Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels ❤️ *MATAR OGA NA* ❤️ SHORT STORY MALLAKI ❤️UMMY AYSHA ❤️ Page one """Da Sassarfa ta fito daga Toilet jin wayar ta nata Ring. Ganin ansa My ya tabbatar mata da OGA'n tane. Zama tayi bakin gadon ta ɗauki wayar ta mayar masa dakira tana sakin murmushi. Saida ta kusa tsinkewa kamin taji an ɗauka Yayi shuru alamar yayi fushi. Ajiyar zuciya ta sauke tace. My...shuru bai amsaba sai hucin numfashinta dake Saukar mata da wata kafurar kasala kota ina duk sadda zai huro shi. Dan Allah My kayi hakuri kaji,ina toilet ne ina wanka, banjima da shigowa daga aiki ba nima ina tare da tinaninka fatana kawai na watsa ruwa nakiraka naji ya kake. Yayi miki kyau yace yana katse wayar. Jin ya katse yasata dafe kanta da sauke ajiyar zuciya zuciyar ta cike da bakin cikin wannan halin bauɗaɗɗan mijin nata, ace kai komi zuciya kamar kafuri som baka da uzuri. Tsaki tayi bata sake bi takan wayar ba ta mike cikin isa da izza ta isa gaban tafkeken mirror ta zauna ta tsurama fuskarta ido. Kyakyawar macace ajin farko,a shekaru zatakai 35 amma inbaka saniba zakai tinanin bata wuce 25 haka saboda yanda Allah ya girka jikinta, farace sol babu d'igon baki a jikinta ko alama,ga wata yalwatacciyar suma dake kwance luf-luf har bisa marfin bayanta, dogon hancinta taja dakeda digon tawwada Allah akai daya karamta kyau, ta saki murmushi tana taune pink lips dinta tare da furta. Ayyah ni Aymah nafara tsufa fa, yanzu nan da 4month zan cika shekaru 36,Cikin kuma wani yanayi ta dan fara bin farar fatar jikin nata da kallo har ta gangaro kan tudun kirjinta da suke tsaye kyam babu alamar Faduwa ko wani jigata a tattare dasu, Dan kirjinta ko na wata budurwar Albarka,Wannan ma ya kara tabbatar mun da lallai cikakkiyar yar gayuce mai tsannin kula da kanta. Mai ta ɗan murza sama sama ko powder bata shafaba ta zirara kwalli ta taje yalwatacciyar girar ta tare da tashi ta isa ga kafceciyar wadrob dinta dake shake da kaya na alfarma ta zubamasu ido, Can ta matsa layin Abayu ta zaro wata Blue Black dake ta shekin duwatsu ta dauki pant da bra ta sanya Tare da zura abinta tabi lungu da sako na jikinta ta murje da turaran Humra UMSAD INCENSE mai bala'in sanyi,Bayan tagama ta ɗakko wasu flat din takalma masu taushi ta zura ga farar kafarta ta fara sakkowa zuwa kasa inda mai aikinta ta jeramata abinci. Masha Allah nace lokacin danaga uwar daula dake shimfiɗe falon nan wanda alkalami yayi kaɗan da lissafawa. Akan Dinning ta isa ta fara bubuɗe kulolin mai dauke da tuwo da miyar sa da kuma felfesun Yan ciki sai kamshi suke, anan naga ta zuba tuwon semo da miyar ɗanyar kubewa daya sha naman zabo ,ta kwarara man shanu take kamshi ya gauraye ko ina na palon,hannuta ta wanke tanajin yanda yawun ta ke tsinkewa tayi Bissimillah ta faracin abinta tana lumshe ido,Ba karya Baraka ta iya girki wanda duk wanda yaci sai yaji kamar ya zare. Bayan ta gama ta wanke hannuta tare da yin hamdala ta tsiyaya kunun aya mai masifar sanyi daya sha Madara da dabino da kwakwa yayi kyau matuka takora tanayi tana lumshe ido. Keeeeyyy! tafarajin ana buɗe Katon get din su na farko,Domin guda biyu ne duk wanda zaizo gidan nasu ana farko yake ajiye abin hawa daga ita sai maigidan keda damar wutowa har na farkon. A zabure ta mike tsaye ta isa ga window dan tabbatar da abinda take tunani. Ilaiko manyan motocin OGA Natane guda ukku suka kutso kai. Kalle kalle ta fara a cikin palon kamin ta tsayar da hankalinta akan abincin datagama ci wanda ita duk duniya batada abinda takeso sama dashi, Yayin da shikuma mijin nata yake da banbancin ra'ayi da ita, hasalima abinson nata shine makiyinsa wato tuwo. Kamin tagama nazarinta taji an'buɗe palon an'shigo Da sauri ta kalli P.A din nasa ya duka ya gaidata ta amsa tana zubama kofar ido. Lokaci daya wani dattijon mutum da bazai wuce shekara 50 ba ya turo kofar ya shigo hannushi rike da waya fuskar nan tashi babu alamar rahma a tattare da ita. Rawa sosai jikinta ya ɗauka amma ta dake tare da washemai baki ta nufi inda yake da sassarfa da niyyar yin welcoming nashi. Wata wahalalla tsawa ya dakamata yana hura hanci da zubamata jajayen idanuwan shi yace. Kar in sake in ganki gabana ,in kau har kikayi wannan kuskuran wallahi sai na canzamiki kamanni. Sorry sir! kawai tace tanayin kasa da idonta. Siririn tsaki yaja kamin ya kwashi jikkar shi yayi dakin shi na sama. Kiching ta shiga da sauri ta iske Baraka na bacci ta tayar da ita ta hanyar radamata oga ya dawo ta maza tamasa jollop din taliya. Jiki na bari ta amsa kamin ita kuma ta kwashi lemo da ruwa ta haura dakin nashi duk da gabanta na bugawa amma ta dake da Alkawari komi zaimata saidai ya mata amma saita zauna wajen shi. Bayan ta tura plon bataganshiba hakan ya tabbatar mata da cewa yana bedroom. Turawa tayi tashiga ta iskeshi zaune dagashi sai singlet da dogon wandon shaddar dake jikinshi yana amsa waya . Gefe ta rakuba ta zauna tana wasa da yatsun hannunta. Katsewa yayi ya kalleta kamin yace. Duk wahalar danasha daga Abuja har katsina amma ace ruwa zakibani ,kina kau da hankali kuwa kau Aymah? "Ranka ya daɗe yanzu za'amaka banson zaka dawo bane tace itama fuska ba walwala dan tafara gajiya da halin sa . Hannu ya yarfa yace shikenan ya miki kyau,ai dayake ke ba mace bace baki iya tarairaya mijiba ,Dakikaga nayi fushi ai saiki dage damun waya har in sakko ko? amma sai bakiyiba gashi nazo bakomi a gidan. Murmushi kawai tayi batacee komi ba dan dama shi akwai tsogwami kamar tsoho. Au kin ɗaukan mahaukaci ko? Dan samun saukin fadan nashi tace. kayi hakuri Yallaɓai bazan sake ba in sha Allah kaji?. Zan duba ingani in kindace a yafe miki tukunnah ya faɗa a dakile cikin isa da gadara. Shuru kawai tayi batasake maganaba. Wanka yatashi yashiga yayi kamin ya fito ta fiddomai jallabiya da gajeran wando ta feshesubda turare mai kamshi. Bayan tagama ta sauka ta dakkomai abincin da aka dafa ta ajiyemai kana ta koma gefe ta kunna data ta fara chart da kawayen ta . Bayan ya fito yaci ya koshi ya ɗauki computer ya fara aiki bayan ya zura medical glass dinsa. Kallon shi tayi yanda ko damuwa da inda take baiba ba wani farin ciki ya dawo wajen iyalin sa A tattare dashi, bayan watan shi shidda baizo gidaba kai Allah ka gyaraman Adnan ta fada kasa kasa. Ameen! ko kinfara gajiya da nine in sauwakemaki yafada kai tsaye batare daya dago kanshi ba Kirjinta taji yabuga da karfi, cikin rawar baki tacw A'a,kawai naga bakawaniyi farin ciki da ganina ba, Duk yanda ka kwashe watanni bakasani ido ba. Dan murmushi yayi na gefen baki tare da cewa in baccin abinki nida ina cen ina nema miki abinci, kuma ina ajemiki duk abinda kike bukata kana kinamun waya kinajin yanda nike akwai wani abu ba wannan ba. Ganin dai zata cutu kuma ba ganewa yake ba yasata mike wa tafara wani tako mai jan hankali ta isa ga inda yake ta ɗauke computer tare da kamo hannuwansa duka biyun ta zuba idonta cikin nashi na dan lokaci kamin ta janye tace yallabai kason ni ba dutsi bace ,yar adam ce kamar kai,kason inacin mai kyau in sha mai kyau,akwia bukatar najika kusa dani,dan Allah na rokeka ka ajiye aikin nan ka bani kulawa kamar yanda kowane miji kebama matar sa,wallahi nayi missing dinka dan Allah takarasa cikin rawar murya idonta na cika da hawaye.. Rai ɓace yace kinji abinda ke hanani zuwa wajen ki wallahi Aymah Jaraba,da aikin zanji koko da bata lokacina bisa ke,wannan abun zai iya daukar man lokaci akallah 5mnt, to na tabbata wannan lokacin ya isa in ciccike wasu takaddu masu Mahimman ci, Dan Allah kibani sarari in naji ina da bukata zan miki magana tashima kije Ɗakin ki Allah ya bamu Alkhairi... Tashi tayi tanajin wani mugun sarawa da kanta ke mata ta fita daga Ɗakin ya bita da ido yana zubamata harara da jan tsaki yacigaba da abinda yake.... *Akwai zaffan magunguna dana kawo masu karkato da hankalin maigida duk bala'in taurin ransa kuwa, kai dai ka yarda da Allah kawai babu boka babu tsubbu ikom Allah ne kawai dakuma sanin mkamar aiki in sha allah,kasa tsoron Allah kamin kayi amfani da maganin mu dan neman karin bayanin kamin magana ta Whatsapp Number nah 07038423451* Nayi cancel mijin zee saboda wani dalili, akwia masu mun korafi to ga wani nan zai wakilci wancen don yamafi shi in sha Allah. Daga masoyiyar ku har kullum Ummy Aysha ❤️ ❤️ *MATAR OGA NA*❤️ SHORT STORY MALLAKI ❤️UMMY AYSHA ❤️ *Page two* ____Tana shiga ta faɗa Toilet ganin gab ake da sallah mangariba ta watsa ruwa da dauro Alwallah, bayan ta fito ta zura riga marar nawie har ƙasa da dogon hijjob dayamata masifar kyau tayi zaune gefen gado tana azkhar din yamma kamin akira Sallah. Ido ta lumshe batabari sheɗan yasata kokonto ba har taji sadda aka kabbara sallah ta tashi ta gabatar,bayan ta ida ta daga hannuwanta sama hawaye na silalomata tace. Yah Allah kason halin da nike ciki, Allah kafini sanin kaina, Allah kazama gatana, Allah ka karemun mutuncina kabani dangana daga halin da nike ciki, Allah ka fahimtar da mijina cutar dani dayake , Allah ka shiryamun shi,Ta dade tana addu'a kamin ta shafa ta mike ta koma bisa gado ta ɗauki karamin Alkur'ani ta tafara rera karatu cikin sanyin muryarta mai fitar da haruffan tajweed tiryan -tiryan. Ana gama sallah isha tayi sallah tashiga toilet tayi wanka sosai tazo ta zuba Humra masu kyau da kamshi ta fesa turaruka,wani sanyin daɗi ke tashi daga jikinta,Wata pink din riga ta ɗauka marar hannu ta sanya, kasancewar kirjinta Cike yake hakan yaba riga damar yin tsaye kyam akan farin fatarta,dogon hijjob ta zura tayi ɗakin shi da sallama tashiga, a falo ta cire ta yar tare da nufar bedroom ɗin sa. Kuri ta iske shi Yayima computer gaban sa, ba Alamar yayi Sallah dan aiki kawai yake tamkar agwogwo. Murmushi kawai tayi cikin kawar da damuwar ta tace... My sannu da aiki Allah yama jagora sannu kaji,Badon banson takan abunba aidana kamama mijina ya huta ko? Ɗagowa yayi tare da cewa. ki dai kasheni kike so kawai,yo ina ruwanki da aikina ko wanda kikeyi rainashi kikai da zaki sama nawa ido, Kai nifa banason kilbibin nan naku na matan hausawa inda matan turawa sukafiku kenan, basa shiga Harkar daba tasu ba,dake watace kina shigowa kika ganni ina aiki zaki koma da baya batare da kinbari ko kofar nan tayi ihun da zai katseni ba, amma kin tsaya saida hali damun iyayi to inkingama jeki na nemeki.. Allah ya musanyama abinda kakemun da Alkhairi tace A raunace kamin ta bude kofa ta fita dan yau tafarajin tsanar halin mijin nata na cin fuska. kai tsaye kiching ta nufa ta iske Baraka zaune . Murmushi tamata tace. Sannu Baraka ki dauka kawai kije. Cikin ladabi tace Haj ba:aima Alhaji komi?. Eh bayacin abincin dare basai kin'mai ba ngd. To ! tace'' ta hada abincinta ta tafi ta bita ta rufe kofar. Akan kujera ta dawo ta zauna ta baza tagumi can kuma ta tashi ta shiga dakinta ta canza shiri ta dauko key din motar ta ta fita daga gidan. Kai tsaye wata katafariya Asibiti dake nan kusa dasu cikin G.R.A ta nufa mai suna U&A SPECIAL HOSPITAL . Aguje maigadin ya taso ya bude mata kofar yana mata sannu da zuwa . Malam Habu ya aikin tace tana zaro 2k tabashi ya karba yana faɗin Alhamdulillahi Haj ngd Allah ya biya ya yaye damuwa da kunci yasa agama duniya lfy . Ido ta lumshe tana fadin ameen Malam habu ta nemi shigewa ciki. Am Haj nace ba! Malam Habu ya faɗa yana sosa kai. Uhm malam Habu kana da buƙatar wani abu ne? ta fada tana zubamai ido. Kanshi ya ɗan sosa yace. Duk yau bansa Baraka da yarana ido ba,Sai nikejin kamar ban masu adalci ba,gashi kuma dare ya soma kana Lawali bayanan balle ya tsayaman in ruga in'dawo Kamar yanda aka saba.. Shuru tayi tana nazari,inama ace mijinta haka yake, gaskiya sometimes dukiya farin cikin mai itane kawai,Zata iya bayar da komi nata data mallaka indai har zata samu kulawa daga mijinta, Malam Habu bashi da komi amma hankalin shi naga matar shi , Yana ganin rashin kyautatawar shi na rashin ganin su yau ɗaya,inaga ita da zata kwashe shekara ko wata shidda bata sanya mijinta idoba,in kuma yazo gidan ma bata ita yake ba, Lallai tarin dukiya bashine farin cikin Rayuwar Aure ba,kulawa tafi komi daɗi da saukar da nishaɗi,ita dai babu abinda ta rasa sai rashin tattalin so daga mai gidan ta. Kiyi hakuri Dan Allah Haj, bawai na fadaba ne dan ɓatamaki A'a kawai inason sauke hakkin iyalina ne da Allah ya wajeb tamun. Murmushi ta ƙaƙalo tana mai jin idonta na cika da kwallah tace. . Baba baka bataman ba hasalima na kara yabawa da halayyan ka,kana rashin Lawali bazai isa hujjar da zata hanaka zuwa ga matar ka da yaranka ba, Dan haka ka kulle get din kawai kaje gidan Allah ya bamu Alkhairi,in yaso da Asuba kadawo. Wani yalwataccen farin ciki ya bayyana ga fuskarshi har kasa ya duke yanamata godiya. Kai kawai ta jinjinamai tare da sake zaro 3k ta mikamai tace . ungo asaiwa yara bread. Aa Haj ni wannan alfarma ma kawai da kikaman ta isheni Allah ya biyamaki bukata yafada zai tafi ta buɗe ta fito tana masa magiya. Da kyal ya amsa fuskar shi na bayyana Maɗaukakin farin ci. Ita kuma ta koma tashiga ciki tana ta tattauna kalaman tsohon nan,shima Mal habu kulle ko ina yayi kamin yatafi yanata washe baki zai kwana cikin iyalin shi,Dan dama bashi da ra'ayin gadi dan bashi da yanda zayyi ne yake yinsa amma shi baya wasa da lamarin iyalin shi, gashi dama tsohone amma mai ran karfe 😜 *Malam Habu mijine ga Baraka mai aikin Aymah ,suna da yara biyu Abdul Kareem wanda suke cema A/K shekarar shi 25 cif-cif sai Nabeel yana da shekara 15 daga nan basu sake haihuwar ba,Kasan su Aymah suke,Baraka da kanta ta bukaci datanaso ta dingama Aymah aiki ta amincemata dan taji mutuniyar kirkice a wajen yan unguwa,bayan kuma ta fara aikin ta ida gane lallai Baraka tana da mutunci ga dattako ga iya girki da tsabta, bayan ta bude Asibitin ta kuma ta ɗauki mijin Baraka aiki tana bashi 50k duk wata ita kuma baraka tana bata 30k wanda hakan ba karamin rufamasu Asiri Yayi ba, dan dama basu dashi basu da hanyar samu suna dai Cikin yanayi kamin Allah ya warware masu. Bayan ta fito ta fara tako cikin sanyin jiki,daka ganta kason tana cikin damuwa, kai tsaye ta shige cikin Asibitin, A reception ta tsaya ta karɓi key din office dinta kamin ta haura sama ta bude wani office da aka rubuta *DOCTOR AYMAH*. Katafaran wajene daya gaji da hadu ga wata lafiyayyan kujera mai kamar gado ta hutawa a takaice dai komi akwai na zamani mai masifar kyau. Hakan yasata bajewa akai ta fara wani wahalallan kuka,Jikinta kau cikin lokaci ya ɗauki rawa zazzaɓi mai zafi ya rufeta. Dakyal ta mike ta dakko paracitimol da ruwa ta balla tasha ta koma ta lumshe ido. Wannan wace iriyar rayuwace,Adnan mutum ne amma kamar ba Lafiyayye ba, Mugun ne , Akwai iya tauye hakkin iyalin shi, Yayin da ita kuma ta kasance mai tsananin bukata,shikam aikin gaban sa yafiyemai faranta mata. A haka taita nazari tana tuno yanda ta fara fuskanta matsal tin bayan Auran su. Ido ta zaro lokacin dataga karfe biyu da rabi tayi na dare, da sauri ta zaro wayarta ta lasa number shi ta shiga kiran shi. Tana gab da katsewa ya ɗauka Tare da faɗin. kina bukatar kudi ne ko wani abu?. Kamar ta ci uwarsa haka taji amma ta daure tace. Dama na manta banfadama zanfita ba nace bari in kiraka. Ohk ! ai nason kina aiki so wannan ba damuwa bane,Nason kinso dai kawai ki Ɓataman lokaci, zaki iya ajiye waya ina aiki. Ajiyewa tayi tare da mikewa ta ɗauro alwallah ta fara sallah da neman zabin Allah akan rayuwarta wadda ta fara isarta gabaki ɗaya,Dan tafarajin tsanar Adnan har cikin Ranta. A haka akayi Asuba, dakyal ta iya sallah tayi azkar kamin ta koma bacci, Washe gari sai karfe 11 tayi wanka tafito dan komawa gida A wajen parking space ta haɗu da Aminiyar ta Haj Asiya. Bayan sungaisa tabita da ido tare da jan hannu Aymah suka shiga mota ta kuramata ido tare da cewa mike damunki Haj Aymah. Murmushin takaici tayi tana mai kama hannunta ta rike sosai tana cije lips kamin tace. *Asiya ina cikin damuwa, Babu abinda na nema narasa agidan Adnan,amma kulawa ko som.bana samu,aikinshi shine farin cikin shi, Asiya kinson ina da matslaa ina bukatar mijina Asiya, banaso nafada halaka dan Allah kitayani Addu'a Allah ya tsareni yakuma bani juriya.. Murmushin takaici Asiya tayi tare da faɗin. wai ke Aymah miyasa kike da bala'in taurin kaine,akan mi,bazaki iya kashe auran wannan Dattijon banza ba,yaje ya auri biro da takar da mana,mutum ko soyayya bai iyaba kamar wani dabba. Hannu Aymah taɗagamata tace. bance kizageshi ba mijina ne,amma kimun addu'ar kawai. Wayarta ta zaro ta fara latsomata wani group Ɗin magunguna na Ummy Aysha mai suna *Kayan gyaran aure*. Anan ta shiga tace kinga wannan group din,indai har kikabi abinda aka ce wallahi wannan mijin naki mai mazuran banza sai yadawo kanki. Kaya ne ake siyar wa na bala'i ko jiya saida Haj Hauwa ta kirani tana kara fadaman kyan kayan,nima sai Abban haneef zaizo zanje in kwaso, Babu kayan banza akwai kaya masu kyau amma akwai kuɗi to amma biyan buƙata yafi dogon buri. Murmushi tayi tace. ina bazan taɓa amfanin da abinda zai karkato hankalin shi akaina ba ,saidai nima ayau nafarajin tsanar rayuwa dashi da nike a yanzu inaso nayi sabon aure na soyayya da kulawa, Adam badan komi ya aureni ba sai dan kar ace ya zauna bashi da iyali, shekarata 15 da auran mu ,amma kullum jiya iyau bazan iyaba sai dai zanbi shawararki wajen mallakar duk abinda zai jawo hankalin shi kaina yayin da Nikuma zan murza kanbuna,sai ya gane bashi da wayo wallahi azeem,dan saina rama duk abinda yaman kamin in barshi in nuna mai wutsiyar rakumi tayi Nisa da kasa. Wata Sassanya guɗa Asiya ta saki dan dama ta dade tana burin rabuwar Aymah da Adnan dan bashi da mutunci, baya barin kosu kawayenta na rabarta duk wani wanda zai kasance zata raba taji dadi baya yarda yafiso taita rayuwa daga ita sai Baraka mai aiki wacce itama dakyal ya amince da zuwanta, Ga Aymah marainiya ce shekara su ɗaya da aure iyayen ta zasu kawomata ziyara sukayi accident suka mutu, danginta kuma kaf dinsu suna Agadas dan buzayene asalin su. Asiya tace yanzu Bara kiga, kinga ba daɗewa yakeba ko,so yanzu zamuje gidan Ummy Aysha mu karɓo sakon kingane,Baru mubi address ɗinta . Kai ta jinjinamata kamin ta lumshe ido, Asiya tafara kiran number ta suka gaisa ta shedamata zuwan su . Kwatancen gidan ta ta masu suka ɗauki hanya. Basusha wahala ba suka gane gidan,. Cikin girmamawa da mutuntawa ta tarbesu suka dan tattauna matsala gidan Aymah kamin ta ɗakko wata jikka mai masifar kamshi gabaki daya ta mamaye palon da suke zaune. Zama tayi tana sakin murmushi tare da ɗakko Wata karamar kwalba kamar ta garin lalle ta jujjuyata ta kalli Aymah data zubamata ido kamin tace . karɓa wannan Humra ce mai tsananin sirri,karkiyi kuskuran wani yaji kamshinta zaki iya cutar da shi,wannan kuma zakiyi amfani dashi ta hanyar tafasa shi ki jefa tsamiya guda daya kisha have cup,sauran bayanin in kindawo mayi magana. Kai ta dagama ta dan ita kanta kamshin wani bala'in yanayi takeji yana jefata duk takasa natsuwa,bayan tabiya kudin suka tashi suka tafi. Aymah ta kalli Asiya tace . Sister wallahi na natsu da matar nan kana daganin abun nan zayyi dan ni bakijima yanda kikeji ba Ta karasa tana ɗaukar Ruwa ta dan watsama fuskar ta kamin ta sauke ajiyar zuciya. Asiya ta kalleta cikkn tausayawa tace" To nima ai gobe zanzo in karɓi nawa kinson oga na hanya . Baki kawai Aymah ta taɓe sukaje Ta sauke Asiya ta wuce gidanta. A palo ta iske shi zaune da computer kamar kullum yana latse latse gefen shi kuma ruwan paro ne mai sanyi. Sannu da gida tace tana neman wucewa. Yaww yace batare daya kalleta ba. Shafashi tai zata wuce a zabure ya juyo yana kallonta batarema da tason yanayi ba. Computer ya rufe tare da lafewa cikin kujerun ya farabinta da kallo yanda take juya jikinta cikin natsuwa Har ta haura sama. Wani masifaffan kamshi yakejin tanayi mai saukar mai da kasala ,wayar shi ya dakko amma kamshin yaki barin hancinshi,bai an'kareba yafarajin canjin yanayinsa. Yah Salam yace a gigice yana mikewa ganin yanda ya zuba uban kere ta cikin jallabiyar sa. Bakin shi ya cika da iska yanajin jijiyar sji kamar ta tsinke, A haukace ya fara haurawa saman bibbiyu ukku ukku fatanshi kawai yaje gareta. Tsaye take kamshin duk ya isheta gabaki daya sai Murmushi take. ahaka ta tsince kayanta burinta tayi wanka amma kamshin hannuta dadin shaka yakemata. Turo kofar da akai yasata kallon wajen a gigice dan tinda take dashi tsawon shekara sha biyar baitaba shiga dakinta ba aganinsa kaskancine yazo wajenta. Cikin mamaki tace lfy Yallabai. Kanshi ya dan sosa yana nunamata saitin jikin shi da ido yace" am inason kebancewa dake yanzu ba anjima ba. Cikin farin ciki tace mai dagaske. Ba walwala fuskarshi yace. " eh kiyi sauri amma inada abinyi naga kincika matsawane nace bari in taimaka miki. Ok ok tace cikin fara'a kamin tace Muje dama nayi wanka asibiti. Fita sukai har dakin shi ,Baibari sun karasaba palo ya fara Rarumar ta. Biyemai tayi tare da ida hargitsa mai lissafi,cikin lokaci ya fara dafe kanshi da kwarara wani uban ihu kamin yayi kanta gadan gadan da Niyyar cimma burinshi. Duk bala'in yanayin jin dadin datake ciki bai hanata sanya duka karfinta ba ta turashi kasa ta tashi aguje tayi dakinta ta mayar ta rufe tare da jingina da kofar tana sauke ajiyar zuciya . Ida zubewa kasa tayi tanajin wani masifaffan yanayi ga cikinta sai kartamata yake. A'Hankali idonta suka fara saukar da kwallah masu tsananin zafi. "Aymah miye haka ki bude nace in taimakamaki Adnan ya faɗa a gigice cikin tashin hankali Yanata saa da marwa. Dakyal cikin rawar murya tace aa kabarshi nagode nasamu gamsuwa ahakama. Wallahi Aymah kikaja jijiyata ta tsinke sainaci ubanki jakar inace ke nace kibude ko dama ban faɗamiki zan nemekiba in ni naso..... *Wallahi babu dadin baki ko wani Abu,ku gwada Humra sirri na kugani,amma gaskiya tana da tsada in kinson baki da halin saye dan Allah karmu ɓatama juna lokaci 07038423451* ❤️ *MATAR OGA NA*❤️ ❤️ *UMMY AYSHA* ❤️ *Page three* ***Jajayen idonta ta ɗago da kyal tana mayar da numfashi kamin cikin wata kasalalliyar murya tace "Yallabai naga dai ni zaka taimakawa kuma nace A'a so kabar ni dan Allah . Ta ƙarasa tana bajewa wajen tare da damke marar ta. Karkarwa sosai jikin shi ya ɗauka yanajin wani iri kamar jikin shi zai tsinke tsabar bala'in mikewa da yayi. A guje yayi dakin shi ya haye gado tare da kwaso filo ya hau tumurmuza amma duka dai abanza. Ƙasa ya sakko tare da dora hannunshi akan kwalkwalin dake kanshi kana ya saki wani marayan kuka yace. Tabbas Aymah saina illataki na muki lahani kamar ni mijin ki zan nemeki amma kicemun a'a, wallahi sai na baki tarbiyya. Ganin wannan bata masaba yasashi tashi ya kara komawa bakin kofar yafara mata fada da nuna isa da gadara amma ko kala batacemai ba dan ita kanta hawaye take . Saida ya gaji ya koma dakin shi ya samu ya shiga toilet yyi wanka da ruwa mai balain sanyi ko yaji relief amma shuru . Samu yayi shape-shape ya zura kayan shi ko mai bai Murzaba ya sakko yana sake kallon sashen jikin shi da babu alamar kwanciya har lokacin kyam yake tsaye kamar falwaya. Tsaki yyi tare da sakeyin kwafa akaro na ba adadi kamin ya ɗauki wayar shi ya kira Driver shi dan su dan fita dan bazai iya tuki ba amma yaji wayar duk kashe. Kanshi ya dafe yana tino magana da yace dasu kowa zai iya kashe wayar shi yaje ya samu dogon hutu na tsawon wata daya kamin su koma bakin aiki ashe kanshi yayiwa tsiya. Babba riga ya zuba tare da fitowa palo yana sake bubbuɗata dan rufama kanshi Asiri. Baraka kawai ya iske tana goge kayan kallo har kasa ta gaidashi ya amsa cikin isa yana niyyar yin waje kuma ya dan juyo yace "Ko mijin ki ya iya tukin mota? Juyowa tayi dan ta tabbatar da da ita yake koya . Kai ya jinjinamata Alamar tabbatar wa. Cikin ladabi tace. " gaskiya aa yallabai som Bai iyaba gadi dai ne yake yi Asibitin Hajiya amma akwai Babban Yaron mu ya iya dan da yana tuka motar makwabcin mu sunayi jigila Dutsama zuwa Katsina Kamin kuma Allah ya.Kawo sanadi mai Abun yayi accident ya rasu aka kuma rasa motar ya dawo gida da xama. Fuska ya yamutsa yace akiraman shi yanzu na bada 30mnt. To tace tana ajiye Kyallen hannuta tare da zaro wayar ta da Aymah ta saimata ta fara neman layin da aka yi save da Wannan Yaron(Alkunya mutanan da wa yaran su na fari) Bayan an ɗauka tace . Wannan Yaron kazo yanzu maza dan Allah nan gidan da nike aiki,eh bayan mu nan,to shikenan ina jira Allah yayi albarka ta karasa tana datse wayar tare da kallen gefen Alhaji Adnan da yaketa mutsu mutsu yanajin kamar an samai maciji cikin wando duk ya kasa sukuni sai uban faɗi yake karama Babba rigar shi. Alhaji yana hanya cikin izinin Allah tace tana mikewa tayi kiching. Kai ya jinjinamata yana auno hukuncin da zaiwa Aymah gashi ta hanashi aikin shi ta kuma ki aminta da shi. Wani tinani yafara wanda kuma cikin lokaci ya aminta dashi ,Tabbas ya aminta dashi dan Babu makawa fitar da tayi jiya wani taje ya kwanta da ita. Ranshi ne ya sake ɓaci yaji matukar zafi a zuciyar shi dan shikan shi ya son yana son Aymah kwarai amma shi bayason matsawa yana bama aikin sa lokacin sa kwarai baya so kamai kutse cikin lamarin Aiki yanzu ka zame masa matsala . Baraka da har ta koma kiching ta sake fitowa har kasa tace ''Alhaji ya iso yana cen wajen get din farko. Fita ki shigo dashi yace batare da ya kalleta ba. Tashi tayi ta fita ba ajimaba suka dawo da wani Matashin saurayi mai tsananin kyau da haiba, Chocolate colour ne irin mai hasken nan wato sirkin madara da milo amma a idon wani zasu iya cemasa fari ma,Yana da doguwar fuska mai dauke da manyan idanuwa masu yalwar Gashi girar shi ciccike ,sumar kanshi kau ya mata wani aski mai masifar kyau sai sheki take da ganin ta kason ta fulanine dan wani kwarya kwara takeyi tsabar kyau da gyara,Ga Wani shegen saje ya adana a kan fuskar tashi daya zagaye suut mai matukar kyau daya kara haskashi,Lips din shi na kasa light pink ne sosai saina saman mai dan duhu kaɗan,Masha Allah zanso kuga wannan haɗaddan matashin da a shekaru baifi 25 ba,Riga da wando ne yan kanti a jikin shi duk da ba sabbi bane amma kuma basu sha wahala ba,A wanke suke tass a goge Sai kamshi yake . Baraka tace wannan yaron ina rokon Allah yasa Alkhairi ne ya kawoka gidan nan. Ameen Inna yace cikin Daddaɗar muryar sa. Sallama tayi ta shiga palon Yayin da Alhaji Adnan ya amsa . Tace gashinan tsaye bakin kofa. Ohk shigo dashi yace yana zubama kofar ido. Fita tayi suka dawo tare da sallama suka shigo su duka suka samu kasa suka zauna cikin sanyin muryar sa mai nuni da natsuwar sa da tarbiyyar sa yace. Yallabai barka da rana . Alh Adnan yace Lfy ka iya mota? Kai ya daga mishi kawai dan in dai isa ce yafi Alhaji Adnan ɗin ma . Key ya bashi yace gashi na daukeka aiki duk wata zan baka dubu hamsin yayima ?, Dan ko bana nan ina so ka dingamun wani aiki ne da saina tafi xan barma shi . Tom Allah ya bani ikon yi yace babu yabo ba fallasa dan ya kula Alhajin ɗan rainin wayone gani yake dan zai bashi kudi ihun murna zaitayi yana .masa doddofa ai aikin wahala zai mai dan haka ba wani murna da zai zage yanayi zayyi godiya ga Allah dan yason shine mai tsara komi kawai... Key ya bashi yace gashi muje ka kaini wajen da zan huta. Karɓa yayi kamin ya juya ga mahaifiyar shi da gabanta ke faduwa ta manta batajamasa kunne ba tason halinsa sarai. Gwiwar kafarta ya dafa cikin sanyi da wani so dake tsakanin uwa Ɗa. Yace Inna mu ki samin Albarka ki kumayimin fatan Alkhairi ga abinda Allah ya zabaman kinji?. Kai ta jinjina kamin tace" In sha Allah Wannan yaron zaka hadu da rahma Allah a duk inda kake , Allah ya tsareka ya baka kariya yasa Albarka a cikin abinda zaka fara kaji, tashi maza kuma karka manta da addu'a duk sadda zaka hau abin hawa. In sha Allah yace yana mikewa. Alh Adnan dai baki ya taɓe yana ganin yaushe xaka tsaya kaita rattafa zance haka kamar tsohon Aku,Kai kanama talakka ai kuka ya dace kaitayi kullum kana tinanin yazaka samu manyan kudi suzo amma ka tsaya doguwar magana wannan ke nuni da cewa bakama nazarin zuwan su(Nidai kam nace Dattijo mai kan kwakwa ka manta Allah ne ke tsara komi😄) Fita sukai inda ya fara xazzagayawa dashi cikin gari shikam ya hakimce tare da sakin rafkeken cikin shi da ya zamema halin da yake ciki Garkuwa. Sun daɗe Yana zaga gari har ya gaji gabaki ɗaya fuskar shi bayyane take da ɓacin rai saboda shidai yaji an'ce wajen shakatawa amma ya tambaye shi pack zasu yace a'a yayita tafiya dai sallah kawai sukeyi su cigaba sai cen yamma suka dawo. Ya sunan ka? ya tambayi Saurayin. Sunana Jameel. Ohk koda bazamu fitaba ina bukatar karfe takwas ta dingama anan gidan ,in ka saɓa lokaci zakaji a kudin ka. Jameel tace'' tom yallabai banki na nakaba amma ina da ka'ida nima. Bana tashi bacci in nakoma bayan Asuba sai ƙarfe goma,Tashina kamin lokacin dana tsara Tamkar rusa rayuwata ne,dan haka ka zafcare farashin awanni da zanyi daga naira daya har zuwa abinda kace zakabani bazan damuba ya faɗa cikin gaskiya da gaskiya ba tsoro ko shakka a tattare dashi. Ido Alh Adnan ya gwalo dan tinda yake babu wanda ya tabamai wannan musun. Ya buda baki zaimai.magama Jameel din ya watsamai manyan idanuwan shi dake nuni da ranshi ya fara ɓaci da maganganun Alhajin nan. Wani irin kwarjini yama Alh Adnan din hakan ya sashi faɗin. Zan shawara ya karɓi key din ya shige ciki yana tinanin wannan ɗan ubanwa ye dayake da isa kamar ba talakka ba . Mtssss Jameel din ya tsaki saki yana gyara zaman wandon shi Ya fara tafiya cikin sassarfa jikin shi ko ina murde yake dam-dam da gani yana bama motsa jiki lokacin sa da kuma ɗaukar Abu mai nawie dayasa Damtsen Hannun sa murɗewa. Wajen pampon daya gani ya isa ya fara wanke fuskar shi kamin yayi Alwallah ganin mangariba ta gabato kamin ya fita daga gidan. Bari mu waiwayo Aymah Tin kwanciyar da tayi bacci mai ƙarfi ya fizgeta bata sake sanin duniyar da take cikiba sai wajen shidda na yamma ta motsa a furgi ce dan batai sallah azahar da laasar ba ga mangariba ta doso kai. Toilet ta shiga cikin hanzari dan gabatar da wanka da kuma Alwallah. Saidai tana shiga ta gane cewa period Yazo mata, ajiyar ajiyar zuciya ta sauke tana mai godiya da Allah dan batason lokacin sallah na shigewa bata gabatar ba. Bayan ta ɓata lokacinta tayi wanka mai kyau ta ɗauki pad ta lika ga pant dinta ta zuge window da niyyar yada Takardar daidai lokacin da ya rufe pompon ya fara tafiya cikin mugun sassarfa. Dum Dum Dum Gabanta ya shiga lugude da batason na miye ba. Kara leƙawa tayi daidai lokacin daya kulema ganinta. Subhanallahi waye wannan tace cikin wani yanayi na mamaki. Som ta manta da abinda ya faru tsakaninta da Adnan riga kawai ta zuro aguje ta fito daga dakin nata tayi nashi ta Banka kofar da karfi tare da fadin . Yallaɓai waye ya fita daga gidan nan yanzu?waye shi? miyazoyi? kason da zuwan sa ne? wajen wa yazo ta jeromai tambayoyin lokaci ɗaya. Yallabai kau dayake gaban madubi cikin takaici yana kallon yanda yayi mugun amalala cikin wandon shadda jikin shi ya juyo a fusace ranshi ɓace ya kaima wuyanta mugun cafka,Tsabar masifa naman fuskar shi har rawa yake wajen cewa ubanwa kika kauracewa? Ido ta zaro dan sai lokacin ta tino ma abinda ya faru amma yanzu ba Wannan ne gabanta ba waye yazo. Cikin wuya da neman wullawa lahira tace. Am.. sa..keni sai nama bayani amma fadaman waye wancen. Kara maƙureta yayi ranshi ɓace ya bugamata tsawa yace . "ubankine,nace ubanki ne shegiya kwartuwar banza kwartuwar wofi daga ganin shi har yawunki ya Tsinke ko,Nace har yawunki ya Tsinke ko,dama ina sane da duk abinda kike ido na zubamiki to yau kinzo hannu ya karasa yana ware hannuwan sa ya kwashe farar fuskarta da mari. Wani wulll tagani na wucin gadi kamin ganinta da jinta ya dawo na dan lokaci. Karfinta tasa gabaki ɗaya ta daddage ta zabgama hannuwan sa cizo iya karfinta. Taurin rai na soja da bakin hali baiko motsa ba sai ma canza hannu da yayi daga rikon wuyanta da yayi daga hannun dama zuwa hannun hagu. Ganin numfashin ta ya fara barazana barin rayuwata yasata kallon saitin wandonshi bata tsaya shawara ba takai hannu tamai mugun riko tare da mai wata makirar matsa data nemi cizgemai makaman yaki. Ihu ya kwallah yana sakinta kamin ya zube kasa warwas yana faɗin" shikenan ta kasheni ta ciremin mafitsara innalillahi wa inna ilaihi Raji'un. Aymah kau aguje ta fita daga dakin tana numfashi sama sama,ta waje ta rufeshi tabar key ɗin jiki,kamin ta shiga dakin ta ta faɗa Toilet ta dinga shan ruwan pampo ta fito tana layi ta fara kwasar wasu kayayyakin ta a gulguje ta fito, kiching ta iske Baraka cikin tashin hankali da rawar jiki tace Baraka muje muje in saukeki karya fito . Waye ? Baraka ta fada a rikice. General ne yana so ya kasheni ne ta fada tana nunamata sashen wuyanta da yayi mugun ja... Gas baraka ta kashe kan kace mi ta watsa dagudu waje gabanta na faduwa Aymah ta rufamata.baya. Tare suka fita Aymah taja kofar Kamin cikin tashin hankali ta kunna motar ta ta bata wuta aguje suka fita daga gidan bayan masu gadin sun wangale masu get. Saida sukaje kwanar su Baraka ta tsaya kamin ta fashe da kuka tana fadin har anzo lokacin duka Baraka nashiga ukku rayuwata ta fara lalacewa ta karasa tana kwantar da kanta akan sitiyarin motar. Baraka daketa raba ido tace kiyi hakuri Hajiya amma Miyayi zafi haka da ake zancen kisa harda wannan shaƙar haka?. Aymah ta ɗago da niyyar bata amsa numfashinta ya tsaya cak jini ya fara fitowa ta hancinta. Ihu Baraka ta kwallah dakyal ta iya bude motar cikin tashin hankali ta fada tsakar gidan su tana fadin "Wannan yaron! Halima! Kabeer! kuna ina zata mutu. Waye zai mutu? Jameel da shigowar shi kenan daga masallaci ya tsinci sauran kalmarta. Ai kamar jira suke gaba daya suka fito daga daki da alama sallah suke. Baraka tace Hajiya da nikema aiki ce takarasa tana nuna musu waje. Gabaki dayan su suka fita da sauri jameel ya fara buɗe mazaunin Driver Aymah tayi luu ta faɗo akan shi yayin da yayi saurin dukewa kasa gabaki dayanta ta fafo akan shi. 500 ne kacal ba yawa kimin magana ta Number Nah 07038423451 Humra sirri. Maganin mata na mussamman Ga kai buka chart me Harkar ta manyan mata ne in kinson baki shiryaba karmu ɓatama juna lokaci wannan nike.haɗa abina da kaina ba tallah nikewa kowaba tawace kashin kaina kunson kuma bazan siyar da akuya ta dawo tana cikin dangaba aheee😜 ❤️ *MATAR OGA NA* ❤️ *MALLAKI* *UMMY AYSHA* *PAGE FOUR* Aslm Alaikum masoyana ina maku fatan Alkhairi da nuna so da kulawa akan duk labarin da zanzo muku dashi. Da fari dai ina so na baku hakuri a dakatar da rashin *Mijin zee* danayi na dasa wannan, saboda wannan din yafi wancen amfani ga rayuwar da mu mata muke fuskan ta. Abu na biyu kuma an samu kura kurai misali wajen sunan Yaron Baraka wato A/K wanda namayar dashi jameel yanzu, Nabeel kuma na mayar dashi kabir,Saboda na daɗe da fara littafin aka fara azumi na dakata sai yanzu naga dacewar cigaba to kuma ban samu page one nd two ba saidaga baya so kawai zamuje da sunan jameel din ne nagode ina fatan kun fahimce ni. *** Innalillahi wa Inna ilaihi Raji'un wannan yaron karfa ace ni na kasheta kason abin fada bayayin wahala wa mutane. Jameel da yaketa kallon sashen wuyanta da yayi sawun riko alamar shaka ya dago jajayen idanun sa ya zubama mahaifiyar tashi tare da faɗin" Inna banson mizamuyimata ba, amma mafita daya akaita Asibiti kawai. Yawwa hakan yayi akaita Asibitin ta kawai tace cikin sauri. Halima ta kama mai kafafuwan ta suka sanyata bayan mota ya shiga mazaunin Driver Inna su ta shiga gefe yayin da sukace da kabeer ya shiga ya kula da gida suka ɗauki hanya. Basu wani jimaba suka iso mahaifin shi malam Habu na zaune kan Benci da redio yana jim labarai ya tashi da fara'a ya buɗe get din Asibitin yana fadin" Hajiya barka da shigowa. Jameel ne ya dan leko yace barka Baba sannu da aiki. Cikin mamaki mahaifin nashi ya sake kallon motar da kuma kara dalla shi da fitila duk da hasken fitulun dake harabar wajen kamin cikin mamaki yace , kaine da Mota Hajiya? Kai ya dagamai kamin ya shiga yayi parking Baban su ya rufe kofar da sauri yayo kanshi daidai sadda Baraka ta fito daga motar. Wani irin sauri Malam Habu ya kara ganin matar tashi da gaggawa ya cimmasu yana mai sanya hannu wansa ya kama na Baraka. Kamar jira take ta fashe da kuka tana fadin "Baban su Hajiya ce gatanan kwance babu lfy tana aman jini ai maza a kirawo ma'aikatan jinya dan Allah su duba ta. Jin hakan yasa shi fadin" innalillahi wa Inna ilaihi Raji'un. Tare da sakin Baraka da sassarfa ya fara kiran nus din cikin lokaci suka fito da whell chair dan sunson bai wuce majin yaci aka kawo ba yake neman kashe masu Dodon kunne... Waye babu lfy malam Habu ka bude baki kanata watsamuna kira haka? Haba da Allah ka dinga daukar rayuwa da sauki. Cewar wata Yar tsamurmura dake sanye da fararan kaya kamar sabuwar gawa sai karairaya take ala dole ita ma'aikaciya ce. Jameel kau dake tsaye ranshi yayi matukar ɓaci cikin bala'in saurin maganar dayakeyi mai haɗe da in ina duk sadda ranshi yakai matukar baci ya nunata da yatsa yace. Ke kikama kanki..ɗi..yar Yara ko in wanke miki fuska da mari, maza kwasheta ku shiga da ita ko in'baki mamaki Ya karasa idon shi rufe cikin muguwar tsawar data sanya jikin su ɓari. Malam Habu ya matsa ya rikemai hannu yana faɗin Kayi shuru kaji yaron kirki,Kyaleta Allah ya tausashi zuciyar Jameelu na,Kuma Jamalun Deedee . Shiru yayi baiko motsa ba kuma bai bude idon saba. Ke kuma Ramatu Hajiya ce ke bata lafiya shiyasa kikaji ina kiran ki da ƙarfi amma kiyi hakuri. Jin haka yasa da sauri suka karaso motar suka fiddota har lokacin kadan kadan jini na zubomata ta bakinta da kuma hancinta. Shikau jameel A'Hankali ya fara bude idon shi da sukayi wani mugun ja, Duk da duhun dake saman sararin samaniya amma kana ganin yanda hasken fitulu suka tona Asirin hawayen dake kwance a cikin kyawawan idanun nashi. Wacce aka kira da Ramatu Kallon shi tayi sadda zasu wuce da Aymah tanajin wani bala'in tsoro da shakkar shi ,ga wani kwarjini da yamata, a wani sashen kuma na zuciyar ta ya bala'in burgeta mussamman sadda yake magana nan Cikin sauri da sauri gashi in inarsa ta motsa saidai ya rufe ido kamin ya samu magana tayi daidai Ya buɗe.. Yana ganin wucewar su yayi tsaki yana kallon Baban nasu. Malam Habu yaja hannusu su duka suka koma gefe dan yason dokar Asibiti ba A bari ka tsaya wajen majin yaci yayin da DOCTOR ke duba shi. Bayan sun zauna nan Baraka ta shiga koramasu bayanin abinda ya faru . Jameel na jin su baice komi ba Amma har cikin ranshi yaji mugu mugun tsanar Alh Adnan dama shi bai maiba tin farko. Baba habu ya gilgiza kai cikin rauni da salon iya magana na Dattijon Arziki yace. " Kai Maman su Allah ya ganar da wasu mazan,hakika wasu mazan na jahiltar zaman Aure,suna ganin duk sadda suka nemi mace suka samu aka basu ita tayi sallama ta shigo gidan su to daga ranar ta zame masu baiwa,ta zamemusu takalmi duk inda suke so zasu taka da ita,Suna ganinta kamar baiwa babu mu'amullah mai kyau da zasu iya yi da ita,nikam aganina daga sadda iyayen ka suka baka mace ka kulle kofa da ita Maman su ai angama maka komi ko? , Sannan matan mu marufin sirrin mune,duk sadda muka kasance masuyin rayuwa mai dadi da matan mu wallahi azeem sai munfijin dadin rayuwa koda ba ko sisi,Ke Baraka banason Allah yabani arzikin da zan gujewa iyalina kwara na zamana cikin rufin Asiri nafi samun lokacin da zan sauke hakkin ku dake kaina,Ta yanda zan karɓi sakamakona da hannu dama a gobe kiyama.. Hawaye Baraka ta sake sharewa tace. " Wallahi Baban su na sani, Kuma ina mai kyautata maka zato,Bazan ce bama faɗaba saboda tsakanin halshe da hakorima ana sabawa ɓalle mutum da mutum,Amma tabbas samun ka a wannan lokacin Babba rabone saboda irin ku kunyi karan ci. Wannan yaron dan Allah kuyi koyi da halin mahaifinku dan Allah, Duk wacce Allah zai baku kumata irin rikon da mahaifin ku kemun ,kunga dai yanda muke rayuwa dashi da daɗi ba daɗi amma babu abunda ya dakushe daga fannin kulawar da yakemun,Bana tinanin tin tashin ku kuntaɓa ganin muna faɗa dashi yace nace,To munayi. Amma adaki,sannan ba ihu yakemun ba,Yana mun nasiha ne ta yanda zan fahimta amatsayina na mace mai karancin tinani,Ina ƙara godiya a gareka Ranka ya dade ta karasa tana haɗe hannayenta waje daya tare da sakin yalwataccen murmushin daya sasu duka darawa. Kai kawai Jameel ya gilgiza dan yason duk Abinda ta fada gaskiyane, kuma shi kanshi baya fatan ace ya zauna da mace dan ya kuntata mata ,Yafiso ya zauna da wacce zata soshi domin Allah, yabata kulawa ta bashi, Ya tarairayeta ya bata lokacin sa itama ta bashi nashi. Suna nan Nursing ɗin nan ta fito tana yanga tana gwatso da neman karewa tace" Dr Aymah na kiran Baraka. Tsaki kawai Jameel yayi jin yanda ake kiran sunan mahaifiyar sa gatsau kawai dan batada kuɗi ,gashi wannan yar shilar har tasamu bakin Kiran sunan uwar su kai tsaye. Da sauri Baraka ta tashi tace da malam habu tana zuwa ya dagamata kai yana fadin . "Kiyi dai a sannu wajen a kwai sulɓi sosai tafi a hankali Kinji. Murmushin gefen baki kawai Jameel yayi soyayyar iyayen nasu na tsananin burgeshi da bashi sha'awa, bakaramin taka tsantsan mahaifin su keyi da mahaifiyar suba bayaso ko ruwan sama na dukan ta( *WAYYO SOYAYYA DAƊI WLH ,ALLAH KA BARMU DA MASOYAN MU NA GASKIYA MASU GIRMAN KAI KAU DAN KAR IYALIN SU SU RAINASU ALLAH YA TSINE MUSU YAN KUTUMAR BURA'UBA*😎) Koda ta mata jagora har dakin da take ta juya Baraka kuma ta rufe Kofar tare da ƙara sawa da sallama tace sannu Hajiya. Aymah da hannuta ke sargafe da karin ruwa tace. yawwa Baraka sannu,Waya kawoni nan?.. Dan Murmushi tayi tace ki gafarceni Hajiya yaro ne nasa ya kawomu da motar ki ganin ki cikin wani mawuyacin Hali. Ido ta lumshe hawaye na zubomata tace. " Baraka wai duk namijin da zai daga hannu ya dokeki yana sonki kuwa,Anya Adnan baya shaye shaye kuwa?.. Shuru tayi kamin cen ta nisa tace. "Kiyi hakuri dai Hajiya aita gayama Allah, Allah zai kawo mafita. Baki Aymah ta cije tana kallon ruwan hannun ta kamin kuma ta tashi ranta ɓace ta cizgeshi ta diro daga kan gadon. Duk yanda Baraka ke mata magiya akan ta tsaya karta tashi amma ina zuciya ya ciyota(A kiyayi ƙure mai hakuri) . Fitowa sukai tana ta sauri kanta hula ce kawai babu ko mayafi sai doguwar rigar data zuba data fito wanka dan ma Allah yasa dare ne ba kowa zai gane ba. Kai tsaye motar ta ta shiga da hanzari Baraka ta buɗe gefe ta shiga kamin a karo na farko ta riko hannuwan ta tace. *Ummu Aymanah*. Da sauri Aymah ta kalleta dan Tinda Iyayen ta suka rassu babu wanda ya taɓa kiranta da sahihin sunanta cikakke kamar yau, batataɓama sanin tason sunan taba dan kullum Hajiya take cemata. Kai Baraka ta gilgiza cikin dattako da girma tace . Duk abinda hakuri baiba Aymanah rashin sa bazai ba,sannan babu abinda ke ɗorewa sai ikon Allah,fushi ba naki bane , Domin ke macace mai rauni ,Aikin mi kike da kika bar damuwa ta shiga ranki,ina Alkur'ani ki?Ina ilim ki da bazakiyi amfani da koyar wa annabi Muhammad sallalahu alaihi wassalam ba ki magance damurmwar ki,Ayma nason ban haifekiba amma kuma inajin ki kamar kanwata,Shawara daya ki kara dagewa wajen kyautata alakar ki da Allah,kana karkiyi zalinci,kina nan zaune zakiga sakayya daga mai sama,ki yawaita sadaka tana magance masifa ko wace irice,Ina mai baki hakuri da baki shawara da karki yarda kije wani wuri a halin da kike ciki yanzu kiyi hakuri ki koma ki zauna daki da safe sai ki koma kibashi hakuri, tana gama fadin haka ta bude motar ta fita tare da zagayowa ta budema Aymah ta kamota kamar jaririya haka suka koma ciki,Kai tsaye office dinta ta nufa Baraka na rike da ita ganin yanda take rangaji kamar wadda tasha giya. Nasiha Baraka ta sakemata kamin tamata sallama tace zasuje gida. Harta sanya hannu zata bude Aymah ta dago jajayen idanunwa ta kalleta tanajin wani girma da mutuncin matar na ratsa ta lungu da sakon ta, akaro na farko taji ya kamata ta girmamata ta daina fadin sunanta gatsau kamar yanda ta saba,Ko ba komi yau ta mata abinda iyaye ne kawai zasuma shi.. Kanta ta mayar a kasa tace nagode Baba Baraka Allah yasaka da Alkhairi,kana kicewa Baba ya rufe get din kuje tare da Asuba ya dawo. Madallah Nagode Baraka tace tafita tanajin tausayin Aymah a ranta , Duk da batacemata ga abunda ke faruwaba amma tana tare da ita tanaganin yanda shakkar mijinta ke hanata sukuni in dai yana nan, ya riga ya samata tsoron shi cikin rai(Nikam nace gidan miji ba barikin sodoji bane Adnanu mai kan kwakwa) Koda Baraka ta fita ta faɗama Baba gida suka wuce sunata tattauna maganar Akan Aymah da Alkawarin sata cikin addu'a su dan ta masu halacci yanzu sular tace suke samun ci dasha har so ukku arana. Jameel dai baice komi ba dan shi dama miskiline na bugawa a jarida magana hamsin zakayi muddum baka sashi ba baya tankawa. *Alhaji Adnan* Tinda ya zube kasa yake ihu yanajin kamar ranshi zai fita,Ya daɗe a wannan yanayin kamin ya samu sukuni yatashi yana kokarin bude kofar amma ta rufe ta waje. Mai gadin gidan ya kira yazo ya bude shi kamin ya samu fitowa yana sakin numfashi sama-sama. Dakinta ya tura ya shiga wayam. Dama Yayi tinanin haka dan sama sama yaji tashin motar ta, kenan nufinta ta hallaka banza , aiko zai maganinta yason duk inda taje zata dawo tinda bata da gidan daya wuce nashi . A daddafe yayi wanka, Bayan ya gama ya fito dakyal yake tafiya,Zaman palon ya fara yaji ya gaji ya koma daki da niyyar fara aiki amma ya kasa gaba daya ta lalatamai wannan ranar yanaji yanagani ga xafin da yakeji kamar zai hallaka shi. Karfe goma da rabi na dare yaji kamar zai mutu ko wando bai iya sawa dole tasashi lalubo number jameel. Saida yamai kira ukku kamin ya dauka yayi shuru. Maza kazo dan Allah ka kaini Asibiti Alh Adnan yace cikin sanyi da murya dake nuni da yanajin jiki. Jameel din yayi shuru kamin kuma yace" to ya ajiye wayar ya tashi ya sanya kayan shi ya fito ya iske Inna su da Baban su waje sunata firar su abin su cikin nishaɗi, gefen su gyaɗa ce Baban su na barewa yana samata a tafin hannu tanaci. Baba Zanje in kai wannan mutumin wani wuri yace fuska ba walwala. Allah ya tsare kawai sukecemai dan sungane wayake nufi tinda inna taba Baban su labarin aikin da aka daukai,sun son in suka cikashi da tambaya zai iya fasa fitar,Dan da alama bayason aikin kawai zayyi ne dan ya magance wata matsala ta gidan. A ƙafa ya tafi har ya iso kai tsaye bakin motar da suka hau ɗazu ya tsaya yamai waya akan ya iso. Kamar jira Hajji Adnanu yake sai gashi ya taho cikin jallabiya yana ware kafa jikin shi sai reto yake kamar wanda ya ɗaura laya.. Wata dariya ce taso kufcema jameel ganin yanda Alhaji ke watsa ƙafa kamar wanda ya hadu da sharrin wanzam. Bayan motar ya buɗe bayan ya bashi key ya shiga da kyal suka dauki hanya. Wata special hospital ya kaishi dakecen kasan su ta Aymah, Bayan an duddubashi aka bashi maganin da zai ragemai radadi kana suka taho gida . Ko Sannu jameel baicemai ba haka yana ajeshi ya juya zuciyar shi fesa dan shi kanshi mamaki yake yanda yajisa cikin farin ciki dayaga Alhajin ma bayajin daɗi. Aymah kau ba sallah zataiba saitayi zaune taita azkar cen ta dauki wayar ta taita chart cikin natsuwa. Tsawon lokaci bacci ya kwasheta ta fara mafalki mai daɗi. A furgice ta falka tana zubama waje daya ido,waye shi,kuma taya,Suwaye wayan nan yaran. Bata da mai bata amsa hasalima saita shiga tashin hankali da kara tsinema Alh Adnan, gashinan halin daya jefata yana neman sa ta halaka har ta fara kwanciya tana mafalki da wani wanda ba halaliyar taba, Ya Allah ka warware mun ka xaɓaman abinda yake Alkhairi A rayuwata . Washe gari da sassafe Baraka tazo ta ganta ita da Malam habu sukamata ya jiki harda dawainiyar saimata kayan fruit. Sosai tasha hakan kuma ya masu dadi dan atare ma suka fito ta sauke Baraka ita kuma ta nufi gidan Haj Asiya. Lokacin da ta isa wani tinani ya faɗomata hakan ya sata sauke Ajiyar zuciya ta juya motar ta ɗauki hanya. Ido na zaro lokacin danaga Ta danna Hon Bakin get din gidan ta. Bayan mas gadin sun buɗemata suka gaishe ta Amsawa tayi kamin ta kutsa kai ta shiga get ɗin na biyu har inda suke parking. Cikin natsuwa ta buɗe motar ta fito daga ita sai rigar jikinta amma ta ɗora lab court akai da siririn farin mayafi. Da sallama ɗauke a bakinta ta tura kofar palon ta shiga .. General ne zaune ya ware ƙafafuwa tare da saita panka akan jikin shi yanata kwasar ganima iska, dagashi sai jallabiya daya ɗageta sama,gefen sa uban magunguna ne kamar za'a buɗe Chemis... Yanajin buɗe kofa ya zabura ya tashi yayin da ko gezau idon Aymah baiba saima kallo data bishi dashi na ƙurullah kamar maison gano wani abu. ❤️ *MATAR OGA NA* ❤️ *MALLAKI* ❤️ *UMMY AYSHA* ❤️ *PAGE FIVE* *ƘORAFI* *MUTANE SUNATA KORAFI AKAN SUNA SO A RAGEMUSU KUDIN LITTAFI DUBA DA YANAYIN GARI DA KUMA YANDA RASHIN KUƊI YAYI ƘARANCI ,TO BA DAMUWA NA MAYAR DASHI 300 KACAL INA FATAN BAZAN SAKEJIN BAKIN KOWA BA NGD* Ga wanda yayi shirin biya ya turo kuɗin Sa ta account number nah *0006454115 Amina dahiru access bank* Shedar biyan ka ta wannan layin nawa *07038423451* """ Matsanan cin rawa jikin shi ya ɗauka, Ranshi in'yayi dubu a ɓace yake,Gani yake duk duniya babu ɗan iska kamar Aymah, Babu kuma wanda yakaita buɗewar ido, wannan ma ya ƙara tabbatar masa da zargin sa tabbas Aymah ta son duniya , Yanzu abinda ta mai har zata iya haɗa ido dashi kuma cikin yanayi na dakewa ba tsoro ba shakka. "Barka da safiya Yallaɓai tace cikin halin ko in kula tare da raɓashi zata wuce. Aymah! Ya dakamata mugun tsawar da ta sata dakatawa cak ba tare data cigaba ba. Mikikazoyi gidana,Ashe zaki iya Neman kasheni kuma ki dawo inda nike? saboda baki da tinani kuma idonki ya gama buɗe wa ko?. Ɗan juyowa tayi tana sakin murmushi . Kamin ta fara tako dai-dai cikin Ƙasaita tana tura hannuwanta cikin lab court ɗinta tace. " Adnan kenan!Mene zanji,mene zai bani shakka da tsoro A tattare dakai,Karka manta Rana ɗaya naga gawarwakin iyayena kwance gabana,Kana tinanin bayan wannan akwai abinda zai sake bani tsoro ya kuma furgita rayuwata,Noo b Ayishi ba,Kana dakaga na dawo gidan ka ai kason bana da inda ya wuce nan ko ka sakeni ne ban sani ba?Abu na karshe Anan shine. Danmi ake koya maku training? Ba saikabani amsaba amma nason dan ku kare kankune duk sadda ka ganka a fagen yaki,Tom ni banje ba, bankuma karantaba, banma iyaba,Amma iya abinda yazo raina kenan dan in kare kaina da rayuwata nama abinda nama. Kallafa. Tabuɗema sa wuyanta da yayi duhun kwanciyar jini. Tace na tabbata da na sake 10mnt ina hannun ka da yanzu an kaini makwancina,Na cijeka inaganin hakan ne mafita amma baima ba saboda bak'ar zuciyar ka,Hakan danama shine dai-dai, kuma wallahi azeem ko yanzu ka sake kwatan ta kai hannun ka akaina sai nama Abinda yafi wannan, karka manta ranka anan yake,Zan jure komi bazan jure duka irin nakaba dan baizo a Shari'a islama ba ta ƙarasa tana juyawa zata tafi. Gabaki daya jikin shi yayi sanyi duk wani kudiri nashi da yayi niyya kasawa yayi a dai-dai wannan lokacin , Wato takurawar da yake mata yakai ga tama daina tsoron sa da shakkar shi, lallai ya yarda da maganar Shekh Aminu daurawa da yake cewa duk yanda kake da mace karka ƙure Hakurin ta , Dan Mace in ta tashi so gabaki ɗaya take af'kawa, hakama in ta tashi ƙi gabaki daya take fitarwa , Ya Rahman ya Raheem yace yana komawa gefe ya zauna yana cika bakin shi da iska. Aymah kau cikin natsuwa ta haye saman tayi wankan ta mai kyau ta sanya wasu riga da wando rigar mai hannun vest ce pink sai wandon Blue yalwataccen gashin ta tayiwa parking ɗin tsakiya tare da ɗaukar katon bnt pink ta ɗaure shi ta saki jelar , kamin tazo zata feffesa turare idonta ya sauka akan ledar Humra data saya wajen UMMY AYSHA. Murmushin mugunta tayi tare da ɗaukar ta ta ɗan goga a hannu ta murje jikinta da bayan kunnanta . Kamin ta sanya flat ɗin takalmanta blue ta ɗauki wayarta da headphone ta liƙa a kunne ta tura wayar Aljihu bayan ta sanya suratul Rahman cikin Qira'a Sheikh Abdullahi gwani wato majabakin Pantami. Kaɗan kaɗan ta fara sakkowa daga step ɗin dan shiga kiching ta samar wa kanta abinda zataci dan tason Baraka ba zuwa zataiba tinda sunyi da ita zata fita wani wuri. Kamshin fitinanniyar Humra tah ya sanar dashi zuwanta. Hakan yasashi yima hanyar ƙuri da ido ganin yanda take jujjuya jiki Kaɗan kaɗan cikin natsuwa, shigar tata ta bala'in karɓeta ta haska farar fatarta tabbas in'bakason shekarun Aymah ba zaka ɗauka layin yan 25 take dan som babu wani abu da zai tabbatar ma da tsufanta ko wani abu daya danganci shekarun ta. Ko inda yake bata kalla ba domin zuciyarta fal take da bakin cikin shi da tsanar sa yanzu mafita kawai take nema daga mai duka. Kiching ɗin tashiga tayi tsaye tana nazarin mima zata dafa. Cikin ɗan sassarfa ta ɗakko cous-cous dan zaifimata saukin sarrafawa. Shuru kuma tayi tana ajiyeshi gefe kamin ta fara nazari ko ba komi har lokacin Adnan mijinta ne ya kamata tabi shawara Baba Baraka ta sauke duk kan hakkin shi dake kanta ta yanda ko agaban ubangijinta zata fita. A'Hankali ta fita daga kiching din kai tsaye inda yake ta nufa ta iskeshi ya daga kanshi sama ya fada duniyar nazari. Yallabai mene kake bukatar a dafama ta fada tanayin gefe da idonta. Kallonta yayi yaga ko ido batason hadawa dashi lllai ya taro match. Gashi Wani kwarjini da kyau yake ganin tana masa ga masifaffan turaran dake kaimai naushi dake ƙarama farashin sa hauhawa cikin lokaci,Sai dai yason ko giyar wake yasha bazai iya aikata komi ba a wannan yanayin inba so yake da kanshi ya illata kanshi ba. A hankali ya nunamata gefen shi tare da faɗin zauna anan Ummu Aymanah. Kallon shi tayi da sauri ya ɗagamata kai alamar tabbatar wa. Wani yamm taji jikinta yayi cikin lokaci taji gaɓɓanta sunyi sanyi (Mata bayin Allah,Maza na amfani da raunin mu suna muna abinda suke so Allah ka shirya mu baki ɗaya) Inda yace ta zauna din ne ta koma ta zauna tare dayin ƙasa da kanta. A'Hankali ya fuskanceta yace . "Kinamun kallon azzalumi ma ha'inci ko Aymah,kina ganin bana da lokacin ki saina kudina ko,Shin Aymah so kike wahalar danasha yarana su shata,Akan mi bazaki bani goyon bayaba akan abinda nikeso,ita mace mai mutunci tana bama mijinta goyon bayane duk sadda ya nunamata yana son Abu balle ni da Halaliyata nike nema, Zahirin gaskiy kika ƙara nunamun wannan tsanar da faɗaman duk maganar datazo bakin ki zanbaki mamaki bar ganin na kyale ki yanzu. Tsaki tayi a ranta tamayi tinanin lallashinta zayyi ko wani abu amma ina girman kan asarar sa bazai bari ba. A zahiri kuma Murmushi tayi tace. " In'banda abinka Yallaɓai ina mukaga Yaran da za'ace ka tayar da hankalin ka a kansu?To nikaina da zan haifama ina kaga lokacina balle na samu rabon su? Ɗan sassanya murmushi yayi yana kara bajewa cikin kujerar kamin ya saki murmushin mugunta yace". Aymah kece bakya da yara amma ni Adnan ina da yara guda biyar cur da Allah ya bani,kuma nema da nike nasune bana kowaba, Dan wahalar da nasha banaso ko tattaɓa kunnena yashata shiyasa na zage ina nema masu ya ƙarasa yana lumshe ido da dora kanshi akan kafaɗar ta dan kaɗan kaɗan iska keta huramai iskan kamshin jikinta mai bala'in saukar mai da kasala jinyar shi ce kawai matsala amma da tabbas yau sai ya karya Alkawari dayama zuciyar sa na tsawon shekara goma sha biyar.. . Murmushi tayi tace ko sama da ƙasa zasu hade bazan yarda da wannan tatsuniyar ba Adnan, ba girmanka bane ta karasa jikinta na rawa duk da maganar bata shigeta ba amma faɗin yana da yara kamar barazana ne ga rayuwar ta,To taya? . Murmushi yayi ya ɗan karkace tare da zaro wata wayar da bata taɓa sanin shi da itaba ya bata yace zaki iya tabbatar wa. Hannunta na ɓari ta karɓa amma ta kasa sarrafa komi. Karɓa yayi ya shiga contact Taga mutum shidda ne kawai aciki. 1f love 2Shaheed 3Nazeer 4Saif 5Ikram 6Waleedah Gallery ya shiga sai gashi wayar cike take da photon zaratan samari masu bala'in kama dashi kaf yaron shine suka biyo Sai wata Dattijuwa da ashekara zatakai nashi koma ta fishi dan fuskar ta ta bayyana girma duk da akwai alamar hutu a tattare da ita haka suma yaran dukan su manya ne babu karami a cikin su dan karamar ma ya wato waleedah zata iya kai 20yrs. Hawaye masu zafi da wani mugun raɗaɗi Aymah taji suna kwararoma ta,Ga nawie Sosai da zuciyar ta tamata dama som bata da lfyn zuciya kuma duk ɓacin ran Adnan ne sanadi danma tana taka tsantsan.. Ido cikin ido take kallon shi Kamin dakyal tace . "miye ribar haka da kayi? Wannan sirrina ne basai kinji ba yace yana juya kai cikin faɗuwar gaban da baitaɓa jin irin taba. Dama shiyasa baka taɓamun zancen rashin haihuwata baya damunka ba. Koko dalilin dayasa tsawon lokacin da muka ɗauka baka damu dani ba? Ina rashin lfy da kaceman kanayi?Miyasa kaci amanata kaci amanar matar ka? Babu amanar danaci taki Aymah. Inada wayan nan yaron bana buƙatar kari Aymah,Kinson in dambu yayi yawa bayajin mai ko,So yara nawa zaku ajiyemun in nace kowa taita tamfatsamun haihuwa,Gashi akwai Alkawari tsakanina da madina mai girma. Ina son matata sosai kuma kema ina sonki amma banaso ke ki haihu nafison naita ganin ki a haka,In shiga duk taron da nike so dake mussamman yanzu da kika gama Karatu kika fara aiki a ƙalƙashin Asibitin ki ta Kanki. "Bazai Yiyuba tace a fusace tana dakamai muguwar tsawa tare da faɗin. Dole murabu, Dole ka sakeni , Dole Adnan nabarka na samu masoyi na hakika ta karasa cikin ihun kuka da gunjin da shi kanshi saida ya furgita Yakuma tsorata dan bai taɓa ganin tayi wannan Burkicewar ba amma dayake bai iya lallashi ba baison ya zai mataba sai ido da yake rabawa. Cikin kuma wani bala'in rawar jiki ta mike bayan ta tsaida kukan sai hawaye dake kwararomata masu zafi ta fara magana. "Adnan sake ni inba hakaba zan ƙarar da kaf dukiyar da Allah ya bani in'makaka kotu,sakeni Adnan Kamin inmaka lahani ko in kasheka in kashe kaina bakin cikin ka ya isheni azzalumai maketaci. . Bazan sakeki ba mutuwace zata rabamu, kan'nan bazaki haihuba saboda ina da dalilina na rashin son ki da haihuwan, in'ce wasu matan ma mahaifar sukeso a ciremusu shashasha kinsamu bandamuba ma zaki kawoman wargi,to daga yau bazaki sake fitaba wallahi azeem kinji na rantse, nidai kike cemawa zaki kaini court ko ? To bakin kofa kika sake takawa batare da na saniba Allah ya isa ban yafemiki ba. Fita kuma in ta zama dole zansa akaiki akuma dawo dake fakat ya karasa yana mikewa yayi daki ranshi ɓace. Wani wahalallan kuka ta sanya tana bajewa akan kujera a dai-dai wannan lokacin ji take inama ta mutu ta huta da bakin cikin da Adnan ke shimfiɗamata,Yah Allah ka kawoman mafita ta faɗa da karfi tare da cigaba da kukanta tsawon lokaci kafin taji an turo kofar an shigo. A Hankali ta fara ɗago jajayen idanuwan ta da suka kumbura sasur sukamata nawie ta sauke su fess a kan kyakyawar fuskar shi dake daure gam kamar kowane lokaci. Shikan shi idon ya zubamata na dan lokaci kamin kuma cikin lokaci ya ɗauke kan shi tare da mikewa da sauri ya fita daga palon yana tsinema Alh Adnanu mai kan kwakwa dayace ya shigo zai aikeshi yayi tinanin babu kowa sai shi kaɗai.. Cikim sassarfa Aymah ta mike da niyyar binshi kamar kuma an tunatar da ita wani abu ta kalli kanta kamin ta zaro ido aguje tayi sama . Tana shiga dakinta ta baje akan gado gabaki daya kukan ta dauke wa yayi sai wani sassanya sanyi data faraji mai hade da saukar yalwa da madaukakin farin ciki a kowane lungu da sako.na jikin ta, Duk wani nawie da zuciyar ta ke mata A'hankali ta farajin Ya yaye, farin ciki na maye gurbin bakin cikin ta. Alh Adnan kau tinda ya shiga dakin sa ya fara safa da marwa gabaki daya ciwon jikinshi jinshi yayi ya dauke,Wani tashin hankali da nadama furucin dayayi mata yakeji,Shidake da buri akanta na har abada miya kaishi fallasa asirin zuciyar shi. Ya zama dole ya sama Aymah matakan tsaro tinda ta fara sanin wasu sirrika daga gareshi dan komi zai faru bazai iya sakinta ba,Adane dai yake tinanin zai iya lamincemata ya rabu da ita musamman dayaga ta cika matsamai da zancen hakkinta hakkinta bayason matsawa neman sa yafiyemasa komi amma ayanzu yanajin bazai iya gangancin nan ba som. Waya ya zaro ya kira Jameel tare da bashi umarnin yayi maza yazo gashi har lokacin daya diba ya wuce. Bayan yaje yamai waya yace yashigo . Shigar dayayi ne idon shi yayi tozali da ita. Alh Adnan kau yana fitowa yaga wayam Jameel baya nan sai wucewar Aymah da gudu . Da ido ya bita kamin ya ɗauki wayar shi ya kirawo Jameel din akaro na biyu. Sallama yayi ya shigo ran shi ɓace kamin ya zauna gefe yace barka da rana. Yawwa Jameel dan Allah ina zaka samomun Manyan kwaɗo na rufe kofa?. Bazai wuyar samuba Jameel din yacemai fuska ba walwala dan jiya zuwa yau ya fahimci mutum ne mai tsananin takurawa ga iyalin shi. Ohk tom. 10k ya bashi yace siyomun masu kyau da kwari guda hudu sauran canjin ka ɗauka. Ngd yace ya tashi zai tafi yace karɓa key din mota kaje ka dawo. Karɓa yayi ya fita yaje ya siyo masu kyau da kwari ya kawomai. Nagode yace tare da daga wayar shi ya kira duka masu gadin gidan. Bayan sunzo suna sanye da uniform ɗinsu na sodoji yace yawwa umarni zanbaku kai tsaye kuduka biyar in'nan. Dayake kowace kofar get mutum biyune sai jameel na biyar. Yes sir suka amsa banda jameel da kanshi ke kasa yana wani nazari . Yawwa jamilu kana jina. Saida ya yamutsa fuska kana ya dagamai kai. Alhamdulillah.... Masu gadin farko yabama kwaɗo ɗaya, da masu gadi na biyu sauran biyun kuma yabama jameel su duka biyun yace gashi kai yanzu Dole aikin ka ya Karu ba iya Driver kawai zaka tsayaba,Kana Wallahi azeem duk wanda yayi sakaci acikin ku saina halbeshi kunji na Rantse. Karkubar uban kowa ya kara shigowa gidan nan kana karkubar ita kanta madam din tana fito daidai da get din farko. Kai jamilu kofar baya zakasama kwado ka kuma sanyama ta palon nan itama kaga nan bakin kofar nan ?to yazamana nan ne wajen zamanka kullum,in kabari ta sake taka baranda wallahi azeem sai ranka ya ɓaci,Mahaifiyar ka zaka iya barinta ta shigo ta tayata zama amma bayan ku biyun nan wani ya shigoman gida sai kunga abinfa zai faru. Gabaki daya sodojin a rikici suke amsawa yayin da jameel kuma tsuke fuska kawai yake da hura hancin sa daya karamai bala'in kyau. Zaku iya tafiya yace. Fita sukeyi kowanne ya dauki kwado ɗaya suka fita shikuma Jameel baiko motsa ba. Kana da magana ne jamilu cewar general. Fuskar sa ya dan yamutsa kamin yace . Oga inkace ka bani wannan shugabancin Da babu takarda zamana ma'aikacin ka kamar ka hanani zaman gaban iyayena ne dare da rana sai dai in tare anan ina gadi,Kana na fadama in'kana da doka nima ina da tawa,Bana tashi bacci sai karfe goma,Banaso ka ɗauki kaslanin(RAGGO) ɗin mai gadi da zakayi dana sani ,Bazan iya wannan dokar ba gaskiya ka canja wani ya karasa yana mikewa tsaye . Zozo jameelu kaji ko Adnan ya faɗa cikin rarrashi dan aganin sa zuciyar jameel da kuma yanda yake kaifi ɗaya zai karama Aymah tsoron nufo kofar dan in ta zaburar da wayancen shi wannan baiga alamar zai dauki raini ba. Ina jinka jameel ya katsemai tinanin sa. To na yarda kazo karfe goman shikenan ko ai yayi ko kuma in baka ɗakin dake cikin farfajiyar palon nan ya karasa yana nunamai wani daki dake kusa da kiching din su. Da sauri jameel ya gilgiza kai yana ganin tsantsar jahilcin Adnan, waishi zai hada muhalli daya da matar shi lallai mutumin nan ƙasurgumin jahili ne . Zanzo karfe goma zan koma shidda na yamma dan nima iyayena na bukatar kasance wa dani, kasancewata babba a wajen su in hakan ya ma shikenan in baimaba kuma zaka iya samun wani.. Yayimun jameel yace da sauri yana kara tsinemai da faɗin zakaci ubanka dan iska sai wahalar dani kake kana talaka ni kuma da azziki na. Kafaɗa ya d'aga sama yana taɓe baki kamin ya tashi zai fita yace. Yanzu zaka dan fita dani su su kula da gidan muje ka kaini Asibitin ta akwai dokokin da zansanya amma kamin nan jirani ina zuwa yace yana haurawa saman dakin Aymah da bacci yayi gaba da ita mai daɗi. Yaji dadin ganin ta haka Saɗaf saɗaf kamar munafuki ya hau bincike ,Sai da ya kwashe kaf abinda yason mai amfani ne a wajenta kudi kam ya gansu kamar banza wannan ya tabbatarmai da wayandama yake bata ba wani amfani take da suba suma saida ya kwashe su tass,Ya sanya hannu zai dauke wayar ta ta falka ❤️ *MATAR OGA NA* ❤️ *MALLAKI* ❤️ *UMMY AYSHA* ❤️ *PAGE 6️⃣* *ƘORAFI* *MUTANE SUNATA KORAFI AKAN SUNA SO A RAGEMUSU KUDIN LITTAFI DUBA DA YANAYIN GARI DA KUMA YANDA RASHIN KUƊI YAYI ƘARANCI ,TO BA DAMUWA NA MAYAR DASHI 300 KACAL INA FATAN BAZAN SAKEJIN BAKIN KOWA BA NGD* *0006454115 Amina dahiru access bank* ,,,,,Wani kallo tamai dake bayyana tsantsar tsanar da tamai kamin tace. " mizakayi da wayata? Shuru ya mata tare da ɗaukar katon akwatin daya loda kayan ya fita. Tsaki tayi tana rakashi da harara dan duk tinaninta wajen aiki zai koma. Idonta ta lumshe tan sake budesu tare da sakin murmushi tace "waye shi"? Adnan kau yana fitowa ɗakin shi yayi da duk kayan ya adanasu adanawa mai kyau kamin ya dawo yayi wanka ya shiry tare da dakko akwatin suka fita. Wani katafaran Bank ne suka isa , Jameel dai zaman shi ya gyara a mota yayin da Adnan ɗin ya shiga ciki. Ya daɗe kamin su dawo tare da wani wanda yake da tabbacin ma'aikacin wajen ne ya damƙamasa komi kamin ya shigo mota yana sauke ajiyar zuciya da sakin nurmushin mugunta... Ta glass din Jameel ke kare mai kallo wani Mugun tsanar shi na tasiri a cikin rayuwar sa,Bai taɓa jin ya tsani abuba kamar yanda ya tsani Alh Adnan, Dan ya fahimci mutum ne mai bala'in son kanshi, Bai kuma damu da kowa ya mutuba in dai shi zai rayu,Sannan ya fahimci mugun mutum ne ga iyalin sa,In bai kuskuran gani ba kuka yaga tanayi daya shigo,To wayasa ta dawo gidan ya karasa tambaya yana sakin ƙaramin tsaki. Hahaha jamily kaga nayi maganin komi cikin sauki ko?Na hanata fita na kuma kwashe komi nata da dukkan ƙaddarata nabama wannan manager bankin,Bance ya hada dukiyarta da tasuba saboda kudin marayu lalata ma mutum arzik suke,Amintacce nane Nan da kake ganin sa , ,Nadaicemai yatafiman dashi gidan shi dake cen janbulo ya adanaman, Aymah kau sai ta zauna dani ko taso ko taki,Yo kotaki mana tinda yanzu bana tinanin naira biyar zata iya samu ,kai asama zata samu ta gidan ubanwa zata fita ta kasheta Bayan nasamata matakan tsaro gaba da baya. Jameel dake son jin labarin yanda abun yake yace. "Oga kayi hakuri da shishigin da zanma. Haba jamilu yi maganaka ba komi ina cikin farin ciki cewar Alh Adnan. Ohk tom dama cema zanyi shagwaɓa maca ne ace ka bata ci ka bata sha kana kuma ka dinga narkamata dukiya,yo ai ba yanda za'ayi tama biyayya kana dasu tana dasu ai tin farkoma ya dace ace hakan ta faru. Hahahha!! Alh Adnan ya sake fashewa da dariya da kuma jin daɗin maganar Jameel din yace" ko kaifa ashe kaima dan hannu ne . Jamee. Hmm yahajj kenan! aini abinda yasa kaga bana dariya ko yawan magana banaso a rainani ne,Shiyasama ni ko aure bazanba dan yanda nike da zuciyar nan ɗan banza duka zandingama matar,Kaga gwara in zamana haka kawai,Gashi bana son hayaniya mace tazo ta cikaman gida da yara nima kuma in cika masu gida da duka ba ita ba yaran ba. Sosai Hajji adna6n ke dariya harda rike ciki wato jameel ma mugun kanshi ne kenan, yanaganin shi haka Ashe zai iya fiye da aikin da yasashi aiko dole ya jawo shi jiki tinda bashi da imani.. Jameel kau idon shi har wani kwallah yake tarawa wanda shi kadai yabarwa kanshi sani dan dakyal yake control ɗin kanshi . Wlh jameel kamun dai-dai, Nima ai ban 'son raini da fitsara ,uwa uba kashiga lokacin aikina zan yaga rigar mutuncinka kuma ka fita raina ko waye kai ko,Kaga ko wannan matar tawa,wallahi shigar da take lokacina yasa na tsaneta kawai ina zaune da ita ne saboda dalilin ta dinga fitar dani kunya in zamuyi taro haka daya shafi tafiya da iyalin mu, sai inje da ita amma aikina ai shine gaban komi,yanzuma gardama zata kawoman cikin lamarin rayuwata Akan saina saketa, nikuma na kwashe komi nata da ƙaddarorinta na kaima wannan manager in yaso ya adanasu sai ranar da naso,Ina so taji wuta taji matsin da dakanta zatabani hakuri ta janye kudirinta na son sakinta da takeso nayi ta kuma karɓi tawa buƙatar da hannu biyu nikuma saina ƙaramata wani abu akan nata in ta amince. Innalillahi wa inna ilaihi Raji'un Jameel yace A ranshi, wani tausayinta na tsargama sa rai,Lokaci daya yaji ya dace yayi amfani da damar da zai samu ya taimaki rayuwar ta dan yagano babban manufa ce Adnan yake da ita akan Aymah. Oga ina Iyayen ta to? baka tsoron su sani cewar Jameel. Haba wane su tini sun wullah barzahu, kuma dama ita kaɗai suka mallaka dangi kuma basa kusa, Suna cen Agadas, kana a Agadas ɗinma babu hadin kai a family nasu dan bason iyayen Aymah suke ba kasancewar su Yan boko wayayyi,Som babu jutuwa a tsakani shiyasama nikaina in'tace zataje ganin gida nike hanata dan yanzu tinda aka gama zaman makokin iyayenta natsaya akabata dukiyar ta na kwasota mukadawo gida kuma bana tinanin har abada zata koma. Ya salam. Jameel yace yana dafe kansji dake saramai...wato marainiya yakema haka dan bata da mai tsayamata,ya rabata da kowa yana kuma azabatar da ita,in'sha Allah zai shiga rayuwarta kuma saiya taimaketa amma dole sai yaji ta bakinta, Amma Wannan auran saiyayi tsayuwar daka ya rabashi dan basu dace da juna ba. Dan Allah jamilu ka Kula da ita saboda na fara tinanin tana fita yawon banza da kuma yin mu'amullah da yan iska wanda wannan ma ya taka Rawan gani wajen sake sani kwace dukiyar datake sharholiya da ita, da kuma tsareta daga fita aikata alfasha, kaga kenan in'kaimaa ka kula da ita, Da tsaronta da kyau zaka samu lada . Keeeyyyyyyyyy motar ta kwacema jameell sukai taga taga suka daki wata katuwar.. *Nace ba* *Kina nan zaune kin buga tagumi kina tinanin taya zaki samu so da kulawa daga mai gida ko kuka kike kullum* *To maza garzayo ki kwashi naki rabon cikin ikon Allah* *Ba tallah ba daɗin baki zahiri ne anan* . *Farko dai ni macace yar uwarku mai kishin ku,Matsala da dama mu mata muna fuskantar ta agidan auran mu,Duba da Irin yanda zamani ya lalace maza suna daukar matayen su tamkar bayi*. *Kar in cikaku da sututu*. Kisa tsoron Allah a lamarinki kiyi Addu'a sosai ki kai kukanki ga Allah kamin kifara amfani da Humrah sirri tah,in sha Allah in mijinki kanshi yakai kwakwa tauri sai kinga yanda zai sakko da makaman yakinsa ya baki kulawa da tarairaya in sha Allah kedai mallaki kayan mu na gyaran aure kisha mamaki da izinin Allah* 1Humrah sirri. 2Kwalaccam 3Turaran gaɓa 14 4Sahihin maganin mata da zayyi tsawon wata ɗaya jikin ki 5Maganin matsi mai balain kyau da zai rikita mai gida kuma wallahi azeem babu Haufi akansa kana baya saka kowane matsala cikin ikon Allah, na yarda da kayan aikina dan saina gwada zan baku. 6 Akwai sabulun kama ruwa da zai kawar miki da warin gaba,Ya matse ki,Zai tsayar da farin ruwa ,Ya miki maganin sanyi Dan zatin Allah,in baki shiryaba kibar kirana kana ina sake faɗa akwai tsada kunson abu mai kyau shike sayar da kanshi. In kuma kayan kamshi kukeso na ɗaki mai sanyaya rai da zuciya gami da saukar da natsuwa ku kirayi UMSAD INCENSE 08028827241 ❤️ *MATAR OGA NA* ❤️ *MALLAKI* ❤️ *UMMY AYSHA* ❤️ PAGE 7️⃣ Sukai taga taga suka kusan kaima wata katuwar bishiya duka kamin suka tsaya cak. Ihu sosai Alh Adnan ke kurmawa dan ya hango mutuwa Rara ainin. Jameel kau Hawayen dayake ɓoyewa ne suka sakkomai yasanya hannu ya share tare da kwantar da kanshi akan sitiyarin motar ya lumshe ido wasu na sake sakkomai, Lallai Alh Adnan mugune kuma akwai manufa akansa sannan bayason Aymah ko kaɗan, Tinda har yake zarginta. A ƙa'ida sharia kuma dama zargi ga aure ma ɓata auran yake baki ɗaya to miye Ribar wannan Auran miye kuma hukuncin sa. Alh adnan . Buɗe marfin yayi ya fito hankali tashe yana kallon jameel ɗin daya rufe ido. "Kai Jameelu mutuwa kai ko buguwa kayi? ya karasa yana jijjigashi. *Jameel* A'hankali ya buɗe jajayen idanuwan shi ya sauke su akan bak'ar fuskar shi,kamin dakyal yana control din bakin sa yace. ciki na kemun ciwo". *Adnan* Kirji ya dafe yace "wai Allah nah jamilu har hankalina ya tashi! kai kayi sanadin mutuwata yanzu ai ba abinda zancemai saidai in'ce Allah ya tsinema albarka kaida iyayen ka,dan wlh yanzu nikejin daɗin duniyar nan, kana yanzu nike bukatar kara bunkasa dukiyata saboda baka daraja awajen kowa sai kana da kudin nan. Jameel Kai wallahi a irin yanda Jameel yaji a wannan lokacin jiyayi kamar ya shake shi zagin dayama iyayen shi har sai ya wulla shi lahira kamin ya barshi, Amma dayake akwai manufa akanshi sai baice komiba sai gyara zamanshi da yayi Yanajin sauyawar yanayin sa. Alh Adnan. Zaka iya kaimu gida koko? Ya tambayi Jameel. Zan iya yace yana kallon katuwar bishiyar da barabon su daketa dan ba karamin bugawa zuciyar shi tayi ba da jin wannan mugun furucin Dayama iyalin sa. Shiga yayi ya tuka suka tafi gida kai tsaye,bayan sun tsaya yace mai gobe zan koma bakin aikina dan banga amfanin zaman da zanba anan kwara in koma cen wajen yarana. Allah ya kaimu yace yanayin ƙasa da kanshi. Ameen Alh Adnan yace tare da fadin ko akwai wata magana ne? Jamil ya sosa kai yace A'a?. Tsayuwa ya gyara yace . Kai jameel na yarda dakai kaji , saboda baka son raini shiyasa naji ka zama nawa fadaman duk abinda kake so . Jameel yace ranka ya dade dama abinda zancema anan shine. "Why not ka saki matar nan taka A ɓoye da Allah ya kamaka gobe kiyama da laifin ta,In yaso sai ka bani ajiyarta in killacema ita nida masu gadin nan naka,Bazatama taɓa sani ba balle ta samu hujja,Dama ba wata alaka ke tsakanin kuba balle abin ya zamana akwai kuskure, ko kuyi zaman da bai halattaba,In yaso sai kayi nesa da ita gabaki daya a rayuwar ka ,In lokacin bukatar ta ya tashi kazo ka dauketa tama rakiya tinda kace sama saboda Aikin ka ko ba haka ba?. Adnan "Haba jameel sai kace ƙaramin yaro da zakabani wannan shawarar ai som batai ba,Ai bana da wani hop da ya wuce ace igiyoyin auran ta na hannuna ,kaga ba ubanda ya isa ya rabani da abata abadan da iman,Amma yanzu nace in'baka naci uban gwari kenan . Rai ɓace kuma a fusace jameel yace to ka sauke nawinta da Allah ya baka mana ya karasa cikin suɓutar baki. Yimin shiru Jameel! zan ya koran ka wallahi ka sake shiga hurumina, ban baka fuska ba dan ka datsaman maganar da kakeso , Zan iya ɓatar dakai a doran kasar nan baki daya saboda ka fara sanin sirrina Da matata , Abinda naima Aymah bai zamema darasi ba ita da take matata,,Ban'faɗama maganaba dan ka rainani duk karsashin ka na fika,Kadai gani sanin sirrinane da tayi yasa na bata wannan dokokin da kwace duk Abinda yasata iya gayaman magana,Balle kai banza bazara dabaka tara 3k ta kanka ba ka kiyaye ko bakaji. Naji jameel yace kanshi kasa zuciyar shi na suya amma tabbas saiya son yanda yayi yasanya ya saketa shikum daga lokacin zai fara nashi aikin,Kana duk abinda yamai zai rama, Dan wannan cin mutunci kesawa ko alaka da mutane bayayi saboda kar ayi La'akari da talaucin sa a kawomai raini. Har ya juya zai shiga ciki kuma ya dawo yace na fasama tafiyar sai na cika lokacin dana diba,Anjima zan nemeka ka tsaya cen ya nunamai bayan part din Aymah. Ohk Jameel yace yana juyawa yayi tafiyan shi. Aymah kau tin sadda taji tashin motar sa ta tashi tayi wanka ta shirya tsab dan saita nunamai bai isa ya zauna da itaba , Daga nan office din kawar ta zata barrister Halima Garkuwa, ta shigar da kara dan dole court ta raba auran nan nasu bazata iyaba dan tana da hujjojin da zasu zame mata sheda. Bayan ta kammala komi ta fara neman key din motar ta amma bata gani ba, Duk inda take sany rai babu A'hankali ta fara binciken wani a locar da take aje kayanta masu mahimmacin ci amma babu komi nata, Duk wani kuɗi ko takaddun kaddarata babu komi. Kanta ta dafe cikin tashin hankali tana tinanin wayamata wannan illar. Adnan". Tabbas shine zai mata haka, A'Hankali ta fara nazarin yanda ta kamashi yanason daukemata waya, ,Sassanya murmushi ta saki tace kai suka shama kai,Kwashemun komi dakai bazai daukeni ya ɗaɗa da ƙasa ba dan na tsani dukiya saboda farin cikin mai itane kawai, Auran miji mai dukiya bashi da amfani ,Balle irin Adnan mai bala'in son kai,kwara ka auri wanda keda rufin asiri kutaru ku rufama juna asiri , kuma ya baka lokacin sa. Mikewa tayi ta fita palo ta zauna dan ko girkin ma ta fasa dan ta riga ta fidda Adnan a ranta a matsayin miji. Tana zaune suka dawo har sadda ya shigo suka hada ido ta kawar da nata shima ya ɗauke kanshi ya wuce kamin ya waiwayota yace . A sama mun abinda zanci bai tsaya jintaba ya wuce war shi. Murmushi tayi tana raka bayan shi da kallo. Tsawon awa ɗaya kamin ya fito da computer shi a hannu da medical glass din sa yana sanye da jallabiya ya zauna ya fara aiki kamin yace. Ɗan kawomin abincin ki haɗoman da lemu mai sanyi. Mikewa tayi ta shiga kiching ta debo danyar shinkafa ta sanya a kula da tattasai da nama ta hadomai ta kawomi ta aje gaban shi tare da hakimce wa gefe. Kallonta yayi kamar zai magana sai kuma ya fasa ya ajiye komi dan bala'in yunwa yakeji ya sakko ya fara bubbuɗewa . Sosai hankalin shi ya tashi ranshi ya baci ya dakamata tsawa da fadin miye haka? Banza tamai ya dinga magana ta kyaleshi kamin a fusace ya mike yayi kanta ta zaro karamar wukar da ke hannuta tace kana matsowa wallahi saina kasheka,Dan nidama ka riga ka kasheni kwara in kare rayuwata a gidan yari da wannan tsinannan gidan naka mai cike da bakin ciki da duhun jahilci. Cak ya tsaya kamin ya koma ya zauna idon shi akan ta yana kuma hango gaskiyar abinda ta fad'a yace. " Aymah zaki iya kashe mutum?. "Aymah Har abada, in'sha Allah Aymah bazata taɓa iya kashe mutum ba,in'kaga nayi kisa to dabbace mai haɗari itama zan kashe tane dan kare kaina daga cutar war'ta. Adnan Subhanallahi kina nufin ni a sahun dabbobo kika ajeni? mijin kine fa!. Aymah Adnan da girman Allah zan zagi ubanka ka sake kiran kanka da sunan mijina,Mijina na nan zuwa kwana kusa da ikon Allah. Tsalle ɗaya ya buga ya kwasheta da mari tare da murɗe hannunta ya anshe wukar ya sake saukemata wani dai-dai lokacin da Baraka ta turo kofar tashigo,Ganin ta ko alama bai sanya Ya saurarama Aymah ba ya dinga kwallo da ita cikin palon nan kamar ya samu jaka. Sosai Baraka ke kuka tana salati tanaso ta shiga tsakanin su amma yaki bata dama dan gabaki daya baya hayyacin sa. Gigitatta tsawa ya dakamata data sata komawa gefe ta zube tana kuka Aymah kau duk uban dukan da yakemata, da jagwalgwala ta da yake zuciyarta ta ke k'ashe babu alamar hawaye a tattare da ita, Dan burin ta yayi ajalinta kawai ko ta huta da bakin cikin zaman da suke. Ganin ya fita hayyacin sa yana dukanta kamar ya samu tsarar sa yasa Baraka watsawa da gudu ,Acen ƙarshen get din taga jameel zaune yayi shuru dan da gaske cikin shi ke ciwo bana wasa ba . Wannan yaron zo zai kasheta tace cikin kuka. Ido ya dan zaro yana kallon ta ta bugamai tsawa. Aguje ya bita su duka suka afka dakin dai-dai lokacin daya sanya katon hannun shi zai kaima Aymah duka a ciki Jameel ya shiga tsakani ya kaimai wannan uban naushin daya sanya gabaki daya duniyar ta juyama Jameel din , Dan gabaki daya guntun ciwon da yakeji saida ya zame mai kamar na mai Naƙuda,Duk da yakai shi kasa amma iya kokarin sa yi yake dan kare Aymah daga wannan mugun dukan da ake saukemata. Aymah kau tinda taga uban naushin daya sakar ma Jameel tayi tsaye cek bata sake gusawaba illah ido data zubamai yana duke rike da Cikin shi da hannusa na dama ɗayan kuma yanata kawomata waigi dan kar a sameta. Cikin ihu tace. Adnan kamasa raunifa Cak shima Adnan ɗin da zai sake wanketa da mari ya tsaya yana kallon Jameel dafe cikin Sa sosai da duka hannuwa biyu, idon shi a kasa bakin shi kuma na digar da jini kaɗan kaɗan. Jamilu! Yace da ƙarfi yana tallabo shi. Baraka kau kuka take sosai tare da kawar da kanta gefe dan tason sun ɓallomasu ruwa, Dan Jamil nada matsala sosai wadda suke Addu'a magancewarta da kuma neman budin Allah Dan su samu amasa aikin da zai samu lfy Amma kudin da yawa ga kuma yanayi. Aymah kau kuka ta fasa tana fadin shikenn Adnan ka kashemin shi wallahi , Dan Allah waye shi dan waye? Adnan zan yafema komi bazan yafema kashemin shi da kayiba har abada, Wallahi sai na ƙarar da kaf abinda na malllaka domin kwatar masa hakkin Sa saboda inaji ajika yana da mahimman ci a Rayuwata,. Adnan ya dakamata tsawa dan yayi tinanin zagin sa take dan som baiji kalma ɗaya acikin maganar taba da yake cikin kuka take magana kuma A hankali amma jameel kau dake cikin yanayi gabaki daya yaji kalamata kuma sunyi tasiri a A zuciyar sa,dan duk azabar da yakeji saida yaji tsaigar jikinsa na tashi sosai . Kiyi wani abu akai man Adnan yace da ƙarfi ganin har lokacin Jameel din ya kasa koda motsawa. Bazan iyaba muje mukaishi Asibiti tace cikin rauni tana share hawaye. Gabaki daya dokar daya samata ya manta Ya ɗaukai ya sashi mota Suka bar Baraka data lafe gefe tana share hawaye Dayi masa Addu'ar samuwar lfy.. Kai tsaye FMC suka nufa Emergency. Cikin gaggawa aka kwashe shi akayi dakin bada agajin gaggawa dashi. Kimanin 30mnt wani Basamuden likita ya fito yana share gumi yace. " gaskiya haniyar nan tasa tana neman fashemasa kuma hakan Babban illace ga lfiyar sa, Dan haka dole ake bukatar manyan kuɗaɗe dan ceto rayuwar sa, Dan ina tabbatar maku da cewa yanzu ko tsayuwa bazai sakeyiba muddum ba a tallafamasa anyi aiki yau zuwa gobe ba... Nawa ne kudin? AYMAH ta tambaya. Yace 90k ne. Aymah da duk fuskar ta ke a kumbure ta kalli Adnan daya juya baya yana tsuke fuska Tinda yaji batun kudi tace. " kaga abinda ka jawo ko,saika biyasu amishi tinda kaine sanadi. Bazan biya ba yace cikin bacin rai ,Ni na haifesa,aikin da yakemun kyauta ne ba kudi zanbashi ba,ina kudin da akeba uwar shi da uban shi da bazasu biya ba. Cikin mamaki ta kalleshi tarr da cewa" ɗan waye. Kafada ya daga yace dan mai aikin kine da mai gadinki. Ido ta zaro kamin tace kana nufin ɗan Baraka ne,shine tana gani bata biyomu ba?. Afusace yace to Tinda munafukace ta ɗauke ni katon banza ai dole ta barmu da wahala, Wallahi biyar bazan badaba,wuce mutafi gida ki sanar da uwar shi tazo ta kama yaronta sutafi gida suyi na wanzamai, ai nima ina da yaran ko.. Kuka tasa tace Adnan kaji tsoron Allah, Ɗa na kowane fa sannan duk wanda yaji tausayin dan wani shima za'aji tausayin nashi, ka taimaka Dan Allah da manzon sa. Ke dakata a ina kika haihu balle tausayin Ɗa da uwa ya shiga ranki? ko dai kina da manufa akansa ne bansani ba, dama kin saba kwalkwale yaron mutane ido na samiki . Allah ya tsareni ya kareni, yakuma karemun mutuncina data abinda zan haifa nan gaba, Adnan bazan taba yafema sharrin da kakemun ba kuma in sha Allah zakagani akan abinda ka haifa. Mari ya kawomata likitan dake tsaye yana kallon su ya rikemai hannu tare da faɗin. " Haba Yallaɓai! macace fa , Dan Allah adaina saurin kai hannu ,zaya iya samun matsala kuma kaima Hakan zai zamema hadari mai girma nan gaba,Ko yanzu ka dubi fatar fuskar ta jibi kwanciyar jini idonta wanda ina da tabbacin mari ne. Tsaki yayi yana faɗin ta wuce sutafi. Bazanje ko inaba Adnan,Nice sanadin faruwar ciwon sa dan haka zan tsaya kai da fata naga na sauke nawin sa daya rataya kaina. Dariya ya fashe da ita kamin cikin shammata ya fizge wayarta yace. " wallahi duk hanyar jin dadin ki saina lalata,Badai dani kike fito na fito ba,To bazan bayar ba , haka kena bazaki bayar ba ,wuce muje wayanda suka haifesa suzo suyi jinyar kayan su. Cikin rauni na ya mace ta durkusa har kasa tana mai hade hannayenta duka biyun waje daya tace'' Adnan! ,Dan girman Allah da manzon sa,Dan son da kakema annabi muhammad SAW kayi hakuri nabi Allah nabika,nakuma yarda da duk ƙudirinka,Kana nagama fito na fito dakai,sannan zan zauna a gidan ka har karshen rayuwata,amma kabani dama,ka kuma bani dukiyata,in bama yaron nan Amasa aiki,Bakason sharrin Ciwon nan nasaba ne, ya fashe A cikin sa zayyi sanadin lalacewar lfyr sa ta ɗa namiji. Tsaki yayi yace aikin kenan kwartuwa,Da anyi abu namiji, lfiyar namiji mtssa. Hawayen bakin ciki da tsanar shi ta share ta durkusa har kasa tace. Ka bani duk umarnin da kakeso nayi Alkawarin yima koma miye. Dariya ya saki yana samun wani ɗan sit ya zauna yace na yarda! sharaɗiin farko . Kinyi Alkawari zakici gaba da zama dani a haka bisa umarnin dana baki. Kuma bazaki sake magana na kusance ki ba. Kana duk abinda nace zakibishi koko.. Kana miye tukuicina in'har na baki kudin ki kika bayar akamasa aiki? Adnan na yarda ka bani kuɗin aikin sa,In yaso kaf dukiyar tawa ka rike nabarmaka ita halak malak, ko awajen Allah baka da laifi wallahi azeem na barma,Asibitina ma na baka takaddun ma acanzasu zuwa naka,Amma dai kabani abinda zan ceto ran sa... Kallon ta yayi kallo mai cike da ma'anoni kamin yace da gaske? Yess da gaske nake ta fada hawaye na zubomata. Dr dake tsaye gefe yana latsa waya ya juyo yana kallon ikon Allah. Adnan ya kalle shi yana faɗin bani pen da byro. Bashi yayi yana ganin tsantsar Jahilcin Adnan amma baice komi ba. Adnan yace in dai har hakane na amince. Sannan daga nan zamuwuce dake kisanya hannuwa. Da sauri ta daga kai Yayi wani dan rubutu ya tura aljihu tare da zaro Wayar shi yace ma Dr ya bashi Account number sa ? Turasu inda zasu biya Yayi tare da zamun waje ya zauna ya zubama waje ɗaya ido. Cikin lokaci akai komi aka gama da niyyar da Asuba zasu shiga dashi aiki. Waji irin walwala da farin cikine ke bayyane a fuskar Aymah,cen ita dama mai taimakoce amma tafi samun farin ciki a yanzu data Taimaki Jameel. Tafiya sukai likitan nan ya bisu da kallo zuciyar sa fal da tausayin Aymah,,ya lura ita kanta ba lfy ne da itaba dan layi kawai take , Amma baiga ta nemi ko paracitimol ba saima sadaukar da abinta da tayi akan wanda sukaji ance dan mai aiki da mai gadine, lallai ya Jinjinama ta kuma yanason yason wace ita waye Jameel waye Adnan. . Adnan kau suna cikin tafiya zuciyar sa fal farin ciki ya dauki hanyar janbulo,kai tsaye gidan manager bank ɗin nan suka nufa, dakyal da taimakon Allah dana waya ya gano wannan gida. Bayan yaje ya kirashi ya fito ya tarbesu. Anan Adnan ke labartamai duk abinda ya faru Suka dinga dariya Aymah na kallon su kallo mai cike da ma'anoni. Mutumin yace to Hajiyar taimako sai azo a rantama muna hannu ko Anan . Ya karasa yana mata kallon sama da kasa tare da bata wasu takaddu. Murmushi tayi ta mike ta fara duba takaddun tare da kallon Alh Adnan da ke gefe yana murmushi kamin ta kalli manager ya dakamata tsawa yana fadin rantaɓamun ki bani. Ajiyar zuciya ta sauke ta sanya hannu duk inda aka gwadamata, gabaki daya ta mayar dasu na Adnan din ,Kudin dake account dinta duka aka mayar dasu account din Manager dan yana nan kanbakan sa bazai hada dukiyarta data shiba wayan nan wata masana'anta zai samu mai mahimmanci ya gina. Saida suka gama komi kamin ya jata suka tafi farin ciki fal zuciyar sa tsuntsu daga sama gasa she ❤️ *MATAR OGA NA*❤️ *MALLAKI* ❤️ *UMMY AYSHA*❤️ *PAGE* 8️⃣ """ A bakin get suka iske Baraka da Malam Habu datama waya ta faɗama halin da suke ciki ya zo,sunyi tagumi daganin su suna cikim damuwa. Daidai wajen su yayi parking dan ya gane Baraka. Malam Habu ya taso da sauri yace. Ranka ya daɗe barka dai! anyini lfy? Dan Allah ya jikin Yaro nah?. Adnan Bazan iya gane halin da yake ciki ba saboda bamu shiga ba, amma dai albishir ɗaya da zan'maku anan shine matata ta bayar da kaf dukiyar ta wajen yimai aiki,An fidda kudin sa sauran sun zama nawa. Baraka da Tinda suka fara magana batace komi ba ta ɗago kai cikin matukar razana, Dan ta fahimci in'da kalaman shi suka dosa . Arikice tace minene kace Alh? Adnan yayi murmushi yana bude mota ya fito Aymah kau sake kwantar da kanta tayi tanajin su sama sama dan wani uban zazzabi ke kawomata farmaki, hakoran ta har datsewa suke. Adnan kau tiryan tiryan ya masu bayani. yakuma sake da cewa kai Malam na dakatar dakai daga aiki,Haka kema,saboda dama bani ke biyan kuba, Ɗan ku kuma shi akwai aikin da zaiman da shama na mayar maku da kayan ku,Dan haka dan Allah daga yau kar wanda ya sake takoman gida ko Asibiti nah, ina fatan kun fahimce ni? Gabaki d'ayan su saida zuciyar su ta buga ba kuma korara su da yayi bane tashin hankalin su a'a sai wannan mugun zalinci da yama Aymah na kwashemata kaf dukiya ,yanaso ta tagayyara kenan a rayuwa, in sha Allah burin shi bazai taba cika ba har abada Baraka tace a zuci. Baraka kau inda Aymah take ta zagaya ta bude tare da kamo hannunta. Aymah da take layi kamar tasha wiwi ta kalleta tana lumshe kumburarrun idon ta. Miyasa kikai man haka Ummu Aymah dan Allah Baraka tace hawaye na zubomata.. Dan murmushin karfin hali ta saki idonta na neman rufewa kamin ta hada hannayenta duka biyun ta dan kalli gefen Baraka alamar ban hakuri. Kimin magana manah Aymah. Baraka tace da ƙarfi kuka na kufcema ta. Karr,.. ki..daa..muu yana..cikin kaddara rayuwata abinda ya faru tace a rarrabe cikin mawuyacin hali. Baraka zata sake magana Adnan ya dakamata tsawa da fadin ta kwashe duk abinda tason natane ta fita tabashi waje . Basai ta d'aukaba,Anan ta samai anan kuma zatabar ma kayan ka,Kana ka sani duk abinda zakai akwai Allah,kana karkayi tinanin kaci bulus ko kuma ka dauki hakkinta Allah ya barka ina,ina mai tsananin tausayama wallahii, amma Allah ya shiryaka malam Habu ya karasa yanajan hannun Baraka dake kuka sosai suka tafi... Adnan kau da harara ya bishi kamin ya zagaya ya budemata ya kamota keyy kamar jaka ya fito da ita tare da rufe motar. Da sauri sauri yake janta har zuwa palo ya ajeta akan kujera yayi wucewar shi d'aki. Koda ya shiga gudar wayar shi ya dauka ya fara latsawa inda yaga kiran matar shi da yaron sa. Bayan ya kirata suka shiga yin waya zakuyi Mamakin Yanda yake sakin kalamai da kuma sassauta murya a maganar tasu,Bayan sun aje yabi yaran ya kira yana wasa da dariya dasu kamin ya aje wayar ya fara aikin gaban shi, Bai damu da ko sallah azahar da la'asar din data kawo kai yayi ba fatan shi ya kammala hada komi kana.. Saida yaji cikin shi na ihun kuka kamin ya mike ya fito cikin masu gadin yasanya suka sawomai abinci ya dawo nan kusa da Aymah dake nishi sama sama ya zauna ya ɓararrake yaci ya koshi yabuga gyatsa kamin ya tashi ya haɗe salloli yayi, yana gamawa ya jawo Computer shi yacigaba da aiki baya ko kallom inda take dan shi yanzu amfanin ta ya kare mai tagama ci tagama sha daga dukiyar sa masu gadin sama sallamar su zayyi dan yason yanzu bata da wani amfani a Rayuwa,Dan biyar bazai bata ba balle ta nemi guduwa.. Aymah Duk iya sonta data tashi tayi wanka ta gyara jikin ta abin ya gagara som, bata da karfin aikata ma kanta komi , inda ta gode Allah ba sallah zataiba shiyasa taita kwanciya bazaka taba gane ai'nafin abinda take ciki ba . Jameel. Daga sadda suka kai shi aka hana shi cin komi,zuwa la'asar ya bude idonshi dan yaji dan ƙarfin jikin shi. "Ina take miya faru da ita ,Ya fara tambayar kanshi amma ba amsa,Hawaye suka shiga zubomai yana faɗin. " Kiyi Hakuri duk yan da naso na tare miki lfy tamin karanci,banson wane jahilin mutum kika hadu dashi ba, banson mi kikaimai ba dayake dukan ki, Dan Allah ki gudu kibar shi zan kasance tare dake matsayin bawanka har abada, Dan Allah ki kashe Auran,ki barshi,kizo gare ni ya ƙarasa cikin ihun kuka yana neman faɗowa daga kan gado saboda fizge fizgen daya dingayi na Alluran da ake bankami cikin ƙarin ruwa. Nursings ɗin dake wajen aguje sukaje suka Rikeshi wasu kuma suka kira Dr daya duba shi. Dakyal ya samu yayi control din Abinda jameel din keyi ya samu ya lalla sheshi kamin ya danna mai Allura bacci yayi gaba dashi. Bai jima da kwanciya ba Baraka da Malam Habu suka shigo dakin bisa ga jagoran wata ma'aikaciya mai share share. Likitan dake tsaye kanshi ne ya basu waje tare da gaidasu a mutunce kamin ya musu bayanin ciwon nashi. Amsawa sukai suna sake mai gdy da fatan nasara kamin ya fita. Malam Habu ya buga tagumi yace. Baraka kinga wata kaddara Allah kuma? Wai akan Jamilu ta bayar da komi nata,Baraka wannan mutumin fa azzalumine kannan mugune taya dukiyar wani zata zama naka? Dukiyar ma ta marainiya Allah. Shuru tayi kamin ta nisa ta share hawaye tace lamarin su Hajiya na bala'in bani mamaki,Har yau nikaina bazance ga irin zaman da sukeba ,Amma inaji ajikina kamar dama auran manufa yayi da ita.akwai abinda yakeso bana tinanin yanason matar nan dan zaman da suke som babu kulawa balle ayi batun soyayya. Shuru yayi kamin yace Allah ka warwarr muna baki daya. Ameen Ameen tace . Wayar shi ce ta fara Ring ya ɗauka da sallama cikin mutunci yace. Barka da dawowa Deedee nah fatan kin dawo lfy. Alhamdulillah Muna asibiti yace cikin ladabi. Ido ya dan lumshe kamin yace. Jameelu'n ki. Kwatance ya mata ya kashe wayar tare da cewa tofa Deedee ta dawo Baraka, Nason zatayi fada sosai mussamman in taji Abinda ya faru. Baraka tace A'a gaskiya zamu fadamata kawai, ai uwace muna buƙatar Addu'a ta. Kimanin 20mnt suka farajin hayaniya Malam Habu ya leko da sauri dan yana da tabbacin mahaifiyar tasa ce dan batabarin sai ta kwana. Da sauri ya isa wajen masu gadin da suka hanata shiga sai zazzaga masu bala'i take hannuta rike da buta. Yace Deedee nah Lfy? Afusace tace barni da yan iska da sukayi kama da masu gadin ɗakin macizzai,yo macizzai mana sai wani juye juye suke suna kaɗa kawuna kamar jikokin an'gulu,Yo ya za'ayi suce bazan shigaba ganin jikana,Jikana a kwance ace bazanje na ganshi ba,Wai sunce ko.l wani abu na kawo Nace a'a. sunce yanzu wanda zai shiga sai dai mai kai abinci to tinda bani da abinci na ɗakko buta masallaci in kaima jikana yayi Alwallah ya gaida mahaliccin sa akwai abinda yafi wannan Fa'ida? Amma dayake kafuraine na farko wai basu yarda ba narantse da Allah saina shiga ko duk in'fasamaku kawuna ku kwanta jinya asamu masu hana har iyayen ku zuwa munafukai Yo daɗi ke kawo bawa Asibiti ta karasa tana ɗakko katon dutsi da gayya ta jefoshi gefem mai gadi daya aguje kau ya Ruga yana rike kanshi. Ta sake ɗakkowa zata jefo shima dayan ya ruga ta sanya hannu ta turo kofar tana murmushi tare da cema zugar dake bayanta ku shishigo kuga dangin ku kunji ko sai nima kuma jikana addu'a.Ai nayi aikin Allah na sadaku da yan uwanku marasa Lfy nason zan'samu Lada. Aiko kamar jira suke mata da maza haka sukaita turawa kowa yashiga kamin ta karasa wajen Malam Habu daya rike kanshi yana murmushi da kallon ikon Allah. Tace kai kuma miye ko jikin jamalun ɗin ne yasaka murmushi in ce ya warke.. Murmushi Yayi yace. Ina kallon jarumar uwata datafi ta kowan.Jameel ɗin ki da sauki,Fatana dai Allah ya kara miki lfy Deedee tah. Ameen tace tana Ganin masu gadin da ransu ke ɓace suna surfamata harara. Dan murmushi tayi tace . Kuyi hakurin Dan uwayen ku kunji ko,Kunson rikicin tsufa! eh nace kunson rikicin Tsufa, Dan Allah kuzo ku garkame get din kar akawomuna farmaki tinda na shiga kuci gaba da aikin ku ta karasa tana wucewa Malam Habu biye da ita yana Murmushi. Tunda ta shigo dakin ake Nunata ana cewa itace tasa aka shigo . Nan fa akaita gaida Deedee tana hura hanci da amsawa cikin isa kamin ta farabin mutane tanamasu sannu har suka shiga ɗakin da Jameel yake.. Ganin yanda yake yasata fashewa da kuka tace shikenan jamalun Deedee,Abu yakai ka kass,gashi an'ki sayen gonar wallahi yanda naje abanza haka na dawo a wofi. Kowa na korafin yanda aka matsama gonar nan da sace sacen mutane shiyasa kowa gani yake jalli joga zai saima kanshi. Baraka tamata bayanin an'biya kudin aiki. Haɓa ta rike tace wannan wane dan aljanna ne ya biyasu ? Nan fa Baraka ta karkace tana kuka tana fadamata abinda ta sani game da Aymah. Koda ta gama Gabaki daya saitaga Deedee tayi shuru tsawon dogon lokaci kamin tace inane gidan nasu? Nan baraka ta bata.kwatancen wajen. Deedee tace karki damu Allah na tare da ita, kuma nima zanje har inda take in'sha Allah, Allah yasanya wannan taimakon datamana yazams silar warwarewar damuwar ta,Kukuma Allah ya maku zaɓin Alkhairi. Ameen suka amsa Baraka ta tashi tayi gida dan samo masu abinda zasuci duk da babu kudi sosai hannunta ta riga tayi sayayya kayan abinci . Ana gama sallah mangariba tayi Asibitin inda ta iske jameel ya tashi amma ko zama baya iyayi sai gadon da aka ɗan dago masa. Kallonta yayi ta kalle shi tare da mai ya jiki. A'Hankali ya amaa yace "tana ina? Gabaki ɗaya suka kalle shi Deedee tace'' wa? Ita Yace yana cije baki. Deedee tace'' Subhanallahi har anzo nan wajajen jamalu,Yaushe aljana ta aure ka da kake jajenta bamu saniba ?kodai zafin ciwo ne ?. Kallon ta yayi yana cije baki kamin ya dan harareta ya kawar da kanshi yana lumshe ido ,gaba ki daya tinaninta ya addabi zuciyar sa,wannan ciwon ya mugun kwafsamai ,Bayan shi wallahi azeem da sai ya gwadama Alh Adnan sabon jini ke yawo a jikin shi dan sai yamai mugun dukan da bazai iya numfashi ba. Amma ko gobe ya ɗauki Alkawari sai ya rama mata dan ko ta yafe shi bazai yafe ba. Hajiya Aymah kake tambaya ne Inna su tamai magana tana zubamai ido. Da sauri ya dagamata kai yana zubamata ido. Tana.nan Lfy bata jima da tfy ba. Kai k awai ya d'aga yana furta Alhamdulillah a ranshi. Fira suka danyi banda shi daya lumshe ido. sai karfe tara Deedee da Inna su suka tafi aka barshi da.mahaifin sa kawai. Aymah. Zata iya cewa tinda take bata taba ganin mugun mutum ba kamar Adnan, Dan duk halin da take ciki ko alama bai tankamata ba, har aka yi Sallah mangariba akayi isha yana zaune sai wajen tara ya mike yayo Alwallah ya hadesu kamar yanda ya tashi ya sanya key a palon ya dawo ya kwanta . Aymah Ma a haka bacci ya tafiya da ita sai wajen karfe ukku ta falka Tare da yun kurawa ta tashi cikin ikon Allah taji daɗin jikinta sosai. Wanka tayi da ruwan zafi sosai ta gasa fuskar ta kamin ta dawo bisa gado ta kwanta ta lumshe ido tana tunanin juyin rayuwa. Washe gari Jameel Karfe Shidda aka shiga dashi theater room sai mumafasa fatan fitowa Lfy. Aymah kau wata fitinanniyar yunwa ce ta tayar da ita . Dakyal tayi wanka ta sake gasa jikin ta ta dan fito palo dan samar wa cikinta abinda zataci. A'Hankali take tafiya har ta iso palo. Ido da ido suka hada ya kawar da kanshi gefe yana amsa waya da sake tsuke fuska.. Ina kwana tace cikin sanyi. Baiko am'saba ya juya kai. Bayan tashiga kiching din ta hada tea na ruwan sanyi dan bazata iya dafawaba tasha abinta. Tana cikin wanke cup din ne taji shigowar katuwar motar tanka har inda daga shi sai ita ke shigowa . Glass ta dan zuge taga katti na fitowa daga ciki ,su dukan su da shigar banza. Gabaki daya suka Dumfaro palon. Hakan yasata watsar da cup din ta fito da sauri daidai lokacin da suka banko Kofar suka shigo... Hajiyoyin kamshi akwaifa UMSAD INCENSE na nan tana muki sabon shirin turarukn ta msu kyau da dadi kun san komi basai na fada.ba .❤️ *MATAR OGA NA* ❤️ *MALLAKI* *UMMY AYSH* *PAGE* 9️⃣ * Sosai jikin ta ya ɗauki ɓari ganin duk jikin su a murɗe. Adnan ya ɗago ido yana kallon su kamin ya mayar akan wayar shi yace" kun kyauta da kukazo kan lokaci ku fara dana sama tass kamin ku sakko nan ko ku rabasu biyu. Da" to" suka amsa wasu suka haura dakin shi wasu sukayi nata duka biyun suka fara kwance kayan'ta suna sakkowa dasu. Daga lokacin data fahimci ya san su sai hankalinta ya kwanta ta ɗauki Hijjob ta sanya tare da lafewa gefe tana kallon yanda Saketa kwashe mata kayan daki . Saida suka cika motar gam kana sauran suka fitar dasu waje suka fara zuwa kai wasu su dawo. Tana nan zaune shima yana saman kujera suka gama kwashewa tass suka zo zasu fara kwashe kayan palon. Tass nan ma suka kwashe har labule basu bari ba . Ido suka haɗa da Adnan ya saki murmushi ita dai batace komi ba. Duka saida suka gama suka tafi bayan ya sallame su. Lokaci ɗaya komi na gidan ya dawo wani iri kamar kango. Masu gadin yama waya yace suzo. Bayan sunzo nan yace ya dakatar dasu su koma Bariki zasuyi waya. Gabaki ɗayan su Amsawa sukai suka tafi suka kwashe kayan su sukai tafiyan su ya rage dagashi sai ita. Dan kallon ta yayi yana wani lumshe ido da sakin murmushi yace. *Aymah Abdulkarim Mai Dala*. Tom yau ina Abdul kareem din ina kuma kudin ina uwar ina uban ina kuma izzar mahaifin naki? ina dukiyar daya wulakantani kanta yakimin alfarma Ya barta yana taramiki? Tom yau gashi an wayi gari bana tinanin abun biyar kina dashi a gidan nan. Ko akwai? Kai Kawai ta d'agamai tana sake bude idonta akan shi. Murmushi yayi yace. gabaki d'aya na canzamiki tsarin gidan nan da kuma rayuwar ki,Inaso kiji yanda naji,Kana ki ƙare a haka har abada,Ke ba mai Aure ba ke ba zawara ba. Aymah zan baki umarni kai tsaye wallahi wallahi kika tsallake saina kasheki. Ido ta zaro da karfi tana kallon shi. Yess zan kashe ki kamar kiyashi ba ubanda ya sani,Ba kowa gidan nan dagani sai ke. In kuma kikayi yunkurun guduwa ..Hmm ya fada yana murmushi da faɗin aka kamoman ke wallhi saikin sani domin nasamaki matakan tsaron da bazaki taɓa ganin suba sai sai su Su ganki.. Kana wannan yaron shine kawai zai dinga zama gidan nan shima Akwai dabbobon da zan aje wanda shine ya cancanta ya kula da su dake da abincin da zakici ,Dan daga sadda zai samu sauki Ya dawo bakin Aiki kin gama girki sai sai A siyomiko na bakin Hanya da yaran talakawa keci.. Murmushi tayi tace. Adnan bazan gudu ba,ko baka aje kowa ba bazan gudu ba,Saboda nason daraja Alkawari karka manta alkawari nayi,Mudddum bakai ka koreni ba bazan bar gidan kaba,So wajen wama zani in nabar Nan. Yace Kimma kanki taimako ya ƙarasa yana mikewa ya shiga dakin shi da ba ko gdo sai doguwar kujera. wanka yayi ya shirya ya zauna ya fara nazari rayuwar shi ta baya da Mahaifin Aymah da duk Duniya Yafi kowa tsanar shi,Dole ya fanshe bakin cikin sa akan Yarsa. ** Alhamdulillah Jameel anyi aiki cikin nasara sai fatan Allah yasa karshen wahala kenan. Deedee tayi murna tayi kukan farin ciki lokacin da akacemata aiki yayi kyau Masha Allah. ,** A'Hankali sauyin rayuwa ya fara kawoma Aymah farmaki inda ta koma kamar wacce ta samu matsala kwalwa gabaki daya ta daina magana. To dawama zatai. Saita kwana batace komi ba,Iyaka zakaga tana sallah tana addu'a sosai,Adnan baya gabanta dan loi kayan kamshin data saya gabaki daya ta mayar da abinta jikka ta ajiye dan tagama tusa kanta inda ba kwarjini ,Duk abinda zata faranta mai yanzu bata son sa. Adnan ya mata abinda ko shine autan maza dole ta barshi yanda yake da manufa wulakanci akanta ,bazatace ga abinda tamai ba Hakama iyayen ta. Amma ta son ya fito yanzu ya gwadamata kiyayya zahiri kana kamar yanda tayi alkawari muddum baibata takaddaba bazataje ko ina ba daj bazata fita da dakon igiyar sa dake kanta ba. Gabaki ɗaya ya fiddamata kaunar Namiji cikin rayuwarta saboda tana ganin kamar duk wanda zata samu abinda yamata shima haka zai mata. Adane take da burin ta fita gidan shi ta sake aure amma ayanzu kam som Babu wannan tunanin cikin ranta. Jameel. Tinda akai mai aikin nan ya susuce ya dawo so silent,Kullum tinaninta yake abin har tsoro yake bashi ,kullum zuba ido yake yaga ko zatazo kamar yanda Maman shi tace amma ina har ya fidda rai gashi har an'kwana biyar . Kullum nazari yake akata,da Tinanin mitake? wani lokacin ma zuciyar sa takan bashi amsa da kilan tanacen ana dukan ta ,In kau ya tino haka burkicewa yake yace sai ya tashi ya koma gida ya warke. sai sunyi da gaske yake komawa ya kwanta yana huci. Yauma data kama sati daya damai aiki kuma yau ake shirin sallamar shi. Kwance yake akam gado daga shi sai gajeron wando da farar vest. Fatar nan tashi tayi lumi tayi kyau na maji yaci. Hancinshi ya kara wani tsawo hakama pink lips dinshi sunyi yarrr dasu alamar jinya yake. Kanshi a sama ya zubama silin ido. Bai an'kareba ya farajin saukar hawaye . DeeDee dake kusa dashi ta fasa kuka tace. " Kai jama'a jamalu nah ka daina kuka ko baka warke ba?. A'hankali ya karkato da kan shi akanta zuciyar sa na zugi da bala'in zafi yace "Deedee nah inaso na ganta wallahi,inajin zafi,inaso nasata idona, Deedee minai mata da bata sake waiwayana ba, DeeDee ko fushi tayi tana ganin da gangan na barsa yana dukan ta Bankwace taba?Ki faɗamata zan rama mata wallahi azeem zan rama mata Deedee nah. Dan Allah kice tazo yanzu ya ƙarasa hawaye sosai na ambaliya akan kyakyawar fuskar shi. Deedee ta sake kallon gefe da gefe dan kara tabbatar ma da ba kowa dan Inna su da Baban su suntafi su huta kamin tace". Wai jamalun Deedee anya allura nan bata tabama kwalwaba,Nifa so ne nike gani cikin kwayar idon ka,Jamalu son MATAR AURE?MATAR OGAN kaface anya akwai hankali anan ta karasa tana ɗora hannu aka da Rusa ihu. Cak ya tsaya yana kallon'ta kamin da kyal ya yunkura ya mike ya ɗan kama hannuta cikin balain sanyi kamin yace. DeeDee nah" SO fa? Wayace miki ? Ni nace miki Deedee? Deedee ya ake gane so dan Allah? Cikim tausayi tace Jamilu wallahi azeem ka kamu da son MATAR OGA ka Tausayinta ne yayi tasiri aranka har ya rikide ya komama SO mai zafi. Bakai murna ka rabu da wannan uban cuta dayakai robar wanke shinkafa girmaba ,Fatan ka kawai ka ganta anan gaban ka sannan zakaji daɗi,idan ba so ba to miye?. Cikin Karaya yace *Tausayine* Deedee. Murmushi tayi tace. Hmm amma dai kam akwai ƙura anan sosai. Amma ba ason Abinda Allah yayiba wannan matar kau tabbas mituniyar kirkice,Kaf wannan kudin da akama aiki ita ta biya, silar haka kuma ta rasa duka dukiyar ta mai yawa,Nan ta shiga koramai bayani . Batama ƙarasaba ya mike tsaye cikin tashin hankali yana neman tafiya. Jawo shi tayi ya fasa wani uba ihu. Cikin rawar jiki tace ka natsu Jameel wallahi wallahi ko rana ɗaya ne saina Ramama Yarinya nan Dukan da yamata . Jameel kau bayajin ta gabaki daya idon shi ya rufe har wani jijjiga bakin sa keyi. Cikim ihu ta kwallah ma DOCTOR kira. Aguje kam ya shigo dan dama zaizo bashi takadda sallama. Dakyal ya maida shi bisa gadon dan burkice mai yayi yana ihu mai gunza da faɗin saiya ganta. Y salam Deedee tace tana dafe kanta. Mama dan Allah bamu wuri inji DR. Tashi tayi ta fita ya mayar da natsuwar shi akan Jameel yace" Abokina natsu ka saurare ni man. Kallon shi Jameel yayi yana cije baki. Murmushi yayi yace" kana sonta ne? Ido ya dan zaro kamin yace" Aa nifa tausayi take bani ai Babba ce Kuma marainiya Bata da kowa!. Sake murmusawa Dr nan yayi yace. Ƙarami baya Auran Babba ne,Annabin mu ya auri Nana khadija data bashi shekaru kuma sukai Aure ,Akwai magana da zan fadama wacce zata zame ma hujja,akwai kuma taimkon da zanma duka rayukan nan biyu ma'ana kai da ita in sha Allah,Fatana dai kayi hakuri,ka kuma iya takon ka,karka bayyana Asirin zuciyar ka kai tsaye ,Saboda irin wannan abin da Mutumin nan kema baiwar Allah nan zai sanya mata ganin bakin maza ciki kuwa har dakai,Tinda a yanda naga ta damu ranar data bada kudin nayi tinanin ita zatai zaman jinyar ka,Bana da masaniyar an barta ko ba abar ta ba amma dai tabbas da saita zo sake ganin ka koda so dayana Amma shuru.. Kayi hakuri ka ida warkewa duka miya rage ?Dan'ma fa baka shan magani bakacin abinci da kwana biyune ko ukku na sallame ka. Shuru Jameel yayi yana nazarin maganar shi ina shi ina son mace mai kudi Mai kyan Aymah,MATAR OGA NA fa kai ina ya faɗa a fili yana jujjuya kai . Murmushi Yayi yace Ni kuma inaji ajikina kwana kusa zaka mallaketa tazama ƙarkashin kulawar ka inda rabo ta haifama yan Babys masu kama daku,Azahirin gaskiya kundace da juna Abokina... Kunya sosai ta kama Jameel wacce saida tasa shi juya baya ya wani saki sassanya murmushi nan nasa daya daɗe Baiba ya wani lumshe ido da fadin anya,To taya? Dariya sosai Dr yayi. har cikin ranshi yake tausayin su su duka , Amma in sha Allah mafita nata ɓullowa kota ina . Haɗa mai komi yayi na maganin sa kamin ya kamo shi kaɗan kaɗan suna takawa suka fito . Deedee ta zaro ido tace lfy? Murmushi Yayi yace Zan aje Abokina gida ne Baba ki dakko kayan amfanin ku. Baki ta washe tace. " Kai Allah yamaka Albarka Ɗan lukuti, inaga yau zaka karya sihirin Aljanin Abokin shi,Yo miskilancin jameel yasa ko Aboki bashi dashi tin na yarinta da ya fada Rijiya ya rassu har yau baisake ba, kullum yana daki kamar mai jego,Yau kau gaka dashi abinda na dade banba Ai sai godiya. Dariya yayi yace Miskili kafi mahaukaci ban haushi zan gyara miki shi kwana kusa. Allahu yasha Yasha Dan lukuti. Murmushi kawai Yayi dan in tana wani abu sai tabashi dariya yana son zama da Tsahhi yasha dariya ya kuma ƙaru da wasu labaran nada.. Yan kayan su da ba yawa ta halhaɗo ta fito dasu anata kallon su da Babban likitan da Bakowa yake kulawa ba. Motar sa ya buɗe ya sanya Jameel gaba kana ya Buɗema Deedee Yan Kayan ya watsa su boot kamin yaja da bismillah suka dauki hanya Deedee na kwatan tamai. Gab da gidan Aymah Jameel ya Kalle shi yace Friend Dan Daraja Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama ku tsaya naganta na mata godiya karamcin ta gare ni. Cak Dr ya tsaya yanabin gidan da kallo kamin yace DeeDee kimasa jagora ku shiga ku fito na ƙarasa daku. A'Hankali ya fito ta kama shi yana tafiya sannu sannu. Faɗa Deedee ta fara dataga yanda suke tafiya taki karewa kamin su iso bakin palo . Akan kujerar robar barandar Aymah ya zauna yana sauke numfashi dan yagaji ba karya amma fatan shi yayi tozali da kyakyawar fuskar ta mai cike da karamci da Kamala. Deedee ta kwankwasa kofar shuru tsawon 10mnt kamin taji an ɗan Budemata. Aynah ce cikin shigar rigar atamfa hijjob dinta har kasa ga cazbaha a hannunta. Kallon kallo sukai kamin kuma tace sannu Inna ina wuni. Deedee dake mata kallon tausayi tace lfy klau sannu. Ni Kaka Jamilu Baraka ce, Ni na haifi mahaifinsa to munzo Muyi godiya . Ido Aymah ta ɗan zaro kamin ta ce sannu Kaka sannu fa shigo. Aa ba sai na shigo Ba Allah ya miki Albarka Ya kuma yaye matsalaki ya baki mafita cikin gaggawa, Allah ya maki Albarka yajikan Magabata.. Ameen tace cikin rauni kamin tayi Shuru Zuciyarta na bugawa dan so take ta tambayi jikin sa amma bakinta ya mata nawie ,bataso ta sake kullah alaƙa da kowane Namiji duk girman shi duk karantar shi. Jameel kau da tin sadda ta fito yakejin wani masifaffan faduwar gaba, ga zuciyar sa sai tsinkewa yake yakuma kasa daina kallon ta.. Kallo ɗaya yamata ya gane ta bala'in rame kuma tana cikin damuwa fatan shi kawai yaji tayi tambayar inda yake dan ya lura som batagan shi ba . Yana so yanda Ya damu da ita yaji koya ne ta damu dashi. Deedee tace to mungode sosai Allah ya biyaki ya kuma baki lada kana ya warware Damuwar ki. Cikin sanyi tanayin kasa da kanta tace "Ameen Kaka nagode,Dan Allah ki gaishemin da Baba Baraka sosai asake bata Hkr akan abinda ya faru Shii..m..a.. ace mai Allah ...ya .sa..wake..y..asa..anyi ...a Sa'a takarasa a rarrabe muryarta har rawa take idon ta na cika da Hawayen data kasa gane ko namiye.. Sassanya murmushi mai sauti ya saki da saida yasata dagowa da sauri idon su ya sarke dana juna. Gabaki daya saida Zukatan su ya buga da bala'in ƙarfi, kowa ya zubama Ɗan uwan shi ido,sunama junan su kallo mai cike da kewa da kuma bege. Aymah ce tayi saurin kawar da kanta gwfe tana dan wasa da yatsun hannuta dan wani girma ya karamata da kwarjini. A'Hankali tace "ya jiki? Alhamdulillah yace A'hankali Narkakkun idon sa akan ta . Ɗan dagowa tayi suka hada ido da sauri ya kawar da kai gefe itama haka . Kanshi ya ɗan shafa yace "Hidimar da ki kaiman Allah ya maye miki gurbinta da farin ciki na hr abada,Zan miki Addu'a allah yabaki tukwicin Aljannah,Ngd sosai nazone na miki gdy ya faɗa yana mikewa dakyal yana dan Cije baki. Ido ta lumshe dan ba karya kalaman sa sun ratsa mata zuciya, sun kuma sanyata farin cikin Da take jin tayi bankwana dashi Abadan.. A'hankali tace Ameen tnx u. Baice komi ba ya fara ƙoƙarin tashi da kanshi. Da kyal ya mike ya fara tako Dan ƙafarshi tayi mugun sanyi . Gab da ita yawani turguɗe zai faɗi. Da Karfi ta kwallah ihu tana Rarumo shi jikin ta gabaki daya, dakuma dukkan ƙarfin ta hankali tashe. Wani irin tsalle zukatan su keyi lokacin da suka zubama junan su ido Yana tallabe A hannuta. Deedee kau kamar ɗiyar roba ta hau Kif-kifta ido dan gani tayi yanda yayi kwanciyar aka tallabe shi kamar wanda zaisha Mama😄 ( Weyyyy Hajja Deedee nasu ba irin naku bane) Last free page in sha Allah ❤️MATAR OGA NA❤️ Last free page UMMY AYSHA. PAGE 🔟 **Aymah kau cikin bala'in sanyi tace."Sannu kar ka fama raunin ka ta ƙarasa tana ɗagoshi A'Hankali. Ido ya dan lumshe mata yana gyara zaman riga shi kamin A'Hankali yana ɗangyasawa Ya fara takawa. Wani irin tausayin sa sosai ya dirar mata Ahankli tace. " zaka dawo bayan ka warke? Cak ya tsaya kamin ya juyo ya kalleta yace "kina buƙatar hakan? Cikin wata shagwaɓaɓiyar murya da batason tana da itaba tace . Babu kowa agidan kuma ina jin tsoro . *Subhanallahi! A karon farko wannan magana tayi tasiri akwalwarsa har ta motsa lfyr sa ta ɗa namiji. Ido ya lumshe mata kamin ya ɗan fara tafiya dan tsayawa kamar tonuwar Asirin sane. DeeDee ta kalle ta cikin tausayi ta kama hannu ta tace. Miyasa kike so ya tsaya Ummu bakya tsoron dokar mijinki yabi ta kanshi Kamar yanda yabi ta kan iyayen shi. A'Hankali tace. Kaka inajin tsoro sosai na zamana ni kadai agidan nan, Babu tsaro ga halin da ƙasar nan ke ciki,Kana dama yace shikadai xai bari yanamun sayayya dan Allah karkuyi fushi in ya warke ki barshi ya dawo gidan nan. Deedee ta kama hannuta ido cikin ido tace.. Kinaso na taimakamiki ki fita kangin rayuwar da kike ciki cikin ikon Allah koko bakya so?. Cikin rawar baki Aymah tace Zanso haka amma Kaka na riga da nayi Alkawari wa Kaina bazanje ko ina Ba . Saboda bana da inda yafi nan ,kana dangina duk sun gujeni bazasu karɓeni ba,Kaka Biyar dinma da zan hau mota bana da ita kibarni kawai inga iyakacin Adnan.. Murmushi Deedee tayi tana karema gidan kallo kamin tace. Shidin banza shidin wofi. su Makashima sunyi yayin su sun shuɗe balle shi da ko Rabin su baikai ba A hatsabiban ci ,gamawa dashi har wani abune bari dai jikana ya warke xan maki zuwan kanki kwana biyu, Yo kwana biyu Mana dan yakin bana dare ɗaya bane. Murmushi sosai Aymah tayi tanajin soyayya kyakyawar tsohuwar har cikin ranta. Murmushi tayi tace ngd Kaka Allah ya kiyaye. Ameen tace cikin sauri ta cimmasa tare da kama shi suka fara tafiya. Sadda zai Fita get din ne ya dan juyo a sanyaye yayin da sukai ido hudu da Aymah dake bin Faffaɗan bayan shi da aikin wahala yasa shi buɗewa da kallo. Ɗan kauda kai tayi cikin aji yayin da shikuma ya ficce suka fada motar Dr suka tafi har kofar gidan su ya ajesu . Deedee tace ya shigo yace A'a zaizo da mangariba. Godiya sosai Jameel yama shi yana dagamai hannu suka shiga ɗan madaidaicin gidan nasu. Da sallama suka shiga Inna su na tuka tuwo Malam Habu na daka Daddawa sai firan su suke, Yayin da Autan ta ke Wanke'wanken . Gabaki daya sunyi farin cikin dawowar shi dan Kabeer rungume shi yayi yanata kuka dan akwaishi da karara zuciya gashi yanason Yayan nasa. Bayan sun xauna sun natsu Deedee ta ƙanƙan ce ido tace . Wallahi wallahi sai wannan auran ya mutu ina mai shedamaku kwana kusa , Saboda yarinyar nan akwai jini ajikinta na yarinta wannan azabar da zai'bata itace zatasa ta zama Kwarangwol kamin nan ya saketa sannan kuma ne duniya zata juyamata baya dan baka da wanda zai auri sauran mutuwa. Kai nifa dana hango palon nan sai Naga kamar babu ko labule!koko idona ne oho. Inaji ajikina Muzguna mata zayyi, to aiko yayi a banza wallahi dan sai yaji a jikin shi Yaseen xanta hurama cikin shege . Gabaki daya suka sanya dariya malam yace . A'a uwata kiyi hakuri karkimasa wannan aikin kinji,Ki barshi wallahii ki zuba ido tin duniya Allah ke sakayya yanzu. Badai dukiyar marayaba Hmm! zai tantance hatsabibancin ta gare shi. Hahahaha Deedee ta shiga dariya babu ko tsaitsaya wa . Gabaki daya ido suka zaro dan tinda sukaga tana wannan kafirar dariya sunson ba karamin balai ta shiryama Adnan ba. Ya rasulu ya manzon Allah. Dan Allah Deedee nah karkije ki tabomuna inda za'a hallakamu Kinga sai sojane. Cak ta tsaya da dariya tace in kaga wani Abu ya faru daga Allah ne , Dan haka karka wani damu. Adnan. Kullum in ya fita baya sake dawowa gidan sai dare,Gidan bude yake amma ya zuba matakan tsaron da in tayi yunkurun guduwa zaisa a cafketa. Ranar daya cika wata ukku cif yayi Shirin komawa aiki dan ya fahimci komi ya kammala dan da niyyar sa wata daya zayyi ya koma, Amma saida ya tsaya ya siyar da Asibitin Aymah da wasu filayenta kamin ya wuce... Garin kwaki mai yawa ya ajiye mata yakai tiyya biyar da uban yaji dakakke sai manja. Baimata sallamaba yasanya Key ya rufeta ya kama gaban shi. Bata taba gane abinda ya shiryamata ba saida taji kwana biyu tsit din tayi yawa anan taga ko kujera dake dakin shi an ɗauketa ga Dakin yayi datti. Tsaki tayi ta koma D'akin ta ta kwanta ƙasa tare da tada kai da jikkunan ta da sune kawai ta tsira dasu Amma ko pilo bai barmata Ba. Yunwa taji tanaji ta tashi ta shiga kiching dan samun abinda zataci dan yanzu har ta saba da maneji . Indomie kau har tasanya zafi ya tasomata saboda cinta da take yawanyi. Cikin natsuwa ta fara tafasa ruwan zafi kenan gas din ya kare ya salam tace tana dawowa ta zauna palo to ta ina zata samu abunda zatai Amfani dashi. Idonta ne ya sauka ga ledar garin Kwakin nan anan ta tashi ta buɗe tayi murmushi dan harga Allah taji daɗi, Dan sadda tana mkrt in taga an'kawoma Ƙawayenta suka Haɗashi har rokonsu take. Manja ta diba ta kaishi ga rana tare da jefa tafarnuwa guda biyu kana ta dawo ta ɗiba ta Jiƙashi. Ya salam tace sadda taga tana kwadashi yawunta na tsinkewa. Sadda tagama taci ta koshi tasha ruwa kamin ta tashi tayi Alwallah ta dawo ta ɗauki Alkur'anita da yazama abokin zamanta ta fara karatu. A haka Aymah keta rayuwa cikin kunci tin tanajin dadin abincinta na yanxu har ta dainaci dan Ta fahimci tsab ya tsanemata Ruwan jiki Sai dai shan Ruwa ,Ace Rogo ne da safe dare rana abin Yayi yawa tayi kuka har ta gode Allah ta hakura.. Jameel kau masha Allah jiki yayi sauki kullum kagan shi kwance daki yayi shuru, wani lokacin kuma yana sakin murmushi da kama pilo . In kuma ya tino wani abun sai yaji shi cikin fargaba da Kunci. Kwana shi Hamsin yaso komawa su Inna suka hana shi da Alkawarin sai Yayi wata biyu. Ranar daya cika wata biyu kam da kuzari sosai yatashi yana fatan zuwa ya ganta cikim aminci. Bayan ya gama shirin shi tsaf Deedee ta kama hannushi ta rike sosai tace. Allah yamaka Albarka , nayi istakhara nagano muna da nasara. Dan haka kaima kaji tsoron akkah karka cuci kowa karkuma ka keta mutuncin matar Aure ta hanyar yawaita fira da ita,in akwai rabo tsakanin ku duk wuya duk dadi zata zama taka,ka kama kanka ka iya takonka kar in'ƙara ganin wannan rawar jikin naka. Murmushi yayi yana dan rungumeta yace ngode Kakar da babu ya ita,Nifa bance Sonta nike ba,Aa kawai ina tausayin ta ne.. Dariya tayi tace haka yake wannan karatun. To Amma in ba so mike kawo Tausayi?. Shuru Yayi yana ɗan sosa kai kamin ya mata Bankwana ya fito . Gaisawa sukai da mahaifin shi dake Tsince Tattasai dan yanzu dole tasa shi kasa cefane kofar gida yana siyarwa kuma ba laifi Allah yasama abun Albarka Yana samun Na cefane,dan Basu da Matsala kayan Abinci Babu Abinda Dr nan Bai ajemasu ba. Jameel kau bayan sunmai addu'a ya fita ya tsaya ya ɗauki wayar shi tare da kiran Alh Adnan. A mutum ce ya ɗauka dan dama kamar jira yake. Bayan sun'gaisa yace . ka warke ko ?zaka iya dawowa bakin aiki dan dama inaso a duba gidan nan aga ya labarin Dabbobin dana bari. Ido jameel ya dan zaro yana tinanin to wace Dabbba Ya aje? Kar yaje ya barshi ya shiga wajen abinda bai saba dasu ba. No in kaje kagani karka damu yanzu turomun account number ka zan sama kudin aikin ka 50k. Sai kuma in sama na abincin dabbobin 10k kayi manege kullum Dari biyu da Hansin zaka kashe in ka kashesu kamin wannan lokacin wallahii nidakai ne. Tsaki Yayi yana Harara wayar kamin yace . OGA bafa xai yiyu kanamin ihu ba karka manta jinya nayi ba sannu ba komi Sai faɗa!in baka bukatana saina tafi ka samu wani Dama ai ka kori Iyayen na ni zaman mi zanma? Shuru yyi kamin yace ina jiran account number xan lissafama komi ya kashe wayar. Minti biyu tsakani yaji alart. Da kuma list din kayan abinci kamar haka. Garin kwaki Manja. Barkono Gishiri. Dariya Jameel yayi sosai yace mugu yanzu bayama iya sammasu abincin gidan kwara amasu Wannan Haɗin Bala'in dan shi duk tinanin shi Karnuka ne. Bayan ya isa gidan wani mutum yayi parking da Machine kusa dashi ya buɗe gidan kamin ya Mikama Jameel din yace . Gashi inji oga in zaka tafi wani wuri kaje dashi kaima muna biye dakai. Cikin mamaki yace biye dani danayi mi? Shuru mutumin yayi tare da tada Machine Yayi gaba. Ganin ba sarki sai Allah ya buɗe gidan yashiga duk compound din yayi kura ,Gashi duk motocin Gidan Basanan. A'Hankali yafara kalle kalle wata Zuciyar nace mai ko harda Aymah yatafi wanna karan dan baiga alamar akwai mutane agidan ba. Karnukan ma bai gansuba ko Haushin su Baiji ba.. Aymah kau tin sadda ya bude ya shigo ta dawo bakin kofa ta bude ta fito barandarvta dan damabkofar a bude take. Ido yajiyo jin motsin abu. karaf kau suka hada ido. Gabaki daya wani mugun zaro ido yayi ganin yanda tayi mugun duhu ga wata uwar rama datayi kamar ba Aymah ba dagani ba wadataccen abinci. Hankalin shi tashe cikin sassarfa ya nufeta yace miye haka jinya kikai. Batace komi ba ta kawar dakai. Wata kafurar tsawa ya bugamata kamar wanda ya girmemata yace . Ba magana nike mikiba mike damunki?... Kuka sosai tasa dake cin ranta kamin ta fara magana cikin rawar murya "Nagaji! Nagaji Wallahi da rayuwar nan, Ya rabbi ka ɗauki ra.... Wani uban tsalle ya daka yana matse bakin ta idon shi yayi bala'in ja cikin rawar murya yace. Da kaddara Allah zakiyi jayayye,shin kenan bazaki gode Allah da Ni'ima dayamiki ba ta barinki da rai,Mike faruwa dake? Miyasa ba zaki godema jarabawar da Allah ya nufe ki da shi.. Cikinta ta nunamai tace . yunwa nikeji sosai,nagaji da abinda ya barmun,Cikina kullum yanamin ciwo,Ga jiri dake matsaman. Miyabarmiki yace yana janyeta daga jikin shi.. Palon taje ta ɗakkomi shi ledar ta gwadamai. Anan ya gane abinda Alh Adnan ke nufi. Wa'iyazubullah Tir da Hakin sa dayake kiran matarshi da dabba ashe kam babu babban dabba kamar shi.. A Cikin Lallami da Kwantar da hankali yace . kiyi shuru kiyi Hakuri Allah na tare da mai hakuri ina zuwa. Dan Allah karka tafi tace cikin rauni da kuka. Bazan jimaba zandawo yace cikin Alhini ganin duk Yanda ta dawo kamar Yarinya . Kuka ta sanya sosai tana dafe cikin ta dan ta Tabbata shima guduwa zayyi ya barta. Jameel kau yana fita kai tsaye kudin yaje ya cire ya shiga kasuwa ya raba kudin shi biyu Dan bama Iyayen shi Rabi kamin ya fara mata sayayya kayan tea irin su indomie ƙaramin gas da Aka samai shi ga Buhu da kayan baki daya harda su biscuits da yan kayan maƙula shi. Kayan Abinci ma saida yamata aune aunan duk abinda yakamta wanda zataci . 10k dinta ya ɗauka yamata cefa ne da nama kana ya doshi gidan da uban buhu a bayan Napep. Koda ya sauka ya bude ya shiga. Ajesu Yayi baranda inda ya barta yace ga shinan kiyi girki kici binda kikeso in sha Allah xan nemo miki duk Abinda kikeso... Wani maɗaukakin farin ciki ya bayyana ga kyakyawar fuskar ta data sanya Ran bankwana Dashi. Ya Salam!,Wani girma mutunci taji yaron nan ya karamata a ido, Lallai yacika Jinin Baraka dan Ta tabbata sunson karamci Yaro ƙarami Da Hankakin Manya. Sassanya murmushi tayi tace wayabaka Kuɗi? kana miyasa ka zabi kashemun? Shima murmsuin yayi yana dan shafa sajensa yace HAL JAZA'U IHSAN ILAL IHSAN... Kai ta dagamai cikin murmushi tare da fara kwararo Masa Addu'a Budi Na Alkhairi dan Tabbas tajishi Har cikin Jinin Jikinta Ashe dama Za'a Samu Namiji mai tausayi A wannan Lokacin.. Ameen yace ya koma ya xauna yayi shuru. Itakam cikin Sassarfa ta cire Hijjob dinta ta fara aiki baji ba gani wani Mugun dadi takeji ga magi da komi irin wanda Maman shi ke amfani dashi ya siyomata. Cikin awa daya tagama abincinta shinkafa Da miya lafiyayya da salat, gefe kuma naman kajine ta soya su sosai ta masu peper chicken Ta ɗora akai. Tana gamawa ta dauki lemun daya sai mata guda biyar wanda harda kankara aciki .. Tire ta samu ta shirya abincin mai rai da lafiya ta dora cokali da ruwa da lemo ta fito waje yana nan inda yake ya jingina da bango. Gashi nagama tace cikin fara'a da murmushi. Kai ya gilgiza yace Laaa Bafa dani zakiyiba ke kadai zakina abincin ki dan ya daɗe miki,zan karɓa na yau amma dan Allah gobe basai kinyi dani ba. Wata shagwaɓa ta kwacemata tace . to ko gani kake ban iyaba ta karasa tana turo baki da Dire kafa. Kai ya Gilgizamata yana murmushi kamin ya dauka ya motsa da Bissimillah ya kai bakin shi Dan tabbas Ya biyemata zata iya sawa Ya zare Area wajen shagala da Kallon ta. Ido ya lumshe sosai yana wani kadasu kamin yace gaskiya Alhamdulillah MATAR OGA NA Ta iya abinci sosai. masha Allah. Fuska ta kwaɓa kamin ta tashi tayi ciki dan tsaf zata iya kuka yana cemata matar oga. Komawar Jameel gidan Aymah ba karamin sauyi ya kawomata ba cikin ikon Allah,dan iya bakin kokarin shi yanayi wajen ganin ya wadata ta da abinci mai dadi mai gina jiki,cikin ikon Allah kuma ta dawo hayyacin ta tayi kyau ,Hasken ta ya dawo bata da damuwar komi dan Jameel ya tsayamata. Jameel kau Sosai yake cikin farin cikin ganin ta dawo cikin walwala sai yaji inama.zai iya tafiya ya barta ya kara neman wata sana'a dan ya wadatata da duk abinda take nema. Amma ina Yanzu tsoro ma yakeji dan tini suka dawo gidan kwana shida kabir anan dakin masu gadin farko suke kwana dan yanaganin kamar za'a iya kawomata farmaki kowane lokaci dan Tini yagama gano Manufar Alh Adnan akanta. Yammacin wata Alhamis ne Jameel na xaune bakin get da wata takarda yana zane zanen gidaje yaji motoci na tsayuwa bakin get din,kamin ya an'kare har An fara Ƙaƙaniyar buɗe get. Fuskar manya sodojine suka bayyana kamin yaji sun fara Ɗurrowa ciki. Da ido ya bisu har suka shiga basu jimaba kuma suka fito gabaki dayan su suka ficce dan dama ba wanda aka bari. Adnan daya aje uban tumbi ya doso wajen da murmushi yace. kayi daidai Jameelu daka kasa ka tsare zakuma ka raka wanna ma ya tabbatar man da rikon amanar ka dan Haka zanje dakai dan nason Zaka iya . Murmushi kawai yayi kamin yace tinda ka samu dawowa zanje gida Ohk ka rufe kofar in kafita.. Wata harara Jameel ya watsamai cikin ɓacin rai da kishin abinda yace kamin ya juya ya tafi Yana sakin Tsaki zuciyar sa nata Hararomai Abubun da zai Faru wai Ya rufe gidan Allah kasanya Karta Saurareka Shashasha. Koda yaje gida dakyal ya fadama Deedee dawowar Adnan amma bai fadamata dalilin bacin ran nashi ba data Tambata yace dai yana tsoron ya mata wani abu. Dariya ta zuba tace bar shege,Ni yanzumafa bari inje gidan Adawiyya mu gaisa kwana biyu tana fama da baseer mai tsiro. Adawo lfy sukaimata ta tashi ta yafa mayafi ta fita. 10mnt ba adauka ba Deedee ta shigo gidan tana rizkar kuka da fadin. shikenan Asirina ya toni Adawiyya ta rassu jama'a kutayani jaje nayi rashin aminiya,Alkah sarki Rabi wayyo ni Hansatu. Gabaki daya sunshiga tashin hankali Malam Habu yace. Ina ake zaman Makokin An kaita ne?. Ido ta zaro kamin ta sake fashewa da kuka tace. wai ashe amma tafi da ita kauyen funtuwa dan asamu Aimata aikin gida Ashe acen rai yayi halinsa, yanzu haka kudin Likkafani ne ya gagara wai canjin nasu bashi da yawa kai jama'a yanzu abinma da zaa rufe tsiraicin Mamaci sai ya Gagareka Ga yaron duk sun kwasa mazan sunyi cen Kauyen yanzu motace kawai da za'a je masu gaisuwa. Sauran canjin 2k din dake hannun Jameel ya zaro ya bata cikin tausayi yace . Deedee to gashi kije ki basu. Toto tace tare da karɓa daya tace. kaima ka rike ɗaya kaji , Ni yanzu bari in'Bisu muje arufe kawata dani kamin lokacinmu yayi. Malam Habu ya mike tsaye yace bari in maki rakiya tasha ... Ido ta zaro tace nace mafa ga mota cen bakin Layi nicemafa na tsaidasu sai nadawo kawai tace tana shiga dakinta ta dauki kayan ta Guda daya ta fito da Zungureriyar Cazbaha da Kwalli sai Powder ( Hoke Dede Yar gayu gidan Mutuwar ake kwalliya kenan😄) Dariya ta sheke dashi kamin ta shiga shagon Iliya mai Likafani ta yanki yadi hudu akamata doguwar riga har kasa da wata kalar hijjob mai madauri. Killace abinta tayi ta sallamai tafara tafiya. Abakin kofar gidan Aymah tayi tsaye dan tagan shi rufe Iyakarfinta tasa ta fara dukan gidan amma ina Ba abude ba. cen taji takon tafiya ana cewa waye? Da sauri ta buya. Adnan yazo ya bude ya Duddu ba baiga kowa ba. Haka Deedee taitayimai yana fitowa yana dubawa baya ganin kowa Itakam tana cikin shukoki baya ganin ta. Ranshi ɓace ya fara Tafiya dan son ganin ko wane shegene dake bugomai gida Yana ɓoyewa Bayan Layi. Da gudun tsiya kamar ba tsohuwaba ta fada gidan sai uban nishi take. A palo ta iske Aymah nata kuka . Inane dakin da baya shiga Deedee tace cikin sauri. Arikice Aymah ta mike tana nunamata dakin su na kasa tace gashinan kaka lfy. Deedee tace in ya fita nafito ta shige da sauri tare da dan nama kofar key ta barshi ciki. Akasa ta zube dan dama agyara yake ta hau sauke numfashi. A'Hankali tace. zakaci ubanka Ɗan Yau. wallahi badai mutum ba Sai dai Allah. Ja dabaya ga rago ba Tsoro bane. Ah toh munga jiya munga yau sai fatan ganin gobe,Yo ashema haka mijin yake ɗan kwat kamar kwandon tsane salat,Sai uban ciki kamar na Akuyar Yan Caina,Ga kai kwal kamar madubi anya wannan ba ɗan uwan su sheɗan bane dan bala'in kama suke da Wanda Na taɓa Gani Cikin Shara wata Rana kauye. (DEEDEE INA KIKAGA SHEƊAN😄) Adnan kau rai ɓace ya dawo ya fara kiran layin Jameel amma basa zuwa. Kafa ya haɗe yana jijjige jijjige tare da fadin bazaki fadaman wanda ya baki wanna gas dinba? Kulolina nasa aka saida aka saiman bana da murhun da zanyi girki hasakima ban iyaba. Oh fine har kina da kaddara da zaki saida kiyi abu to suma bazaki sake sasu ido ba ya karasa yana daga waya ya fara kiran wani layi. Cikin lokaci katti nan sukazo suka sake kwashe komi aka fitar tare da kawo icce da murhu aka aje. Da Hannu ya nunata yace ga sauyi nan na gero da dawa in shi kike so gasunan kison yanda zakiyi ya ƙarasa yana wucewa dakin shi ya kira manager dan Jin kudaden dayacemai akwai matsala shigar su account ko sun shiga. Aymah kau dakin da Deedee take ta isa ta ɗan fara bugawa kasa kasa tace kaka nice. Deedee ta taso ta bude tana mayarwa ta rufe tare da zama kusa da Aymah tace Anan yake kwana ko waje. Da hannu Aymah ta mata nunu da sama tace anan sama yake. Dariya tayi tace maza ɗakkoman Kulki ko Taɓarya Yar nan. Ido Aymah ta zaro cikin Raɗa tace mizakiyi. Oho nace ki dakko Deedee tace tana zaro mata ido. Aymah ta kawomata Deedee ta karɓa tace maza jeki anjima munyi magana. Fita Aymah tayi inda ta dauki sauran garin dake gareta tun na farko ta jika ta diba ta akwoma Deedee sauran. Jameel kau zazzabi sosai ya rufeshi komawar shi kuma ba komi bane sanadi sai rufe kofar da akace yayi ya barsu sosai zuciyar sa ke zafi da tafasa ga tunani barkatai da yake,Zazzaɓin daya rufeshi yasashi kashe wayar sa yayi kwanciyar shi. Adnan kau suna zaune da mangariba aka kawomai abinci Lafiyayye yaji naman kaji sai kamshi yake ga uban lemo da ruwa. Saida ya gama Yayi net kamin ya danyi aikin shi ya haura sama Yana mika. Dakin shi ya shiga ya hau kujera da aka kawomai dawowar sa ya kwanta Ya fara baza munshari. Tsaye take gaban mirron toilet ɗin cikin shigar farar rigarta. Fuskar ta ta sha farar powder kwarmin idon kau cike yake da Bakin kwalli. Farin gashinta ta turo gaba sosai.kamin ta sanya wannan hijjob mai mazugai ta daure tare da kallon kanta a madubin toilet din nan. Ita kanta ta razana Da yanayin nata dan ba Shegen Daya isa yace ba fatalwa bace. Katuwar Taɓaryar ta ta dauka cikin sanɗa kamin Ta fito. Matakan benan ta fara hawa sulu sulu Kamar hawainiya. Dakin farko ta tura ta ganshi ba komi sai kaya kasa da jikkuna wannan ya tabbatar mata dana Aymah ne. Na karshe ta bude A'hankali Tun palon Ta farajin Munshari kamar kukan giwa. Murmushi ta saki tana gyaran zaman tabarya kamin ta tura kofar A'Hankali ta shiga. Tsaye tayi akan shi tana karemai kallo kamin kuma ta dan fara bubbugamai taɓarya dake hannuta a kumatu A'hankali. Sosai yake juya kai kamin kuma ya ɗan Budesu a hankali. Toch light din hannuta mai bala'in Haske tasa ta kashemai Yan idanuwa. Azabure ya mike yana fadin kai waye Anan. Hannuwan ta ta ware akan katuwar fuskar shi ji kake tass Tass tass har so ukku kamin ta fara jijjiga jiki cikin wata murya ta tsahhi sosai datayi Kasa tace AMANAR DA MUKA BAKA KENAN ,ADNANNNNN... Ihu ya kurma sadda ya dawo hayyacin shi wanda tagwayen marin nan ya rasashi. Minaimaku dan Allah. Ku kunnomai Haske ya ganemu Deedee tace da ƙarfi cikin basaja.kuma ta kai ma glop ɗin dakin duka da taharya hannuta saiga Haske ya gauraye palon. La hauka wala kuwati illah billah adnan yace yanajin numfashin sa na neman tsayawa sadda Yayi ido hudu da ita sak taimai kama da mahaifin Aymah. Deedee kau matsawa taitayi gare shi tana wani murmushi tana kusantar shi taɓarya ɓoye abayanta... Alhamdulillah mungama free page Maiso ya biya ɗari ukkun sa ya karanta cikim Aminci. Kamin magana ta Whatsapp number nah sai nabaka account ɗin da zakasa.07038423451 ❤️MATAR OGA❤️ UMMY AYSHA PAGE 11 *Dan Allah dukkan wanda yaman magana yaga ban bashi reply ba Yamun uzuri wayata ce ta samu matsala ba girman kai bane ba kuma izgilanci bane aa kawai Tsautsayi yafaɗa kantane nikaina hakuri Nike Allah kasa ku fahimceni masujin Haushina kuma ku yafeman*. ***Ido ya hau sake gwalewa amma dayake mahaifintane aranshi tsaf ta koma mai shi. "Yaro ina buƙatar samun kusan ci dakai a makwancina Deedee tace tana daga taɓarya nan ta kwaɗama Makunnun hasken ɗakin ya sake yin duhu. Wani Gigitaccen ihu yasa yana ƙoƙarin mikewa ya sake faɗuwa awajen. Yayin da ta Daka tsalle tayi kanshi ta hau yakushi da cizo cikin wata makirar murya mai wani kuka kuka mai tada hankali take fadin sai Yabita kushewar su ya girbi abinda ya shuka. Adnan kau tashin hankalin da yake ciki a daidai wannan lokacin bamai kirguwaba ne, Dan gabaki ɗaya lakkoki jikinsa sunyi mugun week baya ko iya daga Yatsunshi dan Yariga' ya tsadaƙas kawai fatalwar ubanta ne . Deedee ta daga hannu da niyyar sake kwashe shi da mari taji ta cikin ruwa mai bala'in zauri wanda ko ba'a fadamata ba tason fitsarine ya sakomata ranta kau ya kara ɓaci dan Deedee ta tsani zauri kona Gishirin Ƙunci kuwa. Kanshi ta cafka ta dinga kalangu dashi shikam yakasa komi sai wani gurnani yake kamar tsohon rakumi. Saida ta gaji dan kanta ta sake kunna hasken dakin a fakaice tana zubamai ido da sakin wannan murmushin dayake sanya barin jikin shi aiki. "Ya makomar Auran yata take gare ka ?tace tana juya kai da ido. "Fabu Aule na akanta na taketa taki ukku yace cikin mawuyacin hali dan bakin shi ya riga da ya karkace.. (BABU AURENA AKANTA NA RIGA NA SAKETA SAKI UKKU) Wata Sassanya guɗa Deedee ta saki kamin ta dinga juyi firrr cikin ɗakin kamar tantabara ita da likkafanin ta. A idon Adnan kau gani yake kamar tashi zatai sama. Cen kuma ta juyo ta dakamai tsawa tace dukiyar yata? Dukiyar kace daka kwace kai na tarawa? Miye nufinka a kanta? Shuru Yayi sai Ya'u dake dilalomai. Saida tasake juyi kamar sabuwar fanka kamin tass ta kwashe katuwar fuskar shi da mari tace. magana nikema. Cikin wahala yace . Inatan dukiya ! ta balmani ,Alhati kai akuli tan Allah ka kaini atibiti Ɓalin jikina ya tanye. (Inason Dukiya! Alh kai Hakuri dan Allah ka kaini Asibiti Ɓarin jikina ya shanye) Dakyal Didi ta rike dariyar ta jin cikin awanni kaɗan ya koma maganar yara . "Au mu Asibiti mukezuwa? muda muka riga mukai wafati . Babban Asibitin da zaka shine kushewata zan kaika acen ne zakai bacci ka huta harda saleɓa badai takamar ka zalinci ba,Adnan minaima,Miyasa na cancanci haka Wajen ka? Kuka ya fara kamin Deedee ta dakamai tsawa tace rufe ido . Ruff kau ya rufe cikin sakan daya ta ɓaccema ganin shi. Ya rasulu ya manzon Allah yace Cikin ranshi. lokacin dayaga walam kamar an yi walkiya an ɗauke Babu Alh Abdulkarim Mai Dala a ɗakin. DeeDee kau tana sauka kasa ta cire kayan jikinta ta fada dakinta tana sauke numfashi. Wata mahaukaciyar dariya ta hauyi tana tino yanda ya dinga magana da yanda yake zare ido Kamar sabon Angon dake neman Hanya. Cikin dariya tace honi Deedee,In nasa kaina sodojima mantawa suke da matsayin su,Yo mantawa mana ke da ace a siffar jinnu najemai ai da tini yasanya bindiga ya karni amma najemai a siffar da uban kowa ke tsoro wato fatalwa,Gashi yanzu na gano kan gaskiya. Saura Aymah ina so naji wacece ita ya matsayin mahaifin ta da Alh Adnan yake miye Alaƙar su. Allah sarki jamalun Deedee ashe da matarka kake ta samun kusanci shiyasa kaƙi natsuwa, in sha Allah sai nayi tsayuwar daka An daura maku aure kaida Aymah mai kyau in ga yan yaranku tagwai tagwai. Sai kuma ta buga ta gumi tace. To amma ya za'ayi Ɗan shekar Ashirin da shidda ya auri yar shekara 36 ohni Deedee to taya zai iya da ita kar aje asake cutarta a karo na biyu ta karasa tana mikewa tsaye ta fada wanka danjinta take kamar toilet sai zauri take .. Bayan ta gama ta ɗauro Alwallah ta fito ta hau kan sallaya ta dinga nafila da Nenan zabin Allah akan rayuwar da Aymah zata fuskanta dan suma ba wani karfine da suba. Washe gari Aymah ce ta bugo sakko ta fado dakin DeeDee Ta isketa zaune akan sallaya. Bayan sun gaisa tace Kaka yau mizakici naga garin ya kare kuma ni ban iya Amfani da wannan geron da yakawo ba. Murmushi Deedee tayi tace karki damu yar nan ina zuwa amma kamin nan kije ki fara duba mijinki ki dawo ina da magana dake. Aymah ta dan bata fuska tace. babu ruwana dashi kaka kwara na tsaya matsayin daya ajeni. Deedee ta sake murmushi tace . A'a kije dai,kwara ke ki sauke hakkin shi dake kanki kinji Yar Albarka. maza jeki gaishe shi , inma kinga bacci yake ba sai na fitaba muyi aikin tinda baison da zuwana ba. To ! tace ta tashi ta fita ta nufi ɗakin shi dan itama yunwa takeji . Fatanta Allah yasa bacci yake Deedee ta gwadamata yanda zatai amfani dasu. Tin palo takejin mugun wari kamar na mushe ga zarni. Cikin sassarfa ta karasa cikin dakin tana toshe hanci da tambyar ko lfy. Tana tura Kofar sukai ido hudu dashi yanata hawaye ga wayar shi cen nesa dashi tanata haske alamar kira ake. Aymah ta kalleshi tace. lfy ka cika daki da wari haka ?kiye haka?ko gudawa kake?. "Kati nayi yace cikin gwamutsatsar hausar shi. (Kashi nayi) Ido ta sake zarowa dan yanzu ta tabbatar da kaddara shanyewar ɓarin jiki ya kama shi. Sake zubamai ido tayi taga yanda hannushi ya sandare da kafa guda. Adnan matsala ka samu garin ya , faɗuwa kayi ta karasa cikin rauni tana zaro ido. "Ma'aifinkine cila,cine ya jaman,Fatalwa yaman,yakuma taukeni yaje dani kucewalci kaca ta maceni ya karasa yana ɓarkewa da kuka . (Mahaifinki ne sila! Shine yajaman,Fatalwa yaman,Yakuma ɗaukeni yaje dani kushewar shi kasa ta matseni). Duk yanda Aymah taso ta daure kasawa tayi nan ta shiga wata irin dariya idonta jage jage da hawaye, dariya da tasa har faduwa take tana tashi amma ina takasa Tsayawa. Adnan kau kuka yasa dayaga abinda takemai bakin ciki da tsanar ta da ahlinta na kara hauhauwa afarashin zuciyar shi,Ya dauki Babban alkawari duk sadda yaganshi tsaye da kafarsa sai yazama ajalinta. Dakyal ta tsagaita ta saki ɗan murmushi mai bayyana zallar farin cikin da take ciki, Tare da daga hannuwanta sama tace. Allah gafurun rahim, Allah nagodema daka nunaman wannan ranar A tarihin rayuwata , Ina cikin tsananin farin ciki bisa ga sakayyar dakaman cikin gaggawa, lallai Allah ba azzulimin bawan sa bane, Allah bayason zalinci baya kumabari ayi zalinci, Adnan ina takamar ina kudin, dukafa sun shuɗe, gakanan dare daya Allah yayi nashi ikon akan ka. Wayar shi data sake kawo ihu ta ɗauka tayi sallama. Shuru taji anyi kamin cikin sauke ajiyar zuciya taji ance ina "Mai wayar bashi mana miye alakar ki dashi. Murmushi tayi dan tagane matarshi ce. Tace matar shi ce ta biyu,Wacce ya boyemiki zaman dake tsakanina dashi. Ayanzu dai mijin ki ya shiga toilet danyin wanka in ya fito zai kiraki. . Cikin ihun tsawar dattijuwar ta kundumoma Aymah zagi da fadin wacece ita,Ita babu namijin daya isa yamata kishiya balle ma Adnan da tason Baxaitabamata haka ba saboda rantsuwa yayi da Allah akan bazai hadata da kowa ba. Murmushi Aymah tayi kamin tace. in son samune mizai hana kibari lokaci yayi kizo inda yake,yanzu lokacinane in yadawo gareki zaki iya masa wannan tambayar ,Kana da xakice bazai Haɗaki da Kowaba, ina kikaga ilimin da za'a shiga taro dake ke kam ai sai tsaron Yara shine ya dace dake. Cikin ihun kuka tace . wai kina nufin kece wannan dayaceman yana daukar haya in zaije taro? kece dama matar shi? yanzu ni yakecema marar ilimi ?ina yake yazo yabani kaf dukiyata dama ance tsintacciyar mage bata mage na tsani Adnan Allah ya isa tsakainina dashi ta karasa cikin kuka. Murmushi Aymah tayi tace kema kince wani abu kamin ta datse wayar tare da cire sim card din ta aje shi gefe. Kallon shi tayi yanata zare ido da gilgiza kai tashin Hankali mabayyani A fuskar shi. Murmushi tayi tace yanzu Allah zai fara tonamaka asiri. Kibani wayata ai natakeki kitai kibani wuli yace a gwamutse. ( Kibani wayata ai na sakeki kitai kibani waje) Ido ta zaro cikin farin ciki tace'' Alhamdulillah Adnan ka sakeni ta karasa tana jin hawayen farin ciki na zubomata saboda bata taba tinaniba gashi tayi alkawari bazata tabacewa ya saketa ba. Aguje ta mike tayo kasa tana kwalama Deedee kira da fadin" Kaka kaka zo Adnan ya sakeni takarasa cikin farinciki hawaye kwance akan kyakyawar fuskar ta. Deedee ce ta fito tana rike haɓa itama farin ciki kwance a fuskarta tace. Kai haba amma abufa yayi dadi to yanzu ai morewa ya baki dukiyar ki sai kibarmai gidan ki. Aa nabarmasa tace tana wani juyi cikin mugun jin dadi dan gani take kamar ta sauke Kaya.. Kai kai kai Alhamdulillah abufa yayi dadi . Kwan!kwan!!kwan!!!taji anfara buga kofa. Deedee ce ta bude idonta ya sauka akan Dr da Jameel da idon shi yayi bala'in ja kamar wanda Yayi kuka fuskar nan tashi a tsuke ba alamar rahma. Lokaci daya suka sha jinin jikin su daga Deedee har Aymah. Ina Adnan yake yace jikinshi na rawa. Deedee ce data fahimci yau zuciyar ta motsa mai jikinta har rawa yake wajen nunamai dama tana komawa gefe. Dr kau rikeshi yayi yana fadin kabi komi sannu Jameel ban faɗamaba dan Kai aika aika.. Fincikewa yayi kamin agujen ya fara tattaka matakalar. Nan gabaki daya suka rufamai Baya. Deedee kau har tayi rabi ta dawo ta ɗauki farin kayan ta ta sanya ta murje fuskarta da powder ta da Kwalli kamin aguje ta bisu . Jameel kau yana shiga gadan gadan ya banka kofar dakunan baiganshi ba sai ana ukkun ya ganshi bai tsaya tantance komiba ya ware kwanjin shi ya hau dukan Adnan kamar ya samu jaki. Ihu yake cikin karyayyan halshen shi yana faɗin. Suwaye ku minaima Ku. Deedee data shiga da fararan kaya ta bayan su tabi ta wuce tai tsaye saitin da Adnan yake ta tsaya da ɗan murmushin nan nata mai dagamai Hankali. Munkalu wanakili kuyi akuli Natuba facen ƙalaba yace da karfi idon shi akan Deedee. (Munƙaru walakiri kuyi Hakuri na tuba bazan ƙaraba) Aymah kau dariya sosai yabata kamin idonta ya sauka kan DeeDee zata fasa ihu Deedee tamata alamar shiru. Jameel ta samu ta cakumo da karfi tare da Sanya hannuwanta ta sargafo shi ta baya cikin rawar jiki tace" Jameel kallah cen. Cak yaji komi nashi ya tsay zufar jikin shi ya shiga share wa yana maida numfashi kamin ya juyo ya riketa gam suka rungume juna sosai yanajin wani mugun yanayi a tattarr da ita. Ido ya ɗan zaro kamin ya dagata ya zubama Deedee ido danshi kanshi saida gabanshi ya fadi da ganin ta. *Yanzu haka kudin Likkafani ne ya gagara kai jama'a yanzu kudin da za'arufe tsiraicin mamaci ma sai ya Gagareka* Maganar ta ta dawoma Jameel kenan itace gawar kuma nan tayo . Koda yake ai dama itake nunamai dakin duk sai yanzu wannan Tinanin yazomai. Saf saf saf ta shafasu ta fita . Dr ma fita yayi ya barsu daki su ukku. A'Hankali ya dago haɓarta ta zubamai ido shima idon nashi ya zubamata. Wasu sakwanni masu wuyar fassarawa suke aikama junan su kamin da wuri ta kawar da kanta tana maida idonta ga Adnan daya zumabasu ido dan sai yanzu ya gane Jameel ne ashe yamai wannan mugun dukan lallai ma. *Kina da Labarin jiya kika gama iddarki ? Jameel yace cikin wani yanayi da bazai musultu ba. Ido ta zaro tace iddah ,iddafah kace Jameel... Ga masu bukatar saye ku turo ta account number nah kamar haka 9064260199AMINA DAHIRU OPAY BANK Shedar biya ta Whatsapp number nah 07038423451 ❤️MATAR OGA ❤️ MALLAKI. UMMY AYSHA PAGE 12 *ASLM ALAIKUM DAN ALLAH ADAINA SAMUN KATIN MTN BANA AMFANI DASHI SAI CHART GLO KAWAI NIKESO NGD* Fararan idanuwan shi ya lumshe yace . Tabbas ya sakeki tin ranar da kika biya kudin aikin da akaman Asibiti. Hannuta ya kama suka fito suka dawo palo inda suka iske Deedee da Dr zaune tana bashi labarin komi yana dariya. Bayan sun sakko Deedee ta zubamasu ido tabbas sun dace da juna matuƙa . Wayar Dr ya karɓa ya shiga inda videos suke ya nemo wanda ya masu ba tare da duk sun sani ba. Anan aka shiga haska takarda da Adnan ya karɓa wajen Dr yana rubutu itakuma tana kara jaddadamai tabarmai duk dukiyarta, da alƙawarin vazata taba guduwa ta barshi ba Har sai in shine ya buƙaci hakan. Ya salam ! tace tana dafe goshi wannan wane irin bala'i ne da masifa! miye manufar Adnan na tozarta ta haka? dama so yayi taita zama karkashin wahalar dayake ganamata itakuma tanamai biyayya har karshen rayuwar ta. Lallai Allah nagodema tace a bayyane tana sake kwanciya akan kafaɗar Deedee hawaye na zubomata.. Jameel yace . Kinga abinda ya miki ko,yanzu miye mafita?. Murmushi tayi tace. Jameel bana da wata mafita ayanzu ,ina zani ina zan zauna Allah masani. Ya haɗani da family na bazasu karbeni ba,Nima bazan fara yarda na kusance suba,Banama da kudin da zan iya barin garin nan yamun kat ya kwashe ni. DeeDee tace'' zaki iya zama damu a gidan mu amma muma ba masu karfiba ne?. Shuru tayi dan tana ganin zamanta dasu kamar D'aura dawainiyar ta ce gare su,Kawayenta kuma bata fatan kowama Yasani dan wannan sirrin tane. Dr ne yace Yanzu Deedee abinda yadace anan shine". Zansa mai gadin gidana ya mayar da Adnan kauyen su zan dinga biyansu suna kulawa dashi adan kwana biyu,In yaso sauran magana ma idata bayan ya dawo. Deedee tace nifa inaso sanin tarihinki Aymah wai ubanwa yasa kika aure shi? Aymah ta share hawaye tace Deedee tsautsayi da kuma Yaudara dayaman ashe fuska biyu gareshi. Deedee tace Ina jinki cikin ƙaguwa. "Sunana Ummu Aymanah. Mahaifina da Mahaifiyata yan uwan junane saboda family nasu Auran junan su suke kamin daga baya kuma suka janye wannan Al'ada,Sukaba kowa damar zaɓen wanda yake so. Nataso cikin gata da kuma wadataccen ilimi na addini dana zamani. Mahaifina yana daya daga cikin masu arzikin family nasu koma nacemaku yafi kowa dukiya dama wajen mahaifan sa shine kwallin kwal kamar yanda nima nidaya ya Haifa . A labarin daya bani Adnan Tsohon Driver sane ta fannin Hito na shinkafa da suke fitowa daga maradi su shigo da Ita Nijeriya Su sayar. Daga baya kuma Adnan din suka rabu da mahaifina amma bai dai faɗaman dalilin rabuwar tasuba yace dai sun samu saɓani. Ina gab da gama karatuna na secondary Adnan ya dawo rayuwar mahaifina bayan ya nemi affuwar laifin dayamasa kasancewar Babana mai hakuri ne Kuma bashi da Riƙo ya yafemai suka dawo harkokin su na rayuwa . Sosai adnan kemai biyayya duk da kasancewar lokacin yana da Babban matsayi a fannin aikin daya fara na soja Amma bai manta Halaccin Mahaifina gare shi ba . Bayan na kammala secondary sch ne Adnan ya nunama mahaifina ya Dade yana sha'awar ya aure ni tin ina Ƙaramata. Yana so yabashi ni daganan ya dawo dani cikon garin katsina dan in karasa Karatun danike so nayi na likita. Sosai mahaifina yaji dadi har dai ya sameni da magana nima na amince dan ina ganin mutuncinsa yana kyautatamun duk da Babban mutum ne naji na amince dashi Sosai. Bayan anyi aure na dashi ne ya kawoni nan katsina inda ya zameman uwa uba gata na gidan duniya babu wanda Adnan bayamun mussamman dayaga Bantada Hankalina ba akan Rashin lfy dayake da itaba,Babu abinda ya dameni nidai kulawa da yakebani ya wadatar dani. Duk sadda zai tafi aiki kau haka xan kwana kukan rabuwarmu dakyal dai nike barinshi yaje . Akwana a tashi nima ya mayar dani karatuna nan na fara gadan gadan. Adnan kanje dani taron su na manyan Sodoji da akeyi wanda ya hada da iyalin su . Duk sadda naganni dani dashi nakanji dadi sosai yanda yake nunama duniya yana sona. Adnan ya taka rawar gani ta fannin ilimina dan ya tsayaman har nakai matakin zama Babban Dr . Sadda na cika shekara 14 da Aure mahaifina ya budeman Asibitin da aka kwashe shekara biyu ana ginata tawa ta kaina wacce ni banma saniba duk tinani Adnan ya budeta dan shine kan gaba wajen komi. Ranar da aka kammala komi ne suka dakko hanya dan zuwa ayi taro dasu saidai akamana waya akan sun samu accident dukkan su sun mutu. Bazan iya musultamaku tashin hankalin da najiba a wannan lokacin nayi kuka nagode ALLAH. Acen Agadas akayi zaman gaisuwa. Kwanan ukku da rassuwar su Adnan ya Tatamasu rashin mutunci akan sai sunbani Hakkina da iyayena suka mallakaman dan ya fahimci sunyi caaa akan dukiya ta. Babu yanda basuyiba akan yabari amma ya nunamasu kakinsa na soja da son kawar da duk wanda zaici zalin dina. Wannan abu ya masu zafi suka hada duk wata kaddara da take tawa suka bashi gabansu ya damkaman kana ya kamo hannuna muka fito. Har munzo mota ya kamani muka koma ya bugemasu warning akan duk wanda ya cika dan halak karyazo inda mukeya isheni komi na rayuwa. Anan suka hau rantsuwa akan zasu nunamai jinin buzaye basa magana biyu. Suma suka sake koramu dan sunfisata mussamman da sukaga nayi shuru duk tinanin su bayan mijina nike goyo . Nikam Alhini rashin iyayena ne ke damuna bata ihun da suke nike ba. Bayan mundawo gida yasake shedaman na tattala dukiyata kuma na fara fita aiki shima zai koma bakin aiki an'ma maidashi Kaduna baki daya dan da yakanje yadawo.. Toh nace nan washe gari ya yi shiri ya koma wajen aikin sa nima natafi wajen aikina da bana iya komi sai tinanin iyayena . Haj asiya kawata ce sosai tare mukai karatu . Da kaina na dauketa aiki ina sallamata kudi mai tsoka . Duk sadda zata fadaman matsala maza bana yarda saboda ni naga nawa ya tsallake na kowa duk da yaceman yana da matsala hakan baitaba damunaba tinda yanabani kulawa daya dace dani muna kuma addu'a da fatan samun Rabo mai Albarka. Wannana tafiya ta Adnan itace sanadin watsewar zaman auran mu dan bai waiwayoniba saida akai wata shidda cur,bayan yazo kuma yazoman da ayyika baya da lokaci na,in'kau yana aiki namai magan sai tsawa hantara rashin mutunci daga karshe kora ya biyo baya. Nayi kuka Nagode Allah saboda bansaba ba , Nayi nayi ya fadaman minaimasa yakiya kullum korata yake da hantara waya kau namasa ranar nabani zai iya zagina shiyasa banayi saiya nemeni. Ahaka dai naita rayuwa ni kadai gashi bayason mutane Asiya ma ya rabani da ita Sai wajen Aiki. Dakyal dai ya barni na ɗauki Baba Baraka bayan nakai ruwa rana tana dan taimakamsn da aiki har zuwa dai yau da Allah ya kawo wannan rabuwar da banmasani ba. Deedee ta numfasa tana sakin murmushi tace. Tabbas akwai wata akasa kuma ina bukatar sanin wane saɓanine ya hadasu har takaiga rabuwa kuma aka sake dawowa. Kanan miyasa ya kyautatami ki gaban idon su bayan idon su kuma ya kuntatamiki ? Mutuwar iyayen nakima inaji Ajikina akwia sanya Hannu. Ido Aymah ta zaro jikinta ko ina ya dauki ɓari tace. Kina nufin zai iya kasheman Abbah nah da umma nah ? Deedee tace ko daya. wanda dai yayi wannan zuciyar ta barinka kuma daga baya ya dawoma sai inga kamar fansa yazo ɗauka amma dai bari zamuji daga gare shi wata rana. Jameel yace bari na tambayo shi. Kamo hannushi Dr yayi yace bakaga matsalar daya samuba a yanzu,Magana zatamai wahala,kana bayyi laushin da zai iya fadin gaskiya ba kabarni da shi. Kabari kawai a mayar dashi cen wayoyin shi kuma ka kawoman su nan na ajesu. Am'sawa sukai da hakan yayi kamin suka tashi suka tafi Deedee kuma ta rike ciki tace . ke ina geron yake na hada ko furace nasha. Aymah da tabi Jameel da ido ganin duk yanayin sa ya canza ko kallonta baiba tace'' am nace yana kiching. Deedee tace tom bari mutashi kamin nan ina zuwa ta karasa tana haurawa dakin Adnan . Inda yake nan ta iske shi kwance yana bacci cikin wahala. Tsaki tayi tana daɗe hanci kamin ta shiga bude bude taga jikkar aikin shi . zugewa tayi taga kudine gasunan Available. Murmushi tayi tace to ai hikenan tinda dama kalkashin ka muke dole kacidamu dan uban ka. Masu yawa ta kwasa sosai cikin kallabin ga kamin ta fito tana hura hanci tace da Aymah ke kwashe geron nan anjima ayi sadaka dashi nidaikam nashiga kasuwa dan yomuna cefane dan yanda ya lalace bazamu yarda kudin nan su lalace da warin kashi ba. Murmushi Aymah tayi rashin tsoron tsohuwar na burgeta da jajircewa tace tom Kaka kidawo lfy. Yawwa tace ta dakko mayafi ta fita. Adaidaita sahu ta hau taje kasuwa ta kwaso kaya na alfarma kaji kau saida Deedee tasai Ashirin aka yankemata su aka gyara cikin wayo tana nuna masu Abincin saidawa zata dingayi dasu.. Napep guda tayo ta dawo . Gab da zasu shiga kwanar taga mai sayar da Yalo ta saya kamin suka shige. Mai napep din ya kamamata ya hau kaima ta ciki tana samai Albarka. Tana kokarin bashi kudin shi motar Dr tayi parking suka fito shida Jameel da wani ɗan Dattijo da matasa guda biyu. Bayan sun kamama Deedee takai kayan tasasu zubomasu gas kana ta shiga Aiki. Wow masha Allah zanso kuji yanda gidan nan ya d'umame da girkin dattijuwar nan da babu kauyanci A lamarinta dan gas kai kace tasaba aiki dashi kodan yana karami oho. Su Jameel kau duka palon suka zauna kowa yunwa na sake tasomasu Saboda kamshin Girkin Deedee. Yayin da matasan suka haura sama dan gyara Adnan. Kwance suka iske shi ya baje yana kuka kashirɓan da surutun da ba'agane miyakecewa cikin karyayyen Halshen sa. Dakyal suka gane ashe Allah ya isa Abdulkarim yake cewa ba kakkautawa yana kuka. Dariya suka fashe dashi kamin dan iskan cikin su yace baka tubaba ɗan Kwal uba ya karasa yanama Adnan cakulkulo da faɗin" kamoshi nan ɗan nakasashen Banza Mai kan kwakwa kamo shi nan yakarasa yana matse hancin Adnan. Kuzo kuga zillewa wajen Adnan da kwabe fuska da sakin maganar shi cikin sauri. Dariya gudan yahauyi harda rike ciki kamin sugama iskanci suka burkitashi kamar kayan wanki sukamai tsirara. Nan ma saida suka dinga tsokanar shi kamin su toshe hanci suka kai shi Toilet gaban shower suka kwantar dashi ƙasa suka kunna ruwa mai bala'in sanyi ya dinga sauka kanshi. Far far far yadingayi da ido kamar zai shiɗe kamin su kashe suna fadin ubanwa zai sanya hannusa jikinka katon banza sai kace ka daukemu jahilai irinka dole ka Bari ka jiƙa kana asama tsintsiyar da zata fiddaka. Saida kau suka bari an dauki lokaci kana suka sanya Tsintsiyar kwakwa dake Toilet din suka hau durza shi kamar sun samu turken Dabbobin da ba'ataɓa wankewa ba. Sosai Yake kuka yana Ɓare baki amma ba wanda yabi ta kanshi saida suka gama suka burkitashi da tsintsiyar suka hau yimai tsarki suna sokamai ita cikin fata da gangan sai ihu yake yana gwaranci. Bayan sun gama suka sake Kamoshi kamar Ragon da aka yanka suka maido daki suka samai kaya kana suka kamoshi suka fito dashi palo daidai lokacin da Deedee ta gama girkin lafiyayyan tuwon semo dinta dayasha miyar kuɓewa danya ga tantakwashi aciki da manshanu sai kamshi yake. Akaro na farko Adnan yaji yana bala'in son tuwo da wannan miyar mai tado tsohuwar yunwa. Waigawa ya fara yana baza ido yana fadin. "A tubomani yunwa niteti Azuboman yunwa nikeji. Deedee ta kalle shi tace yunwa kakeji yaro a zuboma? Da sauri ya dagamata kai tace . zakaci abinci kuwa tinda dama ka kasayar ai dole ka nemi sabo. In dai wannan ne nama tanaji tayi kiching ta dakko wata robar almajirai ta kawo gaban shi tace. Dama ai saida na dibarma rabonka kar Allah ya kamamu ta karasa tana turamai kwanon robar gaban shi. Da ɗayan hannu shi ya lallaɓa ya buɗe . idon shi ya sauka akan garin kwaki da yaji da manja. Kallonta yayi irin kallon ke wacece. Ni makwafciyar kuce nazo zama da itane kamin Allah yabata miji nagari tayi auranta kaikuma kai maza ka gama akai ka kauye dan ubanka Deedee ta karasa tana zaromai ido. Su Jameel dake cin tuwo suka hau dariya sosai irin yanda take abu da kwarin gwiwa. Tura kwanan yayi gefe kamin yace. Tete mate ta falko da dan fala katewa a layuwata kamin wannan tegun dukkan tu wallahi ya nuna wayanda sukamai wanka da su Jameel. ( Kece mace ta farko Arayuwata da zan fara kashewa kamin wannan shegun) Idonshi ya suaka akan Aymah dake cin abincinta cikin natsuwa. Kete ta karshe matiyatiya. (Kece ta karshe matsiyaciya) Murmushi tayi tace kamin ka kasheni aini gashi na kashe rayuwar takanwawa kawai bakauye ,Jahili yanzu zan nunama kai ba komi bane ta watsamai yawu a fuska. Iya takaici yaji gashi kowa abinci yake ci babu mai kallon shi. Ganin zai iya mutuwa yaja robar yafaraci da hannu sa mai lafiya. Ukku yaci ya ture dan baitaɓa cinsa ba. Babu wanda yabi ta kanshi saida suka gama Deedee tace'' Kai Jameel dauki wayar banza kirawo yan iskan nan masu bakin glass da matar shi tace suna zuwa ɗaukar shi cemasu yace abari zai nemosu bayajin daɗi. To yace ya dauki babbar wayar tashi yaganta da security. Miye possword naka yace yana kallon shi. Adnan ya juyar dakai cikin tafasa zuciya da tinanin abinda zaimasu duk ranar daya ganshi tsaye da kafar shi. Ganin zai batamasu lokaci yasa Jameel fizgo hannuwansa ya dangwala ta bayan wayar take ta bude ya fara shige shige last call din shi da yayi ne yabi. Bayan an dauka ya mikama Aymah anan ta sanar dasu bayajin dadi yace subari zai nemesu. Fatan Alkhairi suka mai ya aje wayar Aymah tace. tom tashi kabar gidan dan kaine da bari nikam dai zama daram daram sai na nemeka kazo. Zai fara kururuwar ihu katti nan da suka hau gyara saman dakin nashi suka sakko sukai sama dashi . Wannan Dattijon dake nuni da shine mai gadin Dr ya bisu yana nunamasu hanya. Cen wani kauye mai bala'in nisa suka kai shi aka jingine kasan bishiya bayan sunba wanda zai dinga kula dashi 5k da ledar garin kwakin shi sukai gaba Abin su. Ɗan sauran kudin Adnan Deedee ta dauka da yamma ta saimasu katiffai don tace ta dawo gidan saitaga abinda zai turema buzu nadi. Dan barinsu agidan kamar sun tonama kansu asirine kuma idon mutanan shi zasu dawo kanshi wannan shawarar da suka yanke yasa Dr ba Aymah wayar tashi da suka riga suka ciremata possword gaba daya dan duk wanda zai kira ya sameta.. Da yamma Deedee taje gida tamasu bayanin abinda yafaru duka sunsha mamaki daganan sukai fatan Allah yasanya Alkhairi ta nunamasu saboda kadaici tanaso ta zauna da Aymah dan debemata kewar Iyayen ta. Amsawa sukai baki daya dan sun aminta da shawarar Tata Rayuwa suka fara mai daɗi Tsakanin Aymah da Deedee komi cikin jin dadi da walwala .zaman Deedee gaban Aymah ya mugun debe mata kewa da kuma dawo mata da farin cikin data rasa na rayuwa. Adnan kau ba kasafai take tinashi ba tinda ba Alkhairi bane a rayuwarta. Jameel kau sosai yake cikin damuwar da duk iyayen shi sunyi tambayar duniya yaki cewa dasu komi. Da yamma yayi shirin shi tsaf yayi bala'in kyau cikin wata brown din shaddar daya dinka ga wata sallah dabai fiya sata ba ya kafa hula coffee ya fesa turaran sa mai saukin kudi wato Emergency. Tinda ya fito Malam ke fadin masha Allah yau kuma sai ina Jameelun Deedee kamar wanda ya samomuna sirika matsala daya dai babu walwal a fuskr ka. Dan Murmushi yayi yace zanje naga Deedee. Murmushi kawai Inna su tayi tace dan Allah ka gaishesu da Aymah. Tom yace kamin yakama hanya ya tafi. Zaune suke a tsakar gidan da yanzu yazama wajen shan iskan su Deedee ta dafamasu gyada sai cin abinsu suke suna fira. Da sallama ya shiga dukkan su suka zubamai ido bayan sun amsa. Deedee ya gaida kamin ya dan saci kallon Aymah ya ɗan turo baki. Itama Kallon nashi tayi kamin tayi dan murmushi tace" ina kwana Jameel. Lfy yace yana dan hade fuska . Deedee ta rike haɓa tace Jamalu minike gani haka wanga lamari tafa girmema?. Pink lips dinsa ya turo yana fadin to ni ba Namiji bane . Ido suka zaro su duka kamin Aymah tayi dariya tace "hakane kam sannu da zuwa ta tashi tayi ciki dan kawomai ruwa. Zama yayi Deedee ta kamo hannushi tace "Dan Allah da manzon sa mike damunka Jameel, mahaifinku yace na tambayeka dan Allah minene ko son umma ne yamaka yawa? Aa Deedee,Abu daya ne ke damuna arayuwata. Taya zan iya samun sana'ar da zan rike ku a halin yanzu. Deedee kayan abincin kufa yayi kasa. Aymah maca ce Deedee tana bukatar yan Abubuwan rayuwa na mata. Deedee tayi tagumi tace wallahi hakane da ɗan pampas din nan na zamani da suke likawa in suna haila da kuma Turaruka gata da son gayu ni nama Manta bansawo mataba danaje sayayya. DeeDee zan koma sana'a ta ta da gaskiya bazan iya ganin Aymah ta tagayyaraba asanadina ta salwantar da dukkan abinda ke garetafa Deedee. ❤️ MATAR OGA NA ❤️ Mallaki Ummy Aysha Domin mallaka naki ki biya kudin ki ta account Number nah kamar haka 9064260199 Amina dahiru OPAY BANK saiki turo shedar biyan ki ta Whatsapp number nah 07038423451 Page 13 Deedee taja numfashi tace. Hakane! shiyasa nima kaga Dukkan wani abun da zanyi na faran ta mata inayi saboda wannan yarinya Wallahi inajinta tamkar kai din nan, ina son Ummu tana da kyakyawar alaka ,tana da kuma saukin kai ,bata da kyamar talakka som. Kai namiji ne Jameel jajirtaccen daya kamata ya tsaya da kafar sa. na baka goyon baya dari bisa dari. Dukkan abinda kasan zakai da karfinka da gaɓɓan ka in dai aikine na halak, kai koda kwasar kashi ne kam na baka dama kaje kayi ka wadata da abinda Allah ya Hore ma.. Mahaifin ka Kuma tinda Allah yasama sana'ar shi Albarka kabar shi ya rike nashi iyalin ,kai ka zamemata garkuwa ko nace ka zamemuna, Allah ya sanya Albarka ga dukkan abinda zaka taba yamaka jagora zuwa ga neman Halaliyar ka duk inda take. Ameen yace yanajin dadin addu'a ta. Aymah kau dake tsaye bayan su tin sadda taji ya ambaci sunan ta ta tsaya cak. Wasu hawaye masu bala'in zafi suka zubomata,ashe duk inda take kai farar zuciyar su Deedee da zuria ta sun wuce myan,Taya,zai wahala yazo ya kashemata? Akanta kawai. Idon ta ta daga sama tana wani nazari. Saidai ina lokacin bayyanuwar hakan bai ba gareta, Bayyana wannan ɓoyayyan sirrin nata kamar watsa sabuwar rayuwar da xata gina ne anan gaba . A'hankali cikin sanyi jiki ta karasa inda suke ta ajiye masa flat din da tasamasa ruwan pure water mai sanyi dan tini suka maido fridge din Adnan palon ta na kasa. Daya ya dauka yace Nagode kamin Deedee tace'' Aymah wai yau kodai bakyajin dadine naga idon ki ya kumbura ko zazzabi kike?. Da sauri Jameel ya ɗago kai ya zubamata ido baya ko kyaftawa sai zujiyar sa dake tsalle tsoron shi daya kar ace wani abu ke damunta . Cikin sanyin ta tace banajin komi kaka kawai dai hakanan naji sauyin jikina. To ko muje Asibiti. cewar jameel yana zubamata ido cikin kulawa. Dan murmushi tamai tace A'a bai kai nan ba. Fuska ya ɓata ya mike ya zura takalman sa yace" Deedee bata mayafi muje Asibiti Amma Hijjob ba gyale ba. Deedee tace kwaraiko kuje! Hijjob kuma wannan baka isaba abinda take so shixata sanya. Ido ta zaro sadda taga ta mike cikin shagwaɓa da takema Deedee datake gani kamar uwarta tace" nifa gaskiya bazanjeba amun allura, kana bake ce kikace ya koma aikin sa na daba dan ya samomun kudi ,nikuma baki fadaman miye aikin ba ko na wahalane oho ta karasa tana turo baki da Dire kafa kamar yar 17yrs... Sassanya Murmushi ya saki yana yin kasa da kai da sauke ajiyar zuciya jin dadi da tace ba komi ke damun taba . A'Hankali yace "madallah da wannan halitta mai dumbin Alkhairi.. Deedee kau haba ta rike tace ƙudura sama liman da wawan zama ! Yanzu dama duk akan wannan karama matsala kika saki lokaci daya? yo nace in bai nema mikiba wazai ba?. Murmushi tayi suka hada ido dashi ta d'agamai gira kana tace shi din nan kanena ne Deedee,Hakkina ne na tashi tsaye wajen neman nawa na kaina dan samar mishi abinda zan gina shi. Kai wai kai mene ma matakin karatunka ta karasa tana zaro mai ido da daure fuska irin ita Babba nan. Kai ya shafa yana murmushi dan ya lura so take ta kasheshi da salan ta kamin yace "ai mace bata girman namiji som, Yanzu haka da wani abu xai shigo gidan nan ita kanta wannan Deedee data baje anan aguje zatai ciki nine dai zakin da zan tsaya naji mike shirin farauta Iyali...datse harshen sa yayi da karfin masifa tinowa dayayi da katoɓarar da zayyi. Deedee kau dariya tashigayi yayin da Aymah bata gane hausar tashi ba . Deedee ta dauki ɓawon gyaɗa ta hau jefamasa yana caɓewa. Tace Allah ka shiryaka yaron nan .. Aymah kau murmushi kawai tayi tana wani nazari. Anan unguwar Yayi sallah mangariba da isha kamin yaci abinci ya masu sallama ya tashi. Washe gari ana gama Asuba bayan yagama duk kan azakar nashi yama su Baba sallama ya fita. Kai tsaye tasha ya nufa wajen abokan sa na da. Sun kau yi farin ciki matuka da ganin shi dan tinda ogan shi yayi accident shima yabar zuwa. Jiki na rawa aka hau bashi key na motoci dan kowa yason shi da zafin nama gashi baya wasa da Hakkin kowa. Motar Dutsama kawai ya karbi key dinta dan bayaso yana nisa dasu yafiso yaje garin dake kusa da nasuya dawo cikin ikon Allah. Karfe tara akama motar lodi ya hau ta da addu'a. Cikin kwarewa yake murza sitiyarin ya kaisu lfy ya sake yin wani lodin na katsina ya dawo . Bayyi kasa a gwiwaba ya sake hadawa ya koma. A takaice saida yayi tsawu ukku kamin aka raba kudin ukku akabama mota daya, shi daya , Mai mota ɗaya . Ba laifi ya samu kudi a ƙallah dubu 8k Koda ya dawo gida ya zubema Inna su shi sosai suka samai Albarka sukamai murna. Yace su ɗauki nasu ya kaima su Deedee sauran. Baba dake gefe yace A'a bazaayi hakaba gaskiya. Ka kaimasu sai kaima ka rike wani abu ni Alhamdulillah wanda nike samu Ya ishemu . Aa yace yana mikewa yace babu abinda zanyi nida gobema in sha Allah fita zanyi wannan ai na farko ne dan Allah ku dauko wani Abu.. Albarka suka sake samai Inna su tace to ga 5k ka kaimasu mu bari mu dauki biyu kai kuma ka dauki daya kayi kalaci. Godiya ya masu kamin yace wai Inna mu ina wannan Halima dake zuwa gidan nan ne. Malam ya harare shi yace sai yau ka tinota yarinya datama bauta da iyayen ka kamar zata mutu ta gaji ta koma garin su. Baki ya dan tabe kamin ya shige dakin shi ya dakko kayan wankan shi ya dibi ruwa yayi wanka ya daura alwallah mangariba. Bayan ya zira kananun kaya masu baylain kyau ya fesa turare kana ya dauki hanya gidan Aymah. Da sallama ya shiga gidan bayan an'bashi izini ya shiga palon kasancewar akwai wuta firar su kawai suke wayoyin Adnan gaban Aymah tana dan lallatsawa Akai akai . Ido ta dago tace kanena sannu da shigowa. Wata harara ya dan ballamata yana faɗin. gaskiya zan daina zuwa kinacemun haka Deedee kimata magana. Tom'tom sorry Yayana na daina sannu tace tana murmushi. Yawwa lovely sst tnx u. Deedee tace cen dai ta matsemaku kai gyambo da san girma ita kuma tana biyema taɓarar ka. Karkacewa yayi ya zaro 5k din yace gashi ku fara sayen abinda babu dan Allah zuwa gobe. Aymah ta zaro ido tace kai Jameel miye kayi ka samu kudi. Sata nayi. Ya bata amsa kai tsaye yana zubamata shanyayyun idon shi. Ido ta zaro tare da hada hannaye tace" bance ba! Amma Dan Allah wane aikin wahala kayi yabaka wannan kudin . . Deedee tayi murmushi tace mota fa yafaraja yanabin garuruwa dama aishine sana'ar shi. Sosai Aymah ta mayar da attention dinta kaf kanshi tare da zubamai fararan idanun ta da a hankali hawaye keta kwanciya ciki. Shima din kallon ta yake amma irin kallon nan na tsoro da bazaice ga nufinta a zuciba shin kudin ta raina koko oho dai. Tsawon lokaci kamin cikin sanyi tace" Duk akaina ka fara wannan wahala? Deedee tayi Murmushi tana fadin' bari dai in watsa ruwa inzo mungode Allah ya tsare ka daga sharrin abin hawa. Ameen yace yana gyara zamanshi har lokacin zuciyar shi bugawa take dan baison hukuncin Tambaya da Aymah ta masaba. Tana ganin wucewar Deedee ta rarrafo inda yake gab da junan su kamin tace" Jameel. Dan kallon ta yayi yace" na'am. Miyasa ka zabi komawa abinda ka bari saboda ni? Kafada ya daga kamin yace kawai hakanan sabida kasancewar ki marainiya ayanzu baki da gatan kowa saina Allah dani,to gani ai bazan amince ki fita nema ba,Kana karki manta saboda nine kikayi missing kaf abinda kika mallaka,So in ban tashi na nemar miki ba waye zaibaki ?. Hawaye suka zubomata kamin tace. Jameel dan Allah da manzon sa in dai nice ka daina ,kabani lokaci kalilan dan Allah,Kana wallahi badan kai na rasa komi ba,Yana cikin ƙaddarata,Karka manta komi a rubuce yake a kaddara bawa fatan mu dai Allah kabamu ikon cinye jarabawoyin mu... Ameen Ameen.. Amma in'dai Hakane kinga kenan nima komawata wannan aikin yana cikin ƙaddarata so kimun Addu'a kawai. Murmushi tayi tana dan kallon shi tace" kai ko,nizakawa wayo?. Shima murmushin ya mata yace" A'a kawai dai inq bisa sunnar maganar kine komi kaddarane a rayuwar bawa. Tom Allah ya mana zabin Alkhairi,amma ni yanzu nafiso koda neman zakai ka tattalawa kanka kaga ka dan fara girma kyanshi ace nan da shekara ukku zuwa biyar in aurar dakai, kana bikin ka ba irin na kowa bane dole muyi dogon tanaji.. Ido ya zaro kamin ya k'ank'ance ɗaya akanta yace Biyar?,dan bakya sona, sai nayi shekara biyar ba aure,in sha Allah nan da shekara biyar yaron mu ko yarin yamu sun kai shekara hudu. Kaf fara'a fuskarta ta dauke jin furunci shi cikin wani alhini tace " Kenan dama kana da wacce kake so amma baka fadamana ba. Murmushi yyi yana shafa kanshi yace" Allah mas@ni ,muna dai lalubune a duhu. Deedee ce ta fito tana baza kamshi tace "wai har yau firar bata kareba ni inacen har nayi nazarin Abinda zai fishe mu. Aymah tace kaka miye kika nazar ta?. Deedee tace "bazamu zubamasa ido kullum Yaje ya nemo ya bamu muga Randuna sai dai mu girke ana zubamamu muna lashewa. Dan haka nida yar jikallena tsaye zamu tashi wajen neman na kanmu sana'a zamu fara in sha Allah , Gobe goben nan zanje kasuwa Naga abinda ya dace nayi. Dariya ya hauyi harda rike ciki abinda bai fiye yiba. Sosai Aymah ta shagala da kallon baiwar kyan dake tattare da matashin bawan Allah nan mai jini ajika. Deedee kau rai ɓace tace" ai dole kayiman dariya ka daukan mahaukaciya nadai gama ma komi tinda na kawo ubanka duniya. Cikin danne dariyar sa yace "kema Deedee daga shiga har kinyi bacci da mafalki saiki hango abu har ya tabbata. Takalman kafarta ta cire tana fadin tashi kabar gidan nan gwauron banza ko in'bugama aka. Mikewa yayi yana bude hannu da fadin "ko baki koramba tafiya zanyi nan ya masu sallama yatafi. Ajiyar zuciya AYMAH ta sauke tana lumshe ido. Washe gari Jameel karfe takwas ya bar gida sadda ya isa tasha shine kawai ake jira . Kamar yanda ya zama akidarsa fara addu'a kamin hawan karfe haka yayi kana ya kunna suka dauki hanya sai fatan dawowa lfy. Deedee kau tana tashi ta damamasu kunun tsamiya da kosai suka zauna suna kalaci Aymah kau sai santi take dan ita duk bata iya wannan kayan galgajiyar ba gata da son su shiyasa in Didi nayi kamar kunnan ta ya tsinke. Bayan sun gana tashiga gyaran palon Dede tamata sallama ta fita kai tsaye kasuwa ta nufa. Zobo ta auna kwano biyu da aya kwano biyu da citta da kanunfari na 500. Wajen masu fruit ta nufa suka hadamata kwakwa Dabino cocumber kankana Kashu Abarba kana tayi gida zuciyarta fess. Koda Aymah taganta da kayan itama dariya tayi tace . miza'ayi da wannan Deedee karki manta G.R.A muke batasu ake ba kar abinki Yayi kwantai. Cikin bama kai kwarin gwiwa Dede tace in sha Allah bazaiba na fadamiki tsaya dai kiga ta karasa tan aje mayafi ta ɗauki Ayarta ta surfa ta wanke sosai ta cire tsakuwar kana ta samata ruwa ta aje ta hau tafasa zobon dayaji citta da kanunfari da bawon abarbar data saya. Cocumber da kankana da Kashu da sauran Abarba tasa Aymah ta mata blending nasu. Zoɓon na tafasa ta tace tare da juye kayan fruit din ciki ta ɗauki sugar da foster dinta mai kwakwa da gwaiba ta juye aciki wani ni'imtaccen kamshi ya fara tashi kota ina. Aymah ta ɗibi wani a roba tace" tun kamin yayi Sanyi yawuna ya tsinke tasa a fridge. Deedee tace ja'ira kyama sake fada ta dauki markadan Ayarta da kwakwa da dabino ne kawai aciki sai citta da kanunfari tace . Natafi kai markaɗe. Aymah tace kawo nakaimaki tace A'a bashi dai na fita. Da kwatance ta gane wajen mai markaɗan nan tayi tsaye ta wanke injin din tass da kusan rabin jarka ruwa. Mai markadan natamata dumin ta karar da ruwan taa. Shuru Deedee tayi tana kissima yanda zataimata . Ana'mata fashi ukku tace. Baiba saida akayi biyar kana ta dauki goma ta bata tace ungo kyasai ruwan wannan kuma darin markade ne gobe in zandawo nazo da ruwana kazamar banza. Takaici ya kashe matar ta bita da kallo Deedee ta mata murmushi tace bye inji Anna (Arna) Koda taje gida ƙanƙara tasamu takai biyar ta dinga fasawa tana juyewa kamim ta samu suyi ta tace ta xuba shiga tare da kulla abinta tsaf ga leda da duk ta saya tashiga sawa a fridge. Karfe biyar na yamma komi yayi sanyi sosai. Tayi wanka, ta shirya Tare da fesa turare ta dauki karamin boket ta zuba komi goma goma yace aymah xanje in dawo. Ido Aymah ta zaro tace badai tallaba. Aa haba sadaka zanyi ina zuwa. Fita tayi ta fara shiga makwaftan dake kusa dasu duk in an'gaisa zatayi kwatancen gidan da take suyi barkwanci da masu gidan kamin tace to sana'a nike gashi a a ɗan Ɗana kamin azo asaya. Duk kau gidan data ba sai sunsha gabanta suna santi wasu subata kudi da niyyar zasu bita su kara saye wasu kuma suce zasuzo saye ahaka dai tashiga gida goma cur kamin tadawo gidan su Yara biye da ita da zasu karɓa nan ta shiga zubama kowa abinda yake so. Karfe shidda yayi sallama ya shigo gidan hannusa rike da leda. Wani milk din yadine jikin sa mai saukin kudi an'mai ɗinki zamani ɗan madaidaici yamasa masifar kyau. madaidaiciyar sumar sa tasha gyara sai kamshi yake. Sannu da zuwa sukaimai Aymah ta tashi ta kwasomai kunun Aya da zobon Deedee ta kawo da jallop din taliya da suka dafa. Allah yasakamiki da Aljannah yace yafara Bissimillah yanaci suna dan fira da Deedee dan Aymah kau hankalinta naga wayar Adnan. Suna zaune akaita shigowa sayen zobo kan kace mi abu yayi kasa saida Deedee tace babu kana aka kyalesu tace kai kaji gantalallu an'saba shan lemu mai karas yau anji nawa ana so azuke man koni banshaba. Dariya yayi yace wannan ne kike Sayarwar ? Eh mana yayi dadi Ko. Sai magana yaga Aymah tayi maza ta mike tare da daukar Hijjob din Deedee sauri sauri tace ina zuwa Kaka ta fita da sauri... Kallon juna sukai Kamin Deedee tace "lfy kuwa? to ina zata waye ta sani . Kamar tunamai tayi da sauri ya mike ya mara mata Baya. Yana fita get din ya hango wani mai Machine ya juya baya ita kuma tayo ciki tana ɓoye abu. Waye shi yace idon shi na sauyawa zuciyar sa namai mugun zafi kamar zata fasa kirji ta fito. ❤️MATAR OGA NA ❤️ MALLAKI UMMY AYSHA LITTAFINAN NA KUDI NE KIBIYA KI KARANTA CIKIN AMINCI HAJIYA ACCOUNT NUMBER 9064260199 AMINA DAHIRU OPAY BANK SHEDAR BIYANKI TA WANNAN LAYIN 07038423451 Page 14 "Kallon shi tayi na lokaci kamin ta ɗaure fuska gam babu alamar fara'a ko wani wasa a tattare da ita ta nemi raɓashi zata wuce batare data bashi Amsa tambayar sa ba. Aymah maganafa Nike miki Jameel yace yana bin bayanta. Juyowa tayi itama idonta sunyi jawur tace. Kaga Jameel bai'dace kanamun haka ba dan kaga na baka fuska,Kana da Babban matsayi a Rayuwata kaida iyalinka amma wannan bashine zaisa nabaka fuska kana tuhumata kamar yar cikin kaba,karka manta a shekarun da nike dashi zan iya tantance gyara zan kuma iya tantance b'arna,karka matsama Rayuwarka da tuhumata akan Duk abinda kaga nayi,kazuba ido kayi kallo,kana karkacika matsaman da son jin abinda bani na buɗe baki na fadama ba,in har mukatafi akan haka sai kafi kowa jin dadin zama dani ina fatan ka fahimceni ta karasa tana juyawa tayi tafiyar ta . Jameel kau da kallo yabita. kallo mai cike da mamaki da maɗaukakin tashin Hankali. Yanzu har akwai abinda zai iya zama sirrinta wanda bazata fadamaiba,shine take kallo take fadama wannan bakar magana akan kawai yanaso karemata mutunci! Aiko saiya gwadamata namijin duniyane shi, kana shekarun shi bazai zama Hujjar da zata iya rainshi ba. Wannan dalilin ya ɓatamai rai sosai ko sallama bayyi da DeeDee ba yayi tafiyar shi gida ranshi na suya. Aymah kau tana shiga ta Haura sama kamin ta dawo kasa ta cire Hijjob ta aje. DeeDee ta bita da ido ganin ba walwala fuskarta sai batacemata komaiba illah ruwa datace taje tasha. Ruwan kau ta ɗauka tasha sosai kamin ta ajiye tayi sama da kanta ta fara nazari. "Son Jameel yamata shigar bazata A zuciyar ta bayan tasanya makullin kiyayyar Ɗa namiji ta rufe, Amma Dole soyayyar da takemai tasa ta karfin tsiya ta bude ta bashi babban matsayi a zuciyarta. Ita kanta har mamaki take yanda lokaci ɗaya son yaro ƙarami yayi ma zuciyarta shigar farmaki haka cikin sauki. Tana da burin Alkhairi wa Jameel da Family nasa amma kuma lokaci baiba da zata bayyana amatsayi hasken rayuwar sa. Tana kyautata mishi zaton Alkhairi amma kuma bazata bashi damar Sanin abinda batai niyya ba ayanzu. Cikin rauni tace'' Am so sorry My Jameel karkayi Fushi kaji. . Jameel kau kamin ya isa gida wani zazzafan zazzaɓi ya saukar mai dan shi halittar shi muddum aka ɓatamai rai ko bakar magana sai ya kwanta ciwo tamkar mace. Da sallama yashiga gidan nasu yana Layi. Inna su ta kamashi tana fadin "Kai lfy?. Kaina ke ciwo yace dakyal yana sauke numfashi. Sannu tamai tare da rakashi daki ta kira kabeer akan yaje ya taimakamasa ya cire rigar. Kamin ma ya shiga ya iske ya cire kayan daga shi sai vest da wando yayi kwance ya lumshe ido. Ganin hakan yasa Kabeer din fita dan bashi waje yayi bccin sa. Yana ganin fitar sa ya gyara kwanciyar sa kanshi na kallon kwanon ɗakin. Wasu hawaye masu masifar zafi suka zubomai. Ya Yadda son Aymah A jinin shi yake. Ya yarda da kaunar ta aka halicce shi,Baitaɓa tinanin soyayya A rayuwar sa ba. Yana ganin ɓata lokacine da shirme,amma yau ɗaya Ta ɓatamasa rai akan wani gantalallan tsamurmurin saurayin da tayi wanda ko yayi rantsuwa bazai kaffaraba babu abinda zai kaishi. Shine Dan'yayi kishinta zatamai faɗa,koko tana ganin dan yayi zama kalkashin su bai cancanci ya tsaurara tsaronshi akanta ba bayan amanar shi yake ganinta ahalin yanzu Tinda yana da Babban buri akanta. Cikin rawar murya ya fara magana. "Aymah ina son ki ,ina kuma matukar Kaunar ki wlh, Duk da ina tsoron bayyanamiki hakan dan nima nason bandace da keba Gaba da baya kinfi karfina,,To Amma shi so ba ruwan sa. Karkiyi amfani da girman shekarun da kika fini ki'ki bin umarnina hakan zai iya jefani tashin Hankali da bashi da magani,Dan Allah AYMAH ki fahimceni,ba nufina nayi takura wake ba,Inaso ne dai na kare maki mutuncinki,aganina ayanzu baki da dan uwan dayafini , bai'dace ace akwai abinda kike ɓoyeman ba nazama ke kinzama ni in abun Alkhairi ne zan baki goyon baya, wanda naga zai cutamiki zan nisantaki dashi haba man Aymah ya karasa haƙoran shi na haɗewa dana juna tsabar masifar zazzabi . Malam ne ya shigo yana fadin sannu jamilun Deedee ashe bakaji daɗe ba Allah yabaka Lfy ga Paracitimol na siyoma. Mikewa yayi ya karɓar yasha ya koma ya kwanta. Cikin lokaci bacci yayi gaba dashi . *Kauyen Abukur*. Tsintsiyar kwakwace Hannun Wata mata tana shara ranta ɓace ta juyo ta fallama mutumin da kan shi ke ƙasa mari. Cikin fushi tace. "Jakin inane kai akan ana bamu 5k na kula dakai shikenan saika zauna kai tamana kazanta yanzufa na gyara wajen nan sai kuma ka sake ɓatawa dan ubanla. Bance in kana da buƙata kayimana Haushi akira Malam ya kaika ba tinda baka magana,Katon banzakai ka sake ka gani yanda zanma. Kanshi ya ɗago anan nima na zaro ido ganin yanda lokaci kankane yanda halittar Adnan ta juye yayi wani masifaffan baki idon shi duk sunyi zuru zuru alamar yunwa ta faramai illah. Kai yashiga d'agawa dan ko magana baya iyayi. Kunnen shi ta rike sosai tana murɗawa tace zaka sake. Da sauri yashiga jujjuyamata kai Hawaye na sakkomai bana komiba sai na bakin ciki. Kanshi ta dungure tace Ɗan wahala kawai kimanin wata daya amma jibi yanda siffarka ta dawo kamar ta ifritu mina jinni, in sake ganin yaman kazanta wajen turken awakina yaga yanda zan yimai sabuwar kaciya ta karasa tana xaro wuka da zaro mai ido... Sosai kau ya furgita dan zaman da yayi da Ladidi ya fahimci duk abinda tace zatai mai yimai take dan batada tausayi balle imani ko kaɗan a ranta. Aranshi kau Ya ɗauki Alwashin yanda zai samu kakkafar wukar da zayyi mitsi mitsi da naman jikinta Duk ranar daya ganshi tsaye da kafarsa. Hmm akwai daba ,Dole ya haɗa kogo guda na jinin makiyansa na fili dana ɓoye.. Washe gari. Aymah ce waya akunnan ta cikin tashin Hankali tace" Dr ga Yan wajen aikin sanan zuwa yanzu gidan nan Duba shi ina cikin matsala ya zamuyi? Deedee ce ta dawo daga kasuwa bayan tayo sayayya kayan kununta da zoɓo. Dan Asuba fark kuɗaɗan mutane sukazo hannuta tace. Lafiya kike Safa da marwa Aymah?. Hawaye ta sharce tace Deedee " Mutanan wajen aikin sune zasuzo duba shi gashi nacemasu yana gida yanzu haka suna hanya na kira Dr yace bari yazo. Tsaki Deedee tayi tace dallah nasama wani abune. "Kice basai yazo nan ba yasanya a dakko Adnan din inda aka kaishi akawo nan. maza azo da wayan nan mazajen da suka kaishi suma. Ihu Aymah ta fasa tana rungume Deedee da sumbatar goshinta kamin ta ɗauki waya ta kira Dr ta shedamai. Shima rikicewar da Yayi baisa wannan tinanin yazomai ba saida ta faɗamai. Cikin farin ciki ya juya akalar motar sa kuwa zuwa gidan bulo din daya dakko matasan. Ganin motarsa yasa suka taso suna ihu. Bai tsaya komi ba yace su shiga kawai. Kai tsaye suk faɗa ya fara kwasar gudu kamar zasu tashi sama. Cikin lokaci suka isa kauyen . Inda yake suka isa suka iske ba'a dade damai wanka ba dan ya tika kashin safe. Basu tsaya komiba yace su kwaso shi aka sanya mota yana ta harara Su. Bayan sun shigo Cikin gari suka kaishi akai mai Aski tass aka gyara mai fuska kana sukayo gida. Umarni ya basu akan su sake mai wanka. Wanka sukamai mai kyau . Deedee tace su samai Harda malum malum saiga Adnan kamar ƙadangare cikin Babba riga duk yayi wani iri. Shinkafa da miya da Nama Deedee ta zubo ta aje kusa dashi sai zaro ido yake. Murmushi Deedee tayi tace Noo inji turawa wannan duk cikin basajane irin wadda kake ma mutane. Hon suka fara ji kamar za'a fasa gidan ashigi hakan yasanya Deedee aguje matsawa kusa dashi ta fara bashi abincin yanaci da sauri sauri. Matasan nan suka fita suka budemasu get din tare da zama cen wajen, Yayin da Dr ya kara gyara zaman glass din sa da abin aune aunen dake sargafe wuyan sa . Aymah ce cikin shiga ta kamala Hijjob har kasa ta fita ta masu jagora harda manyan shi suka shigo palon da ko kujeru Babu. Wulcum shanaye inji Deedee tana murmushi. Ɗaya daga cikin su ne yayi dariya da alama yajita yace Mama shanaye kuma. Tace to ai naji tana ta cemaku wulcum sir nikuma ai ƙara inyi jimla karwani yaji zafin bancemai ba . Sannu ku dai mala'ikun Duniya ga Abokin kunan Bakaken aljannu sun shanyemai Dukkan gaɓɓai yanzu haka bamu da komi agidan duk ta sayar wajen neman masa magani... ❤️ MATAR OGA NA ❤️ Mallaki Ummy Aysha Domin mallaka naki ki biya kudin ki ta account Number nah kamar haka 9064260199 Amina dahiru OPAY BANK saiki turo shedar biyan ki ta Whatsapp number nah 07038423451 Page 15 "Wani da ya hakimce tsaye Saboda rashin mazauni da alama ogan su ne ya kalli Dede ya gaidata cikin hausar shi data ke zau ta sakota wa yace "Mama ya mai jiki. Deedee ta karkace saiga hawaye tace" Kabari kawai Yallabai abun babu sauki ciwon anne (Arne). Lami lafiya fa yazo daga wajen aiki nima nazo ganin yar kanwata wato matar sa. Yaji anata dukan kofa kason soja da fusata ya fita yaga wata mata tace ya sammata abinci batada abinda zataci. Maimakon ya bata hakuri Aa saiya hau tsulamata mari dai yanda Wani makwabcin su ke faɗaman dayake yana wajen Abun ya faru. Tom yana cikin dukan natane ta ɓacce shima ya faɗi nan Yana Rawar Banjo . Haka dai Aka kawomana shi nan ciki muna kuka da tinanin ko pamalise ce Inji yan boko wato dai shanyewar Ɓaran jiki ya samai. Wannan likitan shine nan Babba Asibiti yake aiki wato Asibitin kwarari . Duk aune aune dai da Akai basu nunamana komi ba yadaice afitar dashi waje. Yanzu haka yau kwanan mu biyu da dawowa dan gajiya sukayi suka koromu ko silifas bamu saba suka furgaɗomu. Gashi ko magana Bayayi ma yanzu gabaki ɗaya kwara da Yana Haniniya irin Ta Doki,To yanzu ko Haniniyar sauro Bayyi hakadai Yake tamkar butum butumi na India. Tom Yanzu dai sana'a na fara da zansamu murafawa kai Asiri aita nema masa Magani kaga sheda cen yanzu nadawo kasuwa Ah toh maula zanyi kwara inyi da karfina.. Dukkan su saida tausayin Dattijuwar ya tsargasu Dan sun hango mugun alhini a fuskarta gata da shiga rai. Adnan kau soi rarraba ido yake yanajin kafurar karya da Wacce baison ko wace ba take keto mai. Ya rabbi ka budeman koda bakina ne in karyata tsohuwar nan yace aranshi yanajin kamar ya fashe da kuka,Shida ko Chemis basu kaishiba amma Ance yaje kasar waje Yah Allah. Ɗaya daga cikin sune ya kallai yace "Kuma kamar yanason yace wani abu Mama. Deedee data dakko kayan sana'a ta tace" Yo ai haka yake wata rana ma gani zakai Yana zillo Kamar tsohuwar motar dataci Cikusoba. To dai Ina ganin Aljanar ce kemai Cakulkulo.. Gashi fa Nan gani yake duk kun'mai tsaye kamar masu gadin jahannama yaganku Cikin kaya masu Ruwan ganye. Yanzu bala'in tsoron mutane yake balle ku da zai ganku da yawa. Kuma ina laifin ku shigo da dai-dai amma kamar zaku Rakiyar kansilan kauye ku shigo daki duka sai kace an'tadaku daga Asambali. Dadama daga cikin su dariya suka hauyi dan akwai hausawa Sosai wayan da Basajin Hausar kaɗan ne. Nan dai sukaita Alhini suna kuma jerama Dr tambaya yana basu amsa cikin natsuwa. Babban ogan sune yace da DeeDee" Mama ko kina ganin mu maidashi Bariki cen kalkashin kulawar mu.?. Haɓa ta rike zatai magana Adnan ya zabura yana gur'nani. Deedee ta taɓa hannu tace "Alhamdulillah! Da da bakina nace wani abu saiku karyata to kungani da mazajen idanun ku. Som Som Aljannun Basuson matsawa daga ko ina, Sunfison zaman nan din dai kamar kabari . Ina mai tabbatar maku da cewa kuka kaishi cen saiya ida haukacemaku baki daya Ƙarshe ma ya gudu. Abarshi nan inta kula dashi ainima d'ana yake balle ni daban taɓa haihuwaba sai najisu kamar sun Ketani sun kutso ta Jiki Na. Aymah ta danyi murmushi lallai ta yarda duk wanda yaja da Deedee ruwa yake tsullugudum,Yau da Babu ita da Batason ya zatayi.ba .. Addu'a suka hau jeramai ogan nasu yace yanzu dai zamu tafi zamu iya barmaki masu kula dashi ko mutum biyar haka,irin wannan ciwon wahala garai dole saida majiya ƙarfi. Hawaye ta share tace" Kai ina! Ka ganni nan Arayuwata ina tausayin yaran da basa gaban iyayensu da iyalin su Saboda nayi Maraici banji Daɗin saba .. Ga matasanan bakin get dake nan kusa damu sune muke neman Alfarma suna kulamana dashi gakuma ita matar tashi Da take Maharramasa.. Indai taimakon zakumana kwara ku dinga sallamar su kun'rageman nawie ,su kuma wayan nan abarsu Su koma ga iyalan su Lami Lafiya.. Dukkan su am'sawa sukai Cikin gamsuwa. Dayawa daga cikin su kuma sunkara sonta dan kowa ya farajin faduwar gaban barin shi da za'ayi jinyar mai laluri irin ta Adnan. Nan fa zaratan maza suka buɗe bakin Aljihu suka fara fiddo kudi sunawa Deedee Alkhairi tana kauda kai da fadin kai duk ku kwashe abunku ni kulawarma da kukai da jikana kawai ta wadatar. Hakuri suka shiga bata kamin su mike ogan su yace Mama zamu dauki Nawin ku na tsawon lokacin da zai warke in sha Allah. Duk wata zamu baki 250k ina ganin zata isheki kiyi manege. Yanzu ga motar kayan Abinci nan zansa akawomaki Allah yaba shi lfy sukuma masu kulawar dahi Ace dasu zamu basu 50k duk wata Allah yabiyaku da Aljannah. Ameen ta amsa tana murmushi da samasu Albarka. Harya fara tafiya ya dawo ga Aymah ya kara kallonta kallo na tsanaki kamin yace "banji ɗuriyar yaran nashi ba? Dam gaban Deedee ya faɗi dana aymah da sauri Kuma DeeDee tace'' Deedee tace ai kason su biyune ita waccen ta nemi saki tin zuwan farko da tayi yaran kuma sunyi hankali suna wajen dangin Uwar tasu sun ruke kayan su. Cikin gamsuwa da kalamanta ya daga kafaɗa tare da fadin" Taiwa kanta kukuma Allah yabaku ladar jinya. Ameen Deedee tace tana masu Rakiya suka shishiga suka dauki hanya tana rakasu da Addu'a. *** Jameel kau da Asuba ya tashi lfy klau jikin ya sauka amma fuskar shi babu walwala. Kamar yanda yasaba shiri yayi yama iyayen:sa bankwana ya fito da kudin da jiya baiba su Aymah ba. Ya dauki hanyar Gidan su kenan aka mai waya motar ya cika dole ya tafi ya dauki hanya zuciya ba dadi. Deedee kam tana shiga ciki ta Ɗanɗara guda tace Adnanu kagani ko?. Kai kayi nufin Alkhairi wa zuciyar ka kaga in komi bai warwarema ba Dan Butar ubanka. Yanzu gashi gabanka Alkhairin Allah ya saukar muna shashasha mahaukaci, Allah kadai yason abinda ka shuka shiyasa ya nannaɗeka Haka Kamar fanke waje guda,Ka tuba kaga in Haske bai Ratsa Rayuwar kaba. Abincin ta turamai gaban shi tana harar shi kamin tace da Aymah tisamun kudin Nan. Ta kalli Dr tace wai nikam Ina Jamilu ne Tinjiya ko Bankwana? Yace tindazu nike kiranshi baya ɗauka Allah yasa dai lfy. Deedee tace tom Ameen dai. Zai tashi ya tafi ta tsaidashi da faɗin ya raba kudin ya ɗauka.. Dariya yayi ya A'a Deedee in banbaki ba bana karɓa ba baccin kokorin Naki ne. Wannan Hakkin kine wallahi daɗi sukaji suka baki babu kudin kowa anan . Dariya tayi tace hakane likita wai kai ya sunan ka ne. Murmushi yayi yace tsawon wata hudu sai yau ake tambaya to Dr Abba sunana. Dariya tayi tace'' To Abba mungode da dawainiya Allah ya sakamaka da Alkhairi ya biya dukkan bukata na Alkhairi. Allah kasanya kagama tsire mazaunan kowa lfy, Allah kasa kar hannun ka ya karkace ka caki wani inda cutar shan inna zata kamshi. Dariya sosai ya hauyi AYMAH na tayashi daidai lokacin da Jameel ya turo kofar da sallama yashigo . Ƙasa tsayawa sukai da dariya yayin da kallo daya yamasu ya ɗauke kai ya zauna kusa da Deedee ya gaidata. Amsawa tayi tana fadin" lfy kakecin magani muna cikin hali na farin Ciki. Ɗan yake yayi yace ba komi dama nadawone nace bari inkawomaki kudin cefane xan koma. Aymha ce ta dakata da dariya tana binshi da ido kamin tace'' Ya aiki. Kamar ya kyaleta kuma ya juya yace Alhamdulillah tare da mikewa yaba Dr hannu yace zai wuce. Sosai taji ba daɗi tason kuma abinda tamai ne yasa shi kasa sakin jiki dasu yau Allah dai yasa ba wani abu ya zarga game da itaba. Shikam Dr Abbah mikewa yayi yakama hannun Jameel din suka fito Abakin Get sukaga Su Sadam Yaran da suke kula da Adnan. Nan ya faɗamasu bukatar zaman da akeso suyi da shi dan bazasu sake maidasu Kauye ba. amma su maido shi Dakin Baki . Godiya da murna suka shigayi Kamin suce zasuje su dawo. Abincin da ka kawo masu yace su fara shiga dashi ciki kamin su wuce. To sukace suka fara Jilarshi shikuma suka ƙarasa bakin motar Jameel din suka tsaya ya dan kama kyauran motar Jameel din kamin ya shiga zayyano mai abinda ya faru da faɗin. kai bakama lura dashiba naga Yamafara bacci.. Murmshi Jameel din yayi yace Som idona baigan shiba. Lamarin Didi sai Addu'a .Allah dai yasakamaka kaima da mafificin Alkhairi muna godiya. Ameen yace tare da sake rike hannun Jameel din yace. Ya maganar soyayyar ka da Aymah kana sonta ko ka janye danni banga wani abu ba?. Ɗan murmushi Jameel din yayi da yafi kuka ciwo yace" Tom mundai barwa Allah zaɓi kawai. Amma ina ganin kamar nike haukan banza na ita som batani take ba hasalima daukar yaronta takeman ka kauga ba'a aure haka kwara in kyaleta . Murmushin Dr yayi yace lallai kai sabon shigane a soyayya. Ba'aima soyayya gadara, ba'amata fushi, komi sai sa sai da ake binsa saikaga an'cimma nasara. Karka manta isa da gadara da banzatarwa yakai Aymah da mijinta wannan matsayin da suke Jameel. Kaikuma yanzu kobakace AYMAH i love you ba akwai hanyoyi da dama da zaka isar da sakon ka, kana dole ka iya kawar da ido akan duk kan abinda zakagani.. Na maganar nata bakomi saika magantaba karkasanya tayimana jimla akan duk haka muke dan Allah kabi komi a sannu kaji. In kana nan aka kirata so goma ka kawar da idonga Jameel in dai Allah yasa rabonkace to ba makawa Sai tazama taka. Kana yanzu kai ai abinda zaka rufama kankan Asiri ya dace ka samu ni wannan jigilar motar ma fa Banason ta. Kabari asamarmaka aikin sumogal kaga yanda cikin lokaci Abubuwa zasu zama tarihi ,Kayi saurin Gina kanka Ka kwashe matar ka. Sosai yayi murmushi yanajin nawin zuciyar sa na sauke wa yace. wallahi sai yanzu naji natsuwa amma da wani kunci ke kawoma zuciyata ziyara. inajin nazama wani kaskantacce wallahi ngd matuka da shawararvka gareni kuma kamar yanda kace zangoyamata baya akan duk abinda tasa gaba daga yau Insha Allah,Nason wannan ma kadai zaisa Tabani matsayi Babba A zuciyar Ta. . Hannu Dr ya bashi suka kashe tare da daukar motocinsu ko wane ya doshi aikin gaban shi. Deedee kau da aka kilga kudin data samu 600k ne cif da cif. Harda yar rawarta ta taka tana sake godema Allah da Ni'ima dayamata. Anan ta kalli Adnan daya tashi tace'' zan dungama sadaka shinkafa saboda abinda nasamu ta sanadinka kagama cin gari kaji ko,Zansa adinga kaima cen dakin da zasu mai daka... Shuru yamata yanabinta da kallo kasa kasa Mikewa tayi tace" Aymah gyaraman ayar nan ina zuwa bani awa daya Inje in dawo suma su Sadam din yanzu zasu zo su debe maki shi. Tom tace tana dariya da tashi tashiga aikinta itakuma Deedee ta fita. Kai tsaye Kasuwa ta nufa ta sai Frizer lg guda ɗaya mai kyau na 2700k. Da katon inji mai kyau dayakai Dubu 130k aka samata a mota tayo gida. Ana shigomata dasu Aymah ta rike baki da rangada guda tana faɗin. kaji tsohuwar mai ran karfe, bata dogara ga kowaba Allah Ya kamamiki Dede nah . Deedee ta buda hannu tace "Ameen,fada ki sake faɗa ummu nah yar aljannah allah ya kara kawo haske a rayuwar ki kinji. Ameen AYMAH ta amsa kamin ta shiga Buɗa Kwalin Fridge ɗin.. Wayan da suka kawomata kau Duk saida suka hadamata komi kana suka tafi. Deedee kam sake fita tayi wajen wannan mai Markadan suka gaisa ta bada markade. Matar nata kumburi Deedee tabata 500 tace ke karba yau abinda zanbaki kenan kudin markade . Ihu matar tayi na murna kamin suka shiga fira da kanta ta dinga tisama Deedee har saida taga yayi kamar na jiya kana ta bata. Deedee tace Almajirai nikeso majiya karfi ba yan yaraba kana masu tsafta ba kazamaiba inaso mudinga kasuwa dasu... Da sauri tace. Takwana gidan sauki tana kwalama almajirin dake ta jidomata ruwa kira tace ina. Ibrahim da Sani da naseer dake neman aiki kace gasu ya samu maza. Aguje ya aje jarka sai gashi kau cikin lokaci da matasan yara yan 17 aguje suka zube suna gaida su. Dede ta bisu da ido ba laifi fess suka ba alamar kazanta jikin su. Tace tom yanzu dai ku dauka muje in samaku dokoki Akan kasuwata. Da sauri suka dauka Tayi sallama da mai Markadan tayi gida... ❤️ *MATAR OGA NA*❤️ *UMMY AYSHA CE* *PAGE 16* *Koda suka isa gidan su Sadam na nan bakin get sunsa Benci sunata fita abunsu Da wasu abokan nasu da Alama majalissa zasu maida wurin . Sannu da zuwa suka mata ta amsa da masu sannu da aiki. Yawwa Kaka sukace ta shige ciki Almajiran na biye da ita. A baranda tace su tsaya kana ta samu kujera ta zauna tace tom". Da farko dai Sannuku da zuwa gidan Sanyin Haj Deedee mai Haɗa Alkhairi da warware Sharri. zanje kasuwar in Siyomaku kaya banaso naga ko kafar wando ta kece balle A kaiga tsagewar Hantsar wando Al'aura ta samu damar shan iska. Abu na biyu . Wanka!. Dole kuyi wanka kamin kuzo da safe, hakama kamin ku ɗauki tallana dan banshirya biyan kuɗin Asibitin wanda kwalara ta kama ta dalilin kayana da Mutum yasha ba. Sannan dole kuna dawowa ku aje boket din ku anan kufara wanka ga bayi nan wajen get akwai ruwa kamin ku shigoman muyi issafi . in dai Kukaiman Haka to zakuga Alkhairin da zanmaku kuma zan rikeku amana Har In mutu in sha Allah. Cikin sauri suka amsa da yimata godiya tayi murmushi tace kujira inzo. Ciki ta shiga inda ta iske Aymah ta gama maya duka zobon ta kullemata ta jera sai faman latsa wayar Adnan take da alama abu mai mahimmanci take. Ganin hakan yasa Deedee sallama da faɗin. Aymah na dawo. Da sauri ta dago kanta kamin tace" Sannu da zuwa Deedee nah ya gajiyan markaɗe?. Murmushi tayi tace haba mu agayamana gwagwarmayar rayuwa Aymah ba wata gajiya. nayi Almajirai gasunan su zasuma dinga kaiman markaɗan da Talla. Yanzu zan tace kunun inje in'dawo. Aymah ta tayata murna tare da tashi ta karɓa ta tacemata ta hadamata kamar yanda taga tayi . Deedee kam yara taja suka sake komawa kasuwa layin yan gwanjo ta samar masu masu kyau da sauki kala biyar biyar kana suka biya wajen masu injin markaɗe nan ta sai guda aka doramata a napep sukayo gidan Su jameel. Sosai Inna su taita murna da ganin Deedee dan ba karya tayi missing nata ,Tanason zuwa ta ganta amma wani dalili na hanata. Dede tace Baraka gafa aiki na hadaki Dashi banaso yanzu ahlina su sake zaman banza dan naga illar sa. Kinga mijinki na ƙoƙarin nemomaku na abinci kema tinda ba inda zaki ga inji nan na sawomaki na markaɗe ki aika makwafta ki sanar dasu kinga dai yanda muke wahalar abun markade a wannan Unguwar. Ga azumi dama yana kusantowa ba karamin Alkhairi zaki samuba in dai kin tattala,Shima Jameel yanzu abarshi ya tara nashi yayiwa kanshi Amfani.. To gashinan dai nidai kam na saimaki halak malak dan Keɗin diyata ce. Har kuka saida Inna tayi dan tana da burin ace yau ga binda zatana Ɗan sarrafawa wanda zai kawomata kudi ko dan ragema mijinta dawainiyar wani abun gashi Allah ya kawomata sirika mai kaunarta ta siyamata. Sosai tama Deedee gdy kana Deedee ta tashi tafiya ta bata 5k akan ta rike ta fita shima malam habun tabashi sukamata gdy kana taja yan Almajiranta sukayi gida sunata murna da kayan da tabasu. Wanke kayan tasa sukayi suka shanya kamin cikin Nasu suka ɗakko masu sabunta sukazo aka shiryamasu tallah suka tafi . Jameel kau cikin nishaɗi ya dawo ya biya ya karɓin sabon dinki daya bada amasa na wani maroum ɗin Yadi mai kyau da saukin kuɗi.. Bayan ya dawo gida kamar yanda suka saba ya zuba uban wanka cikin wannan yadin dayamasa masifar kyau kamin ya dakko turare ya fess ya gyara sumar shi ya fito yamasu sallama yatafi . Sai da yabiya Bakin layi ya masu kunshin Tsire mai zafi babba kamin ya wuce gidan . A waje suka gaisa dasu sadam kamin yayi ciki yana tako dai-dai . Kwance take tana fuskanta kofa Wasu fitinannun kananun kaya ne jikinta da suka mata mugun kyau. Wani Black Wando ne jikin ta bai kai kasa ba yafi kuma karfin 3quater. Sai white din shirt data ɓalle maɓallin saman guda biyu kana Hango bakar brah ɗinta. Daga kasa kuma Ta ɗan ɗaure rigar sai yabada wani tsari mai kyau. gashinta zube agadan baya sai kyalli yake batasa hulaba sai Black bandana da tasanya ko bant bata saba Tana ta latsa wayar Adnan Yayin da Deedee ke gefenta tana kilga kuɗin da aka kawomata ta ware ribar ta ta aje ,ta warema Almajiran nata masu hazaka nasu ta aje , sauran kuma na sayayya gobe ne dan da alama Allah yasama abin Albarka ko daya basu maido ba ga gida anata nema ga majalissa dasu sadam suka fara haɗawa sai shigowa ake saye dole gobe ta ƙara mudu in sha Allah. Da sallama ya turo kofar yashigo kanshi tsaye dan yason dukkan su suna cikin kyakyawan yanayi sai dai kash an samu akasi dan Zuciyar AYMAH baitaɓa bata zuwanshi ba duba da Yanda yamata da safe . Cak ya tsaya wuri guda kamar an dasa shi yayin da kanshi yayi kasa zuciyarsa na bala'in tsalle,Baitaɓa ganinta a wannan yanayin ba sai so ɗaya kuma shima bai ƙure ganinta ba saɓanin yau da ita ke fuskantar kofar tana kwance akan carpet ranar kau duke take ƙasan kujera tana kuka. Deedee ce ta dago da sauri tana binshi da kallo tace" Sannu da zuwa Jamalun Deedee lfy ka tokare nan ko ka haɗu da sharrin Baseee mai tsiro ne? Karamin bakin shi ya turo still bai dagoba sai wasa daya kama da hannu shi yana Taune lips da kyal ya iya cewa " ina wuni . Aymah kau data kalle shi murmushi Tayi kamin ta tsareshi da ido sai kuma tayi karama dariya tana tashi zaune ta gyara zaman rigarta kullin datama ta kwance ta gyara wuyan daya bude batare da saninta ba kana tace " Bissimillah. Duk tunanin shi Hijjob ta sanya shiyasa tace mai haka da sauri kau ya dago idon shi yana watsamata harara kuma cak ya tsaya da ganin shi akan baiwar ƙirar zatin da Allah yamata. Duk iya son Ya kawar da kanshi akanta kasawa yayi saima wani masifaffan yanayi daya tsinci kanshi aciki... A'Hankali ya hau matsawa inda suke idonshi still akanta baya ko kyaftawa.. Wannan kallo ya tadamata hankali dan batai tinanin hakaba. cikin lokaci ta kasa natsuwa da sukuni da suri ta mike dan haurawa ta canza kaya. Saidai kash saurinta da kuma gushewar Hankalin da yayi yasa bata an'kareba sukayi mugun Karo gabaki daya ta faɗa jikin shi. Yayin da shikuma ya mata wani mugun cafka ya riketa gam zuciyar sa na daka tsalle Yanajin inama inama😜 . Deedee kam ido ta shiga kyaftawa kamin da rarrafe ta shafasu ta shige kiching tana fadin. " Yan banza wannan ai sai kuka tunoman da Malamina Allah sarki kamar banci Uwar sabadaba ni Saude,Dafa tsabar gayu haka nike zamana gaban malam dagani sai ɗan Kanfai da vest in baza murjanai da jigida ina yawo ɗan tsakar gidan mu in maida idon bawan Allah nan kamar Danjar besfa yayita bina da kallo Yana mazurai. Hahaha ta sheke da dariya da faɗin Allah ya jikan ka Malam nayi kewar ka. Da Allah yama tsawon kwana da Har yanzu ina nan ina bazama gayu da kasheka da Kallo na mai tada hankalin Lafiyayyen Dattijo . Sai kuma ta saki fari kamin ta shiga buga kwano kasa tana fadin. " kwara kuji ƙara ku dawo hayyacinku kar Allah ya kamani munafukan banza duk kun gama ɓoye ɓoyen an faɗamaku dama so Mahaukaci ne. Buga kwanan Deedee kam yayi tatsiri dan gabaki daya sun shagala da duniyar da suke da saurin su suka mike Jameel kau jin jiri zai kada shi cikin wani mugun yanayi ya cafko hannun Aymah data nemi haurawa sama kana ya rungumeta tsam a jikinshi yana sauke numfashi zuciyar shi na bada sautin fat fat fat da karfi. Ayyah sorry! tace tana shafa kwantaccen gashin kanshi kamin ta shiga neman kwace kanta amma yaro yamata rikon manya. Cikin wata murya mai sanyi sosai na mai neman taimako yace. " Kibani dama dan Allah,kibani chance na shiga rayuwar ki,Ki budeman kofofin yarda da Aminci ,Kibama zuciya da gangar jiki damar cika muradinsu,Karki duba rashin Cancanta ko Yarinta a'a tausayi da taimako zakiwa aiki ,Ina so.... Mugun tsalle zuciyarta ta dingayi mussamman da ya datse kalman shi ta karshe taso jin furuncin sa kodan samun sauƙin abinda ke dawainiya da ita . Jameel kau Jajayen idonshi ya ɗago yana cije lips kamin ya saketa ya tallabo haɓarta ya jefa kwayoyin idonsa cikin nata yace".. Kiyimin yafiya akan abinda y@ faru ,Bazan sakeba na miki Alkawari,Kar wannan yasakimun fassara ba ɗabi'ana bane takura kowa balle ke da kika zama tamkar Amanata. Ummu ina bayanki akan duk abinda kika sama gaba in dai bai Saɓama Shari'a ba,Duk abinda kikason mafita ne a rayuwarki ki tunkare shi kai tsaye, in kuma kina neman agaji kimun magana zan tsayamiki da karfina in sha Allah. Abu na karshe kibani dama dan Allah kamar yanda nace miki na shiga Rayuwar ki kai tsaye ma'ana Inaso Babbar akala mai girma tashiga tsakanin mu. "Kunya sosai ta kamata sai taji ta duk wani iri tabbas Ba karya ta girmi Jameel nesa ba kusaba amma kuma a sigar jiki wani zai iyacewa shine Babba mussamman Yanzu da girman keta sake masa kutse ya fita tsawo sosai gashi da faffaɗan Jiki dan baya cikin layin Ramammun maza Dan ita kanta ta sheda haka dan wani masifaffan daɗi taji lokacin daya sakata jikinshi ya Rungume wannan kaɗai ya nunamata in'garman namiji ne Babu inda bazai leka ba. Ido ya zubamata ganin tashiga duniyar tinani. A'Hankali ya huramata iskar bakinshi mai kamshin Tomtom Yana langwaɓe kai kalar tausayi Yace "Ya dai Ummu nah. Ɗan farr tayi da ido kamin Cikin sauri tace" mene ma kacemun?. Ido ya ɗan juya yana shafa kanshi kamin ya zubamata ido yace. *Kina sona* Wow... Wani mugun dirar mikiya maganar tashi tamata dan ko a mafalki batayi tinanin Jin wannan tsadaddar kalma a bakin shi ba dan yanzu. Dan alayin maza masu mugun zurfin ciki tasa Jameel mussamman akan abinda suke so tanaganin kamar bazai taɓa iya furtawa da wuri haka ba. Ya tsunshi yasa ya d'an murzasu akan fuskar ta kamin Yace" kinji!.kodai na miki yaro ne..kafaɗa ya ɗaga yana taɓe baki yana wani lumshe ido cikin gaskiya da Gaskiya yace" Aymah nifa ba yaro bane wallahi kinji na rantse miki. Ido ta zaro kunya sosai ta kamata aguje tayi sama yabita da kallo yana sakin dariya da shafa kai yace" kinbani kam,Nafara gajiya da ɓoyemiki dole nayi saurin ɗaukeki dan in'dinga ganinki cikin wannan shigar mai kwantar min da Hankali. Deedee ce ta kwalamai kwano aka tace" munafuki ashe dama kana magana haka shine ni in zamuyi magana kaitacin magani kana budeman Hanci. Cikin nishaɗi yace" to ke auranki zanyi da zan buɗe baki naitai miki kalami,Dan Allah Deedee nah kitayani yaki akan soyayyarta wallahi yanzu ina sonta , In dai ta shirya zama dani a haka Zanyi iya bakin kokarina naga na tsayama rayuwarta bance saina mata komiba amma nayi alkawarin bazatayi kuka ba, Dan Allah Deedee nah kicemata ta soni kinji Murmushi tayi tace "karka damu ka barwa Allah, a halin da muke ciki yanzu bazan turasasa Aymah son kaba Jameel. in naimata haka kamar ban kyautatamata ba,Saidai kai namiji ne dole kabi dukkan hanyar da kason zata fisheka ta kawo kanta da kanta,Ai bazai yiyu daga cewa kana sonta ba ta amsa kabari tayi shawara,Balle ma ni inaji ajikina tana sonka, yo wazaiki jinin Deedee ai sai wanda bai samu ba,Kadai ganni da tsufana amma yau dattijon da zai haɗaman injin markaɗe sauran kaɗan ya faɗamai ga kafa yo ai mune kyau wlh. Dariya yayi kamin ya rungumeta yace "ina sonki yar kyakyawar Kakata gagara ba dau an'buga dake an barki.. Faɗa ka sake faɗa Jameelun Deedee tace tana bashi hannu suka kashe dukkan su cikin farin ciki. Naman daya wullar ya dakko ya bata yace Anyi kiran sallah yau na dawo da wuri zanje sallah na dawo mikika dafa? Tace Taliyace na silala maza ka dawo kaci ka mayar da fura akai. Fita yayi yana kallon sama ko Aymah zata sakko amma ina bata fito ba. Saida ya biya Toilet din waje ya tsarkake kanshi da wanke dogon wandon sa kamin ya daura Alwallah yayi masallaci. Aymah kau tinda tayi sama ta fara daka tsalle na murna tanajin wani dadi tanajin rabin matsalarta ta kau a daidai wannan lokacin. Cikin farin ciki tace na Amince my jameel amma inajin kunyar faɗama gaskiya. Wanka tashiga tayi ta canza kaya da pad kamin ta fito waya makale a kunnan ta. Sosai taji tanajin kunyar Deedee gani take kamar tason komi. Deedee kam wayan cewa tayi da faɗin Aymah ga namanki nan keda Jameel. Murmushi tayi tace mungode zai dawo ne? Kai kawao Deedee ta dagamata tana kabbara sallah. Aymah kau wayar ta dauka tashiga latsawa cikin lokaci kuma ta mike ta dauki Hijjob ta fita. Bayan sun gaisa dasu Sadam ta buɗe get ta fita dukkan su suka bita da Kallo. Bai yarda ya fitoba saida akayi Isha kamin ya fito farin ciki kwance a kan Kyakyawar fuskar shi. Daga nesa yake Hango kyakyawar fuskar ta dake jike da Hawaye. A'Hankali ya fara tahowa zuciyar sa na bugawa. inda yakejin sautin maganata kasa kasa wasu takaddu rike a hannuta tana faɗin. "Babu yafiya tsakanina dashi yamun babban tabo,Badan ina kai zuciyana nesa'ba da tabbas da kaina zan kashe shi,Badon rabbi ya bani danganaba da bazan iya haɗa makwanci dashi ba. Amma na yarda kar akai magana Court abarshi ya girbi abinda ya shuka tin anan Duniya. Mutumin da ke zaune akan Machine kanshi rufe da p-cap ya fara magana. Aymana ko kinso ko kinki hujjoji sun kammala sai na makashi court. Cikin kuka tace A'a...Nace aa dan Allah ta karasa cikin mugun kuka. Jameel kau sosai kanshi ya ɗauki zafi tabbas yason wannan mai magana , Amma ina? kuma waye shi a wajen ta? waye zasu kai court? minene akaimata miye Aymah ke ɓoye masa ya salama ya fada yana karasawa inda suka cikim sassarfa. Mai Machine din da ba'a ganin fuskar shi ya tada Machine yayi tafiyar sa tinda yaga kussantowar Jameel. Aymah!. Jameel ya fada yana kama hannuta. Da sauri ta juyo bata tsaya komiba ta fada jikinshi ta hau uban kuka... Kafaɗarta ya shiga bibbugawa kamin ya kama hannuta suka ɗan matsa gaba da gidan wajen dake da karancin haske. Akan wani Ɗan Dandamali ya zaunar da ita kamin shikuma Ya ɗora gwiwoyinsa kasa. Gabaki daya hannuwan sa ya haɗe yace dan Allah dan Annabi Kiyi Hakuri,bazan takuramiki.ba Aymah akan sai Nason mikike ɓoyemun. Amma dai inaso kiyi tawakkali, Kana duk Rintsi kalmar kisa ta daina zama bakin ki,Babu mai cuta a wannan Rayuwar ya zauna lfy. Kana babu abinda ke dawwama sai ikon Allah. Kiyi hakuri dan Allah in dai bakyaso wannan yanayin naki ya kwantar dani... Idonta dake cike da Hawaye ta dago tace Jameel minaima Adnan A Rayuwata. Mi iyayena suka tare masa. Jameel ko kason Adnan ne Ya tura Babba motar da ta latse iyayena????? ❤️ *MATAR OGA NA*❤️ *UMMY AYSHA* Page 17 ""Innalillahi wa inna ilaihi Raji'un yace yana dafe kansa da rintse idonsa sosai Hawayen tausayi dana jimami na zubomai . . Lokaci daya kuma wannan masifaffan zazzabin dakemai sallama ya fara hayayyaƙomasa gadan- gadan. Kan ta an'kare sai dai tafarajin dakuwar hakoransa kaf kaf kaf kamar zai taune halshen sa. Kallonsa tayi a tsanake ganin kamar ya fara fita hayyacinsa a razane tace. " Jameel miye?. Kanshi ya ɗago duhun wajen bai hanata ganin yanda kwallah ke rige rigen saukar masa ba, da yanda bakinsa ke ɓari. Cikin mabayyani tashin Hankali tace'' miye haka dan Allah ka tashi mutafi Jameel na hakura wallahii na barwa Allah miye haka kake kayi man magana Please. Magana yakeso yamata akan ta natsu amma bazai iyaba, "wannan masifa tayi yawa wai waye Adnan din nan ne? ina iyayen sa ne da ya zama kamar Arne som bashi da imani, iyayen matar ka zakasa a kashe?Wai miye manufarsa ne akanta. Aymah kau da sauri ta tashi tana kalle kalle dan ta samu abinda zata taimakamasa amma ina ba komi . Aguje tayi gidan su saigata dasu sadam suka kamashi aka shiga dashi nan wajen Deedee har lokacin da zazzabi jikinsa sosai sai layi yake. Sosai Hankalin Deedee ya tashi cikin kuka ta ce" wai dama baka rabu da wannan masifar ba Jameel."AYMAH wani abu akamasa ne ko wani abu ya faru dashi Jameelu ka zama kamar mace abu kadan ya kayar dakai kai jama'a. Aymah dake kallon yanda yake haɗewa waje guda ta share hawaye tace" Deedee kawai na faɗamasa ne cewa Adnan ne silar kashe iyaye na. Ido Deedee ta zaro kamin itama ta nemi wajenta zauna tace" nasani, wallahii nason za'a rina,Ai dama na fadamaku amma bantaɓa tinanin da gaske wannan matsiyacin zai iya kisan kaiba, Wai Aymah bakison abinda ya haɗasu bane Har yanzu?. Hawaye ta share tana zama kusa da jameel tace" Tukunma dai! Yanzu dai video abun ne muka gano muna kan binciken dalilin daya kawo haka ta karasa tana shafa Bakin Jameel dake karkarwa.. Deedee ma gefe ta matsa ta fara rera kuka tana jama Adnan Allah ya isa da fadin sai ta sake tashi ta nema ta kwatoma Aymah Hakkin ta.. Aymah kau ganin tsananin da jikin nasa yake yasa ta tashi cikin dauriya tanajin kanta kamar zai fashe ta shiga kiching ta debo ruwa a roba. Haurawa sama tayi ta ɗakko towel mai kyau tazo dashi gaban shi ta ɗan jika ta mikawa Deedee tace "gashi ki dan gogemasa jikin sa. Cikin kuka Deedee tace" kyaleshi dan uban sa ban gogewa,Kai shikenan da kaji abu ba'a jaje dakai sai kayi Raɓe Raɓe ka baje, To bazanma ba dan ubanka Tacigaba da kukan ta . Aymah tace Deedee wallahii ba laifinsa bane. Halittace kowa da kalar tashi. Suna da raunin zuciyane, Shiyasa kuma irinsu sunfi tausayi da iya kulawa da abinda suke so. Karkiga laifinsa alhinine yake tayani,wannan ma yakarama Jameel martaba da kuma girma a idona . Hawaye ta share tare da mikewa tace'' kyaleshi yagaji ya tashi tayi waje kai tsaye dakin Adnan ta nufa a fusace. Aymah kau ganinta ta maido kanshi cikin tausayi to taya zata iya masa abu shiba muharraminta ba? Wata zuciyar ta shedamata cewa ai tana da damar taimakon duk wanda yake da bukatar hakan kasancewar ta ma'aikaciyar lfy . Ido ta lumshe kamin ta rintse ido hannunta har rawa yake ta sa ta dan d'aga rigar sa sama. Farar vest din shi dake fara sol sai kam shi take tabi da kallo a sace. kamin itama ta dagata tana juya kai zuwa bakin kofar... Sake tsoma abun tayi ta sakeyobkan fatar tashi data kasance fara sol. Cikin mamaki tace ashe jikinshi tass tass yake har wani Yellow Yellow fatar keyi ga masifar taushi kamar mai ma fatar Dilka . Gashin dayama kirjin nasa k'awanya kadai ya isa ya burge lfyayya mace. Ido ta ɗago da Sauri ta kalleshi taga idon shi a lumshe yake amma ya daina wannan rawan sanyi. Hannunta tasa guda ta rufe idon ta kamin taci gaba da dan gogamasa yanda ya dace . Saida ta tabbatar jikin ya ɗan rage zafi kamin ta mayar masa da vest din ta sake jika abun tayi kan kyakyawar fuskarshi da yaune kawai ta taɓa kureshi da kallo Haka. Masha Allah ta faɗa abayyane tana dan gogamasa akan fuskar tashi har zuwa kan sajen sa dake kwance luff luff... Rayuwa Aymah na bala'in son Namiji me saje amma Adnan kullum fuskar shi kamar bayan fai-fai ba komi,Kanshi uwa gidauniyar sulba sol waishi soja. Sadda tagama ta kalle shi fuskar tayi fess sai sheki yake kamar wanda akama wanka. Murmushi tayi tana matsawa da Hancinta akan nashi ta dan goga nata akan Tsinin nasa tare da fadin kana da Sahihin kyau tamkar mace. "A jiyar zuciya yaje a kasalance yace . Namafi macen kyau ya faɗa yana bude idonsa da d'agamata gira guda. Ya Subhanallahi tace tana neman mikewa tsabar bala'in kunya, bata taɓa tinanin idonsa biyu ba. Karfinsa yasa ya cafko hannuta tare da mayar da ita ya zauna shima ya tashi ya zauna ya gyara zama yace " Akan mi zaki gudu bayan baki ida aikin ladar kiba? Gaskiya Allah ya biyaki ya miki Albarka. Tabbas ke din mai albarkace , jini yau ɗaya daga kin dora lallausan hannuki akan gangar jikin dake cike da rauni da cuta farat daya ciwo ya ɗauke, Ngd Allah ya sakamiki da Alkhairi ya baki tukuicin gidan Aljannah. Aymah ina mai baki hakuri da kuma sake tausar zuciyarki akan abinda ya faru. Tabbas Adnan ya zalinceki zalinci mafi muni. Saidai karki manta duk abinda zai faru dama tsare yake cikin kundun kaddara bawa. Allah shine ke kashewa ya kuma Raya saidai ɗan Adam ya zama sanadi. Adnan ya zama sanadin iyayenki tabbas wannan yayi Kuskure mafi girma wanda in kika zubamai ido muna nan zakiga D'aid'aicewar da zayyi Ya lalace ,Tun yanzuma kinfara gani dai,Gashi nan ba baki ba kafa kuma babu wanda Allah yasa ma tausayin ya taimaka masa saboda mugun Halin sa.. A shawarar da zanbaki ki tsaya iya tsayawar ki karki yarda akai maganar nan court. Kibarwa Allah domin kuwa ya isar miki. Shikuma wanda yake iƙrarin sai anje ki nusar dashi mahimmancin Hakuri da juriya Akan Jarabar da Allah ya kaddara maki. Wallahii wallahi mai hakuri baya lalace Aymah . Sai dai nasabar shi har kullum tayi sama Aymah. Kana Allah zaikawo mafita a rayuwarki ya ɗaga darajarki ta inda baki tinani... Jikin shi ta fada ta sanya kuka tace" na yarda Jameel maganar ka haka take kuma in sha Allah zan tsaya akan bakana na ganin maganar nan bata fitaba dan yanzu tin duniya Allah ke hukunta azzaluman bayinsa. Hakkin rayukan daya ɗauka kadai bazai barshi yaji dadi ba. Bayanta ya dan bubbuga yace masha Allah Dakika fahimta. sorry Kinji my Dear wata rana sai labari. Kai ta jinjinamai tana dan Murmushi tace" ka warke Yanzu?. Kai ya dagamata yace "yeah. Likitan zuciyana ta bani magani tini ciwo yayi gidan sa sai fatan Allah kabama iyayenmu aljannah fiddausi. Ameen tace cikin jin daɗin kalaman sa wa iyayen ta. Kallonta ya sake ido cikin ido Yace" Aymah zaki iya aurena ? Ido ta waro tare da neman tashi tabar wajen ya mike ya cafko kafaɗunta ido cikin ido fuskar shi na canzawa yace" A karo na biyu na Roke ki kuma Inaso kiman magana ɗaya dan in'san inda kika ajeni Aymah, kar naita aikin banza kullum sonki na huda jinin jikina yawo yakeman a dukkan sassan da kika sani, nema yake yaci ɓargona shin so kike ya karni ? Dan Allah ki tausayaman ki tausayama zuciyar data daɗe tana dakon sonki, in kau har kince bakyasona to tabbas cikin dayan biyu. Na farko Kina ganina talakka kaskantacce Mahaifina da mahaifiyata sunyi zama kalkashin ki sunci sun'sha. Na biyu namiki Yaro kina ganin bazan taɓa wadataki da abinda ya shafi Rayuwar Aure ba. Amma karki manta matar Annabi Muhammad SAW Nana khadija ta girmema Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam. Amma kiji yanda Sukai Aure suka kuma raya sunna Babu tawaya aciki. Zanbaki dama Aymah daganan Har tsawon wata daya wallahi inason sanin matsayina a wajen ki. In kinbani muhalli acikin rayuwarki zanfi kowa farin ciki. Haka zalika idan kikaga zaki cutu kika nuna bakyayina zanyiwa Allah gdy dan nason shiya tsaraman hakan kuma hakan shine Alkhairi na a Rayuwa. Wallahi azeem bazanga laifin kiba som,sana duk abinda nason zan miki kiji dadi wallahi zanmaki da iya iyawata in sha Allah Saboda kin riga kin zama jinin jikina.. Shuru tayi shikuma ganin haka ya shafata zai wuce zuciyarsa ba dadi dan yagaza gane ma'ana shurun nan nata wallahi ba karamin tayar mai da Hankali yake ba.. Yasa hannu sai bude kofar tace Jameel. Bai juyiba amma ya dakata da fitar . Ganin haka yasa tace. Jameel bakajin tsoron ace da kananun shekarunka ka auri mace kamarni? baka gudun Abokan ka suma dariya ace kana auran wacce ta girmeka Jameel? zaka iya jerawa dani kacema duniya nice matarka bazakaji komi ba? Dan juyowa yayi yana sakin murmushin takaici yace" AYMAH basai kinmin jurwaye mai kamar wanka ba. Nasan so kawai kike kiceman Kinajin kunya duniya taga nine mijinki ina talakka iyayena sunyi bauta a Kalkashin ki, kakata na kalk..... Kaiman shuru Jameel tace da karfi cikin kuka. "Ya kake magana haka Jameel,miyasa kakeson muna samun matsala,kai kuma taka salon soyayya haka take,Duk sadda zaka fadaman haka inaji . Kamar kana lumamin wukane a ciki ,Koba soyayyarka a zuciyata iyayenka iyayena ne ballema ina sonka ina sonka ta fada da ƙarfi tana cakumo wuyanshi da fashewa da kuka dan harga Allah ta tsani yanuna shidin kaskantaccene a wajenta ita mai mutunci ce tason kuma mutuncin duk wanda take tare dashi balle su dasukamata halacci. Shikam wani bala'in dadi da farin ciki ya ziyarci zuciyar shi. Kafadarta ya rike ya hau juyi da ita cikin tsananin farin ciki. Habarta ya kama ya ɗago tare da goge hawayenta yace "really kin amince ban tursasaki ba. Harara ta watsamai kamin tayi sama abinta tanajin zuciyarta wasai da ta amayar da abinda ke damunta . Shike Ƙaskantar da kanshi awajen ta amma shidin mai matsayine sosai a rayuwarta som batajin dadin abinda yake cewa game da shi da family nashi da suka zame mata garkuwa,Ita kanta da baya zata dawo gaba ai bazata taɓa yarda mahaifiyar shi tayi aiki a kalkashin ta ba,Dan abin namata ciwo duk sadda ta tina. *** Deedee kam cikin kuka ta fita kai tsaye dakin da Adnan yake ta nufa . Su sadam na zaune palo sun sanya tvn su da suka dakko gaba suna kallo da abokan su. Gaidata sukai ta amsa tayi ciki. Kwance ta ganshi yana bacci iya karfinta tasa ta yankamai mari sai gashi ya tashi yana neman Hanya. Cikin kuka sosai ta zauna gaban shi tace" kai asararran mutum ne wahalalle fajiri marar amana butulu kawai, takarasa tana tofa mai yawu. ""Yanzu dama kaine ka kashema Aymah iyaye ko? to mungano komi kuma zaka girbi abinda ka shuka da kanka dan Uban Baban ka da wannan Wukar zan kasheka matsiyaci ta nunamai sabuwar wukar dake kyalli hannunta... ❤️MATAR OGA NA ❤️ MALLAKI ❤️UMMY AYSHA ❤️ Page 18 Paid book MAISO CHART ME.....07038423451 """ Gabaki d'aya yanayin sa saida ya sauya ,wata irin rawa da jijjiga yafara yana zaro ido da kad'a kai tashin hankali bayyane akan bak'ar fuskar shi. Mari ta kwasamai tace." Da ubanka nayi kama ko da tsinaniyar uwar data kawoka duniya ne da kake kallona? ko nima kashenin zakai? Ido yaci gaba da zubamata cikin mugun tsanarta data ke hangowa abayya ne ga fuskar shi. Hannu ta shiga taɓawa tace "Yanzu kai Babu alamar saduda a lamarin ka,Aiko yau sai kaci ubanka tashiga kwalama su Sadam kira,aguje suka shigo ta fashe da kuka da fadin" ina zamu samu wanzami yanzu cikin daran nan wannan mahaukacin na iske da Hakkin tsintsiyar laushi yana kwal-kwale kwal-kwale yana ganina maimakon ya zaro sai ya turata cikin jikinshi ina da tabbacin ta daɗe magudanar Bawalin sa dan alylah akirashi ya dan yimasa gyaran shayin sa. Gabaki daya suka fashe da dariya suna tafawa kamin cikin mugunta sadam yace "Shege gashi a lankwashe amma ya iya iskanci, to ai hikenan muna zuwa ya karasa suna tafawa da abokansa suka fita suna kwasar sariya.. Abokin sadam din ne mai suna Bash ya fashe da dariya cikin mugunta yace "kai wallahii Isa Abba zamu kira kason bashi da mutunci ko awajen Jariri ne kau, Dan haka dole ayi dogon bincike agano inda yakai wannan hakkin suka fashe da dariya Sadam yace "shegen yana cikin wannan halin ma shiga Ayu sai yayi ciyayya. Dakyal suka samo Isa Abbah ya hado duka kayan aikin shi suna sake fadamai yanda abin ya kasance sai kada kai yake yana Fadin ai aikin sune ,Mutum ko shekara arba'in yakai sai yamai kaciya balle wanda tishi ne kawai. Koda suka isa gidan Deedee dai-dai lokacin da Jameel ya fito baibi ta kansu ba farin ciki yasa ya bude gidan yayi tafiyarsa zuciyar sa fara tass yanajin sa cikin mugun nishaɗi yayi gida. Da sallama suka shiga har lokacin Deedee na tsaye tana mashi masifa shikam sai gurnani yake mai nuni da faɗane kawai yake ba la'asar jikinsa yayi ba. Da sallama suka shiga inda Dede ta sake saka kuka tace" ni tindama nike na taɓa ganin wannan abu yar ɓula da ba wani abuba amma ka saka abu baka gudun ka toshe wata jijiyar taka kai Allah kabama marar Hankali lfy. Dariya Isa Abba yayi yace." kar kidamu mudama mukema maguzawa shayi da girmansu balle shi wannan da aikine kawai za'amasa sai anga abun yayi yawa sai aɗan raba mazakutar tasa biyu a fidda cutar. Ɓererererrrrr!!!! Adnan ya fara haushi yana neman mikewa. Deedee kam cewa take wayyo sannu sannu dole kaji zafi,yo ba haka aka taɓa sama Ashiru mai faci robar fitsariba sai gashi ta mayar dashi Mai Yoyon fitsari ba, ko dariya yayi sai ya canza sabon tsarki dan fitsari ke zubomai wannan yar ɓula ai batason bako kamar ido take. Shiyasa ma bance muje cenba nason aikin arziki ai saiga wanzamai tinda su sunfi kowa sanin abinda wajen keso da wanda bayaso sannu Isa Abba Ɗan gado kunfi ƙarfin Haye. Cikin jin daɗi Isa Abba yace" cau-cau kakus fada ki sake fada kanki tsaye, kai ku budeman sutura tashi ku rike man hannusa abani fitila mai haske dan in'ƙara ƙarfin ganina.. Dariya suka sanya Deedee tace to bari in'jiraku falo aibana kallai ba Harka duk ta masu Alkalami ce ta koma palo tayi zamanta tana kaɗa kafa da kashe ido daya tana tinanin Rayuwar Aymah mai Cike da riski da Kalubale. Shikam da karfi yasa aka tale Adnan dake ta ihu ya gwalemasa cinya tare da cafkar Jikin nashi dayayi mugun yaushi tamkar Tsohon Allayyahu . Afusace yace dan ubanka kadan tashi dan mussan inda zamu samo abun, Kaman kwance kamar ruwa kaɗan kumbura nace ma'ana ka mike ba tsayeba saita abun naka ka mike shege da mace ka gani ai da tini ka zama Pencil ɗin yaran boko. Su Sadam kau misuke inba dariya ba harda sakin Adnan dan bil hakki Isa Abba ya fusata. A fusace Isan yace wallahi ko kuyi aikin ku ko in mayar daku mata maza ku dukkan ku kananun Yan iska... Da sauri suka natsu suka sake banƙare mai Adnan. Adnan Kau kai ya shiga gilgizawa hawaye na zubomai. Isa Abba kau afusace ya ɗakko wata katuwar kibiya mai lankwasa kamar kwarashin saka ya danna cikin ɓula yana jujjuyawa da faɗin" dole ayi saka awajen nan indai ana a samo abinda a keso shegen gaban kamar na tsuntsu ance ku dinga gyara amma bakwayi. Ihu sosai Adnan keyi yana gwaranci danshi kaɗai yason azabar da yakeji adai dai wannan lokacin. Iya bincike Isa Abba yayi baiga komiba ya dauki yar askar su yace bari adan maka tishi muga. Daga palo Deedee tace" A'a barshi In baku ganshiba kar ya isheni da wari, in kuna da magani bashi kawai shiyasani kamar ba taimakonsa za'ayiba banza kamar yaro sai iskanci yake barshi ya kume masa a ciki. Afusace isa Abbah ya wankamai mari yana nishi yace" Shege duk ya bani wahala dole a dafamaka Dauri abaka kasha in dai anason ganin dai-dai.. Tashi sukai Deedee ta zaro 1k tabashi da mashi godiya suka rakashi ya tafi suka dawo. Sallama ta masu ta koma daki inda da iske Aymah na sama alamar ta kwanta . Dakin dake ƙasa tashiga tayi Alwallah tayi Isha dan tama makara a ƙallah goma saura duk tana wajen wancen dan iskan. Bayan tagama tayi shafai tare da addua bacci dan dama sai ta tashi cikin dare take wuti ri. Som bacci kasa zomata yayi tausayin Aymah cike da zuciyar ta wai ace wanda ke tare da kai amma shine sanadin iyayen ka wannan wace Irin rayuwace. Washe gari Asubar fari ta tashi tashiga ta haɗamasu kalacin kunun tsamiya da ƙosai mai zafi ta zubamasu ita da Aymah takaima su Sadam sauran da fadin su dibarwa Adnan a ciki. To sukace sukaje suka cinye suka fita waje suka siyomai garin kwaki na talatin sugar Ashirin suka hadamai suka bashi ba yanda ya iya haka yasha. Aymah ce ta sakko cikin shirin riga da siket na atamfa sunyi tsam ajikinta katon mayafine akanta da alama fita zatai. Bayan sun gaisa da DeeDee tayi shiru. Deedee tace "Aymah ina zuwa hala naga kamar kinyi shirin fita?... Kanta ta dan shafa tace" zanje wani wurine Deedee kimin Addu'a nasara. Tom Aymah ak6kah ya tsareki ya baki saa akan dukkan abinda kika sanya gaba. Ameen tace tana mika hannu ta dauki ƙosai daya taci. Deedee ta zaro ido tace ke badai kina nufin bazakiciba zaki fita. Eh Deedee nah saina dawo bazan jimaba in sha Allah zan dawo . Ohk tom adawo lfy tace tana tashi tanufi kiching dan samata nata a kula. Aymah kau tana fita wata mota na parking kofar gidan nasu cikin natsuwa ta bude tashiga aguje akaja motar sukabar layin. Tafiya mai nisa suka isa wani ɗan kauyen dake da ragowar al'umma . Bakin hanya suka ajiye motor suka fara kutsawa ciki saida sukai tafiya mai bala'in nisa kamin suka iso wata tsohuwar bukka . Wanda suke tare da ita ya juyo cikin gajiya yana warware rawanin fuskar shi. Ido nazaro ganin Manager ne wato wanda Adnan yaba ajiyar dukiyar Aymah ma'ana manager sa. Sallama sukai bakin bukkar wani ɗan farin dattijo ya fito da sanda a hannusa yana dogarawa ya tsufa sosai Dagani yana cikin wahala Rayuwa. Ido ya zubamasu kamin ya saukesu kan Aymah yace "Amamatu Baba. Itama isyon ta zubamai cikin balain nasari wanda ke cemata Amamatu Baba. Amamatu Baba baki ganeniba? Ido ta zaro kamin kuma ta nuna shi da yatsa bakinta na rawa Tace" Baba Ali dama kaine,Baba akace ka mutu tinma Abba nada rai Baba da Allah kaine takarasa a rukice Idonta na kawo ruwa. Dan murmushi Yayi yana nunamasu wata tabarma kaba dake ƙalƙashin bishiya yace su zauna. Gabaki ɗaya suka zauna harda shi. Ido ya sake zubama Aymah cikin lokaci kuma hawaye suka sakko mai yace Allah Sarki Amamatu duk yanda naso na kare mahaifin ki daga sharrin Black driver amma abu bai yiyuba Amamatu ki yafemun dan Allah... Cikin kuka sosai tace Baba dan Allah kayiman bayani yanda zan gane miya faru wane sharri ke tsakanin Adnan da mahaifina da har ya iya sanya masu Babba mota bin takansu? Hawaye ya share yace. Aymah kinson dai ni Amintaccen mai gadin mahaifinki ne tsawon shekaru, kinson harkar mahaifinki harkace ta bukatar taimakon al'umma dan mutum daya bazai iyaba kinson harkar fito dai. Mahaifinki na da dribobi da dama da suke masa tukin mota in sun dawo zaima kowa sallama ta kirki wanna dalilin ne ya karama shi farin jini kowa nason yayi aiki a kalkashin sa. Yanada wani aboki Alh Hamza ɗan sanata babban aminin sane kuma duka harka ɗaya suke saidai an'fison kayam mahaifinki sosai saboda ragowar farashin da yake dashi... Hamza baya Kaunar mahaifinki ko kadan amma bai taba yarda ya bayyanaba ko afuska hasalima kullum goyan baya yake samu daga mahaifin naki. Wata rana muna zaune gidan dawakan mahaifinki saiga Alh Hamza da wani yaro kaca kaca yaron yasha wahala Daganin shi a tagayyare yake ashekaru baifi 25 ba. Bayan sun gaisa yakecewa da mahaifinki Alh ga yaro nan na kawo kason ni yanzu harkata ta farayin ƙasa bama da empty motar da zanbashi ka taimakamasa yana bukatar taimako saboda ya kula da mahaifiyar shi. Abban ki mutum mai tausayi cikin lokaci yaji yaron ya bashi tausayi . In takaicemaki aranar ya bashi sabuwar motar gwarama dakuma kayan abinci yace yakaima iyayensa. Yaron na har kuka saida yayi daganan fa shima ya dage ya rike amana yazo ya sharce dukkan sauran dribobi kokari gashi kaifi daya kuma baya zalinci da wasu keyi sana duk abinda akai zai kawoma mahaifinki bayacin ko sisin sa, ke ko mota ta lalace baya faɗa sai dai yasa kudin sa ya gyara wannan fa shine yakarama mahaifinki soyayyar yaron nan mai suna Adnan da Dribobi yan uwan sa ke cemai Black driver ya jawoshi jiki ke saida ya mayar dashi tamkar ƙanan sa wanda suke uwa daya uba daya babu inda zaishiga bakiga Adnan a bayansa ba,Uwa uba inda ya ida saye Baban ki wajen son da yake maki da baki kulawa duk inda yaje yadawo tsarabar ki daban... Sun samu shekara takai biyar suna cikin wannan jin dadin rayuwar kwatsam wata rana Adnan din yazoma mahaifinki da son Ya aramishi kuɗi tsabar 100ml. Mahaifini kuma lokacin ya kwashe yawancin kudadansa wajen turomasa da wasu sabbin kayan da basu riga sukayi magana da Adnan dinba ya bashi hakuri da nunamai ya Bari sai komi ya kammala zai bashi Yanzu ga ƙudirin sa. Wannan abufa yama Adnan zafi ganin lokacin da suka ɗauka amma ya kasamai Alfarma kawai yasha alwashi sai yabar aiki kalkashin sa tinda amfani kana tare da mutum ya taimakama ranar da kake da buƙata. Bayan kwana biyu yazo da kanshi muna zaune bakin get din gidanku ya cillama mahaifinki key tare da mai munana kalamai ta hanyar nunamai shiɗin mutum ne mai masifar son abin duniya uzirin sa kawai yasani baison na kowa ba Allah ya hada kowa da rabon sa. Iya wuya mahaifinki yashiga tashin Hankali yin duniya Adnan ya tsaya yaji uzurinsa amma yaki daga baya ya nuna mai shi ya hakura da nashi uzirin yazo yabashi amma yaron nan ya shure kafa ya tafi cikin zafin zuciya dan dama bakar zuciyane dashi som Abokan aikin suma basu son shi gashi dama Mahaifinki yafi sonsa dasu akwai wannan kishin A ransu. Amamatu wallahii Alh Abdulkarim kuka yasa sosai yana faɗin" Dan Allah kuce yazo wallahi zanbashi banaso wannan abun yashiga tsakanina da yaron nan Baba Ali banaso kowa yaga baƙina kar Adnan ya daukeni maison kai kamar yanda yace. Ban'cemai komiba illah tashi dana yi cikin sassarfa nabi bayan as Adnan dan in samo in lallaso shi .. Daga nesa nike hangosa banyi tinanin kwala mai kiraba illah binshi danacigaba dayi har muka fara shiga cikin gona ki inda cak ya tsaya kalkashin wata bishiya tare da zaro sigari yasa a bakin shi ya ɗauki waya ya fara latsawa. Koda aka dakko wayar cikin muryar sa ta yan daba da bamuson yana da itaba yace" Yahajj komi yazo kwana ɗan iskanan fa yashiga tashin hankali ya kake gani akarɓa koko abar shi da Alhini,aini dama wallahi ba wani sonsa nikeba nutum ana tare dakai muke wahala amma arziki nakane kullum jinike kamar in karshe shi wallahi shida ɗiyar nan tasa mai ciman kudi har cikin raina in nasaimata Abun biyar shikam yayita washe baki dan ubansa yanajin dadi zasuzo Hannu ai... Jikina ɓari ya kama tashin hankali mabayyani ya bayyana agare ni da jin furucin wanda banyi tsammaniba . Jin yacigaba da waya yasani dade bakina nayi kasa cikin ciyayi inajin yana fadin. Yo dayason halacci ko Billion nace zai bani ai zai girmama bukatuna amma ba komi nayi alƙawarin Sai naga bayan shi ,sai nayi gutsun gutsun da naman jikin shi ,wanna Yar tashi kuwa sai na lalata rayuwarta badai ita yakema wannan ɓata lokacin ba, Wallahi wallahi yau ko gobe saina watsamata rayuwa nayi mata daga daga na keta mutuncin ta shikuma bazai sake sani idoba sai bayan shekaru zanzomai ta sigar da baitaɓa tinaniba. Kuka ya kufceman da karfi wanda yasa shi juyowa a razane nan mukai ido hudu dashi jikina ya fara bari na fara ja da baya yana biyoni da fadi" kai Ali tsohon banza dama laɓe kakeman aiko daga kaina ka gama yasa hannu ya zaro wata katuwar wuka yayo kaina . Dan ceton rayuwata na juya na fara gudu yana bina sai dai sabon jini da tsohon jini sunsha banban ganin zanbashi wahala yasa shi jefoman wannan Wukar takau saman anan ya gwadamasu wajen wuyan shi kamin yace ganin nafaɗi ciki jini ya biyoni ya haye ruwan cikina yace tinda kaji sirrina nida Hamza sai kabar duniya ,Zan kuma datse hannuka guda saboda kaida ɓarawo hukuncinku ɗaya dan kayi satar maganata. kara cakaman wukar A ciki Yayi yakuma sata ya datseman Wannan hannu ya karasa yana gwadamasu guntun hannusa dake cikin riga.. Kuka Sosai Aymah keyi yayin da manager ke share hawaye Anya Adnan mutum ne kuwa.. Yacigaba da fadin..ganina cikin Wannan halin ya tabbatar mai da bazan sake rayuwaba nan ya jani har gab da gidan gonar Mahaifinki ya ajiyeni kamin ya kama gabansa tafiyar da yayi mai dogon zango. Ni dai kam a labarin da naji nan wasu manoma suka tsinceni aka fadama mahaifinki nan aka zo aka kawoni Asibiti Cikin garin katsina. Babu wamd yabani ran tashi sai gashi cikin hukunci rabbi Allah yasa ina da tsawon kwana a gaba..wani zuwa da mahaifinki yayi ganina naita gamashi da Allah akan banaso Abokin sa yasan ina raye.. Yaso yaji dalili na fadamai dai ba komi in lokaci yayi zan fadamai. Amamatu kinson bashi da matsala son jin abinda bakai niyya faɗamai ba. Bai matsaman ba hakama bai faɗamasu ba, koda na warke gidan shi aka mayar dani ya sanya masu kula dani ana gadina. Bayan naji sauki sosai mahaifinki yasa aka dawo dani cikin iyalaina saidai hankalina a tashe yake ina tinanin taya zan iya sanar dashi manufar wayan nan azzaluman akansa. Wani lokaci nayi shiri asace nabi dare dan zuwa in samu mahaifin ki Muyi magana aka shedaman bakwa kasar naji zafi sosai dan sabon mai gadin nasama dakeman kallon kamar mugu abinda yaceman bazaku sake dawowaba sai nan da shekara goma. Nakauji dadi nakumaji na natsu da hakan na dawo cikin iyalina na cigaba da aikin gonata nida yan uwana hankalina akwance dan nason bakwanan ko Adnan ya dawo bazai iskeku ba. Bayan shekara biyar wani wanda nike ɗan samun labarin gidan mahaifin ki yakeceman wai an ɗaura Auran ki da Adnan kana kina shekara 20 Amamatu nayi kuka nashiga tashin hankali nayi jinya duk akan wannan Auran naki da bantaɓa tinaniba. A binciken da nayi na gano cewa Ashe saida Adnan yayo Babban shiri ya tun kari mahaifinki . Shikam Baban ki a sannan Babban burin shi kar ya sake ɓatama Adnan shiyasa duk abinda ya nema yake mai jiki na ɓari har auranvki duk mahaifinki baya hayyacin sa, ke karshema rabashi yayi da danginsa baki daya sai shi kawai, Alh hamzama watsar dashi sukai baƙi daya basu sake bi takan shiba. Saida ya tabbatar ya ginu da dukiyar mahaifin ki kana ya fara tinanin kawar dashi dan ya ida mallake komi. Sadda kika kammala karatunki mahaifinki ya fara shelar son kowa yaje mishi Walimar buɗe Asibitin ki, bayan naji labari nabi dare dan zuwa wajen shi sai dai banson wake lura dani ba wasu suka kamani suka kulle tsawon kwana biyu baci ba sha ajikin bishiya. Da yammacin da nike niyyar kwana na farajin ihu dana saurara da kyau naji kuka Yarana ne biyu da Allah yabani mace da namiji sai mahaifiyar su nan aka kawosu gabana aka yar, Adnan ya bayyana da zafgegiyar wuka yana murmushi yace" Ali kenan babu abinda bansaniba agame da binciken da kake domin ni , Sai dai awannan karon bazan ma ko kwarzaneba bakin ciki zai sanya zuciyar ka bugawa suma wayanda kakeyi dominsu gobe war haka ana shirin kaisu kushewa koma an binne su. Gama wannan maganar keda wuya ya sanya wuka yama matata yankan rago da yarana biyu yasa aka binnesu ko wanka ba amasu ba. Aiko maganar shi tayi tasiri dan nima nan wutata ta ɗauke sawon lokaci ashe har taɓin hankali ya sameni dana dawo hayyacina ake faɗaman mutuwar Iyayen ki Aymah nayi kuka nashiga tashin hankali. Ganin ba sarki sai Allah na dawo nan dajin ina rayuwa ba wanda na sani babu wanda ya sanni. Kayan itace sune abincina. Wani lokacin kuma in hakura in kwanta gabaki daya duniya ta juyaman baya Aymah Allah ya sakamana dan Adnan ya mana tabon da bazai goge ba... Wani irin kuka Aymah keyi jikinta kau wane na Jameel ya riga da yayi zafi. Manager ma kuka yake Sosai yace Baba naji dadi da taji daga bakinka ada tana ganin wani abun bazai yiyu Adnan ya mataba. Dukiyar tama tace wai ta barmashi dan kawai tayi Alkawari yanzu irin wannan mutanan za'a barwa ƙaruwa?. Murmushi Yayi yace wane shi Amamatu. Manager ya kalla yace waya faɗama inda nike??? Kuka sosai Manager yayi kamin yace Baba nayi kuskure a baya amma a yanzu ina son gyara laifina watakil ku yafeman kai ko baka yafeman ba nima zankai kaina court .. Nine wanda..... ❤️ *MATAR OGA NA* ❤️ UMMY AYSHA PAID BOOK PAGE 19 ""Nine wanda ya dakkoma Adnan iyalin ka har inda aka daure ka, amma wallahi azeem bai faɗaman kashe su zaiba, ya dai sanar dani cewa Aima barazana dasu wacce zatasaka guduwa daga garin baki ɗaya..Baba ni yaron sane babu abinda ban saniba na Adnan, amma daga lokacin dayama wannan zalincin naji na tsane shi ina neman kuma hanyar da zanbi in gyra kuskurena,nasha wahala sosai kamin in samo inda kake dakyal wani mutun Almajirine yanzu daya kasance Aminin ka a lokacin shike baka labarin rayuwar gidan su Aymah ya bani wannan address din naka,Shima yace a nemamasa gafarar ka domin kuwa Rashin kudi ya kamashi ya zagaye yaci amanarka wajen sanar da Adnan bibiyarsa da kake Har abinda ya faru ya faru dakai.. Murmushi sosai Baba Ali yayi kamin yace" ba komi Allah ya yafemana ,kai kuma na yafema suma kuma dasuka rigamu gidan gaskiya Allah ya gafartama su ya yafemasu kura kuran su. Amma tabbas Aymah yau ba gobe ba sai dukiyar ki ta dawo hannu ki dan gumin mahaifin kine,Hakki kuma naki ne bana Adnan ba.. Dakyal ta iya ɗago idonta dan kanta da kirjinta masifar ciwo yake ta zubamasu ta kasa cewa komi. Ganin haka yasa hankalin su tashi manager ya tashi yana faɗin ta taso sutafi amma jikinta yayi bala'in sanyin da ko yatsanta bata iya mikewa. Addu'a sosai baba Ali yashiga yimata kamin A'hankali ta fara sauke ajiyar zuciya. Cikin maganar ta da bata fita sosai tace" Baba dan Allah kabini muje gida ina so mu ida magana ne acen Banajin daɗi. Sosai ya nuna rashin amincewar sa saida tasamasa kuka tare da bashi labarin su Deedee tace''. ina so kai ka zameman uba inaso ka gyara Alaƙar dake tsakanina da yan uwan Baba na,har yanzu zaune tsaye bata kareba tsakanina da Adnan, ga matar sa dake shirin shigowa danma manager na dakatar da ita banaso ta fara zargin wani abu ayanzu kaine hujjana na karshe Baba dan Allah ta karasa tana rike kirjinta Sosai dake barazana rabewa.. Cikin gamsuwa da kalamanta ya mike zai dauki kayan sa kala guda wayanda biyune dama yake rayuwa dasu ,yau in yasa wannn gobe ya wankesu da ƙafa tinda ba hannu ya shanya. Hanashi tayi da faɗin muje kawai Baba. Dakyal suka fito daga Wannan jejin، sadda suka kawo bakin mota Aymah ko gani sosai batayi saboda bala'in jirin datakeji daga jiya zuwa yai taji abinda yafi ƙarfin tinaninta shiyasa duka yanayin ta ya sauya. Hanya suka ɗauka tafiya kamar ba gobe Baban kanshi saida ya gaji. *** Jameel kau farin ciki hana shi bacci yayi Asubar fari ya samu Mahaifinsa da maganar, Sosai kuwa yaji daɗi da fadin ta wannan hanyar kawai zaka sakama Aymah dan Allah ka rikeman ita a mana Jameel kaga yanda ta sadaukar da farin cikin ta akan naku.. . In sha Allah yace yana dukar da kanshi. Inna su ce tafito daga ɗaki. Da sauri ya tashi ya koma daki tabishi da kallo dan duk taji abinda suka tattauna Murmushi kawai tayi ta zauna tace" yanzu Baban su kana ganin taya zai iya Auran Hajiya Aymah? mace yar gayu data tashi gidan hutu Jameel ko gidan da zasu zauna babu ,gashi babu abinda zai mata koda lefe .. Shuru Malam Habu yayi yace . Duka abin Aure na Allah ne , Insha Allah kuma nima gobe zanje nasamu Deedee muyi magana,in yaso gonar nan inje kauye da kaina asake sata kasuwa muga abinda Allah zayyi. Amince mai tayi da addu'a Allah ya zaɓamasu Alkhairi... Duk abinda suke faɗa akan kunnan Jameel sosai yaji dadi haka kuma sun bashi tausayi shawarar Dr Abba ta fadomai . Nan ya ɗauki wayar shi ya kirashi akan yanaso su hadu su tattauna akan batun kasuwancin da yace... Sosai kam Abbah yayi farin ciki inda yabashi izinin ya iskeshi officer dinsa yanzu. Ba ɓata lokaci yayi wanka ya shirya ya kira Abokan sa ya shedamasu bazai samu damar zuwaba sai washe gari. Fatan Alkhairi suka mai shikuma ya sallami iyayensa ya doshi hanya Asibiti. Bayan sun gaisa yake sheda mai Amincewar sa akan bukatar da yataɓa zomai da ita dan yanaso da kanshi yayi hidimarsa ba tare da ya dorama iyayen sa nawie ba. Yaji dadi sosai nan ya kira dan uwansa yashedamai harkar da Jameel keso ya fara amma bayaso abashi driver kai tsaye yake so ya tsundumashi cikin Harkar, ga 500k ya bashi gudumuwarsa halak malak Allah yasa masu Albarka. Faɗamaku halin farin cikin da Jameel ya shiga awannan gaɓar ɓata lokacine domin kuwa har hawayen farin ciki yayi kyautar irin wannan zazzafan kudi lokaci daya ba dangin iya bare na Baba. Dr Abbah kau lallashin sa kawai yake yana nunamasa muhimmancin taimakama wanda bashi dashi. Tare sukaje gidan ɗan uwan Dr Abbah nan suka zauna suka fara gaisawa kamin ya fara masu magana. "kaga yanzu man petur muke kaiwa Nijer sukuma su bamu gas. Dr Abbah yace to kamar ya ake harkar Yaya Nura? Gyara zama Ya Nura yayi ya fuskance su sosai yace a ƙallah million biyu zata iyamaka wannan harkar. Na farko dai sai kasai mota ka kuma sai jarkoki uwa uba zaka sai man petur din .. Misali Duk jarka biyu in kabasu zasu baka jarka guda ta gas kai kuma in kazo nan Najeriya ka saidata zaka iya samun ribar 5k duk ga wannan jarkar,to saika lissafaman in ka kai jarka dari nawa zaka samu riba.? Sosai kam suka gigice dajin wannan uwar riba dake shigowa. Murmushi yayi yace. Amma fa akwai kalubale, saidai kamin ya afkama zaka iya mayar da dukkan kudin da ka kashe cikin sati biyu zuwa ukku mussamman in'ka samu Driver Arziki ɗan amana da bashi da wasa. kalubale kuma shine kamawa da Costume keyi. In suka kamafa shikenan sai dai hakuri da fatan Allah ya mayar da Arziki. Cikin gamsuwa da bayanin sa Dr Abba yace" Amma dai yaya ai ba kullum zasu kamaba ko? Murmushi yayi yace haba Alh ai da kaima saika binciko aikin ka, in'kau akace kullum muma da bamuyi ba. Cikin farin ciki sosai yace. Yayah munji zan bashi aron Million daya da rabi ya fara ,Kaga dana yana da 500 a wajena in yaso sai a fara masa ko zuwa sati mai zuwane. Murmushi yayi yace Babu damuwa Abbah duk yanda kuke so kuma nima in sha Allah zan dubamasa cikin amintattun drebobina in bashi wanda zasuyi harka tare.. Jameel yace "Yallabai ko ni zan iya wallahi. Da sauri Dr Abbah yace" A'a kai dai abar shi hakan sune masana harkar tashi muje iyaka kai komi yayana zai maka ka ganshi nan yafini ilimi nesa ba kusaba amma kuma baya da ra'ayin aikin gomnati sai wannan harkar amma fa wlh shine Attajirin family namu kaima haka nike fata kaxama kaf Family naka. Rungume shi Jameel yayi Yanajin wani mugun kaunar shi har cikin ranshi. Mikewa Yaya Nura yayi yana dariya ya haɗasu ya rungume cikin wayewa yace. kai dai munbari kai tama mutane Allura, mukuma munfison kullum Bugun Abuja suyita shigo wa. Kai kuma kanena Allah yasanya ka fara asa'a,Ka gabatar da istakhara kamin farawa, kana ka yawaita Addu'a ka dinga sadaka zakaga haske in sha Allah,... Godiya sosai suka mai suka tafi suka shiga motar Dr Abbah. Jameel ya fara mishi godiya ya tsaidashi yace. Jameel harkar sirri zamuyi dakai. Saida gaban Jameel ya buga jin wannna magana cikin mamaki yace bangane ba?. Dan murmushi Dr Abbah yayi yace" Jameel inaso karka bari Aymah ta sani,inaso ka aure tane kana cikin wannan yanayin naka na Driver mota,Ina so yazamana iyayenka kawai zaka sanarmawa a sirrance dan su sama Albarka, kana in kuka yi auran ko haya ka kama muku ku zauna. Agefe ribar da kake samu kaje ka samu katon gida Lafiyayye ka gina kai atsayema in dai kanaso zaka iya samu. Cikin Amincewa da bukatar shi Jameel ya rungumes hi tsamtsam yace" nagano manufarka Allah yasaka da Alkhairi, in sha Allah haka za'ayi ita kuma Aymah inaso nan da watanni kalilan amana Aure, ko bata tareba wallahi inaso najita ƙalƙashin inuwar aure na. Wannan mai saukine yace yana tada mota. Cikin jin daɗi yace" muje gidan ta inaso na ganta. Motar ya tada yana zaulayarsa nan suka ɗauki hanya suna isa motar manager na tsayawa . Gabaki daya suka fito motar shida Jameel inda manager kuma ya bude motar shi shima ya fito idonshi cikin na Jameel. Wani mugun tsuma jikin Jameel ya fara dan rass ya gane shi. Ranshi ɓace yake nuna shi da hannu yace" ubanmi kazo yimata anan? Ko ina dukiyar matata take munafuki yayi kanshi gadan gadan. Dakyal Babb Ali ya iya buɗe gaban motar ya fito Yana daga sandarshi yace" Kayi hakuri yaro komi zai tafi daidia wannan ba macuci bane kamar yanda kayi zato kaji... Cak Jameel ya tsaya yayin da manager da jikinshi ya dauki rawa yace "Wallahi babu niyyar cutar Aymah a Rayuwata, gatanan ka tambayeta ya faɗa yana bude bayan motar. Nan ta bayyana kwance tana sauke numfashi kadan kadan da alama Athma ta ce ta tashi dan sai haki take. Cikin wata tafiya ta mazajen zakuna Jameel din yayi bayan motar inda yaganta cikin wannan hali. Ya subhanallahi, faɗar tashin hankali da yaron nan yashiga a dai-dai wannan lokacin ɓata lokaci ne... Domin kuwa idon shi ganemai yaadingayi kamar bata numfashi. Wani irin ihun kuka yasa yayi kanta gadan-gadan ya cakumota yana fadin. Aymah dan girma Allah da manzon sa kitashi ki faɗaman misu kai maki,karkiman haka kar ki tozartani, karki yaudari zuciyar data ɗauka so da amana ta baki , Allah ne gatana sai iyayena ayanzu bani da gatan kowa sai naki, Wallahi rasaki a rayuwata tamkar rasa rainane, karkiman haka kibamu dama mu mallaki juna mu haifi yara inma tafiyarce sai mutafi dan Allah, kibari murayu a kalkashin inuwar aure, Aymah nah dan Allah yafada jikin shi ko ina na rawa zufa na ketomai hawaye kam kamar an bude pampo.. Dr Abbah ne yaja shi yace. ka dubafa tana numfashi Jameel bafa mutuwa tayi ba ,a halin yanzu ma taimako take nema jibi yanda numfashinta ke barazana barin jikinta ko dai tana da Athma ne?. Baba Ali yace. Tabbas tana da ita dan ba shakka ta gadeta ne wajen mahaifin ta, ba abin mamaki bane ace itama bazata rasata ba. Kagani ko maza dakkota muje Asibiti Jameel kukuma kushiga ciki Deedee na nan yace da manager. Baba Ali yace. A'a bazamu shigaba zamubiku munason sanin halin da take ciki.. Jameel kau tinda yaji tana da rai bai sake bin takan kowa ba ,aguje ya saɓeta kamar baby sukayi cikin mota Dr Abbah ya rifamasu baya. Kai tsaye FMC suka nufa Emergency ganin su da Babban Dr babu wanda ya tsaya neman katin su. Likitoci ukku ne akanta dan ƙoƙarin ceto numfashinta, Yayin da Jameel kuma keta safa da marwa yana Addu'a,, Gefe kuma tinanin miyatasomata da wannan ciwon yake , kana miye alakar ta da wannan manager Abokin mijinta nefa maci amana ,abu na karshe waye Wannan Dattijon, kana ina sukaje haka sukadai da wannan ranar?.. Dr Abbah ne ya dafashi yana goge zufar fuskar sa yace. Gaskiya akwai matsala Jameel,Banson wace irin damuwa Aymah tashiga ba wacce ta fara neman taɓa lafiyar zuciyar ta,A yanzu haka maganar da nikema ba Athma da muke tinani bace ta tashi kumburine zuciyarta yayi abin babu dadin ji. Mafita daya shine ayi gaggawa yimata aiki.. Ya Salam. Jameel yace. Ya rabbi ka rabamu da shiga tsaka mai wuya yace yana dararashewa kasa. Yau garana dukiya,da yana da ita babu wata fargaba da zayyi ,koda kai zasuce zasu fita wata kasa amma ahalin yanzu ko maradi akace yaje bashi da wannan halin. Manager da suke jinshi ya taso yakara neman bayani Dr Abba ya masa yace babu Damuwa A fara shiri kawai. Dr Abbah yace. Tom Babu damuwa,Sana gaskiya inaga Deedee bazata iya da wannan jinyar ba dan abune mai wahala. Jameel dai shuru yayi yana binsu da ido dan bashi da ta cewa. Manager ya kalli Jameel ya kalli Dr Abbah ya dan ja hannusa zuwa gefe nan suka shiga tattaunawa na wani lokaci kamim su dawo inda yake yayi tagumi zufa sai ketomai take. Jameel in sha Allah yanzu da an'fito Sallah azahar zamu daura maku aure kaida Aymah ,Kana Aikin ta gobe da asuba ne Allah ya bata lfy zamuje wajen Baban ka yanzu. Ido kawai Jameel ya zubamai dan bashi da abin fada a daidai wannan lokacin. Ganin halin dayake ciki yasa Dr Abbah kamashi suka zauna akan kujera ya hau lallashin sa da nusar dashi mahimmancin aikin da za'amata , ba wani abu bane mai wahala, ai an maka kagani ko? Kai kawai ya shiga ɗagamai, Tare da mikewa yaje inda window wajen yake yayi tsaye amma baya ganin ta. Ganin haka Dr Abbah ya kama shi suka shiga Ciki inda take kwance tayi wani kyau tayi fresh gashinta duk a balbaje ga na'urar shakar iska makale a hancinta. Gefen da take ya matsa yayi shuru, inama ace tana zaune da kafarta akamai albishir din wanna auran da kullum yake fata. Dr Abba kau Hannu shi yaja suka fito tare da neman excuse suka sake hawa motoci sukayi gidan Deedee inda suka isketa zaune ta buga tagumi ga Uban zobo data gama hadawa amma batasa fridge ba. Suna shiga ta taso tana binsu da kallo da leka bayansu ta kece da kuka tace" Dan Allah ku nemoman yar marainiyata wallahi tin safe ta fita banson inda ta tafi ba... *Babu editing bana da charge* ❤️MATAR OGA NA ❤️ MALLAKI UMMY AYSHA PAID BOOK NE . Page 20 ""Dr Abba yace . kwantar da Hankalin ki Deedee Aymah na tare damu , Yanzu haka akan maganarta muka zo miki.. Zama tayi tana zubamasu ido ta kasa cewa komi. Cikin natsuwa ya shiga koramata bayanin ciwon Aymah da aikin da suke so amata. Ya salam ! Deedee kamar ta shiɗe tsabar masifar kuka.. Dakyal tayi shiru tashiga kwararo Addu'a neman dace wa Aymah akan aikin da za'amata. Suna cikin magana ne sukaji sallama baƙin kofa. Dr Abba ne kawai ya fita yaga iyayen Jameel ne da kuma Baba Ali sai manager. Sannu da zuwa Deedee ta masu tana sake matsamasu da carpet gefenta. Yayin da Inna su Jameel kuma ta dawo kusa da ita ta zauna. Bayan an gagggaisa nan ta kalli su manager tana fadin" ban wayeku ba?. Bayan sun gaisa nan ya fara bata labarin rayuwar da sukai da Adnan, da Baba Ali, kamin ya kara da cewa .. Mama wallahi nayi nadama mafarin kenan sadda Adnan yajeman da batun son sa Aymah ta rattaɓa hannu akan takardun kaddarata na bata wasu takaddun na bogi dayake ba Allah a ransa som baima gane ba. Ita kanta saida ta kalle ni a lokacin tsawa na dakamata akan ta sanya. Alakata da Aymah ta farane sadda Adnan ya kwanta wannan jinyar, a binciken da take a wayar sa ne take gano wasu abubun dayake nufatar ta dasu da irin magana da yakeman nason yanda ya tsara kassara dukiyar ta ina kara ɗora shi akan hanyar da yakeso. Anan ita kumaa ta ɗauki number nah taman magana akan son sanin manufar da Nike da ita akanta,Taya zan bama mijinta shawarar akanta sannan kuma naki yarda na bata Original ɗin takaddun kaddarata yah haka miye nufina akanta? . Saida na gamsu da itace. Nan na koramata bayani asace da son taman Alkawari babu wanda zaiji har sai a fara bincike akan wasu abubuwan da har yanzu bamu gane ba.. . To Wannan dalilin ne yasa nayi tsayuwar daka wajen gano wasu ɓoyayyin sirrikan nashi har muka gano video da yasanya akaje akamasa lokacin da mota kebin takan iyayen Aymah. Dukkan su saida suka share hawaye Jameel kau bakin shi karkarwa yake sosai. Kai dole Aymah tayi jinya masifar nan ta isa ace mijinka, Wanda kuke kwana tare ku tashi, shike da manufar sharri akan ka Da iyayen ka . Baba Ali ya numfasa yace" Adnan Akwai Hakkin al'umma sosai akansa ,sai dai fatan in mai shiryuwane Allah ya shirya shi. "Ba Ameen ba Dattijo... Deedee tace a fusace tana fadin "kai dole matsiyacin nan yaji hukuncin duniya kamin na lahira. Murmushi Baba Ali yayi yace "A'a Hajiya ya daifi abar shi da mahaliccinsa,Kamar yanda yayi ba tare da sanin kowaba haka ya kamata abar shi ya koma wajen mai sama zaima kowa sakayya dai dai da hakkin sa... Malam Habu yace" haka ne Deedee dan Allah kiyi hakuri. Kwafa kawai tayi amma ranta ya ɓaci.. Manager yace . Yanzu Deedee wannan jinyar ta Aymah akwai bukatar adinga kulawa da ita, kana dukkan mu babu wani makusancin daya dace ace an'barta dashi,shine muka yanke hukunci hada auran su da Jamilu tinda ya tabbatar ma Dr Abba da amincewarta a daran jiya. Kuzo kuga washe baki kamar ba ita ke kuka ba. Hannu ta taɓaa tace. Shikenan na amince Allah subhanahu wa ta'ala ya tabbatar da Alkhairi. Nan ta tashi tashiga daki sai gata da kudi ta aje gaban Malam Habu tace'' Abada sadakin Jameel, da wannan 50k din Allah ya tabbatar muna da Alkhairi. Godiya sosai suka shiga yimata nan suka mike da niyyar zuwa suyi shiri su wuce Sallah Juma'a daganan za'a daura auran kamin su dawo dan akwai bukatar zama da Adnan. Fatan Alkhairi tama su suka fita suna tafiya manager ya bayar aka kawo kaji da cefane da kananun kayan abinci akan Ayi girki dan rabama Muta ne . Nan da DeeDee da Inna su Jameel dake ta murmushi jin daɗi da Almajiran Deedee aka zage suka shiga aiki bakama hannun yaro, wannan zoɓon datayi dama batayi kunun Ayaba aka saka a fridge aka hau bashi wuta. Dr Abba kau waya yayi ya shedama su Yaya nura Auran gaggawa daya taso ma Jameel,. Ya shedami zuwan su in sha Allah cikin lokaci.. Daganan yaja shi suka tafi wani katafaran shago ya sawo mai wata farar shadda mai masifar kyau mai tsada da hula da takalma da agwogo ya biya wajen masu aski aka gyarama Jameel din fuska.. Duk da fuska tashi ba walwala amma zanso kuga yanda baiwar kyau ta bayyana ga bawan Allah nan. Kai tsaye gidan Dr Abba sukaje anan dakin saukar da baki yabama Jameel din umarnin ya shirya shima bari yashiga ciki ya kimtsa.. Ba kuzari amma haka ya shiga ya watsa ruwa ya haɗi da Alwallah ya fito, mai kawai ya ɗan murza yayi zaune ya zubama mirro ido.. Shifa ba Auran ne ya dameshi ba , Ya ga ta tashi zaune da mazaunan ta shine fatan shi,zuciyar shi namai sakar abubuwa marasa daɗi dakesa gaban shi Bugawa. Guntun hawayen daya zubo mai ya ɗauke A'hankali yace. " My wife zakiyi farin ciki da ni in sha Allah,da yardar Allah sai na gusar da dukkan damuwar ki,na maye miki gurbin bakin cikin da kika tsinci kanki da farin ciki,Nayi Alkawari da sanina bazan taɓa saɓamaki ba,Zan bada farin cikina domin naki,banason komi naki kawai ke nikeso,farin cikin da kika rasa daga yau zaki fara samun sa in sha Allah,I love you so much Sweetheart. Dr Abba ne ya Turo kofar ya shigo cikin wata dakekiyar shadda Milk sai zuba kamshi yake... Turus yaja ya tsaya ganin Jameel nata sambatu. Kai ya gilgiza cike da tausayinsa kamin ya matsa wajen shi ya hau lallashi da nusar dashi mahimmancin ɗaukar ƙaddarata aduk sadda tazoma. Sosai kam hakan yayi tasiri a zuciyar Jameel din ba kadan ba ya samu saukin raɗaɗin da yakeji nan ya tashi ya shirya shape shape. Ya subhanallahi. Wallahi ba kadyan ba kayan nan suka karɓi fatar shi, sun mai mahaukacin kyau ga wani fresh da yayi ,ya fito Angon sa sak. Turare Dr Abba ya dauka ya shiga fesamai ko ina kamin ya gama suka fito suka shiga Sabuwar motar Dr suka dauki hanya Yana ta sake ƙoda kyan da Jameel ɗin yayi... "Hmm Wai yau zan mallaki Aymah matsayin mata yace yana lumshe ido. Murmushi kawai Dr Yayi yace. Al'amarin Allah ai ba abun wasa bane, kana kaima ayanzu zakai amfani da damarka ta fannin ƙaryata tinani da take na ganin ka yaro ,Ka nunamata Yaron ma namiji ne... Akaro na farko ya saki murmushi yana dan cije lips ɗinsa da taune na k'asan da karfi ya daga gira guda sama yana ɗan turo halshe kamar zayyi fito. Dr Abbah ya juyo karaf suka hada ido gabaki daya kuma suka sanya dariya . Hmm wallahi kardai ka manta ni likita ne, babu abinda bazan karantaba daga fuskar ka Yaro, A dayyi A'Hankali, Dan kayi jinya muka baka badan kashe ƙishin kaba tsohon tazuru. Ido Jameel ya zaro kamin kuma ya jawo haɓar rigarsa ya lulluɓe fuskar shi ganin ya gano manufar sa. Dariya sosai Dr yayi a haka suka shiga Masallacin dake cike da al'umma dan dama babban masllacine gashi kuma ranar ta kama Juma'a. Bayan gama gabatar da huɗu ba aka hau sallah, ana idarwa su manager dama sun sanar da Ɗaurin auran, nan limamin ya tsayar da mutane . Bayan an daura Auran akan sadaki mafi ƙanƙanta dan samun Albarka aure. Nan manager ya zage ya dinga ɓarin kuɗi da Su Sweet ,goro, da dai sauran su. Fatan Alkhairi sosai aka shiga yima su Jameel wasuma duk baison suba yaƙe kawai yake masu. Yah Nura ne da zugar yan uwa da abokan su suka zo suka tsokane shi tare da tayashi murna, daganan suka hau motocin su suka dauki hanya gidan Aymah. Ido nazaro ganin yanda aka kawata harabar gidan da wasu manyan runfuna da kujeru ko wanne ɗauke da table da mutum hudu zai iya zama akai. Ga abinci nan mai rai da lfy kai kace an shiryama bikin dama. Cikin gidan na fada nan idona yayi tozali da Hajiya Deedee cikin wani mahaukacin farin lace mai tsada,sai sheki take ta zuba murjanan ta. Ga wani coge data buka illahirin farin gashi ta na fulanin usuli ya sakko mata. Kamshi kau kai kace Daga Dubai tazo.. Lokacin da motocin suka tsaitsaya nan fa mutane Harda yan gulma aka hau shigowa ciki dan samu a cika teɓa da abinci da kuma gulma, dan sun tabbata mai gidan ce zatai aure kuma anson mijin na nan to amma miye dalili? Amsar nan kowa so yake ya same ta. Jameel ne hannushi cikin na Dr suka shiga har katon palon da aka kawata da babban carpet. Bakowa ciki sai Deedee da kawarta Hajiya murja Dan batayi gayyaba.. Tana ganin shi ta hau guɗa sosai tana farin ciki da jero addu'a zaman lfy Ana amsawa da Ameen. Daga karshe suka shiga photina dan tarihi. Akunan ta yace Ina Inna mu bazata shigo ba? Cikin raɗa tace kai ta tafi kunya takeji. Murmushi kawai yamata yana kauda kai. Sai da aka gama tashiga daki ta dakko powder da kwalli ta aje gaban ta kamin ta nebo ruwa a yar madaidaiciyar roba ta gyara zamanta kamin ta kece da kuka. Attention din mutanan wajen duka ya dawo kanta . Saida tayi dan kanta ta gaji kamin ta wanke fuska da wannan ruwan ta dauki powder da kwallin ta shafa ,kamun ta dago tana murmushi tace ah toh ubanwa zaice nayi kuka? Gabaki daya kau suka fashe da dariya dan da yawansu sunyi tinanin wani abu akai mata. Jameel ne kawai da Dr da sukason hali basu damuba. Kai ta gilgiza tace" Kukan farin cikine, Fatana Allah ya tadoman da Amanata lfy. Kunson Allah banajin dadi duk da abin farin ciki ya samemu amma abun baiba da cittaba akan ace idonta Bude cikin koshin lfy. Dr yace in sha Allah komi zai tafi yanda akeso kumata Addu'a. Nan suka tashi suka fita suka ci suka sha masu tafiya suka fara tafiya, sai bayan la'asar kowa ya watse kamin Suka haɗa motoci dan zuwa dubo Aymah. Lokacin da suka shiga da bibiyu suka shiga suka ganta har lokacin bacci take cikim natsuwa ba wani fargaba. Dr Abbah ne yayi murmushi yace Alhamdulillah haka muke so ta samu relief zamu iya tafiya gidan Deedee dan gabatar da abinda ke gaban mu kamin ta tashi. Ina Baba Ali?. Manager dake cikin shirin Babba riga yasha uban kyau yace . Yana cen bamuzo dashi ba, shima saida nasa aka dan karamasa ruwa baima samu halarta daurin auran ba ,amma na tabbata zuwa yanzu ya dan dawo daidai zamu iya iske shi gida.. Fatan samun lfy suka mai suka dauki hanya . Abakin dakin da Baba Ali yake sukai sallama suka shiga, lokacin Sadam nata bashi abinci yana jeramai sannu cikin tausayi da jin kai. Koda suka shiga idon shi ya dago ya bisu da ido kamun ya danyi murmushi yace . Masha Allah. Alhamdulillah, wannan ganin dana maku ya tabbatar mun da kun bada auran Amamatu nah wajen mutumin kirki, Allah ya hada kawunan su ya kawar da fitina ,Allah kasa karshen wahalar baiwar Allah nan ne yazo. Kowa da Ameen ya amsa kamin suka shiga mai sannu da tambayar abinda yake bukata ? Yace Babu komi gatan da akai mai ma da lfyr sa baya da tace wa. "Baba zaka iya tashi muje dakin wancen Yaron ko ko? Cewar manager. Ɗan shuru yayi kamin yace "tom yaro nah,ba matsala muje ya yunkura da hannusa daya zai tashi da sauri Sadam dake hawayen tausayin dattijon ya kamashi ya rike suka fito su duka harda DeeDee sukayi dakin Adnan. A kwance suka iskeshi yana kallon sama da alama wani abu yake tinani. Baba ne yabishi da Kallo na tsoro da kuma fargaba gami da tausayi, kamin cikin rawar murya yace" Black Driver Haka rayuwa tayi dakai dama?. Ya salam. Zanso kuga irin zaburar da Adnan yayi ya na mayar da ganin shi kansu, ido ya zubamasu. . Murmushi Baba yayi mai ciwo tare da bude hannun shi dake cure yace" in d@i har ka manta da wannan fuskar wanna hannun daka Yar a ƙasa bana tinanin ka manta, sai dai in dama ba shine na farkon wanda ka fara yankewaba ya karasa cikin kuka mai cin rai kamar sannan abun ya faru. Cikin Wani tashin hankali mabayyani Adnan yace.. Ali Mai Gadi dama kaine.. Deedee Sadan Dr abba Bash. Jameel. Manager Duka ido suka zaro jin yayi magana babu ko alamar karaya halshe. Wani irin gilgiza ya fara na son muke wa zaune yana faɗin. "Wallahi saina kashe ka koda hakan zaizama sanadin Rayuwata...... *Aman uzuri gobe biki gareni na Sst nah*.. ❤️MATAR OGA NA ❤️ PAGE 21 Paid book ...Dukkan su da kallon mamaki suka bishi. lamarin nashi ya daina basu mamaki sai dai tsoro,Ace kai arayuwar ka som Babu nadama bale ka fara tuba wa mahaliccin ka. Kukan kuran da Yayi ne da niyyar tashi a fusace Jameel ya sanya tafin k'afar sa ya daki kirjinsa, nan ya silale yana gunjin ihu kamar mayunwacin zaki. Cikin Rawar da jikin shi keyi in ranshi ya ɓaci ya duka tare da masa wata kafurar shakar data sanya Adnan din ɗauke wuta yayi gum. Cikin sauri mai haɗe da in ina yake masa magana Kaji.. kunya,kakumayi asara duniya kayi ta lahira jahili marar hankali,, wallahii Abun Alfahari ne wa bawa yayi laifi daga baya ya tuba,amma kai ba alamar wannan azuciyar ka sai kudirin sharri,to kasani akan ka zai ƙare in sha Allah, Gabaki d'ayan mu babu mai nufatar kowa da sharri sai khairan , Kuma zamuga Alkhairin Allah a tattare damu, Kai kam babu mamaki in akayi dogon bincike agano asalinka tattaba kunnane ga Sheɗan,In'kuma ka fasa tashi baka haifuba ya jijjigashi kana ya kwala kanshi ga Bango. Ido kawai Adnan ɗin ya rintse,tabbas jikin shi ya daina aiki amma zuciyarshi babu abinda batafasaba ,,kuma yanaji ajikinsa bazai dawwama a hakaba dole ya ɗauki fansa dan zuciyar shi cike take dam da bakin cikin abinda sukai mai... Manager ne dake kallon shi yayi Murmushi yace "Dubu ta ɓarawo daya tak ta mai kaya, A da kasani aikata abinda ba daidai ba amma ayanzu wallahii karyar ka tasha karya, ina so na haɗu da mahaliccina lami lfy sai na bima kowa hakkin sa. Gabaki ɗaya dukiyar Aymah zata dawo hannun mijinta gashinan gabanka ya nuna Jameel,Kai ko gidan nan kafi kowa sanin na Aymah ne dai ko! to zaka tashi ka barshi ta zauna kayanta ita da mijinta mai sonta da son farin cikin ta shida iyayen sa.. Miji ! Mijifa kace,Aymah ce tayi aure,waye ta aura ya karasa yanabin kowa da kallon kaskanci. "Nine nan mijinta,mai sonta domin Allah,, ban aureta ba dan dukiya ko kyau A'a inason maye mata gurbin farincikin data rasa ne daga gareka. Dariya sosai Adnan yashigayi datavba mutane mamaki . Cak kuma yatsaya kamin yace "lallaima yaro bakason wuta ba saika taka.MATAR OGA taka zaka aura? Hehehehe,Wlh da mafi girman kuskuran da zakayi kenan arayuwarka da zai hanaka zaman lfy kaida matsiyatan iyayen ka masu azabar kwaɗayi. Shawarar anan ka bar wannan mafalkin. Saboda ban mallaki Aymah ba babu kuma uban daya isa ya mallaketa,Iyalan A/k bazasu taɓa jin dadin rayuwa ba har abada da bakin ciki xasu mutu,,Saboda bashi da mutunci Mutun ne mugu mai son...Zafafan marukan da Baba Ali ya yarfamaibne yasashi tsayawa cak. Jikin Baban har rawa yake idon shi na zubar da kwallah ya hau fadin. " karya kake Wallahi!! karya kake,wannan auren mutu ka raba ne agaban ka zamuyi komi in sha Allah,Da munyi niyyar samarwa Aymah gida ko ince mu canzamaka gida tinda nan mallakinta ne bana ubanka ba, nasani kuma kaima kasani,amma ayanzu in sha Allah kana nan zaune kamar Dabba zakaga yaran Aymah suna yawo cikin gidan nan harma suna jifar ka da kalmar Mahaukaci,banza dabba marar iklasi. Ku wuce muje,kaima a haka xamu barka ka kare rayuwarka a gantale,kai ba kai ba mai raiba,, kai ba matacce ba suka juya suka fara fita. Deedee ta kalle shi ta kashe ido ɗaya kamin tayi kwafa ta fita da kudiri sosai akan ta. Abakin kofar suka tsaya Manager yace" Yanzu Mama aikin Aymah ne agaban mu, in komi ya kammala in sha Allah anan zamuzo abama kowa dukiyar shi dan harda waccen matar tashi, Mama Adnan ya wuce duk sanin ku a mugunta,sai dai lokaci yayi kwaji daga gare ni. Fatan Alkhairi sukai mai da gdy akan ƙoƙarin sa . Bakomi yace yana fita Jameel da Dr Abba suka mara mishi baya . Deedee tayi daki wajen kawarta Sadam kuma ya kama Baba dayakejin soyayyar sa har cikin ranshi suka tafi d'akin da aka ware ma Baban suka zauna suna fira har bacci yayi gaba da Baban kamin Sadam ɗin ya fito. Sai da ya tabbatar babu mai kallon shi kamin ya fada dakin Adnan ya mayar ya rufe. Robar da suka sha Lacasera da daddare ya dauka ya cikata dam da fitsari kamin ya shiga dakin Adnan din ya iskeshi kwance sai magana yake kasa- kasa da ba'ajin Miyake cewa. Katashi kasha Sadam yace yana ɓata fuska. Da kallo kawai ya bishi yana dauke kai. A fusace sadam din yace "Wallahi sai kasha dan tafiya zanyi, Sadam yace yana haye ruwan cikin Adnan din kamin ya ɗago kanshi,ta karfin bala'i ya danna mai robar nan cikin baki,duk yanda yaso janyewa kasawa yayi saboda hancin shi daya riƙe. Ganin zai mutu yasa ya hankade baki yashiga sha. Saida sadam ya tabbatar ya kusa shanyewa kana ya ɗauke ya mike yana faɗin" matsiyaci, kamar ni ace ina fitsari a toilet baccin gakanan babban shaiɗani ina ma wahala,ai'daga yanzu kagama shan ruwa wannan ruwan fitsarin. nawa shine abin shanka azzalumi. Akaro na farko Adnan ya kece da uban kukam dake cike da zallar bakin ciki da takaici,gashi yanzu yama kasa tashi sakamakon dukan da Jameel yamasa. Dariya sadam yasa kamin yaja kofa yayi tafiyarsa zuciyar sa fess, dan yayi alkawari sai Adnan yaji ga jikin shi, hukuncin zai mai na lalama. Jameel kau a hanyar su ta zuwa Asibiti ne akama Dr Abba waya akan ta falka ,gudu ya karama motar suka isa cikin lokaci sanye da kayan su na mutunci. Abakin Asibiti suka tsaya suka sai kayan fruit kana suka shiga dashi. Kai tsaye dakin da take suka shiga inda suka iske numfashin nata babu dan laifi ya daidaita. Jameel ne yayi tsaye kanta cikin tausayaawa. A'Hankali yace "sannu my wife. Fararan idanuwanta dake lumshe ta buɗe ta zuba'mai, Cikin sassanya murmushi ya dagamata kai yace" yes my wife,sannu ,mikikeji,ina ke miki ciwo? Lamarinshi mamaki yakebata Jameel akwai karfin hali. Azahiri kuma Murmushi ta dan sakar mai tana lumshe ido da kaudasu daga kanshi. Ashagwaɓe yace. bakyaso naji natsuwa dan Allah, Kimin magana Allah zan miki kuka uhm uhm ya fara shaagwaɓa yana dire kafar sa a ƙasa .. Wani irin zaro ido tayi lamarin yaron Nan nason kasheta tin kwananta basu tafiba. Dr Abba ne ya matsa kusa da ita a hankali yace" sannu Ummu Aymah, ko bakyajin zaki iya magana ne?. Ido ta lumshe hawaye na zubomata,dan bala'in nawie kirjinta ke mata, A'Hankali ta ɗora hannuwanta akan kirjinta kamin kuma ta yarfasu alamar zafi. Da sauri Jameel yace" nawie wajen ke maki. Da sauri ta daga mai. Cikin rauni da tausayi Yace" sannu in sha Allah zaki warke ba,da izinin Allah kwana kusa,.. Dr Abbah ne yaja hannunshi waje yace" kai aikin kafa ya fara,ya kamata ka dan ragemaga kayanta na ciki . kadai gane?,sala kuma kaje inda ba'ace kajeba daganan kasata motsa ciwon. Ido ya zaro kamin kuma yayi murmushi da sauri ya juya.. Dr Abbah ya jawo hannushi da ƙarfi suka fuskanci juna. Ido suka hada suka fashe da dariya. Cikin zaulaya yace" munafuki wallahii har ranshi yaji dadi amma wai ni yakejima kunya bazai nunaba ,ni zaka nunama tsoro kakeji? Dan dariya Jameel yayi Yace" A'a wallahi banajin wani tsoro,daga sadda nawie Amarci ya hau kanka kaima aikason dole lafiyayyen mutum ya samu wasu gudummuwa daga sassan jikin sa ba,sannan nawie ya hauka wanda wajibin ka ne ka sauke ,amma fa wannan tinanin na mai hankali ne,ni ban lamunce wani yayi jinyar matana ba saboda ina da raina kuma gani tsaye da k'afana, Sannan komi zan iya ajewa domin mallaka mata lokacina wannan ba damuwa bane,. Sosai Dr ya rungumeshi yana fadin" hankalin ka da iya kalaman ka na karamun kwarin gwiwa son kasancewa dakai Jameel, kamata duk abinda yadace saika fito. Ngd yace yana sanya kai ya shiga. Bayan ya rufe kofar ya sanya key kamin yayi tsaye akanta yana zubamata mayun idanun sa masu bala'in kyau da sheki. Ido ta dan d'ago tana yamutse fuska . Da sauri ya janye nashk idon akanta kamin ya matsa kusa da ita yaja kujera ya zauna tare da kama hannuwanta masu tsananin taushi ya fara murza tafin hannun cikin wani salo mai narkar da zuciya. Hankalinta a tashe take kallon shi tare da zaro mai ido alamar ya daina. Murmushi yayi ya mike tsaye yana jan kumatun ta yace "Da mijinki kike tare ki saki jiki kinji my Aymanah. Magana takeso tayi amma bazata iyaba ,wai mike damun sa kodan yaganta kwance bata iyama kanta komi ne shiyasa yake sarrafata yanda yake so? Shikam Jameel baibi takan kallon da take mai ba illah ma labulayen daya saki kamin A'Hankali ya ɗan tasota zuwa jikin sa. Gabaki dayan su saida suka sauke ajiyar zuciya da duk sadda jikinsu zai hadu sai sunji wani irin shock.. Ido ya ɗan lumshe kamin ya zubama zef din rigarta ido,tinanin farko daya zomai shin taya zai iya cireta, sama zayyi da shi ko ƙasa?. Ya rahman yace tare da daurewa ya sanya yatsunsa yajashi zuuuuuu har kasa saiga rigar ta ɓalle duka ta rabu biyu. Baki ya rike yana faɗin "sorry ban iyaba na lalatamiki( A tunanin sa ɓarna yayi😜) Aymah kau a wannan gaɓa wani mugun tashin hankali takeji, wai ya Jameel zaimata haka dan kawai tabashi fuska shikenan sai akace aure aka daura masu da zai iya taɓa jikinta yanda yake so harda cire mata riga to mizaigani?. Jameel kau gabaki daya lallausar farar fatarta ta tafi da imaninsa,bayan Aymah fari sol,kamar yanda jikinshi yafi fuskar sa haske haka itama jikinta yaci uban fuskar ta so zata goma haske,ga wani tsantsi da laushi na fatar. Ya salam yace yanajin yanayinsa na canzawa. A hankali kuma ya dan dai-daita tsawon shi zuwa nata ya rungumeta tsam, tare da shafa bayan nata,Inda ƙarfen brah din dake wajen yashiga lalube,idon shi daya tara kwallah jaraba ya kai wajen karfunan daya ganine yasashi sake bude ido har ya gano ta yanda suke. Dakyal ya iya balle su. Ido ya daga ya kalleta yaga kanta kasa yake amma kuka take sosai.. Wani irin tausayi ta bashi da kuma sake burgeshi da tayi, wannan ma ya tabbatar mai da macace mai kamun kai da kunya. Akan kujera da yake yakoma ya zauna yana sauke ajiyar zuciya da lumshe ido kamar wanda yasha giya. Hannunsa yasa kamin ya sake kama hannuta amma ta fizge cikin mabayyani fushi ta zubamai idonta dake cike da ɓacin rai da takaici.. Sake kaiwa yayi Akaro na biyu amma ta fuzge. Kujera ya tura baya tare da zubewa kasa warwas ya haɗe hannayen sa yace" Aymah kisa aranki babu haramun a abinda nike miki,wallahi wallahi bazan iya amfani da jinyar kiba na cutamiki, Aymah abubuwa sunfaru a yinin nan wanda kwanciyar ki ce sanadin su,Aymah yakamata ki ƙarema shigata kallo kison cewa sabon ango nike,bawai hakanan nike kama jikinkiba ke kinson ba ɗabi'a nabane sai dai in akasi aka samu, Dan Allah kibani dama na kula dake domin ke din halaliyata ce kinji ?..... Jajayen idanuwan ta dago tana kallon fuskar shi. Tabbas bataga karyaba a kalamansa,amma miyasa tun yanzu ba za'a bari taji saukiba😭(uwaki Aymah mai kan kwakwa zakison muhimmncin haka agaba muje dai zuwa). Lallashin ta yashigayi saida ya tabbatar jikinta yayi sanyi kamin ya mike ya kai hannu jikinta yace" kin aminta na ciremiki akan umarnin Dr saboda zafin da kikeji.. Ido kawai ta lumshe tayi kasa dakai batare da tace komi ba. Abunda tayi yabashi tabbacin amincewarta hannu sa har ɓari yake wajen kaiwa jikinta ya shiga sauke rigar A'hankali dan samun damar zare ta ciki. Ya Subhanallahi yace da karfi yana juyawa , tare da matsawa sosai ya wani rungume kyaure gam yana rintse ido da bala'in ƙarfi.... ❤️MATAR OGA NA ❤️ UMMY AYSHA Page 22 ""Idon data lumshe ta bude tare da dagowa ta zubama cikakkun kirjinta da suka bayyana ido. Batare data gyaraba takai kallonta gare shi inda taga jikinshi har wani bari yake sai neman fasa ƙofa yake tsabar riko. Cikin rawar murya Sosai Tamkar mai zazzaɓi yace" Please Aymah dan Allah ki ceci rai ki mayar dasu wallahi...shuru yayi yana sauke ajiyar zuciya a zafafe ,Yakai 3mnt kamin kuma A'Hankali ya silale ya zauna batare da yajuyoba sai gumi ke tsattsafo masa.. Aymah kau karamin Murmushi tasa kamin ta cije lips dinta ta cire brah din , Tare da sata kason pilon datake akai. Na shanunta da sukayi suntuma suntuma kamar kan Jameel ta mayar cikin riga batare da ta gyara zip din ba dan bata da Wannan karfin ta koma tayi kwanciyarta dakyal tana lumshe ido,ga mararta cike take dam da wani fitinannan fitsari amma batajin zata iya magana. Jameel kau ji yayi kamar ya ɗora hannu aka ya zunduma ihu,zai iya rantsuwa da Allah baitaba ganin tsiraicin mace ba ko alama,Lallai Aymah babbar mota ce da Jahilin mutum n kawai zai iya rasata ya kuma zauna lfy .Da yaganta cikin kananun kaya ya furgita ina ga yanzu daya ganta kasiyatum Ariyatun, ya Subhanallahi,dama haka kike yakarasa yana damke mararsa dake cakar shi tana barazana ga rayuwar sa. Kwankwasa kofar da aka fara ne yasa da karfi ya dago kanshi tare dayin sauri ya mike tsaye. Jikinshi yabi da kallo wata irin kunya na rufeshi, cikin sauri ya sake baza babba rigar shi tayrr da kallon inda Aymah take asace . Ganin ta mayar da idonta ta rufe yasan bacci ta koma. Ido ya juya tare da matsawa kusa da ita yace" Aymah to taya zamuyi jinya a haka,majin'yacin naki mai masifar rauni ne wanda kuma kece sila, wallahii kin hadu Aymah nah da bansameki ba danayi.babba asara a Rayuwata,yanzu nan komi nawane.. kwaɓe fuska yayi kamar zayyi kuka yakuma daga hannu sama yana fadin" Allah ka gusar da bukatana na gama biyan ta baiwar nan taka, Allah kabani dama juriya da jajircewa Akan baiwar nan taka, wallahi AYMAH kina da sura,banson kowace mace ba saike, Allah na godema daka rufe idona ka rufe ganina akan kowa sai akan matata,Shiyasa daka tashi bani sai kabani Zarah acikin taurari, ina sonki my AYMAH , ina son kayan alatunki sunyi daidai da tsarin Rayuwata,,yana daya daga abinda nikeso inason su sosai kibani dama zan kula dasu sosai ya fada yana rufe ido cikin kunya kamar tana ganin shi. Aymah kau sauran kaɗan dariya ta kufcemata lallai jameel za'aga rawar kafa Ashe baida kunya kum haka ya iya rattafa zance,Hmm Allah yashirya kawai tace kamin kuma kadan kadan ta fara motsawa. Da sauri ta juya kai dan kirjin nata wani mahaukacin casu yake.. Auchhh!! karki karni dan Allah daidaitamun su yace ashagwaɓe yana zubama su ido. Idonta ta ware akan shi kamin tamai alama da minene yake cewa?. Idon shi yashiga juyamata kamar yanda Deedee keyi in taga abu. Sassanya murmushi tamai akaro na farko dan fuskar shi tamata kama data Deedee tah,Yau ɗaya tayi kewarta . Ahhh washhhh Aymah kinyi kota ina, karki karni dan Allah yace yana kashemata ido daya . Cikin shagwaɓa ta ɗan sake bankaro kirjinta tare da ɗora hannunata akan marar ta . Wani kafurin yawu ya haɗe jaraba kwance a idon shi yace "Ya salam! mikekeso ? Yakarasa yana ƙara kallon hannun nata. Da hannu tamasa nuni da Toilet. Ido ya dan waro kamin yace zaki shiga. Kai ta dagamai tana yarfa hannu alamar A matse take. Ohk ohk bara nakira akai ki .. Ido kawai ta zubamai kamin ta Juya kai. Yana kai bakin kofa kuma ya tsaya cak Tare da nazarin yan'zufa duk wanda zai kaita saita kalle mishi ita ,ina bazai yiyuba ya zama dole komi zai faru ya faru amma bazai yarda wani yayi aikin dayayi alƙawarin yiba.. Kofar ya bude Dr Abbah ya dube shi yana ɓata fuska yace" Jameel aikin 10mn din ne ya daukeka Wannan lokacin?. Hannu ya yarfa yace" banson ya zanba ,Dan Allah fadamana amma wlh inajin wani masifaffan feel... Daya hanani kasa komi. Sama da kasa yabi Jameel din da kallo ganin sa duk baya hayyacin sa. Da sauri Jameel din ya juya yana sake buda babbar Rigar sa da saki karamin tsaki dan sai yanzu ya fahimci ya saki layi. Dariya sosai Dr yashigayi data sa mutanan dake wucewa yimasa kallon mamaki dan mutum ne da baka ganin hakorin sa. Cak kuma ya tsaya yace" wallahi ka bada maza Jameel,bugawar farko ace an kaika kas,ashe dama jarumtar taka a bakine, Jameel jibi kayanka yanda ka.ɓatasu da sp....to sai ka wuce kaje gida kayi wanka dan lokacin mangariba ya kusa. Bala'in kunya yaji kamar yaci babu, wai dama haka yake koko ganin Aymah yasa shi shiga wannan yanayin, Kai wallahi ganin tane a bayyane ya tadamasa tsohon tsumin sa. Dr Abbah Yace" Jameel wallahi kana batamana lokaci,in akwai abinda takeso kaje kamata ,ka wanke mata baki ,ka ɗan bata fruit din taci kadan na fadama bamaso za'ama mutum aiki yaci abu mai nawie in ka sake 30mnt wallahi bazan bari ko ruwa ka bataba ya rage naka in lokaci Yayi baka aikata komiba zansa amata wallahi kuma babu yanda zakai. Afusace Jameel din ya juyo ya fara zaf gamai harara kamar idonsa zai fado kamin ya banka Kofar yashiga ya danna key. Dr kau dariya yashigayi yana kada kai wallahi sha'anin angoncin Jameel akwai ban dariya .. Aymah kau tagaji da jira wani kuka ya zomata yanda take cikin wannan halin kowaye zai kamata tanaso, ita burinta kawai akaita ta sauke lodin daya cika marar ta. Da Sauri ya karasa wajenta yana fadin" sorry My wife nine ko?. Shuru tayi sai sauke ajiyar zuciya take.. Hular shi ya aje yana dan satar kallonta tare da cire babba riga ya aje gefe yabi jikinshi da kallo,babu wanda ya isa yace ba fitsari yayiba Saboda lema.. Cikin dubara ya ɗauketa cak, ɗauka irin ta jarirrai.. Ido kawai ta zubamai wannan kyakyawan sajen nashi na tafiya da imaninta,shikam kai ya dauke gefe dan kallonta zai iya sashi sakinta su tuntsire batare da sunshirya ba. Koda ya buɗe toilet din komi tsaf yake. Ya ilahi yace sadda hannushi ya fara rawa da zai cire mata panta. Ido ya rintse da masifar karfi ya ciremata ya saitata akan sit din kamin ya juya baya yana taune lips sosai kamar ya hudasu.. Itakam harara ta zubamai ganin saida ya gama bata wahala kamin ya mata abinda takeso.. Ganin an ɗauki lokaci bata ko motsa ba yasa shi mikamata karamar shower dake gefe. Kallon shi tayi tana tabe baki alamar badasu zatai ba. To mikikeso?. Babban pampon ta nunamai da lips dinta. Ohk nashi kikeso? Nan ma kai ta dagamai alamar A'a tare da juyamishi kai. Kamar yayi kuka Yace'' Aymah banganeba Please kimin abun da zan gane. Wayarshi data kusa faɗowa ta zaro ta shiga message tayi rubutu kamar haka .. ( *Bana using da ruwan sanyi ka taramin masu d'umi*) Kan shi ya dafe yace" tom shikenan. Wajen pampon ya gusa ya tarbamata yanda tace kamin yazo yabata. Tana karɓar butar ta sakeshi da ƙarfi jin kirjinta zai fashe . Sassanya kuka tasa tana kwantar da kanta akan jikinshi da yarfe hannu alamar bazata iyaba. Kan uba nizan maki yace yana gwalo duka idanuwan sa. Cikin dakiya ta dago kanta tare da sanya shower ruwan sanyi ta tsarkake kanta tana cije baki ta mike tare da dafa bango zata fita duk da jirin da takeji.. Da sauri ya kai hannu zai kamata cikin fusata ta juyo cike da rawar murya tace''karka taɓani Jameel baka da amfani, ka rubutaman takardata dan baka dace daniba , Tinda ka kasa bani lokacin ka ina cikin wannan yanayi...Tul tul tashiga tari lokaci daya jini ya ballemata ta hanci da baki. Suuu tayi zatafaɗi ya daka tsalle yayi kanta hankalinshi a bala'in tashe ya fara jijjigata yama rasa ya zai mata. Cikin ihu ya fara jeramata kira amma ina idonta rufewa kawai yake neman yi. "Tir da halina wallahi,Tabbas ban cancanci zama miji gareki ba nima nasani,wallahi wallahi narasaki bazan yafema kaina ba Aymah, wallahi nayi Alkawari akaro nabiyu dan Allah kitaimaki rayuwata yace cikin tashin hankali rigar tashi kam duka ta lalace da jinin ta,idama cire ta yayi tare da dorata jikinshi ya fara kwakumeta cikin gushewar Hankali kai kace nono zai bata. Aymah ! Aymah tashi,wallahi zaki tonaman Asiri, Dan Allah kirufaman Asiri Aymah nah karkimun haka dan Allah raina fansane ga lfyn ki Aymah kitashi, Wallahi kika mutu sai na biki,domin zamana bashi da amfani, Deedee'n ki zata tsanane,iyayena zasu tsaneni,mutanan da suka bani ke zasu tsaneni, Dr Abba zai tsane Ni Kinji. Ajiyar zuciya kawai tahau saukewa kamin ta dan bude ido ta kalleshi kwallah na zubomata maraicin datake ciki kadai ya isa ya sata kuka tin dazu suke abu daya ita mace bataji kunya ba tinda ya fadamata yazama mallakinta tazama nashi ta bashi ragamar rayuwarta, Amma zai tsayamata wasa da hankali. Ganin ta bude ido yasa ya mike da sauri yana fadin Alhamdulillah yah Allah. Jikinshi har rawa yake wajen dorata a kujera dake ciki kana ya shiga hada ruwan wanka,zafi zafi yake komi,cikin sauri ya ciremata rigar nata tare da cire sket din baki daya. Zo kuga sauke ajiyar zuciya wajen Jameel, dauriya kawai yake amma Aymah ta kashe shi tagama da rayuwar shi. Tsabar rudewa da killing yasomata wanka saida ta lura ta mirro kamin ta janye ta nunamai sabulu. Zanso kuga yanda akai wannan wanka mai cike da laguje laguje da neman sanya matashin Saurayin nan sumewa,dan sai yayi nisa a wankan sai yaja numfashi da ajiyar zuciya da karfi kamin jinin jikinsa ya dawo aiki.. Saida yagama mata komi kana ya nadeta a sabon towel din dake wajen ya fita da ita ya gyaramata gadon kamin ya kwantar da ita yana tinanin abinda zai samata. Lokaci ya kallah a kallah sunci fiye da 30mn har an'mafara kiran Sallah. Da sauri ya ɗauki kayan fruit din ya dan bata kamin ya bata ruwa ya gyara mata jikinta yasa ta fuskanci alkiblah daga kwance ta gabatar da sallolin da ake binta.. Toilet din ya fada rigar shi yabi da kallo da suk ta ɓaci. kai kawai ya gilgiza yafito ya dauki Babba rigar yasa ya bude kofa zai fita dan zuwa ya tsarkake jikin shi ya canza kaya. Ido hudu sukai dasu Deedee gabaki dayan su harda Maman shi dasu Manager Dr Abbah tsaye gefe yana zare ido. Deedee kau kuka ta fasa tace *wannan ai shine ƙudira sama liman da wawan zama*, to kai jinya kayi ko fyaɗe kamata, Jamilu jibi rigar ka jibi shigar ka .... ❤️MATAR OGA NA ❤️ UMMY AYSHA Page 23 ""Jameen kau Gabaki ɗaya kunyar duniya ce ta rufe shi, kai Deedee bataiba akwai taɓargaza,cikin satar kallo ya kalli Inna su dake bin rigar sa da kallo bata ko kyaftawa.. Idon da suka hada yasa da sauri ta juya kanta gefe gabanta na bugawa. "Jeka shirya Jameel kayi sallah kaji manager yace yana ɗan murmushi. Wucewa yayi Dr Abba na mara mishi baya yayin da Deedee tace. Kai kutsaya nan naga sai ƙoƙarin turo kawuna kuke kamar macizzai ai kwabari nashiga naga wane yanayi take ciki ko. Da to suka amsa suna yaba rikicin Deedee dama ba shigar zasuyi ba fa. Da sallama tashiga tana sake rushewa da kuka tace "Aymah ashe shegen yaron nan hawan ƙawara yamaki,kai jama'a kaga mutum sumul sumul kai akas ashe mugune.Yo aini in an'shekara ceman Jameel zai iya bugama mace iska wallahi ba yarda zanba sai gashi naga ishara,Yo wannan ai dole likita yazo ya dubaki dan wannan jini yafi karfin na budurci sai dai in mahaifarki ya taddo dogon banza dogon wofi.. Aymah kau tanajin surutun Deedee dakyal ta dan fara bude ido kamin ta saukesu tass akanta. Dan murmushi ta saki tana mikamata hannu cike da so da kewar Dattijuwar data zame mata uwa uba . Hawaye ta share tace. "sannu Aymah ciwo biyu baiwar Allah,nidai kam baccin ɓargona ya fara taushi danayi jinyarki, Da ace da baki ake jinya da wallahi sai dai aga kin mike ras to amma gaɓɓai ke aiki. Aymah kau cikin ƙarfin hali taso magana nan danan jinin nan ya sake ɓallemata. Ido Deedee ta zaro kamin ta kwallah ihu agigice tana fadin" lukuta kai dokta, zo dan uwarku zo kuga nabani wallahi ba shaketa nayiba aduba matakan tsaro na na'ura da kukesawa kuna ganin mutum da aljan dan Allah ashe Jamalun Deedee ba fyaɗe ya aikataba hifufuuuuu ni Deedee mai kunun aya za'a ɗaure ni kwana na bai kareba ta karasa cikin gaskiya da gaskiya tana rushewa da uban kuka. Aymah ta galabaita sosai Wannan aman da tasake hakan yasa tayi luuuuu numfashin duka ya ɗauke. Tashin hankalin da Deedee tashiga bazai faɗu ba, da kyal da rarrafe dan kafarta bata daukarta ta karasa wajen kofa ta buɗe. Ido ta zubamasu kamar mage takasa magana. lokacin yayi daidai da karyowar kwana Dr Abbah da wani DR Cikin sauri da zafin nama . Da hannu ta dinga nuna masu ɗakin aguje suka shiga yayin da Maman jameyel ta kama Deedee dakyal ta mike tsaye kafarta na wani mahaukacin rawa , hawayen ma sunki sakkowa yanzu sai buguwar zuciya balle taji dadi, kawai tana ganin Aymah ta tafi ta bar ta dan bataga alamar tana numfashi ba.. Dr Abbah kau yana ganinta cikin wannan halin aguje ya fito ya fara kwalama Nursing ɗin kira . Bayan sunzo ya umarce su da su shirya Emergency theater yanzu. Okh sir! suka amsa a guje suka wuce. Jameel Kai tsaye officer din Dr Abbah ya faɗa som zuciyar shi ba daɗi. Yana turawa Dr Abbah ma na turawa rai bace yace" Jameel miye haka?. Dan kallon shi yayi kamin ya kawar da kai yace" kaima ka yarda da rikicin tsufan ta,? wai miyasa Deedee ke sakin magana ne duk sadda tazomata,dama A riga za'aga alamar namata fyaɗe? Hmm kajifa yafada yana cije lips ɗin sa sosai cikin takaici. Ajiyar zuciya Dr Abba ya sauke tare da bashi wata leda yace *"ga kayan nan na sawomaka ka shirya kayi sallah, sukuma wayan nan sai kaje kasamata. Karba yayi yamasa gdy ya aje saman kujera yashiga Toilet dan tsarkake kanshi.. Abinci yafita ya samo mashi dan yaga baici komi ba koda suka je gidan Deedee. kamin ya dawo ya aje da niyyar in jameel din ya gama yaci Wata Nursing ce dake reception ke sanar dashi dakin mai Number 5 akwai matsala mafarin fitar tashi kenan ya haɗu da Dr Abbas suka tafi Ashe Aymah na cikin mawuyacin hali. Jameel kau bayan yayi wanka ya ɗauki haɗaɗan pakistan ɗin daya saimai yasa kana ya fara Sallah. Yana cikin Sallah yaji wayar da Abokin nashi keyi,dakyal yagama yana sallamewa ko Addua baiba ya fita. Daidai lokacin da aka turo Aymah dake sanƙame akan gado zasu shiga da ita. Yah Allah yace cikin karaya yana kama gadon aka shiga da ita. Wasu hawaye ne masu zafi suka zubo mai na zallar tausayinta da kuma shaukin so da begenta daya nunku a zuciyar sa. Cikin rawar murya ya faramata Addu'a. Yah Rabbil Alamina kasa aikin nan ya zama silar yayewar damuwarki Sweetheart, Allah ya koro da farin ciki cikin rayuwarki Aymah,ke mutuniyar kirkice bazaki taɓa wulakantaba in sha Allah,Ribar hakurin ki na nan kusa in sha Allah, Allah yabada Sa'a matata ya karasa yana sakarmata wani zazzafan kiss a goshi. Gabaki daya saida matan dake wajen jikin shi yawani bada yarrrrr dan sun fahimci sahihin son da yakemata wanda maza ke wahalar bayyana wa a yanzu gashi dama sun mugun dace da juna.. Dr Abbah ne ya shigo cikin shiri da wasu Dr's A bayan sa.. Dan ɓata fuska Jameel din yayi cikin kishi daya gansu tare da haɗe fuska. Murmushi Dr Abbah yayi yana buga kafadarsa yace" in sha Allah komi zai tafi daidai kaji,ka koma wajen su Deedee ka lallashe su. Bayaso ya shiga hurumin su da bazai fito ba. Amma haka ya daure ya fito kofar farko yayi zaune yana buga tagumi. Ganin babu inda zaman zai kaishi ne yasa shi tashi ya hau wani carpet din dake gefe ya fuskanci alkiblah ya fara sallah isha kamin ya ɗora da nafila yana fadama Allah damuwarshi da nema mata sauki akan aikin da za'amata. Kimanin awa daya biyu amma basu fitoba Ya salam zuciyar shi har wani dakan sittin sittin take. Lokaci daya Jikin shi ya fara rawa tsoro ƙarara ya bayyana ga fuskar shi. A kasalance ya mike ya turo kofar ta biyun ya fito. Gabaki dayan su yanda suke haka sukayo mai cah kamar k'adangarun da sukaga Taliya da manja. An kammala Jamalu? Deedee tace hankali tashe dan tin dazu datayi mutuwar tsaye bata sake maganaba sai yanzu. Kai kawai ya gilgizamata tare da komawa gefe ya zauna yanajin wani sanyi na huda kowace ƙofar huda gashin dake jikin sa. Karfe 10:15pm aka bude kofar Dr Abbah ya bayyana yanata hada gumi dashi da abokan aikin nashi .. Rufamashi sukai kowa tambaya yake ya lfyn ta. Alhamdulillah da sauki munyi cikin nasara sai fatan Allah ya tadata lfy, yanzu muna bukatar akawomata mayafi.. A zabure Deedee tace ba komi akwai ɗan buje jikina bari in baku wannan , kanma suce wani abu ta fizge nata ta bashi tare da sauke mayafinta kasa. Jameel ta kallah afusace tace to mata maza zazzabin gadon ne ya lulluɓeka ko kanajin ana faɗin an'kammala kai jama'a nikam badan ni na wanke kaba na kaika akama shayi wallahi da cewa zanyi mata mazane... Banza yamata ko kallon ta baiba Saima Hankalin shi daya mayar kan kofar har inda yaga an turo gadon da Aymah ke kwance akai kamar gawa. Da sauri ya mike ya isa wajen yana zubamata ido. Tayi wani fresh tana sanye da blue din rigar asibitin sai Yar hula mai net da aka tura gashinta ciki, fuskar nan tata fayau,gashin gabon goshinta kam yayi luf-luf kamar wanda yasha ruwa. Gadon ya kama A'hankali suka dinga turata har dakin da aka ware mata a vip site. Fadar tsarin wurin ma ɓata lokacine dan komi yaji,ga na'ura sanyaya daki (AC)sai busawa take. Sadda suka shiga Jameel yayi mata shimfida suka samu dakyal suka kwantar da ita a kai tare da sanyamata wasu naurorin a jikinta . Dr Abbah kam Su Deedee yama iso suka shigo suka dubata cikin natsuwa kana suka fito. Jameel ya bisu abakin wajen suka tsaya yanata watsama Deedee harara kasa kasa batama gansa ba. Inna su tace "Wannan yaron Dan Allah ka kula da ita duba da halin da take ciki,na tabbata in itace zatama abinda yafi haka kaima shedane.. Deedee tace "ah'toh Baraka kwara dai ki waye ki faɗamasa gaskiya tinda ni ya rainani, kullum kanki ƙasa kamar k'unk'uru waike dan fari kike jima nawie, kuyita cutar kanku kuna wani sussun ne kai ,Ai Wlh babu wanda yaman nakuda babu wanda ya isa yaja kuma na ɓoye soyayyar yarona a cikina ta kumeman ko ba hakanan ba Habu? Yo koshi yarone tsayama kuga. kamoshi nan kamoshi nan ta fada tana jan gemen malam. Habu. Gabaki dayan su dariya sukasa har Jameel dake cikin damuwa saida yayi murmushi. Tace yawwa Alhamdulillah zamu tafi zan bada sako Sadam ya kawoma na abinci da abun sallah, zai biya ta gidan ku ya hadoma da yan kayan buƙata.. Dr Abbah yace su barshi ya tanadar mai komi gobe sun kawo . Gdy suka mai suka wuce. Ciki ya koma yaja kujera ya zubamata fararan idanuwan sa masu shegen kyau ko kyaftawa bayayi. Dr Abba ne ya shigo da kaya A hannusa ya aje tare da ma Jameel Bankwana akan zaije gida anjima Dr Abbas zai shigo ya dubata. Kallon shi yayi yamasa gdy tare da fadin wannan kayan da aka jibgamata bai yawaba kuwa . Ido ya zaro yace bakaji Sanyi ba Jameel. Kai ya sosa yace zan Iya ragemata su .. ❤️MATAR OGA NA❤️ UMMY AYSHA Page 24 Ido Dr abba ya zaro yana nuna mishi cttv camera dake ciki kota ina dan lura da abinda ke faruwa daga majin yacin su cikin sauki. Ɗan tsaki yayi yace amma acen ɗakin farko babu ko? Dr yace "Baka da gaskiyane da kake tambayata acen babu ko kayi wani abun ne?. Ido ya dan juya yana hura hani yace "ai halaliyana ne koma miye yafaru lada zamu samu. Murnushi kawai yayi yace lallai yaro yayi baki jiya kadai da doramasa igiya. Murmushi sosai Jameel yayi yace Saima ta warke. Sai da yaga Jameel ɗin ya ɗan natsu kana yamasa sallama ya fita yayin da Jameel din ya rakashi ya rufe kofar. Toilet din ya shiga ya watsa ruwa ya ɗauro alwallah ya fito. Akan kujerar da yake akai ya zauna yana daukar Drinks ɗin exotic ya sha dan bayajin cin komi . Sadda ya gama ya tashi ya hau sallah yana nema mata sauki wajen mai duka. Har ƙarfe ukku yana zaune kana ya farajin kamar motsin ta ,yana mikewa yaji ana bugo kofar . Dr da zai dubata ne kamar yanda aka cemai, nan ya sake dudduba jikin nata ya mata allurai da sake samata sabon drive bacci ya karayin gaba da ita. Shikam Sai da ya gabatar da Asuba kana ya samu ya dan kwanta jin yanda bacci ke fuzgar sa. Bai jima da kwanciyar ba ya farajin nishinta kasa kasa tan fadin" Ruwa. A zabure ya mike ya isa inda take,idonta fess akan shi, haka shima nashi da suka canza kala zuwa na mai bacci ya zubamata su a narke,cikin kuma farin ciki yace" sannu kin tashi,mikike so? ina ke maki ciwo? yanzu kin fara magana? Dan murmushi tayi tare da jan hannunshi cike da tausayin sa dan tama jima da tashi taga ya dan fara bacci. Cikin muryarta ta majinyaci tace "sannu da kokari rabbi yabaka tukuicin Aljannah kamun bautar da bazan taɓa mantawa ba, kana ka nunaman kai ɗan Halak ne daya gaji karam ci. Murmushi yayi yana sumbatar hannun nata yace "duk cikin Hakkin kine daya rataya wuyana, so wannan ba damuwa bane yiwa kaine kinji... Ido kawai ta dan lumshe mai cike da mabayyanin so. Gira ya daga yace toya muje ayi wanka? Harara ta bankamai ya saki murmushi da faɗin ina zuwa ya bude kofar ya fita. Office din Dr Abbas din yashiga nan yaganshi yana sharara bacci,sallama yamai bayan sun gaisa ya fadamai ta tashi. Tare sukayi dakin Aymah ya dubata tare da faɗin" Alhamdulillah aikin nan yayi kyau yanzu duk zamu ragemata wayan nan karafunan ya karasa yana jajjanyesu,tare da kiran wata nurse tazo ta fitar mata da robar fitsarin dake jikinta wacce tinda aka fito da ita akabar ta da ita. Kallon Jameel yayi yace zaka dan mata brush ka wanke mata jikinta da ruwa mai ɗumi, amma sai kasa yan dubaru ba'ason tana motsawa sosai saboda ɗinkin mukesl ya haɗe... In sha Allah yace ya rufe kofar kamin ya cire rigar jikin nashi,ya aje gefe dagashi sai dogon wando da vest ya shiga toilet ya dakko wata karamar roba tare da bude sabon brush din da Dr Abba ya ajema su, ya matsa maclean ya dan d'ago gadon kamar yanda ya cemai. Haaaaaaa!! yace yana dan zubama gashin girarta ido data lumshe su sunyi yarr abin su .. Kadan kadan ta fara budesu. Ido ya zaro yana dan ja baya yace" Aymah minai miki ko na famamiki, sannu zan kiyaye in sha Allah bazan ƙara ba kinji?.. Kai ta gilgizamai cikin sanyin muryarta tace. "Ashe dai kaine zaka zama farin cikin rayuwata, Ashe Allah zai nunaman ranar da zanga nima anaman tarairaya danake so kuma nike nafalki,ashe zan iyajin dadin miji a rayuwata,ashe zan iya moruwa da hidimar mijina akaina,Ina sonka Jameel ina sonka,ina rokon Allah yabani ikon kyautatama,ka maye mun gurbin duk abinda na rasa,na tabbata ko bana da kowa a duniya, kai ko daga sama na faɗo nason bazaka gujeni ba,ina sonku kaida family naka haduwarmu Alkhairi ce.. Cikin jin dadi da addu'arta gare shi ya ɗan gyara tsayuwa cike da burgewa yace . shin inba ma matata ba waye zanwa,kana awajenki ne aiki amma awaje na hakkin kine nike saukewa,Aymah ke ɗin nan kin man halacci a Rayuwata da har kika iya auran bawan ki. Karki manta Nifa ALMAJIRIN GIDAN ki ne,Amma kika kyautataman ta hanyoyi da dama , Daga karshe kika aminta da muyi AURAN YARITA dani,ni yaro ke babba, Baki taɓa damuwa akan ZAMAN TASHA danayiba, Amma kika bani so da yarda,kinyi hakuri akan zaki zauna dani duk da bana da zurfi a karatun boko amma baki damuba koda duniya zatace kin AURI UZTAS da baida ilimin boko, kedai baki damuba saboda kin duba kin hanga kinga babu wanda ya CANCANTA dake saini, AYMAH taya za'ayi bazan tashi tsaye ba koda zan zama ƊAN DAKO dan kyautata miki,,Wallahi kinmin halacci sosai kin kuma nunaman ke ƊIYAR SHEIKH ce da kuka samu tarbiyyar rashin gudun talakka,Shiyasa nayi wuf na Biya SADAKIN AURE tin kamin wani yaman kafa,Ngd ma Allah daya bani ke amatsayin MATAR AURE Na da nike alfahari da ita,Agefema zan iya gdy wa Adnan daya daukeni aiki har na haɗu dake gashi yanzu duniya ta shedacewa na Auri MATAR OGA NA.. Kuyi hkr ba yawa hannu daya ne nike amfani dashi bana sauri MATAR OGA NA UMMY AYSHA PAGE 25 Ɗan farr tamai da ido kamin cike da so tace " ina sonka,ina son kalaman ka masu sanya natsuwa. Gdy nike Hajiyata yace yana fara goge mata baki cike da lallami da kalamai masu daɗi.. Bayan ya gama yaje ya zubar ya debo ruwa a boket masu ɗumi.. Ido cikin ido yace. zamuyi wanka Hajiyata gyara. Ido ta zaro tace A'a ina? Nikam ka barni kawai. Nooo jiyafa har duka na kikai ,kikace na sakeki, kawai dan naji kunyarki na kasa miki,shine kuma yau zaki canza bayan kin wayar mun dakai kin mayar dani cikakken Namiji,ina bazai Yiyuba ni zan goge matana da kaina. Murmushi tayi tana tino kalamanta najia, sosai taji kunya ita kanta tason ta saki layi,kasa tayi da kai tace. jiya ina bukatar taimakon ne,amma yanzu Alhamdulillah da sauki zan iyafa. Yeh nasani amma dai kiyi hkr bazan kalleki ba zan miki ido rufe kin yarda ? Amma fa nasamiki Yaji a ido zan kai kaina Court da ba Afuwa kin yarda?. Aaaa Aaa Babyyy som ban yarda ba,Babu wanda ya isa ya taɓan lfyn ka ya zauna kalau,Zan yi yaki da dukkan wanda zai taɓa rayuwata tace cikin shagwaɓa tana turo baki. Ya salama saida Jameel yaji kalmar Tata har cikin kwalwar sa. Akasalance shima yace. To naji Sweety nah Nagode kadan kadan zanmiki,banaso jikin ki ya miki nawie ba.. Shuru tayi tare da lumshe ido. Ahankali ya yaye zanan dake rufe jikinta ba komi kam kamar yanda Yayi tinani , tsaye yayi yana zubama halittar ta ido mai tsananin kyau da ruɗa lafiyayyan mutum,tsawon lokaci kamin ya sauke ajiyar zuciya ya fara jika towel din cikin ruwan dumin yana gogeta tass, a dubarance kuma yana yamutsa ta duk abinda yake tana jinshi amma ta kasa bude ido dan wata irin kunya takeji kai aure akwai sirri acikin sa. Shikam saida yagama kana ya ɗauki sabon zanan gadon dake gefe na Asibiti ya rufamata. Gefe ya koma ya jingina da kofa A'hankali yace" Sweetheart. Shuru tamai sai idonta daketa kyaftawa alamar batai bacci ba. Dan Allah kibuɗe idonki inaso naga kwayar idonki. Uhm uhm ni kunya nikeji tace tana turo baki. Munfa zama daya Aymah haka zamuje gidan mh kinamun,kina so na kalli wata awaje,kinaso ki tauyeni ne har nafarajin sha'awar mutanan waje,Ki zage kimin abin sa nike so shi zai sa babu wata ya macen da zata burgeni ko kinaso namiki kishiya?. Da sauri ta buɗe idon ta ta watsamai harara tace. gaskiya karka sake cewa zaka kalli wasu ashe zaka iya haɗa sona dana wata ? Zaka iya shearing dina da wata da har kake tinanin min kishiya Baby? Dariya yayi kadan ya matsa wajen ta yace" bagashiba nasa kin bude kinyi kyau sosai ,Ina mai miki Alkawari da yar dar Allah kece kawai a birnin zuciyana,Koda Allah ya tsaraman zanyi fiye da ɗoya to namiki Alkawari bazata kaiki ba balle ma bana da wannan ƙarfin na rike mace har biyu.. Ido ta lumshe tana murmushi tace Allah yasa da gaske, Allah kuma ya dorar da son da kakeman har abada. Nayi missing Deedee nah sosai fa ina kewar ta . Ameen sweetheart. Hmm kibar Tsohuwar nan nikam babu kewarta danayi dan yanzu Deedee tana ta samun rikicin tsufa,nan yashiga bata labarin abunda tamai jiya. Murmushi sosai ta dingayi wanda da tana da lfy sai tasha dariya. DeeDee nah kenan Allah ya karamata lfy da nisan kwana.. Ameen Sweetheart mizakici?mikuma kike so na miki. Mifa zan bukata ina tare da kai,duk wani abun da nike so kamin,bana buƙatar komi Baby. Tom naje nayi wanka kin yarda? Kai ta jinjinamai tace kaje saika fito. Kiss ya mannama ta a goshi yace *zaki rama wanda nake miki in kika warke fa ki sani bashi ne kike ci,in so goma na miki in har kinji sauki tom sai kin min so goma kin yarda?. Ido ta rufe cike da kunya shikuma yayi murmushi kamin ya mike yashiga toilet din. Sadda ya fito tayi bacci hakan yasa shi bude kofar ya fito dan son zuwa gida ya ɗakko mata abinda take so. Ahanya suka hadu da Dr Abba da da matar shi sai yaron su guda biyu ɗaya namiji sai mace hannusu rike da basket. Ango ango yashiga zaulayar sa tare da faɗin. munbarku ba komi Sorry fah madam ce ba lfy sosai shiyasama muka fito yanzu.. Bkm Dr barka da kwana ya fada yana mikamai hannu,Baya sun gaisa ya juya suka gaisa da matar . Ango ya mai jiki? . Alhamdulillah da sauki sosai yafada yana bama yaron hannu suka gaisa. Ya sunan ka ya tambayi Yaron. Sunana Abul khairi, Nikuma sunana Ummul khiri inji macen tana turo baki. Dariya yasa cike da sha'awar yaran yace khairi, kin san ni? Aa ban s@n kaba Daddy ne yace muzo muga Friend nasa da Aunty bata lfy. Cike da son yaron har cikin ranshi yace hakane to muje sai kuga Aunty kumata ya jiki ba. Da to suka amsa yamasu jagora suka shiga har dakin Aymah. Bayan ya ɗan duba wasu magungunan nata yace . Jannat ki zauna da ita zan dan ganshi muna zuwa Dr Abba yace. Ohk my Love sai ka dawo ta fada tana aje ledar hannuta kusa da gadon. Hannun Jameel ya kama suka fita kai tsaye office din shi suka nufa suka mayar suka rufe. Kula ya jawo ya shiga zuba masu felfesun yan ciki daketa tashin kamshi kana ya aje ledar Bread kusa da su ya tsiyayamasu Black tea mai kayan kamshi. Abokina muci wannan na tabbata baka ci komi ba. Murmushi Jameel yayi yace naci mana. Tom naji wannan na daban ne. Nan suka wanke hannu sukaci suka koshi bayan sungama yaba Jameel katuwar ledar daya sawomashi kaya sunkai kala goma yace" ga gudun muwa ta nan bayawa,sauran na wajen tela. Baki Jameel din ya sak kamin a raunace kuma yace wai miyasa kakeman hidima haka ne,jibi fa abinda kamana dan Allah,. Kafi karfin komi Jameel awajena bakason yanda na daukeka bane, Jameel an yaudareni anci amanata abokin dana yarda dashi ya rusa rayuwata,shi nike ba sirrina yayin da ya daukan sakarai daga karshe ya nemi lalata da matata Jameel daga lokacin na kasa samun Aboki ko guda saboda na tsorata,kai kam na yaba da halaccinka na yaba da kirkinka da rike takonka Jameel, som baka da rawar kan matasan zamani,nakara sonka ne tun sadda naji Deedee nama faɗa akan baka tarayya da kowa shiyasa na kutsa kaina awaje ka har nasamu ka aminta dani,Dan hala nike da gdy ,ga matana nan Jameel ina so ka hadasu zumunci da matarka ina fatan Allah ya dorar da zumuncin mu har abada,albishir da zanma anan shine yau an'hadama motarka in sha Allah, da Daddare zasu fita gobe su dawo Allah muke roko yasanya albarka da buɗi acikin kasuwar nan. Cikin farin ciki yabrungume shi yace* wallahi ni nai sa'a, kuma in sha Allah zaka sameni mai amana Abbah zan ruke iyalin ka tamkar nawa ngd sosai Allah yabamu Sa'a rayuwa da mutuwa. Nan yashiga duba kayan yaga kananun kaya ne masu shegen kyau da tsada na yan gayu , sai jallabiya guda biyu da vest da gajeran wanduna masu yawa a takaice lefe ya hadama Jameel. Gdy yamas asosai kana ya fada Toilet ya sake zabga sabon wanka ya fito ya shirya zanso kuga mahaukacin kyan da yayi ga sajen nan nashi dake kara kawata kyakyawar fuskar sa. Da hannu Dr Abba ya nunamai wata kujera yace hau kayi bacci in ta tashi zanma magana. Ido ya zaro yace bacci kuma? Ina jinyar matar nawa?. Yeah bacci naga bakayiba som kar kaima na kwantar dakai oya maza yakara yana ɗaure fuska.. Murmushi yayi dan Baya da ta cewa hakan yasa shi cire rigar ya hau kujera dan danan kau bacci ya kama shi. Acen daki kau yaran ne suka natsu akan wani karamin gado suka hau game da wayar Abul khairi. Jannat ma wayar ta hau latsawa suna zaune sukaji an'turo kofar ana faɗin" Aymah nah i milisu ( miss u) yau som banyi bacci ba ,wai dan uban sheɗan saida yaga asuba tayi dan dai yaja Allah yakamani ya lallaɓo ya dingaman kalamai masu sanyi sai gashi najini Bangaladash sai tara na tashi shegen yayi nasara ayau amma In sha Allah bazai sake ciba har abada, Sannu . Murmushi Jannat tayi tace" Deedee ina kwana?. Laaa wacece ke mutum ko jinnu? a ina kika sanni baiwar Allah Deedee tace hankali tashe idon ta kamar zai faɗo akan Jannat. Murmushi Jannat ɗin tayi tace" Dr na bani labarin ki sosai muna nishaɗi,shiyasa kina magana na gane kece. Washe baki Deedee tayi tace laa wai ke matar Dr Abba ce , Allah sarki,nan idonta ya kai kan yaran tace kwaraiko ga macen nan Tuleliya kam tayi kama dashi,yoke maimakon kibar Namijin ya biyo ubansa saike kika gadosa. Dariya yaran suka hau yi aguje kuma suka yo kanta suna faɗin yau munriga Daddy ganin Deedee shi. Haɗa su tayi tace wannn haka yake Yar lukutar dadi nidai kam ga miji na nan ke kam kishi yace tafada tana ba Abulkhairi hannu suka kashe. Kuka khairi zatasa Deedee ta jawota tana murmushi tace ke wasa nike duk kan ku I lobilu wallahi .. Gabaki daya suka sanya dariya kana ta juyo wajen Aymah nan taga ta tashi ta bude ido sai murmushi take. Da sassarfa ta ƙarasa wajen ta tace sannu Aymah na sannu,jiya kinbi layin tinkiyoyin likita kinsh wuka, Allah yabaki lfy sannu kinji. Yawwa Deedee nah nayi kewar ki,ina zoɓo ina kunun aya? Haba Aymah nayi su yanzu ai nacika yal'bura uba,bari nayi inga lafiyan ki kana,kajin kwai ma zan saya asaka ɗakin Adnan. Murmushi tayi tace Allah ya samiki Albarka. Ameen ta amsa kamin ta juya ga Jannat daketa murmushi ta bata hannu tace sannu Mrs Abbah. Cikin kulawa Sosai Jannat din ta bata nata tace sannu Mrs Jameel kuna lfy ya karfin jiki Allah yasa an'maki a Sa'a. Alhamdulillah Ameen ya rabbi sannu ku ta fad tana kirawo su Abul khairi nan suka gaidata cikin ladabi. Cikw da aon yran da kaunr su ta hau amsawa tana dan tamhayar su abinda ya shfi karatun su sun bata amsa. Deedee tace kai ammafa naji dadi wallahi jikin yayi kyau Aymah,jiya kau yanda kikason zaa maidaki yar mafiya haka aka dora maki karafuna a kirji da kai kai munga masifa Allah ya kara lfy Ameen Deedee nah kowane bawa da nashi kaddara. Eh ina fatan wannan yazama nah shine silar farin cikin kin Rayuwar ki har abada. In sha Allah tace tare da waigawa ganin bataga Jameel bah. Duk da kallo suka bita Deedee tace . wai Aymah ina Jameel na dauka bayan gida ya zagaya amma har yanzu shuru ko haihuwa zaiyi ai sai haka? Yafita shida Dr Jannat ta basu amsa tana bude kulolin ta shiga zuzzuba masu abinci , Yayin da ta hadama Aymah mai ruwa ruwa ta bata tanaci suna fira saida taga ta koshi kamin ta zauna taci . Suna haka Aka turo kofar Jameel ya shigo. Sanye yake cikin kananun kayanshi sai baza kamshi yake kana ganin fuskar shi kason bacci yayi. Ido suka hada da Aymah ta kawar da kanta tana turo baki alamar tayi fushi. Kanshi ya shafa yana fadin kiyi hakuri sweetheart laifin Dr ne shine yasani kwanciya. Murmushi tayi tace"Au nakau godemasa cikon tekun maliya tinda har yasa ka huta Allah yabiyaka da Aljannah ka cancanta wallahi. Ameen yace yana karasa wajen ta ya zauna gefe gadon tare da dan shashafa fuskar ta ya gyara zanan jikin nata A'hankali yace" zamu kara wankan yanzu ko sai Anjima?. Laaa haula wala kuwati illah billa,yanzu Aymah dama lfyn ki klau har wanka kukayi tare amma kika naɗe kafa kika koma gurguwar ƙarfi da yaji kai jama'a ni Deedee shekaru na sun tashi a iska dana kasa tantance wayon ku. Jannat ce dake dariya harda hawaye tace kai Deedee kefa kin ganema idon ki Daddy yabani labarin har suma kikai kika kasa magana , shine zakice karyane,kinson ba wanka zatayi ba so akwai bukatar ana kula da jikin nata dan taji daɗi ko kuwa? Oho yanzu naji zance kinson su sun'waye yanzu bama tani suke ba tace afusace. Deedee wallahi zaki fita waje kina ma matana ihu Jameel yace yana zubamata harara. Uwaka Jameel tashi bar dakin na raba auran ku ni zanyi abinda kakeyi... MATAR OGA NA UMMY AYSHA PAGE 26 Dariya sosai yasa yace. "Wannan kuma baki da hurumin sa. Atakaice haka suka zauna cikin nishaɗi da farin ciki mamaye a zukatan su. Bayan azahar Manager yazo shida Baba Ali suka ganta da jiki suka aje masu kayan dubiya kana suka tafi.. Adnan Wani mugun azaba sadam ke gana mai wacce tin yana da kudirin daukar fansa har ya fara sanyi yana so kawai ya samu mai taimakon sa ya dauke shi daga gidan tin kamin sadam ya kashe shi. Fitsari kam kullum sai ya bashi so daya arana ya taushe shi dole yasha. Wannan hali da yake ciki yasa Adnan din fara son kuntatama sadam din ta hanyar kwantar da hankali ya tiƙa uban kashi dan yaba su Sadam din aiki. Shikam Sadam ganin haka yasa yace to ai hikenan tinda ni zakaba aiki kwara ahutar da kowa zaka rayu in da ya dace dakai.. Katon buhu suka samo suka dora Adnan din akai suka dinga jan shi har zuwa toilet din dake cikin get ɗin. Akan shadda dake wajen suka ɗorashi babu ko wando yace to kaitayi in ka gaji ka sake wani dan buhun ubanka munafuki mu bamu fika Hatsabiban ciba. Yasha kuka ya gaji gashi ko gusawa baya iya yi, ga masifar sauro da kwarin Toilet dake dallamai cizo tinda babu Kulawa,Sosai yashiga nadama abinda ya shirya gashi ya gina Ramun mugunta abin kuma ya rufta dashi.. Abinci kam a cikin leda suke kawo mai da ruwa guda su jefa su kama gaban su. Wannan rashin kular ba karamin matsala tajaza mai ba, dan cikin lokaci jikin shi ya fara wani irin wari marar fasali,kafarshi kam da bata da lfy har wani ruwa ruwa take masu masifar Ɗoyi. Awannan lokacin ne ya fara kuka da hawayen shi akan halin da yake ciki. Ta ɓangaran Aymah kau Abin sai son barka ,Dr Abbah da matar shi sun shayar dasu mamaki ta hanyar bada dukkan kulawarsu ga Wannan ahli, Jameel ya sake tabbatar da haduwar su da Dr ba karamin Alkhairi bace,Aymah kau in'ka gansu da Jannat zaka yi tinanin dama tare suka tashi dan shakuwa. Ta bangaran Manager kam abin sai son barka Hidima sosai yakemasu bakin rai bakin fama . Bayan sati daya Ya kama kwana takwas kenan da aikin Aymah.. Turo dakin yayi ya isketa zaune tana ƙoƙarin mikewa tsaye alamar ta fara samuwa. Cike da farin ciki ya buɗe hannu yace oyoyo matana ta kusa dawowa hannun Babyn ta tarama masa wankan da yake mata. Cike da shagwaɓa data kware da ita yanzu tace. Nifa gaskiya A'a kai zakaitamun Bazan iyaba wash Baby kirjina zai faɗo ta fada tana dafe wajen da akai aikin. Da sauri ya kamata yana fadin ki daina tashi ba,kinga gashi an sallamemu Jannat zatana kula dake gida tinda itama Nursing ce,Ga hutu mijinta ya bata saboda ke Har sai kin warke. Cikin mamaki tace da gaske? Yeah da gaske nike bara na dakko whell chair na tura yar gurguwata mu wuce ko, gasucen duka gidan ki ke kawai ake jira.. Murmushi tayi tace good dana zama gurguwar taka ba ta kowa ba. Gida kuma ada ne yake nawa,a yanzu ni Aymah na baka wannan gidan halak malak,Banso kace komi in ba haka ba zamuyi fada bazan sake yarda kanamun wannan abunba ta faɗa tana juya kai cike da kunya... Dariya sosai yashiga yi kamin ya sake rungumeta yace dan Allah sake faɗa naji, akwai dad'i dama kina so?.. Aa banaso tace murya ƙasa -ƙasa. Ban yarda ba yace yana huramata iska a kunne tsawon 5mnt kuma ya daina. Jin yayi shuru yasata dago idonta da sukayi jawur har ruwa ruwa ke kwanciya aciki ta zubamai su alamar yadai.. A kasalance shima ya zuba nashi cikin nata yace. kikace bakyaso ga idonki nan ya fallasa sirrin zuciyar ki,Allah ya karabaki lfy Aymah, na fara kosawafa sosai wallahi yanzu burina ɗaya naji nayi ajiya a wannan wajen ya fada yana shafa cikin ta. Cikin kasalalliyar murya datafi tashi yin low tace. Ka manta bana haihuwa,Shekara 16 da aure fa ko ɓatan wata banba ,kai sai kasanya rai zan haihu a gidan ka?. Sosai ya dinga sakin murmushi da kalaman ta har saida ta kai aya ya juyo ya fuskanceta tare da rike kafaɗar ta yace. Matana ba juya bace som,Kema kin son haka,da kuma kikaga kin kai wannan lokacin karki manta wani baya Haihuwar ɗan wani,Sannan dama tin farko Allah ya rubuta zan ba Adnan aron'kine kamin na girma na bunƙasa na iya rikeki na kuma iyautata zaman takewar mu,yanzu kuwa bagashi an maidoman abata ba, Gashi duniya ta sheda zan iya Rikeki a halin yanzu,kuma kema kin sheda hakan,jinyar nan taki itace tazama shamaki a tsakanin mu,amma ni ina da tabbacin In sha Allah duk ranar da Mukai wasan dambe dake aranar zan jefa kwallo a raga in Allah yaso ya yarda ki rubuta ki aje nikaina na yarda da kaina , ko zakiga zahirine? Da sauri ta ɓoye kanta a kafaɗar shi tana kai masa k'ananun duka akafaɗa tace. Som yanzu bakaji,ada ba haka kake ba,ada ustaz ne kai,amma ayanzu idonka ya buɗe why?. Masha Allah da kikason da ni ustaz ne, Ustaz fa dukkan abinda yason halaliyar sane to bazaki samai dajin nawie a wajen nan ba,in kuma abu ya zamto na saɓama Shari'a musuluncine zaki samai mai kaffa kaffa da abin saboda bin umarnin Allah,Karkiyi mamaki dan Yanzu na waye akan wasu abin nawinki fa ya hau kaina kana idona ya sake budewa da kallon Kyakyawar surar ki,ke in'ma baccin abinki Aymah waye zayyi ido huɗu da kyakyawar mace kamar ki bai gane cewa shi lfyayye bane, wallahi tin washe garin zamanki Asibiti na kara tabbatar da lfy nah,kai Alhamdulillah Allah kulli halin ya karasa yana bata wani lafiyayyan kiss a goshi. . Zatai magana yace ina zuwa ma idata agidan ki, akan gadon mu,kanki a cinyana,hannuna a br.... Bakin shi ta daɗe da sauri dan kar ya ƙarasa. Shikam dariya yayi ya mike da sauri yafita tare da cewa matsoraciya. Naji! tace tana gyara zamanta Murmushi kwance a fuskarta,Kai Auran wanda keda rufin Asiri Duniya ne,yanzu ta tabbata da Adnan ne sai dai ta rub'e ta lalace bazai iya bata koda awa daya Acikin a wannin saba, gaskiya da mata zasubi shawarar ta su daina cewa sai mai manya kuɗi,su samu mai rufin asirin da zai basu lokacin su ya basu kulawa,amma wallahi mai dukiya bashi da cikakken lokacin kowa saina dukiyar sa da tinanin mi zai shiga ya fito,miye in yayi zai bada riba ba faduwa ba,kullum tinanin shi yanda zai sake yalwata canjin sa,ciwo in yakama matar shi bazai iya sashi zuwa ganinta ba sai dai ya turo kudi dan yana ganin sune maganin matsala komi ,baison kaga mutum kusa da kaiba ma kawai arzikine Babba,kai taga banbanci dari bisa dari. Ahankali tace" gashi yaro jagab,kuruciya bai'baye dashi,ga kamala,ga iya soyayya,ga iya sarrafa mace,iya sarrafa halshe yayin furta zance,wow Jameel kayi sosai, Allah kabama wanda suka daura mana auran nan tukuici da gidan Aljannah. Jameel kau Dr Abbas yaje ya kira ya sake dubata kana ya sallame ta ya fito da ita cike da kulawa da tarairaya mutane sai kallon su suke, yayin da wasu suke tinanin Yan uwan junane, wasu kuma suna tinanin miji da matane duba da irin tarairaya dayake bata. Bayan sunje gaban mota ya sungumi abinshi ya kwantar da ita A'hankali tare da kwantar mata da sit din kana yaba wani ma'aikacin jinyar kujera ya mayar masu shikuma ya tada haɗaɗɗar motar suka tafi. Cike da mamaki tace Baby wannan motar fa?. Murmushi yayi yanajan kumatunta yace ta aroce.. Shuru kawai tayi tana dan cije baki,zuciyarta cike fall da tausayin sa, wato har yau baima mallaki koda keke na shiba amma yake rayuwarsa cikin farin ciki , Yah Allah kabani ikon bawa bawan nan naka dukkan abinda na mallaka, Allah duk quya duk daɗi karka taba bama zuciyata damar yin gori gareshi a matsayina na ya mace mai rauni, Allah ka cikaman burina Allah ka karaman son sa azuci shima ka karamasa nawa. Ameen my wife ,in dai Jameel dinki ne karkiyi kokonta akan son da yake miki Aymah, sonki ya fara tasirine a zuciyata tin haduwar farko da mukai dake kina cikin halin jinya,Kai naga abu, a wanna fa ranar duk iya satar bacci kasa daukata yayi,abin har mamaki yake bani yanda na afka sonki baki daya lokaci daya,wallahi Aymah bayan iyayena babu wanda nike so sama dake, Sai dai bansaniba ko zaki iya zama dani a halin danike ciki,kar tafiya tayi nisa Aymah ki juyamun baya,kinson Annabi Allah ma yace kaji tausayin wanda ya saba da dukiya farat daya kuma ya tsinci kanshi cikin hali na rashi,Inaso Allah ya samaki hkr zama dani a cikin ko wane hali,kedai kin sani karama sana'a nike Aymah ba Babba ba.. Lips dinta ta dan cije tace . Jameel!!! Koda babu Kafa, Hannu hanci Kunne Baki . yatsu A tattarr dakai nayima Alkawari tsakanina da Allah zan zauna dakai na tarairayeka kuma wnanan halin bazai iya sani in juyama baya ba. Bana daya daga cikin matan dake gudun mazajen su dan wani abu balle kai daka zameman garkuwa kaida iyayenka,wani abun tabbas Adnan na samun sassaucin sane daga gareni sabida kai,bakai ka daɗe da sona ba nima na daɗe danaka wanda ya samo asaline tin ranar farko danaga juyawarka jameel. bayan ka kadai fa nagani amma nakasa sukuni,wallahi ina sonka da dukkan zuciya na da ruhi. I love you so much Ɗan Saurayina tace cikin shauki tana jan gemen sa. Murmushi yayi yana sakarmata kiss a laɓɓa yace me too My Aymah nah Tasha mamaki sosai lokacin da suka isa kofar gidan ta suka iske an gyareshi yasha sabon penti,bata ida mutuwar zaune ba saida aka bude masu get suka shiga falfajiyar gidan ya rasulu ya manzon Allah,kai Abin bazai faɗu ba . Aget din su na biyu sukai parking tana ta bin gidan da kallo. Bayan ya buɗe ya fito ya zagayo ya budemata. Wata irin guda Haj Deedee ta saki kamar zata cire hancinta. Gabaki dayan su kallon ta sukai sosai lokacin data zube cikin uwar ranar ta hau sujjadah shukur dan sosai tayi kewar Aymah . Deedee nah Dan Allah kita shi karki ji zafi akwai rana nayi kewarki nima Aymah tace cike da son Dattijuwar tana bude mata hannu . Cikin sassarfa kau Deedee ta tashi tare da sharre hawaye tayo kansu ta kama hannun su tace . Alhamdulillah Aymah wallahi dadin danaji bazai misiltuba,dan karkuceman butulu da wallahi sauran kaɗan in kwashe kayana in gudu, yo gidan kango ya komamin saboda babu fitulun dake haskaman shi,Dole tasani fara dire kujera a tsakiyar su sadam da Baba Ali ana zantawa dani. Dariya Aymah tayi tace ai yanzu na dawo in sha Allah babu abinda zai rabamu sai mutuwa. Noo Baby nine nan zan rabaku,yanzu kam ai dole ta barni dake ba, tinda tason wata kusan tafi wata wanda akai abaya Allah ya amfana ya karasa yana murguda baki da jefama Deedee wani kallon dayasa su duka fashewa da dariya. Kunnan shi ta kama sosai ta rike tace kai yanzu har ka kai minzalin da zaka fadaman magana Jamalu? To ka bini sannu dan yanzu nice komi tsab zan manta da uban komi in hanaku tarewa kai kason ni baka bukatar tini. Murmushi yayi yana dan rungumota yace haba tawan ta gaban goshin amma fa in Baby na Toilet. Duka ta kaimai tana fadin" Ni zaka mayar shawaraki saima ta shiga toilet kana? to ai shikenan sannu ku da zuwa . Cikin farin ciki ta nemj yi masu jagora . yace jeki muna zuwa. Batace komiba tayi gaba shikuma ya sungumi Aymah bai direta ko ina ba sai bakin kofa ya kamata suka shiga. Ashe kallo na palo.. Wasu lafiyayyun kujerune da labulaye da carpet komi na ciki gold colours ne palon yayi wani kyau na ban mamaki . Deedee ta juya tace ya kukaga aikin manager,wallahi manager ubane harda kari bawan Allah dan dai duk yakara son goge lefin sa,duka gidan nan shine ya fitar mai da wannan kudin ya gyarashi,saima kin haura sama Aymah inda dakin ki yake nan zakisha kallo. Wannan abu yama Aymah dadi har kukan farin ciki tayi. Jameel mah sosai jikin shi yayi sanyi. Wayar shi ya zaro ya shiga kiran shi. Bayan ya dauka yace Daddy barka da kwana. Cikin mugun farin ciki manager yace Jameel,kaine,yau da kanka kake kirana Daddy?. Sosai kunya ta kama Jameel dan da haushi yake bashi wanda ya rasa dalili. *nikam nace kishine kawai ya ke dawainiya da zuciyar ka*. Kayi Hkr Daddy mun.. Karkace komi Jameel bari ganinan zuwa yau ai ance dama za'a sallameku amma banyi tinanin da ranaba anjima da la'asar ko bayan magariba in kun huta zan shigo in sha Allah. Tom daddy mungode. Aha bye my son ya fada yana kashe wayar muryar shi cike da farin ciki. Sosai Aymah taji Jameel din ya burgeta mussamman dataga ya sakko. Deedee kam abinci ta shiga saukewa gaban su tana ta rawar kafa diyarta ta dawo. Jameel yace ina zuwa Deedee bari muyi wanka. To sai kun sakko tace tana sake gyara zama tana kallo. Aymah ya ɗauka cak suka haura sama sai rigima take mai akan ya sauke ta. Lallai kallo na sama na maganar Deedee. Tsayawa tsara kyan palon nan bata lokacine. Dakin Aymah yashiga inda yasha hadaddan kayan daki komi milk da maroum kamar yanda kujerun palon suka kasance maroum da milk.. Bayan ya zaunar da ita akan gadon yace yaufa tare zamuyi yafada yana fara kwaɓe kayan sa duka. Ido ta zaro tare da neman kwallah ihu ya haye gadon tare da jawota jikin shi ya rufemata baki... 😳😳😳😳 MATAR OGA NA UMMY AYSHA PAGE 27 Miye haka Aymah? dubafa kiga ina da wando ya fada yana tsareta da ido. Gaskiya A'a nidai ka mayar da kayanka duka dan Allah banaso wannan ai karami ne. To kinfiso na jikesu da minene zan koma gida? Ba wanka zan miki ba?. Aa Nidai Ka hadaman ruwan zan iya da kaina. Ohoo da gaske zaki iya? Eh zanyi tace tana turo baki. Hmm zan kamaki yace yana shigewa Toilet din.. Saida yayi wanka ya ɗauro alwallah kanan ya hadamata ruwan ya fito. Kayanshi ya mayar sannan yace zaki iya tashi ? Eh zanyi tace tana mikewa tare da ɗaukar babban towel dinta tayi Toilet din. Cikin natsuwa tayi wankanta ta dauro Alwallah ta fito. Akan gadon ta iske ya ajemata kayan ta na shan iska masu fadi . Sallah ya kabbara yayin da ta zura rigar tayi zaune a kan kujerar dake wajen tayi sallarta daga zaune , Bayan sun gama ta fara hamma alamar bacci. Kallon ta Yayi yace Sweety nah Bacci?. Kai ta d'agamai a gajiye. Yace zaki fara cin abinci kana ko? Aa saina tashi ka manta ban dade da shan tea bah. Ohk tom muje ki kwanta ya faɗa yana kamata suka koma akan gadon. Wutar dakin ya kashe dakin yayi duhu kamin ya hau gadon yace ki bar ciwon nan ya sha iska tinda akwai nepa ya faɗa yana zame mata rigar kasa. Bacci ke idonta sosai kasa hanashi tayi . Shikam yana cirewa yashiga jagula jikinta tsawon lokaci kamin ya samu natsuwa ya tashi yayi wanka kana ya gyaramata kwanciyar ta ya fita dan zuwa gidan su. A palo ya iske Deedee na zuba gyangyadi. Fuska ya ɗaure gam kamar bashiba yace" zan tafi gida. A furgice ta tashi tace kai kuwa kafaracin abincin mana ina Aymah take. Bacci tayi yace yana zama tare da bude kulolin yaga waina ce da miya sai dagen naman kaji. Ya kauji daɗin ganin wainar dan tana daya daga abincin da yake mutuwar so A rayuwar sa. Bayan yaci yasha ya ce kin'daina kayan saidawarki ne?. Tace mizai hana ni,Ai Aymah Na dawowa hankalin ta na fara nagaji dama da zaman banza, yanzu haka nason yan Albarka suna kan hanya ga naku nan an maku na mussamman ta ɗauki jug ta shiga tsiyayamasa.. Saida ya take cikinsa dam kana ya mata sallama ya fito. D'akin Baba Ali ya biya suka shiga gaisawa kamar sun dade da sanin juna kamin ya samai albarka ya fito nan yaji ihun su sadam sunata chapter. Kamar ya buɗe yafita yakuma fasa ya tura dakin da sallama ya shiga. Hannu ya basu suka shiga gaisawa kamin ya sanya kai bedroom ɗin. Yallabai Adnan kake nema ?sadam yace. Eh . Ai yana Toilet cen muka mayar dashi kashi yake muna a wando da gayya .. Ya salam! akan mi,haba kaikuwa sadam baidaceba wallahi,ku barshi da dakon zunubin dake kansa kaɗai ma ya isheshi kunci,basai kunbi ta kanshi ba mutumin da bashi da hankali,nasiha Sosai yashiga masu batare da ya musu cin mutunci ba. Gdy sosai suka shiga yimai kamin ya fita yabude get din yafita . Sukam duk jikin su saida yayi sanyi hakan yasa suka tashi suka Dumfari wajen. Wani mahaukacin wari mai azabatar da bawa suka dinga juyowa daga dosar wurin. Gabaki dayan su saida suka dade hanci. Sadam ne yace kunji mi nikeji ko kashi yake?. Kai A'a wallahi bana tinanin haka wannan ba warin kashi bane kamar na gawa . Ido suka zaro kamin Su zunduma da gudu. Kwance suka ganshi kudaje, kwarikka nabi har cikin idonshi sai nunfashi yake sama sama. Yanayin abin dai som babu tsari, Duk yanda yake basu haushi saida takai ga sunji tausayin sa. Kama shi sukai suka fiddo daga toilet din da reza suka samu suka cire rigarshi zuciyan su na masifan tashi ko wane tuƙan amai yake ji. Wanka sukai mai tare da kaishi wani karamin daki dake kusa dana Baba Ali suka aje suka zo suka dauki riga cikin kayanshi. Koda suka samai kayan sunmai mugun yawa. Ngd yace cikin bala'in sanyi dan ko magana sosai baya iyawa tsabar wahala. Toilet din suka koma suka shiga aikin sa dan ya basu masifar tausayi, ga abincin da suka kawomai nan na kwana biyuma baici ba . Saida sukasha wahala suka gama gabaki dayan su babu wanda bayyi amai ba. Jameel kau cikin nishadi yake tafiya har ya iso kofar gidan su. Bayan ya rufe motar ya fito yashiga ciki. Inna su ya iske zaune da Baban su sunacin shinkafa da wake a flat daya sunayi suna labari. Dukkan su sunji daɗin ganin shi nan suka shiga tambayar jikin Aymah yana amsama su . Key din motar ya zaro cike da murmushi a fuskar sa yace. Baba kusamun albarka, na fadamaku kwana ukku daya wuce dama aka fara mana aiki,to shine yau da safe Dr Abbah ya kawoman wannan motar wai da kudin ya sai man dan in rage Kudin abin hawa,in yaso yanzu sai a hadamasa nashi. Sosai suka shiga murna Inna su harda hawaye daga baya suka masa fatan Alkhairi. Malam habu yace to yanzu ina zaka ajeta? Toh nidai na fara tinanin ajeta gidan su Kamal tinda basa Nan,Amma ina so na nemi alfarma mai gadin ne sai yasanar da mi gidan yanda sukayi shikenn dan ba yanzu zan hautaba sai gaba. To to shikenan Allah ya sanya Albarka ya tsare ku,Ai mu haduwar mu da bayan Allah nan wallahi Alkhairi ne,Yanzu bama da haufi akan komi,Jibi mahaifiyar ka har tayi kiba ta sake kyau abinta,Bata jiran sisi nawa in nabata ta amsa,in banbata ba kuma tayi amfani da nata,Rashin tinani ne kesa wasu mazan hana matan su kasuwanci amma wallahi ba karamin ragema mutum hidima suke ba,Fatana ka rike Aymah da amana,shine kawai abinda zakamana ka biyamu,kaga ko lokacin da muna kalkashinta bata taba wulakantamu ba,, kullum kyautatawa ce tsakani mu,Ba ƙaramin Sa'a kayiba Jameel,Fatana da addu'a nah Allah ya kamama, ya kuma kara budama ka hanyoyin Arziki da walwala. Ameen Baba ngd matuƙa kuma zanbi shawarar ka yace yana mikewa zai shiga daki Inna su tace wai baka tambayi autana ba. Kanshi ya shafa yace na manta dashi som. Murmushi tayi tace shikenan jeka tom baza'a faɗi inda yake ba. Hannayen sa ya hade cike da son jin inda jinin nashin yake yace dan Allah Inna mu yana ina. Baban su yayi dariya yace kace ka manta dashi,to sunje kauye da Mai unguwa suna hanya. In sha Allah. Fatan dawowa lfy ya masu kana Yayi dakin shi ya kwanta. Duk irin gajiya da baccin da yakeji kasawa yayi, juyi kawai yake,ya saba kwanciya kusa da ita,dan ko Asibiti tana yin kwana ukku yaga ta fara dawowa normal ya koma bacci bayanta haka yake jefata jikinshi suyi baccin su cike da Nishaɗi. Ganin kwanciyar bazatai maiba ya sashi tashi yayi wanka ya masu sallama ya hau motar shi yaci gaba da zaga gari har bayan mangariba kamin ya juya kan motar zuwa gidan su Aymah,awaje ya ajeta kana yashiga da kafa. Abakin Baranda ya iske Deedee zaune da uban kudi tana ta kilgawa Almajiranta zaune suma gefe sunacin tuwon datayi da miyar kuka tasha Namijin zakara sai kamshin man shanu take. Bayan ya gaisheta yace" kiraba dani. Murmushi tayi tace to tinda dakai nayi wahala ba. Tana ina yace yana kallon kofa. Tana ciki ni ai nariga na bar dakin nan Jameel tinda naga idonka ya bude Yanzu. Sosa kai yayi yace amma fa inajin kina fadama innamu ta dainajin kunyarmu nikuma sai kisaman ido akan matana? Kina so a zage a nunama danki soyayya nikuma kizameman shamaki?. Ido ta gwalo tana fadin yanzu da girmana da Mutuncina kake so kaman sharri, wallahii kaji tsoron Allah a ina na samaka ido,kawai wannan dakin na dawo dan in sakata in wahala ta nuna karamin part din dake kusa dana Aymah. Tace kai kuma kaga saika zauna anan ka karasa jinyar tata kamin kaje ka samar maku wajen da zaku zauna. Kanshi ya sosa yace ina sonki Deedee nah kin kawo shawara mai kyau . Kamar gaske tace tana zuba fara'a. Mikewa yayi yace babu karya a kalamina yakarasa yana tura kofar ya shiga. Bata kasan hkn ya sashi haurawa sama Zaune ya isketa palon sanye da wani gajeran wando milk wanda da kadan yafi pant,sai rigarshi data kasance mai net itama milk,Sai zani dake bayanta da gani ta ajeshi dan in wani yazo ta saura. ,. Jameel kau da kyal ya iya yin sallama ganin halittun nan nata sunyi curko curko suna nema fasa rigar su fito. Ido ya dan lumshe yace" Sweetheart wannan jan raine miyasa bazaki sanya manyan kaya ba kinson Any time zan iya faɗowa. Idonta dake lumshe ta bude tare da zubamai a shagwabe kuma ta juya kai tana turo baki tare da daukar zanan ta dan yafashi akan jikin ta . Minene? fadaman kar wani yaji kanmu, mu kashe mu binne Abin mu kinji matar so ya karasa gunta yana rike kunne. Ohk ba kaine ka tafi ka barni ba, bazakamun ko sallama ba kuma sai yanzu ka dawo,nidai tom mu koma Asibiti tinda acen nafi ganin ka . Kyakyawan Murmushi ya saki yace. Naji dadin wannan maganar taki Sweetheart,kuma nason nidin na dabanne awajen ki tinda gashi har kewana kike in bana nan,sai dai Karki manta a yanzu jikin ki ya fara kyau, da son samune nan da sati daya ace kina gidana,Kinga dole kimin uzuri in fita in dinga nema mana na abinci kinji. Zamanta ta dan gyara tana mikewa ta zauna tare da kama hannusa tace. kamar bakaji maganar da namaba dazu Asibiti,ko bakason kyautar da nama ne,Nace na barma gidan nan halak malak,ko baka yarda dani ba ne,ko akwia abinda kake tsoro,ko kana gudun a kiraka da mijin Hajiya ne?. Aa Aymah bana tsoron komi sai Allah,kuma kema kinson na yarda dake dari bisa dari tinda har na iya auran ki kuma ina burin mallaka miki kaina abadan, kawai hakanan,inaso nima nason yanda ake sauke nawin iyali wannan shine,kana bana tsoron aceman mijin Hajiya som, Tinda inba aceman ba mijin Alh za'aceman, A ganina daɗin zama ai shikesa ace da mijin iya Baba. Hannuwa ta ware tana juya ido tace ohk fine in'dai har abinda kaceman hakane tom na yarda kai kuma ka karba. Dan... Kasa bari yayi ta ida maganar tata ya tausa halshensa mai Sanyin Tomtom cikin bakinta,wani juyi da tsotsa mai rikita kwalwar Bil'adama yashiga Mata babu ko tsaitsayawa tsawon 10mnt kamin ya saketa ya jingina da kujera yana numfashi, yayin da itama ta jingina tana dora kanta saman ka faɗar shi ta lumshe ido. Cikin sanyin jiki yace mukara Hakuri Sweety ko,kema naga kamar kinzo ending haka ne? Aa tace tana juya kai. Tom saka idonki a Nawa ki fadaman. Kin yarda tayi saima mikewa da tayi tace ina zuwa. Zai magana wayar shi ta shiga ring ya zaro yaga Manager ne. Yana dauka yace ku sakko kasa. Ohk Daddy yace murya kasa tare da mikewa ya gyara zaman wandon shi. Kai ya dago da sauri idon shi ya fada cikin na Aymah data kasa shiga dakin dan jikinta ya mutu saidai ta jingina da kofa ta zubamai ido gashi ya kamata . Cikin jin matsanan'ciyar kunya kamata da yayi tana kallon shi tafara neman tafiya kamar ta kife. Da sassarfa ya bita ya cafko hannunta yace zo miye kike kallo? Ni nifa bakai nike kalloba banmaga komiba cen gefe nike kallo tace a rude. To In'fadamaki abinda kike kallo?. Ido ta gwalo tace aa dan allah ka bari ni kanasani jin kunya wallahi wai yaushe kazama haka. Hmm tin Ranar da aka mallaka man ke,sannan bazakije ko soron gidana da wannan kunyar ba Aymah in sha Allah, Saboda zata cuceni,ni Babyn kine mai son lallashi mai bukatar kulawa sosai,Kuma ina da tabbaci zan sami komi daga gareki. Murmsuhi tayi cike da kunya kai aure Akwai sirri,bata taba tinanin rayuwa da wani namiji ba inba Adnan ba ,gashi ta samu kanan kananta data ba shekara goma a matsayin miji ,shiyasa sai taɓara yake mata son rai, wani abunma yamata sai taji nawie ya kamata. Jameel kau hijjob din sallah ta ya dakko katuwa ya samata. Bara na fara wanka tukun sai muyi sallah. Habarta ya dago yace yanzu har wanka ya kamaki?. Ya salam saida taji kamar ta tona kasa tashiga wai miyasa yake mata hakane. A rikice tace nifa banfa ceba ,wankan minene zai kamani ma? Ok Na fadamaki yace yana tsareta da mayun idon sa dake cike da fitina ta matasan yaran zamani😜 Aa tace da sauri tare da faɗin ina zuwa. Dariya yayi Yace'' sorry manager ne ke neman mu muje yace yana kama hannunata Sannu sannu suka sakko idon mutanan dake palon yayi cah a kansu. Kasa ta danyi da kanta Yayin da shikuma ya sake tamke fuska Gam, Jameel akwia dattako da kamun kai,in:kaga rawar kafarsa jikin matar shi yake. Bayan sun sakko ya dan kallesu nan yaga su Deedee ne dasu Dr Abbah da Jannat, sai yaran su ,sai manager da wata mata da matasam samark guda ukku yam mata biyu. Wannan ce matar Adnan din matar dake zaune tace. Noo matar Jameel dai, a dane take matar Adnan Jameel yabata amsa idon shi kamar ya faɗo tsabar harara. Tabɗi jan, Yanzu dama kece kika rike min miji munafuka tsawon wata ukku ba zuwa ba aike, sai Aukin karya da gaskiya da kuke shiryaman keda wannan munafukin manager, to ta Allah ba takuba abokan aikin sa sun fadaman duk munafuncin da kuka shirya dan haka yanzu kun shigo hannu shaheed ce su shigo.. Cike da rashin kunya saurayin ya tashi yana shagwaɓa da kara kwale wando kasa kasa yake faɗin wai ina Daddy nah Yake mom, kince da munzo zamu gansa kin tsaya ɓata lokacin ki akan wayan nan talakawan maciya haram. DeeDee kam cike da masifa take lumshe idanuwan nan nata kafafunta daya akan daya ta daiki furta komi amma kai ba sai ance maka zuciyar ta tafasa take ba. Kai dai jeka kadawo shalele matar tace. Yana fita sai gashi da zugar sodoji sun kai mutum goma duka da bindigogi. Aymah Manager Jameel Deedee Dr Abba Jannat Babu wanda fuskarshi ta bayyana wani tsoro saboda tsaro . Ina kuka ɓoyeshi. ɗaya daga cikin su ya fada a fusace yana ƙara bindiga akan Jameel. Kulll wlh,Karku tabaman Miji Aymah tacw a fusace tana mikewa tsaye rai ɓace. Kema bamu barkiba dan muna tuhumarki da rashin fadamana gaskiya da kikai saboda mugun nufi. Kana taya zaki auri miji biyu kina mace,ko ganin wancan ya samu nakasu ne yasa kikai aure kan aure ina shi Adnan din yake. Deedee ta dauki wayarta ta shiga lallatsawa tanayi tana kanne ido . Sadam ne,yawwa to ku shigo da mushrikin nan,ohk tom takarasa tana kashe wayar. Hajiya waya baki umarnin daukar waya kiyi kira bayan kina kalkashin hukuma saboda muna zarginki da zabgamana karya akan abinda kika fadama shuwagabannin mu da farko sann... Wani wawan mari Deedee ta yankamai jikinta har rawa yake tace. shekara 63 A duniya ba dan tsinanniyar da yaceman kaziba saikai ,nace saiki? shege da katon kirjinka kamar Allon Ƙirya,to ubankama kaje kace nace uwarsa,kai da hukuma da wanda ya kirkiro hukuma kun tile kun kwashe kan babba bura ubaku.. Sosai su AYMAH suka gilgiza da bala'in Deedee dan basu taba ganin ta cikin wannan yanayin ba ga zagi kamar wacce ta tashi tasha. Rai ɓace yake sosa kumatin sa kamin ya dauki Bindiga yashiga nunamata tare da fadin shiga gaba. Deedee kam a zafafe ta kwaceta ta shiga rattaɓamai ga kwalkwalinsa sai huci take,lokaci daya kuma ta cire dan kwalinta ta jefar gefe ta fara wani ihu tana kururuwa da bude hannuwa.😳 MATAR OGA NA UMMY AYSHA Page 28 Zanso kuga yanda hankalin kowa ya tashi a palon nan, Aymah kau kuka ta fara sosai,Jameel kau hankali tashe ya doshi Dede. Cikin wani irin ɓari da take tare da daka mai tsawa akan karyayi kuskuran zuwa wajen ta, inba hakaba sai ta kashe kowa cikin mnt biyu. Aguje manager ya jawoshi hankalin shi in yayi dubu a tashe. Dr Abbah kau tsawa yashiga dakama sodojin nan cikin ɓacin rai Yace'' ga abinda kukajawo muna, kuyi takanku tin kamin tazama ajalin ku dan ba lafiyayya bace kundaiga alama. Kunson maza da tsoron jinni cikin kurin baki daya daga cikin su Ya fara matsawa yana faɗin. " ai'dai zamu dawo, Tinda ba haka zata dawwama ba,dole mu binciketa yakarasa yan kama hannun wanda ta kwalama Bindiga aka,. Zanso kuga yanda kanshi yayi malolo kamar an buɗe fatar an adanamishi lemom tsami ,kusan waje goma duk ya kumbura ya tashi sai kan ya koma kamar bishiyar mangoro. Yaran Adnan kau bayan Maman su suka lafe Jikinsu duk ɓari yake xukatan su cike da tsoro. Ita kanta matar Adnan din shuru tayi gabanta sai bugawa yake taga wadda tafita masifa. Mtssssa aikin banxa tsinannu haihuwar shabiyu saura kwata na rana ,yo har kun'buga dani,Sharrima in yaganni guduwa yake balle kai banxa bazara da wani tsinannan kanka kamar gidauniyar silba, zaka wulakantani ka karyatani a gaban Jikokina, bayan nason na girmi uban uwarka. Kaiiii Yaran ɗan ta Adda. ta dakama yaran Adnan tsawa. A gigice suke kallo ta.. Ido ta zaro masu kamar zasu faɗo tace . Naci uban ku dukkan ku,na daka tsalle na mari uwarku,na shake uwarku tayi aman haramcin da taci,zan zabgama kowannan ku mari dari dari in baku tashi kun dawo nan kasaba,tinda kujerun bana uban ku bane, shaggu kamar yaran turwa da ganin ku babu tarbiyya,kai Dan ubanka har zakazo muna mussulmai ka zazzage wando tsagar mazaunan ka abude da shegen Ƙugi bakikirin kamar bayan tukunyar gidan gandu,to zankoyama darasi kamar yanda na koyama Wancen katon banza uban naku. Zanso kuga yanda katon nan da akallah ya kai shekara 23 ya fara kuka yana Mama bazan karaba karki dakeni. Duk yan palon saida dariya taso kufcemasu lallai yaron nan basu samu tarbiyya ba sun sangarce da yawa. Manager dan Allah ka ceci ran yarana Matar Adnan tace cikin tashin hankali dan itama yanzu ta karaya Ainun. Babu ruwana Madina tinda ke ai a ganinki Amanarki zanci,bayan munyi magana dake ta fahimta akan in Aymah ta warke zamu baki address kizo gidan nan akwai magana,amma dan ki tozartamu da uwarmu da mukejin dadin zama da ita shine kika kwaso wayan nan sukazo suka mata rashin kunya,to babu abinda zan iya,cen kuda ita... Cikin tashin hankali ta fara rarrafawa gaban Deedee tace" dan Allah mama kiyi hkr karki tabaman lfy yarana wallahi zan sallame su yanzu,magana ta gaskiya ogan nin mijina basumason xan zonan ba,Wayan nan dai sune nasamu labarin komi a wajen su bayan nama su Alkawari kudi mai tsoka akan in sun kawoni zan basu. Shewa Deedee ta saki tace . To maza korasu furgada su, mnt biyar suka kara wallahi saikin sani ubanwa zasuyima barazana da bindiga,nida ubanama ke zama gabana Yana hada boma bomai( KAI HAJIYA DEEDEE 🤭) A guje kam Madina ta ɗauki wayarta ta sata Speaker tace suje bayason aikin. Gardama daya yaso kawomata ta faramai masifa da fadin zata tona mai asiri dole yasa ya kashe wayar suna zaune sukaji tada motar su. Zatai magana kenan aka turo kofar aka shigo su Sadam ne dauke da Adnan da suka sakemai wanka .. Da sauri madina ta mike tayi Wajen shi, Yayin da yaran ma sukayo wajen shi da sauri kowa na zaro ido . Cikin wutar kishi sosai take kallon shi kallon sama da kasa,kallon da babu tausayi balle Rahma,kallo mai cike da kiyayya da nuni da ka munafunceni.. A fusace ta faramagana. Ba shakka,ai dayake namiji kake,maci amana,Allah na godema, Allah ya kara kassaraka ya kuma kara kwashema albarka,kullum zuciyata ƙaryatawa take akan bazaka iya hadani da kowaba kamar yanda kace, Amma gashi,jibi wacce ka rayu da ita,nikuma inacen ka barni da yara Niga wahallalla,to Wallahi azeem dukiyata kaf sai kabani abina matsiyaci,Ka manta yanda na aureka,kana cikin haki na kunci,biyar baka da ita, Adnan wane gatane ke banmaba,amma sakayya farko shine zakaman kishiya,kishiyar da bantaba ji ko labarintaba daga wajen ka,Kullum nunawa kake nice ta farko ta karshe,hmm namiji kenan.. Idonta ta mayar ga ayimah ta zubamata ido tsawon lokaci kamin cike da dogon nazaro tace kai dakata!!!. Wannan ba itace kake ceman kayi hayar taba in zaka shiga taro tana rakaka saboda ni banajin turan ci? itace dama matar taka,lallai kacika mugun makaryaci,ina fatan kuma Allah ya ɗai-ɗaita karshen ka mugu azzalumi takarasa cikin kuka sosai. Kuka sosai yasa yace madina karkiman haka,karki furta mugayen kalmomi akaina,Madina ke kinfi kowa sanin duk wahala da nake sabodake da yaranki,sannan wallahi babu son ta ko daya a zuciyata face ɗaukar Fansa dake cike da ruhina,madina dubi halin da nike ciki. Maimakon ki kasanceman jagora da zata tsayaman akan a kama wayan nan mugayen Azzaluman a garkame saboda abinda sukaman,kiji yanda suka barni na dawo,jin Bi ruwan da kafana keyi mai ɗoyi wanda ni kaina damuna suke,amma ko Chemis basu taba kai niba,ko paracitimol basu taba baniba,dan Allah ku kwatar man yancina yace cikin kuka tare da faɗin yaku nan yarana yana bude masu hannu. A yatsine suka dinga kallon shi lokaci daya kuma suka dan fara matsawa bayan uwarsu suna noke kafada Alamar bazasu ba. Hankali tashe yake kallon su yana fadin mikenan idona ke fadaman. Uwakace sanye da dan buje kafara gani Deedee tace tana gilgiza kafa. Madina kau tace. Gaskiya yarana bazasuzo wajen ka su kwashi wannan cutar ba,sannan ai akan munafurci kayi auran baka fadaman ba to babu abinda zai sani shigema gaba,batun kuma yara karka sake cewa naka dan Wallahi wallahi bazan iya bari yarona daya ya raɓeka ba da sunan zaman jinya,Kuma takarda dole kabada,sannan gida daman ai nawa ne tinda na mahaifina ne, ko sisi na uwarka ko uban ka babu banza butulu. Madina ki fahimceni banci amanar kiba wlh, tambayeta kuncin da nasata gatanan,Madina bantaba yarda na Bata koda Cikin tsuntsuwaba saboda banason hada iri da ita , Wallahi so biyu ma na kus... Lafiyayyan mari Jameel ya dankaramai zuciyarshi cike da bakin cikin jin mugun kalaman da yakema matarsa. Cikin tafasar zuciya da fitowar kwallah daga idonsa yace . Jahili kai dama baka isa ka bata ciki ba ko ka hanata, Allah dai ya isa tsakanina da kai Adnan,kana kuntataman zuciya duk sadda ka ai'banta wahala daka ba matata,kana sani kunci,kana kasheman walwala,inajin kamar in sanya wuka in daɓama ita ga zuciya ka mutu uban kowa ya huta, Wallahi wallahi kai asararre ne jahili marar hankali. Kuma yau yau din nan sai kabar gidan nan tinda babu ko sisin tsoho da tsohuwa. Karka sake zagina Jamilu kajirayi fansata gareka, bazaima dadiba tinda har ka iya sanya hannu kana dukana Adnan yace cikin bacin rai. Okh fine mu zuba nidakai shege ka fasa. Madin kam taɓe baki tayi tace" to in kama koreshi gidan wa zaije,nidai kam nayi iya wahalata dashi bazan iyaba,Saboda na sashi inuwa ya jefani rana. Afusace Deedee tace to ai ga yaranshi nan masu siffar rakumin gwangwani su dau kai suyi gaba Man. Ikram ce cikin damuwa tace" mom yanzu fa akace wannan shine baban mu wallahi love bazai iya aurena ba ko waleedah. Kuka walidah tasa tace'' wallahi Nima Nason yaseer bazai iya haɗa iri da niba ace Daddy mu ke rike da mata biyu,sannan dubar safa duk ya lalace ya zama kazami mom ya daina wanka sai wari yake, dan Allah mutashi mukoma mom banason ganin sa. Kuka sosai Adnan yasa yana taɓa hannu da fadin" karkumin haka yarana duk abinda nike kutino domin ku nayishi,karku juyaman baya bazan iya jure rashin kuba.. Manager Yace'' taya kuka haɗu Madina. Hawaye ta share tace Adnan macucine kuma ALLAH ina da kokonto a kansa yanzu. "Ni dai kam haifaffar garin kaduna ce,acen natashi da iyayena mu ukku ne a wajen su,yayyena biyu maza dukkan su ba anan suke ba suna legos da matayen su kasancewar suke rike damu mahaifina ba shi da karfi sosai. Nayi Aure na auri wani Attajirin mutum harma na haifi da namiji guda daya a wajen sa,Ban dade da haihuwar ba aka sanar dani rassuwarsa bayan anyi zaman makoki na fita iddah dole tasa nadawo gaban iyayena nida yarona Bashir da aka raba gado akabani nawa da nashi ashema ba mai tsawon rai bane .Shekarasa biyu yayi kyanda ya koma ga mahaliccin sa. Tsawon shekara goma 10 ban sake aure ba lokacin kuma zaman gidan ya isheni duk da ina ɗan taba kasuwancin kayan mata na atamfa lace jikkuna da sauran su. Wata rana ina yawo cikin gari mota na ta lalace a waje mai karanci mutane. Cikin tsoro dai na fito da in dan dudduba kamar wasa naga mutum biyu sun zagayeni fuskarsu nade da rawani,hannu suka bani akan na basu key din motar da wayoyina da kudadena. Jikina na rawa na mikamasu key din da wayar . Cikin tsawa sukace in cire kayana ko su zabgaman wuka. Kuka na fara ina gamasu da Allah cikin rashin tausayi daya ya yankaman mari tare da sanya wukar hannushi ya keta riga na daka sama har kasa . Gigitaccen ihu nasa lokacn da naga na bayyana tsirara. Dariya suka fara ba kakkautawa kamin kuma inji sun tsaya,kaina a kasa na farajin suna bada hkr. A gigice na dago dan ganin misuke ba hkr haka nan idona yayi gamo da matashin saurayin da ke gwara kansu,kana ganin shi kason shima dan duniyar kanshine dukda na tabbata na girme masa nesa ba kusaba , zabgegiya bindiga naga ya zaro yana fadin zai kashesu. Hkr suka hau bashi amma Saida ya masu dukan mutuwa kamin ya ansheman komi yabani ya juya zai tafi ba tare da ko kallona yayi ba. Bawan Allah nace jikina na bari ina kankange jikina. Kallona yayi sama da kasa kamin yace wani abu. Dama gdy zanma dan Allah ka taimaka ka ajeni gida karsu dawo su iskeni na fada ina mikamai key din motar Kamar bazai an'saba kuma ya karba cikin ikon Allah ya dan jajjagula motar ta tashi muka tafi. Har gaban iyayena ya ajeni yama su bayanin abinda ya faru suka masa gdy Sosai. Nikam farat daya naji na natsu dashi Saboda inason jarumin Namiji a rayuwata da kaina naimasa tayin kaina bayan nabashi lbr mijina daya rasu da harkokin da nike yaceman zayyi shawara. A takaice wannan haduwa da mukai da adnan kamar wasa ya zama gaske har yanazoman fira.. Ganin haka yasa Abbah na cemasa ya turo iyayen sa. Anan yake fadaman shi bashi da iyaye ɗan Nijer ne wanda ke rike dashimane ya koreshi shine yazo kaduna neman aiki Har muka hadu. Sosai muka tausaya mai babu wanda yayi dogon bincike aka sanya ranar auran mu . gida hadadde na saya nabashi ba tare da sanin kowaba har iyayena saboda son da nike mai. Bayan bikin ne nikuma saboda son da nikemai da Tausayi na samar mishi Form din aikin soja. Ranar yayi farin ciki sosai ya saman albarka tare da rantsuwa da Alkur'ani akan bazai tabaman kishiyaba saboda halaccin da namasa. Naji dadi sosai kam dan ina son sa banaso ya hadani da wata. bayan ya cike ni nayi duk hada hadar da zanyi wadda ta zama wajibin da.. Ankai shekara goma da fara aiki sannan ya samu babban mukami yayin da nikuma nike da yara biyar maza ukku mata biyu . wata rana yake shedaman zaije yayima mai gidan sa daya koreshi Alkhairi ya nunamai yanda duniya tahi dashi. Naji dadi nama sa fatan nasara . To bayan ya dawo kuma yake shedaman sun daidaita harma ya bashi wani kwangila aiki da zai kawo mahaukatan kudi amma zasuyi shekaru. Sosai na bashi goyon baya dan ina son cigaban sa. Cikin damuwa yake shedaman bayason yin nisa dani na kwana ɗaya balle shekaru. Sake nunamasa nayi ba komi ko karshen wata ne yazoman . Haka dai ya dawo katsina da wannan zama yaceman yana aiki da brek ɗinsu . Nama murna sosai akan shima ya bani Shawara da mizai hana in'bashi dukiyata ya jefata cikin kasuwan ci ya juyaman ta hanyar shigo da motoci daga kwatano zuwa kano,Na amince naji dadi na bashi duk abinda na mallaka,yacigaba da juyawa duk wata in zaizo yana bani kudi mai tsoka hakan yasa na sake sakankancewa da bashi dukkan yarda. Wata rana yake ceman First love anaso a dinga turani manyan wuri da zamu tafi da iyalan mu dan tattaunawa da manyan mu amma ke bakyajin turanci. Shuru nayi gabana na bugawa,Raina ya bani ko dai Aure zayyi dan yaga gaba da baya tsufa ya tasoman haikan. Murmushi yayi yace karki taba tinanin zan hadaki da wata saidai bansaniba ko zaki amince na dauki hayar wata mata duk in haka ya kama muje da ita. Da sauri na amince ina sauke ajiyar zuciya . Bayan dawowar shi yan gidan mu sukazo ganina. Yah Hashim Da Yah Lawal Bayan mun gaisa suke sanar dani sun samu labarin ashe gidan da muke ciki ni nasaya to bazasu hanani kyautatama.mijinaba amma dai yazama dole in basu dukkan dukiyar da nike da ita. Nan fa rigima ta kaule tsakanin dasu aganina dan su kuntatama mijina ne suka ɓullo tanan. Wannan rikici dai har Adnan yaji inda ya basu hkr da cewa su bashi wata daya ya ida sayar da kayan da aka Sawo zai kawomasu da kanshi. Nan suka tafi rai ɓace ko sallama nikam ban masu ba. Washe gari Adnan yaman sallama alan zaije ya hado koda kudin nane ya basu dan mu.zauna lfy. Kwana ukku da maganar nan aka sanar dani kamawar da gidan mu yyi da wuta cikin dare wacce ba ason miya assasataba,Gabaki daya iyayena da Yayyena da sukazo tacinyesu. Fadara tashin Hankali bazai faduba. Amma Adnan ya taka rawar gani Sosai wajen dawo da walwalata fan kiri kiri hawan jini ya nemi kayar dani Allah ya tadani har naji sauki kamin ya dawo. A takaice dai Saida akai shekaru kamin ya koma cen da zama sai yayi watanni kuma kamin yaceman zaizo ganin kasuwancin shi na nan . Wannan shi ne tarihin mu amma a yanzu inada shakku akan ka Adnan,ina tinanin kai ka kasheman iyaye hakane??. Kan shi ya dago idon shi jage jage da hawaye. Gaskiya magana Ba... Ya isa Adnan fadamata Gaskiya da bakin ka, a wannan palon ba'a karya Manager yace fuskar shi ba walwala idonshi sunyi jawur . MATAR OGA NA UMMY AYSHA Page 29 Cikin matsanancin kuka yace. Tabbas Madina ina sonki amma nafison kudi da kowa a duniya,Kuma nayi alkawarin duk wanda zai Saɓaman akansu sainaga bayan shi,ba karya kikaiba nine nan nasa aka ma gidan ku wuta, domin danace miki na tafi babu inda naje hasalima ni nayi aikin da hannuna. Zahirin gaskiya tinda na tashi nidai kam banyi wayon sanin dadin iyaye ba saboda mugun takaucin su,duk a titi nayi rayuwa dan ganin na samu kudi amma bansamu ba, banson kowaba sai kyarar al'umma,shiyasa ban tashi da tausayi ko wani imani ba saboda inajin zafin masu kudin da ke shagali mukuma muna masu wahala, Bala'in takaucine yasa Babana guduwa yabar mama mu data kasance makauniya. Bata wani jin dadina dan bana mata biyayya saboda natashi da zafin zuciya takaicin haka dai yasa itama tayi lahira nikuma naci gaba da gararin rayuwata dan babu dan ginsu dake sona,A hankali nazama cikakken ɓarawo,daganan na fara fashi ina kwace dan dai inyi arziki amma ina,A haka dai zuciya ta bushe duk abinda zai bani matsala kawar dashi nike in huta cikin sauki,Kece kawai nike dan ragama wani abun saboda yaran da Allah ya bani dake,Aymah tasha wahala ta tin bayan dana mallaki kaddarorin mahaifinta,Daga baya na haɗa da nata saboda nason na rabata da duk kan wanda zatakai karata wajen shi,ashe Manager munafuki nane wallahi bazan taɓa yafema ba saboda dakai aka hada baki akaci amanata. Ke kuma madina yanzu ina rokon ki da ki bar komi ya wuce ki daukeni mu koma cen muyi rayuwar mu mai daɗi da dukiyar da na taramana. Dariya sosai Deedee tasa da bata cika yiba tace. Wannan ai shine xama dakyal tashi dakyal,yanzu kai dan Allah har kana tinanin rayuwa mai dadi,to ya labarin rayukan daka kashe,ai wlh azeem bazaka taɓa yintaba,rai ɗayama ka kashe kaki samun sukuni balle rayukan da basa kilguwa mugu azzalumi, wallahi bazamu taɓa kaika court ba saboda munson basa hukuncin Allah,amma zamubarka hakanan kara zube ka wulakance ka bankaɗe. Aymah kau hawaye ta share tace Adnan kaida Allah akan duk kan abinda kayi,Ka Auran ne dama dan daukar fansa mahaifina akan k'in arama kudin da yayi,Ka kashe iyayena akan Abin duniya,ka kashe na matar ka akan sunaso su son halin da dukiyar yarsu take ciki,ka kashema Baba Ali Mata da yaran sa ka sare masa hannu,ashe baka girma da iyayen kaba to su waye kake kaini wajen su. Kanshi a kasa yace hayar su nike duk sadda bukatar hakan ta tashi amma daga sadda iyayenki suka mutu ai baki sake jin d'uriyarsu ba ko saboda Aikin su ya kare. Deedee tace aikin su ya kare ko dai kwanan su ya kare suma.ka masu yankan rago ba,anya ba sheɗanin Aljani yayima uwarka cikiba,wlh ba shakka ,yanzu haka fitsari ya matseta shegiya ta kasa Rikewa ta yanka da gudu ba addu'a ta an'taya toilet tayi na tsaye shikuma yayi wuf jikinta,kai hakamane, gashinan ta dire mana bala'i a ban kasa. Kallon ta yayi yana dauke kai som baiji zafiba saboda ba sune gaban shiba shi mantawama yake da iyayen nasa. Madina tace Lallai Adnan, ni dakai har abada, wallahi wallahii bani bakai, kabani mamaki amma Laifina ne dana yarda dakai na baka amanar rayuwata sabosa son da nikema nake sirri dakai wanda wayanda suka kawoni duniya basuma saniba gashinam kamin illah mafi muni a rayuwata ka rabani dangina . Manager yace kagani ba,kaga abinda rayuwa tama,to kason dai nine komi naka duk wani dukiyar kowa ina da ita a rubuce, To Alhamdulillahi dama ina biyemane dan nima karkayi sanadin kaini kas nawin bayin Allah na kaina, bawai dan ina tsoron ka kasheni ba a'a sai dan ina tsoron ka samu wani maimaka aiki wanda zuciyar shi ke irin taka A linke bayin Allah nan,Amma yanzu Alhamdulillah zan sauke nawie ya fada yana mikewa tsaye ya dakko manyan jukkuna da duk sunyi kura daga Motar sa. Agaban Aymah ya aje tare da mikamata duk kan takardunta yace. Tom gashi, Alhamdulillah na sauke nawinki AYMAH, ruwanki ne kiba mijin ki ruwankine ki rike abinki nidai kam na fita. Kai ta jinjina tare da zamewa ta sakko kasa cikin ladabi ta durkusa gaban Jameel hannu biyu ta bashi tana murmushi idonta tab da hawayen kewar iyayen ta tace . Baby Kai da kaya zasu iya zama mallakin wuya hakane?. Kai ya dagamata cikin so da tausayi. . Tace Masha Allah,kamar yanda Allah yabaka ni a matsayin mata,yakuma bani kai a matsayin miji,wanda nasamu natsuwa dashi dari bisa dari,. Ni Ummu Aymanah na mallakamaka dukkan abinda Allah yabani a matsayin kyauta,Nakumayi Alkawari zanyi biyayya ga auren mu in sha Allah, bazan taba duba girman danamaba ko dukiyar danafika Jameel kai ni keso, Tinda aure na na kamu da tsananin kaunarka duba da yanda nayi rayuwa da family naka masu dattako dakuma mutumci,duk mace ta kwarai tana so ta samar wa ɗiyanta uba nagari,nidai kam nason nayi sa'a Alhamdulillah,kuma na yarda da karin maganar nan wani hani ga Allah baiwane, Allah yabamu zaman lfy ya kuma sama auran mu Albarka. Murmushi ya saki cike da shaukin so yana sake matsawo ya karɓi duk kan abinda ta bashi ya aje gefe kana ya kama hannuta ya zaunar da ita akan kujera yace . Ameen Sweetheart,Ni Jameel nayi Alkawari tsakanina da Allah zan rike matata saboda son da Nikemata domin Allah da tausayin da Nikemata matsayinta na maraini,in sha Allah bazan taɓa barin kiyi kukan maraiciba,kana inaso ku zama sheda mutanan palon na zan karɓi dukiyarta amma dan haɓɓakamata ita bawai dan na mallakama kaina ba aa,ke nake So Aymah bawai dukiyar kiba,jin'dadin da kikebani yafi dukkan abinda kika bani na dukiya, Fatana Allah yabaki lfy kinji. Gabaki daya aka amsa da Ameen kowa na yabawa da dacewar da sukai da juna.. Adnan kau kuka ya fasa yace wallahi bazan tashi babun ba ɗilihuba, ba kudi ba mata, kai wallahii na mayar dake dake babu shegen da zai iya auranki na mayar dake na mayar dake nafada har so ukku. Mahaukaciyar dariya palon ya dauka ciki kuwa harda yaransa da suke masa vidio shaheed na faɗin bari mu samu na dorawa a TikTok. Deedee kam murmushi tayi tace'' akwai wani darasi a wannan yaran naka Adnan. Som babu wanda ya damu da damuwarka,Babu wanda ya nuna alhini akan rauninka,ko miyasa?. Ido ya zubamata baya ko kyaftawa. Murmushi tayi tace'' nason baka da ilimin bani amsa. To bakomi bane face abinda kayi akema,baka kula da nakaba gasu suma batakai sukeba,wannan ya nuna cewa babu ɗigon tausayi da so a ranka,Gashi Allah da nashi ikon kai kuma ya dasama son su dan ya jarabceka,Ina baka shawarar da kayi gaggawa tuba tin kamin lokaci ya kurema. Manager daya gama hada kudin madina kaf da takaddunta da ribar dukiyarta ya mikamata yace yafayi wannan tinanin barshi Deedee. Madina gashinan kema an sallameki ga uwar kudin ga ribar duka ya mallakamata Yace'' Hakkin kine ki bashi abinda kikayi Niyya sabosa babu sisin sa Anan duk kudin da yake samu wajen aikin aka hidimar banzar sa yake karewa,Dan dama.saboda wannan lokacin nike bashi shawara da kar ya hada dukiyar sa data marayu to kam gashi yanzu kwalliya ta biya kudin sabulu. Aymah kema ga takaddaun Asibitin ki dan ni nakai wayanda yace yanaso su siya na nemi alfarmar su da su rike asibiti zuwa wani lokaci. Yanzu haka Aminiyarki ke kula da komi Haj Asiya, amma ba tare da sanin kowaba dan ni Nahanata , ga takaddun sun dawo gareki, in mijinki ya amince saiki koma aiki in bai aminceba kiyi biyayya Auren ki.. Nan suka shiga tattaunawa madina na neman alfarma wa Deedee akan zasu kwana gobe su koma tace bakomi. Shaheed din Adnan ne ya mike yama Mahaifiyar su rada akunne yace. zanje in ga wani abokina dake nan garin na dawo ya turomin Address . Kai ta dagamai sauran yan'uwansa maza suka bishi. Da fitar su ko 10mnt b@ Aibah wayar madina ta fara Ring. Zarota tayi daga jikka tana fadin shaheed miya faru ko baka gane takan garin ba? Ihu ta fasa tana fadin sun mutu fa kace,Yaran nawa dukkan su,kankace mi ta yanke jiki ta fadi a sume.. MATAR OGANA UMMY AYSHA PAGE 30 ""Hankali tashe Manager ya ɗauki wayar ya kara a kunne . A kiɗime yake fadin miya faru dasu, Innalillahi wa Inna ilaihi Raji'un gamunan zuwa yajefa wayar yana mikewa da sauri agulguje yama Deedee bayanin abinda ke faruwa. Fadar tashin Hankalin da Adnan ke ciki ɓata lokacine domin Kau batun butumi yazama,Dakyal ya iya dakko kalmar Yaran nawane suke mutu,kai ina basu bane,su sunanan da ransu zasu rayu dani,dana Warke zanci gaba da neman kudi ina basu na tabbata zasu dawo sona,haba haba yama za'ayi su mutu ai ba yanzuba sai sun tsufa amma yaran da ko 25 babban su baikai ba gaskiya bazai yiyuba . A yanda yake maganna tamkar mahaukaci sabon kamu,Yan palon kau jikin su yayi mugun sanyi waleedah kau da ikram kuka suka fara sosai suna jijjiga Mamar su da faɗin ta tashi karta mutu . Deedee mah dai Saida tausayin su yakamata matuƙa, hakan yasa tace Dr Abbah ya taimakama Madina. Jannat ya ɗauki ruwa yaba yana mikewa tsaye yace. bari muje inda abin ya faru. Manager mah da jikinshi ya dauki rawa nan suka tashi Jameel dake ta lallashin Aymah ya mike ya bisu Bayan yaba Jannat umarnin Yimata Allura dan tasamu relief duba da jikin nata ɗanye ne. Babu wani tazata tsakanin su da inda abin ya faru, Dan kan kwanar shigowa layin ne sukaga taron al'umma. Motar suka aje aguje suka fara kutsa kai cikin dandazon mutanan daketa salati. Dukkan su saida sukayi hawaye domin kau yaran ne zube kasa babbar mota tabi takansu ta wuce baka ma gane fuskar su sosai yanda sukayi damege. Cikin ɓarin jiki Dr Abbah ya hau duba jijiyoyin hannuwan su amma babu mai numfashi a cikin su . Innalillahi wa inna ilaihi rajiun yace yana mike tare da faɗin dukkan su Allah ya ɗauki abin sa.. Da dama jama'a sunyi alhini wani mai shago yace ni inaga basu kware da tukin ba, Saboda basu ko duba hanya ba suka shigo da tasu Motar shikuma yayi gaba dasu kuma bai tsaya ba akan idon komi ya faru. Babu wanda yace mai kala sai ma Taimakon al'umma da aka nema aka sasu a mota jikin su nata zubar jini akayi gidan Aymah dasu. Anan harabar gidan aka aje gawar tasu.. Palon Aymah kau Jannat ce ta faramata dubarar su ta ma'aikatan lfy Aymah na kara nunamata hanya tinda ita likitace har dai ta falfaɗo kamin Jannat din taja Aymah sama tamata Allura itama kana ta sakko ganin ta samu bacci. Madina kau tana tashi tace abinda ya faru ya faɗomata arai,Idonta cike da hawaye tace da gaske ne ko Adnan duk sun mutu?,adnan kaga ishara daga rabbi ko,Kaga abinda ya faru damu rai ukku lokaci ɗaya tacije baki tare da ɓarkewa da sabon kuka su Deedee na tayata. Cilin kuka mai tsanani yake fadin . Basu mutuba,na tabbata suna raye,Yarana na nan,sharri magauta ne kuma wlh su zankashe amma ba yarana ba.. Zatai magana sukaji ana bude get da hayaniyar mutane. Cikin tashin hankali Gabaki dayansu sukayo waje akabar Adnan ciki na gunzar kuka dafaɗin. !! Sadam!! Dan Allah zoka daukeni in karyata abinda Zukatan su ke faɗamasa ( Dama wanda bai sana da abuba baya daukar tawakkalin sa). Su Deedee kam suna fita ana shinfiɗe gawar matasan harabar gidan akan tabarma. Kuka sosai suka fara Deedee na faɗin. ke rayuwa ina zaki damu,cikin awa biyu muna zaune dasu amma gashi Allah yayi nashi ikon cikin 10mnt,Adnan Allah kasa mutuwar yaran nan tayi sanadin tubanka wannan tashin hankali dami yayi kama. Baba Ali Dake share hawaye yace ɗana Sadam fiddo mahaifin su yazo yaganema idon sa. Sadam dake kuka sosai danshi ya ɓudemasu get da zasu tafi har da 5k Shaheed ya bashi amma gashi yanzu harya mutu. Hawaye ya share ya doshi kofar nan ya kinkimo Adnan ya fito dashi. Agaban gawarwakin ya direshi. Jiki na ɓari yasanya hannusa ya yaye bedin da akasamasu dan yaga tabbaci. Take kam ya fasa wani gigitaccen ihu tare da lailayo ashar yashiga d'urawa baji ba gani,cikin matukar zafin zuciya ya daddage ya kashe fuskar gawar Autan shi saif da mari yana faɗin" dan uban Baban ku ku tashi baku mutuba,In fa baku tashi ba wayan nan makiyanane zasuje su binneku da ranku,zafin kasa zai kashe ku,zafin kasa yafi na harsashe zafi,kutashi kunji ko yarana banason rasaku yakarasa cikin gushewar Hankali. Janye shi akai yana zabga ihu da faɗin basu mutuba sharri magautane. Madina kau hawaye ta share cikin tawakkali kamin ta tsugunnah gabansu ta hau yimasu addu'a da tasamu daga bakinta, kamin ta lumshe ido tace. Ya rabbi nason kai kabani kuma ka karɓa nakuman godema dan nason wanima haka zaizo duniya kuma ya koma gareka batare daya samu ba, Allah ina rokon ka da kabani juriya da hkr akan rashin yaran nan,Allah ka shiryaman matan nan kabani ikon basu tarbiyya danagazabama yan uwansu,nima nason mai kuskurece ta fannin tarbiyya yarana,Gashi ban zaɓama su uba nagariba gashinan alhakin abinda yayi ya fara bibiyar yaran sa,Gaban Adnan ta matsa tace kagani ba,Yakamata wannan abun ya zamema izina Adnan,ka kashe iyayena mu da yaran bawan Allah nan ba tare da kataɓa la'akari da irin ciwon da zukatan mu zasuyiba,Yau kaima gashi ka tsinci kanka acikin layin masujin kewa da kadaicin ahlinsu, Adnan baka isa kama Allah wayoba,kana dukkan wanda Yace ya barka da Allah yagama da rayuwarka,ina rokon Allah yasa mutuwar yaranka ta zamema izina da sauran masu hali irin naka,Nidai na yafema nakuma yafe masu Allah kabasu Sa'a shiga makwancinsu na gaskiya ta karasa cikin rawar murya. Dariya yashiga yi sosai yana kwaikwayon maganarta da faɗin baki da hankali dama madina ke ai kan zabo gareki. To wallahi wallahi babu ɗan daya isa ya kassara yarana na barshi ina bakison darajar subane dama,dan haka duk kan inda mutumin nan yake sai an nemoshi na dauki pansa,Sai na karar da kowa nashi,Saboda yarana sune rayuwata. Manager ya dakamai tsawa rai bace yace to kamar yanda ka saba kashe mutane baka bayyana kanka haka shima ya kashe su batare daya tsayaba, in zakabarwa Allah kamar yanda suma suka barka dashi ya sakamasu yazo kabari kazo kamasu addu'a ashiryasu akai su makwancinsu, in'bakayi kuma mu muyi dan neman yardar Allah. Bazan ba dan kutumar ubanka Manager munafuki, kuma bance kowane a cikinku ya taɓaman yaraba azzalumai ina nan bi takan ku shege juyi marar haihuwa,shine ka hada baki da mai mota ya takeman su dan kaga kai ko zakara baka ajeb, to zakason dani kake. . Wannan abubuwan daya dingayi ya sashi bakin jama'a sosai dan da dama gani suke rashin tawakkali ne akan jarabtar bawan sa wasu kuma suna tausayamai ganin yara har ukku lokaci ɗaya( Allah ina ruwan sa ,inma yaso yanzu saiya kifar da duniyar). . Deedee kam ganin wannan masifar tayi yawa yanata taramasu mutane tayima mahaifin Jameel waya akan yazo da liman nan sukazo aka gayyato mutane aka shiryasu tare da masu sallah aka dauki gawarwakin dan kai su gidan su na gaskiya. Adnan dake kwance yana ihu yaga za'a fita dasu ya fara kunduma ashar. Da liman din, da Ladan din, da gawarwarkin kunci kutumar ubanku yan bura'uba shaggu,in'baku maidosu ba sainayi kararku haka yayita wannan hauka yana binsu da ashar har suka fita. Kuka yafasa sosai yana kara tsinema wanda yayi sanadin mutuwar yaran sa da wanda yaki maido mai su gaban shi dan ko tsutsa zasuyi kwara abar su agaban shi yana ganin su da aturasu rami mai zafi ( Hauka maganin ka Allah, kai rayuka nawa ka kashe baka taba wannan tinanin ba sai yanzu da abu yazo kanka oh'ni Hafsah) Wani nawie da zugi zuciyar sa ta shigayi,Gefe da gefen sa ya fara kallah yaga babu wani Abu, akan window ya hango wata ƙaramar wuka,tsintsiyar dake gefen sa yasa ya bugota ta fado gab dashi ya sharto ta gaban sa ya dauka .. A zafafa ya zare wandon shi yana faɗin kwara in biku uban kowa ya huta saboda ina rayuwane akan son ku da nema maku ba akan kowane katon banza ba ya karasa yana d'aga Wukar ya raba gaban sa biyu. Gigitaccen ihu yasanya yashiga ɓillayi da kururwau yana wasu surutai. Su Deedee kam da Dukkan su sun shiga ciki tinda aka fita da gawawakin suka fito waje aguje jin ihun sa. Ya salam, jinin da suka ganshi a ciki ya tayar masu da hankali Nan sukayi kanshi suna dagoshi sukaga abinda ya aikata ma kansa,sakin shi sukai suka koma gefe suna salati da ganin wannan bakar rana da basu taɓa tinanin taba. Jannat ce tayi karfin halin kiran Dr Abbah ta sanar dashi halin da ake ciki. aiko saigashi yazo cikin lokaci shida Jameel. Hankalin su yayi matuƙar tashi lallai Adnan Baison kaddara ba som,waya yayi asibiti dan kawo ambulance akaishi Cikin gaggawa. Ana zuwa daukar shi yana cikawa bayan ya sanya wani irin ihun da yasanya Aymah tashi. A takaice dai haka akamasa wanka shima akabi bayan yaran shi Dashi kamar yanda yake faɗa Haka akayi zaman makoki jikin kowa a sanyayye da halin wannan rayuwa,yanzu Shikenan tashi ta shuɗe, duk abinda ya shuka zai girbi abinsa a inda bbu kowa daga shi sai halin sa khairan ko sharran Allah kasa mugama da duniya Lfy. Bayan sadakar ukku nan aka raba dukiyar daya bari Wacce bama wani yawa garetaba akaba Madina da yaranta . Kin karɓa tayi tace aje ayi rijiya dasu ladar allah yakaima Yaranta da uban su ( Mata da miji sai Allah) Anayin sadakar bakwai ta tattara takoma Kaduna bayan su Deedee sunmata alkawarin zuwa bikin su ikram din in lokaci yayi. Gdy sosai tamasu suka rakota ta dauki hanya akan motar da manager ya bayar akaita.. Ajiyar zuciya Aymah ta sauke tana kallon Jameel da shima idon shi akanta yake ganin duk ya da tayi sanyi. Su Jannat ne suka mata sallama akan sai ankwana biyu suka masu gdy suka wuce . Deedee mah tace to ai Shikenan bari kai bawa kaje ka dan runtsa gobe in dawo sana'a ta dan kar talauci yasamu fuskar tinkaroni,Dma saboda kar madina taga banmata karaba,oh'ni Adnanu anacen , hmm rayuwa kenan Allan ka bamu ikon shuka Alkhairi. Ameen suka ce ta buɗe kofar ta ta shige ta mayar ta rufe. Hannuta ya kama suma suka haura sama. Abakin gado ya zaunar da ita yana sauke ajiyar zuciya da cika bakin shi da iska. Ya hkr Sweetheart Yace yana kafeta da ido . Cikin rauni ta fara hawaye sosai wani na korar wani.. Shikam wani irin zafi yakeji a zuciyar shi ganin har lokacin tinanin Adnan ke ranta tama kasa bashi Amsa. Tsaye ya mike yana wata tafiya ta zakuna ya saki labullayen dakin kamin ya cire kayan shi baki daya ya daura towel dinta. Har lokacin bata dawo daga duniyar tinanin data wullah ba. Lips ɗinsa ya ciza ya faɗa Toilet yayi wanka tare da ɗauro alwallah ya fito. Inda take yazo ya tsaya yana yarfamata ruwan hannusa yace tashi kiyi wanka ki dauro Alwallah.. MATAR OGA NA UMMY AYSHA PAGE 31 Bata da tabbacin lokacin azahar yayi dayake mata maganar sallah amma takasa cemai Komi ta shiga toilet din ta gabatar da wanka mai kyau ta dauro alwallah ta fito. Akan sallaya ta iskeshi sanye da jallabiya da hula irin ta ustazan nan taɓani kaji hadith. Jiki a sanyayye ta ƙarasa gabam mirror ta shafe jikinta da turaruka masu sanyin daɗi kamin ta zira rigarta tayi tsaye kai a kasa. Abin sallah ya shimfidamasu kamin ya jasu sallah. Mamaki sosai ke A ranta amma bata da ta cewa. Raka'a biyu sukayi kan ya juyo ya rike kanta yamata addu'a sosai kamar yanda sunnah ta koyar damu,bayan ya gama ya tambayeta akan ibadarta kuma bai samu matsala ba kamar yanda yayi tinanin. Zuwa wannan lokacin kau Aymah sosai gabanta ke faduwa dan ta fahimci inda kalamansa suka nufa saidai bataga fuska magana dashi ba ya tsare gida kota ina ya dawo Jameel din shi nada babu wasa ko alama a fuskar sa. Shikam ganin haka yasa ha kama Hannuta ya yana dan murza tsakiyar tafin hannun yace kina da buƙatar abinci haka ko abinsha? A tsorace take gilgizamai kai Alamar a'a. ''Kimin magana Ummu ba d'aga kaiba?. Cikin rawar murya dake bayyana tsoronta tace ka manta bamu jima da kalaciba banajin yunwa. Ok fine. Aymah kin Aminta da na xama cikakken miji a gareki yanzu ba anjimaba? batare dana baki kazar da kowace amarya keci ba adaran farkon ta,Zaki bani kyautar kanki yanzu da rana saboda ina cike da kishi na son kasancewa dake,Amma in baki amintaba duk yanda naso da matsuwa zan hkr. Ya salam! sosai zuciyarta ta buga bata taɓa tinanin zuwa wannan lokacin zasuzo nan ba, duba da ganin duka sati biyu da kwanika tayi da tashi daga jinya.. Uhm ina jinki yace yana tsareta da mayun idon sa. Shuru tayi tana kara sadda kanta kasa. Baki Amintaba ne ya tambaya yanabinta da kallo. Nan ma shuru tamai saima kuka da ta nemi samai dan kalaman sa sunmata tsauri sam batama cikin natsuwar ta.. Dan murmushi yayi yana mikewa tsaye ya cire jallabiyar jikin shi, tare da kama hannunta ya zare hijjob din da jallabiyar dake jikinta yace sun'miki nawie muje ki kwanta tom tinda baza'a bani ba. Bata cemai komiba haka suka isa akan gadon ta kwanta shima ya hau bayanta ya lafe yana sake rungumota jikin shi. Tsawon 30mnt bataji yamata komiba hakan ya saukar da natsuwa sosai ajikinta takuma saki jiki har bacci ya fara fizgarta. Kamar wasa tafarajin hannuwansa na yawo a sassan jikinta har indama bashi kaiwa amma yau saigashi yana zuwa. Abufa kamar ama tinzirasa ta dingajin saukar numfashinsa da sauri sauri a cikin kunnanta ,ga wani dogon nishi dayake dake nuni da abin na kaimasa har tsakiyar kwalwa. Aymah nah Dan Allah, Dan Annabi ki mallakaman kanki,karki hanani ,zan iya rasa rayuwata a wannan gabar, washhhh Aymah marana zai tsinke Aymahhhhh yafada da karfi tare da tashi daga jikinta da sauri yana karato Addu'a datazo muna a sunnah duk sadda zaka kasance da iyalinka. Allahumma Jannab na shaidàna.... Har dai zuwa karshe. Nidai kam kafana na kwaso nayi plo gudun makancewa. Tsawon 30mnt na dingajin salatin Aymah da karfi ita dashi yayin da shikuma yaketa kabbara kai kace limamin makkane,Ya salam ita tana kuka tana fadin ya daina zafi shikuma yana fadin walhamdulillahi khasiran,wa subhannallahi bukhratan wa Aseelah yah ummu Aymah nah,yake uwar kowa ciki hardani . A takaice dai ɗumi dai Jameel babu wanda baiba dan har Adnan saida yadinga kwararoma addu'a neman gafarar Allah a Wannan kwogi daya tsinci kanshi ciki mai ɗumbin Albarka. Tsawon hr 1 kamin ya fasa gigitaccen ihu mai razanarwa kamin kuma yayi shiru yana sakin gurnani. Wannan ihu yasani ɓarin jiki matuka, ai A guje nayi dakin dake da matsanancin duhun da bana iya hango komi kai kace tala tainin dare ne. Zama nayi ina raba na mujiya amma banji komiba sai saukar numfashinsu yayin da Aymah ke Sauke ajiyar zuciya akai akai. Tsawon 30mnt naji saukar numfashin Jameel, Kamin Cikin natsuwa ya matsa gefe yana sauke numfashi da ɗan ƙarfi,Ido ya rintse da karfi wani so da kauna gami da shauki na tsaga dukkan lungu da sako na jikin sa,Yin kwatancen farin ciki da yake ciki ɓata lokaci ne,zai iyacewa baitaɓa jin dadin da yakai daɗi ba sai da ya shiga kogin daɗin Aymah yayi linkaya.Ga annashuwa mai cike da nishaɗi yakeji A tattare dashi,kai baiwar Allah nan ba a fuska kadai take da kyauba kogintama cike yake dam da ruwan zuma dn yafi karfin madara,Gata lafiyayyan mace yafada yana shafa kirjinsa data shiga yimasa feshi kamar an bude pampo. Aymah kau likis tayi Idonta a lumshe harda sawun hawaye,Zahirin gaskiya taji masifar dadi lokacin dayana wasa da sassan jikinta amma tinda ya kawomata ziyarar bazata taji sabon sauyi daga dadi zuwa wahalar da zata iya rantsuwa bata shataba a First nyt ɗinta. Domin som halittar Jameel data Adnan ba daidai suke ba,, Lallai kadaina raina jariri wata rana Angon ne,Bata taɓa zato ko tsammanin hakaba,bata taɓa tinanin girman Jameel zai iya sata kuka ba A ɗaukar da take mai,amma sai gashi kuka sosai take tana gama sa da Allah akan yabar hakarta hakanan, ga wani masifar ciwo da gabanta ke mata kamar an watsamata barko no,jitake kamar yanzu aka ɓareta a ledar,koda yake yanzu din ne ya ɓare ta tinda duk tsawon lokacin da sukai da Adnan so biyu ya kusanceta shima baya ko 5mnt yagama ya juyamata baya yace bashi da lfy ta ɗa namiji. Ta ɓangaran Jameel kau a Hankali ya yunkura zuwa inda take ya yaye rufar jikinta cike da shauki yace Babylov,Ngd Sosai da wannan kyauta da kikaman kinji,Naji daɗin da bakina bazai iya furtawa ba,Kin kara samun Babban gurbi a Zuciyata da har Abada bazai goge ba,dan Allah karki taɓa juyaman baya har abada nima namaki Alkawari bazan taɓa gujemaki ba. Shuru tayi tare da sake rufe fuskata dan Wlh kunyar shi takeji matuƙa da bata taɓajin kwatankwacinta ba sai yau. Cigaba yayi da cewa. Yah Allah ga baiwarka nan mai dumbin ni'ima da zallar baiwar daka bata, Allah ka dawwamar mata da daɗinta har Abada, Allah kafi kowa sanin halin farin ciki da nashiga ta dalilinta, Allah kabata tukuici da Aljannah kah ta fiddausi,Yah rahm.... Da sauri ta bude ido tace. Amma in addu'a zakai ai kabari ka tsarkake jikin ka ko ta karasa tana zubamai harara. Murmushi yayi cike da shuki yace"laifin kine, kin gigita karamar kwalwata Babylov. Baki ta turo cikin shagwaba dabatason ta iyaba tace babu ruwana dakai tinda haka kaman,ina ganin ka mai tausayi amma shine ... Bakinta ya rufe da sauri ta Hanyar hade nashi da nata waje daya yashiga bata hadadda sumba datasanya jikinta likis takasa ƙarasawa,shikam a cikin lokaci yanayin nasa ya fara sauyawa dan wani irin sabon yanayi yaji yana rasa shi, ashe inbakason abuba kafi hkr saɓanin ka son dadin sa. . Aymah kau jin yanda yake zungurar ta yasata fashewa da kuka sosai tana fadin . miye haka kai kuma naka salon kenan,Wai Jameel baka ganin aikine jikina har yanzu ban ida samun lfy ba fa. Ya salam yace da Sauri yana direwa daga kan gadon,kanshi a ƙasa sai faman matse jikinshi yake dayakejin yana barazana tsinkewa dan wata mahaukaciyar shawa'awa ya sake samun kanshi a ciki. Tsawon lokaci kamin ya tashi yayi wanka ya gasa mazaunansa da ruwa dan sai lokacin yaji Azababan ciwo kamar zai haihu( TA YARO KYAU TAKE BATA ƘARƘO) Bayan ya gama ya hadamata ruwan wanka kamin ya fito palon dagashi sai towel dinta . Cak ya dagata yayi Toilet da ita. Idonta a lumshe har ya gama mata batare da ko dayansu yace komi ba dan yace ya tanka tsab zai iya kaimata sabon farmakim da bazai iya saurarama uzurinta ba . Kiyi wanka tsarki ki fito yace da sauri yana kama kofar ya fito tare da zama gefen gadon ya dauki wayarshi ya shiga dubawa,ido yazaro ganin 4:44 gashi ko la'asar basuyi ba,Misscall din daya ganine na Deedee yasashi yin shiru yana wani nazari. Aymah kau yana fita ta kara hada ruwa sosai ta gasa kanta takumaji dadi kamin tayi wanka ta fito idonta a kasa gabaki daya karamin yaron nan ya hanata sukuni yau wannan ai shine raba raini, Wai jaki ya kusanci kaza😜 Tinda ta fito yake bin dogayen cinyoyinta da kallo cikin tsananin jaraba. Kamar ance ta dago kanta karaf idon su ya sarke dana juna,gabaki daya ya saki towel din nashi bajenar sa a waje gandandam kamar An adana masa muciyar tuwo. A rikice ta doshi kofa da niyyar fita ya mike batare da ya daura towel dinba ya kamo hannunta Yace'' ina zakijene,ke kanki nason kina cike da k'ishin ruwa Baby ki bani dama mu sake gamsar da junan mu,Jibi fa yanda lokaci daya kika rikice daga ganina babu towel,Wallahi AYMAH sai kincire kunya,nason ina sa bukata amma zai yiyu ke yanayin ki ma ya zarce nawa jibi idonki fa. Lallai namiji duk inda yake bashi da kunya jibi abinda yake fadamata. Bazan taɓa jin kunyarki ba saboda munriga munzama daya nazama ke kin zama ni,sirrina nabaki kin bani naki to miye abun jin kunya?. Shuru tamai dan batamason magana ta fito fili ba. Zai magana wayar shi ta shiga ring yana dauka yaga Deedee ce, ɗan tsaki yayi tare da jawota yace inajin ki mutum na wajen iyalinsa sai kirana kike miye? A zafafe tace kai dan kutumar ubanka ina yar mutane ? karka maidani katuwar banza mana,ya zanyi raɓe rabe cikin gida kamar tsohuwar agwagwa kana aikata abinda kake so da ita,baka lura da jikin yarinya nan miyasa waiku yaran yanzu baku da hkr som,jarabane daku kamar ayu,wannan wane tashin hankaline kwanantafa 16 kacal da yimata aiki amma kaiga hakilu har ka hakemata dan kaga batada hayaniya,Bakama ko tsoron ka rufzamata da kirjinta zuciyar tayo waje,kai bakama da tausayi dai a takaice takarasa tana rushemai da kuka. Aymah kau bakaramin daɗin abinda Deedee tamata tajiba ko ba komi ta ceceta daga hannun sa dan har ta fara sadakas wa. Toilet ta koma ta sake e Ɗauro Alwallah ta fito yayin da shikuma ya aje wayar shi a sanyaye dan magana Deedee ta ratsashi yashiga wanka yazo yayi sallah la'asar dan ita har tagama Tata. Mikewa tayi ta isa wajen wadrob din ta tazaro wata atamfa mai kyau ta zura, ko mai bata shafa ba sai turare data feshe jikinta mai daɗin kamshi ,tana gamawa ta fara kacaniyar bude kofa dan ta fita. Aguje ya kama hannunta jiki a matukar sanyaye yace Aymah Allah yasa kema ba kallon azzalumi kikeman ba,Allah kasanya ba kallon marar Tausayi kikeman ba, Wallahi kishine ya sani Kusantar ki Aymah naga kina tinanin wanda tashi ta riga ta shude,naga muddum banzama keba baki xama niba bazaki taɓa sani a rankiba yanda nike so. Murmushi tayi tana zuba idonta a nashi tace aa som,kawai abune baka saba dashiba kason komi sai A'hankali, inamaka fatan Alkhairi tana fadin haka ta shafa sajen sa kana ta sauka kasa cikin natsuwa,bayyi karya ba taji zafinsa Amma yanzu tamasa uzuri matsayin sa na sabon shiga. Bata jima da zama a palon ba ya sakko cikin sabuwar jallabiya fuskar nan tashi fayau amma kuma ya tamketa tsaf baka taba cewa shine. Kusa da ita ya zauna yana faɗin" babu abinda ke miki ciwo dai ko? Ki ta dagamai tana fadin babu sai kace yarinya dai. Hmm hakane fa,Ashe dazu a mafalki naji kina neman taimako da fatan kin gamsu da yarinta mijin naki. Murmushi tayi tana fadin kaiko.. Deedee ce ta turo kofa ta shigo a yanda ta iskesu yasata raba ido kamar mage dan batayi tsammani ba. Kai Jameel ya haka,dazu ihun waye nikeji kamar na Aymah . To nima dai ke nike jira kizo kiman bayani dan naga dazu bani kike nemaba kawai kin hau mutane da fada . Shuru tayi kamin tace gaskiya tom akwai matsa,kila kuma dukan da walakiri kema Adnan ne yasa shi fasa gigittaccen ihu har nan gidan. Gabaki daya saida suka saki dariya ta zauna suka dan fara fira kamin tace toh Alhamdulillah komi yatafi daidai yanda akeso Aymah,ni zan shirya domin komawa inda na fito,ba fahariba nason na barki inda za'a kulaman dake. Take idon aymah ya cika da hawaye ta fara gilgiza kai da fadin" Dan Allah da manzon sa Deedee nah karkimun haka,ina son kasancewa dake har abada,dan Allah Deedee nan gidan zaman kine karki taba kawoma kanki cewa waini sirika nike awajenki ko zaki takuramin ko wani abu wlh ko daya,bama keba ko waye zan iyabashi wuri agidan nan ko Baby ,dan Allah Baby kasa baki wallahii bazan zaunaba saina bita takarasa hawaye na sakkomata. Allah mai girma toke ayimah yanzu ba muna kusaba duk sadda kike son ganina kimin magana mana kawai zaki ganni . Noo Deedee kidai zauna din kawai zaman ki anan shine farin cikin mu. Zatai magana a Aymah ta karbe wayar Jameel dayayi shuru ta kira manager yana dauka tasa kuka tace Daddy Deedee zata koma gida, kuma wallahi bazan zaunaba gashinan zuwa yace ta mike cikin tafiyarta A'hankali ta bude kofa zata fita duk da kallo suka bita Deedee kam kamar idonta zai fado ganin yanda take takawa sannu sannu. Aymah zoki zauna nafasa tafiyar tace tana kauda kanta . Da sauri ta juyo tace da gaske zaki zauna dani. Wlh zan'zauna dake tace tana watsama Jameel dayayi kasa da kanshi harara. Yauwa Deedee nah I love you. Dariya tayi tace ina zuwa. Tom tace tana komawa ta zauna Deedee kuma ta fita dakinta ta rike mazaunai tace'' jar uban nan amma Jameel baida mutunci wallahi ,ni dai kam dama nason kunnena baiman gizo ba,bayama ko bari ta warke agyarata sosai dan ubansa zai farmata aiko zaka gane kuranka tace tana dakko kudi ta fita abakin get ta kira Almajiran ta da suke hutawa taba ɗaya a ciki tace maza Kaje Abba tuwa ka sawoman budurwa kaza da sassaken malmo nan bakin kasuwa da kayan Hadin sa( WLH SIRRIN MOLMO DUNIYA NE HAJIYA). To yace ya tafi. A hanyar komawa taga Baba Ali kwance akan tabarma yana hutawa redio a hannusa. NAN tasa kujera suka shiga fira tace wai Baba Ali ina dan naka ne Sadam Yaje ya dawo sai anjima yace yana kara kasa da volume din . To shikenan Allah ya maidoshi lfy. Ameen yace suka shiga fira suna haka suka ji tsayuwar motar kamin kuma suji an bude get din farko an shigo har zuwa na biyun da suke. Manager ne ya shigo yana faɗin Deedee kin tasoni ina hutawa . Dariya tayi tace'' fitinar Aymah daice wai da tsiya saina zauna to mizaka zaunayi gidan yara tinda dai komi ya kammala . Murmushi yayi yana sadda kanshi kasa sosai ya sosa kai yace,. Ai dole duk wanda ya zauna dake yace bayason a rabu,sana nima dama ina Son ganin ku ku biyu muyi magana, Deedee ba tare da bata lokaciba naga lokacin tsallah ya taho. Dan Allah A matsayina na d'a gareku ina so ku amince a daura auran ku keda Baba Ali,kinga yana da laluri gashi tsufa ya fara cimmasa ke kuma da kwarinki koyane ya samu saukin wani abun.. MATAR OGA NA A UMMY AYSHA PAGE 32 ""Kash ! Kash!! Kash!!!.. Wannan wace irin maganace kazo da ita babu wando balle akaiga rigar rufe nono Manja suke cemai ko olgah(Manager)? Ku Shikenan bakuson kowa ya zauna kalau ba nawie komi akansaba sai kun kakabamasa,haba dan Allah ku dainaman haka. Dariya sosai Manager yayi yace nidai nason manager nike kema kin iya fada yau daine aka mayar dani manja kuma a matsayina na babban danku da Allah yabani iko a kanku tsab zan aurar daku in dacewar hakan ta Tatashi. Murmushi tayi tana fadin" kai kai Allah ka kyauta ,Nidai kam kamasani jin kunya bari in mike in'tai inyi sallah. Baba Ali daketa washe baki yace. tsaya tsaya Deedee'n yara,ai fadamasa gaskiya zakiyi. kice ya za'ayi ina da kyauna na filanin usuli in tsayama wannan dattijon da ko cikakkun hakora bashi da shi ,uwa uba bashi da hannu guda musakine,San.. Subhanallahi Yanzu Baba Ali sharrin da zakaman kenan to aiko zan musaya tinaninka , Kai manager na amince daureman shi gam aka zai gane da Deedee yake. takarasa tana wuce warta ciki. Manager kau Baba ya kallah suka saki dariya. Baba yace namata dubara har ta fada, ai Deedee ku mutuniyar kirkice,samunta a wannan zamanin abune mai matukar wahala. Manager yace hakane Baba in sha Allah jibi juma'a za'a daura auran. To Allah yakaimu da rai da lfy yakuma sama rayuwar ku Albarka. Ameen yace kamin yatashi ya zubama Baba Ruwan Alwallah. Aymah kau tashi tayi Jameel ya kamata suka haura sama tayi alwallah saida ya kamota ta fito ya shimfidamata abin sallah kamin ya shirya yatafi masallaci. Bayan yadawo yazo dakinta inda ya isketa zaune tana Karatun Alkur'ani cikin sassanya muryar ta mai saukar da Natsuwa. Murmushi yamata yace sannu da kokari malamata. Kai kawai ta dagamai tacigaba saida taka inda takeso kamin ta rufe ta ajesa muhallin sa. Idonshi ya kawar daga kanta yace DeeDee na kira. To tace ta tashi ta sakko yana biye da ita. A falo suka iske Deedee ta daure fuska gam. Dukkan su saida jikinsu yayi sanyi. Aymah tacw Deedee nah lfy. Klau Aymah, ke kam Ai bakya laifi,Yanzu dai batare da bata lokaciba Jameel so nike ka dauke kafarka daga gidan na na tsawon wani lokaci hr sai Diyar nan ta warke daga wanna jinyar tata,bance ka daina zuwaba aa matar ka ce hakkin ta na ciyar wa kazo kabata da kalamai masu dadi dan samun damar saye zuciyar ta,amma dai zance ayi raɓe raɓe daki baitasoba nason kun fahimceni. Ido ya zaro yace Deedee kinson mikike fadakuwa? matata cefa,akan mi zaki raba alakar da Allah ya hada?. Ba rabaku zanba Jameel ina dai sone ta samu gamsashiyar lfy ta dawo kamar kowa,kai a takaice dai bari in maku gwari gwari a matsayina na likitan galgajiya. Yanzu ke ba zuciyarki aka fasaba akayi aiki? Kai Aymah ta daga tanayin kasa da kanta. Yaww,to yanzu in kika samu ciki ke kinson halbin da yara keyi a ciki kuwa balle yaran yanzu masu rawar kai da zakiga tun ciki suke iya shege waisu yayan risilin,kiga yaro ya daddage ya daki kirjin uwarsa sai anyi dakyal zuciyarta zata daidaita inagake dake da rauni,Ba fataba kika samu ciki a wannan yanayi Aymah sak Kirjinki zai zama kyauran kofa saidai muga ya wangale zuciyar ki namana Disco,inba Sa'a ba tsoro yana iya sawa muma duk muyi barzahu,To maganin ayi kar asoma. Innalillahi wa inna ilaihi Raji'un Jameel yace yana zaro ido danshi harga Allah ya yarda da kalamin Deedee. Aymah kau kai ta sunkuyar tana Murmushi sosai,Kai duk kan wanda zai buga da Dee Dee ruwa yake gashi ta rikitamata ɗan miji. Deedee tace to badai fataba kar dai azo ayi abinda za'atashi ba uwar ba uban ah'toh ga kaddara yaran zamani da wuyar ɗauka,In kaji shawarata toh ,in bakajiba kanka ta tashi ta kama gabanta tana fadin ɗan kwal uba sai fiddo ido yake kamar zomo ai yanzu ka gudu dan kanka yaro kamar cingom . Jameel kau Da sauri ya kama hannu Aymah Yace'' Sweetheart yanzu dama kinson da haka shine kikaman shuru ?da nasani wlh bazanba koda zan mutu ya Allah, dan Allah Tashi mutafi Asibiti a dubaman ke . To ai banason ka mutu ne shiyasa nabaka kuma ai Allah ne ya wajeb tama ina matsayin Aymah ina hanawa,kwara ni narasa ran nawa akan kyautatama umarnin ka nason gobe kiyama zan samu rabo mai Amfani. Rungumeta yayi tsam tsam idonshi cike da hawaye yace" Ngd Allah daya bani mace mai hangen nesa da tawakkali,na kuma kara yarda da a shirye kike da bautar auranki Aymah Allah yabaki tukuicin Aljannah, Kuma in sha Allahu Bazan sake miki ba har sai an tabbatar mana da samun lfyn ki. Ngd kaima inama addu'a Allah yabaka hkr kaji... Murmushi yayi Yace'' Ameen, bara natashi in tafi dare yayi ki huta ko?. Sosai tsananin tausayin sa ya diramata, taji kamar tace yayi kwanciyarsa amma babu wannan halin karta ɓata aikin Deedee. Rakiya tamai har bakin kofa kamin yatafi yana dagamata hannu har ya fita kamin ta sauke ajiyar zuciya ta shige part din Deedee. Haɗa Ɗan kamshin data dingajine yasanya yawunta tsunkewa da sauri ta afkah. Deedee nah mikike dafamana haka. Da sauri Deedee ta fito daga kiching tana leka bayanta tace yatafi cingom din naki? Baki ta turo tace gaskiya kidaina . A fusace tace ke dallah tafi cen namiji bakamishi wargi, basu da kunya som,sannan kansu suka sani, yanzu da ba'amasa hakaba da yanzu yana nan kamar bindi yana binki,yanzu shigo ga kayanki na hadamaki kwara kiyi amfani da wannan damar ki gyara kowane lungu da sako na jikin ki,duk k'aranta namiji Babbane akan mace balle wannan dayayi kala da samudawa ai ni nason komi . Zama tayi tana murmushi dan wlh babu karya a maganar Deedee, tabbas halitta Jameel daban take acikin halittun maza. Deedee ta dakko hadaddan kwano mai kyau ta bude,dagen kazar maganine da bazaka taɓa ganewaba saboda masifar kamshin da yake,( AKWAI KAZAR AVAILABLE 5K GAMAI BUKATA WAYANDA SUKA CI SU BAKU LABARI BAMA ABUN BANZA). Lomar farko saida Aymah ta lumshe ido saboda masifar dadi,ga wani kamshi na Musamman som bazakace akwai wani maganiba saboda cikin kwarewar girki akayi hadin. Saida taci rabi kana tayi gyatsa tace Deedee nah na koshi. Toh aje a fridge da safe kyaci. To tace ta tashi ta aje ta wanke bakinta ta dawo suka shiga fira sai goma suka kwanta. Jameel kau bayan yaje gidan su suka shiga gaisawa da iyayen sa inda suke tambayarsa lfy Aymah yace da sauki, babu wanda yacemai komi yashiga dakin shi ya kwanta,som baya cikin natsuwar sa saboda lfy AYMAH tafiye mai komi. Wayarshi ya zaro yashiga kiran Dr Abbah. Bayan ya dauka yace ango kaine da daran nan. Cikin rashin walwala Jameel yace akwia matsala wallahi,nan yashiga koramai bayanin abinda ya faru da kuma abinda Deedee tace . Dariya sosai Jannat keyi dake kusa da Dr Abbah dan taji komi, cikin kasa da murya tace kace masa hakane. Dr Abbah dake zuba murmushi lamarin Deedee yace . Hakane jameel,in akaima mutum aiki ai ba'aso yana aikin wahala, Tsawon wata ukku ake ɗiba ko buta ba aso ya ɗauka saboda condition din da yake ciki,amma ba damuwa In' sha Allah akwia maganin da zanba Jannat ta kaimata gobe, Allah ya kiyaye gaba kaji. Sosai muryarsa ta shiga rawa yana fadin Allah ka taimakeni Dr in Aymah ta samu matsala bazan yafema kai naba Kayimata addu'a kawai yace cikin tausayin Jameel din danshi ya tabbata Aymah ta warke dan batada k'anjiki. Ohk ohk in sha Allah yace yana kashe wayar ya tashi ya dauro alwallah yashiga nafila da nemamata sauki, Bayan yagama yaga biyu saura na dare nan ya dauki wayar shi dan kiranta,tinowa yayi da ko waya bata da ita dama data Adnan take amfani kuma da yaran sa zasu tafi tabasu abinsu dan acikin hakkin su take.. Tsaki yayi yana aje wayar dajin babu daɗi. Aymah kau sosai tasha bccinta cike da gajiyar daya taramata. Washe gari karfe goma Deedee ta shigo part din Aymah tace. Aymah zanje kasuwa yau in masu daukar tallah nan sunzo kuce masu abari sai gobe. Toh Deedee sai kin dawo. Yawwa tace tana daukar hanya,a bakin get suka hadu da Baba Ali da sadam suna fira. Kallon Baba Ali tayi da sauri kuma ta dauke kai tana gyara mayafin ta. Shikam murmushi yayi Yace'' Deedee yara sai ina haka batare da sallama ba?. Murmushi tayi tana dawowa kusa dashi cikin ladabi ta gaidashi da tambayar ya tsufa. Dan murmushi yayi yace tukunna dai. Dariya sosai Sadam yayi kamin yace" toh yau Baba yaro yake bari inzo yayi dakin shi yana dariya. Deedee kam mikewa tayi tace toh ni bara naje ksw nadawo. Kanshi ya maida bisa wuya yace ko narakaki namiki dakon abinda zaki siyo. Laaa kaiko ka iya sakarma Babba kunya , A'aa malam bashshi ka huta saidai ka fadaman in akwai abinda kakeso zan zoma dashi.. Cikin jin dadi yace to azo da binda ya dace da dattijo kamana. Aaa malam ba wani dattijo,saidai nadawo. Toh allah ya kiyayeman ke amaryata yace yana washe baki. Dariya tayi tana wani sake sabon tako kamin ta fita daga gidan tana murmushi da fadin dattijo bawan Allah,yaga komi tsamtsam,yo uban dama zaiki ribibina ai sai marar Sa'a,yanda Allah yasaman tausayin ka zakasha hidima,dama gaka dan cakwal kamar muciya harma fallan zani saina sawo in dinga saɓaka ga baya inyi aikin gida dakai.. Kai tsaye kasuwa ta tafi ta shiga ta Sassawo kayan tsumi hadaddu irin na UMMY AYSHA masu tasiri ga jikin lafiyayyar mace,data gama ta zauna aka hadamata maganin sanyi (infection ) kudin tabiya ta tsayar da mai Napep tayi unguwar su. Kai tsaye gidan Asaben mai unguwa ta nufa. Murna sosai suka shigayi da junan su nan tace ke akwai labari, tashi muje gidan Haj murja nason kona je gidan ta cewa zatai bata iya tafiya kimson ciwon cin nama duk yacinye yan guntayen gaɓoɓin ta. Dariya Asabe tayi tabata hannu suka kashe tace. mu kau gamunan daram,ciwoma baiga fuskar hayemu ba som Aa Asabe karkiyi shishigi cikin hurumin ubangiji,Adai dinga cewa in sha Allah, ah toh tashi muje. Allah ina gayamaki Deedee,ni som bana ciwo. Hmm tashi dai muje ina da abinyi nabaro Aymah da malam banmasu girki ba. Tashi tayi ta ɗauki mayafi tana kara koɗa lfy jikinta. Deedee tace nidai Asabe kin isheni wallahi da alfahari akan lfyn ki to waye jemamme ne haba. Ke walh Deedee dole inyi alfahari, ciwo som bai samu fus... Kanta karasa wani shakiyin yaro ya yanko da gudu da baro yayi gaba da Asabe. Zanzo kuga yanda yake gudu da ita. Deedee mah ta dage da yan ledojinta tana gudu tana binsu, shikam gudu yake yana dariya da Fadin Baba Asabe akara wuta ne. Uwarka ubanka inajin jiri dan Allah ka saukeni kajikaina Asabe tace tana zindima salati. Tsayawa yayi yana kwasar dariya tare da ziddota daga baran. Asabe kau tangal tangal tafara tanajin yanda bango ke Matsowa da gudu yana matsawa baya tsabar jiri,duk abin nesa kusa yake dawomata kamin kuma ya koma nesan sa. Deedee kam tana karasowa taja burki tana Sauke numfashi da faɗin. Kai amma wannan jikan Hanne abokiyar zaman ki bai kyautaba shege kai kamar dutsin guga. Kema Asabe ai kina da laifi, kingani dai ko,kinga saida nace duk abinda zakice kibar cika baki kuma kalmar in sha Allah ta kama bakin ki ko. Kuka Asabe tasa tace Dan Allah ki tsaidaman mi motar nan Deedee karki barshi ya gudu, DeeDee ya kassara matanta kata na kece wlh. Dariya sosai DeeDee tasa tana an'sar bokitin ruwan da wata yarinya ta debo ta shekama Asabe. Ajiyar zuciya taja tana sauke numfashi da goge fuska tace wai Allah nah. Deedee ta kamata tace muje dai cen kin huta. Dakyal Asabe ta tashi Deedee takamata suka karasa tafiya kadan suka shigo gidan Haj murja. A soron gidan suka isketa zaune ta mike ƙafafuwa daya daga cikin jikokinta suna mata tausa. Deedee tace kingani ko Asabe,ai dama nace maki tana nan ana lindarta ina ma amfani,ga yan gaɓoɓin gudul - gudul ba wani tsawon azziki kamar karas din goma.. Hararata Haj murja tayi tace ke Adije tashi nason wannan matar wulakanci dama tazo taman. Tashi ɗiyar tayi tana gaidasu tare da sakin dariya . Tana wucewa suka zauna Deedee ta kalli Asabe daketa fiddo ido dan hr lokacin ba dai-dai takejinta ba ta tabe baki tace wai kunson minene? Gabaki daya suka hada baki wajen faɗin aa. Hmm saidai ta dauki lokaci kamin tace Aure fa zanyi .. Au...me suka hadabaki wajen tambaya. Gira ta dagamasu tana fadin rass kau Aure,bayan shekara ashirin da biyar da mutuwar muji ga wani kuma ya dallo kai. Gabaki daya suka kwashe da dariya suna faɗin ikon Allah. Haj murja tace'' aiko za'abugi kwarya aci uban sabada wlh,bikin DeeDee ai namune, yanzu dai Deedee abinda yakamata muhada kudi wajen fara gyaraki ciki da bai. Gama wata bagaruwa cen sabuwa ce mai kyau zan samo ganyen magarya atafasa shi ki fara shiga ciki koya kuka ce?... MATAR OGA NA UMMY AYSHA PAGE 33 Kai amma wlh bakuda kirki kukam,Yo ubanmi zan dasashe,ni wlh tsohone zan aura tuguf,auran buta zamuyi,iyaka insamu lada,in dai an daura auran ina gayyatar duk kawayen mu azo aci asha ature kallabi ,amma ko paracitimol basha zanba ai ba lalataccen tsufa ya sameniba,kai wlh murja kinma kasheni sai gani cikin katuwar roba kamar kifanya wai da sunan ina so na matse,to kofar gugama taci uwatar ta. Gabaki daya suka fashe da dariya nan ta tashi tace dallah ni bani bagaruwa in tai in kaima jikata yafiyeman wannan maganar taku marar amfani dama banzoba tsaffin banza danayi Aure watsar daku zanyi tinda gantalallu ne ku.. Aa miyayi zafi Deedee cewar Asabe tana mika jin gadon bayanta na ciwo. Haj murja kuma kira ta kwalama Adije tazo ta kawo masu, Deedee tace tashi mutafi Asabe. Asabe tace wllhi babu inda zan tafi sai dare ya tsala,wannan dan iskan daya kwasheni nason jirana yake,jeki kawai sai munyi waya ko kuma gobe ina nan zuwa dan har yanzu jiri nikeji. To tace tamasu sallama ta fita kai tsaye gidan danta ta fada Malam Habu da sallama. Layi ne sosai na yan marka de cike da gida. cikin farin ciki tace kai Alhamdulillah amma naji dadi wlh Allah yakarama ksw albarka Baraka. Inna su Jameel kau ganin Deedee yasa ta kashe injin din tana oyoyo Deedee mu maraba lale ina tacewa zanje in ganki. Ke matsacen Baraka kibani waje,kedai kullum kanki a tulu yake wlh banson sadda zaki waye ba,gabaki daya Jameel ya samaki jin kunyar Aymah ko sakin jiki da ita bakyayi ai saitaga kamar baki sonta, ai ba haka ake surukuta zamani ba,ke bakiga yanda na makiba,Yanzu dai tashijeki ki idamasu kidawo ina mai gidan?. Baraka tayi dariya tace aiko Deedee sunje kauye amma munyi waya dashi yana hanya in sha Allah yanzu kingan shi. To shikenan jeki bari in Tina baya ta ƙarasa tana fadawa dakinta inda komi yake tsaf,kwanciyarta tayi akan tabarma tana tinanin to ina Jameel da kabir ne oho. Tana wanna tinanin taji an kashe injin din Baraka na fadin Deedee ko kinyi bacci. Aa miyayi zafi na baro Aymah tah takarasa tana fitowa da faɗin Allah ya kara dawwamar da tsaftarki baraka,yo ai'nasa tinda nayi balaguto in nazo zan iske dakin ya cika dam da shara. Murmushi tayi tan fadin ga maganar su malam nan kofar gida. Oh toh madallah tace'' tana zama bisa tabarma da aka shinfida sai kam gashi sun shigo dashi da Jameel da Kabir din. Sannu suka hau yimata yayin da Jameel yayi kasa da kai bayan ya gaidata yace. ya jikinta. Ido ta zubamai kamin tace . To da dan sauki yanzuma magunguna na sawomata ta nunamai ledojin hannuta. Ya Subhanallahi Deedee dan Allah wane haki take ciki,Kuma shine sai kibarota ita kadai,miyasa bakya mun waya nazo. Aaaa to sannu jikan zubaida,kamar abinjira sai tambaya,Kai dai nacema da dama Jameel ba hikenanba, nidai ban haneka zuwa ba iyalinkace amma dai akiyaye dan Allah saboda budewar kirjin. Ai batama rufe bakiba ya tashi ya zura takalmanshi sauri sauri ya fada motar shi yayi gidan Aymah kamar zai tashi sama. Inna su kau itama a ɗan rude tace Deedee bata da lfy ne Aymah?. Oho rawar kai dai zai fara na takamai burki kinson yaran zamani. Shuru tayi tana sauke ajiyar zuciya tare da dan satar kallom malam Habu ya sakarmata murmushi ta dauke kai kunya fal idonta. Malam Habu kau ledar Viva bakace dake hannushi ya zazzage duka yace kin zo asa'a Deedee,kinga duk wahala da muka dingayi akan a sai gonarnan akaki,to gashi aiki yabiyo ta kanta anaso a fitar da service aka kiramu aka bamu wannan million goma ce cifcif. Da kuma katon fili dake cikin shagari low-cost. Hadadda guda Deedee ta rangada tace kai Alhamdulillah, Sa'a ta kawoni kam,kai amma fa naji dadin da baki bazai iya furtawaba, kaga binda mukaitafama abamu ko 500k ne dan ama jamilu aiki aka ki shine aka bamu wanna makudan kai Alhamdulillah nayi farin ciki arziki ya taho in sha Allah. Murmushi yayi yace in sha Allah. Tace toh Alhamdulillah yanzu dai wannan gona zamu iya cewa taka ce Habu, tinda gadon mahaifinka ne,nikuma abinda akabani kaga shine nabayar akasai wannan gidan ko,to yanzu dai dukiya takace ka sarrafata abisa tsari da koyarwa mussulun ci. Murmushi yayi yace Deedee ina dake saina tsaya tsara abu,ai tinda Allah dai ya bamu kawai kifadi abinda kike so ayi. Ido ta kanne tsawon lokaci kamin tace masha Allah Alhamdulillah na samo dabara. Mizai hana wannan dan gidan a rushe shi ku sai wani , Wannan kuma amaidamaka shi babban shago asamaka kayan tireda tinda dai ba wani zurfi gareka a karatu ba. Shawaraki tayi Deedee nah yace cikin farin ciki Tacw yawwa Alhamdulillah hakan za'ayi, zanje gidan yarancen naga dai sauri yake nabashi waje yasha iska Ba. Cikin kunya Inna su tace anjima Baban su kabari muje gidan mukara ganin mai jiki ko. Sosai Baraka yanda kikace yafada cikin sauri. Murmushi Deedee tayi tace. Abu nagaba kaji zancen da yaran na su manja suka shigo dashi ko?,nifa abun som baiman dadiba ai yakamata in an'girma ason an'girma koko. Murmushi yayi yana sunkuyar da kanshi yace. kiyi hkr ni kaina da suka tunkare ni da maganar da ban amince ba amma daga baya naga fa'idar haka,saboda taimakon da zakiyi. Baki ta tabe tace ku kuka sani ta mike tamasu sallama ta fita,tana fita tace yan banta uba nimafa ina son sa,ina kuma tausayi sa,akan hanyarta ne ta biya tasai zogala da ƙuli masu kyau tayi gida. Jameel kau Allah ne yakaishi lfy kai kace wata doguwar tafiya zaiyyi da yake xabga gudu. Bakin get din farko ya aje motar cikin sauri ya ƙarasa ciki ,bata palon kasa bata na sama a bedroom din da yabar tarihi ya tura yashiga da sallama. Kwance ya ganta tana bacci daga ita sai have vest da wani wando da dukkan mazaunanta bude suke, ta wani kife alamar baccin yamata dadi,. Wani yawun wahala ya hade kamin ya karasa wajen ya zauna akan gadon yana burkitoto dan gyaramata kwanciyarta. Ahankali ta fara bude ido ta sauke shi akanshi yayim da shiman nashi ke cikin nata. Saitin raunin nata yasanya hannusa masu taushi ya hau murzawa da tofa addu'a. Murmushi tamai tana mikamai hannu da fadin ina kwana ya kake. Amsamata yayi yana tambayar lfyn ta. Badai ciwo ko. Kai kawai ta dagamai suka danyi fira yamata sallama akan zaije yadawo. Rakiya zatamai ya hanata tare da fita da sauri kamar zai fadi ta bishi da kallon tausayi dan tason shigartane ta ruɗashi, Abakin kofa sukayi kicibus da Deedee tace kaiko baka da mutunci yanzu kwara in daɓo sayyada daka kawoni bisa wannan motar taka mai siffar agwagwa.. Kiyi hkr yace yana shafata ya wuce ya fada mota. Ya dade zaune a cikin mota kanshi akan sitiyari jin wani fitinannan felling. Yadade kamin ya wuce gida yayi wanka yayi wajen Dr Abba. Aymah kau wanka tayi ta sakko kasa nan taga Deedee na kwada zogala suna ta fira abinsu har tagama ta zubamata ta mike zata kaima Baba ali aka Turo kofar da sallama. Wani irin ihu Aymah tayi aguje kuma tayi bakin kofar tana faɗin Hajiya Asiya. Da sauri suka rungume juna lokaci daya kuma suka fara kuka baji ba gani .. Nidai dan Allah ku saki juna haba wannan ai iskancine nidai miji nason ana rungumewa amma ke Aymah dan wulakanci na hanaki Rungume mijinki dan lfyn ki shine zaki rungume wata salom kirjinki ya ɗaya ace nazama babba banza cewar Deedee a fusace tana dakko iccen mopa... Ayi hkr b yawa MATAR OGA NA UMMY AYSHA PAGE 34 Da sauri suka saki juna suna fashewa da dariya yayin da itama tasa dariya tace'' sunga icce sun watse matsorata. Hajiya asiya ta juyo tana dariya sosai ta Rungume Deedee tace. ga Deedee mu da labarinta kullum ke jemun kullum son ganin ki nike amma sai yanzu. Zama Deedee tayi suka gaisa kamin tace tana zuwa. Tana fita suka sake rungume juna kamin su zauna idon kowa akan juna cike da kewa. Aymah tace haj Asiya dama rai kanga rai, ashe kina nan amma baki taba nemana ba nayi fushi. Hmm Aymah kenan ke kinson kina makale araina, kawai wannan tsarin manager ne ganin yanda Adnan ya tsaurara tsaro akanki da Dukiyar ki shiyasa muka bi komi cikin siyasa,amma bagashiba cikin ikon Allah komi ya shide,ga babba tsaraba nayomaki ta karkace tana bude katuwar ledar daketa tashin kamshi. Manyan kwalaben humra sirri ne daketa tashin sihirtaccen kamshi tace gashinan daga wajen mutuniyar muke ummy Aysha, ga kayanan iya kaya,qannan kuma kwalbar kwalacca ne itama zakiga yanda namiji zai koma miki,wannan kuma turaran tsugunni ne zakiji yanda zaki matse ko yatsanki biyu bazai iya wucewa ba,wannan kuma akan mararki zaki shafa yayin kaima oga ziyara,ga kwallin sirri bayan ke babu wata azuciyar mai gida,ke wlh ko mace goma zayyi sonki saiya babbanta dana sauran,gashi dama mijinki saurayine kyakyawa ajin farko Aymah dole kiyi duk abinda zkaiyi wajen sake jawoshi jikinki,ki saki jiki dashi daganin sa kamili ne,kibashi hakkin sa in so goma ya zo nema saboda daganin sa jajurtaccen namiji ne,karkimai rowar kanki daidai da rana daya dan in baki bashiba zai fara zuba idonsa a kallan matan banza,Ni inaji ajikina Allah ne yakawo shi rayuwarki dan yamaki maganin matsalar ki dama cen baki dace da wannan Adnan ɗin ba,ga maltina mata nan kisha zakibani labari,wannan kuma dan la'asar ne zakisha shabiyar duk sadda za'ayi,ga wani ruwan magani nan kafi budurwa ukku ki tatse leda daya ki hada tea ki juye aciki kisha na kwana ukku Aymah wallahi azeem kin wuce da kwalwar yaro sai dai baban yaro dan mata na iske gidan suna neman sa,kinga ,tashin hankali masifa ta da namiji saidai kiji wani wajen anayi amma kekam sai gani sai hange zaki zamemai ƙadan garan bakin tulu a zuciyar sa. Rungumeta sosai Aymah tayi tace ngd aminiyar arzikin da babu kamarta ina alfahari dake,shiyasa nayi kewarki matuka,to amma kinson bana da lfy kuma wlh kamar yafi karfina nason ni mabukaciyar macace Asiya amma ƙarawa daya jarumin nan ya kaini kas har yau jinike kamar baniba . Shekeke ta kalleta tace. To tashi tsaye zakiyi da neman magunguna masu inganci saboda irin su saisu raunata ka,Yanzu kifara shan galan din nan na maganin sanyi in yaso kisha sauran magungunan daga baya, wlh sai dai kukai juna kasa ,Amma dama taya za'ayi kibashi dama batare da kingyara kankiba ai dole ki jigata,Zancen jinya kuma banason iskanci ke bakinson in kin warke ba ko baki warkeba,ina dai fatan yabarki bayan kun gama Amarci ki dawo bakin aiki. Dariya tayi tace kumafa hakane,to yanda dai yace . Zatai magana Jannat ta turo kofa ta shigo nan suka rungume juna suka zaune cike da wayewa suka shiga fira itama ta bude jikka ta debo Turarukan wutar UMSAD INCENSE Masu masifaffan kamshi da kama gida tace gashi to nawa gudunmuwar fatan mu ayi zaman lfy mai dorewa(in dai kamshi kuke nema wlh nagida to ku neme ta) Sosai tamata gdy Haj Asiya tace tsaya kiga bari in hadamata abubuwa naganta abun akwai sanya. Nan tashiga kiching ta dauki tea spoon ta zuba rabin maganin data zo dashi saboda karfinsa ta ba Aymah ta sake hada wani taba Jannat. Karba sukai suka sha Aymah tace Ya banga kin hada naki ba. Murmushi tayi tace to ba mai aure keshan magani mataba sadda nasha nasha. Cup din Aymah ta aje cikin furgici tace bangane ba. Murmushin takaici tayi hawaye suka zubomata tace Aymah naga butulcin maza,tini mijina ya sakeni amma nakusa Aure. Innalillahi wa inna ilaihi Raji'un miya hadaku Asiya. Hmm akan zai kara Aure yarinya tace bata bukatar zama da kishiya shine yabani takadda da saki har biyu yanzu kuma yana bukatar na koma saboda an'fasa bashi sunce tinda ya iya sakina yar suma zai saketa to nikuma namai nisa yarane kuma Allah ya shiryasu duk inda suke, gasu maza dama duk inda nike sun iskeni. Sosai sukaji ba dadi daga karshe suka hau lallashinta suka shiga fira. Deedee kam koda takai ma Baba Ali kwad'an ta zauna sukai fira nan yake shedamata gobene fa. Dariya tayi tace kai kam dai malam baka gajiya,sai kace wasu yara sai rawar kafa kake. Dariya yayi yace mai Sa'a ai shine zai sameki Hajiya Deedee ,dan mi bazanyi rawar kafaba nason ko bayan raina za'aman tsarkakakiyar takaba. Hmm malam kenan Allah ne kawai yason gawar fari ka daina wannan magana banaso tafaɗa tana tashi tayi tafiyarta ta fara aikin tsumin Aymah. Bayan tagama ta aje yasha iska tayi wanka tayi kwanciyarta dan ta huta. Da yamma tashiga wajen Aymah ta bata galan din da cup tace susha. Nan fa duk wanda yashashi cikin su saida ya gilgiza dan lokaci daya suka farajin yanayi ,Asiya kam sosai tashigama Aymah balai dan ita tace ta dandana taji gashi ita ba miji b balle tasanya ran samun relief in sun gaisa. Dariya Aymah tamata duk da yanda takejin marar ta ta daure gam. A takaice nan suka yini Sai mangariba Asiya ta wuce da Jannat da niyyar zasu dawo bayan kwana biyu . Sallama sukai suka shiga waje Deedee daganan suka wuce kamar sunsaba da juna sai fira suke cike da wayewa.. Bayan isha Jameel ya shigo gidan hannusa dauke da manyan ledoji ya ajema Aymah gabanta tare da bude wata karama mai kyau ya zaro kwalin wayar iphone mai kyau ya mikamata yace ga tukuicin Farin cikin da kika sani, sannan inaso muyi magana dake kuma inaso ki fahimceni dan Allah. Murna tayi sosai tare da jeromai Addu'a karin budi na Alkhairi. Ameen . Aymah inaso musai wannan gidan naki bansaniba ko zaki saidaman, inaso na haɗe family nah waje guda ba ace ni ina gidan kiba iyayena suna wani wurin,bama da yawa kamar yanda kema babu wani naki a kusa dake,Idon kau muka hada kanmu zamuji dadi fiye da tinanin ki,ko yaran mu suka taso gasu ga kakannin su,ga kuma kema Deedee ki a kusa dake, Ido ta zaro tana aje mai wayar shi gabanshi fuska daure tace yanzu Baby bazaka dai iya karba kyautana ba ko, saidai in na siyar ma . Aa amfanin siyarwa anan shine... Nan yabata labarin abinda yafaru dan gane da gonar su da hukuncin da Deedee ta yanke na rushe gidan su aginama mahaifin su daga karshe yace. Dr Abba da Daddy ne suka bani wannan shawarar ke kuma Aymah sai abaki kudin abaki wancen filin in yaso kina iya yin abinda zai zama sadakatu jariya wa iyayen ki,ko kigina masallaci,ko kiyi islamiya duk dai wanda kike so. Cikin gamsuwa da kalamansa tace to shikenan na yarda da hakan. Rungumeta yayi yana shakar daddana kamshin kwalacca ta yace ina sonki . Murmushi tayi tace nima haka.. Sallama su manager ne da Deedee ta katse masu hanzari nan suka zauna aka gaisa manager yace Aymah kinki shawarar da muka bayar ko,ina ganin hakan shine daidai tinda wannan gidan dai babban gidane,kuma in yana wajen Jameel kamar yana wajen kine tinda gidan mahaifinki ne,kana natsuwarku kuduka ku hade waje daya kuzama tuwona maina,ni dai matsayina na mahaifi gareki na amince. Daddy nima na amince . Yawwaa madallah Allah yamaki albarka. Yanzu mikikafiso ayi islamiya ko makaranta. Kanta a kasa tace in zai yiyu duka ayi in akwai wani filin akusa asaya sai in bayar da kudin sa a hade kawai. Aaa Aymah wancen filin babba ne ya isa ayi makaranta da Islamiya baki daya. To tace Jameel yace nikuma zangina maki shi yanda kike so in sha Allah ,ai iyayenki nawane sun gama min komi da suka haifa man ke. Ido ta tsura mai tace wayabaka kudi to? Murmushi yayi yace kanki na sayar. Dariya duka yan dakin sukai nan suka tashi suka tafi. Washegari aka daura auran Deedee da Baba Ali,Zanso kuga lefen da aka kawo kamar na budurwa kauye abun sai son barka. Su Aymah kau da sukaji labari sunyi farin ciki ranar ta kashe kudi kamar mi, an'daki kwarya kamar yanda DeeDee tace anci ansha kawayen Deedee sunmata kara sosai. Bayan isha Angon ya shiga dakin amaryar sa da katuwar ledar kaza sai fatan mutuwa ta raba. Bayan wata daya. Aymah ce tsaye part din da su Baba zasu dawo tasa an'samasu hadaddun kayan daki batare da sanin kowaba daga ita sai kawarta Hajiya Asiya suke harkarsu Dan wani filine data taɓa saye batare da sanin kowaba tasa aka sayar aka subamasu kaya na more rayuwa a part din da Adnan yayi jinya Kabeer kuma aka gyaramasa dakin da Baba Ali ya tashi. Saida ta Tabbatar komi yayi yanda take so kamin su turare wajen su fito. Daganin yanda take tafiyar kason tagaji sosai. A palon ta suka zube Hajiya Asiya ta bita da kallo sosai kallo na kurullah tace anya matar nan klau kike kuwa?. Fuska ta yamutsa tace kalau nike kawai nagaji ne wlh .. Murmushi tayi tace ina Angon naki . Ido ta lumshe tace yau satina biyu da kwana ukku bansashi ido ba, nayi kewar sa sosai, basanan shida Dr Abbah sunyi tafiya. Ohk Allah ya maidoshi lfy. Ameen tace tanayin shuru kan kace mi kuma bacci yayi gaba da ita. Dariya Hajiya Asiya tayi tana daga hannu sama tace . Alhamdulillah naji dadi Allah ka inganta, Allah kuma ka kawomata da sauki,Mahakurci mawadaci,ashe kema zakiga naki . Suna zaune Deedee ta shigo da sallama Haj Asiya ta amsa tana fadin Deedee Sannu. Yawwa au bacci take? wannan bacci na Aymah yanzu yana damuna,ko fira kuke sai bacci kamar kasa,Ba mamaki shawarace ke damun ta dole inje nemo maki magani anjima in sha Allah bari malam ya tashi bacci. Murmushi Haj Asiya tayi tana Dawowa kusa da Deedee ta rike hannuta. Tace Deedee Aymah fa ba shawara bane, tanada shigar ciki amma ita kanta bata saniba,kawai tana ganin gajiya ne. Ido ta gwalo tare da tura kanta cikin filon kujera ta saki guda da zubewa kasa tace Alhamdulillah,lokaci daya kuma ta mike ta fara rawa abin gwanin dariya itanan duk murna ne. Dariya sosai Haj Asiya keyi. DeeDee tace ke mijinta k Na hanya dan Allah akirawo mana mai lalle ta zanemata kafar tass dan dole in mikata wajen mijinta ɓargon ɗan su ya ida bunkasa kalkashin kulawar iyayen su . Baki da matsala Hajiya Deedee tace tana daukar wayarta tashiga kiran kawarta akan ta basu mai lallan ta, nan tabasu address din gidan . To gatanan zuwa suka wayar. Bayan mnt na kadan ta tashi tana yamutsa fuska da binsu da kallo ganin suduka kallonta suke. Fuska ta yamutsa tace Deedee yunwa nikeji kamar banci komi ba. Baki a washe Deedee tace angama mizakici Aymah nah. Komima amma mai yaji tace tana mikewa dan wanke bakinta da fuskarta. Kamin ta dawo Deedee ta ajemata dambun shinkafar da tayi yaji kayan lambu sai peper chicken akai. Nan ta zauna ta karamasa yaji sosai tahau ci tana lumshe ido dan yamata yanda take so. Kantagama sukaji sallama mai lallan nan ta bisu da kallo. Hajiya Asiya tace lalle nikeso aman biki gareni. Da sauri tace inaso dan Allah afaraman . To shikenan gama Amaki sai amun. Sauri sauri ta cinye daidai sadda wayarta tayi ring,ganin Jameel ne yasa tayi dakin da DeeDee ta taba zama nan kasa tafada akan karamin gadon tana lumshe ido da fadin. Baby nayi kewarka sosai wallahi ,inason jinka kusa dani takarasa tanamasa shashekar kukan dake cike da shagwaba dan da gaske take, kwana biyu kewar sa take har mamaki take yanda takejin masifaffan feeling akan sa ,sai dai ta danganta hakan akan maganin da ta dinga sha. Jameel kau a kasala ta saukar mai lokaci daya,cikin low voice dinsa. Yace'' Sweetheart baki kaini ba wlh ,dakyal nike bacci,duk abinda zanyi ina rike da tinanin ki,gashi bana da natsuwa saboda dandanonki da kika lasaman yana hana zuciyana sukuuni,inaso nazo na ganki sai dai banso hakurina yakai karshe,bana tinanin a wannan karan zan iya samaki ido ,shiyasama na yanke shawarar sake ko wata biyu ne kamin ki warke duka ko.. Kuka sosai tasa mai tana fadin nifa wlh na warke dama Deedee ne ke abinta amma ni ai na warke dan Allah kazo nayi kewarka, gasu Inna mu yau zasu dawo, kaxo mu tarbesu tare kaji b Babyyyy. A yanda taja sunan saida yaji kamar ya saki sitiyarin motar z dakyal ya taka burki yana sauke ajiyar zuciya. To in nazo zaki barni na gaisa dake. Da sauri tace mizai hana duk abinda kakeso zanma kaji da gaske zaka zo. To mizaki ajeman in zanzo kuma wane tarba zakiman. A kagare tace dan Allah Baby kace zakazo din nikuma wallahi zanbaka mamaki dan nayi kewarka sosai. To shikenan in sha Allah zanshigo yau .. Ihu ta fasamai har saida ya dauke wayar yana dariya yace Sai nazo Sweetyy nah. Lafiyayyen kiss tamasa kamin sukayi bankwana. Da sauri ta fito palon tana rungume Deedee tace Ga beby nan zuwa Deedee. Baki Deedee ta washe tace haba Aymah ai sai yakara sa Watanni nan gaba, ashe Kema kin fahimta dayake likitocine kai wllahi naji dadi. Cikin rashin fahimta inda kalamanta ya dosa tace minene na fahimta. Da sauri Hajiya Asiya dake dariya sosai tace tana nufin ga Maigidanta nan zuwa fa DeeDee. Laa ah toh Aymah naji tace Beby. Yawwaa nikam magungunan nan dana baki zaki bani saura in akwai dan zuwa yanzu sunyi enfiya ( expired) cewar Deedee cikin sabon turanci. Dariya suka fashe dashi tace ai bana da komi duka na shanye. Hannu ta dora akai ta kwallah ihu tace Aymah lfyn ki kuwaz yanzu har galan biyu nan kinshanye. Baki ta turo tace to ni daɗin sha yakeman kikaroman ma ina son bauri baurin sa. Tureta tayi tace wallahi har abada sai shekara mai zuwa, Allah ka dubeni da idon rahma karta haifoman ɗa mai ganye aka. cewar Deedee cikin damuwa. Haj Asiya tace haba ba damuwa Deedee mu. Zama Aymah tayi aka shinfidamata lalale hadadde tana gamawa ta dakko kayan dilka da Asiya tasaimata wajen ummy Aysha ta shafe jikinta da shi bayan awa daya tayi wanka da sabulun dilka mahadin man dilken. Zanso kuga hatsabibin Kyan da tayi. Mai lallan dake zaune tanacin abinci ta bita da kallo ganin ta fito ciki sha'awa tace. Aunty dan Allah ki zauna na maki make up ,ga kayan kwalliya nan dama wata mai jego zanje namawa sai nafaramaki. Murmushi Aymah tayi tace ngd kanwata nan ta zauna aka bata lokaci akan gyaran ta,zanso kuga kyan da baiwar Allah nan tayi cikin shigar shadda mai masifar kyau Red colour gashinan ya sha gyara yayi luf luf abin sai son Barka.. Zafafan photo akaimata masu masifar kyau da ɗaukar Hankali a wayarta ita kanta tason ta hadu.. Karfe biyar suka farajin ana bude get din gidan motoci suka fara shigowa ajere Har guda ukku. Da sauri Aymah ta zubama window ido ganin wane bakine sukai. Idonta ya sauka akan jarumin nata dayayi wani masifffan kyau, yana sanye cikin wata farar shadda kan nan yasha hula ga wani fitinanna glass baki ya kwama kamar kullum fuskar nan tashi tamke gam.. MATAR OGA NA PAGE 35 Cikin mamaki sosai take kallon shi ganin canjin dayayi ga wani masifaffan haske dayayi kamar mai bleaching,kana ganin Jameel kason hutu yazo kudi ya zauna dan fatar shi ta murje sosai kamar wanda akama wankan inji. Key din hannun mutanan ya karɓa sukai magana saida yaga sun juya kamin ya doso ciki Kabeer biye dashi. Kasa daurewa tayi aguje tafita kamar yarinya tana fdin Babyyyy. Yana ganinta ya waro ido Cikin farin ciki tare da bude mata hannu takau fada kirjinsa tayi lamo jin sassanyan kamshin da yake mai tsananin dadi . Jameel kau kiss ya manna mata agoshi yana tattaɓa bayanta cikin tsananin kewa, Cikin shaƙaƙa muryarsa data disashe Saboda jin kamshin fitinaniyar Humra ta dake dukan Hancin sa yace. Kinyi kyau matuka Sweety ko haka kika tsaya kin gamamin komi, nayi missing naki sosai sana na samu tarba da nike so,Nason bani kadai nayi kewar kiba gashi kema kin fiddo da taki zahiri. Cikin kewa da farin ciki ta dago kanta tasa ya tsanta babban ta lakace hancinsa tace nine ke kewarka jibi yanda na rame akan tinaninka kaikam kaje ka huta ka xama kato jibi teɓa da kai. Sosai yake dariya yace dakau ban yafema kaina ba akace nayi teɓa dan nasan ke xancuta xan karamiki nawie yakara she yana kashe mata ido daya. Murmushi Tayi ta kama hannun sa da fadin sannu da zuwa Baby ya gajiya. Yawwa Sannu ki ina yan gidan. Deedee dake bayansu tana ba Baba Ali abinci abaki tace gamu a kusa, wata kuson tafi wata ,yau nima mijin nawa yatashi da gudawa jikin ba ƙarfi,Ya kuke ka kadawo Lfy ina Dr Abbah. Subhanallahi sukace suna karasa wajen, Kabeer yace Aunty Ina wuni. Ido Aymah ta zaro sai kuma kunya takamata Ashe yana tare da Jameel amma bata gansa ba. Cikin matukar nawie tace Alhamdulillah kanena ya kake. Lfy klau yace yana ajemata jikkar Jameel din yace bari inje mukarasa aikin gida . Tace ohk munanan muna baza ido. Dariya yayi yafita yana yaba kirkinta. Bayan sunma Baba sannu Jameel yace tin yaushe bayajin dadi. DeeDee tace yau da safe. Aymah tace kuma Deedee baki fadaba akaishi Asibiti?. Tace kai bafa komi kawaii mu tattalin mijine damu, duka fa so biyu yashiga toilet din,to amma mu kunson mutanan da dana yanzu ba dayaba nan jinike kamar yayi shekara bayajin dadi shiyasa nima bana da sukuni takarasa tana tsaki. Dariya duka suka sanya Jameel ya mike Aymah ta dauki akwatinsa suka masu Allah yasawaka sukayi ciki. Suna shiga palon a zafafe yawani juyota cike da kewa ya tausa halshansa anata yashiga sarrafawa cike da kwarewa dakuma zallar kewa,tsawon lokaci tsayuwa ta gagare su dan ita kanta zagewa tayi tana mayar masa da martani dan ba karya a kame take. Ido rufe ko gani sosai basayi suka zube akan lallausan carpet din wajen, Daga nan wasan ya canza,ba karya sun murji juna kuma kowa yaji dadi ,Farin ciki sosai bayyane ga fuskar su,bayan sunyi wanka sun dawo palon ya zubama carpet din ido kamin ya dago ya kalli Aymah cikin nishadi yace Sweetheart amalala kikamana a palo. Kallon wajen tayi lokaci daya ta sunkuyar da kanta tana fadin koma miye kaine sila kakai jarumine da dole abinda yafi Haka nayi,Duk banson wannan abunba sai awajen ka,Banson yanda zanji dadiba sai awajen ka,Ina da bukata amma banyi tinanin daɗin da akeji zai iya kai wannan ba . Rungumeta yayi yana fadin naji daɗin wannan yabon,nakuma gode Allah da akaina kika san komi,nasha fadamiki dama matana ne aka Arama Adnan,gashi yanzu ai tadawo gareni, dan zaki ya girma,yanzu rufe ido. Gam kau ta rufe tana murmushi ya buda tafin hannuta ya damkamata wani karamin kwali dakuma abu kamar key yace xaki iya budewa. Tana budewa taga kyautar key ne na mota sai kuma zabban gwal masu masifar kyau manya dasu daganinsu basai ance komiba wajen tsada. Cikin farin ciki tace Baby wannan fa ko kana nufin nawane? Eh kyautàr dadin da kika banine. Gdy sosai tashiga mai kamin tace Baby dan Allah kayi hkr akan magana da zanma,inaga hakkina ne nason sana'a ka ko,inaji ajikina ba iya Driver kawai kake ba. Dan bazai baka wannan kudin ba. Murmushi yayi yana jawota jikin shi ya shiga labartamata komi yace dama bari nayi sai na sallami duk mai bina bashi kinga yanzu Dr Abbah daya bani kudin naba shi , Yanzu dukiyar da uwar tawane babu abinda zance dashi sai gdy shida family nasa,ina kara gdya ga Allah daya hadani da Abba, wlh Abbah mutumin kirkine Aymah,bilhakki yake sona,yanzu tafiyar nan da mukai karkiso kiga yanda abubuwa suka bude masha Allah, munsamu mun hadu da manyan mutane Abokan Huɗa,ga aikin safa ya aje tsawon wannan lokacin dandai duk ya hadani da Abokan ƴaƴan nasa dayace muje mugan su, to kinga kau sai gdya,yanzu mota ukku na saya naki daya nawa daya na Baba daya,. Taya ba sosai, tamasa fatan Alkhairi takuma kara ganin mutuncin Dr Abbah Sosai da karamcin sa gare su.. Yace yawwa saura ke akwai wani katon fili da aka sayar mana zan miki gidan gwona dashi da kudinki sai a zuba abinda ya dace kema kinsamu na taimakon al'umma, kana ya maganar aikin ki kina da ra'ayi koko? Murmushi tayi tace kai nike saurara. Yace tom shikenan in dai kinaso kiyi ,in bakyaso muzauna gida muyi soyayya,in kuma nafita ki zauna ki huta,In ina nan kibani daɗi na more. Ido ta juya tace nazabi zaman gidan,Dan fuskar ka tafi haske Yayin da zaka fadi xabina na biyu. Sosai kam yaji dadi nan suka koma ruwa baji ha gani waje kashe Arna. Bayan isha su Malam Habu suka dawo gidan a palon Deedee suka hadu su duka aka shiga firar zumunci, Aymah kau sosai tajejin kunyar Maman Jameel yayin da itakuma ta saki sai ƙoƙarin jawota jiki take. Ranar dai sunyi farin ciki Sosai , Jameel yace Baba wai kason ashe Aymah duk ita tasamaku kayan daki. Nan fa sukayo caaa akanta da gdy cikin kunya ta mike tabar dakin yamasu sallama yashigo ta tare shi tana shagwaba da kukan danmi zaice itane,itafa bata so. Hkr yabata daganan suka haura sama sukayi shirin bacci cikin nishadi suna Rungume da juna. A takaice wannan family dai zuwa yanzu zukatan kowa cike yake da nishadi basa tare da fargaba komi ,Zumunci tsakanin Jameel da Dr Abbah kau abin ba'ace komai hakama Jannat da Dr Asiya. Aymah kau sadda ta farga tana da ciki ranar rufe kanta tayi daki tayi kuka tayi Sallah gdy ga Allah, dan bata taba tinaniba,Jameel kau shiru tayi bata fadamai ba duk kau yanda yake fadin Baby su shuru ba dare ba rana ina noma amma har yanzu dif ba wani motsi ko bashi da Lfy ne. Dariya kawai take tace komi lokacine kuma mijinta lafiyayye ne. Sadda cikin nata yakai wata hudu ya fara motsi lokacin ne ya dan taso kaɗan mussamman in tana tsaye kafi ganin sa. Wata laraba suna zaune palon Deedee kamar yanda suka tsara duk bayan isha acan sukecin abinci sai tara kowa ya koma dakin shi bayan anyi firar zumunci. Deedee kina da fura yau banason abincin nan cewar Jameel yana yamutsa fuska. Eh Aymah mikomasa. Tamike kenan kamar yanda yasaba yabita da kallo nan yaga dan tashin da cikinta yayi,Da ido kawai yabita saikuma yayi tinanin Ko tumbine ta dan aje. Koda suka koma kasa hkr yayi nan ya kwantar da ita akan kujera ya d'aga rigarta tare da dora hannunsa akan cikin nata dayayi tauri sosai ya tasa. Lumshe ido kawai tayi tana murmushi. Shikam Jameel saitin hannun nasa yaji dan motsi kadan kaɗan. Ya Subhanallahi zanso kuga zaburar dayayi amma dai bai gasgataba saida yakai kunnan sa nanfa yaji. mofsi sosai kamar jira dama Baby yake. Wani irin cafka yakaima ta cikin wani zallar farin cikin da bata taba ganinsa cikin saba. Baby dan Allah da gaske dan Allah, karki musaya tinanina akan abinda bashi bane dan Allah ki gasgataman farin cikana,da gsk yanzu nine zanzama Daddy, wallahi Azeem jininane acikin ki Tabbas naji tabbaci. Cikin mamaki take kallon sa dan bata taba tinanin farin cikin da zayyi yakai hakaba da batama fara ɓoye masaba. Cikin natsuwa ta mike ta zauna tanamasa kallon tausayi tace kayi hakuri Baby banyi tinanin farin cikin da zakai zai kai haka ba, Wlh da ban boyemaba,nadai bari ne kawai yakara girma yanda zan baka mamaki gashi kuma Alhamdulillah, ka tsinci kanka cikin farin cikin da Nike fatan ganin sa akoda yaushe a fuskar ka. Wata nawa Baby yace cikin nishadi. Tana murmushi tace cikin na biyar yake in sha Allah amma zanje dai Asibiti inga. Fadamaku tattali da kulawar da Aymah ta samu a wannan daran bata lokacine ,dan duk abinda zai mata sannu sannu dai kar ta samu matsala ko ita ko Babyn ta. Haka sukaita rayuwa cike da so da kauna kaf dangin sa,yanzu dokin haihuwar suke Maman Jameel dinma tagaji da kunya ta saki jiki inka gansu da Aymah kace wasu yan uwa ne shakikai gabaki daya sun rungumi so da kauna sun dora a cikin Aymah . Deedee mah ba'a batta abayaba dan sosai take kulawa da lamarin Aymah danma cikin baya bata wahala iyakai dai abinci ne bata wasa dashi sai bacci, sai ko ɗaukin mijinta any time. Malam habu kau angyara shago an zuba kaya yashiga cikin nasara sai fatan Allah kasa mudace. Sadda cikin Aymah yayi wata tara yayi wani Uban girma zama dakyal tashi da kyal, komi sai an'mata any time Jameel kau na tare da ita ko agida ko a waya, wani lokacin kuma haka zai kama hannuta sudan fita su zazzagaya ta motsa jikin ta. Wata juma'a da Asuba bayan sun gama Sallah suka koma ,cen Cikin bacci taji wani azabataccen ciwon da tinda ta leko duniya bata taba jin saba,Azabure ta mike tafara safa da marwa tanayi tana yarfe hannu,Wani irin juyi taji cikin ta yayi dakyal ta iya daga kafarta tashiga toilet,Ta bude sit da niyyar ta hau taji Abu ya fashe da kuma dannowa kan yaro lokaci daya. Gigitaccen ihu ta kwallah daya sanya Jameel dake bacci yankowa da gudu. Banka kofar yayi cikin azaba ciwo tace yaron mu Baby zai fado. Azabure ya dagota cak yayo kan gado da ita yana kwantar da ita dan nafitowa baki daya ya tsanyara kuka. Gigicewa sosai Jameel yayi aguje kuma yayi niyyar fita ta dakatar dashi tana sauke numfashi. Inda kayan aikinta suka ta gwadamai da sauri ya dakko ta Yanke cibin tayi kwance tana numfashi sama sama. Sannu ya hau jeramata yanayi yana kallon fuskar kyakyawar Babyn Dake masifar kama da uwarta sak ,gatanan tayi shuru sai hannu data sanya abaki. Aymah kau Alhamdulillah taketa jerawa kamin ta dago ta kalleshi ta saki Murmushi tace" Baby yazama Dr ya karbi haihuwa mi muka samu. Ajiyar zuciya ya sauke yace sannu Sweetheart Kinsha wahala,Ashe haka ake haihuwa saura kadan na hade zuciyana wlh, yanzu in'kira DeeDee ta taimaka miki ko, wlh kinyi jarumta da ba kowa zai iyataba? Kai ta kadamai tana fadin kaida kayi aikin kai zaka ida . Takarasa tana mikewa da cire rigarta da mahaifa ke ciki, leda dake kusa da ita tasamu ta sanya kana ta cira kafarta dakyal tayi Toilet,ta hada ruwa tanajin jiri jiri tayi wanka cikin karfin hali, kamin ta duba kanta tana lumshe ido nan taji tabbacin bata samu karuwaba ta daɗa hutawa kamin ta fito akan kujera ta iske shi zaune shida Baby ya Zubamata ido fuskar shi cike da Murmushi yace . Yace Ummu Aymah wannan wace irin jarimar uwace kika samu,kijifa gida cike da mutane amma babu wanda yaji ihunta Allah yasa kiyo halin Maman ki ya manna mata kiss agoshi soyayyar ta na ratsa lungu da sako. Dan murmushi Aymah tayi tana zama gefen shi ta karbi Baby ta zubamata ido cike da so da kauna,Tace Baby ngd abisa karar da kaman ALLAH yasamata Albarka. Ameen yace yana karamata sannu. Tace ,pant da pad zaka hadaman. Dakkowa yayi ya shiryamata komi ya bata yace wazai Ma Ummu nah wanka? Tace ba yanzubu tukunna dai. Kayan shafa Baby ta gwadamai ya daukomata tagoge mata jikinta tass kamin ta samata fararan kaya ta fesheta da turare ta dorata akafada. Wani baccin wahala yayi gaba da ita shikuma ya sauke Baby ya azamata ita gefenta kana ya shiga yaye zanan gadon ya kai toilet ya wanke tass kamin ya fito ya goge gadon duk da ba ta batashi ba, dan babu jini ko digo haihuwar Aymah sai uban ruwa . Bayan yagama ya fesa turaruka ya canzamasu zanan gado kamin ya dauke su ɗaya bayan daya yakai gefe ya zauna yana zuba Murmushi dayima Allah gdy daya basu wannan kyauta. A fili yace zan barku ku huta sai anjima kowa ya ganku,nan yakoma gefen Baby ya kwanta Shima bacci yayi gaba dashi. Wajen karfe 12:30 Aymah ta tashi tajita garau sai uban yunwa datakeji,wanka tayi lafiyayye da ruwa mai zafi abinka ga likita tason komi,bayan ta gama ta zuba daurin kallabi ta feshe jikinta da turare. Babyn ta dauka ta zauna ta shayar da ita sosai tanayi tana lumshe ido saboda zafi. Bayan ta gama ta sake gyara jikinta sosai lokacin da shima ya fito wanka suka shirya tsab yana kallonta da Murmushi yace mai haihuwar mamaki komi naki daban yake Jarumata ina sonki. Murmushi tayi tace Ngd mijin Aymah,Baban Aymah. Fada ki sake Matar Jameel yakarasa yana masu photo masu zafi kana ya kamo hannuta suka Sakko gwanin sha'awa yana rike da Baby a kafada. Kai tsaye kofar suka bude suka fito sukayi part din Deedee ganin takalma cike ya basu mamaki amma sunson Deedee mai jama'a ce.. Aymah ta fara shiga fuskarta cike da annuri yana biye da ita. Palon cike yake da mutane gaba daya attention dinsu ya dawo kansu. Deedee data fito da tire din dake cike da lemuka ta bisu da kallo sama da kasa ,lokaci ɗaya ta saki tiran tana dafe kirji da fadin la'haula wala kuwaata, Habu,! Baraka! kuzo kuga danku yabi zamani wallahii yaje shida matar anyo masu kyankyasar yaro Ashe asabe batai karyaba datace yanzu kwai ake kyankayashewa na yara amma Jameel ka cuceni yanzu dan jikan nawa dama dan na'uwarane mai kwakwalwa saida Batter ma kila zai dingayi takarasa tana kecewa da kuka.. MATAR OGA NA PAGE 36 Duka mutanan dake dakin saida suka ɗauki dariya. Aymah kau batabi takansuba ta karasa wajen Deedee ta durkusa tana kama hannunta tace haba Deedee nah kallifa ga baki kinyi kina kuka,kema kinson ko jiya da daddare muna tare dake kuma da ciki a jikina,haihuwa Allah ne yakawoman ita da sauki cikin mnt na kalilan ,To kuma kinga ba laifi nason wani abun zan iya taimakama kaina matsayina na ma'aikaciyar jinya,Dan haka nida Baby muka karbi haihuwar nan shizakima gdy ga diyar ki nan a'hannu ki karɓa kisamata Albarka . Baki sake Deedee ke kallon su shikam Jameel hankalinsa nakan Baby sai wasa yake mata kamar zararre ko kallon Deedee da mutanan palon Baiba. Amamatu Baba Bakigane wayan nan ba?. Baba Ali dake gefe ya fada. Da sauri ta kalli inda yake karaf idon ta ya sauka ga fuskar mutanan da bazata taba mantawa ba,Mutanan data fitar da ran sake sasu ido,mutanan da takejin nawie tunkurarsu da sunan Ita din yar suce saboda biyema Namiji da tayi, jikinta har rawa yake tace gwaggo, Aunty Aysha, Aunty Hadiza,,dama zan ganku. Dukkansu kuka suke suna fadin kaico da cin amanar marigayi da mukai amma ba laifinmu bane mijinki ne sila kuma kinson zuciyar kawunku shiya hana kowa kussantar ki,Amma yanzu muna neman yafiyarki Ummu Aymah, saboda munson bamu kyautaba,baikamata mubiye halin namiji mu wofintar dake ba matsayin ki na jinin mu hannuka baya ruɓewa ka yanke ka yar,,muna rokon gafarar ki,munzo katsina nemanki yafi a kilga Amma munkasa gane gidan . Wannan bawan Allah mijine nagari na kwarai babu abinda zamuce dashi sai gdya, Allah ya sakama mijin ki da Alkhairi shine yaje wajen mu ya nausar damu kuskuran da akayi da matsala data faru dake da Tsohon mijinki, har zuwa yanzu da yake matsayin miji gareki. Aymah kau Jameel ta zubama ido lokaci daya ta fada jikinshi tana sakin kuka, Jameel ya gama mata komi,ya dai-daita farin cikinta ya kuma je har kasar su ya hadata da family nata,tana yawon tinanin su amma kuma tason bata da damar tunkarar su Saboda abinda ya faru,Amma dayake mijine na gari shi maisonta da tausayin ace da nashi kawai take rayuwa gashi yaje yasha wahala ya nemi nata dan dai ya hadamata gurbin farin cikinta gaba daya . Deedee kau da sauri ta ɗauke ɗiyar dake kafardashi tana fadin nidai ban yardaba muga halittar ki in cikakkace bada battery kike amfani ba ta karasa tana zama zuciyarta fall da kaunar Baby ta cire mata kaya har pampas ta duba ko ina ta sauke ajiyar zuciya tace Alhamdulillah,ga gabantanan damdam masha Allah ba ma'adanin battery,Fatartama cuss bata ɗiyar Robaba Allah nagodema da yanzu saidai in hada kayana inyi kauye ko cikin network ɗin ne da bala'i in zauna nida Malam. Dariya sosai yan palon suka dingayi . Baba Ali yace duk inda kike muna biye Hajiya Deedee. Jameel kau bayan Aymah kawai yake shafawa yana zubamata kalamai masu dadi,tsawon lokaci suna a haka kamin ta koma cikin danginta suka shiga firar yaushe gamo tana ta masu tambayoyi akan danginta . Wasu ace suna nan wasu ace sun rassu. Jameel kuma da Deedee sukayi sashen Su Malam Habu da Baby cike da nishaɗi a zukatan kowa. Ba karamin mamaki suka shaba daganan aka hau bugama yan uwa da abokan arziki DeeDee kam aka fiddo katuwar tukunya aka shiga dafa ruwan zafi akashiga store aka kwaso gero aka kai unguwarsu gidan Asabe dan a masu dakan kunu. Kiching ta koma ta hadoma aymah lafiyayyan abinci mai rai da lfy ta zauna ta tsareta tana washe baki tace wallahi AYMAH ta tafi ta kowa jarumar mace,zamanki likita baizama aikin banzaba,amma wasu katton banza likitocin kiga suna dukan mace in zata haihu sukau in zasu haihu sai an'sama munafukan kafafuwan su mari saboda ihu da kai ma bayin Allah Naushi.. Dangin Aymah kau dasukazo su biyar dariya sosai suke daganan suka kira sauran dangi suka sanar dasu haihuwar ta nan fa kowa yafara shirin zuwa Katsina. Aymah kuma ta dauki waya ta kira Aminan arzikinta kan kace mi gida da yamma yacika sosai kawayen Deedee gasunan zube sai basu labarin jarumta Aymah take.. Zaman jego mai kyau da tsafta akai Anci an sha danginta sun taka rawar gani sosai dan hidima babu kamaf hannun yaro yinta suke. Saura kwana biyu suna Danginta kaf suka zo. Sabuwar Rayuwa mai cike da walwala da farin ciki sukayi a wannan rana an tina da anyi kuka anyi Dariya..Ranar suna kau katon holl suka kama akaci akasha akayi photo tarihi kana aka watse da kyautatuka masu yawa dagani kason haihuwar an'mata tanajin nera . Bayan wata biyu da haihuwar ta aka daura auran manager da Hajiya Asiya, bikin da Aymah da Jameel suka taka rawar gani kamar ba gobe. Ana gama bikin kuma suka shirya zuwa kaduna wajen madina dan bikin yaranta ya tashi,sun kaimasu shatara ta arziki taimasu tarba mai kyau ta mulmuje har ta sake sabon aure ita kanga,ankai yara gidajensu masha Allah. Suna dawowa taje ganin gida nan fa taga so da kauna ta zahiri duk abinda akai ada ya wuce yanzu kowa ya mallaki hankalinsa, satin su biyu suka dawo da tsaraba tagani ta fada. Jameel kau shekarasu biyu da aure Allah ya karomasu budi sosai inda ya fitar da kujera ukku ta hajji. Baba Maman shi. Deedee. Sadam kuma da Abokin sa Bash kudi masu soka ya basu da kyautar filaye nan fa suka hau gdya kowa yaje ya kama sana'a. Zanso kuga badakala da akai kamin Deedee tayi bacci ranar da aka sanar da tashin jirgin su tin dakinta tafara safa da marwa,abun ba acewa komi sai son barka. Shekara na zagayo Shida Aymah suka cala suka bar ummu a wajen su Baban su. Bayan sun dawo Baba Ali da Kb suka je Umara saboda yanayin jikin tsufa na Baba Ali bazai iya Hajji ba. Bayan shekara biyu. Ummu ce yar shekara Hudu mai masifar wayo kyau ko ba'a magana,Zaune take hannuta rike da chocolate tana tsotsa kafarta daya akan daya tana waya da Abul khairi sai cuno baki take tana fadin yaki zuwa ya dauketa sutafi gidan su. Kuka tasa ta kashe wayar tana tillata gefe. Jameel dake gefe yana tajema Aymah kai yace yadai Jarumata keda Yah Abul ɗin ko,miyamiki? Cikin kuka tace wai nace yazo yazo yakiya wai sai ya gama jarabawa Daddy wlh auran shi zanyi kullum in ganshi kamar yanda kake ganin Mamy itama. Gabaki dayan su ido suka zaro kamin su sanya dariya ya zaro waya ya kira Dr Abban bayan ya dauka yace Aminina yaufa diyar ka ta ballo ruwa wai a aura mata Abul khairi ta dinga ganinsa kullum. Sosai yake dariya yace Ummu kinajina,?. Cikin kuka tace inajin ka Daddy Yawwa Ummu Abulkhairi shi kikeso ki aura? Cikin farin ciki tace eh mana kaga kullum muna tare kamar Daddy da mamy tinda in anyi aure ana tare Kullum ko?. To shikenan Baby nah in sha Allah baki da wanda yafi yayanki kinji, zaki dage kiyi krt sosai sai kiyi saurin girma sai Abul khairi ya aureki ko? Ihun murna sosai taitayi aguje ta fita tana fadin Deedee aure zanyi. Deedee dake damama Baba Ali fura ta dago kai tace kai jama'a Ummu wannan wane irin kirane zaki tsorataman miji jibi saura kadan ya fado daga kan kujera Baki ta turo tace to ba aure zanba nace in fadamaki nama fasa fadamiki natafi wajen Inna. aguje kuma ta juya tayi part dim kakarta nan suka shiga wasa da Kabeer daya dawo school. Jameel kau yanaganin fitar ta sukai sallama ya ce Sweetheart kindaiji abinda yarki ke cewa ko,to wlh maza maza muje noma ko masamu rabo mai amfani,Kindaiga ita aure zatai karta barmu empty. Murmushi tayi tace'' Baby ai saidai ka inganta lfy Babyn ka, waikai yaushe zaka dinga gane cikina ne yanzu ciki wata hudu amma ka kasa ganewa. Aiko taga tsagwaran so da kauna akan wannan cikin nan suka haura sama sukasha soyayya kamin suyi wanka su sakko suka shiga gari. Bayan wata biyar ta haifo yaranta yan biyu duka maza masu kama da Ummu amma basukai hasken fatarta ba na Daddy su suka ɗakko. Sunan mahaifin AYMAH da Baban Jameel akasa amma ana cema su. Areef da Arfaat. Rayuwa sauyi sauyi, tafiya tayi tafiya inda Jameel ya gina masu katon gidan dayafi wanda suke ciki suka koma aka cigaba da rayuwa mai dadi sai fatan tsawon rai da samun zuria masu Albarka. Baban Jameel kau kasuwan ci sai son barka dan yanzu yaboɗe reshi reshi na business Babu inda basuyi sunaba saboda ragowar farashi dasukafi yan kasuwa. Tammat bi hamdulillah.. ina mika gdya ta ga Allah daya bani damar kammala shi lfy, kuskuran dake ciki Allah ya gafartamana. Ina mika sakon gdya ga masoyan book dinnan Allah yabar zumunci. Bazan manta dakuba Yan paid group ina sonku so mai tsanani fatan zumunci mai ɗorewa abadan Ya Allah.. Mrs Chief Fatima kanam Aysha adam Maman areef Aunty Mrs Bash Mame Ibrahim Nijer Mamagee Aisha A Hdz Dutsamma Maryam bako Mommy mokhdoom Mon asas Ummu ilham Ruky amarya Kai da dai dukkan sauran mabiya da bazan iya lissafo yawonkuba ina gdya Allah yabar zumunci. Ban manta dakeba Deedee❤️🤍❤️ takwara Hajiya Deedee mai kunun aya Allah yabar zumunci . In sha Allah bayan sallah akwai free book na wayanda suka saba sayen book dina kawai mai suna MATAN HAMXA Banaso daya daga cikin ku yayi missing dan an hada cakwakiya mai zafi sai in Allah ya nuna mana Ayi sallah lfy🥰 I miss You so much Wlh 🥺 Kadan daga cikin matan hamza. . Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels