Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels  *🔥 SARAUNIYAR KYAU 🔥* _-_👑ƚαƙυɳ ƚʂαƙιყα👑_-_ _-_ҽρ.1_5 *بسم الله الرحمن الرحيم* *MALAM AMINU KANO INTERNATIONAL AIRPORT* Daga yadda gaba ɗaya mutanen dake cikin filin hawa da saukar jirgin, suka bada hankulan su akan kallon ta, hakan zai tabbatar muku da cewa lallai takai a kalle ta. Wasu kai tsaye zasu kira ta da suna *SARAUNIYAR KYAU* ta duniya koma fiye da hakan idan akwai. Ɗoss, Ɗosss Haka sautin takalman da ƙafafuwan ta suke ciki yake tashi a wurin, kai daga Kallon ta sannan ka kalla shigar tsadaddun kayan jikin ta, zaka tabbatar da cewa lallai ba ƙana nan ƙuɗaɗe aka kashe akan ta ba. Ko nace ake kashewa. Matashiyar budurwar ba zata haure shekaru Ashirin ba a duniya. Za'a iya cewa Princess Gown ne jikin ta, duba da yadda doguwar gown ɗin ta sauka ma ta har ƙasan gwawowin ta, daga ƙirjinta zuwa ƙasa na gown ɗin a buɗe yake, ma'ana dai a tsage wurin yake. Golding color ce gown ɗin. Ƙafafuwan ta rufe cikin wasu tsadaddun takalma Strappy Heels, kanta kuwa da gashin yake a waje, kuma a baje, an gyara shi in Blonde wavy hair, launin gashin nata dark brown, Kyakkyawa fuskarta wada ce da make-up na nunawa, gaba ɗaya jikin ta indai wuri ne da za'a saka abin ado tofa akwai, kama daga kunnen ta, yatsun ta, wuyan ta, babu inda ba'ayi ado da gold ba, sheƙi kawai take yi kamar zinariya. Ƙari sawa tayi wurin Ƴan matan su uku da suke matsayin manyan ƙawaye a gare ta. Kuma tamkar ƴan uwa. Ibtihaaj ƴar asalin ƙasar Austaraliya mazauniyar Dubai, mabiyiya Addinin Buddha ita da mahaifan ta, sai Ansha, haifaffiyar Najeriya, girman Turai, ta kasance banasariya ce, sannan sai Aahila ƴar ƙasar Malaysia. Dukkannin su tare suka taso, abin nufi su ɗin ƙawaye ne tundaga primary school da suka yi tare a ƙasar Amurika har zuwa secondary, lokacin shiga University ne ma ƙawancen nasu yaja baya sakamakon ko wacce su abin da take karanta daban, sannan ra'ayin su yasha banban ta wasu fanin. Sun ɗauki tsawon shekaru biyu basu haɗu da junan su ba, sakamakon yanayin karatun ko wannensu, sai yanzu Ubangiji ya ƙaddara sake haɗuwar su, dalilin Birthday Party na Ansha da mahaifan ta suka shirya ma ta a ƙasa Nijeriya, wanda shi ne zuwa ƙasar na farko da kowannen su tayi harda Ansha da take haifaffiyar ƙasar. Cike da farin ciki kyakkyawar budurwar cikon ta huɗun su da sai yanzu ta samo ta shigo ƙasar ta rungumo su duka cike da murna na sake ganin juna da suka yi. "Samiupter D'Souza, ashe zamu sake haɗu wa dama, nayi tunanin shikenan tun da kika koma India mun rabu har abada, sai gashi sanadin Birthday na mun sake haɗu wa gaskiya nayi farin ciki sosai, da hakan ta kasance." Murmushi budurwar da Ansha ta kira da Samiupter D'Souza tayi tana gyara salon riƙon da tayiwa akwatin dake hannunta, zatayi magana wayar Ansha tayi ƙarar shigowar kira. "Oh Pappa ne yake kirana guy's mu tafi kawai lokacin fara shagali ya yi, jiran zuwan ki Samiupter shi ne ya saka ma ban yanka cake ba, amma tun da gaki kin hallara muje kawai, daga baya zamu tattauna akan bayan rabuwa da." Motar su mai tsadar gaske suka shiga gaba ɗaya su huɗun, Aahila ce take Driving nasu, sannan suka bar Airport ɗin. Samiupter D'Souza dai ta kasance haifaffiyar Amurka ce, sai dai dangin mahaifiyar ta a India suke kuma ƴan ƙasar ne, yau ga Samiupter D'Souza a Najeriya, ƙasar da bata taɓa zuwa ba, sannan kuma gaba ɗaya Ahalin ta babu wanda yasan tazo ƙasar domin Birthday Party.🩸 *MENENE ZAI FARU GABA?.*😏 *ABUJA* *NAJERIYA* A kalla takai mintuna goma da parking motar, a cikin gidan ƙanwar ta Sailuba. Ƙafarta ɗaya ta fara fitowa da ita, bayan wani lokaci kuma ta fito gaba ɗayan ta daga cikin motar, kai tsaye babban palon ta nufa. Sallama ɗauke a bakinta ta ƙari sa shiga cikin palon. *Fadeelah* Yau bata da lecture saboda haka, tana zaune a palon tana kallon wani Turkish drama. "Wa alaikumus-salam WarahamatuLlahi Wabarakatuhu." Ta amsa sallamar da taji tare da juyawa don ganin mai yin sallamar. Tsakanin tashin ta daga inda take har ƙari sawar da tayi wurin baƙuwar tasu, ta tarbota da farin ciki bayyane saman fuskarta, ta gaisheta ta, ta amsa, taje kitchen ta samo ma ta abin taɓa wa, ta kawo ma ta, cikin girmamawa, har fitowar mahaifiyar su, Hajiya Sailuba daga Bedroom ɗin ta, da shigewa Bedroom da suka yi, su barta anan palon. Duka lamarin ya faru ne fuskar Fadeelah wadace da murmushin farin ciki da jindaɗi. Tana matuƙar girmama Momy Rafi'at sosai, a sakamakon buri da take dashi, sannan tasan muddun ba tayi ma Momy Rafi'at biyayya tun yanzu ba, tofa hakan zai iya hana burin nata cika. *A TUNANIN TA* Burin tayi ta kammala kallon da take yi domin zuwa Gidan Uncle Mai Kyau, don ganin Yaya Maleek da ake faɗa ma ta ya dawo gida. Sai kuma gashi Momy Rafi'at tazo gidan wurin Hajiya, hakan kuma ya yi ma ta daidai. Ba tare da wani ɓata lokaci ba, da shigar Momyn nasu da kuma Momy Rafi'at Bedroom, ita ma ta miƙe ta nufa Bedroom na ta domin ta yanke zata bi Momyn ne kawai zuwa gidan Uncle Mai Kyau ɗin. Kayan ta kala goma ta saka cikin akwatin ta sannan ta haɗa da duk wani abu da zata buƙata, tayi wanka tayi make-up ta shirya ta zauna gefan gado tana jirar fitowar Hajiya Rafi'at. *KANO* *NAJERIYA* Da sauri tayi reverse da motar cikin tsananin tashin hankali yayin da ta ɗa go kanta a hankali don ganin ta kaɓe wani ko wata. Don kuwa yadda taja baya da motar da kuma yadda taji ta burge wani abu, tunaninta bata yake yi ka karɓe wani. "Afeefah kina lafiya kuwa, dawo back seat kawai, bari ni karɓa tukin naga kamar bakya hayyacin ki, gashi zaki saka muyu accident a titi." "Kafin nan mu fara duba motar da ta bige, wata ƙila ma tayi musu ɓarna." Cewar Mah'eesha tana kallon Lailah wacca tayi wa Afeefah maganar cike kulawa. Fitowa suka yi daga motar bayan Afeefah tayi parking a gefe, domin kuwa a titi suke. "Kuyi haƙuri fa, mun kusa muyi muku ɓarna a mota, sorry Afeefah ɗin ce sai a hankali kuma take tuƙi our apologize." Mah'eesha ce da tare da Lailah suke wannan maganar wa Ƴan matan da Afeefah ta bugewa mota. "Oh nothing, ae bata mana ɓarna ba, babu komai fa." "Yauwa Sister mun gode sosai." Lailah ta amsa wa ɗaya daga cikin ƴan matan wacca ta basu amsa. Yayin da idanunta suke a kan su duka, sai dai ɗaya take yiwa kallon sa ni. Komawa mota sukayi sannan Afeefah wacca bata fito ba, ta matsa gefe Lailah ta zauna a mazaunin driver sannan ta ja motar kai tsaye har Gidan Yaya Shahid dan nan suka nufa dama su uku ne, ita Lailah ɗin sai Afeefah da kuma Mah'eesha, Deejarh taso ta bisu amma ciwon mara da take yi yasa Afeefah ta ce ta zauna a gida kawai. Da isarsu gidan mai gadi ya buɗe musu gate ta shiga ciki, ta daidai ta parking, sannan suka fiffito a tare suka nufa palon gidan. Kwankwasa ƙofar palon Mah'eesha tayi tana ƙara wa cikin ƙunƙuni, dama tasan indai wannan baƙar Aeezath ɗin ce sai ta shanya su, sannan zata buɗe ƙofar. "Au dama haka kuke ma ta idan kun zo ke nan. No wonder take muku abin da take yi, don ko ni ce dai dai Abin da tayi zanyi fa." Afeefah ce take wannan maganar a yayin da take kallon Mah'eesha ɗin. "Me kike nufi da wannan maganar Afeefah ban gane ba, menene nayi ɗin?, nasan dai iya knocking nayi kuma taƙi tazo ta buɗe dama haka ta saba halinta ne." "Bafa halin ta ba, fisabilillah yanzu da ƙari sowar mu nan bakin ƙofar, ko fa mintuna biyu bamu yi ba, amma harkin fusata saboda batazo ta buɗe ƙofa ba, kiyi ma ta uzuri mana, kika sani ko tana kitchen ne ko kuma tana sama, kodai tana wani abun?, Gaskiya Mah'eesha a wasu abubuwan da kuke faɗin tana muku, kuma harda laifin ku fa, duk kun bi kun tsaneta haba." Iya kar gaskiyar ta Afeefah take faɗa wa Mah'eesha haka ɗin, domin kuwa ta fara fahimtar abubuwa da yawa akan su duka, daga ita Aeezath ɗin wacca ko taɓa haɗuwa ita Afeefah ɗin bata yi ba, sakamakon lokacin da aka yi auren Yaya Shahid ɗin bata ƙasar, shekaru biyu baya, tana India wajen jinya, kuma sannan ba'a ƙasar ya zauna da matar tasa ba, ko watanni huɗu basu yi da dawowa Nigeria ba, tsakanin jiya da yau ta fahimci wasu daga cikin halin rashin kirkin da su Mah'eesha ɗin suka ce matar Yayan nasu Aeezath take nuna musu, su suke ja ma kansu, domin idan ta duba da labarin da Haseeya ta basu jiya da dare na cewa wata ƙawar Mah'eesha ɗin taso Yaya Shahid sosai, amma yaƙi aurenta ya aura Aeezath. Idan ta cinka a iya tunanin ta saboda Yaya Shahid ɗin yaƙi auren ƙawar ita Mah'eesha ɗin ce shiyasa ta tsana matar da ya aura Aeezath. Shiru Mah'eesha tayi bata ce da Afeefah ɗin komai ba, sai dai tunani take a zuciyarta ko shin Aeezath ta taɓa musu wani abu da basu ji daɗi ba, wanda kuma basu suka jama kansu ba, bata taɓa musu kallon rashin kirki ba, har sai sun fara ma ta tukunna take biye musu. Buɗe baki Lailah tayi zatayi magana, sai dai maganar cak ta tsaya a bakinta sakamakon ganin mutumin da ya buɗe musu ƙofar palon da tayi. Dogo murɗaɗɗe dashi kuma Kyakkyawa mai kama da Uncle Sagir sanye da normal singlet da wanda 3 quarter. Kawar da idanunta tayi daga Kallon sa yayin da a bakinta take furta kalmar gaisuwa garesa, suma su Afeefah suna gaishe sa. Bai amsa musu ba ya basu hanya suka shiga ciki, sannan ya mayar da ƙofar ya rufe yana mara musu baya. Saman haɗaɗɗun kujerun palon suka zazzauna suna kuma gaishe dashi, sai da ya zauna saman kujerar Dining da yake sannan ya amsa musu yana haɗawa da tambayar ya ya suke. Cike jindaɗi Afeefah ta amsa masa tana haɗawa da masa tambayar. "Muna lafiya lau, Yaya Shahid hala dai Anty Aeezath ɗin ba nan ne?." "Masha Allah, wai Darling tana kitchen qiwa ne ya hanata tashi tun safe sai yanzu wuraren ƙarfe sha biyu take haɗa mana breakfast, duk ta bar muku ni da yunwa." "Lallai anty Aeezath ta cancanci tuhuma tunda har tabar mana Yaya Shahid guda da yunwa har sha biyu, bari na bita kitchen ɗin sai naji dalili." Afeefah tayi maganar cikin dariya sannan ta miƙe tsaye bayan ta a je mayafin kanta a saman kujera ta nufa kitchen ɗin. Murmushi Yaya Shahid ɗin ya yi yana bin bayan Afeefah da kallo, Yarinyar tana burgesa tun daga kan nutsuwar da take dashi, kyawunta, da sauran su, shiyasa ko cikin yaran dangi yafi shiri da ita, daga ita sai Husnee da kuma Zaynerb yake sakarwa fuska, wani lokacin harda Lailah. "Lailah yakike?, wai da gaske Maleek ya dawo, na fa kasa yarda." Yaya Shahid ya yi maganar bayan ya mayar da kallon sa akan Lailah da take zaune gefan, Mah'eesha da tayi tsit a palon dan kuwa ba kaɗan ba take tsoron Yayan nasu, domin babu wasa. "Eh wallahi Yaya Shahid ashe ka sama labari yau ina ga kwanan sa uku ke nan da dawowa fa." Lailah ta basa amsa tana gyara zamanta cike da son suyi fira dashi. "Ɗan kwal uba yaji wuya ya dawo, ae naso ace ina nan lokacin da ya dawo da bazan bari Uncle Mai Kyau ya yafe masa da wuri ba Allah kuwa." Dariya Lailah tayi jin abin da Yaya Shahid ɗin yake faɗa, dama sun saba irin haka da Maleek ɗin domin sa'annin junane su ɗin, duk da dai Yaya Shahid ɗin ya bawa shi Maleek kusan shekara, Yayin da shi kuma Maleek yaba mah'fuz da Yasir shekara da watanni shiyasa duka suke kansu ɗaya, kuma abokai, domin kuwa idan Maleek da Shahid suka haɗu wuri ɗaya rantse wa zaka yi abokan wasa ne, saboda yadda suke abu kamar wasu abokan wasa. "Huh Yaya Shahid ke nan, ina baka labari sai ma lokacin da Daddy yake cewa bai yadda Yaya Maleek da ya zauna masa a gida ba, har sai ya fito da mata, a lokacin kwatsam yace Husnee yake so, ita kuma tsaban gulma harda wani faɗin zata je tayi shawara, ina faɗa maka ta shige Bedroom ɗina ta sha rawa da waƙa ta fito, tana wani kyaɓe fuska na wai ta ce amince."🤣 Dariya Yaya Shahid yana a je cup of coffee dake hannun sa yace. "Kaji ƴan rainin hankali dukansu son junan su su ke yi, dama tun kafin yanzu na daɗe da sanin cewa Maleek yana son Husnee, dan haka amfani ya yi da damar sa kawai a ranar ya jefa tsuntsaye biyu da dutse ɗaya, babu komai zai gamu dani, zamu haɗe, Allah ya kaimu nazo Abujan." Dariya Lailah keyi nan dai suka ci gaba da fira dashi, Mah'eesha tana daga gefe tana ɗan tsoma baki idan an sakata a wani abin.😉 Da sallama ta shiga kitchen ɗin yayin da take hangen matar da ta juya baya tana aiki cikin kitchen ɗin. "Wa alaikumus-salam WarahamatuLlahi Wabarakatuhu." "Barka dai Matar Babban dama nazo tayaki aiki ne, Yaya Shahid yace qiwa ya hanaki tashi sai yanzu kike masa breakfast." Cewar Afeefah bayan Aeezath ɗin ta amsa ma ta sallamar da tayi. Murmushi tayi tana faɗin "Lallai ma wannan mutumin sai kace bashi ne ya hana ni motsawa ko nan da can ba, shi ne zai wani ce qiwa ya hana ni yi masa breakfast Aikuwa zai gamu dani tabbas."😚 Dariya kawai Afeefah ta kuma yi tana faɗin "Yaya Shahid ke nan, wato shi ne yazo qiwa ya hanaki ko Humm. Ni bama wannan ba, Matar Yaya ni fa kama kike min da wata ƙawata da muka yi school tare a Jamus gaskiya kuna kama sosai." "Allah Sarki shin ko dai Adivat kike nufi?." Aeezath ta tambaya tana kallon Afeefah ɗin. Cike da farin ciki Afeefah ta amsa ma ta da "Eh wallahi sunan ta Adivat school ɗaya muka yi da ita a Jamus, tunda muka rabu, ban sake haɗu wa da ita ba." "Ayya Aikuwa ta kwana gidan sauƙi domin ƙanwa ta ce uwa ɗaya uba ɗaya muke da ita." Zaro ido Afeefah tayi tana kuma kallon ta ciki gyaɗa kai take faɗin "Babu shakka domin kuwa ga alamu nan ya bayyana ɓaro ɓaro kuna kama sosai ita, Allah Sarki ko yanzu tana ina oho." Afeefah ta ƙarisa maganar nata da alamun tayi kewar ƙawar karatun nata Adivat. Aeezath tana ɗauraye plate's dake hannunta ta amsa ma ta cewa. "Ai Adivat yanzu tana can U.s tana karatun ta a can tama kusa kammala, domin ina ga a wannan shekarar zata kammala, kin san karatun likitanci take shiyasa ma ta daɗe bata kammala ba." Karɓar plate's ɗin Afeefah tayi tana faɗin "Allah Sarki kice abu ɗaya muke karanta da ita, aikuwa Insha Allah kafin mu koma Abuja zan karɓa lambarta a Wurin ki." Afeefah tayi maganar tana jere plate's ɗin a wurin da ya kamata sannan ta ci gaba da taya Aeezath ɗin. "Okay babu damuwa, in ce dai ba yau ne zaku koma na ko?." Aeezath ta tambaya "Yau ne anjima ma kuwa, Around 4:30pm Insha Allah mun sauka a Abuja ma." Afeefah ta bata amsa tana ci gaba da cewa "Amma Please na tambaye ki mana, wai menene a tsakanin ki dasu Mah'eesha ne haka, na lura sam bakwa shiri fa, ko zan iya sani Please?." Afeefah ta ƙari sa maganar ne a daidai lokacin da Mah'eesha ta shigo kitchen ɗin, batare da kallon su ba, don taji Abin da Afeefah ta faɗa, ta wuce can ta ɗauki ruwa a fridge sannan ta buɗe gorar ruwan tana sha. A daidai lokacin kuma Aeezath take bawa Afeefah amsa da cewa "Kin san a rayuwar nan kowa abin da yaga zai iya yake yi. Ni a tsarina indai mutum ya nuna baya yi na, to nima fita harkar sa nakeyi, na sani ana cewa bani da kirki, sai dai rashin kirki na akan wanda ya gwadamin rashin kyautawa nakeyi, sun nuna ban musu ba, shiyasa na fita harkar su gaba ɗaya, yanzu idan aka min magana ae zan kula Mutum, bazan sha re shi ba, wasu kawai suna wahal da kansu ne akan ga ba dani wallahi." Gaza haƙuri Mah'eesha tayi sai da ta juya ta kalla Aeezath sannan tayi ma ta tambayar da ta daɗe a zuciyarta tana so tayi ma ta bata sama dama ba, sai wannan lokacin. "To idan maganar ki haka ne, me saya ranar da muka fara zuwa gidan nan wurin ki ni da Haseeya da Hameeda kika kulasu baki kulani ba?." Murmushi Aeezath tayi sannan ta bata amsa da faɗin "Saboda a lokacin na sama labarin kece wacca bakya so na cikin familyn Shahid saboda ya aure ni, bai aura ƙawar ki ba, ko ba haka bane?. Wannan ne yasa bana shiga harkar ki ba komai ba." Shiru Mah'eesha tayi ba ta ce komai ba, sai zare ido.🙄 *Mrs Mai Kyau* "Sailuba ke fa nake jira baki ce komai ba tunda na faɗa miki maganar da ta kawoni wurin ki fa?." Momy Rafi'at tayi maganar tana kallon Ƙanwar nata Hajiya Sailuba domin jin amsar da zata bata akan maganar da tazo ma ta da'ita. Dogon numfashi Hajiya Sailuba taja tana kallon Yayarnata cikin nazarin maganar da ta faɗa ma ta tun shigowar su Bedroom ɗin. Sannan ta ce "Yanzu idan na bari Fadeelah ta aura Maleek kamar yadda ki ka so shin bakya ganin hakan zai iya kawo matsala tsakanin, Yaranki da dangin Mahaifin su, kuma naji kince Maleek ɗin ya riga ya zaɓa wacca zai aura cikin yaran dangi, to menene manufar ki akan cewa kina so ya aura Fadeelah, ni fa gaba ɗaya ban gane inda kika dosa ba Wallahi sam." Ƙayataccen Murmushi Hajiya Rafi'at tayi tana juya idanunta akan ƙanwar nata Sailuba sannan ta ce "Ina da dalilai da yawa da yasa nace miki ina so Fadeelah ta aura Maleek, biyu daga ciki kawai zaki iya sani, sune na farko, idan Fadeelah ta aura Maleek Yarona zumuncin mu zai ƙara haɓaka sosai, na biyu kuma saboda dama can inada burin haɗa auren Maleek da ita Fadeelah ɗin, kuma lokaci ɗaya sannan rana ɗaya nakeso ayi dana wacca zai aura ɗin, domin kuwa bazai yiwu ya aura dangin ubansa yabar na uwansa ba, bani da yadda zanyi a fasa wancan shiyasa nace a haɗa duka." *Turƙashi* Hajiya Sailuba ta faɗa hakan ƙasa ƙasa tana kallon Yayarnata. "To amma bakya ganin cewa Maleek ɗin ba zai so hakan ba?." Ajiye spoon dake hannunta Momy Rafi'at tayi tana faɗin "A'a sam bazai ƙi ba, saboda Yarona yana yimin biyayya, ga duk abin da naso ya yi, sannan kuma a halin yanzu idan nace masa ya aura Fadeelah bazai min musu ba, sakamakon jiya sosai na nuna masa ɓacin rai na akan abin da ya yi mana sai yanzu ya tuna dani da ƙannin sa ya dawo gida. Saboda haka bana nada matsala dashi, sai dai ita Fadeelah ɗin ban sani ba ko tana da ra'ayi a kansa, shiyasa tun farko nace miki ita Fadeelah ɗin ta biyo ni zuwa Gidan ta ɗan yi kwanaki, nasan zan fahimci komai idan tana da ra'ayi akan Maleek."😒 *A TAƘAI CE DAI* Momy Rafi'at bata bar gidan ƙanwarta Sailuba ba, har sai da Sailuba ta amince da maganar da taje ma ta da ita, sannan kuma tare da Fadeelah suka bar gidan, dama ita Fadeelah sara ne yazo ma ta daidai da bakin gatarin ta, domin tanada burin bin Momy Rafi'at ɗin, sai kuma ita Momy Rafi'at ɗin da kanta ta nema su tafi gida tare tayi ma ta kwanaki a cewar ta, Aikuwa babu musu Fadeelah ta amince. *JIDDARH* Har wa yau mamakin Abin da taji Auntie tana faɗa wa Heesham bai gama barin ta ba, "*KA NEMA SOYAYYAR JIDDARH*." Wannan magana idan Jiddarh ta tuna tana ƙara mamaki, tunaninta menene abin da ya sa Auntie take so Heesham ya Aureta tunda har ta ce ya nema soyayyar ta. Abu na biyu da ya kuma ɗaure ma ta kai game da Auntie shi ne hana su zuwa Gidan su Juwairiya Jabir Bici da tayi. Gefe ɗaya kuma ga Budurwar da suka haɗu da ita acan gidan su Juwairiya ɗin bayan sun je ba tare da sanin ita Auntie ɗin ba. Tabbas idan idanunta daidai suka gani a lokacin bala'in kamani taga suke yi ita da budurwar da aka ce ita ce*SARAUNIYAR KYAU* ta Abuja. Gaba ɗaya ta shiga cikin damuwa tarin tambayoyi ne masu yawa a tare da ita, sai dai bata san wurin waye zataje ya bata amsoshin su ba. Yanzu haka tafiya take yi izuwa garden wurin Heesham. So take idan taje taji dalilin sa da ya sa yace Humaira ta kira masa ita. "A gaskiya ina cikin damuwa sosai, sai naji ina kewar iyayena, Allah Sarki ni gaskiya kawai zan je wurin Auntie ita da Abba nace su bani lambar Mahaifiyata indai tana raye ina so na ganta face to face, na tambaye ta dalilin da ya sa tunda ta tafi ta barni a tsumma na haihuwa bata kuma wai waya ta ba." Da ire iren waɗanda tunane tunanen Jiddarh ta ƙari sa garden ɗin wurin Heesham. *AFEEFAH* Basu bar gidan Yaya Shahid ba har sai da taga ta ɗan daidai tsakanin Aeezath da Mah'eesha, duk da dai ita Mah'eesha ɗin ce sai a hankali, amma ita Afeefah ɗin tayi abin da zata iya. Around 4:10pm_-_ "Kaka ta tohm saduwar Alkhairi mu dai zamu yi gaba izuwa garin Abuja sai kun sake ganin mu idan akwai rabo." Afeefah ta kammala faɗa wa Amma kakar tasu hakan a lokacin da take daga tsaye cikin palon kakar tasu. "Afeefah dawo ki zauna ina da magana dake kafin ki fita." Juyowa Afeefah tayi tana kallon kakar tasu da tayi maganar in seriously daga inda take zaune kamar kullum litattafan Addini gabanta tana dubawa, ba tare da musu ba Afeefah ɗin ta koma ta zauna, yayin da Mah'eesha dake zaune saman 2sieter ta zuba musu ido tana kallo dan jin abin da ita Amma ɗin zata faɗa wa Afeefahr. "Faɗa min gaskiya kina cikin damuwa ko?." Amma ta tambaye ta. Da mamaki Afeefah ta kalla Amma ɗin jin irin tambayar da tayi ma ta. "Amma wai ni damuwa kuma tona menene ke nan?." Ita ma Afeefah ta tambaya. "Kalle ni nan da gaske nake tambayar ki bada wasa ba, ki faɗa min iyakar gaskiya kina da wani abu da kike ɓoyewa wanda yake sakaki a damuwa?." Ajiyar zuciya Afeefah ta sauke wasu siraran hawaye suna zubo ma ta, wai ashe duk ɓoye damuwar ta da take yi saboda kar a gane, sai da wannan Kakar tasu ta an kara. Tana share hawaye wasu suna kuma biyo baya ta fara magana. "Tabbas haka ne, Amma ina cikin damuwa sosai, kuma ina da wasu tambayoyi da nakeso a amsa min sai dai ban san waye zan tun kara da tambayoyin nawa ba." Shiru tayi tana nazarin ta ci gaba da magana ko kuwa ta tsaya. Tsawon mintuna biyu sannan ta ci gaba da cewa. "Abu na farko shi ne, ina yawan yin mafarki a waɗannan kwanaki, mafarki ma munana waɗanda basu da daɗin faɗa. Abu na biyu, gaba na yana yawan faɗuwa kuma ban san dalilin hakan ba, ji nake kamar zan rasa wani abu wanda yake da matuƙar muhimmanci a gare ni. Abu na uku, jiya da muka tafi wani gida naga wata yarinya wacca muke matuƙar kamanni da ita sosai, kuma tanamin kama da Mahaifiyata da na sani a hoto, yarinyar an ce ita ce *SARAUNIYAR KYAU* ta nan Kano. Abu na huɗu, munyi wani Challenge dasu Lailah akan za'a haɗa lambobi a kira waya, duk wanda ya ɗauka zan faɗa sunan sa da address nasa, kuma zamu ƙulla abota dashi ko wanene. Toh anyi hakan komai ya wuce su Lailah suna takuramin akan saina kirasa. Sannan tunda nake kiran sa sau uku kawai ya taɓa ɗauka, sauran kiran sai dai ace switch off, ko kuma layin baya tafiya. Kuma ina yawan mafarki da muryarsa yana roƙona wai naso shi.🥺 Amma tsoro nakeji kar yaje da Aljani nake waya na rasa yadda zanyi da kaina ga gaba na da yake yawan faɗuwa na rashin dalili ki bani shawara kaka ta." Ƙarishe maganar Afeefah tayi cikin zubda hawaye har tana shiɗewa. Tsuru tsuru Amma da Mah'eesha dake gefe suka yi suna kallon Afeefah da tayi maganar, sannan Amma ta nisa tana mai girgiza kai tare faɗin "Ayya, yanzu Afeefah waɗannan tarin damuwowin suna damunki amma babu wanda kika faɗa ma, kina da hankali kuwa, yanzu idan wani abu ya faru dake fa, ya ya kike so Mahaifin ku da ya ɗauki son duniya ya ɗaura miki uhum, yanzu abu na farko da zaki fara shi ne Addu'a ki riƙe Addu'a ƙam da azkhar na safe da marece, kana ki dinga yawaita karatun Alkur'ani mai girma, sannan ki rage yawan zama ke ɗaya, duk da dai nasan ba haka kike ba, ki riƙe Addu'a sosai kamar yadda na faɗa miki domin ita addu'a takobin Muminine. Sannan da kika yi maganar Yarinyar, kika ce kuna kama, wannan abu mai sauƙi ne a wannan zamanin, domin ana samun irin haka, ga Misali nan ma da Doppelganger's ae kinga mutane ne ma banbanta masu matuƙar kama fiye ƴan biyu, koma waɗanda suka fito ciki ɗaya, saboda haka zai iya yiwuwa kamanni irin na doppelganger's ɗin kawai kuke yi ke da ita. Sai maganar saurayi da kika yi, wannan zai iya yiwuwa son sa ne kawai ya kamaki shiyasa.😯 Sai Abu na ƙarshe da kika ce kina yawaita faɗuwar gaba, da kuma mafarkai marasa kyau, duk sharrin zuciya ce da kuma shaiɗan ki riƙe Allah kawai, sannan ki dage da Addu'o'i wannan shi ne, nima kuma zan tayaki kuma nasa ka a dingayi harda saukan Alkur'ani domin Allah ya kawo sauƙi a lamarin."🙏 Shiru Afeefah tayi tana sauraren Kakar tasu Amma, har sai da taji takai aya, sannan ta sauke ajiyar zuciya. "Amma na gode sosai da nunatar wa kuma Insha Allah, zan kiyaye kuma na ci gaba da ƙara kaimi wurin yawaita Addu'o'i da kuma azkhar." "Masha Allah, ae haka ake so, sai dai gaskiya Afeefah da'ace zaki bi shawarata da kin haƙura da shiga Gasar SARAUNIYAR KYAU na ƙasa da za'ayi, saboda Inajin tsoro sosai, cuz of kyawunki ya yi yawa sosai, zaki iya samun maƙiya ta ko'ina wallahi." Mah'eesha ce tayi wannan maganar fuskarta ɗauke da damuwa, domin ita ma tuntuni taji faɗuwar gaba mara wanda hakan ke nufi da wani mummunar abu zai faru.👹 "hahahaha Mah'eesha ke nan. Ni na yarda da Allah, kuma na yarda da ƙaddara ko wata kala ce, saboda haka shiga gasar babj fashi, domin Zama SARAUNIYAR KYAU ta duniya burin mahaifina ne sannan kuma Mafarki na ne zama hakan."💃💃 "Saboda haka ki kwantar da hankali ki kawai Insha Allah babu abin da zai faru sai Alkhairi."🙏 *Ten Days To Go* *Kwanaki Goma Gaba* "Yauwa Saira wannan Chinese recipes ɗin muke buƙata yanzu yanzu domin kuwa Afeefah tasa mun kwaso yunwa wannan uban yawo Restaurant Restaurant da muka sha." Lailah ta faɗa hakan yayin da take miƙa wa Ma'aikaciyar Restaurant na mahaifin nasu book da jadawalin recipes na Restaurant ɗin suke ciki bayan ta kammala duba abin da suke buƙata ita dasu Afeefah ɗin sai kuma Deejarh da tayi musu rakiya. Ɗan murmushi Afeefah tayi tana gyara zamanta saman kujerar da take a kai, su uku ne ta ɓangaren su na musamman cikin Restaurant ɗin, ita da Lailah da Deejarh da suke zazzaune. Sun sha yawo sosai domin kuwa Restaurant biyar suka je suka duba yadda komai yake tafiya, bisa umarnin Mahaifin su Mister Mai Kyau, da yake ƙasar Jamus bai dawo ba, abin da yasa sai sune suka je Ma'aikacin da yake kula da ɓangarorin baya ƙasar shiyasa Afeefah kawai ta ce zatae shi ne Lailah da Deejarh suka ma ta rakiya. Zuwa halin yanzu sosai faɗuwar gaban da take fama dashi ya ragu sosai, dalilin dage wa da tayi wurin yawaita Addu'o'i da azkhar da kuma sallolin dare babu fashi, sannan wannan munanan mafarkan da take yi, ta rage yi sosai, Abin sai godiyar Allah. "Kai kai kai gaskiya abincin Chinese duniya, kinji irin daɗin da nakeji kuwa Lailah?." Deejarh ce take zubo wannan maganar yayin da take yagar wawukekan cinyar namar kaza da aka yi ma girki irin na Chinese da kayan haɗin su. Lumshe ido Lailah tayi ita ma dai dai lokacin da takai loman spaghetti irin na Chinese da irin tsinken su baki, sannan bayan ta lamushe, take faɗin. "Kedai Deejarh bari kawai ae ina faɗa miki abincin Chinese ya yi ba'a Magana koba haka ba Afeefah?." Tayi maganar tana mayar da kallon ta akan Afeefah da tayi shiru tanaso ta tabbata tarwa da kanta sautin da take ji yana fitowa daga ina ne kuma na menene?. Juyawa tayi sai tin hagun ta nan ta hangowa idanunta abin da take so tabbatarwa. Matashiyar mata ce wacce ba za ta haura 27years ba, da tsohon ciki tare da ita, tana zaune daga gefan su, nishi kawai matar take fitarwa na wahala da alamu haihuwa ce tazo ma ta.😓 Cike da azama Afeefah ta miƙe tsaye da sauri ta ƙari sa wurin ta, sannan ta kamo matar, riƙe ta tayi ƙam, tana ƙwalawa su Lailah kira hardama Saira. "Saira na ce akwai wani spare room ne wanda za'a iya haihuwa a ciki?. Na lura ta galaɓaita sosai bazai yiwu a kaita hospital a halin da take ciki yanzu ba." "Eh Miss akwai wani, bari na taimaka Miki a kaita ciki." Saira tayi maganar tana ƙari sawa sannan suka kama matar ita Afeefah suka shiga da ita cikin wani spare room dake can gefe cikin Restaurant ɗin. Shimfiɗar da ita suka yi saman katifa dake ɗakin sannan Saira ta fita, kana ta dawo ta bawa Afeefah wani fallen zani, karɓa Afeefah tayi ta rufe matar daga ƙasa, yayin da Deejarh da ta biyo su ciki, tayi tsuru tsuru da idanu, imani na ƙara shigarta na ganin irin nishin wahalar da matar take fitarwa kamar ranta zai fita, yayin da hannayenta duka suke ƙanƙame dana Lailah wacca ganin kalar ruwan da matar take fitarwa, yasa ta fara fita hayyacin ta, hankalin ta a tashe da kyar take iya numfashi, juyi kawai take ji kanta nayi cikin gajimare, yayin da ita kuma ta Afeefah take ta ƙoƙarin ganin ta taimaka wajen fitowar Yaro. "Yauwa Lailah ɗan zo ki taimaka min ta nan bazan iya ni kaɗai ba." Afeefah tayi maganar tana yiwa Lailah nuni da wurin da take. Cikin dauriwa Lailah ta miƙe tsaye domin ƙari sawa wurin Afeefah ɗin, sai dai tashin hankalin da take gani yasa kafin ta ƙari sa ta zube ƙasa sumammiya. Cike da takaici Afeefah tabita da kallo tsaban takaici kasa magana tayi. "Balarabiyar India ba kallon ta zaki tsaya yi ba, ki ƙoƙarta Yaron ya fito matar nan tana shan wahala sosai sosai, bari ni kuma na taimaka miki ta nan." Deejarh ce duk take wannan maganar a yayin da ta ƙari sa ta tsuguna kusa da matar sannan ta kamo hannun matar da hannunta ɗaya, yayin da ɗayan hannun take ɗan bubbuga cikin matar tana faɗin "One two push, one two push." Haka kawai take faɗa tana ƙara wa. Yayin da ita ma Afeefah ta ci gaba da ƙoƙartawa wurin ganin ta taimaka matar ta haihu. "Sorry miss, Breath deep, follow the rhythm, don't move around and just breathe, breath breath. Just breathe evenly. And just relax, you will be fine. Kawai ki daure ki ci gaba da numfashi kinji ki daure." Afeefah tayi maganar tana kallon matar tana ƙara faɗin tayi numfashi, sannan ta mayar da kallon ta kan Saira dake gefe cikin faɗin "We have to boil some water. We have to prepare." Da sauri Saira ta fita tana amsa ma ta sannan ta Afeefah ta kalla matar tana kuma faɗin "Breathe deeply, control your breathing. Don't worry, you'll be just fine Insha Allah." Dawowa Saira tayi da abubuwan da Afeefah ta buƙata sannan ita da Deejarh suka riƙe matar suna ƙara bata baki. Cikin ƙanƙanin lokaci Afeefah ta kammala bawa matar taimakon da ya kamata ta ciro Baby girl Saira ta taimaka ma ta wurin yanke cibi da sauran su, sannan suka ɗan gyara Room ɗin. After some minutes Ambulance tazo ta ɗauka mai jego da jariri domin kaisu asibiti a ƙara kula da lafiyar su. Shiga motar tayi tana ɗaga kiran Haleesat da ya shigo wayar ta, sannan ta zauna mazaunin driver, yayin da Deejarh da kuma Lailah wacca bata gama dawowa hayyacin ta ba, suke back seat zaune. "Hello Anty Haleesat what's going on?, Kin ƙari sa gidan Ummyn Farhana ɗin ne?." Afeefah tayi maganar tana kunna motar sannan suka fita daga Restaurant ɗin. Dama sun yi da Haleesat ne akan, idan ita Haleesat ɗin ta fita wurin reception na wata ƙawarta Maryam, zata wuce gidan Sunainah domin tambayar ta akan Heart Cheng, ko sunada alaƙa ne domin kuwa kamar tasu tayi yawa. Tunda suka dawo daga Kano dukkanin su babu wacca ta sama lokaci saboda school. Tafiya Haleesat ta ci gaba da yi daga ɓangaren ta, daidai lokacin da ta isa ƙofar palon gidan Sunainah ɗin take bawa Afeefah amsa da faɗin "Eh, yanzu na ƙari so gidan, zan ma shiga palon ne bari na mayar da kiran ta video call kawai yadda zakiji komai idan Ƴan uwa ne suɗin." "Okay Tohm babu damuwa, bari nima na mayar " Cewar Afeefah tana mayar da kiran ta video call. "Sannu da zuwa Zaynerba kece a gidan namu ko kuwa dai ba ita bace, kinsan fa ni ba ganeku nakeyi ba." Cewar tsohuwa Babah Dije tana bawa Haleesat ɗin hanya sannan ta shiga palon. "A'a Babah wannan Haleesat ce ƴar uwan Zaynerb ɗin, bawai ita ba, Allah ya sa dai Ummyn Farhana ɗin tana..." Shiru Haleesat tayi sakamakon ganin mutane zazzaune a palon da tayi. Kyawawan Ƴan Mata ne su biyu, sai kuma wasu jigaggun kyawawan Samari su biyu zazzaune saman kujerun alfarma dake palon, Ƴan matan fira suke yi da Sunainah cikin harshen Ingilishi domin kuwa da ganin irin shigar jikin su da alama idan ba Ingilishin ba basa jin wani Yaren. "Ah ah wata sabon gani Haleesat kece a gidan nawa yau lale lale, barkanki da zuwa " Sunainah ce take wannan maganar tana kallon Haleesat da ta zauna a 1sieter, yayin da idanunta suke kan waɗannan ƴan matan, tsaban ruɗewan da tayi na ganin kyawawan ƴan matan da samarin da suke zazzaune a palon da tayi, kasa magana tayi, gani take waɗannan ƴan matan sunfi mata kama ma da Heart Cheng ɗin bisa Sunainah. "Barka Ummyn Farhana yakike ya ƙarfin jikin, ya unborn ɗin mu, fatan yana ko tana lafiya?." Haleesat tayi wa Sunainah maganar tana saita wayarta saitin waɗannan samarin. Aikuwa Hakan ya yi daidai da ɗagowar da ya yi kyawawan idanun sa take bada ɓata lokaci ba suka shiga cikin na Afeefah dake tuƙi tana saurare da kallon abin da ke faruwa a palon. Wani wawan burki taja wanda sanadin hakan har sai da tayi gaba sannan tayo bayan kanta ya bugu da kujera, wayar kuma ta faɗa ƙasa wurin ƙafafuwan ta. Lailah kuwa da take back seat ita da Deejarh har tana haɓo sakamakon bugewar da hancinta ya yi ta bugi kujerar dake gabanta. "Ouch Afeefah kashemun kike son yi hala?, Wayyo hancina." Lailah tayi maganar cike da jin raɗaɗi a hancin nata. Durƙusawa tayi ta ɗauki wayar sannan tayi saurin rejected call ɗin gaba ɗaya zuciyar ta na mugun bugu, na ganin kyawawar fuskar sa da tayi, toh ya ya ma za'ayi ta manta da wannan fuskar cikin sauri haka. "Ah ah ban gane ba Official da kake cewa zaku tafi, yanzu shikenan daga nan sai Bauchi ko kuwa ƙasar zaku bari?. Ni da aka cemin su Taahira ɗin kwana zasumin, ko fa five hours bakuyi ba anan?." Sunainah ta masa tambayar tana miƙe tsaye da cikin ta da ya shiga wata na bakwai ke nan. "No, daga nan kai tsaye airport zamu wuce zuwa Sweezland, kar ki damu da ga kin haihu. Ni da kaina zan kawo Miki su Taahira ɗin tun da naga kinfi son su akai na." Ya bata amsar a yayin da gaba ɗaya suka yi waje, harda ita bayan ta ɗan yima Haleesat dake zaune Magana, sannan ta kuma cewa dashi. "A'a Official bawai haka bane gwara kai, baka sati baka shigo nan ƙasar ba sakamakon yanayin aikin ka, su kuwa wannan ne fa karo na farko da suka shigo ƙasar. Ni Wallahi da'ace nasan acan Bauchi suka zaune tsawon three weeks da zuwan su, da da kaina zan je na ɗauko su mu dawo nan, tunda na lura sunfi son Ƴan Bauchi akai na, banda haka mai zai sa suna Najeriya tsawon three weeks ban sani ba, sai yau." "Oh Aunty Sunainah kana da gaza juro fa, yanzu ba gashi mun taho ba." Ɗaya cikin ƴan matan tayi maganar da gurɓatacciyar Hausanta, wai nan ma a haka ita ce ta iya yaren Hausa sama da sauran." Taɓe baki Sunainah tayi tana faɗin "Ki jiki Shaakira da wata Hausar ki a wurin, da'ace nan kuka zo tun farko, da yanzu Hausa ta daɗa zauna a bakinki sama da hakan." "Okay, don't worry Insha Allah next time before you go labor, we will reaturning back Insha Allah." Ɗayar budurwar ita ma ta faɗa cikin harshen Ingilishi, dan kuwa tasan ta ce zata gwadayin Hausa dariya kawai za'a ma ta, shiyasa ta rufawa kanta asiri tayi Yaren ta Ingilishi. "Tohm Ƴan ƙannina Taahira da Shaakira, Official da kuma wannan Bardia ɗin nan wanda ko sanin abin da muke tattaunawa akai bai yi ba, na rasa mai kakeyi da waya haka, tun shigowar ku fa." Sai da Official ya zauna a motar sannan ya bata amsa da faɗin "Rabu da wannan Ɗan soyayyar domin kuwa ba jinki yake yi ba, hankalin sa da ruhinsa yana gare ta ta cikin wayar." Ƙayataccen Murmushi Sunainah tayi cike da jindaɗi take faɗin "Masha Allah kace dai Bardia mun kusa shan Biki, amma Wacece haka mai Sa'a?." "Karki damu zan baki labari idan na dawo next, Bye." Amsa masa Sunainah da faɗin "Okay Tohm, Bye Allah ya tsare hanya Bardia a gaishe da ƙanwar tawa." Murmushi mai kyau Bardia ya yi a karo na farko da ya tsoma bakin sa cikin maganar nasu yace. "Okay, Sweet Anty, Bye." Sallama suka yi cike da kewar juna, har motocin su guda huɗu suka bar gidan dama tare suke da rakiyar guard's. Komawa cikin palon wurin Haleesat, Sunainah tajin kewar su tun kafin a je ko'ina duk da cewa ba wani shaƙuwa bace tsakanin ta dasu, da suke yaran Uncle Mohammed Yaqub Muhammad. Afeefah Sai da tabbatar ta dawo hayyacinta sannan ta tashi motar suka nufa gida. Koda ƙari sawar su Gidan ba tare da ɓata lokaci ba, dukkanin su ko wacce tayi Bedroom ɗin ta cike da gajiya, barin ma dai Lailah wacca har lokacin bata cikin nutsuwar ta. Afeefah tana shiga cikin haɗaɗɗen Bedroom ɗin ta, wanka ta fara yi, ta gurje ko'ina da ina na jikin ta, dan kuwa ita kanta tasan tana ƙarnin jini. Da fitowarta ta hango wayar ta tana ruri alamar kiranta ake yi, ƙari sawa tayi sannan ta ɗaga kiran cikin sauri ganin Daddyn su ne M.M.K. Haleesat Duk yadda taso Sunainah ta faɗa ma ta ko shin su na da wata alaƙa ne da Heart Cheng, bata sa sama amsar da take ba. Domin kuwa ko da ta nunawa Sunainah ɗin Hotunan Heart ɗin. Girgiza kai kawai Sunainah tayi lokacin sannan ta ce. "Bata san ta ba, kuma bata taɓa ganin ta ba, sai yanzu." Abin ba ƙaramin ɗaurewa Haleesat kai ya yi ba, ƙiri ƙiri ga kamannin su tana gani amma Sunainah ta ce bata san Heart ba. Ba don ta yarda da maganar Sunainah ba, ta kamo hanyar gida bayan sun ɗan taɓa fira da Sunainah ɗin. Sosai Afeefah suka sha Fira da mahaifin nata, dan sai da suka kusa one hour suna wayar, sannan suka yi sallama dashi, yana saka ma ta albarka cike da alfahari da ita. Dan kuwa tuni labarin taimakawa mata mai juna biyu da tayi a Restaurant ya zagaye ƙasar ciki da wajen ta. Ko minti goma basu yi da gama waya da Daddyn nasu ba, sai ga kiran Zaynerb ya shigo wayar, da sauri tayi picking, nan ma dai duk magana ɗaya ce, a kan karɓar haihuwar matar da tayi ne, sai da suka kwashe fi ye da twenty minute's suna waya da Zaynerb, sannan suka yi Sallama Zaynerb tana faɗa wa Afeefah ɗin gobe ne zata dawo nan Abujan daga Kano ɗin, sosai Afeefah tayi farin ciki da murna, dan kuwa tayi kewar Yayar nata Zaynerb sosai. Koda gama wayarsu da Zaynerb, kiraye kiraye ne kawai suka ci gaba da shigowa wayar nata. Duka daga na masu fatan Alkhairi a gare ta, sai masu yaba ma ta bisa taimaka wa mai juna biyu da tayi a matsayin ta na cikakkiyar SARAUNIYAR KYAU, sai kuma ƙawayenta na school a masu kiran nata, har da Ƴan uwanta na nesa da kusa, har ma da Fan's ɗin ta. Daga ƙarshe da ta gaji palo ta fito, nan ta sama su Lailah da Fadeelah zaune harma da Haleesat wacca ba ta daɗe da dawowa gidan ba. Yayin da Deejarh take Bedroom ɗin Zaynerb tana gyara ma ta. Deejarh Sosai ta gyara Bedroom ɗin na Zaynerb tsaf tsaf komai ya yi clear. Tana shirin fita daga Bedroom ɗin daga can gefan bed side drawer ta hango wani ɗan akwati da ya tafi da tunanin ta saboda shaining da yake yi gunin ban sha'awa. Ƙari sawa wurin tayi batare da ɓata lokaci ba, ta janyo akwatin tayo kusa da ita dashi. Hannu takai domin taji ko'a buɗe yake, ga mamakin ta a buɗe akwatin yake. "Oh ni Dije ta ƙauye, ko menene anan?. Wata ƙila ma Anty Zaynerb ɗin mantawa tayi tabar shi a buɗe." Deejarh tayi maganar tana kuma kai hannu ta ciro wani ɗan jotter a ciki. An kananan naɗe saman shi da igiyoyi masu kyau ƙanana, hannu tasa ta cire igiyoyin da aka kanannan naɗe jotter ɗin dasu. Take Manyan rubutun da aka yi da manyan baƙi saman jotter ɗin suka bayyana ɓaro ɓaro anyi rubutun ne da jan Biro. "MY REAL LOVE STORY." Haka Deejarh ta furta abin da aka rubuta. Buɗe shafi na farko tayi nan ma anyi rubutu ne, in stylish da red Biro. "Don't you read this book because it's secret." Murmushi tayi bayan ta karanta haka tana faɗin "Ni kuwa wallahi tunda aka rubuta haka saina karanta naga abin da za'a iya" Tayi maganar tana buɗe next page. "My Sadness Love Story😫." Shiru Deejarh tayi bayan ta karanta hakan, tunani take ae idan ba za ta manta ba, akwai wata rana suna zauna a Palo, Lailah take cewa SOYAYYA ce silar rushewar farin ciki a rayuwar Yayarsu Zaynerb. Tuna wannan abu da Deejarh tayi ya saka cikin sauri ta miƙe tsaye har tana kusan tuntuɓe da ƙofa wurin fita daga Bedroom ɗin. Da gudu ta ƙari sa palon, sannan ta tsaya tsaye a tsakiya tana sauke haki faɗi take cikin nuna musu jotter dake hannunta "Balarabiyar India, Anty Lailah, har dake Anty Haleesat wannan shi ne littafin da labarin SOYAYYAR Anty Zaynerb yake ciki, a Bedroom ɗin ta na gani da ina gyarawa." Za'a iya cewa tsakanin Lailah da Haleesat ba'a san wacece ta riga tashi tsaye ba, ta ƙari sa wurin Deejarh ta karɓa jotter ɗin. Sai dai kawai ganin jotter ɗin suka yi gaba ɗaya hannun Lailah. Komawa Haleesat tayi ta zauna taso ace ita ce ta fara sanin ya ya labarin soyayyar Zaynerb yake, wani irin ƙalu bale ta fuskan ta a ciki da har takai ga dawowa Nigeria, sannan kuma da halin shaya shaye?. "Tunda haka ne ki karanta mana a fili kawai musan abin da yake ciki." Afeefah tayi maganar tana tashi daga inda take ta koma kusa da Lailah ɗin ta zauna a saman tattausar carpet na palon, dan kuwa ita ma a mugun matse take da jin labarin soyayyar Zaynerb ɗin. Buɗe shafi na biyu na littafin Lailah tayi bayan ta karanta abin da aka rubuta a bango na jotter ɗin da kuma shafi na farko. Karantawa ta fara a fili kamar haka.... Mgnr Payment fa *The Phone Number* *08081129487* *The Acct Number* *8081129487* *The Bank Name* *Palmpay Bank* *The Acct Name* *Khadeejarth Sabi'u Yahyah* ~Karku bari a baku labari fa🤩~ ~*SARAUNIYAR KYAU*~🔥🔥Takun Tsakiya_-_ *Iya kuɗin ki iya shagalin ki Hajiya* *🔥 SARAUNIYAR KYAU 🔥* _-_👑ƚαƙυɳ ƚʂαƙιყα👑_-_ ɯ&ʂ_-_📖🖋️📲 💓 The Nainarh Kd 💓 _-_ҽρ.6_10 *Last of free page's idan kinsan bakiyi payment ba, ki gaggauta yi domin ki ci gaba da samu Update's da zafi zafi akan lokaci 💃💃💃💃* 💞💞ƚԋҽ ҽxƚɾασԃιɳαɾყ ρҽɾϝҽƈƚ ʅσʋҽ ʂƚσɾყ Ⴆιƚɯҽҽɳ ρҽɾϝҽƈƚҽԃ ʅσʋҽɾʂ💞💞 *Zaynerb Mai Kyau*: "Shi ne sunan a kafi sani na dashi, sannan ake kira na Especially ma ƙawayena da ƴan school namu. Yammacin wata Ranar Lahadi ne, nayi sallama da Ahalina da suka rakoni har filin jirgi na ƙasar Jamus. Cike da farin ciki, wani ɓangaren kuma da tunanin kewar mahaifina da kuma ƙanwata Afeefah nake a Ranar, harna shiga jirgi na saita zama na. Karon shi ne farkon shigata public jet. Sam ban wani iya ɗaura belt na jirgi ba, domin kuwa ko da zamuyi wata tafiya, ko zuwa wani wuri da Ahalina, tofa sai dai Daddyn mu ko kuma Afeefah, tofa ɗaya cikin su ne yake ɗauramin, suyi ta min dariya. Ni kuwa babu ruwa na. Yanzu haka ma ƙoƙarin da nakeyi ke nan, na ganin na ɗaura belt ɗin dai dai, sai dai kasawa nayi, don ban sakawa raina dama zan iya ba. Tsaki kawai nake faman ja, ganin ƙiri ƙiri na kasa ɗaura belt na jirgi. A ba za ta naga fararen hannayen sa biyu ya saƙalo ɗaya ta ƙugu na, sannan ya dai dai, cikin ƙanƙanin lokaci ya gama ɗauramin belt ɗin. Galala nayi da baki ina kallon sa, yayin da idanuna suke lumshewa a hankali, ina kuma buɗe su saman kyakkyawar fuskar sa mai cike da kwarjini da haiba, sam na kasa masa magana, sai idanu dana zuba masa ina kallo. "Hello Miss do you hearing, move on this side." Ƙara lumshe ido nayi jin daddaɗar muryarsa tana ratsa dukkanin magudanar jini da jijiyoyin kaina kai tsaye izuwa ƙwaƙwalwa ta. Ban matsa gefe kamar yadda ya so ba sai da ya kuma magana, sannan na dawo hayyacina. Da sauri na matsa gefe ina zare ido, sam naƙi bari mu haɗa koda idanu dashi. Har jirgin mu ya tashi sararin samaniya, yana daga zaune gefena. Tabbas a jikina Inajin ana kallo na, sai dai da na juya sai naga bani yake kallo ba, idanun sa suna kan littafin dake hannun sa. Haka har tafiyar mu tayi nisa dan kuwa mun kusa kai mintuna talatin da tashi a lissafina. Wani irin jijjiga jirgin da muke ciki ya yi sannan wani irin ƙara ya ziyarci dukkan wani fil_adam dake cikin wannan jirgin, ga wani irin jijjiga na tashin hankali da jirgin yake damu yana gefe da gefe tamkar zamuyi ƙasa. A mugun firgice ina zare fararen idanuna nake kwalla ihun neman taimako kamar yadda sauran mutanen dake cikin jirgin suke yi. Sam ban san lokaci ba, sai ganina nayi ɗare ɗare saman jikin mutumin dake gefena, na ƙanƙameshi ƙam ina fitar da ihun wahala da tsoro. Idanuna a lumshe wasu hawaye suna biyo wa, ganin cewa gaba ɗaya mutuwa zamuyi, gani da burika kala kala a duniya ban gama cika su ba, gashi zan mutu sanadiyar hatsarin jirgin sama, dan kuwa a wannan taƙin babu wanda ya yi tunanin zamu tsira. Cike da firgici da tashin hankali nake faɗin "Wayyo! Wayyo! Wayyo ni Zaynerb Ɗiyar Mai Kyau jikar ƴar mutan sudan... Shikenan kwana na ya ƙare zan mutu, shikenan, wayyo ni Afeefah Daddy Yaya Maleek zan mutu na barku, shikenan wayyo." Ban ma san iya adadin abin da nake faɗa ba, kawai sambatu nake yi cike da tsananin tsoro, na kasa addu'a sai shirme. Sannan ƙam na riƙe shi ina wannan zare ido da sambatu. "Hey, Miss relax mana just relax, baki iya Addu'a bane sai ihu da sambatu ki nutsu mana." Haka kawai yake faɗi yana kamoni a ƙoƙarin sa na ganin na kwantar da hankalina. Ina jinsa ban kulashi ba, sai dai ina mamaki ganin babu tashin hankali ko tsoro tare da shi. *After Twenty Four Hours* Lumshe kyawawan idanuna nayi ina ƙare wa haɗaɗɗen filin sauka da hawan jirgin sama dame ƙasar Amsterdam nayi. Awanni ashirin da wani abu baya, banyi tunanin zan rayu ba. Sai dai cikin ikon Allah, jirgin aka samu ya tsaya da jijjgan da yake yi, sannan aka saukemu a wata ƙaramar ƙasa dake tsakanin Jamus da Amsterdam. A wurin muka kwana domin kuwa dare ya yi sai washe gari wani jirgin ya kwashe mu ya iso damu Amsterdam ɗin. Wai ashe dalilin hatsarin da muka kusa samu da jirgin mu shi ne, shashashan Driver na jirgin bai duba lafiyar jirgin yadda ya kamata ba, ya tashi damu ya kusa jama na mu mutu. Aikuwa yasha tsinuwa da zaki kala kala daga wurina dan kuwa bayan samun labarin da muka yi, ya sama rabon zagi da tsinuwa wurina, bama ni kaɗai ba harda sauran jama'an jirgin. Sai dai nasha mamaki kuma na shiga tunani, na rashin ganin wannan haɗaɗɗen saurayi da muka haɗu da shi a jirgin farko, da banyi ba wannan karon har muka sauka yanzu. "Wata ƙila ma ya canza jirgi ne tun jiyan." Haka kawai zuciya ta bani. Ci gaba da tafiya nayi ina gurgura ɗan keken da wasu abubuwa nawa suke ciki, ina kuma jan akwati na. A ba za ta naji saukar wasu kyawawan furanni masu fidda ƙamshi na musamman da kuma wasu ƙa na nan balloon's saman kaina. Washe baki nayi ina tarosu da hannayena. Ban gama shan mamaki ba gaba ɗaya mutanen dake zagaye dani a wurin suka fara tafi raf raf suna dariya. Yayin da daga gefe kuma wasu samari da ƴan matan turawa suka fara sakin kiɗa da wasu ababen ƙila dake hannayen ko wannen su. Ban gama shan wannan mamaki ba, wani abin mamakin ya kuma faruwa sakamakon Juyowar da ya yi yana fuskan tana hannayen sa riƙe da flower's ya tsuguna ƙasa kusa dani fuskar sa akaina bakinsa yana furta kalmar. "I Love You...Do You Winning To Marry Me?..." Hakan yake furta wa A gareni.... Yayin da mutanen wurin cikin tafi suke faɗin. "Say something for him, please say you love him please please." Haka kawai suke faɗa suna ƙara wa, yayin da shi kuma gwanin idanunsa suke kaina yana jiran amsa na, kuma bai fasa daga miƙo min furannin da yake yi ba. Tsaban mamaki da al'ajabi kasa magana nayi, na zama tamkar Statue ina kallon su gaba ɗaya mutanen dake wurin, sannan na mayar da idanuna akan sa. Tabbas Guy ɗin Jirgi ne, toh menene yake nufi da wannan bazatar nasa. Abin tamkar wani shirin Film, da za'a ga saurayi ya yi surprising masoyiyar sa irin wannan. Dariya nayi dan kuwa wannan abin dariya ne a wurina, banda haka kawai daga ganin sarkin fawa a kasuwa sai Miya tayi zaƙi?.....🤔 Kallmashe ƙafa ɗaya nayi saman ɗaya ina gyara tsayuwata tare da gyara goyon da nayiwa backpack ɗi ta, na wani juya idanu fuska ta ɗaure da murmushin rainin wayo nake faɗin "Kai! Lallai ma kai ɗin nan, toh gaya maka aka yi niɗin wata ƴar Baba nace da zaka shirya wannan ƙaramin wasan domin jan hankalina iyye, bani amsa ta." Nayi maganar ina kallon sa sannan na ci gaba da cewa "Toh wannan salon bai burge Zaynerb Mai Kyau ba a canza wani." Na faɗa hakan ne dan ina da tabbacin cewa baisan sunana ba, toh na faɗa ne saboda ya riƙe aha.🤣😁 *The Next Day* Zaune nake a palon Gidan Madam Joy wacca na sauka Gidan ta, domin bani da burin zama a ɗakunan makarantar da zan fara, Shiyasa Daddy ya nema min Gidan wannan Baturiyar. Dariya kawai nakeyi na tuna abin da ya faru jiya a Airport. A lokacin koda na faɗa abin da na faɗa jan Akwati na nayi na nufa motar drivern Madam Joy da yazo ɗauka na. "Ke Kyakkyawa ta ki sani muddun muka kuma haɗuwa a gobe, tofa tabbas kina so da ƙauna na." Ya yi maganar cike da Qwarin gwiwa cikin Murmushi yana bubbuga faffaɗan ƙirjin sa alamar tabbatarwa. A lokacin Murmushi mai tsada nayi ina basa amsa da faɗin "Ina maka fatan rashin sa'a." Dariya na kuma yi tuna hakan da nayi, in banda abin sa ma, ae ba yau zan fara zuwa school ba, sai next week. Ina cikin haka Lovely Ƴa ɗaya tilo wurin Madam Joy ta fito zata tafi company na Architecture's don zaɓar kalar gidan da zata zauna ita da Saurayin ta bayan sun yi Aure, don Auren nasu ya kusa. A lokacin naji ina son ganin yadda birnin Amsterdam yake dan ban taɓa zuwa ba. Saboda haka magana nayiwa Lovely akan ta jira na shirya zan karata. Bada ɓata lokaci ba, na shirya cikin Gown doguwa har ƙasa ta Shadda galilan milk color sannan ba tare da na ɗaura kallabi ba na yafa Veil ɗina shima brown kalar aikin dake jikin Gown ɗin sannan na saka flat shoe. Na fito Palo wurin Lovely dake jirana muka fita zuwa mota, sannan muka ɗauka hanyar company. A motar muna zaune na kalla Lovely ina faɗin. "Ni kuwa Lovely menene sunan mamallakin company ɗin da zamuje ne, da kuma sunan ɗan sa, sannan ɗan nasa shekarun sa nawa?." Na jero ma ta tambayar don ina da dalili. Bani amsa tayi cikin turanci da faɗin "Sunan sa Mr.John ɗan sa kuma Andrew yana karatun injiniyanci ɓangaren gine-gine." "Okay..." Na furta bayan ta faɗa hakan. Da isar mu katafaren company ɗin muka fito daga motar mu, sannan muka shiga ciki, Elevator muka shiga domin ƙara sawa office na MD. Na company ɗin. *After Some Minutes* Zare fararen idanuna kawai nakeyi ina haɗiye yawu, tunani nake anya kuwa wannan mutumi mutum ne kuwa?.🙄 Fisabilillah nan ma sai da yasan yadda ya yi ya biyo ni?.😚 Hannu nakai zan ɗauka cup of coffee da aka kawo mana ni da Lovely. Cikin rashin sa'a kuwa muka haɗa idanu dashi. Ƙayataccen Murmushi ya yi min yana mai kashemin ido ɗaya. Da sauri na kawar da kaina gefe, ban kuma yin gigin kallon sa ba, har suka kammala maganar da suke yi. Kallon na Lovely tayi tana faɗin nazo mu koma gida sun kammala. "Am nace ba, ki ɗan bani aron ta five minutes kawai?." Ya yi maganar yana kallon Lovely ɗin. Girgiza kai tayi tana faɗin "Okay.." Sannan ta fita, da kallo na bita, Lallai ma Bature babu kai. Yanzu daga cewa ta bashi arona ta amsa lallai. "Toh ya ya shin yanzu zamu iya magana da kyakkyawata kuwa, nasan dai zuwa yanzu ta kware min?." Murmushi nayi ina juya idanu sannan na juya da kujerar da nake kai ina fuskan tar sa, nake tambayar sa. "Garin ya ya, me yasa?." Murmushi ya yi sannan ya gyara tsayuwar sa yana bani amsa da faɗin "Duka saboda ke, jiya bayan rabuwar mu a Airport ban zauna ba, har sai da nasan gidan da kika sauka, nasan matar gidan da Yarinyar ta, na kuma san dalilin da zai sa Ni Da Ke mu sake haɗu wa yau, gashi kuma mun haɗun."🥰 Ya yi maganar yana sakin kyakkyawar Smile 😎 Taɓe baki nayi sannan na miƙe na ƙari sa kusa da shi Sannan na ja tunga na tsaya. Hannu nakai na ɗan kamo Tie na shirt ɗin jikin sa, ina faɗin "Humm, babu laifi, You will try, sai dai fa karkayi tunanin zuciyar Zaynerb nan kusa take, um'um kaɗan hakan ya burgeni fa, ka ƙara zage damtse wata ƙila nayi tunani akan ka, Malam..." Shiru nayi dan ban san sunan sa ba, ɗaukar handbag ɗi ta nayi, sannan na nufa ƙofa, na kama handle na ƙofar zan fita najiyo daddaɗar muryarsa yana faɗin "Okay, babu damuwa, sannan naji daɗi da hakan ya burgeki, zan ƙara zage damtse kyakkyawata kafin nan, Aasief nake karki manta da wannan." Murmushi nayi ba tare da na juya ba nake faɗin "Ina maka fatan Alkhairi Malam Aasief, zan zuba idanu domin ganin naka salon a soyayya."💓 *Ten Days To Go* Ƙara kallon agogon Apple dake hannuna nayi, yau tsawon kwanaki shida ke nan da fara zuwa ta University. Kuma tun daga wancan Ranar bamu sake haɗu wa da shi ba. Na ɗan shiga damuwa kaɗan, don ina tunanin wata ƙila, yaji bazai iya bane, ya kama kansa. Tsaye nake ina jiran taxi domin Drivern Madam Joy da yake zuwa ɗaukata bai sama damar zuwa yau ba, sakamakon matar sa dake naƙuda, ita kuma Lovely bata state ɗin ma gaba ɗaya, yayin da Madam Joy aiki ya yi ma ta yawa a office saboda haka ba za ta sama damar zuwa ɗaukata ba. Ba tare da tunanin komai ba, na shiga cikin taxi ɗin da tayi parking a gaba na, ina faɗin Address da za'a kaini tare da tambayar kuɗin "Okay...Madam babu damuwa ae ba saikin biya komai ba, kyauta zan kai ki." Da sauri na dakata daga ɗauko kuɗi da nakeyi a handbag ɗi na, cikin firgici na juya ina kallon sa. Ba kaɗan ba naji daɗin ganin sa, sai dai ban nuna masa ba, saima kyaɓe fuska da nayi ina faɗin "Har yanzu Ban san komai akan ka ba, gashi kanata bibiyata." Nayi maganar ina kallon gefen titi dan kuwa so nake nasan wani abu a kansa, shin kuwa shiɗin Balarabe ne ko kuma Bature?. "Firstly Sunana Mohammed Aasief Yaro wajen Hasheem Mai Waje!." Ni da Ahalina gaba ɗaya muna zaune ne a ƙasar America. Ina karatun Injiniyanci ɓangaren gine-gine sannan ina matakin ƙarshe. Hakan ya isa ko kina son sanin wani abun?." Ya yi min maganar yana kallona ta madubin motar. Fuska ɗauke da murmushin dana kasa ɓoyewa nake cewa "A'a hakan ma ya isa." "Uhum bani labari mana?." "Labari kuma akan ne?." Na tambaye shi "Akan ki mana da kuma Ahalin ki." Ya bani amsa. Shiru nayi dan ban san ta yadda zan fara basa labari akan kaina ba wallahi. Wawan burki yaja da ƙarfi wanda sanadiyyar hakan sai da nayi gaba na bugu da kujera sannan na dawo baya kaina ya bugu. Cikin zafin rai ya ɓalle murfin motar ya fita, ƙari sawa wurin Baturen da motar sa ta bugi namu muka kusa hatsari ya yi. Cikin zafin rai da ɓacin sa ya shiga bawa wannan Baturen mari yana ƙara wa. Faɗi yake. "Baka da hankali ko wato kasha giya kazo kana tuki salon kaja mana hatsari." Bugun sa yake yana ƙara wa haɗe da Ball da shi, a titin. Cikin sauri na buɗe motar na fito sannan na ƙari sa wurin ina jansa baya cikin basa haƙuri ganin yadda yake dukan Baturen babu ji babu gani, kuma nasan duka akaina ne, sakamakon buguwar da nayi ne ransa ya ɓaci, jansa baya nake ina basa haƙuri cikin faɗin "Ya isa Aasief ya isa haka baka ganin jini kake fitar masa ya isa mana." Bai kulani ba sai ma ƙara kaimi wurin ball da Baturen da ya yi. *Tashin Sence* Zuwa lokacin fa na fara tsorata da irin zuciyar da yake da shi. Baya nayi ina kallon ikon Allah cikin rashin abin yi. *A Taƙaice* Bamu muka bar titin nan ba har sai da police suka zo suka ɗauka report. Da kyar suka barmu muka tafi wai dan ma an gwada Baturen ne an tabbatar giya yasha kuma yake tuƙi. Fushi nayi sosai da abin da ya faru domin kuwa ko na gansa bana masa magana domin tsoron irin zuciyar sa nake. Tsawon Sati guda muna hakan Kullum sai mun haɗu, takai har makarantar mu ya fara zuwa domin na kulasa, amma naƙi. Daga ƙarshe da takurar sa ya isheni haƙura nayi. Muka ci gaba da mu'amula kullum kafin ya tafi nasa makarantar sai ya fara zuwa ya kaini nawa sannan ya wuce. Cikin Wata ɗaya da zuwa ta ƙasar Amsterdam da kuma haɗuwa dashi sosai muka shaƙu da juna abin kamar almara, sai dai muna yawan samun matsala dashi akan zafin zuciyarsa, amma daga baya komai tsananin faɗan da muka yi muna dawowa mu shirya abin mu. Sai dai har yanzu fama yake dani akan na furta masa ina san sa amma naƙi. Yauma zaune nake saman table a cikin wani wurin shaƙatawa da kuma buga Troupe.(Wasan Tebur). Kallon nake cikin Murmushi ina gyara riƙon da nayiwa Jakata a kafaɗa nake faɗa masa. "Ka iya sarrafa fushin ka Aasief, hakan ba daidai bane ka dinga ɗaukar fushi akan ƙana nun Abu." Nayi maganar ina juya fuska ta gefe tuno abin da ya faru yau da zamu shigo wurin, duka sosai yayima wani matashi akan yayimin kallon bariki. "Nima banason wani abu ae." Ya bani amsa yana daka tawa da abin da yake yi. Da mamaki na saki baki ina kallon sa. Shi kuma ya ci gaba cewa. "Abin da kike yi ne, har yau da baki ce ki naso ba! Ah sam bana son hakan." Murmushi nayi ina miƙe wa tsaye cikin gyara Jakata. "Saurayi idan ya nuna ƙaunar sa a wurin Budurwa, ta ce saita tsaya tayi tunani kafin ta yanke hukunci, hakan yana nufin tuni ta amince, sai dai mu ce mun amince ne, sam bamayi." "Me yasa?.". Ya tambaya cikin sauri. Murmushi na kuma yi. "Irin daɗin da kuke ji idan mace ta mutu akan ku, toh muma irin daɗin muke ji, idan Namiji ya dinga bibiyar mu. Humm. Kasan irin jin kan da muke yi kuwa yayin da muka ga Namiji yana bibiyar mu, mu haka mata muke. Ka fahimta?..." "Toh ke nan tun daɗe wa kika amince dani?." Ya tambaya. "Kana tan tama ne?." Na basa ina juyawa zan wuce. Fuskata ɗauke murmushi na musamman cike da jindaɗi. *Bayan Wani Lokaci.* Shaƙuwa ce ta musamman mai zaman kanta ta ƙara shiga tsakanin na da Aasief Mai Waje, sai dai har lokacin bance da shi ina son sa ba, haka kuma yake haƙuri dani sosai, domin abin da nakeso yake yi komai wahalar sa kuwa. Cikin Abokan karatu na da ma ƴan makarantar mu sosai suka saba dashi saboda yawan zuwa makarantar wurina da yake yi. Yau ma kamar kullum muna zaune ni da shi saman Benchi doguwa muna fira a cikin makarantar mu wurin hutawa. Miƙe wa tsaye nayi cikin tsananin tashin hankali da tsoro, hango Tantiri a makarantar mu da nayi suna tahowa wurin da muke shi da abokan sa wajen su bakwai dukkanin su mabanbantan ƙasashe suke. Leo Tantiri ne na ƙin ƙara wa a makarantar mu ya tara Laifuka akan sa babu adadi cikin makarantar, kuma babu abin da ake iya masa sakamakon kuɗaɗen da iyayen sa suke dashi. Asalin sa ɗan ƙasar ne, cikin Tantiran Abokan sa akwai Rahul ɗan ƙasar India, akwai Indivisi ɗan Poland da dai sauransu, suna tsula tsiyar su yadda suke so, babu mai taka musu burki. A haukar sa Leo ɗin wai sona yake tun ganin da yayimin na farko a makarantar yake bibiyata, ban taɓa kulasa ba, kuma ban faɗa wa Aasief ba sanin irin zuciyar sa. Kuma duk zuwa makarantar da Aasief yake basu taɓa haɗuwa da Leo ɗin ba. Gashi yau komai ya rincaɓe Leo ya ganni da Aasief ban san menene zai biyo gaba ba.😓 Ƙari sowa wurin sukayi ja-ja-yen idanun sa akaina, nima nawa akansa, yayin da na Aasief idanun sa suke akan mu duka cike da mamaki. Karɓar wani abu kamar gyalle kamar igiya siriri ya yi daga hannun Rahul, sannan ya miƙo min yana faɗin. "Karɓa wannan." Karɓa nayi da mamakin menene abin. "Kin san wacce rana ce gobe?." ya tambaya A'a Na basa amsa, ya ci gaba da cewa "Ranar shagalin raki ce, bisa al'adar Indiyawan nan makarantar kowa a yau yake shagalin sa Saboda haka karɓi wannan ki ɗaurawa mai." "A'a." Na basa amsa. "Ki ɗaura mai." Ya kuma faɗa "A'a." Nima na kuma faɗa in seriously Tsawa ya buga min da faɗin "Ke ba haka nace ki ɗaura masa ba?." Je far da abin da ya kira da raki ɗin nayi ƙasa ina basa amsa da faɗi cikin tsawa. "Nima ba nace a'a ba." Tsayawa kowa daga ɗaliban makarantar ya yi da Abin da yake yi suka mimmiƙe tsaye suna kallon mu. Kallon kallo muke tsakanin Ni da Leo sannan na fara magana cikin ɗa ga murya. "Zan iya kiran ka da Yaya." Na nuna sa, sannan na ci gaba. "Na kira wannan, na kuma kira wancan, zan iya kiran ko wani Namiji da Yaya a makarantar nan, amma banda shi, saboda Ina Son Sa..." Juyawa nayi ina kallon Aasief dake sakin ƙayataccen Murmushi na jindaɗi sannan ta ce ina kallon cikin idanun sa "Aasief Ina Son Ka, da duka zuciya kuma zan Aure ka." Juyawa nayi na kama hanya nabar wurin fuskata a ɗaure tamau. "Ke Kyakkyawa ta nima Ina San Ki!!." Murmushi nayi ba tare dana juyawa ba. Kallon gargaɗi kawai Aasief yake bin Leo da tawagarsa dashi yana karkaɗa hannu. Sannan cikin sauri ya biyo baya na cike da jindaɗi, yau dai na faɗa Ina San sa cikin tsakiyar makaranta gaban dubbanin ɗalibai.💃💃 *Zaynerb 💓 Aasief 🤙* Tun daga wannan Ranar wannan lokaci cikin wannan taƙin. Salon rayuwata da na masoyina Aasief ya canza. Dan kuwa wani irin so da ƙauna mara misaltawa muke yi wa junan mu, abin kamar almara. *One Month Later* Yauma tsaye nake gefan titi ina jirar ƙari sowar Bus da zata kaini zuwa paint class da yake bani lecture Ranar. Sanye nake da Doguwar riga da kuma wando irin dai na Pakistan nayi rolling kaina da mayafin rigar, sosai nayi kyau, ina saɓe da handbag ɗi ta. Gefana kuwa mutumin nawa ne tsaye shima sanye cikin t-shirt da wando jeans ya saka p-cap idanun sa rufe da glass hannayen sa cikin aljihun wandon sa. "Idan kin kammala ƙare min kallon ki matsa gefe." Saurin kawar da kaina gefe nayi jin abin da yace ashe yana lura dani. "Gefe kuma saboda me?." Na tambaya da mamaki. "Ke dai ki matsa nace idan kuma ba haka ba, Karki zarge ni da koma miye ya biyo baya aha." Dariya nayi sannan kuma ban matsa ba, don ni kaina nasan ina da mugun taurin kai. "Tabbas idan baki matsa gefe ba zaki sumba ce ni a wannan taƙin." Dariyar rainin wayo na kuma yi ina faɗin "Lallai toh ma na karɓa Challenging ɗin sannn." Ban rufe baki ba, na zaro manyan idanuna cike da tashin hankali ina kallon ƙaton karen turawan da ya tunkaro ni, wani ƙato dashi jikin sa gaba ɗaya gashi ne, launin Fatar sa brown, daga bayan sa mai kula da shi ne yake biye da shi cikin fella gudu a son sa na ya tsaya, sai dai ina wannan tunkaro ni kawai yake tamkar wanda ake basa umarni. Kwata kwata na kasa motsi sai faman zare ido nakeyi ina jiran tsammani don kuwa banajin karen nan idan ya ƙari so wurin bazai yi yaga yaga da nama na a ɗanye ba. Cikin zafin nama Aasief dake gefena ya kamo hannuna da hannun sa ɗaya yayin da ɗayan ya jefa wa wannan karen key's dake hannun sa. Gaba ɗaya na binsa nayi, nauyin da nayi masa yasa gaba ɗaya mukayi ƙasa ina daga sama nayi masa rumfa. Unfortunately lips ɗi na suka sauka cikin nasa ja-ja-yen laɓɓan. Oh my God kasa motsi dukkanin mu mukayi, ga mutane har sun fara taruwa kanmu cike da son ganin kwakwaf.😅 Cikin yardar Allah na samu na miƙe tsaye ina kama baki cikin zare ido, tuna wai da gaske sumbatar sa nayi.😹 Cikin sauri na nufa Bus da ta ƙari so wurin ko gigin juyawa garesa banyi ba. "Ke Kyakkyawa ta, ya ya dai baki da abin faɗa ne?." Tambayar ya yi min cike da shaƙiyanci, ni kuwa ƙin juyawa nayi, da sauri na shige cikin Bus ɗin ina Dariya.🤓 _-_*-_ Rayuwar Duniya daɗi idan ka sama wanda kake so yake ƙaunar ka tsakani da Allah. A wannan zamanin mace abar tausayi ce, tabbas wurin samun Namiji wanda yake ƙaunar ta da gaskiya. Yawancin Mazan mu na yanzu bamu suke so ba, jikin mu kawai suke buƙata, yayin da kuma mu Matan yawanci kuɗaɗen samarin muke so. Ni dai nayi dace na zama mai sa'a cikin masu sa'ar, na sama haɗaɗɗen lu'ulu'u na Aasief Mai Waje, kyakkyawan matashin Saurayi na.😇 Na gwadashi ta ko wani ɓangare amma halayensa masu kyau kawai nake gani, ban taɓa ganin sa da wani mummunar siffa ko hali mara kyau ba. Aasief ɗi na irin waɗannan samarin ne na kirki waɗanda kafin mace ta sama kalar su sai tasha wahala gaskiya. Soyayya muke gudanar wa mai tsafta tsakani na da Aasief Mai Waje kyakkyawa na. ** Murmushi nayi dai dai lokacin da na shiga Elevator da zai sadani kai tsaye izuwa Room na Saurayi na Aasief. Jiya da dare ina kwance saman Bed saƙon sa ya shigo wayata, wai na samesa a estate nasu yau misalin 4:50pm. Ba tare da tunanin komai ba, yau na shirya cikin kyakkyawar shiga na fito daga Gidan Madam Joy. Kai tsaye na hau Taxi na taho zuwa Address ɗin da ya rubuta min a saƙon, koda na sauka a taxi bayan na biya sa kuɗin sa. Sosai nasha mamaki ganin ba tare da binciken komai ba. Gate man dake tsaron Babban gate na Estate ɗin ya buɗe min na shiga ciki, haka shima mai tsaron gate na biyu. Ban kawo komai a raina ba, don duk tunani na, shi Aasief ɗin ne ya yi musu umarni da hakan. Hannu nakai domin knocking Room ɗin nasa, ga Mamaki na a buɗe yake. Saboda haka cusa kaina ciki nayi. Wannan karon shi ne farkon zuwa ta Estate da yake kuma farkon shigata Room ɗin sa. Palo ne haɗaɗɗe na gaske, wanda tsantsan kyawun palon ne ya sa na kasa gaba na tsaya ƙare wa palon kallo. Subhanallah! Na furta a fili sakamakon hango Boxer da nayi yashe a tsakiyar palon. Humm wata ƙilama gajiya ya yi jiya Shiyasa bayar Boxer a ƙasa kuma a palo. Nayi maganar ina mai gaskata kaina da haka ne abin da na faɗa. Ƙari sawa nayi sannan na kai hannu domin kawar da Boxer ɗin. Wani irin zilo zuciyata tayi kamar zatayo waje tsaban mamaki da tashin hankali na ganin abin da na gani. Wai fa da gaske Brazia na gani gefan Boxer ɗin. Cikin sauri naja baya tamkar wacce shock na wutar lantarki yaja. Cikin tsananin juriya da dan ne abin da naji yana taso min a ƙahon zuciyata. Nake takawa a hankali ƙafafuna suna son ƙari sawa dani cikin Bedroom. Yayin da zuciyata shawara kawai take bani da na juya kawai. Hannu nakai ba rufe baki jin kuka yana ƙoƙarin suɓuce min sakamakon ƙara ganin Pant na ma ta da nayi gabda zan shiga Bedroom ɗin. Dishi dishi idanuna suka fara nunamin abubuwan dake gaba na, sakamakon hango sa da nayi kwance saman Bed daga shi sai short yana kwasar bacci. Juyawa da idanuna da suka yi jajur lokaci guda nayi domin neman hanyar fita. Cikin rashin sa'a idanun nawa suka sake kallon abin da zuciyata ba zata iya jure gani ba. Cikin tsananin mamaki da tashin hankali nake ƙoƙarin furta sunan wacca na gani tsaye bakin bathroom da alama fitowarta ke nan daga ciki, kuma ga dukkan alamu wanka tayi, ganin yadda dogon gashin kanta da yake brown color yake ɗigar ruwa gata ɗaure da towel a chest... "Erisha!!." Na furta cikin rarrabe war murya, zuciyata tana barazanar fasowa waje. Tashin hankalin da nake ciki yasa na kusa zubewa ƙasa ba tare da sanina ba, tabbas wannan Erisha ce a gaba na toh Menene haɗin ta Aasief. Inna-lilahi-wa-inna-illahir-raji'un Wannan wata kalar cin Amana Aasief ya yi min?. Fisabilillah ya rasa wacce zai yi tarayya sai wannan arniyar kafirar Erisha. Ta kasance University ɗaya muke da ita, class ɗaya course ɗaya, Benchi ɗaya. Tun farkon ganina da Aasief da tayi hankalin ta ya tashi ta kasa sukuni wai a haukar son Aasief take. Lokacin da labarin haka ya sameni sosai nayi ma ta warning akan ta fita harkar Saurayi na, idan kuma ba haka zatayi da ta sani. Ashe kallo na matsayin shashasha kawai suke yi daga ita har shi, tunda gashi yanzu na gansu tare, cikin yanayin da zuciyata ba za ta iya jurewa ba. Inna-lilahi-wa-inna-illahir-raji'un Kawai furta wa ina mai mai yawa, wannan wata kalar mummunar ƙaddara ce?. Cikin zafin nama na miƙe tsaye na ɗauki wayata da ta faɗi ƙasa, ba tare tunanin sake kallon Aasief dake kwance kamar gawa ba. Ko kuma ita Erisha ɗin. Na nufa hanyar fita daga Bedroom ɗin ina sha re zafafan hawayen da suke wanke min fuskata. Wasu na ƙara biyo baya masu raɗaɗi fiye da garwashin wuta.🔥 "Nace bakiji ba, please idan kin fita ki rufe mana Room ɗin ko." Inna-lilahi-wa-inna-illahir-raji'un Ji nayi gwara na mutu na huta zaifi min sauƙi bisa wannan mummunar rana da nake ciki. Ban kulata ba, haka zalika ban juya na kalleta ba. *** Tun daga wannan Ranar gaza jurewa nayi, gaba ɗaya na shiga damuwa sosai na abin da ya faru, ya kasance bana iya zuwa University, bana ɗaukar wayan da Aasief yake bugomin ba dare ba Rana. Na rame na fita hayyacina bansan haka ciwon so yake ba, balle kuma ni da aka yaudara. Tun daga wannan Ranar bamu sake haɗu wa da Aasief ba kuma ni ce bana basa damar haɗuwa da ni, toh idan ma mun haɗu menene zai ce min?. Wasa wasa tsawon wata ɗaya muna haka dashi zuwa, yanzu ina ɗan zuwa school sai dai wallahi bana fahimtar komai sai dai kawai naje. Ita kuwa Erisha ita ma tun daga wancan Ranar ban sake ganin ta ba koda a school ne kuwa. Daga ƙarshe da Aasief ya dameni da kira karairaya SIM card ɗin nayi gaba ɗaya sannan nayi plushing ɗin sa a toilet. *** Sama sama nake juyo hayaniya daga wajen gate, da alama mai gadi ne shi da wani. Mutsike idanuna da bacci bai ishe su ba nayi ina miƙa. Ya ye curtains nayi domin ganin abin da yake faruwa. Nan da nan zuciyata ta fusata damuwar da ta fara rabuwa da ni two days ta dawo sabuwa fil, duka sakamakon hangosa da nayi wurin gate ashe da shi ne gate man yake hayaniya. Ban san lokaci ba kawai tsintar kaina nayi ina taku ƙafafuna ko takalma babu haka na ƙari sa wurin gate ɗin nan muka shiga kallon kallo tsakani na da shi tsawon mintuna, sannan ya katshe shirun ta hanyar buɗe baki da niyyar ya yi min magana, cikin tsananin sauri da tafarfasan zuciya na dakatar da shi idanuna a rufe nake faɗin "Menene kazo kayimin?, ko kuwa kazo ka ƙara tayar min da ciwon da na samu ya fara warkewa ne. Mayaudari maci Amana Aasief ka yaudareni bazan yafe maka da Abin da kayimin ba wallahi." Maganganu kawai nake sakar masa babu adadi kuma ba tare dana tauna su ba. Daga ƙarshe da ya tunzura iya tunzura nan shi ma ya fara aman zafafan kalamai a gare ni, waɗanda sai da suka saka na zubar da hawaye maganganu kawai yake sakarmin tamkar ba shi ne ya yimin laifi ba. Cikin maganar sa ta ƙarshe da ya yi ne wacce ta daki zuciyata iya duka. Cewa wai ya yi. "A haukar ki bansan abin da yake tsakanin ki da Leo bane ko mene, ko kuwa an faɗa miki banga pictures da kukayi tare da shi a mashaya bane?...." Inna-lilahi-wa-inna-illahir-raji'un Ta nan kuma ya ɓullo?...... Na tambaya zuciyata, yayin da jikina ya ɗauki rawa na ɓacin rai. Buɗe idanuna da suka yi jajur fi ye da baya nayi, domin nima na gasa masa maganar da tafi wacca ya yi min. Sai dai kash.....!!!! Cikin rashin sa'a naga wai har ya bar wurin ya shiga Taxi. Gaza jurewa nayi domin kuwa a lokacin yadda zuciyata take tafasa idan bawai na faɗa masa magana mai zafi fi ye da yadda ya faɗa min ba, ina ganin tarwatsewa zuciyata zatayi tsaban baƙin ciki da ƙiyayyar sa da nake ji lokacin yana taso min. Haka ƙafafuwana ko takalma babu sannan a yadda jiki na yake sanye da Doguwar riga ta bacci kaina da hula. A hakan nima cikin zafin rai na tare mai taxi nima na shiga, akan ya kaini can Estate ɗin ayi ta ta ƙare a yau ba gobe ba....... *Abin Takaici* Ashe ba Gidan ya tafi ba kai tsaye, domin ko da na ƙari sa ban ganshi ba, domin kuwa a kulle naga ƙofar tasa. Kai koma yana nan, toh rufe ƙofar ya yi ta ciki. Ba haka naso ba, sai dai bani da yadda zanyi, haka na juya nabar ƙofar Room nasa, sannan na shiga Elevator. Saukowa ƙasa nayi ina shirin fitowa, dai dai lokacin wata kyakkyawar matashiyar budurwa ita kuma ta shigo cikin Elevator ɗin. Hannun rungume da jaririya. Ƙoƙarin fita nayi ina sha re bisassun hawayen fuskata. "Ah nace ba, please Madam a hawa na nawa Room na Aasief Mai Waje yake?." Tambayar da Budurwar tayimin ke nan, wacce tasa na kasa koda motsi. Cikin shiga tashin hankali sama da baya na juya ina kallon ta, sannan kuma ina ma ta tambayar da take cin zuciyata. "Aasief Mai Waje kika ce, wata kalar alaƙa ce tsakanin ki da shi?." Murmushin da ya bani mamaki tayi sannan ta bani amsa da faɗin. "Ae Miji na ne shi, gama Jaririyar mu, Surprising nasa nakeso nayi, Shiyasa dana shigo ƙasar ban tuntuɓe sa ta waya ba." Tayi maganar tana dariya kuma tana min nuni da jaririyar dake hannunta. Inna-lilahi-wa-inna-illahir-raji'un "Wai shin Wanene wannan Aasief ɗin, da mai yake taƙama ne haka?." Na tambaya zuciya yayin da nayi saƙale ina kallon ta. Cikin dauriya na kalleta cikin dan ne zuciyata na faɗa ma ta lambar Room nasa. Inaji tana yimin godiya, sai dai ina..! Nayi nisa bata ita nake ba, tafiya kawai nake bansan inda zan je ba. *** Allah Sarki ni Zaynerb Mai Kyau, na tsinci kaina cikin wani hali mara daɗi, Soyayya ta wahalar dani sama da tunanin mai tunani. Na ƙara ramewa na fita hayyacina har takai ta kawo ko makarantar bana iya zuwa. Halin da na shiga silar Soyayya bana fata wata Ƴa mace ta shiga kalarsa.😓 Tun daga wancan Ranar Rayuwata ni Zaynerb Mai Kyau ta tashi daga layin farin ciki, na koma bani da aiki sai tunane tunane, wanda hakan ya haifar min da babbar illa. Tsawon Wata da watanni ina cikin wani mummunar hali sanadiyyar Soyayya, ta kai ta kawo ba bacci bana samun damar yi. Daga ƙarshe dana haɗu da ƙawa wacce bata kirki ba, ta jefa ni cikin halin shaya shaye. Takai ta kawo idan ban sha kwalbar barasa ba, bana iya taɓuka komai. A shekarar farko da shiga University, shekarar farko na karatuna na tashi Carry Over. Hankalina ya ƙara tashi sosai, naji na tsana ƙasar Amsterdam ɗin ma gaba ɗaya. Daga ƙarshe ma tattara ya nawa ya nawa nayi na dawo nan Nijeriya na ci gaba da Rayuwata da Ahalina kuma na fara karatuna amma na canza course madadin ilimin halittar furanni, na koma karantar Shari'a. Tun daga wancan Ranar ban sake haɗu wa Aasief Mai Waje ba, ko ma Erisha dasu Leo gaba ɗaya cikin su babu wanda na sake haɗu wa da shi. Kuma hakan ya yimin daidai domin ko idan na haɗu dasu ban san menene abin da zai biya baya ba.🔥 Na dawo Nijeriya amma halayyar Shaye Shaye taƙi rabuwa dani, haka ma soyayyar Aasief Mai Waje, ban san dalili ba kuma. *This Is My Badly Sadness Love Story* *Zaynerb Mai Kyau* *End Zaynerb & Aasief Babu ƙara Soyayya Har Abada*👎👎👎 _____ "Me yasa kika tsaya ne, ki ci gaba mana, Dan Allah Anty Lailah ci gaba da karantawa, so kawai nake naji ya ya Anty Zaynerb suka ƙare wa da shi." Deejarh ce take wannan maganar cikin kuka hawaye shaɓe shaɓe. Cike da tsantsan tausayin Zaynerb Lailah ta a je Jotter ɗin a gefe, ita ma cikin sha re kwalla take bawa Deejarh amsa da faɗin "Menene zan ci gaba Deejarh?. Ai iyakar labarin ke nan, Allah Sarki Anty Zaynerb yanzu duk ta iya jure duk wannan, wayyo rayuwa." "Kuka ba shi ne abin yi ba yanzu, hasa lima banga amfanin yin sa ba." Cikin sauri Lailah ta katse Afeefah da tayi wannan maganar da faɗin "Yanzu idan bamu yi kukan tausayawa Anty Zaynerb ba, menene kike so muyi, na'am ki faɗa min?." Ko kafin Afeefah ta bawa Lailah amsa, Haleesat ta rigata da faɗin "Abin yi yanzu shi ne musan yadda za'ayi soyayyar su ta dawo..." "Ban gane abin da kike nufi ba, Humm wai so kike kice mana, kina da yadda za'ayi Anty Zaynerb su ci gaba da Soyayya da wannan mayaudarin?." Lailah ce tayiwa Haleesat ɗin wannan tambayar cikin sauri. Ko kafin Haleesat ta nema amsar da zata bata, suka jiyo Muryar da basu yi tsammani ba, ta bayan yana faɗin "Qwarai kuwa, tabbas abin da ya kamata ayi ke nan yanzu, musan yadda za'ayi soyayyar Zaynerb da shi Aasief yake ko wane?, ta ci gaba da gudana, saboda kwata kwata banma yadda wai shi ɗin zai iya Yaudarar ta ba, duba da yadda ya nace ma ta da farko, da'ace cin Amana ko yaudara ne a zuciyar sa tabbas ba za suyi daɗewan da suka yi a tare ba." Maleek ne duk yake wannan maganar yayin da yake saukowa daga saman Staircase's na part nasa, sannan ya ƙari sa palon ya zauna daga gefan Afeefah saman 3sieter. Ashe tun farkon fara karanta labarin soyayyar na Zaynerb da Lailah tayi yake tsaye daga saman Bene, tabbas yaji komai, kuma sannan har zuciyar sa bai yarda cewa Aasief yaci amanar Zaynerb ba. "Tabbas nima ban yarda ba wallahi, duba da yadda ta rubuta labarin, cewa tayi fa wannan Leo yace yana son ta, sannan ita ma Erisha ce ko, ta ce tana son Aasief, idan kukayi duba da irin Abin da Zaynerb tayiwa Leo ɗin a tsakiyar makarantar, gaban dubban ɗalibai, da kuma irin rashin mutuncin da ta ce tayiwa ita Erisha ɗin, Tabbas a tunanina zai iya kasancewa Leo da Erisha sun haɗa kai ne..." "You are right sister Haleesat ni ma haka nake tunani." Cewar Deejarh tana yunƙurin kuma cewa wani abu suka haɗa idanu da Maleek, da sauri tayi ƙasa da kanta tana rufe bakinta, ita fa wallahi waɗannan rikitattun idanun nasa tsoro suke ba.😁 "Duka kunce wani abu amma yanzu Menene abin yi?." Fadeelah ce tayi maganar yanzu, duk da cewa ba wani shiri ne tsakanin ta da Zaynerb ɗin na azo a gani ba, amma wallahi sosai ta tausayawa Zaynerb jin wannan labarin nata a soyayya.💓 "Abin yi ɗaya ne yanzu, shi ne mu fara sanin Wanene shi Aasief, musan ƙasar da yake, musan su waye familyn sa, da komai nasa, sannan koma menene sai ya biyo baya." Maleek ne ya faɗa hakan, don a tunanin sa hakan ne yafi kamata ayi cikin wannan taƙin da suke ciki. Sannu a hankali Momy Rafi'at da ita ma taji kuma ta saurari komai na abin da ya faru da Zaynerb a soyayya, ta fara ja da baya, Allah Allah take ta koma sama, don bata fata wani daga cikin su ya fahimci taji komai. Cikin zuciyar ta kuwa faɗi take. "Ohoo Very very amazing, wai dama haka labarin soyayyar Zaynerb ɗin ya kasance, lallai kuwa idan haka ne, sara ne yazo ma ta daidai da bakin gatarin ta..." Da isar ta Bedroom bata tsaya jiran komai ba, ta lalubo lambar sa cikin sauri sauri ta danna masa kira, domin ya faɗa ma ta abin da ya kamata tayi, don kuwa kanta ya ɗaure, ba za ta iya komai ba, sai da shawaran mutane ukun nan da ta yarda dasu sama da komai a duniyar ta. A palo kuwa ci gaba suka yi da tattaunawa akan yadda zasu ɓullo wa al'amarin, sai dai sun yanke iya su zasuyi, Daddy ko Momy Rafi'at koma ita kanta Zaynerb ɗin, babu wanda a cikin su zai san da wannan nufi nasu. Sosai suka tattauna da Yayan nasu Maleek akan al'amarin soyayyar na Zaynerb. Da yadda zasuyi komai ya koma daidai. *KANO* *STATE* *Jiddarh Komai Naga*💃 💋*Sarauniyar kyau ta Kanawa*💋 Daga zaunen da take saman Dressing Mirror tana fesa daddaɗan turaren ta mai tsadar gaske, ta jiyo Muryar Auntie (Mrs Komai Naka) tana kwala ma ta kira ita da Humaira. Cikin sauri ta mayar da kwalbar turaren ma'ajiyar sa, sannan ta fito daga Bedroom nata da sauri, saukowa Down tayi, kana ta ƙari sa wurin Auntie tana faɗin. "Gani Auntie wannan kira haka, Allah ya sa dai lafiya?..." Kallon Jiddarh Hajiya Jamila (Mrs Komai Naka) wato Auntie takeyi daga sama har ƙasa, dan da nan wani takaici ya ziyarci zuciyar ta, ƙiyayyar da take yiwa mahaifiyar Jiddarh ɗin ya dawo sabo fil cikin zuciyar ta. Ita fa ta tsani wannan Yarinya Jiddarh sama da komai a Duniyar ta, ace Yarinya sai shegen kyau kamar wata huru'in. Dan ne abin da take ji, tayi kamar yadda ta saba a kullum. Sai da ta saita nutsuwar ta, sannan ta fara magana cikin sakin fuska da dariya, nuna musu Magazine na Daily Just dake hannunta ta yi tana faɗin. "Yarana Jiddarh da Humaira ku duba wannan abin farin ciki da ya samemu haka, wai fa Abban ku ne (Alhaji Jafar Komai Naka) shi ne Mai Arziƙi na Bakwai a Nijeriya, shi ne ya fito cikin jerin mutanen da sukafi kowa kuɗi a ƙasar nan fa..." Cike da mamaki game da farin ciki Jiddarh ta washe baki kamar gonar auduga faɗi take. "Lah lah Auntie wai da gaske kike Abba ne ya fito cikin jerin mutanen da suka fi kowa kuɗi a ƙasar nan, lallai dole yau musha shagali a gidan nan." Tayi maganar tana karɓar magazine ɗin daga hannun Auntie ɗin don sake tabbatarwa. Ita kuwa Humaira tsaban farin ciki kasa magana tayi, sai mamaki, huh Allah mai iko, mamaki take yaushe Abbansu ya yi dukiya haka?. *Zaynerb Mai Kyau*🥰 💓*Queen Of Love*💓 Da sauri taja wani wannan burki sakamakon buguwar da motar su tayi da motar dake gaban su, kuma ita ce da laifi, dan kuwa juyawar da tayi tana yima su Mah'eesha da Haseeya da suke back seat zazzaune magana ne, yasa ta bugi motar gaban su ba tare da ta sani ba. Ƙasa tayi da kanta gaban ta mugun bugu, Addu'a take Allah ya sa bata kaɓe kowa ba. Sannu a hankali ta ɗago da kanta tana kallon titin. Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta buɗe murfin motar ta fito. "Kuyi haƙuri Dan Allah ina mai baku haƙuri, akasi aka samu, na kusa buge motarrr...." Kasa ƙari sa maganar tayi zuciyar ta na mugun bugu da sauri sauri sakamakon ganin mutumin da ya fito daga motar da tayiwa ɓanar tare da wasu Ƴan Mata biyu. A yadda ya fito daga motar ransa a mugun ɓace, niyyar sa ya yi wa koma uban waye ya bugi motar sa, dukkan mutuwa. Sai dai mai?.... Cak ya dakata daga ƙoƙarin ƙari sawa wurin da ya yi niyya. Kamar ta tsaya cak tana bin sa da Kallon mamaki. Toh shima Aasief a nasa ɓangaren haka abin yake. Da farko kwata kwata bai gane wacece ba, har sai da ya kusa ƙari sawa dab da ita. Sannan ne ya fahimci wacece, kuma ya gane ta. Duk da cewa ta ƙara girma, tsayi, haske,da kyau, sai dai tana nan a yadda ya santa babu ƙiba.🙃 *After One Hour* "Zaynerb! Zaynerb!! Wai bada ke nake magana ba, menene haka kike ƙoƙarin yi ne, Kawai tashi guda kice zaki koma Abuja da yamma nan, wai menene abin da ya faru, kuma Wanene wannan Mutumin ki faɗa min?." Dakata wa Zaynerb tayi daga ƙoƙarin ta na cusa kayan ta cikin Akwati, sannan ta juyo tana kallon Mah'eesha da take ma ta tambayoyi, tana mai bata amsa da faɗin "Eh tabbas Abuja zan koma, saboda bazan iya kwana da gari ɗaya da wancan mayaudarin ba wallahi." "Me kike nufi da mayaudari, kina nufin kice shi ne wanda kuka taɓa Soyayya da shi a ƙasar Amsterdam?." "Yes, of course, shi fa." Zaynab ta bata amsa, tana ci gaba da cusa kayan cikin Akwatin ta. "Okay, Toh Menene da hakan dan ya kasance kun taɓa samun matsala da shi?." Haseeya ce tayi maganar a yanzu. "Oh ni Zaynerba wai bakuji menene abin da yake faɗa min ba, cewa fa yake ni ce da laifi bawai shi ba.... Kai!! wai mutumin da na ga mace a Room nasa, shi yake faɗa min baya da laifi. kuma kuna goyon bayan sa kukeyi ke nan?, lallai ma." Maganar take cikin huci da ɓacin rai, sannan ta ci gaba da cewa "Kuna dai gani ɗazun a gaban ku komai ya faru, har wani Challenging yake bani kuji fa. Wai sai dai dama can Burin Yaudarar sa nake, wai wata ƙila ni ce na shirya komai, kuji fa Mah'eesha... Na rantse yau babu mai hanani konawa Abuja da daren nan." Ta ƙari sa maganar tana jan ƙaramin Akwatin ta sannan ta fito daga Bedroom ɗin, kai tsaye parking lot ta nufa, da yake Momy Suwaiba ba ta nan, shi ma Uncle Sagir bashi. Biyo bayan ta Mah'eesha da Haseeya ɗin sukayi, Haseeya tana faɗin "Tun da kin matsa zaki koma, kiyi haƙuri mana kibi jirgi, kinsan tafiyar mota ba zai yiwu ba, saboda hanyar bata da kyau, baya da hakan Yamma ya yi sosai, yanzu fa 5:55pm kiyi haƙuri Zaynerb ki dawo." Haseeya ta ƙarishe maganar cikin lallashi da son Zaynerb ɗin ta fahimce ta. Duk yadda Haseeya da Mah'eesha harma da Mah'fuz da ya dawo gidan, ya tarar da abin da yake faruwa, duk yadda suka so Zaynerb tayi haƙuri ta bari, zuwa washe gari ta koma Abuja, ƙi tayi. Zaynerb tana da mugun taurin kai sosai, ba'a sakata, ba'a hanata, duk lallashin da aka ma ta akan ta haƙura ƙi tayi. Daga ƙarshe haka suna ji suna gani Zaynerb ta shiga Mota Driver yaja suka nufa hanyar Abuja da wannan Yammacin. *Aasief Pov* "Neelarh! Neelarh. Kina ina ne, ma za ki shirya yanzu yanzu zamu koma Abuja bazamu ƙara kwana a garin nan ba." Cike da tsantsan Mamaki take kallon ƙanin nata, jin abin da yake faɗa, gani take kamar baya hayyacinsa, idan ba haka ba, mutumin da yazo da niyyar ya yi ma ta one week, ko two days basu yi ba, shi ne zai ce zasu koma. "Aasief wai menene abin da kake nufi ne, da kake maganar Neelarh ta fito ku tafi, kodai ka manta one week zakuyi min?. Sannan nayi maka tambaya akan Budurwar ɗazu baka bani amsa ba, menene abin da kake nufi?." Tayi masa tambayar tana shimfiɗe Jaririyar ta mai watanni huɗu a duniya, saman sofa, zama tayi tana jiran amsar da zai bata. "Sister Raadwa na roƙe ki, da kibar yimin tambaya akan abin da ya shafe ta, sannan yau kuma yanzu nake da buƙatar mu koma Abuja da Mata ta, dan bazan ƙara kwana a nan State ɗin ba...." Katse sa tayi ta Hanyar faɗin. "Aasief ke nan a tunanin ka ban fahimci komai ba ne, ae fahimtar komai ne yasa nace ba zaka koma Abuja da Matar ka Neelarh a yau ba, har saika faɗa min Wacece waccan Budurwar da kukayi cacan baki da ita ɗazu, gaskiya ka bani kunya, ace kamar ka, kake biyewa mace a tsakiyar titi...." "Ya isa Raadwa ki dakata haka, tun da so kike kisan Wacece ita, toh ita ce ZAYNERB..." Ya bata amsar yana kawar da kansa gefe domin zuciyar sa ba za ta iya jurewa ba sam. Wani irin bugu zuciyar Neelarh da ƙari sowarta wurin ke nan taji abin da Aasief ya faɗa na ƙarshe tayi na hankali. "Inna-lilahi-wa-inna-illahir-raji'un." Kawai take iya furta wa daga farko har ƙarshe. Shikenan ɗan farin ciki da take tunanin zata samu tare da shi ba zai yiwu ba, shikenan Zaynerb ta dawo Rayuwarsa, zata tarwatsa musu farin ciki. Da kyar take iya tafiya haka ta ƙari sa palon, ta tsaya daga gefe tsumu da ita tana jiran abin da zai biyo baya. *Zaynerb* Tsaban buguwar da kanta ya yi, sakamakon burki da Driver yaja a tsakiyar Dajin, yasa ta kasa buɗe idanunta da suka ma ta nauyi yadda ya kamata. Ƙarar harba harben bindigun da suka ji ta ko'ina na dajin ya ɗauka ne, yasa tayi saurin toshe kunnen ta tana rumtse idanu cikin tsananin tashin hankali. Ƙari sowa wurin motar nasu wani ƙaton jibgegen Gardin Basamuden Mutumin ya yi. Hannu ya kai ya fasa gilashin motar, sannan ya buɗe motar ya finciko Zaynerb da idanunta suke lumshewa a hankali tana gani dishi dishi. Da hannu ɗaya ya fito da ita daga cikin motar. Watsar da ita ya yi daga gefan wurin da suka tara Ƴan Mata daban kamar wata kayan wanki haka ya watsar da Zaynerb. Tsaban azaba yasa ko motsi kasayi Zaynerb tayi. Yayin da shi kuwa Driver gefan maza aka watsar da shi. Shi ma bayan anyo waje da shi daga motar. Can gefen da suka tara motocin mutanen da suka yi Kidnapping cikin Dajin, wannan Gabjejan mutumin da ya ɗauki Zaynerb, yaje ya aje motar su Zaynerb. Sannan ya dawo kusa da ƴan uwansa kidnapper's ɗin maza da mata wurin su Ashirin cike da dajin hannayen ko wannen su ɗauke da gaggan makamai masu haɗarin gaske. *Zaynerb* Tamkar a mafarki haka take Ganin al'amarin da yake kan faruwa dasu a halin yanzu, wai fa da gaske kidnapper's ne suka yi Kidnapping na ta. "Inna-lilahi-wa-inna-illahir-raji'un." Ta furta laɓɓanta na rawa, tana bin ƙaton dajin da kallo, da kuma waɗannan gaggan Kidnapper's. Akan tulin mutanen da suka yi Kidnapping idanunta suka sauka. Mutane ne kala kala maza da mata yara da manya. Masu kuɗi da talakawa, ɗalibai da ma'aikata. Wurin da suka saka ƴan mata daban wurin maza daban haka ma wurin ƙana nan yara daban. "Na shiga ukuna ni Zaynerb, wannan wacce kalar ƙaddara ce ta kawoni hannun waɗannan mutanen?....." Zaynerb tayima kanta tambayar hannu a ka cikin tsananin tashin hankali, gani take kamar mafarki take yi bawai da gaske Kidnapping nata akayi ba. Baya Baya motar da ta shigo dajin tayi kamar zata koma inda ta fito. Cikin sauri da an karewa gaba ɗaya kidnapper's ɗin suka sassaita manyan bindigun su ga motar da shirin su harbe koma uban waye a ciki, muddun ya nema yi musu taurin kai. Ƙari sawa wurin motar, wannan Gabjejan mutumin baƙin ƙirin da shi ya yi, sannan ya saka baƙin hannun sa ya buɗe motar. Da alama halinsa ne finciko mutum daga cikin mota. Dan kuwa duka ƙarfin sa ya saka wajen finciko mutumin dake cikin motar. Sai dai da alama wanda yake motar shima mugun ɗan taurin kai ne. Duba da yadda Baƙin mutumin ya dage wajen ƙoƙarin finciko shi, yayin da shi kuma na cikin motar yaƙi basa damar hakan. "Inna-lilahi-wa-inna-illahir-raji'un. Aasief ne wallahi shi ne, na shiga ukuna ni Zaynerb inna-lilahi-wa-inna-illahir-raji'un." Zaynerb tayi wannan maganar cikin tsananin tashin hankali na ganin mutumin da wannan ƙaton Arnen ya sama damar fitowa waje da shi ba kowa bane fa ce Aasief. "An kara! An kara!! kwalawa sun sama labari, kai GADDAFI ya kamata muyi gaggawar barin wurin nan kafin su ƙari so, su tarar damu fa." Ɗaya daga cikin kidnapper's ɗin ne ya yi wannan maganar ga Ƴan uwan nasa kidnapper's a lokacin da ya mayar da wayar da aka sanar da shi abin da ke faruwa ta cikin ta cikin aljihun rigar jikin sa da take ta tare alburushi. "Wannan munafukin ne ya faɗa musu shakka babu, domin kuwa ga waya nan a aljihun sa." Baƙin mutumin da aka kira da GADDAFI ya faɗa hakan a daidai lokacin da yake sakarwa Aasief ɗin Alburushi a tsakiyar ƙafafuwan sa. Wani irin ihun neman taimako Neelarh da take tare da Aasief ɗin ta saki tana mai kiran sunan sa cikin tsananin tashin hankali. Zaynerb kuwa kusan susu cewa za'a iya cewa tayi na ganin yadda jini yake tsata ta daga ƙafafuwan Aasief da ya zube ƙasa cikin tsananin Azaba..... Mgnr Payment duk wacce tasan bata biya 300 na littafinan ba, kuma ta karanta gaskiya ina ga ban yafe ba, fisabilillah 300 ne fa kacal. 👌👊 *Idan kina shirye da biyan ɗari uku (300) kisha karatu cikin kwanciyar hankali, to ki biya ta wannan details ɗin.* 👇👇 *The Phone Number* *08081129487* *The Acct Number* *8081129487* *The Bank Name* *Palmpay Bank* *The Acct Name* *Khadeejarth Sabi'u Yahyah* _____ *🔥 SARAUNIYAR KYAU 🔥* _-_👑ƚαƙυɳ ƚʂαƙιყα👑_-_ ɯ&ʂ_-_📖🖋️📲 💓 The Nainarh Kd 💓 _-_ҽρ.11_15 *💝ƚԋҽ ҽxƚɾασԃιɳαɾყ ʅσʋҽ αɳԃ ɾσɱαɳƈҽ ιɳ Ⴆιƚɯҽҽɳ ȥαყɳҽɾႦ $ ααʂιҽϝ💝* *Lailah Mai Kyau* A hankali take bubbuga yatsarta akan cup of coffee dake tsakiya saman teburin da suke zaune. Kyawawan idanunta suna saman kyakkyawar fuskar sa mai cike da haiba, tana ƙare masa kallo zuciyar ta na bugawa kaɗan kaɗan. Tun bayan kammala yadda ya kamata su ɓullo wa al'amarin Zaynerb da Aasief da suka yi, ita da Afeefah suka shirya kai tsaye suka wuce Hospital domin ganin matar da Afeefah ta taimakawa ta haihu a Restaurant. Koda suka je anan ne suka haɗu da Sabbir, ashe wai matar da Afeefah ta taimakawa ɗin, matar Yayar shi Sabbir ɗin ne. A lokacin sosai Sabbir da Lailah suka sha fira abin su, dama kuma suna ɗan yin waya jefi jefi da shi. Washe gari yau ke nan, sune rakiyar Afeefah izuwa wurin tantancewa na Miss Nigeria da za'ayi anan Abuja, kiran Sabbir ya shigo wayar ta, koda ta ɗauka cike da zumuɗi sai yace ma ta, su haɗu a Restaurant ya bata Address sannan ya ƙara da faɗin haɗuwar tasu tana da muhimmanci domin akwai wata magana da yakeso ya yi ma ta. Ba tare da ɓata lokaci ba, cikin gaggawa da zumuɗi ta shirya, sannan ta taho Address na Restaurant da ya yi ma ta kwatance. Tsawon mintuna da zaman su a wurin, amma bai ce da ita komai ba. Ita ma haka ba tace da shi ƙala ba. Ƙarar da wayar ta tayi ne, yasa suka dawo hayyacinsu daga Duniyar tunani da kowannen su ya lula. Murmushi tayi bayan tayi picking call ɗin, ganin Afeefah ce ta kira ta. "Hello Miss Nigeria To be, toh ya ake ciki ne, ya ya tantancewar ta kasance ne, Allah yasa dai munyi Nasara?." Lailah tayi maganar cikin son jin yadda tantancewar ta kasance. *The Queen Afeefah*💓 Murmushi tayi mai kyau, tana zama cikin haɗaɗɗiyar motar ta sannan ta bawa Lailah amsa da faɗin "Tantancewa ta tafi yadda ya kamata, domin na shiga cikin jerin Ƴan Mata goma sha Takwas da zasu shiga Gasar Miss Nigeria da za'a Gudanar a Lagos nan da ƴan kwanaki." "Kai Masha Allah, gaskiya naji daɗi sosai sosai, ki ce daga Miss Nigeria sai Miss World idan Mai duka ya nufa." Lailah tayi maganar cike da jindaɗi tana Dariya. Dariyar ita ma Afeefah ta yi a ɓangaren ta, sha re maganar Lailah ta yi tana faɗin. "Yanzu haka ma wata ƴar ƙwarya kwaryar Party da wannan Jiddarh take ko, wannan dai Queen Of Beauty ta Kano tohm ita ce ta shirya mana Party yanzu haka ma wurin na nufa kai tsaye." "Iyye kaga manya harda wata ƴar ƙwarya kwaryar Party za'ayi, tohm Allah ya tsare hanya yasa ku kammala lafiya ki dawo gida Muma muyi namu acan, dan nasan zuwa yanzu ya isa ace Jirgin su Aunty Zaynerb ya sauka anan Abuja tunda da wuri ta ce miki zata taho jiya da kukayi waya ko?." "Eh haka ne, ta ce da wuri zata taho." Afeefah ta bawa Lailah amsa cikin Murmushi. "Okay Tohm Allah ya sauke su lafiya, ke kuma Miss Nigeria To be, asha shagali lafiya, tunda babu gayya ta." Dariya kawai Afeefah tayi bata ce komai ba, sannan suka yi sallama. "Uhum Mister Sabbir Mai Naira, ka wani zubamin idanu ina waya, sai kace baka taɓa ganina ba." Lailah tayi ma Sabbir Maganar tana mayar da wayar nata cikin haɗaɗɗiyar jakar ta. "Uhum Miss Lailah Mai Kyau ba dole na zuba Miki idanu ba, wannan kyau haka kamar wata SARAUNIYAR KYAU gaskiya kin haɗu sosai." Sabbir ya bata amsa cikin zabga Murmushi idanun sa akan ta. "Okay Nagode sosai, sai dai inaga muyi maganar da ta haɗa mu anan, kace Kanada maganar da zaka faɗa min mai muhimmanci, saboda haka Go ahead ina sauraren ka." Lailah tayi maganar tana gyara zamanta idanunta akan sa, kamar yadda nasa suke akan ta. Shiru Sabbir ya yi da alama yana tauna maganar da zai faɗa ma ta ne, bayan ƴan sakanni yaja ajiyar zuciya still idanun sa akan ta sannan yace. "Ina son ki, Lailah da gaske ina ƙaunar ki, please zaki Aure ni?." Tamkar saukar aradu haka Lailah taji maganar da Sabbir yake faɗa ma ta cikin tsakiyar kanta. Ware idanunta tayi tarr, tana masa wani irin kallo mara fassara. "Sabbir I You Mad?. So fa kace, wai kuma da gaske Ni ce kake so?, Lallai baka da aiki." Lailah tayi maganar ranta a mugun ɓace tana miƙe wa tsaye zata bar Restaurant ɗin. "Yes Lailah I'm Mad akan ki, tabbas na zare akan ki." "Sabbir wallahi bani da lokacin ka fa." Lailah ta basa amsa tana ƙoƙarin barin wurin zuciyar ta na bugawa da sauri sauri. "Ki dakata Lailah da gaske nake Auren ki nakeson yi, wai duk menene hakan, bakya so na ko mene?." Dakata wa tayi da tafiyar da take yi sannan ta juyo tana kallon sa da idanunta da suka yi jajur take basa amsa da faɗin "Yes Sabbir bana sonka, kuma ban taɓa son ka ba, kawai dai a matsayin aboki na ɗauke ka, bawai saurayi ba, please ka rabu dani, bani da niyyar sonka balle kuma Auren ka, wallahi tallahi kaji ma na rantse maka?." Da gama faɗin hakan ta saka kai ta fice daga Restaurant ɗin, bata damu da irin kallon kinyi rashin mijin Aure da ƴan matan Restaurant ke bin ta dashi ba. Tamkar wani sakarai ko nace zararre haka Sabbir ya koma ya zauna daɓas saman kujerar ya yi zaman ƴan bori. This is the first time da wata ƴa mace ta kalla tsaban idanun sa ta furta bata son sa balle kuma tunanin Auren sa. Saboda haka sosai maganar da Lailah ta buga masa ta bugi zuciyar sa. Ya kasa koda kwakwkwaran motsi a wurin. "Bata sona kuma bata da da niyyar sona." Haka Kawai Sabbir yake faɗa tana maimaita wa a fili zuciyar sa na tuƙuƙi. Inna-lilahi-wa-inna-illahir-raji'un Shi kuwa yake furta wa cikin tashin hankali, ya ya zayyi da Dakon sonta da ya ɗauko babu gammo.😣 *The Queen Afeefah*💓 Sosai suka sha Shagalin da Jiddarh Komai Naga, ta shirya musu isu isu Ƴan Mata da aka tantance domin shiga Gasar Miss Nigeria. Sun ƙayatu iya ƙayatuwa da shagali, sun yi lafiya sun watse lafiya ko wacce ta koma state nata harda Jiddarh, dama Afeefah ita ce kaɗai ƴar Abuja, sai dai sauran suma akwai Waɗanda suke zaune a Abujan. Karon da taji tayi da mutum ne, yasa ta ɗago kyawawan idanun ta domin ganin ko wanene?. A dai dai lokacin shima kuma ya ɗago nasa Blue eye ɗin ya zuba ma ta. "Lah ashe ma kaine, na ganeka fa, ba kaine mutumin da na haɗu da kai a Shopping Mall ba, har muka yi magana akan inaso ka bani perfect perfume, kaƙi ka bani, kuma kaine wanda na gani lokacin da muke video call da Haleesat a gidan Sunainah, ko duk ba kai bane faɗa min?." Afeefah tayi maganar ne tamkar wacce ta yi tatul da barasa, zama tayi saman kujera dake wurin idanunta da suke lumshewa akan sa. Da hannu ya yi ma Bodyguard na sa alama da karya ƙari so wurin, dan ya lura niyyar ƙari sowa wurin yake da shi. Haka kawai yaji yana marmarin magana da ita, ba tare da dalili ba, don kuwa ji ya yi tamkar ya taɓa jin kalar muryarta a wani wuri bayan haɗuwar da suka taɓa yi a shopping Mall. "I You in drink?." Ya yi ma ta tambayar da take bakinsa bayan ya zauna a kujerar dake fuskantar wacca take kai. Zare fararen idanunta tayi cikin sauri tana ware su akan sa jin abin da yace da ita. Kamar wata ƙaramar Yarinya haka Afeefah ta koma cikin taɓe baki da shagwaɓa kamar mai shirin kuka take faɗin. "Wayyo Daddyna, ga wani yana kiran Shalelen ka da ƴar basara, kazo ka taimake ni..."😆 Tayi maganar kamar dai bata hayyacinta tana zaro wayarta daga Aljihun tsadadiyar jakar ta sannan ta lalubo lambar Daddyn wai da gaske kiran sa zatayi ta faɗa masa abin da aka ma ta.🤓 Sai dai rashin sa'a domin wayar a kashe take. Dariyar gefan fuska wacca bayyi shirin fitowarta bane ta kufce masa. "Kaga kayimin laifi huɗu ke nan ko?. Na farko ka hanani perfect perfume. Na biyu idanunka sun kusa sakawa nayi Accident. Na uku ka kira ni Ƴar barasa. Na huɗu kana yimin dariya saboda na kira Daddy wayar sa a kashe. Saboda haka saina kira maka Saurayina yanzu yazo ya ramamin...." (_-_Mun bani🥺 Anya kuwa Afeefah qalau take kuwa 🤔_-_) Idanunta suna lumshewa kamar mai jin bacci, a hakan Dan bala'i take lalubo lambobi cikin tsadadiyar wayar hannun ta, gajiya tayi batasan wata lamba zata kira ba, yasa ba tare da tunanin komai ba, ta danna kira da lambar da hannun ta ya kai kai. "Kasan menene kuwa, Saurayina yana sona sosai kuma fa sunan sa 'Rishi' sannan..." Gajiya da surutun ta da ya yi ne yasa shi tambayarta ta hanyar faɗin "Do you know who really i am?." Kallon sa tayi tana lumshe ido, ita ma ta mayar masa da kalar tambayar da ya yi ma ta da cewa "Kasan ni Wacece kuwa?." Shiru tayi sakamakon ƙari sowa wurin da wani daga cikin securities nasa ya yi. Miƙa masa waya Baturen security ya yi cike da girmamawa sannan ya juya ya bar wurin. "Okay pick up." Ya faɗa a gajarce idanun sa akan Afeefah. Murmushi ta saki ganin an yi picking call da take yi, kara wayar tayi a kunne tana faɗin "Hello Rishi Dear kana inaaaa..." Tsitt Afeefah tayi tana zazzare fararen idanunta sakamakon jin muryarta da tayi raɗau tana fitowa daga cikin wannan tsadadiyar waya ta gaske dake hannun sa. "Lah wai kaine mutttt..." Shiru tayi tana kuma zare ido dan batasan abin faɗa ba. "Wai kina nufin kice kece Yarinyar da take takuramin da kira muddun na shigo ƙasar nan, Ke nan kece 'RISHITA'?." *TASHIN HANKALI*😳 Rasa abin yi ne yasa Afeefah ta miƙe tsaye sannan ta ciro Takalma masu tsini dake ƙafafunta, ta gyara jakar hannunta, sannan ta kallesa tamkar wata ƙaramar Yarinya tayi masa Grin (Gwalo) kana ta ruga a guje ta ƙari sa wurin motar ta da sauri sauri gaban ta buga wa take faɗi ga Mosses Driver. "Mosses yi sauri ka ja motar nan mu bar wurin nan tun kafin wancan mutumin mai shuɗayen idanu ya kamani." Tayi maganar tana jefa jakar ta cikin motar sannan ita ma ta shiga ciki, shi kuma Driver Mosses ya ja motar da gudu duk ya tsorata, ya bar Park ɗin da ita.🤣😂😘 *Three Hours To Go* Wuntsilowar da tayi daga saman Royal Bed nata ne tare da azabar da ya ziyarci dukkan ilahirin sassan jikin ta, yasa ta saki wani marayan ihu tana gungure a tsakiyar Room ɗin jikin ta nan naɗe da Blanket gaba ɗaya gashin kanta ya barbaje ya rufe ma ta fuska. A hankali take buɗe fararen idanunta da alama Bacci bai ishe ta ba. Miƙa tayi tana jan wata doguwar hamma, kama sumar kanta da ya rufe ma ta fuska tayi sannan ta ɗaure a tsakiyar kanta. Hannu takai tana laluben ta wurin da zata jiyo wayar ta, jin babu alamar wayar ne yasa ta miƙe tsaye magagin baccin da tayi bai gana sakin ta ba. Bathroom ta shiga ta wanke fuskarta sannan ta fito kai tsaye Palo ta fita dan tanada tabbacin Deejarh ce ta ɗauka ma ta wayarta ba kowa ba. "Deejarh! Deejarh!! Wai kina ina ne zo nan ki bani wayata kafin na nemo ki." Afeefah tayi maganar daidai lokacin da ta ƙari sa ƙofar Bedroom na Deejarh sannan ta shiga. Can saman Bed ta hangota ta juya baya da alama Game take bugawa. Hawa saman ɗin tayi sannan ta karɓe wayar daga hannun Deejarh ɗin tana faɗin "Ke Deejarh yaushe kika san password ɗin da na sakama wayata?." Tayi ma ta tambayar tana nufar hanyar fita daga Bedroom ɗin ya yin da ta dan nawa Jiddarh kira ta wayar, ba damuwa da amsar da Deejarh zata bata tayi ba. Palo ta fita sam bata lura da Lailah dake kwance tayi nisa a Duniyar tunane tunane ba, ta ƙari sa saman 1sieter ta zauna, Deejarh da ta biyo ta a baya tana faɗin "Lallai ma Balarabiyar India ai ba password mai wahala kika saka ba, just 'Perfect' fa kawai kika saka abu mai sauƙin." Deejarh tayi maganar tana zama ganin Afeefah ta fara waya ne, yasa ta mayar da kallon ta kan Lailah cike da mamaki dan ita ma bata lura akwai mutum zaune a palon ba. Sai yanzu. "Hello! da Queen Of Beauty na Kano wato Jiddarh nake magana, ko kuwa ba ita bace, dan kuwa idan ita ce Bala'i zata sha na ƙin ƙara wa..." Dariyar ƙeta Jiddarh tayi daga ɓangaren ta tana faɗin "Tabbas Jiddarh ke a kan layi, wacece ke magana?, idan Queen Of Beauty ta Abuja ce wato Afeefah toh ta riƙe layi akwai labarin da nakeso na bata." Katseta Afeefah tayi da faɗin "Tabbas wannan muryar ta Jiddarh ce mara kirki kawai, wai ma da farko menene kika sakamin da lemon da kika bani ne?." Dariya Jiddarh ta tuntsire da ita, tuna tsiyar da ta shuka, sai da tayi mai isarta sannan ta dakata dan kanta tana bawa Afeefah amsa da faɗin. "Allah kuwa da gangar nayi duk abin da nayi, domin kuwa gani nayi kamar kina damuwa bakyama kowa Magana a wurin anata shagali banda ke. Shiyasa ni kuma na saka miki kwayar da zai sa ki dinga zuba taɗi ko ba'a tambaye ki ba, a lemo sannan na baki ke kuma ƴar qwalama kika kwankwaɗe lemon."🤣 Jiddarh ta ƙari sa maganar cike da shaƙiyanci tana dariya cike da nishaɗi "Inna-lilahi-wa-inna-illahir-raji'un, Aikuwa Queen Of Beauty kin cuceni kin saka na saki baki a wurin da bai kamata ba nayi abin da bai dace ba."😑 Zaro ido Jiddarh tayi cikin Dariya tana tambayar Afeefah abin da ya faru Cike da takaici Afeefah ta kwashe duka abin da ya faru tsakanin ta da Official ta faɗa wa Jiddarh ta ƙara da cewa "Kuma fa yanzu nasan kallon wata Fan's ɗin sa ko kuma wata muguwar masoyiyar sa yake yimin fa." Afeefah ta ƙari sa maganar tana kyaɓe fuska cike da takaici Jiddarh ta cuceta Jiddarh tsaban dariya batasan lokacin da ta faɗo ƙasa daga saman kujerar da take ba, faɗi take "Aikuwa Queen Of Beauty Wannan Drama naki ya kusa kala guda da nawa, sai dai nawa akwai takaici ciki bisa naki fa." "Okay, ke Menene ya faru dake ɗin Afeefah ta tambaya cike da qwulewa na dariyar da Jiddarh take ma ta, ga kuma Deejarh kamar wata mahaukaciya ita ma daga ɓangaren ta tana dariya na jin labarin da Afeefah ta bawa Jiddarh, ita ma Lailah duk da bata cikin yanayi na nishaɗi sai da abin da Afeefah tayi ya bata dariya. Sai da Jiddarh ta saita nutsuwarta sannan ta koma ta zauna sannan ta fara cewa "Queen Of Beauty Ina baki Story mun iso nan Kano lafiya mun sauka a Jirgi ni da Humaira da tayimin Rakiya, anan Airport naga wani haɗaɗɗen Guy ina baki labari kyakkyawa da shi, ƙarshe a kyau Guy nan yake. Kin sanni bana gani na gyale, ganin yadda gaba ɗaya Ƴan matan Airport suke binsa da wani mayen kallo ne, yasa ba tare da shawara ko tunanin komai ba, na cire facemask dake rufe da fuskata sannan na cire After Dress dake saman kayana, nan fa na bayyana cikakkiyar SARAUNIYAR KYAU na, nan hankalin mutanen Airport ya dawo kaina waɗanda suka gane ni suka ƙari so wurin da muke nida Humaira cikin tafiya na gayu, gaba ɗaya suka rufe ni daga masu roƙo akan na tsaya muyi pictures, sai masu bani Biro da takarda wai nayi musu sa hannun ƙauna. Abin takaici wanda nayi hakan danna na burgesa ya bar wurin, amma waɗannan mutanen basu gyaleni ba sai da kyar fa nake gaya miki.." Dariya Afeefah tayi tana tambayarta da faɗin "Ke nan dai idan na fahimta kinyi abin da kika yi ne, saboda ki burge wannan Guy sai kuma aka yi rashin Nasara mutane suka shiga tsakani ko?." "Yes of course haka fa nake nufi." Jiddarh ta bata amsa. Nan dai suka ci gaba da shan fira ko wacce tana bada labarin abin dariya tamkar waɗanda suka yi one Year ko fiye da haka da haɗu wa, bacin sau biyu kawai suka taɓa haɗu wa. Sai da Afeefah ta kammala waya da Jiddarh sannan ta kuma dan nawa Daddyn ta Mister Mai Kyau dake Jamus kira dan tayi kewar sa sosai. "Assalamu Alaikum Daddy wato shi ne koka kirani ko?. Ae nayi fushi ma."😩 Afeefah tayi maganar cike da tsantsan shagwaɓa ga Daddyn nata. Ƙayataccen Murmushi Mister Mai Kyau ya yi daga yadda yake zaune a hamshaƙe saman kujerar sa ta alfarma cikin haɗaɗɗen ofishin sa dake hawa na ƙarshe cikin katafaren company nasa dake can Germany (Jamus). "Wa'alaiki Salam WarahamatuLlahi Wabarakatuhu. Kaina bisa wuya Shalele uzurori ne suka yiwa Daddyn ki yawa sosai, shiyasa ban samu na kiraki ba, sannan ae nayi tunanin Zaynerb ta dawo ne, kodai ba yau ne zata dawo daga Kano State ba?." Wani irin bugu na tashin hankali kuma mara dalili zuciyar Afeefah tayi jin Daddy ya ambaci Zaynerb, ita fa wallahi shaf ta manta yau Zaynerb zata dawo Abuja, cikin sauri ta ciro wayar daga kunnenta ta duba Time 4:50pm hankali a tashe ta mayar da wayar kunnen ta tana faɗin. "Subhanallah, Daddy Anty Zaynerb fa bata dawo ba, nifa gaba ɗaya na manta yau zata dawo, kuma tun jiya da muka yi waya da ita ta ce Yau zata dawo bamu ƙara waya ba fa, wayyo Daddy tsoro nakeji kar wani abu ya sama Anty Zaynerb na..." Jin yadda Afeefah take maganar hankalin ta a mugun tashe ne. Yasa Daddy saurin tarar ta da faɗin. "Ki kwantar da hankalin ki wata ƙilama Zaynerb ɗin ta fasa dawowa Abuja yau ɗin ne fa, amma dai gudun zargi riƙe waya, barina tuntuɓi Uncle Sagir naku muji." Da "Toh." Kawai Afeefah ta amsa masa amma bata tunanin zata iya kwantar da hankalin ta, bacin batasan halin da Zaynerb Yayarta take ciki ba. Tsuru tsuru Lailah da Deejarh harma da Haleesat wacca tashin ta daga Bacci ke nan ta fito palon a gaɓar da Afeefah take faɗin Zaynerb bata dawo ba. "Assalamu Alaikum Babban Yaya. Yau Harkokin Kasuwanci sun bari an tuna damu ke nan, tun da naga kira da Yamma nan." Uncle Sagir ne duk yake waɗannan maganganun cike da farin ciki na ganin kiran da Ɗan uwan na sa ya yi masa. "Sagir ba wawan ne a gabana yanzu ba, wai nace Zaynerb ta fasa dawowa Abuja ne, sai ta ƙara kwanaki ko kuwa, Afeefah ta kirani tana faɗin Zaynerb bata ƙari so ba har yanzu." Cikin sauri Uncle Sagir ya katse Daddy da faɗin. "Zaynerb kuma wata Zaynerb ke nan, wai dama ba tun jiya Zaynerb kuka ce ta koma Abuja ba?." Ya yi tambayar yana kallon Mah'fuz dake zaune gefansa yana jin abin da ke faruwa. "Zaynerb kuma Abhu anya kuwa, ae Zaynerb tun jiya tabar nan, ta ce zata koma Abuja, babu yadda bamu yi da ita ba, akan ta tsaya gari ya waye saboda a jiyan babu Flight, amma Zaynerb taƙi ji saboda taurin kai da Yammacin ta ɗauki Driver da mota suka nufa Abuja, gashi kuma har yanzu Drivern bai dawo ba..." Duk wannan maganar Mah'eesha ce take zubosu a lokacin da ta ƙari sa shiga cikin palon mahaifin nasu sannan ta a je masa kayan maƙulashe da ta kawo masa saman center table. "Inna-lilahi-wa-inna-illahir-raji'un, na shiga ukuna Daddy kanaji fa wai cewa suke Anty Zaynerb ɗita tun jiya ta kamo hanyar zuwa nan, gashi kuma har yanzu batazo ba, Daddy tsoro nakeji kar'a cutar min da Yayata Daddy please kayi wani abu kaji Daddy i'm begging you please Dad say something to me pleased......" Ƙari sa maganar Afeefah tayi cikin tsananin kuka muryarta na fita da kyar kuma cikin wahalar fitar numfashi. "Subhanallah Afeefah menene nakeji kike faɗa ne, wai kina nufin Zaynerb bata dawo ba, inna-lilahi-wa-inna-illahir-raji'un menene ke nan yake faruwa i'm so confusing fa." Uncle Sagir ne yanzu ya yi maganar jin muryar Afeefah da kuma irin abin da take faɗa. "Afeefah! Afeefah!! Kina jina kuwa, please kiyi magana mana?...." "Na'am Daddy ina jinka domin ban mutu ba, tukunna amma muddun ba'a nemo min Ƴar uwata Zaynerb ba. Tabbas Daddy zan iya mutuwa a kowane irin lokaci...." "Subhanallah Afeefah kina da hankali kuwa kin san menene kike faɗa, nace ki kwantar da hankalin ki Zaynerb ba ɓata tayi ba Insha Allah za'a ganta kinji Shalele ta!?...." Tanaso tayi magana sai dai abin da ya tokare ta a maƙushi shi ne ya hanata yi magana. Ji take a maqwoqwaronta tamkar ana jajjagen yaji a ciki duk yadda taso tayi magana abin cutura ya yi. Zubewa tayi a ƙasa sumammiya yayin da bakinta yake fitar da wani irin kumfa tamkar wacca tasha poison. Da gudun tsiya gaba ɗayan su tun daga Haleesat da Lailah har da Deejarh suka ƙari sa kanta suna kiran sunan ta cikin tsananin tashin hankali. Sai dai ina Afeefah ba jinsu takeyi ba domin kuwa tashin hankalin da ta shiga ne yasa ciwon ta yake ƙoƙarin tashi. *TASHIN HANKALI* *WANDA BA'A SAKA MASA RANA* Tofa fi ye da haka gaba ɗaya Ahalin Mai Kyau suka shiga domin kuwa Afeefah ciwo ya tashi kuma yazo da mugun gardama. Yayin da ita kuma Zaynerb an tabbatar da saceta akayi. Sai dai a yadda labarin yaje musu bawai ita kaɗai kidnapper's ɗin suka sace ba harda wasu mutanen. A Ranar da abin ya faru M.MK ya dawo ya biyo ta private jet. Nasa ya dawo ƙasa Nigeria cikin tsananin tashin hankali domin kuwa abin haɗe masa biyu ya yi ga ciwon Afeefah wanda baya jin magani ga kuma ɓatar da Zaynerb tayi. gaba ɗaya yabi ya fita hayyacin sa, danma wani abun Maleek ne yake yi da kansa musamman akan binciken nemo inda Zaynerb take. Gaba ɗaya Ahalin sam basa cikin kwanciyar hankali na abin da yake faruwa, tsawon kwanaki uku ke nan da sace Zaynerb kuma babu ita babu labarin ta, sannan kidnapper's basu kira sun faɗa adadin kuɗaɗen da suke so a basu ba. Wanda hakan yasa aka fara zargin da wuya idan saboda kuɗi suka yi Kidnapping nata. Babu shiri gaba ɗaya Ahalin Uncle Yusuf suka tattaro suka dawo Abuja Gidan Mister Mai Kyau da zama har zuwa Ranar da kidnapper's ɗin zasu kira su faɗin Abin da suke so. A 6angaren Momy Rafi'at kuwa za'a iya cewa tafi kowa shiga tsananin damuwa na sace Zaynerb da aka yi da kuma ciwon Afeefah. Sai dai na ciki na ciki, Dan ita kaɗai tasan Gadar Zaren da take shiryawa *WANNAN KE NAN* *KAƊAN DAGA CIKIN IRIN HALIN DA AHALIN MAI KYAU SUKA SHIGA SAKAMAKON KIDNAPPING ZAYNERB DA AKAYI* *ZAYNERB*😣 "Na kammala fa." Tayi maganar tana kawar da idanunta da kallon sa, sai dai cikin rashin sa'a suka shiga cikin na Yarinyar da yake tare da ita kuma ta ambaci kanta da matar sa. Rumtse idanun nata tayi ƙam tana nuna kalar baƙar wahalar da suka sha hannun waɗannan kidnapper's. A lokacin da ɗaya daga cikin su ya sanar police sun sama labarin wurin suke, cikin gaggawa gaba ɗaya kidnapper's ɗin, suka tattara mutanen da suka yi Kidnapping, cikin wasu motoci tamkar awaki haka suke zuba mutane a motocin. Sannan suka bar wurin dasu, tsawon kwanaki biyu suna tafiya dasu suna shiga dasu cikin tantagaryar daji, sannan bayan shafe kwanaki biyu da sa'o'i suka ƙari so da su wani ƙurman gida ƙaton gaske cikin dajin. Sosai mutum zai yi mamakin ganin irin wannan gida a daji. Cikin gidan suka shishshiga dasu Zaynerb kamar wasu awakai, sannan ne aka fara neman wanda zai cire wa Aasief harsashin dake ƙafarsa, da muka wata Budurwa ita ma da alama tayi musu taurin kai ne, suka harbeta a kafaɗa. A lokacin cike da Qwarin gwiwa Zaynerb ta ce dasu ita likita ce saboda haka zata iya kula da masu raunuka. Ba tare da ɓata lokaci ba suka ware ma ta wani ɗaki a cikin gidan sannan suka kai ma ta kayan aikin da zata buƙata. Nan ne fa da shigarsu ta fara ƙoƙarin cire masa harsashin. Ta sha wahala sosai sannan da kyar ta samu ta cire tana haɗa uban haɗa gumi sannan take cewa da shi ta kammala. A hankali ya janye ƙafar tasa yana rumshe idanu saboda azaba. "Karka damu na haɗa maka da Allurar kashe zafi, zuwa anjima zaka nema zafin ka rasa." Zaynerb tayi maganar ba tare da ta kallesa ba, bayan ta buɗe idanunta sannan ta ƙari sa wurin ɗayar Budurwar da aka harba a kafaɗa. Cikin taimakon Allah Zaynerb ta samu tayi ma ta treatment da ya kamata, sannan ta kalleta tana ƙare wa irin shigar dake jikin Budurwar kallo, ta tambaye ta "What is your name?." Tayi ma ta maganar da turanci ne dan ta fahimci da wuya idan tanajin Hausa "Samiupter D'Souza..." Budurwar ta bata amsa. "Daga wata ƙasa kike, kuma menene ya kawoki nan ƙasar, sannan garin ya ya waɗannan mutanen suka yi Kidnapping naki?." Zaynerb ta jero ma ta tambayar kamar wata ƴar jarida idanunta akan Budurwar da ta kira kanta da ' Samiupter '. "Ƙasar Indiya nake yanki kudanci, nazo Birthday Party na ƙawata ce, a hanyar mu na zuwa Abuja daga Kano waɗannan mutanen suka yi garkuwa damu, kuma sun kashe Ansha, dama tare da ita nake. Ta ce zata rakani Abuja saboda ban san kowa anan ƙasar ba."😭 Cikin kuka Samiupter ta ƙari sa bawa Zaynerb labarin muryarta har dashewa tayi saboda tsananin tashin hankali da wani irin hali da take ciki. Rungumo ta Zaynerb tayi tana lallashi cike da tausayin ta. Yayin da shi kuwa Aasief ido ya zubawa Zaynerb ɗin yana kallon ta. Neelarh kuwa tuni baccin wahala ya yi gaba da ita tana daga gefen sa ta jingina da kafaɗarsa. "Zaynerb kin canza sosai kamar bake ba, kuma ban san dalili ba, kece kika yimin laifi, amma ni kika ɗaura wa laifin..." A hankali Zaynerb ta juya ta kallesa jin irin maganar rainin wayo da yake son kawo ma ta, ranta a ɓace ta basa amsa da faɗin. "Aasief kaine ka canja ba kamar yadda na sanka ba, ka canja daga Aasief mutumin kirki dana sanka, gaba ɗaya halayyar ka basu yi ba, ban taɓa tunanin ka da irin halin da na tsinceka ciki ba a wancan lokacin, ka rasa wacce zakayi Alaƙa da ita sai wannan Arniyar Erisha haba wallahi ka bani mamaki ba kaɗan ba." Zuwa lokacin kansa ya fara ɗaurewa da kalaman Zaynerb, sam bai fahimci abin da take nufi ba kwata kwata. "Kiyimin bayani yadda zan fahimta, nifa cikin ruɗani kawai maganganun ki suke jefa ni, dan ban san inda suka dosa ba sam." Wannan karon kallon sa tayi da kyau idanunta na cika tab da kwalla take faɗin. "Haba mana Aasief ya kakeso ka mayar dani shashasha ce, ko an gaya maka wancan Ranar da kace na sameka Gidan ka banga komai bane?." "Me kike nufi ne Zaynerb, wacce Ranar kuma?." "Kaji ko ƙara raina min wayyo kakeyi fa, wancan Ranar mana da dare da saƙon ka ya shiga wayata kana faɗin nazo Estate naku gidan ka, ko kuwa dai ka manta Ranar?...." Dafe kansa dake mugun sara masa Aasief ya yi wani tunani tana ɗar suwa a Ransa, cikin sauri ya kalleta don ya ƙara tabbatar da tunanin sa, yake tambayarta da faɗin. "Ina jinki a Ranar menene ya faru da ki ka zo Estate bayan kin ƙari so Room nawa, menene ya faru, please Zaynerb Tell me anything everything, please ki faɗa min duka abin ya faru da kuma wanda kika gani?." Cikin tsorata da irin yanayin da ya fara shiga, idanun sa sun yi jajur na ɓacin rai Yayin gaba ɗaya jijiyoyin kansa suka tatashi, kai kana ganin sa kasan ransa ya yi matuƙar ɓaci. Bai damu da kalar raɗaɗi da kuma jinin da ƙafarsa da aka harba take fitarwa ba, ya miƙe tsaye ya ƙari sa wurin ta. Jijjiga ta yake yana roƙon ta akan ta faɗa masa abin da ya faru a lokacin, ihu da kuma maganar da yake ma ta da ƙarfi yana jijjiga kafaɗunta ne, yasa Neelarh da Samiupter suka farka daga ɗan baccin da ya fara ɗaukar su a firgice suna zazzare ido cike da tashin hankali. Wani irin ban ko ƙofar akayi Sannan wannan ƙaton Gardin wato Gaddafi ya shigo ɗakin cikin ƙatuwar muryarsa kuma cike da bala'i yake faɗin. "Wani mara rabon ne, yake mana ihu anan wurin, da alama ya gaji da rayuwar sa ne..." Ya yi maganar ne yana ƙari sawa wurin da Aasief yake a durƙushe bai dena jijjiga Zaynerb yana faɗin ta faɗa masa gaskiya ba. Cike da tsantsan mugunta ƙaton Gardin yakai hannu ya finciko Aasief ya miƙar da shi tsaye sannan ya saita bakin bindigan hannunsa a ta bayan Aasief ɗin yana ƙoƙarin juyo da shi. Cikin Wata kalar da fusata da zafin nama Aasief ya juya gaba ɗayansa sannan ya dunƙule hannayen sa yakai ma masa wani wawan naushi a ido. Zubewa Gaddafi ya yi ƙasa cike da azaba idanun sa na fitar da jini. Bin sa ƙasan Aasief ya yi Dan bala'i, yana kai masa naushi a fuska ta wurin da ya tabbatar yana masa rauni, cikin wata kalar murya kakkausa yake faɗin. "Dan uban ka ina tambayarta abin da ya faru shekaru biyar baya, shi ne zaka shigo tsakani da wannan jahilar Muryar taka, wato dama bakasan haushin ka nake ji ba, kaine ka harbeni ko zakaci uban ka yau." Maganar Aasief yake yana kuma kai masa naushi a ta ko'ina na fuskar sa, Aasief bai dena dukan Gaddafi ba har sai da yaga ya daina motsi alamar ya suma... Sannan ya dakata sannan cikin fitar da huci na mugun ɓacin rai ya juya kamar wani kububuwa yana kallon Zaynerb wacce ganin abin da yake yi, yasa idan banda rawa babu abin da gaba ɗaya ilahirin jikinta yake yi, tun kafin yace da ita komai ta fara masa bayani. Cikin lokaci ƙanƙani Zaynerb ta koroma Aasief gaba ɗaya bayanin abin da ya faru lokacin da taje Room nasa, ta faɗa masa irin tashin hankalin da ta shiga da kuma irin maganar da Erisha ta faɗa ma ta. *Aasief* Wani wawan naushi ya kai ma bangon ɗakin wanda har sai da gaba ɗaya ɗakin ya amsa. Idan banda huci babu abin da Aasief yake yi tunda yake a Duniya ransa bai taɓa ɓaci ba irin na yau. Wai ashe duk waɗannan shekarun da aka kwashe idan Zaynerb zata tuna sa, tuna sa take yi a matsayin Mazinaci mayaudari.... Inna-lilahi-wa-inna-illahir-raji'un Zubewa ya yi a ƙasan idanun sa na fitar da ruwa. Miƙe wa ya yi a fusace ya fara zagaye ɗakin faɗi kawai yake. "Saina kashe Leo, Tabbas da hannuna zan kashe Leo da wancan kafirar Erisha ko tabbas sai nayi musu KISAN GILLA." Tabbas indai lissafin sa ya tafi dai dai yadda tunanin sa ya basa ke nan dai Leo da Erisha su ne suka shirya komai na abin da ya faru tsakanin sa da Zaynerb... "A wancan Ranar ba Ni ne na turo Miki da wannan saƙon ba, domin kuwa sace wayata akayi a Ranar, nasha wahala sosai wurin neman ta amma ban gani ba, haka na haƙura na nufi hanyar komawa gida cikin motata a hanyar ne na haɗu da Accident, ban farka ba sai washe gari na ganni a Room na ga Leo a gefe na, yana faɗa min wai a Hanyar sa na komawa gida ne, ya ganni nayi Accident shi ne kawoni gida..." Shiru Zaynerb tayi tana sauraren abin da yake faɗa ma ta kuma yana ma ta maganar bada kakkaurar murya ba, cikin murya ma dai dai ciya yake ma ta bayanin. "Dama Leo yasan Estate naka ne?." Zaynerb ta tambaya har lokacin jikinta bai bar rawa ba, ga kuma siraran hawaye da suke bin fuskarta. "No bai sani ba, kuma a lokacin ban tambaye sa ta ya akai ya sani ba." Da bata amsar, miƙe wa ya yi tsaye yana gogen jinin dake fita a ƙafarsa. "Ku taho muje..." "Ina ke nan?." Zaynerb ta tambaya tana kallon sa cikin faɗuwar gaba. "Barin nan zamuyi, ada banyi niyyar guduwa ba, amma wannan labarin da kika bani yasa na yanke shawarar mu gudu saboda banaso Leo yakai Yammacin yau bai mutu ba." Zaro ido Zaynerb tayi cikin tashin hankali bakin ta na rawa take faɗin "Mu-mummtuwa fa kake faɗa....." *ABUJA* *Haleesat* Baya tayi ta jingina kanta da kujerar motar ta, idanunta akan Babban Ofishin bincike reshen manyan laifuka dake Abuja. C.I.D. Sosai ta shiga matsanancin tashin hankali da kuma damuwa na sace Zaynerb da kuma rashin lafiyar Afeefah. Wanda sanadin haka ne koda University bata samu taje, cikin haka ne wata ƙawarta ta bata shawarar zuwa ofishin c.i.d. domin basu report duk da cewa shima Daddy yana iyakar bakin ƙoƙarin sa haka ma Maleek. Ranar ta fito daga bathroom ta duba wayarta nan ne taga message da Maryam ta turo ma ta, cikin hanzari ta buɗe ta fara karantawa. "Sunan sa Suhais Sulaiman Interval, just 'Interval' aka fi sanin sa da shi. Rank Officer. Batch Number T3,783 :: D8... Specialization. Shekarun sa Twenty something..... D.O.B...... Iya kar abin da na sani akan sa na faɗa miki, kije wurin sa Insha Allah zai taimaka da nasa binciken domin shi ɗin qwararren Jami'i ne wanda yasan makamar aikin sa, sannan bayada wata matsala." Ajiyar zuciya Haleesat ta sauke a lokacin bayan gama karanta saƙon. Nan ba tare da ɓata lokaci ba tana gama shiryawa ta ɗauki mota ta tuƙa har zuwa Babban Ofishin. Koda isarta ofishin ta nema a haɗa ta da shi. Da farko Jami'in ƙi ya yi, amma tana faɗa masa Wanene mahaifinta a ƙasar, cikin rawar jiki ba tare ɓata lokaci ba, shi da kansa Jami'in ya kaita har gaban Yallaɓan Officer Interval, sai dai kuma menene zai faru bayan ganin sa da Haleesat tayi?..... *What Next* _______💓💓💓 The Nainarh Kd 💓💓💓_________ Sam Haleesat ta kasa nutsuwa tayi masa bayani yadda ya kamata a lokacin, sakamakon ganin wannan jami'in ba kowa bane fa ce, Mutumin da ta haɗu da shi a Mashaya, kuma tayi Drawing face nasa As masoyinta sannan kuma take ƙaunar sa har tayi masa laƙani da Souvenir.... Doguwar ajiyar zuciya taja bayan ta kawo nan da tunanin nata sannan ta saka hannu ta buɗe motar ta fito. Kai tsaye office nasa ta nufa domin kuwa shi da kansa yace ta dawo yau akan binciken nasu. Sallama ɗauke a bakinta ta shiga cikin haɗaɗɗen ofishin. Amsa wa ya yi ƙasa ƙasa idanun sa akan Laptop dake gaban sa, ba tare da ya kalle ta ba. Zama tayi ƙoƙarin yi a kujerar dake fuskantar sa, sai dai jin muryar sa da tayi ne yana magana, yasa ta miƙewa tsaye da sauri tana sakin Murmushi domin kuwa ayyana wa kawai take yi anga Zaynerb an wuce wurin. "Mun sama labari akan wani wuri da ake zargin kidnapper's sun ɓoye Kansu ciki, yanzu haka can wurin zamuje, idan ya kasance anan cikin Abuja ko kafin Abuja aka sace ta, Confirm zai iya yiwuwa waɗanda muke zargi ne, idan kuma tun acan Kano ɗin ne..." Katse sa tayi da faɗin. "Bana tunanin anan Abuja aka yi Kidnapping nata, sai dai kuma ban sani ba, yanzu ne zamu tafi can ɗin?." Kallon ya yi a nazarce kuma a gajarce jin abin da ta faɗa. "What do you mean, do you think dake zamu tafi, ko kuma mene?." Dariya tayi na rainin wayo tana basa amsa da faɗin. "Of Course Ƴar uwata ce fa aka sace, idan ba'a tafi binciken nemo ta dani ba, ina kake tunanin za'aje dani?." Haleesat tayi maganar da gaske kuma fararen idanunta tar akan sa. Shigowar da wani jami'in ya yi yana faɗin, "Sun gama shiryawa shi ake jira ne." Yasa ya dakata daga kallon ta sannan ya miƙe tsaye ya ɗauki bindigarsa yana gyara alburusan ciki. "Yauwa idan ka gama gyarawa nima ka miƙomin tawa bindigar Yallaɓai Officer." Haleesat tayi maganar a dake kuma tana masa nuni da gaske take binsu zatayi. So yake yaga iya gudun ruwanta da iyakar taurin zuciyar ta da jarunta. Saboda haka ba tare da yace da ita komai ba, ya miƙa ma ta ƴar ƙaramar bindigar da ya fito da ita daga cikin locker a ofishin. Sai dai ga mamakin sa karɓa tayi tana gyara zaman alburusan ciki. Cike kuma da tsantsan qwarewa, tamkar dama can ta saba da amfani da bindigar. Toh haka ma koda aka zo tafiya, dagewa Haleesat tayi akan dole dole da ita zasu tafi, idan kuma sun ƙi zata kira Daddyn ta faɗa masa. Zuwa lokacin ran Interval ya fara ɓaci sai dai ya shanye. Bisa umarnin na sama da shi a aikin wato Chief Murtala Dawood da yake shugaba a duka Ofishin badan Interval yaso ba. Haka suka kama hanyar zuwa can wurin samamen da zasu kai tare da ita, bayan an bata rigar tare alburushi ta saka kamar dai sauran Jami'an. Duka su takwas zasu tafi sumamen duk da Haleesat ce suka zama tara, sai kuma wata mace ita ma Jami'a ce amma ta kasance Likita ce tana taimakawa waɗanda suka sama rauni a filin da ga. *Aasief* Da dabara da taimakon Allah suka samu suka fito daga cikin wannan Gabjejan gidan, yana saɓe ne da Neelarh wacce a lokacin da suka zo fitowa daga gidan, wani daga cikin kidnapper's ɗin kuma mai kula da gidan ya gansu. Ya saita bindigar sa zai harba Aasief ita kuma ta tare, harsashin ya wuce ta saitin kunnen ta da wani ƙara fiiiooo, wanda dalilin hakan ji da ganinta na ɗan lokaci ya dakata, tayi ƙasa zata faɗi, Aasief ya tarota bayan yakai ma mutumin mahangurɓa ɗaya ya zube sumame. Zaynerb kuwa hannunta yana cikin na Samiupter ne, yayin da ɗayan hannun ke riƙe ƙam cikin na Aasief. Gudu kawai suke falfalawa na tashin hankali, gudun suke amma tamkar basa yi, tun kafin Rana ta sauka suke gudu basu dakata ba, har sai da duhu ya yi gaba ɗaya dajin ya gauraye da duhun dare. Cike da tsananin gajiya suka zube bakin wata doguwar hanyar da ta rabu gida biyu ɗaya yabi left ɗayan Kuma right. "Wayyo Allah na shiga ukuna ni Zaynerb wannan wata kalar mummunar ƙaddara ce, inna-lilahi-wa-inna-illahir-raji'un, Allah ka kawo mana ɗauki..." Maganar take yi a galaɓaice cikin fitar hayyaci idanunta suna buɗewa da rufewa da sauri sauri kuma lokaci ɗaya. Dukkansu sun sha wahala sosai, wahala kalar wacce ko wannensu bai taɓa tunanin zai shiga makamancin ta ba a rayuwa. Especially ma Samiupter D'Souza ita da take Bama ƙasar take ba, amma da yake haka zanen ƙaddara yake gata yau ta wayi gari cikin wani hali. "Neelarh kiyi haƙuri Kinji, duk ni ne na janyo kika shiga halin da kike ciki a yanzu, da'ace nayi haƙurin mintuna talatin kacal mu sama jirgi da duk ba hakan ba." Zaynerb uban tagumi ta zabga hannu bibbiyu tana kallon sa, yayin da wasu hawaye waɗanda ba za ta ce na Menene ba suka cicciko ma ta a idanu. Allah Sarki ita, ga ita Neelarh tana ma da wanda zai kalleta ya bata haƙuri ya lalleshe ta As a partner. Ita kuma fa, one zero ke nan, ko kafin ta an kara wasu hawayen sun ƙara wanke ma ta fuska. "Allah Sarki Afeefah ta, wayyo rayuwa da ƙaddara Daddyna kuyi haƙuri nasan kun shiga damuwa sosai, amma ni nasan kaso Tamanin bisa ɗari na abin da yake tsakiya da faru dani, ni ce ma jawa kaina tabbas..." Ƙarishe maganar zucin tayi cikin ƙunar rai da kuma tarin da tasani mara amfani, mugun fusatar zuciya ta kaita ta baro. Kallon Samiupter dake kwance tayi ɗai ɗai a tsakiyar kwalta Zaynerb tayi tausayin kanta dana Yarinya yana ƙara cika ta. *SHIN ZAKU IYA YARDA IDAN NACE A WANNAN WURIN SUKA KWANA GABA ƊAYA?.....* Tabbas haka ne da gaske anan wurin suka kwana cikin duhu da cizon sauro ga sanyi, gashi cikin daji, gaba ɗaya Ƴan matan saman jikin Aasief ko wacce ta sama wurin maƙalewa, sakamakon wani irin tsoro da suke ciiki da ji, domin kuwa can cikin dare suka dinga ji kamar muryoyin mutane cikin kuka, ko kuma da ƙarar raki marasa daɗin sauraro, hardama ifa ce ifa ce na mutane dana dabbobi harma dana Alhan.👹 Shima Aasief dan ya cika cikakken Namiji ne, haka suka kasance sun kwanta a wurin maƙale da shi kowacce tana sakin numfashin wahala cikin bacci, yayin da shi kuwa Aasief haka ya kwana idanun sa a buɗe, domin kuwa bai ga sukunin da har zai samu ya yi Bacci ba. Koda gari ya waye haske ta ko'ina tan garas, haka gaba ɗaya su ukun suka yi tai mama suka fara jero sallolin da babu adadi, sannan kuma ta inda zuciyarsu ta raya musu nan ne Alƙibla. Yayin da Samiupter tayi tsuru tsuru tana kallon su. Basu motsa daga wurin ba, koda suka idar da Sallahr a wurin suka dakata ko zasu sama wani na kirki da zai biyo hanyar. Toh kodama sunce zasuyi gaba basu san wacce daga cikin hanyoyin da suka rabu biyu zasu bi ba sam. *RAYUWA KE NAN*😓 Wai yau an wayi gari ga Zaynerb Mai Kyau tsakiyar titi tana neman taimako, wanda zai rage musu hanya. Faɗi take..... "Taimako a taimake mu Dan Allah ku tsaya ku taimake mu mutane mu wayyo mu tsaya...." Haka kawai take faɗa cikin yarfe hannu a tsakiyar titi, Aasief yana daga gefan ta shi ma yana iyakar nasa ƙoƙarin wurin ganin sun sama na kirki da zai taimaka musu. Cikin yardar Allah kuwa wata babbar mota irin na kiwon shanu ta taho zata wuce ta hanyar. Ihun neman taimako da Zaynerb keyi Neelarh na tayata ne yasa Driver motar ya dakata sannan ya fito daga motar shi da karen motar (mai kula da fasinjoji) da farko a tsorace suka fito, ganin mutane tsakiyar titi mata uku da Namiji suna neman taimako, ga Zaynerb wacce fuskarta tayi buɗu buɗu da ƙura, idanunta sun yi zuru zuru dasu. Ta zama kamar wata Dodo da ita.😟 Amma daga ƙarshe da suka fahimta bayan ƙari sawa wurin da suka yi, Zaynerb ke faɗa musu su taimake su kidnapper's ne suka yi garkuwa da su yanzu sun samu sun kubta ne da yardar Allah. Kuma Abuja suke so a ƙari sa dasu. Jin abin da Zaynerb da ta fi zaƙewa ta faɗa ne yasa karen motar yaji tsoro yana shirin arcewa ana kare.😆 Amma sai Drivern ya dakatar da shi, sannan cikin tausayawa Dattijon Driver da bazai haura shekaru hamsin da ɗauriya ba. Ya kalla Zaynerb yana miƙa ma ta gorar ruwa da ya ɗauko, sannan yana faɗin. "Karku damu Yarana Insha Allah kun tsira tunda har kun haɗu damu. Dama kuma Abuja muka nufa kai tsaye." "Masha Allah, Mun gode sosai Baba da wannan taimakon." Cewar Aasief yana shafa kansa, sannan yana miƙowa Neelarh gorar ruwa da Zaynerb ta basa bayan ta sha, ba tare da ya sha ba. Kwankwaɗar Ruwan Neelarh tayi sosai, sannan tabawa Samiupter ita ma tasha cikin wahala, dama magwogwaronta a mugun bushe yake ga yunwa. Nan batare da ɓata lokaci ba gaba ɗaya suka shishshiga motar a baya, don gaba ya yi musu yawa a bayan wurin da shanu da tumaki suke zama nan suka zauna, wai danma babu dabbobin a motar ne, sunje kudu sun siyar sun dawo, shi ne fa a hanyar suka haɗu dasu Zaynerb ɗin. *RAYUWA KE NAN WAI YAU GA ZAYNERB MAI KYAU KWANCE CIKIN MOTAR KWASAR TUMAKI.*😭😭😭 *TABBAS KIDNAPPING SU ZAYNERB DA AKA YI, SHIRYAWA AKA YI,😣 SAI DAI WANENE YA SHIRYA HAKAN?.*🥺 🔥*WHO IS THE MASTER PLANNER??*🔥 Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels