Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels *👩‍❤️‍👨💞 WAYAFI K'AUNATA 👩‍❤️‍👨💞* (Love Story) PAID BOOK #500 MALLAKIN *©ZAHRA ROYAL STAR* *Littafin kud'i ne wadda ya shirya yin tafiyar dashi zai iya turo kud'insa, ko katin MTN ko hoton katin saika turo shaidar biya #500 ne kacal* 8130479973 *FATIMA RABI'U OPAY BANKA* Zaka turo shaidar biyanka ko hoton katin ta wannan number d'in, (08130479973.08035023054) Free Page 1-2 بسم الله الرحمن الرحيم العالم Gombe state Kauyen AKKO, Babban kauye ne kusan ma kamar Local Government ne Amma ba a bashi LGA ba, garine na fulanin asali kana Shiga ba sai an fada maka ba, Maryam Muhammad Amadu mai Shano shine cikakken sunana na tasu cikin Babban gida mai d'auke da sassa daban-daban Amadu mai Shano shine asalin mai gidan yana da matarsa guda d'aya mai suna Kubura wacce muke kira da Iya, da y'ay'a biyar Baffah na Muhammad, sai Kawu Sule shine mai bima Baffa na sai Kawu Iro sanan sai Kawu Mamman sai autar su Gwaggo Fati, dukan su mazan a cikin gidan suka yanki fili ko wanne da shashinsa dukan su suna da aure Kawu Sule yana da mata Rabi da y'ay'a biyar Abbas shine Babba sai Mansur Hafiz sai Gaje da Hajara itace auta , sai Kawu Iro yana da mata mai suna Hindatu da yara uku Naja'atu Sa'ida sai dan auta Ismail, Kawu Mamman shima yana da mata da yara guda biyu, Khamis, sai Zeena, takan bar y'arta Zeena ta kula dani, tun sadda na taso na taso na tarar da kaina a cikin gidan Baffah na ya rasu tun ina k'arama, Umma na kuma ta fita daga cikin gidan Amadu mai Shano tayi wani auran, ta barni wajan dangin Baffa na tun tasowata gidan mu hud'u ne sa'anin juna ni sai Naja'atu sai Hajara da Sa'ida sannan Zeena tun farko na kasance rikon kaka dan haka na taso ba kyara ko tsangwama a gidan bani da matsala da kowa sai Inna Rabi wato matar Kawu Sule ta tsaneni a gidan a cewarta wai na tare wa y'an uwana jin d'umin Kakarsu Iya dan haka nakan d'an jima ban lek'a sashin Kawu Sule ba, duk da kasancewar shid'in da yaransa suna matuk'a sona idan aka cire mutum d'aya Ya Abbas ya tsane ni kamar mi baya ma son gani na nima na taso da tsananin tsoronsa mugune nak'in k'ari a cewarsa na fiye shagwab'a da son jiki dan haka sam tamu batazo d'aya dashi ba, a duk sanda yazo garin hutu da yake yana karatu ne can cikin birni, nakan sha jinin jikina har sai ya koma nake samu na sake bani kad'ai bama duk yaran gidan tsoronsa suke, sai Ya Hafiz shi yana matuk'ar kulawa dani sosai duk sadda zai fita ya dawo da kalar tsaraba da zaiyi min duk sadda zai shigo sashin Iya da murna nake tarbarshi, tunda Inna Rabi ta nuna bata son duk wani d'anta ya nuna min kulawa, sai ya rink'a cewa Iya yayiwa tsaraba, amma duk haka tana ankare da yadda Ya Hafiz yake nuna tsananin kulawa a kaina tayi fad'an harta gaji kullum idan tana mai fad'a ta rink'a cewa Ya Abbas ne kawai shine ya d'akko halinta dan gani take yasan abinda take so yasan abinda bata so, shi ko a duk sanda tace haka basarwa yake abunda ta kasa ganewa ga yaron nata shid'in sawun keke ne, baka gane gabansa bare bayansa, sanan ya kasance miskili ne ba kowa yake ganin dariyarsa ba a duk yaran gidan amma kuma ni a yadda nake gani duk yafi tsana ta akan kowa, Gwaggo Fati dake aure a can cikin birni a wajanta yake zaune yana karatunsa,sauran mazan gidan duk anan sukai karatun nasu, shi yasa nafi zuwa sashin Kawu Mamman a kullum can nake yini matarsa bata da matsala ta d'auke ni kamar ita ce ta haife ni, dan haka shi yasa nafi sakewa da ita, Kakata Iya Mai dogon zango tana k'ara sona ita ko Inna Rabi tana k'ara tsanata da d'anta Abbas yayin da Ya Hafiz ke nuna min tsantsar kulawa a gefe guda wasu har sun fara zargin ko sona yake, ga K'awaye na kuma y'an uwana abokan wasana suna d'ebe min kewa, Irin wannan rayuwar ke gudana a ahalin Amadu mai Shano wannan kenan mu shiga cikin labarin kai tsaye. Tafiya muke gaba d'aya y'an matan gidanmu tasowar kenan daga islamiya, cike da farin ciki muka shiga cikin gidan namu sai dai, fara'ar tamu ce ta rage shigarmu gidan jin yaran gidan na cewa wai Ya Abbas ya zo yau, wani irin miyau na had'iye dan nasan had'uwar bata dad'i, ko wanne b'angaransu ya nufa daka kallemu kowa ya k'ara shiga taitayinsa jin Boss ya iso gari Allah ya gani har bamu so yazo garin saboda bak'in halinsa. Kai tsaye sashin Kakata na, nufa tun waje nake faman kiranta ina faman cewa "Iya ta na dawo kina ina ne", wani tsaki naji anja daga baya na da sauri na waiga ido na ne yayi min tozali dashi, dake zaune kan tabarma, alama gaida Iya yazo yi, bud'e baki yayi cike da miskilancinsa ya ce "wai ke yaushe zakiyi hankali ne kullum kina girma amma ba hankali, yanzu da kike kwala mata kira muryarki na tashi kamar ba mace ba, baki iya bari ki k'ara so gaki ga ita kina abu sai kace mahaukaciya" zunb'uro baki nayi ina k'unk'uni Allah ya gani da nasan yana wajan Iya da bazanyi ganganci shigowa ina kwala mata kira ba, Iya dake fitowa duk taji mi yake cewa tana sababi tana cewa "wai ni kam Abbas miye wannan yarinyar ta tare maka ne kasa yarinya a gaba ka hanata rawar gaban hantsi, bana son irin haka fa, idan takurata kazo kayi tashi-tashi bana son gaisuwar, haka kawai abi a takurama marainiyar Allah", tashi yayi ya fice yana murmushi dan ya saba da matsifar Iya indai aka tab'a wannan yarinyar Maryam, Niko cike da farin ciki Iya ta shigar min na rungume ta cike da shagwab'a na ce "Iya tun d'azo nake d'okin ganinki shine fa dama na sanar dake ashe wannan Ya Abbas d'in yazo ni banso zuwansa ba wallahi", na idasa maganar ina kwab'e fuska, dariya tayi tana saki na ce "keni sake ni uwar son jiki kamar mage kuma ki rage shiga harkarsa kinsan abun kad'an yake jira dama ya had'a ku", zunb'uro baki nayi ina bubbuga k'afa na ce "amma Iya ai kinsan bana shiga harkarsa shine ma yake shiga tawa kifa duba tunda na shigo ko lura banyi dashi ba amma ya fara zazzaga min matsifa sai kace jirana yake", "jiran naki yake mana kinga ki wuce ki cire kayan islamiyar nan ga abinci can ki wuce kici ki manta da al'amarinsa fad'anku ai baya k'arewa na rasa mi yasa hakan", cewar Iya. *KADUNA* POV Zaune take akan cinyar mijinta sai zuba mai shagwab'a take k'ara rungumeta yayi, cike da tsananin sonta ya ce "Ohh my Noor kina ritani da shagwab'ar nan taki fa minene kake so", shafa d'an k'ara min sajenshi tayi tana kallon cikin idonsa cike da son mijin nata ta ce "to ai sonka ne yake azalzalar zuciya ta indai muna tare sai kayi hakuri da rigimar tawa", ta idasa maganar cike da wata shu'umar murya wacce ta kashe mai jiki da ruhi "Ohh my Noor wannan salon naki shi yasa kullum kike k'ara shiga raina", cewar Ramadan, Tashi tayi tsaye daga ita sai wata y'ar ficiciyar riga iya gwaiwa, ta fara d'an tafiya cike da jan hankali, binta yayi da kallo kamar wani tsohon maye yana lumshe idanuwansa da suka fara canza launi. Suna cikin wannan yanayi kamar daga sama suka tsinkayi muryar Ya Aysha cike da tsana Aysha ke bin Munnira da kallo, ganinta da wata y'ar ficiciyar riga yasa cike tsanarta ta ce "to makira ai da wa'innan y'an iskan kayan naki irin na karuwan farko kika gama da K'anina tashi ki bamu waje ina son magana dashi" ta idasa maganar tana warga ma Munnira dake tsaye hararara Munnira kuwa wani irin kuka ne take jin na shirin taso mata, da gudu tayi uwar d'aka Allah ya gani dangin mijinta basa sonta, hatta uwar mijinta, sun taso ta gaba, daga aure duka shekararsu biyun dayin auran har sun fara mata gorin haihuwa abun na mugun ci mata rai bata da matsala da mijinta amma danginsa sune babbar matsalar ga abunda ke k'ara mata fargaba suna son tusamai dole sai ya k'ara aure gani suke kamar ta asirance masu d'an uwa abunda basu sani ba tsantsar kulawa ce da take ba mijin nata, kuka ta fashe dashi tana fad'awa kan gado. Ramadan dake zaune rantsa idan yayi dubu ya b'ace, wallahi baccin Ya Aysha Yayarsa ce da sai ya mata rashin mutum ci, kodan sunga kusan shine k'ara mi a cikin su shine zasu rink'a wulak'anta mai mata, d'aure fuska yayi tamau, zaunawa tayi kusa dashi tana tab'e baki tana cewa "ai dole ka d'aure min fuska mana an tab'a y'ar gwal to sak'on Hajiya ne ta ce a gaya maka ta baka nanda sati d'aya kaje tana son ganinka, kuma zata kawo ma matar da take so ka aura dan baza mu zuba ido mu barka da wannan shu'umar matar taka ba ehe" wani irin kallo yabi Aysha dashi cike da tsananin b'acin rai ya ce "ni gaskiya bana da niyar k'ara wani aure wai mi Munnira ta tsare muku ne ni banga wani abunda take muku na rashin dacewa ba sai ma k'ok'ari take taga ta kyautata muku, amma bakwa gani ya kuke so tayi ne wai?" ya idasa maganar cike da tausayin kansa da kuma matarsa yasan halin Hajiyarsu muddun ta tsani mutum to ya bani idan taso abu kuma sai anyi Aysha kuwa da ta tashi cike da matsifa ta ce "kaga dakata Ramadan bani ce zaka ba wannan amsar ba Hajiya zakaje ka bawa kuma da kake kare matarka uban mi take a cikin gidan nan idan ba taci ta kwanta ba Mtsww aikin banza kawai tama ji da kyau wallahi sai Halima ta shigo gidan nan" tana idasa maganar ta fice daga cikin gidan. Ramadan kuwa zaro ido yayi yana mai-maita Halima badai Halima d'iyar Kharima ba k'awar Hajiya ba wadda bai san Kharima da bin bokaye da Malaman tsubbu ba, yanzu irin wannan matar take so ya aura idonsu ya rufe basa ganin gaskiya. Cike da tashin hankali yake kallon Munnira dake tahowa tana zama kusa dashi taci kuka kamar ba gobe idonta sunyi matsifar ja, d'an kwantawa tayi jikinsa cike da tausayi ya k'ara rungumeta zai bud'e baki yayi magana ta tari lumfashinsa ta ce "mijina basai kace komai ba na sani ba laifinka bane sana kayi biyayya ga abunda Hajiya ke so shine zaka ga dai-dai bazan tab'a iya hanaka kabi umarnin iyayenka ba " ta idasa maganar hawaye na zuba a cikin idonta, shima kansa idonsa ya kad'a yayi jawur, cike da rauni ta fad'a jikin mijin tana, fashewa da kuka tayi, ta kasa rik'e kukan zuciyarta sai zugi take mata..............✍️ ZAHRA ROYAL STAR CE SHARE FISABILILLAHI 🥰🙏 *👩‍❤️‍👨💞 WAYAFI K'AUNATA 👩‍❤️‍👨💞* (Love Story) PAID BOOK #500 MALLAKIN *©ZAHRA ROYAL STAR* *Littafin kud'i ne wadda ya shirya yin tafiyar dashi zai iya turo kud'insa, ko katin MTN ko hoton katin saika turo shaidar biya #500 ne kacal* 8130479973 *FATIMA RABI'U OPAY BANKA* Zaka turo shaidar biyanka ko hoton katin ta wannan number d'in, (08130479973.08035023054) Free Page 3-4 بسم الله الرحمن الرحيم العالم D'akina na shiga ina mita a zuciyata harna gama cin abincin ina k'unk'uni da takaicin Ya Abbas shi dai idan bai k'untata min ba, baya jin dad'i. Iya ce ta shigo tana kallo na ta ce "nikam Maryam kin shiga wajan Kawunki Mamman Zeena ba lafiya ki gano ta?" d'an tashi nayi da sauri ina cewa "ayya Iya ai ban sani ba, da kamin ma na shigo nan saina lek'a na gano ta" Iya dake zaune kusa dani ta ce "eh ya kamata dai kije yanzu daga nan ki wuce shigon d'an lami mai kanwa ki sayo min, zanyi ma wancan mai bak'ar zuciyar d'an wake". Tashi nayi ina b'ata rai tunda naji ta ce d'an wake nasan dama shi zatai mawa amsa nayi ina cewa "Allah danke zanje amma indan halinsa ne baza ka mai komai ba, nikam duk yau banga Ya Hafiz ba?" na idasa maganar ina kallon Iya, tafiya na farayi naji maganar Iya tana cewa "dan Allah karki dad'e Hafiz kuma zaki gansa k'ila dakin fita ai uwarsa ce mai bak'in hali itama inaga ita ta hanasa shigowa". Nidai idasa ficewa nayi ina jin Iya ta fara masifa danmi zasubi su takura min, mina tare musu ne?, haka kawai sun taso ni gaba, ina tunani na idasa sashin Kawu Mamman, da fara'a matarsa ta tarbeni kamar yadda muka saba, sai da na duba Zeena da jiki har tana jana wai dodo na ya dawo, dariya nayi na ce "dodon kuwa dai, Allah bawan Allah nan ko a hanya banso mu had'u, kinga fa daga dawowarsa sai da yayi min masifar tasa" na idasa maganar ina jan tsaki har cikin raina nima nake jin na tsani Ya, Abbas kamar yadda ya tsaneni, dariya tayi min tana cewa "hmm bari Maryam nima nan tsoro yake bani jiki na har kyarma yake idan muka had'u ko a hanya, bare in ni kad'ai ce, wai amma a haka Sa'ida ke sonsa har wani yanga take idan ta gansa k'arfin halinta mamaki yake ban" tashi nayi ina cewa "uhm ita taji zata iya wahala, Zeena yoni ko mazan duniya sun k'are ai bazan tab'a zab'ar Ya Abbas ba, kinga bari na tashi na tafi aiki na fa Iya tayi". Tashi tayi tana d'an b'ata fuska ta ce "kai Maryam daga zuwa sai tafiya kinga daga zuwanki har ji nayi na warke ma" dariya nayi mata na ce "kinsan halin Iya dama ta ce karna dad'e tasan idan na shigo sashin nan har mantawa nake lokaci ya ja", daga bayanmu mukaji muryar Aunty (mamar Zeena kenan haka muke ce mata), tana cewa "a'a duk zaman nan dama harda aike akai miki maza to tashi kije kar taga kin dad'e, idan kuna labarin nan naku ai bakwa ji baku gani". Dariya mukai gaba d'ayanmu Zeena na niyar raka ni da sauri na ce "la kiyi zamanki kinji ki da k'arfin hali keda baki da lafiya, bari yanzu zan dawo wancan mugun wai Iya zatai ma d'an wake" na idasa maganar ina ficewa daga sashin. Ina gaf ficewa daga zauran gidan namu kawai naji munyi karo da mutum kamin nayi wani yunk'uri naji an hankad'eni ana d'auke ni da mari tasssss dafe kumatu nayi hawaye na zubo min, nasan ba kowa bane sai Ya Abbas shi d'in ne kuwa jin saukar maganarsa a kaina kaina, na k'asa sai da na d'ako ba shiri jin wata uwar tsawa daya daka min yana cewa "wai ke dabbar ina ce kwata-kwata ba kiyin abu cikin hankali kina tafiya buguzun-buguzun sai kace ba mace ba gidan ubanwa ma zaki?, da yammar nan dare ya kusa" wasu irin hawaye ne naji sun k'ara zubo min zuciya na tuk'ukin bakin ciki naji zafin maganarsa ta farko daya kira ni da dabba, ko kallo bai ishe ni ba, na k'ara jin saukar maganarsa a kaina "ba magana nake miki ba ko sai na tattakaki a nan wajan shashasha kawai", bud'e baki zanyi domin yin magana kawai kuka ya k'ufce min. Maganar Ya Hafiz ce ta katse mu gaba d'aya cike da kulawa ya matso kusa dani kama hannu na yayi yana bin Abbas da kallo tsaki Abbas yaja "Mtswww" yana barin wajan, kallo na Ya Hafiz yayi yana sa hannunsa ya sharemin hawayen dake sintiri akan kumatu na ya ce "shittt kayi shuru haka nan idan kina mai kuka a koda yaushe to kullum zai rink'a saki kukan ne, kiyi hakuri kinji inda sabo yaci ace kin saba da halinsa, muje na raka ki, mi zaki sayo ne?" murmushi na d'anyi ina jin zuciyata na yin sanyi dan ganin Ya Hafiz d'in na bud'e baki na ce "kanwa zan sayo kuma mugun fa shi Iya zatai ma abinci" da sauri yasa hannunsa mai taushi ya toshe min baki ya ce "Ohh my Maryam bana hana ki kiransa da mugu ba ki daina ba kyau kinji Yayanki ne shi", zunb'uro baki nayi cike da shagwab'ar da ta zame min jiki na ce "to amma Ya Hafiz ai mugunne shi" Ya Hafiz dake murmushi yana kallo na wannan shagwab'ar tawa tana matuk'ar birgesa ya ce "kashh bana hana ki fad'a ba?" dariya nayi yadda ya kwaikwayi muryata yayi maganar yasa na tushe baki na ina dariya na ce "na daina Ya Hafiz", Haka muka idasa har shagon muka sayo muka dawo, muna wasa da dariya dashi, yana ta gaya min kalamai masu dad'i har yasa na manta da wani wai shi Ya Abbas, harda abunda ya had'ani dashi, sai dai muna shigowa harabar gidan muka iske Inna Rabi tsakar gida tunda muka shigo take binmu da hararara daga ni har Ya Hafiz, da sauri naja jiki na daga garesa ina matsawa gefe shima kansa yasan wallahi ku za'a yanka ta sai tayi maganar da ta saba yi, ai ko kamin ya gama tunani a zuciyarsa muka ji saukar maganarta akanmu cike da masifa tana cewa........ *KADUNA* POV Washe gari haka Munnira ta tashi duk jikinta a sanyaye ganin mijin nata shima duk zuciyarsa ba dad'i yasa duk ta kori wata damuwa dake d'awainiya da ita ta fuskanci mijinta. Tashinsa kenan daga bacci yana zaune yana kallon silin d'in d'akin yayi zurfi cikin tunani yasa da sauri Munnira ta zauna akan cinyarsa ta d'an kwantar da kanta a k'irjinsa tasa hannunta tana d'an shafa faffad'an k'irjin nasa mai cike da gargasa a hankali ta ce "mijina tunanin mi kake?, pls tunanin ya isa haka nan, na had'ama ruwan wanka", ta idasa maganar tana kamo hannunsa murmushi yayi shima lokaci guda ta mantar dashi wata damuwa da kanta ta taya shi yin wankan cike da jan hankalin mijin nata. Sanye take da wata riga ta shan iska iya cibiya sai d'an k'aramin wando iya gwaiwa mijinta yafi son yaga mace kullum da k'ananun kaya, shi yasa kullum itama tana k'ok'arin ganin ta faranta masa rai, parlo suka fito sai da ta ciyar dashi abincin safe sana suka dawo parlo suka zauna suna fira jefi-jefi har lokaci ya d'anja, d'agowa tayi tana binsa da kallo cike da sonsa tasa hannu tana shafo fuskarsa ta ce "ya kamata my kaje yau wajan Hajiya tunda ta ce cikin satin nan take son ganinka ya kamata kaje yau kawai" kallon matar tasa yake cike da so, ya sakar mata murmushi ya ce "insha Allahu yanzo dana fita sallah zan wuce unguwar tamu" ya idasa maganar zuciyarsa na d'an bugawa, lumshe ido tayi cike da jan hankali ta ce "to yau mi kake so na dafa ma da rana uhum?" murmurshi yayi ya ce "komi kika dafa zanci ai bari na tashi naji an fara kiran sallah", tashi tayi daga jikinsa, yana gaf ficewa ta kira sunansa tsayawa yayi, k'arasowa tayi kusa dashi kamar yadda ta saba ta had'e bakinsu waje d'aya wani irin kiss ta aika mai dashi ai ko yaji sakon har tsakiyar kansa, ya lumshi idonsa yana k'ara rik'eta sun dad'e a haka sana ta sake shi tana cewa "mijina Allah ya kare min kai ya dawo min da kai lafiya ya kareka da dukkannin sharri ya dawo min da kai cikin aminci", sosai yaji addu'ar tata, duk da ta saba mai haka amma koda yaushe da kalar addu'ar da zata mai shi yasa kullum sonta k'aruwa yake bawai raguwa ba. Haka suka rabo zuciyoyinsu cike da begin juna, Yana fita ta d'an tsaya tana cewa "to mi zan dafa mai?," can kuma saita d'an girgiza kai tana murmushi. Kitchen ta shiga ta d'akko b'arzazzar shinkafa ta d'akko roba ta juyeta a ciki ta wanke ta fas, sana ta d'akko tukunyar ta zamani sitima, tasa ruwa a k'asanta, tasa hawa na d'aya, ta d'akko mai da magi fari da d'an gishiri kad'an, duka tasa a cikin b'arzazzar shinkafar nan data wanketa, tasa mai fari mai d'an dama-dama, sana tasa farin magin nan da gishiri, sai tasa ludayi ta motsa ta had'esu, sai kuma ta d'an taro ruwa kad'an tasa a ciki, sai ta d'akko tukunyarta mai hawa-hawa ta fara zubawa gida uku ne ko ina tasa sai kuma ta d'akko gyad'a wadda ta daka ta sama-sama tasa a ciki, ko wanne gida sama-sama ta barbaza ta, ta had'a su waje d'aya ta rufe saman tukunyar da marfinta, ta d'ora akan gas. Tana gama wannan ta d'ora wata tukunyar ta d'akko d'anyan naman kaza dake cikin firiza tasa a tukunya, ta yanka al'basa a kai ta d'ora a d'ayan gas d'in, sai kuma ta d'akko tafarnuwa ta dakata da kayan k'amshi tana gama dakawa ta juye a tukunyar data d'ora naman kazarta a ciki, sai da naman kazarta ya tafasa ya fara k'amshi ta d'akko markad'ad'd'und'on kayan miyarta ta juye a ciki ta rufe, sai da miyarta ta fara dafuwa, sana ta bud'e tasa kayan d'and'ano, danda nan gidan ya fara d'omewa da k'amshin girki, sai da miyar taja sosai sana ta d'akko manja tasa a miyar ta rufe, sai kuma ta rage gudun gas d'in, ta koma ga danbun shinkafarta ta bud'e sama tasa cukali ta d'ebo, ya daho yayi wara-wara ta sauke ta juye a kula, sai da ta kai darning sana ta dawo ga miyarta, tana bud'ewa har mai ya fito sosai ta kashe gas d'in, ta juye ta itama a kula, ta kaita darning, ta dawo kitchen d'in ta gyara ko ina, sana ta bud'e firiza ta d'akko ayarta da dabino da kwakwa ta wanke su ta tsaftace su tasa a bilanda ta had'esu ta markad'e sai da ta tabbatar sunyi laushi sun markad'u, sana ta juye su, ta tace su ta d'akko wani jok mai tsawo ta juye a ciki, sai kuma ta d'akko madarar da ake yin iloka da ita, guda d'aya ta juye rabi a ciki, tasa cukali ta motsa ko ina ya had'e, saita d'akko k'ank'ara ta fasa ta ta juye a cikin kunun ayarta, ta aje gefe guda ta k'ara gyara kitchen d'in ko ina yayi kyau, sana ta fita ta aje shima kunun ayar akan darning. D'an zaunawa tayi tana rik'e k'ugunta saboda ta gaji sosai, sai da ta d'an huta sana ta shige bathroom tayi wanka ta sake fashe jikinta da turare tasa turaran wuta tasa hijabinta ta rufe kanta dashi sai da ta tabbatar ko ina na jikinta ya d'au k'amshin turaran wutar, sana ta aje shi a gefe yana ba d'akin k'amshi, sallah tayi ganin har hud'u tayi, tana gamawa ta fito parlo ta zauna jiran mijin nata. RAMADAN POV Sai da ya gama sallah a masallaci sana ya shiga motarsa ya nufi unguwarsu, yana zuwa mai gadi ya wangale mai get ya shiga harabar gidan nasu yayi parking d'in motar yana kallon harabar gidan naso a cikin zuciyarsa yana tunanin da Abbansa yana raye da duk wannan matsalolin basu faru ba, sai da suka gaisa da mai gadi sana ya nufi cikin gidan naso. A babban parlon gidan nasu ya tadda duka y'an gidan da k'annansa guda biyu sai Yayyansa guda biyu Ya Aysha ce kawai babu itama dan tayi aure su kuma Inteesar da Nawwara Auntys d'insa kenan basuyi auran ba sai k'annansa guda biyu Hasana da Usaina. Suna ganinsa suka gaida sa shi kuma ganin Yayyan nasa mata na mai wani kallo yasa ya murtuke fuska yana gaida su badan yaso ba. Amsawa sukai ba yabo ba fallasa Hajiya ce ke sakkowa, d'aga kai yayi yana kallonta ganin irin kallon da take aika mai dashi ne yasa yayi k'asa da kansa, tana k'arasowa har kasa ya duk'a ya kwashi gaisuwa, sai da ta zauna ta d'ora kafa d'aya kan d'aya tasha mur ta bud'e baki cike da isa ta ce "sai yanzu kaga damar zuwa ko kuma sai yanzu y'ar gwal d'in taka ta baka umarnin zuwa?" ta idasa maganar tana tsaresa da ido, shi kuwa cike da mamaki yake bin Hajiya da kallo, shikam ba duka jiya ne Ya Ayshar ta zo ta gaya mai sakon Hajiyar ba, katse mai tunani tai da cewa "koma dai minene ka sanar da ita cewa nanda wata biyu masu zuwa zaka k'ara aure, nanda sati biyu kuma zanzo har gidan naka da amarya, zata zab'i inda yayi mata koda d'akin da Munnirar take zaune ne kuwa, idan ta nuna nan ne yayi mata dole ta kwashe komatsanta taba amarya waje, kaji na gaya maka karma kace ban sanar dakai ba", wani irin kallo mai wuyar fassarawa yake bin Hajiya dashi wannan k'iyayya har ina kai jama'a ta ina zai fara ne, Hasana ce ta buga tsalle dama ba kunya ne da ita ba tana cewa "haba ai gara ta matsa taba amarya waje duk ta kanainaye komai dama... Kamin ta idasa maganar Ramadan ya tashi a zuciye yana d'auketa da wani gigitaccan mari ji kake tasss tasss, su duka sai da suka tashi tsaye, Hasana sai hawaye tana b'oyewa bayan Hajiya ganin yadda yake huce kamar zai rufeta da duka, Hajiya cike da masifa ta rufesa da fad'a tana cewa.........✍️ *Washhh Allah na gaji mu had'u zuwa gobe idan Allah ya kaimu* ZAHRA ROYAL STAR CE SHARE FISABILILLAHI🥰🙏 *👩‍❤️‍👨💞 WAYAFI K'AUNATA 👩‍❤️‍👨💞* (Love Story) PAID BOOK #500 MALLAKIN *©ZAHRA ROYAL STAR* *Littafin kud'i ne wadda ya shirya yin tafiyar dashi zai iya turo kud'insa, ko katin MTN ko hoton katin saika turo shaidar biya #500 ne kacal* 8130479973 *FATIMA RABI'U OPAY BANKA* Zaka turo shaidar biyanka ko hoton katin ta wannan number d'in, (08130479973.08035023054) Free Page 5-6 بسم الله الرحمن الرحيم العالم Muka ji saukar maganar ta akanmu cike da masifa tana cewa "kai dai Hafiz ban san irin ka ba wallahi, shin wai mika gani wajan wannan yarinyar mai kama da aljanu?, ka wani mak'ale mata, to tun wuri bari na gaya maka idan wani abunne a zuciyarka wallahi kayi gaggawar cire shi a ranka" ta idasa maganar tana hararara ta gaida ta nayi ina cewa "Inna Rabi ina wuni" wani banzan kallo data yi min tana cewa "da ban wuni ba kin ganni uwar iyayin tsiya, kai kuma bita zai-zai sai ka ciga ba da bin bayan ta kamar wani jelar doki, ai shi yasa d'an uwanka yake birgeni ya za'ai ma ya tsaya da wannan kucakar yarinyar", ta idasa maganar tana jan wani dogon tsaki tayi gaba abinta. Shi kuwa girgiza kai kawai yayi yana kamo hannuna ganin nayi k'asa da kaina ya ce "Maryam" ya kira sunana a hankali d'agowa nayi ina dubansa cike da sona ya sake cewa "am so sorry my Maryam... Da sauri na katse shi da cewa "kai Ya Hafiz miye na bani hakuri to?, ai itama uwata ta ce dan tayi min fad'a ba wani abu bane" murmushi ya sakar min yana k'ara kallon kyakkyawar fuskata, shi dai Allah ya sani ina matuk'ar birgesa. Ganin lokaci naja na ce "Ya Hafiz bari na shiga daga ciki kar Iya taga na dad'e" saki na yayi yana cewa "Ohh na ma manta aiken mu fa aikai oya jeki ina nan shigowa sashin naku" da to na amsa inayin gaba. Da sallama na shiga Iya na zaune, ta tasa fulawar da zatai d'an wake a gaba tana jira na, murmushi na saki ina zama kusa da ita, tashi tayi tana d'ebo ruwa ta zauna tana cewa "yanzu fisbilillahi Maryam tun d'azo na aike ki sai yanzu kikaga damar dawowa saura masifaffan can ya shigo duk ya damu mutane" tana maganar dai-dai ta gama kwab'a d'an waken tashi nayi ina cewa "kai Iya wallahi a hakama nayi sauri kuma harda shi ya tsayar dani yana faman min tsiyar daya saba min yanzu dai kawo na jefa d'an waken" sakar min tayi, tana zama a tabarma, dama tuni ta d'ora ruwan zafi harya tafasa, zama nayi gefen murhun na fara jefa d'an waken, Iya dake kallona ta ce "yanzu sabo da Allah shi dai duk inda ya ganki hankalinsa bazai kwanta ba saiya jaki fad'a, ni na rasa wannan k'iyayya taku keda shi, to idan Allah ya k'addara zaku zauna inuwa d'aya fa..... Kamin ta idasa maganar da sauri har ina shirin zubar da kwab'un d'an waken na ce "kai Iya wannan wane irin fata ne kike min dan Allah ki daina ma wannan maganar karma mala'iko suji su amsa ina dalili ina zankai rigimar Ya Abbas kashe ni zaiyi wallahi", dariya ta sakar min tana cewa "ke ki bimin sanwa a hankali karki zubar min da kwab'i , wasa nake miki koni bazan bari a had'a ki da wancan mai bak'ar zuciyar ba". Tashi tayi bayan na gama jefa d'an waken na d'akko roba da ruwa a ciki ina tsamewa ina cewa "yauwa Iya ta ai nasan baza ki bari ba Allah sarki da Kakana mai shano na nan ai da mai wannan bak'ar zuciyar bazai min duk wannan abubuwan ba", Iya dake zaune cike da damuwa da kewar mijin nata yau kusan shekaru bakwai da rasuwa, ta ce "Allah dai ya jik'an Malam" da amin na amsa nima zuciyata ba dad'i Allah baya barin wani dan wani yaji dad'i. Bayan na gama Iya ta ce nasa mai nashi a kula, sai da nasa masa na aje gefe, na had'a mana nida ita muka zauna muka fara ci d'an waken yayi mun dad'i sosai saboda yaji kayan had'i an yanka su tumatur dasu albarsa harda kwai a ciki. Bayan mun gama na shige d'aki nayi alwala ganin har mangaruba tayi ina cikin sallah naji muryarsa ya shigo suna gaisawa da Iya data idar da sallah, jawo mai d'an waken tayi ta zuba mai, saida ya fara ci yana tand'e hannu sai da ya gama ci tas ya wanke hannu yasha ruwa ya goge baki, da kamar bazai tankama Iya ba can kuma sai ya ce "na ce dai Iya ba wannan k'azamar yarinyar taki ce kika ba ta jefa min d'an wake ba" wani dogon tsaki Iya taja tana cewa "kai Abbas bafa nason rashin ta ido ka kalli zabar ido na sai da ka gama lashe abinci zaka zo kana kawo min wani suki burutsu, to ita ce tayi, kaga saika amayoshi ko", ta idasa maganar cike da gatse tashi yayi yana murmushi wadda Iya ce kawai take ganinsa zaro kud'i yayi zasu kai dubu uku ya aje mata yana cewa "haba Iya ta kar aji kanmu mana yanzu ga wannan ladar yimin d'an wake da kikai ne" tashi Iya tayi tana washe baki dan Iya akwai son kud'i ta ce "yauwa d'an albarka yanzu kayi zance mai kyau to na gode Allah shi k'aro bud'e" da amin ya amsa yana ficewa daga sashin. Ni kuwa dake cikin d'aki, fitowa nayi ina sane nak'i fitowa yana nan samu nasan bazamu kwashi ta dad'i ba nida shi kamar wuta da ruwa ne. Zaunawa nayi ina zunb'uro baki gaba ina cewa "Iya kinji fa mi ya ce wai ni ce k'aza ma" na k'arashe maganar cike da jin haushinsa a raina tashi Iya tayi tana d'aure kud'in daya bata a hab'ar zaninta tana cewa "ke kinga ni bana son wannan sokiburutsin naku keda shi wadda baya k'arewa ba kinsan halinsa ba?, fad'a yayi fa dama dan kiji haushi ai", tashi nayi ina cewa "yauwa Iya candynmu fa ya kusa na gama secondary school kuma kinmin alk'awari zan wuce ko ina so nima nayi karatun likitancin nan", Iya dake zama kusa dani ta kunna rediyon ta tana cewa "eh nima ina son haka amma dole sai mun zauna da Iyayanki kinsan dai bake kad'ai zaki gama makarantar ba bansan mi suka yanke a kanku ba idan aure suka yanke a kanku haka zakiyi hakuri kiyi shi banda ta cewa tunda bake kad'ai ce ba" hankali na yayi mugun tashi matsowa nayi kusa da ita ina cewa "Iya aure kuma?, ni dai gaskiya wallahi Allah ban shirya mashi yanzu ba dan Allah Iya karki bari a durkusar min da rayuwata duka nawa nake da za'a ce wai aure", tashi Iya tayi tana janye ni daga jikinta itama kanta zata so na wuce d'in sai dai kuma abun zai zama abun magana a cikin gidan ta ce "Maryam bawai bana so kiyi karatu bane a'a abunne zai zama abun magana dama yanzu ana min surutu nida ke cewa nafi sonki, ke kuma kin tare ko ina kin hana sauran jikokina suji d'umin jikina, kuma ba haka bane ke kad'ai ce marainiyar babu wadda zaki rab'a kiji dad'i idan ba niba, ina suke so kije to? shi yasa nake k'ara jawoki a jikina dan bana so kiyi kukan maraici amma gani ake kamar son kai ne nake nunawa a kanki gani suke kamar soyayyar da nake ma Mahaifinki ce ta dawo kanki, Maryam Mahaifinki sadda yana raye kwata-kwata baya so yaga kuka na ko b'acin raina yana min biyayya sosai koda zai cutu kuwa , duk cikin y'ay'ana nafi jinshi a raina badan komai ba sai dan harga Allah zuciya na son mai kyautata mata, Mahaifinki kullum cikin kyautata min yake, to taya za'ai bazan so jininsa ba?, kawai kiyi hakuri muga miye suka yanke komi Allah ya tsara miki Maryam a rayuwa ki karb'esa hannu biyu-biyu kinji?", shigewa nayi kawai jikinta ban k'ara cewa komai ba dan baki na yayi min nauyi......... *KADUNA* POV Hajiya cike da masifa ta rufesa da fad'a tana cewa "kai kai kai tsaya daga nan na ce, dukanta zakai akan waccar abar akan ta fad'i gaskiya, ai gaskiya ta fad'a, uban miye take a cikin gidan naka inba taci ta kwanta ba, tabi ta kanainaye komai, sai abunda ta ce shi kakeyi, dan haka karka sake ka k'ara kai hannunka akan yarana indai akan waccar matar taka ce", ficewa yayi daga gidan gaba d'aya ranshi idan yayi dubu ya b'ace. Yana fita Nawwara ta ce "ai wallahi kin min dai-dai wallahi waccar matar ba'a banza ta barshi ba kina ganin daga anyi maganarta ance tayi kaza harya tashi a hargitse", zaunawa Hajiya tana jawo Hasana dake bayanta ta ce "ke kuma gobe ki k'ara shiga harkarsa idan yayi miki illa ke kika sani" k'unkuni ta farayi tana zama kan kujera Inteesar ce da har yanzu bata sa baki ba tana danne-dannen waya ta ce "nifa wallahi wani lokacin ban ganin laifin Munnira saboda tsantsar kulawa ce take bama mijinta kun kasa fahimta ne ba wani asiri a ciki", da sauri Hajiya ta ce "kinga Inteesar ki fita ido na rufe ki fita samgar wannan sha'ani tunda naga kema ta shanye ki ta gama dake, dan haka karna k'ara jin bakinki a ciki, tunda naga keda Ramadan d'in kamar an canza min ku, ke Nawwara maza idan kin gama abunda kike ki kira min Halima", da to ta amsa Inteesar kuwa tab'e baki tayi tana tashi tabar masu parlon dan ita Allah ya gani bata ga wani abunda Munnira take na rashin kyautawa ba kawai dai dama can Hajiya ba son Munnirar take ba. Ramadan yana isa gida ya saita kansa baya so ya shigar mata da b'acin rai bata ji ba bata gani ba, Amma duk da haka Munnira na ganinsa tasan ransa a b'ace yake, ruwa mai sanyi ta kowa mai ya sha yana sauke ajiyar zuciya bata ce mai komai har sai da ta taimaka mai yayi wanka ta kaishi har darning ta zaunar dashi sai da ta zuba mai abinci, yadda k'amshin girkin ya bigi hancinsa yasa ba shiri ya lumshe idonsa har miyan bakinsa na tsinkewa zama tayi kusa dashi tana d'an tsotsar alawa dake bakinta kallonta yayi ya ce "minene kika ta tsotsa ne wai?" murmushi ta sakar mai, mai tsada ta ce "alawa ce fa" jawota yayi jikinsa yana cewa "oya zan sha bani nima" turo mai d'an k'aramin bakinta tayi, ta had'e da nasa ta tura mai alawar cikin bakinsa sai kuma ta d'an kamo harshansa tayi mai wata irin tsotsar da yasa lumfashin Ramadan d'aukewa na wucin gani, can kuma saita sakar mai bakin har yanzu idonsa lumshi yake yadda yake jin zak'in alewar da miyan bakinta sai suka bashi wani irin gard'i kamar karta saki idonsa harya canza launi murmushi ta k'ara sakar mai tana jan kujerar da yake kai ta zauna akan cinyarsa ta fara basa abincin da kanta, shima haka tana bashi yana bata haka har suka gama cin abincin, satin abincin kuwa ta shashi kamar mi ji yayi kamar kunnunasa zai tsinke tsabar yadda abincin yake jin dad'insa. Suna gamawa ya fita masallaci saboda jin ana kiran sallar magaruba bai dawo gidan ba sai bayan anyi isha'i koda ya shigo bai ganta a parlo ba kai tsaye bedroom d'in ya shiga, tana tsaye bakin madubi tana d'an shafa man baki, rungumeta yayi ta baya lumshe idonta tayi jin yana hura mata iskar bakinsa a dai-dai wuyanta wata wawar ajiyar zuciya ta sauke tsigar jikinta na tashi. D'aukarta yayi cak sai kan gado kwantar da ita yayi yana mata runfa da faffad'an k'irjinsa, had'e bakinsu yayi waje d'aya yana sa hannunsa ya cire mata y'ar ficiciyar rigar data sa, ajiyar zuciya ya sake jin hannunsa a ciki na shanonta sakin bakinta yayi yana kai bakinsa a kansu wata irin ajiyar zuciya ta sauke tana k'ara tallafo kansa yadda yake shan na shanonta kamar wani yaro cike da wani irin salo tasan mijinta ba abinda yafi k'auna yake kuma d'auke mai hankali irin su. Sai da komai ya lafa har sunyi wanka suna kwance manne da juna har yanzu yana wasa da na shanonta sai jagwalgwala su yake son ransa, yi tayi kamar zata mik'e ya d'an kwafe fuska yana cewa "please ki k'ara min nasha kinji" wata irin kasala ke k'ara saukar mata ta ce "anya my idan muka haihu zaka bar yara su sha kuwa?" dariya ya saki yana cewa "hmm gaskiya sai dai suyi hakuri" ya idasa maganar cike da zolaya murmushi ta saki tana kamo kansa ta ciro guda d'aya tana manna mai a baki kamar wani jariri haka ya kama ya fara sha haka sukayi bacci d'aya yana bakinsa d'aya yana shafawa...........✍️ ZAHRA ROYAL STAR CE SHARE FISABILILLAHI🥰🙏 *👩‍❤️‍👨💞 WAYAFI K'AUNATA 👩‍❤️‍👨💞* (Love Story) PAID BOOK #500 MALLAKIN *©ZAHRA ROYAL STAR* *Littafin kud'i ne wadda ya shirya yin tafiyar dashi zai iya turo kud'insa, ko katin MTN ko hoton katin saika turo shaidar biya #500 ne kacal* 8130479973 *FATIMA RABI'U OPAY BANKA* Zaka turo shaidar biyanka ko hoton katin ta wannan number d'in, (08130479973.08035023054) Free Page 7-8 بسم الله الرحمن الرحيم العالم Washe gari haka na tashi suku-suku ko arzik'in shiryawa naje makaranta banyi ba, yau ta kasance al'hamis ne duk da muna ta shirye-shiryen gama school d'in amma maganar da mukai jiya da Iya ita ce duk ta sakar min da gwaiwa. Iya ce a kaina kallona take tana nazari na, ta ce "nikam Maryam makarantar ce bazaki ba ko kuwa?, idan ma zaki saki ranki ki saki ranki ni banga abun tada hankali a nan ba, duk abinda Allah ya rubuta a cikin kuddun k'addararki to tabbas sai faru da kai, babu mahaluk'in daya isa kawar dashi, ki tashi ki shirya ki daina wannan k'uncin dan Allah?", tashi nayi ina d'an zunb'uro baki na ce "nifa Iya yau bana jin zuwa makarantar ne shi yasa hutawa nake so nayi" fita Iya tayi tana cewa "ai shikenan sai kiyi ta zama". Wajajan k'arfe biyu na fito Iya na tsakar gida tana aikin danbu ina ganin yadda take murza danbun na ce "kai Iya yauma dan Ya Abbas zakiyi danbun nan na sani daya zo garin nan sai abunda yake so shi kike yi" na idasa maganar cike da jin haushinsa murmushi Iya tayi ta ce "kinga bana son kilbibi kema duk da rashin jituwar taku irin abinci d'aya kuke so keda shi kunfi son abincin gargajiya dannayi kuma sai kice danshi nayi, kinga ki wuce inda zaki nasan sashin Kawu Mamman zaki sai kin dawo". Tafiya na farayi ina cewa "eh Iya can zani ina so mud'anyi fira da y'an uwa na nasan suna can kar ayi ba ni", ina jin maganar Iya na cewa "ai dai duk kun kusa bamu waje duk ku tafi gidan mazajan ku" nidai harna idasa barin sashin bance k'ala ba dan wani irin haushi nake ji idan akai maganar auran nan wallahi, toni wama zan aura dan gaskiya ni a cikin zuciyata har yanzu bazance ga wadda nake so ba ko Ya Hafiz kawai shak'uwa ce amma bana jin sonsa a raina. Ina tunani na idasa sashin Kawu Mamman ai kuwa na taradda yawanci y'an matan gidan na sashin sunje duba Zeena zama nayi cikinsu dan dukkan muna samun jituwa dasu garama Sa'ida ita ce mai d'agin kai cikinmu ba wani shiga harkarta nake yi ba. Hajara ce ta ce "Ohh ni tun jiya rabon dana ganki Maryam" d'an gyara zama nayi ina cewa "hmm ina zaku ganni Boss d'in gidan nan ya dawo shi yasa ko son fita bana yi danma karmu had'u dashi" dariya suka sa gaba d'aya can Sa'ida uwar iyayi an tab'o mata inda ke mata k'aik'ayi ta ce "hmm bari kedai ai Ya Abbas yayi wallahi matarsa ta more daga gani zata ga soyayya irinsu ne basa da sakin fuska ga jama'a, amma ga iyalansu ba'a magana irinsu idan kaga suna nunama matansu soyayya zaka sha mamaki wallahi" duka sakin baki mukai muna kallonta na ce "ke amma Sa'ida baki san wadda suka iya soyayya ba yo ni Allah na tuba mi Ya Abbas ya iya idan ba d'aure fuska ba, haka zaije yana ma matar tasa yayita firgita d'iyar mutane ko wacece ma" na idasa maganar ina rik'e baki. Shewa suka saki gaba d'aya Zeena ta ce "ai kuwa irinsu sun iya soyayyar Maryam kuma sun iya gigita mace nanne dai zasu nuna mana jan ido", da sauri Sa'ida ta ce "yauwa kin gane kenan" tab'e baki nayi ina cewa "ku kuke ganin haka, kuda kuke da samari a hannu, ai dole kusan wadda suka iya soyayya a cikin maza" shewa suka k'ara saki, har suna had'a baki wajan cewa "kai Maryam kema fa kina soyayyar nan ina Ya Hafiz d'in kika barsa" dariya na saki ina d'an jawo kwanon da Zeena kecin waina na ce "ke ba tayi kin tasa abu gaba sai narka kike?" na fad'a dan ina so a kauda zancan da sauri ta turo min kwanon tana cewa "yanzu fa nake shirin tashi na zubo miki nasan kina sonta sadda zaki shigo duk su Hajara sun gama ci" idasa cinye ta cikin kwanon nayi ina cewa "yanzu dai tashi ki k'aro min dama yunwa nake ji yau Iya ta tsiri danbu saboda Boss har yanzu bata gama ba", tashi tayi tana d'ebo min ta kawo min sai kuma ta zauna tana kallon Sa'ida dake cewa "ya kamata fa mu fara shirye-shiryen gaba school d'inmu tunda kusan dukanmu zamu gama a tare" na cika bakina da waina na ce "nima nama Iya magana zata ban wasu kud'i zamuje shago mu sayo irin su alawa zanje a bugo min sticker kuma amma ba mai pictures ba, mai suna nake so" da sauri Hajara tayi karaf ta ce "nima gaskiya bana son mai hoto mai rubutu nafi so nima, amma ni inaga Bashir zai kawo min a ranar" dariya muka saki muna cewa "ahh kaga masu samari", bugu ta kaima Sa'ida data fi mata tsiya tana cewa "kuma fa da samarin nan naku kowacce tana dashi wallahi, shawarar da zan baku ma karku wani wahalar da kanku zaso yo muku ne su kawo muku" dariya aka saki ana shewa, dama idan muka had'u kamar zamu tada waje. Muna cikin fira Aunty dake madafa har yanzu tana tuyar waina muka ji maganarta suna gaisawa da Ya Abbas, ai ko danda nan kowa cikin mu ta shiga hankalinta. Lek'o d'akin yayi bayan sun gama gaisawa yana zafga mana hararara da manyan idonsa ko waccanmu sai da ta had'e wani miyau, banda ni dake cin wainata ko kallo bai isheni ba sosai na kama kaina dan bana ma son disginsa. Cikin kakkausar muryarsa ya ce "dakuka zo kuka rarrashe nan kuna surutun banza da wofi ina islamiyar?" Sa'ida ce cike da iyayi ta ce "Ya Abbas ai yau al'hamis" tsaki yaja ba haka ya so ba, so yayi na tanka mai ya samu kafar da zai min rashin mutumci, nima shi yasa nayi kunnan uwar shegu dashi, nayi kamar bana wajan, duk da haka sai da ya samu kafar da zai tanka min, kallo na yayi yana cewa "ke kuma kici a hankali mana kina cin abinci sai kace akuya nacin abinci ke komai idan za kiyi bakya duba cewa ke macece kiyita abu na rashin dacewa da'alla" wani tuk'ukin bakin ciki ne ya rufe ni na bisa da kallo ya gama yab'a min bak'ar magana yayi gaba abinsa ko a jikinsa kamar bashi yayi ba. Da kyar na had'iye wacce ke bakina Zeena na ban hakuri shuru kawai nayi, can naji muryar Hajara na cewa "ke yanzu Sa'ida a haka kike son Ya Abbas komi kayi baka iya masa ba, ga shegen miskilancin tsiya da fad'an da babu gaira babu dalili, yanzu dan Allah miye cin abincin Maryam yayi da zaice wai kamar akuya nacin abinci kai jama'a, ni a yadda nake gani ma ita da yanga take cin abincin ta, amma shi yanzu ji abinda ya ce" girgiza kaina nayi ina jin abincin ya fice min a rai tashi nayi ina wanko hannuna na wanke baki na na dawo, Sa'ida da jikinta yayi mugun sanyi wasu abubuwan da yake min ba akan idonsu bane shi yasa harta kwallafa rai a kansa, shi ya yarfa ka gaban mutane ba abu bane mai wuya a wajansa................ *KADUNA* POV Nawwara tana gama abinda zata yi ta dannawa Halima kira ta waya, Halima dake zaune a babban parlon gidansu tare da Hjy Kharima Mahaifiyarta duk duniya Kharima Halima kad'ai ce d'iyarta shi yasa ta sangartata da yawa kuma ita ta reneta Babanta sun rabo da Kharima da tsiya ta karb'e d'iyarta, tunda baida wani k'arfi da tsiya ta amsu Halima wajanshi tasa Malamanta suka rufe mai baki bai iya cewa komai ba. Da sauri Halima ta tashi tana cewa "kinga Momy Nawwara ke kira" da sauri Kharima ta ce "yi sauri ki d'auka inaga maganar auranku ce da Ramadan ta taso" ai da hanzari Halima ta d'au wayar tana sata a amsa kuwwa, bayan sun gaisa da Nawwara sai taba Hajiya inda Hajiya ke shaidama Halima tana so gobe zuwa jibi ta shirya tazo zasuje gidan Ramadan zata zab'i sashin da take so koda na Munnira ne idan dai har yayi mata, wani tsallan murna Halima ta saki tana cewa "insha Allahu tana nan shigowa zuwa jibi", da haka Halima ta katse wayar. Kallon Mahaifiyarta tayi ganin yadda ta saki wani k'asaitaccan murmushi tana d'ora k'afa d'aya kan d'aya wata shegiyar dariya ta saki tana cewa "lallai Hajiya basirarki ta toshe tunda har kikayi tunanin had'a jini dani, d'an naki da kike tak'ama dashi, kike ikirarin wata ta mallake sa to yanzu ne za'a mallake sa da gasken-gaske ai naku wasa ne" tafawa sukai ita da Halima suna sakin shewa Halima ta ce "ai Momy sai nasa ma Hajiya hawan jini bana ruwa ba saina maida d'anta kamar d'an korena sai abinda nake so shi zaiyi kai saina basa umarni ma idan zaije wajanta" tafawa suka sake yi Kharima ta ce "Hajiya kin d'akko ruwan dafa kanki, shiri zamuyi babba gobe zamuje can dajin zango wajan wani boka aikinsa kamar yankan wuka tun kamin ki shiga gidan za'a gama dashi". Nan suka zauna suna tsara yadda abun zai kasance. Kamar yadda suka tsara tunda dugu-dugun safiya suka d'au hanyar zango sunyi tafiya mai nisan gaske sana suka fara kutsawa cikin jejin mai duhun gaske tun a bakin hanya suka aje motarsu da k'afa suka rink'a kutsawa cikin uban jijin kwata-kwata ba ko d'igon tsoro a tare dasu bare gajiyawa daka kalli yadda suke kutsa kai cikin uban duhun jejin zaka san sun saba zuwa dama, a yadda suke bin hanyar data mik'a cikin dajin, sai da sukai tafiya a k'alla takai ta minti talatin sana suka iso wani waje wadda fili ne ba alamar akwai wani rai wadda ke rayuwa a wajan, amma ga mamaki na wata bukka ce ta bayyana kamar k'iftawa da bismililla, dajin ne ya d'auke wata irin girgiza da wata irin mahaukaciyar dariya, sai wani irin gurnani dake fitowa daga cikin bukkar, tsabagen yadda guguwa ke tashi da wasu irin koke-koke yasa Kharima da Halima had'ewa waje d'aya suna zazzare ido, wata irin murya sukaji ta kewaye su mai cike da kauri da kaushi amonta ba dad'in ji tana rarrabuwa kashi-kashi, ana zayya ne musu duk abinda suke tafe dashi. Danda nan Kharima ta ce "eh boka mai jan aiki uban la'anannu uban shaid'ano waya ce dake ba kai ba boka mai zamani mai tafiya da zamani" wata irin mahaukaciyar dariya aka kece da ita ana cewa "kware kuwa nine ubanku la'ananun Allah, ga wani magani nan gabanku ta tabbatar sai ta shiga cikin gidan a matsayi mata, ta tabbatar duk wani abun shanshi ko na wanka tana sa wannan maganin a ciki, sai wani d'aurin gashi nan shi kuma ta tabbatar sai idan zai sadu da ita zata sashi a gabanta, ta tabbatar tayi aikin yadda akace idan ba haka ba k'aik'ayi ne zai koma kan mashek'iya, ku aje kud'in ku b'ace min daga gani". Ai da sauri suka aje mai damen kud'i suka d'au maganin da kawai sai dai suka ganshi a gabansu, suka kama hanyar barin jejin cike da murna da samun cikar burinsu................✍️ ZAHRA ROYAL STAR CE SHARE FISABILILLAHI🥰🙏 *👩‍❤️‍👨💞 WAYAFI K'AUNATA 👩‍❤️‍👨💞* (Love Story) PAID BOOK #500 MALLAKIN *©ZAHRA ROYAL STAR* *Littafin kud'i ne wadda ya shirya yin tafiyar dashi zai iya turo kud'insa, ko katin MTN ko hoton katin saika turo shaidar biya #500 ne kacal* 8130479973 *FATIMA RABI'U OPAY BANKA* Zaka turo shaidar biyanka ko hoton katin ta wannan number d'in, (08130479973.08035023054) *from this PAGE's freebies are over guys, hurry up and pay for your trip* *END OF FREE PAGE'S* Free Page 9-10 بسم الله الرحمن الرحيم العالم A kwana a tashi har candy mu ya matso sosai, inda y'an gidanmu nata shirye-shiryen gama makaranta. Muna gaf mu gama yin candy Ummah tazo gari ba k'aramar murna nayi ba da zuwanta, inda ina mak'ale jikinta, muna zaune can saita kalle Iya ta ce "Iya dama nazo ne domin na tafi da Maryam can inda nake aure domin ta cigaba da karatun ta" shuru Iya tayi tana kallo na yadda nima jikina yayi mugun sanyi duk da murnar dake cina hakan baisa na fasa yin fargaba ba, saboda tuno maganar mu da mukai da Iya. Iya ta gyara zama itama cike da farin ciki ta ce "Umman Maryam nima gaskiya zanso haka amma ki bari magabatan ta suzo tukun kinsan nima ban isa yanke hukunci a kanta ba". Tun daga nan Umma ta ta d'an bari zuwa kwana biyu taji mi ake ciki, sai dai amma kwatsam sai muku tsinto maganar Kawu Mamman wai zancen aurar damu ake miye na sai na wuce karatu, gaba d'ayanmu suke shirin aurar damu, ba wata maganar wucewa karatu, wai d'an-d'an Hakimin garin mu shine yake son aure na, sosai na shiga tashin hankali tunda bansan dashi ba, kuka kawai nake kwana biyun nan sosai nayi bak'in cikin hakan amma babu yadda na iya dan Ummata tana gaf tafiya ta ce bazata iya zama tana ganina cikin damuwa ba, zaune nake akan cinyarta ina kuka d'agoni tayi tana cewa "Maryama kalle ni nan" d'agowa nayi ina kallonta idona cike tab da hawaye ta ce "nasan Kakarki ta baki tarbiyya yadda ya kamata banyi nadamar barinki a wajansu ba, kuma dama sunfi ni iko dake, naji za'a kira ki domin tabbayarki, Maryam karki cuci kanki ki fito ki sanar dasu idan baki son wannan yaron d'an gidan Hakimi, ina Yayanki Hafiz mi yasa bazaki zab'e shi ba?, na tabbatar zai kula min dake, shawara na baki a matsayi na na mahaifiyarki nasan kuna da jituwa dashi Yayanki Hafiz na tabbata shima yana sonki, tunda nazo gidan nan na lura hankalinsa shima ba kwance yake ba saboda yaji labarin anzo neman auranki, ya kasa fad'a ma manya ne saboda uwarsa tayi mai mugun gargad'i a kanki, amma ai ba a nan gidan zaku zauna ba, again ba a kanta zaku zauna ba, karki duba rashin jituwar ku da ita ki cuci kanki ki fito fili ki fad'a masu abinda kike so dan sunce baza su yi miki auran dole ba, kina jina?", tashi nayi a jikinta ina share hawaye tabbas naji dad'in maganarta, ko banza Ya Hafiz yafi min wannan D'an gidan Hakimin gara na auri Ya Hafiz duk da bana jin sonshi shima a raina kwata-kwata. Amsa mata nayi da "insha Allah Ummah zanyi anfani da abinda kika ce" tunda daga nan Ummah ta wuce birni inda take aure bayan tafiyarta da kwana biyu, ashe shima Ya Abbas nata shirye-shiryen tafiya k'aro karatu k'asar waje inda school d'in su da yake karatu an zab'esa cikin masu zuwa k'asar waje dan cigaban karatun su, dama yana karantar likita ne ta b'angaran mata ta b'angaran lalurar su. Shima Ya Hafiz ashe ya kasa hakuri sosai yake ta rokon alfarma gurin Iyayenmu maza dan ganin sun amince masa da kudirin aurena, har lokacin ina cikin matsananciyar damuwa har yanzu bazan ce bana son Ya Hafiz ba, sai dai shid'in bai damu da rayuwar birni ba, duk da cewa shid'in kyakkyawa ne kamarsu d'aya da Ya Abbas amma Ya Abbas yafi shi komai nesa ba kusa ba, kuma ko a nan cikin garin namu shid'in dan gayo ne wayayye, sai dai shifa ba ruwansa da harkar birni shine kawai matsalar sa, Kawu Iro da Kawu Mamman sune suka kirani domin tabbaya ta fisabilillahi ina son Hamza d'an gidan Hakimi dan basa so suyi min dole. A can gefenmu ashe Ya Hafiz na kusa na hango shi ya jingina da bango yana kallo na wani irin kalar tausayi ya bani, da sauri na girgiza kaina ina cewa "ni gaskiya Ya Hafiz nake so", da sauri Kawu Mamman ya ce "kin tabbata?", kai kawai na iya d'agawa san nan na duk'ar da kaina k'asa, shuru sukayi kafin su ce "na tashi na tafi kawai". Tashi nayi jikina a sanyaye ina hangen Ya Hafiz dake sujjada ta godiya ga Allah ina hangen fuskarsa cike take da tsananin farin ciki, ji yake kamar ya goya ni dan murna sai jifa na yake da wani shu'umin kallo harna b'acewa ganinsa. Bayan kwana biyu Inna Rabi da taji irin had'in da akai da yaranta inda Hajara ita da saurayinta, ita ko Zeena da Hashim d'an abokin Kawu Iro sai kuma Sa'ida da Hamza d'an gidan Hakimi ni ko tare da Ya Hafiz duk muna murna da hakan, bare ni bazan ce bana so ba, ba kuma zance bana ra'ayi ba, duk dai Sa'ida taso Ya Abbas amma ba yadda ta iya ta hak'ura. Inda Inna Rabi ta tasa Kawu Iro gaba da masifa danmi za'ayi irin wannan had'in masifa take tana cewa "ni gaskiya an cuce ni ba'a kyauta min ba danmi za'a had'a Hafiz da waccar yarinyar mai bak'in jini" tashi yayi kanta rantsa ya d'an fara b'ace ya ce "koke keda ikon aurar dasu, idan kin isa sai ki suke auran na gani" tashi tayi itama a zuciye tana banbamin masifa tana cewa "ai dole ka ce haka mana saboda an tab'a y'ar so, kuma wallahi indai na isa da Hafiz bazai aure wannan yarinyar ba bazata sab'o ba wallahi bazan yarda ba a maida min yaro yadda aka ga dama ba a maida min shi kamar wani lusari, waye bai san uwar wannan yarinyar ba sadda take aure a nan gidan, sai da ta maida Yayan naku kamar wani bawanta", wata irin tsawa ya buga mata idonsa ya kad'a yayi jawur, ita kanta sai da ta firgita ganin yadda mijin nata ransa yayi mugun b'ace ba shiri ta rufe bakinta cike da b'acin ran dake taso mai ya ce "wallahi Rabi kika sake kika tada zancan nan wajan Hafiz ko kikai mai maganar ya fasa auran nan to kema a bakin auranki............. *KADUNA* POV Zaune Munnira take tun jiya gabanta yake wata irin mahaukaciyar bugawa tun tana daurewa har wasu irin hawaye suka sami nasarar zubo mata wadda bata shirya zubowarsu ba, tashi tayi ta shiga d'aki, domin Ramdan ya fita zuwa wajan aiki d'akko wayar tayi ta dawo ta zauna Yayarta ta kira mai suna Hafsa wadda suke uwa d'aya uba d'aya su kad'ai suka rage ma junan su, iyayansu sun rasu tun suna y'an yara, itama Hafsar tana aure ne a Kadunar amma ita tana auran wani d'an siyasa ne mai kud'i, suna matuk'ar son junansu. Bayan ta d'au wayar jin an d'auka ta sauke ajiyar zuciya can cikin wayar Hafsa jin kamar y'ar uwar tata tana cikin damuwa yasa ta ce "Munnira lafiya kuwa?, na jiki kamar ma kuka kike miye yake faruwa ne?" Munnira kam bata san sadda ta fashe da kuka ba, dama damuwar ta mata yawa, ta rasa wadda zata fad'awa ta samu sauk'i a zuciyarta abinda yasa bata yawan kai kukanta wajan y'ar uwarta indai tana cikin damuwa to itama ba k'aramar damuwa take shiga ba, cike da tashin hankali Hafsa ta ce "wai miye yake faruwa ne?, Munnira karki sa na wanko k'afata yanzu nazo gidan naki minene yake faruwa ne dan Allah?", share hawayen tayi tana girgiza kai kamar tana gabanta tana cewa "a'a ba sai kinzo ba amma Hafsa zuciyata ta kasa samun natsuwa akan wannan auran da Ramadan danginsa suke so yayi, wallahi Hafsa zuciyata bugawa take" cike da tausayin y'ar uwar tata tasan kishiya a yi maka ita da ciwo bare ita danginsa basa sonta wacce suke so ita za'a auro, cike da sanyin murya da son kwantar mata da hankali ta ce "ki kwantar da hankalinki dan Allah ki daina sa damuwa a ranki idan kika ji irin haka ki rink'a mai-maita Innalillahi wa'inna ilarhir raju'un, sana Munnira ki rink'a karanta Alqur'ani mai girma ki yawaita yin azzakar, insha Allahu koda da niyyar cutar dake ta shigo Allah bazai tab'a bata ikon hakan ba", sosai Munnira taji zuciyarta tayi sanyi. Inda Hafsa ta ce zata shigo gidan zuwa gobe su k'ara tattaunawa, da haka sukai sallama. Tana nan zaune kawai taji tsayuwar motoci a cikin harabar gidan nata ba shiri yadda zuciyarta ta buga ta tashi ta lek'a ta wundo, ganin masu fitowa a cikin motocin yasa ta d'an zare ido, da sauri ta zawo hijabinta ta sa tana cewa "to mi ya kawo Hajiyar Ramadan da Yayarsa guda d'aya Nawwara?," ta tabbayi kanta, can kuma saita tuno ai dama sunce zasu zo, addu'a take Allah yasa su gama abinda suke su tafi karma su shigo cikin sashinta dan taga sun shiga d'ayan sashin wadda tasan nanne amaryar zata tare bayan anyi auran. Tana cikin tunani taji an banko k'ofar parlon, da sauri ta waiga tana kallon su yadda suke bin parlon da kallo yasa cike da fara'a ta ce "Hajiya ku shigo ina wuni" ta idasa maganar tana kaiwa har k'asa tana gaishe da Hajiya dake binta da hararara da kallon wulak'anci, Halima ce dake cin chingum tana bin ko ina na parlon da kallo tana jefama Munnira wani matsiyacin kallo ta juyo wajan Hajiya tana cewa "dama Hajiya wannan kucakar ce matar My Man ai na zata zanzo na tadda wata uwar mata a yadda kuke ikirarin wai ta mallake sa a hakan", ta idasa maganar tana nuna Munnira, tafawa sukai ita da Nawwara ta ce "hmm kema kin gani dai ya rasa uban mi yake ci tare da wannan tsohowar guzumar matar tasa kullum suna mak'ale da juna" wani irin taku Halima tayi tana matsowa kusa da Munnira tada dake tana kallonsu bak'in ciki ya cika zuciyarta amma ta dake tana son kawar da fushinta, ko kad'an idan ka kalli fuskarta baza ka ce abinda suke fad'a game da ita ya bata haushi ba, Halima dake kallonta cike da tsana da hassada saboda taga ta fita ta ko ina kyanne kyan jiki da diri da komai kawai ta fad'i hakan ne danta bak'anta mata rai sai dai tana kalli fuskarta sai taga sab'anin haka dan kuwa fuskar Munnira wani kalar annuri ma ke fita da kwarjini, ta bud'e baki ta ce "ai daga yanzu a shirya dan ba mutum shi kad'ai keda shi ba, kuma idan banda jaraba ta d'a namiji ina wani abun so da abun mak'alewa a nan", shuru Munnira tayi dan tasan shine alkhairi baza ta so tayi cece kuce a gaban sirikarta ba kuma tun kamin ma ta shigo tsayawa fad'a tana fad'a kamar zubar da mutumci ne da kima. Shurun da tayi kuwa ba k'aramar shak'a sukai ba ta maida su mahaukata kenan cike da isa Hajiya ta zauna kujera tana d'ora k'afa d'aya kan d'aya tana nunama Halima gidan ta ce "fatan dai wancan sashin yayi miki idan ma baiyi miki ba, wannan ne yayi miki zata iya kwashe kwamutsanta ta baki waje mai gurin yazo mai tabarma ai dole ya nad'e" wata dariya Halima ta saki ta jin dad'i ta ce "ai Hajiya nafi k'arfin na zauna a inda ta zauna sabon waje yayi min ina ni ina zaunawa inda ta tashi ai nafi k'arfin haka Hajiya tayi zamanta dama bakiga wajan ba duk an maida shi wani iri" Hajiya data gyara zama ta kai dubanta wajan Munnira dake tsaye ko ci kanku bata ce ba, wani banzan kallo ta watsa mata tana cewa "da alama gidanku basu iya tarbar bak'i ba ko?, kinga mutane bazaki basu abin tab'awa ba kin wani tsaya kin tsare mutane da idonki irin na munafukan farko, nazo gidan d'ana amma ko arzik'in ruwa bazan samu nasha ba, saboda baki da mutumci dama marar tarbiyya ce ke", sosai taji maganar Hajiya ta b'ata mata rai amma saita d'an k'ak'aro murmushin k'arfin hali ta ce "a'a Hajiya ba haka bane baku zauna bane na gani, kunata wasu maganganu ne wadda bai shafe ni ba, bari nayi wai ku gama idan kuka zauna saina gabatar muku da abun motsa baki" cike da mamaki suke dubanta au yanzu duk maganar nan da suka yab'a mata bata dameta ba, kam uban nan kayyasa kai rik'e baki Nawwara tayi, Halima kuwa sakin baki tayi tana duban Munnira dake shigewa kitchen, harta kawo masu ruwa da lemo suna tsaye cike da mamakinta. Hajiya dake zaune ta cika tayi fam ai gani take kamar gayamata magana Munnira tayi, ai kuwa Halima data harbo jirgin Hajiya ta bud'e baki domin k'ara zuga tana d'aukar robar ruwa ta zuk'a tana watsa ma Munnira shi a fuska, ta ce "ai wannan maganar da tayi Hajiya gaya miki magana kawai tayi wallahi" runtse idonta Munnira tayi tana jin ciwon watsa mata ruwa da Halima tayi, Halima dake kallonta ta sake cewa "ke har kina da abunda zaki bamu mu ci?, saura muma a gama damu komi kike nufi?", Munnira dake shirrin yin magana suka ji wani irin k'arar mari tasssss tassss mai azabar k'arfe k'arar mari ta mamaye parlon su duka har rige-rigen dubawa suke waye aka zafga ma mari haka..........✍️ *To laifin dad'i aka ce k'arewa, Jama'a nima zanso inji waye aka zafga ma mari haka, mu had'u a PAID BOOK akwai k'ura fa, shin yaya rayuwar Maryam zata kasance a gidan Ya Hafiz ne?' shi kuma Ya Abbas wai miye yake nufi ne da Maryam?, akwai cakwakiya a wanga littafi, ta b'angaran su Munnira ma fa yanzu wasan zai fara yanzu aka soma tafiyar*...... ZAHRA ROYAL STAR CE SHARE FISABILILLAHI🥰🙏 Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels