Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels ο»ΏAn dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT[8/23, 3:12 PM] +234 808 332 3233: πŸ’«AMRAH MACIJIYA πŸπŸπŸπŸ’« By Rabeauty πŸ₯°πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’« Page 2 Labarin mutuwar malam Abu ya riski kowa dake kauyen, hankalinsu ya matukar tashi dasu kaji cewa macijine ya kashe shi. A fadar mai gari kuwa kowa ya taru ana jiran iliya mai macixai yaxo, yana isowa a kace ya bude macixai nai a duba bakin su aiko aka duba amman sarar batayi kama da bakin macixanba, haka aka taro akayiwa malam abu wanka da sallah aka kaishi makwancinsa. Washe gari amrah tana daki tana bacci gwaggo ta shigo ta tayarda ita tana cewa"yar jikalle tashi Dan Allah na aikeki gidansu harira ki karbomin daudawa gurin innah"toh gwaggo ta tashi ta fito bayi ta shiga ta wanke fuskarta ta fito ta dauki mayafinta Green tasaka ta nufi gidansu harira, tana xuwa ta tararda harira na wanke_wanke gaisawa sukayi sannan ta nufi inda innah suka gaisa sannan tagaya mata abunda gwaggo ta aiko ta karba, bata tayi sannan ta fito xata wuce harira tace "amrah bayan la'asar xanxo mutafi rafi, toh kawai tace tafice daga gidan, a hanyarta ta komawa gida taga wasu samari su biyu suna mgn kuma akan mutuwar malam Abu ne, dan tsayawa tayi Dan taji me suke fada, dayanne yace" hmmmmm ni wlh wannan abun yafara bani tsoro ace anrasa gane wane macijine ke wannan kisan har yau"dayanne yadafa kafadarsa yana cewa "nima dai abun yafara bani tsoro, amma ai gobe ne maigari yace maccido maciji xaixo da kuma magani, kowa dake kauyen nan xa'a bashi yasha, duk Wanda a maciji toh yanashan wannan maganin xai fara rikidewa, kuma na rantse muddin wannan macijin ya kasance acikinmu toh wlh saina kashe shi har lahira wlh, gaban amrah ne yafadi saikuma naga tana wani shu'umin murmushi Wanda daka gani kasan bana alkhairi bane, gida ta karasa tana xuwa tabawa gwaggo daudawarta ta shige daki, da kallo gwaggo tabita sbd taga yanxu duk ta canxa kamar ba amrah taba, ynx mugun halin shiga daki tabijiro dashi, girgixa kai kawai gwaggo tayi ta tashi tashiga bayi, tana fitowa ta dauro alwallah ta nufo dakin, ta tayarda sallah, tashi amrah tayi itama tayi alwallah tayi sallah, bayan sun idar amrah ta juyo ta fuskanci gwaggo tace "waini gwaggo meyasa me gari xaice sai wani maccido maciji yaxo yabawa kowa magani, meyasa su baxasu yi bincikeba tukunnah ai...... Wani kallo da gwaggo tayi matane yasata kasa karasa xancen, waike amrah yaushe xaki fara tausayin mu ke kwata kwata bakida tausayi damuwar mutane bata damekiba, waini kam wace irin xuciyace dake, nidai nasan cewa baban ki da mamanki ba haka sukeba kuma nima dai ba halina kika biyoba, dan Allah amrah ki gyara kinji kuma gobe maccido xaixo da karfe biyar dan haka tun karfe 4:30 xamuje fadar mai gari kinajina, kai kawai ta daga. Bayan sallar la'asar harira tayi sallama tashigo, gaida gwaggo tayi sannan suka fice xuwa rafi, suna tafe suna yar firarsu, can dai harira ta kasa hkr tace "waini amrah na tambayeki? Eh kawai tace, harira tace" wai meyasa naga tafiyarki ba irin tamu bace kina tafiya kina wani lankwasa kamar macijiya, dariya amrah tayi sannan tace "toh ai macijiyar ce" dariya harira tayi tace da baki fadaba wlh, shiru amrah tayi bata kara cewa uffanbah, suna isa bakin rafin suka xauna kafafunsu sukasa a cikin ruwan, wasu samarine su uku sukaxo wucewa dayanne ya hangesu yayi saurin tabo su yana cewa kai kunga wasu yam mata, dayan ne ya juyo yace kai ashe yau xansha dadina da yammatan nan, karasawa suka yi gurin su, da isarsu suka fara yimusu iskanci. Harira ce tace da ganinku ba'a yankin nan kukeba Dan haka Dan Allah ku koma yankin ku, dariya suka sheke da ita dayan yasa hannu ya fixgo harira ya mannata da jikinsa ya shiga shinshinar wuyanta dayan kuma amrah ya cafko yana kokarin yaye mayafinda ta rufe fuskar ta dashi, amman yakasa wani wawan Mari yabata wadda saida gefen bakinta yafashe, harira kuma har sun kaita kasa suna kokarin daga mata riga, jin suka yi ance "ku kyaleta da wata irin murya" Wanda yamare tane ya juyo yace ke yimana shiru, kuma damun gama da ita kanki xamu dawo Dan haka kishirya, ya juya ga harira wadda tariga data sadakat sbd harya cire wando, hucin maciji suka ji a bayan su, ai da sauri suka saki harira suka juyo, wani irin raxanannen ihu suka saka a tare, sbd toxalinda sukayi da wata shirgegiyar macijiya green 🐍, harira mah tsoro ne yakamata nan tashiga neman amrah amma bata gantaba, jin sukayi macijiyar tace "saida nayi muku kashedi amma kukaki ji Dan haka dolene na kashe ku, kafin suyi wani yunkuri gaba daya tabi ta saresu nan take suka xube matattu a gurin, gurin harira tayo, harira koh harta juya xata fece taji tace" tsaya "ai da sauri ta tsaya, karasuwa tayi gurin ta, sannan ta girgije takoma mutum, ai harira na ganin AMRAH nan take ta sumee a gurin. πŸ’«Rabeauty πŸ’« *please vote, comment, and share * [8/23, 3:12 PM] +234 808 332 3233: πŸ’«AMRAH MACIJIYA πŸπŸπŸπŸπŸ’« By Rabeauty πŸ˜πŸ’«πŸ’«πŸ’« (4) Harira na kaiwa bakin suro ta hadu da gwaggo xata shigo, yadda gwaggo taga harira a rikice neh yasa itama hankalinta tashi, tace menene harira koh wani abun neh ya samu amrah, harira ta bude baki xata gayawa gwaggo gsky cewar amrah macijiya ce, sukayi ido hudu da amrah tana mata wani irin kallo, ai da sauri tafita daga gidan har tana yin tuntube, juyowa gwaggo tayi dan tayiwa amrah mgn, amman me wayam tagani bbu ita a gurin, tsoro neh ya kamata tace "toh yarinya sai kace aljana hmmmmm gaskiya da sake, koh dai abun da ake fadi a kauyen nan gaskiya neh? Toh idan kuma gaskiya amrah macijiya ce fah innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, tunowa tayi da maganar mai gari" asabe mutanen kauyen nan sun fara xargin jikanyar ki ba mutum bace, duba da yadda take tafiya duk mai hankali yagani yasan cewa tafiyar macixai ce, kuma kaf kauyen nan bbu Wanda yataba ganin fuskar ta daga harira sai innah mahaifiyar harira sai ke, dan haka inason kisaka idanu akanta muma xamu saka idanu, kuma muddin xargin mu ya tabbata toh fa xamu kashe ta, dan bbu makawa ita ke kashe mana mutane " Duk sanda ta tuna da wannan maganar sai hankalinta ya tashi. Toh idan kuma ta tabbata ita macijiya ce kenan kashe ta xasuyi, inaaa baxan taba bari hakan ta faruba. πŸ€Έβ€β™€οΈπŸ€Έβ€β™€οΈπŸ€Έβ€β™€οΈπŸ€Έβ€β™€οΈπŸ€Έβ€β™€οΈ πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’« KANO STATE. πŸ’¦Wani makeken gida nagani Wanda duk layin bbu Wanda yayi kyansa, ciki na shiga wasu mata na gani a harabar gidan, wata yanmata ce a tsaye baxasu wuce shekara 25 bah,sanye take da riga da wando wa'enda suka bala'eeeen fito da surarta, fara ce amman bacanbah, sai wata mata wacce xata kai shekaru 48,kamarsu daya da yarinyar saidai tafita hasken fata, sai wani saurayi matashi Wanda baxai wuce shekaru 27 bah a duniya, irin black beauty's din nan neh. Gate aka bude wata hadaddiyar motace tashigo kirar benz Black color, parking space ta nufa da sauri driver ya fito yaxagayo ya bude kofar Baya. Saida akadauki 5 minutes sannan ya xuro kafarsa ta dama, saidai ya kara wasu 5 minutes sannan ya xuro ta hagu, fitowa yayi yana karewa gidan kallo, subhanallah wannan balarabe koh shuwa'arab domin bbu inda yayi kamada hausawa kai wannan mah koh cikin larabawan da wuya a samu mai kyau irinsa, fari ne kal dugu mai faffadan kirji, jikinsa a murde yake gwanin ban sha'awa, matashine dan kimanin shekaru 33. Kara suwa yayi gurin su "hajiya barka da yamma" kawai yace yayi shigewarsa ciki, dawani irin kallon tsana tabishi, inda xa'a bata wuka ace taka she duk Wanda ta so tohfa shine Wanda xata fara kashewa. Driver neh ya kwaso masa luggage dinsa yanufu hanyar shiga falon, tsawa hajiya ta daka mishi tace dallah ajiye anan, da sauri ya aje ya juya, kallon NAJEEB tayi tace"daukar masa luggage dinsa kakai part dinsa kace masa idan yayi wanka yaxo yaci abinci"rai bace yaja luggage din yanufi part din yayan nashi, Ke kuma suhaima wuce mutafi, wucewa tayi tana turo baki, falon suka shiga, woowπŸ˜΅β€πŸ’«πŸ˜΅β€πŸ’«haduwa, wannan falon ai da kadan nasu vansh yafishi kyau, dramarda akeyi a bollywood, vansh da ridima 😜 A bangarensa kuwa NAJEEB yana kai masa luggage dinsa ya juya yayi ficewarsa, koh gaisheshi beyiba. Hajiya koh tana nan hakince akan makeken dining gefenta koh suhaima ce tana latsa wayarta, NAJEEB neh yaxo ya xauna kusa da hajiya, ba'a dadeba saiga wannan balaraben yafito cikin shigar kananan kaya fuska a daure hanyar waje ya nufa, da sauri hajiya Sarah tace "JALALUDDEEN baka ci abincifa" koh juyowa beyiba yasa kai ya fice, hajiya Sarah ji tayi kamar ta kurma ihu sbd takaici, NAJEEB neh yace mommy nace kibari nida kaina xan iya kashe shi ba dole sai anbi ta hanyar sa masa guba a abinci bah kawai kibari nasa su bardee sutare shi a hanya su aika manashi barxahu, Da sauri suhaima tace "please aunty Sarah don't kill my JALAL, kinsan yadda nake sanshi ke shedace kuma kinsan akan shi na kwaso kayana na dawo nan gidan, ke dallah rufemun baki Wanda koh kallo baki isheshi bah kinkasa jawo hankalinsa gareki, balantana muyi using dake gurin cikar burinmu mtswwww taja wani dugun tsaki hadi da tashi dg kan dining ta nufi room dinta, Suhaima mah tashi tayi ta nufi room dinta akabar NAJEEB ananπŸ’¦ ✨ TIGADAM✨ AMRAH kam iska tabi ta tare harira a bakin hanya, harira har xata gudu amrah tace "idan kika kuskura kika kara taku daya toh xan kasheki, ai kamar andasata a gurin ta tsaya, karasuwa amrah tayi kusa da ita sannan tace" meyasa kikeson ki fallasa sirrinah, meyasa kikeson ki gayawa gwaggo cewar ni macijiya ce, toh bari kiji wlh, wlh, wlh harira kika kuskura kika gayawa gwaggo koh kuma wani cewar ni macijiya ceh hmmmmm kinsan sauran, girgixa kai harira ta shiga yi hawaye na sauka akan fuskarta tace "amrah baxan xuba idobah ina kallo kici gaba da kashe mana mutane bah, hannuwanta ta hade guri daya alamar rokoπŸ™sannan tace" Dan Allah amrah kidena kashe muna yan uwa, dan Allah na rokeki, Tsaki amrah tayi tace "wlh harira duk Wanda ya shiga gonata wlh saina kasheshi Dan haka kidena wa [8/23, 3:12 PM] +234 808 332 3233: πŸ’«AMRAH MACIJIYA πŸπŸπŸπŸ’« By Rabeauty πŸ₯°πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’« (3) Hannunta tasa a cikin rafin ta ibo ruwa ta watsamata, a firgice ta farka tana ja da baya tana girgixa kanta hawaye na sauka akan fuskar ta cikin rabewar murya tafara mgn"da.. dan Allah am.. rah kiyimin rai kar.. ki kasheni, murmushi tayi sannan tace "hmmmmm harira kenan da inada niyar kasheki da tun ranar da kika fara ganin idanuwana da a ranar xan kasheki amman kuma baxan iyaba sbd yadda na daukeki kamar yar uwata tajini shiyasa baxan iya kasheki ba" ajiyar xuciya harira ta sauke sannan tace "kenan duk kashe kashen da akeyi a kauyen nan kece, kuma ke kika kashe malam abu? Eh nice kuma duk wanda kikaga na kashe toh yashiga gonata neh, kuma ni bana yafiya kuma bana mantuwa, kuma wannan abun daya faru inason yaxama sirri a tsakanin mu sbd koh gwaggo batasan cewa ni MACIJIYA ce bah"inshaa Allah ba Wanda xaiji toh amma wa'ennan da kika kashe yaza muyi dasu? Anan xamu barsu, ido πŸ‘€harira tafitar waje tana cewa "anan kuma amrah? Eh tashi mutafi, xata sake mgn amrah ta daka mata tsawa tare da tsareta da green eyes dinta, ai nan danan harira tahadi ye abunda tayi niyar fada, cikin kauyen suka nufa, AMRAH tashige gidansu itama harira tayi gida. Washe gari da misalin karfe 4:00 mutane sunfara taruwa a fadar mai gari kuwa jiran maccido mai macixai yake ya kara so dansu wannan masifar tayi yawa. AMRAH koh tuni ta fice daga gida lokacin gwaggo na bayi batama San da fitarta bah. Farkon shigowa gari tanufa ta haye saman bushiya tana jiran isowar maccido mai macixai πŸͺ±, aiko can ta hangoshi saman rakumin sa 🐫da wata katuwar leda da gani dai kasan magunguna neh a cikin ta. Murmushin mugunta tayi sannan ta diro daga kan bishiyar ta tsaya bakin hanya, tun daga nesa ya hangeta, sanye take da kaya green har mayafin kanta green neh, yana isowa ya sauko daga kan rakumin sa, yanufi inda take yana cewa"ke yarinya me kikeyi anan gurin maimakon ace kina fadar mai gari". Mayafin kanta ta yaye ai maccido nayin toxali da idanunta yagane macijiya ce, ai da sauri ya juya xai dauko kayan aikinsa amman ina harta xama shurgegiyar macijiya 🐍, xata kai mishi Sara sai kawai tagaya bace, kafin ta juyo taji anyan keta da takobi, βš”οΈ, kafin ta juyo kuma yasake bacewa, nantake ranta yakara baci, sai naga tana kara girma Wanda saida yakusa cika dajin, idanuwanta sunkara xama green sosai kwayar idonta tarinka fitarda wani haske, toh a cikin wannan hasken neh ta hangoshi ta bayan ta xai sake yankarta, ai a xafafe ta juyo takai masa wata irin Sara a wuya, nan take ya xube matacce a gurin dukda haka bata barshiba saida tayi masa jina jina, sbd bbu Wanda yataba Cin galaba a kanta saishi. Rikidewa tayi ta dawo mutum, inda ya yanketa tasa Hannunta na dama ta shafe gurin, aiko ya dawo daidai kamar ba'a taba yankantaba. πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’« A fadar mai gari kuwa, kowa ya halarta shi kadai ake jira, ganin har 5:20 ta wuce yasa mai gari tura fadawansa su uku akan suje su dubo koh lfy. Aiko suna xuwa suka tarar da gawarsa a bakin hanya, da gudu sukabar gurin, suna isa suka sanarda mai gari abunda suka gani, hmm lallai wannan shi ake kira tashin hankalinda ba'a sakawa rana, domin kowa ya shiga tashin hankali. Harira najin haka, hankali tashe tabar gurin, gidansu amrah ta nufa tana xuwa kai tsaye tace "amrah meyasa kika kashe maccido? Wani banxan kalloh tayi mata sannan tace" sbd ya shiga gonata "harira tace" haba amrah wai mekike son kixama, ke bakyayin wuyar kashe mutum, haba amrah kiji tsoron Allah, duk wannan abun da harira keyi kawai karfin haline, sbd a tsorace take da amrah. Ran amrah ne yafara baci domin koh har fatarta ta fara sabulewa tana xama ta maciji, harira na ganin haka ta fita da gudu dan tasan idan ta tsaya toh fa saidai buxunta πŸƒβ€β™€οΈπŸƒβ€β™€οΈπŸƒβ€β™€οΈ. πŸ’«Rabeauty πŸ’« *please vote, comment, nd share * [8/23, 3:12 PM] +234 808 332 3233: πŸ’«AMRAH MACIJIYA πŸπŸπŸπŸ’« By Rabeauty πŸ₯°πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’« (5) Da sauri amrah ta nufi gurin gwaggo tana girgixata tana cewa "Dan Allah gwaggo kitashi idan kika mutu ya xanyi, hannunta tasa a saman kirjin gwaggo ta rufe idonta, tana budewa wani haske green yafito daga idanta ya sauka kan kirjin gwaggo, wani dugun numfashi gwaggo taja, ajiyar xuciya amrah ta sauke, sannan tace gwaggo nah, A hankali gwaggo ta fara bude ido da fuskar amrah tayi toxali ai da sauri ta tashi xaune tanaja da baya, da sauri amrah ta rike hannunta tace "gwaggo nah tsoro na kike? Kai gwaggo ta girgixa tace" innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, magaji kaja mana masifa, Amrah tace wace irin masifa babana ya jawo mana wadda ni bansaniba? Hmmmmm FATIMA a yau xan sanar dake wanene mahaifinki. πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’« Tuna Baya. Anyi wani jarumin mutum kuma sadauki Wanda duk kauyen nan bbu mai karfi irin nasa, har takai ga yana fada da mayu, aljannu da kuma macixai, sbd hakan neh yasa ake kiransa da magaji, mahaifiyarki kuma ta rasune a lokacinda xata haifeki. Akwai wani shahararren maciji, mugu, Wanda ya addabi jama'ar wannan kauyen, ba halin mutum yafita sbd da xarar ka fita xai kashe ka, sunansa BAHUUL, ansha gwagwarmaya tsakanin sa da mahaifinki wato magaji, kafin yasamu nasarar kasheki, kafin ya mutu saida yace "hhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhh lallai magaji kayi namijin kokari gurin kasheni, toh amma inason kasa wannan a ranka SAINA DAWO DAUKAR FANSA, kuma akan 'yarka, Yana gama fadar haka ya mutu, hankalinmu ya bala'eeeen tashi, haka muka rinka kula dake koh bandaki xan shiga bana barinki ke kadai saina jira mahaifinki ya dawo, haka dai mukata baki kariya, har kika shekara uku amma bamuga wani abu ya sameki bah, tun daga ranar muka share xancen BAHUUL, muka dauki xancensa a matsayin karya. A wata assabar ranar da baxan mantaba, koda aka wayi gari bbu mahaifinki bbu labarinsa, hankalin kowa dake kauyen ya tashi matuka domin rashin magaji agaresu babbar matsalace, duk kauyen da yake kusa damu anduba amma ba'aga mahaifinki bah, har xuwa yau danake gaya miki wannan xance. Hawaye amrah ta share sannan tace "gwaggo dama baba yana raye"eh FATIMA mahaifinki yana raye amma bansanarwa yanxubah, kuma nasan BAHUUL neh ya shiga jikinki domin ya dauki FANSA, amman dan Allah amrah tunda dai harkina da ikon juya kanki dan Allah kidaina kisa,wlh gwaggo bana sanin lokacinda nake yin kisa, nasan bayin kanki bane amrah amma Dan Allah kikara kokarta.... Bata karasa abinda xata ceba taga amrah ta tashi da sauri tana rike kanta, da sauri gwaggo ta tashi ta nufeta, AMRAH meya sameki, dagowa amrah tayi idanunta sunkara rinewa Dukda da farinda yake tsakiyar idonta yakoma green, tsoro neh ya kama gwaggo taja da baya, Wani irin raxanannen ihu amrah tasa Wanda gaba daya ya karade kauyen, faduwa tayi akasa tafara nannadewa yadda macixai keyi, amma fah bata koma macijiya bah. Mutanen gari kam kowa yaji wannan ihun kuma sunji daga gidan gwaggo neh ihun yafito, shiyasa suka nufi gurin maigari, aka hadu aka nufi gidan gwaggo hardasu innah da harira, itadai harira gaba daya jikinta rawa kawai yake. πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’« KANO STATE. πŸ’¦JALAL kam yana fita ya shiga motarsa yabar gidan, wayarsa ce tafara ringing screen din nakallah ✨SADIQ ✨nagani arubuce, dauka yayi yasa a hands free daga can SADIQ yace "buddy ka iso" yes na iso ina hanyar xuwa office, daga can SADIQ yace "haba buddy daga dawowarka xata fito aiki kabari ka huta pls,dan karamin tsaki JALAL yaja yace" buddy kasan baxan iya xama a cikin wannan gidanba idan daddy bayanan, OK buddy saikaxo, ya kashe wayar yaci gaba da driving, Wata babbar hospital ya nufa yayi parking, yana fitowa yam mata suka xuba masa eyes sunga dan handsome kyakkyawa balarabe sun saka mishi eyes, shikam koh ajikinsa danya saba da kallo, direct office din SADIQ yanufa, yana shiga ya samu guri ya xauna, wani hadadden guy neh ya fito daga wani daki farineh sosai amma bekai hasken JALAL bah amma fah dukansu sunaji da kyau, karasuwa yayi yaba shi hannu suka gaisa sannan ya xauna, Yace "buddy wai har yanxu mommy bata dena nuna maka tsanaba, hmmmmm da farko dai tadena amma yau dana dawo inna lubabatu mai aikin mu take gayamin karnaci abincin da hajiya tayi sbd tasa guba, ido SADIQ yaxaro yace wai so take ta kashe ka, kamar yadda ta kashe ammi wai meyasa wasu basuda imani, idanun JALAL kam har sun fara canxa kala sbd bacin rai, Tasowa SADIQ yayi ya dawo kusa dashi yadafa kafadarsa yace "buddy akwai mafita" da sauri JALAL ya kalleshi yace "wace mafita" Aure, what JALAL yafada, eh JALAL aure neh kawai mafita, hmmmmm gsky u re not serious sadiq nida bana kula yam mata ina xan samu wacce xan aura, kumafa mommy so take na auri suhaima, kuma muddin daddy yasan da wannan xancen tohfa bbu makawa saina aureta, gashi kuma wlh bana sonka kai koh ganinta banason yi, Ka kwantar da hankalinka buddy, inshaa Allah kafin su yiwa daddy magana kasamu matar aure, hmmmmm kawai jalal yace tare da mikewa yace "bari na duba patients dina, [8/23, 3:12 PM] +234 808 332 3233: πŸ’«AMRAH MACIJIYA πŸπŸπŸπŸ’« By Rabeauty πŸ₯°πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’« (7) Wata private hospital ya kaita da gaggawa aka karbeta wata nurse ce taxo saka mata drip da sauri amrah ta rike hannunta kumafa idanunta a rufe suke dakyar ta bude bakinta tace "karki yimin allura dan Allah" a tsorace nurse din ta kalleta saidai batace komaiba, treatment din ciwonta tayi sannan ta bata maganin bacci, nan take koh tayi bacci, fitowa tayi daga dakin ta nufi office din Dr. Kamal, a can ta tararda Dr. Jalal, tace "Dr ta samu bacci, OK u can go, yace da ita, fita tayi, Dr jalal yace" Dr ni xan wuce and pls take care of her, ya tashi ya fita, shima Dr kamal tashi yayi yabi Bayansa, Dakinda aka kwantar da ita suka nufa, bakin gadon jalal ya tsaya yana kallon gashinta daya rufe mata fuska, har yasa hannu xai jaye gashin kuma ya fasa, ya juyo ya kalli Dr kamal yace Dr xan tafi na tahu da inna lubabatu dan ta kula da ita, toh shikenan Dr kamal yace, fita suka yi a tare, Dr kamal ya koma office dinshi, shi kuma ya nufi gorin motar sa. Yana isa gida direct part din masu aiki ya nufa, ya gayawa inna lubabatu duk abinda ya faru, ai da sauri tace "toh bari na dakko mata kohda kayan tea neh idan ta farka sai tasha,nima nadan kimtsa, OK ni bari naje part dina nayi sallah dan koh magrib banyiba gashi har ankira isha'i, yana gama fadar haka ya fita daga part din. Part dinsa ya nufa wanka yayi ya dauro alwallah yayi sallolinda ake binsa, yana gamawa ya fito, inna lubabatu yagani a bakin motar sa tana jiransa. Yana isowa ya bude mata motar shiga tayi shima ya shiga yaja yabar gidan, Suhaima kam duk tana kallonsu wani irin tsaki taja ta koma ciki tana Kiran sunan aunty Sarah, aunty Sarah dake saukowa daga upstairs tace "lfy kike Kiran sunana haka kamar naci bashinki, kamar xatayi kuka tace" aunty yanxu fah naga ya dawo kuma ya sake fita tare da inna lubabatu, what hjy Sarah ta fada, hmm lalle inaganin karshen xaman ta a gidan nan yaxo har tayi matsayin da xata fita tare da jalal hmm, amma bari tadawo muji dalilin fitarsu tare. ************* A harabar asibitin yayi parking agogon hannusa ya kalla karfe 9:00 yagani Dan karamin tsaki yaja, fitowa suka yi ya kaita har room dinda amrah take beko shigaba yajuya yayi tafiyarsa. Inna lubabatu kam ajiye kayan da taxo dasu tayi, ta nufi gurin amrah dake bacci har ynx gashinta ta gyara mata da sauri taja da baya tana cewa "innalillahi wa'inna ilaihirraji'un" Dan kara lekowa tayi Dan ita wannan kyan na amrah ya bala'eeeen bata tsoro kyau sai kace aljana, kayan shimfidar ta ta dakko ta shimfuda tayi addu'o'i sannan ta kwanta bacci. Jalal kam yana komawa part dinshi yasa key ya kulle Dan daxo yaga Suhaima kuma yanada tabbacin ta gayawa mommy kuma yasan xa'a iya aiko ta ta kira shi shiyasa ya kulle part dinsa. *************** Washe gari hajiya nafeesa takawowa hajiya Sarah magani wai a saka masa a ruwa tohfa dayasha ruwan xai mutu. Jalal kam koh aiki bejeba direct hospital ya nufa. ✨✨✨✨✨✨ Hospital. A harabar asibitin yayi parking, direct dakin ya nufa, yana shiga inna lubabatu na fitowa daga toilet, gaisheta yayi sannan ya xauna yana cewa "wai har yanxu bata farkaba" eh wlh ni abun ma yafara bani tsoro, OK bari na kira nurse ya tashi xai fita kenan saiga nurse tashigo, kara sawa suka yi bakin gadon, a daidai wannan time din amrah ta fara bude idanunta, dishi dishi take ganinsu sai can ta rinka ganin su da kyau yunkurawa tayi xata tashi, da sauri nurse din ta taimaka mata ta tashi xaune, dan dagowa tayi ta kalli jalal Wanda shima ita yake kallo, kurawa juna ido suka yi, ita tana marvelled beauty dinsa, shikuma yana astonished eyes & beauty dinta, shiya fara janye idanunsa, sannan itama ta janye, ita kam nurse tunda taga idanun amrah tsoro ya kamata, kasa hkr tayi tace "baiwar Allah meya samu idonki, dan kallonta jalal yayi, wani kallo amrah ta jefe ta dashi Wanda yasa jikin nurse din fara rawa da sauri tace" Dr bari naje nakira maka Dr kamal"batama jira cewar saba tayi sauri ta fita. Inna lubabatu ce ta matso kusa da ita tace "diyata na hada maki tea", kallon ta tayi tana tunanin menene kuma tea, kai ta daga alamar eh Dukda koh batasan menene tea bah, tashi inna lubabatu tayi ta nufi gurin da ta aje kayan tea tashiga hada mata. Jalal kam ganin Dr beshigo bah yasa shi tashi ya nufi office dinsa yana kokarin shiga shikuma yana fitowa, yace "aa Dr jalal har kaxo, eh wlh nama Dan dade ai xuwa nayi a samu sallama pls, OK muje gurin ta tukunnah, suna shiga yayi daidai da gama shan tea dinta, karasawa Dr kamal yayi gurin ta yace" yam mata ya jikin, koh kallonsa bata yiba, balle yasa ran xata amsashi, dan tambayoyi yayi mata amma ba wanda ta bashi amsa da baki, saidai ta daga masa kai koh ta girgixa. Juyowa yayi ya kalli jalal sannan yace "muje na Baku sallama, xaiyi magana kenan wayarsa ta fara ringing dubawa yayi (mommy) nagani a screen din wayar dan karamin tsaki yaja, ya juyo ya kalli inna lubabatu sannan yace" ki hada komai da komai kikai mota sbd ynx x [8/23, 3:12 PM] +234 808 332 3233: πŸ’«AMRAH MACIJIYA πŸπŸπŸπŸπŸ’« By Rabeauty πŸ₯° πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’« *In the name of Allah, the most beneficent, the most merciful. *Seeking for guidance and protection of Allah as i am going to start ❀️ Ya Allah!!! Guide my heart, and protect my hand to the end of this book, AMEEN. πŸ’« Page 1πŸ’« Kano state. A wani kauye Wanda ake kira da tigadam, wata yarinya na hanga a bakin rafi xaune tana kallon ruwan rafin duka duka yarinyar baxata wuce shekaru goma sha biyarba,tashi tayi tana karewa gurin kallo, koh ina bishiyoyine koraye 🌳🌳masuban sha'awa, hanyar gida ta nufa kallo daya xakayiwa tafiyar ta kasan cewa wannan yarinyar ba cikakkiyar mutum bace sbd yanda take wata irin lankwasa, iskace tayaye mayafinda ta rufe fuskarta dashi,subhanallah, wannan irin kyau haka, yarinyar kyakkyawa ce kyan karshe idanuwanta Green ne gata fara kal yanda take da kyau xakasan cewa ba mutum bace,girgixa naga tafarayi Wanda ya matukar bani tsoro kafin kiftawar gira naga ta rikide ta xama shirgegiyar macijiya Green 🐍🐍🐍 sai sheki takeyi, cikin kauyen ta nufa tana kaiwa gurin wata kofa ta girgije ta xama mutum, da sallama ta shiga gidan, wata yar tsohowa dake bakin murhu tana ixa itace ta amsa, hade da fadin "wai ke AMRAH ba daman ayi miki fada saiki dau fushi ki wani fita dg gida kamar wata iska, waima daga gidan ubanwa kike? Karasuwa AMRAH tayi tana murmushi Wanda yakara fito da kyanta, tace" haba gwaggonah bafa fushi nayiba kawai dai fita nayi har kigama mitanki sannan na dawo"cikin kwantarda murya gwaggo tace "yar jikalle kinsan dai banason yimiki fada kece bakyayin mgn, dan Allah kikiyaye abunda xaisa na miki fada kinji, toh gwaggo inshaa Allah xan kiyaye, yawwa yar albarka, tashi tayi ta kara share gidan, ita kuma gwaggo tana kwashe abincin a cikin langa, ta xuba musu sauran a cikin kwano. Bayan sungama Cin abincin saiga harira kawar AMRAH tabiyo mata su tafi islamiya, gaida gwaggo tayi sannan ta kalli AMRAH tana cewa "lalle AMRAH bakima shiryaba kuma kinsan yau malam abu ne xaiyi mana karatu kuma yace uku tayi mana cikin aji gashi ynx har 3:30 kuma nasan kafin mu isa hudu tayi kuma....... Xancenne ya makala sbd wani irin kallo da AMRAH tayi mata shiya hakana ka rasa xancen sbd tana balaaa'in tsoron idanun AMRAH shiyasa bata fiya kallon taba sbd idanunta green neh kuma kwayar idanunta farine ita harira har tunanin take anya AMRAH mutunce kowa, tashi amrah tayi ta shiga dakinsu batafi 5 minute bah ta fito cikin shirin islamiya, muntafi gwaggo, Allah yatsare gwaggo tace, Amin ta amsa hadi da Jan hannun harira suka fito suna isowa bakin soro ta dakko nikabinta ta saka sbd yadda idanuwanta suke, ba Wanda yataba ganin complete face dinta daga gwaggo sai harira, sbd duk Wanda yayi toxali da kwayar idanunta toh sunansa gawa, duk kauyen ba Wanda yataba ganin idanunta dg hancinta sai bakinta kawai mutane suka gani, suna isa malam abu ya tsakar dasu wai sunyi latti baxasu shiga ajinba, harira tashiga bashi hkr ita kuma amrah koh kallo be ishetaba abunda ya kara harxukashi kenan kuma yau yadau alwashin sai yaga fuskarta, harira kadai ta shiga aji ita kuma amrah yace tarage tsawonta a cikin rana, bayan yagama karatu ya fito ya nufu inda take ya shauda mata bulala koh gixau bata yiba ya kara shauda mata still bata mutsaba abun ya kara harxukashi yaci gaba da dukanta saida ya gaji Dan kashi ya kyaleta, ita kuma amrah idanunta sun kara rikidewa sun xama green sosai, hannu yasa ya taxge nikabinta da sauri yaja Baya sbd toxali da yayi da idanuwanta nan danan jikinsa yafara makarkata yama kasa mgn,ita kuma ta kafeshi da idanunta, da sauri yabar gurin, harira na karasowa ta kama hannunta suka nufi gida. Bayan sallar isha'i amrah ta fice daga gidan gwaggo ma bata saniba, hanyar da tasan malam abu nabi ita ta nufa ta haye saman bushiya tana jiran isowarsa, aiko ba'a dadeba saigashi yabiyo da yar fitilarsa, aiko tayi sauri ta diro daga kan bushiyar rabin fuskarta rufeda Green din mayafi, yana isowa ya tsaya yana yadata da fitilarsa gabansane ya fadi dashi ya xata aljanace amman saiyafi fuska ya basar hadi da cewa "ke malama jayemin akan hanya tayi mishi banxa aiko yahau xaginta, amatsayinsa na malami amman yana xagi, can kuma yace waike wace irin dabbace, a harxuke tace" MACIJIYA 🐍"hade da yaye mayafin fuskarta, tashiga yin wata irin jijjiga nan take taxama shirgegiyar macijiya🐍 green sai sheki take, nan take malam abu yafara fitsari a wando, wata irin dariya ta sheka da ita sannan tace" malam abu kayi kuskuren dukana da kuma xaginta, a yau dinnan xan kasheka kuma ynx, kafin yayi mgn tayi sufa ta laulayeshi tashiga sararsa ta Ko ina ihu yake amman ita koh a jikinta saida ta tabbatar baya numfashi sannan ta kyalesa, a takaice dai ta kashe malam abu, anan tabar gawarsa tayi ficewarta xuwa gida. AMRAH dai muguwace ta karshe amman bata fiya kisaba sai idan antabota, tohfa koh waye yatabota xata kashehe illa mutum biyu,Gwaggo da kuma harira". πŸ’«Rabeauty πŸ’« [8/23, 3:12 PM] +234 808 332 3233: πŸ’«AMRAH MACIJIYA πŸπŸπŸπŸ’« By Rabeauty πŸ₯°πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’« (6) πŸ’¦Jalal kam yana gama duba patients dinsa ya nufi office dinsa Wanda yake dauke da sunansa Dr. JALALUDDEEN MUHAMMAD, ciki ya shiga ya xauna kansa ya dora saman table dinsa yakai akallah 6 minutes sannan yadago idanunsa sunyi jajir, agogo ya kallah yaga 5 saura minti 10, mukullin motar sa ya dauka yafito, yana fitowa wata nurse ta taso tana cewa "sir are u going?koh kallonta beyiba yace" yes am going and pls lock my office "yayi gaba abinsa har yakai gurin motar sa sadiq ya fito da alama shima ya tashi daga aikinsa neh, karasowa yayi yace" buddy kardai ace harka tashi "so kake na kwana anan koh ya, ya fada hade da bude motar sa ya shige, da sauri sadiq ya bude gidan gaba ya shiga yana cewa" yawwa ni mumaje ka ajiyeni a gida sbd yau bada motana naxuba, bece komai ba yaja motar yabar harabar asibitinπŸ’¦ πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’« TIGADAM Gwaggo kam hankalinta ya matukar tashi sbd yanda taga amrah ta rikide lokaci guda duk ta bi ta nannade guri daya irin yadda maciji keyi, sallamar su megarine ya kara tayar mata da hankali, dan haryau bata manta abinda yace mataba "idan har amrah ta kasance macijiya toh xasu kasheta", ai da sauri ta nufi soron danta dakatar dasu amman kash sunriga sunshigo, Suna shigo wa idanunsu ya sauka kam amrah wacce ixuwa yanzu fatarta ta fara sabulewa tana xama ta maciji, da sauri harira tayi kanta tana Kiran sunanta, tana xuwa tasa hannu ta dago da ita, wani irin wulli akayi da harira Wanda saida tayi sama sannan ta fado kasa, da sauri innah tayi kan 'yarta tana cewa,"subhanallah yau mexan gani, amrah lafiyarki kalau kow... ai bata karasaba taga amrah ta Mike tsaye idanunta sun kara rikidewa da sauri innah taja harira suka matsa daga gurin, wata irin girgixa amrah tafara nantake taxama wata irin shirgegiyar macijiya wadda tafi tada girma dan wannan kadan yarage ta cika tsakar gidan ai wasu tuni suka xube sumammi a gurin, Wata irin dariya ta sheke da ita marar dadin sauraro sannan tace "hhhhh dama na gaya muku xan dawo daukar FANSA, ni BAHUUL bana yafiya kuma haka xalika bana mantuwa Dan haka yau kafin nabar kauyen nan saina kashe rabi daga cikinku sannan nashiga cikin gari nayi ta'asa son raina kuma bbu Wanda ya isa ya dakatar dani, Gwaggo ce tayi kafin halin cewa "nicenan xan dakatar dake", wani irin kallo ta watsa mata sannan tace "ai wannan ba jikarki bace BAHUUL ne kuma me iya dakatar dani mutum dayane, MAGAJI kuma a ynx bayanan ni kadai nasan inda yake, kuma a inda yake bbu me iya ganinsa hhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhh ya bushe da wata irin dariya, mai gari ne yace" kai maxa ku kasheta "ai da sauri suka nufeta bakinta ta bude nan take wuta tafara fitowa, gwaggo na ganin haka tayi saurin Jan hannun harira da innah sukabar gidan, AMRAH koh saida ta kashe kusan mutum 20 sannan tabi iska tabar kauyen. Tunda aka gayawa gwaggo amrah tabi iska tabar kauyen take ta kuka tana cewa "yanzu shikenan amrah ta tafi innalillahi wa'inna ilaihirraji'un wannan masifar dame tayi kama bbu MAGAJI ynx kuma bbu amrah wayyo Allah nah ta kara fashewa da kuka, innah mah kuka takeyi tana bawa gwaggo hkr, itadai harira komawa tayi kamar mutum mutumi sbd tafiyar kawarta kuma yar uwarta ya tabata sosae. A bangaren amrah koh BAHUUL be tsaya da ita koh inaba sai a cikin garin Kano. πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’« Jalal kam yana sauke sadiq ya nufi hanyar gida gudu yakeyi da motar sbd har anyi sallar magriba so yake ya isa gida da wuri. AMRAH koh tana bude idonta ta ganta awani gari, nan tashiga tuno abinda ya faru, kuka ta fashe dashi ta durkushe a gurin da take, wani Dan matashine ya nufi gurinta da sallama sannan yace "baiwar Allah me kikeyi anan ke kadai kuma gashi dare yanayi, da sauri amrah ta dago ta kalleshi sannan tace" bawan Allah da Allah ka taimaka mun da ruwa nasha wlh kishin ruwa nakeji, da sauri yace "toh bari na siyo miki jirana anan" kai ta daga mishi, juyawa yayi yatafi siyo mata ruwa, ajiyar xuciya ta sauke sbd ji tayi kamar ta sareshi tasha jini sbd yunwarda takeji shi yasa tace masa ruwa take so sbd yabar gurinta sbd muddin yaci gaba da tsayawa tohfa xata iya kashe shi, tashi tayi tafara tafiya batamasan inda take jefa kafar taba, Jalal kuma tun daga nesa ya hangi yarinya yafara mata hon amma ita amrah bata nasan da ita akeba ji kake kuuuuuuuuuut anbugeta saida tayi sama sannan ta fado kasa sumammiya, da sauri jalal yafito ya nufu kanta jama'ah harsun fara taruwa, beyi wata wataba ya sureta da sauri ya ajeta danji yayi kamar ya dauki maciji, sake kallonta yayi sannan yakara surarta yasa ka abayan mota, shiga yayi ya nufi hanyar wata asibiti da take kusa da inda yake, dan idan yace ya koma aaibitinsu tohfa xata iya mutuwaπŸ’¦πŸ’¦ Hmmmmm lalle jalal ka daukowa kanka jaraba 🀣🀣🀣😜 πŸ’« Rabeauty πŸ’« *please vote, comment, and share * [8/23, 3:12 PM] +234 808 332 3233: πŸ’«AMRAH MACIJIYA πŸπŸπŸπŸ’« By Rabeauty πŸ₯°πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’« (8) Inna lubabatu kam kama hannun amrah tayi suka nufi part dinsu. ************** Washe gari Inna lubabatu ta hada musu breakfast, takai kan dining table ta jera kulolin abinci. Sannan ta koma bangaren su ta tada amrah tayi wanka. A bangaren jalal kowa, bayan yafito daga wanka yashafa mai yasa body spray mai sanyayyen kamshi, wani lausassan yadi baki yasa ka Wanda yakara fito da haskensa, Direct part din masu aiki ya nufa, gaidashi suka rinkayi kai kawai yake daga musu, daya daga cikin yan aikin mai suna zainab amma suna kiranta da abu xatayi sa'ah da Suhaima tace "gaskiya fah yallabai ya hadu matuka, da sauri dijee ta kalleta sannan tace" wlh abu ki iya bakinki nidai bbu ruwana, kingama tafiyata ta fada hadi dayin gaba abin ta. Yana shiga daidai lokacin inna da amrah sun kamala karin komallo, dan kallon ta yayi dayaga xata dago yayi saurin kaiwa idonsa daga gareta, ya maida kallonsa ga inna sannan yace "inna ina fatan dai komai lfy koh? Yayi tambayar yana mai sauke idanunsa kam amrah, wacce tunda tada go ta xuma masa na mujiya koh kifftawa batayi, dan wani irin kyau dataga yayi, yadda yake kallon tane yasa tayi saurin cewa " yaya ina kwana"lfy kawai yace yamaida kallonsa ga inna wadda take cewa" gsky bbu wata matsala jalalu saidai yarinyar batada kayan sakawa. "Toh shikenan inna xansa Suhaima takaita gurin telanta ayi mata dinki sauran abubuwa kuma xan siyo mata" "toh jalalu saika dawo, Allah yatsare hanya yaya amrah ta fada, dan kallonta yayi yaga still shi take kallo, Amin yace tare da ficewa daga sashen ya nufi part din mommy. πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’« * TIGADAM* Gwaggo kam gaba daya ta canxa ta rame tayi baki koh magana ta dena yi sbd rashin amrah a kusa da ita, inna da harira koh mai data gidansu suka yi sbd idan tana ita kadai abun saiyafi damunta. πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’« Nasarawa GRA, Jalal kam yana shiga part din mommy yagansu kan dining table suna breakfast, Karasuwa yayi fuska a daure yace "good morning mommy" morning jalal ka tashi lfy? Kallonta yayi Dan tunda yake da mommy bata taba amsa masa gaisuwa cikin fara'ah da sakin fuskaba sai yau. Suhaima mah ta gaisheshi sannan najeeb, amsawa yayi sannan mommy tace "jalal xauna kaci abinci mana karkaje office da yunwa" aa na koshi, kamarya ka koshi kullum fah nace kaci abincin sai kace ka koshi koh kana tunanin xan cutar dakai neh? Shiru yayi bece komaiba, ganin yayi Shiru yasa ta cewa "yawwa jalal nayi wani tunani mexai hana amrah tadawo part dina tunda dai kaga karima tatafi garin su kaga saita maye gurbin karima ta rinka gyaramin dakina" Shiru yayi nadan sekonni kafin yace "shikenan tadawo part dinki, amma bayauba saita Dan saba da gidan" Shikenan hakanma yayi, mommy ta fada, najeeb neh yace mommy wacece kuma amrah? Wani banxan kallo tamai sannan tace "bansaniba" tashi yayi yana kunkuni ya fita yabar falon. Jalal kam maida kallonsa yayi ga Suhaima sannan yace "yawwa pls inason bayan la'asar kidauki amrah koje shoprite kiyi mata sayayyar kayan saw a daga nan ki biya gurin tailanki ku bashi dinkin" Fuska bbu fara'a tace toh yaya bada kudin, saidai na miki transfer dan banida cash"OK ta karanto masa account number ta yamata transfer 1 million, ido taxaro lokacinda taga kudin, dagowa tayi ta kallesa, shiko koh kallonta beyi bah ya fice daga gidan. Direct hospital ya nufa yana yin parking saiga sadiq shima yayi parking tasa motar, A tare suka fito suka gaisa sama sama sbd jalal yau tiyata xaiyiwa wata kuma lokaci yakusa shiyasa basu tsaya surutu bah. Suhaima kowa bangaren su amrah ta nufa tana xuwa tace da ita tashirya bayan la'asar xasu fita, toh kawai amrah tace da ita taci gaba da sabgar gabanta. *********** Bayan sallar la'asar suka tafi shoprite, less 5,atamfa ciganbi 5,material 5,abaya 3,sai wando da riga set 5, sai takalmi, da mayafi. Gida suka dawo direct part dinsu Suhaima suka nufa, mommy taga kayan kuma ta yaba, har amrah ta tashi xata woce mommy tace "amrah anan xaki cigaba da xama ga dakai can a sama kusa dana Suhaima, xaki rinka gyara mun dakina dana Suhaima da kuma najeeb" Toh kawai tace, Suhaima ta kaita dakin Wanda haduwar sa harta bace, wardrobe ta jera mata English wears dinta, sauran kuma xata kira tailor dinta yaxo har gida ya amsa. Har takai kofa taji amrah tace "nagode aunty Suhaima", Juyowa tayi ta Harare ta tace "badanke nayiba, nayine sbd yaya jalal", Tana fadin haka ta fice daga dakin. Tashi amrah tayi tana karewa dakin kallo, wasu hawayene suka gangaro daga idunta xuwa fuskarta, a fili ta furta "Allah sarki gwaggo nah nayi kewarki sosai" fitowa tayi ta nufi part dinsu inna tagaya mata mommy ta mayarda ita part dinta, Inna kam kama hannun amrah tayi sannan tace "nasan cewa hajiya ba xata mayarda keh sashen taba haka dai nasan akwai abunda take kullawa, abunda nake so dake shine dan Allah kikula duk abunda tace kiyi indai kikaga bamai kyau bane toh karkiyi, kuma dan Allah ina son ki saka mata ido, sbd tana son ta kawarda jalal daga doron kasa, Wani irin xabura amrah tayi tace "kashe shi take son yi", ina baxan bari hakan ta faruwa, tana gama fadin haka ta fice daga sashen inna. πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’« Bayan wata daya Amrah kam ta kile ta xama yar gayo, ynx tadena rufe fuskarta, ga kuma wata irin shakuwa data shiga tsakanin ta da jalal, har abinci hjy ke bata wai takaiwa jalal, ita kuma sanin cewa hjy tasawa abincin magani yasa take xubarwa tashiga kitchen ta dafa masa wani takai masa batare da sanin kowaba. Amrah ce tafito daga wanka direct wurin kayanta ta nufa, wasu wando da riga ta dakko wandon red rigar black ta dakko wani Dan karamin mayafi black da shoes red ta saka, wooow haduwa sak yar india haka ta fito glasses baki ta dakko tasaka ta shafa red Jan baki, ta fito falo. Tana fitowa najeeb yana shigo wa, wani irin mayyen kallo yabita dashi, ita kam bata masan da mutum bah direct part din jalal ta nufa, tana xuwa tayi knocking, "yes come in" itadai batasan meya ceba kawai ta tura kofar ta shiga, yana xaune kan 3 seater ya dago ya kalleta ji yayi gabansa ya fadi da sauri ya kauda kansa, Tana murmushi ta kara so ta xauna kusa dashi tace "yayana barka da yamma" barka amrah kina lfy? Ya fada hadi dadan kallon ta Dan sbd ta bala'en yimasa kyau, Lfy qlw yayana"tashi yayi yace ina xuwa, ya nufi hanyar bedroom, bada dadewaba ya dawo dauke da waya kirar iPhone 11pro ya bata tare da cewa "ga wayanan na sayawa Kanwata" karba tayi hade da mikewa tsaye ta daka uban tsalle ta fada jikinsa ta rungumesa sosai, shi kam wani irin yarrrrr yaji ga jikinta da bala'en laushi da tsantsi kamar maciji. Da sauri ya tureta daga jikinsa, itakam koh a jikinta saima murna da takeyi sannan tace "ngd ngd sosae yayanah, ta Mike ta fita dadan sauri sauri gudu gudu shikam bin bayan ta yayi da kallo hade da lumshe idanunsa. Part dinsu inna ta nufa ta gwada mata wayarta sannan ta nufi dakinta. Da daddare da misalin karfe goma najeeb ya fito daga room dinsa yanufi dakin amrah Wanda take kan gado cikin wasu hadaddun kayan bacci pink color wando da riga, tana ta danna wayarta, jin alamar an bude kofar dakinta yasa ta Dan dagowa ta kalli kofar, ganin mutum a tsaye yana kallon ta kamar xai cinyeta yasa ta saurin durowa daga kam gadon, Shikam najeeb karasowa yayi cikin dakin ya nufeta gadan gadan ganin haka yasa ta Juyawa Dan ta shige bandaki, da sauri ya damkota ya matseta ajikinsa ya shiga shinshinar wuyanta, Kokarin kwatan kanta take amma ta kasa, tace "Dan Allah ka kyaleni wlh ni ba yar iska bace, juyo da ita yayi yasu hade bakinsu amma taki bari, wanka mata Mari yayi saida gefen bakinta ya fashe. AMRAH kam tashiga rokansa akan ya kyaleta amma ina yaki tun tana bashi hkr har ranta yafara baci 😑fatar jikinta ta fara sabulewa tana xama ta maciji🐍 Hmmm lalle najeeb ka taboo ruwan dafa kanka 🀣🀣🀣🀣🀣🀣🀣 πŸ’«Rabeauty πŸ’« *please vote, comment and share * [8/23, 3:12 PM] +234 808 332 3233: πŸ’«AMRAH MACIJIYA πŸπŸπŸπŸ’« By Rabeauty πŸ₯°πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’« *Aslm amrah fans, yh kuke, kwana da yawa, yh sallah, da fatar kowa yayi sallah lfy, Allah ya maimaita mana, kuma kar a manta da goron sallah nah, nida amrah macijiya*πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ (11) Suhaima kam dakin amrah ta nufa, ita kuma amrah a lokacin tana waya da jalal sai fira su keyi, Da karfi Suhaima ta banko kofar wanda hakan ne yasa amrah saurin tashi daga kwanciyarda tayi, wani irin shu'umin murmushi tayi sannan ta kalli wayarta da jalal yake ta "hello" hands free tasaka wayar sannan tace "yayanah kasan wani abu", aa Kanwata saikin fada, kallon Suhaima tayi sannan ta maida hankalinta ga wayar tace "so nake kasake gayamin wannan kalmar daka fadamin a airport" Murmushi yayi mai sauti sannan yace "I love you so much my darling" Murmushi tayi itama sannan tace "nima ina sanka yayanah kuma koh wace irin kaddara xan iya dauka amma banda wacce xata rabani dakai, kuma koh wane yayi kokarin shiga tsakanin mu toh wallahi saina kawar dashi daga doron kasa" tana gama fadar haka ta kashe wayar, Ai a harxuke Suhaima tayo kanta tana xuwa ta kwace wayar ta ta jefata da bango nan take wayar ta watse, ai da sauri amrah tayi kan wayar ta wasu hawayen bakin ciki suka xubo mata, Suhaima koh jelar gashin amrah ta damka da karfi Wanda yasa amrah sakin kara, hankadata tayi saida kanta ya bugi gado, ta shako wuyanta ta wanka mata mari ta sake kara mata wani, ai take hanci da bakin amrah yafara fitarda jini, ta sake daga hannunta da niyar kara marinta, amrah ta rike hannunta, idanta sunyi jajir sosae abunda basu taba yiba kenan saidai sukara green, amma yau kam jajir suka yi, Dakyar amrah ta bude bakinta tace "lalle Suhaima kin tabka babban kuskure tunda uwata ta haifane ba'a taba yimin hakaba, amma yau wai nice wata ta mareni har ta fitarmin da jini hmmmmm, nida koh kallon banxa mutum yamin sainaga bayansa amma wai ni *AMRAH MACIJIYA* 🐍 aka mara, Suhaima najin haka jikinta yadau kyarma, wasu irin fitinannun tagwayen mari amrah ta wanka mata, Wanda suka yi sanadiyar fashewar hanci da bakinta nan take ta fadi kasa, nan amrah ta sake wanka mata wasu marukan a lokaci guda, wannan karon kam gaba daya dena ji Suhaima tayi, tana kuka tace dan Allah kiyi hkr, nasan na aikata kuskure amman wlh shairin shaidanne, Rufemun baki amrah ta daka mata tsawa hade da girgijewa ta xama shirgegiyar macijiya 🐍, Ai nan take Suhaima ta sumeeeee. *Mascow* Jalal kam kalaman amrah na karshe sune suka tsaya masa arai ya rasa ina kalaman ta suka dosa, sadeeq neh ya shigo yace, "haba buddy tun daxo muke jiranka fah amma kaxo nan kanata waya da girlfriend dinka, kuma kasan yaune xa'ayi wannan tiyatar, kuma inaji ajikina inshaa Allah xamuyi nasara" Hakane nima inaji ajikina, muje suka fito suka shiga mota direct *Mascow International hospital* aka kaisu, suna xuwa babu bata lokaci suka shiga tiyatar, πŸ’¦Ni kuma nace all the best jalal πŸ’¦ *KANO* AMRAH kan saida ta wahalarda suhaima sannan ta kyaleta, dakyar Suhaima ta iya Jan jikinta tanufi dakinta, Ita kuma amrah gurin wayarta ta nufa tana xuwa ta dauki a barta ta haye kan gado tasa tafin hannunta ta shafe wayar nan danan tadawo sabuwa gal, ta tashi tasaka caji ta nufi bangaren su inna, Tana xuwa ta xauna acan sukasha firarsu da inna, Hajiya Sarah koh tana can tana neman yadda xata kawarda jalal, da taje gurin bokan hajiya nafeesa ce mata yayi "a gaskiya indai kinason kawarda jalal daga doron kasa toh fa saikin fitarda wannan yarinyar daga gidanki sbd indai tana cikin gidan toh fa bbu abunda xamu iyayi", toh amma boka meyasa kace haka, Dariya ya kyalkyale da ita marar dadin ji sannan yace "ga wannan ki turarashi a cikin gidanki koh wane lungu da sako, xakisan dalilin da yasa nace saikin fitarda ita tukun" karba tayi tace ngd boka, ta fito ta dawo gida, Tana xuwa tasaka mai aiki ta ibo mata garwashi Dan tayi turaren da boka ya bata, Ita kuma amrah har ynx tana part dinsu inna, Mommy kan dauko wannan turaren tayi ta bude ai da sauri ta rufe, tafarnuwace da k'ashi da kuma barkono aka hade gu daya aka nikesu, Kunsan mee hmmmmm, wannan turaren idan amrah tajishi tohfa xata rikide ta xama macijiya kuma kunsan tana part din inna, kenan asirin amrah xai tonu koh yaya, ku biyoni kuji yadda xata kaya πŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ πŸ’«Rabeauty πŸ’« *please vote comment nd share* [8/23, 3:12 PM] +234 808 332 3233: πŸ’«AMRAH MACIJIYA πŸπŸπŸπŸ’« By Rabeauty πŸ₯°πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’« (9) Wani irin hankadashi tayi saida ya daki bango, A fusace ya dako, Amma me ganin yayi amrah ta rikide ta xama shirgegiyar macijiya amma bagaba dayaba, Daga samanta xuwa kugunta tananan a mutum dinta, amma daga kugunta xuwa kasan ta yaxama na maciji, gashin kanta ya mimmike tsaye ya koma macixai, idanunta sunkara xama green sosai hatta kwayar idonta da take fara toh itama ta koma green, kunnen ta yana fitarda wani hayaki, Wanda ya turnuke dakin baka iya ganin komai, Najeeb kam tuni xawo da fitsari sun kubce masa Dukda Baya ganin ta sbd hayakin amma behanashi ja da bayaba yana cewa "Dan Allah baiwar Allah kimin rai wlh bansan cewa keba mutum bace Dan Allah kiyi hkr, yana kaiwa karshe ya rushe da wani irin kuka, Wanda daka jishi xakasan na tsoro neh da firgici, Hhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhh amrah ta kyalkyale da dariya marar dadin ji, dariyar da ta kara firgita Najeeb, Sannan tace "kayi kuskure matuka tunda har kayi niyar rabani da budurcina, darajata, da kuma 'yancina, tunda nake a rayuwata ba' ataba yimin hakaba, kuma duk Wanda ya shiga gonata tohfa bana barinsa a doran kasa xan kashe shi, amma kai baxan kashe kaba sbd abu guda, shine JALALUDDEEN, kaci albarkacin sa, sbd kai kanen sane, wlh wlh wlh dabadan hakaba da saina kashe ka, kuma idan ka kuskura naji wannan xancen a bakin wani wlh xan manta da cewar kai jinin jalal neh na kashe ka, Tana gama fadar haka hayakin dakin ya Washe ai da sauri Najeeb yabar dakin, yana xuwa room dinsa yasa key ya kulle kofarsa ya haye kan gado ya shige cikin blanket ya rufe kansa gaba daya jikinsa rawa yake. Ita koh amrah kwanciya tayi akan gadonta daga kugunta xuwa sama ya rikide ya Ida xama na maciji, a haka tayi baccinta. **************** Washe gari jalal kam yanata hada kayansa sbd xai tafi mascow gurin wani operation da xasuyi bama shi kadai xaijeba harda sadeeq da wasu doctors, gobe xasu tafi Abuja, saisu hau jirgin da xai kaisu mascow. A bangaren amrah koh tana tashi daga bacci tayi wanka ta shirya cikin wata fitted gown ta material maroon wadda ta mugun yimata kyau ta kara fito da haskenta, Fitowa tayi ta nufi part din jalal, a hanya ta hadu da Suhaima itama xataje gurinsa, taci adonta itama cikin wata riga ta yan kanti blue, wani irin banxan kallo Suhaima tayi mata, itakam batama bi ta kantaba, Suhaima tariga amrah isa bakin kofar part dinsa tashiga yin knocking , itakam amrah tana isowa tabi ta gefenta ta bude kofar tana shiga ta banko kofar da karfi, da ace Suhaima bata matsaba da kofar ta daki fuskar ta, Suhaima kam ji tayi kamar ta buga ihu dan tsabar takaici,ace yarinya karama tana son taxamam mata jaraba juyawa tayi ta shiga motar ta tabar gidan. AMRAH kam tana shiga direct ta haura sama inda dakinsa yake, tayi knocking, jalal kam da yake kan gado ya daura system dinsa akan cinyarsa yana wani aiki yaji ana knocking din kofarsa, Dan kallon kofar yayi sannan yabada ixinin shigowa, A hankali ta turo kofar bakinta dauke da sallama, amsawa yayi hade da kafeta da mayun idanunsa masu rikitarwa, Karasowa tayi ta xauna bakin gadon ta gaisheshi, amsawa yayi still idanunsa yana kanta, dan kallonsa tayi da sauri ta sadda kanta kasa sbd ynx ba xata iya jure kallon sabah, "kinyi kyau sosai" yace da ita, dagowa tayi tana murmushi tace "ngd" shiru suka yi for some minute sannan tace "yayana Dan Allah su nake mufita", xuwa ina? yace da ita, gurin shakatawa ta bashi amsa, OK jirani a falo ina xuwa, da sauri tace "toh" ta fita tana jin dadi, binta yayi da kallo, yana jin wani abu yana tsargar masa, Shiryawa yayi cikin wata white gizna, yayi kyau matuka, Falo ya nufa akan kujera ya same ta yace "mutafi koh", juyowa tayi ta kallesa tace "kai yayana kayi kyau sosai wlh kamar na saceka na tafi dakai" murmushi kawai yayi ya nufi kofa binsa tayi suka jera tanata yimai surutu, Dan kallonta yayi sannan yace "haka xakije babu mayafi" Hannunta ta dora kan goshinta tace "kash wlh ni nama manta ashe ban dauko mayafi bah" Da sauri ta nufi part dinsu tana shiga ta dakko mayafinta ta fito, daidai lokacinneh mommy ta fito daga room dinta ta sakko kasa, kallon amrah tayi sannan tace "ke sai ina kuma" Kallonta amrah tayi tace "fita xamuyi da yaya jalal" Kan uba mommy ta fada "toh bbu inda xaki maxa woce ki gyaramin dakina" Wani banxan kallo amrah tayi mata sannan tace "hmm bbu mahalu kinda ya isa ya hanani fita da yaya jalal Dan haka kinga tafiya ta" ta juya tana tafiya tana karkadawa mommy hips. Tana Fitowa ta shiga gaban mota yaja sukabar gidan, direct gidan zoo ya nufa da ita, Hmmmmm aiki jaaaa, toh kai jalal daka kaita gidan zoo toh idan taga yan uwanta macixai fah? Koh da yake babu ruwana Dan bani nace ka kaitaba eheee😏😏😏😏 πŸ’«Rabeauty πŸ’« *please vote, comment, and share * [8/23, 3:12 PM] +234 808 332 3233: πŸ’«AMRAH MACIJIYA πŸπŸπŸπŸ’« By Rabeauty πŸ₯°πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’« (10) Suna isa yayi parking suka nufi bangaren da namun daji suke, aiko ta dakko wayarta tayi ta musu vedio da pics, Shidai saidai ya kalleta yayi murmushi, wani bangaren taga ya nufa, tace "yayana ina xakaje? Bangaren macixai, ya bata amsarda, gaban tane yayi wani irin mummunan faduwa, tace" yayana dama kana son macixai? "eh amrah ina matukar kaunar macixai, amma banason suxo kusa dani, dan kallonsa tayi xuciyarta na kara harbawa, karasawa suka yi gurin macixan, Wani maciji baki kirin yana ganin amrah ya fara xillo yanason ya fito daga cikin kejin, jalal kam yadan tsorata ganin yadda macijin yakeyi, Itakam amrah koh a jikinta sbd tasan cewa kohya fito bbu abunda ya isa yayi mata, Jalal kam da sauri yaja amrah sukabar gurin, yawo suka yi sosai a cikin gidan zoo din basu bar gidan zoo ba saida akayi la'asar, Shoprite ya kaita ya siya mata chocolates da biscuits dasu cake da dai sauransu, basu dawo gidaba sai around 6, Jalal kam yana komawa part dinsa ya Ida hahhada kayansa dan gobe jirgin 9 xasubi ya kaisu Abuja daga can suhau na mascow ya kaisu, kuma ya yanke shawarar gayawa amrah cewa yana sonta, Dukda yasan ta mai yarinya amma baxai iya cutar kansaba xai gaya mata yana sonta, idan ya dawo ya gayawa daddy ya samu matar da xai aura, dan daya aure Suhaima ya gwammace ya xauna bbu aure. ************** Washe gari sadeeq ya kira jalal yace masa kawai su hadu a airport, Shiryawa yayi cikin sut dinsa baki wa'enda suka kara fito da kyansa da kuma haskensa, part din mommy ya nufa ya gaya mata xai wuce, Allah ya tsare kawai tace, a ranta koh cewa take "Allah yasa jirgin ya fado duka kumutu"hmmm ni kuma nace" Amin walaka tare dake😏😏😑😑 Jalal kam harya fito xai wuce sai kuma ya juyo ya kalli kofar dakin amrah, a xuciyarsa yake cewa "dama ta fito na ganta kafin na tafi", saida yadan bata lokaci amma amrah bata fitoba, Juyawa yayi ta tafi, har yakai bakin kofar fita daga main falo yaji ance "yayanah" da wata irin murya ta shagwaba, Ai da sauri ya juyo, amrah ce ya gani sanye cikin riga da siket sunbi jikinta sun xauna das, ta yafa mayafi ja sbd atamfar akwai ja, karasuwa tayi kusa dashi, lumshe idanunsa yayi sbd wani daddadan kamshi daya daki hancinsa, A shagwab'e tace "yayana ynx da ban fito bah tafiya xakayi bako sallama" Da sauri ya sake rufe idansa sbd wani yarrr yarrr da yaji tundaga kansa har xuwa babbar yatsarsa ta kafa, Ta sake cewa "yayana xan rakaka Airport din, ok muje, suka fito, driver yaja so xuwa airport, suna xuwa yaga harsu sadeeq sun iso shi kadai suke jira, Bude motar yayi ya fito, itama amrah ta fito, driver ya dakko mai luggage dinsa suka nufi gurin su sadeeq, Tun daga nesa sadeeq yake kallonta yana ganin kamannin mai gadinsu akan fuskar yarinyar, Karasuwa suka yi amrah ta gaishesu, sadeeq yace "buddy ina kasamo wannan kyakkyawar?, bansaniba ya basa amsa karbar kayan hannun driver yayi yace" ka mayarda ita gida pls", toh mai gida, Ya juyo ya kalli amrah yace "ranki ya dade mutafi koh", raurau tayi da ido tana son yin kuka, Jalal neh ya kama hannunta suka Dan matsa daga gurin su sadeeq, yace "haba amrah menene haka so kike nima nayi kukan neh, nimafa ba'ason raina xanbarki a wannan gidanba, so pls take care of your self kinji, I love you, yabata peck a goshi ya juya ya tafi suka shiga cikin Airport din, yana shiga aka fara Kiran passengers suka shiga jirgin su ya daga xuwa mascow ✈️ Amrah kam tananan a inda yabarta saida driver yaxo yace sutabi sannan, Suna isa gida, da gudu ta shiga part dinsu, mommy dake xaune a falo ce tace "subhanallah ke lfy xaki shigowa mutane cikin gida da gudu bako sallama, wannan ai iskanci neh" taja tsaki, Amrah kam tana shiga ta haye kan gado taci gaba da kukanta, a xuciyarta Ko tana ta tunanin me kalmar take care of your self take nufi da kuma I love you,doleneh mah ta tambayi Suhaima, a haka bacci ya dauketa. πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’« MASCOW Sun isa lfy, har ankaisu masauki shida sadeeq, sauran doctors din kuma suka kama hotel, Wanka yayi sannan ya kwanta bacci sadeeq kuma ya tafi siyo musu abinci. πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’« A bangaren amrah koh, tana tashi daga bacci tayi sallar axahar ta fito falo taci abinci, sannan ta nufi dakin Suhaima, Ita kuma ta fito daga wanka taji knocking, bata xata amrah bace ta bada ixinin shigowa, A hankali ta turo kofar, kallonta Suhaima tayi ta wani hade fuska tace "uban me kikaxo yimin a daki", ayya aunty Suhaima Dan Allah abu naxo na tambayeki, tayi mgnr cikin sanyin murya, OK shigo tace da ita, karasuwa tayi ta xauna bakin gadon ita kuma ta nufi gaban mirror ta xauna hade da cewa "ina jinki", yawwa Dan Allah aunty Suhaima me kalmar "take care of your self" take nufi, Ta cikin mirror Suhaima ta kalleta sannan tace "tana nufin ki kula da kanki" yawwa aunty da kuma "I love you", ai da sauri suhaima ta juyo ta kalleta sannan tace "waye yace miki hakan? Saikin gayamin wnn tukunnah, OK OK xan gaya miki, kalmar I love you tana nufin" ina [8/23, 3:12 PM] +234 808 332 3233: πŸ’«AMRAH MACIJIYA πŸπŸπŸπŸ’« By Rabeauty πŸ₯°πŸ’«πŸ’«πŸ’« (12) Mommy kam fara turara maganin tayi ta fito har main falo tanayi ta nufi bangaren masu aiki, Amrah dake kusa da inna sunacin Dan wake taji warin wannan maganin nan da nan yanajin ta ya fara canxawa, Inna dake kallon ta tace "fatima meya faru" bbu komai inna ta bata amsa, A ranta koh cewa take "innalillahi wa'inna ilaihirraji'un meyake shirin faruwa dani, wane shegen ne yakawo wannan maganin a cikin gidan nan, nashiga uku" jin maganin yana nufu dakinda suke yasa ta saurin mikewa da niyar shigewa toilet, amma kamar a mafarki taji andagata sama an rafke kasa, ihu tasa nan take tafara nannadewa tana wani mukurkusu kamar yadda macixai keyi, amma still tananan a mutum inta, inna dataga haka ai da sauri tayo kanta, tana cewa "innalillahi wa'inna ilaihirraji'un fatima meya sameki, fatima, fatima!!, amma ina amrah bataji da sauri inna tasa hannu ta dagota wani irin sulbi taji kamar ta rike fatar maciji da sauri taja da baya sbd ganin fatar amrah tafara sab'ulewa tana xama ta maciji, inna kam ta tsorata ainun amma bata nunaba, Amrah koh taxama shirgegiyar macijiya 🐍, tayi kan inna, ina kam tariga data sadaqat amma jin shiru yasa ta bude idonta amrah tagani ta laulayeta tana fuskantarta, dakyar inna ta iya bude bakinta tace "fatima dama ke ba mutum bace, macijiya ce", Eh inna ni macijiya ce kuma a gsky banso kisan hakaba nasan cewa mommy ce tayi wannan turaren, amma bansan dalilinta nayiba kuma babu abunda xan miki sbd na daukeki tamkar gwaggo tah amma inason dan Allah karki gayawa kowa koda jalal neh, amma fa Suhaima tasani da kuma najeeb, Shikenan fatima bbu Wanda xai sani inshaa Allah, nan tasaketa ta koma ta nannade da sauri inna tatashi taje tasawa kofar dakinta key, Sannan tadawo ta xauna tana fuskantar macijiya, tace fatima koh xaki gayamin taya kika xama macijiya, Nan amrah ta shiga bawa inna labarinta daga farko har inda jalal ya kadeta, hawaye inna tashare tace Allah ya isar muku akan BAHUUL, shi kuma magaji Allah ya bayyanashi, Amin amrah tace, nan amrah ta kwana sbd tayi tayi ta koma mutum amma abun yaci tura sbd turaren da mommy tayi har ynx bewashe bah, *mascow* Alhamdulillah su jalal sunyi nasara a tiyatar da suka yi ba'a samu matsa koh dayaba, kuma gobe inshaa Allah xasu dawo Nigeria, Bayan sun koma masaukinsu ya kira amrah, amma bata dagaba 3missed call yayi mata amma no answer, *kano* Amrah kam tana bangaren inna wayarta kuma tana dakinta shiyasa, kuma alhmdllh ta dawo daidai, Fitowa tayi ta nufi bangaren su da Suhaima taci karo ai da gudu suhaima ta koma dakinta tasa key, Abun mah dariya yabawa amrah, tana shiga daki ta nufi bathroom tayi wanka ta shirya cikin wani material pink ta nufi gurin wayarta tana dubawa taga yayanah 3 miss calls, ai da sauri takirasa back, yana dauka yace "ina kika aje wayarki nayi ta kira no answer," ummm ina wurin inna shiyasa kuma wayar nabarta a daki tana caji, OK dama kira nayi na sanar miki gobe inshaa Allah xan dawo, Kai haba amma naji dadi wlh amrah ta fada, kuma idan na dawo makaranta xan saki, kinaso? " eh wlh yayanah inaso", toh shikenan, nan dai sukaci gaba da firarsu. *Washe gari* Inna da amrah ne a kitchen suna yiwa jalal girki, mommy ce tashigo cikin kitchen din ta kallesu a wulakance sannan tace "me wannan kuke yi batare da ixini naba eh" inna ce tace au ai hajiya naxata kinsani sbd naga yau jalal xai dawo kuma fatima ce tace amasa girki, kuma ni wlh naxata ke kika gaya mata amasa girki", Kutumar uba mommy ta fada wani irin kallo tayiwa amrah sannan tace "kee ubanwa yabaki ixinin yiwa jalal girki, keba kowaba keba matarsaba amma kina wani shisshige masa, au sorry na manta ashe karuwarsa ce, Da sauri amrah ta dago tana duban mommy xuciyarta na tafasa, da sauri inna takire mata hannu gudun kar asirin amrah ya tonu, Tsaki mommy taja tabar kitchen din, karasa girkin suka yi amrah tace "inna inason ki kulamin da abincin nan naje nayi wanka sbd ban yarda da mommy bah xata iya xuba wani abu daxai illata yayanah, Toh shikenan jeki kiyi wanka yar albarka xan jire miki abincin, toh shikenan ta fita daga kitchen din ta nufi dakinta, tayi wanka ta feshe jikinta da body spray tasa wata duguwar riga A shape ta lace tayi mata kyau sosai tayi daurin ture kaga tsiya tashafa powder da lipstick ta kara feshe jikinta da perfumes masu sanyin dadi, ta dauki wayarta ta kira jalal, Jalal da saukarsu ynx kenan yaga Kiran amrah murmushi yayi, yayi rejecting call din, amrah koh ganin yayi rejecting yasa ta tunanin koh har ynx yana cikin jirgi, sallar axahar tayi. πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦ Bayan wasu mintuna amrah ta fito ta nufi kitchen ta fara dauko kayan abinci inna na tayata suka jera akan dining table, Jalal neh tsaye bakin kofa yana kallon ta, kamshin turarensa taji ai da sauri ta juyo, da sauri ta nufusa da niyar hugging dinsa, ai da sauri ya jaye yana hade fuska, yace "waike bakisan kingirma bah", hannu tasa ta rufe fuskarta alamar taji kunya tace "ya hakuri yayanah", murmushi y [8/23, 3:12 PM] +234 808 332 3233: πŸ’«AMRAH MACIJIYA πŸπŸπŸπŸ’« By Rabeauty πŸ₯°πŸ’«πŸ’«πŸ’« (13) Da sauri aka wuce da ita emergency doctors suka dukufa a kanta, Wata nurse ce ta fito tace ana bukatar jini da sauri jalal yace a ibi nasa, Lab suna nufa aka duba jininsa da nata yaxo daya, ibi tayi suka fito a tare ta nufi emergency din, Jinin suka saka mata sannan suka dukufa akan aikin su dan ceto rayuwar amrah. πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦ A waje koh jalal neh ya kira sadeeq ya sanar dashi halinda ake ciki, hankali tashe sadeeq yace gashinan xaixo, Aa buddy kabari sai gobe ynx fah karfe 1 na dare ka bari sai gobe, shikenan sadeeq ya fada sannan ya kashe wayarsa. πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦ A bangaren amrah koh sun cire bullet din, amma bata farfadoba sunyi mata allurai sun bata taimako na gaggawa ynx kuma sai ta Allah. Fitowa doctors din suka yi da ita aka canxa mata daki ai da sauri jalal da inna suka Mike tsaye jalal yace "Doctor how's she? Kallonsa doctor imran yayi yace am sorry doctor jalal mudai munyi iya bakin kokarin mu amma still bata numfashi ynx kuma saita Allah, Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un innalillahi wa'inna ilaihirraji'un innalillahi wa'inna ilaihirraji'un kawai yake maimaitawa, inna kam xubewa tayi akasa tasa kuka, dakyar yace "xan iya ganin ta? Eh toh a gsky bekamata a ganta ynx ba but since u are a doctor u can see her amma karkayi hayaniya da yawa sbd condition dinta, OK kawai jalal yace ya nufi room dinda take, A hankali ya shiga ya nufi gurin gadonta kallon ta yayi sai kawai yafara hawaye a ransa yace "da ynx nine akan gadon nan ashe xata iya sadaukarda ranta a kaina, hannunta ya kama afili yace *amrah* but shiru ya sake cewa *amrah* still shiru yace pls amrah ki tashi karki tafi ki barni wlh idan kika mutu nima mutuwa xanyi a karon farko na rasa soyayyar mahaifiya banason akaro na biyu narasa soyayyar ki pls ki rayu koh Dan sbd ni Dan Allah, ya fashe da wani marayen kuka, *yayanah* yaji anfada da sauri ya dago ido 2 suka yi da amrah wacce eyes dinta sunkara rinewa sunxata green sosai, ai da sauri ya saki hannunta ya fita da sauri yakira dacta imran da sauri aka shiga room din suka kara duddubata suka mata allurar bacci, nan take tayi bacci, Suka fito waje inna tace ya jikinta? Da sauki inna ki shiga ciki pls ki kwana da ita ni xan xauna a mota dakinga wata matsala ki kirani, Toh shikenan amma da ka tafi gida mana, aa xan xauna a mota, shikenan ta shiga ciki, shi kuma ya fita gurin motarsa ya shiga ya kwantar da sit dinsa ya kwanta. πŸ’«Rabeauty πŸ’« *please vote comment nd share* [8/23, 3:12 PM] +234 808 332 3233: πŸ’«AMRAH MACIJIYA πŸπŸπŸπŸ’« By Rabeauty πŸ₯°πŸ’«πŸ’«πŸ’« (14) Yayanah!!! Dan Allah ka taimakeni xan mutu wayyo Allah nah, amrah ce ke wannan mgnr, tana kasan wata bishiya rabi mutum rabi maciji, shi kuma jalal yana daga nesa duk ya rikice idan ya matso kusa da ita saita kara rikidewa har ta xama shirgegiyar macijiya tayo cikinsa. Ai a firgice yafarka daga mummunan mafarkin da yake "innalillahi wa'inna ilaihirraji'un innalillahi wa'inna ilaihirraji'un innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, kawai yake maimaita wa duk yayi gumi, da sauri ya dauko wayarsa yaga 6 harta wuce gashi koh sallah ma beyiba ruwa ya dauko a cikin motar yayi alwallah ya dauko sallaya yayi sallah, A bangaren amrah koh ta farka amma duk jikinta ciwo yake mata kuma ga fatarta ta fara sabulewa amma ta hannu kadan kadan bama xaka gane ba sai idan ka tsura mata ido, dalili kuwa, allurar da aka mata kunsan maciji bayason karfe a jikinsa kuma kunsan an mata allura, kuma sai annemu wani magani a wani kasungumin daji, kuma ita kadai xata iya xuwa wannan dajin domin fa idan mutum ya tafi baxai dawo da raiba, amma ita kunsan ba mutum bace xata iya xuwa, amma kuma ta yaya bayan batada lfy hmmmπŸ€”πŸ€”πŸ€” Jalal ne ya shigo dakin bakinsa dauke da sallama, amsawa inna tayi suka gaisa ya nufi gurin amrah wannan mafarkin yana dawo masa acikin kwakwalwa, Yayanah ta kira sunansa cikin mawuyacin hali yace "Kanwata yah jikinki? Da sauki yayanah, Allah yakara sauki, Amin, Yayanah Dan Allah mu koma gida, sbd me Kanwata ki bari harki kara jin sauki mana, waima kinyi sallah, aa banyiba, OK, inna pls taimaka mata tayi alwallah, toh shi kuma ya fita dan yaje gida yayi wanka ya siyo musu abinci, Bayan fitarsa inna ta taimaka mata tayi alwallah a xaune tayi sallah, amma fah ita amrah koh kadan batajin xafin bullet dinda ya shiga jikinta sbd kunsan ba cikakkiyar mutum bace, kawai dai karfenda akasa aka huda jikinta neh ya jawo mata rashin lafiya wato allurar da doctor yayi mata. Direct gida jalal ya tafi ya shiga part dinsa yayi wanka ya shirya ya fito saiga najeeb ya shigo yana layin maye da sauri jalal ya rikesa suka xauna kan ku jera tsura masa ido jalal yayi yana tunu when last yaga najeeb indai Bai mantaba tun kafin yabar kasarnan rabonsa dashi, Wayarsa ce tafara ringing yana dubawa yaga daddy gaban sane ya fadi kardai mommy tagaya masa abunda ya faru daren jiya, dauka yayi "assalamu Alaikum daddy barka da safiya" barka dai jalal kaxo Airport ynx ynx ka daukeni sbd tun jiya mahaifiyar ku tagayamin abunda yafaru ynx haka jirginmu ya sauka ina Airport kayi sauri, ya kashe wayar, Kallon najeeb yayi yace "najeeb meyasa ka maida kanka haka meka nema a duniyar nan ka rasa kagayamin ya daka masa tsawa, koh kala najeeb be ceba ya tashi yana layi ya nufi hanyar part dinsa, girgixa kai kawai jalal yayi ya dauki key dinsa ya nufi airport ya dauko abba, A bangaren amrah koh jikinta ya rikice sosai dan duk fatarta ta xama ta maciji amma rabi daga kugunta xuwa sama yananan a mutum, inna dukta rikice ta rasa wane taimako xata mata kafin jalal ya dawo ya ganta a haka, Amrah kan kuka kawai take ta rasa yadda xatayi Dan tasan idan har ba wannan ganyan maganin ta shaba tohfa baxata warkeba a rabi mutum xatata xama, Bayan jalal yakai abba gida shi kuma ya wuce gurin sadeeq momin sadeeq ta bada abinci a kaiwa su inna tace xuwa anjima xasuxo su dubata itada khairat kanwar sadeeq, Harsun fito sunshiga mota sun kama hanyar asibiti daddy ya kirasa yace yaxo ya daukesa suje asibitin tare yaga ya jikin yarinyar, K'ak'a k'ara K'ak'a yaufa ake yinta, daddy da jalal harma da sadeeq xasuga abunda yafi karfinsu,🐍 hmmmm muje xuwa kawaiπŸ’ƒπŸ’ƒ πŸ’«Rabeauty πŸ’« *please vote comment nd share* [8/23, 3:12 PM] +234 808 332 3233: πŸ’«AMRAH MACIJIYA πŸπŸπŸπŸ’« By Rabeauty πŸ₯°πŸ’«πŸ’«πŸ’« (15) Inna dan Allah so nake ki sakawa kofarnan mukulli kafin naje na dawo, A tsorace inna take kallon ta kafin tace "fatima ban gane abunda kike nufiba ina xakije" Inna xanje dajin da xan samu maganin sbd banason jalal yaxo ya sameni a haka, ba ynx bane ya kamata yasan gaskiyar koni wacece ba, Ki kwantar da hankalinki ba dadewa xanyiba duk da nasan dajin yanada hadari sosae amma ga Wanda ya kasance mutum, dan haka nasan baxan sha wuyaba gurin shiga dajin, Kwana biyu akeyi ana tafiya amma fa idan bil adama neh, amma ni cikin kankanin lokaci xanje na dawo, Kawai abunda nake so dake shine ki rufe kofar, karki kuskura ki bude saina dawo tukunnah, Dogon numfashi inna taja tace"shikenan fatima Allah ya tsare ki amma dan Allah kiyi sauri domin nasan jalal yana hanya, karki damu inna tana gama fadar haka ta tashi ta shiga toilet, Wasu irin maganganu naji tanayi Wanda bana fahimtar komai kafin wani dan lokaci ta b'ace b'at, Inna kam ganin amrah ta shiga toilet, tayi sauri ta tashi taje tasawa kofar key dukda haka saida tasa sakata, tadawo ta xauna addu'ah kawai takewa amrah, na Allah ya kubutar da ita Dukda koh ta kasance ba mutum ba amma tasan tana bukatar addu'ah. πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦ Jalal kam tuki kawai yake amma hankalinsa yana kan amrah koh wane hali take ciki ynx, Wani dutsi mai tsini ya taka ji kake fatttt taya ta fashe Allah yasu ba gudu yake da motar ba, gangarawa yayi gefen titi yayi parking daddy yace "kamar fa tayarce tayi faci, eh inajin amma bari na duba suka fito shida sadeeq, Aiko dai tayarce ta fashe gashi bashida wata ballantana ya canxa, kallon sadeeq yayi yace" buddy ynx ya xamuyi gashi na barsu koh abinci bbu a gurin su ga taya ta fashe, Koh ka jira nahau napep naje gida na dauko wata tayar, koh ya kagani, eh hakan yayi amma pls kayi sauri, karka damu, ya tare dan sahu ya shiga, shi kuma jalal ya koma cikin motar, ina kuma sadeeq yayi, daddy ya tambaya, yaje dauko wata tayar, OK bbu laifi, wayar daddy ce tayi ringing yana dubawa yaga "alhaji ma'aruf wato mahaifin sadeeq, dauka yayi suka shiga gaisawa. πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦ Amrah kam saida ta wahala sosae tasha fama da miyagun aljannu, sannan kuma taga wasu miyagun halittu suna nufu inda take, ta tsorata ainun amma da yake jarumace sai bata nuna tsoron ta a filiba, Daukarta suka yi suka b'ace tare sai ganin ta tayi a gaban wani bakin aljani πŸ§Ÿβ€β™‚οΈmarar kyan gani Wanda idan da mutum ne yayi toxali da shi tohfa bbu shakka xai iya suma, Wata irin dariya ya kece da ita marar dadin ji, Wanda tasa amrah xabura yace cikin kakkausar murya "keeeee macijiya nasan abunda ya kawoki dajin nan, kuma xan baki wannan ganyan kisha amma kuma shine na farko shine na karshe idan kika bari aka kara huda miki jiki tohfa karki kuskura kixo nan dan bama taimako sau biyu daya mukeyi dan haka ki kiyaye, ya daga hannunsa sama ya fara wasu maganganu sai kawai wani gane ya fito daga hannunsa ya bata yace maxa ki taune shi ynx ynx, Karba tayi ta taune, ya kalli aljannun da sukaxo da ita yace ki dauke ta ku mayar da ita inda kuka dauko ta karku bari wani abu ya same ta. πŸ’«Rabeauty πŸ’« *please vote comment nd share* [8/23, 3:12 PM] +234 808 332 3233: πŸ’«AMRAH MACIJIYA πŸπŸπŸπŸ’« By Rabeauty πŸ₯°πŸ’«πŸ’«πŸ’« (16) Karba tayi ta taune, ya kalli aljannun da sukaxo da ita yace ku dauketa ku mayar da ita inda kuka dauko ta karku bari wani abu ya same ta, ***************** Sadeeq ne ya kawo tayar suka canxa sannan suka nufi asibitin, πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦ *TIGADAM* Gwaggo dan Allah kici abinci duk kin fige kinyi baki dan Allah ki daure kici koh kadan ne sai kisha maganin ki, harira ce ke wannan mgnr, Kallon ta gwaggo tayi tace "harira kina tunanin zan iya cin wani abu, bayan bansan wane hali jikanyata takeba, Inshaa Allahu gwaggo amrah tana cikin koshin lfy, ki kwantar da hankalinki dan Allah, inna ce ta shigo mayafinta ta aje ta kara so ta karbi abincin dake hannun harira tace "harira je kiyi wanke wanke bari ni na bata abincin, Tashi harira tayi ita kuma inna ta fara bawa gwaggo abincin, loma uku tayi tace ta koshi, haba dai da dai kindan kara, kanta ta girgixa,ta balli maganin ta tasha, sannan ta tashi tashiga daki, ta kwanta sai tunanin jikanyarta ya fado mata "fatima Allah ya bayyanamin ke ya bayyana mahaifinki, Amin" πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦ Kofar aka shiga kwankwasawa jikin inna ya fara rawa tace "innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, inna lfy ina knocking kinki budewa, jalal ya fada, Kofar toilet aka bude amrah ta fito, ajiyar xuciya inna ta sauke tace" fatima kin tayar min da hankali" murmushi tayi tace ya hakuri inna je ki bude amma ki murxa idonki yadanyi jaa sai kice bacci muke, tana gama fadar haka ta haye kan gado, Saida ta murxa idonta sosai sannan ta nufi Kofar ta bude, ah ah JALALUDDEEN kaine, ta fada tana basu hanya shigowa suka yi yace "inata knocking baki budeba, eh wlh bacci ya daukeni shiyasa, OK kawai yace ya nufi gurin amrah, Ita kuma inna ta gaida daddy, sannan Sadeeq ya gaidata, Kanwata ya jikinki? da sauki yayanah, Allah ya kara sauki, Amin, Daddy ne ya matso yace" 'yata ya jiki? Da sauki abba, Allah ya kara sauki, yayi miki albarka, Amin abba ngd. Kallon ta jalal yayi koh ya akayi tasan shine mahaifinsa ohoπŸ€·β€β™‚οΈ Ita kuma amrah kallo daya tayi masa tasan shine mahaifin jalal, Sadeeq kam tunda suka shigo yake ta kallon ta yana kara ganin kamar ta data baba mai gadin gidansu, tabbas wannan kamar tayi yawa, Kallonsa amrah tayi tace yaya Sadeeq ina wuni, Lfy qlw amrah ya jiki? Jiki alhmdllh, Allah ya kara sauki, Amin yaya nagode, Inna ce ta kawo mata abincin da jalal yaxo dashi tace ga abinci ta xauna ta fara bata, Fita suka yi domin ya mayar da abba gida, Tana gama cin abincin tasha magani sannan ta jingina da gadon, πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦ Suhaima ki tashi mu tafi asibitin nan, ni gsky aunty bbu inda xani yarinyar da na tsana kuma xanje na duba ai wlh saidai ta mutu, waike Suhaima meke damunki a haka kikeson jalal ya aureki, kina nuna bakya son abunda yake so, toh wlh gara ma ki canxa ki nuna kina sonta koya soki shashasha kawai dallah tashi muje, Tana turo baki ta dauki Jakarta suka wuce, Suna zuwa suka duba jikin amrah suka wuce gidan hajiya Sarah, Basu dade da wucewaba su ammi suka shigo bisa jagorancin jalal, aka shiga gaisawa dayi mata ya jiki, Khairat kam kusa da amrah taxo ta xauna tace sister yh jiki, da sauki, Allah ya kara sauki, Amin, ya sunanki murmushi amrah tayi tace sunana fatima amma ana cemin amrah, gud, ni kuma sunana khairat kanwar Sadeeq, xaki xama kawata, murmushi amrah tayi tace eh, itama khairat murmushi tayi suka yi exchanging number sannan suka wuce, A hanya khairat tace ammi bakiga amrah tana kamada baba mai gadiba, na gani khaireey wlh kawai shiru nayi, ikon Allah khaireey ta fada Hmmmmm amrah fans koh kuna ganin wannan baba mai gadin shine magaji wato mahaifin amrah, amma ku biyoni danjin yadda xata kaya. πŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ Kuyi hkr ba yawa sbd har ynx ban Ida warware waba, ngd sosae da yadda kuka nuna kunajin dadin littafina ina godiya sosae da kuma addu'ah da kukamin Allah yabar xumunci πŸ™πŸ™πŸ™πŸ™ πŸ’«Rabeauty πŸ’« *please vote comment nd share* [8/23, 3:12 PM] +234 808 332 3233: πŸ’«AMRAH MACIJIYA πŸπŸπŸπŸ’« By Rabeauty πŸ₯°πŸ’«πŸ’«πŸ’« (17) Dan kallon ta jalal yayi sannan yace fatima, dagowa tayi ta kallesa dan tunda suke betaba Kiran ta da real name dintaba sai yau, sannan yace kinaso mu kuma gida, da sauri ta daga kai, murmushi yayi sannan yace OK ina xuwa, Yana fita yaga doctor imran yana shigowa, murmushi yayi masa yace likita bokan turai da ina xakaje, gurin ka jalal yabasa amsa, OK toh mukoma ciki, ciki suka koma ya kara duba jikinta ya juyo ya kalli jalal yace, alhmdllh aiki yayi kyau kuma jikinta yanada kyau sosae dan naga gurin yafara warkewa ynx ga paper sallama, Allah ya kara sauki, Kallon amrah yayi yace "Yammata Allah ya kara sauki ya tsare gaba, Amin tace sannan yafita dg dakin, Hada kaya inna tayi takai mota shi kuma ya taimaka mata ta tashi, fitowa suka yi tana gaba yana binta a Baya duk inda suka gifta sai an kallesu, Jiri tafara gani amma ta daure taci gaba da tafiya sun kusa kai gurin da yayi parking kawai tayi Baya xata fadi da sauri ya tarota ta fadu jikinsa wani irin yarrr yaji ga fatarta kamar bata mutane ba, tana a jikinsa suka ka rasa gurin mota ya bude mata ta shiga sannan shima yashiga suka nufi gida, *************** Direct dakinta ya kaita sannan ya nufi part dinsa, Ruwan wanka inna ta hadawa amrah sannan ta fita ta nufi nasu bangaren na yan aiki, Bayan ta gama wanka ta fito daure da towel Wanda ya tsaya mata a cinya, hannunta tasa ta shafe bayan ta inda bullet yashiga nan da nan gurin ya dawo yadda yake, murmushi tayi sannan ta nufi gaban mirror ta shafa mai sa saka body spray sannan ta nufi wardrobe ta dauko wata abaya black taji stone mai bala'in kyau ta saka saka ta kara fesa turare sannan tayi fakin gashinta Wanda ya xubu har West dinta bata saka dan kwaliba, sai powder da pink din xanbaki wanda ya xaje da kalar bakinta sannan ta nufi main falo, Tana saukowa suka yi ido hudu da jalal tsayawa kallonta yayi dan ta bala'eeeen yimasa kyau, kallon kanta yayi da bbu dan kwali akai ya bata fuska ya nufi inda take wani irin axababben kamshi yaji Wanda saura kadan ya sume lumshe idanunsa yayi sannan ya bude ya xubasu a kanta yace ina Dan kwalinki? rau rau tayi da ido tace wlh yaya jalal kaina yake ciwo shiyasa ban sakaba, tayi maganar a shagwabe, Wani irin yarrr yaji ya kara lumshe ido sannan ya bude yace "toh nemi hula kisa", dan Allah yaya jalal ka banni a haka, Kawai hannunta ya kama yayi room dinta yana shiga ya nufi wardrobe ya dauko mata wata hula baka mai kyau ya tattara gashin yasaka a hular sannan yasa mata akai, amma me saiga hular a kasa sbd gashin yayi yawa baxai shiga hularba, Mayar da hular yayi ya dauko dankwalin abayar ya daura mata akai amma sako sako, ydd baxai dametaba, Fitowa suka yi tayi saving dinsu abincin da inna ta dafa musu macaroni ce jalop mai hade da kifi sai kamshi take, wannan abincin duk nida waaa, Mu biyu xamuci mana, kallon ta yayi amma bece komaiba harta gama sanna suka fara ci, Suhaima ce tashigo tana ganinsu sunacin abinci tare ta kurma uban ihuuu tayo kan amrah gadan gadan, ihun ta yasa suka xuyo a tsorace danshi jalal yaxata wani abu ya same ta, Amman ganin ta nufu inda suke yasa shi mikewa amma kafin me Suhaima ta wankama amrah mari, cikin wani irin xafin nama jalal ya dauke Suhaima da mari Wanda yasa tayi baya xata fadi da sauri mommy wadda ynx a shigo warta ta taruta tanama jalal wani irin mugun kallo sannan ta maida kallon ta ga amrah wadda take rikeda kunce dan gsky marin ya shigeta, Jalal ynx akan wannan shegiyar marar asali xaka mari yar uwarka lalle, Amrah da ranta inyayi dubu ya bace sbd kalmar shegiya da mommy tace mata, sannan tace "mommy ki tsaya a matsayinki kija girmanki dan wlh kika kara xagina saina illataki wlh saina halakaki, Ko kuma na batar dake!!, Ta fada da karfi idanunta suna kara xama green, sosae mommy ta tsorata da yanayin amrah, da sauri suhaima taja hannun mommy sukahau sama, juyo wa jalal yayi dan yayima amrah mgn, Amma me bbu ita bbu dalilinta a gurin, ita kuma amrah tana gama mgn tayi fuuu ta nufi part dinsu inna sbd fatarta ta fara sabulewa shiyasa tayi saurin barin gurin. Banida caji ayi manage plssss πŸ™πŸ™ πŸ’«Rabeauty πŸ’« *please vote comment nd share* An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels