Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels [8/30, 1:19 PM] Abokiyar Fight💜💖: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 *BANBANCIN KABILA* _(Short story)_ 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 *TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION* *_🔱((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))_* *T.W.A* _____________________________________ https://www.facebook.com/Tambari-writers-Association-106058867819812/ _____________________________________ *WRITTEN BY ZAYNAB* _(zeexee)_ MARUBUCIYAR *-RAYUWAR HUSNA* - *MAHAKURCI MAWADACI* _(2020)_ 1️⃣&2️⃣ ```Barkan mu da kara haduwa awani littafin, Allah yasa ku ji dadin shi, kuma Allah yasa ya amfane mu duk.``` ```Wannan littafin it's a work of fiction, so in ka/kin ga ya zo similar da rayuwar ki/ka, kasan it's not intensional.``` ```Am dedicating this page to my fam "my Mummy, my Daddy and my brave lil sis Nana Hauwa. I love you all loooooooadssssss.``` _Bismillah_ Zaune suke a balcony, suna hira, sai kanin ta ya taba ta, ya ce "aunty Olamide, yau she zaki koma school ne"? Ya fada yana yatsuna fuska. "Gaskiya kam aunty, yaushe zaki koma". Kanwan ta ta tambaye ta, ta na daga gira. "Mu kam mun gaji da mita ko Farida". Kanin ta AbdulHakeem ya tambayi Farida. "Ooooh owk, kun gaji da ni ko, zan bar maku gida nextweek. Amma ku sani, kafun in koma, sai na gasa ku". "Otobe! (Baki isa ba) mahaifiyar su ta fada. "Kawai haka ki dinga takura ma yaya na, nextweek dinnan yayi yazo ki koma, ko yara na zasu ji sakat". "Haba Mummy, harda ke yanzu kin gaji da ni"? Ta fadi kaman zatayi kuka. "Ae sosai ma, addu'a na yanzu Allah ya kawo miji kiyi aure, kinga zamu samu kwanciyan hankali, ba mai mana mita, kije can kiyi da mijin ki". "Kai Mummy è ni fe mi ni (baki so na ne)"? "Of course ina son ki mana, your trouble is just too much". "Shikenan, tunda my trouble is too much, bari in bar maku wajan, kuma ba abunda zai kara hada ni daku, in ba gaisuwa ba, da major things, har in koma school". "Da mun ji dadi ko Boder (yaya)"? "Sosai ma". Abdulhakeem ya amsa. Afusace ta bar wajan, ta shiga dakin ta tana huci. *WACECE OLAMIDE* Kaman yanda kuka sani, Olamide sunan yarbawa ne, although sunan ta Faiza, amma kun san yarbawa da son amfani da sunan yare, shekarun ta ashirin, tana aji uku a jamia, a B.U.K. Yarinya ce mai hankali, ga son jama'a, ga lada bi da biyayya, tana ba kowa girma, ba babba ba, ba yaro ba. Gashi tana da fara'a sosai, ga wasa, da duk qualities masu kyau dai, amma fa Olamide akwai masifa, ga uban mita. Mahaifin ta ya rasu tun tana primary school, alokacin shekarun ta shida, toh tun lokacin mahaifiyar su ta zama ko mai nasu da ita da kannan ta. Sunan mahaifin ta Alhaji Abdullahi, sunan Mahaifiyar ta Alaja(Hajiya) Fausat. Kannan ta biyu, da Abdulhakeem da Farida. Shi Hakeem, kaman yanda suke kiran shi, shekarun sa sha'takwas, yana aji daya ajamia, a ATBU Bauchi, Ita kuma Farida shekarun ta sha'shida, tana secondary school ne, tana ss2. Although su yarbawa ne, amma suna zama a arewa, anan ma aka haifi mahaifan su, harda su, in short nan duka Familyn din su suke, kawai dai muna yarbawa ne, dan basuma san hanyar garin yarbawa, although dai sun iya yaran kadan kadan. Suna zama ne a jahar Niger, agarin Suleja, sunma zama yan gari awajan, amma kun san bayarbe da kishin yaran sa. ~Wanan kenan~ Data shiga ciki, su ka fashe da dariya. "In dai Mide tace, duk abaki take yi, da kan ta zata fara magana da mu". Mummy ta fada. "È ma dalon( kar ki damu) mun saba Mummy". Hakeem ya fada yana dariya. Ita kuma Farida, tayi shuru, kaman bata wajan. "A'a goggo Farida, lafiya? Naga yanzu muka gama dariya, ina magana kuma ki kayi shuru, kaman na tuna maki da wani abu".Hakeem ya fada. "Hmmm boder ba zaka gane ba. Kasan baku zaku kwana da aunty Faiza ba, tunan nin masifan da zan sha nake yi". Ta fada kaman zatayi kuka. Tana maganan, Mummy da Hakeem suka fashe da dariya. Hakeem na dariya har ya fado daga saman kujeran da yake zaune. Cikin fushi tace "wallahi boder matsala ta da kai kenan. Kai zaka jawo fada, amma ni zan sha masifa". "Toh ni nace ki sa baki ne? Ai da nake magana, baki ji nace Farida kisa mun baki ba" "Toh ai kaima ka san bazan iya shuru ba" ta fadi tana goge fake hawaye. Ita ko Mummy sai kallon ikon Allah take. "Eya, amebon(gulman) ki ne yayi yawa. Kinga bani ke saki ba kenan. Kuma indai masifa ne, yau zaki sha shi buhu buhu. Amma in baki son ki sha masifa, ki bi Mummy dakin ta, ku kwana tare". Hakeem ya fadi. "Toh ai boder Hakeem baka sani ba, nightwear dina na dakin". Ta kara fada tana yi kaman mai kukan gaske. Wani sabon dariya Abdulhakeem ya kara yi. "Wato aunty Mide ta zama doodo agidan nan kenan". "Idan ma akwai abun da ya fi haka, toh ta zama shi, ni dai anu è ni tiyo fe won mon gbo( tausayin wanda zai aure ta nake ji)." Farida ta fada. "Wanda zai aure ta ko ya'yan ta, ai ya'yan ta kam sun shiga uku". Wannan karon Mummy tayi magana. "Bari kawai Mummy". Haka suka cigaba da hiran su. Ita kuma Faiza (Olamide), data shiga daki, taje ta zauna akan gadon ta, don daman kowannan su (ita da Farida) na da gadon sa. Ta zauna tana ta huci, wai ita ce suke kira mai mita, da masifa, ai zasu ga masifa da mita kuwa, dan yau din nan, sai Faiza tayi kuka, shi kuma Hakeem, sai idon sa ya raina fata, dan zata jijjiga su sosai kafun ta koma. Tana cikin tunani, lokacin sallan magrib ya yi, ta tashi ta shiga toilet din dake hade da daki, ta yi alwala, sannan ta fito tayi sallah. Suma acan waje, suna jin kiran sallah, ko wannan su ya tashi. Mummy ta wuce dakin ta, shima Hakeem ya shiga dakin shi, yayi alwala, sannan ya wuce masjid. Ita ko Farida, tana bakin kofa, ta kasa shiga daki. Tasan indai ta shiga dakin nan, toh akwai problem, dan yau mai ceton ta sai Allah, ko in Mummy ta nuna mata bacin rai. Sanda taga Olamide ta fara Sallah, kafun tayi sanda ta shiga dakin, ta dauki hijjabin ta, ta fita da sauri, ta wuce dakin Mummy. Nan ma ta samu Mummy ta fara sallah, sai ta shiga toilet din Mummy, ta yo alawala, kafun ta fara sallah. Olamide na idar da sallah, tayi addu'a, ta nike Hijjab, da sallayan data yi amfani da shi, ta sa kowannan su a mazaunin sa. Data gama, ta zauna saman gado, ta fara dariyan mugunta. Ta ce "zaki gane ai yarinya, bani ba"? 〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️ "Umma ta, yau fa naji jiki sosai, ji nake kaman ban taba aiki ba arayuwa na" Wan saurayi ya fadi. Kana ganin shi, kasan wanan bafulatani ne, ga shi dogo, amma fa ba sosai ba, dan normal dinan, shiba siriri ba, kuma ba shi da kiba, normal size din nan ne. Ga kyau mashaAllah ba'a magana, gashi fari ga dogon hancin nan kaman pencil, ga idanuwan sa manya manya, yayi fitting din shi sosai. "Yau aka fara? Ai kaidaman ba ranan da bazaka dawo daga aiki bakayi complain ba, kuma kullum aikin ke maka wuya". Matar da ya kira Umma ta amsa mai. Itama matan, ba'a magana, tana da kyau sosai mashaAllah, gata ita ba fara ba, kuma ba baka ba. "A'a Hajiya, bana son kina ma auta na haka fa".wani dattijo ya fada. Toh kana ganin dattijon nan, ka ga saurayin, saboda suna kama sosai, har ya baci. Amma babancin shine, shi wanan ya fara tsufa, shi kuma wanan saurayi ne. "A'a Abba, kasan wanan yaron is very lazy, abu kadan sai yace ya gaji, yana abu ne kaman mace. Ina ji ma matar ka, saboda ita zata dinga aikin na miji agidan ku". Yayan saurayin ya fada, shi wanan yana kama ne da Umma sak. "Abba na ka kyale su kawai". Ya na fada, ya tashi yana mika, sanan ya wuce dakin shi. "Lazy woman kawa" yayan shi ya fada. "Subhanallah, auta na ba woman ba ne, man ne, kuma a very strong man". "A'a Alhaji adai fadi gaskiya. Ai wanan ya ma fi woman lazy". Tana fadan haka, yayan shi ya fashe da dariya. Da ya shiga daki, ya cire tie din dake wuyan shi, ya na yi yana hamma. "Gaskiya I need to get married, atleast in ina da aure, irin yau dana dawo agajiye, ita zata cire mun tie, ta fara tarba na tun daga bakin kofa, ta amsa briefcase dina, ta hada mun ruwan wanka, kafun in gama shafa mai, ta kawo mun abinci. Gaskiya aure kam akwai jin dadi, no wonder Yaya Sudais na kiba, amma I wonder why almost everyday yana gida, instead ya bari nima in mori su Umma, amma sai yazo suna hada hannu da Umma suna tsokana na". Ya fadi yana murguda baki kaman mace. Daya gama cire kaya, ya shiga toilet, yayi wanka, yana gama wanka, yayi gab da an kira sallah, kawai yayi alwala kafun ya fita, ya yi dressing, ya fesa turaruka, ya fita parlor, nan suka hada hanya da Abba, saboda by that time Yaya Sudais ya tafi gidan sa. *WAYE WANNAN SURAYIN?* Sunan shi Abdallah, shakarun sa 25, medical doctor ne, kuma yana zaune ne da iyayen sa a jahar Gombe. Bafulatani ne gaba da baya. Su biyar iyayen sa suka haifa, Sudais ne First born, sai Bilkisu, sai Wasila, Fadila, sai shi Abdallah, autan su. Familyn su ba Familyn masu kudi bane, amma alhamdulilah, akwai rufan asiri sosai, gashi kuma Allah da ikon sa, duk yaran suna da aiki masu kyau, hatta matan, Saboda Alhaji Umar Muhammad Yero baya barin yaran sa suyi aure basu gama karatu ba, sanan sai ya san yanda zaiyi, su samu aiki a wanan kasan tamu da samun aiki nada wuya. Sunan Mahaifin sa kaman yanda na fada Alhaji Umar Muhammad yero, sunan Mahaifiyar sa Hajiya Rukayya Muhammad Yero. Abdallah akwai shagwaba tamkar na mace, ba ranan da bazai dawo daga aiki baiyi complain ba, kuma kullum complain din na chanzawa. Shi mutum ne da baya cika son hayaniya, indai ba da Familyn sa ba, amma in ya fita wajen, zaka rantse bai ma iya magana ba, saboda tsabarage miskilanci irin na sa. Amma agida kam, sai a slow, dan akwai tsokana agida, ga shagwaba. Yayyin sa Mata duka na biye masa sosai, dan duk abun da yake so suke mai, ba su son suga ran sa ya baci. Amma Umma da Hamma Sudais, kullum cikin tsokanan sa suke. Suna da extended family sosai, kuma every end of the month, suke meeting, nan suke haduwa da duka cousins din su, aunties da uncles. Awannan meeting din ake hada wasu daga cikin su su auri juna, amma if you are so lucky, za'a bari ka auro daga waje, but she must be fulani. Tun lokacin daya fara aiki, shekara biyu kenan, ya san dole fa wata rana ayi tambayan mata, ko kuma ahada shi da cousin din sa, shi kuma kaf cikin su ba wanda ta mai, so duk sanda zasu yi meeting, either yace baya jin dadi, ko kuma ya daure fuska, ko ya zauna shuru kaman baya wurin don kar ma ayi noticing din shi. ~Wanan ke nan~ Da suka dawo daga masjid(shi da Abba), basu tsaya ako ina ba, sai a dinning. "Umma ina abincin ne, karfa ulcer ya kamani yau" ya fada ashagwabe. "Kai Auta, ai yanzu zata kawo, ka dan yi hakuri kaji, kuma In Sha Allahu bazaka kamu da ulcer ba". Abba ya fada yana jan hancin shi. "Kama mutu ne ba ulcer ba. Kana zaune anan ba zaka zo ka taya ni dauko abincin ba, amma kana mu maganan ulcer, ya dadde bai kama ka". Umma ta fadi tana dauke da kuloli. "Haba Hajiya, auta ne fa"? Abba ya fadi yana zaro idanuwa nan nashi kaman zasu fado,dan mashaAllah, Abba kam akwai manyan idanuwa, kuma kaman yanda kuka sani, magaji mafiyi, so Abdallah ma akwai su mashaAllah. "Fada mata Abba, ni na rasa abun da yasa ta tsane ni" ya fada yana faking din kuka. "Mtchwwwwww" Umma ta ja tsaki, sanan tace "ka tashi kaje kitchen, zaka ga plates da spoons, da cups, ka kawo su dinning". "Duk wannan ni kadai zan dauka, haba Umma nifa na miji ne, kuma mata aka sani da shigan kitchen ko Abba na "? Ya fada ya na kallon Abba. "A'a ni ban san da wanan ba, saboda baya cikin Alqur'ani ko hadiths". Tunda yaji Abba ya fadi haka, ya san Abba bazaiyi bailing din sa ba, ya tashi ya tafi kitchen, ya kwaso abubuwan da Umma tace ya kwaso, daya bayan daya, sanan Umma tayi serving dinsu. Cikin natsuwa, suke cin abinci, har suka gama, nan ma shi ya washe plates ya kai kitchen, sanan suka dan taba hira, kafun kowanan su ya wuce dakin sa. 〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️ Farida na idar da Sallah, sanda Mummy ta bari tayi addu'a, ta ce kilode (meya faru), me yasa bakiyi adakin ku ba"? "Wallahi Mummy Aunty ce, mon beru (ina jin tsoro)." "Manta da ita, ba abunda zata miki kinji ko"? Mummy tayi magana tana daga gira. "Toh Mummy Allah yasa. Kinga ma na manta ban dauki night wear dina ba". "Karki damu, in muna cin dinner kije ki dauka kinji". "Toh Mummy na". Ta fada Da Hakeem ya dawo, yaga parlor, ya ga wayam, shima ya shige dakin sa. Abun ba wuya, har ankira Isha, nan ma yaje masjid, Mummy da Farida su kayi tare adakin ta, ita kuma Olamide tayi adakin su. Kowanan su na idarwa, yayi addu'a, duk suka fito daga dakunan su. Daman suna idar da Isha, suke fitowa dan suci dinner. Farida na ganin Mide, ta manne ajikin Mummy, tana tsoron karta cafko ta, itako ko ajikin ta, dan kitchen straight ta tafi, ta fara kwaso kuloli, da kayan da zasu ci abinci da shi, ta kai parlor, tasa masu a tsakiyan parlor akan center Capet. "Yau kuma ba'a dinning zamu ci ba"? Hakeem ya tambaya. Mide ta mai shuru, kaman ba da ita yake ba. Farida ce tace "ka manta ta ce bazata yi magana da kowan nan mu ba". Hakeem ya fashe da dariya, ya ce " ai na manta ta zama kurma". "Ni kam ba ruwa na, ka ga dai saboda da kai yanzu ina cikin trouble ko". A fusace ta ce "kuyi shuru ku ci, ko kuma ku tashi mana anan". "A'a e ma binu (a'a kiyi hakuri), ba zamu kara ba" Farida ta fadi. "Ni kam zan cigaba". Hakeem ya fada yana dariya. Abun ya bata mata rai sosai, sai ta ja tsaki ta bar wajan. Tana tashi, Farida da Mummy suka kalli Hakeem, Farida ta ce "shikenan ka ja mana wani masifan, kai baka san aunty Mide sai da rarrashi ba, ga shi ban dau nyt wear dina ba" ta fada kaman zatayi kuka. "Ni kam Farida ki daina damun mu da maganan night wear, ba zaki rasa adaki na ba. Kai kuma Hakeem, ka san yanda zaka lallabi yayar ka, ta daina fushi, dan kai kaja komai". Ya ce "toh" yana wani hura hanci. "Amma Mummy kin san ba zata saurare ni ba yau, sai dai gobe in Allah ya kai mu". "Allah ya kaimu". Mummy ta fada. "Amin" Hakeem da Farida suka amsa. Aranan, ran Olamide abace tayi barci. ```Ya kuka ga wanan salon? Allah yasa dai kunji dadin shi.``` Thanks for reading, karku manta da sharhi, saboda sharhi is life🤪🤪🤪🤪🤪. Comment Like & Share ~Zeexee ce~ 🖊️🖊️🖊️ [8/30, 1:19 PM] Abokiyar Fight💜💖: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 *BANBANCIN KABILA* _(Short story)_ 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 *TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION* *_🔱((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))_* *T.W.A* *WRITTEN BY ZAYNAB* _(zeexee)_ MARUBUCIYAR *-RAYUWAR HUSNA* - *MAHAKURCI MAWADACI* _(2020)_ 3️⃣&4️⃣ ```Dedicating this page to those who commented on the first chap, I love you guys loooooooooooods.``` _Bismillah_ Around 3:30 am na dare ya tashi, yayi sallan dare, yana yi har lokacin Fajr yayi, ya yi raka'a taini fajr, sanan ya fito parlor, suka hada hanya da Abba, suka je masjid. Da suka dawo kuma, tunda yana da dutyn safe, ya fara shirye shirye. "Ya ilahi, gaskiya I need a wife. Da ina da mata, duk wannan shirye shiryen ita zata mun. Kawai sai dai inji tana tashi na, ta ce qalbi ka tashi kayi wanka, ta cire mun kayan da zan sa, ta sa mun coat dina da briefcase di na waje daya, ta ciro mun covered shoe dina, shima ta sa mun a one side. Ina fita kuma ta mika mun ina sawa, in ta gama dressing dina, sai tace qalbi muje dinning ka ci breakfast. Ba kaman Umma ba, da zata dinga mu fada. In kuma na gama cikin breakfast, sai ta rike mun briefcase, ta raka ni har mota, sannan ka fun in shiga, tayi hugging dina, sai in shiga mota, ta mika mun briefcase, ni kuma in diga mata flying kisses, sannan in kuna mota, ita kuma ta dinga waving dina har in bar haraban gidan mu". Ya fadi ya na wani irin smile. "Amma gashi yanzu ni ke komai. Da ma lokacin da adda Fadi take nan ne, maybe data mun. Duk da cewa muna fada sosai, dan ita nake bi, still na san zata mun". Ya fada with frustration. Haka ya ita surutun shi shi kadai, har ya gama shiri, ya fita ya je dinning, ya ga ba kowa. Tun dama da kyar suyi breakfast tare inba weekend ba, ko kuma ran da yake da dutyn rana. Rai abace, ya shiga kitchen. Yana son ya fara girka indomie, yaga note akan kula. " ka ci, ba dan halin ka ba". Yana ganin handwriting din, ya san na Umma ne. Sai ya saki murmushi, ya dauki abincin, ya kai dinning, ya ci. Sanda ya koshi kafun ya kwashe kwanonin, ya kai kitchen. Daya gama kintsa komai, ya je dakin Umma, ya mata sallama, ta mai adawo lafiya, da addu'oi, ya je dakin Abba, shi ma ya mai, sannan ya fita, ya kama hanyar asibiti. Yana driving yana bin kira'an sheik Abdulrahman Sudais, sai kawai ya fara addu'an Allah ya ba shi mata, shi ya fara gajiya da irin rayuwar nan, shima yana son yayi kyau kaman Hamma Sudais. Haka ya ita tunani har ya isa asibiti. 〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️ Around 4:00 Am, Mide ta tashi, daman ita kadai ta kwana, Farida ta kwana da Mummy ne, dan data shiga daki, data sha masifan da bazata taba mantawa da shi ba . Da Mide ta tashi, ta shiga toilet tayi business din ta, sannan ta yi alwala, ta fito ta fara nafls. Da lokacin raka'a taini fajr yayi, tayi, sannan tayi sallan fajr. Tana idarwa, ta fara karatun alqur'ani, tayi azkar din safe, da wasu addu'oi, sannan ta ninke sallayan, tasa a mazaunin sa, kafun ta fita taje dakin Mummy. Ta shiga da sallama, Mummy da Farida suka amsa. Data shiga, ta tsuguna, ta gaida Mummy, Mummy ta amsa, ta sa mata albarka. Sai Farida ta ce "aunty mi (aunty na), e dakun(please) ki yi hakuri, bazan kara ba". Tayi magana kaman za tayi kuka. Olamide ko tayi kaman ma bata san tana yi ba. Ta tashi zata fita, Mummy ta ce ta dawo. Cikin respect, ta dawo ta tsuguna gaban Mummy, dan daman Mummy da Farida na zaune ne akan sallaya, Farida na ma Mummy karatun ta da aka masu a islmiyya, ita kuma Mummy tana gyara mata. Da Olamide ta tsuguna agaban Mummy, Mummy ta ce "wai ni wace irin zuciya gare ki? Ba yafiya kwata kwata a zuciyar ki. Ya zaki kwana da mutum azuciyar ki, baki tsoron ki mutu, ko kuma shi wanda kika sa arai ya mutu? Fisabilillah! Ai wannan ba hali bane, ko tun iwa re se (ki gyara halinki), kafun lokaci ya kure maki". Ran ta abace, amma cikin sanyin murya ta ce "Mumny fa ni kadai kike ganin fault dina fa, baki ganin na su, barin ma Hakeem, kema dai kin ga abubuwan da yake mun, amma sai ki dinga cewa ni ke da fault". By this time, tana magana tana zubar da hawaye. "Toh ai ke ce babba, ya za kiyi, dole ki dinga hakuri. Fushi fa ba abu mai kyau bane. Na san abubuwan da suke miki na bata miki rai, amma su fa a matsayin wasa suka duki komai". "Toh ni bana son irin wasan. Kullum su ita tsokana na kaman kanwar su. Harda ke ma". Ta fada tana kallon Farida. "Shekaru nawa kika san na girme ki da shi, shekaru hudu fa, amma in aka fara magana, ke kike leading. Gwanda ma Hakeem, age gap din mu ba yawa, amma ke fa. Ko shi din he has no right or what so ever to disrespect me". Tana cikin magana, sai ga Hakeem ya shigo. Su na hada ido, ta dauke idon ta. Sanda ya gaida Mummy, sanan ya ce "Aunty ina kwana". Ta ki amsa mai. Ya kara cewa "na san na miki laifi, but I was only joking, wallahi wasa mu ke dake. Amma na ga kaman wasan mu na bata miki rai, saboda haka, ina mai baki hakuri, dan Allah kiyi hakuri, ki yafe mana". Still tayi shuru, sai hawayen da ke zuba a idon ta. Abu kadan na sata kuka, she is always emotional. "Haba Olami, ba zaki yafe masu ba, haba my first fruit, you were the first person who made me know how wonderful and exciting been a mother is. Ke ce first din komai na, dan Allah dari jin wan (dan Allah ki yafe masu)". Cikin kuka, ta ce "na yafe maku, amma ku san irin wasan da zaku dinga yi da ni". Tana gama magana, ta tashi zata fita, Mummy tace ta dawo. Da ta dawo, Mummy ta ce da su, suyi group hug. Su kayi group hug dukan su, Mummy na sa masu albarka. 〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️ Yana isa asibiti, ya shiga office din sa, ya zauna. Kafun ku sani, har patients sun fara shigowa. Ya na kiran next, wata budurwa ta shigo, yarinya akwai kyau ba laifi, gata fara. Tana shiga ta gan shi, ta fara gyara mayafin ta, tana gyara kayan ta. Shi ko ya riga ya gano ta, dan haka majority din yan'matan dake shigowa suke. Sai su dinga wani gyare gyare. Wasu ma har cewa suke, zasu iya samun numbern sa incase idan ciwon su ya kara tashi, sai su fada mai, it's either yayi kaman bai ji ba, yana next, wani ya shigo, su kuma su fita disappointed, ko kuma ya basu amsa rudely. Daya ga gyare gyaren ta bai kare ba, ya ce "can you have a sit please, we still have other patients waiting out there". Ta gyara murya, ta ce "uhmmm sorry". Sannan ta zauna. "Toh me ke da mun ki"? Ya tambaye ta. Ta fada mai abun da ke damun ta, ya rubuta mata magunnuna, ya bata. Ta fita kuma ya zama problem, ta ce "kaman na san ka ". "Ya ce Allah ko"? "Ae, dan na san ina ganin face dinnan sosai". "Hanya kuwa, dan ni ban san ki ba". " Okay, amma ka san Fadila Umar Muhammad yero"? "Ae na san ta, ya akayi". "Haba no wonder, kuna kama sosai. I think ina ganin hotunan ka awayan ta ne. Actually munyi BASUG(Bauchi state university) tare da ita ne, amma snr dita ce, dan tana level 4, ina 1, amma mun shaku sosai". "Allah sarki, nagode". "Uhmmmm na ce ba, kana iya bani numbern ka, kaga sai mu cigaba da zumunci ba". "Numbern na ko na ta, dan naga ita kika sani". "Na ka, ai ina da nata". Ta fada tana murmushi. "Toh ai tunda kina da nata, alhamdulilah. Ita kika sani ba ni ba. Please here is the door. Next patient, ya fadi. She was soo embarrassed, ta dau bag din ta, ta bar wajan. Ba zata wuci 22 years ba, so ya girme ta. Tana fita ya fashe da dariya, ya ce "ai ko mata sun kare, ba zan iya zaban ki ba. Na san mata ta na can itama ta kosa mu hadu. Ya Allah Kasa mu hadu very soon". Yana cikin addu'a, patient ya shigo. Bai bar asibiti ba, sai around 2:30 PM. Instead ya je gida, sai ya je gidan adda Wasila. Yana horning, aka bude mai gate. Mijin adda Wasila na da kudi sosai alhamdulilah. Ba ita ce first wife din sa ba, first wife din sa ta rasu, ta bar yayan ta uku, after shekaru hudu da rasuwan ta, ya auri adda Wasila yanzu shekarun su 8 da aure, yaran ta biyu, da Zaynab da Faiz. Su kuma yaran Mijin, da Jamila, Nana Hauwa, da Abdulazeem, amma suna kiran sa Azeem. Akwai zaman lafiya dosai, yaran na son ta sosai, dan bata babanta su da nata yaran ba, duk daya suke awajan ta. Yana horn aka bude mai, gate, mai gadi na ganin shi, ya ce "a'a auta! Kai ne haka da ranan tsaka"? "A'a bani bane, kai ne". Yana fadan haka, shi da mai gadin, mai suna lawali, suka fashe da dariya. "Kai auta baka gajiya da tsokana. Allah yayi dai yau ka zo Hajiya bata je wajan aiki ba yau". "Ai na sani mallam, ba asibitin mu daya ba"? "Awww haka ne fa". Lawali ya fada, yana sosa keya. "Kar ka damu, in zan fita zamu hadu". Abdallah ya fada, ya je ya gyara parking. Shiko Lawali, sai washe baki yake. Abdallah na sallama, yaran suka zo da gudu. "Oyoyo uncle! Oyoyo Uncle". Suke ta fada, suna hugging din sa one after the other. Bisa duka alamu dai yanzu suma suka dawo daga school. Sai ya tambaye su Mummyn su, suka ce tana sama, yanzu muma muka shigo". Zaynab kenan, ta amsa. "Toh Jebu, je ki fada mata best din ta ya zo". Zaynab ta bata rai, ta ce "best din Ummi ko best din Zaynab". "Toh best din Zaynab". "Yauwa uncle auta". Tana fada ta bar wajan da sauri, kar ya buge mata baki. "Zaki dawo ai yarinya". Ya fada. "Me ka kawo mana". Nana Hauwa second born din gidan, shekarun ta 14, tana jss3 ta tambaya. " Ku da kuka je school, bai kamata a kawo maku kayan dadi ba, kar yazo ya dagula maku lissafi". "Kai! Uncle auta, ka iya zuki". Jamila babban cikin su, wanda shekarun ta 15 yanzu, kuma tana ss1 ta fada, ta bar wajan da sauri, dan ta san halin shi, yanzu zai bubbuga mata baki. "Ai da ke da Zaynab, mai kwace ku sai Allah. Ni na maku kama da autan ku ne? Wannan munmunan autan na ku" ya fada yana kallon Faiz. "A'a kar ka bari mu fara, ka daina ce ma handsome dina ugly tohm". Adda Wasila ta fada. "Ko dan gaisuwan nan babu, sai fada? Ko kema kin shiga group din su Umma ne"? Ya fada yana bata rai. "Na isa? Ai ban isa ba. Toh autan mu, ka zo lafiya? Ya aiki yau"? Ya amsa mata, daga nan suka fara hira, suka ci abinci. Suna gama ci, suka kara taba hira. Suna cikin hira, ta ce "Abdallah!" yana jin yana yin yanda ta kira sunan shi, ya san akwai magana kenan. "Na'am adda". Ya amsa. "Yaushe zaka yi aure ne? You are not getting any younger". "Hmm adda kenan, zan yi, lokaci ne bai yi ba. Ko nima na kosa inyi, amma har yanzu ban samu wace ta mun ba". Ya fada. "Kar ka tsaya ruwan ido, inba haka ba, ka kwaso nonsense. Kuma kana wani cewa baka samu kowa ba, yan'matan dake family fa? Ga yaranan kyawawa, ga kyaun hali, amma kace baka samu ba"? "Ba haka bane, I don't just have interest in them. Basu zauna mun a rai ba. Amma na san My wife na can tana jira na, lokacin haduwan mu ne kawai bai yi ba". "Toh Allah yasa ahadu soon, inba haka ba, kawu Dajjo ya hada ka da wata acikin family". "Ba amin ba, In Sha Allahu soon zamu hadu". Bai bar gidan ba sai 5:PM. 〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️ "Toh goge hawayen ko". Mummy ta fadi. Olamide ta goge hawayen ta, ta ce "Mummy ban san abun da yasa nake kuka haka ba, kuma bana iya controllimg din shi". "Kya koya ai, in kika yi aure, zaki koya". Olamide ta sa hannu agoshi, ta ce " Mummy abu kadan kice aure. Ni kam ba yanzu zanyi ba, kuma ma fa bani da ko mashin shini". "Hmmm, bari in bar maku dakin". Hakeem ya fada. "Nima haka". Faiza ta fada. "Dawo nan munafs. Yanzu in kuka fita, ba abun da zaku yi in ba munaf ba". Olamide ta fadi "Kul, ma ban be awon omo mi ni munafukai( kar ki kira mun yara na muna fukai)". Mummy ta fada. "Toh alhaja Mummy". Olamide ta fada. Ko wanan su ya fara morning duty din sa, da suka gama, suka ci breakfast, Farida ta je school, su kuma suka koma dakin su. "Aunty Mide, ina son in danyi wani dan talk da ke" Farida ta fada. "Ina ji, kuma ki fadi sensible thing, inba haka ba ki sha mari". "Am serious fa". Ta fada tana making serious face. "Toh am all ears darling Faree". "Daman akwai wani ne, cousin din su Eyman, ya ce wai yana so na, baki gan shi ba, yana da kyau sosai fa". Farida ta fada. "Zo, matso kusa". Olamide ta fada. Farida ta matso kusa da ita. Sai Olamide ta taba wuyan ta, ta ce "gashi jikin ki bai yi zafi ba, toh me zan ce yana damun ki". "Aunty fa am serious. Ai kin san Eyman, wanan kawa ta din nan yar Maid, kin san how much I love kanurai ai". "Ki tashi anan kafun inyi ball da ke. Kina ss2, intsead ki dinga tunanin yanda zakiyi passing din third term exams din ki, kina tunanin na miji, ko ni nan banda saurayi, kuma ina 300l. Common ki tashi kije kiyi assignment dinki kafun inyi ball da ke". Afusace, Farida ta ce "ko dan wanan halin na ki, ba zaki samu saurayi ba". Tana fada ta bar dakin. Ita ko Olamide, maganan ya dame ta, maybe maganan Farida gaskiya ne, shi yasa haryanzu bata samu saurayi ba. Amma kuma to hell, ta san lokaci ne baiyi ba, dan in lokaci yayi, ko cikin rami aka sata, sai sun hadu da mijin ta". Thanks for reading, ayi sharhi abeg, because sharhi na oxygen ooooohh🤭🤭🤭🤭🤭. Comment Like & Share. ~Zeexee ce~ 🖊️🖊️🖊️ [8/30, 1:19 PM] Abokiyar Fight💜💖: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 *BANBANCIN KABILA* _(Short story)_ 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 *TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION* *_🔱((Home of Expert and Talented writers, da tambarin mu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))_* *T.W.A* _____________________________________ https://www.facebook.com/Tambari-writers-Association-106058867819812/ ______________________________________ *WRITTEN BY ZAYNAB* _(zeexee)_ MARUBUCIYAR *-RAYUWAR HUSNA* *-MAHAKURCI MAWADACI (2020)* 5️⃣&6️⃣ ```Am dedicating this page to my washi Wasila, aka washi buje🤭🤭🤭🤭🤭🤭🤭. I love you wujiga wujiga``` 🤣🤣🤣 _Bismillah_ Abun ba wuya, yau Olamide ta koma school. Faridan data ce tama fi kosawa ta wuce, ita ta fara kuka, wai zata yi missing din ta. Kuka take sosai, har ta sa Mide ma kuka. Hakeem da Mummy ko sai kallon ikon Allah suke. Har gareji suka raka ta, nan ma sanda suka yi kuka. Daman ko man fada da argument din da zasu yi, basu iya rabuwa da juna, Farida da Mide na mugun son juna. Shima Hakeem, ya na son sisters din sa kaman ran sa. Ita kuma Mummy, kwanciyar hankalin ta bai wuci taga kan yayan ta a hade ba. "My Faiza! Welcome back to school dearie". Kawar ta Nafisa ta fada. "Oyoyo my Nafy". Olamide ta fadi, sannan suka yi hugging din jun. "Nayi missing din ki like crazy wallah". Nafisa ta fada. "Awwwn, nima fa nayi missing din ki. All those fight, wasan da muke a kan hanya kaman yara, ko kuma duk wanda yayi approaching din mu, mu sille shi tas, sannan mu zo muna tsoron kar azo akama mu, da dai sauran su". "Wallahi fa kawa ta. Ko kuma randa bamu jin yin girki, mu ita shan garri hhhhhhhhh". Olamide ma tayi dariya, ta ce "ai Nafy muna tsiyan mu yanda muka ga dama. ". "Am telling you bea". "Toh yanzu dai mu bar surutu, ki taya ni daukan kaya". "Aww nama manta, wallahi ganin ki da nayi yau, yasa ni nishadi sosai mama na". "Allah sarki, nima am soo happy to be with you again mama na" sai suka yi dariya. Daga nan, Nafisa ta taya Olamide daukan kayan ta, har cikin dakin su. Daman a off campus suke. Tun suna level 1 suka hadu, lokacin Olamide na neman abokiyar zama, ita kuma wannan na neman daki. Haka dai suka hadu, tun lokacin suke zama tare, sai Allah yayi kuma halin su yazo daya, ga shi department din su daya. So komai nasu tare suke yi. Ita dai Nafisa yar Bauchi ce, ita kadai iyayen ta suka haifa. Mahaifitar ta fulltime house wife ce, mahaifin ta kuma yana aiki ne a ministry of works. Although ita kadai ce, iyayen ta basu shagwaba ta ba ko kadan. Da suka kai komai ciki, suka gyara ko ina. Daman tun jiya which was saturday Nafisa ta dawo, ita kuma Mide ta zo yau which is sunday. "Allah sarki kawa ta, na san kina jin yunwa ko, bari in kawo maki abinci". "Kaman kin sani Fisa baby, ban ci komai ba ahanya". "Ai nasan halin ki". Nafisa ta fada, sannan ta kawo mata rice and stew, da nama, sai ta hada mata Fresh, strawberry flavour cikin jug, sannan ta sa mata agaba, da cup din da zata dinga sha da shi. "Nagode sosai habibty, Allah ya bar mun ke. Kin ga bari in cire hijjabi, sai inyi justice akan abincin nan. Dan Allah kema kawo chokalin ki, muyi justice tare". Olamide ta fada, tana cire hijjab. "Ai habibty, kema kin san ba zan ki ba, sai munga karke rice din tab, if possible ma mu cinye naman". "Gaskiya ne, nima na kawo stew ai, ga kuma soyayye nama". "Nima na kawo soyayya. Mu cinye na stew dina yau". Nafisa ta fada. "Allah ya bamu sa'a toh". "Amin mama na. Gwanda muji dadin mu yanzu, kafun lokacin scarcity ya hantayo". "Gaskiya kam". Olamide ta fada. Su biyu suka rike spoons, Nafisa ta ce "it's time mr rice, 1, 2, go". "Bismillah suka fada atare, sannan suka fara ci. Sanda suka ci suka koshi, har su ka kasa tashi, sai suka kalli juna, suka fashe da dariya. "Gaskiya Mide muna tsula tsiya". "Bari kawai, am soo happy Allah yasa mun hadu". "Ko ni fa. Tunda mukayi two weeks, na kosa adawo, na fara missing din ki. Kinsan agida banda abokiyar hira in ba Ummi ba". "Allah sarki my habibty. Ai nima in fada maki, sanda muka samu matsala da su Hakeem last week". "Ai na san za'a rina. Ai ba vacation din da baza kuyi fada ba". "Kyale su, yaran nan sun raina ni ne. Amma yau da zan dawo, kinga yanda muke kuka ne, ni da abokiyar, kaman irin za'a kai amarya dakin ta". Sai su biyu suka fashe da dariya. "Yauwa ga ruwa nan nayi plugging, ki duba in yayi zafi kiyi wanka ko habibty"? "Yes Mummy habibty". Mide ta amsa. Olamide ta duba ruwan, taga tayi zafi, sai ta juye, sannan ta shiga toilet tayi wanka, kafun ta fito, aka kira sallah, ta yi alwala. Da ta fito, ta shirya cikin night wear din ta, ita kuma Nafisa ta shiga tayi alwala, itama tazo suka yi sallah. Da suka idar, kowanan su ya ninke hijjabin sa, Olamide ta ninke masu sallaya. "Gobe zamu fara registration ko"? "Ae, it's going to be stressful wallahi". "Gaskiya it's going to be. Kinga muna idar da sallan isha, zan yi barci". "Nima haka, amma zan dan karanta wani sabon book ne, mai suna Uncle sadiq". "Toh, waye marubuciyar"? "Eyman". "Aww, harta fara wani"? "Ae ta fara". "Kai! Ni dai gobe zan fara karantawa". Olamide ta fada. "Toh Allah ya kaimu. Yauwa kina karanta izzar mulki ma by Hafsat Khalil, da mijin Zarah by Phateema lawal"? Nafisa ta tambaya. "Ae, mai zai sa inyi missing? Kin karanta Mahakurci mawadaci by zeexee"? Olamide ta tambaya. "Dole na ai, na karanta. Yanzu ma tafara wani, mai suna babancin kabila". Nafisa ta fada. "Ai na fara katantawa". Olamide ta amsa. "Toh masha Allah, novels din su nada dadi fa sosai". "Gaskiya kam". Suna cikin hira, aka kira isha, sannan ma suka yi sallah, Olamide ta hau katifan ta, ita ma Nafisa ta hau nata. "Sai da safe" Olamide ta fada. "Allah ya tashe mu lafiya". Nafisa ta amsa. "Amin. Kar dai ki dade, kinsan akwai sallan dare ko"? "Ae, bazan dade ba In Sha Allahu". Nafisa ta amsa. 〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️ Da Abdallah ya koma gida, Umma kadai ya samu cikin parlor, tana kallo. "Assalamu alaikum my darling Umma, na same ki lafiya"? Ya fada yana hugging din ta. "Waalaikumus salaam my troublesome son". "Kai Umma, kin iya ruining din moment, wai troublesome son, abun da zaki ce My handsome son, ko my cool and quite son" ya fada ashagwabe. "Ohh ni Rukayya! Ya zan yi da kai ne, shagwaba sai kace mace"? "Toh ni Umma wani shagwaba na maki yanzu"? Ya kara magana ashagwabe. Da Umma ta daga hannun zata dake shi, ya tashi da sauri. Ta ce "zan kama ka ai. Ai ni da ace kai mace ce ko, ai da anga uwar shagwaba da laziness, da mijin ka ya sha wuya. Amma alhamdulilah, tunda kai na'miji ne, kaga inka fara samun responsibility akai, maybe ka dai na". "Umma ai in fada maki, mata ta shagwababiya ce, sai dai mu ita zuba ma juna shagwaba. Kuma dan Allah Umma kar ki buge ni, yau din nan na dawo agajiye ne, aikin nan is not easy at all". "Ni kam rashin kunyan ka har ina, Allah dai Ya shirya mun kai. Kuma tun da ka shigo, nake ta jiran ka mun complain, naji shuru, nayi zaton ka chanza ne, amma ina mai hali baya chanza halin sa. Kai da tun 2:30 ka bar aiki, sannan kaje gidan Wasila, sai ka zo yanzu kace ka gaji. Aiki kaje mata ne"? Umma ta tambaya. "Kai Umma, ni dai kawai baki sona. Abu kadan ina fada, shikenan zaki fara mun fada, ina Abba na ya ke, dan shi kadai ke sona yanzu". Ya fada ashagwabe. "Gani nan dan albarka". Ya ji muryan Abba. Daya juya, yaga yana shigowa ne daga waje, he was thinking maybe yana dakin sa ne. Bisa duka alamu, fita yayi. "Oyoyo Abba na mai so na". Ya fada yana kallon Umma, sannan yayi hugging din shi. "Can ta matse muku". Umma ta fada. "Oyoyo my Auta. Ya aikin yau, hope dai bai gajiyar da kai ba ko"? Abba ya tambaye shi, hannun Abdallah acikin nasa, suka zauna tare. "Ai Abba na ka bari kawai, na jijjigu yau sosai". "Allah sarki Auta na, sannu. Ka dinga hutawa fa". Abba ya fada. "In Sha Allahu" ya fada, yana ma Umma gwalo. "Au ni ko, zaka sani ai". "Abba kaga Umma ko, ban mata komai ba fa". Ya fada kaman zaiyi kuka. "Kayi hakuri ka kyake ta, kishi take, kasan ba mai nuna mata irin wannan son". "Haka ne, Hamma Sudais bai zo ba yau, shi yasa". Abdallah ya fada. Umma ta kada kai, taki amsa masu, dan ta san indai ta amsa, haka zasu cigaba da tsokanan ta. "Kaje kayi wanka, ka warware gajiya. Then In Sha Allahu yau bayan Magrib, ina da magana da ku". Abba na gama magana, ya bar parlorn, ya wuce dakin shi. "Toh Allah ya kai mu".Umma da Abdallah suka fada atare. Shima ya tashi, ya bar parlorn, ya je dakin sa. Yana gama wanka, yayi alwala, ya fito, yayi dressing cikin ash jallabiyan sa, ya fesa turare, sannan ya fito parlor, suka hada hanya suka tafi masjid tare. Da suke hanya, dan masjid din na can kasan gidan su ne, Abdallah ya ce "Abba, akan me zaka mana magana, ka dan bani clue mana". "A'a, ka bari in muka koma gida zaka ji". Abba ya fada ba sign din dariya afuskar sa. "Toh Abba". Abdallah ya amsa. Daga nan ba wanda ya kara magana acikin su, har suka isa masjid. Suna idarwa, suka kama hanyan gida. Acan gida ma Umma ta idar da sallah, tana jiran su aparlor. Tana ta tunani, mai Alhaji yake son fada masu ne haka, Allah yasa dai su ji alheri. Har suka dawo gida, basu ce ma juna komai ba, nan hankali Abdallah ya tashi. Wanan da Abba bai danyi hira da shi ba ahanya, toh abun da Abba zai fada, must be very serious. Suna isa gida, suka yi sallama, Umma ta amsa. Ko wanan su ya samu wuri ya zauna, sanan Abba ya gyara murya. Ya fara magana. "lokacin da na fita, Baffa Dajjo ya kira ni, yace inzo gida, naje. Da muka gaisa da shi, sai ya ce mun wai yana da magana ne akan Abdallah". Ya fada yana kallon Abdallah. "Kuma gaskiya maganan daya mun, ya taba ni sosai. Kuma dai kun san yanda yake, inya fara yarba ma mutum magana, especially mu da yake ganin mu as low class". Abba ya fada. Ran Abdallah ya baci sosai, dan yasan mutumin nan, ba abunda bazai iya fada ba, kar Allah yasa ma yayi embarrassing din abban sa ne. "Kuma dai kun san shi, bayi da mutunci". "Ae" Umma da Abdallah suka amsa. "Maganan akan auran Abdallah ne". Abba ya fada yana kallon Abdallah. "Wai yaushe zaka yi aure ne, wai shi yanzu yana expecting kace ga wanda kake so, amma shuru. In kuma baka samu bane, wai baga yan mata nan da yawa acikin gida ba, mai ya hana ka zaban daya acikin su. Na ce mai ban sani ba, sai fa ya hau ni da fada, wai bamu iya training ba, duka yaran mu da nasu salon, Sudais kawai ya auri yar family, wai kar mu bari ya maka na dole. Ni yanzu ina son ka fada mun ne, baka da kowa ne"? "Allah sarki Abba na, ban ji dadin abun da Kawu Dajjo ya maka ba, kuma In sha Allahu zan nema. Wallahi Abba na, dukan su ne basu da features din da nake so, they are just indecent. Sai ma sun zo asibiti, su dinga misbehaving. Amma nasan In Sha Allahu na kusan samun wanda ta mun, In sha Allahu ba zan baku kunya ba". "Hmmmmm, gaskiya bana jin dadin abun da mutumin nan ke yi. Ya bi ya raina mu haba. Ni kam kar ma ka kawo mun wata yarinya cikin familyn nan gidan nan". Umma ta fada. "Gaskiya ko ni am not in support ka auri yaran nan. Allah ya kawo maka ta gari". "Amin ya rab". Aranan dukan su sun yi shuru, ba mai ma wani magana. Duk basu ji dadin abun ba. Shi kuma Abdallah, abun ya masa yawa, ga takaicin abun da kawu Dajjo ya ma Abba, ina kuma zai fara neman mata? Thanks for reading, ayi sharhi filis, sharhi is life 🤪🤪🤪🤪🤪. Comment Like & Share. ~Zeexee ce~ 🖊️🖊️🖊️ [8/30, 1:19 PM] Abokiyar Fight💜💖: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 *BANBANCIN KABILA* _(Short story)_ 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 *TAMBARI WRTER'S ASSOCIATION* *_🔱((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))_* *T.W.A* ____________________________________ https://www.facebook.com/Tambari-writers-Association-106058867819812/ ____________________________________ *WRITTEN BY ZAYNAB* _(zeexee)_ MARUBUCIYAR *-RAYUWAR HUSNA* *-MAHAKURCI MAWADACI (2020)* ```Dedicating this page to Fatima Zarah Eyman aka abokiyar bus🤭🤭🤭🤭🤭. I love you loooodie loooodie``` 7️⃣&8️⃣ _Bismillah_ "Babe wake up, it's time". Olamide ta tashi Nafisa. "Dan Allah habibty ki bari in ankira sallah, wallahi jiya ban yi barci da wuri ba". Nafisa ta fada. "With all the warnings, kuma kin san bazan tashi ban tashe ki ba ko"? "Am sorry, bari in tashi kafun kiyi fushi dani". "Ko ke fa". Olamide ta fada. Da kyar dai Nafisa ta tashi, tayi alwala, ita kuma Mide, ta riga ta fara sallah. "Kai habibty, today is going to be stressful fa, ki ci abinci da kyau". Nafisa ta fada. "Wallahi na koshi haka. Ko so kike inyi loosing din shape dina ne"? Olamide ta tambaye ta tana daga gira. "Toh! A yau kuma? Ai ke kam no matter what you eat, ba zaki taba yin kiba ba. Just imagine, ni dake zamu narka abinci, at the end of the day, kiga ciki na ya karu, amma naki na nan flat". "Kai habibty, banda karya fa? Kema fa cikin ki ba wani babba bane, sai an lura ake gani". "Ae, ai still dai ana gani ko"? Nafisa ta tambaya "Ban sani ba". Olamide ta amsa mata tana yatsina fuska. Ta kara cewa "ni dai kiyi sauri mu wuce, indai abinci ne, zamu samu a cafeteria" "Toh naji uwar masifa". Nafisa ta fada "Yauwa uban masifa". Suna isa school, suka fara zuwa bursary, suka bada receipt, dan daman sun riga sun biya school fees din su a bank. Daga nan suka fara biyan student unions, sukayi online reg ma. Arannan dai sun dade a school, dan basu bar school ba, sai misalin 5:30pm. Agajiye suka koma gida. Suna shiga gate din gidan, wasu neighbours dinsu su biyu, suma student ne, suka rungume su. "Oyoyo Olami's" daya daga cikin su mai suna Hafsat ta fada. "Oyoyo my yar'fara". Olamide ta amsa. Nafisa kuwa, abun ya kai mata har wuya. Ta tsani taga ana shishige ma habibtyn ta haka. "Ooh Olami's, ko dan kiban nan baki yi ba. Ni na rasa irin wanan jikin naki, ba ya karuwa, kuma baya raguwa". Halima dayan kenan, ta fada. Halima da Hafsat, dakin su daya suma. Gidan da suke, one room apartment ne, bedroom, kitchen, and toilet. Kuma apartments hudu ke gidan. "Nima na rasa roomie. Kuma gata da zubin fulani. Abun dake bata show, shi ne inkaji ance Olamide. Nan ma in baka san ita bace, toh zaka nima Olamide ka rasa". Hafsat ta fadi. "A'a Hansey, kar muyi haka da ke. Kuma bari mu shiga daga ciki tukun, kunga yanzu agajiye mu ke". Olamide ta fadi. "Awww, haka ne fa. Fisa baby, ya gajiya, na ma manta kina wajan". Hafsat ta fada. Nafisa kuwa ta riga ta cika, tayi fam, amma bata son su gane, sai tayi faking din murmushi, ta bar wajan. Olamide ko ta riga ta san abun dake damun kawar ta, sai tayi murmushi, ta ce masu Hafsat "zaku biyo mu dakin mu ne yanzu, ko kuma sai bayan isha ku shigo kaman yanda kuka saba"? "Hmmmm, zamu zo bayan isha, saboda alokacin hira ke yin pepper ko Hafsah"? Halima ta tambaye ta. "Ae hakan ma yayi. Amma Olamis, baki kyauta ba, ko kiyi tambayan su Khausar da su iklima". "Awww sorry, na ma manta da su wallahi". Olamide ta fada "Sun ce sai next week zasu dawo. Kinsan Khausar da Hafiza cousin's ne, kuma rana daya suke zuwa. Su Iklima da Mufida ma, suma sunce sai next week". "Gaskiya ne, zamuyi complete kenan next week. Allah ya dawo dasu lafiya". "Amin". Halima da Hafsah suka amsa. "Yauwa, kunga bari in shiga ciki, na gaji sosai". Tana fadan haka, ta bar wajan, bata ma tsaya jin amsan su ba. Data shiga ciki, ta samu Nafisa ta jingina da pillow, tayi lamo kaman bata jin dadi. Ta cire hijabin ta, tayi hanging din jakar ta, ta sa takalmin ta amazunin shi, sannan taje kusa da Nafisa, ta taba ta, tace "ya akayi ne habibty, tun awaje naga mood din ki ya chanza". Sanda tayi wani nishi, ta ce "babu, me kika gani"? "Don't ask me that, na san akwai abun da ke damun ki, ki fada mun mana please, kar ki bari hankali na ya tashi". "Babu komai fa, am just resting ne kawai". "Please stop telling me that, kin san bana taba kaunan in gan ki ahaka, hankali na na tashi". Olamide ta fada helplessly. "Ba komai my habibty, let just say ina missing din gida ne". "Ban yarda ba Nafisa, ban yarda ba. I thought am like a sister to you, then what is my role as a sister"? Mide ta tambaya. "To always be there for me in any situation, and vice versa". "Then why are you not letting me play my role". Alokacin, har idanuwan ta sun kada. "Bakomai, kawai dai, kawai dai". Bata iya completing din statement din ta ba, ta fashe da kuka. Abun so ya samu, Olamide ma ta fara kuka. Sai suka rungumi juna suna kuka, Olamide na rarrashi Nafisa. Cikin kuka Nafisa ta ce "na sani inga ana miki shishigi, yana kona mun rai, na tsani inga mutum na nuna maki so agaba na, sai in dinga jin wani iri. Wallahi na dauke ki tamkar yar'uwa ta ta jini, shi yasa kika ga nake kishi akan ki. Kina nuna mun son da maybe in ma ina da yaya ko kanwa, da kyar sununa mun. Kuma soyayya bai tsaya akan ki ba, harda Mummy da kannan ki, kuna nuna mun so sosai. Shi yasa in naga wata na kokarin shige maki, sai inji kaman za'a kwace mun ke". Ta fada tana kara volume din kukan ta. "Shiiiiii, ya isa haka habibty, bana son kukan nan, kar ciwon kai ya kama ki". Ita ma ta fada tana kuka. "Zan daina, amma sai kinyi promising dina ba zaki bar ni ba, zaki tsaya da ni kaman yanda true sisters ke tsayawa da juna". Nafisa ta fada. "Am not perfect, and I don't know what tomorrow holds, amma ina son ki sani I will always be there for you ore mi( kawa ta)". "Shikenan, na daina kuka, kema ki daina. Kuma nima na maki alkawari, I will always stand by you". "Yauwa, ki daina kishi, Fai'za ta Nafisa ne, itama Nafisa ta Fai'za ce". "Ae". Nafisa ta amsa, tana goge hawaye. "Kinga tashi muyi alwala, ana kiran sallah". "Okay toh. Amma me zamu ci ne da daddaren nan, wallahi yunwa nake ji". "Toh mu ci talliya mana". Olamide ta fada. "Gaskiya kam, tunda muna da stewssssss". "Hahhhh, gaskiya kam muna da su". Da suka idar da sallan magrib, suka sa talliya awuta, kafun isha, har ya dahu sun ci, kafun suyi isha. Suna idarwa, kaman su Halima na ganin su, suka shigo. "Ooooh yes Olamis, mun zo shan hira. Kinsan jiya da kika dawo, bamu nan, munje gidan aunt dina, nan muka kwana". Hafsah ta fada. "Hmmm haka ne. Ko dai anje hmmm....". Olamide ta fada tana murmushi. "Kefa mun chanza, mun daina". "Allah yasa". Nafisa ta fada. "Ke zan mazge ki fa". Halima ta fada. "Ki mazge ta, adalilin me"? Olamide ta fada. "A'a aunty, kar kiyi fushi. Mun san baki son ana tsokanan habibtyn ki" "Gaskiya kam bana so, ko kadan". Halima ta amsa. "Ku manta da wannan, mu sha hiran mu kawai". Hafsah ta fada. "Ae ku sha hiran ku. Ba shekaran jiya na dawo ba, me ya hana ku zuwa shan hira"? Nafisa ta fada. "Babu, kema fa kin san mun fita, kuma ai da muka dawo mun dan shigo ai". Halima ta amsa. "Ya isa. Kun san me"? Hafsat ta tambaya. "Ya zamu sani"? Olamide ta fada. "Kai habibty, you always have answers to every question". Nafisa ta fada, tana dariya. "Kuyi shuru mana". Hafsat ta fada. "Mun yi". Suka fada a tare. "Aha, Nabila fa ta kusan aure". "Wace Nabilan"? Olamide ta tambaya. "Nabila kawar ku mana, bata fada maku ba ko? Actually nima dai ba ita ta fada mun ba, naji ne, kin san gidan su ba nisa da gidan aunty na". Hafsat ta fada. "Ai ko in bata fada mana ba, baza mu je ba ko habibty"? Olamide ta tambayi Nafisa. "Ae, mu bamu gayyan sodi". Nafisa ta amsa. "Kai! Why is your blood rushing, ai bata fada ma kowa bako, kuma dai kun san zata fada maku". Hafsat ta fada. Olamide tayi wani dariya, sai ta ce "abun ya yuwu da dan gombe kenan". Tana fada, suka tafa da Nafisah. "Toh ku ma yaushe za'ayi naku"? Halima ta tambaya. "Randa Allah yaso. Kuma kema kin yi ne"? Nafisa ta tambaya. "Toh ai na kusa, next year In Sha Allahu, maybe june'. "Allah ya kai mu, amma still you have no right to ask us, tunda ba'a gwanjo ake samo mazan ba". Olamide ta fada. Duk suka fashe da dariya. "Gwanjo kuma habibty? Kin san gwanjo ma akwai grade ko"? Nafisa ta tambaya. "Ae da anan ake samun su, da zamu dinga zuwa da wuri, dan mu samu grade, ba zamu ba in 9:am yayi , sai dai ya same mu acan". Olamide ta fada. Duk suka kara fashewa da dariya. "Kai Olamis, baki da dama. Shiyasa nake son hira da ke. Although kin iya shunning din mutum, amma still kina da ba mutum dariya, but banda angry part din ki, lokacin da kike mantawa kinba mutum nickname, sai ki kira sa da sunan sa". Hafsat ta fada. "Bari kawai yar'faran habibty, ai in habibty tayi fushi, ta na mantawa da soyayyan da take nuna ma mutum. Kinga in tayi fushi, alokacin zaki ji tana NAFISA SULAIMAN". Duk suka fashe da dariya. "Bari kawai ba zaku gane ba. Ai alokacin, nickname baya mun dadin fada, sai dai sunan mutum". "Toh Allah ya shirye ki. Ya zaki yi da mijin ki, ko shima da sunan sa za'a na kiran sa, in ya kai ki neck"? Hafsat ta tambaya. "Ke abu kadan miji, baki gajiya ne. Toh ko shima, zan kira sa da sunan sa, so he will know am serious". "Toh ai it's not my fault, at this stage of life, abun da ya kamata mu damu da shi kenan. In mu kayi aure kuma, mu fara maganan yara". Hafsat ta fa. "Toh sannu marriage consultant. Kai yar'fara, wanan aikin zai miki kyau fa". Olamide ta fadi. "Sosai ma". Halima da Nafisa suka amsa. Su Halima basu bar dakin su Olamide ba, sai 9:39pm. Nan ma, saboda Olamide ta masu complain cewan suna jin barci ne. Inba haka ba, basu ki aita hira ba har cikin dare. Wani hiran ma sai sauran hudun sun dawo. 〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️ Da kyar Abdallah yake cin abinci, saboda tunani ya mai yawa. Of course shi ya san yana son aure, amma da wanda za'ayi shi ne matsalar sa. Ina zai fara. Kuma ko su Umma basu fada ba, shi bazai iya auren cousins din sa ba. Hamma Sudais din daya yi, yaga zai iya ne, kuma ma ai yayi hitting din jackpot, saboda matar shi akwai hankali. Ko adda Wasilan da take cewa ya zaba daga cikin su, ta manta da abubuwan da duka fada akan ta ne, ita da suke cewa zata auri mijin ta ne saboda kudin sa. Amma data yi aure, ta fara fita, tana daukan wanka, suka soya hali, ko wannan su ta zama yar dakin ta, iyayen su ma suka zama abokiyar ta. Ita kuma Adda Bilkisu, tana da kudin kan ta, kar ma ayi maganan na mijin ta, yasa suke ribibi akanta, ita da ma ba'a nan take zama ba, tunda Allah ya buda ma mijin ta, ya samu aiki a dubai, suka fara son ta, harda yayan ta. Basu ki yayan suce masu suzo su taka kan su ba, saboda tsabaragen son abun duniya. Ita kuma Adda Fadila, mijin ta akwai rufin asiri, ba laifi. Dan itama ba zaka ganta ka raina ta ba. Amma abun mamaki, sun raina iyayen su, amma suna son yayan su saboda abun duniya. In shima ya auri daya daga cikin su, shi ma zai zama dan so. But to hell, bazai bi abun da kawu Dajjo ke so ba. In sauran nayi, shi bazai yi ba. Shi zai bi umarnin iyayen sa ne. "Abdallah! Abdallah!! Abdallah!!! Sanda Abba ya kira sunan sa sau uku, kafun ya amsa. "Na'am Abba na". "Naga baka cin abincin ka ne"? Abba ya tambaye shi. "Bakomai Abba, ai ina ci". "A'a, Abdallah bamu saba ganin ka haka ba, kai da you are always there to make us laugh". Umma ta fada. "Toh ai shi ne". Abba ya fada. "Bakomai. Bana ma jin yunwa, sai da safen ku". Ya tashi zai tafi dakin sa, Abba yace ya dawo. "Gani Abba na". "Zauna". Ya zauna. "Nasan abun dake damun ka, kar ka damu da abun da tsohon nan ya fada, na shi kawai yake fada. Ni yanzu zan bari ne ya maka auran dole ne? Kuma in aure ne, lokacin ka ne baiyi ba auta, in lokaci yayi, ba mai iya stooping din shi. Saboda haka, ka saki jiki ka ci abinci". "Ai kuwa. Ka daina damuwa da bad energy. In yaga sauran na dancing to his tones, toh ai ya kamata ya san mu kam bamu cikin su. Kuma ka auri koma waye, but make sure she will be a good wife and mother to your kids". Umma ta fada. "Am in support of what your Umma said. Ba dole bane ka auri bafulatana ba, ko bahushiya ka samu kuma ta zauna maka, ko shi bazai daura auren ba, ni zan daura agidan nan. Nine uban ka ba shi ba". Daga yanda yake magana kasan ran Abba ya baci sosai. "In Sha Allahu, nagode sosai Abba na da Umma ta, Allah yasa ku dade mana, Allah ya saka maku da aljannah, thanks for the support". "Bakomai, ai responsibility din mu ne as iyayen ka ko Hajaju"? Abba ya tambayi Umma. "Kwarai kuwa". "Barci nake ji, gobe ina da morning duty". Abdallah ya fada yana hamma. "Toh, kuma kar adawo gobe ayi mana complain, dan naga yau da wuri za'a yi barci". Umma ya fada. "Toh ai ina huta gajiyan yau ne, gobe ma ai zan yi nashi gajiyan ko Abba na". Abdallah ya tambaye shi". "Haka ne auta na., ko wani rana nada gajiyar sa". "Wannan kuma ku kukasani" . "Manta da ita Abba na, kishi take" Abdallah ya fada. Yana magana, Umma ta dau pillow, ta jefa masa, amma yayi sauri ya bar wajan. Da yaje office, yayi attending to patients, lokacin komawa gida yayi, ya dauki briefcase din sa, ya cire coat din sa, ya rike a hannu. Yana kan tafiya, wani ya kira sunan sa "Dr Abdallah!". Yana jin sunan sa, ya juya, yana juyawa, yaga abokin shi ne Dr Farouk. "Bana ce maka akwai magana ba"? Farouk ya tambaye shi. "Am sorry, na manta ne. Kasan stress din patients dinnan". "Gaskiya attending to patients ba karamin aiki ba ne". Farouk ya fada. "Wallahi. So what up"? Abdallah ya tambaye shi. "Muje mu zauna akan bench dinan dake karkashin bishi yan nan". Suka je suka zauna, Farouk ya fara magana " Guy kasan ansa aure na da Nabila bayan sungama wanan semestern, amma yanzu sun chanza, wai inba damuwa, ayi shi nan da two weeks, twoo weeks fa". Ya fada yana nuna yatsun sa biyu. "Congrats man, Allah ya sanya alheri". Abdallah ya fada. "Am serious fa, kuma kasan worst part din, su Abba sun yarda, wai hakan ya fi". Farouq ya fada. "Toh me ke ciki, ayi abun da za'ayi kawai ka huta. Yours is even good, mufa yanzu muka fara hunting". "Toh kai aganin ka hakan ya fi kenan"? Farouk ya tambaya. "Ae, wallahi, na maka murna fa sosai. Ka ce dai mu fara shirin zuwa kano, ko muma zamu samo wata acan". Abdallah ya fada. "Toh mashaAllah, tunda abun ya zauna cif, nima nayi relaxing. Amma da'a I was so worried". "Kar ka damu, your brother in islam is here". Abdallah ya fada. "Yeah thanks for za support. Sai yanzu ma maganan ka ke flashing. So ba ma raka ni zakayi ba, kaima zaka je neman mata ne"? "Ae mana, ai yanzu na fara wife hunting, kuma I want it soon, bana son ana raina mu iyaye". Abdallah ya fada. "Ban gane ba, wake son raina Su Abba"? Farouq ya tambaya. Nan ya fada mai komai, sai Farouq ya ce "aiko, ko ni am in support. Allah yasa ka samu. Dama ka samu bahaushiya, muga expression din wanan kawun na ku". "Amin aboki na, muga iya gudun ruwan sa, muga ko zai kashe ni ne, ko kuma me. Shi din daya ke magana, ai second wife din sa bajara ce. Amma ya bi ya takura mana, wai sai bafulatana dole". Abdallah ya fada. "Kyale shi, dan yaga shi ne babba ai, shi yasa yake mulki akan ku yanda yake so. Aboki na, Allah ya baka bahaushiya, muga karke Kawu". Farouk ya fada. "Amin ya rab aboki na. Shi yasa neke ji da kai". ```Thanks for reading, sharhi is bea, kaman yanda kuka sani. ``` ~Zeexee ce~ 🖊️🖊️🖊️ [8/30, 1:21 PM] Abokiyar Fight💜💖: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 *BANBANCIN KABILA* _(Short story)_ 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 *TAMBARI WRTER'S ASSOCIATION* *_🔱((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))_* *T.W.A* *WRITTEN BY ZAYNAB* _(zeexee)_ MARUBUCIYAR *-RAYUWAR HUSNA* *-MAHAKURCI MAWADACI (2020)* ```Dedicating this page to my Kawallie (Hansey)🤭🤭🤭🤭 and my kanwas(boddi'am). I love you guys soooo much, long live the three musketeers💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼 .``` 9️⃣&🔟 _Bismillah_ Da suka gama hira, Abdallah ya je gidan adda Wasila. Saboda yanayin sa, ko mai gadin gidan ma bai mai wasan da suka saba. Da ya shiga ciki, yaran ta na ganin shi, suka san yau kam uncle auta ba lafiya. So they just greeted him, su ka bar wajan. Adda Wasila ma tasan ba kanta. "Uncle auta! Lafiya kuwa yau"? Adda Wasila ta tambaye shi. "Ba lafiya, dan na zo ne na miki magana tsakanin kani da yaya". "Toh Allah yasa dai inji alheri". Adda Wasila ta fada. "Amin. Gaskiya adda, da zaki ji nawa, ki daina wani kula wannan tsohon familyn mu. Bashi da respect for our parents, even an atom. He talks to Abba anyhow, but you always think his decisions are right, duk da kema ya maki rashin mutunci alokacin da zaki auri Uncle Hussain, ba irin wulakanci da ba'a miki ba, amma yanzu kam na kasa gane direction din da kike". Abdallah ya fada yana huci. "Toh Abdallah ya kake son inyi, shi ne fa babba fa a familyn mu, so kake inyi disrespecting din sa"? "Bance kiyi disrespecting din sa ba, amma ki daina sake masu, dan shi ne abokin shawaran ki. Ni ban sani ba ko neman gidin zama kike oho maki. Adda fa duk wanda baya son iyayen ka, baya son ka ne. Kullum fa cikin raina Abba mu yake". Yana magana duk jijiyoyin wuyan sa na fita. "Gaskiya Abdallah, bazan bari ka zo gida na ba, ka dinga mu maganan banza ba. Ni yayar ka ce, shekaru kusan hudu ke tsakani na da kai, kasan yanda zaka mun magana. Kuma kana cewa neman gidin zama nake, toh na neman. Idan ka shirya yi mun magana cikin hankalin da natsuwa, ka mun, in kuma baka shirya ba, here is the door, you can leave". Ta fada tana nuna mai bakin kofa da hannun ta. "Wow! Wow! Adda, nagode sosai. Wallahi kina bani mamaki, amma dai tunda kin nuna mun kofa, bari in wuce. Amma karki manta, wallahi in baki guje shi ba, wata rana, sai ya wulakanta iyayen mu agaban ki, kuma ki kasa cewa komai. Amma ki sani, duk randa na samu labari, toh za'a yi ta." Yana gama magana, ya duki wayar sa da ya ajiye akan center table, ya parlor, ya je wajan da suke parking din motoci, ya shiga motar sa. Yanda Lawali yaga yake driving, yasa ya hanzarta, ya bude masa gate. Daya bude masa ma, kaman zai buje shi, sanda ya matsa da gudu. Idanuwan sa duk sun bi sun kada sunyi jazur, gashi jikin sa sai bari yake. Last time ma saboda maganan kawu Dajjo, su ka samu sabani da ita, kuma fa duk akan wulakancin da yake ma iyayen su ne. Shi bai san wata iri ce ita ba. Wai mutum ka dinga ganin anama iyayen ka nonsense, amma ka dinga jurewa, saboda kana son a dinga yabon ka, toh sun dade basu yabe shi ba. Driving yake da gudu, ya iso wani green gate, ya fita a motar, ya buga gate, wata farar mace ta fito, mai kama da Abdallah sak, da yaron ta da bazai wuci 2 years ba yana biye da ita. "Waye ne"? "Ni ne, ki bude mun". Abdallah ya fada. "Aww yau kam an tuna da ni kenan". Ta fada tana bude gate din. Data bude, sai ya shigo, ya bude duka gate din, ya shigo da motar sa, ita kuma tana gafe, dan ta na manne da ita. Da ya gyara parking, ya fito. Yana fita ya ce "chewing gum din Mummy, baza'a gaishe ni bane"? Yaron ya ki motsawa, instead, ya kara manne ma Mumnyn sa. "Mu shiga daga ciki, Afran ka na can, ka bar mun da na". "Ko baki fada ba, me zanyi da wannan mai kiwan". Da duka shiga ciki, ya zauna a parlor, Afra na jin muryar sa, ta fito tana "oyoyo Uncle". Ta zo da gudu ta rungume shi. Bata wuci shekara hudu ba, tana kama da Umma takwaran ta. Dan asalin sunan ta Rukayya ne, amma suna kiran ta da Afra. Abdallah na mugun son Afra tamkar shi ya haife ta, although niece din sa ce, but he has a fatherly love for her. "Oyoyo my Afra. Ya kike"? Ya tambaye ta. "Lafiya kalau Uncle. Baka tambaye ni ya school ba". Ta fada tana tura baki. "A'a afuwan Afran Uncle. Ya school"? "Fine, an bamu homework". Ta fada. "Toh mashaAllah, adage da karatu ko my Afra? Kuma fa a dinga zuwa islamiyya, a daina karyan ciwon ciki". "Ina zuwa, ko Mummy"? Ta tambaya, tana kallon wanda ta kira da Mummy. "Bawani, sai na hada da bulala kike zuwa". Matar ta fada. "A'a adda Fadi, bazan yarda kina dukan mun ya ba. Ina yi aure, zan zata fara samun saida, saboda yau tana nan, gobe tana can, dan haka ki rike amana kafun lokacin". "Toh Abdul". "Yauwa". Sai ya kalli Afra, ya ce ki tafi daki zanyi magana da Mummyn ki". "Toh Uncle, amma baka kawo mun choclate da bobo ba yau". Ta fada kaman zata yi kuka. "A'a, kar ki sa hankali na ya tashi, kafun in wuce, zan siya maki". "Owk Uncle, mi yatti". Tana fadan haka, ta wuce daki. "Kaga ma ko tayin ruwa ban maka ba". Adda Fadila ta fada. "Toh ai nayi zaton baza'a bani ba". "Ai ban isa ba, bari in kawo maka drink, ko ruwa zalla kake so"? "Toh kaji jikar Dajjo, ki kawo mun duka biyu. kuma na san baza'a rasa small chops ba, ahado mun, dan nasan ina gama magana, zan bukace su". "Shikenan an gama my brother." Ta tashi, zata bar wajan, dan ta ya rike mata kafa. Kai! Irfan, kar ka fadar dani fa, kaje wajjan addan ka, nima ka bari nayi attending to my brother". "Wannan dan ki mai ido kaman mage zai bar ki ne? "Kai bro, ka daina zagin heartbeat fa". Ta fada, sai ta duki Irfan, ta tafi kitchen da shi a hannu. "Ni kam na ga ikon God yau, naga yanda zaki kawo mun abubuwan nan da shi ahannun ki". Ya fada. Daya bayan daya ta kawo mai drink, da snacks ta sa mai agaba. Data gama jera mai komai, ta zauna akan kujeran da ke opposite da Abdallah, ta sa Irfan akan kafan ta. "Toh me kake son fada mun"? Ta tambaye shi tana daga mai gira. Sanda ya numfasa, sannan ya ce "Daman akan Kawu zanyi. Gaskiya abunda yake ma Abba mu ba kyau kwata kwata, ya bi ya raina mana iyaye". Abdallah ya fada ran sa a bace. "Hmm bari kawai brother, abun na kona mun rai sosai wallahi". Ta fada, ta dafa goshin, tana jijjiga kai. "Wallahi fa, yana bata mun rai. Kin san abun da ya ma Abba mu ne jiya"? "Sai ka fada. Amma kuma kardai wani rashin mutuncin ya masa, kasan meeting ya kusa, yana neman abun da zai yi disgracing din iyayen mu ne". Adda Fadila ta fada. "Ai kuwa, saboda su samu abun fada ba. Yace ma Abba wai yaushe zanyi aure, Abba yace lokaci ne baiyi ba, ya hau Abba da fada, wai baga yara a family ba, mai ya sa bazan zaba daya daga cikin su ba. Kuma to be frank, keh ma kin san basu game ni ba ko kadan. Abba yace bai sani ba, sai yace wai Abba bai bamu tarbiya ba, dukan mu da salon mu muke zuwa,maganganu dai na rainin hankali. Wallahi Fadi, sai kin ga yanda Abba yake magana, zaki san ransa ya baci sosai ba ka dan ba. Daya fada mana ma, keh ma dai kin san Umma, ta fara magana, nan suka ce mun wai I shouldn't be in a hurry, Allah zai bani in lokaci na yayi, kuma ba dole sai bafulatana ba, ko bahaushiya ce, zan aure ta, kuma ko kawu ya ce shi bazai yarda a mai taro agida ba, toh a zo gidan mu ayi". Yanda Abdallah ya ke magana, kasan ransa ya baci sosai. Ita kuma Adda Fadila mai saurin kuka, har idanuwan ta sun kada. Sai ta kira Afra, ta bata Irfan, su ta fi daki tare, kafun ta yi magana. "Wai ni ya zamu yi ne mu karban ma iyayen mu yancin su a cikin family, ae mun yarda Abban mu is not flowing in dollars, amma bai taba zuwa gidan ko wannan su roko ba, amma sun bi sun raina shi saboda wannan azalimin da yake babban gidan Yero Family. Shifa in bai ga kana flowing in naira's ba, toh fa kai ba kowa bane, kuma rainin hankali kala kala zai dinga ma. Wallahi ko ni am in support, Allah ya baka bahaushiya, alokacin zai san bawai Abban mu bai san abun da yake yi bane, kawai barin sa yake. Amma kasan abun mamaki brother, suna mugun son hamma Sudais, adda Bilkisu da adda Wasila. Kasan shi hamma, duk da cewa baya biye mai, amma ya auri yar family. Ita kuma adda Bilkisu, saboda abubuwan da take basu, inta dawo daga dubai, in suka zo hutu. Ita kuma Adda Wasila, saboda mijin ta akwai kudi, kuma tana masu kyauta, sannan sun maida ta money making machine, suna washe mata baki anyhow, suna wani bata girman karya, ita kuma abubuwan na ruda ta". Ta fada, kaman zatayi hawaye. "Toh ai shi ne, wallahi adda Wasila na bani mamaki sosai. In fada maki, yanzu dai daga gidan ta nake". Abdallah ya fada. Nan ya kwashe mata komai, ya fada mata. Adda Fadila bata san lokacin data fara kuka ba, ta ce "wani wata irin zuciya gare ta, adinga raina maki iyaye, amma ki ce su din kike so". "Ki daina kuka adda'am, komai mai wucewa ne, kuma In Sha Allahu, sai na karban ma iyayen mu yancin su. Kar ki damu kin ji masoyiyar auta, mai ji da shi, amarya a gidan Sadiq, Mummy Rukayya da Irfan, yar gaban goshin Goggo Khadija". Abdallah ya fada yana murmushi. Sai ta goge hawayen, kalaman, su kwantar mata da hankali. Duk da cewa shi ke bin ta, basu wani fadan nan na masu bin juna, instead, suna nuna ma juna soyayya ne sosai, basu taba son ganin bacin ran wani daga cikin su. Har yan'biyu ake kiran su, saoda shekara daya Fadila ta girme shi dashi, ga kaman da suke, kaman identical twins. "Kin san me adda Fadi"? "Sai ka fada autan mu". "Auran Farouq fa saura sati biyu". "Sati biyu? Ba bayan yarinyar ta gama first semester dinnan za'a yi ba"? Ta tambaya surprisely. "Ae, amma wai sunce ayi in two weeks time, kuma kaman za'a mata transfer ne ta dawo nan". "Hmmm, toh Allah ya kai mu, kace kana da zuwa journey kenan, ga shi kai ne babban abokin ango, sai kai ma ka bude ido ka neman mana wata a kano, amma fa banda yar bleaching, duk da nasan kowani gari akwai masu yi, amma na kanawa is just too extraordinary". "In Sha Allahu, kar ki damu". Abdallah ya fada. Suka fara wani sabon hira kuma, bayan sallan Asr, ya bar gidan, ya koma gida. Nan ya sami Abba da Umma, suna hira, yayi complain din gajiya, Umma ta yi mitan ta, Abba kuma yayi supporting din sa. Yayi route din sa, sannan lokacin barci yayi, yayi barci. 〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️ "Madam ki tashi, an mana fixing din lectures fa". Nafisa ta fada tana tada Olamide. "Keh! Wani irin lectures kuma, ba ana registration ba har yanzu"? "Ae anayi, amma ai this is not the first week, third week fa kenan ". Nafisa ta amsa. "Toh sai me, ni ki kyale ni, barci nake ji". Olamide ta fada. "Okay in kyale ki ba, salon in kika tashi ki mun masifa ba, ai baki isa ba, you must wake up". Nan Nafisa ta ita jijjiga ta, tana "wake up sleepy head, wake up sleepy". "Ohhhhh, keh fa habibty, disturbance din ki na iya sa sabon ciki zubewa haba". Olamide ta fada. "Oho, ko tsofon ciki ne, ni dai ki tashi, by 11 mu ke da lectures din zuwa 1". Nafisa ta fada, still tana jijjiga ta. "Mo daran(na shiga uku)! Dan Allah ki kyale ni. Me ta ma yanzu? Indai 9:30 bai yi ba, toh ki bari inyi barci har 9:30, I promise kina tada ni zan tashi". Olamide ta fada. "Yanzu dai it's 8:15. Kinyi promising, kar kiyi breaking din shi, ina tashin ki, ki tashi". Nafisa ta fada seriously. "Ba wanka na da shiryawa ne kike tsoro ba, ai na chanza yanzu, bana bata lokaci kuma". Olamide ta fada. "Allah yasa. Bari in bar ki kiyi barci ko habibtyn Fisa"? "Yauwa habibtyn Fai'za". Olamide ta fada. 9:30 dot Nafisa ta tada Olamide. "Ki tashi, it' 9:30 now". Da'a zata yi masifa, sai ta tuna ita tayi alkawarin zata tashi alokacin. Olamide ta tashi, ta shiga toilet, tayi wanka, sannan ta dawo ta shafa mai, ta sa wani red colour satin, mai belt. Data sa kayan, ta daura belt. "MashaAllah, babibty, yau kam na yarda kin chanza. Within 30mins har kin shirya, keda almost 1 hour kina shiri. And yes, nima irin wannan zan sa". Nafisa ta fada tana tura baki. "Kina wani tura baki, ba ni ya kamata ayi ma shagwaba ba. Ki sa mana, wani kaya zaki sa da'a. Kema kin san indai we both have the dress, we wear them on the same day". Olamide ta fara ana demonstrating da hannun ta. "Yauwa kin ga wanka kawai nayi, na kara sa night wear, bari in sa nima". Nafisa ta fada. Sharp sharp, sun gama shiri, suka shafa powder, da lip gloss a lebe, sannan suka dauki Black hijabs, suka saka, suka sa black flat shoes, sai suka dauki red side bags, suka yi slinging din shi a shoulders din su. Suna gama shiri, suka fito, nan suka hadu da su Hafsat da Halima, su ma zasu shiga school, suka tafi tare. Suna sauka a adaidaita, suka raba hanya da su Halima, dan su sun zo ida registration din su ne, su kuma suka wuce inda zasu yi lectures. Suna zaune, wata black beauty, ta shigo, taje inda suke zaune, tayi taping din shoulder din Olamide. "Ore'mi(kawata) yarinyar ta fada. "Hahhhhh, ashe kin zama bayarbiya bamu sani ba". Nafisa dake ta ciki ta amsa, saboda Olamide ke ta baki, shi yasa tayi taping din ta. "Su Bila beauty, an shigo yau". Olamide ta fada. "Ni dai ku masa mun in zauna, kafun ku tsare ni da surutu, kar adinga kallo na". Nabila ta fada. "Awww, bari in matsa, kema habibty sai ki matso ko"? Nafisa ta fada. "Butan kashi, wato ni in zauna a tsakiya, akan wannan karfe, toh naki". Olamide ta fada. "Kai Ore, kin san fa ke ce siririyar cikin mu, kuma ai karfen baya tokarin mutum". Nabila ta fada. "A'a, naki, ban ki in zauna ata baki bakin nan ba, amma naki in zauna aciki". Olamide ta fada tana wani murda baki. "Toh yana iya dake, matsa mun in shiga". Nabila ta fada. Olamide ta tashi, Nabila ta samu ta shiga, sannan Olamide ta zauna a baki bakin. Da suka gama balance, Nabila tace "daman ina son mu hadu ne, kafun in maku wata magana, saboda zan so ace muna tare, shi yasa ban fada maku ta waya ba". Nabila ta fada. "Toh muna sauraro ko habibtyn Fisa"? Nafisa ta tambaya. "Ae habibtyn Fai'za". "Toh daman kun san biki na, is suppose to be done after this semester is finished, amma Baffan mu, yace wai ayi yanzu, that is two weeks to come, kuma iyayen yaya Farouq sun yarda". Nafisa ta fada ta na rufe fuska, wai ita nan mai kunya. " Ashe abun ya matso, ina ankon"? Nafisa ta tambaya. "Kai habibty, ai ba maganan anko zaki fara mata ba, ai kya ce Allah ya sanya alheri tukun. Yauwa Bila, don't be shy. Amma ina da tambaya. Toh in kika yi auren, ya batun school, ko zaki bar mu kenan"? "A'a, zan cigaba anan, kin san cousin dina ne, so anyi magana da iyayen sa, ance inayi kaman two weeks acan, sai indwo. Amma zan dinga zuwa once in a while. Ga shi kinsan asalin mu yan gombe ne, so zan hadu da familyn mu da yawa". Nabila ta fada tana murmushi. "Toh amarya Farouq bada kan ki asare". Nafisa ta fada. "Toh ai ta riga ta bada. Am soooo happy ore, at least zamu cigaba da haduwa da Bilan mu aunty Bils". Olamide ta fada. Itako Nabila, sai ta rufe fuskar ta da hannun ta. "Am soooo happy for you oren mu, Allah ya sanya alheri, ya kawo zuriya daiyiban. Allah sa kyawawan maza su zo, inyi wuf da daya". Nafisa ta fada. "Amin ya rab". Nabila ta amsa. "Amma ni habibty, me ke damun ki ne, yanzu baki da kunya"? Olamide ta fada. "Toh me ke ciki, ni kam ki tsaya awajan, zaki ga nayi wuf da wani, ke kina nan ". Nafisa ta fada. "Ai kuwa, babban abokin yaya, handsome ne sosai, kin gan shi ne, gashi shima doctor ne". "Wow mashaAllah, kice dai in fara shiri, because am ready to do za wuf with him". Nafisa ta fada. "Gaskiya kam ki shirya, sai kuyi wuf da juna. Ke Olamide ba zaki yi wuf da wani ba, ina fa da handsome cousins". Nabila ta fada. "Wa zai yi wuf da yar yarbawa, sai dai kuyi wuf da juna, nima in jira yoruba prince dina yayi wuf da ni". Olamide ta fada. "Kai habibty, ni kam in kika koma gida, ki tambayi Mummy, hanya ba karere kuke ba, saboda kina kama da fulani tooo much. Kuma me ke ciki in kika auri bafulatani, ai Allah ya halice mu duka". Nafisa ta fada "Gaskiya kam, Allah created us all, kuma bai banbanta mu ba. Wallahi da muka fara haduwa da ke ko, I thought fa ke fulani ce, sai lokacin da kika fada mun yoruba name din ki, na yarda ke yoruba ce". Nabila ta fada. "Haka ake cewa, amma nasan I claim Niger state kawai, because that's where we know, ba mu ma san hanyar garin yarbawa ba". Olamide ta fada. "Toh it's maybe possible maybe garin yarbawan ma kunje ne. Saboda duk wayanda kike nuna mana as family, suna kama da fulani ne, especially cousin din ki din nan, aunty Hasinah". Nafisa ta fada. "Oho, mu kam abun da aka fada mana zamu yarda da shi".Olamide ta fada. Aiko tana rufe baki, lecturan su ya shigo. Ana gama lectures, suk fita. "Yauwa my ore's, yaushe zaku fitar anko ne, kun san kune manyan kawaye fa". Nabila ta fada. "Ko gobe ko jibi". Nafisa ta fada tana kallon Olamide. "Ae hakan yayi. Kuma mu sanar ma yan dept din mu, da kawayan mu". Olamide ta amsa "Toh mashaAllah. Ba zaku zo gaida hajiyar ku bane". Nabila ta tambaya. "Ai gaisuwa ya zama dole, ala ma mu biki yau ko habibtyn Fai'za". Olamide ta tambayi Nafisa. "Hakan ma yayi". Nafisa ta amsa. ```Thanks for reading.``` ~Zeexee ce~ 🖊️🖊️🖊️ [8/30, 1:21 PM] Abokiyar Fight💜💖: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 *BANBANCIN KABILA* _(Short story)_ 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 *TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION* *_🔱((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))_* *T.W.A* *WRITTEN BY ZAYNAB* _(zeexee)_ MARUBUCIYAR *-RAYUWAR HUSNA* *-MAHAKURCI MAWADACI (2020)* ```Dedicating this chapter to my jikoki, Fatima and Ayusha (Jiks 1 and 2)🤭🤭🤭🤭🤭🤭🤭🤭. Your comments make my day.``` 1️⃣1️⃣&1️⃣2️⃣ _Bismillah_ Suka fita daga school premises, suka nemi kekeh da zai kai su anguwan su Nabila. Da aka sauka su awani dan madaidaicin gida, amma fa gidan akwai kyau sosai, tun daga wajan gidan har ciki, akayi decorating din shi da flowers, so flowers din sun fito da kyaun gidan sosai. Nabila ta kwankwasa kofar, aka mude masu. "Sannu baba" suka fada a tare. "Yauwa sannun ku, kunzo lafiya"? Ya tambayi su Olamide. "Lafiya kalau". Nafisa da Olamide suka amsa. Cikin wani kofa suka shiga, nan suka cire takallaman su, sannan suka shiga parlor da sallama. Suna shiga, suka samu mahaifiyar Nabila, kanwar ta Safina da yayan ta Faeeq. Da sallam suka shiga, Hajiya Hajara na ganin su, ta ce "sannu ku da zuwa my daughters". A kunyance suka tsuguna a gaban Hajiya, suka gaishe ta. Ita kuma Safina, ta rungume su, ta ce "nayi zaton ko ba zaku zo kuga autar Hajiya bane". "Mun isa"? Nafisa ta tambaya. "A'a bamu isa ba" Olamide ta fada. "Toh ni baza ku gaishe ni bane? Especially wannan bayarbiyar". Yaya Faeeq ya fada. "Ina wuni yaya Faeeq. Ni dai na gaishe ka, saura yoruba princess din ka". "Tab!! Allah ya kiyaye".Olamide da Yaya Faeeq suka fada tare "Ni kam Faeeq ka bar mun ya'a fa. Zo ki zauna kusa dani yar'lele ta". Hajjiya ta fada. Da sauri Olamide taje ta zauna kusa da ita. "Ni wallahi Ummi shiyasa bana son zuwa gidannan in yaya Faeeq na nan". Ta fada a shagwabe. "Ki kyale shi. Ni nasan yana son ki ne, kuma bazan bashi ke ba". Hajiya ta fada tana murmushi. Duk yanda yaya Faeeq yake da keyi da Olamide, dukan su ke noticing. Abun kadan sai yayi maganan ta, ko tana nan ko bata nan. Ga shi yanayi da yake mata magana ma ya bayyana. "Allah ya kiyaye, me zanyi da ita". Yaya Faeeq ya fada. "Nima Allah tsare ni nayi soyayya da kai". Olamide ta fada tana hararrar sa. "Ki shiga hankalin ki dani, ki bar ganin ke ba muharama ta bace, zan dake ki ne black and blue". Ya fada yana ya making serious face. "Kai!! Wani baku gajiya ne? Kullum ku dinga fada kaman cat and dog. Yaya Faeeq mun san kana son Olamide ne, ba sai kamana corner corner ba. So ka fada mata kawai, kunga sai ahada auran ku". Safina ta fada. Tas taji abayan ta. "Ina wasa dake ne"? Yaya Faeeq ya tambaya. "Faeeq!! Bazan yi tolerating din haka ba. Ka tashi ka bar mana parlor, I want to have a girlie moment with my girls, kaga ya dade bamu hadu ba". Hajiya ta fada. "Bai sai kin fada ba Ummi, daman ina da niyyan tashi, amma naso in koyama bayarbiyar nan hankali. But anyways gwanda in bar ta da halin ta". Yaya Faeeq ya fada. Sai yayi pointing din Nafisa, ya ce "ke kuma lokacin biki, kar ki yi wuf da wani ki gani, zan neman maki tsoho. So it's better ayi da yaro kafun ran Faeeq ya baci. Yaya Faeeq na gama magana, ya bar wajan. Yana tafiya kaman wanda kafafuwan sa bazasu taba kasa ba, yi yake kaman yana tsoron in suka taba kasa, zasu bata. Sun dade a gidan su Nabila, dan sai bayan isha, Hajiya tace ma Yaya Faeeq ya mai da su. Nan ma sanda Nafisa ta ita raba fada. Shi Faeeq, baya gajiya da tsokanan ta, ita kuma bata gajiya da bashi amsa, so shi yasa suke prolonging din issue. "Wallahi Olamide, in kika bani haushi, anan zan sauke ki. Kuma kin san baki son a bun da zai sa dare ya same ki a waje, zanga yanda zaki koma gida". Faeeq ya fada a fusace. "Ka sauke ni mana, sai me? Ai ba mutuwa zan yi ba. Inada kudi na da zai kaini har gida". Itama ta fada tana huci. "Sai ya tsayar da mota, ya fita, ya je side din da take. Daman tana back sit ne, Nafisa kuma na passenger's sit. Kuma anyi hakan ne, saboda kar suyi fada, amma ina abun nasu a cikin jini yake. Daya tsaya abakin kofar, ya bude, sai ya ce "ki fita". Kaman jira take, ta yi hanging din jakarta , dan daman tasa jakar saman cinyar ta ne. Tana hanging din jakar, ta fito. Nafisa na ganin haka, ita ma ta fita. Sai ya ce "baki da case Nafy, ki koma ciki. Daman wannan yar rainin hankalin ne". "Gaskiya bazan iya kallon habibty na haka ba, so duk hukunci daka dauka akan ta, kaman akai na ka dauka. Ka wuce kawai, mun gode, dan na san da kyar in habibty zata kara shiga motan nan". Nafisa ta fada. "A'a ke ba ruwan ki, ki shiga, kuma ita din ma, nasan zata shigo ai, ba yau muka fara ba". Yaya Faeeq ya fada. Faeeq da Nafisa annan suna settling matter, ita ko tana can tana neman adaidaita. Tana samu, tayi ciniki da shi, sai ta ce "habibty kizo na saman mana adaidai ta, kizo mu wuce time na tafiya". Ai ko tana jin haka, ta taho, suka shiga keken, ya wuce dasu. Shi kuma yaya Faeeq, takaici ya kama shi, bai yi zaton zata samu abun hawa ba, gashi shi yaso ko in zata wuce, ta bar mai Nafisa. Kowa na ganin kaman Olamide ya ke so, but in real sense Nafisa yake so. Me shi zaiyi da yar yarbawa, su da akace suna da masifa, ga fada. Ai gashi ma ajikin Olamide, yarinya sai shegen tsiwa. Allah ya tsare shi, yaje ya aure ta, duk randa yan'borin ta suka tashi, tasa shorts, suyi fada. Gwanda ma Nafisa. Suna sauka a bakin gate, Olamide ta ciro kudi ta ba shi, sannan suka shiga ciki. Suna shiga, Allah yayi akwai wuta, sai suka kunna fanka, kowanan su ta cire hijabin ta, ta ninke, ta cire bag, suka yi hanging din shi, suka sa takalman su a mazaunin su. Sannan Olamide tayi plugging din ruwa acikin kettle. Tunda suka shigo, ba wanda ta ce ma wata kala, kowannan su nata harkan gaban sa. Ita dai Nafisa, bata son ta fadi abun da zai bata ma Olamide rai ne, ita kuma madam, sai huci take, tana regretting din zuwan su gidan su Nabila. Ita bawai ta sake masa ne ba, amma ita gaskiya ba zata bari yana zagin ta tayi shuru ba, lokacin da suke 100l, ta na dan jin kunyar sa, bata maida mai magana. Amma yanzu kam she can't take it. Mutumin da ba akan ta zagin ya tsaya ba, ya zage ta, ya zagi yaran ta, kuma abun da bai sani ba is that she is very proud of her tribe, duk da dai bata san garin su ba, amma she is still proud. Kuma ai Allah ya halice mu, yanda Ya halici baki, haka ma fari, ya halice mu in different nations, state, colours, tribes e.t.c, why not mu dauki juna as one, we are all Allah's creation. Amma wasu kam baza su iya ba. Inba racism be, toh tribalism, kuma yana everywhere. In yana ma wasu, suna barin shi, toh ita baza ta bar shi ba. Tana cikin tunani, wayar ta ya fara ringing. Data duba, taga sunan daya fito kan screen, tayi murmushi, ta daga. "Assalamu alaikum Ummi". "Waalaikumus salaam ya'a. Kun isa gida lafiya"? Hajiya Hajara ta tambaya. "Lafiya kalau Ummi". Ta amsa. "Toh Masha Allah. Ina Nafisa"? Hajiya Hajara ta tambaya. "Gata". Olamide ta fada, ta mika ma Nafisa wayar. Suka gaisa da Nafisa, kafun ta sa masu albarka, suma suka mata godiya, sannan suka kashe wayar. "Habibty danAllah kiyi hakuri ki daina fushi please". "Ba fushi nake ba. Kawai dai Ina regretting ne. Da ban san Nabila ba, da bazan hadu da tribalist dinnan ba. I hate his character wallahi. He should even thank his stars, ya girme ni, inba haka ba, daya fi haka shan maganganu a waje na, dana masa tas wallahi" Olamide ta fada. "Kiyi hakuri kawai, ki dubi relationship din mu da Nabila, ki yafe mai". "Daman ai saboda Nabila nake ragan masa, inba haka ba, dana dinga bashi amsoshin da zai kasa sa kan sa a pillow". Olamide ta fada. "Ko ni, bana jin dadin yanda yake maki". Nafisa ta fada. Suna cikin magana, kettle din ruwan da Mide tayi plugging, ya masu signal. Da sauri Mide ta kashe, ta zuba cikin bokiti, ta kara cika shi da ruwa, ta yi plugging. Ta dauki bokitin ruwan zafi, ta wuce toilet, tayi wanka, sannan ta fito. Tana fita, Nafisa ta shiga, itama. ```BAYAN SATI DAYA``` Su Olamide kawayan amarya, sai shiri suke, sun dau anko har sun kai dinki, sun raba invitation, sunata shiri, don next week Saturday kam In Sha Allahu Nabila zata zama amarya. Kuma duk zuwan da suke gidan su Nabila, Olamide bata haduwa da Faeeq, hankalin ta ya kwanta sosai, ta sake sosai a gidan, duk Familyn su Nabila da suka zo, su Olamide sun shiga masu rai, especially Olamide. Wasu macewa suke wai karya take ba bayarbiya bace, wai bata da halin su, kuma bata kama da su. Amma ai kun san ta da baki, ta ce masu wato kowani yare nada kaman sa kenan, kuma ko wani yare na da halin sa, ai ita bata taba sani ba, abun data sani shi ne, Allah ya halince mu duka. Hajiya Hajara ko sai nuna ta ma kowa take, wai yar ta ce, although ba ita ta haife ta ba, amma yar'ta ce, ita ce yayar Safina. ```WEEK DIN BIKI``` Kawayan amarya ansha lalle, itama amarya, ta sha gyare gyare, Hajiya Hajara da yan'uwan ta, sun gyara ta spiritually, physically, ta mentally, sai kyali ta ke, black skin din ta yayi kyau sosai, Nabila ta dawo kaman ba ita ba, tabi tayi kyau sosai. Yau Friday, za'ayi kamu, yan matan amarya, sun sha makeup kala kala, da wanda nata yayi fitting din ta, da wanda nata baiyi fitting din ta ba. Nafisa ma ba'a barta a back ba, makeup artist da aka dauka, ta rangada mata makeup itama, tayi kyau sosai, inba kasan ta ba, baza ka gane ta ba. Olamide kuwa anyi anyi da ita a mata makeup, taki, wai su foundations, din da za'a sa mata, zai sa zafi ya kama ta, kuma ita baza ta iya juriyan safi ba. So powder, da wani nude colour lipstick ta sa. Itama tayi kyau daidai gwargwado. Sai shiri ake za'a kamu by 4:00pm. 〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️ A matsayin sa na aminin ango, tare suke zurga zurgan biki, suje nan suje can. Gidan da za'a sa amarya ma, sanda suka ga gidan was looking it best. Abdallah ya kai makulli, lokacin da aka zo jere. In suna tare da Farouk, ya ita tsokanan sa, sai kuma ya shiga land of dreams din sa, ace shi ne ma zai yi auran, daya ji dadi, sosai. Ranan Friday da safe, suka tafi kano, da shi da ango, da sauran abokanan su. Suka sauka awani hotel, kafun lokaci yayi, su tafi venue din da za'ayi kamun. Bayan asr, suma suka fara shiri, dakin ya dauka da kamshin turaren maza kala kala. Sunyi kyau sosai, abunka da fararen maza, amma still cikin su, ba'a rasa bakaken ba, suma sun sha kyau sosai. Basu bar hotel din ba, sai 4 dot, suka kama hanya, suka je venue din event, nan suka samu, wasu kawayan sun zo, amarya da main girls din ta basu zo bako, amma within 5mins, suma suka iso. Suna isa, Nafisa ta fara fita daga cikin motan, tana wani kyali. Abdallah, ya kallie Farouk, ya ce "Guy baka fada mun amarya nada extraordinary beautiful friends haka ba. Just take a look at this one, although dai tayi makeup, kuma kasan I don't go for madeup girls". Yana cikin magan Olamide ta zura kafafun ta ahankali, ta fito. Ai anan bakin shi yayi full stop, yama kasa cewa komai, sanda Farouk yayi taping din shi sau uku, kafun ya ce " subhanallah, which of the favors of your lord would you deny". ```Thanks for reading, please kuyi maneji. ``` ~Zeexee ce~ 🖊️🖊️🖊️ [8/30, 1:21 PM] Abokiyar Fight💜💖: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 *BANBANCIN KABILA* _(Short story)_ 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 *TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION* *_🔱((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))_* *T.W.A* *WRITTEN BY ZAYNAB* _(zeexee)_ MARUBUCIYAR *-RAYUWAR HUSNA* *-MAHAKURCI MAWADACI (2020)* ```Dedicating this page, to my Moza(Xulley sparks)🤭🤭🤭 and my abokiyar fada🤭🤭💃🏽💃🏽💃🏽. I love you guys overdose🤭🤭🤭🤭.``` 1️⃣3️⃣&1️⃣4️⃣ "Which of the favors of your lord would you deny". Abdallah ya fada. "Non ya akhi". Farouq ya fada. "I can wait to see my Bila wallahi". Farouq ya kara magana. "Ni kam I have seen my qalbi, amma ya rage yanda zata zama nawa, don kasan heart dita ce, dole na samu yanda zan daidaita ta". Abdallah ya fada yana rubbing din palms din sa. "Gaskiya ne, daga ganin yarinya har ka fara maganganu"? Farouq ya tambaya. "Dole na fara, saboda Allah's creation is sooo beautiful, full of beautiful features. Just take a look at her, batayi wani makeup ba kaman sauran, amma tafi su. Kaga daa bahaushiya nake nama, amma Allah ya kawo mun bafulata a sawwake". Abdallah ya fada. "Toh Mallam ka dauke ido, only first look is halal. Gaskiya kam, kana da over assurance. Amma idan bai yuwu ba, sai mu fada ma Bila, sai ta taimaka ma rayuwar ka. Kuma to be sincerely speaking, ban taba ganin kana ma mace haka ba, but just looking at her made you this way, what if ta yarda, maybe you will loose a knot". Farouq ya fada. "Ai naga haka kaima kayi loosing din knot, kaga dole in bi sahu". Abdallah ya fada da wasa. Olamide ko, data fito daga cikin motan, ta gyara tsuwar ta, Nabila ta fito. Kai sunyi kyau sosai. Daman ankon Olamide da Nafisa, daban ne dana sauran kawayen, kuma style din su daya. Da Nabila ta fito, Olamide ta ce dan gombe bai iso bane"? "Ke baki gani ne, ga dan gombe can da wani handsome kusa da shi". Nafisa ta Fada. Su Abdallah na ganin fitowan Nabila, suka kara sa inda suke. Duk yanmatan da suka wuce, kallon su kawai suke, amma ina ango da abokin ango, anyi nisa. Nafisa na ganin suna zuwa direction din su, tace "subhanallah, Bilatu, wannan shi ne wanda kika fada mana ko"? "Ae shi ne, harkin fada a tarkon sa ne"? Nabila ta tambaya. "A'a, ya mun haske da yawa. Nikam na bayan nan, daya ke bayan angon ki directly, ya shiga mun rai, ala dashi za'ayi wuf". Nafisa ta fada tana dariya. "Ohhh Asim! Ai shima Doc ne. Yawancin abokan yaya na, Doc ne". Nabila ta fada. "Habibty, yana ga kin yi shuru ne, ba zaki tofa naki ba"? Nafisa ta tambayi Olamide. "Toh me zance, duk basu mun ba. Bana imagination akan abun da nasan da kyar ya zama gaskiya. Ai suna jin koni wata yare ce, zasu fara nuna mun tribalism, kuma kunsan bana taking shit. So in other to avoid that, gwanda na auri bayarbe ko dan Suleja, hankali na kwance". Olamide ta fada. Nafisa na son ta yi magana kenan, su Abdallah suka iso. Da suka jeru, Olamide da Abdallah suka kasance side by side, Nafisa taso ace ita da Asim suna side by side, unfortunately, yana bayan wanda ke side din ta, kaman tace masa suyi exchange da Asim. Da kowa ya samu wuri ya zauna, kawayan amarya suka zauna kusa da ita, akan stage. Ai ko Abdallah ya ita satan kallon mide, tun bata sani ba, har suka zo suna ido 4 har sau uku. Na hudu kuma, Mide ta harare shi, ta murguda mai baki, amma ko ajikin shi, instead ya ragu, sai kallon ya karu. She was feeling soo uncomfortable, sai tace ma Nafisa "Habibty, inaga zan tashi anan in koma inda jama'a suke, am feeling uncomfortable". Olamide ta fada tana daure fuska. "Kai habibty, haka bai dace ba, kinga mune manyan kawaye, ya kamata mu tsaya da ita, wallahi zata ji wani iri inta gan ki a can". Nafisa ta fada. "Ni kadai nasan abun dake damuna, amma I will be patient. But if I keep feeling this way, gaskiya zan bar wajan nan" Olamide ta fada fuska a daure. "Ae, ki bari, zan maki coverup a lokacin, but for now ki zauna please". "Shikenan" Olamide ta amsa. Bayan some mins, aka fito rawa, Olamide tayi gum kaman bata wajan. Amma Nafisa kuwa ana can Ana cashewa. Abdallah ma yaki shiga wajan rawa, ya zauna kan kujeran sa kaman wani boss, yana ta dubawa ko zai ganta cikin masu rawa, amma yaga bata wajan, sai yaga Fisa ana cashewa. "Hmm, yarinyar nan akwai busy body. Although nasan na yaba mata, amma bata da natsuwa. Amma ga qalbi na, bata shigo cikin wannan hayaniyan ba, qalbi na natsasiya ce. Da Olamide ta gaji da kallon masu rawa, ta tashi zata bar gurun, wayan ta yayi ringing, tana duba wanda ya kira, taga Hakeem. Ciki jin dadi da walwala, ta daga, sannan ta fita daga hall din, saboda kara yayi yawa. Abdallah na juya kan sa, ya gan ta zata fita, ya tashi cikin natsuwa, ya biye mata baya, nan yaji tana waya. Ya aza ko saurayin ta ne take waya da, har heartbreak ya fara kama shi, sanda yaji tana cewa zata dake shi inta dawo, shi yasan bayanda zata ce zata daki saurayin ta. Hakalin sa bai gama kwaciya ba, sai lokacin da yaji tana kiran Fa'iza da autan Mummy, sannan hankalin sa ya kwanta. Yana ta ears dropping, har ta gama waya. Yana jiran yaga ta juya ta shiga hall, sai yaga ta nemi kujera, ta zauna. "Wato qalbi bata son damuwa da hayaniya kaman ni, hmm maybe in mata magana yanzu, because banda time kuma, gobe daurin aure, kuma ana gamawa, zamu kama hanyan Gombe, gwanda kawai na fada mata yanzu". Sanda yayi addu'a ya tofa ma kan sa, dan according to him, this is a life changing matter. Da Olamide ta gama waya, ta ce bari ta zauna kafun masu rawa su gama rawan su, sai ta koma. Sai ta nemi wuri ta zauna, ta kunna data, tana WhatsApp. Tana cikin chatting din ta, taji ana mata sallama. Daya gama addu'a, ya tofa, ya kara cewa "ya Allah, kaga niyya ta akan ta, I don't mind getting married to her in the next two to three months, but Allah you know best, if she is going to be good for me, ya Allah kasa ta yarda dani, in kuma she will not be good for me, ya rab kasa karma ta saurare ni". Da bismillah, ya fara takawa har inda take, yaga duk hankalin ta na kan wayar hannun ta, sai yayi sallama. A hankali ta dago kai, ta amsa mai. Olamide na ganin shi ne mai kallon ta a hall, ta fada a zuciyar ta, tace "ai kuwa sai ka fada mun dalilin daya sa ka kure ni da ido, sai kuma na maka lectures, saboda Islamically, only first look is halal, we are meant to lower our gaze, both male an female". Tana cikin tunani, taji yace "ina iya zama akan wannan kujeran"? "Ka zauna ma, tunda dai baa kai na zaka zauna ba". Ta fada tana wani bata rai". Tana fadan haka, ta maida hankalin ta kan wayar ta. "Dan Allah ki dan bani attention din ki, magana mai mahinmanci zan miki". Abdallah ya fada. "Toh ina sauraran ka". Olamide ta fada, sanan ta kashe kawar. "MashaAllah. Gaskiya ban san daga inda zan fara ba, amma let me start from anywhere. Please try and understand me, cause have never done this before". Abdallah ya fada. "Ba damuwa ina jin ka" Olamide ta fada. "MashaAllah. Gaskiya kin burge ni, yanayin ki ya burge ni sosai. Yanda kike babbar kawan nan, da wata ce data caba fuskar ta da makeup, kuma tasa kaya anyhow, irin yanzu da ake rawa, ta zaman gaba awajan, kuma ta dunga rawan kai, amma ke kam ko ajikin ki. Wallahi tun da kika fito daga mota, nake ta observing din ki, and subhanallah, I found the feature in you, although yau na san ki, kuma yau din ma bai wuce 1hr ba, amma ji nake kaman na san ki da'a". Haka Abdallah ya ita zuba, ikon Allah, mutumin da baya wani sonyin magana dayawa da mutani, Olamide ko sai kallon shi take. "Baki ce komai ba sister. Sorry, ban mayi tambayan sunan ki ba, am very sorry for that. So please zan iya sanin sunan beautiful creation din Allah"? Abdallah ya yana murmushi. "Uhmnn Olamide". Olamide ta amsa mai. Cikin surprise, Abdallah yace "Olamide, ai wannan sunan yarbawa ne, ko akwai wannan sunan ne cikin Fulani, amma ban taba ji ba". "Toh ni nace maka ni Fulani ce? Shi yasa ma bana son yan north na mun irin wannan maganan, dan yanzu zaku fara tribalism din Ku, mtchwwww" ta ja tsaki, ta maida hankalin ta kan wayar hannun ta. "A'a sister, ni dai am not one of them, amma wallahi nayi zaton ke bafulatana ce". Cikin zafin rai, ta kashe wayar ta, tace "tunda kaji ba bafulatana bace, sai ka tashi ta koma inda ka fito, dan daman anan ka same ni". "A'a kar muyi haka da ke. Saboda ke ba fulani bace, doesn't mean zan nuna maki banbanci, although akwai *BANBANCIN KABILA* tsakanin mu, saboda hakan yasa nakara son ki miss Olamide. So can I have digit please, kinga sai mu fara zumunci". "Hmm ban san shi a kai ba". Bata gama magana ba, taji muryar Nafisa tace "ni nasani". Nan taba shi digit din Olamide, ita kuma tana ta fushi, dan still bata so bashi numbern ta ba. " So Mr Handsome, inba damuwa, zan dan rage maka jindadi, saboda Mide has to be inside likewise you". "Ba damuwa, nagode maki sosai kawar mu". "Awwwnn my pleasure mijin habibty. Amma sunana Nafisa". Nafisa ta fada tana murmushi kar kunne. Olamide na ganin yanda Nafisa keyi, tasan zata yi worst, sai ta bar wajan. Nafisa ko ko a jikin ta, saboda daman ta riga tayi promising kan ta, duk wanda yace yana son habibtyn ta, kuma ya zauna mata, toh sai ta san yanda zata yi ta hada union din. "Baka fada mun sunan ka ba"? Nafisa ta tambaya. "Soo sorry for that, ko Olami ma ban fada mata ba, sunana Abdallah Umar Muhammad Yero". "MashaAllah, wayaga Abdallah weds Fa'iza. And yes wannan sunan, Olami din daka bata, yayi dadi sosai". Nafisa ta fada. "Daman sunan ta Fa'iza "? Abdallah ya tambaya. "Ae, amma tafi amfani da sunan yoruban ta. Mu wuce ciki, kaga sai muyi hira a hanya, kafun mu shiga, kasan our presences is important". Nafisa ta fada. Suka tashi, suka kama hanyan hall din. Sai kuma ta ce "kasan Olamide nada wani tsoro, ka daina ganin ta kaman she is tough, tana da tsoron kar familyn wanda ke neman ta su zo ba suyi accepting din ta ba, azo ana mata gori, shi yasa kwata kwata bata son ace mata zata auri dan north. Amma danAllah, inka san kaima zaka nuna mata *BANBANCIN KABILA*, kar ka ci gaba da neman ta. Olamide kaman yaya take gare ni, forget the fact din we are in the same level, ta girme ni with almost a year. Toh duk abun da aka mata kaman ni akayi wa. So am begging you in kasan kai da familyn ka zaku nuna ma habibty na banbanci, karka ci gaba da neman ta". Sanda ya numfasa, ya ce "my parent may not be the problem, amma ina da wani strict uncle, shi ne ma head of the family, da shi kawai za'a iya samun matsala, dan ya kafa mana dokan sai bafulatana kawai. Amma iyaye na are ready to accept anyone, in as far as am happy with my decision". Ya fada yana murmushi. "Hmm, wallahi bana kaunan inga habibty na cikin matsala, shi uncle din naka hope bazai muzguna ma ta ba, dan wallahi ina ji labari, ina iya zuwa inmai rashin mutunci enh". Nafisa ta fada tana murguda baki. "Ai ko da kin burge ni". Abdallah ya fada, sai su biyu suka fashe da dariya, sannan ya kara cewa "danAllah kema bani digit din ki, kinga kaman ta keh zan samu kan qalbi ta". Ya fada yana murmushi. Nafisa ta kara fashewa da dariya, shi ma yayi joining din ta. Sai tace "su qalbi manja. Ai ko habibty na son sunan. Kaga bari in baka number na, kasan mun iso hall, kafun mutani su fara kallon mu". Nafisa ta fada. Nan ta ba shi numbern ta, sannan ya ce mata zai kira ta, da qalbin sa, sai suka yi sallama, suka shiga ciki, Nafisa taje side din mata, shima Abdallah yaje side din maza. A cikin hall din kuma, ashe Asim ya gan su lokacin da suka zo kusa da kofar hall din, kuma lokacin suna dariya, sai yaji haushin kan sa, saboda a ganin sa, an riga shi samun ta, amma In Sha Allahu zai san yanda zai samu kan ta. Ba'a gama ba tun 4:30 da aka fara event, sai 6:30. Da suka fita, suna shiga mota, Asim yasan yanda yayi da Nafisa, ta bashi numbern ta, ita ko bukatan ta ya biya, sai murmushi take, gaskiya auren Nabila is blessed. Shi kuma Abdallah, sai kallon Olamide yake yana jin wani irin dadi na ratsa shi. Gakiya ne Fulani/Yoruba, kawu Dajjo be ready, dan na wuce inda kake tunani. Olamide kuwa tana ta jin haushin habibtyn ta, da ko magana Nafisa ta mata, sai tayi tsaki, amma ko ajikin Nafisa, sai ma tsokanan ta data ita yi. Da Farouq ya ga yanda Adallah ke kallon Mide, sai yace "Akhi! Kamata magana ne"? Ya tambayi Abdallah. "Kana wasa da autan Umma, tuni na karba numbern ta, harda na habibtyn mu". Ya fada yana murmushi. "Kai so easily, nayi zaton zaka sha wuya ai, amma naga kaman ba hakan ba". Farouq ya fada. "Hakan ne fa, ai habibtyn mu ta bani. Ina da aiki a gaba na sosai, dan sai nayi breaking din guards din ta down". Abdallah ya fada. "Wani irin guard kuma"? Farouq ya tambaya. "Ka bari sai mun isa masaukin mu, zaka ji, for now let's wait till they leave this venue safely, muma mu wuce".Abdallah ya fada "Ni kam har na kosa mu isa ka bani gist". Farouq ya fada "Gulmanme kawai, you are not even concerned about how amaryar ka zata isa gida, gulman tawa kake son ji". Farouq ya fada. ```Thanks for reading loves``` ❤❤❤❤. ~Zeexee ce~ 🖊️🖊️🖊️ [8/30, 1:21 PM] Abokiyar Fight💜💖: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 *BANBANCIN KABILA* _(Short story)_ 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 *TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION* *_🔱((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))_* *T.W.A* *WRITTEN BY ZAYNAB* _(zeexee)_ MARUBUCIYAR *-RAYUWAR HUSNA* *-MAHAKURCI MAWADACI (2020)* ```Dedicating this chap to my one and only Bilus (Bilkisu), ina son ki, so fisabilillah. Wallahi words can't explain how much you mean to me my sis from another mum🤭🤭❤❤💘💓💗💖.``` ```Even though I know you won't be seeing these until it's turned into doc, but still I love you my Bilus❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤. May Allah make our friendship a lasting one Amin.``` Da suka isa gidan su Nabila, dan daman tun last three days su ka koma gidan su Nabila, nan suke kwana. Da suka shiga dakin Nabila, duk suka cire kanyan jikin su, su kayi sallan magrib, isha ma yayi suka yi, su kayi wanka, kowannan su tasa nightyn ta, suka fara hiran kamun, da wasu close cousins din Nabila, sai dai ba tare zasu kwana da su Nabila da Olamide ba. Duk hiran da suke, Olamide bata sa masu baki ba, it's either tayi "hmm", ko tayi faking din dariya. Duk abun da take, Nabila ke noticing. Sanda ta bari suka gama hira, cousins din ta suka bar dakin, suka koma guest room, sannan tace "Ore, yana ga kaman you are not happy ne, ko dai baki ji dadin event din bane"? Daman suna kwance ne akan gado, sai Nafisa tayi wani mika, ita kuma Mide tayi fake smile, sannan tace "naji dadin shi mana". "Ni na bata mata rai". Nafisa ta fada tana murmushi. "Haba ke ko fisa, ya zaki bata mata rai, kuma kina da bakin fada". "Am serious, ni ce na bata mata rai. Amma abun alheri na gani, kuma naga zai dace da ita, shi yasa, na tsaya mata, kaman yanda kawaye masu son cigaban juna ke yi. Kuma bazan fasa ba, sai naga nayi nasara". Nafisa ta fada. "Toh!" Nabila ta fada tana zare ido, ta kara cewa " toh meye kuma wannan abun"? "Keh kawar mu ce, baza mu boye maki komai ba. Abokin angon nan, Abdallah, yace yana son ta, kuma kin san view din ta akan mazan arewa, naje wajan ne yana tambayar numbern ta, sai tace mai bata san shi a kai ba. Although ban san abun da suka fada ba kafun in isa wajan, sai nace mai ni na sani, na bashi number". Nafisa ta fada. "Hmmmm this serious, so dan kin ba Abdallah numbern ta, shiyasa take fushi"? Nabila ta na fada ta fashe da dariya, Nafisa tayi joining din ta. A fusace Olamide ta ce "wato abun dariya ma ya baki ko? Ku kun san tsoro na, amma kuna mun haka"? Tayi maganan kaman zata yi kuka. "Kai Ore, we know, but am pretty sure Abdallah won't hurt you, have known Abdallah since the first time I and yaya Farouq started dating, kuma ni I don't think zai taba discriminating din ki, mutumin da a Ogun State yayi serving, daya dawo yake cewa idan baka je garin yarbawa ba, you won't know how nice they are, duk abubuwan da ake fada akan su is not real, yanda ake cewa basu da kamun kai, basu da rike addini, akwai masifa, ba tsafta, da dai abubuwa kala kala, yace duk karya ne. Dan da shi yaje ya gano ma kan sa, yasan dukan mu daya ne, bamu da banbanci, kuma duk abubuwan da ake cewa suna yi, yana faruwa a duka yaren duniya, basu kadai keyi ba, har yace shi ya rasa abun da yasa aka dauki tsana a arewacin Nigeria, aka azama yarbawa. Mutum da yace shi daya je, ya so yanu shi yafi su addini, suma suka bi shi, kaman basu da shi, sai sanda suka fara correcting din shi, dakan sa yaja baya. Yanzu haka ma shi da yaya Farouq na da wani aboki wanda sukayi NYSC tare, yana da addini sosai, ustaz ma ake kiran shi. Na san zaki ce mai yasa nake zuba haka, I just wanted you to know that you are in save hands, Yaya Abdallah bazai taba discriminating din ki ba. Sannan ki duba surrounding din ki, you are surrounded ba Hausa/Fulani, and bamu discriminating din ki, so why have this fear when it's comes to love"? Nabila ta fada, tana rike da kafadan ta. "Exactly habibty, why are you scared when it comes to love with an arewa guy, why"? Nafisa ta fada tana rike da dayan kafadan. Alokacin har Olamide ta fara kuka, cikin kukan tace "my fear is nothing but the fact that I will be discriminated, idan shi yana so na, what about his parent and relatives? Are they going to accept me like they will accept you guys? Ni nasan Yoruba men na auran hausa girls, kuma ana samun kwanciyan hankali, but idan yazo wajan da Yoruba girl zata aure su, alokacin discrimination kala kala ke tashi. Ni kuma wallahi azim, bana cika son problem, ku daina gani na kaman mafadaciya, masifaffiya, wallahi problems na ba ni tsoro ba kadan ba. I can't be enjoying my husbands love alone, his family's too matters". Ta karashe magana, tana kara fashewa da kuka. "Ki dai na cewa haka habibty, wallahi sai dai wanda addini bai zauna mai bane kawai, zai yi discriminating din ki saboda *BANABANCIN KABILA.* Amma midin addini ya zauna ma mutum, toh bazai yi discriminating din ki ba. Abunda Allah ma cikin alqur'anin sa mai girma, ya ce he created us in different nations, different colours, different tribes, e.t.c. So who are we to discriminate one another, we are nobody. Karfa ki manta, Bilal baki ne sosai, amma he was among the companions of the prophet, the prophet (S.A.W) and other companions, never showed any discrimination to him, he was the one who calls adan, he left Madina after the prophet's death saboda Madina will always remember him of the prophet (S.A.W), ba koran shi akayi ba. Ki duba historical books ma, zaki ga abubuwa da yawa. So if the prophet accepted Bilal, then who are we to discriminate one another, we are nobody wallahi". Nafisa ta fada tana share ma habibtyn ta hawaye. "Gaskiya kika fada Fisa, mai karancin addini ne zai yi discriminating din ki". Nabila ta fada. "I wish kowa ma zaiyi understanding, amma it's impossible". Olamide ta fada tana shashakan kuka. Suna cikin magana, wayar Olamide ya fara ringing, tace ma Nabila ta mika mata, sai ta tambaye ta waye ke kira, Nabila tace number ne. Cikin jin dadi, Nafisa tace "your fulani prince ne". "Ya kika sani"? Nabila ta tambayi Nafisa. "My instinct told me". Ta fada tana wani jujuya wuya. "Gashi miss, kafun ya tsinke. And please behave normal, no rude talks please". Nabila ta fada. "Yes please habibty, no rude talks". Nafisa ta fada palms din ta a hade. "Naji" Olamide ta fada, sannan ta daga kiran. Tana dagawa, taji very cool muryar sa, ya ce Assalamu alaikum"! Ahankali ta amsa masa da "waalaikumus salaam, dan Allah wake magana"? Sanda yayi clearing din muryar sa, yace "Ni ne Abdallah, although ban samu na fada maki suna na dazu ba, nine disturban nan na ki yau". Sai tayi murmushi, ta ce "it's good you know you are a disturber. Soooo ya akayi"? Ta tambaye shi. "Yes I know am one. Olamide! I will like to know you more, and I will also tell you about myself, let's take everything gradually, if you can please give me a chance". Ya fada pleadingly Daman ta sa wayar a speaker, sai su Nafisa suka kada mata kai, alamun tace okay. Sai tace "okay, am okay with that. So what do you want to know about me"? "Anything you are ready to tell me, am all ears". Abdallah ya fada. "Hmm okay, am Faiza Abdullahi by name, but am mostly called Olamide, dan dashi ma ake kira na a gida. Am from Niger state, Suleja local government, but my mai origin is Oyo state Ogbomoso. My origin says there, amma ba muma san hanyar wajan ba, bamu da garin daya wuci Suleja. Shekaru na 20, ina 300l a BUK, ina karanta sociology. Ni ce first born among children of 3, mahaifi na ya rasu tun ina 6 years old. Toh shikenan kaji nawa, saura naka". " First of all, Allah ya jikan magabata, yasa ya huta, yasa aljanna ce makomar sa, ya raya ku". "Amin" ta amsa, su Nabila ma suka ce "amin", amma yanda bazai san suna wajan ba, kawai sai wayar Nafisa ya fara ringing, ta na ganin strange number, tayi murmushi, ta ce "Asim". Da sauri ta daga wayar, itama ta fada anata duniyar. Nabila ta kalle ta ta jijjiga kai. Su Olamide kuwa, Abdallah ma ya fara bata tarihin kan sa. "Kinga ke first born, ni kuma auta, combo din mu fa zaiyi sugar. Ga kuma fulani/Yoruba. To be sincerely speaking, iyaye na basu da matsala, amma akwai wani kawun mu, wanda yake da matsala sosai, amma he is not a problem, because I can do anything just for my love" Abdallah ya fada yana murmushi. Farouq din da yake wajan, sai bakin shi yayi hanging. Itama Olamide, sai taji kunya ya kama ta, Nabila ko ta rufe bakin ta, tana dariya. "Uhmmmm who is that love of yours"? Olamide ta tambaye shi. "You want to know my love right"? Shi ma ya tambaye ta. "Yes I do" ta fada a kunyance, kaman yana ganin ta. "Okay since you want to know. My love, is non Other than Olami, Fa'iza". Ya fada yana murmushi, kaman tana ganin shi. "Congrats, you managed to get 4points today".Olamide ta fada. "Wow mashaAllah, am so glad I deed". "You should, because you deed what others couldn't". "Am glad for this position too. So bari in bari kiyi barci. Please dress as simple as you deed today, because you took the breath of many even without makeup, I hope I will be the lucky one". Ya fada yana murmushi. "In Sha Allah I will. If you keep this behavior on, you maybe the lucky one. Good night Auta". Ta fada a kunyance. Nabila ko sai kallon ikon Rabbi take. "This name sounds better in your mouth, it have never been better called, like the way you called it today. Gaskiya ke din na daban ce Olami. Good night, sweet dreams, don't allow the bed bugs bit, kuma kar a manta da azkar, ko da nasan za'ayi, lastly, dream about Auta". Abdallah ya fada. "Uhmmm you too, dream about Olami". Tana fadan hakan, ta kashe wayar ta. Tana kashewa, yayi gab da Nafisa ma ta kashe nata. Nabila ta yi wani irin kara, tace "wow! Wow! Wow! Wonders shall never end. A she ma pretending kike, Nafisa kinyi missing, baki ji yanda Ore keta buga soyayya ba. A she ta iya soyayya haka, ni da nayi zaton sai mun koya mata, a she ita zata koya mana". "Uhmmmm, habibty is that so, kice dai abun yayi sweet kenan". Nafisa ta fada. "Sosai fa Fisa, abun nasu ya bada masoro". "Hahhhhhhhh" Nafisa da Nabila su kayi dariya. All this while Olamide ta rufe fuskar ta, saboda kunya. Ita ma bata san zata yi haka ba, amma Abdallah is irisistable. "Madam ki bude fuskar nan ki bani labari". Nafisa ta fada. "Ai ni zan baki labari, kin san Ore ba zata fadi gaskiya ba". Nan Nabila ta bata labari dalla dalla. "Am sooo happy, finally habibty have found love". Nafisa ta fada. "Toh kema bamu labari, dawa kike waya". Olamide ta fada. "Da Asim". Nafisa ta fada. "Kut! Babe baki wasa fa, har kun fara soyewa"? Nabila ta fada tana daga mata gira. "Aww kina wasa da Nafisa Suleiman. Amma fa bani nace ya bani numbern sa ba, da kan sa yazo ya same ni, mu kayi exchanging din numbers". Nafisa ta fada tana wani harare harare. "Gaskiya ne, habibty baki wasa. Amma my advice for you, ki bi ahankali, karki yi saurin jumping, ku dauki komai stage by stage". Olamide ta fada. "Gaskiya kam, dan naga kaman sauri kike. You should know that slow and steady wins the race". Nabila ta fada. "In Sha Allah, kar ku damu". "Yanzu Bila gobe zaki barmu, gobe zaki fita a league din single, ki zama married? We are definately going to miss ya our aunty Bila, our black beauty". Nafisa ta fada, sai Olamide tace "true to that, wallahi we will miss you. Good thing din shi ne you will still be schooling with us". Haka suka ita emotional talks, har sukayi barci. 〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️ Su Abdallah Kuma, da suka isa masaukin su, Abdallah ya labarta ma Farouq komai, sai Farouq ya ce "ai wannan ake kira from frying pan to fire. From Fulani, to Hausa, and final choice Yoruba .Gaskiya kawu Dajjo na da aiki, dan sai hawan jini ya kama shi." "Ai ko harda heart attack". Abdallah ya fada, suka tafa, suna dariya. Daya gama waya, Farouq yace "aboki na kayi dace fa, ya kamata a sanar da ustaz kayi amarya yar yaren su". "Gaskiya kam, da Ismail yaji dadi sosai. Zan fada mai, amma sai bayan bikin ka". "Kawu Dajjo dai is in big trouble". Farouq ya fada, "sosai ma". Abdallah ya fada. "Kai kuma Asim, dawa kake waya ne"? Farouq tambaye shi. "Da love of my life Nafisa". "Kace kana waya da habibtyn mu Kawai". Abdallah ya fada. "Habibtyn ku kuma"? Asim ya tambaya. "Ae, ai habibtyn Olami ce". "Gaskiya ne, three friends marrying three friends. Abun na mu na bada flavor". Farouq ya fada. ```Thanks for reading.``` Comment Like & share ~Zeexee ce~ 🖊️🖊️🖊️ [8/30, 1:21 PM] Abokiyar Fight💜💖: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 *BANBANCIN KABILA* _(Short story)_ 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 *TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION* *_🔱((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))_* *T.W.A* ____________________________________ https://www.facebook.com/Tambari-writers-Association-106058867819812/ ____________________________________ *WRITTEN BY ZAYNAB* _(zeexee)_ MARUBUCIYAR *-RAYUWAR HUSNA* *-MAHAKURCI MAWADACI (2020)* ```Dedicating this page to my Sally💃🏽💃🏽💃🏽🥰🥰. Love you unlimitedly. Can't wait to come back to BH, mu yi plan din mu😉😉😉😉``` 1️⃣7️⃣&1️⃣8️⃣ "Gaskiya ne, 3-3. Amma nawa combination din yafi naku bada flavour". Abdallah ya fada dreamly. "Toh! Sannu Mallam. Kai da naka combination din zai ja ma best kawun mu heart attack, shi ne zaka wani ce kana ne best combination? Tab ai acikin dukan mu, nawa ne best nothing to complain about, kaga cousin dita ce, so ba mai mun complain". Farouq ya fada. "Dan Allah mallam park well. Naka ai family ne, ba Ku da probs, bai ma kamata ace kuna da matsala ba. Amma kunga nawa is the best. Nifa ba dangi komai, amma ba complain, kawai dai garin mu ba daya bane". Asim ya fada. "Toh dukan ku mun shuru. Nawa combination din is the best, saboda na nuna ni cikakan dan Nigeria ne mai kishin kasan sa, ku kuma kun nuna you are selfish, dukan ku yaren ku daya". Ya fada yana yatsina fuska. "Ba selfish ba, selsardine ne. Kai da zaka ja ma tsohon familyn mu ciwo, inya mutu saboda kai, toh sai mun kai ka court". Asim ya fada. "Wallahi kam, kawai haka ka sa ma best tsohon mu ciwo". Farouq ma ya fada. "Ya dade bai yi ciwon ba. Na san zasu rako amarya, at least za suyi kwana 2, kun ga in aka kai ta gobe maybe by 4 sun isa, jibi su dan tsaya da ita, kaga jibin nan, zanyi convincing din ta muje gidan fav sis adda Fadi". Ya fada dreamly. "Gaskiya ne, abun yayi kamari. Allah ya sanya alheri". Farouq ya fada. "Amin". Abdallah ya amsa. "Kun ga muyi barci fa, gobe is gonna be a big day". Farouq ya fada. "Gaskiya kam". Asim ya fada. 〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️ Da suka tashi, suka yi sallah, nan aka fara shiri, gidan su Nabila cike da mutani kala kala, da family, da abokan arziki, sun zo taya murna. Gashi first auren da za'ayi kenan a gidan su Nabila, so anyi mugun cika. Nabila ta sha kyau sosai, akayi dressing din ta cikin wani lace mai mugun tsada, ga kyau. Su Olamide ma suka sa nasu suma mai kyau, ko yau dinma Olamide taki yin makeup, ba yanda baayi da ita ba, hatta Ummin Nabila, taki wai ita bata so. Amma kuma hajja Nafisa, tasha makeup, kuma yayi fitting din ta sosai. By 10 aka sa lokacin daurin aure, a masjid din dake kusa da gidan su. Suma can, su Abdallah, da sauran manyan family din, suka shirya, by 9:30am, suka bar hotel din, suka kama hanyan anguwan su Nabila. Abun ba wuya, har an daura auren Farouq Ismail Ardo, da Nabila Muhammad Ardo bisa sadaki 100,000 naira. Ana gama daura aure, Farouq bai ma bari sun bar masjid din ba, ya kira Nabila, yace "Bila'am, Allah yayi yau kin zama tawa, kin zama matar Farouq". Yana gama fada, ya kashe wayar, anan kuma tasa wayar a speaker, su Olamide naji suka fara ihu, ita kuma Nabila ta fashe da kuka. Su kuma suna ta mata dariya, su Nafisa harda kwaso shoki. Tana cikin kuka, suka fara jin muryar maza, suna gaisuwa, ana amsawa. Da shike dukan su family ne, Farouq bai wani ji kunya ba, sai dariyan da ma yake. Sanan yana ta rarraba ido ko zai ga amaryar sa, amma bai ganta ako ina ba. Sai wata cousin din su tace "you are making it obvious brother, tana dakin ta". Ta fada yanda su biyu kawai zasu ji. "Kai! Salma, akwai ki da sa ido. Hope dai bata kuka"? Ya tambaya. "You shall see for yourself in kuka isa dakin". Salma ta fada. Da suka gama gaishe gaishe, Farouq da Asim da Abdallah, sai kuma Salma dake gaba, suna biye da ita a baya, suka je dakin Nabila. Suna isa bakin kofan dakin, Salma ta yi sallama, suka amsa, sanan ta fara shiga, tace masu ga ango da abokanan sa, su kimsa. So da suka ji haka, kowa ya kimsa jikin sa, sannan suka ce tace su shigo, sai ta leko waje inda suke tace masu bismillah, su shigo. Suka shiga da sallama, Nabila ta sauke kanta a kasa, itama Olamide ta sukar da kan ta, wai ita me kunya. Da suka ga yanda Farouq ke kallon Nabila, suma suka tashi sumie, suka bar dakin harda abokanan sa. Suna fita, Asim ya kira sunan Nafisa, ta amsa, nan suka fara hira, ita kuma Olamide, suna fita, ta rike hannu Safina, su ka bar wajan, suka tafi dakin Safina. Shi kuma Abdallah yana ta neman ta, sai Nafisa ta ce "ai ka makara, saboda habibty is faster than you think, ta bar wajan nan amma nasan bazata wuci dakin Safina ba". "Okay, ki dan kira mun ita mana, ta same ni a compound". Abdallah ya fada. "Kai baka ganin tana tare dani bane"? Asim ya tambaya. "Am sorry please, dan Allah bari ta kira mun ita please man". Abdallah ya fada yana taping din kafadan sa. "Baka da case auta". Asim ya fada. A kunyance Nafisa ta bar wajan, ta je dakin Safina, ta samu Olamide da Safina na daukan hoto. Sai taje kusa da ita, tace "kema fa kin san dole fa sai yayi magana dake, amma kika gudu ko"? Nafisa ta tambaye ta tana daga gira. "Ke ni fa bana son ana yawan hiran nan fa, bazaka san lokacin da mutum zai fita a ran ka ba". Olamide ta fada. "Toh! Aunty waye kuma wannan". Safina ta tambayi no one in particular. "Wani ne, baki san shi ba, amma zaki zo ki san shi". Nafisa ta fada, sannan ta juya hankalin ta kan Olamide tace "haba habibty, wulakanci ba kyau. Just for some minutes, kafun su koma, please now". Nafisa ta fada. "Ohoooo, wallahi bana son damuwa. Amma muje toh". Ta fada tana zumburo baki. "Kai habibty, please kar ki fita ahaka, put a little smile on your face". Nafisa ta fada tana mata puppy face. "Naji, muje" Olamide ta fada. "Nima zani". Safina ta fada. "A'a". Suka hada baki. "Dan Allah mana". "A'a". Suka kara fada, sannan suka bar dakin, suka je compound, suka gan su awajan hutawa a cikin compound. Olamide ta koma bayan Nafisa, ta buya, sai Nafisa ta juya, tace "dan Allah habibty banda yaranta. Muje please". "Kunya nake ji fa". "A'a kunyo, da kuke hira jiya kina fadan maganganu baki sani ba". Nafisa ta fada. "Toh muje". Ta fada tana wani hada rai. Da suka isa wajan, Olamide ta zauna a gaban Abdallah, itama Nafisa ta zauna agaban Asim. Nan suka fara hira. "Haba Olami, kin san fa zan maki magana, amma shi ne kika bar wajan ko"? Abdallah ya fada. "Bahaka bane". Olamide ta fada kan ta a sunkuye. "Toh meye Olamin auta". Ya fada yana murmushi. "Babu". Ta fada still kan ta a sunkuye. "Akwai aiki, indai haka zaki dinga yi". Abdallah ya fada. Ita ko tayi shuru bata fadi komai ba. "Hmm so how was your night".? Abdallah ya tambaya "Fyn alhamdulilah, yours"? Olamide ta fada. "It was fyn alhamdulilah too, but I kept dreaming about you over and over again, and even when I woke up today, you were on my mind, ana daurin auren nan, ji nake kaman na mu ake daurawa. Gaskiya a ranan namu, ban san yanda zan yi ba, dan sai kowa ya san Fa'iza ta zama mata a dakin Abdallah. I can't just stop thinking about you. Crazy right, daga haduwan mu jiya, har ace na fara irin tunanin nan, but I want you to know that ina son ki so fisabilillah, kuma baa matsayin budurwa nake son ki ba, instead ina son ki a matsayin mata ta ta sunnah, ina son ki zama uwar yaya na, I want to get old with you, I want our love to be till jannah, where there is no death, where love and happiness exist without any test, where life is everlasting. All I want is your love and trust, and also your cooperation, then everything will go well. Kuma nima In Sha Allah I will love you, trust you, and give you the care and affection you need". Abdallah ya fada. "Kai! Let's take baby steps please, you are just talking, iyayen mu ma basu san we are both in a relationship ba, ka fada ma iyayen ka, nima zan sanar wa mahaifiya ta, duk abun da suka ce, sannan we will know if to take it forward or not, because gaskiya bazan so ace na baka zuciya ta ba, at the end kuma inzo ina regretting ba, dan gaskiya my heart have been broken so many times, even without the relationship going forward, it's either a week or days, saboda bamu kai conclusion ba, amma ni kuma na riga na sa rai". Olamide ta fada. "It's okay with me, amma ina son ki sani, hakan ba zai faru ba In Sha Allah, ina son ki yarda da ni". Abdallah ya fada. "Allah yasa" Olamide ta fada tana murmushi. "Amma kuma ina son ki Sani, this life comes along with a lot of challenges, so zamu dinga samun sabani, dan zaman rayuwa zo mu zauna zo mu saba ne. Kuma ina son in haka ta faru, kar ki ce zaki bar ni, kuma nima bazan bar ki ba, instead muyi sorting out din problem din mu kin ji qalbin Abdallah". Abdallah ya fada. "Qalbi kuma, har na zama zuciyar ka? Anyways, In Sha Allah I will, kuma nima zan so ka so ni so na gaskiya, so tsakanin ka da Allah, kar kayi wasa da zuciya ta, saboda zuciya akwai rauni, ni kuma ina da saurin yarda, gashi ina fara son mutum, I love them with my whole heart, shi yasa I get heartbroken, even when the person am in love with don't know, am found of having one sided love". Olamide ta fada. "Kar ki damu, baza ayi hakan ba, saboda you are my first love, kuma have never had a one sided love like you deed, and I hate the fact that you have had that, amma ina son ki sani In Sha Allahu, I will give you the love you need, da har zaki manta da one sided loves din da kika yi. Su kuma da suka sa kika yi one side love, ina son ki san sun yi asara, saboda sunyi missing din innocent and pure love din ki". Abdallah ya fada. "Toh Allah yasa". "Amin Abdallah's qalbi". Su na cikin hira, Safina ta zo ta kira Nafisa da Olamide, wai ana kiran su aciki, sannan ta kare ma Abdallah kallo, sai ta ce "ba kai ne crush dina ba"? Ta tambaye shi. "Ni kuma"? Shima ya tambaye ta. "Ae kai". Ta amsa tana murguda baki. "A'a bani bane". Abdallah ya fada. Sai Olamide tace "Safina muje". "A'a aunty, bari na mai explaining ko zai gane". Safina ta fada. Kawai sai Olamide taja hannun ta, suka bar wajan. Ita kuma Fisa, ta dinga dariya, sanda Olamide ta harare ta, ta daina. Da suka isa dakin, har zuhur yayi, kowa yayi sallah, Nabila ta sake wanka, aka chanza mata kaya, tasa atamfa Exclusive, wanda aka dinka shi da style mai kyau, ga kayan sun zauna ajikin ta, sunyi kyau, aka sake mata makeup, alokacin kuma anfara shiri, zaa akai amarya dakin ta a garin Gombe. Sanda aka gama mata, aka kai ta wajan manyan Familyn su, suka mata nasiha one by one. Nabila ta ci kuka, bari ma lokacin da Ummin su ke mata. Haka suka rungume juna suna kuka, ita ma Safina tayi joining din su. Shi ma Faeeq, yayi hugging din ta, kaman ba zai sake ta ba. Sanda Faeeq ya ma Farouq warning, kaman ma basu da alaka, daman shi Faeeq, ba ruwan shi, duk abun da yazo bakin sa yake fada. Da zaa sa amarya a mota ma, sanda aka sha drama. Daman amarya da ango, da abokan sa guda biyu, da kawayen amarya biyu, ta jirgi zasu, sauran kuma su bi ta hanya. Nabila kam ko da suka shiga jirgi, suka zauna, taga jirgin ya tashi, ta fara new version din kuka. Tana ganin fa jirgi ya tashi, tasan bye to kano, sai dai inta dawo, bayan two weeks kuma. Olamide da Nafisa kuwa, suna can suna ta shirmen su. Suna ta ma juna dariya, wai first time din da zasu hau jirgi, iye, auran Nabila kam yayi favouring din su sosai. Sai tabe tabe suke, suna dariya kadan kadan dan kar aji su. Kafun kace me, har sun isa Gombe, suka fara sauka agidan iyayen ango. Daman wayanda zasu bi jirgi ba, sun riga sun fara tafiya, saboda su isa Kafin su Amarya. Da aka gama komai, by 4:00pm, aka kai ta gidan ta. MashaAllah gidan yayi kyau Sosai, gaskiya Farouq yayi kokari sosai. "Kai Nabila a gidan flower zaki zauna". Nafisa ta fada yanda su uku kawai zasu ji, sai suka fashe da dariya, kallo kuma ya dawo kan su, sai suka yi shuru da suka ga yanayin kallon. Cikin gidan ma shi ma mashaAllah kawai, dan gaskiya Ummi tayi ma Nabila kaya sosai ba kadan ba, ko ina yayi kyau, kayan suka yi rhyming da kalan gidan, so cikin gidan ma ya bada light sosai. Gidan three bedroom flat ne, da dan guestroom din sa a parlor. So da dare yayi, tunda familyn da suka rako ta, almost dukan su a Gombe suke, wayanda aure kuma ya kai su wani gari, suka je family house din su, nan suka kwana, yan gari kuma suka koma gidaje su. Su Olamide kuma, suka kwashi kafafuwan su sai guest room. Da suka shiga room din, sun samu shima a gyare, komai yayi dai dai, yayi kyau. Kan gado su biyu suka fada, sai Olamide tace "wallahi your bed and pillow are among those things that give you comfort, without asking for anything in return". "Gaskiya kika fada habibty. Ko wani irin gajiya ka kwaso, toh bed and pillow will make you forget, by comforting you to sleep". Nafisa ta fada. "Am telling you. Kinga duk da cewa bed and pillow are comforting, shima wanka is comforting. So bari inyi wanka, in chanza into night wear, inba haka ba, I may wakeup sick, saboda and soo exhausted". Olamide ta fada, tana mika, sannan ta tashi ta shiga toilet, tayi wanka, ta fito ta shafa mai, sannan ta sa nightyn ta. Ita ma Nafisa ta shiga wanka, ta zo ta shirya cikin nighty, basu ma wani tsaya hira ba, kowannan su tasa kai akan pillow, su kayi azkar, sai suka lula cikin duniyan barci. ```Thanks for reading, and also been patient with me for not updating when I was meant to.``` Comment Like & Share. ~Zeexee ce~ 🖊️🖊️🖊️ [8/30, 1:21 PM] Abokiyar Fight💜💖: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 *BANBANCIN KABILA* _(Short story)_ 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 *TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION* *_🔱((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))_* *T.W.A* ______________________________________ https://www.facebook.com/Tambari-writers-Association-106058867819812/ ______________________________________ *WRITTEN BY ZAYNAB* _(zeexee)_ MARUBUCIYAR *-RAYUWAR HUSNA* *-MAHAKURCI MAWADACI (2020)* ```Dedicated to precious lady and Ummu Jannan❤❤❤❤❤❤. Comment din ku na nishadar dani💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽❤❤❤❤❤❤❤, thanks so much.``` 1️⃣9️⃣&2️⃣0️⃣ Shima Abdallah, suna gama duk abun da zasu yi, ya wuce gida, tunda dare yayi. Yaso yaje gidan Adda Fadi, dan suyi magana, amma lokaci ya wuce, ga shi ma agajiye yake. Daya isa gida, suka gaisa da su Umna da Abba, Umma tace ga abinci nan a dinner, ya ce shi ya koshi. Wata zuciyar ta ba shi wai ya fada masu shi ya samu wace yake so, wani kuma yace a'a kar ya fada, wannan maganan na neman natsuwa ne, dole sai kowannan su na cikin farin ciki, kafun ya iya tunkaran su da wannan maganan, kuma ya fara fada ma Adda Fadi, tunda she is more closer to him, and she understands him better. "Tunanin me kake ne auta na"? Abba ya tamyaye shi "Bakomai abba na, na gaji ne kawai, ka san wannan harkan akwai gajiya". Ya fada yana mika. "Kai kam akwai randa ba zaka dawo kayi complain ba kuwa, gaskiya banga rannan ba, maybe nan gaba". Umma ta fada tana jijjiga kai. "Subhanallah! Abdallah ya fada yana dafa kai. "Wai ni ni kam Umma me yasa baki so na ne? Kullum sai kin yi complain, kar ki damu, na kusan barin maku gida, ko kya huta da da complain". Ya fada. "Ai kuwa dana ji dadi sosai. Amma in tambaye ka, har ka samu mata ne"? Umma ta tambaya, idon ta a kan sa. "Kai Umma what do you mean, amma dai something like that, but it's not settled yet, when it is, In Sha Allahu zaku ji". Yana fadan haka, ya dau jakar sa, ya bar parlorn da sauri, gudun kar Umma ta kira shi da marasa kunya. Yana barin wajan, Umma ta ce "ni kam me yaron nan ke nufi ne"? Ta fada tana kallon Abba. "Oho, nima ban sani masa ba. Amma baya ce zamu ji ba in komai yayi settling, so have sabr my dear wife". "Okay I will, amma idan suspicion dina ya tabbata, I will be soo happy, saboda at least wannan tsohon ba zai kara maka maganan banza ba". Ta fada tana huci. "Bari kawai, ni zan ma fiki jin dadi. Kin san jiya ma dana je gaishe shi, sanda ya tada maganan, kinga irin kallon rainin daya ke mun ne, worst part din shi ne, dana je, na samu Wasila da mijin ta da yayan ta, wai sun je mai gaisuwan jumma'a. Wasilan da rabon ta da gida, almost one month, amma dana ce me tazo yi, Baffa yace wai sun zo gaisuwan jumma'a kaman yanda suka saba zuwa. Toh shiyasa kika ga jiyan nan sun biyo ni, saboda kunya". Abba na fadan hakan, ya sake numfashi. "Nima gaskiya na rasa wace iri ce Wasila. Tunda tayi aure, ta guje mu, kiran ma da Sudais, da Bilkisu da Fadila ke mun kullum safe, ita kam sai taga dama take kira na. Ta bi ta dauki mutumin nan tamkar mahaifin ta, mu kuma ta dauke mu tamkar iyayen goyon ta. Kuma bata son taga laifin sa sam, shiyasa bana ma wani shiga shirjin ta, saboda duk abun da akayi a gaban ta, sai tsohon nan yaji. Shi yasa ma mijin ta yafi ganin mahinmancin tsohon nan, akan mu". Umma ta fada rai a bace. "Ya muka iya, tagan mu talakawa, amma ta sani, acikin wannan gidan ta girma, ci da shan ta, da sutura, duk mu muke mata, bata taba ganin tsohon nan ya bamu kobo ba. Kuma ke kika dau cikin ta tsahon wata tara, kuma kika raine ta. Amma tun da rayuwar da tayi choosing kenan, Allah ya bada sa'a. Ai ni ban ma san suna baya na ba, dan dana ga yanda aka ita share ni, nima na tashi, na fita. Ban kai su kudi bane, amma ina da mutunci, bazan bari su raina ni ba. Ina fita na shiga mota, Idi yana ganin expression dina, ya san ba lafiya, shima ya ja mota, muka bar gidan. Ashe dana fita, sun biyo ni abaya, shiyasa kika ga mun shigo tare ai". Abba ya fada. "Hmmm, wallahi da bani na haife ta ba, dana cire hannu a cikin alamarin ta, amma yana iya, sai dai in ci gaba da mata addu'a. Ada ko Wasila ta fi su hankali duka, amma yanzu kam sai hamdallah". Umma ta fada. "Kaman yanda kika fada, mu ci gaba da mata addu'a kawai". "Ya muka iya, ai dole". Da Abdallah ya bar parlorn, dakin sa ya tafi, nan ya watsa ruwa, ya fito ya sa PJ din sa, sannan ya kwanta kan gado, ya jawo wayar dake saman bedside drawer, yayi dailing din numbern Olamide, amma ya ita ringing, ba'a daga ba, ya kara kira, still ba'a daga ba. Sanda ya kira almost 7times still the same, sai ya mata sms, ya saurari reply almost 20mins, still ba reply, sai yayi concluding maybe tayi barci ne, gobe zata gani, Allah Yasa ta kira shi. Ya ajiye wayar, ya shige blanket, ya kwanta kan hannun daman shi, yayi azkar, ya shafa, aiko nanda nan barci ya dauke shi. 〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️ Cikin dare, alarm din Olamide ya fara kara, a tsorace, ta tashi, dan tama manta ta sa alarm, soboda irin gajiyan da suka yi. Tana tashi, taga alarm ne, tayi snoozing din shi, after 5mins, ya kara ringing, ta gaji sosai, amma it's time for tahajjud, haka ta tashi, jiki ba kwari, ta dauki toothbrush din ta da toothpaste. Daman indai Olamide zata je hutu, ko a ina ne, sai taje da brush, toothpaste, da soson wanka, da kuma sabulu, shi yasa ma bata ma wani damu ta tambayi Nabila komai ba. Tana daukan toothbrush din ta da toothpaste, ta shiga toilet din dake cikin guestroom, tayi business din ta, sannan tayi brush, kafun ta yi alwala, ta fito daga toilet. Data fita, taje ta side din da Nafisa ke kwance shame shame kanan wata gawa, ta fara tada ta, da kyar ta samu Nafisa ta tashi, kafun ta rike hannun ta, tayi leading din ta zuwa toilet, ta tura ta, sannan ta rufe kofar. Luckily akwai sallaya adakin, ta shinfida masu, ita ta fara sallah. Acikin toilet kuwa, Nafisa nata faman zuba ruwa a fuskar ta, ko idanuwan ta zasu budu garau, amma ina, sai kara rufewa suke. Da kyar dai ta samu tayi alwala, ta fita a toilet, ta saka hijabi, itama ta fara sallah. Suna idarwa, ko wacen su ta dauki wayar ta ta bude Islam pro app, suka karanta alqur'ani, sannan su kayi addu'a safe da maraici. Suna gamawa, da kyar ma suka iya nannade sallayan da suka yi sallah akai. Sharp sharp suka hau kan gado, suka koma barci. 〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️ Cikin dare Abdallah ya tashi, yayi sallah, lokacin fajr yayi, ya samu Abba a parlor, suka hada hanya, suka tafi masjid tare. Da suka dawo, yayi tillawa, yayi addu'an safe da maraici, sai ya kwanta, dan haryanzu gajiyan bai gama barin jikin shi ba. Yana cikin barci by 9:00am Umma ta zo ta kwankwasa kofar sa, yana ji ana kwankwasa, amma yayi zaton ko yana mafarki ne, sanda yaji tas abaya, ya tashi arazane. "Kai Umma, wai me yasa kika tsane ni ne haka? Haba Umma na, wani laifi na maki ne". Ya fada yana shafa bayan sa da ta dake shi. "Toh ai kai din ne baka ji, kasan abun, amma kullum sai na tuna maka". Ta fada tana jan kunne sa. "Oush Umma, laifin me nayi kuma yau"? Ya fada yana kokarin cire hannun ta. "Laifin rashin zuwa cin breakfast da wuri". Tana fadan haka, ta sake mai kunne, ta kara cewa "ka tashi kazo ka ci abinci, ka san fa jiya baka ci dinner ba, and that is not good for your health at all". Umma na gama magana, ta bar dakin. Tana fita, shi ma ya tashi, ya shiga toilet, ya kuskure baki, ya wanke fuskan sa da ruwa, sannan ya goge da towel, kafun ya fita, ya wuce dinning, ya samu shi suke jira, ya samu wuri ya zauna, nan suka ci abinci tare. Yana clearing din kwanonin da suka ci abinci da su, wayar sa ya fara ringing, sai ya ajiye kwanonin hannun sa da sauri, dan a tunanin shi, maybe Olamide ke kiran shi. Ya na ganin sunan Asim, yaja tsakin takaici, sai ya yi picking. "Assalamu Akaikum". Ya fada. "Waalaikumus salaam. Nace kar dai ka manta yau zamu je gidan Farouq". Asim ya fada. "A'a ban manta ba, ai baku fada time ba". "Toh su Ahmad sun ce wai by 10, sai muyi kaman 30mins or less". Asim ya fada. "Toh hakan ma yayi, sai ku biyo mun, kun san nike kusa da hanyar gidan". "Shikenan, sai mun zo. DanAllah ka shirya da wuri, banda nawa". Asim na fadan haka, ya kashe wayar. Abdallah ko yayi murmushi, ya jijjiga kai, sannan ya ci gaba da aiki, yana tunanin dalilin da ya sa Olamin sa bata kira ba, Allah yasa dai lafiya. Kuma yau In Sha Allah, in suka bar gidan ango, gidan Adda Fadi zai fara zuwa, suyi magana, kafun ya koma ya dauke ta, su koma gidan Adda Fadi. Amma still Allah yasa Qalbin Abdallah na lafiya. Duk abun da yake, hankalin sa bai kwanta ba, yanzu suna hanya ne, da shi da sauran abokanan sa zasu gidan Ango. Tunanin qalbin Abdallah yake, Allah yasa dai lafiya. Su Olamide basu tashi ba, sai 9:30am, shi din ma saboda Nafisa tazo tada su, dan misalin 8:30 cip cip, aka kawo masu abinci daga gidan su Abdallah, sannan wasu cousin din ta through Ummi, sun zo, sun dan mata arranging din wasu abubuwan, da sharan inda aka bata jiya. Data ita jiran kawayen ta, taji shuru, shine taje duba su, ta ga barci suke, sanda ta jijjiga kan ta, tace "ragwaye kawai", tana fadan haka, ta zuba masu tafin hannun ta biyu a bayan su, a zabure suka tashi, ita kuma ta fashe da dariya. "Bani ya kamata ina barcin nan ba"? Nabila ta tambaye su tana daga gira. "Dan Allah Bilatu ki kyale mu, wallahi ba zaki gane irin gajiyan da mukayi ba, gashi in muka koma gobe Monday, Tuesday zamu je school ". Nafisa ta fada tana mutsuka ido. Olamide ko sai hamma take. Nabila na jin maganan Nafisa, ta zauna akan gado, ta ce "wallahi in nace maku ban ji dadin abubuwan da kuka mun ba, toh nayi karya. Kun yi kokari sosai akai na, kuma bani da abun da zan ce maku ko inyi maku inba godiya ba, nagode maku sosai, kuma nagode ma Allah daya hada ni da ku, Allah ya bar zumunci, ya bada lada, ya bar kauna, ya hada mu a aljannah, Allah ya kai mu ranan na ku ma, nagode nagode, nagode maku sosai, wallahi bazan iya paying din ku abun da ......." Basu bari ta gama magana ba, su kayi hugging din ta. "Dan Allah godiyan ya isa haka, fisabilillah muka maki komai, so bamu bukatan godiyan ki ko habibty"? Olamide ta tambayi Nafisa. "Haka kam". Nafisa ta amsa. "Bari in bar ku kuyi waka, abokanan yaya na zuwa, kuma su Nana ma sun zo. Kuyi wanka, zan aiko Nana da abincin ku". Nabila ta fada, sai ta bar dakin. Olamide ta fara shiga wanka, Nafisa ma tazo ta shiga. Suna cikin shiri, cousin din Nabila Nana, ta shigo masu da abinci, ta fara gaishe su, kafun ta ajiye masu abincin, ta juya. Suna gama shiri, suka fara cikin breakfast, alokacin ma har 10 yayi. All this while, Olamide bata ma duba wayar ta ba, ita dai lokacin data bude wayar da asuba dan tayi amfani da Islam pro, taga notification din missed calls, da message, amma bata duba ba. Sun gama cikin abinci kenan, suka fito rike da plates a hanu, suka samu Farouq da Nabila a parlor, da su Nana, Mufida, da Humaira, duk suna zaune, nan suka gaida Farouq, Nana da Humaira kuma suka karbi plates din a hannaye su. Ana karban plates a hannun su, Olamide ta juya, ta koma guestroom, ita kuma Nafisa, ta samu wuri, zata zauna kenan, taji muryar gardawa har 5 sunyi sallama, ta daga kai, suka hada ido da Asim, ai bata san lokacin data maida kan ta kasa ba. Su kuma suna shiga, su Nana suka gaishe su, su ka bar parlorn, suka koma guestroom. Nafisa tama rasa daga inda zata fara, sai ta bone Kawai, ta gaishe su, ta bar parlorn ita ma, ta wuce dakin da su Olamide suke, tana maida numfashi. Olamide ta kare mata kallo, sannan tace "lafiya?" "Ba lafiya, yanzu su Asim suka shigo". "Toh sai suka cije ki ko me?" Olamide ta tambaya. "Ba zaki gane ba, I felt uncomfortable, I can't wait for tomorrow morning, mu koma Kano". Ta na fadan haka, itama ta zauna akan gado. "Gaskiya me too, am feeling uncomfortable". Olamide ta fada. Nan suka fara hira, su Nana nata sa su dariya. Suna cikin hira notification ya shigo mata na new massage. Ta duba, sai taga Abdallah ne, alokacin ma taga ashe shi ya kira ta, kuma ya riga ya mata message da'a. Sai ta karanta na jiyan, sannan ta karanta na yau. "Haba qalbi, har kin gaji dani ne? I know I can be a pest, at least reply, in san kina lafiya. Nasan kin san muna gidan nan, amma yanzu zamu wuce, kuma muna fita In Sha Allah, zan je gidan Adda Fadila, to tell her about our relationship like you requested. Although na san kin ce parents, amma I think I should tell her first, sai in kai ki kuga juna, amma ki fada ma habibty ma ta shirya, saboda tare zamu, kin san ba kyau ace opposite sex na tare without someone been with them, because shaidan is the third party there, kuma ba abun da bazai iya samu yi ba. I hope you will understand, waiting for Abdallah's qalbi reply." Sai tayi murmushi, a cikin zuciyar ta tace "mashaAllah, I love his manners." Sai tamai reply, tace "Okay, we will be ready, and I will only inform my Mum about this relationship when I see your sisters reaction, and it will have to wait sai na koma school." Tana tura massage din, ta kara murmushi. "Murmushin me kike ne madam"? Nafisa ta tambaye ta. "Mele. Ki shirya, zaki raka ni wani wuri, amma ba yanzu ba, sai ya kira ni". Olamide ta fada. "Baza ni inda ban sani ba, so gwanda ki fada mun". "Ko mu bar maku dakin ne"? Nana ta fada tana murmushi. Daman ita ce babban cikin su, bazata wuce 14yrs ba. "A'a no need"Olamide ta fada tana hararan Nafisa. "Aww ba zaki fada ba kenan, wato baki yi trusting dina ba kenan". Nafisa ta fad rai abace. "A'a ba haka bane, I trust you sosai wallahi. Kuma fa hmmm hmmm." Olamide ta fada tana sosa kai, sai ta ce "ai dai kin gane shi, ya ce wai zamu je gidan addan sa". "Ni dai ban san hmmmm ba. Wace aciki?" Ta tambayi Olamide. "Wai adda Fadila". "Toh Allah ya kai mu". Nafisa ta fada. "Amin". Olamide ta amsa, sai Nabila ta bude kofan, tace "sun wuce, shima yaya ya fita. Kan nan sa zasu kawo mana lunch bada dadewa ba. "Okay toh". Olamide da Nafisa suka amsa tare. Sanda suka bari ta zauna, Olamide ta ce "Ammm Ore, anjima zamu fita." "Ina kuka sani a gari Gombe da zaku"? Nabila ta fada tana zare ido. "Hmm, hmmmm, wai zamu je gaida Adda Fadila." Olamide ta fada. "Toh! Sunan Abdallah kika kasa fada?" "Toh ai shi ne, nima hmmmm ta fada mun." "Toh Allah ya kwata. Allah ya kuma kai mu anjima." "Amin suka amsa." Suna cikin hira, text ya shigo Mata (Olamide) daga Abdallah, yayi replying. "Ba damuwa qalbin Abdallah, sai yanzu na isa gidan ta, In Sha Allah, everything will be alright, ki jira sai na zo". Olamide na karanta Sms din, ta yi numfashi, acikin zuciyar ta tace "Allah yasa relationship din nan ya zo to past, saboda irin abubuwan nan da mutum zai ce sai yayi shawara da wani da dai sauran su, ke sa take loosing din masoyan ta, yanzu dai addu'an ta shi ne Adda Fadila kar ta nun banbanci tsatanin su, gashi ita ce best din sa, kar tazo tayi convincing din shi yazo ya dai na son ta." Hmmm, taja numfashi, sai ta kwanta, tama manta su Nabila na daki, tayi lamo kaman marasa lafiya. Allah yasa dai komai yayi dai dai, kar Allah yasa dai karshen maganan ta kenan da shi, dan gaskiya ta fara son shi. Shi kuma Abdallah, daya isa bakin gate din gidan Adda Fadi, yayi horn, bata bude gate ba, sai ya fita, yayi knocking, yaji muryan mijin ta, wai yana zuwa. Daya bude mai karamin kofar suka gaisa, sannan Abdallah ya shigo, ya bude babban gate, ya shigo da motan shi, daya gyara parking, sai ya rufe gate, sannan suka kara gaisawa da kyau, kafun suka shiga ciki tare. Da suka shiga, adda Fadi ta kawo masa juice, suka gaisa, yayi tambayan yara, suka fada mai suna gidan kakan su. Sanda suka yi hira kadan, mijin ta, ya basu guri, ya koma daki, su kuma suka cigaba. Sanda suka kara taba hira, yace abu ya kawo ni fa fav, kuma the part am taking is very risky, but I have to do it, and it has gotten my heart now, your support is all I need, I hope zaki yi supporting dina." Ya fada idon sa akan ta. "I will In Sha Allah, say what's on your mind, am all ears my lil bro". ```Thanks for reading and been patient with me. As usual, sharhin ku nake bukata. ``` Just a little reminder, dan Allah mu dage da ibada cikin wayan nan kwanaki goman, kar muyi devoting din precious time din mu akan social media, mu dage da ibada please, Allah (SWA) swore with this ten days, and good deeds are more precious during this days, it is said that charity in this ten days, are better than the last ten days of ramadan, so please let's not endeavour to miss the blessings of this days. ⬇️⬇️⬇️ قال الشيخ العلامة محمد صالح العثيمين رحمه الله:  والعمل الصالح متنوع: قرآن، ذكر، تسبيح، تحميد، تكبير، أمر بالمعروف، نهي عن منكر، صلاة، صدقات، بر بالوالدين، صلة للأرحام، والأعمال الصالحة لا تحصى، إذا تصدقت بدرهم في هذه العشر وتصدقت بدرهم في عشر رمضان فأيهما أحب إلى الله ؟ الصدقــة في عشر ذي الحجة أحب إلى الله من الصدقة في عشر رمضان [اللقاء الشهري (10/2)] Shaykh, al-Allāmah, Muhammad Sālih al-‘Uthaymeen [may Allāh have mercy on him] said: “Righteous actions are of various types: the recitation of the _Qur’ān_, _dhikr_ [the remembrance of Allāh], _tasbeeh_ [uttering Subhān Allāh]; _tahmeed_ [uttering Alhamdulillāh]. [ _tahleel_ [uttering Lā ilāha illAllāh]]; _takbeer_ [uttering Allāhu Akbar]. Enjoining the good and forbidding the evil; the prayer; spending in charity; being obedient/dutiful to one’s parents and upholding the ties of kinship, therefore righteous actions are immeasurable [in reward]. If you donated a _Dirham_ in charity during these [blessed] ten days [of _Dhul-Hijjāh_] and you donated a _Dirham_ in charity in the ten days of [the blessed month of] _Ramadān_, then which of them is more beloved to Allāh? Charity in the [blessed] ten days of _Dhul-Hijjah_ is more beloved to Allāh than charity in the ten days of [the blessed month of] _Ramadān_.” Al-Liqā’a ash-Shahri, 2/10 | Volume 2, Page 10 | Shaykh Muhammad Sālih al-‘Uthaymeen [may Allāh have mercy on him] Translation: Authentic Quotes COPIED🔝🔝 Comment Like & Share. ~Zeexee ce~ 🖊️🖊️🖊️ [8/30, 1:21 PM] Abokiyar Fight💜💖: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 *BANBANCIN KABILA* _(Short story)_ 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 *TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION* *_🔱((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))_* *T.W.A* *WRITTEN BY ZAYNAB* _(zeexee)_ MARUBUCIYAR *-RAYUWAR HUSNA* *-MAHAKURCI MAWADACI (2020)* ```Dedicating this page to all those silent and secret readers😏😏, I hope you guys will start commenting and stop doing labe.🤭🤭🤭🤭``` 2️⃣1️⃣&2️⃣2️⃣ "Hmm da mu ka je Kano, acikin kawayen amarya" sai ya sosa kai, yana kallon ta yana murmushi. Tace "ka ci gaba, am listening". Ita ma ta fada tana murmushi. "Toh ki daina kallo na haka mana". Ya fada yana kara kauda ido. "Toh ya kake son in kalle ka, ni dai just tell me the good news please lil bro, basai munyi arguing ba". "Toh naji. Daman acikin kawayen amarya, kema dai kin san bazan yi zabin da ba zai amfane ni ba, kuma bazan zaba anyhow person ba. Nasan akwai dan banbanci tsakanin mu, amma buri na daya, shi ne kuyi accepting din ta." Ya fada pleadingly. "Toh ai baka fada mun ko ita din wacece ba, bale in san yanda zan yi reacting. Kuma I trust your choice, na san ba zaka yi zabin banza ba, and I promise to support you, just tell me". Ita ma ta fada pleadingly. "Okay, thanks for trusting me. Actually tana cikin manyan kawaye, kuma presently yanzu tana Gombe. Yarinya ce mai hankali wallahi, bata da wani abun da zaka tsana a jikin ta, although ran Friday nan na san ta, amma ta gama mamaye zuciya na. Ita ce ma tayi suggesting wai in fada a gida, duk abun da aka ce, sai mu sani in zamu ci gaba ne, ko kuma akasin haka. Amma wallahi I don't wanna loose her to another man, saboda duk namijin da ya same ta a mata, ba karamin nasara yayi ba, wallahi she is whom every man dream of, she is the dream of every man to become his wife and a mother to his children, amma matsalan shi ne akwai *BANBANCIN KABILA* a tsakanin mu, kuma when I mean banbanci, I mean a very big one. Although girman arewa ne, kuma according to what she told me, bata ma san hanyar garin su ba, saboda ko iyayen su basu sani ba". Sai yayi numfashi. All this while, Adda fadi kallon sa take. Ita dai a rayuwar nan, bata taba gani ko ji kanin ta ya yabi wata ya mace ba, sai dai yayi shuru ko ana maganan mata, amma wai shi ne yau yake yaban wata haka, that means she most be soooo sweet, ya zama dole tayi supporting din shi. Amma wani banbanci ne haka a tsakanin su? Ta tambaye kan ta. "Yana ji kayi shuru, wani banbanci ke tsakanin mu ne haka, ai su Abba sun ce zasu auran maka ko waye, indai ta zauna maka, kuma kana da assurance a kanta". "Ae indai assurance ne, ina dashi, yaran mu ne matsala, amma in ku family dina zaku yi supporting dina, toh bani da case". "In Sha Allahu zamu yi, ai you too have always supported us". Adda Fadi ta fada. "Toh nagode. Bayarbiya ce, amma tana da zubin fulani, inba ta fada maki bane, ba zaki taba sani ba". Ya fada, expression din shi na nuna damuwa. "Bayarbiya! Bayarbiya fa kace?" Ta fada tana zare manyan idanun ta. "Ae, amma ai banga wani aibu aciki ba, wallahi tana da hankali. Kuma ai Allah ya halice mu, we are all one in the eyes of the creator. Wallahi you will love her, support din ki kawai nake bukata, in kika yarda, zan kawo maki ita har gida yau, saboda gobe da sassafe zasu koma kano. Kuma ma ba akano take ba, a Suleja take. Karatu ya kai ta Kano kuma acan Sulejan ma, sanannu ne". "Hmm naji, Allah ne ya halice mu duka, kuma ba wanyanda suka fi kusan ta dashi inba mumine ba, so am ready to accept am sister in law In Sha Allah. Amma kawu fa? Kasan yanda mutumin nan yake, yanzu zai sa iyayen mu agaba". "Ki kyale ni dashi, shi din ba matsala bane, ai ya saba yi ana barin shi, this time around zanyi breaking din rules, kuma inyi maganin shi akan iyayen mu". Ya fada yana murmushi. "Toh mashaAllah, kana da hoton ta ingani"? "Ae, I snapped her without her knowing". Yana fadan haka, ya ciro wayar sa, ya shiga gallery, a camera, ya samo pics din, ya mika mata. Tana gani tace "wow mashaAllah, attention din ta ma was not on you, amma kalli yanda tayi kyau, gaskiya beauty ce. Kuma nima da baka ce mun bayarbiya bace, dana ce yar fullo ce. Gaskiya yarbawa ma nada kyawawa, kaman yanda ko wani yare ke da kyawawa, da kuma mashaAllah, kasan no one is ugly, everybody is beautiful in there own way, and beauty is in the eyes of the creator. I will like to meet her. Amma ba lokacin biki ne nan ba"? Ta tambaye shi. "Ae, jiya ne ma, da aka gama daurin aure, me kika gani?" "Naga bata yi heavy makeup bane, she looks simple but beautiful". Adda Fadi ta fada tana shafa screen din wayar. "Am telling you, she doesn't like heavy makeup. Toh a bani waya na kar acinye mun wifey". Ya fada yana kwace wayar sa. "A'a spicy ne, ai nima sister in law di ta ce. Kuma ni bazan yi irin naka ba, inta zo, zamu dauki hoto tare". Ta fada tana hura mai hanci. "Oho dai, she is will be mine In Sha Allah". Suna cikin magana, Mijin Adda Fadila ya fito, lokacin sallah zai tafi masjid, sai suka tara hanya da Abdallah, yayi da Adda Fadi, bayan sallah, zai je ya dauko ta, ita kuma tace ya bari sai bayan Asr, alokacin yaran ta sun dawo, kuma ta girka mata abu, gashi yace ba ita kadai zata zo ba, yace mata toh, amma daga masjid, ba zai dawo ba, sai ya kawo Olamide. A hanyan masjid, Abdallah ya fada ma mijin Adda Fadi komai, ya taya shi murna, bai ba nuna wani shock ba, da Abdallah ya ce mai bai nuna damuwa ba, da shi yace mai bayarbiya ce, sai yace mai, ai Allah ya halice mu duka, kuma daya halice mu, bai ce wannan yaren sun fi wannan yaren ba, ai yarbawan ma mutani ne, in saboda kawu Dajjo ne, kar yaji komai, dan duk abun da Allah yace "Be, it shall be." Abdallah ya ji dadin maganan sosai, sai godiya ya ke, har suka isa masjid. Suna fita daga masjid, suka koma gida tare, Abdallah bai shiga ciki ba, ya bude gate, ya fita da moton sa, sukayi sallama, yace sai ya zo da yanma, shi kuma yace Allah ya kaimu, Amin ya amsa, ya ja motar sa, ya bar gidan. Gida ya wuce direct, ya gaida Umma da Abba, sannan ya koma dakin sa, ya cire kayan daya sa, yasa jallabiya, ya hau kan gado, ya fara barci, da niyyan zai kira Olamide inya tashi, dan daman still a gaijiye yake. 〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️ Yanda Olamide tayi shuru data gama karanta msg, duka su Nabila ke noticing, sai Nabila ta taba ta, tace "Lafiya kuwa? Daga karanta msg kuma sai ki kwanta kaman marasa lafiya, ko rasuwa akayi ne?" "A'a ko daya, na gaji ne kawai, kin san stress." Ta fada tana mika. "Wani irin stress kenan daga karanta msg?" Nafisa ta tambaya. "Normal stress mana, wallahi habibty, you can ask silly questions." "Bawani silly, gaskiya ta fada. Koma me ke damun ki, ki fada mana, we are all friends, ain't we?" Nabila ta tambaya. "We are. Am just scarred, what if addan sa tayi poising din shi akai na, what if ya daina sona idan tayi poising din zuciyar shi." Ta fada, idon ta ya cika da ruwa. Sai suka yi hugging din ta. "I don't think Abdallah will do that, he loves you more than you think, just be positive and stop been negative". Nabila ta fada. "Like she just said, stop been negative, and be positive, hope for the best". Sai suka sake ta. Ta daga kai ta kalle su, tace "what will I do without you guys, you guys have be come a part of me wallah, Allah ya bar mu tare. In Sha Allah I will think positive. Suna Nana ko sai kallon ikon Allah suke. Ana cikin haka, aka kira zuhur, suka tashi suka yi sallah, suna idarwa, suka ji muryan wasu suna sallama. Daman da aka kira Sallah, Nabila ta koma dakin ta. So tana jin sallama, ta fito, taga kannan Farouq su biyu ne, daman sun saba, sai sukayi hugging din ta. "Ku zauna, ina ta expecting din Ku tin dazu, me ya hana ku zuwa?" "Aunty ki bar shirmanmiyan nan Hafiza, kin san ta ai, inba'a ci kwalliya ba, ba'a fita, shi yasa muka dade, hakan ma Umma ta koro mu". Kanwar sa mai suna Nusaiba ta fada. "Nikam Allah ya yaye maki wannan cutar, dan in kika yi aure, kuma zaku fita da mijin ki, sai dai ya bar ki a gida". Nabila ta fada. "Uhhmmmmm uhmmmmm, su aunty anyi aure, har ansan logic." Hafiza ta fada. "Toh kar insan logic ne, Mtchww. Yauwa kawaye na guestroom, muje ku gaishe su. Suka gaisa da su Olamide, aka kawo ma su abinci, suka ci, amma still hankalin Mide bai gama kwantawa ba, amma ta kasa nuna ma kawayen ta. Shi daya bar gidan Nabila by 11:30, ace har almost 2:00 pm, bai kira ta ba, hanya kuwa? Hawaye taji ya jiko idanun ta, sai ta tashi ta shiga toilet kaman zata yi fitsari, ta fara kuka, a hankali, yanda baza su ji ba. Bata kai 5mins ba, aka kwankwasa kofar toilet, Nusaiba kanwar Farouq, tace "Adda wayan ki na ringing". Olamide najin haka, ta fito da sauri, ta karbi wayar, tana ganin wanda ya kira ta, ta yi wani irin murmushi, sanda tayi hamdallah, kafun ta daga wayar. "Assalamu alaikum! Ta fada zuciyar ta na bugawa, although taji dadi ya kira ta, amma bata san sakamako ba. "Waalaikumus salaam qalbin Abdallah." Olamide taji wani irin dadi a zuciyar ta, sai ta amsa mai da "na'am ifemi". Tama manta da akwai mutani a dakin. Suko sai kallon ikon Allah suke. Abdallah ko data kira shi da sunan, sai yaji wani irin dadi na ratsa shi. "Qalbin Abdallah guess what?" "Ifemi I am not good at guessing, just tell me". "Toh shikenan, bazan so inga zuciya na a wahale ba, so, adda Fadi is ready to receive her in law to be In Sha Allah, tace muzo bayan Asr". "MashaAllah, naji dadi sosai, I thought bazata yarda ba, I thought this will be the last time da zamuyi magana, but mashaAllah she accepted me the way I am". "Alhamdulilah, she is sooo ready to accept you, ko mijin ta ma yana expecting din zuwan ku. So ku shirya keda habibty, by 4 dot zan zo". "Toh shikenan, sai kazo". "Please takecare of my heart, dan bana son inga zuciya na a wahale. Take care of Abdallah's qalbi". "Okay, you should also take care of mine". Tana fadan haka, ta kashe wayar, sai a lokacin tayi realizing ma akwai mutani a dakin, wani kunya ya kamata, zata koma toilet, Nafisa ta jawo ta. "Dawo nan marasa kunya. Wato ifemi, daman nasan pretending kike, akwai kalamun soyayya sosai abakin ki, sai ki dinga cewa zamu koya maki in lokaci yayi, ai yanzu kam sai dai ki koya mana." Nafisa ta fada tana hararan ta. "Haba habibty, kya dan tsake ni ai, kin wani rike ni kaman kin kama barauniya, dan Allah tsake ni. Kuma ni bana pretending. Then duk abunda nake yi, awajan ku na koya, especially Nabila". "A'a kar kiyi karya da ni, mu dai sai mun zo lectures ko Fisa?" "Gaskiya kam". Suna na kan teasing din ta, suka ji muryan Farouq ya dawo, da sauri Olamide ta riko hannun Nabila, ta kai ta bakin kofan daki, ta tura ta waje, sai tace "je kiji da mijin ki." Ta fada tana mata gwalo. Kannan Farouq ma suka fita gaida Farouq. Tayi facing din Nafisa, ta ce "kin san Nabila ce power din ki kuma bata nan, toh ki shiga brain din ki. And yes wai mu shirya by 4 dot zai zo ya kaimu." "Toh mummy Olamide, amun afuwa, kar a cinye ni. Kuma in kika sa wasa, bazan je ba". "Haba habibtyn Mide, am sorry my sweet miyan kuka". "Baki ma ga abunda zaki kira ni ba sai miyan kuka, ba damuwa". Nafisa ta fada tana faking hurt. Daman kan gado suke, sai Olamide ta riko hannun ta, ta ce "haba habibtyn Mide, ban san ki da fushi ba, ki yafe ma troublesome habibtyn ki." "Naki, sai an bani cin nose." "Kaman me?" "Kaman shawarma". Nafisa ta amsa. "Amma fa sai mun koma school In Sha Allah". "Naji bakomai". Nafisa ta fada tana murmushi. "Amma in na mutu ki yafe mun." "Ai dole na, Allah yasa mu cika da imani, ya jikan magabata." "Amin". Around 4dot Abdallah ya shigo gidan Farouq, ya fara parking, daman Farouq ya san da zuwan shi, sai ya shiga ciki suka gaisa, kafun ya mata text wai gashi nan ya zo. Sanda suka shafa almost minti 10, kafun suka fito. Suka sallame cousin din Nabila, da kannan Farouq, saboda maybe kafun su dawo sun wuce, kuma ma daga yau ai shikenan, sannan suka ma Nabila da mijin ta sai sun dawo. Da suka fita, Abdallah ya ce su tsaya a inda suke, bari ya kawo motan nan. Suka jira shi, ya kawo motan inda suke, ya bude ma Olamide gaba, akunyace ta shiga, ita kuma Nafisa ta bude bayan da kanta, ta shiga. Sanda suka daidaita zama, sannan yaje gate yana horn, gateman din gidan ya bude gate, suka fita sai gidan Adda Fadi. Su Olamide sai kale kale suke, shi kuma duk exciting place din da suka wuce, sai ya fada masu sunan, ya kasa boye murnan sa. Nafisa kawai ke magana, ba yanda bai yi da Olamide ta sake ba, amma taki. Ita kuma a bangaren ta, kunya take ji, shi ya hana ta sakewa. Daya ga yayi yayi bata sake ba, sai yayi tunanin abun da zai fada, yasa tayi magana, wani idea ya zo mai, yace " kin ga garin ifen ki, kuma where you will be staying very soon In Sha Allah". Tayi murmushi, tace "Allah yasa." Saboda maganan tashi ma kunya ya bata. Daya ga kaman baza yi magana ba, yayi shuru, domin ya gane kunya take ji. Haka ya suka yi shuru, har suka isa gidan. The only time din data yi magana, shi ne da suka wuce wani shago, ta ce ya tsaya, dan daman sunyi da Nafisa, zata siyan ma yaran Adda Fadi abu. Daya tambaye su me suke so ya siya masu, tace bakomai, sai yace bakomai ne kuma tace ya tsaya, sanda taga da gaske yake ta fada mai, yace su zauna zai siya, tace mai a'a, ita zata siya, because it's a gift from her, and zata so ta siya da kanta. Sanda yaga ta dage, shine ya kyale ta, amma yace mata Afra ta fi son chocolate, shi kuma Irfan ya fi son sweets, but suna son biscuit, but those are there best. Da suka isa, instead yayi horn, ya mata flashing, ta fito, ta bude karamin kofar, ya shiga ta wajan, ya bude gate, ya shigo da motar sa ciki, ya gyara parking, sannan ya fita, Nafisa ta fita, sanda Olamide tayi addu'a, ta fito. Tana fita ita da Nafisa suka taka har inda Adda Fadi take, suka gaishe ta, ita kuma tun fitowan su, take ta kallon su, shi kuma Abdallah ya je rufe gate. Da Olamide taga sun gaishe ta bata amsa ba, ta kara gaishe ta, dan alokacin har tayi give up, sai taji tace "common, you guys shouldn't just stand there, give me hug." Adda Fadi ta fada hannun ta a bude. A kunyace sukayi hugging din ta. Ta riko hannaye su, tace su shiga ciki, su Afra da Abban su na can. Suka shiga, Abdallah na biye da su, kuma ya ji dadin yanda Adda Fadi ta tarbe su. ```Thanks for reading, and always been patient, zeexee loves you guys.``` Comment Like & Share. Zeexee ce 🖊️🖊️🖊️🖊️ [8/30, 1:21 PM] Abokiyar Fight💜💖: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 *BANBANCIN KABILA* _(Short story)_ 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 *TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION* *_🔱((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))_* *T.W.A* *WRITTEN BY ZAYNAB* _(zeexee)_ MARUBUCIYAR *-RAYUWAR HUSNA* *-MAHAKURCI MAWADACI (2020)* *SAKON TA'AZIYA ZUWA GA PHATEEMA LAWAL* Ina me miki ta'aziyan rasuwar kakan ki, Allah Ya ji kan ta, Ya mata rahama, Ya gafarata mata zunuban ta, Ya haskaka kabarin ta, Yasa aljannah ce makomar ta. Sorry for the lose sister, Allah ya baku hakurin rashin ta, Amin. ```Dedicating this chap to those who post my book. Thank you soooo much, I can't thank you guys less, I really appreciate your efforts.``` 2️⃣5️⃣&2️⃣6️⃣ Da suka isa gidan Nabila, Abdallah yayi horn, aka bude mai, ya shiga. Da za su fita acikin motan, Abdallah yace "kinga lokacin sallah ya kusa, da mun dan yi hira. I can't wait for you to be mine, then I won't need any permission to be with you. Dan Allah kaman yanda kika yi alkawari, in Kika koma school, dan Allah ki ma mummy magana, nima zan ma su Abba magana. Kin san annabi Muhammad (SAW) yace; shi bai ga abun daya fi dacewa da mutani biyu dake son juna ba, inba aure ba. So why should we take long on a mere relationship, mu fahimci juna, even if it's for 2 to three months, if we are okay with each other, we should take it further, amma idan vice versa ne, kai Allah ma ya kiyaye, In Sha Allahu zamu fahimci juna. Amma still ya na da kyau iyayen mu su san muna cikin relationship. Am going to miss you so very much, sai na kara zuwa kano In Sha Allah." "Kar ka damu, zan fada mata. Addu'an shi ne iyayen mu su yarda, ni dai na san side dina ba problem, domin a familyn mu, zaka iya auren kowaye, in as far as yana da addini, kuma yana amfani da shi, sannan in suka yi bincike akan shi da familyn shi, kuma ya zauna masu, toh they are good to go. Gaskiya ne maganan ka, ko ni ma bana son long relationship. Nima zanyi missing din ifemi (my love), amma I will wait for the right time. Kazo fa, inba haka ba, inyi fushi." Ta fada tana rufe fuskar ta wai ita mai kunya. "Toh shikenan Olamin Abdallah, aka qalbin Abdallah, In Sha Allah, baza'a samu matsala ba ta side din su Abba ma. Karki damu, in iyayen mu suka yarda, maybe wannan hutun naku, akai goron tambaye. And In Sha Allah I will come." Wani irin kunya ya kama ta, a kunyace, tace "toh, Allah ya tabbatar mana da mafi alheri. Kaga ana kiran sallah, bye". "Okay bye, take a very good care of my heart please". "In Sha Allah." "Toh habibty, nagode da kika bamu time din ki, Allah ya sauke ku lafiya, ya bar ki da Asim." "Sai yanzu kuka san dani kenan. Amin, nida yaya Asim dina." "A'a habibty, ai muna sane da ke. Amin, Allah ya bar ku tare." "Amin. Toh bye". Nafisa ta fada, sannan suka fito daga cikin motan, Olamide nata waving din shi, har ya fita. Da sallama suka shiga, suka samu Nabila da kannan Farouq a parlor. Nafisa taje tama Nabila side hug, amma sai taga tayi shuru, bata yi reciprocating, su kuma kannan Farouq suka fara dariya, abun ya ba Nafisa haushi, sai tace "meye haka dan Allah?" Alokacin Nabila ta dago kai ta kalle su one by one, ita da Olamide, sai tace "ai da kun kwana ne kawai." "Ban gane damu kwana ba?" Wannan time din, Olamide tayi magana. Suko kannan Farouq, kokarin danne dariya suke, amma yaki dannuwa. "Ae mana, da kun kwana. Ku da kuka san gobe zaku wuce, amma kuka dade haka, kuma fa kun san duk da cewa zan dawo in the next two weeks, am still going to miss you. Saboda ku ne fa naji bana missing din gida, amma nasan daga gobe kam shikenan, komai zai dawo square one, gobe zan san ae na bar gida, instead ku dawo da wuri ku kwantar mun da hankali, amma sai yanzu kuka dawo." Ta fada tana hawaye. Olamide da Nafisa suka kalli juna, kawai Nafisa ta fashe da dariya, ita kuma Olamide taje kusa da Nabila tayi hugging din ta, tace "haba my black queen, ki daina kuka please, bada gangan muka ki dawowa da wuri ba. Naso mu dawo tun 6pm, amma Adda Fadila ta ita jan mu da hira, kuma wallahi we thought about this, tambayi Fisa. I know you are going to miss us, and we too will, na san yau din nan, we are meant to be with you, make you forget your worries, but man propose, God dispose, wani sain ba yanda kayi plan abun ke zuwa ba, so ina me baki hakuri, nice sillan haka, so am sorry. Amma if you can stay with us har 10:pm yau, we will pet you, till you get tired ko habibty?" "Ae mama Olamide. Amma kin san har na fara jin haushin maganan ki, I was even ready to answer you back, ashe shagwaba kika, iye, su bila an iya tada hankalin mutum." Nafisa ta fada tana daga ma Nabila gira, Nabila bata san lokacin data fara murmushi ba, yanda tayi murmushin, ya basu dariya, sai suka fashe da dariya, daman kannan Farouq na danna nasu, kawai sai suka yi bursting at the same time. Sanda suka yi ma ishi, kafun Olamide tace "bari muje muyi sallah ko uwar shagwaba." "Ai kuwa, dan in muka biye maki, baza muyi ba." Nafisa ta fada. "Toh ai nima ban yi ba, daman ina jira ne ku shigo. Amma yaya kam tun 6:25 ya fita, sai kuma my marasa tausayi cousins, masu mun dariya." Nabila ta fada tana hararan su Nusaiba. "Su kuma suna jiran driver ne inya kawo dinner, su tafi dashi. All the time din da nake complain, suke ta dariya." "Toh kin ga laifin su ne? Ko nima nayi dariya bale su." Nafisa ta fada. "Ni kam a bar surutu, muje muyi sallah." Olamide ta fada. "Toh uztaziya". Nafisa ta fada. "Ba zan biye maki ba, saboda baki ki a ita surutu ba har gobe." Olamide ta fada, ta bar wajan, sannan kowan man su ta mara mata baya, amma banda Nabila, dakin ta ta wuce. Suna idar da sallah, yayi gab da drivern gidan su Farouq ya zo. Nusiba da Hafiza suka yi hugging din su Olamide kaman sun san su daa, harda su we are going to miss you. Suma su Olamide suka raka su har cikin compound, inda suka shiga mota, sai Hafiza tace suyi exchanging din numbers dukan su, suka yi exchanging din numbers. Sun idar da sallan isha, har sun ci abinci, su uku suna zaune a guestroom, Olamide ta jawo ledojin da Adda Fadi ta bata, ta mika ma Nafisa nata. "Ina kuka samo wannan ledojin kuma?" Nabila ta tambaya. "Adda Fadila ta bamu." Olamide ta amsa. "Very good, nama manta ban tambaye ki how far ba, amma tunda naga haka, nasan it went smoothly." Nafisa ta fada. "Gaskiya kam it deed, am so happy for you habibty. Kinga yanda ake tarerayan mu ne? Gaskiya ita da mijin ta akwai kirki. Ga yar su ma Afra, very funny wallahi, kuma akwai saurin sabo, kawai dai Irfan that's second born din ta, ya ke makale da ita, baya barin a taba shi, but everything went smoothly." "Allah sarki gashi da har kin fara damuwa, kinga this alone is a good sign, gaskiya naji dadi data tarbe ku da kyau, saura iyeye yanzu. Kar ki damu suma din zasu iyi accepting In Sha Allah". "Allah yasa, dan ni yanzu wallahi duk wanda ya raba ni da shi, zai zama babban enemy na, wanda baya son ganin farin ciki na." Olamide ta fada. "Kar ma ki damu, In Sha Allahu yaya Abdallah na qalbin sa ne." Nafisa ta fada ta na shafa mata baya. "Naji dadin yanda kika kira mun shi, da ina da goro dana baki." Olamide ta fada tana rufe baki, saboda kar tayi dariya. Ita kuma Nabila ta fashe da dariya, tace " ai baza'a rasa ba acikin unguwan nan." "Zan maku rashin M fa, no be only goro, na garawgaraw." Nafisa ta fada tana hararan su. "Yauwa Fisa, dan Allah bani labarin yanda Ore ta yi behaving a gidan please." "Enh, wato kin maida ni amebo business center ko, aka AK47." "Haba na isa, ai ban isa ba, kawai dai kin iya bada labari ne sosai." "Gulmanma kawai." Olamide ta fada tana hararan ta. "Nayin, gulman ma iyawa ne." Nabila ta fada itama tana hararan ta. "Zaku ci gaba ne, ko in fara baki labari?" Nafisa ta tambaya. "Ki fara ooohh dear na." Nabila ta amsa. "A'a bani bace dearn ki ba." Nafisa ta fada, daga nan ta fada ma Nabila duk yanda aka yi, ko mistake bata yi. "Wow gaskiya har naji ina mugun son ta, I can't wait for ranan da zai kai ni gidan ta, kuce dai harta fola ma friendship din mu ma, gaskiya ina son ta duk da ban san ta ba." "Hanya kin kai ni son ta, wallahi ta shiga rai na sosai, ga shi suna mugun kama da yaya Abdallah, difference din kawai shi ne shi namiji ne, ita kuma mace." Nafisa ta fada. "MashaAllah, gaskiya ina son ganin ta, ko kuna da hoton ta." "Ae, mun duki hoto tare, harda yaran ta." Olamide ta fada, ta dauki wayar ta, ta bude galary, ta je camera, ta mika ma Nabila wayar, wai tana scrolling, zata ga hotunan. Nabila ko sai faman mashaAllah take. Da Nabila ta gama kallon hotuna, sai tace su bude ledojin mana aga abun da sweet in law tasa. Olamide ta fara bude nata, atamfa ciganvi ke ciki, design din da colour combination din yayi kyau, sai kuma wani flat shoe carton brown mai mugun kyau. "Wow mashaAllah, wallahi matan nan na son ki, gashi kaman ta san abun da zai yi fitting din ki, ki kira ta ki mata godiya gaskiya." Nabila ta fada. Sai Olamide tace "kaman kina cikin zuciya na, amma bari habibty ta bude nata ma mu gani. Ai da mun duba tun dazu, da mun mata godiya alokaci data kira, gashi tana ta mana godiya akan common chocolate da sweets din da muka siya, gaskiya har naji kunya." "Gaskiya ko ni, kunga bari nima in duba, mu kira ta tun da wuri." Nafisa ta fada, ita ma ta bude nata ledan, sai taga takalmi ne, itama flat, amma golden colour, yayi kyau sosai, kuma zaiyi fitting din kafafuwan ta ita ma sosai. "Gaskiya tana da kirki sosai, ku kira ta yanzu nan please. Kyauta haka, ai mungode". Nabila ta fada. Sharp sharp Olamide ta dau wayar ta, ta kira Adda Fadila, nan suka ita mata godiya, har sunyi magana da Nabila ma, tace mata nata ma na nan, amma sai tazo. Suka kara yin godiyan wannan ma, Afra ma ta masu magana, kafun suka yi sallama, suka kashe wayar. "Kai gaskiya I really love her." Nabila ta fada. "Wallahi me too." Nafisa ta fada. "Ya isa, kar ku cinye mun ita da baki please." Olamide ta fada. "Mun ji." Nabila ta fada "Lokaci yayi fa, ki wuce dakin ki. Nafisa ta fada. "Gaskiya kam, to 10 fa, ya kamata ki wuce dakin ki." Olamide ta fada. "Toh kora na kuke?" Ta tambaya kaman zata yi kuka. "A'a, amma ya kamata ace kina tare da mijin ki, don't forget you are now a married woman, and you have responsibilities to take care of, please you should go." Olamide ta fada. "Gaskiya kam, you have responsibilities, unlike us." Nafisa ta fada. "Toh naji, amma am really really going to miss you girls wallahi, you guys have become a big part of my life, thanks for always been there. Bari in wuce, kuma fa kuyi barci da wuri, kun san da sassafa zaku tafi." Ta fada hawaye na zuba daga idon ta. "Dan Allah kar ki sani kuka please, wallahi even we are going to miss our three musketeers circle wallahi. This is how life is, we go from stage to stage." Olamide ta fada ita idanuwan ta suka cika da hawaye. "A'a, please no crying, ke kuma Bilatu, ke kika ce kina so, da baki ce kina so ba da ba'a baki shi ba, so ki daina mana fake tears." Sai kuma dukan su suka fara dariya. "Gaskiya kam black queen, ke kika ce kina so, toh gashi an baki shi kuma kina kuka." Olamide ta fada. "Wallahi baku da dama, kunga bari in wuce, har 10." Sai tayi hugging din su daya bayan daya, kafun ta masu sai da safe, ta fita a dakin, ta tafi nata. Data fita, suna hira, suna gyara kayan su. Basu wani dau lokaci ba, suka kammala abun da suke yi, suka yi alwala, suka yi barci agajiye. 〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️ Kafun Abdallah ya koma gida, ya fara tsayawa a nearest masjid, yayi sallan magrib, kafun ya koma gida. Daya isa gida, ya same iyayen sa a parlor kaman kullum, ya gaishe su, sai Abba yace "daga ina kake ne auta?" Sai ya sosa kai yace "naje gidan fav ne." "Ka same su lafiya?" Abba ya tambaye shi. "Lafiya kalau suke." "Toh mashaAllah." Abba ya fada. Sai ya Kalli umma, yace "umma na, yana ga kin yi shuru ne." "Bakomai." "Toh." Ya fada, sannan ya zauna kusa da ita, ya rike hannun Umma, ya ce "Umma ta, am so happy today wallahi." "Toh mashaAllah, may Allah keep us happy always." Suka dan sha hira, kafun isha yayi, su Abdallah suka wuce masjid, ita kuma Umma, tayi a dakin ta. Da suka dawo dinning suka tafi straight, Abdallah ya shiga kitchen, ya taimaka ma Umma, suka yi setting din dinning, kafun suma suka zauna, Umma tayi serving din su, suka ci abincin su silently. Da suka gama Abdallah ya kwashe kwanuka, ya kai kitchen, sannan suka koma parlor, suka fara wani sabon hira. Sanda Abdallah yaga sun yi nisa cikin hiran, yace " Abba Umma, kun san me?" "Ya zamu sani in baka fada mana ba?" Umma ta fada, shi ko Abba inba dariya ba, ba abun da yayi. "Daman akwai wani aboki na ne, da muka gama secondary dashi, amma muna communicating, shi ne yau muka hadu, sai yace mun wai shi ya samu wacce yake so, amma matsalan wai bayarbiya ce, kuma family din su, suna iya barin mace ta auri koma waye, amma mazan su kam, daga fulani sai fulani, shi ne wai in ba shi shawara, ni kuma na rasa abun da zance masa." "Hmmm this is serious. Amma idan iyayen sa are very understanding, zasu iya bari. Amma in tambaye ka mana?" Abba ya fada. "Toh Abba na." Abdallah ya fada. "Ya fada ma iyayen sa ne, kuma me suka ce?" "Gaskiya kam, ya kamata ya bi umarnin iyayen sa." Umma ta fada. "Gaskiya bai fada masu ba, yana tsoron amsan su." "Ya dai fada masu, sai yaji opinion din su koba haka ba hajiya?" Abba ya tambaya ya na kallon Umma. "Haka ne. Amma kuma yabi umarnin iyayen sa, dan a hakan zai samu nasara a rayuwa." Umma ta fada. "In Sha Allah zan fada masa, nagode." Abdallah ya fada. "Bakomai autan mu." Abba ya fada, yana ja'a mai kumatu." "Awwsh Abba, zaka cire mun kumatun ai." Abdallah ya fada a shagwabe. "Sannu auta na, bazan kara ba, kaga daman babu kumatun, kar azo kuma ya cire, ana neman cuko." Abba ya fada. "Ko kai ka fada. Mutum siriri haka? Dama ana iya kyautan kiba ne, dana ce yayyin ka su baka, duk da dai suma ba wani kiba gare su ba, amma sun fi ka, but still banda Fadila, dan itama gata ga irin ta." Umma ta fada. "Hahhhhhhhhhh, kai hajiya baki da dama. Wato dukan su ba auki, ai in kika duba, haka yan gidan mu suke, ko wannan fitinan nan tsohon nan ma haka yake, kaman a hure, amma fitinan shi, ya fi most fatest person kiba." Abba ya fadi. Abdallah da Umma suka fashe da dariya. Haka suka ita hira. Sun dade suna hira, dan har 10:30pm suka kai. Da Abdallah ya shiga dakin shi, yayi realising din time, yasan ko ya kira qalbin sa, ba zata daga ba, dan he is pretty sure tayi barci. Shi ma yayi shirin barci, ya yi azkar kafun yayi barci. Asuba ta gari. ```Thanks for reading, Allah ya bar kauna, zeexee ma na son ku.``` Comment Like & Share. Zeexee ce 🖊️🖊️🖊️ [8/30, 1:21 PM] Abokiyar Fight💜💖: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 *BANBANCIN KABILA* _(Short story)_ 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 *TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION* *_🔱((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))_* *T.W.A* *WRITTEN BY ZAYNAB* _(zeexee)_ MARUBUCIYAR *-RAYUWAR HUSNA* *-MAHAKURCI MAWADACI (2020)* ```Dedicating this page to sis Khadija (Hadiza). Nagode sosai da encouragement din ki, Allah ya bar dankon kauna💜💜💜💞💕.``` 2️⃣3️⃣&2️⃣4️⃣ Da suka shiga, Afra ta ita rarraba ido tana kallon su, Adda fadi tace da ita "baki iya gaisuwa bane?" Sai tace "ina ini". "Ina gajiya, ya kike?" Nafisa da Olamide suka fada tare. "Lafiya kalau alhamdulilah". Ta amsa. Aunty Fadi tace ku zauna mana". Ta fada tana murmushi. Da Abdallah ya shigo, Afra taje wajan sa da gudu, tayi hugging din shi, tana fadan "oyoyo uncle'am". Shi kuma chewing gum din mummy, ya je ya boye a ta kafan Adda Fadi. Abdallah ya daga Afra sama, tana ta dariya, sannan shima ya nemi wuri ya zauna. Ya ce "ni kam meye ruwa na da kai, kaje can ka karata da Mummyn ka". Adda Fadi tace "oho dai, my son ya fi ka kyau, ko Irfi?" Shi kuma ya kada kai. Adda Fadi ta tashi, ta je kitchen, ta kawo masu chilled drinks da ruwa, da snacks, tasa masu a gaba. Sai tace "banda pulako fa, ku fara taba wannan". Nafisa tace "toh". Abdallah yace da Afra, "kinga amaryar uncle and future mummyn ki In Sha Allah." "Wacce acikin su uncle?" "Kiyi guessing, zan baki dairy milk". "Allah zaka bani dairy milk?" Ta tambaye shi excitedly. "Uncle ya taba saba alkawar?" "A'a. Bari in nuna maka ita toh." All this while, Olamide nata satan kallon su, tana son irin wannan relationship din su, bisa duka alamu, Ife(love) nada son yara, so he will make a good father In Sha Allah. Tana cikin tunani, taji hannun Afra cikin nata, tace "ita ce wannan ko uncle?" "Very good, saboda wannan task din da kika yi passing, zan siya maki packet din dairy milk." "Woo" ta fada exictedly. Sai ta kalli Olamide da Nafisa, tace "kuna da kyau sosai kaman uncle dina". Kunya ya kama Olamide, Nafisa ko tace "ki dai fadi gaskiya, kice tana da kyau kaman Uncle din ki " ta fada tana pointing din Olamide. "A'a tana kama dani dai, ai nafi Uncle kyau, ko Uncle?" Ta fada tana kallon Abdallah. Duk suka fashe da dariya. Shiko Irfan, ya bi ya makale da mummyn sa. "Ku ci fa." Adda Fadi ta fada tana pointing din abun da tasa masu agaba. "Ai In law din ki akwai kunya." Abdallah ya fada. "A'a, kima cire kunyan nan, dan ba inda zaki in baki ci ba." "Zan ci." Ta fada a kunyance. Da kyar ta bude ruwan, ta sa a cup ta fara sha, Nafisa sai kallon ikon God take, ashe habibty nada irin kunya nan. "Ya kuke ya school?" Adda Fadi ta tambaya. "Alhamdulilah." Suka amsa tare. "Wallahi da ba dan bro yace mun ke bayarbiya ce ba ko, wallahi da fulani zan kira ki". Sai Olamide tayi murmushi, tace "haka ake cewa". "Gaskiya kam, dole afada. Amma ke kam fullo ce ko?" Ta tambayi Nafisa. "Ae daga Bauchi." "Ashe ma bamu da nisa. Gaskiya in law, kin shiga mun rai sosai, am sure su Abba ma will be excited ta accept you In Sha Allah. Bari in kira maku Abban su Afra ku gaisa ko?" "Toh" suka amsa. Da Adda Fadi ta bar wajan, sai Abdallah yace "qalbin Abdallah, dan Allah ki sake kin ji?" "I will". Ta fada tana murmushi. "You should please. Adda Fadila bata da matsala wallahi, kuma in kika sake, zaki ji dadin ta. Inma so kike in bar ku tare ne anjima inzo in dauke ku, am okay with that, I just want you to be comfortable." "No, ba sai ka bar gidan ba, In Sha Allahu zan yi kokarin sakewa. Kuma tunda ina tare da habibty, sakewa kam ya zama dole." "That's good. Habibty ki sa ta sake sosai please." "Baka da case ai." Ta fada tana murmushi. Sai Afra ta zo kusa da Olamide, tace " kece wife din Uncle, wai kunyi dinner ne?" Maganan ta ya basu dariya, Nafisa ta ce "Afi bama aure ba, dinner suka yi." "Ae, ai dinner shi ne aure, ko Uncle?" Ta fada tana kallon Abdallah. "Ni kam ban san wannan ba Afin uncle, amma maybe qalbin uncle ta sani." Ya fada yana kallon Olamide. "Sunan ta kenan qalbi?" "Ae sunan ta kenan qalbin Abdallah, amma zaki iya kiran ta qalbi." Ya fada still idon shi na kan Mide. Sai taje kusa da Olamide kuma, tace "qalbi ai dinner shi ne aure ko?" Olamide ta kalli Nafisa, ta kalli Afra, ta kara kallon Nafisa, ta kara kallon Afra. "Ki fada mata mana, tana jiran amsan ki qalbi." Nafisa ta fada. Olamide taji kunya sosai. Data ga still Afra na kallon ta in a way that says I need an answer. "Amm Afra baby, dinner ba shi ne aure ba, dinner is just a party which takes place during wedding functions. Shi kuma aure, is the coming together of two different people, to become one." "Okay toh. Amma kuma zaku yi dinner?" "A'a" suka hada baki. Sai kuma suka kalli juna suka yi dariya. "Toh aure kawai zaku yi kenan?" "In Sha Allahu." Abdallah ya amsa. Sai ta kara komawa wajan Nafisa, tace "kema sunan ki qalbi ne? Kema zaki auri uncle ne?" "A'a ni kam sunana Nafisa, kuma wani uncle din zan aura In Sha Allahu ba wannan ba. Ai wanan na habibty ne ita kadai." Nafisa ta fada tana taba kumatun ta. "Wacece habibty kuma?" Tayi tambaya confusely. "Aww sorry, amma qalbi habibty ta ce, kuma qalbin uncle din ki." "Toh naji." Suna cikin hira, Afra na masu questions, su kuma suna amsawa, Adda Fadi da mijin ta suka yi sallama. "Ina ini" Olamide da Nafisa suka fada tare. Sanda ya zauna, yace "an yi ni lafiya" "Lafiya kalau. Mun same ku lafiya?" Su biyu suka fada. "Lafiya kalau alhamdulilah. Kun zo lafiya, ya gajiyan biki?" "Lafiya kalau alhamdulilah." Suka amsa. "Toh MashaAllah. Ina amaryar mu acikin ku, ko bata zo ba ne?" Mijin Adda Fadi uncle Isah ya tambaya. "Kai love, wannan kuma wani irin tambaya ne. Ga amaryar nan mai jallabiya bakin nan." "Haba dan Allah! Wannan ai bafulatana ce." Ya fada in shock. "Kai ma dai zaka fada. Wallahi da Abdallah bai fada mun asalin ta ba, da ban yarda ba." "Ni dai haryanzu I find it hard to believe. Zan baki dan wani assignment amaryar mu, ki yi tambaya agida, afada maku asalin ku, dan ko kawu Dajjo ya gan ki, kuma ba'a fada masa yaran ki ba, bazai sani ba." "Haka ake cewa, kuma munyi tambaya, duk wanda muka tambaya, suce mu yarbawa ne". "MashaAllah. Shi yasa discrimination ba kyau, Allah mai yanda yake so da bawan sa. Allah ya kai mu lokacin auren ku." "Amin"Abdallah ya fada da karfi. "Kai auta ko kunya" Adda Fadi ta fada. "Toh kunyan me zan ji, addu'a aka yi kuma na amsa. "Toh yayi". Ta fada tana hararan shi. Haka suka ita hira, suna dariya, har Olamide tazo ta sake. Cikin hiran ma suna ta tambayan ta questions, kuma alhamdulilah tana amsawa yanda ya kamata. Sun ci sun sha, saboda Adda Fadi bata bar su ba, sanda taga suna ci, kuma suna shan duk abubuwan data kawo masu. 6:pm nayi, Olamide ta ma Abdallah text, wai ya koma da su, yasan dai gobe zasu koma, so they are things they will like to do before going back. Yana ganin message din ya share, yayi kaman bai gani ba, ya dago kai suka hada ido, ya dauke idon sa. Ta kara mai wani message din, yaki. Sanda tace "ammm Adda Fadi, zamu wuce, kin san gobe zamu koma, ya kamata mu dan zauna da kawar mu kafun mu koma, kuma zamu shirya wasu abubuwan mu." "Baki yi karya ba, amma why not ku bari anjima?" "Haka nima nace, amma ta ki." Abadallah ya fada. "A'a ba wai taki bane, gobe fa da sassafe zamu koma, kun ga ya kamata mu tafi yanzu." Nafisa ta fada tana murmushi. "Toh in kuka koma, sai kuma yaushe?" "Yaushe?" Olamide ta tambaya, sai tayi wani irin murmushin da dukan su suka yi dariya. "Sai anyi auren kenan ko?" Adda fadi ta tambaya. "A'a fa ban ce ba." Ta fada a kunyance, tana wani rufe ido, muryar ta kasa kasa, amma sunji ta. "Oho dai, mu dai munsan maanan haka." Adda Fadi ta fada. "Allah ya kaimu lokacin, ya daura ku akan duk wani makiyi, ya sa iyayen mu su yarda, kar suma su nuna banbanci, su yarda da wannan union din, saboda hadin nan In Sha Allahu zai yi kyau." Uncle Isah mijin Adda Fadi ya fada. "Amin" kowa acikin parlorn ya amsa. "Toh Adda zamu wuce". Abdallah ya fada. Ai suna jin haka, suma suka tatara jiki suka tashi tsaye. "Gaskiya ban ji dadin wucewan ku din nan ba, amma na ji dadin zuwan ku sosai alhamdulilah. My prayer is also for this union to happen wallahi, saboda kin gama mamaye zuciya na qalbin Abdallah. Allah ya sa iyeyen mu su yarda, kinga alokacin, zamu dinga haduwa anyhow. Gashi kema Fisa, idan Allah yayi, kema nan zaa kawo ki, wato three three kenan kuka yi. Allah yasa ayi auren ku kuma, ku zo Gombe, ku dinga zuwa wajan wannan addan ta ku, maybe ma by that time mun saba da Nabila, dan nasan Farouq zai kowa ta wajan fav sis din su." Ta fada tana murmushi. "Toh Allah yasa." Olamide ta fada. "Mu tafi." Abdallah ya fada. Zasu fita, Adda tace ku jira ni ina zuwa, bari in sa hijab. Tana barin wajan Olamide ta mika ma Afra leda, na thank you, cike da sweets da chocolate, wafers, da dai sauran su. Tana mika ma Afra, ta gani, tace "yay chocolate, nagode sosai qalbin uncle da adda Fisa." Ta fada tana hugging din su. Abban su ma yayi godiya, sai ga Adda Fadi ta shigo, itama da leda cikin hijab, ba zaka gane ma ba, sai ka kare mata kallo, ta ce "muje." Duk suka fita waje, Abdallah ya bude gate, sannan, ya fita da motan sa, alokacin Adda Fadi ta jawo hannun Olamide, tace "In Sha Allah, me and him, zamu san yanda zamu yi da family members din mu, dan Allah kema kiyi kokarin convicing din mummyn ki, wallahi ban taba ganin kani na yaso wata ya mace ba haka, kuma daga bisa duka alamu, kema kina son shi. Wallahi zuwan ki yau yasa nayi clearing kai na and my thinking akan tribalism. Am soo happy I met you wallahi. In Sha Allah I will always put you guys in my du'a. Kar ki ce a'a, dan Allah ga wannan." Ta mika ma Olamide. Olamide ta amsa, ta mata godiya. "Adda nagode sosai, Allah ya saka maki, ya raya maki yara. In Sha Allahu zan fada ma mummy, moreover, nasan ta wajan mummy bakomai, but still zan fada mata and thanks for accepting me, I can't thank you less wallahi." Olamide ta fada, bata ma san lokacin data yi hugging din Adda Fadila ba, har da wayen ta. "A'a kar ki mun kuka Abdul ya gani yace na fada maki abu ne." Adda Fadi ta fada tana goge mata hawaye, suka ji ana horn, sai Adda tace "ga wannan ki ba habibtyn ki, mu je kafun ace ina tsungulin ki." Dariya su biyu suka yi, sannan suka fita, Olamide ta shiga gaba, daman Nafisa ta riga ta zauna a baya. Data shiga, suna ta waving din juna, har suka bace ma juna. ```Thanks for reading.``` Comment Like & Share. ~Zeexee ce~ 🖊️🖊️🖊️ [8/30, 1:21 PM] Abokiyar Fight💜💖: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 *BANBANCIN KABILA* _(Short story)_ 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 *TAMBARI WRTER'S ASSOCIATION* *_🔱((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))_* *T.W.A* *WRITTEN BY ZAYNAB* _(zeexee)_ MARUBUCIYAR *-RAYUWAR HUSNA* *-MAHAKURCI MAWADACI (2020)* 2️⃣7️⃣&2️⃣8️⃣ Anyi sallah lafiya, Allah Ya maimaita mana. Haryanzu dai ba wanda ya bada goron sallah, but am still waiting lol. Allah ya naimaita mana, may we witness more and more eid's to come. Like I promised, nace zan rubuta suran pejin nan bayan sallah, toh alhamdulilah, gashi yau na cika alkawari. Asha karatu lafiya, kar ku manta da sharhi, because it's like an oxygen of a writer. _Bismillah_ 4:am alarm din Olamide ya fara ringing, cikin barci taji karan shi, gashi ta sa shi kusa da kunne ta, so har cikin kwakwalwar ta take jin Kara. Da sauri ta tashi, ta kashe, sannan tayi addu'an tashi daga barci, ta sauka daga kan gado, ta shiga toilet, tayi business din ta, tayi brush, sannan tayi alwala, ta fito ta tada Nafisa. Da suka idar da sallah, suka karanta qur'ani a islam pro app, suka yi addu'an safe da maraici, kafun Olamide ta fara shiga wanka, sannan Nafisa ma ta shiga. Suna cikin shiri, Nabila tayi sallama ta shigo, tace "kaman kun san nazo duba ku ne ko kun shirya, gashi Allah yayi kun shirya. Amma yaya yace sai kaman 7-7:30 zai kai ku park. So in kuka gama dressing, akwai kwai a kitchen, ku soya, jiya yaya ya siya maku bread, kuma akwai kayan tea, then ku duba store ma, akwai sardine." Nabila ta fada. "Toh mama Nabila. Amma ko gaisuwa?" Nafisa ta fada. "Allah sarki kuyi hakuri, tun jiya maganan nan ke rai na, shiyasa, amma amun afuwa, ina kwanan ku." "Ina gajiya, ya gajiyan jiya, ya dawai niya da mu? Allah ya bada lada, ya baku zaman lafiya, ya kawo zuriya dayiban." Nafisa ta fada. "Kalau, gajiya kam akwai shi. Amin amin, nagode sosai kawayen albarka. Kuma Allah yasa muga naku, nima in kai ku dakunan ku." Nabila ta fada tana murmushi. "Amin" suka amsa tare. "Baby, kin ga 6 something yanzu, bari muje mu hada breakfast din, mu maki wanke wanke, kar mu bar maki plates." Olamide ta fada. "Ai kuwa, the earlier we start, the better." Nafisa ta fada. "Sai me in kuka bar mun wanke wanke?" Nabila ta fada, tana turo baki. Basu bata amsa ba, Olamide ta riko hannun Nafisa, suka tafi kitchen, Nabila na biye da su. Suna breakfast, suna hira, magana daya biyu, sai Nabila ta fada masu yanda zata yi missing din su, su kuma su ita fada mata maganganun da zasu yi calming din ta. Haka suka ita yi, har suka gama hada breakfast din su, suka ci, Nabila ma ta ci da su, sannan suka yi mata wanke wanke, duk da ta nuna masu bata so, amma haka suka yi. Da suka gama clearing din komai, suka koma daki, itama ta koma dakin ta. Da suka shiga, Olamide ta samu wayar ta na ringing, ta yi suri ta dauki wayar, sunan mummy ya fito a screen din, ta daga cikin murna. Sun yi 20 mins suna magana, tayi tambayar Farida, Mummy tace tana nan tana shirin school. Daman Hakeem ya koma school shi ma, so mummy da Farida suka rage a gida, Mummy ta masu addu'an Allah ya sauke su lafiya, tace ta ba Nafisa wayan, daga nan suka yi sallama, suka kashe wayan. Ai ko bai fi 5mins ba, kiran Abdallah ma ya shigo. Cikin kunya, ta daga. "Assalamu alaikum ifemi." "Waalaikumus salaam qalbin Abdallah. Kin tashi lafiya, ya gajiyan jiya?" Abdallah ya tambaya. "Lafiya kalau. Kai fa?" Olamide ma ta tambaya. "Same alhamdulilah, but I kept dreaming about Mrs Abdallah Umar Muhammad Yero. I can't wait for you to be mine yide am (my love)." "Me too ifemi, I can't wait. But meye ma'anan yide am kuma." Ta tambaye shi confusedly. "Aww, ashe sai na dinga koya ma yide am fulatanci." Abdallah ya fada, su biyu suka yi dariya. Olamide ta ce "ae mana, kar azo ana zagi na." "Haba qalbin Abdallah, bazan taba zagin ki ba, ko wani naji yana zagin ki, mai raba ni da shi sai Allah, sai ni na zage ki? Toh maybe am mad then. So yide am means my love. Or ain't you my love?" Abdallah ya tambaye ta. "Aww, ashe ma'anan shi kenan. Of course am your love yide am." Ta fada a kunyance kaman yana ganin ta. Suna cikin waya, ita kuma Nafisa sai kallon ta take, Nabila ta shigo, tace ma su su fito, yanzu zaa kai su gareji. Nafisa ta tashi, ta dauki handbag din da suka sa kayan su, da side bag din ta, ta ma Olamide signal da hannu ta dauki nata bag din, da wani amebo leda. Olamide tayi nodding kan ta. Sai ta ce "uhmm ifemi, yanzu yaya Farouq zai kai mu gareji, zamu yi waya anjima." "Okay, kinn ki in kai ku park din. But anyways, in kuka isa park, ki kira ni. Bye, mi yidi ma yide am. Meaning ina son ki masoyiya ta." Abdallah ya fada. "Bye, mo ni ife re emi na ifemi. Meaning I love you too my love." "MashaAllah, zan koya maki fulatanci, keh kuma ki koya mun yarbanci. I really love the way this words came out of your mouth, although am not seeing you. Anyways bye qalbin Abdallah." Abdallah ya fada, sai ya kashe wayar. Ba abun da Olamide ke yi inba murmushi ba, gaskiya Abdallah na faranta mata rai sosai, Allah yasa iyeyen sa su yarda, saboda ta san from her side, bata da matsala, mummy zata yarda, dan a familyn su, akwai wayanda suka auri wasu kabilan. Ita ma ta sa hijab din ta, ta dauki side bag din ta ta rataya a kafada, sannan ta dauki amebo ledan, suka bar dakin tare da Nafisa. Da suka shiga parlor, suka samu, Farouq da Nabila na jiran su, su Olamide suka gaishe shi, sannan dukan su suka fita, Farouq ya sa ma kofar key, suka shiga mota, Nabila a gaba su Olamide kuma a baya. Farouq yayi horn, mai gadi ya bude mai gate, ya fita, sai gareji. Luckily, suna zuwa, akace mutum biyu ya rage motan ya cika, sharp sharp aka yi loading kayan su, nan suka ita hugging din juna, Nabila harda kwalla. Da suka shiga motan, ta yi waving din su, Farouq ya riko hannun ta, suka matsa ma motan ya samu hanya ya wuce, suka ita waving din juna, har motan su ya bace masu, sannan still hannun Nabila cikin nasa, ya bude mata gaban motan ta shiga, sannan ya je driver side, shima ya shiga. Sanda ya ita rarrashin ta, kafun tayi shuru, shima ya ja motan, suka koma gida. Su Olamide kuwa, motan su na barin gareji, ya kama hanyar barin Gombe, ta ce "kai Habibty, gaskiya garin Gombe nada kyau fa sosai." "Bari kawai. Am going to miss this state, duk da cewa bamu san ko ina ba, still garin ya kwanta mun. Balle ma, muma fa nan zaa kawo mu, zamu ga garin, har ya ishe mu." "Hahhhh habibty, wallahi kin ban dariya, wai nan za'a kawo mu." Olamide ta fada tana dariya, data ga mutani na kallon ta, ta rufe fuskan ta da tafin hannun ta. "Toh daa karya nake, kema dai kin san nan zaa kawo mu, inda rai da rabo In Sha Allah." Nafisa na rufe baki, wayar ta ya fara ringing, sunan Asim ya fito, sai ta kalli Olamide, ta daga mata gira, tace " bye sweety, ki kira ifen ki." Nan Olamide ta tuna yace ta kira shi in suka isa gareji. Sai ta dauki wayar ta, ta fara kiran Mummy, ta sanar da ita motan su ya tashi, suna hanya, mummy ta yi masu addu'a, sai ta kira Hakeem ma, tace mai ga shi gari kusa kusa suke da school din sa, amma ba halin su hadu. Suka dan yi hira, kafun yace mata yana da lectures, zai tafi school, ya masu addu'an safe trip, ya kashe wayar. Zata kira Abdallah kenan, kiran Ummin Nabila ya shigo. Ta daga, ta gaishe ta, ta ita masu godiya, tace ta ba Nafisa, tace Nafisa na waya, ta masu addu'a, suka yi sallama, ta kashe kiran, sannan ta kira Abdallah, har kiran ya katse, bai daga. Yana tsinkewa, bai fi 2mins ba, kiran sa ya shigo, ta daga, tayi sallama, ya amsa. Ya ce "sai yanzu kuka isa gareji, this is 8 something fa qalbin Abdallah, gashi na ita kira, ana ta ce mun line busy, da wa kike waya haka ne?" "Da mutani nake waya." "Toh su mutanin basu da suna ne?" Abdallah ya tambaya. "Nace maka mutani, ka bar wannan zancen, and wish us a safe trip." "A'a gaskiya bazan iya barin zancen nan ba, why is it so hard ki fada mun sunan su?" Ya tambaya. "Nothing." Olamide ta amsa. "Then tell me please, inba haka ba, my mind won't be at rest." Abdallah ya fada. "Nifa bana son kishi wallahi ifemi. Kuma da mummy, da Hakeem, da Ummin Nabila muke waya." "Toh what was hard there yanzu. Kuma gaskiya indai kishi ne, sai dai kiyi hakuri, dan ina matukan kishin ki, amma in the right way." "It's better be in the right way gaskiya, dan ni kam bana son bakin kishi. So wish me safe trip." "Toh yide am, Allah ya sauke ku lafiya, ya tsare maku hanya, ya kare ku daga sharin karfe, da duk wani sharrin dake kan hanya." "Amin my young doctor." Olamide ta amsa, tana murmushi har kunne. "Yauwa qalbi, nima yanzu zan shiga office, so ina Samu break, zan kira ki." "Okay toh, Allah ya baka saa, banda kallon yan mata." Tana fada haka, ta kashe kiran, tana murmushi. Shima yayi murmushi, dan yaji dadin maganan ta sosai, wato tana kishin shi, shine take cewa bata son kishi. Daman baya kallon su, gashi yide(love) tayi warning din sa, gashi islamically, it is said to lower your gaze, so abun yazo daidai. Throughout lokacin da Abdallah yake aiki, yaki kallon female patients, sai dai yaji complains din su, ya karbi card, ya rubuta masu magani, ya mika masu, next patient ya shigo. Haka ya ita yi, har lokacin break yayi, suka hadu da Asim, suka fara zuwa masjid, suka yi sallah, kafun suka aiki wani cleaner, ya siya masu drink da biscuit. Saboda basu son cin abincin a waje, gashi ba wanda ya kawo lunch daga gida acikin su. Never the less, by 2 something zasu bar wajan aiki. Kuma gaskiya sunyi missing din Farouq Sosai, click din su bai yi complete ba without him. Da Mide tayi cutting din call din, ta dinga murmushi, kaman ya na ganin ta. Bai fi 5mins ba, Nafisa ma ta gama waya. Sai ta kalli Mide, taga fuskar ta na dauke da murmushi, kuma if she could recall, she have been smiling like this for the past 5mins. Ta taba goshin Mide tace "naji jikin ki ba zafi, balle ince high fever ke damun ki." "High fever kuma, me kika gani?" "Ae high fever. Keda tun dazu kike ta murmushi, kinga abu na damun ki." Nafisa ta fada. "Kema haka, saboda kema murmushin kike." Olamide ta fada tana murguda mata baki. "Kya ji da shi ai." Nafisa ta fada. Olamide ta sa kan ta saman cinyan Nafisa, tace "barci nake ji, amma in aka shigo garin (Bauchi), dan Allah ki fada mun, saboda ina son inga garin ku." "Ai dole na, dole na tashe ki kiga garin habibtyn ki. Wai gani zan wuce gida, amma bazan shiga gida ba, this is too bad." "Baki so zuwa gidan ku ba dai." Olamide ta fada. "Haba habibty, kema fa kin san tun da muka koma, bamu samu munyi concentrating a karatun mu ba, sai ince mu kara zuwa gidan mu? Ai sai dai mu kwashi carryover wannan semestern. Moreover ma Abba bazai bari mu zo ba, baki ga ma da kyar ya bari inzo Gombe din nan ba. Cewa fa yayi, inba bikin habibtyn ki bane, ba zaki ba. Sanda na ita explaining, Ummi ma tasa baki, kafun ya bari." Nafisa ta fada. "Toh naji Hajiya, ni dai in muka iso BH, ki tashe ni." Olamide ta fada, tana gyara kwanciya. "Toh naji kasa." Nafisa ta fada. "Oho koma meye, endavour to wake me up, kar kiyi barci fa." "Naji Mrs Yero." "Yauwa Mrs meye naki ma. Kinga Bila nata Mrs Ardo, ni Mrs Yero, naki fa?" Sanda Nafisa tayi wani irin murmushi, kafun ta ce "Mrs lacca ce." Nafisa ta fada tana rufe fuska. "Toh! Harda guntun kunya? You try Mrs lacca. Yanzu abun yayi sweet. Ardo, Yero and Lacca. Anyways kar ki manta ki tashe ni." Olamide ta fada. "Naji uwar mita." Nafisa ta fada. Olamide bata amsa mata ba, dan tasan inta amsa, haka zata ci gaba da jan ta da surutu, har su iso garin (Bauchi), gashi barci take ji. Abun ba wuya, har sun iso Kano. Daman da suke hanya, Ummin Nabila ta kira Olamide, tace Faeeq zai zo daukan su, ya kai su gidan su Nabila, in suka huta, ya maida su. Kaman tace a'a, sai ta tuna, yanzu Ummi zata ce suna son juna ne, kuma bata son hakan ya faru, tace mata taji. Suna sauka, daman Faeeq na jiran su, suna sauka, ya hango su, yana ganin Mide ya bata rai, sanda yaga Fisa, ya yi murmushi, yana jin dadi, alanbaran yaga masoyiyar sa, masoyiyar da bata ma san yana yi. Da sauri, yaje inada suke tsaye, taje ta side din Nafisa, ya ce "sannun da zuwa arewa angel." Sai ya kalli Olamide ya wani harare ta, itama ta maida mai martani. Nafisa ko murmushi kawai tayi, dan ta san yana neman tsokanan habibtyn ta ne. Sai kuma yace "kawo jakar in rike maki Fisa." "A'a na gode yaya Faeeq." Nafisa ta fada tana mai faking din murmushi. Yayi yayi da ita, amma haka taki, dan ta san duk abun da yake yi, yi yake dan yaba Mide haushi. Da suka isa motan, Nafisa da Olamide suka zauna a sit din baya, sai Faeeq ya kalle su, yace "kun san niba drivern Ku bane. Maybe wannan yar yarbawan ta koya maki halin nan, dan gaskiya na san ba haka kike bane." Maganan shi ya bata ma Nafisa rai sosai, bata son yanda yake ma habibtyn ta. Rai abace, ta fita ta shiga gaba, ta zauna. Duk yanda yaso ya ja ta da jira, taki amsa mai, sai kuma ya koma yana ta neman tsokanan Olamide, ita ma ta ki amsa mai, daya gaji, yayi shuru. Da suka isa gidan su Nabila, an tarbe su da kyau, duk da ba Nabila, ummi bata nuna masu banbanci ba, suna shiga, suka gaida kowa da kowa, da shike basu gama komawa ba (yan biki), Ummi tace suje dakin Nabila, suka je, nan suka kira wayanda zasu kira, suka sanar masu sun sauka. Da suka fada ma Nabila suna dakin ta, ta fara kuka, wai ita tayi missing din su, in short tayi missing din komai. Through wayan suka ita rarrashin ta, har tayi shuru. Ummi ta aika akawo masu abinci daki, suka ci suka koshi. Basu bar gidan ba sai bayan asr. ```Thanks for reading y'all, I appreciate.``` Comment Like & Share. ~Zeexee ce~ 🖊️🖊️🖊️ [8/30, 1:21 PM] Abokiyar Fight💜💖: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 *BANBANCIN KABILA* _(Short story)_ 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 *TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION* *_🔱((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))_* *T.W.A* *WRITTEN BY ZAYNAB* _(zeexee)_ MARUBUCIYAR *-RAYUWAR HUSNA* *-MAHAKURCI MAWADACI* _(2020)_ 2️⃣9️⃣&3️⃣0️⃣ _Bismillah_ Da suka koma gidan su (a school), suka gyara ko ina, daman Ummin Nabila ta riga ta basu abincin da zasu ci da daddare. So da suka gama, suka shiga wanka one after the other, sannan suna alwala. Bayan isha, suka ci abinci, suka kai plate kitchen, kowanan su ta kwanta saman katifan ta, suna dan taba hira kadan, kiran Abdallah ya shigo. Tayi murmushi, ta kalli Nafisa, sai Nafisa tace "na san mai kira, you don't have to behave like this, ki daga kar ya katse." "What am I doing din, bana son shishigi fa." Olamide ta fada, ta murguda ma Nafisa baki, sannan ta daga wayan. "Asslamu alaikum!" Olamide ta fada. "Waalaikumus salaam qalbin Abdallah. Ya kike, ya gajiyan yau?" "Am fine alhamdulilah, gajiya ma ya koma gidan sa." Ta fada tana dan dariya. "Baki da dama qalbi. So nace ba, yaushe zaki fada ma mummy, saboda mu san level din relationship din mu. "Have patience, yau fa na dawo, ka dan bari ko jibi, a lokacin na dan yi settling." "Jibi kuma qalbi, I don't think I can be that patient, why not gobe ki fada mata please, wallahi I want to know the level of our relationship, ina son in san wani matsayi zamu sa soyayyan mu, mu sani idan zamu yi taking din shi further." Abdallah ya fada yana shafa kai kaman tana ganin shi. "Toh naji, In Sha Allah gobe zanyi kokarin inga na fada mata. Kai ma, ya kamata ka fada ma su Umma da Abba, ka san dai there decision will also be needed." "Kar ki damu, amma inaga ba yanzu zan fada masu ba, sai naga na fada ma siblings dina, kin ga zasu samun baki, alokacin da zan fada masu. Kema dai kin san ni zan fara auran wace ba Fulani ba, so a hankali zan bi su. Kuma kinga idan suka yarda, in kika shigo family, ba zasu bari a wulakanta ki ba, kuma zasu duke ki tamkar 'yar su ta ciki." Abdallah ya fada. "Ban gane ba, ai ba haka muka yi da kai ba, iyaye fa muka ce zamu fada ma?" Olamide ta fada tana kokarin danna fushin ta. "Na sani, amma irin haka bai taba faruwa a familyn mu ba, ni ne fa na farko, kinga in ina son su yarda, dole sai na bi a hankali. Shi yasa nake son yayyi na su sani, saboda in lokacin fada masu Abba yayi, suma su sa baki, kar abun ya zo masu kaman shock." "Hmmmm naji." Olamide ta fada, without any emotion. "Bazan taba yaudaran ki ba, bana son muyi aure azo ana wulakanta ki ne, ina son kowa ya dauke ki da mutunci, ba zan so ace Umma ko Abba zasu sa ki agaba, kinsan aure is a life time commitment, so bana son situation din da zaki dinga samun sabani da surukan ki." Abdallah ya fada calmly. "Toh na ji, Allah yasa hakan shi ne mafi alheri." "Amin." Abdallah ya amsa. Daga nan, suka ci gaba da hiran su. Da suka gama, ta ajiye wayar ta, ta kalli inda Nafisa take, taga tana waya, sai ta kwanta da kyau, ta fara tunanin maganan da suka yi da Abdallah. Allah yasa dai kar su samu matsala, dan tana ji a jikin ta kaman soyayyan su ba zai taba zuwa ko ina ba, tana ji kaman ita da Abdallah sun kusan rabuwa. Tana tunani tana hawaye. Wai meke sa ake nuna banbanci ne tsatanin mutani, me yasa iyaye basu son yaran su su auri outside yaren su ne, kar Allah yasa irin haka ya faru da ita, kar Allah yasa a raba ta da Abdallah, saboda in aka yi haka, gaskiya ancuce ta, saboda bazata taba mantawa da shi ba. Da Nafisa ta gama waya, taji shashakan kuka, ta tashi ta je katifan Olamide da gudu, ta daga kan ta. "Habibty me ke damun ki, ko iyayen shi basu yarda bane, dan naji kuna maganan iyaye?" Nafisa ta tambaya. Sanda tayi kukan ta, har hankalin Nafisa ya tashi, itama idanuwan ta sun yi ja'a, sannan ta ce "a'a, amma ina jin shi a jiki na kaman baza su yarda ba." Olamide ta fada, wasu sabon hawayen na zuba. "Kar ki ce haka please, tunda bai ma fada masu ba, just be positive, nifa I thought basu yarda bane, kuma kun rabu. Please stop crying, I will cry too if you continue crying." Nafisa ta fada tana goge mata hawaye. "Naji habibty, amma ina jin tsoro kar hakan ya faru." Olamide ta fada. "In Sha Allahu hakan bazai faru ba. Toh me ma ya fada maki daya saki kuka haka, nifa indai tun ba'a kai ko ina ba, zaki fara koke koke in kuka gama waya, ni kam ku rabu." Nafisa ta fada jokingly. "Ji bakin ki, kema ki rabu da Asim mana." Olamide ta fada tana hararan ta, sannan ta labarta mata komai. Data gama, Nafisa tayi hugging din ta, ta ce "kar ki damu, wannan hanyan da zai yi using ma is okay, kinga idan yayyin sa suka sani, kuma yayi convincing din su suka so ki, toh baza'a samu matsala ba." Nafisa ta fada tana comforting din ta. "I know, but am just scared wallahi, am very scared." Olamide ta fada, idanuwan ta suka kara cikowa da ruwa. "Don't be please, don't be scared, just pray for the best." Nafisa ta fada tana hugging din ta. Haka Nafisa ta ita consoling din ta, har ta daina kuka, suka dan yi hira, sannan suka yi barci. Cikin dare, suka tashi suka yi sallah, tun daga lokacin suka fara shirin lectures, saboda by 7:30am suna da lectures. Suka ita shire shire. Da suka gama shiri, kowanan su ta dau side bag din ta, tayi slinging din shi a shoulders din ta, duka fita, nan suka hadu da su Hafsat, suka gaisa, su kama hanyar school. 〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️ Shi kuma Abdallah, tunda ya dawo daga aiki, bai wani yi hira dasu ( umma da Abba) ba, saboda yau daga aiki straight gida ya dawo. Yana ta aikin tunani, ya rasa daga inda zai fara, koya fada masu Umma ne ko a'a, nan wata zuciyar ta bashi wai ya fara fada ma yan'uwan sa, amma banda adda Wasila, saboda kanwar Dajjo ce, zata bata alamarin, so hamma Sudais da adda zee kawai suka rage ya fadama, tunda ya gama da side din adda Fadila. Haka dai ya ita sa'ke sa'ke a zuciyar sa, lokacin sallah yayi, suka tafi tare da Abba. Although iyayen sa sun yi noticing din shuru shurun da yake yi, basu wani damu ba, saboda daya dawo, ce wa yayi, shi ya gaji sosai, so suma basu wani dame shi ba. Da suka dawo daga sallan Isha shi da Abba, dinning straight suka nufa, nan ya je kitchen, ya taimaka ma Umma, har suka yi arranging din dinning, suka ci abincin su in peace, ba hayaniya. Da suka gama ma, ya kwashe plates, ya kai kitchen, shi ma yaje ya same su a parlor, dan ya masu sai da safe. Daya shiga parlorn, Umma da Abba na zaune, suna kallon Islam channel, sai yace "Umma na, Abba na, sai da safen ku." "Sai da safe kuma? Yau din ba hira ne, ko gajiyan ne?" Abba ya tambaya. "Toh shi ne nima na gani ai, wani irin gajiya ne haka?" Umma ma ta tambaye shi. "Normal gajiya ne fa, am just tired ne kawai, and I will like to rest." Abdallah ya fada. "Toh shikenan Allah ya tashe mu lafiya." Umma da Abba suka fada. "Amin ya amsa masu, ya koma daki, alokacin ya kira Mide, suka yi magana. Da suka gama waya, ya fara tunani, hanya tayi trusting din shi on these kuwa, hanya ba gani take kaman baya son ta ba? Ya ilahi, this is not easy at all, he is trying to do everything in his power, yaga bata samu matsala da iyayen sa da yayyin sa ba. Indai na sauran family ne, shi bai damu ba, amma iyayen sa are a big part of his life, and he will like them to accept what he wants without problem, amma in suka ki, ya shiga uku, dan bazai so saba ma su ba. Ahaka ya ita tunani, har ya fara jin barci, ya tashi yayi alwala, ya dawo ya kwanta akan gadon sa, yayi azkar, bai san lokacin da barci barawo ya dauke shi ba. Cikin dare, ya tashi, ya ita nafils, yana ta addu'a, Allah ya taimake shi, Allah yasa soyayyan su yayi winning, kar Allah yasa a raba su, Allah yasa siblings din sa da iyayen sa su yi accepting din su. Haka ya ita addu'a harda hawaye. Da lokacin fajr yayi, suka hada hanya suka tafi masjid tare. Da suka dawo, ya fara shirin aiki, saboda yana morning duty ne, ya shirya cikin suit, ya dau briefcase din sa, da coat din sa, ya shiga kitchen, ya hada ma kan sa shayi, ya zauna a dinning ya shanye, ya dauki lunch din sa, sannan ya je dakin su Umma ya sallame su, daga nan, ya tafi asibiti straight. ```Thanks for reading, nasan pejin yayi kadan, kuyi maneji please. ``` Comment Like & Share. ~Zeexee ce~ 🖊️🖊️🖊️ [8/30, 1:21 PM] Abokiyar Fight💜💖: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 *BANBANCIN KABILA* _(Short story)_ 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 *TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION* *_🔱((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))_* *T.W.A* *WRITTEN BY ZAYNAB* _(zeexee)_ MARUBUCIYAR *-RAYUWAR HUSNA* *-MAHAKURCI MAWADACI* _(2020)_ ```Dedicating this chapter to zeexee's novel group one and two, I love you guys so much, Allah ya bar mun ku.``` 3️⃣1️⃣&3️⃣2️⃣ _Bismillah_ *BAYAN SATI BIYU* "Mun yi magana da adda Zee, kuma kin san surprising thing din?" Ya tambaya. "A'a ban sani ba, sai ka fada." "Ina fada mata, tace mashaAllah, at least someone in our family has liver." Ya fada yana dariya, itama ta fashe da dariya. "Wato kai ne first to break the rules." "Exactly, haka hamma ma ya fada, wai zasu bani award." "Gaskiya kam ya kamata." Ta fada. "Hmm, kin san me?" Ya tambaye ta. "A'a." Ta amsa. "Naji dadi lokacin dana kira Hakeem, kuma ya mun magana with respect, amma fa yayi warning dina, wai in na sake na bari aka wulakanta ki, ko kuma na saki kuka, toh indai shi ya ji, sai ya manta da cewa na girme sa, shi zai mun tatas." Abdallah ya fada yana dariya. "Haba! Gaskiya ne, ashe yana so na, baya son bacin rai na." Olamide ma ta fada tana murmushi kaman yana ganin ta. "Gaskiya yana mugun son ki, ya mun warning fa da yawa, wasu are a secret." "Toh ai tsakani na da kai ba secrets." Olamide ta fada. "Haqqun babu, amma wannan tsakani na da junior bro dina ne." Abdallah ya fada yana danna dariyar sa. "Toh shikenan, ai nima ina da snr bro yanzu, ga snr sisters." "Oho dai, nima ina da junior sis ai." Abdallah ya fada. "Ca'an ta matse maku. Ni dai yanzu su Abba suka rage a picture din, yaushe zaka masu magana." Olamide ta fada worryingly. "Me kike ci na baka na zuba ne sweety, kinga yanzu yayyi na sun yarda, kuma they are in support, kinga na su Umma minor ne, ga adda Wasila kuma, amma karki damu zamu yi maganin ta." Ya fada "Na ji, amma wallahi ina tsoro. Athough mummy ta yarda, bata da wani matsala, amma kasan without su Abba, our relationship is still in the root, shi yasa na damu, ina son in san position din relationship din mu." Tana gama magana ta numfasa. "Kar ki damu, bana son inga ki cikin damuwa, kawai mu ci gaba da addu'a, sannan face your book, kinga kun fara test, ba zan so ki samu matsala ba, cause I won't be happy about that." Abdallah ya fada seriously. "Toh naji, amma gaskiya hankali na bazai kwanta ba sai naji reaction din su suma." Olamide ta fada. "Kar ki damu, keh dai ki ci gaba da yin addu'a, everything will be alright, In Sha Allah kaman yanda muka yi nasara akan sauran, haka zamu yi nasara akan su Abba ma." Abdallah ya fada. "Amin. Kaga gobe ina da test, bari inyi karatu." Olamide ta fada. "Okay toh, Allah ya baku sa'a ke da habibty, ayi karatu fa da kyau, amma kar kiyi stressing din kan ki, sannan kuma ki kwantar hankalin ki, everything will ba alright In Sha Allah." Abdallah ya fada in a comforting way. "In Sha Allah naji, kar ka damu, zan yi focusing." "Yauwa Olami. Bari in bar ki kiyi karatu, sai fijir yide am, meaning good night my love." "Good night, Allah ya tashe mu lafiya." Olamide ta fada, sannan ta kashe wayan. Ran da Olamide ta fada ma Mummy, Mummy taji dadi sosai, dan Olamide bata taba mata maganan saurayi ba, she was so happy, especially ma data ce he is ready for marriage, no wastage of time. Lokacin da ta fada mata bafulatani ne, Olamide was somehow expecting ta nuna damuwa, but to her surprise, bata ce komai ba, she was just so happy. Data fada ma Hakeem ma, he was happy, yayi supporting din ta. Da suka yi waya da Abdallah, ta fada mai, yaji dadi sosai a ranan, yana ta gode ma Allah, bai iya rufe baki ba, yana ta murna. Nan yace ta bashi numbern Hakeem, ta ce mai zata tura mai. Suna gama waya, ta tura mai, ta kira Hakeem ma ta fada mai. Tana cikin tunani, taji hannun mutum a fuskan ta, sai ta zabura, Nafisa ta fashe da dariya, tace " matsoraciya, toh ni ne, wani irin tunani kike haka." "Bakomai, am just thinking of how me and ifemi are making progress in our relationship." Olamide ta fada tana hugging din Nafisa. "That's good, Allah ya bar ku tare, am really happy you guys are making a progress, yanzu dai hankalin ki ya fara kwantawa." Nafisa ta fada. "Ae a'a, ae saboda mummy bata da wani objection, sun zama friends da Hakeem, yayyin sa suna so na. A'a, saboda iyayen sa basu sani bako, bamu san me decision din su ba, are they going to like me or not." Olamide ta fada disturbed. "Ki daina damun kan ki, yanda na sauran yayi sauki, haka nasu ma zai yi sauki In Sha Allah." Nafisa ta fada tana murmushi. "Allah yasa, amma wallahi hankali na ya ki kwantawa, duk da cewa shi ma yana kwantar mun da hankali, amma wallahi hankali na yaki kwantawa." Olamide ta fada. "Kar ki damu, ki ci gaba da addu'a, yanda aka samu na sauran a sauwake, haka na su ma In Sha Allahu." Nafisa ta fada. "Toh naji habibtyn Mide, na gode sosai da kulawan ki gare ni, Allah ya bar mu tare." Olamide ta fada tana hugging din ta. "No godiya. Sannan dan Allah muyi focusing akan karatun mu, kinga fa har an fara test, kar mu zo muyi slacking please." Nafisa ta fada. "In Sha Allah, success is our's." Haka suka fara karatun test din su, cikin kwanciyan hankali, da suka gaji, suka kwanta barci, da niyan zasu tashi cikin dare su ci gaba. 〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️ Da suka gama waya da Olamide, sai yaji hankalin shi ya dan kwanta, saboda ya samu ya dan kwantar mata da na ta, amma gaskiya shi ma bazai yi karya ba, hankalin shi bai wani kwanta ba, ji yake kaman ba zasu yarda ba, gashi su suka ce mai ya auri koma waye, indai ta kwanta mai, amma kuma sai ya ji hankalin sa bai kwanta ba. Yana ta tunani kala kala. Amma tunda yana son ta, yana iya yuwuwa su yarda, gashi ai sun san Ustaz ma (Abokin sa, da suka hadu lokacin da yaje serving), kuma sunce yana burge su, then it will be easier, balle ma ba a garin yarbawa ta tashi ba, inma a garin ta tashi, it's still the same, mutum mutum ne, kuma Allah ya hallice mu duka, kuma a lokacin daya hallice mu, bai ce wani ya fi wani ba, inba muminai da suka fi kusanta dashi ba. Allah said he created us in different tribes, different colours, different nations, e.t.c, the who are we to argue, bamu da ikon nuna babanci tsakanin junan mu, amma Ina'a, mun bari cultural ethics, cultural norms din mu da values, sun bata mana tunani. Da iyaye zasu hada hannu, su gane, su bar yaran su, su auri wanda suke so, indai ta/ya na da hali, kuma ga addini, toh za'a samu zaman lafiya sosai. Amma yanzu kam addu'an shi bai wuci ace iyayen sa basu cikin iyayen da suke toya hakkin yaran su saboda *BANBANCIN KABILA* ba, Allah yasa suyi accepting din decision din sa whole hearted, Allah yasa su so choice din sa, kar su toye mai hakkin sa, saboda idan haka ya faru, toh fa zai shiga cikin babban matsala. Yanzu dai zai fada ma yayyin sa ne tukun, inma hamma Sudais, da Adda Fadi zasu zo ranan ne, su ma su sa baki, sai suyi fixing din date, su hadu a gida su fada masu. Gashi ma Allah yayi, jibi Friday, kuma dukan su ke zuwa, amma yaga adda Wasila ma ta fara zuwa, kar ta zo tace an ware ta, why not su bari Saturday ko Sunday, zai fi. Haka ya ita tunani, har barci barawo ya dauke shi. Cikin dare, ya tashi ya shiga toilet, yayi alwala, ya koma daki ya shimfida sallaya, ya fara nafil, yana yi yana addu'a, Allah ya basu nasara, saboda idan su umma suka yarda, then bukatan su ya biya, kawu Dajjo kuma zasu san yanda zasu yi da shi. Bai daina nafil ba, tun 3:00am daya tashi, sai daya ga lokacin fajr ya kusa, yayi raka'a taini fajr, kafun ya fita parlor, nan ya jira Abba, suka tafi masjid tare. Da suka dawo, yayi morning routine din sa, ya shirya cikin suit, farin lab coat din sa a hannu, ya fita ya je dinning, ya samu Umma ta dafa mai yam and egg sauce (miyan kwai), sai kuma ga tea, amma bata dafa mai lunch din da zai kai wajan aiki ba. Sai yayi deciding, ya kai abincin wajan aiki, ya kada shayin, yayi toasting din bread. Daya gama, ya shiga dakin iyayen sa, ya masu gaisuwa, kafun ya sallame su, suka mai addu'a, kafun ya koma ya dauki briefcase din sa, da farin lab coat din sa, ya fita waje ya dan yi warming din mota, kafun, ya fara driving, yayi horn mai gadi ya bude, sai asibiti. 〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️ By 3:20am, su Olamide suka tashi, suka yi alwala, suka yi nafila bibbiyu, suka yi addu'a, kafun suka kara jawo handouts din su, da jottern su, saboda idan suna da lectures, suna dan jotting, sai kuma wani extra jottern da suke jotting din duk abun da suka karanta. Suna ta karatu, suna daukan break, suna nafil, har lokacin salatul fajr ya kusa, suka yi raka'a taini fajr, kafun suka yi sallah, tunda test din sai 11am, suka koma barci for sometimes, kafun suka sake tashi, suka gyara dakin su, Olamide ta girka masu breakfast, daman ita keda girki. Da suka gama ci, Nafisa ta yi wanke wanke, Olamide kuma ta shiga wanka. Tana gamawa, yayi daidai da Nafisa ta gama wanke wanke, itama ta shiga wanka. By 10:30am, suka bar gida, suka tafi cikin campus. Suna sauka, kiran Nabila ya shigo ma Olamide. "Assalamu alaikumu!" Olamide ta fada. "Waalaikumus salaam. Ina kuke ne?" Nabila ta tambaya. "Yanzun muka iso, muna ma sallaman mai keke ne, ina kike?" Olamide ta tambaye ta. "Gani a karkarshe bishiyan da muka saba zama." Nabila ta amsa. "Okay toh gamu nan zuwa." Olamide ta fada, sai ta kashe wayan. Da suka gama sallaman mai keke, Nafisa ta tambaye ta, tace "ina tace take ?" "Wai tana karkarshin bishiyan da muke zama." Olamide ta amsa. "Okay." Nafisa ta fada. Suka je suka same ta a inda ta fada masu, suka mika na junan su hannu, suna sallama. "Kun san ban yi barci ba, kwana nayi ina karatu, yaya ma yaki yin barci, wai in banyi barci ba shima bazai yi ba." Nabila ta fada. "Ban gane yayan ki bai yi barci ba, yaya Faeeq ko? Saboda mijin ki na Gombe, ya zaayi kice baiyi barci ba." Nafisa ta fada. "Miji na mana, after every 30mins yake kira na, gashi yana morning duty ne, kar Allah yasa yaje yana gengedi a office."Nabila ta fada. Maganan ta ya basu dariya, sai Olamide tace "yayi mana highest in yaga bazai iya daurewa ba, ya shiga wani ward ya kwanta." Duk suka kara fashewa da dariya. Da Nabila taga dariyan ba mai karewa bane, tace "toh ya ishe ku, ku daina ma heartbeat dina dariya." "Oho dai mun dai yi." Nafisa ta fada tana mata gwalo. Zata daki Nafisa da wasa kenan, Olamide tace "kuzo mu tafi inda za'ayi test fa, kar muzo muyi missing. Inya so ma in muka isa, sai ku ci gaba da dukan juna." Da suka isa inda za'ayi test din, har an fara shiga, suma suka yi joining din queue, aka rarraba su, kuma ga two seats interval tsakanin dukan su. Test din yayi hot sosai, duk wanda ya fito, sai yayi complain. Nafisa ta fara fitowa, sai Nabila, Olamide ce last. "Kai habibty, nayi zaton ba zaki fito ba". Nafisa ta fada. "Ko ni, nayi zaton sai kinga karke pen din ki ne." Nabila ma ta fada. "Ae din, koma meye." Olamide ta fada tana murguda masu baki. "Kuga fa muje muyi sallah da wuri, saboda mu samu gaba a hall din da zamu yi wannan lectures din, kunga dai mutani dayawa sun zo test, haka za'ayi cunkoso a lectures ma yau." Nabila ta fada. "Toh suka amsa mata." Nasan maybe wasu are lost, basu gane me Nabila ta zo yi ba a wannan pejin. Kaman yanda dai na fada a baya, cewa bayan bikin ta da two weeks zata dawo, domin ta ci gaba da karatu. Da suka idar, suka nufa hanyan hall din lectures din su, suna tafiya cikin sauri. Luckily for them, sun samu space a gaba, saboda mutani basu fara shigowa ba sosai, suka samu wuri suka zauna su uku. 〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️ Da Abdallah ya isa asibiti, ya je yayi signing, sannan ya shiga office din sa, ya fara aiki, amma hankalin sa baya kwance, yana ta tunani kala kala, da kyar ya samu yayi aikin ranan. Da suka yi closing, su uku (Abdallah, Farouq and Asim) suka hadu a karkashin wani bishiya, duk suka zauna a saman benci. Sai Asim yace "Abdallah, yana ga yau din nan, kaman hankalin ka a tashe yake?" "Gaskiya I noticed that too. I hope dai ba akan Olamide bane?" Farouq ya tambaya. "Ni kam, tun daka hadu da ita, yau kana dariya, gobe kuma hankali a tashe." Asim ya fada worried. "Ba zaku gane ba wallahi. Ni kadai na san yanda nake son ta, ni kadai na san yanda soyayyan ta ya gama mamaye zuciya na, wallahi ina son ta fiye da yanda kuke misali, ina son ta, ina son ta, ina son ta." Abdallah ya fada. "Then what is the problem?" Asim ya tambaye shi. "Exactly, meye matsalan?" Farouq ma ya tambaya. Sanda Abdallah ya numfasa, ya ce "matsalan shi ne ban san yanda zan yi confronting din su Abba ba da wannan maganan ba, sannan ina tsoron amsan su. Wallahi ina ji a jiki na kaman ba zasu yarda ba, ina ji kaman zasu raba ni da masoyiya ta, kuma in aka yi haka, ba karamin cutar dani aka yi ba, dan koma wa zan zo in aura, indai ba ita ba, sai dai muyi auren, ba dan naso ba." Abdallah ya fada, idanuwan sa sun yi ja'a. Da mace ne, data yi kuka, amma tunda namiji ne, yana ta kokarin dannewa, saboda shi kadai yasan abun da yake ji. "Hmmmm this is serious. Amma baka ce mana adda zee da hamma Sudais ma sun yi accepting din relationship din ku ba, then itama mahaifiyar ta ma tayi accepting, sannan kuna communicating da kanin ta, toh ai kunyi mai wuyan, am pretty sure su abba ma baza su zama problem ba In Sha Allah, ka daina damun kan ka please." Farouq ya fada. "Yes please, ka kwantar da hankalin ka, Olamide taka ce In Sha Allahu, yanda Nafisa ma tawa ce da yardan Allah." Asim ya fada yana murmushi. "Na gode maku sosai, Allah ya bar mu tare. Amma kun san me, ko ita ma hankalin ta a tashe yake, wai tana tsoro, and have been trying to make her cool her mind down. Kuma In Sha Allahu ran Saturday ko sunday nake son nida su hamma Sudais da adda Fadila mu fada masu, ku taya mu da addu'a, Allah yasa su yarda. "Amin kar ka damu, In Sha Allahu zasu yarda. Kuma ka cigaba da kwantar mata da hankali ita ma." Farouq ya fada. "Zamu taya ka da addu'a, your love will win In Sha Allah, and it will be an eye opener to other parents with this character, su abba zasu sa other parents su yi realising cewa tribe is not a fault in marriage In Sha Allah, now cheer up young man." Asim ya fada. "Na gode maku, Allah ya bar mu tare." Abdallah ya fada. "Amin suka amsa mai." 〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️ Da su Olamide suka tashi, driver din gidan su Nabila ya zo daukan su, ya sauke su Nafisa har gida, sannan ya wuce da Nabila gida. Su Olamide sun mugun gaji, duk abun da suke, a gajiye suke yin shi. ```Thanks for reading.``` Comment Like & Share. ~Zeexee ce~ 🖊️🖊️🖊️ [8/30, 1:21 PM] Abokiyar Fight💜💖: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 *BANBANCIN KABILA* _(Short story)_ 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 *TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION* *_🔱((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))_* *T.W.A* *WRITTEN BY ZAYNAB* _(zeexee)_ MARUBUCIYAR *-RAYUWAR HUSNA* *-MAHAKURCI MAWADACI* _(2020)_ 3️⃣5️⃣&3️⃣6️⃣ _Bismillah_ "Na samu wace nake so." Abdallah ya fada, kan sa a kasa. "MashaAllah, shi ne sai ka wani kira yayyin ka?" Umma ta fada. "Toh ai shi ne, I don't see the need for this." Abba ya fada. "There is need for it." Abdallah ya kara fada. "Then what is it." Abba ya tambaye shi. "Gaskiya dai yarinyan na da hankali, ga kamun kai, ga addini, she is very loving. Ai sun hadu da adda Fadila lokacin bikin Farouq, kuma she can testify to her character." Abdallah ya fada. "Yes I can, tana da hankali sosai wallahi, data zo gida na, kaman na hadiye ta, she is so loving." Adda Fadi ta fada. "I don't still see the need for you guys coming here." Abba ya fada. "Kai! Abba kai dai be patient. Amma dan Allah zan so ku duba alamarin nan da kyau kafun ku bada amsa." Hamma Sudais ya fada. "Toh muna sauraron ku." Umma ta fada. "Toh da farko dai ba a Gombe take ba, kuma, kuma, kuma." "Kuma me?" Umma ta tambaya. "Uhmm bayarbiya ce, amma tashin arewa." Abdallah ya fada kan sa akasa. Ai umma da abba, sun ji maganan ne kaman saukan aradu. Ji suka yi kaman an zuba masu ruwan sanyi, sai kallon Abdallah suke. Da Abdallah ya ji shuru yayi yawa, sai ya kalli yayin sa pleadingly, su ma su sa mai baki. "Abba yana ji kun yi shuru ne, gaskiya according to what the both of them told me, tana da hankali sosai, gashi ma dana ga hoton ta, I thought ma Fulani ce, ba zaku ma san bayarbiya bace." Hamma Sudais ya fada. "Umma! Abba! Dan Allah say something, am sure zaku so ta, tana da hankali sosai wallahi, she is every sister's dream for her brother, and she is also a gem every house hold wants." Adda Fadi ta fada. "Me kuke son mu fada, ai wannan maganan ya fi karfin mu. So kuke a dinga zagin mu cikin family kullum, ku kenan burin ku a dinga zagin abban ku ako wani family meeting?" Umma ta fada. "A'a, kwanciyan hankalin ku nake nema, kuma kullum ina cikin neman yanda zan faranta maku rai." Abdallah ya fada. "Kana son ka faranta mana shi ne kake son ka kawo mana yarinya marasa dabi'a cikin gida, shi ne ka ke neman yanda zaka zubar ma mahaifin ka dan sauran mutuncin shi da familyn ku suke gani, kana son faranta mana, shi ne kake neman sa mana hawan jini? Toh ka sani ba'a gidan nan ba." Umma ta fada ta tashi daga inda take zaune, shi ma abba ya tashi, domin shi yama rasa abun da zai ce. Su Abdallah na ganin iyayen su sun tashi, suma suka taso da gudu. Abdallah da hamma Sudais suka je wajan abba, ita kuma adda Fadi, ta je wajan umma. "DanAllah abba kayi magana, wallahi ina son ta, kuma tana so na, gashi tana da hankali, kuma tana da tabi'a mai kyau. Ku bata chance, zaku ji dadin ta." Abdallah ya fada. "Wallahi umma tana da dabi'a. Ki bar ganin bayarbiya ce, tama fi wasu fulanin hankali. Wallahi umma zaki ji dadin ta, dan Allah ku ba soyayyan su chance dan Allah." Adda fadi ta fada. Da umma ta wani harare ta, ta cire hannayen ta a jikin ta, ta ce "in kika gama, ki wuce gida, ki gaida mun namesake dina da Irfan." Umma na gama magana, ta wuce dakin ta. Shima abba, duk rokon da su Abdallah suke yi, sai shiga ya ke ta kunne dama, yana fita a na hagu, dan daman sun rike shi ne, sai ya balla hannayen su, cikin sukuni ya bar wajan. Zai bar parlorn kenan, Abdallah yace "kar ka manta, ku kuka ce kowa na samu, indai ta zauna mun, then you guys will support my decision." Abdallah ya fada idonuwan sa jazur. Abba bai ma bashi amsa ba, ya bar parlorn, ya wuce daki. Su Umma na barin dakin, Abdallah ya tsuguna kasa, yaji jiri na daukan shi, ya dafa kai. Su Hamma Sudais da Adda Fadila suka zo kansa da gudu. "Common be a man, kayi hakauri ka basu time. Kasan basu taba ganin irin haka ba a family, kai ne na farko, so they have to think, kafun su iya baka amsa." Adda Fadila ta fada. "Gaskiya kam, you should give them time, kaman yanda Fadila ta fada, ka kyale su for sometimes, In Sha Allahu everything will be alright, yanzu kam they are in shock." Hamma Sudais ya fada. Suna cikin lallaban shi, wayar sa ya fara ringing. Da kyar ya iya ciro wayan daga aljihun sa, ya duba screen, yaga sunan Adda Zaynab ya fito. Da kyar ya iya daga kiran. Muryar sa kaman zai yi kuka, ya ce "assalamu alaikum adda!" Adda Fadila ta mai signal ya sa a speaker, sai ya sa. "Waalaikumus salaam mijin Faiza, amma ya naji muryar ka haka." Sanda Abdallah yayi nishi, sai yace " Adda am not good at all, nothing went well. Gwanda Umma ma tayi magana, tayi objecting. Amma kin ga abba, bai ce komai ba, he just stood up and left." Abdallah ya fada idanuwan sa cike da ruwa. "Subhanallah! Ya za'ayi kenan? Ina hamma da Fadila ma tukun?" Ta tambaya. "Gamu." Su biyu suka amsa. "Me kuke yi da baku sa baki ba." Adda Zaynab ta tambaya. "Ban gane me muke ba, ke kin tambaye shi kuma yace maki bamu sa baki ba?" Hamma Sudais ya tambaye ta. "Kayi hakuri Hamma, amma dai you all know it that I hate to see auta miserable, that why I said that. Amma toh yanzu ba abun da zamu iya yi ne? Ko in masu magana ne?" Adda Zaynab ta fada disturbed. "You should, ala in suka ga kema kin sa baki, maybe su yarda. Dan yanzu kam basu ma son su ga fuskokin mu, dan umma harta sallame ni." Adda fadi ta fada. "You should also try your luck." Hamma ya fada, sai ya kalli Abdallah, yace " we are with you, everything will be alright In Sha Allah." "Yes we are." Adda Zee da Adda fadi suka fada. "Nagode maku sosai, Allah ya saka maku, ya raya zuriya, ya hada mu duka a jannah." Abdallah ya fada da jajjayen idanuwan sa. "Amin amin autas." Suka fada. "Toh auta, anjima zan masu magana, kaga by that time maybe sun sauko." Adda Zaynab ta fada. "Toh. Allah yasa su ji naki." Abdallah ya fada. "Amin" yayyin sa suka amsa, adda Zee kuma tayi hanging up. Su Hamma Sudais sun kai 30mins, suna kwantar ma Abdallah hankali, da kyar suka samu ya daidaita. Da suka wuce, shima ya koma daki, ya hau kan gado, ya jingina da pillow, sai tunanin Olamide ya fado mai. Me zai ce mata yanzu in suna waya? Inma ya fada mata, hanya bai zai yi loosing din ta ba? Haka ya ita tunani, har lokacin sallah yayi, yayi sallah acikin dakin shi. Daya idar, yana cikin addu'a, wayar sa ya fara ringing. Ya duba wanda ke kira, sai ya ga sunan Olamide (my qalbi) boldly akan screen, nan ya fara jin heart din sa na beating, yama rasa mai zai yi, ya daga ne ko ya bari. 〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️ Sanda Nafisa ta bari bayan 30mins, sai taje kusa da Olamide akan katifan ta, Olamide na ganin ta, ta juya fuska. Yanzu kam tama daina tunanin yanda iyayen Abdallah zasu yi reacting, haushin Nafisa take kawai, saboda ita baza ta iya fada mata haka ba, ko suggesting din shi baza ta yi ba. Da Nafisa taga ta juya kai, sai ta juyar mata da kai tana kallon ta, tace "Allah sarki habibty, wallahi I care for you, I care about everything about you, bana son ganin hawayen ki. Kuma na fadi hakan ne saboda I really care about you. Kuma indai kin saurare ni da kyau, toh bance kuyi breakup ba, cewa nayi da baki son shi yanda kike son shi haka, dana ce maki kuyi breakup." "Toh naji ki, sai da safe." Olamide ta fada, ta juyar da fuskan ta zuwa dayan gefen. "Haba habibtyn Fisa, I really care about you, shi yasa kika ga na fada haka. Wallahi na tsani inga kina cikin damuwa, balle azo ga kuka, amma ina mai baki hakuri, kiyi hakuri da wannan stupid friend din naki, bazan kara ba." Nafisa fada. "Toh naji." Olamide ta fada. "Baki ce kin hakura ba." Nafisa ta fada. "Ban hakura ba." Olamide ta fada. "Haba habibty na, wallahi I care about you, kin ga idan kika ci gaba da haka, education din ki ma zai yi slacking. Bana son situation din da zaki dinga slacking a komai." Nafisa ta fada. "Toh naji na hakura, shikenan?" Olamide ta fada ta juya kai tana kallon ta. "A'a, ina son ki hakuran gaske, ba irin wannan ba." Nafisa ta fada a shgwabe. "Wani irin hakuri ne yafi wannan, har ina amsa maki, toh na hakura, amma I don't want to talk to you." Olamide ta fada, ta tashi ta zauna. "Haba habibty, so kike inyi ciwo, ya zaki ce kin hakura, amma baki son yin magana da ni, ki tuna fa I love you more than you can imagine, your happiness is my, and your sadness worries me too." Nafisa ta fada kaman zata yi kuka. "I know you love me, and I also love you too, you mean a lot to me, but you should have consoled me, bawai ki dinga bani irin advice din nan ba at that moment. Wallahi alokacin nan, comfort nake so, ina bukatan ki kwantar mun da hankali ne. Ko kin san idan iyayen sa basu yarda ba, hakan na iya zama sanadiyan rabuwan mu, so I need comfort, not that type of advice. You can advice me that any day, banzan yi fushi ba, but I was hurt when you deed it at that time." Alokacin Olamide tana magana tana kuka. "Ban san abun daya sa nake da saurin kuka ba, amma this is me." Olamide ta kara fada. Nafisa bata san lokacin da ta yi hugging din ta ba, ta ce "am very sorry habibty, bazan kara ba, I just said it, ban yi tunani ba, danAllah kiyi hakuri." Nafisa ta fada. "Nayi, amma Fisa na dauke ki as sister ta, ko kin mun laifi, bana iya fushi dake." Olamide ta fada. "Am very sorry, banzan kara ba." Nafisa ta fada. Da suka gama koke koken su, su dan yi hira, Nafisa ta ita kwantar mata hankali, su kayi barci. Da suka tashi da safe, suka yi dutyn su, suna ta hira, ranan ya kasance Saturday, gashi basu da lectures, so suna ta huta duka gajiyan da suka yi tun monday. Ana cikin haka, Abdallah ya kira ta, ya sanar mata da cewa bayan asr zasu fada masu Abba, tun lokacin mood din ta ya canza, amma tana ta kokarin danne shi, not to make anyone around her worried. Around 3 data ji shuru, sai Nafisa ta bata advice wai ta kira shi, da tana ta contemplating. Sai bayan sallan asr ta yi concluding kawai ta kira shi, kawai ta kira shi. 〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️ Sanda wayan ya kusan tsinkewa, ya daga. Daya daga bai yi magana ba, sanda ta ita sallama, kafun ya yi clearing din muryar sa kafun ya amsa. "Baka amsa mun ba tun dazu ina ta salama." Olamide ta fada. "Kiyi hakuri, yanzu na tashi daga barci shi yasa." Abdallah ya fada. Allah ya ga baya son yin karya, amma ya ya iya, ba zai iya fada mata abun daya faru ba. "Toh yayi, shi ne ka bar ni da damuwa ko?" Ta tambaye shi. "Kiyi hakuri, su adda could not make it, shi yasa muka chanza timing din, sai duk ran da they are free again." Abdallah ya fada. "And you didn't bother telling me. Kasan yanda na damu kuwa? Gashi instead ace muna progressing, sai baya mu ke zuwa. Gaskiya ni bazan iya irin relationship din nan ba, our parents need to know about us. But if you don't want that, we can call it a quit." Olamide ta fada, sannan ta kashe wayar. She was soo frustrated, ta rasa abun da yasa Abdallah yake mata haka. Shi ya sata agaba, sanda ta sanar ma mummy, amma ya sanar ma iyayen sa ya zama matsala. Shi kuma Abdallah, data kashe wayar, ya rasa yanda zai yi da rayuwar sa, the pressure is too much, ya rasa abun yi, ji yake kaman ma ace he is not Abdallah any more. ```Thanks for reading``` Comment Like & Share. ~Zeexee ce~ 🖊️🖊️🖊️ [8/30, 1:21 PM] Abokiyar Fight💜💖: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 *BANBANCIN KABILA* _(Short story)_ 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 *TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION* *_🔱((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))_* *T.W.A* *WRITTEN BY ZAYNAB* _(zeexee)_ MARUBUCIYAR *-RAYUWAR HUSNA* *-MAHAKURCI MAWADACI* _(2020)_ 3️⃣7️⃣&3️⃣8️⃣ _Bismillah_ Da su umma suka shiga ciki, Umma tace "wai ni alhaji me ke damun yaran nan ne in aka zo zancen aure?" "Ai kuma ba ni zaki tambaya ba Hajiya, su zaki tambaya. Ina ganin sakewan dana masu ne yayi yawa." Abba ya fada rai abace. "Gaskiya kam, sai ko wannan su zai yi aure ake meeting akan mu kullum." Umma ta fada. "Hmmm bama wannan ba. Kin san me Abdallah ya fada?" Abba ya tambayi umma. "A'a alhaji." Umma ta amsa. "Kin tuna ran da na dawo nace baffa Dajjo ya mun maganan auren shi, kuma muka ce mai koma waya ya auro, in dai ta mai?" Ya tambaye ta. "Haqqun na tuna. Kar dai shiyasa ya nemo mana bayarbiya. Yarbawan da basu da tarbiyan?" "Shi nake gani nima ai, saboda da na kusan fita a parlor, yake cewa ai mun ce ya auri koma waye, indai ta zauna mai." Abba ya fada yayi tsaki. "Toh shine yaje ya samo bayarbiya, yarbawan da kowa ya san halin su? Be ma nemi yar arewa ba, yar kudu ya nemo." Umma ta fada takaici na kama ta. "Ai shi ne. Ni fa when we said that, I only thought about someone from arewa, me zamu yi da yar kudu?" Abba ya fada ya dafa kai. "Ai shi ne na gani. Me ma ya kai tunanin sa zuwa nan?" Umma ta fada. "Oho masa." Abba ya fada. "Ni kam gaskiya bazan yarda ba, saboda gaskiya yanda mutum ke jin labarin yarbawa, they are not people we can live with." Umma ta fada. "Gaskiya they are not people to live with." Abba ya fada yana kada kai. "At all. Kuma kar mu yarda gaskiya alhaji, saboda ban zan yarda ace mu zama abun zagi a gari ba." Umma ta fada. "Ai baza mu yarda ba, ya ma san inda dare ya ma sa." Abba ya Fada. "Ai kuwa." Umma ta fada. Haka su Abba da Umma suka ita maganganu. Abdallah ya kara kiran Olamide, bata daga ba, ya kira ta yafi sau bakwai amma ta ki dauka, sai ya kira Nafisa. Olamide ta tambaye ta ko shi ne, ta ce ae, Olamide tace mata kar ta daga. Har sau uku ya kira ta, itama bata daga ba. Although ta so dagawa, amma Olamide ta ki, tace kar ta daga, inba haka ba zasu yi fada. Ita kuma gudun kar kawar ta tayi fushi, ta ki dagawa, amma ta kuddura a ran ta, anjima zata kira shi. Rashin dagawan da suka yi, ya tada ma sa da hankali sosai, yaji ba abun da ke mai dadi. He felt so heart broken, ya rasa inda zai sa kan sa. Olamiden da ta kamata ta kwantar masa da hankali, ita ma tana fushi da shi. Aranan kam Abdallah ya rasa yanda zai yi da kan sa, dan su abba ma sun ki kula shi. Inma ya masu magana ba kula shi suke ba. Abun duniya duk yabi ya ishe shi, ji yake kaman ya je tsakiyan compound din gidan su, ya dinga ihu, ko zai dan ji relief. Bayan isha ya kira adda Fadila, yayi ringing sau uku, ta daga. "Assalamu alaikum auta." "Waalaikumus salaam. Wallahi tunda abun yau ya faru kuka koma gidajan ku ko, ke kadai kika mun magana normal. Ko qalbin Abdallah ma fushi take dani." Abdallah ya fada sadly. "Don't be sad brother, your fav sis na tare da kai in every situation. Ka fada ma qalbin ka abun daya faru ne? Indai ka fada ne, toh baka kyauta ba kwata kwata." Adda Fadi ta fada. "No, ban fada mata ba, yama zan fada mata irin wannan abun, ita da tsoron ta kenan, shi yasa tace na fada masu, mu san inda muka dosa." Ya fada weakly. "Kai ! Subhanallah, this is not good at all, gwanda ma da baka fada mata ba. Gashi tsoron ta yazo true, kuma am pretty sure in ta sani, maybe tace kuyi breakup. Kuma wallahi ba zan ga laifin ta ba, what is the need of staying in a relationship din da yan uwan guy din basu son ki. Amma yayi kyau da baka fada mata ba, maybe su zo su yarda in adda Zee ta masu magana. "Toh Allah yasa su yarda, saboda da ta kira ni, ta tambaya ko na fada masu Abba, sai na mata karya nace a'a, shi ne fa tayi fushi, wai ni na takura mata, har sanda ta fada ma mahaifiyar ta, amma ni in fada ma su Umma ya zama matsala. Wai ina mata wasa da hankali." Abdallah ya fada. "Allah sarki, ta matsu ne ta san level din relationship din ku, if it's going to make a progress or not. Amma it's still good da baka fada mata ba, muma sai muyi kokarin ganin su abba sun yarda, saboda gaskiya ni kam ina son ta, bazan iya jure rashin ka da ita ba, wallahi ta gama tafiya da zuciya na." Adda Fadila ta fada. "Da zuciyar ki ko nawa. Ai irin soyayyan da nake ma qalbi, in su abba suka hana ni ita na auri wata, toh ko min son da nake mata ba zai taba kai na qalbi na ba, saboda she owns my heart." Abdallah ya fada. "Allah sarki kani na, kar ka damu, komai zai yi daidai, ka kwantar da hankalin ka, saboda Olamide taka ce In Sha Allah." Adda Fadila ta fada. "Amin, nagode sosai da support din ku, Allah ya bar mun ku." Abdallah ya fada. "Amin amin." Adda Fadi ta fada. "Toh mu kwana lafiya, bari in kira qalbi na." Abdallah ya fada. "Toh, agaishe ta, mun ma dade bamu yi waya ba, maybe in kira ta gobe." Adda Fadi ta fada. "Okay. Dan Allah in kun yi waya, ki kara kwantar mata da hankali please, kice mata ta daina damuwa, very thing will be alright In Sha Allahu." Abdallah ya fada. "Toh naji, amma in kun yi waya, kai ma ka kwantar mata da hankali." "In Sha Allah. Bye." Abdallah ya fada. "Allah ya tashe mu lafiya, bye." Adda Fadila ta fada, sai ta kashe wayar. Da suka gama waya, sai ya nemo sunan qalbin sa, yana gani, zuciyar sa ya fara tsinkewa, Allah yasa dai ta daga. Yayi dialing din numbern, ya ita ringing baa daga ba, Olamide ta gani, ta ki dagawa, sanda ya kira sau uku, Nafisa tayi forcing din ta ta daga. Rai abace ta daga, tayi sallama. "Waalaikumus salaam qalbin na." Abdallah ya amsa sallaman ta. Sai kuma shuru ya biyo baya, ba wanda yayi magana acikin su, da abun ya ishi Mide, tace "daman ka kira ni ne kawai, ba dan kayi magana da ni ba ko? Toh na gode, bari in kashe....." Bai bari ta gama magana ba, ya ce " ba haka bane qalbi, wallahi I just became speechless ne, amma am sorry for the silence." Abdallah ya fada. "Toh. Ina jin ka." Olamide ta fada without emotion. "Daman na kira ne in baki hakuri qalbi na." Abdallah fada. "Hmm ifemi kenan, lokacin da zan fada ma mummy, ka sani a gaba, in dai fada. Amma ka fada masu abba ya gagara. Toh me kake son inyi, dole nayi fushi ai. Ni wallahi gani nake kaman kana wasa da hankali na ne kawai." Olamide ta fada. "Haba qalbi, me zai sa inyi wasa da hankalin ki, you are too specially in maki haka." Abdallah ya fada. "Am not! Because if I was ba zaka dinga mun haka ba. Kullum sai kace you love me, amma you are finding it hard ka fada ma su abba mu san inda muka dosa. Bana son situation din da zan zo in sake da yawa, su zo su ce basu son ka auri kabila." Olamide ta fada. "Kar ki damu masoyiya ta, hakan ba zai faru ba, ina son ki kara hakuri, nida siblings dina mun na plan ne akan yanda zamu fada masu da baza'a samu damuwa ba." Abdallah ya fada. "Ni kam ban yarda ba, gani nake kaman kana wasa da hankali na ne kawai. Amma ba damuwa, I will be patient, but you should know, next time ba zan ji komai ba, we will just find our ways kawai." Olamide ta fada. "Hakan ma bazai taba faruwa ba In Sha Allah. Ki kwantar da hankalin ki please, saboda kwanciyan hankalin ki shi ne nawa." Abdallah ya fada. Da kyar ya samu ya shawo kan ta, har suka dan taba hira kadan kafun tace ta gaji barci take ji, suka yi sallama, ya kashe wayar. "Ya ilahi, Allah kaga niyya na, bana son yin karya, amma ya na iya, this is the only way I can keep the love of my life. Bana son situation din da zai raba ni da ita. Na san yanzu dai su Abba are in shock ne, amma they will come around, har su zo su yarda da soyayyan mu. Kuma In Sha Allah zan yi duk a bun daya kamata, har su zo su gane ina son qalbi na, kuma qalbi na nada hankali, ga illimin addini, ga dabi'a mai kyau, ga respect. Kuma ai ko wani yare nada salihi da dan iska, ba yarbawa kadai keda su ba. Nama rasa abun daya sa iyaye suke irin wannan tunanin, kuma na rasa abun dayasa aka sa ma yarbawa lakanin nan. Ya Allah please guide me through, I hope our love conquers." Abdallah ya fada yana thinking aloud. Haka ya ita tunani, har barci ya dauke shi. 〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️ Olamide kuwa da suka yi sallama ya kashe wayar, ta kalli Nafisa dake kwance kusa da ita, tace "na kasa yarda da shi, ina jin shi ajiki na kaman karya yake mun, kaman akwai abun da yake boye mun, saboda da safen nan fa ya kira ni ya fada mun wai bayan zuhur zasu hadu, amma in kira sa bayan asr kuma yace mun basu hadu ba, wani wai yana barci ne, kuma muryar sa bai yi kamada wanda yayi barci ba sannan yanzu kuma yana wani ce mun wai suna planning din yanda zasu masu magana just imagine habibty, is this not suspicious?" Olamide ta fada. Ita kuma Nafisa inba kallon Mide ba, ba abun da take. "Habibty fa dake nake." Olamide ta fada tana daga mata gira. "Toh me zan ce?" Nafisa ta tambaye ta. "Mele." Olamide ta fada tana murguda mata baki. "Toh, amma you should trust him, relationships don't work without trust." Nafisa ta fada. "I know, but am just finding it hard, saboda yanda yake magana ma zaka san there is something he is hiding, but I will put my trust in Allah, dan na san he is the only one that will never disappoint me." Olamide ta fada. "Yes he is. Ki kwantar da hankalin ki kin jin bibtyn Fisa?" "Naji bibtyn Fa'iza." Suka ci gaba da hira, Nafisa na ta bata advice, har suka gaji, Nafisa ta koma kan katifan ta, kowannan su tayi barci. ```Thanks for reading and been patient, wallahi abubuwa suka mun yawa .``` Comment Like & Share. ~Zeexee ce~ 🖊️🖊️🖊️ [8/30, 1:21 PM] Abokiyar Fight💜💖: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 *BANBANCIN KABILA* _(Short story)_ 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 *TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION* *_🔱((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))_* *T.W.A* *WRITTEN BY ZAYNAB* _(zeexee)_ MARUBUCIYAR *-RAYUWAR HUSNA* *-MAHAKURCI MAWADACI* _(2020)_ ```Dedicating this chap to my sweet and lovely cousins aunty Jamila and Jamila. I love you guys sooo much💕💕💕💕❤❤❤❤❤.``` 3️⃣3️⃣&3️⃣4️⃣ _Bismillah_ Ranan Friday, tunda short day ne, Abdallah ya dawo da wuri, nan ya samu, har sisters din sa, da matar hamma Sudais da jikokin gidan duka sun zo, amma banda na adda zee, saboda basu countryn. Ya na fita daga motar sa, kananan yaran suka zo suna mai oyoyo, one after the other ya rinka daukan su. Manyan kuma, suka zo suna gaishe shi. Haka suka bi sa a baya, ya gaishe da kowa da kowa, kafun ya tafi dakin sa, saboda yayi wanka, sannan ya chanza kaya. Daya gama komai, sai ya koma parlor, ya samu kowannan su a parlor, suna hira. Ya kira baban cikin su, Jamila (yarinyar mijin Adda Wasila), ya mika mata leda cike da su chocolate, sweets, chewing gum, da dai sauran su, ya ce ta raba masu. Ya kalli umma a shagwabe ya ce "umman auta, ina jin yunwa fa". Adda Fadila na jin haka, ta ce "ai ba sai ka fada ma umma ba, ko ni sai ka fada min, bari in kawo maka. Anan zaka ci ko a dinning?" Ta tambaye shi. "Anan zan ci." Ya fada a shagwabe. Yana fadan haka, ta tashi, ta wuce kitchen, ta je kawo mai abinci. "Kai auta! A lan an kwaso gajiya ne ko?" Abba ya fada yaba shafa bayan sa. "Sosai abba na, na gaji." Abdallah ya amsa. "Sannu Uncle auta, ai kana kokari sosai." Aunty Aisha matar hamma Sudais ta fada. "Ni kam ku bar shagwaba shi, wai ku baku san ya isa ace yana da yara ko yaro ba ne da zaku dinga wani shagwaba shi kaman baby." Adda Wasila ta fada. "Ai shi ne, ji yanda kuke yi dashi." Umma ta fada, sai ta kalli Abdallah, ta ce "kai kuma ka tsaya a wajan a dinga maida ka yaro." Tana gama fadan gakan, sai ga Adda Fadila niki niki da Abincin Abdallah a kan tray, sai ta tura stool, tasa a gaban shi, kafun ta ajiye abinci, ta ce "A ci lafiya auta." Suna hada ido da Umma, taga irin hallon da take mata, sai ta kau da kai. Umma tace "ku kuka sani, in yaso ku maida shi dan shekara biyar." "A'a Hajiya ya ishe ki haka. Yaro ya kwaso gajiya, instead ki lallabe shi, kina kara mai gajiya akan gajiya. Ya samu masu mai kuma kina complain. Kar ki damu, inya yi aure, ya rage ni dake, zaki san value din auta. Ko auta." Abba ya fada yana kallon shi. "Sosai ma, idan na auri Ola...." Sai yayi shuru, ya ma manta, bai san lokacin da sunan ya fito daga bakin sa ba. "Ka auri wa?" Adda Wasila ta tambaya. "Babu, ina auri all my wives nake son fada." Abdallah ya fada yana murmushin dole. "All your wives kuma? Ashe mata da yawa zaka aura a rana daya." Umma ta fada. "Kai Umma, ai uncle auta ba haka yake ba, kawai dai wasa yake. Kuma ai yana da ikon auran matan hudu." Aunty Aisha ta fada. "Toh ai shi ne, in yaso ya aure su a rana daya, but the fact still remains, zaki yi missing din auta." Adda Fadila ta fada tana murmushi. Haka suka ita hira, Umma da adda Wasila na zolayan Abdallah, kafun shima hamma Sudais yazo, teams din suka cika 3-4, wannan team din na zolayan Abdallah, wayannan kuma na bada amsa. Daman idan 6:pm yayi, ko wannan su ke komawa gida. So by 5, Abdallah ya ma hamma Sudais da adda Fadi text, yace su hadu a balcony, shi zai yi kaman yayi fushi, ya fito, su kuma su biyo shi. Haka ko aka yi, adda Wasila na dukan shi a baya da wasa, ya hada rai, ya tashi ya bar wajan, suma suka biyo shi a baya. Da suka fita, suka yi dariya kasa kasa, hamma Sudais yace "toh me kake son fada mana ne, ka fada yanzu, kafun su ga mun dade, a fara suspecting din wani abu." "First of all, ina son in maku godiya for like her, na gode maku sosai, Allah ya saka maku da jannah." "Amin." Su biyu suka amsa. "Secondly, akan yandan zan fada masu abba ne, nace ko zaku zo ne gobe ko jibi, ku taya ni mu fada masu please." "Any day is okay with me, but zanyi preferring din Saturday more." Adda Fadi ta fada. "Toh muzo Saturday. Allah yasa su yarda, Allah ya sa ka auri Olamiden ka, they will be pleased and happy to accept your relationship In Sha Allah." Hamma Sudais ya fada. "Amin suka amsa tare." Sai suka koma ciki, aka ci gaba da hiran, da su. 6:pm nayi, alokacin sun taya Umma girka dinner, kuma suma sun ci, kafun ko wannan su ya ja motar sa ya bar gidan, amma banda adda Fadi, saboda ita bata dashi, so sanda ta jira mijin ta, ya zo ya dauke su, ita da yaran ta, kafun suma suka bar gidan. A rannan dai, Abdallah ya kwana ya na tunanin yanda gobe zai kasance in Allah ya kai mu da rai da lafiya, Allah yasa su yarda. Daya fada ma Mide ma lokacin da suke waya, ta nuna mai damuwa, yana ta kwantar ma da hankali, alhalin ko shi ma hankalin sa bai kwanta ba. 〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️ Da Abdallah ya kashe wayar, ta tashi da sauri, ta shiga toilet, ta yo alwala, ta fara nafls, saboda hankalin ta yaki kwatawa kwata kwata, sai taji kaman this phone call was there last goodbye, amma daya ita kwantar mata da hankali lokacin da suke waya, she felt a little bit alright, but still ba wai hankalin ta ya kwanta bane. Ta ita yin nafil, tana kuka, ya ilahi, she true loves Abdallah, but what will she do idan iyayen sa suka ki relationship din su, ina zata sa kan ta. Haka dai ta ita sallah tana kuka, tun kuka baya fita, har ya fara fita. Da Nafisa taji kaman tana kuka, sai ta bari sanda ta yi tayya, tayi sallama, kafun taje gaban ta, tace "what is it again habibty, wai me yasa almost every time idan kuka gama waya sai kin yi kuka, kuma idan akan iyayen sa ne, kar ki damu everything will be alright. Wallahi if not because you are already in love with him, dana yi advising din ki kuyi breakup haba what is it self, kullum ke kenan cikin tashin hankali, baki da natsuwa, kullum sai kuka. Ni kam idan relationship din nan ba zai sa ki dinga samun kwanciyan hankali ba, toh ki bari gaskiya." Da jajjayen idon ta ta kalli Nafisa ta ce "abun da zaki ce kenan?" Ta tambayi Nafisa hawaye na zuba a idon ta. "Ba haka bane, amma ni fa kwata kwata bana son inga hawayen ki." Nafisa ta fada tana share mata hawaye. Cikin jin haushi ta ce "ki kyale ni. Say the truth, tunda muke tare, na taba irin halin? "A'a, ni fa habibty, bance ki daina son shi ba, I said da baki son shi yanda kike son shi ba, dana baki advice kuyi breakup." Nafisa ta fada. "Shi yasa nace ki kyale ni, if you can't give me advice, just let me be. Ni kadai na san abun da nake ji, ni nasan irin son da nake masa, so if you can't be with me in this time of worry, then ki kyale ni." Olamide ta fada, sai ta tashi ta je ta kwanta akan katifan ta. Takaici duk ya bi ya dame ta. Nafisan data kamata ta kwantar mata da hankali, tana mata irin wannan maganganun. Ita kuma Nafisa, tama rasa abun fada, saboda Olamide bata fahimce ta ba. 〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️ Da Abdallah ya tashi, yayi routine din sa, yau din sai yaji duka jikin sa a mace, yana jin wani iri, Allah yasa yayi nasara, Allah yasa su Umma su yarda. Banyan zuhur suka ce zasu zo (hamma Sudais da adda Fadila), so ana idar da sallah, da suka dawo daga masjid da abba ya ji hankalin sa ya kara tashi, kawai ya yanke hunkuncin instead ya dinga tada hankalin sa, why not ya ita addu'a saboda du'a is the sword of every muslim, and with Allah everything will be alright. Da su hamma suka zo, sun samu umma da abba da Abdallah zaune a parlor. Da suka zauna, adda Fadila ta je ta kawo masu drinks ita da hamma, suka sha. Sanda suka bari sun yi nisa sosai da hira, kafun hamma Sudais yace " Abba, Umma, kuma kun san wannan zuwan mu kam da dalili, saboda jiya muka zo, kuma ace gamu kuma yau." "Tabbas, ina son ma in tambaye ku ne." Abba ya fada. " Abdallah ne yake da magana da ku, amma our presence is needed." Hamma ya kara fada. "Toh kai Abdallah, me kake son ka fada mana ne da har sai yayyin ka sun zo?" Umma ta fada "Daman, daman akwai. Abdallah ya kasa ci gaba da magana. "Kayi magana mana?" Umma ta fada. "Na samu wace .........." ```Thanks for reading, please kuyi maneji.``` Comment Like & Share. ~Zeexee ce~ 🖊️🖊️🖊️ [8/30, 1:21 PM] Abokiyar Fight💜💖: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 *BANBANCIN KABILA* _(Short story)_ 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 *TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION* *_🔱((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))_* *T.W.A* *WRITTEN BY ZAYNAB* _(zeexee)_ MARUBUCIYAR *-RAYUWAR HUSNA* *-MAHAKURCI MAWADACI* _(2020)_ 3️⃣9️⃣&4️⃣0️⃣ _Bismillah_ *BAYAN WATA DAYA* "Baza mu yarda ba and that is final." "Abba dan Allah, am begging you guys please." "Wai kai wani baza mu yardan ne baka gane ba?" "Dan Allah umma kar ku mun haka, one month kenan fa ina rokon ku, dan Allah, kuyi ma Allah da manzon sa ku yarda, wallahi Olamide is not like that, kuma yanda kuke cewa yarbawa basu da dabi'a haka ma wasu fulanin." Abdallah ya fada da hawaye a idon sa. "Toh masani fada mana, ka san ni da Abban ku bamu san komai ba." Umma ta fada. "Wallahi umma ba haka bane, am just trying to make you guys understand that's why. Dan Allah ku yafe mun indai magana na ya bata maku rai, amma dan Allah ku yarda da ni, wallahi bazan yi disappointing din ku ba." Abdallah ya fada. "Ka tashi ka fita kafun rai na ya kara baci inyi abun da dukan mu zamu yi regretting." Abba ya fada rai abace. Jiki a sanye Abdallah ya mike daga inda ya tsuguna, ya fita a dakin, hawaye na zuba shar shar a idon sa. Yana fita Abba ya ja wani irin tsakin da har Umma ta firgita. "DanAllah ka yi hakuri Alhaji, na rasa me yar yarbawan nan ta mai. Ala ma asiri ta mai, ka san yarbawa da asiri." Umma ta fada. "A'a Hajiya, kar ki fadi abun da baki sani ba. Ina jin zan neman mai yar aboki na ne kawai. Bana son auren hadi, amma he has left me with no choice." Abba ya fada. "Am in support, indai bai daddara ba, kawai ka neman mai wata acikin yaran aboka, zai fi mana da ya kawo mana yarinya marasa tarbiya." Umma ta fada. "That is what I will do kawai." Abba ya fada. Shi kuma Abdallah, daya shiga dakin sa, ya rufe kofan. Although ya kamata ace yana shirin zuwa aiki ne yanzu, but he has no energy for that, so sai ya ki Farouq, yace ya mai reporting cewa baya jin dadi. Ya zauna akan gadon sa, ya fara kuka, me yasa hakan ke faruwa da shi ne? Ba Allah ya hallice mu duka ba? Toh me yasa mutani ke haka ne? Me yasa mutani basu son yaran su na auran kabila ne haka? Haka ya ita tunani, yana hawaye. Daya ga hawayen sa baza su chanza komai ba, sai ya tashi ya shiga toilet, yayi alwala, ya fara nafl. Daya idar, ya fara tunanin abun da zai fada ma Olamide in sun yi waya. Gashi yau yace mata zai ma su Umma magana, and to make matters worst, tace this is the last time, saboda for one month yanzu ce mata yake bai samu time din fada masu ba, aiki ya mai yawa. Gaskiya he doesn't want to loss her, ya zai yi yanzu. Yana cikin tunani wani idea ya shigo mai, maybe ya fada mata, amma ba zai fada mata everything ba, kawai dai zai fada mata sun ce zasu yi tuni akai, saboda ta san first time din su kenan. 〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️ 〰️〰️〰️〰️ "Habibty ki yi sauri fa, time is not by our side." Nafisa ta fada. "Toh naji, bag dina kawai zan dauka." "Oho ni dai kiyi sauri, su Hafsah ma na jiran mu." Nafisa ta kara fada. Baa fi 3mins ba, Olamide ta fito. "Toh gani uwar masifa." "Wani masifa ta maki, so kike muyi laty ko?" Halima ta fada tana daga mata gira. "Ya isa dan Allah, ku din ma da kuke magana zaku samu latty." Hafsa ta fada. Suka kama hanya suka fita, suka nemi keke, ya kai su har school. Yau been the last paper din su na semester, kuma ya kasance papern da safe ne, yasa suke ta sauri, ga zumudin zasu koma gida. Suna isa school, suka tafi inda zasu rubuta exams, suka samu ma har anfara shiga, suma suka yi joining din queue, nan Nabila ma ta zo ta same su, itama tayi joining din queue. "Wow! Today's exams was superb wallahi." Nabila ta fada tana hugging din Oamide. "Yes it was." Olamide ta fada moodly. "Habibty yana ga reply din ki bai zauna mun ba, ko exams din bai maki honey bane?" Nafisa ta tambaye ta. "Bakomai, yayi dadi sosai kaman taliya da manja da yaji." Ta fada tana faking din murmushi. Ita Nafisa ta san ba lafiya, amma sai ta share, ta kudura a ran ta in suka koma gida zata tambaye ta, tunda su gobe zasu koma ba yau ba. Suka taka zuwa inda ake samun keke, Olamide ta ce " Bila yau zaki koma ko?" "Ae In Sha Allahu. Yaya yace kar in kwana, in dawo yau tunda papern safe ne. Ko akwai sakon da zaki bani ne na ba." Nabila ta fada tana kashe mata ido. Nafisa kuma ta fashe da dariya, tace "gaskiya kam, ko akwai message for ife ne." "Kar kiyi coverup da ita, in kema kina da sako ne, ki bada atoh." Nabila ta fada. "Ai shi ne. Wallahi ko Bila, habibty is too secretive with her relationship, ko tana da shi baza ta fada ba." Olamide ta fada tana hararan Nafisa da wasa. "Zan fasa maki ido fa." Nafisa ta fada ta buga ma Olamide ido da wasa. "kan balai, zan karya ki fa idan kika kara taba mun ido na." Olamide ta fada. "Ya ishe ku. Ku daina wasan manya please." Nabila ta fada. "Wallahi nayi zaton wasan yara zaki ce, dana fasa maki mouth." Nafisa ta fada. "Ki fasa ma Farouq baki, sai dai ki gan shi a nan." Olamide ta fada. "Ko kunya, ki kira sunan miji na gatse haka?" Nabila ta fada. Inda su biyu ke arguing, Nafisa ta tsare keke, duk basu sani ba, suna can suna arguing, harta shirya da me keken. Da ta gama shiryawa da mai keken, ta daka masu tsawa. "DanAllah ni ku daina wannan abun kuzo mu tafi." "Kai har kin tare keke?" Olamide ta tambaya. "In muka shiga zaki tabbata koma meye." Nafisa ta fada. Da suka isa gida, suka dan huta, Nafisa ta sa masu abinci a wuta, ita kuma Olamide ta cigaba da shirya kayan ta. Although da Nafisa ta tambaye abun da ke damun ta, ta ce bakomai, ta fara wasa so that zata yi covering up, deep down she was feeling anxious, kuma her anxiety akan abun da Abdallah yace zai fada ma iyayen sa ne. For a month yanzu yana ta mata yawo da hankali, and within these one month, soyayyan sa ta kara karfi a zuciyar ta. Amma tana tsoro, kar azo yanzu ace ba zai aure ta ba, gashi ta gama fadawa cikin tarkon kaunan sa. Tana aiki tana tunani. Hanya zata taba samun Abdallah a matsayin mijin ta kuwa? Ita kam bata jin shi ajikin ta cewan zai zama mijin ta, kullum ji take kaman they only have a little time left before they part ways. Tana cikin tunanin, taji wani abu mai sanyi a jikin ta. A zabure ta ce "subhanallah!" "Matsoraciya. Ni ce toh." Nafisa ta fada. "Kin tsorata ni fa sosai. Me yasa hannun ki yayi sanyi haka ne?" "Oho mai. Tunanin me ma kike hakan, na kira sunan ki fa almost sau biyar, amma baki amsa ba." Nafisa ta fada. "Bakomai, just normal thinking ne." "I see, continue normal thinking. Amma kafun ki ci gaba, mu ci abinci, saboda ni kam yunwa nake ji." Nafisa ta fada. "Nima haka." Lokacin da suke cin abinci, tana ta dannewa, gudun kar Nafisa ta gane. Saboda gaskiya hankalin ta yaki kwanciya kwata kwata. Da suka gama ci, Olamide ta dauki plates, ta kai kitchen, ta wanke su. Tana ta expecting wayan ta yayi ringing, amma shuru kake ji. Tana wanke wanke, tana duba wayar ta. Wata zuciyar ta ce maybe ya tafi office ne, tunda yau is a working day. Amma yace zai fada masu da safe, maybe bai samu fada ba. "Wai ni habibty me ke damun ki ne?" Nafisa ta fada. "Bakomai." Olamide ta fada, sannan ta ci gaba da wanken wanken ta. "Ki daina mun karya please. Tun dazu nake nan fa, amma sai tunani kike." Nafisa ta fada. "Bakomai fa, am just thinking of how hutun nan will be without you my habibty." Olamide ta fada. "Kar ki maida ni karaman yarinya fa, I don't wear pampers anymore please. If you don't want to tell me kawai ki fada mun, but ki daina mun wasa da hankali." Nafisa ta fada. "Allah sarki my habibty, kar kiyi fushi da ni. Wallahi na gaji da maki complain akan abu daya ne. Ni ke nan kullum cikin yi maki complain akan relationship dina, amma ko sau daya baki taba mun complain ba." Olamide ta fada. "Gama wanke wanke, bari in je in ci gaba da gyara kaya na, na san by the time din da zamu gama komai, lokacin zuhur yayi. Kin ga bayan zuhur, sai mu samu muyi maganan nan cikin nastuwa da kwanciyan hankali." Nafisa ta fada tana robing din bayan ta. "Okay toh." Olamide ta amsa. Nafisa zata bar wajen kenan, Olamide ta kira sunan ta, ta yi hugging din ta, ta ce "na gode sosai Fisa, Allah ya bar mu tare, Allah ya hada mu a jannah." "Awwwn amin amin habibty ta." Nafisa ta amsa, sannan suka daina hugging din juna, Nafisa ta koma dakin su, ta fara gyara kayan ta. Ita kuma Mide, ta cigaba da wanke wanke. Daman wanke wanke ba yawa, saboda tunanin da take yi ne, da ta gama. Da suka gama komai, bayan Zuhur, basu ma tashi akan sallayan da suka yi sallah a kai ba, Nafisa ta tambayi Olamide abun da ke faruwa, Olamide ta fada mata, kuma ta nuna tsoron ta, yau din nan dai ya mata ransuwa zai fada masu, kuma ya bata feedback, so tana tsoron result din. Nafisa ta ita kwantar mata da hankali, tace mata kuma zai kira, maybe yana wajan aiki ne, amma ta kwantar da hankalin ta, everything will be alright. "I hope so habibty, I hope so. Kema dai kin san mutanin ku da wannan shegen aladan ko? Da kyar su yarda." Olamide ta fada. "Kar ki damu, ai ba duka aka hadu aka zama daya ba. Kuma zai kira ki In Sha Allah, and everything will be the way we want it. In kuma bai kira ki ba, ke ki kira shi. Amma fa ba yau ba, kaman gobe ko jibi." Nafisa ta fada. "Jibi kuma! A'a goben dai." Olamide ta fada. "Duk wanda kika ga ya kwanta maki, shi zaki yi. Amma fa kin san maybe goben nan you may be tired. Anyhow dai, am sure zai ma kira ki my bibty." Nafisa ta fada. "Toh Allah yasa. Nagode sosai da kulawar ki habibty, Allah ya baki lada." Olamide ta fada, sannan tayi hugging din Nafisa. "Amin amin, Allah ya bamu lada duka. I love you sooo much." Nafisa ta fada. "Me too. Am also sad tomorrow we will be leaving each other." Olamide ta fada. "Me too wallahi. I am going to miss you soo much my habibty." Nafisa ta fada. Haka suka ita emotional talks akan yanda zasu yi missing din juna. 〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️ Tun da safe Abdallah ya kasa kiran Olamide, ga shi har 9 din dare yayi. Maybe kawai ya kira ta, sai ya dinga canza magana idan zata yi tambayan abun da su abba suka fada. Amma gobe inta koma gida, sai ya fada mata cewa sun ce zasu yi tunani akai. Haka ko aka yi. Ya kira ta, yayi wishing din ta best in all the exams she wrote, in taso ta tada maganan, sai ya canza topic, har suka gama wayan, bai bata opportunityn da zata tada maganan ba. "Allah sarki my qalbi, Allah ya ga bana son in maki karya, amma yana iya, iyaye na basu son union din mu. Duk da cewa basu san ki ba, sun bi sun sa tsanan ki a zuciya, saboda *BANBANCIN KABILA.* Amma karki damu, zan san yanda zan yi dasu. Haka Abdallah ya ita tunani, har barci ya dauke shi. 〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️ Tunda suka tashi around 4, ba wace ta kara runtsawa. Suna ta shirye shirye. Suna idar da sallah, suka karanta qur'ani, suka yi addu'an safe, Nafisa ta fara shiga wanka, Olamide ma tazo ta shiga. Suna gamawa, kowannan su ta shirya, suka rurufe ko ina, su ka kashe duka sockets, sannan kowannan su ta dauki jakar ta, sanan suka yi sallama da sauran mutan gida, kowannan su ta nemi keken da zai kai ta tasha, nan suka yi hugging din juna, kaman baza su bar juna ba, kafun suka shiga, suna waving din juna. Olamide na isa tasha, luck was on her side, saura mutum daya motan ya cika. Ita kuma Nafisa, saura mutani hudu. "Madam what are you looking at, have been calling your name." Olamide ta ji tap din mutum a shouldern ta, tana jin muryar, tasa this is definitely her mum. Da sauri, ta juyawa tayi hugging din ta. "Mummy mi, nayi missing din ki sosai." "Me too. Muje mu shiga mota. You look tired baby girl." Mummy ta fada. "Muje. Kaman kin sani mummy, na mugun gaji." Olamide ta fada. Da suka isa gida, Farida ta fito da gudu, tayi hugging din Olamide, itama Mide tayi farin cikin ganin kawan wata. Duk sunyi complete, amma banda Hakeem, sai next week zai dawo. Ta shiga dakin ta, taga an gyara ko ina, sai ta kwanta saman gadon ta, ta ce "wow home sweet home." Ta dan huta akan gadon, kafun taje ta shiga toilet, ta dan watsa. Sun dade suna hira, aka maida Mide yar'lele. Da suka gaji da hira, mummy ta wuce dakin ta, Mide ta Farida ma suka tafi nasu. Farida ta kwanta a nata gadon, Mide ma ta kwanta a nata, tana kwantawa, taji idanuwan ta na rufuwa, tama manta da zance iyayen Abdallah, saboda tsabaragen gajiya. Asuba ta gari. Da suka tashi da safe, suka yi morning routine din su, suka yi wanka, suka hadu a dinning, suka yi breakfast. Suna gamawa, ta ki Nafisa, Nafisa ta gaisa da mummy da Farida, itama Mide, suka gaisa da Ummi da abba. Nafisa ta tambaye ta ko Abdallah ya kira, tace ae, amma lokacin tayi barci, so zata kira shi idan sunyi hanging up. Sun dade suna hira, kafun suka yi sallama. Da suka gama waya da Nafisa, Olamide ta koma dakin ta, nan ta kira Abdallah. " Assalamu alaikum ifemi" "Waalaikumus salam yide'am. An tashi lafiya, kin same su lafiya? Ya gjiyan hanya? "Fyn alhamdulilah. Kaima ka tashi lafiya?" Olamide ta tambaya. "Lafiya kalau." Abdallah ya amsa. "Baka je wajan aiki bane?" Ta tambaye shi. "A'a, yau ina afternoon duty ne." Abdallah ya amsa. "Okay toh, Allah ya kaimu afternoon." Olamide ta fada. "Amin amin yide'am." Abdallah ya amsa. Sai kuma shuru ya biyo baya kafun Abdallah yayi breaking din silence din. "Akan maganan nan, na fada masu." Ya fada zucuyar sa na bugawa. "Okay, me suka ce toh, I hope it's not what am thinking." "Nope it not. Kin san this is the first time this is happening in our family, toh wai zasu yi tunani akai." Abdallah ya fada yana runtsa idanuwan sa, yana astagfirullah a zuciyar sa. Allah yaga baya son karya, amma at this point, this is the only way out. "Hmm toh shikenan, at least basu zage ni ba, kuma basu ki ni ba Alhamdulilah, Allah yasa suyi thinking positively. Kaga sai anjima, yanzu mummy zata fara kira na, inta ga na dade ban fito daga daki ba." Olamide ta fada. "Okay bye qalbi'am. Abdallah ya fada, sannan ya kashe wayar. ```DanAllah kuyi hakuri da kuka ji ni two days shuru, I was kind of busy ne, shi yasa, amma am back now💃🏽💃🏽💃🏽.``` ```Thanks for reading and always been patient, zeexee loves you guys 75, 50, 100%🤭🤭🤭🤭.``` ~Zeexee ce~ 🖊️🖊️🖊️ [8/30, 1:21 PM] Abokiyar Fight💜💖: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 *BANBANCIN KABILA* _(Short story)_ 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 *TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION* *🔱(( Home of Expert and Telented writers, da tambarin mu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))* *T.W.A* *WRITTEN BY ZAYNAB* _(zeexee)_ MARUBUCIYAR *-RAYUWAR HUSNA* - *MAHAKURCI MAWADACI* _(2020)_ 4️⃣1️⃣&4️⃣2️⃣ _Bismillah_ Bayan sati biyu, kowa ya dawo, gidan mummy ya cika jif, it was a complete home. Around 5:pm, Olamide da Farida suna daki, suna hira, sai wayar Olamide ya fara ringing. "Duba mun wake kira na." Olamide ta fada. "It's yaya Abdallah. Amma bakin ce yau bazaki yi picking din calls ba?" Farida ta tambaye ta. "Meya dame ki, bani abu na, kuma ki fita." Olamide ta fada. Farida ta mika mata. "Toh ki fita." Olamide ta fada tana nuna mata hanyar kofa da hannu. "Ni kam bazan sa kunni a conversation din ku ba, just please let me stay." Farida ta fada tana mata puppy face. Olamide taja tsaki, sannan ta daga wayar. "Assalamu alaikum!" "Waalaikumus salaam Olami." Abdallah ya fada. "Toh ya kake, har ka dawo daga wurin aiki ne?" Ta tambaye shi. "Lafiya kalau, ke fa? Na dawo fa, amma na bi na gaji wallahi." Abdallah ya fada. "Nima lafiya. Allah sarki, sorry. Wannan aikin na ku is very stressful wallahi." Olamide ta fada. "Bari kawai qalbin Abdallah, aikin is very very stressful." Abdallah ya fada yana mika kaman tana ganin shi. "Allah sarki ifemi, may Allah make it easy for us all." Olamide ta fada. "Amin amin yide'am. Kina cikin mutani ne?" Abdallah ya tambaye ta. "A'a, nida Farida ne kawai, ya aka yi?" Olamide ta tambaye shi. "Daman akwai wani magana mai mahinmaci da nake son muyi ne, kuma I will need your full attention. So in ba damuwa, ina son ya zamanto ke kadai ce, so that zaki bani full attention din ki." Abdallah ya fada stressed. "Okay toh." Ta fada, sannan tama Farida signal da hannu ta fita. Rai abace, bakin nan a zungure, ta fita. "Toh am alone. Amma lafiya kuwa?" Ta tambaye shi. "Lafiya ba lafiya." Abdallah ya fada. "Ni kam ifemi ka daina tsoratar dani." Ta fada hankali a tashe. "Karki tsorata please, wannan maganan da zan maki, na fahimta ne, zan so mu fahimci juna ne." Abdallah ya fada yana shafa kai. "Dole na tsorata ai, the way you are talking is not pleasing at all. But anyways ina jin ka." Olamide ta fada. "Toh ki kwantar da hankalin ki." Ya fada. "Toh naji. Me kake son ka fada." Olamide ta fada. Sanda yayi wani irin numfashi, kafun ya ce "Olami, kin san this is the first time din da irin abu haka zai faru a familyn mu kenan, kaf cikin familyn mu, mutum daya ce kawai ba bafulatana ba, matar kawu Dajjo kenan, amma ita ma she is from the North. Amma namu is different, we come from different parts, so it's really hard to come to a conclusion." Ya na son ya cigaba, Olamide ta katse shi. "What do you mean, just go straight to the point please." Ta fada muryar ta na rawa, kana ji ma, zaka san a tsorace take. "It's really hard for my parent, kafun ma akai ga Uncle dina. Harga Allah, ina son ki, kuma so fisabilillah. Kuma wallahi bazan iya son wata ya mace kaman yanzda nake son ki ba." Ya kara shuru. "Just go straight to the point please." Olamide ta fada. 〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️ "I have made my decision and that's final. Zan hada ka da yar Alhaji Madaki ne. Kuma I don't want to hear anything about that yoruba girl again." Abba ya fada yana huci. "Allah sarki umma ta ki sa baki mana, kar ki bari a cutar dani mana, danAllah ki ba Abba hakuri." Abdallah ya fada da hawaye a fuskan sa. "Me kake son in fada ne? Me kake son in fada. Kai da aka baka chance, amma kayi misusing din chance din ka? In ma tambaye ka, wai mata sun kare ne a arewa?" Umma ta tambaye shi. "Allah sarki umma, ita ta zauna mun, ai ta ma fi wasu yan arewan natsuwa." Abdallah ya fada. "I can see you are sick. Abban ku ya riga ya yanke decision, kuma bani da ja akan decision din sa. Then kar ma ka fada ma yayyin ka, saboda zaku bata lokacin ku ne." Umma ta fada. "Ka tashi ka fita mun kafun in maka abun da baza ka ji dadi ba." Abba ya fada. Jiki a sanye ya tashi ya bar wajan, ya koma dakin sa. "Wato shikenan zasu raba ni da masoyiya ta, yanzu kam kasancewa na da masoyiya ta ba tabbas". Daman bai yi asr ba, sai ya shiga toilet, ya yo alwala, sannan yazo yayi sallah. Ya dade akan sallaya yana addu'a, Allah ya kawo mai mafita. Daya gama addu'a, ya ninke sallayan, yasa a mazauin sa, sa ya zauna akan sofa, ya fara tunanin mafita, sai wani idea ya shigo masa, ya dauki wayar sa, ya kira Olamide, to him that will be the best decision to make. 〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️ "To be sincerely speaking, su Abba are still having doubt, har yanzu basu yarda ba, kin san irin haka bai taba faruwa a familyn mu ba, so suna doubting akan decision din su." Abdallah ya fada. "Atakaice dai basu sona ko?" Olamide ta fada da hawaye a idon ta. "Ba haka bane, waye zai ki ki a rayuwar nan, ai ke abun so ce. Kawai dai suna kan tunani ne. Gashi kin san babban familyn mu kaf ma nada nasa matsalan, so sai sun shirya sosai." Abdallah ya fada. "Toh naji. Amma why am I not believing these, ina ji kaman karya kake mun, ina ji kaman sun ce basu so na ne, and you are just covering up." Olamide ta fada. " So you don't trust me, what is the use of a relationship without trust ?" Abdallah ya tambayi Olamide rai abace. "Nifa bance I don't trust you ba, amma ina ji ne kaman you ain't saying the truth. Amma ba komai, kayi hakuri in na bata maka rai." "Sai anjima." Abdallah ya fada, ya kashe kiran. Jiki a sanye, Olamide ta kalli wayar ta, wasu zafafan hawaye suka fito mata. Tayi kuka ta gode ma Allah. Abdallah bai taba fushi da ita ba, amma yau yayi, gashi kuma to be sincerely speaking, with the way he is talking, kasan karya yake, he is trying to cover up. Ana cikin haka, lokacin sallah yayi, ta tashi ta shiga toilet ta yo alwala, ita ma Farida ta shigo, ita ma taje tayi alwala. Tana son ta tsokane ta, taga yana yin ta, sai tayi shuru, tasan ba lafiya. 〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️ Frustration ya kama Abdallah, sai yaji ma baya son yin magana da kowa. Shi dai yasan a yanayin yanzu kam, da kyar idan zasu yi aure da Olamide. Gashi baya son saba ma iyayen sa, amma a yanda yake son Mide, hanya bazai saba masu ba? He was feeling very frustrated that he could do anything at this moment. Sai hawaye yake shar Shar kaman karamin yaro. Who said men don't cry? Men do cry, but not in front of people, they are also humans, they have hearts. Ana cikin haka, lokacin sallah yayi, ya shiga yayi alwala, yana gamawa, ya fita ya tafi masjid shi kadai, yaki jiran Abba. Da Abba ya fito, yayi knocking din kofar sa, ya ji shuru, sai ya bude kofar, yaga baya nan, ya jijjga kan sa, yace "wato dan na hana sa yarinyar nan, shi ne yaki tafiya da ni masjid ko? Hmm kar ma ya bari in sa next week ayi auren nan." Abba ya fada. A fusace ya bar wajan, ya ce "zamu gamu ai." Da suka dawo daga masjid, Abdallah ya shige dakin sa, ya rufe dakin sa. Daman daya fito daga masjid, bai jira Abba ba. So da Abba ya jira ya jira, sai ya koma gida. Yana shiga, yayi sallama, Umma ta amsa mai, ya ce "ina Abdallah?" Ya fada ran sa a bace. "Na ji shigowan sa, kaman ya wuce dakin sa. Lafiya?" Umma ta tambaya. "Ba lafiya. Ba lafiya saboda Abdallah ya raina ni, Abdallah ya maida ni dan sa, ya manta ni na haife sa. Amma kar ya manta, decision na hannu na ne, I can do and undo in this house. Wallahil azim, inya bani haushi, sai ayi auren sa da yarinyar nan next week Friday." Abba ya fada yana huci. Aiko Umma na jin haka, ta tashi daga saman kujeran da take zaune a fusace, ta je dakin Abdallah, ta fara knocking. Yana jin knocking din ta, ya ki tashi, sanda yaji abun yaki karewa, ya tashi, ya bude kofar. Yana budewa, ta finciko shi, ta ja shi har parlor inda Abba yake zaune yana fushi. "Ka tsuguna ka ba mahaifin ka hakuri yanzun nan." Umma ta fada. Sai ya tsuguna a gaban Abba, ya bashi hakuri. "Wallahi! Kaji nace wallahi, inka sa wasa, next week Friday zaa daura auren ka da Safiya. Mahaifin ta bayi da matsala, yanzu zamuyi komai, inje in fada ma Baffan mu, sharp sharp zaayi komai." Abba ya fada. "Dan Allah Abba kayi hakuri." Abdallah ya fada. "You better be careful with me. Ka shiga hankalin ka ka bari mu yi abun nan yanda nake so. Kuma ban yafe ba in na kara ji kayi magannan yarinyar nan. Kuma inma ka kara magana da ita, it should be that you will be telling her ku rabu." Abba ya fada, ya tashi ya bar wajan. "Kaga irin ta ko?" Umma ta tambaye sa. "Aya umma ba laifi na bane, amma hukuncin daku ka yanke mun bai yi ba ne, na rasa inda zan sa kai na." Ya fada da hawaye a idon. "Mtchwww umma ta ja tsaki ta bar wajan. 〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️ Olamide na idarwa, tayi adu'a, tana ta rokon Allah yasa ba dai karya yake mata ba. Tana gamawa, ta ninke sallaya, ta dau wayar ta, ta kira Nafisa, ta zaiyana mata komai. "Toh tunda yace maki it's been hard on them, you should believe that. Truly this is new to them, baa taba hakan ba a family din su. Just pray for the best, and believe him." Nafisa ta fada. "Toh naji Fisa, but am scared. Ni fa mahaifiya ta bata dau time ba, ta ce toh, then why is it hard for them? Ai muma yarbawa muna da kishin yaren mu, muma bamu cika auren wanda ba yaran mu ba. Amma mummy ta yarda. Bakomai dai, let's hope for the best kawai." Olamide ta fada. Thanks for reading. Kuyi hakuri kun ji ni shuru, waya ta ta fada a ruwa shi yasa. Comment Like & Share. ~Zeexee ce~ 🖊️🖊️🖊️ [8/30, 1:21 PM] Abokiyar Fight💜💖: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 *BANBANCIN KABILA* _(Short story)_ 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 *TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION* *🔱(( Home of Expert and Telented writers, da tambarin mu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))* *T.W.A* *WRITTEN BY ZAYNAB* _(zeexee)_ MARUBUCIYAR *-RAYUWAR HUSNA* - *MAHAKURCI MAWADACI* _(2020)_ 4️⃣3️⃣&4️⃣5️⃣ _Bismillah_ *BAYAN SATI BIYU* A ranan Mide ta tashi bata wani jin dadi, ji take kaman an mata rasuwa. Tunda ta tashi, tayi sallah, ta gaida mummy, ta koma dakin su, ta fara jin wani iri, kwata kwata ba abun dake mata dadi. Within this two week, ita da Abdallah suna soyayyan su, amma ba kaman da ba, basu wani dadewa suna waya, gashi ta riga ta fada a tarkon son sa. Kullum in suka yi waya, in ta ga bada tone din daya saba mata magana yake ba, in tayi kokarin fada mai, sai yaji haushi, ya ce she is not appreciative, he is trying everything possible just to love her, even though soyayyan su is a forbidden one for now. Wani sain, in suka gama waya, sai tayi hawaye, saboda ba Abdallahn data sani ne wannan ba. Unkown to her that he was breaking his parents rules just to be with her. Tana cikin tunani, wayar ta ya fara ringing. Ta dauki wayar akan bedside drawer, ta duba mai kiran ta, taga sunan Abdallah. Tana ganin sunan, taji rate din da heart din ta is beating, was too fast. Sanda ta saki wani irin numfashi, sannan tayi bismillah, kafun ta daga still heart din ta na bugawa 3³. Taji dadi ma Farida bata cikin dakin, tana caan dakin mummy. "Assalamu alaikum!" Olamide ta fada. "Waalikumus salaam. Kin tashi lafiya?" Abdallah ya tambaye ta. "Lafiya kalau. Kai fa?" Itama ta tambaya. "Not too good. Anyways that's not why I called, ina da maganan da nake son muyi, kuma ina son ni da ke muyi accepting din haka as qadr din mu." Abdallah ya fada. "Ban gane muyi accepting din shi as qadr mu ba." Olamide ta fada confusedly. Sai wani idea ya shigo mata, ta kara cewa "na gane yanzu. Wato iyayen ka basu yarda ba ko?" Ta fada wasu zafafan hawaye na fita a idon ta. Sanda yayi wani irin numfashi, kafun yace "bazan maki karya ba, iyaye na basu yarda ba, amma ina son ki san ina so...." Olamide bata bari ya gama magana ba, ta kashe kiran. "Inalillahi wa'ina ilahil rajiun! Ya zan yi da kai na, ya zan yi da zuciya na?" Haka ta ita tambayan kan ta questions kala kala tana kuka. 〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️ Tun ran da Abba ya ma Abdallah Allah ya isa, Abdallah ya rasa yanda zaiyi. Ya fada ma yayyin sa, suma suka ce ba wani mafita, ya fada ma Mide kawai. Shi kuma ya kasa fada mata kai tsaye, shi yasa within those two weeks, yake ta mata abubuwan da zai dinga bata mata rai, maybe soyayyan sa zai ragu a zuciyar ta, amma yaga ina, abun sai karuwa yake. Shi yasa yau din nan ya yanke decision zai fada mata. Kafun ya kira ta ma, sanda ya ita practicing din words din sa. Ya san in ya fada mata, zata shiga wani irin hali kuma ba ita kadai ba, ko shi zai shiga wani irin hali. Bale ma shi ya riga ya shiga tun da dadewa, maneji kawai yake. Daya kira ta, suka dan gaisa, kafun ya fada mata reason har ta fada. Nan yaji wani irin zafi a zuciyar sa. Yama kasa fada mata abubuwan daya so ya fada, saboda ga bisa duka alamu, kuka ma take. Gashi he wanted to tell her words that will make her calm, but she cut the call. What sort of life is this, me yasa ba wanda yake son yayi supporting din shi ne, instead kowannan su na kara mai zafin da yake ji a zuciyar sa. Ya kira Olamide ya fi sau goma, amma ta ki dagawa. Tana gani bawai bata ganin ba. 〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️ Olamide nata kuka, ta rasa wa zata fada ma damuwan ta. Sanda ya bari ta gama son shi, sanda ya bari ta gama planning din yanda future din su will be, shi ne yanzu ya ce su hakura da juna, ai ya cuce ta. Kuka take na fitan hankali. Ana cikin haka, wayar ta ya fara ringing. Tana dubawa taga Abdallah ne, sai tayi tsaki. Ya kira ta sau goma, amma taki dagawa. Daya ishe ta da kira, ta kashe wayar ta. Baa fi 5mins ba, sai ga Farida ta shigo. "Aunty gashi yaya Abdallah yana son yin magana da ke. Farida ta fada. Ki ce mai bana son inyi magana da shi. Olamide ta fada kan ta a kasa, saboda bata son Farida ta ga hawayen ta. "Yaya tace bazata yi magana da kai ba." Farida ta fada. "Kin san me?" Abdallah ya tambayi Farida. "A'a." Farida ta amsa. "Ki sa wayar a speaker, ki sa kusa da ita, sai ki fita please." Abdallah ya fada. "Okay toh." Farida ta amsa, sai ta sa wayar a speaker, sannan ta sa a kan bedside drawer, ta fita. "Na san kina jina. I want you to know that is was never my choice, kuma Allah na da reason din sa daya sa hakan ya faru da mu. Let's take this as qadr din mu. You are my first love, and you will always be the only woman I will love with all my heart for the rest of my life. Although zaa hada ni da wata, koman son da zan mata, bazai taba kaiwa wanda nake maki ba. I may be with another woman, but my heart belongs to you Abdallah's qalbi, kece zuciya ta, kuma zuciya daya muke dashi, and my heart belongs to you Mide, you are my heart." Abdallah ya fada a lokacin shima ya fara hawaye. Alokacin kuma Olamide tana kuka sosai, sai taji kaman ranan mahaifin ta ya rasu. Cikin kuka ta ce "bazan so ace ka saba ma iyayen ka ba saboda ni, sam sam bazan so hakan ba. Ka bi umarnin iyayen ka, kuma In Sha Allah zaka ga dai dai. I pray this will be the best for me and you. I also love you, and my heart belongs to you too. Goodbye ifemi, have a great life ahead." Olamide ta fada tana kuka mai cin rai. "I love you too yide'am, I love you soooo very much qalbin Abdallah. If there was another word that is more than love, then I have that for you qalbin Abdallah. Please take care of my heart for me, ko bamu zama daya anan ba, I pray Allah makes us one in jannah. I love you soooo much yide'am, I love you soooo much qalbin Abdallah. Goodbye." Abdallah ya fada yana kuka itama tana kuka, sai Mide ta kashe wayar. Olamide ta ci kuka, kuka ta ke na fitan hankali. Shikenan ta rasa Abdallah, she wish she was with Nafisa, at least she will have a shoulder to cry on. Bata son ta fada a gida, kar hankalin mummy dana kannan ta ya tashi. 〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️ Da Olamide ta kashe wayar, shima ya fara wani shafin kuka. Ya ci kuka kaman ran sa zai fita. Zai bi umarnin iyayen sa, amma yasan ko ya nuna mata so, bazai taba kaiwa wanda zai nuna ma Mide ba. Yana cikin kuka, wani idea ya shigo ma sa, sai ya dau wayar sa, ya kira Nafisa, ya fada mata komai still yana kuka. "Inalillahi wa'ina ilahil rajiun! Wannan kuma wani irin damuwa ne? Allah sarki habibty na, abun da take tsoro kenan, amma muka bata assurance cewan hakan bazai taba faruwa da ita ba. Man proposes, but God disposes. This is you guys destiny, kuyi accepting din shi, Allah ya hada kowannan ku da rabon sa, ka daina kuka, it's breaking my heart wallahi. In kai kana irin wannan kukan, habibty na fa, ya zata yi. Allah sarki, I wish we were together, I would have consoled her. But any ways, this Saturday zamu koma school, and today is Wednesday, so it's not too far." Nafisa ta fada. "Please console her even from the phone, saboda qalbi na is going through alot wallahi. Ina son abi na, amma iyaye na basu so, bazan iya bijire ma maganan iyaye na ba. I hope she forgives me for giving me her heart, but I hope she keeps my heart for me. Thank you for been a good friend to my heart, Allah ya saka maki da jannah." Abdallah ya fada sai ya kashe wayar. 〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️ Olamide na cikin kuka, taji wayar ta na ringing. Bata so dubawa ba, amma her heart was giving her to check it. Tana dubawa, taga sunan Nafisa. Ta daga da sauri. Tama kasa mata sallama, ta kara fashe da kuka, tana cewa "shikenan nayi lossing din ifemi, shikenan ni da shi har abada? Wallahi I can't love anyone man other than him. Na shiga uku na, me zan fada ma mummy? Mummyn da she is really happy about these whole thing, me zan fada mata?" Haka Olamide ta ita maganganu tana kuka. Da kyar Nafisa ta samu tayi consoling din Olamide, tayi shuru. Amma tana kashe wayar, ta cigaba da kuka. Har 10:30am Olamide bata fito ba, tun mummy bata yi magana ba, har tazo ta je dakin su Olamide da kan ta. Mide na jin foot step na zuwa towards dakin su, Olamide ta tashi ta shiga toilet, ta bude tap. Mummy na shiga, ta ji alamun ruwa a toilet. Bata fita ba, ta zauna akan gadon Olamide. Olamide na fita, ta fara mata masifa. "Kinin seyo na (meke damun ki ne wai)? Tunda safe baki fito ba, wa kike son ya dafa maku breakfast? Wannan wani irin dabia ne? Wato ke kina nan kina barci, mu kin bar mu da yunwa." Haka mummy ta ita ma Olamide masifa. Allah sarki Olamide ta ma kasa ce mata komai in ba mummy kiyi hakuri ba. Mummy taja wani irin tsaki, har tana hararan Mide, sai tace "if you like stay there, sorry din ki zai dafa mana brakfast." Mummy na gama magana, ta fita ta bar dakin. Tana fita, Mide tasa hannun ta a kai, tace "yau kam na ga ta kai na. Dame zan ji, da mummy ko heart?". ```Thanks for reading, zeexee love y'all.``` Comment Like & Share. ~Zeexee ce~ 🖊️🖊️🖊️ [8/30, 1:21 PM] Abokiyar Fight💜💖: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 *BANBANCIN KABILA* _(Short story)_ 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 *TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION* *🔱(( Home of Expert and Telented writers, da tambarin mu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))* *T.W.A* *WRITTEN BY ZAYNAB* _(zeexee)_ MARUBUCIYAR *-RAYUWAR HUSNA* - *MAHAKURCI MAWADACI* _(2020)_ 4️⃣6️⃣&4️⃣7️⃣ _Bismillah_ Har Allah yayi yau Saturday, Olamide zata koma school, ita kadai ta san irin dadin da take ji, at least she will have a shoulder to cry on. Saboda within Wednesday to this Saturday, ita kadai ta san abun da ta ji. Ko zata yi kuka ma a boye take yi, saboda bata son yan gidan su su sani. Kana ganin ta, ka san abu na damun ta. Ko su mummy ma sunyi noticing, da suka tambaye ta, ta ce bakomai, tana jin ciwon kai ne, aka sata dole ta sha maganin ciwon kai. Jiya which was Friday, da Mummy taga yanda Mide ta rame, ita da daman ba wani jiki gare ta ba, ta kara ramewa, sai wani uban kan daya karu. Mummy was so disturbed, ta tambaye ta abun da ke damun ta, ko bata jin dadi ne bata fada ba. Sai tace ma mummy wai maleria kedan damun ta, amma ai tana shan magani, ta samu maganin maleria a cikin first aid box din su. Mummy tace ko zata bar zuwa school zuwa next week, saboda a mata treatment mai kyau, da sauri tace a'a, bawai ciwon na wani damun ta bane, ta san abu kadan ke ramar da ita. Mummy tace haka ne. Amma Hakeem ya kasa yarda da maganan, shi yasa jiyan da daddare, ya je dakin su ya same ta cikin blanket, daman Farida bata ciki, yayi sanda, har ya isa inda take, sai yaji shashakan kuka, ya yaye blanket daga kan ta, a zabure ta tashi, tana goge hawayen ta. "Dan Allah Hakeem me haka? Baka san meye knocking bane ko sallama, ko kuma rashin hankali ke damun ka." Olamide ta fada mai kan ta a kasa, a dole tana rufe mai fuska karya ga hawayen ta. "Koma meye, shi ke damu na. Ance maki ban san karya kike ba? Tun ran Wednesday nake ta noticing change in you. Tun ranan fa idanuwan ki a kunbure suke, kuma suyi jazur. Na san mummy ma ta san karya kike, ta kyale ki ne kawai. Yanzu dai ina son ki fada mun tsakanin ki da Allah, kar ki mun karya. Ni dan'uwan ki ne na jini, kuma baki da yan'uwan da suka wuce ni da Farida. A matsayin ki na babban yaya wanda bata taba son taga bacin ran kanne ta, ki fada mun abun dake damun ki." Hakeem ya fada hannayen sa akan shoulders din Mide. Maganan sa yayi touching din heart din ta. Truely bata da wanda yafi su, ko Fisa ma a bayan su take. Ta kara fashewa da kuka, sannan tayi hugging din kanin ta. Ta kasa fada mai komai, inba kukan da take ba. Da AbdulHakeem yaga wannan kukan ba me karewa bane, sai yayi thinking of an idea din da zai iya sa ta bar kuka, ya ce "ko kina da ciki ne?" Hakeem bai gama rufe baki ba, yaji saukan mari. "A'a ciko nake da shi." Olamide ta fada tana hararan shi d jajjayan idon ta. "Am very sorry aunty ta ta kai na, I hate to see a strong woman like you cry. Me ke damun ki ne please?" Hakeem ya tambaye ta disturbed. "Hmm Hakeem, abun dake damu na ba kadan bane, amma karka dau wani mataki, and promise me bazaka fada ma mummy ba." Ta fada. Olamide ta san idan ta fada ma Hakeem, yana iya kiran Abdallah ya mai rashin mutunci, kuma gasiya bata son hakan ya faru, dan koba komai sunyi soyayya, kuma har yanzu suna son juna, kaddara ne dai kawai. "I promise." Hakeem ya fada. Nan Mide ta fada mai komai. Hakeem yayi fushi sosai, yace mata sai ya kira Abdallah, daya san a familyn su baa yarda a auri wani kabila, me yasa yace yana son ta, wato ya san hakan zai faruwa, amma ya zabi yayi breaking din heart din sister din sa. Da kyar Olamide ta samu tayi calming din shi down, sannan ta tuna mai da alkawarin daya dauka. So a gidan su, Hakeem kawai ya san abun daya faru. Da sassafe Hakeem da Farida suka raka Olamide tasha, inda zata hau motan kano. Hakeem ke driving. Farida kuma nata fada mata how much she will miss her, duk da cewa ba randa baza su yi fada ba. 〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️ Tun ran da Abdallah ya fada ma Mide abun nan, ya dawo kaman marasa lafiya. Ran Thursday ma daya je gurin aiki, da kyar yake attending to patients, sai ya rubuta medication, sai ya kara gogewa, saboda rubbish kawai yake rubutawa. Ko kuma inya tambayi patient abun dake damun su, in suka fada mai, kafun ya rubuta medication, sai ya manta abun da suka ce ke damun su, sai kuma ya kara tambaya. Daya isa wajan aiki ran Thursday, ya fada ma abokan sa komai, duk sun tausaya masa. Farouq yace Nabila bata sani ba ne, data fada mai maybe. Yace ai jiya abun ya faru, kuma shine ma ya fada ma Nafisa. Asim yace toh kar Allah ya sa Nafisa ma tayi fushi tace bata son shi. Abdallah yace mai, karya damu hakan bazai faru ba, ai ba banbancin komai a tsakanin su. Suma din kaddara ce ta fada akan su. Yau Saturday, dutyn rana gareshi, so by 8:am, ya je kitchen, domin ya taimaka ma umma da arranging din breakfast a kan dinning table. Umma da Abba sunyi noticing din chanji game da shi, amma suka yi ignoring din sa, saboda daman bukatan su ya biya, ya bar soyayya da yar yarbawa. Da suka gama arranging din komai, suka zauna, suka ci breakfast. Suna gama ci, Abba yace Abdallah ya kai plates kitchen ya dawo, suna da magana. Abdallah najin haka, heart din sa ya fara beating da karfi. Allah yasa dai lafiya. Da Abdallah ya gama clearing din dinning, ya koma ya zauna. Sanda Abba yayi clearing din muryar sa, yace "nayi magana da Alhaji Madaki, kuma ya yarda, ba matsala. Kuma tunda gobe ranan hutun ka ne, kana iya zuwa gidan sa gobe dan ku gana da Safiya." Abba ya fada. "Kai MashaAlla, naji dadi sosai." Umma ta fada. "Banga use din zuwa na gidan ba, tunda ku iyayen kun riga kun gana, ku sa date kawai." Abdallah ya fada. "You are very stupid for saying that. Kuma in ka cika kai dana iska ne, kar ka je. Ku kuke sa mutum yake fade fade. Mtchww." Abba ya ja tsaki ya bar wajan a fusace "Kaga irin ta ko? Duk dan daya ki bin umarnin iyayen sa, duk abun daya faru shi yaja ma kan sa." Umma ta fada, itama ta tashi ta bar dinningn. "Na shiga uku na, wani laifi na ma su Abba ne a rayuwar nan? Ya ilahi, gani gare ka. Kun ce in rabu da zuciya na, na rabu da ita, amma still kun ki bari na. Bakomai, zan bi umarnin ku, saboda naga daidai a rayuwa na." Abdallah ya fada da hawaye a idon sa. Sai ya kara cewa "koya qalbi na take oho, Allah sarki qalbin Abdallah, I hope you will forgive and learn to move on, and lastly keep my heart save." Abdallah ya fada da hawaye still a idon sa. Daya share hawayen sa, shima ya tashi ya tafi dakin sa. Daya shiga dakin sa, ya hau kan gado, ya kwanta, ya rufe kan sa da blanket. Sai hawaye keta zuba a idanuwan sa shar shar kaman karamin yaro. Haka ya ita kuka har yayi barci. 〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️ Su Farida basu bar wajan ba, sanda suka ga motan ya tashi. Olamide bata isa Kano ba sai 3:30pm. Daman Nafisa na riga ta isa, so duk sanda ta koma school, her habity is always there to welcome her. Tana sallama, Nafisa ta fito da gudu tayj hugging din ta. Ita kuma Mide ta wani fashe da kuka. "A'a habibty kar kiyi haka, bari mu kai kayan nan ciki tukun. Nida nayi zaton zaki yi hugging dina yanda muka saba." Nafisa ta fada tana share mata hawaye. Suka fara kwashe kayan Mide zuwa dakin su. Da suka gama, Nafisa ta ce Mide ta zauna, ita kuma ta shiga ta kawo mata ruwa. "Habibty ga ruwa ki sha." Nafisa ta fada, sannan ta zauna kusa da Mide. "Nagode habibty." Olamide ta fada, sannan ta karbi ruwan ta sha. Data gama sha, tace "habibty shikenan nida ifemi? I miss his sweet voice wallahi. I miss him saying qalbin Abdallah, I miss him saying yide'am. I just miss everything about my love. I miss Abdallah so much wallahi. My Abdallah, my autan umma, my bloody." Alokacin Olamide tana magana tana kuka. Nafisa too felt soo emotional hearing all this. Haka tayi hugging din Mide tana kuka itama. "Habibty have lost the love of my life just because of a stupid reason. Nayi zaton mutani sunyi changing din view din su akan *BANBANCIN KABILA* ne, amma I was wrong. Iyayen sa sun rabamu saboda wannan reason din? Habibty ba Allah ya hallice mu duka ba?" Olamide ta tambayi Nafisa. "Allah ya hallice mu duka." Nafisa ta fada. "Then meyasa aka rabani da shi saboda *BANBANCI KABILA* ?" Olamide ta kara tambayan ta. "Saboda har yanzu Allah bai ganar da su bane". Nafisa ta amsa. Haka Mide ta ita tambayan Nafisa questions, kala kala, ita kuma Nafisa, tana ta bata answers din da zasu sa tayi calming. Olamide ta sha kuka ba kadan ba, itama Nafisa ta taya ta. "Habibty kukan nan ya isa, kar yasa kiyi ciwo fa?" Nafisa ta fada. "I don't care habibty, I miss ifemi." Olamide ta fada tana kara sautin kukan ta. ```Thanks for reading, I appreciate. For those who comment, you guys have my heart wallahi. I love you all, may Allah bless you all.``` Comment Like & Share. ~Zeexee ce~ 🖊️🖊️🖊️ Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels