banji nashiba. Yace Maji na Baba daban ne nasan ya dade yana son harkan noma don haka noma nake son yafara bana sosai akwai kudin da zan bashi wanda zai dan isheshi yafara dasu. Allah yai maka albarka sadauki takara fadi a fil kowa yace amin cikin jin dadi da farinciki. Gardama ya fara a tsakanin Amira da maryam gurin rabon kayan su nan ya fitarwa kowa da wanda ya sayo mata ya mika masu. Bintu dai tana gefe tana kallon ikon Allah da jin dadin uwayen dakin ta ganin farin ciki ya sauka masu yau. Maji tace ban fa gane ba sai duk suka joyo suna kallonta don jin may zatace dashi. Tace naga kayan su Amirah amma banga na diyana,ba mana ko ita ba yar uwarka,bace. Shiru sukayi gaba daya don su sai a lokacin kan su ya kawo wuta ga hakan. Shiru yayi bai bata amsa ba kamar badashi takeyi ba ma sai da takara tambayan shi ne yake cewa ban sayo da itaba Maji. Don may sadauki shiru yayi kawai yana dakilar wayan shi bai bata amsa ba. Ta juta gurin su Amira tana ffadin ku miko min kayan nan a,kasa uku kowa ya kwasa. La Mama don Allah kibar masu watarana idan ina da rabo za,a sayo dani ai. Ba zaiyuyu ba gaskiya ku miko min nan kawai kunji tafada cikin bacin rai yace Maji bar masu sai a sayo mata a nan. Amma maji bata saurare shi tai masu jan ido suka miko kayan inda ta raba daidai ta cirewa Bintu suna ta bata rai don may za ai masu haka. Waya ma dole bai basuba saida dare ya shigo da guda hudu sai dai na Bintu baikai nasu kudi ba. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,, A LOKACIN MU KE,,,,, Yau kwana arbain da,wasu yan kwanaki da tafiyan Sadauki don haka a wani yammaci Alhaji ya dawo kasu Maji ta tafi gaishe shi yake ce mata. Maijidda kunyi waya da Umar yau kuwa tace bai kira mu ba don kasan kiran shi nada wahala ta nan. Indai ba shine ya kiramu ba ni ban faye kiran shi ba gaskiya, ya dan juyo yana kallonta ciki kada kai yace haba maijidda ya wuce ki kashe dubu daya da dan kai gurin jin lafiyan shi kawai. To Alhaji kudin fa ai yazama cacan kudi kulun gaskiya ace dubu dubu haba dai idan dai ya kira muji lafiyan shi ai. Yace tau yace min insha Allahu gobe zai karaso gida don yau jirgin su ya,sauka Nigeria da safen nan. Wani irin murmushin jin dadi Maji ta sauke a lokaci guda afili kuma tace Allah ya kawo muna,shi gida lafiya. Alhaji ya amsa mata da Ameen yace da farko naji tsoron tafiyan yaron nan amma kinga da muka,bar ma Allah zabin shi gashi har sunje sun dawo lafiya. Maji tace a hankali Alhaji nafika jin tsoro don ina gudun yaje ya kara hinjire muna a can. Ai kawai al,amarin daga Allah ne maijidda don dai ni san ba wai rashin tarbiya bane ya jefa yaron nan cikin wanan yanayi. Jerabawa ne kawai daga Allah ya zo min ta hanyan shi wanda mafi yawan mutane yanzu kowa da kalar tashi jerabawan da,ake jarabtar shi dashi. Allah ya sauwaka Maji ta fadi a fili tareda mikewa don tabar dakin don tasan idan takai wani lokaci a ciki yana iya zama masu matsala da maigirkin ranan watau mama Asiya. Ta koma dakin ta ta samu yaran ta kowa da waya a hannun shi suna dakala. Sai Bintu ce da bata da waya ta ke zaune tana karatun littafin islamiyan ta da take bita. Shigowan ta yasa su dan dogo kai suna kallon ta don sun saba idan ta je gaida Baban su tadawo suna kallon yanayin ta idan bada bacin rai ta,shigo ba don gudun ace yayan su ya aikata wani abin asha kuma. Sai dai sunga tsatson farin ciki a fuskan ta inda kafin su tambaya take ce masu Amirah ance gobe insha Allahu yayan ku zai dawo garin nan yau sun sauka lagos gobe zai karaso gida da yardan Allah. Gaba dayan su dadin wannan labarin sukaji don sun san tun da har yakai warhaka kuma ance sun dawo komai ya tafi normal insha Allahu . Ba kamar yadda suke daridari ba da farko don gudin kada yaje yai shaye shayen shi a koro masu shi. Washe gari tun da safe suka fara dan gyaran wuri da kuma yi mashi abinci na musan man dan taron shi. Maryam ce da Bintu suka gyara mashi dakin shi tsab don komai sada suka fitar suka share suka goge mai sabon zanin gado maji tabayar suka shimfida mashi. Wanda karfin aikin ma duk Bintu ce tayi shi ita kadai maryam sai karatun ta take a cikin wayan ta kawai. Ganin suna aikin yasa yan sa idon fahintar kila mai dakin zai dawo ke nan. Mama Asiya ce ta fara samun Umma da zancen cewa yau naga mutanen ki sai wani jin dadi sukeyi harda gyaran wuri. Nafisa tace da zan shigo dazun naga suna,gyara dakin yaya sadauki ai. Muga atsiyar da ya tsinano masu a can ai sai rawan kafa suke wai yatafi ya dawo. Wanan dan shaye shaye may kike zaton zai ita tsinano masu a can, ai yadda yaje haka zai dawo tsula dashi dan ganye kawai. Ranan sai kawai aka kafa dandali a tsakar gida don gulma katuwar tabarma suka shimfida wa kan su nan aka baje ana ciye ciye ana hira wai. Maryam ce tashigo gidan tana cewa yau kan gulma yakai gulma a gidan nan bakiga har tabarma,aka baza ba manya da yaran su a tsakar gida don kawai aga may yaya zai dawo dashi. Ni dai Allah ya kawo min shi gida lafiya yasa wanan tafiyan ta zama mai silar shiryuwan shi. Suka amsa mata da Ameen maji. Sun zage sai faman goge gogen falon su da babu komai sukeyi don dai ya haske kawai. Sun gama dan har wanka sunyi lokacin suna zaune falo suna dan hira jefi jefi tsakanin su. Suka jiyo muryan shi ya shigo gida da sallama a bakin shi, kamar muryan yaya sadauki naji a,waje Amira take fadin haka. Hamdala Maji tayi a fili tana fadin shine ba kama ba ai taji dadi don ko ba komai ta tsinkayo canji ga yanayin shi sosai don gashi ya shigo gida har da sallama a bakin shi yau. ,Nan sukayo waje don taron shi da saurin su hae suna karo da junan su. Kamar yadda ya tafi daga shi sai yar jakar shi wanan karon ma haka yadawo masu sai yar karaman jakar daya goya a bayan shi. Daga inda matan gidan suke zaune da yaran su suna shan rake suka tsura mai ido kawai. Shine yake ce masu sannun ku da gida mama daga haka bai karasa ba ya juya zuwa part din mahaifiyar shi. May na fada maki Asiya na fada maki tsula ya tafi tsula zai dawo muna rabu da dan matsiyaciya kawai masu gadon tsiya ta ko ina. Dariya suka sa dasu da yaran su a lokaci guda wanda sai da ran sadauki ya dan sosu don yasan dariyar a kan shi ne. Sai dai ya dake ya rugumi kannen shi da suka sheko suka rugumay shi suna mashi sannu da zuwa. Banda Bintu wace take tsaye daga gefe sai dai da murna a fuskan tana cewa, Sannu da zuwa yaya cikin yar muryan ta ko bai jita bane yadai ja kannen shi suka shige kawai abin su ciki. Bayan su tabi suku suku da ita tana dan dariyar yake a fuskan ta. Inda MMaji take zaune ya isa cikin farin cikin shi ya zauna kasa tare da sa kan shi saman cinyarta yana cewa Maji yaya na samay ku? Murmushi maji tayi tace anya Baba na kwallo kaje kuwa kaga yadda duk ka canza min a lokaci guda. Murmushi yayi yace kai haba dai maji kwallo ko naje wallahi ban ramay bane? Sai tai dan murmushi wanda rabon haka a tsakanin su ya matan lokacin shi. Maji ta,waiga inda Bintu take rakube tana cewa, Fatima kawo wa yayanki ruwa ko yasha Amirah tace da abinci ko gaba daya. Nan suka shiga kitchen din tare wanda Bintu ta fara dauko abin shan da suka shirya mashi takawo mashi. Ta duka ta aje zata juya yake cewa ke wata irin bakauya ce kinga mutum ya dawo baki iya gaishe shi ne. Amira dake aje tire din abinci take cewa aiko ta gaida kai yaya sai dai in bakaji bane. Maji tace kadawo ke nan ko hutawa bakayi ba zaka fara takura min yarinya ko. Ya juya inda suka aje mai kayan abinci a gaban shi yana fadin kai kai kai Amira duk ni kadai wanan abinci haka mai yawa. Ga,wacce tayi su nan ai da yawa tana nuna mashi Bintu dake can gefe kujera a zaune kasan ties a dakin. Amira tace ta ba bako yake ba yau ai batai laifi ba ko don ance bakon ka annabin ka. Sosai yaji dadin wanan karamawan da kannen shi da mahaifiyar shi sukai mashi haka wai duk shi sadauki keda wanan taron. Shigowan hjy Kubura dakin shi ya katse hiran jin dadin ganin shi da suke yi a lokacin Tashigo da fara,a a fuskan ta tana cewa yanzu su Anwar ke fada min wai bakon ghana ya dawo ina shigowa. Murmushi yayi yana cewa mummy mun samay ku lafiya ko? Lafiya kalau sadauki yaya hanya yaya can kuma I hope komai normal.dai ko ? Inda dane Maji zatace tsakani da Allah tazo taron shi amma yanzu data rage ta, sai take kallon makirci ne ya kawo ta kawai. Nan ta kare kitihin ta ta fita daga dakin daga inda Bintu take zaune tabi da kallon makira kawai ita da maji da suka san komai. Maji bayan yaran sun kaure da hira tadan fito tsakar gida tun daga inda su mama suke zaune aka jefo ta da hausa. Tsula ke nan wai tafiyan sundundun madundun yadda aka tafi haka aka dawo zaban kunya. Dan nagada ai bai iya gado ba dama taya za,ace kagaji abu kuma ka ketare shi. Maryam dake bayan Maji bata san tafito waje zubar da bawan lemun da suka,sha ba, sai jin muryan ta maji tayi daga bayan ta tana cewa. Mu dai mun gode ma Allah ai yaje lafiya ya dawo lafiya yan bakin ciki da suka so kada ya dawo sai su mutu. Da sauri Maji ta juyo kanta tana cewa ke maryam ban son rashin kunya fa da suke zancen su sun ambaci sunan wani ne. Sadauki da suke daki suna jin amsar da maryam ta bayar sun san akwai magana a waje sai sukai shiru daga ita har sadauki din lokaci guda. Maryam ta shigo tana turo baki gaba tana cewa yan bakin ciki kawai dama nasan sheri da ganin kwam ya,zaunar da su ai a gurin kuma sun gani. Maji ta shigo dakin don haka maryam din tai shiru don tasan in taji tana mita,yanzu zata balballeta ne da fada. Sai da maji ta zauna ta dube su a nutse take cewa abinda nake so daku maryam shine. Duk wacce taji a na,sake magana a gidan nan inda ba sunan mu suka ambata ba kada wacce ta kara tankawa kowan su. Amirah tace Maji su wasu irin mutane ne da son fitina daga dawowan mutum zasu fara sakewa mutane magana kamar suna jirace da shi. Maji tace suna jirace mana ba hassada bane kawai rudin shedan ai komai mutum zai iya yi don jan fitina. Fitana,suke so don sunga yadda yaje haka ya dawo masu shine abin dariyar su ai tunda dan matsiyaciya ce shi. Murmushi kawai Sadauki yadan yi yace su suna nan da halin nasu har yanzu wai. May zasu fasa tunda kullun mugin nufi suke sakawa akan mutane inji Amirah tana mikewa take fadi hakan. Haka fa jiya naji Nafisa tana zagin Bintu wai yar ci rani ba bu ranan komawa gida anga wuri. Maji tace sai dai su mutu kuwa,don ko babu ranan komawan Fatima gida a gidan nan. Bintu tadan ji kunya ta,sunkuyar da kanta kasa tana wasa da yatsun ta. Maji tace gani sukayi yar ci rani tafi su mutunci da sanin ya kamata shine hassadan su, don babu wanda zaice tai mashi laifi a gidan nan tunda bata shiga harkan kowa. Ta juya inda Bintu take zaune tana cewa don haka Fatima ki saki jikin kawai ki dainawa kowa dari dari tunda ba wanda ya isa ya koreki cikin su. Wama ya isa inji Amirah bakin ciki ne kawai da hassada don ko ranan naji yaya Imirana yana cewa, wai ina aka samu yar kwara ne haka wai. Sai naji Umma tana mashi fada wai ina kwara din take yarinya haka da fari kamar zabaya. Duk kan su dariya suka sa Maji tace cikin dariya kai bakin ciki ho ina Fatima tai irin farin zabaya kuma in ba,sheri ba. A fakaice ya dan saci kallon farin Bintu da ake magana shi dai baice masu uffan ba a cikin zuciyar shi kawai yake magana shi kadai kan al,amarin kishiyoyin mahaifiyar su. Tun suna yara yake jin suna kirawa Maji kalman tsiya har su kan su din diyan ta. Mikewa yayi a lokaci guda yana fadin zan je dakina maji ina key dina yake ne wai ? Yana fita daga dakin daga gurin da Bintu take zaune bata san lokacin da ta sake ajiyan zuciya ba a fili. Duk suka juyo suna mata dariya Amira tace dodon ki ya fita ke nan ko , don naga idan yaya yana guri zakiga Bintu a,takure kamar wace za,a yanka. Ba dole ba yana son firgita min yarinya da mugun halin shi ki saki jikin ki Fatima haka halin shi yake baudade ne shi ko yaushe. Murmushi kawai Bintu tayi batare da tace masu uffan ba,sai mikewa tayi tafara kwashe kayan da suke a tsakar falin nasu. ****** ********* ****** Yaron yana tsaye tana loda mashi ruwa a,sabon roban da ta,sayo mashi wanda yafi na farko da yake fita dashi girma. Don yanzu ya dan fara sabawa da,tallan ya iya,ba kamar farko da yake dawo mata dashi ba idan ya fita. Tana gamawa ta juya inda yake tsaye tana fadin na jakka da hamsin ne na saka maka kai sauri ka,sayar kadawo kafin mafadacin ubanku ya dawo gidan. Ya dauki ruwan da,kyat yai mata,sallama ya fita, hat ya yi nufin zuwa inda ya saba kaiwa gurin masu wasan ball sai kuma ya fasa yace bari yakai wani guri da yaga ana aikin gina. Yana,tafe yana fadin a,saya,ruwa mai sanyi ruwa dai, mai sanyi, Sai yaji ance daga wani gefe pure water da sauri ya juya zuwa gurin har yana,dan tuntube. A bakin wani shago wasu matasa ne zaune su hudu suna hira sukackira shi. Yun bai karaso ba dayan yake cewa kai amma yaron ga gaskiya yana da kyau gashi dan tallakawa yana,talla amma tsab tsab dashi wallahi. Ai kasan wasu iyayye suna da kokarin gyara yaran su kafin su fito yafi kazo sayen abu gun yaro kazanta ya hanaka iya,saya. Ysron na karasowa gurin su dayan yace sauke mana dama tin da,zun nake nema ruwa masu sanyi wallahi don layin mu jiya babu wuta wallahi. Nan suka fara zukan ruwan sai da kowa yasha leda biyu biyu dan sanyin da,ruwan yayi sosai ga dama ana,dan karen zafi a garin. Ganin da Aliyu yayi yanzu yanzu yayi cinki yasa shi dan samun guri dan nisa kadan dasu ya zauna kafin su sallamay shi su bashi kudin shi ya tafi dama ya gaji nauyin ruwan yai mashi yawa. Da haka mutanen dake wucewa suka zo suna saye har ruwan ya,saura kadan a roban. Sai ga,wata mai abinci tazo ta zauna daga gefen shi take ruwan ya kare ya karbi kudin shi ya juya gida da sauri ya,karo wani. Wasa wasa,sai yagane gurin ana,samun ciniki fiye da inda yake zuwa da,farko don haka ya mayar da,wurin gurin kai tallan ruwan shi ko yaushe. Yana mayawa kusan biyar a rana kafin ya koma gida don zuwa makaran ta da,sukeyi da yamma. Watarana kuma in yan tsiyan sunackan maria sai tace mai idan sun tashi cin breakfast ya gudo yazo ya fita mata da ruwan ta. Da sannu yan gurin suka fara sabawa da yaron har suka yarda dashi suka,fara dan aiken shi sayen taba abinci da sauran su. Yakai yanzu inva ruwan shiba basu sayen ruwan kowa do shi ko yaushe ruwan shi zaka samay shi da sanyi sosai koda ba,wuta don freeze maria yana aiki sosai duk yadda aka kawo wuta zaiyi saurin daukan raba yai sanyi. Tun maigidan yana zargin tabarbarewan karatun dan shi yana fada har yagaji ya,saka,mai ido do uwar bata bari ya,fadi tinda tasan abinda take shukawa a bayan shi. Sosai maria take jin dadin yadda danta yake mata,talla haka tana cewa Allah ya,bashi kan ciniki sisai tayi sa,an haihuwa ita. Tan godewa Uwarta data,bata wanan shawaran da badon haka ba da yanzu tana,nan tana,wahalan neman dan talla bata samu ba. Kulun bankin ta,sai bunkasa yake don yana samun canji suna shiga mashi yadda ya dace. Yanzu ji take koma mijin ta yasani baida yadda zaiyi da ita don bazata iya hanawa dan ta wanan tallan ba. Shiko maigidan mutane da dama sun shatare shi suce sunga Aliyu yana tallan ruwa da yazo yai magana bai gand komai gareta. Don haka yaja,bakin shi yai shiru har ranan da zai kamasu da hannun shi ranan yai alkawarin zai dauki mataki a kanta, sai ta rena kanta ga hakan. ****** ********* ****** Tunda sadauki ya fita zuwa dakin shi bai fito ba ya,samu guri ya kwanta,tare da,karewa,dakin da yasha gyara kallon mamaki. Don yasan ba aikin su Amirah bane wanan wa yan nan malalata yaushe ma,suka,iya,gyarawa Maji guri yai kyau balle na,wani. Da,sauri zuciyar shi da,tafara tunane tabashi amsa,da,fadin ba,aikin kowa,bane sai wanan yar kauyen ta Maji. Bakowa zai iya wanan aikin haka,ba,sai ita wata irin yarinyace bata jin ciwon jikin ta ita aiki bai isanta ko yaushe a,tsaye take ita. Nan dai har barci ya dauke shi inda bai farka,ba,sai da yamma lis don gajiyan da,ya,debo. A,tare ya hada,sallah dake kan shi yayi ya,zauna gurin har lokacin da,aka,fara kiran sallah magariba,ya,wuce masallaci akai jam,i dashi. Yaushe rabon shi da,yin haka,mutumin da komai nashi a,tsabare yake abinshi bai shiga mutane kamar mugu yake ko yaushe, sai yawan nisanta kanshi da mutane yakeyi. Tun a masallaci suka hadu da mahaifin shi ba karamin dadi yaji ba na ganin Sadauki a jam,i tashin farko da,dawowan shi. Sama sama suka gaisa da mahaifin nashi don akwai mutane da yawa lokacin. Yai matukar manakin yadda mutane ke kokarin gaisawa dashi yau sabanin da can baya da mutum zai wuce ya,wuce abinshi ba mai gaida wani cikin su. Shi girman kai mutane kuma suna kyamar dabian shi da ya tsira acikin al,umma. Ana idar da,sallah direct cikin gida ya,shiga gurin mahaifiyar shi don bai gaji da jin dadin ganin ta,da,yayi don dan,kwana biyun da,sukayi basu tare a lokacin yasan dadin Maji sosai gare shi. Ashe ma yawan fadan dayake ganin tana mashi wani babban gata ne gareshi. Don zaman ta kusa dashi yafi rashin ta a kusa dashi ko yaushe. Yana shiga falin duk suna zaune ga dan busashen falon nasu kamar kullun suna hira. Sannu da dawowa suke mashi gaba dayan su a cikin murna kamar su lashe shi don jin shi da,suke ajiki ranan. Cikin harshen turanci yake ce masu daidai lokacin da yake zama kai I miss you people fa. Ina yawan tuna ku ina can ko wani lokaci wallahi, Yace ina Maji take ? Tana part din Baba tana hada mashi abinci yace ok yau itace da duty ke nan ? Maryam ta bashi amsa da eh, Zaunawa yayi dakyau yace Amirah may aka dafa ne da,daren nan ? Amirah ta bashi amsa da tuwon semo da miyar kubewa danya. Jeki kawo min na dan ci na fita,na,samo maku dan wani abin sha kafin dare yayi. Maryam mai kwadai tasa ihun kai canji yaya wallahi har naji dadi har cikin raina, Yace common see yo mai kwadan tsiya kawai tace ba haka na,bane bakaji har gori ake muna wai mu saidai abamu abamu kullun. Wallahi wanan abin ya dade yana,bata min rai bafa rokon su muke ba kuma,da kudin mahaifin mu ake saye amma,don diyan sune a,kasuwa shine ake wa Maji gori da mu. Bintu da,taga basu da niyar bashi abinci ta mike taje ta hado mashi takawo mashi don dama zaune take gefe tana sauraren su. Ga abincin yana kallo ya tasa a gaban shi amma maganan da maryam tayi ya hana,shi cin abincin. Yasan daga shi har yan kannen shi biyu ba karamin hakkuri sukayi ba agidan nasu. Don sun taso suna ganin kalubali rayuwan iri, irin tun suna yara har yanzu da,suka mallaki hankalin su. Shikan shi ada can baya kafin ya fara dan shaye shaye yana kokarin dan dauke masu wanan nauyi. Amma tunda yafara shaye shaye komai ya,dagule mashi a lokaci guda. Shi kan shi ba zai iya cewa ga dalilin da yasa ya tsiri yin shaye shaye ba,a rayuwan shi. Haka kawai ya,wayii gari yaji yana,da ra,ayin yin haka a,ran shi. Tunanen shi ya katse ne don jin muryan maji da yayi a gaban shi tana cewa may kuma ya faru ka,tasa tuwo a gaba kana tunane, Ko baka iya cin abincin mune yanzu ka koyo cin dankunun mutanen kasar ghana. Murmushi ya dan sake a gefen fuskan shi wanda sai ka kula zaka gane murmushine yayi haka. Maji takara tanbayan shi komay yasa may shi taga yana tunane haka karo na biyu, duk yan uwan dake surutu basu kula da,damuwar da ya shiga ba. Yace wallahi ba komai Maji gajiya ce kawai danayi yasani yin shiru haka. Ya jawo kwanon abincin a gaban shi yafara diba a hankali a cikin plate din dake gaban shi. Kadan yadan tsakula ya ture plate din yana fadin ya koshi da abincin. Maji tace amma sai ina ganin kamar ba gajiya yasa kaki cin abincin ba dai, ai gajiya bai hana cin abinci tunda har naga kayi wanka ko? Ya mike a lokaci daya bayan ya wanke hannu yana cewa bari na,dan fita na,dawo yanzu. Da,sauri maryam tace tau yaya adawo lafiya cikin gidimi. Maji tace dakata ina zaka bakaje ka gaisa da mahaifin ku ba daya dawo duk da yace min kun hadu a massalaci dazun. Yace Maji da nace saida safe kafin yafita naje mu gaisa da shi da kyau nai mashi bayanin komai. Daga inda maryam take tace shine daidai Maji bari ya fita yadawo din kawai da,safe suga juna da,Baba din. Akwai dai abinda kuka,kulla nake gani kukuka,sani koma may ye ai ta juya zuwa cikin dakin ta. Bayan wani dan tsawon lokaci ya,dawo da ledoji irin na super market manya har guda uku a hannin shi. Da murna suka tare shi suna karban ledejin maji dake fitowa daga daki tana fadin Fatima don Allah kada ki gaji kinji dauko min abinci naci nima. Zataci gaba da magana sai ganin abinda ke wakana falon nata tayi, takai idon ta ga ledojin da su Amira ke budewa. Drinks ne snacks, su apple da nama gudan mai yawa na rago da kaza gassashe. Take kamshi ya,gahraye falon nata a lokaci guda sai faman binsu da kallon mamaki takeyi daya bayan daya. Bintu da ta riga tamike take cewa a hankali Mama na debo maki abincin ne? Yace ke bar abincin nan dauko mata plate kawai ki zuba mata wanan taci tasha drinks din. Cikin mamaki maji takai zaunr a saman dayan kujeran ta tana cewa haba Sadauki kai da ya kamata kai tanadi shine zaka biyewa wa yan nan makwadaitan ka,fara almubazaranci da kudi haka. Murmushi kawai yayi azuciyar shi yace mamana bakiga komai ba ma tukun ai. Amma a fili cewa yayi ai maji wanan bai hana ai tanadi don su wa naje wasan badon ku ba aci kawai bai sa ya kare ai. To amma sadauki kana dai jin har an fara min gori yaddackaje fa haka ka dawo wa mutane tsula dakai. Maji kada ki damu da zancen su wanan magana da sukeyi takine a gare mu yanzu. Bintu tana kawo plate din tamikawa Amira dake ta faman bude kayan, inda Amira ta dago kai tama cewa maji may zan yago makine daga ciki? Dakuwa Maji tamika mata tana fadin ungo naki nan ta juya inda Sadauki yake zaune tana fadin kada ka biyewa wayan nan yan kwaden don basu san ciwon kasu ba,su ba abindake ran su sai kwadayi. Kai tanadi ga dan abinda kake samu don gaba nada yawa don kaine muke gani wani gin shikin mu gidan nan. Maji kada kiji komai kuci kawai ai don hakane na,sayo maku din don naga kunci kun sha daga gareni nima. Komai da ya,sayo saida Amirata sawa Maji inda shima sadauki ta zuba mai a cikin dayan plate din. Ta juya inda Bintu take makure tana cewa bisimillah mana zo muci ko,? Maryam data fara kaiwa abaki tace ,a,a bazataci ba kin san ita akwaita da filanci ai. Shigowan yaron Asiya da,aka turo don yafa may suke a dakin saboda dariyan su da akeji, Amma sai ya fake da yazo gayar da yayan sune da dawowa. Maji tace Amira ta diban mashi inda ta yaga mai rabin kaza guda da yan sauran tarkace tabashi yafita. Maryam tace munafuki gulma dama tazo yi ba duk gaisuwa yakawo shi ba fa. Kai ke kan maryam wallahi ki rafe yawan zargi ina laifin shi yadawo yahi dan uwa yadawo yazo ya gaidashi. Kila ba inji Amira maji tace ku dai kuka sani don bakujin magana. Bintu dai na gefe tun da ta dauka saudaya,sai faman taunan shi take ta kasa hadewa duka. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,, A LOKACIN MU KE,,,, Bai yarda ya,fita daga gida sai yai wanka ya gyara jikin shi kamar yadda yaji ana yabon shi da tsabta ko yaushe, Yanzu yana ciniki fiye da farko a baya don ko bai sayar ba mutanen gurin zasu saye na karshe suce zasuyi amfani dashi da dare dashi, don da dare ana wuyan samun pure water. Haka yasa yaron ya kara kwantar da hankalin shi da mutanen gurin da yake zaman don yanzu duk sun saba dashi ko sosai sun kuma yarda dashi yaron nada kirki yana da,wayo, Don duk inda suka aike shi da gudu zai tafi kuma bai bata ranshi. Ya kai yanzu taban da ake aiken shi saye ya canza sallo don dai shi bai san wani irin taba bane shidai a ganin shi ai duk taba tabane. Amma sai dai yasan wanan yafi wanda yake sayo masu don sai anyi warning din shi akan ya boye idan an bashi kuma idan ya sayo kada ya,basu infront of mitune yai hiding din shi. Haka ko yake ko wani irin sako zai bayar in secret zai ba mutum abin shi. Duk hiran da matasan zasuyi a kan idon shi ne cikin kunnen shi yake shiga. Akwai wani wanda idan ya sai ruwan shi ko nawa ne canji zaice ya bashi kawai bai karban canji gurin yaron. Haka yasa Aliyu har Allah Allah yake yafita tallah koda lokacin fitan nashi baiyi ba. Suma gurin da ya tun karo zaka ji suna smally ya iso ke nan yaro kana wanka,fa. Shiko yarinta sai yaji kan shi ya,fashe yana mai jin dadi yana kokarin yin wasa da su don sun saba dashi ko. Nan za,a fara smally sayo min sigari zo ka sayo min abinci tsalaken titi da dai sauran su. Irin haka,watarana yazo sayen sigari sai ga wani abokin mahaifin shi yace ,a,a Aliyu wa ya aiko sayen sigari kuma? Yace wani mutum ne a van tsalaken titi ya aiko ni aka mika mai yatafi, sai mutumin yake fadin kai amma gaskiya haka bai dace ba a aiko karamin yaro sayen irin wanan abin baidace ba da karamin yaro. Mai shagon yace aiko kullun sai yazo ya,saye kashi da kashi ake aiko shi ni nazata ma ko mahaifin shine ke aiko shi saya. Ina mahaifin shi ai bawan Allah ne, ina mutumin nan mai dako a bakin kasuwa mai wuce wa tunda safe yana fitowa kwanan can na malam sale. Mai shago yace nagane shi dan shine ashe yace wallahi dan shine kai wanan mutumin ai ba ruwan shi wallahi. Mut8m ya hadu da mijin maria yake fada mai abinda yagani da idon shi a kan yaron shi. Bai ji dadin zancen ba, nan ya koma gida da fada anyi sa,a ya samu Aliyu a gida nan ya haushi da fada harda dukan shi sai da yayi ranan kuma yai mai fada daga ranan duk wanda ya tareshi ya aikeshi sayen taba yace Baban shi ya hanashi zuwa. Washe gari da,aka ake shi yake fada masu cewa, an fadawa Baban shi yana zuwa sayen taba harda dukan shi akayi kan hakan. Kai mutane dai wallahi muna fukai ne yanzu har mahaifin ka,saida ya,samu wanan dan labarin kamar wani abin sheri can. Nan suka,bada shawaran ya canza shago kawai inda baza,a sani ba yana zuwa. ****** ********* ****** Tun dawowan su ka fara karo da kwalayen da akai amfani dasu a dakin Maji na kayan da aka haka, duk da an kwashe anzubar da saura ga kuma shirgin kayan da aka fitar a inda suka barsu dazun. Yaran su ne suke fada masu cewa yau basu nan an sha aiki a dakin Maji don an gyara mata dakin ta kamar na amarya. Mama Asiya bata yarda ba saida ta shiga hardakin don ganewa idon ta abinda yaran ke fada masu. Tun daga labulen falon tafara shock don bata ma taba ganin su ba da idon ta gidan kowa ba. Kujerin da tai tozali dazune suka saka gaban ta wani irin faduwa, don tasan bana kasar nan bane da ganin su. Juyawa tayi don babu kowa a falon bata tsaya ba sai dakin Umma wadda itama shigowan ta gidan ke nan a lokacin. Yaya waiko kinga abinda idona yau yaganan min may kuma kika gani zaune takai tafara lissafawa Umma abinda tagani da idon ta. Amma sai Umma bata dauki abin da muhinmanci ba ta zaci kawai idon Asiya ya rufe ne har take dada abinda akasa don ina zasu samu kudin irin abinda take fadin tagani a dakin Maijidda. Maji da ta idar da adduoin ta da mika godiyan ta da neman tsari a gurin Allah tafito don yi masu sannu da zuwa. Don kullun suka dawo dama sai tai masu sannu da dawowa bata gajiya duk da gwatsaleta da watarana sukeyi. Har ta juya sai kuma ta tsaya tana cewa yaya baku nan fa abin arziki yau ya samay ni don dan ki ya sayo min kayan daki da kudin da ya samu. Wani dan nawa Umma ta tambaya a gwatsale cikin basar wa maji tai murmushi tace dan ki sadauki mana. Umm,uummm, dakin dai Maijidda tunda gashi uwarshi ya sani inda danane ai da ni zaiwa. Tace idan kin huta sai kije ki gani ki samin albarka a ciki, ta juya ta fita zuaa gaida mama Asiya . Itama ta fada mata yau abin arziki ya samay ta daga dan ta tazo tagani don Allah. Nani kawai tace ba wani adfuan alheri akan wanda yayi din dama ita da tasamu din. Hjy kubura dai dama sai yamma lis take shigowa gidan kullun koda kuwa sun tashi daga gurin aiki ne bata dawowa sai ta gama gantalin ta take shigowa gidan da yaran ta a gala baice da yunwa. Maji tana shiga daki tafara cirewa kowa tsaraban shi kamar yadda suka tsara ita da diyan ta. Matan gidan dai sun samu turamay yan ghana masu kyau da tsada turmi biyu, biyu sai yaran su maza bandir din shadda kowan su koda kuwa yaro karamine, Yan matan kuma dogayen riguna da turamay suma aka basu, masu kyau sosai. Nan gida ya kaure da surutu kowa da abinda yake fadi inda babu wanda yazo godiya cikin su sai yaran ne duk wanda akabawa zai zo yayi godiya da jin dadi masu bakin hali irin na uwayen sune basu shigo ba. Hjy kubura da aka kai mata sakon cikin mamaki tace sadauki fa ya kawo muna wanan haka don harda kwallon da danta yaba da soko saida aka sayo mashi Bata san da zancen gyaran dakin ba saida ta shiga taga ikon Allah dare daya Allah ya kai su gaba haka. Tace may nake gani haka hjy maijidda kice min ci gaba yazo ke nan nan ta shiga sauran dakunan tana kallo tana kada kan ta cikin mamaki don bata taba zaton haka ba. Falo ta dawo tana fadin kai Maijidda kin ko tambayi yaron nan akan kwallo ne ya samu wanan kudin haka? An fa kashe kudi yakai miliyan biyu a nan ma kawai fa tanayi tana kara latsa kujerun don jin kwalitin su. Tace ina dan nawa yake sarki yan kwallo ke nan ace mutum shigan farko ya dawo da haka. Sai bayan ta mike take cewa ja iri yako tafi da dabun da nai mashi na tafiyan kuwa. Maji tace ai yace yaji dadin danbun sosai shi uake ci ma a can yasha ruwa kawai don bai saba da irin abincin su ba sosai ,a lai kan naga alama.ai. Tafita tana tunanen hitan su da yan office din su dazu da safe da suke cewa ashe dan kwallon gidan ku yadawo tace cikin tabe baki yadawa yadda yatafi shiririce mana. Wanan dan iska wani tsiya dama zai tsinanowa mutane a can ban da tambadan daya saba nasan ya tafi yana shaye shayen shi sun koro shi. Sai dayan dake rubutu take cewa ,a,a nifa naji kanina na fadin shine ma yazo na farko don ya samo kudi sosai wallahi. Ba gaskiya bane wallahi yadda yaje haka ya dawo tsiya tsiya dashi wallahi don ina ga baiko maganin sisi ma. Don ya samu wani abu da naji ko gurin Alhaji ne ko inga suna facaka ko ba abinda ya tsinano. Sai daya tace balle ma mashayi kafin fa suyi sai an bincike su agani idan kana shaye shaye basu yarda ka buga kwallo yanzu. Balle ma bai samo komai ba suna dai ganin hakane tunda ya tafi har wani kasa yin wasa. Sai gashi ta dawo gida ta samu zancen abokiyar aikin ta ashe gaskiya ne ke nan boyon kurwa yai masu dama. Maji dai ta rakata da harara tana fadin muguwa aniyar ki tabiki dakin ki munafuka yar sheri, Allah ya shirye ki kawai. Maji tace wa Amira gobe ina son a kwashe tsofin kayan nan akai wa mai masa gidan ta ita ma,ta canza. Nan Bintu tafara murna tana godiya kafin hjy masa tazo tayi mai karfi da bakin ta. Sai da yamma da Alhaji yadawo ya samu wanan labarin gurin mama Asiya da ta fara tsegunta mashi ciki tsigar gulma. Yace masha Allahu kai amma ko naiwa maijidda murna haihuwa ta fara rana ke nan yau Allah ya amsa mata adduan ta . Sai ga maji da nashi tsaraban shaddoji da su turare masu tsada ta zube mashi su a gefen kujeran da yake zaune. Ya kalleta cikin murmushi yana fadin yanzu Asiya take fada min abin arzikin da ya samay ki ashe sadauki ya fara fitar da uwarshi. Maji tai murmushi tace kai haba Alhaji kai kuma da kanka zakai min sheri kuma. Suna cikin magana sai ga hjy Bintu dauke da tsaraban ta dana yaran ta tana ta faman washe baki tana fadin ga abin arzikin da mutanen ghana suka kawo muna. Yace mata nima kinga ga nawa nan yanzu aka kawo min shi ko dubawa ban gama ba. Mama Asiya mai girki tashigo ganin kayan hjy Kubura dana yaran ta yasa take kallo don taga sun fi yawa ga idon ta. Nan take cewa hmm muma fa anbamu har yaran nan gaba dayan mu gidan. Masha Allahu inji Alhajin ya fadi yana mai kai ruwa a bakin shi yace haka ake son samu idan ka samu kowa ma yasan kasamu cikin yan uwan ka. Yana gama cin abinci ya nufi dakin Maji don yaga abinda ake ta faman zuzutawa, Yako gani kuma yai murna da farin ciki sosai sai faman sawa dan shi albarka yakeyi. Bayan fitan su Amira tace ikon Allah yau Baba ne da kan shi kewa yaya sadauki wanan adduan haka. Amma da can an zuga shi a kan shi sai faman cin mutunci da tonon asiri yakewa mutane a tsakar gida. Maji take ce mata wanan ai haka yake duk uwa mai haihuwa sai ta samu bacin ran mahaifi akan dan ta watarana. Don duk abinda yayi mara kyau laifin uwa ne maikyaune na uba ni dai na godewa Allah daya takaita min wanan bakin cikin da wuri. Maryam dake kunna tv take cewa amma ai basu daina kiran shi da sunan mashayi ko? Don ko dazun naji Umma tana fadin wai tsaraban yan shaye shaye suka samu take fadawa yaya Imirana da ya shigo. Ba sai ta dawo dashi ba tunda bata son kayan mashayi da aka bata maganan banza kawai. Maji dai shiru tayi batace masu uffan ba har suka gaji sukai shiru. Da safe ne sadauki yaba mahaifin shi check din kudi yace yana so ya fara noma dashi ko za,a samu anan ma din Bayan Alhaji ya karbi kudin yaga yawan su yake cewa sadauki duk wanan kudin haka akan kwallone kawai ka samay su. Ya dan dukar da kan shi a kasa yace Baba a nan na samay su don ma ban yarda bane da,har wasu club sun so su sayeni amma,nace masu a,a subarni cikin club dina kawai har gaba. Ikon Allah ashe Alhaji Sani gaskiya yake fada min cewa idan nai hakkuri Allah yasa maka hannu watarana sai na dara akan kwallon ka. Murmushi kawai sadauki yayi ba cewa mahaifin nashi komai ba yana fita hjy kubura tana shigowa suka gaisa dashi ya fita. Alhaji ke ce mata kingani ikon Allah kudi sadauki ya kawo min wai na fara noma dashi. Maimakon yaji tayi murna yadda ya zata sai ji yayi tace Alhji adai binciki a gani wanan harkan amma abin yai yawa wallahi. Ya juyo cikin mamaki yana kallonta yake cewa ban gane hausan ki ba fa kubura. Tace ni gani nayi kamar wanan kudin sunyi yawa ace duk a saboda kwallo aka samo su haka gaskiya abincika dai aji. Yace to kina ganin kamar da akwai wata a kasa ke nan ko ya tambaye ta don son jin may zatace. Tace gaskiya kasan halin dan yau fa kada ya yaudare ku da,wasan kwallo ya fada wani harka na tir da Allah waddai. Cikin mamakin jin abinda ta fadi yace assha kubura ban zaci jin wanan magana daga bakin kiba wallahi. Sai lokacin ta tuna tayi barambarama fa don mahaifi mahaifine ai,da sauri ta gyara zancen tana cewa a,a ba wani abu nake nufi ba kasan halin dan yau ne shi yasa na ce a dai bincika kawai ba wani abu ba. Nan dai taita kamay kamay ta tafita shi dai yana jin ta kawai baice mata komai. Kwana biyu sai gashi zance na yawo a gari da unguwa wai ya samu kudi ba,a san inda yasamo ba sai facali yake iyayyen shi suna jin dadi. Wasu suce wai ba kwallo aka dauke shi ba zuwa akayi dasu suka fita da kwaya kasan waje shine aka fake da kwallo kafa. Maji dai da zancen yazo kunnen ta da farko ta so tayar da hankalin ta don sai da ta tsure sadauki a dakin ta take tambayan shi gaskiyan zancen abinda taji. Murmushi shi na rabin fuska kawai yayi mata yace haba Maji idan wani ya fadi an yarda aike bai kamata ki yarda da wanan zancen ba don kin fi kowa sanin halina. Ban son raini da wullakanci shiya sa na roki Allah yai min mafita na dogara da kaina. Nan dai hankalin ta ya kwanta tace koma,waye yai muna wanan sherin mun barshi da Allah shikw nan. Takara ja mashi kunne akan ya futar da ita da yan uwan shi daga kunyan duniya don mutane yanzu ake kiwo ba dabbobi ba. Bata hakkura ba ranan da take da girki ma saida ta samu maigidan su da wanan zancen. Yace au kema ashe zancen yazo kunnen ki amma ya kamata ace kin san halin abinda kika haifa. Ni ban ji ko dar ba akan maganan nasan kawai hassada ne irin ta mutanen yanzu kawai. Amma ai watarana gaskiya zatai halin ta don shi kwallo ba,sanar boye bace duniya tana sanin mutum a lokaci guda. Ki dai yi mashi fada yai tanadi kada yaga kudi suna shigo mashi haka dayawa lokaci guda yace zai bullo da shashanci cikin rayuwan shi. Haka yasa tattara zancen ta watsar tabar masu hassada akan danta suna zuba mashi taki. ****** ********* ****** Sadauki yana zaune a cikin falon Maji duk kannen shi sun tafi makaranta sai ita dake final exam din ta yanzu. Wayan shi yake dakila ta hanyar yin game da ita,Bintu tafito daga cikin dakin kwanan su bata san da yana falon zaune ba a lokacin. Tana saye da da dogon riga na atamfa a jikin ta, style din dinkin da akaiwa rigar yai matukar mata kyau a jikin ta. Tunda ta sanyo kai falon ta gashin a zaune sai taji gaban ta ya fadi don a rayuwan ta ta tsani ta gan shi a falon zaune don yawan takuran da takeyi. Jin motsin da yayi a zaton shi ko Maji ce tafito daga cikin dakin yasa shi daga kai ya kalleta. Bintu ce ya gani tana kokarin komawa cikin dakin da tafito din,cikin sauri. Yace cikin daure fuska ke zo nan kina abu kamar muna fuka dake, cak taja ta tsaya tare da juyowa inda yake zaune. Yace ina Maji take ne ban ji motsinta ba ya tambaya cikin ci gaba da latsan wayar shi . Tana dakin Baba tana gyarawa amma yanzun zata dawo,,, Hannu ya daga mata yana fadin ban tambayeki ba bani abinci na naci yace cikin gadara da daure fuskan shi. Haka ta karasa fitowa ta gaban shi ta wuce ba don taso ba inda yabi bayan ta da dan tsuki yana fadi a ranshi jita dan Allah kamar zata kare, mace haka ba kiba ko kadan. Tafito da abincin cikin sabon kulan shi da ake saka mai abinci ta aje a gaban shi ta juya zata dauko ruwa ya kara binta da kallon haushi. Yadan kara jan guntun tsuki wanda yai daidai da shigowan Maji falon, tace, a,a Baba na kai dawa kuma ke wanan tsuki haka kai kadai? Yace kai tsaye ni da wanan yar kauyen mana tafito taganni shine kuma wai zata gudu anya maji yarinyar nan kuwa tana da gaskiya ya fadi tare da,dago kan shi yana kallon Maji. Wani kallon da yaga tana mashi yasa shi shan jinin jikin shi ta,wuce zuwa ciki ta aje kayan dake hannunta. Jima kadan tafito ta zauna tana fuskantar shi tace gaskiya banjin dadin irin yadda kakewa yarinyar nan, Ko banza taci albarkaci na nida na ajeta a gurina bawai bata da gata bane a,a itama tana da gatan ta rayuwane kawai yasa ka ganta anan din. Amma yarinya tana tsaye tana iya kokarinta a kan mu kai kuma,sai binta da hattara kakeyi da wani zataji na rashin iyayyenta kusa da ita ko kuwa da halinka zataji. Ban son karatun yarinyar nan ya tsaya ne shiyasa kaga ana ajeta a gurina don itama watarana iyayyenta suyi alfahari da ita. Ashe ba dadin ku bane yau ace a sanafin mu ta zama wani abu a duniya, ban rokeka komai don na tallafa mata ba. Amma kasa yar mutane gaba haka da tsangwama tare da hattara ba yau ba ina lura balain tsoron ka fatima takeyi wallahi. Wani kunci ne yaji ya rufe shi a ranshi ya mike ba tare da ya gama cin abincin da yake ci ba ya bar falon cikin fushi. Maju da tabishi da kallo ta,tsuki tace sha sha kawai mara hankali mutane suna bakin cikin zaman ta anan kaikuma kace zaka tsiro min da naka kalar tsiyar a kanta. Tsayin sati daya sadauki yana fushi a kan maganan gashi ya hana Bintu sakat a sashin nasu don da ya shigo ya kama hararan ta ke nan da kuma tsuki. Allah Allah Bintu keyi ta gama exam tabi gwagonta kauyen su don dama zaman dole take a gidan. Hankalinta yana gurin iyayyen ta da yan uwan ta don tunda tazo bataje gida ba,bata kuma ga kowa ba cikin su sai gwago dakan dan zo ta kwana biyu ta koma. Allah ya taimaketa kafin su gama exam aka kirasu Abuja inda ya kwashi komatsen shi yanufi gurin kiran da akai masu. Hakan ya,dan ba Bintu daman sake jikin ta har maji ta fahince ta tafi sake jikin ta idan baya nan ke nan. Amma tana gama exam ta fito da zancen son zuwa gida don tagano yan uwanta. Hankalin Maji yai matukar tashi a lokacin inda take tambayan ta cikin lalashi ko an mata wani abine take son zuwa gida. Bintu tace cikin sanyi murya da,sauri a,a mama ba ai min komai ba ina dai son zuwa,nagan su ne tunda nazo banje gida ba shiyasa nake son zuwa nagano babana da yan uwana. Maji ta sauke ajiyan zuciya tare da,tambayan idan kin tafi yaushe zaki dawo Fatima? Don nasan ko kwana,nawa zakiyi acan saboda na tura a dauko ki in lokaci yayi. Bintu tana,wasa da yan tsunta,da,harde su guri guda tana cewa mama sai na tafi tukun don ban san hukuncin da mahaifina zai yanke a kaina ba yanzu tunda na gama karatu na ko. A,a Fatima idan hakane ki bari mu tafi tare sai mu kwana daya mu dawo, tare. Da sauri Bintu ta dago kai tana fadin mama har gurin mahaifiyata nake son zuwa don mun dade bamu ga juna,ba da ita. Eh to gaskiya hakan yana da kyau kuma ina ga,dai kila zakiyi sati biyu zuwa uku ke nan eh mama Bintu ta bata ansa da hakan wanda ta dai fadi ne don su rabu lafiya da maman nata sabuwa. Amma yadda tajeji bata sa ran cewa zata dawo wanan gidan ba kuma da sunan zama duk da dai ba ai mata komai ba amma gidan ya fita ranta don tana gudun kada sanadin ta mama tai fada da dan ta daya shiryu yanzu. Tsaraba sosai Maji ta hadawa Bintu na gidan mahaufinta da yan uwan ta daban wanda zata kaiwa mahaifiyarta daban. Mota akai mata shata ita kadai Alhaji yabiya tare da bata kudi da zata rike don amfanin ta a can. Kamar yadda akai alkawari da driver hakan yayi har kofan gida su Bintu ya kaita inda aka,ganta a bazata don ba wanda yasan da zuwan ta. Irin kayan da,akaga a na,shigowa dashine yasa hankalin matar uban ta ya tashi, har ta kasa boyewa da zuwan Bintu din. Nan dai kowa ya,wayance sai sannu da zuwa ake mata ana kallon yadda a lokaci daya ta canza kamanin ta gaba daya ta koma wata yar Birni da ita. Kafin wani lokaci har zancen dawowanta ya zagaye dan kauyen nasu kowa na fadin Bintu ta dawo ta koma yar Birni da ita. Saida dare ta samu ganawa da mahaifinta wanda ya dawo daga gona a lokacin ana gabanin magariba. Nan suka kebe tana bashi labarin zaman ta a burni da kuma mutanen arzikin da gwagon ta,tabarta gurin su. Takawo sakon da maji tabata na,tsaraba ta bashi yana ta murna da farin ciki. Bintu ta sheda mai ta kare karatun ta har matar dake rikon ta tace zata ci gaba da karatun ta idan jerabawan ta ya fito. Mahaifinta yai farin ciki da jin wanan albishir din da tai mashi sai dai kuma yasan abune mai wuya yadda ta girma haka yan uwan shi su barta taci gaba da karatu sai dai in Allah ya nufa zatayi din. Washegari Bintu kamar yadda ta,saba zuwa daukan karatu a lokacin da take gida hakan ta shirya zuwa islamiyan su. Sai dai ta samu yawanci yan matan da suke karatun tare sunyi aure a lokaci, dan kauye basu bari yarinya tagirma sosai suke mata aure. Malamin nasu yai farin ciki daganin hazikan daliban shi ta dawo kuma bata watsar da karatun ta ba don taje birni. Taso ta fara a inda ta,tsaya da karatu a gurin shi amma da,tafara biyawa sai yaji ta,wuce tsanmanin shi. Don haka yace ta dauka a inda,take can birni haka yasa taci gaba don ta sauka bita take yanzu. Ganin duk idon sauran dalibai yana kanta kuma suna sauraren yadda sabon sallon karatun ta yake fita. Duk sai sha,awan ta ya kama su nan suke zuwa wai ta koya masu yadda take fitar da haruffa cikin kara harshe. Nan fa samarin kauyen masu jin sun isa suka fara kawo kan su gareta da,sunan sun gani suna so. Itako mama ta,bawa matar ubanta tunda ta kyala ido taga kayan maihaifiyan Bintu da maji ta bata ta sa a ranta su take so. Bayan nata da,takawo mata da yaran ta duk sai da Maji ta ba kowan su tsaraban da zata basu in tazo. Haka ta,bawa tasa Bintu da mahaifinta gaba da masifan kan lalai sai dai ta dauki turmin wajen ina da aka bata takai mata. Har abin yaso yakawo sabani a tsakanin ta da mininta watau mahaifin Bintu. Don haka Bintu ta tsiri tafiya garin da mahaifiyarta take bashiri don tabawa sai fada takeyi wai bayan tagama wahala da ita yanzun anga dadi yazo shine zatace tasan uwar ta. Bintu dai murmushi tayi kawai tana hada kayanta tare da tunanen yadda zata zauna gida da wanan masifanna matar mahaifin ta kulun. Ta hada duk dan abinda tasan tana so tana bukata a cikin kayan ta tafito tare da,yi masu sallama ta tafi abinta badon ta tashi zuwa ba. Ganin ta kawai mahaifiyarta tayi a bazata don rabin ta da ita tun tana aji hudu na primary bata sake zuwa ba don maigidan ta baida dadi ko kadan. Bai son yaga Bintu tazo wajen uwarta ya shiga fitina da mitan shi baison zuwanta tana zuwa tana hure mata kunne don ta koma gidan mahaufinta. Ta,samu mahaifiyarta da tsohon ciki a jikin ta kuma yana bata wahala don haka tun zuwan ta bata huta ba. Da maigidan ta ya dawo daga Kasuwan kauye ya samu Bintu tazo ya dan fara daure fuskan shi. Saida yaga abin arzikin da tazo masu dashi don har shima ya samu shadda yadi goma. Shine har ya dan sake fuskan shi, yazo har dakin su fuska a sake yana cewa ,a,a Bintu harda tsaraba muka samu haka mai yawa. Har yana tambaya ko taci abinci da tazo nan dai ya karaci surutin shi ita dai Bintu kai kawai ta gyada mashi har ya fita. Washe gari tun da safe Bintu ta tashi ta gyara ko ina na gidan nan gidan yakoma wani fes dashi. Sai zuwa rana ta fahinci ko abinci basu dashi a gidan nan ta saka katon hijjab din ta har kasa ta fita can sai gata da kayan cefanen ta niki niki mai mashin ya kawota gida. Bata tsaya ba ta girka masu abinci suka zauna ita da yan kannen ta suka ci suka koshi harda mahaifiyarta dake auren wahala. Maigidan sai zuwa rana ya dawo yana yan kamay kamay shi wai tunda ya fita ko sisu bai samu ba sai dan fura da akabashi da nono yace a dama,mashi, Matarshi ta mike da kyat ta shiga daki sai gata dauke da kwanon abinci yana mamakin ina tasamu kudi har tai masu girki. Bayan ta aje yake tambayan ta don ya zaci taciwo mashi bashine don diyarta tazo ta girka masu abinci. Matar tace mashi yaringa ce ta sayo ta girka muna nan ya wani washe baki yana bude kwanon yai tozali da shimkafa da miya harda nama a ciki. Yashiga ci yana sakawa Bintu Albarka tare dakai lomar abinci a bakin shi. Bintu da ke daki tausayin mahaifiyarta ya kamata don tasan wanan susun mijin nata bai aje komai ba sai bakin shaye shayen da yakeyi kawai. Abu tun bata da,wayo yake haka har yanzu data girma ta zo ta samay shi a hakana. Dalilin da yasa ke nan take matukar tausayawa Maji akan shaye shayen da dan ta yakeyi don tasa mugun abune mawuyacin abune mutum ya daina shi a rayuwan shi. Da yamma sai gashi da dan kunshin a leda yana wargale baki yana fadin ina,diyata ne gashi ba,sayo mata dan abin mu na kauye taci don nasan can birni basu samun shi. Bintu najin haka tafito daga dakin tana gyara daurin dan kwalinta ta nacewa gani Baba. Ya mika mata ledan ta,karba batare da,tasan abinda ke cikin ledan ba yana fadin ki gyara kici abin marmari ne gare ku. Ta dauko kwanon ta bude ledan zogalane da rogo dafafe da zafin shi ya sayo mata harda kulikulin da zata gyara shi ya hado mata. Bintu ta zauna ta gyara tasamo wani kwanon silver na miya ta zuba mashi azaton ta,bazai karba ba sai gashi ya karba har ya riga su cinyewa ko. Sai faman santi yake zubawa sosai taji dadin ganyen don ta dade bataci ganye ba haka mai yawa. Kamar yadda tai masu girkin rana haka ta girka mazu na dare inda tai tuwon garin masara data sayo da miyar kuka yaji daddawa da kayan yaji sai kamshi ke tashi ciki. Haka ta zauna gidan mahaufiyan ta don yafi mata dadin zama gidan mahaifinta da matar uban ta ke sakata gaba da fitina kyashi kishi da hassafa duk ta dagwara mata shi. Satin ta biyu a kauyen bata fita ko ina kulun tana gida da yan kannen ta suna hira ko tana koya masu karatu. Ranan dai mahaifiyarta ta matsa mata akan tafita taje gidan yan uwan ta,su gaisa. Ba don Bintu taso ba ta shirya tare da yan kannen ta mata biyu suka fita zuwa gidajen dangin su. Suna gap da zasu dawone suka hadu da,wani matashi daganin shi kasan bako ne a garin ko kuma dai yazo ne ba,a nan yake zama ba. Saboda yanayin shigar shi jikin shi da suturun shi ya banbanta da na mutanen da yake tare dasu a gurin. Tun da su Bintu suka tunkaro idon mutimin yake kanta duk da katon hijjab din dake jikinta bai hanashi kallon ta ba. Sun kawo daidai inda suke Bintu tai masu ina wuni gaba daya suka amsa cikin washe baki, a hankali mutumin ya tambayi wanda suke tare wanan a garin nan take ne ? Har zasu wuce sai dayan mutumin yace wa dayar kaunan Bintu a,a Dije bakuwa kukayine yarinyar ta tsaya tana cewa eh yayan mu dage Birni ne tazo. Su dai suka wuce zuwa gidajen da Inna ta tsara masu sutafi sukai Bintu ta gaida su. Agajiye suka dawo gida lokacin yanma tayi ko gashi batai sallah la,asar ba don haka ta shuri buta ta nufi gurin alwala don kada lokaci ya shige. Inda ta idar da sallah tana zaune mahaifiyarta take tambayan ta kawo mata abincine tace sun koshi tasha fura a gidan kakanta. Sai ga,yaro yana sallama yace wai ance ana sallama da bakuwar gidan nan. Bintu dake daki a ran ta tace ai kaji matsalar wallahi shiyasa ban son fita ko ina wallahi. Bata so fita ba amma mahaifiyarta ta takura mata akan sai tafita badon taso ba haka ta shirya tafita cikin katon hijjab din ta kamar kullun. Wanan mutumin da tagani a cikin gari dazun shine tsaye a kofan gidan nasu ya jingina jikin shi da motar shi baka henixe, Yana dan kada makulin motar dake hannun shi a hankali, yana ganin fitowan ta ya dan fadada murmushin shi. Yana cewa barka da fitowa gimbiya sai kika gannin kwasan kofan gidan ku babu tsanmani kuma ko? Murmushi tayi tana fadin ina wuni yace shaf kinga na manta bamu ko gaisa ba ko ya kuke ya garin kuma? Ta amsa da Alhamdullahi, Yace ko da yake nasan ke bakuwa ce a wanan garin don ban sanki ba a garin namu. To nidai sunana Mohammed Kabir kuma ni haifafen wanan garin ne ina aiki a abuja ne ina da mata biyu da yara biyar. Jin haka Bintu ta dago kai tadan saci kallon shi yace yes kwari kina mamaki ko nayi yaro da,tara iyali haka ko? Gashi kuma nagani ina son karawa ta uku ke nan insha Allahu idan an yardan min. Mahaifina shine hakimin wanan garin nine kuma dana uku a gidan mu don yan uwana da kowa nawa suna garin nan da zama nine kawai Allah yakaini wani nahiyar zama. Ina aiki a Federal houses ne a can da fatan kin gamsu da bayani na. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,, A LOKACIN MU KE,,,,,,, Zau ne take a tsakar dakin da ta gyara da sunan ta wanda babu mai shiga daga ita sai kawayen ta dakan shigo gidan jefi jefi. Kwalaben kayan shaye shayen ta ne ta zube su a kasan tana dan mixed din su a cikin wani drinks dake gaban ta. Mahaifiyarta ce tashigo dakin unexpected taji muryan ta a bayan ta tana fadin, Raihanatu ina kika shiga ne haka tun safe robon ki da gidan nan ne? Daga sama taji muryan uwar nata a dakin shigowan uwar bai hanata yin abinda takeyi ba a lokacin. Idon mahaifiyar kar akan kwalaben maganin da take juyewa daya bayan daya. Wanan kuma may nene kike yi haka tambayan ta ya koma akan abinda taga Raiha din tanayi a zaune daga ita sai yar farar shimi dake jikin ta. Raiha tace cikin rashin damuwa ko tsoro magani nake hadawa na dan sha kafin na kwanta. Amma ai wanan maganin haka masu yawa kamar ba na ciwo bane? Raiha ta juyo tana facing din uwar ta take cewa, ba wai na ciwo bane ko wani abu kawai dai don naji garau ne a raina. Da mamaki mahaufiyarta ke kallon ta tace kiji garau da shan wanan uban kwalaben haka. Raiha tai murmushi tana cewa kai haba mama wanan aiba komai bane kawai dai muna shan shi ne don ya karawa mutum lafiya da karfi. Raiha, Raiha kodai shaye shayen da yan unguwa suke fadi a kan kinayi gaskiya ne. Hmmm Umma kada ki dauki zancen hassadan su a gaskiya mana hassada ne kawai irin na mutune da zaran sunga kaci gaba. Tana fadin haka ta dauki cup din da ta zuba drinks din a ciki ta kwankwade Umma na cewa ke, ke, ke Yanzu Raiha wanan uban maganin zaki durawa cikin ki kina da hankali kuwa Raiha? Haba Umma relax ba zai min komai ba don ba yau na fara shan shi ba ai. Innalillahi wainna alaihim rajiun, Umma take fadi yaunzu Raiha irin rayuwan da kika zabawa kanki ke nan? Mace da ke kike shaye shaye haka ko acikin shaye shayen kuma sai naga naki yafi ma wanda nakeji karfi. Hmmm kawai Raiha tace tare da kokarin mikewa tsaye take wani jiri ya dauke ta takoma ta zauna. Umma ta kara saka salati tare da tafa hannun ta biyu tana fadin na shiga uku ni Lami yanzu Raiha ashe da gaske kina shaye shaye, Sai kuka tajuya tabar dakin cikin tashin hankali ta samu mijin ta dake daki zaune yana shan shayin data hada mashi. Ganin matar shi ta shigo tana kuka yasa shi saurin cewa, may yafaru Lami,? Gefen shi ta samu ta zauna tana cewa malam ashe, zancen nan da muke ji gaskiya ne akan wanan yarinyar Raiha. Zancen may ye gaskiya Lami? Ya tambaya cikin son jin ba,asin zancen da tazo mashi dashi wanda bai fahinta ba. Tace zancen shaye shayen da Tanimu yazo maka dashi tana yi bamu bincika ba muka haushi da fada. Yau sai gashi Allah ya nuna min nagani da idanuwa na ta fashe da,wani irin kuka cikin tashin hankali. Malam bai san lokacin da ya cire hular kan shi ba ya fara fifita dashi a hankali. Yana fadin Inna lillahi wa,inna alaihim rajiun, yanzu ita Raihan abinda take yi ke nan har a gidan nan. Ya mike cikin sauri ya nufi dakin Raiha inda ya samay ta har syrup ya fara aikin shi a kanta tana kwance daga ita sai dan shimin dake jikin ta tai dadaya da ita. Yace ke Raiha, Raiha fa dake nake magana ko bakijina ne wai? Raiha ta dago kai cikun mayen da ya dauki caji a jikin ta tace haba Baba please ka barni barci nake ji . Inna lillahi yake maimaitawa don ganin abinda idon shi yagane mashi kan yarsu Raihanatu dake buge lis a cikin maye. Haka suka kwana cikin tashin hankali a wanan daren don sun kasa runtsawa. Malam sai fadi yake yanzu ashe kallon da mutanen shiya suke min ke nan ban sani ba suna min kallon mutumin da,ya,kasa tsare tarbiyan gidan shi. Mutumin da baida kwabo ko tace ga iyalin shi suna,min kallon mahaifin yar maye a cikin shiya. Lami tace nifa malam dama na dade ina,zargin wayewan yarinyar nan yai mata yawa wanan facali da take da kudi yadda,ranta ke so a ina take samun su haka. Mijin yace bar wanan zancen Lami yanzu zancen shaye shayen nan zamuyi muji yaushe ne tafara shi har girma mata haka. Washe gari Raiha bata tashi da wuri ba sai musalin karfe tara na safe tafito daga dakin ta don yuwan ne ya,tashe ta. Dama shi kayan maye haka yake da zaran ya sake mutum sai ya ji cikn shi tankar babu ko hanji a cikin sa. Sai neman abinda mutum zai zuba a cikin shi a haukace zai far ma duk abincin da ya samu yaci. Brush tayi ta na kokarin shiga daki taji muryan mahaifinta yana kiran sunan ta alokacin. Tai mamaki da taga har wanan lokacin baifita ba kamar yadda yasaba fita tun da farar safiya zuwa sana,an shi ta aski da yake wanzanci. Nam Baba ta amsa mashi cikin nuna jin wani dar da kiran shi don bata san wai tayi laifi ba. Tazo ta tsugun na gaban shi tana cewa gani Baba, wani irin kallo ya watsa mata amma ko ajikin ta. Gani baba ta kara maimaita mashi cikin ko in kula da kallon da yake mata a lokacin. Yanzu Raihanatu shaye shaye kikeyi a,rayuwan ki bamu sani ba ashe. Kallon inda mahaufiyar take tayi cikin wani yanayi daya ba uwar tsoro sosai don bata san yarinyar takai haka ba ma sai yanzu ta hango a bubuwa da dama daga diyar tasu. Baba bafa wani abu mai karfi sosai nake sha ba wanda kawai zai kara min karfi ne ta fada cikin nuna rashin jin tsoro a ranta. Malam baisan lokacin da ya mike ba yafara kai mata duka amma Raiha ko gezau batayi ba. Ganin haka yasa shi samun guri yazube sai wani zufa ya fara karyo mashi. Raiha ta juya zuwa dakinta, babu ko damuwa da yanayin da taga uban ta ciki sai uwar ta ce take ta faman rusa kuka wiwi. ****** ********* ****** A Abuja an kira manyan yan kwallon da aka ga sun cancanci a kira su, daga various state din wanan kasan, Inda sadauki ya samu daga sokoto aka sashi su uku suka wakilci jahar tasu ta sokoto state. An kara,fahintar dasu wasu abubuwan kara wayar da kai inda anan kuma aka yaba wa su sadauki da suka halarci wasan da akayi a kasar ghana da suka tafi. Ban wasu yan wasan suka,fara sanin su a lokacin inda akai masu bayani kan zasu dawo nan bada dadewa ba don fara wasan da zasu shiga kasashen duniya,yi. Da zasu dawo gida anbasu kudade masu tarun yawa wanda zai amfane su a rayuwan su. Daga haka suka,shirya dawowa gida a jike dasu ga mata sai wace mutum ya zaba amma shi sadauki duk basu a gaban shi saboda mace bata a cikin ran shi gaba daya bai ma,taba jin wai son wata mace ba,a,ranshi. Kuma Allah ya kare shi daga cikin matasa masu sha,awa ko yaushe, shi kawai baida, wani guri sai kawai ta iyayyen shi da yan uwan shi. Cikin dare suka sauka sokoto inda yai tashan mota ta kaishi har gida da ga shi sai, yar jakar shi kawai daya,rataya kamar kulun. Yana isa gida cikin gida ya,shiga inda ya fara karo da Nafisa kaunar shi taci kwalliya zata fita, Bata ce dashi kalla,ba,shima baice da itaba sai ganin da tayi bai da niyan kaucewa a hanya yasata dan jaye jikin ta ta bi bango har ya shige ciki ita kuma tafice daga gidan kawai. Ba sabon abu bane wanan gare shi don in so goma zasu hade da Nafisa bazata taba tanka mashi ba ita. Maji dake zaune a falon ta taji shigowan shi da sallama a bakin shi, cikin fara,a take cewa a,a kai kana hanya ne dama ashe? Yai murmushi yake cewa, yanzun muka sauka ai bamu jima da isowa ba garin. To yaya hanya ya kuma taro da,fatan komai ba matsala dai ko?. Yace cikin aje jakar shi saman kujera komai Alhamdullahi Maji mun samay ku lafiya,dai ko ? Lafiya kalau muke sai godiya ga Allah . Jin shiru yake cewa ina,su wa yan nan suke ne naji gidan shiru mana maji ta,bashi amsa da cewa. Amira bata dade da, shiga nan gidan su Aisha ba,wai zata karbo wasu takardu a gurin ta ita ko maryam tana ciki wai wanka zatayi. Ya zauna da kyau saman kujeran yana fadin kai na dai kwaso gajiya,wallahi tun safe bamu zauna ba muna fitowa kuma na kamo hanya don ban iya kara kwana can kuma. Shiru baiji ance ga abincin shi ba yake cewa wai ina ita wanan yarinyar ne tazo ta bani abunci naci yunwa nake ji Maji. Yadan fadi cikin tsigar shagwaba da kuma langabe kan shi saman kujeran da yake zaune akai. Maji tajuyu tana fadin wa Fatima kake nufi wai ko wa?. Sunan ta ke nan wanan yarinyar dake nan dakin nake nufi dai. Fatima kan ta koma gida tun gama exam din ta da tana nan kaima ai kasan da yanzu tafito gaida kai kuma ta baka abinci. Amma wayan nan sakarkarun basu san wanan basu sai faman dakilar waya kawai suka iya su. Ke Maryan, maryam fa baki jin yayan ku ya dawo ne fito ki bashi abinci don Allah. Sai ga martam ta fito daga ciki da murnan ta tana fadin yaya sannu da,zuwa wallahi banji dawowan ka ba. Nan suka gaisa da ita yana tambayan ta ya makaranta tabashi amsa da Alhamdullahi. Ta juya zuwa kitchen don dauko mashi abincin maji tace baka bugo waya kana tafe ba,balle ai maka girkin kwarai Allah yasa dai ka iya cin jagwalgwalen nasu dai ma. Taliya ce akai jeloup din shi da manja sai kifin da,suka,dan zuba cikin shi kadan. Tun a ido yaga abincin bai mashi ba shi yanzu da,yasaba cin girki mai dadi a gida ko yaushe shine za,a bashi wanan busashen abincin yaci. Yana, kai cibin farko a bakin shi yaji bai ma iya hadiye wa don salaf yake kamar ba komai a cikin shi. Kai wa yai wanan mugun girkin haka kuma,ba test ba komai abu haka,busashe dashi? Ai dama nasan bazaka iya ci ba,don wa yan nan komai basu iya ba ni ai tun tafiyan Fatima, wallahi duk komai ya jagule min. Yanzu dubi falon nan kamar ba yan mata ke cikin sa ina ga,rabon shi da samun gyaran kwarai tun Fatima na garin nan, Sai lokacin ya daga ido yabi falon da kallo yaga duk a hatgitse yake ba kamar yadda Bintu da take nan take gyara shiba. Maji tace ina da kaman wa yan nan ba zan zauna ina masu girki da,gyaran daki su sau dai suci su mike kafa kawai. Abu na farko da yazo mashi a,rai shine yanzu ya fara sanin advantage din zaman Bintu gurin Maji da take fadin zaman yarinyar yana da matukar amfani a,gare ta musanman yanzu daba lafiya gare taba sosai. Ya juya gurin maryam yana fadin idan bakuyi wa Maji abinda ya dace ba,sai wa zakuyi wa a haka zakuyi aure baku iya komai ba,a,rayuwan ku ? Amira ta shigo tana mashi oyoyo ya,dakatar da ita,da,fada yana cewa dallah gafara mara wayo kawai yanzun ace kuna gidan nan amma zaku bar muna uwa da aiki dubi falon nan Yanzu dubi girkin nan waye zai iya cin shi haka duba,fa ki gani abu haka,busashe dashi. Yamike tare da tsalake abincin zai fita zuwa dakin shi maji take cewa ai gashi nan in anyi magana kace Fatima yar kauye ce to ga ranan yar kauye yau don tafi yan bitmrnin iya komai. Shi dai yafita zuwa dakin shi ya,sakey ya,bude saida ran shi ya,baci yadda yaga dakin nashi duk dashi ya barshi hakana da datti ya tafi. Amma ai yaga da ko yana gari yakan dawo ya samu an gyara mashi shi tsaba ya shige cikin jin dadi da,shakan kamshi. Haka ya daure yana abu tsanda tsanda tunda yanzu yafara zuwa birane yana ganin komai net sabanin yadda yakw da,can baya. ****** ********* ****** Tun zuwan Kabir gurin Bintu sukai musayan nomba dashi tun wanan lokacin bata da,shakat dashi daya koma abuja ko yaushe a cikin waya suke. Tun bata saba ba tana,darrr dashi har ta,fara sake jiki tana,bashi amsa idan ya,bugo yana tambayan ta,abu. Gashi da,tambaya kamar dan jarida yake bai minti biyu bai mata tambaya kan wani abuba ko wanda ya shafi rayuwan ta ko kuma,na kauyen su. Taji dadin zaman ta da mahaifiyar ta don dan kudin da Baba ya,bata da,wanda maji tabata sai nata da tazo dashi da kuma kabir da zai tafi yabar mata su take gubtsurawa suna amfani dashi da uwarta. Kauye ne ba,wani abin saye inba,abinci ba ita kuma dama yarinya ce da bata damu da kashi kudi ba ga banza da wofi. Uwarta yanzu kan tai matukar kyau, don duk komadan nan da ciki yasa ta da,yunwa yanzu duk sun bace ta murje tayi kyau da ita. Don yanzu tana ci tana sha sau uku ga yini sabani da can da,dakyat take samun koda sau daya a wuni. Takan kira maji ko Anty Amira da maryam suyi waya dasu don su kadaine dama take da nomban su, sai wasu class mate din ta na can sokoto din. Maji takan tambaye ta Fatima yaushe zaki dawo ne sai dai tayi dariya tace mama ai zan dawo idan mamana ta haihu. Maji kance to Allah ya sauke ta lafiya ta ansa da Amin mama kawai sai dai a zuciyan ta takan ce wai sai dai Allah ni da,dawowa gidan nan kan. Amira kuma takan kira ta suyi ta mata korafi don Allah ta dawo au fitinan yaya sadauki ya ishesu duk abinda sukayi basu iya,ba,sai fada da,zagi yake masu. Bintu takanyi dariya tace halin yaya ai sai shi ni wallahi har gobe tsoron yaya nake ji gada ya,makeni. Ke nan harda tsoron shi yasaki gudu Bintu ai bari ya,shigo sai na fadama shi abinda kikace, Yanzu antu maryam ko kin fadi nai mashi nisa ina zai ganni ya,ma manta akwai wata yar kauye dama ya matsu na bar gidan nabar mashi amma yasani wallahi ban bar mashi mama ba, Au haka kikace ai gashi zaune wallahi yana jinki duk abinda kike fadi tace ai gaskiya na fadi mama ce bai so na kwace mai ni da mama kuwa sai gani sai hage mutu karaba. Ta kashe wayan dif tana dariya don tasan babu inda zaigan ta a yanzu sai dai a,waya kuma baida nomban ta ai. Amira na kashe wayan tana dariya ita,kadai Maji take tambayan ta ita dawa haka,tana,dariya ita,kadai? Nan take fadawa Maji yadda,sukayi da,Bintu da,amsar da,Bintu din ta,bayar akai. Ai gaskiya,ta,fadi yayi dawani kuma ita,dai tayi gaba kuma,bai iya,rabani da,ita din. Anyi dace lokacin da maman Bintu ta haihu mai masa tazo zagayen gidan su don haka,maji taba da sako na,barka,da haihuwa akawo wa,Bintu tabawa mahaifiyar ta. Gwagi bata,kawo kayan ba,sai ta biya gurin mahaifin Bintu ta,gwada mashi abin arzikin da aka aiko albarkacin Bintun shi. Nan tabawa ta shiga sake magana wau kura da,shan bugu gardi da kwasan kudi, yanzu ne da yarinya ta girma ta juya mata baya,bayan ta gama wahala da ita ta kama uwar ta. Ita ko uwar ba kunya don taga gurin ci shine zata wani dinga haba haba da yar da ta watsar tun tana yar ficiciyar ta sai ita tasha,wahalanta yanzun kuma,an gujeta, Gwago ce ta,bata amsa da cewa ke tabawa kiji tsoron Allah wallahi har wani wahala kikai wa Bintu gidan nan Ko dai Bintu ta,wahala dake da,yaran ki tana,maku bauta dare da,rana, Ai ke baki da ko bakin magana don kiri kiri kisa yarinyar nan takasa zama gidan uban ta don bakin matsin ki na tsiya. O lalai dangin miji dangin tsiya dama ai nasan abinda kuke fadi ke nan har kukai muna,funcin da,sai da,kuka,dauke ta don kuga yadda,zanyi. To da,kuka,dauketa don tana,min bautan da kukace na mutune ko kuwa wai. Tabawa ban dai baki ko tsunke a cikin kayan nan wadda akace akawai ita din zan kaiwa abinta don ban iya cin amana ba ni. Gwago ta tattara kayan suna sa,insa da,tabawa tabar gidan dasu zuwa kauyen da,Bintu take gurin uwar ta. Ba maman Bintu har ma Bintu din kanta saida tai mamakin wanan kyauta na bajinta da Maji ta,aiko mata dashi. Nan aka,shiga nunawa mutane kun san bakauye ba ya boye alheri komai kankantar shi . Anyi suna lafiya don itakan mahaifiyar bintu sai tace shigan Bintu Birni alheri ne a gare ta. Don wanan haihuwan da alheri yazo mata sabanin wanda takeyi a baya can busai busai sai kamay kamay kawai. Don ko Muhammad Kabir da ya mutu son Bintu yanzu sai da ya aiko da nashi alherin duk da ma Bintun bata fada mai ba ji yayi gurin abokin shi na kauyen dayasa ya saka mai ido akan al,amarin Bintu din da bata masan yasaka a saka mata ido ba. ****** ********** ****** Bayan haihuwan mama da sati biyu na shirya komawa gida garin mahaifina tunda naga mama ta yi karfi yanzu, Ba yadda batayi dani ba akan na tsaya na kara kwanaki amma naki, tsayawa. Mama tace to idan Kabiru yadawo bai samay ki ba fa nace mama nifa ba,wai yana gabana bane mutum da mata uku yaya zanyi dashi gani da tsoron tsiya. Asalima ni saboda,shi zanbar garin nan idan ya tambaya kice mai na koma sokoto gaba daya. Tace kaiyya saikace ke ba diyar hausawa ba kuma musulmai zakice kina tsoron kishiyoyi. A,a mama ba zan iya ba naga yadda mamana na sokoto take fama da,nata don haka abin tsoro yabani. Gara na samu yaro bakauye dan uwana,a zarga min dashi yafi min ruwan idon sunan muna Abuja. Dariya naba mamana take cewa kai yaro dai yaro ne ai abin sa,a ne ni yanzu da nake shan wahala a,nan kishiya gare ni? Mama,naku daban ne nace ni dai zan tafi na kwashi komatsena sai yar karamar tashar garin amma,sai na rasa mota . Akan kada,na kara kwana a garin yasa na tare wani mai mashin mukayi ciniki dashi la,asar sakaliya, sai gani garin mu har kofan dan gidan mu. Tun daga kofa nafara jin harshen mama ta,bawa tana fada da,wata yar yan uwanta da,ta dauko riko. Na,shiga gidan da sallama na inda na samu kafin na,shiga mama ta kewaya ban daki a lokacin. Dakin da nake na nufa da kaya na nasamu dakin duk kashin awaki ya bata shi kuma,wai akwai mai kwana acikin sa hakana. Ina ciki na fara gyarawa naji muryan ta tafito daga ban dakin take zuciya ta ta tsinke, don na san nadawo wa turke na mai cabo ke nan. Na fito waje a tsorace nake da ita nafito ina cewa sannu da gida mama mun samay ku lafiya. A darara ta amsa min da yauwa anga dama andawo ni dai nasan ai ba gurin zuwa sai gona. Na juya zuwa cikin dakin naci gaba da gyarawa kamar yadda,na fara da farko kafin wani lokaci dakin yai neat duk da dakin hakine da,daben kasa a,kasan shi. Na idar da,sallah magariba naji shigowan mahaifina nan nafita zuwa yi mashi sannu da,zuwa. A bazata yaganeni yace a,a Bintu andawo ke nan yaya,su wajen maman naki nace duk suna lafiya suna gaishe ku. Na mike na koma dakin mu tare da kunna dan chager daki mai aiki da battery. Daga cikin dakin namu ina jin mama tabawa tana,wa Baba na mita wai gashi na,dawo wurin ta, na kasa zama da uwar nawa. Naji Baba yai gyaran murya yana cewa tabawa ina son ki sani nan gidan uban Bintu ne bata da gidan dayafi mata wanan don haka tana da incin duk lokacin da taga dama ta shigo ta zauna iya adadin kwanakin da take son yi. Jin firinan su zauyi nisa yasa na jawo wayana na kunna kira,a ta yadda ma,ba zanjiyo hayaniyar su ba. Ban fita ba daga dakin sai washe gari tun da safe nafito na fara gyaran tsakar gidan mu dama har ta,wajen gidan. Dama aikinane da nake gari da ban nan kuma ba mai yi kowa baida lokacin yin shi. Na tara wanke wanke nafara saiga mama tafito tana wani yatsune fuska wai ita a lokacin ta,tashi daga barci. Muryan ta naji daga bayana tana fadin kada kuma mahaifinki da yan uwanku su gani suce ina sakaki aikin bauta. Bance komai ba,sai cewan danayi mama ina kwana. Ta amsa,a,wulakance tana aikin girkin dumamay tana minti kan fadan su da Baba akaina jiya da dare sai fadi take dadin abindai nima na haifa a gidan don haka na wuce gori ga kowa balle ace min ni juya ce. Ina kallo suka cinye dumay mayn su ita da,yaran ta ban damu ba na,shige daki sai zuwa rana dana yunwa zai kashe ni nafito zuwa bakin wani shago na,dan sayo garin kwaki yakai mudu biyu da,dan sugar na na,saka a hijjab dina na,shige dashi bata gani ba. Ina zaune ina sha idona yana kawo hawaye sai ga,wanan yarinyar da mama ke riko ta dan zo gabana tanayi tana leken kofan mama tace don Allah ki san min nasha nima basu bani dumamay ba wai ba yawa su Lawal taba suka cinye da ita sai cewa tayi na kankare kanzo naci. Kuma kanzon ba gishiri ba,komai wai haka zanci shi dan kadan ne bai isheni ba. Gaba daya na tura mata kofin garin nace yi sauri ki shanye kafin ta fito tagan ki tace zan koya maki munafunci. Tas yarinyar ta,shaye garin gaba daya tafita da,sauri take tabani tausayi. Tun ranan duk dan abinda naci tare muke ci da ita, komai rashin yawan shi kuwa don a daki guda,muke kwana da ita. A haka dai nai ta,zaman hakkuri a gidan mu da matar mahaifina watarana tabani abinci watarana kuma tace bayawa ancinye. A haka kwanaki suka shude min zuwa satittika har wata ina gidan mu zaune kamar wata bare can. Wata rana ina zaune na gama duk abinda nakeyi na gida kamar kullun sai ga wani yaro ya shigo yana cewa wai ana sallama da Bintu. Kafin in magana mama ta karbe da fadin wanene kuma wanan da yamman nan. Yaron da aka aiko yace yace nace mata wai kabir ne kafin mama tai wani magana na mike kawai na fada daki sai gani tayi na fito saye da hijjab dina har kasa cikin wanda Maji ta dinka min lokacin ina gurin ta. Nace mama zan fita na gan shi daga garin su mamana yazo, ban tsaya jin may zata ce ba na,sakai na fita zuwa waje. A jingine yake gabab motar shi kirar hilux irin ta,shiga kauye, ya,sanya wata koriyar shadda da akaiwa dinkin Jamfa harda hular ta kalar kayan. Tun daga fitowa na yake sakar min murmushi, sai dai wanan karon ya dan kara min hasske da kiba kadan. Barka da fitowa, kalman da ta tare ni dashi ke nan da na iso inda yake tsaye, Tuni naji wani wani kunya ya lulubeni saboda tafiyan da nayi ban fada mai ba kuma,nan garin mu da nazo ba,services ko dayaushe. Na dan rusun na kadan na,gaishe shi, tare da,tambayan shi yaya hanya. Cike da,fara,a yace hanya Alhamdullahi mai gaskiya, Murmushi nayi nace gaakiyan may kuma nayi har ake kiran min ita cikin kunya na,fadi hakan. Sai murmushi naji yayi ya dan kalleni ya kada kan shi kawai, Yace wallahi Fatima baki kyauta min ba haka,kawai ki kama hanya ki wuto baki fada min ba ko a waya, Sai kawai da naji shiru natura a,diba min ko lafiya ake ce min wai ai kin dawo nan. Gashi kuma ban samu zuwa ba,don an turani wani course a lagos sai last week na dawo gaskiya banji dadin yadda kikai min ba. Cikin yar muryata nace to kayi hakkuri nima,tafiyan tazo min bashiri ne. Yace gaskiya banji dadi ba don sai ma na,fara zargin kodai ban samu karbuwa bane a gurinki shi yasa. Dan satan kallon shi nayi tukun, san nan nace a kunyace ,a,a ba hakana ne gaskiya. Sai naji ya sauke ajiyan zuciya yace tau Alhamdullahi, Amma kuma kin shirya zaki iya auren mai mata har biyu ki zama ta uku? Dammm naji gabana ya fadi don an tambayeni abinda nafi kowa tsoro yanzu watau kishiya. Na dan kwantar da murya cikin dakewa nace idan Allah yayi hakan ne ai ban isa naja da ikon shi ba. Sai ya dan zuba min ido can yace tau kin gama magana ke nan ai tunda kince Allah. Ban nuna wani alama najin tsoron maganan shi ba amma sai nace ai Allah shike komai dama. Nan dai muka dan taba hira dashi yana min karin bayani a kan, shi. Yace matar shi ta farko yar uwarshi ne garin su daya auren gida akai masu shida ita duk da dai su suka hada kan su. Azuciyata nace kaji matsalar ba yace sai tabiyun ita soyayyace ta hadani da ita kaunar abokina ne dake sokoto lokacin ina,aiki a sokoto kafin na koma Abuja mukayi aure da ita yanzun yaranta biyu dani. Ya,kare da,cewa sai kuma yanzu da wata farar tantabara ta,sace min zuciyana a lokaci guda duk da can baya banyi niyar karin aure ba ina ganin matana biyu sun isheni rayuwa. Sai gashi ganin farko da nai maki naji kin kwanta min a zuciyata fiye da tsanmani na. Dafatan zan kara samu karbuwa a gurin ki bayan mun dan taba hira yake ce min zai koma don gobe yake son ya koma,sokoto ya dauki matar shi tare suka,shigo amma ya barta sokoto taga gida. Yace min ina zan samu yara su sauke min kaya a,bayan motan shi Nace cikin yar murya lah, dama ka barshi zuwan da zakayi gurina shine harda dawainiya. Yace ai nasan baku rasa ba amma ni ban saba zuwa guri babu tsaraba ba. Yaran makwabtan mu dake wasa a kofan gidan su na kira inda suka shiga da kayan cikin gida. Nayi sa,a mama tafita zuwa uguwa don bata zaci lokacin zai tafi ba nasan da bata fitaba a lokacin. Kafinta dawo nida Farida yarinyar da take riko muka tsince kayan tea da su indomie muka,boye inda bata gani. Sauran muka barsu kofan dakinta inda inta dawo zata gani. Tana ko shigowa tai tozali da kayan sai cewa tayi cabdi jam wanan kayan alherin kuma haka fa nake gani. Farida tabata amsa dace wa Bintu aka kawowa su, mutumin da yazo kafintai wani magana sai ga babana yadawo daga gona shima tambaya yake. Tace yarka aka kawowa su sai ka tambaye ta ko waye nidai in kun kwaso rigiman birni babu ruwana. Allah ya,sauwaka babana yace sai ya samin kira nafito ina mashi sannu da zuwa. Yakece sai na dawo na samu wanan uban kayan haka na tambaya akace waikece aka,kawo wasu. Nace eh Baba Kabir ne dan hakimin Rabah yakawo min su dazun dayazo. A ina kika san shi Bintu, Baba ya tambaya cikin son jin inda na san Kabir, nace Baba da naje gurin mamane shine muka hadu dashi a can. Allah ya kyata yace inda ya isa gurin kayan buhun shinkafa dan gote sai jarkan mangyda da doya mai yawa sai tumatur din leda katon guda da taliya leda biyu, Dankari inji Baba duk wanan din muke dashi haka nace eh Baba mu yakawo wa tsaraba yace, Baba yace Bintu idan kin san bakya son shi kada muci kayan shi yazo yai muna,tasau watarana nidai k8nga banda,shi. Shiru nayi ban yi magana ba baba ya juta zai futa nace baba zan dauki doya da taliya naba su Ama don su suka kwaso min kayan zuwa cikin gida. Yace hakan na da kyau ki baau yadda ya dace azato mama tabawa bazata kalli kayan ba amma dana dauki doya manya zai kaiwa su Ama sai ji nayi tace kai amma kedai baki san ciwon kanki ba, Wana abin duka zaki basu don kawai sun kwoso maki kaya maza rage su kinji nace to mama. Nan aka,shiga sha,ani da kayan mukan mun boye namu bata sani ba ni da farida mun samu na karyawa safe da yamma mu faki idon ta,muyi amfani da abin mu. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,, A LOKACI MU KE,,,,, Zancen neman da Kabir yake min ya kewaye kauyen mu,sai ga yan uwan shi har gidan mu sunzo gaidani wai kuma suga ko wacece ni din. Gami kuma da nuna goyon bayan su dari bisa dari akan neman da dan uwan su ke min. Kamar yadda,dangin miji suke nuna goyon baya idan dan uwansu ya,tsiri aure, komai mutuncin da akeyi da uwargida sai an samu masu hakan daga dangin shi. Nima hakane ya kasance dani don yan uwan kabir maza,da mata haka suke shigowa ganina,tunda ance masu nima ba a kauye nake zaune sokoto nake zama. Basu san cewa ko a,sokoton labe nake zaune a gidan mutane kamar kuku. A gaskiya da farko naso Muhammad Kabir kodon na samu inda na labe na,rufawa rayuwa na,asiri na huta da guzuban mama tabawa da nake ciki. Yakan zo kusan duk karshen wata gida cikin irin zuwan da yakeyi sai yazo har garin mu da dan tsaraban shi na abin arzki yakawo muna. Wata rana Kabir yazo wurina sai dai wanan zuwan bai dade ba kamar yadda ya saba dadewa idan yazo inda nake. Ya ce zai koma na ya bude mota ya miko min wasu kaya dinkakku yake ce min anko yai min tare da,sauran matan shi. Na karba nai godiya sai kuma ya kawo kudi masu yawa ya bani, amma sai nace ya,bar kudin kayan ma,sunyi min. Amma sai ya,aje min kudin saman hijjab dina ya,shiga motan shi sai horn din shi naji na,dan daga kai ya sake min murmushi tare da jan motar shi yabar gurin. A dakin mu saman tsohuwar katifan kadan da muke kwana akai amma na,gyara, shi mutum bai sani tsohuwace ta yagalgale saboda bed shirt da na,sa na,rufe shi lif ba,a ganin sirin ciki. Dinkin kayane irin ta yan birni jakkuna da,takalma masu tsada sosai, sai kayan makeup set mai kyau dasu turaren suma masu kamashi sosai. Kayan abinci yadda ya,saba kawowa haka ya ke jibge su a,kofan gidan mu yanzu tabawa shiru kake ji tsakani nada ita,sai lalashi. Afili amma,a,kasan zuciyar ta,tankar ta soke ni takeji a rayuwan ta don kishi na take balain ji duk kiyayyan da,takewa uwana ya koma a kaina yanzu. Sai dai tana dan waye wane kawai don tasan wani lokacin nima nakan dan tsula mata tsiya yadda naso. Don ban san ya,akayi tasan muna boye wasu kaya,ba,sai ranan ta zaci ko yanzu iri dane da,zata kwace min abina tabawa diyan ta har yan agolan da tazo aure dasu gidan mu sun fini dara a lokacin. Sai ganin Tabawa mukayi a kofan dakin mu tayi tsaye kerere ta re da,daga labulen dakin cikin tijaran ta na yan iskan matan kauye take cewa, Ke Bintu kwaso sauran kayan nan da kika,boye wanda aka kawo muku wai ke munafuka,shine kika boye kayan shayi wai don kada na,sha, Ti jiya banyi barci ba ina jinku kuna sha ke da muna fukan can Farida, don haka na leka naga may kuke don haka kifito dashi nan. A zatonta zan mike na dauko mata kamar yadda da can nake mata cikin rawan jiki. Amma,sai taji murya na yau ina cewa, Eh ko kingani fa, Sai may, Ina dai ba,sata,nayi ba,nawane ni aka,kawo wa ko ? Don haka sai yadda,naga dama da abina Farida ce idan kince na barbata abarta mana yunwa ya kasheta. Baki bamu abinci yadda ya dace sai dai kibawa diyan ki Don Allah yai muna mafita shine kuma zaki nuna halin ki na hassada haka. Eh lalai kuwa Bintu sai yau na,kara yarda kin shiga Birni tunda har ina fadi ki fadi haka, Nace mama kece kikaja hakan don yakamata ace yanzu na ci ragowa gareki ko dan dan girman da na,kara. Amma ke kullun sai kokari kike kiga kin mayar dani baya kin tausheni kin ha,ince ni kin fifita diyan ki a kaina. Don banda,uwa agidan ai ina dai gidan gidan ubanane dole ko abarni na zauna ciki. Nan tafara rafa hannayen ta cikin mamaki da lalami tana fadin eh lalai zaman bariki ya nuna kan shi yau kan. Baba yana dawowa tafara fada mashi bata kai karshen zance ba yakwala min kira nazo, nace gani ba. Yace Fatima yanzu na dawo gida maman ku ta tare da,zancen da ban san halinki bane. Nan na koro mai duk kan maganan har karshen yadda mukayi da ita,da,safe. Ya juya gurinta yana cewa Tabawa kiji tsoron haduwar ki da Allah horo da,yunwa ko dabba,ba,ai ma,shi balle mutum dan adam mai tunane. Yanzu ba gashi a,sana din ta alheri yana sauka muna duk karshen wata sai yaron ga dan gidan hakkimi ya kawo muna abinci ba. Nan dai har sun hau da Baba ko may ta gani sai gata ta sauko don kanta ta, dawo tana cewa haba Bintu ke diya tace kada ki yarda mutane su zuga ki ki min rashin mutunci suyi dariya. Nace komai ya,wuce amma da safe indan Baba ya fita sai ta turo yaran ta da,kwano wai na yan mata kayan shayi ta dan kada. Da,nafita iyawa sai na,zuba mata dan kadan a cikin roban nace akai mata hakana,baida yawa. Shine samun saukina a gidan mahaifina da mama tabawa yanzu kadaran kadaham muke da ita. ****** ********* ****** Shine yau da Kabir yazo ya,tafi da,wuri ashe tare da,matan shi yazo sun zo yin bukin wata diyar yayan shi ne a,Rabah. Shine yazo da iyalin shi gaba daya amaryan shi bata zama a,kauyen sai dai tazo ta,wuni takoma gidan su. A nan aka,samu wata,tsegumama ta tsegunta mata zancen neman auren da kabir keyi yanzu. Nan ta,tayar da,hankalinta sosai har ta tambaya,akai mata,kwatancen gidan mu sai gata,ita,da,kannen zawarori biyu. Ni dau ina daki kwance ina kallo a,wayana,da,aka,karbo min caji sai ji murya mukayi ana,cewa,da karfi sallamu Alaikum ko nan ne Kabir Rabah ke neman aure a fitsarance suka shigo muna gidan. Eh nan ne inji Farida da,bata san da may suka shigo muna ba, Eh lalai ashe dole a haukace a so mai mata,biyu an matsu a,tashi gidan haki akoma alminium zalla. A,a sannun ku da,zuwa sai wani kallon banza suke watsawa,mutane su ga yan birni a dole. Ina, ita gajar da kabir din ya,wullakanta kanshi yazo har nan gidan wai neman aure. Saye nake da,wani dogon riga baki cikin wanda yaya,sadauki ya,sayo muna,ghana, a jikina don dashi naiwa Kabir kwalliya da,yazo don haka ban cire ba yana a jikina. Nai rolling din kaina,da dan kwalin kayan tsaye nayi harde da,hannuwa,daga kofan dakin mu ina kare masu kallo irin wanda,suke ma gidan mu da yan uwana . Sai da suka juyu ne mukai arba dasu, gaba dayan su ido suka tsura min, A cikin min kallon kurrullah tun daga kafana gar zuwa kaina o lalai kice min farar fata yabiyo mana kin sanshi maye farar mace ce ko manyace. Nace ballw ba,farin ya,jawo shi ba,nan sai hali, don may yuyuwa yaga abinda ya,rasa,a,gida ne yazo nan. Ke kama kanki don ko ba,a,fada,ba,nasan kece yake nema don kece ki kadan yi kama,da zubin yan birni kadan. Ba shirmay ya,kawo mu ba ni matar Kabir ce ta biyu na,zo ne nai maki kashedi akan mijina,wallahi, Don ko ita bakauyar dake gida, ban dauke ta wata tsiya ba balle ke dake shirin kawo kanki. Nace hmmm mijin ki ko mijin mu yar uwa, ba,a kara aure aka,auro ki ke naga dani dake din duk ba,matan gado bane, Balle ki manta ki kirashi da su nan wai mijin ki aikin makara da,baki tsaya kin auri wanan mai matan ba da,sai ki tsaya,ki auri wanda baida mata,a kiraki matar mai shi. Yanzu ko tunda mijin wata zamu aura da ni dake kinga kalman mijin mu ya,shigo ke nan. Ke wallahi, kama kanki dama ku yaran kauye haka kuke da iya magana tankar tsofafin mata. Nace mazan mu da matan mu kuwa din shi kika gani ga bakauyen mijin ki har ya,rude ki kika,aure shi. Sosai mukai musayan harshe da su su fadi in fadi wai tana min kashe di na rabu mata da mijin ta,inva haka ba zaki shigo ki samu balai a gidan shi. Nace kai dama baki zo ba da,ban san balai ke gidan Kabir ba Don da ma kabir bai a,raina saboda bai min ba amma yanzu zuwan ki sai naji ina,matukar sha,awan auren shi na zama koda ta hudu ne. Gaskiya,zuwan ki yai min rana sosai din haka kikoma,ki fara shiri nima zan shigo da shirina sai na zo. Ina fadin haka na juya zuwa cikin daki dama gidan ya fara cika da,mutane don jin hayaniyar da akeyi yayi yawa. Mata ko suka,saka,su gaba da ihu da,tur da,Allah waddai da halinsu kishi wai hauka,ne da zaku zo gari wa gari ku na kishin hauka wa mutane. Sai bayan naji tayar da motan su na sauke ajiyan zuciya saboda karfin halin da nayi don duk a,tsorace nake, kada suyi min dan banzan dukan tsiya tunda nice banda gaskiya, nike bi masu mijin su. Lokacin da,labarin cin mutuncin da matar shi tazo har gida tai min hankalin Kabir yai matukar tashi sosai tunda safe sai gashi kofan gidan mu. Da Baba na yafara ganawa, kafin daga baya asa a kira ni nafito ina daure da fuskana tamau, Tun fitowa na,Kabir ya kura,min ido yana kallon yanayin da,na,fito dashi don yana son fahinta da sauki ko akwai magana. A mutunce na durkusa na gaishe su sannan na koma gefe nace Baba gani, Mutanen da Kabir yazo dasu suna zaune saman tabarman da aka,shimfida masu idanuwan su a,kaina karrr, Baba yace Bintu Kabir ne ya samu labarin abinda matar shi tazo hannan gida tai maki shine yazo ya,bada hakkuri akan sabanin da aka samu da ita. Kaina na sadda kasa nace cikin yar murya Baba gaskiya ayi hakkuri da wanan zancen don tun ba,a shiga ba an fara irin hakan Ina ga in an shiga gidan baki daya sai ai marus ke nan lokaci daya sukace ,a,a wanan ma,ai baiyuyuwa sam. Duk da sun fahinci kan zance na ina nufin nafasa ke nan sai suka shiga ba da baki da gyaran zance . Shiko kabir yana zaune yai shiru kawai abin duniya ya,kai mai ko ina abinda matar shi tazo tayi ta bashi kunya. Baba dai da yaji irin yadda suke bada hakkuri ni kuma na kafe akan sai dai a,rabu. Sai baba yace Bintu tashi jeki ciki kawai ma,karasa,maganan dasu. Namike nashige ina jin yadda Kabir yake sauke ajiyan zuciya daga inda nazo wucewa ta gaban shi. Ban kara jin zancen ya tashi ba sai bayan kwana hudu sai gashi yazo har lokacin bai sake jikin shi ba dani. Na fito saye da zani da rigar atamfa mai ruwan jan kalla, dinkin shi yai matukar karban jikina da kyau. Son in mashi kwalelenka, ranan gyale na yafa ajikina sabanin hijjab din da ko yaushe nake rufe jikina dashi. Na durkusa na gaida shi a cikin ladabi da biyayya tare da,tambayan shi gajiyan buki. A,sanyayw yace Fatima kinga yadda kika,wahal dani da,kalman ki dakike fadin wai kin fasa aurena. Don Allah Fatima koda nine nai, maki laifi, kada kice kin fasa aurena, don baki san irin wahalar da na,sha ba na ganin za,a raba ni da wanan kyakyawan halittan mai suran larabawa a hannu na. Don Allah Fatima koma may ye kada ki kara cewa zaki rabu dani akan wata, wacce dama ita bukatan ta ke nan nayin haka. Wallahi ranan da,muka,bar nan nayi tunane dubu a raina don sai na kasa banbance so na yasa kika ce hakan ko kina. Nan yadan zubo min ido yanaxmai kare min kallon kurullah , akunyace na dan rufe fuskana da hannayena . Yai ajiyan zuciya yace nagode Fatima don ko hakan ma,sheda ce ta kin sauko zaki yarda dani. Mun jima muna hira dashi yana bani labarin irin fitin matar tashi saratu yadda sukw kwasan masifa da uwargidan shi a kan lalai ita ala,dole abar mata miji ita kadai ko da ya zo tafiya sai yace kin hana ni shakat wallahi Fatima gashi haka nazo ban riko maki komai ba. A hankali nace mai babu,komai, ko haka,na gode ai, Ya ce sure ? Nace, mashi insha Allahu. Haka yatafi ba don ya,so ba yana ta,faman bani hakkuri ya,wuce abinshi. Anyi wanqn rikicin da Sati biyu ina gidan mu gaban iyayyena hankali a kwance abina na fitar da komai a raina, Ina zaune ina gyaran ganyen da mama,tabawa tasayo lanbu zamuyi miyan dare dashi. Ina cikin gyaran ganyen ne sai naji karan diran mota ta tsaya a kofan gidan mu. Dan dakatawa nayi da aikin nawa ina sauraren ko anyi bakine gidan daga bisani dai naci gaba da aiki na. Gwago na ce ta shigo gidan da sallaman ta saura kiris na zubar da ganyen da nake gyarawa don murnan ganin ta danayi. Fuskanta dauke da yalwatacen fara,a take ce min dana karaso gurin ta cikin daukin ganin ta. Bintu baki da kirki banzaci zaki zo ki share ki zaman ki haka a kauye kin bar uwar dakin ki sai damuna take tunda na koma. Ledan dake hannun ta na karba daidai lokacin da mama tabawa takw dawowa da makwabtan su. Mama tabawa tace a,a yau gwagon yara ce a garin kwana biyu kin shige birni abinki. Nan dai suka dan taba wasa tsakanin su sai kuma gwago take tambaya yayanta yana gona ke nan ko bai dawo ba har yanzu kuma tana son ganin shi. Ba ,a jima,ba Baba na ya dawo daga daji, sun jima suna hira da babana wanda akasarin hiran akan yar uwar suce da gwago tai jinya takare. Can tun ina jin hiran su sai na bar jin tashin muryan su, ma,ana dai za ai magana ta,siri a tsakanin su ke nan. Zuwa can Baba na ya daga murya ya kira ni nazo, na,samu guri dan nesa dasu kadan na,tsugun na. Baba na yace Bintu gwagon ki tazo tafiya dake ne akan umurnin mijin uwar dakin ki, na can. Don haka,sai ki harama ki shirya ku kama hanya don kinga mota,sukutun ya bayar azo a tafi dake don ba,ayi zaki zo ki zauna haka,ba harki dade. A take na bata rai na,tare da,dukar da kaina a kasa, baba na yace ko baki ji may nace bane Bintu. Cikin yar karamar murya nace naji Baba yace tau yau din nan ki hada kayan ki ku tafi tunda sunyi mutunci haka nima idan na samu lokaci wuri yasha iska zan shigo naga inda kuke. Na dago kai din nai magana gwago ta watsa min harara dole na noke kai bance uffan ba. Namike jiki ba karfi idanuwa na,sun ciko da,hawaye amma,ba,wanda ya kula da damuwa na nafara ashirya kayana. Kafin sallah magariba haka gwago tace sai muyi hara man tafiya kada muyi dare sosai a hanya. Nan na,dauko yan abubuwa nabawa Farida yarinyar da zantafi na bari cikin uku ban mama tabawa, Komai da muke boyewa,nabar mata,ban dauka,ba, sai kudin dana,bata ta boye ta tafi garin su dashi idan taga wuya,zai kashe ta a gidan. A sanyaye na gama hada kayana raina a bace don kwata kwata ban son komawa gidan su maji don bani bukatan zama cikin wanan babban gida mai cike da tarin rikici a cikin shi. Saboda wancan karon ma banji dadi ba don a tauye nake cikin su sai dai na kulla a raina wanan karon kan zasuga canji sosai a gare ni don su barni na,dawo kauyen mu. Munyi sallama da kowa mun kama hanya sai dai kallo daya ya ishi mutun sanya alaman tambaya a kaina din yadda nai kicin kicin da raina. Sai ranan naga mama tabawa ta,tausaya,mun tana fadin haba baban binta in bata son zuwa abarta mana. Daga Baba har gwago na ba wanda yabita kanta sai kyaleta sukayi kawai. Mun hau titi da kyau mun saki hanyar dajin mu gwago ta kalle tana cewa Bintu kin bani mamaki sai kace wace za,a kai mugun guri. Acikin wata raunaniyar murya da take gap da,narushe da kuka nace gwago bawai mugun wuri bane. Amma zama gidan da,baka,da,alaka da kowa,sai zaman girma,da,arziki kawai, shine nake jiyewa. Tace da kika zauna wancan karon anyi wani abin ne sai da na nisa kadan nafara fada,mata,duk yadda aka,kwashe da,bata,garin. Tace ni na sani ai ba yau ba Hajiya kubura munafukace ta,karshe wallahi ko. Tsayin lokaci muna,tafiya muna hira har muka fara hango cikin garin sokoto. Unguwan sama road muka dosa inda muka tsaya a kofan gidan Alhaji habu. Lokacin dare yayi ko don har anyi sallah isha,i don haka cikin gidan muka shiga kai tsaye. Na zaci gidan mu zamu shiga amma,sai naga sabanin hakan kawai mun shiga gidan masu hali. A dan tafiyan da,nayi na,samu canji na sauyin launin gidan sosai an canza abubuwa da dama a gidan. A kofan da aka,sake wanda ban zaci na,maji bane muka tsaya tana sallama daga kofan shiga. Muryan maryam ce naji tana a,a mai masa,oyoyo harkin dawo ashe? Sai tafara leken bayan gwago tagani ko ita kadaice tazohangini tayi ina,saye da lace din da Kabir ya dinka min da matan shi cotton lace ne mai laushi sosai da duwatsu caaa a jikin shi. A razane tace maji yau kan ga yarki ta dawo gare ki gwago ta cika alkawari kowa ya huta dada. Da sauri ta karaso gareni ta rugumay ni cikin jin dadin ganina a lokacin. Jin abinda ta,fadi yasa Amira fitowa daga dakin ta cikin sauri tana min sannu da zuwa cikin murna da jin dadi itama. Maji tafito a hankali daga daki ganin yanayinta yasani saurin fahintar bata da,lafiya a jikin ta. Inda,take na nufa da,sauri na,fada jikin ta sai ta rungumayni cikin jin dadi. Ta,dago kai ta kalli gwagona tace mai masa nagode da,wanan karamcin da kikai min dawo min da Fatima,a kusa dani. Kai amma dai Bintu badai a kauye kike ba dai ko gaba daya kin canza kin koma wata big girl dake haka. Nan aka faea hiran yaushe rabo bayan nadan huta anmin tayin abinci nace na koshi. Sai Maji tace naje na gaida Baba kafin ya,shige da sauran mutanen gidan gaba daya. Ido na,runtse gami da,cewa ya Arhamanin Rahimin, ahankali na mike nafita,duk kallo suka,bini dashi. Ina fita maryam tace maji gaba,daya, fa diyar ki ta,sake ta canza kyaunta ya,dada,fitowa a fili, jita kamar wata wace take zaune a abuja ba kauye ba. A falon Baba na samu hjy kubura na shiga da sallama na itace tafara cewa wa nake gani haka kamar Bintun hajiya maijidda. Na karasa inda suke gefe kadan na tsugunna ina gaishe su Baba ya nuna j8n dadin gani sosai tare da min ba,a naje gida na lake na manta da karatu a gabana. Na dan kai lokaci a gurin Baba yana dan min tambayoyi a kan noman mutanen kauyen mu nai masu sallama nafita daga dakin. Dakin Umma da nake jin haya niyar su na fara shiga duk sunyi mamakin gani na a wanan lokacin da kuma yanayin da suka ganni ba,wani fita hayacin da nayi banda kara kyau. Nan dai duk na zagaya nagaida su na,dawo dakin mu nan aka zauna a ta hira inda maji da gwago suna can gefe suna,maganan su ta mayan wanda bamu san akan may sukeyin shi ba. Sai dai yanayin Maji ya nuna min cewa tana a cikin damuwa sosai ko ba,a fadi ba. Ban dade dasu ba na mike ina fadin zanyi sallah dake kaina. Nan dai bayan na idar na mika,kukana ga Allah akan ya,kareni daga duk wani rintsi ko matsalar da zan fuskanta agidan mutane. Ban fito ba na koma na kwanta amma kuma na kasa barci sai sunayen Allah maigirma nake kira ina neman agaji a gurin shi. Tun dawowana kula,da lafiyan maji ya koma kaina ko yaushe ina daki tare da ita. Banga Sadauki ba kuma,ban tambaya ko ina yake ba nasan dai kila baya garin ne. A hankali natsuwa yazo min da zamana dasu don suna nuna min kulawa sam mutum bai gane cewa ba Maji ce ra haifeni ba a gidan. Satina biyu a,sokoto nagane yanzu yanayin gidan ya kara canzawa sosai ba ruwan wani da wani a gidan har yanzu. Amma,akwai ci gaban rayuwa,sosai da,suka,samu don yanzu budi ya kara sanuw masu sosai. Hankalina yafara kwanciya sai dai kullun ina kewan iyayyena da yan uwana adan zaman da mukayi da,mamatabawa da sauko da,akidar nuna min tsana,a fili datakeyi. Kuma wani abinda ya,tsaya min a,rai shine tunanen Kabir yadda zaiji idan yazo ya,samu banan nan nabar gari bada sanin shu ba. A haka takardan makarantana ya fito wanda ban san baba yai min process ba saida yazo a hannuna. Ranan nai murna da farinciki garda kuna don murna,saboda ban taba zaton zan samu ci gaba da karatuna ba. Na fara zuwa makaranta tare da Anty maryam muke tafiya don makarantar daya da ita state university muke. Wata rana mun taso daga makaranta ga hadari ta gauraye garin da kyat muka samu Napep din da zai kawo mu gida. Ganin iska da kura ya,taso a lokaci guda nace wa mai Napep malam don Allah ka,samu dan guri ka Parker har iskan nan ya dan rage yawa don tafiyan mu a haka hatsari ne. Guri ya samu kamar tadda nace ya dan tsaya a gefen titi kamar ance na daga kai na hango Nafisa a cikin motan wani matashi. Yanayin dana ganau yasa gabana faduwa da,sauri na juta gurin da Maryann take zaune sai naga hankalinta a,waya yake ita, don haka naja bakina nai shiru ban fada mata ba. Can naji mai Napep na cewa bari mu lalaba don ga alamar ruwa nan tafe da sauri yake tuki sai gamu a unguwar mu har kofan gida yakaimu daidai ruwa yana fadowa da karfin Allah. Take ruwa ya zubu ga iska sai kamshi yanayin garin ya canza launi alaman sabon damana yazo ke nan. Haka muka sauka shiga gida ruwa,na kada mu yana daga muna mayafin jikin mu. Yaya Imirana na hango can tsaye daga kofan part din shi tawani kura muna ido kamar tsohon maye. Da,sauri muka nufi hanya shiga cikin gida duk habar kafan mu iska na dagawa yana fita a fili. Daga inda yake naji muryan shi yana fadin kai ashe cikan nan tadawo ne tubarkallah dai kan komai tsab wallahi akwai kayan dadi a gurin nan. Banzaci maryam taji shi ba saiji nayi tace dan iska a haka dai zaka kare gindin mata. Mukan da,sauri muka karasa ciki muna kankamay kayan mu daya jike sharkaf da,ruwan da,akeyi. Da karfi maryam ta rura kofan falon maji muka fada ciki a guje saukar da ajiyan zuciya nayi yain da naji ruwan bai dukan mu. Ashe maji na,falon cikin damuwan rashin ganin mundawo kafin ruwa ya fado din sai ce muna take sannuku ku shiga ku cire wa yan nan kayan kafin sanyi yakara hawan ku. Sam ban lura da mutum a zaune ba a lokacin sai ji da nayi Anty maryam ta,saji kara da karfi. Da sauri na juya zan kona,waje da gudu sai naji tana fadin oyoyo yaya sadauki. Najuya da sauri inda naga ta nufa yana zaune fuskan shi dauke da murmushi. Yace jeki cire kayan sanyin nan kafin yai maki illa, Cikin shagwaba tace yaya ni har na manta dasu ina murnan ganin ka ai. Nikan ban tsaya ta kan su ba na,shige daki nafara rage kayan jikina tare da zuwa faban mirror dakinmu nayi wata futu, futu dani don jikewan danayi. Na fada ban daki nawatsa ruwa tare da,dauro alwala nazo nai sallah. Saida na,gama komai nafito falon ina,saye da,wata doguwar riga dark blue doguwa ce rigar har kasa hannun ta shara shara nazo na zauna falon har lokacin yana zaune suna hira da kannen shi. Zamana yai daidai da kiran wayana da akayi na dauka ina mamakin wanda ya kirani a wanan lokacin haka. Sai na,dan basar ban dauki wayan ba don ban san mai kiranaba alokacin. Sai kuma ga,kiran ya kara shigowa again na dauka da,sallama ban damu da cewa wai na daga daga falon ba. Don nasan daga inda suke babu wanda zai iya jin abinda nake fadi don tsabar kwantar da muryana da keyi. Bayan na gaisa da may shi na nuna bangane mai magana ba. Yace haba Fatima na zaci ko a mafarki kikaji muryana zaki sheda ai tau Kabir dinki ne wanda aka gudo akabari a kauye. Maganan shi ce ta dab sani dariya sai duk suka juyo gareni hardashi suna min kallon mamaki. Nan na,fara bashi hakkuri ina,fada mashi yadda tafiyan yazo min a bazata nadawo sokoto. Amma yayi hakkuri dan banda nomba shine yasa ban fada mashi ba yakara complain kan cewa ban damu dashi badaine tasa hakan. A hankali nace na tuba sake ba insha Allahu, abin mamaki sai naji ya kwashe da,dariya tana is alright hakan ma yafi min don yanzu zan dinga samun ki available, Uhhm kawai nace cikin murmushi. Ina dago ido mukai arba da yaya sadauki da ya maka min wata uban harara na kawar da kaina tare da ci gaba da waya na. Kabir yace min yanzu yana hanya zai tafi wani gurin aiki ne amma idan ya,dawo zai kirani. Nace tau Allah yakaika lafiya Allah ya,tsare min kai. Ina kara dago ido muka kara arba dashi dole nace mashi cikin yar murya sannu da zuwa yaya ya hanya. A daure ya amsa min kamar wanda akasa shi amsawa dole. Nikan namike zuwa daki sai Maji take cewa ina kuma zaki ba,aci abinci ba nace sai anjima zanci mama. Kai Fatima kina dai wasa da cin abinci har yanzu mutum haka bai damu da cin abinci ba. Nikan na shige abina daki ban tsaya ta kansuba don wanan mai mugun halin dake zaune a falon. Ban dade da shiga ba naji ruwa yakara tsinkewa kamar da bakin kwarya. A hankali na mike don na rufe window din dakin mu dake bude don feshin ruwan dake shigowa. Karan mota naji za,a fita daga gidan mamaki ya kamani wake da karfin halin fita daga gida a,wanan lokacin da ake tsula ruwa haka masu yawa. Mantawa nayi ina,son nasha ruwa sai na koma falin na dauka nan nasamu Maji na magana cikin takaici. Tana cewa yanzu fita yayi cikin wanan ruwan haka ba ko ina zai tafi ba sai gurin shegen shaye shayen su. A duke nake gaban fridge ban san lokacin da na dago ba nace mama yaya ya koma shane kuma ? Cikin takaici tace min Fatima bari ke dai, Allah dai ya kawo min saukin wanan al,amarin kawai. Abu sai yayi kamar ya sauki sai kiga yaron nan ya kuma koma ma halinshi lokaci guda. Nace anya mama wanan abin ba ci gaba ake da tufka ana,wal,wala ba kuwa? Amirah tace nima dai hakanace daki na koma hankalina a tashe da zancen danaji mara dadi. Sai yanzu nagane abinda ya jawa maji ciwon zuciyan da akace yana barazanan kama ta. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,, A LOKANCIN MU KE,,,,, Da, tuna ne na kwanta barci bai dauke ni ba har tsawon wani lokaci ga ruwan da akeyi ba a dauke ba har cikin dare sai tsula ruwa ake kamar da bakin kwaraya. Hasken wutan mota ce ta haska dakin da muke0 kwana a ciki nida Anty maryam don gyaran da akayi dan yi a gidan yanzu. Part din Maji ne farkon shiga gidan don sauran suna daga ciki suna ganin sun shiga ciki kusa da part din maigidan. A hankali na mike zaune na juya inda maryam ke ta barci ta yarda wayanta sai massage ke ta shigowa mata. Window dakin na dan leka naga, mai shigowa a lokacin yaya sadauki na hango yana kokarin rufe motar shi. Tafiya take a cikin rangaji irin nasu na yan maye kamar zai fadi ya dan dade a tsaye kafin ya bude kofan dakin shi ya shige. Na koma bakin gado na zauna zuciyana naji ba dadi ko kadan tausayin Maji ne ya rufe min zuciya na. Ina nan zaune naji motsinta hakan yasani sanin cewa batai barci ba idon ta biyu ke nan tana dakon dawowan dan ta tilo daya da masifa ta haushi na shaye shaye. Haka na kwana ina matukar jin tausayin ta a raina har garin Allah ya waye muna. Ranan bamu shiga school duk muna gida gaba dayan mu bayan na gama muna,abin karyawa don yanzu Maji ta raba muna aiki kowa da ranan girkin ta. Na fito saye da wani buje da riga dinkin yan Niger, da hjy kubura ta sayo muna da suka je da Baba ta sayowa duk yan matan gidan hardani na samu shiga. Ina zama nake cewa mama ina key din dakin yaya mu gyara mai, da sauri maryam take cewa nikan ba zan iya ba nagaji gaskiya yau hutu nake son yi. Ina ganin ai yana ciki don banga ya shigo ba Amira tace naga fitan shi da safe da kayan wasa a jikin shi. Mikewa, nayi tsam na dauki kayan gyaran wuri na fice daga part din mu nasa key din hannuna dakin ya bude. Bin dakin nake da kallo duk da dan sauyi da dakin ya samu an saka mai kayan zamani a cikin sa. Kafin na fara gyara na fara aiwatar da nufina da yakaini dakin, daga nan daga can ina bude wani kwali dana gani saida naja baya da sauri don tsoron da naji. Kwayoyi ne ciki irin masu tsada da,akai muna lecture a kasan makil a cikin kwalaye. Gaba daya na kwashe su da,sauri nakai toilet din dakin na watsa ciki nai flushing din su suka wuce, Haka nauwa sauran syrup din da nagani kai duk wani magani sai da na turashi a toilet din ya wuce. San nan na,gyara mashi dakin tsab nafito da sauri kafin ya,dawo ina fitowa nazo na zauna ina jiran yadda zamu kwashe dashi. Bayan wani lokaci muna zaune sai hira muke kwasa tsakanin mu ya fado dakin idanuwan shi sun kade sunyi ja dasu. Yan uwan shi ke mashi sannu da zuwa amma ni ko kallo bai isheni ba don nama raina da,al,amarin shi gaba daya. Magana suke mashi amma,bai iya,basu cikaken amsa sai cewa yayi Maji wa ya gyara min daki na. Wani kallo ta,watsa mai kamar na tsana tace wakasan yake da,kokarin haka,ba Fatima ba. Inda nake zaune da,waya ina game ya,kalla kamar zaiyi magana sai ya kuta kawai mikewa yayi har yakai kofa yace tare da kallon inda nake zaune. Ke kawon min abin karyawa na daki zan watsa ruwa ne yanzu. Maji tace bana son suna shiga dakin ku idan kuna gida bari mana ta mika mai maji Amira ta fadi hakan a lokacin har na mike ko tsaye don na,shiga kitchen. Ance abu ga manya ashe uwar ta dan fahinci da,akwai wani abu don haka ta kyale mu. Saida na dauki kayan zuwa dakin ta saka hijjab din ta tabiyo bayana batare da sanin kowa ba. Ina shiga ban san yana tsaye daga kofa ba sai ji nayi an kai min shaka da karfi yana fadin Uban wa ya baki izinin shigowa dakina ki kwashe min kaya. Ina kikai min pills dina yar iskan yarinya kawai mara mutunci. Idanuwa na,sun futo sunyi ja don matsan da nasha jinake kamar zan shude. Yakara cewa uban wa ya,aikoki ki kwashe min kayana? Muryan maji mukaji daga bayan mu tana cewa, ubanka ya turo ta ta,kwashe mara mutunci kawai sake min yarinya kaji. Ya sake ni da sauri sai da naji wani iska mai sanyi ya ratsani lokaci guda, ta juya tana kallona take cewa ina abinda kika kwashe mai din? A hankali nace mata na,yi flushing din su a toilet sun wuce, tace kwayan ke nan ko nai shiru ban bata amsa ba. Ta nuna min hanya tace zoki wuce kinji rabuda dan iska mara mutunci kawai, da,sauri na,fita zuwa part din mu a hirgice dani. Azuciya ta ina cewa anya zan iya kuwa wanan irin shaka haka kamar zan shude lokaci guda. Na zauna jiki ba karfi sai mazurai nake da idona can sai ga maji tashigo na zaci zatai min magana amma sai naji tayi shiru batace min uffan ba. Ina nan zaune sai gashi ya shigo dakin cikin shigan shi na mutunci zaka dauka wani mutumin kirkine can idan ka gan shi a lokacin. Magana yake wa Maji babu wanda yaji may yace mata sai dai mukaji tace Allah ya tsare kawai. Ba irin yadda ta saba mai addua ba idan yace zai tafi wani gurin. A,a yayana tafiya kuma zakayi yau bayan jiya kadawo?. Yace ba dadewa zanyi ba kaduna zan tafi akwai wasan da zamuyi ancan yau da yamman nan gobe zan dawo. Har kofa suka,rakashi cikin jin dadi a ran su suna tayi mashi adawo lafiya yana daga masu hannun shi. Maji batai min magana ba sai da rana na idar da sallah ta kwala min kira nazo da sauri ina fadin gani mama. Samu wuri ki zauna tace min ida na na kai zaune a kasan ties din dakin nata. Fatima fada min komai kada ki boye min don naga ke kina da hankali kinfi sauran tunane. Nafara magana,saiga Amira tashigo hakan bai hanani fasa maganan da zan fada mata ba. Nace tun fitan shi cikin dare jiya ana ruwa nagan shi ta,window dakin mu har ya dawo a cikin maye banyi barci ba. Naga kuma yashigo da leda yana tangadi haka yasani sanin cewa da kayan mayen ne ya dawo a hannun shi. Shiyasa da,safe nace zan gyara dakin nashiga ba fara neman su sai gasu na gani nan na nuna mata hoton su dana dauka a,wayana dakuma yadda nai flushing din su. Allah yai maki albarka Fatima, da yanzu duk wanan abin shaye su zaiyi a cikin shi tayaya wanan bazai wa mutum illa ba wai. Nan take fadawa Amira tun da yazo rai a bace yana tambayan wa ya gyara mai daki nasan akwai magana shiya da yace takai mai abinci don ban taba jin yace haka ba nasan akwai wata a,kasa. Bin su nayi na,samu ya shaketa wai sai tafito mashi da kayan shi sai gani. Amira tajuyo inda nake race kai Bintu akwaiki da karfin hali wallahi ai danice sai kawai na,suma. Nace niko muddi ina gidan nan anty naga yayi abin shan sa na dauki alkawari sai nai mai magana. Baki, gani zai kashe muna uwa da bakin cikin shine anty? Murmushi Maji tayi sai ta kara jin Bintu ta,shiga mata a,rai sosai fiye dama baya yanzun saboda ita tai wanan kasadan haka. Amma a fili cewa Maji tayi kiyi a hankali Bintu kin san karfin ku ba daya,ba dashi badon Allah ya kawoni ba da Allah kadai yasan irin dukan da zai maki kan kayan mayen shi. ****** ********* ****** Tuki yake amma zuciyar shi sai faman tukuki takw mai yana kitayatta idan ya samu sa,an Bintu irin dukan da zai mata watarana. Haka ya isa ya kira maji tana kallon kiran shi amma taki daukan wayan nan ya gane har yanzu fushi take dashi ke nan. Da yamma ma bayan sun gama,ball yakira sai Bintu dake falon ta dauki wayan tasan shine amma sai cewa tayi mai wayan bata kusa ta kashe wayan kit. Haushi da takaicin yarinyar suka rufe shi a lokaci guda yace a fili, I will deal with dis girl. Bari na dawo zata sha mamakina don naga akwai raini a kanta. Ance kowani mahaluki danasa irin baiwan sai dai wanda ya,rena nasa kawai amma kowa da irin wanda,Allah yai mai. Hakane ga,sadauki don yanzu yana cikin matasan da kasa ke alfahari dasu a fagen kwallon kafa. Don idan yana a cikin kwallo Allah na bashi sa,an jefa kwallo ga raga, yaci duk tsananin wasa idan ya kama sai yakai gola. Suna gama wasa washe gari ya kamo hanyan sokoto bai iso garin ba sai zuwa yamma sosai ya iso gida. A lokacin muna,gyaran falon Maji duk da,ba aikina,bane amma ina tsaye ina,taya anty maryam mofing din kasa. Sallaman shi yasa gaba daya suka juyo kan shi suna,mashi sannu da zuwa. Amma banda ni da na zage ina,aikina hankali a,kwance. Sadauki ya samu kujera ya zauna akan daya daga cikin kujerun falon nan suke ta tambayan shi ya hanya ya wasan su na can. Naso na share shi don ina cike da takaicin makuran da yai min jiya kafin ya tafi tafiyan dayayi. Sai nai tunanen bari dai nagaida shi kodon mahaifiyar su dake zaune din bata,rage ni da komai ba na rayuwa. Don yan magana,sunce ko lahira wani tana cin albarkacin wani, na dan waiga gurin da yake zaune ya wani lumshe idanuwan shi nace. Sannu da dawowa ? Tankar a mafarki ya tsinkayi zakkakan muryan na ina,gaidashi. Da sauri ya,wani bude idanuwan shi, yana kallo na na zaci ba zai karba sai naji yace yauwa. Ban kara bin ta kan shi ba naci gaba da,abinda nakeyi a lokacin, ganin da nayi bai bar cikin falon ba yasa na aje mopan ina cewa anty maryam ki karasa sauran zan shiga ciki. Dakin mu na nufa duk da magariba ne amma sai na,fada kan gado in tunanen ashe kuwa zan iya taimakawa Maji kuwa. Shigowan Anty maryam din daki yasa ni dakatar da,shawaran da nakeyi a lokacin. Tace lalai ma Bintu watau gudowa kikayi kikaki karasa,min aikin ko? To tashi yaya yace ince ki hado mai abin sha yasha kafin ya tafi sallah. Nace anty ke mai zai hana ki hada mashi nifa ban iya masifan shi wallahi. Mutum ko yaushe a murtuke kamar mugu sai faman bakin rai da hararan mutane. To naki yake so ai yana ganina,baice na,hado mashi ba,sai ke, yake son ya,wahalal. Ta fadi hakan cikin yanayin zolaya tare da yin dariyar keta a fili tana ta darawa. Nace wallahi anty badon mama ta haife shi ba,sai nace yayi gadon mugun ta,sosai. Maryam ta juya tana fadin lalala haka,kikace mashi bari naje na,fadawa Maji kince yayi gadon mugun ta a,gurin ta don haka,baki hado mashi. Da sauri na mike na,sha gaban ta ina cewa don Allah anty yi hakkuri kada ki hadani da mama barin fito na kawo mashi. Dariya tasa min tace koke fa aikw ce da shegen rashin ji kike taba mai kayan shi. Na,jera ruwa a jug da,cup cikin dan tiren su na,roba nafito mashi dashi falon . Yana zaune a,falon har wanan lokacin ya,dauki kafan shi daya,ya,dora,a,dayan yana,kallon news din da ake a,tashan NTA. Na kai turen gaban shi na aje da zuman na bar gurin. Yace waye zai zuba ruwan da kika girke kamar wata,bakauya haka dake sai shegen sa ido. A ya,tsine nace ai dama yar kauye ce ni. Yace ke baki da kunya fa don naga kina,son raina ni a gidan nan don kin samu guri. Nace a hankali badai a,guri ka,na,samu gurin ba ai, da hanzari na,mike na,shige ciki kafin ya,furta,wani abu. Nan na barshi baki bude yana mamakin da,alajabina sai ya kuta, Yana kutawa daidai Maji tana,fitowa da,alwalan ta,do ita,saidai ta jira kiran sallah kullun haka dabian ta yake. Ta bishi da harara tana cewa kada ka,soma taba min yarinya wallahi za,ajimu dakai a gidan nan. Da,dare muna,zaune abinci kowa ke ci sai gashi ya shigo falon wanan karon ya canza kayan jikin shi zuwa wasu kanan kaya masu matukar kyau na maza. Ya zauna ba,wanda tai azancin mikewa ta bashi abinci nima da nake taimakon shi ina,bashi sai na,share shi kawai don yanzu ban ganin kimar shi kaman da can baya. Waya na dake gefe yai kara don haka nakai hannuna da sauri na dauka don ganin kowaye mai kira,na. Kabir ne, yake kirana da,sauri na dauka don kada kiran ya tsunke a lokacin. Da murmushi a,fuskana nake cewa Assalamu alaikum sahibi rayuwa, Ya,amsa da cewa haba Fatima kishin ruwan rashin jinki da,ganin ki yana,son illantani amma,ke ko a jikin ki baki damu daki kirani ba. Na dan langabe kaina kamar yana,kusa dani nace, cikin yanayin tausayawa. Nace wayyo Muhammad Kabir dina,wallahi ba,haka,na,bane kasan yanayin karatun dana,fara ne ba hutu yanzu, amma nima na damu da na gan ka ai. Ya ce hummm saika ce dagaske Fatima keda har yanzu baki iya,sakewa dani idan ina kusa dake. Ni dai yanzu ina,rokon ki rage wanan masifan kunyar taki haka,na adan bani gurbi nima. A hankali na,dan saki wata,yar dariya mara sauti nace yadda kake jin rashi na a kusa dakai hakana nima yanzu nake jin naka ai. Yace aiko danafi kowa sa,a a duniya zukekiyar yarinya kamar ki tana jin kewan tsoho kamana haka. Maganan shi ta,sani yar dariyar da ban tashi yi ba tare da langabe kaina a hankali saman kujeran da nake kusa dashi. Wani irin tsaki mukaji ya,sake tare da,mikewa tsaye yana fadin maji ni zan dan shiga gari sai da,safe. Tace abincin fa,bazakaci bane yace No abarshi kawai tea zan sha idan nadawo. Ya fita maji na fadi zaka gurin mugun halin naka ko don nasan dai can ka nufa. Baice uffan ba sai yar guntuwar murmushin da yayi iya yake. Yana fita daga falon maryam tace Bintu yanzu gaba,daya kin canza daga Bintu kin koma wata mara kunya,can dake. Wayan ma,a,gaban mutane kike ba,kunya,ba tsoron kowa, Amira tace barta sai watarana yaya ya,fasa wayan nan din karamar aikin shine hakan tambayi maryam kisha labari. Nace aiko da,ya,biya ni koda yake inma ya,fasa,aishi ya,saya,min dama shikw nan yayi amai ya lashe ke nan. Nan suka,sani gaba suna min sheri wai suna son gani Kabir din nan daya sace min zuciya haka,ya,mayar dani wata,mara kunya haka. Nace anty Amira,bafa yaro bane matan shi biyu da yara,biyar. Kafin nakara,furta wani abu sukace a lokaci guda mata,biyu da yara,Bintu ? Shine har kike wani rawan kai haka akan mai mata da,yara baki tsoron kishiya ne ke? Nan na,basu labarin irin takakan da matarshi takawo min hargidan mu a,kauyen mu. Cabdijam wallahi kin fara,gani ke nan may ke cikin auren mai mata yanzu banda,tarin rashin kwanciyan hankali. Nace cikin yar murya,to anty wanda ya samu badashi za,ayi ba idan hakane yafi min zama,alheri arayuwana Allah ya,tabbatar min. Amira,tace wallahi kina,da karfin hali ashe haka Bintu nikan danice da tun zuwan matarshi gidan mu mun rabu dashi wallahi din alama,ya nuna ko a gida,akwai matsala,ke nan. Kafin nai magana,sai mukaji maji tana cewa, ke kada ku zugata Alkah ya,hana,auren mai mata,ne halan. Idan ku bakuyi ita da,tasan ciwon kanta ai bataki abinda Allah ya, kawo mata,ba. Maji aini wallahi yadda,naga,kunayi a,gidan nan bani ba,auren mai mata,kuma. Tsuki uwar tayi tace tunda,kece Alkah basai ki zabawa kanki abinda kike so ba mugani. Nan dai mukai tahira,akan Kabir da iyalin shi dakuma inda yake aikin shi. Washe gari tunda safe muka,tashi da,raba tsaraban mutanen kaduna ashe dankalin Iris ya,sayo mai yawa inaga,buhu guda ne da,manjan miya,wa kowan su saida safe mukaita kasawa,aka kaiwa kowa nata,kason suka,karba,suna,godiya cikin basarwa. Maji tana da,wanan halin komai kankantan abu sai ta,rabashi tabawa kowa agidan sai dai in abin ya tsaya,wamu, yaran tane kawai. Bai shigo gida,ba,sai misalin sha,dayan rana,lokacin mun fita,zuwa gidan wata kawar Amira da,matar yayanta ta haihu. Maji kawai ya,samu a part din tana,zaune tana, gyara,tasbahan ta,daya,tsinke ya,shigo. Su gaisa take tambayan shi sai a lokacin ke nan yatashi ko yace Maji kin san na kwaso gajiya shiyasa da,muka dawo sallah na,kara kwantawa. Yace ina yaranan suka,tafi ne ina,son a danyi min aiki ne kadan wani magani wani mutum ya bani na,hausa nake son su dafa min. Sun fita,zuwa gidan kawar Amirah yanzun nan amma,aiba jimawa zasuyi ba a can din. Shiru yayi sai zuwa can kuma yace amma maji wanan yarinyar sai naga kamar fitsarta, ya,fara yawa fa? Maji tace wake nan kuma ? duk da tagane wa yake nufi din. Yace wanan bakuwar yarinyar taki mana, Wa wai Fatima kakw nufi kowa dai? Ita din ke nan don ban san sunan taba ni. Fitsaran may tai maka,ko don ta,ceci rayuwanka da,halakan shan kwayoyin data,kwashe a,dakin ka shine fitsaran da,kake gani tana dashi. Kai haba Maji ni ba nufina,ke nan ba,wallahi amma ki duba,yadda,take waya,da,namiji a gaban mutane babu kunya a,idon ta. Au to idan batai waya da mai sonta,ba,dakai zatayi ke nan ko? Koko anan zan tabbata,dasu basu aure su a,rayuwan su. Kai ni Maji ba haka,nake nufi ba,fa kawai dai ina gudun kada ta bata,sauran yaran nan ne kawai da irin fitsaran ta. Ita Fatima ce zata bata yaran ko kai dakw abin kunya a gaban su suna,kallo kuma,babu yadda zanyi dakai. Akwai fitsaran daya,fi yau da,girmanka,ana ganin ka a cikin maye babba da,yaro ana min dariya. Dukar da,kan shi yayi kasa yana,dayasanin maganan dayayi a,lokacin daya sani kawai ya dauke matakin daya kudurta a,rayuwan shi final. Nan tace gaba da,fada mai maganganu masu tsuma zuciya na irin zabar mata da mutuncin ta,da,yakeyi ga idon mutanen duniya. Kanshi na,duke sai tafasa,zuciyar shi takeyi yarasa irin son da Maji takewa wanan baren yarinyar haka wai. Wani irin zafin rai yakeji a lokacin tankar aradu ce ta,sauka,mashi a kirjin shi duk sanyin AC dake ratsa falon hakan bai hanashi zufa ba . Muna,shigowa gidan da murnan mu yanayin da,muka,gan su a ciki sai da ya,tayar muna da hankalin mu. Suna gaida shi ya,dago idon shi da,suka kada,sukai mashi ja kamar garwashin wuta ya amsa masu. May yafaru kuma,yaya Amira take tambayan shi tare da,duban fuskan uwar su dake zaune tana abinda takeyi. Yace babu komai Amirah kaina,ke ciwo bari naje nasha,magani dakina. Yana,fita Amira ta juya, gurin maji tana tambayanta da,cewa anyi wani abin ne kuma,Maji ? Shi dai ya,sani inji maji gaskiyane baiso k8n san da,anyi mai fada,sai ya,koma kamar wani namijin zaki dashi. Shiko yana fita gidan sashen shi ya nufa yafada kan katifan shi yai lamo dashi kamar wanda,yake barci,sai dai ba barcin yake ba . Damuwa ce ke damun shi na baisan abinda zaiyi ya,farautawa uwar shi rai yaji dadin ta,ba. A hankali wasu siraran hawaye ke zubo mashi yasan Maji tana,da,gaskiya don yau ba mai son cikin dubu ace nashi ne ya lalace. Ya juya,yana,cewa,wayyo ni wanan rayuwan may nayi rayuwana,ya,koma,haka,alokaci guda. Ba dadi ga,uwana,ba,dadi ga yan uwana,haka ma wasu al,umman garin danake tare dasu ada can baya. Shi dai yasan yayi iyawayin shi akan ya,daina wanan harkan amma,sai yayi kamar ya,bari sai kuma,ya,tsunci kan shi dakara komawa gasha kuma. Ya Allah ka kawo min agaji cikin wanan halin rayuwan da nake ciki. Ai hakkuri da,wanan bayawa yau nagode da,bani lokacin ku da kukeyi kullun Allah yasa,mu gama,da duniya lafiya yan uwa ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,, A LOKACIN MU KE,,,,, Yanzu al,amarin Aliyu yakai har gidaje masu sayen ruwan pure water shi suke aiken shi. Ko kuma,su aike shi dakunan su na,gwauraye yakai masu abu ko ya dauko masu idan ya dawo su dan yi mashi dan ihi sani na kudi ko wani dan abin kwadai. Uwaye lokaci muke yanzu da,ba,yarinya mace ce kawai zaka,nisanta tata irin wa yan nan abubuwan ba har da,namiji idan kina dashi dole idon ki yana a,kan shi tun dai in ya fara shiga adolarcent year din shi na,balaga. To yanzun ma yakai ko yaro baikai wanan shekarun ba,yawon yara,yai yawa don sun san komai na,rayuwa,da birni da kauye. Maria ba abinda ya damay ta binciken al,amarin dan ta sai alfahari take Allah ya hore mata da mai hazaka ga kan talla gare shi yana da sa,an samun ciniki sosai. Bata kula da cewa wani lokaci idan yadawo baya damuwa da cin abincin gida sai dai yace mata ai ya koshi. Daga cikin masu aiken shi a kwai wani matashi anace dashi sisko don irin wankan da yakeyi na matasan zamani. Amma shi ba ruwan shi da yan mata sai dai yawan son wasa da yara musan man maza. Haka yasa sisko ya ke son Aliyu sosai a rayuwan shi don yana yawan ba yaron kudi ya sayo mai abu idan ya dawo da canji ko nawa ne sai yace ya barshi kawai. Haka yasa har Allah Allah Aliyu yake da,sisko yafito majalisar su hira idan bai gan shi ba ya kafa tanbayan yau sisko bai fito bane wai. Shiko idan ya fito ya,shiga wasa da yaron ke nan yana dan matsan shi cikin jikin shi. Har sai yagaji tace yaje ta sayo masu wani abu daga cikin kayan zaki ya dauki rabi ya,ba yaron rabi tace ya,dauka duka. Su kuma mutanen dake zama,gurin basu damu da saka masu ido ba,su dai kawai suna ganin tasu ce tazo daya,kawai kamar yadda,jin mutane kan hadu. Rana Sisko bai fito ba har kwana,biyu don haka Aliyu ya matsa,har saida,akai mashi kwatancen gidan su Sisko din. Yana zuwa,ya,samay shi a dakin da,yake haya,daga wajen wani gidan haya kasancewar shi gwaro yake daga,dakin kofan gida. Kwance yake dakin rubb da ciki yana kallon wani film a tv dakin shi, Yaron ya dan tsaya daga,waje yai sallama ya gane muryan shi yake cewa,a,a Aliyu mai pure water shigo mana. Waya gwada ma gidana yaron yace tambaya nayi aka nuna min ance baka da lafiya shine nazo dubaka. Yace wa yaron ya zauna su nan zaune yana dan mashi wasa ne yake cewa ya ya karbi kudi ya sayo masu cock su sha da maltina. Yaron ya,sayo suna,sha,suna hira yake tambayan shi ruwan nawa ya,dauko yace mai ta,dari uku ce yaciro dari uku ya,bashi yana cewa, idan baka,son talla tunda kaga,dakina,sai ka,dinga,zuwa muna,kallo sai na,saye ma,ruwan ko. Cikin jin dadi Aliyu ya,karbi kudin yafita yana godiya tun daga wanan ranan take zuwa gurin Sisko don yasan lokacin da yake gida. ****** ********* ****** Raiha yanzu bata shayin kowa don ta riga ta bushe fitilar ta ko, a wani yammaci sun shirya da Nura zasu wani bukin wata kawar Nura din a wani unguwa. Acika an yi yawa gurin taron ida shahararun yan mata ke gwada kwalliyan su. An fara program din ne Raiha da Nura suka,ratso ta gaban mutane suka,shigo inda ake reception din. Idon mutane caaa a kan su don kwalliyan su gaskiya,ba laifi ko a gidan wa zasu iya zuwa a hakan. A hankali suke duban gurin da babu mutane da yawa a saman kujerun zaman dake gurin . Can suka hango wata yarinya zaune ita kadai dan nesa da,bango take zaune. Don haka can suka nufa suma,suka zauna sun so su basar da juna amma,sai take ce masu sannun ku fa. Su ma,suka amsa da,yauwa ya,garin dai ta ansa da lafiya kina tare da,wani ne ? Nura dake gyara zaman ta take tambayan yarinyar da,suka,sama a gurin ita kadai. No ni kadai ne ina jiran wani ne dama kuma,ba,a barshi ya shigo ba wai baida pass. Kallon junan,su sukayi sai kuma,suka,danyi murmushi kawai au shi wanan bukin har da wani pass ake nunawa cikin sa. Yarinyar tace wai haka sukace maza ba kowa za,a bari ya shigo ba,wai sai wanda yake da pass din. Ok ke kuma,sai kika kyaleshi kawai a,waje ya zauna yana dakonki kawai. Sister maye naki a cikin, ne wai mu dai ba mun samu wajen zama ba kawai. Abinda yaba yarinyar mamaki shine yadda haddadun gayu ke zuwa kawo wa su Raiha gaisuwa har saman table din da suke. Wasu sukanyi zaton tare da yarinyar suke sai su dan so kutsa kan su gare ta sai Raiha ta dakatar dasu tana cewa kai wanan bakuwar hannu ce fa,bata san kaiba tukun. Bayan su mata san masu ji da kan su sun tafi Nura ta juya gurin yarinyar tana cewa waike ya sunan ki ne. Ta dago daga dannan wayan da takeyi tana cewa, wani tace ke mana. Yarinyar tace hmm sunana Nafisa Abubakar ok anan garin kike da zamane ta amsa da cewa cikin dan dago kanta, Eh nan ne gari mu muna zama a sama,road ne nida iyayyena. Nan dai Nura take dan jan ta da fira da,zasu tafine sukai musayan waya. Nafisa ta riga su fita don haka sai abin hawa yai mata,wuya a lokaci don matasa na cikin hole din sosai ana ta shan shagali a ciki. Sunzo wuce wa ne Raiha dake driving ta hango Nafisa tsaye sanan titi sai faman kallon inda zata samu abin hawa takeyi. Nurace tace don Allah tsaya mu ragewa wanan yarinyar hanya don yarinyar taimin wallahi. Ban gane tai maki ba,damay tai maki ne wai a,a kema kin sani don idan ta,waye ai zata faso itama. Nan dai Raiha tai ribas suka tsaya,suka taya mata shiga su sauketa a gida bata musa ba kodon a ganta da,wa yan nan haddadun gayun abin bajintane ai. Tashiga suna tafe Nura tana marming din wankan dake tashi a motar tare da dan dakilar wayan ta da yazama rabin rayuwan mutanen yanzu. Can ta dago ta juya kadan inda Nafisa take zaune komai na yan matan yana burge ta wallahi don sun matukar wayewa. May ma,sunan ki kace tace a hankali Nafisa nake , tace ok ban nombanki watara ai za,ai zumunci ko Nafisa taji dadi dama tana so tana gudun ta zubar da kan tane garesu. Nan sukai musayan nomba a tsakanin su inda takirata da nombanta itama tace a hankali wazan sa don ban san sunan ku ba . Nura tace a baki bukaci hakan bane mukan ai mun tambayi naki don kin bamu gurin zama. Nuratace zaki iya kira na da Nuriya ko Nura ita kuma wanan driver din zaki iya ce mara Raihanatu. Wallahi sister zamuyi tsiya dake idan kina bata min suna ba Raihanatu ba yar iskan banza sunana Raiha kiji baby. A daidai kofan gidan su da tai masu kwatance suka tsaya da motan su a daidai lokacin da Bintu ke fitowa daga cikin gidan ita da maryam. Wani kallon banza suka,watsa masu suka,wuce su nan Nura ke tambaya wanan yaran yan gidan nan ne naga sun wani hade rai da,suka gan mu mana. Kyale su yan kishiyane bakin ciki suke kawai dashi kuma zasu mutu yan hassada kawai. Sukai sallama ta shiga gida suka,wuce sai sautin kida ke tashi daga motan su. Bayan motan sadauki dake fitowa yagani tare da,bin Nafisa da harara ta make gefe ya fice abinshi. Tana,shiga ciki take cewa,uwarta ni ban san may naiwa wanan dan mayen ba,sai ya wani kama hararana. Da,sauri uwar ke cewa wa sadauki wallahi ahir din shi dake bari ma,na,samu uwar shi tun yanzu. Ta mike sai dakin maji sunyi daidai da ita a tsakar gida take cewa Hawau kiwa danki fada wallahi ya,fita idon Nafisa don ban haifar mashi ita ba. Shidake da abin fadi tab ga tsuliyane har zaicd zai sakawa wani ido akan may? Da yake iskancin shi a gidan nan waya hanashi yin abinda yaga dama da zai wani sa,wa yarinya ido. Baima da kunya da bai kalli inda Nafisa take ba,sau nawa yake zubar da abin kunya babu mai kwasa a gidan nan. Kai bama gidan nan ba,duk gari kowa yasan irin tabargazan dayake mai abin kunya kala kala har basu faduwa ma. Tana juya sadauki yana tsaye sai su maryam da Bintu daga gefe Amira tana tsaye daga kofan su cikin mamaki don ba dama ta tanka saboda mahaifiyar su ta hane su da hakan. Maji tace tau yaya in ma sadauki nada abin fadin da har bai faduwa ina dai uban su daya da Nafisa ni ban san yadda zan raba tsajanin su ba. Umma tace in baki sani ba,aini na sani don ba kare bin damo yabar ganin dan wanan abinda yake torokon yana samu ko zai rudeni na kasa daukan wa diyata incin ta. Wallahi duk randa yai gigin taba min yarinyar ranan ba kwaya, yaje sha ba ko dan babule yake sha zai gane kuren shi. Abin kunya ma hada alaka da irin ku ko barnan suna har yana wani kirarin wai yar uwan shi ce ita. Wai may akayi ne Maji ? Sadauki dake karasowa yake tambayan mahaifiyar tashi cikin bacin rai. Hannu kawai Maji ta daga mashi tace babu ruwanka bari ta fada min abindake ranta dama,ba yau ba take dashi. Kada ki min rashin kunya kan wanan tabararen dan naki mara mutunci wanda ya zama abin nune ga mutane. Ina fatan Allah ya,shirye shi dashi da,duk wani mai irin halin shi ma. Daga,baya ke nan bayan an kasa,ba,yaro tarbiya,tun farko sai yanzune za,a roki Allah kuma. Ta,wuce a fusace tana fadin wallahi shege ka,fasa a gidan nan ni daku marasa mutunci kawai masu abinfadi lodi lodi kawai. Daki suka,shige gaba dayan su suna fadin wai may kuma yafaru yanzu yanzu ne wai ? Maimakon uwar tai magana,sai kawai ta,fashe da kuka mai tsuma zuciyan duk wanda ke kusa a lokacin. Sadauki yace wai maji don Allah may yajawo wanan cin mutuncin ne haka wai? Kai ma , Wazai ja min in bakai ba mai abin fadi lodilodin da akace aiba karya aka fadi ba ba a fadin ne ko yaushe. May yakai ka ga yarta wata yar tata kuma ya tambaya da sauri don bai san kan wanda ake zance ba. Maji tace Nafisa mana, May naiwa Nafisa kuma ya tambaya a cikin mamaki? Ai duk abinda kai mata ka,sani tunda baka rabuwa da yarta bayan kasan gorin da zai biyo min baya. Wallahi azeemun ban cewa Nafisa kala ba kuma Allah ne shedun hakan wallahi. Koma dai maye kaka sani kaita hi kana jamin gorin da banda baki akan shi. Mamaki takaici, bakin ciki suka rufe mai zuciya sai muryan Bintu sukaji tana cewa aiko kowa nada abin fadi don itama ai ta haifi yar iska. Ranan ai ganin Nafisa nayi kwance saman jikin namiji a mota shiba iskanci bane. Ke Fatima kada kiwa yar uwar ki sheri don ta bata min rai don sheri kare ne mai shi yake bi, don haka ki bari. Haka Allah yaso zamana acikin su don haka sai kowa yayi hakkuri. Da,wanan bai fitar da kanshi daban acikin halin yan uwa ba da duk ban ga hakan ba. Ta mike zuwa ciki ranta a bace mata don zafin maganan da aka,fada mata bata da,bakin mayarwa. ****** ********* ****** Wanan magana wasa wasa saida yakai maji kwace don tun lokacin da akayi shi Maji bata,kara lafiya,ba a jikin ta haka ta koma,sukuku don zancen Umma yana,gasa mata zuciyar ta sosai. Bayan kamar sati da maganan zazzabin Maji ya tsananta ranan kwana mukayi ba muyi barci ba , Gashi sadauki baya gari yai tafiya Baba ma bai nan ya tafi kasar Niger state zancen noman shi. Nace wa su Amira gaskiya ya kamata da,safe muje asibiti don bazamu zauna da ciwo ba haka a gida. Amma sai Amirah take ce min wai mu dai bari Baba ya,dawo tukun muji mai zaice. Da,asuba nazo tayar da ita tai sallah naga irin yadda take numfashi yana fita dai,dai. Nace a raina kai wallahi nikan asibiti zamu da safe don in mun biye mata zata halaka a daki kwance sai paracetamol muke dirka mata. Muna idar da,sallah Na samu Amira a kwance, nake ce mata zan fita na nemo mota idan gari yadan haska muje asibiti da mama. Da wani mota zaku kin dai san babu mota yanzu a gida dashi akewa baba aikin gonan shi. Nace ai akwai na haya ko?. Ta zaci zance kawai nakeyi nafita ina mamakin hali irin na su Amira halin ko inkula da sukeyi uwar mutum ba lafiya amma su kamar ko a jikin su. Gari na dan haske na,saka hijjab dina nafita daga gidan sai bakin titi nai sa,a na samu mai adaidaita sahu irin masuyin sakko gurin neman kudi. Muka,shirya dashi nace ya kaimu asibitin koyarwa ta gawon nama, watau teaching hospital. Na leka dakin su Amira suna,barcin su hankali a kwance na koma gurin Maji na samu sai nishi take guda, guda. Cikin matsanancin tsoro da,firgici nace mama tashi muje asibiti aduba,ki. Batai min mussuba kamar yadda na,zata, don haka na,dauki hijjab na,saka mata tare da son mu fita . Cikin karfin hali take ce min, dauko jakata akwai kudi a ciki mu tafi dashi kada muje mu wulakan ta. Har muka fita daga gidan kamar babu mutane kowa na,dakin shi rufe na,sayawa su Amirah kofa muka fita daga gidan. Ban taba zuwa asibitin ba amma haka na daure muka shiga don ba wani nisa ne sosai a tsakanin mu ba. Munyi sa,a don sanmakon mu yai muna rana muna zuwa aka kaita emergency don sunga yadda muka shigo da ita. Bayan yan aune aunen da,sukai matane likitan yake cewa ke yarta ce na amsa mashi da eh, Yace to ina manyan ku suke aka bari ke karama dake kika kawo mara lafiya haka acikin wanan yanayin asibiti ? Nace, Baban mu baya gari shi da yayan mu sunyi tafiya yace alright yanzun dai zamu bata gado tare da bata taimakon gagawa tukun kafin mu auna ta muga may ke damun ta haka? Sai da na,tabbatar da cewa an bamu gado anyi komai har an saka mata ruwa na dauki waya na kira Amirah wace cikin gigin barci take min magana. Nace Anty gamu fa asibiti da mama an saka mata ruwa ma ko. But tamike da mamaki azaton ta wasa ne don shirmay ta amma tana dubawa dakin Maji sai taga wayau har falo taje babu mu. Bayan kiranta kamar kada na kira yaya sai dai nace bari na kirashi dai yasan halin da uwarshi take ciki. Babana ta rubuta wajen sunan shi na danna kiran layin baifi ringing uku ba ya dauka yana cewa, Maji yanzu nake son kiranki naji ya jikin don jiya Amirah ta fada min kina jin jiki sosai. Nace ba mama bace nice Bintu gamunan asibiti da mama an bata gado. Yace cikin wani irin murya what, anba Maji gado a,wani asibitine kuke? Nace na,gawon nama watau Usman dan fodio teaching hospital. Yace ke ba Amirah wayan please nace Amirah tana gida bata iso ba tukun To wa ya kawo ta,assibitin ita Amirah tana mayye nace ta tsaya hada break ne. Tsuki yaja tare da kashe wayan ashe bayan ya kashe Amirah yakira yace yaya jikin na maji wai may ke faruwa ne. Tace wallahi yaya ban masan sun tafi Asibiti ba Bintu ce ta kirani take fada min yanzu wai suna asibiti. Yace you are very stupid Amira yanzun saboda shegen barci tsiya har aka fita da Maji gida baki sani ba ke kina may ye har wanan yar kauyen yarinyar ta kaita asibiti. Tas yai mata tare da umartan ta duk abinda take tai maza ta samay mu asibiti kafin ya bata mata rai. Ina zaune na tasa maji da ta samu barci a gaba sai ga Amirah da maryam a gagauce. Sun wani fuske sun dauki zafi dani ban damuba don nasan ni don Allah nayi masu. Don danabita nasu sai dai ta halaka a gida saboda sanyin jikin su da narkewa. Muna nan zaune sai ga likita yazo da takarda magani a rubuce yace suna bukatan wa yan nan. Karba Amirah tayi tare da ficewa dakin dagani sai maryam ke kan mama din. Ajima kadan sai gata tadawo da takardan tana fadin ke Bintu nifa ban san inda ake sayar da maganin su ba. Nace a tambaya mana take cewa wai wa zata tambaya amsa nayi tare da daukan kudi ga post nafita. Da tambaya,na gane gurin sai gani da maganin cike da leda nashigo dakin nan na mikawa nurse din dana samu tana gyara ruwan dake tafiya a jikin maji din nayi. Shiko sadauki yana gama waya da Amirah mahaifin shi ya kira yake sheda mashi abinda ya faru da uwar su. A gagauce Baba ke tambayan shi yanzu maijidda tana ina wai? Yace tana asibiti an bata gado ita da wanan bakuwar yarinyar Fatima dake dakin ta. Su su Amira fa suna inane da sauran mutanwn gidan da har za,a bar Fatima karamar yarinya takai ta asibiti da kanta duk an rasa wanda zai dubaran daukan ta zuwa asibiti sai Fatima karamar yarinya haka da ita. Sadauki yace yanzu nakira su Amira ga,waya mazasu tafi asibitin suga halin da ake ciki don dai tace wai an daura mata ruwa a,jiki ko. Allah ya sauwaka insha Allahu gobe zan dawo nazo naga abinda ke faruwa hakanan. Suna kashe wayan sadauki ya dab furzo iska daga bakin shi kadan tare da dan gyara tsayin shi. Agogon shi ya fara dubawa ya san idan yace zai taso daga anambara zuwa sokoto ba karamin tafiya bane don haka ya yanke shawaran samun jirgi zuwa abuja daga abuja koda da motane sai ya karaso. Karfe, Biyun rana yana garin Abuja bai bata lokaci ba ya samu shatan mota sai sokoto,. Suna zaune sai nice ke ta faman zirga zirga wai su yan gaye a hankali maji ta bude idanuwan ta da ta kusa yini tana barci. A lokacin bani daki sai Amira ce zaune mun fita da maryam zuwa wani guri tace na,rakata. Bayan ta bude ido tafara bin dakin da,kallo can tace, Fatima, Fatima, sai Amira ta mike tazo inda take kwance. Maji kin tashi ne tace wa uwar ta, sai uwar ta ce mata eh ina Fatima ne ?, bata nan tabata amsa. Sai ta mayar da idanuwan ta takara rufe su a hankali, kuma again. Muna,shigowa take fada muna mama,ta,falka tana tambayan ki Bintu da sauri na isa gurin ina,fadin wani abin take so ne Anty tace batace komai ba sai ta koma barcin ta. Ana maggariba ya iso garin a lokacin hajiya kubura ce kawai tazo duba mama sauran basu zo ba har lokacin. Ban san da zuwan shi ba don natafi dauko kayan da za,a bukata a gida. Ina dawowa daga gida na sauka mashi sai naji ana cewa ke pretty, Fatima, Jin fatima yasani dan dakatawa na waiga inga mai kirana haka nan don ban sheda sunan mai shi ba. Ya karaso gurina da murmushin shi yana wasa da key din motan shi a hannun shi. Yace ai tun gida na,biyo bayan ki dama na dade ina son in samu time nai maki magana. Kin gane ne wallahi kinyi min irin tsarin macen da nake son ke nan ba wani bata lokaci ki yarda dani kawai muji dadin juna dake zan maki komai wallahi koma may kike so idan kinyarda dani zan dinga saya maki anything, anything just kawai ki bani hadin kai mu more junan mu muji dadi idan gida akwai idon mutane zan sama muna wani scret place da zamu dinga hadu ehy kin gane ko. Wani irin bakin ciki da taikacin shi suka rufe ni ban kai karshen tunane na ba,sai ji nayi yana fadi dibki don Allah wanan idan na samayki nagama neman mata wallahi. Yana kokarin kai hannun shi ya taba min wuya ban son lokacin da nayar da pillow dake hannu na ba nakai mashi mari fayauuu, Daga inda saudaki yake tsaye tun saukana a mashin da tareni dayayi duk akan idon shine da marin da na kaiwa yayan nashi. Take ya dafe wurin yana cewa ke ashe baki da kunya ashe ke yar iskan yarinya ce ban sani ba. Har ya fara takowa daga inda yake zuwa gurin da muke don yana ganin kamar Imirana zai iya dukana. Sai yaga na daga hannu ina fadin dan iska kawai mara mutunci masu gadon iskanci kaje ai kana da kauna Nafisa ka huta da ita ni ba karuwa bace . Imirana yace wallahi sai kin gane baki da wayau don sai kin bargidan mu wallahi shegiya yar ci rani kawai. Ke Fatima dauki kayan ki, kishige ciki kinji da sauri najuya don jin muryan wanda ban zata ba a lokacin duk kan mu kallon shi muke yi. Imirana yace jimun wanan yar iskan yar kauyen fa waini zata raina wa hankali haka ji mun ita. Hannu ya daga wa dan uwan shi yace please Imirana is OK naga komai tun saukanta mashi ina tsaye gaban ku ai. Daga haka ya kama bina a,baya ina gaba yana biye dani har zuwa cikin female ward da aka kwantar da maji aciki. Amirah na ganin na dawo take cewa yauwa Bintu dauki kayan can da akaci abinci ki wanke su. Sai ganin yayan su tayi a bayana da sauri tace lah yayana ka iso ashe yace eh na tsaya yin sallah ne da na iso. Ban zauna ba na kwashi kayan na,wanko su kamar yadda tace ina dawowa kuma duk suna tsaye suna magana Amira tace Bintu zoki sayo ruwa mu aje kada dare yayi ba ruwa a gurin. Kai haba haba Amirah why komai Bintu, Bintu dai Bintu ku kuna may ye wai please. Nace ina kudin yake na sayo yace ke maryam jeki ku sayo a tare da ita kuna zaune sai faman bada intruction kuke kamar wasu tsufi. Maji da ta farka tace ai basauyi ba sai dai su bada odar yi don su sarakaine. Sai yanzun yagane abinda yasa yarinyar ta,shiga ran maji sosai yarinyar bata da kiuyuya kuma bata fushi. Yace ina son a sake mata daki yanzu zan tafi nai magana gurin nurse yatafi tai mashi bayanin yadda za,ayi. Muna dawiwa muka samu har ya karbo takardan canza daki ko nan muka kwasa sai sabon dakin da aka canza mu. ****** ********* ****** Dakin kudi muka koma mu kadai ne a dakin yana da tsari sosai harda dan fridge da kayan kallo a cikin sa. Maji har lokacin magani bai sake ta ba na kafe ta da idanu sai barci take gashi duk ta wani ramay sosai da ita. Ban san lokacin da tausayin ta ya kamani ba sai jin hawaye nayi sun zubo a idanuwana sai sauka suke a kumatuna. Ban san ya shigo ba yana tsaye yana kallo na may kikewa kuka haka duk suka juto gareni kuka kuma Bintu sai maryam itama ta fara kuka. Tace Tun safe Bintu ke kukan nan idan ta kalli maji nai mata magana taki bari. Likitane yashigo dakin saye da corth din shi baka duk muka gaishe shi yake cewa tare dan taba jikin ta har idanun ta. Zata dan samu sauki idan ta farka amma yaya akayi kuna gari kuka bari har ciwo yaci ta haka a gida. Gaskiya data kara awa a lokacin bata samu taimako ba da zamu iya rasata wallahi. Ya juyo inda nake yana fadin idan ta farka sai ki hada mata tea mai zafi tasha sai ki bata wanan maganin da aka sayo amma don Allah kada kiyi mata wasa da maganin don ba abin wasa bane. Yana fita dakin na mike tare da daukan cup na fita na dauraye shi na,dawo na,saka acikin wani leda baki. Yace Amira waya zo daga gida cikin su Umma eh to Bintu tace ina barci wai mommy ta shigo bayan ita ba,wanda yazo kuma. Muna zaune dakin kowa yai shiru a cikin mu duk kowa da abinda yakeyi sai ga hjy Kubura itace a gaba yaranta na bin ta a bayanta. Suna dauke da kwandon da kuloli a cikin sa da flask din ruwan zafi sai ledojin da yaran suka riko na kayan fruit. Tana ganin sadauki take cewa ,a,a sadauki ashe har ka iso yace cikin dagawa daga saman kujeran da yake zaune kusa da maji don ya bata guri na iso mummy. Da sauri na mike na karbi kwandon dake hannun ta, nakao saman durowan dakin na asibiti na aje. Tace ai natafi wancan dakin na farko sukace min kuna nan ancan guri. Yace eh mummy gurin can bai min ba mutane sunyi tawa baza,a bar mara lafiya yayi barci ba da dadi. Hakane gaskiya amma nan din kaga is ok zata samu hutawa sosai anan din. Likitan ya shigo ko may yace kafin wata tai magana nace zazzabine wai typhod yai mata yawa suka ce ta ce wai da sauki ai nazaci suce ciwon zuciyan tane ke batin tashi. Nace yama ce bata da ciwon zuciya wancan daya fadi haka bai san aikin shiba. To Allah ya sauwaka muka amsa mata da Ameen mummy tace zamu koma don dare yayi sosai gani da yara bandawo da wuri ba shiyasa ban yi girki cikin lokaci ba. Anwar yana lake jikin yayan shi tun shigowan su dakin yagan shi ya lake mashi sai hira suke dashi. Tamike tare da muna sallama tabar dakin muka dan rakata zuwa kofa tace ku koma abinku zanga wata kawana dake duty acan ward din. Tana wuce muka dawo ni da maryam nace yaya a zuba ma abincin kaci ne? Yace No barshi banjin cin abinci yanzu Amira tace yayana bari a zuba maka kaci ko kadan ne don Allah. Hakana jawo plate na,soma zuba mai abincin wanda dafa duka ne da kayan lanbu a cikin shi sai kifi da tai amfani dashi. Sai dan ferfesun kifi danye da tayi daban ta zuba shi a wani dan kula karami. Shina zuba mai don nasan bai shiri da dafa duka shi sai dai da miya ko tuwo. Na koma gefe na zauna maryam tace zuba muna abincin muci mana kin kima zauna. Nace sai dai na zuba maki ni ba yanzu zanci ba Amira tace kinbsan bafillatace sai kafa ya dauke taci. Hmm aini Bintu tabani mamaki jifa yadda tai saurin boye ciwon maji wa mummy harda cewa ance wanda yace tana dashi bai san aikin shi ba. Nace eh mana yanzu da anfadi gaskiya sun samu na fadi kena a unguwa cewa bakinciki ne zai kasheta ai likita yace kaza yace kaza. Maryam tace wallahi kamar kina zaune kuwa don tana komawa zakiga muna fukancan sun tambayeta may ke damun ta kamar da gaske da an fada masu shike nan an samu na fafi ana canza magana. Sadauki wanda yake zaune yana shan ferfesun shi hankali kwance bai ce muna kala ba. Suna cin abincin duk kamshi ya bude dakin sai hira suke kasa kasa kan mummy a gidan su . Yana gama wa yadago kai muka hada ido na daure fuska na yace kwashe kayan nan anan . Sai da ya sha ruwa yace ke may yasa bazakici abincin ba ke nace sai anjima zanci yaya nadan sha lemo dazun. Ya dan kalleni kamar mai nazari can yace su waye zasu kwana anan don dare ya soma sai nakai sauran gida. Maryam tace sai dai abar anty Amira tunda itace babba ko da sauri tace a,a wallahi ban iya tsayawa ni kadai don tsoro nake ji. Baki da hankali ne idan baki zauna ba wazai zauna dama ke dakike babba wallahi yayana ban iya zama ni kadai anan gaskiya. Nace dama ka barsu yaya dama ni anan zan kwana ai tare da mama su tafi gida su huta su. Yace don may za,a barki ke kadai dole dayan su ta tsaya tare dake a nan ya wuce da maryam mukuma muka zauna dakin nan zamu kwana da mama. Azaton mu ya tafi ke nan can sai gashi ya dawo dauke da ledoji ya sayo muna su kayan shayi da kwalayen drinks sai naman kaza mai zafi ya kawo muna. Yamika muna yana cewa kuci naman kubar wa maji idan ta farka kila ta danci Amira ta jawo ledan gamu tana fadin oya muci Bintu nace fara ci ke, nan tafara yagan naman tana kaiwa bakin ta. Zaune yake a saitina yana amfani da wayan shi data dauke mai hankali. Yace wai may yasa ke bazakici komai bane wai, na dan tsuke fuskana san nan na ce haka kawai . Yace amma badon kin ci wani abuba ko kin koshi ba ko? Nace ban karya ba yaya ban dai iyacin komai ne saboda hankalina daya tashi. Yaya na fada maka bar Bintu haka take ita bata damu da cin abinci ba fa ita. Ya dubi Amira yace kina nufin zata iya kwana a haka bata ci komai ba? Haka take ko agida sai maji tai mata fada take cin abu ita. Yace tura mata naman da kwalin drink din tasha ban musa musuba na dauki yaka gudanakai abakina da kyat nake iya taunawa na dauki drinks din nakai abikina sai naji sanyin shi yai min yawa sosai. Haka dai na danci naman nasha drinks din kamar wace za,a kama a lokacin Wayana yai ruri da sauri na nufi side drower dana aje wayan akai. Ina kokarin duba maikirana a wanan lokacin don dai nasan ba Kabir bane don a lokacin yana cikin iyalinshi. Sadauki ya kafe ni da ido don jin waya kirani a wanan lokacin kuma ko zanyi fitsaran dana saba na waya agaban mutane dayace inayi. Na daga tare da sallama sai naji muryan gwagona tana tambayana jikin maji nace gamunan ma asibiti da ita an bata gado. Nan take ce min insha Allahu gobe tun da safe zata shigo gari don yanzu tafi gane ma ta dinga kai kaya gari gari. Ina kashe wayan maji tana,farkawa duk mukayi kanta gaba dayan mu muna mata sannu da jikin ta. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA,BA KA DA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,, A LOKACIN MU KE,,,,,,, Kudi yabashi har dubu daya,yace yaje yasaya duk abinda yake so dashi yaron bai san girman kudin ba yadai san ko nawane don yaka,yaje ya fara sayen abinda ke ran shi. Kayan zaki sai kayan sanyi su ya,kwasa ya sha har yafara kyautawa,abokan shi. Ya dawo dauke da roban shi dakin sisko nan suka zauna ya sa masu wasan turawa suna kallo daga,shi sai shi a daki. Can sai ya sauya tasha inda ake wani wasan shedana zallah. Yaron sai ya,fara kawar da kan shi gefe sisko ya ja mai kafa yana fadi ji dan nema kaida wata rana zaka zama boss da wanan harkan kake kawar da fuska ai gara ka fara koyo tun yanzu. Nan dai har yaron Aliyu yadan fara tsayawa yana kallo ta gefen idon shi ajima kadan yake cewa zai tafi gida sisko yace kai tun yanzu yace lokacin zuwan shi makaranta yayi ne. Jawo shi yayi kamar wandaya,samu budurwa yana dan wani wasani dashi sai da yaji dai,dai ya sake shi da zai tafi sai da ya,kara mai dan kudi saboda jan ra,ayi gobe. Ruwan sai makaranta,wasu, almajirai yakai yace inji wani mutum yace na bayar sadaka anan. Shi kuma ya kama hanyan gida yana murna da farinciki ya isa gida ya mika wa uwar shi kudin ta,saura ya samu guri ya boye. Kamshi turare taji a jikin shi tace kai kai kai ina,kasamu wanan turaren haka mai kamshi. Nan ya shafto karya yana fadi wani yaro ya ysunci kwallaban turare shine muka dan sawa jikin mu. Tace yaci abinci yace sai ya dawo ba yanzu don haka tace yai niya yafita koshi da kyat tasamu ya fita don ya kwata jikin shi yana mai ciwo ga kuna kayan sanyin da ya cika cikin shi dashi fam. Amma ita da yake son kudi ya rufe mata idon ta sam bata hango illa ga rashin cin abincin da yaron baiyi a kwanakin nan ba. Yaro idan ya,fara talla ko yarinya komai zama kamilin yaro kwana kadan da,fara tallan yaro idon shi zai bushe. Idan sau daya kakewa yaro tsawa ya bar abu yanzu sai kayi uku masu karfi kfin ya bat abinda ka hanne shi. Yaro idan ya fara talla baijin naiyi ko kunya fada wa babba magana yadda yaso sai dai kai babba kaji kunya. Yanzu duk irin haka ke faruwa,da,Aliyu amma uwar bata da fahinta ita bukatar ta kawai ya kawo mata kudi a rayuwan ta. Mahaifin yaron ya ga matukar canji akan dan shi sai dai ya danganta halin yaron sai ya dangata shi da girma yasa shi canzawa a baki daya. Tun wanan ranan kullun sai Aliyu ya,tafi gurin sisko saboda dan kudin da yake samu gare shi. Gashi uwar ba ido take sakawa akan yaron ba ita gurinta kawai shine, taga ya kawo mata kudin da yawa. ****** ********* ****** Tun wanan ranan da suka hadu suka zama abokai tsakanin su da Nafisa. Ance abokin barawo barawo ne don Nafisa bata san ya akayi tafara shan abubuwan dasu Raiha ke shaba saidai kawai ta tsunci kanta a cikin shaye shaye dumu dumu da ita. Ga uwar ta,Umma a kullun zancen ta sai zagin sadauki da yiwa uwarshi dariya bata san na dakin ta yafi illa,ba ma. Sai dai tana kokarin ganin kowa a gidan su kada ya,san zancen har a,kyamce ta ita da uwarta kamar yadda akewa Maji da diyan ta gaba daya da abin bai shafa bama. Yanzun takai har fitan da,su Raiha keyi zuwa wani gari tare da Nafisa suke yin shi, don sai ta,shirya karya cewa za su wani gurin yan uwan su ko gidan kawarta sai kawai su fita garin suyi kwanakin da zasuyi ba ta gidan. Gashi ir8n na fitsara ba komai bane a gurin ta don wayewan ta tana ganin yakai haka ita. Al,amarin ciwon maji yasa Alhaji baro aikin shi ya dawo gida don ganin yadda jikin naya yake saboda hankslin shi yaki kwantawa da jin da yayi an bata gado. Yana isowa ya wuce asibiti direct Don ganin jikin nata, ya samu Tana zaune ina tsaye agaban ta ina we, mata lemun tana Dan sha a hankali. Baba yashigo dakin da,sallaman shi Nan muka shiga gaishe shi dadawo daga tafiyan da yayi. Idanuwan shi kyar akan ruwan da ke kafe daga gefen mama ya Kara juyo kallon shi a gareta Yana mata sannu da jiki. Ganin shi yasa mu kokarin Fara barin dakin don mu kauce masu daga dakin. Yake cewa ku tsaya abinku Fatima ance kece Kika kawo ta asibitin har aka baku gado to Yaya likitan yace yanzu . Nace cikin dukar dakai likitan yaiwa Yaya sadauki bayani dazun da safe Kuna ya Kara rubuto wasu maganin da za,a saye. Yace zasu kwantar da it's na sati biyu anan don ta samu Hutu sosai a jikin ta tare da treatment din ta. Ok hakan na dakyau ai said dai ku dinga barinta tana samun barci sosai zaifi Kara mata lafiya . Bai dade dashigowa ba sai ga sadauki ya shigo dakin ya sayo maganin da likitan ya rubuta mai yana fadin da kyait muka samu maganin babu shi nan cikin asibiti. Yaiwa mahaifin shi sannu da dawowa tare da tambayan shi Yaya aiki a can inda ya fito. Muna waje zaune saiga Yaya Imiran yazo don sunyi waya da baba yace sure hadu a Nan asibiti dashi. Zan iya cewa tunda mukazo asibiti bai shigo gurin Maji ba don ya Dubai lafiyan ta Amma salmanu Dan wurin mama Asiya zuwan shi biyu Kuma harda fruit yakawo Muna. Ya na isowa ya gan mu, zaune mu uku nan Suka fara gai da shi cikin ladabi, Banda ni dake zaune ina mashi wani kallon raini kawai. Tambaya yayi ko baba Yana ciki suka bashi da amsa da eh Yana Nan cikin dakin. Yana kokarin shigewa naja wani tsuki da karfi Yana ji sai dai bai juyo ba ya shige ciki kawai abinshi. Muryan anty maryam ce naji tana cewa ke may ya hana kiki gaida yayan mu Bintu? Nace bai isa na gaida shi bane kila don da nagaida shi inda mutumin kirki ne. Fitowan shi yasa su yin shiru suna mashi sai anjima, bintu tace haka dai za,a kare . Wai ke Bintu harda yaya Imiran da ba,ruwan shi da kowa, amma sai k8n tsula mashi halinki na tsiya? Maryam tace a,a anty Amira tunda kikaga haka akwai dai koni ranan mun dawo school bakiji, abinda yake fadawa Bintu bane, Nace aini Anty Amira idan mutum bai shiga gonata ba ni bani shiga nashi don haka kibarni kawai dashi dan iska kawai. Haba Bintu haka,kawai ki dinga zagan muna dan uwa a gaban mu haka gaskiya zamu saka wando kafa guda dake a gidan nan. Nace maida yukanki kube anty Amira ai ni ba haka nake ba da ace da yai min ban dauki mataki ba,ai da ko yanzu bata kare muna,ba,wallahi. Ke dai yanzu kin zama disturb wallah kamar ba Bintu Maji ba wallahi nace lokaci ne idan baka baki sai a shaka a,banza. Wai don Allah may ya,hadaki da yaya Imirana kodai laifin maganan ranan ne har yanzu kike kule dashi. Nace a,a ai anan cikin asibitin muka yi case din mu dashi ban ma,san yaya sadauki na gurin ba,sai da naji ya daka mai tsawa yace mai ya sake min hannu na. Tace ashe kin kuru, ne harda yaya,sadauki a gurin lalaima Bintu kinyi nisa sosai wallahi. Nace marin shi fa kawai nayi saudaya shine wani abu wallahi har yanzu a kule nake dashi a raina . Da sauri sukace mari da,gaske mari Bintu nace don ma banda karfi aida abinda zan mai sai yafi mari wallahi. Yadda yake dan iska haka yake ganin kowa dan iskane shine harda daukan kazamin hannun shi wai zai shafa min jiki niko nakai mai mari sosai Allah yaban sa,a na samay shi da kyau. Da sauri Amira tace don Allah da gaske marin shi kikayi nace wallahi Allah kuwa nan na,basu labarin abinda ya faru a tsakanin mu dashi har takai na mare shi. Maryam tace dan iskan mutum kawai mara mutunci yau da wani ne da uwar shi ta samu abin kasawa a,ture tana baradawa a gari. "Dan kowa ,dan banza ne, nata ne diyan kwarai a duniya, nace wallahi ni ko gobe yai min maganan iskanci sai na,dauki mataki ko a gaban waye. Maryam tace ya ganki haka ya zaci irin yan matan shi da ya saba yaudara ne. Nace shi dai jarabar shi ce ta motsa kawai har idon shi ya rufe, irin yan iskan ga ai su kowa bi suke basu da zabi mace da mai aure da mara aure in sun, samu, duk so sukeyi. Nace Allah ya kyauta Allah dai ya,shirye mu, don wanan shima ba karamin masifa bane wallahi. Don ai zina ya mafi komai muni a rayuwan mutum da ban kyama, ga al,umma. Nifa ban yarda da maza don a mayaudara nake daukan su baki daya inji Amira nace ai ba duka maza bane basu da hali don ko matan ma,akwai marasa hali a cikin su sosai don sai kiga diya,mace yanzun tana abinda wani da namijin ma ba,zaiyi ba. Har Baba yafito shi da su sadauki suka rakashi nan muka mike a inda muke zaune muna mashi a huta lafiya. Sadauki dake tsaye ya bude motan ya dago kai ya kalli gurin da mu ke tsaye, yai muna inkiya da dakin da,maji ke ciki . Nan take, na juya da sauri na nufi dakin suko sauran basu gane may yake nufi ba don haka suka tsaya jiran baba dake waya ya gama. Ina shiga daki nasamu, maji ta farka daga barcin da ya dauke ta, na karasa gurin, da take ina mata ya jikin Tace min ina yayan ku Fatima ya tafine ko yana cikin asibitin nace to na dai barsu waje da Baba zai tafi gida . Kamar kira sai gashi ya turo kofan ganina tsaye a,bayan mama ina gyara mata filo yasa shi karasowa gurin da sauri yana cewa Maji kin falka,ashe ya jikin yanzu da sauki dai yanzu ko? Likita ya shigo ganin ta a,zaune yake tambayan ta mama ya jikin naki da sauki ko Ya dan dubata ya dago yana cewa abata abinci taci zuwa shidda na yamma za,azo ai mata allura. Sadauki yace wani iri abinci ya kamata a,bata yanzu wanda zaifi mata, amfani. Likita ya dago kai yana fadin tea mai kauri da fruit sai kuma anta da koda mai kyau ta dinga ci. Sai kuma likitan yai shiru tare da kurama sadauki ido yace you look like U,F footballer yace cikin dakewa yes iam d one, Nan suka fara shocking din hannun su suna gaisawa mutun yana faman dada wasan yaya,sadauki. Likita baifi yan mintina da fita ba sai ga,wasu group din likitoci sun shigo lokacin yana gyarawa mahaifiyar shi kwanciya suke fadin lalai kuwa shine shine. Nan suka cika dakin da surutu wa yannan group su shigo su fita wasu su shigo har abin ya fara isa ta don sun hana mama samun hutu. Saida dare Baba ya,dawo tare da su Umma da mama Asiya ya,taso su gaba bayan ya gama masu fitina rashin zuwa duba yar uwar su dake kwance asibiti. Inda yace na,tabbatar wallahi da dayan kune a,asibiti da maijidda sai inda karfin ta ya kare. Nan dai yai masu tas yasa fito su zo tare su duba lafiyan ta . Sun kai wani lokaci sai, suka mike zuwa gida, dama duk a matse suke kamar dole suka zo gaida ita. Suna fita Mama tana kwance na mike na gyara ko ina tas a dakin tare da,kawar da,wasu kaya dake waje. Sai ga,Sadauki ya,shigo dakin ya,aje ledan da ya,shigo dasu gurin flask ya nufa ya tsiyaya ruwan zafi tare da hada tea mai kauri sosai. Yazo gabana ina zaune yake cewa gashi na,dube shi nace tasha tea ai kafin ta kwanta. Fuskan shi a daure yake cewa ke zaki sha ba Maji ba, ya kara miko min yace karbi mana kisha idan kin gama ga nama a leda kici tunda wa yan nan sun tafi gida don lalaci. Zanyi magana yace min shishsh bana son magana shaye shi kawai Ban san ya akayi na fara kurban shayin ba saida naji na dan kai cup a bakina karo na farko. Yace yaushe, likitan yace za,a kara mata allura ne wanda ya saura ai mata. Nace ni ban ma tsaya tambayan shi ba,don ya ishi mutane da labarin kwallo kawai ya fita. Ke kuma shine baki so zancen kwallo ko don kina jin haushi da hassada ko? A kwallo ne mutum zaiyi bakin ciki ko kan may aiki wahala. Kallona yake galala,har na, mike tsaye tare da dauko baredin na zauna a makure nasha ya dan kai kurbi hudu batare da bread ba. Na aje tare da son na,rufe sauran sai yake cewa to ki jawo kazan kici don cikin ki ya kara,walwalewa da kyau. Nace wanan ma,Alhamdullahi don nakoshi tace shiyasa bakya kiba har yanzu kamar a kallaki saboda baki son cin abinci. Ya mike yaje bakin gadon mama ya dan tsaya can yake cewa ina ga shidda na safe zasuyi mata allura don gaka idan basu zo ba sai ki bisu. Nace mashi tau ya kai kofa yake cewa idan ta farka kice mata na tafi sai da safe in Allah ya kaimu. Yana fita naja kofan na rufe nan na, dako ledan naman na fara ci tare da karasa shan cup din tea dina. Sai da nai nak na ture dama duk iya,shegena,a gaban mutane ne ban ita cin abinci saboda kawaicin da nakeyi kawai. Zuwa dare maji ta,farka nan na mike ina mata sannu tare da tambayanta ko tana son cin wani abu. Tace a,a tana tambayana su Amira nace yau a gida zasu kwana don likita yace mu dan rage yawa don ki samu hutu. Tace hmmm kai Fatima boye su kuma,zakiyi bayan nasan halin abina sun dai tafi gida don su samu barci yau ko? Banyi magana ba sai hira take min mai kama da nasiha tana ta bani labaran tun kafin nazo gidan su irin yadda su ke kwasa da kishiyoyin ta. Nace mama Allah ya kyauta amma mutane kamar ba,a mutuwa sai a manta da ranan haduwa da Allah. Sai kusan asuba,muka,samu barci sosai Allah ya taimaka na,farka da akazo yiwa mama Alluran karshe. Ban koma barci ba na dauro alwala nahau sallaya na fara sallah har akai sallah asuba ina gurin a zaune abina. Zaune nake inajan tasbi amma kuma zuciyata tana tunane akan hiran mu da maji daren jiya da irin wahalan da tasha a gidan miji amma tazauna tai hakkuri don yaranta. Gashi kuma yau an wayi gari saboda dan tilon danta guda ciwo nason shigan ta. Har na,soma gyangyadi a gurin sai jin muryan mutum nayi a akaina yana fadin ki kwanta mana ki dan huta hakana. Yaya sadauki ne yana saye da kayan exercise na maza dogon wando da rigan shi mai dogon hannu dark blue. Yanufi gadon mama yana duban ta sai ya juyo inda nake ina kallon su yake cewa, tasha maganin an kuma yi mata alluran kuwa? Nace eh sunzo sunyi mata sun bata magani shiyasa mata ke barci haka don maganin barci yake sa mutum sosai. Ya ce ba tare da ya juya ba ina ga daga wanan allura ya kare sai dai magani kawai. Jin nai shiru yasa shi juyawa gyangyadi nake nai barci a gurin hakan ya nuna mai ina son hutu nima. Kujera yaja zuwa gaban gadon mama yana mai kura mata ido cikin jin tausayin ta ta ramay tai baki duk ta canza kaman ta. Yana nan zaune har wata nurse tashigo dakin take tayar da,maji zasu bata maganin safe. Shine dalilin farkawan mu ni da mama din Sai da nurse din tagama ta tafine maji take tambayan dan nata sai yanzu yazo ne. Yai murmushi yace maji na,tsaye nazo maki da,budurwana ta gaida ke sai na samu bata shirya ba . Murmushi naji uwar tayi tana cewa kai kama isa kaida akaiwa mata tun kana karami kasan dai Alhaji ba zai canza maganan shi ba. Sai yace wai wa kike nufi Maji Rahaman Baba Sani ko wa wai? Tace itace mana ba itace matar taka ba da iyayyenku suka yima ko kw canza watace. Yace maji ni may zanyi da Rahama yanzu ga mata yan gayu ko ina suna kawo min hari sai wace na zaba. Dariya uwar tayi tace adaiyi sanni kada ruwan ido yai ma mutum yawa amma dai kasan zancen Rahama ba,tashi yayi ba har yanzu. Wai maji da gaske kuke zancen Rahama har yanzu a da dawasa ne bayan ko wani shekara sai na hada toshin sallah ankai mata. Kwanaki ma naji Alhaji na zancen yakamata wai kuyi aure ku uku tundai kai da kudi yake shigowa yanzu ko yaushe. Yace ni gaskiya da za a bani zabi gaskiya Rahama batai min ba tayi min local da yawa gaskiya. Murmushi uwar tayi tace kai har kana da zabi bayan ka bata tsallen ka ko? Kuma Rahama yar uwarka ce ta jini zata zauna dakai tayi hakkuri ba,ajiku ba akan baren da kake son daukowa kan ka. Nace ko kuma waye Rahama cikin yan uwasu oho koma wacece idan lokaci yayi ai mu ganta. Banji ya kara magana ba sai ma motsin da yaji nayi yasa shi tuna cewa ina dakin lokacin nan ya dakai kallon shi gareni, nikan na kawar da kaina gefe ina cewa kaidai ka,sani. Na kara hada kaina na da bango ina mai lumshe idanuwana ni adole ga mai jin barci. A ranshi yace muna fuka kawai kamar bata jin may ake fadi wai tana gyangyadi. Idona a rufe amma tunanen wacece Rahama ya hanani sukuni wanda ban san dalilin yin hakan ba gareni. Tun ina barcin karya har na gaskiyan yazo ya kamani ban farka ba sai kusan karfe daya da wani abuna rana. Duk ko da hayaniyar masu shigo gaida mama a lokacin nikan sai faman barcina nakeyi hankali kwance. Dana farka sai naga Baba ne zaune a dakin yana ba mama abinci da hannun shi. Naso na sulale na fita amma sai hakan baiyi ba don suna jin motsina baba ya juyo yana cewa a,a Fatima kin tashi sannu kinji. Jeki wanke fuska kizo ki karya kinji sannu da kokari jiya mamanki tace ta hanaki barci ko? Nai murmushi nace Baba ina kwana ya gajiyan tafiya yace Fatima aikece dagajiya ke mai jinya. Bandakin dake dakin na shiga na,wanke fuskana tare da dauro alwala don lokacin sallah ya kusa. Ina fitowa Baba yace oya maza zoki debi abinci ki zauna kici don mamaki tace baki son cin abinci. Inbanda abinki Fatima ana jinya ba acin abinci ai sai ciwo ya kamaki ke ma. Na dai daure na dan dibi kadan a plate Baba yace wanan abin fa kamar za,aba yaro dan goye kin dai ga ko ita mai jinyan taci abinci yau sosai. Alaman sauki ya samu ke nan don haka kara kici kema kada ciwo yakama,min yar amana na. Sallama akayi dakin gwagona ce tashigo tare da sadauki daya dauko ta daga gida don bata san guri ba. Nan suka fara gaisuwa da Alhaji tana tambayan shi ya maijikin da kuma yadda ta kara ji. Baba yace, ai hjy masa yar ki zamanta a gurin mu yai amfani nan ya shiga yaba kokarin da nake masu a gidan. Gwago tace ai Bintu yatinyace maihankali saidai kuma gata abin tausayi don rashin jin dadin rayuwan da ta tashi ciki. Sadauki yashigo dakin rugumay da wasu kayan bukatun da yasayo amma gwago sai faman ba su Alhaji labarin rayuwana da irin wahalan danasha a gurin uwar riko na har yakai Baba na da kan shi yace azo dani birni wurinta ko zan samu sassauci a rayuwana. Mamakin gwagona dake ta zuba yake ta zage sai faman yabon wanan yar nata mara kunya take haka a gaban mutane. Nan dai yake tambayan maji ya jikin nata shine ya katse gwagona yake cewa ko likitan ya shigo da rana dubani idan baizo ba sai ya shiga gurin su. Mama tace ai shigowan shi biyu yau yana tambayan ka nace ka tafi gida. Ya mike yana fadin bari na duba ko yana office din shi inda ya mike zuwa wurin likitan. Ya samu likita a office din shi bayan sun gaisa yake fada mashi yadda maji ta samu sauki fiye da yadda suke tsanmani yace kuma gaskiya wanan yarinyar tana kokari sosai wallahi. Yace a ran shi kai may yasa wanan manyar yarinyar kowa dai yabonta yake ne haka yar kauye kawai. Ya daiji dadin yadda likita tabashi bayanin kan mahaifiyar shi. Don ko ba komai yanzu hankalin shi ya dan kwanta ai. Ya koma dakin har yanzu Baba yana ciki suna hira da gwagona sai Maji dakan dan jefa masu baki jefi jefi. Bai so haka,ba don hutu akace Maji ta samu ba yawan surutu ba gashi gwago tana sata magana kuma. Ga mamakin shi sai yaga Maji ma ta kara sakewa sosai akan baya don yinin da sukayi da gwago suna da surutu batai yawan kwanciyar da takeyi ba ranan. Da,ya,dawo da yamma gwago take cewa ita anan zata zauna da Maji sai dai ni na koma gida. Yasan idan na koma,akwai matsala don gwago jikinta ya yi nauyi bazata iya abinda nakeyi ba kamar ni. Yace ai ba matsala kubarta a,nan don koda ana son yin wani abu sai tai maku. Haka muka zauna tun ranan da gwagona dake kawar wa maji da damuwanta. Sarai Maji ta samu lafiya sosai yanzu har ita da kanta take bukatan sallama amma sadauki ya hada,baki da likita a barta har zuwa lokacin da sukace sunan son su sallamay ta. Bayan na,wanke yan kayan da muke amfani dasu a,sibitin ne sai na fito waje na zauna don nasha iska don zama ciki ya isheni. A nan inda nake zaune ya samay ni yake tambayana barci sukeyi ne dana fito nace mashi eh shiyasa nafito don kada na tayar da su. Nai mamaki danaga yasa hankici daga gefena ya zauna wayan shi tai ruri ya dauka. Magana sukeyi da wani akan zasu fita kasan waje wasa amma yace bazai samu zuwa ba don yana jinyar mahaifiyar shi asibiti. Mutumin yake ce mashi da ya daure su fita don akwai kudi da yawa a wanan wasan da zasufita yi yace gaskiya sai mamana taji sauki zan iya fita wani wasa sai yakashe wayan nashi baijira mai mutumin zai fadi ba. Yana kashe wayan ya furzu da iska daga bakin shi tare da dukar da kanshi saman cinyar kafar shi kamar wanda damuwa ta dama. Tausayi ya bani a lokacin saidai shi ba abin tausayi ba ne don duk wanan halin da mama take ciki shine sanadin hakan ai. Ban san ya akayi ba sai ji nayi ina cewa yaya sadauki don Allah kayi hakkuri da abinda zan fada maka bawai nakai na fadi bane amma dole tasa zan fada ma koda bazakai amfani dashi ba. Kan shi ya dago yana kallona cikin mamaki tare da kura min ido, nikuma banji tsoron shi ba naci gaba da cewa. Ba tare da fargaba,ba nace why baka tausayin kan ka dana mahaifiyar ka? Nace yaya wanan ciwon ban fadawa kowa ba,kaine silar haka ga mama sanadin irin rayuwan da kakeyi yasa mama cikin waban halin. Idan dare yayi mama bata barci ko yaushe tana kai kukanta ga Allah akan al,amarinka. Amma kuma,,, Sainai shiru na kasa,karasa abinda zan fadi yace amma kuma may fa. Nace a hankali yaya sai naga kamar baka sani ba kai don kullun ba batun dainawa kakeyi ba sai kara nausa,kanka kake a cikin wanan harkan ta,shaye shaye kishiyoyinta suna fada maganan banza wanda ke saka,zurciyar ta,kara,fadawa cikin halaka. Shiru nayi kamar yadda shima,yai shiru nace yau abin bakin cikine ace duk yawan gidan nan kaine kawai nata kuma kaine mai jawo masu magana. Kowa fa yana da nashi illar amma sun boye nasu saikai dake yi afili ake ganin naka. Don Allah yaya idan ma,sha zakayi ka tafi can nesa da ita inda ba wanda ya sani kayi abinka. Amma da zaka bari gaba daya shine alheri gareka dama kowa naka don nan gaba ba haka zaka zauna ba. Kaima iyali zaka tara yau idan yaranka suka taso suka ganka cikin wanan halin ashe baka ganin tarihi zai iya maimaita kan shi gaba. Za ai masu gori za aiwa matarka gori za aiwa yan uwan ka gorin hakan. Shi wanan abin an san jarabta ne daga Allah amma kuma sai bawa yayi kokarin nisanta kan shi daga gareshi don gudun zama mujiya a cikin al,umma . Baiwa arziki yaya duk Allah yai maka kamarya da kanka abin alfahari yadda ko wace uwa zataji dadin yin alfahari da zurian ta. Nace amma,,,,, Yace ke dakata haka ya isheni na kuma gode da kika kalli idona kika fada min gaskiyan abinda babu wani mahalukin da ya taba tarona ya fada min irin haka. Nasan kinyi kokari yadda kika kalli idona yau kika fada min damuwarku akaina wanda yan uwana dangina abokaina ba wanda zai iya fada min shi. Koke nasan saida kika shirya fada min don naga saida babu kowa a tare damu kikai min wanan magana ko haka na gode insha Allahu nima ina kokarin ganin na daina don bayanin da likita yai min a officer din shi nasan zancen da Umma taiwa majine last week ya hefata cikin wanan halin. Da sauri nace ashe kaima ka sani yaya mikewa yayi yanackakabe wandon shi yace tundani ba mutum bane yaya zan sani. Ya sakai ya wuce ya barni zaune a gurin take naji kamar ancire min wani dutse a zuciyana nace a raina koba komai dai na samu ya saurareni dole ne kuma daga cikin zance na yai amfani da wani yai mashi tasiri aran shi. Ina gurin a zaune yafito hakan yasani sanin har lokacin barci sukeyi basu tashi ba. Yana isowa inda nake yake cewa ni zan tafi idan sun farka ki fada masu cewa nazo sai na dawo anjima. Yatafi abin shi nabi bayan shi da kallo ga mutum har mutum amma kuma babu shedun alheri tare dashi. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKK8N WASU PLEASE,,,,,, A LOKACIN MU KE,,,,,,,,,,, An sallamo mu daga asibiti bayan gwaje gwajen da akayi kan mama an tabbatar da ta samu lafiya yanzu sosai, Sai dai likita ya kara jaddada muna cewa a guje bata mata rayuwanta, wanan kalamin na likita a gaban kowa akayi shi. Duk yaran mama suna kusa haka yaya sadauki yakoso su zuwa gida motat tashi bata daukan mu duka don haka ni da maryam muka hawo Nepep zuwa gida da sauran kayan mu. A kofan gida muna sauka na hango yaya Imirana da wata yarinya yar makwabtar mu ya rike mata hannu yana wasa da ita. Kawar da kaina nayi tankatmr ban ganshi ba amma da yake baida zuciya muna kawowa kusa sai cewa yayi adon gari kun dawo. Yaya mune kuma adon gari yau inji maryam yai dariya yace inbada abinki maryam ai yan mata adon gari ne ko? Wanan yarinyar da Maji zata ban ita aida na more wallahi ta juya tana wa Bintu yace ita fa. Ai babban adon garice wanan tun dai in ta samu guri zakiga ta baje ne kwana biyi lokacin caji ya fara daukan ta. Nace ba adon gari ba adon dawa mara mutunci kawai, maryam tace ke Bintu yayan nawa kike zagi a gabana yanzu zamuyi fada kuwa. Ban tsaya basu amsa ba na kwashi kaya zuwa cikin gida, ban san yana tsaye ba jikin motanshi sai da nazo shigewa na gan shi a tsaye ya sha bakin glass a idon shi. Ni dai na,shige yabini da harara kawai, tun kan nashigo nake jin hayaniyan yan gidan ga kida na tashi dakin Umma. Haka yasani sanin Nafisa tana gida a lokacin don idan tana na zakaji sauti yana tashi a dakin su. Na samu su mama da gwagona zaune a falo nan na zube kayan suna min kun iso nace eh. Nazauna ina cewa wai Allah mun gode ma, jiki dan tafiyan nan kikewa wai inji Amirah. Kafin nai magana cikin muryan mara lafiya mama tace tunda baki san kwana rayen da takeyi akaina ba ai zaki fada mata hakan. Amirah tace cikin make murya maji tare fa muke kwana da Bintu don dai na daina kwana biyu kawai. Kudai kuka sani ace uwar mutum na asibiti amma ku har kunji dadin kwana a gida. Ashe badon Allah ya kawomin wanan yarinyar ba sai dai na karata can ni kadai. Gwagona tace a,a haba hjy ai bazasuyi haka don dai sunga ita din tana masu kara ne kada su raina mata shiyasa. Mai masa bari yaran nan ban san irin su ba kodan sunga su kadaine min suke min wanan halin ban sani ba. Amirah ta tashi tashige daki tai fushi da maganan mama, nice ma na tashi nabi bayan ta har zan shiga gwagona ke cewa dawo mana ki kwashe kayan zuwa ciki kada a barsu nan watse. Maji tace ai kinga abinda nake fadi din waya fara dawowa cikin su ba ita ba amma batai azancin ta kwashe ba. Suna ganin abinda sauran yaran gidan keyi sun zaci alheri ne basu san cewa suma gidan wani zasuba. Idan kaje gidan mutane kace kai baka iya motsa jikinka kai komai sai dai ai maka aiko akwai aiki babba. Da sannu za,a koya masu tunda basu saba da hakan ba tun farko amma ai zasuyi insha Allahu . Allah dai ya kyauta mai masa yaran nan halin su sai su wallahi basu san ciwon kan su ba. Koma irin yadda ake min a gidan su baya damun su dawasu ne ai basai an fada masu abinda zasuyi ba wanda ya dace. Kiyi hakkuri hajiya kowa da ir8n halin shi amma bari zasuyi idan ana lurar dasu. Na samu Amira a daki tana, waya nashigo dakin , tabini da kallo tace yanzu duk kokarin da nake wai maji bata gani. Nace Anty uwa uwace duk abinda suka,fada muna gyara ne a garemu mu godewa Allah da ya barmu dasu a raye. Wanda baida uwa fa a duniya bai kuma damai kwabamashi fa. For god sake may ye banyi a gidan nan ne wai amma kulun maji tace banyi daidai ba. Fadan iyayye fa takine gare mu anty tun da tace haka yanzu da ta dawo gida sai ki matsa ki kula da ita yadda zata ji dadin ki. Kallo na tayi kamar zatai magana sai kuma tai shiru kawai nikan na koma dakin mu na,shiga wanka don duk warin asibiti nake jin ina yi a jikina. Bayan nafito ne na tara duk kayan da mukai amfani dashi asibiti na wanke su tas sannan nadawo falo na zauna sai naga Amirah tafito. Taje gurin mama tace a kawo maki abinci ki dan ci ko da kadan ne maji don rana yayi lokacin shan maganin ki ya kusa. Uwar taji dadin haka sosai don ta kasa boye farincikin ta tace tau akawo min Amirah. Ta hado ta kawo mata har gaban ta tare da ruwa da maganin gaba daya. Maji tace mata na gode Allah yai maku albarka da haka kuke min wa zaiji mu daku. Gwagona tace tau gashi dai uwata ta gyara yanzu ai shiya fadan yake da dadi ga yaro don ya gyara kuskuren shi. Tajuya inda nake tana cewa ke kuma Bintu wallahi ki bar yi wa maji komai daga yau kibarni ni zan mata. Maryam tace wallahi saidai a raba amma ban yarda nima ai ina son albarkan . Nan dai aka wasance zance ana dariya tajuyo tana daga min gira alaman godiya nima hannu na daga mata alaman komai ya wuce. ****** ********* ****** Kabir yazo duban jikin maji da ya shigo kauyen su kamar yadda ya saba duk karshen wata da yake zuwa. Kabir ya iso gidan namu amma bai shiga ciki ba, ya tsaya daga kofan gida inda ya zauna cikin motar shi. Yana saye da kananan kaya amma dinkin shadda ce akai mashi karamin dinki dashi. Sai kamshin turare yakeyi ajikin shi yai matukar kyau dashi sai annuri yake . Waya ya buga min cewa gashi ya iso a kofan gidan da nai mashi kwatance. Na fito acikin hijjab dina duk da nasha kwaliya daga ciki amma na rufe jikina da hijjab. Waya yake amma hankalin shi yana a kaina yana kallon yadda nake takona ina dan waige don ban sheda motar shi ba da yazo da ita. Saida yai min horn nagane cewa shine acan gefe daya zaune cikin motar shi. Ina isowa inda yake ya kashe wayan shi yana min wani kallo can kasan idon shi. Na dan duka kadan ina cewa barka da isowa ya hanya ya mutanen gida suke? Yace duk suna lafiya suna gaida ke amma uwargida tace tana fushi dake wai baki taba kiranta kun gaisa ba. Nayi murmushi gami da cewa karufa min asiri don Allah, yaya ina ni ina kiran ta tace banda kunya. Yace aiko gara ki daina jin komai don Haulatu tace bata dauke ki kishiya ba a matsayin yar uwa da kuka fito shiya daya ta dauke ki. Nai murmushi kawai tare da cewa Allah sarki aiko na gode Allah ya bamu hakkurin zama da junan mu. Ya amsa cikin jin dadi da fadin amin my love, har kin sa naji wani sanyi a,raina da na ga wanan gidan da kike har na fara fargaban kada wani ya kwace min ke anan. Nace haba yayana ai kyau alkawari cikawa da bazanyi ba tun farko baxaka ga ma fuskana ba ai har mukai haka dakai. Yace nako gode da,wanan karamawan da akai mun yanzun hankalina ya kwanta sosai da jin kala man ki. Nan muka dan dauki lokacin muna hira dashi sai dariya yake bani na yadda zamu zauna a gidan shi. Tun daga nesa na hango motar shi tafe da karfi yazo ya park dan nesa kadan damu. Tun karyo kwanan shi ya hango su mamaki yake irin yadda ya hangota tana dariya abinda bai taba ganin tanayi ba a rayuwan ta. Kallon wanda suke tare yake inda yaga maishi ai ba yaro bane ya ma girmi duk yan gidan su balle shi. Amma shine wanan yarinyar ta tsaya haka har take wasan baki a gaban shi koma may wanan zai iya fadawa budurwa har taji dadi haka. Ko dai dama da wanan tsohon take waya tana wani kashe murya a gaban mutane ba kunya saboda wanan tsamuraren mutumin. Wani ir8n haushi da takaicin yarinyar ne da baitaba jin irin shi ba ya kama shi. Ya fito daga motan shi lokacin Kabir ke tambayana waye shi nace mashi yayanane na nan gidan. Don haka yafuto suka gaisa sama sama dashi kamar mai sauri ya shige abinshi tare da gaura marfin motar shi. Kabir ya juyo inda nake yace tau ikon Allah nace rabu dashi haka yake hutsune dama shi baida mutunci. Dakin shi yanufa yana jin wani gumin bacin rai yana fetso mashi ya bude dakin shi ya shige hakana. Mun dan kara dauka lokaci yai min sallama tare da mika sakon shi gurin mamana da bata da lafiya. Nan yake ce min shi abinda yakawo ma yaji kunya don wanan gidan abin yai kadan wallahi. Cikin mamaki nace haba aiba komai wake raina alheri sai mara godiyan Allah kawai. Nan nasamo yara suka shiga dashi nace sukai dakin maman UF don sunfi gane ma hakan. Mukai sallama yatafi sai banji dadin hakan ba don ban so mu rabi dashi ba don jin dadin dan kasancewar mu na dan lokaci a tare. Har na shigo gida yana tsaye a kofan shi kamar may waya take yaji zuciyar shi na azazzalar shi tankat ya shake a lokacin. Can kuma yai tsuki yace ina ma ruwana da yar iska komay zatayi taje tayi mana may ye hadina da itama dahar na damu kaina. Sai zuwa dan wani lokaci ya shigo gidan inda ya samu kayan da Kabir ya kawo muna a falon mama. Ya shigo wani iri dashi idon shi akan kayan duk da kayan ba laifi amma sai yaga ai duk komatsen banza ne kawai. Ya samu guri ya zauna yana fadin wanan kayan kuma fa haka? Amirah tace surukin kane yazo yaya mai neman Bintu shi yazo yakawo wa Maji na dubiya da Allah sawaka. Ance mai mu bamu iya saye ne sai ya kwaso muna wani tarkace haka ba kyau gani. Ko an fada mai mu makwadaita,,,,, Kai don Allah ya isa kai wani irin suruki ne kuma maimakon kasa albarka sai kuma ka fara fadin maganan banza kawai don Allah kwashe min su zuwa ciki kinji maryam. Maryam ta mike tana fadin ai yaya an fara kawo maku tarkace ke nan tun da maji ta tara zuka zukan yan mata haka har uku a dakin ta. Amirah tace wanan kan nima nawa yana tafe sai aka sa dariya kawai gaba daya maji tace Allah kawo shi lafiya mugani ni dai naga ta ya ta saura naku din. Wallahi Maji kina bata yaran nan haka fa na hango wanan yarinyar a,waje da wani tsoho tana wani washe baki kamar taga wani saurayin kwarai gaban ta. Daga inda nake ciki ciki nace kai kaga tsoho nikan bai min tsufa ba wallahi ai aure ba inda baikai mace. Maji tace wallahi ke dai ya ta ai in an kwana biyu zan fadawa babaku don yasani kada yaga kina tsayi dashi kofan gida yazana,min matsala. Cikin hasala yace may kikace banji ba fadi mana naji ya fifito da idon shi waje. Maji tace kai ban fason hauka ko kuma kayo shaye shayen nakane zaka sauke muna hauka anan. Mikewa yayi tare da kutawa yace wallahi maji duk ke kesa yarinyar nan tana rena mutane bata jin tsoron kowa a gidan nan. Na,sa ubana sai kai min fada ko in ba a zo neman su ba kai za,abarwa su kaita kallon su ko yaya. Ya fita yana fada ba maijin abinda yake fadi muka kwashe da dariya kawai Amira na cewa ni wallahi yaya mamaki yake bani Allah. Kamar Bintu za,ace wai bata isa aje saurayi ba yanzu sai yaushe ko ni Allah yaba maiso yanzu ai fiya da haka zanyi mai. To Allah dai ya kawo wa kowa na alheri ke kuma Fatima sai aita hakuri kuma a kama kai don mazan yanzu sai a hankali. ****** ********* ****** Muna zaune da yamma ranan mukaji sallama wasu mata sai da suka fara shiga gur8n su Umma an dauki lokaci sai gasu sun shigo gurin maji sun zo gaida ita. Nan dai suka fara gaisawa suna mata yaya jiki sai mai dan shekaru a cikin su ke cewa wallahi lokacin da kika kwanta asibiti Alhaji baya gari sai jiya ya dawo. Shine yau mukace zamu zo nan gida mu gaidake yaya kika kara ji ya kuma katfin jikin naki ? Maji tace Alhamdullahi na samu sauki ke nan sai matar tace ai halin dan yau inkace zaka sashi a ranka sai ka mutu ga banza su basu damu ba. Tau anyi wani abin ne kuma hjy Saude? Maji ta tambaye ta tace ba ance zancen yaron nan kika sa a ranki har yakai ki ga son kamuwa da ciwon zuciya ba? Inna lillahi haka kuma kukaji to Allah ya sauwaka ni dai na san zazzabi nayi mai karfi . Sai suka kama kallon junan su cikin mamaki sai ga hjy Kubura ta shigo dakin tana cewa a,a hjy saude yanzu nafito wanka yara kece min kun shigo ai. Kunzo gaida hjy ne gata nan tasha allurai ta farfado kin san maleria yanzu baijin magani kadan sai da ya kaita kwance wallahi kin san bana ana sauro da yawa ita kuma sai tace bata shiga net bata son kuma hayakin coil. Matar tace muko yanzu ake ce muna,wai ciwon zuciya ne ya kamata kan zance Faruk . Kai ina kuma kuka samu wanan labarin haka mutum kan abin tsoro ne wallahi zazzabi tayi nima har gurin likitan nake yake min bayani. Allah dai ya sauwa inji dayar matar da batai magana ba tun shigowan su tace ai yanzu da abu ya samay ka magana ya samu ke nan dada . Aishine inji hjy kubura ta fara tafiya sai tace a,a sarakuwa na ashe kuna gida anyi hutu ke nan ko? Matar tace ai suna gida anyi hutu har sun kusa komawa ma. Ince dai kinga dan nawa ko yafitane hjy maijjida tana kallon maji don son bayani maji dai murmushi tai mata kawai bace komai ba. Duk hiran su a kunne mu yake muna can zaune daga bayan su sai lokacin na fahinci budurwan sadauki ne tazo gaidashi. Ni dai bari nasa akirashi ku gaisa tunda kun shigo don nasan kila yana gida naga motar shi dan shigo gida dazun. Uwar yaran tace wai wa Faruk, kai hjy kubura kina dai zance wallahi. Basu jima ba suka mike suna cewa zasu tafi nabi yarinyar da kallo gajera ce sosai baka bata da haske amma tana da kyauta gaskiya. A rai na nace shine har yake kiran wata yar kauye gatashi wata irin cus da ita sai gajirta. Har kofa maji taraka su duk da suna cewa ta barshi yarinyar ta juyo tana cewa su maryam bye bye da dan daga hannu. Suna fita maryam tace kinga mai dogon rigan nan pink ita ce zata auri yaya sadauki tun suna yara aka hadasu diyar kanin baban mune suma ana cikin gari suke da zama suna tudun wada ne su uguwar su baban mune can. Maji ta dawo daga rakiyan su take cewa kai matan gidan nan basu barin halin su. Yanzu don sheri su hjy Saude zasu fadawa wai saboda sadauki ne na kwanta ciwo wai ciwon zuciya don hana ruwa gudu kawai. Amirah tace ba kowa zai fade shi ba sai mama Asiya don itace yar bakin ciki nidai inajin su imani duk ya kashe . Wai haka kishi yake ne kaitawa dan uwanka zagon kasa da hassada a fili haka haba jama,a wanan wani irin sheri ne kuma. Ka zauna gaban surukan mutun harda sarakuwa kuna sukan mutun haka haba dai duniya. Nan kuma muka fara zancen hjy kubura mama tace ni ko ba komai ai hjy kubura tana min ta wani guri. Amirah tace namay maji jifa wai har gurin likita taje tambayan shi da gulma. Daga inda nake nace kaman nasan haka tunda mukaje na roki likita ya boye muna wanan magana. Ke din Bintu nace wallahi anty tace kinji ba aiko da yanzu an yada shi kashi kashi ko. Hayaniya mukaji daga cikin gida bul su maryam suka fita don saurare wai ashe hjy kubura ce tafito tsakar gida tana fadin munafuki dai baiji dadi ba,wallahi. Yanzu don bata zama shine ake wani fadawa mutane arasa ma inda za,ai gulma wai sai gurin sarakan mutum ace wai surikin su ya haddasawa uwarshi ciwon zuciya. Sai ga umma dunkul dunkul tafito tana cewa in ma gulmace mu muka fada masu haka. Karya ne muka fadi ba shine yajawo mata wanan matsalan ba don bakin shaye shayen shi daya sawa kan shi da rana tsaka. To an fadi din ko akwai abinda zakiyi ke ma nan daban ne baki fadi ne maye baki fadi gurin aikin ku akan shi. Ko k8n zaci bamuji ne sai anzi gida don makirci ki nuna ke tasuce, don kilibibi kawai an fadi din may zakuyi. Haba nan sukai tawa kan su tonon asiri har saida Amirah ta kira mahaifin su yazo ya samay su. Ran shi a bace ya samay su da fada yana cewa kun daiji kunya wallahi yau may yarinyar nan hawau ta tare maku a gidan ita da yaranta. Kullun cikin bakin cikin ta kuke da hassada baku gajiyane wai ku, wallahi duk abinda ke gudana a gidan nan nadani ido kawai na samaku don ta Allah bata mutum ba. Ni sadauki dana ne ko wani hali yashiga ban gydun shi don ba,a canzawa tuwo suna. Kuma ku sani babu wace ta wuce kaddara a cikin ku don haka kowa tashiga hankalita. Inba lalacewa ba yaushe za,aji wanan mugun labarin a bakin ku koda kuwa hakan ya zama gaskiya ne ma. Yanzu inma hakane har zaku iya tonawa yar uwarku asiri a hakan may zaku gane gurin tonawa cikin ku asiri. Umma tace ni banga wani abi gaddama ba agurin nan duk garin nan waye bai san abinda yakeyi ba da har za,a tsaya ana tayar da jijiyoyin wuya hakane wai. Yace oho haka kikace tace dama hakan ne don kai baka son gaskiya shine zakazo kana son danne gaskiya. Kafin mu mu fada masu ma ai suma sun sani ba abakin mu suka fara ji ba tunda in yai bakin shaye shayen a can kan titi yake tanbelen shi. Duk wanan rigiman da akeyi akan idon sadaukine wanda ya dawo gida a lokacin don yai shirin fita gurin wasa. Alhaji yace sai kuci gaba da fadi shege ya fasa indai hakane sai kafara fita kayi shela a waje kafin kazo gurin mu. Nan kowa ya watse yabar gurin suna ci gaba da yada bakaken maganganun su a dakunan su. Bai fasa shigowa gidan ba sai dai bakin ciki ya hana shi yin magana duk ran shi a bace yake yai murtuk da fuskan shi. Ya samu guri ya zauna tare da dafe kan shi gwanin ban tausayi, Amira ce matace mai takawo mai abincine yace No kibarshi kawai Amirah. Ya mike yafita daga dakin don baiga fuska ba gurin mahaifiyar su. Batai magana ba sai ajiyan zuciyar datakeyi kawai, ganin zata sa damuwa nake cewa. Inda daji bai gama cin wuta ba aiba ai wa kututure barka don kowa na da "ya"ya ai, balle mutum yaji dadin zagin nawani. Amira tace ai shine ai Allah ba azzalumin kowa bane yana sama yana kallon kowa. Nace ai shine mudai kullun fatan mu Allah yada ya daina kuma ma ai ya daina zancen su daine kawai. Sai lokacin maji tai magana tace anya Fatima kada fa kiyi shedan zur waya fada maki ya daina? Nace mama da,bai daina,ba ai baki ganin shi haka normal kullun nifa munyi magana dashi asibiti. Da sauri suka kallo ni maryam tace ke Bintu kikai magana da yaya sadauki din nace wallahi ko Allah. Tace cabdijam lalai Bintu kin kai wallahi kikace mashi may nace wanan kuma ai siri ne anty maryam. Amma wallahi ku yarda dani insha Allahu yaya ya daina shan wanan abin saidai ban sani ba ko ya daina kwatakwata, ne Amma gaskiya da,wuya kuma dai kan adai gidan nan ko garin nan akaracewa wai yasha wani abin maye. Da sauri maji tace Allah dai yasa Fatima Allah yasa hakan ne wallahi ta fadin cikin ban tausayi, Nace insha Allahu mama don na yarda da maganan shi zai daina ne din ko kuma ma ya daina kawai za,ace ma. Maji tace Fatima ke alheri ce sosai a gare kuma ke wata haske da Allah ya jefo min cikin diyana. Tunda kikace haka wallahi Allah na yarda da zancen ki don na karanci halinki ko Shima dai din da gaske wallahi naga canji sosai a gare shi don banga alaman wanan shadin ba duk kwanakin nan. Maryam kan sai mamakina takeyi tana matsa min wai sai na fada mata yadda mukayi nace ki bari inyadawo ki tambaye shi anty amma ni ba,ajin mutuwan sarki a bakina wallahi. Wanan dalili fadan nasu yasa ya yanke shawara a ranshi zai nisanta kan shi da gida, don gudun bacin ran mahaifiyar shi kada ciwon ta yazo yatashi mata a sanadin bacin ran shi. Sai da dare ne daya,shigo yake fadawa Maji cewa zaiyi tafiya zuwa kasashen waje kuma yana ganin zasu dan dade a can din. Maji tai shiru kamar bazatai magana ba sai zuwa can tace sadauki ba wai ban son tafiyan ka nisa bane a,a. Halin rayuwa irin naka nake tsoro anan ma da kake yaya aka,kwashe dakai balle kayi nisa da mu inda ba makwabi. Yace Allah nan ai Maji insha Allahu abinda kike zato bazai faruba don wasan mu ba,a yarda mutum yai wanan dabiar ma. Tace to shike nan sai ka samu mahaifinka ka fada mashi don yasan abinda ake ciki kada sai kashirya yaji zancen daga sama. Ya samu mahaifin shi ya fada mashi zasufita zuwa waje kuma zasu dan jima acan suna wasa da sauran kashe nan yaja mai kunne tare da fatan alheri a gare shi. Bayan kwana biyu ya shirya duk muna falo ya shigo sallaman su inda kowa ke mai Allah ya tsare da fatan alheri suna ta bashi sakon abinda zai sayo masu a can. Nidai ina gefe bance komai ba bayan Allah ya tsare da nai mashi ban kara tankawa ba saida zai tafine muka fita rakiyan shi wanan karon hardani da ban fita rakiyan shi saida na fita. Motar shi a gida ya barta yace wa Amira idan zamu school adinga zuwa dashi don dama sun iya mota su. ****** ********* ****** Yau Aliyu yana dauko talla direct dakin sisko ya nufa ya samay shi yafito daga wanka yana daure da towel a jikin shi. Sai yaron yadan tsaya daga waje don ganin shi haka da yayi ba,sutura a jikin shi. Yace shigo mana boy may zai sa ka tsaya daga waje sai yadan aje roban tallan shi daga waje kadan yace shigo dashi mana kada wani yagani kuma asan kana nan. Sisko baiji kunyan cire tawul din dake jikin shi ba wai yana shafa mai haka yasa Aliyu yadan kawar da idanun shi gefe. Dago kan da yaron zaiyi yagani ko yagama sai ganin Sisko a gaban shi gap dashi yayi tsirara haihuwan uwar shi. Ya na mika mashi mai wai ya shafa mashi daidai cinyar shi yaron yakarba ya fara shafa mai sai wani lumshe ido dan iskan keyi a lokacin , Nan wasa yafara canza launi ya shiga yiwa Aliyi wasu abubuwa da yaron ya kasa hana shi yi mashi yana cewa ba kaga yadda muka kalla ba a TV ranan dakai. Shine nake son karafa koyo kaga inka girma ka iya abinka ko nan yaron baiyi aune har yakai ga tube shi ya danne shi sai da ya biya bukatan shi ya sarara mashi sai faman ihu yaron yakeyi don yafi karfin shi sosai. Yaron duk da sisko ya sauka a kanshi bai fasa kukan neman taimakon da yakeyi ba. Yuka ya jawo ya nunawa yaron tare da,bashi tsoron yace idan ka fadawa wani abinda nai maka sai na yanka ka wallahi ka mutu gaba daya wawan banza mai shegen tsoron tsiya kawai. Dakyat ya samu har yaron yai shiru yabar kuka nan yadaga gadon shi ya dauko dubu biyu yaba yaron yace yaje yasai duk abinda yake son ya saya ci . Amma kada ya fadawa kowa abinda yai mashi inba haka ba har baban shi sai ya kashe. Ganin yaron bai iya tafiya yasashi tare mai mashi akaishi gida yana,tajawa yaron kunne. Yaron ya isa gida da kyat yake tafiya ya samu har maman shi ta gama abinci tana ganin shi take cewa a,a yau har ka dawo haka . Tace aje roban ga abincinka can ka dauka kafin babanku ya dawo kadan kara fita. Sai ya shiga daki yafito yakuma koma da sauri ya kasa tsaye ya kasa zaune. Amma sakaren duk bata kula ba sai cewa take wai may kake nemane haka ka zauna mana kaci abinci kafita. Sai yaje gurin frizer su ya dan dafa don ya zauna aiko sai ya saka ihu, da sauri ta aje kwanon da taje debo ruwa ta nufo shi tana fadin wai may nene haka tunda ka dawo nake cewa ka zauna amma kana min wani abu can dabo dabo dakai. Maza zauna kaci abinci kayi kafita sai hawaye shar shar yace mama, mama wallahi ban iya zama. Ikon Allah may yasamay ka da,baka iya zama kuma yaron yai shiru yana dan buga kafan shi tace maza zauna dan bura uba kawai ni zaka kawo wa diban albarka. Yaje zama sai kuma ya mike da karfi yana tsala ihu yace wallahi mama ban iya zama da sauri ta kamo shi lokacin yaron ya tsananta kukan shi sosai. Wandon shi tacire tagani ko kurjine ya samay shi aiko tafara cin karo da ajiyan maza ta hankada shi da sauri bata san lokacin da tace na shiga uku ni mariya wa yai maka wanan ta,asan haka. Ina sai ihu yaron yake wallahi mama na bari take ta saka kuka abuna farko dayazo mata a rai shine uwarta ta kwsheshi tare da rufe gida suka nufi waje nan ta tare mai mashi sai gidan su. Uwarta naganin yanayin su tasan babu lafiya may yafaru may ya samay shine wai? Tana kuka tana mayarwa uwarta abinda ya faru da yaron tambayan duniya sunyi mashi amma basu gane komai ba sai kuka yake yaki fadi. Uwarta ce kinga mariya wanan magana yafi karfina bari mu nemi mahaifin yaron nan tun abu bai lalace muna ba. Mariya tasa hannu akai tace ta shiga uku umma baifa san yana talla ba dama. Tace yau kan ai ba boyo don dole yasani don wanan magana,banamu bane mata. Nan takira samari kannen maria suka dauki yaron zuwa asibiti guda kuma yatafi kasuwa kiran mahaifin shi. A sukwane ya iso asibitin yana tambaya ana fada mashi cewa wani ne yai lalata dashi ta baya kuma asibiti sunce basu taba yaron sai an kira yan sanda. Karasawa yayi gurin yaron yace Aliyu wa yai maka wanan abi haka a ina ka hadu dashi, Bai basu amsa ba sai kukan da yakeyi dole suka nufi gurin yan sanda dashi nan aka tasa shi gaba da tambayin hikima irin na yansanda. Yaron yace yace ina fadi sai ya yankani kuma ya kashe babana da kyat dai aka samu yafara magana cewa. Ummh dama wani ne mai sayen ruwana kullun shine shine yace nazo dakin shi kullun na dinga kai ruwa yana saye shine yau yau danaje sai sai ya kamani ya danne yai min haka? Salati uban yasa yace Aliyu dama kana tallane ban sani? Cikintausayi da langabe kai yai maganan tare da kurawa yaron ido. Ya juya inda yan uwan maria suke tace shike nan maria taci amanata ta cuci yaronta ta tona min asiri a garin nan. Sai yakai zaune darsha ya sake wani irin kuka mai tsuma zuciya inspector yace yanzu ba wanan ba ku tashi muje asibiti a duba yaron nan a gani tukun don a san halin da yake ciki don da gani yana jin jiki. Nan suka dunguma sai asibiti da yaron saida yan sada suka sa hannu likita ya fara duba yaron. Nan yake sheda masu sai anyi mashi aiki an rage mashi abinda ya shiga cikin shi kuma aikin akwai tsada don sai sukanshe kudi dubu dari da hamsin cikin ragowa. Uban yaro yafara rusa kuka yana ya shiga uku ina zai shiga ya samo wanan kudin haka masu yawa. Dole aka fara neman inda za,a samu kudi don a taimakawa yaron dake cikin wahala. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,, A LOKACIN MU KE,,,,,,, Tun bayan fitan yaya Sadauki a falon dakin shi ya nufa kai tsaye ya fada a kan katifan shi ya kwanta yai lamo tankar wanda yake barci, sai dai ba barcin yake ba. Damuwa ce tayi masa yawa a ran shi a hankali wasu yan siraran hawaye suka rika silalowa daga idanuwan shi. Ya dade a haka ya mirgina gefe daya yana fadi a fili, wayyo rayuwata may yasa nake yawan tsintar kaina a cikin mawuyacin halin komai na tashin hankali akaina yake faruwa ni kadai a gidan nan. Allah ya jarabci rayuwana da masifa saka uwata a tashin hankali ko da yaushe . A yadda ya lura maji ta dauki son duniya ta kwallafa mashi shi kuma gashi ya kasa bata farin cikin rayuwa. Ya kai zaune daga kwancen da yake yana cewa ya Allah kada kasa na zamo sanadin jefa uwata a masifan rayunwata. Gashi tunda ya tafi waje bai mai da hankali ga sha ba amma yana dawowa gida sai ji yake zuciyar shi tana azzalzalar shi sai da yaje yasha ya samu natsuwa a zuciyar shi. Ba don wanan yar kauyen yarinyar mai saka ido ba da ta taimake shi da bai san yadda zai yi ba idan maji tafito ranan ta fahinci a buge yake. Can kuma ya tuna zancen baffan shi wai ba zai ba mashayi yar shi ba shi dama Rahama bata gaban shi abudai ne in Allah ya nufe ka dashi ba yadda zakayi. Tuna siffan Rahama yayi bai san lokacin da ya sake wani tsuki ba akan wanan abin har za,ai masu wulakanci shi da uwar shi a cikin gidan su. Yana da,budurwa da ta lake mai yar adamawace amma saboda zancen Rahama da maji ta nace shiyasa ya,fita zancen ta kuma yarinyar irin masu son abin duniya din nan ne ko yaushe cikin bani bani take shiyasa bai son al,amarinta. Sai dai abinda ya daure mashi kai shine kishiyoyin mahaifiyan shi da bai san may tare masu ba haka a rayuwa. A,sanin shi dai komai yana masu wanda ya dace in ma ba yanzun da yaga tsana tayi yawa a tsakanin su dashi ba yake nisanta kan shi da al,amarin su. Kiran wayan shi akayi bai tsaya duban ko waye mai kiran nashi ba ya daga wayan tare da karata a kunnen sa yace hello. Muryan Fatiman adamawa ce tace sweety na baka kirana sai dai ni na kiraka ko? Dan guntun murmushi ya sake iya bakin shi, yace Fatima ya akayi ne, ? Tace my life nayi missing dinka sosai, tunda ka tafi gida baka kirani ba banji daga gare ka,ba. May yasa kake min hakane, baka damu dani ba sai nice ke yawan nuna damuwata a kan ka, Yai yar guntun murmushi yace Fatima bakiyi min komai ba wallahi nima rashin ki yana damuna abubuwane sukai min yawa a nan gida shiya sa baki jini ba. Tace karike min kanka kada kaci amanata don min ni taka ce, ka sani. Yayi murmushi tare da,cewa ban maki alkawarin ni naki bane don haka ban dauka ba. Dariya tayi daga bangaren ta tace kanace ina wasa ne ko gaskiya nake fada maka. Yace ni ban yi alkawari ba don ki sani aure ma zanyi very soon don har an kammala komai ko. Cikin wata irin murya mai karfi tace what are you joking? Yace bana wanan da ke ai gaskiya na fada maki tun farko ina da mata a gida da zan aura. Kalaman Sadauki sin tayarwa Fatima adamawa da hankali don haka sun gama waya bayan ta kashe ta kasa zaune ta kasa tsaye shawara daya ta yanke wa ranta shi kuma zatayi. Washe gari haka na muka tashi ba dadi a gidan kowa zuciyar shi a cushe take mai. Daga cikin matan gidan su mama ba wace ta damu da damuwan mu sai sha,anin su sukeyi da raha da yaran su. Hjy kubura ce kawai ta shigo dakin namu zuwa rana don Saturday ne bata fita ko ina. Ta samu na hada wa mama abin kari ina duke ina zuba mata sugar tai sallama falon. Muka karba mata take cewa, daidai lokacin maji nace nabar mata sugar hakana. A,a hjy maijidda ke ma bakin son sugar ashe da yawa ni gashi na rasa yadda zanyi na daina shan wanan sugar don ba lafiya yake ba mutane a jiki ba yanzu. Murmushi Maji tayi mata tace ni sugar dama bai damay ni ba wanan yar tawa ce ma take yawan son samin sugar ko yaushe. Ta zauna saman kujera a kusa da maji nan muka shiga gaishe ta mummy ina kwana tace lafiya yau ana gida ba,a fita ba ne. Maji tace sun samu hutu ne shiyasa kika gan su a gida tace ayya har hutu yazo ashe? Nan ta juya gurin Maji tace ashe kuma haka Alhaji sani yai muna akan zancen yaran nan ? Maji tai dan murmushi tace kila shine yafi zama alheri a rayuwan su damu ma gaba daya. Amma gaskiya Alhaji sani bai kyauta ba yaci kafa bai yada ganye ba yadda Alhaji ya rike shi har yakai haka kuma yanzu kan yar matsalan rayuwa zai kawo wanan dalili haka. Ai yana da gaskiyan shi don ba mai son ya dauki dan shi ya bayar inda babu tarbiya. Haba sadauki ne baida tarbiya hjy maijidda sai dai ace kawai wanan lalurar dake kan shi. Kuma wanan aiba wai wani abin da za,a ki mutum bane kan shi shidai kawai yana da wata manufa ga hakan ne kawai ya sha zugi daga cikin gidan nan. Tau koma dai maye sai ya,rike dan shi shima Allah ya bashi wata wace tafita ba shi ke nan ba. Hjy kubura tai matukar mamaki a ranta yadda maji tai saurin basar da zancen a lokaci guda. Don ita a zaton ta abin zai jawo mata matukar tashin hankali amma sai gashi tashi daya sunga ta basar da zancen ita ma. Shiru sukayi a lokaci guda falon babu wanda,yai magana a cikin su sai hjy Kubura ta mike, tana cewa dama cewa nayi bari nazo na jajanta maki kan al,amarin. Maji tace nagode Allah ya saka da alheri, ai zaki kai ga sarakuwa ba da dadewa ba insha Allahu. Lokacin Bintu ta shigo dauke da ruwan da maganin maji a hannun ta . Sai ta ce yar gidan maijidda ni dai da ma da Bintu kika hadasu da zaifi don kin san halinta tasan nashi. Gaba daya muka kalli hjy kubura wace ni ban ma fahinci maganan ta ba,sai da naji mama tace ai da hakan zai faru sai nafi kowa farin ciki . Da sauri hjy kubura tace mai zai hana hjy maijidda abu tuwona maina. Fatima tana da mijin ta da zata aura ai bada dadewa ba ma zasu kawo kayan auren ta. Allah sarki ashe har wani ya riga mu niko tun jiya nake anyana hakan a raina, wallahi ni dai da haka zai yiyo da yafi komai sauki wallahi. Gaskiya ba zai yuyo ba a haka ma ya suka kare kullun yana samin yarinyar gaba da hattara sai na jajirce mashi akanta. Wanan ai ba matsala bace don bari zasuyi dasunyi aure amma wanan cin fuskan da Alhaji sani yaiwa mutane ban son a wuce lokacin auren nan Sadauki bai samu wata ya aura ba. Komai na Allah ne inji maji tace an auri mahaukaci ma balle dan shaye shaye, Hjy kubura tace ai shine lokaci ne dai bai yi ba amma sadauki yanzun ai abin so ne ga ko wace mace. Zasu dawo suna da sun sani ai a baya don sun wa yarsu ai ba wani sukaiwa ba amma may ye abin kushe ga sadauki inba wanan harkan ba. Tana fita dakin su maryam suka ce munafuncin banza kawai kamar da gaske. Maji ta katse su tace ko na munafuncine tayi min don shine dama zaman kishin. Tafi sauran dake ta nuna farin cikin su akan al,amarin amma ita dai ko tana da manufa ta dai nuna halarci ai. Sai maryam ta,kwashe da,dariya tace kaji mummy da,wani zance wai Yaya Sadauki ya auri Bintu. Kirmitsi ke nan inji Amirah, tace cikin kwashewa da,dariya, sai kuma tace wallahi fa da sun dace, don itace kawai ta karanci rayuwan shi. Nace don Allah Anty bari zancen nan kina son ya kashe ni ke nan mama tazo ta kwashi gawata. Maji tace da shima na kashe shi ranan yadda ya kashe min "ya. Aka kwashe da dariya a falon nan sukai ta hira suna dariya wanda hiran tasu nake jin yana kona min zuciya daurewa kawai nayi ina dariyan yake. Kada nai magana mama tace nima na kyamaci dan ta duk halarcin da zatai min amma saura kiris nace wa zai auri wanan kazami. Don ni yanzu balain haushin da takaicin shi nake ji don wallahi duk yafita raina kwata kwata. Sannu sannu aka fara rage zancen don sunga wa yanda su keyi a kan su basuma damu da zancen ba don ko a jikin su ma. Min fita zuwa kasuwa don sayo yan abubuwan da ake bukata a gurin mu na girkin mu ni da Anty Amirah muka fita,mun bar maryam tana girki a gida. Komai mun sayo harda ma abinda muka manta bamu saka a list ba duk mun sayo da sauran canjin hannun mu. A gajiye muka dawo gida da kayan mu niki niki, nan muka zube a falo bamu dade da zama ba sai ga yaya yashigo wanda shigowan shi gidan ke nan tun safe da ya fita. Tv yana kunne ya zauna suna kallo da maji suna gaisawa tambayan inda ya shiga take tunda safe haka. Ya dan yamutsa fuskan shi yace wallahi ina cikin gari ina dan zagawa ne kawai. Maganan da ake a tv shi ya daukewa kowa hankali a falon don photos wani yaro aka nuno bai wuce shekara sha, goma ba zuwa sha daya. Wai wani yai mashi fyde ana neman gudun mawan gurin mutane don a,tallafawa iyayyen shi ai mashi aiki. Salati falon ya dauka lokaci guda ga mahaifin yaron annuna yana kuka yana bayani acikin tv. Hankalin kowan mu ya tashi nan maji tace oh wanan duniyar ina zaki damu haka yanzu wani daukan alhakine wanan karamin yaro haka ace wai kato yai mashi aika aika haka ba dadin gani. Maji bari na,dawo abinda ya fadi ke nan ya,mike yabar falon da sauri. Ashe yana fita asibiti ya nufa gurin da aka sanar akai taimakon kan yaron nan sadauki ya ba da kudin aikin dubu dari biyu dana sayen magani amma yace kada a fadawa mutane shine. Amma duk da haka abin yanzu bai boyuwa don saboda al,amarin media da yai yawa. Da dare muna zaune falo sai hira ake yana tare da uwarshi suna maganan da ta shafe su amma mu hankali mu baya a kan su. Maganan da ake a TV ya mayar da hankalin kowan mu akan tv din labari ne akan yaron da aka nuna dazu da yamma. Nan suke sanarwa cewa an samu wani matashi mai kishin kasa da addinin shi yazo yabiya kudin aikin yaron tare da daukan nauyin duk wani magani da za aiwa yaron har yaji sauki. Wanan kuma ba kowa bane sai matashin dake tashe muke alfahari dashi acikin garin nan watau UF. Shahararen dan wasan kwallon nan dake bugawa kasa kwallo yanzu ayaune kuma muka samu labarin yatafi wasu unguwanni na,tallakawa inda yaiwa mata da yara marayu kyautan kudi da kayan abinci da sutura. Waya ya dauka ya kira wani nomba zai fara magana yaga wani irin kallo da uwarshi ke mashi na mamaki. Yace yanzu danace kada a nuna wanan abin sai da kuka nuna amma sai mai labaran ke fadin duk da yace mu boye shi kada mu fadi wanan alheri nashi ga al,umma. Munga ya dace ace mun fadawa duniya don matasa masu hannu da,shuni irin shi suyi kishi da halin shi suma. For god sake banji dadin wanan nuna program din nan ba da kasa ayi cikin fushi ya kashe wayan nashi. Sadauki muryan maji ce take cewa dashi wanan alheri keyi a gari haka bamu da labari. Dukar da kanshi yayi kasa yana cewa maji Annabin rahama yace idan zakai alheri ko hannun hagun ka kada ya sani, Amma kinga mutanen nan sai da suka baiyana ni a fili haka. A dakin Umma kuma tana ganin abinda ake fadi ana yabon sadauki tace cikin wani tsawa don Allah ku kashe min wanan shegen karyan haka kafin na,bata maku rai. Dole yaran suka kashe TV suka kunna kaset suna kallo ba don ran su yaso ba don sun fi son suga labarai akan dan uwan su saboda yanzu akan shi har wani jiji dakai suke a gari. Baba kuma yana zaune a falon shi yaga wanan labarin sai cewa yayi Allah nagode maka da wanan baiwa da kaimin ta tsatsona. Gidan hjy saude kuma tana kallo taja tsuki tana cewa aikin banza adai karata can, sai ga yarta tashigo dakin tana cewa yanzu ake min waya wai anga yaya sadauki yana raba alheri a tv. Ke rufe min baki ki rabani da zancen wanan mashayi mai kyau dan maciji. Nafada maki ki fita zancen wanan mara mutuncin, yaron da baida tarbiya ko kadan. Rahama tace mama amma ni gaskiya na fada maki na ina son shi ko a hakan. Bazaki so shi ba nace yaron da akace idan yasha har fitsari yake a wanda da amai kacakaca shine zaki wani ce nabarki ki aure shi bata karasa maganan taba Rahama tasa kai tabar dakin cikin turo baki gaba. Washe gari mukayi bakuwa a gidan mu kowa bai santa ba sai dai tashigo gidan tana tako daidai da ita tana tambayan mahaifiyar U F. Mama Asiya tai mata nuni da dakin maji cikin binta da kallon ke kuma daga ina. Tana cewa o mun shiga uku U F kuma a gidan mu kamar gidan wasu arnaku can mukan wanan yaro yazama muna jaiba agidan nan wallahi. Daga kofa ta tsaya tana sallamu alaikum daga ciki muka amsa mata. Tashigo yar gaye ce ta karshe ga kyau ga ilimi yana nunackan shi a fili. Sai data zauna take cewa maji tare da dan zaudowa saman kujeran ina wuni mama. Lafiya kalau inji maji tace kunzo lafiya ta amsa da fara,anta lafiya kalau mama. Sai sukai shiru maji ce tai karfin halin fadin ban fahince ki ba don ban sheda ki ba yar uwa. Mama baki sanni ba, well na dai zo ne nan don daki Umar U F ni yar adamawa ce ina son na auri yaron ki ne shikuma ban samu kan shi ba shiya sa nace bari na zo na nuna kaina a gare ku. Don Allah ko daddy din shi yana gida shima mu gaisa dashi, don yasan ni na san shi. Ikon Allah inji maji tace mahaifin nashi yanzu baya nan ya tafita yana kasuwa. Tace ok ba matsala ai ina garin zamuga juna da dare idan ya dawo gida. Sai ta wani harde kafan ta daya saman daya tana taunan cingan a bakin ta kas kas kas. Mukan ido muka zuba mata wanan fitsara haka wai zamani ina zaki damu hakane? Kai A LOKACIN DAI MU KE KAN,,, Juyowa tayi inda muke a zaune tana cewa, sannun ku fa yan mata ya kuke cikin wani daga muna hannu? Ni dai na mike zuwa ciki na hado mata kayan drinks na kawo mata ta karba tana cewa yauwa na gode fine girl. Waya ta dauka ta kira layin shi mun dai ji tana ce mashi yazo gida gata nan dakin mama. Nasan tambayan ta yayi wata mama, sai cewa tayi mummcy mana ta sokoto. Dama na kusa karasa abinci na mike nafita, zuwa kitchen na duba girki na na samu ya dahu nan na tsaya na hado ma,bakuwar mu abinci mai kyau dashi . Daga kitchen ina jin muryanta tana,waya sai kiran abokan ta take tana fada masu tazo sokoto yanzun haka tana dakin mumm din U F a zaune. Sai gashi da saurin shi ya iso gidan tun a kofan gida ya sheda da gaske takeyi tazo garin don ganin motan ta da driver ta dayayi. Tun da sadauki ya diso falon yaji wani irin bacin rai ya kama shi a ran shi yake fadin wai may mata suka mayar da kan sune yanzu? Ya shigo da sallama a lokacin na fito daga kitchen dauke da abincin da zanbawa bakuwar mu. Tana ganin shi ta saki wani shu,umin murmushi tare da cewa my man you think iam joking ko ?. Ta wani shagwabe murya tana cewa I really miss you alot and i can't keep it, Dole na biyo ka don nazo na ganka nakuma ga su mama da little sisters din mu. Sadauki ya dan shafa sumar kan shi da hannun shi na hagu ya dan kalli inda Maji take zaune cikin kallon ikon Allah. Don yasan yau sunga fitsara a gurin Fatima ba kadan ba don ita bata da kunya ko kadan. Tace ya naga ka,wani bata rai ko you are not happy with me here ne? Yace cikin yanayin su na yan duniya No ba haka na bane ban dai yi expecting din ki a nan bane. Tace ai na fada maka zan baka surprise dama to gani yau a,sokoto kuma dakin mummcy. Yace saukan yaushe ? tace wallahi dazun nan na iso dama nasan bazan sha wahala ba gurin gane gidan ku don sha haranka. A kaduna na kwana shiya ka gan mu a wanan lokacin, amma fa gaskiya akwai nisa. Yace to ya hanya? Tai wani har da idanuwanta tare da langabe kan ta tace hanya lafiya kalai tunda na gan ka. Sadauki ya juya inda maji take zaune ta hade rai ba yabo ba fallasa a fuskan ta a lokacin. Ni dai na,aje abinci ina cewa, ga abinci nan tace yauwa sannu little sister wai ya sunanki ne tunda nazo kike wahala dani. Sai da na dago daga duken da nake nace Bintu tace wawwwo, sunan mu daya dake ashe. Amma ki daina cewa kanki Bintu kamar wata yar kauye akiraki da,Fatiman ki kawai ai nice, name ne sunan mu. Sadauki dai yakai zaune daga dayan kujeran nan bakuwar ta mayar da hankalin ta a kan shi suna dan hira jefi jefi. Wanka na,shiga na fito na saka wani dogon riga light gren mai kamar bubu daga sama kasa an mashi sharp yafito da sura na na,daura dan kwalin shi a kaina. Sam na ma manta cewa da bakuwa a falon nan nafito ina cewa Anty Amirah wai yaushe ne zamu tafi gaida baban su Amata. Wai wanan pretty din itace last born din mune gaskiya tana da kyau sosai wallahi. Kamar bazai bata amsa ba sai can yace No diyar sister din maman mu ne ita ga dai sisters dina Amirah ga maryam itace yanzu a,matsayin last born din mu. Yanzu ita wanan din ba blood sister dinka bace yace a dan hasale na fada maki yadda muke da ita ai ko. Take ta hade fuskan ta, tace there's problem here yace akan may fa tace No barshi ina dai magana ne kawai. Maji bata falon tashiga ciki don bata iya,karasa hadiyan takaicin da yazo mata har dakin ta yau. Wanan abin haka ba kimtsi ke kiran kanta da,suna wai sarakuwarta ta ina ? Kai duniya kowa da,tashi matsalar dai kenan yanzu ita haka duk rabin jiki kusan tsirara shine wai tazo nuna kanta a gurin sarakai a haka. Kai wanan tanbadewar da fitsara da may yai kamane haka wai tundaga wata uwar duniya yarinya ki taso kice wai kinzo gurin na miji. Ban kai ga zama ba naji muryan maji tana kirana daga ciki da sauri nake na nufi gurin ta. Zaune take saman gadon ta hannunta yana rike da caunter na zikkiri take ce min har yanzu wanan fitsararar bakuwar taku tana nan ke nan bata tafi ba ko? Nace ai zaci anan zata kwana ne don naga daga nesa ta fito. Tsaki taja tare da kawar da kanta a gefe tace yaro zai jamin wani sabon abin fade a gida yaya zanyi na fada mashi yai gagawan fita da ita gidan nan kafin mutanen gidan nan su ankara da ita. Nace mama bani wayan ki ta mike min gurin sunan shi nai mashi massage kamar haka. Ka gagauta fita da ita kafin mahaifinka ya dawo yasamay ta nan. Na tura mai ina turawa nafito daidai ya fara karantawa wani kallon ke ko yabini dashi. Nace sannu da zama ko wani kallo ta watso min kamar tasan nice na turo mai da sako yanzu tace yauwa. Amirah tace, yau zaki koma dai ko? Murmushi tayi tare da,gyara zama tace a,a har kun gaji da nine ke nan ko Amirah tace a,a ha mutum ai bai gajiya da bakon shi. Yana gama karata massage din ya dagi kan shi sai kai mukai tozali dashi ina kallon matar . Harara ya,kara watsa min niko nai mashi dariyar mugunta a fakaice. Muryan shi mukaji yana fadin Fatima muje na kaiki inda zaki sauka kafin dare yayi cikin diriricewa. May kake nufi da hakan ba a nan zan sauka bane gurin mummcy ? Yace baki da hankali ne a cikin gidan namu zaki sauka don baki da kunya to mu nan ba haka al,adan mu yake ba Yace so ki tashi na kaiki kafin dare yayi ban son daddy na ya dawo ya samay ki a gidan nan haka. Don mu ba haka al,adan mu yake ba ya mike don dale itama bashiri tamike tare da daukan hand bag din ta tana cewa ina mummcy muyi sallama yace ta shiga alwala ke nan. Yana gaba tana bayan shi suka fice daga gidan aiko basu dade da fita ba sai ga Baba ya dawo daga kasuwa a lokacin. Sai da suka bar uguwar ya sauke ajiyan zuciya tare da cewa look Fatima bai nai maki wullakanci bane da hakan amma idan har mahaifina yadawo ya samay ki a gidan akwai matsala babba wallahi. Kakanki kin sani wanan tsarin da kikazo dashi ba tsarin mune na hausa fulani ba. Tai wani wal da idanuwan ta tace nima nasan da hakan amma ban dauki wanan a wani abu can da zai iya kawo maka matsala kamar ka babban yoro haka. Yace wai ma ba wanan ba may yakawo ki garin nan ne wai Fatima ? Fatima tai wani marairaicewa tare da kallon shi cikin wani yanayi tace, Matsala aka samu danaji kace an maka mata agida ana batun auren ka shiyasa na kasa zama naga gara nazo ayita a kare a gaban iyayyen ka. Sadauki ya katseta da cewa dakikazo gaban iyayyena kice masu may ? Yace look Fatima da farko na so na karbi bukatanki gare ni amma yanzu hakan da kikai min duk kin jagula komai don haka idont think zan iyaci gaba da zama dake kuma again. Ran Fatuma ya,sosu da jin maganan da sadauki yai mata sai dai dole yasa ta daure don tana son guy din. Da sauri ta juyo gare shi tana cewa cikin hada hannayen ta biyu guri guda tare da marairaicewa tace don Allah U F kada kayi fushi dani. Yin fushin ka akaina zai iya jefani cikin mawuyacin hali a rayuwana sosai wallahi don na mutu da son ka sosai wallahi. Yayi wani guntun tsuki tare da kawar da kan shi gareta yana cewa don may zaki biyo ni har garin mu don baki da hankali. Tace kayi hakkuri wallahi duk na,rude ne da ka fada min zakayi aure na,rasa may zanyi akai shiyasa nabiyo ka har nan. Sadauki ya kara jan tsuki ya kalleta a wullakance yace na fada maki cewa anyi min mata a gida kuma bazan canza maganan iyayyena ba insha Allahu akaina. Yace kuma ki sani na kyaleki ne yanzu don garin mu kikazo don haka yasa na kyale ki idan badon haka ba da na dauki mataki a kanki sosai. Don bazan yarda ki hadani fada da iyayyena akan ki jamin wullakanci a gidan mu. Ya farka mota da karfi cikin five star hotel da suka shiga da alama ran shi yakai kololuwar baci a lokacin. Nan Fatima ta kifa kai tafara kukan tana rokon shi akan yayi hakkuri ya,aure ta zata zauna da wata su zama matan shi su biyu. Tace na gane wanan far yarinyar dana gani itace proposer taka don naga tafaye shegen kyau. Yanzu akan wanan karamar yarinyar kake min haka may zaka,gane a gurin yarinya karama haka ne please cikin kuka take magana. Yace look Fatima na fada maki tun farkon haduwan mu ni ba mazina ci bane kuma ban iya,neman mata ba ina under control din iyayyena . So kike akan ki na saba dasu ne for god sake don haka ki sauka na sama,maku masauki da safe ku kama hanya ku tafi. And kuma na roke ki tun magana bata kaimu ga bacin rai ba kada ki kara,shiga harkata is over hakana. Nan ya bude mota da zuman tafito su shiga ya kama mata masauki sai ma kunya da yake ji kada wasu su gan shi da mace azaci yazo yin wani masha,ane. Cikin kuka tace no kabarshi zamu koma kaduna mu kwana gobe na koma Abuja. Yace is better for you. Nan tafito tashiga motan ta driver yajata tana kuka suka kama hanyan kaduna da yamma lis sosai. Ya sauke numfashi duk da yaji tausayin ta yasan wanan shine kawai hanyan da zaibi yasamu kan shi daga shu,umancin ta akan shi. A gida kuwa maji takai kololuwa da bacin rai sai jiran shi take ya dawo da yadawo yara yaba sokon maganin mama da kuma kaji da drinks da yasayo masu sanyi. Yace ace yana massalaci zaiyi sallah mamatace koma may zaiyi ai zai shigo ya samay ni gidan nan. Bai shigo ba sai da suka sallamay isha,i yashigo cikin gida kannen shi na gaida shi amma bai iya amsawa ba idon shi yana kan mahaifiyar su don jira yaji may tace mai yakeyi. Ya zauna Amira tana fadin yayana kadawo ya bakuwar ta mu take, nan ma shiru yai mata baice mata uffan ba sai take cewa, a can ka barta ne ?. Don Allah Amirah ki barni na huta haka na wanan tambayan ya isheni wallahi haba gaki kamar yar jarida. Zama yayi ba,wanda yace kallah a cikin su sai zuwa can Maji ke fadi a da can baya idan ance min kana hurda da mata bazan taba yarda ba koma waye ya fada min. Amma yanzu da yake ka fara rike kudin kanka gaskiya nai mamakin ganin wanan irin yarinyar ace wai da,su kake harka. Allah yaceceni in ba kuma wani sabon rayuwan ne ka bulle min dashi ba aji dadin yin min sabon zagi a gidan nan. Maryam na gaba ina bayan ta muka fito daga cikin daki mun samu mama tana mashi fada sosai kan wanan sabon halin da tagani a gare shi. Maryam tai tsagal tana cewa ni dai kwata kwata,batai min ba mace haka yar bariki gata nan da ita sai wani iskanci take wai wayewa ke nan. Maryam ba ga ku nan da irinta ba a gida ina yanzu Nafisa haka take shiga sai kaya ya matse ta sosai duk suran jikin ta a waje. Amirah ke fadin haka wa maryam tace idan zagine kuma ai akwai shi a gidan ku. Maji dai fada sosai take mashi akan mutum yayi hankali da duniya kafin ta kure mashi don duniya,ba matabbaci bace. Baiyi magana ba sai chartting da yake da,wayar shi a zaton mu da bakuwar shi yake fira kafin ya fita zuwa gurin ta. Amma har dare muna dakin zaune tare dashi sai hira yake da wayar shi kawai da amsa call. Maji tace daka bar yar mutane acan may zataci sai a lokacin yai magana yace sun tafi maji. Tace acikin daren nan suka tafi haka basu gudun dare yai masu a hanya. Bai ce uffan ba yana zaune har dare goma da wani abu yamike yana fadin zai tafi ya kwanta sukai mai sai da safe kaina na duke ina karatu tun zaman shi ban yi magana ba a falon. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,, A LOKACIN MU KE,,,, Sun shirya tafiya zuwa lagos gurin Michael don haka Nafisa itama ta nace akan cewa dole sai tabisu. Tare sukai tafiyan inda ya turo masu da kudin suka shiga jirgi sai lagos a gida kuma tace zata gidan wata kaunan mamanta ne ta,kwana biyu. Ranan da takwana uku da tafiya Umma ta kira waya tana tambayanta cewa yaushe zata dawo ne don tace ga jiya zata dawo bata dawo ba kada Alhaji yasan bata gida fa. Tace sai gobe nan uwar tai mata fada kan dole ta dawo ranan don gujin bacin ran su gaba daya. Amma har dare Nafisa bata dawo ba haka yasa Umma ta tayar da wani wanta guda yabi bayanta gidan yar uwarta ya dauko ta. Yaje gidan yar uwar maman nasu tace ai Nafisa batazo ba ma gidan ta kwata kwata. Nan hankalin Umma ya tashi sosai gashi kuma ko sun kira wayan Nafisa basu samu a lokacin. Tun tana boye damuwarta har uwar kwakwaf mama Asiya ta fara ganewa yan dakin na cikin wani tashin hankali amma da ta tambaya sanin hali sai Umma take cewa, bakomai bane dama. Kwanan ta biyar suka dawo sokoto haja haja cikin kudi, nan uwar tasata daki da tambaya ido ya riga ya bude tace buki suka tafi na wata classmate din su gusau ta san ko tambaya Umma bazata bari ba shiyasa tai karya. Imirana ranan kamar ya make ta yai mata fada sosai sai dai basu sani shiga yake yana fita inda ya shiga. Don Nafisa tayi nisa ko batajin kira yanzu don kar take kallon su tasan abinda basu sani bako. Nan uwar taga yadda take facali da kudi take tambayanta sai cewa tayi wani Alhaji ne dan canji ta hadu dashi a gusau shine yabata kyautan dollars kuma yace ma zai zo gida yaga iyayyenta. Umma ta fara jin dadi har ta fara sake magana ita yanzu arzikin bana yaci uban na da don yarta tayo babban kamu sosai . Wasu ko sai dai su zauna idan dan su ya tafi yayo fashi ya kawo masu kowa a gidan yasan Nafisa ta samu dan canji don sai facaka suke da kudi abinsu. Uwar bata san cewa yarta ta wuce sanin ta ba yanzu da ita da iyamurai take hurda su ko suna son yaran hausawa don sunce sunfi iya making, love. Idan kuma ta fita su da su Raiha sufita susha kayan mayen su suyi tatil dasu ta dawo taita barci. Ranan Amira zata shigo taga su Raiha sun dawo da ita yanayin data gan su a ciki sai bai mata dadi ba tashigo maji na ciki take fada muna nace Anty kiyi shiru kada wani yajiki ace kina hassada da samunta tace wallahi hakane amma may zanwa hassada a wanan gurin haka. Yanzu har takai sun fara neman junan su idan sun sha ko kafin su sha sai sunyi masha ansu a tsakanin su sannan su koma,suyi tatil dasu. Idan abinta yai nisa ita Nafisa har kwalba take dagawa don zuwa lagos din da,sukayi saurayinta Johnson mashayi ne sosai a can takoya shan giya. Gashi sai dare ya tsala zata dawo ba,wanda ya sani sai mahaifiyarta ce zasu bude mata gida ta shigo. Amma har lokacin Umma hankalinta baikai ga cewa yarta ta samo sabon rayuwa ba ita gani take gajiyace dai take dawowa dashi. Don Umma na da,wani hali indan ta,dawo aiki ta zube guri guda bata motsa jikin ta, dan damadama,idan ita ke da duty a gidan ranan zata danyi kiza kiza. Hjy kubura ta fara jin zance Nafisa a gurin wata kawar aikinta, amma sai bayata yarda da zancen ba ta dauki maganan ba gaskiya ba tunda kawar tace har gari suke bari zuwa wani guri yawon banza kuma ita tana ganin Nafisa a gida. Kuma abokanta su Raiha sun riga sun gagari iyayyen su babu maijin kwabo su, suji yanzu. Ganin bata san labarin ba yasa kawarta cewa kai kila dai ba gaskiya bane kama daine suka gani suka ce itace. Sai dai Umma ance laifi tudu ne, take naka ka hango na wani, Zance ta shine sadauki yana can kasan waje ya zama tattacen dan iska, yana hurda da,turawa yana sayar da kwaya da fashi. Inda Allah zai kashe mata bakinta ranan sai ga danta ya shigo da sauri yana cewa su Maji dasu mama Asiya ku kuna,tv tashan sport yau su sadauki zasuyi wasa. Nan kuwa suka shiga kunnawa suka kai tashan wasan kwallo har falon Baban su, sai da ya kunna suna zaune aka fara fitar da yan wasa sai gashi saye da kayan wasan shi sun fito, yana saye da rigan shi an rubuta mai Umar sokoto, Nomba 9,,, Haba take yaran gidan gaba daya suka dauki ihu suna,wallahi ga yaya sadauki ga yaya sadauki. Nan aka fara wasa ranan duk gari ya dauki ihu sosai don ganin dangida kuma haifafen dan gari yaje fitar masu da sunan su. Ba atashi wasan ba,saida yai masu ci biyu dada fa ihu ba kama hannun yaro wani haushi yakama Umma tace kai ku kashe min wanan shegen abin sai kace wani abin kwarai wai kwallo kafa kukewa wanan ihun haka. Tasa aka kasshe mata TV ta baba daga dakin shi ya aiko mata su kunna Tv su ga Umar nan ana hira dashi a TV. Rananta baiso ba amma dolen ta, ta kunnawa daidai Sadauki yana fadi cikin turanci da ba,wanda yasan cewa ya iya ta haka slays English irin na turawa yana fadin. Yana mika gaisuwan shi da godiyan shi ga mutanen kasar shi Nigeria dakuma iyayyen shi da,sukai mai tsaye yakai ga wanan matsayin. Haba gida ya kara daukan ihu da murna sai bugo waya mutane keyi suna cewa ku, kunna TV su gan dansu ana hira dashi a NTA sports. Dakin Maji kan ranan ba a cewa komai don farin ciki da murna maji saida tai kwallan hamdala ga Allah. Yayi kyau yai fari sosai hasken shi ya fito da kyau kana ganin shi kasan dadi da ni,ima ya sauka mashi. Kwana da kwanaki bakajin komai sai zance UF kawai ke tashi a gari nan sauran yaran gidan su, suka,shiga barazana da daukan kai a gari. Baba ya kecewa su mama bayan ya tarasu yace yana son yaran nan suyi aure hakana don haka ai zancen zuwa gidan yan matan su ai magana. Hjy kubura tace har da dana ke nan Baba yace aishi ma yakamata yai aure shida ke fita waje ya dade kinga sai ya dauki abinshi su tafi can su karata can. Yace zaiga kanin shi Sani suyi magana kan Rahama don asan abinyi nan dai duk aka aje magana za,a aika gidajen matan su. Sai dai may Baba yana zuwa gurin dan uwan shi kan zancen auren sadauki da yar shi da kowa ya dade dasani sai cewa kanin nashi yayi gaskiya shi sai sunyi shawara da matar,shi da yarsu tukun. Baba yace ikon Allah sani akan auren yaran da,suke duk abu daya shine zakace sai kayi shawara da mace tukun kabani amsa. Yace eh don akwai dan mahawara tun kwanaki akan zancen saboda haka abari ya kara tuntubar uwar yarinyar yaji. Haka Baba ya bar gidan jiki ba karfi don yana da ,wuya ba,a samu matsala ba ke nan amma dai sai yabar zancen a ranshi. Ita ko hajiya saude da mijinta yazo kan zance sai cewa tayi ita gaskiya bada ita bata daukan yar ta, taba mashayi yarinyar da kurciyar ta taje can takama hadiyan bakincikin da namiji ga banza. Yaje can ya samu wata irin shi yar shaye shaye su daidaita tsakani su, amma bata ganin maciji da rana ta tura hannunta ramin shi da dare. Yar ta tazo ta haifi yara lalattatu a rasa yadda za,ayi dasu yace amma dai kin san wanan magana zai iya kawo matsala tsakanina da dan uwana . Tace zumuncin shi yadade bai baci ba ai akwai diyan dangi da yawa yaje mana ya nemay su can ba yarta ce kawai yar dangi ba ai. Sai yaja bakin shi yai shiru don bai iya tunkaran dan uwan shi da wanan zancen gaskiya. Shi mai daurawa sadauki aurene yau kuma ace shi da kanshi ya hana yarshi sai yaya ke nan Maji ko da,sukai waya da saudaki tasa shi gaba kan lalai sai ya hado lefe daga can bai so ba amma don bin umurni ta ya hado kayan shi tundaga kasar Spain da sukaje wasan. Sai murna take cewa dan ta ya kusa zama kamilin mutum tunda zai aje iyali, Duk da dai ba son hada zuria takeyi da yar hjy Saudae ba don kansu guda da umma kuma yaran basu da kunys ko kadan. Bayan kaman Sati uku ya shigo gari nan matasa su kai dandazo gurin zuwa taron shi da,dawowa zakace wani gwauna ne zai zo. Mukan muna school bamusan wainan da ake toya ba a gidan don bamu san zai dawo ba a ranan. Sai after six lis muka dawo duk a gajiye muke a lokacin, nice gaba maryam tana baya ta tsaya ba mai Napep kudin shi. Tun a kofan shiga falon mu na fahinci akwai namiji a ciki don takalman maza danagani daga waje. Ban kawo shi bane tunda nasan baya kasan a lokacin da yar sallamana na shigo falon. Ina saye da,buje da rigan les da,akai min feeted dinkin ya karbi jikina pink color da,farin zare akai mai yan flowers kanani ajikin shi har bakin lace din banyi kitso ba don ciwo da kaina keyi sai dai na,wanke na daure da ribon kawai. Na shigo ina fadin wai mamana yau kan duk nagaji, wallah,,,, Ganin sa kawai nayi zaune ya kara haske yai kyau dashi yana saye cikin wasu kayan maza ko ba,a fadi ba kan san sukai kudin su ga wani irin uban kamshi daya hade muna falo tun daga waje zai tare ka. Haka kawai ganin shi yasa na makale magana ta sai gabana da naji ya fadi yaushe rabon dana dan matsala a gidan mu kusan wata shidda da yan kai ke nan, Tun tafiyan shi don ko suna vedio call dasu Amirah bani zuwa kusa ni balle nagan shi. A hankali nakai zaune saman masangalin kujeran dake daga kofan falon ina fadin sannu da dawowa yaya. Cikin dan basarwa ya amsa min yace kuna lafiya, A taikace na bashi amsa da kalau na mike zan shiga sai ga Maryam tana ganin shi tasaka wani irin uban ihu tai kanshi. Yace ke ke kinfa girma yanzu kinga yadda kuka koma,wasu big ladies da ku kuwa,? Ta wani shake murya tace kai yaya yanzune ma fa zan cika twity cif fa. Itako Bintu she is just 18 da yan kai yanzu kaga mu yarane har yanzu don dai ka dade baka ganmu bane kawai. Yace baki ganin tana ganin ta girma yanzu harda bani amsa any how. Ni kaina na san amsar dana bashi bata dace ba amma yadda ya hade fuska shi ya dace dashi ai, Maryam tace kasan aure zatayi shiyasa ta fara daga kai. Yace aure kuma tare da kallon maji yace badai da wanan tsohon ba dana taba gani. Kai yaya Kabir ne tsoho wallahi dai ba tsoho bane don dai tana da mata ne kawai Yace da karfi cikin tabaya da what? Mata bako guda ba fa ke nan maryam tace ai Bintu babbace itace ta uku a gidan. Yace fir god sake Maji may zaku aurar wanan wajen don Allah kuma wai mai mata har biyu ita ta ukun su, Nace tau bisimillahi matsala ya sauka na,shige abina ciki kan shi kawai ya girgiza yace ok lalai ma yarinya ta girma kan. Har nashiga nai sallah kada lokaci ya karasa shigewa suna falo sai zuba suke shi dai bakajin bakin shi. Nafito dauke da abinci a dan plate na koma can nesa dasu na zauna na fara ci a hankali. Kamar kullun fuskan shi a daure yake ba dariya amma kuma wanan yaudararen dariyan tashi da baikai cikiba yana nan shi amsa da yake ba kannen shi kawai. Inacin abinci na jin sunana da maryam ta kira yadani dago kai shima idanu ya,watso wanda tun ina yarinya nasan da wanan kallon wanda nake dauka kallon tsana. Tace wai Bintu don Allah ba har part mukace zamuyi mashi ba amma maji ta hana mu. Nace kunfi kusa anty maryam ba magana na bane wanan na mike zuwa cikin kitchen din dake attache da falon mu na aje plate na shige don lokacin magariba yayi shima naji muryan shi yana ce masu zai fita yai sallah ya dawo. Bayan na idar na samu mama a falo nace mama dama antanadarwa yaya da abinci ne tace waya fadawa zai dawo yau. Barshi kawai kinji tunda yazo nai mashi magana yace min wai yaci a government house can yafara sauka wai. Nace ,a,a ashe abin nayi ne ke nan abu har gidan gwauna kuma tace bari kedai mutane sun dauki kwallo yanzu kamar wani bauta can. Amira tace ku may kuka gani mudake gida mu mukasha kallo yau kinga yadda aka rako yayan mu kuwa a gidan nan. Motoci mashin mashin kala kala mungan su yau wai duk yaya aka rako gidan nan. Nan dai mukasha hira har muka lakace dare yayi bamu sani ba shikuma ba dawo gidan ba har lokacin. Halinshine idan ya,dawo bai zuwa da,tsara ba sai bayan kwana biyu su iso garin. Wanan karon ma hakanw ta faru don sai bayan kwana uku da,dawowan shi kayan shi suka iso. A gaskiya mun sha,tsaraba sosai don bai nuna,min yan ubanci ba a nawa ganin Amma mama sai naji mama na mashi fada wai bata son haka don may kayan su Amirah yafi nawa kyau. Amira tace Maji haba duk abinda yaya,yaiwa Bintu sai kice ya,nuna mata banbanci mana. Maji tace ban son hakanane nafu idan zai saya maku abu ya saya maku iri daya koda kala zai banbanta. Shi dai shiru yayi kawai baice komai ba yasan al,amarin maji da,wanan yarinyar sai Allah kawai. Wai ma ko yaya akayi har maji tagane hakan da sauri amma ita,wawiyar sai wasan baki take tana godiya. Gaba daya gidan an sheda sadauki ya dawo don har kudi sai da yabawa mutanen gidan. Sai cikin dare ya shigo yace wa Amira ta kira mu tazo mu kwaso kaya a motan shi. Tirka sa don set din akwatina ne har uku mukai ta,kwaso bamu iya daukan manyan dole shi ya kwaso sai da,muka huta muka shiga duba kayan. Ni har tsoro kayan suka,bani abu sai kace diba akaitayi ba kudi akasa aka saya ba don yawan su. Mun gama Amira ta nisa tace wai yaya munga kaya har bamu iya dubawa don yawan su. Murmushi na kullun yayi yace sunyi maku ke nan dai ko da,sauri mukace sosai ma yace yana mikewa maji idan akwai abinda babu aciki sai a,saya anan. Ban san lokacin da nace kai haba sai kace riya wanan kaya haka aiko gidan sarki za,a kai sai haka. Maryam tace, ke Bintu akwai abin dariya wallahi baki taba ganin lefe bane haka nace nikan sai yau gaskiya Allah dai yasawa aure albarka sukace amin gaba daya dakin Muka kwasa sai cikin dakin muka mayar dasu can kuryan maji muka,kawo zannuwa muka rufe ba,wanda yasan anyi a gidan balle afara yadawa. Shafa,i da,wuturi nayi nice farkon zuwa na kwanta zuciyata sai tunanen wanan irin kayan da yaya hado na laife nace a fili Allah ya kara shirya wa maji dan ta. Na sauke wani ir8n ajiyan zuciya tare da cewa Allah gamu gare ka mai kudi yaji dadin shi gaskiya. Wankan da nayi kafin nai sallah yasani jindadin kwanciya sai barci sai dai kuma zuwa dare ban san may ya,farkar dani ba. Amma sai naji dirin mota an dawo da daren nan nace a,raina Allah dai yasa ba yaya bane a cikin daren nan. Sai kawai na tsunci kaina da tashi na leka shi din ne yana rataye da corth din shi kawai sai na zarge shi. Da sauri nai istigifar don zato zubi ne koda ya zama gaskiya da sauri na koma makwanci na. Sai dai barci ya buwaye ni don haka na mike na fara gabatar da nafila har tsawon wani lokaci na koma na kwanta. Sai barci da,safe ban shiga school ko maryam yau bazata dadeba can da,wuri zata dawo. Sai na,dan kara,kwantawa sai zuwa goma nafito don na kama,ma Anty Amira aiki don zata fita yau. Ina fitowa mukayi kicibis dashi kallo daya nai mashi na gane yasha daren jiya. Ban kula shi ba don wani irin tsanan shi naji a,raina ya kare zuben min a idona ko lokacin mama tana ciki tana shiryawa haka ma Amira tana kitchen tana aiki. Ke dauko min abin karyawana yace cikin wata murya na dan kalleshi nai saurin kara dauke idona. Ya zauna yana wani lumshe idanuwan shi nasan abin bai sake shi ba har lokacin. A hankali na,tako inda yake dauke da,kayan karyawan shi na duka saitin shi kamar zan aje kayan . Cikin wata yar karamar murya nace mashi ka,saita kanka kafin mama ta,fahinci halinda kake ciki hankalinka ya tashi. Don nasan kasha daren jiya kadai jin tsoron haduwan ka da Allah ka tausayawa mahaifiyar ka. Na mike da,sauri na,barshi daidai ya mike yana gyara saita kan shi daidai don yai mamakin yadda duk yakamay amma wanan manyar yarinyar wai ta fahinci yasha jiya da dare. Da kyat don mamaki ya iya saita kan shi sai ga uwar tafito kuwa tace a,a babana kana nane zaune ashe yace eh Maji yanzu nazo ahine ma wanan yar taki takawo min abin kari. Fatima to nima kawo min na karya yau da Baba na tun dashi kun bashi. Na amsa daga ciki nace mata gani tafe mama ita dai abinda akayi na kawo mata plantain ne da Irish da,kwai sai tea. Na koma na dauko masu ruwan sanyi nabawa kowa nasa na juya nabar falon inajin su suna hira yana ce mata har yanzu yana da gajiya don bai samu hutu ba. Nasan ya fadi hakane ya kawar da zargin wani abu a ranta nan take fada mashi cewa taji baban su yace zai kira baban su Sani yaji yadda za,ayi kan zancen auren shi. Ban ji amsan daya bayar ba amma naji tace ai ina ga ba wani dadewa za,ayiba ayi bukin. Bai dade ba yafito yabar gidan kada ya sake layi uwarshi ta gane shi tunda ga manyar yarinyar nan ma ta gane balle maji. Da dare muna zaune Baba ya aiko kiran maji tafita zuwa amsa kiran shi andan jima kadan sai ganin ta mukayi tashigo rai a bace. Idanuwan ta sunyi luhu, luhu sun kada sunyi jawur dasu duk muka bita da idanuwan mu muna kallon ta. Amirace tace Maji may akayi kuma yaya sadauki ya dawo magana ya tashi ko. Ta dago fuskanta ba yabo ba fallasa tace bashi bane Amirah na sauke ajiyan zuciya daga inda nake. Tambayan ta suka matsayi nace anty kubar mama harta huce tukun koma may ye kuji daga baya. Dalilin dayasa mukai shiru ke nan gaba daya a falon ba wani mai kwakwaran motsi sai tv dake ta aiki shi kadai. Sai wayan mama yai kara ta dauka da alaman lalashin ta ake ga,wayan kuma kamar muryan Baba ne. Mama na aje wayan sai kawai tasaka,wani irin kuka mai ban tausayi tana cewa ita dai gidan zata bari gaba daya ma kowa ya huta. Da sauri na mike na isa gareta na ce mama don Allah don Annabi koma maynene kiyi hakkuri kibarwa Allah. Ban kai ga fadin wani abu ba,sai ga yaya sadauki ya fado dakin ganin yanayi uwar yasa shi saurin karasawa gare ta yana tambaya cikin tashin hankali. Su Amira sai faman kuka sukeyi suma hankali duk a tashe nima kukan ne yazo min lokaci guda. Kara tambayan ta yayi tare da bata hakkuri kafin ta dan sarara kukan nata sai kuma dakin yai tsit. Tace babana ban taba zaton Alhaji sani da kan shi zai iya muna wanan cin mutuncin ba a matsayin shi na mahaifi gare ka. Amma sai gashi tau ya,wanke ido yana fadawa Alhaji maganan banza a kanka. Yace bazai ba mashayi yar shi ba kaje ka samo maahayiya yar uwar ka ka,aura shi yar bata auren mashayi. Cikin wani murya naji yaya yai magana yace maji shine abin tashin hankali ni haka ma,yafi min nono fari wallahi. Dama don naga kina sone yasa kawai na yarda amma ni ban ga abin bata rai ba kowa ya rike nashi. Ba aba ban ta ba ganin Alhaji na kuka da hawayen shi ba sai yau din nan akan yadda Sani ya rufe ido ya fada mai magana akanka. Kuma yace daga nan gidan aka kai maganan gidan shi don haka ba zai yarda ka lalata mashi ya ba. Furza iska yayi ya mike tsaye yace don Allah maji ki kwantar da hankaliki Allah yabani wata,wace tafita ba,shike nan ba. Amira tace wallahi ko shike nan maji kinga ma,shi bai damu ba. Maji tace Amira baku ganewa ne shima ke nan jini kuya hana yar shi wa zai bashi yar shi a garin nan. Maryam tace gari da yawa ai maye baicin kan sa maji in sun hana yarsu sai may Allah zai bashi wace tafita da yarda Allah kuwa. Ga mata gari da yawa birjit in wani yakika da kwana wani da yini zai nemaka. Shiru mukayi kowa da abinda yake tunane a ranshi har yagaji da zama yafita nasan shima abin yaci mashi rai sosai. Da safe sai gani mukayi su umma su biyu wai zasu uguwa mudai san can gidan zasu sukara bata zancen. Haka ko akayi don gaba daya sun kara jagula al,amarin baki daya kare baici. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,, A LOKACIN MU KE,,,,,,, Maria duk zirga zirgan da akeyi asibiti, hankalinta a tashe yake gashi ta bude kudin bankinta asusu da take tarawa wanda sadauki ke kawo mata baikai ko dubu ashirin ba dama wanda take tarawa agida. Kafin wani lokaci labari har ya zaga, gari ko ina yan sanda suna neman Sisko ya,gudu ya,boye gidan abokin shi can wani uguwa. Amma haka bai sa an fasa bincike ba don a gano shi don har hukuman human right tasan da zancen a hannun ta yake yanzu. Mahaifin Aliyu bawan Allah kamilin mutum abin tausayi sai kuka yake kawai yayi a fili yayi a zuciyar shi. Ya rasa ina zai saka kan shi ya samu kudin da za,a ceto rayuwan yaron shi Aliyu. Haka yasa wani matashi dake jinyan dan uwan shi a dakin yaji tausayin bawan Allah sosai. Shine yakai sanarwa a gidan redio da kafafen yada rabarai na cikin gari don a tallafawa wanan dan karamin yaron dake shan wahala. Shine har Allah ya taimake su labarin yakai ga idon matashin dan kwallon da suke dashi a gari watau U F umar faruk Abubakar yaji sanar wan. A lokaci guda yaje ya biya kudin aikin tare da,bada kudin magani da wanda yaron zaici abinci har da iyayyen shi. Mahaifin ya rasa bakin da zaiwa wanan matashin godiya sai dai yafara jero mashi addu,oi masu ma,ana acikin rayuwan dan adam kawai. Tare da fatan samun nasara a,rayuwan shi ga,duk abinda ya tun kara na alheri. Sisai yaji dadin adduan wannan bawan Allah sai yake gani ai, kawai kamar an zare mai wani dutse mai nauyi a jikin shi tun lokacin. Kwana bibiyu yana zuwa ziyar su idan yana gari don yaga how far jikin yaron yake yanzu bayan an mashi aiki. Sai da malam yaga dan shi ya samu lafiya sosai ne wani yammaci yazo gida yai wanka ya samu maria ita kadai a,gida yaran sun fita zuwa makaranta. Ya dauki bucket ya debi ruwan wanka sai tazo zata karba ta debo mashi yace a,a ki barshi don ni yanzu ba zamana kike a gidan nan ba. Wanan kalman ya tayarwa maria da hankali har yafito ya shirya yafita daga gidan tana a cikin tunanen kalamin shi. Ba bata lokaci ta samu uwarta da zancen daya fada mata nan uwar tahau fada tana fadin shi wani irin mutumi ne da bai san kaddaraba koda talla ko ba talla wanan al,amarin rubutace abune ga yaron nan. Don haka kibarshi zan fadawa wa iyayyen ki maza su samay shi aji may yake nufi. Saidai bata san ya riga yai magana da mazan gidan nasu ba tana samun su da zance sukace babu ruwan su suje su da suka bata su gyara da kan su. Nan yaje gurin malamin shi ida yake daukan karatu har yanzu ai mashi cigiyar yar bazawara koda kauye ne yaura kawai ya huta da halin maria. Shi ko sisko sai bayan kaman kwana ashirin yana ganin an manta da zancen sai gashi ya fito, Dama akwai yan sandan farin kaya da ko yaushe suna zagayen shi suka cafke shi sai police station nan aka fara jibgan shege ana gana mashi azaba sosai. ****** ********* ****** Zancen auren mazan gidan mu su yaya imirana ance sai budurwan shi ta kare jaratun NCE da takeyi za ai masu aure saura,watani su kare karatun su abinda ya,dakatar da zancen ke nan . Amma Umma kullun akan zancen in auren yaran nan ya,tashi zanyi abu kaza zamuyu abukaza take fadi ita da mama Asiya. Wani lokaci sukanyi hirane don maji taji taji haushi ko takaici gasu a,kullun cikin saka kunne suke don suji ko sadauki na nema wani guri suje su suke zancen. Wata diyar kawar maji uwar taso a,hadasu kamar may amma sadauki yaki yarda da zancen yace shi aure baya gaban shi tukun na. Amma su Umma naji sai gasu gidan suka kai suka mai karfi matar tace tasan da zance ai itace matace a hada shi da yarta shi yaki yaron. Suka taso da kunyan su suka dawo gida da kunya da ,bakin ciki A haka kwanaki ke shudewa,suna komawa sati zuwa watanin karatun mu sai ci gaba yake sosai ba kama hannun yaro. Yau ni kadai nafita zuwa makaranta don maryam ta gama exam ita banjin dadin fita amma haka na daure nafita. Sadauki da yakai wata biyu kasan turai yadawo wanan tafiyan tafiyan arzikine sosai yayi don yasamo makudan kudi a can. Sai dana dawo na samu sunyi bako dan takura ya dawo ban samay shi a gida ba ya fita don sunce tun safe suka sauka garin. Amma na samu tsaraba masu kyau harda waya da maryam tace ya canza muna ya sayo muna. Sai da dare kusan tara ya,shigo gidan da sayayan abubuwan bukatu irin su sheltox sabulan wanki abubuwa masu yawa yace a,raba,abawa kowa nashi tun a bakin motan shi ya dinga ba,almajira suna kaiwa sauran part din gidan wakowa nasa. An shigo da na Maji ke nan sai gashi ya shigo yana waya yai wani irin haske ga,wani dan saje daya bari a,fuskan shi, daganin shi komai ya zauna. Har ya zauna bai daina,wayan da yakeyi ba sai da,ya dauki lokaci a hankan yana,wayan shi. Jin ya gama waya yasa na fito daga dakin mu don naimai sannu dazuwa da kuma godiyan tsaraban mu daya kawo muna. Still da,waya a hannunshi haka dai na daure nace yaya sannu da,dawowa?. Mun ga tsaraba mun gode sai lokacin ya dago kai daga abinda yake a wayan shi. Idanuwan shi masu kama da shi ya zana su da kan shi, yaba min sai kace wani tsohon maye. Yana son ya bude baki ya ansa min amma kuma ya kasa maga a lokacin saboda gaba daya na canza mai nai mai wani kwarjini a fuska. Har nabi ta gaban shi na,wuce zuwa gurin TV na dauko littafina amma bai samu damar amsa min ba. Ina ba da baya ya lumshe idanuwan shi a hankali tare da,saurin kawar da idanuwan shi akaina. Yace a ran shi may maji kebawa yaran nan ne haka,wai suke canzawa lokaci guda haka. Ya manta cewa da bazarshi muke taka rawan mu yanzu gaba daya gidan don yanzu ko abinci baba ya daina saye sadauki ya dauke mashi nauyin haka ko. A hankali ya sauke wani sanyayan ajiyan zuciya yana kuma kan aikin shi. Ashe lissafi yake don ya fara business wanda ba kowa yasan da hakan ba a gidan. Sai fili da yasaya ana mashi wani irin mamakeken ginan gida har an kusa kammala aikin ginan ba wanda yafadawa don zurfin ciki irin nashi. Ya dawo da kwana biyu Kabir yazo gurina mama tasa akai mashi girki hadade wanan zuwan akan zancen auren mu da take son ayi badadewa ba yazo gida. Sun gaisa da mama harda hjy kubura da suke daswa naciki na ciki da mama tazo sun gaisa yai masu alheri. Bayan tafiyan sune muna zaune da Kabir saman Carpet dana shimfida muna can gefen wani dan lungun shigowa gidan . Sai faman hira yakw min kamar kullun irin yadda ya kamu da,sona farat daya haka. Yau sai nake jin hiran nan shi kawai banjin dadin shi sosai don yadda yake magana sai umm a,aa nake bashi amsa da eh. Yake sheda min zai fara turo da kayan lefe a gurin maji don ai mata halarcin da take min a nuna mata itama uwace gareni yace daga baya zai turo mota akaita kauye gurin iyayyena da kayan sai a saka muna rana. Yace ko hakan bai maki ba nace yayi kwarai da gaske don in anyi haka nafi kowa jin dadin hakan irin yadda mama take nuna min kauna abin ba,a cewa komai. Yace Fatima ina tausayin rayuwan ki naji duk irin rayuwan da kikayi a,wajen matar babaki shine yasa na kara kwadaituwa da na aure ki Fatima. Ban san lokacin da,wasu hawaye masu dumi suka fara silalo min ba a fuskana. Ni dai ina godewa Allah don Allah yana sona ko yaushe yana hadani da masu kaunana sosai. Kabir na ganin na fara kuka hankalin shi yai matukar tashi sosai yace subbahanallahi Fatima ko magana ta batai maki dadi bane yasakaki kuka haka. Ban daina kuka ka ba,sai kara dan sauti danayi yace cikun murya karyyaya don Allah Fatima kibar kukan nan ki fada min abinda nai maki haka har yasaki kuka. Hankici ya,dauko yasa yafara dan goge min hawayen dake silala a idanuwana yana bani hakkuri. Har yaya sadauki ya shigo get din gidan bamu san ya shigo ba, yana ganin abinda kw faruwa da hanzari yaja da baya numfashin shi yaji yana fita da sauri da sauri idanuwan shi yaji sun rufe mashi lokaci guda bai ganin wuri sai can ya samu ya furta innalillahi wa,inna alaihin rajiun. Yaji wata natsuwa tazo mashi yaji lokacin da kabir ke fadin Fatima ki daina,wanan kukan haka kada ki sakani kuka a gidan mutane. Da kyat nai dan shuru cikin muryan kuka nake cewa ni kukan godiya nakewa Allah da ya hadani da abokin zama wanda yasan kimata da daraja dana iyayyena akullun Allah yana,min gata a,rayuwa na. Haka mama ta rikeni amana duk da batasa koni wacece ba har tazo tasan kowa nawa ashe don may bazanyi kuka ba yaya kabir. Kabir ya sauke ajiyan zuciya yana cewa wallahi duk kin daga min hankali Fatima, Ashe kuwa zan iya rabuwa da mace kamarki a,rayuwa na,macen da,tasan dadin halarci irin haka. Nan dai muka dan kara hira mukai sallama dashi sai mun hadu a gida garin mu akan zancen auren mu. Yai min salama yatafi na dauki kayan da ya,kawo min niki niki zuwa cikin gida dasu sai ganin yaya sadauki nayi yana exercises a kofan shi kusa da inda muka zauna. Ni dai na ratsa shi na shige da kayana ciki yace yar iska muna fuka kamar wanan yarinyar wai tasan soyayya irin haka kiji dashi mara kunya kawai. Ina,shiga gida mama tace ,a,a har surukin nawa ya tafine nace eh, yace sauri yake ya isa gida kada yamma tai mashi a hanya. Nan su maryam suka shiga bude kayan maji tace kai maryam baki da kunya,wallahi tace kai maji nima ranan da,aka,kawo min kaya ai haka tai min matace kun fi kusa ai ba a,shiga tsakanin ku sai mutum yaji kunya. Nace Anty kowa ya dauki abinda yake so aciki amma turare abawa Baba da mama shi. Mama tace aiko wallahi Alhaji ya yaba wacan da,yakawo maki kika,bashi . Nace mama baba yana son turare tace sosai ma,wallahi shi ko yashe cikin saka turare yake. Nace ai yaya sadauki ya biyo shi don ko shin yana part din nan tun daga waje mutum ke gane cewa yana gi,,,,, Sai ganin mutum nayi a gaba na ya,watso min idanuwan shi yace munafuka kawai aikin ke kenan sakawa mutane ido kullun. Dariya su Amira suka kwashe dashi sukace ai munki fada maki ya shigo ne tun da shi dodon ki ne ko yaushe. Na,turo baki ina cewa ni wallahi ban son kalman muna fukan nan an tashi daga yar kauye amayar dani kuma munafuka yanzu. Yace dama may kike ba yar kauyen ba munafukan banza kawai ka ganta sumu sumu da ita kamar ba shakiyiya ba a baya. Kai yafa isa haka kai ke nan in kana gida yarinyar nan bata da,shakat ga rayuwan ta kawai wani irin miskilin mutum ne wai? Yace may yakaita fadin sunana don kawai taja min fitina mara kunyan yarinya kawai shigewa nayi ranan harda kuka sai da nayi ban futo falo ba har dare ina ciki kumshe shikuma yana gida zaune. ****** ********* ****** Haka ya kwanta tunanen halinda ya gan mu da kabir yai matukar tsaya mashi a zuciyar shi inda ya,rasa may yasa abin yadamay shi haka a rai. Wata zuciya tabashi amsa da don itama yanzu ta zama kaunan ka kada wani abu ya samay ta ya samu mahaifiyar ka ke nan. Bai samu barci ba sai dare so sai gashi zuciyar shi tana faman azazzazalar shi kan ya dan sha wani abu ya samu relief tun da ya dawo yakw jin yadan sha wani abu kawai a ran shi. Haka duk yana gida bai da natsuwa inba ya dan samu abin bugarwa ba ko yaya yake ya dan shawa ran shi yake samun shakat. Yanzu kuma gashi dare yayi sosai yan san ko ina kafa ya dauke babu inda zai samu wani dan abu ya taba. Haka ya kwana a wahalce ga tunane ga kuma son shan maye ya addabe shi a zuciyar shi sosai. Washe gari da kyat ya samu jam,i don saura kiris ya rasa jam,i da yanzu ya zama mai jiki haka yasa a uguwar da yake gina saida yai massalaci babba a gurin don mazauna uguwan. Zazzabi mai zafi ya rufe shi da safe yinin ranan bai fita zuwa ko ina ba saboda sana din rashin shan mayen da bai samu yi da,dare ba. Ganin har kusan biyu bai fito ba yasa mama cewa maryam yau ko yayan ku lafiya gaba,daya bai leko gidan nan ba,fa yau. Amirah tace aiko naga breakfast din shi a kitchen dana dawo kila kuma ya fitane tun da safe zuwa wani guri. Mama tace ba halin shi bane hakan in yana gari ko yayane yakan shigo kafin yafita zuwa wani guri. Maryam jeki ki dubo min dakin shi idan baya gidan ne mu sani ko kai maji zai zauna daki har wanan lokacin bai fita,ba,biyu saurafa yanzu. Jeki ke ki du bo min shi ki gani in baya gidan ne musan bayanan yafitans ban son shegen gadamar tsiya kinji. Maryam tana,tura kofan taji a bude yake sai dai bataji motsin akwai mutum a cikin dakin ba sai ta fara dan kwankwasa kofan da hannun ta. Da kyar ya iya bude bakin shi yai magana yace waye ? Tace nice yaya maryam ce, Yace shigo kofan a bude yake ai. Maryam ta tura kofan ta,shiga ta hango shi kwance saman katifan shi ya rufe jiki lif da katon bargon shi. Tace yaya lafiya maji ce dama tajika shiru tace nazo na dubaka ? Yace cikin muryan marasa lafiya, Kice mata yau bana jin dadin jikina ne sosai amma yanzu zan kokarta na fito ai. Da sauri maryam ta juya zuwa cikin gida tana shedawa maji halin da ta samu sadauki a cikin sa. Maji tace subbahanallahi shi ne ko waya ya kasa dagawa ya kira yafadi baida lafiya nan maji ta mikw tare da daukan hijjab din ta ita da Amira sai dakin. Yadda maji ta samu dan nata kwance hankalin ta yai matukar tashi sosai ta haushi da fada haba babana. Baka da lafiya baka sanarwa mutane asani a taimaka maka sai kashige daki ka rufe kai ka dai a ciki. Can tace wai may yake damun kane haka ? Cikin dauriya yake ce mata murya na,rawa, Zazzabine sai amai da nake dan yi tace subbahanallahi shi ka kwanta haka ba,wani magani ko taimako. Barin kira Alhaji aje asibiti yace da sauri No maji barshi barshi kawai zan kira wani yakira min likita abokina yazo ya dubani yanzu. Maji ta juya gurin amira tana fadin ke dauko min wayana a gida da sauri kinji. Jin sunce amai da zazzabi yana jin sanyi yasa na tsaya ban tafi ba sai dana hada mai tea mai kauri sosai naje masu dashi. Na samu sai rawan dari yake yana cikin wani hali sosai a lokacin. Na ce wa mama ga tea mai zafi na hado mashi yasha ko sanyin zai dan rage mashi da kyata ta samu ya tashi ya wanke baki ya zauna bakin katifan daya kwance akai. Ya sha tea din sai yacire baki maji tace ai gara kasha kafin likitan yazo ko ? Muna tsaye daga gefe kofa cirko cirko muna kallon shi ya,shayen tea tsab kamar yadda uwarshi ta umurce shi dayi. Sai ko a take, ga zufa ya karyo mashi a lokaci guda yana gyatsa alaman dan sauki ya samu. Maji tace Fatima ki fimu dabara aini duk na rude wallahi komai na kasa yi ma gaba daya. Shigowan likita da abokin shi Bashar yasa duk da halin ciwon da yake ciki ya dagi kai ya,watsa muna harara kowan mu tagane nufin shi haka muka juya sukuku damu kamar munafukai muka bar dakin sai maji ce kawai ta rage a ciki. Likita ya duba shi ya,rubuta magani Bashar yaje ya sayo masu, bai dade ba,ya,dawo da maganin da allurai a leda akai mashi yamike wai zaiyi alwala a lokacin. Sukace ya dan bari ya dan samu sauki sai ya,tashi yayi sallah haka ya koma ya kwanta yana numfashi guda guda. Ni dai tun wanan zuwan da nayi gaidashi ban kara zuwa ba,suke ta faman rawan kai da abin su. Amira ce mai jinyan shi sosai da yan uwan shi don va laifi sun nuna mashi karamci don suna zuwa gaida shi sosai gaskiya mutanen gidan. Can cikin ran sadauki mamaki take yadda tun ranan bai kara ganina ba zuwa gaidashi ba. Gashi har su umma suna zuwa duba shi balle ni da yasan ina da kokari sosai gurin kula da mutum. Amma gashi duk wanan rashin lafiyan dayayi ban shiga gaidashi ba ko sau daya tun randa yafara ciwon nakai mai tea ban koma ba. Har ya fara samun sauki sosai yana dan fitowa ya,sha iska wajen gidan su. Tun da safe aka kirani wai babana baida lafiya kwana kusan uku ke nan bai masan inda yake ba. Ban,san, lokacin da na kama kuka ba na tayar da hankalina sosai maji ta fadawa baba yabani dubu hamsin yace naje nagani idan abin yai nisa kwarai mukawo shi asibitin gari. Na kama hanyan tun da,safe nai sa,a na samu mota sai kauyen mu gaskiya na samu Baba yana matukar jin jiki wai ma yaji sauki ke nan daga gona ciwon ya kamashi aka kwaso shi zuwa gida. Na sa aka kai shi asibitin nan gari sukace gado zasu bashi mama tabawa tace aikaji irin ta idan an bamu gado wazai biya kudin magani nace ba matsala a kwantar dashi kawai. Tun ranan na kashe kusan dubu goma sha takwasa ga magani da allurai da,za ai mashi. Sai yamma maji ta samu waya na don tayi kira yana kashe bayan mun gaisa take tambayana yaya mai jiki nace mai jiki da sauki gamu asibiti an bamu gado ma. Tace asha ashe jikin ko sosai ne nace wallahi mama duk baba ya ramay yakoma kamar bashi ba wallahi. Nan dai tai mashi fatan alheri tare da,Allah yaba shi lafiya na ce amin mama tace duk abinda ake ciki na,bugo masu su sani. ****** ********* ****** Sai washegari bayan na,tafi ne sadauki ya uya,shigowa cikin gida a,falon maji ya zube bai jin karfin jikin shi ko kadan sai yawan jin amai da yakeyi. Yakai awa biyu baiga gilmawa na ba yace maryam maryam daga inda take zaune ta amsa mashi ta mike tazo gurin shi. Sai da ya dan jima kadan kamar wanda yake wani tunane can ya nisa yake ce mata. Wai ina yarinyar nan take ne ? Maryam jin tambayan nashi tayi a bazata mata sai mamaki ya kamata tace wata yarinya ke nan yaya ? Yace wanan dake nan dakin mana gurin maji. Tace oho Bintu daidai maji tana shigowa falon ke nan Tace wallahi ta tafi gida jiya Baban ta aka bugo waya baida lafiya shine ta tafi yace OK, Maji tace wa yake tambaya ne wai ? Maryam tace wai Bintu yake tambaya. Tace yau kuma lafiya kake tambayan min yarinya kodai wani aikin zaka sata ne? Yace No ban gata ba dai ne kawai tunda na tashi shiyasa maji tace jiya ta tafi gida mahaifin ta ba lafiya tace anbashi gado a can kauyen. Yace subbahanallahi a kauye kuma za,a kwantar da mutum ga asibiti a gari. Tace ba,sai suna da halin kawo shi garin ba Alhaji ne ma da zata tafi yabata dubu hamsi su sai magani tace dashi aka kwan tar dashi din. So nake ka kara jin sauki sai na roki Alhaji ya bari na tafi nag jikin nashi kauyen. Don Fatima na da kokari wallahi sosai yarinyar tana da kirki ga dadin zama ai mijinta ya dace wallahi. Bai yi magana ba sai idanuwan shi da ya lumshe tare da dora hannayen shi saman fuskan shi yai makari dasu. Bai dade falon ba ya tashi ya fita part din shi ya,shiga yai wanka jin karfin jikin shi yasa shi cewa bari ya fita ya dan zagayo ginan shi yagani don ya kwana biyu kwance bai fita ba. A can kauye kuma jikin na Baba na gayanan dai ga kaman shi sai dai muce Alhamdullahi kawai. Haka karama dani, nice komai akace nake kokarin yi ga dan kudin dake hannu na ya,soma karewa,saura dubu uku kawai a hannu na. Gashi yau tun safe mun rasa,gane kan jikin baba yaki mashi dadi sai nishi yakeyi kawai . Hankalina duk a,tashe yakw munyi waya da Kabir yace zai turo da sako akawo min daga kauyen su. Gashi banga dan sakon ba har yanzu kusan karfe dayan rana ake bida a lokacin . Nafito daga wajen asibitin na samu gurin saman wani dutse gindin bushiyan dake farfajiyan asibitin na zauna, tare da kifa kaina saman gwiwayu na nai shiru ina tunane. Kaman daga sama nakw jin muryoyin yan gidan mu Maji tana cewa ko wani daki sukw ma ? Da sauri na dago kaina nace lah mama sannun ku da zuwa ashe kuna hanya tafe ne yanzu. Tace Fatima kece nan zaune yaya mai jikin maimakon na bata amsa sai kawai na fashe da kuka nace mama Baba kan sai yadda Allah yayi kawai don jikin sai munga kamar yaji sauki sai kuma ciwo ya dawo. Sam ban san dashi suke ba sai ji nayi yace to may na kuka kuma haka ? Zaki tari mutane da kuka ki tayar muna da hankali inane dakin da aka kwantar dashi na shiga gaba suna bina a bayan su har muka je dakin da yake kwance. Baba na yana kwance sharkaf dashi sai nishi yake guda guda suna mashi sannu kafin ma nai magana mama tabawa tace kai Bintu akwai ki da,shiririta wallahi. Tun dazun ga mutumi yana wahala kin tai kinyi zaman ki baki dawo ba nace mama wanda zai kawo min kudin ne baizo ba har yanzu. Tace ba Kabir din yace ya basuwa ba shiko mi tsaidashi hakana wai ? Muryan yaya sadauki dake kallon dakin cikin kyankyami yake cewa wai may sukace yana damun shi ne? Sai lokacin nace mama ga mamana nabirni da nake wurin ta ta sun zo da yaranta. Tace ayyo Allah sarki kuna sannun ku da zuwa to a,a hanya yaya sauran jama,an gurin ku, lafiya suke inji maji, ta amsa mata akaice. Kara tambaya yayi tare da matsawa gurin Baba ya kura mai ido a ran shi yace ashe agun shi wanan yarinyar ta,kwaso fari haka. Ga mutun cikin wahala amma farin shi yana nan bai gushe mashi ba natural skin ke nan Yace wa Babana may ke damun ka ne Baba? A hankali Baba na ya nuna maran shi da hannun shi da kyat. Yace shit kun aje mutun haka a kazamin guri haka yana ra wahala ciwo daban magani daban . Ina likitan yake naji may sukai mai anan don musan inda za,a dora akai. Yajuya zuwa gurin likitan muka taka mai baya ni da maryam har zuwa,dan dakin da likitan ke zama ko shi a kazance yake gurin. Yana ganin mu zai fito yafara,washe bakin shi duk goro yasa shi yana fadin ,a,a malam Bintu yau baki mu kayi ne ? Sun zo duba jikin Baba na ko ? Yaya sadauki da haushin yadda dattijo kamar wanan ke wasan baki wai yaga yan mata yace don Allah likita muke nema? Yace mallam ai ni incharge din gurin ka wani kallo yaya,ya,watsa mai yace ina,son in san may ke damuwan bawan Allah nan mahaifin yarinyar nan ya nuna ni sai malamin asibitin yace Fatima Bintu yar ma,aiki. To gaskiya dai munan in munce ma ga ciwon daka damun shi munyi karya abu gudana dai mun bashi taimako don ya dan samu karfin jikinai kawai. To idan babu damuwa zamu tafi dashi birni yau aje aga may ke damun shi a can yace gaskiya na hakan yana da kyau sosai walleh. Ko ina zamu iya samun motan da zata dauke shi ya tambayi likitan yace in anyi sa,a za,a iya samun mota bakin yar kasuwa inda motoci suka tsayi. Bai tsaya jin komai ko gidiya ba yajuya muka bi bayan ahi sai likitan ke cewa ,a,a Fatima Bintu yau tafiya za,ayi abar mu. Daga inda yake munajin tsukin shi mudai bamuce komai ba muka bishi maryam ta shiga gaba ina baya sai inda motoci ke tsayawa a kauyen namu . Munyi sa,a kuwa don mun samu mota daya a layi zasu tsaya dogon jinga dashi yace ko nawane zai biyasu azo a tafi kawai. Muna zuwa ba adauki lokaci ba muka kama hanya sai sokoto da Baba dake kugin ciwo ba barci kwana da kwanaki gareshi dama mu masu jinyan shi. Direct asibiti muka nufa dashi yashiga ya fita nan da nan likitoci suka taru kan babana suka,fara binciken matsalar shi. Sun fara bashi taimakon gagawa tare da,wasu allurai da suke ganin ya dace dashi sai gashi ya samu barci cikin dan lokaci kadan. Muna nan har dare yana barci sai ga yaya da,wasu samari biyu yan uguwar mu yaran shi ne don nakanga suna mashi abu yace muna mu tashi muje gida jinyan namiji sai maza. Komai ya,sayo ya masu na bukatan su da ma wanda zasuci jiki ba karfi na mike nabisu muka tafi har da mama ta bawa mukazo gida da ita. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,, IN KIN TURA MA WASU DA BASU BIYA BA DON KIN BIYA , ALLAH YA ISAR MUNA AKAN KI,,,, A LOKACIN MU KE,,,,, Tun da safe na farka na shirya abin karyawa, da za a kai asibiti na tayar da mama tabawa,ta shirya don mu tafi tare. Dakin mama na leka har lokacin zaune take saman salayan ta ta azzakar a gurin. Na fara gaida ita nake cewa mama zamu tafi asibiti mu dubo Baba na kuma shirya abin karyawan su. Kai ta,gyada min tare da daga min hannu alaman a dawo lafiya ta nuna min post in dauki kudin mota a ciki. Mun fito lokacin duk su Amirah suna barci abinsu hankalin su a kwance sukan. Ban san ya akayi ba ko yaga fitowan mu ne, muna tsaye daidai inda zamu samu abin hawa sai ji nayi ana horn daga,bayan mu, ban so juyawa ba amma jin horn din yai yawa yasa ni dan waigawa. Sadauki ne zaune cikin haddadan motar shi yana saye da kayan wasa farare sai dai wadon dogo ne har kasa haka ma rigan maidogon hannu sai jan da,aka,sa,daga gefen kafada zuwa hannun rigan layi biyu. Fuskan shi a,daure tamau dashi kaman bai taba dariya,ba ganin ya,tsaya,a gaban mu kuma baiyi magana ba na gane may yake nufi. Bude motar nayi nace wa mama ta bawa ta fara shiga, ta sa kai tana fadin bissimillahi rahamanin rahim, ina kwana Alhaji ? Bai amsa mata ba don baiyi tsan manin da shi take ba, sai da ta gyara zama da kyau nima na shiga bayan na zauna tare da rufe marfin kofan mota, Wani kyatci naji yayi tare da,furzo, iska daga baki irin na jin takaicin wani din nan. Ya wani fisgi mota da karfi yan mintina sai gamu bakin UDUTH asibitin koyar da,kwararun likitoci na wanan nahiyar. Na bude wa mama tabawa ta fara fita daga cikin motan nazo zan fita tare da daukan basket din da muka zubo abinci a cikin shi yake cewa. Yarinya,baki sanni ba har yanzu zaki rena min wayo bakauyar banza kawai ni driver gidan ku ne. Naji zafi zagin da yai min amma sai na,share don dan ni ya,taimaka muna nakuma zo abin kunya ana jin harshe na sama tare dashi bai yi ba. Amma badon taimaka wa mahaifina da yakeyi ba da yau ba abin da zai hanani rama zagin da yai min harda cewa gidan mu. Gidan mi koda muke tallakawa ai muna da mutunci a idon duniya don bamu da abin da za,ai muna fade, a kanshi sai talauci halittan Allah kawai. Mu, muka fara shiga dakin da babana yake kwance aciki muka samu mata san suna mashi wanka dole muka dan zauna daga waje har agama mashi wankan. Muna nan zaune shi bai karaso inda muke ba sai zuwa can na hango shi tafe da leda a hannun shi ya nufo dakin. Bai muna magana,ba ya zo ya,shige kamar nace kada ya shiga a gyara baba ne ashe yasan an gama,shirya shi, shine yazo kai tsaye ya shige dakin. Can dayan matashin ya leko yana fadin ance ku shigo angama muka mike sai cikin dakin baba yana zaune Sadauki yana gaban shi yana mika mashi abinci a plate. Mamaki nayi dana samu ya na tsaye a gaban gadon yana shayar da babana abin karyawa da kan shi. mamaki ya rufe ni a cikin raina yadda sadauki mai daukan kai, mai izzan tsiya, mai fadin rai kamar wani mugu can akoda yaushe ba alaman rahama a fuskan shi ko kadan. Amma kuma wai shine tsaye yake shayar da babana mutumin kauye tallaka mai jiran Allah ya kawo aci. Tun daga kofa mama tabawa cikin muryan yan kauye ana magana a na daga murya take fadin a,a malam kan jiki yai kyau wallahi kaga ikon Allah. Nan muka shiga gaishe su tare da,matasan nan biyu da suka kwana da Baba na a daren jiya sai lokacin na fahinci cewa wata kila hayan su akayi don suyi wanan aiki, a biyasu kudin su. Lokaci ne, komai mairai yana gani a wanan zaman da muke a cikin sa haka. Da kudin sai ka zama sarkin dole saboda yanayin lokaci mai kudi yafi basarake daraja a idon al,umma. Suma kansu sarakunan suna zubar da kimar su don kwadayi ga tallaka bawan su don kawai kwadayin kudi . Sai da,Baba na ya,shanye tea,din tas sadauki ya,barshi yana,mashi sannu nan yake cewa matasan nan zasu iya,tafiya,gida su dawo . A tare suka,fita,dashi ya nufi gurin likita inda ya samu bayanin matsalar dake damun Baba na dole sai an mashi, theater. Bai muna bayani ba kada hankalin mu ya,tashi don haka yaja bakin shi yai shiru sai da gwago mai masa,tazo yai mata bayani abinda za,ayi kuma a gobe za ai mashi aikin, Da farko gwago taso ta,rude amma yana daga,mata hannu yace dakata mai masa ban son abin tashin hankali shiyasa na kiraki don na,fada maki saboda zaki fi su kwanaciyan hankali ke. Tace tau sadauki yanzu may ake ciki yace zamu tafi tare dakw ne ki saka hannu a matsayinki na yar uwar shi. Tare suka tafi gwago na ta,saka hannu akan aikin da za,aiwa babana gobe da dare. Washe gari naga shiga da ficen da yaya sadauki yake a kan Baba na yai yawa amma sai na dauka don halinshi ne taimakon yasa yake hakan. Washegari ranan aikin ina sauri na tafi asibiti mama take ce min dakata, Fatima. Sai gabana ya fadi ras,ras tace bari nazo mu tafi tare kuma ban son abin tayar da hankali idan mun tafi ki natsuna sosai banda shirmay. Nace tau, tau,mama gaba na sai faduwa,yake ina ganin kaman wani abu ya samu babana boye min kawai akeyi. Itako mama ta bawa sai hira take cikin daga murya ba abinda ya samay ta kamar wagara. Mun samu har anyi mai theater an fito dashi ko sadauki da,yaran nan suna zaune a gaban shi cirko cirko. Wani kallo cikin tashin hankali muke yiwa Baba dake kwance sharkaf saman gado kamar baida rai. Da,sauri na isa gurin shi ina cewa baba may ya samu baba ina kokarin fasa kuka a lokaci guda. Hannu ya daga min cikin daka,min tsawa yake cewa ke shout up please kada ki muna kuka anan please. Aiki, akai mashi baya son damuwa Fatima mama take fada min haka daga gefena da take tsaye tana,kallon yadda yake sauke numfashin shi a hankali kamar zai shude, Ranan a haka muka wuni cirko cirko tsaye cikin tashin hankali don ance irin aiki da akai mashi is hard aiki matsala,sosai ake samu idan ba,ayi a hankali ba don a marayan maza akai mashi aikin. Gaskiya wanan jiyan banda abinda zance wa mutanen gidan mu (gidan maji) don ba karamin kokari sukai min ba kan ciwon dake damun babana ko aikin shi tsada gare shi sosai. Kwana uku da yin aikin ya,samu sauki sosai don yanzu har zama yake yadan dauki lokaci a zaune. Sai dai ya,wani irin ramaywa yai baki sosai sai ya koma,wani dogo dashi. Da,sallama na,shigo dakin da,yake ban zaci cewa yaya sadauki yana dakin ba,a,wanan lokacin don bai faye shigowa da,rana haka ba. Jin sallama yasa su juyowa su na kallo na har da baba na dake zaune ya dago kan shi da sauri ya dan saki murmushi yace Bintu ke tashi? Na tambayi maman ki tace min ke kwanta kin samu barci. Nace baba na dan kwanta barci ya dauke ni kaina ke ciwo shine na dan kwanta kadan. Yaya dake zaune kusa da babana a bak8n gado ya bashi gassashen kifi yaji hadi yana ci a hankali . Baba na Yace tai zuwa ki nemi paracetamol ki sha keji, kada ya kaiki kwance. Nace tau baba yace ki tai gida ai na gode wallahi Alhaji karami yai min komai duniya da lahira, wadda sunkai min suma Allah yai masu. Mutum baka hada komai dashi ba zanan mutunci dai yai maka haka aiko ankai Allah dai ya kara daukaka da darajja. Duk wanda ke gurin aka amsa da Ameen mamatabawa tace ai halin yarka na yya jja muna wanan alherin haka. Shidai mikewa,yayi yafita,daga dakin har yakai kofa ya tsaya,batare da,ya juyo ba yake cewa make sure kin bashi maganin shi ida uku tayi. Ya sa kai yafita can sai ga wani leburan asibiti ya turo kofa yace ga magani ance nakawo wa Fatima wai natane ta duba yadda aka,rubuta tasha. Mamakin wanan sauyin rayuwa na yaya,sadauki ba ni kadai ba kowa na,mamaki ya koma wani salihi rashin yawan maganan shi ya karu mai. Sai yana yawan aikin alheri sosai ga alumma mabukata da,rabon su ya ratsa ta,gurin shi ni dai zan iya cewa gaskiya alhamdullahi don rabon mu ya,ratsa aljihun shi tunda,mahaifina ya samu lafiya,a sanadin shi. Don da akauye yakw sai yadda Allah yayi dashi kawai a can don ance mutum bai mutuwa,sai kwanan shi sunkare. Sosai babana ya samu sauki gashi daga Alhaji har maji da yaranta zuwa mutanen gidan su sunzo duba ma mahaifina. Wasu dai gulmane wasu kuma tsakani da Allah ne ya kawo su. Kabir yazo nan asibiti ya samu baba tadan jima gurin tsaye shi bai zauna ba don girmamawa, Yana batun wucewa,ne yaya,sadauki ya shigo dakin yana saye da, sworth farare masu kyau da tsada a jikin shi farare zakace ba dan hausawa bane kan shi yaji oil sai sheki yakeyi mai, kafan shi cikin bakaken cover shoes masu tsadan gaske ga agogon da,ya,daura mai matukar tsadan gaske. Hannun shi yana,rike da dan key din motar shi yana juyawa a,hankali, yana shiga dakin yaga Kabir a zaune ya,sheda shi sosai ya gane shi. Su mama tabawa aka,shi gaida Sadauki da yi mai barka da zuwa yana,wani amsawa cikin basarwa,yadda halinshi mai kama da kyankyami yake. Kabir daga inda yake tsaye ya kurawa babana ido yana barci yajuyo gurin miskilin yana mai mika mai hannu don suyi musaba,a irin ta addinin musulunci. Yace mai sallamu alaikum cikin mika mai hannun shi kamar mai jin kyamar hannu ya wa i basar tukun ga hannun kabir a mike can cikin sham kamshi ya dan mika mai hannu tare da,basar wa suka gaisa. Duk da abin baiwa Kabir dadi ba ama sai ya shaye ya,dakw yana cewa sannun ku da kokari fa Allah ya,saka maku da,alherin sa. Kamar bai jiba ya juya yana cewa ni zan tafi idan ya tashi ku kira likita yace a kirashi akwai abinda za,aimashi. Daga haka ya fice dakin ni ina daga waje ban ma san yadda suka kwasa ba a cikin dakin. An dan jima kadan Kabir yafito daga dakin nan na mike nazo ti mashi rakiya zuwa inda motar shi take. Mun dan fara,tafiya,yana cewa,gaskiya jikin yai kyau don da,Alaman aikin anyi sa,a sosai gare shi. Nace sai dai Baba ya ji jiki sosai wallahi ya dai samu gatane shine har yai saurin murmurewa haka. Sunana naji yakira, murya a sanyaye yace Fatimatu don Allah may ke tsakanin ki da,wanan yayan naki na nan garin wanda ya shigo dazun ina ciki. Nace wa ke nan don ban kula da,wanda ya shigo dakin ba ina can baya ni. Yace wanan da,muka,taba gaisawa dashi acan gidan ku mana wani farin guy haka, mai dan tsawo kadan, mai karfi haka. Nace,wai duk wanan kwatancen haka yaya sadauki ne mana dan mamana na,garin nan shi kadai ne danta namiji a duniya. Kuma dan kwallo kila ma kana jin sunan shi don har kasan waje yake fita wasan kwallo sosai. Nace ummumm wama suke kiran shi ne da,guy name din yan kwallo sai can na tuna nace U F sukekiranshi. Yace au shine dama UF dan kwallon jahar nan tamu lalai ina jin sunan shi ko sosai wallahi a lailai guy din dollars sun zauna don yana kawo wuta sosai ga kasan nan anaji dashi. Nace lalai ma ni ban damu da harkan kwallo ba balle nasan wani abu acikin sa sosai. Sai tambayan da ya jefo min ta bazata na a kunnuwa na yana fadin to may ke tsakanin ki da shi Fatima. Da,sauri na juyo tare da,dakatawa,da,tafiyan da nakeyi nai may tambayan hausawa tambaya cikin tambaya. Nace washi yaya sadauki din yace sunan shi kuma ke nan ko nace eh UMAR FARUQ yake shine ma,anan UF din ai yace ok. Nace sai ban fahinci tambayan da kai min ba nacewa may ke tsakani na dashi nace yayana ne mana, dakin mu guda dashi ai dan fa mamane na fada maka tun farko. Yace nasani kin fada min, shima yaja ya tsaya wuri daya tare da fuskanta na da,kyau. Fuskan shi ta nuna min damuwa acikin ta karara nace ba wani abu a tsakani da shi sai yan uwan taka kawai, amatsayin yaya yake gare ni. Sai naga yai murmushi mai ma,ana da magana can ya nisa yace badon na fadi wani magana ai fushi dani ba dana fadi abinda nagani a zuciyar shi. Nace kaga yana matukar jin haushi na ko wallahi haka yake mugu ne tun da nazo gidan su zama yani gaba da hattara da tsangwama. Shi kullun yar kauye da munafuka yakw ce min don kawai yaga mama tana so na. Fatima nace na,am sai yayai shiru can yadan harde hannayen shi gaban kirjin shi tare da kallo na ido da ido yace . Wanan yayan naki sadauki yana son ki na hango kishin ki karara a kwayar idon shi wanda ba kowa ne zai fahinci hakan ba sai wanda ya kwantar da hankalin shi sosai zai gane hakan. Wani kallo nai mashi na amma baka san komai ba nace, haba yaya kabir har may ya rufe maka ido yasa ka fada min wanan magana haka. Mutumin da ko kashe ni yana iya yi don haushi da takaici na da yake ji zakace wai yana so na. Ni may ma zanyi da wanan may bakar zuciyar kamar arnakun farko. Wai tsaya ko don kaga ya taimakawa mahaifina ne yasa ka fadi wanan maganan? Nasan ba,shi yai niyar hakan ba uwarshi ce ta sakashi yai taimaka muna don tasan yana taimakon mara shi a gari. Yace to is OK tunda baki yarda ba amma watarana zakice nace nidai don Allah ki rike min amanan kanki don wallahi ina tsoro don zantafi zuciyana yana min kwankwanto ga abinda na gani. Take naji raina ya baci nace ni wallahi yaya Kabir har ka bata min rai ko na rasa miji may zanyi da wanan mugun mara imani. Dariya yayi yace shike nan tun da naji haka ga bakin ki da zaran an sallami baba zan turo da kaya a kawo wa mama kamar yadda nace don komai an hada kawowa kawai ya rage. Nace ni dai yaya Kabir da dai zakayi hakkuri har na kare karatuna da zaifi sauki wallahi. Yace wa ni ance abari ya huce shi ke kawo rabon wani don haka akarashi a gidana na san na kama abina a hannu kafin ai min sakiyar da ba ruwa. Yabude motan shi ya shiga har ya zauna sai kuma yafito yace wallahi ina ji kamar kada na wuce nabarki da wannan mayen dana hango nai dariya nace kai zuciya mai nashe nashe wallahi. Ni ai wanan da kakw gani yafi karfin aure na don shi ba kalana bane ka bar wanan zancen kawai don Allah. Yace to tunda kince hakana na gamsu yanzu sosai sai mun yi waya ke nan idan na isa gida nace Allah ya tsare idan kaje a gayar min da su Antyna da yaran. Yace zasu ji insha Allahu yatayar da mota tare da yi min horn na daga mai hannu yafice daga harabar asibitin, saida naga security sun daga mai kofa fita daga get din na juya zuwa ciki. ****** ********* ****** Kwana biyu bayan haka aka sallami babana daga asibiti sai dai sunce bayan sati biyu ya dawo a kara duba lafiyan shi da aikin jikin shi. A zatona zasu wuce gida amma sai Baba yace ba zai bari su koma ba ya tsaya gari har sati biyun ya cika gidan gwagona aka gyara mashi nan suka zauna da mama tabawa. Komai sadauki yana masu duk da baya gari amma bashar abokin shi yana zuwa kai da kai yana duba lafiyan su. Hakan yaiwa Maji dadi sosai da yadawo ranan ina jin tana mashi godiya sai cewa yayi haba Maji ai taimako kamar yiwa kaine abinda ka taimaki wani dashi shine rabonka. Ban mata da yadda yarinyar nan itama ta taimaka maki ba da kike asibiti wanan ne kawai zamuyi mata mu saka mata da abinda tai muna muma. Allah yai maka albarka, sadauki halinka na alheri ya bika duk inda kake Allah ubangiji yasa kafi haka a rayuwan ka. Yaji dadin wanan adduan sosai don ya kasa boye farinciki sai cewa yayi Maji ina jin dadin adduan ki akaina ko yaushe tace ba dole na ba baba na . Kaine farin cikin rayuwan mu ni da yan uwanka dama,wasu al,umma dake ci daga gareka. Yace mata zai fita akwai inda yake son zuwa don akwai wani da suke son hada business dashi na mai. Tace to Allah yaba da sa,a har yakai kofa zai fita take ce mai ai na manta za,afa kawo kayan lefen Fatima nan da kwana uku insha Allahu. Don haka nake son kudi don nai shirye shiryen taron su. Yace maji wanan ai maganan ku ne, ni dai bana son ki zauna ba kudi a hannun ki bani jin dadin irin haka. Idan na fita zan ciro maki kudi, sai na kawo maki idan bai isa ba sai akara maku. Har ya juya sai yake cewa amma maji wai sauri may wanan yarinyar takeyi, hakane da take son aure. Wani kallo ta,watso mashi, tace shi aure ga yarinyar da takai sha biyar zuwa sama har wani abu ne yanzu. Fita yayi kawai bai tsaya ba don yasan fadan zai kawo kan shi idan har baiyi hankali ba. Ina wanki duk ina jin hiran su nace tunda kowa irin kane da bai tsoron Allah zauna har mutuwa ta riske ka ahaka. Kamar yadda Kabir yace ranan laraba za,a kawo kayan lefena a gurin mama hakan ne kuwa,don ranan mama da,su Amirah basu huta ba sai aikin abincin masu kawo kaya sukeyi. Maji ta,gaiyaci abokan arzikin ta daga ko ina a cikin gari kamar yadda akeyi. Karfe hudu na yamma gida ya cika da abokan arzikin mama masu zuwa mata karan karban kayan lefen diyar ta. Nayi kwalliya cikin wani swiss lace kore anyi min dinkin riga da siket Amira ta daura min dan kwali gashina ya zubo daga baya. Sai dai ban fito ba ina dakin mu zaune don kunya daga cikin kawayen mama wasu ke fadin basu gane ni ba nan mama ta,tura Maryam data kirani nazo na gaida mutanen ta. Maryam ta shigo cikin dakin ta samayni zaune nayi shiru tace Amarsu ta ango may ye haka kuma ranan farinciki kin zauna kinyi wani tagumi dake. Nace kai anty maryam ni wallahi ina tunanen wanan kokarin na mamana ne kawai . Tace ke taso su hajiya Larai na son ganin ki wai sunce basu san ki ba shine maji tace na kiraki ku gaisa. Nai wani iri nace walkahi Anty maryam kunya nakw ji tajawo min gyale na dake gefe na fari ta dora min akai amma can bayan tuntun kaina ya tsaya. Tare muka fito fallon dasu duk a kunyace nake idona yana kasa sai da nakai kasa na tsugun na a tsakiyan falon nace masu mama ina wunin ku? Tubarkallah masha Allahu suke fadi hajiya maijidda wanan yar taki haka kamar ita tai kan ta dayar matan tace may ma sunan ta maryam na dariya na yadda duk na tsorace tace masu Fatima Bintu. Sukace diyar ma,aikin Allah sai lokacin na daga kai na dan kalle su sake rudewa nayi da ganin su manyan mata ne hamshakai ban taba sanin mama tana da kawaye haka ba don banga tafaye fita,ba ita. Naje gurin matar na zauna tace Allah yasa angon naki shima haka yake kamar ki zama nayi daidai kafar matan tace kaji arziki ba yarinyar da kunyanta yaushe za,a samu yara masu kunya haka wanan nan zamani aida yanzu muna nan dasu suna rawan kai. Matar ta dan duko tana ce min kina karatu kuwa na ce eh tace a ina ? Nace a hankali nan state university nake two hundred level. Masha Allahu duk a kunyace nake zaune cikin su sai hiran duniya sukeyi. Dayar matar take ce min jeki kin ji diyata don naga kinki sakin jikin ki namike cikin natsuwa nabar falon . Ban karasa shiga ba naji wata na cewa kai amma hjy maijidda kin ban mamaki yaushe zaki bari wanan daman ya,wuce ki haka, aida kawai kin kamawa danki wanan zukekiyar yarinyar haka ga yarinya da kunya da sanin ya kamata. Ban fi minti goma ba da shiga masu kawo kaya,suka iso da gudan su yan uwan shi ne mata su shidda suka shigo da,akwatina set biyu masu kyau da daukan ido. Nan nake jin an shiga guda da yabon kaya basu dade ba suka ce zasu tafi aka bisu da kayan da aka hada masu drinks, kajin da aka soya, da su snacks. Sai kudi tukwici dubu hamsin har mota aka kai masu nan aka dawo falo akabaje aka,shiga bude kayan ana yabawa. Naji wata na fadin inji bata da ciwon kai dai ko da sauri maryam tace har biyu kuwa. Kai tana da kishiya fa a,a,a yarinya kinko debo da zafi kamar wanan yar yarinyar ce za,ta shiga cikin mata biyu. To Allah ya tsare ya kare ai sai ku tashi tsaye do dai kema gaki kina fama danaki a gida. Zuwa yamma kowa ya watse gidan aka barmu iyamu hajiya kubura ce zance naji muryanta lokacin da aka kawo kayan har aka tafi tana falon tana yaba kyaun kayan . Sai dare muka samu kan mu sai kuma a lokacin nafito ban kai minti biyar da zama ba yaya sadauki yashigo falon. Ina cikin kwalliya na ban cire ba idon shi suka kai ga,akwatinan yazauna yana cewa har bakin naku zun tafi ke nan. Amira tace su wuce sunzo wallahi kagama kayan da,suka kawo muna can. Maryann tace kai yaya,wallahi kabir yai kokari sosai wallahi yana nuna yana matukar son Bintu ji wanan uban kaya haka haddadu dasu bari na,dauko maka kagani sai ta mike zuwa gurin kayan. Yace ke ina wasa da kene ni mace ce da zan tsaya kallon wasu tarkacen banza can. Da sauri nadago kai ina kallon shi don jin abinda yace, ya watso min harara tare da jan tsuki yace karamar yarinya sai shegen son aure haka. Wanan tarkace kikewa rawan kan aure jekiyi ke kika sani indai wanan tsohon ne dana ga kina rawan kai akan shi. Nace a hankali adaibar min abina ko yafi duniya tsufa ina son shi hakana . Baki da kunya wallahi nike fadawa hakan na juya ina magana kasa kasa nikadai inda nake zaune. Wai sadauki ban san wanan abinba yanzu shi Kabir din ne tsoho kuma koma dai may ye haka take son abinta sai kaje can kaji dashi. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,, IDAN KIN TURAWA WA WANDA BAI BIYA BA BA MU YAFE MAKI BA ALLAH YA ISAR MUNA AKAN KI,,,,, Maji ne zaune falon Alhaji dake cin abincin da takawo mashi, abincin yai mashi dadi sosai kullun yana son cin girkin da maji da yaranta ke hada mashi idan itace da girki. Tv daga bangon falon da ka shigo dashi zakai arba ya na aiki yakai tashan CNN yana kallon news da akeyi. Ahmad ne ya shigo falon da wani takarda a hannun shi, yana cewa uban ga takardun an karbo sai ka saka hannu a mayar masu gobe. Imirana kun dawo yaya kasuwan amma kaman baiji gaisuwan da maji take mashi ba alokacin. Saida ya gama bin takardan ya dago yana fadin, bakaji ana maka sannu ne ka kyale ta. Ya dan juya inda maji ke zaune ya watsa mata wani kallo mai kama da harara. Duk a idon mahaifin shi Alhaji yace yanzu kai da girman ka kana namiji kake shiga harka irin ta mata. Imirah yace may kuma nayi baba gaisuwa ce taimin kuma na ansa a rai na ai. Yace to lalai ashe da sauran ka kuma ka bani kunya kai da yau idan na kwanta dama, kaine zaka zama min jigo a gidana. Ashe hasashen na ba haka bane yanzu nasan ko bani Umar zai iya hada ku ya rike min don shi banga ya banbanta wata daga cikin gidan nan ba. Ni dama baba ai nasan baka daukan mu yanzu da wani matsayi tunda mu bamu ,,,, Cikin tsawa Alhaji yace ashe rashin kunyan naka Imirah har yakai haka ban sani ba ? Yau ni kake kallo ina fadu kana fadi haka kai tsaye babu jin kunya. Imrah baiyi magana ba ya juya yafita daga dakin rai a bace sai dakin uwar shi. Maji tace Alhaji da baka biye mashi ba ai, don ni wanan halin na riga na saba dashi ko a gidan nan . Babu wani yaron gidan nan dake kallona da daraja a matsayin uwa sai diyan hjy Kubura kawai. Tace don haka don Allah ka daina fadan abinda da duk kaga sunyi min a gaban ka. Don bazasu daina ba saboda kullun huduban shedan ake masu a kaina. To Allah ya,sawaka amma gaskiya ba zan lamunci irin haka ba a gidana. Sai muryan Umma sukaji tana fadin anki agaishe ki din ke waye da sai angaisheki. Shi da ya mayar dake wata tsiya sai ya zauna yai tayi amma babu mai tirsasawa diya na akan wata mace can marasa asali da ta cika muna gida da diyan tsiya diyan taulali da suka zama ma mutane alkakan kafa. Maji dai ta fito daga dakin maigidan da kayan abincin da,ta kwaso daga gurin shi. Muna fuka kawai tun shigowan ki gidan nan kan Alhaji ya burge saboda bakin kilibibin ki wai ke ga,saliha. Maji tace yaya Allah ya baki hakkuri indai akan zancen nan kike magana ko ni ba da son raina yai mashi fada ba. Rufe min baki bakar munafuka sai kinyi annamincin ki kizo kinawa mutane wani marairaicewa. Kin iya kitihin da zaki raba miji da matan shi da yaran shi . To wallahi hawau kiji na fada maki kinyi kadan a gidan nan muddi kikace zaki shiga tsakanin diyana da uban su. Ke har ina diyan naki dayake kirarin zasu rike mai gida bayan ran shi? Ba dai wanan bakin mashayin dan naki ba da duniya tasan da zaman shi yana yawo cikin gari a wukance yara na kallon shi. Masu abin fadi har ba iyaka saura wa yan nan muna fukan masu kirarin su kamilai ne a gida a waje ko tantiran yan iska. Kuma kin sa Alhaji yaci zarafin imiran a gaban ki, kinji dadi to ki sani indai ni na haifi Imirah har abada ba zai gaishe ki ba bashi ba duk diyana a gidan nan. Tsiyan banza duk wani a halina ma bazai taba yin mu,amula da kuba idan kuma kin insa sai ki sa Alhaji ya sa wuka yai ta yankan su don basu gaidake ba. Haka zai sa nasan yaji zafin, basu gaida ke ba tun da ke dashi kuka daukan min nauyin cikin su na haife su. Banzan bazara dake mai gayyan tsiya gida masu abin fadi tab ga tsuliya kawai. Allah ya sauwa inji maji ta nufi dakin ta da kayan dake dauke a hannun ta. Sadauki tagani tsaye a kofan ta ya dafa, dan gishikin dakin da hannun shi daya. Batai mashi magana ba ta shige dakin ta kawai,ran ta a bace tana mamakin irin wanan halin na uwargidan su. Bai shiga ba juyawa yayi ya fita daga gidan ran shi a bace don wanan cin zarafi da akewa mahaifiyan su yana matukar damun shi a rayuwan shi. Tun da safe yabar garin don bai iya tsayawa yana ganin irin wanan takaicin haka a rayuwan shi. ****** ********* ****** Zaman shi a turai yasa ya manta da bakin cikin da ya baro a gida. Sai dai kusan kullun zai kira mahaifiyan shi su gaisa yakuma tambaye ta yaya suke da sauran kannen shi. Yana kiran mahaifin shi shima suna gaisawa har su dan taba dan hira a tsakanin su. Bangaren Bashar kuma komai yana tafiya masu daidai don yana da rikon Amana sosai . Gashi kuma sadauki ya yarda da Bashar din don tun suna kana suke tare dashi, lokacin mahaifin Bashar na da rai yafi mahaifin su sadauki kudi sosai shine ke yi masu komai. Koda sadauki ya fara shaye shaye bai hana bashar yai mu,amula dashi ba duk da hanashi da mahaifiyar shi tayi da farko. Amma da taga alakarsu abin daga Allah ne sai takawo ido ta samasu kawai don tasan shakuwar su daga Allah ne. Hankali shi sosai yake a kwance yana sha har yanzu sai dai ba irin na can farko ba irin shan kauyanci da kurciyan da yayi a baya. Don yanzu ko mutum yafi aula dubara ba zai iya gane cewa ya sha wani abuba. Haka yasa mutane ke ganin ya daina sha ne kwatakwata a rayuwan shi. Wani yammaci ya bugowa mahaifin shi waya a yanayin da yaji muryan shi sai baji dadi ba. Yake cewa Baba lafiya kake kuwa murmushin manya Alhaji yace lafiyata kalau sadauki sai dai dan zazzabin da ba,a rasa ba kawai. Yace to Allah ya sawaka basuyi wani dogon hiraba yai mai sallama ya kashe wayan. Washegari tun da safe sai yaji bari ya kira Baban yaji lafiyan shi saboda jiya, yana jin jiki. Sai dai yana kira hjy Kubura ce ta dauki wayan suka gaisa take ce mai sadauki Alhaji ba lafiya amma gamu asibiti dashi don jiya anan muka kwana. Hankalin shi ya tashi cikin rudewa yake tambayan ta komay ya sami mahaifin nasu. Tace mai hawan jini ne akace kuma har ya fadi jiyan sai dai da sauki don yanzun ma ya bude idon shi amma dai har yanzu akwai jikin. Hankalin shi yai matukar tashi yace mata don Allah ayi duk abinda ya dace dashi kafin ya iso garin. Sukai sallama da ita hankalin shi a tashe tun a lokacin ne yafara shirin tafiya dawowa gida don ganin halin da mahaifin shi yake ciki. Washegari Sai dare ya shigo garin don nisan inda yafito a lokacin. Kai tsaye bai yo gida ba yace Bashar ya,wuce dashi asibiti nan ya samu yan gidan su gaba daya a gurin mahaifin shi. Umma tana zaune a bakin gadon da Alhaji yake kwance ya shigo dakin daga cikin su wasu sunyi mashi sannu da zuwa. Wasu ko sai harara shi kawai sukeyi yana saye cikin swoth na maza baki mai guntun hannu daga ciki yar rigace itama pink mai guntun hannu. Sai dai bai sa aninin rigan saman ba haka yasa za,a hango tacikin sosai a fili. Ganin Umma ta babake gaban gadon ba wanda ya isa ya matsa bakin gadon bai hana shi karasawa gaban mahaifin nashi ba. Tare da rage tsawon shi ya duka gap da kan mahaifin nashi ya dan rike hannun shi yana fadin Sannu baba ya jikin naka yanzu. Alhaji Abubakar ya dan juyo tare da bude idon shi da suke mai a lumshe yace, Alhamdullahi na samu sauki sadauki ya ya hanya har ka iso ne ? Yace eh Baba, Likita yace kada a damay shi da surutu abarshi ya huta kawai, Umma ce ke fadawa sadauki hakan. Yasan nufin ta bai biye mata ba yace wa mahaifin nashi Baba amma ya kamata a fita dakai zuwa wani kasan a dubaka sosai zaifi zama haka anan. Murmushi yayi tare da rike hannun yaron yace kada ka damu Faruku ai naji sauki sosai. Kana dai jin abinda nake fadi likita yace kada asa shi yawan magana ko ? A hankali ya dago kai ya dan kali inda take zaune tana shimfidawa sauran iyali ikon ta. Daga bayan ta hjy Kubura tace haba ki barsu su gana mana yanzun fa ya iso shi. Kada ki fada min magana Kubura don ke ba kunya ne dake ba yaya zan kyale shi yana sashi magana bayan likita yaba da doka. Hannu Alhaji ya daga masu yace don Allah ya isa hakana please, Idan shi zakuyi min ku koma gida gaba dayan ku, Sadauki dai yana duke ya kurawa mahaifin nashi ido dake cikin wani hali gwanin ban tausayi. Can ya mike ya juya gurin hajiya Kubura yana fadin wani likitane mai duba shi mummy ? Tace tau kasan likitocin yawa gare su amma dai doctor Ango shine yake shigowa akai, akai gurin shi. Man let's go yace wa Bashar dake tsaye daga can kofan shigowa dakin. Ajima kadan sai gashi da likitan sun shigo dakin tare nan likita ya bukaci kowa ya fita daga dakin a lokacin. Umma kaman zatai magana sai tai shiru tamike ranta a bace suka bar dakin yaran ta suka bi bayan ta. Har an rufe kofan sai gashi an leko akace hjy kubura ta shigo. Wanan abin yai matukar harzuka ran Umma sosai take ganin shi sadauki da hjy kubura sun fitane ga Alhajin da za,ace ita ta fita daga dakin. Mikewa tayi ta nufi kofan ta tura da sauri likitan dake duke kan Alhaji ya dago kan shi hjy kubura tana kokari kamashi a daura mai abin gwaji. Likita yace haba mama munce ku dan tsaya a waje har mu gama abinda zamuyi mashi ko. Wani haushi ya kumay ta ta buga kofan ta wucd fuuu tana cewa yaranta su zo su tafi tunda basu da amfani a gurin. Dan ta Sagir yace haba Umma yaya zamu wuce don kawai ana mashi gwaji ance mu fito. Sagir kai dama nasan baka da zuciya wallahi, baka san ciwon kanka ba ko kadan a gidan nan. Sagir yace ni dai ba zan tafi ba gaskiya tace zauna wanan mashayin ya gwada maku iko anan. Mama ma mikewa tayi tabi bayan Umma suka bar asibitin cikin fushi suna sake bakar magana kai kishi ho. Likita yace mai nan da kwana biyu idan ya kara jin sauki zasu iya fita dashi din don dai yanzu yana jin jiki tukun na. Sai dare sosai Sadauki ya bar asibitin don yazo gida yacewa Sagir da Mustapha zai je ya gaida maji ya dawo idan basuyi barci ba. Ya samu har mun rufe kofa don mama bata zuwa asibitin da dare don habaici da gori ne idan taje suna nan. Wanka yayi yajuya sai asibitin a can ya kwana gurin mahaifin shi a zaune tare da kannen shi biyu. Cikin dare Alhaji ya falka ya gan shi zaune saman kujera a gaban shi yana barci yake cewa a ranshi Allah sarki . Ya Allah ka kara shirya min wanan bawa naka Allah ka shirya min duk zuria ta baki daya. Jin kaman motsin Alhaji yasa shi saurin bude idon shi ya mike yana cewa Baba yaya ne may ke damun ka ne? Uban yai dan guntun murmushi yace Umar Faruk Allah yai maka albarka Allah ya kara shirya min kai. Jinkin sadauki yai sanyi zuciyan shi ta fara bugawa don hankalin shi yai matukar tashi sosai a lokacin. Nishi ya fara guda guda alaman yana jin jiki shi sosai a lokacin da sauri sadauki ya ke kiran Sagir yana cewa. Yi sauri kira min nurse a waje sagir ya mike da sauri ya fita shiko yana tsaye sai sannu yake wa mahaifin cikin damuwa. Nurse yashigo da sauri yana cewa bari akwai Alluran da dama za,ai mashi yanzu zai samu sauki insha Allahu. Bayan anyi alluran da yan mintoci ne, sai ya samu barci sukan yaran basu barci ba suna tsaye a kan uban nasu har safe. Jin kiran sallah yace su sagir su fara zuwa suyi sallah in sun dawo sai shi ya tafi. Sagir yace yaya ku tafi kawai idan kun dawo ni sai na tafi haka sukayi suna dawowa sagir ya fita yai sallah. Can Alhajin ya bude idon shi lokacin gari ya dan fara haske yace ba,ai sallah bane sukace mashi anyi Baba. Yace ku taimaka min kuyi min alwala sai nayi sallah da taimakon diyan nashi su kai mai alwala yai sallah daga kwance inda yake. Sai kuma ya koma barci suna gurin zazzaune ba wanda ya gusa daga cikin su har lokacin. A gida kuma tun da asuba muka tashi muka hada abin breakfast don mune da girkin gidan. Ni da anty maryam ne muka dauka zuwa asibiti don mukai wa wan yan da suka kwana dashi abin karyawa. Muna shiga dakin da,sallama yana tsaye yaba da baya jin sallaman mu yasa shi juyowa. Sai da gabana ya fadi danaga yadda ya sake min muka karasa muna masu ina kwana ya amsa da kyat cikin yanayin damuwa. Yaya yaushe ka dawo yace mata jiya da dare daga inda nake tsaye ina kallon yadda Baba yake a kwance na dan dago kai nace mai, Sannu da dawowa yaya sai lokacin ya dago kai ya dan kalle ni da sauri ya kawar da kanshi tare da cewa yauwa. Yace ya maji suna lafiya jiya na shiga na samu kun rufe kofa ai. Maryam tace yaya shine baka buga ba mun kai sha biyu bamuyi barci ba ni da Bintu ai. Bai bata amsa ba yake cewa sagir su tashi su karya ga abin karyawa nan. Sagir yace kaifa yaya naga alaman baka ci komai ba tunda kazo fa? Yace No don't mind zan tafi gida yanzu na dawo sai karya a can idan na dawo sai ku tafi kuma kuyi wanka ku dan huta. Bashar ya kira yace yazo ya kaishi gida yanzu, ba a dauki lokaci ba nacewa maryam mu tafi, Tace zamu koma idan Baba ya tashi muna gaidashi don Allah. Batare da ya juyo ba yake cewa, No ku tsaya Bashar yazo mu tafi tare ko kunzo da mota ne ? Dariya tayi tace kai haba yaya wani mota kuma ina muka gan shi sai dai mu tare Napeo mu hau. Dan dariya ciki ciki yai mata ba,adauki lokaci ba saiga bashar cikin jallabiya ya shigo suka gaisa yana tambayan jikin mahaifin nasu yace Not bad gaskiya. Mukai masu sallama muka fara fita daga dakin kafin su fito mu tafi. Muna fita maryam tace tau dada ga dodon maza ya dawo yanzu za,a fara ke nan ko ? Nace ni gida zan tafi sai ya tafi na dawo ban iya zama mugun nan yana gari wallahi. Ganin sun fito yasa nai shiru ba don na tashi ba yana cewa mutafin ku ko? Nan muka bisu a baya suna gaba muna biye dasu magana suke akan jikin baba. Baya muke Bashar na jan motar shi kuma yana gaba yana waya yadda naji wayan da abokin shi yake wayan. Har muka kai uguwar mu waya yake cikin wani yanayi nikan mota na tsayawa na bude na fita abina ban tsaya ba. Na shiga na samu mama tana zaune suna magana da Amira tana cewa ko sai yaushe zai shigo garin yazo yaga mahaifin nashi . Na zauna sunacewa mun dawo nace eh tare suke tambaya yaya jikin Baba nace da sauki mun samu yana barci ne. Tace Alhamdullahi ai barci alaman sauki ne ga mai jinya. Maryam tashigo da ledan da ya bata a hannu n ta daganin ledojin na kasar waje ne shi ya mayar da hankalin su mama a kan ta lokacin. Tace Maji kina da bako fa ashe yaya ya dawo tun jiya wai yazo ya samu mun rufe kofan mu. Sai gashi ya shigo nan suka fara murna suna mashi sannu da zuwa, suka gaisa da shi. Nan suka zauna ana magana akan rashin lafiya Baba da halin da yake ciki. Maji tace akwai abinda ke damun shi don tun ranan da ya dawo daga kasuwa rai a bace washe gari yace ba zai iya fita ba shine har abin ya kai shi kwance haka. Amirah tace wallahi yaya na zaci ko Baba ba zai tashi ba yadda aka kai shi asibiti rai a hannun Allah wallahi. Sadauki yace to may Baba yake tunane haka har ya ja mashi wanan matsala kai tsaye. Maji tace tau ana raba dan adam da damuwane ko al,amarin iyalin shi ai ya ishe shi abinne dai bai faduwa kawai. Maryam tace ni dai nasan akwai wani abu mama don ranan mun fita da Bintu zamu tafi makaranta naga yan sanda da yan hisbah a kofan gidan nan. Suna magana dashi kuma wallahi baba sai rantsuwa yakeyi bai zuwa ko ina shi. Akwai dai gaskiya amma ko may ye ai muji idan yai wari. Ka karya ne uwar take tambayan shi yace No sai nai wanka zan karya na koma asibitin na duba Baba. Bai jima ba ya fita daga falon yabar mu nan a zaune can yafito cikin shirin shi yana fadin. Abashi abin karyawan shi inda nake mama ta dan juyo tana fadin Fatima ba yayan ku, abin karyawa kinji. Har na fara tafiya na juya inda yake ina cewa na hado ma da indomei ne ? Yace see you may zanyi da indomie ni kaman wani karamin yaro can? Kayan tea nafara kawo mashi na juya na dauko mashi kwai da irish su yaci bai sha tea din ba sai ga kira yazo likita ya shigo. A hanya ya hadu su Umma suna jiran napep su tafi asibitin nan ya tsaya ya dauke su a tare suka tafi dashi sai wani shan kamshi Umma take a bayan mota. Sun zasu Alhaji a zaune likita yana dubashi suka gaidashi tare suka fita da likitan yana fada mashi yadda suka kwana jiya dashi. Maganin da aka rubuta da irin abincin da za,a bashi ya tafi ya sayo a nan ya samu da hajiya kubura da maji sun dawo suna sauka da Napep mamaki ya faea wai ina motan Baban sune ? Zai iya cewa tun wancan karon ya fara ganin kaman arzikin mahaifin su ya fara ja baya sosai. An bashi maganin da abinci yacu sosai ya kwanta barci don maganin da yasha. Sadauki ganin su gaba daya yasa shi cewa dama ina son nai magana da ku don ina son nasan da,wa za,a tafi da Baba India ? Umma tai farat tace kaman yaya dawa za,a tafi dani mana za,a ? Hjy Kubura tace wanan ma ba magana bane wanan zance ne na jinya babu son kai a cikin shi. Mama Asiya tace to may kike nufi ke zaki tafi ke nan ko kuwa? Dama aikin sani, Wallahi baki isa ba don baki kai muna can ba ni din dai da baki son a tafi dani da ni za,a tafi. Fitayayi ya bar su dakin cikin dan hatsaniyan su da suka saba har suka falkan da Alhaji daga barcin da yake yi. Nan yake jin abindaya hadasu fadan yace dama kun bari don ni bazan tafi India ba dan dama dama da saudiya ne ? Sadauki ya shigo da abokan shi suka gaida Baba nan yake cewa kace za,a kaini India ?. Yace eh Baba, Yace to ba zan yafi ba inda dai saudiya ne zan iya zuwa ko don na sauke farali a can nai Umurah. Yace tau Baba idan can kake son a tafi sai a tafi din ai yace dawa za,a tafi don mu shirya passport din tafiyan. Gaddama ya kara kaure tsakanin matan sai cacan baki sukeyi a tsakanin su. Maji na zaune tun fara magana bace uffan ba a zance duk kuyi min shiru ban zuwa da kowan ku, da Hawau zan tafi. Tsit sukayi don jin furucin shi, yace tun da abin naku rashin hankali ne baku damu da halin da nake ciki ba. Dama haka zakace don ka gyara mata rai tunda dantane ya biya. Sai dai dadin abin kowa ma dai ya hafa a gidan balle yanzu don ana ganin kaman danta ya kawo karfi, za ai muna cin fuska. Umma na fadin haka tamike tana daukan jakkan hannun ta zata fice daga dakin. Sadauki yace ba matsala sai aiwa kowan ku passport a tafi ai umuran can sai a dubi lafiyan ka. Hjy Kubura tace Allah yai maka albarka sadauki wanan dawai niyan haka tace tau sai a mayar da yuka a kube, don dan albarka ya yanke hukunci. Wani kallon banza ta watso ma hjy kubura tace yanzu ke ake ji mara kunyan yarinya kawai ni ba sa,an yinki bane, Yaushe kuma muka zama daya tunda bori guda mukewa tsafi ni dake yanzu. Maji dai mikewa tayi tana fadin ni zan koma Allah ya sauwa Alhaji hjy kubura tace tsaya mu tafi tare anjima nadawo. A waje suka samu sadauki shi ya dauke su zuwa gida, a hanya yace mummy bani son wanan yawan fitinan da kukeyi da Umma ko don hallin da baba yake ciki yanzu. Kai Sadauki wallahi yaya ta faye abin haushine ita kullun sai ta mulki mutane tamayar damu da diyan mu abin banza. Nikuma bazan yarda tayi zaune shirim tana zuba muna iko da mulki ba kaman ita ta aje mutane. Hajiya maijidda suka samu suke mata abinda suka ga dama a gidan gaskiya ni ban daukan hakan. Indai sheri ne ai ta matsa yanzu tunda kazo kaga Nafisa asibitin nan da sauri maji ma tace yaya akayi. Tace may nene ba,agiba yan hisba suna neman su sun hada party na iskanci a gari, akai ta shedana da iya shege. An kama yan uwanta su su gudu su masu party amma ce uwa tayi wai zata Abuja ne gurin Atika kaunan ta. To ko shine ya jawo wa Alhaji wanan abin hjy Kubura tace shine ma da dan banzan ga na wurin Asiya Ahmad dayaje ya dauko rikici. Dole Alhaji ya sayar da kayan shi har motar shi ya biya milayan biyar da wani abu. Sun dauka ba,a sani bane kawai don mutum baison ya fadi a ce ga bakin shi akaji. Amma ni Nasir dina yake fada min tun dashi ya boye muna bai son a sani amma ai sune suka jawo mashi hawan jinin ba wani ba. Daga gaban mota sadauki yace to amma may yasa Baba bai fada min ba duk wanan zancen. Tace ina zai fadi kasan shi da zurfin ciki ai in sun kashe shi ai an huta ko ? Har suka isa gida ba wanda yai magana a cikin su sai dai kowa da abinda zuciyan shi ke saka mai. Waahegari bai zauna ba sai shirin tafiya yakeyi na iyayyen shi, Imirana yace aikin banza ne wanan shi yaushe yake da kudin da zai fitar da Baba waje har da matan shi. Sai ranan tafiya, ne suka tabbatar inda suka shirya sai kasa mai tsarki, ba tare sukai tafiyan dashi ba zai samay su daga baya amma komai da za,ayi a can ya hada su da abokin wasan shi dan kwallo dan kasan sadiya da yaya sagir suka tafi. Tafiyan su da kwana biyu duk gidan babu dadi haka dai muke zaune amma sauran yaran sai harkokin su sukeyi. Na dawo daga sayo muna kayan miya zan shigo gida ban san da mutum tafe ba sai cin kara nayi dashi. Ina daga kai ya wani daga min gir irin na yan iska, har na zauda shi zan shige ya rike min hannu yana fadin. Yau shigeya kobaki so sai na kwashi gara gare ki, gidan nan sai da in munafukan uwar ki ta dawo tayi abinda zatayi. Dama na dade ina son in more wanan lafiyen jikin naki kafin wacan gara da zaki aura ya more. Sai naji ya jawoni gaba daya yana kokarin daukana zuwa dakin shi nasa hakora na iya karfina na cije mai kunnen shi da sauri ya sake ni ya makure yakai min mari gashi ba wanda yafito daga cikin gida balle ya taimake ni. Na samu wuyan hannun shi na kara kaimai cizo iya karfina yaji zafi ya dinga kai min nashi a bakina. Naji zafi na sake sai nishi yake ban san lokacin da yanka wani irin ihu ba da karfi. Yakara cakumoni na samu sa,a na murde mai gaban shi iya karfi na ya yanka wani irin ihu daidai lokacin, sadauki dake jin kamar ana danbe a waje daga dakin shi ya leko, Zan gudu yakara finciko ni nakara kai mai wani cizo tare da kamawa da karfin Allah. Daidai nan naji an kai mashi nashi a bakin shi sai da ya fadi ta baya zaune dirsha. Yace dabba kawai sauna mara hankali da,wayo kai dabban wani gari ne karasa wanda zakaiwa haka sai Fatima da take zaman kaunan ka. Tir da halinka halin dan akuya kawai kayi girman banza wallahi, ji ka raggo kawai ji yadda ta mayar dakai jina jina amma baka ji kunya ba kace sai ka danne ta da karfi. Ya furzo miyan daga bakin shi duk jini ne kila ma hakkoran shi sun zube ne. Ya juya inda nake tsaye ina kuka yace dauki kayan ki ki shiga gida ke kuma. Na duka na dauki ledan da na sayo kayan miya duk sun watse a kasa da takalmana da suke warwatse a gurin nai cikin gida da kuka na barsu nan suna fadawa juna magana. Yana ce wallahi ba dan kwallo kake ba sai naga bayanka a garin nan yace Bisimillah shege ka fasa in baka ga nawa ba ni zanga naka ai. Sai lokacin naga yan gidan duk sun fito waje ashe suna tsaye cirko cirko cikin tashin han kali. Ina shiga gida na zube kasa gaban Anty Amirah ina wani irin kuka mai tsuma rai da ban tausayi. Tana kukatake tambayana bai maki komai ba dai ko na girgiza kai cikin kuka nake fada mata ,a,a yaya sadauki ya ceceni gurin shi. Maryam tafita ta dinga kantara mashi zagi da,ashar kamar ranta zai fita sai da sadauki yazo yace ta shiga gida hakanan. Wayan shi ya fitar ya kira Bashar yazo ya samay shi a cikin damuwa ya yasamu abokin nashi. Yana fito ya samay shi bakin kofan gida su dama Bashar yafita da motan shi shiyasa Imirana bai gane yana gidan ba a lokacin. Yaya akayi man? Ya kara cewa wai may ke faruwa ne naganka haka a ya mutse? Yace hajiyan ka tana garine Bashar yace eh yace zan kwashi yaran nan nakaisu gurin ta har su baba su dawo. Anyi wani abune ? Yabashi amsa da anyi a takaice. Ina fito da kayana falo ina fafin wallahi Anty Amirah ban kwana a gidan nan garin mu zan tafi sai gashi ya dago labule ya shigo falon . Fuska a daure yace ke Amirah maryam ku hada kayan ku dake kuzo na kai gidan hajiyan Bashar don gobe zanyi tafiya bazan barku a gidan nan ba. Yan gidan na kallo muka fito da kayan mu mun kashe komai na,wuta a part din namu tare da rufo kofa muka fita daga gidan. Daga cikin diyan mama Asiya ta buga ma mutanen saudiya waya ta fada masu halin da ake ciki a gidan. Anso boye wa maji amma sai hjy kubura ta tsinci ana maganan itace ta fada mata abindake faruwa da mu. Hankalinta yai matukar tashi sosai ranan bata iya barci ba, don gani take kila yakai gare ni boye mata akayi kawai. Gashi tayi kiran layin mu duk bata samay mu ba har sadauki din bata samu ba. Ita ko Umma fada takama yi wai don anga bata gida za,a kullawa dan ta sheri haka. May Imirana zai yi da wanan kwailar yarinyar mara fasali sai fari, duk tsiyan da aka kwaso don anga Allah ya azurta ta da yara shine ake mata hassada a gidan. Sai ga kanin Imiranan ya bugo mata waya yana kuka yace gaskiya Umma abinda yaya yaki baida kyau fyde wa ya tashi yiwa Bintu yau saida yaya sadauki yacece ta kuma yace sai ya kashe yaya sadauki ya fadi a gaban kowa. Nan ta hau yaron da fada tace har dashi ke nan za,a kullawa dan uwan shi sheri a gidan. Yace wallahi Umma ba sheri bane a gaban mu akayi baki yadda akai mai jina jina ba wallahi zaban kunya. Kashe wayan tayi don bata iya sauraren takaici gashi a gaban hjy kubura suke wayan. Nan tahau banbami cewa dama ankawo sune don an hada baki a tozarta mata da acan bayan ta. Hjy Kubura tace ai ba wanda yasaki zuwa ko kin manta fada dakikayi kan sai kin zo dakin zauna gida da yara ai da duk haka baifaru ba. Amma kun kwaso jiki kunbar yaran can maynene ba zai faru ba tunda basu da tarbiya. Nan wani sabon fitina ya fara kamar ba a kasan saudiya suke ba saboda bakin kishin su. Muna gidan maman Bashar matar bata da matsala itama tana da yan mata guda biyu sai wata yar karamar yarinya jikan ta. Bamu da matsalar komai a gidan don tana bamu kulawa yadda ya dace uwa tabawa diyan ta. Gasu da addini duk da sun girma basubar zuwa isalamiya ba daukan hadda da sauran litattafai. Zazzabi nayi na kwana biyu da wahalan da nasha Bashar da maman shi suka kaini asibiti sai da nasha allurai na mike. Hankalin mu a kwance muke komai a gidan babu tsangwama kuma su kadaine a gidan. Zamu zauna da uwar muyi hira da ita cikin sake jiki babu ruwan ta. Sadauki ko ya samu jikin Baba yai sauki sosai don har yafita yai dawafi duk da da sauran jikin shi. Sai dai yasan cewa Umma tana hake dashi don irin yadda take mashi tunda ya iso kasan. Bai kula taba don maji taja shi a gefe tunnisowar shi take tambayan shi abinda ya faru. Hakalin ta ya kara tashi sai dai da taji cewa ai yaranta yanzu suna can uguwar arkilla gurin mahaifiyar Bashar hankalin ta ya kwanta. Kwana shi uku tare dasu ya tafi garin Riyahd ya barsu gurin wasu yan team din kwallo. Nan ma ya,bugawa wasa inda ya samo riyar masu yawan gaske don yan kan har taya shi sukayi akan yadawo kasan su da wasa amma yace masu kasan shi ma suna bukatan shi. Ya dawo suna shirin tafiya ya ba su kudi kowa tayi tsaraba wa yan uwa da yaran ta. Umma tai matukar rudewa da irin kudin daya basu a can hankalinta ya tashi tasan in bata zake damtse ba sai wanan yaron ya zarce tunanen ta. Maji ta samu kudi ta sayo muna kaya masu kyau da,tsada zannuwan gado masu kyau da sauran tarkacen daya dace a sayo. Sai kuma Umna abin ya tsone masu ido wai yabawa uwar shi kudi yafi nasu ya nuna masu banbancin cewa ita ce ta haife shi ke nan. Maji dai tana gyaran kayan ta sai murmushi tayi kawai batacewa mama Asiya uwa ka iya komai ba. Don umma ta zugata itace ta fito fili tana maganan cikin hasala da bacin rai. Sai dai duk iya shegen su basu yarda suyi a gaban Alhaji don yanzu zaici masu mutunci ne. Satin su biyu da kwana hudu suka iso sokoto zakace ba jinya sukatafi ba da bauta don duk suyi kyau abinsu. Ga zancen tafiyan su ya bi yan uwa da abokan arziki kowa ya san da cewa dan kishiyan su ne da suke kira mashayin gidan su yakai su saudiya umar da jiyan mijin su. Saidai kan kowa na ciki na ciki jira ake a dawo gida a zazzage balain da aka kullo. Kafin su dawo mun shigo mun gyara ko ina na part din mu muka koma gidan su Bashar muna jira su dawo gobe. Mahaifiyar su bashar tasa ai muna gyara jiki kitso har kumshi saida ta sa akai muna, siffa mai kyau mun koma kamar wasu amare da mu. Sai bayan sun dawo har sun huta yaya sadauki yaje ya,kwaso mu har mahaifiyan Bashar din ta rakomu gida. Mun samu gida ya rude da murnan dawowan iyayyen su ko wani daki sai hayaniya akeyi. Gaba dayan mu muka fada jikin mama cikin murna da farin cikin ganin ta a lokacin. Maman su Bashar sai kallon mutake cikin sha,awa nan mana ta fara mata godiya, kan karamcin da tayi mata na rike mu a gidan ta. Tace haba ai ba komai yaro ai duk na kowane dama absan haka tun farko da can suka zauna harku dawo. Yaya sadauki da Bashar na zaune sai kallon mu sukeyi duk nabi na takura da zaman su a gurin. Na mike tare da fara daukan jakkunan kayan mu da muja dawo dasu yanzu zuwa cikin daki. Maji tace Fatima bazaki bari har ki huta ba nai dan murmushi nace mama bari na shiga dasu kawai. Ina shiga maman Bashae tace ai Fatiman nan taki akwai kokari wallahi ko can haka nake fama da ita gurin aiki. Mama tace ta riga ta saba bata son zama da kazanta ko kadan . Ashe aure zatayi bada dadewa ba jiya nake jin suna mata sheri wai angon ta yazo yaga wanan kwalliyan nta sai nake tambya suke fada min an kusa bukin ta har an kawo kayan lefen ta. Hakane hjy nice ban aika maki ba. To Allah ya sanya alheri ai mijinta yai sa,a ya samu yatinyar kirki ta san ya kamata sosai. Kai wanan yarinyar dai shu,umace kowa sai kaji yana yabonta ko akan may oho. Bai zaci maganan zucin shi yafito fili ba sai jiyayi Bashar na fadin kaine kake ganin ta shu,uma amma ai Fatima mutunce wallahi. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,,, IDAN KIN TURAWA WANDA BAI BIYA BA, BA MU YAFE MAKI BA ALLAH YA ISAN MUNA,,,,, Bayan dawowan su maji daga saudiya da yan kwanaki jin ba wanda ya tayar da zancen abinda akai min agidan, Maji ta kawar da kaiwaici a idon ta inda ta samu Imirah ya dawo daga kasuwa ke nan zai shigo gida take ce mai, Imirana ji mana sai ya dan waigo yai tsaye kerere yana kallon ta cikin rashin mutunci. Yace ina jin ki, Ganin babu mutunci yanzu a tare dashi yasa maji cewa ,yanzu Imirah baka ji kunyan abinda kayiwa yarinyar nan ba da bamu nan? Amatsayinka na babba a gida anbar maka amanan yaran nan shi ne kuma kaida kanka kai kokarin keta mata haddinta? Fuska a daure yace dama don wanan maganan kika tsayar dani ? Saurayi nake ita kuma nudurwace zan iya shigar da kai na akanta ko hakan kuma illa ne. Murmushin takaici maji tayi tace amma tir da halinka na dan akuya, halin maha,inta. Idan zina abin yine jeka ka nemi yar uwar yin zinanka can kuyi tayi amma ba yar mutane da aka bani amana ba. Murmushi yayi yace Maji kada kiga laifina yar taki ce da shegen kyau wanan aiba komai bane, Allah ya shirye ka,Allah kuma ya tsare amma ni dai Hauwa,u ina maka kashedi akan diyan mutane a gidan na wallahi muddin ka kara yi mata wani abin tashin hankali again zan ba mutun mamaki don shiru ,shiru ba tsoro bane kuma in mutum bai jiba ya gwada ya gani. Sai muryan Umma daga bayan su akaji tace tau isassarsa masu gida wallahi duk sherin ki baki na kakan ki ba. A hir din ki akan diyana ina fada maki Hauwa,u ki sakan min maran diya don bani nasa danki yayi tambada ba abaya. Haka,kawai don yar kauyen diyarki zaku saka min yaro gaba dasheri don kawai a bata mai suna. To wallahi ta Allah ba taku ba kuma karya kukeyi nagaba yayi gaba nabaya sai labari. Kuma kijawa karuwan diyar ki kunne da take kokarin cusa kanta gare shi tayi kwantai a kauye ankawo ta gari ana neman mashinshini a cafke. Murmushin takaici maji tayi tace kaice yaya a matsayin ki na uwa kuma diya mace kin san zafi da munin irin abinda Imirana ya tashi aikatawa yarinyar nan amma idon ya rufe da kin gaskiya. Babu komai ai Allah ba azzalumin kowa bane yana sama yana gani duk bayin shi. Ta juya inda Imiran ya fara tafiya tace wallahi kaji na fada maka duk ka sake kokarin ketawa yarinyar na hadin ta sai kayi mamakina a gidan nan. Tashige cikin part din mu duk muna jin yadda suka kwashe da Umma da dan ta maji tace kai Allah dai yasa kin kusa aure ma kowa ya huta, ki bar wanan gidan namu mai tarin fitina cikin shi. Muryan Baba ne daga waje yake fada kamar haka amma dai ke kan anyi uwar banza wallahi. Yanzu ashe abinda yaron nan yaiwa yarinyar nan ke nan bansani ba shine har kike fada don kunya bai ishi idon ki ba ke, Ida da yarkice wani katon gardi haka yai niyar illantawa haka zaki fadi an mashi kazafi ne ba gaskiya bane hakan Dama ai nasan hakace zai kasance muddin kaji ba ka tsaya kai bincike irin yadda ya dace, Tunda da matar so dinka ake fitina to ku sani ni diyana basu da gadon iskanci masuyi dai kowa yasan su don haka sherin mutum yabishi can cikin kayan shi . Haka Umma ta tare ta hana Alhaji ya,tsaya yai fada akan wanan zancen don idan ya matsa zagine da tonon asiri zai dawo akan sadauki da,uwar shi . Wanda yanzu daga uwar har dan tausayi sukw bashi sosai don duk abinda zasu gujewa gudun magana agidan suna kokarin yin shi don kimar su ta riga ta zube , Su Umma da mama an samu gurin zagi da gori da habaici koda akan da tsinke ne. Shiyasa yakan kawo ido yasa,wa Umma inda ita ko tana ganin kamar tafi karfin kowane a gida sai yadda tayi da kowa agidan baki daya. Hjy kubura ce kawai bata samu ta mallake yadda ranta ke so ba amma ko ita din ba laifi don bata iya kifar mata da,gwaunati a gurin mijin su ba. Amma wanan munafukan Hauwa,u zamani amarcin ta Alkah daine yanufi takai wanan lokacin a gidan Alhaji don gaba daya hankalin shi ya koma ga majine kamar ita kadaice mace. A ganin su Umma ke nan a lokaci amma kuma a gurin Alhaji tausayin Maji yake jin don ya dakatar da ita ga karautun ta yadauko ta ya hada cikin matan da ke aikin gwaunati suna da abin kansu. ****** ********* ****** Yanzu abinda ya,rage bukina baifi wata bakwai ba don an dagar da zancen bukin da babana yai ciwo ne shi ya roka abari har guri ya sha iska sai ayi. Haka kawai kwatsan ranan muna zaune sai ga sadauki ya shigo ya fito daga cikkin garine fun safe safe ya fita sai da yamman nan ya shigo gida. Suna hira ne da maji yayin da mu muke harkan gaban mu can ya sa murya ya kira sunan Amirah ta amsa da sauri tana fadin na,am yayana. Yace zaku iya yin aiki hajji bana kuwa don tare nike son in tafi daga club din mu na samu kyautan kujera har har biyar. Kinga dani dake da maryan nake son mu tafi sai tsagal Maryan tace da Bintu ko? Tsit falon yayi don sun san maryam tayi tsaga da fadi gaskiya. Yace wanan bakauyan taje mijin ta ya kaita mana nidai ni dake da Amirah nace kina min gayyan wasu takarce can daban. Kai ban son rashin kunya Fatima ce takarce kuma yace ba tana da miji ba taje ya kaita. Ai dai kasan zai iya kaita tunda yana da halin shi shima maji ta fada mai hakana. Don Allah dai yaya ka hada,harda Bintu mu tafi ita ma ta sauke don Allah tana fadin cikin dan marairaicewa kamar karamar yarinya. Yace maryam ashe ke karamar yarinyar ce yaya zai kai ta saudiya bayan tana da miji idan yai karana fa na kai mai mata saudiya bada sanin shi ba. Don haka ki bar wanan zance don Allah nikan da naji ta matsa zance ina duke kaina akan littafi. Nace Anty maryam bar zancen nan nima ban faye saka kaina inda Allah baikaini ba. Nafi kowa murna yau dajin yan uwana zasu gabas su sauke farali at early age din su. Muryan maji ne tace ai yadda Allah ya bashi ikon , biya wa yan uwanki ko ke haka zai bashi ikon ya biya maki atafi dakw kafin kiyi aure. Maji na fada maki wanan kujeran kayautan su na,samu nima daga wa ni kungiyan mu dake can kasan Dubai. Jin nan babana ban son tsaya wani kace nace kawai ka bari yaran nan su tafi da yar uwar su . Kai kanka kasan da cewa, bamu taba tsan manin irin haka ba a rayuwan mu. Shiru yayi har maji ta gama fadan ta baice uffan ba nidai takaicin irin wanan halin da yakw min sun kai min ko ina amma indai har nai aure na bar gidan su na huta da komai ma. Can ya dan furzo iska yace yauwa Maji na dade ina son in tambaye ki naji sai abubuwa sukai min yawa ban samu lokacin tsayawa tambaya ba. Fadi ina jikin muma dai shiru mukayi muna saurarwn shi sai da dan garani ina kokarin yin abindake a gabana ne alokacin. Yace Maji wai akwai wa ni tsoho da naje gurin shi kwanaki bashar ne yakaini gurin mutumin To da zan dawo sai yake cewa idan nazo gida na fadawa mahaifiya na kada ta manta da alkawarin da tayi na cewa zata kaini da kanta gurin da aka bukaci ta kaini. Ni din nan inji maji ta fadi cikin dan murmushi da mamaki a fuskan ta a lokaci guda. Tace kai mutane akwai yaudara wallahi ko sai mutum yai karya ne zai samu abu daga gurin mutane ? Shiru nayi idona akan littafi amma kuma zuciya ta tana nazarin wani zance can a baya tun farko. Amma maji wanan mutumin wallahi tsoho ne sosai kuma ban tsan mani yaudara bane yadda yai min maganan Don zanfita cikin murmushi yace nacewa mahaifiya na tayi niya ta tafi inda tai alkawarin zata kaini da kanta in ba haka ba gaskiya akwai matsala,babba nan gaba. Don tana tunka ana walwale mata ne za,a mayar da hannun agogo baya sosai . Mai makon naji maji ta tuna alkawarin da tayi a baya sai naji sun buge da zagen tsohon mutane kawai. Suna kiran macuci ne ma yaudari don taci kudinw yake fadin haka Allah yasa dai ni ba mai zuwa gurin malamai bane da yan tsubbu neman taimakon su na dogara ga Allah. Amirah tace ba dai maman ba kan yaje can ya yaudari wasu gaba amma ba nan ba kan. Batare da na kalle su ba don shima mai maganan kanshi na duke ne kawai alaman surutun su yai mashi yawa. Sai muryana kowa yaji a falon ban juyo ba ban dago kai ba nace mama kece ba karya mutumini keyi ba. Da sauri sadauki ya dago kai yana kallona itama uwar hakane ixo ta tsura min don ban taba mata haka,ba duk zamana da ita. Tace Fatima kikace nine nace zan kai sadauki wani guri ban kai shi ba nace eh mama , Kai Bintu yau kuma maji zaki kullawa sheri haka maryam ke nan ke fadin haka cikin dariya. Na girgiza kai na nace bazan taba yiwa mama sheri ko wani nataba har abada. Dan tabe baki yayi daga inda yake zaune yana wani game da,wayan shi na,wasan driving. Don yakan dan taba wasan mota a America tare da,samari yan uwan shi don nishadi kawai haka har kudi suke sakawa ko kyautan wani abu ga wanda yaci. Mama tace dada,Fatima kikace nine nai alkawari na kara cewa eh mama sai dai bazan tuna maki ba sai wani lokaci in kuma kin tuna shike nan. Amira tace a to dama dai ba,a shiga tsakanin Bintu da maji don sun fi kusa, kila tare da ita akai zancen. Nace ai harda ke anty don gaba dayan mu musan da zancen sai dai mantuwa kawai . Dan dariya yayi yace wanna yarinyar Allah munafukace Maji baki dai son ana fadi ne kawai amma ji daurewa wai kowan ku yana gurin. Dakata Babana tunda Fatima ta kuke da haka akwai magana ke nan ya mike tsaye yana fadin ni kan na fita don bsn iya sauraren shirmayn yarinyar nan gaskiya. Yana ba da baya na,shake murya nace mama kin manta maigani yace kikai mashi sadauki inda gwago mai masa ta tafi. A,a,a anyi haka Fatima shiku jin ina kus,kus da maji yasa shi juyowa ta ce tabbas anyi haka Amirama,tace wallahi na manta muna zaune kuwa aikai maganan. Cikin wani fargaba Maji tace babana dawo ka,zauna don Allah da mamaki yake kallon mahaifiyar nashi don bai san may shu,umar yarinyar na tafada mata ba a lokaci guda yaga ta birkice. Tace don girman Allah ka fada min yadda aka fada maka ka fada min a take ya kara nanata mata, sakon da tsohon ya fada mai. Tace inko ba wani ikon Allah ba yaya akayi wani yasan wanan zancen don dai ba,a nan akayi shi ba. Mamakin yadda maji ta rude a lokaci guda haka ya bashi mamaki matuka yace Maji injin dai lafiya ko yace cikin kallon fuskan ta ido cikin ido. Take ya fahinci da akwai matsala ke nan yace please Maji may ke faruwa ne wai? Ko zancen mutumin gaskiyane dai yake fada don ni ban dauki zancen da wani muhinmanci ba kada haka ya tayar maki da hankali. Maji a sanyaye ta,ke ce mai gaskiya Babana akwai matsala saboda akwai wani mutum da haduwa kawai nayi dashi ranan ina asibiti ya shigo gaida mu yake cewa kana da matsala don Allah nayi kokari nazo dakai gurinshi ya ganka. Nai alkawarin zan kaika amma kuma kaga na manta shaf wallahi inba yanzu da Fatima ta tuna min ba. Ban san lokacin da na sauke ajiyan zuciya ba jin yadda Maji ta canza maganan a lokaci guda. Don dama ina gudun ace daga gwagona zancen yafito yace zata koya wa uwarsu bin bokaye nima yana iya sakani gaba da zagi don nasan halin shi. Yace amma Maji kin dauki zancen serious ke nan ko?. Tace idan ba serious matter bane yaya za,ayi zancen ya fito daga gurin wanan tsohon. Kaga ke nan maganan mutumin gaskiyane tunda ga zancen yafito a gurin ka. Jikin maji yai sanyi sosai a lokacin don sai ta shiga tunane watau ke nan masu sherin basu daina ba ake nufi ke nan. Tai mamaki da taji yace yanzun za,a tafi gurin mutumin ke nan tace ya kamata gaskiya . Zan samu lokaci sai mu tafi kafin na koma ke nan don na kusa tafiya ba kuma zan dawo ba sai nazo daukan yaran nan mutafi don ta inter national zamuyi tafiyan. Maji tace amma na fada maka da diyata za,a atafi baice komai ba har ya mike zuwa kofa sai lokacin ya ke cewa Maji sai ki shirya mu tafi dake kenan don bazan kwashi wa yan nan ba duka su zama min wahala a can. Don nima ina son nayi inganttacen ibada banda lokacin taulali dasu gaskiya don kin san yar ki bakauya ce matar bakauye kuma. Yana fadin haka Fita yayi daga dakin nima sai yau banji haushin shi ba don ya gama min komai a duniya. Mutumin da adalilin shi zai shiga kasa mai tsarki ai yagama min komai wallahi ko a duniya dole nayi hakkuri dashi don iyanzu na fahinci halin shine haka gwatsale mutum a take don bai son raini. Nikuma yar kauye ce baruwan mu da banbants babba da karami gurin fadin magana. ****** ********* ****** Maji ta tsara Baba hat ya yarda cewa zadu duba jikin Baba na ne akauye don haka muka fara shirin zuwa gurin da akai magana. Don ta kira gwago ga waya sunyi magana akan tafiyan mu kuma gwago taiwa dan uwan nata magana yasan da zuwan mu gurin shi. Sadauki ne dai bai san cewa da mu za ai tafiyan ba sai lokacin da za,a tafi yaga duk mun shirya tafiya yake cewa Wa yan nan fa kuma Maji ? Tace dasu zamu tafi don suma ina son na kaisu gurin mutumin ya gan su. Kaman zai yi magana sai kuma yai shiru yana tsaye tsakar falon ya harde hannayen shi guri guda. Can yace sai dai da Bashar zamu tafi ban tsan mani motar zata dauke mu ba fa. Tace ai zamu iya matsawa mu hudu a bayan dukkan yace da yake ita wanan yar fillon ba jiki gareta ba ko? Yadda maji tace hakane mu hudu muka matse a bayan motan muka kama hanys sai garin. Tun shigan mu mota banyi magana ba don idan na shiga mota amai nakeyi ko yanzu shi ke damuna. A hankali na bude ledan da na riko na shige cikin hijjab dina naita kwarara amai tun ina yi a boye har Maji ta gane da sauri tace subbahanallahi. Fatima amai kikeyine ? Da sauri ya juyo yana fafin oh shit, Don Allah Bashar parke motan da sauri kada ta damay mu da wari a mota. Fada yake yana fadin kin san baki da lafiya don gulma shine sai kin biyo mutane kuma? Yaja tsaki aka fito da sauri na samu guri nai ta shara amai mama tana a kaina sai sannu take min. Da ya tsaya min muka shiga mukaci gaba da tafiya, an fara tafiya cikin jan tsuki yace i hate naga ana amai wallahi. Bashar tace kasan wasu mutane idan sun shiga mota sai su dinga amai don warin petror. Da kyat naga,mun kawo garin kaina yana,duke sai ciwon kai dake damuna a lokacin sosai. Gida ne irin ginan kauye na haki da itattuwan dake basu innuwa manya manya a kofan gidan. Suka tambaya kamar yadda aka fada masu wani yaro ya shiga yai masu iso akace a shigo daga zauren. Maji ce tafara shiga taiwa mutumin bayanin komai yace to a shigo babu komai dama irin matsalan nan sai anyi wa mashi dabara. Dattijone fari dogo dashi baida jiki sosai sai dai yana da fatin gemu mu bamu shiga ba muna zaune a bayan mota. Sai Bashar dake tagaba sosai bai shiga ba har sun shiga sadauki ya fito yai mashi hannu daya biyo su mana. Sun zauna aka gaisa yake tambayan shi yaya jama,a ya aiki ya amsa tare da bin zauren da kallon irin littafan dake tare a cikin zauren da ido. Malam ga yaron kamar yadda kai umurnin nakawo maka shi yace nagan shi hjy. Hannu ya mikawa sadauki inda shima ya mika mai azaton shi gaisawa zasuyi sai yaji ya rike hannun nashi idanuwan shi ya lunshe yana fadin ikon Allah. Can yace umm,umm Allah mai iko, aida sun barka da sun sha alheri fiye da tsanmanin su. Sai ya sake hannun sadaukin yana girgiza kai yace mutane basu da imani yanzu duniya tai nisa wallahi. Agida akwai matsala sosai hjy hakama a,waje akwaishi. Sai dai ita matsalar ta waje ba wani matsala bane akan harkan samun shi ne. Nan ya dago kai yacewa sadauki ka na iya gane wani bakin mutum daga cikin ku mai dan saje a fuska sai dai ma naga kaman ba musulmi bane. Yace akwai ranan da yaba wani abu a cikin leda fari kai kadai baiba kowa ba. Sai dai anyi sa,a kana zuwa gida ka manta bakaci ba sai bayan kwana biyu kaga ledan ka bude amma sai kaga abin ya zama baki. Shiru yayi yana son ya tuno wanan ranan sai zuwa can yanisa yace anyi haka malam, Amma Daniel ne abokin wasa na ne saida iyamurine shi ba musulmi bane. Yace nagani ai . Yace Allah ya kareka da kaci yadda wanan anin ya koma baki da haka jikin ka zai koma ayi maganin duniyan nan sai dai Allah gaskiya. Yace amma idan baka yarda ba abinda zan baka yanzu idan ka gwada zakaga insha Allahu ba yin mu ba da yardan ubangiji bazai yarda ko hannu ya kara hadawa dakai ba. Burin shi shine saboda kaine bai daga ba kakai mashi ko ina don yana ganin kaine ka,tare mashi wuri. Ikon Allah inji maji tace ko ina da matsalan dai, malam yace yanzu muna A LOKACIN NE, Ai yanzu duniya ba,ai mata hawan kawara sai dashiri ake shigan ta don mutum yana barci ana mashi nasari ne. Bashar yace kaji abinda nake fada maka kullun amma kai baka ganewa ne shiyasa. Shi dai nisawa kawai yayi. Hankalin shi na gurin tunanen Daneal kawai yasan bai kaunan shi tun farkon haduwan su suka fara samun matsala amma daga baya sai ya daina tsanar shi. Yace hjy sai zancen gidan ku gaskiya bazan boye maki ba akwai matsala sosai a gidan. Nan ya fara basu bayani tiryan tiryan amma bai fada masu sunayen masu wanan aikin ba kamar yadda yaiwa gwago bayani a baya dama kuma,shirin da suke a yanzu. Har kan yaranta mata da aka,asirce mata su akan suyi ta zama ko kare bai kaunan su balle mutum. Nan kan ran sadauki yai matukar baci cikin bacin rai yake fafin wai Maji may mukaiwa wa yan nan mutane ne haka a duniya. Kagin tai magana malamin yace hassadane kawai don sun san kokai waye shiya kawo haka kawai.. Maji tace yaran suna nan nazo dasu ai yace na sani don nagan su su uku ko? Sai dai dayar bataki bace Allah daine yakawo maki ita cikin hikima irin na ubangi wanda duk abinda kaga ya tsara ba,a banza yake tsara shi ba. Zaman ta gareki alheri ne sosai koda yake bama sai na fada maki ba ai kema kin sani. Sai dai zatai aure amma dai auren yanzu gaskiya sai Allah don banga yuyuwan shi a halin yanzu. Malam daga gurin mijin ne ko kuwa yace Allahu,a,a lamu sai gaibu sai lillahi gaskiya. Cikin ran sadauki yace aidama nasan wanan mutumin yaudaran tane zaiyi sai yaji malamin na fadin amma akwai abinda zanba kowan su insha Allahu komai zai walwale da yardan Allah. Sauran ma insha Allahu mazajen su zasu fito bada dadewa ba ai. Nan dai yaba yaya sadauki abubuwan da,suka dace tare da kara jaddada mai yadda zaiyi amfani dasu. Sai yace ace mu shigo idan mun fito sadauki ya shigo shi kadai sai uwarshi akwai maganan da zai yi dasu wanda siri ne. Nan dai yai muna duk abindaya dace da kowan mu muka fito da yan ledojin kulin maganin daya bamu daga zauren. Ni a lokaci duk a galabace ma nake don ni ban san wai ina da matsala ba,su dai ne na dauka masu matsala kawai. Muna fita sukai magana ta siri sosai da mana ta fada mashi damuwan ta yai kuma alkawarin taimaka mata. Sadauki ya shigo ya zauna mutumin ya kalle shi yace kai babban mutum ne watarana zaka tuna da magana na matsalan ka dayane shine wanan shaye shayen da kakeyi. Duk da naga abinda sauki yanzu sosai akan ka don abin yarage maka fiye da baya can. Yace sai kuma ka kara da hakkuri don ko yaushe biyayya na iyayye yana kai mutum ga alheri. Yai mashi nasiha sosai akan duniya tare da kara mai wasu yan abubuwa irin nasu. Inda yace ya tabbatar kagin ya tafi gurin neman shi yayi abinda ya bashi din. Kudi masu yawa ya ba mutumin sai yai dariya yace ba haka nake ba ni dari biyar kawai zaku bani ko shi kada kuce naki karba ne da ban karba ba wallahi. Sunyi mamaki sosai muka kama hanya sai sokoto koda zamu dawo naita kakarin amai saidai da yake cikina ba komai sai kumfa kawai nake zubowa. Bashar dasu mama suna ta faman yi min sannu amma,shi ko kallo ban ishe shi ba. Da la,asar muka iso gida tun lokacin kowa ya fara abinda aka bashi yayi daga gurin bawan Allah. Don har bashar saida ya anso nashi shima don mutimin shi da kan shi ya bashi taimakon. Tun dawiwan mu nikan ina dunkule saman dogon kujera harda barcin wahala saida nayi. Anty maryam ce ta dafo min liptop da lemun tsami na dan sha shine na dan ji dama sosai. Ya shigo falon yayi wanka ya,sauya kayan jikin shi a lokacin yasa wando da rigan na maza mai dogon hannu. Gani a kwance na dunkule yasa ya dan tsura min ido sai yaji na bashi tausayi sosai. Yace ke may ke damun kine yanzu kuma? A sanyaye nace cikin bata fuska kaina ke min ciwo. Bari in nafita sai a sayo maki magani kisha. Nace nagode. Wanan gidiyan da nakan yi mai idan yai min alheri yakan ji matukar dadi a,ran shi don shi mutum ne mai son yaji ana godiya gare shi. Sosai ya mayar da hankali shi ga maganin shi da mutumin ya bashi don yai matukar yarda da zancen mutumin ba din komai ba,rashin amsan kudin su da mutumin baiyi ba. Ya dawo ya,sayo min magani harda na amai da kuma drinks mai sanyi na kwali. Ina kwance na na dunkule a saman kujera su na kallo ni kuma gani kwance a dunkule sai dai ba barci nakeyi ba idona biyu. Muryan shi naji yana tambayan su ita wanan barcin takeyi har yanzun ne ko jikin ne ke damun ta? Maryam tace tace kanta kawai ke ciwo yanzu yace ke tashi ga magani ki sha ko zai lafa maki. A hankali na mike zaune daga kwancen da nake sai dai still ina dunkule ga hijjab ga kuna blanket dana yafa ajikina. Na karba tare da bare maganin na kai abakina saida na dago kai naga ya tsura min ido ashe ni yake kallo daga inda yake zaune. Da sauri na dukar da kaina kasa bban tsaya shan drinks din ba yake cewa bazaki sha juice din ba ne? Nace a,a ban iya sha yanzu sai nakai kwance daga inda na tashi yamike zai bar falon yana cewa idan bai bari ba sai akaiki asibiti ke nan. Ya fice daga dakin na lumshe idanuwana tare da komawa barci a lokaci guda. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,, IDAN KIN TURAWA WANDA BAI BIYA BA BAMU YAFE MAKI BA ALLAH YA ISAR MU NA AKAN KI,,,, Tun kawo laife na yaya sadauki ya kara tsananta min a gidan su, dan abu kadan zanyi ya dinga min fada cikin hasala da bacin rai. Wanda shi kanshi bai san dalili yi min haka ba haka,kawai yake jin haushin yarinyar a ranshi. Duk da maji tana mashi fadan haka amma ya kasa rangwanta kiyayyan da yake ji nawa a ranshi. Idan yana gida ban fitowa falo sai naji ya fita daga gidan zan fito falo don nima haushin shi nake ji yanzu don a matsayin mugu macuci nake ganin shi. Nasan kuma don saka mai idon da nakeyi ne abaya shine yasa yake jin takaicina haka. Maji sai shirin bukina dake kara matsowa takeyi a hankali, irin su kayan kitchen da wasu uan abubuwa su take sai min. Kabir yace idan anyi aure a sokoto zan zauna a gidan shi na garin sai idan anyi hutu zan diga zuwa gurin su Abuja. Maji yakira ya fada mata tsarin da yayi akaina da ta tambaye shi kan al,amarin karatuna da nakeyi. Sadauki ya shigo ya samu mama tana wayan da Kabir yana jin duk abinda suke fadi a karshe Kabir din ke cewa mama ko tsarin bai maki ba haka? Maji tace gaskiya naji dadin hakan Allah ya albarkaci rayuwan auren ku, ya amsa cikin jin dadi da Amin mama. Mama tace Kabir don Allah ka rike min Fatima amana don Fatima yarinyace dake bukatan kulawa yace insha Allahu mama kada kiji komai nima nasan da hakan. Yana zaune ya fahinci da wa mama take waya ya lumshe idanuwan shi jin hiran nasu yake kamar a fili Kabir yake ya shake shi. Sai tsuki yayi lokacin suna sallama zata kashe wayan yace tsohon banza kawai. Kaidawa kuma kake tsuki anyi wani abin ne ko may? Yace cikin daure fuska kawai dai nayi ne don wanan shirmay danaji anayi. Shi waye da zai dinga yiwa mutane barazana kamar wani attajiri can. A,a ikon Allah waikai sadauki ina ruwanka da zancen nan ne? Ina da ka mayar da kanka abin kwarai agurin kane za,a zo neman auren yaran nan. Yace wani maji da ban bashi ba kawai mutum ya tsufa amma yana halin yara . Idan aure yake so bai zuwa ya samu bazawara su shirya sai yafake zai bata yar mutane. Ya juya inda nake zaune raina yabaci don abinda yake min yafara isata, yace jita don Allah daga kawai ance mutumi a abuja yake duk kin wani rude a kan shi don kawai kije abuja. Baki tsaya kin tsarawa rayuwan ki abinda zai fishekiba mutum da iyali haka ke karama dake may zaki gane a gurin shi inba wahala ba. Kai dakata ya isa haka na,rasa gane dalilin dayasa kake wanan abin haka Yadago ya kalli uwar yace may nakeyi maji iyaka dai ina fadin gaskiyane ni kawai. Duk abinda na hango mata kun kasa hangen shi sai faman rawan kai takeyi ita zatayi aure wawiya kawai doluwa. A,a wai sadauki kana da hankali kuwa da may wanan abin yai kama hakane wai? Mikewa nayi fuuu, nabar falon cikin fushi na shige ciki abina don ban iya tsayawa sauraren wanan shirmay na shi. Tun ranan idan yaya sadauki ya shigo falon duk hiran da ake haka zan mike tsam na shige daki abina. Ranan muna tahiran mu cikin dariya har maman tamu tana saka muna baki a hiran mu don hiran wasu samari da suka zo wai suna son maryam muke yi muna dariya. Ya shigowa suna mashi ina wuni da jan shi da hira yana batun zama namikw tsaye tsam daga inda nake zaune, ina cewa. Zan shiga na kwanta maryam tace wazai kwanta yanzu ke da baki barci koda rana shine yanzu da yamman nan zakice wai zaki kwanta. Ya dago lumsarsun idanuwan shi masu nuna a gajiye yake a lokacin don tun safe yafita daga gida . Ya dora su a kaina gaba daya yaga na canza mashi na koma wata fresh sosai dani don nima ban san may mama take yawan bamu ba muna ci muna,sha na gyara jiki kawai . Ko kiftawa bayayi don mamakin sauyawa na a lokaci guda da yaga nayi mashi a lokaci guda. Mama taga yadda yake kallona sai abin ya bata mamaki kwarai da gaske amma sai ta dauka wani sherin yake son fadi akaina kuma. Don haka tai shiru tana sauraren taji abinda zai fadi a lokacin tai mashi tsiya. Maryam dai tasan yar tsama muke duk kwanakin nan ta dai dubeni saboda ta san ba,kwanciyan zanyi ba ganin yaya ne kawai yasani barin falon nashige tana ce min atashi lafiya ko? Nashige batare da na,kara,waiga inda yake ba ballw yace ga abinda nai mashi kuma. A bangaren sadauki kuwa, fuska ya kara,daurewa batare da ya kara bi ta kaina ba don yasan mama tana jiran shi ne. Maryam daga inda take tai mashi kuri da ido tana dariya cikin kyata tace ban san wanan fadan na yaya da Bintu ba wallahi. Bai tanka mata ba sai tsukin da yaja ya dan dafe kan shi yana fadin rabu da,wawiyan banza kawai gaskiya ne bata so a fada mata. Daga gurin da maji take cikin takaici tace gaskiyan may kada tai auren ko may ? Yace ni fadan gaskiya nake mata saurin may take da,bazata iya tsayawa ta karasa makatantar taba ne wai, duk tsoho ya, hure mata kunne bata jin kiran yanzu sai When it's too late to her zata gane kuren ta ai. Allah dai ya tabbatar muna da abinda yafi zama alheri a gare ta. Ina shiga daki kamar jira kabir yakw na shiga dakin sai ga kiran wayan shi ya shigo min. Mama ta kwalla min kira wai nazo za ai program din da nake so wasan kwaikwayo a NTA sokoto wanda nake so ina kallo ina dariya don shirin irin namu ne na mutanen kauye. Hakan bai hanani yin wayana ba don can na manne gefe guda yadda,ba mai jin abida nake fadi. Kallo daya zakai min ka fahinci cewa ina cikin nishadi da wayan da nakeyi ga kuma kallon film din da nakeyi a tv duk a lokaci daya. Muryan kabir ce ta ratso dodon kunne na yana cewa Fatima nayi rashin ki kwana biyu aiki ya hana nazo na gane ki. Nayi murmushi tare da lunshe idanuwa na na gyara zama da kyau. Ban bashi amsa ba sai yar murmushin da nayi har yana jiyo ni a,wayan a lokacin . Ya naji kina murmushi ko baki yarda na damu da nazo na ganki bane wai? Na koma yin murmushi mai hade da sautin dariya wanda ya jawo hankalin kowa a kaina a lokacin. Nace may zai hana na yarda duk da dai nasan akwai wasu a,tare da kai ba,wai wani damuwa zakayi sosai hakana ba ai. Yace kowa daga cikin ku ina bashi hakkin shi ai nace ai nasan da hakan, yace da kyau da kika fahince ni. Yace wai kin san wani abu kuwa nace a,a cikin dan girgiza kaina kamar yana gani na a fili. Nace sai ka fada dai, Yace wai ko Fatima kin san yadda nake jinki a cikin raina kuwa, ? Wallahi da ina da iko ko kuda bazan yarda ya sauka a kanki ba. Don ina ji a jikina ke wani abune da,Allah ya jefo min a cikin rayuwana mai muhinmanci a gareni. Murmurshi nake irin mai kyalkyatawan nan nace kai amma kuwa nikan nayi sa,a,a,rayuwana wallahi. Insha Allahu zanci gaba da kullan maka da kaina a duk inda nake . Nace ni wallahi zancen kama har yasa na manta ban tabayeka lafiyan anty na ba da yara. Yace duk suna nan lafiya yanzu tare muke da uwargida ta dan shiga shago tayi sayayyane. A rude nace wai har na zaci ai a gaban ta kake waya dani haka wallahi. Yace aiko a gaban ta sai nayi don ba ta damuwa tama fini matsuwa kizo gidan ai yanzu. Na saki wata yar siririyar dariya nace kai ka taba ganin kishi har tafi ango damun akawo mata kishiya a duniya. Yace baki san halin ta bane shiyasa amma ni nasan zanji dadin zaman ku a tare sosai wallahi. Nace ni dai ka rufa min asiri kada dayar matarka tani tace zamu hade mata kai don muna shiya daya da ita. Yace ai itama tasan cewa Haulatu na waya dake tai fada harta gaji tunda babu yadda zatayi. Nace ni nasan dama idan ta sani sai anyi rikici don bata da dama,wallahi gurin kishi. Maryam tace kai kai wanan matar dai tun ba,a shiga ba na hango ita ce matsalar ku ke da Kabir . Dariya na kama tare da kashe ina cewa kai anty maryam watau kina jin hiran mu ashe? Tace duk abinda kuke fadi inajin ku ai in ya damu ba sai yazo ya zauna ba yai ta kore maki kudan da baison yasauka a kanki. Ya suke da hiran mu yakai geji yakawo iya wuya sai yaga fita dakin yafi mashi jin takaici kawai. Ya mike yanace maji zan fita sai na dawo tace mai a dawo lafiya tare da ci gaba da kallon ta. Yana fita Amira tace ke Bintu watarana sai yaya ya make bakin nan naki akan wanan wayan da baiso. Mutum da mijin shi zai make ta idan yaji takaici yaje ya samo tashi matar mana shima inji maji takeba Amirah amsa. Bai dauki lokaci ba sosai yakoma tafiyan shi don yanzu bai zama a gida shi sosai ga,wasan kwallo ga kuma business din daya fara gadan gadan na sayar da motoci da mashin mashin, Haka yasa baida lokacin zama a gari yana fita business din shi da neman kudin shi. Cikin dan lokaci guda sai ga sunan sadauki ya daga sosai a gari. Abinda su mama suke gudun dai ya faru Allah ya nufi sai ya faru din don suna gani kuma suna jin yadda Allah yai ikon shi akan abinda suka so kada ya faru da dan kishiyan su. Mama Asiya ce suna zaune suna hira take cewa, wallahi yaya wanan yoron shigen yaro ne kidiba fa,ba yan mu ba yanzu ko uban shi ya tsushe nisa ba kusa ba . Umma tace ni wallahi ba inda na fara sanin haka zai iya faruwa damu sai wani rana da natafi dasu gurin buki. Wata mata irin matan nan masu ido a bude take ce wa daganin na shigo da yaran gidan lokacin suna kananan su. Matar tace wai wai wai wake da wanan hamshakin yaron haka? Wai akwai magana nan gaba a gurin nan yaro karami haka da,wanan baiwa irin haka. Don Allah ku daina fita dashi don gudin idon makiya don wallahi wanan da kuke gani ba karamin mutum bane gurin nan aje. Umma tace na dauka fa da yaron nan take (Imirana) sai naga ta kama hannun Sadauki kawai tana wani zuba mashi kirari har da dukawan ta. Tace a lokacin na dauka ko shirmay su ne na yan bori ko neman kudi sai kuma nakarajin shi a gurin maigadin ma,aikatan mu ranan shi ma ya kawo min sako gida sai ga sadauki yafito naga yana kada kai yana fadi cabdi babban mutum Allah ya raya muna kai watarana,akwai magana gidan nan. Wallahi Asiya tun ranan nasan in bamuyi hankali ba diyan mu na zama shara a gidan nan muna ji muna gani. Hmmm ashe bani kadai nasan da haka ba tace ni wallahi a gurin baffa malami na fara jin haka. Ranan da,suka rakani na gayar dashi duk cikin su ba,wanda ya cewa yazo inda yake zaune saman buzun shi wai sai sadauki. Naji yana cewa manyan gobe Allah ya taya riko Asiya ki rike yaron nan don watarana shine gatan ku ke da yaran nan. Wallahi baki yadda wani mashe ya sokeni ba sai da na dawo gida abin ya tsaya min arai sosai wallahi. Nasan baffa kamar mai rafanne yake da,wuya yai magana ya zama karya wallahi. Kinga wanan makiran nasan itama tasan komai shiyasa take wani wayayya,tana nuna ita tana kaunan shi fiye da kowa. Shekaran jiya Adamu ke ce min wai motar da yasayo yana shiga yanzu takai miliyan goma. Ke don Allah dai ki bari tace wallahi yace haka yaji ana fadi a gari wai ba kowa kedashi ba yanzu a kasar nan. Hmmm lalai Hawau takai makiran mace amma baki ganin wani alaman facakan kudi atare da ita kuma kin dai san yana bata dai. ,A,a ba gashi yaron nan yana fada min ba,wai shi yayowa uban odan kayan da aka,shigo masu dashi wanan wata yace kuma kayan sun samu shiga sosai. Ai harda noman da Alhaji keyi yanzu shine mai bada kudi anayi don dai ranan naji suna,waya dashi. Dan banzan yaro maikama da dutsen tsakar ruwa , Asiya karkare mata da cewa, wai bai san tudu ana rana ba. Yanzu don Allah wazaice dan banza zai iya irin wanan dabara duk kwaya ta halaka shege kullun gashi a bushe kaman kayan rani. Sai suka sa dariyan keta har suna tafawa tace aiko yanzu in sun san wata ai basu san wata ba ko? Da yammaci, ranan laraba sadauki ya shirya yafita zuwa masana,antar shi don yaga halin da,su Bashar ke ciki da sana,an tasu. Ranan shirin musulunci yayi wanda da,wuya kagan shi saye da tufafi irin na,al,adan hausawa. Shadda ce gezenah mai ruwan kasa,sai maiko takeyi, sai dai dinkin gajeren hannu ce,anyi ma,rigar aiki a gaba mai kyau da daukan ido. Sai yar hular da ya dora akan shi mai tsada kalar kayan jikin shi,takalman shi bakake sai shining sukeyi sunci polish. Ga kanshi na tashi kamar duk kwalban ya juye a jikin shi a lokaci guda. Gurin maji yafara shigo ya sanar da ita zai fita don har yanzu kudi bai hana shi yiwa iyayyen shi biyayya ba. Kuma baisa yace don yayi gina yabar gidan mahaifan shi ba yanan ciki tare dasu saidai ya gyara gurin shi sosai harda na yan uwan shi. Ina zaune antu maryam tana min kitso sai faman masifa take min ita gashina yai yawa wahala kawai nake bata. Azaune nake ba dama na gudu daga falon gashi fuskana yana facing din inda yake tsaye yana dauko wayan shi dake ruri daga Aljihun shi. Yace hello Bashar yaya akayine ? Yanzu nake son fitowa tun dazu ina daki ina barci kasan wasan last week yabamu jiki sosai. Saidai duk da waya yake idonbshi yana kan kitson da Maryam take min kur dashi gashi dole muna facing din juna dashi. Yana kashe wayan ya mayar da shi cikin aljihun shi inda ya ciro ta da farko. Yace maji fa? Yanzun ta shiga ciki nasan zatafito tunda taji muryan ka ai inji maryam din. Maryam tace yaya wanan wayan taka tayi wallahi ni dai taban sha,awa Bintu gashi kaman wanda mukaga Kabir dinki dashi ranan. Da sauri yace ke maryam ban son iskanci wallahi ki daina hadani da wanan tsohon mai zarin tsiya. Na muguda baki cikin tsiwa nace nikan banga tsoho ba wallahi. Ban san ko tako nawa yayi ba,sai gashi gabana ya danko gashin kaina da karfi sai da na,sake wani irin kara,da sauri mama tafito tana fani kai kai yayane kuma wai ? May haka dan Allah kasheta zakayine ko may ? Wallahi maji yarinyar nan ta raina ni wallahi kan wani tsohon mijin ta can take son ta zage ni, ta zage ka tace maka may? Maryam sai dariyan keta takw min idanuwana,sun kawo kwalla ko don har cikin raina naji dankan da,yai min. Kadai zama babban kwabo wallahi ka ishi yarinya da sherin mijin ta tsoho ne basai ka,samo mata saurayi ba kowa ya huta. Allah dai ya,sauwa wake son wanan bakauyan haka ko dressing ba ta iya ba balle gyara irin na mata. Kyalkyalkyal maryam ke min dariya Amira da,tafito daga kitchen don jin karana take cewa, a,a yayana aiko wallahi yanzu ba may cewa Bintu bata iya dressing ba gaskiya. Kallonta yayi yaja tsoki ya juta gurin maji yana fadin maji zan dan shiga gurin su bashar na,dawo yanzu. Sai ka dawo tace mashi tare da samun guri ta zauna tana man fada na daina shiga harkan shi kada ya halakani ga banza. Nace cikin dan kuka ina,share hawaye da bayan hannu na mama,wallahi duk anty maryam ce taja min. Ban san may yakaita danganta,wayan shi dana Kabir ba,shine yake cewa wai za,a hada shi da tsoho kazami. Dariya abin yaba mama tace ni dai na rasa wanan kiyayyan na sadauki da Kabir wallahi Allahbya sauwaka. Amira tace jinin su ne bai hadu ba yace min wallahi haushin shi yake ji. Wai babba dashi yazo zaiwa yarinya wayo itako sai shegen son maza duk ta mutu akan tsoho. Dariya suka sa nace tunda yana jin haushin shi ba,sai ya kashe shiba in ya isa. Har lokacin ina jin zafin dankan da yai min don har kaina naji yana sarawa wani iri. Tafe yake cikin motan shi sai dai a hankali yake tukawa don akwai motoci da yawa saman titin a lokacin. Wani iri yaji kamar ina cikin motan na,sake wanan razananen kara da na sake lokacin da yaja min kai. Yace natural hair ne haka gare ta ashe nibna,dauka ko kari take ko yaushe ai. Wawiya can zata karata dashi gurin dan tsohon ta babu ma gyara kila a karshe. Yana faka motan daga inda ya tsaya yafito yasa remote ya kulle motar nan ya taka a hankali zuwa gurin da office din Bashar yake don yasan yana nan yaga motar shi a fake can ne sa. Bashar na zaune yana cika wasu takardu sadauki ya shigo office din . Bashar ya dago yana cewa kadai samu fitowa ke nan yanzu din na dauka sai ka tsaya ka cinyewa tsohuwa dan tallenta ka fito ai. Murmushi yayi yana kaiwa zaune yace don wa ake dafa tallen dama ba don mu ba. Gaskiya ya kamata ace kayi aure haka wallahi man, don Maji ta huta da katon gwauro haka kullun yana lashe mata talle. Sadauki yai murmushi tare da daukan wani takardan dake gaban shi yace aiko nai aure tallen maji ba zai huta dani ba. Kana ma min zancen aure ga babban tazurai basuyi ba balle ni. Da sauri cikin daga kai Bashar yace wa wai Imiranah kake nufi da Ahmad? Yace su mana kai dan Allah rabu da wanan shashan yayan namu . Cikin dare fuska sadauki yace ban son iskanci ba yayan nawa ne kuma sha sha. Ce wallahi shi duk gari yanzu kowa yasan shi sai aukin bin yan yara masu tallah yana latsawa a kasuwa. Kaifa dan iskane wallahi wanan kuma ai sheri ne nasan dai yana da shegen son mata amma ban san da wanan ba kan. Yace aiku na gida baku sani kwanaki ma naji ana kudundumin yaiwa wata yarinya mai kai shikafa layin su ciki ko yaya case din ya kare. Bashar yau dai da sheri ka tare ni ke nan dai don nazo gurin ka dana sani na zauna gida abina ko natafi stadium. Wallahi ba sheri bane don ina ga Baba ma yasan da wanan case din ai . Zai iya don kwanaki a gabana wallahi Fatima ta mare shi babu ko kunya wallahi. Naso na lalatsata ai amma sai naga tana da gaskiya din taba tayi kasan bata da kunya itako ta kwashe shi da mari kayau. Wata Fatima ke nan kuma? Ya dan bata fuska yace wanan dayan sister tawa dake gurin maji mana da zama. Au kace min pretty mana gaskiya mutumina yar8nyar nan ta hadu sosai wallahi ni dai tana min. Dariya sadauki yayi mai kama da yake yace aiko dan tsohonta zaici ubanka wallahi. Waye dan tsoho kuma babanta yace wanda zata aura dai wani guy ne mai mata biyu wai itace ta uku . Zokaga shegiya yadda take rawan kai nace kici uban ki indai kince rawan kaine. Kai kai amma gaskiya an kwabsa wallahi gurin nan . Wai ma kai kana may har ka bari haka ya kasance ga ka har kabari akaba wani kuma can. Wani kallon rainin hankali ya watso mashi gani sai ayi may kuma ? Yace yar gida gida mai tuwona maina kawai musha buki mukan . Kasan fa yarinyar wallahi matar manya ce sai ta samu gurima zakaga yadda zata baje sosai wallahi. Kai don Allah ni bashi yakawoni ba wai how far ne akan kayan can da suka shigo. Bashar yace baka son zancen ke nan dai mubarta anan kawai ko? Yace zancen may kuma may zanyi da wanan mai zubin yan arab da ita. Bashar yai wani dariyan keta yace kaidai sai naba Maji shawara tafara maka hayaki da rukiya wallahi. Ya jawo wasu takardu daga drawer shi yana mikawa Sadauki yace duba nan ka gani kafin mu koma topic din mu don gaskiya ni iam serious wallahi. Ko tayi miji ai ana iya tayar da zance don gida bai koshiba ba a kaiwa dawa. Karanta takardan yake bai bashi amsa ba sai can ya dago kai yace ikon Allah so quick haka sun samu shiga da,wuri. Yace yanzu haka ma munyi magana da SMG yace min kila zasu sa mukawo masu sabon sanfarin su din suna son su rabawa sarakuna shi. Amma ko gaskiya in haka ya kasance da muyi sa,a sosai wallahi ko. Nan dai suka kara dan tattaunawa akan business din su inda suka fito don dama suna da alkawrin zuwa wani guri da Bashar ya damu sadauki su tafi. A hanya sadauki ya nisa yace amma gaskiya banji dadin labarin da ka bani ba na Imirana . Yace kai kana ga zancen ne har yanzu yace ai wallahi duk ya zubar da mutuncin shi saikace ba Alhajin ku ya haisu ba. Shifa Ahmad cewa akayi yana sanan kayan sata sai asato mota ko mashin ya saya . Innalillahi da karfi sadauki ya furta tare da waigo inda Bashar yake zaune a gefen shi yace wallahi man . Wai kai kana nufin duk wanan zancen baka san dasu bane ko yaya? Yace ina zan sani tunda ba shiga gati nake ba yawo iyakata idan ina gari ina gida ko nan gurin ka,sai ko can site din da nake gina na kawai. Lalai na yarda baka gari gama,wanan sister din naku kwanaki saida yan hizba suka kamasu wai ance sun hada party suna abin banzan ga da mata keyi tsakanin su. Da karfi ya taka burki yace Nafisa ko? Yace ita wallahi naji kunyan wanan abin sosai wallahi ance ai shaye shaye takeyi sosai yanzu kowa yasani ma agari. Subbahanallahi ya,furta yace how comes abubuwa suke zo muna haka agidan mu kaman mu kadaine a gari. Kadai Allah ya,sauwaka kawai amma ai abin ba dadi wallahi. Can suk shiga kasan gari gurin ginan shi irin na mutanen dana daganin gurin mutum zai gane cewa tsohon gari ne gurin. Da,kwatancen da Bashar ke mashi suka isa gidan da suke son zuwa, Daganin gidan basai anfadawa mutum ba gidan wani masani ne na alkur,ani maigirma don ga alluna nan na almajirai daga waje birjit dasu. Nan suka,tura ai masu iso da,maigidan sai ga,yaron ya,dawo yace ance su shigo daga cikin zauren gidan. Wani tsohone ya tsufa sosai yana zaune saman shimfida irin ta mutanen da can baya masu fada aji. Bayan sun gaisa da tsohon ne Bashar ke cewa malam ka gan mu sai yau muka samu zuwa ko yace tau harkokin ku na mutanen yanzu yawa gare shi. Nan dai suka kara gaisawa Bashar yace malam kaman yadda na,fara maka bayani ne akan al,amarin wanan abokin nawa dai. Yau gashi nazo dashi malamin yai shiru can ya dan mike zaune tare da kallon su da kyau yace. Karbi wanan yana mai mika mashi tasbahan hannun shi dayake ja, yace ka zabi guda ko wanine ma daga ciki. Ya dauki wanda ke kusa da farko sai, tsohon yai dan murmushi yace ai abin yazo da sauki tunda naga baka da zari. Don da,wanine na tsaka zai dauka yana ganin yafi mai killla yawa. Ya dinga karatu mus,mus mus dabaki can yace umm,umm Allahu akabar to Allah ya sauwaka. Su dai suna zaune suna kallon shi can yanisa yace Alhamdullahi Bashar don al,amarin abikin ka ba acewa komai don yanzu ma kuka fara insha Allahu, Sai dai gaskiya akwai dan matsa dana gani yanzu dai tunda bashi yakawo ku ba harkankuce ta sana,a takawo ku bati muyi abindake nan. Nan dai yai masu wasu bayanai yakuma basu yan abubuwa tun ana gaban shi yace su sha. Sadauki da cukin kyankyami yake ya matsu subar gurin don shi bai son irin harkokin nan gaba daya a rayuwan shi. Bashar ne ma ya matsa mashi kan lalai sai suzo don yanzu duniya ba,a shigan ta haka kai tsaye don A LOKACI MU KE. Sukai mai godiya tare da mikewa zasu fita bayan sun bashi, dan abincin goro don yace bai karban komai nasu don abokin kakan Bashar din ne sosai. Sadauki dake gaba ya dafa zauren na kasa zai fita sai tsohon yace ji mana idan kaje gida kacewa mahaifiyar ka kada ta manta da zancen baya da tai alkawari kai ka gurin da aka bukaci ta kai ka a baya. Don idan bata maida hankali ba hannun agogo kullun zai dinga koma mata bayane. Da mamaki sadauki ya kalli tsohon sai dan tsohon yai murmushi cikin kada kan shi yace abinda nace zaka fada mata ni dai bata sanni ba ban san ta ba. Yace cikin mamaki toshike nan malam zan fada mata insha Allahu kaman yadda kace na fada mata yace Allah bada sa,a suka ce amin suka fita daga zauren. Duk zukatan su fam yake da tunanen zancen tsohon saida suka fara hanyane Sadauki yace kai guy man din nan fa ya bani mamaki. A ina ya san maji kuma may yake nufi da sakon shine wai? Bashar yace nima naji mamaki amma sanin halin malam babba yasa ban damuwa nasan wani zance ne can ya hango akan ka kuma. Baidai son ya fadine kawai kila tunda bashi yai aikin ba. ****** ********* ****** Maji ke da duty a gidan ranan duk da dai su girkin su bawai na duka gida bane gaba daya. Wace dai take da girki ranan itace zata girka abincin part din ta dana maigidan kawai. Ba ruwanta da sauran part din gidan kowa shi zai girka nashi da yaran shi. Komai da ya dace a girka sungama da wuri kamar kulun sai ta wuce sashen maigidan don ta gyara mashi daki kaman yadda sukeyi kullun kafin ya dawo gida daga kasuwa. Amirah ta tafi kitso a wani shago cikin unguwa maryam kuma ta shiga makwabta don ganin wata kawarta da tayi rashin lafiya. Tare zamu tafi sai banda lafiya kaina da akaja min yana matukar damuna da ciwo hakan yasa tatafi ita kadai. Ina kwance saman doguwan kujeran dake falon na rufe fuskana da littafina da na dauko don na karanta amma na kasa karantawa saboda kaina dake damuna da ciwo. Sadauki ya shigo falon don ya ga mahaifiyar shi akan maganan da malam yai mashi. Nan ya hangoni a kwance,kyakyawan suran jikina danabi kujera na kwanta rigingine yafito a fili. Farin kafa na da yake fari sol dashi ya dan baiyyana a fili sunyi fari sol gasu lub lub dasu tankar wace bani taka kasa. Sadauki yai saurin kawar da kan shi dan ganin irin yanayin da nake a kwance cikin yar doguwar rigata mai dogon hannu da,sharp. A hankali ya tako zuwa inda nake kwance din ya dan rage tsawon shi ta hanyan dukowa ga kirjina ya dan ban karo gaba. A hankali yasa hannun shi ya cire min littafin dana kare fuskana dashi, Da sauri na bude idanuwana da suke min a lumshe don ganin waye ya cire min littafi haka a fuskana don part din shiru yake a lokacin. Daga cikin tsakiyar kaina da hancina naji kamshin turaren shi amma banzaci cewa shine a gabana ba. Nai saurin bude idanuwana da suke a lumshe alokacin shi nagani tsaye kerere a kaina . Haka yasa nai saurin yunkurin tashi zaune a lokacin tare da jifan shi da wani fitinanen kallo na tsana. Yace ke ina mutanen part din suka shigane wai ? Wani guntu tsuki naja da ban yi niyar ja ba don cike nake dashi a lokacin saboda ciwon kan daya haddasa min. Ke ni kika ja,wa tsuki ashe baki da kunya haka ban sani ba? Nace cikin turo baki da kokarin tashi tsaye ni halan nai maka tsikine ? Yakai hannun shi ga dan bakina iya karfin ya murde shi da karfin tsiya, ban san lokacin da nasa kuka ba da karfi ina cewa. Ya sadauki nimay ne maka katsane ni haka kaja min ciwon kai yanzu kuma kazo ka murde min baki. Na karashe fadi cikin wani irin kuka nace in gidan kune baka son ganina sai in bari nima fa diyace kamar kowa. Na juya zuwa cikin dakin da kuka na sai muka hafe da Maji dake shigowa falon, hannun ta dauke da kayan su jik dinta, da hapic na wanke bathroom. Tsaya tayi cikin mamaki takaleshi ta kalleni cin son jin may yafaru bayan futan ta . Sai kukana take ji a cikin dakin daga inda take tsaye, tana mai wani irin kallon tuhuma. Tace may kai mata sadauki? Cikin ko in kula ya nufi saman kujera ya zaune, yace shagwaba take ji kawai dai. Kai may kaimata nace? Tambaya kawai nayi ina kuke sai tai min rashin kunya nikuma na murde mata baki. Kana ko da hankali sadauki? Shin yarinyar nan tobashiyar kace ko kuwa wai? To bari kaji wanan kukan da ka sata ko ka bata hakkuri koo na rama mata abinda kai mata. Wa zan ba hakkuri Maji? Tace Fatiman. Yace cikin mikewa kai haba maji don Allah ki bari kada ta kara raina ni mana. Kai har wani raini kake gudu bayan wanda kajawa kan ka? Ya mike kawai yabar dakin don shima kukan da yake ji yafara shiga zuciyar shi a lokacin. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,, I DAN KIN TURAWA WA WANDA BAI BIYA BA MU YAFE MAKI BA ALLAH YA ISAR MUNA A KAN KI Bayan mun dawo gida sokoto babu abinda mama keyi sai lalashi na tana kokarin taga na saki jikina sosai. Amma na,kasa sakin jiki saboda shakuwa ba karamin abune ba ga dan adam. Na kasa cire Kabir a raina gaba daya ko yaushe zaka ganni nayi zaune nai shiru ni kadai ko idan ana hira ni na zauna naita tunane ni kadai. Yau ma zaune nake saman dogon kujeran falon sai hira suke a tsakanin su akan Ahmad dan wurin mama Asiya. A zahiri kallon su da sauraren su nakeyi amma zuciya na tai nisa da inda suke zaune. Sai da naji murya mama cikin fada tana magana ko shi sai da Maryam ta dan taboni na,zabura firgigit dani. Yaya Sadauki na gani tsaye cikin kaya bakake sai kwalan rigan ke da jan kwalla daga saman shi, kamshi na tashi daga jikin shi. Kallon mamaki yake min irin yadda na koma a lokaci daya na koma Bintu shiru shiru dani ban magana kamar ba nice ba. A hankali ya tako zuwa inda nake zaune saman kujera na takure kaina guri daya ina makure kamar mai jintsoro. Zama yayi daga gefen kujeran da nake zaune na dago ido in kallon shi a cikin mamaki don, bai taba zama haka a kusa dani ba. Yace, Fatima har yanzu baki sake jikin ki ba ko kin fi son ki tayarwa maman ki da hankalinta ne,? Na ce tare da girgiza kaina da,a,a, yace may yasa bazaki hakkura da ikon Allah ba Fatima. A hankali na sa gefen hannun na ta baya na,share fuskana yake tabayan kinci abinci kuwa? Kafin na bashi ansa sai muryan maryam tace maryam bata cin komai da koko sai dan ruwan liptop da take sha . Ya mike yana cewa kina,son ke ma ki kashe kanki ke nan kibi Kabir din ko ?. Yakareshe zancen tare da mikewa ya,bar dakin a lokacin don dama fita zaiyi. Na dan na dan fara sake jiki saboda irin matsin da suke min gaba dayan su a part din mu. Tun dai mama wani lokaci sai ta nuna min bacin ran ta karara a,fili nakan shiga taitayina na kama kaina. Gaba daya nakan ji komai bai min dadi nakaji zuciyar ta a bushe komai ban so ban ra,ayi ko kadan. Idan suna hira ko yar dariya sai naga basu damu ba ko don basu akaiwa mutuwar bace abin bai damay su ba hakanan kaman yadda yake damuna ako yaushe. Yadda Sadauki yake kokarin nuna min kulawan shi na yan uwantaka tankar ciki daya muka fito dashi. Shidai tausayi ma nake bashi yanzu don yasan mutuwa abune mai cin zuciya sosai kafin ya fita. Ina mamaki ni kaina yanzu ko bai ganni ba sai yace a kirani idan nazo zaice kinci abinci ko ? Nakan bashi amsa da eh ko a,a sai yace a dauko naci a gaban shi mama tana jin dadin yadda yake matukar nuna min kulawanshi sosai akan abinda ya samay ni. Da zai tafi sai da ya kara yi min nasiha sosai yace kuma idan yatafi yaji ance ina wani abinda bai dace ba zai zo da kan shi ya dauki mataki. Nace a hankali insha Allahu yaya bazanyi komai ba ai na hakkura insha Allahu. Yace da yafi maki don kin san halina dai zan iya maki abinda nace din. Da zai tafi hardani muka rakashi bakin motan da Bashar zaikaishi airport har ya zauna nakecewa a hankali yanzu Anty maryam shima yaya jirgin zai shiga ne ? May waccan take fadind wai ? Yana tambayan maryam. Dariya take tana fada masu abinda nace nikan fuskewa nayi kawai. Yace ko na fasa na shiga mota kada nima na mutu ko? Bashar yace Fatima ai da motan da jirgin ko basu idan kwanan mutum.ya kare mutuwa zaiyi. Sadauki yace kasan bakauya ce ta dauka jirgine kawai ke kashe mutane. Har motar ta daga yace ke zo nan . A hankali na isa inda yake zaune yace kin dai ji abinda na fada maki ko? Nace eh yace kwana nawa wani tsohon zai bullo maki idan kinyi hakkuri don haka bana son naji kin kara somay wa maji a daki kuma. Dariya akasa suka, wanda nima dariya abin ya bani har fararen hakorana suka dan fito yace to ke fa kullun kina cikin shawa mutane toka agida waike tsofo ya tafi ya barki. Suna bacewa, daga layin Bashar ya sauke ajiyan zuciya yace, wallahi tausayi yarinyar ke bani Allah. Yace akwai tausayi shiya nake kokarin gani she feel free don kada abin yai mata illa gata karamar yarinya. Amma gaskiya ya kamata fa asan abinyi anan man don wallahi ni dai ina maka kwadayin wanan yarinyar Allah ko. Kai Bassh kada kaja min raini please kaunata ce fa don Allah bari kada ta raina ni. May ye abin raini anan kuma aure ne fa kasan lokacin da zaka lume ciki kana I love you baby, I miss you, Wallahi kadai dan iska ne ga,wanan yar yarinyar bakauya zan tsaya ina wanan shirmayn haka sai kace wani soko can. Dariya Bashar yayi yace kanace wasa nake yi to gwada kagani in baka samu kan ka ga stage din nan ba. Jeka gwada kai da baka,san kunya ba yace nikan anan ban sani ba gaskiya sai ma ka dawo zaka gane ban sani ba ai don zaka samay ni dumu dumu wallahi. Agurin wanan yarinyar ko a ina ai ita takace da ka ganin gurin tunima, A wani gurin dai da nake shirin shiga very soon. Don akawar da zancen ya jefo mai zancen kasuwancin su da haka suka isa airport din. Sannu sannu na,fara sakewa na far normal life dina kaman yadda na,saba a baya, can. Sai kuma na dan fahinci ashe na dan saba da yaya sadauki kwana biyu ban sani ba. Sai yanzu da baya gari na fahinci muna kewan rashin shi agida abinda bantaba ji ba idan bai nan a rayuwana. Saidai nasan kila dan kulawan da yake bani ne kwana biyu yadan ja muna shakuwa tsakanin mu. ****** ********* ****** Bayan kaman wata uku da rasuwan Kabir ba laifi gaskiya don zuwa yanzu na dan sake sosai na rage yawan damuwan nan da nakeyi. Shima acan idan yai waya yakan ce abani mu gaisa kamar yadda yakan gaisa dasu Amirah. Sai dai ni ba wani dogon magana ne mukanyi dashi ba yakan dai tambaye ni yaya karatu ya kuma gida. Sai dai idan mun gama,waya kamar yadda nakan ji shima din haka yakanji a ranshi sai dai kosan mu yana daukan haka a zumunci ne kawai. Yadda bai taba jin yana sona ba nima haka kowan mu dai yana son dan uwa na yan uwantaka ne kawai ba wai wani so ba can. Yau saye nake cikin dogon riga din kin kasar Dubai da mayafin rigar ne na yafa a kaina ya dan rufe min har rabin fuskana kadan. Na samu mama a,falo nake gaishe ta, ganin yadda nai kwalliya haka yai yasa mama tambayana yau kuma,sai ina haka Fatima? Na ce cikin dan sakin fuska tau gani nan dai mama gidan su maman arkilla nake son zuwa nagaida ita. Cikin mama Maji take cewa yau din ashe hjy tayi sa,a yau ranan nata ne nace Anty maryam ki daure mu tafi please ? Tace na,fada maki ban zuwa gidan nan sai lokacin da zuwan yazo min a,rai zan tafi. Banyi fushi ba sai murmushin da nayi ina fadin ya kamata ace ki daure mu rafi tare yafi min zuwa ni kadai. Ranan da na tafi aini kadai na tafi kemay may kika hana kan ki rakani. Nima yau Allah ya ban sa,an ki sosai wallahi, haka naiwa su mama sallama na tafi gidan, Na dan dade a,saman titi kafin na,samu abin hawa sai ga wata,mota tazo wucewa tin daga nisa na gane cewa mace ce ke tuka motar a lokacin. Naso na,sheda su amma sai na,rasa gane a ina na,san su ne ma abin ya, shige min a,rai. Kwanan zuwa gidan mu suka nufa, suna shigewa ina samun mota na shige abina. Maman su Bashar tayi murna kwarai da,ta gannin don bata tsanmaci zuwana ba. Nace na shigo na gaida ita,na kuma yi mata kokarin da,tai min da,rasuwan Kabir di na. Da hanzari tace kai Fatima kin taba ganin don iyayye sun wa dan su abu yace yazo godiya, nakai wani dan lokaci tana ta m8n nasiha a cikin hiran na mu wanda shi yafi yawa. Nai mata sallama na kama hanyan sai gida ina,shiga na samu anyi dandali a tsakar gida. Nace wai yau sa idawannan kuma nan aka baje ne ina gaishe su na juya,sai cikin shiyan mu bankai ga shigewa ba naji ana fadin a haye duniya tai masu dadi an mutu anbar mata kaya sai shiga da fice takeyi a cikin su. Maji na ganina take cewa a,a shin har andawo ne wai yanzun fa kika fita Fatima. Murmushi nayi raina a bace mama tace may kuma akayine wai naga kin futa cikin dadin rai gashi kin dawo muna a murde kuma. Nace cikin hawaye mama kinji abinda umma take fada min wai duniya tai min zafi an mutu anbar min gadon kayan lefe sai yadda naga dama. Tace kai Fatima ki barta mana tunda ta zama tsohuwar banza kamar ki zata tsaya kuma ta yadawa magana haka? Ina ruwanta da ke da har wanan irin zancen zai rika shiga tsakanin ku da ita kuma? Amira dake fitowa tana ji tace halin su ne kawai na bakin ciki da hassada irin nasu, da yarta ce ai baka jin zamcen komai akan ta. Amma tunda zance ya kawo nan shine abin bakin ciki kuma, bamu san lokacin da yar iya tafita ba tana cewa to ai in wanan rigunan ne na jikin Bintu duk muna dashi harda Siyaman mummy a sayowa irin shi ba cikin kayan mamacin bane ta saka. Umma ta fahinci maganan Maryam daga inda suke zaune take cewa kai shi yaro idan baida kunya bai tsoron uban kowa walleh. Ku daiyi tayi ai anan zaku tsufa dakin uwar ku kuna taya ta kishi ko kare bai zuwa sunsuna inda kuke. Sai kyashi da hassada in kunga yan uwa sun samu sabbin samari idon ku na sama sai kun yi kitihin da kuka rabasu dasu. Yan banza masu abin fadi waike mara kunya kinzo mayar muna da martani ko ke da baki da kunya. Ni ko mashayin yayan ku bai isheni ba wallahi balle ke abin banza har gobe dai ba mai abin ashha kamar ku a gidan nan, mutane kawai marasa mutinci. Karan buga kofan shigowa gidan da,akayi da karfi shiya mayar da hankalin su gaba daya ga mai shigowa gidan. Wasu matane su uku tallabe da,wata yar yarinya dul jikin ta jini ne tako ina kaman an yaka rago cikin tashin hankali suke fadin ina mahaifiyar, Imirah gidan nan ? gaba daya hankalin kowa ya koma,gare su matar sai kuka take da yarinyar tallabe a hannun ta. Kafin wani yai maga saiga "yassanda mace ta shigo tana fadin waye uwar imiranah gidan nan? Da sauri maryam tace kufito ga yan sanda a gidan mu wai ana neman uwar imiranah. Hajiya kubura shigowan ta ke nan tun a kofan gida taga mutane dafifi take tambaya wani makwabcin su ke fada mata wai anzo kama Imiranah ne, Tana shigowa takai ido akan yarinyar dake kwance jina jina hannun iyayyen ta Tace innalillahi wa yai mata fyade kuka shigo muna da ita gida haka ne? Yar sandan tace wani a gidan nan something Imiranah ko waye shine wai tun da safe da yarinyar tafito tallan kunu ya jata yana lalata da ita shine yai mata wanan aikin haka. Salati muka saka gaba daya manya da yara umma ko duk karfin halinta yau sai gata tana kuka ta,shige daki. Hjy kubura itace ta kira Alhaji tazo gida ya iske wanan tashin hankalin mai muni a gidan shi. Ga matasan unguwa su yi dafifi a kofan gidan sunce sai an fito masu da Imirah ko su bankawa gida wuta don ya ishe su a cikin shiya da dannan masu yara. Ranan munga tashin hankali mugan fitina a filin Allah don ga matasa na bugun gida sai an fito masu dashi wallahi. Sai da Baba ya dawo shida kan shi yaba da umurnin a shigo a duba ko ina sako da lungun na gidan shi ko an boye shi idan za,a ganshi. Ashe yana daga bayan dakin maji yan sandan nashiga suna fita maji ta gan shi cikin dubara ta jefa mai hijjab ya sa yaboye fuskan shi ya zo shigowa dakin mu na ganshi zanyi magana maji tai min signal da ido nai shiru, batare da wani ya gan shi ba yashige ciki, Allah yasa wani ba wanda ya gane shi har yashige ciki, don anyi yawa sosai wani baigane wani a gidan saboda cika ga hijjib din babbane har kasa yake. Can ta kaishi ban dakin ta ta boyeshi ta dawo waje ana taneman duniya ba a gan shi ba a gidan. Akace tunda bai nan ya gudu sai dai a kama baban shi ko mahaifiyar shi, Nan wani sabon fitina ya tashi a lokacin ne maji taji kaman ta fito da Imiranah duk da tasan ranan matasa na iya kashe shi yadda suke wanan ihu da ashar akan afito da Imirana din. Baba yarinyar da akaiwa fyade yafara fadin idan na bari aka tafi da Alhaji ban kyauta mashi ba, irin yadda suke muna kokari a unguwan nan shi da dan shi Umar Faruk Sadauki. Bani ba duk wani magidanci a uguwa nan yasan irin mutuncin da sukewa mutane don haka ni ba Alhaji ko matar shi ce tai min laifi ba dan shi Imirana ne kuma shine nai kara gurin hukuma ya bata min yarinya. Mutanen gurin suka ce gaskiya kayi kokari kayi gaskiya a bari har aga shi macucin babu ruwan Alhaji don bai aike shi ba. Nan Baba yake cewa ya kamata a taimaki yarinyar a tafi da ita asibiti kada tazo ta mutu saboda jinnin dake mata zuba yai yawa sosai. Fita da yarinyar shine dalilin da yasa mutane suka,kwasa,aka fita daga gidan tare dasu Alhaji akatafi asibitin. Masu kuka nayi masu bata fuska nayi da yaudai kan yau ne don dara taci gida zancen kiran wasu yan iska ya kare a gidan nan don ashe kowa nada dan iska har da tantirai a dakin shi. Hjy Kubura ce take fadin haka yayin da take tafiya zuwa part din Alhaji ta nacewa yau yadda akai tonon asiri da fallasan da yakai wanan cin mutuncin da akai muna kato har cikin makewayin mu don wani katon mazinaci. Mu kan yau wallahi ancuce mu gidan nan wanan cin fuskan da may yai kama aiko munga iyakan iskanci a gidan nan . Umma na ciki tana jin ta amma ta kasa magana don yau baki ya mutu murus. Ga tashin hankali tasan yai Imirana sai Allah sai Allah Allah takeyi kada a ganshi a kashe shi. ****** ********* ****** Maji saida taga an watse ta shiga dakin ta ta bude bayi tace mai yafito yace cikin rawan murya wallahi maji idan nafito kashe ni zasuyi. Tace nace kafito muyi maga duk sun fita don ba waje zan fitar da kai ba ai. Yafito duk jikin shi rawa yakeyi ta zauna bakin gadon ta shikuma ya zube a kasa sharkaf ya dukar da kan shi kasa. Tace Alhaji karami yaya akayi kai wanan aika,aikan haka wa yar karamar yarinyar nan. Shiru yayi tace gaskiya baka kyautawa kan kaba kuma baka kyautawa iyayyen ka ba. Mutum yana barin abin fadi kodan bayan shi da mutuncin gidan su. Yace cikin sauke ajiyan zuciya wallahi maji sherin shedan ne kawai amma ayi hakkuri tace yanzu wanan abin ni ban san yadda za,ayi ba ma wallahi. Tace gashi dan uwanka baya gari shikuma Ahmad nasan kona fada mai kana nan zai iya fallasaka asani. Tace amma ka zauna anan har dare yayi mugani don kada ka fito ko fallo ne a san kana nan. Ta mike zata fita sai kuma ta juyo tana tambayan shi da cewa kaci abinci ma kuwa? Yace maji ban iya cin komai ma wallahi don gaba daya ban san yadda akayi nai wanan abin ba. Maji tace bari nazo sai tafita daga dakin muna falo tace Amirah hadowa yayan ki tea mai kauri ya sha. Da sauri suka juyo suna kallon ta da mamaki azaton su ko ta rude ne tace wa Amirah tashi mana ki hado mashi. Tace wani yayan mu Maji ? Tace Imiranah mana. Yana ina maji ke ban son tambayan tsiya kuma ku kama bakin ku wallahi. Baba basu dawo ba sai guraren sha dayan dare yazo ya shiga dayake girkin Hjy Kubura ne bai dade ba suka rufe kofa don cikin tashin hankali yake. A lokacin da mama taji sun rufe kofa tasaka hijjab dinta tafita sai dakin Umma. Umma na zaune a kasa sai waya take bugawa ko anga Imiranah wa yan uwanta cikin tashin hankali. Ganin maji a dakin ta ya ta dan daure fuska a zaton ta tazo mata jajen munafuci ne na kishiya. Sai da maji ta zauna take cewa yaya ya mukaji da hakkurin wanan tashin hankalin na yau. Tace ai bai kare ba tunda ban san inda ya shiga ba har yanzu, don ina tsoron kada mutane su ganshi su illanta min shi wallahi. Maji tace bazasu ganbshi ba ma ai don yanzun ma shiya kawo ni gurin ki. Ina son mu san yaya za,ayi mu fitar dashi daga gidan nan mu san ku ma maynene abin yi yanzu? Kina nufin yana gidan nan ko may Hauwa,u ? Maji tace yana gurina yaya shiyasa ma nazo yanzu don ban son ko Alhaji yasan yana nan. Wani irin ajiyan zuciya Ummata sauke tace yanzun yana inane wai ? Yana na dakina tunda rana nakaishi ciki lokacin da taron nan yai yawa mutanr basu gane ba na bashi hijjab ya shiga ciki. Umma da yaranta suka ce wai har sun danji sanyi wallahi . Yanzu yaya za,ayi Sagir ? Sagir yace wanan dai hijjab din zamu saka mai shine kawai za,a iya fita dashi daga gidan nan ko shi a cikin dubara don wallahi naga matasa a zaune kofa group group nasan ko shi suke jira ya dawo. Nan dai aka hada plain yadda za,a fitar dashi daga gidan muna zaune sai ga Umma da maji sun shigo dakin da yaya Sagir. Can mukaji sun fito mani tace Amirah ke da Fatima ku sako hijjab kuzo ku fita da yayan ku can gaba da layin nan Sagir zaizo ya dauke shi sai ku dawo. Haka akayi muka futa tare da munafuki, yana bin mu solai solai har muka wuce matasan nan sai hiran sukeyi suna cewa yau suna nan ba inda zasu sai yadawo don sun san idan dare yayi ai zai dawo gidan ne. Bamu dade tsaye ba saiga yaya Sagir da mashin yazo ya dauke shi yaciro muna hijjab din maji muka dawo mata dashi. Garin aka bari dashi zuwa wani kauye da yan uwan su suke can. Muna shigowa still su Umma na dakin da mama da sauri suke tambayan mu sun tafi mukace eh ya dauke shi sun tafi, Tace cikin ajiyan zuciya wai Alhamdullahi yanzu dai sai asan abinyi don Alhaji ya hau sosai wallahi. Duk abinda ke nan abari da safe sai a san abida ya dace ayi. Suka fita daga dakin tsomai tsomai dasu cikin tashin hankali nan akaje aka rufe gida. Haka yasa mutanen dake dakon shi suka fara watsewa daya bayan daya daga zaman jiran shi da,sukeyi. Washegari haka muka,wayi gari da yansanda sun dawo kara tambaya still sai da suka kars search din gidan ko yana ciki. Ganin bsina suka wuce suna fadin da zaran angashi a hanzarta kai shi ga hukuma kafin su dauki mataki amma dole Alhaji ya tafi ya saka hannu a furin su. Ranan kan anga tashin hankali don Baba ya ce sai Umma ta bar maigida ta nemo danta in ba haka ba zai dauki mataki a kanta. Umma kuka ranan yaranta kuka cikin tashin hankali duk gida ya rude da kuka. Sun matukar ba mutane tausayi sosai ga irin yadda Baba yai mata kaca kaca a tsakar gida. Ganin haka yasa maji takira sadauki a waya yana dauka yake cewa maji yanzu nake batun kiran ki ai. Na kira Baba wayan shi bata shiga lafiya dai yake ko don hankalina ya tashi sosai. Babana kabar duk abinda kakeyi kazo gida akwai matsala babba ya taso a gida jiya. Maji may yafaru da Baba ? Tace ba Alhaji bane yayanka Imirana ne kaddara ta hau kan shi yaiwa wata yarinya karama fyade abin ba kyau wallahi. Salati ya saka yace yanzu Imiranah yana ina maji? Tace yana can anboye shi nan dai ta dan bashi bayani a takaice ta dora da fadin nasan Alhaji zai dauki mataki mai zafine akan shi yadda ya hasala din nan. Yace to gani nan zuwa maji zan taso yau insha Allahu. Sadauki bai shigo ba sai guraren shidda na yamma ya iso garin shida Bashar suka zo gida. Ina daga ciki mukaji muryan shi ana gaidashi shine muma muka fito don gaidashi da dawowa. Hankalinshi a tashe yake sai fada yake akan abinda Imirah yaja masu a gari. Bashar yace yanzu mataki guda ne mu ganshi muje dashi gurin yan sanda asan abinda za,ai mai sai kuma muga iyayyen yarinyar mu basu hakkuri haka zai kawo dan sauki abin. Yaya abinci fa inji maryam ? Yace maryam bari kawai mu fita mu san yadda za,ayi wanan al,amarin. Gurin Umma ya shiga yace ina Sagir tace yafita yace Imirah din yana ina ne yanzu? Tace yana bodinga gidan yaya hassan tun shekaran jiya da dare. Daga haka suka fita duk ta ramay tafada kamar tai ciwon shekara daya. Basu tsaya ba sai gatin BODIGA can gidan yayan Umma sun samay shi ya ramay ya koma wani iri dashi. Sunyi masu bayani kamar yadda suka tsara da farkon maganan duk da haushin dan uwan da yake ji amma ya matukar bashi tausayi sosai daya gan shi. Gidan mahaifin yarinyar da abin ya sama suka fara zuwa tare da dattijan da suka dauko daga unguwan. Nan dai aka,shawo kan mutumin sani Allah sani manzo har ya hakkura suka basu kudi har dubu dari uku wai aiwa yarinyar magani dashi tare da biyan kudin maganin da akai mata asibiti. Nan kuma aka dunguma sai gurin yan sanda suma a kai rana dasu don sunce dole sai sun kuleshi har hukumar dake da Alhakin wanan shatian suzo. Haka yasa aka nemo masu alhakin irin wanan matsalan suka zo suma saida aka shafa masu nasu rabon aka kashe case din sai dai anci kudi sosai wallahi. Daga can suka kwaso zuwa gida gurin mahaifin su yana falon shi akace ana mashi sallama. Yana fitowa yaga su sadauki da wasu dattijan shiyan ya juta zai koma aka dinga bashi hakkuri akan ya dauki al,amatin a matsayin kaddaran rayuwan yaron ne. Yace aiba yaune yafara haka ba kungan shinan shedanin yaro ne don har wata yarinya ya taba yiwa ciki yanzun haka dan zaman shi yakeyi. Yaro yace ya zauna bai mayar da zina bakin komai ba. Yace yabasu su uku nan da wata uku ko mutum bai shirya ba sai yai mashi aure da kan shi. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,, IDAN KIN TURA WANDA BAI BIYA,BA BA MU YAFE MAKI BA ALLAH YA ISAN MUNA AKAN KI,,,,,,, Sadauki bai koma ba sai dai yayi duk yadda malamin nan ya umurce shi da yi a baya. Ya kama hanya yatafi an muna E,passport na batayi tare da duk wani clearing din da ya dace aiwa masu tafiya. Na kira kabir nai mashi albishir kamar yadda ya dace nan fada mai don ya,sani . Sai na fahinci bai yi farin ciki ba da hakan take naji raina ya naci nace, amma ka bani mamaki yayana da zakaji alheri haka ya samay ni ka kasa tayani farin ciki. Yace umma gaskiya Fatima ban iya munafunci ba don haka idan nace maki nayi farin ciki to na munafunce ki giskiya. Cikin mamaki nace Yaya Kabir lafiya kake kuwa ? Yace lafiya ta kalau Fatima , Wanda dai ya kaiki saudiyane ban yi naam dashi ba gaskiya. Kana nufin wai yaya sadauki ke nan?. Yace shi nake nufi Fatima ya,fadi a takaice kawai ba shakkan komai Yace ina matukar kishin zaman ki da yaron nan gida guda Fatima, a duk lokacin da na tuna cewa a guri daya kuke sai naji banjin dadi wallahi. Don ni mutum ne mai matukar kishin iyalin shi sosai ina kokarin ganin matata bata mu,amula da wasu maza koda yan uwanta ne ko nawa. Nace amma dai kasan ni ba,watsa,tsa bace haka shima wanda kace baka kauna din ba dan iska bane hakana. No Fatima baki fahinci magana ta bane don haka mubar zancen haka nan Allah ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya ba shike nan ba. Nai fushi na kashe wayan ba yadda na,saba yi mashi shagwaba ba idan zan kashe wayan. Ni kadai maganan tai ta cina a,rai har na gaji na sake don kaina. Nai fushi da yaya Kabir da kyat ya shawo kaina muka shirya dashi yana ta kamay kamay, wai shi ba wani abu yake nufi ba, Hakalin shi, bai kwanta bane don kada yaya sadauki ya kwace mashi ni yahana ya aure ni ace yar gida gida za,ayi. Jin maganan nayi cikin haushi da takaici, don may zai hada ni da yaya sadauki mutumin da yake a matsayin yayana yake a gareni. Nan na nuna mashi ban ji dadin yadda yake min ba a matsayin yaya fa,sadauki yake gareni. Amma shine zai ce, wai sadauki na iya kwaceni daga gareshi, ya aureni wanan maganan tai min zafi yadai bani hakkuri aka zauna lafiya. Munsha magana gurin mutanen gidan mu da,ma,wasu yan sa ido akan zancen tafiyan mu, ****** ********* ****** Mun isa kasa mai tsarki, saukan asuba mukayi a garin kafin agama muna screening har anyi kiran sallah asuba ko. Wasu motoci muka samu suna jiran mu su suka kwashe mu sai masaukin mu a cikin garin madina. Bamu dauki tsawon lokaci ba muka fita zuwa masallaci don muyi sallah da ziyara kamar yadda yazo ga sunah. Ibada muke sosai ba kama hannun yaro daga mu har uwar mu da yayan mu sai yaya,Bashar da muka zo dashi. Aiki tukuru komai bamu da matsalan shi sai mura da ya kama mu kawai a garin don sanyin Ac da ruwan sanyi da yai muna yawa. Yaya ke sayo muna duk wani abinda zamu bukata sai ya tambaye mu ko may zamuci daga haka har ya gane favorite abincin da kowan mu ke so. Kwanan mu tara a na goma muka kama hanya sai garin makka nan ma mun samu anyi muna masauki inda zamu sauka . Bamu kwana ba sai da muka je mukai dawafi a can muka kwana sai safe muka dawo masaukin mu. Barcin gajiya mukayi bayan munyi wanka muka kwanta, mun tashi mun samu har mama ta farka tana zaune tana waya a gida. Zaune muke a falon dagani sai ita su Amirah ana can an baje ana barci a cikin A,C. Bashar da yaya sadaukine suka shigo dauke da abincin rana da zamuci. Ganin da sukai min zaune a kasa gap da kafan mama nake zaune kamar wace zata koma ciki . Fatima ke har k8n farka ke nab baki gajiya dai, mama ta karbe da cewa ai kai dai Bashar wanan yarinyar har mamaki takw bani karama da ita amma yawan ibadan ta kamar wata babban mace can wallahi. Daga inda yake zama idon shi ya na a kaina yake cewa, addu,a takeyi wa mijinta kila ko kuma maman ta. Ai na gode da Allah ya ban diya irin Fatima mai ibada ga sanin ya kama ta a tare da ita ko yaushe. Kai maji kina da fasawa wanan yar kauyen yar taki kai koda yake yanzu naga,ta fara wayewa,ai don ina Allah Allah kada,tai muna,kauyancin ta, ta,bayar damu a cikin mutane muji kunya. Nace cikin dan jin nauyi da kunya kai haba yaya wai kai kullun dai a bakauya nake a idon ka ne? Kyaleshi Fatima ba abinda zai gwada maki yanzu na wayewa jirgine dai kin haushi don kin gama sanin komai. Kai mama don Allah bari kada ta dauka ko jirgi shine karshen kauyanci a duniya. Kada fa ka,zabo matar da tafi Fatima zama yar kauye muga tsiya wallahi don dai yanzu kasan Fatima ko kai sai kayi da gaske zaka gwada mata wayewa. Aiko cikin auri yace don Allah MAN ka bari ka fa san a kasa mai tsarki muke kada yan amin su karba muna. Nan suka dinga mashi sheri suna ta dariya yace aiko da na karkarya yar kauyen banza da duka. Dariya nima na kama nace ni yanzu yaya idan ,al,amarinka ne bana jin haushi balle nayi kuka akan zancen ka. Da can bayane da ban san halinka ba nake kuka yanzu ko kin waye ko? Ya tambaya cikin son jin amsata daga bakina amma sai nai shiru don maji tace na kyale shi duk abinda zai fadi na dai fishi ne yasa yake jin haushi na kawai. Bai da rowa ko kadan sai da,wanan tafiyan ya hada mu na tabbatar da hakan don duk abin da kannen shi sukace suna so shi zai masu ko nawane. Munyi ibada munyi rokon Allah sosai ba dare ba rana muka kammala aikin mu muka fara shirin dawowa gida. Naiwa iyayyena da yan uwana tsaraba haka naiwa Kabir shima nashi kalar tsaraban da ya dace da shi. Munyi mamakin dawowan mu, gida muka samu an gyara ma mama part din ta gyara sosai na gaske akai mata na zamani mai kyau,. Tafita daban daga sauran part din matan gidan an sauya mata komai nata ya koma side din ta daban yake a cikin sauran sai dai still a gida guda ake kuma farfajiya guda. Mun shiga gida mun zama wasu abin sha,awa gurin mutanen gida sai sabon hassada ya kunno kai kuma. Kishi kumallon mata nan zance yafara yaduwa cewa ba kudin halas bane shine muke tin kahon mun tafi saudiya wa mutane. Wasu su, ce ai shi kan shi sadauki baya taimakon kowa,sai uwarshi da yan uwan shi ya sani kawai. Sun manta duk irin taimakon da yake masu a cikin gida yanzu komai shine yake kawowa ayi amfani dashi a gidan don yanzu Baba yai sanyi sosai ga arzikin shi. Ya rage saura wata biyu kacal buki na da Kabir, don haka bayan mun dawo su Baba sun shigo taron mu shida mama tabawa da wata kawar ta da tazo gulmq taga inda nake. Nan Baba Alhaji yake bawa babana shawara kan kada ya tayar da hankalin shi akan zancen aurena. Duk wani abinda za,ayi agurin bukin shi zai dauki nauyin yi da shi da matar shi Maji. Baba na yace amma Alhaji auren ta na farko ke nan ya kamata ace a dan bari nima na taima a wani gurin inda ya dace dani na kauye. Babu komai ai duk yiwa kaine don Fatima ta cancanci ai mata komai a rayuwa ai. Sun dan yini muna sukai sallama na basu tsaraban su suka kama hanya sai gida suka koma, inda nace masu zan shigo karshen wata don nazo naga mahaifiyata . A bangaren Kabir kuwa ji yake tankar ya lashe ni don irin so da kaunan da yake nuna min abi yai yawa sosai. Duk da lokacin ya matso sosai amma shi gurin shi shine yadai ga an daura muna aure ace ni mallakinsa ce. Sai kuma gashi ya dan bijiro da wani zance, wai yana son a dan kara matso da bukin don yana son zuwa wani course a lagos na wata daya. Da zancen yazo wa Maji sai cewa tayi ace yayi hakkuri tunda an fadawa kowa sai wanan lokacin za,ayi bukin. Da kyay dai na samu na shawo kan shi ya hakkura sai lokacin za,a daura aure daga baya sai na tare idan ya dawo. Maryam itace ke shirya komai a kan sha anin bukin sai dariya mama da Amira suke muna. Shiko yaya,sadauki yabi ya koma wani silent dashi koda yaushe fuskan shi a daure take bai wani walwala, Shi kan shi din ma ba zai iya cewa ga matsalan shi kawai dai haka yake jin jikin shi ba dadi. Haka ya daure yana yan al,amururinshi cikin rashin kuzari da walwala a tare dashi. Kumshi da kitso da gyaran jiki duk su akai min zan fara zuwa na hadu da Kabir da,zai shigo inga mahaifiyana sai na,dawo sokoto sai gobe daurin auren mu zai dawo garin don suna,aiyuka yanzu sosai. A gidan mahaifiya na ya iso da yamma na fito na sanay shi yana tsaye jikin motar shi nafito daga cikin gidan namu. Murmushi a fuskan shi har na karaso gare shi yake cewa kai Fatima kinga yadda kika koma kuwa tun auren bai karaso ba kin koma haka? May mamatake baki haka ne wai ? Murmushi nayi kawai , Yace ban yarda ba don dai kawai baki son nima abani na koma hakane kamar yadda kika koma din. Yace ya naga fusksn ki yau duk kwalliyan da kikayi amma babu walwala sosai. Nace cikun dan yake wallahi kaina ne ke min ciwo sai faduwan gaba dake yawan damuna duk kwanakin nan. Ya kara dan matsowa gap dani yace shine baki fada min ba ? Kuma tun yaushe kike jin hakanne wai? Na lumshe idanuwana nace tun kan nazo ne nake fama da hakan. Yace da kinga likita tun acan Fatima, don asan abinda ke damun ki don kin ga nan kauye ne. Wani irin kamshin turaren shi ne ya daki hanci na,wanda har na dan sauke ajiyan zuciyar da ya baiyyana a fili, saboda matsowan da yayi gap dani a lokacin. Yace ko mu tafi ne ki ga likita sai mu dawo ? Na bude fararen idanuwana ce na samu sauki ai ba matsala. Yace da gaske kinji sauki kodai baki son zuwa ne likita ya duba min ke ? Na girgiza masa kai nace ba hakana bane kawai dai ba,wai sai naga likita bane. Yace toh bari na bude maki mota ki zauna a ciki don kada tsayin ya damay ki ko? Ya bude motan na shiga dayan bangaren na zauna, sai ya rufo min kofan, Shima yya zagaya ya shiga ya zauna daga dayan bangaren . Wani irin sanyi ne da kamshin motan ya ziyarce hanci na dana zauna a motan Take naji wani irin kasala ya dan fara rufeni a hankali, nan muka danyi hiran mu dashi a,tsatsaye don na matsu na koma gida na kwanta. Waya ce aka bugo mai a yadda na fahinta daga ma,aikatan su ne suke magana dashi kan ana neman shi a gurin aiki. Bayan ya gama wayan ya kashe ya ja tsuki yake cewa kai baz,a bar mutum ya huta ba da amaryan shi. Yanzun kuma wai aiki zamu tafi a wani kasan shine ake neman mu. Murmushi nayi nace ai neman halak ne don haka muna son aiki ko yaushe tafi zaman jiran tsanmani. Yani sa yace wallahi haka kawai sai nake ji kamar nace na fasa don ban son rabuwa dake ko kadan Fatima. Nace cijin yar murya har kwana nawa ya rage ka mallake ni a gidan ka idan kayi hakkuri. Ya shafo fuskan shi yana cewa hakane kuma fa gaskiya dai sai naga ni lokacin ma yai min tsawo sosai. Abinda bsi taba min ba shine yau yai min don kamo hannu na yayi ya hada da nashi ya matse guri guda ba,tare da ysi min magana ba na,wani dan lokaci mai tsawo. Cikin yar siririyar murya nace mai sakeni yaya don har yanzu fa ka san,akwai sauran lokacin hakan gare mu. Yace cikin murya mai kasala hakane Fatima yanzun dai ina son idan kin koma saiki fadawa maryam duk wani abinda ya dace ku shirya shi da,wuri don da an daura aure abuja zamu wuce acan zaki sha amarcinki. Kunya maganan shi ta bani da sauri na bude kofan motan kafana daya a waje nace maganan ka tana sani jin nauyi da kunya wallahi. Yace nima haka ya dan kwaikwaye ni. Mukai sallama dashi tinda safe ya kama hanya sai Abuja don aikin su ba hutu. Sai da na kara kwana biyu a gurin mamana nazo gurin Baba na nai kwana daya na dawo sokoto da zama. ****** ********* ****** Mamana ta sokoto cikin gyarana take sosai abubuwa take bani na kara lafiya da gyaran jikin na. Nai kyau nasha gyara sosai na canza gaba daya duk wanda ya ganni sai yai maganan hakan. Amma har lokacin banjin dadi a cikin raina nasan cewa jimamayn rabuwa da su mamane yake damuna a zuciyana. Don in suna min sheri sai naji kamar nai kuka ban son zolayan da,suke min na amarya ta angi yar shagali yar biyan bukata yar garali. Amirah tace makullin mota ke akaba, wani sauran canji ke akaba, nikanji wani iri a raina sosai. Ko yaushe Kabir muna waya dashi yake ce min zasu tafi kasan Benin wani taro na kasa da kasa. Cikin dare yaya,sadauki ya dira a sokoto sai ganin shi mukayi kwatsam. Murnan ganin shi kamar kullun yan uwan shi da mahaifiyan shi sukayi nima dai nai farin ciki da ganin shi don ban boye ba sai dana baiyyana a fili. Ranan har ina mashi tayin abinci sai lokaci ya,dago yana kallona gaba daya sadauki yaga na sake mai . Da sauri ya kawar da idanuwan shi daga kallona na kara tambaysn shi da cewa. Yaya a kawo maka abinci ne kaci? Yace au yau kuma duk murnan za,a gidan tsoho ne yasaka ake min tayin abinci haka? Kasan fa amarya ce dole abita sannu yaya duk cikin murna ne hakan ai. Na bata fuska na dan marairaice nace haba Anty Amirah sai ana maganan gaskiya kuma ki jefo wani zance can na fadi cikin shagwaba. Yaushe rabo da kiba yayan mu abinci Bintu ? Nace kai anty Amirah nifa yayanane yadda kike son shi haka nake son shi don haka kada ki bata ni gurin yayan mu ko yayana ? See her bakiji kunya ba ni wai maji yar taki duk murnan auren ne yau take cewa nima yayan ta ne? Yaya ni kima yar kaunar taka har zakai shakkan haka a gareni nifa yanzu banda kaman ka a duniya don ku ne uwata da ubana. Murmushi yayi ciki ciki, yace to kawo min abincin na wuce ina yar dariyan jin dadin mun shirya da yayan mu yau. Nakawo mai abinci na aje nace ko na karo ne yaya ? Yace kai Maji wanan yarinyar taki fa ta rainani da yawa may kika mayar danine wai ? Yaya nace a taikace. Na dora da fadin wanda yafi min komai a duniya . Yace har da dan tsohon mijin ki ke nan? Nace ai shi mijine kai ko dan uwa rabin jiki. Sosai yaji dadin zance na har cikin ranshi yake cewa a rayuwan shi ashe haka yarinyan nan take sauki kai ne da ita haka, ninr dai ban fahince ta ba ashe? Waya da Kabir ya bugo min ne ya dakatar dani nabar gurin zan wuce niji yana fadin tsoho yai kira ke nan ? Na dauki lokaci muna waya dashi sannan na fito falon na samu yana cin abinci suna fira da mahaifiyar shi. Yana fada mata cewa maji mutumin nan fa abin tsoro ne wallahi sosai don yanzu. Daniel bai yarda ko mu hada hanya dashi duk yadda muke da yawa a guri zakiga ya koma gefe daya. Nace mugu ke nan dan ban Allah yafishi wallahi don ba abinda zasu iya dakai don kai daga Allah kake. Dariya sukayi nace wallahi anty na rasa may yasa mutane suke yawan saka ma yaya wanan irin kiyayyan haka. Maji tace hassadane kawai Fatima kin san in Allah ya haska mutum dole dama sai ya samu wanan kalubalin daga mahassada. Mukan Allah ya kara tsare muna kai a duk inda kake yaya sai kuma addu,a don Allah akara zagewa don makamin mumunine. Yau kan ni naga yar taki ta canza fa. Dama haka take kaine dai baka gane ba kana ganin tana maka kokari kaiko kana ganin kamar sa idone. Ya ce na sani maji. Ta faye kauyancine shiyasa nake sake mata layi. Bintu Kabir har yanzu bai dawo bane daga Benin din ? Nace yace ysu da dare zasu sauka a lagos sai gobe zai karaso abuja zuwa jibi ya iso nan. Ku dinga sa insha Allahu mana a zancen ku Fatima inji maji. Nace insha Allahu mama,, Kokefa to kuna magana kamar ba musulmai ba. Ita fa maryam ta matsu Kabir yazo ta amshi dumus don zancen ta na kudine kawai. Ya mike yana cewa zai shiga yai wanka yaje gun Bashar don yana son ganin shi. Munyi hira sosai da daren kafin mu kwata bayan nai wanka nai shirin kwanciya saiga wayan kabir yana fada min suna lagos yanzun suka sauka da safe zai karasa gida. Mundan jima muna fira sai na kwanta da farinciki a raina. Mafarkin danayine yasa na tashi ina sallah kafin ai kiran sallah tare da rokon Allah sauki koma maye. Da safe na dan makara nai sallah nai wanka a gaban mirro na kalli irin yadda nasha gyara na canza gaba daya kamar bani bace Bintu. Wayan Kabir ne ya shigo yana fada min zasu wuce zuwa Abuja nai mashi Allah ya kai su lafiya nan ma sai da ya dan taba min yan maganganun soyayya sosai mukai sallama dashi. Ga abin karyawa a gaba sai hira su Amirah keyi amma na kasaci a lokacin. Mama tace badai auren ne ya saki tunane ba har kike kallon abinci haka a gaban ki. Nai murmushi nace kai haba mama aure kuma bayan gaki ? Tace gani ina gadai Kabir dinki ko ? Amirah tace da ciwon kanki ba inji mama Sare da tace haka ranan. Nace ni ai basu gabana Anty don duk fitanan matar shi bai taba daga min hankali ba ni. Hajiya Kubura ta shigo da manyan ledoji guda uku nan muka shiga gaida ita. Tace hjy maijidda ni dai ga dan nawa gudun mawar ba yawa sai ayi hakkuri dashi. Kai hjy harda dawi niya haka takarba tana budewa ledan farko kuloline set har da flask din su sai dayan ledan turaren wutane masu kyau da kamshi sosai. Dayan kuma kayan matane aka hada masu tsadan gaske a cikin wasu robobi masu kyau. Godiya sosai mama tai mata su ka dan taba hira kan bukin tana cewa insha Allahu da ita za,a tafi kauyen mu gurin daurin aure. Mama tai mata godiya tace kai haba ai shine zama tare din. Wayasan inda zaici albarkacin yaro shima watarana Bintu ai mutum ce sosai wallahi. Zata fita suka hade da saudauki dake shigowa a lokacin nan suka gausa dashi tafice daga falon. Yai zaune ragwab saman kujera fuskan shi babu annuri acikin sa sai mama ke cewa may kuma yafaru nagan ka haka ? Yace wallahi maji yanzun nake jin news wai Jirgi yai accident daga lagos zuwa Abuja da safen nan kuma akwai wani abokina da zai zo Abuja yau nasan yana cikin jirgin. Da karfi nace Kabir,,, Nace wayyo Allah na mama wallahi da Kabir a cikin jirgin nan dazun yai min waya gashi zai shiga jirgi zuwa Abuja. Daga haka kuma ban san may yafaruba again ? Ganin na tafii suuu, zan fadi yashi tsale daya yakamoni na fada a jikin shi suuu a somay. Innalillahi don Allah ku taimaka min kubani ruwa mamatake fadin hakana a gigice cikin rudewa. Su Amira duk sun rude suma tana cewa a bincika mana aji idan dashi a cikin jirgin ko ? Ke debo muna ruwa a fridge don Allah kin tsaya kina surutun tsiya sadauki ke fadin haka cikin tsawa wa Amirah. Ana yayyafa min ruwa nai ajiyanzuciya na bude idona da sauri na zabura daga jikin shi nace mama da gaske Kabir ko ? Tace dagata a bincika inyana cikin jirgin dauko wayanta mu kira shi mugani? Anyi kira wayan wai yana kashe. Kara komawa nayi suuu na sumay a jikin shi yace kama nin ita ina zuwa don Allah. Maji ta karbeni daga jikin shi tace kiramin hjy Kubura maryam. Sai gasu tare a gigice tana fadin may ya faru maji take fada mata a takaice abinda ya faru. Salati ta cika tace sai Allah idan bai ciki wallahi ku kunna Tv mugani don Allah. Suna kunnawa ga jirgin annuno inda yafadi a wani daji ga yan ceto suna ta faman kawo agaji ga jirgin. Sadauki ya shigo dakin yace bari mu kaita asibiti maji tace gaskiya kan. Ita da hjy kubura sukazo dani asibiti nan likita yace bari a dan min allura na samu barci a gani. Hankalin kowa a tashe yake don har Alhaji yazo asibitin da wayana sukai amfani gurin kiran matanshi dana rubutawa yaya babba. Wayan na rigin ba,a dauka ba sai gap da zai tsinke ne wani dan yaro ya dauka yana fadin. Maman bata nan yanzu akazo aka kwashe wai baban mu yayi hatsarin jirgi sun mutu. Salati suka saka daga inda yake yakai kallon shi gareni ina kwance sharkaf kamar gawa sai numfashin da nakeyi kawai a lokacin. Sadauki ne ya fara ganin sunayen wa yanda ke cikin jirgin sunan Kabir ne na ashirin da biyar daga jerin sunayen list din wa yanda abin ya faru dasu. Kuma babu wanda ya tsira daga jirgin duk wanda ke ciki ya mutu a jirgin. Ban falka ba sai da la,asar na dan bude idona a hankali nake bin dakin da kallo sai dai ban fahinci inda nake ba sai muryan mama naji tana fadin. Fatima kin tashi ne sai abinda ya faru ya fara dawo min arai a hankali wasu hawaye suka fara dan silalo min a hankali daga idona. Dafani mama tayi tana fadin Fatima kiyi hakkuri kinji duk mairai mamaci duk wanda lokacin shi yayi tafiya zaiyi. Allah baiyi Kabir mijin ki bane, sai kiyi hakkuri kibarwa Allah . Allah da ya halicce shi yafi mu son shi ya karbi abinshi a lokacin da yaso. Nace a hankali cikin wani murya mai ban tausayi ,mama Kabir ya mutu ko ? Tace Fatima sai dai hakkuri Kabir yariga mu gidan gaskiya. A hankali na fara rera kuka mama tana dan buga min baya tana fadin kiyi hakkuri kin ji Fatima. Shi yanzu adduan mu yafiso da wanan kukan da kikeyi. Kubarta tayi kukan don shine zai dan sa ta samu relief. Nai kuka sosai na wani lokaci can na mike zaune da sauri suke fadin ina zaki kuma,? Nace sallah zanyi mama naga kamar azahar tayi mamatace sai dai la,asar yanzu kan don har munyi sallah mu. Bayan nayi sallah na zauna gurin ina addua sai kuma na barke da wani irin kuka gwanin ban tausayi dani. Kiyi hakkuri suke ta fada min shigowan babane yana fadin ashe ta falka Fatima sannu kinji. Kiyi hakkuri haka Allah ya nufa dake kada ki kara wanan rudewa ki zama musulma mai imani da duk irin kaddaran da Allah ya kawo maki a rayuwan ki. Mama taso a sallamay ni amma sai Baba da sadauki sukace abarni harda safe aga yadda jikin nawa yake sai a sallamay ni. Washegari ganin na samu sauki sosai sai dai ban magana da kowa don wani iri nake ji kamar zan shude. Mun dawo gida inajin ana fadin wai ance a garinsu za ai sadakan ukun shi. Baba ya shirya tafiya inda zamu ai sadakan uku damu inji Baba. Haka yasa sadauki ya shiya don tafiyan yaso zuwa gurin mutuwan abokin shi duk daba musulmi bane amma saboda tafiyan mu yace sai an dawo ya wuce. Motoci uku muka kama hanya dashi har da hajiya kubura da mama Asiya umma tace wai bata jin dadin jikin ta suka barta gida. Muna isa tun daga nesa muka hango taron mutane a kofan gidan su Kabir, din haka ya kara sani sabon kuka sosai da kyat mama ta samu nai shiru suna min fadan na natsu na daina kuka. Muna fitowa idanuwan mutane caaa akan mu nan aka fara fadin Allah sarki ga su Bintu nan sun iso Nan kowa ya fara fadin Allahu akbar Allah bai nufi a zarga aure a tsakanin su ba haka ya kasance. Sai gaisuwa ake muna nan muka shiga cikin gida a dakin mahaifiyan shi muka shiga. Mutane sukayo caaa zuwa dakin don ganina ina saye da hijjab amma duk da haka mutum zai iya gani kwaliyan amarcin da akai min a jikina. Mahaifiyan shi kamilar dattijuwa tana zaune da tasbaha a hannun ta mu kai mata gaisuwa ni dai ban iya magana ba don kukan da yaci karfina a lokacin. Tace Fatima haka Allah ya nufa tsakanin ki da yaron nan Allah bai nufi akwai zaman aure a tsakanin ku ba. Nan kuka na ya fito fili mutanen dakin suna fadin kiyi hakkuri kinji Allah yabaki wani wanda yafishi. Sai naji an rikoni tabaya ana kuka Fatima Kabir ya tafi ya barmu Fatima. Kabir ya tafi yana mutuwan son ki a ranshi kullun yana min nasiha akan narike ki amana idan kinshigo mu zauna lafiya amma Allah bai nufa ba Fatima. Sai muka sa kuka nida ita duk da ban dago naga fuskanta ba. Hakkuri aje tabamu ana muna nasiha sosai mai kashe jiki. Nan mukejin ana fafin wai shi ko gawan shi ba,a gani ba sai alkur,anin shi da tasbaha da agogon hannun shi. Nace Kabir Allah ubangiji ya karbi bakuncin ka. Kowa ce Amin Bintu kiyi hakkuri kinji haka Allah ya nufa daku. Can wata tace zoku gausa da dayar matar tashi gata can dayan dakin da yan uwanta. Ni dasu mama muka shiga dakin mun samay ta tana waya muna gaida ita bata gaisa ba. Sai mutanen dakin ne suka gaisa damu watake cewa wanan ce dama yarinyar da zai aura din ? Wace ta rakomu dakin tace itace Wallahi, Allah baiyi aure a tsakani ba. Mukan ai sheri aka kwaxo muna farar kafa yaja muna hasara. Kai amma kuwa bakiyi ba wallahi gaki dai kamar mai ilimi saidai ashe baki da tauhidi? Hajiya kubura ce taba ta amsa da hakan. Tace banda tauhidi aiku kuna dashi aja muna tsiya ace kada mu fadi. Kika dai jawa kanki ke da kishi har akan mamaci inji mama Asiya ta karbe. Kamata yayi asamay ki cikin jimamay ba cikin kishi ba haka kamar ba wace tai rashi haka ba. Ku tashi mutafi mu gausuwa mukazo maku ba tsiya yakawo mu ba nan. Mun fita muna jin su suna zage zage nace a raina ai in sakwatawa kuke kun hadu da mama da hjya kubura a raina. Bamu dadeba su baba sukace mu fito nan maji ke fadawa mahaifiyar shi cewa za a aiko da kayan lefen da yai min. Ko yanzu don anzo gaisuwane yasa ba,a zo dashi ba. Matan sukace haba haba habadai da zafi haka. Sai mahaifiyar shi tace wanan ai kyautane tsakanin ta dashi tun yana da rai don haka mun yafe mata ba namu bane rabontane daga gare shi. Allah ya bata miji nagari idan antashi auren ta a fada muna kada zumunci ya yanke. Uwargidan Kabir da zamu tafi tayi kuka sosai muka rike juna tana min addua tace zata dinga bugo min waya. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,, . YA ALLAH DUK WACE TA TURA MIN NOVEL GA,WANDA BAI BIYA BA ALLAH KAI MIN BAKAR ISA AKAN MAISHI YA ALLAH DAMU DA WANDA DUK YA KARANTA A SANADIN TA,,,, A yammacin da aka,sallamo sadauki baba ya tara duk ilahirin iyalin shi a falon shi yana masu magana a cikin takaici da bakin ciki. Ku san Nafisa ce ta karshen shigowa falon tana saye cikin wani dogon riga da yai matukar matse mata jikin ta sosai. Baba ya bita da kallo na tsana da yakaici yace cikin bacin rai ke ina hijjab dinki zaki shigowa mutane kusan tsirara haka. Tace cikin wani bakon murya mai baiyyana wani sabon al,amari a gareta, Baba,,, nifa ba tsi, tsira rarra nake ba don a saye nake da, da da riga a jikina. Ido ya kura mata cikin nazarin ta yace Nafisa kanki daya kuwa yau din nan? Warassss nake Baba may ka gani kafin yai magana Umma take cewa daga barci take fa take wanan ita shegen haka. Yace maza jiki sako hijjab dinki na baki minti uku ki dawo nan mara mutunci kawai. Ya juya gurin Umma yana fadin Atika ina son idan ina magana da yara na ki daina saka bakin ki daga yau. Ki bari idan na sako sunan ki a ciki ki saka bakin ki, idan kuma kinga kamar fadi nayi kawai to kici gaba da hakan. Yanzu saboda mugun halinki na yaro yayi laifi ki tsare ba ai mashi fada kinga abinda wanan fasikin dan naki ya jawo muna a gida. Wai dana mane yau tunda yai laifi ko? Au to ba danki bane dan waye a gurin nan , saunawa kina fadin ke kikai daukan cikin abinki don haka abar maki kayan ki. Zaitai magana yace cikin daga hannu da daka tsawa ki min shiru don ban son jin kazamin kalamin ki yau a gurin nan. Yace Imirah kai kuma abinda kai min a idon duniya banda abinda zance maka sai dai nace kaje duniya tana da fadi. Don daga yau ina son ku sani na cire Imirah ga duk wani harkan kasuwancina. Don ba a hada biyu a lokaci guda zina da neman arziki basu tafiya daidai. Don haka tafi nima nema nayi Allah ya bani kaje ka nemi na kanka amma da kudi na ni Abubakar ba za,a dinga zina dashi ba. Wanan kalamin na Alhaji ya tayarwa Umma da yaran ta hankali sosai don sun wani babban komawa baya ne ya samay su. Yace daga yau duk wanda ya dauko min magana irin ta zubar da mutunci da kima a idon duniya wallahi ku sani na tsamay ko wanene daga cikin zuria ta. Ni ba mazinaci bane kowa ya sani a garin nan don kaucewa zina yasa na aje iyayyen ku haka a gidan nan. Duk wanda ya ganin a gurin mace to ka tabbatar aure ne yakaini ba yaudara ba. Yanzu ina riba ga illanta wa mutane yarinya da kayi amma fa ka sani shi zina bashi ne karike ka aje hakan a ranka. Haba Alhaji kada kai mashi baki mana mama Asiya ta fadi haka da sauri ta tare mashi numfashi. Yace Asiya ki shiga hankalin ki duk kune barayin na,tsunta da baku iya kwabawa diyan ku kun bar yara sun zama ni alkakan kafa a gida na. Sai yai shiru can yanisa yace Maijidda ke kuma kada ki ga kamar ban san komai ba da kikayi. Nasani kuma nayi mamakin yadda kika boye, wanan mugu munafuki mazinaci akan mumunan laifin da ya aikata haka. Dukar da kai mama tayi tare da dan nisawa Baba yace ina kwana ki akanki yaso sauke wanan iftila,in kan yar amanan da aka aje a gurin ki. Idan da ita yaiwa hakan ashe boye shi zakiyi ke nan kici amanan iyayyen yarinyar da aka danka maki. Gaskiya kin bani mamaki kuma kin bani kunya matuaka dana ji hakan a kan ki. Sannan ke mai da mai hali ko ? Kika saka danki a gaba sai da yazo ya fitar da,wanan fasikin dana so ai mashi daurin rai da rai ya karata can gidan yari inga yadda zai samu wata yar kuma ya lalata. Cikin karfi hali maji tace Alhaji ni ba na boye shi bane don kada a hukun tashi kokuma wai ba mumunan laifi yayi ba. Gani nayi a lokacin yadda mutane su kai dandazo suna neman shi zasu iya illanta shi. Yace da tsawa shi da ya illanta yar wasu fa ? Tace idan sun kashe shi ko sunyi mashi wani mugun abin a lokacin Alhaji sai abin yafi na farko muni. Kai kuma ka hau sosai a lokacin ba shawara zaka ji ba don yadda ka hasala. Wanan dalilin yasa nai hakan . Amma da aka samu natsuwa ai an fahinci juna don kaddarace shima ai da yayi abin ya koma mashi ciki. Sannan ita wanan yarinyar mutane sun sheda ta da haka take watsatsa ce ita dama. Yace ai shi ya fita watsewa, Maji tace na kira sadauki ne don yazo ya san yadda zaiyi akan al,amari don duk kan mu nan ai matsalar ta shafa don ba wanda bai shiga tashin hankali ba daga cikin mu. Ke da danki ya shiga wani hali a gidan nan wa hankalin shi ya tashi ina a tsakar gida ake tsayawa ai maki gori dare da rana. Wanan kuma ai ba komai bane don kowa ma uwace ai don dan sune suma. Amma ni idan abinda nayi laifi ne don Allah ayi hakkuri a yafe min. Sadauki ne yai magana yace Baba don, Allah ayi hakkuri tunda abin ya riga ya faru. Kai dakata don Allah ai kaima zanzo gareka ne watau kai yanzu ga mai kudi ko ? Shine zakai amfani da wanan dama gurin tallafa ma alfasha idan haka ya kasance daga daya daga cikin kannen ku yaya zakuji ne wai ? Abinda nake son ku gane ke nan idan a cikin diyan mu akaiwa wanan keta haddi haka aka gurbata rayuwan su ashe taimakawa mai fyaden zakuyi a sake shi ? Shiru falon yayi ba,wanda yai magana kowa na tunanen zuci daga cikin su. Sadauki ne still ya kara yin karfin halin yin magana yace Baba don Allah ayi hakuri tun da iyayyen yarinyar sun hakkura. Ido mahaifin shi ya watsa mashi cikin takaici yace eh maganan ta mutu ma na tunda kai mai kudi ka basu kudi ba. Amma ni a gurina wallahi case din nan bai mutu ba dayan biyu ne ko na kai shi kotu ko kuma ya yarda cewa da zaran yarinyar nan ta kara dan tasawa zai aureta. Da sauri kowa ya ke kallon baba cikin dago kawunan su. Imiranah da,sauri ya dago yace haba Baba wanan yarinyar yar kauye yar talla ko boko fa batayi ba. Au baka san haka take ba ne har ka turata daki ka kwamashe ta har ka kai ga halaka ta ? Shiru kowa yayi ba wanda yace uffan Baba yace sannan kuma kaine zaka dinga dauka duk wani nauyi nata daga yau har zuwa lokacin da za ta tare a gidan ka. Kuma ku sani wallahi ko bayan raina duk wanda ya tayar da wanan magana ban yafe ma maishi ba. Daga haka ya mike zai shige ciki sadauki yace amma Baba don Allah ka barshi yaci gaba da sana,an shi da yakeyi. Baba yace wani ai nagama magana ta yaje ya nemi tashi shima, don nima nema nayi ba gado nayi ba. Ya shige abinshi yabar su nan a zaune kowa yai jigun jigun tsakanin su, hjy Kubura ta mike tana fadi yau dai ga irin ta nan. Yanzu kowa na da abin fadi ke nan a gidan nan tab da tsuliya bamu kadai bane masu abin fadi ashe? Ke tsohuwar kilakiya dama nasan a farin ciki kike don haka ya faru kuma nasan duk kece mai wanan shirin. Iyakar ki ke nan zagin wasu naji ni dadewa nayi banyi aure har mijin ki yazo ya,aure ni gani kuma gidan zama daram ba inda zan tafi wallahi. Ba kince lokacin da na,shigo kin bani wata uku ba dashi yau gani wata uku ya shude har da riba gasu nan min. Sai da ki shirya don kilakiya tana nan dakin ki zaune ko kinzaci bamu san komai bane wai ? Ni ba irin hajiya maijidda bace da kike wa yadda ranki yaso wai don takaici har da taimaka maku. Nan da Sadauki ke dan shaye shaye a baya may nene bakuyi mata ba a gidan nan. Yau gashi ita da dan da kike mata gori kullun sun taimake ku ai da kun gane kuren ku wallahi da ankamashi fasikin banza kawai. Nan fada ya kici may masu hjy kubura tai masu tas ta fita maji dai tana ganin su sarke tabar falon zuwa part din ta. ****** ********* ****** Ina zaune a falo ni kadai don ban tafi gurin kiran da Baba yai wa iyalin shi ba don nasan magana ce da yashafi sirin iyalin shi. Sadauki ne ya fara shigowa falon su maryam na bayan shi, nan ya samu kujera ya zauna tare da furzo iska daga bakin shi. Daga inda nake zaune cikin yar siririyar muryana nace sannu yaya. Sai da ya nisa yace yauwa sannu Fatima ke ma. Maryam tace Fatima dauko muna salad din mu, mu sha kinji. Namike na nufi kitchen na dauko salad fruit din dana gyara mu a a cikin wani roba mai fadi da cups din da zan zuba muna aciki. Shina fara zubawa fruit din idon shi suna a lumshe na aje mai a gaban shi nace yaya ga naka nan na juya zan wuce. Kamar mai rada yace ki zo ki dauki kayanki inba zaki juri bani hannu da hannu ba kuma ki tsaya nasha naji ko may nene? Wani din nayi kamar na wuce sai kuma nai wani tunane tare da dukawa na dauko cup din na mika mai, Bai ce min kala ba ya karbi cup din daga hannu na, zan juya na wuce yace amma kinji abinda nace maki ko? Dan guntun tsuki naja wanda ban san zai fito fili ba yace, ai da ma na barki ki tafi din yau kiga abinda zan ma shegen kunnen nan da baijin magana. Babu shiri na dawo daga gefen shi na dan tsaya tsaye. Yace ya haka kuma kamar wata soja can ko bodyguide, zama nayi daga kujeran gefen shi ina cewa Anty maryam ki zuba naku kada yai sanyi har nazo. Bai ce min kala ba ya fara kurban salad din da cibin dake cikin cup din a hankali. Ya kai cibi uku ya dago kadan yace me sunan wanan abin kuma ne wai ? A hankali nace fruits salad ne. Ya dan mayar da hankali ga sha can yace waya hada shi haka ? Nace nice nayi shi dazun da safe. Ya nuna cup din yace ina son kullun da safe da yamma idan ina gari ki dinga hada min shi. Zan so na sha shi kafin nasha komai da safe haka da yamma kafin na kwanta. Kaina na gyada mashi kawai. Yace baki ji may nace bane ? Da sauri nace tau yaya. Maryam tace Bintu zo dauki naki mana kafin yai sanyi ki sha. Na yunkura zan mike sai naji tasa kafan shi ya take min kafa, wani mugun zafi naji ban san lokacin da na sake wani dan kara ba da karfi. Da sauri na daga kai na dubeshi sai naga shi sai shan salad din shi yake hankali a kwance. Da sauri su Amira suka dago kai amma basu ga abinda nakewa ihu ba hakanan. Gashi shi kuma yaki daga kafanshi daya danne min nawa dashi idan na dan motsa kafana wani irin mugun zafi nake ji sosai. Kuma yaki koda kallon inda nake balle yasa alaman cirewa. Take idanuwana suka fara kawo hawaye, mama ce tafito daga dakinta don jin karan da nayi tana tambayan maye haka kuma kikewa mutane ihu haka Fatim? Ban ce komai ba sai dan kukan dana kara da sauri takai kallonta ga ketan da yake min. Tace kai amma ko anyi babban banza anan wallahi yanzu mai tai maka kake mata wanan cin amanan haka sadauki ? Kamar badashi mama take magana ba tace bazaka cire mata wanan kauren kafan naka ba da yasha buga ball. Sai lokavcin su Amira suka gane wani keta yake min duk tsawon wanan lokacin su dai sunga kawai ina kuka ne. Mama ta kara cewa wai bada kai nakeyi bane sadauki ? Jin haka yasa shi daga kafan shi a kan nawa yana yamike tsaye yana fadin, ai na fada maki sai nai maganin rashin jiki a gidan nan. Yan tsun kafan nawa a take sukai wani irin jawur dasu bansan lokacin dana duka ina murzasu ba a hankali sai hawaye nake zubarwa shaaaa. Can na mike cikin dan dan gyasawa nafara tafiya zuwa daki ina kuka raina a bace ina fadi a raina wanan ai cin zallun ne don kafi karfi sai ka cuce ni haka kawai. Muryan mama maji tana fadin haba kana son wallahi in maka abin da bakai tsanmami ba kan yarinyar nan. Yanzu mai taimaka da kai mata wanan cin amanan haka, ko kaima dai ka canza ne wai ban sani ba don ban sanka da wanan halin ba haka. Ya ce kai maji munafukan yarinyace fa har may nai mata ne wai da zata sakawa mutane kuks haka don shagwaba kawai. Uwarka kai mata nace, Da sauri ya dago kai yana kallon maji don ya dade baiga ranta ya baci haka ba har tai mashi wanan kalman da fada. Sai gashi yau akan Fatima ta zagi uwan shi, maimakon yayi fushi sai murmushi yayi yace dama haka take son ji ai munafukan banza kawai. Fita min daga shiya mara kan gado kawai kasaka yar mutane gaba da kyashi da hassada kawai. Maji Fatima ce zanyi kyashi kuma ? Sai ya wani dan bushe da dariya don abin ma dariya ya bashi shi har may zai kyashe akan Fatima kuma. Yana dariya yafita daga dakin don shi kalaman kyashin ma dariya yake bashi sosai wallahi. Yana fita su Amira suka kwashe da dariya suna cewa kai maji wai kyashi yayane kuma zaiyi kyashin Bintu kamar wata hamshakiya can. Ta juya gare su tana fadin in ba kyashi ba mai ya kawo haka don Allah kuma ? Wallahi abin haushi da takaici yabani Allah kuwa haka kawai katon banza ka dannewa yarinyar mutane kafa da karfin Allah don cin amana. Ina daga ciki naji muryan ta tana kirana da karfi na amsa da na,am nafito still dan gyasawa nakeyi har lokacin. Tabi kafan nawa da kallo har na iso gareta tace wai may kikai mashi ne yai maki haka ? Ina kuka ina mata bayanin yadda mukayi dashi tace bar macucin banza kawai ai zai dawo ya samay ni ne. Something is fishing, something is fishing wooo, something is fishing somewhere, Harara na maka mata Amira ma kallon mamaki ke kuma may ye haka dan Allah bari mana kinga ta sha,wuya tana kuka. ****** ********* ****** Wasa wasa sai ga kafa ya rure min ya dan hau ya kumbura da kyat nake iya taka shi sosai. Take ya,saukar min da zazzabi da sanyi a lokaci guda haka ya jawo kwanciyan dole ban shirya ba. Shiko yana fita ya shiga motan shi sai gurin da yake ginan shi yanzu har kayan gidan komai anzuba mashi a gida zakace ko an tare a cikin gidan ne. Nan Bashar yazo ya samay shi don su fara lissafi, saboda zasu yo odan kaya kwanan nan. Bashar na shigowa yabi ko ina da kallo a gidan ya dan nisa yace,kai gaskiya fa MAN ya kamata kai aure hakanan domin barin gida haka hatsari ne ko banza kuma a ragewa Maji consurming . Sadauki yai dariya yace, ai sai naga kaima katon tazuru ne bani kadai ke cinye abin uwata ba. Bashar ga zauna cikin yanayin nishadi da kuzari yana cewa Allah ba,wasa nakeyi ba ni da ka ganni nan na kusa zama family man insha Allahu. Kai dalla jacan da zancen banzan ka kullun da bai karewa mutane saurare. Yace ai ko zakace nace don kwanan zan baka mamaki ne sosai Allah kuwa. Sadauki ya kwantar da kanshi a jikin kujera yace gashi ko kaji tsoho yace wai ya bamu wata uku ba. Bashar ya mika hannun shi ga kafadan Sadauki yace na fada maka kayar da wanan daukan kan naka kawai bori ya hau idan baka iya fadawa Maji ni sai na fada mata. Da sauri Sadauki ya dago kai ya dan kalleshi yace ka fada mata may kuma? Cikin kashe ido Bashar yace zancen yarta mana Fatima tunda naga kai wanan shegen fadin ran naka bai bari ka fadi abinda ke cikin ranka. Kai dai wallahi wani irin dabbane dan akuya kawai don banda kuya na rasa wace zan aura sai Fatima. Illa ne auren Fatima din don dai kana so wallahi girman kaine kawai irin naka ke cutan ka. Wai kasan Allah? Bashar yace niko nasan Allah sosai wallahi ko. Ce to ni wallahi daidai da rana daya ban taba jin digon son yarinyar nan a raina ba Allah ko. May ma zan so ga jikin wanan maikama da takarda ne wai ? Yanzun ma saida muka kwasa da Maji akan ta kaga na gudo nan don naga maji tahau sosai har uwana ta zaga yau akan yar kauyen nan nata. Yace mai kawai Fatima din kuma kai ? Nan yake bashi labarin abinda yafaru yakare da cewa kasan shagwababbane kuma muna fuka shine harda kuka da ihu don uwarta taji ta zageni. U see aina fada maka wallahi son ta kakeyi amma kana wa mutane wani noke noke haka? Yace ban fa son iskanci idan kuma na daina kulata ace ga batu ga zance kuma. Wai yaya kuke son mutum yayine wai ? Don Allah ni let's do what we here for. Sun dauki lokaci a gidan suna lissafi yadda ya kamata tare da tsara abinda ya dace suyi a karshe. Sai sadauki yace amma gaskiya wanan riban da muka samu ina son mu kasa shi uku bashar yace inajinka. Yace ka kwashi kashi daya kashi daya mubawa iyayen mu dayan kuma mu samu wani abin tallafawa tallakawa dashi. Wanan ma babban shawara ne amma nawa da kace gaskiya yayi yawa ni kadai. Sadauki No kada muyi haka dakai please kaga kace zaka yi aure soon, to dole ne kuma kaima kafara dan wani abin dogaro da kanka hakana. For me kaga ni banda matsala ina dai samu gwargwado gaskiya ga harkan ball din don haka bawai sai kabi ta nawa ba. Ina fatan ka gamsu da magana ta dai ko? Shiru Bashar yayi yarasa may zai cewa abokin nashi can yace man gaskiya ban yadda zan gode maka ba irin wanan kokarin da kake min. Ksi don Allah just forget ni kafi min komai wallahi in har ma badon rayuwa ba ni ko abinda na mallaka ne zan iya baka duka. Basu bar wajen basai gap da magariba suna gidan suna hiran duniya a tsakanin su. Da zasu rabu sunyi cewa bayan sallah zaifito akwai inda zasu tafi ganin wani mutum. Sukai sallama kowa yaja motan shi suka nufi gida maigadin gidan ya rufe kofan kuma. ****** ********* ****** Sai bayan an gama,sallah ishai ya shigo gida a gajiye yakw a lokacin maji tana falo zaune da tasbaha a hannun ta. Sai da yake zaune yafara gaida ita da gida ta amsa mashi a dan darare ba sakin fuska. Su maryam ma sun gaidashi tare da ci gaba da abinda sukeyi a lokacin. Yana zaune shima waya yafara hsr tsawon wani lokaci kafin ya kashe wayan sai maryam take tambayanshi yaya abinci fa akawo ne? Yace maryam banjin yunwa gaskiya amma ina yarinyat nan Fatima ne abinda nace ta hada min ta hada din ne ? Eh ta hada tunda boyar kace, Ka halaka yarinyar mutane kuma wai kazo kana tambaya tai maka aiki ne ? Maji na halaka ta kuma dan taka kafan da nai mata wai shine matsala kuma dai ? Wallahi yaya yazama mata zazzabi sosai tana dakima a kwance yau ta wuni don kafan ya kumbura sosai. Kada ke nan dan wanan takin shine har da matsala haka kuma ? Tana ina yanzu ya tambaya cikin damuwa da nuna kulawan shi akai, tana kwance mana tunda haka kake son ganin ta. Shiru yayi na dan tsawon lokaci yana tunane shi har wani taki yai min da za,ace saboda shi an kwanta ciwo kuma. Ai dama nace kaida ka halakata kai zaka sayo mata magani indan kadawo macuci kawai. Murmushi yayi yace maryam kira min ita mugani yaya kafan yayi mata ne wai ni wanan cutar da maji ke kiramin. Maryam ta mike tashiga kirana ina kwance na dunkule acikin blanket wani irin zazzabi ne ya kamani lokacin mai karfin gaske. Ta kware bargon tana taba jikina tani yadda nake nishi yabata tsoro da sauri tafita daga dakin ta nufi falo tana fadin,. Wallahi maji sosai ne fa jikin Bintu bakiji yadda jikin ta ya wani gashe ba sai nishi take da karfi ni har naji tsoro wallahi. Zubur ya mike yana fadin wai tana inane ma tana dakin mu kwance tabashi amsa . Dakin ya shiga ya samay ni a rufe yadda ta samayni da farko a hankali yadan tabani yana kiran sunana. Ke Fatima fatima fa ? Na amsa da kyat , Yace may ke damun kine wai nace a hankali zazzabi nake ji. Da may kuma? Da kyat nai dan mika tare da nisawa nace kafata ke min zugi sosai. Oya taso kizo falo mugani. Sai ya juya yafita daga dakin yadawo falo shiru shiru ban fito ba maji tace ina take ne wai? Tana ciki nace tafito maga kafan nata ne ? Ganin ban fito ba yasa mama mikewa da kanta tana tafiya tana bakar magana ita kadai zuwa dakin. Yadda ta samay ni itama dai hankalin ta ya tashi da kyarta tashini in fito falon na sako kafana daga saman gado zuwa kasa sai naji wani irin zafi da nishi na karasa saukowa kan gadon. Namike cikin karfin hali amma sai na kasa tafiya dafa bango nayi na fara bi ina daga kafa ta da kyat da kyat nakawo falon. Bina yayi da kallo cikin tausaya min nakai saman kujeran dake kusa da kofan na dan zauna saman hannun kujera tare da dan kwantawa gurin. Mama tace kagani ko sadauki kaga abinda kajawa yar mutane yanzu gurin mugun halin ka. Wanan kakausar kafan naka daya saba buga ball zaka illata min ya dashi, kafan yabi da kallo yaga ya kumbura daga inda ya taka har yana walkiya. Yace tashi muje asibiti a duba kafan nan kafin yafi haka. Tsoron asibiti gare ni don ban son ace allura ko magani sam ban son su gaba daya. Tashi ya kaiki asibiti kinji Fatima kada kafan ya kara hawa kuma yafi haka ko ya hanaki barci da dare. Ke maryam dauko mata hijjab ku tafi tare da ita don Allah, mikew yayi yana cewa ku samay ni a mota. Yana zaune a motan shi muka fito daga cikin gida ni da maryam dana dan dafa kadan ta muna tafiya a tare. Ido ya tsura muna har muka iso bakin motan maryam ta bude baya muka shiga yata da mota sai asibiti Muna hanya Bashar ya kira shi yana tambayan shi yaya bai gan shi ba har yanzu ga dare yanayi? Yace sorry wallahi ganin zamu tafi asibiti ne yanzun haka muna hanya ma. Waye kuma baida lafiya Bashar ya tambaya ? Yace Fatima ce kafan ta ya kumbura shine zamu tafi da ita aduba mata nan yai mashi kwatancen inda zamu tafi. kusan a tare muka iso da Bashar gurin wani pravet asibiti ya kaimu gurin yana da matukar kyau dagani sabon guri ne don komai nasu gurin tsab yake. Likatan yace dole sai an da jamin kafa sai ai min allura da magani don na daina jin zugin da yake min. Wata sabuwa ai likitan yana fara taba kafan na yanka wani irin ihu da karfi duk yadda yaso yaja naki yarda don zafin da gurin ke min daidai dan karamin yatsan kafana sai walkiyan kunbura gurin keyi yana kyalli. Bashar yace ki tsaya aja maki kafan kiji Fatima kada ya hanaki barci da dare. Ban san yadda akayi ba sai ji nayi an rike ni ta baya nan likitan ya samu sa,an jan kafan da kyau nai wani irin juyawa wai kwace amma ina rikon da yaya yai min bai ma san inayi ba. Duk rabin jikina yana cikin jikin shi ina gurji ina kiran wayyoni Allah na don girman Allah ku sake ni wallahi da zafi kwarai akwai ciwo sosai. Don Allah yaya ka sakeni kada ya kasheni wayyo don giman Allah ku taimaka min kuji tausayina mana. Kuka shabe shabe nake yi naba maryam matukar tausayi sosai, yadda nake ihun tasan zafi nake matukar ji sosai. Suna gefe da Bashar take cewa kafan yai mata tsamine ko har zazzabi ya sakar mata. Bashar yace idan ba,a ja ba zaifinan anjima ya hanata barci gara kawai a ja din shi yafi Likitan ya dauko wani mai ya shafa min mai sanyi a kafan na noke kaina a jikin yaya ina kuka cikin ban tausayi. Ya dan buga min baya yace is ok ya isa hakana please ai an gama jan kafan. A hankali na zare jikina daga nashi ina share hawaye cikin wani irin dan kuka kasa kasa. Haka gurin allura nace maryam ta rike ni amma ta kasa dole dai sai a jikin yaya akai min aka bani magani tare da muna bayanin yadda za, aiwa kafan. Amma kuma cikin ikon Allah sai naji kafan yana rage ciwon da yake min da farko. Mun fara fitowa muja barsu aciki dan anjima saiga su sun fito daga cikin asibitin Yaya ke cewa baku shiga motan bane kuka tsaya a,waje ga sanyi na dauka ai a rufe motar take inji maryam Bashar yacewa maryam jimana maryam sai ta dan tsaya ya samayta a gurin nikan na dan ja kafana zuwa bakin motan na tsaya magana sukayi a tsakanin su sai naga ta danyi murmushi tace taji. Shima yaya Sadauki wani kallon mamakine naga yanawa bashar din na bangane ba fa? Zan shiga baya yace wa maryam bari ta shiga gaba a nan na zauna ita tana baya zaune. Mun fara tafiya maryam ke cewa wai Bintu ba dai raki ba kan anya ko kina iya haihuwa yadda nake ganin nan . Ke wai wani irin jikine maki haka wai dan taki kadan shine kika rakwabe haka dake ? Banyi magana ba sai dan jingina kaina da nayi ga glass din window motan kawai ina kallon titi. Gurin wani mai gasa kaji saman hanya ya faka motar shi can dan nesa kadan yafita. Sai gashi da ledoji har uku a hannun shi ya bude ya shiga ya zauna har ya zauna zai tayar da mota ya juyo inda nake zaune yace yaya jikin naki nace a hankali da sauki. Sai bayan ya tayar da mota ya fara hanya sai naji kaman yace kiyi hakkuri kinji ban san haka zai zama maki ba. Dan murmushin ciki nayi nace bakomai kaddarace haka Allah ya nufa dani. Yace nagode. Har muka kai gida ba wanda yai magana a cikin mu muna fita ya mikawa Maryam ledan karbi wanan kibata taci tasha fresh milk din sosai. Muna shiga gida mun samu mama a cikin damuwa tace kun dawo na samu guri na zauna a dan takure. Maryam tana shigowa tace wai maji yau munsha ihu wallahi, saida yaya ya danke ta tabari akaja kafan sosai. Ya jikin naki yanzun Fatima? Nace naji sauki mama. Lokacin ya shigo mama tace haka kawai kajawo wa yarinya wahala haka. Maryam tace ai ya bata hakkuri maji kuma tayi hakkuri shike nan ko? Ke ban son shegan taka hakkuri may zai bata bayan ya cuce ta ko. Kai maji wa yaya zai wa laifi ya bashi hakkuri inko ba Bintu ba yau. Daga inda Amirah take tace ban taba ji ba gaskiya nima sai yau. Shi dai baiyi magana ba guri ya samu ya zauna tare da kallon inda mama take zaune yace maji yanzun haka za saka ido ga hukuncin da Baba ta daukan wa yaya Imiranah a gidan nan. Ni yanzu sadauki may kake so nace kasan halin mahaifin ku sarai idan ranshi ya baci sai ya ga dama don kan shi zai huce. To amma ni naga barin shi a haka ba zaiyi ba gaskiya anyway zan ga baba din gobe a kasuwa na kara bashi hakkuri. Amirah tace niko dai naga da kun kyaleshi wallahi, mutanen da basuki ace mune a cikin wanan irin matsalan ba. Kamar ya akyaleshi Amirah dan uwankine fa ashe har ke zaki iya jin dadin ganin wani naki cikin damuwa ?. Nikan naga suna hira sai na mike zan shiga na kwanta, don barci nakeji jikin still jikina da dan zazzabi har lokacin. Kin sha maganin da aka bakine muryan yaua sadauki ne yake tambayana hakan. Cak naja na tsaya na dan bata fuska nace ban sha . Koma ki zauna kisha kafin ki kwanta yace min ba mussu na koma na zauna idan na daga . Maryam tace ga maganin bazaki sha milki din ba kafin kisha don bakici komai ba ma. Naman kaza da fresh milkin din takawo min kurba biyu nayi bakina ba dadi sai na aje kwalin don bazan iya sha ba zakin shi naji ya kara bata min baki. Still magana sukeyi da mahaifiyar shi amma hankalin shi yana a gareni ganin ban ci komai ba yace maji kiwa yar ki magana ta ci tasha magani. Fatima ko tea zakisha in baki iya shan wanan din don naga kaman yana da sanyine ko ? Nace ,a,a mama nasha ai na dan kara kurbawa kadan na aje kwalin nan nakoma saman kujeran na zauna da kyau can kuma saina dunkule guri guda ashe barci ya dauke ni a hakan ban sani ba. Sai da mama tai magana sukaji shiru shine suka fahinci nayi barci ne. Maji tace gaskiya banji dadin yadda kaiwa yarinyar nan ba kadaina wanan halin karfin ku ba daya yake dasu ba. Ko banza ita mace ce fa ysushe daga dan magana kadan zakai mata wanan horon haka ? Shiru yayi baiyi magana ba don koshi yadda yaga ina wahala sai baiji dadin abinda yai min din ba. Ga yanin yadda na kwanta yasa shicewa maryam ta da ita taje ta kwanta wanan kwancin sai kafan ya kara ciwo ai. Bai wani jima ba yamike zuwa dakin shi don ya kwanta sai dai bai shiga dakin ba ya zauna daga waje gurin furanni kofan shi don ya sha iska. Mamaki yayi dayaji har a lokacin jikin shi yana kamshin turare na na white musk danake amfani dashi ajikin shi. Take ya tuna da yadda yaji lokacin da nake kuka a jikin shi da likita ke ja min kafa. Tsukiyi dan ja daya tuna yadda likitan ya rike dan farin kafana wai yana shafa min magani a kafan nawa. Haushin da yasa shi mikewa ke nan yabar gurin da yake zaune ya fada dakin shi cikin takaici. To kai takaicin may kake ji da hakan yaba kan shi amsa a fili da oho, wanka yashiga yafito kusa da rigan da ya cire yasa kan shi. Kamshin ne ya kara bugo hancin shi abinda ya sashi dan lumshe idon shi ke nan haka barci ya dauke shi. ****** ********* ****** Washegari kodana tashi na danji saukin kafan nawa sai dai yana da dan sauran kunburi still. Ban fito ba sai zuwa 9,30 nafito don na karya nai wanka na saka dogon riga baka abuga farin mutum sai rigan ya haskani. A falo yana zaune da abinci a gaban shi yana ci yana waya fitowa na ina dan dan gyasawa yashi bina da ido. Ina kwana nai mashi Amirah tace kin tashi ashe Bintu nace eh anty tace to yay jikin naki ? Da sauki anty na zauna yana kashe wayan yace zonan naga kafan nan ko yai sauki ? Idan baiyi a koma a kara jamaki shi da safen nan da sauri nace a,a wallahi naji sauki yaya. Dariya suka saka min yace no ki bari akara ja maki for second time mana zaifi sakewa. Wallahi yai sauki sosai yaya abarshi kawai ki karya kisha maganin ki kada fever ya dawo maki. Na amsa da to nabar gurin shi zan shiga kitchen sai ga maryam dauke da wayana dake ringing da sauri na dauka. Bashar ne a layin yake min yajiki yace yanzu yace maryam tabadhi layina yakirani. Na koma na zauna don ba zan iya tsawon tsayi a tsaye ba ina amsa wayan nashi. Ya dain bani hakkuri nace wallahi ba komai nagode ai ina taka kafan yanzu nace ka gaidasu mama. Ina kashe wayan yana watso min wani irin mugun kallon dayasani shan jinin jikina lokaci guda. Sai na tuna ya saka min idon kancewa ina waya da maza a gaban kowa haka yasa lokacin da marigayi Kabir keda rai na daina waya a falo gaban su. Daga inda maryam take tsaye gaban tv tace yayanane yakira ki halan nace eh shine. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BA KI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,, YA ALLAH DUK WACE TA TURA MIN NOVEL GA WANDA BAI BIYA BA ALLAH KA ISAR MIN AKAN MAI SHI,,,, Suna zaune sai hayaniya suke a tsakanin maryam da Amira suna hiran wai sun kalli wani film din biri jiya da,dare shine suke hira a tsakanin su. Ina zaune a kan kujera na jingine jikina saman makarin kujeran nai shiru ina sauraren hiran su. Sai dai anihi na sha jinin jikina sosai daga irin kallon tsana da yaya sadauki yake min daga gefen da yake zaune. Na fahinci wayan da nayi ne yanzu ya jawo min wanan tsanar haka to amma ai saboda shine ,aka gaisa dani din. Hannun shi saman goshin shi ya dan dafe kai yakai bayan shi a makarin kujera yai kwanciyar balance saman kujera ta hanyar mike kafafuwan shi. Ganin haka nima na murde nawa fuska babu wallawala acikin sa ko kadan. Ganin yaki ya bar falon yasani mikewa ina tafiya cikin dan dan gyasawa na nufi kofan shiga daga ciki. Yabi bayana da kallo a hankali yana duban yadda nake taka kafana still a cikin wahala. Yace ke zo nan kawo kafan nan nan na kara ganin yadda yayi sai a shafa magani . Kamar na wuce don yadda yake magana cikin nuna isa, da gadara kamar dan wani sarki shi mutum ne muskilin karshe kilama shiya sa yake cin kwallo don in ya kama sai ya kai gola kamar abin tsafi sai yaci kwallo. Shigowan Maji falon ne, shi ya katse min zancen zucin da nakayi tsaye . Sai maryam ke fadi lah Bintu ba dai wai tsoro kike ji ba haka tun dazun yaya yace ki kai kafan ya duba ya gani, ko sai an koma asibitin ne ? Nace cikin daurewa ni kafata normal take don banjin komai yanzu, Yadda nai magnan tare da dan murguda baki kadan yasashi cewa cikin takaici wanan yariyar typical yar kauye ce wallahi. Shigowan mama yasa take kallon mamaki da son tambayan ko lafiya yace cikin rashin nuna tsoro ko damuwa. Wanan local yarinyace ance tazo a duba kafan takewa mutane maganan nosenses, wai da kafan ma baka,barta ba sadauki? Yanzun kuma may ne mata, maji, kawai don za,a duba lafiyan kafan a shafa mata magani shine abin magana kuma. Maji zatai magana sukaji muryan mata kaman da dan yawa suna kwada sallama a kofan dakin maryam dake tsaye tafito don taga ko waye? Suna gaisawa daya daga cikin matar tace ance a nuna muna dakin hajiya Atika da hannu Bintu tai masu kwatance su tafi can. Su na dauke da akwatina sa sauran kayan tarkace irin wanda ake kai kayan lefen mace kayan aure. Maryam na fadawa Maji ta ce kayan lefe kuwa a gidan nan kaya waye ke nan kuma. Amirah tace kila Nafisa ce ta samu miji ko Rukaiyya, shine aka kawo kayan su. Can muka ji suna fadin bamu ba aura wa yar mu mazinaci mai abin kunya abin fadi irin haka. Nan dai suke ta sake bakaken, magan ganu iri iri suna aibanta Imirah dashi haka yasa duk muka fahinci cewa ashe kayan lefen da akakai na auren Imiran shine gidan matan suka dawo dashi, wai sun fasa saboda labarin da suka samu na abin kunyan da yayai wa yar mutane a gari. Daga inda nake zaune nace Allahu akbar yanzu a take Allah ke gwadawa mutun laofin shi tun a duniyan nan. Gashi dai Umma da kafatan suka je gidan su Rahama suka aibanta yaya uwar ta tace am fasa auren yaya da yar su. Ranan kun, manta babu irin maganan da su mama basu fadi ba, a gidan nan su ke cewa aure sai da muga anayin shi shiyan nan. Yau ga shi Allah ya mayar masu da martani abinda suka shuka tun ba,a je ko inaba sun fara girban abin su. Masha yin da suke fadi abin kyama gashi sai a zauna dashi ayi koma hankali a kwance sabanin dan ta katon mazinaci da ko maza yan uwan shi tsoron shi suke ji balle mata. Muna ta hiran mu hankali kwance ban san cewa yaya Sadauki ya dawo falon ba duk abinda nake fadi a kunnuwan shi. Ganin Amira tana kallon kofan shigowa falon yasani juyawa naga may take kallo ne wai. Ganin shi nayi tsaye kinkam ya harde hannayen shi a saman kirjin shi, Ya zura min ido fuskan shi babu walwala ko kadan a cikin shi ya sha mur sosai dashi. Ina ganin shi tsoro ya shi ya dan kamani indai har baiji abinda nace gamay da tsohuwar budurwan shi ba. Sai kawai nai shiru tare da dukar da kaina kasa dariya maryam takeyi tace kai Bintu yanzun fa kike ta masifa kan anwa yayan ki wullakanci yau gashi Allah ya rama mashi. Maimakon nayi magana sai ma dan kai kaina saman kujera nai shiru tare da lumshe idanuwa na kawai. Fuska a murtuke ya karasa takowa zuwa tsakiyan falon yana cewa wani gulman takeyi wa mutane ne wai? Nace ai bani kadai bace magulmaciya kowa ma anan gulman yakeyi akan abinda ya faru. Yace see your mouth muna fuka ta iya maida magana kamar wata tsohuwa can da ita . Yarinyar ta iya babban magana da gulma kamar bayerabiya. Haushin abin da ya fadi naji nace kai nifa wallahi in mutum bai daina kirana da mugun suna ba wallahi zan ramane wata rana. Ni natsani wanan kalman na munafuka da kake kiramin in hakane ai kaima mugune na karshe. Cafka guda yai min akaina na yanka ihu da dan karfi ido suka sako muna gaba dayan su da mamakin yadda halaiyan yayan su ya canza yanzu da irin mugunta da yake min. Bai sake min kai ba nikuma sai fadi nake wallahi zan fadawa mama don Allah yaya ka bari wallahi akwai zafi sosai. Ba kince ke baki da kunya ba bari na gwada maki mugu nake naja shegen kan nan mai tsawon banza ba gyara. Ji kan ta kamar ba mace ba kullun a yamutse ko gyara bata iya ba irin na mata, sai shegen gulman tsiya karama dake. Wai Sadauki may yake damunka ne ban san wanan irin iskancin ba da kake wa yarinyar nan a gidan nan Tace karya take ba mugun kake ba dubi yadda ka rike mata gashin kai kaman wani mayanki. Ya dago kai don jin muryan mama a bayan mu ya koma ya dubi gashin da tace ya rike min bai sake ba har lokacin. Yace wallahi maji Fatima ta raina ni gulmana nasamu tayi da su Amirah shine nake koya mata hankali. Koyon hankalin ne a haka? Yace maji wallahi duk kin bari ta raina ni Allah ko. Tace rufe min baki mara kunya kawai ina maka kashe di akan wanan yarinyar amma bakaji da Baban ku zan hada ka tunda ni ka raina ni. Jin abinda maji tafadi yasa shi sake min kai tare da kutawa yace sai na balballa ki wata rana. Ya juya yana gyara hannun rigan shi da yai dan squeezing. Maji ta girgiza kai tace sai nayi maganin ka wallahi akan Fatima. Yana fita daga falon ta juyo gare ni tace Fatima ki kiyayi sadauki don ba hankali gare shi ba kada ya halaka ki a banza. Wallahi mama ban mashi komai ba kawai ya samu muna hirane shine ni ya sauke haushi a kaina. Tace na dai fada maki ki iya kanki dashi mugun yaro ne bai dariya sai bakin ketan tsiya kawai. Amirah tace kai maji yayane kuma mugu yau ? Ba mugun yake ba may yake? Maji wallahi in kina shiga tsakanin yaya da Bintu watarana fa zakiyi kunyane barsu kawai inda kika gansu a dunkule. Maganan da Maryam tayi yasa maji kallo na nace ni wallahi mama karya take min ba,wani abin dukule dana sani. Shiru tayi tare da shigewa daki tabar munan falo maryam na fadi muna ganin wani sabon sallo a gidan nan. Na ce don Allah anty bari kada ya balballani kinji dai ya fadi ni yanzun ma,in yashigo gudu zan dinga yi yafi min wallahi. Hummm kamar da gaske nifa nasan komai wallahi. Tare muka hada baki da Amira muna cewa kin san komai kamar yaya fa? Tace ni wallahi tun a asibiti ranan na kara gane komai. Jifa yadda yaya ya rugumay ki yana lalashin ki. Nace kai anty maryam wallahi kada ki kulla min sheri don Allah rufa min asiri kada kisa yai ball dani a gidan nan. Shidai kawai ya tsanine yasa yake min haka wallahi in gaskiyane yai maku haka mana. Sai naga ta sa dariya tace ji min wanan fa yai muna haka mu kannen sa. O ni ba kanwarsa bane ke nan ko ? Koma dai may kike ai zamu sani watarana Allah dai ya nuna muna lokacin kawai zakuce na fadi ai. ****** ********* ****** Tafiyan shi yasa na sake jikina sosai don yanzu kusan wata biyu bai garin sai da suna waya da kowa a gidan. Ko ina gurin idan an miko min bana karba sai dai nace ace ina gaidashi kawai. Idan sun fada mai sai yace rabu da silly girl kawai inta bata iya bugawa mutum ta gaidashi ne. Ranan da yai nasara a gurin wasan su duk kasa shen duniya sai labaran nasaran da,team din su ya samu sukeyi . Ranan Baba da kanshi ya shigo har dakin mu gurin mama yana ta washe baki da fatin ciki yana cewa. Maijidda kinga iko Allah ashe kowa da inda Allah yai mashi tushen arzikin shi. Yanzu akan wanan wasan ball din Allah ya daukaka wanan yaron haka? Yau mutanen da suka bugo min waya suna min murna da farin ciki Allah ne yasan yawan su wallahi. Yace ba abinda zamuyi sai mu kara godewa Allah da yasa haka ne silar shiryuwan yaron nan dakuma cigaban shi. Da yanzu yana nan yana zaman kunsa muna bakin ciki da bacin rai zube nakashe a cikin garin nan amma yanzu kinga yadda Allah yai ikon shi akan shi. Murmushi mama tayi tace nima abin yau har mamaki nakeyi mutanen yanzu sun mayat da harkan ball kamar wani abin addini. Baba tace Alokaci muke muddin baizai hana shi addinin shi ba ai da sauki al,amarin. Mamatace na kulla tun fara wasan shi bai wasa da harkan addinin shi yanzu ko kadan. Allah ke nan inji baba yace shiyasa ko yaushe adduan iyayye keda tasiri sosai akan yaro wallahi. Ni matsalata guda shine ya aje iyali don gaba dayan su na fada masu su fito da mata suyi aure hakanan. Yanzu shi wanan shedani gashi yarinyar tace ta fasa batayi kinga ni duk abin ya shige min duhu wallahi. Mama tace al,amarin sai adduan mafita yana gurin Allah Allah yasan dalilin wanan jerabawan da muke cikin shi. Da yamma yaya ta bugowa mama waya lokacin duk muna zaune a falon sun gaisa naji tana mashi murnan samun nasaran da sukayi ban san may ya fada mata ba sai dan murmushin da tayi kawai a fili. Amirah tace abata su gaisa dashi itama sun dade da ita suna hira yace abawa maryam itama dai sun dauki lokaci dashi sai halin ta takeyi na yaya ka,sayo min abu kaza ka sayo min kaza. Tace yaya ga Fatima ko may yace naji ta kwashe da dariya kawai tana fadin mutumiyar ce fa gata ta taso takawo min wayan. Na dauka tare da fadin salamu alaikum sai naji yai murushi yace wa,alaikis salam. Yaya ina wuni? Silly girl idan ban wuni ba zaki jini, yanzu ke baki ji kunya ba ke baki iya kiran mutum kullu gaki nan kamar wata bakauya can. Hmm kawai nace mashi yace yar kauye kawai ai zaki gane kuren ki bari na dawo zamu hadu. Nace ni bakama iske ni don da naji zaka,dawo zan gudu na koma kauye inda nafi wayo. Ai bako isa ba,wallahi don har kauyen zanje na dauko ki nace wa Baba gudu kikayi wa maman ki. Murmushi nayi har fararen hakorana suka baiyyana a fili. Nace munyi murna Allah yasa afi hakan nan gaba. Yace nagode da,adduan ki. Na mikawa Amirah dake kusa dani wayan maryam tace wai har an gama fadan ke nan muushi nayi na zauna kawai suna hira da Amirah yana fada mata wai may yasa aka bani waya bakauyan daba tako iya waya ba ma. Kai, yaya wallahi kaima kasan yanzu Bintu ba bakauya bace kana dai mata sheri ne kawai. Maryam tace abata ta manta da wani magana bata fada mashi ba. Amirah zance kusan halin rayuwan su daya da yayanta bata faye magana ba ita kamar maryam. Ga ta da daukan kai da son girma yar gaye ce ta karshe ga tsabta da iya,kwalliya sosai gare ta. Maryam din ma ba laifi gaskiya amma ta fiso son jama,a kamar mahaifiyan su hailayanta yake, ita don tana da son mutane gata da saurin sabo. Nayi sabon saurayi shima dai yana da mata daya da yara biyu yana aikin banki ne shi sunan shi Usman. Shima Usman gaskiya ba laifi sai dai baida hali irin na Kabir, din shi mutum ne mai son daukan aji da kuma nuna shi wani ne. Ban faye son shi ba sosai don halin shi ni gaskiya bai min ba yana da son karya sosai. Ranan da Nafisa ta gan mu tare dashi a kofan gida yazo muna hira yadda naga ta rude mashi ya sani tsinkewa al,amatinta. Ranan na fahinci, halinta yai nisa bata da kunya bata da ta ido don yadda ta nuna mashi ra,ayin ta afili bata boye ba. Ina fadawa maryam abinda tai min tace kyale yar iska nan tafi auki aishi ba jahili bane yasan ko ita wacece da ganin ta. Exam din mu na shiga 300 level yazo don haka ni yanzu ba komai a gabana sai karatu sai ko idan na fito zanyi wani aiki. Awala nayi zanyi sallah la,asar sai na fito falo don nayi sallah don babu kowa a falon mama tana ciki tana wanka don duk yamma sai sunyi wanka sun yi kwalliya kafin dawowan Baba gida. Amirah ko tana ciki tana chatting da wayan ta tun bayan azahar takd daki kwance don bata sallah. Maryam tafita tace zata wankin kai don kanta yana damunta da kaikayi wai. Bayan na idar da sallah nacire hijjab dina na jawo littafina na fara dubawa don nasan in ban dage ba akwai aiki a gareni don ba wani mugun kokari ke gare ni ba. Saye nake da dogon rigan atamfa a jikina mai dinkin bubu anty Amira akaiwa bai mata ba tabar min shi ni dinki sai ya karbe ni kamar ni aka dinkawa shi fun farko. Ban san shigowan shi ba don kaina yana a duke a lokacin, yana tsaye cikin fararen swoth na maza da bakar riga ta ciki mai dogon hannu. Yana tsaye daga kofa tsayin minti biyar ganin yadda na koma yai matukar firgita zuciyar shi sosai. Don min kuwa yaga wata biyun da yayi na matukar canza mashi a idon shi, kallona yake ko kyaftawa baiyi . Wani zazzafan ajiyan zuciya ya sauke wanda yai daidai da jin kanshin turaren shi a hancina abin da yai sani saurin juyo a firgice kenan na kalli hanyan kofan. A firgice na dago kai ina kallon shi, yana tsaye ya zura hanayen shi a cikin aljihun wandon shi gami da zuba min idanuwan shi. Gaba daya na rikice da ganin shi na dan dago ina fadin a yaya sannu da zuwa. Bari na fadawa su mama kila bata san da zaka daao yau bane, cikin lokaci daya nake fadin haka tare da mikewa tsaye. Yace see you haka ake taron mutum duk kin bi kin wani rude dake bakauyan banza kawai. Ban tsaya na karasa sauraron shi nidai na shig ina cewa mama, yaya ya dawo. Ya tako zuwa ga kujera ya zauna tare da harde kafafunan shi, lokacin na kara fitowa na nufi kitchen don na kawo mashi ruwa. Nafito da ruwan a jug lokacin su mama har sun fito ko na ce fa ruwa yaya. Yace ba komai ne sai ruwa yar kauye? Mama tace tau bisimillahi Allah zaka fara ke nan kuma ko kadawo takura ya dawo mata ke nan kuma. Ya dauki cup din ruwan ya tsiyayya yace mama in ba shirmay taba ruwa kawai zata kawo min. May kake son takawo maka runda ba wanda yasan da zuwan ka yau din balle muyi maka tanadin wani abu. Nikan in aje ruwan na koma inda littafina yake nafara tattara su na kwasa zuwa ciki. Ina kuma zaki ke kuma bayan ga yaya ya dawo zaki fara shegen shigewan dakin ki kenan kamar kinga kura shi yasa yake maki rainin hankali ai. Na dan yi dariyan yake nace mama dama zan shiga ne na karasa karatuna aciki. Zauna nace maki ba idan zaki shi dai zai fita ya bamu guri inya gama abinda yakeyi. Ya dan kalle ni ya girgiza kai , ya bude baki cikin kyarmar murya yace, yanzun kuma da dawowa na Fatima zaki kulla min sheri kuma ? Na dan kada idanuwa na nace, cikin yanagin yatsina nace, nikan ban maka sheri ba kaine dai kaiwa kan ka. Yace wallahi maji yar na taki munafukace yanzu dubi da zuwana ta hana ko na samu dan kulawa daga gare ki da nai missing tsawon wata biyu da kwanaki. Bako so hakan ba da baka dawo muna da mugun halika ba yanzun ina laifinta taga bako takawo maka ruwa kuma ka gwatsale ta haka. Nidai hada min wanan fruits din da kike hadawa nasha don da kewan shan shi na dawo saboda can wanda muke saye babu dadi. Murmushi maji tayi tace kai dai baka da kunya wallahi yanzun fa ka gama zaginta kuma kace tai maka aiki. Nace bamu da fruits sun lalace wanda ya rage dariya Amirah tayi tace wallahi maji maryam dama ta fadi kibar shiga tsakanin su. Ke kina fada kada ta hada mai itako kinga sai kokarin hadawa ma take watau tabaki kunya. Nace hai Anty nifa don kawai naga bako ne yau yasa yabano tausayi zan hada mai amma kada ki hada ni da mamana please. Murmushi yayi yace bari na buga Bashar yazo min dashi yanzu don Allah a hada min kafin na fito don yau a gajiye nake da safen nan fa na shigo kasan nan ban huta ba na kamo hanya don nazo na gan ku. Ai ka kyauta inji Maji. Ya ciro wayan shi ya kira Bashar yana sheda mashi ya kawo mashi fruits masu kyau yanzu za ai mai amfani dasu ne. Bashar yace kai nifa yanzu ina hanyan dauko madam dina daga saloon ne kakoga bukin magaji bai hana na magaiya. Kai dai kasani nidai na fada maka yanzun nake so kada kaje ka tsaya bakin I love you din ka can. Dariya Bashar yayi yace kai da baka san shi ba ai sai kaita zama ta zuru kana sa yara aiki. Watsewa zasuyi soon su barka da maji muga tsiya tunda ka zama tsohon tazuru. Murmushi yayi, kawai ya kashe wayan, saida ya mike yake cewa wai ina wanan sodan yau ta tafi, maji tace maryam ke nan ko? Yace ita fa ban ji motsin ta bane tunda na shigo gidan. Ta tafi gurin gyaran kai dazun yanzu nasan ai tana hanya kila. Yafice daga dakin a gajiye dashi uwar tabishi da kallon sha,awan yadda taga ya koma mata yazama wani babban mutum yanzu a idon ta kamar ba sadauki ta mai tabara ba. Maryam ce ta shigo dakin da ledojin fruits da murnan ta tana ina yayan yake tana wani dube dubbe da idon ta ko ina. Ya tafi wanka inji Amirah ta bata amsa tace yakawo muna tsaraba ne ? Kai haba anty daga dawowan mutun baiko huta ba kina tambayan tsaraba. To na hana ko zaki hana kuma ya bamu tsarabane yar gidan mugu. Murmushi nayi nace ni a suwa? Rufamin asiri na zauna da Fatima Bintu takafin kisa a canza min suna Binta munafuka. Dariya tayi tace yanzun ko indai yayane baida wuya ajiku da dawowan shi nace yaushe kuma ai har ya fadi ko. Murmushi mama tayi tace ni na,rasa wanan munafuncin da,sadauki ke kirawa ya ta. Nace mama ni nasani barshi kawai inko don wanan ne ko gobe yayi shi sai nai mai munafunci. Eyye wallahi maji wuyar yar ki yai kauri haka ashe yanzu yaya sadauki kik fada wa hakan ai kin fi kowa sanin halin shi dan kafan ki kawai ya taka amma kika ishi mutane da ihu, Nace wallahi anty ban ma son na tuna don ba karamin wuya nasha ba a gidan nan. Muna jin shi ya kara shigowa amma wanan karon ba dakin mu yazo ba cikin gida ya shiga gaida sauran iyayyen shi. Duk da su diyan su basu zuwa gaida mama sai Sagir ne mai kokarin hakan cikin su don shi gaskiya daban yake a gidan sabodashi uztaszu ustazu ne haka. Tare da Bashar suke ashe sai da suka shigo falon mu ne muka san da hakan, Maryam da bata gan shi ba tafito da saurin ta gudu gudu tana fadin yaya sadauki ashe kana hanya bamu sani ba cikin murna da fatin cikin ta. Ganin tare da Bashar suke yasa ta dan rage rawan kan da takeyi sai naga tawani noke cikin kunya ta dan boye bayan kujera tana fadin. Yaya har fa wata biyu kayi da tafiya, gaskiya mu ka daina dadewa haka muna missing din ka sosai wallahi. A hankali yace maryam nasan ai ba komai kikewa wanan tambayan ba sakon ki ne kuma ban sayo ba tunda ko murna baki min ba. Tace wallahi yaya aiko nafi kowa murna tambayi maji kaji har party nai muna ranan ai nace ke dawa kukai party ? Lalai ma Bintu sheri zaki kulla min don ki hanani samu wallahi na gane shiyasa yaya ke ce maki yar hana ruwa gudu. To anty wai yau kuma lafiya naga kin wani boye bayan kujera kamar wata mara gaskiya kifito fili mana kowa ya gan ki . Murmushi Bashar yayi nace sai cika bakin karya amma kina ganin yaya Bashar kin wani boye can bayan kujera to mun dai san komai mu dai ayi buki musha shagalin mu ko Anty Amirah? Munafuka kawai wallahi yaya na yarda Bintu munafuka ce da gaske shegen saka idon tsiya gare ta kamar wata yar sandan ciki. Wait, may naji wanan yarinyar na fadi ne wai kai mugu ashe ka zama dan akuya ne haka ban sani ba. Dariya Bashar yai mashi yace akan may don ina son kaunata ko may kai wa ya hanaka fitar da naka sai wani kwanaye kwanaye kake wa kan ka abari ya huce dai shike kawo rabon wani. Na kawo masi salad din sosai suka sha shi sai santi Bashar keyi yace kai mutumina kace min ka huta kawai. Fuskan shi a daure yake bashi amsa a zazafe yana fadin wallahi zamu bata dakai idan kaja min matsala da raini Allah Bassh. Wayan shi da aka kira ne ya katse masu challenges din junan su da,sukeyi. Sai da ya ja dan tsuki yace ya akayi ne cikin daure fuska da mace yake wayan kuma tambayan shi take yau she zai dawo ne wai ? Yace yau fa nazo gida shine kike tambayana yaushe zan dawo ko ganin mumm ban gama ba ki dai bari zan kiraki idan na fita. Daga inda muke zaune sai naji wani dan abu kawai a raina ban dai san dalilin jin hakan ba. Shiko yana kashe wayan yana dago kai inda nake zaune yana fadin ke zo kwashe kayan nan kada wanan mara kunyan ya cinye kwanonin gaba daya. Fuska na yana a hade take ya fahinci ban cikin good mood a lokaci guda na koma haka to why ? Sai muryan yaro ya ratso a kofan falon mu yana fadin wai Usman yana wa Fatima sallama a waje. Maryam tace ga mr love lover din ki can ya iso nasan sun taso ke nan yazo ya damu mutane. Na yunkura ina fadin babu ruwan ki anty ba dai ke yake damu ba ai, lah yanzu Bintu rashin kunyan naki har yakai haka a gaban su yaya zaki fice I love you ba kunya. Sai ga mama tafito daga ciki tana fadin ke Fatima kin bar waya a daki sai faman ruri take ita kadai. Na karbi wayan a hannun mama naga Usman ne nasan yakira ba,a dauka ba shine ya aiko yaron. Hijjab din Amirah dake kusa na jawo na saka a jikina ina gyara wuyan hijjab din naji yace . Ke bana ce ki kwashe kayan nan bane ina zaki haka kuma ? Sai ga yaron ya dawo yace wai yace don Allah tazo yanzu yana sauri ne an kusa yin sallah. Nace kace mai gani tafe yanzu don Allah. Mikewa yayi kamar zasu fita shi bai fita daga kofan ba bai shigo ba ma,ana ya tare hanya ke nan ga Bashar daga waje tsaye yana jiran shi. Na fito daga kitchen na gan shi a gurin tsaye a dan raunane nace zan wuce. Tankar da dutse nake magana don ko motsi baiyi ba . Ganin haka na dan jingina jikina gefe a bango ina kallon kafan shi dake cikin socks. Waya na yai ruri na dauka nace gani tafe ai yanzu don Allah. Bata hanya mana ta wuce ko kuma wani sallon muguntane haka kace kuma ga abinda tai maka yanzu. A dan tsorace da jin muryan mama ya ja baya kadan nazo na wuce shi har hijjab dina yana gugan jikin shi. Nan na fita na barsu na samu Usman zaune a motan shi ya saka kida na gaishe shi tare da tambayan shi yaya aiki? Yai murmushi yace aiki Alhamdullahi daga can nake nace bari na biyo na gan ki kafin na isa gida don idan na shiga gida yau da wuya na fito kuma again. Na dan dariya har hakora na suka fito nace anty na itama zata nada nata kambun ke nan ko? Shima dariya yayi yace ai Nabila matsalace wallahi an samu wanda ya kai mata gulman ina neman ki, kuma tace min wai daga gidan nan aka fada mata. Nace ai ko sai ka bari kada ku samu matsala da matar ka yace akan ta zan daina son abinda nake so sai dai ta san nayi. Ban san sun fito ba sai da naji yace ikon Allah dama U F a gidan nan yake ne shine har na dan juya naga suna fitowa daga cikin gida. Nace mai eh ai yayana ne a gurin maman shi nake zaune. Kafin su karaso har ya fito daga motan shi naga ya nufe su yana dariya ya mika masu hannu. Sai dai shi gogan barka kawai yace mai ya zagaya ya shiga mota hakan bai ma Usman dadi ba harni din ma dake tsaye ina kallon su. Ban san gulman da yakaini daga ido na kalleshi ba sai ganin shi nayi ya sha mur fuskan shi tamau yai min alama da zaki fadi da ido kawai. Ko da Usman ya dawo yake ce min ashe ko abinda ake fadi akan dan uwanki da gaske ne kuwa ? Ance ba ruwan shimana amma ni sai naga ya wani basar dani ko don yagan ni da kaunar shine yakawo hakan. Nace ai ba ruwan shi kila dai akwai abindaya bata mashi rai ne kawai yace Allah yasa ba don ni bane dai ? Yana nan har gap da magariba mukai sallama ya wuce abin shi ni kuma na ahiga gida ina tunanen halin yan gidan mu har wa ya gane gidan su Usman yaje ya fada wa matar shi magana. Suna barin gurin batare da ya kallo Bashar ba yace waye wanan guy din , Bashar ? Wa wai wanda ke tare da Fatima yace shi mana a ina yake ne ? Dan nan garin ne mana ni nasan shi da dadewa ina ganin kaman aikin banki yakeyi ne ai. Sai dai guy din dan karyane tun dana san shi bai aje kan shi kusa ba akwai shi da karya sosai wallahi. Zai iya kashe wa mace kudi sosai don ta so shi amma yana da aure don gaskiya na san na taba sanin yai aure a baya. Tsuki yaja yace, wanan yarinyar ko ina take kwaso maza haka kamar ita kafai ce budur wa a gidan nan? Dariya Bashar yayi yace kaida may kake nufi ne wai wanan tsaleliyar budurwa haka wa zai ganta ya barta ko don ma dai tana da kamun kai bata da rawan kai ai da yanzu kofan gidan ku ya cika da samari. Da sauri yace wallahi da naci uban ta kuwa Allah. Dariya sisai Bashar yake mashi yace oho dai indai mutum yace girman kaine ai gurin zurfin cikin tsiya sai asha mutum a banza. Kafito fili kawai kabada kai bori ya hau ka tsaya kana wa mutane kwanaye kwanayen banza haka. Wallahi Bassh kana son ja min raini Allah ni irin kane da zan bayar da kaina ga karamar yarinya haka nagane a gurin wanan yarinyar karamar yar kauye ban da tarin kauyanci. Fatima ce yarinya U F ? Ba yarinya bace tsohuwa ce ke nan ko ? Sai ja tsuki tare da kawar da kan shi ga titi sai dai cikin zuciyar shi tunane yake yadda mazan yanzu basu jin kunyan hada halaka da yara kanana haka? Wai to kai ban san yaya kake daukan kanka ba fa wanda ko 28 bai cika ba kana ta daukan kanka wani old man can. A ganin ka ba ni kan ai nasan yanzu nakai yadda baka tsanmani don kagan ni ban girma ko ? Dariya Bashar yai mashi yake ce mashi niko nafi kowa sanin yaya kake ai ka girmi duniya. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,, DUK WACE TA TURA MIN NOVEL GA WANDA BAI BIYA BA ALLAH YA SAKA MIN AKAN MAI SHI,,,,, Fuskan ta a daure ta watso min harara tace shige ciki da wanan wasan banzan naku, simi simi nabi gefenta na shige cikin gida. Binshi tayi da kallon mamaki shiko ko a jikin shi saima gyara hannun rigan shi yakeyi kawai. Mama batai mashi magana ba sai kutawan da tayi ta shige ciki yace a fili i will dealing with you silly girl kawai. Duk nabi na takura kaina sai jira nake mama tai min maganan amma shiru babu zancen haka yasa na sake gaba daya. Rayuwa tana ci gaba yayin da takuran da sadauki ke min bai fasa ba don duk wani aikin shi nice zai saka komai wahalan aikin kuwa. Zancen Maryam da Bashar har ya kawo gida yanzu don iyayyen shi sunzo gurin Baba. Sadauki sai da ya dauki zafi sosai da Bashar har ya gaji ya sake don kan shi don Bashar din ya nuna mashi halin ko in kula ga yadda yake nuna mashi . Halin zaman kishi na gidan su mama yana nan daram bai gushe ba don sai da suka samu mahaifiyan Bashar da cewa don may zata yarda ta hada zuria da wa yan nan mutane masu jinin tsiya fakirai masu gadon tsiya. Inba yanzun ba da saudauki ya samu abakin may Hauwa,u take a gidan wace bata iya mayar da taro sisi zuciya ya mutu mata. Amma dai yanzu ai Alhamdullahi ko don dama azziki ai gida biyu ne ko kai kayi ko danka yi ? Mahaifiyar Bashar ce take tambayan su da hakan tace ai shi arzikin da yafi na iyayye dadi don zaka koma tankar basarake ne. Baku jin ance bayan wuya sai dadi ba, dama cewa kukayi yarinyar bata da halin mutunci ne kila da sai na duba. Amma Alhamdullahi, na zauna da yaran nasan halinsu don haka aure ne idan Allah yayi a tsakanin su nafi kowafarin cikin hada zuria da kamilan yara irin zurian maijidda a duniya. Sai kuma suka fara cacan baki wai sun gane dama,kwadai ne kawai ya kai Bashar ga maryam don dan abinda yake samu ga,sadauki din. Dama sun sani ai don haka ya raba shi da kowa nashi ya manne mashi kamar cingun. Da,Bashar ya dawo ake fada mashi bai nuna bacin ranshi ba don yasan zasu iya hiya da hakan ma. Amma yana barin gida direct kasuwa ya nufa gurin Baba ya fada mashi komai yace ai masu Umma iyaka dashi da uwanshi. Ran Baba yai matukar baci sosai haka yasa shi dawowa gida a lokacin yai sa,a basu jima da dawowa daga gantalin su ba ke nan. Ganin Baba gida ba lokacin dawowan shi ke nan ba yasa kowa mamakin ganin shi cikin wanan lokacin. Gaba dayan su ya kirasu basuyi tsanmanin zancen bane sai da Baba ya tambaye su da cewa Atika ke da Asiya ina kuka tafi ne yau ? Wana ta dubi waccan suka fara a tsakanin su sai umma ce yar gadara tace asibiti muka shi gaida Hanse yace abisa umurnin wa kuka tafi? Yace bama wanan ba don na riga na barku ga Allah kan fitan da kuke yi bada izini na ba a gidan nan. May ya kaiku gidan marigayi salisu mai engine ? Da mamaki mama ta dago tana kallon su sai hjy kubura ce tace gidan Alhaji salisu mai engine ai gidan su Bashar din da zai auri mayam ke nan mana. Yace eh can din? Shiru sukayi sai Umma tace da muka je ance maka munyi wani abin ne acan. Yace mai zaihana kuyi tunda shi ya kaiku yace da farko da Sani ya fada min kuka soke zancen auren sadauki da Rahama ban yarda ba sai yau din nan nayar da da hakan don kaidin ku ya wuce yadda nake tsamanin ku. Na dauka duk wani "da da ya fito daga tsatsona kamar kuma dan kune a gidan nan kuma. Ya girgiza kai yace ashe nayi kuskuren yin wanan tunanen a kanku don ku din nan ba abokan zaman alheri bane a gareni tun da har kuka, iya wanke kafan ku kuka tafi soke auren yar yaruwan ku. Salati suka saka suna fadin yaushe akai haka su sheri a ka kulla masu kawai daga sun tafi, gaida mahaifiyan shi kawai. Yace to yanzun dai Bashar ya samayni ya roke ni nai maku kashedi akan gidan su da uwarshi don haka duk wacce ta kara shiga harkan shi duk abinda yai mata ita tajawa kan ta tunda daini bada izzina na kuke fita ba gidan nan. Abin bakin ciki da rashin sanin ciwon kai ace kun fi son yaran nan suyi ta zama a gida suna shashanci kamar yadda diyan ku sakeyi suna bata min suna a gari. Abinda Nafisa keyi a garin nan waye zai aure ta a haka da ita watsatsa yau itace wancan party gobe itace gidan mashaya gata kuma gata wai a kungiyan yan madigo a gari. Da sauri Umma tace kan yar ka yar gwal kada ka kulkawa diyata sheri don da baifi daba a duniya. Yace sheri kan Atika aike kika kulawa kanki ke da baki kaunan dan wani da karuwa kina ganin Allah zaibar naki yadda kike so ne ke ? Ran Umma ya baci kan bankada asirin Nafisa da ya yi a gaban kishiyoyin ta nan ta hau sababi tana borin kunya. Yace magana daya ya rage gareku yanzu shine daga mazan har matan duk kowa ta fito da miji tai aure su bar min gida na hakana na huta da fitina haka. Ya girgiza kai cikin takaici jin borin kunyan da Umma ke tayi wai bai kaunan ta ita da diyan ta agidan dabakin shi yake kulla masu Sheri don ya gyara zuciyar masoyan shi. Shidai yafita bayan yai masu warning da gargadi mai karfi kan duk wace ta kara fita bada izinin shi ba har yaji sai tabar mashi gidan shi. Maji ta dawo dakin ta cike da mamakin wanan irin bakin jinin da mutanen nan suke gwada mata haka. Nan take fadawa yaran abinda su Umma sukajeyi gidan su Bashar daga inda nake nace ai sun kai karshen gulma indai gidan su Bashar ne Inna ce ko Bashar din ai suna daidai da su. Waya mama ta dauka takira Inna na ta kwashe duk yadda akayi ta fada mata mama tace Allah ya kyauta nabar su ga Allah. Buki za,ayi a family house din su Baba haka yasa yanzu su mama basu zama a gida sosai don suna zuwa can gidan gurin aikin bukin da za,ayi. Shima yaya sadauki baya zama a gida sosai don ina ga,akwai wani aiki da yasha mashi gaban shi don sai dare yake dawowa gida. Yauma da dare ya shigo har lokacin su mama basu dawo gidan ba suna can cikin gari. Daganin shi a gajiye yake sai dai kuma alama ya nuna min yana cikin halin shi don ya dan sha a lokacin. Maryam waya take da,wata kawarta Amira tana kallon wani season film a tv bayan an gaisa dashi kowa ya juya gur8n harkokin shi. Ni dake zaune da litrafi ina karantawa na mike sai gaban shi na ce mashi a hankali control yourself mr. Da sauri ya dago jajaye idanuwan shi ya watso su a kai na gyada kai nace ka natsu kokabar falon nan tun mama bata shigo ba. Mamaki takaici haushi ya kama shi a lokaci guda yace cikin tsawa ke kin raina ni ko dayawa ? Easy mr behavour self da sauri maryam ta dago ta kalle mu nace akawo maka abincib ne. Ban sani ba ya fadi a fusace sai ya mike cikin rangaji ya bar falon ran shi a bace wanan yarinyar kodai aljannace wai ita ? Maryam na kallona na gyada mata kai alaman ya sha yau tace oh Allah wanan masifa da may yai kama. Mikewa tayi tabi bayan shi, sai nima na biyo su yana tsaye ya dafa bangon dakin shi bai shiga ba yaji muryam maryam tana fadin haba yaya sadauki. Da sauri ya juyo takaraso tana fadin kada kaga laifin Bintu gaskiya take fada maka tsawa ya daga mata lokacin nakaraso gurin. Ya bini da wani mugun harara yace sai na karya ki a gidan nan wallahi yar iska mai balain sa idon tsiya kawai. Sai kuma yai shiru tare da kyatafa kawai ya dafa bango kan shi ya dukar a kasa. Nace yaya kayi hakkuri bani son mama ta fahince ka a hakane wata rana kaji may likita ya fadi a kanta. A guji bata mata rai don dazara akai mistake watara zuciyan ya buga a lokaci guda za,a iya rasata gaba daya. Yaya kana son sanadin ka ace mahaifiyan ka ta rasa ranta kan bacin ran ka ne ko yaya ? Maimakon yai cikin mu da masifan daya fara yadda nai tsanmani sai naga ya dukar dakan shi a kasa. Ikon Allah sai Allah yau gani mukayi yata sadauki yana kuka kuka kuma mai ban tausayi. Yace maryam bani sha a ko ina sai ina garin nan i don't know why nakejin irin haka kawai a garin nan ? Idan ina garin nan in basha ba bana jin dadi rayuwana sam wallahi sai na dinga jin kaman zan kama da,wutane. Amma kudai tayani addua kawai Allah ya kawo min agaji ga halin nan. Bana son ace sanadina uwata ta samu matsala a rayuwan ta ko kadan bani jin dadin hakan idan na tuna. Kuka ne ya dan fi karfin shi maimakon mu bashi hakkuri sai nima nafara kukan abinda yasa Maryann itama kuka ke nan lokaci guda. No no ku bar kuka please zanyi kokari naga cewa na daina hakan insha Allahu. Nace yaya idan ka fara jin haka don Allah ka dinga nafila kana kai kukan ka ga Allah don ka samu sa,idan jin hakan da kake yi. Ya dago ya kalle ni ina makure a bango kaman zaiyi magana sai kuma yai shiru, ya dade a haka yace ku shiga gida kada wani yazo ya samay ku anan. Har na juya nace abinci fa yaya yace No kibar shi kawai I am OK. Kuka sosai maryam tayi bayan shigan mu gida da kyat na samu na lalashe ta har tai shiru tana tausayawa halin da dan uwan ta yake ciki. Bintu fada min yaya kike gane yaya yasha ne wai ? Nai murmushi na ce da farko idan kinga ya shigo da glass a idon shi to yasha sosai ke nan. Idan kuma kin gashi ya shigo ya zauna yai shiru kaman akwai abi dake damun shi to abin yadan fara sake shine hakanan bai son yawan magana sai kasala kawai yake ji. Sai kuma da zaran kinga yana bukatan abinci a gagauce to abinda yasha ya fita kan shi ke nan sai kiga yana jin yunwa sosai. Zakiga yana shiru shiru sometimes to yana cikin dan maye ne zai dinga zama kaman wani salihi can dashi. Bintu baki ganin kaman asirin da akace su Umma sunyi mashi a cikin gidan nan yake kuma kilama a dakin shine ko makamancin haka ? Nace sanin gaibu sai lillahi anty amma hakan kuma fa magana ce sosai. Tace in hakane yabar gidan nan ya koma gidan shi mana da zama zai fi mashi sauki nake gani. Anty yaya zaibar gida baiyi aure ba? Ke kinga alaman aure a gaban shine yanzu Bintu ? Nace ai irin su mata basu gaban su anty duk matar da zai aura matsayin baibar wanan rayuwan ba sai tayi hakkuri wallahi. Don bata gaban shi idan yasha kuma sai dai yai ta tabara yana zubar da kiman shi a idon ta da jama,an da suke tare. Wai ke ina kika san wanan halaiyar tasu ne haka Bintu ? Murmushin takaici nayi nace a gurin mijin mahaifiyata mashayine shima amma shi irin shan nan na yan kauye yakeyi mara fasali. Nan nai ta bata labari na yadda mamana take hakkuri tana kuma nema mashi maganin hakan ? Nisawa tayi tace shiyasa lokacin da su Baba Sani suka hana yarsu daga baya banji haushin su ba wallahi. Don yau babu wanda zaiso ace nashi na cikin fitina ko tashin hankali haka ai ? ****** ********* ****** Washegari Mama ta tilsata mu kan sai mun tafi gurin buki don ayi kamun amare damu tana fada take cewa, ban san may yasa baku son yin zumunci ba wallahi. Zumunci da kuke gani ba abin wasa bane wallahi don igiyace mai kai mutum aljanna idan Allah yaso. Amma rashi sanin darajan shi yasa kuke sakaci da shi alhalin gaku Allah ya baku yan uwa bila,adadin a gari babu gidan wanda kuke zuwa kullun kuna kulle a gida kaman kayan wanki. Ba don mun so ba muka fara shiri bayan sallah azuhar zuwa gurin sa lalain yan uwan su da za,ayi a family house din su na diyan kannen baban su. Ga ba dayan mu dogayen riguna muka saka muka daura dan kwalaiyan su akawunan mu. Shigar tai matukar karban mu sai dai matsala motar da zata kaimu ce babu a lokacin haka yasa yaya sadauki yace mu bari ya kaimu da Amirah tai mashi magana. Amirah ce agaba tare dashi mu muna baya a zaune sai dai ban san yaya akayi na zauna a setin mirror shi ba na gaba. Maryam ke fadi wai yau kan sai mun sha surutu a gurin mutane yaushe rabon da naje gidan nan ni. Amirah tace ni wallahi ba,son zuwa ne banyi ba yadda ake damun mutum yaushe zaiyi aure yake damuna. Daga inda nake zaune nace kai mutane akwaisu da daukan wa rai shifa aure kamar rayuwa yake idan ya tashi koba shiri sai anyi shi haka ma rabuwan shi idan yazo ko bashiri sai anyi shi. Dago kan da zanyi naci gaba da magana muka hada ido dashi ta glass din motan yadda naga idanuwan shi sai naji gaba na ya fadi daga haka naja bakina nai shiru ban kara magana ba don duk na dago kai dashi nake arba sai ma na daina daga kan nawa kawai. Tun a kwanan gidan muka fara ganin dandazon motacin mutane da sukazo gurin kamun. Wata mata tazo da motar ta shige gaban mu maryam tace shegiya mu akewa kurin mota mima watarana insha Allahu ki gan mu da namu. Nace kai anty kin rage mata kaya bata masan kinayi ba ita, Allah Bintu inason naganni da mota ina ja wallahi. Nace in Allah ya nufi ki ja sai ki gan ki dashi kuwa ai tace wai da su Umma sun mutu ranan. Nace su kuma ai zaman su ke nan hassada wallahi basu ko tsoron haduwan su da Allah. Allah suka sani aida basuje gidan su Bashar suke auren maryam ba inji Amirah. Da sauri ya juya gareta yace kamar yaya wai har muka isa inda zamu sauka tana mashi bayani haka yasa bamu fito daga motan ba sai da tagama mai bayanin komai yadda akayi. Mutanen dake tsatsaye daga waje sun matsu sugs ko suwaye a wanan haddadiyar motatar haka ga shi na cikin motan basu fito ba. Sai da suka gama magana ya bude muna tare da tambayan mu karfe nawa zai dawo ya dauke mu Amirah tace shidda daudai yaya. Nice na fara sako farin kafa na a waje daga gefen da nake zauna sai wata tace dama nasan wasu special ne daganin wanan uban motan haka sai gidan gwauna, muna fitowa ashe su Rahaman shi ce a tsatsaye nan shima ya hango su, Kiran mu yayi muka dawo gare shi daya bayan daya yake muna magana kowace tana juyowa da dariya ganin ya gama magana da kannen shi yasa nima na juya zan wuce nabisu sai yace Fatima nace naam yaya yace zo nan na karasa gaban shi. Yace don Allah kada kiyi masu kayanci agurin nan kiga dai duk ido akanku yake. Maganan shi ce tasani dariya a lokaci guda wanda mutanen dake gurin suna zaton ko wani maganan soyayyane yake fada min hakanan. Yana fadin haka yaja mota yana murmushi duk suka bishi da idanuwan su caaaa kowa na son ace itace ta mallaki aana haddaden guy din mai kyaun dan maci ji. Abokan Rahama da yan uwanta ke ce mata kai amma gaskiya kinyi hasaran miji ko dai wanan yarinyance zai aura ne? Tace a kufule kamar yaya zai aureta anfada maku anfasa zancen namu dashi ne halan . Nan suka shiga gaisawa da mutane yan uwa da abokan arziki ana ta masu sheri don yau bukin gidan su ne yasa su fitowa. Buki yayi buki duk guri ya kicimay da kida don an fito da amare su hudu ne gaba dayan su a filin. Muna tsaye gefe sai kallon amaren muke gwananin ban sha,awa nace anty Allah ya nuna muna naku muzo musha bidiri muma. Ameen ke dai Bintu inji maryam itako Amirah cewa tayi nifa duk wanan abubuwan basu damay ni ba fa. Nace nima nafison in zanyi aure aimin walima haddade wallahi duk yafi wana gwatsale gwatselen da mata da yara keyi. Ji mukayi wai ana kiran dagin amaryam su Amirah su fito suyi rawa a fili basu so fita ba kuma banyi tsanmanin zasu jani tare dasu ba sai ji nayi maryam ta jawo hannu mun shiga fili tare ban iya rawa ba don ban ma,taba yi ba don haka takawa kawai nake yi a hankali. Kaina a duke naga su maryam su falle jakkan suna min liki take guri ya hau ihu da sowa sai tambaya mutane keyi wacece ita da suke mata likin kudi haka? Komai namu a gurin a natse muke abin mu cikin nuna sanin ciwon kai da kuma tarbiya. Muna gefe mu kaji guri ya kaure da sowa maryam ke tambayan ko su waye wata tace wai ance wasu mashaya ne yan uwan su amaryan yan mata suka zowa kawarsu kara. Innalillahi wacece kuma maryam taja min hannu Anty Amirah na gaba muka leka Nafisa ce da kawayen ta suke wani irin rawa gasu sunyi shega zakace akwatawan ghana ne su guri ya rude da sowa masu tir da Allah waddai suka shiga bakin su. Daganin su a buge suke don rawan ba rawan kai sake bane har gaban samarin da suka shigo suke shigewa. Kiran wayan da sadauki yaiwa Amirah yasa mu saurin barin gurin muka fice a filin gada ma agan su ace yar uwar su ce. Mun shiga mota su Amira sai yankan fada sukeyi suna tir da Allah waddai da halin rayuwan Nafisa. Maryam tace yau maganan nan sai yakai kunnen Baba ai akwai magana agidan nan yau wallahi. Umma tagama jin kunya da nauyi ya agaban su fa su Nafisa ke wanan rawan tsiya waisu ga yan iska. Allah dai ya shirya su damu baki daya nace daga inda nake a zaune sai lokacin yai ajiyan zuciya bai dai yi magana ba. Maimakon mu tafi gida sai wani hanya ya dauka da mu can hanyan masarauta. Gurin kaman company sayar da motoci ne yana tsayawa naga mutane suna nufomu suna gaiyar dashi daya bayan daya. Amirace kawar shawaran shi da hira dama yace Amirah tace na,am yayana yace kin san gurin nan tace ,a,a yayana yace kallo signboard din can ki karan ta muna alokaci daya duk muka daga kan mu an rubuta da mayan haruffa kamar haka. MAJI ENTERPRISISE da sauri kowan mu ke kallon shi a cikin mamaki maji suna kuma kaman na majin mu? Natane yace cikin rashin ko in kula ya fadi hakan gurin muke zagawa muna duban motocin dake gurin latest masu kyau da tsada yakai mu wani layi yace ga layin na mata da ake yayi nan mukai ta kallon motocin cikin mamaki. Wanan tace ai wancan yafi kyau haka sukai tayi a tsakanin su naga wani assh color nace amma wanan sai naga duk tafisu kyau kai amma dai Bintu baki san mota ba wallahi nace ina kuwa zan san su anty daga jaki sai rakumi na sani dandamama doki. Wani irin dariya suka samin ganin yamma yayi daga inda yake tsaye yanufo yana fadin mujen ku magariba ya kusa yanzun. Muna hanya maryam tasakani gaba da,sheri wai nace jaki da rakumai na sani dan dama dama doki. Shima dariya yai min yace bana fada maku yar kauye bace kunki yarda dani, Amira tace ,a,a gaskiya yaya yanzun Bintu ta wuce irin bakauyan da kake nufi fa. Yau gasgi harda rawa tayi a gaban mutane ida dane waya usa yasa Bintu rawa a bainan jama,a haka. Yace ai bata da kunyane ki shiga rawa gaban mutane kamar wata chuss can dake, da sauri na dago kai muka hada ido a gaban motan da yake Amirah tace ai duk mune don mun fita rawa ita da take wani yauki kaman a gaban saurayin ta take. Kila yana gurinne tunda kukaga tayi hakan kin san yar tara samari ne ita bata da kunya ai. Ai duk rawan karya mukeyi da mukaga uwayen mu sun iso aikowa ya jaye gurin gabadaya aka basu fili. Ni dai har muka iso gida ban yi magana ba shiru nayi kada ya disgani yadda ya saba yi. Sallah muka fara gabatarwa tukun muka dawo falo muka zauna sai ga mama sun dawo daga gidan bukin. Sai faman yi mata sannu da zuwa mukeyi maryam tace maji yau munga abin mamaki gidan saida mota da sunan ki wallahi. Sunana kuma ? Maryam tace wallahi maji har gurin yaya yakaimu mu gani muna ta mamaki. Wayan Baba ne ke kiran mama a lokacin bayan ya tambaya dasun dawo tabashi amsa da eh sun dawo tana gida yanzun haka. Nanmuka ga ta mike ta fita daga dakin zuwa can mukaji hayaniya a tsakar gida maryam tace kuyi shiru mu ji don Allah, Kaman fada ake a tsakan gida muna ji muka kwasa zuwa waje da saurin mu Baba ne da Umma yake ta ja mata Allah ya isa akan Nafisa tana mayar mashi da amsa. Sabon tashin hankali sai ga Amirah tashigo gidan abuge ta ita tayi tatil kawayen ta sun kawo ta kofan gida sun zube ta haka. Ranan muga tashin hankali don Baba zubewa yayi kofan shi da sauri su mama suka tare shi suna mashi fitara. Yaya Sagir yana gida shi ya fara jibgan Nafisa baji bagani cikin bacin rai gida sai koke koke sukeyi . Itako sai tabara takeyi tana fadin magana irin nasu na yan maye bata fasa magana ba shi kuma bai fasa dukan ta ba. Abinka da yan uwan taka sai ganin su Amirah nayi suna rike shi suna bashi hakuri yayi hakkuri kada ya halakata. Yana barin dukanta utakuma Umma ta shiga jibbagan ta kamar an aiko ta tana kuka gwanin ban tausayi da ita. Maryam.takira yaya sadauki ina jin yana kusa shi yazo ya dakatar da Umma yana bata hakkuri ya dauki Baba suka nufi asibiti dashi. Haka muka zauna jigun jigun damu agidan babu dadi don harka ya lalace ranan baki gaba daya ya mutu wa Umma. Can mukaji tana kuka tana fadin wallahi bata yarda yiwa Nafisa akayi talalace kaman yadda dan maishi ya lalace ita wallahi bata barwa Allah sai ta dauki fan sa. Anyi daidai sun dawo da Baba lokacin hajiya kubura tace ji mahaukaciya kawai sai ki matsa ai kaikayi koma kan mashekiya ce akan ku zai kare yan banza. Nan kuma suka shiga sabon cacan baki a tsakanin su da mummy sai zage zage da tonon asiri sukeyi. Kai haba mummy ku tausayawa bawan Allah nan mana ku dubi halin da yake ciki da wani zaiji da fitanan ku ko da abinda ke damun shi. Sadaukine yake wa mummy magana tace ai na bari sadauki amma in Alhaji ya mutu gidan nan da hjy Atika da diyan ta zamuyi kuka wallahi. Yaran kawai gasu nan ba,a gama wani ba su jefa mutumi a wani yaya za aiyi mutum yai lafiya haka ? Muna shiga daki bamu jima ba mama ta shigo dakin ita ma ta zauna jiki ba karfi tare da ajiyan zuciya. Tace ni fitinan gidan nan wallahi ya fara isata abu tun ana da jajjayen sawu har girma yazi baza,a daina ba. Tun farko shiyasa ban so zama ba wallahi babane ta tauyeni wai na zauna na saman ma sadauki abokan shawara a gida shine kukaga har nakai war haka a gidan nan. Mani mukan ai gara da kika zauna da bamusan inda za,a haife mu ba kuma inji maryam cikin dariya. Mama ta harare tace wawiya kawai don baki san irin wahalan dana fito cikin shi ba ko ? Mama al,amarinki kaman na mamana,wallahi haka sukai ta,kwasa da mama ta bawa har mamana tagaji tabar mata gidan gashi ko yanzun dai sai hakali. Maji tace haka abin yake yanzun ai a hanaka zaman lafiya gidan mijin ka in bakakai zuciya nesa ba sai ka bar gurin gaban kuma da kake hange sai dace. Tambayam bazata mama ta jefo min daidai lokacin da na daga kaina sama ina tunanen halinda mahaifiyana take ciki a can kauye. Wanan tunanen bayau na farashi ba walau in naji dadi ko naga wani abinda ya danganta da rayuwan ta. Muryan mama tana ce min Fatima yayan ku ya shigo yaci abincin shi kuwa yau ? Da sauri na dago kai ina kallon ta don tambayan ani ya bani mamaki nace ina ganin baici ba don tunda muka dawo banga ya shigo ba. Tace dubo min shi a,waje ko yanan nai magana dashi naji may zai ba su baban ku gudun mawan buki? Namike tare da zura takalmina ganin a cikin gida zan tsaya sai ban saka hijjab dina na ba nafita haka nan. Na duba waje baya nan kaman nakoma na fada mata sai nace bari na leka dakin shi tunda naga wuta a bude. Na leka sai naga kamar bai ciki hakan yasa na dan kara takawa ciki zaune yake yana shakan wani abu a wabi farin takarda haka. Jin motsina yasa shi saurin dago kan shi da sauri mukai ido biyi da sauri na juya zanbar dakin. Abinka ga dan kwallo tako data ya cafko ni sai jikin shi ta baya zan saka ihu ya danne min bakina da hannun shi daya. Bakina yana matse nake ce mashi mamace tace nazo na dubaka wai tana magana da kai . Saboda hannun shi daya ya taushe min baki bai bari yaji abinda nake fadi ba. Birkito dani yayi daidai fuskan shi muna kallon junan mu face to face ni dashi a hankali yace may yakawo ki dakina muna fuka ? Ya dan sauke hannun shi daga bakina nace mama ce tace nazo na,,, sai ya kara matse bakin iya karfin shi. Mamaki da tonon asiri sai jin saukan hannin shi nayi zuwa kirjina yana fadin abinda kikazo nema ke nan bakar jarababiya kawai. Na girgiza kai idona a rustse nace da karfi wallahi mamace ta aiko ni gurin ka. Bai sake ni ba kuma bai fasa abinda yakeyi min ba a lokacin, wasu hawaye naji sun fara dan silalo min daga idanuwana. Bin jikina yake a hankali da shafa yayin da nake jin saukan numshin shi a kunnuwa na cikin wani bakon yanayi. Cizo nakai ma hannun shi nace da karfi wallahi Allah ba gulma nazo ba mama tace nazo na kiraka wai . Daidai kirjina ya tsaya ya dakata da abinda yake min nace don Allah yaya ka sake ni in tafi wallahi mama ta aiko ni na kiraka . A hankali yakai hanniwan shi saman kirjina yadan shafo su cikin hikima irin ta maza da sauri na dan sulale nai kasa don abinda naji a lokacin. Kara dago ni yayi daga dan dukawan da nayi ya dago fuska na tare da hada shi da nashi ban aune ba yakai bakin shi ga nawa ya dan fara tsotso a hakali. Nan na shiga ture shi daga jikina kaman dutse nake turawa don ko motsi baiyi ba kuma bai fasa abinda yake min ba. Can naji ya turani da baya da karfi tare da dafa bango yace yar iska gobe ki dawo min daki kadan kika gani yau. A hankali na dafa bango tare da dan bugewa cikin kuka nake fadin har nakai kofa wallahi ban yafe mugu mazinaci kawau aiko ta biyoni a guje ban tsata ba sai falon mu. Yaya haka kuma da sauri mama ke tambayana tare da son jin bayani daga gurina tana kallona. Nace cikin kuka ba yaya bane ya kai min nashi wai may yakawo ni dakin shi. Sai gashi ashe yana bayana a lokacin sai kamshi yakeyi kamar bashi ba. Tace kai kuma daga na aika yarinya ta kiraka sai ka kai mata nashi kai dai wallahi sadauki katon banza ne wai dadin may kake ji gurin zaluntar yarinyar nan? Yace haka tace maki nashin ta nayi ? Ai duk ni na ja mata hankan tana zaune zaman ta ta tashi na aike ta kiran ka na manta kai mugune gareta. Inda nake zaune ya dan kalla sai faman zubar da miyau nake ina tofarwa tare da goge bakina da dan kwalun dana cire akaina. Gashina daya sha gyara yana kwance hat gadon bayana yasha gyara sai walkiya yakeyi. Murmushin ke ta ya sakar min tare da dan kashe min idon shi guda daya. Mama tace mai dama zancen abinda zakaba iyayyen kane maza masu buki, don banji kace min komaiba har yanzu kan zancen. Yace ni maji may zan basu kuma ? Sadauki iyayyen naka kuma suna buki zakace may zaka basu bayan kowa yanzu yasan kana dashi. Murmushi yayi kamar wanda yake a cikin nishadi yace OK maji sai ki fadi abin da za,a basu din ai ina ganin is OK. Nasan aljihun kane Baba na balke na shatama ko nawa zaka iya ba iyayyen ka yace, maji ki fadi kawai ba matsala ai tace hamsim hamsin yayi ko yace kai haba haba mji adai basu koda dari biyu biyu ne ai ina ganin is ok for them, Kai yaya har dubu dari biyu biyu baiyi yawa ba yace baiyi yawa ba Amirah bari a basu kawai. Yana fadin haka yace maji abari har da safe sai na ciro masu na kawo maki kiba Baba ko ? Har lokacin ina zaune sai hawaye nake zubarwa ina bakin cikin abinda sadauki yai min yau ashe dan iska ne haka ban sani ba shi da yake ikirarin cewa bai taba zina ba ashe tsohon mazinacine haka ban sani ba. Nai zurfi a cikin tunane na nake jin muryam maryam da karfi tana fadi, da gaske yayan mu yace saka hannun shi ga aljihu yace kowa tazo ta karbi nata key din gashi sai lokacin na dan dago ina kallon su. Keys ne ya ciro daga aljihun shi yana mika masu nakai ido ina kallon keys din . Yace kowacen ku wanda ta zaba dazun shine nata juyawan da zasu gurina sai ganin ina kuka sukeyi. Lah Bintu badai har yanzu kukan dan nashin da yayayai maki ki ke tayi kamar wani nashi can. Ya dago tare da kallo yace au wai kuka takeyi bafa wani nashi sosai nai mata,ba dama nasan kukan shagwaba da jin dadi zaki tsaya yiwa mutane haka. Ya kare maganan shi cikin lashe bakin shi kamar wani maye can nace a fili mugu azzalumu kawai na mike na shige daki cikin kuka. Dan murmushi yayi tare da lumshe lumsarsu idanuwan shi da da tun shigowan shi falo suke mashi haka. Ko may ya tuna sai yai murmushi tare da bude idanuwan shi caraf acikin na maji tace Baba na wai wani irin keta kaiwa yarinyan nan yau haka har kasa ta kuka. Yace bata fada maki ba maji dan kai mata nashine fa nayi kuma ban ma samay ta sisai ba fa. Wallahi kadai ji tsoron Allah gashi don tsaban ket kasa yar mutane kuka haka idan bata ji zafin abinda kai mata bata bacin ka haka yau. Ai ba yau kafara mata kyeta ba amma bata taba fada haka ba ido da ido sai yau ? Wallahi maji bata jin magana ne tafaye shegen gulman tsiya kungan ta nan. Mi dai bata taba muna gulma ba don muke zama da ita sai dai ke da ka saka mata ido don kiyayya kake ganin haka gare ta. Kiyayya kuma maji aiko yayana bai ma Bintu haka kawai dai ke ke ganin hakan wallahi amma ita,ai Bintu ba baya ba itama kingan ta shegen tsokanane da ita. Anty Amirah Anty Amirah wallahi ki iya bakinki akan Bintu da yayan mu, inba haka ba watarana zakiji kunya sosai wallahi. ****** ********* ****** Kwance ya ke saman gadon dakin shi rigingine ya saka hannun shi yai crossing dashi idon shi biyu amma yanayin kwanciyan shi sai kace yana barci ne. Saboda idanuwan shi da suke a lumshe a lokacin a hankali yake tariyo abinda ya faru a tsakanin shi da Fatima. Hannun shi da ya sauke akan kirjin tane ya fado mashi a rai yana tunanen may ya hanashi ya cire hannun shi a jikinta a lokacin. Murmushi yayi da yadda ya samu sa,an bakin ta ya tsose su yadda yake so son ran shi. Wani murmushi yayi naketa yace gobe ki kara yar iskan yarinya kawai gaba abinda zan maki idan na kama ki sai yafi wanda nai maki yau. Dariya ya kwashe yadda maji ke fadan wai ya nashi yar mutane ba gaira ba dalili don cin amana. Yasan da yau maji tasan abinda yai wa yar nata da ya shiga uku a gurin maji da masifa sai yabar garin ba shiri. Yakwashe da wani irin dariyan keta shi kadai yadda ya ga na koma gefe ina kuka a falo dazun da ya shiga. Yace a fili may be this is her time to have romance with somebody ? Ina daki barci ya gagati indona nayi brush yafi a kirga kafin na kwanta don ina ganin ya zuba min abin mayen shi ga bakina kila ga kazantan da nake ji a raina. Har anty maryam tafara zargin may wainake ta wanke ma bakine tun daxu nace mata ina jin bakina badadi ne yau. Tace aike ne dan abu kadan idan yaya yai maki sai ki ta faman mashi kuka shiyasa yake jin dadin yi maki kyata ai. Kema ki zage kai ki dinga ramawa idan yai maki bawai ki zauna kina kuka ba tunda naku sallon takon ke nan a haka. Hararan ta nayi nace don Allah anty barni kada ki kara min bakin ciki naja bargo na rufe jikina don sanyin da akafara a lokacin. Washegari ban fito da wuri ba ina gudun in fito na hadu dashi a falon sai guraren shadayan rana nafito falon . Ban dade da zama ba sai gashi ya shigo falon da sallaman shi nan suka shiga gaidashi ban dani da nai kaman ban gan shi ba. Nan ya dora idon shi a kaina ko kyaftawa bai yi yace ke baki iya gaisuwa bane halan yar kauye? Da sauri na mike tsaye zanbar falon yace kina tako daya daga gurin nan yanzu sai nai maki abinda kike so. Cak naja na tsaya guri guda ban motsa ba daga inda nake yace look at her kamar wata takwarai can nan ko shedaniya ce ta karshe. Na juya nace ni wallahi ba shedaniya bace sai dai in kaine shedan,,,,,,,,aiko ina ganin ya taso na ruga ciki da guda na kargamay kofan daki ina mai da haki. Yace ashe ke karamar yar iskane ai daki bari na samay ki gurin yanzu na wujujugaki wallahi. Daga cikin daki nace anki a tsaya din mugu kawai macuci yace ai kama ki zanyi sai kin fada min waye mugu a gidan nan. Ban fito ba sai da na tabbatar da yafita daga gidan ina fitowa suka kwashe min da dariya Amira tace kai Bintu ga tsoro gajan magana ai shine maganin ki wallahi. A raina nace baku san komai ba da bakuce min haka ba kuma da kun raina shi wallahi. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,, YA ALLAH DUK WACE TA TURA MIN NOVEL GA WANDA BAI BIYA BA ALLAH KA SAKA MIN AKAN MAI SHI,,,,, Zaune yake a falon fuskan shi a daure tun da ya shigo gidan yake hakanan mama ta fahince shi amna sai batai mashi magana ba. Yana nan zaune ya dafe kan shi yai shuru tare da lumshe idon shi Amirah tafito ta gan shi zaune a gurin tace ,a,a yayana ashe ka dawo ne yace eh a takaice kawai. Takara cewa yaya akawo abinci ko don mun san shi ke shigo dashi cikin gidan wani lokaci. No Amira barshi kawai wanan abinda nasha dazun is ok for me, ya mayar da idanuwan shi ya lumshe su. Can yace Amirah ta amsa da na,am yaya. Ina wanan yarinyar take ne? Tace wa ke nan yaya? Yace Fatima. Suna ciki ita da maryam ina ga kaman waya takeyi ma dana fito. Yace kiramin ita please ? Ta mike na fadin toh. A tare muka fito mu uku a lokaci guda tanagaba ina bayan su . Yadda muka samay shi yasa mu dan shan jinin jiki don babu fara,a tare dashi. Nace a yar murya gani yaya ya dago jajjayen idanuwan shi da suka sauya zuwa ja jajir sai da gabana ya fadi. Yace ke a ina ki san wanan guy din dana gan ku tare a waje dashi ? Shiru nayi na dukar da kaina kasa ya dago cikin hasala yace ba ke nake tambaya ba ne ? Nace a,anan garin yake. Kin san ko shi waye da kike tsayawa dashi ne ? Maryam tai tsagal tace yaya a banki yake aiki nan gari yake da zama ai kuma dan ga,,,, Ban tambayeki ba maryam ita nake son ta fada min abinda ta sani akan shi kawai. A hankali nace ban san komai ba akan shi yadai zo yace yana so na ne. To ki rabu dashi daga yau kada na kara ganin kazamin motar shi a kofan gidan nan in ba haka ba sai na sa an kulle shi wallahi. Kai wai yaya haka may yayi shi mutumin da zaka yanke masu wanan hukuncin haka ? Maji ban yarda da shi bane don bai da record mai kyau, shine dalilina kawai. Kallon shi mama tayi kamar zatai magana sai taji na ce nagode yaya na juya na bar falon jikina yai matukar sanyi sosai. Ina tunanen wani irin halin banza ne ga Usman da yaya ya yanke min wanan hukunci a kan shi. Sai kuma nace tau Allsh dai yai min zabi mafi alheri da kan shi. Amma maganan yana ci min zuciya sosai ga Usman yana kirana amma sai naki daga wayan har ya tsinke. Haka yai ta kirana yana min text amma ban bashi amsa ba sai daga karshe yace nagane wanan dan wullakancin yayan naki ne ya hanaki hurda ni. Don dama tunda naga yadda yai min na fahinci shima yana kaunan ki don irin kallon da yai mi tare da kin amsa gaisuwa na. Wanan massage din yasa na dauki waya na kira Usman din nake ce mai tir da maganan shi, don mai zai min wanan furcin ga dan uwana. Fatima kada ki boye min nasan komai wallahi nasan shi ya hana ki kulani kada kice zaki boye min ni ba yaro bane fa. Haushi ya kara bani nace ashe da gaske baka da mutunci usman ni ka sani kawai don matarka na lura tafi karfin ka shiyasa na daina kulla ka kawai amma kada ka kawo min wani magana can na daban. Sai na kashe wayan na fara tunanen zancen Usman may yasa wai duk masu sona suke zargin hakane ga yaya sadauki. Ni dai iya sani na babu wani abin soyayya daya taba hadani dashi banda hattara da tsangwama da kina da yakeyi. ****** ********* ****** Sai bayan kwana bakawai da zuwan shi muka wayi gari da abin arziki don tsaraban mota mama da Baba suka samu inda yai masu Umma kuma kyautan kudi masu yawa. Ni dai ko tsinke bai bani ba dama tun ranan da yai min wanan magan muke zaman yar tsama dashi bani yarda mu hadu dashi. Kaman nasan bani da tsaraba, sai Allah ya rufa min asiri ban ma fito falon ba a lokacin hayaniyan ihun su nake ji suna murna a falon. Maryam ce ta shigo dakin inda nake tana nuna min sabon wayan ta mai matukar tsada daya canza masu da sauran tarkacen daya kawo masu. Nace kai anty amma kun gode yaya yayi kokari sosai wallahi Allah ya saka mai da alheri. Tace mama ta samu mota har da Baba kai ina son irin wanan tafiyan na yaya wallahi don a jike yake dawo muna idan yayi nasara ga ball din shi. Tace a,a na fa manta sai yanzu na tuna banga yaya ya baki, naki tsaran ba ko dai abin yar sirice kuma? Nace don Allah anty maryam daina wanan zancen kin san yaya mugu ne kada yaji zamana a gidan nan yakare da mama. Taso muje ki ga tsaraban mu don Allah kada ta tsanmani wani abu na sauko daga gado muka fito tare da ita. A zatona baya falon amma ina fitowa yana zaune sai dai kwana biyun da banganshi na ya sake min sosai. Gabana ya fadi don sai zuciya ta ta fara zargin ko dai yaya koma ruwa ne wai don yanayi yau da na gani akwai magana gaskiya. Ganin shi zaune yana waya muryan shi kaman mai jin barci ko kasala haka ya kara tabbatar min da zargina akan shi. Na nufi inda mama take zaune, cikin murmushi nace mama ashe alheri ya samay mune haka yau ? Eh amma ai bai gama ba don banga ya nuna min naki ba duk cikin tsaraban. Nace kai haba mama kullun fa ana bani don yau kawai ai ba komai bane kila ya manta da nine kawai. Murmushin manya mama tayi tace ya manta dake Fatima, haba magana dai yana da dalilin yin hakan da yayi kawai. Ya dago still cikin irin muryan farko da yake waya ba ko darr a ran shi ya ce, wai wanan yarinyar ban mata ba ban dai sayo mata bane ai na fada mata tun a cikin waya ba zan sayo mata komai ba. O ko gadarare ya mike tsaye tare da gyara wandon shi da ya dan takure don zama yace eh maji. Sai ya fice ko mama sai da tai mamakin wanan irin tsauri da yai mata yau ido da ido haka don ba halin shi bane bata ansa a tsatsaye. Yana fita dakin shi ya shiga dakin duk a hargitse haka ya kwanta rubb da ciki don tun daren jiya yai mugun hadiye kwayoyi ko zai rags damuwan shi a ran shi. Duk abinda nake hankalina yana ga yaya sadauki don haka nace wa mama zan shiga gurin gwagona don tana gari tana fama da ciwon kafa. Tafe nake ina tunane abinyi sai wata zuciya tace min gwada dai ki gani ko zargin ki hakane ? Ina tura kofan ga mamakina dakin da yake a rufe ko yaushe, sai na samau shi a bude, kamar na koma don na hango shi a kwance rubb da ciki kamar yana barci. A hankali nake bin dakin da kallo har na hango wani farin roba saman dan stoll din dake dakin yana dagwara kaya akai, Na jima gurin ina kallon roba don zargina ya zama gaskiya ko naga evidence da idona. Zan juya naji yace Fatima, Jikina ya dauki rawa kamar na ruga a guje don tsoro, ya ce may ya kawo ki dakina ? Bance kallah ba nai shiru, Yakara cewa uban wa yakawo ki dakina nace maki? Ya dago daga kwancen dayake yana fuskan tana idon shi duk sunyi ja jajir dasu. Bance kala ba sai karasa shigan danayi na taka har zuwa inda roban drugs din yake na dauka nace ga abinda ya kawo ni dama kuma nagani. Komawa yayi ta,kwanta,lamo kamar ya koma,barci nikuma ina tsaye na kasa daga kafata nai bar mashi dakin shi. Lokaci mai dan tsawo na zaci barci ya koma duk a tsorace nake a lokacin, Nafara tafiya sai naji yai yar dariya da sauri naja na tsaya cikin tsoro da sauraren shi. Ga tsoro ya kamani ban san gulman da ya kawo dakin shi ba don gani kwam kuma a part din samarin gidan gaba daya. Hawaye ne na fara zubar wa daga idona a hankali ba tare da ya dago ba yace kuka kuma again cikin magana kamar rada ya fadi hakan? Don Allah yaya kayi hakkuri dama zargi nake tun dazun dana gan ka a haka ? Murmushi yayi tare da mikewa zaune yace, ashe bayan gulma har kin zama C I D ban sani ba ? Haka kawai na tsinci kaina cikin karfin halin fadin gulman da nakeyi a inda ya dace nayi nakeyin shi ba hakana kai tsaye bs ga abinda ba damuwa na ba. Fuska a daure yace, lalaima yarinyar nan ta raina ni wallahi sosai, zaki gane baki da wayo don gobe baki karawa wani bakin shishigin tsiya irin haka. Wani irin naji cikina ya ansa kululu nace a raina yau ko na shiga uku nakawo kaina da kaina. Amma afili nace duk abinda zakai min nasan akan kauna mama kai min don irin halarcin da take min a rayuwana komai zan iya yi akan farin cikin mama don bata nuna min banbanci ba a cikin ku. Shiru mukayi dagani har shi ba wanda yai magana don kukan da yaci karfina a lokacin. Ba tare da fargaba ba naci gaba da cewa why yaya why baka tausayin mahafiyan ka why please ? Kai kadaine da namiji da Allah ya bata a rayuwan ta kaine take tunanen samun farin ciki a gurin ta. Yan uwanka da ma mu dake a karkashin inuwan ku gare ka muke fatan samun budi a rayuwan mu, Amma kai yaya baka tausaya mata baka jin kan ta baka tuna irin gorin da ake mata tsawon lokaci a gidan nan a kan ka why baka tausayawa kan ka da mahaifiyan ka ne please? Kafi son ko da yaushe ka zama abin kyama ga al,umma da kuma abin kwatance a gari yaya kawai Allah kabar wanan harka ka dage da rokon Allah da bayar da sadaka akan Allah ya rabaka da wanan halin kodon goben ka. Ina kaiwa nan na fara tafiya zanbar dakin yace Fatima, naja na tsaya tsaye cak guri guda. Ido ya zuba min na dan lokaci yace wanan magana ta tsaya iya ni dake a nan. Na girgiza kaina nace har abada bazan taba tona asirin dan uwana ba ga wani kai dai kadai tsoron Allah idan wani baigani ba ko yaji ai Allah daya hanamu shan maye yana kallon ka. Murmushi yayi tare da mikewa tsaye daga zaunen daya ke ban tsan mani har ya kawo gareni ba sai ganin shi nayi a gaba na ido da ido muke kallon juna dashi. Banyi wata alaman ta razana ko kadan kada ya gane a razane nake lokacin dashi. Ya nuna ni da yar yatsan shi yace ban san koke wata irin shu,umar yarinya bace da baki da tsoro haka nima ina mamakin kaina da nake tausaya maki amma tafi babu komai zamu kara haduwa wata rana. Nace kadai tausayawa mahaifiyar ka da kan ka kafin har mukai ga kara haduwan. Kuma bani fatan haduwan ya kasance irin wanan zargin a kan ka sai da ya zama wani abin alheri can daban. Roban kwayan na hannu na fita daga dakin tabi bayana da kallon mamakin irin karfin halin dake gareni haka. Sam banda tsoro ko shayin wani a idona yadda ya hango cikin kwayan idona gaskiya ce sahihiyar ta na fada mashi kuma na fita. Ina tafe ina sharan hawaye har nakai gidan gwagona sai da na samu gidan yana rufe tafita ke nan . Na juyo na dawo gida tareda boye roban kwayan a jikina har sai da na kai part din mu ina shiga mama tace har kin dawo ne nace bata nan tafita. Amma kuma ya fuskanki kamar kinyi kuka na dan yi yake nace kuka kuma mama? Banyi kuka ba mama daga haka na shiga daga ciki sai kuma mama ta fara zargin ko dai tsaraban da sadauki bai kawo min bane ya bata min rai har nai kuka? Ina kwance daki saman gadon mu kaina sama kafana suna zufe daga kasan gadon, na dan jingina jikina da kan gado. Ban san shigowan ta dakin ba don nai zurfi ga tunanen da nakeyi a lokacin. Fatima naji ta ambata abinda yasani saurin dago kaina ke nan ina kallon ta da sauri ina kokari gyara zamana da kyau. Itama dai zama tayi daga gefe na kadan tare da kura min ido kamar mai nazarin wani abu a gare ni. Abinda yaron nan yai maki ne yasa ki kuka ko? Da sauri na girgiza kaina nace wallahi Allah ko daya mama ko kadan ban sa haka a raina ba. To may yasamay ki kai kuka da fitan ki yanzu, don ba haka kifita ba a gidan nan. Dukar da kaina nayi kasa nace a hankali ba komai mama,. Yanzu har takai lokacin da zaki iya boye min wani magana a cikin ranki. Da sauri na kara dago kai nace wallahi mama ban boye maki ba sai nai shiru. Bazaki fada min ba ke nan ko? Maimakon nai magana sai na sake kuka shiru tayi tare da kura min ido har tsawon lokaci can tace nace zancen tsaraban da ya rabane yai maki cin fuska kin ce a,a. Wallahi Allah mama bashi bane kuma ba komai, ikon Allah inji maji ba komai kike wa kuka ba to may yakawo kukan? Mama yaya ne sai kuma nai shiru don, na tuna da zancen alkawarin da nayi bazan fadawa kowa ba. Hakali a tashe tace yaya yai maki may hankali a tashe take tambaya may yai maki Fatima ? Fada min mana nace may sadauki yai maki ne wai,? Taba ki yayi ko may ? Nace da sauri a,a mama don nagane may take nufi da tambayana tabaki yayi. To may yai maki nai shiru nace mama ba komai bane cewa yayi wai na faye yau shiyasa maza ke ganina . Sai naji tai ajiyan zuciya tare da dafa ni tace kyaleshi ai munyi maga in don zancen Usman ne ya fada min yaron ba mai gaskiya bane. Nace cikin kuka tau mama ta ce ki kwantar da hankali Allah zai kawo maki wani wanda yafi Kabir insha Allahu. Tace karbi wanan kayan daga cikin kayan lefen da ya aje ne na debo maki kema a matsayin naki tsaraban. Da sauri cikin girgiza kai nace mama a barshi wallahi ko kadan raina bai baci da rashin kawo min ba don ai yasaba kawo min. Au kyautana ne kuma baki bukata ko may na girgiza kaina da sauri na sa hannu na karbi kayan dogayen riguna matsu kyau da masifan tsada har guda hudu. Nace amma mama kaman kayan su yi yawa fa tace nifa na baki Fatima nace na gode mama. ****** ********* ****** Da yamma daya daga cikin rigunan nai kwaliya dashi kaman yadda suma su maryam shi suka saka sai dai nawa yafi nasu tsada da haduwa, nisa ba kusa ba. Sam ban san yana cikin falon ba nafito cikin dogon rigan mai maroon clour sai tsakiya a bude yake an yi mai kwalliya da wani silk dark blue da duwatsu har kasa, hannun rigan manya manya ne shara shara dashi . Kwaliyan yai matukar karbana fa kamshi turare na na white musk da ko yaushe shi nake shafawa a jikina da tufafina. Haka kawai ganin shi zaune yasa kirjina bugawa a lokaci guda yana zaune cikin shiga ta kamilan mutane. Masangalin kujera kawai na dafa nace ina wuni yaya ? Kamar kullun wanan yaudararen idon nashi ya watso min ya na kallona a fakaice, da su. Kai Bintu wanan hadaden rigan fa kuma maryam ke tambayana don bata san dashi ba. Nace daga mai kauna na, a takaice. Kan shi kawai ya girgiza don jin amsan dana ba maryam din a lokaci guda, wayancewa yayi don yasan inda magana ta dosa. Na kalli maryam nace akwai wani tambaya ne kuma anty ? Ai ni dama nasan da,wata a kasa tunda naga ba,a baki taki a fili ba nasan zance ya canza ke nan. Nace wanan kuma zargin ki ne anty ni uwata mai kaunata tabani shi don tasan nina dace dasu. Da sauri suka juya gurin Maji da idanuwan su suna mamaki wanan riga mai bala,in kyau yaya akayi tabani shi gasu. Maji bata bada fuskan tambayan ba balle su san gaskiyan maganan don haka sai kowa ya share zancen. Ganin yanayin shi duk a tsarge ya ke lokacin saboda yana ganin sai na fadawa mama zancen kwayoyin dana kwaso daga gurin shi. Yana zaune ya rafka uban tagumi sai sauraren zancen, kanne shi yakeyi ba tare da yai magana da kowa ba sai kace wanda aka aiko ma wani sakon tashin hankali. Daga inda mama take a zaune muka ji muryan ta tana cewa ku tashi ku bamu guri zanyi magana da yayan ku. Hakan yasa muka mike daya bayan daya muka koma daga cikin dakin mu. Shiko jin abinda mama ta fadi yasa shi saurin dago kan shi da sauri yasan ta faru takare kenan yanzu sai da munafukan yarinyar nan ta tseguntawa maji zancen nan aiko sai ball da yar iska gidan nan algunguma kowa ya huta. Tace Baba na magana nake son yi da kai akan Fatima, yace shike nan yar iska tafadi ashe. Ba karamin kokari yayi ba gurin gyara natsuwan shi tare da dan dagowa daga kujeran yana fuskantar uwar. Mama tace ina son ka fada min gaskiya may ya hada ka da Fatima dazun da rana tashigo gidan nan tana kuka? Yace maji ita may ta fada maki nayi mata da ta shigo? Kai ma kasan halin Fatima da zurfin ciki da kyat na samu ta dan fada min wai kace tana kwaso samari kala kala a gidan nan. Yanzu har wasu samari Fatima ke dasu ina bayan wancen da Allah baiyi auren su dashi ba sai wanan da kace baka amin ta dashi ba kuma ta daina nagani. A jiyan zuciya ya sauke yace ta rufani ke nan ashe ai nazaci bata da,wayo ne ? Tace tunda kai mata fada kuma taji banga abinda zaisa kuma ka kara matsa mata ba akan zancen. Murmushi yayi yace maji ni fa duk abinda nake mata a saboda ke nake matashi don tana karkashinki ne. Idan da a, wani dakin take mai zai kaini saka mata ido da daukan mataki a kan ta amma tunda bata son fada ai shike nan. Maji tace dakata malam yarinyar nan fa amana take a gurina ka sani amma irin yadda naga ka dauko tsangwama mata bazan lamunci hakan ba gaskiya. Yanzu irin cin fuskan da kai mata ka bawa kowa tsaraba a gidan nan amma ita ka hana mata kayi daidai ke nan Baba ? Amatsayinta amma a guri na ina duk abinda kaga naiwa yan uwanka ita ma ya dace kai mata tunda ni bani banbanta tsakanin su. Waya san ta hanyan da zata taimaka muna itama watarana shi mutum fa rana garw shi ta inda ba,ai tsanmani ba. Yace maji yin haka bada wani manufa nai mata hakan ba kawai dai dama alkawari nai mata cewa idan bata gayar da mutum bazan mata tsaraba ba. Tace wanan matsalar kace don ni na bude akwatin kayan lefen dake aje na zaba mata wanda ta dace da ita. Ya dago kai kamar zaiyi magana sai kuma yai shiru can yace ai shike nan ko? Idan kuma akwai abinda ya dace akara mata daga ciki sai abata suma su Amirah abasu man shafin da turare da sauran abubuwa suyi amfani dashi. Tunda ba wani abin kuma za,ayi da kayan ba yanzu ai, ko ? Kamar yaya ba wani abin za,ayi da kayan ba ka manta da maganan mahaufin ku ne da yace nan da wata daya ku fitar da matan da zaku aura. Murmushi yayi yace maji ni ina zani na nemo mata nan da wata daya hakkuri dai Baba zai yi muna har lokacin yayi. Mama tace wanan kuma maganan ku ne da mahaifin ku idan baka fitar va ai shi ya maka mata da kan shi. Ya zaro ido yace haba maji kamana za,ace za aiwa mata kuma ai ni yanzu na wuce wanan ko. Wancan ma da kukayi da farko ba,aji dadin shi ba balle yanzun ace za,a sake wani kuma again idan lokacin yi yayi ai za,ayi din ne maji. Ina ruwana ina zaune ni a dakina matsalan ku ne da mahaifin ku ni banda na cewa ai. Duk hiran da suke da uwan hankalin shi yana akan zancsn abinda ya faru da rana tsakani na dashi. Mama ta kwala muna kira tace ku fito tun dan uwan ku bai fita ku kara mashi godiya ya baku kayan kwaliyan dake cikin akwatinan shi gaba daya wai ku raba ku uku. Godiya mukai mashi sai dai yana kokarin ganin idona danake boyewa a bayan Amirah. Mikewa yayi don wayan da akai mashi yafita lokacin naji dadin sakewa sosai a falon. ****** ********* ****** Sannu sannu na dan sake jikina na koma normal na bar zancen komai a raina sadai kallon mai bisa ruwa nakewa sadauki doni na tsinke da lamarin shi yanzu. Maryam tafito tana tambayana na bata wani handout din muna chemistry na 200 level nace ta duba a cikin jakad litattafaina yana ciki don ina kitchen ina aiki. Zaro takardan da zatayi sai ganin roban wanan drugs din dana dauko a dakin yaya tayi. Saman gado ta zauna tana kallon maganin tare da karanta shi a fili ta furta drugs kuma a jakkan Bintu. Hankalin ta ya tashi sosai a kitchen ta samay ni tace Bintu zo nan ganin hankalin ta a tashe yake yasa ni bin bayan ta zuwa dakin mu. Sai da muka kai zaune ta zaro roban daga inda ta boye fuska a daure take ce min Bintu may ne ne wanan nagani a kayan ki? Cikin kura min ido bata ko kiftawa don son jin bayani daga gare ni cikin damuwa. Nace ba nawa bane anty nima dauko shi nayi a wani guri na boye shi a nan da kika gan shi. Bintu fada min gaskiya a ina kika dauko wanan roban in ba naki bane ? Na nisa nace wallahi anty ba nawa bane nagi maki kama da mai wanan halin daidai da rana daya ne ? Tace shi ya bani mamaki ai nake son sanin nawaye ? Nace na dauki alkawarin boye zancen anty don Allah kiyi hakkuri amma,wallahi ba nawa bane Allah. Sai naji tace na yaya sadauki ne ko ? Da sauri na kalle ta nace ni ban ce ba anty. Amma kin san zaman su haka a gurin ki hatsari ne babba kuwa a gare ki ? Yanzu dabanice nagan su akayan ki ba kuma nasan halinki may kike ganin zai faru ? Nace nayi kuskuren barin su a tare dani amma na aje su don sheda kawai. Tashi kiyi flushing din su yadda kikayi a ranan tun wani bai gani ba hankalin maji ya tashi. Yadda tace din haka nayi na zubar dasu a cikin toilet suka bi ruwa suka wuce. Nan na barta zaune tayi shiru tana tunanen dalilin da yasa na boye mata tasan cewa na yayan sune duk yadda akayi. Da dare da Bashar yazo ta samay shi yadda ya fahinci bata cikin hayacin ta ya sa shi matsa mata da tambaya may yake damun ta hakane wai ? Tace matsalan yayan mune yayana ina ganin kamar bai daina shaye shaye ba har yanzu. Da sauri yace, kai may kika gani ban tsan mani yana sha ba kuma har yanzu gaskiya. Tace koma may nene Bintu ta san komai sai dai tana boyewa ne, nan ta bashi labarin yadda mukayi da ita da rana. Ya nisa bayan yaji maganan ta yace tabsa tunda kikaga taki fadi akwai magana gaskiya amma yaya akayi ta samu wanan abin a gurin ta in ma nashi ne. Tace nima shi nake ta tunane nasan tayi hakane don farin cikin maji don kada hankalin ta ya kara tashi kuma ? Tace nima abinda na fhinta ke nan hakan take boyewa don kada aji hankalin shi ya tashi amma ba matsala gobe da safe zanzo na kaiku makaranta anan zan fito mata da zancen muji. Yadda suka tsara haka din ne kuwa da safe sai ga Bashar mun gani a jenction din gidan mu yana jiran mu. Muna shiga muka gaida shi yafara hanya sai dai tuki yake a hankali, sai naji yace malama Binta ya garin dai nace lafiya kalau yaya Bashar. Ya ce ranan sai mutumina ke fada mai ta,asan da kikai mashi da kayan shi ? Da sauri na dago kai na kalli maryam sai na dukar da kaina nai shiru bance mashi uffan ba. Yace Binta yaya akayi kika kwaso abubuwanan a gurin shi shiru nayi babu amsa. Yace look Binta ba boyo ki fada min komai nai maki alkawarin bazan fada mashi komai ba akai don hanyan da zamu ceto rayuwan shi nake son mu bida a cikin sauki. Nace shi may ya fada maka don nasan na daukan mashi alkawari bazan fadawa kowa ba wanan magana. Sai Bashar ya nisa tare da buvun sitiyarin motar shi yace ina ganin baki fahince mu bane kawai. Nace yaya Bashar kadai gane cewa nashine ne ko to abar maganan don Allah, kyau alkawari cikawa. To shike nan na fahince ki yanzu, amma don Allah yadda Allah ya hore maki gane irin halin rayuwan da yake shiga ina son muyi amfani da wanan daman naki guri gano abinda ke saka shi a irin wanan halaiyar. Sai yai kaman ya bari sai kuma ya koma ciki tsunbul dashi al,amari gaskiya akwai daure kai a cikin sa sosai. Nace nima na fahinci haka amma gaskiya ban tsan mani zan iya ci gaba da wanan aikin ba saboda yai min warning sosai akan mashi shishigi ga al,amarin shi. Zaki ya mana inji Bashar abinda nake so dake shine kamae yadda baki tsoron fada mashi gaskiya haka zaki daure ki ci gaba da fada mai a kai tsaye. Murmushi nayi nace anya yaya zan iya hakan kuwa yace kwarai kuwa Binta ai zaki fitar da tsoro ne ga komai ki kama aikin ki,amma fa kuma kin san aikin nason jan mutum a jiki sosai. Nace da sauri yaya zanhi in ja yaya sadauki a jiki mutumin da kullun yake cikin hattarana da tsangwama. Yai murmushi kafin yace wanan kuma,wani haline nashi nan dai ya fara fada min ga yadda zanyi akai nace to ba matsala zan gwada nagani amma idan naga da,wahala gaskiya bazan yi ba. Yace zakima iya tunda kina da hakkuri kawai ki dan sake dashi shine farko. Muna kaiwa school ya sauke mu tare da min fatan alheri nace Allah yasa muyi nasara dai. ****** ********* ****** Yana tsaye ya bada baya waya yakeyi kuma a handfree yasaka wayan nashi a lokacin. Magana yake da wata mace sai dai magan tankar fada sukeyi yake cewa na fada maki ni mace bata a gaba na yanzu. Don haka ki daina yaudaran kaki don baxan aure ki ba koma zanyi aure yanzu akwai qualities din abubuwan da nake so ga matar da zan aura ke kuma baki da ko daya daga cikin su so kima daina yaudaran kanki a kaina. Ban san may yarinyar tace ba sai ji nayi tace wanan kuma matsalar kine ni da kika gannin ban taba zina ba a rayuwa ta kuma akanko ba zan fara ba. Da sauri na juya don nashige ciki sai nai karo da dutse ina batun faduwa naji ya riko ni bai bar wayan ba kuma bai sake ni ba. Nace a kakausan murya sake min hannuna kaji malam, wani kallo ta watso min na ki shiga taitayinki kinji ko. Sai da ya gama wayan ya juyo gare ni yace ashe kuma banda sa ido harkin fara lebe ne kuma ? Cikin tsiwa nace, akan may zanyi labe Allah ha rabani da annaminan ci ni fita zanyi nagan ka kuma zan koma. Murmushi yayi yace idan ma baki taba ba ai yau gashi kinyi ko? Amma anyway zan baki bashin na yau don kin min alkawari a baya don haka nima ya kamata nai maki uzurin na yau. Nace aini ba don ka nayi ba don mama nayi amma ba saboda kai ba sake min hannuna na wuce. Yai dan murmushi kadan abinda bai saba yi min ba yace ba abinda yakamata kice ke nan ba Fatima kice dai kin boyeni don baki son ace ni din mashayi ne ko ? Amma ko banza dai ni koma maye aikin min alheri ko Fatima don haka nima zanso ace nadan yi maki ko na rana guda nane kamae yadda kikai min din. Cikin wani shu,umin murmushi yace min tafi sai kin jini nan gaba, nima, Na dan kalli hannuna da yai ja saboda riko da yasha a hannun shi nace mugu kawai ashe yajini yace may kikace da gudu na zura zuwa cikin gida kada ya kamani sai ganin mama nayi a gaba na tsaye. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,, ALLAH DUK WACCE TA KARANTA BATA BIYA BA KAINE SHEDA INA BINTA BASHI,,,,, Zaune take duk abin duniya ya damay ta a ranta ga shi yanzu daga ita har dan ta sun zama abin magana a gari. Ko a gaban ta zataji mutane suna bayar da labari yadda ma ba,ayi abin ba haka za,a zake ana labarata shi. Kowa da,kalar abinda yake fadi a bakin shi ba dama yaron ya fita sai yara abokan wasan sbi su fara gudun shi kaman sunga dodo. Haka zai dawo gida yana kuka yana fadin abinda yara yan uwan shi sukai mashi. Abin duniya ya ishi mariya a ranta tai kuka har tagaji ta hakkura don kan ta babu wanda zata kai kukan ta gare shi. Gashi zaman gidan kawai takeyi tun lokacin da aka dawo da ita daga gidan su daya tura ta manyan suka zo suka bashi hakkuri. Ba don yaso ba ya hakkura da ita haka na amma zama takeyi ba abinda ke shiga tsakanin su. Koma cefane ne idan ya shigo dashi sai dai ya aje mata a kofan daki ba tare da yai magana ba. Idan kuma tana son wani abu sai dai ta tura yara su fada mashi abin da ake bukata a gidan. Ranan dai taga yana ta gyaran wani kangon dakin shi a zaton maria shine zai koma ciki don ya bar masu dakin su sai bata kawo komai a ran ta ba. Don dai tasan ba aure zaiyi ba mutumin da ko kudin cefane sai ya fita ya nemo masu abinda zasu ci. Ranan wani laraba ta zaune tana wanke wanke taji wasu mata su biyar sunyi mata sallama. Suka gaisa da ita sai suke fadin wani ne dakin da aka gyara daya daga cikin su tace, tana ganin wancan ne da ke da sabon siminti. Basu bi takanta ba suka nufi dakin suka shiga ciki suna dan dubawa anan suka barta tsaye da mamaki. Bata iya masu magana ba suka fita sai gasu da kaya suna shigowa dashi. Kasa daurewa maria tayi tace wai bayin Allah daga ina haka bakuce min komai ba kun kama shigo da kaya cikin gidan mutane. Dayar matar tace a,a shi mai gidan bai fada maki yai aure bane yau matar zata tare ma. Ai mu amarya muka kawo yanzun haka munzo gyaran dakine ma kagin anjima mu kawo ta. Allah ne ya taimaka maria bata fasa ihu a gaban su ba amma sai ta fada dakin ta can ta fasa abinta ita kadai tana fadin na,shiga uku yanzu da wani zanji halin da nake ciki ko da zancen kishiya kuma? Bata fito ba sai da taji fitan matan daga gidan mayagin ta ta dauko sai gidan su ga girkin da ta dora a saman wuta nan tabarshi ta fita. Da kuka ta samu uwar ta tana fada mata abinda ya samay ta nan uwar tashiga zagi tana fadin amma Atiku ya cika tsohon macuci wallahi. Yanzu da yake nan yana yawo kaman almajiri ashe har yana da kudin da zaiyi aure, bamu sani . Nan sukai ta kullawa ita da uwarta a tsakanin su har dare ya soma ta fito zuwa gida. Koda ta koma ta samu har girki ta ya kone wuta ya mutu don kan shi nan dai ta kwashe shi haka na don bazata iya girka wani ba yadda take ji a lokacin. Atiku na shigowa gida ta tare shi da masifa da jidali nan ya dakatar da ita yace. Maria ki shiga hankalin ki wallahi kada na bata maki rai a gidan nan kin dai san ina da haushin ki dama to ki iya kan ki dani wallahi ko ayita a akare a gidan nan don dama kin kai min ko ina wallahi. Nan ta shiga zage zage tana kiran shi macuci azzalumi dama ashe yana da kudi yake ce masu baida shi yanzun ina ya samu kudin aure. Yace wanan aure kikace dole na samo shi don naji dadin rayuwa na kuma duk mata ta shigo gidan nan kikace zaki daga muna hankali wallahi sai dai ki koma gidan ku kinji na fada maki mara mutun ci da tausayi kawai. Ke abinda kikai min a duniyan nan har kina da bakin magana don zan kara aure. Kuma ai dole na kara aure na samu wace zata kwantar min da hankali na wadda zanji dadi da sanyin rai a gurin ta. Ba irinki da kikai shekaru da shekaru kina gwada muna boni ni da diyana ba a gidan nan. Don tsaban iya cutan ki harda dan ciki kika zalunta dakanki da kanki kin mayar damu abin zunde da kwantance a gari saboda tsaban kwadayin ki. Yana fadin haka yai alwala ya fita, daga gidan ran shi a bace yana kutawa shi kadai. Bayan sallan magariba kaman masu jiran a idar da sallah sai ga yan kawo amarya da gudan su sun shigo gidan. A zaton maria za,a kawo mata amarya dakin ta irin na al,ada sai taga sabanin haka. Sai ma jin da tayi lokacin yaran ta suna cin abinci a,waje matan na gardama a tsakanin su cewa. Ko wanan ne akaiwa fyaden cikin su dayan tace karamin ne fa akace sai dayan tace a,a fa ance babban ne mai sayar da pure water uban ma bai ko san tana aza mashi tallah sai ranan da abin ya faru ya sani. Kai amma wanan matar ta cika azzaluman mace ita tajawa dan ta wanan bakin sunan haka har ya mutu ana kwatance dashi a gari. Wani irin zafi da radadi maria taji a ranta take ji kaman ta fito ta basu amsa amma kuma ita kadaice a gidan kada su taru su yi mata tsinanen duka don taga a tsaye suke su ma. ****** ********* ****** Haka kawai ranan na tsiro da tafiya kauye ba,shiri nacewa mama dake shirin zuwa gidan buki zan tafi garin mu yau. Da sauri ta juyo ta fasa daurin dan kwalin da takeyi tace zaki kauye Fatima ? Na dukar da kaina a kasa nace eh mama mamana ce bata da lafiya jiya ake fada min a waya da dare. Tace assha amma gaskiya ban son tafiyan ki a motan kasuwa yanzu da zaki bari zuwa jibi idan angama bukin nan sai nasa a kaiki. Nace mama yau nake son zuwa don na dawo da wuri insha Allahu ba abinda zai samay ni mama ki kwantar da hankalin ki. Ta je gun jakkan ta na hannu ta dauko min kudi sun kai dubu goma tace gashi kiyi kudin mota dashi idan min tafi yadda kika samu jikin nata sai ki min waya nace nagode mama. Sai da na gama shiri na tsab na fito falon lokacin su Amira ne kawai a falon ganina da jakka kamar may shirin tafiya suke tambayana. A,a gaki kamar may shirin tafiya mana Bintu ? Nace eh anty zani kauyen mu ne yau, gurin mamana har ma gurin babana zan leka na kara dubo shi insha Allahu. Maryam tace yaushe zaki dawo nace sai na kwana biyu gaskiya to Allah ya kiyayye hanya. Har kofan gida inda zan hau Napep din da zai kai ni tasha maryam ta rako ni na tafi. Sai dai a cikin ranta bawai ta yarda da zanyi tafiya bane don ganin mahaifiyata kawai dai na gudu ne don kaucewa yayan su sadauki. Amma sai ta sa a ranta zata saka ido taga shi wani reaction zai yi akan tafiyan nawa. Takira Bashar din ta take fada mashi da kuma abinda itama take kullawa yace haka daidai zan tayi saka ido nima insha Allahu. Ban isa gida ba sai da yamma don ban fito da wuri ba kuma motan bata tashi da guri ba. Ina isa gida sai ganina mama tayi kwatsam tace a,a ke kina hanya ne ashe nan muka gaisa nafito da dan tsaraban da na kawo masu aka shiga rabawa. Dakin da bakowa suna aje tarkace a cikin shi sai wani dayan kani na da ya dan tasa ya dan girma. Nan na gyara na kai yar jakata a ciki tare da shimfida tabarman kaba sabo da mama ta bani na dinga kwantawa akai. Ranan haka na kwana ina juyuyi don yaushe rabona da kwana saman tabar ma, zaman birni ya fara bata ni yanzu. Sai tunane nakeyi ko may su maryam suke yanzu don nasan dai basu kwanta ba saboda a can dare baiyi ba sosai kila suna can suna kallon season film din da muke bi a zeecilmer . Miskili jarababbe mugu azzalumi na furta a fili nace yanzu ai sai ka samu wata ka lalata ba dai ni Fatima Binta ba kuma. Nace ko hutu ya kare ban dawowa sai naji ka tafi kabar kasan zan dawo macuci kawai. Allah kadai yasan irin iskancin da yakeyi can bariki idan ya tafi babu kowa nan ma gida ya yi shaye shayen shi balle can inda babu kowa tare dashi. Mazina ci kawai mai boye kama ashe shiyasa yake wani kallon mutane duk shakiyai ne irin shi gashi kirkiri ya rabani da Usman ba wai ban son usman bane amma saboda bakin zargin shi dole na rabu da Usman din ba don naso haka araina ba. A haka har barci ya dauke ni ban sani ba sai washe gari kiran sallah da ya tayar dani a lokacin. Bayan na idar da salla ban kwanta fitowa nayi na gyara gidan ko ina don yana bukatan gyara. Ga karan gidan da akai danni duk ya tsufa har ya dan dadare daga yadda aka jera shi da farko. Makewayin su ma haka tsufin tsumane na wani tsohon babban riga aka tare bayin dashi. Ga kwata ya taru sai diyan sauro da kuda da gurin ya tara ya wani canza launi duk da kasa ne yashi amma rashin samun gyara yasa gurin ya canza launin shi. Nan ma sai dana gyara nasa musa kanina ya debo tsakuwa da yashi muka zuba ya dauko wani falalen dutse muka kara dagwarawa a saman gurin don mutum ya samu gurin hawa yai wanka. Kafin dan wani lokaci gidan ya koma tsab dashi kaman bashi kaca kaca da farko na dora ruwa muka dama kunu ina gamawa na dora sauran tuwo na gyara ma ma yaran don dashi suka saba karyawa. Sai dana gama nai wanka na shirya tsab dani dakin da nake na gyara kafin lokacin sa girkin rana yayi. Sai da mijin mamana naji ya fita daga gidan don bai tashi sai rana ya raba wani lokaci ma alokacin zaiyi sallah. Na shiga gurin ta na samu tana nade kayan wankin da na samu tayi jiya da na zo. Nace ta bari dakin na zo na gyara mata dama nan kuma na shiga gyara nafito da tulin shara daga dakin don irin gyaran da ake mai na sama sama ba,a kwakwalo komai da kyau. Dakin sai gashi yafito tsab dashi kamar dakin mace nace mata may za,a girka ne da rana Tai murmushi tace ai bamu girki rana sai dai da yamma idan ya dan samo muna sai mu girka jiya ma da kikazo ai sa,a ki kayi yasayo muna dawa shine nan nai muna tuwon shi har kika samu. Haushi ne ko tausayin ta zai kamani na rasa may mama ta zaunayi gidan wanan mashayin har lokacin nan. Yanzu gashi har sun kai ga tara yara har shidda dashi babu zancen fita gare ta kuma ke nan. Bance mata komai ba nafita na kira musa ya sayo muna rogo da zogala a bakin yar kasuwan su. Nai zaune na gyara shi kowa yaci ya koshi muka sha ruwa abin mu nayi hakane don mu kyale mugun mijin ta da baida katabus ga iyalin shi ko yaushe. Dan na lura yanzun idan nazo komai bai saye in an tabaye shi sai yace a tambayi Bintu ko tana da canji a sayo. Yana ko dawowa yake tambayan ba,a gika komai bane a gidan mamana tace ka kawo abin girki ne halan ? Yace baga Bintu tazo ba bata sayo bane a girka din ? Naga idan tazo takan dan yo muna dabara yanzun aci shiyasa yanzun nake farin cikin zuwan ta furin mu ai don nasan idan tazo hankali na a kwance yake da kayan bani banin ki. Tace to bata sayo ba yau don haka sai ka canza tunanen ka kafita kasamo muna. Yace kin tambaye tane tace maki babu a gun ta da zaki ce na fita in na fita ina zan samo tunda ba sana,a nakeyi ba ni. Sai kawai naji yana kirana ke Bintu Bintu fa na amsa daga dakin da nake nace na,am Baba na fito. Yace cewa nayi baki zo muna da komai bane wanan tafiyan don naji shiru har yanzu bakice muna komai ba? Nace ban zo da shi ba a takaice. Kallona yake don jin yadda na bashi amsa duk nima ban so bashi amsa a haka ba don ko banza mijin mahaifiya na ne shi. Ina fafin haka na juya ban tsaya ba balle naji may zai kara fadi kuma tunda ba ta ido ne dashi ba. Yanzun kai bakaji kunyan tambayan ta wanan magana ba haka wani sana,a takeyi ne a can kokuwa itama ba karshin wasu take bane wai ? Yace na dai fahinci abin akwai rainin hankali watay kin hada baki da uwar ki kada ku taimaka ko to oho akan ku zai kare ai munafukai kawai. Idan naga abin rainin wayo ne sai yarinya ta koma gidan uban ta wallahi tunda nan ba gidan su bane ? Zance ke nan kake fadi ai matsawan ina gidan nan dole ne yarinyar nan ta zauna a gidan nan ita ma. Yafita yana fadin oya shege ka fasa ni daku kuwa a gidan nan mama tace ai ni wallahi dana huta ta wanan wahalan. Ni dai ina jin su nace mashayin banza kawai a raina a haka zaka kare har girma yazo maka baka bar tabara ba har yanzu. Muryan kani na musa dake zaune ta waje naji yana fadin ni wallahi mama da ma kin gudu din mu huta da halin baba mu koma can birni gurin yaya Bintu muma mu huta kawai. Daga daki nace kai musa baka da hankali ne ina ruwan ka da saka baki ga maganan man ya ne wai ? Da yamma muka shirya nace su rakani unguwa duk da ban fadi inda zan tafi ba sai gidan su marigayi Kabir naje gaida mahaifiyan shi. Matan bata gane mu ba sai da muka shiga har dakin ta muka gaisa da ita, sai dan shiru can tace ban ko gane ki ba. Nai dan murmushi nace Fatima ce diyar Hausin dan Amo, tace Allah sarki Fatima kuwa haka akayi gaskiya ban gane ki ba wallahi. Nan ta,rasa inda zata sani don murnan gani na tace yaushe kika zo garin namu nace mata jiya nazo Inna. Nan muka zauna muka kara gaisuwa dasu da sauran matan gidan suna kara jajanta min mutuwan Kabir din. Nan suke fada min iyalin shi yanzu suna sokoto zaune don karatun yaran shi daya bari. Nace Allah sarki aiko ban sani ba dana shiga inda suke tace min dama ai a uguwar GRA yake da gida an raba gado anba kowa nashi shind ita Saude da yaran ta suka samu gidan . Nan dai nan dan zauna har zuwa dan wani lokaci nai mata sallama muka bargida bamu ratse ko ina ba sai gida. Mun shigo bamu dade ba sai ga yaron gidan ya biyo mu da sakon wai inji mahaifiyan su. Ana wata ga wata sai ga wani dan kanin Kabir da suke uwa daya dashi ya aiko wai yana so na da aure yana son ya maye gurbin yayan shi da ni. ****** ********* ****** An wuni an kwana har dare duk shigowan da yakeyi a gidan baiga Bintu ba a ran shi yake tambayan wanan ko lafiya take ne ban gan ta ba duk kwanakin nan ?. Yana son ya tambaya sai daibai son raini ko tuhuman wani abu ga tambayan da zaiyi na ina nake kwana biyu baya gani na. Da yamma ya shigo gidan baiko shiga part, din shi ya wuto cikin gida direct nan ya zube a falon mahaifiyan shi. Wayan shi ya jawo daga aljihun shi, bayan sun gaisa dasu rasa may ke mai dadi shine ya ciro waya. Ya fara yin game da ita sukosai hiran su suke suna kallo hankalin su a kwance abin su sabanin shi dake a cikin damuwa. Can yace maryam Ta amsa da na,am yayan mu . Yace wai ina wanan yarinyar take ne kwana biyu bana ganin ta ? Tace yaya sadauki Fatima kake nufi ? Yace ita din mana. Tace ta tafi kauyen su yau kwana uku ke nan taje gun mahaifan ta ne wai zata kwana biyu a can. Wani irin faduwan gaba yaji a lokaci guda, yace a ran shi kodai saboda abinda ya faru ne a tsakanin mu ta bar gidan nan don ni. Duk sanyin AC dana gari da akeyi bai hana ahi feso wani irin zufa ba a lokaci guda. Take kamannin shi ya sauya a cikin, lokaci guda, idanuwan shi sun sauya kala zuwa ja a lokaci guda. Tankar wanda aka watsa wa barkono yace a kasale yaushe tace zata dawo ne wai ? Tace zata kwana biyu a can don haka ba rana ke nan sai dai idan mun ganta kawai. Yace ba kun kusa komawa school ba shine zatai tafiya taje ta zauna har wani lokaci. Maryam tace ai muna da sauran lokaci ga hutun mu yaya kila sai hutun ya kare zata dawo ai? Maryam tace lafiya kuwa yaya kake tambayan ta cikin son kara tuhuman ta akan shi. Yace No babu komai dama zanyi bakine shine nake son ta hada min wanan abin dama yan wasu abubuwa. Daga haka yaja tsaki ya mike tsaye yabar falon a lokacin maryam ta dan matsa gurin Amira bakin ta tab da gulma tace a hankali. Cikin yanayi irin ta mai rada tace wai anty may kika fahin ta ga yayan mu da yake tambayan Bintu. Tace eh nima nai mamakin jin yana tambayan Bintu don naga shi bai damu da kowa ba ai. Hmm baki fahinci komai ba,wallahi amma ni nasan yaya yafara kamuwa da son Bintu wallahi. Kai haba wata Bintu can wanda ke shiga duniya yana ganin mata kala kala shine zai tsaya son wata Bintu can. A ganin ki ba tunda ke baki san so ba har yanzu kina nan zaune a na soyewa a gida baki sani ba. Ke dai wallahi akwai ki da shirmay tsiya maryam may zaiyi da Bintu wace kullun cikin fada suke a gidan nan . Mugun takaicin ta fa yake ji shine ke ko yar kayan soyayya kike ganin kamar shi suke yi. Maji da tasamu suna firan tace waye wai,? Amirah tace wai yaya sadauki take cewa wai soyayya suke da Bintu kila a boye haba may zaiyi da Bintu ga yan mata yan gayu iri iri a gari ko ina. Eh tun da ita Fatiman ba mutum bace ko ke kin fita kama mai kyau ba da zakice hakana. Shi damay yafita ? Ai da ta taimakawa rayuwan shi wallahi dayayi arziki in ya aure ta. Ita Bintu din dai maji ? Oh baki san shi al,amarin aure ba ke nan ashe da sauran ko ke tunda baki da fahintan komai. Ni na dade da sanin abinda yakeyi kyaleshi kawai nayi kada najawa yar mutane matsala. Kai haba maji don Allah kubar wanan zancen mana kada ku ja wani matsala kuma yarinya na zaman zaman ta yasa ta agaba. Kai amma dai anty Amirah nan . Watarana kice na fada maki ai. Ita dai Amirah jin su takeyi kawai don tasan haka ma bazai taba yuyuwa ba ai. Wata Bintu can yar kauye kuma ba diyan kowa ba, a gari. Sai ma taji ranta ya ba i kawai da zancen don abin haushima ya bata ita a ran ta. Yaya sadauki na barin falon dakin shi ya shiga ya fada kan gadon shi yayi lamo saman gado. Tan kar wanda yake barci, sai dai ba barcin yake ba yar damuwa ce da bai san dalili ba ya dami zuciyar shi kawai. Can ya tambayi kan shi wai may yasa har yake son damun kan shi akan yar karamar yarinya hakane. Gashi a yadda ya lura da yarinyar bata ma gama sanin komai ba na rayuwa don akwa childish a tare da ita har yanzu a rayuwan ta. Karancin shekaru uwa uba kauyanci bata san ko inaba daga sokoto sai kauyen su kawai. Shi dake son mace nagani nafada na gwadawa tsara shima ya faso zai tsaya ga yar kauye kuma karama haka dako twenty bata cika ba har yanzu. Sai yaji take wata zuciya tana gargadin shi dacewa kai baba ina kai ina wanan tunanen kuma wai ? Washegari tunda safe yashigo yana cewa shi zai tafi Abuja yanzun nan maryam tace a,a yaya wai ya zancen bakin da kace kuma zakayi har ina shirin masu abinda kace ai masu din. Yace No maryam ki barshi kawai sun fasa zuwa din zanyi tafiya ne nima yau din nan. Bashar yana jiran shi a kofan gida nan suka samay shi da suka rakashi, Bashar ko a,gaban kowa bai ita boye kaunan shi ga maryan yanzu sai ya baiyana shi a fili. Don suna fito tana dauke da yar jakan tafiyan yayan ta, da ta karba ta saba a kafadan ta. Daga cikin mota da Bashar yake zaune suna karasowa idon shi akan maryam yake cewa Madam how far? Ita ko tai wani shake murya tace bakomai yace ya su mama tace suna lafiya. Har sadauki ya zauna a mota Bashar sai soyewan shi yake yi hankali a kwance. Dallah malam ja mota mu tafi da wanan bakin shirmay naka babu kunya da kake min. Easy man, take it easy bani nakar zomon ba fa, kaga ni fa ban hanaka ba don ni ba motsoraci bane irin ka. Wani harara yakai wa Bashar yace wallahi zaka kaini makura Allah da wanan halin rashin kunyan da ka tsiro wa mutane daga sama. Bashar dai yaja motan shi yanawa sahiban shi bye bye, suka bar gurin suma suka juya zuwa cikin gida. Airport ya kai shi nan ya shiga jirgi da ya tashi da sha biyun rana suka tafi Abuja, bai so buga wanan wasan ba amma halin da yake ciki yaji kawai gara ya je ya buga ball din shi ko zai samu sauki a zuciyan shi. Duk da kwallon da ya buga bai hana shi jin abinda yake ji a zucuyar shi ba har yanzu. Suna waya da mutanen gida amma bai, taba jin wani yai zancen yarinyar ba ko yaji an anbaci sunan ta ko a waya. Gashi girman kai ba zai iya barin shi ya tambayi kowa labarin ta ba don sai yana ganin kamar abinda yai mata ne yake ganin bai kyautawa yarinyar ba. Don yana gani ai kaman zaman kaunan shi yarinyar take a gareshi amma shedan ya rude shi yai mata haka. Yace a fili, kai kai gaskiya ban kyauta why don Allah why har haka ya kasance a tsakanin mu ne wai. Ya dan kai wa katifan da yake kwance nashi da hannun shi na hagu da karfi sosai har sai da ya dan jin zafi a hannun shi. A haka ya kai har sati biyu acan suna da wasan da zasu buga sati mai zuwa amma ya juyo ya dawo gida haka kawai. ****** ********* ****** Ina gurin mama na zaune na sake raina ba abinda ke damuna yanzun in ba matsalan mijin ta ba da kulun a cikin tashin hankali suke a tsakanin akan ban kawo masu komai ba. Amma nazo ina cinye mashi abincin gidan shi a banza shi gaskiya ba zai zauna da agola ba a gidan shi. Naso na bar garin amma sai na dake na tsaya inga iya gudun shi ko zai kore ni ne ni kuma nasan yadda zan girgiza mashi auren shi. Sai dai ya shigo yayi haukan shi ya fita babu mai tsinka mashi a cikin mu dan dama ma ita mama sukan kwasa dashi idan abin ya ishe ta. Gidan kowa ban zuwa kullun ina gida zaune kamar wata matar aure can dani. Ganin shi kawai sukayi da yammacin jumma,a ya diro garin nan suka gaisa mama take tambayan shi yaya akayi kuma ya dawo ba yace suna da wasa wani sati ba sai satin sama zai dawo gida. Yace eh maji nadawo ne nai wani abu a garin kuma da akwai wasu takardu dana manta ban tafi dasu ba da zan tafi. Yakai wani lokaci a zaune baiga giccina ba hakan yada shi sanin cewa har lokacin ban dawo ba ke nan garin. Ya mike ya fita kaman wani mai jin kasala a lokacin, Bashar ya kira yazo idan an fito sallah su fita. Ranan Monday maryam tafito a cikin shirin ta zata shiga makaran ta,a waye ta samay shi ya fito daga gurin exercise . Sun gaisa yake tambayan ta ita wana har yanzu taki dawowa ba kun koma makaranta ba tace eh munyi waya da ita tace bata san ranan da zata dawo ba kila ma, Fuska a daure yace ina ne garin su? Tace, a yaya baka san garin su Bintu ba kai, duk zaman ta a gidan nan? Yace don Allah malama fara bani amsan tambayana kafin kiyi min halin ku na yan kasa tukun na tambaya cikin tambaya. Tace can rabah take nan dai tai mashi kwatancen yadda ake zuwa garin yace inda muka tafi gaisuwan wancan mutumin da tatashi aure kenan ya rasu ko tace mashi eh can ne ya amsa mata da ok good. Zaka tafi garin ne yaya ta tambaye shi tare da kallon fuskan shi yace ban sani ba tambayan ki kawai nayi. Sai batan kamar kwana biyu da tambayan maryam ranan da safe yace wa Bashar ya shirya zasu tafi wani dan kauye su dawo. Sam Bashar bai kawo komai ba a ran shi nan yazi ya dauke shi shi yaja mota suka tafi. Ban zuwa gidan kowa amma ranan haka kawai nace zan je na gaida kakanin mu kafin na tafi don saura kwana biyu na tafi. Mun fita gida da kaman awa biyu suka shigo garin wani mai faci bakin titi suka tambaya gidan dan Amo shayi akai masu kwantacen gida. Da farko da suka isa gidan yaso yai gardama ko banan ne gidan ba saboda ganin yadda gidan kaman ma yafi ko wani gida na uguwar lalacewa a shiyan. Sallama suka ce ai masu da maigidan yaron da suka tura yace kai mai gidan kan yanzu ba,a samun shi gida yana can gurin moli. Basu gane may yaro ke nufi yace yashiga yace wai bakine daga sokoto sun zo ganin Bintu. Mamana tanajin haka tace, Bintu bata nan tafita amma ace su waye yace ace yaron hjy ne yazo tafiya da ita. Jin haka yasa mama tace ace su shigo daga ciki ai su yan gidane nan ta tura yaron ya kirani gidan kakan nina, basu so shiga gidan ba amma dole suka shiga. Shi dai bashar sai kallon ikon Allah yakeyi kawai don abin ba mamaki ba daure mai kai yayi. Bin gidan yake da kallo da mamakin yadda dan adam ke rayuwa cikin wanan rubaben ginan haka da akoda yaushe yana iya rushewa. Bai san cewa shigina in har akwai mahaluki a cikin shi ba Allah na karewa yadda yaso. Tabarma mana ta shimfida masu daga dakin ta nan ma yai matukar mamaki wai dakin da ake rayuwane, acikin shi haka. Ruwa ta debo masu acijin wani kufin silver ta sabo ta kawo masu bashar ya karbi ruwan ya dan kora a cikin shi. Shikan bai san yaya zai iya kai wanan cup din a bakin shi ba gaskiya don tun bashar baisha ba yaji kaman yai amai. Bayan mama ta dan fita dauko masu abin fitara ne Bashar yace wallahi kasha ruwan nan don ba haka ake neman aure ba. Cikin tsawa yace Bashar you are very stupid wallahi. Neman auren wa kuma can sai dai idan kaine kazo neman auren ban sani ba don kai baka raina mata naga alaman haka ? May ye abin rainawa ga abinda mutum ke so a ran shi ? Shiru yayi don mama ta dawo a lokacin tana mika masu abin fitaran tana fadin kuyi hakkuei akwai zafi wallahi. Sai ga wata akuya tashigo nan ta hau saman tsadaddun takalman su ta sake mai fitsari a na shi. A hankali yace oho shit da ido yaiwa bashar din signal ya kalli kofa abinda akuya take mashi. Murmushin keta bashar ya sake mashi, yace don't mind my friend duk ciki ne ai. Lokacin na shigo gidan da mamakin ko su waye aka ce sun zo nemana a lokacin daga sokoto. Sam ban kawo cewa shine ba don sai ina zaton mamace ta turo wani ya dauke ni kila. Ina bullo daga kofa mukai arba dashi zaune cikin fararen shaddan shi yaci starch. Nai matukar mamakin ganin su a gidan mu dakin uwata musa ne ya hango akuyan tai fitsari akan takalmin dayan su ya shiga koran akuyan ya debo ruwa ya zubawa takalman. A hankali na tsaya daga kofa ina masu sannu da zuwa, duk na shiga rudewa da ganin su. Bashar yace min humm Bintu kinzo kinga mama shike nan kin manta da zancen an koma makaranta ko ? Nai dan murmushi nace ban man taba yaya kawai dai ban tashi dawowa bane a lokacin nan. Da sauri yaya sadauki yace sai yau she baki da hankali ne wai ana karatu zaki zo ki samu guri ki zaman ko a kauye. Ganin zai sake layi yasa Bashar tare da fadin yanzu dai mama tace muzo mu dauke ki yau din nan don an koma school tun ranan Monday kin sani kuma. A hankali nace yau din nan yaya yace eh haka ta bamu umurni shiyasa muka zo ai daukaki din. Nace ni gaskiya ban shirya ba fa sai dai idan na shirya zan dawo anytime. Kafin wanin mu yai magana sai mamana ke fadin may zaki shirya kuma ina kin yi wanki jiya kitashi kawai ku tafi tunda har kikaga hajiya ta aiko a dauke ki. Ban so ba haka na shirya zan bisu su suka fara fita yakawo kudi masu yawa yabata yace tayi hakkuri babu kudi a jikin shine. Sai da zantafi nace mama ki boye kudin nan kafin mijin ki ya dawo ya kwashe su kiba musa yakai maki gidan su kakale a boye maki su ku dan samu abincin abincin rana dashi. Nakawo sauran kudin dake hannuna sunkai dubu goma nace tace ga abinda aka bata. Mukai sallama dasu muka fara hanya ina baya sai tunane nakeyi kawai a raina. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,, IDAN KIN KARANTA KO KIN TURAWA WANDA BAI BIYA BA ALLAH NE SHEDAN MUNA BINKI BASHI,,,, ALOKACIN MU KE,,,, Mun kama hanya sai hiran su suke shi da Bashar niko ina bayan mota zaune a takure cikin damuwa. Bashar ne daga inda yake zaune ya dan juyo yace min Bintu gaki kinyi shiru mana. Nai dan murmushi yake kawai nace ba komai yace ko kina son a sai wani abune? Kai kawai na girgiza mai nace idan mun kai wani kauye zan sai dan tsaraban da zan kai wasu mama kada naje masu hannu sake. Sai faman gudu yake shararawa da mu har sai da naji tsoron gudun da yake da mu nace komai nashi dai na muggai ne ko kashe mu yake son yi ne wai ? Kafin wani lokaci sai gashi mun fara hangen garin sokoto daga nisa mun da kara gaba nani ya taka burkin motan da karfi sai dana nan dan firgita bani ba har Bashar dake gaban mota sai da ya kalleshi. Muna nan zaune shiru ya bude mota yafita zuwa gefen da nake zaune ya bude marfin mota fuska a daure yace nafito ina fitowa ya mayar da marfin motan ya rufe . Ina tsaye jikin mota ya daro hannau shi guda saman kan mota dayan kuma ya sashi daga gefen kunkuruna sai dai mota ya dafa. Take naji cikina ya kada min fuskan shi a daure tamau yace ke dakata kiji kada kikaga nazo na dauko ki naji wanan zancen a gida ran ki zai baci sosai wallahi duk kika bari maji taji cewa nine nazo na dauko ki sai na bata maki fiye da tsanmanin ki. Nace baka son asani may yasa kazo ka dauke da ka barni mana har lokacin da na tashi dawow,,, Bakina ya murde dakarfi yace ke baki da kunya ko ina magana kina magana who is the master? Jin zafi a bakina yasa na dan zille na duka sai ya komane sai saman kirjin shi na fada. Da sauri na kara dagowa hakan yasa muka tsaya muna facing din juna face to face. Ya dan dade yana kallona sai ya kuta ya juya ya shiga mota yana fadin kinji warning din da nai maki wallahi duk naji zancen nan sai ranki ya baci dani wallahi. Na shiga mota idona yai ja kaman zanyi kuka ina cewa ni wallahi wanan cin zalin ya isheni don anfika karfi sai a dinga cuta maka kawai. May kike fadi yace sai lokacin Bashar dake muna dariya yace haba ka barta hakana mana please? Ya tayar da mota muka ci gaba da tafiya, bai tsaya ba sai wani guri da ake sayar da kayan irin na kauye na ciye ciye. Nan suka fita sai gasu da sayayan kayan tsaraba mai yawa irin na kauye ana lodawa a buth din motan. Muka bar gurin nidai ban san may damay suka sayo ba a lokacin muna shiga gari a play over ya samu guri ya tsaya. Can ya tare wani mai Napep yake cewa, ya kaini gida tare da mai kwatancen inda zai kaini, yabiya shi kudin shi nan mutumin ya loda kayana a cikin motan shi. Su mama suna zaune sai ganina kawai sukayi a bazata kawai nan suka shiga cewa la Bintu ashe kina hanya ? Yaran da suka shigo min da kaya na diban masu rake gyada dafafa na basu suna ta jin dadi suka fita. Naje gurin mama na rusunna na gaida ita cikin jin dadi da gani tace Fatima shike nan kinje kin samu guri kin share ai har ina batun binki ne da banga kin dawo satin nan ba. Nai murmushi nace mama ai zan dawo tunda an koma makaranta, tace yayasu wajen mamaki suna lafiya ko nace duk lafiya kalau mama suna gaida ku. Ta kalli tsaraban da nazo dashi tace Fatima wanga tsaraba haka mai yawa fa dariya kawai nayi a raina nace aikin mahaukaci ne. Nan muka shiga hira dasu anty suna min sheri wai naje naga mama na kasa dawowa. Sadauki bai shigo ba sai da yamma lokacin ina cikin daki maryam ke fada mai Bintu fa ta dawo yaya. Yace taga daman dawowa ke nan ta samu kauye ta zauna kaman wani birni can. Tasa min kira na fito sai ganin shi nayi a zaune nace yaya ina wuni ? Ya amsa a kasalance da lafiya? Kinga daman dawowa ke nan ko ? Murmushi kawai nayi mashi na karasa gurin maryam nace gani anty tace dama yaya na kiraki ku gaisa ta fadi tana dariya. Na juya kawai na koma ciki, ina gyara kayana ban fito ba sai bayan magariba don nasan lokacin bai nan. Ina cin abinci kawai sai gashi ya fado falon saudaya na daga kai na kalle shi ban kara ba. Maryam ce take ce mai yaya adebo ma tsaran Bintu na kauye yace kai maryam kayan kauye ai sai yan kauye. Daga inda nake zaune nace, muko dashi mukafi wayau kayan kauyen don yafi bada lafiya ai. Yace ke yanzu lafiya kike ke nan a haka kamar a karya ki? Kafin nai magana maryam tace a,a yaya aiko yanzu Bintu ta yi kiba in kuma tafi haka ai bata kyau. Ni wallahi duk da mace ce amma nafi son mace haka silynder da ita sharp din mutum duk dress din da yayi sai yai ma mutum kyau. Ga Bintu kuma dagowa ce ga wanan uban farin nata kamar yar larabawa da ita. Kai maryam don Allah ya isa haka kada kisa kan Bintu ya fashe wanan dadin haka inji Amirah? Maryam tace wallahi anty da har haushi nake ji idan mun fita da Bintu yadda matane ke yabata amma yanzu nima nasan gaskiya suke fadi. Watarana fa muna alwala a makaranta wata na ganin gashin Bintu ta yanka salati wai ikon Allah yanzun ke kina da wanan gashin haka kike faman boyon shi ga hijjab kullun ? Sai lokacin yaya yai magana yace, shiyasa ta bude ai don su gani su yi magana. Nace kai haba yaya haka kawai zan bude kaina wa nake son ya gani kuma? Ke kika sani dai tunda an gani an yaba din ai yadda kike son agani din. Shiru nayi wani takaici ya kumay ni a raina nace ni wallahi wanan ai zargine kawai? Yace nakara jin kin bude wani part dinki a jikin ki sai na bata maki rai gidan nan. Dan Allah yaya ji yadda maryam ma take wani zuzuta fatima wallahi sai kace wata sarauniyar kyau can. Su dai suka sani shedanun yara ne wallahi kin gan su nan shiya sa duk suka fita sai maza sun biyo su don suke kiran su. Wanan sheri da may yai kama saboda Allah haba dai yaya kana biyewa Anty Amirah tana zuga ka kawai yaya. Ni dai wani haushi da takaici bai bari na ko iya dago kaina ba a lokacin don irin takaicin da nakeji. Amirah tace maza kan na zuwa har ana masu yanga da kuri kafin a dauki wayan su tafadi cikin dariya. Kai haba anty ai wanan sheri ne kawai kike kulla muna gar wasu maza muke kulawa mu don Allah, Baiyi magana sai shirun da yayi can ya dan bude abincin da aka aje mai agaban shi ya fara ci nikan na mike na shige dakin mu. Amirah tace kibar gudu ai don kada a ci gaba da zancen zaki shige ko? Shima bai bi ta kaina ba yaci abincin shi ya tafi abin shi kawai. Ban san yaya akayi Bashar ya fadawa Anty maryam su suka daukoni daga kauye ba ranan da na dawo. Amirah na falo ta dunkule saman kujera tana chatting maryam na zaune tana gyaran farcen ta. Maji na zaune tana gyaran wayan ta da ke hannun ta ruwa ya dan zubo mashi da take sha. Nafito da plate a hannu na da abinci zanci na zauna na fara ci ban dade ba sai ji nayi maryam tace. A humm wai ashe ke Bintu yaya sadauki ne yaje har kauye ya dauko ki da zaki dawo? Da sauri na dago kaina kalle ta cikin mamaki sai banyi magana ba don ina mamakin ina taji wanan zancen ita. Amirah tace ke kan Maryam wallahi uwar sheri ne wata Bintu ne can yaya zai je har kauye daukowa? Maryam tace au kina nufin karya nakeyi ke nan ko,ai ga Bintu nan shi in ba shi yaje tun daga nan ya daukota ba wallahi. Kin ma raina yaya Allah shine zai tafi har kauyen nan mai uban nisa akan Bintu. Don in nunawa Anty Amira na kai nace to anty maryam don ya dauko ni wani abune halan ni nace yazo ? Ni da ban ko shirya dawowa ba amma yasa ni tasowa ba shiri saboda zuwan shi. Bintu da gaske yaya ya dauko ki wai ko may? Nace su sukaje sukazo dani ban ko shirya ba amma ya matsa min wallahi saida mama tace na shirya su zo dani. O lalai ma yayana shine yai pretending kamar ma bai san komai ba a ranan da ta dawo. Bake ne ba idan ana magana akan yaya da Bintu sai ki wani kakarw ki hana a fadi ni dai ban kara magana ba ina mamakin yadda maryam taji zancen ga kunya mama duk ya kamani lokaci guda. Nace dama,na,sani kawai tun ranan in fada mata tare dasu nadawo da yafi min yanzu gashi anji ko. Amirah bata bar zancen ba sai da ya shigo gida har kowa ya manta ashe ita abin yana ranta. Yashigo cikin yar fara,an shi bayan ya zube saman kujera yake, cewa maji yau naga wanan kawar taki da tun muna tsohon gida kuke tare. Maji ta dago kai tace wata kawana kuma ke nan yace ko yar Rabin isha ake ce mata ba ? Au kace uwar goyon ka dai ai itace tai giyon ka lokacin tana amarya a unguwar na mu da anyi maka wanka sai gidan ta. A ina kagan ta yace can wani unguwa naje duba wani tsohon gida da akai min talla tun kwanaki ban samu zuwa ba sai yau din nan. Naji ance wai ba sadauki maji bane nan yace wallahi ban gane taba maji ta tsufa duk ta lalace sosai dagani tana cikin wahala. Tace Allah sarki, tun lokacin da mijin ta ya dauke ta suka koma kauye ban kara jin duriyan taba. Yace lalai na gan ta yau kan maji tace inji ka samu abinda ka bata ? Yace dubu goma kawai na samu na bata banda kudi ga aljihuna a lokacin amma nai mata kwatancen gidan nan ai tace zata zo. Yauwa yayana wai ashe kai ka dauko Bintu daga kauyen su ranan da ta dawo ? Da sauri ya daure fuskan shi kaman bashi ke fara,a ba yan dakikoki kadan da suka wuce. Yaba ta amsa da eh mu muka dauko ta wani abin ne akayi kuma ? Inda nake ya kalla fuska a daure nima na daure nawa tare da dukar da kaina kasa. Amirah tace da nace karyanr wallahi da maryam ke fadi dazun ban yarda ba wallahi. Yace naga bata da niyan dawowa school ne gashi ankoma shiyada naje nazo da ita ai. Daga haka yai shiru maji najin su batace kallaba ko wanan lokacin ban da cewa da tayi Allah yasa yar Rabi dai tazo gidan nan wallahi na dade ina tuna ta sosai wallahi. Mikewa yayi yana cewa zan shiga daki maji duk nagaji yau wallahi zan dan huta. Yana fita na sauke ajiyan zuciya a hankali don nasan nawa ya samay ni kuma tunda yai min gargadi kada na fadi. Ban taba sanin yaya yana da nombana ba sai yau ina daki ina shirin sallah naji wayana na ruri. Ina dauka naji yace ke ashe baki da hankali gulman ki hae yakai can ban sani ba dana ce kada ki fadi sai da gulman ki yakai kika fadawa maryam abinda na hana ki. Na marairaice nace wallahi Allah yaya bani na fada mata ba ban san inda tajiba wallahi ko. Sai naji ya kashe wayan dip nabi wayan da kallon mamaki tare da sauke ajiyan zuciya. Kwanana biyu da dawowa ya sa kai ya tafi zuwa kashen waje gurin wasan su don can yafi dawowa a jike idan ya tafi. Tafiyan shi, na dawo normal kullun ina cikin yan uwana muna mu,amulan mu yadda muka saba dasu. Bamu da matsalan komai a gidan yanzu don gaskiya Alhamdullahi, mota kowan su na dashi, haka ma sutura duk muna dasu matsu tsada, waya kowacen mu babba take riko a hannun ta duk shi ta saya muna, gurin abinci sai wanda ran mu yake so zamuci, ga uwa uba makka da muka tafi kowan mu da hakoran makka a bakinta irin na adon mata yana walkiya. Matsala guda yanzu shine matsalan gidan su maji na fitina a tsakani kullun ga Nafisa yanzun abinta yai kamari sosai gwanin ban tausayi da ita. Idan iskancin ta ya ishi Baba haka zaifito tsakar gida yai masu tas ita xa uwarta, sai in Umma ta gajine takan tanka itama tace. Ba kan diyana aka fara lalacewa ba ai a gidan kan suyi ai wasu sunyi kuma nasan hannu aka samin suka lalace. Don haka koma waye na sani kada maishi yaga kamar yaci bulus wallahi indai nice bashi akaci wallahi. Don sheri saboda mutum yaga nashi ya lalace sai ya mayar da dan kowa lalatace a gida. Badai na su kawai duniya zata fada ba sai an fadi na mutum tukun. Mummy tafito daga dakin ta tace kai amma dai hjy Atika tauhidi bai sheki ba wallahi. Ashe shi wanda kike nufi hannu aka saka mashi ke nan a lokacin yazama haka bamu sani ba ko sai yanzu da yakawo akanki ne kika san haka ne. Kada ki manta iskancin namiji ado ne a gare shi duk yadda ya iya lalacewa bai rasa macen aure a duniya itako diya mace fa ? Ke tsohuwar kilakiya kada ki manta mun san komai wallahi, nan kikagama tambadewan ki ba mashinshine in bashi alhajin dayazo yatara ba ya dauko muna masifa a gida. Kin ishe mu kin ishi diyan mu wai ke adole ga yar bariki to anriga ki indai barikine a gidan nan don gidan kikazo. A haka cure ake barikin don shifa bariki iyawa ne dama don kinga ashe nafiki iyawa ke nan tunda kika fadi. Dariya mummy tayi tace wai a haka ashe ke bariki kikeyi ke nan ba,a sani ba ko ? Nafisa dake daki tayi tatil da ita ta leko tana fadin Umma rabu da wanan gajar matan mai muna mazuru muna shaho. A,,,, mu,,mun,,san komai,,,wallahi, ikon Allah ai gara kija yar mayer yar ki daki kafin wani ya shigo yaga wanga tabaran nata a fita damu waje. Haushi da takaici ya kama umma da Nafisa ta bude bbaki zatai magana ta wani daka mata tsawa tace don Allah rufa muna baki kinji kin jawa mutum gori a gida kawai. Haka sukan ta faman jidalin su ita da mummy da bata iya hakkuri idan tana habaicin ta. Maji dai bata kan tanka mata sai dai tai shiru kawai tace tabar ma Allah kuma Allah ya tsare mata zurian ta. Irin wanan jidalin yakan tayar wa Baba da ciwon shi wani lokaci sai ya kwanta asibiti saboda bakin ciki dake damun shi gashi duk wanda ya sanshi sai yai mashi korafi akan Nafisa abinda takeyi baida kyau a gari. Ranan dai ya tara iyalin shi yai masu fada sosai yace da mazan da suka isa aure da matan kowa ya fiddo da miji da mata aure duk aurar dasu zaiyi gaba daya kowa ya huta a gidan dasu. Yace kai Imirah na fada maka ka kawo mace kafin na zaba ma da kaina wallahi kaji na fada maka. Ya juya gurin mama Asiya yace danki yace min muje gidan yarinyar da yake so aiyi zancen auren su. Mama tace ba dai wanan yar iskan ba da ta tsohe mashi ga shekaru da komai yace shi din maye inba halin su daya ba a ina suka hadu da ita? Tunda yace ita yake so kuma shi zai zauna da abin shi ke ina ruwan ki da zancen su ne wai? Zan tura iyayyen shi suje nema mashi auren ta nan dagobe insha Allahu. Mama ta tubure tana fada tana zagin Ahmad tace badai ya auri wanan karuwan yarinyar ba agidan nan. Baba yace ai sai mu zuba mu gani tunda kece zaki zauna mashi da ita ai kina bani mamaki wallahi. Ki fara tambayan danki yaya ya hadu da ita kafin ki fara zagin yar mutane haka nan. Ya juya gurin mamana yace idan danki ya dawo ina son ko fada mashi sakona yafito da mata na da karshen sabon wata duk aure zasuyi muddin ina raye a duniyan nan. Mama tace shi sadauki yana da mata kuma na yaba da tarbiyan ta kwarai yace mashs Allahu haka nake son ji dama. Duk gurin sun so sanin wacece matar don su sani ko yar gidan maikudine ko wani kusan gwaunati can. Don kada yazo yafi diyan su zaben yar gidan mai kudi azo ana mazu feleke a gida. Haka dai akabar falon kowa da abinda ke cikin ranshi manya da yaran su na gidan da aka kira. Ina daki a zaune suka shigo kowa sai gunaguni takeyi maji dai ta shige tabar mu nan zaune muna hira. Amirah ce takira yayan ta da waya take fada mashi hukuncin da Baba ya yanke akan su. Yai dariya yace Amirah kice mun kusa shan buki ke nan yan kanne na sun kusa zama amare. Tace bamu ba ai harku yaya don yace wa su Maji wallahi duk fito da matan aure a aura maku dariya yai mata kawai. Tace yaya kai kaga abin dariya ma ni wallahi duk na rude na rasa may nake ciki ma aallahi. Yace ina samarinki ba sai ki fitar da daya ba kawai a zarga maki dashi, tace yaya ni duk fa basuyi min bane na ma rasa wa zan tsayar a cikin su ni wallahi komai ma ya jagule min yayana. Yai dan murmushi yace kibari zandawo month end sai mu san abin yi tace ni dai da Baba zai min hakkuri ne har faba dayafi min. Yace No Amirah ki godewa Allah fa gaki har kin gama karatunki ma may kuma kioe so yanzu inba aure ba kuma. Tace yaya ke nan bazaka bashi hakkuri ba har zuwa gaba yace wa ni rufa min asiri please bari mu rabu lafiya da Baba don Alla dai. Tace yaya naji maji tace wa Baba wai kai kana da mata shine mu bamu san wanan lucky girl din ba da tai wanan sa,an haka? Yace No,No Amira maji ta dai fadawa Baba hakane kawai don ta kare ni gare shi ammani for nowa ban da kowa a kasa tukun na. A kwai da wata wadda nake son fada masu akan ta don yar kasar ghana ce sai dai akwai matsala gaskiya. Matsala kuma yaya ? Yace eh don ba musulma bace Christian ce ita sunan ta Linda. Yaya kafira kuma ? Yace eh amma ai idan munyi aure zata musulun ta ne insha Allahu. Tace ashe kuwa akwai case ke nan nasan maji da wuya ta yarda gaskiya don yadda bata kaunan kafirai ko kadan. Ni dai daka jaye zancen ko zaka samu wata nan gaba ku shirya yar asali yar gari. Yace ban ma san ni may yasa suke son mutum yai aure bane yanzu wallahi. Amirah tace kasan maji kance ita dai muyi aure don yanzu Life is to short knowadays. Hakane kuma fa Amirah gaskiyan maji ne rayuwan yanzu dan kalilan ne gaskiya. Yace ni nasan zamu kwasa da parents din mu dama both don ko ita parents din ta takw ji yanzu. Shiyasa tace zata zo Nigeria sai muyi auren mu kawai sai daga baya iyayyen ta su sani. Amma ban yarda da wanan ba ni don ban son ni ai min haka gaskiya. Tace yaya ai matsala shine yaran da zaku haifa zasu zama ruwa biyu ke nan fa? Yace kai Amirah akwaiki da shirmay wallahi ni fa ban ko tunanen yin aure yanzu balle wasu iyali can . Yaya kadai yi tunane kafin kazo da maganan nan gida don za,a samu matsala sosai wallahi. Ki bari kawai idan nazo sai mu san yadda zamu bullo wa zancen cikin sauki haka zaifi ai. Tace ni wallahi maji nakejiwa akan zancen nan don nasan halinta akan abinda bai mata ba. Yace ke dai kawai kiyi shiru ban son kowa ya ji wanan zancen a bakin ki sai nazo tace shike nan . Nan sukai sallama,dashi yace ta kwantar da hankalin ta yana nan zuwa month end insha Allahu. Suna gama waya gulma yaci Amirah ta kasa barin zancen a ranta tace wata sabuwa wai yaya kafira zai aura fa ashe? Muna hada baki da maryam gurin cewa kafirah fa kika ce antu ? Tace wallahi yanzu yake fada min wallahi wai yar kasar ghana ce ita Sunan wai ko Linda ? Nace wayaga Leather ke nan kuma ? Kai baima yuyuwa gaskiya kafira arniya mai fitsari a tsaye zai ce zai dauko muna. Muji da wani irin gori da habaici gidan nan kuma ba,a gama wani ba har yau a fada wani ke nan kuma. Ai da su Umma an samu abin dariya ke nan a gidan nan wallahi don shi za,a aza a faifai kuma ana talla lungu lungu inji maryam ke ta sababi haka. Tace ni wallahi har girman shi ya zube min wallahi arniya fa Allah tsare mu da ita a gidan nan. Diyan shi sai su girma suma su zama kafirai ke nan ko ? Nace to shine daidai daahi don shima ai zuben yare ne gare shi baka taba ganin yaya kace mai dan hausawa ne kullun yana cikin kananan kaya irin nasu. Ke Bintu inji Amirah yaya din ne mai zubin arna kuma? Nace rufa min asiri anty kada yajini nawa ya samay ni a gidan nan kuma . Maryann tace na rasa may yasa mafi yawan yan kwallo suke auren diyan kafirai wallahi. A ji anty marayam fa ba,a cikin su suke ba suna ganin su kullun may zai hanasu fadawa tarkon su. Shine ai tunda dasu suke mu,amula can suna ganin su fa ko yaushe inji Amirah. Sai da muka watse ne zancen ya tsaya min a rai na nace cikin zuciya na ai dama muguntan mutum ke cin shi. Yaya za,a kana dan musulmai kace arniya zaka aura a haka ma yaya aka iya dakai balai ka auro kafira mara sallah kuma. Wanan kan sai yadda Allah yayi dashi kan don ba ranan shiryuwa gare shi ke nan kuma. Ai su gasa junan su da mugun hali sune ma daidai da halin shi, ai tunda shi yace shi mugu ne su karata, can wallahi. Maji suna waya take ce mai ka sayo kayan da aka taba a cikin kayan lefen ka don a cika. Yace cikin murmushi maji ai yanzu angama yayin su kawai a rabawa yaran nan sai na hado wasu kawai amma kada a taba gold din don akwai wanda na sayo da tsada tun lokacin. Mani tace zan dai zabi na kwarai na aje idan ka kawo sai akara ciki kawai yace duk yadda akayi maji shike nan insha Allahu idan zan dawo zanzo dasu din. Sukai sallama tana mashi fatan alheri da saka mashi albarka tana rokon Allah ya tsare mata shi ya shirya su baki dayan su. ****** ********* ****** Kamar yadda yace karshen wata zai dawo hakan ne da yammacin asabar sai gashi a gida nan aka shiga murna ana zuwa gaidashi. Nikan tunda muka gaisa na gudu falon na shige don ina tsoron wani disgi kuma ba wuya gareshi ysi min shi yanzu da dawowan shi. Sai hira sukeyi maji da bata san bani falon ba tace don Allah Fatima dauko min jakata a daki na. Maryam tace wata Fatima maji Bintu kan ai dodon ta ya dawo tashige ciki tun dazun. Itace ta shiga ta dauko jakar ta leka ina kwance daki tana min sheri wai yaya yana kirana nace o,o, ni ya su may zan mashi kuma ne wai ? Tace ke wasa nake maki dan Allah kwantar kada kiyi fitsari a wandon ki please ? Ban sake ganin shi ba don bamu hadu ba dashi tun ranan da ya dawo daga tafiyan shi. Kwanan shi biyu kawai ya juya ya koma Abuja sai da yai kwana goma sha uku ya dawo gida a jike da abin arziki. Ko ni na lasa don ba cikin gidan ba har makwabta sun san sadauki ya dawo garin su Umma ya canza masu motar shiga don yace yana bakin cikin ya gan su a motan kasuwa suna shiga. Ranan munyi kallon kayan lefe mun baza kauyanci bani ba har su Amira yan birni sai da sukayi kauyanci ga kayan . Mummy tashigo ta gani sai faman mamaki takeyi da yaba kyan kayan tana cewa kai wace yar sa,an keda wanan kayan haka. Ina son naga wanan mai kayan nasan ba karamin gida za,a kai suba haka kan. Hjy Kubura ai shi kyawon aure albarkan shi kawai yar masu hali da yar tallaka duk dayane ga Allah Allah dai yasa andace kawai. Hjy kubura tace gaskiya kan shine magana ai shima mai kayan da dan tallakawane yanzu baga ikon Allah ba. Maryam tace mumuy ai sai kinhaji daganin ta gidan nan ke da sarakuwan ki kune fa yan kai kayan in Allah ya yarda. Tace hakane fa kedai mairamu sai fa na gaji abuna namu maganin akwabe mu. Su Umma basu shigo ganin kayan ba wai su ba,a gaiyace su suzo su gani ba don haka basu zuwa. Mummy tace kyale yan baki ciki duk hasadane da kyashi ke cin su kawai ba wani ba,a fada masu ba ko anfada masu ma basu zuwa aini na dawo raka wa yan nan mutane ko dan basu da imani. Inkana binta nasu sai su kona mutum ga banza da wofi da jahilcin su wallahi. Maji batai mai magana ba sai da yakai kaman kwana goma da dawowa tace tana magana dashi. Ya shigo suka danyi magana da Amirah mutumiyar shi ya shiga gurin maji don dama idan zasuyi wani magana da yake serious daki suke shiga shi da ita. Ya samay ta zaune a bakin gadon ta ya zauna asaman kujeran dake cikin dakin nata. Yace maji yaya zancen su Amirah ne tace ai akan zancen ne nakira ka nan. Tacs baka nan babanku ya tara mu kan zancen auren ku yace yana son gaba daya kuyi aure lokaci guda nan da karshen sabon wata. Yace ni maji dama akwai yarinyar da muka shirya da ita akan zamuyi aure sai dai matsala daya shine ita ba musulma bace gaskiya. Da sauri maji ta dago kai tace kafira ke nan ko may sadauki? Yace eh maji Christian ce ita, yar kasar ghanace amma idan munyi aure nasan zata musulunta ai. Kai dakata ba cikin kayana ba wallahi. Kada kasoma ka kara min zancen nan wallahi don zan bata maka rai sosai fiye da tsanmanin ka. Kai baka jin kunya ban gita cikin wani gorin ka ba zaka jefani wani idan su yaya suka samu labatin nan ina kake son na jefa kaina. Ban taba sanin rashin hankalinka yakai haka ba sai ysu din nan da har ka dubi idona ba kunya kazo min wai da zancen auren kafira da bakin ka ko kunya bakaji ba. Idan da kana da kani ko danka yace zaiyi wanan danyen aiki yaya zakaji a ranka. Shiru yayi bai ce uffan ba sai ya dukar da kanshi kasa ya hada hannayen shi guri guda yana dan jijiga kafan shi a hankali. Itama mama shiru tayi don bacin ran da ya ziyarci zuciyar ta a lokaci guda bai barin tayi magana. Sai dai shi a zuciyar shi tunane yake ta hanya Baba zai gwada yagani ko da sa,a don yasan ance Baba ne yai tsayewa Ahmad har zai auri wacce zai aura din. Amma nashi dai akwai banvanci saboda zaman kafira bare kuma ba kabilar hausawa ba. Muryan maji yaji tajefo mashi tambayan da sai da ya girgiza mashi zuciyan shi tana cewa. May ke tsakanin ka da fatima ne ? Da sauri ya dago ya kalle ta yace wata Fatima kuma maji ? Fatima nawa ke gidan nan da kasani? Maji badai Fatiman nan taki ba ko ? Tace inba ita ba wata Fatiman nake nufi ? Yace kai tsaye ni babu komai a tsakani na da ita maji? Ance maki wani abu a tsakani na da ita halan ? Maji tace sai an fada min ko tunda ni yarinyan ce? Wallahi maji ni ba komai a tsakani na da ita Fatima ai a matsayin kaunata nake daukan ta in ma,wanan ne shine kawai. Shiru sukayi ba wanda ya kara magana daga cikin su ganin maji bata da niyan kara mai magana yasa shi mikewa yana fadin shike nan maji tace tafi shike nan. Har yakai kofa tace dakata wallahi sadauki duk ka sake har zancen arniyan nan yafito a gidan nan sai na bata maka rai yadda ka bata min a gidan nan kagin kasa a zageni acikin gidan nan dagari sai na fara yima tukun mara hankali kawai. Yana fitowa fuskan shi ta canza kala yayin shi gaba daya ya canza a lokaci guda kaman ba yanzu ya shigo da fara,an shi ba. Amirah tana magana dashi amma ko kallon ta baiyi ba ya fice cikin bacin rai. Duk muka bishi da kallon mamaki muna ko may yafaru dashi oho mashi. Sai ga mama tafito dakin tana fada ita daya tana fadin ban taba sanin rashin hankalinka yakai haka ba sai yau din nan? Maji may kuma yayana yai maki yau kuma? Sai da ta harari Amirah kamar da ita take fada tace bar mahankali da rashin tunane kawai wai wata arniya yake fada min zai aura don ya gwada min shi dan duniyan gaske ne. Ashe ko dagaske yaya keyi da zancen wanan arniyan ya fada maki maji ? Au dama kukun sani ne ke nan ko ? Shi yanzu aka rasa wanda zai fada min a cikin tun baizo ba na tare shi mara hankali kawai. Maji ba yana son ta bane kuma shi zai zauna da ita abarshi mana yayi abinsh,,, Bata karasa ba aiko maji tai cikin ta da fada sai da Amirah ta kwamce da bata tanka ba gaskiya. Maji tace ai dama zubin ku daya dashi baku san mutuncin kan ku ba balle kiji zafin danaji. Ranan kan naga fadan mama da bacin ran ta ance mai hakkuri bai iya fushi ba sai ranan na tabbatar da hakan. ****** ********* ****** Da yamma da baba ya dawo maji taje gaishe shi tayi sa,a babu kowa agurin nan take fada mashi Alhaji dama ina son in fada maka cewa. Yaron nan fa yar gida yake son yi don da Fatima ce zasuyi aure ban dai fada maka bane sai komai ya daidaita a tsakanin su dama. Yanzun ko yazo angama magana itace kawai naga ta dace ya aura don yarinyar nada natsuwa da hakkuri. Cikin farin ciki Baba yace ikon Allah haka abin yake gaskiya nai farin ciki yau dajin wanan labari don ni kaina na dade ina wanan tunanen a raina. Sai gashi Allah ya karba min addua na a cikin sauki da dadin rai maganan tazo min . Zanga sadauki din in mashi murnan wanan babban albishir din da kikai min. Tafita ta barshi da dadin rai sai murna yake har ya kasa boye farin cikin shi a fili. Washe gari Baba ya aika akira mashi sadauki anyi sa,a ya dawo daga exercises din safe da yake fita da zaran sun fito daga sallah. Rigan jikin shi ya sauya, ya nufi falon mahaifin shi don amsa kiran shi da saurin shi don yasan ba kasafai Baba ke aikowa kiran shi ba. Da sallama ya shiga falon ya samu Baba ya daga kofi zai kurba tea da yake sha. Yana ganin dan nashi ya sauke kofin ya fasa kurbawa yana cewa sanda sadauki sandagagare. Zo nan zonan ka zauna yau in gwada maka farincikina dana kwana inayi jiya. Mamakin may baba yaji akanshi yakeyi don rabon da yaji wanan kirarin da baba kan mashi inyai abin jin dadi tun yana karamin yaron shi kafin ya fara shaye shayen su bata. Yace matso mana Babaatsonan kusa dani naji albishir din Alheri a gurin uwar ka jiya da dare . Tazo tana fada min kun shirya tsakanin ka da yarinyar nan Fatima zan iya cewa nafi kowa farin cikin wanan hadin naku don na dade ina maka fatan haka a raina don Fatima yarinyar arzikice a gareka duk wani namiji da yasan kan shi zai so ace ya mallaki wanan yarinyar a matsayin uwar yayan shi nan gaba. Duk bayanin da baba keyi sadauki ji yake kaman an watsa mashi ruwan zafi tun daga saman shi har kan shi . Yadaga kai ya fadawa Baba ba gaskiya bane wannan zancen, amma sai yaga farin cikin da mahaifin shi ke ciki yafi karfin ya musulta shi a lokacin. Ya san da zaran yace zai fada mashi gaskiyan zancen shi bai san komai ba akai farin cikin rayuwan shi zai iya sayawa zuwa bacin rai ta zama mashi sana din tashin ciwon shi. Wanan dalilin yasa yaja bakin shi yai shiru, yana karba irin adduan fatan Alherin da mahaufin nashi ke mashi akan zacen. Sukai sallama ya mike gwiwan shi duk ya mutu da kyat yake iya daga kafan shi da yake takawa a kasa dakin shi ya nufa cikin wani yanayi na susucewa a lokaci daya. Yana shiga ya fada kan katifan gadon shi yayi yayi a lokacin ya samu ko dan kuka yayi ko zai samu relief, amma abin ya faskara mai. Wayan shi dake gefe ke ringing har yagaji ya katse don kan shi bai daga ba sai kuma ga kiran ya kara shigo mashi lokaci guda ya daga daniyar zagin mai damun shi. Bashar ne ya daga wayan yana tsaki yace yaya akayine wai Bashar din yace yana kofan gida. Yace shigo ina dakina yana shigo yanayin da yasamay shi a ciiki yabashi tsoro sosai. Lafiya may ya samay ka haka kuma ? Ya watso maahi wani harara yace ban sani ba mugu ai kana daga cikin munafukan dake son wargaza min rayuwana nasani ba yau ba. Bashar na zama yace may kuma mukayi mi muna fukan da bamu son ganin farin cikin ka? Maimakon ya bashi amsa sai ya juyar da kan shi kawai gefe daya bai kalleshi ba. Wai may ke faruwa ne wai ka koma haka lokaci guda kaman wani tababe yakara tambayan shi mikewa yayi zaune daga kwanciyan da yake yana cewa. Kana nufin baka san sherin da maji ta kulla min bane agidan nan wai ? Innalillahi kana da hankali kuwa yau man ? Maji ce kuma zata kulla ma sheri a rayuwanka ? Wani kallo ya watsa mashi yace ba sheri banr may nene? Murmushi Bashar din yayi yace don Allah may akayi ne wai ? Yace kaaai wai maji ta fadawa Baba wai mun shirya tsakanina da wanan yarinyae mun amince zamuyi aure. Wata yarinya ke nan kake nufi wai? Wata yarinya kake damuna akan ta gidan nan ? Yace kana nufin wai Bintu? Yace ita mana. Alhamdullahi Alhamdullahi kai wani hikima sai manya wallahi tanan maji tafito muna Allah mun gode ma. Ya dago jajayen idon shi yana kallon Bashar dake ta kwada hamdalla haka cikin mamaki. Yace wanan abinda maji ta kulla min da may yakama Bassh? Maji tarasa wace zata lakaka min auren ta sai wanan solaman yarinyar da kwatakwata bata cikin tsarina. O Lindan ce tsarin ka ke nan ko yar arniyan ka mai dan buje ko ? Wani wawan nashi yakai ma bashar din ya kauce ma nashi ta hanyan ja baya. Sadauki ya mike tsaye yace haba man may zanyi da wanan yarinyar ko maryam dina fa batakai shekaru ba a duniya wai itace za,ace na aura ?. Ita Fatima ba mace kake kallon ta ba ke nan ko ? Wallahi zakasha mamaki kace na fada ma dan hakin daka rai shike tsone maka ido watarana. Kai may ya kawo kane ? Yace manta yau zamu zamfara ne dakai ko kuwa? Yace bazan tafi ba. Dariya ya kama mashi yace kafara angwancin ke nan ko? Zanci ubanka fa Bash wallahi idan ka kara bata min rai yanzu zan rufe daki dakai nai maka tsinanen dukan tsiya. Bashar yace sai dai yanzu kuma ka rufe daki da Fatima amma bani ba Bashar ba ya juya yafara tafiya yace bari ma na shiga cikin nai ma maji godiyan wanan babban albishir din da kai min. Da sauri sadauki ya jawo shi ta baya yave kada ka farashi wallahi har ta zaci ko nayi na,am ne da zancen har ina farin ciki da zancen ne. Farin ciki kan ka kanayin shi komai dadewa zakace na fada maka ai. Wallahi kada ka fara kaje gurin maji na fada maka, Bashar yace mai da yukan ka a kube kamanta nima maji sarakuwa tave ina kunyan ta yanzu. Kaima kuma ya kamata ka fara kunyan ta daga yau dan ta zama sarakuwar ka kaman ni daga haka yafita dakin da sauri don yana iya shakoshi ta baya yadda yaga ya hasala. Dan iska da ka tsaya kaga tsiya a dakin nan ya dade tsaye dafe da bango sai tsaki yake shi daya a dakin. Sai can yaji taahin motan Bashar daga gidan ya sauke ajiyan zuciya kawai ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,, IDAN KIN KARANTA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA ALLAH NE SHEDAN HAKA MUNA BINKI BASHI,,,, O lala ka kai mara mutunci sadauki ka gwada min baka da tarbiya yau, dana so nace sai na bi ra,ayin Fatima akan wanan zance amma yanzu tunda haka ne abin bari kaji indai har ni ce na haife ka ko bana raye sai ka auri Fatima. Kuma idan ka sake ta ban yafe maka ba a rayuwa na, ba sadauki ba har ni da ke tsaye sai da nakai zaune cikin kuka ina fadin. Don Allah mama kada ki min haka wallahi bashi ba koni ban ra,ayin wanan hadi bani son shi mama na tsane shi kamar yadda na tsani mutuwa na. Inda nake ta karaso tare da dafa ni kadan tace Fatima, bani son ki da fadin haka nasan baki so amma don ni da Allah dashi kan shi mara tunanen abinda zai je ya dawo idan ya auri wata can sabba zakiyi. Kaina na noke a cikin kafafuna ina rusa kuka wanda baka yasa mama ta kasan lalashina a lokacin. Sai ji nayi tana fadin kafita min a shiya tunda ban isa da kai ba baka kaunan farincikina baka damu da rayuwan ka ba balle nawa. Zai yi magana tai mashi alama da hannu ya rabu da ita don Allah ya dan tsaya jin sai yaja kafan shi ya fita daga dakin. Kaina ta dawo ta zauna a gefe na tare da dafani tace Fatima ina fatan kin fara fahintar manufana na son yin wanin hadin danake kokarin yi. Don haka nake son fada maki sai kin jajirce sosai a cikin wanan al,amarin don akwai aiki sosai ja a nan gaba kafin komai ya dawo muna normal life. Cikin kuka nace mama ni ba zan iya ba don bazan iya zama da miji mai duka ba bai da tausayi mama bai san darajan mace ba ko kadan. Tai dan dariyan manya tace zaki iya Fatima zaki iyane na fada maki kuma ko bani raye zaki fadi da bakin ki, taimon da zaki min ke nan daya a rayuwana shine ki auri sadauki. Don ke ce kadai yanzu nake ganin mafita a gurin ki, kece wace zata kwato min shi daga duk wani sherin rayuwa dake bibiyan shi. Don Allah Fatima ki daure ki kanne ki fitar da duk wani shakku dake damun zuciyar ki, ki saka a ranki zaki sadaukar da rayuwan ki ne don Allah don ni kuma. Sai naji ta fara kuka a hankali cikin kukan tana fadin Fatima ban da wani mafita da yafi wanan a yanzu haka yasa kike ganin ban tausaya maki ba. Wanan hukuncin dana yake insha Allahu shine zai kawo karshen azzalumai masu bibiyan shi dashi wanda ba wai sun fasa ba ne har yanzu. Don haka kada ki zargeni a zuciyar ki na nuna son kaina a gare ki yadda na haifi Amira da maryam haka nake daukan ke ma din nina haife ki da cikina. Don duk abinda uwa ko da zaiwa mahaifiyan shi Fatima kina min a rayuwana may zai sa na bari wanan daman ya wuce wanan yaron ina kallo yaje ya dauko min wata sabuwar fitina cikin dakina. Dan uwan mahaifin shi ma yakasa bashi yarshi kan halin da yake ciki balle wani bare can sabba ya ba shi nashi a zauna lafiya. Hakan da nayi shine daidai a gare mu baki dayan mu sai dai a yanzu kurciya ba zai bari ki fahince ni ba. Ba dago fuska na dake shabe shabe da hawaye nace mama na yarda insha Allahu duk abinda yaya zai min zanyi hakkuri na zauna dashi saboda Allah da kuma ke. Ta rungumoni zuwa jikin ta tana fadin na gode Fatima na gode yadda kikai min Allah kema ya baki zuria masu albarka a rayuwan ki. Insha Allahu bazakiyi dakin sani ba ga wanan auren da yardan ubangijin mu. Tace tashi kije ki gyara fuskan ki kada wani ya shigo ya samay ki a haka a dauka ko wani abin ne can daban. Yadda tace haka nayi na mike na shige dakin mu sai dai ban fito ba na zauna cikin dakin kawai. Amirah dai ba ruwan ta dani don tamafi yayan ta daukan zafi akan zancen don kwata kwata ta daina min magana gaba daya a gidan. Sai harara da habaici kawai ne a tsakanin mu da ita, maryam kan ce na fita zancen ta na kyale bata da wayau ne da bata biye wa son ranta ba. Ina ji ina gani yanzu na koma wata abin boyo a cikin daki ban zama falo ko yaushe kunshe nake a cikin dakin mu ban san komai da akeyi ba a gidan. Karatuna ne kawai ya tsayar dani garin don da na gudu na koma kauyen mu gurin iyayyena da zama amma kuma ba daman haka don karatuna zai iya tabuwa. Ranan dai da dare na ce bari na dan fito cikin su a falo na dan zauna kadan na samu daga Amira sai maryam zaune suna hira. Maryam na ganin na fito take cewa a,a matar yaya yau kin gaji da boya ne kin fito ki sarara ke ma kina wani shigewa daki kina kumshe kan ki a ciki kamar lalle kafa. Nai dan dariya ina zama nake cewa anty maryam yanzun dai ke ake ji zama nake ina karatu don exam da ya kusa. Kwadayi dai mabudin wahala ne wallahi, in mutum yace ba zai iya tsayawa inda Allah ya aje shi ba ai yana tare da wahala a ran shi. Zaman daki kan yanzun aka farashi tinda mutum yace shi dan shishigi ne ya kai kan shi inda Allah bai kashi ba. Ban yi magana ba sai samun guri nayi na zauna da kyau, tare da mayar da hankalina ga TV dake aiki a falon a lokacin. Kada dai mutum ya manta matsayin shi ga Allah ya dauki kan shi ya kai inda Allah baikashi inji maryam. Anty maryam please bar zancen nan don Allah kada mama takai ga jin may mukeyi a falon nan. Idan ma taji ai haka kike so ke don yanzu nasan abinda ya kawo ki cikin mu kuma kuke kullawa keda munafukan gwagon ki. Nai matukar jin zafin zancen sai na dan ritse idanuwa na tace yanzu basai ki zauna ki auri maji din ba tunda shi wanda ki ke son mannewa din ya tafi sai muga wanda zaki aura yanzu. Ko shekara dubu zai yi a can dole dai watarana ya dawo gida aiko? Zasu ci gaba da sokawa juna magana sai ga mama tafito daga dakin ta da waya a hannun ta tanayi. Da wata kawarta take waya tana cewa Insha Allahu ranan laraba mai zuwa za,a je kai kayan shiyasa na bugo na fada maki don ki shirya. Amira ta kasa kannewa da uwar ta gama waya tace kayan wa za,a kai maji ? Kayan auren yayan ku mana. Can kauyen ko ina? Ki tambaye shi mana kiji daga bakin shi ko? Amirah da ta cika ta mike zuwa daki cikin kunan rai, waya ta dauka takira dan uwanta kira daya ga na biyu ya dauka. Yace Amirah yaya akayine? Tace yaya yanzu nake jin maji na waya wai ranan laraba za,a kai kayan auren ka kauye. Dariya taji yayan natayi yace as maji wish zan kyale ta tayi duk abinda zatayi don lafiyan ta da kuma gujewa fadawa fushin ubangijina akan hakkin ta da ke kaina. Amma ai nine mai auren ko let the vegan come into my house zata rena,kanta da kanta barni da yar iskan yarinya kawai. Amira tace amma ni gaskiya yaya ina son ka dauki mataki gada ma ayi wanan auren kwatakwata wallahi don ina jin kunua ace wai Bintu ce matar ka gaskiya. Class din ka ka kare ga wata Bintu can yar kauye wallahi nayi hating din yarinyar nan baka ga yadda ta wani kara komadewa bane ma yanzu. Dariya yayi yace common Amirah fita zancen kawai ki bar su maji da munafukan nan maryam da Bash duk sune masu kara zuga maji ai zata zo ta same ni ne. Suna gama wayan da Amira sai yaji gaban shi yai wani masifan faduwar gaba don ua tuna maganan maji da sukayi kaeshe dashi kan zancen auren. Yadda ke kullawa zai wa Fatima muddin ta shigo gidan shi ga maji tai mai sharti akai. Domin yadda yake ji a cikin ranshi a lokacin zai iya aiwatar da komai kan wanan manyar yarinyar dake son taiwa rayuwan shi karan tsaye. Shi yasa ma yai saurin kashe wayan da sukeyi da Amira don maganan ta na kara tunzura mai ziciyar shi ce. Duk yadda yake son yaiwa mahaifiyar shi biyaya akan auren zabin ta da tai mashi bai tsanmanin zai iya yin adalcin aure akan wanan yar kauyen dako Abuja bai iya fita da ita balle wani uwan duniya. ****** ********* ****** Kamar yadda maji ta fada haka din ne cikin satin da ya zagayo aka kawo lefen auren mu gidan mu. Muna school har masu zuwa kai lefen suka taru suka dauka zuwa kauyen mu gurin kai kayan. Akwati ne har guda goma sha biyu dankare da kayan irin na zamani, tsayawa fadar abinda aka zuba acikin akwatinan, sai abin ya zama tankar kauyancine saboda babu kadai ba asaka a ciki ba. Nan abin yazama turiruwa ga matan kauyen zuwa kallon abin arziki. Su gwago da yake sun san yadda ake a birni su ma basu bari abarsu a baya ba don suna tallakawa, suma sunyiwa yan kawo lefen abinda ya dace suyi. Rago gassa abin sha da sauran takarce na kauyawa irin su fura da nono dakar hannu mai kyau cikke a raba mai marfi. Yan kai kaya suka dawo suna yaba karamcin da akai masu a kauyen mu cikin jin dadi nan su hjy kubura aka shiga rabawa masu zuwa abinda aka samo don ita mama tabarwa yuka da naman zancen. Har da su Umma da basu tafi ba ankai masu nasu sai dariya sukeyi wai ana gaba an koma baya. Duk matan dake cikin gari yan gayu diyan masu kudi sunki dole an koma kauye inda ba asan ciyon kai ba an dauko yar kauye. Amirah ta bugawa dan uwanta waya ta fada mashi duk abinda akeyi a gidan nasu har zagi da dariyan dasu umma keyi saida ta fada mashi. Sadauki ya kira waya don ya shedawa mahaufin shi shifa gaskiya ba zai iya auren Fatima ba don yana da wace yake so Linda. Don haka yake shirin fada mai ko zai samu mahaifin nashi ya fahince shi ba da son shi maji ke shirin wanan auren ba. Don a kullun zuciyar shi taki yarje mashi Fatima a matsayin mata a gare shi abokiyar rayuwa. Babs ya dauki wayan tare da sallama yana cewa Umar sanda babuga sadauki. Sai kaji irin alheri da taron da mutanen arzikin nan gidan su Fatima sukayiwa yan kai kaya ko? Ai ni nasan ban taba dana sani akan ka sadauki bar wa yan nan wawayen iyayyen naka su Atika suna zaton auren wayayya shine zani ga aure. Sai gashi su gidan nasu sarakan ko ruwa ba,a mutane sun sha ga wullakancin da sukai wa yan kai kayan sai kiran babu babu kaza a ciki sukeyi. Nasan dakai da mahaifiyan ka dama mutanen arziki ne ba yau ba don komai naku a cikin nazari kukeyin shi. Yace lafiya dai ka kirani yanzu ko? Sadauki da ya rasa may zaice a lokacin don duk jikin shi yai sanyi sosai dajin yadda mahaifin shi yake a cikin farin ciki yace. Dama kawai na kiraka ne mu gaisa naji lafiyan ka don bamu samu gaisawa ba jiya. Nan dai mahaifin ya shiga sa mashi albarka tare da fatan gamawa da duniya lafiya. Suna gama waya da mahaifin nashi ya kira mahaifiyar shi sun gaisa sai kuma shiru sai uwar ke fadin kaji dai ankai lefen ko kuma sunyiwa mutane halarci sosai a can. Cikin murya mai nuna damuwa yace Maji ni may zance akan wanan magana tunda zabin kine. Yanzun ma nakira Baba na fada mashi zancen nawa auren na zabina da nake so sai shima yake min magana akan wai ankai kayan lefen ko amma ni ban so akai kayan nan duka ba tunda ba wata bace can da suka san darajan kayan. Sadauki wace irin banzan magana ce wanan kuma ko kayi shaye shayen naka ne kake son mayar da mutane kananan yara ? Jin dadin da kayi ne yasa har kake son watsa wa mutane kasa a ido ko may. A kan wata arniya can har idon ka ya rufe kake son yimin cin mutunci ko may ? To wallahi kaji na fada maka, ko da wasa nakara jin zancen arniyar nan a bakin ka sai na bata maka rai fiye da yadda kake tunane. Don haka idan an aura maka Fatima sai kai gunduwa gunduwa da ita ka zuba a buhu ka kawon gawan ta nan. Sakaran banza mara tunane an maka gata shine kake son yiwa mutanr rashin mutuncin ka da ka saba ko ? Haka ya kashe wayan ran shi a bace yasan dai yanzu baida wata mafita yadda mahaifan shi suka hau zancen sai anyi wanan auren dole. Da kyat ya ja kafan shi zuwa bakin window dakin da yake zaune cikin wani katafaren hotel na kasan LasVegas. Tun ranan kuma baida sauran wata walwala a tare dashi ga Amira ta ishe shi da kiran waya tana mashi kwarmato wai taga maji ta karbi keys din gidan shi a hannun Bashar zasu tafi da mummy su duba gidan. Idon shi ya rufe da jin wanan bakin labarin suka soma canza launi, zuciyar shi ya dinga mashi wani radadi da zogi ya mike tsaye ya nufi fridge din falon shi nan ya bude ya dauko wani dan mitsitsin kwalba ya kafa a bakin shi. Yana shaye abinda ke cikin kwalban ya wurgashi kasa gefen shi kwalban ya tarwatse. Dafe kan shi yayi yana wani irin huci mai fitar da zafi daga bakin shi, yana fadin why maji why zakiyi min haka please? May zanyi da wanan yarinyar da ko na yini daya bata iya daukan lalura balle na zama dindin din. Kai ba shakka wannan yarinyar ta zama mashi kafen ka al,amarinta ya na matukar caza mashi kai. Yasan idan baiyi da gaske ba zuciyar shi na iya kamuwa da wata lalura da zai ja mashi komawa baya ga harkokin shi. Yana kwance ya saman dogon kujeran falon ya dinga karanto addu,an samu sauki a cikin mayen da yake. Ya jawo dan filon kujeran dake gefen shi ya rungumay filon a kirjin shi tare da rintse idanuwan shi. Yadda rayuwan shi zai kasance da zama da wanan yar kauyen yarinyar a gidan shi, wacce ko kwaliyan kirki bata iya ba kullun tana dunkule,a cikin hijjab. A haka zazzabi mai zafi ya rufe shi, ga dubin damuwa da kadaici daya ishi zuciyar shi. Duk da shi ba likita bane yasan gap yake da BP shi ya hau a lokacin. Don irin yadda yake jin kan shi yana mashi sai matsanacin kasalan dake damun shi,. Gaba daya sai ma yaji zaman garin ya ishi ra shi baki daya tankar ana hura mashi wuta. Haka ya wuni kwance a dakin shi ko wasan motsa jiki ya kasa fita yayi sai shawara yakeyi kawai ya koma gida ai koma maye a gaban shi zaifi mai. ****** ********* ****** Sosai mama ta mayar da hankalin ta gurin gyaran mu a cikin hikima irin ta manyan mata. Ta hayan gyaran jiki da kuma magunguna na hausa da zasu karawa mace, ni,ima a jikin ta. Lokaci guda duk da damuwar da nake ciki da tashin hankalin wanan kaddararen auren. Amma haka bai hana ni canzawa ba nai matukar kyau, tankar ni nai kaina a lokacin. Cikin dare ya iso garin muna folo a zaune gaba dayan mu har mama dake ta waya da kawarta kan wasu kaya da take son a hado mata. Da murna suka tare shi duk da dare ne amma hasken fila ya haska kowan mu. Saudaya ya daga kai, ya kalleni inda nai mashi sannu da zuwa kaman yadda kowa yai mashi sannu din. Cikin dan sakin fuska kadan mama tace kai kana hanyane ashe bamu sani ba? Yadan kai zaune a kasale yake cewa wallahi tafiyan dai gatanan kaman ba shiri nayi ta nima maji. Maryam tace Allah yasa ka dawo ke nan har a gama buki yaya don idan baka nan ba zamu ji dadi ba. Maji ta kwantar da murya cikin tsigan lalashi tana fadin haba ya dawo ke nan mana ina kuma zai koma ai gara ayi komai dashi yana garin don jama,an arzikin shi. Amira ta saki wani irin tsaki tana cewa kai maryam ke wallahi baki da kunya sai kace kanki ne farau din aure. Maji tace basu bane farau saidai su yanzun ne zasuyi dole suyi dauki kuwa. Sai kuma Amira tai fushi wai da ita maji keyi don ita bata tashi aure ba yanzu a matsayin ta na babba cikin mu. Ta mike cikin fushi zata shige tana cewa, Allah dai yasa ni ban iya kutsawa aso ni ba balle na kawo wanda bsi sona. Maji tace cikin takaici wawiya kawai mara hankali shekaru yakai bata sani ba sai hauka. Sadauki da idanuwan shi suke mai a lumshe yana sauraren kowa sai dan murmusawa yayi yace, Maji ba dake take ba ai da maryam mai shegen rawan kan tsiya take magana ai. Zaka ci abinci ne inji mama data ga dan nata cikin alaman damuwa yake. Yace ban jin cin komai yanzu maji dan dama dama dai ko tea na dan walwale hajina dashi kawai. Maji tace Fatima hado ma yayan ku tea mai kauri ya sha don yafi mai zama haka nan. Na mike don dama a takure nake zaune a gurin na shiga kitchen don hado tea din. A fakaice ya bini da satan dan kallo duk abinda yakeyi akan idon mama amma tai tankar bata gan shi ba. Nafito da tea din hade da jug din ruwa cikin dan karamin tire dan madaidaici nakawo mashi gaban shi. Na samu ya rike goshinshi dake damun shi da halbawa da hannun shi daya. Nace cikin dakewa ga tea din yaya, ya bude idanuwan shi da kyat yai min alama da na aje a gaban shi. Sai da ya ciro magani daga aljihun shi ya bare tare da hadewa tukun ya fara dan kurban tea din a hankali don zafin shi. Baja jin dadi ne naga kasha magani mana mama take tambayan shi da hakan ? Da kyat yasha cokali kamar shidda ya aje cibin tare da mayar da jikin shi saman kujera ya kwanta da bayan shi a hankali. Muryan maji yaji don a lokacin na koma cikin dakin mu, maji tace mashi. Ka sa damuwa a zuciyar ka ko dubi yadda duk ka lalace lokaci guda, kana ganin zan cutawa rayuwan ka ne ko may sadauki? Ya dago kai tare da bude idanuwan shi yace namay kuma maji ? Tace akan auren da kake gani ina son tirsasa makayi ba da son ran ka ba mana. Yace maji ni fa banda zabin daya wuce naki a rayuwana akan may zan tayar da hankalina ga abinda kike shirin yi min gata. Mama taji dadin kalamin shi sosai a ran ta har fuskanta ya dan baiyyana murmushi kadan. Nan ta shiga mashi nasihohi akan hakkin aure tare da saka mashi albarka kwando kwando na mata biyayyan da yayi tana mashi fatan alheri. Sosai ya dan ji sasauci a zuciyan shi dan kasancewan da sukayi da mahaifiyar ta shi na dan lokaci, abinda ya dade baiga hakan ba a tare dashi tsakanin su. Ni dai tun wanan lokacin ban kara bi takan komai ba don ko kallon inda yake banayi balle nasha harara. Hakan yana matukar bata mashi ran shi sosai yakance a ran wai wanan abar ce zata zauna da mutum har ta farauta mashi ran shi yaji dadi a haka? Mace komai bata iya ba ban da dunkulewa a cikin hijjabi kulun kaman munafuka ko muguwa. Wama yasani ko maganan Amira gaskiy ne asrice maji sukayi don suci arzikin su. Don shi baiga abinda maji tagani gacwanan yarinyar ba har take kokarin yi mashi baki a kanta inba hasken fata ba kawai. Gashi baida yadda ya iya dole yasawa zuciyar shi hakkuri da wanan auren kaddaran don ya dadawa mahaifan shi rai kawai tunda suna so amma shi kan yasan an tsere mashi gurin matar gwadawa tsara kan. Ta ko wani bangare na gidan kowa sai shirin buki yakeyi banda mummy da babu nata ko daya a cikin bukin don ita yaran ta kanana ne kwarai agidan. Sai dai kusan tare suke harkan bukin bangare mama da ita don ta saka kanta tsunbul a ciki inda su umma ke fadin wai kwadai ne kawai ya kaita ciki don taga gurin ci. In bashi ba ai su ma yaran su ai diyan mijinta ne may sa zatafi bada karfi a dayan shiyan kawai. Ta bangare na ni kan ba wani abinda na shiryawa aure sai harkan bukin Anty maryam kawai nake yi kamar nima ba amarya bace, In dan anyi min magana nakance ni ba wani bukin da zanyi sai dai dan dama dama walima indan zan samuyi. Su mummy sun tafi sun gyara gidajen mu yadda ya dace duk da ba wasu abu za akaiba mai yawa saboda ko wani ango yasaka kayan komai a nashi gidan. Baba yai fadan haka yace don may zasuyi mashi haka da su bari shima yai wa diyan shi nashi bajinta da ko wani abu kewa yar shi idan zatayi aure. Kayan aiki ne aka kai muna irin na amfanin mata ko shi ba wasu masu yawa ba don sauran abubuwa irin su gas, su tv, fridge, toaster da yan kayan kitchen electronics akwaisu a kitchen din. Yan zuwa jai kaya suka dawo suna fadawa mama abinda ya faru a gidajen mi mama tace a daikai nata da ta saya muna hakk8n mune ta sauke muna ai. Saura kwana hudu buki ya shigo cikin gidan duk gidan a lokacin cike yake da baki yan zuwa buki yan uwan hauhuwan maji da ga garin su sunzo. Dakin ta ya samay ta da wata yarta ta dagin su mama take ce mai bayan sun gaisa dama ina son na gan ka don gobe ko jibi nake son akai Fatima gurin iyayyen ta don su ma suyi nasu bukin a can tunda ita yar fari ga mahaufin ta. Shiru yayi bai dago kai ba tace don haka sai naji naka shawaran akan tafiyan nata don ban san ko kana da wani shiri ba ? Yadago idon shi da suka canza launi yace maji ni wani shiri nake dashi duk abinda kuka tsara ai daidai ne. Ta kara cewa ina son ka basu mota da sauran kayan da zasu bukata a can akai masu don zirga zirga da amfanin su. Baiyi magana ba nan ma shiru yayi yana tunane wa maji ke son na tura wanan bakin kauyen ya kwana can gari ba wuta ba wani abin more rayuwa can. Ranan da za ai kamu gidan mu ya cika makil da mutane yan uwa da abokan arziki ta ko ina na bangaren dakunan gidan. Mata mu hudu ne maza ukku, sai dai a lokacin na bata tsarin abin don duk yadda akayi dani na fito zuwa gurin kamun naki futowa nashige bandaki na kulle kaina ciki. Mama tace a kyaleni tunda bani son fitowa agan ni ai hakan ba ibada bane ga mutane yan gulma da basu sanni ba sun cika gurin don son ganin kwam. Sai da naji ba kowa a shiyan duk sun watse sun tafi gurin kamu nafito na zauna a bakin gadon mu nai tagumi ni kadai a dakin. Sai ganin mama nayi tashigo dakin abinda ya dan sani firgita ke nan zan tashi tace koma ki zauna abinki na fahinci baki son ai maki kamu a garin nan sai a gaban iyayyen ki ko? Don haka kada ki damu gobe insha Allahu za,a tafi dake can zamu washe gari muyi maki naki a gidan mahaifan ki. Kuma kinyi gaskiya don wanan halin naki yasa nake kara kaunanki Fatima a raina don baki dauki karyan duniya ba ke a ran ki. Muna nan zaune tare da mama a daki har mutane suka fara shigowa tana kara yi min nasiha akan duk rayuwan da zamuyi na daure nayi hakkuri watarana sai labari insha Allahu. Ganin mutane sun fara shigowa yasa ta barni ta koma dakin ta sai lokacin ne na dan sake jikina nan na fara shirin tafiya don tace da safe zamu tafi garin mu. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,, IDAN KIN TURAWA WANDA BAI BIYA BA YA KARANTA ALLAH NAGANIN KI ZAI KARABAN MIN BASHINA GOBE GARE KI,,,, A LOKACIN MUKE,,,, Amaryam kan ta tare gidan angon ta Atiku maria haka ta kwana a cikin bakinciki ranan don tashin hankali. Washegari da safe ko kafin ta gama barcin ta data saba tafito ta samu har amarya ta fito ta gyara gida ta dora ruwan zafi a wuta. Ganin maria ta fito lokacin tana tsaye tana tara kwanon da tukanen maria, da yaran ta suka bata tun safen jiya har yau. Bingidan maria tayi da kallon yadda ya sha gyara ko ina, ina kwana ? Amarya Sadiya tace mata, cikin haushi ta amsa mata tace lafia kawai, Ta wuce zuwa bayi ta kewaya tafito tafara alwala duk abinda amarya keyi tana binta da ido. Bazata gwada wa amarya sadiya shekaru ba itma dai sadiya din zasu zo sa,a daya da maria din. Kafin duk yaran maria su tashi har sadiya ta dama kunu, ko sai ga maigidan ya shigo wanda tun fitan shi masalaci suna can suna zikiri bai dawo gida ba sai yanzu da gari yadan haska. Yana shigowa ya samu sadiya ta zuba kokon da ta dama ga sabbin robobin da tazo dasu gidan. Inda taimashi sannu da dawowa ta dauka takai katon roba mai kunu kofan Maria ta girke masu ta dauki nata da mijin ta tashiga dashi dakin ta. Sai gata tafito da sabon bucket a hannun ta ta deban mashi ruwan wanka takai mashi bayi. Zata fito ne ta samu maria ta idar da sallah tafito waje tace mata ga kokon ku nan a kofa na aje maku sai ruwan wanka dana sa su fito su fara wanka kada su makara zuwa makaran ta . Wani kallon banza maria ta watsa mata tace da baki gidan wake basu ruwan wanka dama kada ki kawo min sallo da iyawa don gidan kika shigo. Kuma ki koma ki dauki munafukin kokon da kika aje don mu baza musha abin sihiri ba wayasan inda kika fito da tarkacen tsiyan ki da zaki wa mutane sihiri kice wai kin dama. Haba yar uwa gumbane fa akayo muna shi wanda zamu amfana dashi kwana biyu a gidan nan. Munafuka mun san irin ku wazaki cuta sai dai shi daya daukowa kan shi, bata karasa ba Atiku yafito daga dakin amaryan nashi. Yace ke Maria wallahi ki shiga taitayin ki idan kikace zaki tirka min tsiya agidan walle na lahira nafin ki jin dadi. Ke ga kina iskancin ki nakawo ijjiya na saka maki ba fa fin karfina na kin yi ba. Raga maki dai nakayi don wa yanga yaran dakin ka gani ko suma yaran ba tausayin na kikayi ba da kina tasaya masu da baki kaisu mahalaka ba ke illata masu rayuwan su. Duk wace tace tashin hankali da diban albarka zata aza min agida bani daukon shashan ci yanzo don zama da mace ba dole na ba. Aliyu kai, Aliyu ina kake na ? Sai ga yaron ya fito yana sharan fuskan shi yace baba gani. Yace ku tai zuwa sallah in kun dawo ku taho ku karya kutai zuwa makaran ta kajiya. Sai amaryam tace gama ruwan wanka ceniya ga na aza masu suyi wanka sutai zuwa makaranta. Yace ke baki kunya ba maria, yaushe kika tashi warhaka har ki dama masu kunu su sha suyi wanka da safiya haka. Kuna na dai ko inke baki sha diyana sha sukai inga ta tsiya yau inkin isa, in tsiya kika so ko wane irina samunai ki kai ga Atiku. Ya juya ya wuce bandaki zuwa wanka nan yabar maria na fadi ashe akwai wadda akai agidan ga don walle in mace tace makirci ta iya gida nai ta taho wallah. Ni dai ba tashin hankali nishigo gidan ku yi ba aure na yakkawoni kuma ni tsakani da,Allah nika zama da kowa a rayuwa na don banda mugun nuhi akan kowa. Amma fa ki sani inkice ba wanga zama kika,bukata a gare ni ba duk wadda kika so yinai zamuyi keji na hwada maki wallah. Ta juya ta shige dakin ta tafara gyarawa kafin mijinta da ya,shiga wanka yafito ta saka turaren wuta daki ya dauki kamshin safiya. Maria na jin kamshi har dakin ta rayuwan ta yai matukar baci tace a fili karuwan banza kawai. Mamakin ta bai kai karshe ba sai da taga Atiku ya fito cikin wankakun tufafin shi Sadiya ta rako shi har kofan fita daga gidan ta kai tsugunne tana fadin. Ya Allah ka tsare muna bawan ga na ka bashi sa,a da rabo na alheri, ka bashi sa,a ga abin daya fita nemowa yaciyar da mu ta hanyar halal ya Allah ranan taga dariyan Atiku har sai da hakoran shi suka baiyyana a fili. Duk maria tana daga kofan ta tana kallon bakon al,amarin da ya shigo masu a gida. Atiku yafita cikin jin dadi yana fadin Ameen Sadiya nagode nagode Alkah yasa ki zama min alheri a rayuwana. Yana fita daga gidan maria tace wai sabon kicihi can muka fito har takalman ya tsinstinke indai namiji ayi dai mu gani gidan ga. Sadiya kamar bataji may maria take fadi ba ta,share ta dakin ta takara gyarawa tsab tafito kofinan da yara suka sh koko kafin su fita ta tattara su ta wanke da sauran kayan da tai aiki dasu. Kagin amarya tai kwana hudun ta maria ba karamin wahala tasha ba saboda Sadiya mace ce mai tsabta da mijin su ya dawo gida kayan da ya cire na aikin shi bata bari ya kwana bata wanke su ba. Haka dakin ta duk da ba komai a cikin shi sai ta gyarashi sau kusan hudu a wuni. Maria sai habaici da bakar magana take yaddawa cikin gida tai ta faman fada da yaran ta tana sauke haushin uban su, a kan su. ****** ********* ****** Wanka nayi don shirin kwanciya saboda ban tsaya dogon hira ba gobe mu da lecture mai zafi da zamuyi. Dogon riga fari mai dan hannu na dauka na saka a jikina ina kokarin daure kaina sai ga mama tashigo dakin namu. Tace dauka niyi ai keyi barci Fatima? Nace a a mama yanzun dai naka shirin kwanci wani abu zan maki mama ? Na tambaya cikin dan kallon ta a cikin ladabi da nake mata a koda yaushe in muna magana da ita. Tace, dama magana naka son muyi dake inba ki komai ke jiya. Nace walle mama mi nikai mashin ? Kwacinya dai naka shirin yin yanzu don gobe muna da lecture da safe insha Allahu. Ta juya tana fadin ki saman a daki na yanzun in ke gama. Daga haka ta juya tafita daga dakin ina gama daure kaina nabi bayan mama dakin ta. Na samay ta zaune a saman gadon ta sai dai yanayin ta kaman tana a cikin yar damuwa a lokacin. Ganin na shigo takw ce min zonan ki zauna Fatima tana dafa gado daga gefen ta alama take min a gurin zan zauna ke nan. A darare na zauna dan bakin gadon kadan dan nesa da ita, sai naji ta dafa hannu na daya tana fadin Fatima magana nake son yi dake don haka ki fahince ni kuma idan magana na da takura a cikin shi kada ki damu kanki don Allah Fatima. Nace mama hwadi dai maganan ki ai babu komai walleh na fadi cikin murmushi don nasan dai kila laifi nayi zatai min magana. Tace Fatima ina fatan bazaki fassara min magana ta ba da wani fasara gani ke dai kinka cancanci hakan shina yasa na aiwatar da hakan akan ki. Tace, bakomai na ba so dai nakai ki auri sadauki don dai ta kin ka san halinai kuma kina iya hakkuri akan duk wani baudaden hali nai. Kamar a mafalki naji zancen mama take duk da sanyin da dakin ta keyi na A C sai da naji zufa na karyo min. Tace na san cewa keta zaki iya hakkurin zama da yayan ki kuma ki rufa mai, asiri ga duk wani rayuwa nashi. Wanga dalili dana hwada maki shina yasa na yanke hukunci a raina keta zabina dama shi din. Tace Fatima nasan cewa a ranki zaki iya cewa missa nai maki wanga mumunan zabi a rayuwan ki . To maganan gaskiya gani nayi duk matan da yay aure babu komai cikin wanga aure nashi in ba tonon asiri ba a garai. Har da nima uwatai, ke har yan uwa nai sai gori ya ishe su gidan ga. Ba yau ba na dade ina wanan hwatan ni kadai a rayuwa ta, amma na rasa yadda zan hito maki da zancen. Amma yanzu nasan ke dan tasa shekarun ki yakai ta fahinta shinasa naga gara na hwada maki dai don ki san abinda naka kullawa a tsakanin ku. Wagga magana kuma da naka hwadi Fatima har tai kunnen Baban ku yasan da ita. Shima dai ya nuna farin ciki nai akan zancen, sai naji muryan ta ya canza tana cewa cikin murya mai kuka. Fatima Allah yasani ban yi wanga hadin don dai na cuta maki ba, nayi shina dai don samun farin cikin ku baki dai. Nasan cewa har yanzu bawai ya bar shan abinda yakasha bana ke ma ke san da haka Fatima, hwada min faina bakiyi. Don kina gudun bacin ran da zan shiga ciki nai shina yyasa baki son na sani. Fatima ance wanda ya rigga ka kwance yana riga ka tashi na san komai da sadauki kayi, a rayuwa nai don nita na haifi abina,. Nasan halin rayuwa nai sarai shi dai nayi don gujewa masifan da a ciki nai tunda ya boye min shina yasa nima nabar abin aboye kaman yadda kuka boye min din. Shin Fatima macen da ka irin wanga halin ai ta san kan ta na inda baki san kan ki ba duk wadda naka gwada maki halarci sai kin tai kin hwadai wani gurin. Ko ni ki hwada min nasan mi yaka ciki, amma kinka iya boye zancen sai kokari kikai kiga ya bar wagga har kan ke dai. Fatima kiwa Allah ki taimaka min akan wanga yaron don ban san mi, Allah ka nuhi ga auren ku ba. Nasan cewa na hada ki da aiki Fatima, amma gani nayi ke ta kadai ka iya tayani wanga kwaran ba tare da anjiya ba. Sai tai shiru kuka ne yafi karfin zunciyan ta a lokacin don haka ta kasa ci gaba da maganan ta. A hankali na zamo daga saman gadon da nake zaune tare da durkusawa daidai kafan ta nima dai din kuka nake sosai. Kaina ta dafa tace nasan baki son wanga hadin da naka shirin maku don shi ba son kina yakai ba. Amma na sani Fatima an, walleh sadauki sonki yakai so daina bai sani bashi, a ruyuwa nai. Kuma in kunyi aure duk bari shikai da yardan Allah ba zai wulakantaki ba Fatima an kuma ni ban barin hakan ya hwaru tsakanin ku. Jin tai shiru ni kuma ina duke na kwantar da kaina saman cinyan ta sai darzan kuka nakeyi. May zan bata amsa dashi nace ban son mashayin dan ta ko may, ? Inace bata kyauta min ba don batai man adalci a rayuwana ba duk da nasan batai min ba din ko may zan ce mata? In ce, mama kin cuce ni da kika hadi da danki mara mutunci mara tarbiya lalattace ko may? Ince bata kyautawa rayuwana don da itace ta haife ni da cikin ta bazata taba min wanan zaben da tai min ba ko may? Haka yasa naja bakina nai shiru sai kuka nake yi wanda na rasa kukan mana wani cikin tunane na nakeyi? Shiru itama mama din tayi tana nata kukan tana sauraren nawa da nakeyi cikin tashin hankali. Fatima nasan zaki ce ban kyauta maki ba a yanzu don bazaki gane may nake nufi da wanan hadin da nayi ba. Amma nasan nan gaba idan ina raye insha Allahu zaki gane haka kuma zaki gode min a rayuwan ki. Fatima gida bai koshi ba ai ba akaiwa dawa muma nan mu na bukatan kki a cikin mu, don haka mi zai sa in bari wanan baiwan taki ya tai gidan wani ina kallo bayan muma nan muna da bukatan ki a cikin mu. Ban iya cewa uffan ba har lokacin sai naji muryan mama tana fadin tai ki kwantawan ki keji indai kega da takura ki hwada min sai a hwasa. Da kyat na mike na fara tafiya kuka yaci karfi na don haka dashi na fita dakin mama tabi bayana da kallo tace a fili. Fatima am sai dai kiyi hakkuri don abinda ka hissheni na nakayi ke kadai ta ka iya halin wanga baudaden yaron da Allah yya ban. Kuka sosai nake a daki ni kadai gashi uwayen kallo suna can falo har wanan lokacin suna kallo. Maryam kamar an tsikare ta sai gata tashigo dakin dan wakan ta, sai ganina tayi a kwance na kifa ciki ina darzan kuka ni kadai a dakin. Mi nika gani haka shin? Missa may ki Bintu? Sai ma kara sautin kukan dana dan yi ban bata amsa ba, itakuma bata fasa tambayana ba tare da zaunawa gap dani tana tabani. Bintu baki hwada min ko missa may ki shi,? Ko sai na tai na hwada ma maji ta taho ta tambaye ki da kan ta? Ba amsa sai ta mike zuwa kiran mama don tazo ta tambaye ni da kan ta. Riko hannun ta nayi nace cikin kuka anty don Allah ki dawo kada kitai wurin mama don tasan ko may nakewa kukan. Shi wai minana dan Allah missa may ki kika wanga bakin kuka, wane irin bakar dabi,ata haka shin? Cikin wanga dare ke zauna a daki ke kadai sai kuka kikai kaman wadda aka aikowa mutuwa? Shi ko wani na yya mutu anka bugo maki waya wai ? Na fada jikin ta nace anty na shiga uku na lalace anty mika shirin hwaruwa dani na wai ? Shi wai mi an kayi na wai baki hwada min don Allah na sani ? Gashi kece kan na kira maji ta taho tagane ki shin minana hallan? Ina kwance a jikin ta nace anty na ga boni na lalace shi mi nai wa Allah da wanga bakin rayuwa ka shirin fada min ? Wane irin rayuwa na ka son hwada maki ? Wai yaya sadauki mama ka son na aura Anty yaya sadauki mutumin da duk duniya baida bakiyiya irina don dai ina hwada mai gaskiya. Wani kallo ta watso min tace Bintu auren yaya sadauki na kika wa wanga kuka haka shi ? Dama ba soyayyana kukai dashi bana ? Da sauri na girgiza mata kai nace ba wani zancen arziki da ya taba shiga tsakanina dashi ni dai nasan kaman annabi da kafiri muke ni da shiya. Maji na ta hwada maki haka ko wa? Nace ita ta ttakirani dakin ta taka hwada min bukatan ta garan. Yanzu kibar kuka Bintu muyi magana ta fahinta da keya don wanga kuka da kikai nima kuka na kason yi. A hankali na sasauta kukan da nakeyi don inji may zata fada min, ganin na rage tace shin Bintu ke baki son yaya na ? Nace walleh anty ban taba so nai ba a rayuwata mi zan yi da mutumin daya tsane ni a rayuwa nai? Tace ke yanzu zaki iya hwada ma maji baki so nai? Ta kura min ido cikin kuka nace walleh ban iyawa anty amma da ma mama na tai min wagga magana ba gaskiya hwada ma mai shi magana nakai. Tace to ke gani. Ni yanzu shawaran da nika baki shina hakkuri dai zakiyi kada maji ta fahinci haka gare ki. A yadda nasan halin nai shina kashirin balgace auren da kan shi ke ga dai ke komi bai hito ta bangare ki ba. Ko mi kki gani ga magana ta ? Maganan ta dutse don shine mafita a gare ni nace cikin kuka anty na gode shawaran ki na zanbi don shina kadai mahita agaran. Tace to ke gani amma a,a kika zama cikin daki ke dai kina wanga irin darzan kuka mi da baki kirani ba tundazun muyi shawara shin. Tace ke ga yanzu in yya jiya nasan ba karamin rigima zaiyi a gidan nan ba, tun da shi arniya mai dan buje yaka so. Wanan magana shine ya kwantar min da hankalina nan muka raba dare muna magana akan zancen har barci ya dauke mu zuwa asuba. ****** ********* ****** Tun ranan da akai zancen naji ban kara ganin shi bani haka nake ba walwala tare dani ko kadan yanzun ma idan na dawo daga school ban zama a falo ina dakin mu. Don ni idan da hali badon na gudu mama tace ban mata diyyauci ba da na gudu daga gidan gaba daya. Shima haka sadauki bai shigo ba gidan tun ranan da Baba yai mashi magana. Haka ya gaji da fushin shi ga kiran da Amirah ke damun shi dashi tana tambayan shi ko yai tafiyane bata ga ya shigo ba don ita batasan dawan garin ba. Maryam bata fada mata ba don ta fahinci Amirah bata kaunan hadi tsakanina da yayan ta don ita a ganin ta yayan ta yafi karfi wata Bintu can yar kauye can. Don idan maryam na magana tana min sheri kan yaya Anty Amirah bata iya boye kin da take wa hakan a zuciyar ta. Tashiga fada ke nan da maryam tana cewa kefa baki da wayyo don Allah may ye kuma na wanan magana ba dadi ina yaya zai kai wata Bintu can kuma haka. Ina gani maryam din tagane zuciyar yar uwar ta ne yasa ta ki fada mata komai akan halin da ake ciki. Mun tafito zamu school muka ganshi tsaye a kofan gida shi da wani mutum da gani dai mutumin ya girmay shi sosai. Ina ganin shi na dukar da kaina kasa ban yarda na kalli inda suke ba inajin maryam tana gaida shi ni kan ban tsaya ba na wuce abina. Sai dai shi muna fitowa idon shi akan mu don yana facing din hanyar fitowa daga cikin gida. Ya ramay ya dan fada kadan sai dai ba kowane zai gane hakan ba sai wanda ya sanshi sosai zai iya gane hakan. Ina tsaye tazo da motan ta ta dauke ni muka fara hanya, sai da muka dan yi nisa take cewa Bintu nace na,am anty. Mayasa baki gaida yaya ba ? Shiru nayi ba amsa tace indan kina haka maji bazata ji dadi ba gaskiya na fada maki ki nuna bakomai a zuciyar ki haka zai sa tafitar da zargin komai a kan ki. Nace anty ni wallahi ban son ganin shi ma yanzu bakiji yadda nake jiba a halin yanzu dana gan shi a zuciyata. Kada ki damu insha Allahu komai zai zama normal amma sai inkin bi shawara na fa. Don haka dakikeyi kin san yafi wayo zai iya hada ki da maji laifin ya koma akanki don haka ki gyara halinki tun wuri har inkina son kanki da lafiya. Ban tanka mata ba shiru nayi tare da kwantar da kaina ga glass din motan ta kawai. Can tace dama ina son indan mun tashi daga makaranta na fara koya maki mota. Da sauri na dago kai ina kallon ta nace, mota anty ni ina zan samu mota kuma? Dariya ta kyalkyale dashi tace kin san abin Allah ne yar uwa da zakice haka? Muna wucewa ya shiga gida bayan bakon shi ya wuce daga mamane sai Amirah zaune a falo suna karyawa a lokacin. Amirah tana ganin shi take cewa kai yayana har zan kai cigiya da sanarwa gidan redio da talabijin a kan ka. C U yace an fada maki ni raggone da zan bace ko ni bakauye ne da zanbace maku? Ya juya gurin mama yace ina kwana maji cikin dukar da kan shi yake gaishe ta. Ka gama fushin ne dakakeyi halan mara hankali kawai? Fushi kuma maji akan may zanyi fushi da abinda kike so akaina ? O nice ma mai so bakai ba ke nan ko mara tunane kawai, dariya yayi don zagin da maji ke mai bai san dalilin shi abugi mutum kuma a hanashi kuka ke nan yace a ran shi. Zama yayi tare da cewa bani breakfast dina Amirah ya fadi Amirah dake masu kallon mamaki bata fahinci komai ba a fadan tace. Yayana may kuma kaiwa maji hakane wai? Yace wallahi ban sani ba kaunata kawai dai maji na son min fada ne don taga ban shigo ba kwana biyu ni kuma aikine yai min yawa. Amirah tashige kitchen ta hado mashi abin karyawa tafito koda tafito ta samu maji na fadin. Kai akwai gatan da za,ai ma dayafi na daga kayi arziki ka samu yarinta gari yar arziki zata rufa maka asiri daga shi har Amirah kallon maji sukeyi don jin abinda ta fadi a lokacin tace eh ba rufa maka asiri zatayi ba may zatayi, kai may ya saura a jikin ban da ragowan maye sai ball. Yace maji nine yarinyar nan zata rufawa asiri ko zan rufa mata dai kece kike ganina haka maji amma ai duniya ta san ba abin banza nake ba yanzu. Wallahi maji inkina fadi haka a gaban ta dadi zataji ta raina ni don bata da kunya Allah. To ubana sai ka rufe min baki tunda kakawo karfi yanzu ka wuce fadana yace ni bance maji cikin dariya duk yana kokari yaga ta sauko daga fushin ta. Maji wai wata yarinya ta ki ka yiwa yayana sababi a kan tana haka? Cikin bacin rai ta dago tace mata Fatima mana ko da me ya fita oho? Itama Fatima in ba tauye tan danayi bata iya musa min ba mitakai dashi haka ba makari. Maji mi yayana zaiyi da Bintu kuma yar kauye da ita ba asali ga mata yan asali da yawa a cikin gari. Da may yahita da zakice haka, nice hwada min damay hita, ? Shi har wani asali yakaso yabar kyau ne tun wurin wanka ai yanzu ya makara da wanan ko? Da mamaki furcin mahaifiyan shi ya dago kai yana kallon ta sai abinci yake cusawa a cikin shi kaman dolle yake ci. Amma gaskiya maji kaman mara galihu zakice wai da Bintu zaki hada shi Bintu may can don Allah dai Amirah ta fadi haka cikin yanayin bacin rai. Walle Amira kihita min ga ido tun banci kaniyaki ba gidan ke ko kwatan Fatima kin kaine asali ne mi ake bukata ga asalin ba uwa da uba ba. Hwada min wane ta rasa daga ciki? Ko shi arzikin ga dakika gani Allah ya bashi kikawa katobara, haka. Ita ke san inda Allah zai aje tane halan ? Nikkara jin keyi wani magana mara dadi akan Fatima walle saina lahira yahiki jin dadi a gidan nan marasa ta ido kawai. Amirah tahau ta cika ranta ya baci ta kalli dan uwanta hadade guy ye haka son kowa kin wanda ya rasa amma ace ga Bintu yar tallakawa zai kare. Sai dai ba dama ta muda ko tak yadda uwarsu hau tasan yanzu nata na samun ta. Bai jima zaune ba yamike yana fadin shi zai fita, maji bata tanka mashi ba don haushi. Mun dawo gida a gajiye don an kusa fara kiran magariba a lokacin saboda huturu yayi. Amirah ce a falo, zaune ina shigowa naga wani ir8n kallon banza da wulakancin da tai min. Take nasha jinin jikina da zargin akwai wani abu bani ba har Maryam sai da ta tsargu . Mun shiga saida mukai sallah muka fito maryam ta fara fitowa bata dade ba nafito nima falon. Zama nayi tare da cewa anty Amira an fara film din end of love ne? Kamar batajini ba ta kyaleni maryam tace min yanzu za,a fara time yayi ai. Can taja tsaki tace dama kwadai ya kawo mutum ai don kwadayin tsiya abi an asarice muna uwa da tsafi sai yadda akayi muna da ita. Komai tsafun mutum dai wallahi sai ya bar mu kuma sai ya bar gidan nan don yawan kwadai ma har diyan mutum ba,a bari ba. Ke dawa ye kuma Anty inji maryam, ke tambayan ta cikin kallin fuskan ta. Ke dalla kyaleni da takaicin daka damuna yanzu don kwadai sai a asirce muna uwa tasa dan ta ya tillatawa kan shi wata gaja can mara asali. Kai amma anty Amirah na raina maki wallahi, wanga magana kuma ina ya fito maki haka da girman ki. Shi yaya din yace maki lakaka mashi ita akayi kan dole ko wa ya fada maki ? Maryam kifita idona wallahi kafin na bata maki rai a gidan nan don naga ke kina ganin kin girma wawiya kawai da batasan ciwon kan ta ba. Kasa hakkuri nayi nace Anty Amirah kamar yadda kike gani an lakakawa yaya sadauki ni haka nima aka lakaka min shi. Don ni yaya sadauki baiko cikin irin namijin da so na aura a,rayuwa na, don kwata kwata baya burgeni. Shi kuma asali da kike nufin bandashi uwane banda ko uba, bski fini uwa ba baki fini uba ba. Tsafi kuma ni bamu san shi ba a gidan mu a gidan ku nazo naga a na tsafi. Aiko tayo kaina wai zata mare ni maryam ta shiga tsakanin mu tace wallahi baki bugun ta don amsan maganan ki tabaki. Jin hayaniya yasa mama fitowa ta samay mu tana tambayan basin may yafaru kuma mayye haka wai ? Nan maryam ke dada mata abinda ya faru tsakanin mu da amsan da na bata. Tace Fatima shiyasa nake son ki don baki shayin kowa gurin fadin gaskiya. Wawiya kawai sakariya kinga har tabar ganin girma ki ta baki amsa ba yau ba nake ganin take taken ki kan Fatima gidan nan. Uba kika fita ko uwa ki fada min nace ? Gurin ubanki ko uwarki tazo maula kin taba jin Fatima ta roki wani abu a gidan nan duk zaman ta damu. Ku arziki yake rudi har ya rufe maki ido kika manta da Allah, da tazo gidan nan gurina may nake dashi. Shiru Amirah tayi karshe bata tsaya falon ba ta tashi fuuuu ta shige ciki can ta kira sadauki ta fada mai abinda ke faruwa a gidan yadda maji tai mata. ****** ********* ****** Ranan bamu zuwa school misalin sha biyu da rabi na rana maryam na baya tana wanki mama tana dakin ta tana barci. Sai ganin mutum nayi tsaye a kaina ban san shigowan shi falon ba sai da na gan shi tsaye a kaina. Ya nayi yana dan waige waige kamar mara gaskiya yace cikin daure fuskan shi ke jinan. Na dago na kalle shi saudaya na dukar da kaina yace wallahi duk kika sake kika yarda har maganan maji ya zama gaskiya a kan mu sai na halakaki garin nan. Mara mutunci kawai banza dake ina mai shawartan ki da kiyi maza maza ki sanarwa maji baki son wanan hadin kema. Jiki dan Allah ko na rasa mace a duniya may zanyi da kucakar mace mara fasali irin ki. Duk da zagin ya bata min rai sai nai murmushi a fili nace amma kaima kana da bakin fada mata ko don naga kaman yan maye basu da ta ido kaga kaine daidai ka fada mata idan kayo mayen ka. Ni kasan lafiyata kalau don haka ina da kunya da daraja ba zan iya kallon idon mama na fada mata ido da ido don ban da kuya ba wai ban son dan ta gudan jinin ta. Amma kaika nasan zaka iya tunda bata idone dakai ba inkai haka ka taimaki rayuwana da ga auren kaddara aure alkakai da zan tsinci kaina acikin shi gidan mashay,,,,, Kau ya kwashe ni da mari daidai maryam na shigowa falon daga waje, bata tsaya ba tai ciki gurin maji. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,, IDAN KIN KARANTA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA ALLAH NE SHEDA HAKA MUNA BINKU BASHI,,,, Tun da safe na na shirya komai nawa ina jiran ace nafito ne kawai, a lokacin don ko karyawa ban yi ranan. Ina nan zaune a takure maryam ta shigo dakin tana cewa a,a matar yaya ba dai har kin shirya ba kamar mai gudun mu kuma ? Hararan ta nayi idanuwa na sun dan ciko da hawaye a lokacin cikin murya mai kama da ta shagwaba nace haba dai anty maryam. Nice kuma matan yaya don Allah dai ki bari mana please wallahi kina kara tayar min da hankali Allah. Dariya ta kwashe dashi tace au to yanzu kuma may ya rage maryam ai kin zama matan yaya ko shafawa kawai ya rage insha Allahu. Abinci mama ta aiko min ni da maryam din wai mu karya da taimakon ta na samu har na dan kurba ruwan shayi a cikina. Ina nan ina zaman jira ina saye cikin wasu lace brown color sai duwatsun da akai mai ado dashi don nafi son dinkin riga da zani a rayuwana. Tun lokacin da naji wa,azin mace ta rasu an rasa zani a cikin kayan ta da za,a yafa mata zuwa makabarta nake jin tsoron dinka skirt sosai, ina dinkawa amma ba ko yaushe ba. Mama ta shigo dakin guri na muna zaune saman gado da maryam take ce min Fatima har kin shirya ne? Maryam tace ai tuni da anbi ta nata ma ai da yanzu mai kaita ya dawo ko tundazu. Murmushi mama tayi tace ai yau insha Allahu kuna zuwa ba fashi sai dai ban son ki kwashi kaya da yawa tunda kwana biyu kawai zakiyi a can. Nace cikin yar muryana kala hudu kawai na dauka mama tace yayi kyau haka sai ki hada duk wani abinda kike so anjima su hajiya lami zasu kai sauran kayan ki can gidan ina son naga kafin buki ya kankama na gama da komai naku ko. Mama koran mu ma ake kenan inji maryam tace ai muna tare balle ku da zaku zauna kusan uguwa daya da junan ku ai ba a rabu ba. Da sauri na kalli maryam tace nima haka naji ana fadi wai nesan gidan baikai gida goma ba a tsakani. Tace mama amma dai Bintu idan an dawo sai andawo da ita ta nan kafi a wuce ko? Tace sosai ma kuwa tare da masu zuwa daurin aure fa zasu dawo kuma kinga su nasu can da safe ne goma na safe za,a daura naku kuma sai da rana karfe biyu na rana. Don haka tana nan gida za, a daura naku ai insha Allahu, ko akwai wani magana kuma ? Maryam tace a,a shike nan ai dama ina ce ko shike nan daga yau dai mun rabu ke nan. Kun rabu mana tunda kowa zata kama dakin ta ku barni da wanan mara hankali muyi ta fama da ita. Mama tace bari na fita kinji Fatima na aika akira min sadauki naji yaya zancen tafiyan naku kada ai rana ba,a tafi ba kuma. Yana daki kwance yaji wayan mama ya shigo mashi ya dauka a kasale yana fadin salamu Alaikum. Ta amsa mashi yadda ya dace tace baka shigo ka karya ba mana tin dazun ga wanan yarinyar Fatima kuma zancen tafiyan ta fa may ka shirya akai? Yace maji bazan iya shigowa gidan nan ba yanzu don mata sunyi yawa wallahi, dariya yaba mama tace to ai duk uwayen kane a dakin zallan mu kawai. Yace No maji gaskiya ba zan iya shigowa ba saboda yawa ba zan sake ba anan. Tace ko abada akawo maka dakin ka ne yace shike nan maji hakan yayi. Sai da aka shirya komai na karyawan mama tace nazo na kaiwa sadauki breakfast din shi yana dakin shi. Wani irin faduwan gabane ya kamani amma dai haka na dake na fita da kayan a hannuna. Ina fita na samu Abdul dan wurin mama Asiya zai fita na bashi nace don Allah ya kaiwa yaya sadauki. Yace kai amma dai ke Bintun nan ke da mijin ki kuma kice baki iya kai mashi abin karyawa da kanki. Na dan marairaice nace yi hakkuri yaya Abdul bashi kadai bane a dakin shiyasa nake jin kunya. Yana min sheri ya karbi kayan ya shige mai dashi ina ganin ya shiga na juya cikin gida da sauri na. Abdul na shiga ya samay shi a kwace ya fara gauda shi tare da aje mai kayan abincin yace kai amma dai Bintu shine tace min wai tana jin kunya bakai kadai bane a dakin bazata iya shigowa ba don Allah na taimaka na kawo ma ashe wayo tai min ke nan. Murmushi yayan nashi yayi yace kyale yar kauye bata son shigowa ne tai maka haka . Yace ai zamu hadu da ita ne sai na rama nima har yakai kofa zai fita yajuya yana cewa yauwa yaya UF dama ina son ka bamu kudi zanyi party da kuma ball na mu yan unguwa akan auren ka. Yace kai Abdul party may kuma kawai da ka share da zancen wani party can ni kaga ba wani shirin da naiwa wanan auren. Kai yaya auren da muke son aji labarin shi a gari zakace haka auren ka ne fa na farko yaya muka gaskiya zamu cashe sosai ne wallahi. Sadauki ya mike zaune tare da jawo kulan abinci a gaban shi yace ka bari karfe biyar sai na ganka ba shi ke nan ba. Yana cin abinci yana tunanen rainin wayyo irin nawa common abinci da zan kawo mai wai bazan iya ba sai na bayar akawo mai. Kuma yasan da wani manufa maji tace ni na kawo mai abincin da kaina. Yai tsuki tare da fadi a fili yar kauyen banza kawai wai a haka zan zauna da ita kuma. Kiran wayan maji yayi tace maji yaron da kika ba abinci ya kawo min bai kawo min ruwun sha ba fa. Tace yaro kuma ba Fatima nace ta kawo maka ba yace ni Abdul ne ya kawo min abinci yanzu. Murmushi mama tayi tace kai Fatima wanan kunyane wai ko tsoro har yanzu ? Kaga abinda nake fada maka gashi ka saka tsoron ka a ranta tun yanzu yaushe zata sake dakai kana mata mugun ta haka. Tana gama waya ta nufi dakin mu ina kwance na kifa cikina a saman filo naji tana fadin Fatima yayan ku yace baki kai mai ruwan sha ba fa. Kara faduwan gaba naji na dai ansa a fili da to mama ina mikewa zaune kamar da gaske. Har tajuya tace ki tabbatar kece kika kai mai ruwan da kanki don in akwai maganan da zakuyi kafin ki tafi kan bukin ki sani. Kunya ya kamani na sanin da mama tayi bani ce nakai mai abinci ba kamar yadda ta umurce ni. Dogon hijjab dina na saka tare da daukan ruwa a jug na nufi dakin sai faduwa gabana ke yi a lokacin don nasan cewa zan samo wani sabon bacin rai ke nan kuma again. Dan sallama na tsaya daga kofan dakin inayi cikin yar muryana yagane nice sarai sai yaki karbawa. Na kara dan daga murya da sallaman naji yace please kada ki cika min kunne da wanan muryan naki kamar na munafukai don Allah. Jin haka na sa kai cikin dakin yana kwace rigigin gine daga shi sai dan wando three quarter a jikin shi da yar singileti. Na kai ruwan inda naga kayan abincin farko suke na aje tare da juyawa zan fita daga daki. Naji yace manya kawai watau sai da kika nace sai kin aure ni ko don bakin jaraban ki da nacin tsiya. To ki saurara sai ki shirya zama da U F don baki san koni wane ba da baki yarda da wanan bakin hadin auren ba. Murmushi nayi nace niko nasan ko waye mijina fiye da kowa don ni san akwai aiki ja a gabana na sharan amai da fitsri irin ta mashaya. What ya yunkuro kafin na karasa fita ya cafko hijjab dina ta baya sai naji gaban ya shake ni sosai, na sa kara da dan karfi ya karasa riko min kai tare da rufe min baki yana fadin . Ashe ke yar karamar yar iska ce tukun may zaisa ki gudu tunda kin isa nine mai amai da fitsari ko? Nace baka taba min bane karya nai maka idan ka manta aini ban manta da hakan ba, kaga nafi kowa sanin halinka ke nan. Yanzu abinda yarage min na goge na kwashe idan kuma nayi arziki baka hada min da kashi ba ai na gode Allah. Wani irin shaka da karfin shi yakai min sai da idanuwana suka fifito waje kwala kwala kaman zan somay. Yana fadin zaki ci uban ki kuwa inkince ke yar iska ce don zaki dan dani wahalan ki a gidan. Yace good haka ma nake so gara ki shiga shegiya na gasa maki kwakwa ga hannun ki, kagin na wullakantaki na mayar dake karamar bazawara gidan nan. Nace shine dama sauki na in har kai min haka da sauri ka ceci rayuwana don, zaman kaddara dama kawai zanyi da kai. Yakai wa kaina bugu da karfi sai da na gwauro da bango idona ya kawo hawaye nace dama duk matar mashayi wanan ne sakamakon ta ai duka da zagi da cin zarafi banyi mamakin haka ba don na shiryi taron irin wanan ddaga gare ka tun tuni. Akan mama zan iya hakkuri da duk wani cin zarafin da zakai min matsawon hakan zai mata dadi a ran ta. Don nasan darajan mama nasan kimar mata a rayuwana kuma ban manta da irin halarcin da tai min ba a baya. Don haka kaga tunda wanan ne kadai hayan da take ganin zan iya saka mata da alherin da tai, min ashirye nake da na rugumi duk wani kaddaran da zan tunkara a gidan ka. Fita min daga daki yar kauyen banza kawai mara tarbiya wace bata san komai ba sai rashin kunya. Nace nagode na gyara hijjab dina na fito daga dakin, idona taff da hawaye, sai da na saita kaina na shiga cikin gida. Dakin mu na koma na kwatan ina tunanen makomar wanan auren da ake shirin kullawa a tsakanin mu a haka. Ni dake fanin da safe zamu tafi sai gamu sai sha biyu da rabi na rana muka bar sokoto zuwa kauyen mu. Tare da rakiyan yan uwan mama da suka zo daga Niger state gurin buki sai kawaye na muyi yan layin mune kuma school din mu daya dasu tun secondary school muke tare dasu. Mun samu gidan mu ya cika makil da yan uwa da abokan arziki, da suka zo gurin buki nai matukar mamaki yadda na samu an gyara gidan mu a lokaci guda haka. Dakin da zamu zauna an saka katifa maya guda biyu a cikin shi, nan muka sauka bakin da muka zo dasu basu dade ba suka koma don akwai event din da za,ayi na matar Ahmad gidan su suna son zuwa. Sai bayan mun hutane nake jin wai mamana tana gari ta zo amma tana gidan su. Da yamma aka sakani lalai kamar yadda al,ada yake a garin mu nan aka shiga shagalin buki, sai abinci ake ta faman tukawa na farar shinkafa. Muma munzo da kayan cima da abokaina zasuyi amfani dashi a garin don haka ba sha wani wahala ba sosai. Sai da safe naje gaida mahaifina yake ce min Fatima Bintu kinzo kin samu alherin da mutanen arzikin nan sukai muna a gida nan ko? Alhaji ya aiko daga can birni an gyara muna guri don baki masu zuwa daurin aure sai kuma jiya gashi da safe kafin ku iso anzo da abinci da katifo wai daga marikiyar taki ta aiko dashi. Nace an gode Baba ya ce tau Fatima sai dai ban tsanmanin zamu kara samun lokaci irin haka dake ba. Abinda nake son ki sani shine shi zaman aure dan hakkuri ne don yanzu so ya kare a tsakanin ku sai hakkuri. Yi nayi bari na bari inji manya sai a zauna lafiya, kin dai san ance mijinki mutum mutane ne gashi kuma dan gidan yawa. Don haka ki zauna da kowa da halin ki duk da nasan ki amma ki kara da hakkuri Fatima, shi hakkuri baya karewa fa musulmi. Duk da a hasashe na ina fanin kaman wanan aure aure ne na hadin iyayye a tsakanin ku dashi halinki shiya ha har suka kwaidaitu da son zaman ki da dan su. Don haka ki kara wani saman wanda suka sanki dashi sai kiga akarshe ke ce da riban hakkuri. Take naji idona ya ciko da hawaye har na kasa control din su sai da suka zubo min nan dai baba yaita min nasiha akan hakkuri da zamantakewan aure da kuma sabon rayuwan da zan shiga ciki. Mukai sallama dashi yana ta saka min albarka tare da fatan samun zuria dayyaba. Yinin ranan haka nayi shi a kwace babu walwala tare da ni ga mutane sai masha,an da sukeyi kawai. Da dare gwagona mai masa tazo tace nazo mu tafi gidan su mahaifiya na don ko can akwai yan uwa da suka zo buki. Mun shiga gidan mutane sai jin dadin gani sukeyi suna ga amarya tazo gaida ku. Nan muka shiga gaisawa da mutanen da na dade banga wasu ba sai ranan. Sai wani lokaci na samu kebewa da mahaifiyana a wani daki dagani sai ita muka zauna a dakin. Tace tau yarinyar ga gashi dai Allah yayi zaki aure yanzu don Allah idan kin je kiyi hakkuri da sabon rayuwan da zaki tsunta a sabon gidan ki. Ance zo mu zauna zo mu saba ne sai dai mu mata da hakkuri aka san mu dan namu yafi na maza don mune a kasa garesu. Kina dai ganin irin rayuwan da nake ciki ba sai na fada maki ba kin san hakkuri nake dashi don da ban hakkuri da tuni nabar gidan nan na,watsar da yaran nan. Amma sai naga idan na fita na barsu dawa kuma zasu zauna har ya basu tarbiyan da nake son su samu saboda kinga shi wanan ba irin naki mahaifin bane. Ina jin haka sai wani irin kuka mai karfi yazo min don tausayin mama na dani kaina. Da kyat ta dan lalashe ni na sasauta cikin kuka nace mama ina ganin kusan rayuwa guda Allah ya jefo muna na aure. Don kinga shima din mashayi ne ne kaman baban su musa sai dai dan banbancin su kadan ne don akwai wayewa a cikin nashi. Mama bana son shi na tsane shi natsane shi a rayuwa na amma sai gashi magaifiyan shi ta nemi alfarma a guri na akan na rufa mata asiri na aure shi. Mama may zanyi da mutumin da bayaji tsoron sabawa Allah bai dauki sabawa Allah a bakin komai ba. Mama don mahaifiyan sadauki zanyi wanan auren don ba zan iya mussa mata fa bukatan taba a gare ni. Mama ta katse ni tace amma kin bani kunya wallahi yarinyar ga ina iliminki da tarbiyan ki ya shiga da har kike ganin ba zaki iya taimakawa hajiya ba yau. Tace da kikaga hjy ta zaboki a cikin dubu ta bukaci ki auri dan ta kina zaton don kyau kine ko arzikin ki ko wani abu can. Tayi hakane don tana hasashe watakila tagare ki zata samu nasaran raba dan ta da waban halaiyar tashi. Bafa don bata sonki ne tace ki auri dan ta ba suna da kudin da zasu aura mao duk macen da yake so a duniyan nan. Amma kikaga ta nace akan sai dai ke din take so ki zauna dashi, nasan kuma tai hakane don tana ganin ke ce kila zaki iya kawo karshen wahalan nashi. Shi fa hanyan sabon Allah shiga rai ke gare shi sosai, daga lokacin da akace wanan abin baida kyau haramun ne, sai kiji zuciyar mutum na tura shi aikata shi a ko wani lokaci. Shiyasa akace an zagaye wuta da abin sha,awa wanda zuciya ke so, an kuma zagaye aljanna da abubuwan ki wanda zuciya bata so. Don hakane duk wanda ya kama hanyar aljanna zai ta haduwa da abubuwan da zuciya bata so, haka kuma shi wanda ya kama hanyan wuta zai hadu da abubuwan da zuciya ke so. Shiyasa akace daga cikin hakkurin da ake son mutum yayi shine harda biyayya ga Allah da manzon sa dama magabatan mutum da kuma hakkurin gujewa sabon Allah. Hana zuciya aika ta sabon da ya ginu a kanta farat daya abu ne mai wahala so sai sai mai hakkuri. Idan kana da hakkuri zaka iya jure jawo hankalin mai yawan sabon Allah sannu a hankali ta yawan nasiha da lurar da mutum illar abinda take aikatawa. Uwa uba kuma addu,a da nasiha ga mutum har Allah ya bada sa,a ya bari ko ya rage. Yin fushi da mutum ko kaurace mashi baya hana mutum sabawa Allah sai dai ma ya kara kangarewa kawai. Amma jan mutum zuwa jikin ka shike sa mutum ya rage watarana har ya tuba ya daina gaba daya. Don haka ita hajiya taga cewa, kece kadai zaki iya taimaka mata gurin wanan yakin. Don haka yaki babba a gaban ki yar ba don hajiya ta dora maki nauyi mai girman dauka gare ki. Fushi zagi gori da kawar da kai ga abinda yake aikatawa yanzu ba naki bane yar baba. Don haka wani kawar da kan ki gare shi ko ki kyamace shi ba naki bane yanzu. Don idan kinyi haka tankar kin kara tura shi ga halaiyar da yakeyi ne na kyamata da uwarshi bata son ganin shi a ciki. Hajiya ta wuce ki watsar mata da bukatan ta gare ki, sai dai ki kara runguma kawai da hannu bibiyu. Zata ci gaba da magana gwagona ta leko tana cewa fito mana Bintu, dare fa ta soma kin san ba wuta garin. Haka yasa nai sallama da mahaifiya na tana ta jero min addua irin da yadace duk uwa taiwa yar ta da zata dakin auren ta. ****** ********* ****** Waagegari tun da safe wata mota ta iso da kujeru da rumfuna suka shiga hakawa sai kuma fa mota da abinci ruwan sha na gora da leda sun iso. Inna ta bawa ranan ta arare ta yafe itace kirjin buki arziki ya sauka mata a gida sai yadda tayi zuwa tara da rabi sai dirin motoci ke tsayawa a kofan dan gidan mu. Haba take guri ya kaure da yan ma,abba sai kirari sukeyi fa Alhaji wani ga Alhaji wani yazo. Zuwa can wani mai murya ke sanar da jama,a ta lasifikan shi Allah yayi lokaci yayi yau an daura auren Umar faruq da Fatima Bintu akan sadaki naira dubu hamsin. Sai wata matar babana ta rangada wani irin guda tana fadin yau Fatima Binta kin gwada muna kin haihu a zariyan Ibrahim da maimunatu don kin jawo muna arzikin da bamu taba sanin akwaishi na garin nan. Allah yasawa auren ku albarka yakawo muna zuri,a dayyaba masu albarka arayuwa. Bayan dan lokaci muka ji mata na fadin ance ku gyara ga angonne nan zasu shigo gaida ku cikin gida. Ina can boye kuryan dakin Inna tabawa naji matan tsakar gida na fadi wanan na tsakiyan dogon ai shine angon lalai Bintu kan kin yi sa,an miji wallahi da ganin shi ba karamin mutum bane. A raina nace baku san komai ku kumbu a rufe ganin kyaun dan maciji kuke mashi haka dahi nanan cikin shi. Ba wani bata lokaci matan da aka zo dasu suka fara cewa wai a fito da kaya zamu tafi take na saka wani sabon kuka mai tsuma zuciya. Bashar ne ya dauko ni a motar shi sai kaunan mahaifiyata wata malaman arabiya ce ita sai gwagona dana zo birni a wurin ta, kawa yena su biyu haka muka shigo mota daya dasu. Tun da muka fara hanya ina a dunkule sai kuka nake rusawa a hankali gwagona tana min fada wai zan jawa kaina ciwon kai a banza kamar wace za aika gidan mugun abu. A raina nace kyace haka mana tunda kin ja min mugun rayuwa a sanadinki duk na fada cikin wanan rayuwan haka ai. Bashar yace gwago kyale Fatima tai kuka yau don zata fada sabon rayuwa kuka ta zama dole gare ta. Magana ce yai mata a cikin magana wanda duk cikin motan nasan sai ita kadai ce zata fahinci hakan kawai. Gida ya cika yacika ya batse kamar may yan uwa da abokan arziki nisa da kusa birni da kauyen an hadu. Muna na isa aka fara futowa zuwa taron mu yan uwan mama da yan uwan mahaifin su yan uwan umma da mama nasu suma ya ishe su ranan. Ga Nafisa tayi halinta suyi party tayi tatil haka tashigo gida tana ta watsewan ta gidan Amarya yaya Ahmad kuma suma suyi nasu bushewan sai tir da Allah waddai akeyi masu ta ko ina. Part din maji ne ba wani abin asha da akaji don bukin yaran ta neat akeyin shi cikin mutunci da sanin ya kamata. Ina rike da hannun kaunan mahaufiyata da yan uwan ubana don atare muka iso da sauran yan kawo ni daga garin mu, Wanan kauna mamana ta dan duko tace saka kafan ki na dama ki ja basmalah kafa ashirin da daya tare da karanta, (fihizuma, wa huwa ala kulli shai in kadirr,,,, kafa ukku) Nan mukaja muka tsaya kaman muna wani abu na karanta tace kin gama nace eh tace ubangiji Allah yasa ki shiga da kafar dama Fatima. Mama tana jin mun shigo ta taso da kanta tazo ta tare mu ta rungumoni jikin ta tana maraba da diyata sannun ku da zuwa. Dakin mu na shige da kawaye na na samu su maryam dakin ya cika da kawaywn ta. Suna ganina ta saka ihu tare da shekowa ta tareni da murnan ta nan muka zube na hira ni dai ban da kuzarin bata amsa sosai a lokacin. Zan iya cewa ni dai tunda aka fara shagalin bukin mu ban saka Amirah a idona ba har naje na dawo din ban gan ta ba ga gida ya cika ya make da mutane. Nace niko banga Anty Amirah ba fa tace wa tana can gidan yayan mu da wasu baki ma, ana dai ince maki tana gidan ki can ta tare yau tun safe suke can da kawayen ta wai suna wa bakin shi abinci. Kin san ita yar ba ruwan mu ne daga cikin mu adole a bayan yaya take bata san zatai kunya ba idan yaya ya shiga hannun wanan matashiyar matar tashi da nake gani. Nace kai anty zaki fara ko tace wallahi Bintu bakiga yadda kika koma ba yau gaba daya kamar wata yar kasan etopia can. Kin san sune yakar kyayo acikin jin sin na yan adam. Karfe daya da rabi a kaje daurin auren yaya Ahmad wai na yaya Imirana tun bakawai na safe aka daura don su haka akeyi gidan matar shi. Biyu da rabi aka daura auren su Anty maryam da Anty Nasmatu diyar mama, ita ba ruwan ta da sha,anin kowa a gidan mu irin masu akidar ra,ayin rikau ne ita. Muna nan akace wai za,ai dinner da karfe bakwai zuwa takwas na dare. Haka yasa ana idar da sallah magariba mummy tace kowan mu ta fito dama muna cikin shiri tun yamma kowa ta kimtsa tafiya gidan ta. Nice farkon kaiwa don tare aka fita dani da maryam anty Nasmatu yan uwan uwar ta suka kaita ita ma. Jin an dakatar da mota yadan sani bude fuskana kadan gidan da nagani sai da gabana ya fadi don zakace ba cikin garin sokoto kake ba a gidan. Hankalina yai balain tashi ina yaya ya samu kudin da yai wanan gida haka ba dai a ball kawai. Ina jin Inna tabawa na fadin dankari ba fashi wanan gidan haka shine dai gidan Bintu ko kuwa? Ina makalle ga hannun kaunan mamana wacce dama ina ganin don haka yasa tazo daga bangaren mamana. Tace idan zaki saka kafan ki akasa ki karanto fatiha kafa uku, ko wani da bissimillah. Sai ki karanta Basmalah irin na dazun kafa ashirin da daya ki karanta falaki da nas ki hada da ikilas uku uku Allah ya sawa aure albarka ya kare muna ke daga duk wani abin ki na cikin aure. Ina idarwa ta kama hannu na tare da rada min ki dinga karanta Hasbunallahu wani imal wakeel har mu shiga ba adadi. Muna tafe masu guda sunayi masu suraitai nayi niko ina saman bakina har abinda batace ba idan yazo min janakeyi na neman tsarin daki. Nan aka shiga bin gidan da kallo mun samu yan uwan mama acan sune suka tari amarya. Muna nan dai akace afito akai maryam nata gidan ba nisa sosai don unguwa daya muke. Wata kawar anty Amira mai makeup ce tashigo dakin bayan an watse tace amarya nazo nai maki makeup na fita dinner ne. A hankali na kware rufin da ke kaina sai naga tare da su Amira suke da kawayen ta naji mai makeup din tana fadin masha Allahu friend wanan ce kike kira da yar kauye haba waban aiko a fashion sai haka mana. May kuma ake bukata ga mace ga kyau ga wayewa duk a gurin nan tsoki tayi tafita daga dakin tace ma sauran su fita su bar mu. Ta busu tarufo dakin tace na taso na saka kayan da suka shigo dashi a jikina kallin kayan nayi da mamaki nace wanan kayan zan saka tace eh shine angi ya sayo na dinner. Ba yadda na iya dole na saka kayan hakana a jikina ba don naso ba sai da zan saka nagane akwai wani daga ciki mai tare jikin mutum. Tana min kwalliya tana min gulma wai may yasa Amira take ta faman kusheni ne haka ita bata taba zatin haka zata ganni ba. Don Allah kada na damu da duk abinda Amira da yan uwan ta zasuyi min hassadane kawai take gani yana damun Amira. Nace haba anty kin taba ganin mutum yai hassada da dan uwan shi nima fa kaunan tane halinta dai ne baku sani ba amma haka take ita. Tana min magan ganu akan rayuaan mazan yanzu abinda zakayi wanda zaka kama miji da sauri a hannun ka ni dai umhumm kawai nake ce mata har muka gama komai da ita. Ba matar ba ni kaina nasan na hadu haduwar da ban taba sani ina da shi ba irin haka sai yau. Sai tara da rabi akazo daukan mu zuwa gurin dinner wata irin haddan motace aka bude min baya in shiga. Duhu bai bari mutim ya gane ko mai a ciki sai da na shiga na zauna a zatona zamu je daukan shi inda yake ne . Sai da mota ta fara tafiya a hankali naji an matse min hannuna dana dauka kujeran motan ce na dafa. A hankali ya kare tankware hannun nawa yace welcome to ukuba house baby Fatima. Wani irin faduwan gaba naji amma na dake yakara cewa da fatan dai kin shirya danmaran taron abinda kika fada a shekaran jiya ko? Nace shirye nake tsab da su don nasan cikin shi na shigo dama yace good baby good. Haske fitilon da ya haska gurin zakace rana ne a lokacin motoci kanan duk motan dake garin aka kwaso ranan. Zaka ji kida na tashi daga duk inda kake a farfajiyan gurin da kewayen shi. Sai dan wani lokaci wasu mace da namiji suka zo inda muke dafa baya na gane summaiyace kawata da mukaje kauye da ita sai wani da ban sani ba namiji. Sadauki yadan rankafo daidai kunne na yana fadin idan kika bani kunya da halinku na kauyawa wallahi nima sai na disga ki a taron nan kinji na fada maki. Tare muka jera dasu zuwa wani dan karamin kofa shiga wani guri a hole din sai ganin maryam da Bashar din ta nayi. Mune a gaba shiga hole din suna bayan mu naji bashar na fadin Ubangiji Allah ya sakawa maji da gidan aljanna da wanan hadin da tayi haka. Muna shiga saida gabana ya fadi don irin taron da na gani a gurin mutane sai kace ana wani taron addinine. Nace hasbunallahu wani, imal wakeel a hankali. Wani haske da kamshi da wasu abubuwa ake watso muna take guri ya dauki ihu up U F kayi daidai wallahi. Sai wani dan washe baki yake kamar da gaske yana so mun zauna aka fara event yadda akeyi a ko wani buki na dinner. Gurin yanka cake a tare mu duka hudu muka mike ko wani ango yana rike da hannun amaryan shi, Sai dai ni nawa angon rikon keta yai min don yatsuna duk sunyi ja saboda matsa da yayi masu na kyata. Shine ya fara yankawa yabani ba dan guntsura kadan aka hau tafe sai ni kuma na yanko kato na kai mai a bakin shi mugun sai ya hada da hannuna ya tauna sai da nai kara aka saka ihu. An fitar da mu wai muyi rawa ni dai ina tsaye shine dai ya dan taka kadan sai lokacin nasan wai yan kwallon su na kasa sunzo taya shi murnan aure ashe. Nan suka zagaye mu suka fara ruwan dollars akan mu suna fada mashi wai yaya akayi ya iya zaben mata haka gani kuma very young dani. Duk wanda yazo zai mashi farin ciki akan ya iya zaben mace komai nashi a sa,a yake shi. Sai sha biyu da rabi nace nifa barci nake ji gaskiya zan je na kwanta ga photo da muka sha har nagaji ranan. Hakan yace wa Bashar akai mu gida naji bashar na fafin kaifa yace yaya zan tafi nabar abokaina ka kuma san ina da bakuwa sai na lalabata fa yace kadaiji tsoron Allah wallahi. In banji tsoron Allah ba bashat tsoron ka zanji kafasan yanzu wallahi surukin ka nake ka tuna. Bashar yace nima ai surukin ka ne tunda kaunata kake aure kaga munyi one one ke nan ai. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,, IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANI MUN BARKI DA ALLAH,,,, A LOKACIN MUKE,,,, Maria ta rasa may ke ma rayuwan ta dadi yanzu don gaba daya hankalin Atiku na gurin sabuwar amaryan shi da tashigo mashi da sauyin yanayin rayuwa. Duk wani ladabi da biyayya na aure amaryan maria ta iya shi haka yasa take ta sace zuciyan Atiku don dama haka maza ke so . Gashi da ita da dan ta abinda ya faru dashi na kaddara yaki gogewa gare su. Kusan kullun sai yaron da akaiwa fyade ya dawo mata gida da kuka wani yai mashi gorin abinda ya samay shi. Itama dai din idan gidan buki ta tafi ko unguwa haka mata zasu dinga cewa Allah sarki ashe itace abin ya faru da dan ta. Abin kunya harda yan uwan ta na jini sai su dinga fadar maganan yadda hankalinta zai kara tashi taji kaman a ranan abin ya faru da Aliyu. Ga maigidan ta da yake yawan musguna mata a gida duk abin da tayi bata iya ba yanzun gareshi. Saboda tabon abin da ta aikatawa dan shi ya matukar tsaya mashi a zuciyar shi sosai. Ta ramay tai baki sosai gashi sanyi ne yanzu bata cinikin ruwa ko kadan kuma ko banza bata da mai mata talla yanzu. Wanan bakin cikin da take ciki da yai mata yawa yasa ta tafi gurin mahaifiyan ta cikin tashin hankali. Nan uwar take ce mata ai sai ki zauna ki ta hadiyan bakin ciki, in kina fidda kudi, kije ai maki aiki ki samu kan mijin ki ki fitar idan kuma kin boye su sai dai ki zauna kina hadiyan bakin cikin da namiji kina kallo zai zama mijin ta ita kadai. Hakalin maria yai mugun tashi da maganan mahaifiyan ta nan dai ta bata shawaran ta dawo akwai inda zata kaita don mutumin aikin shi kaman yankan yukane saboda gwanancewan shi da iya aikin shi. Take maria taji kamar an cire mata damuwan ta don sai take gani kamar har tayi nasara ma ko a lokacin. Ta dawo gida da farincikin ta ta samu har amaryan ta ta gyara gida sai kyali ,gidan keyi don ko yaushe a cikin gyara yake yanzu. Tai ma Maria sannu da dawowa ta amsa mata a tatsune ta fada dakin ta don ko sallah batayi ba a lokacin. ****** ********* ****** Ina idar da sallah na fito na fara gyaran gidan kafin wani lokaci gidan ya dauki kamshi gaba daya, nan na fada kitchen for the first time don na fara girka abinci da akaina. Kayan aikine na electronic gasu nan kala kala a kitchen din na fara tunanen wani simple abinci zan yi a lokacin. Ina bude store din kitchen din naga kayan abinci da na,shaye, shayen, kwali da sauran duk abinci da sha tap a store din. Na dan dade tsaye ina bin kayan da kallon mamaki don abin yayi yawa sosai a store din. Dankalin iris na debo tare da kayan miya nai tunanen yin dan fate mai ruwa na sa naman koda dake cikin fridge din na dan yi amfani da danyen attarudu. Sai ruwan shayin dana dafa yaji kanunfari kamshi na tashi daga cikin shi. Ina tsaye a dining ina gyara kayan abinci naji ya shigo gidan cikin kayan motsa jiki yake. Ban san baya gidan ba sai da naga dawowan shi daga inda nake tsaye nace mai ina kwana. Lafiya kawai ya amsa dashi ya shige part din shi kai tsaye inda ya shiga wanka. Nima wanka na shiga na gyara jikina ina tsaye bakin wardrobe dina da hijjab dina don sai da nai sallah walha, zan dauki kaya naji an shigo dakin. Na juyo a firgice ina ganin shine nace cikin daure fuska don may za,a shigo min daki haka ko sallama babu kuma. Kallon mamaki yai min tare da daure fuskan shi sai kuma naga ya dan dara yace dakin ki fa kikace yarinya? Nace au nan din dakinkane ko kaga ni nashiga naka dakin ne da zaka ce nan din ma nakane? Yace lalai yarinya kina da karfin hali wallahi ni da gidana kuma yau ake son kafa min doka akai. Yace to bari na tunatar dake in har kin fara shagala kin samu gidan zama. Ki sani duk wani abinda ke cikin gidan nan gaba daya har ke mallakana ne don baki san yadda na samay su ba. Saboda haka ina son ki shiga hankalin ki daga yau don kada ki wani mike kafa wai ke ga maigida tunda kinga banza ko ? Ashe shiyasa jiya nida gidana da kayana har kika sawa daki key wai ke ga mai daki ko? Nace saukin abin dai nima ba kasuwa aka dauko ni ba dai yace towa kuma yasani sai anbincika wanan. Raina yai balain baci nace kamar yadda kaima akwai alaman bincike akan ka dole. Sadauki yai murmushi saboda yaba ma karfin halina yace yarinya idan zamuci gaba da haka zanfi kowa farin ciki da hakan a gidan nan. Yace ai duk macen da zatayi abinda mijin ta ke so ana kyautata zaton samun sakamako mai kyau a gurin ta. Don haka mu zuba dake a haka a gidan nan aga wanda zai sha wahala. Ya fara tafiya yake cewa sai ki fito muci abinci don ban yarda dake ba kada ki kashe ma uwana ni. Nace bazanci ba idan kaci sai ka mutu don kai ke tsoron mutuwa yanzu kuma ma na kashe ka nakai tarin zunubin ka ina ? Yai murmushi yace ban dai yarda ba na fada maki ina jiranki a falo don nasan halin yan kauye da son banza don a gajewa uwata da yan uwana dan abinda aka gani. Ya sa kai ya fice daga dakin yana dariyan keta raina yai balain baci haka na karasa shiryawa ina mitan maganan shi a raina. Kaman bazan fita ba amma kuma sai tsoro ya kamani kada yazo wani abu ya samay shi ace nice nafito tare da dan saka takalmin na tare da daura dankwalin rigana ga kaina sai karamin hijjib na saka iya kafada na. Saye nake a cikin redmaid din dogon rigan abaya maroon color nafito nima sai kamshi ke tashi a jikina. Yana zaune yana waya yana jin motsin fitowana ya kura min ido da sauri naga ya kawar da kan shi gareni. Ashe gaban shi ne yai wani mugun faduwa ganin yadda na sake mai a lokaci guda. Naja kuran dake gefe zan zauna yace kaji min yar kauye yana kashe waya yake kallona yace wancan kujera zaki dinga zama mai fuskantar wanan don kada wani ya shigo ya samay ki cikin zaman kauyawa ace yar kauye na kwaso gida na. Ban zauna ba sai jawo plate din da nayi na fara zuba mashi abinci komai da ya dace na dan zuba mai yadda muka saba zuba mai a gida. Na koma na zauna a inda ya umurce ni yana daukan spoon yace one warning again daga yau idan ina gidan nan bana son ganin wanan takunkumin hijjabin naki kamar zaki cin kasuwan kauye dake. Nace ai ni ba don ka na saka ba don Allah nake saka abina dama. Yace kin makaro da wanan dakin zauna gidan ku sai kita faman saka abinki amma ba gidan Umar ba kan. Haushi ya kamani ganin ya kura min ido yana jiran na cire hijjab din dake wuyana. Dole na dan sa hannu na zare hijjab din daga wuya na gaba daya surana yafito a fili. Sai lokacin naga ya fara cin abinci nikan na kasa sai naji yace may kike nufi ko dai da gaske kinyi barbaden ne a ciki wai? Nace banda gadon wanan amma ban sani ko ku kunayi a gidan ku shiyasa kake ganin duk mata haka suke. Dago kai yayi ya kalleni yace dakata kada wautanki ya kaiki ga zagin gidan mu yanzu na koya maki wayyo a gurin nan. Shiru nayi don nasan zai iya idan na kara magana na fara shan dan faten da na zuba a plate a hankali. Banyi ko rabi ba naji na koshi sai na fara juya cibin kawai ina wasa dashi a plate din a hankali. Yana kallon abinda nakeyi bai min magana ba har yagama ci na mike zan fara kwashe kayan. Yace shiyasa baki kiba oya maza ki cinye abincin nan kafin nazo na sure ki dashi yanzun nan. Don bakin barna kinga banza yasa kika dafa da yawa kin san baki ci? Na turo baki gaba nace nifa gaskiya na koshi don ban jin yunwa saboda ba abinda na hade balle yunwa ya damay ni. Tsawa ya daka min yana fadin will you finish it my friend ? Dole na dan fara turawa kamar zanyi amai ga nauyi da kunya da suka cikani lokaci guda. Ganin saura kadan ya mike ya bar gurin na zaci fita zaiyi amma sai naga ya koma saman kujera three seater ya kwanta tare da dora kafan shi daya saman kan kujeran. Kitchen na shiga na wanke kayan da muka bata na kara gyara gurin da mukaci abinci na juya zan shiga daki naji yace. Waye dan gadin gidan ki kina daki ina falon ina maki gadin gida maza ki dawo nan ki zauna mara kunya kawai. Nace ikon Allah nifa ba boya bace don naga kana son mayar dani kamar wata wacce ka sayo. Yace amma ke yarinya ce karama ba,a fada maki cewa sadaki na biya bane lakadan ba bashi ba kikazo gidan nan ne ba wai. Don haka ina da right din da sai abinda nake son za,ai min a cikin gidana idan kuma kince ba haka ba sai na kira maman naki da taci kudin sadakin nawa tazo nan tabani abina yanzu. Don ba zan biya kudina ba don bukata na kuma a kun tata min a banza yadda nace dole shi za,ayi a gidan nan kinji na fada maki daga yau. Haka na dawo falin na zauna ina jiran wani sabon cin mutunci daga bakin shi kuma. Bai min magana ba sai wayan da yake ta bugawa ana kuma bugo mashi wanda akasari murna ake mashi kan auren da yayi. Sanyin A C da yai yawa a falon yasa na dan takure a guri guda har barci ya daukeni a zaune ban sani ba. Jin kaman nai barci a inda nake zaune yasa shi juyowa yaga ina barcin kuwa. Ido ya kura min har tsawon wani lokaci yana bin ko ina na jikina da kallo har tatsun hannu na da kafa sai da ya kare masu kallo lokaci mai tsawo. Nikan sai barcina nake hankali kwance jin kaman an tabani yasa ni farkawa furgigit idon shi a kaina. Na turo baki tare da gyara wuyana da yai min tsami nace ni dai in mutum yana maita ne ko shan jini wallahi kurwa na kur akan shi. Dariya yayi yace yar kauye kona kara maki karfin A C din ne don naga kinji dadin hakan har da sake min baki kina barci. Nace inda bamu dashi ne a dakin uwata sai kai min gori dafin abin kafin kayi kudin ka kaganta dashi. Yace ai nasan shi ya jawo ki yanzu tunda can kauye babu shi anzo an samu na banza ana sha nan. Nace dakata wallahi gida gidane haka uba ubane kada ka kara zagan min gidan iyayye na nima. Yace idan an zaga may zakiyi nace na rama aiko yayo kaina cikin tako daya duk yunkurin mikewan da nayi nagudu sai da ya cin min gurin. Nan ya matse ni saman kujeran muna shakan nunfashin juna yace ki rama din ina sauraren ki. Shiru nayi ina fadin ka sake ni kawai mugu sai kara matseni a kirjin shi da yayi bai sake ni ba. Wani irin bugawa naji kirjin na yi fal, fal gashi kuma bai sake ni daga jikin shi ba. Nace cikin karfin hali mugu kawai ka sake ni wallahi ko na fadawa mama cin amanan da kake min yanzun kuwa. Yace go ahead kirata yanzu tunda baki da kunya ki fada mata na matse ki ko ? Sai da ya gaji don kan shi ya sakeni daga jikin shi na tashi da sauri nai daki ina fadin mugu kawai ni bari ma na cire kayan nan don sun haramta gare ni daga yau. Yace wallahi duk kika cire kayan nan sai na tube ki zindir a gidan nan naga tsiya. Ke har wata mace ce can da kike ganin kamar kina da wani ajine wai? Daki na koma na zauna a bakin gado idanuwana suka ciko da hawaye don takaici. Nace a raina may kullun yake nufi da fafin wani har mace ce da za,a gani aji sha,awan ta ko may ? Muryan shi naji daga falo suna gaisawa da wasu haka yasa da sauri na saita kaina nasan baki mukayi a gidan. Ashe yan uwan mamane suka zo gaida mu da kuma yi muna sallama washe gari zasu koma gida. Shi ya shigo yana fada min zuwan su tare da jamin kunne na saita kaina in har na bari suka fahinci wani abu har naja sukai mashi fada sai na yabawa aya zaki. Nafito ina murmushin dole nace lah mama kune ashe sannun ku da zuwa. Maimakon na zauna saman kujera sai na zube kasa ina gaida su a cikin girmamawa. Masha Allahu Baba kaikan wallahi kayi dacen mata a rayuwan ka yarinya haka da ladabi, yaushe yaran yanzu masu rawan kai zasu tsaya yiwa sarakai wanan gurmamawan haka. Baba don girman Allah ka rike matar da daraja ku mutunta junan ku, ku rufawa kan ku asiri a tsakanin ku. Darajan miji shine na mata yadda ka mutunta matar ka haka duniya zasu mutunta maka ita. Ke kuma Fatima don Allah basai mun fada maki ba don yaran yanzu boko yasa kun san komai na rayuwa zaman takewan aure sai dai idan kun ki amfani dashi kawai. Don haka kin dai ga yadda uwar ku take rayuwan ta a gidan ku idan kinyi koyi da halin yayan mu da kika zauna da ita babu wani rayuwan da zai gagareki hakkuri a duniyan nan. Don haka yi nayi bari na bari abinda duk mijinki bai so kin sani, don kun zauna guri guda gwargwado kin san halin shi yasa naki. Gaba dayan ku idan kuka ba da kunya uwar ku kuka tozarta ita da taga dacewan hakan ta hada ku. Komai yaya bata boye muna ba na hadin da tai a tsakanin ku kuma ku yanzu bazaku taba fahintar manufan ta ba sai nan gaba. Don haka ku taru kuba mara da kunya ku kashe ku bisa a tsakanin ku ba komai ne ma ita yayan sai taji shi ba tsakanin ku duk abinda zakuyi ku boye sirin auren ku tsakanin ku don gujewa shigan ta wani hali. Kai kuma Baba don Allah duk wani abin kurciya da akayi sai abarshi a matsayin kurciya ne yanzo kakai ga tara iyali nan zuwa badi war haka in Allah ya kawo rabo sai kuga mun dawo taron suna gidan nan kuma. Nan dai sukai muna nasiha ma ratsa jiki suka zauna nan tare dani sai dare suka koma gidan mukai sallama cewa bazasu dawo ba kuma. Har kofa na raka su suka tafi suna muna fatan alheri da samun zuria ta gari. Suna wucewa na koma ciki wanka nayi tare da sallah ishai na zauna ina zikiri naji dawowan shi gida tare da rufe kofan gidan. Hakan yasani sani bazai fita ba ko ina ke nan again ganin shi nayi tsaye da farar leda a hannun shi, na dago kai na dube shi ban san yaya akayi ba naji bakina yana mashi sannu da zuwa a lokacin. Ledan ya miko min yace na dafa mashi liptop din dake cikin ledan naman kuma na kai mai falo saman dining zai fito yaci. Inda ya aje min saida na shafa namike zuwa yin abinda ya sani na fara dafa ruwan liptop din batare da na tsaya karan ta kona maye ba. Na fito na aje mai naman da zafin shi a table tare da ruwa da drinks mai sanyi. Ina kitchen naji fitowan shi, falon ya zauna ya fara cin naman da na aje mashi. Sai da na juye ruwan ga wani dan karamin flask na hado da cup na nufo falon yana zaune yana cin naman shi hankali kwance nace ga shayin na dafa. Ya dago kai yace injin baki zuba sugar ba a ciki nace mai a,a hakana na dafa don ban san ko na may ye ba. Da hannu ya nuna min na aje anan ina ajewa na juya zan shige yake cewa ke bazakici naman bane ? Na koshi na bashi amsa a taikace yace may kikace ban fa son shegen gardaman nan naki kinji na fada maki. Nace naci abinci a dasu mama na koshi dazun kafin su wuce don sai da nai masu girki sukaci da yamma. Baice min komai ba na juya na shige na zaci daya gama zai shigane amma sai naji ya kunna TV dake falon ko da ban fita ba wasan kwallo akeyi a tv nace bissimillahi Allah nazo gidan masu yi. Ni dai har barci ya kwashe ni ban san lokacin da ya shige ba sai tsakar dare na falka naji shiru na kara jan bargona na gyara rufe jikina da kyau. ****** ********* ****** Haka mukaci gaba da rayuwa a gidan zaman doya da manja ba wani abinda ke shiga tsakanin mu sai in yana bukatan wani abu zai shigo daki ya fada min. Sai dai a nawa bangaren ina hankalina a tashe yake don ina ganin bazan iya cika alkawarin mama ba akan shi don a halin yanzu ban san wani rayuwa ma yake ciki ba agidan sunan muna gida daya ne kawai dashi. Satin mu uku da aure na gama komai gashi hutun mu ya kusa karewa zamu koma school wani sati. Sai ganin shi nayi dakin lokacin ina kwace na kifa cikina a saman gado ina sauraren kira,a a wayana kaina babu dan kwali na daure gashi na da ribon ta baya , Ganin ya shi ya shigo yasani saurin lalabo dan kwalina na daura akaina kallona kawai yayi ya basar kamar bai san may nakeyi ba. Yace ke nazo na fada makine yau da dare zan koma gurin aikina don haka sai ki fada min abinda kike bukata a sayo maki idan na fita. Nace ni ban bukatar komai sai dai Monday mai zuwa zamu fara school insha Allahu. Yace gashi ke baki iya mota ba balle na bar maki motana kiyi amfani dashi sai kuma idan wani driver zan samo ya dinga kaiki. Nace ai ko da kake daukata yar kauye ba wai doluwa nake ba yadda kake tunane don ni mota kuma yanzu sai dai na koyawa wani tuki. Fatan kawai yanzu Allah ya hore min yadda ya horewa kowa na samu nawa na kaina insha Allahu. Kallon mamaki take min kaman zaiyi magana sai kuma yai shiru kawai yafita daga dakin. Duk da nace komai akwai shi a gidan amma sai ga kaya niki niki maigadi ya shigo dashi wanda kusan yan kayan lashe lashe ne a cikin kwalayen. Sai da yai wanka yafito ina kitchen ina girka abincin dare ya zo bakin kitchen din ya tsaya yake ce min zancen motan da mukayi dazun na binciki maryam ta fada min ki gwane don kece ke jan ku zuwa school don haka ga motana nan zan bar maki ki fara amfani da ita kafin na duba wanda ya dace a sayo maki. Ni zan shiga gurin maji nai masu sallama kagin dare yayi min sai ji nayi nace ni dawa zan zauna cikin wanan katon gidan haka. Yace kedawa kikazo gidan nan dama baki san gidan yadda yake bane kika shigo kai tsaye. Shiru nayi nace to don Allah ko na roka kanina musa yazo ya zauna dani kafin ka dawo. Yace no kada ki fara min aanan tarkace inama laifin ki ce nace Amirah tazo ta zauna dake har na dawo. Nace amma kana gani ita anty zata yarda tazo gidan nan saboda ni kuwa ? Gidan ki ne ko gida na Amira fa yar uwatace kada ki man ta da hakan don haka ki barni da tsarina kawai. Ya juya yafita na ce o Allah takawo ni gidan gwauna kaida sai dai obey the rules kawai ba jin views din mutum. Ya samu mama zaune falo tana zaman kadaici na rashin mu tare da ita bayan mun gaisa take tambayan shi lafiya na yace ina lafiya kalau. Tace da fatan dai ba wani matsalan komai a tsakanin ku ko? Ya kai haba maji matsalan may kuma dai ni nama zo ne nai maku sallama yau zan tafi Spain ne muna da wasan da zamu buga har agentina zan tafi ina ganin kuma zan kwana biyu a can idan na tafi. Da sauri mama tace ita matarka da,wa zata zauna tsawon wanan lokacin haka dake fadi? Yace da cewa nayi ko Amirah zata koma can har na,dawo, amma ita kuma naji tana fadin wai ko za,a dauko mata kanin tane agida ? Sai dai na kashe wanan magana don ban yarda da yan kauyen na su zo su zauna min gida ba suyi min barna. Kana da hankali kuwa yan kauye kan tunda ka dauko diyan su ai kashiga ganin su ke nan a gidan ka. Ina yaron kanin tane uwarsu daya kuma ba wani babba bane can fa shi yaron. Kuma ma ita wanan malaciyar inba kwanciya ba may zata yi a gidan amma shi yaron ko wani aike ne ko aiki ai zata iya saka shi yayi mata ko ? Kada fa kace zaka hanata zumunci da yan uwanta, tun yanzu dan sune gatan ta. Ya ce maji ba wai zan hanata zumunci dasu bane kawai gani nayi dauko yaron kaman wani long process ne kuma yanzu. Mama tace aa ka aje da zai kaita makaranta kuma don dazun maryam ke fada min wani sati zasu fara school insha Allahu. Yace mun gama wanan magana ko zanbar mata motana tayi amfani dashi don ashw maryam ma ta koya mata mota ko. Tace madallah ubangiji Allah yai maka albarka Allah ya baka zuria masu albarka da zasu tausaya maka kaima. Yace amin maji nan ya ciro kudi masu yawa ya bata yace ta rike a hannun ta idan da bukatan wani abu a bayan shi sai ayi. Yadda ya saba tafiya a gida ba tare da daukan kaya ba yauma haka yayi sai yar bakar jakar tafiyan shi kawai ya rataya. Ina zaune falo don na kasa zama daki kamar mai tsoro yafito ganina zaune a falo tasa shi zama a falon shi ma yana waya ina ganin bashar ne don naji yana fadi ya biya ta gida yazo da Amira kafin ya wuce. Sai da ya gama waya ya miko min kudi yana fadin karbi na nan nakali kudin tare da karba sai baice min komai ba. Cikin karfin hali nace namay nene kuma yace ki rike a hannunki don amfani idan kuma ma da wani matsala bashar yana gari sai ki nemashi. Ni gaskiya kudin nan sunyi min yawa ban da abinda zanyi dasu haka dubu biyu ma sun isheni saboda naga komai akwai a gidan ai. Kallon mamaki yai min yace wanan kudin ne sukai maki yawa dubu darine fa kawai idan kuna son sayen wani abin fa bana gari. Nace ni dai sunyi min yawa don ban saba kashe kudi ba komai mamane take saya muna na fadin cikin sanyin murya. Ok sai ki aje a gurin ki idan na dawo sai na karba don ban saba alheri ba na karba ni. Bashar suka shigo da Amirah sai wani shan kamshi take kamar an sata zuwan dole ne nake gani. Amma tana ganin shi ta dan sake tana fadin yayana dazu shine kaje gida ina barci baka sa atayar dani ba sai dana tashi maji ke fada min kazo wai yau zaka koma. Yace Amira ai ina ce baki gidan ne ma a lokacin da dake zanyi magana yanzun dai ga wanan nan zaki zauna min da ita har na dawo ba zan dade ba nake gani sosai sai dai kuma yadda tafiyan ya kaya min dai idan naje. Kudi yabata itama madu yawa yace ina tsan mani akwai komai da zakuyi amfani dashi abinda babu dai ga Bashar sai ku tuntube shi kawai. Bashar ya shigo ina gaishe shi yake fadin kaunata ashe yau wanan mayen ball din zai koma ya bar min ke ai yayi arziki hutun ku ya kare da kafanshi kafan ki wallahi. Tsaki sadauki ya mashi yace dan Allah mu tafi ni ban iya shirmay ka da ka saba kaji. Sai naga na mike nima da suka mike kallo na yayi cikin yanayin da bazan fahinci na maynene ba, sai suka fara tafiya daga ni har Amirah muna bayan su tafe. Sheri bashar ke mashi wai ashe shine bakauye yana kira min kauyan ci murum zaiyi tafiya mai nisa shine zaiwa matar shi wanan sallaman haka. Yace kai dai kasani jarababen banza ni yanzu ma har ina tausayawa maryam da wanan shegen jaraban naka da ka samo. Yace ni matata ba irinka bane don chakwai muke abin mu ban kuntata mata bata kuntata min kaine aka bari da jan ajin banza kawai. Suna shiga mota muna masu Allah yakai lafiya ya bada sa,an tafiya. Sai da suka bace muka shigo ciki mai gafi ya rufe get inda suma naga ya tsaya ya basu wani abu. Muna shiga ciki batai min magana ba naga tafara jan dan troler din ta ta nufi dayan dakin dashi nace ,a a anty ba anan zamu zauna tarw bane. Ta wani juyo a wulakance ta dube ni tace ina ko kin mata ni bani zama da kowa daki dayane don ban son yawan takura. Sai kawai taci gaba da tafiyan ta can kuma taja ta tsaya ta juyo duk ina tsaye ina kallonta tace Bintu kada fa ki manta gidan dan uwana ne nan ina da right din shiga duk inda naga dama batare da wani shamaki ba. Kiyi hakkuri anty ni bada wani manufa nai magana ba gani nayi gidan nada girma mu zauna daki daya kawai shi yafi. Tace to ba zan zauna ba sai inda naga dama zan zauna kuma kada ki kara cewa zaki min katsalandan ga al,amarina kinji na fada maki ko. Ni dai nabita da kallon mamaki don ban san laifin da nai mata ba har muka koma haka da ita kaman wasu makiya can. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,, IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI DA ALLAH,,, ALOKACIN MUKE,,,,, Tunda nai wanan mafalkin na tashi jin kaina nake yana min wa ni irin ciwo gani banda sukuni a tare dani. Haka na daure nai muna abincin rana tare da na dare a lokaci guda sai dai ina sake sake a raina kan mafalkin kabir da nayi may hakan ke nufi ne wai? Kudi na fito dashi da abinci nace ma musa ya bayar min da sadaka a waje ya samu karamin yaro ya bashi. Na gama shirya dining table da kayan abincin dana girka nashege daki na kara wanka. Dogon rigan atamface a jiki dinkin shi mai hannu daya ya matse ni sosai rigan wanan dai kan sai zaman gida don da aka kawo dinki naita fada da anty maryam akan dinkin. Ina fitowa ban san da dawowan shi ba sai ganin shi nayi falo kwance saman dogon kujera ya sa hannun shi daya ya rufe fuskan shi dashi. Dagani tunane yakeyi ko may yake tunane oho sai da nakai daidai kan shi na tsaya daga bayan kujeran tare da dan rakwafowa saman kujeran nace. Sannu da dawowa yaya kamar daga sama yaji murya na sai naga yai sauri cire hannun shi firgigit da sauri yana bude ido mukai arba dashi. Cikin mamaki ya amsa min fuska a daure yana cewa yyawa nace akawo ma abin sha ne ? Eh kawai ya,bani amsa na juya zuwa inda fridge yake, na dauko lemon five alive mai sanyi da cup. A kasale ya mike zaune daidai ina isowa da drinks din a hannu na sai dana aje cup na bude lemon na fara tsiyayawa a cup din. Na dauka tare da mika mashi sai naji ya sauke ajiyan zuciya yana karba daga hannu na. Sai da na samu kujera na zauna ya kai cup din a bakin shi ya fara dan kurbawa a hanlali tare da lumshe idanuwan sh. Sai da ya kurba kusan sau biyu naji ya ce may ya hada ki da Amira ne wai ? Shiru nayi ina wasa da yatsun hannu na kaina a kasa sai ji nayi yace bake nake tambaya ba ne ? Nace wallahi yaya ni ban san wani abu ya taba hada ni da ita ba. Kwayar idona ya daga idon shi ya kalla don tabbatar da maganan da nayi yace kin tabbatar da hakan da gaske ba abin da ya hadaku bayan bana nan ? Kai kawai na daga mashi da eh haka ne din amsa na . Yace shi ke nan ai idan ma wani abu kikai mata ai zanji don zan dauki mataki akan hakan. Don ba zan yarda matar da nake aure ta wullakanta min yan uwan haihuwa na ba ko kadan. Dan murmushi nayi nace nima ai yan uwana ne don banda wanda sukafi a garin nan yanzu don may zan mata wani abinda ranta zai baci akaina. Wanan kuma ai matsalar ki ce ni dai kin ji may na fada maki ai sai ya mike tsaye zai fara tafiya nake cewa abin yana saman dining tun dazun. Sai nayi sallah zanci ya bani amsa ba tare da ya juyo gare ni ba nan nabi bayan shi da kallo kawai. Dogon mutum ne sai dai ba irin can din nan ba kuma karfafa ne mai fadin kirji ga shi da dan dogon fuska da hanci irin zubin fulananin kasan sokoto sak dashi. Musa ne ya dawo yana cewa anty na dawo dazun na samu bakya falo. Sai a lokacin na dawo daga tunanen wanan zaman da baudaden mijina da nakeyi. Don nidai yanzu ban san kuma wace irin kulawa ake so na bashi ba wanda yafi wanan da nake mai yana mai dani kamar wata shakatafi can. Na saki ajiyan zuciya a fili tare da dan murmusawa nace ga abinci can fa na zubo maka ne musa. Yace anty lokacin sallah yayi alwala na shigo nayi naje massalaci hakan yasani mikewa nima na shiga don nai sallah. Bayan na idar da sallah ban mike ba ina zaune a gurin da nai sallah na dan jingina jikina da gadon dakin sai tunane nakeyi. Shine ya shigo dakin daga kofa ya tsaya yana fadin abinci fa ? Sai da na shafa nace gani tafe har musa ma yana zaune falon nashigo. Direct dining na nufa na fara kokarin bude kulolin abinci lokacin suka karaso suka zauna. Sosai yake cin abincin hankali a kwance sai can ganin ban zuba nawa ba yake cewa ke bazaki ci bane nace na koshi. Da sauri ya kara dago kai hannun shi rike da spoon din da ya debo abinci zai kai a bakin shi yake cewa. Da kikaci may kika koshi nace breakfast din da mukayi dazun bana jin yunwa yanzu. Tsuki yayi yace will eat now my friend ban son wasa da yunwa kada ki jawo wa mutane matsala. Na dan turo baki tare da tabe fuskana nace ni wallahi ban jin cin abinci a koshe nake yace ko kici ko na dura maki shi yanzu kuwa. Dole na zuba kama spoon hudu na dan fara ci sai dai kuma na kasa ci sosai don banjin ci din. Daga inda yake zaune ya taso sai ganin shi nayi a gabana yana fadin oya open your mouth. Wani kallo na watso mashi nace ni wallahi na koshi musa na ganin yaya ya mike ya nufe ya mike dama yagama cin nashi yafice a falon bayan ya dauke plate din. Ganin da nayi da gaske yake zaiyi feeding dina da kanshi yasa na fara tura sauran abincin da sauri a bakina yana tsaye yana kallo na gani saura kaman spoon daya yasa shi jan tsaki yace kan cin abinci sai na saba maki a gidan nan. Tunda na gane so kike kija min fita gurin maji tace na barki da yunwa cuta ya kamaki don sheri. Ina gamawa na kora da ruwa tare da dan dafe kaina a hankali wanan ai cin zalin ne na fadi a hankali na dauka ya wuce ne ashe yajini. Sai kawai naji ya kamo min baki yana fadin wanan bakin mai bakar magana da tsiwan tsiya sai na yi maganin shi. Zan bude baki nai magana sai hannun shi naji a bakin nawa mikewa nayi don na gudu sai ji nayi ya rugumoni ta baya ya matse ni a jikin shi. Cikin wata yar kara nace don Allah yaya ka sake ni na daina wallahi kayi hakkuri please ka sake ni. Maimakon ya sake ni sai ji nayi ya kara rugomoni sosai ajikin nashi ya shiga bin jikina a hankali. Kafana naji ba zai dauke ni ba a loka in don irin abubuwan da yake min a lokacin. Sosai ya matse ni yadda ran shi ke so a lokacin kuma gashi na kasa hana shi. Sai ganin abin nashi yana son wuce gona da iri nace cikin wata kasalaliyar murya don Allah dai yaya ka kayi hakkuri na tuba na daina zan dinga ci. Hannun shi yakai a kirjina abinda yasani saurin zillewa da karfi nai kasa ke nan da sauri Allah yaban sa,a ya sake ni. Wani irin numfashi ya sauke tare da shafo kan shi ya juya zuwa dakin shi ya barni a gurin a tsugun ne. Cikin jin haushin abinda yai min naja kafana zuwa dakina saman gado na fada a rigingine idanuwa suka shiga kawo hawaye a lokaci guda. Na furta ya Allah ka bani ikon cinye wanan jerabawan da nake cikin sa a cikin sauki. Shima dakin shi ya shiga kwantawa yayi yana mamakin kan shi don bai san yadda akayi har kai ga taba wanan yarinyar ba haka yau. May yake bukata gurin wanan yar kaunan bayabayan shi haka ne wai ? Sai kuma yai murmushi zuciyar shi tace may tarasa acikin abubuwan matan da kake bukata ita . Ba gashi yanzu yanzu kashiga wani bakon yanayi ba a zuciyar ka ka kasa controlling din kan ka akanta sai da ka dan taba ta ka samu natsuwa a ranka. Ranan bai kara fitowa ko falo ba yana ciki a kumshe nima dai hakan ne ina dakina a kwance don yanzun haka kunya yadda zan hada ido da yaya yau nake ji. Yadda yau ya hagula min jikina haka son ranshi yanzu a haka yana mashayi zan dinga bashi jikina yana yadda yaga dama dashi son ran shi. Oho ni Fatima naga ta kaina zama da mashayi hada jiki dashi don raya sunnan ma,aiki don gujewa zunubi a kaina. A hankali na lumshe idanuwa na har tsawon wani lokaci sai tunanen makomar rayuwa na ke yi kawai. Bayan sallah la,asar naji fitan shi daga gidan haka yasani sauke ajiyan zuciya na fito falo na zauna da musa nan mukai ta hira akan matsalan mahaifin su. ****** ********* ****** Har kwana biyu ba wani abinda ke hadani dashi don tun ranan da ya matse ni ban yarda sam mu hada ido dashi bani ma fitowa sai naji baya gidan zan fito falo na zauna. Yau tun safe sai nake jin bacin rai a zuciyana haka naje makaranta na dawo ban iya anyana komai ko a school. Tunda na dawo bai gidan har karfe tara na dare ganin bai shigo ba ya dan sani cikin dan damuwa. Ina son kiran wayan shi amma na kasa don gada ya dauka wani abune kuma zan tsiro mashi. Musa yace min anty zan kwanta barci nake ji nace tun yanzu yace wallahi yau wasan kwallo nayi da yan unguwan nan kuma naje gidan anty maryam nai ta hawa keke da yaran unguwar kina school. Ganin ni kadaice a falon yasa ni mikewa don nakashe tv dake aiki naje na kwanta. Kofan shigowa aka turo tare da shigowa falon tafe yake cikin dan sagala corth din jikin shi ga kafa dan shi. Kallo daya nai mashi na fahinci yau yayi halin shi na baya ke nan saboda yadda nagan shi yana tafiya. Ban ko ce mai sannun da na saba ba yazo ya wuce ni hakana ya shige dakin shi. Dakina na nufa raina a bace har na kwanta na tuna baici abinci ba duk yinin ranan. Gashi nasan halin shi tun a gida baya cin abinci a waje shi duk inda yatafi sai ya dawo gida yake cin abinci. Mikewa nayi tare da bude kofana na nufi dakin nashi a lokacin. Ina tura kofan yadda na samay shi zube a kasa saman center carpet din dake tsakiyan dakin baki gado a kwance rigigin ne dashi. Yadda na ganshi kwance sai tsoro ya kamani ga rigar shi ta sama ya wugar a gefe daya. A hankali na karasa gaban shi idanuwan shi suna rufe alaman barci ne ya dauke shi a haka. Durkusawa nayi a gaban shi idanuwana suna fitar da hawayen bakin ciki. Hannu nasa a hankali na fara cire mashi takalman kafan shi sai socks da na fara zarewa a hankali. Idanuwan shi ya bude a hankali ta dan kalle ni ban daina abinda nakeyi mai ba sai da na cire mai takalman da socks din a kafan shi. Yace da kyat cikin wani murya ciki ciki leave me alone Fatima i want be alone for now. A sanyaye nace mashi ka tashi ka haugadon ka ka kwanta please. Ya lumshe idanuwan shi yace ki bar ni a nan iam ok here. Nace ka tashi please ka haugado kada ka kwanta haka a kasa please sai na mika mashi hannu da niyar nakamashi ya mike zuwa kan gadon na shi. Shima hannun ya mika min sai dai karfi ba daya ba sai maimakon na dago shi ya mikw sai jana yayi zuwa jikin shi. Tankar na kurma ihu a lokacin don irin yadda nake jazuciya na a lokacin. Kokarin mikewa nayi amma sai naji ya sake rike ni a jikin shi tare da fadin shiii Idanuwa na na lumshe cikin bacin rai, don na gane may yake nufi da hakan da yace min wai nai shiru. Yayi wani irin jan numfashi har sai da naji shi a cikin raina a lokaci guda. Cikin karfin hali nai magana a hankali nace ka tashi ka hau gado ko kai wanka ko zakaji karfin jikin ka. Ya kara bude idanuwan shi da kyat yace tunda kina son inyi kamani nai wanka please ? Mikewa nayi da na samu ya sakeni na nufi bathroom na hada mai ruwa da kyat na samu ya mike yana rike da hannu na na dago shi rike da hannu zuwa kofan shiga bayin tun a gabana naga yana kokarin cire kayan jikin shi haka yasa ni komawa baya da sauri na bar dakin. Muryan shi naji yana fadin don't go anywhere na fada maki ko na bata maki rai. Na ja na tsaya tare da rintse idanuwa na shiga wani irin damuwa mara fasalin fadi. Gurin wardrobe din kayan shi na nufa na ciro mashi wasu kayan barci na aje mai saman gadon shi. Na tattara kayan da ya cire na watsa su inda yake tara kayan wankin shi. Fita nayi zuwa kitchen na hado mai ruwan shayin da yake sa na dafa mai duk dare. Na shigo dakin da flask da cup a hannu na yana zaune saman gado daure da towel a jikin shi iya kugun shi. Sai da na aje flask din nake cewa ka sanya kayan ka gasu nan a gefe na aje maka. Bai yi magana ba sai kallon kayan da na aje mashi saman gadon yayi kawai. Na sake cewa ga ruwan shayin ka nan idan zaka samu sha yau. Bina kawai yayi da ido kamar a ranan ya fara gani na. Juyawa nayi sai muryan shi naji again yana cewa kada ki fita ki tsaya a nan zaki kwana. Dam dam naji gaba ya bada na dago kai da sauri ina kallon shi. Sai kuma naji jikina yai wani irin san yi cikin sanyi murya nake cewa zan je na kashe wuta a dakina. Daga haka nafita daga dakin na dade zaune a bakin gadona ina faman tunane kala kala a zuciyata. Banda yadda zanyi dole na mike na shirya yadda ya dace mace tayi idan zata turaka gun maigidan ta kwana. Kwace na samay shi a dakin yayi dadaya a saman gado hakan yasa na gane cewa yayi barci ne a lokacin. Duban flask din da na aje mai nayi yana nan yadda na barshi bai taba ba, a hankali na taka gefe daya na gadon na kwanta a hankali kada yaji motsina ya falka. Nasa hannu na kashe wutan dakin na makure a gefe daya a tsorace don yauce karo na farko da zan hada makwanci da na miji. Kuma sai gashi mijin sunnan nawa a buge yake a cikin kayan maye don dole kuma nai mashi biyayya a hakan. Cak naji hannun shi a saman jikina tare da mirgino ya kan kamay ni a hakan. Ji nayi duk da ina a tsorace ya sake wani irin ajiyan zuciya lokaci guda idanuwa na naruntse cikin jin kuna haka a raina. A sannu yafara bin part din jikina yadda yake so sai runtse idanuwa nake don bacin ran dake addabana a lokacin. Sannu sanu yake komai zakace ba,a cikin maye yake ba a lokacin, don irin yadda yake takon sallon shi a gare ni. Duk irin yadda nai tsanmani zai kasance don a buge yake abin na sadauki ya wuce haka. Don sosai ya canza min sallon shi a ranan wani irin mahaukacin soyayya da maza keyi ya nuna min a wanan daren don sai kusan asubu nasamu ya sarara min. Nai kuka nayi ihu nayi yakusa duk a banza nakeyi don babu maceci a cikin wanan daren gare ni. Haka yasa barcin dana dan samu yasa mu makara sai guraren tara na safe na falka da kyat na bude idanuwana da sukai min nauyi. Dakin nake bi da kallo har nakai idanuwa na inda yake kwance ya kifa cikin shi daga shi sai dan towel din daya yafa daga saman shi kadan ya rufe al,auran shi dashi. Da kyat na iya mikewa a hankali na lalubi rigar barci na dayake a kasa yashe, na nufi kofan dakin bayan na saka rigan. Nabar dakin zuwa dakina a falo naji motsi a kitchen ashe musane yake min wanke wanke a ciki. Dakina na shiga na fada bayi tare da sake majikina ruwan masu zafi ban san lokacin da na saka kara ba. Sai da na gasu sosai a cikin ruwan sannan nai wanka tsarki na fito da kyat na tayar da sallah. Haka na daure nafito na hada abin karyawa wanda dakyat nagama hadawo don zazzabin da ya rufe min jikina a lokacin. Dakina na koma na kwanta ke nan wayana dake gefe na yai kara a lokaci daya da kwanciyana. Maryam ce ina dauka take cewa banga kin shigo school bane yau madam. Da kyat na iya bude bakina nace banda lafiya ne yau anty tace subbahanallahi may ke damunki Bintu? Maimakon na bata amsa sai na sa mata kukan takaici kawai hankalinta a tashe tace kashe wayan gani nan zuwa yanzu. Zazzabine mai karfi ya rufe ni a lokaci daya ina dunkule a cikin bargo idanuwa a rufe naji an shigo dakin. Bai min magana ba sai tsayawan da yayi yana kallon yadda nake kaduwa a cikin bargo kawai. Takawa yayi har bakin gadon tare da yanen bargon a hankali dunkule nake idanuwa na a rufe hannun shi yakai a saman wuyana a hankali. Zanfin da yaji a jikina yasa shi faduwan gaba don shi kanshi yasan yadda yai min bai kyauta min ba a daren jiya din. Dan tsuki yayi tare da daure fuskan yace ke nasan idon ki biyu may ke damun ki ne haka ? Nikan gyara kwanciya nayi tare da kara dunkulewa dakyau guri guda. Muryan maryam ce dakw ta kwada sallama daga kofa yashi amsawa tare da fitowa daga dakin suka gaisa yana tambayan lafiyan ta. Tace ina Bintu take ? Ya bata amsa da tana ciki ya wuce baiso shigowan maryam gidan ba a lokacin. Da sauri ta karaso gareni tana cewa Bintu subbahanallahi ashe serious ne haka may ke samunki ne wai haka ? Banda lafiya kawai na bata amsa dashi tare da kara dunkulewa kawai. Fita tayi ta samay shi zaune yana cin abincin breakfast tace yaya an ashe Bintu bata da lafiya ne naje school ban ganta ba shine na biyo ta nagani. Yace mata Umm kawai yaci gaba da kurba shayin shi kawai. Ta sake cewa tasha magani ne to ? Yace may tace maki yana damuntane ? Batai magana ba sai dai hawayen da naga tanayi kawai a idanuwan ta. Bari yanzu zan fita na sayo mata magani yabata amsa tace ba,a zuwa asibiti naji zafin jikin sosai ne fa. Yace fir god sake ki barni da surutun nan kamar wata yar jarida can nace maki zan sayo mata magani yanzu idan na karya ko? Shiru tayi ta mike zata koma dakin yaks cewa ba barci takeyi ba ki barta kawai ki tafi ai ina gida bazan tafi nisa ba . Kallon mamaki tai mashi kamar mara gaskiya kodai yaiwa yar mutane wani mugun abune wai. Bari nai sallama da ita na tafito ke zo ki fice min a gida ban son gulman tsiya ya fadi cikin daure fuskan shi. Da mamaki take kallon shi batai magana ba ta juya zata fita yace ke dakata sai taja ta tsaya guri daya yace idan naji kin fadawa wani Fatima bata da lafiya wallahi sai na saba maki harda munafukin mijin ki kuwa. Fita tayi daga gidan kamar yadda ya umurce ta gida ta koma bata koma school ba ranan. Bashar yai mamakin ganin ta a gida yake tambayan ta ko lafiya ta dawo a lokacin . Tace lafiya sai dai Bintu ce wallahi bata da lafiya sosai naje gidan kuma yaya ya koreni harda gargadina idan na fadawa wani sai yaci mutunci na. Dariya taga Bashar din nayi mata yace ai maganin ki ke nan ina ke ina zuwa gidan mutane gulma kuma. Shima fa haka yace min yace kingani tace wallahi yace kokai na fadawa sai ya saba min . Dariya yayi yace mugu yasan abinda yaiwa yar mutane shine yake jin kunya mana kada aji. Kallon shi tayi cikin mamaki tace may yai mata yaya yace auke kin manta da naki ke nan ko abinda akai maki da kikazo gidan nan kika lamay muna ahine shima nake ganin yau yai mata. Sai wani shu,umin murmushi ta sake tace Allah sarki Bintu har tabani tausayi wallahi. Amma kuma shine don keta zai hana a taimaka mata wallahi yaya sadauki mugune Allah, bakaga yadda ya sha min toka ba wai na fita na bar mashi gidan shi. Sun kai wani lokaci da Bashar suna maganan cikin tausaya min ya fita yabar gidan. Kiran wayan Sadauki yayi yana ina yace yana gida kuma bai samun fitowa yace gashi tafe kafin yace kada kazo har Bashar din ya kashe wayan shi ko. Ina kwance naji yana tabani cikin barci na bude idanuwa na da kyat shine tsaye da cup din ruwa da magani a hannun shi. Yace cikin daure fuska tashi kisha magani nace a hankali naji sauki ban sha sai ya tuna ban son shan magani dama yace idan baki sha ba wallahi zan kira ai maki allura yanzu ragguwan banza kawai. Jin za ai min allura yasa namike da sauri ina hararan shi na karbi maganin nasha da kyat na iya hadewa. Na koma na kwanta ina wai wai tare da kara rufe kaina gyara min kwanciya yayi ya kashe A C dake aiki a dakin. Yafita falo ya koma ya zaina shida musa yana fada ma musa wai yau banda lafiya ne shiyasa nake kwance. Can yaji anshigo gidan ya daga kai Bashar ne ya gani yace cikin daure fuska kai kuma may yakawo ka ne wai nace ma yau hutu nake so fa. Yace au don nazo nayi laifi ke nan ko yace dana sani na wuce school wajen madam dina yafi min zuwa nan ai min wulakanci haka. Ya zauna yana fafin kaunata tana school ita ma ko ? Yace bataje bata jin dafin jikin ta yau da sauri bashar yace subbahanallahi may yasa may ta kuma ? Sai da yai dan tsuki yake cewa fever ne kawai ke dan damun ta. Kallon yadda sadauki ya daure fuska yayi ga dariya nadon kamashi amma ya dake inda ya yakushe shi a wuya da gefen fuska dana wuya yace subbahanallahi may kuma ya yakushe ma fuska haka kamar kayi dabe da mussa haka? Yace kai dan iska ban sani ba mutune kaman yan jarida dakai da matarka ban san wanda yafi gulma ba wallahi. Don Allah daka ta man kaman fa kasha yakusa nake gani jiya dakata mu gani mana. Filon kujera dake gefwn shi ya dauka ya jefa mashi a fuska ya cabe yana cewa oho yanzu nagane kace min ka shigo gari kawai mutumina. Fita min gida kaima watau munafukan matar ka taje ta fada maka shine kazo don ka karas da idon ka ko ? No kadain kiramin da mata munafuka ni Maryam bata dawo gida ba tana makaranta kuma ba abinda ta fada min zuwa nayi mutafi illela gurin zancen kayan nan da zasu shigo muna. Yace cikin taba baki ni yau ba inda zan tafi don wanan raguwar banzan ta kawo min cikas sai shegen rakin tsiya kamar wata jaririya can da ita. Kai man wallahi ka fadi gaskiya abinda ake lalashin mace kodai kai kai mata may gaba daya ne wai ka illanta masu yarinya ga banza saboda alluran ku na yan kwallo na maka caji ko ? Kaidai dan iska ne wallahi bashar kashe ta ma nayi ba illantawa ba bar gida don Allah naji da abindake damuna ni please. Sai yaja tsuki yace ni wallahi maji ce bani ma son taji zancen nan Allah, bashar yace a ina zataji shi. Gurin maryam mana bashar yace haba kai ina tana ma fara fadin wan nan magana ina bazata fadi ba zanyi warning din ta ai. Amma sai dai sun makara don suna magan har maryam takira wayan mama tana fada mata cewa maji yaufa sai ki dafawa yarki bagaruwa don komai zam wallahi. Murmushi maji tayi tace masha Allahu nan take cewa sai dai bata da lafiya tana can nade kuma na tafi yaya ya kore ni. Suna gama waya mama tashirya sai gidan mu wanan ne karo na farko da tazo gidan namu tun bayan gama bukin mu. Suna hiran su a falo suna dariya sai jin sallaman ta sukayi a falon kawai. Damm gaban shi ya fadi ya dukar da kanshi a kasa haka kawai yaji yau ba zai iya hada ido da maji din ba karo na farko kenan a rayuwan shi. Suna gaishe ta bata tsaya amsa masu ba da dadi take fadin ina dakin fatiman yake ne da hannu ya nuna mata. A hankali tasa hannu ta daga bargon da nake ciki a rufe a lokacin saboda maganin da nasha har na fara zufan jin sauki fever ya dan sauka min sai dai jikin nawa akwai sauran zafi still. Jin an tabani yasa na dan bude idona a hankali mamace na gani tsaye a kaina tace Fatima yaya jikin naki ina kokarin tashi take ce min koma ki kwanta abinki. Kinsha magani ko nace mata cikin karfin hali eh mama ta kara min sannu da jikin na amsa da kyat tare da dan mikewa zaune na dukar da idona sam ban iya hada ido da mama din yau. Bathroom naga ta nufa saida ta cika kwamin wankan da ruwa ta kawo wani gari ta zuba tace na tashi nashiga ciki na zauna zan dan ji daman jiki na taimin sallama ta fita abinta. A falo ta samay sunyi zaune zugun da su sai jira yake yaji fadan da zatai mai sai dai tanafito ta dan zauna tana cewa nashigo ban tsaya mu gausa ba hankalina ya daga naga hakin da diyata take ciki. Tace sai ai ta hakkuri da mata Allah yai maku albarka yabaku zuria dayyaba na gari masu albarka irin ku. Ni zan koma sai anjima kazo ka dauko maku abinci kazo dashi tunda nasan bazata iya komai ba ita. Mama ta mike ta fita tana masu sallama ta wuce zuwa gida nan ta barsu zaune cikin kunya. Yace sai na batawa maryam rai wallahi haba dai akan may kuma may taimaka zaka saba mata kuma daga taimako Kwarai naji dadin abinda mama ta taimaka min dashi haka yasa dana fito ban kwanta ba sai yunwan da nake ji kawai. Shigowan shi dakin yasani saurin dukar da kaina yace yaya jikin naki da sauki nace mashi kawai. Kin karya kuwa ya tambaye ni cikin son sani ko na karya sa safe nace a,a a hankali juyawa yayi yafita daga dakin. Zuwa can sai gashi ya shigo dauke da cup din tea mai kauri a hannun shi daga gefe na ya zauna tare da mika min cup din. Yana fadin ki shaye shi don ki dan kara samun saukin jikin naki wayan shi ce tai kara ya dauka sai da suke magana na fahinci da mama suke magana . Yadda suke magana na fahinci mama tana cikin matukar farin ciki da walwala a tare da ita tana cewa ka fara ganin al,amarin Allah ko. Nikan raina kamar an fasa min guduma tsakiyan shi nake ji don nasan dada shike nan ni tawa ta kare ke nan. Shiko sai wani lumshe idanuwan shi kawai yake abu ya taru yai mai yawa a zuciyar shi. Na farko tunanen irin ni,iman da ya diba daga jikin yarinyar da yake ma kallon kitse saman ruwa don bai taba zaton haka zai samu ba daga gurin Fatiman daya raina da farko . Suranta sai gizo yake mashi a idanuwan shi ya kasa mantawa da abubuwan da suka faru a tsakanin a daren jiya din. Idon shi ya sauke ga dogayen yatsuna dake rike da kufin da nake kurban shayi a hankali bai san lokacin da ya sauke wani irin ajiyan zuciya ba wanda har yasa na dago kai ina duban shi. Sai kuma nauyi da kunyan yadda ya kasa sarara min har takai yai min rauni a jiki ance dama dan hakin da ka raina shikw tsona maka ido. Nauyi da kunyan maji sun rufe mai zucita don bai taba tsanmanin cewa akwai wani rana da zaiji nauyi da kunya maji ba sai ya din nan. Kofin nake kokarin ajewa a gefe ya kura min ido cikin daure fuska yake cewa kin shanye ne. Na dan marairaice ina cewa, nasha yaya hannu ya miko min yana karban cup din gani sauran tea a ciki yake cewa wanan fa ? Na dan marairai ce nace na koshi yaya please tausayi na bashi ya dauki cup din ya fita dashi. Ba,a dauki wani lokaci ba saiga sako daga mama ferfesu ne na kaji da kayan cikin rago sunji kayan kamshi na gargajiya, sai kuma gassan naman rago mai zafi . Da kanta ta bugo min waya akan na tashi na ci abin da akakawo tare kuma da jaddawa yaya akan ya tsare ni naci sosai. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,, IDAN KIN BIYA KIN TURAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH,,, A LOKACI MUKE Washegari kamar yadda na saba tashi na kamala muna abin karyawa ina yi ina duban kofan dakin da Anty Amirah take ciki har na gama bata bude kofa ba. Wanka nayi na gyara jikina duk da ba wani kwaliya nayi ba amma nayi kyau zani da riga ne na atamfan super the most classic one na daura. Falo na fito na fara karyawa sai da na kusan gamawa ne, na ji ta bude kofan ta tafito daga dakin. Cikin murmushi nake gaishe ta, inda ta amsa min cikin ko in kulla tare da zuwa tafara bude abinda na girka muna. Sai can bayan ta zauna take cewa yanzun duk wanan abinda kika dafa haka wa zai ci su ne wai? Nace dani dake ne fa anty sai masu gadi da zan dibanwa nakai masu. Humm,ummm lalai dan tallaka bai iya samun guri ba wallahi, Bintu tun ba,a je ko ina ba kin fara wanan nan irin barna haka ? Nace haba anty ina kuma barna haka ni dana tashi gurin mama ne kuma zan ce na yi barna. Masu gadi fa har mutum uku ne gidan nan kuma shi da kanshi yace na dinga basu abinci suna ci. Dakata Bintu may yakawo zancen yaya a nan magana ce iya ni dake mukeyin ta ko? Kada ki soma kice zaki raba muna zumuncin mu da dan uwan mu don tare kika gan mu ke haye kawai kikai muna daga sama. Kodan maji ta cuce shi ta mashi wanan cushe na auren ki har kike ganin kamar ke wata tsiyace yanzu. Bari kiji koda ace auren so kukayi da yayana wallahi ke Bintu kinyi kadan ki rabani da dan uwana ana magana kin wani kawo zancen yaya kin saka a ciki mafari ki samu wani sheri ki kulla kice nace kada kiyi abinda yace kuma. Kallon mamaki nake mata nace haba Anty may nai maki ne haka wai yanzu kike nuna min irin wanan rayuwan a tsakanin mu nifa kaunar kice anty. Koshi yaya din bai gwada min irin wanan kiyayyan da kika dauko gwada min . Yar uwar wa ai dake yar uwatace da killa zan dan raga maki ta wani guri amma ina hadin kifi da kaska kuma. Sanan shi yaya ina yaga gurin nuna maki wani abu kisa uwarshi ta tsine mashi yana zaman zaman shi akan wata banza can. Anty nice banza kuma yau ? Kila da hafsatu nake magana . Cewa mahaifiya ta data haife ni wai da ita take magana na dago cikin mama idanuwa sun kawo kwalla nace nagode Anty. Kada ma ki gode din don wallahi ki sani Bintu nifa na tsane ki a rayuwana tunda kika sa maji taiwa yayana haka. Murmushi nayi tare da mikewa ina kokarin daukan kulolin abinci na juye wa su maigadi nake cewa nagode babu komai. Ina juyawa naji tana fadin mace a haka ba gaba ba wani fasali na mata kamar solama dake. Mamaki nake ina tafiya yadda cikin dan lokaci ta sake akaina gaba daya duk ta manta da rayuwan mu a baya don kawai wanan auren na dan uwan ta da aka sakaniyi bada son raina ba. Naji tana fadin wallahi duk wani muna funcin ki ke da gwagon ki tun farko na fahince ku kwadai ne kawai yakawo ku dama cikin rayuwan mu. Allah ne shedan hakan kuma nace mata batare da na juyo ba tace ko kina so ko baki so sai wata tashigo gidan nan yar arziki taci arzikin yadda aka iya cin shi. Haka zaman mu da ita ya kasance a gidan ba ruwan wani da wani har zuwa karfe hudu na yamma. Sai iko da mulki take zuba min a cikin gidan har na kwammace dama ni kadai na zauna dayafi min. Sallama yaya Bashar mukaji a falo ganin yadda muke a zaune yasa shi fara fahintar akwai matsala azaman mu da Amira a gidan. Jin ayi wani sallama yasa na dago da sauri anty maryam ce sai kani na musa biye dasu da yar jakar kayan shi a hannun shi. Na rasa wa zan tara a cikin su don murna na rugumay maryam ina murna tare da fadawa jikin ta. Itama murna da ihun ganina takeyi sai wani uban tsoki da mukaji anty taja tare da mikewa tabar falon ta dan kalle tace taufa matsalan da kuma aka kawo maki kega a gida yar uwa. Nai murmushi nace aikin san anty hukuma ce sai lalashi don ita halinta daban yake kin san. Na juya gurin kanina ina mashi sannu da zuwa tare da tambayan shi mutanen gida na dago kai nace wa yaya Bashar nagode yaya yace ba ni bane mijin ki ne yace na dauko maki shi ai. Yace madam ni zan tafi sai after eight zan dawo mu tafi lokacin kun gama gulman ku. Mukai dariya na ce yayana ai bazata fara tai min gulman ka ba nakyale ta yace haka ne fa kuma Fatima shiyasa nake yin ki. Yana fita na kawo masu abinci maryam ta harare ni tace ko kin man ta nima madam ce yanzu sai dana girka mukaci muka fito. Nakai kani na dakin dake farkon shigowa falon wanda ina ganin dan baki aka gina shi. Muka koma dakina muka baje dama ta matsu ta samu abar mu, mu biyu mu wala. Dakin tabi da kallo tace dankari gaskiya Bintu yaya yayi kokari wanan irin daulan haka gaskiya ki godewa Allah da hakan. Nace da mama kuma ko da tai sanadin kawoni ciki ko? Nace, anty maryam nifa duk wanan bai a gabana kawai dai ni gurina mu samu zaman lafiya a tsakanin mu. Ta dafani tace, haba Bintu ki kwantar da hankalin ki komai zai zamo daidai a tsakanin ku da yaya. Tun da safe fa shi ya tayar damu daga barci akan aje yau azo maki da musa tunda kince kina son yazo, Bai dade da kiran shiba kuma sai ga maji itama ta kiramu tana fadin aje a zo maki da dan uwan ki don ta san Amirah ba zata tsinana maki komai ba. Nai murshi kawai tace kai Bintu aure fa rahama ne wallahi, sai yanzu na gane dalilun da yasa iyayye kan damu da yarsu tai aure ashe. Kin koga yadda yayana ke wani haba haba dani ko kuda bai son ya tabani kuma da zaran ya ga na dan shiga damuwa ya shiga tambayana ke nan may ya samay ki may yafaru kuma. Tace kai bari ke dai yanzu ga yaya ya bata ni idan ban ji shi a jikina ba wallahi har damuwa nake shiga wallahi. Dariya sosai tabani nace kai anty maryam wallahi baki dai barin halin ki watau, tace bari mutumiyar wallahi duk na matsu na ganki na dan baki wasu hit,. Nan dai tata min hiran irin rayuwan dadin da suke yi da yaya bashar sai nake ji ashe ni ba ma aure nayi ba. Jin nayi shiru sai sauraren ta nakeyi, tace yaya kuma kin barni sai faman zuba nakeyi ni kadai na san dai yaya sadauki yafi yayana waye wa. Murmushi nayi nace anty kufa auren soyayya kukayi da yayana bashar niko da akai mashi dole akaina ina zan samu wanan daulan haka. Allah dai kawai ya kyauta ga sabon fitina anty Amira abinda take fada min ko wanda akaiwa dole a kaina bai gwada min hakan. Tace dan Allah fita batun ta yar bakin cikine ita da fadin rai ta dauki duniya da girma ita. Tace ni yanzun dai na fahinci tunda kika shigo baki samu kan yaya ba ke nan ko? Nace kamar yaya anty ni har wani kan shi zan samu can mutumin da akai mashi dole a kaina. Tace ji nan Bintu kefa mace ce kuma ki tuna aljannan ki ta na a,karkashin kafan shi ne don haka idan zaki kama jiki ki ma gurin gyara gidan ki. Nace anty wani gyara kullun fa sau biyu nake gyara gidan nan a wuni may kuma ake bukata bayan hakan ? Kai amma ke ma Bintu ashe da gaskiya ke yar kauye ce wallahi. Dalla ni ba gyaran gida nake nufi ba kinji ki saurara ki ji ba wani boyo ko kunya a tsakani na dake don ke yar uwata ce Bintu. Da farko zaki fara shiga ta daukan hankalin shi ta yadda don ubanshi sai ya gigice a kanki badon Allah ba shifa namijine. Namiji kuma kamar kenwa yake gurin son jiki abinci mai jan hankali zaki dinga mashi. Sai tai shiru can tana fadin ke Bintu ke ma yar iska ce wallahi don nasan yanzun haka yar tsama kuke a tsakanin ku kuna yabawa juna magana. Nace idan ya fada min nima ai dole na mayar mashi tace kin fadi wallahi. Kwaran ki yake don kece da zunubi duk abinda zai fada maki ke yazama wajibi dole ki kwanta don kece a kasa. Ladabi ya zama dole yanzu akanki idan abinci zaici ki tabbatar kina zaune tare dashi, ruwan wankan shi da suturan da zai sa duk kece da Alhakin hakan don ki sani. Tace gyaran dakin shi duk a kanki ya rataya idan ya dawo sannu da zuwa idan zai fita Allah ya tsare ya bada sa,a. Duk kika tsare haka wallahi ko baiwa Allah nina fada maki dole ya sauko ku daidata a tsakanin ku. Gama sauki yanzun yadda yai tafiyan nan waima kuwa kin kirashi kuwa? Nace ni kan ko lanban shi ban dashi tace kin shigesu wallahi Bintu wai ke kina ganin yadda yaya yake kaman ba masu son shi ko? Wallahi ki kama jiki Bintu, don na fada maki shine kawai bai damu da mata ba in ba don haka ba da sai kin raina kanki wallahi. Ki dinga kiran shi kina mai sannu da sauran tare da tambayan lafiyan shi idan kuma zai dawo ki bashi mamaki hada mashi abincin da kika san yana so ki gyara gida da jikin ki tsab. Kada ki tsaya wani jan aji can ki mai kyakyawan taro sai kiga yadda zaki juya abinki cikin ruwan sanyi wallahi. Kai gaskiya nikan bazan iya ko daya ba mutumin da ke har hasashen wai ina son na kashe shi idan nai mai girki yace dole sai naci ya gani kada na kashe shi. Dariya tayi tace ku takon kainan ku ai daban yake Bintu don baku bari agane har afahinci komai. Muna ciki bamu san cewa har lokacin sallah magariba ya kawo jiki ba sai jin kiran sallah kawai mukayi a masallacin kofan gida. Mun idar kuma tashiga kara min wasu haske sai mamaki nake wai ita a ina duk tasan wanan abin haka ne wai? Takwas da yan mintina mijinta har ya iso daukan ta baiji kunyan idanuwan mu ba yake ta faman shige mata ajiki a gaban mu nikan sai faman kawar da kaina nake cikin jin kunyan abinda sukeyi. Yaya bashar ne yace Fatima bari na baki layin mijin ki don ya sauka kasan waje ko tun da magariba ya bugo min waya. Mukai sallama dasu sai lokacin da suka tafi na samu ganawa da musa nan mukai ta hira dashi har gurin karfe goma da wani abu na dare muka shige don Amira tun fitan su maryan da ta dan fito bata kara leko falon ba kuma har lokacin da muka shige muka kwanta. ****** ********* ****** Kwance yake saman gadon dakin da ya sauka waya yayi da wani abokin shi dan kasan saudiya da suka shaku dashi sosai. Yana gama wayan ya fara juyawa a saman gadon gami da zubawa wayan dake hannun shi idanu . Saboda wani mugun takaicin Fatima da yake ji a zuciyar shi yau kwanan uku ke nan baya gida amma wanan yar kauyen yarinyar mai fadin rai ta kasa daga waya takira shi. Gashi yana son jin lafiyan su amma sai yake ganin kirata gare shi kamar kasawa ne hakan. Itama da take mace mallakin shi zaman shi takeyi bata kirashi ba sai shine zai kirata akan may ma wai ? Don yasan koda ya kiratan ba wani magana bane mai dadi zai samu a gareta banda bacin rai da zata saka mashi kawai. Ya kifa kanshi a filo yana tuna maganan Maji dazun da suka gausa take tambayan shi kana ko waya da matar ka yaba amsa da eh maji muna gaisawa ai ina tambayan ta lafiyan ta? To yanzun idan maji din ta bugawa Fatiman waya tace bai taba kiranta ba ko sau daya yaya zata dauke shi a makaryaci mayaudari mara rikon amana zuciyar shi ta bashi amsa da hakan. Take yai matukar tausayawa kan shi do min kuwa yasan acikin garari rayuwan shi take zuciyar shi ta kara bashi shawara ka kira ta kawai don ka kirata shine wani abu. A haka har barci ya dauke shi bai sani ba sai dare sosai ya falka tare da jin barci ya kauracewa idon shi alwala ya mike yayi ko zai samu relief a zuciyar shi idan yai sallah dare. Hakan ne kuwa ya kasance dashi don sai yaji shi wani wasai dashi da rana ma bai sa wani abu a zuciyar shi ba. Satin shi biyu cif da tafiya sai zaman doya da manja muke da anty Amira a gidan gashi ta hana min dan uwa shakat a gidan. Da yai abu kadan yanzu zatayo cikin shi da masifa da zagi yadda ran ta yaso ita ko haka abokan ta zasu shigo suyi yadda ransu ke so agidan. Ta mayar dani kamar wata kukun ta can tace Bintu zokiyi min kaza Bintu zoki dauke abu kaza haka nake takure da ita a gidan. Lokacin komawan mu school yayi ranan da zan fara fita shiga nayi na mutunci irin ta matan auren da suka san kan su. Ga socks da katon hijjab na saka a jikina fuskanane kawai mutum zai iya gani a lokacin. Na samu anty zaune a falo na gaida ita nake fada mata zan shiga school ne. Ko adawo lafiya ban samu ba har na fara tafiya na tuna da key din motan da ya bani na koma na dauko na kara fita. Motar dake a rufe tasha wanki tun jiya yaya Bashar yasa aka wanke ta aka kuma cika ta da mai, fam. Ina fita ashe sai Amira ta leka tana fadin yar iska ki taki sayyada ai a kafa don sai dai kije titi ki hai taxe . Babu uban da zai kaiki da mota in kince kwadayi kuka iya ke da uwayen ki ai kunkai karshe gurin yaya sadauki. Lekawan da zatayi ta hago har na zauna a mota ina service din ta wani irin ashar ra mulmulo daga bakin ta tana fadin kan uban can motar yaya sadauki fa. Ashe akwai bura ubah a gidan nan kuwa ko ni ban shiga motan shi ba balle wanan bakar jakar kauyen ta ce shi zata shiga. Nikan har maigadi ya bude min get nasa kai ina ganin fitowan ta cikin matsifa ban tsaya ta kanta ba nafice daga gidan. A cikin masifa ta koma cikin gida tana masifa da zage zage wai sam bazata yarda ba da hakan. Tayi kiran layin shi lokaci yana gurin wasa wayan shi yana kashe bai shiga ba. Maji takira a cikin fada take fadin maji kinga abinda kika jawowa yaya ko kamar Bintu zatace ta shiga motan yaya ta fita da ita? Amira kina da hankali kuwa mata da motar mijin ta har kike fadan wai ta shiga ke kije ki shiga ta mijin ki mana. Kashe wayan tayi don har kukan takaici sai da tayi a lokacin gashi sai faman kiran wayan shi takeyi bai shiga a lokacin. Ina isa makaranta idanuwan mutane yayo kaina caaa suna son ganin wake cikin wanan irin motan haka kamar yadda mutane ke saka ido ga abinda bai shafe su ba yanzu. Sai da na gama na kulle ko ina na sako kafana dake cikin takalma mai hill wanda duk kwakwan mace da wuya ta samay shi a kasan nan. Zan iya cewa a lokaci daya muka shigo da maryam don a lokacin itama ta fito har ta rufe motar ko. Ina tsaye ina gyara tsayin hijjab dina da ya sauka har kasa naji tace madam you are welcome to new world. Dariya nayi nace ,a,a anty kema shigowan ki ke nan dai yanzun ko ? Tare muka jera da ita zuwa cikin makaratan sai kowa ya nufi department din shi. Idanuwa akan mu don komai na jikin mu sai ya koma sabon yayi kasancewan mu amare sabbin fitowa. Ban tsaya wani gaisawa da mutane ba don gujewa sabawa Allah don balain tsoro gareni. Ban fito ba daga class sai da lokacin sallah yayi na tafi school mosque inda muke zuwa sallah. Maryam ce ta kirani ga waya tana tambayan inda nake wai muci abinci. Nake bata amsa da ina mosque tace nasan dama baki wuce can ai gani kofa idan kin idar kifito ina jiran ki. Nafito na samay take cewa ga abinci can da tazo muna dashi don tasan idan tanice bazanci komai har mu koma gida. Nace a ina zamu zauna ya ustaziya dariya nayi nace nice kuma ustaziyan yau kuma anty ? Nace sai dai mu shiga motar ki don gaskiya bazan zauna a fili ba can muka nufa muna ci muna hira akan matsalan anty Amira. Sai after six na iso gida a gajiye dani nasamu musa a takure yana jirana don fitana da ya gaji da zama ga takuran anty Amira ya koma gurin su maigadi ya zauna. Dakuma yagaji ya dan fita mike kafa yabi titi har saida ya gaji ya juyo ya dawo gida yana kofan gida zaune na shigo gidan ya taso da fara,an shi a tare muka shiga gidan . Babu kowa a falon nan muka zauna muna dan hira dashi nace bari na dan shiga na dafa mashi abinci. Dakina nashiga na kwabe na koma kitchen nafara dafa abinci mai saukin dafuwa don a gajiye nake a lokacin. Ban san zuwan ta ba sai muryan ta danaji a bayana tana fadi ke mara kunya yanzu ashe harke kina ganin kin isa shine kika fita da motan yayana. May kike nufi da hakan dakikayi don duniya tasan dake ko kuwa kinyi ne dan gadaran kan ki ? Nace anty banda amsan baki ni amma kina iya tambayan dan uwan naki ai kiji daga bakin shi don shikeda amsan tambayan ki. Wani tsuki taja ta jyya tana fadin zaki gane kuren ki wallahi na aikat hakan da kikayi. Nace wai may ke damuwan anty Amira ne haka duk ta wani bi ta canza rayuwan ta lokaci guda. Yaya sagir ne ya shigo gaida mu karan shi na biyu ke nan bayan tafiyan dan uwanshi yana zuwa duba mu a gidan. Shima yaya Abdul yazo amma saudaya ya zo gidan ya dubamu yana min sheri wai yaga na canza may ye sirin ne dayake shi mutum ne mai son barkwanci da mutane duk inda ya ke sai anyi dariya. Nafito muka gaisa yana tambaya na ba dai matsalan komai ko nace ba komai yaya lafiya kalau muke. Bai wani dade ba mukai sallama ya tafi don irin sadauki ne shi miskiline bai magana sai wanda yaso yi dashi. ****** ********* ****** Duk muna falo a zaune musa da yashigo abinci yake ci yana kallo, sai wayana yai kara na duba nomba bata kasar nan bace ta kasar waje ne. Nai matukar mamaki da tambayan kaina waye kuma ya kirani haka ne wai? Har kiran ya katse ban daga ba naci gaba da abinda nakeyi tana zaune sai faman dakilan wayan ta takeyi. Wayan ya kara kara sai naga ta kalleni cikin zargi yanzu tsoron ta nake ji don ta canza gaba daya. Haka yasani daga wayan don gudun zargi kada ta kulla min sheri gashi yau nafita zuwa school. Mai shi baiyi magana ba nake ta fadan Assalamu Alaikum amma shiru ba ai magana ba nace please don't called this nomba agai iam marriage woman. Murmushi naji anyi yace wata irin matar aure ce da bata san hakkin mijin ta ba sai kuri fadi da baki. Sai a lokacin nagane cewa shine online ashe cikin yar murya nai murmushi don kafe ni da idon da tayi tana son tasan dawa nake wayan. Nace shine zaka kira mutum kaki magana ni wallahi har ka ban tsoro ma naga nomban kasar waje ban san mai ita ba kuma. Mikewa nayi tsaye don barin gurin kada taji fitinan mu don nasan shi zamuyi tunda ya fara fadin haka ina fadin. Yaya ina wuni? Tabini da harara tana fadin munafuka kawai wakike boyewa maganan ku indai yayanane baki taba fari a gareshi. Ina shiga daki yana fadin dan baki da kirki da tarbiya shine koki kira kiji yaya na isa balle yaya nake ke wai wata irin yar kauyen yarinya ce haka ? Nace da iska zan kiraka ko da guguwan nomba zan bugo maka ? Yace dan rashin kirkin ki bazaki iya tambayan ko Amira ta baki nombana ba ki gaidani. Nace banga zan iya wanan ba don ba damuwa kayi da asan lafiyan juna ba ai ? Yanzun kuma da ka damu aika kira kaga na samu lamban idan zan iya sai nakira. Ke baki da kunya wallahi idan kika fada min maganan banza ko a waya ne wallahi gobe zan shigo garin nan naci maki mutunci son raina. Nace kai dade idan kaso ma ka taso yau din nan ka iso anjima ba sai gobe ba dip naji ya kashe wayan tashi. Tun ranan bai kara kirana ba nima dai haka ban kara kiran nashi ba har lokacin. Maryam ce ta ishe ni da korafi inda ta matsa min akan sai nakirashi a gaban ta kokuma wallahi mu bata da ita. Ba yadda na iya dole na dauko wayana daga cikin hand bag dina na kira wayan na shi a lokacin kuma shi yana zaune tare da Linda. Sai ganin kirana yashigo a wayan shi da sauri ya dago kanshi tare da cewa hello, Nace wa,,alaikum sallam. Ina wuni yaya ya amsa da lafiya a takaice sai nai shiru maryam dake gefe na ta kafeni da ido don jin may zan kara fadi kuma. Jin nai shiru yace min kuna lafiya dai ko? Lafiya muke na bashi amsa a lokacin naji muryan mace tana tambaya cikin harshen tiranci da wa yake waya ? Naji yace mata sister din shi ce . Lafiya dai ko naga kin kirani yau? Nace ai kaji matsalar sai ba lafiya zan kiraka dama ni sai anjima kawai. Dakata sai na tsaya ina sauraren shi yace nasan wani ni yasa ki kirani dole ko? Nace eh. Anty maryam ce gata a zaune tace sai nakiraka ko mu bata da ita shiyasa na kiraka. Ok Maryam dake gefe na tace shit ta karbe wayan daga hannuna tace hello yaya ta damay ni fa da zancen ka shine nace takiraka mana taji lafiyan ka. Murmushi yayi yace maryam kin san fa yar kauye ce bata san darajan miji ba balle ta san kiran shi taji lafiyan shi. Daga inda nake a zaune nace, gara zama da kauyanci da hurda muranen banza ai muryan mace naji tana magana dakai yanzu. Dariya magana ta tabashi don ya fahinci nasan kishi ke nan nima don har na kasa boyewa na fadi a fili. Yace maryam fada mata Linda ce my wife to be nake tare da ita ba irinta yar kauye da batasan komai sai kauyanci da rashin kunyan su na yaran kauye. Haushi naji nace komai kauyanci mu dai mun san darajan kan mu da mutuncin iyayywn mu dip maryam ta kashe wayan tana fadin. Kinji halinki ko Bintu ke wanan bakin naki wai bai mutuwane nace cikin fada wallahi muddin bai daina kirana yar kauye ba bazamu taba shiri dashi ba kinji na fada maki. Tace kai Bintu ada kema kice mashi kowa ma kauye ne asalin shi don mu kauyen mu fa har yanzu babu ko titin mota ba wuta ba ruwa. Nace nagode anty aiko zai rana kanshi don daya fada zance mai munfi mutane kauyen tureta ai. Ranan daga school maryam tace min mu tsaya salloon din dake kusa da school din mu gyara kan mu baki ba don da wuri muka tashi. Wanke min akai akayi tare da zuba min kayan kamshin da tazo dasu masu kyau sai nace a dan gyara min kafana da yatsun hannu na haka akaimin gyara nafito wata yar birni dani. Sai da zamu rabu take ce ban sa zamu hadu ba sai zuwa next week amma ina son ranan Friday don Allah kiyi girki mai dadi ki gyara gida da kanki sosai yadda yaya zai gane cewa yanzun ke ba bakauya bace don ina sa ran Friday din nan zai shigo garin suyi waya da yayana yace yana Abuja. Muka rabu ina shigowa gida Amirah ta kasa boye haushin gyaran da nayi a zuciyar ta tace sai dai kikare haka Bintu miji kan sai dai kamahi shi. Murmushi nayi a raina nace kai kodan na kure anty Amira dole nabi shawaran maryam. Friday na yi kamar yadda tace sai bina da kallon mamaki Amirah keyi. Kasa hakkuri tayi tace wa da ni yau wani kuma sheri kike son yi a gidan nan ne haka ko bakin yan kauyen ku zasu zo ne wai? Nace anty ashe kin gane bakin kauyan mune zasu zo yau gidan kuma anan zasu kwana tare da mu. Na gama komai na koma daki ganin biyar saura nan na bata lokacina gurin gyara jikina zakace wani gasan gwajin kyau zan tafi a lokaci don har musa kanina saida na bashi sabbin kayan da na,sayo mai ya saka yai aski irin ta matasa. Falo muka dawo muka zauna ganin haka yasa Amira fitowa daga daki nasan ta hake ne taiwa bakina wulakanci a lokacin. Bamu dade da zama falon ba da kamshi ke tashi cikin shi mukaji ana nocking din kofan shigowa don a rufe yake musa na tura ya bude kofan. Yayin da Amirah ta sako idanuwan ta don ganin mai shigowa falon a lokacin don a shirye take da cin mutunci a ran ta. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKK8N WASU PLEASE,,,, IDAN KIN BIYA KADA KI TURAWA WANDA BAI BIYABA,,,, Shine ya shigo gidan kai tsaye yana saye a cikin kananan kaya farare cikin mutunci musa da ya gane shi yake mashi sannun da zuwa . Murna da yar tsalle Amira tayi sai a gaban sho tana fadin yayana ashe kana hanya shine ban sani ba tun da,safe. Yace common yanzu ba gashi kin sani ba what else ? Har lokacin yana tsaye daga kofa yana rataye da yar jakar shi ta maza mai dogon igiya da suke ratayawa,a,kafadar su. A hankali na karaso garesu cikin tako daidai har na iso gare su jakar kafadan shi na sa hannu ina cirowa daga kafadan shi tare da mashi sannu da dawowa cikin wata murya sai ido ya bini dashi cikin shagala da kallo na. Da kyat ya iya amsa min da hanya lafiya saboda hannu na da ya dan taba jikinshi ya sakar mai da wani irin kasala lokaci guda. Daga inda Amira take tsaye tare dashi sai kallon mamaki take binshi dashi a cikin mamaki, can ta saki wani irin ajiyan zuciya jin haka yasa shi saurin juyowa gareta daga shagalan da yayi ga kallona. Tace yaya na ko shiga baka karasa yi ba mun barka tsaye a kofa tau matar gidan ce wata barkatatta da ita can. Ya saki ajiyan zuciya a hankali tare da lumshe idanuwan shi cikin wani yanayi yana shafo fuskan shi da hannayen shi . Cikin falon suka karaso tare dashi inda suka zauna akan kujerun dake falon gaba dayan su har musa kani na dake tsaye daga gefe daya. Drinks ne mai sanyi na jera a wani dan tiren silver mai ruwan golden da cups din shi ture din tafiya nake zakace wai sallon jan aji nakeyi wanda ban san dalilin kara shagalan da yakeyi ba haka. A gaban su na girke tire din ina masu bisimillah tare samun dan guri daga gefe daya na zauna na dan zamo daga kujera inda saboda dan dukawan da,nayi gaban rigana ya baiyyana suran jikina a fili, da sauri ya lumshe idanuwan shi da sauke ajiyan zuciya a hankali, Cup din da na tsiyayawa abin sha na dauko na mika mashi ina fadin ga ruwa mai sanyi yaya. Yakarba ba tare da ya juyo gare ni ba nace abinci fa ko sai kai wanka ne zakaci cikin wata irin yar siririyar murya da ban san ina da ita ba a lokacin. Ya dan girgiza kan shi tare da kara lumshe idanuwan shi sai dai fuskan shi a dauresuke mai yadda,na,saba ganin shi a koda yaushe. Kamar da kyat ya iya furta cewa bari nai wanka idan na dawo daga sallah zanci abincin kafin na kwanta. Yana dan kurban drinks a hankali yana wani lumshe idanuwan shi abinda ya daurewa Amira kai ke nan ta kasa fahintar yayan nata gaba daya. Shi da kan shi yai masu bisimillah tare da cewa musa bissimila dauki mana may ma sunan kane please Musa ya bashi amsa cikin dan murmushi da fadin musa yace malam musa ke nan naga kaman kai ustaza ne ko? Musa dai murmushi yayi saboda ba sabawa sukayi ba bai sake jiki dashi tukun. Dawowa nayi falon tare da dafa kan kujeran da yake zaune nace yaya ga ruwan wanka can an hada maka magariba yana kusan towa. Duk da yana mamakin ganin sauyi a tare dani amma sai yake daukan hakan a matsayin wani sabon yaudara ne na ke kula mashi don naga Amira a gidan. Amira bari na je nai wanka yace mata tare da kokarin mikewa tsaye daga falon zai shige ciki. Yana shiga daki mamaki ya kara kamashi ganin yadda dakin yasha gyara ga kamahi ko ina yana tashi daga dakin. Jiki a sabule mashi yadan bi ko ina na dakin da kallin mamaki gaba daya tarasa may nene dalilin wanan sauyin da ya gani a gare ni lokaci guda haka amma zai natsu ya fahinci may abin ke nufi ne wai. Daga Amira ko maryam ko kuma dai akwai wani plain a kasa nake boyewa. Haka ya shiga wanka zuciyar shi fam da tunane a cikin ta na tambayan kan shi may ke faruwa ne haka akwai yaudaran da nake shiryawa a boye. A lokacin na juya zuwa cikin dakina na bar falon da suke zaune sai da na kwatanci ya shige bayi na budo turare a jikina, sun kai kala uku nafito falon sautin takalman dake kafana, yasa Amira saurin dago kai tabi ni da idanuwan ta. Sai ga kamshi yana taron hancinta a lokaci guda sai taji wa ni irin wani abu ya tokare mata makoshin ta a lokaci daya. Dakin yaya sadauki na nufa nai sa,a na samu ya shiga bathroom a lokacin cikin sauri na bude wardrobe din kayan shi, na fito mai da doguwan jallabiya fara kal mai laushi da,santsi jikin shi na bishi da turaren shi masu kamshi na fashe rigan, na aje mai wani wando gaje daga cikin kayan shi dake wanke na tafito nabar dakin kafin ya fito. Yana fitowa kamshi ya daki hancin shi sai lokaci yaga komai da zai bukata na aje mai a saman gadon shi ko. Musa kaje kayi alwala na fadi tare da shigewa dakina na muka barta a falon zaune ita kadai kamar manya. Tana batun mikewa don ta gane nice silar a,watse a,barta a gurin zaune ita kadai sai taji motsin kulle kofan dakin dan uwan nata. Da fara,a a fuskan shi yake cewa Amira kina nan zaune ne bari na dawo mosque nazo mu zauna ko ? Tare da musa suka wuce zuwa sallah mukuma kowan mu ya,shige dakin shi a lokacin. Wanka nayi na fito nai sallah tare da canza sutura a jikina irin da ya dace mace taiwa na miji shiga dashi da dare tankar wace zata halartan wani bukin dinner can. Dogon rigane mai hannu kamar ta shimi za,a iya ganin hammatan mace a fili daga ciki sai zuwa kasan riga an matse shi an fitar da sharp din mace sosai wanda ko wanene yaga wanan shiga sai ya yaba da shiga na daure gashina da ya sha gyara a cikin dan kyallen riga mai kama da ribbon din daure kai. Ba yaya saudauki ba har anty Amira da muke zama koyaushe a gida guda, Ina fitowa falon wanda shigowan shi ke nan daga sallah nafito ina kamshi ina fadin sannun ku da dawowa tun da nake da Anty Amura babu wanda yasan cewa na iya wani yare sai yau din nan dana canza harshe da musa ina mashi yaren uban su wanda nima da karfin hali na iyaren mutanen Niger din. Kallo biyu suke min na mamaki kwalliya na da kuma jin canza harshen da nayi wanda basu san ina da,wani yare a,harshe na ba sai yau din nan. Inda yake zaune na nufa sai da,na kai zaune gefen hannun kujeran na fara gaidashi tare da kara mashi sannu da zuwa . Amirah ta cika fam tun zamana a gurin ta wani hade rai hankalina ya dauke ga kallon tv gaba dayan mu duk wani film din action ake a lokacin. Sai da aka gama gurin da ya dauke muna hankali na dan juyo gare shi cikin kwantar da murya nake cewa abinci fa yaya. Yace kin shirya daning din din ne nace mai eh tare da mikewa yace malam musa muje muci abin ko. Ko ba komai ni dai sai naji dadin yadda ya kula min da dan uwana batare da nuna mai yadda nazata ba daga gare shi. Sai da suka mike da musa yake cewa Amira taso mana sister ta wani bata rai tace naga kaman ka fara mantawa danine ai yaya. Kai haba Amira wani irin magana ke nan kuma yace mata kin taba ganin mutum ya mata da dan uwan shi ne ? Sai bayan sun zaunane nazo na fara zuba mai abincin sai wani faman lumshe idanuwan shi yakeyi don kamshi da desire dake damun zuciyar shi. Kujeran da yace itace nawa na zauna akai tare da dan zuba abinci kadan a plate wanda zanci . Bai wani ci abinci ba amma yasha fruits salad din dana zuba mai sosai da ruwan kayan yajin da nai mashi drinks din hausa dashi. Yana ci aka bugo mai waya nan hankalin shi ya dauke da hannu ya yafuto ni da alamar nazo sai na zo inda yake ya daina waya yana ce min ki dauko liptop dina ki dan dafa min kafin na kwanta zan sha. Dakin shi na nufa naga liptop din gasu nan da yawa kala kala na dauko wani mai steberry na nufi kitchen dashi. Musa yana gamawa ya mike tare da komawa gurin tv yaci gaba da kallon shi. A flask na zuba mai tare da daukan cup na nufi dakin shi da ruwan shayin zalla ba madara a ciki na kai mashi. Ban fito ba sai da,na kara gyara dakin tsab nafito don na samu kayan da yacire a,watse inda yake ajewa na feshe dakin da airfreshiner. Dakina na koma don nagaji gani na san tunda yana gari gobe dole akwai aiki gare ni. Sallah nayi tare da dauko rigan barci na na saka har zan kwanta sai na tuna ban sallami MUSA ba . Nafito a cikin yare nai mashi magana cewa idan ya gama kada ya dade yaje ya kwanta yace min to Allah ya bamu alheri. Duk da zani ne saman rigan ya san shirin da nayi alokacin na kwanciya ne. Daki na koma ban dade da kwanciya ba naji barci ya fara dauka na gashi ban sawa kofa key ba yadda na saba sawa nufi idan na falka zanyi sallah sai na rufe kofan. Can cikin barci naji kamar ana tsaye a kaina duk da rufe nake a cikin bargo bai hanani jin nauyin mutum aikana ba. Da sauri na bude bargon dake rufe har kaina yana tsaye ya harde hanbayen shi biyu a saman kirjin shi ya dan jingina jikin shi da bangon daki haka ma kafan shi a harde suke mai. Ganin shi a dakin yasa nai saurin mikewa zaune cikin dan rudewa nake cewa wani abu zan makane kuma? Ke dakata yace min cikin daure fuskan shi tambayan ki nake son yi . Wani muna funci kike kokarin kulla min a gidan nan kuma ? Cikin mamaki na dago kaina tare da dan kallon shi ganin ni yake kallo ido da ido yasani dukar dakaina a kasa. Yace tambayan ki nayi may kike kullawa akaina don ban fahinci wanan bakin ladabin shegun da naga kinayi ba tunda na dawo gidan nan. Murmushi nayi kawai tare da kokarin mikewa zaune da kyau banyi magana ba sai da na mike tsaye da kyau tare da manta yar rigar barcin dake a jikina. Sai da naga wani mayen kallon da yai min nai saurin koma da sauri na zauna tare da jawo zanin da ke saman gado na kara dan rufe jikina dashi. Idanuwan shi na a lumshe yake ce min ke nake saurare zakiyi magana ko sai na saba maki yanzun nan. Nace laifi ne kuma idan mata ta kyautatawa mijin ta ashe nace kada ka manta nauyin ka yanzu a kaina yake. Duk wani nauyi da nasan naka yana a kaina shi nake kokarin ganin a matsayina ta matar gidan nan na sauke shi a kaina ko kuma hakan shima sabawa ne ga Allah. Bai yi magana ba bai kuma fita daga dakin ba sai lumshe idanuwan shi kawai da yayi a lokacin. Can naji ya furzo iska daga bakin shi yana fadin idan kika kuskura kika kulla min wani makirci har na fahinci haka wallahi sai na mugun saba maki kinji na fada maki. Daga haka naga ya juya yafita daga dakin hakan yasa na mike nabi bayan shi na sakawa dakina key kawai. Amirah da taga shigan shi guri na shiru shiru taga bai fito ba ta mike cikin bacin rai ta shige dakin ta sai sauke ajiyan zuciya takeyi kawai. Tana cewa a ranta may yaya sadauki ke nufi da wanan yarinyar badai yana nufin har ya mika kan shi gareta bane mai zai gane gurin wanan bakauyan yarinyar da maji ta nace a kanta. Tace kai yayana ban taba zaton haka ba daga gareka gaskiya kai mai tsadane kai mai daraja ne sai yar manyan mutane ta dace da irinka. Bintu bazan taba bari ki samu farinciki ba a zuciyar yayana har abada sai dai ki zauna zaman gadin gidan nan kawai ****** ********* ****** Washe gari kafin kowa ya tashi na gama hada komai na gyara ko ina na gidan sai kamshi ke tashi na koma ciki na gyara jikina tare da saka kaya wani dogon riga Afr abaya mai simple design. Ina zaune gaban mirror wayana yai kara na dauka ina mamakin mai kira na da safiya haka. Anty maryam ce ina dagawa tace amarya kina kamshi fa, yaya labari. Dan tsuki nayi nace kai anty maryam ni dan Allah ki rabani da wanan zancen kinji. Tace cikin daga murya may kike nufi wai wallahi Bintu kiji tsoron Allah duk wanan nasihan da nai maki kina nufin baki dauka ba ko may ? Nace haba Anty yaya kike son nayi da mutumin da baidamu dani ba zargina mafa yake wai bai yarda da sauyin da yagani gare ni ba. Dariya naji tayi tace bashi bane ya fara kamuwa ke nan kedai kawai yi yadda na fada maki shi da kan shi zai kawo kan shi gare ki sai dai in ba mace ta haife shi ba. Amirah ta koma ne nace tana nan what wani gulma ya tsayar da ita kuma a gidan ku amma dai Anty bata da kunya wallahi. Yanzu zan sa maji ta aiko a dauke ta tunda ita bata san ya kamata ba don may zata zauna maku gida ta haku walawa. Shi musa nasan namiji ne ba zai tsaya saka maku ido ba namaji yayana na fadin makarantan kwana yake so ya sama mashi nagari ya kai shi. Wani mugun dadi naji a raina nace da gaske Anty tace wallahi jiya naji yana magana cewa yana nan yana mai process don baya son ya koma kauyen nan kuma don yaron nada kirki. Nace wai ban ma san urin godiyan da zan ma yaya Bashar ba wallahi na dade ina tunanen mafita akan kannne na anty don haka suke zaune ba karatu wallahi. Tace a sannu duk sai ai masu mafita yanzun dai mu samu kan wanan baudaden mijin naki tukun shine mafitan komai. Nace nifa anty ba wai ya damay ni bane kawai ko hakan ma da muke is ok ai. Tace kina da hankali kuwa Bintu mace baliga kamar ki zaki zauna danamiji sai kallo ni na fada maki sa ido kiyi kallon yadda zamu kamashi wallahi. Mun dan kai wani lokaci muna waya da ita tana kara fada min abinda zanyi, mukai sallama da ita. Muna gama waya ta kira mama tana cewa bayan sun gaisa ko anty Amira na kusa na kira wayan ta bai shiga ba tace ba tana gidan yayan ku ba ko kin manta ne ? Tace bata dawo gida bane mai takeyi a gidan kuma bayan maigidan ya dawo ? Yaushe ya dawo inji mama tace jiya da yamma mana ya shigo gari haba dai ita ko gidan amare mijin mutum ya dawo may zata kuma zauna yi masu a gida? Maji tace ai yanzu zan tura Abdul ya dauko min ita bata da kunyane da bata zauna a tsakanin su ba ai. Bayan sun gama waya da Maryam mama ta kira wayan yaya tana cewa ashe ka dawo ne Baba na? Kunya yaji da ta fadi haka yace cikin dan kamay kamay wallahi yanzun nake shirin nai wanka nazo gida ai. Tace babu komai ka huta abinka har zuwa yamma ka shigo ai wanda ke da iyali kuma ina zaka da dawowanka. Sai dai ka fadawa kaunan ka ga Abdul nan zuwa yanzu ya dauke ta maza ta dawo gida. Ban san may ta tsaya yi maku gida ba kuma bayan tasan kana bukatan hutawa da iyalinka. Murmushi yayi kai haba maji jiyane fa na dawo ai ba komai takeyi ba zata dawo anjima idan zan zo . A,a maza yanzu ga Abdul nan zuwa zai dauko ta dawo gida haka na ladan ya isa kuma. Suna gama waya da mama ya shiga wanka sai da ya shirya tsab cikin kanan kaya kamar yadda ya saba shiryawa, ya fito daga dakin shi sai annuri da kamshi ketashi gare shi. Amira ce zaune a falo nan ya zube gurinta suna gaisawa da ita sai wani shan kamshi take wai tana fushi ya shiga guri na amma shi bai ma fahinci may take nufi ba da hakan. Yace maji tace ki shirya ga Abdul tafe yanzu zai tafi dake wai. Bata so batace tunda safen nan kamar abin kora kuma ? Yana zaune idon shi na akan kofana amma babu alaman fitowa na a lokacin. Mikewa yayi tsab ya nufi dakin nawa tsaye nake ina shirin fitowa ke nan Allah ya ingizo shi dakin. Ina ganin shi na zube kasa ina fadin ina kwana yaya? Yace ba tare da ya amsa ba Amira zata koma gashi kayana basu iso ba har yanzu. Nace ko zata tsaya har su iso ne juyawa yayi yana fadin umurni ne daga maji. Ki fito ki bamu abinci kafin Abdul ya iso daukan ta mun samu bata falon a lokacin haka yasa na bita dakin ta. Da sallama na shiga amma bata karba min ba nake cewa anty ashe yau zaki koma yanzu yaya yake fada min haka. Tace eh zan koma nabarki kiyi yadda ranki ke so ai nasan kece da aanan kullin don na tare maki guri jarababban yarinyar kawai. Haba anty may kika tare min aiko kina nan ba,a fasa abinda za,ayi kinga ashe zaman ki bai hana komai. Bintu kada fa ki kawo min rashin kunya wai ke adole ga wace ta san dadin namiji ko ? Dariya nayi nace anty aure ne fa kema idan kikayi zaki gane haka ba wai jaraba bane dadin aure ne kawai. Lalai yau Bintu har nikikewa gorin aure har wani aure ne kikayi har kika san dadin shi ke. Kai haba anty kema aikin gani gashi kuwa kamar har ya damay ki kullun kina magana a kan shi. Da ki baro idan kayan yaya yazo ki karbi tsaraban ki zaifi ki koma hakana don kada mutanen gida suga kin dawo empty. Dama sjine gurin ku ai ku mamaye komai nashi ya zama naki ke da yan uwanki kawai. Ba abinda zaki taba sai nazo gidan nan don nasan halin yayana dole nice mai raba mashi kayan shi. Nace da ke nan kuma anty yanzun kan ai akwai mairabo tsakanin ku ina fadin haka na fito daga dakin na barta tana yabo min magana. Mun karya duk da a takure nake amma ban yarda Amira ta fahinci komai ba akan zaman mu dashi a gida. Munan cikin karyawa Abdul ya shigo gidan nan suka shiga gaisawa da yayan shi ina gefe nace yaya Abdul ina kwana ya juyo gareni yace sarautan mata yaya kike? Nace mai na zubo ma, abinci ko yace kaman kin san bar karya ba nace nasani mana yaya tunda gauro kake. Bintu yaushe mijinki yai aure da zaki fara kira min gauro saurana fa kusan shekara bakwai ko takwas. Kai yaya wallahi kada kaiwa kanka baki nasan komai fa ina Nadiya take da zakace haka? Yana zaune yanajin hiran mu da yaya Abdul inda ya juya kan Amira yace kin shirya ne ku tafi ? Yaya ko kaima kora na kakeyi ne kaman wanan mara kunyan yar kauyen dake fanin ta samu guri. A,a Nafisa yaushe kuma kuka fara haka da Bintu ina Bintu tai kama da yar kauye ko ada can balle yanzu da ta zama wata princess can da ita. Nace yaya Abdul fada mata dai ko zata bude idon ta tagani ni dai nasan akwai wata a kasa tsakanina da Anty kawai amma ni nasan nawaye ai yanzu. Dariya magana ta tabashi yadda nai magana waina waye Amira tace kaiyya haka kike gani ashe ke don kinga yanzun kina rayuwa a cikin wanan gidan . Abar rayuwan kauye ko nace kai anty ho ke manta ni diyar mamace tun yaushe mama ta mayar dani yar gatan ta. Dama ai shine gurin ku ashigo a mamaye komai ai aleale sai yadda akayi da dangin miji ko? Kai Amira tashi ku tafi please bani son irin maganan nan for god sake kaunan kice fa kubar wanan irin maganan mana ? Yaya Bintu ce kaunata ko wa shiru yayi yadda na fahinci baiji dadin kalaman ta ba a gare ni. Kallon mamaki take mashi tamike tare da shiga dakin da ta mayar nata ganin tafito da jakar tasa namike zan karba. Tace kada ki soma taba min jakkana munafuka zamu zuba ni dake don babu gurin zama agidan nan gurin ki. Ido muka hada yai min wani shu,umin murshi na mugunta tafita batare da tace dashi uffan ba. Mikewa yayi yabi bayan su ina mata agaida mutanen gida. Gurin da mukaci abinci na gyara muna tare da kawar da duk wani abinda ya dace a gidan . Daki na koma ina zaune ban san barci ya dauke ni ba a gurin can yadawo suna falo da musa ya mike zai fita yace ina zaka tafi ustaz yace akwai inda nake fita gurin mai shago muna hira ko dasu maigadi. Yaron nafita yaji zaman falon ya ishe shi don haka ya mike zuwa waje jin dayayi shuri ban fito ba yashiga dakin. Dakina ya shiga ina kwance na dunkule saman gado kamar wata yar jaririya dani. Kallon yadda na dunkule kamar mai jin tsoro yayi ya dade a kaina saida na dan gyara kwanciya tare da kara dunkulewa yabar dakin. Ikon Allah sai gashi nai mafalki da Kabi yanace min Fatima yau ina iliminki da,wayon ki suka shiga. Kina kokari kasa cin jerabawan ki zaki halaka kanki kin kuwa san irin dumbin masifan da zaman dakika zaba da mijin ki yake haifa maki? Ubangiji babu ruwanshi da halin shi rayuwan biyayya da zaman takewan ku zai duba abinda yakeyi tsakanin shi da Allah shi ne. Muddin baki bi mijinki ba Allah zai kamaki da laifin haka, kuma makomar ki shine wuta. Fatima kibi mijin ki kinji sauda kafa don Aljananki yana karkashin kafan shi ki faranta mashi ko yaushe kinji kaunata kad ki halaka kanki. Sai nafara kuka murmushi naga yai min kawai yajuya yafara tafiya kaman cikin wasu duhun itatuwa ya bace abinshi. Zubur na mike tare da salati sai zufan da yafara karyo min a goshi na kawai duk da A C dake aiki a dakin. Kabir na furta a fili wasu irin hawaye naji suna zubi min nace Allah ya jikan ka bawan Allah kila sadaka yake so nai mashi. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,, IDAN KUMA K8N BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA NA BARKI GA ALLAH YAR UWA,,,, A LOKAC8N MUKE,,, Tun ranan da wanan abin ya shiga a tsakanin mu na kasa sakin jikina a gidan. Ban yarda mu hadu da yaya sadauki ko da a falo ne ganin na dan samu sauki yau natshi tunda safe ina son shiga school kasancewa monday ce yau din. Tsaye nake a bakin zinc na kitchen ina dauraye kayan da akai amfani dashi daren jiya. Ga kuma girkin dana dora ina sauri ingamawa kada na makara ko ya futo yasamay ni ban fita ba. Jin kaman mutum tsaye a bayana yasani sauri juyowa ina kallon kofa shigowa kitchen din, . Gaba nane yai mugun faduwa da ganin shi yana tsaye ya saka hannayen shi biyu ya raba kofan tsakiya jikin saye da kayan exercise din shi sunyi matukar yi mashi kyau a jikin shi. Dan daburcewa nayi daganin shi bansan lokacin da nakai kasa ba a tsorace ina cewa ina kwana yaya. Bai amsa ba,sai karasa shigowa daga cikin kitchen din da yayi gaba daya ina durkushe. Tsayawa yayi tare da jingina jikin shi da bayan inda nake tsaye da farko yace wa kike boyewa kwana biyu a gidan nan. Mikewa nayi don ganin bazai amsa min ga tambayan da ya jefo min kuma lokaci guda. Fuskewa nayi nace may zan boyewa kuma ni don banda lafiya ne kawai. Murmushi yayi yace may yasamay ki baki da lafiya kuma? Turo baki nayi na karasa dauraye plate din dake a hannuna, na juya ji nayi ya finciko ni tabaya na. Tsoro ne ta kamani jikina ya dauki rawa a lokaci guda don balain tsoron shi nake ji yanzu . Idanuwa na a runtse tare da sauraren abin da zai biyo bayan rikon da yai min a lokacin. Hannuwan shi naji saukan su a saman kirjina tare da rankofo kan shi a daidai wuyana a hankali. Yana fadin abinda kike min rowan su ke nan gasu yau na kama su a hannuna. Idona na ritse gam don jin abinda yaya ke min wanda ban taba ma kawo tunen hakan ba a tsakanin mu. Cikin wata yar murya nace da kyat don darajan Allah yaya kadai na wanan abin please ? Don Allah ka bari kada musa ya shigo ya samay mu a haka please. Murmushi yayi yace idan yashigo and so what bada matata ya ganin ba. Kara rintse idanuwa na nayi cikin rashin fahintar abinda yake min a lokaci zafi ne ko haushi ko ko dadi. Da karfi na zille daga jikin shi na koma gefe ina mai da numfashi kaina a duke. Murmushin keta yai min yana cewa matsoraciya kawai yau ina bakin naki yashiga kuma mai fadar bakat magana. Idona da yakawo hawaye na dago kai nace don wanan cin zalin da ka dauko yi min a gidan nan bashi zai sabakina ya mutu ba ai mugu kawai mai ruwa biyu. Murmushi yayi ganin da nayi ya juyo kamar zai yo kaina na zille akasa tare da kare fuskana da hanaye na sai naji yai dariya yace ashe bake bace ? Har ya kao kofa ya juyo ya tsaya yace, kuma idan na kara shigo na samu kin boye zakiga abinda zan maki gidan nan. Yana fita na sauke ajiyan zuciya tare da mikewa na karasa abinda nakeyi ina yi ina kwallon kofa kada ya dawo again. Sauri sauri nagama komai tare da shiryawa zuwa school don lokacin har dining sai dana hada komai na fito a cikin hijjab dina kamar kullun. Naso nafita batare da na,sallamay shi ba sai naga rashin dacewan hakan gareni don haka na nufi dakin nashi. A hankali na tura kofan daki da yar sallama a bakina, yana kwance saman gadon shi yai rigingine fuskan shi na kallon ruffing din dakin nashi. Daga kofa na tsaya ina fadin zan tafi school, sai na dawo. Da kyat ya iya dago kanshi idanuwan shi kamar yafara barci ne a hakan. Kallo na yayi tun daga samana har kasa na sai ya mayar da kan shi yana fadin akwai mai a motan, nan kuwa nace ranan da na fita last akwai mai a cikin sa sai dai ban sanar ma yau din nan ba. Mikewa naga yayi ba tare da yai min magana ba yafita a dakin nima bayan shi nabi muka fita a tare dashi . Motan ya bude ya shiga ya tayar da ita ya dan dade a cikin ta yana service din motan ina tsaye daga gefe ina kallon shi. Yafito daga cikin motan bayan ya gama warming dinta tare da ce min sai kin dawo ya juya ya shige gida. Mun hadu maryam a school duk yadda taso ta zolaye ni taji yadda muka kwasa da yaya sam naki bada fuskan yin haka. Dole ta gaji ta kyale ni muka canza hira kan hiran matar yaya Ahmad da akace sunyi fada har da buge buge har gurin yan sanda sukaje. Amma kuma sun dawo anshirya kamar basuyi ba nace ai dama irin su irin matan nan yan duniya ne daidai dasu. Tace ita kuma matar yaya Imirana ance kazama ce kumai tana dan kurba syrup akai akai, Sai dana gama saurare nace wai ubangiji Allah ya kyauta kawai zamuce ga al,amarin don yanzu abubuwa daban daban lokacin nan da muke cikin ta. Ba mu dawo gida ba sai yamma lis after six na shigo gidan agajiye dani daki na shiga na cire hijjab dina na fito kitchen don dora girkin dare. Misa ne yashigo yana ce min sannu da dawowa yace yanzun ko yaya ya bargidan nan yana tambayan baki dawo ba. Nace may zan mashi idan na dawo din sallon son yaiwa mutum muguntan shi dayasaba kawai. Kai haba anty yayane kuma mugu ni dai wallahi yana bani shawa wallahi don ba ruwan shi rayuwan shi akwai sauki sosai. Murmushi nayi a fili a zuciyata nace baka san komai ba yaro da baka fadi hakan ba. A gurguje na hada girki na koma dakin shi dake a hargitse na gyara mashi tare da wanko bayi na feshe ko ina da kamshi nafito nazo na samu shikafan dana dora ya tsane na tuka tare da kwashewa. Kafin a gama kiran magariba na gama hada komai na shige dakina wanka nayi tare da dauro alwala nafito. Ban daga ba sai da nai sallah ishai na fito tare da kara feshe falon mu da kamshi kafin ya shigo gidan. Na koma na zauna tare gyara jikina wani riga da wando na saka daga cikin kayan lefe suke English wear ne na gyara gashina da ribon jelae shi ya sako a baya. Dan karamin gyale na yafa ga kaina na fito falo na samu musa ya shigo nace mai ya dibi abinci yaci dare ya soma yi. Ya dabe ya dawo inda muke zaune ya faracin abincin muna hiran mu ta zumunci labarin rayuwan garin sokoto da ya gani yake bani ina dariya. Haka yasa bamuji shigowan shi ba sai ganin shi mukayi har ya kawo tsakar falon. Sannu da dawowa muka fara mashi ya amsa tare da zubewa saman kujera da alaman daga gurin wasan su na ball ya fito a lokacin. Sai ya kasance shigan da nayi na takura da zama falon dan wani kallon da naga yai min ya wani lumshe idanuwan shi. Can ya bude bakin shi da kyat yace musa ina gani gobe zaka wuce school don an gama maka shirin komai ko. Daga ni har musa dago kai mukayi muna kallon shi a cikin kasala yake maganan shi yace. Ban san ko akwai wani abinda zaka bukata ba kaje cikin buth din motana ka kwaso abinda akasoyo ma ka gani idan akwai abinda zaku kara sai ku duba ku gani. Mikewa musa yayi yafita yabar abincin don dauki sai lokacin na dago kai na kalle shi ya rike goshin shi da hannun shi daya nace yaya mungode Allah ya saka da ,,,,,, Hannu ya daga min yace is ok please nima ai kanina ne musa. Kara cewa angode bai yi magana ba sai mikewan da yayi ya bar falon tunawa nayi ban hada mai ruwan wanka ba a lokaci da sauri na mike nabi bayan shi. Na samay shi a tsaye yana kokarin cire kayan jikin shi sallama nayi na shigo ya bini da kallo kawai. Bathroom na shige tare da joner mashi heater ruwan zafin da zai yi wanka dashi. Nafito bayan na matsa mai su maclean da subulun da zai bukata na aje mai a gefe nafito din. Nazo zan wuce yana daure da towel iya kugun shi da sauri zan wuce naji ya finciko ni zuwa jikin shi. Yar kara nayi nace cikin wata irin murya wayyo yaya please kayi hakkuri don Allah matse ni yayi gam yana kokarin hada bakin shi da nawa. Sai kokarin zillewa nake don gaba daya balain tsoron shi yanzu ya cika min zuciya na don bangane wannan son yawan hada jikin shi da yake son yi dani ba akoda yaushe. Sosai ya tsayar dani sai tsotson bakina yake cikin wani irin sallo da shi yasan irin shi. Kafafuwa na ne naji basu dauka na a lokacin gashi ya cika min baki da harshen shi ban iya maganan komai a lokacin jikina sai kyarma yake min. Shi kan shi yaga dama ya sake ni tare da bina da shu,umin dariya yace zamu hadu dake ai matsoraciya kawai. Sai dana sai ta kaina a tsaye inda nake tare da bin bayan shi da zai shige bathroom. Lokacin ne na kara sheda girman jikin yaya sadauki sosai ashe karfafan mutum ne haka ban sani ba. Na samu musa a falon ya kwaso kaya gasu nan birjit a gaban shi. Jakkuna na kaya guda biyu na hango sai na karasa gurin yace anty kinga abinda yaya ya sayo min haka. Nan muka shigo budewa daga kaya sawa takalma uniform sai kayan abinci na gwagwani da na sha su madara da sauran abubuwan sha. Kallon kayan nake cikin mamaki don ba karamin kudi ne aka kashe ba gurin sayayyan wanan kayan masu yawa haka su bucket da kulan da zai ci abinci duk an sayo mashi man shafi su maclean da sabulun wanki dana wanka da turare. Musa yace kai yaya I love you wallahi ban ma san irin godiyan da zan mashi ba idan yafito wallahi. Murmushi nayi kawai naji dadi kwarai a raina don nuna kaunan da yayi wa dan kanina haka. Can yafito cikin wasu yan kananan kaya a jikin shi rigan mai dan karamin hannu iya hammata sai wando three quater da yasa fari kal dashi sai kamshi ke tashi a jikin shi. Direct dining erea ya nufa hakan yasa na mike na nufi gurin tare da daukan flask na fara zuba mai tuwon shikafa fara da miyan water leaf yaji agushi sosai da nama. Dan kadan na tsakurawa kaina a plate a shiririce nake ci inda ya zauna ya kwashi abincin shi sosai. Sau biyu yake cin abinci a wuni da safe idan ya karya sai kuma da dare wani lokaci kuma fruits salad kawai zai sha yakan ce wai ina son dirka mai abinci yaci yai kiba kwana biyu ya kasa yin wasan shi. Waya yake yi yana kallon yadda nake wasa da abincin dake gabana duk da rashin yawan da baida shi. Da ido yai min magana alaman maza na cinye shi na make kafada na alaman banyi, sai dai ban daina cin da nakeyi ba a yangance. Mikewa nayi tsam na fara kwasan kayan zuwa kitchen ban fito ba sai da na tsaya na wanke kayan don na rage yawan aikina da safe. Na dawo nasamay shi da musa yana gwada mai wasu takardu a hannun shi ashe takardan addmition ne na makaran tan da zai tafi. Zama nayi a gefe daya ina satan kallon su duk da hankalina yana gurin tv dake aiki a lokacin. Musa ya tatara kayan shi ya kwasa cikin jin dadi zuwa dakin shi tare da muna sai da safe nasan zai tafi yyakara baje kayan ne yasake kallon su a tsanake. Shiru falon yayi ba wanda ke magana a cikin mu sai tv dake aiki shi kadai ana ta watsa turanci ganin ankirashi a wayan hankalin shi ya dauke yasa ni mikewa nabar falon. Bathroom na shiga da niyan nakewa sai naga kawai nai wanka na ji dadin kwanciya kawai nafito na dan shafa mai laushi tare da saka yar rigar barci na dana feshe da turare, light pink mai dagwari biyu sai dai iya cinya ya tsaya min rigar. Ina zaune saman gado naji ya turo kofan daki sai dai ya sauya kayan jikin shi saye yake da wani wando mai laushi iya gwaiwan shi kamar three quarter da rigan shi mai kama da dinkin banga na maza. Sau daya na daga kai na na kalle shi na dukar da kai kasa inda nake zaune a dan stoll din mirror yazo ya zauna tare tare da kura min ido. Muryan shi naji yana fadin tashi muje mu kwanta tunda ke baki san abinda ya dace mace taiwa mijin ta ba sai an fada maki. Na dan bata fuska tare da turo bakina nace ni anan zan kwanta murmushi naji yayi tare da riko min hannuwa na ya mikar dani tsaye. Look at me yace, sai na dan dago kaina kadan na kalle shi amma ban iya jure kallon shi ido da ido dole na dukar da kan nawa, kasa. Yace daga yau ban son sai na kara biyu ki a dakin ki don ko zo guri na ke baki san right din ki ba ne a gare ni. To bari kiji bazan biya kudin sadaki na ya tafi a banza ba ni ina gabas kina yanma kudi nabiya dole kuma a bani hakkina. Jin abinda yace yasa ni watso mashi harara au harara na ma ki keyi ko ba biya nayi ba ne ? Cak ya daukeni kamar ya dauki babyn roba sai dakin shi ya dire ni saman gadon shi yana cewa this where you support to belong every night. Rankwafo wa yayi tare da raba hannaye shi yasani tsakiyan shi kokari yake sai mun hada ido dashi amma na kasa lumshe idanuwa na nayi. Yayin da naji yafara canza min sallon wasan shi a hankali yafara bin sassan jikina da wani irin romacig. Tun ina iya daurewa har na fara dan nishi, kadan kadan cikin neman agaji sosai yake gwada min wani irin mahaukacin kauna wanda ni kaina ban iya cewa ga inda nake a lokacin. Mun dauki tsawon lokaci dashi sai da ya gaji dan kan shi ya sarara min tare da rugumay ni a jikin shi yana sauke numfashi a hankali. Al,amarin yau da dan sauki bisa ga daren farkon mu dashi don banyi mugun jikita irin na wancan ranan ba. Gaba dayan mu shiru mukayi kowa da abinda yake sakawa a zuciyar shi a lokacin. Ni dai tunane nakeyi anya kuwa zan iya da yaya sadauki ashe mutum haka bai da tausayin mace ko kadan. Ko dai dama haka yake ne wai yana mu,amula da wasu matan ne acan baya. Da sauri nai istigifari don ance zato zunubi ne koda ya zama gaskiya don haka nai saurin janye wanan tunanen a raina. Shiko tunane yakeyi wai dama ashe abinda Bashar ke ta fihintar dashi ke nan akan mace. Tabas yanzu ya yarda da zancen bashar da yake cewa dan hakin daka raina shike tsone ma ido ashe ni,ima da baiwane tattare da wannan yar kara mar yarinyar da ya raina a idon shi. Bai tsan mani a rayuwa zaa samu mace haka mai tarin ni,ima da baiwa ba irin na Fatima ba yarinyar da bai taba samun wani jindadin rayuwa ba irin wanda yake tsinta yanzu a jikin Fatima ba. A hankali ya kai hannun shi saman kaina naji yana shafa a hankali ban san lokacin da na saukw wani irin ajiyan zuciya ba mai karfi. Ji nayi yakira sunana a hankali yana fadin FATIMA na amsa a hankali da fadin naam . Sai naji ya rugumay kamar wani zai kwace mashi ni a lokacin yace. Don Allah ina son kiyi hakkuri da halina kizama mai dauriya acikin duk wani al,amari na zaman takewan mu nidake. Idan har kin min haka kin gama min komai bazan taba son na samu matsala ba daidai da rana daya da mahaifiya na koke don rayuwa a yanzu akwai akasi a cikin shi kala da kala. Shiru nayi ina sauraren shi, yayin da idanuwana suka ciko da hawaye wanda ba zan iya fadin ga dalilin zubowan su ba a gare ni. Kukane ya kubuce min jin yadda nake kuka yasa shi kara manna jikin shi sosai da nawa shi bai lalashe ni ba kuma bai iya furta komai ba . A haka barci ya daukeni ban san manayi barci ba sai dai dana falko nagani a saman chest din shi kwance nayi filo dashi. Gyara kwanciya na nayi dakyau abinda yasa shi dan motsawa ke nan ya kara jawoni zuwa jikin shi. Da safe da kyat na mike na nufi dakina can na gasa,jikina sosai da,ruwa masu zafi haka yasa na dan samu saukin ciwon jikin da nake ji dana tashi. Nai matukar mamaki kwarai da naga yaya yana sallah jam,i bai wuce shi duk asubahi sai naji fitan daga gidan zuwa masallacin uguwan sallah. Ya dawo daga motsa jiki ya samay ni tsaye ina hada table din cin abinci a cikin kunyan abinda ya faru a tsakanin mu daren jiya yasani dukar da idanuwa nakd gaishe shi da kwana. Ya kara so tare da dan rike ni daga bayan na yana cewa, ke baki gaji bane har kika tashi ki aiki haka mai yawa? Kunyan shi nake ji ban yi magana ba sai dan murmusawan da nayi nace yanzu zakaci abinci ne? Ba abinci nake son ci ba ke dai nake so yanzu ya bani amsa fuskan shi a daure tamau kamar ba wani magana yayi ba a lokacin. Da sauri na kalli agogon ban gon dake falon sai na ji ya furzi iska yace zan makarar dake ke nan kike nufi ko? Ya juya ya fara tafiya yana ffadin ok a dawo lafiya sai dai kafin ki dawo zan kai musa school din su sai kuyi sallama dashi. Daga haka ya shige dakin shi ya barni gur8n tsaye koda na shirya nashiga yi mashi sallama na samu ya shiga wanka a lokacin. Don haka na cire mai kaya daga cikin wardrobe din shi haka zai sa yagane na shigo dakin na juya nafita da sauri don na kusa makara ranan. Bayan yafito kayan da ya samu na fitar ma saman gado don yasa yasa shi gane cewa na shigo dakin a lokacin sai daya gama shirin shi yafitone musa ke fada mashi nace na tafi don na makara yau. Yana gamawa dama musa duk ya kagu su wuce don haka,basu bata lokaci ba suka fita zuwa school din da za,a kai shi na kwana. ****** ********* ****** Haka muka kasance da yaya kullun a tare muke kwana dashi yana yadda yaso dani tun ina jin nauyi da kunyan shi har na dan fara rage kunyashi da nakeyi sosai. Yanzu yakai basai yace nazo dakin ba don kaina nake shiryawa naje don ma inhar banje ba shida kanshine zaizo ya dauke ni cak yatafi dani. Ya gama binda yake ya koma gefe daya yana sauke numfashi a hankali tare da furzo iska daga bakin shi. A raina nace wai dama maza basu da kunyane haka wai kamar ba shine mutumin da ke ta cika bakin shi ba abaya akan dole ne maji ta lakaka mashini. Yanzun gashi shine harda wasu irin kalamai da ina ganin ba a hayacin shi yake fadar su ba idan mun kasance a dukule tare. Idan kuma weekend ne zan iya cewa kusan a tare muke zama muyi shi agidan bai son fita nan da can yana nan ciki ya hanani shakat a gidan sai yayi yadda ranshi ke so zai sarara,min. Watan shi daya cur a garin da dawowa bai fita zuwa koda Abuja bane yanan cikin gari. Ranan ya shigo da yamma yake ce min na shirya zamu fita zuwa gida mu gaida su baba don baba bai jin dadi jikin shi ya tashi. Na dan rude ina fadin subbahanallahi may kuma ya faru da,baba ni dai Allah yasa ba wani mugun abin aka aikata ba har ciwon shi ya tashi. Tun karfe bakwai na fara shiryawa na saka wani atamfan super exclusive, mai ruwan yellow da zanen ganye kore zani da rigane sai gyalen da na yafa karo na farko a gidan aure na. Takalma da handbag duk na fitar da zan saka sai wani irin mayen kamshi dake tashi ajikina na dade ina bata lokaci gurin gyara jikina kamar wacce zata gidan wani shugaban kasa. Nasan idan na samu matsala ga shigana ba su Umma da mama ba har Amira sai na samu musguna daga gare ta. Sai gashi ya shigo dakin yana wani kamshi dashi yai mugun haduwa don shadda ce gezenah a jikin dark blue sai wani maiko da yauki takeyi har hulla sai da ya saka yau nace dankari a raina wani abu ko sai mahaifa. Yadda yake kallon shigana nima haka nake satan kallin nashi shigan don duk wanda ta fan mu komai bakin cikin mutum dole ya kyasa muna. Karasowa yayi har inda nake zaune a gaban mirror ya kura min ido can naji ya numfasa yace wai ke ashe haka kike dama kike ta faman boye kanki cikin mugun hujjib kullun kamar wata munafuka can. Nace ai dama sunana ke na a bakin ka kuma boyewan danakeyi ai ba kaina naiwa hakan ba don da baka samay ni ba kai. Namike ina cewa dama nasani na dinga kwalliya irin na anty Nafisa tunda shina ga yafi burge mutane yanzu. Yace dako na halakaki tun lokacin don ba zaki jawa maji zagi ba, nace ai naga shine ra,ayin ku ku. Murmushi yayi tare da kamoni yana mikar dani tsaye yace ki tabbatar da kin rufe min wanan jikin naki da kyau don kinsa akwai kardawa a gidan . Yayyen nawa ne kuma gardawa ashe kardawan yawa gare su bamu sani ba masu kalle surar kannen su . Yagane maganata sai yai murmushi kawai yace ai ban kalle ba sai dai ina shirin kallo don gada wani ya bani labarin abinda ban sani ba nida abina. Da sauri na dago kaina nace may kake nufi da hakan ya wani lumshe idon tare da furzo iska yace ma,ana har yau ban san komai ba akan matata da rana ganin dare kawai nake mata koshi ma a,wahalce ga cizo ga yakusa da zagi. Murmushi nayi na dukar da kaina kawai don natuna first night din mu dashi yadda naitakiran shi azzalumi macuci mazina ci kawai. Isan kin shirya sai ki tashi mu tafi kada ki bata muna lokaci don ina da abinyi ni idan mun dawo don ba wani dadewa zamuyi ba can. Kallon mararaicewa naimashi nace tare da turo baki, ni wallahi kullun abu kullun abu ba tausayawa mutum. Yace wani abu kuma cikin kasheni da idanuwan shi don son jin amsa na. Banyi magana ba sai gyalena da ke tashin kamshi kawai dana yafa akaina nan na kara fitowa wata shar dani nai marukar kyau har ya kasa dauke idon shi akaina. Yarinya ke kikace kina so dabakice kina so ba da ba,abaki ni ba, yasani gaba muna tafiya yana min waka a baya na. Wata landdrove jeep nagani a waje dark blue sai shaki takeyi van san da ita,ba a gidan sai wanan lokaci ko ba afada nasan ansha miliyoyi a waban gurin . Ita muka shiga shike driving kamar bai son tukin motan nace amma ya kamata mu dan sayi wani abinda zamu shigawa baba da su Umma dashi kada mu je masu hannu a sake. Kamar baiji mai nake cewa ba yai banza dani a raina nace bahagon mutum kawai wanda ba,a gane kallan shi kaman ba shine yanzu yake min waka ba gashi mintina kadan ya wani sha toka ya murde fusaka tamau dashi. Gaban wani katon shago ya tsayar da motar shi sai da ya kashe motan ya juyo yana ce min fito mu tafi. Har mun fara tafiya yace gyara rufe jikin ki dak yau don kinga an fara binki da kallo kiyi shiga kamar wata budurwa can. Gyara tsayin gyalena nayi da kyau tare da bin bayan shi munyi sayayya sosai a shagon har sai da nai mamaki leda kusan bakwai akayo muna muka nufo gida dasu. Ina ganin get din gidan nai wani lumshe idanuwana don jin dadin ganina a gidan da nai rabin rayuwana a cikin shi cikin jin dadi. Muna fita gab da zamu shiga gidan sai naji ya riko min hannu na kallon hashi nayi ba tare da ya kalle ni ba yace eh haka nake son maman ki ta ganmu don tasan na rike mata amana. A haka muka shiga gidan mun fara cin karo da yaya Abdul yace tun daga nesa a,a,a Allah yayi hadi a gurin nan sai kace kuka hallici kan ku haka. Murmushi ya sauke kawai tare da kara rike min hannu da kya yaya Abdul yace kaga zabe gaskiya kan nan ba irin wa yancan da suka zabo mata ba kamar suna barci. Muna shiga cikin gida Rukaiyya diyar mama Asiya tana waje tsaye tana waya tana ganin mu ta wani watso muna idanuwan ta gaba daya a kan mu. Dakin maji yace a fara shiga da kayan bayan ya cire wasu leda guda uku daga cikin ledojin da,muka shigo dasu yace min a hankali kiba wa su Umma kowa guda guda nace angode. Dakin Umma muka faea zuwa tana zaune da yaran ta sai jin sallaman mu tayi har mun kawo kofan shiga ko duk sai ta daburce da ganin mu. Zama yayi kan kushi na zauna kasan carpet daidai kafan shi muna gaida ita . Cikin hali irin nata na shan kamshi take amsa muna kallo daya tai muna wani mugun hassada da bakin ciki ya darsu a zuciyar ta tace kina nan kina ta hakkuri da halin mijin naki ko don ba fasawa zaiyi ba na sani. Murmushi kawai mukai mata don duk mun fahinci nufita amma muka kyale ta Bamu dade ba muka mike na karasa gaban ta ina cewa mama ga wanan ba yawa dan tsara bane ta amsa a wullakance tana tabe baki tana fadin angode. Na juya har na fara rafiya sai najuyo ina cewa yaya sagir fa idon ta nagani tana kallin kasan zanina da harara tabini ta tabe baki tace yafita dazun nan. Dakin mama Asiya kuwa muna shiga dama Rukaiyya ta riga data fadawa mamata zuwan mu ko da ta gan mu. Idon kyam a kaina yadda mukayi dakin mama haka mukayi a dakin ta bamu dade ba mukafito namika mata ledan tace to har da wani tsaraba can to angode. A daiyi ta hakkuri don kin san abinda kika aura dama don haka sai a daure da hakan . Muna barin gurin sai dakin mummy sai dai a rufe dakin yake yaran ta dai ne kawai a ciki alaman tana dakin baba a lokacin. Yaran suka yo kanmu suna muna sannu da zuwa cikin rugumay mu Imirah yace yaya nace mummy takai mu gidan ka tace wai zamu damay ka kana hutawa . Muma yaya kazo ka kaimu mu huta tare da kai kaji, ya shakan shi yace zanzo na dauke ku. Yaran sukaji dadi suna ta murna yayan su yace zaizo ya dauke su zuwa gidan shi namika masu ledan tsaraban su wanda daban yake saboda akwai alawan yara acikin shi. Sai dakin mama muka nufa kuma suna falo zaune da Amira muka shiga da sallama ina rike a hannun shi kamar wata yar yarinya can dani. Sannu ku da zuwa mama tai muna Amira tana dago ido kallo daya tai muna naga tai sauri kawar da kan ta gefe daya tana cewa sannu da zuwa yaya. Nace anty ina wuni ta ansa a wulakance da lafia kawai ta juya kan ta ya kalle ta yai murmushi yace sister ke nan yaya gidan gaban mama na tafi na durkusa a gaban ta nace mama ina wuni ? Cikin jin dadi da ganin mu haka tace ashe kuna tafe ne yanzun tashi ki zauna Fatima kinji Allah yai maku albarka ai yanzu yaro yashigo da leda yake cewa kune kuka shigo. Sadauki yace maji yaya na barku dazun haka yasa nagane cewa yashigo da rana ashe nice dai yakawo nagaida Baba da jiki ashe. Mama tace mai lafiya muke yace to yaya jikin na baba tace a,a Alhamdullahi ai ya samu sauki sosai har ya tashi yayi sallah ko dazun. Ta juyo gareni tana cewa Fatima kuna lafiya ko cikin jin kunya nake cewa lafiya kalau muke mama. Tace ashe musa an tafi makaran ta saiga babana yazo dashi ya sallamay ni ranan . Cikin jin kuya nai murmushi tare dukar da kaina kawai nace wallahi mama yaya ne yai mashi wanan kokari kuma yasaya mai komai da zai bukata acan . Sai a taya mu godiya gurin shi mama tace ince maki sun gode kwarai Allah ya saka da alheri. Mama tace kai haba waban ai yiwa kaine kawai wa yasan abinda zai zama watarana kuma in Allah ya raya abinshi. Kina dai waya da su ko don ki dinga jin lafiyan su akai,akai don haka na dakyau. Gurin da Amira take zaune ya koma ya zauna saman hannun kujera yana cewa may kikeyi ne wai kin wani fuskewa mutane haka. Tace cikin da yake yaya kawai dai hakanaji ashe zaka dawo yace eh waccan nakawo ta gaida baba da jikin shi don dazun ya tambaye ta. Hummm wanan muba fukar matar taka ai ta iya sace zuciyar kowa da makircin ta harda ma wanda bamu zata ba duk ta sace munafuka kawai. Kai Amira Fatima ce kuma muna fuka munafuncin may taimaki kuma haka ne wai . Sai lokacin ta dago kai tace humm yayya ni wallahi mamaki ma kake bani yanzu dan ban yarda amma yau na shedawa idanuna gaskiyan zargina. Yanzu kai yaya har ka iya fito da wanan a gari a matsayin wau matar ka har kana wani jerawa da ita, kamar wata mai mukami can. Kasa kasa suke maganan su amma duk zancen su ni yana a kunne na don ina dan kusa dasu mama ce kawai bazata ji ba a lokacin don ita sai farin ciki da murna takeyi tagan mu a cikin farin ciki a tare. Can ya mike don ba zai jure sauraren Amiraba don tana bakanta mashi rai da zancen ta gap yake da ya dauki matakin da bata zata ba a lokaci guda. Idan nake a zaune ya kallo yana cewa taso muje gurin baba ki dauko wancan ledan muje mashi dashi. Yana gaba ina bayan shi muka tsaya daga kofan falon baba muna mashi sallama. Aka ansa muna muryan mamane take ce muna mu shigo ganin mu tare yasa baba dake a kishigide ya dan dago zaune cikin fara a yake cewa,aa Fatima tare kuke ashe? Har gaban baba naje na duka ina gaida shi shima a kasa yaa zauna kamar yadda na zauna yana gaisawa da Baba din tare da tambayan shi karfin jikin shi. Mun dan jima zaune suna hira da baba da mummy ni dai kaina a duke banyi magana ba. Sai can baba yace sadauki gaskiya nayi farin ciki kwarai da ganin ka haka ji yadda ka kara murjewa nasan wanan duk aikin diyata Fatima ce don tasan abinda ya dace. Ba kamar matar wanan mahaukacin ba da tazo gaidani dazun kaga nan yana taba kujeran gefen shi yace a nan ta zauna wallahi. Baba yace wanan irin abubuwan dole su jefa mutum a cikin damuwa yau ace irin tarbiyan da na,baku a gidan nan amma a cikin zuria ta ake samun irin haka. Sai yai shiru tare da girgiza kan shi can yace wallahi yaran nan suna kashe min zuciya. Baba kayi hakkuri ka daina sa irin abubuwan nan a ranka kaga ba lafiyane a jikin naka bba yanzu. Nan dai baba ya kara dan muna nasiha mukai masu sallama don dare ya somayi sosai. Mun koma dakin mama mukai mata sallama tana ta saka muna albarka muka fito daga gidan. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,, IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH YAR UWA,,,, A LOKACIN MUKE,,,, Yau ya shirya unexpected ya samay ni daki bayan na dawo daga school yakw ce min zaiyi tafiya ne zuwa Mexico gurin wani taron yar kwallo da za,ayi kuma yana cikin wa yan da aka gaiytata su tafi taron. Shiru nayi sai jin zuciyana kawai nayi ba dadi ban san har hakan ya fito a fuskana ba saida naji yana fadin baki son in tafi ke nan don engine din ko? Ban fahinci may yake nufi ba da gakan cikin mamaki na dago kaina nake tambayan shi engine kuma ? Yace eh mana ko karya nake yanzun ba kullun kike bukatan service ba na fahinci may yake nufi yanzu don haka najuya baya ina fadin wallahi, ni kan Allah ya kiyayye min abinda ake min a dole zaka wani ce can wai na saba ko nafiso indon tani ce wallahi mu zauna a hakana mana aga wanda zai sha wahala cikin mu. Jinayi ya rugumoni ta baya yana fadin anki a zauna hakan sallon kijewa maman ki da kuka kice anki yi maki service kwana biyu kuma. Allah dai ya kiyayye min wallahi kai wanan ya dama ni bai a gabana wallahi yace to tsaya mugani idan bai gaban ki da gaske din. Gudu naje yi amma na makara nan ya samu sa,a na ya shiga aika min da sallon sakon shi. A cikin mamakina sai gashi na zake nima yau ina mayar mashi da martani yadda yake bukata. Mun dauki tsawon lokaci a dakin muna abu guda har sai da magariba ya kusanto sosai ya sarara min. Rugomo ni yayi zuwa jikin shi tare da dan sinsinan wuya na yana fadin zan dauki tsawon lokaci a wanan tafiyan da zan yi don haka ki kula min da kan ki please . Lumshe idanuwa na nayi ina sai dai a fili cewa nayi Allah ya kai lafiya ya bada sa,an tafiya. Mun dauki lokaci ba wanda ya iya yi wa dan uwa magana a cikin mu sai can yadan min peck goshina naga ya mike ya fita daga dakin. Maimakon na tashi daga kwancin ga lokacin sallah yayi amma sai kawai na lumshe idanuwa wani zurfafan tunane na shiga yi na yadda zan zauna kwana biyu bashi a gidan. Irin yadda muka dan saba da juna a yanzu dashi. Da kyat na iya mikewa na shiga bathroom don nai wanka nai sallah don har lokaci ya shige gashi takwasa zai tafi. Ina idar da sallah namike da sauri na nufi dakin shi na samay shi tsaye yana gyara aninin gaban rigar shi. Jin nashigo yasa shi dan juyowa gare ni cikin sakin fuska yau yake ce min ai na zata bazaki iya tasowo bane. Karasowa nayi nake ce mashi mai za,a shirya mane wai? Kinga ina tafiya da shirgine ni acan ina da kayan da nake amfani dasu ba sai na tafi da wani abuba daga nan. Miko min yar hand bag dina na rataya kawai natafi don bashar yace min gashi ya taso zuwa kaini airport. Na duka zan dauki jakar naji yana fadin wanan karon ma da Amira ke nan zaku zauna ko? Murmushi yake nayi na karaso gaban shi nace duk yadda kace haka za,ayi yace ok zan fadawa maji ta turo ta idan nafita. Ki dai dinga cin abinci ko zaki kara cikowa kafin na dawo nace idan haka bai maka ba sai ka karani mana. Murde bakina yayi yana fadin wanan bakin wai yaushe ne zai mutu da bakar magana ne bari dai Allah ya dawo dani lafiya nasan maganin ki ai. A tare muka fito falo dashi sai ga yaya Bashar ya shigo gidan nan muka gaisa dashi yana tambayana yaya kwana biyu. Dago kai yaya sadauki yayi yace min tau ni zan tafi ke nan sai na dawo Allah yakai lafiya Allah ya sa ai nasara ga abinda akaje nema Allah ya tsare muna kai ya dawo muna da kai lafiya. Yaji dadi matuka da addu,ana yake ce amin nagode bashar yace bakani dadin auren ba riba biyu mama tai maka ga kuma Fatima na sharto maka addua haka. Dan bugo yakai ma bashar daga haka suka fita daga gidan ina tsaye rakube daga kofan shigowa falon mu. Sai da naga subar haraban gidan najuya na shigo gida zuciyana a cunkushe min, fadawa nayi a saman kujera na dade zaune a guri, ina ta faman tunane kala kala ni kadai can dai ganin dare ya soma namike tare da rufo kofan gidan don ban tsan mani anty Amira zata shigo ba har wanan lokacin. Ina shiga daki naji wayan na yana ringin da sauri na isa gurin, da wayan take shi ya kirani na dauka a kasalance ina fadin Assalamu Alaikum. Yace wa alaikis sallam baki barci bane Fatima nace yanzun dai nake shirin yi. To may ya hanaki yin barcin har wanan lokaci sai nace a raina kaine mana ka hanani a fili kuma sai naji yace nine ko? Nace ni karatu na tsaya yi kawai shine ba makara don ina test da zamuyi satin nan insha Allahu Murmushi yayi yace to ki kwanta hakana ki huta don nasan kina da gajiya a tare dake. ****** ********* ****** Ya sauka lafiya don yana isa Abuja da safe suka daga sai Mexico gurin taron su. Yakira wayana kafin su tafi tana kashe ina cikin class ban samu magana da shi ba. Yinin daya da sadauki yayi batare da Fatima haka yayi shi a cikin tunanen ta. Sai a lokacin yake sanin cewa akwai wani babbban alamari a zaman ta kusa dashi ji yake tankar itace jagoran duk wani farin cikin rayuwan shi a halin yanzu. Bai samu lokacin kiran ta ba,sai da ya dawo masaukin shi a lokacin dare yayi a can. Yana kwance dakin shi saman gado tunane Fatima kawai ke cikin zuciyar shi har zuwa wanan lokacin. A nan ya fara tina abubuwan da sukai ta faruwa a tsakanin su abaya. Irin yadda yake yawan mata tsanani da hattaran ta cikin gidan su yana daukan ta a matsayin itace mai mashi gulma a gurin maji. Sai yanzun ne yake gane cewa bata fadawa maji komai a gamay dashi sai dai nata kokarin da takeyi gurin ganin cewa ta saka mai ido ya daina shaye shayen daya ke yi kawai. Wani irin bacin rai ne yaji sai yanzu yake gane cewa ashe son shi takeyi da,alheri take hakan gare shi. Yana jin ciwon irin abin da yai ta aikatawa yar mutane a baya a bisa gaskiyan ta. Haka yasa yamike ya fara dan zagaye dakin a hankali yana zargin kanshi da aikata abinda ba daidai ba akan Fatima din. Lalai dole ne ya gyara tsakanin shi da Fatima yadda zata fahince shi ta yadda zata daina mai kallon mugun da take mai koda yaushe. Yace in har bai gyara tsajanin su ba baiyi wa kan su adalci ba don haka zasu dinga zama suna samun matsala a tsakanin su ko yaushe. Gurin tagan dakin ya koma tare da budewa yana shakan fresh ai dake fitowa daga window. Ya daga wayan shi da ke a hannun shi ya kira nomban Fatima bugon farko da,wayan yayi sai da yaji wani iri a zuciyan shi . Ina hanya zan dawo gida naji wayana na ringing, hakali na dauka na duba yaya sadauki ne a layin. A hankali cikin wani murya bayan nayi receive din call din nace hello yaya. Ya dan rikice da jin muryana yana cewa Fatima kina inane haka naji dan hayaniya. Nan dan ajiyan zuciya sai nace ina hanyane yaya nafito school zan koma gida ne yanzu. Sai nace kana lafiya yaya yaya gajiyan hanya da taro sai da yai wani lunshe idon shi ya amsa da taro Alhamdullahi Fatima mun fara yau din nan. Allah ya bada sa,a nace mashi ya amsa da amin fatima. Yace kiyi tuki a hankali don nasan yanzu titi ya cika da motoci yamma yayi nace mai insha Allahu. Yace nakiraki ne naji muryan ki don na kira ki da safe wayan ki baya shiga. Nace ina class alokacin na rufe wayana ne ya sake cewa gashi na kasa barci sai naji muryan yar kauyen matata yaya zanyi da raina dole na kira ki naji ki don mu nan yanzu daryayi sosai . Nace shine kaki bari da safe ka kirani yace abinda ya dace ke nan nayi don na kasa samun natsuwa rashin jinki . Kwata kwata rashin jinki a tare dani ya hanani sukuni Fatima yaya zanyi dole ne na kiraki ai. Take zuciyana ya narke sai naji kamar na shige cikin wayan na isa inda yake din naga kyakyawan suran mijina da nai missing. Yaci gaba da cewa Fatima ina kewan bakar maganan ki ina kewan wanan fadan namu da muka kwana bamuyi shi ba. Murmushi nayi yace kin dauka ina wasa ne ko sai idan kinga nadawo maki don kawai muyi shi zaki gane. Nace a hankali ina murmushi haba yaya don fada kawai zaka dawo na rokeka kayi hamkuri ka zauna har kagama abi da yakai ka. Har nakai gida muna waya dashi inda na ke ce mai na iso gida sai da zanyi sallah mukai sallama dashi yakashe wayan. Wayan dake hannu na dan kalla na ce ikon Allah yau kuma mai ya samu yaya haka ne ya sauya min gaba daya. ****** ********* ****** Yau kwana yaya uku da,tafiya amma Amira shiru batazo ba tun ina saka rai da zuwan ta har nagaji na,fara fitar da rai ga zuwan ta gidan. Yaya da yakirani ya tambaye ni Amira bata zo bane nake ce mai bata iso ba tukun. Ranan Na dawo gida da yamma a gajiye neke a lokacin sai dai ina shigowa get din gidan na hango motan anty Amira a kofan gidan namu. Nashigo gidan da yar fara,a na a fuskana don ganin ta tazo tana zaune saman kujera tayi daidai da ita sai waya take yi abin ta. A sanyaye nai sallama ta dago kai ta kalleni a dan wullakace nace Anty sannu da zuwa. Hannu kawai ta daga min ba tare da ta amsa min ba taci gaba da wayan ta da takeyi. Ido nabi ga yadda ta kaca kaca da falon da yake a gyara tas kafin na wuce da safe. Ganun bata da niyan gama waya yasani na nufi daki na don rage kayan dake ajikina a lokacin. Sai d nai wanka nai sallah nafito falon har lokacin tana zaune a inda na samay ta da farko. Ina batun na zauna take cewa ke ina key din daki na yake na bude naga a rufe yake. Nace au yana gurina anty bari na dauko maki taja uban tsuki tana fadin don isa da sa.un guri zaki kulle ma mutane daki wai ke ga matar gida ko. Nace fita zanyi ai shiyasa na kulle ko ina na gidan kuma ma ban san kina tafe ba yau ai. Dalla Bintu ki dauko min key ni bani son yawan zuba haka kinji. Kallon mamaki nake mata nace yau kuma nice mai zuba anty ki dai gyara maganan ki. Au to abin har yakai kuma zaki min rashin kunyane Bintu ? Wanan ba halina bane anty kinfikowa kuma sanin hakan don ban tabayiwa kowa rashin kunya ba. Kai ta gyada tare da kutawa ta dauki jakar ta bayan na bata key din ta wuce zuwa ciki ran ta a bace. Kitchen dama a rufe yake na dauki abincin dana aje zanci idan na dawo tunda safe na shige daki da abina nace can nafito nasawa gidan key na shige abina na kwanta. Ban fito ba sai da safe na hada breakfast na bar gidan ko fitowa batayi ba tana dakin ta kwance. Bayan fita data gaji da barcin ta tafito ta zauna taci abincin da ta samu na aje mata. Inda taci anan tabar min kayan sai dana dawo na kwashe su na wanke na gyara gurin. Ban fito na girka na dare ba don a gajiye nake nashige kawai abina nai kwanciya na kawai. Amira tafito tasamu babu komai saman tabld din tai mamakin hakan ta nufi dakina lokacin ina bathroom ban maji tana buga kofan ba har tagaji ta,wuce. Tunda safe ina kitchen sai gata ta shigo daga kofa taja ta tsaya tace ke Bintu wai may kike daukan kanki ne halan. Nace namay kuma anty? May ya hana jiya ki girka muna abinci da kika dawo ki ka barni da yunwa na kwana. Nace kiyi hakkuri anty wallahi na gajine jiya sosai kuma ga yamma yayi dana dawo. Eyye samun guri ke nan ke ashe har kinga gurin hutu ke nan to wallahi ki kama kanki da ni. Murmushi nayi kawai naci gaba da aiki har ta fara tafiya ta juyo ki girka abinci dasu salma don sunce anan zasuyi breakfast yau. Yadda tace haka nayi mata na sauri na fita yadda na dawo daga gajiya da yamma haka na samu gidan sai da raina ya baci. Ban fito ba haka nabar falon sai da safe na tashi na shiga gyaran gidan sai da nai ko ina tas har bayin falo duk sun bata shi . Sai na dora muna girkin rana ina tsaka da yine sai ga Anty tafito ta ce yau ma su salma sunce a nan zasu wuni kiyi girki dasu. Ina gama muna girkin na koma dakina na kwanta can na fara jin hayanin yan su har da yan ihun su. Nace yau kuma din nan wai may ke damun anty Amira haka tana son bata rayuwan ta. Ki fito ki gaida su salma naji muryan Amira daga sama ina kwance na dago ina kallon ta kawai. Kamar bazan fito ba sai dai na mike na fito da fara,ana a fuskana nake ce masu sannun ku da zuwa. A lalace cikin kallon banza suka amsa min banji dadin haka ba amna na dake na dan samu guri daga gefe na zauna. Sai naji dayar na cewa wai ashe musty ya auro wata gajar matace can yar kauye da ita. Ke haba inji saura tace wallahi ko kada kiso ki ganta ga gida ga komai ya hada amma ina ba matar gwadawa tsara don bakauya ce wallahi. Sai Amira tace anyi biyu ke nan muma ga.unan da irin matsalan ai a gidan mu kin san yan kauyen nan su iya bakin asiri su mallake miji. Yanzu bari ki gani kwana biyu idan an aaruce shi zakiga ya fara wani bakin rawan kafa bai jin kunyan kowa akan ta. Nagane maganan ta shagube ne amma sai na dake suna sako min magana ina jin su. Bai mata ba sai cewa tayi ke Bintu kwashe kayan nan ki girka muna indomie kubura zataci tace. Kallon mamaki nai mata may anty ta mayar danine yar aiki ko may wai ? Ina gama kwashe kayan sai dana wanke su na,shiga daki in fito sai naga wace tace wa Kubura dauke da cup din tambulan yaya da nake mashi amfani dashi tana shan drinks a cikin. Kamar na wuce sai na dawo nace anty da kun canza cups don wanan din na amdmfanin yaya ne shi. What Bintu may kike nufi lalai ma Bintu kin kai wuyan ki ya isa yanka ashe ? To baza ,a mayar ba sai kiyi abinda zakiyi don an dauki cups din yaya ko sannu mai yaya. May kike gurin yaya din ke nace mata a daure mata mana mai miji kuwa. O lalai naga alama tunda har kin fara bani ansa to baza a mayar ba din tunda daga gidan ku kikazo da shi. Nace may yai zafi haka anty harda giri da zagin gidan mu kuma haka ? An zaga ko zaki ramane ki nuna min wuyanki yai kauri yanzu. Nace bazan rama ba amma koda banzo dashi daga gidan mu ba nawane dai ke ma sai ki jira naki. Aiko sai saura sukacs iyye gorin aure kuma zaki mata Bintu don ke kin samu an maki auren hadi ko ? Nace au haka ta fada maku ashe idan yin hadi banza ne wasu suje ai masu mana mugani. Na bada amsa haka sai na juya zan wuce ji nayi an finciko ni ta baya sai kawai naji mari kyauuu. Cikin mamaki na dafe kumcina da ta mara nace anty abin har da duka kuma sai sauran na fadi kyale ta please kada ta kulla maki shiri kin san su da sheri irin matan nan. Banyi magana ba na juya kawai idona tab da hawaye na,shigd daki ina mamakin wanan irin cin zarafin da Amira tai min a gaban kawayen ta haka. Kiran yaya sadauki ne yashigo min yake kirana na dauki wayan bayan na goge fuskana. Na amsa mashi sallama da sauri naji yace Fatima may ya samay ki ko baki da lafiya ne. Na daure nace may ka gani babu komai yace please nace may ke damun ki ne wai ba komai nace mashi. Baiyarda ba sai dai kawai ya kyaleni tunda nace mai babu komai ina daga kwance nake tunane dole na dage na futar da kawaici na fara gwadawa Amira nima na iya. Bayan kaman awa daya sai gata bazaki dafa abinda nace maki kubura tana so bane ko may ? Ban bata ansa ba na kyale ta haka suka gaji da zaman su har suka bargidan. Da safe ma washe gari haka na gyara gidan tea na hada nasha na koma na kwanta abina. Can cikin barci naji takai min maka a baya da gigin barci na falka ina kallon ta. Bazaki muna abin karyawa bane yau gashi har sha daya da,wani abu na rana. Nace bazanyi ba . Bazakiyi ba fa kika s tsuki nayi na koma na kwanta abina sai ji nayi ta nufo zata kara kai min maka na dago ido waje nace kada ki soma kara tabani don zan rama. Ko dazun ma arziki kikayi a gaban kawayen kine kada ki matsayi yata na disgaki a gaban su shiyasa na barki. Yadda taga na nuna tasan za,a samu matsala sai ta juya tana fada tafice daga dakin. Tana fita wayan yaya sadauki takira tana fada mai wai na hana mata abinci taci. Yace ina ganin bata jin dadin jikin ta nd don tun jiya nake jin ta hakana. Tace shiyasa ban son zusa gidan nan wallahi sai yarinya tai batun raina maka wayon , Kashe wayan yayi yana mamakin iri wanan hali haka da ta sakd lokaci guda. Tun daga wanan rana ban kara girka komai ba koma nayi iya cikina nake girkawa naci ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,, A LOKACIN MU KE,,,, Tashin hankali a gidan su sadauki haka aka kai dare a cikin shi sai da kyat ya shiga dakin ya lalashi Nafisa dake ta faman hauka aka samu tai barci bayan irin tonon asirin da take zubawa umma da mama kawai tana kiran su da munafakai masu bin boka da malam. Haka ya dawo gida ranan rashi a bace ina daki naji shigowan shi musalin takwas da aani abu na dare. Nafito daga dakina saye cikin wasu kananan kayan da ya sawo min a cikin tsaraban daya zo min dashi. Ina fitowa ya sako min mayan idanuwan shi har sai da naji kunyan hakan da yai min din. Sannu da zuwa nai mashi idon shi na akaina ga damuwa karara a duskan shi. Gefen hannun kujeran da yake zaune akai na zauna tare da cewa yayana may kuma ya faru ne naga kamar kana cikin damuwa. Murmushi yayi a fili amma a zuciyar mamaki yake yadda nake saurin fahintar halin da yake ciki ko yaushe. Yace ba komai Fatima dan matsalane kawai aka samu a gida da sauri nace subbahanallahi injin bada mama ba. Yai murmushi ya jawoni zuwa jikin shi yana cewa don mamace kadai taki a gidan ko ? Nace cikin murmushi ba hakana bane yaya ban dai son ace wani abu ya samu mama din ne kawai. Yace yana sauke numfashi, Umma ce dai da Nafisa kawai ta dan shawo ne tazo gida tana hauka har ta jin ma umma din ciwo a kafan ta. Nace innalillahi wa inna alaihim rajjiun Allah yai muna sauki wanan al,amarin kawai. Oo ita anty Nafisa bata da ranan gyara rayuwan ta ne wai bata ganin cewa ita mace al,amarinta daban yake dana maza. Ajiyan zuciya naji yayi yace zan samu lokaci ai na zauna da ita don na dan fahintar da ita ko Allah zaisa ta gyara halin ta amma gaskiya abin baiyi ba wallahi. Allah ya kyauta nace tare da numfasawa na fara tunanen aanan halin rayuwan na shaye shaye gamu da acikin ta don ban sani ba ko wani hali shi mutumin nawa yake yanzu ko ya daina ko yana ciki tsunbul. Jinayi yaja min hanci na shiyasa na sake sauke numfashi ji nayi yace kina tunanen naki mijin ko? Murmushi nayi nace aini nawa mijin Allah ya,kawo mai sauki da sauyi a rayuwan shi Nafisa dai nake tausayawa kawai da sauran al,umma masu hali irin nata. Idan kin gama tunanen ki nima sai ki taimaka min da dan ruwan wanka na watsa ko zanji dadin jikina. Mikewa nayi sai naji ya kara jawoni na koma jikin nashi yake cewa amma fa zaki cika ladan ki don ke ce zaki min wankan don banjin lakkan yin da kaina ko kadan. Da sauri na dan juyo ina kallon shi sai yake cewa eh haka na fadi ko baki ji ba nace amma yaya gaskiya sai kuma nai shiru yace to shike nan barni hakana na kwana da dauda. Jin abinda ya fadi yasa jikina yai sanyi hakka na mike na nufi dakin nashi murmyshi ya sake tare da bin bayana da kallo kawai. Sai da na hada ruwan wankan na aje brush din dana matsawa maclean da soso da sabulun wankan shi na fito daga bayin. Yana zaune a ida na barshi a falon na ce a sanyaye na hada yaya yace ok sai naga ya miko min hannayen shi alaman na kama shi ya daga ke nan. Murmushi nayi nace ni ina zan iya tayar da kato dan kwallo haka kulun cikin motsa jiki. Dariya nabashi ya kara mika hannayen shi inda nima na kama hannayen nashi na mikar dashi din kamar yadda ya bukata din gare ni. Amma kuma kamar ina daga dutse gashi na saka duk karfina na dago shi amma na kasa jawoni yayi na fada a jikin shi tsab ya mike tsaye dani a hannayen shi. Bai dire dani ko ina ba sai tsakiyan dakin shi kawai ya tsaye kimkam yace sai ki fara aikin ko? Kallon shi nayi yace uhumm bissimilah ki cire min kaya ko ? Kallon shi nayi fuskan shi a daure dole na fara kokarin cire mashi rigan dake jikin shi. Nakai ga wandon shi ina kokarin cire ina kawar da kaina a gefe tsaya yake kimkam dashi sai murmushin abinda yaga ina yi na kawar da kaina gefe daya. Ina na cire wandon na kara dukar da kaina kasa, ashe akwai wani gajeren wandon maza daga ciki jin bai motsa ba yasani dan dago kaina. Kai ya gyada min tare da kashe min ido alaman saura wanda ya rage daga ciki din . A hankali kaina a duke na karasa cire mai wandon sai naji ya sauke ajiyan zuciya da sauri na mike na nufi inda towel yake na dauko ina mika mashi tare da kawar da kaina gefe daya. Hannu naji yariko da kyat na iya dago kai tare da juyowa na dan kalle shi kai ya gyada min alaman bai bukatan towel din yau. Nashiga uku na furta a raina ashe har a fili na fadi hakan ban sani ba sai naji yace akan may kika shiga uku fatima ko rabi ban bari ki shiga balle har uku. Muje kiyi min wanka please da sauri na shige gaba tana bina a bayana sai faman kawar da kai kawai nakeyi gefe daya don ban son dago kai na kalle shi, don wani irin mugun kunyan da nake ji a lokacin. Zama yayi a cikin bahon ruwan inda na fara yi mashi brush sai na hau yi mashi wankan idona a rufe har muka gama muka fito. Dan towel na dauka ina goge mai jiki dashi sai faman lumshe idanuwan shi kawai yakeyi a lokacin. Kayan da zai saka na dauko mai wani dan riga daga cikin kayan barcin shi sai wando gajere don nasan ba zai fita zuwa ko ina ba kuma. Falo muka dawo ya ci abincin shi da ya kare ya koma saman kujera two seater ya zauna ni kuma na kama kwashe kayan nagyara ko ina tsab. Inda yake a zaune na dawo na zauna a dayan kujeran dake daga gefen shi waya yake amma sai ya yafito ni da hannu alaman na dawo gare shi. Abin da ya buka ta nayi inda na dawo daga gaban shi na zauna a hankali ya fara kai hanayen shi saman jikina yana aiwatar da wasu abubuwa can na ma,aurata. Tun ina lumshw idanuwana har nima na dan fara mayar mai da martanin abinda yake, min nan muka shagalar da junan mu a falon . Lokaci mai tsawo muka dauka a hakan cikin wani irin yanayi mai shagalar da mutun a inda yake. Sai da ya tabbatar da kowan mu ya gamsu da dan uwa sannan ya sarara min. Dakina na koma nai wanka na gyara jikina tare da saka rigan barci na na nufi dakin shi don nasan dai duk wani abinda zaiyi a ranan yariga yayi shi a falo ko sai dai kawai mu kwanta kawai mu huta. Shima dai na samu yayi wanka ya kwanta a hankali na hawo gadon ta bayan shi tare da rugoma shi daga bayan shi. Murmushi naji yayi tare da juyowa gare ni yana jawoni jikin shi nai mamaki dana ji kan shi da bakin shi a saman kirjina again. Sai da gabana ya fadi nan ya shagala a saman kirjina tun ina rutse idanuwana har yakai nima ina jin dadin abinda yake min. Sosai muka tsotse junan mu a karshe ta shigeni yadda ranshi ke so sai barci mai nauyi yai gaba damu. Washe gari bamu tashi da wuri ba sai after nine na safe don haka mukai sallah a makare . Ya ce kada na girka komai na koma na kwanta idan mun tashi zaifita ya samo muna abin karyawa. Nan muka koma barci sai to one muka tashi wanka kowan mu yayi lokacin duk muna bukatan abinci. Nafito falo naji ana sallama na nufi kofa naga ko waye yaya Bashar ne tafe dauke basket dauke da abinci daga gurin maryam. Nai sauri na karba ina gaishe shi tare da bashi hanya ya shigo ciki lokacin sadauki ya fito daga daki shar dashi kayan da yasa sunyi matukar yi mashi kyau sosai. Nan suka zauna suna hira na nufi dining da kayan na fara had gurin yadda ya kamata bayan na bude ne naga tuwo semo ne da miyan yauki. Nace mai ga abincin can na hada mashi, a dining yace ok bari na dan ci abinci bassh. Yace bari dai naje gida nima jirana ake muci nafito zuwa gurin ka kasan maryam yanzun ba ita kadai bace. Ita da waye ya tambaye shi yace a anfada maka ni irin kane raggo sai iya jefa kwallo fa raga kawai amma ba ka iya jefa shi inda ya dace a jefashi ya shige. Dariya yayi tare da kaimai nashi ya gwauce mashi yana fadin baka da kunya,wallahi wai ka manta cewa ni surukin ka ne. Har zai fita yace kuna ko da labarin Umma bata da lafiya idan kaje ka fada mata please. May kuma ya samay ya tambaya cikin son ji hankalin shi a tashe ya bata fuskan shi yace kawai dai dan matsalane ita da Nafisa shine ta gwauce kafan ta. Yace mashayiyar ta shawo ke nan tazo tana hauka a gida ko yace raban ma acan na gane ta ta bugu a hanya duk dan taxes din ta tsare sai yaki tsayawa ni na daukota zuwa gida tana min tanbele a hanya. Yafita yana maijin haushin halin rayuwa irin na Nafisa da ta jefa kan ta a ciki yanzu. Sai wani dukar da kaina keyi don balain nauyin shi da kuyan shi nakeji yau din sam ban iya hada idona dashi. Can yace ke na ce naam yace dago idon ki ki dube ni nan da kyat na iya daga kaina kalleshi sai nai saurin dukar da kaina kasa kawai. Murmushi yayi yace wai wanan kunyan na may ye kuma haka ko abin bai sheki bane na kara maimata maki fiye dana jiyan ko? Da sauri nace don Allah dai yaya kayi hakkuri kawai dai ban san yadda zan kalle ka bane dai. Ok yanzu zan kawar da kunyan nan ai daga yau bazaki kara jin shi ba aiko da gudu na kwasa sai cikin dakina harda saka key na rufe daga ciki. ****** ********* ****** Kaya irin na marasa lafiya muka saye sai gidan su mama kwana biyu ke nan da faruwan abin amma kafan ya hau yai sundum dashi. Tana ganin mu duk da nishin da takeyi amma bai hanata daure fuskan ta ba a lokacin. Mun gaida ita tare da mata yaya jiki cikin daure fuska ta amsa muna Allah ya sauwaka nai mata tare da mika kayan gaisuwan da muka zo mata dashi. Na mike na fita na barshi a dakin nasu dakin mummy na shiga na gaida ita na fito zuwa dakin mu. Ina fita a dakin umma yaya sadauki yace ina Nafisa take ne wai ? Umma bata amsa mashi ba sai sagir ne yace mahaukaciya tana ciki mana yar iska kawai. Kira min ita yace wa sagir din nan ya mike ya shiga har dakin Nafisa yace tazo yaya sadauki na magana da ita. Tafito jikin ta babu ko riga tace cikin wani yamuste fuska yaya sadauki ina wuni ya amsa mata cikin girgiza kai tare da tausaya mata. Yace Nafisa ina son ganin ki don Allah gobe a gida na idan babu damuwa. Tace ina ne gidan naka nema wai ? Yai mamaki da wai batasan ma gidan shi ba yace sagir zai kawo ki idan kin tashi goben. Tace kai tsaye niba zan shiga mota dashi ba ya illanta ni ga banza kawai mugune kagan shi nan wallahi yaya . Tausayi tabashi don abin ya fara taba ta sosai dole ne a taimaka mata. Ya mike yana fafin kada ki manta please sai nagan ki ko ya ciro kudi ga aljihun shi yana mika mata yace ga kudin mota ko idan zakizo. Sagir yace kada ka bata yaya wallahi wanan shegiyar maye zata sha dashi don dama shi take nema kaga ta lafa a gida tana neman na wanda zata ware dashi idan mai shi yai sakaci. Yace ka barta dasu ai zata zo din kasan Nafisa akwai cika alkawari tace nagode babban yaya irinka muke so ko yaushe ba masu hana abamu ba. Amira ce kawai a falon lokacin mama tana daga ciki na gaida ita tare da mata yaya kwana biyu. Banza tayi dani kamar bata san ina gurin ba ma a lokacin sai wayan ta kawai take dakila a hankali a lokacin. Nace anty har yanzu kina kallon film din queen of south ko kin daina ne don shirin yai nisa sosai. Ke Bintu kikama kanki dani wallahi don idan kikai min tsiya yanzu na lahira zaifiki jin dadi wallahi ko. Haba anty daga tambaya kuma shine laifi Allah ya baki hakkuri nacs mata sai ko ta dago da nufin kai min duka ji tayi daga kofa yace kada ki soma wallahi yanzu zan bata maki rai sosai wallahi. Yar kice koko kaunan ki da duk lokacin da kikaga dama zaki dinga dukata son ranki. Duka kuma dukan wa kuma wai ban fahinci may kuke magana ba akai wa ake duka ne wai ? Bai fasa magana ba yace kin san ina da hayshin marin da kikai mata ranan yau kuma don samun guri zaki kara dukan ta to bisimillah gaki gata shege ka fasa. Tambayan ku nake wa ake duka ne wai yace maji rabu da yar rainin wayo yarinyar nan ban san yaushe ta zama haka ba wallahi. Har gidana fataje ta samu Fatima da mari ta tara shegun kawayen ta a gida suna juyata kamar ta samu yar aiki. Bai isheta ba kuma yanzun daga tambaya shine wai zata duke ta again. Duka shin Amira ko may dukan Fatima fa akace kinyi ko may ko kin fara shaye shaye ne kema bamu sani ba? Bata fara komai sai rainin wayyo kawai ta ji na fada mata duk ta kara dora hannun ta akan matata ko zagi wallahi sai na bata marai Allah. Nikan mikewa nayi na cire hijjab din dake a jikina na fara gyarawa mama falon ta da duk ya wani yamutse kaman bashi ba. Na gama na koma can uwar dakin da dama nike gyarawa nai mashi kwal na kwaso shara gudan mai yawa. Mama tace ki duba ki gani yadda muke zaune a cikin shara haka saboda shegen son jikin ki kin kasa gyara muna mazaunin mu sai fama da dakilan waya. Nagama na dawo na zauna yace ke in kin gama tashi mu tafi akwai inda zamu biya in mun fita. Tun muna hanya bayan mun baro gidan su mama nake jin marana yana murda min a hankali alaman period zai zo min ke nan. A hankali na dan ya mutsa fuska na sai kawai naji yace ba tare da yakallo niba may nene kuma ya faru. Sai da na sauke ajiyan zuciya nace ba komai yace shine kike yamutsan fuskan ki haka kawai. Murmushi nayi nace bakoma mun tsaya wani shago naga yayi sayaya yafito aka sa mai a bayan motan shi. Bamu tsaya ba sai gidan Inna mahaifiyar Bashar naji matukar dadin haka muka shiga a tare mun samay ta da yaran ta zaune suna hira suna ganin mu suka shiga murna. Nan muka zube muna gaushe ta ta matsa sai mu tashi mu hau saman kujera bamu dade ba don yamma yayi a lokacin. Mun isa gida duk nagaji ga marana yana min ciwo sosai a lokacin daurewa kawai nakeyi. Na shiga yin alwala naga har jini yazo min ko nan na dan daureye jikina na fito ina tunanen yadda zan fadawa yaya ina period yau. Ban fito falo ba ina kwace rike da marana dake min ciwo yashigo dakin yasamay ni na kifa kai a filo sai nishi nakeyi. Yake tambayan wai may ke damun kine haka kinki fada wa mutum ko so kike ki halaka kanki ne wai?. Da kyat na iya cewa marana ne ke min ciwo tun dazun, yace shine baki iya fadi na sai maki magani tun a hanya. Shiru nayi ba amsa yace ko period zakiyi ne wai a hankali na gyada mashi kai tare da cewa har ma yazo min ai. Yace ashe ko da gaskiyan Bashar ni raggo ne tunda na kasa jefa kwallo a wana jan ragan naki. Turo baki nayi yai murmushi tare da mikewa har yafara tafiya yace kwana nawa kike yi dashi ne wai ? Nace sati daya da karfi naji yace what ? Sati daya fa ko baki da lafiyane zaki dinga sati kina fitar da abu daya haka nan ? Kara kife kaina nayi kawai batare da nai mashi magana ba naji da abinda ke damuna kawai. Fita yayi zuwa can ya dawo min da magani da lemo mai bawa da sauran kayan fruits . Sai da nasha maganin na samu ya dan lafa min na fito falo yana zaune yana kallon ball . Guri na samu na zauna tare da gaishi shi ga kayan fruit da naman da yaci saman table a gaban shi. Yace yaya jikin kuma nace yai min sauki sosai dana sha magani . Zauna ki ci nama ga milk nan kuma kisha baida sanyi sosai nace na koshi yace kin koshi da kikaci may kuma ? Banci komai ba na dai sha lemon da ka kawo min sai naji na koshi sosai. Oya ki kara da,naman kisha milk din ko zakiji jikin ya kara sake maki ban yi musu ba na fara cin naman a hankali sai dai duk bakina ba dadi cikin shi ko kadan. Yace kisha milk din mana ina kaiwa a baki naji kaman zanyi amai nan na cire cup din da sauri a bakina . Na mayar da kaina baya saman kujera ina mayar da numfashi guda guda cikin wahala. Ban san tasowan shi ba sai jin shi nayi a gaba na yace oya kwanta ki mike shi da kan shi ya gyara min kwanciya nan ya shiga dan tausa min ciki na a hankali. Naji dadin hankan har na fara lumshe idanuwa na ban sani ba sai barci bai bari ba sai da yaga barci ya dauke ni sosai. Sannan ya daina yadan kura min ido yaga yadda nake barcina a tsanake nan ya koma saman kujeran da ya taso kada ya tayar dani. Mukai wani lokaci a falon yana kallon shi bai son ya tayar dani na falka daga barcin da na keyi. Sai da dare yayi sosai ya tayar dani muka koma daki sai dai makale ni yayi haka muka kwana dashi. Washe gari na gyara jikina nai wanka nashirya tsab nashiga kitchen hada muna breakfast, ina tsaka dayi ya dawo daga gurin motsa jikin shi. Kitchen din ya shigo ya samay ni yana cewa har kin ji sauki ke nan ko idan bazaki iya ba ki barshi kawai sai a sayo muna muci nace zan iya ai har na kusa gamawa ko. Yace yau fa kina da bakuwa don Nafisa zata shigo gidan nan don Allah idan tazo ba runki da ita don kin san yanzu ta burge sosai. Sai misalin sha daya da rabi suka shigo gidan su uku ne da kawayen ta da ganin su tantiran yan duniya ne sauran don sun fita,wayewa sosai. Da fara,a na fito daga dakina ina masu sannu da zuwa duk suka zubo min idanuwan su nan dai bayan mun gaisa na kawo masu abin sha suna godiya. Nace gashi ko yaya ya fita ya jiraki baki zo ba yace zai fita amma ba nisa zai tafi ba. Kada ki damu ai zan jira shi ta bani amsa nace anty may zan dafa maku ne yanzu. No ki barshi inji wace tafi haske daga cikin su nace ,a,a Allah bari na girka maku abinci mana kafin ku wuce. Na juya nan na barsu a zaune suna bin gidan da kallo na shiga kitchen na fara hada abinci. Basu dade sosai da zuwa ba yaya ya dawo gidan shi da Bashar ne wanan karon. Suka gaisa dasu fuskan yaya a daure nagan sbi nafito muka gaisa da bashar nakoma ciki. Yaya ce wa yan nan fa tace tie friends dina ke nan yaya wanan Raiha akace mata amma anakiran ta da Rayye ne ita kuma wanan Nura ance mata Nuriyya. Yace ok sai dayan tace amma sai naga kamar na sanka da dadewa ko sai dai in ba kai bane amma nasan wanan fuskan gaskiya. Nafisa tace ke banza shine fa U F da kike jin ana fadi dan kwallon wasan duniya. Yadda tai maganan kamar a buge yasa kowa yin dariya a lokacin banda yaya daya daure fuskan shi. Nakwao masu yaya ruwan sha da drinks na aje masu nakoma gurin girki na. Yaya yace amma ba yanzu zaki wuce ba ko don kin san nace ina son ganin ki ko. Tace ai shine nazo mana ko don nazo da kawaye nane baka samun ganin nawa. Yace ashe kin gane nufi na nafito masu dauke da kulan abinci da plate na aje masu tare da masu bisimillah. Can dayan tace na tuba inda na sanka yanzu muna haduwa da can baya gurin Brosha mai kayan harka ko? Daure fuska yayi kamar badashi take magana ba Nuriya ta jawo kula ta bude abincin dana aje masu tace wowwo kamshi ke nan aiko mu gode wallahi dama yunwa nake ji sosai. Sam basu da kunya atare dasu ko kadan sai wani girgiza suke yi adole sunga maza mata sa yaya yace muje na sauke ka gida Nafisa ki jirani fa kinji na fada maki. Nan muka zauna dasu suna cin abinci muna hira jefi jefi dasu dayan take tambayan Nafisa ita kadai ce matar shi halan Nafisa taba amsa da eh. raiha tace wai amma kan zakiyi fama da arnan yaki ga mijin ki matashi kuma mai lokaci ai akwai aiki. Sai da sukaci abinci suka koshi yaidda nai masu sunji dadi haka sosai basu boye min ba don cewa sukayi da suka gama kai amma gaskiya munji dadin yadda kika tare mu ba kamar gidan wancan yayan naku ba da mukaje suna ce muna wai yan kwaya sun shigo gidan su. Nace subbahanallahi ai ba wanda ya wuce jerabawan ubangiji don kuma ba haka kukaso ba a ran ku. Shiru sukayi sai Nurace ke dai ganan min hanya yar uwa ina mamakin mutane wallahi mutum na da abin fadi amma sai ya takw nashi yaje fadin nawani. Nace Allah Allah dai ya yayewa kowa wahala kuma Allah ya kawo maku mazajen aure ku huta duniya yanzu ba tausayi wallahi. Raihane ta jefo min tambaya halan ke yar wace garice sister kafin na bata amsa Nafisa ta ce yar uwar muce fa agidan mu ta tashi ai. Ai ko ban taba sanin taba gaskiya nai dariya nace niko nasan ku ai yakai sau uku muna hafuwa daku ai. Allah sarki ban ko gane kiba wallahi, tace min suka mike suna cewa zamu tafi mungode kwarai da taron da kikai muna nace kai haba ba komai aiku yan uwa na ne. Suna fita nan Nafisa takife saman kujera sai barci koda yaya ya shigo ya samay ta tana barci sai baita da ita ba dakina yashiga ya samay ni zaune yace ita wanan barci tai muna anan. Nace ina ruwan Anty Nafisa taci ta koshi sai barci abinci yace na bashi nabi bayan shi muka fita tare sai da ya zauna yake cewa ina ganin yau zanyi tafiya fa. Amma sai dai yadda nagani amma iyakata Abuja zan tsaya kawai. ****** ********* ****** Bayan Nafisa ta tashi yana falon zaune ganin shi yasata mikewa zaune yace har kin gama barcin ke nan tace tana mikewa zaune wallahi fa yaya. Yace haba Nafisa ya kamata ace yanzu kin wa kanki fada fa gaskiya baki kyauta wa iyayen mu musan man ma Umma da take mace tana zama dake a gida ko yaushe. Shiru tayi tare da dukar da kan ta kasa yace lokaci yayi nafisa da zaki bar wanan harkan haka duk da nasan abune mai wuyan bari amma don Allah kiyi kokari ki dan rage wasu daga cikin halaiyar ki don Allah dai ba don niba Nafisa. Abin mamaki sai gata kawai tana hawaye tace wallahi yaya nima kaina ban san may ke kaini sha ba ko naso na bari sai naji kwata kwata bazan iya ba. Lokacin nafito falon ganin suna magana yasa na juya zan koma ciki sai yace No dawo ki zauna aikema maganan ya shafe ki tunda ya shafe ta. Tace wallahi yaya ni ina ganin Alhakin kune da maji ne ya sauka aikaina dakin mu don irin mugun abinda Umma da mama suke shuka maku kullun tun ina karama nakejin irin tugun da suke kullawa akan maji da ku. Dariya yayi yace kai haba Nafisa ai shi zama kishi ina ganin haka yake sai ta share hawayen tace yaya bazaka gane bane wallahi. Amma nasan ko nayi rantsuwa ban kaffara don su Umma ne suka sa kayin shaye shaye a baya. Na fadawa umma su bari kada Allah yajerabesu watara tundai ina suna zagin ka da mashayi dan maye mukan mata magana ni da yaya sagir amma umma bataji. Munafukan ga mama bata bari umma tabar aikin ta yaya yaya kake ganin zan iya dainawa idan su basu daina sheri ba. Tace umma tana sakaci da yawa tana yarda da mama asiya batan cewa muguwa bace ta karshe har yanzu bawai sun dai jifan ku bane fa. Allah daine ke kare ku kawai amma kai kan ka da,wuya in ka daina sha yanzun haka? Da sauri na dago kai ina kallon shi sai naga yai murmushi kawai yace Nafisa koma maynene ki sa a ranki cewa zaki daina sai kikaga kin daina din. Ki samu miji kiyi aure koma may nene kike so ni nai maki alkawari zan sai maki duk lokacin da kika tashi aure. Kai ta kifa tafara wani irin kuka take nima bansan lokacin da na fashe da kuka ba shima dai ina ganin kukan yakeyi a lokacin yadda na ga ya dukar da kan shi kasa. Can ya mike ya shige dakin shi ya bar munan muna kuka tai matukar bani tausayi namike zuwa inda take na dafata. Duk da nima kukan nakeyi amma sai na dafata ina bata hakkuri kawai sosai nake mata nasiha har nagama batace min kalla ba nace tazo tashiga tai wanka ko zataji dadin jikin ta. Ta kalle ni da mamaki tace Bintu ke baki kyamanane yadda sauran yan gidan mu ke yi min yanzu nace kyama kuma anty akan may zan kyamace ki kina da cutane ko may. Tace har fa ciwon aids mama Asiya da yaya Ahmad ke fadin ina dashi yanzun haka kallon mai cutar aids wasu mutane ke min. Nikuma wallahi komai mayena ban bari mutum ya shige ni baida roba a jikin shi. Ban san lokacin da na runtse idona ba danaji abinda tace min ba kunya take fada min tana amfani da maza haka. Dakina nakaita tai wanka na bata wani dogon riga na mai kyau tasaka muka dawo falo nan muka samu yaya yace tazo ya sauke ta gida don can zai tafi yanzu. Tare sukafita da ita tana min godiya nace haba anty aiyiwa kaine tausayin ta yai matukar kamani sosai. A hanya ma sosai yaya yaita mata nasiha ya na kwantar mata da hankali na ta natsu ta daina wanan harka baida amfani don babban illa da cikas yake kawowa mutum a rayuwan shi. Sai yamma ya dawo yake ce min tafiyan shi yana nan yace ko bazan iya zama ni kadai bane yaiwa Inna magana maman su Bashar a turo min daya daga cikin yan matan ta nace a,a zan iya zama mana yaya. Ai yanzun na saba da gidan ban jin tsoron komai kuma kamar baya yai min sallama bayan ya shirya ya wuce Abuja . ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,, IDAN KUMA KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA NA BARKI GA ALLAH YAR UWA,,,, Zama muke na zaman kwari tsakanina da Amira don iyanzu takai ni inda bani son mukai tun farko da ita. Ina zaune a dakina naui zugun ina tunanen irin wanan halin takuran da Amira take kawo min har a cikin gidana. Sai hakkuri nake tayi ina hadiyewa don ban son mahaifiyar su su sami labarin halin da muke aciki. Amma ranan da maryam tazo gurina ta fahinci akwai matsala a zaman mu da Amira. Gaba maryam ta sakani sa tambaya iri nata har dai na warware mata duk irin zaman da mukeyi da kawayen ta da take kwaso wa su zo su dinga min abu isa isa a tsakar gidana. Rayuwan maryam yai matukar baci tamike tana fadin wallahi sai tayiwa Amira magana Amma na sha gaban ta na bata hakkuri tare da fadin idan Allah ya yarda ni da kaina zan dauki mataki a kan ta. A kwana atashi ba wuya a gurin Allah sai ga shi yai har wata daya da kwana goma sha da tafiyan yaya sadauki. Munan da Anty Amira muna ta kwamawa a cikin gidan don gaba daya yanzu na fitar da tsoron ta ko shakka da kawaicin ta da na ke ji da farko . Karatuna nake don yanzu exam mukeyi hutu zamu fara next week banda wani lokaci sosai na kaina a gida gaba daya. Tsaye yake idanuwan shi suna a lumshe dan murmushi ne ya sake don tuno da yanayin Fatima, da murmushin ta da take a boye tsiwanta da fushin ta da takeyi a lokaci daya , Sai dai kuma duk karancin shwkarun Fatima hangen nesa ta da kyakyawan zuciyan ta da manufan ta akan kowa haka halitta ne a gare ta. Yana gyara tsayuwan shi yake cewa Fatima ke ba diyan masu hali ba amma kuma kina da,diyauci irin na masu halarci. Su iso Lagos da yamma don ta nan jirgin su ya sauka Nigeria a gurin su basu dauki tafiya a bakin komai ba don haka ya tsaya yai clearing din kayan shi da ya shigo dasu. A lokacin mun kammala exam na dawo gida satin nan ba fita duk wani motsi na da,wani taku na yana kan idon Amira da ta saka min ido a agidan. A kullun tunanenta shine yadda zata kawo was Fatima cikas din rayuwa ta hanata jin da dadin rayuwa a gidan Sadauki. Don ita Amira a watau ta sune yan uwanshi na jikin shi sune ya kamata suci arzikin shi fiye da,wata mace can da tashigo da sunan zaman auren sai su mamaye komai na miji ya zama na au suda yan uwan su kawai. Shiko miji da dangin shi sai yadda akayi dasu kawai a gidan sun zama yan bi ke nan a dinga juya su yadda rai yaso, Hakan ke matukar bankan ta mata rai ita bata kaunan ace dan uwanta sai wata ta bata doka akan shi Amira na cikin irin jinsin mutanen dake adawa da matan yan uwan su maza a duniya. So take sai yadda tayi da shi da matar shi sai dai ta dinga bada commad ana bi kawai shine zaman lafiyan kowa da ita don bakin ran ta da yai yawa. Takan ce dan uwa dai dan uwan tane babu mai raba shi da ita don a tare aka gan su don haka sai dai mace ta kare kutin gwilar ta tabar da dan uwan ta saboda babu wanda zai kawo wani shamaki a tsakanin su. Haka mukai ta zama da ita a cikin fitina da gori habaici bakar magan cika baki sai dai wanda ba bu shi don duk nagani ga Amira lokaci guda. Gashi kuma yadda take samun, gashin kanta yanzu a gidan namu tayi kiba tai fari ta kara dan girma da ita. ****** ********* ****** Suna zaune falo da kawayen tabar gazan ta wai su wayayyu su salma kubura da Fauziya sai jin motsin turo kofan shigowa falon gidan sukaji. Idanuwan su na kan kofan don suga mai shigowa falon a lokacin don yanzu sha daya saura na safe muke ciki. Cikin mamaki Amira tace yayana dama yau zaka dawo ashe bai amsa mata ba sai bin falon yake da kallo cikin mamaki bayan ya gama kallon fuskoki wa yanda ke zaune a falon lokacin. Daya bayan daya yake kallon su har ya kai karshe Fatima bata falon. Hakan yasa shi wuce wa direct dakina yagani don sai yaji zuciyar shi tana mashi wani irin kuna a lokaci guda. Yana bude kofan zaune nake na sallamay sallah walha, ina dan jan tasbaha bayana yana jingine da fadon dakin Jin an turo min kofa yasani saurin dago kai ina kallon kofan dakin wanda nagani a tsaye ya harde hannayen shi guri guda yana min murmushi yasani saurin dan sakin murmushi tare da yunkurawa in tashi. Na nufoshi a a cikin fara,a ina cewa sannu da zuwa yaya yaya hanya ya can ? Murmushi yayi tare da,ware hannayen shi na sheko da dan gudu na na shige ciki ya mayar da hannayen shi ya rufe ni dasu . Sai da muka dan dauki lokaci a haka muna shan dumin junan namu ne yake cewa cikin wata irin shakkakiyar murya su waye nagani a falo kuma a ina suka fito hakane da au kuma ? Nai dan murmushi tare da dan dago kaina daga jikin shi nace ban san da ga ina suke ma amma kullun dasu muke wuni a gidan nan sai dai na girka na basu idan kuma sun gama na kwashe na gyara gida idan da duk ya baci. Yace a bisa ga umurnin wa hakan ke faruwa min a gida ban sani ba nace umurnin second command ne Anty Amira don haka sai ka tambaye ta bayanin komai. Ina rike a hannun shi yaja hannuna zuwa falon muna shiga suna ganin mu suka sauri dawo da hankalin su a gare mu irin yadda suka gan mu a tafe ne ya kara daure masu kan su. Zama mukayi a saman kujera daya nidashi ya dago fuskan shi dake a daure yana fadin wa yan nan kuma fa daga ina suke ne haka ? Shiru babu wanda ya amsa ya dago kan ahi yana kallon inda nake yake yana cewa nace su wayen haka kuma don ban san su ba. Nace ka tambayi anty Amira don tare na gan su dasu kuma ta fada min sunfini daraja a gidan nan kaga ni dole sai dai na bisu don yan uwankane na ji aiko. Sai dana fadi haka ya dago kai ya kalli inda Amira take zaune wani irin haushin ta ne da kiyayyan ta ya darsu a zuciyar shi a lokaci guda. Yace su waye haka kika tara min a gidana sai cewa tayi yaya sadauki salma ce fa diyar gidan baba prof da take mutuwan son ka wace nasha fada maka zancen ta tana karatu a london yanzu itama tagama ne ta dawo gida. Wani mugun kallo ne ya watso mata yace kina da hankali kuwa Amira look kwashe min wanan mugun tarkacen da kika tara min a gida don yanzu na gama sanin inda kika dosa. Salma da ta zage akan ta aamu shiga tunda ta samu kaunar shi nason ta sai yadda tayi dasu. Dalilin ma da aka kitsa ke nan su dinga zuwa gidan don ta san halina da kuma yadda zata saba da gidan kafin ta shigo. Haba UF inji salma data mike tsaye tace kaima kasan da ina son ka shi yasa kaga har nazo gidan ka kawai . Amma daba, son ka nakeyi mai zai kawo ni wanan nan gidan nazo na zauna har wanan yar matsiyatan daka aje tace zata kawo muna raini kawai. Don mun sauki cups din amfanin ka ta kama muna haushi ai badon Amira da ta dauki mataki a kanta ba da na so na gwada mata koni wacece. Wani irin kallon mamaki kawai yake masu take idanuwan shi suka rikide zuwa ja kamar gauta a lokaci daya. Yace cikin wani irin murya please get out in my house before i take a desition on you. No no UF kada kace zakai min haka please already mun riga mun gama maganan nan da kai ko. Tazo har inda mukw a tsaye tana cewa tare da nuna ni da hannun ta wa an yar kauyen matar taka bata dace dakai ba don tafi dace wa da masu gadin ka kawai. Fauuuu muka ji kara mari tace ido rufe maza su kwashe subar mai gida mara sa kunya fitsararu ko mata sun kare a duniya mai zaiyi da ita mace da taje london ta gama watse wanta zai dauko ya kawo wa kanshi fitina a gida . Tas yai masu suka fice simi simi da kunya wai su tantire sai gashi su hadu da wanda ya fisu iya fitsara yai masu tas gaban matar shi. Wanan karon tare da tsaraban ahi ya shigo gari don koda su salma zasu wuce wata hilux data kwaso mai kaya daga airport tana sauke kayan a kofan gidan mu. Ana shigo da kayan ciki yai tsaye yace Amira tafito ta wuce zuwa gida sai ya zo zai nemai ta a gida. Aiko Amira ta ce yaya may kake nufi korana zakayi don munafukar matar ka tai muna hadi a gurin ka hau kazauna akai. Babu inda zan tafi sai ka bude kayan nan a gabana kowa ya gani haka wancan karon nazo nai zaman banza komai baka ba.u ba yadda ka saba ta kwashe takai kauye inda,ba,a san darajan su ba ma. Amira waiko anya kanki daya kuwa, ina dai gani kanki ba guda bane kawai don hakan da kikeyi abin naki ya zarce sanina gaskiya. To bazan bude ba kuma maza ki kwaso kayan ki tun ban bata maki rai ba a gidan nan. Idan Fatima ta kwashe abina nakine ta kwasa ko nawa ina ruwan ki da kayana Amira Fatima matatace ko kina da abinda zakiyi kan zaman ta matata. Yaya ta furta tana mashi kallin mamaki tace kan Bintu kake fada min haka yaya Bintu fa Bintu dai. Yace Idan na kara jin kin kira Fatima da Bintun nan da kuke kiranta dashi don rainin wayo wallahi sai kinyi mamakina Amira fito kawai ki tafi gida zan zo zamu hadu agidan ai. Haka yai mata kora na kaskanci kan abinda tai min wanda tun yana can Bashar ya fada mashi komai duk irin halin da muke ciki da Amira a gidan, da bayana ranshi yai matukar baci shine ya zo muna a bazata batare da ya fadawa kowa zuwan shi ba. Wanka ya shiga don ya rage gajiyan jikin shi ina kitchen ina hada mashi abinda zaici na juya zuwa dakin na shi inda na samu ya fito daga wanka na yana saka kaya a jikin shi. Jin motsin shigowa yasa shi dan juyowa yana kallo na tare da sake murshi a fuskan shi. Yace batare da ya dago kan shi gare ni ba mai yasa kika boye min halin da kuke ciki a gidan nan da Amira. May yasa tun wancan zaman baki fada min ga irin rayuwan da kukayi da ita a gidan nan ba. May yasa ki ka bari Amira ta tara yan iska suna wullakanta min ke ne haka a cikin gidana. Ya dan dago kai kamar a fusace yake magana yace may yasa zaki boye min irin wana mugun halin da Amira taita gwada maki. Nace yaya Anty fa yar uwatace komai tai min kanta taima bawai, ni kadai tai wa ba don wata rana zai bata mata rai yadda tai min din. Nace yaya duk abinda Anty ke min a saboda kaine don taga ban cancanci na aure ka ba saboda matsayina bailai na hakan ba. Sau dayawa nakan rasa laifin may nai wa anty Amira take min haka yanzu , sai da ta fada min akan gangancin da nayi na auren ka yasa take min wanan halin. Hawaye ya gangaro min a fuskana nace yaya sadauki nasan nayi gangancin auren da matsayina baikai gare shi ba. Haka kuma wanan ba shine irin rayuwan da ya dace dani bayar tallakawa kamata bata dace da irin ku diyan masu kudi da matsayi ba a duniya. Ya sadauki kaima kanka kasani bankai matsayin da za,ace ka aure ni ba kasani ba irina ce ta dace dakai ba a gidan nan kamar yadda anty Amira ke fada min nima yanzu nasan gaskiya take fadi don ban kai matsayin hakan ba a gare ku. Yaya kayi yadda yan uwanka da masoyan ka ke son ganin ka tare da,diyan attajirai irin ku masu matsayi a duniya bani yar takawan kauye ba Fatima. Ba so tsakanina da kai sai zumunci na wa yanda suka tashi a daki daya irin na yan uwantaka kawai. Kamata yayi ace na auri maigadin gidan ku ko wani dan aikin gidan ku wanda baida matsayi irina. Sai faman kallona yakeyi kamar talabijin da mamaki ya lura ina a cikin damuwa da kuncin rayuwa mai yawa don bai taba ganina acikin irin wanan yanayin ba haka. Sai na fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya a lokaci guda na durkushe a bakin gadon shi ina rusa kuka. Cikin kuka nace Allah kadai da mama suka san dalilin wanan hadin da sukai muna. Amma da zaka daure ka auri wacce tafi dacewa da zama a matsayin matar ka hakan zai matukar saka anty Amira farinciki a rayuwan ta. Hankalin shi yai matular tashi a lokaci guda yace tabbas Allah ba zai yafe min ba Fatima tunda nine yakamata na daukakaki a idanuwan mutanen duniya tun farko Fatima amma na kasa yin hakan. Matsalar duk nawane da na kasa fitowa fili na nuna cewa ina matukar son matata batare da duniya na mata kallon wacce aka tilsata min da ita ba. Dole ne komai yacanza daga gareni yadda kowa zai iya fahintar Fatima ta wuce yadda suke tsanmani a gurina. Ahankali ya tako zuwa inda nake a tsugun ne ina kuka shima ji yake kamar ya fashe da kuka a lokacin. Ya dago ni tare da kokarin mikar dani tsaye ya rigumay ni zuwa jikin shi muka zauna saman baki gadon shi a hakan. Yace Fatima ki kwantar da hankalin ki ki saurare ni dagani har ke zan iya ce hada mu akayi amma kuma ba bisa kuskure ba. Maji ta fahinci kiyayyan mu ba kiyayya bace illa kainace mai wani sabon launi ta hango abinda mu bazamu ita hango aa kan mu bane a lokacin. Fatima komai nawa ya canza a rayuwana adan zaman nan da mukayi dake tunane yanayi da komai nawa yanzu ya canza min a dan lokaci guda. Don haka ki fitar da zance su Amirah da wanan salman a ranki ,kimai da al,amarinki ga ubangiji don shi yafi mu sanin me ke boye yafi kowa sanin abinda bamu sani ba gaba dayan mu. Sannan ina son ki saka a ranki daga yau ni Umar faruq sanda ina sonki Fatima, ina kuma kaunar ki fiye da tsanmanin ki Fatima ke alheri ce babba a gare don ko nina tabbatar da hakan da kaina. Ina maki so na hakkika Fatima wanda ban taba tsanmani akwai wata mace bayan uwata da zanyi wa wanan irin son ba a duniyan nan. Ni Umar Faruq nai alkawari har ga Allah zan rike amnan da mahaifana danaki suka bani akanki zan . Zan taimakawa rayuwan ki naga kinyi abinda kikayi niyaryi, zan taimaka maki tako wace hanya inga burin ki yacika akomai. Ki sani yaya sadaukin ki nai maki alkawari Fatima muddin muna a raye insha Allahu zan maki komai don wanan Umar din zuciyar shi da gangan jikin shi wanan kirjin da kike son kwanci akan sa duk nakine ke kadai Fatima zarah,. A kullun zaki kwanta akansa kuma zan share maki hawayen ki harta inda baki zata ba Fatima. Fatima muddin ina a raye duk abin kike so shi zan maki don haka ki share hawayenki Umar nakine ba wani wanda zai shiga rayuwanki ni da ke , sannu a hankali muddin ni mijin kine kina a matsayin matata zakiga gurinki suna cika daya bayan daya. Yana dan buga min baya yake fadin Sadauki nakine zan maki duk maganin matsalolin ki don zan share maki hawayen ki. A hankali na dago kaina na kara shigewa cikin jikin shi ina fadin cikin kuka nagode yaya sadauki Allah yabar min kai a rayuwana yabamu hakkurin zama da junan mu. Yace Amin Fatima nima nagode Fatima da kika fahince ni a cikin sauki tashi muje ki bani abinci naci yunwa nake ji banci komai ba tun jiya dasafe don kawai nazo naci girki yar matata naji dadi. Murmushi nayi tare da mikewa ina gaba yana bina a baya mukaje falon sai da ya zauna na zuba mai abincin ya fara ci. Mikewa nayi na fara gyaran falon da suka bata kaca kaca wanda a kullun sai nayi gyaran shi fiye da sau uku suna batawa. Yana cin abinci yana kallona a fakaice yana tinanen ashe zancen da bashar ke fada mai Fatman shi ta koma kamar boya a gidan kan abinda Amira ke fada mai. Bayan na saka kamshi ko ina yafito neat ya mike ya dawo saman kujera yana waya. Daki na shiga na kara wanka na gyara jikina tas nafito falon ina kamshi inda yake zaune na nufa da hannu yai min nuni da nazo saman kujeran da yake a kai na zauna. A hankali yakai hannun shi saman jikina yana waya yana wasa da part din jikina a hankali. Yana gama wayan yake cewa idan kin huta zuwa dare ki bude kayan nan da nazo da su, naki ne sunfi yawa daga ciki sauran zaki iya zabawa maryam da Amira sai kuma wanda kika so aba. Nace mai mama fa yace atamfar Holland ce sunan nan zaki gan su kema ki zaba tunda naga kina son su sosai amma ki min dinki da zai fitar min da suran ki a fili. Nace kai haba yaya abinda ake fadakar da mutane ba,a son anayin su yanzu yace ba ani zaki sawa ba ko wani ne zakiyiwa kwalliya bani ba. Nace an gama yaya indon wannan ne kawai mikewa nayi na shiga fitar da kayan ina matukar yaba yadda ya iya zaben kaya haka kamar mace. Gaba daya gidan su sai dana fitar wa kowa da nashi kaso har yaran mummy da suke kanana sai da suka samu tsaraba haka yasani fahintar tafiyan da yayi akwai sa,a sosai a cikin shi ke nan don haka yakeyi duk yai tafiyan da yayo nasara zamu sha tsaraba masu tsada muma a gidan. Ranan kan naji jiki a gurin yaya sai dai daurewan danayi kawai don iyan zu na fara sabawa da halin shi ko. Da safe bayan mun karya ne yafita zuwa kai tsaraba gida bayan na rubutawa kowa suna a nashi yadda zai gane. Ranan kowa ya fahinci na fara jan ragamar aure na a gidan sadauki don ganin kayan kowa da sunan shi a jiki. Dakin su Umma cewa mama Asiya tayi waiko kin gane cewa wanan yarinyar itace ta zabawa kowa kayan nan don ga suna kowa a jikin su . Rukaiyya ta tare su da cewa amma kuma mama ai atamfan duk suna da matukar kyau wallahi don ni sun bani shawa,awa sosai wallahi. Ke rufa wa mutane baki ke may kika sani ba sai tazabi na iyayyen ta yafi kyau ba ta bamu matasa kyau. Kai haba mama wallahi haka baida kyau fa ina laifin Fatima gida su yaya ko tsuki sun taba kawo maku ne yakamata ku daina irin wanan halin wallahi inji yaya Sagir. To sannu uban mu inji Umma yan uwan naka zakaiwa gori kuma don bakin kwadayi. Mashayi dai ne ba wata tsiya ba can don har yanzu ba fasawa yayi ba ai tana cikin fadin haka sukaji hayaniya daga tsakar gida. Nafisa ce tayo mugun sha take ta watsar da duk abinda tagani a waje da sauri suka fito hardasu mama dake dakin su cikin tashin hankali. Ga kayan jikin ta yai futu futu sai ashar take zubawa tana fafin nagane duk munafukaine gidan nan don babu wanda ke sona. Sai kuma tasa wani ihu kamar wata yar daji da taje farauta tace yau zan ci kazar uban duk wanda ke gidan nan munafukan banza xa wofi kawai. Kuke nan kullun ku shige daki kuna kulla yadda zaku kashe UF ko wooo UF ko yafi karfin ku wallahi sai UF up up UF buga muje yayana ikon Allah . Umma tafito rai a bace ta nufe ta tana fafin Nafisa abin naki kuma ya koma haukane ko may . Tace Umma ni kika ceqa ma haukaciya yau ko zan gwada mamu ni ma ma mahaukaciyace a gidan nan saiko ta dauko tabaryan dake yashe a tsakar gida tayo kan Umma gadan gadan dashi. Ganin da gaske zata rotsawa umma ne yasa umma juyawa da gudu saiko ta fadi kasa ku caaa gap da ta rotsa mata Sagir dake daki yafito jin yadda kowa ke ihu yayo kanta yakai mata shuri sai da ta fadi kasa takife bakinta ya fashe. Kara dagowa tayi tana fafin wallahi yau sai na kashe ka gidan nan ni zaka daka haka ? Nan ya samay ta yai ta jibga saida aka tare shi ganin haka yaran mummy suka sa ihu maji ta jasu zuwa dakin ta taboye su a ciki. Yaran duk sun tsorace Umma tayi tayi ta tashi abu yaki kafa ya rike mata ashe tayi targade ne ba,a sani ba. Ganin haka yaran ta suka saka ihu suna kuka neman taimako ga uwar su. Mama Asiya ta bugawa Maigidansu waya yazo gida ba lafiya suna tare da sadauki dayaje gurin shi kasuwa. Tare suka iso gidan cikin rudewa gashi an taru akan umma sai hawaye take tanaji kamar zata mutu. Mummy ma dawowan ta ke nan ta samu wanan tashin hankalin daukan mama akayi dakyat zuwa asibiti sadauki da sagir da mama. Yaran mummy suka fito dakin a tsorace suna ganin uwar su sukayo kanta suna kuka. Ta rugumay su tana fafin yau kuma wanan iftila,in ne yazo muna agida haka kai Allah ya kyauta kawai. Nafisa na cikin dakin uwarta sai ashar take ta zubawa da tonon asiri wa uwar ta. Alhaji yana tsayevsai zufabke karyo mashi na tashin hankali mama da mummy suka nufe shi suna cewa yashiga ciki ya zauna kada kuma yajawa kan shi matsala. Sai wani lokaci aka dawo da Umma duk ta jirkita ga uban bandejin da aka lailaiye mata kafa dashi. Baba najin muryan su sun dawo yafito da sauri yace Atika kada ki shiga min gida dauki mahaukaciyar yar ki kubar min gidana. Cikin yashin hankali aka shiga bashi hakkuri amma ina ya hau baji alokacin da kyat sadauki dasu mama suka samu ya koma dakin shi. Umma tace tana kuka ai dama nasan shetine wallahi sai Allah ya isar muna duk wanda keda hannu cikin lalata min rayuwan yata. Kai kaji kuma wani wauta wa zai tsa yiwa Nafisa wani sihiri kuma ga abin kwarai ba ai masu ba sai wanan barkatatan taki. Haba hjy kubura a dai bar zancen ai Allah ba azzalumin kowa bane duk mai wa wani sheri ai zai girbi abinshi tun anan duniya don Allah bai barin bashi yanzu. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,, A LOKACIN MU KE ,,,,, Ba karamin jiki umma taji ba sanadin kafan nan ta abu ga mai babban jiki irin ta. Duk halin da take ciki bai hanata makirci ba daga zaune take kulla sheri kulun. Ranan mama Asiya tazo tanawa Umma gulma wai taga maji da wani sabon waya tana ganin Sadauki yazo mata dashiba cikin tsaraba. Umma tace shine mu bai bamu ba ya mayar damu mutanen kawai ko indai waya ce kowa ma na iya saye ai. Asiya tace wallahi kona sa sace wayan ma gaba daya mu batar dashi kowa ya huta. A dole ita yanzu ga mai da mai hali komai sai dai mu ganshi gareta ina haka ma wallahi bai yuyuwa ko alama. But Nafisa dake daki tana shirin ta tana sauraren su tafito tace kaikayi dai koma kan mashekiya. Kullun ku ke nan cikin kullawa matan nan sheri ita da diyan ta Allah na kareta ya na komawa kan diyan ku amma baku fasawa ku daina. Don haka yau wallahi sai na fadawa maji wanan sherin da kuke kulla mata don ta kama wayan ta. Yaya sadauki ya nuna min so da kauna wanda duk duniya yanzun ban da kaman shi don ni ko bai min komai ba ya bani so da kauna na yan uwan taka da ba wani dan uwa da ya taba bani shi. In kin yi haukan e da gaske yau ina son ki gwada min kije ki fadawa Hauwau din ga abin da muka ce mata. Murmushi tayi ta koma dakin ta kawai taci gaba da shirin ta har sai da ta gama tsab tafito tace to ni zan fita. Ba dama Umma ta hanata ta ci mata mutunci tunda baba ba gida yake zama ba shi don shi gar yanzu tana dan tsoron shi. Tana fita ta samu mummy da mama a tsaye suna magana kan wani makwacin su da baida lafiya suna son zuwa gaida shi. Nafisa na fito mummy ta bita da ido caaa maji na kallon ta saudaya ta kawar da kan ta tana fadin a zuciyar ta Allah ya shirya kayan shi. Maji sai ki kama wayan ki don gasu can ciki daki suna kulla yadda zasu raba ki dashi kowa ya rasa. Don kin san su kullun cikin kulla sheri suke basu bari ki kama kayan ki don tun da suka ce sai sun dauke shi sai sun daka din don ba yau suka fara sheri ba. Daga haka ta juya,ta,wuce abinta, mamaki ne ya kama su maji da mummy suka shiga magana kan Nafisa. Mommy ne tace aiko tunda kika ji sun fadi haka wa yan nan macutan su na da niyar yin hakan don haka sai kiyi taka tsatsan da kayan ki ba waya ba komai manaki sai ki dinga hankali dashi don wa yan nan mutanen basu da imani ko kadan. Bai wa mummy ba da baba ya dawo sai dai ta fada mai abinda Nafisa ta fada ma su. Ran Baba yai matukar baci ya mike sai dakin Umma don a zaune take kafan ta har yanzu ba lafiya. Yana daga labule suna zaune tare da mama daga kofan ya tsaya yake cewa to muna fukan Allah . Duk wanan isharan da Allah ke nuna maku bai maku ba sai kunci gaba da kulla makirci don baku da imani. Shege ya fasa sace wayan maijidda a gidan nan daga ku har muna fulan diyan ku da kuka lalata da mugun abu. Yau gashi abin kuya ke Atika yar cikin ki da Allah ya mayar haka tazo tana tona maki asiri akan sherin ku. A na dai kallon Nafisa haka amma ke Atika kece silar mayar da rayuwan, Nafisa haka kuma har gobe dake nake kuka a gidan nan. Ku biyun kune silar duk wani balain da yarana suke ciki gaba dayan su don duk da hannun ku ga lalacewan su. Allah ya isar min akan da duk wani da nawa da kuka lalata min a gidan nan kada kuce ban san duk wani sherin da kuke kullawa bane. Wallahi nasan komai na dai barku ga Allah ne kawai ya fitar min da hakkina a kan ku. Daga haka ya juta rai a bace yana fadin Allah ya isa tsakani na daku. Tunda baba yafara magana jugun sukayi duk kunya da bakin ciki mamaki ya baibaye su sosai. Yana ficewa mama Asiya tace yanzu yaya ashe saida ja,iran yarinyar nan ta fada masu zancen nan. Amma ko nafisa takai la,ananna wallahi kidaina zaginta haka kada aji tsakanin mu idan la,anewan yafi haka kuma a kanta yaya kike son nagan ta ne. Duk fa kece kika jawo muna wanan tsinuwar haka wallahi ina zaune zamana kika shigo min da wanan tsurkun kinga sabon waya hannun Hawau, Ni yaya ina nasan wanan mai bakin tsiyan tana dakin bata fita aida ba zan soma maganan komai ba wallahi tun ita ta zama abinda ta zama. Umma tace sun dai zama gidan nan waye baida abin fadi tab a tsuliyan shi sai dai na wani yafi na wani kawai. Anan dai sukai ta yaba wa junan su bakar magana dama a haka hitan nasu ke kare a karshe kuma a dawo a samu sun shirya kafin wani dan lokaci. ****** ********* ****** Yana dai zaune Abuja ne amma kwata kwata hankalin shi yana a kan yar matan shi da yanzu yake jin ta ta zama mai wani rabin rayuwan shi. Wata rana yankayi matukar mamakin kan shi don bai san lokacin da har son Fatima yai mashi illa ba haka a rayuwan shi. Murmushi yayi ya mike daga kwancen da yake tare da dan murmusawa tunanen yake yadda har yanzu kunyan shi bai fita a idon Fatima ba. Ya kamata ya san yadda ya fitar mata da wanan kunyan nata hakana lokaci yayi da ya kamata yai wani abu akan ta don kawar da kunyan dake idon ta dakuma sauran yarintan dake cin ta hakana. Yana son mace wace ta san kan ta tasan hanyar da zatabi ta gyara mashi shimfidar shi. Fatima zata zata iya zata iya mana, kwai dai wanan bakin kunyan nata ne ke hanata aiwatar mashi da yadda yake so da ita amma yanzun kan dole ne ya san yadda zai batar da kunyan nan nata. Ta dawo daidai irin yadda yake son macen auren shi ta kasan ce mai a rayuwan shi komai normal. Yana zaune sai faman tunanen al,amarin Fatima ya keyi yaji anyi nocking din kofan shi kafin ya amsa sallaman shi yaji an turo kofan dakin don dama a bude take. Linda ce tashigo dakin abinda yasa shi saurin tashi zaune ke nan a lokaci guda. Da sauri ya mike zaune da kyau cikin dan kaduwa don baiyi expecting din zuwan ta saboda sun dade basu hadu ba da shi, tun lokacin da ya sasanta da Fatiman shi yaji gaba daya linda tafita mashi a rai. Linda may yakawo ki gurina again bayan na fada maki abinda nake bukatan kiyi kince bazaki iya ba. Ta watso mashi wani mugun kallo na see you tace to maye don anzo gurin ka saboda wanan karamar yarinyar daka aura ne da batafi sixth ba. Yace don't dear insult my wife she is part of my life now. Ganin da gaske yake nufin maganan shi har cikin ran shi irin yadda taga ya hade rai a lokaci guda haka don tasan halin shi sarai gurin rashin mutunci idan ya tashi yi. Ta dan marairai ce tace haba my man kada ka mance da alkawrin dake tsakani na da kai mana please. Yace kema kin manta da alkawarin da nayi cewa idan ba zaki musulunta ba ba zan iya auren ki a haka ba. Rashin yardan ki yasa har iyayyena sukai min zabin mace da kan su wanda yakai yanzu na gane cewa gata sukai min da hakan. Don haka tunda kin zabi son iyayyen ki a kaina nima yanzu na zabi zabin iyayyena akan ko wace mace. Don haka ki tashi kifice min a gida i don't want to see you again, dont ever think about me again its over now. Linda tace my man ni kake fadawa haka akan wanan little girl dinka wai wife kake nufin kayi komay. Ka sanni ni na wuce ka wullakantani akan wanan yarinyar don kasan asalina ka kuma san waye ubana a kasan ghana. Amma tunda kace haka jeka zaka gane kuren ka zaka gane ni Linda ba abin wullakantawa bace a take lafiya. Ya ja dogon tsaki tare da nuna mata hanya yace babu abinda zangani sai alheri tunda bake ce Allah ba banza dake kawai. Kije ki rike addinin ki da iyayyen ki nima na rike nawa koba shike nan ba. Tsayawa tayi na dan lokaci tana kallon shi babu abinda zata iya don tasan ba saurarenta zai yi ba ma yadda yayi. Ta juya kawai tafice kamar yadda ya umurce ta da yi ran ta a bace tabar dakin nashi. Komawa yayi ya kwanta ranshi a bace da Linda duk da yasan tana matukar son shi amma ya zama dole yanzu ya kawo iyaka a tsakanin su kawai don Fatiman shi tariga da tai masu zara ko ta ko ina. Ya sake wani dogon tsuki kawai tazo ta bata mashi jin dadin shi da yake ciki a lokaci guda na Fatiman shi. ****** ********* ****** Nai wankan tsarki a yau don haka na baro school da wuri don ina son a wanke min kaina a gayara min shi. Shagon da muke zuwa da maryam gyaran kai na nufa daga gyaran kai har na jiki sai da matar tai min shi ban dawo gida ba sai yamma lis na shigo gidan. Ina farka motana sai ga mai wankin mu Atiku yazo inda nake tsaye ina kokarin rufe motar ke nan yake cewa. Hajiya barka da dawowa, sannu da zuwa dama tun dazun nake jiran dawowan ki. Na juyo nace a,a baba baka tafi gida bane yau yace wallahi hjy ban tafi ba na dan tsaya don naga dawowanki ne don wallahi ina da bukatane. Shine nace bari na kawo maki koke na ko zaki taimaka min ki bani koda dubu goma ne idan anyi biya saina mayar maki ko kuma a cire daga cikin albashi na wanda dai yafi sauki daga ciki. Wallahi matata ce amarya na ba lafiya don tana fama da laulayin ciki ina son ta tafi asibiti dana kuma Aliyu ya gama makaranta zai shiga secondry gashi har an fara karatu amma shi yana gida a zaune. Tausayi mutumin yabani don gaskiya gaba dayan su yan aikin gidan suna da matukar mutunci sosai. Nace mai ya bari na zo ita kuma mara lafiyan Allah ya bata lafiya mai karatu kuma Allah yabada sa,a sai na shiga. Kudin da yaya yake bani ne bani kashewa na dauko dubu ashirin daga ciki nafito dashi. Nabashi goma naba maigadin dare dana rana dubu biyar biyar su raba. Atiku yace hjy nagode insha Allahu da anyi biya zan dawo maki da kudin ki da yardan Allah. Nace haba Baba ka barshi na bakane kawai kaje kayi amfani dasu idan zai ishe ka. Da sauri ya juyo yana cewa hjy kin bani wanan kudin haka dukka ? Ikon Allah sai naga yakai tsugune tafara fadin Hjy nagode nagode yadda kika rufa min asiri Allah ya rufa maki duniya da lahira. Allah yabaku zuria masu albarka a rayuwan ku, Allah ubangiji ya tare ku daga sherin makiya nagida dana waje. Nace amin baba nagode da adduan ka baba sai ga sauran sun karaso suna min godiya da addua su ma. Nagode masu na shige ciki don duk nagaji a lokacin wanka nake son yi nai sallah kawai sai na nemi abinda zanci a raina. Ina shiga malam musa yace Atiku kaga ikon Allah ko yau inane baka shiga ba a garin nan dan neman rance amma baka samu ba. Yanzu kaga ikon Allah ko yar arziki irin albarka nikan ai gobe gidana cefane lafiya na lau insha Allah. Kai mutane mutane magindanta suna cikin wani hali yanzu na bukata saboda motsalolin rayuwa da yaiwa mutane yawa a wanan lokacin da muke ciki. Duk yadda kake ganin kanka a cikin matsi wani nacan yafika don haka ko yayane ko ba yawa ka taimaka wa na kasa dakai don ita addua ba,a san inda take kamawa ga bawa ba. Da wanan irin tunanen na shiga wanka nafito sai na jini wasa ina idar da,sallah naji abinci kawai nake bukatan ci a lokacin. Don haka na fito na nufi kitchen don agazawa cikina dake dan kugin yunwa a lokacin gani ni kadai a cikin gida kamar mayya dani. Hakan yafi min da zama cikin tashin hankali da anty Amira ke zuwa yi min wai da sunan zama. Indomie na dafa na dan cika mai attardu nan da nan ya dafu na zauna naci nasha ruwa na kawar da kayan danaci abincin. Kofa na rufe don karfe takwas na dare nasan babu wanda zai zo kuma gidan a lokacin. Dakina na koma bayan na kashe duk wani kayan wutan dake falon, wanda shigana yai daidai da rurin da wayana ya soma a lokacin. ****** ********* ****** Yaya sadauki ne a layin da murmushi a fuskana na dauki wayan nace Assalamu Alaikum. May ye hakane sai yace min babu ko dan irin honey, darling, sweet heart din nan sai ki wani ce min wai assalamu alaikum kawai ? Nace haba yayana ni wani suna kuma kake so na canza ma,bayan wanda Allah ya dora maka a kaina na yayana. Yace No ban yarda,ba gaskiya ni suna nake son kawai a canza min nagaji da yaya din nan kamar wani mai yaye miya yabar tuwo gaya can dani. Ban san lokacin da maganan tashi tabani dariya ba nace kai haba yaya baka son girman ke nan kuma ko? Yace kin daiji na fada maki ni dai ban son wanan sunan yayana din don haka yanzu basai gobe ba sai naji sunan da aka rada min din. Shiru nayi ina tunanen ni yanzu wani suna kuma zan kirashi dashi indai ba son matsawa rai ba. Ke fa nake saurare Fatima na nisa nace to yaya love yace daya nace my life ko? Sai naji yai murmyshi yace to ke fa amna kamar wata tsohuwa can wai kullun yaya yadan make muryan shi yana,kwakwayona yadda nake kiran shi da sunan yaya. Nace kai yaya nidai wallahi kana son ace min banda kuya daine wallahi amma idan akaji na canza maka suna ai za,a kalleni wata mara kunya can ne. Yace da sauri mutane mutane su zasu hana ki dadada min zuciya ko kuwa ? Shiru nayi yace abar wanan zancen yaya bakon ki yatafine ko yana nan ? Da,mamaki na tambaye ina fadi bako kuma yaya ? Waye yaya ko da wani kike magana,ne acan kusa dake ? Nai sauri na tuna ina cewa wai yaya love wani bako kake magana ne wai ? Wanda ya hanani farincikina da aka saba min mana, duk hakan bai sa na kawo tunane na akan period yake maganan shi. Murmushi na dan yi a hankali nake cewa yananan har yanzu bai tafi ba da karfi yace what kina nufin har yanzun mesestration kikeyi nace eh yaya. Shiru na dan tsawon lokaci baiyi magana ba sai can yace ok kina lafiya dai ko? Nace mai Alhamdullahi dan hira,muka taba sama sama ya kashe wayan yana min sai da safe. Har barci ya kwashe ni a gurin inda nake a kwance sai faman tunanen shi nakeyi ina matukar mamakin wanan sauyin nashi nace Allah ke nan mai iko yau wai ni Fatima ce yaya sadauki ke wa wanan kulawan haka yanzu. Washe gari bayan nayi sallah na fara aikin gyaran gida da ta ko ina duk da gidan ba wani dauda ke gare shi ba sosai amma,sai kyalli gidan ke yi kawai. Haka kawai nace bari nai girkin abinci rana mai kyau da haduwa ,sosai na zauna na girka .. Sai da ga abincin na gama amma kuma na kasa cin komai daga ciki sai kallon shi nakeyi a gabana kawai. Abin mamaki sai gani ina kewan ganin yaya sadauki don ina bukatan ace yanan yaci wanan girkin dana hada. Ban kai ga karshen tunane na ba naji bell din gidan yana ringin a kasalance na mike zuwa duba wanda dake sallama a kofan gidan. Yana tsaye rataye da coth din shi a kafadan shi sai yar jakar kayan shi dake sabale a hannun shi. Na kasa boye farin ciki na dana gan shi a lokacin na ji kamar na fada mai a jikin shi na rungumay shi amma kuma bazan iya yin hakan ba. Kamar wanda ya karanci zuciya ta a lokacin sai naga ya ware min hannayen shi da sauri ba bata lokaci na fada tsakiyan hannayen shi. Ya mayar ya rufe ni dasu ina jin yadda yake sauke ajiyan zuciya a hankali kamar yadda nima ajiyan zuciyar na sauke ina cewa sannu da zuwa yayana. Dago kai yayi tare da dan ture ni baya kadan nai mamakin hakan sai ji nayi yace niba tsoho bane da zaki dinga kirana wani yaya can na fada maki kuma sai kin biya bashin hakan da kika fasa min tunda na fada maki bana so. Da sauri nace iam sorry my life ai min afuwan please bazan kara ba da yardan Allah. Murmushi naji yayi tare da cewa yana tafiya ina tafe a bayan shi tare da jakar dana ansa a hannun shi. Zubewa yayi saman kujera yana lumshe idanuwan shi a hankali dakin shi na wuce na kai jakar na dawo na dauko drink hade da cup na nufo shi. Idanun shi suna a lumshe hannun shi na saman wuyan shi yana kokarin cire nicktie din da ya daura a wuyan shi. Na tsiyaya mai ruwan lemo a cup tare da dago cup din ina cewa uhmm, yaya love ga ruwa kajika makoshin ka dashi ko. Sai a lokacin ne ya dan bude daradaran idanuwan shi ya sauke idanuwan shi a kaina. Sai ce min yayi bissimilah ko tare da gyara zaman shi yana nufin na bashi. Gaban shi na dawo na tsugun na kadan tare da mika cup din a bakin shi a hankali yake kurbawa ina yi ina cire cup din daga bakin shi a hankali har ya sha fiye da rabin wanda na zuba mai a cup din ya daga min hannun shi yana cewa thanks. Haka yasa nagane cewa ya koshi ke nan na aje cup din daga gefe dayan saman table din. Nace mai abinci fa my love? Zan so idan na samu amma bari na watsa ruwa na sauke gajiyana tukun . Shigan da nayi yai matukar burge shi sosai don kayan sun min matukar kyau sosai english wear ne a jikina wando da riga yar rigan daga baya ne ya dan sauka min kadan amma daga gaba bude yake yana yauki sosai idan mutum ya motsa da jikin shi. Yana matukar bukatan matar shi a lokacin amna sanin cewa tana cikin period yasa shi daurewa tare da jan guntun tsuki kawai yana kokarin mikewa tsaye. Dakin shi muka nufa da taimakona ya shiga wanka ni kuma na kwashe kayan zuwa kaiwa mai wanki ya wanke su. Tsab na shirya dining din na jera mai komai yadda ya dace na aje shi tare da komawa dakin nashi don nagani ko yafito daga wankan. Na samay shi a tsaye gaban wardrobe din shi yana ciro kayan da zai saka a lokacin da sauri na kara tare da taimakon shi. Na fitar mai da wasu masu saukin sakawa a jiki na mika mashi sai da ya shirya muka fito daga dakin a tare da shi. Sosai yaji dadin girkin yafara ci cikin jin dadi da kwanciyan hankali sai dai yana mamakin yadda ya samu nai girki haka kaman nasan da zuwan shi garin ranan. Sallama mukaji a tare muke kallon mai shigowa gidan yaya Bashar ne sai su maigadi dake shigo mai da katan shi har dining din yaya Bashar ya karaso yana fadin kai mutumina dama dai an san da zuwanka ke nan wanan girkin haka ? Yai murmushi yace nima dai shine nake mamakin hakan kunyan maganan yaya bashar naji nai dan murmushi kawai. Gyaran jikin da akaimin jiya yasa nai wani irin balain kyau sosai kurciyana ya kara fitowa fili sosai a lokacin. Yaya bashar zama yayi sukaci abincin a tare suna hiran bayan robo a tsakanin su ganin lokacin sallah azahar yayi na sulale zuwa dakina nai sallah. Ko da na fito na samu sun fita hakane yasani sanin sun fita zuwa sallah ne. Bayan sun dawo a falo suka zube ranan a tare suka wuni a gidan can bashar yace kai bari na tafi gida nima gashi na hanaku walawa kaida yar kaunata. Dan tsuki yaja yana fadin kai wani angwancewa tun tafiyana fa take zuban jini wai har yau bai tsaya ba wanan ai yazama matsala ke nan ko? Haba wani matsala kuma kai mutumina badai har ka fara damuwa da rashin mace ba ke nan tare da kai. Yace I dont know gaskiya amma kila hakan ne kasan ina under training din ka ne ai dole ne na ji hakan . Kai ban son sheri kaji kai dai kawai kazo hannu ka shiga gari kawai amma ni yaushe na taba baka wani training can. Wanda kulkun kana cikin jajayen mata da bakake kuna kallon ko wace kala har gida ake kawo maku tayi fa nasan a raha don fatin jinin ku kawai. No no no kada kai min sheri wallahi bash ni idan ba a kan matana ba tunda nake ban taba aikata haka ba wallahi iyakata kiss kawai da mace ko shi ba wai wani can ba mai yawa. To yanzun kan kaunata ta cira tutan ta akan haka ta kawar da wanan rantsuwan ai a zuciyar ka ko? Ban sani ba yacd je gata can daki ka tambaye ta ina ganin zakafi samun amsanka a gurin ta. Yace wani don Allah rufa min asiri kaji kada kasa ana daukana da daraja na koma shasha . Sadauki yace dama may kake dan iska ita daine da bata san halinka ba take daukan ka wani kamili can. Nafito daga daki na samay su sai kwasan dariya suke tayi sai dai wanan karon akwai hijjab a jikina kasan cewan yaya Bashar yana a gidan haka yasani rufe jikina don shi tunda ba muharamina bane shi. Da hannu yaya sadauki ya yafuto ni lokacin zan shiga kitchen ke na hakan yasani na juyo garin su nuna Bashar yayi da hannun shi yace ga mai magana dake nan dama. Kallon yaya bashar din nayi wanda kunya ya rufeshi sosai yace Fatima kyale shi kin ji sherin shi ne kawai na juya kawai da murmushi na bar gurin su. Kayan tsaraba ne sosai yazo muna dasu na nan gida Nigeria daga doya manja mai kyai na kwarai irishi har buhu guda aka sayo. Na juya naji muryan shi yake cewa cire mashi kayan su yatafi yabar mutum ya huta cikin iyalin shi. Ni dai nabar gurin inda aka tara tsaraban na kalla gasu birjit dasu komai na girki an sayo bayan muna dashi. Na debo wa yaya bashar da yawa nakai mashi na koma tare da hado wasu masu yawa zan fita dashi yake cewa nawaye wanan din kuma ? Nace wai da su maigadi zanba don su suka shigo dashi gida yace yana da kyau hakan. Murna sosai masu gadi sukayi suna ta zuka min albarka tare da godiya kamar nice na,sayo kayan. Ban tsaya ba nafitar da namu dan kadan sauran na,shirya su na don za a kai can cikin gida gurin su mama. Haka muka kwana bai tabani ba sai faman juyi da tsuki yakeyi shikadai a inda yake kwance. Sai washe gari na barshi yana ta faman rankon barcin da bai samu ba daren jiya. Haka muka wuni ya fita zuwa gida ya gaida su mama da sauran mutanen gida. Bai dawo gidan ba sai da yamma lis bai bata lokaci ba yafita sallah Na idar da sallah magariba ina addua ban san da shigowan shi dakin ba sai jin shi nayi yace uh,umm, haba Fatima kin fara sallah shine baki fada min ba ko yaune kika fara sallah dai. Girgiza kai nayi yace what Fatima tun yaushe kikai wankan tsarki nace kwana biyu da ya wuce ke nan. Wani irin kallon mamaki kaman take kuma fuskan shi ya sauya a lokaci guda sai naga ya juta ya bar dakin . ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,, A LOKACIN MUKE,,, Suna zaune tayi murtuk da fuskan ta yarasa mai zaiyi wanda zai iya jawo hankalin ta ta sake mai fuskan ta ko zai dan ji sanyi a ranshi. Shi dai tun auren su shi dai ba zai ita cewa ga wani dadin wanan amaryan tashi ba da yaji a zaman su. Kullun a cikin bashi commad take yau tace wanan take so gobe tace wancan take so. Gashi iyanzun duk dan zarahin shi ya tafi baida wani kudi da zai juya a tare dashi. Gashi kuma a bangaren ta idan ba kudi ne ya kashe mata babu zaman lafiya a tsakanin su ko kadan. Shi da gidan shi amma har kofa sai Jamila ta rufe mashi don cin mutunci sai ya samo mata kudin nan da ta furta mashi tana so a gurin shi. Jin sunan shi da ta ambata yasa shi saurin juyowa da sauri a dan firgice da tace Ahmed fa dakai nake magana ka zauna kana min wani tunanen can dakai. Kaji na fada maka dubu dari shidda nake so ina son na kai babana asibiti saura kuma zanyi amfani dashi ne akwai bukin kawata da za,ayi ina son nasai mata abu mai munhinmanci don tasan inayin ta sosai. Nisawa yayi tare da gyara zaman shi yace Jamila wallahi ban san inda zan samu kudin nan ba yanzu don wallahi dan abinda ke hannu na kwata kwata baifi dari uku ba ma in har sunkai shine kuma nake dan juya muna. Rufe min bakin ka kai baka ji kunyan fada min haka ba kai dan gidan Alhaji Abubakar deller shine har zaka fada min haka ? So kake na yarda da karyan ka kana nufin haka zan zauna dakai ba wani karuwa sunan ina auren dan mai kudi ko may wai ? Kaji na fada maka in har kana son zaman lafiyan kakan ka nemo min wanan kudin dana fada maka. Ehe, don shine kawai kwanciyar hankalin ka don a zauna lafiya kawai kaji abinda na fada maka daga haka ta mike tashige dakin ta tare da rufo kofan dakin garam da karfi yamike yana fadin Jamila Jamila tsaya mana ki saurare ni. Amma ina har da key taiwa kofan dakin nan ya dafe kan shi yace oh my god wanan balin na jamila da may yai kama ne wai. A falon ya kwanta saman dogon kujeran su a takure haka ya kwana shida gidan shi ya koma kwana falo don masifa. Washe gari ma da masifan suka tashi a gidan don yana zaune ta hado abin karyawa duk dashine yasayo amma yana zaune, yana kallo tana shan shayi da kwai a gaban shi har ta shanye tass Ga jamila bata wasa da ci duk yawan abin nan zata iya cinye shi tas ita kadai yace a ran shi shiyasa take mulkan dan bura uban kiba haka tana curewa ita kadai. Shi ko sai rama yake yana aje dan dogon wuya kamar matikin lema dashi ganin babu sarki sai Allah yasa shi mikewa don fita ya dan samu abinda zaiciwa ran shi tun jiya da ya karya bai ci koma ba don fitan jamila a kan shi yai yawa . Gidan su ya nufa gurin mama Asiya don ya dan samu abin karyawa a can , duk yasan kullun yaje neman abinci sai mama tai mashi korafi kan shi matar shi da bazata girka mashi ba shi ke nan kullun zuwa gida cinye masu abincin su. Yau ma yadda yai tunanen masifan mama hakane a kan shi don fada ta haushi dashi tana fadin sai da nai maka gudun haka amma ka dage kai sai wanan yar daban matar taka zaka aura yanzun ga shi ko abinci ba ta iya baka sai ka kama labe labe gidajen mutane. Bai damu shi dai yace Rukaiyya ta debo mashi abinci kawai yaci nan ya hago kayan tsaraban da sadauki ya labto masu a gida. Yace kai mama har yanzu tsohon nan yana sayo maku abinci haka mai yawa ashe. Tace wani tsoho kanin ka dai sadauki shine ai yanzun zance mai muna sayen abinci duk wata. Kamar Alhajin ya barshi da wanan nauyin ne kasan su da son neman suna da iyayi waishi gamai hali kowa zai gwadawa hali . Dama ba musan uwarshi bace matsiyaciya yar taulali kawai su suka sani da shegen iyayin su wai su ga yan iyawa ke nan. Nan dai ya kwashi abincin shi sai da yai kat dashi yana ta sake sake a zuciyan shi. Sai da ya gama yamike yana cewa zai shiga gari yaga may gari ya waya yau kuma. ****** ********* ****** Ganin ya juya zuwa dakin shi yasani fahintar fushin abinda nai mashi na rashin nuna mashi nai wanka da yadawo yayi. Sai da na bata lokaci na sosai gurin gyaran jikina a gaban mirror na mike ina sake sake a raina na na kashe wutan dakin da A C nafito na nufi dakin nashi. Na samu ya kwanta ya kashe wutan dakin a lokacin jin motsina bai sa shi koda dan motsawa ba a lokacin inda na tako zuwa bakin gadon na kwanta a hankali a bayan shi. Bai motsa ba don jina saman gadon a tare da shi ganin ba zai motsaba nakwanta a hankali tare da dora hannuna a bayan shi. A hankali na dan fara shafa mai bayan shi amma bai sashi motawa ba sai dai ya dan sauke ajiyan zuciya kawai da naji yayi. Ban daina mai abinda nake yi ba sai ci gaba da nayi da mashi a lokacin ina kai gayi har na kai ga,tura hannu na acikin blanket din da yake rufe a jikin shi. Inda na sauke hannu na a kan abin shi na fara dan amfani da hannuna ina dan shafan shi a hankali tun yana daure ma abinda nake mashi sai gashi ya gyara kwanciyan shi da kyau ta yadda zaiji dadin abin da nake mashi da kyau. Ganin haka danayi yasa na ci gaba da mai yadda yake so sai kawai naji ya rugumoni shima ya shiga mayar min da martanin abinda nake mashi da farko. Mun dauki lokaci mai tsawo muna farautawa junan mu rai a tsakanin ni dashi har sai da naga na kawar da fushin da akeyi dani da farko. A hankali muke sauke numfashin mu don yadda muka aikatu da junan mu. Hannun shi naji saman kaina a hankali yake kwantar min da gashin kaina da ya tarwatse a lokacin can ya sauke ajiyan zuciya yana fadin. Fatima may yasa kika min abinda kikai min kika hanani more abinda Allah ya halasta min a kan ki. Shiru nayi sai da ya kara maimata min tambayan nace a hankali yaya kayi hakkuri please ni da naji ba ka tambaye ni ba shi yasa na kyale ka kawai don na dauko hutawa ne kawai kakeyi a ran ka. Fatima hutu,? Hutun may zan bukata a kan ki ke fa Allah ya kawo min ke daga cikin jin dadi na don may har kike bukatan wani huta na a hankan. Yaya don Allah kayi hakkuri hakan ba zai sake faruwa ba insha Allahu. Daga haka yai shiru tare kankamay ni a jikin shi sai dai naji ya furzo iska daga bakin shi kawai. Washe gari nan na barshi kwance yana barci bayan sallah asuba da mukayi nima har koma na kwanta amma ganin yana barci yasa na dan zare jikina nafita daga dakin na gyara gida tare da doro muna breakfast. Sallaman yaya Ahmed shiya sa na je na tayar dashi daga barcin da yakeyi. Sai da ya dan dauki lokaci ya mike yafito falon yana saye da bakar jallabiya a jikin shi mai laushi. Yaya Ahmed yana zaune sai bin falon yake da kallo ko ina yaya din yafito bayan har na kawo mai abin sha a gaban shi. Yaya sadauki yace Normal kai ne yau gidan namu da safen nan haka ? Yai murmushi tare da kurba drinks din shi yace na ce bari dai nazo tunda kai ba lokaci ke gare ka ba yanzun na mutane. Yace kai haba kaine dai kawai bamu haduwa da kai amma ai muna haduwa da surfaco yana nufin Imiran. Sai da suka dan kara gaisawa suka dan taba hira sai dan shiru ne ya biyo bayan kuma. Fahintar da yayi yazo da magana ne kuma yana jin nauyin yin magana yake ce mai yaya dai akayi ne Normal ? Yaya Ahmed ya dan murmusa tare da gyara zaman shi yace wallahi abin ne duk ya jagule min UF kwata kwata yanzun harkan san,ana yana son tsaya min gaba daya. Don dan abinda ke hannuna da nake juyawa yanzu sam kokari ma yake na koma ba komai a hannun nawa gaba daya. Gashikasan irin matar da nake aure yanzu sai a hankali ba kirki ke ga jamila ba ko kadan. Sadauki na sauraren shi sai murmushi yake yana dan kada kafan shi a hankali daya harde su guri guda. Yace yanzun yaya kake so ne don ban fahince ka bane inda zancen ka ya nufa gaba daya. Yace so nayi ka dan ranta min wasu yan kuli don na samu naci gaba da harkoki na dasu kada abin ya kwanta min. Sadauki yace kaman nawa ke nan kake bukata yace koda miliyan daya da rabi ne koma dai dayan ne idan zan samu zanci gaba da juyasu hakanan. Ok ba damuwa inji sadauki yanzu kabari idan na fita don tashi na ke nan daga barci amma nan zuwa two insha Allahu zakiraka kazo ka samay ni can site di na. Zai fara godiya ke nan ya daga mai hannu yace no haba ka bari mana wanan ba komai bane ai zan kiraka anjima insha Allahu. Yai mashi tayin ya tsaya su karya tare amna Ahmed yace sauri yakeyi ya fita da murnan samun nasara gurin dan uwan nashi. Wanka yaya yashiga yafito cikin kanan kayan shi masu kyau yya zauna ya karya sai dai kiran wayan shi da ake tayi yasa shi barin gidan da wuri hakanan. Zai fita ne nake cewa yaya dama nace don Allah mutanen nan naka ko zaka dan taimaka masu da dan wani abu don naga wata yai nisa kasan abu ga masu iyali. Kallon mamaki yake min yana gyara wuyan rigan shi yace wasu mutane na ke nan fa ? Nace cikin yar murya karama masu gadin ka tunda a karkashin ka suke da zama nagani. Humm kawai yace min ban samu amsa ba sai ce min da yayi sai na dawo ke nan ni zan fita ki bar wanan girkin zan samo muna abinda zamuci har na dare. Don naga kaman aiki yana son yai maki yawa zan wa maji magana ta samo maki wacce zata dan dinga taya ki aikin nan haka. Kawai nafi bukatan ki kwanta ki huta sai dai kawai ki kula min da shimfidana da kuma na yara in Allah ya kawo su. Nace kai yaya har ina wani aiki dagani sai kai kawai a gida in ma hakane don debe kewa kawai da a taimaka min na roko kaunata Aisha ta dawo guri na ko boko itama ta samu tayi. Shima shiru yayi bai min magana ba sai cewan da yayi ni na fita sai na dawo ki kwanta ki huta please. Yana fita na kammala komai da zanyi na koma dakina kaman ko yasan ina da gajiya a jikina sai barci. Yana fita har ya tayar da motar shi abu de mai get zai fita daga gidan yaja ya tsaya da sauri musa ya iso gare shi ya sauke glass din motan yace . Malam musa uwar dakin tace min kuna a cikin bukata na taimaka maku dashi sai dai ban da kudi mai yawa a hannuna amma ga ashirin ku raba har muga abinda zai biyo baya kuma. Nan yaja mota ya barsu suna ta zabga mashi godiya suna muna fatan alheri. ****** ********* ****** Ban falka ba sai kusan uku na rana na tashi a gagauce ne sallah tare da watsa ruwa a jikina na fito falo ke nan ban dade da fitowa ba ya shigo gidan. Da ledoji guda uku a hannu da sauri na mike na karbi ledojin dake hannun shi nan ya zube saman kujera yana ce wash duk nagaji wallahi. Bude ledan nayi inda naga take away ne yayo muna hadaden fridrice ne sai drinks da kuma naman rago mai zafi sosai. Ba mu ko je dining ba nan na dauko plate muka zauna, muka ci muka sha a tare sannan muka dan dauko hiran zancen abinda su Umma sukai wa mama Nafisa ta fada mata. Shi ya kawo min zancen amma a karshe ni ya bari da magana don shi ba ma,abocin son magana mai tsawo bane sosai. Muna nan zaune aka kirashi da waya yafita fitan shi bai dade ba da fita sai gasu nafisa da kawayen nan nata biyu sun shigo gidan. Suke ce min wallahi yunwa suke ji shine sukazo su ci abinci ban tsaya ba namike zuwa kitchen na dora masu abinci dafa duka nai masu yaji kayan hadi sosai. Sai da sukaci suka koshi muna ta hira dasu suna ban labarin wani mutum da yaso ya yaudare su duk sun tsorace dashi suka ce suna ganin kamar dai mutumin dan cult ne ma. Nace Anty ubangiji dai Allah yakawo lokacin auren ku ku huta da wanan rayuwan haka na. Kowan su tace min amin amin sai yamma lis suka bar gidan nai masu godiya suna jin dadi suka tafi abin su na koma ni kadai a gidan. Har na kara komai da zanyi na shiga nai sallolin na nafito falo musalin takwasa da yan mintina a kai. Nai kwaliya na don nasan duk inda yake bai nisa da dawowa gida a lokacin. Shiru shiru bai dawo ba har goma ya shude nayi sa,a ina kallon wani action film daya dauke min hankalina a lokacin. Ko da zan daga kaina na kalli a gogo har shadaya da wani abu na dare a lokaci don haka namike tare da kashe kayan kallon na koma dakina. Ban dade da shiga ba naji horn din shi ya shigo gidan maigadi yana bude mashi get. Shiru shiru banji motsin shi ba don nasan idan ya shigo sai ya fara leko dakina don nasan cewa ya dawo. Jin shirun da nayi ne yasani fitowa daga daki na falon yana da dan duhu sai na nufi gurin kunna wutan falon. Zaune na hango shi saman kujera shi kadai ya dafe kai yyai share share yana barci a zaune. Karasowa nayi inda yake a kwance din take na fahinci yau hannun agogo ya koma min baya yayi halin nashi ke nan. Gani haske wuta yasa shi dan bude idanuwan shi da suke mai a buge ya dan kalle ni a cikin mayen da yake. Cikin karfin hali muryan shi kasa kasa yace min ke kashe min wutan nan please ? Sai da na dan tsaya a kan shi na dan tsura mashi ido na wani dan lokaci na juya na kashe mai wutan na shige dakina na kwanta tare da fashewa da wani irin kuka mai tsuma rai. Sai dai duk yadda nayi nai barci na kasa yi don hankali na yana gare shi don nasan zai iya kwana a haka idan na barshi a gurin. Tashi nayi tare da share hawaye na na nufi falon har lokacin yana a yadda na barshi da farko a gurin. Dan bugun kafadan shi nayi nace mai ya tashi ya shiga daga cikin daki yace ke wani daki kuma nan ma gadon ai yayi min. Da kyata har da zagi na samu ya shiga daki ya kwanta na cire mai takalman dake kafan shi don har dasu ya haye gadon gaba daya ya kwanta dasu. Na jawo mai kofa na wuce zuwa dakina nasaka key kawai amma barci yaki daukana sai tunane nakeyi tausayin kaina dashi ya kara kamani nan naci kukana ba mai bani hakkuri har zuwa dare sosai barci ya dauke ni. Da asuba na tashi nai sallah na koma na kwanta don idona cike yake da barci kodana falka har naso makara zuwa school ranan. Gashi monday ne a guguje na shirya nafice daga gidan abina na samu masu aiki suna aiyukan su a waje nan suke gashe ni da min godiya jiya maigida yai masu alheri yace daga gare ni ne sakon. Murmushi nayi kawai na masu sai na dawo na fice gidan zuciya tab da bacin rai da bakin cikin wanan irin rayuwan da na shiga. Ina isa school na samu har lectura mu ya shiga ko na samu yabarni nashiga na zauna. Bazan iya cewa ranan na fahinci abinda akayi ba a lokacin don irin yadda nai nisa ga tunane. Sai sha daya saura ya falka ganin yadda lokaci yakai yasa shi mikewa da sauri ya fada bathroom yai wanka yazo yai sallah. Inda ya idar da sallah ya zauna yana tunanen abubuwan da zai iya tunawa a lokacin . Tabbas yasan nasan yasha ta juya ya kalli godon nan ya fahinci ban ma kwana a dakin ba ke nan. Hakan yasa jin wani iri bai so shan komai ba ta yadda zan fahinci akwai abinda yasha amma sai yasha dozes da yawa yadda za,a fahinta yasha din. Baiji dafin yadda yasha har na fahince shi ba sai yaji kunyan kan shi kawai ya kamashi da wani ido zai kalle ni yau. Yuwan da yaji yasa ahi mikewa zuwa dining yaci abinci amma ya samu babu komai ya leka kitchen din yaga ba alaman ma na leka kitchen din yau. Dakina ya nufa yaji shi a kulle sai lokacin ne ya tuna ai Monday ce nafita gidan ke nan zuwa school. Koda muka futo daga class sallah nayi na koma cikin motana can na zauna nai kukana mai isa na maryam tana ta nana bata samay ni ba sai da tai dabaran zuwa gurin mota ta hangoni. Ta kwankwasa min glass din da kyat na bude mata bayan na saita kaina . Kallin mamaki take min motan ta shiga itama ta zauna tana min wani kallon zargi. Can tace Bintu may ke faruwa ne wai? Babu komai na bata amsa tai murmushi tace haba Bintu babu komai zaki shige mota ke kadai kina kuka haka? May yafaru ki fada min nace ba komai anty tace da komai kan yaya ne ko ? Shiru nayi saida takara cewa yaya ne ko ya tayar da halin nashi ke nan ko ? Ban san lokacin dana fashe da kuka ba itama kukan ta fashe dashi tana cewa watau ashe yaya baibar halin nan nashi ba ke nan. Nifa kwanaki yaya ke fada min cewa bai bari ba amma yasan zaki taimaka mai ya bari insha Allahu. Nace ni anty yaya zanyi da wanan halin na yaya may yake son nai mai wanda ban mashi da zai min wanan sakauyan haka? So yake idan na fita mutane su dinga nunani ga matar mashayin can ko may ? Anty bazan iya ba gaskiya duk son da nakewa yaya dole na barshi yafi min sauki wallahi. Tace haba Bintu inkiyi haka baki kyauta mashi ba dashi da maji dama mu yan uwan shi. Baki ganin auren ki dashi ya kawo mai sauyin rayuwan shi da dama ya canza sosai kamar bashi ba. Hakkuri zakiyi kawai ki jajir ce mashi ke ma kinuna mai yanzun kina da fawa akan shi kamar yadda take dashi akanki. Tana saki yana hanaki kema din nuna mashi ke jaruma ce ba wai abin hannun shi kike so ke shi kike son ya gyaru ba wai abin alatun da yake kashe ki dashi ba. Nan dai taita bani shawara take ce min kuma zata fadawa maji halin da yake ciki don itama ta tsawata mashi. Da sauri nace kada ki fada mata anty ki bari na gwada nawa sa,an mugani idan bai bari ba sai mu sanar da ita. Tace to shike nan amma gaskiya badon kince haka ba dana fada mata don ta san bai dena ba har yanzu. Sai yamma na shigo gidan na shiga dakina nai sallah nan ma kuka na zauna nayi sosai a gurin sai da naji yunwa namike don neman abinda zanci tea nasha don hanjina ya dan warwale a lokacin. Sai da nai sallah magariba ne na zauna ina tasbihi har akai kiran sallah na mike na gabatar da ishai. Wanka na kara yi na koma kan gado na na kwanta sai ga kiran anty maryam ya shigo min muna cikin magana da ita ya shigo dakin. Ban ta da kai na kalle shi ba na ci gaba da wayana kawai shima bai fita ba tana tsaye ya kura min ido kawai. Sai da mukai sallama da ita ne yake cewa kin dawo ashe ? Umm kawai na bashi amsa dashi batare da nai magana ba na juya ina saka wayana a caji kawai. Ganin ba zan juyo gare shi ba yasa shi cewa abinci fa naga banga komai ba a table. Ban yi ba na bashi amsa a takaice kawai. Bakiyi bafa kikace nace mashi eh kawai. Ya dan tsura min ido take ya gane cewa nasha kuka yadda idanuwa na suka koma luhu luhu dasu. To may zaki ci dabaki girka ba nace ban jin yunwa ni daga haka na mike ma nashige bathroom don ban ko son ganin shi wallahi. Ganin nashi bathroom yasa shi juyawa ya fita daga dakin fita yayi daga gidan zuwa sayo muna abinda zamuci da daren. Jin yafice yasani fitowa na sawa daki na key kawai na koma na kwanta abina can bai wani dade sosai ba ya dawo gidan. Murda kofan tayi yaji shi a kulle ya kwankwasa ban bude ba ya kira wayana jin kiran shi na kashe wayan gaba daya na kwanta abina. Ganin bafa zan fito ba yasa shi ya zauna yadanci abinda yasayo muna duk da ba dadin ci yake ji ba a lokacin. Haka yamike yaje ya kwanta cike da tunane kala kala ta yadda zai bullowa al,amarin namu. Yasan baida gaskiya amma haka zai daure ya dakatar da abinda nake shirin haifarwa a lokacin nan. Don shi yana ganin don may zan so takurawa rayuwan shi kawai ina ruwana da bukatan shi may ya rageni dashi na rayuwa da zance zan hanashi nashi kalar rayuwan. Har barci ya dauke shi bai gama tunanen abinda ya dace ya aiwatar a kaina ba hakanan. Washe gari ma kafin ya dawo motsa jiki har na bar gidan ko na fita yai mamakin hakan shi da kan shi ya nemawa kan shi abin karyawan da zaici. Da wuri na dawo nai girki na aje mai saman table nashige ciki abina ban kara fitowa ba. Yana shigowa a lokacin idon shi akan table yaga abinci a gurin yakai kallon shi ga kofana yana saye yasan dai ina ciki a lokacin tunda babu inda nake zuwa. Dakin shi ya shiga yai sa,a yau ma na gyara dakin bakamar jiya ba da na hau sosai. Murmushi yayi kawai ya shiga wanka a lokacin yafito yasaka kayan shan iska don zafi akeyi sosai lokacin. Dakina ya nufa don ganin har lokacin ban fito falo ba ina dakina a kwance nake kasa saman ties idanuwa na a rufe ina bin kira,an dake tashi a wayana a hankali. Ya dan dade tsaye sai jin nauyin mutum ya shigo dakin danayi yasa ni bude idanuwa na da suke min a rufe. Yana tsaye a kaina ya saka hanayen shi a cikin aljihun wandon shi tare da kura min idanuwan shi. Ganin shi tsaye a kaina bai sa na bude idanuwan nawa ba sai kara lumshesu danayi kawai. Dan tsugunowa yayi tare da rage tsawon shi ya tabo kaina da sauri na bude idona na watsa mai wani irin kallon tsana da ban masan lokacin da nai mashi shi ba. Yace ki taso muci abinci nace akoshe nake ya mike tsaye yana cewa to sai kizo ki zuba min ai. Nace ai banice mai zuba maka kwayan ka ba idan zaka sha don haka sai kaje mai baka kayan mayen ka ta baka amma bani Fatima ba. Da mamaki ya kalleni yace ke kada ki soma kice zakiyi min rashin kunya wallahi. Nace da ke nan da nake daukan ka a mutum ba yanzun da ka zube min ba. Ke ni kike fadawa haka watau kin raina ni ko don kin ga kamar ke kin isa ko may wai. Nace aini ban isa ba kuma ba kowa nake ba don haka kowa tashi tafishe shi kawai. Kaman zai yi magana sai kuma ya juya yafita daga dakin ran shi a bace yana ci yana kallon kofa na ko zan fito daga dakin amma shiru har ya gama babu alamana a falon. Gaba daya taji gidan ba dadi ban fito ba sai ma da naga tara da rabi na dare kawai na kulle kofana na kwanta kawai. Goma da rabi ya kashe kayan kallon da komai na falon ya shiga daki sai da yasa kayan barcin shi har ya kwanta ya mike zuwa dakina ya murda a rufe kofan yake a lokacin haka ya juya ya koma don yasan bazan bude ba. Bai taba tsanmanin cewa akwai shakuwa haka a tsakanin mu ba kuma ba zai iya daure rashi na ba a yanzu sai da yaga yai rabin kwana yana lalaban gefen da nake kwantawa bai jini ba. Nima a nawa bangaren kusan hakane na kwana da kewan shi duk da haushin shi da nake matukar ji a lokacin. Kowan mu da tunanen dan uwan shi ya kwana a ran shi cikin damuwa muke . Tun da safe ina kitchen ina hada abinci yazo bakin kitchen din nai matukar mamaki da bai fita motsa jikin shi ba yau. Kamar ban san yana gurin ba na share shi ya tako har zuwa cikin kitchen din inda nake tsaye ina motsa dankalin dake saman gas. Ganin da yayi bazan mai magana ba yasa shi cewa kin tashi lafiya ? Nabashi amsa da lafiya kawai. May yasa kike rufe min kofan ki kwanan newai Fatima ? Dagowa nayi muka hada ido kawai sai na kawar da kaina naci gaba da abinda nake yi ina tunanen watau bai masan abinda yayi ba ke nan koko tsaban rainin wayyo ne hakan ? Ke nake tambaya ya maimata min . Kaina na girgiza mai nace ina kwashe dankalina a tunkuya a hankali. Nace ban da amfanin komai a gare ka don shaye shayen ka yafini daraja a gare ka nagani. Don haka kaje kayi abinka kabarni na yarda na zama ma yar aiki kawai a gida don shine ya dace dani. Murmushi yayi ganin zan wuce ya dan ja dabaya ya bani hanya yana fadin wanan kuma maganar kice amma ni shana baida alaka da kusantar ki a gare ni. A ganin ka ba amma ni bazan taba mu,amula da mutumin dake a cikin sabon Allah insha Allahu. Ido ya zuba min don jin abinda nace ya fahinci a shirye nake na zuba mai bakaken maganganun dake a bakina a lokacin. Shiru yayi ya dan dade tsaye a gurin yana kallon yadda nake aikina a cikin tsabta da gwanewa sai ya juya kawai yabar kitchen din zuwa falo ya zauna cikin damuwa. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,, A LOKACIN MU KE,,,, Gaba daya na daina kwaliya a gidan na daina fitowa falo yadda na saba na zauna a tare dashi, gashi wasa wasa mun fi sati daya haka sai zaman yar tsama mukeyi a tsakanin mu. Shi kan shi har bashar ya fanhici yana da yar matsala a tare dashi sai dai bai san daga ina matsalar take mai ba. Tunda zurfin ciki irin nashi bai bari ya fadawa kowa halin da yake ciki balle a bashi shawaran da ya dace dashi. Zaune suke ga system ya aje a gaban shi amma ya kasa sauraren bayanin da bashar yake mashi a lokacin. Shiru bashar yayi yana kallon shi can yake cewa wai may ke faruwa ne sadauki naga fa duk kwanan kana cikin dan damuwa. Guntun tsuki yaja yace may ga nine wai lafiya kalau nake bashar ya hade hannayen shi biyu guri guda ya tagumi dasu ta kasan gemun shi yana kallon abokin nashi na tsawon dan lokaci. Can yace tabbas akwai matsala a tare da dakai wanda nake gani kamar daga gida ne ko gurin kaunata Fatima? Nace maka babu komai murmushi bashar yayi yace wallahi akwai komai kan don ni nagani kafada min may ye matsala please ? Don nima shawarana da matsala bata wuce ka akan may kai zaka dinga boye min damuwan ka wanda a gaskiya banjin dadin hakan wallahi ko. Kallon bashar yayi yasan abinda yafadi gaskitane har cikin ran shi ya dan ja tsuki ya mike tsaye tare da saka hannin shi a cikin aljihun shi ya nisa gurin window office din ya nufa yana kallon waje can ya nisa kadan ya juyo inda bashar yake zaune yace. Bashar wallahi Fatima tana son jefani a cikin wani hali saboda dan dalilin ta mara amfani. Ai tasan yadda nake ta amince ta aure ni amma kuma may zai sa yanzun sai da na yarda da ita zata bijiro min da,wasu akida nata na daban can. Bashar ya ce tare da mikewa ya dan tako zuwa inda sadauki yake a tsaye yace ban fahinci tasan halinka ba ta yarda ta aure ka haka nan ? Yace kai tsaye kwarai eh ai tasan koni waye tasan ina sha aiko ? Bashar ya rintse idanuwan shi don takaici yace haba haba man kaida bakin ka har kake ikirari da sabon Allah haka why why please. Lokaci yayi fa da zakaiwa kan fada kafin ai maka yau tun kuna kubiyu kaida Fatima inaga sai yaran sunzo an fara masu gori a makaranta akan shan ka. Idon shi ya rutse yace kaga abinda yasa ban sha,awan auren ba hausa tun farko amma maji tanace akan wanan yarinyar sai nayi. Ita Fatima har ta isa ta hanani abinda nakeyi ko nai niyar yi kamar ta who is she bad way ? Itace ko wani abu don gashi saboda ita ka shiga bakon yanayi kana gani Fatima ba wata haske bace a rayuwan ka halan. Ya dago ya kalli bashar ido da ido yace haske haske fa kace yace to haske may Fatima take a gare ni kuma? Bashar yai yar dariya tare da dan buga kafadan sadauki yace ko wani irin haske nw a yanzu kafi ni sani wallahi. Halan ka shawo har ta fahinta da hakan ko yace wai shine takewa fushi kwata kwata yanzu ta daina kulani har yar kwaliyan nan ma ta daina yin shi kullun tana daki a kumshe tana hadiyan bakin ciki. Bashar yace da sauri kagani kagani zaka kashe yar mutane saboda mugun halin ka ko ? Yace oh nima ma zan kasheta ba itace zata kashe ni ba ita da takasa bani hakkina dake a kanta. Wallahi ta shiga hankalin ta don tasan idan yau nace zan cika uku a gida na zan iya wake da hasara ba ita ba. Dariya bashar yayi yace wallahi da watan kunyan ka ya kama a garin nan don kafin ma ka gama zagaye dakin su ka dawo gareta gari yasan ko kaiwaye ko ? Jeka auro mata uku yau kagani waye a matsa in ba kai ba zata kwabe mawa. Kana zaune kalau da matar ka kai mata abinda bata so ta dauki mataki maimakon ka bata hakkuri ka lalashi abinka tunda kaine baka da gaskiya amma wao kai shine har kake neman hanyan kuntata mata Allah ya baka sa an auro mata ka tara a gida tinda kana da kudin hakan . Wallahi batin fada maka mata da kake gani suna da nasu ranan idan kace bazaka bari ba itama rana da hanyan rama cutar ta akan ka sai ka shiga hankalin ka. Fatima dai ce ba yadda zakayi da ita don tai maka zara a zuciya kuma muddin bakane me shiri ba har mama taji naka ya samay ka kuma ji zarayi tunda inta gidana ta samu labarin halin da kuke ciki. Dariya yayi yace ashe kaima kasan maryan magulmaciya ce ke na kyashan ta manne da sarki. Yace to dakata don kawai tana gyara shine zakai mata mugun lakanin suna kawai wallahi yanzu zamu saba dakai akan maryam. Kallon bashar yake yana dariya yace kai dai ka fadi da bakin ka bashar yace ai mantawa nayi a gaban makiyin mu nake. Yace wallahi kaje kasan yadda zaka rarashi fatima ku fahinci juna idan ma kana fasa wanan shan yafi maka alheri don ko wata mace bazata ji dadin ace mijin ta ko dan ta yana sha ba ga mata da gorin tsiya wallahi. Sun dauki lokaci suna musayan magana kan zancen karshe bashar yai mashi sallama akan zai tafi gidan Inna ya gaida ita bai samu zuwa da safe ba. ****** ********* ****** Yashigo gida fuskan shi a sake ya samay ta zaune a falo ta kunna tv sai kida da rawa na yan iska ake a wani tasha na kasar ghana. Zama yayi a gaji saman kujera ta watso mashi harara tace kasamo kudin ne da ka dawo min gida haka? Kallon mamaki yai mata yace cikin karfin hali wai Jamila may yasa baki son a zauna lafiya ne ke ? Tace lafiya kudi kaima kasan idan ba kudi ni ba zaman lafiya gare ni don dasu nasaba. Kasan wallahi inda ba kudi kai Ahmed baka isa ka aure ni ba don kasan da wa yanda nake hurda a baya. Murmushi yayi yace Jamila ke dai in ba kudi sam babu zaman lafiya dake ni yanzu fa ban son abinda ya taba min rayuwan yar matata don ashirye nake akan duk bukatanki ko ina zan shiga na samo maki don kiji dadi kawai. Hararan shi tayi tace in kana son kaji dadi na mike min su kawai inji dumus sai kaji dadin nawa. Hannu ya tura a cikin aljihun shi yana fadin angama inda za a bar ni yau na shafi wanan body da ake min kwalelen ka dashi kwana biyu. Kudi ya mika mata da sauri ta fisgi kudin tare da sake wani murmushi tace dama nasan kana dasu ai boyewa kawai kayi don kaji may zanyi. Ajiyan zuciya ya sauke a ranshi yace don baki san zubar da kaina danayi na samo su bane don kwadayin ki da masifan ki kawai. Yana matukar son jamila a ranshi do ba laifi yarinyar ta iya gado sosai gurin ma irin hakane suka hadu da ita har yaji ya kamata ya aure ta kawai yanuna mata karya ya auro ta din duk da mama asiya taso kawo cikas ga maganan amma yai sa,a ba ya yarda akayi abin. Ranan kan yasan ya kawo kudi don tun wurin suka fara harkan ma,aurata a tsakanin su duk bashin da ke kan su na kewan junan su sai da suka biyawa kansu. Don jamila irin matan da basu iya kwana biyu ba tare da namiji bane ya kusance ta. Tun a gaban shi bayan sun huta tafara kashe kudin gurin sayen banza da wofi yana kallo ba yadda zai yi don son da yake mata. Ranan da dare ma tare suka fita yawo da ita ya kara kashe mata dan canjin dake hannun shi kuma. ****** ********* ****** Ina zaune a dakina kayana da aka wanke nake kokarin nikewa a lokacin don najera su a wardrobe dina. Dakin ya shigo saye yake cikin kayan barcin shi sau daya na daga kaina na kalleshi na kawar da kaina tare da ci gaba da abinda nakeyi a lokacin Karaso yayi bakin gadon da nake zaune yai tsaye akaina tare da kura min idon shi na wani dan lokaci. Can naji muryan shi yana cewa kina ganin kamar wanan abin da kika zaba zai fishe mune Fatima. Banyi magana ba illa mikewan da nayi tsaye na kwashi kayana zuwa cikin wardrobe dina dasu. Ina ajewa na juyo ban san yana tsaye a bayana ba sai ji nayi ya rike ni kawai na dago idanuwa na da sukai ja don bacin rai nace may ye haka malam. Oh tambaya ma kikeyi don na taba mata ta ko may ? Zan wuce daga gefen shi sai naji ya kamoni yace ina zaki sai kin fada min may ye wai matsalar ki ne a gidan nan. Nace cikin kukan da ya kubce min kai yaya kai kaiyaya sadauki kaine matsalata yaya. Murmushi yayi ya jawo ni zuwa jikin shi duk kubce kubcen danakeyi sai saman gado na ya dire ne. Nan ya shiga kokarin cire min kayan dake jikina har yai nasara rabani dakayana. Nan ya shiga sarafani yadda yake so raina yai matukar baci tankar da dutse yake amfani a lokacin . Har yagama abinda zaiyi ya koma gefe daya yana mayar da nufashi a hankali. Kuka nake sosai don abinda ya aiwatar min a yanzu yai matukar bata min rai. Nace cikin kuka abin yakai kuma har da fyede ka koma yi min kasani wallahi idan ka zalunce ni sai Allah ya isar min. Dagowa yayi da mamaki don bai taba jin makamancin wanan kalman ba a gare shi yace. Fatima nikike jawa Allah ya isa don na taba ki kawai ko may ? Nace bayan na dan daga ina kallon shi da idanuwa da sukai ja nace kai bakaji kunyan tabani ba kana cikin rashin tsarki? Nine banda tsarki Fatima nace ina kaga tsarki mutumin da ya mayar da sabon Allah abin yin shi. Mutumin da bai tsoron haduwan shi da Allah cikin ko wani irin halin zai riske shi ko a maye ko a kalau. Mutumin da baida mu da halinda na tare dashi suke ciki ba akan mugun halinda yasa wa kan shi don son zuciya. Ni wallahi yanzun ko da ake cewa wai yimaka akayi kake halin nan ban yarda ba har da hali ma. Ka cuce ni wallahi daka kusance ni a cikin rashin tsarkin zuciyan ka wama yasani ko ka shawo ne kazo min a haka tunda ba imani ke gare ku ba. Idan kace wanan halin baza ka daina ba nima wallahi bazan iya zama da mashayi ba tubur na haifi diya ana masu gori na fita gidan buki ana zunde na nashiga mutane ana nunani. Kuma wallahi,,,, Ke ya ishe ki hakana nagaji da jin mugun kalamin ki a kaina haka na ko don kinga na damu dake ne zaki tsaya kina fada min magana son ranki. Damuwa damuwa fakace yaya da kadamu dani dabakai haka ba wallahi dakaso abinda nake so maka a ranka. Ni dana damu dakai aina fahinci abinda kake so da wanda baka so kuma na kiyayye su don azauna lafiya. Yadda kake ganin an tursasa maka aurena wallahi nima haka aka tursasa min auren ka badon ina so ba. Amma nai hakkuri na zauna ina maka addua a kullun na Allah ya shiryaka kamar yadda mahaifan ka suke maka a kullun. Amma kassh kai yaya baka sawa ranka daina wanan halin mayen ba kaduba fa yadda kainan ka Nafisa maye ya mayar da rayuwan ta. Idan badon Allah ya nufa mamatana tsaye da addua ba akan ka da yanzun ka fita lalacewa a hakan. Nikan gaskiya ba zan zauna da dan maye ba don idan akwai abinda na tsana shine maye a rayuwana amma kuma ina kaddara ta riga fata yau gani Allah ya nufe da mai shaye shayen da baida ranan barin shi a rayuwan shi. Yana sauraren maganan da nake fadi sai dai baiyi magana ba har lokacin karshe ji nayi barci ya dauke shi. Har na mike na shiga bathroom nai wanka nafito nai nafila na zauna ina kara kai kukana ga Allah akan al,amarin nashi. Nagaji na taso daga inda nake na kwanta daga gefen gadon nan nima barci ya dauke ni ban sani ba ina cikin tunane. Da safe ko da na falka na samu yafita daga dakin bai kuma tadani ba don ganin da yayi ina barci a lokacin saboda yasan ban samu barci ba a daren jiya din. Bayan na sallah na kimtsa jikina na shiga kitchen na hada abin karyawa na jera su atable na shige daki abina na kwanta. Har ya gama abinda yake ba alama na a falon haka yasa shi leka dakin kwance nake rub da ciki kamar mai barci sai dai yasan ba barci nakeyi ba a lokacin. Daga kofa yake ce min shi zai fita sai yadawo ban dago ba kuma banyi magana ba haka yasake labule yafice daga gidan. Jin fitan shi yasani fitowa daga daki na gyara ko ina nagidan tsab na dora muna abincin rana again. Bai shigo ba sai bayan la,asar naji shigowan shi ya shige dakin shi ina zaune ya shigo cikin shirin shi yana cewa ni zan tafi ga wanan ki rike a gannun ki sai badawo. Da kyat na iya bude bakina nai mashi adawo lafiya yafita daga gidan ranan ban rakashi ba yadda na saba yi mai wanan abin ya kara bata mai rai. Sai washe garine yaya Bashar suka zo gidan da maryam mun gaisa da su muna zaune tana min sheri wai na kore mata yaya a gari saboda halina. Idona ya kawo kwalla nace cikin wata murya ta mai kararen zuciya haba anty don kawai baison a fada mashi gaskiya kawai. Muryan bashar ne yake cewa Fatima kiyi hakkuri shi kan shi yasan bai kyauta maki ba kuma yaji nauyi da kunya da ya sani. Hakan da kikai mai kin kyauta gara da kika rufe idon ki kikanuna mashi abinda yayi ba alheri bane. Don idan mutum yana aikata barna a doron kasa bai samu wanda zai rufe ido ya fada mai gaskiya ba komai dacin shi sunan wanan mutum din tabbabe wallahi don baida ranan daina a rayuwan shi. Amma kuma ke kuma kin tauye shi da yawa Fatima kin hana mashi hakkin shi bayan kin saba farauta mashi. Kunyan maganan shi naji na saddada kaina akasa yace gaskiya kin hora min abokina wallahi. Yace ko yar kwaliyan da kike mai da taro haba haba duk kin daina yi mashi su haba Fatima adai dan sasauta mashi mana. Maryam tai tsagal tace akan may zatai mashi tunda shi baisan ciwon kan shi ba har yanzu ba gara ta kama kan ta ba. Yace to gama dama ai yace shawaran ku daya da ita kece coordinater din ta. Dariya mukayi nace babu ruwan anty kada yaga laifin ta a banza bataci batasha ba halin shi daine bai min ba yaya. Yace to kiyi hakkuri Fatima tinda dashi Allah ya hada ki zama nifa ina ji ajikina insha Allahu zai daina nan gaba. Tinda kinga yanzu yarage sosai inda dane ai abin ba dama wallahi don baku san irin halin da na shiga dashi bane a baya kafin ya aure ki. Amma aikinyi sa,a ma yana shayin ki yana tsoron yayi ki gane ko ranan ina ganin akasi aka samu kawai. Duk wanda yai mai asiri bai fasa ba mai shi yana kan yi har yanzu don dai suga ya lalace kawai a rayuwan shi. Maryam tace ina fa suka fasa kwanaki da nafisa tai shaye shayen ta ai ta fadi amma aka mayar da abin haukan tane kawai yatashi take fadin hakan. Bashar yace ai zan koma gur8n mutumin nan da muka taba zuwa don wallahi Alokacin ya daina kwatakwata dawowa abin yayi. Kuma zan fada maki wani sirin shi idan yana son sha zagiga idon shi sun rine sunyi ja jajir dasu yana dafe kan shi yana dan murzawa to yana sin yasha ke nan. Kuma ko a gidan yana da kayan maye har na shayin su da yake sa kina dafa mashi da hannunki amma ke baki sani ba. Nazaro ido nace wallahi ko duk dare yaya sai na dafa mashi bakin shayi mara sugar da madara yasha. Yace to sune yake sha yanzun dai kafin ya dawo insha Allahu zan koma kauyen nan naji may ke ciki akan al,amarin don idan akwai wanda zaki bashi yaci batare da yasani ba sai ki hada mai. Nace nagode kwarai yaya yace kiyi hakkuri kinji ban son mama taji wanan zancen ko kadan don kada ciwon ta ya tashi. Nace nima shine wallahi amma badon mama ba ranan wallahi dana gudu gidan nan yaya. Yace no no don Allah kada kije ko ina kefa haske ne a gare shi Fatima. Zamaki tare da Sadauki wani falala ne ga kowa ga masu gadinku suna fada min irin alherin da yake masu akan ki. Idan kinyi haka mama bazata ji dadi ba masu hassada akan auren ku kuma zasuyi farin ciki sosai. Maryam tace ai bata ma zuwa ko ina mutu ka raba ita da yaya sadauki sai dai yan bakin ciki su mutu. Mun kai wani lokaci dasu suna bani shawaran yadda zan kara bullowa al,amarin. Sukace zasu tafi don zasu shiga gaida Inna gidan ta a lokacin nai masu rakiya har waje suka tafi yaya bashar yace yace akawo maki kayan abinci sai gobe za,a shigo dasu don ina ganin zai dade a can ne. Har ya shiga mota yake cewa kin ko kirashi kinji saukan shi na dukar da kaina ina dariya yace don Allah ki kirashi nace mashi to kawai . Amma bazan kiraba nace a cikin zuciyata indan yadamu yakirani in kuma bai kira ba ajira har ranan da ya dawo din. Jin za,a kawo min wasu kayan abinci na shiga kitchen na auna shinkafa da taliya don tun na garan mu sunanan ba ai komai dasu ba na kira malam Atiku na bashi kowan su leda guda guda da dubu uku uku na cefane akan Allah ya yaye mai wanan lurar tashi. Suna ta godiya suka fice kowa yakai nashi gida don dama a bukace suke a lokacin don abin sai shukaran kawai. Na idar da sallah la,asar naji anata kwada sallama daga kofa nafito ina karba sallah ma. Na so sheda matar amma na manta ida na san ta a baya muka gaisa da ita cikin sakin fuska take ce min baki gane ni ba ko hajiya ? Nace na dai so na gane ki tace Allah sarki yanzu maji tai min waya wai nazo na zauna dake don maigidan bayanan kuma tace ma zata bugo maki waya ai. Nine Rabin dan musa uwar goyon sadauki a baya nace cikin sakin fuska Allah sarki wallahi mama ban gane ki ba saudaya na taba ganin ki ranan da kika zo gaida mama ina gida lokacin. Na mike tare da amsan ledan bakon dake a hannun ta na shiga mata dashi dayan dakin da anty Amira ke sauka a cikin shi. Nace mata ga daki nan inda zaki zauna mama tana washe baki tace ai da ko nan kika barni ma yayi min wallahi ko. Nace kai haba dai nan a waje mama tace ina wajen yake nan na je na kawo mata abincin mai yawa taci sai da ta koshi tana godiya. Mun dayi hira sai da magariba ya gabato muka shiga daki don yin alwala da sallah. Da dare ma mun dan taba hira da ita take ta bani labarin irin zaman da akayi a baya a gidan su sadauki yadda maji tasha wuyan su Umma da mama a baya. Sai zuwa goma mukaiwa juna sai da safe kowa yanufi dakin shi ya kwanta. Washegari kafin duk ince nafito na samu ta gyara gidan tas ta goge ko ina tai wanke wanke nace bayan mun gaisa haba mama baki huta ba kuma wanan aikin haka tace min haba to may yakawo ni gurin ki ba don na taimaka maki ba na zauna kuma ina kallon ki haka uwar dakina. Tun ranan itace mai gyara gida iyakata nai muna girki kawai wanda zamuci ko girkin ma tace bata iya ba da abinda mukeyi sai da icce amma in koya mata don watarana. Shine dalin idan zanyi girki muke shiga kitchen da ita tana kallon yadda nake aiyuka na. Yau satin shi daya da tafiya baikirani ba ban kirashi ba muna zaune a falo da Iya take ce min wai ke yar nan ni banji kuna waya da maigidan ba mana. Sai da na kakaro murmushi a fuskana don tambayan nata yazo min a bazata lokacin . Narasa may zance mata sai nace cikin murmushi lah iya ai shi sai tsakandare yake bugo waya kin san lokacin mu ba daya bane dasu can namuna rana sukuma suna dare ne. Tace Allah sarki ni kan dai ince yaran yanzu baku wasa da waya da mazajen ku shiyasa na tambaya ai. Takara cewa ba dai dan nawa yana lafiya ba dai ko nace lafiya yake yana ma yawan tambayan ki na ce mai kalau ki ke. Tun da na fadawa Iya Rabi haka shikenan bata sake tambayana komai a kan shi ba kuma. Abu kamar wasa yau satin sadauki biyu rabon shi da gida amma ba waya daga gare shi da farko abin bai damuna amma daga baya sai abin ya fara ci min rai kuma. Mun shiga daki kenan munyi sallama da iya Rabi sai naji wayana yana ringing da sauri na isa furin don na dauka murja ce wata course mate dina da muka dan shaku da ita. Nobar kasar waje ne daga US na dauka da sallama a bakina naji ya amsa sallaman nawa cikin wani murya. Sai kuma mukai shiru gaba dayan mu can yake cewa Fatima yanzun kan na sheda dole akai maki a kaina don yadda kika nuna baki damu ba dani. Nace dole dai akai muna da juna aikama kasan kabar mai gadi gidan ka baka damu dani ba. Hmm naji yace yace wanan kuma mafanan ki na rasa ke wata irin yarinyace haka mai taurin kai dake. Kina nufin idan munzuba ni dake waye zai sha wuya a cikin mu ne wai kefa mace ce ba kowa ba. Nace oh don ina mace shine akace ban san right dina ba ko komay ? Idan kina ganin halin da kika dauko yi min zai sa na daina abinda kike ganin zan daina sai ki matsayi ai gafili ga mai doki. Nace ban ma son ka bari don ni ai nafison kabari don Allah da iyayyen ka da zurian ka masu zuwa. Yace oh ashe kin sani kik matsawa wa kanki nace ni ban matsawa kaina da komai ba sai dai kawai ina tsoron mu,amulane da wanda baida tsoron Allah kawai. Yace na gode nima haka nabashi amsa sai naji ya furzo iska yake cewa ance Rabin dan musa na gurin ki ko ? Nace oh iyaba tananan yanzun ma ta kwanta don muna tare yace ok ina son ki kula da ita sosai don tana da mutunci sosai nace insha Allahu zanyi yadda kace. Bashar ta kawo maki kayan abinci nace eh amma kasa akwai su dama kuma ka karo wasu shiya sa na diba wanda muke dashi na ba su maigadin ka su ma yace ok haka yana da kyau idan kuna da wani matsala dai bashar yana nan sai ki fada mai ko ma may ye. Nace bamu da matsalan komai don iya tana da kirki matuka kuma tana debe min kewa sosai a zaman kadaici. Murmushi naji yadan yi yace akwaita da,son hira ai sai kingaji kintashi inda Rabi ce. Na katse shi da cewa ina fatan kana wa kanka adalci acan ka daina wanan shan mugun abin mai bata maka tunanen ka akan komai. Tsaki naji yaja yace yacd ai da kika damu da hakan da sai ki shigo jirgi ki gani don gulma ko ? Yace kin ga malama idan kikace zaki saka min ido haka arayuwa na wahala zakisha wallahi. Raina ya baci da kalamin shi nace dama ai zaman wahalan aka kawo ni yi don raina yai ta baci a banza tunda ba fasawa zakayi ba kai. Amma kin san ko ni waye kika yarda aka daura ni dake haka na ko don kin ga ban maki yadda na kulla ba shine har kike jin dadin samun gurin ke ki cutata min ko ? Naga idan ban kashe watan ba haka zamuyi sa insa dashi akan zancen yasani kashe wayan dip na ji dul jikina ya mutu a lokaci guda. Mikewa nayi na ahiga wanka na dauro alwala raina duk abace ina ta faman tune watau shi wanan dai bazai daina halin nashi ba ke nan yake nufi tinda da anyi zancen fitina yazo ke nan dashi. Washe gari da safe yaya bashar ya samay mu da iya mun gaisa da yake iya mace mai fahinta sai taba guri dashi. Wasu kulin magani ya ciro daga aljihun shi ya kashe murya yana min bayani yadda zan yi da maganin idan yadawo sosai nai mashi godiya da fatan Allah yasa mu dace gare shi yace amin ya kara jadda mi na tabbatar da na zuba mashi fa yaci sosai nace insha Allahu nai murna kwarai sai nake gani kamar har maganin yaci ko a lokacin. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,, IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA NA,BARKI GA ALLAH,ALLAH SHI ZAI KARBA MIN HAKKINA A GARE KI ,,,,, Saura yan kwanaki a fara azumin watan ramadan ko ina,kasa shen musulmai sai shirye shiryen taron wanan wata mai alfarma da albarka dake tafe a,wanan lokacin aketayi manya da yara da,tsofi duk farin ciki suke da wanan wata mai albarka . Zan iya cewa rashi dawowan sadauki a cikin lokacin da nake gani kamar har za a kama a azumi bai dawo ba garin a lokacin. Babu wani abin da na rasa,a gidan daga na ci da,sha da sauran abubuwa amma kuma sai na kasa gane may ke yawan haddasa min bacin rai haka na rasa ganewa. Gidan baba sai abin arziki yake samu daga diya da sarakain shi da,abokan arziki na gari. Ba kunya mama take habaici wa baba wai gashi dan na shi bai kawo ba amma fa wa yanda ba,a so sun kawo don sune ,ba,a so da alheri gashi Allah ya hore masu sin kawo mashi ya karba yana washe baki . Kai tun abin yana damuna har yakai yanzu na daina damuwa da rashin dawowan shi wanda wata biyu.ke nan rabon shi da gida. Sai yaya bashar mijin maryam abokin shi shine kawai ke dawainiya da mu tako wani fanni duk da,ban taba cewa muna bukatan wani abuba a gidan na rayuwa. Maryan yanzu cikin ta yakai wata biyar ke nan a jikin ta don har ya turo sosai mutum zai iya gane haka atare da ita duk cikin mu ita kadaice Allah yabawa haihuwa. Da kafa takan tako daga gidan ta zuwa gidan mu don motsa jikin ta idan zata koma tare muke fita har Iya mu taka mata mu rakata gidan ta don bamu da nisa sosai. Da dare muna cikin falo zaune ni da Iyan Rabi muna hira waja jen karfe tara na dare a lokacin . Sai jin sallama mukayi kamar daga sama muka ganshi har ya shigo tsakiyan falon a lokacin. Sadauki ne ya shigo muna gidan da sallaman shi ya murje yayi wani kyau yayi haske kamar wani dan kwara dashi. Cikin fara,an shi da walwala ya shigo muna a lokacin daga ni har Iya sai sannu da zuwa muke mashi a lokacin. Ganin da nayi fuskan shi a sake yake, yasani nima taron shi a cikin farin ciki kamar babu komai a tsakanin mu can baya. Zama yayi saman kujera tare da fadin wassh Allah Iya tace sannu na wurina da kokari andawo yaya hanya yaya aiki da sauran jaman can. Na,dawo daga,kai jakar kayan shi daki na nufo shi tare da dan dukawa na rugumoshi ban damu da wai iya tana gurin ba shima dai rungumoni yayi zuwa jikin shi. Iya dai kunya taji ta juya zuwa kitchen abinta tana murmushin yadda taga mun burge ta sosai a yanayin mu. Zauna da ni yayi saman cinyan shi yana sauke numfashi tare da kai hannun shi a saman wuyana a hankali yana dan shafawa cikin lumshe idanuwan shi. Daga inda Iyatake a tsaye take cewa uwar dakina nace ko sabon girki zamu dorawa yaron nawa ne ? Itace tadawo muna da hankalin mu muka tuna a inda muke zaune a lokacin. Da,sauri yace a,a kubar shi kawai zan sa,akawo abinda zanci yanzunan kafin nai wanka. Mikewa nayi daga cinyan shi nake cewa Iya zo zauna ki huta abinki ai dan naki bai faye danuwa da abinci ba idan bashi yaso ci ba kuma bama komai ne yake ci ba shi dole yanzun sallon abincin mu ya canza ai . Maimakon tazo ta zauna sai ta shiga dakin ta yana tambayana yaya muke yazaman mu da Rabin dan musa nace bata da wani matsala wallahi ita ai mutum ce mai dadin zama ga tsabta ga aiki bata gajiya wallahi. Sai ganin Iya mukayi da dan jakar bakon ta tafito daga daki tana fadin uwar dakina nikan zan tafi tunda maigidan yadawo yanzu. Da sauri dani dashi muke hada baki cewa haba dai ina kuma zaki kuma iya yace Rabi ina kike nufin zaki kuma ina anan zaki zauna gaba daya kina debe muna kewa kuma. Tace a,a haba nawa ina zan zauna a tsakanin ku na hanaku shakakatawa kuna sabbin ma,aurata da ku. Iya bafa inda zaki idan kika tafi dawa kike son na zauna a gidan nan idan ya fita shi ko baya garin ? Ba sai na dawo ba idan yai tafiya din amma zan zauna na hanaku hutawa a tsakanin ku ? Murmushi yayi tare da mikewa ya nufi inda take tare da karban ledan hannun ta yana cewa wai maji bata fada maki cewa zama zakiyi muna a gidan nan ba. Tace zama Alhaji yace ai babu inda zaki don kinzo kenan nan zamu zauna dake gashi kuma nayi sa,a uwar dakin naki naku yazo daya da ita yanzin . Murmushin jin dadi iyan Rabi tayi tace ai Alhamdullahi don kayi sa,an mace tagari da kowani namiji ke bukatan samu a rayuwan shi. Murmushi yayi ya shiga dakinta ya aje mata jakar kayan ta yafito bayan yabi dakin da kallo yaga komai akwai shi dakin na rayuwa yafito bai zauna ba don ya fahinci zaman shi zai takura mata sai ya wuce zuwa cikin dakin shi direct. Cewa iya nayi bari naje na hada mai ruwan wanka ya dan watsa yaji dadin jikin shi. Tace afiti lafiya hajiya nabi bayan shi zuwa dakin yana duke yana cire takalman cover shoes bakaken dake kafan shi da safa. Da sallama na shiga ya ansa min yana dagowa daga duken da yake yadda ya ansa min a cikin sakin fuska yasa na karasa gurin shi. Cikin kwarin gwiwa ya zuba min idanuwan shi na ce yaya hanya ya gajiya kuma? Kalau yabani amsa da hakan nakai gare shi tare da kokarin fara balle mai aninin rigan shi ta gaba. Cikin sanyin murya naji yana cewa kin huce ke nan da mijin naki Fatima ? Nace don girman Allah yaya ka daina wanan maganan adai gyara gaba please ? Wallahi yaya yadda kasan mama bata kaunan wanan abinda kake yi haka zalika nima bani kaunan ganin ka cikin wanan irin yanayin don kwata kwata ban iya controlling din kaina a hakan. Nakan jini ne kamar wata mara sa,a acikin mata don sai nake ganin kamar dunuya zata zageni a dinga nuna ni. Wata uwar harara ne ya balla min bashiri na kama bakina na kasa cigaba da maganata. Cikin maganan tausayi yace min don kina son na daina Fatima shine zaki dinga nisanta kanki dani ? Saboda kin mayar dani shasha haka kike zaton kowa yana dauka na a idon shi ko ? Na katse shi da cewa kasan halin mutane yanzu yaya bazasu iya fada maka gaskiya ba a gaban ka don abin hannun ka. Yana da kyau kai nazari akan zance na zaka gane manufata a gare ka ba don na rainaka bane ko wani abu a,a yaya gani nayi idan ban fada maka gaskiya ba a yanzu waye zai fada maka shi. Tsaki naji yaja yace kinga malama idan kin zo ne ki taimaka min kiyi abinda ya kawo ki . Idan kuma har yanzu raina manin wayyo ko hankali zakiyi ki fice min daga daki rainin hankalin naki yana son yai min yawa. Ke yarince dake zaki min wa,azin da mahaifana basuyi min ba ko may ? Naga baki son mu zauna lafiya a gidan nan dake don nafahinci kina son ki wuce matsayinki a gare ni. Raina ya baci nace amma yaya dama inaga dai ka yadda ka auri ni ne don ka dinga ci min mutunci ko ? Kiyi wa Allah idan kasan bada zuciya daya kake zaune dani ba baka sona ne ka sallamay ni na tafi gidan mu ka huta dani. Wani irin kallo yai min yace Fatima ke da bakin ki kike fadar na sallamay ki kikoma gidan ku? Shiru nai mashi yace ok idan haka kike so sai kikoma ki fadawa wanda suka hada mu sai su raba mi tunda shi kike bukata ke ? Naga idan na biye mai daga dawowan shi zamu sake samun matsala kuma again. Sai nai amfani da shawaran yaya bashar da anty maryam na wuce shi zuwa bathroom na hada mai ruwan wanka tare da,aje mai duk wani abinda zai bukata na amfanin shi ciki. Yana shiga nafita daga dakin raina a bace da yan maganganun da mukayi da shi yanzu na koma dakina na zauna a bakin gadona ina tunane. Shima dai yana can yana wanka tunanen maganganun da mukayi dashi ne yasan ina da gaskiya na amma bai bukatan na shiga harkan shi har takai na takurawa zamantakewar mu dashi haka. Yafito ya shiya cikin rigar barcin shi falon ya dawo sai dai babu kowa a falon sai tv dake aiki shi kadai a lokacin. Kamar ya shiga dakina amma sai yadake kawai ya zauna tare da canza tashan zuwa na kwallon kafa. Jin motsin shi afalo danayi na sauke ajiyan zuciya maganganun su yaya Bashar da suka fada min na dole ne sai na kwanta mashi sosai zan iya,aiwatar da,shiri na akan shi yasa na sauke ajiyan zuciya tare da mikewa na fita. Rigan barci ke jikina alokacin sai faman kamshi ke tashi a jikina dan na gyara jikina bayan fitowa daga gurin shi nima. Murya na yaji a bazata daga bayan shi don baiyi tsanmanin zan kula shi bakuma har yadan shiga dan damu akan yaya akayi ya bari muka dan sake samun sabani bayan yaga na sauka daga fushin da nakeyi da farko dashi. Cewa nakeyi abincin da kace za,a kawo maka kaci fa kuma gashi baka bari mun dafa maka ba ? Ya dan dago kai inda nake yana cewa No ki barshi kawai banjin cin komai yanzun ma zai sha drinks da tea na sai na kwanta. Nace lokacin dana karaso inda yake a zaune yaya drinks kuma shi zai sa ka koshi yace is ok kawai. Zan zauna yace dauko min laptop dina na duba wani abu a daki please ? Juyawa nayi zuwa dakin nashi na dauko mai system din nashi maishegen kyau da tsada. Mika mashi nayi na juya zuwa kitchen tare da dora ruwan tea din nashi sai dai na faki idon shi na barbada garin maganin da,akabani in bashi yasha din a ciki. Najuyo mai tare da dauko drinks da cup har dan flaska din shayin nakawo mai. Yace inji lemon baida sanyi don kinsan mutum bai shan ruwan zafi dana sanyi a lokaci daya don gudun cancer. Nace baida sanyi sosai amma dai bari na zuba ma a cup sai ya huce kafi ka sha. Dakin Iya na wuce don jinta shiru danayi yau ba hira ke nan ta boye a dakin ta don ganin shi a gida da tayi. Na samay ta tayi barci sai rufo mata kofa tare da kashe mata wutan dakin dake a kunne lokacin. Na samu har ya bude system din shi ya fara aiki da zaiyi dashi a kan three seat yake zaune nima saman na zauna tare da kaiwa kwance ina kallon tv dake aiki. Can na dan ja tsaki tare da mika hannu na daga kwance na dauko remote zan canza chanel din naji yace baki son wasan ball ke nan dai ko ? Murmushi nayi tare da kai kaina saman cinyan shi nai filo dashi nace wallahi ni ban taba fahintar may ake ba a cikin shi don ban san komai ba akai. Dariya naji tayi yace kai amma shame on you matar dan kwallon duniya kuma bata san ball ba aiko kinji kunya wallahi. To yaya kunyan may tunda badani ake zuwa yin ball din ba can nan kuma ina diyan hausawa yaya zan san wani ball can a rayuna. Yace aiko ya zama dole ki sani don kada wata rana a tambaye ki mijinki dan lanba nawa ne ki kasa bada amsa naji kunya. Duk hiran da mukeyi hankalin shi na,wurin abinda yake acikin laptop din shi lokacin baidago kan shi ba. Muryan shi na kara ji again yana fadi amma ki saka a,ranki kulba dade kul ba jima akwai ranan da,zaji hade da yan jarida zasuyi mako inter view akaona da kan ki don har sai ki fara shitleya basu amsa da zaki fada masu. Da sauri tare da dan dagowa daga kafan shi ina kall9n shi nace ni nidai din yaya. Yace cijin murmushi kekuwa Fatima din nan rana da lokaci sina tafe muddin muna araye zasu tambaye ki. Komaqa nayi na kwanta kamar yadda nake da farko tare da ajiyan zuciya nace ashe akwai aiki kuwa ke nan. Dariya sosai na bashi yadda yake dariyan yana ci gaba da,aikin ya ban sha,awa ban san lokacin da nakai hannuna ga fuskan shi ba na shafo a hankali. Wani irin irin ajiyan zuciya ne naji ya sauke tare da lumahe indanuwan sho gyaea kwanciya nayi akan jikin shi nace. Basai ka fada min abinda zan fada masu ba ko kuma nace ni ban san duk wani tambayan da sukai min ba ma. Ban san har ya rufe laptop din nashi ba sai ji nayi ya mike ya nufi gyrin tv ya kashe tare da kashe sauran na,urorin falon inda nake yazo ya dauke ni cak ya hada da computer din shi sai dakin shi. Saman kado ya dire mu ya jaye laptop din ta fado min saman jikina yana fadin barin fada maki abinda zaki fada masu tunda shine kawai kika sani a gamay dani. Bakina ya lalabo ya fara kai min kiss mun dade a haka can ona jin dadin abinda hannayen shi suke min sai kuma naji ya tsaya tare da zare bakin shi a cikin nawa a hankali Ya juya yana mayar da numfashi a hankali can yake cewa sorry fa kada kuma na sake maki fyede again . Ban san lokacin da dariya ya kamani ba nace yaushe kuma ai kasaba min yanzun ma gashi kayi min din again. Auto ashe bari ma na karasa tinda har nayi maki ma waida kada nai lefi nake gudu nace cikin dariya ai kaf8n kai min wallahi sai na rama nima don yau nice zan maka fyede da kaina. Kafin yasan may zanyi har na juya na haye mai ruwan cikin shi ko a hakali na cire mai rigar jikin shi bai hanani ba nan nashi ga nuna mai wani sallon da ni kaina ban ban san ina dashi ba. Sosai muka gwadawa wa junan mu how far we miss each other a lokacin, tsawon lokaci muka shayar da junan mu zuman ma,aurata ranan masha godiya ba adadi a gurin shi kamar ba yaya sadauki bane mai izzigilancin nan. Bayan komai ya lafa a tsakanin mu sai zancen shayin dana hada mai da magani yafado min a raina. Gabana ya fadi kada yazo baisha ba ai hasaran maganin gashi yaya bashar ya jadda min na tabarar da yasha ahi sosai fa. Ikon Allah sai naji yace ni wallahi har kin sani jin yunwa ma sosai wallahi nace ai ruwan shayinka na nan baka sha ba. Yace anya yadda nake ji din shayin nan kuwa zai dauke ni a yanzu gaba na ya kara faduwa kada yazo bai sha ba fa. Muryan shi ne yake fadin tsiyayo min insha kada kice zaki fita yin wani dahuwa da daren nan kuma. Don keta sai da na zuba mai da yawa kuma nai sa,a duk ya shanye cup din gaba daya. Sai da ya shanye yake cewa amma sai naji shayin ya dan canza test yau ko ya fara expire ne dai nace ko kuma don ya dade a bude yai sanyi yasa shi canza test ba yace indai a bude yake shi ya kawo hakan gaskiya. A haka muna dan hira naji yayi shiru barci ya kwashe shi lokacin ga gajiya ga aikin magani ke nan. Mikewa nayi nashiga bathroom nai wanka tare da dauro alwala nazo nai sallah raka,a hudu ina rokon Allah yasa mu dace ga maganin. Muna barci can shiyoyin asuba naji cikin barci yana wani irin nishi sosai abinda ya falkan dani ke nan a dan firgice cikin tsoro yadda naga ya dunkule guri daya ya dafe cikin shi. Cikin tsoro nake magana yayana may ya samay kane may ke damun ka kuma ? Cikin shi ya nuna min da hannu nace a dan razane subbahanallahi ciwon ciki kuma ko may ya gyada min kan shi da kyat . Nacw daure mu shiga bathroom kadan yi wanka ko zakaji dama sai na fita na hada ma abinci ko yunwane don kaga jiya bakaci komai ba ka kwanta hakana sai ruwan shayi . Ban samu amsa ba sai murde murden da yakeyi a lokacin kawai na ciwon ciki na mike na shiga na hada mai ruwa na dawo ina yake kwance. A hankali na duka cikin kunnuwan shi ina rada mai ya tashi mu shiga bathroom din yai wanka hannun shi ya miko min da taimakona muka shiga har bandakin . Ranan dole yanayin da yake ciki na cire kunya na hada mai ruwa da kaina nai mashi wanka wankan tsarki ne kawai ya daure yayi da kan shi lokacin. Ba laifin wankan ya sa yaji dan sauki ana kiran sallah mukai sallah ya koma ya kwanta nafito zuwa sama mai abinda zaici inayi ina lekashi dakin shi. Ranan a daki nakai mai ya dan daure ya tsakura kadan yaci yace baijin dadin bakin shi ko kadan. Koda Iya tafito ta samu na hada abin karyawa ko sai gyaran gida kawai tayi nafito daga dakin a cikin shirina na samay ta tana aiki muka gaisa da ita. Tana tambayana kwanan dan ta nake fada mata wallahi Iyya yau dannnan naki ciwon ciki ne ya hana shi barci . Tace da sauri subbahanallahi ciwon ciki kuma da sauki dai ko nace da sauki don ya ci abinci yace idan ya tashi zai sha magani . Dakin na koma sai dai bai saman gado yana bayi ina na tsaye har zan juya sai naji yana kakar8n amai daga cikin bandakin . Da sauri na isa gurin amai yake shekawa wani irin bakin amai ba dadin gani. Wasa wasa amaiko yaki tsayawa sai faman sheka amai yakeyi hankalina yai matukar tashi sosai na fita na kira wayan yaya bashar na fada mai sadauki fa ba lafiya ciwon ciki da amai ya damay shi. Yace subbahanallahi gani nan zuwa yanzun nan muna gama waya dashi nake shawaran kiran mama na fada mata . Itama kiran ta nayi don kada taji daga baya taimin fada gata tana a cikin gari kuma. Tana ganin wayana tunda safe haka gaban ta ya fadi ta dauka take tambayana Fatima lafiya ko nake fada mata abindake faruwa tace subbahanallahi gamu tafe yanzu. Yaya bashar ne ya fara shigowa lokacin muna ban daki dashi har bedroom din yashigo nan yasamay shi yana wanan bakin aman nashi. Yace subbahanallahi man may ke faruwa ne kuma yadago kai da kyat jin muryan aminin shi idanuwan shi sun canza launi sosai. Yace wallahi ban sani ba man ciwon cikine sai kuma amai da ya biyo baya da kyat yake iya magana a lokacin . Shi ya kamashi ya kwanta bai dade da kwanciya ba sai ga baba mama da mummy sun iso suma. A falo suka fara zama nazo na gausa dasu suke tambayana nake fada masu abinda yakeyi ai sai aje asibiti baza a barshi a gida ba hakana bamu san may ke damun shi ba . Naji tsoro sosai a raina kada aje asibiti ace poison aka bashi fa yaci nawa ya samay ni garin neman kiba na samo rama kuma. Mun shiga inda yake kwance sai faman murdan ciki yakeyi sosai yana juyi mummy ta dan dubashi tare da bashi tace Alhaji aje asibiti kawai. Ina gefe daya a rakube hankalina a tashe yace No abari kila zai bari ai baba bai yarda ba suka sashi a gaba ya tashi aje asibiti dai. Inda nake tsaye idanuwana suna fitar da hawaye ya dan kalla yace cikin karfin hali Fatima dauko min kaya na saka. Jin haka suka fito daga dakin suka barmu a tare sai kuka nakeyi cikin karfin hali bayan ya gama sa wando ya jawoni jikin shi yana cewa. Ki daina kuka mana Fatima bakya son ki rasani ne ko ? Ban bashi amsa ba na saka mai rigan tie shirt tare da dan shafawa fuskan shi dan mai sai ajiyan zuciya yakeyi sosai. Bashar ne ya leko yake cewa yagama ne mu tafi nace mai eh a lokacin ina rugumay a jikin shi muka fito daga dakin da kyat yake tafiya. Har sun fita bashar ya dawo cikin gida kaman zai dauki abu yace min a hankali kin bashi maganin ne nace mai eh yace ok dama ance zaiyi amai ya wahala sosai kada ki damu komai basu ganewa ai. Shiru shiru suna,asibitin dashi muna gida da Iyya hankalin mi a tashe sosai a lokacin dashi. Mama ce ta bugo waya tana fada min in kwantar da hankalina likitoci suna kan shi suna bincike yanzu haka. A raina nace ina naga kwantar da hankali asirina zai tonu haka kuma daga taimako . Sai guraren sha biyu da wani abu bashar ta dawo gidan yake fada min an bashi gado asibitin sunce wai canji ruwa ne ko kuma yaci wani abu a can wanda suke gani kamar bai dace da cikin shi ba. Nan yake ce min mama tace yazo yaje dani yanzun don suna son zuwa gida suyi sallah su tinda yadan ji sauki . Mun isa mun samay shi kwance yana barci har ya fada sosai bashar yake tambaya baiyi aman ba ko sukace yayi har sau biyu bayan tafiyan ka ai. Ina tsaye kan ahi na kura mai ido ina kallon yadda ya koma a raina nake cewa wabda duk yai maka wanan asiri Allah ya saka maka. Muryan mummy ne take fadin bari muje gida mu dawo sai azo maku da abinci nace ai da a barshi Iyya tana can tana hadawa ai. Sun wuce aka barni da yaya bashar basu dade ba maryam suka iso da mahaifiyar yaya bashar din nan muka zauna atare dasu. Sai dai mama tana bugo waya akai akai tana tambayan ko ya tashi a lokacin ko yana aman har yanzu ? Nace bai kara yi ba yana dai barci ne tace Fatima kada ki yarda a cika dakinbda suruti kinji ku barshi ya huta please nace to mama. Nan kuwa muka fara ganin yan uwa da abikan arziki harda ma wanda bamu sani ba suna shigowa gaidashi. Mummy tagama shiryawa tace wa mama su fito su zo mama tace haba hajiya kubura kamar ban gode ma Allah ba ke nan ai. Gaki ga matar shi da yan uwa a kan shi may kuma zan koma yi adduan mu yake bukata kuma ya samu ko? Allah dai ya bashi lafiya sai kun dawo agaida su mummy taji dadin hakan sosai suka tafi tare da,Abdul. Yadda yan uwa suka nuna mai yasa na gane cewa sadauki dan gatane sosai don sai ga yaya Imiran da matar shi tare da abincin sukazo muna. Nan dai guri ya cika makil Nafisa da kawayen ta sun shigo su ma nan suke cewa yanzu Naffy ke fada muna mukace bamuga zama ba ai uwar dakin mu na cikin tashin hankali. Kowa yai mamaki jin abinda suka fadi may ye hadina dasu kuma sai cewa Raiha tayi muna zuwa muna cika cikin mu ana muna,taron arziki ai dole ne mu zo gurin ki. Wani likitane ta ke duba shi ko na kira P M O ne yazo da kan shi ya duba muna shine dai. Kowa yasan zasu uya don sunyi kamari wuce pmo ma balle director gaba daya. Yaya Ahmed suka shiigo da matar shi jamila a lokacin dressing din ta kawai ya isa mutum ya gane ko ita wacece. Sai yatsune yatsune takewa mutane tana kallon shi tace au ashe shine ban ma taba ganin shi bani. Sosai na mayar da hankalina gurin su Nafisa da kawayen ta muna hira maryam sai haushina suke ji da Amirah. Suko yadda na ke tare da,su yai masu dadi sosai a ran su don sai jana suke da hira ina dan murmushi. An cika duk yan gidan su ne gungun gungu a haraban gurin falkawa yayi da karfi yake kiran Fatima Fatima da sauri yaya bashar ya shiga dakin Abdul ne yakirani. Na mike da sauri gabana yana faduwa idanuwa aka sako min caa da kyat nake tafiya a lokacin. Jamila matar yaya Ahmed bata sanni ba sai ranan take fadi au matar tashi ke nan ashe ? Ina shiga ya falka Bashar yana tsaye a kan shi lokacin na karasa gurin shi ya miko min hannun shi yana cewa zauna kija min hannu na da kafa please. Mummy ma tashigo dakin don ganin ya falka a lokacin tana mashi sannu da jiki ya amsa mata da kyat da sauri ya dago yana son mikewa yace amai yake ji sosai da sauri na dauko roban da aka sayo don ya dinga yi a cikin shi. Amai yayi sosai bakikirin dashi nan hankalin duk wanda ke gurin ya tashi sosai sai kawai ya rufe idon shi ya zama colarbs jiki ya sake mai da sauri na karasa ina kiran sunan shi bashar yace na fita dakin . Don kuka yaci karfina a lokacin ganin na fito ina kuka yasa mutanen da sauri suka karaso jikin maryam na fada ina kuka tace may yafaru nace baya numfashi maryam da sauri mazan gidan su suka shiga gurin shi dakin Ina nan naga bashar yafito da sauri ya nufi gurin likita duk wanda ke gurin hankalin shi a tashe yake sosai naji dadin su Nafisa da kawayen ta don sun nuna damuwan su sai akaina. Likita yazo da sauri suka shiga dakin yana fadin suma yayi bayan ya duba shi ai hankalin kowa a tashe can sai ga baba da su umma sun zo. Ikon Allah sai Nafisa ke fadin to baidai mutu ba balle aji dadi ba,azo ba sai yanzun da akaji ance baya da rai yana nan daram. Taba wasu haushi musaman yan uwanta amma babu yadda suka iya da halinya dole aka saka mata ido uwayen dai sunji kunya sosai. Yana falkowa yake fadin Fatima jamin hannuna da kafa please, sai da yaba kowa tausayi a dakin na koma dole dakin duk da ga iyayyen shi amma ina dan matsa mai hannayen shi da kafa a hankali. Har dare muna tare da mummy don cewa tayi anan zata kwana amma sai yaya bashar yace duk mu tafi gida dashi da sagir da Abdul zasu kwana gurin shi. Hakana na kwana a cikin zullumi tun da safe washegari ina asibitin gurin shi. Ance mutum mai yawan bautar Allah yakan zama wani lokaci kamar waliyi ne saboda yawan ibadan shi. Hakane ya faru da mama don tai sallah nafila tadan zauna tana tasbihi kafin a kira sallah asuba tayi sallah. Nan tai mafalki ana ce mata kada ki damu taimakon shi Fatima tayi amma zai mike. Ta falka firgigi da ita tana cewa subbahanallahi Fatima kuma haka yasa zuciyar ta zargin akwai wani abu a kasa amma koma may ye zata binciki Fatima din taji. Sun shigo gaida shi da safe ne ta kirani gefe muka gaisai da ita can ta dafani tace ki kwantar da hankalinki insha Allahu zai samu lafiya kinji. Can naji ta dafani sosai tace Fatima may kuka ba saudauki ya shane haka mai karfi don nagani a mafalki na yau. Ras, ras gabana ya fadi uku uku lokaci daya nadaugo kai na da sauri na kalleta tace ba boyo tsakani na dake fada min nace cikin kuka mama yaya bai bar sha ba har yanzu. Shine yaya bashar ganin muna yawan samun matsala ya koma gurin mutumin nan shida maryam suka anso wani wanda zai amaye abinda yasha gaba daya a jikin shi. Ina fadin haka na dago kaina kalle ta murmushi naga tayi ta dafani tace Allah yai maku albarka Fatima kun karasa aikin dani ce ya dace nayi shi tun farko. Kuma duk halin da kuke ciki na sani maryam ba ban sani bane amma tunda kikayi yadda nake so dake rufin asiri a tsakanin ku yasa na ja bakina nai shiru dashi. Tace ban son jin zancen nan a bakin kowa daga Allah sai ku da kukayi don koshi kada ki yarda ya fahince ki don zai dauka wanan wahalan da yakeyi kashe shi kuke son yi ba taimakon shi ba . Don haka ki rike wanan sirin a ranki ki boye sirin mijin ki danaki a kowa kinji Allah yai maku albarka nagode Fatima abinda nai hasashe ke nan tun farko akan ki. Tare da mama muka dawo dakin yana zaune ya ramay ya fada sosai kamar bashine yadawo bulbul dashi ba. Ya samu sauki don aman ya tsaya sunce har cikin dare sai da yayi aman sosai bakikirin dashi. Yanzu sai barcine ya ke damun shi da ya dan falka sai ya koma yaci gaba da barcin shi. A sibiti muka fara azumin wanan shekaran da wata ya kama na azumi amma ya samu sauki sosai. Azumi uku mukayi a asibitin aka sallamashi ya dawo gida nan naci gaba da jinyan shi da kaina. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,, IDAN KUMA KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI DA ALLAH YAR UWA,,, Ya ramay sosai sai dan wuya da ya aje a lokacin ga wani irin barci da ko ysushe yakeyi ni da iya ne kawai muke azumi don shi bai iyawa a lokacin. Abinci ma sai da kyat nake samu ya dan tsakura yaci yasha magani. Yau hudu ga watan azumi ya fito falo ya kwanta tun safe yake kwance a falon sai shige da fice masu zuwa dibiya sukeyi a gidan zuwa azahar bayan a watse ba kowa a gurin shi gurin da ya idar da sallah yake zaune. Nafito zan shiga kitchen gurin da iya take a zaune ta na fere dankali na nufa sai ji nayi ya kira suna na a kasalance da Fatima. Na amsa tare da juyowa gare shi kan shi na a,saman kujera baida lakka da gani a jikin shi. Na karaso tare da zama a saman kujera da kanshi yake sama gyara kan nashi yayi tare da dora kan shi saman cinya na da kyau. Yace wai may ake cikine ban ji kin ce min komai ba ba hannuna na dora saman kan nashi dake saman kafafuna na a hankali ina shafa mai kai dashi. A hankali naji ya sauke ajiyan zuciya tare da lumshe idanuwan shi ya kara sako min nauyin shi a jikina. Nima lumshe idanuwa nayi a lokacin nace yaya love kamar may fa ke nan ? Yace may za,a ba mutane ne na azumi don na dawo da niyar na tambaye ki naji yaya za,ayi ne may ya dace aba mutane na azumi. Na lumshe idanuwa again nace yaya bazaka bari kaji sauki ba sai ayi maganan ? Murmushi naji yayi yace ai naji sauki mana ya kamata ayi wani abu don lokaci yana ja gashi ina son zuwa umurah cikin watan nan. Nace to Allah ya kara baka lafiya yaya yanzu may kake ganin za,ayi ne ke nan ? Naci gaba da cewa su baba ma nasan kaine mai tallafa mashi yanzu gashi kuma lalura yazo ya gifta akai. No ki bar zancen na su baba da mutanen Rabah na riga nai masu tana din nasu ko yanzun dai ina son ki taimaka min ki yi list din mutanen da kika ga yadace aba wani abu sai na gani nace to bari na dauko pepper da biro sai na fara a gaban ka ko ? Sai dana je gurin Iyya a kitchen na bata hakkuri taci gaba da aiki zan dan yi wani abu yanzun ne. Tace haba hajiya dama dai aike ce baki zama amma komai da kuke bukata ai na iya yanzu wanda ban iya ba zan kiraki ki duba min . Na dawo gurin shi ida na fara rubuta sunayen makwabtan su na can gidan baba. Inayi ina lissafo mashi wa yanda nake rubutawa har na kawo gurin na ugun da muke zaune a yanzu shine ma yake kara tuna min da wasu gidajen idan na manta. Yace banji kin sa sunan mutanen ki ba mana suwa ke nan yaya na tabaya cikin sonji su ? Yace masu gadin ki mana nace Allah sarki wallahi har na manta dasu nan rubuta sunayen su ciki. Nace shike nan ko ina ga an gama ya dan dago kai yana kallo na, yace kin san ban san mutanen arzikin ki na can gida ba fa ? Murmushi nayi nace har dasu yaya za ,a rubuta yace ki rubuta su mana su ma. Mutum kusa goma na rubuta mai yan uwana dana mamana har da yayan mama tabawa ciki. Yace motan da nai odan kayan sun shigo sukace don haka bashar zai zo sai a bashi list din kinga ga musa ya dawo sai yakai na mutanen ku shi da driver ko ? Yadda ya fada haka akayi washegari nan gida ya kace may su yaya Sagir yaya Abdul da yaya Jibrin kannen shi sai yaya bashar da wasu ma,aikatan su ne sukai ta faman rabon wanan kayan shi yana daga ciki tare dani ina kula dashi sai dai duk wanda ke son ganin shi yaya Bashar ya hana a shiga gidan sai da shi da kannen sadauki kawai suke shigowa gidan. Take labari yakai ko ina sai ga al,uma bayin Allah masu bukata sun yo caaa a gidan. Nan yace ma bashar da ya shigo ya fada mai araba masu sauran sai a karo buhu hamsin a hada masu dashi. Ba karamin mamaki nayi ba da irin wanan abin alherin da yaya sadauki yayi ba koda yake ba mamaki don yagaji alheri ga uwa da uba ne. Ankai kayan azumi a gidan mu ida abin ya zama abin magana a gari ashe ya ba da buhu biyar na shimkafa yace a rabawa mutane gari kuma ban sani ba sai da musa ya dawo ne yake fada min. Nai matukar mamaki duk da ba,a mamaki da ikon Allah wai a kwallon kafa ne yaya sadauki ya samu wanan kudin haka. Ikon Allah ke nan yau sadauki ne da,wanan irin alheri ga al,umma haka ubangiji Allah ya kara albarka. A kwana na shidda ne da azumi yace zai tashi da azumin naso yadan kara sha amma yace zai gwada ya gani. Lafiya yakai azumin shi ranan haka yaci gaba da azumin shi kuma yanzun yana fita zuwa site din su ya dan duba su. Ranan ya dawo da dare bayan mun gama buda bakine yake cewa ina fatan kin fara shirin tafiya ko ? Nace zuwa ina yaya ? Yace umurah mana daga can kuma zamu wuce chaina akwai wani aiki da zanyi don ina son bude kamfanin karfe anan sokoto insha Allahu. Ban san lokacin dana fada jikin shi ba na ma manta da wata Iyya Rabi a gurin lokacin. Shima rugumoni yayi yana murmshi yace cikin harshen turanci kin san dama fa bamuje honey moon din mu ba kin ga sai muyi shi acan tunda kuna hutu. Dan jaye jikina nayi tare da cewa kai haba yaya wani honey kuma bayan wanda ka lashe a nan cikin gidan ka yace to bari kigani idan mun tafi ai. Koda na farga ashe iyya dake zaune tana kallon sallah a kasar makka ta bar falon . Nace lah ashe iyya bata falon nan ban ma san tashin taba wallahi kaga ka koreta ko yaya ga Iyya da son kallo wallahi. Yace kin dai koreta ke bake ce kika rugumay ni a gaban ta ba ya kamata fa ace an saka tv a cikin dakunan nan don kallo kinga ko musa na lura idan ina falon nan kamar ina takura mashi shima. Washe gari kuwa sai ga masu hada starlight sunzo gidan suka hada ako wani daki na gidan kowa da nashi receive din a dakin shi. Nan naita faman koyawa iyya yadda zata dinga kamo tashan da take so a dakin ta ita kadai. Ashe tafiyan har su babane da su mama za,ayi shi sai da tafiyan ya matsone saura kwana biyu mu tafi naga ya shigo da passport din masu tafiya. Daga iyya sai Musa na muka bari a gidan na fada mata don Allah kada a manta da masu gadi gurin girka abinci idan sunyi. Naje gidan gurin su mama na samay su suna shiri gaba dayan su ban fita ba sai da na gyara mata kayan ta da daki da yake wuni zan dayi masu a gidan take ce min ai gwagona ce zata zo ta zauna mata daki da Amira don bata tafiya ta barta ita kadai a gida hakana. Anty Amira sama sama muke don haushina da take ji babu abinda ya canza a ciki sai ma ince ya karu ne kawai yanzu. Sai bayan la,asar na bar gidan zuwa gidan anty maryam can muka lalace da ita wanda hiran namu akan mazajen mu ne mukayi shi. Na dawo gida na samu Iyya ta gyara ko ina ta gama komai yadda ya kamata sai bayan sallah magariba ya shigo gidan. Muna falo gaba dayan mu sai mashi sannu da shan ruwa mukeyi a kasalance ya zauna don har yanzu ba wai karfin jikin nashi yake ji ba sosai. Nan muka shiga jera mai kayan buda baki a gaban shi bai ci wani abu ba sai kayan fruits din da ya sha kawai ya kai kwance fuskan shi yana kallon tv ana sallah asham a saudiya tv. Yace iyya Rabi gobene fa tafiyan mu insha Allahu zamu tafi mu barki da Musa sarkin son yawo kingan shi kada ki bari ya wuce takwas bai shigo gida ba kun rufe don tsaro. Tace insha Allahu nawaje na za,ayi yadda kace yace kai kuma kaji may nace ko? Musa yace naji yaya ai ba inda zan tafi ga tv nan muna kallo ai da rana ne kawai nakan dan fita can bakin shagon. Daga haka yai shiru idanuwan shi suna a lumshe sai da akai kiran sallah suka fita tare da MUSA. ****** ********* ****** Washe gari da azahar muka bar garin sokoto zuwa sadauya mun sauka da dare inda akai muna screening motan da ke jiran mu muka shiga sai wani hotel nan muka kwana a jidda sai da safe muka wuce zuwa madina. Ibada sosai mukeyi ba kama hannun yaro har su umma da mama sun bani mamaki sosai yadda naga suna ibadan su sai dai bawai sun bar halinsu bane ko acan. Adduoina sun fi yawa ne akan Allah ya shirya min yaya sadauki da samun zuria masu albarka dam yan uwa musulmai da suka fada cikin irin wanan halin . Sai dai a can ni da mummy muka zama kamar kawaye sai mama da muke tare da ita wani lokaci don mama bata da time din wasa ko kadan ko yaushe cikin ibada take . Mun bar madina mun nufi makka a can mukai kwana goma muka fara shirin dawowan su gida mu anan zamuyi sallah two days after sallah zamu wuce chaina din. Ana gobe zasu tafine ina makale da mama da mummy da wani iri shakuwa ya shiga tsakanin mu yanzun da ita. A can nice mama take sakawa na zaba masu abubuwa ni da mummy wanda kusan sayayan na Amira ne da naji ance wai zatai aure bada dadewa ba. Har gado nice yaya yasa a gaba na zabi gadaje har guda biyar masu kyau. Da,safe mukai masu rakiya suka tafi muna tsaye muna kallon su ba yadda zan yi ban san lokacin da hawaye ya zubo min ba. Muna motane yai dan murmushi tare da rungumoni zuwa jikin shi na langabe kaina ina share hawaye a hankali yace baki son rabuwa da mama ko? Ban yi magana ba sai ajiyan zuciyar da nayi kawai muka kai masaukin mu wanka mukayi muka nufi masallaci gurin sallah sai dare sosai muka dan huta kwana biyu duk a cikin masallaci mukayi shi. Ranan sallah na saka wani dogon rigan mai tsananin tsada da ya sayo min a wani katon shago na kayan mata. Rigan da gani ta matan manya ce irin tasu sai wace ta isa take sayanta Na yafa mayafin rigan take na koma kamar irin matan manyan larabawan da muke gani ko kuma matar wani kusa a kasan mu. Ga zubbunan gold da na saka guda biyu a yatsuna wuyana kuma Diamond ne kiran Dubai sai takalma mai tudu da yar karamar jakan takalma dana rika a hannu na sai wani kamshin turaren larabawa ke tashi a jikina. Yana falo zaune na fito a cikin shirina wani irin mugun kishina ne ya darsu a zuciyar shi. Na karaso inda yake zaune shima kayan maza yasa na larabawa masu tsada na karaso inda yake zaune cikin wani takon da ban san inayin shi ba. Wani kamshi ne ya daki hancin shi har ya saukan mai da kasala a lokaci daya. Ya sake idon shi yana kallona har na karaso gare shi tare da,dan fadawa jikin shi ina cewa yayana barka da sallah. Yace Fatima anya kuwa kece haka ko dai an canza min matane nace bari ka tabbatar da ni dince to na dan kai mai wani guntun cizo a kunnen shi ya dan saki wani dan kara yace muguwa. Na mike ina dariya yace Fatima kinyi kyau kinyi kyau sosai wallahi ban san may yasa duk dogon rigar da zaki saka sai naga tai matukar karban ki kaman don ke aka dinkata ba ? Gaskiya kafin mu bar garin nan sai na kara saya maki irin dogayen rigunan nan da yawa koda mun koma gida ki dinga min kwaliya haka dasu. Nace kai haba yaya kaface da tsada ka,sayo su fa ai biyun nan ma sun isa haka please. Yace Fatima shigan ki a cikin suturun alfarma shine mutunci na ga idon idon jama,a shigar ki shine zai nunawa duniya ni Umar ina sauke hakkina akan iyalina. Ya jawoni da hannu daya na fada a jikin shi yace bakin san ko waye mijin ki ba ko bakin U F ba ko Fatima ? Nai dariya tare da dan shafo fuskan shi da hannu daya yai murmushi nace niko nasan waye mijina don ni nasan kayana. Yace to ki godewa Allah daya baki Umar a matsayin mijin auren ki uban diyan ki nan gaba kuma. Yace Fatima mijin ki mai tsada ne mai daraja kuma a idon jama,a sai dai a idon mutum biyu zuwa uku ne kawai yake mai rauni. Dariya nayi nace idona dana mama ke nan na ukun ne ban sani ba yace na ukun shi ne baba. Kai yaya kada kaiwa baba haka wallahi tun haihuwan ka har yau baba baida wani da dayake ji dashi kamar ka a duniyan nan. Iyya fa ta fada min irin son da baba ke maka tun haihuwan ka har ya kai su Umma suna kishin ka tun kana karami har yanzu. Murmushi yayi tare da jawoni jikin shi yana sinsina na kamar ya samu handkici mai kamshi yacs nasani Fatima nima nasani wallahi. Iyya Rabi batai karya ba son da baba ke min yasa su imma suka sakani a gaba da horo tun ina karami ga mamanki da shegen hakkuri duk abinda akai min kona fada mata bata cewa komai sai dai tace min inyi hakkuri kawai. Ya kara motsoni a jikin shi yace kin san may fatima nace ,a,a yayana yace watarana har nakan zargi su Umma a raina akan da hannun su a cikin lalacewa na a baya. Sai dai zato zunubine koda ya zama gaskiya Astagafullah amma yadda suke gwada min bana jin dadi Fatima. Sun hana diyan su hurda dani sun hana mutanen shiya ma hurda dani haka yasa na kasance ban da aboki sai bashar. Bashar yai min kokari a rayuna na Fatima banda kamar bashar a duniyan nan kuma na san har gobe banda kaman shi wallahi. Yace humma Fatima idan ina tuna wasu abubuwa bazan iya koda gaisawa da Umma da mama a duniyan nan. Yace akwai lokacin da maji tai tafiya wallahi abinci hana min shi sukayi haka nake takawa da kafa har gidan su bashar a can zanci insha sai dare zan kamo hanya na dawo gida da kafa. Wata rana ruwa ya hana naje gidan su bashar cin abinci na shiga gida ko zan samu wanda ta tausaya min cikin su ya bani ga abinci ina gani amma sukace min wai na Ahmed ne da Imirana. Nadawo dakin mu da yuwa sai ga Bashar cikin ruwan nan ya aro mashin din makwabcin su bai ko iya tuki sosai ba yakawo min abinci shi naci har dare na kwanta. Ga maji bata dawo ba aai ashe tayi yaji ne ta tafi gida ban sani ba lokacin tana goyon Amirah. Kin san may nacece mai a,a lokacin duk jikina yai sa yi ga labarin da yake bani yace wallahi a lokacin ne na fara shaye shaye tun ina da fifteen year Fatima. Idanuwana na runtse don jin abinda ya fadi nan yai ta bani labarin irin musguna mashi dasu Umma sukai tayi har mama ta dawo. Yace ni mummy batai min komai ba wallahi don daidai da rana daya duk da nasan itama tana kishina kan wai baba yafi so na da diyanta amma tana boye zafin kishin ta akaina. Don Allah Fatima duk zafin kishin ki a kaina kada ki mu,amula da masu sihiri bala,i ne da fadaqa halaka ga mai irin wanan halin daga karshe. Kara shigewa jikin shi nayi nace kada Allah ya bani kwandalan zuwa gidan boka ko malam wanda zan illanta rayuwa wani bawan Allah. Munje sallah idi muka dawo bamu sake fita don ansha ruwa ba azumi muna gida muna farautawa nunan mu rai. ****** ********* ****** Mun sauka a China inda na kara tsinkewa yaya ke nan irin abokan da nagan shi da su can har sun so sufi na saudiya ma don ko a can naga yadda yake hurda da yaran masu kudin kasan ga kyautan dana samu har tsoro abin ya bani. Mun tafi wani katafaren hotel mai shigen tsawo da kyawo sosai kauyanci kan wallahi nayi shi sosai na lumshe idanuwa na daga inda muke zaune a bayan mota nace Alhamdullahi Ala Kulli Halin. Yace jawoni yace may kikace Fatima nace godiya nake mikawa ga uban gijina da ya nufe ni da hakan . Tsayawa bada labarin hotel din zai bata muna lokaci amma gaskiya nasha kallo Allah ya horewa mijin kowa yakaita kashen duniya tai kallon abin mamaki a can. Munga karamawan ta ban girma a gurin abokan shi na can nikan sai faman godiya nake ga Allah da ya daukaka min rayuwana haka. Ina rungumay a jikin shi muka bar gurin haraban hotel din zuwa masaukin mu a tare muka zube agado dashi. Na lumshe idanuwa na tare da ajiyan zuciya yace yaya akayi ne Fatiman yaya ? Nace ni may ma zance yaya dariya naji yayi yace kice kina son U F dinki sosai Fatima . Ki dinga gyara min kanki ina kallo ko yaushe gadona yazama ready ba sai na nema ba abani idan kin min haka kin gama min komai Fatima a rayuwana. Murmushi nayi nace ai baka da matsalar haka din ko yanzu yaya . Yace umm haka din ne amma ba sosai yadda nake so a raina na ba jinayi ya shiga zuge min zif din rigar dake jikina a hankali tare da fada min wasu kalamai da bazan iya fadin su ba anan. Nace ko wanka ba zamuyi ba yau kuma yace wanda mukayi kafin mu fita may mukaci dashi kada fa ki manta honey moon dina nake yanzu. Rugumashi nayi nace ai kayi abinka tin a gidan ka na sokoto sai dai ka dora inda ka tsaya kawai. Yace hakan za,ayi ranan kan nafitar da duk wani kunyan shi a idanuwana na nuna mashi nifa ba yar kauyen da yake kirana da ita bace. Rayuwa sosai na jin dadi mukayi da yaya a kasan China satin mu biyu a can ya sanya hannun jari a kamfanin yin karafuna da yake son yi a sokoto. Mun dan kara kwanaki muka wuce har Hong Kong nasha mamaki sosai yadda yaya yasan kasashen duniya haka da mutane kuma cikin yan shekarun kwallon shi. Daga karshe muka dira a Dubai a lokacin banda matsalan komai a raina ban da na tuhumar ko yaya yabai daina sha ba har yanzun . Don wanan irin mutanen da naga yana hurda dasu haka dole ne idan mutum.baikai zuciyar shi nesa ba ya yi aikin sabawa Allah. Amma sai naga shi akan ibada baida wasa ko kada ko wani kasa yana da time din sallah su ko baya gida zai bugo min waya yace lokacin sallah yayi na tashi nai sallah. A kasan Dubai kan kamar a gida Nigeria muke don yan Nigeria dake kasan maza da mata gasu nan manya da yara kana gani. Nan naga matan manyan kasan mu yadda suke hurda da matasa ko ina zai tafi tare muke zuwa yana nuna masu ni a matsayin matar shi. Mutane da yawa suna cewa basu taba tsanmanin yai aure ba ma a rayuwan shi don basu ji ba ana fadin zancen auren shi akasa ba. Akwai wata hjy wai shi take so ranan da ta ganmu mun fito gurin wani shakatawa sai da ta girgiza da ganin mu. Nagane hakan a fuskanta tun da muka hadu gasu su uku hamshakai sai wani shakiyancin duniya sukeyi wai su karuwai. Bayan mun rabu dasu ne naso na tambaye shi ko su waye su amma sai kawai na basar da zancen su. Shi da kan shi naji taja tsaki yace rabu da mahaukaciya wai a haka sona takeyi bata san ni ba irin shashan matasan nan bane masu kwadayin tsofin mata ba. Ni yanzu ko budurwa bata gabana balle wata tsuhuwar kwama can na banza. Har Lindan shi sai da muka hadu da ita a Dubai wai tazo tare da mahaufin ta wani business nace tir da kafurci ta sa ni dan skirt dan mitsitsi iya cinyar ta kawai duk komai nata a fili. Ita kanta Linda ranan da ta ganni sai da ta girgiza sosai don yadda taga nai mata kyau ga dress din jikina ya karbe ni nan tasan dole ne U F ya manta da wata Linda can. Tasan lalai yanzu Fatima ta sace zuciyar U F din ta don babu ta inda za a kwata mu da ita gashi kuma addinin mu daya dashi gamu yan uwa kishi ya rufe ta taji kawai tasakawa ranta hakkuri ga tunanen zai dawo gare ta wata rana. Daga ita har mahaifinta da muka hadu wanda yasab soyayyan su da yaya sai da suka bimu da wani irin kallo . Mahaifin Linda yake tambayan wanan ce matar shi daya aura din linda tace ita ce dadd. Yace so young pretty how are you tare da mika min hannun shi na girgiza kaina nace mashi dai yana lafiya tare da tambayan family din shi. Yaji dadi yai murmushi yace sorry na manta addinin ku ya hana hakan nan ya shiga muna murnan aure ya dafa yaya yana cewa kinga shi nan ki rike mijin ki da kyau don mijin ki big man ne sosai yana cikin lokacin shi. Dariya mukayi a tare har dan dimple dina ya dan lutsa kadan . Linda taja tsuki tace ai dole ne UF ya rikice dadd a kan wanan karamar yarinyar ji yadda ya mayar da ita kamar wata queen can . Ta juya tabar gurin ya ce don't mind her she is jealous of you taga kin fita komai baby ki rike mijin ki kinji yarinya. Nai mashi godiya ya bani kyautan wasu irin mahaukatan kudi kamar bau san zafin su ba. A mota hanyan mu na dawowa ne na ciro kudin ina bawa yaya yace na may ye fa nakine fa kece akabawa don haka kibar abinki gurin ki. Tsaraba kan nasha shi gurin yaya don bai bari na kashe koda kwandala ba daga cikin kyautan da nake samu. Mun baro kasan mun dawo gida Nigeria don hutuna da ya kare ba don yaya yaso yakare din ba don bai gama morewa ba can. Sai da mukai kwana uku a Abuja san nan muka ahugo jirgi zuwa sokoto birnin shehu cikin jin dadi da walwala muka iso gidan mu. Nai mamaki kwarai yadda muka samu yan uwa sun cika muna gida gurin taron mu. Anty maryam na ganina lokacin cikin ta ya tsufa sosai ya kara girma tazama wata mama da ita. Muka rugumay juna muna murna daganawan mu again ta sake ni tace wai ko Fatima don Alkah kece haka kodai yaya yakaiki cikin injin ne please. Na dan shafo cikin ta nace masha Allah ubangiji ya raba lafiya ya bamu mai albarka. Nan muka samu yan uwa sun cika falon sai faman sanu suke muna kowa kallon mamaki yake min don ganin yadda gaba daya na sauya na koma,wata yar larabawa dani abu ga dana,asalin buzaye. Mun samu a girka abinci kala kala wanda nasan aikin maryam ce haka na. Ban lura da Anty Amira a falon ba sai da naji yace mata haba sweet sister ba ko gaisuwa ne ? Sai lokacin na dago na dubi inda yake kallo tana zaune ta yi irin zaman dacta saba yi ta dunkule saman kujera sai chatting takeyi abinta. Ashe tun shigowan mu ta daga kai ta kalle mu taji wani abu ya tsaya mata arai irin yadda gaba daya taga na koma wata matar manya ko diyar manya can dani sai kamshi da annuri ke tashi gare ni. Gani cikin wani irin dogon riga kore yaji duwatsu tun daga sama har kasan shi hannayen rigan shara shara na yafa mayafin rigan a kaina ina rataye da jakka ja da takalma mai duwatsu kamar na rigan. Ga yan uwan su sai haba haba sukeyi dani mu kamar sunga wata basarkiya can daban. Haushi ya kumay ta tace wai wanan Bintun kauyen ne yau ta murje ta zama haka da ita kai kai maji why please maji taja wani dogon tsuki tamike tana fadin ita zata tafi gida ke nan. Nace a,a haba Anty Amira yanzun nan da shigowan mu hatta hausana ya sake ba sakwatancin nan sosai a cikin shi . Tace a,wulakance wani abun kuma zan tsaya nai maki bayan naga kun sauka lafiya ko so kike na tsaye ina,fadanci a kanki kuma ? ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,, IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH YABI MUNA HAKKIN MU AKAN KI, Yana isa zuwa yamma ya bar garin ya wuce zuwa lagos inda zai tafi ghana daga can gurin business din shi. Yana can ya bugo min washegari lokacin na tashi nai wanka ina shiryawa wayan shi yashigo na dauka tare da gaidashi yake tambayana jikin yayi sauki ko nace na samu lafiya sosai. Dama ai idan na shiga mota ne kawai nai tafiya mai nisa nake jin haka. Mundayi hira yana tambayana mutanen gida nace duk suna lafiya yace nagaida su nai mai Allah ya tsare yaba da sa,an tafiya muka kashe waya. Sai dana shirya ne mama tashigo dakin tana ce min karyawa fa nace mata da,dai akwai dumamay tuwo ne shi nake son ci. Tuwon aka dumamon an saka mai man shanu shi na danci kadan still ina jin tashin zuciya har lokacin. Nan mama take tambayana yaya za,ayi da kayan da mukazo dashi nace a fitar wa Baba na da nasu sai su raba sauran amma sabulu da clean abawa makwabtan su. Yadda nace haka mamana tai rabo na adalci don har na Baba na yafi yawa sai da nazo nagani nace a,a daidai za,a raba ita dashi. Mutanen da aka kai ma tsaraba sukai tashigo yi muna sannu da zuwa naji dadin yadda mutane sukai ta nuna min karamci haka. Ice dake gidan mama a karkashin shi muka mayar gurin zaman mu ni da iya sai dare muke shiga daki don rana haka na wuni kwance rijib ba lafiya. Iya ta matsa wai na fadawa maigida banda lafiya asan abin yi nace mata haka nakeyi dama idan nai tafiya. Sai mama ne da iya dake taya ta aiki suke ta faman kai kawo a tsakar gida kawuna yazo amsa kiran mamana da ta aika tana neman shi. Nan suka kebe tai mashi bayanin komai kuma ta kawo kudin aikin ta damka mashi don shi a garin yake zaune dama gurin shi tazo har mijinta ya ganta ya aureta. Sun gana da maigidan mama da kawu yace aiba matsala wanan taimako ne ai akai mashi da yamma kuwa sai ga masu aiki sun shigo gidan suka fara awon yadda za,a fitar da plan din ginan. Dakuna guda biyu na mama ciki da falo dayan kuma single ne sai wasu biyu a gefe daya su ma sai na samari washe gari yan aiki suka fara aiki akan idona akafara komai ga katan aiki kawu har ya sawo an fara aiyuka ko. Da dare daga ni sai mama na a daki Iyya na waje kwance wai zafi take ji. Nace mama dama ina son mu samu lokaci in fada maki wani magani da aka anso muna naba yaya yasha wanda ina gani shine sanadin barin shan abin maye da yakeyi. Nan dai nai mata bayani da kuma garin don ba nisa tace tagane mutumin ai dan uwan mahaifina ne tace insha Allahu zatayi kokari taje gurin shi. Muna cikin hirane yaya sadauki ya kirani muka gaisa yana jin murya na yace Fatima na amsa may ke damun ki nace may kagani ne yace you sound like baki da lafiya na kakaro murmushi nace daga barci na tashi yanzu barci na somayi kata dani. Ina ganin bai yarda ba sai naji yace humm kawai yace ina mama nace gata tare dani barin bata ku gaisa dama tana son maka godiya. Yace No No godiyan may kuma don nayi wa mamana alheri haba kada ma ki bata idan hakane kice ina gaida ita nace to ya kashe wayan. Koda ya kashe wayan hankalin shi bai kwanta ba yadda yaji muryana sai hankalin shi yai matukar tashi. Amma kuma baida yadda zaiyi tunda nace mai lafiya nake da ance sokoto nake da ya zo gobe gobe taga yanayin da nake ciki. Dole jiki ya matsa min ban samu tafiya ba ranan da muka ce zamu tafi sai da dare ya samu time ya bugo min waya yana tambayana mun sauka lafiya da kyat nake magana don da zazzabi na wuni. Yake tambayana ko mun sauka lafiya yaya baba nace cikin karfin hali ban samu wucewa ba yau yaya. Ya rage fara,anshi yana tambayan saboda may nai mai shiru yace baki da lafiya ko Fatima ? Shine kika shige kauye kika zauna da ciwo yana cin ki ajiki haka. Watau ke kin samu su mama kin manta da lafiyan ki ko ? Na rasa abinda zance sai da ya kara tambayana may ke damun ki ne ma wai ? Na rasa abinda zance mai sai can nace zazzabine amma naji sauki shine mama tace na bari sai gobe mu tafi idan na kara jin sauki. Yace a zaune zaki ji sauki bakiga likita ba ko may nace nasha magani ai na samu sauki yace ina Iyya take ne wai nace tafita. Yace gobe goben nan ki koma sokoto zan ma bashar magana yazo ya kaiki asibiti idan kun isa kafin na iso. Gabana yai matukar faduwa gashi banje gurin babana ba kuma yasan munzo. Na marairaice nace don Allah yaya kayi hakkuri naje gurin baba nai kwana daya jibi sai na karasa gida. Bai jira may zance ba ya katse layin bayan dan tsokin da yaja. Mama dake zaune gefe na takale ni a tsorace tace so yake ki koma gida baki isa can ba ? Na bata fuska tare da jan tsuki nace wai haka yake nufi ni kuma ba zan koma ba banje gurin baba tunda ba bari yake nazo ba. Tace a,a yar baba kirashi ki roke shi idan ya yarda sai ki karasa gurin su idan kuma yace lalai sai ki koma gobe din sai ku shirya ku koma din. Na dai daga wayan badon naso ba ga mama ta tsareni da ido na kirashi na zaci ba zai daga wayan ba dana kira. Amma sai naga ya dauka yace yaya akayi kuma ? A hankali na ce mai kayi hakkuri yaya don Allah naje gurin baba gobe nai kwana daya sai na dawo kada yace ko gudun shi na soma yi na rike uwata. Yace as you wish ai jikin ki ne nace kadai yi hakkuri please gobe da safe zamu karasa can mu kwana da safe sai mu taso. Yace na fada maki da kun kwana daya ki dawo gida kije asibiti aduba lafiyan ki nace insha Allahu jibi da safe zamu taso da yarda ubangiji. Yace is ok Allah ya sauwaka nace nagode muka kashe wayan mama tace ai kinga haka yafi da ran shi ya baci yakawo ki cikin dadin rai kuma akoma ana haka baiyi ba gaskiya. Nai mamaki irin tsaraban da mama ta hada muna mu tafi dashi wai kaji, man shanu fura da nono kwakwamayti kuka daddawa da kuli kuli da kwanzabbi mai yawa. Mijin mama ma yabani mamaki rago yasa akayanka aka,soya shi sai da ya cika bucket din penti yace nashi tsaraban ke na da mazzakwaila mai yawa. Tun da safe mukai masu sallama na wuto da kauna ta Sa,ade muka bar Asma,u tana kuka nai mata alkawari itama zan dawo in dauke ta ai tai makaranta haka yasa tai shiru. Sai kauyen mu nan na samu baba bai gida da farko kamar mama tabawa bazata karbe mu ba amma tana ganin an fara jido kaya ana shigowa dashi tafara washe bakin ta tana cewa sai yau Hjy maryam tun fa shekaran jiya akace muna kina Rabah. Nai dariya nace wallahi mama munje daniyar nai kwana biyu nazo nan nakarasa kwana uku sai ga ciwo ya rike ni acan. Tace assha subahanallahi inji da sauki dai ko nace naji sauki mama. Nan muka basu tsaranan su na aika,wa kakanina da nasu sukai ta godiya. Da baba yadawo shima na bashi nashi sakon yai ta saka albarka kwanan mu daya tunda safe muka kama hanya sai sokoto. Rijibb na iso garin na kwanta bamu jima dashigowa ba wayan yaya ya shigo yana cewa yaya kun taso ko nace gani dakina kwance yace ki shirya bashar yazo yanzu kuje asibiti. Ba adade ba bashar yazo muka wuce asibiti ganin likita duk a lokacin na jigaye na wahala sosai. ****** ********* ****** A gurin da zanga likita ma sai dana dan kwanta kafin shiga ya kawo kaina banda kuzari sai yawan jin kasala dake damuna ko ruwa nasha sai na fitar dashi san nan naji shakat a raina. Nan yakira wayana nace gamu asibiti muna jiran layi yazo kan mu ne. Yace wai may ke damun ki ne Fatima haka ? Na lumshe idanuwa na nace ban sanni ba yaya komai naci dai sai na amaye shi kuma banjin kuzari a jikina ina dai ganin maleria ne yai min yawa a jikina. Yace bari a shiga gurin likita muji may ke damun ki haka kilama ruwan kauyen ku ne bai karbe ki ba kike wanan wahala haka ? Mun shiga gurin likita yai min yan tambayoyi irin nasu ina bashi amsa can dai yajefo min tambaya yaushe rabona da period ne ? Gabana ya fadi sai lokacin na tuna zancen wani period can nace gaskiya ina ganin kamar yakai kusan three month yanzu sai dai koda nake gida ai nakan yi irin haka din. Test akai min cikine dani har wata uku da kwana takwas nan dai suka rubuta min magani tare da,son na samu hutu don nayi weak da yawa. Kunyane ya rufe ni da akewa yaya bashar din bayani tun nan yaya bashar yake min congrats. Muna fitowa wayan sadauki na shigo mashi yace wai may ake cikine kunga likitan. Yace eh mungan shi gashi mun fito zan da tsaya na sai mata magani ne mu koma gida. Yace may sukace yake damun ta yace may ko zasuce banda cutar daka zubawa yar mutane mugu kawai. Gaban sadauki ya fadi shidai yasan baida wani cuta a tare dashi asalima shiba mane min mata bane balle. Yace for god sake may ya samu fatima din Bashar wani cuta ke gare ni da zan zubawa Fatima shi ? Yace kaiko keda cuta gatan kana kayan shi cikin wando kullun kana durawa yar mutane wahala. Nan yake ta tsokanar shi har yagane ciki yake nufi ke gare ni yace don Allah da gaske kake yi ko shirmay ka bashar ? Lokacin yake shigowa mota yake ce min karbi wayan maryam ki fada mai da kanki tunda ni ya mayar dani makaryaci yanzu. Kuma ka shirya tukwaici na wallahi don wanan ba karamin albishir bane nai maka. Yamiko min wayan yace ga fitinanen mijinki kiyi mashi bayani da kanki ko zai yarda murmushi kawai nayi mashi. Na dauki wayan cikin sanyin murya nake cewa hello yaya. Bai amsa ba sai cewa yayi wai wanan munafikin maganar gaskita yake fada min ko wasa yakeyi nace uhumm kawai tare da murmushi na mikawa yaya bashar wayan shi. Nan sukaci gaba do zolayan kan su har muka isa gida yaiwa iya bayani kan ance ana son in samu hutu sosai don haka kada ta bari inyi aikin komai please. Barci ne ya dauke ni mai nauyi ban falka ba sai misalin karfe takwas na dare koshi amai din ne ya tayar dani a lokacin. Sai dana natsu na jawo wayana kirane ciki barkatai na mutane nashi yafi yawa amma. Ban kirashi ba don yanzu ko hayani kwarai ban so sosai na shiga whastff nan naga yayi posting din suraitai barkatai na farin ciki. Ban dade ba nafita na kwanta sai ga Iyya tashigo dakin take min yaya jiki nace mata naji sauki sosai. Tai min tayin abinci nace tea nake so na ruwan liptop kawai ba madara ba sugar tace ikon Allah shi ta hado min na zuba zuma ciki dan kadan nasha shine har naji dan dadin bakina nai sallah na kara kwantawa. Da safe kiran mama ne ya tayar dani daga barcin tace Fatima ashe kin dawo kuma ba lafiya nai dan muushi nace wallahi mama. To yaya jikin da sauki yanzu ko nace naji sauki sosai mama tace shima yace insha Allahu yau zai dawo zuwa yamma don yana abuja babu jirgin safe yau. Nace Allah yakawo shi lafita tace amin ki kula da kanki kinji Fatima Allah ya inganta banyi magana ba don kunya. Falo na fito na samu Iyya da Saade azaune suka gaishe ni tare da min Allah ya sauwaka. Can nace Iyya afito da tsaraban nan kiraba abawa mutane nasu tace to nace man shanu da nama akai wasu mama shi idan kin dibi naki tunda munan akwai nama su zai masu a.fani suna da yawa can nasa ta diban ma anty maryam nata da Inna mama bashar kwai nace akaiwa mummy ta soyawa yaran ta. Yadda nace haka iya tayi kayan miyane kawai tabar muna don muna da bukatan su sosai. Iyya ce da kanta takaiwa kowa nashi mama tai matukar jin dadin yadda nayi don Iyya ta labarta mata komai kwai danace akawo wa yaran mummy da kwakwamayti ya matukar burgeta har mummy din suka ce suma suna nan shigowa su gaidani. Nan mama ta debarwa ko wani daki ta aika masu tana fadin ga tsaraban Fatima nan da ta dawo dashi suka karba suna gyatsire fuska kuma suka shiga ci. ****** ********* ****** Bayan sallah azahar mama da mummy suka shigo tun a kofa mummy take fadin ina yake tun bai fito ba na kwali kan na yana wahalar min da yarinyana haka ? Kunya naji sosai na dan dukar da kaina,a kwance suka samay ni saman dogon kujera na mike da kyat muka gaisa dasu nan mummy take fadin tun da dare sadauki yakirani yake fada min ai ban san lokacin da nai ihu ba har Alhaji saida yafito. Mama tace kai in ma ba abin kurciya ba yaya mutum zaiyi ciki har wata uku ba,a sani ba tun fa tafiyan su ke nan ta dawo da cikin nan amma haukan shi bai bari ya sani ba. Taron dai kurciyane hajiya inbashi ba ai ko ita zata gane tana da ciki a jikin ta ma kawai dai duk kan su kurciya yana cin su ne. Mummy tace mazajen ki na gaishe ki sunce sunga tsaraba sun gode sunace suna murna wai yayan su ya samu baby Banan da haukan ta wai nazo da ita ta dauki baby. Murmushi nayi nace lah mummy shine baku zo min da ita ba tace ban iya kiriniyan ta barta can suzo idan yayan su yadawo yakai su yawo ai yasaba da kwaram din su shi. Mama tace a,a Sa,adatu din ke nan ai ni dani kuka ba ita ta debe min kewan ku wallahi gata kamar ku daya wallahi nace mama ai munfi kama ko da Asmau sosai idan kingata kaman mu yayi yawa tana can mun barta tana kuka wai ita ma sai tazo mukai mata wayo nace zanzo na dauke ta daga baya yanzun ba wuri. Amma ko Fatima baki kyauta ba kikabar min Asmaun nawa kaunata ce ina ji da ita duk cikin kanne na wallahi. Bari ya dawo ai zan sashi ya tura azo min da ita tunda ku baku son zama da ita nan. Naji dadin jin haka kuma haka nake so don ina son yaran su fito suyi karatu itama mama ta dan huta yawan iyali. Idan kuma ta zauna gurin mama zata sha dadi sosai a gurin ta don mama uwace bata fada ba. Basu wani dade ba sukai muna sallama suka tafi akabarni da Iyya da Sa,ade a gida musa ya fita abin shi. Sai da dare ya shigo garin ina,falo kwance na dunkule yashigo gidan Sa,ade naji tana mashi sannu da zuwa don tare muke zaune Iyya tana kitchen. Yashigo idanuwan shi na akaina har ya karo inda nake kwance ina kokarin mikewa zaune daga kwancen da nake. Yace No don Alla kwanta abinki yazo ya zauna bakin kujeran da nake kwance haka yasa Sa,ade mikewa ta nufi kitchen gurin iya tana fada mata dawowan shi. Ya dan kai hannu shi a saman wuyana yana tabawa a hankali yaji ba zafi sosai yace how the you feel now ? Nace a hankali da sauki ya daga hannuwana ya rike a cikin nashi gama yace I dont know what to say but nagode Fatima na gode kwarai da wanan babban kyauta da kikai min. Na lumshe idanuwa na a hankali tare da kwantar da kaina ga jikin shi nace yaya I miss you. Yai dan murmushi ya shafi fuskana yace kina hakan da fa fushi nake dake da kikaje kika zauna da ciwo a kauye kamar wacce bata san zafin kanta ba. Amma yanzu kin wanke kanki ko gare ni komai ya,wuce ko yake cewa yanzun may kike ji kuma ne wai ? Nace ba komai yaya bandai jin karfin jikina ne kawai sosai kamar farko yace ina zakiji dadin jikin ki kina haka Allah dai ya rabaku lafiya kawai. Wanka ya,shiga yafito ya dawo falo inda muke don ni na kasa tashi ma,a lokacin sabada jiri dana ke ji. Da dare ma dai haka muka kwana dole washe gari aka sa min ruwa don amai yai min yawa sosai. Wani irin ciki ne wanan kuma bai bani wahala ba da farko sai yanzu gashi yana son kawo min cikas ga karatuna. Haka nake daurewa na je lectures na dawo gida a,wahalce yau ciwo gobe lafiya. ****** ********* ****** Wasa wasa baba sani ya saka sadauki a gaba da zancen Rahama duk da mama tace bata yarda ba ita. Ido da ido sukayi da baba Sani take fada mashi indai ita ta haifi sadauki wallahi ba,a auren nan sai dai in bayan ranta za,ayi shi. Tace yanzu kasan suna da zumunci kamanta lokacin da kaiwa mutane cin mutunci kace dan shaye shaye ne shi baka aura mashi yar ka naje cikin dangina na nema mashi. To na nema mashi din kuma yanzun sai hassada da kyashi ya biyo baya nace ba ayin auren idan kuma ka isa sai ayi mu gani. Yace ke wallahi hauwa baki isa ki raba muna zumuncin ba sai dai ki mutu amma sai anyi wanan auren muddin ina raye kuwa . Mama tace to ayi mugani idan kaika haifa min dan dakace na bari ya baci da shaye shaye saboda sakaci na a baya. Sai da baba ya tsawa ta masu yace subar zancen zai yi tunane yaga mai yadace yasan maji na da gaskiya kuma baitaba ganin ta rufe ido tayi sa,insa da wani ba haka sai ranan. Takira sadauki tun a waya ta falfalleshi so sai har hankalin shi ya daga tace katatake mutanen da basu kaunar ka da alheri su shiga cikin jikin ka. Yar matar ka kuna zaune lafiya za,a shigo a tarwatsa maku farincikin ku da tsagumi yace wallahi maji ni wanan magana ma bai gabana don na riga na fada mai gaskiya ko. Ana haka ma tafiya wasan su ya taso ban tashi ji ba sai bayan tafiyan shi da Nafisa tazo take ce min . Ke ashe wanan munafukan wai yanzun kuma yayana suke so ya auri Rahama bayan sun gama ciwa mutane mutunci. Gaba na ya fadi nace wata Rahama kuma ? Nan dai tabani labarin abinda ya faru da Baba Sani da mama ranan a gidan su tace wallahi maji tabani sha,awa yanda ta mayar mai da amsa son ranta. Munafukin mutum ne fa tare suke makircin su dasu Umma kullun akan yayana ko yanzun ma kila wani makirci ne suka kulla suke son ayi hadin. Duk da hankalina ya tashi ban nuna mata ba sai cewan da nayi kai anty baba kikecewa muna fuki kuma ? Au ke baki san munafuki bane dama mugune wallahi duk shi ya cinyewa baba kudin shi haka suke so kuma yanzu su shigawa yaya su cuce shi shida yaya Imirana kuma fa duk su Umma ke turasu don basu da tausayi dakika gan su nan. Tausayi tabani nan ta kwanta tai barci ta tashi tace tana son shan tea ni da kaina ba hado mata tea din da nai mata hadin da bata sani ba acikin shi. Tana gama sha tace zata tafi nakawo alheri dana saba mata idan tazo nabata dubu biyar da su man shafa da turare tai min godiya ta tafi nace Allah yasa a dace . Aiko da dare tafara gala baita hankalin uwar ta yai matukar tashi sosai a ka kwasheta sai asibiti ranan can aka kwana da ita hankali a tashe. Sai da tai kwana biyar tana abu guda a asibiti aka gaji aka sallamota. Ko yaushe muna makale da waya da yaya muna hira akan dai zancen ciki yake min surutun shi sai nagaji nace zan kwanta. Da safe ma,shi zai kirani ya tayar dani yana min yaya jikin haka na zan shirya na tafi makaranta da alolayi . Ranan nakewa maryam magana kan zancen Rahama tai mamaki inda na samu labari tunda mama tace kada abaru na san zancen ina cikin lalura haka. Ban fada mata inda naji ba sai dai cewa danayi ni ba wai shigowan ta nakewa tsoro ba wullakanci nake gudu tunda ita yar gida ce ni bare. Tace yar gidan wa Fatima don Allah ki daina kiran kan ki da bare a cikin mu please. Tace balle ma may yaya zaiyi da,wata Rahama can bakiga yadda takoma bane yanzu fa yan wahala wai harda ranon anko sukeyi fa. Nan naji hankalina yai matukar tashi sosai ranan har saida jikina ya tashi cikin dare dole aka kaini asibiti a can na kwana kwanana biyu Allah ya taimakeni anyi hutu sai mama tace a wuto dani gidan ta tunda dai jikin yakiya kuma shi bai gari. Daga ni har Iyya da Sa,ade muka koma gurin mama can gidan su amma ina matular jin jiki. Maryam ke fadawa mijinta har da zancen Rahama da nasawa raina ke kara damuna. Yakira sadauki ya fada mashi suna kashe waya sai ga kiran shi yake cewa uban wa ya fada maki zan auri wata Rahana can da zaki tayar da hankalin ki haka kina batun kashe kanki Fatima ? Murmushi nayi nace haba yaya akan Rahama zan kashe kaina don may zanyi kishin yar uwar ka ce fa ba,a aure ka aure ni ni ? Yace waya fada maki auren Rahama zanyi ne wai Rahama may ce ni bata ko a cikin lissafina wallahi. Sai da ya gama fadan shi yake tambayan jikina nace mai naji sauki yace kina cin abinci kuwa nace eh mama tana saka ni gaba na sha koko. Yace kokon may kuma can Fatima koko abinci ne da zakice kina cin abinci. Zan wa maji magana ta saka ki gaba sai kin dinga cin abinci sosai na dan marauraice nace ko naci wallahi bai zama a cikina wahala kuma yake sakani. Ya kashe wayan nace namiji ke nan kamar badashi ake wanan zancen ba ji wau Rahaman may can kamar ba a baya sun sha soyayya tare ba. Yadda ma nake jin labari duk abinda ya samu su yake kaiwa ita da uwarta shi yasa bai kawowa maji komai a lokacin. Amma da suka tashi bashi baya suka rufe ido sukai mashi cin mutunci ta uwa ta uba. Baba da kan shi yake zuwa har dakin maji da safe ya duba lafiyata wanan abin yana matukar ciwa su Umma da mama rai sosai. Sunyi gulma har sun gaji sun kyale shi suna zunde wai don ina matar dan son shi ne yake min haka. Ya bugo min waya muna zaune da mama da Iyya yake ce min gashi wani shago yazo shopping din kayan jarirai wani iri zai zabo antambaye shi yace a bari ya tambaya. Sai naji yace Fatima mace ce ko namiji a cikin ki innalillahi na furta da sauri suka kallo ni mama taju tsoro ta karbi wayan a hannu na lokacin da ya kara tambaya yana cewa fada min mana please. Mace ne ko namiji ba ance kuna ganewa ba idan mace tana da ciki don in san wanda za zaba. Mama tace to mara kunya ita ba irin ka bane mara ta ido kai kasan wanan ita batasan shi ba kada Allah yasa ka sayo din insai tafada maka abinda ta kumsa. Kaida kaicikin bakasan ko wani iri bane ka saka mata a cikin sai itace zata sani mara hankali kawai. Amira da ke zaune ko kallo bamu ishe ta ba tai tsuki tace maji tambaya fa kawai yakeyi killa yana son sayo kayane a can. Shidai yana jin fadan mama ya kashe wayan yana dariya kawai. Wani irin mahaukacin sayayya yayi kamar bai san zafin kudi ba yadda ya kashe su akan kayan baby kawai. Har su kayan wasan yara saida ya sayo sukekuna da gadaje ya hada da kayan uwar jego gaba daya, ya sako su a jirgi kaya guda dasu. Sai da dare ya kirani yana cewa watau dazun kika hadani da maji ko don kina muguwa na dauka abin siri ne tsakani dake amma kika mika mata waya don keta. Nace to naga sune manya su suka san abinda ya dacs asaya shiyasa nabata wayan ta fada maka abindake cikin. Kai dan kwallo dai bai jin wahalan kashin kudi kodan samun shi sukeyi any howa balle shi dayake ya,shara dan kwallon duniya ne shi yanzu kasa kasa ana hayan shi ya buga masu wasa. Don nan yanzu sun dauko sheri wa yaran musulman mu sai su hana su buga masu wasa idan za,a tafi. Haka yasa yanzu yai watsi da yan Nigeria yake bugawa wasu kashe she sai daga baya kuma suke son wai ya dawo masu yanzu ya dinga buga masu. Amma shima yaja masu aji ayace yabarsu can inda yake sunfi sanin darajan su suna biyan su da tsada fiye da nan da,ake masu kyat. Yayi kudii fiye da tsanmani don dai yana,bogon kurwa ne ba,a gane yawan kudin shi sai wanda yasan kan abin. Yana can yana gina gida a abuja wani irin maithigh house na gani na fada ba wanda ya sani sai yaya bashar da Baba kawai da mama. Don gudun yan baki irin su Umma don gujewa sherin su da munafunci don zasu iyacyin komai suga bayan shi. Zaman mu gurin mama yakaiwa Anty Amira ko ina don yadda mama take ririta sai take jin haushin hakan a ranta. Cewa takeyi wai shagwabane nakeyi ba wani ciwo dake damuna don dai naga kawai ana kulla min ne. Sai ranan da dare fever ya rufe ni sosai taga an rufa min bargo amma jikina sai shocking yake ina rawan sanyi Shine washegari har na samu sannunta take min yaya jiki yaya Sagir ne ya kai mu asibiti ni da mommy muka tafi akece wa fever ne na masu ciki yakamani. Kila sauro ya cije ni ne sadauki yana ji yaturo bashar a gyara AC a canza fanka a saka neat a window mama da kofa. Amira tace lalai ashe abin nayi ne wai duk a bintu ake wanan abin haka wani aiki kan sai malam. Ina jin ta nai murmushi nace lalai kam malam yai aiki saura biya tace Allah dai na ganin ki wallahi idan ma daure min dan uwa kukayi ke da mai masa dama ta iya bakar shige shige ai wa mutane balle nata. Nace ai wanda tayi ma saka ta akayi tayi din ba yinkan ta bane tayi don haka ashe masu ahige shige suna da yawa. Aiko tace wai na zage ta nai mata cin mutumci nan tafara min masifa mama tashigo tasamu tana min zari tace a,a ashe rashin tausayin naki yakai haka yarinya bata da lafiya mijin ta bai gari kice zakiyi mata rashin mutunci. Ke na gaji da wanan bakin halin naki wallahi Amira nan gidan su Bintu ne tunda gidan mijin tane kema kije ki nemi uwar mijin ki can ku karata can da ita. Amma baki zuwa ki saka min yarinya haka a gaba bata da lafiya kin isheta da masifan tsiya haka. Haka taita tunzura ta kwashi fushin ta tashige daki itama maji tafice zuwa waje. Iyan Rabi tace kinyi daidai wallahi wanan yarinyar kamar ba hajiya ta haifeta ba wallahi mugun halinta yayi yawa Allah. Nace haka take ita bara da,son jama,a yaniyin take tunda tace kai dan Allah wallahi dai halinta baiyi ba. Mutum bai da lafiya ace kuma bakai mashi sannu ba sai bakar yadiya. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,, IDAN KUMA KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH,,, Mun kai wani lokaci mai tsawo tare da yan uwa ana ta yaushe rabo a tsakanina da su wanda yawanci duk wasan su akaina ne su na min wasan kanin miji. Ganin yai shiru nasan halin abina bai faye son surutu mai tsawo ba shi sai dai a dan yi ai shiru yasa na fahinci taron hayaniyan ya dan ishe shi ke nan a lokacin. Na dan mike zuwa gaban shi nace tare da dan rakwafowa gare shi yana zaune ya rike goshin, shi da hannu daya yana dan murzawa a hankali idanuwan shi a lumshe gaba daya. Jin muryana kusa dashi ina magana ina cewa yaya may za,a zuba maka ne kaci ? Bude idanuwan shi yayi ya sauke a fuskana da nake duke gap dashi na kara cewa may zakaci ne yaya? Ya dan sauke min murmushi yana fadin duk abinda kikaga ya,dace dani ki zubo min. Gurin dinin na tafi na fara hada mai abincin gargajiya wanda mun dade bamu ci shi ba sai yau da muka dawo gida. Tare da zuba muna ferfesun kayan cikin rago dana danyen kifi manya masu tsoka sosai. A plate daya muka ci abincin da yake ba,a saman table bane kowa yana kasa nan kowa ya fara diban abinda yake so muna ci muna hira tsakaninn mu. Nice na fara mikewa tare da dan fuskan tar yaya nace zan dan shiga ciki na kewaya wai irin kallo yai min wanda yasa dul wanda idon shi ya kai ga kkallon a lokacin sai yaji wani iri. Don da ido yai min magana na taimaka mashi shima na shige dashi a cikin dakin shi. Hannu na mika mashi ya kamo tare da mikewa tsaye muka shige daki dakin shi muka fara shiga sai da ya shiga wanka na fito zuwa dakina wanda nai watanni ban a cikin shi. Wani kamshi ne mai tuna min da abubuwan da suka shude a baya da dama kamshin dakin nawa ya,tuno min. Maryam ce ta biyo bayana muka zube tare da su a dakin nan na shiga wanka na shirya cikin wani riga dogon milk color mai guntun hannuwa. Na mulke jikina da kayan kamshi masu kyau da tsada na gyara na fito inda kowa yake bayan nayi sallah. Mazan sun fita zuwa masallaci mu matane muka rage a cikin gida sai ga Nafisa da kawayen ya sun shigo taron mu. Da murmu muka tari juna da su kowa yana mamakin dalilin shakuwa na da su darrr ake zaune dasu kamar ana ga masu cuta a jiki ko kuma masu wani aikin kissa. Sun fahinci cewa kowa yana jin haushi zuwan su gidan a lokaci da yake basu da kunya sai cewa Nafisa tayi ni dai ba gurin uban kowa na taho roko ko maula ba gidan dan uwana ne nazo dole kuma nayi yadda kowa keyi. Nam suka so kaurewa da maryam da ita dama ba shiri tsakanin su tun gida Allah ya kawo yaya ya daka masu tsawa tare da masu fada suka daina. Kamar yadda Nafisa tace yadda kowa yayi haka zatayi don gidan dan uwan ta ne hakane kuwa tayi. Don mikewa tayi ta kwaso abinci gudan mai yawa ita da kawayen ta komai na gurin sai da ta debo masu shi duk an saka masu idanuwa na ce su zo muje dakin Iyya can muka zauna tare da ni dasu da ma maryam din . Karshe suka shiga bamu dariya tun maryam na daure fuska har ta shiga dan murmusawa hiran da sukeyi mun dauki lokaci da sune sukace zasu tafi ina tsaraban su don shi ne sukazo tun yau kada a wawashe a barsu. Nace tsaraban ku ya na hanya sai zuwa ranan Thursday ku shigo na baku naku Raina tace kai uwar dakin mu walleh kada ki sa muyo tahiyar banza mu taho bamu ga yan, kudin man, mu kuma bamu ga tsaraba. Nace shim banita nice ku taho ba walleh na,sayo maku tsaraba tun can da sunan ku na sayo shi . Wani ihun dadi suka yi suka tafa tare da shewa shiya sa muka son ki uwar dakin mu don ke dauki duniya simple ba ruwan ki da wani jiji da kai ko kyamatar halin mu gare ki. Nace kai amma dai anty akwai ku da wani irin magana lalura ta Allah shi yaye maku ita bayan ita minana gare ku na kyama tunda dai nagani da idona kuna sallah to miyarage kuma watan azumi anan kuka daukan abin buda bakin ku to mi aka so. Nan dai mukai sallama dasu na fito na raka su har bakin kofa na juyo muna dariya. Yaya Sagir yace Fatima ina kika kwaso wanan gayyan tsiyan haka,wa yan nan mu,amula dasu ba alheri bane fa . Yaya bashar yace ai kuma kaji matsalan mutanen mu ke nan wallahi sai a dinga gudun mutum shi ke kara jefa su ga halaka sosai wallahi . Yanzu yadda kaga Fmta sake da Fatima haka duk yadda ta juya ta zata bi don bata kyamace ta ba kaga zata iya mata nasiha har yai tasiri a kanta idan ma wani magani ne yadda da shakuwa zai sa ta yarda tasha koma may nene. Shiru Sagir yayi yana sauraren maganan bashar yace bai kamata ace kuna nuna mata kyama haka ba kujawo abinku ga jiki da sannu kuna mata nasiha kuna bata taimako har ta gane gaskiya idan tana da rabon dainawa. Amma gaskiya nisan ta kai daga mai shaye shaye yana kara jefa su ne a cikin halaka kawai. Shi kan shi yaya Sagir maganan tayi tasiri sosai a ranshi sai yake ji daga lokacin zai yi kokarin ganin ya jawo Nafisa a jikin shi ya taimaka mata. ****** ********* ****** Washe gari muka tafi gidan su mama muka gaida su suke cewa ai da mu bari suzo su samay mu su tare mu . Yaya yace haba kai ai mune masu neman albarka a gurin ku dole muzo inda kuke mu nema. Mummy tazo dakin mama ta samay ni nan muka zauna ana hiran tafiyan mu tare da mukayi a saudiya. Duk hiran mu Amira na gefe a zaune mugun halinta yana cinta a lokacin bata saka bakin ta ba. Mummy da ta fahinci haka tace aike Fatima sai ki godewa Allah don Allah shi ke azurta bawan ya duk sanda yaso. Yau ga shi kece a wanan kasashen duniya ga yaran gidan mu da suka tashi a cikin daula wasu ko Abuja basu sani ba balle wanan irin kasashen da kika shi ga haka. Maji tace ai ubangiji miskarraziratin ne shi ke yin da yaso da bayin shi a duk inda yaso. Yanzun baga shi ba hajiya da gidan wani akakai wanan auren ai wani abin sai dai mu hanga a cikin gari ko a makwabta kawai. Amma yanzu kinga hikimar manya da mijin da matar komai gida,yake dawowa gaba daya shine ai ake cewa duk abinda babba ya hango yaro ko ya hau sama baya hango shi. Yaya sadauki dake gurin Baba tun shigowan mu yana mashi bayani akan tafiyan mu irin nasarorin da yayo a gurin wasu masananta da ya saka hannun jari acikin su a waje. Yace to ke tashi mu tafi hakana ko mun bar iyya gida ita kadai mama tace yanzu yarinya na zaune tana hira zakace wai ku tashi ku tafi. Mummy tace yanzun fa ya san dadin iyalin shi bai son zama inda muke kuma . Yai murmushi yace wallahi mummy ba hakana bane kawai da Iyya Rabi da muka bari a gida ne ga kuma mutane suna zuwa taron mu har yanzu. Mummy ai da zaku bamu daki a gidan nan sai munfi jin dadin zama a kusa da ku dariya sosai yaba mummy har saida tayi tagaji don kan ta. Mama ta saki ajiyan zuciya daga inda take zaune bayan mummy ta fita daga falon tace Allah sarki ubana har na rasa farin ciki da jin dadin da zan nuna dana gan ku a gaka wallahi. Yace kai haba maji falalar adduan ki ne fa yakaimu ga haka baki dayan mu ko Amirah yana takalar Amira da yaga ta cika ta batse da shi. Mama tace kai amma babana baka da zuciya duk wanan iskancin da take shukawa mutane don taga ta samu guri. Amma katsaya wani kulata can wallahi Amira da kake gani na kusa fita bayan ta muddin bata fitar da miji tai aure ba mu huta da bakin iya shegen nan nata. Sadauki ya kwantan da muryan shi kasa cikin sanyi yace maji kiyi hakkuri don Allah nima wanan karon na dawo da wanan kudirin a raina ina son naga tayi aure itama ta kama dakin ta hakana ta huta da fadan ki. Damu da ita dukkan mu dole ne muyi maku biyayya kada ki damu maji zata fito da miji itama tai aure badadewan nan ba zamu sha buki insha Allahu. Mama tace Allah ya bada ikon yin hakan ga maryam har tana batun haihuwa ita ko ajikin ta. Sai wanan lokacin Amira tai magana tace ikon Allah maji gama wanda suka aure basu da komai saini da ko auren banyi ba ake min gori. Wani iri naji a raina da magansn da tayi nasan ni takewa gori a fakaice naji sadauki na fadin lokaci ne baiyi ba Amirah wata rana sai labari. Kiyi hakkuri gaskiya ake fada maki ba wai ba,a sonki bane aure shine darajan diya mace zan zo mu zauna dake sai muga may yadace ayi. Baba ya aiko akira mashi sadauki yafita yakoma dakin baba din ina zaune nai shiru don gaba daya jikina yai sanyi da maganan Amira. Don na fahinci so take ta jawo min wani sabon matsala a rayuwa na ganin yadda nai shiru cikin damuwa yasa mama kokarin sani magana tace. Waiko Fatima na kin ko ga yadda kika koma kamar wata diyar larabawa dake can aini da a hanya nagan ki bazan gane ki ba gaskiya babana ya iya kiwo sosai wallahi haka duk uwa ke son ganin diyan ta a cikin farin ciki. Sai aita hakkuri da rayuwa don hakkurin bawa bai taba tashi a banza insha Allahu. Amirah ko maganan mama bai mata dadi bane sai mikewa tayi kawai tashige ciki abinta tabar mu inacewa mama. Mama insha Allahu kuma yaya baida matsalan komai wallahi don duk wanan halaiyar nashi ina gani kamar yanzun duk ya kawu. Sanan mama irin mutanen da yaya yake zama dasu abune mai wuya mutum bai fada cikin halaka irin tasu ba. Amma sai naga shi yana kokarin yaga ya kare hakkin addinin shi a cikinnsu da muka je can. Mama taji dadi tace masha Allahu Allah na gode ma abinda nake matukar son ji ke nan Fatima nan mukaai ta hira iina bata labarin tafiyan mu har haduwan mu da Linda a can da mahaufin ta. Sadauki yana shiga gurin baba ya samay shi zaune yadda ya,barshi da carbi a hannun shi yana tasbihi jin sallaman dan nashi ya dago kai da sauri ya kalli dan nashi mummy tana daga gefen shi a zaune. Yace na manta na fada maka cewa muna umurah an shigo dakin nan nawa an min barna wallahi. Da sauri sadauki yace subbahanallahi baba yace wallahi an kwashe min duk agogaiya na masu tsada dama wasu yan abin amfani na bazan ma iya cewa ga iya abinda aka dauka ba ciki. Sadauki ya saki ajiyan zuciya yace amma baba sai naga kamar barawon waje zai iya shigowa gidan nan kuwa ashe ? Babada mummy sukace ba daga waje bane koma,waye a cikin gidan nan yake daya daga cikin yaran nan ne yai min wanan aikin. Sadauki ya kara ajiyan zuciya yace indon agogo ne aida ka fada min tun muna can da an sayo maka wasu daga can munzo maka dasu ko yanzu naga kamar Fatima ta sayo ma agogo guda biyu a Dubai masu tsada da kudin da abokaina suka bata can. Baba yai murmushin jin dadi yace ikon Allah kaga hukuncin ubangiji ko ? Yace Allah yai maku albarka yabaku zuria masu albarka a rayuwanku. Mummy tace nifa abinda yafi tayar min da hankali shine takardun gidan nan da ba a gani ba har yanzu wallahi. Sadauki a razane yace subbahanallahi may kuma za,ayi da takardan gida da za,a dauka ? Baba yace nayi zaton ko suna ganin kamar takardan wani abune suka hada hardashi akwai dai abinda sukazo nema a gidan nan. Sadauki yace insha Allahu zan sa aimin bincike a tsanake ko za,a gano wanda yai wanan aikin haka. Sun jima suna maganan shida baba da mummy ya kwantar wa baba da hankali yai masu sallama yadawo dakin mama. Nan yasamay mu yake cewa mama ashe abinda ya faru ke nan bayan tafiyan mu anshigawa baba dakin shi. Mama tace ni ina ganin yaran gidan nan ne sukai wanan aiki Allah dai ya shirya ko wanene abin baiyi dadi ba wallahi don ta gurin A C din shine suka shiga yadda ba wanda zai gane an shiga dakin. Muna hanya yake cewa kai gaskiya ko waye yai wanan abin bai kyauta ba takardun da aka dauka yafi tayar min da hankali wallahi. Nace Allah ya tsare kada mai shi yayi wa baba bar na da takardan yace nima shine damuwa na wallahi. Har muka kawo gida ba wanda yai magana a cikin mu kowa da abinda yake tunane a zuciyar shi. ****** ********* ****** Sai bayan kwana hudu kayan mu suka shigo gari nan na fara rabawa kowa tsara ban shi har gida sai da na aika masu kuma nace zan tafi amma sai yaya ya hana yace na bari sai an kwana biyu don zamu koma school lokacin. Maryam ta gama karatun ta saura ni na rage yanzu don haka na koma ni kadai ce ke moving a makaranta. Ga idanuwan mutane a kaina duk da ina kokarin kama kaina a matsayina na matar aure kuma musulma. Amma sai kaji ana gulmana wai suturun danake sawa da motan da nake shiga ya zarta na sauran mutane. Kullun fa a cikin hijjab nike amma mutane saboda sa ido har suna fahintan may ke cikin jikina. Dole ne don duk wanda ya sanni a baya babu mai ganina yanzu bai san akwai canji a rayuwana ba. Banda matsala don ina maida hankalina sosai ga karatuna ba sai na tsaya wani loveying ba akan makin dina. Na dawo a gajiye daga school da wuri na shigo gida don yau Friday na idar da sallah ina kwance saman sallayan da nai sallah hannuna da carbi ina ja. Ya shigo dakin nawa yana saye da farar shadda tasha aiki a jikin ta sosai sai maiko take yi. Na dago kaina a hankali na kalleshi yadda na ganshi na fahinci bai cikin dadin rai a lokacin . Mikewa zaune nayi da kyau ina mashi barka da jumma,a ya amsa min tare da zama a bakin gadona. Inda yake zaune na tako na zauna daga gefen shi na kalleshi cikin natsuwa na sakan mai lalausar murmushi don in isar ma zuciyar shi da sako. Nace wa ya taba min sadaukina kuma yau haka zai bata muna jumma,an haka ? Ya dan kakaro guntun murmushi tare da dan jan guntun tsuki yana cewa . Fatima al,amarin yaran gidan mu ne yake bata min rai wallahi yanzun ace duk yadda Baba yai kokarin ganin ya inganta rayuwan mu amma babu wanda ya mayar da hankalin shi ga abinda ya koya muna. Nace yaya ai yan uwanka duk yan uwan ka ne don haka ni sai naga kaman yanzu abinda ya dace shine ka taimakawa yaya Sagir da yaya Abdul su da ke tasowa yanzu ko Allah zaisa a dace ta gurin su. Murmushi yayi tace tunanen mu yazo daya danaki ke nan abinda na dade ina kudurtawa a rayuwana ke nan a kan su. Zan dauko sagir na saka shi a jikina sosai yadda zan samu Allah yasa muna hannu ko za,a samu dama ga al,amarin. Don kinga yanzu ni nan da wasu shekaru dole na bar zancen buga ball din nan da nakeyi don in girma ya kara kama ni ba zan dawma ga wasan ball ba. Shiyasa yanzun ma nake ta kokarin ganin na samu inda zan kafu da kafana koda na daina wasa ya kasance ina da wani madogara da zamu ci musha a cikin shi. Tausayi ya bani don nasan yaba da nauyi da yawa yanzu a kan shi don duk wani lalurar gidan su shine maiyin a yanzu. Nace bayan duk munyi shiru ba dan lokaci mai dan tsawo kowa na tunane a ran shi. Yaya yan uwaka ne na jini dukkan su kuma bakai kade suke yan uwanka ba a yanzu nima sun zama yan uwana na jini. Duk abinda su Umma suke gwada maka kan su,suke gwadawa, abinda basu so su gani yau Allah ya yayi suna gani da idon su. Kaine kuma mutum mafi daraja a cikin gidan mu a yanzu don haka saka masu da,alheri sai aniyar su ta koma masu. Nakai kaina saman kafadan shi tare da dan shafo fuskan shi nace sai kai tunanen inda ya dace ka saka su. Rugumoni yayi zuwa jikin shi tare da sauke ajiyan zuciya yace maganan ki Fatima ya bani kwarin gwiwa a yanzu sosai zanyi yadda ya dace dasu din zuwa wani sati zajiji may muka shirya akai idan naga bashar. Nace nagode yaya aikin na Alheri allah ya kara daukaka shi akoda yaushe Allah kuma ya tsare muna kai daga duk wani abinnki. Ba mu sake junan mu ba ina makale a jikin shi ina shakan kamshin jikin shi maidadin amowa. Sannu a hankali bayan ya dan samu natsuwa naji yai dan gyaran murya a hankali ya soma yi min magana yana cewa ina ta kokari naga kin fara sana,a Fatima. To amma kuma bazan iya bari kina fita ba akoda yaushe don sana,an mata abune dake yawan dauke masu hankali ga harkokin su na cikin gida. Bazan so hakan ya kasance dake ba Fatima nafi son kalar sana,an da kina gida kudin ki suna shigo maki ga account din ki kawai. Wani irin sanyi ya sauka min cikin raina nai maza nace mashi nima yaya ba zanso abinda zai sani na raja,a da bautan Allah na ba ko kadan. Cikin zuciyana naji kanar nace mai to ko muyi sanan kayan dakin mata show room.kawai sai da ma,aikata maza kawai su zauna a gurin. Amma sai naji tsoron fadin hakan don ban san irin tanadin da yai min ba a zuciyar shi. Yana makale dani a jikin shi yake cewa zan kara dubawa nagani idan akwai wani harka mai sauki da zai yiyu. Amma don Allah koma may nene za,ayi ki yi kokari kiyi adalci tsakanin mu kada ki so kanki da yawa a ciki. Nace mashi insha Allahu yaya bazan raja,a ba ga son duniya akan ka yaya sai naji yayi murmushi kawai alamar yaji dadin a ran shi. Sai da ya mike har ya fara tafiya yake cewa yau fa ina ganin mutumiyar ki kamar tana labor ne don nakira wayan Bashar dazun yake ce min wai suna asibiti da ita tun safe. Da sauri nace anty maryam Allah sarki nan na fara murna da adduan Allah ya raba lafiya . ****** ********* ****** Bai dade da fita ba sai ga wayan ta ta bugo min tana fada min ta sauka lafiya nan na yanka wani ihun murna na nufi falo da zuman fada mai yana zaune ya cin fruit don yanzun ya rage yawan cin abin sosai kamar baya sai dai fruits da yan sauran abubuwan gina jiki kawai. Murmushine a fuskan shi na iso da murna na nace yaya yace kun zama su mama yau ko nazauna ina fadin wallahi fa. Nace yaya na tafi asibitin ne na dubo ta yace dauki bai bari ki tsaya mu tafi tare ke nan ko? Naji kunya nace sorry barin tsaya kagama mu tafi, nasan zolayana yake yana ta shiririnta ci har yagama muka kama hanya zuwa asibitin da ta haihu din. Nice nai driving din mu yana gefe zaune sai waya yakeyi yana fafin sister shi ta haihu ta samu baby boy. Muna shiga dakin muka samu yan uwa da abokan arziki harda mummy a gurin don itace tazo daga gidan mu. Yaron yana nade a cikin showel a,saka mai rigan sanyi sky color mai kyau ta jarirai a jikin shi. Ita ko maryam tana kwance saman gado sai murmushi takeyi na karbi yaron na mikawa yaya shi ya dan kalle ni yace Fatima ban fa iya daukan yaro ba fa. Na gyara mai tare da nuna mai yadda za rika yaron ana muna dariya yaya idan naku yazo yaya zakayi inji sister din Bashar nace ai shine fadila Inda maryam take a kwance ya taka yana ce mata sannu yar gidan maji yau kan kin san kin shigo duniya ko? Murmushi tayi cikin jin kunya tace kai haba yaya dama ban san nashigo bane yace to yaya jikin naki normal dai kike ko don naga dan nawa so health dashi. Murmushi kawai tayi tace ummhumm yaya Bintu over to you now ko ni kan na sauke na huta . Ke ban son Bintun nan na fada maku ku daina kiran ta da aanan sunan kauyawan hakana please mutum da sunan shi mai kyau kuna bata mashi da,wani Bintu can. Kai malam yayane kuma mutum yayi fitan kutsu haka shine zaka kama min mata da fada tana kwance a gadon asibiti. Kai dan iska wallahi jawa matar ka kunne duk ranan da naji sunan nan haka a,bakin ta ba hauhuwa tayi ba ko duniya ta haife ranan sai na nashi shegen bakin nan nata. Aiko da sai fada kawai za,a raba mu dakai donbda sai na rama mata yace ga Fatima zaka ramay ko ankan wa . Bashar yace akan ka dai kaida kai min laifi ba kaunats da bataji tagani ba yace ko zaka gwada ne yanzu Baba. Tun da kaga yau ka zama Baba kana gani kamar karfinka yazo ke nan ko yaro. Yaro fa kace min maye kagani anan kuma ni yanzu ai sai dai baba kawi aka bushe da dariya a gurin. Naso yaya ya barni gurin Maryam amma yace mu koma gida gobe zai kaini na wuni a can yanzu mutane sunyi yawa sosai. Haka na tafi gashi muna son kebewa da maryam nasha labarin abinda tasha. Muna hanya yana waya ina tuki ban yi magana ba saida ya gama waya ya furza iska nace kana can kana fada ga abinda ya dace kaiwa fada akan shi. Yace may ke nan fa ? Nace kiran mamana da Majin da kukeyi mana don Allah ua kamata ku canzawa mama suna hakana please. Kuma fa yaya duk kaine ka saka mata wanan sunan don Iyya ta fada min wai baka iyannkiran ta maijidda da baba ke kiran ta shi ne ka dafa mata wai maji can. Mirmushi yayi ya shafo kan shi yace na dai ganecwallahi Iyya Rabi tana min tonon silili a gidana . Nace lah may ye laifin iyya yaya don ta ban kado min sirin baya tafa fada min irin yadda kai ta wahal da su mama wallahi. Yace hummm yai shiru tare da kwantawa da kyau saman kujeran mota ya rufe fuskan shi da hular kan shi kawai. Mun kusa shiga kwanan layin mune naji yace Fatima cikin wani irin murya nace na,am yaya yace wallahi yanzun ban san may yasa ba ina matukar son baby nima sosai wallahi tun dai yanzu dana ga na maryam din nan. Please Fatima will you give my baby too please Fatima ina son naga nima na haihu wallahi. Idanuwana na lumshe cikin wani irin yanayi da tausayin kan mu don ya fadi ne a baki amma ni na riga shi furta hakanna raina. To waye mai laifin a cikin ni dashi da muka kasa samo ma kan mu farin ciki irin haka ? ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,, IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYABA MUN BARKI GA ALLAH YABI MUNA HAKKIN MU AKAN KI,,, Maganan yaya yai matukar tsaya min araina nace a raina wanan kuma matsalar Allah yasan dalilin shi amma har yaushe ma mukai aure da za,a dinga damuna kan haihuwa hakane wai ? Ban fito ba ina dakina don abin yadan damay ni a raina sai nake jin ba dadi a tare dani kawai. Kira,an sheck Ahmad suluiman kano na saka a wayana shine yake tashi ina zaune ina bi a hankali nai makari da gadona ta baya kadan. Dakin yashigo yana saye da doguwar rigar jallabiya a jikin shi yake ce min lafiya kike kuwa ? Dan murmushi ne na kakaro a fuskana nace lafiyata kalau kawai dai sai naji nagaji ne. Yace ok ni zanje gida naga baba nakuma yiwa maji barka daga can don yar gaban goshin ta ta haihu nasan tana can tana murna yau. Nace ba dole ba duk wanda nashi yai ciki kuma ya sauka lafiya ai abin farin ciki ne haka sosai. Nace adawo lafiya yace baza,a sayo komai ba ko idan nafita ? Nace yaya ai akwai komai nake gani adai dawo lafiya muna gaida su kafin na shigo nima. Koda yafita yaje gida bai samu komai ba sai bacin rai kawai don yasamu mama da Baba suna jidali akan Ahmad. Wai yana zuwa duk abinda aka sayawa mama yana koshewa yakai gidan shi shi da matar shi mara kunya suci. Yaya ya samu dakyat yaba Baba hakkuri sai cewa baba keyi idan saye yana da dadi shi ya dinga saya suna amfani dashi mana can. Aishi yace yaji yagani ita yake so ga Imirana nan da lalacewan shi da komai yana fita yana samun nakan shi ai. Amma shi sai darga da rikicin kayan mutane da yasawa ran shi yakeyi duk ya zubar min da mutunci ga mutanen arzikina. Shine yau zuwa gurin wanan gobe yana gurin wancan yana bakin roko da yaudaran daya saka kan shi ciki. Umma dake daki tace ai babu dan kwarai a gidan nan yanzu sai dan son ka don shine mai abin hannun shi. Dama Atika aike butulu ce baki da godiyan Allah yanzu in ma don abin hannun shi ne ai tare dai dake muke cin komai ko ? Yaya ya samu baba ya shiga dakin shi da kyata ya kwanta da murya yana bashi hakkuri sai faman fada yakeyi. Yana cewa nai nadama da zama da matan a rayuwana ni nasan iya tsawon rayuwan da nayi suna,wahal dani suna cutar dani da sauran iyalina a gidan nan. Bai dade ba gurin baba yafita zuwa gurin maji dake zaune falon ta duk abinda akeyi sunaji ita d Amira. Ya gaisa da ita tare da mata barkan haihuwan maryam tace ni wanan gidan fitinan shi yana bani tsoro wallahi. Kullun ba,a san an girma ba sai anyi jidali a tsakani kuma na rashin gaskiya. Karo na farko maji taji yakira ta da mama yace mama hakkuri zakuyi kawai don kowa da irin halin da ke gare shi dashi kuma ake zama da mutum. Nan dai suka dan taba hira kan zancen yadda gidan ya koma yanzu yace shi zai tafi don dare yayi a lokaci. Ko da ya dawo ya samu nayi barci a lokacin ina kwance a dakin shi bai ta daniba shima ya kwanta sai da dare dana falka nagan shi kwance yana barci. Da Asuba yafita zuwa masallaci nikuma na koma part dina nai sallah na kara nadewa a gado na nakoma barci don weekend ne yau. Ya dawo daga masallacine ya samu wayan shi tana ringing a daki da sauri ya daga wayan mamace a layin take kiran shi. A ranshi yace lafiya kuwa maji take kirana da safe haka ? Ya dauki kiran da,sauri yana sallama yana fadin maji lafiya dai ko ? Tace lafiya lau babana na idar da sallah ne nace bari na kiraka naji yaya jiya ka koma kafita da bacin rai a gidan. Yace a ran shi Allah sarki maji ashe takwana tana tunanen shi ke nan tunda ta kurashi da safe haka. Yace lafiya na isa mama tace nima ina zaune ne ina addua akanku Allah ya kara tsare min ku yabaku saukin rayuwa da haske ga,al,amarin ku. Don na fahinci har yanzu su yaya basu san Allah ne mayin yadda yaso ba ga bayin shi. Ya saki ajiyan zuciya yace mama ki kwantar da hankalin ki ai tunda basu iya komai damu muna kanana ba ko yanzun ma Allah bai basu sa,a . Tace kaga kwanaki haka Alhaji sani yazo gidan nan yai min kaca kaca wai ni na hanaka hurda da kowa a cikin yan uwa sai yan uwana dana matanka kawai yanzun ka sani. Don wai yaji labarin irin abin arzikin da kake tura masu a can kauyen su nan kabarsu hakana. Kai maji ni har yaushe ma nakewa iyayyen Fatima ma,wani abu mutanen da ma nake matukar jin kunyan su sosai ban fako je ba tunda mukai aure. Dasu da baba tsoho wallahi suna a raina ina son mu samu lokaci na ziyar ce su. Baba tsohon da yake nufi mahaifin mama dake zaune a Niger state shi da sauran iyalin shi noma ya mayar dasu can sun zama yan kasa yanzu ko. Yace amma zan ga baba sani din sai asamu abinda akai mai bashi ke nan ba. Mama tace kaifa baka da zuciya babana duk wanan abinda sukai maka shi da su yaya maganan su fa daya ne Yadan kwantar da murya yace maji kiyi hakkuri don Allah don kin ga akanki suke sauke haushin su ko yaushe don haka zan masu yadda yake so a zauna lafiya. A hankali mamatace Allah yai maka albarka ya baka ikon kyautata masu ko yaushe. Yace amin maji tace ina fatima yace ta koma barci yau weekend bata fita tace yana dakyau ta dan huta don nasan anjima kadan yau gidan maryam zasu dire. Yace kaman ko kin sani mama aini dai yanzun nasan ni da samun kanta,sai sun gama bukin nan kan. Tace kaima ka sani tsakanin maryam da Fatima ai sai Allah yace da yake muna fukai ne ba sun hade wa sister na kai su biyu. Ba wani hadin kai halinta dai ne sai ita Amira tafita daban a cikin ku sai kace diyar umma. Dariya tabashi cewan da tayi sai kace diyar umma take yace itama dai zatai auren ai ta huta da fadan kowa hakana. Dadai yafi mata alheri taje kowa ma ya huta da bakin halin ta hakanan. Suna gama wayan da mama sukai sallama kowa yana cikin farin ciki duk kan su. ****** ********* ****** Sai da nai barci na mai ista na tashi batare da ya tayar dani ba nata shi wanka na fada nafito ne ina zaune ina shafa mai ya shigo dakin. Shima yai wanka don a shirye yake a lokacin idanuwan shi a kaina yace ashe barcin ba mai nisa bane inace ko sai biyu zaki tashi. Nace cikin murmushi da yau anty maryam ta yankani ai tun fa safe take kirana a waya. Sai da na shirya duk yana zaune a bakin gadona yana dakilar wayan shi tsab na gama nace mashi nashirya yaya. Yadago kai yana kallona yace au yaune zakuyi bukin ke nan da sauri na,ware idanuwana nace yau kuma yaya ? Yace to wanan uban kwalliyan haka dana ga kinyi aina dauka zumudi zai sa kuyi shagalin bukin ne yau ? Yamike yana cewa ni dai yanzun nasan ba a da time dina sai dai yadda Allah yayi dani kawai. Nace haba dai yaya yanzun ne ma fa zan bar gida to eleven fa yanzu ake nema kamata yayi ace ina gidan tun bakwai ai. Eh tunda gaki ungwazoma ba sai kije bakwai kiwa jariri da uwar shi wanka ko. Dariya nayi kawai nace tau ni fa ai yanzun komai zanji amma bazanyi fushi ba tunda ina son abar ni na tafi. Shi yajamu zuwa gidan ya sauke mu a kofan gidan ni da iya don maryam tana dakin ta bata koma gida ba. Uwar mijin ta daine tadawo gidan nasu da zama inda yake zaine na dan kalla tare da gyara tsayin mayafina don gyale na saka yau nace sai mun dawo ke nan yace four zan dawo na dauke ku fa. Kaina na langabe nace haba yaya four fa inace ko sai magariba yace idan kika bata min rai wallahi yanzun zaki shiga ki fito mu wuce nace da sauri iam sorry sir don nasan karamin aikin shine hakan. Ko don ya batawa maryam din rai na bude mota zanfita naji yace ban son fitina fa da kowa kuyi lafiya a watse lafiya nace insha Allahu yaya. Nafita ina cewa mun gode sai ka dawo yaja mota yanajin dadi komai kankantan abu sai nayi godiya akan shi. Ya furta a fili simple life . Muna shiga gidan tun a kofa muke jin hayaniyan mutane yan uwan yaya bashar sun cika gida sai surutu sukeyi. Nai sallama iya tana bayana nagaidasu ina fadin to abani ruwan zafin ajuyo nai mata wanka duk aka kwashe da dariya. Inna dake gefe tana gasa jariri tace hai Fatima kwana nawa ance ma maye ga nama. Daga daki maryam ke fadin ki koma ban so tunda bakiyi farin ciki da zuwan baby naki ba sai yanzun ne zaki zowa mutane. Na daga labulen daki tana zaune da cup din kunun kanwa a gaban ta sai zufa takeyi tako ina nace bura uban nan wani abu ko sai haihuwa wallahi anty kece haka kace kace cikin zafi. Na zauna saman gado ina cewa wayyo Allah na wallahi duk na gaji sai kace nice na haihu wallahi. Ta kurba kunun tare da lumshe idon ta tace da waye ya haihun bake ba ni sunan nai cikine kawai ai dan nakine. Nace kada ki sa na gudu dashi fa yau gidan mu tace aida yayan ki ya tare maku a gida kinko ga jiya da kyat inna ta samu yatafi ya kwanta ya barmu wai shi anan zai kwana nace Allah yabaku maryam. Ke da yaya wallahi kuna sha,anin ku harara ta kara watso min tace kunan daban ne Bintu ? Tace wai da sauri na manta ina gadon asibiti ma nace Bintu ance za,a balbalani balle yanzu ina dakina zaune. Wanan dan rikici halin shi sai shi wallahi yanzun ma cewa yayi wallahi idan nai tsiya dani dake yanzun zamu shiga mu fito tace dako na hada shi da maji wallahi. Nace kina hada shi da ita nabi mijina don ban son fadan nan dakike sa ana mashi ko yaushe. La la la Bintu ni kike fadawa haka yau kan yaya eh lalai kan mage yaji gishiri kuwa. Waya na jawo na fara dan dana nomba sai ko naji ya dauko yana fadin hello na,shake muryana nace yaya love kaji anty maryam tana ce min Bintun daka hana ko. Ya ko hau fada maryam wallahi zan zo na balbalaki tace iyye watau karana kika kai ma ke nan lalai Bintu wai Fatima wuyan ki yai kauri ashe. Nace sorry yaya ta gyara yanzu tace Fatima din kayi mata hakkuri tsuki yaja yace mashiririta kawai kuka sani nace asauka lafiya na kashe wayan. Tace yar iska ke dai kin kirashi da,wayyo kiji muryan shi kawai ba,wani kai karana da kikayi. Indai yayane wallahi naga take taken shi yarinyar har tausayi kike bani don nasan baki da hutu. Nace abu cikin duhu sirine ne tace kwarai kuwa nayarda sirine don nagani yanzu a zahiri. Sai lokacin Iyyan Rabi ta leko dakin tana gaida maryam din na tuna nace Allah sarki iyya na manta fa kina waje kiyi hakkuri kinji. Muna nan dakin sai hira mukeyi shigowan matan yaya Imirana dakin shine yasa muka kwasa muka yo waje can sai ga wasu yan school din mu da suka kare da ita sun shigo. Wasa wasa gida ya fara cika iya ta mike zuwa inda ake aiki takama masu aiki. Shigowan matar yaya Ahmad tanbele ya tashi sai hira take muna ana kwasan dariya wanda hiran nata duk kusan batsa take yi wai ita hira ke nan. Sai ga Umma da mama sun shigo barka da wata kawar mama makwabciyar mu nan muka shiga gaidasu sai dai yadda Jamila matar yaya Ahmed tayi masu banji dadi ba. Don ta nuna rashin da,a sosai a gare su kamar bata san sune ba abin duk ya bamu mamaki ganin su baisa ta fasa abinda takeyi ba sai ma ci gaba datayi da abinda takeyi. Basu dade ba sukai sallama suka tafi har kofa muka rako su ni da matar yaya Imirana Hadiza wace ke da dan matashin ciki yanzu. Gani bai sa umma ta fasa fadin abinda tai niya ba don cewa tayiwa Hadiza ki yi haraman komawa gidan ki don banga abinda kukai wani taruwa nan kunayi ba kamar haihuwan gidan sarki. Tace ai shine zai zo ya dauke ni yace tace to kindai ji na fada maki ki maza ki koma gidan ki ban son irin shige shigen nan. Sai da muka dawo cikine take cewa sai mutum nason ya shigo yan uwan shi amma aita hanashi . Jamila tace walleh ke an nan nikan anso akawo min wanan control din amma tuni na wuce gurin don ban yarda uwar miji ta hanani shakat. Hadiza tace nikan sai lokacin da yazo zan tafi mutum yana cikin yan uwa yana dan walawan shi amma sai duk a takura maka. Jamila takara cewa yanzun dadafa ke akaji inda tsofin gana walleh har yanzu su kishi sukai harda diyan su kosu kegane su kaman kan su a hade walleh cin kan su suke tsakanin su. Kowa gulman dan uwane yakai idan daya baya kusa ni jiranakai watarana su shiga gonana nai masu tas wallahi. Nidai da maryam bamuyi magana ba muna jin su don da mun tanka namu ne zai fita nasu ya boye. Nan dai muka wuni anata faman shiririta irin na matasan mata idan sun hadu zallansu. Sai naji ranan naji dadin haduwan mu haka saboda bamu taba haduwa haka ba tsakanin mu sai bayan sallah la,asar muka fara watsewa daya bayan daya nikan yaya yai min halarci sai yamma lis yazi daukan mu muka koma gida. Yace ma Iyya kada ta damu kanta da zancen girki zai sawo abinda za,aci da dare. A gajiye nake don kai da komon da mukayi a gidan maryam wanka nayi nai sallah muka fito falo yana dawowa shima wanka yayi yafita gidan. Nan muka zauna da iyya muna hira tsakanin mu tana bani labari akan matar yaya Ahmed bata da mutunci ko kadan bama wanda ya zaci har zasu kai wanan lokacin dashi ai. Iyya ta dan tausa muryan ta kamar wani na jin mu tace ke irin su Nafisan Umma ta fa duk harkan su guda. Nace Allah mai iko watau kowa dai Allah ya bashi a dakin shi ke nan ba mai fadawa wani kuma. ****** ********* ****** Sannu sannu suna yana matsowa sai shirye shiryen bukin suna akeyi inda yaya sadauki yaiwa maryam duk wani nauyi da iyayye suke dauka na yar su. Nice mama tasa a gaba akan na auwatar da komai daya dace da shirin sunan. Haka yasa ban zaunu ba don ma na samu iyya tana da kokari itace na samu take yawancin zirga zirgan na komai a gidan. Komai mun hada Alhamdullahi ranan suna yaro yaci sunan mahaifin uban shi wanda dama tun kafin suna Inna ke kiran shi da Alhaji karami. Cikin yan uwan Inna da sukazo ne nazo zan wuce naji wata na fadin wai ba Fatima bane nan najuyo na kalli matar naga kamar na san ta. Sai dai nace mata nice batare dana gane ko wacece ba sai cewa tayi halan baki ganeni ba dai ko nace gaskiya ban gane ki ba. Tace Asmau matar marigayi Kabir da kika tashi aure nace Allah sarki ankoyi haka wallahi. Nan na tsaya muka gaisa da ita na tambaye ta yaran ta tace sunan lafiya sun girma yanzu suna makaranta. Tace min ai tayi sabon aure ta auri wani miji amma dan sanda ne tana nan cikin gari yanzu. Nace ina anty tace itama tayi aure anan gari tana auren wani malamin yan izala masu da,awa tana zaune a arkilla ne. Nan nakawo mata abubuwan abinci dana buki na karamata sosai takuma ji dadin haka tace nai mata kwatancen gida na zata zo. Nawuce ina tunanen duniya matar da da take jin kan ta wani abu yau itace takoma haka kai duniya abin tsoro ne wallahi Allah dai yasa mu gama da duniya lafiya kawai. Anci ansha maijego tafito yadda ya dace duk wanan abin da mukeyi zakace Amira ba yar uwar maryam bace tana tsabare abinta ita dai haka Allah yayi ta kawai nake gani. Munyi photuna sai da mutane da sukazo sunan inda aka hada walima wata malama tai wa,azi akan hakin iyayye ga yayan su dakuma hakkin diya ga iyayyen su. An raba gift na robobi da yan wasu kayan sha taro ya,watse lafiya akabar mu mu zalla yan gida da dare bayan na idar da sallah maryam tana zaune tana shayar da yaron ta na kura mata ido ina tunane. Tana tambaya ko an aikawa makwabtanta da abinci gidajen su banji may take fadi ba sai da take ce min wai may kike tunane ne haka Fatima ? Na lumshe idanuwana nai murmushi tare da sauke ajiyan zuciya nace wallahi ba komai anty tace ba komai kike zurfin tunane haka. Nace maryam yaya ya fara min zancen haihuwa fa tace to may ye abin damuwan kai ciki. Ya baki mana yagani in baki dauka ba wayasani ko lefin shine banaki ba kadama ki damu kan ki da wanan har yaushe akai auren da za,a fara wanan magana haka. Ba kowa ya zuga shi ba nasan Nafisa ce tun ranan naji tana ce mai wai ita yanzun baby din shi kawai take jira suzo don ita sune yaran ta. Kuma nasan tana fada mai hakane kawai don ya maryar da hankalin shi ga zancen. Idan ma yai maki magana kice mashi yabaki aiba kece zakiba kanki bako ? Maganan ta yai min dadi sai da na shirya mata komai sanan na kirashi yazo ya dauke ni tace na dauki duk abinda nake so daga cikin abinda ta samu. Dariya nayi nace haba dai anty aiko da ban gode ma Allah ba yanzun haka fa ina da turamay sunkai ashirin da ban dinka ba aje. Tace kaji masuyi don jallah inda nice ai ban iya ganin turumi ban din ka ba tace da tuni nagama dasu. Na dan bata rai nace kin san halin yaya shifa yafi son ko yaushe ya sayo min dogayen riguna irin na kasashe da yake zuwa kuma yafin yaga na sasu. Tace kuma wallahi suna maki matukar kyau ko dazun naji wasu na gulman ki ai wai duk shigan da kikayi kamar kece kika halicci kanki. Nace kai kaji mutane da gulma kuma ina ruwan su dani tace wallahi Fatima kin dace da Allah yasa yaya yazama mijin ki da bakece matar shi ba da sai dai muyi taganin abu a gidan wasu. Allah yana da hikima da basira kila dalilin hakane ya jefo rayuwan ki a cikin mu fa? Nai murmushi nace sanin gaibu sai lillahi anty amma gaskiya yaya baida matsalan komai inba wanan shan ba kuma yanzu sai nake gani kamar yama daina yi. Mun ware turame wasu umma da Inna harda iyyya Rabi saida maryam tace aba turmi daga ciki da kannen mijinta su sahura su biyu. Sai goma yazo ya dauke ni muka bar gida zuwa namu gidan kowan mu har iya duk mun gaji a lokacin. Wanka mukayi don kowa a koshe yake sai kwanciya ba school yasa na kwanta washe gari bamu fito ba sai after eleven muka fito daga daki kowa agajiye yake. Nan muke falo ranan bai fita zuwa ko ina ba sai dai wayan da yake ta faman bugawa kawai. ****** ********* ****** Ranan bayan suna da kamar sati biyu wanda bai zaunu ba don ginan sabon site din su da akeyi ya mayar da hankali sosai ga aiki. Ya dawo da la,asar don ya huta yace yabajin kan shi na mashi balain sarawa a lokacin. Sai wayan shi yai kara Baba sani naji yace yadauka suka gaisa dashi baba din ke fadin yana son ganin shi da dare anjima ya amsa da to Baba ina nan zuwa insha Allahu. Magani na kawo mashi cikin wani dan karamin plate da ruwa a cup ya hadiye maganin. Can naji yaja tsuki yana fadin ko kuma yau mai baba Sani ya samu yake nemana a gidan shi. Mutumin da abaya ya tsane ni kamar may ko gidan shi cewa yayi bai son yana gani na,shida baba Shaibu ni tun lokacin suka fita raina wallahi. Zancen auren Raiya ne ma da baba ya matsa lokacin sai anyi yasa nake dan zuwa kada ran shi yabaci idan yaji banzuwa. Amma haka idan naje kiranta zasu yi tamin wullakanci yara da samarin gidan suna cewa ga dan wiwi din nan yazo. Na dan yi murmushi don nasan cikin bacin rai yake magana nace ba babanka bane yaya duk abinda sukayi ai don kan su wallahi. Kadai je kaji may yake neman ka dashi yafi kada yace kuma yakiraka kaki zuwa kiran nashi. Yace ai zan tafi naji may yake nemana dashi kuma ne wai kwanaki fa da haihuwan na na maryam sai da maji tasani gaba na basu yan kudade duk kan su har gwagwanin mu. Nace Allah ya saka da,alheri ai duk yiwa kaine hakan ma. Sai da yai sallah ishai ya shirya cikin wani shadda mai ruwan maku dinkin garen hannu haka ma rigar iya cinya akayi mai shi, ya nufi gidan baba sani ban kawo komai ba tun da kanin mahaifin shi ne. Yana isa ya buga waya yace gashi kofan gida ya iso baba yace ya iso mana yashigo yana falo zaune. Yasamay shi zaune tare da matar shi ya gama cin abinci suka gaisa duk cikin kyankyamin yadda falon ya koma yake. Ya tambaye shi harko ki shi da matar shi yace duk Alhamdullahi. Can baba yace dama ba wani abu bane yasa na kira sai akan zancen ka da yar uwar ka Raiya ne naga gara kawai ace anyi abin nan tunda dai ita ba wai auren tayi ta kuma gama karatun ta bana. Dama dai can kuna son junan ku dan matsalane aka samu na munafunci ya shiga tsakani. Ba karamin mamaki Sadauki yaji ba yadda baba yau ya murje idon shi ya iya mai wanan magana. Ya manta yadda yaci wa mahaufin shi fuska yana kirarin wai zai bawa yar shi mashayi dan wiwi dan giya. Ya kuma tuna Irin halin da maji tashiga a lokacin irin cin fuskan da akayi mashi kan wanan auren hadin da akaso yi bayan tun Raiya tana karama duk sallah sai ankai mata kayan toshi. Itama kanta Raiya din sai da taci mai fuska daya buga mata waya lokacin da yaji labarin sai ce mashi tayi. In aure ka in kaika ina kama big girl ace na tsaya auren wani mashayi wanda baida aikin yi sai shaye shayen tsiya kada ka kara kirana daga yau na fada maka . Yana tuno haka ya dago kai yai murmushi yacd Baba naji abinda kace amma na farko kasan nayi aure ko. Nabiyu kuma ita Raiya fa ta bude bakinta tace min bata sona bata kaunana idan na haihu cikin maji kada na kara kiranta. Don haka Baba don Allah abar zancen da yawuce yawuce kawai Allah ya bata mafi alheri a gareta ni yayan ta har gobe najini zanyi duk wani abinda duk wani yaya yakewa kaunar shi. Mama suwaiba tace haba Umar ai kasan halin yarinta har nawa Raiya take hakkuri zakayi tunda kuna son juna. Yamike yana cewa gaskiya Baba abar wanan zancen ba zai yuyu ba tun da tun farko an fara shi da tsegumi masuyi kuma ba fasawa sukayi ba. Baba yace dakai da Raiya duk daya kuke a gare ni don haka ina da ikon yin komai akan ku murmushi kawai yai masu yace shi zai koma ayi hakkuri. Raiya da yan uwan ta suna labe sunajin yadda akayi sukace kingani kin wa kanki tace aiko yaki ko yaso sai na shiga gidan nan wallahi koda tsiya ne. Jifa irin kafirar motar da ranan mukaga matar shi naja dayan tace kice dai ta koma kamar diyar wani presedent da ita. Dan iska kudi yake samu har na tsiya wallahi ba ance albashin su ma,wai yafi na wasu gwaunoni ba kudi. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,, IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH YABI MUNA HAKKIN MU AKAN KI Tukin mota yake yana tunanen wanan hali na Baba sani wanda ya rasa gane kan shi. Son kaine ko kuwa rashin tunanen may yadace ne don yai matukar jin wanan magana daga bakin Baba Sani din. Ko da ya iso gida ya samu har nayi barci ko shima sai da ya gama duk abinda zaiyi ya hawo gadon ya kwanta. Inda nake kwance ina barci ne ya kalla kamar ya tayar dani sai kuma ya fasa ya dan kura min ido yana kallon yadda nake barcina a tsanake. Tausayi yaji na bashi yasan dani da iyayyena sun mai komai yadda suka dauke ni suka bashi . Bayan nashi jinin sun kyamace shi sun ki shi saboda halaiyan shi da sukace baida kyau. Amma kuma shine yau kuma da ake ganin kamar ya zama wani abin kwarai zasu dawo suce wai dashi zasuyi. Kai wai mutanen duniya ne suka lalace koko duniyan ce ta lalace haka da kan ta. Yanzu shi Baba Sani har ya manta da cin fuskan da sukaiwa mahaifin shi shi da matar shi ne da zasu dawo suce shi ne kuma suke son ya auri yar su ko may ? Da kyat dai ya samu har barci ya dauke shi yana cikin tunanen irin halin Baba sani da wasu mutanen da basu san kunya ba. Da safe koda muka tashi ganin shi nayi kamar wanda baijin dadi don yau ko fita judging bai samu yi ba na safe. Har nai wanka na shirya nafito naji shi shiru a daki na nufi dakin nashi na leka shi. Yana kwance a saman gadon shi ya kifa cikin shi alaman motsin da naga yanayine yasa na gane ba barci yakeyi ba a lokacin. Na nufi bakin gadon nashi ina fadin ina kwana yaya love? Sai lokacin ya dan dago kai ya juyo gare ni har na kawo bakin gadon na dan zauna daga gefe tare da tokaro hannu na daya ta baya saman katifa na sa shi a tsakiya. Yace yaya dare naga jiya kin samu barci sosai baki ma san dawowa na ba. Murmushi nayi tare da dan dukar da kaina daidai saitin fuskan shi nace nima wallahi ban san yadda akayi har nai barci ba haka da wuri daga fa wai na dan jiraka kadawo shine barci mai nauyi ya dauke ni hakana. Nace tashi kai wanka ka karya yaya yace ki tayar dani to duk banjin dadin jikin nan nawa yau. Da sauri nace subbahanallahi yaya may ya samay ka kuma maimakon yabani amsa sai ya jawoni zuwa jikin shi yana sauke numfashi a hankali. Can naji yace Fatima na amsa na,am yaya yace tunda kun samu hutu sai ki shirya nakai ki kiga su mama duk da ba haka naso mu tafi masu ba don akwai dan planing din da nake son yi a kan su. Wani irin sanyi naji ya sauka min a raina ina fatan zaki je ki dawo batare da wani matsala ba dai. Nai maza nace mashi matsalan may kuma yaya bayan gida na tafi gurin su mama. Yace to fada min inji da kanki kwana nawa zakiyi a can idan kin tafi don inji ko kina da adalci . Shiru nayi ina nazari nace nace ko nace sati uku don na samu na zagaye dangi da yan uwa da abokan arziki. Sai kuma nai tunane ko a gidan baza su amince min nan da Rabah nai wanan kwanakin ba haka. Amma a fili cewa nayi ko kwana nawa kace nayi ai zanyi ne na dawo , yadan shafo fuskana da hannun shi yace. Ai ni nace ki fada don idan kin wuce nima zan tafi ghana ne akwai kayana da suka makale a can nake son zuwa na duba su. Don haka ki fada naji sai dai kada ki manta duk hukuncin da zakiyi a tsakani na dake na rokeki kar ki so kanki a kaina da yawa kiyi tsakani da Allah. Dariya maganan shi tabani don yasan na dade ina binshi kan ina son zuwa gida na duba su Baba amma ya hanani zuwa. Yace No na san kin sani bayau ba kike min zancen zuwa gida ina basar dake kada yanzu kiji nace ki zaba kimin rashin adalci. Kin san dai ina son ki Fatima kuma ko ban furta maki ba ke kin sani don kinga alama yafi a kirga. Don haka ina kara jaddada maki ina matukar sonki a rayuwana Fatima fiye da duk yadda zaki tsammani gaba daya fatana da buri na shine bai wuce na nuna maki ba a kullun irin halarcin da kikai min ba. Nace yau kuma duk may ya kawo hakan ne don zancen tafiya gidan ne ko dai baka da sha,awan ina raban iyayyena ne yaya ? Yayi murmushi yace haba haba subbahanallahi ko daya wallahi bandai son kiyi nisa danine ko kadan yanzu Fatima. Nace to nayi sati daya idan na tafi ko ? Naji yayi murmushi tare da dago kai ya kalleni yace har sati Fatima sati daya fa kika ce.? Nace a hankali to ka rage yaya idan yayi yawa ne, yace zaki iya yin kwana biyar ko nasan zai ishe ki kiyi duk abinda kike sonnyi can. Nace to na gode yaya nagode yaji dadin hakan yana mikewa zaune na gyara mashi ya zauna da kyau. Yace sai ki fara shiri don ni na gama maki shirin tafiya ko gobe insha Allahu zan kaiku ke da musa idan kuma iyya Rabi tana son tabiki ne sai ku tafi tare idan bazata ba sai ta tafi gida har ki dawo a rufe gidan. Murna da dadin jin gobe zan tafi gida duk ya cika min zuciyata ina matukar kewan mahaifiya ta dana dade ban gan ta ba ya cikani. Yace ni in nai wanka zan fita zuwa gida sai na fadawa mamanki zaki gida gobe goben idan mun shirya zamu wuce sai na biya dake ki sallamayta. Nace nagode nagode yaya ya mike yana kokarin shiga bathroom don yai wanka. Na juya zuwa dakina sai ma dadi ya kasa barina nasan may zanyi akai lokacin. Wardrobe dina na bude tare da jawo troler dina na fara zaban kaysn da zan tafi dasu. Idona yakai ga kan atamfofina da suke ajere ban faye amfani dasu ba nan nashiga zabo masu saukin dinkin da nasan mamana zata iya sawa na tara a gefe na. Wanda nai yan matanci dasu kuma na jawo wani ghana most go na loda a aciki inkai a rabawa mutane shi. Inda turamay suke na bude akwatin na fitar da wasu masu kyau suma na tara guri daya. Ina tsaka ga aikin ne ya shigo dakin tare da bin kayan da kallo yace duk wa yan nan kayan fa haka ? Ba dai duk na tafiyan bane sai nai mashi bayanin manufa ta dasu yai yar murmushi ya karaso inda nake a zaune saman godo yace No bazaki kai wa maman mu tsofin kaya ba Fatima ki bari a sayo mata nata kawai da zaki mata dasu idan nafita ban mashi musu ba sai nuna farin cikina da nayi. Da zai fita ne yake cewa sai kiwa Iyya magana muji ko may ye ra,ayin ta ita kuma ga tafiyan. Nace ok yanzu zan fita naje gurin ta naji yadda za,ayi akai. Yana fita na samu iya a kitchen nake fada mata yadda mukayi da yaya din da kuma tambayanta may ta yake shawara akai. Tace haba uwar daki na idan ma na zauna a garin may zanyi ai kafarki kafata tare zamu tafi dake nace Iyya na gode da wanan karamcin da kikai min. Itama nan ta fara shirin tafiya na bata atafofi guda uku masu kyau tana ta godiya da jin dadi. Tunda yaya ya fita gidan da safe bai dawo ba nima a cikin zumudi na wuni. Ya shiga gidan su ya gaida mutanen gidan yadawo gurin mama suka gaisa da ita. Yace bayan sunyi dan shiru gobe ne nake son Fatima ta tafi gida ta duba su insha Allahu. Cikin mamaki mama tace gobe goben nan dai shine bamu da labari kan tafiyan sai yanzu zamu ji may kake so na hada mata na zuwa gida a matsayinta na karon farko kenan da zata ganin su. Yace nima jiya ne naji ya kamata su tafidon dan hutun da suka samu din nan sai taje ta gan su ai ba dadewa zatayi ba,kwana biyar zasuyi ta dawo. Baka dai kyauta min ba kama yayi naji da,wuri na dan hada mata tsaraba taje dashi mana. Yace ai babu komai maji za,ayi abinda ya dace ayi kafin su wuce din nima zanyi tafiya zuwa ghana inshs Allahu. Sai dan shiru bayan tai mai adduan Allah yakai lafiya a dawo lafiya da tace mai. Lafiya kake kuwa yai dan murmushi yace lafiya nake maji tace naga kamar kana da damuwa a ranka yace ba komai maji. Can yace Baba Sani bai zo gidan nan ba gurin Baba ? May kuma ya faru mama ta tambaye shi da sauri yace jiya ya kirani da dare naje gidan shi. Shine yafito min da zancen wai yana son a tayar da zancen aure na da Rahama. Da sauri mama tace ba zai yuyu ba wallahi ko alama. Shi yanzu baiji kunya ba da har zai fito maka da wanan zancen yanzu don yaga Allah ya mayar da kai mutum ko ? May yasa mutane basu da ta idone wai haka ? Idan ma kai ka yarda ni wallahi ban yarda ba da wanan zancen ko alama hakan ma ai tatsuniya ne. Yanzu ko da yaga Allah ya daukaka shine har ya manta da irin cin mutuncin da sukai muna ya kalli idon Alhaji yace ba zai aura wa yar shi mashayi ba. Kaje duniya tana da yawa ka samu irin ka yar shaye shaye ka aura shi yafi ma. Shine yanzun don baida kunya zaice wai wani a tayar da zance to nima yanzun nace ban yarda ba duk abinda zaiyi yaje yayi amma wallahi baka auren Rahama. Wa yanda sukaje suka bata ka garesu ai suna da diya yaje ya aura masu ita mana. Wai ko akan zancen kake son tura Fatima gidane wai ? Yace wallahi mama ban son Fatima ma tasan da wanan zancen shi yasa nace zan tura ta tafi ni kuma sai na tafi bashi ke nan ba. Idan Fatima ta samu wanan labarin nasan akwai rikci sosai a tsakanin na da ita wallahi. Bata ma komai amma baza,ayi ba na fada maka yace nima maji yanzu ba ida zan kai Rahama kuma don ta fita raina kwatakwata wallahi. Don dai ka fadawa Fatima zancen tafiyan ne wallahi da ba inda zaku shi din may wai da har zaka gujeshi ? Idan ma kun tafi ai dawowa zakuyi dole tunda ba inda zaku sai gida tun wuri zan ma Alhaji magana kada ma a soma zancen. Nan dai sukai ta maganan yafito tare da mata sallama akan gobe zai kawo ni nai masu sallama kafin mu wuce. ****** ********* ****** Sai bayan la,asar ya shigo gidan yace kun shirya dai ko? Nace mashi eh tafiya kawai ya rage muna gobe insha Allahu. Yace kunyi magana da Iyya din ko ? Nace eh tace tare zamu tafi da ita sai yai dan murmushi yace dama nasan bazata zauna ba ai. Yace komai an shirya don na dan yi maki tsaraba sai dai basu da yawa sosai suna a cikin motan da zamu tafi dashi akwai kaya nanan na Baba ne sai wanda zaki kaiwa mama din. Idan na kaiku na dawo Hamza zai samay ku can da motan da zakiyi amfani da ita har ku dawo. Nace na gode yaya Allah ya kara daukaka ai mai yawa ke nan don kai baka kyauta kadan nasani. Yace min karbi wanan ki saka a kayan ki idan kinje ki zauna da mama kuyi magana ki samu wanda ya dace kiba da aikin gidan su a fitar mata da plan yadda take so idan bai isa ba sai muyi waya a karo maku. Ban san lokacin da nace yaya na ina son ka ba wallahi ban ma san bakin da zan maka godiyan hakan ba. Yai murmushi ya kamoni zuwa jikin shi yana cewa wani godiya zakiyi min bayan yau ki barni nayi na ban kwana kwana biyar aiba wasa bane. Nai dariya nace kai yaya kai baka da magana sai na wanan zancen kawai yace a,a toke in banda abiki ina dan kwallo inbayi wanan ba may zanyi tunda ina jin lafiya ajikina. Nan dai ya zauna bai kara fita ba muna ta shiririta a gida sai zuwa yamma ne naji baba sani ya kirashi a waya. Nai mamaki danaga ya mike zuwa dakin shi amma abin da da mahaifi nasan kila wani maganan siri ne zasuyi sai da,ya shige ne naga ya bar A T M din shi a falo na dauka nabi shi ina shiga dakin naji yana fadin. Kada kaga laifin maji baba na fada maka tun jiya bazai yuyu ba taje Allah ya ,,,, Sai gani ina nuna mai katin daya bari a falo din yace sorrya tare da mika min hannu na bashi na mika mai na juya nabar dakin. Bai fito ba sai da magariba yafita zuwa maslaci yai sallah nima ina daki naji fitan shi . Hakama da dare muna tare sai hira,akeyi yana waya yana fadin gobe insha Allahu tafiya zai yi zuwa waje. Har dare yayi muka kwanta ranan kamar ba zamu sake haduwa ba again sai da ya gaji don kan shi ya barni. Da safe bayan mun karya akafita muna da kayan mu zuwa waje aka loda su a cikin mota. Kwalliya sosai mukayi daga ni har shi har su iya da zasu rakani ita da musa na. Sai bayan nafito ne naga ashe da mota biyu zamuyi tafiyan danashi da hilux din shi sabuwa dal da ita. Dani dashi da iya da musa a mota daya sai wancan dayan motan dake da kaya naga mutum biyu muka gaisa dasu naiwa su maigadi sallama muka kama hanya. Kafin mu isa gidan su mama ne na kira maryam ina fada mata zancen tafiyan don jiya zumudi ya hana nakirata. Ainan ta hauni da masifa inda take shiga ba nan take fita ba sai dai hakkuri kawai nake bata. A gidan su mama ma tayi nata korafin na samu ta hada min nata tsaraban su sabulu man shafa clean parket parket tace na rabawa mutane mukai mata godiya nafito na sallami sauran mutanen gida. Mummy takawo turare mai kyau da,tsada tace nakaiwa babana turmi naba mama. Nai godiya mukai sallama muka kama hanya mun dan sha kwanan kadan dagida ya jawo hand bag dina dana aje a gefena ya ciro kudu masu yawa ya zuba aciki wanda ban san ko nawa bane a lokacin. Ya mikowa Iyya da musa yan dari bibiyu yace su rika acan ko saga abin saye su saye. Tuki yake a hankali bai wani irin sharara gudun nan da ya taba yi da mu ba a baya daya taba zuwa ya dauko ni ba. Nakalle shi naga yadda yake tuki a tsanake naji dadi araina ganin irin natsuwan da yake ciki a yanzu. Gashi mutum mai cikakken halita ga iya kwaliya da tsabta ga kwarjin shi ya kara fitowa a fili sosai. A hankali na lumshe idanuwana tare da mayar da kaina kan seat din motar ina sauke ajiyan zuciya. Bai juyo ya kalle ni ba sai cewa yayi yaya akayi ne yan mata ? Nadan bude idanuwana a hankali tare da dan sauke numfashi again nace babu komai. Na dai kalli irin haduwan mijina ne da Allah ya mallaka min shi a matsayin uban yayana nan gaba. Watarana insha Allahu idan zamu irin tafiyan ga killa a full family zamu tafi da yaran mu. Shiru yayi sai dan murmushin da yayi kawai yace hummm a fili . Can naji cikina yana murdawa zuciyana yana tashi take na tuna idan na shiga mota amai nakeyi dama. Aiko nan dana amai yazo min da sauri na jawo leda a jakata na fara amai. A rude yaya yace ko na tsaya ne wai cikin karfin hali nace mai mu tafi babu komai zai tsaya. Sosai nai amman sai da Iyya ta miko min goro tace na saka a bakina sai naji aman ya dan tsaya min. Sai dai jikina da yai dan nauyi a lokacin kaina yana sara min sosai kamar zai tsage min a lokacin. Tafiya mukeyi ba wanda ya kara magana a cikin mu sai tunane nakeyi cikin al,amarin aure na dashi kawai. Auren da daga farko kowa ke hango min zaman ukubar da zanyi a gidan shi wanda nima kaina nasan zaman ukubane kawai zanyi a lokacin. Tunane nayi sosai irin yadda Allah da ikon shi yau gashi ya mayar da,sadauki wani kamilin mutum bawan Allah wanda kowa ke sha,awan zama irin shi a rayuwa. Yau dubi irin abin arziki da ya labto min nakai wa iyayyena duka a gidan mu da yan uwana. Aman ya kara yunkuro min na danyi kadan nakoma na kwanta saman kujera sai faman sannu yake min yace wai kodai mu koma ne a fasa tafiyan nan ? Nace da sauri haba yaya kayi hakkuri please mu tafi ai zai tsaya min nakoma na kwanta naci gaba da tunane na danakeyi akan shi. Gaskiya yau sadauki ya gwada min shi din na miji ne cikakke mafi darajan mutum da nake ji dashi a zuciyata da ruhina. Nasihan mahaifiya ta ne lokacin da zamu rabu ya fado min a,raina yau gashi maganan ta dutse hasashen mama ya zama gaskiya ke nan. Muryan shi ce ta katse ni da yake cewa idan kinje ne zaki zo da yarinyar da kikace din . Da sauri na juyo ina kallon shi nace wa Sa,ade ? Yace sunan ta ke nan ko ? Nace to ai ban fadawa mama ba kafin na wuto kada ta ganni da yarinya haka kawai ga kuma musa already a guri na. Yace ina ruwan maji may zasuyi mata tunda ba,a gida daya muke dasu ba. Nace to sau naje naji yadda zamuyi da mama din akan magana zan buga na fada maka komai. Yace gurin mama ke nan yau zaku fara sauka ko? Nace haka nake so muyi kwana uku sai mu dawo gurin baba mu karasa kwana biyun mu kafin mu dawo. Haka muka karasa tafiyan ina jigibce sai faman sannu kawai suke tayi min dukan su. ****** ********* ****** Mun isa gida lafiya nan mutane ke bin motan da kallo suga gidan da za,a sauka sai kofan gidan mijin mamana muka tsaya. Abin mamaki sai gashi yana ganin mu ya fara murna da fara,a hardashi ake shigo da kaya daga cikin gida. Dakin mama muks shiga gaba dayan mu har yaya sadauki din da Iyya data rakoni. Mama farin ciki ganin mu duk ya kashe ta ta rasa inda zata saka mu don ganin bazata ne tai muna a lokacin. Mijin mama duk ya rude sai cewa yakeyi kai musa je wajen Isa mai shago kasamo maku ruwan sanyi. Yaya ce No abarshi kawai ai da ruwa ma a motan sai bin gidan yaya yake da kallo yana tunanen yadda zan yi kwanaki acikin wanan irin gidan haka ? Yadago ya kalleni yaga ni sai masha,ana nakeyi kawai ba abinda ya damay ni da komai bai jima ba yace zai koma don yai zai bar garin shima. Namike na gyara mayafin jikina nabi shi a baya a kofan gidan muka tsaya dashi yake cewa tau ni zan tafi Fatima sai in Allah ya dawo damu ke nan ko nace to yaya Allah ya tsare na gode yace ki dai sha magani idan kuma kinga jikin zai matsa maki sai ki buga waya Bashar yazo yaje dake ko ? Nace kai yanayin tafiyane kawai dana dade banyi ba kasan dama ina amai a mota ai. Yace niko na sani nida kikaita ma amai a mota sai da nima naje gida naita shararawa har da ciwo sai da kika sani. Nace kai yaya banda sheri yamiko min kudi yace kiba mijin mama wanan idan na wuce don tausayi wallahi mutumin yake bani. Murmushi kawai nayi nace angode ni haushi yake bani ba tausayi ba abu tunda kurciya gashi yanzu har yafara farin gashi amma bai daina halin shiba na kurciya. Suna wucewa na koma ciki kaina yana damuna da ciwo naki fada agaban shi kada hankalin shi ya daga yace mu koma. Na dan kwanta sai barci ya dauke ni bamu ko gaisa da mama ba ban falka ba sai da akai kiran sallah azahar na tashi nai sallah na samu angyara dayan dakin. Amna wanan karon mu a dakin mama zamu zaune mijintane zai zauna dayan dakin da musa. An dafa abinci amma,banci ba nace hura zan sha shi aka,sayo iya ce ta dama min na dan sha jin zuciyana yana tashi na ture kwanon gefe daya. Sai lokacin ne muka samu kebewa da Mamana tace ashe kuna tafe bamu da labari bamu shirya ma zuwan naku ba. Banji dadin yadda mijin ki yazo bai sha ko ruwa ba ya koma hakana da yunwa. Cikin dan murya nace haba mama ai ba komai koma an dafa bazaici ba nasani don ba komai yake ci bashi sai abinda yaso. Tace wani irin tsaraba kukayo muna haka mai yawa yar baba nace wallahi mama ni sai ma yanzun da aka sauke nagani tsaraban yayane duka. Nace sai su baba da in zan tafi za,a ware masu nasu muje masu dashi tace har can zaku isa ke nan nace ba dole ba mama. Kada baba yace na fara gudun shi yanzu kuma don naga nayi aure. Mama ta tabe baki tace aiba gudun shi kikeyi ba halin matar shine baida kyau kuje dadi dadi a kare da,tsiya kuma. Nace nikan insha Allahu lafiya zamu rabu ai yanzu na riga na gano takon ta sai a zauna lafiya. Ranan har dare muka raba da mama muna hira sai da dare ne nake fada mata sakon da yaya sadauki ya bayar akawo na gyaran gida. Mama ta saki lalausar murmushi tace oh ikon Allah ni Amina yau ke da,wanan babban sa,an haka ? Nikan banda abinda zan sakawa hajiya da zurianta sai addua da fatan gamawa da duniya lafiya nagode nagode bari wanan baudaden ya,shigo muji yadda za,ayi amma bazan nuna mashi kudin yana nan tare dake ba,sai dai naga yaya salisu asan abinyi dasu. Don har yanzun da kikaganshi nan ga girma yazo amma bai fasa halin shi ba ni kadai nasan irin kuncin rayuwan da nake ciki a gidan nan ke dai. Shiya sa tunda kika fada min zancen mijin ki ban sake rufe idona a gidan nan nayi barci ba gayawa Allah nake matsalan mu. Nai murmushi nace da alama kuwa yanzu mama Allah ya karba muna rokon ki. Don yanzu gaskiya ko yanayi ba irin nada can baya ba kamar farko sai dai kila aboye idan yanayi din. Mama tace Allah dai yasa ya bari kwatakwata a rayuwan shi. Yau gashi wanan hadin na hajiya da kike gani kamar son kai tayi maki ya zama aure mafi daraja da ko wace uwa ke mafalkin samun shi a rayuwa. Dukar da kaina nayi don jin nauyi maganan da tayi tace ga sako da ake aiko muna dashi ta hannun mahaifin ki duk da nasan ba duka yake kawo muna ba. Nace kai haba mama yaya baba zai rage maki sakon ki kuma tace ai bashi ba wanan munafukar matar tashi dai itace zata rage su. Cikin natsuwa nace mama tabawa zata iyashi mama don bs imani ne da ita ba wallahi. Haka muka kwana muna hira harda Iyya da,ta kwanta waje da,farko har barci ya dauke ta nasan tai hakane tabamu guri mu zanta ni da mamana. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BA KI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,, IDAN KIN BIYA KADA KI TURAWA WANDA BAI BIYA BA PLEASE DON HAKKA CIN AMANA NE MUN BARKI GA ALLAH,,, Zamana a gidan su mama yasa na dan kara walwalewa na dan samu sauki sai dai har yanzun ba dama naci wani abu a ciki. Don da zaran naci yanzun zan shiga na mai ke nan sai kunu kawai zan dan sha ya zauna min a cikina. Ana cikin haka yaya saudauki ya dawo daga tafiya da tarin abin arziki don kusan watan shi biyu ke nan a can gurin tafiyan da yayi. Sai da yaje gida ya,shirya ya tafi inda muke a lokacin ya dawo ya samu matar yaya Imiran ta haihu ta samu diya mace. Muna zaune a falo mama gaba dayan mu mama da Iyya suna hira ni kuma ina dunkule saman kujera na nade kaina har kafa a cikin hijjabina. Anty Amira da,wayan ta a hannu tana chatting sai Sa,ade da ta kurawa tv ido tana jallo don ita kallo baya isan ta. Da,sallama ya shigo falon gaba dayan mu muka mai da hankalin mu a kan shi. Duk da dare ne mutum zai iya ganin canjin da ya samu a tare dashi sosai a lokacin daya haka. Zama yayi suka gaisa da kowa dake cikin falon tare da mashi yaya hanya suna mai fatan alheri. Sa,ade ta mike har gurin da yake tana gaida shi yace a a wa nake gani haka kamar yar kauye don yanzu sunana a kanta ya koma kuma. Daga inda mama take zaune take cewa ,a,a kabar kira min yarinyata da yar kauye don yanzun ta waye kai ma nake jira kadawo kakai muna ita makaranta gata sai zama gida ba karatu. Yariko hannunta yana cewa mama wanan bakauyan zata iya karatu ne a haka ? Kaita a gani mana inji mama ta bashi amsa tare da cewa kai yaya akayi ka iya ba koyo kayi ba kaima. Ita dai Sa,ade sai murmushi takeyi kawai don bata sake jiki dashi ba har lokacin duk yana dan mata wasa jefi jefi. Gurin da nake zaune ya kalla yace madam yaya kuke wai har yanzun dai jikin ne haka ? Ya mike zuwa inda nake zaune bai damu da akwai mutane a falon ba ya zauna a bakin kujeran da nake a kwance tare da dan shafo fuskana a hankali. Wani irin mugun zafine yaji jikina dashi yace kai maji haka jikin nata yake da zafi ko yaushe? Su ka dan kallo mu tare da saurin kawar da idanuwan su don ganin irin zaman da mukayi dashi a lokacin. Mama tace aima jikin yai sauki yanzu gata har tana dan fitowa falo yanzu aida ko yaushe tana daki a dunkule. An ko koma asibiti da ita kuwa ya tambaya ? Yau sati daya ke nan da aka kara mata ruwa da magani ai abin yazo mata da akasi wallahi haka nan nai cikin maryam kusan duk sati biyu uku sai na sha ruwa ga zafin jiki da ciwon kai duk na kare a lokaci sai dana haihu kamar anzare min kaya naji komai ya wuce. Iyya tace hjy ashe maishi ya biyo gwagon shi ke nan da ga jini wani ciki kara gare shi sosai wallahi. Ya mayar da hankalin shi gare ni tare da tausa muryan shi yana tambayana may nakeji ajikina ne wai ? Nace ba komai yaya ai naji sauki nace mai yaya hanya yace cikin bata rai Alhamdullahi. Sannu yaya jikin to yanzun kuma nace da sauki yaya. Maji ko zan fita da itane waje idan nan basu gane may ke damuwar ta ba ? Dariya sukayi mama tace ji shirmayn ka ciki may ye bai zuwa wa mace dashi kowa da kalar daukan cikin ta ai. Yadda ya mai da hankali akaina muna magana kus kus yasa Anty Amira jin haushi matuka tana gani idan da dane daya dawo itace yar gaban goshin shi amma yanzu tunda ya shigo hankalin shi yana a kaina baima ko yi mata wani magana ba bayan gaisuwan da sukayi kawai. Mikewa tayi tare da tsuki tabar falon daidai lokacin da yake tambayan ina kuwa cin abinci yaga duk na ramay gaba daya haka,? Baima san tanayi ba tashige tana gunguni wai an asirce shi yanzu bai ganin kowa da gashi sai ni da yan uwana kawai. Mama tace mai bata cin komai sai ruwan kunu kaganshi nan a gefen ta aje koshi bai ludayi uku ba idan ma tasha din ke nan ai. Nan ya fara tambayana zakici abu kaza ko na sayo maki kaza ne nace yaya ban son komai Iam ok haka ma na koshi. Ya dan tsuki tare da kura min ido yana tausayawa halin da nake ciki sosai can mamatace mai. Matar dan uwanka fa tana gidan nan kasan na fada ma ta haihu banda gobe suna. Yace au a gidan nan take zaune ne mama tace eh daga asibiti uwar su tace a kawo ta nan. Yace amma naga maryam ita a dakin ta ta haihu ai bata dawo gida ba ? Mama tace kasan kowa da irin ra,ayin shi nata ra,ayin ke nan yin haka din Alhaji ma ido yasa masu don yasan ba a wanyewa lafiya indai yaya ne. Sun dan yi hira ya mike zuwa cikin gida dakin Umma idan ya duba jaririya. Ya samu su umma da uyalin ta a falo yai masu barka suka tambaye shi hanya yace Alhamdullahi. Da zai tafi bayan maijego tafito sun gaisa da ita yakawo kudi masu yawa ya bata yace ta sai wa yarinya sabulu dashi. Yana fita yaji Umma tana tambaya nawane halan ya basu ta nuna masu raffan yan dari biyar sabbi tace akawo a kara ga laluran buki dashi. But Nafisa dake daki tafito tana cewa a,a Umma ki bar mata kudin ta don Allah don dai ita aka ba itama ai tana da abin da zatayi dasu ko? Umma tace kada ki kawo min diban albarkan ki da kika saba yiwa mutane wani lalura gare ta wanda yafi namu kuma ? Ita dai Shafa,tu mikawa Umma kudin tayi amma sai Nafisa ta rike tana cewa wallahi ba,a bayarwa tunda ita akaba. Ai ya ganki baice maki gasu ba ya mika mata idan yabaku naku da ita zaku raba ta shige cikin daki da kudin a hannun ta umma tana kwalla mata kira amma ta kyale ta. Nafisa ke kan ke kan wallahi Allah ya waddaran hali ir8n naki na tir da Allah waddai tace daga ciki ban dai bayarwa wallahi. Bai dade ba yace zai tafi ya kwanta don a gajiye yake lokacin mukai mai sai da safe ya fita daga gidan. Ji nayi kamar na bi bayan shi da zai fita sai dai babu halin yin haka dole na zauna a gurin mama don nan ya samay mu. ****** ********* ****** Kwanan shi biyu da dawowa sai faman sintiri yakeyi bai gidan mu baya gidan maji gurin mu. Yau an tashi da bukin sunan matar yaya Imirana inda yarinya taci sunan Umma kowa na kiran ta da Ummi don sunan ta na Umma da taci. Sai naji kawai ranan ina marmarin alale na gwangwani don haka na fadawa Iyya Rabi abinda nake son ci. Baita kasa a gwiwa ba ta shiga shirin yi min alaila ta samo gwagwani gurin wani mai shayi a unguwan ta hauyin alalen da nake son ci. Ba bata lokaci ta gama min ina daki ina shiyawa zan fito falo yau na kokarta na yi dan kwalliya a jikina don jama,an da suka cika gidan. Cikin atamfar super nake dark blue dinkin shi mai shara sharan hannuwa half gown na daura dan kwalin kayan a kaina. Cikin dake jikina kayan yasa yafito don lokacin ya kai wata shidda a jikina sai dai ba kowane zai iya ganewa ba sai wanda ya sanni da farko. Nafito falo na zauna Iyya Rabi tace yauwa yanzun nake batin kiran ki kifito kici shi da dan zafin shi kada kuma ya fita ran ki. Zama daidai da shigowan maryam gidan da ita da kannen mijin ta da suka rako ta gurin sunan. Suna dauke da danta a hannun su sai wata makwabciyar ta data rakota kuma again don ita tana hurda da makwabtan ta sosai. Suna zama aka kawo alalen da ita muka hada hannu muna ci a plate daya naji dadin shi sosai muna ci muna hiran yaronta irin yadda yake yawan alolayi sosai. Muryan Baba mukaji a tsakar gida yana kwalawa matan shi kira cikin tashin hankali. Gaba daya suka fito daga dakunan su sai gidan yai tsit kowa nason jin kiran don daji bana lafiya bane. Mama Asiya tana fitowa ya kalleta yace Asiya kuncuce ni kunci amana keda dan ki bazan taba yafe maku ba a rayuwana. Mummy ce cikin karfin hali yadda taga Baba a rude take cewa wai may yafaru ne Alhaji kuma ? Yace Ahmed ya sayar da gidan nan yau wata uku ke nan ban sani ba ashe ? Salati kowa ya saka sai ihun mama Asiya kawai mukaji daga waje abinda yasa mu fitowa ke na daga dakunan mu duk wanda ke gidan sai da yafito don tashin hankali. Baba yaci gaba da fadin yanzun haka wanda yasai gidan yana waje yace yazo ne yabamu notice din tashi don anyi dashi nan da wata uku zamu bar gidan wai . Lokaci daya aka saka salati masu kuka sunayi masu salati da tir sunayi a lokaci daya. Sai ganin kawai akayi Baba yai suuu zai fadi da sauri mama da mummy suka tare shi bai kai kasa ba sai dai ba rai. Idanuwan shi a waje inna lillahi wa inna alaihim rajiun,,, Ihu da tashin hankali a ranan mun gane shi a gidan da gudu wasu suka kwasa zuwa kiran maza a waje. Yaya saudauki yana tare da yaya Bashar suna hanya kiran maryam ya shigo wayan shi . Yace kai munafukan matar kace fa ke kirana yanzu, bashar yace wa maryam lafiya kuwa ya dauki kiran tana kuka take ce mai yaya don Allah kazo gida Baba. Cikin wani irin murya yace Baba may fa ? Sai kuka takeyi tace don Allah yaya kazo Baban mu ya rasu inna lillahi wani irin burki ya taka da ya daki motar dake kusa dashi. Ga you turne din sokoto da tsawon tsiya haka ya kwashe su da gudu Allah dai ne ya tsare su sai gida cikin yan mintina suka kawo. Irin mutanen da ya hango sunyi cincirindo a kofan gidan su cikin tashin hankali ne yasa hankalin su ya kara dagawa sosai. Wani irin mugun parking sukayi ya bar mota a bude ya nufi cikin gida da gudun shi irin na yan kwallo bashar tana bayan shi. Sai wani yaro makwabcin su ne ya kashe motan ya gyara parking gefe yana shiga get su Sagir sun dauko Baba ya tare su tare da kamashi suka fita zuwa waje da shi sai asibiti cikin tashin hankali. Suna zuwa emergency aka nufa dashi nan aka samu da kyat ya farfado duk ilahirin iyalin shi suna gurin sai yaya Ahmed ne kawai da matar shi basu gurin. Koke koke kawai ke tashi tashin hankali ne ga duk fuskan wanda ka kalla a lokacin. Muna tsatsaye tare da su anty maryam da anty Nafisa don tare muka zo asibitin da su. Wani iri nake ji dole ssuka samomin guri na zauna ga alalen da naiwa mugun ci sai taso min yakeyi ina jin zanyi amai a lokacin. Maryam ce ta dafani take cewa Fatima ko zaki koma gida ne kinga baki da lafiya fa a jikin ki gaki da lalura kada tashin hankali ya kamaki kuma ? Nace ba komai ai anty aiko sai aman da nake taushewa ya taso min nan na duka naita sharara shi hankalin mutane kuma ya dawo a kaina. Daga cikin daki da Abdul ya shiga inda su yaya suke a kan Baba da ake neman jijiyan shi yake cewa ga kuma Fatima can wallahi ita ma a waje sai a hankali sai amai take shararawa kawai. Da sauri suke cewa harda ita da bata da lafiya tazo ne yaya sadauki ya dago rai bace yace may yakawo ta ita da bata da lafiya kuma ? Bashar ya fita da sauri halin da ya samay ni ciki yace su maryam su kamani muje gurin likita. Muna zuwa likita mace ce muka samu tace ina bukatan bedrest a lokacin nan nima aka kwantar dani asibitin. Dole rabin yan uwa suka dawo gare ni barci ya dauke ni mai nauyi sosai har ban san inda nake ba ma. Da kyat aka samu baba ya farfado tana kiran Ahmed Ahmed ka cuce ni wallahi ka cuci iyalina Ahmed. Nan sadauki yake cewa haba Baba yi hakkuri a samo lafiyan ka tunkun na koma may nene please. Sagir ne ya jashia gefe daya can kusurwan gadon da Baba yake kwance yace yaya sadauki baka san may ke faruwa bane ko ? Yace may kuma ya faru ne Sagir ? Sagir yace wai yaya Ahmed ya sayar da gidan mu shine ya jawowa Baba wanan matsalar haka. Cikin wata murya sadauki yace what Ahmed ya sayar da gida fa kace nan dai Sagir ke fada mai duk yadda abin yake don a gaban idon shi akai komai. Yace mai gidan yazo da bukatan yana son a kwashe a bashi gidan shi don wa,adin aka bayar ya cika. Innalillahi sadauki yace may yasa Normal yai wanan mugun aika aikan haka da lafiyan shi kuwa ? Waye ya sayi gidan ya tambayi Ahmed cikin dago kai da idanuwan shi suka kada sukai ja a lokaci daya. Nan Bashar ya shigo yanayin da ya gansu ne ya tayar mai da hankali ya karaso yana fadin may ke faruwa ne kuma man ? Yace humm bari kaidai man wani sabon labari nake ji wai Normal ya sayar da gidan baba ga wani mutum. Yace what da dan karfi yace no warder ake ce min yanzu anga yana bushasha da kudi ya samu lafiya. Kai amma guy din nan baiyi ba wallahi wanan ne ya jawo wa Baba matsala ke nan ko ? Bai bashi amsa ba sai cewa yayi yaya ita Fatima din kuma take yanzun ? Yace itama an bata gado tana bukatar bedrest wai sukace . Yace o my god wata sabuwa kuma again Allah gamu gareka yace a zuciyar shi amma a fili cewa yayi tana ina yanzun kuma ? Tana gany room a can suka kwantar da ita har tayi barci shine na fito zuwa nan don gaskiya tana jin jiki sosai wallahi. Sai da yaga komai ya saitu wa baba ne ya fito zuwa dakin da nake kwance ina barci maryam da Nafisa sun sakani a gaba suna kallo na. Shigowan shi yasa suka juyo suna kallon shi tare da tambayan shi jikin bana yanzu. Yace masu ya farfado idanuwan shi a,kaina ya kura min ido ina barci cikin wahala ga ruwa daure a hannu na lokacin. Takowa yayi zuwa bakin gadon ya dan tabo fuskana ban ma san yanayi ba don nai barci sosai. Ya dade a tsaye baiyi magana ba ya juya tafita daga dakin ya nufi gurin Baba shima barcin yakeyi yasa shi fitowa don likita yace kada a shiga dakin abarshi ya huta haka yasa akabar su mama da umma da mummy kawai. Fita sukayi daga asibitin shi da bashar bai mashi magana ba shine dai ya karbi key yajasu barshar din. ****** ********* ****** Ina muka nufa yake tambayan shi kai tsaye yace kaini gidan Normal please inji daga bakin shi. Sai gidan yaya Ahmed bashar ya tsaya suka fita gidan yana a rufe amma akwai mutum don kara kidan disco daya karadw erea din a lokacin daga gidan. Nocking din kofan gidan sukayi kusan sau uku kamar baza,a bude ba can jamila tabude kofan gidan. Tana cikin wani matsatsen wandon jeans da ya matse ta da wani dan riga ja mai guntun hannu a rubutawa rigan crazy girl. Tana ganin shi ne tace up UF yau kaine gidan da kanka cikin wani yanayi na farr da idanuwan ta. Yace mai gidan fa a taice ? Baka ma bari mu gaisa sai tambayan dan uwaka watau shi ka sani kawai ko ? Yace please ina Normal yake nake tambayan ki ? Normal kan baya kasan ya tafi kwatano dauko mota tabashi amsa ganin da tayi ba wasa a fuskan shi. Ok kawai yace ya juya yabar gurin bashar yabi shi a baya mota suka shiga suka bar unguwan . Baiyi magana ba da suka fara hanya sai sa hannu yayi ya dafe goshin shi da hannun shi daya kawai. Zuciyar shi tana mai wani irin suya don bacin rai hankalin shi a tashe yake lokacin. Bashar ne yace yanzu kamata yayi mu nemi mutumin mu fara jin yadda sukayi dashi first. Yace wa yasan mutumin sai bashar yace bari mu nemo Sagir ko yasan labarin mana ? Asibiti suka dawo har looacin Baba yana kwance sharkaf dashi sun dan dade a kan shi ba wani motsawan da yakeyi sai dai numfashi kawai da zai nuna ma yana raye. Fita yayi ya kira yaya Imiran da Sagir din shima Abdul ya biyo bayan su dashi da bashar. Yace wani mutumine ya sayi gidan baba din hannun Normal Sagir ? Gaskiya ban san shi ba sai dai ina gani a GRA kamar nake ganin motan shi idan naje gurin aboki na dake can. Abdul daga bayan su yake cewa wanan guy din da suka zo dazun yace eh shi yace dan masani ne mana guy din nan mai sayen gidaje dake GRA ko ? Mota biyu suka tafi dashi gidan mutumin sai dai baya nan ance masu yafita cikin gari . Yanzu yaya kuke ganin zamuyi ke nan ? Bashae yace lauya zamu fara nema mana shine farko don nasan dole abin sai ya hada da lauya ai. Wani lauya kake gani duk garin nan zamu iya samu ya tsaya muna kan wanan magana don ba karamar case bane fa ? Nan suka fara kawo sunayen lauyoyi da suka san cewa yakai lauya da zai iya tsaya masu karshe dai suka tsaya akan barister Nuraddeen mohammed moroki dake zama a gusau zamfara state. Shine zai tsaya masu a matsayin lauyan su matashine wanda yasan aikin shi da sanin darajan tallakawa akan aikin shi sosai. Sun samu lamban lauyan inda suka kira shi tare da mashi bayanin komai dake faruwa shima yana tambayan su wasu abubuwan da ya dace ya sani daga cikin maganan. Haka aka shigar da kara a koto ranan basai ma gari ya waye ba don da zafi zafi ake buga karfe. An aikawa dan masani da sammacin sayen gida ba bisa kan kaida ba a hannun dan maigida da yayi. Yana karantawa yai dariya yace shi may ye nashi sana,anshine ba yau aka fara irin wanan ba ai Allah ya kaisu kotun lafiya. ****** ********* ****** Falkawana yai daidai da su Mama suna dakin lokacin ma magariba ya gabato sosai na bude idanuwa na a hankali. Sai naji suna sannu Fatima yaya jikin naki nace a hankali da sauki na daga ido na kalli gurin daki ne na asibiti ashe nake ciki a lokacin. May ke damunki yanzun Fatima mummy ta tambaye ni ? Da kyat na bude baki nace mata juwa nake ji tace bari a kira likitan ya dubaki. Likita sun dawo tare da su yaya nan suke gaishe mu likita yace su dan rage daga dakin nan aka barmu ni da yaya da likitan kawai. Bayan yan tanbayiyi idanuwa na suna a lumshe yai yan rubuce rubucen da zaiyi ne yake cewa dole sai nayi bed rest a cikin asibiti don yana gani baby dake jikina yayi weak sosai zai iya fitowa indan an matsa mai wanda hakan babban hatsari ne sosai gare shi. Idanuwan shi ya runtse tare da tausaya ma halinda nake ciki lokacin nan dai aka yanke shawaran zan zauna asibiti har wani lokaci a gani. Iyya Rabi ce zata zauna a tare dani don dama tare muke itace ke ta fama da lalura na ko a gida. Hankalin kowa a tashe don yadda baba yake matukar jin jikin shi ko matsi bayayi sai na,uran taimako da,aka saka mashi ke aiki. Zancen karan da akayi an tsayar da magana dole sai anga Ahmed anji ta bakin shi za,a,san yadda za,ayi. Gashi har lokacin bai dawo garin ba kullun akaje gidan baya gari Jamila take fadi. Ashe ta dawo ya samu labari gurin wani abokin shi shine yake boyewa kada su ganshi. Sai dare sosai yake komawa gida ya kwanta tun da safe ya bar gidan ya koma maboyan shi ya boye. Duk wani dan gidan hankalin shi a tashe yake yadda baba ake hasashen ya samu faralazy ne barin shi guda na dama. Gashi har zuwa lokacin yana unconscious bai san inda yake ba sai cewa likitoci keyi akwai improvement ga lafiyan shi. An yanke shawaran za,a fita dashi waje wani abokin sadauki likita yace a kawo shi gurin su su duba shi a Germany. Komai an cika na tafiyan su waje da baba lokaci kawai ake jira na fita da mummu kawai sai shi sadauki da,Sagir aka shirya tafiyan da za,ayi. Ina zaune Iyya tana tsaye a kaina ta wade min lemo zan sha ya shigo dakin zai min sallama. Tana ganin shi ta fara gaudashi tare da mashi yaya maijiki yace Alhamdullahi Iyya zamu tafi yau da,daren nan lagos gobe da safe zamu daga dashi. Iyya tace kai duniya gaskiya wanan yaron wallahi bai kyauta muna ba wallahi wanan sallon yaudaran nashi yayi yawa ina zai kai alhakin wanan bawan Allah da,sanadin shi ya mayar haka ? Ya tako zuwa inda nake ina tsotson lemun da Iyya ta wade min a hankali yace yaya jikin naki Fatima ? Nace naji sauki yaya yaya jikin baba din yake ya dan lumshe idanuwan shi a hankali yace yaji sauki yau insha Allahu zamu tafi. Ki kula da shan maganin ki Fatima kin dai ga yadda kike fama ban how long zaki yi ba anan yadda likita yai min bayani zasu dan rike ki suga yadda jikin naki zai kasance kafin su sallamay ki daga nan. Idanuwana na lumshe ina jin wani ba dadi yace naso mu aikawa mutanen gida don su san halin da kike ciki amma maji ta hana tace kada mu tayar masu da hankslin su suma. A bari har aga yaya jikin naki zai kasance tukun sai a fada masu amma ni naso su sani kila za,a samu wanda yazo daga can ya zauna dake. Shiru nayi ban da ta cewa sai dai naga aiko yayane ya kamata a basu hakkin su a matsayin su na mahaifa na. Don idan sunji bazasuji dadi ba daga baya sai dai banda yadda zanyi don ban da tacewa ni yanzu. Muna tare muna hira jefi jefi dashi wanda na lura bai a cikin hankalin shi a lokacin. Yace zai tafi gida ya shirya ya bar zancen makarantan Sa,ade a hannun bashar yana ganin zuwa wani Monday za,a kaita makaran ta. Musa ma Bashar zai kula da zuwa mai visiting kamar yadda ya saba zuwa mai. Nace na gode a hankali ya mike yace zai tafi ya dawo idan ya kimtsa nace Allah ya tsare ya fita. Da yamman ne wani abokin bashar ke fada masu cewa yaga yaya Ahmed yana garin don sun hadu dashi da rana a,wani shago yana sayayya. A gida kuma mama Asiya da yan uwanta suna cikin matukar tashin hankali sosai don tana gudun wani abu ya faru da mijinsu a sanadin dan ta. Wanda tasan ba zasu yafe mata ba don halin da danta ya jefa gidan ko yanzu bata da shakata a gidan kowa sai zagin su yakeyi tanaji tana gani babu yadda zatayi akai sai hakkuri. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,, IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BAKI GA ALLAH YA SAKA MUNA AKANKI YAR UWA,,, Ya dawo acikin shirin shi ina kwance Iyya tana kokarin fita da ta gan shi yace, Iyya ni zan tafi don Allah mutumiyar ki a kulla da ita sosai naso ace ina garin don na bata kullawa sai dai hakkan baisamu ba. Nasan ban da matsalar hakan don ke da maji kuna kusa da ita bana son tana wanan rashin cin abincin da batayi yana matukar damu na sosai ko ba dadi abata koda kadan ne please. Iyya tace uban dakina kada ka damu tsakani da Allah nake zaune tare da ku zanyi wa Fatima duk abinda kasan zan iya yiwa yar cikina shi insha Allahu. Ya ciro kudi masu yawa yabata yace ga wanan ki rike a hannun ki ku dinga lalura dashi a nan din. Tai mai godiya ta fita daga dakin ta barmu mu biyu dagani sai shi a dakin. Isowa yayi inda nake kwance yana cewa na,shirya zamu tafi yanzu bakin gadon da nake kwance ya zauna ya kamo hannuwa na. Yana fadin Fatima don Allah ki kula da kanki ki tausayawa abinda ke a jikin ki please. Idan baki ci abinci ba yaya zaki samu kuzari har baby na ya samu shima please ki tausaya min ko ba dadi ki dan dinga cin yan abubuwan gina jiki don kuzarin ku. Kune rayuwana Fatima kune zan kalla nayi farinciki don kune jindadin farin cikina. Nasan bakya jin dadi amma ki kara tausayawa kanku please badon ni ba for the sake of our baby please. Idanuwa na na dago sun ciko da hawaye nace yaya ina son ci amma ko naci din fitina yake zama min nai ta amai sai na fitar da abinda naci nake dan samu lafiya. Ya dora kanshi saman goshina ta yadda muke iya shakan nufashin junan mu. Yace sorry my baby nasan kina wahala wallahi dada halin karban ciwon nan a hannuki da na karba maki kin huta ke ma. Hawayen da nake dannewa ne suka silalo daga idanuwana a hankali. Yasa hannu ya goge min yace ko bakya son na tafine Fatima? Sai na barsu mummy da sagir su tafi su kadai na zauna nai jinyanki da kaina. Nace cikin kada kai tare da bude bakina da kyat nace no yaya Baba yafi bukatan ka a hanlin yanzu. Tausayin ka kawai nake jin irin yadda rayuwa yazo muna cikin wanan dan kankanin lokaci haka komai ya jagule a lokaci daya. Yace cikin dan murmushi tare da rugomoni zuwa jikin shi da kyau yace duk bawa yana da tashi kalar jerabawan a kullun don haka wanan wani sabon gwajin Imanin bawa ne yazo muna. Ki kula da rayuwan ki don likita ta fada min kina matukar bukatan hutu sosai saboda kalar mahaifan ki ba mai daukan wahala bace haka. Nace insha Allahu yaya zanyi yadda kace Allah ya tsare min kai a duk inda kace yace amin cikin dadin rai. Yace Fatima wanan baby ya wahal da maman shi da yawa udan yafito ashe bazan yi punished din shi ba kuwa? Dariya nayi dama shi yake son ji gare ni kafin ya tafi nace ni har cewa nake a cire min shi na huta wallahi. Sai naga ya sake ni ya lame kwance saman gado yana fitar da numfashi tare da furzo iska daga bakin shi. Yace Fatima ko bakya son nawa ne da gaske da har kika iya furta wanan kalman haka a gabana ? Nace haba yaya kaima ai kasan ina son ka wahala dai ne yai min yawa wallahi yaya. Yace to kiyi hakkuri please ki haife min shi nai maki alkawari baku kyakyawan kulla dake da ko maynene a tare da ke insha Allahu nace naji yaya. Kudi ya ciro masu yawa yabani yace karbi wanan ki boye a gurin ki don ban san abinda baya zai yi ba. Nace ni may zan saye anan wanda akace zai kwana biyu a cikin asibiti yace karbi dai ki rike a hannun ki in case zai maki amfani. Ya rugomayni na dan tsawo lokaci ya mike yana cewa zamu tafi nima kokari saukowa nake daga saman gadon da nake kwance. Ina kuma zaki tafi na dan marairaice nace ina son ganin tafiyan baba ne yaya. Ido ya kura min kamar zaiyi magana sai kuma ya mika min hannun shi alaman nazo mu tafi tare muka fito bayan na saka dan silifas a kafana tare da saka hijjib dina. Tare muka fito daga dakin yana rike da hannuna nan naga kowa na gidan mu yana gurin maza da mata manya da yara. Idanuwan su akaina har muka karaso suna gaisawa dani bai saki hannu na ba har lokacin muna tare muka shiga inda Baba yake kwance harkaf an shirya shi kamar ace ya tashi ya tashi. Har bakin gadon muka karasa yaya yadan duka daidai kan shi yace Baba ga Fatima tazo tai maka sallama. Yadan jawonin zuwa kusa da Baba nace Baba Allah ya tsare hanya Allah ya baka lafiya ka dawo cikin mu lafiya. Ikon Allah sai kawai baba ya dan bude idanuwan shi a hankali wanda sunce ya kwana biyu bai bude idon shi ba. Yana bin mu da kallo a hankali na kara cewa Baba Allah ya baka lafiya ka dawo ka dauki jikan ka da hannun ka. Sai ya dan sake murmushi a hankali wanan yasa kowa dake gurin jin dadi sosai har likitan dake tsaye yana gyara shi yace gaskiya da za,a samu irin wanan da yake so a tare dashi ko yaushe za,a samu improvement sosai ga lafiyan shi. Nace muyi addua kafin a wuce nan na gyara na dinga kwararo mashi adduoin samun lafiya ana karbawa da Ameen. Muna tsaye aka fito dashi aka saka shi a ambulance din asibiti zuwa airport. Sai da aka rufe motar yaya ya dawo har inda nake bai damu da,wai mutane suna gurin ba yai hugging dina a jikin shi yana dan bubuga min baya kamar yana lalashi na tace be strong Fatima Allah ya baku lafiya. Ya juya ya tafi kowa sai kuka yakeyi don yadda aka fita da baba ko mutum baida Imani sai ya tausaya mashi. Da gata na kwato bawa daga hannun Alah da gata ya kwato Baba cikin wanan halin rayuwan da yake ciki a wanan lokacin. Gaba daya diyan shi yan uwanshi abokan arziki jikoki saraikai duk suna gurin tsaye cikin tashin hankali a lokacin. Rahama tana gurin da iyayyenta a gaban idon ta komai yafaru tana kallo. Wani kishi ya rufe mata idon ta don ganin yadda yaya yake wani jiji dani kamar diyar wata da wani. Tace sai tayi magani na sai ta mayar da wanan son tsakanin mu ya koma kiyayya watarana a cikin ranta take zancen ta. Uwarta ma kishine ya rufe mata ido suna hanya take magana cewa jifa yadda yaron nan yake wani jiji da yarinyar nan. Ai don dai baki tare dashi ne idan kina gidan wane ita yar talkawan tsiya kawai. Baban yace ai barshi da gaiyya zan daura masu aure inga yadda zai yi da ita idan nakai mashi ita gidan shi. Muna kallo suka fice daga asibitin suka barmu nan aka fara watsewa daya bayan daya ana mai fatan samun lafiya. Na kalli duk taron nan watsewa zasuyi su tafi su barni a cikin asibitin ni da Iyya kawai . Sai naji wasu hawaye sun zubo min Nafisa ta kama min hannu tace kada ki damu matar yayana Allah na tare da ke. Tare da ita muka koma dakin da nake bayan nayi sallama da mutane mama da maryam da mijinta ne suka biyo ni zuwa dakin. Sun dan jima a gurin mu sukace zasu tafi sai dai da safe idan sun dawo kuma insha Allahu. Nafisa tace ita yau a gurina zata zauna mama ta zaci wasa takeyi sai da tace Allah maji yau a nan gurin Fatima zan kwana na debe mata kewan yayana. Nan mama ta tafi tabarta sai dai mama bataso haka ba don tasan halin Nafisa na watsewa. Amma batai komai ba wallahi sai hiran da mukeyi akan matsalan baba kawai da zamu kwanta ta hau dogon kujera iya tasa bargo a kasa ta kwanta sai safe. Washe gari da muka tashi Nafisa bata tsaya an kawo abin karyawa ba ta wuce gida. ****** ********* ****** Sun isa Germany da baba lafiya an kuma duba lafiyan shi har ana samun sauki sosai suna isa yaya yake kiran layina tare da tambayana karfin jikina. Ganin an wuce da baba yasa yaya Ahmed fitowa daga maboyar shi ya na komai nashi normal. Sun buga suna fadawa sadauki fitowan shi yace abar case din har ya dawo don kotu ta fadawa dan masani cewa bai da hujjan tayar da maigida a gidsn shi sai ya samu lafiya an yi sharia. Sadauki baya son ayi maganan kan zancen sayar da gidan nasu na gado da akayi duk da zancen ya karade gari anji labarin abinda Ahmed yayi wa mahaifin shi. Mama Asiya hankalinta yai matukar tashi yadda taga kowa gidan ya tsane ta ita da danta. Don laifin Ahmed ya shafe laifin duk wani laifin yaron dake gidan gashi Alhaji bai ko yarda ya gaisa da ita a waya. Ko yana waya akace ga mama zata gaida dashi zai kashe wayan yaki dauka. Balle ga mummy kusa abin nema ya samu dama ba shiri a tsakanin ta dasu ko kadan. Duk da baba yana asibiti cikin halin lahulai amma idan mutum ya shiga gidan zai ga kamar hankalin su a kwance yake. Irin yadda suke busha shan su agidan ba wani damuwa a tare dasu a lokacin. Ga wani shakuwa da yashiga tsakani na da Nafisa yanzu don ko wani lokaci tana gurina a asibiti muna tare. Wani lokaci anan kawayen ta ke samun ta nan zasu wuni suna debe min kewa. Banda matsala dasu wani lokaci idan suna hiran busha shan su a gabana nakan ce haba anty kamata yayi ace cikin maneman ku ku cafke daya ku aura. Nura kance ke kaunata nifa mijin ki nake so na aura nakance aiko danaji dadi anty idan har zakiyi aure ki zauna ba sai mu zauna lafiya ba. Kin sanni na san ki kinga ba fada a tsakanin mu sai so da kauna mu rike mijin mu tsakani da Allah. Nuriya wallahi idan kina wanan maganan zamu sami sabani sosai wallahi Raiha ke fada mata haka duk lokacin da tai irin wanan magana. Nafisa kuma takance may zaiyi da honko haka may ya rage jikin ki baya cus kin sha burga kamar rijiyar kwakwara da ke. Nace ba komai zamu gyara ko anty Nura ai mace mai gyara bata baci ko ? Raiha takan sha toka tace please abar wanan zancen bata so su ko watace sukaji mijina yana nema sai inda karfin su ya kare akai. Tace Fatima kin muna fa wata matar aure ce zata sake jiki damu haka abinda ake gwada muna kyama keko kin muna rikon tsakani da Allah kamar wasu yan uwan ki naji fa kika mayar damu. Yan uwan mu ma naji yanzun haka basu hurda damu don kaaai wanan halin da muka tsunci kan mu a ciki. Mutane suna manta cewa ko su Allah yana iya jarabtan su a kan haka? Duk lokacin da ya tashi yin ikon shi a kan mutum na tabbatar da yan gulma suna fadawa mijin ki kina hurda damu haka amma sanin koke wacece yasa bai damu ba duk dai yana halarci ne akan yar uwar shi dake cikin mu amma duk da haka Fatima kunyi muna wallahi. Nan zamu wuni da su ai ta shiririta suna matukar bani tausayi ina yi ina masu gyara. Yau ma sunzo mun jima muna hira dasu sosai har barci ya kwashe ni na barsu da Iyya suna hira sun sayo nama mai zafi da drinks sun baje suna ci. Amira ne tashigo dakin da nake kwance wanda yanzu ya zama min dakina na komai. Suna gaida ita amma,sai wani basar dasu takeyi sukaci gaba da harkan su kawai. Bakin gadon da nake kwance ta karaso tana tayar dani daga barcin. Iya da Raiha ke cewa haba kin san tana son hutu barta mana tai barcin ta kada ki tayar da ita. Tace waye zai hanani tayar da ita Rabin dan musa ko wa wai takai hannu ta tabani na bude idanuwana. Ina kallon ta nace anty kin shigo ne ashe tace a wulakance may wa yan nan sukeyi a nan ne haka ta nuna su a wulakance. Sai sha,anin su sukeyi kamar basu san da ita ba afurin ko tanayi ma ba wanda ya kulata. Na dan kakaro murmushi a fuskana nace anty kawayen anty Nafisa ne fa. Tace and so what Nafisan may can kuma wai kinga bani son na kara ganin su a tare da ke kinji na ffada maki ko? Tace sai dai ban sani ba ko kema harkan taku dayane dasu don banza bai kai zomo kasuwa. Wasu hawaye suka zubo min nace haba anty cin fuska baida kyau haka wani abu mukeyi banda mutunci da zumunci kawai. Tai mun wani kallon wulakanci tace zaki gane wallahi Nafisa tace Amira wallahi yadda kike da Fatima nima haka nake da ita don haka baki isa ki rabani da ita ba don bakece kika hadamu ba. Tace yanzu ko da yake ba mamaki tunda naga yazama dan uwanku don abin hannun shi ai. Tajuya tare da yi min wani kallon mamaki na wullakanci tafita daga dakin. Tana futa tun a haraban asibitin ta kira dan uwanta cikin fada take mai batanin karya da gaskiya. Yace Amira badai zuwa kikayi kika tayarwa Fatima da hankali ba tana fama da kanta ba nan tace don may zata dinga tara wa yan nan yan iskan haka tare da ita. Yace kin san halin Fatima fa Amira bazata taba bari tayi wani abin asha ba insha Allahu a rayuwan ta. Kuma ai don Nafisa suke zuwa tace min nafusa ko yaushe tana gurin ta tana debe mata kewa ke da baki son su zo may yahana ki tare a gurin su. Lalai ma yaya dama ba yau ba nasan cewa Bintu ta gama dakai gaba daya baka son a fadi abinda tayi don ta shanye ka. Baiyi magana ba don ranshi yakai kololuwar baci mama ya kira yana fadin daga yau kada Amira ta koma gurin mamatata don bata san zafin ta ba. Don may zataje ta tayar mata da hankali bayan ta san irin yanayin da take ciki likita yace a bata hutu. Kai wai may ke faruwa ne haka wai nan dai ta kwashe yadda sukayi da Amira ya fadawa mama komai. Mama tace ji mahaukaciya kawai Nafisan da koda Fatima ke a gida tana nan like da ita ko yaushe a dakin nan. Ko ranan da kuka wuce fa a gurin Fatima Nafisa ta kwana tace bazata dawo gida ba zata tsaya ta debe mata kewa. Yace balle zaman Nafisa da fatima Allah ne ya hada su ai maji. Mama tacs kuma tun yayatana fada har ta gaji yanzu ta daina ta saka masu ido tsakanin su don waya sani ko hakane zai zama silan shiryuwan ta ma ? Nan dai sukayi magana sosai ta kashe wayan tana jiran dawowan Amira gidan. Mummy dake kusa dashi taji fadan da yakeyi tace kai Amira ma dai ita fa bazata iya tsayawa tayi yadda ya dace ba Fatima da yanzun take son wai raba tsakanin Nafisa da Fatiman. Zaman Fatima da Nafisa fa yakawo sauyi sosai yanzu a rayuwan Nafisa fa don yanzu kan zaman Fatima a gida zata iya kwana barkatai bata fita waje ba. Aiko wanan abin sai ace abune na dubawa sosai wallahi tabar irin wanan cin fuska haka baida kyau ga dan adam wallahi. Baba ta najin su wanda yanzu bakin shi ya dan fara budewa yake cewa Fatima Fatima ai alheri ce a cikin zuria ta wallahi. Amira na shigowa gida zata fara fadawa maji mama tai cikin ta da fada sosai har sai da ta raina kan ta a lokacin. Ta shige tana cewa indai kan Bintu ne wallahi bazan sake saka kaina ba a al,amarinta da yardan Allah kuwa tashige ciki abinta. ****** ********* ****** Amira na fita wasu hayen bakin ciki suka zubo mata nace yanzu ni may laifina kuma? Idan naki Nafisa kuma zagina za,ayi ace bani son dangin mijina balle ni Nafisa tsakani na da ita yanzu sai hamdala kawai. Duk da ta girmay ni amma idan nai mata magana takan daina abinda takeyi a lokacin. Amma may zai sa Amira tace wai kila harkan mu daya dasu bayan ta san koni wacece takuma san halina din. Yayan ta ma ya ganni dasu bai ce komai ba don shine ta jawota gare ni . Allah sarki yaya sadauki mutumin kirki mutum mai adalci wanda ta san ya kamata . Muryan su naji suna fadin sister indai don muna hurda dake zamu jawo maki matsala zamu daina zuwa gurin ki gaskiya. Nace akan may anty wanda ya ajeni baiyi bakin ciki da zamana da ku ba sai don anty tazo da wani zancen ta can na daban. Nace ba inda zaku idan dai ba maigidan da kanshi yace min bai son hurdana da ku ba. Wayan shi ne ya shigo a lokacin jin ina kuka yasa shi cewa Amira tazo ta bata maki rai ko? Yace ina Nafisa take nace mai gata nan yaya yace bata waya na mika mata wayan nace yaya yana magana da ke anty. Ta karbi wayan daga hannu na yan uwan suka tsura mata ido don son jin may zai fada mata a lokacin. Mun dai ga tana cewa ai ba komai yaya duk abinda tai min yar uwata ce ita tace ba komai komai ya wuce ai don badon ta muke zuwa ba ai dama. Sukai sallama ta miko min wayan ya tambayi jikina nace naji sauki ni so ma nake a sallamay ni na koma dakina wallahi. Yace sallama Fatima likita yace min sai kin haihu zasu sallamayki fa don bazasu bari ki fita asibitin nan ba hakana. Banji dadin wanan zancen ba ina cikin asibiti har tsawon wani lokaci ni wani irin ciki ne dani haka wai ? Gashi muna batun fara exam haka nake karatu a asibiti sai idan lokaci yayi zasi yarda na tafi na zana koshi tare da wata nurse zamu tafi suka ce. Yadda suka fada ko hakane haka zan shirya da safe yaya bashar yazo ya dauke mu zuwa school dani da,wata nurse da aka dauka haya don dubani ba dama nayi wani dogon motsi dana gama zamu juyo zuwa asibiti tare da ita a sauke mu. Bai tafiya gida sai yaga anbani magani na kwanta zai bar asibitin har na kare exam dina da mukayi. Gaskiya yaya bashar mutum ne don yana bani duk wani kulawan da ya dace wanda zai sa banji kewan mijina ba gurin kula. Haka zai kawo min maryam mu wuni da ita muna hira sai dare sanan yazo ya dauke ta. Mama ma takanzo sosai kuma abinci dare da rana yana saman hanya ana kawo muna duk abinda muke so. Ba laifi don yanzu da cikina yake wata shidda da yan kai saura kiris ya cika wata bakwai ina dan iya cin abinci kadan. Sai dai ba mai yawa ba don idan har naci mai yawa ranan sai na fadawa aya zaki gurin wahala. Haka dai nake zaune Iyya tayi min halarci matuka a rayuwan na don komai itace ke min shi iyakana naiwa kaina wanka kawai. Bayan shi duk wani abin bukata na itace mai aiwatar dashi da kan ta zatai min komai. Yan uwa sai faman zarraiya suke zuwa gurina duba ni zuwan Baba na biyu yana duba lafiya na a,asibitin. Haka ma a bangaren mamana saida sukayi mota daya ita da abokan arzikin ta da yan uwa sukazo duba ni. Don haka ban da wani damuwa a tare dani sai na kadaicin mijina a kusa dani kawai zance yana damuna. Acan ma Germany ya wuce gurin buga wani wasa da akayi mai zafi inda kuma team din su na basilona da yai ma,wasa yai nasaran lashe wasan da suka buga. Ba karamin kudi ya kwaso ba sai dai bai dawo gida ba ya koma gurin su baba asibiti. Baba yanzu ya dan samu lafiya don likita yace zasu iya dawowa dashi nan da sati biyu masu zuwa idan an tantance lafiyan jikin nashi da kyau. Sai kuma ga,wasa ya taso mai zai tafi arabian kingdom ya bufa,wasa wanda ake tsanmanin zasu samu makuddan kudi idan har sunyi nasara ga wasan da zasu buga. Jirgi ya samu ya kammala komai akan tafiyan su Mummy da baba sai yaya sagir da zasu dawo gida. Ya basu kudi kowa ya sawo tsaraban da zai zo gida dashi inda,zasu dawo tare suka fita dashi ya kaisu sukai sayayya inda yaya sagir ya kwaso laptop da kudin shi zaizo dasu ya,sayar itako mummy kayan yaranta da,wasu abubuwan anfanin ta ne ta sayo acan kasan. Ranan da zasu dawo kowa yana cikin farinciki da dawowan su gida anshirya ma dawiwan baba din sosai yanzu. Muna asibiti labarin dawowan shi ya riske mu sai dai ance bari dayan baba bai aiki gaba na ne ta yanke yafadi ras. Amma Rukaiyya tace min sai dai gaskiya idan kin ganshi ya samu lafiya sosai wallahi. Tun bayan fitanta nake jin marana yana dan yanka min kamar zanyi period nake ji. Sai ban damu ba don nasan tunda ina da lalura mai zai tayarwa kaina da hankali dashi. Wasa wasa ban daina ji ba har cikin dare sai barci ya gagare ni ina kallon iyya da ta samu barci tana barcin ta hankalinta a kwance abinta. Jin mara din ya matsa min ne na mike zaune aiko zama yace bai sanni ba can da naji wani iein ciwo na sauko na kama karfe gadon na dan nisa tare da murde bakina don dan zafin danaji a lokacin. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,, IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH YA SAKA MUNA,,, Kukan dan jarin da ya fado ne ya saka Iyya dake kwance dan bude idon ta a hankali. A lokacin da nake fadin Iyya Iyya tashi ki gani abin cikin cikina ya fito Iyyah ko na haihu ne ? Tamike tana fadin subbahanallahi ikon Allah uwar dakina kin sauka ne ? Sai kuka yaron dan karami dashi sosai yake tsalawa duk Iyya tabi ta rude taje inda ake kunna wutan dakin ta kunna tana cewa. Kinko haihu wallahi uwar dakina amma sai dai killa bakwaini ne kika haifa don yaron yai kankanta da yawa. Ta dan taba yaron yakara tsala ihu tace namiji ne sai dai bakwaini ne da sauri tafita daga dakin zuwa inda nurses suke kwana ta kira su. Sai gasu da saurin su sun shigo tare da ita taimakon gagawa suka fara ba yaron nan suka rabashi da uwar tafiya Allah yasa akwai reza da na anty Raiha ta sayo min sai ta sayo parked din shi gaba daya. Dayar nurse din taje dakin doctors takira likita mace wacce tai adimin dina a,asibitin ranan ita ce akan duty. Tana zuwa ta danyi dube duben da zatayi ta tambaye ni banjin komai na fada mata komai bana ji. A cikin daren akaiwa yaron wanka nima nai wanka Iyya tace a kira gida ne a fada masu nace tabari harda safe sai a kira gida don yanzu kowa yayi barci hankalin su zai tashi tunda ina lafiya. Sosai likitan taita gwada yaron tace min lafiya yake sai dai premature baby ne idan da rabo zai rayu insha Allahu. Nace daga inda nake zaune a bakin gado anty zai rayu kuwa ? Tace insha Allahu zai rayu ai seven months ne yanzu kike da kwana biyu. Sai dai da,safe zan so muyi shawara muji idan zai yuyu sai a dan saka shi a kwaba yadan kara tasawa tukun. Bamuyi barci ba sai da,asuba muka dan runtsa kadan shigowan nurse din dakin ya,samu falkawa Iyya ta tafi sallah ni kuma ina kwance ina kallon yadda sukewa baby din. Bakwai da yan mintina Iyya tashigo dakin nace ta bani wayana , numban mama na fara kira har ya kusa tsunkewa ta daga da,sauri ba ko gaisuwa hankalinta ya daga don ta ga ban kiran ta da farar safiya irin haka. Tace Fatima lafiya dai ko ? Nace a hankali mama na haihu ne. Cikin wani murya tace kinyi may fatima nace na haihu ne mama. Sai naji ta kashe wayan maryam na nema tana barci wayana ya tayar da ita na fada mata na haihu sai Nafisa. Koda na kira nafisa ina jin muryan mutanen gida a na yaya nasan zancen ne mama ta fada masu a lokacin. Kafin wani lokaci naji kiran sadauki ya shigo yace batare da gaisuwa ba Fatima is that true o you are joking yanzu bashar ya kirani. Kafin na bashi amsa yaron da nurse din ta daga ya dan yi kuka na kara mashi a waya yaji. Yace it means yaron yana da rai har yanzu ke nan nace mai eh kawai sai aka turo kofa su mama ne da mummy da mama Asiya suka shigo dakin a rude. Idon su akan nurse din dake shirya yaron za,a kaishi pediatric asaka a kwalba. Gurin nurse din suka nufa suna kallon yaron dan karami dashi a cikin zani na da aka nade shi. Muna kallo suka fita da yaron mummy da,su sagir suka bi bayan su harda mama Asiya. Sai lokacin mama ta karaso inda nake zaune a bakin gado take cewa Fatima lafiya dai kike ko ? Na kakaro murmushi don hankalina a tashe yake nake cewa lafiya kalau nake mama. Tace to ki kwantar da hankalin ki idan yaron Allah yayi shi rayayye insha Allahu zai rayu. Nakoma a hankali saman gado na kwanta na lumshe idanuwa na shigowan su maryam ne yasa na bude idanuwana a lokacin. Maryam tana fadin tare da,waige waige ina yaron yake maji ? Tace sun tafi dashi nan tafada masu komai basu tsaya ko a gaisa ba suma suka bi bayan su da sauri. An saka shi a cikin wani dan karamin gado mai naurori tare da saka mai wani dan rigan sayi a ciki. Kafin likita ya shigo dakin sun fada min zan tashi daga wanan dakin da muke na gany room zuwa maternity room. Sai da,aka gyara komai suka mayar damu dakin lokacin yan uwa da,abokan arziki sun cika a dakin ko. Sai hira ake yayin da niko zuciya na duk a cunkushe yake min ban majin farin ciki ko kadan ni. Duk da kowa yazo fadin yake ai anyi arziki wata bakwaine insha Allahu zai iya rayuwa da yardan Allah. Barci ne ya dauke ni a lokacin mai nauyi sai mama Asiya ne naji tana tayar dani wai na tashi na sha tea da aka hada min. Na mike zaune ta miko min tea din yana wani irin tururi tace na kafa kai nasha shi hakanan. Har na daure na kafa kai zafi ya konani nai saurin cire bakina daga cup din ga tea din gudan mai yawa dashi. Lokaci daya suke ce min a,a a Fatima anya kuwa kafa kaifa zakiyi ki shanye shi duka yanzu. Nace a dan marairaice mama duka fa wallahi akwai zafi mummy tace kin manta cikin ki akwai miki a cikin shi maza shanye shi don Allah kinji. Haka na shanye tea din ina zufa take naji bakina ya dauki zafin kuna sai dai tea din yana shiga cikina naji wani irin dadi a jikina da nake jina yau kamar banawa ba. Ban dade ba na koma barci mama Asiya da mummy sukace a dan rage a dakin don na samu barci. Barci nayi sosai sai zuwa sha biyu da rabi na rana wata nurse tashigo dakin wai na tashi naje naba yaron nono. Tare muka tafi da maryam da Nafisa da mummy a ka dauko shi na zauna na fara bashi nono sai dai bai iya kamawa. Mummy ce ta gyara shi da dan kyau ya dan tsosa kadan ya koma barci don ba komai a nonon ma lokacin. Likita ya shigo yana cewa sannu madam ashe haka abin yazo muna kuma dai. Allah ya raya muna,shi ga baban shi yace yau yana da ball da mungashi yazo. Haka muka wuni yan uwa da abokan arziki sai zuwa suke gaishe ni allura akai min sai magani da,suke bani kawai. Bayan shi ni banda wani matsala a tare danj gaskiya mama ta bugawa iyayyena waya ta sheda masu yadda haihuwan yazo min haka. Sai dare aka rage a gurin mu inda aka barmu da Iyya sai mama Asiya da tace itama zata tsaya wai. Nafisa bata bar gurin mu ba sai zuwa sha dayan dare wani yazo ya dauke ta tafi. ****** ********* ****** Bayan kwana biyu da haihuwa ne likita yace zasu iya sallamana na koma gida sai dai zasu bani time da zan dinga shigowa ina bawa yaron nono. Karfe biyar na safe , tara na safe sha biyun rana karfe biyu na rana zuwa hudu sai shidda na yamma kuma zuwa takwas na dare idan da hali sai na dawo da,sha biyun dare ko sha daya da rabi. Yaya bashar yace insha Allahu za,a kiyayye zan dinga zuwa ina bashi nono din. Haka na dawo gidan don da aka bugawa sadauki waya cewa yayi na koma gidan shi kawai tunda ance lafiya na kalau. Gwagona ta zauna dani tare da Iyya a gidan tana min wankan jego gadai jego ina yi haikan amma babu baby a gida. Sai time yayi yaya bashar zaizo ya dauke ni ya kaini asibiti aba yaron dake karkashin kulawan likitoci nono ya sha. Satin mu daya Alhamdullahi yaron yana ta kara murmurewa sosai don yana samun kulawa gashi ba,a barin kowa ya dauke shi sai ni idan zan bashi nono ko ganin shi ba,a bari yan uwa suyi yana ciki a rufe. Kwanan mu goma da haihuwa yaya sadauki yashigo Nigeria da,tarin arzkin da yasamo a rayuwan shi sosai. Don andage suna sai yaron yayi kwari sosai zaa saka lokacin yin suna bisa shawaran da likita ya bayar ayi. Koda ya,shigo sokoto ya samu ina shiri ina jiran zuwan yaya,bashar don time din zuwan mu ba yaron nono yayi lokacin. Ina saye cikin atamfa zani da riga don nafi jin dadin ba yaro nono hakanan. Yana rataye da corth din shi a kafadan shi daganin shi a gajiye yake a lokacin. Direct dakina ya nufo da ya,shigo ina zaune a bakin gado nayi kyau dani don jego ya karbi jikina sosai a lokacin.. Jin shigowan shi dakin ne yasani daga idona na kalle shi shima dai ido ne ya,tsura min a lokacin yana takowa zuwa inda nake zaune. Sai da ya karaso inda nake nake ce mai sannu da zuwa yaya. Yace aikece da,sannu Fatima ya kai zaune gap dani yana cewa yaya kike nace lafiya kalau yayana. Yace yaya baby din yake kuma yanzu nace lafiya yake yanzun ma can zamu tafi bashi nono yaya nake jira yazo. Yace to na tashi mu tafi tare dashi nace bazaka huta ba tukun yace ina zan huta banga baby na ba Fatima. Tare muka tafi dashi da yaya bashar daya ja motan ranan an barsu sun shiga don shi. Shiya fara daukan yaron da muka samu idon shi biyu a lokacin sai watsalniya yake da kafafuwan shi. Ya dade da yaron dauke a hannun shi yana mashi addua ga sauran yara a gurin kwance suna barci zasu kai su biyar a lokacin. Mun ba yaron lokaci sosai muna tare dashi muna kallon shi muka aje shi ba don mun so ba muka fito daga dakin. Haka na dinga zuwa yaya ya na kaini har akai wata daya yaron ya dan yi wayau sosai a lokacin. An saka mai sunan Baba watau Abubakar an yanka rago da shanu anyi sadaka da naman wa mabukata. Likita ya bada shawara da yaron ya kai wata takwas akan zamu iya tafiya dashi gida a lokacin. Ranan da muka dawo gida da yaron naga dan mutum sosai a gidan masu zuwa min barka aka saka suna sati mai kewayowa za,ai taron suna irin na al,ada hausawa musulmai. Sai faman shirin suna akeyi Jamilan yaya Ahmed da ita ake komai a taron wanda mama ce ta saka ta yin haka dole. Don su taushi zuciyar sadauki akan maganan gida dake aje a kasa ba,a tayar ba tukun don wanan al,amarin sunan dake gaban shi. Ranan suna gidan ya cika makil da jamaa masu zuwa taron suna wanda na sani da ma,wanda ban sani ba yazo gurin taron sunan. Anyi walima sosai tare da ciye ciye da lashe lashe yan uwana sun zo da yawa sosai gurin sunan. Yan uwan mama ma sun zo da yawan su daga Niger state dasu akai sha,anin bukin sunan yaron wanda muke kira da Amir. Yai wayo sosai amma gwago bata bari ana daukan shi kamar yadda mukeyi ranan suna duk wace tazo sai ta dauki yaron ta ganshi. Likita ya hana haka yasa itama gwago ta hana a dauke shi yana gurinta a wani dakin da suke kwance a saman gado. Duk wace tace ina yaro sai dai ace mata yana lafiya yana can gun kakan shi anyi rabon kayan buki masu armashi da tsada aka saka acikin ko wani jakkan da za,a ba mutum. Zuwa yamma Nafisa suka shigo gidan da mutanen ta nan kallo ya koma kan su kuma sai gulma ke tashi a kan su. Kuryan daki suka kutso anan muka zauna dasu wanda hakan yai masu dadi sosai don ni bani nuna masu kyama ko kadan. Don nasan Allah ne ya jarabce su da yin hakan kuma muna rokon Allah ya yaye masu hakan a rayuwan su. Basu dade da shigowa ba sai ga tawagan Rahama da kayen ta sun kai su goma suma dai sai a hankali wallahi. Su ko suna ganin burgewa ne hakan suna jaye da troler har kuryan dakina inda nake suka kutso kai. Sai dai suna shigowa ganin tawagar Nafisa tab a dakin yasa jikin su yai sanyi akan wulkancin da suka kullo suzo suyi a gidan. Don sun san gaba da gaban ta wa yan nan yan daban da suka gani sun cuna masu gurin iskanci sau milayan albarka . Don su basu tsoron ta kwana balle ta bare masu ko kadan sun saba da casa juna a daba ko. Daya daga cikin su tace ga kayan yaron Rahama nan takawo mai aita saka mai har kala ashirin ba dai. Daga cikin yan daban Nafisa daya ta cabe da cewa kai amma kuma ta makara don tasamu har uwar yaro da uban yaro sun saya mai kaya na kasan waje masu tsada ba yar sokoto central ba. Sai ta koma da abinta ko ta samu cikin dangi a basu su suka don shi wanan yaro ko ta sunan shi mai tsadane balle suturan shi. Ke kuma a suwa gayyan na anya waya gaiyato ki nan yar daba mai arna dubu. Tace yanzu dani dake aga wanda aka gaiyato wanda ke tsaye ko wanda ke zaune kafin ai haka ashe Nafisa ta mike sai ji mukayi kawai ta kwashe Rahama dake gefe tsaye da mari kayau. Abin nema ya samu kafin haka su Raiha da Nuriya har sun mike tare da sauran su sai ko daki ya rude da danbe in bakaci bani guri na sudade na bar dakin ina haki nagudu dakin dasu gwago suke zaune. Take gida ya cika harda maza sunyiwa su Rahama kaca kaca da suturun su duk anyayaga masu shi. Sadauki yana site din shi mummy takirashi a waya sai gasu gidan yazo a hasale tsawa daya yai masu kowa yaja ya tsaya. Yace maynene haka wai please may kuke min haka a gidana ne wai wata mata tace muna aha,anin mu na lafiya wai ko yan kungiyar Rahama sukazo muna da fitana duka da zagi da habaici wai gida nasu ne sunzo ne kuma ba,wanda ya usa ya kore su a gidan. Idon shi ya runtse yana maijin takaici yace ma Sagir dake bayan shi ya kira mai mobil police yace kuma a rufe gida ba inda zasu. Take tan sanda suka shigo aka kwashe su sai police station aka rufe su kan tuhumar sunkai mai fada a gidan shi sun tayarwa mutane da hankali. Baba Sani ranan kamar zaiyi hauka gashi ya kira wayan sadauki yafi a kirga amma wayan a kashe take wayoyin shi duk ya kashe su. Yaje police station ance baza,a bada bellin su ba sai sadauki yazo da kan shi. Har dare ba wanda yasan inda yake ashe yana can sabon gidan shi da yake ginawa gaba kadan da inda muke duk dai a unguwa daya ne da inda muke yanzu. Baba Sani yaje gida duk da Baba baida lafiya amma haka yai ta yankar kauna da tashin hankali yana zagin Nafisa da kawayen ta. Ranan munsha zagi don har dani sai da Baba Sani ya hada ya zage a cikin fadan shi da yakeyi. Har yayi ya kare ba wani mataki da za,a dauka don ba,aga sadauki ba sai cikin dare lokacin mutane sun rage ya shigo gidan ya wuce dakin shi ya kwanta bayan ya fadawa masu gadi kada a bude wa kowa gidan. Baba ya zo da wasu makwabtan shi amma masu gadi suka ki bude mai gida. Haka ya hakkura ya koma da tarin takaici fam a zuciyar shi ba yadda zaiyi. Asuban farko yazo gidan da masifa inda yake shiga ba nan yake fita ba yana fadin don sadauki na ganin yana da dan hali shine har yake gani zai iya taka kowa ya zauna lafiya. Dama ba yau ba yasan cewa shi shedanin yaro ne shiyasa al,amarin shi bai mashi ba. Duk hayaniyar da yakeyi bai san yanayin gidan bai bari a sani ba a banza yake ihun shi a,waje. Na shirya a cikin wani dogon riga tare da daukan Amir a kafadana muka nufi dakin shi mu gaida shi. Na samay shi a tsaye yana saka aninin dogon rigar shirt da ya saka a jikin shi jin shigowan mu yasa shi juyowa gare mu yana murmushi a fuskan shi. Na karaso inda yake tsaye nace yaya na ina kwana yace maman Amir an tashi lafiya ko yaya gajiyan jama,a dai ? Jama,a sunyi dadi sai dai abinda ba,a,rasa ba kawai da kaje ya dawo na halin taro. Nace gaskiya yaya jiya banji dadi da kasa a rufe su Rahama ba kuma kai tafiyan ka Baba har dare yana zuwa gidan nan neman ka ba,a ganka ba. Yace ko yanzu yana a,waje ya tafi can gida jiya ance yaiwa baba tas da mutanen gidan. Amma kina nufin kinji dadin irin wullakancin da sukazo har cikin gida su sukai min ko ? Nace ayi hakkuri son kane ya rufe mata ido har ta aikata hakan ba wani abuba. Kuma aiko banza Rahama yar uwar kace yaya sai hhakkuri kawai wallahi amma basu kyauta ba gaskiya. Nifa shigowan ta baidamuna sam don a tare na ganku gidan ku daya yar uwan kace Rahama ta jini. Hannun shi ya mika yana son karban yaron sai bai iya ba don bai kan dauki yaro shi sam. Zama yayi bakin gado yace min zoki gyara min shi please ban iya daukan yara ni. Na zauna gap dashi ya tsurawa yaron dake barci nade a ciki a showel a hannun shi. Na zauna ina cewa ai yanzu naga zaka fara dauka tunda dai Amir din badani yai kama ba. Dawa yai kama ya tambayeni cikin dago kan shi yana mai kura min idon shi. Ina dariya nace ai kaima kasani ni bai biyo ni ba,duk kaine ko yaya sagir ne ko yaya Ahmed oho ?. Da sauri yace Ahmed kuma Fatima please ki bar hada min yaro na da,wanan mara mutuncin mutum wanda bai san Allah ba. Nace hakkuri za,ayi yaya tunda ya riga da ya aikata yanzu baba ne abin tausayi wallahi don na san har gobe koda yake haka abin yana damun zuciyar shi. Yace ai Monday zamu shiga kotu dama zancen ne na suna ya hanani sukuni don naga mutumin da yasai gidan baida mutunci ko kadan wallahi. Yadda naso mu rabu dashi lafiya hakan baiyuyuwa sai anyi rashin mutunci dashi za,a wanye lafiya. Don kamar ma da gaiyya ya,sai gidan don Sagir yace min wai yaji yana fadin zai saka a rushe gidan yayi maikatan shimkafa ne a gurin don idon gari gidan yake. Nace ikon Allah kada Allah ya bashi ikon yin haka a,rayuaan shi da ya barwa mutane abin gori har tarihi. Nace amma yaya yanzu mama Asiya tayi matukar sanyi sosai sai neman shiri takeyi da mutane. Ko dana haihuma tare da ita fa muke kwana a,asibiti har aka sallamay ni. Yace wanan dadin bakin sai tai maku kuda bakusan halinta ba ai kaikayine ya koma kan mashekiya. Don ni suka so na lalace na aikata hakan uwana tashiga balai Allah ya karw ni. Ya mike yana fadin barin fita zuwa wajen wa yancan marasa mutuncin inji yaya zamu kare da su. Nace suwa ke nan fa ? Yace Rahama da kungiyar ta na yan iska mana da tazo min da fitina gida. Nace sai anyi hakkuri suma basu zaci cewa al,amarin zai kai haka ba ai, sunzo ne suyi son ransu suyi muna iskanci su tafi. Sai Allah yafisu suka samu wa yanda suka fisu balai a gidan suka jamay dasu. Wai ki fada min gaskiyan yadda abin ya faru don in san abin fadi a can. Tsaba na mayar mashi da komai yadda akayi akai fadan yace ai bari zanyi maganin su don zan masu kashedin shigo min gida watarana ne wallahi. Nace amaryan naka zakaiwa wanan furucin haka kasan fa itama nan gidan ta ne tana da ikon da zata shigo ko ina take so a gidan. Harara ya watso min yace a,a kila dai kece zata aura bani ba dai kan don ni wallahi har gobe na tsani mutanen nan marasa mutunci. Jiya wata matace ra rufe ido take fada min abindaya faru ne haka naso nagane ta amma ban gane taba. Nace ai matar Atiku mai wanki ne mana matar da kullun take godiya kan taimakon da kaiwa dan ta a baya Aliyu mana. Yace Allah sarki itace wallahi gar gobe ina son in taimaki yaron ya zama wani abu idan ya girma don na wanke mai wanan bakin tabon a rayuwan shi. Allah ya nufa nace mashi yace sai ya dawo nai mashi Allah ys tsare yafice daga gidan. Yana fita ya samu mutane cinjim a kofan gidan shi iyayen yaran da Rahama ta, gaiyyato su rako ta nan suka shiga bashi hakkuri akan ya jaye maganan don yan sanda sunce wai kotu za,a kaisu. Sai ga Baba sani da motar shi ko kashe motar baiyi ba da kyau yafito cike da masifa babban riga yana jan kasa. Yace ashe baka da mutunci haka sadauki ban sani ba kai har ka isa kasaka a kule muna yara su kwana a caji office. Sadauki yai murmushi yace amma Baba kaji irin rashin mutuncin da,suka zo gidana sukayi ko? Kai har ina gidan yake da kakewa mutane wanan wulakancin haka kan shi akan wanan yar matsiyantar matar taka kake son wullakanta muna yara kamar wata mai asalin kwarai can. Baba maganan ya tsaya iya ni daku kada ka hada da yar mutane please ? Ko nima zaka saka a kulleni ne idan na zageta din ? Bai mai magana ba don yasan dalili yake nema kawai ya shiga motar shi ya nufi police station din inda ya samu su Rahama sun ji jiki sosai dan kwana dayan da sukayi a rufe. Nan yasaka akai masu warning akan kada su kara shiga mai gida gaba dayan su idan ba haka ba zai yi karan su again a kulle su kuma. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,, IDAN KIN BIYA KIKA,TURAWA WANDA BAI BIYA BA DAKE DA ALLAH,,, Munyi arbain yaro yayi matukar kyau dashi gashi sai kara murjewa yakeyi yana kara haske da kiba sosai. Ga sadauki yanzu sai ahari,a akan gidan su sukeyi da dan masani wanda yaja sosai a kan zancen. Anyi nasaran kama yaya Ahmed an kulle shi a cewar Baba ma kada a sake shi a rufe shi don matsayin shi daya da barawo a gare shi. Tunda gidan shi ya shigo mai ta dakin shi ta baya ya fasa ya shiga ya kwashe mai duk wani abin kwarai nashi a lokacin. Don haka sata yazo yai mai a gida kuma ya kwashe mai takardu da ga baya yazo ya kwace mai gida. Hankalin mama Asiya yai matukar tashi sosai jin irin hukuncin da baba yace a yankewa yaya Ahamed. Sai gata a gidan mu tunda farar safiya ta sallama muna lokacin na gama shiri na tsab nayi kwalliya Iyya tayi wa Amir wanka takawo shi ya sha nono. Don shan nono kawai ke kawo Amir gurina da ya gama kuma zata goya shi sai idan ya falka ko tana daki su kwanta tare. Haka nake fita na barsu zuwa school don ina semester karshe yanzu ga karatuna. Sallaman mama yasa mu fitowa daga dakina ina rike da yaro a hannu ina bashi nono muka fito falon. Mama Asiya ce zaune saman kujera ta rafka uban tagumi cikin damuwa take. Nace a,a mama sannu da zuwa ashe kece mama shine kika zauna a falo baki shigo ba. Tace Fatima ba zama nazo ba mijinki na zo gani Allah dai yasa yana gida bai fita ba ? Nace yana nan mama tace yi min magana dashi don Allah Fatima kice gurin shi nazo. Na nufi dakin tabini da kallon yadda na koma wata fresh dani sosai kamar ba Bintu ba can. Yana kwance ya kifa ciki yana barci na,shigo dakin na samay shi a hakan . Sai da na zauna bakin gado na dan fara taba shi a hankali ya bude idon shi ya dago kai yana kallo na. Ina zaune ina kallon shi ina gyara yaron a nono nace ina kwana ina dare da fatan an tashi lafiya ? Ya dan goga kan shi a filo ya gyara mirginowa yana kallon mu yace my friend har ja tashi kai wanka ni ina kwance ko ? Nace tuni mukai wanka kaima ka tashi kai wanka sai ka karya sai dai mama tana falo tana jiran ka. Yace mama tare da kallon agogon bangon dakin shi da ido yace wata maman ke nan ke jira na kuma ? Nace mama Asiya ce mana Asiya kuma may kuma ya kawo ta nan gidan ko dama takanzo ne wai ? Nace gaskiya bata taba zuwa haka ba babu wani dalili sai yau kawai tazo ya ja tsaki ya mike zaune da kyau sai da ya shiga bandaki yai brush yafito daga dakin. Ya karbi Amir a hannu na ya fice da shi ina bayan ta jin motsin fitowar mu daga dakin ta dan gyara zama da kyau tana cewa kafitu Sadauki ga mamakin shi sai yaga yau itace ma mai gaisheshi kafin ya gaida ita. Yace lafiya dai mama naganki da sasafe hakan ga ko wani abu kuma ya faru ne a gida. Maimakon mama tayi magana sai kawai ta fashe da kuka mai tsuma rai sosai. Yace haba mama may yafaru ne ban son wanan kukan da kikeyi ni fa dan ki ne mama don Allah may ke faruwa ne please. Mama ta dan tsagaita kukan ta tace sadauki nazo gurin ka ne neman taimako akan dan uwanka da ke a tsare. Don Allah sadauki ka saka baki wa baban ku ya dan sasauta kalamin da yayi akan wai a daure Yaron nan da yace. Yace mama amma dai kin san Ahmed bai kyauta wa Baba bai kuma kyautawa mu yan uwan shi ba. Babu abin kunyan da yafi ace wai dan uwanka yasayar da gidan ku na gado ga kuma mahaifin ku da rai. Tace na sani sadauki yaron nan bai kyauta ba ba ku kadai yaiwa tozarci ba har ma dani mahaifiyar shi tunda ina a cikin gidan yanzu. Tace kaiwa Allah ka taimaka a tsare shi a lalabeshi ina sauran kudin suke aji idan yaso idan zai biya sauran da gabaya ne sai muji yadda za,ayi. Sadauki ya gyara rikon yaron dake a hannun shi yana cewa mama ai antambaye shi babu kudin a hannun shi yanzu yace yayi sayayan kayan part da yake sayarwa saura kuma matar shi ta sai abubuwan bukatan ta. Tace da karfi dama na,sani aidama nasan wanan shegiyar matar tashi yarinyar banza itace ta saka shi a,wanan halin. Sadauki yarinyar nan tun farko na fadawa yaron nan ba matar auren shi bace ita yarinyar da ta san kaduna tasan lagos itace zata zauna zaman aure agidan wani. Ko fa,abinci bata iya yi mashi gashi nan kullun cikin yawon zuwa saye ko yazo gurina yaci sai Alhaji yai mai fada yanzu ya bari. Idan dai tace ga abin da take so duk inda zai shiga ya samo shi sai ya shiga ya samo mata shi ake zaunawa lafiya in ba haka ba ko ba,su da zaman lafiya ita dashi ke nan. Yace kai amma gaskiya bata kyauta ba wanan aiba so bane kamar ba auren soyayya sukayi a tsakanin su. Mama tace soyayyan may can kuma dama aiba son shi takeyi ba karya yai mata shi mai kudi ne kuma dan mai kudi. Kakaga ko akwai karya acikin wanan yanayi koba gaskiya ba . Yace Allah ya kyauta mama tace amin cikin damuwa tare da nisawa takara fadin yanzu don Allah jika kaida Fatima gwanin ban sha,awa da ku ga zuria Allah ya fara baku a tsakanin ku. Kowa yaga yadda zaman ku yake sai yai maku sha,awa sosai don ga yi nayi bari na bari ba irin wancan mai bakin auren tsiya ba da duk ta halakamai rayuwan shi ko. Mama yanzu ki koma gida naji bukatan ki insha Allahu zan san abinda akayi abin yazo da sauki ai Ahmed dan uwana ne najini ba zan so naga ya,wullakanta ba nima. Godiya sosai mama tai mashi har da saka mai albarka da fatan gamawa da duniya lafiya (kudi ke nan) Nan dai ya mike itama ta mike yai mata rakiya har kofan gida ta,shiga motar ta wanda ya fara jin jiki yanzu sosai. Sai da yaga fitan ta daga gidan ya sauke ajiyan zuciya ya tsaya suna gaisawa da su maigadi har suna tambayan lafiyan Amir dake a hannun shi. ****** ********* ****** Mama tana komawa gida dakin maji ta shiga ta samay ta,a zaune tana karyawa ganin ta a,shiri kamar fita zatayi yasa take kallon ta da mamaki. Sai da ta samu guri ta zauna take cewa daga gidan sadauki nake yanzun haka. Gidan saudauki maji ta tambaya tace eh na tafi na samay shi ne kafin ya fita akan zancen yaron nan. Don ya taimaka Alhaji ya jaye zancen daurin da yace sai anyi mashi nasan yayi laifi mai muni amma sai ina ganin daurin da yace aimashi kamar zai iya kara jefa shi a cikin fitina kuma ya kara hinjirewa yafi haka. Don Allah idan sadauki ya shigo ki ka taimako na hjy maijidda kiyi mai magana duk da dai yai min alkawari akan na kwantar da hankalina zai duba al,amarin da idon basira in Allah ya yarda. Maji tace ai tunda kin mashi magana zai duba din da ke dani ai duk daya muke a gare shi don duk uwanshi muke Ahmed kuma ai dan uwan shi ne. Tace amma zan kara mashi magana nima akan magana don ya duba al,amarin. Tace nagode tare da mikewa tana fadin barin tafi na duba yaran nan na barsu basu ko tashi ba na fita daga gidan. Allah ya sauwaka mama tace mata tace Amin tana tsaye take cewa aini godiya na ga Allah shine sadauki yana da abin hannun shi da zai iya taimakawa dashi. Hakane inji maji tace da yanzu ai duk munsan inda muka nufa tunda mai gida yace yana bukatan gidan shi da,wuri haka. Sai da ya gama abinda yake ya shirya ya fita daga gidan ya nufi gidan su ganin iyayyen shi. Ya samu mama a dakin ta suka gaisa nan take cewa dashi sai ga hjy Asiya kun gani da sassafe haka yace eh tazo dazun itace ma ta tayar dani daga barci ai yau din nan. Nan yake fada mata yadda suka kwashe da mama din tace tunda taje har ta ganka sai kasan yadda zakayi da shi yanzu. Kayi kokari ka taushi mahaifin ku yayi hakkuri akan maganan da yayi yace ai babu damuwa maji. Ya nufi gurin mahaifin su don ya gaidashi ya samay shi zaune a keken dake taimaka mashi ga tafiya wanda shi sadaukin ne ya kashe kudi masu yawa ya saye shi don baba din ga shawaran da likita ya bashi a can. A mutunce ya durkusa ya gaida baba din sanan ya tambayi lafiyan jikin shi ? Baba yace Alhamdullahi can baban yace yaya zancen kotun naku yakaya ne cikin maganan shi da ba fita yake sosai ba. Kan shi ya dago yace Baba ai mun yi magana ta fahinta da mutumin yace a jaye karan idan har zan biyashi kudin shi na,kara mai riba a sama. Baza,a kara mai ba inji baba aiko shi mai laifi ne don ba gaskiya bane yasan ina a raye ya sai mingida ga hannun dana. Sadauki yace hakane baba ai yanzu shi lauyan tanan ya bullo mai shine yasa hankalin shi ai ya tashi sosai. Don da da farko yana ganin zaici riba ga maganan amma yanzu jikin shi ya fara sanyi kan case din. Ance halinshi ke nan ko mutuwa akayi sai ya kwace gidan marayu ya,saye a araha ya cuce su. Baba yace shine ni bai jira na mutu ba yazo cin nawa ko? Kayi hakkuri baba kaddarane duk haka ba kyau ma gana tuna aanan zancen a zuciyar ka don kara tayar ma da hankali kawai maganan zaiyi. Insha Allahu gidan ka har yanzu yana a matsayin naka illa iyaka mubashi kudin shi daya,bashi Ahmed din shike nan a zauna lafiya. Shiko Ahmed din ku kulle dan banza can yayi iya rayuwan shi a gidan yari don banga amfanin haihuwan shi ba ni. Hakkuri dai za,ayi baba ai yanzu shima a cikin tashin hankali yake ko yaushe. Wanan yarinyar da ya,aurace ke kaishi ga halaka akace don ba yarinyar kirki bace wallahi. Bashi ya aurota ba inji baba sadauki yai dariya yace baba kaine fa ka,yarde mai bayan mama ta hana abin . Shiru baba yayi yana daya sani a,ranshi don yai nadaman zaman Ahmed da,wanan yarinyar mara mutunci da ita. Yana fita gurin baba bayan sun gama magana dashi kotu suka nufa shi da yaya bashar sun samu danmasani ya ce idan zai samu kudin shi ya janye maganan shi. Ba bata lokaci sadauki ya saka hannu akan zai ba mutumin kudin shi miliyan bakwai da Ahmed ya karba a hannun shi. Nan aka zauna ranan ya biya kudin a ka rufe case din tare da sako yaya Ahmed yakai shi har gidan shi gurin matar shi ya nufo gida don lokacin har duhu yafara yi ko. Bai shigo gida ba sai da aka sallamay sallah yashigo gida agajiye dashi. A sanyaye ya samay mu a falo muna hira Amir yana hannun Sa,ade tana mashi wasa. Sannu muke mashi yana karbawa da kyat ya fada saman kujeran dake kusa da wanda nake zaune. Na kalle shi yadda na ganshi a wahale dashi nace ko zakai wanka ne ka ji dadin jikin ka ? Yace shine daidai tun safe muna koto ana zirgazirga kan zance yanzun dai mun samu ankashe case din mun karbi takardun mu ko. Nace masha Allahu yau baba idan yaga takardan shi a hannun shi kila hankalinshi zai kara kwantawa hakanan. Ya lumshe idanuwan shi yace ban tafi na,kai mai ba,sai da,safe idan Allah yakaimu. Nace Allah ya kaimu na mike na nufi dakin shi na hada mai ruwan wanka a can kafin ya taso yayi. Sai washe gari ne ya shirya tafi gurin baba ya kai mai takardan gidan nashi da,aka anso gurin mutumin da ya sai gidan hannun Ahmed din. Sai da baba ya tara kowa diyan shi da matan shi da,aka kirasu a,waya yake cewa dama akan zance gidan nan ne gashi yau Allah yayi Sadauki ya karbo gidan a hannin azzalumai macuta. Don haka daga yau ina son ku sani gidan nan ba gida na bane gidan sadauki ne da uwarshi don haka ko bana raye kowa ya rike wanan zancen a ran shi. Duk suka dago kai suna kallon baba da mamaki don jin abinda yace wai gida na sadauki ne da uwar shi yanzu. Sadauki ya tare baba da cewa haba baba gidan nan na kowa ne baba tunda gida nakane har yanzu ni bawai na karbo bane don ya zama nawa ba. Baba ya daga mai hannun shi da kyat yana cewa wanan magana danayi ba fashi a cikin shi sadauki gida nakane yanzun ba nawa ba. Idan kuma kana,son ganin bacin raina ne a yanzu sai ka matsa da magana mu gani. Dole yaja bakin shi yai shiru yana gudun yai magana wani matsala ya faru da baba. Baba yace Ahmed dai yanzun sai kuyi kuka dashi da uwar shi don shine yaja ma kowa wanan bani ba. Don ni Allah ta gani nayi yadda ya dace nai maku muhalli wanda ko bayan raina iyayyen ku daku zaku iya zama a ciki am.a ya,sa kafa ya take tausayin kowa dani daku yasayar wa banza irin shi macuci. Don haka yanzu na fada maku gida yana a zaman sadauki ne bani Abubakar ba kuma. Sai kowa ya,watse na gama magana na ke nan ya juya inda mummy take zaune tai tagumi sai sauraren shi ta yake yace ke turani ki maidani dakina nagama maganan da zan yi kenan. Mummy ta mike duk jiki ba kwari ta fara turashi zuwa uwar dakin shi cikin rashin kuzari. Nan ya barsu a,zaune kowa jikin shi ya mutu ana shigewa dashi Nafisa ta fara mikewa tana fadin yau dai shi ke nan tafaru ta kare kurun kus kan kutsu sai kowa ya fara neman madafa. Maganan ta yai matukar ba kowa haushi uwarta ta kalle ta tace ke kan anyi sakariyar yarinya wallahi nan. Ke kan baki san ciwon kanki ba ko kadan yau wanan abin tashin hankalin da may yai kama harda kike fadin wai takare. Takare mawa ke nan kike nufi yanzu mu ko ku da baku da madafa kamar kowa. Ai mu muna da gidan iyayye sai mu koma can mu zauna ku kuwa ina zaku kuda baku da gidan uba. Mu dai wallahi ancuce mu anzalunce mu sai dai muce Allah ya isar muna kawai ancuci na kauye. Saboda hainci da zalunci dan gidan ma da za,a tsira dashi akama a sayar wa mutane su rasa matsuguni sai rabe rabe. Sadauki ya mike tsab ya fara fita daga dakin bayan fitan Nafisa yabi bayan ta. Sai mama da Amira da maryam suka mike suma suka fice daga dakin ran su a bace. Lokacin Umma ke fadin muna fukai kawai kun kai ga yadda kuke so ai dama gurin ku su ke nan duk su mamaye gidan to gashi Allah ya cika maku ai gida ya zama naku. Sagir dake zaune kasa saman carpet yace haba haba Umma yanzu may yw laifin yaya sadauki a gidan nan. Mai laifi daban wanda bai da laifi ya taimake mu ya raba mu da gararanba a saman titi kuma za,aga laifin shi a banza. Gaskiya wanan ba adalci bane kuyi wa kanku nasiha ku san may ke a gaban mu ba,wai mu zauna kuma muna cusa kiyayyan junan mu ba a haka. Ya mike yafita daga falon shima,ranshi a bace ya,saka takalman shi ya bar falon. Nan dai sukai ta watsewa daya bayan daya a falon kowa jikin shi ya mutu don basu taba zaton wanan hukuncin baba zai iya yankewa akan su ba. ****** ********* ****** Da,sannu yau Allah yayi mun gama exam din final din mu gaba daya sai dai fatan alherin Allah ya ba da sa,a kawai wa kowa daya zana exam din shi a matsayi finalist. Muna gamawa da sati biyu muka daga zuwa waje da yaya sadauki inda ni kaina ban san tsawon lokacin da zamu dauka a can ba indan mun tafi. Mun fara zuwa kasar hongkong, inda muka share kusan wata daya a kasan muna hutawa kawai. Dani dashi sai dan mu Amir da yanzu yayi wayo sosai zakace watan nin shi ya zarta ya kai shekara ma. Sosai nake jin dadin yadda muke rayuwa a wanan kasan a tsakanin mu ukun nan inda sone da kauna tsantsanta ake gwadawa junan mu. Don kowan mu yana son dan uwa mun shaku da juna fiye da tsanmani komai a tare mukeyin shi. Zai kwashe yai ta yawo da mu muna ganin gurare tare da yin photuna masu kyau. Mun bar kasan zuwa kasar Beselona inda zasu buga kwallo da,aka dauke shi wani contarack mai tsada da kudi masu yawa. Ina zaune ina kallon shi yana shirin abubuwan da yake bukata da zamu tafi dasu a gurin wasan Can ya dago kai ya kalle ni ya sake min laulausar murmushi ya ce kina kallon yadda mijin ki ke fita,gurin neman kudi halaliyar mu ko ? Tsab ya,shirya cikin wasu kananan kaya sai ga wani abokin shi Daniel yazo dashi zamu tafi na,dauki dan jakkan da na saka kayan mu a ciki muka kama hanya sai gurin da za ai wasan ball din. Muna isa ranan naga inda,akasan muhinmancin wasan kwallon kafa don naga taron dan mutum da ban taba gani ba a duniya. Wata baturiya ta karbi Amir a hannu na da sauri tace nima na biyo ta nan muka shiga wani daki ta miko min riga mai tambarin yan wasan inda shima Amir din ta saka mai rigan yan kwallo na yara mai tasu tambarin. Hijjab ne a jikina irin dan karamin nan ta karba taje ta sa aka buga mai tambarin su nasaka rigan saman dogon rigan dake a jikina tare da hijjab din na take na saje da duk wanda yake a gurin. Suka miko min wani dan abin wasa kamar hure wai na rika nikan na samu abin yiwa Amir wasa dashi. Muna fitowa a wani guri da,sai wanda aka yarda dashi zai shiga gurin nan naga yan wasan kwallon duniya birjit dasu suna ta mota jikin su kafin a,shiga filin. Can na hango sadauki rana,na,farko dana fara ganin shi saye da kayan su na yan kwallo yana ganina ya bar abinda yakeyi yanufo ni yana murmushi. Nan sauran abokan shi ke tambayan shi wai matar shi ne da dan shi yadda ya rugumay mune ya tabbatar masu da amsan da suke son ji daga bakin shi. Don hada kaina da nashi dana,Amir yayi guri daya a hankali yake fadin kiyi min addua Fatima Allah ya bamu sa,an wanan wasan da za,a buga a yau. Nace yaya Allah ya tabbatar da alheri yasa a,dace da abinda akazo nema ta hanyan alheri. Yace amin nan yan jarida da sauran median suka shiga daukan mu hotuna kalakala. Kyau, kudi, ilimi yanzu duk Allah ya bani don haka gwargwado zan iya gogaiya a cikin wa yan nan mutane. Muna sahun gaba cikin officials muka fara fitowa bayan yace wa matar nan ta kula damu amana please. Muna futowa guri ya kaure da wani irin ihu wanda yasa na daga kai na kalli fadin gurin sai da gabana ya fadi sosai naga gurin yana juya min. Kujeru aka bamu muka zauna bamufi minti biyar da zama ba suka fito a jere dasu ana taken team din su. Sai flowers ake watso masu ta ko ina can na hango wasu da irin furen da aka bani a hannkali nakewa dana wasa dashi yana dariya. Sai daukan mu hutuna akeyi tako ina nan bayan sunyi taken kasan tasu aka fara shirin fara wasa. Wasa yakai wasa guri ya rude sosai mutane sai faman ihu suke inda sai ranan nan nasan muhinmancin kwallon kafa da kyau. Tun ina kallo ban damu ba,sai gashi da,wasa yai wasa da kaina nake daga Amir ina nuna mai wasan . Wanda idan mutum.ya gani zai dauka cewa wani wasan jin dadi nake mai a lokacin. Har aka tafi half time suka dan huta suna dawowa wasa ya tashi sosa kafin atashi wasan sai da sadauki da wani farin fata suka ci cibiyu babu ko daya . Haba aiko guri kaure da ihin murna nan muka kutsa muka shiga filin akai ta muna hutuna tare dasu suna ta daukan Amir kowa da kalan maganan da yake idan ya dauke shi akai masu photo suna kiran shi little UF. Washegari Naga karamawa ranan sai shaye shaye da lashe lashe da tsotson juna akeyi. Abinda yaban mamaki shine ina zaune na dawo a gajiye wayana ya nuna min sako yashigo. Ina dubawa yaya sagir ne ya turo min da photuna da akai muna a gurin kala kala wasu ma ban san anyi suba ni. Yana tayani murna na mayar mashi da amsa dana gode yayana kawai. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , , , IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH, , , , A hankali na sako kafana waje wanda don samun daula yai wani lub lub dashi fari fatte gwanin ban sha, awa. Yan uwane da abokan arziki birijit a gidan ba masaka tsinke a ko ina na gidan sai motoci xa suka haraban gidan da wajen gidan. A hankali ya zagayo inda nake a tsaye ban yi aune ba sai ganin yan jonarlist nayi a gaba da kayan aikin su. Nan suka fara jero min tambaya ina rike ga hannun sadauki daya makale ni. Sun fara da tambayana suna na da alkata dashi na fara da sallama irin ta addinin musulunci wanda ni ban san ma wai hausa ya canza salo ba inji mutanen dake gurin. Nace sunana Fatima Abdullahi mata a gidan Umar faruq da ake kira da UF dan wasan kwallon kafa na international. Sukace hajiya wani irin farin ciki zaki nunawa mutane a wanan tafiyan da duniya ke ganin kunyi da maigidanki mai tarin nasarori a cikin sa. Nace to Alhamdullahi don gaskiya bazan iya nuna farin ciki da dadin da naji ba a cikin wanan yanayi da muka samu kan mu a cikin sa ba. Sai dai kawai nace nagodewa Allah ubangiji da yakai mijina a cikin wanan matsayin tare da kara godewa Iyayyen maigidan nawa wanda da taimakon adduan da iyayye ke muna muka kai ga wanan matsayin da muke ciki a yau. Nace ina matukar alfahari da godewa Allah da kasancewa mijina a cikin wanan matsayin da ubangiji ya nufe shi da zama a yau. Ina ma kowa fatan alheri a rayuwan shi da fatan kara samun nasara ga duk wani abin alheri da wani ke bukatan yi a rayuwan shi. Mutanen da suka zo taron mu kuma ina mika godiya na a gare su akan lokacin su da suka bayar gurin nuna muna farincikin su a gare mu Allah ya mayar da kowa gidan shi lafiya. Nan suka juya zuwa gare shi suna tambayan shi nashi farin cikin da zai nuna shima. Mai interview din yace Umar faruq Abubakar kayi namijin kokari sosai gurin haska muna kasan mu ga idanuwan duniya a matsatin ka na babban da wasan duniya da ake ji dashi a wanan lokaci tare da kuma jawo wa kasan mu nasarori gurin harkan ci gaban ta. Wanda a yanzu babu abin da zamu ce sai mu maka godiya don wanan halakar nasarorin da kajawo wa kasa zata kawo ragewan zauna gari banza ga matasan da suka gama karatu babu aikin yi a tare dasu. Yace insha Allahu haka nake fata don wanan kamfanonin da za, a bude zai bukaci ma, aikata kimani dubu ashirin da biyar a ko ina na sassan kasan nan maza da mata indan har mutum yana da takardun da muke bukata a gare shi. Dama wanda baiyi zurfin ilimi ba za, a samu daidai dashi asaka shi a inda ya dace. Mai tambayan yace masha Allahu mujin dadin jin wanan dibin nasaran da kasan mu ta samu ta dalilin ka wanda muke fatan samun haka ga sauran matasan kasan nan masu kishin zuci kamar ka nan gaba. Sai dai baza mu barka haka ba ko zaka iya fadawa duniya da masu sauraren mu ko shekaran ka nawa a yanzu. Sai da yai dan murmushi tare dan jawoni a jikin shi kadan yace yanzu shekarana talatin da daya cif insha Allahu. Yace yayan ka nawa matan ka nawa ? Yai dariya tukun yace matata daya gata nan a kusa dani kana ganin ta sai yaro na daya Amir wanda yaci sunan mahaifina watau Abubakar. Yace itace matarka ta farko ko akwai wata a gaban ta? Yayi murmushi yace itace mata ta tafarko kuma ta karshe . Don yar uwata ce aure mukayi na zumunci da ita wanda ta zama muna aure na soyayya daga baya. Hakan yasa mutanen dake tsaye suna kallon interview din wasu suka numfasa daga gefe don jin abinda yace . Mai tambayan yace daga karshe wani irin godiya zaka mika ga mutanen da suka taru a nan saboda kai. Ya dan murmushi tare da daga kanshi ya kalli inda mutane suka taru don shi yace ni Umar banda abinda zance wa tan uwa da abokan arzikin da suka taru a nan don ni kawai da iyalina. Sai dai nace inawa kowa fatan alheri a rayuwan shi kamar yadda suma suka taru anan don ni da iyalina. Ina ma kowa fatan alheri shima mutumin yace na gode da lokacin ka da ka bamu shima yace ya gode. Nan suka jaye kayan aikin su suka bamu guri inda muka shiga gaisawa da mutane dake jiran mu a haraban. Can na hango anty Amira da wani dogon mutum a tsaye daga gefe daya na zare hannuna daga rikon da sadauki yai min na nufi gurin ta. Da dan sauri na na rugumota a jikina itama dai ba laifi ta riko ni din tana dan murmushin yake a fuskan ta. Nace anty nayi missing din ku mun samay ku lafiya tace mun dai yi missing din dan uwan mu kawai Bintu. Nasan magana ta fada min don tana fadan haka bata tsaya ba ta wuce zuwa gurin sadauki mutumin yabi bayan ta tabar ni a tsaye nan. Naji an dafa kafada na ina juyawa anty maryamce tace kada ki damu don ko kin saba da halinta yanzu ai. Shigowan su Nafisa ya katse muna zancen mu nan suka rugumoni da farin ciki suna fadin kai matar yaya kin bamu kewa wallahi sosai. Barin Nafisa da mutumin da take tare dashi wanda ta gabatar mai a matsayin wanda zata aura wai. Yayi ya nufo inda nake tare dasu nafisa nan suma suka shiga gaidashi tare da mashi sannu da zuwa suna mai taya shi murna samun karuwan da yayi. Hannuna ya kama zuwa kofan shiga gidan namu wanda yake a rufe a lokacin don za, abude shi da addua don shiga ciki. Malaman da aka gaiyato ne suka bude gidan da addua tare da fatan gamawa da duniya lafiya. Mun shiga gidan da farinciki gaba daya mutane sai yaba kyau da tsarin gidan suke yi. Abincin da aka girka don taron mu aka shiga ci kowa sai da ya wadata yaci ya koshi zuwa yamma mutane suka dinga watsewa daya bayan daya kowa a cikin farin ciki. Ganin an dan rage yawa sai yan gida tsiraru suka rage ba yawa yasa na juya gurin anty maryam nace zan dan shiga ciki anty . Tare da ita muka shiga dakin da yake a matsayin mallakina wanda yasha kayan alatu sosai na zamani don komai daga waje aka shigo dashi a gidan. Yana zaune tare da Amira da Bashar dasu yaya sagir da yaya Abdul suna hira. Muna mikewa ya bini da wani irin kallo na so da kauna yana cewa maryam ki barta ta huta please koma may ye ai zata labarts maki idan kun natsu. Don nasan bakunan nan naku tab yake da gulman da kowan ku ya tara ya tsiyayawa dan uwa. Nace kai haba dai yaya kana iya raba anta da jini ni da anty maryam sai Allah fa. Yace ai na gani na kuma sani don gashi ta haki zaki barni a nan ni kadai. Kai kade kuma yaya inji Amira yace kin san na saba da matata yanzu bamu raba second a tare. Amma wanan da kike gani naga yau tana son nisanta ta dani idan ban yi niya ba. Amira ta kawar da kai gefe daya don ta fahinci i yanzu ba karamin ji dani yaya sadauki yake yi ba har bai iya boye feeling din shi a gaban kowa. Ga wani irin kyau da haske dana kara tare dani ga wani annuri da take gani yana fita tare dani. Lalai kam Bintu tayi sa, a da dace a rayuwan ta na jajircewa da tayi ta mallaki zuciyan sadauki da ma ruhin shi a baki daya. Lalaikam shima din yayi dace samun Bintu a matsayin matar aure a gare shi don mace mai kyau da addini rahama ce ga namijin daya samay ta. Kalli yadda ta koma yana wani ji da ita da dan shi wanda ko dan kukan yaron bai son ji komai nasu gwanin burgewa. Gaskiya yayi sa, an samun mace mai kyau a rayuwan shi da Rahama ce ai bazai wani jin dadin nunata haka ba a duniya. Ba Amira ba kowa ya kalle mu zancen zuci yake a kan mu don ko mun dace da junan mu sosai. Don sadauki za, ace mutum ne mai sa, a a rayuwan shi ga dukiya mai tarin yawa Allah ya daukaka shi dashi. Ga mace ya samu mai kyau da tarin addini tare da ita ta gyara mai rayuwan shi don duk wanda ya ganshi yasan ya watsar da halaiyar shi ta da can baya. Hassada dangin shedan tuni Amira ta mike tana fadin ita zata tafi gida sai anjima kuma. Sadauki yace haba Amira tun yanzu ki tsaya mana har ayi sallah sai ki tafi gida tunda ba koranki ake ba? Tace no bari kawai na tafi don naga kamar kana son hutawa ne da iyalin ka tafice tana cika tana batsewa a ranta. Ya gurgiza kan shi yabita da kallo don yasan abinda take nufi akan Fatiman shi ne take wanan cikar haka tana batsewa ita kadai. Sun dan jima suna hira akai kiran sallah suka mike zuwa sallah nikan muna dakina mun baje da maryam muna hiran yaushe rabo da ita. ****** ********* ****** Bamu samu jan mu ba sai bayan karfe tara kowa ya watse yarage daga mu sai iyya a gidan da take ta faman gyaran guri. Ya fito daga dakin shi a cikin jallabiya baka mai gajeren hanni yace haba iyya wanan aikin yai maki yawa fa gaskiya. Nace a nemo muna wasu masu taimaka wa agidan mutum biyu aikin ki kawai ke yanzu shine kula da Matar gidan da yara ba ruwan ki da wanan aikin kuma haka. Tace haba Alhajina har ina aikin yake a nan ai ba sai an nemo wasu ba zan iya ko ni kadai. Yace a, a iya na gama magana ko gobe ne insha Allahu masu aikin zasu fara zuwa sai ki gwada masu komai daya dace suyi. A lokacin na fito ina saye da wani dogon riga dinkin shi simple ne irin na zama gida mai launin jikin kura, kaina da hula dana daure gashina a cikin sa. Nan nake cewa , a, a iyya baki huta ba hakana har yanzu don Allah ki huta kibar aikin nan haka har da samay ga Amir kuma goye a bayan ta tare dashi take aikin. Tace wai na dan rage kayan nan kafin safe kada gurin ya kwana haka da kazanta. Badai tsabta ba kan Iyya don mace da bata haihuwa dama ance tsabta gare ta sosai haka ne ya kasance ga iyya din don yar ta daya a duniya. Kima tayi aure sai dai ba wani dadi a gidan auren don wahala take sosai sunan ta suwaiba. Yatana da yara uku ga mijin bai wani aiki sai dan buga bugan da yakeyi kawai iyya tasha min magana akan wanan zaman na Suwaiba haka nan. Haka yasa na sa a raina zan wa yaya magana akan wanan matsalan don ya kamata a taimaka ma rayuwan su don Iyya gaskiya ba laifi mace ce mai rikon gaskiya da amana. Fruit muka zauna muka dan sha muna hira yaso fita da daren zuwa gida don yaga iyayyen shi sai dai yana tare da gajiya. Waya naji sunyi yana ba baba hakkuri sai da safe zai shigo ya duba su insha Allahu. Bamu jima ba muka shige ciki muka kwanta iyya ta bukaci na bar Amir a gurin ta wanda naji dadin hakan. Don ko banza an kunsa yaye shi ma a lokacin don haka yana bukatan dan jayewa daga gare mu. Don ya manta da nono da sauri a cikin sauki batare da ya wahala ko ni na wahala ba. Washegari ma masu zuwa muna sannu da zuwa sun kara cika muna gida ba wani hutu sosaia lokacin don jama, a kada su ce ina masu fadin rai Kowa haba haba nake da zuwan shi don duk abu daya ne ya kawo su da mai kudi da tallaka sunzo ne don nuna farin cikin su gare mu. Na fahinci mutane mu suna a cikin wani hali na haula, i don wahalan da ya ishi mutane haka yasa duk wanda yazo naga yana da dan rauni nake taimaka mai wasu zan basu sabulai da kudi wasu kuma sun fi karfin karban kudi a gurina sai dai na basu tsaraban abinda ya dace dasu wanda ankawo min abubuwan da zan rabawa mutane dake shigowa taron mu. Sai bayan kwana biyu da dawowan mune na fahinci an canza muna ma, aikatan mu dana saba dasu abaya. Ma, ana anbarsu a tsohon gidan mu da muka taso haka yasa banji dadi ba nai magana da yaya yace zai duba al, amarin. Da yamma kuwa sai ga Atiku da iyalin shi sun zo taron mu na tare su da farin ciki nake tambayan su yaran su sukace suna lafiya. Tare ma suke da maigidan su yana waje nace a, a shine zai tsaya a waje ku shigo dashi mu gaisa mana. Amaryan shi ta fita ta shigo dashi nan muka gaisa nake tambayan shi mai yasa bai dawo nan inda muka dawo ba. Yace hajiya ance nan kayan aikin ku duk yanzu na naura ne bazan iya aiki dashi ba nace haba haba basai a koya maka ba. Gaskiya daga gobe gaba dayan ku har su baba musa duk a nan zaku dawo da aikin ku sabbin a kai su wancan gidan. Nan ya shiga min godiya nake tambayan shi Aliyu fa suke ce min yana nan gida kudin makaranta yai tsaye tunda maigida baya nan. Banji dadin jin haka ba nace gobe yazo da yaron za, a san abinda za, ayi akai insha Allahu. Nakawo tsaraba da kudi na basu shi kuma mijin na bashi kudi ga sayi shinkafa dashi. Nan ya dukar da kai sai hawaye ya fara zubo mai yana cewa hajiya ban san irin godiyan da zan maki ba keda maigidan ki akan irin taimakon da kuke muna a rayuwan mu ba. Ga yaron nan Aliyu maigidan ki ya taimake mu a baya an mashi aiki ance da ba, ai aikin ba haka zai koma dan luwadi shima don abin zai ta damun shi idan bai yi ba. Yanzun ko kinga zancen ya koma tarihi a sanadinku ke da maigidan ki da kuka taimakawa rayuwan mu. Nace haba malam atiku babu komai ai duk yiwa kaine may ye amfanin kana tare da mutum baka taimaka mashi ba. Munyi sallama dasu zasu tafi sai ga maigidan ya dawo nan suka tsaya suna gaisawa dashi. Yace malam Atiku hajiya tace sai a dawo daku gidan nan ko nai magana da Bashar yace duk zaku dawo nan da aiki daga gobe insha Allahu. Nan ya shiga godiya nace ai na manta maman Aliyu don Allah ina son kuyi min wani taimako keda abokiyar zaman ki. Sai gaba daya hankalin kowa ya dawo a kaina nace ina son don Allah duk safe a dinga dama muna koko da kosai ana kaiwa makaran tan dake da almajirai sadaka da yamma kuma ina son duk ranan jumma, a a dinga dafa shimkafa da wake buhu daya ana kaiwa sadaka a wanan makarantan. Don haka sai kuyi min lissafin abinda kuke bukata daga kayan aiki da kulan da za, a dinga zubawa sai naji na aiko maku da kudin. Kara zubewa sukayi a gurin suna min godiya cikin jin dadin wanan ci gaban da suka samu na rayuwa. Tunda dama manejin rayuwa ne sukeyi ba wani sana, an da sukeyi yanzu zaune kawai suke a gida dan abinda mijin su ya samo ake amfani dashi. Munyi sallama dasu akan zanji sako daga gurin maigidan su idan ya zo gobe aiki. Suna fita sadauki ya juyo inda nake zaune yana sauke ajiyan zuciya yace wanan sabon hikimar kuma ta maynene queen ? Nace godiya da neman kariya ga ubangijin mu yaya na kasan duk wanda Allah yai ma baiwa ya kamata ya gode masa. Sai nake ganin yaran almajirai masu bara a titi zamu taimaka da dan abinda zasu ci suji dadi a ransu muma muji daga ni, imar su. Yace haka yana da kyau sai kuma may kike gani ya dace ayi don kudin kwallon da na samu wanan karon ina son inyi amfani dashine a sadakatuljari,a Nace akwai magidanta mabukata yaya da abinda zasu ci da iyalinsu yake masu wuya akwai kuma marayuwa da ke neman taimako don Allah ya kamata ayi awani abu akai yace insha Allahu angama queen. Na kuma gode da wanan shawaran taki zan duba nasan abinda za, ayi na taimako ga alumma daya dace ayi. Sai da mukai kwana uku na shirya na tafi gaida su mama don lokacin mutane sun dan tsagaita shigowa muna sosai gaida mu. Wanda wasu gulma ne kawai ke kawo su gidan don suga yadda gidan namu yake ne. Shiga nayi na alfarma dagani har Amir da Iyya muka tafi gidan namu sadauki ne ya jamu a mota. Mun samu su lafiya sai dai gaskiya duk akwai sauyin canji a tare dasu mama ce kawai zaka kalla kasan bata da wani matsala a tare da ita. Amma sauran gaba daya duk sun wani jemay kamar basu ba Umma duk kiban nan nata yanzu ya tafi tsufa ya taso mata sosai tare da ita. Ga furfuran dole daya bata masu kansu ita da mama Asiya yanzu kana ganin su kasan suna cikin wani bakon yanayin da basu saba ba a baya. Mama tai matukar farin ciki sosai da ganin mu ta shiga haba haba damu a gidan. Kaunata dake gurin ta ta murje tayi kyau da ita sosai harda tsayi naga ta kara min da haske ga sabon da naga sunyi da mama sosai yanzu. Itako yar bakin rai na kusa awa daya a dakin bata fito ba tana can tana ji da kanta a daki don suna da wata yar dattijuwan da ke masu komai a shiyan su basu ko kauda kara sai matar ce mai aiki. Can tafito tana wani cika tana batsewa nace a, a anty Amira ai na zata kin fitane ban san kina ciki ba wallahi. Ta zauna tana cewa ina ciki na kwanta ne ina jin shigowan ku bandai fito bane kawai. Nace Allah sarki mun samay ku lafiya tace Alhamdullahi a takaice inda Amir yake zaune yana wasa ta kalla tace my boy kaine wai kazama wani bulele haka dakai? Nace anty aiko yama ramay sosai don tun shekaran jiya da muka dawo bai faye lafiya ba baya son cin abinci sosai sai anyi da kyat yake dan shan tea. Ai dolr kuyi kiba kuna cin gashin kanku kun manta da kowa kina kokarin raba muna dan uwa damu. Nace kai haba anty ni na ma isa na rabaki da yayan ki kin dai fada ne kawai ra,ayinki. Amma ai tsakanin ki da yaya sai Allah tace lalaikan gani nan bari nan takalmin kaza. Murmushi yayi daga inda yake zaune kusa da mama yace wai ke yaya zance da mukayi ne na ma,aikacin bakin da kikace min kin samu. Ta wani lumshe ido tare da bin lafiyan kujeran da take zaune akai tace yana nan yaya. Naga baka da lokaci ne ai sai na matan ka yanzu shi yasa ban fito ma da zancen ba ranan da kazo. Yace kin san Fatima yanzun queen ce lalaba abata nakeyi a hankali don banson ganin bacin ranta akan komai. Haka kuma duk wanda yai niyar bata mata rai wallahi sai inda karfina ya kare akan mai shi don bazan dauki rozarci akan iyalina ba ko kadan. Tasan da ita yake wa warning don haka taja bakin ta tai shiru tana sauraren shi har ya kare zancen shi. Yace mata ki fadawa mutumin yazo mu gana gobe da dare karfe takwas don kafin aiki ya taso min idan son samu ne ma har aurwn nake son ayi akafin lokacin. Sai ya mike tsaye yana fadin shi zai fita nace don Allah yaya rogo nake so da zogala na dade ina son cin sa tun muna turai nake kwadan shi wallahi. Na juya gurin mama ina cewa mama akwai man shanu ai ko ? Tace akwai shi fatima yace yau kuma abinda kuke son ci ke nan kuma kayan yan kauye. Abinda aka samu a turai ina shi ina kwadayin abincin yan kauye kuma maimakon yai kwadayin kayan sanyi. Mama tai murmushi don sai yanzu ta fahinci wanan mugun kyau din da nayi bana banza bane ashe dama tai hasashen hakan amma sai taga ai Amir ko shekara daya bai kaiba watan shi ma na takwas ke nan da haihuwa. Ko iya sai lokacin tagane ciki gare ni tace kai masha Allahu uwar dakina Allah ya raba ku lafiya yasa wanan karon ba dan zama asibiti bane kuma aka samu kamar maigidana cewa Amir. Au ita yanzu cikine kuma da ita ina ruwan naga banza wai kina nufin kiyi saurin cika gida da diyan ki kafin wata ta shigo ko may? Banza kuma Amira wai ke wata irin shashan yarinya ce mara wayo haka dake ? Abin arziki ya samu maimakon kiyi farin ciki da karuwan da aka samu amma mugun halinki yakaiki ga hasashen banza kuma. Kai maji nidai ba dama nai magana akan Bintu sai an zageni don tabi ta hada mutane da ku baku ganin kowa sai ita haba maji. Nace nima anty wallahi ban so cikin nan yanzi ba Allah dai ne ya kawo shi don ban manta da wuyan da nasha ba gana wanan din. Amma to yaya zanyi Allah ya riga da ya kawo shi basai na yi hakkuri ba da ikon Allah. Amira kada fa naji kinzo kina karamin murya naba yara suzo maki weekend na hanaki kice zakiyi fushi ya fada mata hakana. Komai Amira tai mai yana kokarin shanyewa ne don ya fahinci ita haka Allah yayita da bakar magana. Shi kadai ne kawai nasu ke zuwa masu daya koshi don baya biye mata ne kwai suke zaunawa lafiya amma ita haka take da kowa ba dadi nata kalar rayuwan ke nan kuma ita. Shi dai ya fita da yaji fadan mama ya tsanan ta akan Amira din yana cewa haba mama kiyi hakkuri da yar sister na ta dai kusa wucewa tabar maki dakin ki itama ta huta hakana kamar kowa. Bai dade da fita ba sai ga yaro da rogo cike da zogala nan na zauna da kaina na shiga gyarawa hankali kwance kowa sai da yaci banda Amira da take ta faman fushi ita kadai. Mukan sai faman hira muke da mama da su iyya da yar aikin mama din don mama bata dauke ta wata yar aiki ba can. Ina basu labarin abubuwan mamaki da na gano a tafiyan mu da irin daulan da na gani a gidan Abu sifiyanu mai kudin duniya. Duk sun natsu ina ta basu labarin irin daukakan da yaya sadauki ya samu a duniya ta wasan kwallo. Tsukin Amira mukaji ta mike fuuu ta shige ciki cikin bacin rai dama kuma don ta kule ne nake kara bada labarin tunda na gane ita yar hassada ce a rayuwan ta. Don maganan da tayi kan cikin dake jikina ya bata min rai dakewa kawai nayi kada mama ta fahince ni ta kara mata fada. Baba ya aiko yana kirana nan na mike na saka gyale na nufi dakin shi nan na samay su zaune da mummy kusa dashi. Na shiga da sallama na tare da gaishe shi yake cewa yanzu kubura take fada min cewa kun shigo ina barci nace takiraki mu gaisa. Nace eh baba ance ka samu barci shine nace a barka tunda anan zamu wuni mun samay ku lafiya ko ? Yaya karfin jikin naka kuma yace Alhamdullahi Fatima ai iyayyen ki gasu nan suna bani kulawa sosai wallahi. Kinga ita wanan ma yanzu ta aje aikin ta don lalura na itace take min komai ita da hauwau. Jiki kan naji sauki sai dai tafiyan da ban iya yi ne kawai har yanzu matsala koshi likita yace insha Allahu da sannu zan dan iya fara takawa. Nace Allah ya nufa baba ya amsa da Ameen Fatima yaya maigidan naki kuna dai lafiya ko? Nace lafiya muke baba ai tare ma muka shigo dashi ya tafi ys dawo ne yabar mu anan. Fatima Allah yai maku albarka a rayuwan ku ina mai alfahari da kasancewar ki mata a gurin sadauki. Don nasan wani abin tare da taimakon ki ne yake yin shi a rayuwan shi yasa Allahda Annabinsa sukace ku auri mataye na gari don ku sama ma diyan ku uwaye na gari a rayuwan su. Ke alheri ce sosai Fatima a rayuaan dana wanda ina matukar alfahari da hakan ko yaushe kasancewan shi tare dashi yasa sadauki gaba daya ya sauya daga sadaukin da muka sani a baya. Duk wani mumunan halaiyar shi yanzun yazama tarihi a gurin mu da bakece ya aura ba da sai dai muce Allah ya kyauta kawai. Gashi natashi kudi suna shigo mai ta ko wani hanya may zai sashi tunanen gyara wani mugun halaiyar shi can na baya da basu da kyau da ai saidai kawai yaci gaba da gurbatacen rayuwan shi babu mai kwabon shi a kai. Amma duk irin kokarin da kikeyi a kan shi ina da labarin komai a kunne na Fatima. Allah dai yai maku albarka yasa ku gama da duniya nan lafiya yabaku zuria dayyaba masu maku biyayya kamar yadd kuke muna. Na amsa cikin kunya da Amin baba na gods nima da kuka mai da rayuwana haka don kune silar komai da nake ciki a yanzu. Yace kai haba dai Fatima ai mune dai da godiya a kanki yadda kikai muna biyayya haka yau gashi ya zama muna alheri ga baki dayan mu ko. Haka dai nabar gurin baba yana ta saka muna albarka da fatan gamawa da duniya lafiya a rayuwan mu kamar yadda ko wani da ke bukatan addua ga mahaifan shi kullun. Sai dare ya dawo ya kwashe mu muka bar gidan zuwa gidan mu cikin farin ciki a ran mu yadda iyayyen mijina suke zuka ma rayuwan mu albarka haka. Muna hanya nake cewa ashe mummy tabar aikinta ne akan rashin lafiyan bab ? Yace wallahi fa haka sagir ya fara fada min da kuma naje gun baba din shima yake fada min haka din. Nace ai ko ta kyauta wallahi don haka shine zama tare yace ai zan duba akan al, amarin don asan abin da za, ai mata akan haka din. Nace yaya bafa mummy ba kawai dukkan su sun bukatan taimako wallahi don alama ya nun sun a cikin wani hali wallahi ba dadi da ganin su. Yace nima nai tunanen hakan amma banji kince komai ba shi yasa nai shiru nima. Nace kai haba yaya nice kuma zanyi magana akan taimakon iyayyen mu yace bakece P A ba ke ce ya kamata ki tsara abinda ya dace a kan su ai. Nan na shiga zaiyano mai abinda ya dace ai masu din don a taimakawa rayuwan su har muka kai gida kowa ya shiga part din shi don watsa ruwa ajikin mu ko zamuji dadin hakan. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: I'mIDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,, IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH,,,, Washegari aka hada lifaya, don taya murnan samun nasaran da sukayi akan wasan su da suka buga na kwallo. Mun sha kwalliya sosai a lokacin in cikin wani dogon riga mai launin dark blue wanda yaji duwatsu a jikin shi sosai. Nai rolling din kaina da dan kwalin shi wanda shima yana da duwatsu da aka jera mai a jikin bakin shi. Ga zobunan gold sun cika min yatsu na dama duka hudu, daya sayo min wuyana saye da English gold. Na saka wani takalma mai dan tudu akafana sai yar karamar jakar hannu dana rike. Shigar tawa duk wanda ya ganni sai ya yaba da ita shi kan shi sadauki dana fito sai da ya kasa boyewa a ran shi ga kamshi dake tashi na jikina saboda mayukan danake amfani dasu a can yanzu. Haka Amir shima yaji kwaliyan shi irin ta yara maza mai tsada sosai tare da saka mai hula irin ta yaran turawa. Wayan shi ya dauko ya fara daukan mu hoto dashi, yana yaba kyawon mu ni da yaron. A cikin wata irin dirkekiyar mota muke tafe dagani sai shi sai Amir wanda yake rike a hannun mahaifin shi yana waya. Muna Isa gurin munga karamawan ban girma a gurin mutanen da muka samu suna jiran isowar mu gurin. A gaskiya wanna mutane suna matukar girmama yan was an kwallon a rayuwan su. Yana fitowa ya zagaya a bangaren da nake zaune ya bude min motar da kan shi yayin da idanuwan mutane yake a kan mu caaa. Wasun su da yawa a gurin basu san cewa sadauki yana da aure ba don su ganin su a gurin su shekarun shi yai karami da aje iyali haka. Hannun shi harde acikin nawa muka shiga babban holl din wanda yake makil da jinsin mutane kala kala. Duk wanda yake da iyali acikin su tafe yake da iyalin shi a gurin. Nan aka shiga gaisawa da mutane ana introducing din juna ga manyan masu kudin kasan turawa. Inda matan dake gurin suka shiga kallon kalar shiga ta wanda ke baiyyana musulunci a fili. Don haka aka shiga gimamani don suna matukar daraja matan musulmai sosai. Ga wasu flowers da ake watsowa daga sama sai shagali suke suna shaye shayen su irin na al,adan su. Nan sadauki suka hade da wani balarabe mai kudi dan kasan Dubai mutum ne mai tsananin arziki da tarin dukiya acikin nahiyar Arab side. Gaba daya shine mutum na farko da yazo na daya a duk duniya arziki da tarin dukiya. Gashi da ra,ayin son wasan kwallon kafa don matashi ne shima haka yasa ya kyasa taimakawa yan kwallo musanman matasa musulmai irin su sadauki. Yana kuma da kamfani na kera gwala gwalai da diamond nashi na kanshi ga rijiyoyin mai da yake dasu kasa kasa na duniya. Yana da kamfanin kera jiragen sama da na ruwa wanda yake mallakan shi na kansa. Hannu Abu sufiyanu ya mika ya karbi Amir dake a hannu na ya dan yi mashi wasa tare da sumbatar yaron. Cikin wasa yake cewa sadauki ya bashi Amir don yaron ya shiga ranshi. Sadauki yake cewa ya bashi yace ya gode tare da kissing din yaron inda ya juya gurin na hannun daman shi yai mai magana. Mutum ya amsa da insha Allah. Nan yaja hannun sadauki wanda nake biye a bayan shi sun dan jima suna magana irin ta Siri a tsakanin su. Wanda ashe alakace ta business suke kullawa a tsakanin su a lokacin, mutane da yawa sun San ba kebewar banza Abu sufiyanu yake da sadauki ba a lokacin. Da hannu ya yafito na nufin na karaso inda suke a tsaye, yake ce min nai wa mutumin godiya. Duk da ban San ko na may ye ba amma nai mashi godiya irin ta addinin musulunci wanda ya kara sawa mutumin jin dadi a ran shi. Don shi mutum ne wanda yake son mutane masu yi mashi godiya da nuna farin cikin su gare shi. Nan dai sukai ta gaisawa da mutanen arziki na duniya kala kala ina rike a hannun shi har taro ya fara watsewa. Muka Fara ficewa daga sahun farko muka bar gurin don a lokacin a gajiye nake sosai ga Amir da nauyi ba kadan ba. Muna a mota ya dan sasauta tie din wuyan shi yana juyowa inda nake zaune yana cewa my queen kin gaji ko don nasan baki saba irin wanna kwaram din namu ba ke. Idanuwana na Dan lumshe nake cewa nauyin daukan wanan din dai ya isheni . Yace Kai ni dake son na samu ma yafi haka girma idan son samu ne a gurina. Nace kai Yaya idan Amir yafi haka kiba kuma ai sai dai na dinga barin shi a zaune guri daya don ina zan iya daukan wanda yafi wanna girma haka. Yanzun ma a Yaya nake iya daukan shi balle ya kara yafi nan kuma ? Ya dan juyo a mamaki yace Queen baban nawa zaki bari a zaune don tsaban mugunta kuma ? Nace ai nima babana ne ko ko kamanta nima shi ya haife ni ne wai ? Nace sune fa gata yanzu a duniya don sune sillar wanna rayuwan da nake a ciki yanzu. Murmushi yayi don jin abinda na fada yasan ba karya na fadin ba haka zancen yake ko yaushe Ina matukar godewa mama da baba din. Yace tare da kwantar da kanshi saman kafada ta nauyin ya karu min biyu wanda a lokacin ba nauyi naji ba sai wani sanyin dadi da naji a raina kawai. Don farin cikina yanzu karuwa yake a kullun Ina mai godewa Allah na da biyayyan da yabani iko nai wa Maji ban butulce mata ba ga bukatan ta a gare ni na auren dan ta da duniya kewa kallon lalatace. Matsalata daya yanzu shine ban gama tantace ko sadauki ya daina halin shi ba ko yanayi har yanzu. Haka ne yakan rage min jin dadina a kullun na tuna da wanna rayuwan nashi na shaye shaye. Ai fa tuni idanuwana ya ciko da hawaye yana magana jin nai shiru yasa shi dago kanshi daga kafadata ya kalleni. Ganin da yai min a cikin rashin walwala komai ma na duniya yafita min arai a lokacin. Da sauri ya Kara dagowa yana kallona acikin mamaki tare da kamo hannuna ya rike gam a cikin nashi yana tambayana may kuma ya faru haka queen ? Na sauke ajiyan zuciya tare da zubo hawayen dake a cikin idanuwana kasan fuskana. Yasake maimaita tambayan shi da wai may ya faru bana son ganin ki ko kadan a cikin damuwa queen. Na sauke ajiyan zuciya tare da mayar da kaina ga nashi kafadan ina sauke ajiyan zuciya a hankali a karo na biyu. Da sauri ya kara jawoni a jikin shi ya rugumay mu yana cewa kada kimin haka Fatima kinsan kwanciyan hankalinki shine nawa yanzu. Na dauka yanzu zakifi kowa farin cikin gani da idon ki da kikayi na irin baiwan da Allah yai ma mijin ki. May ye kuma ya samay ki a lokacin da nake tsanmanin farin ciki a gare ki Kuma ? Na goge kwallan da suka fara zubo min a idona nace Yaya love tunanen bayane yazo min kawai. Maganan tawa ta doke shi har ciki ranshi yace tare da riko min hannayena duka biyu. Yace kiyi hakkuri Fatima nasan cewa na bata maku rayukan ku sosai a baya dake da iyayyena wanda nima a yanzu idan na tuna wanna rayuwan bana jin dadin shi a raina ko kadan. Ki daina damuwan kanki da yawa don sai ma ince ki godewa Allah saboda na San kece sillar daina duk wani mugun rayuwan da nayi a baya Fatima. Ni kaina nasan har abinda ke kanki baki san kina yi ba akaina don wanna rayuwan da nayi a baya yana bata maki Rai sosai da sakaku kunya ga jama,a. Fatima nasan kina son na fiye da son da Maji take min a baya wanda a baya nake ganin babu wani mai sona bayan maji da mahaifina da yan uwana biyu da Allah ya bani. Amma sai haduwana dake Fatima na fahinci cewa Allah kan jefo wasu mutane a rayuwan bawan shi don kawai su taimakawa bawan shi a wani halin taimakon dayake bukata a rayuwan shi. Hakane Fatima ke alheri ce a rayuwan mu gaba daya don a sanadin ki Abubuwa da dama nawa sun gyaru Fatima ta sanadin ki a rayuwana. Most especially zan iya ce maki ibadana gaba daya a sanadinki Allah ya nufa na gyara shi. Kin min Abubuwa da dama wanda ke baki San na San dasu ba a rayuwana Kuma bawai kina son na sani din bane kinyi ne kawai don ki taimaka min kawai. Wanna maganan da yayi itace mafi girma da tsoro danaji don ban San may yasani wanda nai mashi a rayuwan shi ba. Nace Yaya love idan abin da naima ya bata ma rai a lokacin ka yafe min don Allah don ba a cikin hankalina nai maka ba. Ya langabe kan shi tare da girgizawa yace Fatima bata taba yi min abinda ba daidai da rayuwana ba dana sani. A lokacin motar mu ta tsaya a kofan hotel din da muka sauka a ciki ya karbi Amir daga hannuna muka fito daga motan. A gajiye muke don ba karamin gajiya muka kwaso ba daga inda muka fito nace ya kawo Amir din na kama mai don nasan shi ba gwanin rikon yara bane sosai. Yace ki barshi don nima in son ya saba dani ko kin manta da sunan wanda yaci ne a gurina. Ya ce don haka ke kuma sai ki dinga kokarin kina Sanya mu a cikin farin ciki da ni,imar ki. Kina kashe Muna kishin ruwan sha,awan mu daga ni,imar da Allah ya tana dar muna a gareki. Kunya ya kamani daga maganan da yayi haka yasani dan murmusawa kawai Ina biye a bayan shi. Duk da gajiyan da muka debo Bai hana mu kasancewa a tare ba a daren wanda sai faman sanbatu yake akan irin ni,imar da Allah yai min a jikina. Har muka bar kasar na yoghuslabea bai barni na huta daga jikin shi ba ga sabon kasalan da ke yawan taso min wanda nake gani sabon yanayin jin dadin da na samu ne hakan. ****** ********* ****** Watan mu cikin na uku ke nan yanzu rabon mu da gida ga wani irin mahaukacin soyayya da so da kaunan da yake gwada muna ni da Amir din. Abin har yana bani tsoro irin yadda ya ke kashe muna kudi haka har sai da yakai nace mai yayana kayan nan fa sun Isa haka. Sai dai ya girgizawa min Kai kawai yace Queen idan ban kashe maku ba na kashewa wasu wa kudi haka a rayuwana. Nikan ban da tacewa dole na saka mai Ido na bishi da kallon mamaki don sai nake gani kamar ba Yaya sadauki dana sani a baya bane . Wanda tsaraba ma idan ya sayo babu rabo na a cikin sa sai idan mamana tai min ci da karfi nake samu daga gare shi. Allah mai iko sai gashi yau nice dungurungun a gurin sayan kayan baki daya. Haka Amir yasha kayan wasan yara su kekuna da jirage teddy ga abin koyon haruffa na English da Arab kala kala ko wani da kalan sautin sa. Bayan yasan cewa akwai su a gida wanda ya sayo tun yaron yana cikin ciki. Kafin mu bar kasan ya turo da kayan gida ta hannun Yaya Bashar kayan zasu fada . Wayanda na sani kenan wanda ban sani ba sai idan mun Isa zan gansu a can idan Allah ya Kai mu. Daga can bamu nufi Dubai din ba wai suna da meeting a US da zasuyi acan na yan kwallo. Sai da muka share wata daya a kasan inda ya kara hada business da wasu turawa na kasan don ya saka hannun jari atare da su. Nan ma bai barmu hakana ba sai da yai min sayayya kamar wanda zai hada kayan lefe. Suturu na alfarma da atamfofi masu tsadan gaske ya saya muna anan kasan. Ni kaina a lokacin nasan na zama wata daga cikin matan manya a kasata ke nan. Gashi nai wani irin kyau fatana yai wani irin lub lub dashi tankar dai irin matan, larabawan Pakistan din nan hakan ni da kaina nasan na samu canji a rayuwana. Mun shiga kasar Dubai wanda a lokacin watan mu hudu rabon mu da gida kenan har na Fara kewan gida da yan uwana. Duk da Ina waya da duk wanda nai kewan shi a raina amma duk da haka Ina son gani na a gida. A kasan Dubai naga mata kasa she masu ji da kansu duk da na taba zuwa amma sai wanan zuwan ya zama min kamar na farko a rayuwana. Ga matan Nigeria Nan zakace tankar a gida Nigeria kake Nan na Dan sake jiki naji Dan sauki shaukin gida da nakeyi a raina duk da irin kullan da muke samu a gurin shi. Sam sadauki baya yarda nai hurda da matan hausawan da muke haduwa dasu a can acewan shi Bai yarda da hurda da irin wa ya Nan matan ba dake baro gida su zuwa wata uwar duniya da sunan neman kudi ba. Gashi suna son yin hurda dani amma sai yace masu ni matata boye ta nakeyi don matar kulle ce ita. Mutum zai yi mamaki yadda matan manyan kasar mu suke acan birjit dasu zakace a gida Nigeria ne mutum yake ganin su ba wani boyewa ba ne kamar nan da ba,a ganin su sai da ticket. Gashi da farin jinin jama, a a tare dashi duk kowa na son shi wanda hakan ne muma iyalinshi ya shafe mu don mutane suna haba haba da mu a can. A nan nuna min halarci so sai a kasan don sun it's taron bakin su dake zuwa masu ko yaushe. wani buki da aka shirya na yan kasan Nigeria inda akai ma Naira kaca kaca a gurin. Don ko a can sai wanda ya Isa zai halarci wanna taron da aka shirya ida yan bussines din kasan mu suka baje nairan su a gurin. Shiga sosai ta alfarma mukayi wanda nan ma wani dogon riga na saka mai balain kyau kamar alkyabba rigan take. Bayan na saka wani English wear daga ciki na kawo rigan daga sama na dora akai. Alkyaban irin mai tsananin tsadan nan ce ta matan manyan ko manyan ma sai wace ta isa take saka ta don yakai jarin wata a kudi. Hular rigan yai min wani irin rufi yana rike da wani dan mayafi da yake like a jikin rigan Idan kinga dama zaki iya Dan zarga shi akai shi ma. Sai ki koma kamar kin yafa idan kuma baki ra,ayin haka zaki sake shi ya biyo bayan alkyaban ne. Haka na dan yafo shi yai min matukar kyau sosai ajikina kamar wata yar labawa masu fada aji. Wuyana Kuma diamond necklace dan Kiran Dubai sai su awarwaro da zubbuna masu tsada na saka. Yaya sadauki yake cewa gaskiya da nasan haka rigan nan yake da kyau da akwati daya zan saya maki nashi. Nace Kai haba dai Yaya har guda biyar fa ka saya min su duk da tsadan dake gare su. Yace Queen ba tsada ba shagarki na fada maki shine mutunci na a idon jama,a da kuma matan abokaina. Ina amfani mijin ki yana rike makudan dollars haka amma babu fitan kwarai ga iyalin shi ai sai duniya ta zage ni kamar ban godewa Allah ba ke nan. Nafi son duniya su San cewa ke mai tsadace dariya ya bani nace to nagodewa Allah da irin baiwan mijin da ya bani yace to ke fa. Isowan mu yaja hankalina mutanen dake gurin fitowan mu ya mayar da hankalin mutane sosai a kan mu don shigan mu ko makiyi dole ya kyasa muna ga Dan mu a hannun shi ya dauka a kafanshi Wanda barci yakeyi shi yaron duk da yasha kwaliyan shi sosai. Matan da basu San mu ba sai tambayan sukeyi halan matar waye wai shin wanna guy din dan Nigeria ne wai ? Aka fada masu Dan wasan kwallon duniya ne da ake Kira UF Dan jahar sokoto din nan da matar shi. Lalai yayi abinshi don su keda lokaci gaskiya inji wasu Mata dake zaune saman wasu kujeru dayan tace matar shi yar wanene a Nigeria ita Kuma ? Dayan tace ba yar kowa bace diyar tallkawa ne auren hadi ne ma akai masu shi ya mayar da ita haka da kike gani. Kalleta cikin shigan matan manyan duniya kamar diyan wani hamshaki can da ita. Matar dayan tace gaskiya ba laifi don first class ce gurin gwadawa tsara wanna don bata da makusa ta ko Ina gaskiya dubi dan data haifa mai mai dan karen kyau da shi don Allah. Wata daga ciki taja tsuki tace kalli yadda yake wani tarairayan ta kamar diyan wani can. Dayan matar tace ke ko aita isa yai Mata haka don gaskiya ba laifi akanta gara yai haba haba da abinshi don akwai muggan tsofi a gurin nan kema kin sani. Gaskiyan shi kan gara ya kula da abinshi don tsofin nan da kike gani basu da dama gurin mace maikyau balle suna ganin ta haka yarinya danya da ita. Dayan kuma tace ke ko ai mace rahamace fa ga mijinta gara yaji da abinshi kowa ya gani a fili. A gaban matan dake gulman mu muka karaso suka shiga daga muna hannu muma hakan mukai masu muka wuce zuwa inda aka tanadar muna mazauni. Sun bimu da kallon rigan dake jikina yasha jinin jikin su sosai wanda ko shagon sayar da irin su basu iya shiga don tsadan gurin. Amma gashi a jikina Kuma mai high quality din na saka a jikina a lokacin. Sai yatsune fuska suke su na rayawa a ransu dama sune a wanna matsayin haka ko diyan su a haka. Don haka aka shi ga girmama ni a gurin don matsayin baiwan da Allah yaiwa mijina kawai don sun san ni din nashiga cikin sahun matan manyan yanzu. Ganin saukin kan dake gare ni yasa wasu suka sauke girman kansu suna zuwa muna gaisawa dasu cikin mutunci. Bamu wani jima agurin sosai ba don dare ya soma yi muka koma masaukin mu sai dai nayi kawaye da suka nuna ra,ayin su akan hurda dani duk da Yaya ya hade rai bai son hakan dani. Washegari a masaukin mu sabbin kawayena suka kawo min ziyara nan muka sha hira dasu suna ta yaba irin kyawon da nayi a daren jiya gurin waliman da akayi. Tare dasu da wasu abokan Yaya mutum uku muka Kai ziya gurin Abu sufiyanu daya gaiyace shi da kan shi. Karban girma akai muna a gidan nashi inda muka samay shi don suna da appointment da Yaya da suka aje kan tana son ya dora shi jagorantan wani company da yake son yi a Nigeria na mai. Da sunan zuwa yini muka shiga gidan sai gashi munyi kwana buy a tare dasu cikin kullawa da mutunci. Ya dankawa Yaya duk wani abinda ya dace na mallakan company da yake son yi a Nigeria din. Don ya zamo masu babban wakili a can idan min koma gida Nigeria don samun nasaran shi. Taron nasu ya samu halartan wasu manyan engineers yan Nigeria wanda wanda shi halinshi ne ya daukaka matasa na kasashen duniya don ci gaban su da kasan su. Mutane sunyi murna da wanna anin alherin da sadauki ya jawo wakasan mu Nigeria. Gashi matashi mai tashen zamani sun San matasa zasu samu aiki da dama a wanna harkan insha Allahu. Ga kyauta na alfarma da sukai muna nagani a fada bamu ba harda su Salma kawayena dasu ka raka mu sun samu alheri sosai a gurin su. Haka yasa na tuna da masoyiyata yar uwata Maryam wace nai alkawari a raina duk abinda na samu nima tare da ita zan raba shi. Don Maryam ta nuna min so da kaina da bazan iya mantawa dashi ba a rayuwana don itace silar komai da nake ciki a yanzu. Ba don ta gwada min so da kaunan ba da ban Kai haka a gidan su ba da tuni na gudu na koma kauyen mu duk da halarcin da mama itama take nuna min. Idan da ban jin dadin zama da Maryam indon ta Amirace kawai ba zan iya zama na tsawon lokaci ba a gidan. Na samu kyautar mota daga matar maigidan irin da matan su ke yayi a lokacin. Tare da wani dan karamin kit wanda ke dauke da gwalagwalai a cikin sa Kiran kamfanin su ta alfarma wanda sai wanda ya Isa ne zai saye su a nan Dubai din ma. Ranan da zamu bar gidan matar tana rike da hannu na tana yabawa da halaiyar mu na kirki don har su Salma da muke tare da su sai da ta yaba da halinsu. Kwanan mu biyu a masaukin mu na Dubai din muka dunguma zuwa airport inda zamu biya kasar saudiya muyi umurah a can kafin mu dawo gida Nigeria. Mun Isa kasan muyi ziyaran fiyayyen halitta manzon rahama, a Madina muka dan fi dadewa acan din. Ranan jumma,a muka shiga garin makka muka fara umarah tare da sallah jumma a. Adduoin danayi a can sun fi yawa akan samun shiryuwa da kariya na zuria da neman zaman lafiya a gidan aure na tare da mijina da sauran yan uwan shi. Muna Shirin dawowa ne zazzabi da nake fama dashi ya tsanata a kaina wanda dole muka tafi asibiti ganin likita a can din. Bamu sha wahalan ganin likita ba sosai kasancewa da wani abokin wasan su sadauki dan kasan muke tare. Nan a ka shiga min duk wani test da binciken da ya dace ai min a lokacin inda a take results yafito cikine a jikina Dan wata uku Kuma again. Ya kara auna ni tare da min wasu binke komai nawa normal yabamu shawara Alan Amir da zaran ya dan Kara shan nono na wata daya mu cire shi daga nono. Yabamu magani na yara da zamu dinga bashi Yana sha kafin a yaye shi daga nonon. Muna barin asibiti masaukin mu muka koma inda sadauki ya rugumoni zuwa jikin shi yana murna tare da fadin my queen ban San irin godiyan da zan maki ba a rayuwana ba. Don kin min komai a rayuwana gashi a Dan kankanin lokaci zaki wadatani da zuria a gidana kyawawa abin son kowa. Nan ya nemo bakina muka mannewa junan mu sai kalman godiya yake sako mun tare da kara manne ni a jikin shi. Bamu dauki lokaci ba dana ji sauki sosai muka dawo gida Nigeria cikin yan uwan mu tare da tarin arzikina alheri mai yawa da muka dawo dashi a gidan. Mun kwana bit a garin Abuja kafin mu Kama hanya zuwa sokoto birnin shehu inda yan uwa da abokan arziki muka samu suna jiran mu a airport din. Yawancin masu taron mu yan zuwa taya shi murnan samun wanna babban nasara ne na shugabancin wanna babban kafanin da zai jagorantan a kasan mu Nigeria. Mun sauko daga matakalan jirgin cikin shiga irin ta alfarma dana saba yi a yanzu don fitar kunya. Idanuwan mutane Cass akan mu wanda nai mamakin ganin wanna taron da akai muna a gurin. Yana sabe da dan shi a kafadan shi yayin da nake biye a bayan shi Ina saukowa a hankali daga matakalan jirgin. Nan aka shiga watso muna wasu flowers masu kyau da kamshi ana ta muna sannu da zuwa. Acikin taron nan haka Maryam ta kutso kai naji ta rungumay ni ta baya take muka rungumay junan mu a cikin murna da saukin ganin junan mu. Dan wani lokaci kadan ta sake ni tare da dagowa ta Dan kalle ni tana cewa wai Fatima kece haka ko dai mafalki nakeyi. Nace kai haba anty na bagani a gaban ki ba tace kin koga yadda gaba daya Kika koma kin zama wata irin big madam dake Fatima. Murmushi nayi na Kara jawo ta nai hugging din ta tare da rada mata cewa aikin yayan ki ne haka yar uwa. Muryan shine a cikin taro yana fadin ke uwar surutu agajiye take please ki barta ta huta tukun kin wani tsare ta da gulman ki. Nace haba Yaya baka ko tausayin mu yaushe rabon mu da ganin junan mu ne wai? Ya jawo hannuna tare da watsa mata harara yake cewa kwayi gulman a gida idan kin hadu a can. Gaba daya da masu taron mu muka wuce zuwa gidan mu sai dai nai matukar mamaki da ganin an canza hanyan da na sani zuwa gidan namu. Inda naga an shiga wani irin mamakeken gida mai wani irin katon get ginin gidan ba sai na tsaya fadin shi ba don har da bene a gidan. Nan ma yan uwane Mata dam a gidan a hankali ya rada min cewa welcome to our new house queen. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , , IDAN KIN BIYA KADA KI TURAWA WANDA BAI BIYA BA IDAN KINYI HAKA MUN BARKI GA ALLAH. Alheri sosai ya tanadarwa su Mama da Umma da mummy har motar shiga sai da ya canza masu tare da gyara masu dakunan su tsab. Wanan ya zamo karo na farko da sukaji dadi a ransu abinda taya sadauki yake masu na alheri wanda hassada baya bari suga irin alherin da yake masu abaya. Yanzun ko abu yakai babu gare su duk yadda mutum yai masu alheri komai kankantan shi suna godiya sosai. Don yanzu wanda suke samu gurin shi watau baba shima ta kanshi yake yi baida komai duk diyan su sun wawashe mai shago baida wani abin hannun shi kuma inba gonan da sadauki ya saya mai ba farkon fitan shi wasan kwallo da yafara zuwa. A takure suke komai da suka fi karfi a baya yana basu sha, awa yanzu shi yasa suke ganin wanan kyautan na baya yazo masu kamar kyauta na farko da ya taba masu. Har daki mama Asiya ta samu mama tana mata godiya wanda mama ma a lokacin bata san da wanan alherin ba inba yanzu da mama Asiya tashigo mata da zancen ba. Mama tace ikon Allah wallahi yaya banda labarin wanan zancen yanzun ma nake jin shi a gurin ki. Godiya dai ta karayiwa maji tare da fatan alheri tana ta saka albarka wanda maji ke gani yau kamar a mafalki. Mama Asiya ce sakawa dan ta albarka haka akan alherin da yai mata don jin dadin zuciyar ta. Mama Asiya tana fita har tsakar gida tana godiya Nafisa ta gamu da ita dakin su tashiga gurin mahaifiyarta tana cewa kina nan zaune halan may ya faru naga mama tana ta godiya a waje tafito dakin maji. Umma tace nasan taje godiya ne godiya akan may kuma Umma ? Tace yanzu Sagir ya samay mu da kyautan alherin da yayan ku dan kwallo ya aiko muna dashi mu uku motace ya sake muna da kujerun daki da gadaje sai kudi wai mu saka mai a mota da kayan abinci. Nafisa tace tirkasa amma ko Allah ya saka mai da alheri wallahi to umma shine kike zaune ke baki zuwa kiy godiya? Koda yake yadda naji kina magana kamar har yanzu kin saura hassadan abinda yafi karfin ki fada. Dadai kin sakawa ranki ruwan sayi kibi kici arziki dayafi maki wanan hassadan da kukeyi shekara da shekaru yaki kare. Ga yar uwar munafuncinki ta sulala taje tayi godiya tabarki nan kina hassada ga banza. Kallon takaici taiwa yar tata da suke dauka a matsayin mara hankali ga maganan ta da dabiun ta amma kuma gaskiya ai Nafisa ta fada mata don tasan mama Asiya yanzu tana zare jikin ta tana hurda da al, amarin maji da yayanta. Nafisa kan dakin ta tashige takwanta abinta yanzun ta daina sha sai dai bata bar harkan bazan ta ba da ta saba. Sagir ya shigo ya samu umma zaune tayi tagumi ganin shi ya dan sata sake jikin ta tana mashi tayin abinci. Yace Umma na fada maki yanzu a gidan yaya sadauki muke karyawa ni da Abdul komai dare sai Fatima ta kira mu muzo muci abincin mu yana aje haka ma dasafe. Umma taji wani iri a ranta ba dadi tasan cewa ko ba komai anyi hadin zumunta a gurin kafin takai karshen tunanen ta taji muryan shi yana cewa. Wai ko Umma kin san wani abu fatima fa tai muna kanfen gurin yaya ga sabon gurin aikin da za, a bude a abuja nasu. Shi da kanshi yaya sadauki din ke fada muna cewa wai yar uwar mu ta nuna son kai ta matsa ita sai dai muma a nema muna babban gurbi a can mu kama aiki dasu ko kuma wanda ke nan sokoto. Umma wallahi yadda suke gwada muna halarci irin haka ni abin ma har kunya yake bani yadda a baya mukai ta gwada masu kiyayya a filin Allah . Amma sai gashi yanzu da ya samu mune na farko samun alherin shi harda mota fa yace zai saya muna wallahi. Bamu kadai ba har dasu yaya Imiran naji ana magana a kansu suma za, a basu appointment a gurin. Tace kai amma ko da ya kyauta muna wallahi don zaman banzan nan na Imiran ya fara ista wallahi. Umma yanzun dai jekiyi naki godiyan kafin wani lokaci kuma kin san irin wanan alherin na bazata shi ake kira da kyautan dan aljanna. Kyantan da zaizowa bawa a lokacin da bawa yake a bukace da wani abu a rayuwan shi dubi fa wa yan nan kujerun yadda suka koma kamar tsunma ni har kunyan nake jin azo agansu a dakin nan haka wallahi. Bai bar dakin ba sai da yaga Umma ta mike yaga ta nufi dakin maji hankalin shi ya kwanta. Don bai zai yuyuba ana masu alheri irin haka amma ace su har yanzu basu daina hassadan su ba da sukeyi. ****** ********* ****** Allah mai iko a yanzu ankai duk inda sadauki ya sa kafan shi yana tare da manyan body guard masu tsaron lafiyan shi dana iyalan shi wanda goverment da kansu suka bashi su don tsaron lafiyan shi. Saboda gashi karamin matashi amma yana daya daga cikin manya masu shigo da manyan ababen amfani daga kasashen duniya. Haka yasa ya zamo abin kula sosai a gurin manya na kasa da suke fada aji. Saboda ya zamo daya daga cikin yan kasa masu kishin kasan su don sun cigaban matasa. Gashi akan kamfanin da suke son kafawa har guda biyu na mai dana manyan jiragen ruwa da zasu dinga shigo da kaya daga waje. Ga manyan injima na haska wutan lantarki da za, a shigo dasu kasa don amfanin kamfanonin da za, a gina nan n Nageria. Ban fita sosai zuwa yanzu don cikina da yai matukar girma don ko a wanan ma likitoci sun kara bani bedrest sai dai ba kaman wancan na baya ba danayi na Amir din. Ina kwance saman dogon kujera a falo na dan mike kafafuna na da sukai min nauyi. Yashigo gidan a gajiye dashi su Sagir suna take mai baya shi da Abdul dauke da dan briefcase din takardun shi da laptop dinshi a cikin case din. Ya zauna yana cewa kai nagaji da yawa wallahi nazaci a nan idan na dawo ko zan huta amma gashi duk ba wani hutu da mutum ya samu tare dashi. Na dan lumshe idona tare da kokarin mikewa zaune don na karbi case din zuwa dakin shi. Yace da sauri No No kwanta abinki ki huta barshi idan zan shiga zan shiga dashi ai. Bayan ya karasa kaiwa zaune ne yake cewa duk rashin samun hutu ya saka har kirjina yana min ciwo wallahi. Da sauri na dago ina kallon shi nace amma gaskiya tunda ka fara jin haka ya kamata ka samu hutu ka zauna a gida koda na kwana biyu da zaifi ma. Yace na kwana daya dai Fatima kwana biyu yai min yawa ga mu da tulin aiki mai yawa a gaban mu. Idan ba naga angama gina muna komai ba hankalina bazai taba kwanciya bane ai kinga dukiyar mutane ne nauyin shi ya hau kaina dole na kula masu da abinsu ko? Nafisa ce tashigo gidan da alamun damuwa a fuskanta nan muka zauna da ita ana hira suko abinci suka wuce ci a dining. Yana gamawa ya shiga ciki ya dan jima bai sauko ba yana sama koda zai fito ya sauya kaya jikin shi a lokacin. Tun bai kai zaune ba ya soma magana yana cewa gaskya kauna ya kamata ace kifito da miji hakana kiyi aure na hada ku da Amira dama yan sa, a daya kuke kinga kowa sai ya huta abar Rukaiya har su karasa nasu karatun. Cikin wani langabe kai tace ni yaya wama zai aure ni kawai ni na fitar ma da rai ga wani aure can Da sauri nace haba anty ce astangafurullahi mana yaya zaki magana kamar ba musulma ba dake. Tace to madam wakike gabin zai aureni a haka yadda nake duk masu zuwa gurina ba da sunan aure suke zuwa min ba sai dai da tasu bukata kawai. Gaba dayan mu tausayi tabamu ga maganan ta don mun san cewa gaskiya ta fada maganan ta. Amma kuma ai abin Allah ba a yanke kauna a gare shi nace anty gaskiya yaya ne ki natsu ki rage wasu halaiyar ki ko Allah zai tausaya maki. Don kinga ai Allah miskaraziratin ne ba abinda ya gagari ubangiji sai kinyi mamakin irin mijin da Allah zai kawo maki idan kin natsu. Kafin tabani amsa wayan ta yai kara jin sunan wace ta kira da Raye yasa na gane da Raiha take waya a lokacin. Tambayan ta tayi tana ina tabata amsa da cewa gani nan gidan su madam ina shan sanyin A C. Tabata amsa da gata nan tafe tana gamawa yake ce mata kinga ni maganan ki bawai ya karbu bane gareni fa kiyi tunane a kai ki gyara halaiyar ki Nafisa . Mace fa dan guntun lokaci ke gareta tun anayi daku watarana masu neman naku gudu za, suyi su koma ga wasu yan matasan Ta amsa a marairaice da tau naji yaya insha Allahu zanyi kamar yadda kace amma zaka dinka min hijjabbai na fara sakawa ko? Murmushi yayi yace gatanan yana nufin ni zata dinka maki ko guda nawa kike so kaunata. Nidai kawai ki natsu ki daina wanan halin please. Shigowan Raiha ne yasa muka daina zancen suka gaisa da shi ya mike zuwa babban falon shi na waje da yake taron baki a cikin sa yabar mu nan zaune a na cikin gida da waya a hannun shi yanayi. Nan muka fara hira dash nake tambayan Nuriya suke ce min wai tabi wani saurayinta dan Ibo sun tafi lagos tare. Banji dadi ba na kasa boye bacin raina nake cewa haba dai haba ace kuma mutum yana hurda da harda wanda ba musulmi ba kuma ai abin yayi muni gaskiya. Raiha tace madam kawai dai Allah ya gafarta muna zamuce don dai gaskiya nima yanzu da hankali yafara zo min na gane hakan ba daidai bane. Ni yanzu fatana kawai Allah ya kawo min miji wanda zai soni tsakani da Allah wallahi ko yaya yake zan zauna dashi na natsu bakiga yadda al, amarina har yasakawa iyayyena cutan hawan jini ba. Tace to mazan ne yanzun sai a hankali wallahi na rasa wanda zaizo ma da tsigar so na gaskiya bada bukata ba. Nafisa tace maganan da muka gama ke nan da yayana kafin ki shigo abinda na fada mai ke nan kema yanzu sai gashi kinzo dashi. Tace wallahi muna son auren bawai bamu so bane to amma wazaka aura shine matsalan. Istigifar bai bar komai ba ku koma ga Allah kwana biyu kuga ikon Allah wallahi bana jin dadin irin wanan rayuwan da kukeyi yanzu ya kamata ace kunyi wa kan ku fadan hakan. Shi yasa nake son ki madam wallahi kece kawai zan iya cewa a yanzu kina tsayawa ki nusar da mutum hanyan alheri bayan kowa ido yakawo ya saka muna. Ana jiran da garin Allah ya waye kai wani abin asha asakaka ga faifai a tallata ka. Yaya sadauki ne yashigo yana ce min sai ki shirya don muna da bakin da zasu duba gurin da za, a gina kamfanin shimkafa a garin nan Gashi sunce min ba, a hotel zasu sauka ba anan gidan zasuyi masauki don haka sai ki samo wanda zasu yi aikin abinci idan kuma bayarwa zakiyi ai masu duka daya. Kafin ma ya karasa zancen shi sai cewa Raiha tayi bagamu ba yaya aikin may mukeyi dabaza mu yi ba mu. Baiyi magana ba don na lura hankalinshi bai kwanta da al, amarin Raiha din ba wanda shine bai fahince ta ba sauki kaine da ita sosai. Amma shi yana ganin sune suke jefa yar uwarshi a cikin wanan mumunan harkan da sukeyi tare. Bai san tafi su zama shedaniya ba don ita ta hure fitillar ta sosai ma fiye dasu. Mun jima dasu muna tatauna abinda ya dace muyi da wanda zamu saya na bukatun mu. Har sai bayan sallah magariba suka tafi mukai sallah suna cewa idan an shirya na kirasu. Bayan yashigo gidane yake fada akan cewa may zaisa na yarje ma wa yan nan mashiririta suyi mai aikin abincin bakin shi yaushe ma suka zauna balle su san yadda ake girki su. Nace haba yaya sai kace ba mata ba su gani kuma ga iyya a gurin ai zamu taimaka masu da wani abin. Yace da sauri No no kada ki soma cewa zakiyi aikin komai kin dai san yadda condition din ki yake please kada ki fara ki taba komai idan ma bazasu iya ba sai a kira wasu suyi final nace ballema insha Allahu zasu iya duk abinda suka lissafo zasuyi din. Bai kara magana ba haka muka bar zancen don yaga na aminta dasu sosai yasa ya kyale badon yaso ba. Izuwa yanzu alherin da sadauki yaiwa iyayyena bazan iya lisfoshi ba don muna waje sun tafi sun sauke farali ga gyaran gida da abin sana, a da ya sayawa kowan su a sanadiya na iyayyena da yan uwana sun fita a cikin talauci yanzu wanda hakkurina da biyayyana ne yajawo muna wanan alherin haka. H Yan uwa dama yan garin mu sukan zo neman alheri a gurina wanda nakan yi masu shi gwargwadon halina. Lokacin zuwan bakin shi yayi bayan sati ya zagayo yabani kudi masu yawa akan abubuwan bukatan su. Ban masu kyata ba na ba kudi fiye da wanda za, a kashe sosai suma su karu daga ciki suka shiga kasuwa saywn abubuwan bukata duk da wasu muna dasu a gida. Ranan har anty maryam da Rukaiya sai da suka zo da mummy tare akai aikin komai dasu na fita kunyan baki yadda ya dace sai da aka hada abinci kusan kala goma sha biyu nau,i daban daban suka kara gyara katon falon muna na baki an saka kamshi da komai a falon yadda ya dace ayi. Bakin basu shigo gida ba sai misalin karfe uku na rana dirin motocin da mukajine yasa muka gane cewa gidan mu ya dauki manyan baki yau don har dasu jiya da alaman akwa wasu manyan kusa a cikin su ke nan. Nan aka shiga fito da kayan ci dasha bayan wanda aka kai masu da farko wa drivobin su. Gida ya rude da hayaniya sai kai da komo su Anty Nafisa sukeyi a gurin ana yaba aikin da sukayi. Allah da ikon shi a wanan sanadin Allah ya hada su da masu son su a gurin sukai wa yayan su magana kan ya basu kannen shi din nan yace yabasu. Wasa wasa magana ya zama babba don ita Nafisa ta hadu da wani ustazune manager din wani babban company dake garin Abuja. Ita ko Raiha wani sojane babba wanda gwaunati ta turo shi as a security guard na kasa ya kyasa mata. Amira da mama tace tazo ta taya mu aiki tace ita ba yar aikin kowa bane ba inda zata tafi nan mama ta ganta ta kyaleta. Amma daga baya da taji sun ba da tukwaicin dubu dari biyar wa masu aiki sai kuma ta shiga fada tana ganin laifina Wai dama ni yar bakin cikine shiyasa na gaiyato yan iska su cika min gida shiyasa ita bata tafi ba. Karshe kuma sai ga zancen auren Nafisa da Raiha da taji Allah ya hadasu da wasu manya sai dai ba yara bane su. Nan kuma ta shiga zage zage kamar mahaukaciya wai ta yarda ni yar bakin cikine ta karshe sosai don ban son ta da arziki nafi bukatan komai sai a gani a gurina kawai. ****** ********* ****** Bukin anty Amira ya taso sosai ba kama hannun yaro don haka muke ta zirga zirga ba hutu don mu ke gudanar da komai akan bukin duk da gwatsale ni da takeyi tana nuna bata bukatan saka hannuna acikin al, amarinta sam. Hakan bai sa na daina duk wani abinda nake da niyar yi ba don ba don itace nakeyi ba dama don Allah nakeyi da mijina da kuma mahaifan su. Bata san ina da rana a gare ta ba sai da masu zuwa ganin dakin da za, a saka mata kaya sukaje suka dawo da labari mara dadi don ashe a family house za, a aje ta. Kuma ga dakunan ba wasu dakuna bane maigirma a jere suke ita da uwargidan ta wace yar uwace ga mutumin da zata aura. Da labarin yazo ba karamin tayar da hankalin ta tayi ba sosai nan ta tuburewa mutane akan Ibrahim ya cuce ta don cewa yayi gida zai kama mata haya don may yazu zaice a gidan su zai aje ta. Sosai ta tayar da hankalinta akan bazatayi auren ba ta fasa hankalin mama yai matukar tashi gashi an gama komai akan shirin buki ga yan uwa na nesa har sun fara hallara a gurin bukin. Kuka wiwi takeyi akan ita kan wallahi ta fasa sai dai akai wata ba ita ba don bazata wanan gidan da ake bada labarin shi ba babu tsari. Mama kuma da yan uwa sun kafe kan lalai sai anyi auren nan sai dai ta mutu idan an kaita don bazata basu kunya ba. Ganin matsalan yai yawa ga tashin hankali ga fuskan kowa idan ka duba ya sa na tashi daga inda nake zaune lokacin cikina yai girma sosai wata bakwai saura kwana goma nake. Dakin da take na shiga na samay ta ta kifa kai ga filo ita kadai a cikin dakin tayi buji buji da ita kanta duk a hargitse dashi. Zama nayi bakin gadon don bazan iya tsayi tsaye ba a yadda nake lokacin don karfi hali kawai nakeyi da kaina. Duk da taji anshigo dakin bai sa ta dago daga yadda take a kwance ba cikin yanayin tashin hankali. Cikin yar siriryar murya nace Anty Amira ki tashi muyi magana musan mafita akan wanan al, amarin don kuka ba shine mafita yanzu tunda kinga mama ta kafe akan sai anyi auren nan ba fashi. Jin muryana yasa ta dago kai a cikin fushi tace Bintu for god sake ki barni naji da abinda ya damay ni please ke har wani taimako zaki iya yi min ? Wani matsayi ke gare ki da har zaki dauka zaki iya taimaka min dashi a matsayinki ko don kawai kinga kina auren dan uwana kina juya shi yadda kike so to ni ba shi bane ko maji ki sani. Murmushi nayi kawai nasan ban taba fari a gurin ta amma ni don Allah kawai nai niyar taimaka mata. Nace a fili ba matsala anty ni don Allah nazo gurin ki don mu san mafita kawai idan kina da lokaci ki tashi muyi magana dake mu san abinyi tun ba, a kai maki kayan ki ba a wancan gidan yawan. Wani kallo ta watso min kafin tace ina sauraren ki nace nagode naci gaba da fadin nasan bawai baki son Ibrahim bane a yadda nasan kun dade tare dashi kuna soyayya. Kawai dai wanan matsalace ta gurin zama yasaki bacin rai irin haka sai nake gani idan yace zai canza maki gurin zama duk wanan matsalan zai iya wuce a tsakanin ku tunda soyayya ce ta hada ku ba kiyayya ba. May kike fadi mutumin da ya kafe akan shi baida kudin da zai karasa ginan shi kuma baida wanda zai iya kama min hayan irin gidan da nake so a yanzu. Nace insha Allahu anty idan don gurin zamane na rokeki Allah ki kwantar da hankalinki ayi wanan bukin cikin farinciki. Yadda kowa yazo lafiya don farin ciki ya koma gida da farinciki a ranshi anty baku gaji yin kunya ba a rayuwan ku balle kuji kunya don Allah ni dai yanzu abinda nake so shine ki kwantar da hankalinki ki koma kamar babu abinda ya faru a baya don marasa da suyi kunya don yanzu kinga ido aka sakawa mama aga yaya zata kaya ana farin ciki zaki shiga gida mai kuntatawa. Wani kallone takara watso min tare da cewa wanan shine dama maganan da zaki fada min din. Nace eh anty don Allah tunda kuna son juna da Ibrahim kiyi hakkuri ki daure ayi wanan abin cikin rufin asiri insha Allahu bazaki zauna a wanan gidan ba. Tsuki taja tare da marya da kanta a saman filo tace na zaci wani shawaran arziki kikazo min dashi har na bata lokacina a kanki haka. Na dade a zaune ba tare da tajuyo gare ni ba ga wayan ta dake ta verviration taki dagawa. Wanda nasan ba kowane ke kiranta ba a lokacin sai angwan ta wanda yake a cikin tashin hankalin kan cewan da tayi bazatayi auren ba ta fasa. Nagaji da zama ina batun tashi anty maryam ta shigo dakin kallon mamaki tai min ganina da tayi a zaune ga maidakin ma kamar bata san ina zaune a gurin ba. Tace ke kuma may kikeyi anan ina can ina neman ki mama tace wai wanan kayan kitchen din da aka fitar a mayar dasu a kwali tunda babu inda za, a saka su a gidan. Tajuyo cikin zafin rai daga inda take a kwance idanuwan ta sunyi ja jajir dasu don kukan da tasha sosai. Tace sai naga iban da akewa shirin auren da har ake maganan rage wasu kayan daki can akai badai ni ba. Nikan da kyat na mike tsaye muka fita maryam tana mata dariyar mumuke muka fice. A gajiye na bar gidan don dare yayi a lokacin yaya Sagir ne ya kaimu gida da kan shi don ban driving saboda matsalan cikin dake jikina. Sai da nai wanka nafito falo na samu Iyya tana gyaran abin da zamu karya dashi tana kwaba abin da zatai muna sanasir dashi. Ina zama ana kirana ga waya yaya sadauki ne wanda bai ma kasan yai tafiya a lokacin. Mun gaisa yake tambayana ko mun dawo gida ko muna can gidan su mama har lokacin . Nace mun dawo tun dazun har munyi wanka gani a falo ma zaune zan sha magani na kwanta. Yace maji ta kirani tana fada min iskancin da wanan mara hankalin kewa mutane tun jiya wai ta fasa auren ko ? Nace yaya bafa fasawa tayi ba kune dai baku fahince ta ba bawai bata son Ibrahim bane a, a gidan da za, a kaita ne bai bata ba don a cikin family house din su ne inda uwargidan shi take zaune. Kaga kasan halin anty Amira da tsandan mutane bata son yawan hayani ita tafi son ta zauna koda yaushe silent bata son yawan hayaniya. Ya karba kafin naci gaba da fadin don taita mugun hali ko? Nace haba yaya ya kamata a taimakawa anty please bai kamata abar rayuwan ta a haka ba don Allah. Yace ok yanzi so kike nima na biyewa haukan ta nace a fasa auren taita zaman gida ko? Nace ba nufina ke nan ba yaya abinda nike nufi shine ka taimaka da baiwan da Allah yai ma na falala ka sama mata inda zata zauna don wanan auren nata yai karko kamar na kowa please ? Ban fahince ki ba Fatima kima nifin nine zan bada gurin da Amira zata zauna da mijin ta ko may ? Nace ai ba mijin ka zakaiwa ba yar uwar haihuwan ka zaka taimaka kamar yadda Allah ya taimake ka kaima ka sama mata gurin zama yadda take so. Don yin haka kawai shine shedan dan uwata ya samu kuma mai taimako ne ga jinin shi don kaga ba Amira ba kawai wallahi har mama hankalinta a tashe yake akan wanan magana daurewa kawai mama keyi don ta bata karfin gwiwa amma ran mama baiyi dadi ba ace a wanan gidan za, a kai Amira gaskiya. Yanzun dai na fahince ki yace nine zan aurar da ita kuma na bata gurin da zata zauna kamar na matsu da ita a gida ko ? Nace wallahi yaya ba haka nake nufi ba ni nufi na shine kawai ka taimakawa rayuwan su tunda Allah ya hore ma abinda zaka iya yin haka din. Idan kai haka ba karamin lada zaka samu ba har a gurin Allah don shine shedar zumunci yanzun fa kaine uwar mu kaine uban mu gaba dayan mu har kai. Amira ba ko Nafisa ce da irin wanan matsala din zaka iya taimaka mata idan kaso saboda Allah. Ji nayi ya katse layin tare da jan guntun tsoki haka yasa banji dadi ba a raina nasan bai yarda da shawaran da nake gani shine a matsayin mafita ba ni. Bayan mun gama waya nasha magani na mun dan taba hira da Iyya akan zencen tana fadin ahi yasa ba, a son mutum ya faye bakin hali wallahi don karshen shi baya kyau. Yanzu ga irin ta nan ai tace ita tafi kowa bata ganin kowa da daraja kamar ba mamace ta haife ta ba tafita daban a cikin yan uwa. Nace Iyya kin san kowa da kalar halin shi ita nata rayuwan ke nan haka Allah yayi ta daban. Ai ba za, a biye mata ba idan ana son auren yai karko sai a taimaka mata anyiwa banza ma balle ita. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , , IDAN KIN BIYA KADA KI TURAWA WANDA BAI BIYA BA IDAN KINYI HAKA MUN BARKI GA ALLAH. Alheri sosai ya tanadarwa su Mama da Umma da mummy har motar shiga sai da ya canza masu tare da gyara masu dakunan su tsab. Wanan ya zamo karo na farko da sukaji dadi a ransu abinda taya sadauki yake masu na alheri wanda hassada baya bari suga irin alherin da yake masu abaya. Yanzun ko abu yakai babu gare su duk yadda mutum yai masu alheri komai kankantan shi suna godiya sosai. Don yanzu wanda suke samu gurin shi watau baba shima ta kanshi yake yi baida komai duk diyan su sun wawashe mai shago baida wani abin hannun shi kuma inba gonan da sadauki ya saya mai ba farkon fitan shi wasan kwallo da yafara zuwa. A takure suke komai da suka fi karfi a baya yana basu sha, awa yanzu shi yasa suke ganin wanan kyautan na baya yazo masu kamar kyauta na farko da ya taba masu. Har daki mama Asiya ta samu mama tana mata godiya wanda mama ma a lokacin bata san da wanan alherin ba inba yanzu da mama Asiya tashigo mata da zancen ba. Mama tace ikon Allah wallahi yaya banda labarin wanan zancen yanzun ma nake jin shi a gurin ki. Godiya dai ta karayiwa maji tare da fatan alheri tana ta saka albarka wanda maji ke gani yau kamar a mafalki. Mama Asiya ce sakawa dan ta albarka haka akan alherin da yai mata don jin dadin zuciyar ta. Mama Asiya tana fita har tsakar gida tana godiya Nafisa ta gamu da ita dakin su tashiga gurin mahaifiyarta tana cewa kina nan zaune halan may ya faru naga mama tana ta godiya a waje tafito dakin maji. Umma tace nasan taje godiya ne godiya akan may kuma Umma ? Tace yanzu Sagir ya samay mu da kyautan alherin da yayan ku dan kwallo ya aiko muna dashi mu uku motace ya sake muna da kujerun daki da gadaje sai kudi wai mu saka mai a mota da kayan abinci. Nafisa tace tirkasa amma ko Allah ya saka mai da alheri wallahi to umma shine kike zaune ke baki zuwa kiy godiya? Koda yake yadda naji kina magana kamar har yanzu kin saura hassadan abinda yafi karfin ki fada. Dadai kin sakawa ranki ruwan sayi kibi kici arziki dayafi maki wanan hassadan da kukeyi shekara da shekaru yaki kare. Ga yar uwar munafuncinki ta sulala taje tayi godiya tabarki nan kina hassada ga banza. Kallon takaici taiwa yar tata da suke dauka a matsayin mara hankali ga maganan ta da dabiun ta amma kuma gaskiya ai Nafisa ta fada mata don tasan mama Asiya yanzu tana zare jikin ta tana hurda da al, amarin maji da yayanta. Nafisa kan dakin ta tashige takwanta abinta yanzun ta daina sha sai dai bata bar harkan bazan ta ba da ta saba. Sagir ya shigo ya samu umma zaune tayi tagumi ganin shi ya dan sata sake jikin ta tana mashi tayin abinci. Yace Umma na fada maki yanzu a gidan yaya sadauki muke karyawa ni da Abdul komai dare sai Fatima ta kira mu muzo muci abincin mu yana aje haka ma dasafe. Umma taji wani iri a ranta ba dadi tasan cewa ko ba komai anyi hadin zumunta a gurin kafin takai karshen tunanen ta taji muryan shi yana cewa. Wai ko Umma kin san wani abu fatima fa tai muna kanfen gurin yaya ga sabon gurin aikin da za, a bude a abuja nasu. Shi da kanshi yaya sadauki din ke fada muna cewa wai yar uwar mu ta nuna son kai ta matsa ita sai dai muma a nema muna babban gurbi a can mu kama aiki dasu ko kuma wanda ke nan sokoto. Umma wallahi yadda suke gwada muna halarci irin haka ni abin ma har kunya yake bani yadda a baya mukai ta gwada masu kiyayya a filin Allah . Amma sai gashi yanzu da ya samu mune na farko samun alherin shi harda mota fa yace zai saya muna wallahi. Bamu kadai ba har dasu yaya Imiran naji ana magana a kansu suma za, a basu appointment a gurin. Tace kai amma ko da ya kyauta muna wallahi don zaman banzan nan na Imiran ya fara ista wallahi. Umma yanzun dai jekiyi naki godiyan kafin wani lokaci kuma kin san irin wanan alherin na bazata shi ake kira da kyautan dan aljanna. Kyantan da zaizowa bawa a lokacin da bawa yake a bukace da wani abu a rayuwan shi dubi fa wa yan nan kujerun yadda suka koma kamar tsunma ni har kunyan nake jin azo agansu a dakin nan haka wallahi. Bai bar dakin ba sai da yaga Umma ta mike yaga ta nufi dakin maji hankalin shi ya kwanta. Don bai zai yuyuba ana masu alheri irin haka amma ace su har yanzu basu daina hassadan su ba da sukeyi. ****** ********* ****** Allah mai iko a yanzu ankai duk inda sadauki ya sa kafan shi yana tare da manyan body guard masu tsaron lafiyan shi dana iyalan shi wanda goverment da kansu suka bashi su don tsaron lafiyan shi. Saboda gashi karamin matashi amma yana daya daga cikin manya masu shigo da manyan ababen amfani daga kasashen duniya. Haka yasa ya zamo abin kula sosai a gurin manya na kasa da suke fada aji. Saboda ya zamo daya daga cikin yan kasa masu kishin kasan su don sun cigaban matasa. Gashi akan kamfanin da suke son kafawa har guda biyu na mai dana manyan jiragen ruwa da zasu dinga shigo da kaya daga waje. Ga manyan injima na haska wutan lantarki da za, a shigo dasu kasa don amfanin kamfanonin da za, a gina nan n Nageria. Ban fita sosai zuwa yanzu don cikina da yai matukar girma don ko a wanan ma likitoci sun kara bani bedrest sai dai ba kaman wancan na baya ba danayi na Amir din. Ina kwance saman dogon kujera a falo na dan mike kafafuna na da sukai min nauyi. Yashigo gidan a gajiye dashi su Sagir suna take mai baya shi da Abdul dauke da dan briefcase din takardun shi da laptop dinshi a cikin case din. Ya zauna yana cewa kai nagaji da yawa wallahi nazaci a nan idan na dawo ko zan huta amma gashi duk ba wani hutu da mutum ya samu tare dashi. Na dan lumshe idona tare da kokarin mikewa zaune don na karbi case din zuwa dakin shi. Yace da sauri No No kwanta abinki ki huta barshi idan zan shiga zan shiga dashi ai. Bayan ya karasa kaiwa zaune ne yake cewa duk rashin samun hutu ya saka har kirjina yana min ciwo wallahi. Da sauri na dago ina kallon shi nace amma gaskiya tunda ka fara jin haka ya kamata ka samu hutu ka zauna a gida koda na kwana biyu da zaifi ma. Yace na kwana daya dai Fatima kwana biyu yai min yawa ga mu da tulin aiki mai yawa a gaban mu. Idan ba naga angama gina muna komai ba hankalina bazai taba kwanciya bane ai kinga dukiyar mutane ne nauyin shi ya hau kaina dole na kula masu da abinsu ko? Nafisa ce tashigo gidan da alamun damuwa a fuskanta nan muka zauna da ita ana hira suko abinci suka wuce ci a dining. Yana gamawa ya shiga ciki ya dan jima bai sauko ba yana sama koda zai fito ya sauya kaya jikin shi a lokacin. Tun bai kai zaune ba ya soma magana yana cewa gaskya kauna ya kamata ace kifito da miji hakana kiyi aure na hada ku da Amira dama yan sa, a daya kuke kinga kowa sai ya huta abar Rukaiya har su karasa nasu karatun. Cikin wani langabe kai tace ni yaya wama zai aure ni kawai ni na fitar ma da rai ga wani aure can Da sauri nace haba anty ce astangafurullahi mana yaya zaki magana kamar ba musulma ba dake. Tace to madam wakike gabin zai aureni a haka yadda nake duk masu zuwa gurina ba da sunan aure suke zuwa min ba sai dai da tasu bukata kawai. Gaba dayan mu tausayi tabamu ga maganan ta don mun san cewa gaskiya ta fada maganan ta. Amma kuma ai abin Allah ba a yanke kauna a gare shi nace anty gaskiya yaya ne ki natsu ki rage wasu halaiyar ki ko Allah zai tausaya maki. Don kinga ai Allah miskaraziratin ne ba abinda ya gagari ubangiji sai kinyi mamakin irin mijin da Allah zai kawo maki idan kin natsu. Kafin tabani amsa wayan ta yai kara jin sunan wace ta kira da Raye yasa na gane da Raiha take waya a lokacin. Tambayan ta tayi tana ina tabata amsa da cewa gani nan gidan su madam ina shan sanyin A C. Tabata amsa da gata nan tafe tana gamawa yake ce mata kinga ni maganan ki bawai ya karbu bane gareni fa kiyi tunane a kai ki gyara halaiyar ki Nafisa . Mace fa dan guntun lokaci ke gareta tun anayi daku watarana masu neman naku gudu za, suyi su koma ga wasu yan matasan Ta amsa a marairaice da tau naji yaya insha Allahu zanyi kamar yadda kace amma zaka dinka min hijjabbai na fara sakawa ko? Murmushi yayi yace gatanan yana nufin ni zata dinka maki ko guda nawa kike so kaunata. Nidai kawai ki natsu ki daina wanan halin please. Shigowan Raiha ne yasa muka daina zancen suka gaisa da shi ya mike zuwa babban falon shi na waje da yake taron baki a cikin sa yabar mu nan zaune a na cikin gida da waya a hannun shi yanayi. Nan muka fara hira dash nake tambayan Nuriya suke ce min wai tabi wani saurayinta dan Ibo sun tafi lagos tare. Banji dadi ba na kasa boye bacin raina nake cewa haba dai haba ace kuma mutum yana hurda da harda wanda ba musulmi ba kuma ai abin yayi muni gaskiya. Raiha tace madam kawai dai Allah ya gafarta muna zamuce don dai gaskiya nima yanzu da hankali yafara zo min na gane hakan ba daidai bane. Ni yanzu fatana kawai Allah ya kawo min miji wanda zai soni tsakani da Allah wallahi ko yaya yake zan zauna dashi na natsu bakiga yadda al, amarina har yasakawa iyayyena cutan hawan jini ba. Tace to mazan ne yanzun sai a hankali wallahi na rasa wanda zaizo ma da tsigar so na gaskiya bada bukata ba. Nafisa tace maganan da muka gama ke nan da yayana kafin ki shigo abinda na fada mai ke nan kema yanzu sai gashi kinzo dashi. Tace wallahi muna son auren bawai bamu so bane to amma wazaka aura shine matsalan. Istigifar bai bar komai ba ku koma ga Allah kwana biyu kuga ikon Allah wallahi bana jin dadin irin wanan rayuwan da kukeyi yanzu ya kamata ace kunyi wa kan ku fadan hakan. Shi yasa nake son ki madam wallahi kece kawai zan iya cewa a yanzu kina tsayawa ki nusar da mutum hanyan alheri bayan kowa ido yakawo ya saka muna. Ana jiran da garin Allah ya waye kai wani abin asha asakaka ga faifai a tallata ka. Yaya sadauki ne yashigo yana ce min sai ki shirya don muna da bakin da zasu duba gurin da za, a gina kamfanin shimkafa a garin nan Gashi sunce min ba, a hotel zasu sauka ba anan gidan zasuyi masauki don haka sai ki samo wanda zasu yi aikin abinci idan kuma bayarwa zakiyi ai masu duka daya. Kafin ma ya karasa zancen shi sai cewa Raiha tayi bagamu ba yaya aikin may mukeyi dabaza mu yi ba mu. Baiyi magana ba don na lura hankalinshi bai kwanta da al, amarin Raiha din ba wanda shine bai fahince ta ba sauki kaine da ita sosai. Amma shi yana ganin sune suke jefa yar uwarshi a cikin wanan mumunan harkan da sukeyi tare. Bai san tafi su zama shedaniya ba don ita ta hure fitillar ta sosai ma fiye dasu. Mun jima dasu muna tatauna abinda ya dace muyi da wanda zamu saya na bukatun mu. Har sai bayan sallah magariba suka tafi mukai sallah suna cewa idan an shirya na kirasu. Bayan yashigo gidane yake fada akan cewa may zaisa na yarje ma wa yan nan mashiririta suyi mai aikin abincin bakin shi yaushe ma suka zauna balle su san yadda ake girki su. Nace haba yaya sai kace ba mata ba su gani kuma ga iyya a gurin ai zamu taimaka masu da wani abin. Yace da sauri No no kada ki soma cewa zakiyi aikin komai kin dai san yadda condition din ki yake please kada ki fara ki taba komai idan ma bazasu iya ba sai a kira wasu suyi final nace ballema insha Allahu zasu iya duk abinda suka lissafo zasuyi din. Bai kara magana ba haka muka bar zancen don yaga na aminta dasu sosai yasa ya kyale badon yaso ba. Izuwa yanzu alherin da sadauki yaiwa iyayyena bazan iya lisfoshi ba don muna waje sun tafi sun sauke farali ga gyaran gida da abin sana, a da ya sayawa kowan su a sanadiya na iyayyena da yan uwana sun fita a cikin talauci yanzu wanda hakkurina da biyayyana ne yajawo muna wanan alherin haka. H Yan uwa dama yan garin mu sukan zo neman alheri a gurina wanda nakan yi masu shi gwargwadon halina. Lokacin zuwan bakin shi yayi bayan sati ya zagayo yabani kudi masu yawa akan abubuwan bukatan su. Ban masu kyata ba na ba kudi fiye da wanda za, a kashe sosai suma su karu daga ciki suka shiga kasuwa saywn abubuwan bukata duk da wasu muna dasu a gida. Ranan har anty maryam da Rukaiya sai da suka zo da mummy tare akai aikin komai dasu na fita kunyan baki yadda ya dace sai da aka hada abinci kusan kala goma sha biyu nau,i daban daban suka kara gyara katon falon muna na baki an saka kamshi da komai a falon yadda ya dace ayi. Bakin basu shigo gida ba sai misalin karfe uku na rana dirin motocin da mukajine yasa muka gane cewa gidan mu ya dauki manyan baki yau don har dasu jiya da alaman akwa wasu manyan kusa a cikin su ke nan. Nan aka shiga fito da kayan ci dasha bayan wanda aka kai masu da farko wa drivobin su. Gida ya rude da hayaniya sai kai da komo su Anty Nafisa sukeyi a gurin ana yaba aikin da sukayi. Allah da ikon shi a wanan sanadin Allah ya hada su da masu son su a gurin sukai wa yayan su magana kan ya basu kannen shi din nan yace yabasu. Wasa wasa magana ya zama babba don ita Nafisa ta hadu da wani ustazune manager din wani babban company dake garin Abuja. Ita ko Raiha wani sojane babba wanda gwaunati ta turo shi as a security guard na kasa ya kyasa mata. Amira da mama tace tazo ta taya mu aiki tace ita ba yar aikin kowa bane ba inda zata tafi nan mama ta ganta ta kyaleta. Amma daga baya da taji sun ba da tukwaicin dubu dari biyar wa masu aiki sai kuma ta shiga fada tana ganin laifina Wai dama ni yar bakin cikine shiyasa na gaiyato yan iska su cika min gida shiyasa ita bata tafi ba. Karshe kuma sai ga zancen auren Nafisa da Raiha da taji Allah ya hadasu da wasu manya sai dai ba yara bane su. Nan kuma ta shiga zage zage kamar mahaukaciya wai ta yarda ni yar bakin cikine ta karshe sosai don ban son ta da arziki nafi bukatan komai sai a gani a gurina kawai. ****** ********* ****** Bukin anty Amira ya taso sosai ba kama hannun yaro don haka muke ta zirga zirga ba hutu don mu ke gudanar da komai akan bukin duk da gwatsale ni da takeyi tana nuna bata bukatan saka hannuna acikin al, amarinta sam. Hakan bai sa na daina duk wani abinda nake da niyar yi ba don ba don itace nakeyi ba dama don Allah nakeyi da mijina da kuma mahaifan su. Bata san ina da rana a gare ta ba sai da masu zuwa ganin dakin da za, a saka mata kaya sukaje suka dawo da labari mara dadi don ashe a family house za, a aje ta. Kuma ga dakunan ba wasu dakuna bane maigirma a jere suke ita da uwargidan ta wace yar uwace ga mutumin da zata aura. Da labarin yazo ba karamin tayar da hankalin ta tayi ba sosai nan ta tuburewa mutane akan Ibrahim ya cuce ta don cewa yayi gida zai kama mata haya don may yazu zaice a gidan su zai aje ta. Sosai ta tayar da hankalinta akan bazatayi auren ba ta fasa hankalin mama yai matukar tashi gashi an gama komai akan shirin buki ga yan uwa na nesa har sun fara hallara a gurin bukin. Kuka wiwi takeyi akan ita kan wallahi ta fasa sai dai akai wata ba ita ba don bazata wanan gidan da ake bada labarin shi ba babu tsari. Mama kuma da yan uwa sun kafe kan lalai sai anyi auren nan sai dai ta mutu idan an kaita don bazata basu kunya ba. Ganin matsalan yai yawa ga tashin hankali ga fuskan kowa idan ka duba ya sa na tashi daga inda nake zaune lokacin cikina yai girma sosai wata bakwai saura kwana goma nake. Dakin da take na shiga na samay ta ta kifa kai ga filo ita kadai a cikin dakin tayi buji buji da ita kanta duk a hargitse dashi. Zama nayi bakin gadon don bazan iya tsayi tsaye ba a yadda nake lokacin don karfi hali kawai nakeyi da kaina. Duk da taji anshigo dakin bai sa ta dago daga yadda take a kwance ba cikin yanayin tashin hankali. Cikin yar siriryar murya nace Anty Amira ki tashi muyi magana musan mafita akan wanan al, amarin don kuka ba shine mafita yanzu tunda kinga mama ta kafe akan sai anyi auren nan ba fashi. Jin muryana yasa ta dago kai a cikin fushi tace Bintu for god sake ki barni naji da abinda ya damay ni please ke har wani taimako zaki iya yi min ? Wani matsayi ke gare ki da har zaki dauka zaki iya taimaka min dashi a matsayinki ko don kawai kinga kina auren dan uwana kina juya shi yadda kike so to ni ba shi bane ko maji ki sani. Murmushi nayi kawai nasan ban taba fari a gurin ta amma ni don Allah kawai nai niyar taimaka mata. Nace a fili ba matsala anty ni don Allah nazo gurin ki don mu san mafita kawai idan kina da lokaci ki tashi muyi magana dake mu san abinyi tun ba, a kai maki kayan ki ba a wancan gidan yawan. Wani kallo ta watso min kafin tace ina sauraren ki nace nagode naci gaba da fadin nasan bawai baki son Ibrahim bane a yadda nasan kun dade tare dashi kuna soyayya. Kawai dai wanan matsalace ta gurin zama yasaki bacin rai irin haka sai nake gani idan yace zai canza maki gurin zama duk wanan matsalan zai iya wuce a tsakanin ku tunda soyayya ce ta hada ku ba kiyayya ba. May kike fadi mutumin da ya kafe akan shi baida kudin da zai karasa ginan shi kuma baida wanda zai iya kama min hayan irin gidan da nake so a yanzu. Nace insha Allahu anty idan don gurin zamane na rokeki Allah ki kwantar da hankalinki ayi wanan bukin cikin farinciki. Yadda kowa yazo lafiya don farin ciki ya koma gida da farinciki a ranshi anty baku gaji yin kunya ba a rayuwan ku balle kuji kunya don Allah ni dai yanzu abinda nake so shine ki kwantar da hankalinki ki koma kamar babu abinda ya faru a baya don marasa da suyi kunya don yanzu kinga ido aka sakawa mama aga yaya zata kaya ana farin ciki zaki shiga gida mai kuntatawa. Wani kallone takara watso min tare da cewa wanan shine dama maganan da zaki fada min din. Nace eh anty don Allah tunda kuna son juna da Ibrahim kiyi hakkuri ki daure ayi wanan abin cikin rufin asiri insha Allahu bazaki zauna a wanan gidan ba. Tsuki taja tare da marya da kanta a saman filo tace na zaci wani shawaran arziki kikazo min dashi har na bata lokacina a kanki haka. Na dade a zaune ba tare da tajuyo gare ni ba ga wayan ta dake ta verviration taki dagawa. Wanda nasan ba kowane ke kiranta ba a lokacin sai angwan ta wanda yake a cikin tashin hankalin kan cewan da tayi bazatayi auren ba ta fasa. Nagaji da zama ina batun tashi anty maryam ta shigo dakin kallon mamaki tai min ganina da tayi a zaune ga maidakin ma kamar bata san ina zaune a gurin ba. Tace ke kuma may kikeyi anan ina can ina neman ki mama tace wai wanan kayan kitchen din da aka fitar a mayar dasu a kwali tunda babu inda za, a saka su a gidan. Tajuyo cikin zafin rai daga inda take a kwance idanuwan ta sunyi ja jajir dasu don kukan da tasha sosai. Tace sai naga iban da akewa shirin auren da har ake maganan rage wasu kayan daki can akai badai ni ba. Nikan da kyat na mike tsaye muka fita maryam tana mata dariyar mumuke muka fice. A gajiye na bar gidan don dare yayi a lokacin yaya Sagir ne ya kaimu gida da kan shi don ban driving saboda matsalan cikin dake jikina. Sai da nai wanka nafito falo na samu Iyya tana gyaran abin da zamu karya dashi tana kwaba abin da zatai muna sanasir dashi. Ina zama ana kirana ga waya yaya sadauki ne wanda bai ma kasan yai tafiya a lokacin. Mun gaisa yake tambayana ko mun dawo gida ko muna can gidan su mama har lokacin . Nace mun dawo tun dazun har munyi wanka gani a falo ma zaune zan sha magani na kwanta. Yace maji ta kirani tana fada min iskancin da wanan mara hankalin kewa mutane tun jiya wai ta fasa auren ko ? Nace yaya bafa fasawa tayi ba kune dai baku fahince ta ba bawai bata son Ibrahim bane a, a gidan da za, a kaita ne bai bata ba don a cikin family house din su ne inda uwargidan shi take zaune. Kaga kasan halin anty Amira da tsandan mutane bata son yawan hayani ita tafi son ta zauna koda yaushe silent bata son yawan hayaniya. Ya karba kafin naci gaba da fadin don taita mugun hali ko? Nace haba yaya ya kamata a taimakawa anty please bai kamata abar rayuwan ta a haka ba don Allah. Yace ok yanzi so kike nima na biyewa haukan ta nace a fasa auren taita zaman gida ko? Nace ba nufina ke nan ba yaya abinda nike nufi shine ka taimaka da baiwan da Allah yai ma na falala ka sama mata inda zata zauna don wanan auren nata yai karko kamar na kowa please ? Ban fahince ki ba Fatima kima nifin nine zan bada gurin da Amira zata zauna da mijin ta ko may ? Nace ai ba mijin ka zakaiwa ba yar uwar haihuwan ka zaka taimaka kamar yadda Allah ya taimake ka kaima ka sama mata gurin zama yadda take so. Don yin haka kawai shine shedan dan uwata ya samu kuma mai taimako ne ga jinin shi don kaga ba Amira ba kawai wallahi har mama hankalinta a tashe yake akan wanan magana daurewa kawai mama keyi don ta bata karfin gwiwa amma ran mama baiyi dadi ba ace a wanan gidan za, a kai Amira gaskiya. Yanzun dai na fahince ki yace nine zan aurar da ita kuma na bata gurin da zata zauna kamar na matsu da ita a gida ko ? Nace wallahi yaya ba haka nake nufi ba ni nufi na shine kawai ka taimakawa rayuwan su tunda Allah ya hore ma abinda zaka iya yin haka din. Idan kai haka ba karamin lada zaka samu ba har a gurin Allah don shine shedar zumunci yanzun fa kaine uwar mu kaine uban mu gaba dayan mu har kai. Amira ba ko Nafisa ce da irin wanan matsala din zaka iya taimaka mata idan kaso saboda Allah. Ji nayi ya katse layin tare da jan guntun tsoki haka yasa banji dadi ba a raina nasan bai yarda da shawaran da nake gani shine a matsayin mafita ba ni. Bayan mun gama waya nasha magani na mun dan taba hira da Iyya akan zencen tana fadin ahi yasa ba, a son mutum ya faye bakin hali wallahi don karshen shi baya kyau. Yanzu ga irin ta nan ai tace ita tafi kowa bata ganin kowa da daraja kamar ba mamace ta haife ta ba tafita daban a cikin yan uwa. Nace Iyya kin san kowa da kalar halin shi ita nata rayuwan ke nan haka Allah yayi ta daban. Ai ba za, a biye mata ba idan ana son auren yai karko sai a taimaka mata anyiwa banza ma balle ita. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , , , , IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH , , , , Washegari da kyat na shirya muka kwasa saigidan su mama gurin shagalin bukin da akeyi na samu yan uwan mama saura sun iso nan na shiga gaisawa dasu cikin mutunci da girmamawa. Na samu guri na kai zaune don indan huta saboda tafiyan da nayi sai ga mama ta fito daga cikin dakin ta tana ganin mu tace , a, a kun karaso ashe. Nace eh mama nai mata ina kwana tare da tambayan ta ya gajiyan jama, a ta amsa da fara, a da alhamdullahi. Maryam ta rigani isowa sai gata tafito da alama a tare da mama suke a dakin. Nan muka shiga gaisawa da ita tana min ba, a wai bata tsanmani ta gannin ba yau yadda na gaji da jigila jiya. Muryan mamane mukaji tana cewa Fatima ke da maryam kuzo ba bata lokaci muka bi bayan mama din data shiga dakin ta. Zama tayi saman kujera yayin da ta umurce mu da zama a bakin gadon ta sai dai kafin mu kai ga zama tace maryam kira min wanan yar butsar maryam tace wa anty Amira? Mama tace ita mana a takaice maryam din ta fita ta barmu ni da mama a dakin sai dai babu wanda yai magana a cikin mu dagani har mama din har suka shigo dakin. Kowan su guri ya samu ya zauna muna sauraren abin da mama din zata fada muna. Fatima dafarko dake zan fara abinda ta fada yasani saurin dago kaina da sauri na dan kalle ta sai kuma nai saurin mayar da kaina a kasa. Tace ban san irin godiyan da zan wa Allah ba da yahadani dake a matsayin diya kuma sarakuwa ta gari a cikin zuria ta. Fatima ke alheri ce a gare mu abin alfaharin kasancewa a cikin zurian gidan nan a baki daya. Jin yadda mama take yabona bamu san dalili ba dukan mu yasa Amira saurin daga kai tana kallon mama da mamaki may yakawo wanan yabon haka ne wai. Mama taci gaba da fadin fatima kin yi abinda ko wace sarakuwa take gurin gani ga ko samu ga matar da danta ya aura a cikin zurian ta. Nasan baku san abinda yasa nake mata wanan yabon haka ba sai na fada maku. Yau da asuba yayan ku ya kirani yake fada min cewa Fatima ta kirashi a cikin tashin hankali tana mashi magiya kan lalai sai ya sayawa Amira gida nata na kan ta inda zata zauna. Yamzun dai in takaice maku tsohon gidan shi daya gina ya tashi a ciki ke maryam na kusa daku ya mallakawa Amira shi halal malak. Ke kuma yace idan ya dawo za, a duba gida kwatankwancin wanan din ko ya gina maki naki a matsayin naki kema maryam. Gaba daya sukayo kaina da murna suka rike ni nayi mamaki yadda yau Amira ta sauko haka lokaci daya kan abin duniya. Tace cikin muryan kuka Bintu ban san godiyan da zan maki ba duk da dai bake ya kamata naiwa godiya ba amma kuma ke ce silar hakan. Nace anty babu godiya a tsakanin mu don ku yan uwa nane na jini dole mu taimakawa junan mu idan ya dace amatsayin mu na uwa daya uba daya duk dai ni din bare ce acikin ku amma banda uwa da uban da suka fi min baba da mama a duniya har lahira don sun min komai a rayuwana nakarasa a cikin kuka nace don may nima bazan dinga kokarin gani saka dan uwan mu a hanya ba tunda Allah ya hore mai abinda zai kula damu. Fatima mungode da wanan karamcin don ba kowane akewa alheri ya samu ya tuna baya ba haka. Yayan ku ya fada min baki taba rokon shi da ya taimakawa kowa naki ba a duniyan nan ba sai idan shi yaga ya dace yai masu wani abin. Amma mu sai gashi kina ta iya kokarin ki gurin ganin ya kyautata muna nasan ko alherin da yaiwa iyayyen shi kwanaki shawaran kine wanan. Nan dai mama ta kara ja muna kunne na mu hada kan mu da zurian mu koda bayan ta don haka shine tabbacin dauruwan zumunci mai karko. Nan dai muka dan taba hira akan yadda za, a bullowa al, amarin bukin da saura kwana daya a saka lalle. Nice nace mama yanzu shi Ibrahim din ya kamata mu kira muji tashi shawaran ko zai yarda da hakan ko ? Da sauri anty Nafisa take cewa kamar yaya zai yarda idan bai yarda basai a fasa ba don ni wallahi Allah ban zama a wanan gidan nasu na yawa. Kinji halinki ko inji mama ta fada a cikin fada da sauri na tare nace anty don Allah kibi al, amarin nan a sanu shi fa sauri baya haihuwan alheri ke da Ibrahim dai kuna son junan ku baida shine ne anty yanzun kuma tunda Allah ya hore mai ai ba zaiki ba ko. Abar maganan a hannun yaya shi yasan yadda zai bullo mashi da maganan don kin ga wanan magana ce ta maza. Haka yasa kowa yai shiru dakin don sun san magana ta gaskiya ne mama tace mu tashi mu tafi shi ke nan . Maryam da ta riga mu mikewa take cewa sai muje gidan muga abinda ya dace ayi ciki ko don kayan dake ciki yaya za, ayi dasu kuma ? Nace wanda za, a cire aba su mama Abu mana bashi ke nan ba sai dai kwasan su daga nan zuwa can ne aiki ai inji maryam nace ba wani aiki da anyiwa yaya bashar magana suna da manyan motoci sai a kwasa akai masu har gida. Mama kan dadi ya hanata magana don bats san may zata fada kuma irin wanan alherin haka samun dan uwa shine samun kowa ai namike ina fadi nabar dakin. Kamar yadda muka tsara din ina fita na kira yaya akan yaiwa ibrahim din maganan tare da kuma yi mashi godiya sosai. Yace haba queen nine fa ya kamata na gode maki bake ba kin kuwa san irin albarkan dana sha kan wanan zancen gurin mahaifa na. Idan baki halkantar dani ba hakan yaushe tunane na zai barni na kai ga tuna hakan da akayi kinga ai yanzu an wuce gurin ko? Ya kira ibrahim din yai mai magana tare da bukatan idan ya dawo ya kawo takardun shi zasu samu ida suka sakashi a maikatar su. Ya tun kari mahaifiyar shi da maganan taso ta musa mashi amma a hankali ya fadakar da ita alherin dake cikin yin hakan dole ta yarda data ji cewa harda aiki za, a sama mai. Karshe cewa tayi ya daiyi adalci a tsakanin iyalin shi yace insha Allahu mama. Shi da kanshi yazo har gida da yamma yai muna bayanin amincewar mahaifiyar shi a kan zancen wanda dama muke hasashen matsalan komai daga gare ta ne don bata son yabarsu. Ba bata lokaci aka tafi gidan tare da masu gyaran guri decoration din gida mun masu bayani komai yadda zasu gyara mata shi wanda a shagona aka sayo duk kayan da aka saka mata a gidan na miliyoyin naira. Sosai akai ta shagalin bukin da har su Umma ance mai hali baya barin halin shi har sun fara gulma akan zancen. Amma da sukaji gidan sadauki tsoho za, a aje Amira kuma ba gidan iyayyen mijin ta ba sai kuma sukai gum. Anyi angama lafiya shima sadauki ya dawo ran daren daurin aure sune suka shugabanci bukin. Amarya ta tare gidan ta lafiya kowa sai murna da farin ciki yakeyi yadda dan uwanta ya kashe mata kudi haka na. ****** ********* ****** Bayan buki da kwana biyune na tashi ban jin dadin jikina nasan dan jigilan bukin da mukasha ne dole naji ba dadi haka dama don yawancin event din ma a gidana akayi shi. Gashi washe gari yaya zai koma Abuja gurin aikin su don yanzu sam baida lokaci ko kadan yanzun ma don shagalin bukine ya dan dauki hutun kwana hudu kawai. Har yafita motsa jikin shi wanda yanzu bai faye fita waje ba yi akwai kayan motsa jiki kala kala da ya sayo yakeyi saboda tsaro. Kwance ya samay ni yarda ya fita ya barni da farko yana cire rigan jikin shi hankalin shi yana akaina. Lafiya kike kuwa har yanzu baki tashi ba karfe kusan tara fa yanzu na safe. Na dan bude idanuwana da sukai min nauyi nace a hankali wallahi ban dai jin dadin jikina ne sosai yace zan shiga wanka hada min abincina kafin nafito ina son zuwa gurin baba ne nagan shi. Da kyat na samu na mike zaune yana shiga bathroom din lokacin na sako kafana kasa da zuman na mike tsaye. Yadda naji an tokare ni ban san lokacin dana sake yar kara ba na koma na dunkule guri daya. Jin karan da nayi ne yasa shi saurin fitowa daga bathroom hankali a tashe yana tambaya cikin kidimaywa may nene may ya faru ne wai ? Cikin daure wa nace ba komai bane mara nane kawai ya yanka min da dan ciwo. Yace oya mike mugani aiko mikewa ya gagareni na sake jin an kara yankoni kasan marana da karfi na sake wani dan kara again. Yace cikin rudewa O god kingani ko ina ta fasa maki cewa kiyi a hankali kin san condition din ki amma duk baki jiba yanzu gashi zaki jawowa kanki matsala kuma. Yace barin watsa ruwa sai muje asibiti a gani ko may nene matsala ya juya yana min sannu ya shige bathroom da kyat na samu na mike zuwa dakina. Dakyat nake iya daga kafana zuwa daki ina shiga kamar an kara min ciwon maran ne a lokacin. Tsaye nayi na dafa mirrona ganin abin ba na wasa bane yasa na dan duka a gurin wasa wasa nakai durkushe cikin tsananin ciwon mara dake damuna. Shigowan shi yana fadin kin shirya mu tafine yai arba dani cikin wani hali sai zufa ke karyo min tako ina da sauri ya karaso inda nake duke yana fadin subbahanallahi. Abinka ga geant din mutum ya yunkura zai dauke ni da sauri cikin wani murya nace mai ya dakata don Allah. Ido ya kura min daga gurin da yake tsaye yana kallona danaji abu tafe min ban san lokacin dana rike shi gam ba iya karfina na nisa da karfi sai ga yaro ya fado kasa rikon da nai mai duk da karfin shi sai da yaji shi sosai a jikin shi. Ganin yaro ya fado ne yasa na dan sasauta rikon ina mayar da numfashina a hankali take yarude hankalinshi ya tashi sosai. Ga yaron yana ta faman tsala ihu a kasa saman ties na nuna mai zanina dake gefe ya miko min na saka yaron a ciki. Shi kuma yafita daga dakin da sauri hankali a tashe yana kwallawa iyya kira cikin tashin hankali. Iyya tafito dakin da sauri hankali tashe ganin yadda ya rude bakin shi na rawa yake fadin don Allah Iyya shigo da sauri ki taimakawa Farima ta haihu yanzu a dakin ta. Haihuwa Alhaji haihuwa fa takara fadin hakana cikin sauri ta nufi dakin hankalinta a tashe sosai takaraso inda nake tsugune. Reza take fadi nace tabude drower akwai reza a ciki da sauri ta dauko ta yanke cibin yaron dake ta faman kuka cikin zani. Ta juyo inda nake tana fadin sannu uwar dakina ke kuma haka haihuwanki yake wata bakwai. Tsab tagyara ni ga gyara yaron shi yana falo ya kasa zama kuma tsoro ya hana shi ya shigo daga ciki. Yana ganin iya tafito diban bakin sabulun da ta hada a dakin ta ya tare da sauri yana fadin. Iyyya yaya dai tana lafiya ko kuma yaron zai rayu kuwa yana ma dai rai kuwa ? Tace insha Allahu zai rayu ba haka ta haifi magidana ba yau bagashi kamar zakaran turawa ba. Haka nata haihuwan yake wata bakwai take haihuwa ita ke nan. Ya sauke ajiyan zuciya nan ya jawo waya yashiga fadawa su mama can gida. Yan uwan mama dake shirin tafiya suka tanbaye ta da sukaji tana fadin ikon Allah ta haihu fa kace yace wallahi ko mama yaro namiji ta haifa. Nan kuma gida ya rude kowa yana mamaki suna tausaya min sai cewa suke yi boyar Allah bata zauna ba duk jigilar bukin nan da ita akayi shi ashe tana jin abinda take ji a ran ta . Nan aka kwaso zuwa gidan mu ba bata lokaci kafin duk su iso maryam ta riga kowa zuwa ta samay ni na fito wanka ina saka kaya a jikina. Tace madam haka kuma abin ya kasance dake ashe ta nufi inda yaron yake dan karami dashi ta dan bude zanin da iya ta nade shi a ciki tana kallon shi. Tace wanan ai duk Amir ne aje wallahi duk uban su suke kwasowa yaran basu biyo ki. Nai murmushi ina kaiwa zaune nace yafini karfin jini ne shiyasa hakan tace yadai fiki kwazo ragguwa kawai nace nadai ji. Shigowa yan gida yasa gida ya kara rudewa lokaci guda sai sannu suke min. Yace wa mummy sai mu tafi asibiti aji idan na shirya don a duba yaronkuma aga lafiyan shi. Dole haka na fito muka kwasa sai asibiti ni dashi da mummy da maryam. Anyi duk aune aunen da za,ai muna antabbatar dagani har yaron muna da lafiyan mu. Haka yasa hankalin shi ya kwanta sun so wai a aje yaron amma mummy bata ba da surport ba kan hakan muka dawo gida. Nan kuma na fara jego ba shiri don haihu a bazata sosai ake kulla da yaron yadda aka kafa muna doka akan shi. Wanka sau daya ake mai a wuni koshi ba kamar yadda akewa sauran yara ba towel ne za, a dan dinga jikawa cikin ruwa dumi ana goge shi dashi a hankali wanda mummy ce keyiwa yaron . Babu mai daukan shi don wasu saboda kwakwafi sai suce abasu yaron su gani. Mummy ta hana ko mama Asiya dake zama da dare a gurin mu nan take kwana a tare da mu. Naga yan uwa da abokan arziki masu zuwa barka don wasu ma ba sanin su nayi ba . Shiko sadauki duk hankalin shi bai kwanta ba yana ganin yaron zai mutu ne ba zai rayu ba. Ranan suna yaro yaci sunan mahaifin Umma watau Abdullrahaman nima sunan nawa mahaifin ke nan amma shi Abdullahi yake. Sai da komai ya koma normal ne ya samu komawa gurin aikin shi tare da jaddada muna akan mu kula da yaron wanda a hankali yake ta hiling. Nan dai komai ya koma normal a gare mu anyi auren su anty Nafisa wanda mijin dake son ta ya bukaci anyi da wuri sadauki ne ma yadan ja lokaci don ta samu tayi istibira,i kafin auren. Nan ta dawo gidan mu ta zauna kafanta kafana ko tafiya zanyi tare muke zuwa da ita. Har Allah ya taimaka tagama aka saka ta lalai muka sha buki muka kaita kano gidan Iyayyen mijin ta muka barta can. Mutane ne masu matukar addini da sanin darajan bako don ko sun daraja mu sosai ga abin arzikin da mukaje mata dashi sai dai ita a Abuja zata zauna a can mukai mata jeren kayan takayan gara ne kawai muka kai kano gidan mijin ta. Ko a kanon ma an gyara mata dakin ta na can kano din sosai komai acan acan dashi. Bayan kamar wata hudu akai bukin Raiha aka kaita maiduguri gidan mijin ta shima dai a Abujja yake aikin shi na soja. Itama dai zama tare yasa sadauki ya taimaka mata sosai don yai mata goma na arziki sai da tai kuka don murna. Iskancin su bai bari sun aje komai ba na kasan su sai iskanci da bushasha kawai suka saka agaba ashe. Itakan Nuriya bata da ranan aure a rayuwan ta cewan ta ai aure tauye rayuwane kawai ba incin kai. Wanan dalilin yasa na daina hurda da ita don naga bata da alaman kintsuwa tare da ita. Ko tazo bani ma bari ta gan ni har tagaji ta daina zuwa dama don Nafisa muke mutunci yanzu kuma Allah ya rufa mata asiri takama kan ta. Nan dai al, amarin sadauki ya bunkasa ya zama daya daga cikin miloniyan matasa na kasa masi fada aji yanzu. Yarana sunyi wayo sai masu kyau dasu kamar diyan turawa gashi bamu faye zama kasan ba ko yaushe muna kasan waje tare dai da iyya muke tafiye tafiyen da mukeyi don kula da yaran mu. Na kara samun wani ciki shima da namiji na kara haihuwa wanda naso ace diya mace na samu don ina son diya mace a rayuwana sosai. Sunan shi ya sakawa yaron sai dai duk yafisu zatin girma sosai. Gaba dayan su yaran kamar su daya idan ka gansu gwanin ban sha, awa dasu ga kula suna samu sosai dani dasu a gurin mahaifin su. Naso ace na huta hakanan wanan karon amma sai dai ina sai kuma ga wani cikin ya kara samuwa again. Na tayar da hankalina sosai kan hakan amma babu yadda zanyi dole na hakkura dashi. Don ya bata ranshi kancewan da nayi zan zubar da cikin har karana yakai gurin mama inda tai min fada sosai dole na hakkura takuma ce na bashi hakkuri. Na bashi hakkuri amma sai da yai min fada yana cewa wai kila shine banso yasa nake gudun haihuwa dashi yanzu. Nace haba yaya idan ban son ka wa zanso kawai dai naga abin ne ba hutu ko yaushe daga goyo sai ciki nasone kawai na dan huta har gaba. Yace basai ki jira gaban ba amma ciki ya zama rai don baki da imani zakice wai a zubar dashi akan may zan biye maki muyi kissan kai a tare. Nace ni dai ayi hakkuri abar zancen hakana tunda ankai karata gurin mamana har tai min fada. Ikon Allah wanan haihuwa ban haihu wata bakwai ba kamar sauran sai da cikin ya cika wata tara da dan kwanaki na haifo yar diyata mai kama dani sak. Yana shigowa dakin ya kalli yarinyar yaji wani sonta ya matukar shiga ran shi sosai a lokaci daya. Yadauke ta ya rugumay ta ajikin shi yana mai jin dadi a ran shi take ya kira yarinyar da uwata nan nagane sunan mama ke nan yarinyar taci. Ranan suna aka rada mata hauwa, u suna kiranta Ummi kowa na gidan. A ran daren suna ne jikin baba ya motsa mai akatafi asibiti dashi amma kafin safe yace ga garin ku. Allah yasa sadauki yana gari a lokacin don haka yayi sa, a a hannun shi kamar yadda baba ke da gurin ya cika dan shi na gari. Allah ya karba mai ya rasu a gaban shi cikin yadda ake son ko wani musulmi ya cika da kyau da imani. Sai bayan sun yi sallah asuba ne suka fara sanar da yan uwa da abokan arziki rasuwan baba din. Ya bugo waya ya sanar da mu ni da kaina najamu zuwa gida hankalin mu a tashe don rashin da akai muna. Take gida ya cika fam da yan uwa nesa dana kusa an kawar da baba akai zaman kwana uku kowa ya watse. Baba ya tafi ya bar iyalin shi a cikin rashin jittuwa a tsakanin su yadda yaso. Sai bayan sati biyu ne aiko yaya Ahmed ya tayar da kayan baya akan a raba gado abashi nasa. Haka ya kara tayar wa kowa da hankali sosai lokacin sadauki baya gari amma an buga mai waya yace abari yazo. Amma yaya Ahmed da matar shi ta zugo shi yace bai san wanan ba dole araba ai sadauki ba girmuwar shi yayi ba. Haka ne ya tunzura ran sadauki yace ana iya rabawa amma banda gida da gona don baba ya sayar mai dagona tun yana da rai yace sagir ya kai takardun kowa ya gani. Ai kuma sai zance ya koma wani sabon tashin hankali don dama gidan yakewa da gonan a raba a bashi ya sayar sai ga zance ya koma kasa kuma. Ya buga kasa yace sam shi bai san zancen baba ya sayar da gona ga wani sadauki can ba. Mummy tafito tace anyi haka kuwa don ita tasan da zancen don ita sheda ce a hakan. Ya sayar ya gina masalllatai da kudin shi yayi gyaran wasu kuma duk da kudin. Babane hanata ya ce kada ta fadawa kowa sai bayan ranshi za, a sani don haka kowa yaje ya nemi takansa. Sai na kashe sadauki wallahi yaya za, ace yafi mu kudi yafi mu komai kamar shi kadai ne kawai dan da aka haifa a gidan nan. Ya zare kamar wani sabon mahaukaci yana cewa idona idon wanan mugun guy din sai na halakashi wallahi. Hankalin maji ya tashi sosai yadda taga Ahmed din ya zare masu a lokaci daya ya koma kamar wani mara hankali dashi. Wayana ta kira take ce min naiwa masu gadin gidan mu magana su kula ga abinda Ahmed yace zaiyi kada yazo bai samu sadauki ba yaiwa jikokin ta illa. Nima hankalina ya tashi danaji nace a kidimay mama kefa dake gidan kada fa yazo yai maku wani illa a gidan. Mama tace Fatima niku nakejiwa dai don naku yafi damuwa na sosai wallahi hankalina a tashe yake Fatima da kalamin yaron nan gashi na kira mijin ki ban samu layin shi ba. Nace mama bazaki samay shi ba don suna meeting ne da tun safe da suka shiga yace sai uku zasu fito. Bayan munyi sallama nima sai hankalina ya tashi don nasan yaya Ahmed mugu ne zai iya yi komai daya fada. Nakira sadauki na samay shi a waya nake fada mai abinda yaya Ahmed yace akan shi din Dariya yayi yace kai Ahmed din may can insha Allahu bazai iya komai ba da yardan Allah. Duk da haka ya kafa matakan tsaro sosai a kan mu ganin hankalina dana mama yai matukar tashi sosai a gidan. Ranan da sadauki ya shigo gari ya tafi gida gurin mama take kara fada mai yadda akayi da Ahmed din yace mama Kwantar da hankalin ki Ahmed ba abinda zai min naso ya bari mu rabu lafiya dashi kamar yadda nake fatan mu rabu lafiya da kowa. Haka dai ya kwantar mata da hankalin ta sosai har ta aminta da zuciyar ta sosai. Bayan tafiyan shi da kwana biyu yara zasu tafi makaranta mai daukan su yazo har sun fara hanyar fita na ji zuciyata tana halbamin. Namike tare da cewa Nura direba ya bari nazo mu tafi tare mu sauke su a school din. Tun bayan fitowan mu a layin mu ne na hankalta da wata mota dake bin mu a baya na fadawa Nura driver abindana gani waya muka bugawa security din mu suka biyo mu a baya aiko mu motar kebi da gakiya don muna shiga titin da zai kai makarantan motar tasha gaban mu suka take mu da bindiga wai mu fito. Muna kokarin fitowa ne Allah ya takaita muna wahalan mu security din suka iso gurin aka fara musayan wuta dasu na tara yarana a jiki na kwanta masu sai rokon Allah nake yakawo muna agaji. Allah ya rufa muna asiri yansanda suka kawo muna agaji nan Allah yabada sa, a aka kama wasu daga cikin mutanen. Mu kuma aka tafi damu gida cikin tsaro ai kafin wani lokaci labari ya karade gari. Sadauki yana samun labari hankalin shi yai matukar tashi sosai duk da yaya bashar ya kwantar mai da hankalin shi amma bai hanashi dawowa gida ba hankali a tashe. Nan ya sa na shirya yara yana fadin garin zai bari damu baki daya duk yadda naso ya barmu bai yarda ba tare muka bar garin dashi muka kwasa har da Iyya sai Abuja. Sai bayan tafiyan mu ne muka samu labarin ashe yaya Ahmed ne ya turo mutanen nan suyi kidnapping din mu Ran yaya sadauki yai marukar baci bai san kiyayyan ya kai haka ba har ga iyalinshi sai da wannan abin ya faru akan iyalin shi. Kuma wai dan uwanshi najini uba daya yasa ai mashi wanan irin aika aikan haka. Da Ahmed zaice ya bashi duk abinda yake dashi da zaifi mashi sauki akan dauke mai iyalan shi daya saka ayi ko kuma shi yai mai wani abin can ba yaran shi da matar shi ba. Anso a daure Ahmed amma yaya sadauki ya hana karshe ma ya bashi kudi masu yawa a matsayin jari a gare shi don yasan talauci ne ya jawo mai wanan batar haka. Daga wanan lokacin zaman mu ya koma rabi Abuja da anyiwa yara hutu kuma mubar kasan zuwa waje. Haka rayuwan ya dinga ci gaba iyayena da yan uwan mijina kowa yana moriya daga gare shi har ni da yarana. Kowa yana alfahari da samun shi an manta da baya abubuwan da suka faru adduan iyayye yayi amfani Allah ya shirya kayan shi ta yadda ba, a zata ba. Don haka Addua mahaifa take da amfani ga yaran su komai dadewa insha Allahu zamu samu riban adduan iyayyen mu. Dafatan Allah ya bamu ikon yawaitawa yayan mu addua ta alheri don ganin cigaban rayuwan su a kullun. Nagode da lokacin da muka bawa junan mu gurin tsayawa karanta wanan guntun labarin dafatan duk wani dan fadakarwan dake ciki zai amfane a gidajen mu da al, umman mu Ka taimaki wanda ke bukatan taimako koda addua ko da karfin ka don kaima Allah ya taimake ka ta hanyar da baka zata ba watarana. Sai mun hadu a sabon novel din mu maizuwa insha Allahu da fatan kuji dadin labarin a zukatan ku wanda duk banyiwa daidai ba ta yafe min don Allah. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels